Welcome to Scribd. Sign in or start your free trial to enjoy unlimited e-books, audiobooks & documents.Find out more
Download
Standard view
Full view
of .
Look up keyword or section
Like this
3Activity

Table Of Contents

0 of .
Results for:
No results containing your search query
P. 1
hausa-quran

hausa-quran

Ratings:
(0)
|Views: 95|Likes:
Published by readquran

More info:

Published by: readquran on Apr 27, 2011
Copyright:Attribution Non-commercial

Availability:

Read on Scribd mobile: iPhone, iPad and Android.
download as PDF, TXT or read online from Scribd
See more
See less

06/21/2015

pdf

text

original

 
You can change style by CSS.
Chapter 1 (Sura 1)
VerseMeaning1Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.2Godiya ta tabbata ga Allah, Ubangijin halittu;3Mai rahama, Mai jin ƙai;4Mai nuna Mulkin nar Sakamako.5Kai muke bauta wa, kuma Kai muke neman taimakonKa.6Ka shiryar da mu ga hanya madaidaiciya.7Hanyar waɗanda Ka yi wa ni´ima, ba waɗanda aka yi wa fushi ba, kuma ba ɓatattu ba.
Chapter 2 (Sura 2)
VerseMeaning1A. L  ̃. M  ̃.2Wãncan ne Littãfi, bãbu shakka a cikinsa, shiriya ne ga mãsu taƙawa.(1)3Waɗanda suke yin ĩmãni game da gaibi, kuma suna tsayar da salla, kuma daga abin da Muka azurta su sunaciyarwa.4Kuma waɗanda suke yin ĩmãni da abin da aka saukar zuwa gare ka, da abin da aka saukar daga gabãninka,kuma game da Lãhira suna yin yaƙĩni.5Waɗannan suna kan shiriya, daga Ubangjinsu, kuma waɗannan su ne mãsu cin nasara.6Lalle ne waɗanda suka kãfirta(1) daidai ne a kansu, shin kã yi musu gargaɗi kõ ba ka yi musu gargaɗi ba, bazã su yi ĩmãni ba.7Allah Ya sa hãtimi a kan zukãtansu, da a kan jinsu, kuma a Kan ganin su akwai wata yãna; kuma suna dawata azãba mai girma.8Kuma akwai daga mutãne wanda(2) yake cewa: "Mun yi imani da Allah kuma da Yinin Lãhira." Alhãli kuwasu ba muminai ba ne.9Suna yaudarayya da Allah da waɗanda suka yi ĩmãni, alhãli bã su yaudarar kõwa fãce kansu, kuma bã susakankancħwa!10A cikin zukãtansu akwai wata cũta. Sai Allah Ya ƙãramusu wata cũta, kuma suna da azãba mai raɗaɗisabõda abin da suka kasance suna yi na ƙarya.11Kuma idan aka ce musu: "Kada ku yi ɓarna a cikin ƙasa," sukan ce: "Mũ mãsu kyautatawa kawai ne!"12To, lalle ne su, sũne mãsu ɓarna, kuma amma bã su sansancewa.13Kuma idan aka ce musu: "ku yi ĩmãni kamar yadda mutãne suka yi ĩmãni," sukan ce: "Zã mu yi ĩmãni nekamar yadda wãwãye suka yi ĩmãni?" To, lalle ne su, sũ ne wãwãye, kuma amma bã su sani.14Kuma idan sun haɗu da waɗanda suka yi ĩmãni,sukan ce: "Mun yi ĩmãni. "Kuma idan sun wõfinta zuwa gashaiɗãnunsu,(3) sukan ce: "Lalle ne muna tãre da ku: Mu mãsu izgili, kawai ne."15Allah Yana yin izgili(4) gare su kuma Yana taimakon su a cikin ɓatarsu, suna ɗimuwa.16Waɗannan su ne waɗanda suka sayi ɓata da shiriya, sai fataucinsu bai yi rĩba ba, kuma ba su kasance masushiryuwa ba.17Misãlinsu(1) shĩ ne kamar misãlin wanda ya hũra wuta, to, a lõkacin da ta haskake abin da yake għfensa (naabin tsõro), Allah Ya tafi da haskensu, kuma Ya bar su a cikin duffai, bã su gani.18Kurãme, bħbãye, makãfi, sabõda haka bã su kõmõwa. 
27.04.2011 www.qurandatabase.orgfile:///D:/Downloads/Hausa-122.htm 1/244
 
19,yãtsunsu a cikin kunnuwansu dãga tsãwarwakin, dõmin tsõron mutuwa. Kuma Allah Mai kħwayewa ne gãkãfirai!20Walƙiyar tana yin kusa ta fizge gannansu, ko da yaushe ta haskakã musu, sai su yi tafiya a cikinta, kuma idanta yi duhu a kansu, sai su yi tsaye. Kuma dã Allah Yã so, sai Ya tafi da jinsu da gannansu. Lalle ne Allah akan dukan kõme Mai ĩkon yi ne.21Yã ku mutãne! Ku bauta(3) wa Ubangjinku, Wanda Ya halicce ku, kũ da waɗanda suke daga gabãninku,tsammãninku ku kãre kanku !22Wanda Ya sanya muku ƙasa shimfiɗa, kuma sama gini, kuma Ya saukar da ruwa daga sama, sa´an nan Yafitar da abinci daga ´ya´yan itãce game da shi, sabõda ku. Sabõda haka kada ku sanya wa Allah wasukĩshiyõyi, alhãli kuwa kuna sane.23Kuma idan kun kasance a cikin shakka daga abin da Muka sassaukar ga Bãwanmu, to, ku zõ da sũra gudadaga misalinsa (Alƙur´ãni). Kuma ku kirãwo shaidunku (4) baicin Allah, idan kun kasance mãsu gaskiya.24To, idan ba ku aikata (kãwo sura) ba, to, bã zã ku aikata ba, sabõda haka, ku ji tsoron wuta, waddamakãmashinta mutãne da duwãtsu ne, an yi tattalinta dõmin kãfirai.25Kuma ka bãyar da bishãra ga waɗanda suka yi ĩmãni. kuma suka aikata ayyuka na ƙwarai, cħwa lallene,suna da gidãjen Aljanna, ƙõramu na gudãna daga ƙarƙashinsu. Ko da yaushe aka azurta su da abinci dagawasu ´ya´yan itãce daga gare su,(1) sai su ce: "Wannan shi ne aka azurta mu da shi daga gabãnin haka,"Kuma a je musu da shi yana mai kama da juna, Kuma sunã da, a cikin su, mãtan aure mãsu tsarki, kuma su,cikin su madawwama ne.26Lalle ne, Allah bã Ya jin kunyar Ya bayyana wani misãli, kõwane iri ne, sauro da abin da yake bisa gare shi.To, amma waɗanda suka yi ĩmãni, sai su san cewa lalle shi ne gaskiya daga Ubangijin su, kuma ammawaɗanda suka kãfirta, sai su ce: "Mħne ne Allah Ya yi nufi da wannan(2) ya zama misãli?" na ɓatar da wasumãsu yawa da shi, kuma Yana shiryar da wasu mãsu yawa da shi, kuma bã Ya ɓatarwa da shi fãce fasiƙai.27Waɗanda suke warware alƙawarin Allah daga bãyan ƙulla shi, kuma su yanke abin da Allah Ya yi umurni dashi a sãdar, kuma suna ɓarna a cikin ƙasa, waɗannan sũ ne mãsu hasãra.28Yaya kuke kãfirta da Allah, alhãli kuwa kun kasance matattu sa´an nan Ya rãyar da ku, sa´nnan kuma Yamatar da ku, sa´an nan kuma Ya rãya ku, sa´an nan zuwa gare Shi ake mayar da ku?29Shi ne Wanda Ya halitta muku abin da ke a cikin ƙasa gaba ɗaya, sa´an nan kuma Ya daidaita(3) zuwasama, sa´an nan Ya aikata su sammai bakwai. Kuma Shi ga dukan kõmai Masani ne.30Kuma a lõkacin da Ubangijinka Ya ce ga malã´iku: "Lalle ne, Ni Mai sanya wani halĩfa ne a cikin ƙasa,"suka ce: "Ashe, zã Ka sanya a cikinta, wanda zai yi ɓarna a cikinta, kuma ya zubar da jinainai alhali kuwamu, muna yi maka tasbihi game da gõde maka, kuma(1) muna tsarkakewa gareka" Ya ce: "Lalle ne, Ni Nasan abin da ba ku sani ba."31Kuma Ya sanar da Ãdam sũnãye dukansu, sa´an nan kuma ya gitta su a kan malã´iku, sa´an nan Ya ce: "Kugaya mini sũnayen waɗannan, idan kun kasance mãsu gaskiya."32Suka ce: "Tsarki ya tabbata a gare Ka! Bãbu sani a gare mu, face abin da Ka sanar da mu, lalle ne Kai, Kaine Masani, Mai hikima."33Ya ce: "Yã Ãdam! Ka gaya musu sũnãyensu." To, a lokacin da ya gaya musu sũnãyensu, (Allah) Ya ce:"Ashe, ban ce muku(2) ba, lalle Ni, Inã sane da gaibin sammai da ƙasa, kuma (Inã sane da ) abin da kuke bayyanawa da abin da kuka kasance kuna ɓõyewa?"34Kuma a lõkacin da Muka ce ga malã´iku: "Ku yi sujada ga Ãdam," Sai suka yi sujada, fãce Ibilĩsa ya ƙi,kuma ya yi girman kai, kuma ya kasance daga kãfirai.35Kuma muka ce: "Ya Ãdam! Ka zauna kai da matarka a gidan Aljanna, kuma ku ci daga gare ta, bisawadãta, inda kuke so, kuma kada ku kusanci wannan itãciyar, har ku kasance daga azzãlumai."36Sai Shaiɗan ya talãlãɓantar da su ga barinta, sai ya fitar da su daga abin da suka kasance a cikinsa. Kumamuka ce: "Sãshenku nã maƙiyi ga sãshe, kuma kuna da a cikin ƙasa matabbata da jin dãɗi zuwa ga wanilõkaci."37Sai Ãdam ya karɓi wasu kalmõmi daga Ubangjjinsa, sabõda haka ya karɓi tũba a kansa. Lalle ne Shi, Shĩ ne Mai karɓar tũba, Mai jin ƙai.Muka ce: "Ku sauka daga gare ta gabã ɗaya. To, imma lalle shiriya ta je muku daga gare Ni, to, wanda ya
27.04.2011 www.qurandatabase.orgfile:///D:/Downloads/Hausa-122.htm 2/244
 
 bi shiriya ta to, bãbu tsõro a kansu, kuma bã su yin baƙin ciki."39"Kuma waɗanda suka kãfirta, kuma suka ƙaryata game da ãyõyinMu, waɗannan sũ ne abõkan Wuta; sũ acikinta madawwama ne."40Yã Banĩ Isrã´Ĩla(1) ! Ku tuna ni´imãTa wadda Na ni´imta a kanku, kuma ku cika alƙawariNa, In cika mukuda alƙawarinku. kuma Ni, ku ji tsõro Na.41Kuma, ku yi ĩmãni da abin da na saukar, yana, mai gaskatãwa ga abin da yake tãre da ku, kuma kada kukasance farkon kãfiri game da shi. Kuma kada ku sayi ´yan kuɗi kaɗan da ãyõyiNa. Kuma ku ji tsõrõNa, Nĩ kaɗai.42Kuma kada ku lulluɓe gaskiya da ƙarya, kuma ku ɓõye gaskiya, alhãli kuwa kuna sane.43Kuma ku tsayar da salla; kuma ku bãyar da zakka; kuma ku yi rukũ´i tãre da mãsu yin rukũ´i.44Shin, kuna umurnin mutãne da alhħri, kuma ku manta da kanku alhãli kuwa kuna karatun littãfi? Shin, bãzãku hankalta ba?45Kuma ku nħmi taimako da yin haƙuri, da salla. Kuma lalle ne ita, haƙĩƙa, mai girma ce fãce fa a kan mãsutsõron Allah.46Waɗanda suka tabbata cħwa lalle ne su mãsu haɗuwa ne da Ubangijinsu, kuma lalle ne sũ zuwa gare Shimãsu kõmãwa ne.47Yã banĩ Isrã´ĩla! Ku tuna ni´imaTa, wadda Na ni´imta a kanku, kuma lalle ne Ni, na fĩfĩta ku a kan tãlikai.48Kuma ku ji tsoron wani yini, (a cikinsa) rai bã ya wadãtar da wani rai da kõme, kuma ba a karɓar cetõ dagagareshi, kuma ba a karɓar fansa daga gare shi, kuma bã su zama ana taimakon su ba.49Kuma a lõkacin da muka tsĩrar da ku daga mutãnen Fir´auna, su na taya muku muguntar azãba, su nayayyanke ɗiyanku maza su na rãyar da mãtanku. Kuma a cikin wancan akwai jarabawa mai girma dagaUbangijinku.50Kuma a lõkacin da Muka raba tħku sabõda ku, sai Muka tsĩrar da ku kuma Muka nutsar da mutãnen Fi´auna, alhãli kuwa kũ kuna kallo.51Kuma a lõkacin da muka yi wa´adi ga Mũsa, dare arba´in, sa´an nan kuma kuka riƙi maraƙi daga bãyansa,alhãli kũ, kuna mãsu zãlunci (da bauta masa).52Sa´an nan kuma muka yãfe muku daga bãyan wancan, tsammãninku, kuna gõdħwa.53Kuma a lõkacin da Muka baiwa Mũsa Littãfi da rarrabħwa, tsammãninku, kuna shiryuwa.54Kuma a lõkacin da Mũsa ya ce ga mutãnensa: "Ya mutãnena! Lalle ne ku, kun zãlunci kanku game dariƙonku maraƙin, sai ku tũba zuwa ga Mahaliccinku, sai ku kashe kãwunanku. Wancan ne mafi alheri awajen mahaliccinku. Sa´an nan Ya karɓi tuba a kanku. Lalle ne Shi, Shi ne Mai karɓar tũba, Mai jin ƙai.55Kuma a lõkacin da kuka ce: "Ya Musa! Bã zã mu yi ĩmãni ba dõminka, sai munga Allah bayyane," sabadahaka tsãwar nan ta kamaku, alhãli kuwa kuna kallo.56Sa´an nan kuma Muka tãyar da ku daga bãyan mutuwarku, tsammãninku, kuna gõdħwa.57Kuma Muka sanya girgije ya yi inuwa a kanku, kuma Muka saukar da darɓa da tantabaru a kanku; "Ku cidaga mãsu dãɗin abin da Muka azurta ku." kuma ba su zãlunce Mu ba, kuma amma kansu suka kasancesuna zãlunta.58Kuma a lokacin da Muka ce: "Ku shiga wannan alƙarya. Sa´an nan ku ci daga gareta, inda kuka so, bisawadata, kuma ku shiga ƙofa kuna masu tawalu´i, kuma ku ce; "kãyar da zunubai" Mu gãfarta mukulaifukanku, kuma zã mu ƙãra wa mãsu kyautatawa."59Sai waɗanda suka yi zalunci suka sake magana watar wannan da aka ce musu, saboda haka muka saukar akan waɗanda suka yi zãlunci da azãba daga sama sabõda abin da suka kasance suna yi na fãsiƙanci.60Kuma a lokacin da Mũsa ya nemi shãyarwa domin mutãnensa, Muka ce; "Ka dõki dũtsen da sandarka." Saimarmaro gõma sha biyu suka ɓuɓɓuga, haƙĩƙa, kõwaɗanne mutãne sun san wurin shansu. "Ku ci kuma kusha daga arziƙin Ubangijinku, kuma kada ku yi fasadi, a cikin ƙasa, kuna mãsu ɓarna."61Kuma a lõkacin da kuka ce: "Yã Mũsã! Bã zã mu yi haƙuri ba a kan abinci guda. Sai ka rõƙa manaUbangijinka Ya fitar mana daga abin da ƙasa take tsirarwa daga ganyenta, dumanta, da alkamarta daalbasarta. Ya ce: "Kuna nħman musanya abin da yake mafi ƙasƙanci da wanda yake mafi alhħri? Ku saukawani birni (daga cikin birane), domin lalle ne, kuna da abin da kuka rõƙa. "Kuma Muka dõka musuwulãƙanci da talauci. Kuma suka kõma da wani fushi daga Allah. Wancan sabõda lalle su, sun kasance suna 
27.04.2011 www.qurandatabase.orgfile:///D:/Downloads/Hausa-122.htm 3/244

Activity (3)

You've already reviewed this. Edit your review.
Saadu reviewed this
I write to congratulate the publishers of the Holy Quran in Hausa, may Allah grand you good in this world and hereafter. Amen.
1 thousand reads
1 hundred reads

You're Reading a Free Preview

Download
scribd
/*********** DO NOT ALTER ANYTHING BELOW THIS LINE ! ************/ var s_code=s.t();if(s_code)document.write(s_code)//-->