You are on page 1of 17

Matsayin Daawah Da Muhimmancinta A Rayuwar Musulmi

Sashin Koyar Da Aikin Akanta, Jamiar Ahmadu Bello, Zaria


abellodogarawa@gmail.com

Ahmad Bello Dogarawa

A Matsayin Takarda Da Aka Gabatar A Wurin Taron Bita, Da Kwamitin Daawah Da Kula Da Harkokin Masallatai Na Jihar Kaduna Ya Shirya Wa Limamai Da Sauran Masu Daawah, A Xakin Taro Na Janar Hassan Usman, Kaduna

2005

1.0

GABATARWA

Musulunci ne addinin gaskiya da Allah Ya yarda da shi ga mutane. Imani da shi, da xabiantuwa tare da shiryuwa da tsare-tsarensa da hanyoyinsa da hukunce-hukuncensa wajibi ne a kan kowane mukallaf. To sai dai kuma, wajibin mukallafai bai tsaya ga imani da shiryuwa da Musulunci ba kawai. Ya qetara ga kiran mutane zuwa gare shi, da kwaxaitar da su a kansa, da yaye rufin rafkana da vata daga zukatan waxanda suka juya masa baya. Za a yi hakan ne, kasancewar Musulunci shi ne addinin gaskiya, da babu makawa ya game duniya, kuma ya cika sasanninta. Aqidar Musulunci da ke tsaye a kan asasi na tsarkakakken tauhidi da bauta ta gaskiya, dole ta kasance ga Allah. Tilas ne a kiyaye tsarin rayuwa ta Musulunci; karantarwarsa da hukuncehukuncensa su wanzu; kuma alummar Musulmi ta ci gaba da zama fiyayyar alumma da aka fitar ga mutane.
Matsayin Daawah Da Muhimmancinta A Rayuwar Musulmi, Ahmad Bello Dogarawa,

6/12/2010

Wannan babbar manufa ta Musulunci ba za ta tabbata ba, har sai an xauki alamarin daawah da muhimmanci, nasiha ga juna ta zamanto xabiar kowane Musulmi, umurni da kyakkyawa da hani da mummuna su kasance tafarkin kowane mumini. Wannan ya sa daawah ta zamanto ita ce qashin bayan Musulunci da rayuwarsa. Domin kuwa ita ce hanyar ci gabansa da yaxuwarsa; kuma matakin kiyaye gwagwarmayarsa da tsare karantarwarsa. Allah 3 1 Wannan qasida za ta yi tsokaci ne a kan Matsayin Daawah da Muhimmancinta a Rayuwar Musulmi, tare da Gudummuwar Mai Daawah wajen Wayar da Kai ta Kafafen Yaxa Labarai. Qasidar ta qunshi vangarori guda bakwai. Vangare na biyu zai yi magana a kan matsayin daawah da hukuncinta a Musulunci. Vangare na uku zai tattauna a kan falalar daawah da faidodin tsayuwa da wajibcinta. Vangare na huxu zai yi magana a kan rukunan daawah. Vangare na biyar zai yi tsokaci a kan abubuwan da ke buqatar kulawa ta musamman dangane da daawah ta kafafen yaxa labarai. Vangare na shida zai yi ishara ga waxansu kura-kurai da aka shigar cikin daawah, saan nan kuma vangare na bakwai ya qunshi kammalawa. Ina roqon Allah Ya yi mana muwafaqa. 2.0 MATSAYIN DAAWAH DA HUKUNCINTA A MUSULUNCI Ya ce:

Alquani da Sunnah da Ijmai sun tabbatar da wajibcin daawah wato kiran mutane zuwa ga alheri da umurtarsu da kyakkyawa da hana su mummuna. Allah Maxaukaki Ya ce: 125 104

Matsayin Daawah Da Muhimmancinta A Rayuwar Musulmi, Ahmad Bello Dogarawa,

6/12/2010

Dangane da umurni da kyakkyawa da hani da mummuna, Allah Maxaukaki Ya ce: 110 Ya bayyana soyayyar muminai da jivinta alamuransu ga juna da yadda su ke yi wa juna daawah:

71 Ya bayyana cewa farkon wajibi a kan kowane Musulmi da Allah Ya tabbatar wa da mulki da jagoranci a cikin qasa shi ne tsayar da sallah da yin daawah: 41 A cikin wasiyyar da Luqman ya yi wa xansa, kamar yadda Alqurani ya zo da shi, akwai maganar daawah: 17 Alqurani ya zo da kyakkyawan yabo ga wata qungiya daga Ahlul Kitab (kafin aiko Manzon Allah ) da ta kasance a tsaye kan addinin Allah da daawah zuwa gare shi: 114 113 Haka nan, Alqurani ya zo da bayanin tsinuwa ko laanar da aka yi wa waxansu, saboda kafircinsu, da qasqancin da ya same su, da faxuwar daraja, saboda rashin yin daawah: 78 Sunnar Manzon Allah (tsira da aminci su tabbata a gare shi) ta bayyana wajibcin daawah, da muhimmancin umurni da kyakkyawa da hani da mummuna. Manzon Allah ya ce:

Matsayin Daawah Da Muhimmancinta A Rayuwar Musulmi, Ahmad Bello Dogarawa,

6/12/2010

Alummar Musulmi ta yi ittifaqi a kan wajibcin daawah tun daga zamanin sahabbai zuwa yau. Kuma ko da wanda ke yin daawah ba ya aiki da abin da ya ke kiran mutane a kai, dole ne a tsayu da aikin daawah. Sai dai kuma bayan an yi ittifaqi a kan wajibcin daawah, malamai sun yi savani dangane da nauin wajibcin: ne ko ? Amma maganar da ta fi dacewa ita ce: daawah zuwa ga alheri da umurni da kyakkyawa da hani da mummuna wajibi ne a kan kowane Musulmi. Illa iyaka daawah za ta zama wajibi ne kai tsaye a haqqin waxanda ke da iko da cancanta. A haqqin waxanda ba su da ahaliyya kuwa, wajibinsu a vangaren daawah shi ne ba da goyon baya, da gudummuwa gare ta da waxanda ke yinta. Za a yi daawah matuqar hakan ba zai haifar da fitina ba, ko ya zama dalilin kuvucewar abin da ya fi muhimmanci, ko aukuwar wata sabuwar varna, ko samun cutuwa ga kai ko dukiya. Sakaci da rashin tsayuwa da daawah na haifar da matsaloli da dama. Daga ciki, akwai: Bijiro wa fushin Allah da azabarSa a duniya. Allah 25 Ya ce:

Dangane da fassarar wannan aya, al-Haafidh Ibn Katheer ya naqalo Ibn Abbaas ya ce: Allah Ya umurci muminai da su yi inkarin dukan mummuna, ko kuma Ya lulluve su da azaba. Manzon Allah ya ce:

Qasqanci da wulaqanci tare da gabar abokan qiyayya Tabbatuwar varna da gurvacewar alamura
Matsayin Daawah Da Muhimmancinta A Rayuwar Musulmi, Ahmad Bello Dogarawa,

6/12/2010

Rashin amsa addua, kamar yadda Manzon Allah

ya ce:

3.0

FALALAR DAAWAH

Babu shakka, daawah na da falala mai girma da lada mai yawa. Allah ( Ya sanya daawah, da umurni da kyakkyawa da hani da mumm una a matsayin mafi kevantacciyar siffofin Manzon Allah : 157 Allah Ya sanya umurni da kyakkyawa da hani da mummuna daga siffofin muminai:

112 Daawah ce babbar alama ta alherin wannan alumma: 110 Neman ilmi don tattali ga harkar daawah da umurni da kyakkyawa da hani da mummuna yanki ne na jihadi: 122 Manzon allah mutanen farko: ya tabbatar wa masu daawah da irin ladan

Shahada na samuwa ta hanyar daawah:

Akwai faidodi da dama na tsayuwa da daawah. Waxansu faidodin sun shafi mai daawar, waxansu sun shafi wanda aka yi wa daawar, a yayin da waxansu sun shafi alumma ce gaba xaya.
Matsayin Daawah Da Muhimmancinta A Rayuwar Musulmi, Ahmad Bello Dogarawa,

6/12/2010

Faidodin da suka shafi mai daawar sun haxa da: Kuvuta daga azabar Allah: 165 Rabauta da yardar Allah da samun aljannah:

72 71 Samun adduar neman gafara daga halitta, hatta kifi Samun lada kwatankwacin mutanen da aka yi wa daawar Tsayar da hujja a kan mutane Ci gaba a harkar daawah, ta yadda zai tashi daga maduw daaee Samun xaukaka da jagoranci da jefa haiba a tsakanin mutane Faidodin da ke komawa ga wanda aka kira, sun haxa da Dalilin musulunta: ya zama

Faxakarwa daga rafkana da samun istiqama: Faidodin daawah ga alumma sun haxa da Tsare qasa daga fasadi da sharri, ta hanyar tabbatar da aqida sahihiya da kiyaye larurorin rayuwa guda biyar , kamar yadda ya ke qunshe cikin Hadisin masu jirgin ruwa. Xaukewar azaba da za ta mamaye alumma idan ba su yi daawah ba:

Matsayin Daawah Da Muhimmancinta A Rayuwar Musulmi, Ahmad Bello Dogarawa,

6/12/2010

Dalili na samun xaukaka a kan abokan gaba Tabbatar da `yanuwantaka da taimakekeniya 4.0 RUKUNAN DAAWAH

Daawah ta qunshi abubuwa ko rukunai guda biyar: Mai daawah, Wanda za a yi wa daawah, Abin da za a yi daawah zuwa gare shi, Yadda za a yi daawah, da kuma hanyoyin yaxa daawar. 4.1 Mai Daawah

Mai daawah shi ne rukunin farko na daawah, kuma mafi girma. Shi ne wanda ke kiran mutane zuwa ga alheri, ya umurce su da kyakkyawa, ya hana su mummuna. Daga cikin siffofi da ladubban mai daawah, akwai: Ikhlas Ibn an-Nahhaas ya ce:

Ilmi 108 Aiki da abin da ya ke kira zuwa gare shi, ta yadda zai zama jagora, kuma abin koyi, kamar yadda Annabawa ( ) suka kasance. Allah Ya ba mu labarin Annabawa da yadda suke aiki da abin da suke kiran mutane zuwa gare shi. Misali, Ya ba mu labarin miqa wuyar Annabi Ibrahim da sallamawarsa ga Allah, da umurnin da ya yi wa `ya`yansa da yin haka (Baqarah: 131-132). Ya ba mu labarin qyamar Annabi Shuaibu ga sava wa mutane cikin abin da ya ke umurtarsu (Huud: 88). Ya tabbatar mana da imani da miqa wuyar da Annabi Musa ya yi kafin kowane mutum daga cikin jamaarsa (Aaraaf: 143) Babu shakka, mutumin da ke daawah amma ba ya aiki da shi, abin zargi ne a wajen Allah da Manzon Allah da sauran alumma.
Matsayin Daawah Da Muhimmancinta A Rayuwar Musulmi, Ahmad Bello Dogarawa,

6/12/2010

Allah Ya yi inkari ga masu imani da ke faxin abin da ba su aikatawa (as-Saf: 2); Ya zargi waxanda ke yin daawah, amma ba su aiki da ilminsu (Baqarah: 44); Ya kamanta Yahudawan da ke da ilmin at-Taurah, amma ba su aiki da ilmin, da Jaki (al-Jumaah: 5); kuma Ya kamanta malamin da ba ya aiki da ilminsa da Kare (al-Aaraaf: 175-176) Manzon Allah ya saukar da malamin da ba ya aiki da ilminsa a matsayin jahili [Ahmad da Ibn Maajah]; ya kamanta shi da faqon qasa mara amfani [Bukhaari da Muslim]; kuma ya kamanta shi da fitila da ke haskaka wa mutane, amma ta ke qona kanta [Xabaraani]. Bugu da qari, akwai azaba ta wulaqanci da ke jiran mai daawa, amma ba ya aiki da abin da ya ke karantar da mutane. Haqiqa, daawa na samun cikas, idan mai yin ta ba ya qoqarin xabbaqawa da kansa. Sanannen abu ne cewa, mutane na laakari da irin aikin da mai daawah da waxanda ke qarqashinsa su ke yi, kuma hakan na yin tasiri mai yawa a kansu. Kuma duk da cewa ba shi daga cikin sharuxxa na karvar gaskiya, a ce wanda ya faxi ko ya yi daawah dole sai ya yi aiki da ilminsa, amma ya tabbata cewa mutane sun fi saurin karvar gaskiya da amfani da ita, idan wanda ke karantar da su na aikatawa. Haka nan, sau da yawa, mutane kan yi watsi da daawar mai daawa, idan sun fahimci ba ya aiki da ilminsa. Kyakkyawar xabia da muamala da ta dace. Wannan ya qunshi: Tausasawa da rashin tsanantawa da kore mutane ta hanyar kausasa lafazi da gallaza magana da nuna isa da raini gare su. Allah Ya ce: 159 44 Manzon Allah ya ce:

Matsayin Daawah Da Muhimmancinta A Rayuwar Musulmi, Ahmad Bello Dogarawa,

6/12/2010

Haquri a kan cutarwar da za ta same shi: 17

Tsantseni da rashin nuna kwaxayi. Al-Ghazaali ya ce:

Adduar neman fahimta da shiriya ga waxanda a ke yi wa daawah 4.2 Waxanda Za A Yi Wa Daawah

Waxanda za a kira sun haxa da Musulmi da waxanda ba Musulmi ba, kuma kowane ana laakari da buqatarsa. Saan nan, ana ba da muhimmanci sosai ga shugabanninsu 4.3 Abin da Za A Kira Mutane Zuwa Gare shi

Farkon abin da ya kamata a kira mutane zuwa gare shi, shi ne tauhidi da gyara a kan aqida, kasancewar hakan ne usulubin Annabawa. Manzon Allah da ya tura Muadh bin Jabal Yamen don ya kira su zuwa ga addinin Musulunci, ya ce masa: Farkon abin da za ka fara kiransu zuwa gare shi, shi ne: shaidawa babu wanda ake bauta wa bisa cancanta sai Allah [Bukhaari da Muslim] Saan nan a bi tsarin tare da laakari da . Wannan tsarin ne ke tabbatar da haxin kai da kawo fahimta a tsakanin Musulmi. Rashin ba da
Matsayin Daawah Da Muhimmancinta A Rayuwar Musulmi, Ahmad Bello Dogarawa,

6/12/2010

muhimmanci ga tauhidi, ko farfagandar ajiye maganar tauhidi da aqida gefe xaya, don samun haxin kai, ba za su kai Musulmi koina ba. Sanannen abu ne cewa da zarar an rusa tauhidi ko an cire maganar aqida sahihiya daga zukatan Musulmi, an ruguza masu kome. Hadisin Muadh da Bukhari da Muslim suka ruwaito, ya isa hujja dangane da wajibcin gabatar da kyautata tauhidi da gyaran aqida a harkar daawah, kafin kome. Manzannin da Allah ya turo ma, dukansu sun fara kira ne zuwa ga tauhidi, kafin kome. 4.4 Allah Yadda Za A Kira Mutane Ya ce: 125 A cikin wannan aya, Allah Ya bayyana hanyoyin daawah guda uku, waxanda mai daawah ke buqatar fahimta don samun nasara cikin daawarsa. Hanyoyin su ne: . Ibn al-Qayyim ya ce: Mutumin da ya amsa kira, ya ke shirye da ya karvi gaskiya, kuma ba ya girman kai ko gangare wa gaskiya, za a yi amfani da hikima wajen yin masa daawah. Wanda ke karvar gaskiya, amma yana da rafkana da yin baya-baya, za a kira shi ta hanyar kyakkyawar magana. Wanda kuwa ke girman kai da gangare wa gaskiya, sai a yi amfani da jayayya mafi kyau. Hikima ta qunshi daidaituwar magana da dacewar aiki, da tabbatuwar raayi da sahihin tunani da ke xaukaka mutum zuwa matsayi babba a rayuwar duniya da lahira. Kalmar ta zo da maanar littafan sama, Annabta, shiriya, ilmi, adalci, haquri da fahimtar addini. Hikima suna ne da ya tattaro dukan wata magana ko ilmi da ake kiyaye maslahar halin mutane, da aqidarsu, maslaha ta din-din-din. A harkar daawah, hikima ta qunshi: Fahimtar zamani dacewar maudhuin magana da halin da ake ciki, da rashin qosarwa Laakari da bia, da xabia, da yanayi, da aladar wuri; da tarihi, da zamantakewa da sanaar waxanda ke wurin. Misali, akwai abubuwan da ba a buqatar tattaunawa a waxansu wurare, kasancewar ba su a wurin.
Matsayin Daawah Da Muhimmancinta A Rayuwar Musulmi, Ahmad Bello Dogarawa,

6/12/2010

10

Laakari da waxanda ake yi wa daawah. Wannan ya shafi shekaru, fahimta, wayewa, jinsi, da sauransu Abdullah bin Masood ya ce:

Aliyu bin Abi Xaalib

ya ce:

Manzon Allah ya kasance yana laakari da yanayin mutane, da zurfin ilminsu, da daxewarsu a cikin Musulunci, da wayewarsu, idan zai ba da fatawa, ko kuma zai karantar da wani abu. Haka nan, ya kasance yana bin tsarin sannu-sannu wajen karantarwa. Wannan ya sa, lokacin da Abu Hurairah ya tambaye shi game da , sai ya sanar da shi: imani da Allah, da jihadi don Allah, da aikin Hajji da ya kuvuta daga savon Allah [Muslim]. Amma da Abdullah bin Masood ya tambaye shi, sai ya ce: sallah a kan lokaci, da biyayya ga iyaye, da jihadi don Allah [Muslim]. Saan nan kuma ya gaya wa Abu Zarr : imani da Allah, da jihadi don Allah [Muslim], kuma ya gaya wa mutumin Khath`am : imani da Allah, da sadar da zumunta, da umurni da kyakkyawa da hani da mummuna [Abu Yaalaa]. Haka nan, lokacin da Abdullah bin Amr ya tambaye shi , sai ya ce: ka ciyar da abinci, kuma ka yi sallama ga wanda ka sani da wanda ba ka san shi ba [Bukhaari]. Amma da Abu Moosa ya tambaye shi, sai ya ce: wanda Musulmi suka kuvuta daga (cutarwar) harshensa da hannunsa [Bukhaari]. A vangaren fatawa, Manzon Allah ya hana matashi sumbantar matarsa a lokacin da ya ke azumi, amma ya halasta wa tsoho [Xabaraani], kuma ya hana saurayi rungumar matarsa alhali yana azumi, amma ya ba tsoho damar yin haka [Abu Dawud]. Bayan wannan, Manzon Allah ya kasance yana musamaha a kan wani alamari na wacin gadi, saboda wata maslaha. Misali:
Matsayin Daawah Da Muhimmancinta A Rayuwar Musulmi, Ahmad Bello Dogarawa,

6/12/2010

11

Mutanen Thaqif sun sharxanta cewa za su musulunta a kan ba za su ba da sadaka ba, kuma ba za su yi jihadi ba. Manzon Allah ya yarda da hakan, saan nan aka ji yana cewa: za su yi daga baya [Abu Dawud] Ya haqura da rubuta Bismillah, Rasulullah, da sauransu, a lokacin da aka yi sulhu a Hudaibiyah, saboda maslaha [Bukhaari] Ya hana yin haddi ga wanda ya yi sata a wurin yaqi, don gudun ka da ya koma cikin abokan gaba [Abu Dawud, Tirmidhi, Nasaai da Daarimi] Ya haqura dangane da mayar da ginin Kaabah kamar yadda Annabi Ib rahim da Ismaail suka gina, kasancewar mutanen Makka ba su daxe da musulunta ba [Bukhaari] Sai dai kuma lallai ne mai daawah ya fahimci cewa waxannan misalai ba su nufin a qi faxin gaskiya, ko kuma a yi musamaha wajen kira zuwa ga tauhidi. A wannan vangare, ba a yin sakwa-sakwa, kamar yadda waxansu ayoyin Alqurani da Hadisai suka tabbatar. Bin mataki-mataki ( ), saboda Hadisin Muadh

Amfani da kalmomi masu sauqi, gajejjeru da ke isar da saqo, kuma su qwanqwasa zukata, ba tare da ruxarwa ko faxawa tarko ba 52 51

21 20 19 18 Jawo hankali da cusa aminci 59 Annabi Nuhu, da Hud, da Saalih, da Lux, da shuaibu ( ) sun yi amfani da kalmar da za ta natsar da zukatan mutanensu, ta yadda za su amintu, kuma su saurara.

Matsayin Daawah Da Muhimmancinta A Rayuwar Musulmi, Ahmad Bello Dogarawa,

6/12/2010

12

Annabi Shuaibu (

) ya ce wa mutanensa: 84

Annabi Musa (

) ya ce wa mutanensa: 5

Kyakkyawar magana ( ) ta qunshi abubuwa muhimmai guda biyu da mai daawah ya kamata ya kula da su: Magana mai taushi, da sassauci, musamman ga waxanda ke da shekaru mai yawa da masu mulki Fasaha cikin magana, da rashin amfani da kalmomi marasa kyau Jayayya da mafi kyawu ( ) na nufin yin bayani tare da dalili mai qarfi da zai rushe dukan wata shubuha ko shakku da za a nemi jefawa cikin zuciyar mai daawah ko waxanda ke sauraro [Kahf: 32-42, Sabai: 35-37, da Baqarah: 111-112] 4.5 Hanyoyin Yaxa Daawah

Hanyoyin yaxa daawah sun kasu gida biyu: hanyoyi na kai tsaye, da waxanda ba na kai tsaye ba. Hanyoyin isar da daawah na kai tsaye na da vangarori guda biyu: mai daawah da wanda zai kira; da kuma mai daawah da jamaa masu yawa. Vangare na biyu ya haxa da: Khutbah: Jumaa, Idi, Arafa, Kusuf, da bayan rufe mamaci Muhadara Karantarwa: Taalim da xaukar karatu Taron qara wa juna ilmi ko taron bita

Hanyoyin yaxa daawah da ba na kai tsaye ba sun haxa da: Rubutu a cikin Jaridu ko Mujallu, da gabatar da qananan takardu ko wasiqu Rubuta littafi, da ba da aron shi don a karanta Kaset (sauti da hoto) Manna takardu a masallaci da sauran wuraren da suka dace Amfani da hanyar naura mai qwaqwalwa (e-mail)
6/12/2010
13

Matsayin Daawah Da Muhimmancinta A Rayuwar Musulmi, Ahmad Bello Dogarawa,

Amfani da kafafen watsa labarai 5.0 ABUBUWAN LURA WAJEN AMFANI DA KAFAFEN WATSA LABARAI Daga cikin hanyoyi mafi sauqi da yawan shahara wajen yaxa daawah a wannan zamani, akwai Talabijin da Rediyo. Waxannan kafafe guda biyu sun zama wasila mafi qarfi da tasiri wajen isar da saqo ga mutanen birni da karkara, maza da mata, manya da yara. Saboda amfanin kafafen watsa labarai a yau, qasashen duniya, musamman na yammacin turai, na amfani da su a matsayin makamin yaqi ko ruguza duk wani abu da suke xaukarsa barazana ga ci gabansu. Wannan ya sa, gwabnatocinsu ke kashe maqudan kuxi, don tabbatar da nagartar waxannan kafafe. Ta cikinsu ne ake farfaganda, musamman ga Musulunci, domin a cusa qyamarsa a zukatan waxanda ba mabiyansa ba. Musulunci ya ba isar da saqo muhimmanci sosai. Idan saqo ya kasance mai rikitarwa ko yiwuwar haifar da savani a cikin alumma, wajibi ne a yi bincike don tabbatar da sahihancinsa. Allah Ya ce: 6 Dangane da sahihin labari da za a yaxa shi cikin jamaa, Alqurani ya kwaxaitar da jivinta hakan ga waxanda suke da ahaliya. Don haka, ba shi daga ladubban zamantakewa a Musulunci, a miqa ragamar isar da saqo ko yaxa daawah ga waxanda ba su cancanta ba. Allah Ya ce: 83 A qarqashin wannan, waxansu Malamai sun fahimci cewa wanda zai yi daawah ta kafafen watsa labarai na buqatar ahaliya ta musamman , don gudun ka da ya yi abin da rashin amfaninsa zai fi amfaninsa yawa. Sanannen abu ne cewa wanda zai yi daawah ta Talabijin ko Rediyo na buqatar taka tsan-tsan fiye da wanda zai yi waazi a cikin masallaci. Bambancinsu shi ne, wanda zai isar da saqo ta kafafen watsa labarai, bai san adadin mutanen da za su saurara ba, kamar yadda bai san irin fahimtarsu da zurfin ilminsu ba. Kuma ba lallai ne waxanda ba su fahimci wata magana da ya yi ba, su iya
Matsayin Daawah Da Muhimmancinta A Rayuwar Musulmi, Ahmad Bello Dogarawa,

6/12/2010

14

neman qarin bayani, ko kuma waxanda suka fahimci kuskure, su gyara masa. Idan kuwa a masallaci ne ko a makaranta, abu ne mai sauqi a nemi qarin bayani ko a yi gyara. Don haka, mai daawah ta kafafen watsa labarai na buqatar kiyaye abubuwa kamar haka: Tabbatar da sahihancin abin da zai faxi, ta hanyar qaidar ( ). Hakan na nufin ya yi nazari cikakke kafin gabatar da karatu, kuma ya nisanci faxin abin da bai tabbatar da ingancinsa ba, ko ba da fatawa dangane da abin da bai sani ba. Laakari da waxanda ke saurarensa ko suke ganinsa, da bambancin fahimtarsu. Sai dai hakan ba yana nufin mai daawah ya voye gaskiya ba ne ko ya yi tawilin wani abu tabbatacce, ba tare da wani dalili mai qarfi ba. Amfani da usulubi da yanayin magana mai sauqi, ta yadda za a fahimce shi gwargwadon iko. Nisantar amfani da kalmomin da ke xaukar maana dabam-daban masu savani da juna, abu ne mai kyau ga mai daawah, musamman ta kafafen watsa labarai Rashin aibanta mutane ko cin mutuncinsu ko tozarta su, ba tare da dalili na sharia ba. Lallai ne mai daawah ta kafafen watsa labarai ya tuna cewa Allah Ya haramta shiga mutuncin jamaa, ba tare da haqqi na sharia ba 6.0 KURA-KURAI DA AKA SHIGAR CIKIN DAAWAH

Nazari cikin harkokin daawah na nuna cewa akwai kura-kurai da dama da aka shigar cikin harkar daawah a wannan lokaci. Daga ciki, akwai: Xaukar cewa idan mutum ya gyara kansa shi ke nan ba sai ya dage wajen yin daawah ba Tunanin cewa sai an tara ximbin ilmi ake yin daawah Taallaqa ga daawah, ba tare da neman abinci ba Rashin ba da fifiko ga abubuwan da suka fi buqatar fifiko, da yawan rigima a kan masalolin ( ) Rashin taawuni tsakanin masu daawah, da rashin tsari da manufa. Amma taawun tsakanin masu daawah da mu ke nufi, shi ne wanda za a yi shi a kan karantarwar Alqurani da ingantacciyar Sunnar Manzon Allah
Matsayin Daawah Da Muhimmancinta A Rayuwar Musulmi, Ahmad Bello Dogarawa,

6/12/2010

15

, bisa fahimtar magabata na qwarai. Duk wani haxin kai da za a nema ba bisa wannan tsari ba, da wuya a kai gare shi. Rashin mayar da himma wajen karatu da karantarwa Mayar da hankali wajen daawah, ba tare da tarbiyya ba. Hakan ya haifar da yawan savani da rashin girmama juna 7.0 GODIYA DA KAMMALAWA

Daga qarshe, ina godiya ga kwamitin Daawah da alamuran Masallatai na jihar Kaduna, da ya ba ni damar gabatar da wannan qasida, a matsayin gudummuwa ta ga limamai da masu daawah na wannan jiha. Abin da ya ke daidai, daga Allah ne, kuma ina roqon Ya ba mu lada, kuma Ya ba mu ikon aiki da shi. Kuskuren da ke ciki, daga gare ni ne, kuma daga shaixan; Allah da ManzonSa sun barranta daga gare shi. Ina roqon Allah Ya yafe mani, kuma Ya ba ni ikon fahimtarsa, don in gyara.

Matsayin Daawah Da Muhimmancinta A Rayuwar Musulmi, Ahmad Bello Dogarawa,

6/12/2010

16

You might also like