(Se lfless Servi ce par Excel lence

)

N.E. 139 Mu’azu Street, Central Mosque Zone, Nasarawa Ward, Minna–Nigeria E-mail: trustmuazu@yahoo.com Sunday, April 29, 2007

Songs Of Mallam Mu’azu_ Composed in 1910 Bismillahir Rahmanir Rahim, wa sallallahu ala sayyidina Muhammadun rasulallahi wa alihi wa as’habihi wa sallama taslima 1 Bismillahi na fara da sunanka - rabbi samu cikin shiri 2 Don rasulu Muhammadu wa alihi – rabbi karka bari mu bace bari 3 Nai yabo ga Muhammadu wa alihi wa as’habihi kulluhu 4 Na roke ka Allah tsaremu kammu fada aikin munkari 5 Mun iso bisa lokacin da talakka yaddara mai gari 6 Zamani na rodi rodi – baka samun mai fari 7 In furar wani taji nono – barta – kai sha kasari 8 Zamani na gashi ya zama ba tudu ba gangare 9 Bar bidan iko ga yanzu- in kana so nai bari 10 Tara kaji zanka kiwo- bar bidan dokin hari 11 Donka gyara kasan wuyanka bar bidan mai gatari 12 Tun kana bisa malmala ba ka koshiba sai bisa kankare 13 Bar bidan cin dukiyar wani kar asaka cikin mari 14 In kwadanka abin mutane a zuba maka sasari 15 Baka tara ruwa cikin malka su taru cikin fari 16 Banda son hutu a inuwa ban da son yawon gari 17 Inda ka samu aiki bar kasala zaburi 18 Dubi dansanda ga aikinai ka dubi na dogari 19 Masu yawon rana na nan wasu kau na tsakan dare 20 Duk nufarsu su sami damri babu duk wani hanzari 21 In kaga tsoho yayi aiki sai kace dan jinjiri 22 Sai kayo zance na banza nan ka tashi kiri kiri 23 Sai kayo karya ka kare ba a ce maka kai kure 24 In kana aikin mutanenda sai a ce maka sakare 25 Zamani na babu yaki duka kausuwa duka ta kare 26 Ba sarauta babu yaki babu daukan ko kare 27 Dada ya kamata mulura yau komai ya bure

28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50

In ka lura ga yanzu kasan ba sauran cin wuri Babu abin da ya kamata garemu sai muyi ta neman gargare Ba a tsoron masu geme anfi tsoron shagirai Babu a bin da yafi garemu illa hankuri Banda barna babu komi babu mai aikin gari Lokaci ya tsufa sai guri muke mun kantare Ya kamata mu lura zamaninga ya zama gangare Zamanin nan ba shari’a ba’ason aikin kwarai Mai karya adda galba mai gaskiya sai hankuri Zamanin nan ba sarauta babu ko wani kokai Kaga sarki an ajeshi an hana masa yunkuri Duk shari’a a tsareta a hana masa yunkuri Ba shari’a ta Allah ba adalci sai dibara akai an kantare K Kaga mata masu aure basu kulle yawo sukai sun bantsare Amri yar haihuwan nan karka yarda da dadiro Sai mu roki tsari ga Allah inda sauran jinkiri Wagga waka alkalin Minna yayyita can da tsakar dare Ranar daren sallah ta hajji a gida gefen gari Sai barci ya kamani naso ta kai baiti dari Na bari nai kwana sai na ajeta rabin dari Tammat bihamdillahi waka na nacikata da marmari Nai yabo ga Muhammadu da sahabbai da alaye nai har su Abdulqadiri

Central Working Committee, Mallam Mu’azu Trust, Minna Working Committee Members: Abdullahi Aliyu, Usman Aliyu, Rilwan Aliyu, Yunusa Abubakar Umar Mohammed

Sign up to vote on this title
UsefulNot useful