You are on page 1of 13

Shugabanci na Gari

Dr. Ahmad Bello Dogarawa, Abu Abdir-Rahmn


Sashen Koyar da Aikin Akanta, Jamiar Ahmadu Bello, Zaria +2348026499981 (abellodogarawa@gmail.com)

Me ne ne Shugabanci?
Shugabanci ya qunshi damar da wanda ragamar jagorancin alumma ke hannunsa ya ke da ita ta yin umurni da hani ga jamaa, bisa manufofin addini da kyawawan aladu jamaa wajen ba da tsaro da kariya ga addini, da kyautata alamuran rayuwar duniya, da kula da dukiyar alumma, da yin tsuwurwurinta, da amfani da ita

yadda ya dace.

Siffofin Shugaba na Gari


Gaskiya Iyawa da qwarewa

Rashin son kai

Haquri

Tausasawa da dogewa; shawara da sadaukarwa

Dalilan Samar da Shugaba


Tsai da dokoki a cikin qasa bisa adalci Tsara alamura da kyautata gudanarwa

Tsare garuruwa daga maqiya da mavarnata

Haxuwar alumma a kan madaidaiciyar kalma

Ba da tsaro da kariya ga

larurori biyar

Larurorin da Shugaba ke ba Kariya

Addini Hankali Dukiya

Rayuwa
Nasaba da Mutunci

Hanyoyin ba da tsaro ga Larurori Biyar Addini


Samar da kyakkyawan yanayin da kowa zai yi addini ba tare da tsangwama ba Yin adalci ga mabiya addini mabanbanta Tamakawa masu kira zuwa ga addini Tsare martabar addini daga duk wani tsari ko alada da

ke karen tsaye ga karantarwar addini


Ba da muhimmanci ga alamuran addini

Hanyoyin ba da tsaro ga Larurori Biyar Rayuwa


Haramta taaddanci ga rai Toshe kafar da za ta kai ga yin kisa

Qisasi ga kisa
Xaukar matakin da zai hana mutane su kashe kansu saboda quncin rayuwa ko rashin sanin qimar rayuwa

Hanyoyin ba da tsaro ga Larurori Biyar Hankali


Hana duk abin da ke vata hankali Zartar da uqubar da ta cancanta ga wanda duk ya sha/zuqi abin da ke sanya maye Hukunta waxanda ke xaure wa `yan qwaya gindi Hukuncin gani ga wane ga duk wanda ke amfani da

`yan qwaya don cin ma manufofin rayuwa (kamar amfani da `yan sara-suka ko `yan kaleri ko `yan daba)

Hanyoyin ba da tsaro ga Larurori Biyar Nasaba da Mutunci


Kwaxaitarwa game aure, da yin aure a kan lokaci Haramta kashe `ya`ya ko zubar da ciki bayan an hura rai Tsawatarwa game da kore nasaba ko kuma tabbatar da ita ba bisa gaskiya ba

Haramta zina da tanadar haddi a kanta


Haramta qazafi da wajabta haddi a kansa

Hanyoyin ba da tsaro ga Larurori Biyar Dukiya


Hana amfani da dukiya bisa varna Hana almubazzaranci

Ba da haqqi ga masu shi


Tsare dukiya daga wawaye Kare dukiya da tsare martabarta Haramta sata da yin haddi ga wanda duk ya sace ta

Manufar Tsare Lurori Biyar


Adalci Sauqaqa cuta Gusar da qiyayya da qyashi

Aminci da ci gaba

Halin da Shugabanci ke Ciki a Yau A yau, shugabanci na [1] cikin matsala. Da yawa daga

shugabanni da wakilan jamaa a siyasance suna wakiltar kawunansu ne kawai, kuma babu ma ruwansu da dokokin da suka naxa su a kan muqamansu. Da yawa daga shugabannin siyasa sun siffantu da:
Rashin kyakkyawan wakilci da jagoranci nagari Maguxin zave Rashin girmama doka Sanya wakilci a hannun waxanda ba su cancanta ba Kusantar da mutanen banza, da nisantar da mutanen

kirki bisa maaunin alaqar siyasa

Halin da Shugabanci ke Ciki a Yau Rub da ciki da yin watanda [2] da dukiyar alumma, da sace

ta, da amfani da ita ba bisa qaida ba Alqawuran qarya, da kuma cin amanar alumma da qasa Raina hankalin jamaa Amfani da muggan makaman zalunci wajen danne alumma: jahilci da talauci Qoqarin zubar da mutuncin masu mutunci Yaxa nauoin varna a cikin qasa Amfani da addini ko vangaranci wajen cin ma buqatun kai

You might also like