0% found this document useful (0 votes)
1K views351 pages

Reina

The document is a fictional narrative centered around characters Saudat, Kamal, and Yaseer as they navigate family dynamics and social interactions during a wedding event. It highlights themes of familial relationships, societal expectations, and the struggles of individuals within a community. The story unfolds through dialogues and interactions that reveal the characters' emotions and perspectives on their roles and treatment by others.
Copyright
© © All Rights Reserved
We take content rights seriously. If you suspect this is your content, claim it here.
Available Formats
Download as DOCX, PDF, TXT or read online on Scribd
0% found this document useful (0 votes)
1K views351 pages

Reina

The document is a fictional narrative centered around characters Saudat, Kamal, and Yaseer as they navigate family dynamics and social interactions during a wedding event. It highlights themes of familial relationships, societal expectations, and the struggles of individuals within a community. The story unfolds through dialogues and interactions that reveal the characters' emotions and perspectives on their roles and treatment by others.
Copyright
© © All Rights Reserved
We take content rights seriously. If you suspect this is your content, claim it here.
Available Formats
Download as DOCX, PDF, TXT or read online on Scribd

*REINA 💍*

_Book 1_

*By Saliha A. Na'ibi (Seemahwrites)*

*Women of words writers*

*Sadaukarwa ga my dear Hanifah shamaki da addaririya ta Ramlat abdulrahman manga(mai dambu). Ina
godiya da sahihiyar ƙauna, Allah ya barmu tare❤️.*

*Disclaimer: Ban amince a sauya min littafi ta ko wace irin siga ko a ɗaura min a wata channel na
youtube ba tare da izini na ba, yin hakan babban kuskure ne kuma zai sanya mu saka ƙafar matsatstsen
wando ɗaya da mutum*

_Any resemblance to any figure or event, deceased or living is purely coincidental_

‫بسم الله الرحمان الرحيم‬

01...shi zumunci a wannan zamanin na mai shi ne, ga masu hannu da maiƙo ake sada zumunta mai
bushashshiyar hannu kuwa saidai shi ya sada ta"

Taɓe baki Saudat tayi tana gyara kwanciyar Suhail a jikin ta wanda tunda iskar napep ta kaɗa shi barci
yayi awon gaba da shi
"Amma abin yayi yawa Abban Yaseer. Ko wani hidima nasu muna kan zirya a hanya amma ko sau ɗaya!
Ko sau ɗaya fa ban taɓa haihuwa mutanen nan suka ɗago ɗaya daga cikin su yazo mana barka ko suna
ba saidai mu ko yaushe muna kan faman kashe kuɗin adaidaita zuwa gidajen su.

Yamutsa fuska yayi alamun baiji daɗin zancen ta ba, ga Yaseer ɗin dake zaune a tsakanin su ya kafe shi
da idanu yana dakon amsar da mahaifin nasu zai bayar don da gaske ko shi mai shekaru 12 ya fahimci
cewa yawan zirya da suke ma ƴan uwan mahaifin nashi ba buƙata ko appreciating suke yi ba balle kuma
mahaifiyar da ta haife su.

"Ƴan uwana ne fa Saudatu. Ki taya ni son su mana"

Girgiza kai tayi "nifa ba son ƴan uwan ka bane bana yi, kawai yanda suke treating ɗinmu ne bani jin daɗi
gaskiya. Su basu ɗauke mu a matsayin ƴan uwa ba sai kaman masu aikin su kuma ba don basu da isassun
masu musu hidima bane A'a! Don kawai a gwada mana matsayin mu ne"

"Nima idan na shiga wasan su Jamal kora ta suke yi wai wasan su ba na ƴan ƙauye bane" cewar Yaseer .

Kama baki Saudat tayi. "Kaji marasa kunyan yara, duk baka girme musu bane don sun samu ma kai ke
binsu har zasu na maka rashin kunya?"

Kamal ya ɗaura hannu saman cinyar Yaseer ɗin gudun kada ya biye wa mahaifiyar shi su mulmula
ƙaramin zance zuwa babba.

"Kuɗi shi ke bada matsayi ba shekaru ba. Ku lura mana cikin su Alhaji Tahir ne ƙarami Amma shine gaba
a komi na hidimar family, ko family meeting za'a yi ba mai fara magana sai yayi, kuma idan ya bada
shawara a take zai rikiɗe ya koma umarni, ba mai ja dashi a kan adalci ko rashin adalcin sa ba don komai
ba sai don Allah ya wadata shi fiye da sauran. don haka kada kaji komai don ka girme su tunda nasu
gidan kazo sai ka lallaɓa su har su barka ka shiga wasan ko?".

"Oh shima koya mishi jurar wulaƙanci kenan zaka yi?" Saudat tayi kicin-kicin da fuska.

Bai samu damar bata amsa ba kasancewar sun iso. Motoci ne kala-kala jere har kusan ƙarshen layin, shi
yasa a tsallake mai napep yayi parking yana jiran su fita su sallame shi.

Kamal ya ɗauki Suhail dake barci saudat kuma ta janyo ƙaton cikin ta da ƙyar ta fito tana gyara zaman
wuyan hijab ɗinta da baƙar jakar ta ƴar kullum wanda kwance ne Hajiya Fauziyya ta bata shine ya zamo
mata na shiga taro.
Ta riƙo hannun yaseer yayin da Kamal ya biya mai adaidaita ya tafi sannan suka nufi gate ɗin
tamfatsetsen gidan suna gaisawa da masu gadi don an riga an san su aka buɗe musu ƙofa suka shige.
Saida suka ɗan taka suka sake shigewa gate na biyu kafin girman gidan ya daɗa bayyana da kuma
mutanen dake hada² a cikin ta.

Saudat bata san me yasa jikin ta yayi sanyi ba ganin ta kusa saduwa da su sai dai shima kamal ɗin haka
take a gurin sa, taya su murnar biki suka zo yi amma ba lallai a basu muhimmanci ba domin jiya da
shekaran jiya ma haka ta kasance idan suka gama musu ayyukan da suke buƙata toh har su tafi ma babu
wanda yake lura, kuma ko sallamar kayan biki ba'a musu tunda su ba komai suke kawowa ba. Saudat da
tayi musu gudumawar kayan su muciya, bulogari, ƙoƙo, mara, tsintsiyar kwakwa dana laushi harma
dasu kuka, busasshen kuɓewa, daddawa, barkono da kanwa daga ƙauye ce mata sukayi sun gode ba'a
buƙata don an daina amfani da irin wannan tarukucen yanzu, shara da injin vacuum cleaner ake yi kaɗa
miya kuma ga whisker. Shine tace musu har sharar harabar gida ma da injin ake yinta? To ai sai ayi mata
da tsintsiyar sauran tarukucen kuma tayi kyauta da su ga masu buƙata. Haka dai ba daraja suka amsa
ballantana ta saka ran samun godiya, bata bar gidan ba tana ji tana gani aka yi rabon kayan ma sauran
ƴan aiki.

"Ke da Suhail ku shiga ɓangaren matan, zan tafi da Yaseer mu gaisa da masu gidan" Kamal ne ya dawo da
ita daga duniyar tunanin da ta lula.

Gyaɗa kai tayi ya ɗan bubbuga Suhail ɗin ya buɗe ido kafin ya sauƙe shi a ƙasa Saudat ta kama hannun
shi sukayi cikin gidan yana mutstsuka idanu. Da duk wanda suka ci karo a hanya Saudat sai ta ɗan duƙa
ta gaida su haka ma Suhail har suka isa babban falon da manyan hajiyoyi ke manne a kujera ƙafa ɗaya
kan ɗaya kowa tana faman kaɗa warwarayen gold ɗinta don yafi na ƴar uwarta ƙara, wa'inda basu kai su
matsayi ba kuma ke kai komo na hidimar biki.

Samun wuri a ƙasa Saudat tayi ta zauna tana gaida su Suhail ma ya zauna gefen ta, wa'inda suka ga dama
suka amsa gaisuwar sauran kuma suka yi kaman basu san da halittar ta a wurin ba.

Hajiya Hauwa da fitowar ta kenan daga uwar ɗaka bayanta biye da Hajiya Fauziyya ta kalli Saudat, ko
damar gaida ta bata bayar ma Saudat ba tace "yauwa Saudatu sai yanzu kika iso? Dama ana niman masu
wankin waken yin alalar yamma wajen Inna larai, kije ki same su a can".

Bata amsa ta ba sai cewa tayi "ina wuni Hajiya yaya hidima?"
Ɗan ƙaramin tsaki tayi sannan ta amsa da "lafiya lau"

"Toh Allah ya bada zaman lafiya, Allah yasa gidan zamanta ne"

Cikin ƙosawa tace "ameen ba zaki iya taimakon bane in samu wata?"

Nan ma bata amsa ta ba ta gaida Hajiya Fauziyya wanda ta amsa da murmushi saman fuskarta itama
tana ɗauke da zungureren ciki aihuwa yau ko gobe tace "ina Yaseer ko ba'a zo mana dashi bane?"

"A'a yana waje tare da Abban shi."

"Toh yayi kyau" ta juya wurin Hajiya Hauwa "Umman Jamal barin je in shigo da su aunty Zeenat"

"A'a da dai kin bari an tura a shigo dasu, ke da kike fama da tsohon ciki amma sai ɗawainiya kike tun
Safiya "

Kallon cikin jikin ta Saudat tayi, girman shi ɗaya da na Fauziyya ko ma ya fishi girma tunda ita ƙibar hutu
dama cikin yasa jikin ta ya shanye shi, amma na Saudat gashi a ƙasa ranƙwalele shine kuma ake saka ta
surfen wake bama yanka salad ko irin haɗa su zoɓo ba. Ko ita ba ɗan adam bane a cikin nata?.

Murmushi Hajiya Fauziyya tayi tace "zan iya, yanzu idan na shigo dasu zan samu in zauna"

"toh shikkenan a kula dai kar a wahalar mana da ɗa"

Nanma murmushi Hajiya Fauziyya tayi ba tare da ta sake cewa komai ba ta nufi hanyar barin parlourn.

Itama Saudat tashi tayi kafin Hajiya Hauwan ta sake cewa wani abu tace "barin je toh"

"Yauwa da yafi" cewar Hajiya Hauwa sannan ta shiga gaisawa da sauran hajiyoyin da zuwan su kenan
cikin fara'a da annashuwa.

Haka Saudat ta ƙarasa ta bayan gidan wurin da ake faman haɗa kalolin abinci cikin manya manyan
tukwane wanda zai ciyar da ɗaruruwan mutane. A cikin dandazon masu aikin ta tsinto Inna larai ta riƙo
hannun ta don ta samu hankalin ta suka gaisa sannan tace. "Inna ance ana buƙatar ƙarin masu surfen
waken alala, shine nazo"
"Lalala ƴar nan! Da wannan tsohon cikin zakiyi surfe kalan ki haihu a gidan biki ace ni na takalo miki
naƙuda!"

Saudat tayi murmushi kawai "toh kije can ga su Rabi suna haɗa salad sai ki kama musu yanka kabeji ko
kankare karas"

taji daɗin sauyin aikin da Inna larai ta bata duba da yanayin ta wanda wancan makauniyar ta kasa, haka
kuwa tayi mata godiya sannan taje ta fara aikin ta cikin azama suna taɓa hira dasu rabi don sun ɗan
saba.

...

Kamal da ya duba bai samu ko ɗaya daga cikin mazajen bane ya koma wurin masu gadi suna ɗan taɓa
hira shima don zaman cikin gida ba nashi bane. Suna nan zaune motar yankakku kuma feɗaɗɗun shanu
har guda 3 ya iso nan suka tashi ya shiga cikin su don taya mahautan sauƙewa sannan suka ɗunguma
yanka naman gunduwa² da kuma faskaren ƙashi, don haka kafin a gama farar shaddar shi ta Sallah
wanda sawa ta 3 zuwa 4 kenan da yayi mata tayi caɓa² da jini.

...

Wuraren ƙarfe 4:30 na yamma an gama cike motocin kai amarya da suka ƙaraso, saboda girman cikin ta
Alhaji Tahir ya gargaɗi Hajiya Fauziyya da kar ta bisu. Hakan yasa ta yanke shawarar yin zaman ta har
masu kai amaryar suje su dawo in yaso aka zo tafiya dinner da daddare sai taje, gashi dama bata wani jin
ɗaɗi tun da rana ta fara yin sanyi.

Dagewa suka yi saidai ta kai musu amarya mota tunda ba zata bi ayari ba, haka kuwa akayi, ta rungume
amarya Sakina tana faman turawa har jikin danƙareren farar jeep ɗin da aka kawo don ɗaukar ta suka
amshe ta daga nan sannan ita ta koma ciki.

A hanyar ta na komawa Yaseer yayi saurin shan gaban ta. Ta ɗan firgita da gudun da ya ɗibo ganin
sauran kaɗan ya mangare mata ciki amma tana gane shi sai itama ta saki fuska. "Yaseer yaya school" ta
tambaya hannun ta a kan cikin tana fitar da numfashi.

"Ina wuni aunty" ya rusuna har ƙasa don gaida ta.


"Lafiy..." Amsar ta ya katse ganin Yaseer ɗin ya miƙe hannun shi riƙe da ɓawon ayaba da aka ci aka yasar
akan interlocking ɗin wanda ba don Yaseer ɗin yayi saurin tsare ta ba, toh da tabbas ta taka shi zamewa
zata yi ta faɗi.

"Wayyo Allah yarona na gode. Ka ceci rayuwar ƙanwar ka" ta shafa cikin tare da faɗaɗa murmushi.

Shima murmushin ya mayar mata don shi dai matar tana birge shi ba don komai ba ko dan yawan fara'ar
ta. Bata da yawan magana sai murmushi kuma ita kaɗai ce idan ya gaishe ta ko iyayen shi suka gaida ta
take amsawa cikin mutuntawa.

"Kaci abinci?" Ta tambaya cikin kulawa.

Girgiza kai Yaseer yayi alaman A'a.

"Muje ciki a saka maka kaci" ta fada cikin dakakkiyar murya sanin cewa zai iya mata musu don yana da
kawaici, yana buƙatar abu amma idan ka bashi sai yace maka 'A'a na gode' ko kuma 'ki barshi kawai'.

Babu musu ya bita a baya har cikin babban parlourn Hajiya Lubabatu uwar amarya. Sannan tace a saka
mata abinci.

Babu ɓata lokaci aka kawo mata plate ɗauke da fried rice, gefe ga stir fried spaghetti mai ɗauke da
veggies yasha nama sai kuma kwatan kaza a saman shikafar da coleslaw a gefe ga alalen laida da aka riga
aka ɓare mata aka saka wuƙa aka yanka gida hudu sannan aka zuba onion sauce a kai don a tunanin su
ita ce zata ci. Sai kuma disposable cup dake ɗauke da kunun aya an rufe da murfin shi an zura straw a
ciki don sauƙin sha.

Kiran Yaseer tayi ta ajiye mishi plate ɗin a kan dining table sannan tace ya ja kujera ya zauna ya ci.

Ya haɗiyi miyau ganin kayan daɗin da aka shaƙe plate ɗin dashi sannan a maimakon ya zauna sai ya
ɗauki plate ɗin a hannun shi.

"Zan kai muci da Umma na Aunty" haka kowa yake ce mata Aunty tunda bata taɓa haihuwa ba tukuna
ballantana a lanƙaya mata sunan abinda ta haifa.
"Umman kan itama bata ci abincin ba?" Fauziyya ta tambaya cike da mamaki.

Sanin cewa Saudat ba zata iya samun abinci taci ita kaɗai ba tare da ta kira shi, shi da Suhail ba yasa ya
girgiza mata kai kawai.

"Indo kawo wani plate ɗin abincin" ta umarta.

"Ma waye ne aunty?" Indon ta tambaya gudun kada ta sake zuba bajintan ta a sake kyautarwa.

"Ma nice, ki saka min tuwo da zobo kuma ya ji nama"

"Toh Aunty" bata da zaɓin da ya wuce tayi yanda aka ce da ita.

Saida aka gama zubawa aka ajiye a saman dining sannan tace da Yaseer "kaje ka kira umman ka da ƙanin
ka kuzo ku ci a nan" ta faɗa don itama bata kiyaye sunan Suhail ba. Shima da "Toh Aunty". Ya amsa, Ya
fita da gudu don kiran umman tashi".

Mrs Imran ✨

*REINA💍*

BookNest, arewabooks and Wattpad @ Seemahwrites

‫بسم الله الرحمان الرحيم‬


02...... "Toh aunty" ya amsa mata sannan ya fita kiran Saudat. Hajiya Fauziyya bata bar wurin ba har
saida Yaseer ya dawo tare da umman shi da ma Suhail wanda yake ta mata mitan yana jin yunwa shine
Inna larai tace bari taje ta karɓo masa tuwo, kafin ta dawo ne Yaseer yazo yace Aunty na kiran Saudat
amma bai faɗa mata dalilin kiran ba.

"Gani Aunty" Saudat ta faɗa tana shirin kai duka ma Suhail wanda yanzu ya fara kuka saboda yin arba da
abincin dake kan dining a gaban Hajiya Fauziyyan. Miƙewa tayi da ƙyar sannan ta nuna ma Saudat ɗin
kujeran da ta tashi.

"Ki samu ki bawa yaran abinci. Ni barin shiga ciki in ɗan watsa ruwa ko zan ji daɗin jiki na" da faɗar haka
tayi shigewar ta ɗakin dake kusa da dining area wanda na musamman aka bar mata ta tare a cikin sa har
a gama hidimar biki duk da kuwa ba a gidan take kwana ba, da kanshi Alhaji Tahir yake maida ta gida duk
dare saboda kiyaye abinda ke cikin ta.

Tana ƙulewa ciki Saudat tayi saurin zama don itama yunwar take ji. Anyi rabon abinci bayan sun gama
aiki amma ba'a bata ba ganin itama ƴar cikin gida ne tana da damar shiga ciki ta ci, Itama kuma sai bata
yi magana ba har saida Suhail ya fara mita kafin Inna larai ta fahimci halin da suke ciki.

A nutse Yaseer ya fara cin tuwon domin ya bar musu shinkafar su ci. Saudat tasa cokali ta fara baiwa
Suhail a baki amma sai ya janyo plate ɗin saboda ƙaguwa ya luma yatsun shi ciki yana dunƙulo manyan
loma yana jefawa a baki. Cikin ƙanƙanin lokaci ya ɓata wurin ya kuma ɓata kayan shi da maiƙo.

....

Hajiya Fauziyya na shiga ciki ta sanya wa ƙofar sakata kafin ta shiga rage kayan jikin ta ta ɗaura
madaidaicin towel. Har ta isa ƙofar bathroom Amma murɗin da taji cikin ta yayi wanda saida ya saka ta
saki ƙaramin ƙara yasa ta dawo a hankali ta cire sakatar sannan ta shiga ban ɗakin, haka shima tura ƙofa
kawai tayi ta daidaita temperature na ruwan da ɗan zafi sannan ta sake ma kanta shower.

A daddafe ta ƙarasa wankan ta kashe shower, taso ta tsane jikinta tun a cikin bathroom amma abin da
take ji yana niman wuce tunanin ta hakan yasa ta tako a hankali ta fito tana kama garu. Niman wayan ta
ta shiga yi saidai ta manto shi wurin da ta zauna a kan dining.
Fara jero 'hasbunallahu wa niimal wakeel' tayi tana addu'ar Allah ya bata ƙarfin sanya sutura a jikin ta
kafin wani ya shigo ya same ta cikin wannan yanayi.

Ta samu nasarar maida undies ɗinta da ƙyar, amma kafin tayi aune ruwan ta ya fashe!.

Wai-wai ta fara tana yarfa hannuwa, sai dai ganin zata iya kwana a haka babu wanda ya jita gashi abu sai
gaba-gaba yake yi yasa ta ƙwalla ƙara, tana buga jikin gadon da iya ƙarfin ta tana matsar ƙwolla.

....

Sun kusan tada abincin dake plates ɗin duka suka fara jiyo sautin bugun da Hajiya Fauziyya take yi
amma sai Saudat ta basar ganin ba abinda ya shafe ta bane.

"Umma kinji kamar ana bugun ƙofar can" Yaseer ya nuna ƙofar ɗakin da Hajiya Fauziyya take.

"Anya kuwa? Wataƙil wani abun dai take bugawa a ciki". Saudat tayi ƙoƙarin kawar da ko wace irin
mummunan tunani a ranta suka ci gaba da cin abincin su.

Wayar dake gefen plate ɗin tuwon Yaseer ne ya fara ruri, ya jawo ta sannan ya miƙa ma Saudat.

"Umma wannan kamar wayan aunty"

Serviette ɗin da ke tsakiyar dining Saudat ta ciri ɗaya ta goge hannun ta da na Suhail don kada shi ma ya
damƙi wayar ya ɓata musu sannan ta karɓa wayar yayin da kiran ya yanke a take kuma wani ya sake
shigowa ta duba sunan mai kiran don tabbatar da wayar wacece.

'Habeeby Da'eeman' ta gani as caller ID sai kuma hoton bikin Alhaji Tahir ɗin tare da hajiya Fauziyya da
aka yi shi shekaru 2 da suka wuce ya bayyana a ɗan ƙaramin zagayayyen akwati.

Saurin miƙewa tayi ta ƙarasa jikin ɗakin sai a sannan ta fara jiyo kukan Hajiya Fauziyya tare da ihun
niman taimako, ai ko da azama ta bankaɗe ƙofar ɗakin ta shige. Nan ta hango ta yashe a jikin gado daga
ita sai bra and underwear wanda ruwan naƙuda dake bin ƙafar ta yayi soaking ɗin shi.
"Subhanallahi!" Saudat ta ƙarasa jikin ta sai kuma ta rasa yaya zata yi don bata tunanin zata iya ɗaga
Hajiya Fauziyya da cikin dake jikin ta. Wani kiran ne ya sake shigowa wayar Hajiya Fauziyya Saudat tayi
saurin ɗagawa don bata tunanin Aunty zata iya amsawa cikin halin da take.

"Hello Fauza!" Muryar Alhaji Tahir ya doki dodon kunnen ta. Bai tsaya jin ta amsa ba ya ƙara da "kina ina
ne nake ta kira baki picking duk kin saka hankali na ya tashi?."

"Ba ita bace Saudat ce matar Kamal "

Rage sautin damuwar da ya bayyana a Muryar shi yayi "Toh ina Fauzan take?" Ya tambaya a kaikaice.

Kafin Saudat ta bada amsa Aunty ta saki razanannen ƙara da ya saka harta Alhaji Tahir dake ta cikin waya
sai da ya firgita.

"Wayyo Allah Tahir zan mutu ka taimake ni innalillahi!"

"Naƙuda ne ya tashi mata a gidan Hajiya Luba, yanzu zan fito da..." Bai jira sauraren ƙarshen zancen ta
ba ya katse kiran. Itama Saudat jefar da wayar tayi a kan gado sannan ta ɗauki doguwar rigar Hajiya
Fauziyyan ta suturta mata jikin ta.

Fita ƙofar ɗakin tayi, Yaseer yana nan wurin da ta barshi, Suhail ya komo kan cinyar shi.

"Yi sauri ka kira min indo Yaseer" ta umarta tare da hanzarin komawa ciki. Shima Yaseer ɗin sauƙe Suhail
yayi ya fita da gudu jin desperation ɗin dake cikin muryar mahaifiyar shi.

Ba'a daɗe ba ya dawo tare da indo suka samu har Saudat ta riƙo Aunty sun fito. Nan indo ta kama mata
suka yi hanyar waje, ganin halin da ake ciki yasa Yaseer sake ɗiban gudu ya fita kiran driver. Sai aka ci
Sa'a har Alhaji Tahir ya kira drivern ta ya faɗa mishi tunda shi yayi nisa kuma zai ɗauki lokaci kafin ya
ƙaraso duk da kuwa a take ya taso.

Driver yana jiran su a daidai mashiga na babban farlour suna fita duk suka faɗa motan, Yaseer ma ya
shiga gidan gaba ya zauna suka zugi mota suka nufi asibiti aka manta da Suhail.
....

Gadan² haihuwa tazo ma Hajiya Fauziyya don haka suna isa asibiti aka shiga da ita labour room. cikin
ƙasa da minti 30 Alhaji Tahir ya ƙaraso tare da wanda yake bi Alhaji Salisu mijin Hajiya Hauwa dake
lokacin suna tare yayi waya da Saudat. Isowar su bada jimawa ba Alhaji kalabu babban yayan su shima
ya iso haka duk suka jeru cirko-cirko ana zaman jiran tsammani, kafin wani lokaci sai ga ƴan uwansu
mata ma sun ƙaraso daga gidan ɗaukan amarya suma suka shiga sahu.

Bayan awa ɗaya saƙo mai daɗi ya iso gare su. Hajiya Fauziyya ta sauƙa lafiya kuma an samu ƴa mace,
turus suka yi da jin haka don sunyi tsammani namiji zata haifa, yanda Alhaji Tahir yake son ɗa namiji don
ya samu magaji da kuma ganin yanda yake rawar ƙafa akan cikin nan yasa duk suka yi tunanin an riga an
faɗa musu namiji zata haifa amma kuma shi ya riga da ya san kwanan zancen.

Shi ya fara shiga bayan an kai su ɗakin hutu an gama kintsa Fauziyya da ƴar ta aka kwantar mata ita a
saman kirjin ta.

Da murmushi a saman fuskar shi ya ƙarasa jikin gadon. Peck ya fara sauƙewa Fauziyya a kan goshin ta,
daɗin hakan da yayi ya sanya ta lumshe idanun ta itama tana murmushi.

"Nagode. Fauza kin biya ni, Allah ya sanya ki a gidan aljannah" laɓɓan bakin ta ne ya nuna alamun ta
amsa da 'ameen' amma bai fitar da sauti ba.

Hannu yasa da nufin ɗaukan babyn cikin kiyayewa da taka tsantsan, nurse ɗin da ta gama kintsa musu
ɗakin ta taimaka mishi ya rungume babyn shi a ƙirjin shi kafin ta fice don basu wuri.

Kallon tatsitsin fuskar yarinyar yayi tare da furta "Tabarakallah masha Allah. Fauza see her cute little
face" ya faɗa idanun shi kafe a kan yarinyar kamar zasu zubar da ƙwolla.

"I'm sorry T. Ba namiji bane" ta faɗa cikin kasasshiyar murya.

"No Fauza, namijin ma Allah zai kawo. Idan ma Allah bai bamu ba baby mai ta rage mu dashi? Zata zama
magajiya kuma sarauniyar T.K Kingdom ko baby na?" Ya shafa ɗan bayan ta.
Har cikin ranta Hajiya Fauziyya taji daɗin kalamin shi. Ya matso mata da yarinyar ganin ta buɗe idanun ta
tana mommotsa baki. Yatsar ta manuniya Fauziyya ta zura cikin tafin hannun yarinyar ta kuwa damƙe
yatsar, dukkan su suka saki murmushi mai sauti kafin Fauziyya ta ɗan jijjiga yatsar dake hannun babyn a
hankali ta furta "Helloo REINA".

"REINA? Sunan da kike so a saka mata kenan?"

Dariya Fauziyya tayi tace "A'a yana nufin Sarauniya. Sarauniyar dadyn ta kuma sarauniyar T.K Kingdom".
Suka sake sakin murmushi yayin da ƙofar ta buɗe Hajiya Lubabatu ta leƙo.

"Nace a bamu yarinyar mu gani kafin ku gama".

"A'a Addah ku shigo don Allah" Hajiya Fauziyya ta amsa tare da zare hannun ta daga cikin na Reina.

Shiko Alhaji Tahir ba haka ya so ba, don bai ƙi a basu babyn ba, su barsu su ci gaba da zantawa domin ji
yake yi kaman ya haɗiye Fauzar shi tsantsan so.

Suna ganin an baiwa Hajiya Luba damar shiga duk suka yi dandazon shigowa ɗakin ciki harda saudat riƙe
da hannun Yaseer harma da Kamal da ya biyo su a acaɓa ganin mota ya fito daga cikin gidan ya fita da
ɗan iskan gudu ga kuma Yaseer a gidan gaba, sai kuma Suhail ya fito yana kuka an koro shi daga cikin
gidan kuma baiga umman shi ba, ga jikin shi duk datti.

Miƙa musu babyn Alhaji Tahir yayi aka fara passing-passing da ita duk wanda yayi arba da tatsitsin fuskar
ta sai ya ambaci masha Allah gashi ta ware idanun ta dar a kan mutane tana turo harce daga cikin ɗan
bakin ta.

Hajiya Jummai wanda Alhaji Salisu yake bi itace last ɗin karɓa a cikin su sai ya zamo Saudat ne kawai
bata ga fuskar babyn ba jira take idan sun gama su bata amma sai Hajiya Jummai ta riƙe ta tsamm a jiki
ba don bata san Saudat ɗin jira take ba sai don ba zata bayar bane kawai.

"Hajiya bari in ɗan ga jaririyar" Saudat ta miƙa mata hannu ganin bata da niyya.
Kallon sama da ƙasa Jummai tayi wa Saudat, tana jin yanda take tashin tsami² saboda aikin da suka sha a
cikin rana. Abin ka da babu turare mai karfi.

A maimakon ko nuna mata fuskar babyn tayi a hannun ta ba tare da ta bawa Saudat ɗin ba sai cewa
tayi.

"Wai me ma yasa kuka wani tattaro zuga kuka zo ne? asibiti kaman wani gidan biki?"

Maganar ya doke ta. Su ba zugan suka yi ba harda sakawa a je a ɗibo musu yara kaman mai jegon ba
gida zata koma ba?

"Ba don Saudat ba maybe da wani zancen ake yi. Ita ta taimaka min na iso asibiti a kan lokaci don Allah
ku bata Reina taga ƴar ta" cewar Hajiya Fauziyya cikin sassanyar murya yanda ba zata ɓata ran Hajiya
Jummai ba ta hanyar yi ma Saudat adalci. amma duk da haka sai da Jummai ta ƙufula gani take saboda
an haifa wa mai dukiya ƴar So ne har take iya bata umarni tana matsayin yayar mijin ta.

"Wacece kuma Reina?" Kusan dukkan su suka hada baki wurin tambaya.

Ƙasa Fauziyya tayi da kai don bata san lokacin da tayi suɓutar baki ba sunan ya fita.

"Gata a hannun ku, sarauniyar T.K Kingdom" Alhaji Tahir ya basu amsa.

riƙe baki Hajiya Hauwa tayi "tohh, ai shikkenan munyi kamu. Jamal zo kaga matar ka" ta riƙo hannun
yaron ta mai shekaru 9 da nufin su karɓi babyn ya ganta.

Daɗa rungume Reina Hajiya Jummai tayi a ƙirji. "Ko kuma matar Haydar ɗina ba"

"Ko ta lukman dai" Hajiya luba ta tsuke fuska. Da mamaki Hajiya Farida mai bin Hajiya luba tace "haba
yaya. Lukman mai shekaru fiye da 20 me zeyi da babyn da aka haifa yau? Ai kafin ta girma ya zama
magidanci da ƴaƴa"
"Kuma sarauniya ta ba zata zama kishiyar wata ba" Alhaji Tahir ya faɗa. Yana karɓar yar shi daga hannun
hajiya Jummai.

"Shiyasa nace Jamal ɗinne ya dace da ita. Tazarar shekara 9 a tsakani yayi dai²"

Nan suka ci gaba da musu a ƙarshe dai Kamal waje ya fita ganin zancen na manya ne, yarinyar da bata
shaƙi iskar duniya na fiye da minti 30 ba har an mata miji.

Saudat ma har aka ƙarashe kacaniyar su basu bata babyn ba daga ƙarshe ne likita ya buƙaci ganin mai
jego nan kowa ya watse.

Yaseer shine ƙarshen fita bayan Saudat. Har yaje bakin ƙofa ya dawo da gudu jikin crib ɗin da yanzu aka
kwantar da babyn bayan ta koma barci.

Leƙa fuskar ta yayi tare da taɓe baki.

"Caɓdi, ashe mummuna ne ma Reinan aka wani dame mu"

ya faɗi hakan ne sanadiyyar jin haushin banzantarwan da aka yi wa mahaifiyar shi amma ji yake kamar
yayi ta lallatsa fuskar babyn.

Da sauri saudat ta dawo ta riƙo hannun shi. "Yi hakuri don Allah aunty, yarinta ke damun shi."

Murmushi Fauziyya tayi tace "kiyi haƙuri umman Yaseer, sannan kizo kiga baby idan mun koma gida dan
Allah. Na gode sosai da taimakon ki, kema Allah ya sauƙe ki lafiya"

"Ameen, in sha Allah" Saudat ta amsa sannan tayi saurin fita da Yaseer saboda likitan ya ƙaraso.

....

"Ashe an samu ƙaruwa Alhaji, Allah ya raya" cewar Kamal da yayi arba da Alhaji Tahir tare da Alhaji salisu
bayan sun fito daga ɗakin.
"Ameen Kamalu na gode" ya juya yaci gaba da maganar shi da Salisu.

Sunan mahaifinsu gare shi amma yana shan mamaki duk lokacin da suka kira gatsau babu wani sakaye.

Ganin kamal ya ci gaba da tsayuwa yasa Alhaji salihu tambayar

"Yaya dai? Da wani abun ne?".

Yasan cewa environment ɗin da suke bai dace da maganar dake ƙunshe a bakin shi ba amma bayi da
yanda zaiyi ne. Yayi ta niman yanda zaiyi ya haɗu da Alhaji Tahir ɗin amma abu ya ci tura sai yanzu kuma
nan da kwana biyu za'a rufe registration.

"Daman maganar makarantar Yaseer ne. Nace an fara registration na jss1 har ana niman rufewa bamu
samu daman yi ba" rufe bakin shi ke da wuya Alhaji Salisu yace.

"Amma baka da hankali wallahi Kamalu!. Haba! Mutumin da aka yi wa haihuwa a asibiti kake tambaya
kuɗi?"

Shiru kamal yayi don bayi da ta cewa.

Taɓe baki Alhaji Tahir yayi kafin ya zura hannu cikin aljihun shi yana ƙirga kuɗin kafin ya zaro dubu 10 ya
miƙa wa kamal.

"Ga wannan a masa register daga baya sai kazo ka karɓi na uniform"

Godiya kamal yayi yana shirin karɓa Alhaji Salisu yayi saurin wafce kuɗin.

"Haba kai kuwa Tahir, an haifi sarauniya guda baka sallami ma'aikatan asibitin da suka taimaki matar ka
ba zaka cire kuɗi ka bashi? Ai saidai ya biyo ka daga bayan ya karɓa duka".

Gyaɗa kai alhaji tahir yayi alamun gamsuwa. "Toh shikkenan gobe sai kazo gida ka same ni ka karɓi gaba
ɗayan"
Yana gani Alhaji Salisu ya zura kuɗin cikin aljihun shi suka juya suka yi tafiyar su yayin da Kamal ya bushe
a wurin da mamaki. In ba baƙin hali ba me Alhaji Salisu zai yi da naira dubu10 fisabilillahi!?.

*Mrs Imran ✨*

*REINA💍*

‫بسم الله الرحمان الرحيم‬

03.....hankali, a hankali. Kamar zaiyi mata tafiyar haka Alhaji Tahir ke riƙe da Hajiya Fauziyya yana ƙirga
dukkan takun ta cikin kiyayewa har suka shiga Babban parlourn. Kaman daga sama aka shiga saka guɗa
ta ko wani kusurwa har saida Reina dake bacci a hannun aunty Zeenat ta ɗan firgita.

"Lale maraba lale, barka da zuwa sarauniyar T.K kingdom" cewar Aina'u shugaban masu aikin Hajiya
Fauziyya cikin ɗaga murya tana tafa hannu cike da nishaɗi sannan ta saake sake guɗa "ayyyiiririii" tana
taku da baya-baya a gaban su Alhaji Tahir da Hajiya Fauziyya dake shigowa fuskar su cike da annashuwa.
"Ƴar gatan maman ta, Sarauniyar baban ta, ƴar kuɗi jikan kuɗi, walwalan talakawa, babbar mace mai
ƙashin arziki, duk inda kika zauna, duk inda kika rarrafa, duk inda kika kama kika tsaya, duk inda kika taka
sai ya wadata da dukiya in sha Allahu, lale maraba da matar mai tsantsan rabo..." Hannu kawai Alhaji
Tahir ya luma cikin aljihu ya ɗebo abin da ya rage ba tare da ya ƙirga ba ya danƙa ma Aina'u wanda ta
zube a saman guiwowin ta kafin ta amsa tana sake sakin guɗa sauran ma'aikatan suka shiga taya ta.
Daga nan suka ɗunguma da mukarraban da suka biyo shi daga asibiti zuwa ɗakin da aka shirya mata a
ƙasa domin Alhaji Tahir ya yanke cewa ba zata iya hawan bene zuwa ɗakin ta dake sama da ɗanyen jego
ba.

Saida ya zaunar da ita a saman gadon sannan ya zauna suna fuskantar juna, kana ya buƙaci a Bashi Reina
da ta fara ƴan ƙananun koke-koke saboda hayaniyar su ba zai barta ta mayar da barci ba.

Ƙura ma Reina, Jaririyar kwana biyu idanu Alhaji Tahir yayi ya dulmuya cikin tunanin da Allah kaɗai ya
sani, mutanen da suka rako su kuma sun fita tanadar musu da kayan buƙata, kamar ruwan wankan
jaririya da uwar ta, abinci da kuma tea mai kaurin da Fauziyya take ɗirka tun a asibiti don Tahir ya hana
ta shan sirki. A bisa matsawan sa ma suka yi kwana biyu a asibiti dukda cewan dukkan su lafiyar su ƙalau
amma yace a tabbatar tukunna kada sai sun koma gida wani abun ya biyo baya.
"My T" Ta kira shi, sai ya ɗago idanun shi daga kan ƴar shi ya zuba su a kan abin ƙaunar shi tare da sakar
mata murmushi.

"Umm nace wani suna ka saka mata?" Ta tambaya don ta san yayi mata huɗuba yau da safen.

"Reina na saka mata"

Darawa tayi kafin tace "Reina suna ne?"

"Eh mana, ba ke kika ƙala mata ba?" Ya faɗa yana yiwa ƴarsa wasa tare da lakatar ɗan kumatun ta.

"Dan Allah da gaske nake T" ta riƙo hannun da yake wasa dashi ba tare da ta bar dariyan ba.

"Hafsatu sunan ta" yace yana kallon cikin idanun ta, abinda yayi tsammanin kuwa shi ya gani, tsananin
farin ciki da jin daɗi ne ya bayyana a cikin su.

"Sunan Ummi na ka mayar T?" Ta tambaya cikin mamaki don bata yi tsammanin hakan daga gare shi ba,
akwai mutane da yawa da suka cancanci a mayar da sunan su cikin familyn shi amma ya tsallake har
tashi mahaifiyar da ta riga mu gidan gaskiya ya saka sunan nata.

Ya gyaɗa mata kai. Sai ta ƙara ƙarfin riƙon da tayi ma hannun shi.

"Nagode ƙwarai da gaske T. Allah ya saka maka da mafificin alkhairi ya raya mana Hafsatu Reina."

"Anything for you Habeebty" ya ɗan miƙa ya sumbace ta a kunci yayin da Reina ta callara wani ƙaran da
saida ya razana, yayi saurin gyara zama yana tunanin ko ya matse mata wani ɓangare ne na jikin ta. Kuka
take callarawa har tana watsa ƴan ƙiraren hannun ta sama, yayi saurin miƙa ta ma Fauziyya yana faɗin
"yi sauri ki bata nono dan Allah"

Ita damuwar da ta gani a kan fuskar shi ne ya bata mamaki.

"Yanzun nan fa kafin mu baro asibiti na bata, Duk bayan minti 30 ne ake shayar da jarirai?"

"Eh mana. Ai haka abun yake, sai anyi haƙuri kuma ana haɗawa da madara kwanan nan zakiga ta cicciko"

Yamutsa fuska Fauziyya tayi bayan ta buɗe zip ɗin rigar ta, ta saka ma Reina nono a baki wanda tayi
saurin cafka tana zuƙa kamar wanda ta kwana bata ci ba.

Ɗan ciza baki tayi tana mitan "Nikam wallahi na gaji, gashi bakin nonon har yanzu ciwo yake mun"

"Toh ko zamu koma asibitin ne?"

Saurin girgiza kai tayi "A'a don Allah, zai bari a hankali " ganin cewa da gaske yake yi.

Alhaji Tahir bai bar ɗakin ba har saida ungozoma ɗaya ta shigo da kayan wankan Reina ta karɓe ta don a
wanke ta sannan ɗayan ta shige banɗaki tare da Fauziyya don a gasa mata jiki, ba tare da ɓata lokaci ba
kuma aka fara jere mata kalolin abinci, farfesun jan nama da naman kai da kuma ruwan zafi.

.....

Dukan da Saudat ta kaiwa sauron da ya sauƙa a kan ƙafar Kamal ne ya sanya shi farkawa a gigice,
kasancewar ta kai dukan har da na haushin shaƙar baccin shi da yake yi hankali a kwance bayan ita ta
kasa rintsawa saboda zafi ga sauro, da kuma takuri irin na tsohon ciki.
"Lafiya Saudatu?" Ya tambaya yana murtsuka idanu saboda ya samu daman kallon ta da kyau cikin ɗan
hasken tochilan da batirin shi yayi sanyi.

Bata ce mishi komai ba sai tafin hannunta da ta ɗaga mishi don yaga mataccen sauron da ya gama shan
jinin su ya ƙoshi.

Sauƙe ajiyan zuciya yayi ganin tana lafiya sannan yace "yaya baki kwanta ba?"

"Ta ina zan iya barci a cikin wannan zafin ga sauro kaman zasu yanki naman mutum?!" Ta tambaya cikin
faɗa-faɗa.

"Kiyi haƙuri, in sha Allah zuwa gobe zanyi ƙoƙari a haɗa wutan, kinsan register ɗin makarantar Yaseer shi
yasa nayi katt har na bari nepa suka yanke wutan Amma gobe zanje in samu Alhaji Tahir"

Tsaki taja kawai ta juya tana mita sai ya ɗauki mafifici ya fara mata fifita nan da nan barci ya fara awon
gaba da ita amma sai bugu suka ji ƙaɗan-ƙadan a ƙofa.

A ɗarare Kamal ya tashi ya ƙarasa jikin ƙofar yana tambayar waye ne? Bai duba lokaci ba amma yana da
tabbacin dare ya raba.

Saudat ma sake tashi tayi ta zauna ta zuba ma ƙofar idanu.

"Abba Suhail ne ya gagara bacci" cewar Yaseer cikin ƙasa da murya.

Cire sakatan jikin ƙofar yayi ya buɗe ta sannan yaran suka shigo ciki ya mayar ya rufe.

Riƙo hannun Suhail yayi yana tambayar abin da ya hana shi barci.

"Abba zafii" yaron yace cikin muryar kuka ga ƙurajen zafin da suka mamaye kirjin shi, wuyan shi, da
goshin shi. Daɗin abun ma su suna da gidan sauro da abin yayi musu biyu.

"Je ku kwanta in fifita ku"


Da sauri Suhail yaje ya ɗale katifan ya shige jikin mahaifiyar shi daman a can ɗan ɗakin su mai kaman
store shimfiɗi suke yi a ƙasa su kwanta, Yaseer ma ya kwanta gefen mahaifin shi sannan shi kuma yayi
zaman musu fifita har barcin su yayi nisa yana kai, sai ya shiga nanata istigfari da salatin annabi a kan
harshen shi.

Sai wuraren asuba gajiya da kuma tsamin da hannun yayi mishi ya sanya ya haƙura ya kwanta amma
Saudat bata yi saken barin shi ya makara sallar asuba ba.

Suna dawowa daga masallaci shi da Yaseer yayi ma Saudat sallama Sannan ya wuce kasuwar muda lawal
don taya masu motar kaya sauƙe kayan gwari don a samu na sawa a bakin salati mai daɗi. Yaseer ma
bokiti ya ɗauka ya fita ɗibo musu ruwa, sanda yayi sawu wurin goma lokacin rana ta fara zafi kafin ya
karɓi Naira ɗari huɗu wurin Saudat ya shiga maƙwafta siyo musu gawayi na Naira ɗari da kuma ƙullin
manja na ɗari uku.

Yana dawowa ya juye gawayin cikin murƙubur sannan ya nemi takarda ya saka mishi wuta. Har sanda
wutan ya kama sosai kafin ya saka ruwa a madaidaiciyar tukunya ya ɗaura a kai, ya shiga sharan ɗakuna
da tsakar gidan ya lailaye shi tass. nan ya jawo Suhail zuwa banɗaki ya cuɗe shi kafin shima ya shiga
wankan. Ya ɗau lokaci yana tsaftace duk wata kafa na jikin shi kafin ya fito sanye da gajeren wando ɗan
siririn ƙirjin shi na ɗigan ruwa, lokacin har ruwan da ya ɗaura ya tafasa Saudat ta saka taliya laida ɗaya ya
nuna tana tsiyayewa cikin colander.

Da shigar shi ɗaki ya goge hammatan shi da alimun ya saka singlet sannan ya sanya jan riga da wandon
jeans ya fesa turaren shi wanda bayi wuce ɗari takwas zuwa dubu ɗaya sannan ya taje gashin kanshi ya
fito zuwa kitchen ya ɗauki plate ɗin taliyar shi da manja da yajin da yasha tafarnuwa da farin maggi ya
saka cokali mai yatsu ya fara ci cikin nutsuwa.

"Yanzu yaushe zaka dawo kayi shirin Hadda?" Saudat ta tambaya tana daga ƙasar bishiyar neem dake
samar da inuwa a tsakar gidan ta shimfida tabarma tana shan hantsi.

"Umma nayi tsammanin za'a bari sai na haɗa kuɗin uniform tukunna" ya amsa yana kai kofin ruwa bakin
shi.
"A'a niman kuɗi ba zai hana ka karatun addini ba Yaseer, Yana nufin munfi bawa bokon muhimmanci
kenan. kuma ma abban ka yace yau zaije ya kawo in sha Allah"

"Hmm" kawai Yaseer yace kasancewar ya sanar da shi a ina zaije ya kawon. Wurin da akwai ɗin amma
samu da wuya da wulaƙanci sannan a baka abin da be kai ya kawo ba, in ta tashi ne da sun ci gaba da
fafutukar su ne kawai Allah zai basu a lokacin da ya ga dama.

Suhail ne ya fito daga uwar ɗakin iyayen sanye da wandon uniform army green da rigan shi green check
saidai ya saka rigan a baibai.

"Umma ina sandal ɗina?" Ya tambayi Saudat.

Yafato shi tayi da hannu ya ƙarasa kusa da ita ta kwaɓe masa rigan da hannun ta ɗaya da juya shi don
ɗayan hannun manjan taliyar da take ci ya ɓata shi sannan Suhail ya sakalo wuyar shi ta taimaka mishi ya
saka a dai-dai.

Zuwa lokacin har Yaseer yaje ya ɗauko masa sandal, Suhail ya dafa kanshi dake yana durƙushe sannan ya
saka mishi ba'a batun socks dama. zuwa lokacin abokan tafiyan shi sun shigo da ƴar sallamar su.

"Yaya kai sai yaushe zaka koma school?" Ya tambayi Yaseer don yafi son tafiyar su a tare gaba ɗaya, yara
basu iya cin zalin shi kuma shi ya sama masa abokai na kirki wande suka daidaita a matakin karatu dama
mataki na rayuwa. Uwa uba idan da ƴan canji a hannun shi yana ɗan siya musu taɓa ka lashe kuma dama
suhail akwai kwaɗayi.

"Satin gaba zamu tafi tare in sha Allah" ya amsa tare da komawa ya ɗauko mishi jakan bayan shi ƴar
ɗinki mai ɗauke da littattafai guda 3; farin layi, jan layi da gidan dara. Sai pencil ɗinshi guda ɗaya wanda
kullum Suhail sai yayi zaman fere ta tayi tsini, samm bayi barin shi ya duskure shiyasa cikin sati guda
yakan ƙarar da pencil.

Sallama suka yi ma Yaseer da Saudat, suka riƙe hannun juna sannan suka wuce.

"Nima barin hanzarta kada oga ya riga ni isa shago" yace yana tattara kwanon dake gaban Saudat da
wanda Suhail yayi amfani dashi ya kaisu mawanki. Bai ajiye su ba sanda ya wanke su tass harma da
tukunyan da aka dafa abincin. Colandern da rabon Kamal yake ciki ne kawai ya bari sai karamin tukunyar
da aka soya manja.
Ya wanke bakin sa ya sake taje gashin kansa kafin yayi sallama ma Saudat a kan zai wuce.

"Allah yayi albarka yaro na, ya kawo haske da nasara cikin rayuwar ka"

Da ameen ya amsa yana jin daɗin addu'ar ta kafin yaja silifas ɗinshi da ta fara suɗewa ya fice daga gidan.

Fitan shi bada daɗewa ba Kamal ya dawo hannun shi riƙe da baƙar leda. Rigan shi yasha kamɓorin datti
da kuma ruwan kayan miya shima ya bushe.

Sannu da dawowa Saudat tayi mishi daga zaune ganin ba zata iya miƙewa ta tare shi ba.

Ajiye laidan hannun shi yayi a gaban ta. ya fara isa bakin tukunyar ƙasan su dake ɗaukar sanyi kamar
fridge ya ɗebo tare da ɗauƙo kujera ƴar tsuguno ya dire shi ya zauna. Kai kofin bakin shi yayi yasha
ruwan yana maida numfashi.

"Sannu da dawowa, yaya kasuwan?" Tace dashi.

"Kayayyaki suna tsada Saudatu abun saidai addu'a kawai, amma har gwarin ba sauƙi"

Jijjiga kai kawai tayi ta shiga buɗe laidan da ya shigo dashi. Bagen kayan miya ne sai ƙullin cray fish tunda
tace mishi tuwo zata yi.

"Ina kuɓewan?" Ta ɗago tana tambayan shi.

"Ƙuɓewa ta ninka kuɗinta shiyasa kawai na dawo da abinda aka samu don nasan zamu fi buƙatar kuɗin."

"Amma kasan Yaseer bayi son miyan kuka"

"Yaci gaba da haƙuri wata rana za'a ci abinda yake so"

Jan numfashi Saudat tayi tace "Allah ya ƙara buɗi"


Da ameen Kamal ya amsa cikin jin daɗi ya tsoma hannu cikin aljihu sannan ya ciro tsofaffin ɗari biyar
guda biyu, ƴan ɗari bibbiyu, ɗari-ɗari harma da hamsin-hamsin a ciki.

Ya gyara zaman su ya ƙirga sannan ya cire ɗari biyar-biyar ɗin ya miƙa sauran ma Saudat.

"Gashi 950 ne ki haɗa da na wurin ki a ci gaba da cefanen har muga abinda Allah zaiyi. Wannan kuma" ya
miƙa mata sauran dubun hannun shi "zan ƙaro wani abu a tura ma umma, ta fara complain babu kuɗi a
hannun ta ni kuma ga wata tayi tsakiya saidai a lallaɓa har a samu albashi"

Ta jinjina kai don gamsuwa da kudirin shi dukda shima kuɗin albashin an riga an cinye shi a bashi tun
kafin yazo.

Ya miƙe kan ƙafafun shi tare da sauƙe dogon numfashi "Toh barin fara watsa ruwa kafin in karya in wuce
wurin aiki"

......

Reina ce ta tashi Fauziyya daga baccin da ta samu ta mayar da safe bayan daren jiya ta hana su rintsawa,
Mutane 3 a kanta amma kuka ta kwana yi kaman ta ari baki.

Ƙarfe 8 da rabi ne na safiyar Alhamis amma ma'aikatan gidan sun gama tsaftace ko wani lungu da saƙo
da yake gidan duk girman shi kuwa. ƙamshin airwick da turaren wuta haɗe da sanyin Ac wanda an rage
ƙarfin shi saboda masu jego amma duk wanda ya shigo gidan a cikin irin wannan yanayi na zafi ba zaiso
ya fita ba.

Bai jira an wanke su ba Alhaji Tahir ya faɗo ɗakin, lokacin hajiya Fauziyya na ƙoƙarin shayar da Reina ko
zata rufa musu baki.

"Good morning Habeebty" yace da ita yana ƙoƙarin zama ba tare da wani damuwa ba.

Ganin haka yasa mutanen ɗakin kowa ta kama gaban ta.


*Seemahwrites ✨*

*REINA 💍*

BookNest, Wattpad and arewabooks @seemahwrites

https://chat.whatsapp.com/JjjCOoAVsdP4PZbmCDrUOh

04...."My T. Ina kwana" ta maida masa da gaisuwar. Tana ƙarawa da "kaga ƴar rigimar ka ta hana mu
barci ko?"

Ya murmusa, kwana 5 kenan amma har yanzu wani ɓangare na jikin shi ya kasa gaskata cewa wanzuwar
Reina cikin rayuwar su gaskiya ne ba mafarki ba.

"Duk wata Sarauniya ai da rigima aka santa Fauzah ta"

"Oh haka ma kace? To gobe wurin ka zan kawo ta ku kwana"

Saida ya dara kana yace "Da kuwa kinga yanda ake raino mai kyau ba Irin naku na ƴan koyo ba."

Zancen shi ya saka ta darawa itama "ai ko? To kuwa kada daga baya kazo kace ba haka ba"

"Ki gwada ni mana ki gani" yace yana miƙa hannu ya karɓi babyn Ganin ta cire bakin ta daga jikin
Fauziyya.
"Zo nan ƴar albarka, baiwar Allah, Fauzah tana so tayi miki sharri ko?" Yace yana lakatar fuskar Reina ita
kuwa ta shiga murmusawa.

"Masha Allah tabarakallah, Fauzah kaman kakin yarinyar nan kika yi"

Leƙa fuskar Reina Hajiya Fauziyya tayi tace "ni kuwa banga kaman da ake ta cewan ba T. Haka hanci na
yake a nane?"

"Toh ta girma ne kika ga bai tsiro ba?" ya amshe cikin salon karɓa ma ƴarshi faɗa.

"Oh ashe hancin ma shuka ne da zai tsiro"

Ciza laɓɓan shi yayi ya ɗan jijjiga kai. "Idanma bai fito ba zamu yanke naki ne mu dasa mata"

"Lala-lala, Sarauniyar babanta ne ba nawa ba, kuje can ku ƙarata da munin ku" tace tana taɓe baki.

"Munji mun gode kuma zaki maimaita" ya sumbaci kumatun Reina sannan ya maida ta ma Fauziyya yana
faɗin "toh mun fita sai ayi mana addu'a"

"Allah ya kiyaye, ya tsare kuma yasa a samu abinda aka je nima"

Da ameen ya amsa yana juyawa baby ta callara ƙara. "Iyee, to ai sai kazo ku tafi tare, kaga tun yanzu an
fara nuna min fifiko"

Juyowa yayi ya dawo yana faɗin "Don kada ki wuni kuka ne amma da taren zamu tafi" ya sake manna ma
Reina sumba kafin ya juya ya fice yana jin kukan ta a cikin zuciyar shi.
Ba'a ɗauki awa guda ba mai jego ta fito cikin rantsatstsiyar leshi da jaririyarta cikin shawul. Ƴan barka har
sun fara sintiri, da wanda zuwan su na farko kenan da kuma wanda so da girmama abin duniya ya saka
su dawowa a karo na barkatai.

A cikin baby basket aka saka Reina duk mai son kallon ta saidai yaje ya leƙa don kada a saka mata tsamin
jiki a garin passing-passing.

Aka fara shigo da abin kari ma ƴan gaisuwa nan suka zauna suka baje shi tsaff, kafin a ɗaura abincin Rana
shima suyi mishi illa.

Hira ta zauna suka sha da baƙin ta dama wanda bata wayi fuskokin su ba har zuwa jimawa da aka samu
Reina ta maida barci sai ta nemi iznin ta koma ciki don basu samu isasshen barci ba daren jiya.

Bata sake fitowa ba saida aka yi azahar nan tazo ta samu yawan mutane sun ninka na ɗazu kaman ma
yaune suna, haka ta zauna aka sake sabon gaisuwa.

.....

"Yanzu sake komawa zaka yi?" Tace tana jingine da jikin wardrobe ɗinsu da ƙofofin sun ɓaɓɓalle amma
gyara ya gagara saboda damuwowin su na yau da kullum yafi ƙarfin wannan.

"Inada zaɓin da ya wuce wannan ne Saudah? Kina gani dai sati ya kusan ƙarewa yaron nan yana zaune a
gida, gashi kema EDDn ki ya kusa, ba zanso har ki haihu Yaseer bai koma makaranta ba" Kamal ya sanya
rigan da ta ciro mishi ya shiga haɗa botir.

"Kema da kin shirya ne muka je kika yi musu barka, Hajiya Fauziyya ba zata ji daɗi ba idan baki je ba
bayan ta roƙe ki ki dawo."

Taɓe baki Saudat tayi tace "tana zagaye da jama'a ina har zata wani lura da rashin zuwa na?"
"Kiyi haƙuri mu dai je ɗin"

Ta turo baki. "Nifa ba daɗi nake ji ba abban Yaseer."

Sauƙe murya yayi cikin lallashi yace "kiyi haƙuri."

Tana zunkuɗe-zunkuɗen baki ta shiga shiryawa. Shi da kanshi ya fita waje kiran Suhail a wurin wasa
kasancewar yau Alhamis babu Islamiyya, shi kuwa sai murna yake ganin za'a je anguwa. Cikin zumuɗi ya
shirya

Har sun fito ta jawo musu ƙofa Yaseer ya shigo da uniform ɗin hadda.

"Ina wuni Ummah, ina wuni Abba, fita zaku yi ne?"

"Gidan Alhaji Tahir zamu je yin barkan sabuwar jinjira" cewar Kamal.

"Toh sai kun dawo, Allah ya kiyaye" yace yana nufar hanyar ɗakin su da nufin ya ajiye jakar shi don ya
ɗibo yunwa.

"Ai yanzu kam shiryawa zaka yi muje ka taya ni da wannan sarkin rikicin" Saudat ta nuna Suhail da ya
washe ma Yaseer ɗin haƙwara baki ɗaya murna ya cika shi.

Sosa kai yayi "Umma zan shigar da hadda ne"

"Babu jimawa ai zamu dawo, sai mu siyo sabon batir ɗin toci ka shigar da haddan da daddare"

Da toh ya amsa sannan ya shiga ɗaki ya sako T-shirt ɗin gwanjo navy blue da baƙin wando ya fito ya
ɗauki buta sannan ya ƙarasa bakin rariya ya ɗauraye ƙuran ƙafar shi ya koma ya shafa mai a ƙafar da
fuskan shi sai ƙyalli suke, bai manta da taje kanshi ba.
kafin lokacin da ya gama Saudat ta gaji da tsayuwa ta samu kujera ta zauna amma kuma bata ƙosa da
jiran nashi ba dukda ma bayi da sanyin jiki ko kaɗan.

"Muje umma" yace da ita yana kama hannun suhail, kamal ya riga da ya wuce nima musu napep, itama
ta miƙe suka fita.

Zuwan Saudat gidan karo na biyu kenan, tun auren Alhaji Tahir da Hajiya Fauziyya shekaru biyu baya sai
kuma yau da Allah ya azurta su da samun ƙaruwa, amma kuma gani take kaman an ƙara wa gidan girma
da kyau. wai duk wannan gidan mace ce ƴar mace?- take tunani a ranta.

Shi kuwa Kamal ƙiyaste yawan miliyoyin da aka zubar wurin tada gini irin wannan kamar ba a ƙasar shi
Nigeria inda miliyoyin mutane suke fama da yunwa bane.

Yanzu har mutane zasu iya rayuwa su kaɗai a irin wannan wargajejen gida suyi barci cikin kwanciyar
hankali?- tunanin Yaseer Kenan.

Dakatar dasu da security yayi daga ƙofar shiga ne ya dawo da hankalin su zuwa gare shi, tun kan aje ko
ina Saudat har ta fara shiga ɓacin rai bayan yanzu wasu suka shige a gaban su ba tare da an tuhume su
ko an bincike su ba.

"Malam Ina zuwa?" Cewar security da ya toshe Idanu da baƙin gilashi.

Ba zuwar Kamal na farko ko biyun sa ba kenan don haka ya saki murmushi tare da cewa "officer Baka
gane ni bane?"

"Ban gane ka ba kai wa?"


"Ɗan uwan me gidan ne fah! Sunana Kamal, mun haɗu shekaran jiya nazo gun me gidan ka manta?" Ya
ƙarashe da sakin ƙaramin dariyan sanayya don yasan yanzu kam dole ya ɗago shi tunda zuwan shi na
bayan ma hana shi shiga yayi sai cikin Sa'a Alhaji Tahir ɗin ya dawo a lokacin, yace masa yaje ya dawo
saboda abinci ya dawo ci kuma ba daɗewa zaiyi ba ana jiran sa a office.

Yayi tsammanin yau idan ya dawo yana da direct pass na shiga gidan amma sai security ɗinnan ya ɗan
zaro glasses ɗin idanun shi ya lanƙaye ta a karan ƙaton hancinsa ya ƙare musu kallo daga kan Kamal har
Suhail a wulaƙance sannan ya maida glasses ɗinshi ya ƙwama.

"Toh idan haka ne ai muma ƴan uwan nashi ne, Please don't waste my time, ku bar wurin nan"

"Mu tafi" Saudat tace da Yaseer. Ya kuwa ja hannun ƙanin shi suka juya zasu bar wurin sai Kamal yayi
saurin riƙo hannun ta, yasan idan ta tsaya shima Yaseer nata zai bi.

Kamal ya ƙara faɗaɗa murmushi kafin yace "wallahi ni ɗan uwan shi ne officer, mahaifin su da mahaifiyar
mu uba ɗaya uwa kawai suka raba"

Yi yayi kaman bai jishi ba ya juya wurin wani mota da ya tunkaro gidan ya gaida su fuska a sake sannan
ya bada izinin a wangale musu su shiga.

"Abban Yaseer ko aljanna ake rabawa a gidan nan ya kamata mu haƙura haka nan" Saudat tace cikin
ƙosawa da ɓacin rai.

Juyawa yayi ya fuskance ta cikin faɗa-faɗa yace "Haba Saudatu, ki zamo mai hakuri mana, zai barmu mu
shiga fah, ki barni muyi magana dashi"

Jinjina kai tayi "toh shikkenan, munyi gaba sai ka Iso" ta riƙo hannun yaranta da niyyar yanzu ko ya
tsayar da ita ba tsayawa zata yi ba.

Wannan wani irin wulaƙanci ne? Wasu sunzo a gaban su wasu sunzo a bayan su duk a keke napep an
barsu sun shiga dake su sun sanya kaya masu kyau da tsada sun sha kwalliya kamar suna suka zo tun
yau.
Juyawa suka yi suka fara tafiya har sun kusan ƙure garun gidan shi kuwa Kamal yaji haushin ta don haka
bai dakatar da ita ba kuma bai bi bayan ta ba, yaci gaba da roƙon mai gadi ya barshi ya shiga don yaje ya
haɗu da Alhaji Tahir Idan yana ciki.

"Umman Yaseer!!" Aka ƙwala mata kira daga cikin adaidaita da ya wuce su, hakan ya saka ta saurin
waigawa don ganin waye mai kiran. A ƙofar gidan da suka baro mai napep ya faka Inna larai ta fito tare
da yafato Saudat da hannu.

Sakin fuska tayi suka nufi wurin ta, sauran ƴan aikin suna fito da kayayyakin da suka zo dashi. "Kardai
mun sha saɓani umman Yaseer" cewar Inna larai domin a tunanin ta sun fito daga gidan ne zasu tafi.

"Wallahi Inna larai, Ina wuni yaya zafi"

Miƙawa mai keke naira dubu tayi bayan sun gama cire kayan ya miƙo mata canjin ɗari biyu "Lafiya
alhamdulillah, yaya mazaje na?"

Rage tsayi kaɗan Yaseer yayi ya gaidata ta amsa da "mai gida Irin wannan swagger haka! inafa jiran
cefane" sai ya murmusa tare da sosa ƙeya a kunyace.

"Toh ku shiga wannan napep ɗin ya maida ku mana, kinga sauƙi yazo muku ba sai kun take ƙarshen titin
nan da ba'a samun abun hawa cikin sauƙi ba"

Ta luma hannu cikin jakarta ta ciro wani ɗari biyun ta haɗa da canjin hannun ta sannan ta danƙa wa
Yaseer tana cewa "toh gashi na sayi wankar nan don yayi min"

Saurin jan baya yayi yana ƙoƙarin kwace hannun shi amma ba ƙaramin ruƙo tayi mishi ba don tasan halin
shi sarai.

"Ki barshi kawai Inna don Allah" yace kaman zai saka ihu.
"Naƙi na barin, salon gobe ka kunce auren tunda kayi wanka naƙi yabawa?" Ta dunƙula masa kuɗin a
hannu kafin ta sake shi sai ya shiga mata godiya.

Kwatance tayi ma mai adaidaitan na unguwan da zasu je, kana tayi musu ciniki. Saudat kuwa har ta
shige ciki ganin Kamal ya tunkaro su, ta riga ta saka ma ranta ba zata shiga gidan nan ba kada ma ya ɓata
lokacin shi, don haka tace ma su Yaseer suyi sauri su shiga su tafi.

"Inna Larai ba'a barmu mun shiga ba fah" cewar Suhail ganin da gaske komawa gida zasu yi.

Kallon Saudat a kaikaice Inna larai tayi don tabbatar da zancen Suhail, "wai haka Umman Yaseer?"

"Babu komai wallahi Inna" shine abinda bakinta yace amma hannun ta duka ya kaiwa Suhail saidai ya
riga ya gudu ya ɓoye a bayan Yaseer.

"Toh me yasa?!" Ta tambaya a fusace.

Shiru Saudat tayi ganin kamal ya Iso ta kawar da kai gefe shima kallo ɗaya yayi mata ya ɗauke kai ya
gaida Inna Larai sannan ya amsa da. "Kinsan dake an canja masu tsaron gidan shiyasa nake ga wannan
bai wayi fuska ta ba"

Kaɗan ya rage Saudat ta saki tsaki amma ta matse.

Inna Larai ta ƙarasa wurin security "akan mene zaka hana ɗan uwan me gida shiga?"

Saida ya sake cire madubin idanun shi ya kalli Kamal wannan karon a mamakance, daga rigan gwanjon
dake wuyar shi, haɗe da wandon jeans din da duk sunji ruwa sun gama koɗewa gashi basu samu guga
ba, har komai nashi baiyi kama da wanda ya haɗa sanayya da masu gidan da suke gadi ba balle haɗin
jini.
"Oh wai dama ɗan uwan shin ne da gaske?"

Cike da takaici Inna Larai tace "Haba kai kuwa malam ɗan sanda? Aikin da aka ɗauke ku yi kenan saboda
Allah? Idan tsare mutane za'a dinga yi ana musu tambayoyi kamata yayi ana tsare kowa da wanda yazo a
mota da wanda yazo a ƙafa babu bambanci, amma wannan ba yi bane ko kaɗan. Wulaƙanta ɗan adam
ba abin yi bane wallahi..."

Taje ta jawo hannun Saudat, mai napep daman ya riga ya dire ta ganin za'a ɓata mishi lokaci. Har ta
wuce dasu ciki tana balbali, Kamal ma yayi saurin bin bayan su, Suhail sai tsallen murna yake yi, Yaseer
kuwa yunwar cikin shi ne ya dame shi.

Yawan Mutanen da suka tarar a parlourn Hajiya Fauziyya yaso bawa Saudat tsoro har ta fara tunanin ko
dai sun ɓata ƙirge ne yaune suna?.

Yawanci baƙin fuska ne sai ta rasa gaida su ne zata yi ko ta share su? Saidai koma ta share sun bata ga
ƙyallin Hajiya Fauziyya a parlourn ba.

"Zo muje kiga" cewar Inna larai bayan taje ta ajiye laidar hannun ta a kitchen ta dawo ta riski Saudat
tana ta dibi-dibi don haka suka nufi ƙofar bedroom ɗin da hajiya Fauziyya take.

Knocking tayi saida aka ɗauki minti guda kafin kofar ta buɗu Aina'u ta leƙo.

"Ah-ah, Inna Larai kun Iso? Bismillah" ta buɗe mata ƙofar don ta shiga amma ganin su Saudat biye a
bayan ta yasa tayi hanzarin riƙe ƙofar.

"Au Inna tare da baƙi kike ne? Da sun jira mu a parlourn ai"

Kafin Inna Larai tayi Magana daga cikin ɗakin suka ji Muryar Hajiya Fauziyya tana tambayar "Aina'u
wanene?" Rufe ƙofar tayi kafin ta juya cikin ladabi tace "Hajiya Saudatu ce, Matar Kamalun Jama'are"

Fuska ta saki sosai cikin jin daɗi tace "Ahh, Umman Yaseer zaki ce ba sai kin wahalar da kanki da wannan
dogon bayanin ba. Buɗe musu su shigo"
Bata da zaɓin da ya wuce tayi yanda aka ce ba tare da musu ba ta buɗe suka shigo sannan tayi saurin
sake datse ƙofar kafin sauran ƴan parlourn su fara tuttuɗowa ciki.

"Ni nama yi fushi tunda sai yau uwa take zuwa ganin ƴarta" cewar Hajiya Fauziyya tana Gyara zama a
kan gadon tare da sauƙe ƙafafuwan ta ƙasa, ga bakin Reina manne da ƙirjin ta tana aikin ci ba ji ba gani.

Shimfiɗar fuskar da Saudat ta samu ya saka ta sakin fuska itama cikin ɗan jin nauyi tace "kiyi haƙuri
Aunty, jikin ne yaƙi daɗi."

Kallo take ƙarewa makeken bedroom ɗin da take ayyana idan baiyi girman gidan su ba baki ɗaya toh
tabbas zai iya fin rabi.

Ga wani makeken gado da bata taɓa ganin mai kyau da girman shi ba, tsayin saman gadon kuwa ya doshi
taɓa ceiling. Ɓangaren Kayan jarirai kuwa ga wardrobe girman shi kamar na wanda za'a kai ɗakin miji
saidai anyi shi ne Musamman na jarirai abun sha'awa da cartoon ɗin Masha and the bear a jiki. Ga kuma
set na drawers shima, haɗi da gadon jarirai shima pink a gefen gadon uwarta.

Cikin zuciyar Saudat tace "Allah ka azurta mu da mai albarka."

Sai muryar Hajiya Fauziyya ta jiyo Cikin tausayawa tana cewa "Allah sarki, Allah ya raba ku lafiya kema ki
samu mai hana ki barci" ta ƙarashe cikin sigar zolaya.

"Bata barin ku kuyi barci ko?" Saudat ta Isa bakin gadon tana leƙa fuskar Reina dake tsotson mama
idanun ta a rufe daga ɗan nesa.

Gefen ta Hajiya Fauziyya ta ɗan bubbuga mata alamun ta zauna, Saudat bata yi ƙasa a guiwa ba kuwa ta
zauna sannan ta jawo Suhail jikin ta gudun kada yayi musu ɓarna, Yaseer kuma ta barshi a parlour.
*Saliha Ahmad Na'ibi ✨*

*REINA 💍*

BookNest, Wattpad and arewabooks @seemahwrites

05..... Sai da suka gaisa da Inna Larai ta bar ɗakin don zuwa yin abinda ya kawota kafin Hajiya Fauziyya ta
dubi Saudat tace "Hmm.. ai daga sha ɗaya ta gifta toh fa ba zamu rintsa ba sai safiya, haka zata kwana
tana rikici gashi kuma bamu rabuwa da baƙi wataran har sha biyun dare, da safiyan ma haka" ta ƙarashe
tana cire bakin Reina daga jikin ta nan kuwa ta shiga yamutsa fuska tana motsa baki alamun bata ƙoshi
ba, ta gyara mata rufuwa a cikin towel ɗinta mai taushi da kyau yasha turaren yara mai daɗin ƙamshi.
sannan ta miƙa ta a hannun Saudat da bata yi tsammanin hakan ba, tunda ranar da aka haifeta sun hana
ta ɗauka shiyasa ta cire ranta daga taɓa musu ƴarsu.

A kan cikinta ta ɗaura ta ganin bata da nauyi sannan ta shiga ƙarewa fuskar Reina kallo lokacin da ita
kuma ta fara ƙananun koke-koke. Jinjina kai Saudat tayi tace "toh kuma ba wani abun yake damun ta ba?
Ko ciwon ciki? Ko tsamin jiki?"

"Ko ɗaukan ta ƴan gaisuwa basa yi Umman Yaseer saboda gudun ko hakan ne, maganin ciwon ciki kuwa
har su jar gauta mun jiƙa mun bata Daddyn ta bai sani ba, na Islamic da na asibitin ma mun siya mun
gwada shiru babu wani canji"

"Kinsan yaro ba baki yake da shi ba, ciwo zaiyi ta nuƙurƙusan su ba zasu iya faɗa ba, da kuje kuga likita
kada wani abin ne" Saudat ta faɗi hakan ne kawai ba wai don tana tunanin wani abu yana damun Reina
ba domin gashi ta cika fata tayi kyau fiye da yawancin jariran da basu samun kulawa kamar ta, amma
kuma shi ciwo ba'a gane shi da ido.

"Nifa Inaga rikici ne irin na baby Hafsah ba komai ba, soboda bata ƙin karɓan nono ko kaɗan, kuma idan
zamu kwana ina bata ba zaki ji bakin ta ba ni kuwa ina zan iya? watarana har amai take yi tsaban zalama"
Saudat ta murmusa tana jin sha'awar haihuwar ƴa mace yana daɗa shigar ta, fatan ta ace abin dake cikin
ta mace ce da taji daɗin ta domin tafi sha'awar su a kan ƴaƴa maza. "Lallai yarinyar mai babban suna ce"
tace tana mayar ma Hajiya Fauziyya Reina saboda kukan ta ya fara tsanani.

Sake zuge zip ɗin rigar ta ƙasa tayi tana faɗin "Aina'u haɗa mana Madara don Allah, daga wannan na gaji
wallahi".

Mai aikin dake maida kayan Reina da aka wanke aka goge su cikin drawers ta miƙe a take tare da faɗin
"toh Hajiya" sannan ta bar musu ɗakin.

Saudat bata lura ba ashe har Suhail ya siɗaɗa ya ɗauko abin wasa me kacau-kacau yana kaɗawa.

Ta miƙe da sauri ta wafce daga hannun shi tana mishi faɗa.

"Da kin bar mishi ai, tana da wani idan yana so ya ɗauka" cewar Fauziyya.

"A'a wallahi Aunty, ɓarna ne kawai yake ji dashi" Ta mayar da abin wurin da ya ɗauka, "saida nace ma ya
zauna wurin yayan shi a parlour yaƙiya"

Ƙofar ɗakin ne ya buɗe Aina'u ta shigo ɗauke da rubber mai ɗauke feedern Reina a ciki wanda ta tafasa
yanzu za'a haɗa mata madara a ciki.

"Kije parlour ki shigo min da Yaseer Aina'u" tace ba tare da tabi ta kan Saudat ba, daga uwar har ɗan
halin su ɗaya.

Sai da aka bashi izinin shigowa bayan yayi sallama kafin ya turo ƙofar ɗakin a hankali. Ganin shi bai sauƙa
a ko'ina ba sai kan Hajiya Fauziyya dake bawa Reina Nono, yayi saurin sauƙe kanshi ƙasa tare da faɗin
"Aunty gani"

"Toh ƙaraso ciki mana, ko har mun fara surkuntakar ne?" Tace cikin sigar zolaya.
A kunyace ya sosa ƙeyar shi kafin ya taka wurin da suke zaune saman gado.

"Zauna in baka ƙanwar ka" tace tana mishi nuni da tsakanin ta da Saudat da Ido.

"Aunty kema kina da biyewa yara wallahi" Saudat tace tana dariya, har cikin ranta wani karama da daɗi
take ji. abinda take buƙata a gare su kawai kenan, suma ayi treating ɗinsu kaman sauran mutane wanda
Allah ya yassarewa abin duniya, a daraja su a mutunta su shikkenan abin ba wahala, ba don Allah bayi
son su bane ya zaɓi ya hana su, idan da yaso sai sufi kowa arziƙi ma a gidan duniya duk wannan abu mai
yiwuwa ne a wurin shi, amma tasu kalar jarabawar kenan, domin da ya hana su kuɗi bai hana su zaman
lafiya da ƙaunar juna ba.

Yaseer ya zauna Hajiya Fauziyya ta saka mishi Reina a kan cinyar shi, ya kuwa riƙeta da kyau yana kallon
farar fuskar ta da har yellow-yellow yake masa a idanu ga bakin da take faman turo shi yawan tsotso
yasa yayi jajawur, ga kuma nanannen hanci. Amma kuma kumatun ta abin sha'awa .

"Yanzu kam Reina ta fara kyau ko yaro na?"

Da sauri ya ɗago kai ya ware idanu kaman ta karanci zuciyar shi. Gyaɗa mata kai kawai yayi, yana
tunanin amma fa idan hancin nan bai taso ba akwai matsala.

Suna zaune aka fara shigo da trays ɗin abinci, ganin yawan kulolin yasa Saudat yin tunanin kodai baƙi
Hajiya Fauziyya zata yi don haka ta miƙe tare da saka hannun ta a bakin zanin da take ɗaure da shi ta
zaro dubu ɗayan da kamal ya bata da safe wanda za'a kaiwa mahaifiyar shi tunda tana da wani in yaso
sai ta mayar masa.

Ta cikin hijabi ta warware kuɗin sannan tace "Aunty bari mu wuce, Almuru ta gabato, Allah ya raya mai
babban suna ya baki lafiyar shayarwa" sai ta ajiye mata kuɗin a gefen ƙafarta "gashi ba yawa" bata san
ma me zata ce a siya ma jaririya da dubu ɗaya ba, donmin tana da tabbacin ko abin goge kunnen ta ya
bawa dubbanni baya.

"A'a Umman Yaseer saida aka kawo mana abinci kuma zaku tafi? Saboda ku fa na jinkirta mana wankar
yamma"
Maganar su ya saka cikin Yaseer ƙara yin ƙugi ya lumshe idanu a kunyace, shi ba kwaɗayin abincin su
yake ji ba kawai yunwa ne ya dame shi domin yasha trekking daga hadda babu komai a cikin sa.

"Na san Almuru ta gabato ne aunty samun abin hawa."

Ta nuna mata agogon dake bango "kinga ma yanzu za'a kira sallah, ku tsaya kawai idan mun gama in
saka a maida ku."

Suhail da yaga abinci har ya ajiye kacau-kacau ya dawo jikin umman shi yana tsallen murna yana nuna
mata manyan yankan naman da suke masa Hi yana nuna su wa Saudat, "Umma nama" yace cikin jin
daɗi. Sai faman buge mishi hannu take yi saboda kunya Fauziyya kuwa yi tayi kaman hankalin ta bayi
gare su.

Aka gama saka musu abincin duka suka sauƙa ƙasa, Fauziyya kuma aka ɗaura mata nata a kan ɗan
ƙaramin coffee table sannanta karɓi Reina ta ajiye ta don Yaseer ya samu jona maman shi da ƙanin shi,
shima anyi masa plate ɗin shi daban yaji komai.

Kiran Alhaji Tahir ne ya shigo wayarta ta ɗauka suna magana ƙasa-ƙasa, Saudat kuma ta riƙe hannun
Suhail duka biyu tana bashi abincin a baki gudun kada ya ɓata musu carpet.

Sun kusan kammalawa aka yi knocking ƙofa sannan ba tare da niman jiran izini ba suka turo ƙofar suka
shigo, nan hankalin su baki ɗaya ya koma kan masu shigowa, suma masu shigowar idanun su ya sauƙa
kan Su saudat, sai kawai aka tsaya kallon kallo na ƴan sakwanni.

Buɗar bakin Hajiya Hauwa tace "me zan gani haka ni kuluwa, Fauziyya? Su waye kika kawo uwar ɗakin
Tahir?"

Yaseer ne ya fara tsame hannun shi daga cikin abincin ya kawar da kanshi gefe hawaye na taruwa a cikin
idanun shi, cin fuska ko wani iri ne zai iya jurewa amma yaƙi jinin ana cin mutuncin mahaifyar shi.
Murmushi Hajiya Fauziyya ta daura saman fuskar ta kafin tace "Sannun ku da isowa Umman Jamal,
sannu da zuwa Hajiya Addah Bismillah" tace da hajiya lubabatu wanda isa ma ya hana ta magana sai
kallon banza da take bin su Saudat dashi, jin kanta take yi kaman itace uwar su Alhaji Tahir ɗinma.

Haƙura dai suka yi suka shigo ɗin ganin yawan mutanen dake parlourn, bayan su ma'aikata ne ɗauke da
akwatuna niƙi-niƙi suka wuce dasu gaban gadon Hajiya Fauziyya suka dire su a jere sannan suka fice tare
da rufo musu ƙofa. Saudat ta so ta jasu su bar ɗakin a lokacin da ake shigo da kayan amma dandazon su
har ya cika ɗakin duk girman shi, bata da zaɓin da ya wuce ta ci gaba da zama a wurin har suka isota.

"Baki bamu amsa ba Fauziyya, su waye wannan?" Hajiya hauwa ta sake tambaya kaman irin basu san
sun nan ba ganin Hajiya Fauziyya ta share maganar.

"Au, umman Yaseer ne tazo min barka"

"Barka? Shine har cikin uwar ɗakin Tahir?"

Miƙewa Saudat tayi, Yaseer ma yayi saurin miƙewa. Kallon kayan da suka zo dashi tayi, akwati ne mai
huɗu-huɗi set biyu irin manyan nan da basu da kit.

"Aunty mun wuce, Allah ya ɗayyiba"

"Ameen umman Yaseer na gode Allah ya saka da alkhairi, ku gaida gida" gudun kada ta jawo musu
wulaƙanci yasa ta manta zancen kaisu gida da tace za'a yi.

Saudat ta zaga su zata wuce sai Suhail ya sake ɗaukan abin wasan da ya ajiye saboda abinci, da sauri
Jamal yazo ya fauce da ƙarfi sai Suhail ya ɗaga idanun shi da suka cika da ƙwalla yana kallon cikin idon
Jamal da ya zaro su cikin son firgitarwa. ƙarfin hali kawai Yaseer yake kallo ganin cewa mai abun ma ta
mishi izinin ya tafi dashi. "Idan baka daina kallo na ba I'll slap you" ya faɗa yana ɗaga hannu da niyyar
sauƙe mishi marin.
Yaseer ne yazo ya ɗauke shi yana zare nashi idanun ma Jamal da duk taurin kanshi saida ya firgita sannan
Yaseer yayi saurin barin ɗakin dashi.

Kafin saudat ta bar ɗakin taji ana faɗin "A'a haba, wannan kayan barka muka haɗu muka yi, na suna
kowa zai gwada bajintar sa ne...."

Saida suka fita daga cikin gidan suka ga yanda gari yayi duhu sosai, ashe hasken cikin gidan ne ya hana su
ganin ƙurewar lokaci, wannan ai sai ayi sallar isha ma mutum yana zaune baiji ba, gashi babu masallaci a
kusa da gidan.

Bata tsaya duba Kamal na nan har yanzu ko ya tafi ba suka bar gidan domin har yanzu haushin sa take ji.

Tafiya suke a dogon layin da ya dauki shiru, security lights daga manyan gidajen unguwar shi ya haske
musu hanya amma babu kowa a kanta sai motoci ɗai-ɗai da kan zo su wuce.

Tunani take Yanzu ta ina zasu fara samun abun hawa? Idan sun samu ma dame zata biya su? Don kuɗin
da ke hannun ta kenan ta bawa Hajiya Fauziyya.

"Yaseer ina kuɗin da inna Larai ta baka?" Koda ba zai ishe su ba sai su ɗan taɓa tafiya kafin su tsari
napep, don bata jin a yanayin da ta fara ji yanzun nan zata iya kai gida a ƙafa, ga uban nisa kuma.

"Gashi a nan" ya sauke Suhail a ƙasa sannan ya luma hannu cikin aljihun wandon sa saidai mene? Aljihun
ashe ya ɓule don haka bai ji komai a cikin ta ba sai rami.

Daga irin kallon da ya bita dashi Saudat ta fahimci abinda ya faru.

"Allah ga baiwar ka nan, ka shiga lamarin ta ya Allah" ta faɗa a bayyane sannan tace Yaseer ya bar Suhail
ya fara takawa da ƙafar shi in yaso idan ya gaji sai ya ɗauke shi domin tafiyar dake gaban su mai tsawo
ne.
Su taka su zauna su huta, Yaseer ya ɗauki Suhail yabi ya sauƙe shi, yayi ƙoƙarin nima musu lift idan yaji
numfashin mahaifiyar shi yana sama-sama basu samu ba, a haka dai har suka isa lokacin ƙarfe taran dare
ta gifta ko sallar maghriba basu yi ba balle isha.

Ba don abincin da suka ci na yau daban yake ba da hanyar nan ya ɗibe shi duka, suna shiga Yaseer ya zari
buta yayo alwala a tsakar gidan yayi Sallah don ɗaki har ya fara saka zafi. Ganin har ya gama biyan duka
sallolin shi Saudat bata fito yin alwala ba ya saka shi shiga ɗakin amma halin da ya ganta a ciki ya
matuƙar razana shi.

*Saliha Ahmad Na'ibi ✨*

*REINA 💍*

Saliha Ahmad Na'ibi (Seemahwrites)

06.... Durƙushe Saudat take a kan guiwowin ta cikin azabar ciwo, tana faman juya kai da ciza laɓɓen
bakinta, har Yaseer ya shigo ya same ta a cikin wannan hali.

Da gudu yayi kanta ya riƙe ta cikin kaɗuwa yana tambayar abinda yake damunta.

Riƙo hannun shi tayi cikin dagewa tace "Yi gudu ka kira min danejo Yaseer" sannan ta hankaɗa shi kaman
hakan zai ƙara masa sauri ne. Ya kusa faɗi ƙasa yaci da baki amma ya ƙoƙarta ya ruga a guje ya bar gidan
cikin Sa'a Suhail har barci ya ɗauke shi dan ko shima yaji gajiyar a jikin shi.

Buga ƙofar falangen yake da iya ƙarfin shi wanda har sanda sauran maƙwafta suka leƙo shi ta katanga
don ganin ko wani abun ne yake faruwa kafin jikar danejo ta buɗe ƙofar da magagin bacci a idanun ta.
Bai tsaya sauraron tambayoyin ta ba ya faɗa cikin gidan zuwa ɗakin da ya kasance na ƴar tsohuwa mai
shekaru 61 a cikin gidan, da aci balbal ɗinta a bakin ƙofa yana haska mata duk mai shiga da wucewa don
yin aikin gadin ta na sa kai.

"Danejo muje, Ummana dan Allah" yace yana mata rawar banjo kamar mai jin fitsari saboda matsuwa.

"Haihuwar ce tazo?" Ta miƙe da ƴar saurin ta sannan ta janyo zanin ta daga kan ƙofa ta ɗaura a kan
underwear dake jikinta ta nemi riga da hijabi ta saka sannan suka fice a gidan.

A yanayin da ya tafi ya barta suka dawo suka same ta ga baki ɗaya ta jiƙe sharƙaf da zufa amma ruwan
naƙuda bai fashe mata ba tukunna sai nuƙurƙusuwa take dai tukun.

"Jeka ka kira min mahaifin ka" tace da Yaseer. Sai ya tsaya turus, gidan Alhaji Tahir kenan zai koma? Idan
yaje zai same shi a can ɗinma a irin wannan lokaci ?.

"Bayi kusa Danejo gani nan ko menene ake buƙata zanyi mata" ya gyara tsayuwar shi yana saka fuskar
jarumta dukda kuwa gabaki ɗaya jikin shi kyarma yake yi.

Tsakanin shi da Suhail shekaru 6 ne harda rabi an haife shi lokacin bayi da wayo don haka yaune rana ta
farko da yaga mahaifiyar shi na naƙuda da idanun shi.

Ta ɗan gutsiri goron ta kafin tace "to jeka gidan malam iro ka kira min Huwaila, kace tazo Saudatu na kan
guiwa."

Toh yace, ta Juya ta koma ɗakin shi kuwa ya ɗiba a guje ya fice zuwa gidan da aka aike shi.

Tun da ya hango Yaseer a guje zuciyar shi ya tsinke, Kamal yayi saurin tsare shi don Yaseer baima lura
dashi ba. "Ina zaka je? Me ya samu Saudatun?"

"Danejo ne ta aike ni gidan malam iro"


Sai kawai Kamal ya fashe da kuka, shikkenan tashi ta ƙare mishi, Saudat ta mutu a haihuwa ta barshi,
sanin cewa Malam iro shine limamin masallacin da ake bada hayan makara da motar ɗaukar gawa.
Kyarmar da jikin Yaseer yake yi ya tabbatar mishi da tunanin shi, wataƙil an ɓoye mishi ne shi yasa shima
bai fara kukan ba, amma har ya fara jiye musu rashin uwa.

"Saudatu na yafe miki, Allah ya yafe miki, Allah yasa kin huta matar aljannah" yace yana riƙe da hannun
yaseer ɗin gamm hawaye nabin idanun shi.

"Abbah babyn bata zo ba fah, ance inyi sauri ne in kira Umma Huwaila"

Kamal ya ɗago kai yana hanzarin share hawaye, "yanzu Saudatun suna tare da danejo?"

Gyaɗa kai Yaseer yayi, kamal yayi saurin angiza ƙeyar shi, "yi sauri kaje ka kira ta, ka tabbatar kun taho
tare" da toh Yaseer ya ci gaba da calla gudu a cikin lunguna.

.....

Yana jin ihun ta, yana jin nishin ta, yana jin kukan ta, ba kuma za'a barshi ya shiga ya ganta ba, sannan ya
rasa abu ɗaya da zaiyi takammamme ya samu nutsuwa a ranshi, yayi ƙoƙarin shigar da hadda amma
kaman yana zuba ruwa a kwando, har zuwa yanzu da yake da tabbacin dare ya raba a cikin hali ɗaya ake,
har kukan wahalar da Saudat take yi galabaita yasa ya disashe sai gunji kawai ake ji.

Fita yayi kawai yin alwala ya hango mahaifin shi kwance a ƙofar ɗaki saman tabarma yana shaƙar bacci
se faman kai duka yake wa sauro, ai ko halin da Saudat take ciki bai dame shi ba sautin kukan ta ya isa ya
hana shi rintsawa. Yaseer ya girgiza kai ya ƙarasa ya ɗauro alwala ya koma ɗaki yaci gaba da nafilolin shi
yana yiwa umman shi addu'ar sauƙa lafiya.

Wuraren assalatu Danejo ta fito daga ɗakin itama tayi sharƙaf da zufa don da gaske haihuwar tazo da
gardama. Da kamal wanda yayi pillow da dantsen hannun shi taci karo bakin shi a buɗe yawun barci na
dalala.
Ƙafa tasa ta shure shi ya tashi a firgice ya zauna. "Ta sauƙa ne?" Shine abinda ya fara tambaya.

"Ban sanin ba soko kawai! Kaje ka taso mana malam Iro yazo da motar gawa kuma"

Tazo zata koma ciki yayi saurin riƙo ta. "Motar gawa dai kika ce Danejo?" Sai ya sake fashewa da kuka
"Innalillahi wa inna ilaihirrajiun, Shikkenan na shiga uku na a duniyar nan! Yaya zanyi rayuwa babu
Saudatu? Me yasa zaki tafi ki barni a irin wannan lokacin Saudatu?"

"Bata tafi ba tukun amma ta kusan tafiyar tunda sokon miji gareta. Dalla yi saure kuzo da mota mu kaita
asibiti, ko akwai inda zaka samu abin hawa da wannan lokacin?"

Yayi saurin share hawayen "me yasa zamu je asibiti danejo? Naga duka haihuwanta a gida take yinsu
asiri a rufe"

"Toh wannan da gardamar shi yazo ko ni kake so in shiga in jawo shi?" Girgiza kai yayi sannan ya saka
takalmi ya fice da hanzari har yana tuntuɓe da ƙofa.

Haka aka zo da motar bakin lungun su, Yaseer ya ɗauki Suhail ya kai shi maƙwafta da aka ce suje can su
zauna har su dawo daga asibitin idan ta sauƙa amma yana ajiye Suhail yayi saurin dawowa domin bama
zai fara iya zaman har sai sun dawo yasan halin da mahaifiyar shi take ciki ba.

Ya ɗauka musu ƴar jakan kayan haihuwar Saudat da yanzu Huwaila ta haɗa mata ɗan abinda ta samu a
ɗakin sannan huwailan da Kamal suka taimaka mata har zuwa jikin motar, jikin ta duk ya gama laushi, a
bayan motar duk suka jibgu kaman ragunan layya Yaseer yana faman mata sannu, kamal da malam iro
suna gaba har asibiti.

Da ƙyar da suɗin goshi suka yarda suka karɓe ta ganin saida suka bari ta zama sauran gawa kafin suka
kawo ta, sai a Sannan ne Yaseer ya zubar da hawaye domin abin ya fara wuce ɗan ƙaramin tunanin shi,
Kamal kuwa tunin cewa kuɗin da ya samu ya amso daga wurin Alhaji Tahir yanzu duk karɓewa zasu yi
yake yi. Shiyasa bayi son zuwa asibiti, abu kaɗan zasu yi maka amma sai sun ƙwaƙwule maka aljihu.
Ai kuwa ana shiga sallan asuba basu fito ba Saudat ta santalo ɗanta namiji. Aka kintsa su kafin aka bawa
su kamal daman shiga su gansu bayan an gyara su an maida su ɗakin hutu sannan kuma Akwai kuɗin
kayan amfani da suka ara masa aka yi musu amfani, kuɗin buɗe file, kuɗin gado da kuma kuɗin magani,
wai a hakan ma karɓan haihuwa kyauta ne tunda babban Asibitin gwamnati ne.

Saida suka tabbatar ya lale musu dubu sha ɗaya da ɗari shida kafin suka barshi ya shiga ganin jariri, gashi
dai yana murna Amma duk sun gama kwashe mishi tattalin arziƙi daman Dubu ashirin ya samu ya karɓo
daga wurin Alhaji Tahir yanzu sauran dubu takwas da ɗari huɗu.

"Kai Saudatu ma akwai raki, abun nan da an saba yanzu yabi jiki, aida saidai kawai kiyi abin ki ke kaɗai in
yaso da anzo yanke cibi sai ki kira ni in ya gagare ki" abin da kamal ya fara jiyowa kenan yayin da yake
wuce gadajen mata masu sabbin jarirai don zuwa wurin tashi matar da abinda ta haifa.

Saudat kuwa murmushi kawai take don ita tasan azabar da ta sha, tunda dai an sauƙa lafiya falillahil
hamdu, ita karan kanta Danejon saida ta yabi ƙoƙarin ta a daren jiya amma gashi ba'a je ko ina ba ta
sauya magana.

Sallama yayi musu ya ɗaura da "Sannu Saudatu, yaya daɗin jikin?" Da alhamdulillah ta amsa. Yace "Allah
ya ƙara lafiya, sannu da ƙoƙari" kafin ya amshi babyn da Yaseer ya rungume tsaff a ƙirjin shi.

Yana da haske irin na jariran nan amma fatar kunnen shi nada ɗan duhu, ya murmusa tunawa da yanda
mahaifiyar shi ke ƙulafucin ƴa mace gashi haihuwa uku har yanzu Allah bai ga daman bata ba.

Dabinon da ya siya yanzu a bakin asibiti ya ciro daga aljihu ya gutsura ya tauna sannan ya tura shi a bakin
babyn dake barcin shi hankali a kwance. Ya ɗau lokaci yana mishi addu'a kafin ya ɗago kai yace, "nayi
magana dasu goggo sunce suna hanya zuwa azahar in sha Allah sun sauƙa, sai mu hanzarta mu koma
don tarbar su."

Basu ƙara ɓata lokaci ba suka tattara komatsan su kasancewar an tabbatar da cewa daga uwar har
abinda ta haifa suna cikin ƙoshin lafiya don haka basu jira hutun awa shidan bayan haihuwa ba ya saka
matan a keke napep sannan mazan kuma suka shiga motar gawan su suka koma gida.
.....

Idan ka shigo hall ɗin kafin idanun ka yakai kan allon sunar dake kan stage zaka ɗauka wani gagarumin
event ɗin biki ake a cikin ta.

Babu kowa a wurin bayan event planners wanda ke sanye da uniform ɗinsu na aiki, amma an gama
shirya wurin an tsara shi tun daga kan decorations, DJ, abinci da abin sha, dessert station, sannan ko
wani table akwai numbobi a saman shi haɗe da jakar suna mai hoton baby don ba za'a kira shi da laidan
suna ba, bayan snacks da drinks da aka saka a ciki suna ɗauke da jotter hard cover, biro da kuma turmin
zani ko sallaya irin masu kauri da laushin nan, Wanda ke ɗauke da laidoji sune tables ɗin baya-baya
amma shima sallaya ko turmin zani ya bambanta su sai kuma nasu laida ne ba jaka ba amma kuma
komai yaji.

Numbobin dake kan table ɗin shi zai taimakawa kowa gane inda aka amince masa ya zauna wanda yake
matsayi by matsayi, don haka duk wacce aka bata Katin gayyata zata shigo dashi sai ta nunawa masu
aikin wurin su kuma zasu taimaka mata wurin samun mazaunin ta cikin tsari.

Zuwa ƙarfe huɗu da rabi na yamma hall ya kusa cika Dj da abin motsa baki suna taya baƙi hira, uwar
gayya kawai ake jiran isowarta.

Saida aka saka musu kiɗan da ya dace dasu sannan aka buɗe musu ƙofar suka fara takowa cikin hall ɗin
sanye da ashoben su lace mai tsadar gaske na iyayen jaririya, sun sha kyau harda makeup kowa ta zuba
gold a wuya, hannu da kunne iya yanda nauyin ta zai iya ɗauka sai faman hura hanci suke, amma Duk
wankan su basu Isa su dishashe Hajiya Fauziyya ba wannan alƙawari ne alhaji Tahir yayi musu, kayan da
yake jikin ta kawai yayi kuɗin nasu na mutum uku gashi tasha makeup da ya karɓi fuskar ta haɗe da
fara'ar da ya ƙara mata kyau da kwarjini, Baby Hafsatu kuwa na cikin wani hand basket da Hajiya
lubabatu ke riƙe dashi ba zasu ma iya riƙeta a hannu ba saboda abu irin na bidi'a.

Har kan stage suka yi musu rakiya aka cire Reina daga ƙaramin hand basket ɗin aka saka ta a babba da
aka kafa shi a wurin yasha ado da su flowers ya ƙawatu sosai ga wasu manyan teddys da idan ɗaya ya
faɗi a kanta bisa kuskure hala sai dai a ɗauki gawar ta.
Aka gyara mata kwanciya kowa sai ƙoƙarin cusa kai yake a cikin su kafin aka zaunar da Hajiya Fauziyya a
haɗaɗɗen kujeran dake gefen basket ɗin bayan su kuma ƙaton allo ne da aka rubuta 'Welcome to the
world Hafsatu Tahir Kamal (REINA)' shima allon ya ƙawatu abin sai wanda ya gani.

Basu ɓata lokaci ba Mc ya gaida baƙi ya bawa Hajiya Fauziyya mic tayi musu godiya da halarta kafin aka
fara gabatar da agenda na gaba wanda shine gabatar da kayan sunan da aka kawo wa sarauniya Reina
da mahaifiyar ta.

Na mahaifinta aka fara shigowa dasu a jere masu kawo akwatin ma t-shirt ɗin jikin su da hoton Reina
mai nanannen hanci a jiki.

Kowa ya zuba idanu don ganin yawan su, amma abin yaso basu tsoro ganin sai shigo da akwatuna kawai
ake sunƙi ƙarewa. Duk wanda yake na Reina ne a gaban gadon ta suke jerawa na hajiya Fauziyya ma a
nata gaban ake jere mata mutane tuni an fara shooting da wayoyi bayan wanda photographer yake yi
domin a samu na yaɗawa a yanar Gizo.

Saida aka jere akwatuna set uku-uku guda sha biyar kenan ma kowa a cikin su kafin aka ƙara ma Reina
da baskets na baby care, bargon yara, da sauran abinda ba zasu shiga cikin akwati ba.

Baki ɗaya sai jikin su Hajiya hauwa yayi sanyi dukda dai sunyi tsammanin hakan ga Mc kuwa sai washi
yake ma uwa da uban Reina dama ita jaririyar dake cikin tsumma, nan aka mishi albishir uban yarinya
yayi mishi kyautar Naira miliyan biyu, saida ya taka rawar murna.

Ba'a buƙatar ɓata lokaci wurin bubbuɗe wannan kayayyaki don haka aka kira wanda suka shigo dashi
don su fita dashi a saka a mota a maida shi zuwa gidan mai jego ba yare da ɓata lokaci ba gudun kada a
samu matsala, Su Inna larai suna can suna gadin gidan.

Nanfa aka fara gabatar da gudumawar ƴan uwa, da manyan baƙin da aka gayyata. Ƴan uwan Alhaji Tahir
mata kowa tayi nata kayan sai da ta saka mijin ta yayi nashi shima don haka akwati set bibbiyu suka
dinga jerewa a wurin, huɗu na hajiya Fauziyya huɗu na Reina. Baƙi ma sun gwada tasu bajintar matuƙa
don babbar baƙuwar mu matar gwamna sabuwar dalleliyar mota ta bawa baby.
......

*Toh Reina da an tashi daga suna sai ki tuƙa mu a motar ki zuwa gida😹*

*Lallai sunan wannan littafi na shan pronunciation 😂😂😂 daga masu Reena, Raina har su Rayina😂 Ina
godiya da ƙoƙarin bin labarin dai🥰*

*Ku cire 'I' ɗin idan kuka zo furtawa saboda silent ne, sai ku karanta shi a matsayin RENA. ma'anar REINA
kuma a yaren Spanish shine Sarauniya. Ana yawan amfani dashi a matsayin nickname ko endearment
haka tsakanin mata da miji ko saurayi da budurwa*

*REINA 💍*

07... Kan uban chan! Lallai uwar makirai ta tashi kaina, wato sunan yarinya Hafsatu?" cewar Hajiya Farida
tana bushewa da dariyar ƙeta yayin da ta juya kan motar suka ɗauki hanyar fadaman mada zuwa gidan
Hajiya Hauwa tunda shi yafi kusa da Hall ɗin da aka yi event.

Jinjina kai Hajiya lubabatu tayi tare da yin ƙwafa kana tace "Aini tunda naga ana tambayar Tahir sunan
da ya raɗa mata yana wani noƙe-noƙe nasan da wata a ƙasa."

"Ba dole yayi noƙe-noƙe ba yana jin tsoron ya saɓa ma uwar shi Fauziyya ta tsine mai" Hajiya Hauwa
dake seat ɗin bayan Hajiya lubabatu a ɓangaren mai zaman banza ta taɓe baki.

Kyalƙyala dariya hajiya Farida taci gaba da yi ta kuwa yi nasara wajen ƙara ƙular da su "Aini nace miki an
goge min hadda a lamarin nan, kamata yayi ma muje muna ɗaukan darasi don mu ba zaman aure muke
yi ba tunda sai yanda mazajen mu suka yi damu, ita uwar sarauniya kuwa kunga ita ke waina shi kamar
tayar keke"
Muskutawa a seat ɗinta Hajiya jummai tayi tace "Ni abun da ya bani takaici wani sunan Nasara da suka
ɗoɗara mata Wai Raina ne ko menene? Abun ki dai da matsiyaci bai iya samun wuri ba"

"Reina aka cewa ku kuma ƙauyawa, ƴan gayu suna abu kuna ɓata musu" saboda dariya har hawayen da
ya kwanta a idanun ta ya fara saka ta ganin hanya duru-duru dama ga duhun maghriba, don haka ta zari
tissue daga cikin kwali ta goge hawayen ba tare da ta bar ƙyaƙyatawa ba.

"Wallahi Farida zan mari bakin ki idan baki ƙyale mu munji da abu ɗaya ba." Hajiya lubabatu wacce ta
gama ƙufula ta harare ta "Ah-ah, asiri hauka ne? Don kawai mun zuba mata idanu sai ta maida mana
ƙani boyi-boyin ta? Ki kalli fa yanda Tahir yake rawar ƙafa a kan haihuwar nan fisabilillahi, Haihuwar ƴa
mace wanda ba zata amfane shi da komai ba saidai ya gama gina ta ya bawa wani ya aura."

"Shi yasa muke so abun ya dawo gida ai, ta ginu ta auri ɗan dangi ko ba komai munci ƙarfin dangin
matsiyata" Hajiya Hauwa ta ƙarashe tare da murguɗa baki kaman Fauziyyar ce a gaban ta, Wanda idan
ita ɗin ce a tare da ita yanda take nan-nan da ita zaka ɗau ciki ɗaya suka fito.

Ƙanƙance idanu cike da bala'i Hajiya jummai tayi tana fuskantar Hajiya Hauwa "Ke a tunanin ki zata bari
ne? Ko dan ba a gaban ki yazo ya tsuguna yana kuka da hawayen shi shar-shar na aje a roƙa mishi
Hafsatu da Ahmadu su amince su bashi Fauziyya ba?! Kwanar uwar mu 9 fa a cikin ƙasa lokacin, shine
yaya Zuwairah ta tsinke shi da mari don ya dawo cikin hayyacin sa toh tun daga lokacin suka ɗaura gaba
shi yasa baki ganta ta ɓata ƙafar ta zuwa suna ko barka ba. Amma kuma Tahir ya Haihu ya manta da tashi
uwar a barzahu ya saka sunan wata tsohuwar najadu"

Mamaki ne matuƙa ya kama Hajiya Hauwa ta riƙe baki tare da zaro idanu "Hasbunallahu wa niimal
wakeel. Shine kuma kuka bari ya aure ta?"

"Yaya muka iya an gama wanke shi? Barazanar zare hannun shi cikin lamarin kasuwancin mu ya fara yi,
ya shiga fushi da kowa daga lokacin muka gane ba laifin shi bane."

Hajiya hauwa ta jinjina kai "Aini na sha mamaki yanda naga rana ɗaya Abban su Jamal ya amince da
zancen ashe da walakin goro a miya" tana nufin mijin ta Alhaji Salisu.
"toh a lokacin ma kenan balle yanzu da an bashi ya ci, ya sha, ya shaƙa, ya taka ya yi wanka dashi. Kinga
ba abun mamaki bane idan rana ɗaya ma yace ɗaukar iyalan shi zaiyi ya bar ƙasar, muda sake ganin
Tahir hala saidai a darussalam."

Hajiya lubabatu tayi saurin amshewa da "Wallahi indai kuka ga Tahir ya bar Nigeria kai ko Bauchi bai isa
ya bari ba saidai idan ƙasa ce ta rufe idanu na. Auren ma saboda lafiyar shi da hankalin shi yasa muka
barshi ya yi ba wai don Fauziyya tafi ƙarfin mu ba, inba haka ba me aka yi aka yi dangin ta baki ɗaya da a
rana ɗaya naga dama zan iya sakawa a shafe tarihin su baki ɗaya?"

"Uhmm kun dai matsa ma Masarauta iyayen Sarauniya"

saida Hajiya lubabatu ta kai wa Hajiya Farida duka kafin taji daɗi bakin ta kuwa bai mutu ba tana ta ƙara
ƙular da su har suka isa Gidan Alhaji Salisu suka baje capacityn su a can, sun samu sunyi sallar maghriba
haɗe da isha suka ci abinci, domin kare aji ya hana su cin na suna kafin suka ɗaura da caccakar Hajiya
Fauziyya daga inda suka tsaya.

.....

Kwana biyu kenan da zuwan Goggo Halime daga jama'are tare da kishiyar ta da suke kira da Amarya,
daman haka suke tun zamanin yarinta tunda anyi zaman lafiya zaman amana sai kowa a cikin su ta
mayar da lamarin ƴar uwar ta ya dawo nata suna hidimar su tare har tsufa ya kama su gashi ana kan
zuba jikoki.

Tuwon dawa miyar kuka suke ci daga gindin bishiyar neem dake tsakar gidan, hasken cikakken farin wata
shi yake haska musu cikin farantin suna ganin wurin da suke yanka, tunda rashin wuta har ya saka raka ni
kashin goggon ma ta mutu ba caji.

Daga uwar ɗaka Saudat take fifita a hankali yanda goggon ba zata ji ba don ta hana ta amma zafin da ake
kamar zai hallaka mutum har jaririn ma ƙurajen zafi sun dabaibaye masa jiki.

Ga sirkin da aka ciko ƙaton kofin silver dashi yana tururi, tabbas tasha wannan kam zaifi narka ta zaiyi
har hanji.
Wutar da aka kawo ya haska ɗan madaidaicin tsakar gidan da yalon haske. Suhail da yaron huwaila suka
saka shewar "nepaa" kana suka fara wawan abinci don su gama da sauri suje ɗakin Saudat kallo.

Ba'a daɗe da kawo wutan ba Kamal ya shigo sannan ya tsuguna a gaban mahaifiyar shi yana miƙa mata
canjin Naira 300 "gashi sun karɓi dubu uku da ɗari bakwai da ƙyar don an ɗauki lokaci ba'a biya kuɗin ba
shi yasa ma suka yanke.

Hannunta ta tsame daga cikin tuwon ta suɗe shi tass sannan ta zuba idon ta cikin na Kamal, Allah ya gani
bata kunyar ɗan fari da kamal domin idan bata bashi kulawa ba waye zai bashi, tunda gashi ƴan uwan da
ya kamata su ɗauki nauyin shi a ko wani ɓangare na rayuwa sun banzantar dashi.

Shekarun shi huɗu kenan da dawowa cikin garin Bauchi da iyalan shi a kan cewa Alhaji Kalabu zai sama
mishi aiki amma bata san irin rayuwar da yake yi ba kenan, har ita ma idan damuwar ta ya tashi take
turo mishi ƙorafin kuɗi kuma yayi ƙoƙarin mata ba tare da ƙorafi ba saidai a samu jinkiri, ashe ita ma ta
fishi samu tunda ba aikin arziƙi aka sama mishi ba.

Gadin makaranta ce ta firamare ana bashi dubu ashirin a wata, a wannan zamani na tsadar rayuwa ga
mata da ƴaƴa guda biyu yanzu sun zamo uku, ga mahaifiya da ƴan uwa masu bani-bani a ƙauye.

Hannun ta miƙa da nufin karɓan kuɗin tace "kace ma da kaje wurin Alhaji Tahir nawa ya baka?"

"Dubu ashirin" ya bata amsa.

"Babu komai zanje in same shi"

Ta sake mishi kuɗin sannan ta miƙe da nufin wanke hannun ta.

Duban shi ya mayar ga Amarya da bata rabuwa da murmushi a ɗan yamutsattsen fuskar ta, halin su ɗaya
da goggo shi yasa tasu tazo ɗaya, don haka ganin ɓacin rai a fuskar ta yau ya ɗaga hankalin shi matuƙa.

"Amarya ki bata hakuri kada taje ta tayar musu da hankali don Allah"
Murmusawa tayi kaman damuwar shin ba komai bane tace "kada ka damu zuwa gobe zata huce, yanzu
ka ƙaro wa mai jego sikari da canjin hannun ka".

Da toh ya amsa sannan ya miƙe, ya shiga ɗakin kwanan su duba Saudat kafin goggo ta dawo daga ban
ɗaki.

Tana fifita ya riske ta ga gumi nata karyo mata don haka ya jefa mata tambayar, "yaya baku kunna fanka
ba"

Ƙasa da murya tayi yanda na waje ba zai jisu ba tace "goggo tace sanyi zai kama yaro"

Jin sunan goggo yasa bai tanka zancen ba saima sauya akalar zancen da yayi. "Saudatu wani suna kika ga
ya dace mu saka mishi?"

"Duk sunan da kake so ka saka bani da haufi a kan zaɓin ka"

Ɗan shiru yayi yana sosa ƙeya kafin yace "dama ni naso wai ko mu saka mishi Tahir ne tunda naga kaman
shi bayi da takwara"

Nan da nan annurin fuskar Saudat yayi saurin ɗaukewa ta kuwa tamke shi tamau. "Wani irin Tahir kuma?
Mu ke da alhakin mishi takwara saboda Allah?"

"Ai shiyasa na tambayi ra'ayin ki."

Ta san ba lallai zaɓin ta ya faranta ran kowa ba domin tafi son sunayen zamani ita, kaman na Suhail da
aka bata zaɓi, toh yanzu ma in ta sake zaɓa surakanan ta zasu ga taso kanta don haka tace "toh a
tambayi Goggo"
"Idan itama tace a saka Tahir ɗin kuma fa? Koma kalabu? Kinga ba zamu iya ja da ita ba gwanda ki zaɓa
sai ince mata ra'ayi na ne."

Shiru tayi tana nazari kafin tace "toh a saka mishi Sabir."

"Shikkenan an gama amma zan shawarce ta a kan sunan kafin mu saka" gyaɗa kai tayi, ya saka hannu
yana share ma yaron gumin da ya jiƙa farin powdern goshin shi. Yace "ɗan albarka baka da rikici"

Saudat ta karɓe da "gaskiya kam, saidai idan yaji yunwa ko barci amma ko zafin bayi damun shi sosai.
akwai haƙuri kam yaci sunan shi haka muka yi da Yaseer ma, baba na ne mai rikici dai har yanzu."

"Allah ya raya mana shi da imani, ya kuma basu ingantaccen rayuwa baki ɗayan su" da ameen Saudat ta
amsa sai ya ƙara da "baki buƙatar wani abu?"

"goggo ta sayi komai ni har kunya ma ta kama ni wallahi"

"Babu komai, haka iyaye suke koda mun hana su idan suna da halin yi sai sunyi mana, Allah dai ya bamu
ikon kyautata mata muma" ta ƙara amsawa da ameen sannan ya miƙe.

Suhail na ganin zai fita ya maƙale dole ya fita dasu biyun zuwa shagon dake can bakin titi.

.....

Har yanzu goggo bata bar Mamakin yanda Yaseer ya iya komai a cikin gidan ba, yanda bayi barin su su
ɗauki ko tsintsiya Idan dai yana nan.

Shi zaiyi shara, wanke-wanke, wanke ban ɗaki, ɗebo ruwa, wanki, yabi ya wanke yara harda na
makwafta idan sun shigo bayi barin su su fita da dauɗa kuma ya shirya ya tafi makaranta da ya dawo yaci
abinci ya wuce hadda ranar da babu ya tafi shagon ɗinki.
"Saudatu so kuke yi ku kar yaron nan ko?" Goggo ta shiga rikici bayan Yaseer yayi musu sallama ya fice,
daman ita bata yiwa iyaye faɗa a gaban yaro don hakan ba a ko wani lokaci yake daidai ba.

Shiru Saudat tayi don bata da ta cewa, goggo ta ci gaba da zuba zance"kunyi mishi horo mai tsanani yaro
bai san ya huta ba ko kaɗan? Ko mace kuke son maida shi ne iye?!"

Saudat dai tana shiru sai huwaila dake aza ice a ƙasan tunkyar wankan mai jego ne tace "wallahi Goggo
ko kince ya bari bayi bari, haka nan yake da zafin nama jikin shi bayi son zaman banza, ga fannin karatu
ma ba baya ba ance har monita ake bashi a boko a hadda kuwa idan baizo na ɗaya ba bayi wuce na
biyu."

Goggo da Saudat suka saki murmushi a tare duk da ba kallon juna suke ba. Amarya dake daga uwar ɗaka
tana wanke jaririn tace.

"Huwaila bar Halime kishi kawai take kada mijin yace yana son sabuwar amarya kwanan nan tunda
girma da hankali sun zo"

Da haka suka ci gaba da hira cikin nishaɗi Saudat na saka musu baki jifa-jifa idan buƙatar hakan ta taso,
yara kuwa duk an wuce boko Kamal ya tafi wurin aiki.

.....

"Baba kiyi haƙuri Alhajin bayi gida nace miki" mai gadin nan ne na gidan Alhaji Tahir.

Yanzu haka daga gidan Alhaji Salisu suke shima an hana su shiga wai Hajiya da Alhaji duk sun tafi aiki
shine suka gangaro nan don fushi take da Alhaji Kalabu.

"Toh matar gidan fah? Ko itama bata gida?"

"Eh bata nan" ya amsa kai tsaye yana daɗa haɗe giran sama da na ƙasa.
"Mai jegon ne bata gida?" Sai yanzu kamal ya sako musu baki cikin zancen su. "Ko yau ma zaka ce baka
gane ni bane?" Ya ƙara matsowa kusa dashi da confidence yau gashi da shaidar shi a tare da shi.
"Wannan da kake ganin ta ƙanwar Uban mai gidan ne, don haka kafin yazo ka rasa aikin ka bata hanya ta
wuce"

Ƙaramin tsaki yaja sannan ya bada izini aka buɗe musu ƙofar suka shige Kamal har wani boƙarewa yake
kan shi yana mishi faɗi suka shige direct har parlourn Hajiya Fauziyya wanda Wannan shine shigan shi
cikin gidan a karo na farko, duk cikin sauran ƴan iwan ma idan yaje gidajen su toh saidai ya jira a waje.

*Saliha Ahmad Na'ibi (Mrs Imran ✨)*

*REINA 💍*

08.....juye-juye kamal yake yi a tsakiyar parlourn kaman wuyan shi zai tsinke. Ba don shi da ƙafar shi ya
shigo ba zai iya rantsuwa cewa ba a Najeriya yake ba amma wai ƴan uwan shi Hausawa ne ke rayuwa a
irin wannan aljannar duniya.

Sallamar Hajiya Fauziyya ne ya maida hankalin su duka biyu gare ta, tana tafe da jaririyar ta rungume a
ƙirjin ta, kamar kullum fuskar ta ɗauke da murmushi.
"Mama Bismillah ku zauna, sannun ku da zuwa" tace yayin da itama take niman wurin zama a kujeran
dake kallon nasu.

Parlourn tsit babu hanayiya ko kaɗan sai ƙarar na'urar sanyaya wuri dake aikin sa babu gajiyawa. Har
goggo saida tayi mamakin saurin fitowar hajiya Fauziyya don ta ɗauka sai sun gama shanya ta kafin ta
fito kaman yanda sauran matan ƴan uwan Tahir ɗin ke yi.

Gyara zaman Reina tayi a cinyar ta cikin kiyayewa saboda kada ta tashe ta daga baccin da aka samu tayi
da ƙyar bayan ta gama ihun ta ta gaji, sannan ta ɗan zame kaɗan daga kujerar ta gaida Goggo Halime.

"Mama Ina wuni, kun iso lafiya?" Kasancewar yau ne rana ta farko da ta fara ganin ta yasa tayi tunanin
ba a nan cikin gari suke ba, domin bata san kamal ba bata taɓa haɗuwa da shi ba don haka bata san shi
waye ba, masu aikin ta dai sun shaida mata ƴan uwan mai gidan ne, sai dai fuskar shi yana mata kaman
ta san shi a wani wurin amma ta rasa ina?.

A take Goggo Halime ta saki fuska ta ɗauko murmushi ta yafa ganin kirkin matar Tahir. "Sannu dai ƴar
nan, mun same ku Lafiya? Yaya kishiyar tawa?"

Miƙewa tayi da nufin ta miƙa mata Reina ta ganta, tana amsawa da "lafiya ƙalau, an gode Allah" karɓan
ta goggo tayi "Masha Allah, kishiyar tawa jajawur abin ta"

Komawa Hajiya Fauziyya tayi ta zauna tana dariya "Ai da shirin ta tazo na ƙwace mai gida"

"Ta makara ai, tunda har rai yayi halin sa, saidai mu jira wanda zata dirje ta zaɓo mu aure shi tare"

"Allah sarki, Allah yayi mishi rahama" tace cikin alhini.

Goggo ta amsa da "ameen ƴata"


Daidai lokacin masu aikin gidan guda biyu suka shigo kowa ɗauke da tray a hannun ta suka dire a gaban
su.

Na farkon na ɗauke da ruwan gora mai sanyi ɗaya da mara sanyi kuma, sai juice ɗin kwali da kuma glass
cup. Sai ɗayan mai ɗauke da soyayyar naman kaza anyi pepper ɗin shi da kuma kayan ƙwalam na fulawa
irin su donut.

"A'a har da wahala haka?" Tace tana washe baki, murmushi kawai hajiya Fauziyya tayi "Kamalu kaga
zuba min ruwan nasha" ya durƙusa ya bude lemon kwali ya tuttuɗa mata a kofi domin da hankalin shi ba
zai bata baƙin ruwa ba bayan ga mai kala nan a kusa.

Shima ya cika nasa kofin kafin ya koma ya zauna sannan suka shiga gaisawa da Hajiya Fauziyya yana yi
yana kurɓan lemo, kana ya shiga mata bayanin daga inda suke don akwai buƙatar hakan.

"Ban san ko kin gane ni ba, mijin Saudatu ne da tazo miji barka Ranar Alhamis"

kaikaitar da kai tayi tana son tuna wata Saudatu ce, domin yawan wa'inda suka dinga zuwa mata barka a
kullum ba zata iya kiyaye su ba.

Daga ranar suna ne ma Alhaji Tahir ya samu saran dawowa da wuri suna cike a gidan sai yayi musu kora
da hali ko kuma ya ɗauke Hajiya Fauziyya su yi ciki ba zasu sake ganin ta ba, toh fa shine suka shafa musu
lafiya yau babu wanda yazo.

Ganin bata gane ba yasa ya canza akalar bayanin nasa "Ai ni ɗan uwan su Alhaji ne. Goggo nan da kika
gani ƙanin mahaifin su ne uba ɗaya"

Da sauri ta gyaɗa kai "Kai ne baban Yaseer kenan?"

Ya ƙara washe baki ganin yanzu ta gane "eh wallahi Hajiya"

"Yaya jikin umman Yaseer ɗin? Don tace bata ji daɗi ba ranan"
"Ai ta sauƙa ai, an samu ɗa namiji" goggo ta amshe zancen,

Hajiya Fauziyya ta ƙara washe baki."Ah Masha Allah, Allah ya raya, yau kenan ko jiya?"

"A'a yau kwana uku kenan, suna barin nan gidan abun yazo"

Tunawa tayi da alƙawarin da tayi musu na za'a maida su gida, ashe baiwar Allah kanma na cikin halin
naƙuda, Allah dai yasa da suka fita sun samu abun hawa ba wai a sanadin ta haihuwar ta taso mata ba.

"Allah sarki, ai kuwa bamu ji ba, zamu je muga baby in Allah ya yarda"

"Shiyasa ma muka zo ƙafa da ƙafa domin mu sanar da ku don ma kada kuce baku jin ba" Goggo Halime
ta amshe. ina amfanin zumuncin ɓangare ɗaya kawai? Idan ɗaya bangaren suma suka sada nasu
zumucin ai abun zaifi armashi- Take tunani a ranta.

"gashi kuwa baban ta bai dawo gidan ba tukunna, zaku jira shi ina babu matsala?"

Goggo da ta shanye lemon ta tass ta miƙa wa Kamal kofi ya ƙara mata sannan ta tambayi "zai kai dare
ne?"

"Eh gaskiya amma zan kira shi in sanar da shi, in sha Allah zai dawo da wuri"

Ta tashi da niyyar taje ta ɗauki wayar ta ta kira shin a ciki dai-dai lokacin da Reina ta tsalla wani ihu
kaman wanda aka mitstsine ta.

Sauƙe numfashin ƙosawa Fauziyya tayi tare da juyowa tana kallon jaririyar dake ƙara sautin kukan ta har
wani sassandarewa take yi idanun ta kuwa a rufe ruff.
Goggo ta riƙe baki ganin abun nata na yi ne"Kaji min ƴammatan zamani wato tun ban tare a gidan ba kin
ba har kin fara kishi da ni"

Cikin ƙosawa tace "Ni da ku tafi tare ma kawai Mama ko zan samu in ɗan huta da rikicin Reina, bata
gajiya da kuka wallahi"

Dariya Goggo Halime tayi irin nasu na manya tana faɗin "ƴar nan mai aka yi da maza? Har kin gaji?"

Taɓe fuska tayi ta koma ta zauna, Allah ya gani ita ainihin ta ba mai son yara bane balle ta saba da fitinar
su, wannan ma don nata ne daga jikin ta ta fito don haka babu yanda ta iya amma ko ƴaƴan yayun ta ba
ɗauka take ba idan taje musu, tafi gane yaro yayi hidiman shi itama tayi tata kawai.

"Allah mama kukan banzan ta yayi yawa, ban isa in saka kafaɗa na da nufin in huta ba. Raya dare take
tana kuka kaman abun jin baki".

Shawarwari ta fara bata na yanda zasu ke mata idan taƙi yin barci yayin da kamal ya maida hankalin sa
ga talabijin wanda ake nuna wasan ƙwallon raga(tennis).

Bayani take mata tun daga kan yanda ya kamata ake mata wanka da gasa jiki da kuma kwanciya duk da
wasu abun fauziyya jinsu kawai take yi amma tasan ba zata iya ba, kalan taje ta karya ma Alhaji Tahir ƴa
ko ta kashe ta? Yanda taga yana ji da Reina kamar ƙwai?.

Har salon shayarwa saida Goggo Halime tayi ma Fauziyya gyara ta fara gwada mata kalan riƙon da zasu
dinga yi ma Reina ta dinga samun nutsuwa ai kuwa kaman an kulle bakin sai ƙifi-ƙifi kawai take da idanu.

Fauziyya taji daɗin hirar sun don haka suka rashe a parlour suna ta zantawa sun ma manta da zancen
kiran Alhaji Tahir, shikuwa yana ta tara mata missed calls waya na rufe a ɗaki babu wanda ya ji, sai gaba
ɗaya hankalin shi ya tashi cikin gaggawa yake ƙoƙarin kammala aikin gaban shi don ya dawo ya duba ta
ko lafiya.

Har maghriba ta riske su basu ankara ba saida aka sanar mata da lokacin wankan yamman su yayi.
"Mama kuyi haƙuri barin kira shin kafin kuyi Sallah ku ci abinci ya iso in sha Allah"

Bata yi mata musu ba don mutumin da ya karrama ka ya gama maka komai, da kanta ta kai ta ɗakin da
suka yi alwala suka jira aka kira sallah kafin Kamal ya wuce masallaci goggo kuma tayi nata sallan a ɗakin,
tana idarwa aka shigo musu da abinci mai rai da lafiya suka ci suka yi Isha kafin suka dawo parlour
lokacin har hajiya Fauziyya tayi wanka ta shirya sun samu Reina tayi barci bayan ruwan ɗumi ya ratsa
jikin ta, don haka ta barta a ɗakin.

Suna zama Alhaji Tahir na faɗowa gidan kaman daga sama, ko ƙwaƙƙwaran sallama babu. "Fauzah lafiyar
ki?"

Da sauri ta miƙe ganin yanayin shi.

"Ina wayar ki?" Ya sake jefa mata tambayar a ɗan fusace ganin ƙalau take ta ɗaga mishi hankali.

Juyawa tayi ta ɗauko wayar daga matsugunin ta ta miƙa mishi, ya karɓa ya danna hasken wayar ya kawo
sannan ya juya mata screen ɗin zuwa duban ta. "Kina ina nayi miki 13 missed calls baki ɗauka ba"

Karɓan wayar tayi tace "laa, banma gani ba sai yanzu, wayan yana ɗaki ne kayi haƙur.."

Saurin katse ta yayi da "ba nace miki ki daina ajiye waya kina tafiyar kin nan ba? Meye amfanin ta toh
idan ba zai dinga kasancewa tare da ke a ko wani lokaci ba?"

Numfashi ta furzar ganin yanda yake masife ta a gaban jama'a, kaman ma bai lura da su ba don haka ta
sauƙe murya kana tace "Allah ya huci zuciyar ka, ga Mama nan tazo duba mu."

"Na ganta ai" yace tare da ƙaramin tsakin da bai san ma ta fito ba, gabaki ɗaya ran shi a ɓace yake ganin
a kansu ne ta manta da duniyar shi.
"Uhmm Tahir Ina wuni?" Goggo ta gaida shi ganin yanda ya tsaya musu ƙeƙam a kayi.

Bai so ba ya tsuguna har ƙasa kana ya gaishe ta da "Goggo ina wuni, kun iso lafiya? Yaya gajiyar hanya?"
Duk a tare ya miƙa mata gaisuwar don haka sai ta amsa da lafiya kawai sannan ya miƙe ya zauna a
kujera, Hajiya Fauziyya kuma ta tafi kawo mishi ruwa da basu wuri don su zanta tsakanin su.

Tace "Ashe an samu ƙaruwa"

"Eh wallahi, an samu Hafsatu Reina"

Jin ɗayan sunan tayi yayi mata banbaraƙwai tace "Allah yasa cikon addinin Muslunci ne. Shima matar shi
Allah yayi mata sauƙa yau kwana uku."

"Allah sarki, Allah ya raya"

"Ameen"

Daga yanda yake amsa mata magana a tsatstsaye yasa taji shakkar abin da zata faɗa da wani ido zai
dube shi?

Da kamal ma ya gaida shi sai ɗaga mishi kai yayi kawai.

"Tahiru ƙafar ɗayan ku bai sake taka Jama'are ba tunda Allah yayi rasuwa wa mahaifin ku tsawon
shekaru 15 kenan yanzu, kun manta cewa yana da cibiya bisine a can, yana da ƴan uwa yana da dangi ku
kanku kawai kuka sani"

Tunda ya ganta yasan dama sai yaji irin wannan mitan, gwanda lokacin da baiyi aure ba bata sakawa da
shi, duk jidalin tan a kan sauran ƴan uwan shi take sauƙewa sai su ɗan haɗa wani abu su sallameta kana
aji shiru na ɗan wani lokaci kafin ta sake dawowa.
Amma shine yau zata saka shi a gaba kaman wani ɗan ta bayan shima gashi ƴar nan ya ajiye yanzu.

"Goggo yanayin aikin ne wallahi babu lokaci, wuni muke yi mu kwana muna nima, yanzu ma nima na ake
yi a wasu ƙasashen amma babu halin zuwa balle ƙauye"

Ta jinjina kai "eh lallai. Kana da gaskiya, shine kuma babu waya babu aika? Ko sau ɗaya a shekara ka
ɗaga waya kayi wa wannan tsohuwar gaisuwar azumi kana ganin ba zan ji daɗi bane? Da ace nima fa
bani zarya a tsakanin ku da sai inyi ta ganin ku ma a talabijin in kasa gane ku, musamman ma kai tunda
ka tafi ko shekaru ashirin baka cika ba."

Cikin ƙosawa da mitar tata ya miƙe yana faɗin "ton zanyi miki aika goggo in sha Allah, ku gaida gida, mun
gode da ziyara Allah ya bada lada"

Sai ta samu kanta da murmusawa, wato shi mai hali bayi fasa halin sa. Daman shi haka Tahir yake ba'a
taɓa cinsa a zance domin ba zai ma baka damar da zaka tofa albarkacin naka bakin ba.

"Koma ka zauna, tun da kaga nazo har cikin gidan ka na zauna na jira ka kasan da magana nazo"

Kaman ba zai zauna ɗin ba don ƙanwar uban shi ai ba uban shi bane, amma tsufar fuskar ta ya saka yaji
nayin ta ya zauna ɗin yana duba agogon shi cikin matsuwa kaman wanda zaije wani Wurin.

"Tahir Idan mu kun yada mu shi ɗan uwan ku da yazo jikin ku ba zaku taimake shi ba? Ka duba niimar da
Allah yayi maka fah, ka duba daular da kake rayuwa a ciki!"

Shi da Kamal suka sake bin gidan da kallo ita kuwa idanun ta yana kan shi. "Amma shine na ɗan uwan ka
musulmi yake kwana cikin zafi da ƙunci, yaran shi suke zaune a gida saboda kuɗin abin buƙatar da zai
tura su makaranta ya gagara"
Da sauri da Alhaji Tahir ya amshe da "Kamalu, ba kazo har cikin gidan nan ka karɓi kuɗin registration da
uniform ɗin Yaseer ba?"

"Dubu ashirin ɗin?" Mamaki ya kama Goggo ganin har taƙama yake yi da hakan.

"Toh dubu ashirin ɗin ba kuɗi bane? Ba wahala aka yi aka same shi ba?"

Bismillah tayi ta miƙe Kamal ma yayi makan yanda tayi, "toh zan dawo maka da kayan ka in sha Allah. Ni
bance ku bawa kamal kuɗi ba, Alfarma ɗaya na roƙa a wurin ku shine ku sama masa aiki, aiki ko wani iri
ne indai zai iya, amma ba aikin da ake biyan dubu ashirin a matsayin albashi ba, a tunani na muna da
gata a kasar ɗa a yanzu baka samun komai sai kana da hanya, amma ga hanyar baiyi mana rana ba.

Amma kada ku damu, Kamal zai rayu da taimakon ku da babu shi, zumunci kuma ba zamu fasa sadawa
ba in sha Allah, idan kun gaji da ganin mu muka zo kada ku buɗe kofa" sannan tayi gaba Kamal ya bita a
baya.

*Seemahwrites ✨*

*REINA 💍*
09......Tun daga ciki Hajiya Fauziyya ta fara jiyo muryar Alhaji Tahir amma kafin ta fito don ganin mai yake
faruwa har su goggo sun ɗauki hanyar waje. Da hanzari ta bi bayan su da nufin ta tsaida Goggo amma
tayi ficewar ta bata saurare ta ba, ranta ya riga ya gama ɓaci.

Shi kuwa yana zaune hankalin shi a kwance kamar bai yi komai ba, ya cigaba da danna wayar shi.

Juyowa tayi bayan sun rufe ƙofar a fuskar ta ta zuba mishi idanu yana ci gaba da danne dannen shi har
saida yaji alamun idanun ta a jikin shi kafin ya ɗago suka yi ido huɗu tana ta faman cika da batsewa.

"Fauzah a..."

Fuu tayi gaba yayi saurin binta a baya, ɗakin da ta kwantar da Reina ta shige har zata rufo ƙofar yayi
saurin saka hannun shi ya tare.

"Fauzah mai kuma nayi?" Ya kwaɓe fuska Tare da sassauta murya.

"Au baka ma sani ba? Yanzu idan mahaifiyar ka aka yiwa haka zaka ji dadi?"

Hade rai yayi, "yaya kuma zaki dinga hada wata mata ta mahaifiyata?"

"Shikkenan kayi hakuri" ta sake kokarin rufe kofar, wannan karon da ya rike sai ya dan saka karfi ya tura,
bata da zabin da ya wuce ta sake mishi kofar ta koma bakin gado ta zauna yayin da shi kuma ya durkusa
a gaban ta tare da daura hannun shi bisa cinyar ta yana leka fuskar ta da take kokarin kawar wa daga
gare shi.

"Yanzu har goggo ta kai ta saka kiyi fushi da ni Fauzah? Nine fa! T dinki"

Da mamaki sai yaga idanun ta sun kawo ruwa, ya santa da saurin kuka amma a tunanin shi ba a kan
abinda be kai ya kawo ba kaman wannan.

"Fauziyyah?! Ya kira ta cikin tausasawa da mamaki.

"T da Allah bai zabe ka ya baka ba wani zai zo har ya roke ka ne?" Tace hawayen suna samun daman bin
kuncin ta.

"A kan wannan maganar kike kuka?"

"So kake Allah ya azabtar da mu a kan ya wadata mu domin mu taimaki yan uwan mu musulmai da
addinin Allah mun gagara yin hakan? Dan uwan ma na jinin ka T?"

Jan numfashi yayi ya furzar, yaki jinin bacin ran ta ko yaya ne, ko a kan menene.

"Shikkenan zan yi abun da suke so kin ji? Bar kukan"

"Toh amma kanwar mahaifiyar ka har sai na saka baki T? Suma fa suna da hakki a kan ka a matsayin ka
na wanda Allah ya hore wa. Kayi wa dangi na, kayi ma makwaftan mu, har kawaye na kayi musu Amma
sai abokin wasan ka ya gagara?"

Tana nufin abokin wasa cousin amma sai cewa yayi "Ni ban taba wasa da shi ba. Ina ma ya ganni balle
yayi wasa da ni?"
"Okay zancen Mama ya tabbata kenan"

Ya san idan yaci gaba da magana daure jijiyoyin jikin sa zaiyi da kan shi don haka yace "toh kiyi hakuri, ya
samu aiki an gama in sha Allah, ba dai aiki yake so ba? Zan sama masa aiki"

"Kuma tace matar shi ta haihu, zaka siya musu ragon suna"

"An gama, sai me kuma?"

Yace da murmushi a kan fuskar shi ganin yanda take faman kumbure kumburen baki.

Share hawayen ta tayi da bayan hannu gudun kada ta ƙure iyakar ta yasa tace "shikkenan, muje ka ci
abinci"

Lakatar fuskar ta yayi "sarauniya ta tasan inda ta gado kuka kuma idan tayi ace ta cika rikici."

"Hmm yau ba don goggon ba ma da ka san ba zaka zo ka same ta shiru haka ba"

A rikice yace, "Ina ba wani abun ta kawo kika karɓa kika bata ba?"

Ta girgiza kai "ko ɗaya, tsohon hannu kawai ta ji"

"Shikkenan, bari ma inga kyakkyawar fuskar ta duk na ƙagu, ba zan iya cin komai ban saka ta a idanu na
ba. Amma rikicin mummyn ta ya jawo min tsaiko"

Miƙewa tayi tana faɗin "ku kuka santa" ta fice don tabbatar da an tanadar mishi da duk abin buƙata
kafin ya fito."
.....

Daɗin ƙauye ba dai wadatar abinci ba, sai dai ace babu daɗi, musamman ma ƙauye irin Jama'are da Allah
yayi wa niimar ruwa, sarari da ƙasa mai albarka. gari ne da ake noma na bugawa a jarida musamman ma
na shinkafa, don haka mutanen da suka sauƙa yau a gidan Kamal tafe suke da buhuhunan su na abin da
Allah ya huwace musu, kama daga kan shinkafa, hatsi, wake, masara harma da busashshen kifi. suna
hutawa kuma suka shiga gyara da haɗe-haɗen abinda za'a dafa gobe suna, har su kayan miya an siyo,
mai, maggi, sugar da su markaɗe da aka kai sisin kamal bai yi ciwon kai ba.

Toh irin wa'innan mutanen ne zaka samu ka gagara yi musu alkhairi? bayan su basu duba rashin ka
matuƙar zaka sadar da zumuncin ka to nasu nasu ne kawai.

Sun haɗu tare da ƴan unguwa an bazama ana ta ayyuka domin so suke yi goben sai dai kawai ayi ta
ɗaurawa ana sauƙewa, aka fara bugun ƙofar dake a buɗe.

Hakan ya saka jikar danejo fita da gudu don korar yara da tuntuni suke wasa a tsakani, tana da tabbacin
su kaɗai ne marasa hankalin da zasu ga ƙofa a buɗe kuma su ƙwanƙwasa shi. Amma sai karo tayi da
ƙattin maza guda biyu.

"Nan ne gidan kamal baban Yaseer?" Na farkon da yake sanye da ƙananun kaya masu kyau yana tashin
ƙamshi ya tambaya. Bayan shi kuma mutumin tike ne riƙe da gabjejiyar rago. "Eh nan ne" ta bashi amsa.

"Yauwa kira mana shi"

Da toh ta amsa ta koma a guje.

A tsakar gida mahaifiyar ta ta tsare ta da masifa, "da na hana ƙannen ki guje-guje shine ke babbar banza
zaki taya su?"

"Inna wasu ne suka kawo ma Abban yaya Yaseer rago, ƙatoto wallahi mai babban ƙaho"
Jin haka yasa matan dake tsakar gidan barin abinda suke yi suka leka wajen don gaskata zancen ta duk
da sun ji kukan ragon amma anyi zaton na maƙwafta ne.

"Bayin Allah daga ina?" Amarya ta tambaya.

"Direban Alhaji Tahir ne ni, kuma ya aiko mu ne mu kawo ragon suna ma kamal wai"

A take matan suka sake guɗa ganin girman ragon, "ahh wannan jariri yayi goshi, Tahiru yayi abun kai"
aka shiga yaba ƙoƙarin shi, daman sun san tunda kamal ya dawo jikin su shikkenan kayan shi ya tsinke a
bakin kaba, zasu ɗauke masa nauyin komai.

Guɗar tasu ya jawo hankalin goggo ta fito tana gyara ɗaurin ɗankwalin kana ta tambayi ba'asi, baki ɗaya
zufa take da warin hayaƙi don yanzu ta gama fifitan itace a cikin rana ta samu ya kama mata sannan ta
daura tafashen kayan miyan da aka markaɗo.

Bayanin da ya musu shi ya nanata mata,

Bata ɓata lokaci ba tace "Toh ka maida mishi kayan shi kace ba'a so an gode" wato da ya gama mata
rashin kunya shine zai danne ta da wannan yanda gobe idan wani abun ya sake tashi ya samu na musu
gori ko?.

"Haba halime? Yaushe maida hannun kyauta baya ya dawo abun yi?" Danejo ta buƙata da mamakin
faɗin rai irin na talaka.

"Idan kyautar ba da zuciya ɗaya aka yi maka ba ƙwarai maida shi abun yi ne" ta ɗaga hannu ma drivern
tana ƙarawa da "ɗan jira ni ina zuwa" sannan ta kutsa tsakanin su ta shiga ciki tana jin ƙananun maganar
su na tashi.

Ɗakin da Saudat ke ciki ta shiga sannan ta ɗauko kwanon samira a cikin kwaba ta ciro purse ɗin ta daga
ciki.
Kuɗin ciki ta ƙirga Naira dubu ashirin da bakwai ne ya rage a cikin gudumawan da mutanen jama'are
suka yiwa mai jego, bayan ƴan saye sayen suna da suka yi. ta cire bakwai ɗin ta mayar cikin purse kana ta
maida samirar wurin da ta ɗauko shi sannan ta dunƙule Ashirin ɗin cikin tafin hannun ta, juyawar da zata
yi taga idanun Saudat a kan ta, kallon ta take yi amma ba kallon tuhuma ba, sai dai kallo irin na buƙatar
sanin mai yake faruwa kuma ba zata iya tambaya ba.

"Idan Kamalu ya shigo ki faɗa mishi na maida ma alhaji Tahir kuɗin shi"

Da "toh goggo" ta amsa sannan goggon ta fice, a wurin da ta bar driver ta dawo ta same shi, ta kamo
hannun shi cikin nata sannan ta dunƙula mishi kuɗin a cikin tafin hannun shi. "Gashi, daman na rasa
yanda zanyi in maida masa kayan sa don bani son komawa cikin gidan. Toh kace mishi ga kuɗin da ya
bawa Kamalu aro na dawo mishi da kayan shi"

Zaiyi magana tace "babu ruwan ka, bani son kaɗifiri, ba ɗan aika bane kai? Don haka yi abinda aka aike
ka kawai" da haka tayi komawar ta ciki don duba tumatirin ta, tana jin yanda suka fara tuhumar ta abin
da tayi bai dace ba amma ta share su, tana da tabbacin babu mai fahimtar ta a cikin su koda tayi musu
bayanin abinda take karewa. wato mutuncin ta da na zuri'ar ta.

Haka suka ja rago har bakin titi suka ɗaura a ƙurƙurar da suka zo da ita sannan suka koma gidan Alhaji
Tahir.

Driver ne ya shiga ciki ya danna doorbell sannan Aina'u ta buɗe ta bashi daman shigewa parlour ya jira
Hajiya.

Ba'a fi mintuna goma ba Hajiya Fauziyya ta fito riƙe da Reina wanda yanzu rikicin tan da sauƙi.

"Malam Adamu kun kai aikan?" Ta buƙata bayan sun gaisa.

"Wallahi Hajiya wata tsohuwa tace sai dai mu dawo da shi, kalaman da tayi ma basu da daɗin
maimaitawa, harda kuɗi ta bayar wai kuɗin da Alhaji ya bawa Kamalu aro ne ta dawo da shi"

"Innalillahi wa inna ilaihiraji'un, yanzu ina ragon?"

"Yana mota a waje"


"Shikkenan barin turo wani ku koma"

"Sun ƙi karɓa fa Hajiya, harda maganar banza"

"Za'a basu haƙuri, har su karɓa in sha Allah".

Ta miƙe ta koma ƙaramin parlourn ta na ƙasa yanda ƴan uwan ta mata ke baje suna kallo, baki ɗayan su
yau suka zo mata wuni.

Tana shiga autar su Sajida ta karɓi Reina daman saboda za'a bada nono ta bada ita. "Yaya Aina don Allah
ki min wani taimako mana" nan ta zayyane mata halin da ake ciki.

"Dan Allah kada ku bar gidan sai sun haƙura sun karɓa, kice na ce idan suka sake juyo da ku zan fito in
kawo musu da kaina"

Taɓe baki Zeenat tayi tace "kema dai shiga ukun ki yana niman yafi ƙarfin ki, tunda sun ce basu so ba
shikkenan ba? Ko ana kyauta dole?"

"Ana yi mana, tun da muma anyi mana kuma mun karɓa"

Sake taɓe bakin tayi ta maida hankalin ta kan tv don bata da cewa.

Kafin Aina ta mayar da ɗankwali da gyalen ta Fauziyya ta shiga ɗaki ta fito hannun ta riƙe da bundle ɗin
sabbin naira dubu-dubu da babban laidar Diapers, wipes, sai set na kayan shafan yara ta bata. "Kice ga
nawa gudumawar don Allah suyi haƙuri su karɓa kuma ina basu haƙuri da abinda ya faru, ki danne mun
su yaya Aina"

"Toh Amma kuɗin nan baiyi yawa ba fauzee? Ina laifin dubu hamsin? Koma Ashirin tunda ga niƙi-niƙin
kaya?"
Murmushi Hajiya Fauziyya tayi tace "da na baki kaman haka na siyan jaka da takalmi ai da kin bani canji
tunda na san akwai sosai ma".

Kama bakin ta tayi ta miƙe haɗe da rataye jaka sannan tayi musu sallama ta fice.

Firr Aina tace ba zata shiga ƙurƙura ba don haka suka ɗauki motar Hajiya Fauziyya motar rago na biye da
su har unguwar su kamal. Da sallamar ta ta shiga gidan da ake ta faman hada-hada ta samu Huwaila da
amarya suka bata hankalin su.

"Don Allah mai jego nake nima"

Suka yi mata iso cikin uwar ɗakin Saudat aka bata bakin gado ta zauna sannan suma suka nemi wuri suka
zauna a maimakon su basu wuri sannan aka shiga gaisuwa.

"Amma ban wayi fuskar ba" Saudat tace cikin jin nauyi.

"Allah sarki. Yayar Fauziyya ce ni"

"Fauziyya Fauziyya?" Saudat tace tana son ɗago sunan.

"Hajiya Fauziyya matar Alhaji Tahir dai"

"Ayyah Aunty ba? Tana lafiya? Yaya jaririya?" Ita ba zata ma iya tuna inkiyar Reina ba, kuma tasan sunan
wata mai muhimmanci aka mayar mata balle tace Hafusatun.

"Suna nan Lafiya alhamdulillah. Daman shine ma suka turo ni bin sawu da bada haƙuri"

"Ni babu wanda yayi min komai Wallahi, daman goggo ne da abban su, bari a kira miki goggon kada mu
ari bakin ta aci mata albasa"
Huwaila da kanta ta fita kiran goggo kuma tun daga wajen ta fara mata bayanin abinda yake faruwa don
haka fuska a tamke ta shigo ɗakin ta zauna Aina ta gaida ta.

"Daga ina baiwar Allah?" Goggo ta sake tambaya don bata damar maimaita ƙudirin ta.

"Ƴar uwar Fauziyya ce ni matar Alhaji Tahir, saƙon ban haƙuri ta turo ni da shi Mama, don Allah kuyi
haƙuri kada ku maida hannun kyauta baya"

"Kuna ta zancen maida hannun kyauta, shin kun duba kyan shi hannun da ya miƙo kyautar? Kun duba
fuskar da ya bayar da ita?"

"Sai an san anyi wa mutum ba daidai ba ake bashi haƙuri mama, don haka anyi miki laifi amma kiyi
haƙuri, tace kuyi haƙuri da abinda ya faru " sannan ta luma hannu cikin jakar ta zaro bundle ɗin da ta
zare dubu goma a ciki tun a hanya ta miƙa mata "dan Allah ki karɓa goggo ba don halin mu ba, tace idan
baki karɓa ba da kanta zata fito ta kawo miki"

"Lalala raba ni da fito da mai ɗanyen jego haka kawai, kuma ma ita Fauziyya ai ko dan halinta tace in
karɓa zan karɓa amma ko Kamalu uban Tahir bai isa ya wulaƙanta ni ba balle shi ɗan ciki na, shi Tahir ɗin
ya san da haka"

"Kina da gaskiya Wallahi Mama, kuma shima ya gane kuskuren shi ya bada haƙuri, sunce ma ko kwana
zanyi a gidan nan idan baki karɓa ba kada in dawo, to ga ƴan marayu kuma a gidan suna zaman jira kada
a ɗauki hakkin su."

Hannu goggo ta saka ta karɓi kuɗin tana faɗin "toh shikkenan", na haƙura na karɓa zaki iya tafiya.

Godiya tayi ta miƙe tana faɗin "toh bari a shigo da sauran"

"A'a harda wasu saura?" Amarya ta washe baki jin zancen arziƙi.
"Eh akwai rago da kuma kaya a mota, zamu je da yara su ɗauko.

"Ai bama sai anje da yara ba muje in taya ki ƴar nan"

Suka fita suka bada izinin a shigo da ragon a ɗaure shi a cunkusasshen tsakar gidan sannan Aina ta miƙa
ma huwaila laidar pampers da wipes kayan shafar kuwa ta ɓoye su a ƙasan seat.

"Wannan ƙunzugu ai sai a shekara ma yaron bai gama sakawa ba" ta ɗaura da guɗa sannan ta shiga
gidan tana shelar abinda aka kawo din harda kudin.

"Yaro ya samu jibgegegen rago, ƙunzugun shekara da ɗori, abin goge kashi har pakiti biyu da kuma
gudmawar kudi Naira na dukan naira har dubu Ɗari, daga uban shi Alhaji Tahiru da Uwar gidan shi Hajiya
Fauziyya. Don Allah ku taya ni bani da hanci"

Kowa ta kame hanci suka ɗauki kuwwar "Ayyiririiii...."

......

*Wattpad users Please a taimaki Seemahwrites ta cika followers dubu guda🙈 ina godiya wa duk wacce ta
ɗauki lokacin ta wajen danna follow button💗*

*Masu karatun English Novels albishirin ku😂Ayyiririiii ba guɗan haihuwa bane😂 Recent English novel ɗina
mai taken THE BLEEDING ROSE 🌹 ya samu kammaluwa an haɗe shi document full in full kuma zaku same
shi a kan Naira 500 kacal. Ga masu son ɗanɗano ku duba profile ɗina na wattpad zaku sami free pages.
Ina faɗa muku labarin akwai tsayawa a rai, sai wanda ya karanta yaji✨. Ga mai buƙata ya tuntuɓe ni a
wannan lambar 08021689184.*
*REINA 💍*

10.... Har driver sun ɗauki hanya ya tuna bai bada dubu Ashirin ɗin da goggo ta bashi ya maidawa Alhaji
Tahir ba. kaman zai riƙe yayi tafiyar shi tunda sun kawo musu abin da ya ninninka hakan sai yayi tunanin
Idan shi bai ƙara ma mutanen da suke rayuwa cikin irin wannan unguwan ba a kufayin gida toh bai
kamata ya rage su ba, sa'annan ko ba daɗe ko ba jima zance zai iya dawowa kunnen Hajiya Fauziyya ko
Alhaji Tahir.

Parking yayi ya zuge window sannan da hannu yayi alamu ma mai ƙurƙura da ya tafi kawai, kana ya juya
kan motar suka koma hanyar da suka baro.

"Lafiya Malam Adamu? Ina kuma zamu je?" Aina ta tambaya.

"Kiyi haƙuri nayi mantuwa ne, akwai kuɗin da tsohuwar ta bayar in maida wa alhaji shine hajiya tace in
dawo mata dashi." Yayi mata bayani yana ƙara gudun motar don suyi sauri ya samu komawa kafin Alhaji
Tahir ya dawo ya samu bayi nan on standby.

"Har Nawa ne kuɗin haka?"

"Dubu ashirin ne?"

"Shine zamu koma a kan dubu Ashirin bayan mun kai musu kaman shi sau biyar? Ka riƙe kawai mana ko
kuma ka raba mana mu koma muce mun kai"
Kallon ta yayi a kaikaice harma ya manta da tuƙi yake, sai a lokacin idanun shi ya kai kan saiti na kayan
wanka da shafa na yara dake boye a kasan seat ɗin shi. Murmushi ne ya ƙwace mishi yace "baki tunanin
asirin ki zai tonu idan baki basu abin nan ba?"

"Toh wa yace maka nasu ne?"

Dariyan kinma raina min hankali yayi yace "tunda haka kika ce shikkenan"

Da suka isa gidan ma ita ya bada kuɗin don ta shiga ta bawa goggo hannu da hannu. "Sauran kuma ki zari
wani abu a ciki, ta riga da ta san nawa ne, don ita ta ƙirga ta bani"

Baki ɗaya sai Aina taji ta muzanta, tunda har ya buɗe baki yake gaya mata magana haka bayan da
gaisuwar arziƙi ne kawai a tsakanin su ta tabbatar ta gama zubar da mutuncin ta a idanun shi. Saima ta
fara tunanin kodai ta haɗa da kayan shafar ne ta kai musu? Amma daga ganin packing ɗin ta san ba mai
arha bane, kuma komai akwai a ciki harda soson shafa powder na yara da su soson wanka. Idan siyarwa
zata yi zata samu abin da yafi dubu 50 wa'innan mutanen kuma ba sanin darajar kaya mai tsada suka yi
ba.

Babu ɓata lokaci ta shiga ta maida kuɗin ta fito, a ɗarare haka ta shiga motar suka tafi.

.....

Su goggo sun gama shiryawa tsaff da gari ya gama wayewa zasu wuce tasha su kama motar Jama'are.

Dunƙulawa amarya kuɗin Saudat ta sake yi bayan ta maido mata da shi, idanun ta da maiƙon hawayen
kewa tace. "Amarya don Allah ki karɓa ku rage kuɗin mota"

"Ke da'alla, ance miki don ki bamu kuɗin mota muka zo? Da ace bamu da kuɗin mota kinsan ba zaki ga
ƙafar mu ba don haka riƙe kayan ki" ta miƙe ta bar mata kuɗin a wurin sannan ta ci gaba da shirya jikokin
ta.
"Toh Saudatu, zamu koma inda muka fito, Zamu tafi mu barki da haƙurin ki. kina dashi amma ki ƙara,
kina ƙokarin tarbiyya ma yaran ki don mun shaida a kan Yaseer amma ki ƙara sannan kuma ki ƙara
addu'a sosai da sosai, duk macen da ta fara tara zuri'a cikakken bacci a ko wani dare ba nata bane, dole
kina raba wasu dararen kina kai kukan ki ma Allah idan kina son kiga daidai a rayuwar yaran ki"

goggo ta miƙo mata kuɗin da suka haɗa wanda ya tashi dubu sha shida sai kuma dubu cassa'in da Aina ta
kawo, ya tashi dubu ɗari da shida kenan.

Ta samu zannuwa ma wurin guda takwas duk da rabin su rubber ne ko mix cotton Amma goggo da
amarya da wani kawun su mai gold suka saka mata manya har biyu. Haka ma jariri ya samu kaya daidai
gwargwado ga kuma sauran kayan abinci da ya rage an jibge musu a ɗakin su Yaseer, lallai wannan
haihuwa yazo musu da alkhairi.

"Kina samun kanki ki ci gaba da ƴan sana'oin ki, ban yarda ki bawa Kamalu kuɗin nan ba kiyi jari dashi
kinji na faɗa miki."

Karɓan kuɗin tayi da godiya tana jujjuya shi a hannun ta, gani take yi sunyi mata yawa idan har aka ce ba
zata bashi ba, zata iya sana'a koda babu jari don har wankin kuɗi tayi nauyin ciki yasa ta bari. Amma shi
idan ta bashi kudin nan ko teburi zai kafa yana kasa wani abun idan ya dawo daga aiki, Yaseer kam tela
take so ya zama amma da ko shima zai iya taya shi idan ya dawo daga makaranta.

Shima kamal saida yasha tashi nasihar da bata gajiya da mishi a ko wani lokaci kafin ya raka su har tasha
har saida motar su ta tashi kafin ya dawo. Ya samu har Yaseer ya gama komai kaman yanda ya saba shi
da suhail sun wuce makaranta.

Zama yayi a gefen Saudat yana cire taɓani kasha hadisin dake kan shi, "Saudatu goggo ta tafi. Satin ta
guda a cikin gidan nan"

"Wallahi kuwa, bamu da abinda zamu ce sai Allah ya ƙara tsawon rai da albarkan rayuwa."
Ɗaura zancen shi yayi domin ta fahimci abinda ke ranshi. "A wannan sati gudan babu wanda ya leƙo ko
ya turo kai ko Ita su turo direba ya kai musu ita su gaisa idan gidan nawa ne ba zasu iya zuwa ba."

Zata iya rantsuwa wannan ne karo na farko da taji ya koka da su a kan duk wani abun da zasu yi mishi
kuwa, saboda a yanzu mahaifiyar shi suka taɓo.

Yaci gaba da cewa "kuma dukkan su babu wanda banje har ƙofar gida na shaida masa zancen haihuwar
ki ba har matan, da kuma zuwan goggon a karo na farko cikin shekaru 4. Bayan Alhaji Tahir ɗin da muka
samu matar shi babu mai tunanin ko aika ko saƙon gaisuwa."

Ba na gaya maka ba! Shine kalamin dake cikin ranta amma sai cewa tayi, " sai haƙuri, daman haka duniya
take, ba kowa zaka so da zuciya ɗaya shima ya so ka haka ba"

"Hmm, babu komai, Allah ya bamu ladan soyayyar da muka yi musu saboda Allah " da ameen ta amsa ya
miƙe shima ya shirya ya wuce wurin aiki aka bar Saudat a gidan daga ita sai baby suka sha barcin su
tunda ga wutan nepa kuma mai sawa a kashe fankan yanzu bata nan.

......

Da lokacin da kake ƙirga shi da wanda baka bashi hankalin ka ba wanne yafi saurin wucewa ne? Don tun
jiya Hajiya Fauziyya ke mamakin wai har kwanan abinda ta haifa 40 a duniya.

Kuma tun jiyan suke ta tiƙi-taƙa da Alhaji Tahir a kan yawon Arba'in. A karo na farko da zubar da
hawayen ta bai saka ya canza ra'ayin shi ba, ya mata iyaka kuma ya kafu a kan zancen shi, A dalilin Ƴar
shi Hafsatu Reina.

Ya jaddada mata yawan gidajen da ya amince taje daga fannin ƴan uwan ta, da wanda bai yarda ko
unguwar ta leƙa ba. Sannan su wanda ya amincewa ya bata adadin lokacin da zata ɗauka a can ɗin ciki
harda gidan nata iyayen kuwa. Maganan dubo ƴan uwa dake ƙauye kanma bata samu zarafin fara mishi
ita ba.
Ɓangaren da bai kafa mata sharuɗa ba kawai shine bangaren gidajen ƴan uwan shi, saboda matakin da
suke na rayuwa yazo ɗaya hakama tsarin su.

Taso ta fasa zuwan baki daya amma sai taga shi zaifi son hakan ma, kuma ita ce da asara. Haka ta shirya
ranan ta fita suka fara zagawa da driver yana zaman jiran ta a waje, da lokacin da Alhaji Tahir ya bata
kuwa ya cika haka zaiyi ta horn har sai ta fito, wasu gidajen ko ruwa bata samu ta saka a bakin ta. Kuma
haka zaiyi ta addaban ta da kira yana tambayar ta yaya lafiyar Reina idan bata ɗauka ba shima ba zai fasa
kiran ba har sai ta ɗauka.

Ƙarshe da abin ya ishe ta wajen gidaje 2 haka ta haƙura da zuwa tace driver ya kaita gidan su kawai tun
kafin la'asar ma tayi.

....

"Matar Alhaji yaya aka yi?" Mahaifiyarta ta tsokane ta cikin jin daɗin yanda ƴar tata ta murje ta canza a
cikin shekaru biyu, ga cikowar jego ya ƙara mata kyau, ba zaka ce Fauziyya ƙashi da rai bace kamar yanda
ƴan unguwa suka saka mata tsabar rama Saboda rashin cin abinci gata kuma tana da ɗan tsayi shiyasa
ramar yake nunawa sosai (kamar ƙawata Zahra😹)

"Ummi na kusa kamuwa da postpartum depression" tace tare da sauƙe ajiyar zuciya ganin wani kiran na
Alhaji Tahir na sake shigowa cikin wayar ta.

Rejecting kiran tayi cikin jin haushi, duka-duka ko minti talatin bata yi da shigowa ba, kuma tazo ta samu
umman da kanta a kitchen saboda shirin zuwan nasu, sai yanzu ta samu kanta aka zauna za'a gaisa.

"Subhanallahi, depression kuma? Me zai saka miki depression Fauziyya baki rasa komai ba, ko Tahir ɗin
ya daina kula da ke ne?"

Girgiza kai tayi ta saka yatsar ta manuniya ta ɗan zunguri goshin Reina tace "takwarar ki ne take son
shiga tsakanin mu" bata bawa Fauziyya kunya ba ta ɓare baki kaman yanda tayi tsammani kafin tace "kin
gani Ummi, gaba ɗaya ta rikita ni ta rikita shi, Idan kika jini da shi to a kanta ne, ni kawai zan bar miki ita
a nan in koma ni kaɗai idan ta gyara hali sai in dawo in ɗauke ta"
Dariya Ummi tayi kana ta karbi Reina daga hannun Fauziyyar, ta tabbatar tana iya kokarin ta. Daman
Bata da son yara bata da hayaniya, ga ƙananun shekaru, ba don matsawar Alhaji Tahir ba da sai a yanzu
da ta haura Ashirin da biyu zasu yi mata aure lokacin ta gama karatun ta amma ba haka Allah ya tsara
mata ba.

"Idan bata gyara halin ba fa? Sai ki ci gaba da barin ta a nan? Mahaifin ta zai yarda?"

Wani kiran ne ya sake shigowa wayar ta bayan saƙon da saida kiran ya shigo ta lura da shi.

'kada ki kashe min waya Fauzah, ki dawo da Reina gida kafin wani ciwon ya kama ta, kinga jaririya ce
bata da ƙwari'

Taɓe baki tayi da gadara ta sake rejecting kiran ta saka shi a Do not disturb kafin ta maida hankalin ta
wurin Aina da ta shigo da abincin da Ummin ta bar mata ta ƙarasa.

"Yaya Aina irin wannan ai sai yunwa ya kashe mutum" tace lokacin da ta dire tray ɗin a gaban ta.

"Wani ya hana ki cin abinci a gidan ki kafin ki fito? Abinci ma sai kalar da kika zaɓa?"

"Ni da zanci girkin Ummi kuma sai inci wani abun daban? Da yunwa na nazo na musamman don nayi
kewar girkin Ummi na"

"Tuwo ne dai gashi nan miyan yauƙi ummin naki tayi" ta shiga zubawa Fauziyyan saboda tana son tatsar
ta kafin ta tafi.

"Ina wa'innan ƴan cika kunnen suke?" Yaran Aina take nufi, su uku ne kuma kowa da uban shi, ɗaya a
cikin su mutuwa yayi amma sauran biyun rabuwa suka yi kuma ta hana iyayen maza karɓan su gwamma
ita tayi ta faɗi tashin yanda za'ayi, gwamma ma yanzu da Alhaji Tahir yake tallafa musu.
Bata yi rabi da cin tuwon ba sai sallamar Alhaji Tahir ɗin suka ji a ƙofar falon Ummi. Da farko ta ɗauka
kunnen ta ne don haka ta share ta ci gaba da kai loma abinta don yanzu haihuwa ta buɗa cikin.

"Ba nace kada ki kashe min waya ba?" Yace cikin ƙasa da murya yana zama a gefen ta.

Ɗagowa tayi da lomar da bata kai ga taunawa ba ƙunshe a baki ta zuba mishi ido cike da mamaki.

*Saliha Ahmad Na'ibi ✨*

```The Bleeding Rose 🌹 sneak peak```

_So now aside from the constant war between the North and the west kingdom there is a constant War
between me and the queen and I'm not sure if it's stopping without any of us finishing another._

_If I take you with me you will also get involved in that war._

_So I want you to decide if you're going to continue staying here with my sister or if you are coming with
me to the hellish Kingdom._
_However Farah, I won't promise to give you peace, I won't promise to give you love, I don't have any of
it. but I promise I'll put my life on line to protect you, as long as you will serve and protect my mother. If
you want this whole world I'll make sure to get it and place it at your feet, and no matter what will
happen wether you're right or wrong I promise to be by your side._

_This is a promise I will never break. This is a promise from Namir to Farah. And this is a promise from a
Husband to his wife."_

_By this time Gulping is all i can do. I feel like a shrimp comparing my struggle to giant sharks in the
ocean. Whichever path Master Namir decides to follow the consequences will not only be for him but
the millions citizens of North._

_"So you decide by tomorrow if you still want to go with me put off that lantern by your right side. And if
you don't, I'll understand and leave after 10 seconds" he stood up._

_"I leave you in peace"_

*REINA 💍*

https://chat.whatsapp.com/JjjCOoAVsdP4PZbmCDrUOh
11....... Muƙut! Fauziyya ta haɗiye lomar tuwon bakin ta ba tare da ta tauna ba, idanun ta basu bar kan
Alhaji Tahir ta ba, tana son tabbatar da kasancewar shi a wurin a daidai lokacin.

"Ina Reina?" Ya tambaya tare da yatsina fuska ganin kalar miyan da yake gaban ta, wanda yake da
tabbacin ko da kuɗi aka bashi ba zai ci ba.

Saida Fauziyya ta haɗiyi miyau kafin ta iya cewa "Tana hannun Ummi a ciki" ta nuna hanyar ɗaki da
hannun da ta saka a cikin miyar dan ta gwagwuyi ƙashi da kyau.

Miƙewa taga yayi tayi saurin tsare shi da "ina zaka je T?"

Juyowa yayi yana kallon ta sama da ƙasa, baki ɗaya ta yamutse bubun shaddar dake jikin ta, ga stain ɗin
miya da aka goge daga wuyar rigan. fuskar ta duk tayi maiƙon yawo a rana domin da yake tambayar
driver yanda ziyarar tasu yake kasancewa ya shaida masa cewa idan suka je gidajen da suke makwaftaka
da juna ko kuma tazarar su babu nisa sai tace mishi ya jira ta taje da ƙafa ta dawo sai su ƙara gaba.

Kawar da wannan yayi a cikin ranshi tunda na yau ne kawai, amma kuma ta azabtar mishi da ƴa.

"Karɓo ta zanyi!" Ya juya da nufin ci gaba da tafiya ta miƙe da sauri tare da saka hannu bibbiyu ta riƙo
shi.

"Ka rufa min asiri dan Allah, barci tayi aka kwantar da ita"

Yayi saurin ƙwace hannun shi amma ta riga ta shafa mishi miyar dama-dama.

Ya zaro napkin daga cikin aljihun jamfar shi ya shiga gogewa amma warin yajin daddawar har tsakar
kanshi yake ji. Bai iya maida napkin ɗin aljihun shi ba ya ajiye mata a wurin.

Saida ya shinshina hannun yaji warin ya ɗan ragu saboda turaren dake jikin napkin ɗin kafin yace "A
wannan zafin har zata iya barci mai daɗi Fauzah?" har wani fuskar tausayi taga ya yi.

"Akwai AC a ɗakin, kada kasa muji kunya Please"


Da mamaki yace "Duba lafiyar ɗiya ta shine abin kunya? Gidan ku ba gidan mu bane?"

"Gidan ku ne Amma Ummi surukar ka ce. Kayi haƙuri in wanke hannu in ɗauko maka ita."

Yaji daɗin hakan domin ya kawo mata ƙarshen cin tuwon don haka ya samu wuri a saman kujera mai
zaman mutum uku ya hakimce. Hannun shi na dama ya miƙe a saman kan kujerar sannan yayi crossing
legs ɗin shi yana jijjigawa a hankali cike da ƙasaita.

Hayaniyar yara suka fara jiyowa kafin suka shigo cikin ɗakin da gudu Aina na biye da su. "Toh Fauzee ga
yaran naki da kike nima da boxing ɗin su suka shigo"

Idanun ta ne suka sauƙa a kan Alhaji Tahir bayan ƙamshin shi da ya cika ɗakin ya fara shiga cikin hancin
ta. Shan jinin jikinta ta fara yi kafin ta kame kanta tsamm ta ƙarasa wurin da yake zaune ta zuba a ƙasa
tana ɗiban gaisuwa.

"Lafiya Auntyn mu" ya amsa idanun shi na kan yaran da suka shigo da uniform ɗin boko suka zube a jikin
Fauzar shi. Shikkenan za'a ƙarasa ɓata mata kayan! Yace a ranshi. Ita kuwa tana ta faman murmushi don
tayi kewar su harda hayaniyar sun ma sosai.

"Toh kuje ku sauya kaya sai kuzo ku karɓi tsaraba" tace, da gudu kuwa suka miƙe suna rige-rige suka yi
ciki.

Ganin Fauziyya na shirin miƙewa tare da tray ɗin abincin yasa Aina saurin tashi daga gaban Alhaji Tahir ta
tare ta. "Haba dai mai jego, ki bari a fitar miki da kwanukan kaman yanda aka shigo miki da su mana"
tace tana satar kallon Alhaji Tahir ɗin don taga yanayin shi.

Murmushi Fauziyya tayi son ƴar uwar tata na daɗa shiga ranta. Tabbas suna yawan rikici a baya duk da
akwai Yayan ta namiji da Yaya Zeenat a tsakanin su, kuma yawanci Ainar ce take janyo wa Saboda bata
kama girman ta gata da shiga abinda bai shafe ta ba. Sai kuma adawa da Fauziyya take yi da ita a kan
yawon gidajen aure, wanda kusan kowanne ita ke jawo mutuwar su.
Amma tunda tayi aure komai ya sauya, daman ance idan ƴan uwan da suke da ƴar tsama a tsakanin su
suka yi nesa da juna shaƙuwa takan shige su sosai.

Babu musu ta mika mata tray ɗin tare da faɗin "toh muje sai in wanke hannu na"

"hannun ma bari a kawo miki ruwa da Rubber ki wanke, kisha zaman ki kawai ƴar ƙanwata"

Saida ta dara tace "A'a barshi kawai muje, zan ɗauko Reina a bata magani ne kada mu ɓata mishi lokaci"
tayi ƙarya don danne ko wani irin tunani da zai iya ziyartar zuciyoyin su a kan dalilin zuwan Alhaji Tahir
din a wannan lokaci.

Suna fita Ummi na fitowa daga ciki.

"A'a Tahir, sannu da zuwa" tace murmushi shimfiɗe a saman fuskar ta.

Sauƙe hannu da ƙafar shi yayi tare da ɗan zamewa ya gaidata, don baki ɗaya cika masa idanu take yi.

"Ka biyo sawun mai sunar ne ko?" Tace tana son harbo jirgin shi.

Sosa ƙeya yayi a kunyace tare da faɗin "A'a Wallahi, daman Asibiti zamu kaita toh daa nace a bari sai
gobe saboda ina da baƙi a office amma mun kammala meeting ɗin da wuri ma"

Jinjina kai Ummi tayi don babu wanda zai ji wannan dogon sharhi ya ƙaryata, duk da ita Fauziyyar bata
faɗa mata wani magana makamancin haka ba.

"Gaskiya ne, kuma zuwa a kan lokacin shi yafi. Toh bari ta zo ku tafi amma kafin nan ka tsaya kaci tuwo
mana"
Da sauri ya shiga girgiza kai tare da hannu. "A'a wallahi Ummi a ƙoshe nake alhamdulillahi"

"Ko dai baka cin tuwo Tahir?"

Dariyar ƙarfin yake ya saka yana faɗin "A'a wallahi Ummi cikakken bahaushe ne ni fah! ina ci, na ƙoshi ne
kawai sai wani jiƙon in sha Allah" yana cin tuwo don tuwo, kalar miyan ne dai bayi ci.

Ita kuwa ummi murmushi kawai tayi tana tuna Alhaji Tahir ɗin a wani lokaci da ya shuɗe, a lokacin da
yake da buri guda ɗaya kacal, tana da tabbacin a wannan lokacin koda kwatar ƙofar gidan su aka ce ya
sha idan zai samu cikar wannan burin to tabbas zai sha, amma yau taga ƙyanƙyamin abincin su a kan
fuskar shi.

Kafin Fauziyyar ma ta dawo taje ta ɗauko mishi Reina da kanta kuma babu kunya ya saka hannu ya karɓe
ta.

Ta shigo tana tsantsame hannu sai karo tayi dashi yana jijjiga Reina da ta tashi yanzu a tsakar ɗaki ga
Ummi a zaune ta zuba musu idanu. Kunya ne ta kama Fauziyya kamar mene duk da tasan Ummi bata da
matsala samm amma zaƙewar na Tahir yayi yawa.

Saurin ƙarasawa tayi ta karɓe ta cikin ƙasa da murya yanda shi kaɗai zai ji tace "tunda ka ganta dan Allah
kaje zamu dawo anjima"

"Toh asibitin fah?" Yace cikin buɗaɗiyar murya yanda Ummi zata ji ta saka baki.

Kallon shi tayi don ita bata san da zancen wani zuwa asibiti ba, kenan ɗaurawa yayi a kan ƙaryar da ta
fara? Itama maganin ta.

"Toh ai baba bai dawo mun gaisa ba, baiga jaririyar ba ma" tace tana rau-rau da idanu.
"Gobe da saurin zuwa yake Fauziyya. Zai ganta wani lokacin Amma lafiya ita ce uwar jiki don haka kada
kiji komai ku tafi kawai zan miƙa masa saƙon gaisuwar ki".

Ummin ma ta miƙe alamun Rakiya kenan zata yi musu.

Da kanshi Alhaji Tahir ya ɗauka gyalen ta ya yafa mata Aina kuma ta ɗauka mata jaka itama tana
mamakin wannan sabon salo.

Kallon Ummin tayi na sakanni Biyar ita kuma taƙi yarda ma su haɗa ido har suka gama sallama da Alhaji
Tahir ya ajiye musu irin alkhairin da ya saba sannan yaja hannun Fauziyya suka fita bayan ya karbi Reina
daga hannun ta ganin bata da niyyar motsawa.

Bayan sun fita Aina tayi dariya tace "kai Ummi, kora da hali fa kika musu"

Ko a jikin ta tace "toh ina zan iya da wannan mara kunyar? Gwamma ita da ta saba taje can su ƙarata
abun su"

"Ai gashi daga gani shagwaɓaɓɓiyar kuka zata yi masa"

"Ke! Su suka ji wurin" ta ɗauki kuɗin ta miƙe zata shige ciki Aina tayi saurin bin bayan ta.

....

Buɗe mata bayan motar da yazo dashi yayi ta shiga sannan shima ya zaga driver ya buɗe mishi ɗaya
bangaren ya shige da Reina a kafaɗar shi. Suka ɗauki hanya motar da ya kawo ta kuma na biye da su.

Wasa yake yi ma ƴarshi hankali a kwance ita kuwa ta sai murmushi dake ƙara narkar mishi da zuciya take
yi.
"Fauzah kiga hancin yarinyar nan ya fara taso..." Maganar shi ta katse ganin hawaye sharr sharr a kan
fuskar ta.

"Fauzah?! Me aka yi miki kuma yanzu dan Allah?"

Kaman tambayar shin take jira ta saki kukan da iya ƙarfin ta tare da haɗe kai da guiwa.

"Na shiga uku" yace yana ɗaura hannu a saman kafaɗar ta da niyyar ɗago ta.

Ture hannun tayi kafin ta ci gaba da kukan, sai ya rasa ta ina ma zai fara lallashin ta ga Reina a hannu.

"Fauzah I'm sorry. Ban san me nayi miki ba amma I'm sorry kinji?"

A zafafe ta ɗago tana watsa mishi harara "baka san me kayi ba? Kace baka san me kayi ba T? Fisabillilahi
wannan dacewa ne? Awa nawa zanyi a gidan baki ɗaya? Kace in dawo da ƙarfe takwas na ji na amince,
amma ba zaka barni in gana da mahaifi na da ƴan uwana cikin aminci ba? Bayan yaya Zeenat yaya Aina
kawai na samu gani, kada ka manta ba ni kaɗai ka ganni ka ɗauko a cikin gidan ba" taci gaba da kukan ta
mai gunji Reina kuwa ta zuba mata idanu.

"Harara ta kike yi Fauzah?"

Takaici ya kama ta ganin kaman bai ma ji abinda tace ba baki ɗaya. A hasale tace "Idona ne a haka!"

.....

"Yaro bayi da wayo"


Da gudu Suhail ya dawo jikin Yaseer dake dariya a gaban bokitin da yake wankin uniform ɗinsu ya kuwa
ralla mishi cizo a gadon baya har saida yaseer din ya wani gantsare, sannan kafin ya kai mishi hannu har
ya gudu wurin Saudat ya ɓuya a bayan ta yana leƙowa yana mishi gwalo.

Sosa wurin yayi don yaji zafi "yace ai gobe akwai boko zanga mai baka kuɗin tara"

"Umma tace zata bani" yace yana daɗa mishi gwalo.

Kwafa Yaseer ɗin yayi ya cigaba da wankin "ba Lallai sai gobe ba, zaka zo kace in siya maka wani abu ni
kuwa sai na rama cizo na tunda da daɗi ai"

Saudat ne ta ture Suhail ɗin daga jikin babyn da ya koma sakawa yatsa a baki, shikuwa yaji ɗanɗanon
gishirin datti ya kama ya fara tsotsa.

"Wallahi zan buge ka babana, baka jin magana ko? Kafi son sai na tara maka gajiya a cikin gidan nan?"

"Umma to ki ban kuɗi in garin buɗiɗis kuka"

Saida tayi masa danƙwale tace "ka ɓace min daga gani ko sai na tashi na riƙo ka? Fitinanne kawai
kwaɗayayye"

Har ya manta da cizon da yayi wa yaseer don haka ya koma jikin shi yana muryar tausayi "Yaya garin
buɗiɗis dan Allah."

Yaseer bai ce komai ba saida ya bari ya ƙaraso jikin shi kafin ya riƙo shi. "Wa na kama?!" Yace yana
dariyan mugunta.

"Yaya sorry, dan Allah" ya fara ƙoƙarin kwacewa ya gudu don haka Yaseer ɗin ya miƙe yana faɗin "toh da
wa yace ka yarda kudin aika idan dai kana da wayo? Shine zaka cije ni, kuma ka san an hana ka cizo?!"
"Yaya pleash, ba zan sake ba wallahi na bari"

"Ai nace sai na rama" ya sunkuya ya daidaici kunnen shi ya saka a tsakanin hakwaran shi ya ɗan danna
kaɗan amma ihun da Suhail ya ƙwala zaka ce rai aka zare mishi.

"Wayyooo na shiga uku. Ya kashe ni Umma" ya fara kuka harda birgima a ƙasa.

"Me yasa kuke da wasan banza ne?"

Murmushi Yaseer yayi don yasan baiyi mishi komai ba.

"Da girman ka kake biye mishi Yaseer"

Hannu ya miƙa ma Suhail ɗin yana fadin "tashi muje a siyo garin buɗiɗis da tsami gaye ma" ai da sauri ya
miƙe yana share hawaye. "Muje"

Dariya Yaseer yayi "toh bari in ƙarasa wankin nan sai muje, ka shiga ka ɗibo min na baby ma a kan gado "
da gudu Suhail ya ruga ɗakin iyayen su lokacin da Kamal yayi sallama a gidan.

Ɗauraye hannun shi Yaseer yayi sannan ya miƙe ya tare shi tare da karɓan laidar hannun shi ya shigar
ɗaki. Koma menene idan ummar su ta gani zata tantance me za'a yi dashi.

"Sannu da dawowa" tace tana gyara mishi zaman kujeran tsugunon dake gefen ta. Saida ya ƙarasa ya
ɗauki baby da barci ya fara ɗaukan shi kafin ya zauna yana kallon fuskar shi.

"Shikkenan gobe yaro zaije yaga Jama'are" yace hankalin shi na kan jaririn amma da Saudat yake yi.
"Ai babana ma naso mu tafi tare amma bani son yayi fashin makaranta ko kuma ya saka mu dawowar
wuri"

"Ki barshi kawai yayan shi zai kula da shi in sha Allah. Kuma nima zan saka musu idanu, kije ki huta ki
murmure kafin ki dawo"

"Nayi kewar gida wallahi" tace tana jin ɗokin tafiyar na daɗa shigar ta.

"Amma kwana nawa kike da niyyar yi?" Ya tambaya yana taraddadin kada tace zata daɗe sosai, ko yara
zasu jure rashin ta sosai ya san shi ba zai iya ba, domin ita ce komin shi a garin nan, idan ya kwaso zafin
rana da nema wurin ta yake zuwa ya ji sanyi.

"Ba zan wuce sati biyu zuwa uku ba in sha Allah, danejo tace yaran suna zuwa karɓan abincin rana da na
dare a gidan su saboda makaranta, na dai bata shinkafa da gari mai ɗan dama sai dubu biyar a cikin
kuɗin da gwoggo ta bani domin babana akwai fitina Wallahi." Ta ƙarasa tare da miƙewa sannan ta ciro
jakar sauran kuɗin daga kwalla ta fito da shi.

Saliha Ahmad Na'ibi (Seemahwrites ✨)

*REINA 💍*

BookNest, Wattpad and arewabooks (Seemahwrites)


12.....Saida ta mayar da samiran da ta ɗauko jakar kuɗin kafin ta fito dashi wurin da Kamal yake zaune
har Suhail ya ɗibo mishi ruwan sha amma can ƙasan kofi.

"Nagode baban maman shi" yayi dariyan ganin yawan ruwan yasan babu inda ze kai mishi amma sai ya
kwankwaɗe ya miƙa masa kofin. "Ƙaro min, amma ka bar kofin ya shiga cikin randar sosai"

Da fara'ar shi na yayi abun arziƙi ya karɓa ya sake rugawa jikin randan ƙasar kana ya tsumbula kofin
silver a ciki, saidai bai ɗibo wani abun arziƙi ba yanzun ma saboda an ɗaura randar a kan daron ƙasa yayi
masa sama.

Ganin zaiyi ta wahalar da Abban ne yasa Yaseer sake ɗauraye hannun shi ya miƙe ya wafce kofin a
hannun shi ya ciko kofin har baki sannan ya tunkari Kamal da shi. Zubewa Suhail yayi a ƙasa ya riƙo ƙafar
shi yana kuka suran kaɗan Yaseer ya zubar da ruwan amma sai ya cigaba da jan ƙafar da Suhail ɗin ke
riƙe dashi kayan jikin shi na daɗa tumurmusuwa a ɓaɓɓakakken simintin tsakar gidan har suka isa gaban
Kamal a haka sannan ya ajiye mishi ruwan "gashi Abbah"

Ɗagowar da zaiyi idanun shi suka sauƙa a kan Suhail ze kai masa cizo a sha raɓar sa yayi saurin buge
masa bakin ai kuwa ya fasa ihu.

"A'a me yayi maka zaka buge shi Yaseer? Bani son zalunci fah!" Kamal yace bayan ya shanye ruwan.

"Ai daman ba'a cizon mumini sau biyu a rami ɗaya. Madallah, shine maganin ka tunda baka ji" Saudat ta
gwada Suhail dake riƙe da baki da yatsa. "Kuma kazo min nan wallahi sai na ƙara maka. Ka ga yanda kayi
da kayan jikin ka! Jiƙa maka su zanyi sai ka wanke"

Yana tsoron zuwa jikin Abban sun ma ta riƙo shi don haka ya juya ya faɗa jikin Yaseer ɗin yana kuka.
Dariya ne ya kama shi yace "toh muje a siyo kayan daɗi, amma sai kayi min alƙawarin ka bar cizo"
"Wallahi na bari" yace yana murza idanu.

Cewa yayi ya jira shi ya ɗauko kuɗi amma kafan shi ƙafar Suhail suka shige ɗakin ya ɗauko Naira hamsin
a cikin jakar makarantar shi, sannan suka fice daga gidan.

"Alhamdulillah, Allah ya ƙara shirya mana yaran nan, Allah kasa su zama madafan jinginar juna a lokacin
da bamu tare da su" Kamal yace yana bin su da kallon sha'awar shakuwar dake tsakanin su duk da ratar
da suke dashi a shekaru.

"Ameen, amma ka sani don Yaseer yana da haƙuri ne, ba don haka ba ko ni bani iyawa da babana"

"Haka ne, Allah ya ƙara mishi haƙuri toh"

Kuɗin da ta ciro a cikin jakar ta miƙo mishi. "Bani son tafiya da kuɗin nan wallahi don zanje nayi ta kashe
su a banza ne koma su ƙare a tsakanin ziyara, kuma kaga goggo sana'a tace in fara da shi".

Murmushi yayi ganin wayo wai take son mishi yace "Saudatu nace ba zan karɓi kuɗin nan ba, ke da kanki
kika ce goggo tace kada ki kuskura ki bani Amma shine zaki saka ni saɓawa umarnin mahaifiyata ko?"

"Toh ko aron rabi ka karɓa ka fara wani abun, zan yarje maka har lokacin da Allah ya baka sai ka biya ni,
dubu tamanin ne a nan kaga koma wani irin sana'a zan fara dubu 40 zai yi."

Ya girgiza kai. " Ni yunwa nake ji a taimaka a bani abinci" ya ce haka ne don kawar da zancen.

Babu musu ta miƙe ta shiga kitchen sannan ta ɗauko kular dake ɗauke da abincin nashi tare da ruwan
wanke hannu.

Hannun ya fara wankewa ta kawar da ruwan kafin ya shiga cin jollof ɗin shinkafa na manja da wake.
Komawa tayi ta zauna kana ta ɗaura zancen daga inda suka tsaya. "Toh ko buhun gawayi ka siya ka fara
kasawa da ɗan kayan miya, kaga Yaseer ma sai yana taya ka zaman wani lokaci, duk da akwai masu
siyarwa da yawa a layin amma kowa kasuwan shi yake ci ko?"

A zafafe ya ɗago yace "Yaseer dai naji kika ce? Toh kada na ƙara ji! Kada na ƙaaara ji Saudatu!. Yaron da
ya maida hankalin shi a kan karatu kike son a rabawa hankali? Ribar nawa ne zai samu a wani saida
gawayi ko kayan miya da har zai fi mishi karatun shi mutunci?"

"Hmm, Abban Yaseer naga karatu babu a inda ba'a yin shi, ba sai yaje can ɗin yayi ta karatun shi ba? Wai
gani nayi asirin mu ne zai rufu don abin da aka bamu ba tabbata zaiyi ba har abada. Kuma buƙatu kullum
ƙaruwa suke yi, zuri'a tana ta ƙara faɗi yara suna ƙara girma"

"Rufin asiri? Akwai nufin asirin da yafi mishi karatun ne? Kina gani da yanzu ni na jure nayi karatun mai
zurfi kuma ba a ƙurarren lokaci ba da yanzu muna cikin wannan wahalar ne?" Bata barshi ya dire ba ta
cafe da faɗin.

"Naga dai ko karatun ne sai da kuɗi ake yinsa, Idan karatun zai yi dame zamu biya kuɗin makarantar
matakin gaba? Ko shima komawa zamu yi mu sake roƙa a wurin wa'inda suka ajiye mu??"

Jan numfashi yayi yana ƙoƙarin daidaita fushin sa ganin itama ta haura. Ba zai biye mata yau maƙwafta
su fara jiyo abinda ba'a taɓa ji ba a tsawon zaman su a gidan na tsawon shekaru 4, ko zasu yi rikici bata
bari a jiyo muryar su don haƙura take yi bata jaa shiyasa wannan karon yayi mata uzuri.

"Ni dai na faɗa miki Yaseer sai yayi karatu har matakin PHD in dai inada rai da lafiya ta. Aikace-aikacen
gidan nan ma da yake faman yi kamar mace daga yau na soke shi." Ya bangaje kwanon abincin ya faɗi
tare da miƙewa tsaye, juyawar da zai yi idanun shi ya sauƙa a kan Yaseer ɗin riƙe da kunnuwan Suhail
duk sun kafe su da idanu.

Ƙaramin tsaki kawai yayi ya ratsa su ya wuce ya bar gidan, su kuma jiki a saɓule suka ƙaraso ciki.
Abincin da Kamal ya zubar Yaseer ya sunkuya ya fara tattarawa kafin ya rufe kulan ya mayar kitchen. Bai
cewa Saudat komai ba ya ci gaba da wankin sa yana bitar hadda ƙasa-ƙasa don ya samu Alkur'ani ya
kawar mishi da damuwar da yake son shiga ciki.

Kafin dare kuwa sai ga yunwa ta sake koro Kamal ya dawo, siɗin-siɗin ya shiga kitchen ɗin ya ɗauki kular
abincin da ya zubar ɗin ɗazu da ƙasa da komai haka ya zauna ya ci.

Har washegari da ta gama shirin tafiyar ta ya raka ta tasha tare da yaran yana wani ciccin magani don ta
fahimci zancen da ya faɗa mata babu wasa a cikin sa.

"Muma zamu zo muyi sati guda da yaran kafin su fara jarabawar Islamiyya in yaso sai mu dawo tare"

"Toh Allah ya kawo ku lafiya" tace kafin ta faɗa bayan motar, saida ya gama cika aka mishi lodin
kayayyaki kafin Yaseer yana ɗaga mata hannu Suhail na kuka har motan ta tashi.

.....

Hajiya Fauziyya ke faman kai komo tsakanin babban falourn ta da kitchen. Tana shirye cikin sabuwar
maroon ɗin abayar ta ƴar egypyt wanda kalar ya dace da hasken fatar ta matuƙa.

Baki daya yau yanayin gidan daban yake, hada-hadan da ake yi a cikin ta ya ninka na kullum, kalolin
abinci ake faman girkawa ana shake saman dogon dining table ɗin da shi, an share ko ina an daɗa goge
shi, ƙamshin da yau yake tashi a gidan yafi na kullum.

Agogon hannunta ta duba bayan ta ajiye tray ɗin coleslaw, a kowani lokaci baƙin zasu Iya shigowa, don
an ɗauki fiye da awa guda da Alhaji Tahir yaje ɗauko su daga airport da kanshi. ta daɗa gyara zaman
kwanukan da masu aiki suka jera sannan ta tabbatar sun tanadar da duk wani abun buƙata cikin tsari da
ɗaukan ido.

Kiran shi da ya shigo wayar ta ya sanya annurin fuskar ta bayyana domin sun ƙaraso a daidai komi ya
gama kammala, ɗaki ta koma ta ɗauko mayafin kayan ta yane kanta tare da dan gyara fuskar ta da soson
powder kafin ta fito cikin takun ta na manyan mata zuwa farfajiyar gidan a lokacin da baƙi da farin
motoci suka yi parking a ƙofar shiga.

Alhaji Tahir ne ya fara fitowa daga cikin baƙar bayan an bude mishi, Fauziyya ta ƙarasa kusa da faran
lokacin da aka buɗe ƴar yarinya ta fito sanye da riga da wando kanta da kitson da aka zubo da na gaban
a kan fuskar ta.

Suna haɗa idanu da Fauziyya tayi kanta da gudu tana "Oyoyo Aunty" lokacin da dattijuwar mata ta
ƙarasa fitowa daga motar tare da mai gidan ta.

Da mamaki amma cike da jin daɗi Hajiya Fauziyya ta rungume yarinyar don ba wai sun taɓa haɗuwa
bane kwata-kwata tun da aka haife ta sai a wannan karon mahaifin ta ya yarda aka zo da ita Nigeria
amma yanda ta sake da ita yayi mata daɗi.

A hankali ta sauƙe ta tana gyara mata kitson dake rufe mata idanu gashi yasha beads masu kyau.

"My daughter yaya sunan ki?"

"My name is Aicha Abdou Hamissou" tace tana duban mahaifiyar ta domin ta tabbatar mata daidai tayi,
itama cikin jin daɗi ta ɗaga mata kai alamun tayi daidai, sannan ta maido da duban ta wurin Fauziyyar.

"Aunty ance kin haifa mana baby. Ina yake?" Tace tana leƙa bayan Fauziyyar kaman babyn takowa zaiyi
da ƙafar shi ya fito.

"Ina taje dai ko Aisha?"

Girgiza kai tayi beads ɗinta na ƙara "uhm- uhm. Aicha ba Aisha ba"

Mahaifiyar ta tayi dariya kana tace "Ai duk abu ɗaya ne Darling"
"Toh ina babyn? Where is my brother?" Wannan karon bata jira amsar ta ba tayi cikin gidan a guje.

A kunyace Hajiya Fauziyya tace "kuyi haƙuri Ina ta fama da ɗiya ta na barku a tsaye, Bismillah mu shiga"

Alhaji Tahir da mijin matar ne suka fara shigewa ciki kafin ita kuma ta ƙaraso ta rungume Hajiya Fauziyya
ba tare da tayi tsammani ba. "Sai yau Allah ya haɗa fuskokin mu my dear. Mun sha ganin wace irin mace
Alaji Tahir zai dirje ya zaɓo ashe baiyi rawan ido a banza ba"

Ta sake rungume Hajiya Fauziyya dake murmushin jin daɗi lokaci ɗaya matar da ƴarta sun shige cikin
ranta. Ba a banza Alhaji Tahir ke yabon mijin ta ba baki daya familyn su abin sha'awa ne.

Hannun su cikin na juna suka shiga ciki mazajen har sun riga da sun sama wa kansu matsuguni sun shiga
gaisawa da hirar duniya. Sai ga Aicha ta fito daga kitchen tana bin duk wani ƙofa ɗaya bayan ɗaya tana
dubawa.

"Me kike nima please?" Mahaifiyarta ta ƙarasa ta riƙo ta.

"Aunty Ina babyn ban ganshi ba?" Tace idanun ta na kawo ruwa.

Upstairs Fauziyya ta haura zuwa ainihin bedroom ɗinta da jego ya saka ta barin shi, babu daɗewa ta
sauƙo riƙe da Reina cikin purple baby towel mai laushi ta ƙaraso wurin da su Aicha yanzu suke zaune tare
da iyayen ta, kana ta zauna itama tace "gashi zo ki karbe ta"

Cike da zumuɗi ta ƙarasa jikin babyn tana leƙa fuskar ta saidai ganin ɗan kunnen dake kunnen ta da
kuma kalar kayan jikin ta yasa ta fara baya-baya a hankali sannan ta saka kuka.

......
*A wannan gaɓa bayan uban Sarauniya wa ke sonta don Allah Please? Har ta kaiga idan an kalli fuskar ta
ayi kuka? 😂*

*So far labarin wani gida yafi muku daɗi? Na su Saudatu ko Fauzah ko kuma duka?.*

*Saliha Ahmad Na'ibi ✨*

*REINA 💍*

Saliha Ahmad Na'ibi.

13...... Da mamaki Fauziyya ke kallon yarinyar da ke kuka har da bubbuga ƙafa ta koma wurin mahaifiyar
ta.

"mummy ce na ki kai baby boy ne?"

Gwada kanta tayi tana mamakin lokacin da suka yi hakan "Kada ki min ƙazafi Please. Ce na nai an haifi
baby amma ban ce boy ne ba"

"Toh a mayar da ita a karɓo min boy please, baby brother ina so" tace tana share hawayen sakalcin da ya
fara bin kuncin ta.
Riƙo ta Hajiya Fauziyya tayi ta jawo ta a hankali ta dawo kusa da su sannan tace "wannan sister ɗin ki ce,
zata kula da ke idan ta girma idan kina mata kirki"

Fuskar ta dai a haɗe tana yiwa Reina dake barci kallon tara saura kwata.

"Haba Nana, yaya kike mata kallo kamar kishiyar ki na?"

Bata san me kalmar kishiyar ke nufi ba amman sai ta samu kanta da daɗa yamutse fuska, wannan karon
wurin mahaifinta ta nufa tana ƙunƙunin "Ni dai bani son ta"

Haka har aka sake sabunta gaisuwa, aka gabatar da kai ma Fauziyya da bata gama sanin su ba, da
tambayar gajiyar hanya, Aicha na maƙale jikin ubanta.

Da aka zo cin abinci ma sai wurin nanny Fauziyya ta mayar da Reina don firr Aicha ta ƙi zuwa kusa da
dining table ɗin.

Daga mahaifin ta Alaji Abdou har Alhaji Tahir abun baiyi musu daɗi ba amma kuma mai ƴa ɗaya ce da
mai ƴar fari. Kowa a cikin su na ji da nashi kaman kifi guda a cikin teku musamman ma Alaji Abdou da
auren shi kusan shekaru goma kafin Allah ya azurta shi da samun haihuwa, kuma bayan Aicha har yanzu
da take niman shekaru huɗu a duniya shiru babu labari. Ga mahaifiyar tata ma sickler ce yau fari gobe
tsumma shiyasa koda yaso ƙara aure ya sanar da ita ciwon ta ya tashi kaman ba zata yi rai ba ya haƙura
ya aje zancen a gefe suka ci gaba da manejin abinda Allah ya basu.

Hajiya Fauziyya kam ko a jikin ta don ta san fidda fice ne kawai irin na yara, don haka ta ɗauki Aicha ta
ɗaura bisa cinyar ta tana bata abincin a baki suna yi dukkan su suna taɓa hira sama-sama.

Suna gamawa ana kiran La'asar, saida suka yi Sallah sannan Hajiya Fauziyya ta shiga da matan ɗakin
baƙin ta, mazan kuma suka wuce study room ɗin Alhaji Tahir.

"Aunty kin san SpongeBob?"


Gyaɗa kai Fauziyya tayi idanun ta a cikin na Aicha da ta ɗale mata cinya ta tsaya sannan ta riƙo fuskar ta
cikin ɗan tafin hannunta tana kallon ta ido cikin ido domin ta samu hankalin ta hundred percent.

"Na san shi"

"Ina da ƙaton SpongeBob a gidan mu. Babba ya kai haka" ta ware hannun ta don ta gwada girman
teddyn, kana ta sake riƙo fuskar Fauziyya kafin hankalin ta ya bar kanta zuwa ga mahaifiyar ta da suke
hirar arziƙi.

"Masha fah?"

Ta sake gyaɗa kai "Reina tana da teddyn ta itama" Fauziyyar ta biya mata.

"Idan naje gida zan saka nawa a dustbin" tace tare da ɓata fuska, abun har ya basu mamaki ganin fa da
gaske take yi zancen bata son Reina amma ta liƙe wa mahaifiyar ta.

"Kin san Omar and Hana, da paw patrol?"

"Aicha, sauƙo!" Malika tace cikin dakakkiyar muryar da ya saka ta sauƙowa babu musu amma kuma bata
bar hirar ba, sai ma ta shiga bata shirmen labarin duk cartoon ɗin da take kallo.

Mayar da hankalin ta Wurin Malika Fauziyya tayi bata bar gyaɗa ma Aicha kai ga duk abinda tace ba.
"..Toh yaya Nijar? Ina sha'awar ziyartar ƙasar kuwa"

"Nijar alhamdulillah, muna miki maraba, sai kice Tahir ya ɗauko ki kuzo mana ziyara"

"In sha Allah da Reina ta ƙara ƙwari muma zamu zo"


Malika ta kama baki "Toh! Kema halin ku ɗaya da Daddyn Nana. Ina Nigeria ina Nijar da za'a ce sai jariri
yayi ƙwari? Tafiyar jirgi saboda daɗi yayi muku yawa ko?"

Fauziyya ta jinjina kai "nima ba ra'ayi na bane wannan, na nata Daddyn ne. Unguwa a cikin garin Bauchi
ma yace ba yanzu ba sai ta daɗa ƙwari"

"Idan yayi wasa ko sace ta zanyi in gudu saidai ya tsinto ta a maradi" suka saka dariya dukkan su Fauziyya
har tana imagining irin rikicewar da Alhaji Tahir ɗin zai yi.

"Yauwa Fauziyya, faɗa mini wani tanadi kinka yi wa baby Reina?" Cewar Malika bayan ta haɗa Aicha da
huruful hija'iyya a waya ko zata barsu su zanta ta daina damun Fauziyya da surutun da tana da tabbacin
ba ganewa take yi ba.

Dariya tayi "wani irin tanadi kuma? Na aure?"

Itama saida ta dara kafin tace "kina da abin dariya idan kinka so. Ina nufin tanadin raino, tanadin tarbiyya
da kuma tanadin rayuwa irin ta ƴa mace mai buƙatar matuƙar kulawa"

Ajiyar zuciya tayi "akwai wani tanadi ne bayan Allah ya raya mana su da imani?"

Jinjina kai Malika tayi ganin kaman bata da ra'ayi a zancen tace "gaskiya ne, Allah ya kare mana su daga
dukkan sharri kuma ya raya mana su da imani"

Sai ta kaikaita hirar ya koma na duniya, Malika tana bata labarin Nijar haka ma Fauziyya na bata na
Nigeria sannan suka koma na ƙasa mai tsarki da kuma ƴan yawace-yawacen da suka yi na honeymoon
lokacin tana amarya.

Ƙarfe takwas na dare aka sake jere musu dinner suka ci.

Duk yanda Fauziyya da Alhaji tahir suka kaɗa suka rawa firr suka ƙi yarda su kwana a gidan.
"Da gida na da iyali na ka saka ni kwana nan gidan ka Tahir kaman gauro? Lallai ka raina ni" shine abinda
Alaji Abdou yace yana ɗaukar Aicha a hannu kana ya riƙo hannun Malika.

"Gobe da sassafe zani Sabon warehouse ɗinnan in duba tare da masu ƙiyasi sai mu kimanta kayan da zai
iya ɗauka. In yaso daga baya kuma idan na samu hutawa sai mu zauna muyi maganar shigo da kayan da
kuma ɗiban ma'aikata"

Fauziyya na jin maganar ɗiban ma'aikata bata bar shi ya dire ba tace "Yauwa Daddyn Aisha Idan an zo
ɗiban ma'aikatan akwai wanda nake so ayi min alfarma a ɗauka"

Maido da hankalin shi gare ta yayi fuska a sake yace "Babu damuwa amarya amma minana ya karanta?
Don kin san kula da warehouse munfi buƙatar mai ilimin abin da ya shafi lissafi idan dai ba aikin ƙarfi zai
dinga yi ba"

Duban Alhaji Tahir tayi shima ita yake kallo, har ta gaji da ɗago mishi zancen aikin Kamal gashi kuma
abun yaƙi barin ranta, kuma har ga Allah shi mantawa yake yi don bai ɗauke shi da muhimmanci ba,
yana da ɗaruruwan damuwowin da suka fi wannan girma a kan shi.

Saida ta sauƙe idanun ta daga nashi kafin tace "Ban san me ya karanta ba wallahi, amma akwai takardun
shi a wurin Daddyn Reina, diploma ne dai yake da shi, a taimaka ayi mana alfarma dan Allah"

"Haba-haba amarya, ko wanda bai je makaranta ba kinka kawo a bashi aiki sai matsayin da kinka zaɓa,
toh ina amfanin damar idan wanda ke jikin naka ma basu amfana ba?. Idan akwai wasu ma ki ƙaro ko su
ɗari ne duk ba zai gagara ba in cha Allah".

......

Kusan za'a ce faɗowa gidan Danejo kamal yayi don sallamar da yayi bai jira amsar ta ba ko izini ya shigo
yana maimaita kalmar Alhamdulillah a kan harshen shi, fuskar shi kuwa a kallo ɗaya zai gama karantar
maka da saƙon farin cikin dake cikin zuciyar shi.
"Danejo da gaske ne, wallahi da gaske ne, naje har sun ɗauke ni aikin alhamdulillahi Danejo" yaje ya
zube a gaban tsohuwar dake murmushin jin daɗi itama.

Tun daren jiya kira ya shigo wayan Kamal ɗin wanda babu ɓata lokaci ya ɗauka ake sanar da shi ana
buƙatar ganin su interview washe gari kana suka sanar dashi address ɗin warehouse ɗin. duk da hakan
ya taɓa faruwa dashi lokacin da yake yaƙin niman aiki kororo-kororo. da suka je wurin aka tara su aka
musu tambayoyi kaman abun arziƙi sai da ya dawo aka turo masa saƙo wai daga ma'aikacin wurin ne
idan yana so ya shige masa gaba ya kawo dubu hamsin aiki kaman ya samu an gama.

Haka ya kira goggo ya sanar da ita, lokacin itama babu kuɗi a hannun ta don haka ta saka Ragunan ta
ƙosassu a kasuwa aka musu siyan kwasha-kwasha ta turo masa kuɗin ya tura musu. Shikkenan kuma yaji
shiru, da yayi ƙoƙarin tuntubar layin ma ko tafiya bata yi, yayi tattaki ya tafi wurin amma babu su babu
labarin su, rushe tsohuwar ma'aikatar ma ake yi za'a tada sabon gini. Yayi zazzaɓin kuɗin shi a lokacin
amma Saudat ta lallaɓe shi ya ɗau dangana.

Sai dai bai yi sanyin guiwa ba a wannan karon ba ma, da safe yayi sammakon shiryawa yaje, ya dai saka
ma ransa ko Naira biyar aka buƙata daga gare shi bayi bayarwa.

Sai dai tambari da kuma sunan TK Kingdom da ya gani a jikin takardar da suka bashi na letter of
appointment ya tabbatar mishi warehouse ɗin na kamfanin Alhaji Tahir ne.

Kuma information ɗin shi kawai suka ɗauka ba'a yi mishi tambayar komai ba, takardan makarantar shi
ma da yaje da ita basu ko karɓa ba balle su duba.

Yaseer da Suhail dake cin abinci ma suka tsame hannun su, murna suka shiga yi, Danejo da Suhail harda
taka rawa, ya riƙo hannun yaseer ɗin suna juyi da taku a wurin cikin nishaɗi, Kamal kuma numbern
goggo shine abinda ya fara nema ya danna mata kira.

Har hawaye saida ya sauƙa daga idanun shi da yaji irin murnan da mahaifiyar shi ta shiga da kalolin
addu'oin Nasara da kariya da ta shiga mishi tun kafin ma ya fara.

"Mahaƙurci mawadaci kamalu, Allah yasa sauƙi ne yazo ma rayuwar ka na dindindin"


_Mukan yi addu'a da dukkan zuciyar mu, da dukkan imanin mu, kuma muna masu yakinin Allah zai amsa
mana, amma addu'a sauƙaƙa ƙaddara take yi bata sauya shi, domin babu rayuwa gaba ɗayan ta idan
babu ƙaddara, daga ranar da taka ƙaddarar ta yanke daga wannan rana numfashin ka zai rasa
makamashi sai ya ɗauke._

Da Kamal ya gama magana da goggo ya kira Saudat bayan ta fashe da kukan farin ciki cewa tayi. "Gani
zan fito yanzun nan, zuwa maghriba zan iso gida in sha Allah"

"A'a Saudatu, kisha zaman ki ni zan iso gare ki. Zan iso gida in gwada ma masoya na ribar addu'ar Allah
ya taimaka ya shige mana gaba da basu gajiya da yi mana"

Toh tace yana jin yanda take nanata wa mahaifiyar ta abinda yake faruwa cikin ƙaguwa da tsananin farin
ciki kafin ya katse kiran.

"In tafi in barku ko Yaseer?." Yace don ya tsokane su.

"A'a Abbah zamu bi ka dan Allah" Yaseer ɗin ya amsa yana rau-rau da idanu.

Dariya Kamal yayi cikin annashuwa yace "kuje ku sauya kayan jikin ku toh, bari naje na siyo muku sabon
takalmi ko?"

"Eh Abbah" Suhail yace yana tsalle. "Mai huji-hujin nan nake so" yana nufin crocs domin yana ganin yara
a makarantar su dashi yana bashi sha'awa.

Ba canza kaya kawai ba saida Yaseer ya ɗauraye su da ruwan sanyi ya ɗauko musu kayan sallan bara
daga ƙasan kwalla ya saka musu sannan ya kusan tittiɗe musu goran turaren shi, ya saka musu hula suka
fito suka yi kyau abun su kafin kamal ya dawo da laidan takalman.
Addu'a yaseer yayi ya zurma ƙafar shi kana ya rufo musu ƙofa Kamal ya saka ma gidan ƙwado sai
Jama'are.

....

Ta manta da kunya ta manta da kawaici ta manta da idanun magabata da ma ƴan baya dake wurin, ita
karan kanta ta manta da lokacin da ta saka hannunta ta zagaye shi tare da cusa kanta cikin ƙirjin shi ta
saki kuka lokacin da taji yawan albashin da za'a ke biyan shi. Naira na dukan Naira har dubu ɗari da
goma.

Shikkenan hutu yazo, wahala ta ƙare musu in sha Allah.

*Seemahwrites ✨*

*REINA 💍*

14......Gida-gida aka dinga shigowa ana yi ma Kamal Allah ya sanya alkhairi bayan wuri ya rufa kuma sun
samu hutawa.

Yara ke layin rattaɓa sallama ɗauke da ƙwaryan abinci, wasu ma kansu suke lulluɓewa su kawo ko su
tura ƴaƴan su ƴammata.

An saba yi musu tarba makamancin wannan amma tabbas na yau ɗin daban ne, domin kafin almuru ya
gama lulluɓe gari da duhun shi gidan goggo babu masaka tsinke, sun yayyame Saudatu da kamal kaman
sabbin amarya da ango, harda masu kawo ƙoƙon baran su ma ƴaƴan su d kula jikokin su dake karatu a
halin yanzu, suma idan sun sami kammalawa Kamal ya saka baki a sama musu aiki.

Washe baki kawai yake yi yana binsu da kallo, ita nasara tafi daɗi idan mutane basu san gwagwarmayar
da kayi kafin ka same ta ba, saidai a ga murmushin ka amma ba'a san dararen da ka share cikin ƙunci,
yunwa da rashin barci ba.

Sun ci nama, sun sha madara, ga kuma kayan itatuwa da ba'a cika samun shi a cikin gari ba ko da kuɗin
ka kuwa kowa ya tsinko na gidan shi an cike gaban su da shi.

Sai da aka ragu a ɗakin zuwa alwalan sallar maghriba Kafin ya shiga mayar wa mahaifiyar shi yanda abun
ya kasance, don har yanzu jin kan shi yake yi kaman a mafarki.

"Na hana idanu na barci Kamalu, kullum kana cikin addu'a ta amma bayan na je na gano halin da kuke
ciki ban sake samun nutsuwa na ba sai a yau"

Da ace wayewar su ta fi haka zuwa zai yi ya rungume ta, ya gwada mata tsantsan farin cikin da yake yi
kasancewar shi mai sa'ar da ya samu mahaifiya irin goggo Halime. Amma ya gode ma Allah ma tunda
bata masa kunyar ɗan fari ko kaɗan.

"Komi lokaci ne goggo, abubuwa sukan zo ma bawa a lokacin da bai yi tsammani ba"

Ta jinjina kai "haka ne. ni ba ma kai nake ji ba kaman yaran nan nake ji da kuma Saudatu baiwar Allah.
gidan su basu san babu ba basu saba da shi ba, rufin asirin Allah suna da shi amma ko daga wurin Inna
hajjo (mahaifiyar saudat) ban taɓa samun labarin halin da kuke ciki ba."

Tabbas Saudat matar rufin asiri ne, Saudat fitila ce dake haska duhun rayuwar shi, Saudat ɓarin jikin shi
ne, ɓarin zuciyar shi. Lallai zaɓin iyaye ya zamo mishi gata, kuma biyayyar da yayi musu yayi mishi rana.

Hanzartawa yayi zuwa sallan maghriba, sai kuma ya ɗan zauna wurin don gaisawa da abokan arziƙi, kafin
lokacin taron matan cikin gidan su ya ragu sai ya dawo, don yaran da Saudat a can gidan su za su kwana.
....

Dare ya kusa rabawa, Suhail da Yaseer harma da jariri sun samu barci, sai Saudat dake linke kayan Sabir
tana shiryawa a jakar da suka zo da shi. Domin gobe sammakon komawa Bauchi zasu yi, duk da ta yi
kewan gida amma bata jin su biyun za su iya haƙurin ci gaba da zama a nan sanin abinda yake jiran su a
can ɗin.

Kowa ya watse sai makwafciyar su innayi da ta tasa Saudat da inna hajjo a gaba tana zuba kaman ƴaƴan
kurna ko barci bata ji.

Sai da ta bari Inna hajjo ta bar ɗakin kafin ta matso kusa da Saudat cikin ƙasa da murya, ba kamar ɗazu
da take da tabbacin sauran maƙwafta suna jin duk abinda take cewa ba tace.

"Saudatu a baki yarinyar da zata na taya ki da wasu ayyukan mana tun da ga iyalai sun fara miki yawa
yanzu?"

Dagowa Saudat tayi daga abinda take yi tana kallon ta sheƙeƙe cikin hasken jan ƙoyin da ya ƙara ma
bakin Innayi kala bayan rinin da goro ya gama yi mata.

Bata ba ta damar tankawa ba ta ɗora da "ga zulaiha nan ƴar wurin harira ta ƙare karatun ta na sakandare
wannan shekara , kuma mahaifin ta bayi da Ra'ayin barinta ta cigaba, ga shi har yanzu babu wani
tsayyayye, to kinga zata taimaka miki ƙwarai koda Allah zaiyi ta samu mashinshini ta can kinga sai tayi
auren ta a sake baki wata, don ƴammata kam masha Allah akwai su kaman Jamfa a Jos".

Murmusawa Saudat tayi, wato ko wani matakin rayuwa da mutum yake kai kalan kalubalen shi daban?!.
"Innayi ni kuwa ina zan ajiye Zulaiha gida duk samari?"

"Ah-ah to ke ba mace bane? A inda kike wurin zaki ajiye ta. Ni amfanin da zata yi miki nake gani, kinga
har ɗawainyar jaririn nan ma kina kwance zata yi miki komai wallahi"

Inda take na nufin ɗakin Kamal kenan?!, bata san da nufi Innayi ta faɗi hakan ba ko kuwa zuciyar ta ɗaya
ne, amma koma yaya ne Rashin hankalin ta bai kai ta ɗauki kishiyarta da hannunta ta kaita har gida ba.
"Toh yanzu idan auren ya kusa naji ba zan iya rabuwa da ita ba fah? Ko ita zaman gidan ya yi mata daɗi?
Kinga ai sai a samu matsala. Kuma Kina ganin tsayin ƙafar nan na Yaseer ba a banza ba, babu abinda bayi
min sai dai abinda yafi ƙarfin shi."

Taɓe baki tayi ta miƙe tare da kakkaɓe jiki domin abin da ya kawo ta kenan daman. Har ta saka Zulaihan
haɗa kayan ta tayi sallama da maƙwafta gobe sai tafiya amma haka Saudat ta sace mata guiwa. Ba zata
bari ma Inna hajjo ta ji wannan zancen ba don wulaƙancin da zata yi mata sai ya fi wannan.

...

Kuɗin da tazo dashi da niyyan saran wani abun shi kamal ya karɓa yayi alkhairi ma iyayen su. duk wanda
ya shigo musu murna ma saida aka sammusu wani abu da masu ɗari biyar da masu ɗari biyu, ƙananun
yara kuma aka bisu da minti mai tsinke. Kafin su bar Jama'are dubu Arba'in katt ya tafi, amma fatan shi
addu'an da zai samu daga gare su zai yi musu sanadin samun albarka ninkin ba ninkin ɗin abinda ya
ɗauka ya bayar.

An haɗa musu sha tara na arziki kafin suka tattaro suka dawo da safiyar. Da suka sauƙa ma yawan ƴan
unguwa da suka shigo yi musu Allah ya sanya alkhairi ba kaɗan ba.

Sai can yamma suka samu kan su, aka fito da kayan da suka taho da shi ana karkasawa.

"Ga kifin Alhaji Tahir ɗin nan. Ai yayi ko?"

Ta tura mishi gasasshen kifin a cikin ƙaramin kwalin indomie ya duba.

"Yayi in sha Allah, kuma za su ji daɗin ajiyar shi don gashin yayi kyau sosai."

Ta gyaɗa kai sannan ta jawo kwalin don ta rufe shi da kyau.

"Kuma da an fara biyan na albashi zan biya ki kuɗin ki in Allah ya yarda"


Murmushi tayi, "Haba babu komai, ka bar shi kawai, daman na tafi da shi ne zan sari wani abun daga can
in fara siyarwa, amma akwai sauran Rabin da na bawa Huwaila ajiya, zan karɓa in tura ma Inna ta"

Shiru yayi da zancen amma ya saka ma ran shi zai biya ta ɗin koda ba a dunƙule ba.

.....

Yau kam Su Saudat sun sha zaman jiran Hajiya Fauziyya don ma Aina'u tayi tunanin kunna musu tv bayan
ta kawo musu ruwa da abin mitsa bakin da wajibi ne gabatar da shi ma kowani baƙo. decodern yana kan
channel ɗin Nat geo wild; da ake program ɗin tsuntsaye sai kuwa ya ɗauke hankalin su duka.

Bayan kaman minti talatin Hajiya Fauziyyar ta fito ɗauke da ƙaramin hand towel tana tsane hannun ta.

"Afuwan Umman Yaseer na barku kuna ta jira". Tace tana zama a ɗan gefen su kaɗan.

Washe baki tayi tana ƙare mata kallo yanda ta cika idanu ta ƙara kyau "Babu komai wallahi Aunty, mun
same ku lafiya? Yaya mai sunan ƴan gayu?" Da gaske sunan ya gagare ta tunawa.

Dariya sosai Fauziyya tayi tace "Hafsatu fa sunan ta, sunan Ummi na aka mayar mata shi yasa ake mata
inkiya da Reina ɗin"

Dariyar yaƙe Saudat tayi tace "Allah sarki"

Hajiya Fauziyya ta ɗaura da "yanzu na gama wanke ta ma, don kun shigo na riga na rage kayan jikin ta ne
kada sanyi ya shige ta shiyasa. Amma za su fito da ita idan aka gama shiryata"

"Ayyah" tace tana zunkuɗa yaron bayan ta.


"Muga Jaririn mana an ƙulle shi a baya" tace tana miƙa hannu.

Miƙewa Saudat tayi ta warware goyon sannan ta taka ta miƙa shi ma Fauziyya wacce ta karɓe shi da
Bismillah.

"Masha Allah, yanzu kam kunyi arba'in ai, don tsakanin mu ma babu nisa"

"Satin mu takwas da kwana biyu"

"Ahh masha Allah" ta saka hannu a kan goshin shi da kurajen da suka mutu sun bar tabo ga wasu ma sun
fito an mulke su da farin powder, jikin shi a yamushe kaman ba na jariri ba duk da babu yunwa a jikin
shi"

"Umman Yaseer kun kai shi asibiti kuwa aka duba masa kurajen nan?" Ta tambaya da damuwa shimfiɗe
a kan fuskar ta.

"Wallahi zafi ne kawai Aunty, don ma tafiyan mu Jama'are sun ɗan mummutu don yanayin wurin yafi
cikin gari Iska.

"Amma to kina mishi amfani da lotion da sabulun da na tura miki? yana da kyau sosai kwanan nan zaki
ga duk sun baje tabon ma ya ɓace kuma jikin shi zai yi kyau sosai"

Ɗaga kanta tayi kaɗan kaman mai tunani tace "wani sabulu kenan Aunty?. Kaman cikin kayan da aka kai
mana babu sabulu gaskiya"

Shiru Hajiya Fauziyya tayi

Saudat ma tayi shiru

Lokaci ɗaya suka fahimci abinda yake faruwa, Rijiya ne ta bayar da ruwa guga kuma ya hana.
Murmushin ƙarfin hali Hajiya Fauziyya tayi don abin ya dake ta, tana son ta tambaye ta ko an kai mata
kuɗi ma kuma nawa aka bata amma tana tsoron jin abinda yayi saɓani da sanin ta.

"Ina ga na manta ne da nazo haɗa kayan, kin san kai yayi zafi"

Saudat ma taya ta dariyar yaƙen tayi tace "gaskiya kam"

"Amma akwai wani a ciki, kafin ku tafi zan duba miki zaku ji daɗin shi sosai kamfani ne mai kyau"

"Allah ya saka da alkhairi dai Aunty. Ko godiyan abin da ya kawo mu bamu fara ba har an ƙara mana
wani?!."

Ɗan hararan wasa ta cilla mata "Yaya kike wani magana kaman ba'a zama ɗaya ba?"

Kallon annurin dake fuskar ta tayi da kuma yanda ta rungume jaririn ta dake cikin tsumma a jikin kayan
ta mai kyau ba tare da wani ƙyanƙyami ko makamancin shi ba.

Hawaye ne suka cika mata idanu sai da ta ɗan zamo daga kan kujerar tace "Aunty bani da bakin da zan
iya gode miki. Abinda zan iya cewa kawai shine Allah yayi miki abinda kika yi mana, Allah ya rufa miki
asiri duniya da lahira. Allah ya gwada mana ranar da zamu saka miki da kwatankwacin alkhairan da sanin
ki ya jawo mana. Allah ya albarkaci zuri'ar ki aunty" sai ga hawayen ya gagara riƙuwa mata ya samu
daman zubowa a kan fuskar ta sai ta kifa kai kawai tana yin shi a hankali.

Itama Fauziyyar ƙwalla ne cike a idanun ta, sai tayi gyaran murya tare da faɗin "Ameen Umman Yaseer.
Toh yaya sunan baby?"

Ɗago kai Saudat tayi cikin muryar kuka tace "Sabir"


"Ashe shima sunan ƴan gayun ne da shi"

Sai suka saka dariya sannan Saudat ta fara share hawayen ta da ƙasan hijabin ta.

Tissue Hajiya Fauziyya ta zaro mata daga kwalin dake kan table ɗin gefen kujeran ta. Saudat ɗin ta karɓa
ta share fuskar ta da hancin ta sannan ta miƙe ta nufi dan akwatin da take tunanin kwandon shara ne.

"Ki taka abin da ke gaban ki zai buɗe" cewar Hajiya Fauziyya da ta lura da ruɗun ta Saudat ta shiga.

Ta san kwandon shara mai irin takawan nan amma bata taɓa ganin irin wannan ba, cikin shi harda wani
ɗan jan haske idan ya buɗe din.

Dawo da duban ta kan Yaran tayi yayin da suma suka dawo da duban su daga kan mahaifiyar su. Suna
kallon juna ta sake musu murmushi, suma sai suka murmusa mata, kuma wannan murmushi daga ƙasan
zuciyar Yaseer ya fito, yana ƙulla wasu alƙawura da zuciyar shi, yana ajiye su a matsayin su kuma a
lokacin su. Wanda ya saka mahaifan shi murmushi shima sai ya murmusa, wanda ya saka su kukan daɗi
shima sai yayi kukan daɗi.

"Yaseer yaya school? Yana maka daɗi dai ko?"

"Alhamdulillah Aunty, akwai daɗi"

Ta jinjina kai alamun gamsuwa.

"Ina Baby Reina?" Ya tambaya da saida mahaifiyar shi da ta dawo wurin zaman ta ta shiga mamaki har ya
riƙe sunan da ta kasa tunawa.

Miƙewa tayi, "bari ma in duba ko sun gama sai in kawo muku Ita. Ku ƙaraso dining a kawo muku abun
karyawa umman Yaseer"

Abun karyawa kuma da rana tsaka? Shine abinda tace a zuciyar ta a fili kuma ta furta "A'a Aunty a ƙoshe
muke sai da muka karya muka fito, kuma ma yanzu zamu wuce"
A kan kujerar da yake Suhail ya shiga rawa "yayyy zamu ci Nama!!" Yaseer yayi saurin riƙe shi ya tsayar
da shi wuri ɗaya cike da kunya.

"Ga ma bandan kifi da muka kawo muku tsaraba babu yawa yana bakin ƙofa," sun bar shi a waje ne kada
ƙarnin kifin ya cika mata parlourn ta mai ƙamshi.

Da kanta ta fita ta ɗauko, tana shigowa mai aikinta ta ƙaraso da gudu ta karɓe kwalin zata wuce da shi
kitchen ta tsayar da ita, babu daɗi ayi maka kyauta ka gwada oho da shi don haka ta buɗe kwalin ta
ɗauko kifin guda ɗaya tana jujjyawa.

"Masha Allah sabon gashi ne ma, daman ina da yaji na mai daɗi yau babu cin abincin rana kenan a kai
zan dira"

Duka suka saka murmushi kafin ta je ta ɗauko musu Reina bayan ta wanke hannun ta.

Ta matsa a kan su ci abinci zata saka a maida su da suka so yi mata fulako.

Ai ko bata saka a maida su ba wannan karon tafe take da kuɗin abun hawan ta, don ba zata taɓa manta
hanyar wannan gidan da wancan daren ba, tafiyar da ya jawo mata naƙuda.

Sai da suka ci suka yi nakk suka huta ma kafin bayan sunyi azahar suka yi shirin tafiya.

"Yauwa saka min numbern ki a nan Umman Yaseer ana sada zumunci lokaci zuwa lokaci." Ta miƙa mata
samsung ɗin ta bayan ta shiga mata yanda zata ajiye lambar.

Kallon wayan Saudat tayi na ƴan daƙiƙu tana jin sulɓin shi a cikin hannun ta, gashi ƙato amma bayi da
nauyi.

Tana kaffa-kaffa ta saka mata lambar ta mayar mata da wayan da hannu bibbiyu sannan Hajiya Fauziyya
ta danna kira.

Rakani kashin dake jakar Saudat ya ɗauki ruri da ƙara sosai kafin Hajiya Fauziyya ta katse kiran.
"Kiyi saving, kuma nima idan na samu fitowa zan zo miki. Gashi goron Arba'in, na gode"

Da ƙyar Saudat ta karɓi katon laidan, buɗewa tayi a wurin ta leƙa don ta san irin godiyar da zata sake yi.

Kayan shafan yara ne a cikin packaging ɗin shi kaman yanda tayi mata alƙawari. Sai turmin zanin atamfa
da kuma lace ɗin da dangin uba suka yi ashobe a sunan Reina duk da Saudat ɗin bata san da hakan ba
tunda bata je ba, sai turaren yara guda biyu, sai kuma Comfort na wanki.

Don taji yaron na ɗan ƙarnin nono da ta ɗauke shi.

Saliha A Na'ibi (Seemahwrites)✨

*REINA 💍*

15....... Lokaci! Lokaci!! Lokaci!!!.

Tafiyar shi kaman iska yake, baka ganin shi. Kaman fita da shigar numfashi, baka lura da shi. Kaman
bugawar zuciya, bayi canzawa. Amma idan ka ɗan juya baya kaɗan zaka fahimci cewa kamar iskar, zaka ji
shi a jini da jikin ka. Kamar fita da shigar numfashin, yana zuwa da sauye-sauye a lokacin zafi, sanyi,
hunturu da kuma damina. Kamar bugawar zuciyar, ya tafi da shekaru, girma da canzawar halitta.

Fitowa tayi a siɗaɗe daga kitchen ɗin zuwa parlourn da masu aiki ke hada-hada, hannayen ta biyu riƙe da
kwalin happy Hour ga bakin ta yayi kalan orange.
Packet na uku kenan da ta ɗauko ba tare da sanin Auntyn ba domin na biyun ma ƙwacewa tayi kuma tayi
mata faɗa. Sanye take da farin riga daddy mai adon purple iya guiwar ta, shima gaban rigan ya rine da
kalar juice ɗin.

Kwalin ta kai bakin ta, ta kamo straw ɗin da harshen ta kana ta cigaba da zuƙa hankalin ta a kwance tana
tafe tana kallon shirye-shiryen da ake a gidan.

Duk wani kayan fashewa ko na ado da yara za su iya ɓarnan shi suke ɗagawa zuwa ƙaramin parlourn
auntyn masu decoration ma suna ta aikin su na jera flowers da balon balo a ƙaton allon dake ɗauke da
hoton ta da Daddyn ta ya kira photographer na musamman aka ɗauke ta jiya, Gefen hoton an rubuta
(Big 3) sai kuma sunan ta daga ƙasa.

Ƙarasawa wurin masu decoration ɗin tayi tana tura cikin ta da ya tashi ya tsaya kamar mai juna biyu,
tana ci gaba da zuƙan kayan ta tana kallon abin da suke yi.

"Hajiya ƙarama Bari in ɗaga carpet ɗin ko?."

Ta jita sarai, ta fahimci da ita ake yi kasancewar haka duka masu aikin gidan suke kiran ta, Hajiya ƙarama,
amma kula ta ne bata yi niyya ba.

"Hajiya ƙarama!"

Dj dake testing speakun shi ne ya saki kiɗa a wurin, ta washe baki sannan ta fara takawa a wurin tana
tsalle, tama manta da halittar me aikin a wurin.

Har ta gaji da tsayuwa gashi juice ɗin dake hannun Reina ya fara zuba a kan Farin chinese carpet ɗin.
Tsoro ya fara kama ta don an ajiye carpet ɗin a wurin ne saboda ado kawai ba na takawa ba, sai aka
ɗaura masa wani ƙaramin bookshelf da kayan ƙarau da kuma fulawowi a kan shi, ba'a hawan shi saboda
kalan shi.
Amma saboda an riga an ɗaga book shelf ɗin kuma an canza fuskar parlourn yanda zai bawa masu
decoration abin da suke so shi yasa har ta samu daman hawa kai.

"Hajiya ƙarama dan Allah ki sauƙa" tace da ƙarfi cikin ƙaran kiɗan kaman zata saka ihu tare da ɗan taɓa
ta kaɗan amma sanadin bata tsammaci haka ba yasa tayi tangal-tangal zata faɗi.

Riƙo ta mai aikin tayi kafin ta shiga uku, Reina tayi saurin ture hannun ta daga jikin ta tana bin matar da
ta girme wa uwar ta nesa ba kusa ba da kallon banza, kafin ta saki kwalin juice ɗin ya fara zuba a kan
carpet ɗin ta jikin straw.

Tayi saurin duƙawa ta ɗaga kwalin amma kafin ta kai ga miƙewa Reina ta wafce shi.

"Uwar ki!" Cikin Sa'a a lokacin Dj ya kashe kiɗan, yayin da amon ashariyar ya karaɗa cikin falon baki ɗaya
hankalin mutane ya dawo kan ta da mamaki.

Tsoro ne yaso kama ta da yanayin kallon da suke mata, amma taga ai sauran yara ma haka suke faɗa
idan anyi musu laifi, har su Jamal ma da suka girme ta.

Sakin kwalin ta sake yi sannan ta bishi ta daka tsalle ta dira a kai, lokaci ɗaya kwalin ya fashe juice ɗin ciki
ya fantsamu a jikin ta da fuskar mai aikin dake duƙe har kan kujerar dake kusa da wurin. Farin carpet kan
ma ba'a magana don yayi dama-dama.

Ta ware ƙananun yatsun hannunta duka biyu ta yiwa matar danƙwale kafin ta juya ta ruga a guje tayi
ciki.

......

Wani tafiyar lokacin kamar iska, yana wucewa bayi canza komai a cikin rayuwar mutum, yana tafiya ne
kawai da abu marar nauyi kamar laida da yaayi, ya ɗan matsa da shi kaɗan daga muhallin sa zuwa wani
sabon muhallin.
Amma wani tafiyar lokacin tana zuwa ne kamar guguwa. Ƙasa, shara, ƙura, idan yayi ƙarfi har mutum
yakan iya ɗauka, yayi walagigi da shi kafin ya jefar da shi a wurin da yaga dama.

Zuwa lokacin da zai lafa zaka fahimci komai ya sauya ba tare da idanu sun lura ba.

Sallama yayi daga ƙasan maƙoshin sa kana ya shigo ɗakin da Saudat ke ciro kaya daga cikin sabon
wardrobe din da bata daɗe da siya ba domin wancan ya kasa musu a yanzu.

Tsayuwa yayi daga ɗan nesa da Ita ba tare da yace komai ba yana jiran har sai ta lura da kasancewar shi
a wurin kafin ta faɗa mishi dalilin kiran da tayi mishi.

Ɗago kai tayi tana kallon tsayin shi wanda ko ita dake tare da shi kullum tana mamakin shi balle wanda
ya jima bai gan shi ba.

"Baka iya sallama bane?"

Tana ganin yanda wani abu da ya fara taso kai a wuyan shi ya motsa alamun sai da ya haɗiyi miyau kafin
a hankali yace "nayi sallama" ya lashi laɓɓen bakin shi saboda ya gagara sabawa da wannan murya da ba
tashi ba.

"Shine zaka tsaya min sheƙeƙe a kai?!"

Rage tsayin sa yayi ta hanyar sauƙe guiwowin shi a ƙasa yayi zaman tahiya kana ya sake buɗan baki yace
"gani" ai kuwa duk yanda yaso tsuke muryar sai da tayi crack, ya rufe idanu tare da sauƙe kan shi cike da
kunya, shi yasa bai cika son buɗan baki yana magana ba.

Murmushi Saudat tayi don abin nashi ma ya daina damun ta ya koma bata dariya.

"Me kake yi?" Ta tambaya.

"Karatu" ya bata amsa.


Ta san karatun boko yake nufi domin Last year ya sauƙe haddan Alkur'ani, a yanzun kuma yake shirin
zana JSSCE, zuwa SS1.

"Toh daman Aunty ne ta kira ni ɗazu wai tana gayyatar yaran nan badday."

Ya ɗago ya kalle ta tare da kaikaita kai kaɗan yace "wata Aunty?"

"Aunty dai maman Hafsatu"

ta shiga mayar da kayan bayan ta zaɓa wanda Suhail da Sabir zasu saka.

Kenan na birthdayn ƴar ta Reina ce? Shekarun ta uku yanzu! Lallai a kwana a tashi babu wuya a wurin
Ubangiji, last ganin da yayi mata tana tsumma bata wuce watanni biyu a duniya ba.

"Ina za ka iya zaman gidan kai kaɗai? Dan nasan abban ku ma ba zama zai yi ba idan babu kowa, in yaso
sai kayi karatun ka babu takurin kowa.

"Toh shikkenan Umma, sai kun dawo a gaida min da auntyn"

"Zata ji, sai ka ɗebi shinkafa ka gyara ka dafa muku, akwai sauran miyan da nayi jiya a kitchen zai ishe ku,
sai ka ɗuma shi".

Da toh ya amsa yana miƙewa don ya fahimci ta kai ƙarshen zancen ta ya koma jikin littafi kaman ko
yaushe.
Yanzu karatun shine kawai abinda yake yi, domin tun da Abban shi ya samu sauyin aiki ya hana shi zuwa
shagon koyon ɗinki, har umman shi ta so yana siyar mata da kasuwar ta a waje amma ya ƙi, ya hana shi
komai bayan karatu.

Yana faɗa mishi a ko wani lokaci karatu shine gatan shi, shi ba kowa bane idan bayi da Ilimi. Haka ne,
wannan gaskiya ne, duk wanda bayi da ilimi na addini shi ba kowa bane, ilimin addini shine gatan kowani
musulmi. Amma kalamin shi na ƙarshe ya tabbatar mishi da tunanin su yazo bambam.

"Yaseer babu inda zaka je a duniyar nan idan baka da ilimin zamani, haka zaka ƙare ƙasƙantacce, a
wulaƙance,"

Wannan ba haka yake ba, wannan gurguwar fahimta ce. Mutane nawa suka yi arziƙin da ake bugawa a
jarida ba tare da ilimi ko na sakandare ba? Mutane nawa ne suka shiga siyasa ko kwalin jami'a basu da
shi? Sannan mutane nawa ne suke da kwalayen ba ɗaya ba ba biyu ba amma suke kan fama da rayuwa?.

Lallai karatun boko nada amfani musamman a irin wannan zamani da yawancin wurin da mutum zai
shiga a ko ina sai an buƙaci shaidar su? Amma fa ba shine hanyar arziƙi ba, wannan hurumi ne ba
Ubangiji. Ya azurta wanda yaso a lokacin da yazo babu mai tambayar shi me yasa.

Amma tunda burin iyayen nashi shine yayi karatun, zai yi da dukkan lokacin shi, da dukkan ƙarfin shi, iya
iyawar shi.

Sai da ta gama shiryawa cikin leshin da Hajiya Fauziyya tayi mata kyautar shi tun jegon Sabir, don
zannuwan biyu su suka zamo mata na ganin gwamna, bata saka su jdan ba wani wuri mai muhimmanci
za'a je ba. sannan ta shirya yaran suka yi shirin ficewa kafin kuma su sake ɓata jikin su, Yaseer ɗin ya fito
daga bakin ƙofa yana musu Allah ya kiyaye.

kusan karo suka so yi da Kamal, ta dawo cikin tana mishi sannu da dawowa, sannan ya shigo shima yaran
suka yi saurin rungume shi suna oyoyo.

"Har zaku fita"


"Eh ka san maghriba yana yi da wuri yanzu, gwanda muje muyi mu dawo"

"Haka ne. Toh shi yayan mu fah? Banda shi ne?"

"Eh Abbah, ina shirin exams ne" yaseer ɗin ya amsa.

"A'a abu na wuni ɗaya? Yi sauri ka shirya ku tafi"

"Abun yara ne fa Abban Yaseer " ta san da ba gidan su Alhaji Tahir bane koda Yaseer ɗin ya riga ya shirya
hana shi fita zai yi yace mishi ya girma ma ana fita unguwa da shi.

Ko yaushe zai dawo daga rakiyar wannan mutanen ne?

Tabbas rayuwa ta zo musu da sauyi, amma ba irin sauyin da za'a ce mutanen nan sun rungume su hannu
bibbiyu ba. Sauyi na walwalan rayuwa suka samu, sauyin rashin damuwar babu abinda za'a ci gobe.

Sauyin cin mai kyau da kwana a wuri mai daɗi da tsafta.

Amma ko suturar da suke sakawa har yanzu kallo ɗaya zaka yi ma yaran su kayi ma su Yaseer ya
bambance maka ko goma ta zube ta fi biyar albarka.

Kafin ta gama tunani har Yaseer ya shirya cikin wani rigan polo Emrald green da jeans ya taje kan nan ya
saka turare.

Sai Saudat ta gagara fahimtar yayi saurin shiryawar ne Saboda bayi son suna samun saɓani a kan shi
kaman ko wani lokaci ko kuma don yana son zuwan ne da gaske? Saboda bata ga damuwa a kan fuskar
shi ba.
Ta fahimci bayi son zuwa gidan sauran a gaisuwar Sallah ko idan hidima ya tashi an je musu barka. Shi
yasa bata sake cewa ya raka ta idan wurin su zasu je, don itama bata da yanda zata yi ne.

Ɗaukan Sabir yayi a kafaɗa wanda yake tsotsan mintinnda Abban ya kawo mishi.

"Kada ka ɓata min kaya" ya mishi gargaɗi shi kuma ya gyaɗa kai kafin ya cigaba da tsotsar kayan shi.

Laidan hannun shi Kamal ya miƙa wa Saudat, ta buɗe taga packet ɗin sweet ne guda biyu a ciki.

Gashi sai ki basu wannan kuma a gaishe su sosai don Allah.

Karɓa tayi da toh, ya raba sauran wanda ke aljihun shi ma Yaran harda Yaseer don bayi ganin shi ya
girma duk da a yanzun tsaff zasu jera a tsayi saidai ya fishi kaurin jiki.

.....

Tsaye take a gaban kitchen Island ɗin tana jujjuya abu a cikin roba da whisker, amma kallo ɗaya ya isa ya
sanar da cewa bata cikin nutsuwar ta.

A gaban ta cake ne mai hawa uku wanda tayi shi kala daban-daban sannan ta saka butter cream ta haɗe
su wuri ɗaya. Yanzu haka whipped cream da zata lulluɓe cake ɗin da shi ta saka wa condensed milk ta
madara shine take juyawa da hannu.

Amma har ya fara sauƙa saboda sanyin jikin shi ya fara ƙasa saboda jujjuyawar da take mishi ya wuce
iyaka.

Tunanin maganar su da Alhaji Tahir take yi a daren jiya. Hukuncin da ya sake yankewa a kan yaran shi.
Yaran shi mana, tunda ya tabbatar mata bata da iko a kan abinda ya shafi rayuwar su, ikirari yake da su
hakkin shi ne, don haka zan sauƙe wannan hakkin da duk abinda zai iya.
Toh shine kuma hukuncin har ya shafi abin da bai zo duniya ba? Harinyar da sanin jinsin ta ma basu daɗe
ya yin shi ba? Ko shikkenan ita ta dawo injin haifa masa yara bata da iko a kan nata rayuwar ma?.

Ina a kan Reina ne? Ita ce taƙamar shi? Tun da haka ya zaɓa ta fara zuba mishi idanu da shi da Ita tun
tana cikin tsumma kuma zata ci gaba da zuba musu har ranar da za su gane kuskuren su, su juyo ga
gaskiya, idan lokaci bai kure musu ba kenan.

Mangaje ta aka yi har sai da tayi baya tare da tallafo ƙaton cikin ta tana salati. Ba sai an faɗa ba ta riga ta
san waye, ita kaɗai ce mara nutsuwa a baki ɗaya cikin gidan.

A zafafe tace "me yasa baki da hankali ne Reina?! Ban faɗa miki ki daina min guje-guje ba sai na saka
bulala na zane ki?! Wawuya kawai"

Ƙifi-ƙifi tayi da idanuwa don tabbas tana jin tsoron mahaifiyar ta, amma kuma bata iya bada haƙuri ba,
bata san shi ba.

Juyawa tayi zata bar kitchen ɗin da gudu ganin mai aikin da tayi wa rashin kunya ta shigo hannun ta riƙe
da ƙaramin carpet ɗin.

"Ki dawo nan nace miki" ta daka mata tsawar da har ita mai aikin Saida ta razana".

Ta juyo a hankali hawaye na fara bin fuskar ta. "Aunty wayyayi... Aunty wayyayi.."

Idon Hajiya Fauziyya ne ya kai kan rinannen carpet ɗin don itama Reinan shi take kallo.

Ba sai an faɗa mata ba ta san cewa ita ce ta ɓata don yanayin ta ya gwada.

Zagawa tayi ta ƙarasa ta zaro tsintsiyan kwakwa guda biyu ta nufo ta da shi.
Abun ya ishe ta, duka kan sai ta daki Reina idan yaso Tahir ya dawo yayi farfesun ta ya shanye.

Kuka ta saka tun kafin tsintsiyar kwakwan ya kai jikin ta tana tsalle cike da tsananin tsoro "Wayyo Aunty!
na tiga uku!"

Sai ga fitsari tsirrr ta sake shi na tsoro daidai lokacin da aka yi sallama a ƙofar kitchen ɗin dake buɗe
Saudat ta shigo ɗauke da murmushi, Reina kuwa tayi wurin ta da gudu domin ta san duk kitchen ɗin
babu mai iya ceton ta.

Da wani ne yace mishi hancin yarinyar nan zai taɓa tasowa da sai yayi rantsuwa kafin ya musa.

*Saliha Ahmad Na'ibi (seemahwrites)✨*

*REINA 💍*

16....da sauri Saudat ta maida ta bayan ta, ya kasance ta mata shamaki tsakanin ta da Hajiya Fauziyya.
"Dan Allah ki barni in kewaya yarinyar nan Umman Yaseer" tace tana ƙoƙarin janyo Reina daga bayan
Saudat.

Ganin zata iya cin mata daga wurin yasa da gudu ta kauce ta koma bayan Yaseer dake biye da Saudat ta
ɓuya, ta riƙe wandon jikin sa gamm jikin ta na kyarma.

Da wani ne yace masa hancin yarinyar nan zai taɓa tasowa da sai yayi rantsuwa kafin ya musa.

Sai dai ɗan hancin caɓa-caɓa yake da majina saboda kukan da ta sha na tsoro.

"Haba Aunty, kiyi haƙuri mana, wanda ake wa murnan badday kuma ita ake duka?" Saudat tayi ƙoƙarin
tausar ta.

"Idan ba zane ta nayi ba bana jin zata dawo cikin hayyacin ta. Haba! Yarinya kamar wanda ifiritai kewa
fitsari a tsakar ka? Bata ji ko kaɗan? Kiga ta'adin da tayi min fa!" Ta karɓi carpet ɗin tana gwada ma
Saudat.

Karɓan tsintsiyan kwakwar tayi daga hannun ta "yanzu kam ta ji tsoro, ba zata sake ba."

Ta watsa mata harara daga yanda take ɓoye. "Zaki zo a ɗauraye miki jiki ne ko sai na ƙaraso wurin?"

Sai ta ƙara ƙanƙame Yaseer domin ta san idan taje wurin ko da hannun ne sai ta dake ta tunda tayi niyya.

"Kije ba za ta miki komai ba"

Ɗaga kai tayi ta kalle shi, idanun ta sun sake cika da ƙwalla.
"Wayyayi duka na za ta yi"

"Ba zata miki komai ba" ya jaddada mata.

"Toh ka ce wayyayi" ta buƙata don idan ya rantse ta san da gaske yake.

Sauƙe Sabir yayi a ƙasa sannan ya kama hannun ta suka ƙarasa wurin Auntyn, da yanzu aka saka mata
stool ta zauna tana fitar da numfashin ɓacin rai, daman ƙiris take jira.

"Kiyi haƙuri aunty, don Allah"

Harara ta watsa ma Reina sannan tace wa ɗaya daga cikin masu aikin wurin su ɗauke ta suyi mata
wanka.

Sai da taga sun bar kitchen ɗin kafin hankalin ta ya kwanta.

"Ki daina barin karamin abu yana ɓata miki rai a yanayin da kike ciki. Kada ki saka jinin ki ya hau" Saudat
tace tana zuba ruwan da aka miƙo mata a jiki da da kuma ƙafafun ta da suka shiga fitsarin Reina.

Hawan jini na nawa kuma,Tace a ranta. kana ta saki fuska kaɗan tace.

"Ku yi haƙuri kun zo kun same mu kaca-kaca amma yanzu zamu ƙarasa tattarawa. bari a kai ku falon
sama ku sha ruwa kafin a gama kimtsa nan ɗin"

"Kada ki damu wallahi , yaran zasu jira ko a waje ni sai in taya ki da wani abun"
Da faɗar haka, Yaseer ya kama hannun yaran suka fice ita kuma ta ajiye jakar ta da laidar hannun ta a
ƙasa alamun ta shirya ma aiki.

Yanzu kam sosai Hajiya Fauziyya ta saki fuska don ɓacin ranta ya fara washewa.

"Gamu da yawa umman Yaseer sai kin wahalar da kan ki?"

Ƙarasawa jikin cake ɗin Saudat tayi tana kallo "da kan ki kike yin cake ɗin kuma?"

"Eh, amma fa ba na kyauta nake musu ba, biyana suke yi" ta murmusa sannan ta ɗauƙi robar whipped
cream zata mayar da shi fridge don ya ƙara kama jikin sa kafin ta ƙarasa.

Saudat ta hango wasu guda biyu da tayi su tun jiya a cikin fridge ɗin.

"Ah ashe fa kin iya aunty!"

"Ƙaraso ki gani" tace da ita tana wangale mata ƙofofin fridge ɗin, Saudat ta matsa kusa tana kallo cikin
burgewa. Harda wasu doli aka yi masu kyau a kan dogon, guntun kuma an cika saman shi da wafer da
chocolate.

"Ina yin sana'ar gashe-gashe ai sosai tun kafin in yi aure, kuma anyi min ciniki lokacin da ake neman
soyayya ta" tace tana murmushin da ta kwana biyu bata yi wanda ya fito daga ƙasan zuciyar ta kaman shi
ba.

Ita shaida ne a kan soyayyar da Alhaji Tahir yayi mata, irin son da ke saka ta kokwanton ko yana cikin
cikakken hankalin shi.

Amma me yasa auren shi ya fara fita a kanta cikin shekaru biyar kawai duk da irin wannan soyayyar da
yake mata?.

"Ahh kice kin ja ajin ki Aunty"


Gira ɗaya ta ɗaga tana jin kanta tace "sosai ma. Tausayin sa na ji a lokacin na sauƙe farashi"

Ba yi son talaka da talauci ta sani. Ba yi iya ɓoye son zuciyar shi ta sani. Soyayyar shi ya jawo mata baƙin
jini a wurin dangin sa ta sani.

Amma me yasa duka wa'innan basu zamo mata matsala a zaman ta da shi ba sai Reina? Ƴar ta na cikin
ta, ba wai ƴar riƙo ko ƴar kishiya ba?.

......

A hankali yake takawa idanun shi na yaba kyau da tsaruwa irin na garden ɗin. Ga hadari da ya haɗu a
sama yana bada iska mai sanyi wanda ke kaɗa ciyayi, fulawowi da bishiyoyin dake wurin suna bada wani
sauti shuuu mai sanya nutsuwa a cikin kunnuwa.

Jikin lilon dake kafe a tsakiyar wurin yaje ya zauna. Ya ja kanshi baya sosai kafin ya raba ƙafar shi da ƙasa
shi kuwa lilon ya fara yawo da shi a hankali, ya lumshe idanu yana jin daɗin yanayin har cikin gaɓoɓin shi.

Ihun Sabir ya riski kunnen shi kaman daga sama sai kuka kuma ya biyo baya.

Miƙewa yayi sannan ya nufi yanda yake jiyo sautin kukan da gudu, ya kai shi har ƙofar shiga main
parlour na gidan, yanda ya hango Reina tsaye sanye da riga da wando kalar ruwan ɗorawa ga ƙaton cikin
ta da ya bulluƙo ta cikin rigar, tana fuskantar Sabir dake zunduma ihu ga wani abu kalan kashi a fuskar
shi, rigan shi kuma a jiƙe.

"Sabir! Reina! Lafiya?"

Bata firgita da ganin shi ba ko kaɗan, soyayyun idanun ta a kan Sabir ta gwada shi da ɗan tsintsiyar
yatsar ta.
"Gobe ka shake taka ni shai na mammaye ka, dirty boy!"

"Reina!"

Ɗagowa tayi tana kallon shi babu ko digon tsoron da ya gani ɗazu a idanun ta.

"Me kika mishi?"

Water bottle da laidan chocolate dake hannunta ta ɗaga mishi.

"Ina wasa ne ban ssani ba na..."

"Yi shiyu!!" Ta zungure shi tana zazzare idanu. Shi kuwa ba ma iya ganin ta yake yi ba kasancewar
chocolate ɗin ya fara shiga mishi idanu don haka ya rintse idanun gamm.

"Yashin kunya yayi min" ta bada amsa kai tsaye.

"Don yayi miki rashin kunya sai ki jiƙa mishi jiki ki saka mishi abu a ido?" Yace yana rage tsayin shi sannan
ya cire handkerchief daga aljihun wandon shi ya shiga share ma Sabir ido.

Fauce handkerchief ɗin tayi idon ta na kawo ruwa. Sai Yaseer kawai ya tsaya kallon ƙarfin hali, ya dai
samu idon Sabir ɗin ya buɗe.

Da gudu Suhail ya ƙaraso wurin su, daman tare suke a wajen ya bar shi ya shiga ciki da ya ji an saka kiɗa
sai yanzu da aka sake kashewa shine ya dawo.
"Kuje jikin famfo ka wanke mishi fuska" Yaseer ya umarci Suhail da bai san mai ya faru ba tukunna amma
da tuni ya kai wa Reina hannu.

Sai da suka bar wurin kafin shima Yaseer ɗin ya juya zai barta a wurin tayi saurin riƙo ƙafar wandon shi.

"Ai gidan mu yajo"

"Okay, haka kike yi ma duk wanda ya zo gidan ku? Shikkenan, ba zamu sake zuwa ba balle idan Aunty
zata zane ki in ƙwace ki"

"A'a kai kajo amma ban da shi"

"Shi ba abokin ki bane? Yazo miki Birthday ne fah"

"Ni dirty boy ba aboki na bane. Umma ta ce duk dirty boy talakawa ne"

Bai san waye umman ba amma numfashi kawai ya ja tausayin ta na kama shi, saboda mutanen da ke
zagaye da ita basu da hankali.

Ya sauƙa a kan guiwar shi ɗaya don ya daidaita tsayin su duk da a hakan ma yayi mata rata sosai amma
ta fi Sabir tsayi.

Kafaɗun ta ya riƙe duka biyu ga hawayen rashin gaskiya dake bin fuskar ta.

"Kina so in sake dawowa?"

Gyaɗa kai tayi.


"To ki bawa abokin ki haƙuri kuma kada ki sake cewa kowa talakawa"

Maƙe kafaɗa tayi. "O'o ban bashi akuyi ba"

"To shikkenan babu ruwana da ke" zai miƙe tayi saurin riƙo hannun shi.

"Kai ka fa'a wa Aunty pleash"

"Toh idan kika bashi haƙuri ba zan faɗa mata ba."

Hannun riganta ta saka ta share idanun ta sannan cikin dakiya tace.

"Ni ban bashi akuyi ba, ai shi ya faya taka ni"

Laɓɓan bakin shi na ƙasa ya ciza kafin ya kira sunan ta "Reina. Idan aka yi miki laifi ƙara zaki na kaiwa
wurin babba kin ji ko?"

Ta gyaɗa kai.

"Toh muje ki bashi haƙuri"

Ta maƙe kafaɗa.

Girgiza kai yayi cikin rasa abun yi.


Zai sake magana ta ƙwala kiran "Daddyyy" kana ta kwace jikin ta daga riƙon shi ta ruga a guje ta faɗa
jikin Alhaji Tahir wanda ya buɗe mata hannayen shi.

"Sarauniya tah!" Ya shiga juyi da ita a wurin yana bin fuskar ta da sumba ita kuma sai ƙyalƙyala dariya
take yi.

Sauƙe ta yayi ya buɗe bayan motar da ya dawo a cikin ta sannan ya fito mata da farin teddy bear mai
riƙe da jan heart a cikin shi, a jiki an rubuta Reina @3. Ta karɓa cike da murna sannan ta rungume a ƙirjin
ta tana tsalle.

"Thank you Daddy"

"You're welcome my queen"

Ya ɗauke ta da dolin da suke tsayi ɗaya yana faɗin "muje ciki kiga sauran gifts ɗin ki ko?"

"Yayyy" ta fara zillon daɗi a jikin shi kamar wacce take kan doki.

Sai lokacin hankalin shi ya dawo kan Yaseer dake tsaye a wurin yana bin su da idanu.

Lokaci ɗaya Alhaji Tahir ya haɗe fuska ya watsa mishi wani kallo kafin ya wuce ciki da sarauniyar shi.

......

"Ina yi don in samu kuɗi na amma ba ra'ayin wannan kalolin bidi'ar nake ba. Haba ace abu duk shekara
babu fashi? Har na wata shida sai da ya saka aka yi mata fa."
Ta san akwai ne ya saka ake yi amma ko da ace tana da shi, da zata iya ɗin, ita kam abun yayi yawa
kuma, bai bata sha'awa ba. "Amma da sadaka kuke mata kawai a ranar badday ɗin. Ko idan aka yi biki
wannan shekarar a wani sai ku kai kuɗin yanda za'a yi mata addu'ar albarka ma rayuwar ta"

"Ina ƙoƙarin yin hakan tunda duk abinda nace ba fasawa zasu yi ba. Kayan ta ma idan aka cire akwai
wani gidan marayu da nake kai musu sai in haɗa musu da wani abun."

"Toh hakan yayi. Allah yayi mata albarka ya ƙara shirya mana zuri'a. Tarbiyya ne a wannan zamani ba
abu ne mai sauƙi ba"

Matse baki tayi tana ajiye piping bag ɗin hannun ta wanda yanzu ta gama frosting ɗin cake ɗin, sprinkles
kawai ya rage ta zuba mishi ya ƙara haskawa.

Ta kalli Saudat, tana son ta buɗe mata cikin ta ko zata samu mafita, ko zata samu shawara, ko da rage
damuwar ta ne ta samu tayi, amma bata san ta ina zata fara ba.

"Umman Yaseer" ta kira ta da wani irin muryar da ya sanya ta raba hankalin ta daga jikin cake ɗin da ta
gagara gaskata cewa a kan idanun ta aka yi adon shi tun daga farko har zuwa ƙarshe, ta ɗora su a kan
Fauziyya.

"Na'am"

Ajiyar numfashi tayi kana tace. "Abban Reina Ya..."

"Mai kuma na yi?"

Yace yana shigowa cikin kitchen ɗin ɗauke da ƴar gudaliyar shi.

Miƙewa tayi. "Babu komai, Sannu da dawowa"


"Yauwa matar aljannah" ya ƙaraso ya sumbaci goshin ta ya matso da Reina ma da nufin itama ta
sumbace ta amma mugun kallon da Fauziyya ta watsa mata ya saka ta juyar da kanta daga kallon ta
bakiɗaya.

"Daddy mu je a yanka cake" tace don su bar kitchen ɗin.

"Shikkenan, bari in canza kaya ko?"

Yayi ƙorarin sauƙe ta amma firr ta maƙe shi.

Sai a sannan Saudat tayi ƙoƙarin gaida shi sai dai ko jin ta ma baiyi ba don hankalin shi bayi kan ta.

"Fauzah me kika yi ma yarinyar nan a bayan ido na?" Ya bita da kallon tuhuma ganin tsoron da ke tattare
da Reina.

"Ni babu abin da nayi mata, amma Allah ya ƙi ki kishiga hannu na Reina"

Ya ware idanu "Oh a gaban idanu na kike faɗan haka Fauziyya?"

"Ka tambaye ta abin da tayi tukunna, me ya haɗa ta da iyami? Ai gashi da ta san bata da gaskiya ai ɓuya
take yi a jikin ka"

Ba wai don yaji laifin tan ya tambaya ba, sai dai kawai don ya san me ya haɗa ta da wacce aka kira da
iyamin tunda yana da tabbacin mai aiki ne. Masu aikin da ya kafa musu sharaɗi a kan ta, kuma duk
wacce ta tsallake wannan sharadin toh a bakin aikin ta ne.
"Me ya haɗa ki da ita Reina?"

Shiru tayi tana cin farcen hannun ta cikin fargaba kada Daddyn tan ma yace hukunta ta zai yi.

"Ta yi min yashin kunya ne shine nace Uwar ki!"

A tare Saudat da hajiya Fauziyya suka riƙe baki cikin kaɗuwa don basu san da wannan zancen ba, sai dai
zasu iya cewa tambayar da Alhaji Tahir yayi ma Reina shine abin da yafi kaɗa su fiye da wannan
nannauyar ashariya.

"Wani irin rashin kunya tayi miki?" Shine abin da ya tambaye ta.

"T!!!. Fisabillilahi baka ji abinda tace bane? Ni na koya wa Reina ashar ko kai da ba zaka tambaye ta a ina
ta koyo ba?."

Ya buɗe baki zai yi magana, ya dubi Saudat da ta kafe idanun ta a kan kantar kitchen ɗin tana jin dama ta
dawo tsuntsuwa tayi filfili ta bar musu wurin.

Sai kawai ya fasa, suka juya da Reina suka bar mata kitchen ɗin, yayin da ƙafafuwan Fauziyya suka gagara
ɗaukan ta ta koma jikin kujerarta ta zuba a kai idanun ta a jikin ƙofar kamar sun fita sun bar tabon zagin
ne a wurin.

"Na shiga uku!"

......

Bakin ta da na mahaifin ta har kunne, hannun Reina cikin na Fauziyya, nata kuma cikin na Tahir suka
yanka cake ɗin bayan an ƙirga musu daga ɗaya zuwa uku. Nan kuwa wuri ya ɗauki tafi da suwwa Dj ya
cigaba da aikin shi.
Dukkan su uku suna cikin shiga ta alfarma musamman ita celebrant dake cikin wata buɗaɗɗiyar riga mai
walwali iya guiwa kalan emerald green. Kanta da tiara kalar rigar, sai kuma fairy wand da ta riƙe irin dai
na fairy ɗin cikin cartoon ɗin da take son gani mai suna tinkerbell.

Cake ɗin ya fara yanka ya kai bakin Reina ta gutsura sannn itama ta karɓa ta kai bakin mahaifin ta, ya ci
ya goge hannun ta saboda kada ta ɓata jikin ta kafin aka shiga haska su da kyamarori. sun ma manta da
duniyar Fauziyya a wurin, wanda itama a nata ɓangaren ta manta da tasu duniyar.

Cikin gidan da haske sosai amma gari ya gama baƙiƙƙirin hadari sai ƙugi yake, kiɗan da ya cika falon ya
hana su jin buƙatuwar da ruwan sama yake da shi don ya sauƙar da Ni'ima.

Ji take yi duk girman gidan kaman so yake yi ya matse ta, numfashi yana niman kasa mata, ga zufa dake
yanko mata a cikin sanyin Ac da kuma ruwan da ya kece yanzun kaman da bakin ƙwarya.

Daman yanayin damina ya saka su yin hidimar a ciki, ta fara takawa a hankali saidai tana jin ƙafar ta
kaman ba a kan ƙasa yake tafiya ba.

Su Hajiya Farida da suka gama kashe hoto yanzu suka nufo ta suna maganganu sai dai ba zata iya fayyace
me suke faɗa ba. Ba ma zata iya gane su waye a kan ta ba.

Ita dai kawai ta san ganin ta yana dishashewa a hankali har ta daina ganin komai, ta daina jin komai,
sannan ta daina tunanin komai na wani lokaci.

Baki ɗaya mutanen parlourn kowa yayi kanta, Alhaji Tahir bai san lokacin da ya dire Reina a wurin ba, ya
shiga tutture mutanen da suke tsaye a hanyar shi na ƙarasawa gare ta sannan ya zuba a kan guiwowin
shi yana bubbuga fuskar ta cikin tsananin tashin hankali da firgici.
Goran ruwan da ɗaya daga cikin mutanen tayi hankalin miƙowa ya karɓa ya shiga shafa mata amma inaa
babu numfashi. Ganin ɓata lokacin shi kawai yake yi yasa ya ciccibeta da zungureren cikin ta suka yi
hanyar waje da gudu mutanen ma suka bisu yuuuu.

~~~~~~~~~~~~

*Ku faɗa min idan akwai gajiya mu ajiye posting sai bayan Sallah. Wataƙil ko shi yake hana yawan
comment*

*Saliha Ahmad Na'ibi Seemahwrites ✨*

*REINA 💍*
17...... A cikin ruwan nan? Ga yara, mura ya kama su a ɗaura min jinya? Ai sai dai idan ya lafa ko kuma
gobe ma je" Hajiya jummai ke wannan bayanin bayan Alhaji Tahir ya cicciɓi Hajiya Fauziyya sun yi asibiti.

Daga farko sun bi shi yuuu kaman sun damu amma yana shiga cikin mota da ita dukkan su suka dawo
ciki.

abokan arziƙi kam da suka gayyato duk sun bi su a baya cikin motocin su, sai matan ƴan uwan shi aka
bari kawai da yaran su, cake ɗin da aka fara yankawa ma suke ta kasawa a tsakanin su da ma sauran
kayan taɓa ka lashe.

sai kuma su Saudat da basu da tasu abin hawar kuma ƙarfin ruwan ba zai bari su fita har can babban
hanya su samu keke napep ba, Amma hankalin ta dama Yaseer a matuƙar tashe yake don gani suke yi
kamar ba zata tashi ba.

Amma fah duk cikin wannan tashin hankalin bata ga Reina ba, lokacin da iyayen nata suka fita ta so ta bi
su da kukan ta aka ɗauke ta amma tun daga nan bata sake ganin ƙyallin ta ba.

Sai dai Babu wanda ma ya lura, ta kansu kawai suke yi. Na musamman suka ɗauko foil paper a kitchen
suna ƙunshe abin da suke buƙata a wurin don suna da tabbacin bikin birthday ta watse.

Ƙarasawa ta yi wurin da Yaseer ya haɗe kan ƙannen sa ya nutsar da su wuri guda, saboda banɗashen da
ake a wurin ya fara jan hankalin su.

ta taɓa shi. "Ka ga Hafsatu?"

Miƙewa yayi ya bi ko ina da kallo amma babu ita babu alamun ta. "Ko sun tafi tare?"

Ta girgiza kai, "taya ni mu duba ta"

Sai da ya kashe ma Suhail warning don ya fi Sabir kwaɗayi da fitina kafin suka raba hanya suna dubawa.
Suna barin parlourn Ƙofar shi ya buɗe duk idanun wanda ke cikin ta ya kai wurin, kar dai ta farfaɗo ne
suka dawo!. Amma ganin yaran da suka fara shigowa ya saka su sauƙe ajiyar zuciya kafin Hajiya Hauwa
ta biyo bayan su, tana karkaɗe ruwan da ya taɓa ta daga mota zuwa cikin gidan.

"Amma baki iya kiwo ba wallahi" Cewar Hajiya Farida dake lulluɓe kajin da ta tattare kaman babu a gidan
ta.

"Kada ki ce min an ci an cinye babu ni dan Allah, aiki ne ya min yawa a office Wallahi" tace tana
ƙarasowa kusa da su.

" ko zama fa ban yi a gidan ba daga canza kaya na kwaso yaran muka zo"

"Hmm ba wannan ba, show muka sha. Acting dai ko a Bollywood albarka mutuniyar ta iya shi"

Ta bata hannu suka sha kafin ta ce "dan Allah bani in sha, yau kuma wani episode kuka gani?"

"Ina irin scene ɗinnan da mace zata yi suman ƙarya ta ɗaga hankalin miji ya tattare ta sai ta kanne ma
muguwar sirikar ta idanu da murmushin cin Nasara?..."

Hajiya Hauwa ta gyara zama tare da gyaɗa kai.

"Toh fa episode din aka gwada mana a zahiri"

Suka yi shewa tare da sake tafawa, Hajiya Hauwa ta taɓe baki cikin ranta tana takaicin missing wannan
show da tayi.

"Toh mune mugayen sirakanan kenan?"

Hajiya Lubabatu ta tambaya, tana saka abun da bai samu shiga jakar ta ba a cikin na ƴar ta.
"Toh wa ya sani. Idan ma an kanne mana idanun mu dai bamu gani ba"

"Hajiya nace ban ga Rai na ba" Saudat tace daga bayan kujerar da Hajiya Jummai ke zaune.

"Idan ma zuciyar ki ne baki gani ba ina ruwana! Shine zaki tsaya min sheƙeƙe a ka?" tace tana juyowa ta
fuskance ta.

Amma Ashariyar da ta mulmulo mai zafi ya saka duka hankalin su ya dawo gareta.

Bai kai ga hucewa ba Hajiya hauwa ta rako shi da wani.

"Ke Saudatu, uban wa ya baki kayan da ke jikin ki?" Hajiya hauwa ta tambaya tana kallon leshin jikin
Saudat Saboda jiƙewar da hijabin jikin ta yayi tun ɗazu ta kai shi kitchen ta shanya, damuwan gaban su
yasa basu lura da ita ba sai yanzu.

Gwada Saudat da yatsa Hajiya Farida tayi ta juya ta gwada Hajiya Hauwa dake sanye da irin lace ɗin sakk
kafin ta tuntsire da dariya.

"Uban waye ya kyautar da ashoben shi a cikin ku bai sanar da ni ba ya saka ni anko da mutanen
karkara?" Ita dai yau bata fito a Sa'a ba.

Kafin ta kai aya Hajiya Lubabatu ta fara girgiza mata hannu ganin tana niman wuce gona da iri "A'a kama
kan ki ki iya bakin ki baiwar Allah. Idan ba ƙaranta da rowa ba ma wa ke ajiye sutura har tsawon shekaru
3?"

Ba zata iya jiran su, su gama musayya a tsakanin su ba don haka ta kawar musu da shakkun da suke da
shi.

"Hajiya Fauziyya ce ta bani, kuma ya daɗe a wuri na ba kunce bane. Yanzu haka kuma ƴar ta nake nima
na rasa, mun duba baki ɗaya gidan da ma'aikatan ta bamu ganta ba"
"Ko dai mahaifin ta ya ɗauke ta sun tafi tare?" Hajiya Farida ta fara shan jinin jikin ta domin rikici idan ba
da kai ake ba ya fi daɗin kallo. Tana tsoron wani abun ya rutsa da ita a cikin gidan nan don Tahir ba
mutunci yake da shi ba.

Kaman ta tambaya a kunnen shi sai ga kiran shi ya shigo wayar Hajiya Lubabatu.

Tsawa ta daka ma yaran dake ta hayaniya tare da saka yatsa a saman bakin ta, nan wurin yayi tsitt kafin
ta danna ta amsa kiran.

"Hello Tahir, ai ina ta ƙoƙarin kiran ka ya ƙi shiga, yaya Fauziyyar ta farfaɗo? Mu ma gamu nan mun kusa
isowa"

Yarinyar ta dake daga gefe da ƙyar ta iya ƙunshe dariyar ta jin yanda mahaifiyar ta ke yanko ƙarya, ga
muryar ta ya canza zuwa na damuwa lokaci ɗaya.

Ta cikin wayar Alhaji Tahir yace "sun shiga ta ita tiyata kafin a rasa abun cikin ta. Dan Allah Addah idan
akwai wa'inda suka rage a gidan su duba mana Reina a zo mana da ita." Daga jin muryar shi ka san ya ci
kuka ya ƙoshi. Kafin ta sake cewa wani abu ya katse wayan.

Nan suka bazama niman ta har ɗakunan sama amma shiru, zuwa lokacin kam da gaske hankalin su ya
tashi. don haka Yaseer ya fita cikin ruwan ya sanar ma security, babu ɓata lokaci suka sako rigan laida da
tochila sannan suka shiga zagaye gidan.

Haske ya dallara ma abun da ya gani yana motsi cikin duhun rumfar wurin.

Ta rintse idanun ta tare da kare fuskar ta da hannun ta, sai ya sauƙe hasken kana ya ƙarasa wurin cikin
sassarfa.

Sake haskata yayi da isar shi don ya tabbatar da lafiyar ta. Kayan jikin ta da ya kasance kalar rigan jikin
shi a jiƙe, amma har ta fara bushewa saboda daɗewar da tayi da samun mafaka.
Sai kuma ƙaramin cake ɗin nan ta ɗauko shi sukutum ta ajiye a gaban ta ga hannun ta na hagu da take
cin cake ɗin da shi yayi dama-dama.

"Me kike yi a nan?" Ya tambaye ta a dake.

Hannun tan ta ɗaga mishi don ya gani da idanun shi. "K...ket ina ci" tace muryar ta na rawa ko na tsoro
ko kuma na sanyi.

Ya san magana da ita ma ɓata lokaci ne don haka ya riƙo hannun ta mai kyau ɗin.

Ƙoƙarin tirjewa ta fara yi. "Aunty duka, ta hana cin ket"

Sai jikin shi yayi sanyi tuna halin da Auntyn take ciki.

Yanzu idan wani abu ya same ta tabbas koda wasu sun riga Reina kukan rashin ta Saboda ƙarancin
shekarun ta, amma babu wanda kuka da kewar shi zai kai nata tsayi. bayi mata fatan tashi cikin maraicin
uwa, domin wahala yake da shi duk irin daular da kake ciki kuwa.

"Muje zan bata haƙuri ba zata dake ki ba"

Ɗazu ma da ya roƙa mata Auntyn bata dake ta ba dan haka yanzu ma sai ta gyaɗa kai.

"Toh ɗauka min ket ɗin"

Babu musu ya ɗauka.

"Goye ni"
Sai da ya ja numfashi kafin ya tsuguna a gaban ta, ta hau bayan shi ta kwanta luff don sai yanzu ta fara
jin sanyin na ratsa ta.

A haka suka isa parlourn yanda mutanen cikin ta suka yi kansu yuuu.

Bai samu damar sauƙe ta ba Hajiya Lubabatu ta fisgo ta da ƙarfi har sai da ta saki ƙara tace "ke sake ni!"

Bata saurare ta ba ta raɓa ta a kafaɗa sannan ta fara bin Yaseer da kallon tuhuma.

"A ina ka samo ta Yaseer?" Saudat ta tambaya.

Ya buɗe baki zai amsa Reina ta amshe da "Yatir ne ya kai ni cin Ket"

Sai ya ɗan waro idanu jin yanda ta juye laifin kan shi.

Kiran Alhaji Tahir ne ya sake shigowa don haka ba su bawa abinda tace muhimmanci ba tunda a gaban
idon su ya fita nemo ta don haka basu kawo komai ba a ran su, suka yi shirin tafiya asibitin don ruwan ya
tsaya.

......

_Tsakanin Gini da Rusau_

_Tsakanin Rayuwa da mutuwa_

Wani ɗan sanyi ne mai sosa jiki ya ratsa ta kafin komai ya fara. Tana jin shi a sihirce, yana shige mata
cikin ƙashushuwa da ɓargo.
Idonta a rufe, zuciyarta na kaɗawa kamar na mutum da ke neman gudu amma ƙafafunsa na sarƙe da
igiya.

A hankali.. wani haske mai sanyi ya fara bayyanuwa a cikin duhun zuciyarta. Muryoyi masu nisa suna
mata raɗa a cikin kunnuwar ta. Tana ƙoƙarin buɗe ido amma sun yi mata nauyi. Ta so ta motsa hannunta
amma tamkar an daure ta da karfe. Sai zuciyarta ta hau bugawa da ƙarfi – da sauri – da ƙarfi – da azama!

Cikin kankanin lokaci, jikinta ya hau karkarwa. Haƙoranta suka matse da ƙarfi, fuskarta ta tsame, ta soma
jan numfashi a wahalce.

"Fauzah! Kina ji na?" Allhaji Tahir ya damƙi hannun ta sannan ya shiga girgiza ta a hankali, kaman idan ya
kira sunan ta zata buɗe baki ta amsa komai ya dawo dai-dai.

Alhaji kalabu da suke tare a ɗakin ne yayi dabaran danna abun kiran likita daga jikin gadon da take
kwance.

Babu ɓata lokaci har su biyu suka shigo ɗakin da gudu suka yi kan ta.

“Convulsion!” likitan ya faɗa, yana kallon agogo.

“Postpartum eclampsia. Magnesium sulphate, yanzu!”

Ɗayan yabi umarnin shi ya shiga haɗa abun buƙata don sun tsammaci hakan ganin yanda jinin ta ya hau
ga halin da aka kawo musu ita asibitin.

Shi kuma ya fara lallaɓa Alhaji Tahir ya fita ya basu wuri, domin baki ɗaya ya gama rikicewa.
Cikin mintuna kaɗan aka dora mata drip, aka saita na’urorin kulawa. Hancin ta na yoyo, idonta a buɗe
amma ba ta ganin komai. Jikinta na rawa kamar wacce take tsaka da cin karo da wata duniya marar
iyaka.

A can cikin zuciyarta kuma, tana jin wani murya... mai sanyi, mai laushi.

“Fauziyya! Reina na jiranki. Maama ta zo duniya, amma ke ce ke da ita, na yi alƙawari.”

Luff idanun suka koma suka lumshe, a hankali jikin ta ya sake, ta ja dogon numfashi kafin a hankali
numfashin nata ya daidaita.

.....

Tsoro yake yi kada yanzun ma ta sake tashi a yanayin da zai ɗaiɗaita zuciyar sa.

Duk da cewa yana da jibgin ayyukan da basu rabuwa da shi a kullum, duk da ba rasa masu kula da ita aka
yi ba amma ya gagara matsawa ko nan da can.

Ya kasa ci ko shan komai, ko Sallah ma a ɗakin yake yi.

Idan wani abu ya samu Fauziyya yaya zai yi da jaririyar kwana biyu? Yaya zai yi da Reina? Ba wannan ba
ma yaya zai yi da kan shi?.

Ummi ne ta shigo da basket ɗin abinci. Ya share hawayen idanun shi tare da jan hanci kafin ya gyara
zama yana mata sannu da zuwa.

Ƙura masa idanu tayi yanda ya faɗa ya zabge a cikin kwanaki 2 kacal, kafin ta saki murmushin da bai kai
zuciyar ta ba.

"Idan damuwar da kake ciki har ya kai ka dawo haka Tahir ni kuma in ce mene?"
Kallon ta yayi sheƙeƙe, ba don matar nan ita ta haifi Fauziyya ba da yace bata da hankali. Yaran ta nawa?
Yanzu ko mutuwa Fauziyyar tayi ai bata da asara amma shi ita kaɗai yake da, Kuma bayi jin akwai kamar
ta a faɗin duniya. Ta ina ma zai fara hango rayuwar Reina a hannun kishiyar uwa?...

"Gashi cinye min yanzun nan" ta katse tunanin shi ta hanyar miƙo mishi plate mai ɗauke da tuwon semo
miyan taushe.

"A ƙoshe nake Ummi"

"Toh zaka fita ka bar min ɗakin nan kuwa. Kuma ina da hurumin Shari'a da kai a kan dalilin da yasa kuka
bari hawan jini yayi mata tsanani har ya jawo mata sarƙewar haƙori ba tare da sanin mu ba. Idan
Fauziyya tana da ƙaramin tunani kai ma shi gare ka?"

Karɓan plate ɗin yayi yana jin nauyin ta na ƙaruwa mishi.

Yana taryo watannin baya tabbas da laifin shi a cikin damuwar ƴar ta, da ya fahimci tsananin ta yayi
yawa a kan Reina, da yake ganin kamar son ta ne bata yi, ga wasu salon takurawa da ta ɗaura mata da
sunan tarbiyya.

Yayi kuskure da ya biye mata suka dinga samun saɓani da tsohon ciki a jikin ta. Amma gani yake yi komai
lokaci ne kuma a hankali Reina zata girma, zata yi hankali, zata yi ilimi, kuma duk wani rashin ji zata bar
shi. Duk wannan aikin lokaci ne kawai, kuma kowa da haka ya fara.

Yana gama cin abincin kuwa ta fita da kwanon ba tare da ta sake ce da shi komai ba, babu wani nasiha,
darasi ko faɗakarwar da ya wuce halin da ya shiga a yanzu, idan bai canza daga wannan ba toh tayi imani
babu abin da zai saka shi ya canza.

Saudat sun je gaisuwa asibitin lokacin har Fauziyya ta farka amma bata umm bata umm-umm, sai-dai ta
bi mutum da idanu kawai. Amma zasu iya cewa wannan shine karo na farko da suka miƙa gaisuwa ma
Alhaji Tahir ya amsa girma da arziƙi, duk yayi wani sanyi kaman ba shi ba.
Sai da jaririya tayi kwana huɗu a kwalba kafin ta fara shiga hannun mutane, Alhaji Tahir ya saka mata
sunan mahaifiyar sa Zainab ana mata alkunya Da Maama kamar yanda suka riga suka tsayar da Hajiya
Fauziyya.

Tun da ta farka bata buɗi baki ta ce komai ba har sai lokacin da aka saka mata Maama a hannun ta.

"Hafsatu na kin daina kuka?" Ta tambaya maganar na fitowa a hankali ɗaya bayan ɗaya, fuskar ta na
bajewa a sannu murmushi na bayyana a kan fuskar ta.

Matso da Reina dake boye a bayan ta Ummi ta yi zuwa gaban gadon don tsoron yananin Fauziyyar take ji
har ran ta.

"Ga Hafsatu nan" tace mata.

Sai ta ɗago ido ta kalli Reina lokaci ɗaya tana haɗe giran sama da ƙasa. "Wa ya koya miki zagi? Yau sai na
zane ki a gidan nan!"

Ai kuwa ta callara ƙara ganin Fauziyyar tayi wani yunƙuri kaman zata cafko ta, ta koma bayan mahaifin ta
a guje tana kuka, ita kuma zafin fama ɗinkin ta ya saka ta miƙewa a gadon tana cije baki, Ummi ta karɓe
Maama a hannun ta kwalla na cika idanun ta.

Ta san hatsarin sarƙewar haƙori, ta san illar da yake wa rayuwar mutum. Yana raba mace da hankalin ta
ko rayuwar ta baki ɗaya. Wata kuma daga wannan jinyar toh tayi ta fama kenan har tsufa ko mutuwa su
riske ta.

....

Satin Fauziyya biyu a asibiti kafin aka sallame ta suka maida jinyar gidan su. Daga farko Alhaji Tahir ya so
yayi musu tawaye a nan ne Ummi ta tsaya ta nuna mishi iyakar shi.
Kuma da yake bata son ganin Reina a kusa da ita ko kaɗan da ta ganta zata fara masifa wani lokaci tana
yi tana kuka, ya saka Alhaji Tahir tafiya da ita kuma yaƙi kowa ya karɓe ta a cikin ƴan uwan shi, sai dai ya
ajiye ta a wurin su idan zai je aiki da ya dawo yazo ya ɗauke ta su tafi gida.

Idan aka ce a daddafe yayi wa'innan kwana sittin an rage ma tashin hankalin shi girma.

Tun ranar da Fauziyya ta faɗi bai sake sanin abin da ake cewa nutsuwa da kwanciyar hankali ba balle
wani abu wai shi farin ciki.

Gidan ya rikice, duk da Reina tana da nanny Amma a rikice take shi kam ba'a ma magana don a office ma
ba gane mishi ake yi ba.

Yayi ziryan gidan su har ya gaji, sai dai a bashi Maama su ƙarata, ga yarinyar babu ruwan ta, bata iya
rikici ba sai barci kawai.

Fauziyya kuma idan ta fito su gaisa minti 15 yayi yawa za'a maida ta ciki da sunan wanka, shan magani
ko wani abun.

Ba zallan ramewa ba zuwa wannan lokacin har baƙi yayi.

Yau kam ya kuɗurta a ran shi idan basu bashi matar shi ba, waliyyan shi zai turo su ji ba'asi.

*Saliha Ahmad Na'ibi (Seemahwrites)*


*REINA 💍*

*Wannan shafin tukuici ne a gare ku, Maryam gambo da ƙawata Mrs Jay Kakan Reina😅. Ina godiya 💕*

18...... A jikin motar shi ta jingina tare da goya hannun ta a saman ƙirji kaman wacce tazo hira wurin
saurayi.

Tana sanye da baƙar abayar da ya ɗauki hasken fatar ta ga wani haiba da tayi wanda yake tabbatar mishi
da tana cikin hutu da kwanciyar hankali bayan ta bar shi da Reina a cikin ƙunci da Rashin walwala.

"Fauzah?!" Alhaji Tahir ya kira ta cike da mamaki ganin har da taunar chewing gum take, ko Fauziyyar
shekaru biyar baya ba haka take ba.

Sai da tayi ƙoyi da chewing gum ɗin ta hura shi ya kumbura ya fashe kafin ta tauna shi ya bada sautin
ƙasss. Kana ta amsa da

"Na'am my T. Ina wuni"


Ya jinjina kai tare da faɗin "gaskiya ne. Fauzah kin manta da kina da ƴa a wata uwa duniyar, da aure na a
kan ki amma kin dawo gida kin yi zaune abun ki, shin rashin lafiya ya tafi da tunanin ki ne ko me?"

Ta jinjina kai, Tahir dai ba zai canza ba. Wahala da daɗi ba za su saka shi ya daina son kan shi ba. Shi kan
shi kawai ya sani, a kan son zuciyar shi kawai yake jajircewa ba tare da damuwa da yana cutar da wanda
yake tare da su ba.

"Wata ƴa wai? Ga yarinya ta nan Maama, ai Reina kam taka ce, na bar maka ita halak malak".

Ya gyara tsayuwa, yana son yayi mata uzuri amma ya kasa. Ciwo ba hauka bane.

"Mu shiga mota mu yi magana" ya riga ya yanke shawarar da ta shiga locking motar zai yi ya gudu da ita,
in yaso daga baya su biyo ta da Maama, amma wannan rainin hankalin ya gama isar shi.

Kaman ta karanci zuciyar shi, ko dan halin shi ta karanta ne?. Sai kawai ta saki murmushi mai sauti kafin
tace "A'a nan ma ya Isa T. A cikin gida muke, me kuma zamu sirrinta a cikin mota da ranar Allah. Bari dai
in ɗauko mana kujera mu zauna" ta juya zata tafi ya riƙo hannun ta.

"Fauzah ko wani abu kika fara sha ne?"

Da mamaki ta kalle shi amma murmushin dake ƙara tunzura shi bai bar kan laɓɓenta ba tace "me kuwa
zan sha da bani sha a gidan ka? Garau nake"

"Naji, koma meye ki yi, amma yau ba zan bar ƙofar gidan nan ba tare ke ba"

"Tohhh, gashi kuwa Ummi bata min izinin tafiya ba"

"Da ni da Ummi wa yafi wani iko a kan ki?" Taku biyu, sai gani tayi ya cika mata idanu. Anya zata iya isar
da wannan saƙon nata? Ba salon da ta saba da shi ba kenan, tafi ganewa yin magiya da kuka ya mata
abin da take so. Amma tunda sun rage yin aiki a kan shi dole ta bi shawarar Ummi ta dake don tseratar
da hankalin ta da rayuwar ta.

Sai da ta hadiyi miyau kafin cikin ƙarfin halin da ta ƙi bari ya gwada raunin ta a fuskarta tace "kaine
mana, amma iyaye na a yanzu sun goya min baya, ko me ya faru tsakani na da kai zasu bani mafaka. Don
haka banyi niyyar komawa a yanzu ba sai ka ƙara min lokaci" da ƙyar ta kai kalmar ƙarshe don gani take
yi yanda yake huci kamar zai ɗaura mata mari.

"Ni kike faɗa ma wannan maganar Fauziyya? Baki da hankali ne?"

_A'a tarbiyya ne bani da shi, ba'a nutsu an bani ita yanda ya dace ba. Duk da ni ba ƴar kowa bace da irin
riƙon da kake wa taka ƴar iyaye na suka yi min da yanda rayuwa ta da kai zai kasance kenan. Sai abin da
na so, a lokacin da naso, sannan babu kunya da fargaba a cikin lamari na. Ba zan juri ladabi da biyayya ba
domin ban saba da yin shi ma na gaba da ni ba tun a gida. Kalaman kan harshe na babu daɗi saboda ban
iya tace su a rariyar sanin ya kamata ba, duk kaifin abin da yazo kan ta haka zan watsa shi ma duk wanda
ke tare da ni ba tare da damuwa da girman shi ko matsayin shi ba._

Wannan sune abubuwan da take son faɗa mishi a wannan gaɓar, Sai dai idan ta faɗa din da harshe ba
lallai ya ɗauke su ba balle yayi amfani da shi, kamar yanda suka saba yi a baya.

Don haka mai hankali shi ke gane karatun kurma, gwanda ta nuna mishi hakan a aikace ya ji dafin illar shi
a jikin sa.

"Ka san ance rashin lafiyar da nayi yakan taɓa ƙwaƙwalwa, toh hala shine"

"Ai naga alama kam. Bari in tafi kafin ki shafa min ko kuma in yi miki abun da banyi niyya ba" yace tare
da danna key ɗin motar shi yayi ƙaran buɗuwa. Yau ko driver bai ɗauko ba saboda da niyyar kidnapping
ya zo, amma banda ɓacin rai babu abin da ya samu.

Ya shiga ya kunna motar yayi reverse, ta kwala kiran yara daga ciki su zo su buɗe masa gate. Sannan ta
shiga ɗaga masa hannu tana bye bye da faffaɗan murmushi a kan fuskar ta, har da hura masa kiss ɗin da
ya ƙara kawo shi har wuya, ya zugi motar da ɗan iskan gudu yana jin kaman zai tashi da wuta idan bai yi
ya bar unguwar ba.

Yana fita ta zuba a kan guiwowin ta hannun ta a kan zuciyar ta dake bugawa a tamanin-tamanin tana
maida numfashi, bata taɓa tsorata da yanayin shi ba kamar na yau, Amma tun da an ƙare lafiya falillahil
hamdu, yanzu fata ɗaya ya rage shine Allah yasa yayi amfani.

.....

Gidan Hajiya Jummai ya wuce ɗaukan Reina daga wurin, hala idan ya ganta zai ji sanyi a ran shi.

Ta tanadar mishi da abinci na musamman tunda daman ta san da kan shi zai zo ya ɗauke ta.

Da yunwa a cikin shi, ga gajiya, ga ɓacin ran da Fauziyya ta ƙunsa mishi. don haka ha zauna yana ci ba
kuma daɗin abincin yake ji ba, domin ba zallan Fauzah yayi kewa ba harda girkin ta mai shegen daɗi.

kuma a kullum cikin ƙirƙirar sabon abu take don haka ko yaushe a cikin ɗaukin me zai dawo ya ci yake.

"Ina Reina?" Ya tambaya yana kai lomar shinkafa da nama bakin sa, amma taurin naman yasa ya yanki
tissue ya kai bakin shi ya fito da naman sannan ya ƙunshe a ciki, wannan ai sai ya kai gobe bai gama
tauna shi yayi laushi ba.

"Oh sun fita wasa da yaran, ka gama sai a kira maka Ita kada ta zo yanzu ta hana ka cin abincin"

Ya gyaɗa kai tare da kai ruwa bakin shi, amma bai kai ga sauƙe glass cup ɗin ba ta shigo da ɗan iskan
gudu tana "shegiya! Allah ya Isha!" Ta faɗa jikin Hajiya Jummai ta ɓoye don lokacin bata lura da mahaifin
ta a wurin ba.

"My daughter wa ya taɓa ki?" Hajiya Jummai har wani daɗa rungume ta tayi kamar zata shayar da ita
saboda idon Tahir ɗin.
"Jahya ne ta duke ni, Allah ya Isha kawai"

"Zahran Umman Jamal?" Ta tamabaya tana jin daɗin faɗar ba da yaran ta ake ba.

Reina ta gyaɗa kai tana nuna Zahran da yanzu ta shigo riƙe da hannun wata yarinya wacce ke ihu da kuka
idanun ta a rufe gamm.

Dukkan su ba zasu girmi Reinan sosai ba, wacce idanun ta ke rufe ne tace "wayyo Mummy! yaji a ido na
mummy!"

Ta miƙe tare da sauƙe Reina a ƙasa. "Zo mu gani, garin yaya kika saka yaji a idon ki?" Ta tsuguna ta fara
hure mata amma kaman ƙara mata azabar take yi don wanda bai gama shiga ciki bane ɗazu take ƙara
mata, ta shiga tsala ihu da tsalle a wurin.

"Reina ne ta watsa mata yaji a ido, wai don ta hana ta taɓa cake ɗin yaya Haydar a cikin fridge "

Takaicin ta naɗa ma Reina ɗan banzan duka ne ya kama ta amma ta danne.

Ta ƙwala kiran mai aiki da tazo ta ɗauke ta a wanke idon, Sannan ta koma ta zauna tana dariyar yaƙe.

"Ke kuma Zahra ba dukan ta zaki yi ba ai sai ki kawo ƙaran ta, amma kin jawo ta zage ki yanzu. Kuma ma
ai itama ƙanwar Haydar ne, da Haydar da abun da ya mallaka duk na Reina ne" kalmar ta na ƙarshe yana
ɗauke da ma'ana biyu, Alhaji Tahir ya ji ta amma bai kai zancen cikin kan shi ba ma balle ya fahimta, ba
wannan bane damuwar shi ba a yanzu.

Miƙewa daga kan dining ɗin yayi ya maida hular shi yana faɗin "Mu zamu wuce Yaya."

Ya dubi Reina "ina takalmin ki?"


Da hannu kawai ta nuna mishi hanyar waje, ya ja hannun ta ba tare da yayi godiya ma Hajiya Jummai ba
balle ya saka Reina ta bawa Amrah haƙuri.

"Daddy wurin Aunty zamu je?"

"Kina son zuwa wurin Auntyn ne?" Ya tambaya lokacin da ya tada motar.

"Eh daddy, muje inga baby pleash"

Shi daman ya san ba wai dai taje don tayi kewar auntyn ba sai ko don Maama.

"Shikkenan, Amma idan muka je kiyi kuka kice a bamu baby mu dawo da ita gida kin ji?"

Ta gyaɗa kai "Aunty ba jata jane ni ba ko?"

"Ba zan barta ta zane ki ba. Kiyi kuka kina birgima irin wanda kike yi idan aka hana ki cake kin ji?"

"Toh jaka shiya mun Tek ɗin tun da wancan Amyan ta min yowa?"

Yanda take complain ɗin Sai yaga kamar ta da Fauziyya ya daɗa fito mishi, don haka ya tallafo kan ta ya
sumbaci goshin ta yana faɗin "Cake sai wanda kika zaɓa sarauniya ta"

....

Kaman yanda ya umarta da shigan su gidan ko gaisawa da mutan cikin ta basu yi ba Reina ta zube a
tsakar falo tana birgima Ita a bata baby su tafi.
Sahre ta suka yi daga farko, Ummi ta dubi Tahir tana faɗin "Ai ɗazu da aka ce ka zo baka shigo ba nace
toh ko sauri kake yi"

Sosa ƙeya yayi yana dariyan yaƙe "Wani aiki ne ya taso na gaggawa shine aka kira ni, daga nan kuma na
je na ɗauko ita yarinyar saboda ta dame ni tana son zuwa wurin Auntyn ta"

Ummi tayi murmushi irin nasu na manya "ina dai ka gama aikin ko?"

"Eh, na..na gama. Daman saka hannu ne kawai babu ɓata lokaci"

"Toh masha Allah "

Zuwa yanzu kukan Reina ya gama isar Fauziyya.

"Kai zaro min tsintsiyar kwakwa a bayan ƙofa".

Tace da ɗan aunty Zeenat. Shima daman kaman jira yake yi don ta cika musu kunne, ya ciro su dogaye
har guda uku ya miƙa ma Auntyn, ai kuwa tayi kanta gadan-gadan.

Kafin Alhaji Tahir yayi yunƙurin kwatar ta Ummi tayi saurin ɗaga ta. "Zo abin ki mai sunan." Ta ɗaura ta
saman cinyar ta." Ina baby kike so a baki?"

Ta gyaɗa kai.

"Shikkenan an gama. Fauziyya sai ki tashi ki haɗa muku kayan ku, Idan abban ki ya shigo anjima kuyi
mishi sallama ku tafi" still idanun ta na kan Reina take magana.

A razane Fauziyya tace "Ummi ban fa gama warkewa ba" lokaci ɗaya idanun ta na tara ruwa.
Ba wai son komawa gidan bane bata yi, Alhaji Tahir ne bata so ya yi Nasara a kan ta. Kuma tana da
yaƙinin har yanzu bai canza sheƙa ba tunda abun na Reina cikin kwanakin nan kaman ƙaruwa taga yana
yi.

Ummi ta ɗago ta kalle ta "Ta yaya za'a basu jaririya ba tare da uwar ta ba bayan ikon su a kanta suka
gwada mana? Ai sai dai kiyi haƙuri ki je ki ƙarasa jinyar ki a ɗakin ki. Allah ya baki lafiya"

Alhaji Tahir ya sauƙe kan shi ƙasa a kunyace don saƙon ta ya Isa yanda ake buƙata, sauran aiki da shi.

....

Tana cikin haɗa kayan, Ummi ta shigo ɗakin hannun ta ɗauke da laida guda biyu ƙarami da babba.

"Wannan na baƙin laidan su ne magungunan ki, kada kiyi wasa da su don na san ki da ƙin magani shi
yasa na riƙe a wuri na." Ta saka mata a zip ɗin da ke murfin akwatin ta rufe kafin ta gwada babban
laidan.

"Wannan kuma duk na rubuta yanda zaki yi amfani da su, Amma duk abinda baki gane ba ki kira ni."

Godiya tayi a can ƙasan maƙoshi don ji take yi wani abu ya maƙure ta a wuya. Bata yi tsammanin zasu
maida ta ma Tahir da sauƙi haka ba, ta ɗauka sai ya tsuguna a kan guiwowin shi ya basu haƙuri itama ya
bata tukunna.

"Ni na baki shawarar ki zauna har wannan lokacin saboda na ga dacewar hakan, toh yanzu ma na umarce
ki da tafiya ne saboda dacewar hakan da na gani.

Ki wanke duk abinda ke cikin zuciyar ki, ki ci gaba da zama da mijin ki da zuciya ɗaya Fauziyya. Yanzu ko
kin ƙi ko kin so girma ya zo miki, ke uwa ce a yanzu ba zallar kan ki da jin ɗaɗin ki zaki dinga dubawa ba
harda goben yaran ki.

Ba ko wani lokaci ne mutum yake samun adalci a kan gaskiyar shi ba, kamar yanda ba ko yaushe ake
hukunta ka a kan kuskuren ka ba. domin da saki uku yayi ma aure kaɗan idan ba'a hakuri ba'a yafiya."
Ta ja hanci tare da share ƙwalla tana taryo itama rashin adalcin da tayi wa Tahir ɗin a iya zaman su.
Kuma har a gaban Allah zata bada shaidar ya kyautata mata, ya kare mutuncin ta, ya kula da ita, sannan
yayi ƙoƙarin sauƙe hakkokin ta dake wuyan shi.

Ganin Nasihar na ratsa ta yasa Ummi ta riƙo hannun ta.

"A game da Reina kuma... Fauziyya idan ke da kika ɗau cikin ta wata tara kika haife ta kika raine ta kin
guje ta toh wa kike tsammanin zai ja miki ita jiki ya gyara kuskuren da kuka yi a wajen tarbiyyar ta? Yau
idan Hafsatu ta ɓaci ina tabbatar miki kafin a nuna Tahir da yatsa sau ɗaya sai an nuna ki sau goma hala
ma a samu wanda zai zungure ki da shi. Domin alhakin tarbiyyan ta ya fi nauyi a kan ki a matsayin ta na
ƴa mace ke kuma uwa.

Ki jawo yarinyar nan a jikinki ki shiga cikin duniyar ta ki buɗe mata kofofin ciki masu alheri, kada ki barta
tayi ta laluɓe a cikin duhu.

Ki ajiye damuwar Tahir a gefe ki saita yarinya yanda ya kamata, shi dama ba zama yake ba a gidan,
lokacin da zaku ci ku cinye yana ina?.

Na faɗa miki kuma ina ƙara jaddada miki uwa bata taɓa fita daga lamarin yaran ta har Ranar da ƙasa zai
rufe idanun ta, dalilin haka yasa kike tsaye a gaba na a yanzu Fauziyya, kuma nake baki shawarar da zai
amfani rayuwar ki Saboda ni mahaifiyar ki ce, duk duniyar nan wanda zai so ki a baya na yake"

Bata tsaya ganin kukan ta ba ta juya gudun kada ta karya mata zuciya. "Ki yi wanka ki yi alwala gani nan
zuwa" ta fice daga ɗakin, sannan Fauziyya ta zuge zip ɗin akwatunan su ta sauƙe su a ƙasa bayan ta
kammala haɗa kayan kana ta faɗa ban ɗaki.

Tana shafa mai Ummi ta shigo da kasko mai ɗauke da garwashi da kuma wata ƴar jaka a hannun ta. Ta
ajiye kaskon kafin ta fito mata da wani kulaccam da Humrah ta saka ta shafe jikin ta da su kana ta turara
mata jiki, ta turara kayan da zata saka.

Sai bayan Isha kafin Abban ya shigo, itama Fauziyyar sai lokacin ta fito cikin dalleliyar lafaya gashi sai
tashin ƙamshi take, haka duk inda zata yi yake bin ta da idanu.

Daman an riga an faɗa musu abin da za'a faɗa tun auren su sai dai maimaici, don haka ganin zaƙuwar
nashi yasa Abba sallamar su da wur-wuri suka kama hanya.
....

"Juyowa yayi ya sake kallon yanda tayi lamoo a cikin seat ɗinta, Maama kwance saman kafaɗar ta, tana
kallon hanya kamar wata marainiya.

"Daddy a kunna min baby Shat" Reina ta faɗa a kunnen shi, don ba wai ta bar tsoron Auntyn bane.

"Toh sarauniya ta" sai da yayi parking ya gyara mata zama a seat ɗin baya ya maƙala mata seat belt,
kafin ya fito da wata ƴar remote Ya danna play a jikin tvn da ke jikin headrest din shi, daman shi take
kallo a hanyar su ta zuwa, nan da nan ya ɗauke hankalin ta kuwa.

Har suka yi rabin tafiyar bata ce komai ba shi kuma shirun ya ishe shi, sai jin hannun shi ta yi a saman
cinyar ta.

"Fauzah ta yaya akayi ne? Meye labari?"

Da suka haɗa ido ya ɗage mata gira ɗaya, sai ta saki murmushin da ya saka shi jin daɗi a tunanin shi ta
sauƙo ne, ba tare da ya sauƙe hannun shi daga jikin ta ba ya koma tuƙin da hannu ɗaya.

Ta dai mishi shiru har sai da ya tsaya a kofar wani modern bakery don siyan cake ɗin da yayi alƙawari ma
Reina, itama ya siyo mata brownies da chocolate chip cookies.

Karɓa tayi haɗe da faɗin "na gode, amma ka san zan iya abu na da kai na, ko kuma dan a toshe min baki
ne?!"

Nan ya fahimci rikici take nima amma a daren yau ko sheɗan ne ke tiƙa rawa a ƙwaƙwalwar ta shi ba
mahaukaci bane da zai biye mata asara ya hau shi.
"Na san da hakan ai, kinga sai ki huta na kwana biyu tun da an siya"

"Hmm. T kenan"

Sai a lokacin ya ɗaga hannun shi ya mayar kan sitiyari, ya fahimci so take yi ta dawo da halin da ta aro
tun da yammaci. "Ki faɗa min menene farashin fara'ar ki ni kuma zan siye ta duk darajar ta. A mance da
abin da ya riga ya wuce kawai!."

"Ba kuɗin ka nake so ba ka sani"

"Ko menene shi ki faɗa zan yi miki shi"

"Ko menene kace fah?"

"Ko menene Fauziyya "

"Planning nake so in yi na shekaru biyar"

Wani wawan birki da ya ja ya sanya ta ƙara rungume Maama tsam a ƙirjin ta yayin da kanta ya kusan
buguwa a gaban motar.

.......

"Umma Socks ɗin Sabir, na manta ban ɗauko ba"


Fitowa Saudat ta yi da socks ɗin a hannun ta, lokacin Yaseer ɗin ya koma ɗauko back pack ɗin shi a ciki.

Ya taje sumar kan shi, zuwa siririn sajen da ya ƙawata fuskar shi, zuwa ƴar gemun sa dake kan tsirowa
kuma Alhamdulillah yana samun ban ruwa da taki kaman yanda ya kamata.

Kana ya ɗofana Jan Barrett din shi a gayence, ya bi ko ina na ilahirin jikin shi da turare, Kafin ya saka
aninin hannun rigan.

fitowa yayi ya shiga ɗakin iyayen shi ma ya ɗauki turaren mahaifin shi ya ƙara, daman tun jiya ya roƙe
shi kuma yayi mishi izini ko duka zai feshe, domin yau rana ce ta musamman.

Tsayawa yayi a gaban Mirrorn Umma yana kallon kan shi. yau rana ce ta musamman, wannan farin rigan
jikin shi ƙall da ya ɓata lokaci wurin wanke ta da goge ta bayi da jaa a kan lokacin da zai dawo da Ita zata
kasance a rine da kalolin marker da Biro. Yau zai kammala rubuta exams ɗin Waec, saura Neco kuma.
daga yau zai tashi a matsayin secondarian, za su yi candy a yau.

"Yaya Headboy zaka saka ƙanin ka latti fah" cewar Saudat daga waje.

Zanin da ya rufe fuskar ƙanin shi mai shekara ɗaya dake barci ya yaye mishi, sannan ya gyara masa
kwanciya saboda numfashin da yake yi a wahalce yana fita da kyau, kafin ya fito.

Saudat ta riga ta saka wa Sabir socks da sandal dan haka ya zura nashi takalmin kafin ja ɗauko keken shi
ya goya shi a kai Saudat na bin su da addu'o'in kariya. kuma saida Yaseer ya tabbatar sun yi addu'ar fita
daga gida kafin suka bar gidan, Suhail dama ya riga yayi gaba don har gobe a ƙafa suke tafiya shi da
abokan sa.

.....
Paper tayi daɗi ta yi wahala a ranakun da invigilators suka hana shigo da expo. Da yawa a cikin dalibai
sukan kwatanta makomar su a wannan gaɓar, da yawa kuma an yi dafsu ɗin da komai amma ranar da
sakamako zai fito sai a ga saɓanin tunani saboda shi karan kanshi expo ɗin shirme aka kwafa.

Amma ba wannan bane damuwar su a wannan rana. Gurbin ajiye tarihi suke nema a zuciyoyin su,
suturan su, da na'urorin su. Don yawanci sun zo da waya sai dai wainda basu da shi kaman su Yaseer ɗin.

Sai dai fa yanda ake jawo shi ta ko ina ya shiga hoton su ma har ya fi masu wayoyin farin jini. Rubutu ne
ko ta ina a jikin shi.

Hango ƙatotuwar zanen zuciya a bayan rigan shi wanda aka yi da jan marker a ciki kuma an rubuta 'With
Love Yasmeen' ya saka Yar uwar shi a muƙami wato headgirl ta ƙarasa ta cukumi wuyar Time keeper.......
Wuhuhu😂

~~~~~~

*The Longest chapter so far sannun ku sannu na🥲🥰. And Happy Ranan Yara👼🏻. If you've made it this far
please ku yi addu'a ma yara da mutanen da ke rayuwa a palestine. Allah ya kawo ƙarshen wannan
zalunci da ake musu, Allah ya mayar da dukkan sharri da makirici kan masu ita, ya tarwatsa su ya
tarwatsa shirin su. Sannan Allah ya taimaki musulunci da musulmai a duk inda suke a faɗin duniya.
Ameen*
‍*#Free Palestine❤️‍🩹
*

*Saliha Ahmad Na'ibi (Seemahwrites✨)*

*REINA 💍*

19......ki daina cakalar abincin nan Reina!" Fauziyya ta tsawatar mata da kakkaurar murya, bayan ta goge
wa Maama gaban rigan ta da ya ɓaci da maiƙon kifi da handkerchief ɗinta mai laushi.

Zumɓuro baki Reina tayi tana kallon Alhaji Tahir. Ya murmusa tare da tallafo ɗan fuskar ta cikin tafin
hannun shi. "Yaya aka yi ne sarauniya ta?" Ya tambaya da kulawa a cikin muryar shi.

"Daddy bani son wannan abincin" tace tana riƙo hannun rigan shi.

Fauziyya kaman jira take yi ta hau ta da masifa.


"Kin san Allah ko mutuwa zaki yi sai kin ci?! Baki da aiki sai fidda fice baki son kaza baki son kaza Idan ba
shegen ɓaci ba. Kin san mutane nawa suke niman abin da kike samu kike ci a kullum suka rasa?"

"Haba Fauzah, meye abun ɓacin rai a nan kina magana da ƴar shekara 6 kamar wata babba?"

Bata tanka ba, ta maida hankalin ta ga Maama dake ƙoƙarin ɗaukar glass ɗin ruwa ta sha da kanta, don
haka ta taya ta riƙewa tana kurɓan ruwan a hankali har sai da ta ɗaga kanta alamun ta ƙoshi.

"Ya Ishe ki Maama na?" Ta shafa gashin kanta mai cika, laushin sa ya saka ya nannaɗe.

Gyaɗa kai tayi tare da murmushin da ya saka gefen kumatun ta ɗaya lotsawa kasancewar itama
Fauziyyar murmushin ne a kan fuskar ta.

Ayyanawa take yi a ranta, idan Allah zai bata yara dubu kaman Maama ba zata gaji ba. Bata san meye
wahalar raino a kanta ba, gata da shiga rai, ga kyau, ga fara'a, don haka son da take mata daban ne a
cikin zuciyar ta.

"Sarauniya ta me kike so ki ci?" Alhaji Tahir ya maida hankalin shi kan Reina dake wasa da fork ɗin ta a
kan chips and egg dake cikin nata plate ɗin, duk ta gama dama shi da ketchup da kuma baked beans da
aka zuba a gefe.

Alama tayi masa da ya kawo kunnen sa. Ya matso, ya tanƙwaro, kana ta raɗa masa "Rice Krispies ko
Cake"

Fauziyya ta sake amshewa da,

"Ai kuwa ke da sauƙa hala sai cikin kabarin ki idan ana ramewa. tunda kayan maƙulashe da sugar sune
abincin ki a ko yaushe. Haka zaki yi ta zama da funkum-funkum ɗin kumatu kaman ana saka miki yeast,
ciki kullum kaman mai shirin haihuwa"
Rai a ɓace Alhaji Tahir ya miƙe, ya sauƙe Reina daga kujerar sannan ya jata zasu bar gidan baki ɗaya.

Da sauri Fauziyya ta miƙe ta fara bin shi a baya tana faɗin "T. Zata yi shirin tafiya school fah!"

"Ba zata je ba" ya amsa a takaice, daɗi kuwa kaman ya kashe Reina.

Fauziyya ta ci gaba da bin shi har suka fita farfajiyar gidan, aka ƙaraso mishi da motar da zai fita da ita.

"Toh Zancen zuwa ofishin alhazan fa?"

"Direba ya kai ki" shine amsar da ya bata yayin da aka buɗe mishi mota ya fara saka Reina kafin shima ya
shiga babu ɓata lokaci suka bar gidan.

.......

"Umma! Wallahi yau wasu mata sunyi faɗa a kan Yayan mu!!" Sallamar Suhail kenan bayan ya bankaɗe
kyauren gidan su ya faɗa ciki, ya kuwa yi sa'ar riskar Saudat a ƙarƙashin inuwar neem ɗin da ya ƙara
girma da kauri a yanzu, inuwar shi ya kusa lulluɓe tsakar gidan baki ɗaya.

Zaune take tana ƙulla sana'ar ta, sai yaron ta dake daga gefe yana wasa da igiyar tabarma.

Da sauri Yaseer ya riƙo Suhail ya rufe mishi baki da tafin hannun shi amma ya riga da ya fasa ƙwai.

"Nima na gani umma, har da marin mai jan ɗankwali aka yi, aka yaga mata hijabi" Sabir ya ƙara cikin
nishaɗi amma suna haɗa idanu da Yaseer yaga irin kallon da yake masa sai ya sha jinin jikin sa tare da
sauƙe kan shi ƙasa yana matse baki.
"Ashe yayan mu? Zo ka bani labari wacece amaryar mu a cikin su? Wacce ta yaga Hijabin ko wanda aka
yaga mata?"

Hankali a tashe yace "Umma Amarya kuma?"

"Eh mana! Amarya kai! Tunda har an fara faɗa ba gwanda ayi a tantance, Abban ku yaje gidan su ɗaya a
raba gardama ba? Ko ƙarya aka maka?"

"Wallahi Wallahi Umma ni ban taɓa kula ɗaya daga cikin su ba" yace yana durƙusawa a gaban ta don ta
yarda da shi.

Cikin idanun shi ta kalla tana karanta saƙon dake cikin su.

Ta san yaran ta ciki da bai, ta san gaskiyar su tana gane ƙaryar su.

Domin ta sadaukar da baki ɗaya nutsuwar ta wajen ganin ta basu kulawa yanda ya dace.

Ta koyawa kanta zama abin da suke buƙata ba tare da sun nima a wurin kowa ba balle taga ba daidai ba.
Tana zama musu ƴar uwa a lokacin da suke buƙata, ta kan zame musu ƙawa, uwa, malama, majingina,
abokiyar shawara, abokiyar cin mushe, wani lokaci har Matsayin uba ta kan ɗauka idan buƙatar hakan ta
tashi.

Don haka bata da haufi a kan su duk da ana cewa ba'a shaidar ɗan yau, amma ba wai tabbaci take da shi
a kan su ba, A'a. A kan tarbiyyar da ta ɗauki shekara da shekaru tana gina musu block bayan block take
da tabbaci.

Sauƙe idanun ta tayi a cikin nashi ta maida hankalin ta kan abinda take yi tana faɗin "toh yaya aka yi ka
bari suka yi faɗa a kan ka idan baka kula su?"
Ɓalle botir ɗin rigar ya shiga yi sannan ya cire ta ya juya bayan rigan ya gwada mata zanen heart ɗin nan,
kana yace. "Ashe wai Time keeper ne ta rubuta wannan a jikin riga na, ni ban ma san sunan ta Yasmeen
ba, shine ita kuma headgirl ta kama ta da faɗa saboda wai ashe tana yawo tana faɗa ma mutane ni
saurayin ta ne, Saboda muna aikin makaranta tare sai aka yarda. Ni kuma Wallahi ba son ta nake yi ba"

"Toh me yasa baka son ta?" Ta tambaya don taji ra'ayin shi a kan soyayyar baki ɗaya sai ta san da wani
irin kalamai zata yi amfani da su ta taushe shi.

"Haba Umma duka-duka shekaru na nawa? Yanzu kafin na gama karatu in samu aikin da zan iya Aure ai
wannan tana da yara ma"

Ta murmusa "haka ne. Amma daga yanzu idan ka lura wata tana son ka kuma baka da ra'ayin kula ta,
kayi ƙoƙari ka fahimtar da ita saboda kada ta sake yaga ma wata Hijabi" ta ƙarashe da raha, domin ta san
abu mai sauƙi ne ya iya saka abun a ran shi ya dame shi.

"Toh Umma yaya za'a yi na gane idan wata tana so nan?"

Sake baki tayi don da iya gaskiyar shi yayi tambayar, lallai kamar yanda ya faɗa ne, nawa yake?. Ta kaaɗa
baki tace "turƙashi, yanzu dai ku canza kaya ku ci abinci sai mu ƙarasa hirar anjima"

Miƙewa yayi da toh, ya ɗauki Sabir ya fara ɗauraye shi saboda ƙwallon da suka sha a makaranta ƙasa har
kan shi, ya shirya shi ya zuba mishi abinci kafin ya shiga nashi shirin, Suhail kam yanzu ya iya kula da kan
shi sosai.

......

"Sarauniyar Baban ta yau ma da ke anka zo office ɗin?" Alhaji Abdou ya miƙa ma Reina hannu su gaisa.
Hannayen ta da suka ɓaci da icing ɗin cake ta goge a gaban rigan ta Kafin Alhaji Tahir yayi yunƙurin zaro
mata tissue, sannan ta riƙi hannun Alhaji Abdou tana girgizawa da iya ƙarfin ta kaman yanda taga kowa
yake yi a nan ɗin, da taga bayi jijjiguwa mata ma sai ta saka hannu biyu.

"Ai kai ma naga office ɗin daddy na kazo" tace bata bar jijjiga hannun shin ba har sai da ya zare cikin
dabara.

"Toh ai ni abokin shi ne" ya faɗa yana amsar file ɗin da Alhaji Tahir ɗin ya miƙo mishi don dubawa.

"Haba! Maman ku ne friends ko school ɗin ku ɗaya?" Ta daɗa matsowa gaban shi a kan makeken table
ɗin da take har tana ture wasu takardu da kafar ta.

Bai samu daman amsa ta ba saboda abinda yake karantawa ya ɗauki hankalin shi.

"Tahir minana wannan?" Ya tambaya yana ɗan yamutsa fuska cikin ruɗu.

Murmushin kan fuskar shi Alhaji Tahir ya ƙara faɗaɗawa, abin dai da kake gani shine. Deal ne mai mugun
kyau nake faɗa maka, riba za'a samu ba ɗan kaɗan ba"

"Riba? Da aka siyar da mene?" Ya ɗago yanzu yana duban sa.

"That's the best part. Baya buƙatar wani wahala da ɓata lokaci, funding kawai suke buƙata su yi projects
ɗin da kake gani a wurin, kuma cikin wata uku za'a mayar mana da ninki ukun abunda muka bayar. Ko
yaya ka gani? kawai kuɗi zamu zuba musu muma mu samu kuɗi"

Ya ajiye file ɗin a saman table ɗin sannan yayi baya ya jingina da kujeran da yake kai tare da jan dogon
numfashi yana bin Alhaji Tahir ɗin da kallo.
"Yaya kake abu kaman ba ɗan kasuwa ba Tahir? Kaman yau ka fara kasuwanci? Kaman baka san rules na
kuɗi ba? Babu wahalar da baka yi ba don ka tara abun da kake da shi a yanzu, kuma ko wani ma'aikaci a
ƙarƙashin ko wani sassa na Tk Kingdom, albashin da ake biyan sa daidai aikin sa ne. Sai kai ne baka yi
komai ba zaka yi tsammanin wasu daga sama su ɗauki zunzurutun kuɗi su baka haka siddan? Gaskiya
idan barci kake yi kama farka"

Daman yayi tsammanin sai sun kai ruwa rana da shi kafin ya amince don haka bai damu ba ya jira shi
saida ya dasa aya kafin yace "Abdou Hamissou ka gama?"

"Eh na gama Tahir Kamal Jama'are"

Tahir ya ɗan saki dariya kaɗan ganin har ya shaƙa.

Sai da ya ciro wayan shi ya shiga ma Reina kallo a YouTube Saboda ta fara damun shi, kafin ya matso ya
ɗaura hannun shi saman teburin ya harɗe su guri guda tare da tattaro dukkan nutsuwar shi yace.

"Yau muka fara funding projects muna ribantuwa ne? Ko a tunanin ka bani zurfin bincike a kan abu ne da
idan anso cuta na ba zan gane ba? Wallahi ba dan amanar dake tsakani na da kai ba da ko labarin anyi
ma ba zaka ji ba. Shi yasa na jawo ka ciki don kai ma ka mori arziƙi."

"Zai iya zama funzy ne, ko kuma paper company, har wa'inda suka fika arziƙi da bunƙasa ma ana cutan
su Tahir, ka bi a sannu kawai"

Sunkuyawa yayi ba buɗe drawer ya ciro wasu takardu ya ajiye ma Alhaji Abdou a gaban shi. "Gashi na
tura har babban branch ɗin su dake China an duba min. Kuma ana kan bincika min manyan branches ɗin
su dake Germany da Mexico. Kuma a nan Africa suke so su yi rabin project ɗin, kaga riba biyu kenan"

Ya ɗaga takardun ya duba su da kyau kafin ya ajiye "shikkenan, ka bari zan yi tunani kafin mu san abun
yi"
Ya murmusa, "haka nake son ji. Hidima na samu ba wasa tunda shi muka fito yi"

Ya miƙe yana faɗin, "toh ni ina da wasu ayyukan a gaba na, zan ƙoƙarta in gama komai a cikin satin nan
saboda Malika bata jin daɗi Wallahi"

"Allah sarki, jikin ne?" Ya tambaya cikin kulawa.

"Ka san da sanyi ya fara zuwa sai ciwon sun yayi ta tashi"

"Allah ya sawaƙe, amma ka gama tunani mu yanke shawara a kan wannan deal ɗin kafin ka tafin"

"In cha Allah " yace tare da miƙewa da niyyar tafiya. "Amma kaman nawa ne daman kake na niyyar
zubawa?"

"200 million..."

Alaji Abdou ya gyaɗa kai alamun gamsuwa.

"...In Dollars!" Ya ƙarasa

"Mene?! Tahir Are you mad??!" Ya tambaya a kiɗime.

~~~~~~~
*Ayi maneji da wannan gobe zamu sake mai tsayi sosai in Allah ya yarda*

*Saliha Ahmad Na'ibi (Seemahwrites ✨)*

*REINA 💍*

20.......Alhazai sun gama shiri saura tafiya, daga gidan Alhaji Tahir zasu wuce don haka masu tafiyan
wanda suka haɗa da Hajiya Hauwa, Hajiya Jummai da yaran ta biyu, sai Kuma ita Hajiya Fauziyyar. Bayan
su akwai Alhaji kalabu da matan shi duka uku sai kuma iyayen Hajiya Fauziyya da yayun ta dukkan su
Alhaji Tahir ya biya musu, zasu haɗe a airport.

Shafa fuskar Maama dake hannun Hajiya Farida tayi ƙwalla na taruwa a idanun ta, bata ji irin abin da
take ji a ranta yanzu ba lokacin da ta tafi ta bar Reina tana kamar ta. Sai take ji kaman bata yi wa yarinyar
adalci ba, haƙurinta yayi yawa.

Sannan lokacin da ta bar Reina a wurin Ummi ta barta, tana da tabbacin zata samu cikakkiyar kulawa.
duk da lokacin da ƙyar da suɗin goshi Alhaji Tahir ya yarda, shi dai sai dai a barwa ƴan uwan shi ita, sai da
ta gwada mishi idan bai amince ba ta fasa tafiyan kuma a tare zasu je a lokacin kafin ya amince.

Hijabin jikin ta Reina ta ja, ta sauƙar da ganin ta zuwa kan yarinyar da tayi kamar zata fasa ihu.
"Aunty zan bi ki" tayi maganar cikin nuryar kuka.

Wani ɓangare na zuciyar ta na so yaji tausayin ta amma ta san yanzu sai ta yi mata ɓaci, don haka ta
haɗe rai "Kin san Allah idan aka kira ni da complain ɗaya a kan ki Reina tun daga can zan sayi bulalar da
zan shiga jikin ki da ita. Don haka ki nutsu, kina fitowa da assignment ɗin ki daga kin dawo daga school a
taya ki ba sai da safe idan driver na jiran ki ba. Ki nutsu ki ci abinci kuma banda yawan kallo ko a TV ko a
tab. Kuma in ji labarin kin roƙi wani cake kiga yanda zan yi da ke" ta ƙarashe muryar ta na sarƙewa don
kuka ne yake so yazo mata.

Waye zai iya haƙuri da halin Reina ba tare da ta cika mishi ciki ba, kuma tana tsoron kada su mayar mata
da agogon ƙoƙarin da ta fara yi a kanta baya, shi yasa da ace Alhaji Tahir wani ne toh da ma ƙanwar
Ummi zata bada ita.

Hajiya lubabatu ne ta ƙaraso ta janyo Reina daga Jikin Hajiya Fauziyya.

"Ai da kunne na kika zo kika kama kike zuba min wannan kashedin Fauziyya, sai in daɗa ɗaukar su da
muhimmanci don wannan maganar masu hankali ne ba na ƙaramar yarinya ba"

Ta shiga girgiza kai "A'a Wallahi Addah, yarinyar ne bata jin magana wallahi, ga shegen taurin kan tsiya,
ina tsoron kada kisha wahala da ita."

A lokacin Alhaji tahir ɗin da ake jira ya fito yana gyara hula. "Mu tafi ko?!" Yace da su ba tare da ya zauna
ba don lokaci ya riga ya tafi suna zaman jiran shi bai dawo ba, yanzu ma a gaggauce ya watsa ruwan ya
shirya kuma da ya ga tashin su bakin aiki zai koma duk dare.

Ko dan saboda kasancewar shi a wurin Hajiya Luba bata fasa maida wa Fauziyya martani ba "Banda abin
ki yara nawa na Raina na aurar sai ƴar ƙaramar yarinya ce zata gagare ni? Kada ki ji komai, za'a kula da
ita fiye da idan kina nan, kuma za ayi mata abunda bata samu a nan ma, idan kika dawo sai kin sha
mamaki."

"Allah yasa" ta amsa lokacin da Alhaji Tahir yazo ya ja akwatin ta zai fita da shi. Ta sumbaci Maama
hawaye na ƙwace mata don haka ta wuce ba tare da ta sake ma Reina kallo na biyu ba, haka sauran
mutanen suka rufa musu baya suna musu bankwana.
Amma da Hajiya Lubabatu ta sani da bata yi kalamin tabbatarwa a kan Reina ba, domin bala'in da zata
takalo mata Allah ne kaɗai zai iya magance mata don tabbas sai ta faɗa ciki tsamo-tsamo.

......

"Sai me za'a wanke kuma Umma?" Yaseer ya tambaya yana zama a kan bokitin fenti da ya gama shanya
bargunan ciki wanda ya wanke, yana haki sama-sama.

A kaikaice ta kalle shi cikin gatse tace "Saura ni! Tun da ni kaɗai ne abu mai dauɗa da na rage a gidan"
kana ta mayar da hankalin ta kan ƙafar Sabir da take yanke wa farce da reza.

Ɗan ciza labben shi na ƙasa yayi yana murmushi, abunda ya zamo masa ɗabi'a musamman idan yaji
kunya ko ɓacin rai.

"Toh ai Umma ke ɗin ma idan kina so zan iya wankewa"

Hannu ta kawo da nufin mangaje shi yayi saurin kaucewa yana dariya, daman ya tsammaci hakan.

"Allah Umma zaman hakan ne ba daɗi, ashe ma gwanda idan mutum na zuwa makarantar" ya riƙe igiyar
shanyar daga yanda yake tsaye don yana tsoron ya koma kusa da ita bata gama hucewa ba.

"Toh kaga da Abban ka bai hana ka koyan sana'a bane, da sai dai ka buƙaci lokaci amma ba dai yayi maka
yawa ba"

Matse bakin shi yayi alamun bayi son tankawa a kan maganar. Ta kalle shi ta girgiza kai kafin ta ci gaba
da cewa.
"Kuma ai abun yi bayi ƙarewa, ka shiga ka ɗibo mana shinkafa da yawa mu gyara shi, kaga mun rage aiki
daga an ɗiba sai dafawa"

"Toh, ni dambu ne ma nake son ki koya min"

"Dambun tsaki ko na shinkafa?"

"Ko wanne, inaga yanzu shi kaɗai ne ya rage mun ban iya ba. Amma tuwo idan na tuƙe shi ko goggo
albarka" ya ƙarashe da alfahari.

"Lallai fa ma Abban ka zan faɗa ma wannan zance ya sanar ma goggo"

Dawowa wurin zaman shi na ɗazu yayi yana faɗin "ki rufa min asiri Umma dan Allah, kada idan naje hutu
taji daɗin girki ta hana ni dawowa"

Suka saka dariya harda Sabir kafin Saudat tace "kaga yanzu yayi wuri, sai ka bari zuwa an gama gyaran
shinkafar kaje ka siyo kayan dambun, ka roƙi Danejo ta sammana zogale sai ka tsinko"

"Muma dai da shuka ta muka yi zogalen nan Umma. Tunda akwai wuri har biyu ma zamu iya dasawa"

Ɗage kafaɗa tayi "ga fili ga mai doki Yaseer, ai gidan ku ne ba namu ba"

Yanzu kam miƙewa yayi don ya wuce yin abinda ta umarce shi.

Ya ƙanƙance idanun shi yayin da ya ɗaga kai zuwa ga kwallon Ranar da ta haske Safiyar Litinin, gajimare
masu haske da masu duhun launi mai kyau suka yi mata ado abin burgewa. Bata da zafi kasancewar
yanayi na sanyi da ya fara shigowa, Amma hasken ta ya wadaci ko ina, ta haske ƙwaƙwalar mai niman
ilimi, ta haske zuciyan mai niman dukiya.
Miƙa yayi tare da lumshe idanu ya fitar da ɗan karamin gurnani, sai yanzu ya fahimci ashe durƙeshen da
yayi ya saka bayan shi yayi tsami.

"Yauwa Umma dan Allah in je kwallo da yamma?"

Bata cika son zuwan shi kwallon ba dan haka har a zuciyar shi ya raya idan ta hana shi ba zai je ba. Shi ba
kaman Suhail bane mai satar hanya.

"Allah ya kaimu yammacin"

......

Kwana biyu, kwana biyu kacal Amma Hajiya Luba ta gama gajiya da tsirface-tsirfacen Reina.

Ga iyayi gashi bata iya zama wuri guda, gidan kuma ba ƙananun yara suke da shi da yawa ba sai yaran
kishiyar ta da ko ɓangaren ta basu takowa amma har shashin uwar su Reina ke zuwa ta nemo magana,
idan an taɓa ta kaɗan kuma tazo wa mutane da ihu da kuka tana zage-zage.

"Ba zaki ci indomie ɗin ba?" Hajiya labatatu ta tambaya takaicin ta na daɗa kama ta.

Girgiza kai tayi tare da zumɓuro baki ta tura mata bowl ɗin.

"Toh kici ko ƙoyin dan Allah"

Ta sake maƙe kafaɗa "o'o bani sho"

"To me kike so ki ci?"


"Froot Loopsh" tace tunowa da aunty tayi mata kashedi a kan cake amma da cake ɗin zata ce.

"Menene Froot Loopsh kuma ni Luba?"

Yarinyar ta dake gefen ta na hagu ne tace "wani cereal ne, amma wallahi sai ki zagaye garin bauchi kaff
ba zaki samu ba, ba ma a ƙasar nan ake yin shi ba. Bari ki gani"

Tayi minimizing ta fita daga abinda take yi sannan tayi mata browsing ɗin sunan Froot loops ɗin sai ga
hotunan shi sun fito.

"Kin gan shi"

Ta gwada mata abun masu kala-kala, zobe-zobe.

Hajiya luba ta riƙe baki tana sallallami. "Toh a ina kenan ake siyarwa in saka a samo mata"

Ta kalle ta da mamaki "taɓɓ, Hala Abuja ko kano za'a samu. Amma Wallahi mummy kada ki ɓata lokacin
ki a kan wannan abun, ki bata abin da kike da shi idan bata ci ba cikin ta."

Murguɗa baki uwar gayyar tayi tace "Ni ba wannan abun bane shunana Hafshatu Reina Tahir Tk
Kingdom"

Tsaki tayi "Shegiya da dogon baki kamar aku"

"Ni ba shegiya bane, sai dai in ke!"


A zafafe ta miƙe zata kai mata bugu Hajiya Lubabatu tayi saurin tare ta "Rufa min asiri don Allah da
Tahir, ban shirya tafka babban asara ba"

Nuna ta tayi da yatsa tayi ƙwafa kafin ta ɗauki wayarta ta wuce.

Sauran yaran basu ce komai ba don yanzu Uwar zata gwale su amma baki ɗaya haushin Reina suke ji
Saboda shegen rashin kunya, idan kaga bata yi da kai ba toh baka shiga shirgin ta ba, shima sai dai idan
taga alamun baka ɗaukan raini.

.......

"Saudatu ko dai na kuskure a hanya?" Tun da ya samo ƙarin bayani a kan farashin makaranta da kuma
ɓangaren karatun da Yaseer ya cika ya shiga cikin damuwa. Ko dambun tsakin da aka ajiye a gaban shi ya
gagara ci.

Tsura mishi idanu tayi, yanda yake ɗaga hankalin shi a kan lamarin Yaseer, ya ɗaura duk wasu
mafarkayya da burikan sa a kan shi sai yake bata tausayi, amma tana tsoron kada kuma su ɗaurawa
yaron nauyin da ya fi ƙarfin ƙirjin shi ya ɗauka.

"Sai mu ɗauki darasi mu gyara ta tun kafin ayi nisa. Faɗa min menene damuwan?"

Numfasawa yayi kafin yace "Wallahi da aka faɗa min kuɗin registration kawai na jami'ar da yaron nan ya
cika sai da ciki na ya tsure, kuɗi samama Saudatu, ina zamu same shi?" Ya ƙarashe kaman zai yi ihu.

"Toh ai da sauran lokaci ko? Naga sukan yi watanni a gida kafin sakamakon jarabawar su ma ya fito
tukunna azo zancen ɗiban sabbin ɗalibai. Sai mu tara a hankali, amma ya kai nawa haka kuɗin?"

"Hmm, duk da mutumin yace min bayi da tabbaci amma yana da yaƙinin kuɗin ya doshi dubu ɗari uku.
Dubu ɗari uku Saudatu, ko tarawan muka ce zamu yi sai munyi watanni uku bamu ci ba bamu sha ba
kafin mu tara dubu ɗari uku!"

"Innalillahi wa inna ilaihiraji'un." Suka ƙarashe addu'ar a tare.


"Daman ka san makarantu a kudu sun fi arewan mu tsada, toh yanzu meye abun yi?"

"Wallahi ban sani ba, lissafi na ya cushe, bani da dubu ɗari uku bani da dalilin shi."

"Toh a haƙura da makarantar mana mu saka shi a wanda zamu iya, koda irin wanda kayi ne"

Yana cikin yanayin damuwa amma ba shi ya hana shi ɓata ran shi lokaci guda ba. "Allah na tuba ko babu
na yafi haka sai in bar shi yayi poly?"

"Amma naga mutane ne suma wanda suke yin ko? Kuma ma ga makarantu muna da su a kusa menene
sai an ɗauki yaro an kai shi cikin arna? Gaskiya ka canza shawara"

.......

Yau ta kama sallar layya, masu zuwa Masallaci sun je, sauran sun yi kwalliya sun ɗau hotuna sannan suka
koma suka bi lafiyar gado.

Da gudu Reina ta fito ta ƙofar bayan dake kitchen, yanda zai sada ka da babban filin da ma'aikatan ke
sarrafawa iyayen gidan su naman Sallah.

"Bibalo ki duba min kaskon nan, idan ya soyu ki kwashe ki zuba wani daga cikin wancan tukunyar" cewar
Inna larai, tana cire dogon matsamin daga ciki kana ta jingina shi daga jikin kaskon.

Da toh bibalo ta amsa ta ci gaba da tuƙa tukunyar dambun ta, da niyyar sai an ɗauki mintuna kafin ta
duba suyar.
Ita da ubangijin ta kawai suka san me take gujewa, sai kuma wanda tayi wa laifin. Tana gudu tana
waiwaye taci wawan tuntunɓe da matsamin, wanda yayi sanadiyar tankwaro da kaskon daga kan murhu
mai da naman ciki ya wantsalo sai a kafafuwan Ta.

Seemahwrites ✨

*REINA 💍*

*BookNest, Wattpad and arewabooks @ Seemahwrites*

21..... Idan azaba ta wuce fata, ta ratsa jijiyoyi, ta shiga cikin nama, ƙashi, da kuma ɓargon mutum, toh a
cikin zuciya da ƙwaƙwalwa ake jin ta, gashi yarinta da hauka basu hana kuruwa cikin azaba.

Sai da ta ja iya iskar da huhun ta zasu kai ga ƙarshen huruwa kafin ta saki ihu iya ƙarfin ta tare da zubewa
a wurin, abun da ƙwaƙwalwar ta ya bata na gaba kuma shine kai hannu tana murza wurin da man ya
ƙona ta koda zata ji sauƙin raɗaɗin azaba da take ciki, Amma a maimakon haka sai ta kwaile farar fatar
da a yanzu tayi jaa kafin ta fara yin duhu -duhu.

Ihun da tayi ya ankarar da bibalo da kuma sauran ma'aikatan da suke wurin, cikin azama duka suka bar
tukwanen su dake kan wuta ba tare da damuwa da lalacewa ko ƙonewar abin da ke cikin ta ba suka yi
kan Reina.

Bibalo ta riƙo hannun da take murje ƙafar da shi ta riƙe su gamm tana ganin yanda take mazari kamar
mai farfaɗiya.
"Innalillahi mun shiga uku! Hajiya! Inna Larai!!"

Cicciɓar ta tayi zata yi ciki da ita yayin da mutan gidan suka fito itama Inna Larai lokacin ta dawo daga
banɗaki, duk suka yi turus na tsawon second guda suna kallon Reina a hannun Bibalo kafin ƙwaƙwalwar
su ta fara aiki. Rabon Inna Larai da tayi gudu har ta manta amma yau kam shi ta ɗiba zuwa sashen su na
masu aiki ta wuce kitchen, cikin bokitin da suke ajiye kamu ta tsoma hannun ta biyu za ta ɗibo.

Hajiya Lubabatu kuma karɓan Reina tayi daga hannun Bibalo bayan ta gama narka musu ashariyar da har
yanzu bata ji alamun ya ishe su ba. Sai ma ƴar ta ne tayi tunanin kiran driver da wayar ta ya fito da mota
cikin gaggawa.

Inna Larai na dawowa ta shafe ƙafafuwan Reina da kamun nan sannan ta ciccibeta daga hannun Hajiya
Luba tayi hanyar waje da gudu, tana fita kuwa taci karo da driver da kuma mota na diri alamun an riga
an sanar da shi, bata yi wata-wata ba ta saka ta cikin motar.

Zata shiga ta daya ɓangaren Hajiya Lubabatu tazo ta fisgota ta yasar har ƙasa. Kafin ita da yarinyar ta
suka shiga cikin motar da ya karaɗe da kukan Reina, ta gama jiƙewa da zufa, hawaye da majina, driver ya
zuge su zuwa asibiti mafi kusa.

.....

Zai iya rantsewa ko lokacin da aka kira shi aka sanar masa cewa mahaifin shi ya rasu bai shiga irin tashin
hankali irin na yau ba.

Bankaɗe ƙofar ɗakin asibitin Alhaji Tahir yayi ya faɗa ciki kai tsaye.

Hango ƴar shi kwance ƙafafuwan ta zuwa guiwa naɗe a cikin bandeji ya gaskata masa abin da aka kira shi
aka sanar da shi mintuna 17 da suka wuce.
Barci ya ɗauke ta, amma kana gani ka san ba a daɗin rai take yin shi ba. Ga wasu ƙananun kuka da ke bin
numfashin ta Saboda wanda ta sha ɗazu.

Ya ƙarasa gaban gadon ya durƙusa a kan guiwar shi yana kallon ta tun daga kai har ƙafa, Tsoron taɓa ta
ma yake ji, yana ƙoƙarin kimanta yanayin da take ciki a ran shi.

Ya fi tsawon mintuna goma a ɗakin, su kuwa sun ƙame a jikin garu kowa yana tsoron numfashi mai ƙarfi
don basu san da me yazo ba.

Daga ƙarshe dai ya miƙe, ya juya ya fuskance su ɗaya bayan ɗaya, kowa ya sha jinin jikin sa.

Amma kafin ya buɗe baki yayi magana sai ƙaran sauƙan mari suka ji tass.

Hajiya Lubabatu ta sauƙe shi ma Inna Larai.

Riƙe da kunci ta ɗago tana kallon matar da ta girmewa nesa ba kusa ba. Matar da aka yi zaman amana da
daɗi ba daɗi, ta zauna da ita tun tana cikin ƙuruciya har ta hayayyafa ta aurar ta fara samun jikoki a
yanzu.

"Ha...jiya zagin bai... Isa ba harda mari?" Ta tambaya bakin ta na rawa, ga ƴar ta bibalo tsaye a wurin
tana kallo.

"Wallahi kika yi wasa sai na ƙara miki, matsayiyata mutanen banza kawai, wanda basu san mutunci da
alkhairi ba. Duk yanda mutum ya kai ga saka ku a inuwa Sai kun kai shi rana. Ko mene ƙaramar yarinya
tayi miki kamar wannan sai ki ɗau fansa ta hanyar ƙona ta? Saboda tsananin zalunci da baƙin hali?"

Ta yi ƙoƙarin gyara wasu daga cikin halayen Reina, ta so tsanantawa a kan gyaran, ta taɓa hukunta ta a
kan laifin ta, yarinyar ta kalli cikin idon ta tayi mata zagin da ta shekara wurin 30 rabon ta da jin shi.
amma tunda ta kai ƙarar ta wurin Hajiya Lubabatu gudun ta ɗauki mataki a hannun ta aka bi bayan ta
tare da kashe mata warning na ta fita harƙar ta, daga nan ta sare da lamarin Reina.
"Haba Hajiya! Haba Hajiya! Ko menene Hafsatu tayi min me zan ribanta idan na mata lahani? Alkhairan
da Fauziyya tayi min a lokacin da nake tsananin buƙatar su yafi ƙarfin in kalli ƴar cikin ta da wani abu
bayan soyayya. Zagawa nayi ban ɗaki na dawo na samu hakan ta auku, tsautsayi ne Hajiya"

Alhaji Tahir dai na tsaye zuciyar shi na tafasa. amma kuma yana son yaji yaya aka yi har aka haihu a
ragaya shiyasa bai ce komai ba.

"Ni dai ki tattara naki ya naki da sauran wanda kuka haɗa baki. Kaii bani son ganin wata mai aiki ko ɗaya
dake a ƙarƙashin ki a gida na, tunda da su aka haɗa baki, ah toh, idan ba haka ba ace suna zaune a wurin
kuma su ba makafi ba? To wallahi kafin in dawo, duk ku tattara ku bar min gida, idan nan da minti 30
yayi baku tattare komatsan ku kun fice ba sai na saka anyi min fata-fata da ku da shirgin ku"

Babu shakka ta fahimci don ta wanke kanta a gaban mahaifin yarinya take wannan magananganun,
amma menene sai ta ɗaura mata laifi.

"Shekaru Ashirin da bakwai, muna tare tsawon shekaru Ashirin da bakwai Hajiya, anci an birne tare da
ni..."

"Ko minti ɗaya ba zan ƙara a kan talatin ɗin nan ba Larai!" Ta gwada mata haryar waje tana mata
muzurai.

"Allah ya bata lafiya, sai anjiman ku" ta juya ta fita sauran suka bi bayan ta. Ya rage daga Hajiya Lubabatu
da ƴar ta sai kuma Alhaji Tahir da mai ƙuna a ɗakin.

Ta juyo zata fara magana "wallahi, Tallahi, Tahir ban..."

Nuni yayi mata da ƙofa shima. "Kije kawai sai na nime ki"
A kiɗime ta zare idanu, mai yake nufi da sai ya nime ta? Ina zancen sabon kasuwancin da zasu haɗa
hannu su buɗe shi tare? Wanda shine ma ƙarfin tunda shi zai bada kashi 65 na Jarin, shi yasa ma taji daɗi
da ya zaɓe ta a matsayin wacce zata riƙe Reina.

"Billahilla..."

"Addah babu ruwan ki da abinda ya shafe ni ko iyali na daga yau. An baki amana kuma kin ci, na gode.
Dan Allah ki bani wuri kafin alaƙar dake tsakanin mu ma in datse shi"

Cikin sanyin jiki ta tunkari ƙofa idanun ta ya sauƙa cikin na sauran ƴan uwan su mata da maza da suka iso
lokaci guda kaman haɗin baki. Ratsa tsakanin su tayi ta wuce, itama ƴar ta na biye da ita, amma babu
wanda yayi ƙoƙarin tsaida ta ko kuma ya bi bayan ta, sai ma ƙoƙarin kutsa kai da suka yi cikin ɗakin
amma a kan fuskokin su Alhaji Tahir ya rufo ƙofar ya saka masa lock.

Ya ƙara ma Reina gudun Ac saboda zufan da ke kan keto mata kafin ya ƙarasa jikin gadon ya ciro wayar
shi.

Hoton raunin ta ya ɗauka ya tura ma Fauziyya ta Whatsapp tare da saƙon da yake cewa 'Idan kinga dama
ki dawo' ya maida wayar aljihu Sannan ya koma ya zauna cikin rasa abun yi.

.....

Share zufan kan goshin shi yayi da handkerchief ya mayar cikin aljihun 3 quater ɗin jikin shi kafin ya
sauƙe tukunyar daga kan murhu saboda wutan yanzu yayi ƙasa sosai.

Ya zazzage tokan da ya taru, kana ya miƙe zuwa wurin da aka jingine buhun gawayi ya saka parker ya
ɗibo. Juyowar da zai yi yaci karo da Suhail ya saka hannu ya dumbulo dambu yana zubawa a cikin rigan
shi, sai yarfe hannu yake yi saboda zafi.

Taku ɗaya biyu Yaseer ya riƙo shi.


"Mayar!"

"Yayan mu dan Allah, ma su Ibrahim zan kai wallahi, basu yi yanka bane su" yace yana ƙoƙarin ƙwacewa.

Ajiye parkern gawayin Yaseer yayi ya riƙe shi hannu biyu. "Don basu yi yanka ba sai aka ce kai kayi sata
ka basu? Bari yanzu umma zata zo ta same ka".

Motsin fitowar Umman da suka fara ji ya saka Suhail tsurewa. Gashi ko motsi ya gagara balle ya ƙwace
ya gudu, kuma ya san idan ya kuskura ta kama shi toh Allah ne kadai mai iya ceton shi.

"Yayan mu dan Allah kayi haƙuri, wallahi Allah ba zan sake ba, na tuba."

Sai da Yaseer ya mayar da naman tunkunya kafin ya sake shi ya ɗiba da ɗan banzan gudu yayi waje
lokacin da Saudat ta fito riƙe da bokitin wanka.

Kwafa tayi bayan taga ƙyallin wucewar shi.

"Ai da ka jira ni nazo na same ka kayi min bayani da harshen larabci"

Duba suyan dambun tayi tace Yaseer ɗin ya ƙara kaɗan kawai ya sauƙe,

Sannan ta wuce ɗaki don shiryawa.

Da ya gama ya haɗo da tsokar da ta soya ya shigar mata ɗaki. Babu ɓata lokaci ta fara kakkasawa a cikin
laidoji ana ƙara mishi auki da ƙashi da cin-cin tunda naman dama ba wani yawa can yake da shi ba.
Adashen layya su kamal suka yi a wurin aiki fiye da su goma a kan saniya ɗaya madaidaiciya sai kuma
naman da aka basu kyauta daga kamfani.
Amma alhamdulillah duk an ƙuƙƙulla ma maƙwafta kuma su ma zasu samu wanda zai kwana musu biyu
suna motsa baki.

"Umma nace ba" Yaseer ya kira ta yana ƙulle laidar bayan an gama kaso.

"Ina jin ka" ta amsa tana kai soyayyen hanta baki.

"Daman a masallacin idi da safe ne na haɗu da malamin mu na Hadda. Shine yake min tayin koyarwa a
makarantar na wucin gadi tunda ba yanzu zan fara zuwa makaranta ba. Yace ko wani wata dubu Sha uku
albashin, kinga ko na wata 5 nayi zan tara wani abun da zai yi amfani idan admission ya samu."

Ta saurare shi har saida ya kai aya kana tace. "Toh yanzu yaya kake so ayi?"

Ɗan muskutawa kusa da ita yayi yace "dan Allah ki roƙa min Abbah ko zai yarda. Wallahi ina son zuwa,
kuma kinga nima zan samu dama in duba wasu litattafan da bani da ilimin su in sake tisa wanda na fara
mantawa. Kuma ai yafi zaman hakan nan ko Umma?"

"Shikkenan, idan ya dawo zan tunkare shi da zancen in sha Allah"

"Yauwa na gode Umma na. Allah ya saka muku da gidan aljannah"

Ta kalle fara'ar dake fuskar shi, da gaske yana son zuwan ne ba don kuɗin ba. Kana ta amsa da "ameen"

.....

_Sallah da kwana 8_
"Assalamu alaikum" Sallamar su yayi daidai da shigowar su saboda an riga anyi musu Iso.

"Wa'alaikumus salam." Hajiya Fauziyya ta amsa da rabin nutsuwar ta. Sauran rabin kuma na wurin Reina
da take ƙoƙarin kai wa lomar abinci baki amma ta kawar da kai tana ta kuka.

Dungure Bowl ɗin Hajiya Fauziyya tayi ta miƙe cikin ƙosawa da kafiyar ta tana faɗin "kada ki ci!" sannan
ta ɗan saki fuska domin ta gaida su Saudat don baki ɗaya tun da ta dawo a rikice take.

Reina ita ce da ciwo a jikin ta amma ita ke shan wahala.

"Me ya saka ta kuka kuma?" Saudat ta tambaya tana zama a gefen Reina cikin kulawar kada ta fama
mata ciwo don ga ƙafafuwan nan a ɗaure.

"Wallahi ɓaci ne dai da kika santa da shi tun da. Kullum ayi ta fama da ita sai kace ita kaɗai ne ƴa!"

"Toh ana haƙuri dai Aunty, shi jinya daman sai an kai zuciya nesa, musamman ma na yaro don takura su
zama wuri ɗaya yake yi."

Jinjina kai kawai tayi ta canza zancen zuwa tambayar anyi Sallah Lafiya?, saboda idan ma tana complain a
kan ɓacin Reina ranta ƙara ɓaci yake yi.

itama Saudat tayi mata sannu da dawowa da addu'ar Allah yasa anyi Hajji karɓaɓɓe.

"Yauwa Umman Yaseer mu ɗan shiga daga ciki" hajiya Fauziyya ta buƙata tana fara wucewa.

Miƙewa tayi ta bita a baya suka shiga ɗakin ta dake ƙasa suka rufo ƙofa.
Yaseer ya kalli Reina dake faman sheshsheƙar kuka duk sai ta bashi tausayi ganin ƙunan da aka ce ta yin
har wurin guiwar ta.

Haɗa su Sabir da kayan ciye-ciyen da aka kawo musu yayi kafin ya tashi ya koma kusa da ita.

"Reina"

Ɗagowa tayi ta kalle shi da fuskar ta da yayi caɓa-caɓa.

Ta ƙara girma, ta yi ƙiba, kaman ta ya ƙara canzawa.

"Kukan me kike yi?" Ya tambaya tare da bata dukkan attention ɗin shi don yaji menene damuwar ta.

"Ka kira min Daddy na pleash" tace cikin gunjin kuka amma sai dariya yaso kama shi ganin har wa yanzu
bata da S. Sabir bai shekara uku ba harshen shi yayi kyau amma gashi tayi shida da sauran ta.

"Me yasa?"

"Yunwa nake ji"

"Yunwa kuma? Ba ga abinci ba?" Ya ɗago kwanon dake kan coffee table ɗin gaban su. Wani abu ne
kaman macaroni a ciki amma tun da yake bai taba ganin kalan wannan ba, ga wani abu kaman kindirmo
a jiki, shape ɗin shi wani iri amma kuma yana da kyau ko a idanu.

Kawar da kanta tayi "Ni bana ci,"

"Toh me zaki ci a kawo miki?"


"Daddy yace zai kawo min, donut da browniesh da cake ma. Ka kira shi don Allah" sai ga wasu hawayen
ɓaci zirr suna bin kuncin ta.

"Yana aiki yanzu amma idan kika ci abinci zai kawo miki idan zai dawo"

"Toh ai babu daɗi ne"

Da mamaki ya kai cokali ɗaya bakin shi, sai yaji akasin abinda tace.

"Wannan da daɗi fah Reina, taɓa ki ji"

Kawar da kai tayi tana ƙara gudun hawayen ta "ni dai bani shoo"

Ya sauƙe numfashi, dole ran mahaifiyar ta ma ya ɓaci ne, amma barin ta da yunwa ba shine maslaha ba.

"Toh in barbaɗa mana nama a kai sai mu ci tare?"

Sai da ta ɗan tsaya tunani kafin ta gyaɗa kai. Ya ɗauko laidar da suka zo da shi sannan ya ciro kwanon
samirar dake ɗauke da nama da cin-cin, ya ɗibi dambun nama mai ɗan yawa ya saka a kan abincin ya
cakuɗa kafin ya kai mata lomar farko.

"Taɓa kiji, yayi ko a ƙara?"

Jan hanci tayi kana ta gyaɗa kai "yayi"

"Yauwa idan kika cinye har cin-cin zan baki mai daɗi sosai sai kunnen ki ya tsinke" yace don ya lura tana
da son kayan zaƙi. kana ya ciro handkie a aljihun shi ya shiga share mata fuska, harda majinan dake
hancin ta, sannan ya miƙa mata handkie ɗin "toh riƙe mana wannan"
Babu musu ta karɓa ta riƙe, tana cin abincin yana share mata baki da bata ruwa har ta tada bowl ɗin tass
tana ɗan ƙaramin gyatsa.

Fitowar Hajiya Fauziyya kawai sai cin karo tayi da plate wayam.

~~~~~~~

*Zaku iya samun labarin daga farko zuwa wurin da aka tsaya a kan shafi na na Wattpad.*

*REINA 💍*

22....Wasa-wasa lokaci ya tafi.

Lokacin da Yaseer yake ganin zaman gida yayi masa yawa, ya tafi.

Lokacin da Hajiya Fauziyya ta ɗauka na Jinyar Reina, ya Tafi.


Lokacin da Alhaji Tahir ya ɗauka na jirar amincewar Alaji Abdou a kan sabuwar kasuwanci inji shi da faɗa,
shima ya tafi.

Kusan za'a ce abubuwa da yawa ne suka faru a Rana guda amma lokaci mabanbanta.

.....

Kai kawo yake a cikin office ɗin shi, yana kallon agogon dake manne a bango, da wanda ke ɗaure a
tsintsiyar hannun shi, da ma wanda ke fuskar wayar shi.

Tun daga lokacin da ya yanke shawara da zuciyar shi, da ilimin shi, da kuma experience da yake da shi na
shekara da shekaru a kan harƙar samu da kuma sarrafa kuɗi, Hankalin shi ya samu wuri ya kwanta
kaman tsumma a randa. domin yana da tabbacin sai yayi dariya ma Alaji Abdou, kuma zai goranta mishi
rashin amfani da damar da yazo har cikin tafin hannun shi kuma ya bar shi ya suɓuce.

Saidai fa a yau ɗin da lokaci ya ƙarato, a maimakon ya samu kan shi da murna sai kuma fargaba tazo ta
shanye shi. Bayi son zana ko ɗigo na shakku a kan zuciyar shi amma yana tsoron harsashen alaji Abdou
ya zamo gaskiya.

Cikin saabo da hanzari, dogon hannun agogo ya tsallaka kan lamba ta sha biyu yayin da shi kuma guntun
hannu a kasalance yayi nuni da lamba ta goma daga nesa.

Lokacin da suka bashi ya cika!.

Numfashin Alhaji Tahir ya ɗauke cakk na sauran sakwannin da suka ratsa har sai da saƙon Email ɗin da
yake jira ya shigo lokaci ɗaya tare da wani saƙon, wanda ya bayyana sunan ɗaya daga cikin bankunan da
yake amfani da shi a fakaice kafin ya koma sama ya ɓuya, zuwa lokacin da buƙatar mai saƙon zai tilasta
shi ya janyo shi don ya duba.

Sai komai ya tsaya mishi, kunnuwan shi suka daina jin wani abu bayan bugun zuciyar shi, Idanun shi suka
daina ganin komai bayan wayan da ke hannun shi, yayin da yatsar shi ya danna kan saƙon email ɗin ya
buɗe ta sannan ya shiga karanta abinda aka rubuto.
Bai gama yarda da abinda ya gani ba har saida ya janyo saƙon ɗazu da yayi masa ƙwalele ya shiga ciki,
idanun shi suka yi arba da maƙudan kuɗaɗen da suka shigo account ɗin shi.

Dala miliyan ɗari da hamsin.

Jiri yaji kaman yana shirin ɗiban shi, ya ɗan dafa jikin teburin gaban shi amman bai zauna ba. Sake
karanta yawan kuɗin yake yi, yana jin wani diri a cikin kan shi. Ba don bayi da kamar hakan ba, amma ko
a shekara Ribar duk wani reshe na TK Kingdom idan aka haɗa ba zasu ɗare hakan ba. Kuma ba nashi shi
kaɗai bane harda sauran masu hannun jari. Amma yau a cikin wata uku kacal ya samu ribar Dala miliyan
ɗari ba tare da zufar shi ba, wanda idan aka juya shi zuwa naira toh biliyan ne da ɗoriya mai yawa ya
samu a ɓagas!. Sai kawai ya shiga nanata hasbunallahu wa ni'imal wakeel a kan harshen shi don ya samu
nutsuwa ta dawo mishi.

Ruwa ya sha kana ya samu wuri ya zauna ya dannan kiran lambar Fauziyya.

Har ya shiga bugu ɗaya sai kuma yayi saurin yankewa kafin ta kai ga ɗauka, ya maida kiran ma Alaji
Abdou, domin so yake yi ya nuna mishi ɓacin ran shi da ya hana shi shiga da dala miliyan 200 kaman
yanda yayi niyya, ƙarshe da ya gaji da jiran shi ne kawai ya shiga da dala miliyan 50 a sirrance. Gashi ta
hayayyafa har da jikoki.

Saidai ya kira har sau biyu ba'a ɗauka ba. Saida na ukun ma ya kusan tsinkewa kafin Alaji Abdou ya ɗauka
tare da yin sallama muryar shi a sanyaye.

"Wa'alaikumus salam. Abdou daman mai na faɗa maka?... Pro"

"Malika Ta Rasu Tahir. Yanzu zamu kaita makwancin ta" ya faɗa muryar shi na karyewa. "Idan na dawo
zamuyi maganar koma menene, ko zuwa gobe ma, ko anjima da safe, ina zaka iya jira?"

Abinda bai taɓa fata ba shine ganin abinda zai rikita Alhaji Abdou, duk tashin hankali da bala'in ka saidai
kayi ka bar shi, amma yau gashi ya gani.
"Ina hanya nan da awa ɗaya in sha Allah" shine abinda yace amma bayi da tabbacin Alaji Abdou ɗin ya ji
saboda katse kiran da yayi a lokacin.

A gaggauce ya kira Hajiya Fauziyya ya sanar da ita ta shirya zasu wuce Nijar yanzu.

....

Ajiye wayar tayi tare da duban Reina da ta ƙwace glass bowl ɗin hannun Maama wanda ke ɗauke da
butter da kuma sugar a ciki tana ta faman juyawa.

Yarinyar da idan miƙo kaza aka ce mata sai ta kawo maka uzuri guda hamsin kuma idan ba da jan ido ba
bazata miƙo ba.

Reina bata aikuwa bata aikatuwa, saidai idan buƙatar tata ce, toh fa nan kam bata da nauyin jiki.

Domin yanzun ma makaranta ta ki zuwa firr wai ƙafafun ta na ciwo kuma uban ta ya biye mata. Ƙafar da
har India suka je, suka shafe tsawon lokaci a can, aka yi mata aiki sosai saboda kada idan ya gama
warkewa ya bar tabo da yawa.

An ƙarashe third term lokacin tana tsaka mai wuya amma haka aka cinye sabon first term da second
term har wani third term ɗin ya sake zagowa ana shirin exams bai fi na sati biyu taje school ba a cikin
shekara guda. Islamiyya kan ma ba'a magana daman bata shiga da wuri ba gashi ya hana a taɓa ta don
haka babu abinda ta iya bayan fatiha da ƙulaƙuzai, shima Ita ta kai zuciya nesa ta koya mata.

Shine fa mai ciwon ƙafa taji ana zancen za'a yi waffles ta baje a kan kitchen Island tana buga buttern nan
da sugar kaman Allah ne ya aiko ta, sai Maama ta koma kallon ta kawai tana shiru.
"Ki sauƙa ki wanke hannun ki zamu yi tafiya da Daddy" Fauziyya tace don bata son doguwar magana
saboda saƙon mutuwar da ta samu.

Da murna ta dangwara ma Maama bowl din sannan ta taka kujera ta sauƙa don ta san duk inda za'a je da
Daddy toh fa jin daɗi ne.

"Aina'u dan Allah bita ki haɗa musu kayan su kala ɗaya ko biyu"

"Toh Aunty" Aina'un ta amsa.

Har ta juya zata tafi ta kira ta "ba masu ado sosai ba, ɗan na canzawa kawai"

Nan ma da toh ta amsa sannan ta tasa ƙeyar Reina zuwa ɗakin kwanan su ita da Maama, ta ɗauko ƴar
madaidaiciyar traveling bag ta shiga zaɓar kayan.

Karan tsaye Reina tayi mata, ita sai wanda take so za'a saka daga cikin jerin gowns ɗin ta kuma.

Share ta kawai Aina'u tayi ta ci gaba da aikin ta. Sai kawai ta saka mata rikici tana jawo gogaggun kayan
dake ninke tana fatali da su a tsakar ɗakin.

"Hajiya ƙarama dan Allah ki bari!" Tace cikin ƙosawa kaman zata yi kuka sannan ta fara maida kayan
bayan ta barta ta zaɓi wanda take so ɗin an haɗa a kan wanda ya kamata.

Handkerchief ne ya faɗo, Aina'u ta ɗauka zata mayar Reina tayi saurin faucewa daga hannun ta. Ta tuna
da mai ita, kuma tun wancan Ranar Aunty take ajiye da shi a kan idan sun sake zuwa za'a maida mishi
kayan shi.

Cikin jakar kayan sun ta cusa, da nufin idan sun fita sai tace ma Daddyn ta su je gidansu su mayar mishi.
....

Da wayan Saudat yake magana da abokin shi wanda suka yi paper tare sannan shima yaci Jamb da waec
wanda sakamakon su sun daɗe da fitowa har an fara sake sakamakon neco ma.

Kuma tare suka je suka yi physical screening a Atbu tunda zancen University of Ibadan ya gagara.

Kamal ya buga ya buga amma abun yafi ƙarfin shi, don haka da yaga babu sarki sai Allah shine ya shafa
ma kan shi ruwan sanyi ya bar komai a hannun rabbana, gwanda ma Yaseer ɗin ya zauna a kusa a gaban
idanun su yayi karatun zai fi musu kwanciyar hankali.

Ta ɗaya layin aka ce da shi.

"Yanzu na gani kaima ka duba."

"Na taya ka murna Muhammad, zan duba nima yanzu in kira ka"

Da wannan suka gama kiran ya ajiye ma Umman wayan ta sannan ya fito ya same ta a kitchen ya sanar
da ita zai je cafe ɗin da aka buɗe mishi e-mail a duba ko an turo mishi da admission letter.

Ɗari biyar ta bashi, ya canza takalmi daga silifas ɗin ƙafar shi zuwa wani kana ya fice.

Ya ɗauki kaman mintuna 40 kafin ya dawo riƙe da takardu guda biyu a hannun shi, ƙolla cike a idanun
shi.

"Umma gashi sun turo min, sun amshe ni a matsayin ɗalibin su umma kuma sun bani course ɗin da nake
so"
Da murna ta miƙe ta tunkaro shi, yana tsaye a wurin ya gagara motsawa don haka ta amshi takardar da
ɗan guntun turancin ta dai ta duba.

"Masha Allah, alhamdulillah!" Addu'a tayi mishi sosai tana saka mishi albarka sannan tace yaje ya gwada
ma su danejo da gidan Liman, don ko yaushe tambayar su kenan a kan makarantar tashi.

"Toh ki riƙe min wannan umma sai inje in gwada musu ɗayan"

Ya bata ɗaya takardan dake hannun shi.

"Wannan kuma na menene?" Ta tambaya tana dubawa ko shima zata gane.

"Bayanin registration ne a jiki da kuma kuɗin da za'a biya"

"Kuma har nawa?" Ta buƙata.

Dubawa yayi daga kuɗin makaranta, hostel da sauran su.

Sai ya kalle ta. "Umma da yawa fa"

Karɓan takardan kawai tayi tana ƙirga yawan zeros ɗin dake jikin total.

"Miliyan ɗaya nake gani haka ko nawa?" Tace cikin tsananin kaɗuwa.

Ya karɓe takardan don sake tabbatarwa kana ya saki murmushi "Haba miliyan? Dubu ɗari ne da sha
takwas amma banda kuɗin su hostel da wasu abubuwan"
Jinjina kai tayi, In sha Allah ba zai gagara ba tunda sun daɗe suna tarawa. Amma zancen wani hostel kam
sai Kamal ya dawo sun sake shawara.

.....

Ciki Aka wuce da su Hajiya Fauziyya shi kuma Alhaji Tahir ya tsaya a waje wurin karɓan gaisuwa tare da
Alaji Abdou ɗin wanda ya gama yin sukuku har magana tana niman gagaran shi a yanzu.

A yanzun da yaje ya saka Malika a rami da hannun shi mutane suka taya shi ya rufe. Ya tabbatar da cewa
ya rasa ta kenan har abada, kuma shi da Aicha sunyi rashin da zai canza ƙaddarar su baki ɗaya.

Kukan ta shine abinda ya fara riskar su da shigan su parlorn. Tana yi tana kiran mummy.

maƙale take a jikin ƙanwar mahaifiyar ta wanda itama kukan take yi balle a samu ta rarrasheta, Gashi
anyi a raba su abu ya gagara.

"Amma me yasa za'a faɗi mutuwa ma yarinya ƙarama haka?"

Fauziyya ta koka cikin rashin jin daɗi tana ƙoƙarin jawo Aicha jikin ta.

Ganin ita ce yasa ta yarda tazo ta kwanta luff a jikin ta.

"A gaban idanun ta Allah ya ɗauki ran ta. Allah ya jiƙan ki lalla Malika, ashe wannan kwanciya ba na tashi
bane" cewar ƙanwar mahaifin su tana fashewa da kuka.

Sai itama Aicha ta sake fashewa da kuka tare da ɗagowa. "Aunty dan Allah ki kaini wurin mummy na.
Please bata mutu ba, she just fell asleep, idan naje wurin ta zata tashi"

Har yanzu Aicha tayi yarinta ma sanin mutuwa amma sun riga da sun fahimtar da ita, babu ƙyaryar kuma
da zata yi ya rufe mata hakan saidai kawai ta kwantar mata da hankali.
Kitson da ya sauƙo kan fuskarta ta mayar baya ta fara share mata hawaye da hannun ta, wani kukan yafi
gaban tissue. "Ki yi haƙuri Darling kin ji? Zamu je wurin mummy amma sai kin daina kuka"

Laƙanin da tayi amfani da shi sai ya tuna mata da Malika, a ko ina a gaban kowa takan kira ta da hakan,
amma gashi yau mai yanke ƙauna ta raba ta da gudan jinin ta.

Ɗan ƙaramin farin hannu suka ga ya miƙo handkerchief navy blue mai manyan check ɗin light green zai
shiga goge mata hawayen tayi saurin kawar da fuskar ta tare da matsawa daga Jikin Reina.

"Stop crying Please my friend" Reina tace itama idanun ta na kawo ruwa. Ita a lissafin ta Aicha ƙawar ta
ne, tunda daddyn ta yana yawan zuwa wurin nata daddyn a Nigeria, sannan mummyn su ma suna zuwa
gidan juna, don haka Aicha is her friend. Sai ta ƙara matsawa kusa da ita da handkie ɗin, Aicha ma tayi
saurin sake jan baya.

Ita kuma a nata lissafin har yanzu ɗan uwa namiji take so, bata son mace, kuma idan tayi ƙawance da
Reina shikkenan Aunty ba zata kawo mata brother ba don haka take share su ita da Maama ma.

"Ki bar kuka kinji? Please" zuwa yanzu S ɗin ta ya fara fitowa amma irin mai cika bakin nan domin sai ta
fisge shi ta ƙarfi. don haka miyan bakin ta ya tsartu a kan fuskar Aicha, sai ta ƙwace handkie ɗin
hannunta ta goge fuskar ta da shi sannan ta dunƙule shi a hannunta ta kwantar da kanta saman cinyar
Hajiya Fauziyya tana ajiyar zuciya. Reina kuma ta rasa yanda zata yi ta karɓa handkien Yaseer daga
hannunta tunda itama ba nata bane.

~~~~~~~~

*Eid Mubarak 💕*

*REINA 💍*
Instagram, tiktok, arewabooks and Wattpad @Seemahwrites.

23....... Ɗaga kai yayi ya kalli girman mashigar Jami'ar bayan sauƙar shi daga kan mashin.

Shima yanzu ɗalibi ne a nan.

Goye yake da madaidaiciyar jakar baya sai kuma green file a hannun shi wanda ba zai samu shiga jakar
ba saboda ya fi shi tsayi.

Ɗalibai ne kala da iri, mata da maza, musulmai da arna, sabbin zuwa masu riƙe da file irin nashi da kuma
gabatattu, sai kuma motoci da napep ɗin makaranta da ke shigar da wasu ɗaliban ciki.

Ko ƙafa bai ɗaga daga wurin ba yaji sallamar wata daga bayan shi. Ya fahimci yana tsaye a kan hanya don
haka ya matsa mata ta wuce amma sai ta dawo gaban shi ta tsaya, itama tana ɗauke da file irin nashi
amma kalar blue.

"Ina kwana, baka gane ni bane?"

Murmushi ne kwance a kan fuskar ta ga ƙawayen ta da suke tare sun ja gefe suna jiran ta idanun su a
kansu don haka ya saki ƙaramin murmushi shima saboda kada ya disga ta.
"Yi haƙuri fuskar ta ɓace min" yace ba yabo ba fallasa.

Ɗage gira tayi tare da matse baki a yangance tace "kai da wani abokin ka kuka kai ni department ɗinmu
lokacin da muka zo physical screening amma har ka manta?"

Abokin shi ya raka ta dai. amma shi hanyar bursary ya ɗauka ganin zasu ɓata mishi lokaci gashi wa'inda
suka san wurin sun faɗa mishi akwai layi.

Sai kawai yace da ita "oh ayyah, yaya kike"

"Lafiya lau" ta amsa tana wani kashe murya sannan ta ƙara da "kada in ɓata maka lokaci mu shiga ciki"

Hauka take yi zata saka shi jerawa da ƴammata? Itama yayi imani ko sunan ta bai sani ba.

"No, Ina jiran abokina ne bai ƙaraso ba, kuyi gaba kawai kada in tsayar da ku"

Bata ji daɗi ba don tana ganin shi tace ma ƙawayen da tayi a zuwan ta ɗaya makarantar cewa shi friend
ɗinta ne, amma sai bata gwada a fuskar ta ba ta ciro ƴar IPhone ɗinta daga cikin side bag ɗinta ta miƙa
mishi.

"Toh gashi saka min number ka idan mun gama sai in nime ka"

Kallon wayar yayi zuwa kan fuskar ta kai tsaye yace "bani da waya"

Ba zallan ƙawayen ta ba har maza guda biyu da suka zo wucewa ta bayan su saida suka juyo suka kalle
shi.
Daidai lokacin Muhammad ya ɗaura hannu saman kafaɗar Yaseer yana cewa "aboki na iso muje" sai
kuma idanun shi ya sauƙa a kan fuskar yarinyar a take ya washe baki yana faɗin "summy kece?"

Bata kula shi ba ta karɓi wayan ta daga hannun Yaseer cikin ɓacin rai, Bata taɓa haɗuwa da ɗan rainin
hankali irin wannan ba. Ta juya tayi gaba abinta ko bin ta kan kawayen tan bata yi ba, amma haka suka
rufa mata baya, shi kuwa Yaseer an barshi tsaye kasake don bai ga abinda yayi ba, gaskiyar shi kawai ya
faɗa mata.

Hannun Muhammad dake kafaɗan shi ya fara sauƙewa ya ɗan harare shi kana yace "mufa yanzu ba ƴan
secondary bane"

Baki Muhammad ya taɓe tare da faɗin "sorry, let's go" suke jera a tare suka shiga makarantar bayan sun
gwada ma security admission letter ɗinsu an basu damar wucewa.

Student market suka fara zuwa domin su bayar da kuɗin makarantar a biya musu.

Shaguna sun riga da sun cika da wasu ɗaliban don haka suka tsaya a wurin wanda suka baza na'urorin
su a tsakiyar fili sai manyan lema da yayi musu rumfa, suka yi sallama tare da zama a wani benci, saitin
wata budurwa da itama tazo nata registration ɗin sai faman yauƙi take yi kaman karkashi.

Bai bi ta kanta ba domin bai ma lura da ita ba suna taɓa hira da Muhammad, sai yayi ƙasa da murya tare
da raɗa masa "my friend kalli wata zillaziya a gaban mu don Allah."

Zai ɗago ɗin kaman yanda yace sai kuma ya danne kafaɗar shi tare da faɗin "a fakaice, kada kayi ta gane
ta raina mu please"

Bai damu ba ya ɗago ya dubeta, ai kuwa suka yi ido hudu. Fara ce ƙar kuma tana da kyan fuska irin na
fulanin usuli ɗinnan amma bayan nan bai ji ta wani burge shi ba. Mummunan hararar da ta watsa mishi
ya saka shi tamke fuska ya mayar da hankalin shi wani wurin, cikin rashin Sa'a kuma duk dagowan da zai
yi sai sun haɗa idanu kuma bata fasa hararar shi ba, shima sai ya sha kunu kawai.
Sai da aka gama da wata mai niƙab kafin aka zo kanta, tana bada bayanan ta kaman bata son bayarwa
amma shi mai shigarwar sai wani rawar ƙafa yake yi da ta gama ma cewa yayi ta bar kuɗin aikin da ya
mata ba sai ta biya ba, a yatsine ta ciri miƙaƙƙun dubu-dubu guda uku ta zuba mishi a wurin tayi gaba.

Bai damu ba tunda ya ɗauki number wayar ta a kan profile ɗinta ya juyo kan su Yaseer.

Da Muhammad aka fara kafin aka zo kan Yaseer, ya bashi kuɗin da yazo da su ya ƙirga sannan yace masa
saura 1500 kuɗin generating RRR da kuma registration ɗin, harda shirya mishi profile ɗinshi.

Bai san da wannan ba amma cikin Sa'a akwai wasu kuɗin a jikin shi don haka ya cire ya biya, aka gama
komai akayi printing musu aka basu daga nan kuma zasu wuce department su biya deparmental dues sai
kuma kuɗin SUG.

Kafin wani lokaci Yaseer ya cire wurin dubu goma sha biyar wanda bai san da lissafin su ba daga cikin
kuɗin koyarwar da yayi a islamiyya. Ba don Allah ya taimake shi yayi tunanin zuwa da kuɗin ba ma da bai
san yaya zai yi ba.

Cafeteria suka je cin abinci, jin kuɗin plate ɗin abincin yasa ya gwammace siyan eggroll da pop cola suka
samu inuwar cooldown suka zauna suka ci suka wuce masallaci suka yi sallar azahar, zuwa lokacin har ya
fara jigata domin bai ɗauka ɗawainiyar ta kai haka ba.

Daga nan suka wuce bursary domin yin changing teller to receipt. Dogon layin da suka gani yau ɗin ya
ƙara sanyaya musu guiwa amma haka suka jona na freshers suma, domin Muhammad ya bada shawarar
ko su tafi gida suyi sammako gobe amma yaga gwanda su gama baki ɗaya kawai su huta.

Zaune a gefe idanun shi suka hango mishi Summy da mabiyan ta, sai mamaki ya kama shi na dalilin da ita
bata shiga layin ba amma babu daɗewa ya samu amsar shi yayin da wani saurayi ya ƙaraso da receipt
ɗinsu duka ya riga ya shiga gaban wasu ya karɓo.
Wato har a tsakanin ɗalibai ma akwai connection, idan kana da ƙafa babu abinda ba zaka samu a cikin
sauƙi ba. Shi dai saurayin daga ganin shi ba fresher bane saboda ya ɗan manyanta ga kuma ID card dake
saƙale a wuyan shi da tambarin SUG An rubuta 'How may I help you' a jiki, taimakon na masu shafa tozali
ne kenan.

.......

A ɗan zaman da Hajiya Fauziyya suka yi a Nijar Aicha ta samu kulawa sosai daga gareta, ga ƙanwar
mahaifiyar ta ma dake iya nata ƙoƙarin sai duk ta dawo ƴar gata bayan damuwar rashin uwa da take ciki.

An bar Reina da gallafiri a tsakani tunda kaman ma uwar ta bata da lokacin ta ne, ga daɗin cewa Aicha
bata son ganin ta a kusa da ita. Don haka sai ta wuni tana wasa ko game, Alhaji Tahir shi ke niman ta ya
bata abincin safe, rana da kuma dare idan ba haka ba sai dai tasha yunwa abunta ba damuwar Fauziyya
bane, gata da bala'in zaɓe shi yasa ta daɗa fita sha'anin ta.

Amma ko dan rashin shan faɗan auntyn nata a kullum da kuma rashin zuwa makaranta tana jin daɗin
zaman ta a gidan.

Zaune Alhaji Tahir yake yana fuskantar Alaji Abdou dake riƙe da kai.

"Ko kwana bakwai Malika bata yi a cikin makwancin ta ba amma wai so suke yi su ɗaura min wani auren"
yace cikin ƙunan rai.

"Kana buƙatar mai kula da Aisha" Alhaji Tahir ya mayar mishi.

Ɗago kai yayi ya kalle shi da idanun shi da suka gaza daidaita kala na tsawon kwanaki "ba zan samu mai
kula da ita ba sai nayi aure? Ashe dalilin aure yakan iya zama komai? Ƙanwar ta fa suke son aura min? Ta
yaya za'ayi in iya rayuwar aure da wacce na ɗauke ta a matsayin tawa ƙanwar? Idan kai ne haka ya faru
da kai sai ka yarda"

Da sauri Alhaji Tahir ya girgiza kai. "Allah ya kiyaye, Ba zai faru dani ba ma in sha Allah. Ka bamu ita mu
koma Nigeria zata samu kulawar da take buƙata a hannun mu sai kayi ƙoƙarin daidaita komai a nan ɗin"
"Zata takura ma ƴar ka, ka bari in nemi wata hanyar kawai."

Numfashi Alhaji Tahir ya ja ya furzar don ya san gaskiya ne, ba zai iya jurar hantarar Aicha a kan Reina na
tsawon lokaci ba.

"Yauwa maganar meye kace kana son muyi jiya?"

Girgiza kai kawai Alhaji Tahir yayi don bayi son ƙara ma Alaji Abdou damuwa a kan damuwar da ya riga
yake ciki amma sanar da shi alkhairin da ya samu a kan wannan project da yaso hana shi yake son yi da
kuma niyyar shi na sake komawa a karo na biyu da yawan kuɗin yayi niyyar zubawa tun farko.

"Kada ka damu, babu komai, Allah ya jiƙan Malika"

Da ameen ya amsa ya maida kan shi baya ya jingina yana ci gaba da mata addu'a da nima mata gafara a
wurin Allah lokacin da kawunan shi da mahaifin Malika suka shigo ƙaramin parlourn da sallama.

Niman wuri kowannen su yayi ya zauna sannan suka dubi Alaji Abdou da idanun shi ke rufe dukda yaji
shigowan nasu amma sanin abinda suke tafe dashi yasa ba zai kula su ba.

Da faransanci suka fara mishi faɗa a kan yanda ya saka mutuwar a ran shi yana jin su bai tanka ba har
suka ɗaura da zancen auren da suke da niyyar mishi.

"Kaga yanzu ma ɗaura auren ga, ba sai jimawa ba, sabida dukkanin ku kai da ɗiyar ka ku samu nutsuwa,
Mariama zata kula da Aicha kamar ita ta haife ta"

Sai a sannan ya buɗe idanun shi da suka tara ruwan masifa ya zuba musu "haba! Lalla Malika kwana
bakwai batai ba cikin kabari!"
"Ai ba munce tarewa zata yi yanzu ba. Amma a matsayin mu babannin ka hakki nai kanmu mu kyautata
rayuwar ka, don haka sadaki zaka kawo"

Alhaji Tahir dai ya dawo ɗan kallo, yana ayyana haƙurin Alhaji Abdou a cikin ranshi don shhikam ba'a isa
ayi masa wannan iskancin ba.

"Ni babu kuɗi a jiki na"

"Janyo wayarka ka tura, kai ko fa bashi ne sai an ɗaura auren nan" cewar ƙanin mahaifin shi da yafi
zaƙewa a maganar.

Ƙarshe dai Alhaji Tahir ne ya ɗauki alhakin biyar sadakin ganin zasu kai ruwa rana.

A lokacin da aka sanar da Mariama zancen auren kuwa suma kawai tayi. Ai su Alhaji Tahir basu ƙara
kwana ɗaya a Nijar ba suka tattaro suka dawo gida, domin riciki ne ya tashi Mariama harda tada aljanu.

......

A yau aka buɗe portal ɗin booking na hostel, Zuwa ranan Monday kuma za'a fara lectures. Saudat da
Kamal kuma sun gagara samun daidaito a tsakanin su game da zaman shi a gida ko hostel har abin yana
son kawo musu sabani, domin Saudat kafewa tayi kai da fata na cewa zaman hostel ɓata mata tarbiyyar
yaro zai yi, shi kuma kamal faɗi yake yi tana son ya zauna ne don yana yi mata aiki bayan shi a yanzu
karatu ya saka a gaba.

Shi kuma nashi damuwar bai wuce na kuɗaɗen da ya kashe a cikin sati guda ba kawai. Ance dubu ɗari da
sha takwas amma in harda kuɗin da ya cire a jikin shi ba tare da sanin mahaifan nashi ba kusan dubu ɗari
da Arba'in kenan gashi kuɗin kama hostel ɗin ma kawai dubu sha biyar ne, ƙaramin kenan, domin ko
hararar na dubu Arba'in ɗin bai fara ba.

Idan yace a bari ma kuɗin abin hawan zuwa da dawowa kullum da kuma abinda zai ci shima ba kaɗan ba.
"Shirya ka fito kaje ka biya kuɗin" Kamal yace daga bakin ƙofa.

Da sauri ya miƙe ya fito sannan yace "booking ne zamu yi yanzu Abbah ba'a fara biyan kuɗin ba tukunna"

Kuɗin da zai bayar ayi mishi booking ɗin a cafe ya bashi ya shirya ya fito, Saudat tana zaune tana sana'ar
kitson ta ma wata yarinya, ko duban shi bata yi ba.

"Umma barin je in dawo"

Sanin darajar addu'ar iyaye a kan yaran su ya saka ta cewa "Allah ya tsare" amma shi da Kamal ɗin zasu
ce ta faɗa musu.

In ba haka ba mutum yana da gida da iyaye da ƴan uwa ya koma zaman kanshi da sunan karatu? Shi
karatun Addini toh me yasa ba'a yi mishi haka? Wanda zai zauna da su ɗin mai zasu taimaka mishi da
shi?.

*Saliha Ahmad Na'ibi ✨*

*REINA 💍*

24......Dake abun ma rabo ne, ba ƙaramin murna Saudat tayi ba da Yaseer bai samu hostel ba. Hakan bai
hana Kamal kafa mata sharuɗa a kan karatun shi ba, ta dai saurare shi tunda buƙatar ta ya biya.
Bai samu wani matsala ba ta bangaren karatu daga farko saboda zuciyar shi da hankalin shi yana kai.

Kowa na ƙoƙarin tantance ƴammata da abokan da suka dace da ra'ayin su amma shi ba wannan bane a
gaban shi, sanin cewa shi ba ɗan kowa bane ba zai je ya saka kan shi wurin da Allah bai kai shi ba don
haka ya ɗaga idanun shi daga kalan rayuwar da suke yi.

Daga farko Saudat ta fara ɗaga mishi ƙafa a kan komai, don ma bayi dawowa gida sai can yamma ga
lectures har Saturday, Sai da karatu ya fara nisa ne lokaci ya fara kasa mishi. Yawancin ɗalibai har
karatun dare da asuba suke fita amma shi ba zai iya zama a jikin takarda ba yana kallon mahaifiyar shi na
aikace-aikacen gida da ɗawainiyar yara, idan yana son yayi karatu sai dai ya hana idanun shi barci ga
course ɗin da ya ɗauka ba dai wahala ba, ga kuma sammakon fitan sassafe.

A haka dai ya rubuta jarabawar zango na farko a wahalce. Ranar da sakamako ya fito kafin ya duba wasu
wanda suka saka ma rayuwar shi idanu sun riga shi, shi karan kanshi ya sha mamakin ganin shi a VC's list.

Zuwa sabon zango ya riga da ya shiga cikin jerin gurayen da ake ji da su a engineering department. Kafin
kace me ƴammatan ko wani ɓangare sun fara manne masa don ya koya musu MTH 121 da MTH 122 har
ɓangaren su Physics da Chemistry ba'a bar shi ba, gashi bai iya wulaƙanci ba, sai ya dawo bayi da lokacin
sauran nashi karatun, wataran ma bayi dawowa gida sai bayan isha.

Sosai points ɗin shi suka sauƙa da sakamakon jarabawar kammala aji ɗaya ya fito, don haka shi da kanshi
ya roƙa da a barshi ya zauna a hostel wannan karon.

Ganin yanda ya zabge ya lalace ya saka Saudat bata yi musu ba, itama ta san stress yayi mishi yawa
domin har haɓo yake yi yanzu idan karatun yayi mishi yawa.

Zata fawwala ma Allah lamarin sa kawai, ta kuma bishi da addu'a, domin ɗan yau ko a ɗaki kake kulle shi
idan yaso lalacewa zai lalace. Sannan kuma kowani tsuntsu kukan gidan su yake bi, duk da tabbas akwai
masu lalata tarbiyyar yara a makarantu saidai zata saka ido sosai a kan lamarin Yaseer, zata saka Kamal
yana bibiyar karatun shi da abokanan shi a makarantar sannan zasu ƙara dagewa a kan addu'a.

Da taimakon wani Gabata da yake koyawa ƙanwar shi karatu ya sama musu ɗaki shi da Muhammad ba
tare da yayi booking ba ma.
Wannan karon ma ba ƙaramin kuɗi Kamal ya kashe ba har saida ya nemi bashi ya cika, gashi shi nashi
kuɗaɗen sun daɗe da ƙarewa a sayi kaza sayi kaza wanda bayi son ya damu iyayen shi da su, ga wasu
manyan text book masu shegen tsada da ake saka su siya, shikam da bayi da halin siya sai dai yayi ta aro.

Ana gobe zai koma makarantar da zama Kamal yazo da kwalin waya soft touch mai sauƙin kuɗi ya damƙa
mishi.

Ƙwalla ne ya cika idanun shi ya tsura ma wayar idanu a tafin hannun shi, ko gama shan mamakin yawan
shopping ɗin da Saudat tayi mishi bai yi ba, tun daga kan kayan abinci, taliya macaroni, flour, doya,
shinkafa , manja, mangyaɗa, maggi da borkono. kayan amfani irin su sabulu, omo, mai da turare harda
su sabon kaya ta ɗibo mishi gumama set 3 masu kyau.

Toh shi idan bai dage yayi karatun ba da me zai saka ma iyayen shi?. Don haka bai bari shekara ta zago
ba saida ya mayar da abinda ya rasa kuma bai fasa taimaka ma wasu ba koda Allah zai cigaba da duban
shi da idon rahama.

.......

Kiɗa ne ke tashi daga tashar boom a talabijin dake manne a parlourn Hajiya Hauwa.

Reina da sa'oin ta ke cashewa a tsakar parlourn, sai kuma sauran ƴammata da samari kowa ya kama
owners corner daga masu chatting sai masu amsa waya.

Dawowar su daga kallon hawa kenan kowa jikin sa yayi luƙus banda yaran.

wata mace dake kusan tsirara tana twerking a music video da ake gwadawa suke gani suna gwadawa
suma. Harda rawan baɗala da gwamutsen mata da maza keyi shima duk suna kamantawa da ƴan uwan
su, kuma ba'a samu wani mai canza channel ɗin ko ya hana su ba.
Jamal ne ya leƙo parlourn, bayan ya tabbatar Umman shi bata kusa ya sauƙe ajiyar zuciya tare da
shigowa yana kaɗa key ɗin mota, zai yi sauri ne ya sauya kayan jikin shi kafin taji warin wani abu ta fara
masa sababi.

Bai cewa kowa komai ba ya ratsa tsakanin yaran da suka cika wurin kaman kiyashi sai jin ɗaya daga cikin
su yayi ya faɗo jikin kafafuwar shi, har suna niman tatile shi ya faɗi.

A masife ya sauƙe kai zai ɗauke koma waye da mari domin abinda ya zuƙa har yanzu bai gama sake shi
ba idanun shi ya sauƙa cikin na Reina dake ƙifi-ƙifi da idanu.

Murmushi ta sake mishi, shima sai ya mayar mata da murmushin ganin ita ce ya washe baki.

"Amarya na. Yaushe kika zo?" Ya tambaya tare da bata hannu suka tafa.

"Ɗazu Daddy na muka je kallon hawa, shine ya kawo mu nan, harda Maama ma"

"Shine baki zo kin karɓi goron Sallah ba?"

Hannun ta biyu ta buɗe mishi ta haɗe su tare da faɗin "toh ka bani"

Har ya saka hannu a aljihun shi zai ciro kuɗi ya bata sai kuma wani tunani ya faɗo mishi yace "muje ɗaki
na in baki. Harda chocolate da cake ma ina da shi a fridge"

Tsallen murna ta fara wanda ya saka tsokar jikin ta girgiza, kana ganin ta kaga renon madara ga wani
ƙyalli da fatar tata yake yi.

Jamal ya ɗan lashi laɓɓen shi kafin ya ja hannun ta suka nufi ɗakin, sai sauri yake yi kada Hajiya Hauwa ta
fito ta riske su don haka ya yunƙura kawai ya sunkuce ta yana nishi ganin tana mishi saiɓi.
Saida ya mayar da ƙofar ɗakin ya rufe tare da garƙame shi da key kafin ya ajiye ta a ƙasa. Bata damu ba,
tunda wannan ba shi bane karo na farko da take zuwa ɗakin shi yana rufewa, don haka ta ɗale kan
gadon shi ta zauna tana jira.

Kayan jikin shi ya fara ragewa, ya rage daga shi sai singlet da boxers kafin ya buɗe fridge ɗin ya ɗibo
chocolate masu yawa wanda ya ajiye su na musamman domin yana ruɗan yara musamman ma ita da
yake ji har zuciyar shi ita tasa ce, tunda iyayen shi sun riga da sunyi alƙawari, girma kawai zata ƙara ayi
musu aure, amma in ta nashi ne ko yanzu ma ba'a yi sauri ba.

Tana murna ta ɗaga ƙasan gown ɗinta ya zuba mata idon shi a kan ƙafafuwan ta har zuwa pink ɗin pant
ɗinta da ya leƙo.

Ya ɗauki ɗaya ya buɗe mata ta fara sha sannan ya ɗauko wayan shi ya dawo kan kujerar dake ɗakin.

"Amaryata zo muyi kallo" yace da ita.

Cike da rashin wayo ta zuba sauran chocolate ɗin a kan gadon sannan ta sauƙo tana kan shan wanda ya
buɗe mata ta dawo jikin shi, sai ya ajiye wayan ya ɗauke ta ya ɗaura a saman cinyar shi kafin ya kunna
mata cartoon kaman abin arziƙi.

Ko minti 15 ba'a yi ba ya canza zuwa wani American movie da ake zuba baɗala a cikin ta da yafi ƙarfin
nashi ƙwaƙwalwar mai shekaru 17 balle ita mai shekaru 8.

Suna kallon yana shafa ta tana ɗan nonnoƙewa sai ji tayi ya buɗe zip ɗin gown ɗin ya shiga shafa bayan
ta.

Yanda take jin yana mata kaman yawon tsutsa a jiki bayi mata daɗi don haka tace masa "yaya Jamal zan
tafi wurin Aunty"

Bakin sa ya saka ta wuyan ta yana hura mata numfashi sai maƙe kafaɗa take yi saboda yana saka tsikar
jikin ta na tashi.
Da numfashin sa da yayi nauyin jarabar da ya ɗaura ma kanshi yace "bakya son muyi wasa Reina?"

"A'a Aunty ne zata min faɗa" tace idanun ta na ciccikowa da hawaye.

Sai ya kashe wayan jin harma bari zata yi Auntyn ta sani ta saka shi a uku, ya juyo da ita tana fuskantar
shi. "Kinga Auntyn ki tana da faɗa ko?"

Ta gyaɗa kai don tafi kowa sani

"Toh idan kika faɗa mata dukan ki zata yi. Kuma zata hana ki zuwa wuri na kina karɓan chocolate mai
yawa"

"Toh ba zan faɗa mata ba. Amma ka siya min harda cake toh" tace muryar ta na karyewa zuwa na kuka.
taƙi ta bada muhimmanci ne ma abinda take ji yana tokarinta ta ƙasa amma kanta duk ya ɗaure da
wannan yanayin.

Rungumo ta yayi jikin shi yace "shikkenan amma kada ki faɗa ma kowa irin wasan mu ko daddyn ki ko
ƙawayen ki, duk wanda ya sani zai saka Auntyn ki ko Umma na su zane ki."

Ta gyaɗa kai da sauri, sai ya sauƙe ta ya buɗe mata ƙofa ta fito ɗauke da chocolate ɗinta ganin yanda ta
gama firgita, yafi so ya bita a hankali ta saba da shi kada tazo ta tona mishi asiri.

Haka ta ƙare wunin gidan sukuku har Alhaji Tahir yazo bayan Isha ya ɗauke su.

.......
"Wallahi baka da hankali Tahir" ji yake yi inama da akwai halin ya kama shi ya naɗa mishi na jaki ko zai
huta da takaici.

Dariyar da ya ƙara ƙular dashi Alhaji Tahir yayi kafin yace "Nine bani da hankali angon Mariama?"

Dogon tsaki yaja ya miƙe zai bar masa office ɗin kafin ya bashi mamaki.

"Tsaya kaji mana amini na"

Juyowa yayi a karo na ƙarshe ko akwai sauran notin kan shi da bai gama kuncewa ba yace.

"Tahir da kanka kake tona ramin mutuwar ka da hannun ka! Ka san Naira biliyan ɗari nawa ka zuba su a
cikin wuta domin su ƙone? Da biliyoyin kuɗi ka sake shiga Ponzi Tahir? Kana hauka ne?"

Wasu takardu ya miƙa masa yana faɗin "karɓa ka gani"

Tsayawa yayi yana kallon shi yana harsaso masa irin matsalar da zai iya shiga a gaba.

Alhaji Tahir ya sake cewa,

"Karɓa ka gani sai ka yanke hukunci idan ina kan daidai ko akasin haka"

Ƙarasowa yayi ya karɓa yana dubawa. "Takardun meye wannan?"

"Riban da na samu ne a wancan karon, rabona ne ni kaɗai ba tare da kowa ba Abdou. Ka kalli yawan
kadarorin da ya mallaka min"

"Toh sai anka yi yaya?"


"Tunda kai baka da niyyar amfanunwa da garaɓasa sai ka zama min wakili kuma mai riƙon wannan
kadarori, ka bunƙasa min su in biya ka"

Watsa masa takardun yayi a kan fuskar sa tare da buga mahogany table dake tsakanin su yace "Tahir!
Duk wani bala'in da zaka saka kanka ka kuskura ka nemi Abdou Hamissou wallahi sai na wulaƙanta ka
yanda baka tsammani. Ni bani hidima da mutanen da basu da nazari da tunani, so as from today, Idan ba
Abinda ya shafi kasuwancin dole ba kada ka sake nima na kafin nima ka ɗaura ni a hanyar da bata
ɓullewa."

Alhaji Tahir ya san zai dawo, ya san zai yi nadama, ta yuyu shi ya fara tun yanzu shine yake naɗe
tabarmar kunya da hauka, amma har malamai ya saka anyi mishi istikhara kafin ya shiga abun nan kuma
an tabbatar masa da nasara don haka zaman jiran sakamako kawai zai yi.

.......

Zuwa yanzu bashi ya fara yiwa Kamal da Saudat katutu Saboda karatun Yaseer, saboda kullum cikin fidda
fice ake yi buƙatar kuɗin yau daban na gobe daban, ga campus life sai a hankali.

Ga karatun Suhail, Sabir da Ajmal suma, ga kuma ɗan kuɗin da yake turawa ma Goggo a ƙauye, kuma
ba'a fasa ci da sha da sanya sutura ba.

Rayuwa ta ƙara tsada, farashin kayan abinci kullum daɗa hauhawa yake yi, ga ƙarin albashin da suka
samu a tsawon shekarun bai kai ya kawo ba. Sannan Saudat tun baya haihuwar Ajmal ta kamu da cutar
Asthma.

Zauna suke a kujerun can ƙarshe na NLT yana gwada mata Physics 126 da ta samu carry over ɗin shi na
aji ɗaya, amma wai sai yanzu da zata shiga jarabawar gyara shi gobe da safe zata zo ta dame shi ya koya
mata, wanda shima gudowa yayi yazo nan ɗin yanda babu haske ya samu yayi karatun nashi exams ɗin.

"Kinga idan kika gama buɗe wannan, a nan sai ki ɗauko wancan formula ɗin kiyi applying ki ƙarasa
solving"
"Umm" tace hankalin ta na kan zakarar wuyar shi dake lugude da duk kalmar da zazzaƙar muryar shi ta
furta, zuwa kan kyakkyawar fuskar shi, a maimakon ta maida shi kan takardar ta.

"Toh solva mu gani" ya tura mata takarda da biron gaban ta amma sai ta ƙara matsowa daff da shi jikin
su na gogan na juna.

Haɗe fuska yayi, yace "Meesha! Matsa"

Sai ta ɗago ta kalle shi. Suka yi ido huɗu, kaman ranar da ta fara ganin shi a makarantar, amma wannan
karon sai ta sake mishi murmushi a maimakon harara. babu musu kuma ta matsa ɗin domin wannan hali
nashi shi yasa yake ƙara burgeta kuma yasa ya shiga ranta.

Tana son namiji tsayayye, kaifi ɗaya, ba kawai namamajo wanda kowa nashi bane, kuma bata damu da
talaucin Yaseer ba wanda yakan gwada a suturar shi da dabi'un shi, dukiyar mahaifin ta ya ishe su.
Sannan ma ai yana da bright future a gaba, tana yin nasarar kama tashi zuciyar shikkenan daga ya gama
karatu daddynta sai ya sama mishi aiki mai kyau suyi auren su.

"Uhmm... Yaseer!" Ta kira shi cikin siriryar muryar ta mai daɗi.

"Yaya aka yi?" Ya tambaya hankalin shi yana kan wayar shi da yake duba alert ɗin naira dubu biyu da ya
shigo yanzu daga Abban shi.

pocket money ne ya ƙare mishi gashi an fara jarabawa don haka bayi da yanda ya iya dole ya tambayi
Kamal kuɗi shine ya turo masa abinda ya samu. Baki ɗaya naira ɗari biyu da saba'in da biyar ya rage a
account ɗin sai yanzu da wannan ya shigo.

Hankalin ta na kan wayar nashi don screen ɗin ba privacy bane tace "dama wata aunty na ce take neman
lesson teacher ma yaron ta."

Ɗagowa yayi ya kalle ta "ni kuma sai aka ce miki charity foundation ne ni"
Dariyar ta mai kyau tayi tace "zasu biya fah, da kyau ma. Yaron ne dolo ne wallahi sau biyu yana rubuta
jamb tun yana ss2 ya gagara ci, waec da neco ma rubuta mishi aka yi. Shine suke niman wani guru ya
saka ka shi a layi ni kuma kai na sani."

"Okay, for how long suke buƙata?" Tambayar da ya mata daban amsar da yake nima daban, kuma ta
fahimci hakan sai ta ciro iPhone 16 pro ɗinta da faɗin "bari na tambaye ta"

Danna kira tayi babu ɓata lokaci aka ɗauka suka shiga gaisawa "Aunty Hauwa ina wuni, daman maganar
Lesson teacher ma Jamal da muka yi magana ne shine na sami wanda nake faɗa mikin ya yarda amma
yana so ya san duration da kuma pay"

Cike da jin daɗi tace "sau biyu a sati ma yayi, duk weekends daga tara na safe zuwa sha biyu na rana sai
kuma da yamma ƙarfe huɗu zuwa shida. Sannan ko na wata shida aka samu zai yi, idan kuma zai yarda
har zuwa ya rubuta exams ɗin toh zamu fi son haka"

"Okay, salary ɗin shi fah"

"50 thousand ne."

Tayi saurin girgiza kai tare da yatsina fuska kaman tana gaban ta tace "50k yayi kaɗan Aunty hauwa, kiyi
doubling ɗin shi gaskiya. Na faɗa miki guru ne sosai nima shi yake koya min karatu"

"Toh shikkenan Meesha, sai ki turo min numbern shi shima ki bashi tawa"

"Okay no problem, amma fa muna exams sai mun gama zai fara zuwa. And idan aka samu ƙarin student
ko ɗaya ne gaskiya sai an ƙara masa kuɗi"

"Baki da matsala dani Meesha, indai zaiyi abinda ake so kuɗi ba matsala bane" da haka suka yi sallama.
Ta juyo wurin Yaseer da yayi ƙoƙarin rufe bakin shi kafin ta fahimci tsananin mamakin da yake ciki.

"You're hired. The pay is 100k sau biyu ne duk weekends, sai ka tura min account details ɗinka in tura
mata"

Da ƙyar ya iya buɗe baki yace "last week na buɗe opay."

Danne danne tayi na mintuna biyu sai ya sake jin alert yana dubawa yaga 30k ne ta tura masa.

"Wannan kuma na meye?" Ya tambaye ta mamakin shi yana ƙaruwa.

"Baka yi kama da charity foundation ba, don haka ko ruwa ka siya da wannan ka jiƙa maƙoshi, sorry ba
yawa semester yayi nisa"

Dama ta daɗe tana niman account number ɗin shi don tana tallafa mishi da wani abun amma yaƙi bata,
kuma har opay da su moniepoint ta duba bayi amfani da su sai yau tayi nasarar cika ƙuɗurin ta kuma taji
daɗin da ya kasance a lokacin da yake tsananin buƙata.

Idan Yaseer yace bai ji daɗin kyautar ta ba yayi ƙarya don haka yayi mata godiya cike da jin daɗi suka ci
gaba da karatun.

*Saliha Ahmad Na'ibi (seemahwrites)✨*

*REINA 💍*
25....... MAFARI.

_A cewar malaman falsafa 'wani lokaci zuciya na jin abinda idanu basu iya gani, sai daga baya a gane
cewa ji ne na gaskiya'_

Amma Yaseer ya gagara fayyace abin da yake ji a tashi zuciyar fargaba ce ko kuma tsana.

Shekaru tara! Shekaru tara kenan rabon shi da wannan gidan.

Tun Haihuwar Sabir da ya rako umman shi yawon Arba'in aka barsu a waje kuma matar gidan ko fitowa
su gaisa bata iya ba har suka ƙaraci zaman su suka tafi.

Tun daga ranar Saudat ko yaranta basu sake taka ƙafar su a cikin gidan ba, har hajiya hauwa ta aurar da
yara uku, mata biyu da namiji ɗaya, sai a yau da buƙatar su ta tashi gashi sun nimo shi har inda yake sun
gayyace shi ya zo gare su.

Riƙe yake da hannun ƙofar parlourn, yana tunanin ya shiga ne koko ya juya yayi tafiyar sa? Saidai kuma
idan ya tafi asarar waye? Tunda dai ko ba shi ba ya san zasu samawa Jamal wani lesson teacher amma
shi idan ba a nan ɗin ba a ina yake tsammanin samun kuɗi mai yawa haka a ɓagas?.

Da kuzarin shi ya tura ƙofar haɗe da sallama.

Alhaji Salisu ke zaune saman kujera mai zaman mutum Uku yana kallon tashar BBC, sai kuma waya da
yake amsawa a lokaci guda.
Ƙarasawa ciki Yaseer yayi dukda babu wanda ya amsa sallamar shi, ya ƙarasa bakin carpet ɗin dake
shimfiɗe a tsakar parlourn ya zuba a kan guiwowin shi, yana jira Alhaji Salisu ya gama ne ya gaida shi.

Ɗaya bayan ɗaya yaran gidan suke fitowa daga ɗakunan su suna wuce shi zuwa wurin cin abinci, wasu
kuma su ɗebi abincin su koma ɗakin dashi amma babu wanda Yaseer yayi musu da su gaida shi, ko kallo
ma bai ishe su ba.

Sai can jimawa har ya fara ƙosawa kafin Alhaji Salisu ya gama amsa wayar ya juyo ya dube shi.

"Ina kwana Alhaji" Yaseer ya gaida shi ba yabo ba fallasa.

A maimakon ya amsa sai ya haɗe girar sama da na ƙasa yana tambayar "Malam daga ina?"

Ɗagowa Yaseer yayi ya kalle shi cikin idanu, babu tsoro a cikin idanun shi, fargabar da yayi fama da ita
ɗazu ma ta gudu don haka sosai yayi ma Alhaji Salisu kwarjini.

Kafin ya amsa shi Hajiya Hauwa ta fito ɗauke da food flask babba zata kai shi dining. "Yaseer ne fah. Ɗan
gidan Kamalun jama'are, baka gane shi bane?"

A mamakance Alhaji Salisu ya juyo yana kallon yanda ya girma. Itama dai Hajiya Hauwa ta ɓoye nata
Mamakin ne don kada ta kwabar amma Ranar da yazo suka yi magana bata gane shi ba.

Sai Alhaji Salisu ya sake mayar masa da tambayar "toh me yake tafe da kai da tsakiyar watan nan
yasiru?"

Hajiya Hauwa ta sake amshewa da "shine Lesson teacher da muka ɗauka ma Jamal" tana tare-tare da shi
ne saboda yanzu ba da bane, yaron ya girma yayi hankali kuma duk yananin da suka tare shi da shi zai
riƙe su, sannan gashi tun ba'a je ko ina ba sun fara niman alfarmar shi.
"Toh toh toh, ashe har ka gama secondary ne?"

Ƙaramin murmushi yayi kana ya amsa da "Ina shirin shiga aji uku kenan a jami'a"

Sai ya jinjina kai, "Allahu akbar, a wani makaranta kake?"

"Nan ATBU"

"Tahiru kenan ko yaya kalabu suke biya maka kuɗin makarantar? Tunda ni ban san da zancen ba?"

Wani irin kallo ya watsa masa wanda bai san ma yayi hakan ba, sai kuma ya sauƙe idanun shi ganin
girman da yayi ma mahaifin shi ma ba kaɗan bane kuma ba'a mishi tarbiyyar Raina manya ba, don haka
ya amsa da.

"A'a, mahaifina yana da aiki shima"

"Aikin da Alhaji Tahir ya bashi?"

Sai Yaseer ya ja numfashi a ƙoƙarin shi na kai zuciya nesa. Matsayin shi kawai ake son gwada mishi ba
komai ba, kuma ya tsammaci haka daga duka ahalin gidan, sai ya amsa da.

"Wannan kam ban sani ba, saidai idan na koma gidan in tambaye shi"

Dariyar da bai kai zuci ba yayi yace "Kada ka damu kanka, jeka, ayi karatu lafiya"
Bai ƙara cewa komai ba ya miƙe, juyowar da zai yi idanun shi ya sauƙa kan fuskar ta dake ɗauke da
wadataccen murmushi. "Ina kwana Yaseer"

Tana sanye da kayan barci mai santsi babban riga da dogon wando sai gyale mai kauri da ta lulluɓe kanta
zuwa ƙirjin ta dashi.

Sauƙe numfashi yayi, ya nufi hanyar waje ba tare da yace da ita komai ba, ba zai iya magana da ita a
gaban su ba.

bata yi ƙasa a guiwa ba ta biyo shi.

"Meesha a nan kika kwana?" Yace da ita bayan sun fito waje.

Saurinta ta ƙara domin ta jera da shi tana faɗin "I wanted to surprise you, na san kuma you are functual
zaka iso a kan lokaci , ni kuma ban gama barcin hutun gama exams ba I can't wake up before 9, shiyasa
kawai nazo tun jiya na kwana a nan"

"So daga barin ki hostel da yammacin jiya a nan kika sauƙa baki je gida ba"

"Yep" ta washe fararen haƙwaran ta tana mishi murmushi.

Girgiza kai kawai yayi domin idan ka ganta a school ba zaka ce ta taɓa dariya ba.

Ƙarƙashin wani rumfar bunu dake cikin ɗan ƙaramin garden ɗin gidan suka ƙarasa, ya zauna a ɗaya daga
cikin kujerun dake wurin yana jiran fitowar Jamal tunda iyayen shi sun riga sun san da zuwan sa.

Itama jawo wani kujerar tayi ta saka shi yana fuskantar tashi ta zauna, kana tace

"You're not a gentleman Yaseer, tunda baka san ka jama mace kujera ba"
"Ba gashi dai kin zauna ba?!" Ya mayar mata.

Sai ta ɗan harare shi. "Why are you treating me like your sister? Ko dan ina sake maka da yawa?"

"Toh wa yasan miki yanzu kuma" ya ciro wayar shi tare da duba lokaci. 9 ne da minti 28. Kuma duk Alhaji
Salisu ne ya ɓata mishi lokaci tunda ya shigo gidan ma taran bata cika ba.

Turo baki tayi tace "Allah da gaske nake, You should be taking me seriously, cos wa ya sani? Maybe mu
zamo wani abu a nan gaba"

Ciza laɓɓen bakin shi yayi yana ƙarewa fuskar ta kallo. Ita kuma a duk lokacin da yayi hakan sai tana ƙara
jin wani abu na fisgan ta a kan shi.

"In kai wannan kyan naki ina Meesha?"

Kuncin ta da yayi ɗumi tare da jaa a lokaci ɗaya saboda kalamin shi ta dafe tare da yin farr da idanu tana
murmushin jin daɗi kafin ta gyara zama tayi ɗan gyaran murya tace "waye yace maka kaima ba
kyakkyawa bane?"

"Toh shikkenan, naji. Shekarun ki nawa?"

"20" ta amsa a takaice.

"Shekara ɗaya na baki toh"

"Toh meye a ciki? Banda abu irin na Nigeria ma, a ƙasashen waje auren Sa'a da Sa'a suke yi"
"Haka ne, kije ki shirya ki tafi gidan ku." Ya gwada mata hanya a ƙoƙarin shi na kawar da zancen.

"Yauwa, ashe wai Uncle Salis ɗan uwan ku ne?"

Kaman bayi so ya gyaɗa mata kai kawai.

"Why didn't you tell me then?"

"Amfanin me zai yi miki idan na faɗa mikin?"

"Yana nufin mu ƴan uwa ne kenan"

"Taɓɓ, kalen dangi"

Haɗe rai tayi tace "waye mai Kalen dangin? Ni ko kai?"

"Ni mana! Cousins fa suke da uba na, me ya haɗa ni da su toh?"

"Ban gane me ya haɗa ka da su ba? Suma iyayen ka ne a al'adance. Ko akwai wani abu mara daɗi a
tsakanin familyn ku ne?"

Ba zai iya da wannan tuhumar ba don haka ya riƙe hanci yace "don Allah kije kiyi wanka, tsami kike yi, ga
kwantsa a cikin idanun ki"

Da sauri ta miƙe tana shinshina jikin ta, ta kunna cameran wayan ta a selfie tana duba fuskar ta. "Saida
nayi wanka fa kafin na kwanta"

"Toh ni dai ina jin tsami"


"I know you're just pulling my leg, amma muje mu karya toh sai in sake yin wankan"

Taɓe baki yayi "ance miki gidan mu babu abinci ne da zan kai tara ban karya ba?"

Da ba'a yayi mata zancen amma sai taji babu daɗi tace "ba nufi na ba kenan amma kayi haƙuri"

Ya dai samu ya kora ta kafin ta sake ɓaro wani hirar, sannan yaci gaba da zaman jiran Jamal amma har
goma da rabi shiru. Sai dai masu aikin gidan sun kawo mishi sabon white board da kuma kwalin marker
da duster, sai kuma text books na subjects ɗin da Jamal zai rubuta Jamb ɗin a kansu.

Har Meesha ta karya ta sake wanka Jamal bai fito ba.

fitowa tayi cikin dogon rigan material da hula a kanta ta sauƙo da dogon gashin ta a baya, sai ta saka hair
band ta daure shi hawa uku.

tana ɗauke da tray mai goran juice, ruwa da cup guda ɗaya, plate ɗin meat pie da kuma cookies. ta
ƙaraso wurin Yaseer sai baza ƙamshi take yi.

"Da nace miki kina tsami, bance ki dulmuyar damu a cikin zunubi ba, don Allah kije ki saka hijab ko ki
rufe kan ki yanda ya kamata" ya sake toshe hancin shi a karo na biyu idanun shi na kallon wani wurin.

A maimakon ta amsa shi sai ta ajiye tray ɗin a gaban shi ta riƙe ƙugu.

"Kambu! Yaron nan barin ka yayi kana jiran shi?" Ta juya fuuu ta koma cikin gidan.

Kusan minti 10 a tsakani ta fito riƙe da kunnen Jamal wanda ke sanye da guntun wando da tank top,
yana ihu da ƙoƙarin ƙwace kunnen amma ta sha muurr.

Saidai ga mamakin shi ta saka hijab ɗin da yace.


"You're very stupid! Kasan yanda aka yi na samu nayi convincing ɗinshi ya yarda zai koyar da soko irin
ka?" Ta talle ƙeyan shi ya saki ƙara 'Ahh!.'

Tsaki Jamal yayi sai ta ɗaga hannu zata make bakin Yaseer ya dakatar da ita. "It's okay Ameesha zaki iya
tafiya"

Gwada shi da yatsar da take kaɗawa tayi tace "don Allah kada ka mayar da hankali tunda zaman gida bai
ishe ka ba". Da haka ta wuce tana sababi shima bai fasa ƙunƙuni ba, sai Yaseer ya maido da hankalin shi
gareshi.

"Sannu ko Jamal"

Tun daga kan ɗan iskan askin dake kan shi yabi da kallo, zuwa sarkar chain dake wuyar shi, da wasu abun
hannu da ya saka irin na gayu da faracun shi zaƙo-zaƙo kaman mai cin kare.

A yatsine ya kalle shi "Malam kayi abinda ya dame ka"

"Ta ina kuwa zan yi abinda ya dame ni bayan bani son yin wannan aikin na shekaru biyu?"

Ya miƙe tare da ɗaukan jan marker ya buɗe ya rubuta cikakken sunan shi a kan allo.

Sai Jamal ya kalli sunan sannan ya juyo ya kalle shi ya sake kallon sunan. "Yaseer Kamal Jama'are da na
sani?!"

"Eh shi ɗin dai, ɗan kauyen da kuke kora shine zai koya maka karatu a yanzu idan ka mayar da hankali"

"Bantan uba!" Ya miƙe baya a kan kujerar yana mishi dariyar rainin hankali.
Yaseer ya ƙara tamke fuska, "koma na waye ne dai haka zamu yi, domin kaman yanda dole ne ya zaunar
da kai a nan nima haka ne, don haka idan zaka bani haɗin kai muyi abinda ya dace da yafi."

Tsaki yaja ya miƙe zai bar wurin ya hango Meesha na tahowa da dorinar da ta aro a wurin security.

Ya sake jan wani tsakin tare da faɗin "mahaukaciya kawai" dolen sa ya koma ya zauna, ita kuma ta
ƙaraso wurin ta zauna tayi banke-banke tana cinye abin motsa bakin da ta kawo ma Yaseer ɗin.

Haka dai aka yi koyarwar ranar cikin aminci da taimakon Meesha amma Jamal dai kaman kurma duk
abinda Yaseer ya tambaye shi ya gane sai kawai ya gyaɗa kai shi kuwa ya wuce abun sa.

Saboda tsare shi da tayi da surutu bai bar gidan ba sai bayan sallar maghriba. Tun kafin ya fita tace masa
bari taje ta ɗauko mota amma yayi banza da ita yayi wucewar shi.

Motar Hajiya Hauwa taje ta aro ta fito ta same shi yana takawa a sayyada kasancewar dare abun hawan
ba sosai ba a layin.

Horn ta matsa da ƙarfi kafin ta zuge glass ɗin ɓangaren shi haɗe da faɗin "shiga mu tafi"

"Mu tafi ina? Hankalin ki yaje aika ne zaki ɗauki gardi a mota da daren nan? Idan muka je ki dawo ke da
wa?"

"Me zai same ni toh? Ai ba yau na fara fita ni kaɗai a mota ba balle, kuma babu inda zan bi, ina sauƙe ka
zan juyo"

"Ni dai ki koma idan baki son mu ɓata" ya cigaba da tafiya itama taci gaba da bin shi a motar.

"Idan baka shiga ba haka zanyi ta bin ka ina cika maka kunne har mu isa" ta ƙara matse horn da ƙarfi fiye
da na da.
Haka dole ya shiga yana mata kwatance har suka isa unguwar su.

"Ko in biyo ka ne in gaida Umma?" Tace bayan ya sauƙa daga motar.

Harara ya watsa mata "amma kin fara zauncewa ko? Kuma ki saka a maida ke gida a daren nan kinji na
faɗa miki"

"Toh my Yaseer " ta amsa tana daga mishi hannu, ya tsaya yaga ta tada motar ta bar unguwar kafin ya
juya zai shiga lungun da zai kai shi gidan su sai Muryar Abban shi ya ji a bayan shi.

"Har gida suka dawo da kai? Lallai sun kyauta" yace cike da jin daɗi.

Rage tsayi Yaseer yayi ya gaida shi sannan ya amshi ƴar laidan hannun shi wanda ya siyo rake. Suka jera
har gida yana tambayan shi wai ya bashi labarin abinda ya faru a gidan koyarwar shin.

Saudat da yara suna ɗaki saboda akwai wutar nepa suka shigo. Yaran suka yi ma kamal oyoyo tare da
gaida shi kafin ya zauna yana mayar mata abinda yaji daga bakin Yaseer da kuma wanda ya gani.

"Saudatu kinga ƙudirar Allah ko? Har mun fara ganin ribar karatun yaron nan tun ba'a je ko ina ba"

"Hmm" kawai tace domin baki ɗaya hankalin ta ya gagara kwanciya da zancen shigan Yaseer cikin
mutanen nan. Basu da daɗi, basu daraja ɗan adam sannan kan su kawai suka sani, tana tsoron suyi ma
yaronta wani abu na cutarwa.

Kusan kamal shi kaɗai ya ƙaraci hirar shi har aka tashi daga kallon lokacin da aka kira Isha sannan ta kira
Yaseer ya dawo bayan kowa ya fita.
Hannun shi na dama ta riƙo cikin nata biyu, "Dan Allah Yaseer ka iya zaman ka da mutanen nan, babu
ruwan ka da sha'anin su kayi abinda ya kai ka kawai. Kaga mu ke nima a ƙarƙashin su don haka a kai
zuciya nesa dan Allah, sannan ko shi yaron da kake koyarwar ban yarda da hukunci ba, dukda na san
baka da saurin hannu amma ka bishi a lalama har a gama lafiya"

In sha Allah umma, ya amsa da sakin fuska don hankalin ta ya kwanta, daman shima hidiman su ba tsole
mishi idanu yayi ba.

.......

Da Hajiya Fauziyya ta gama faɗa ma Reina a kan yanda take saka Maama a gaba da duka kaman jaka
bayan ita babu wanda ya isa ya taɓa ta shine tayi fushi ta koma parlourn daddynta suka ƙarata a can har
ya shiga ɗaki ya barta tana kallo.

Tashar Nickelodeon take kallo daga farko kafin ta ɗauki remote ta shiga canje-canjen channel har ta kai
wani wanda ake gwada program 18+ sai ta gyara kwanciya tana tunanin inama ace da yaya Jamal suke
wannan kallon, suna yi tana tambayan shi abinda bata ganewa yana mata bayani, harma yana gwada
mata wasu abubuwan da yanzu sun fara mata daɗi ta fara sabawa dasu.

Ana cikin haka Hajiya Fauziyya ta shigo yin light off idanun ta ya sauƙa a kan abinda ake yi a TVn ta
ƙaraso zata kashe shi sai ta hango Reina kwance a kan 3 seater. Ita tama manta da tana nan don har taje
ta kwantar da Maama ta kashe musu wuta.

"Reina?" Ta kira ta domin ta tabbatar ita ɗin ne take kallon wannan abun.

A take ta haɗe fatar idanunta ta rufe su ruff kamar mai barci. Har Hajiya Fauziyya ta zago gaban kujerar
bata ko motsa ba banda zuciyar ta dake lugude.

Itama Hajiya Fauziyyar dake bata jin daɗi don haka bata bada abun muhimmanci ba ta fara canza
channel ɗin kafin ta kashe TVn ta shiga wurin Alhaji Tahir.
Yana zaune a bakin gadon sanye da jallabiya ash yana lissafi kaman yawancin lokuta ta shigo.

"T. kai ne ka bar channel ɗinnan a kan wani program ga yarinyar nan a kwance a wurin? Idan ta farka
taga abinda bai dace ba fah?"

Da mamaki ya ɗago ya kalle ta, yace "SpongeBob ake yi a Nickelodeon tace in bari mata, saidai hala da
aka gama ne take neman wani channel ɗin barci ya ɗauke ta shi yasa ya tsaya a kan wancan ɗin"

Sauƙe numfashi tayi "Idan na samu zama ma duk goge su zanyi"

Yayi dariya "kullum dai haka kike cewa Fauzah".

Sannan ya tura littafin gefe ya miƙo mata hannu, a kasalance ta ƙaraso ta zauna.

"Yaya kufayin jikin yanzu? Ai da kin bari ma yau ni nazo"

"Na ɗan ji daɗi bayan ruwan da aka ɗaura min ɗazu har na samu ma naci abinci"

"Alhamdulillah, amma wannan ɗan daddy yana wahalar damu."

Juya idanunta tayi tace "waye yace maka ɗan daddy ne? Idan kuma wata Princess ce aka sake samu fa
tunda kana da sarauniya"

"Ni ina ji a jiki na ma ɗan daddy ne, In sha Allah namiji zaki haifa" ya amsa yana shafa cikin da bai fara
tasowa ba kasancewar tana cikin watan ta na biyu kenan.

Sai taji jikin ta ya ɗan yi sanyi ganin kaman yanzu ma idan ta sake haifar mace ba zai yi farin ciki da hakan
ba.
"Toh kaje ka kai Reina bedroom ɗinsu sai ka dawo"

"Toh Hajiya. Ya amsa tare da miƙewa"

*Saliha Ahmad Na'ibi (seemahwrites)✨*

*REINA 💍*

26....... Washe gari da Yaseer ya koma gidan su Jamal bai samu Meesha ba, don haka ya saka ma ran shi
wannan karon ma taji maganar shi ne ta koma gida.

Samun wuri yayi ya zauna bayan ya gaida su kaman jiya, shiru yau ma har ƙarfe 10 ta gifta Jamal bai fito
ba. Ya kuma rasa waye zai tura a kira masa yaron gashi bayi son ɗaura ma Meesha nauyi don kawai tayi
mishi Lamuni.
Haka ya ciro wayan shi yana ɗan daddannawa sai ga Jamal ya fito, amma kallo ɗaya zaka yi masa ka san
ba lesson ya fito ba, domin yana sanye ne da wata baƙar leather jacket da skinny jeans, ya ɗaura jan
bandana a goshi, yatsun shi na kaɗa key ɗin motar uwar shi.

Haka suna kallon kallo shi da Yaseer, yana faman fiito ya faɗa cikin motar ya ja yayi masa wuta ya fice a
gidan.

Bayi juran wulaƙanci bayi ɗaukan ta ko kaɗan, amma ai Jamal ba shi ya ɗauke shi aiki ba, don haka ci
gaba da zama yayi duk da ran shi nayi masa ƙuna.

Sai bayan fitan shin da kusan minti talatin kafin Hajiya Hauwa ta saka a fito a bawa Yaseer haƙuri wai ita
ta aiki Jamal.

Shi kuwa sauƙin shi, da Jamal ya maida hankali da bai maida hankali ba idan wata yayi dole zasu biya shi
albashi tunda ya zo, don haka ya koma gida yaje yayi wankin kayan da ya dawo dasu daga makaranta
masu datti.

.......

"Wallahi sai na faɗa ma Aunty" cewar Maama cikin muryar kuka tana matsar ƙwolla, Reina kuma ta
matse ta a jikin bango tare da taka mata ƙafa cike da mugunta.

"Ki faɗa mata don Allah baƙar munafuka, Idan naga dama ko Auntyn bata isa ta ƙwace ki daga hannu na
ba!" Tace tana ɗibe ta da ƙananun maruka saboda kada yayi ƙara a jiyo su a kawo mata ɗauki.

Sanye suke da uniform maroon domin dawowar su kenan daga islamiyya, saboda Fauziyya bata jin daɗi
Aina'u ta basu abinci a parlourn sama, idan sun ci sai ta canza musu kaya. Bayan sun gama ci ne kowa ta
ɗauki plate ɗinta ta wuce da shi kitchen domin ta wanke kaman yanda Fauziyya ta mayar doka a gidan,
shine rashin ganin idon Auntyn ya sanya Reina saka nata plate ɗin mai kyau da tsada a shara saboda
kada ta wanke.
"Kuma wallahi sai na faɗa mata abinda kike kalla kullum a tab ko TVn Daddy, ai ina kallon ki ba barci
nake yi ba!"

A razane Reina ta makure ta cike da tsoro, ta san ta kuskura ta yi sake wannan maganar ya shiga kunnen
Aunty toh wallahi sai dai buzun ta a gidan.

"Ke ni sa'ar ki ce? Don kinga Auntyn ta fi son ki shine zaki na ƙulla min munafurci?!"

Ganin Maama ta fara ƙaƙari tayi saurin sake ta lokacin da idanun ta ya sauƙa a kan Lighter irin na gas a
saman cabinet ɗin sama. Ɗalewa kan kanta Reina tayi da nufin ta ɗauko sanin cewa tsayin ta ba zai kai
ba, Maama kuma na ganin ta saketa ta ɗiba da gudu ta fice daga kitchen ɗin tana ƙwala ma Auntyn kira.

Sai dai bata yi rabin hanyar ɗakin ta ba Reina ta cin mata ta sake shaƙurota ta haɗa da garu sannan ta
kunna lighter ɗin ta kai saitin bakin ta da nufin ta tsorata ta, kaman yanda itama Jamal yake mata duk
lokacin da tayi yunƙurin tona masa asiri ko kuma ita Auntyn ma take razana ta idan tayi Ashar har sai tayi
kuka ta bada hakurin ba zata sake ba.

"Me zaki faɗa mata munafuka! Ni babu abinda nayi algunguma!" Baki ɗaya jikin ta rawa yake yi.

Amma a rashin wayo sai ta kai lightern daff da laɓɓen bakin Maama wanda zafin wutan ya saka ta sakin
razanannen ƙara cikin azaba wanda ya karaɗe ilahirin gidan.

Ba zata ce daga ina Auntyn ta faɗo ba, gigitaccen marin da ya sauƙa a fuskar ta shi kawai ya sanar da ita
zuwan ta. Har ƙasa marin ya kai ta, lightern ya faɗi daga hannun ta shima yayi gefe, haka ma jin ta da
ganin ta lokaci ɗaya suka ɗauke.

Abin bai ishe Fauziyya ba ta saka ƙafa ta hanƙada ta wanda a sanadin tsautsayi da ƙaddara ta fara
gudundulowa daga kan benen tun daga na sama kan ta da jikin ta na buguwa tana ihu!.
Lokaci ɗaya hankalin Fauziyya ya dawo jikin ta, fushi da ɓacin ran da suka makantar da ita suka yaye. Ta
ma manta da ƙaramin ciki a jikin ta don haka da gudu ta fara sauƙa daga benen domin ta je ta ceci ƴar ta.

Sai dai ƙaddara ta riga fata, Mugun ganin da tayi ya saka ba don ta riƙe handrail na stairs ɗin ba to da
itama kifawan zata yi.

Reina bata tsaya a ko ina ba da fasasshen goshi, sai a saitin ƙafar Alhaji Tahir!.

Rana ta farko kenan da Fauziyya zata ce ta ji abinda ake ce ma tsananin tsoro ga kuma tashin hankali,
nadama kuwa ya lulluɓe ta kaman bargo.

A take jikin ta ya kama kyarma gashi idanun ta ya gagara fita daga cikin na Tahir da take hango wutar
dake ci a cikin su.

Ba zata ce ita take sauƙo da kanta ba domin ƙafan ta rawa suke yi amma a haka suka kawo ta har gaban
shi yanda har yanzu Reina take yashe, babu tabbacin ko tana cikin hayyacin ta amma ya gagara ko
sunkuyawa ya ɗaga ta ya nima mata agajin gaggawa.

"T..... Dan Allah...."

Ji yayi kaman ta ɗona mishi wuta yayi saurin ƙwace hannun shi ya matsa daga jikin ta yana mata kallon
tara saura kwata.

"Kin kashe min ita kin huta ko Fauziyya?" Da mamakin ta muryar shi da sanyi.

Girgiza kai ta shiga yi lokaci ɗaya hawaye na wanke mata fuska.

"Wallahi T Maama ta..."


"Ya ishe ni!! Ko yaushe kika buɗe bakin ki Maama! Maama! Maama!!!. Haba! Wata iriyar uwa ce ke?!"
Ya faɗa cikin ɗaga muryar da saida ta rintse idanun ta.

Zuba tayi a kan guiwowin ta ta rungumo Reina jikin ta tana kuka "Don Allah kayi haƙuri T, wallahi nayi
nadama, ba zan sake ba Allah kayi haƙuri!"

Jin haƙurin da take bashi yake yi kaman tana zagin shi, don haka ya sunkunya ya fincike ƴar shi daga jikin
ta hade da faɗin "Tunda zama ya gagare ki da ƴata, Na sauwaƙe miki ki je gidan ku ki baje, ke ba dole na
bane su ne dole na"

Ya juya zai bar cikin gidan da Reina a hannu. A kiɗime hajiya Fauziyya ta sha gaban shi "Na shiga uku, mai
kake nufi T?"

Mummunan harara ya watsa mata yace "Ina nufin na sake ki Fauziyya!, ko baki gane Hausa ne inyi miki
da wani Yaren?!"

Girgiza kai tayi "don Allah kada kayi min haka T. Da ciki fa a jiki na!" Ta rungume shafaffen cikin ta ko zai
tuna ya janye maganar shi.

"To ki ajiye sakin idan kin Haihu sai ki ɗauka!"

Da faɗan haka ya fita ya barta daskare a wurin.

.....
Ko sallama bata iya ba ta isa cikin gidan janye da akwatin ta tana kuka Wiwi.

Ummi dake kitchen tayi saurin fitowa haka ma amarya Sajida dake wanke-wanke a bakin famfo ta miƙe.

Ganin akwatin ya saka gaban Ummi faɗi.

Daman ta sani ta kuma saka ma ranta cewa rana irin wannan na zuwa, ba fata take yi ma Fauziyya ba
amma a yanayin da aka yi auren, ta sani kaman dole ne ko ba daɗe ko ba jima rana irin wannan na tafe,
amma bata yi tsammanin idan yazo zai girgiza ta haka ba.

Jefar da akwatin Fauziyya tayi ta rugo ta shige jikin mahaifiyarta ta saki kuka mai tsuma zuciya.

"Ummi Tahir ya sake ni, na shiga uku Ummi, Reina ta kashe min aure"

Ɓanɓarota tayi daga jikin ta tana kallon fuskar ta. "Kaman yaya?!" Ta tambaya a kiɗime.

Cikin kuka Fauziyya ta cigaba da cewa "ummi ban yi mishi laifi ya sake ni ba, mutane ko ƴan uwan shi
basu shiga tsakanin mu sun saka ya sake ni ba, banbancin dake tsakanin mu bai saka mun rabu ba Ummi
sai ƴar shekara tara! A kan ƴar shekara tara Tahir ya zaɓi ya haƙura da ni."

.....

Sallama Yaseer yayi a parlourn, cikin wanda ke zaune a kujerun cin abincin aka samu masu darajar amsa
shi.

Sai kawai ya gaida su a tsatstsaye kafin su yi tunanin ya zo ya saka su a gaba suna cin abinci, daman
mahaifin shi ne ya wajabta masa gaisuwan ma shi ba ra'ayin ta yake da shi ba don duk takura ne.
Har zai juya ya tafi Muryar ta ya dakatar da shi.

"Laaa kai ne?!!" Ta tambaya da mamaki tana durowa daga kujerarta ta nufo shi, sai ji kawai yayi ta
ƙaraso a guje ta faɗa jikin shi ta rungume kunkumin shi.

Kallon ke kuma daga ina yayi mata, nata idanun ma na cikin nashi tana faman washe masa baki.

Babu ɓata lokaci ya gane ta, saidai kuma kamannin ta da komai ya canja, ta yi tsayi ta ƙara haɓɓaka.

Ɓanɓare ta daga jikin shi yayi ga idanun kowa a kan su, yace. "Yaya kin warke yanzu ko?"

"Bayan ma baka dawo ba tunda ka tafi? Kuma kace zaka kawo min abun daɗi nayi ta jiran ka."

Ta turo baki amma idanun shi na kan ɓarin goshin ta dage rufe da bandage, ga sauran raunukan fuskar ta
da suka warke sun bar ƙananun tabo.

Wato ita wannan yarinyar ko yaushe a cikin jin ciwo take.

"Toh yayi kyau" Juyawa kawai yayi tafiyar shi ya barta tsaye a wurin, har zata bi shi Hajiya Hauwa tayi
saurin kiran ta tazo ta ƙarasa pancake ɗin da ta azabtar dasu a kai.

.....

Yau saboda faɗan Hajiya Hauwa Jamal ya fito zuwa 9 da 40, amma tunda yazo yake faman chat a waya,
ga apples da ya fito da su don yayi ƙwalele ma Yaseer ɗin yana ta gaftara kaman ƙarago.

Awa ɗaya Yaseer yana faman ɓaɓatu a banza don haka rai a ɓace yayi wurgi da markern ya dubi Jamal.
"Wai kana tunanin ni kake cuta ne idan kana rashin hankali?" Barin taunar Jamal yayi ya ɗago yana
kallon shi sheƙeƙe.

"Wallahi idan zaka shekara ɗari da tamanin a gida ba sha takwas ba ni ko a kwalar riga ta. Sannan ba
zaka rage ni da komai daga cikin ilimi na ba banza shashasha"

A fusace shima Jamal ɗin ya miƙe, amma ganin tsayin su akwai rata sosai tsakanin shi da Yaseer ya saka
shi sassauta fushin kana ya nuna kan shi da yatsa yana faɗin "Nine banza shashasha? Ɗan ƙauye irin ka
ne yake kira na banza shashasha??"

"An kira ka banza shashasha ko akwai abinda zaka yi ne? Na ƙara da wawa daƙiƙi!"

~~~~~~~~~~

*Hajiya Fauzah yau ba Tea ba ko buredi ne kina ruwa😂*

*Seemahwrites ✨*

*REINA 💍*
27......Gwada Yaseer da yatsa Jamal yayi kawai, ba tare da yace komai ba ya koma ya zauna. Sai da
Yaseer ɗin ya juya bayan shi ne wurin da idanun Jamal ɗin suke kallo ya hango dalili, ashe mahaifin shi
ne yake tahowa.

Ɗukar da kai Jamal yayi lokacin da Alhaji Salisu ya ƙaraso wurin ya zauna a hakimce, yana kallon Yaseer
ɗin da ke ƙoƙarin daidaita fushin sa.

Sai kuma ya samu zuciyar shi da addu'ar Allah yasa kada su kore shi, domin har ya gama lissafin nauyin
da yake son sauƙe ma iyayen shi da kuɗaɗen da za su dinga biyan shi.

Da haka kawai ne, tabbas da Yaseer ba zai ƙara ko minti biyar a gidan ba bayan zagin da ya ƙare ma ɗan
shi, amma abinda ya faru satin baya ya sauya komai.

Fitan da yayi bayan zuwan Yaseer ɗin a wancan Ranar har mahaifiyar shi ta turo ayi mishi ƙaryar ta aike
shi, bai tashi dawowa gida da ƙafafuwan shi ba sai can dare aka shigo masa da shi a buge a karo na farko.

Tabbas yana sane da cewa Jamal yana shan sigari da su shisha haka saidai ya ɗauki hakan ne a yarinta
kuma da ya girma zai bari tunda shima ya ɗan taɓa a baya, amma samm ba zai lamunci shan giya ko
kayan maye ba.

Domin haka yanzu burin shi ɗaya shine ya tura shi matakin gaba a karatu, ko zai fara sanin ciwon kan shi.

Fuska ya ɗan sake kaɗan yace "a yi haƙuri Yasiru, zai canza dolen sa. Akwai abubuwa da yawa dake jiran
nasarar shi, dole zai nutsu yayi ilimi, wani ma yayi rawa bare ɗan makaɗi?"
Sannan ya juya wurin Jamal yana watsa masa harara, ya fara gwada shi da yatsa yana kaɗawa "Wallahi
wallahi, idan wannan karon baka ci jarabawa ba, na rantse maka babu inda zaka je. kuma zan tsame
hannu na daga nima maka wani taimako, ba kuma zaka fasa maimatawa ba har sai ƙannen bayan ka sun
ƙaraso sun riske ka."

Rau-rau da idanu Jamal yayi, ya ɗago yana kallon shi "Toh... Toh amma Daddy, karatu a waje ba'a
buƙatar jamb fah, da tuntuni na tafi da wallahi na kusan gamawa ma yanzu, tunda ba'a daɗewa, balle
har wasu suna min kallon banza"

"Wanda ya gagara cin ko wani irin jarabawar gama secondary har zai iya gama matakin gaban ta a turai?
Idan na tura ka ma ai asarar kuɗi na zan yi ga ni mai kuɗin banza. Don haka ka maida hankali wallahi "
Alhaji Salisu ya miƙe yana kallon agogon hannun shi, lokacin da mai aikin gidan suka fito da Reina wanda
tayi wanka ta shirya.

"Yaseer!!" Ta ƙwala mishi kira daga ƙofar mashigar gidan, wanda yayi sanadiyar karkatowar hankalin su
baki ɗaya zuwa gare ta, sai ta ɗaga hannun ta sama tana yiwa Yaseer ɗin bye-bye kaman hannun zai
tsinke.

Jamal ne ya ɗaga mata hannu yana washe baki yayin da Alhaji Salisu ya maido da duban shi wurin
Yaseer, yana tsaye ne kawai fuska ba yabo ba fallasa yana kallon ta har suka saka ta a cikin mota tana
murna zata je wurin daddyn ta.

Daman wurin Alhaji Tahir yake da niyyan zuwa, tunda yanzu shi bayi da weekend kullum yana office.

Idanun shi ya mayar kan Jamal yayi maganar da Yaseer ya fahimci da shi yake yi "Idan ka sake zuwa bai
fito a kan lokaci ba, ka tura a sanar da ni." Sannan ya sauƙe murya daidai kunnen Jamal yace "alƙawarin
da na ɗauka last week tabbas zan cika shi"

A firgice Jamal ya waro idanu zai yi magana ya ɗaga mishi hannu. "Please try me and see young man." da
faɗan haka ya wuce ya ƙarasa wurin motar da tun fitowar shi ake warming ɗinta, ya shiga gidan baya
wurin da Reina take, driver ya ja, idanun Jamal da suka ciko da ƙwolla suka mishi rakiya.
Ran Yaseer tass ya buɗe wani sabon marker ya cigaba da bayani daga inda ya tsaya.

Babu laifi ya ɗan saurare shi suka cinye sauran lokacin, sannan Jamal ya koma gida, yaseer ma ya tafi
nashi hidiman sai 3:30 ya dawo yayi sallan la'asar suka ci gaba, sannan bai sake Jamal ba har saida suka
cinye lokacin da aka bashi tass, dukda Hajiya Hauwa ta turo a kira shi ya kai sawu uku.

.......

"Anya Fauziyya ba aljanu gare ki ba? Ko su ne suka aure ki suka hana ki zaman aure?" Cewar babban
yayar mahaifin ta.

Daga kai Ummi tayi ta dube matar amma sai ta mayar da duban ta gefe domin bata da ta cewa.

"Ko kuma dai ta samu mai hure mata kunne ba? Domin kin san idan aka lura mutum na cikin kwanciyar
hankali maƙiya ba su barin shi haka nan" cewar ƙanwar mahaifiyar ta.

"Ba'a hure mata kunne tun tana amarci ba sai yazu da ta shekara fiye da goma a gidan aure?"

Sun haɗu sun tasa Fauziyyar a tsakiya da faɗa a kan abinda ya haɗa ta da Tahir har ya yanke shawarar
sakin ta, bata ce da su kanzil ba, tun da ta san ba don saboda ita suke wannan tada jijiyoyin wuyan ba,
sai don saboda abinda duk familyn suke samu daga gare shi da suke tsoron yankewa.

Bin su tayi da idanu, ba zallan ƴan uwan mahafiyar ta kawai ba har da na mahaifin ta, duk sintirin da Aina
take yi a tsakanin gidajen aure basu taɓa irin wannan meeting ɗin ba.

Hasali ma idan ta tasu ne sun so kiran ta family house ɗin su Abban ta ne ayi mata faɗan a can amma
laulayin dake nuƙurƙusan ta ya saka yanzu bata iya fita ko nan da ƙofa, gashi tun da ta dawo bata komai
sai aikin kuka.
Autar su mahaifin ta ne ta girgiza kai "samm ni bani tunanin matsalar daga gare ta ne, domin ko ɗan
kishiya aka bawa Fauzee zata riƙe har ace ƴar cikin ta take azabtarwa harda yunƙurin Kisa. Sai dai idan
asiri ake mata domin a raba su ɗin"

"Kisa fa kika ce Amina. Ta yaya uwa zata yi yunƙurin kashe abinda ta haifa?" Ummi da abun ya fara isarta
ta amsa.

"Hmm Aunty Hafsatu asiri fa aka ce miki, ai abinda yafi haka ma za su iya saka ta tayi kawai don su ga
sun fitar da ita daga gidan, kuma gashi sun ci riba. don haka zama bai gan mu ba magani za'a bazama
nima mata tayi ta koma"

Miƙewa Ummi tayi kawai ta bar musu parlourn, domin idan ta matsa da bada shawarar a bi abun nan a
hankali gani zasu yi kaman ita ce bata son Fauziyyar ta koma ɗakin ta.

Tana miƙewa yayar ta da bata saka baki a zancen ba ta tashi ta bi bayan ta suka rufo uwar ɗakin.

"Ki kwantar da hankalin ki don Allah Hafsatu, in sha Allah komai zai daidaita. lokacin da za su shirya ya
maida ta ɗakin ta ma babu wanda zai sani sai dai su ji labari"

"Ni tawa jarabawar kenan, a duk lokacin da zan yi auren ƴa sai wata a cikin su ta dawo min" Ummi tace
da ƴar uwar ta cikin jimami.

"Ta yaya zaki ce haka Hafsatu? Keda zaki gode ma Allah duk yaran ki babu wanda ya taɓa rasa mijin
aure? Da sun tasa suke samun manema mu ba ga namu nan jibge a gida ba"

"Haka ne alhamdulillah, amma wani auren da za'a ta yi maka jeka ka dawo ko kuma hankali ya gagara
kwanciya sai nake ga kaman gwanda ba'a yi ba. Sannan ki ga yanda aka yi auren yarinyar nan abubuwan
da suka dinga faruwa. wallahi ban sake samun cikakkiyar nutsuwa a kanta ba tun Ranar da ta saka ƙafa a
gidan shi".
"Kada kice haka don Allah, dukkan mu yanzu fatan mu ta koma ɗin, tunda rabo har biyu ya ratsa ga na
uku a hanya kamata yayi a manta da baya da abinda ya ƙunsa. Ta koma kan yaran ta kawai shi ya fi"

Ummi ta ja dogon numfashi ta furzar. "Gashi duk sun gama razanar da Sajida, tun da Fauzee ta dawo
itama take kukan ta fasa, auren da watanni huɗu kawai ya rage mun riga mun karɓi tambaya da sadaki,
yaro bayi da aibun komai bai mata komai ba kuma, ta ina zamu fara ce masa mun fasa?"

"Lallashin ta zaki yi, ki haɗa su da Fauziyyar ki yi musu nasiha idan komai ya lafa, kinga itama yawan
koke-koken nan zai iya cutar da abinda ke cikin ta"

"Shikkenan, zan ƙoƙarta, Allah ya shige mana gaba"

......

Miƙewa yayi bayan ya gama gaida Hajiya Hauwa ta amsa, ganin Alhaji Salisu bayi kusa ya juya kawai yayi
tafiyar shi.

"Zahra hau sama ki taso Reina ta karya" cewar Hajiya Hauwa da ƴarta wanda zasu kusan zuwa tsara da
Reinan amma ta girme ta.

"Hmm, ba barci fa take yi ba wallahi Umma, tun asuba ina jinta tana danne-danne a tab sai gari ya waye
ki ganta kaman mushe"

Da faɗa-faɗa tace "kul! Kada ki bari Daddyn ku yaji wani magana daga bakin ki a kan yarinyar nan idan ba
haka ba zai iya sassaɓa miki, ki bar ta ta ƙaraci zaman ta har ta tafi...."

Kirif! Yaseer ya rufo musu ƙofar don haka bai jiyo ƙarshen zancen su ba yayi gaba abinsa.
Yau minti 20 kawai Jamal ya ƙara a kan lokaci ya fito, cikin shiga ta mutunci jallabiya har ƙasa. sannan ya
shiga bawa Yaseer haƙuri murya can ƙasan maƙoshi fuska a turɓune, tare da uzurin karyawa ne ya riƙe
shi.

Kasancewar mahaifin shi ya tilasta shi yayi hakan kuma yace zai tambayi Yaseer ɗin kafin ya tafi.

Taɓe baki kawai Yaseer yayi ya shiga abinda ya kawo shi.

karatun dai bayi wani tafiya saboda daƙiƙanci irin na Jamal amma dai Yaseer yana kamanta ƙoƙari.

Ƙarfe goma da ɗoriya ta fito tare da sauran yaran gidan tana baza idanu ko zata hango shi dukda kuwa
bata da yaƙinin hakan, daman zumuɗin zuwa wurin daddynta da ta kusan kwana biyu bata gan shi ba ya
saka ta tafiya a jiyan.

Amma da mamakin ta yau ma sai ta hango shi a wurin jiya.

Da gudu ta ƙarasa Wurin su ta faɗa jikin Yaseer dake zaune bayan ya bawa Jamal classwork yana jiran ya
gama, tana haki da dariya.

"Yaseer ka zo?"

"Baki iya gaisuwa ba ko?"

"Na iya" tace kawai.

"Sai nace ki yi?"

Sai ta girgiza masa kai kawai bata kuma yi gaisuwan ba.


Girgiza kai yayi ya ɗan tura ta daga jikin shi da hannun shi na hagu amma a maimakon ta matsa sai ta
kama hannun ta dafa ta ɗale kan cinyar shi ta sha zamanta tana kan washe masa haƙwara.

Shi kuwa mamaki ya hana shi motsi ganin buskuɗa ƴar nine years mai garin jiki irin ta ma wai har yanzu
tana zama a cinya.

"Baby baki gan ni bane?" Jamal ya kira ta da ya lura baki ɗaya hankalin ta yana kan Yaseer.

Kafin tayi wani yunƙuri Yaseer ya sauƙe ta daga jikin shi ya haɗe fuskar nan kaman bai taɓa dariya ba don
ya lura akwai suntattun notuka a kan yarinyar.

"Babba da ke kike zama wa maza a cinya? Ba'a faɗa miki babu kyau ba a islamiyya?"

Kan kace me har idanun ta sun tara ruwa.

Ta girgiza masa kai. Toh yaushe ma taje islammiyar balle har a faɗa mata ta ji?.

"Auntyn ki bata faɗa miki ba toh?"

"Ai aunty na bata nan, wai daddy ya sake ta" ta amsa da muryar kuka saboda bata saba da wasu bayan
Auntyn ba suna mata faɗa ba.

Yaseer ji yayi kaman an watsa mishi ruwan sanyi a jikin shi, cikin zuciyar shi yace "mai ya faru da har
Alhaji Tahir zai iya rabuwa da ita?" Amma ashe maganar a fili yayi.
"Na ƙona ma Maama baki ne shine ta dake ni na faɗo daga stairs na suma shine Daddy yace wai ta je
gida ya sake ta" ta labarta abinda ya faru babu kwama babu full stop kaman yanda ta ji ƴan uwan
mahaifin ta na mayarwa a tsakanin su.

Shiru Yaseer yayi, don ji yake yi idan har ya sake tambayar wani abun toh Reina zata cigaba da sanar da
shi abubuwan da zasu girgiza duniyar shi.

Domin yanda take amsar laifin ta da ƙwarin guiwa babu tsoro ko fargaba ma ya bashi tsoro.

"Toh yaushe zaka kawo min abun daɗin?" Ta tambaya jin yayi shiru.

"Nima ina da abun daɗi idan kina so" cewar Jamal cikin sigar ruɗin ta kaman yanda ya saba amma Yaseer
bai kawo komai ba domin har yanzu mamakin ta bai sake shi ba.

Maƙe kafaɗa tayi "O'o ni na Yaseer nake so"

"Shikkenan ki je kiyi wasa zan kawo miki" yace da ita don ya daina ganin ta a gaban shi.

"Yayyy" da gudu ta koma wurin yaran da suka baza abin wasa tana murna, Yaseer kuwa kaman ruwa ya
cinye shi.

Haka suka cigaba da zaman shiru, Jamal na ta browsing ɗin classwork ɗin a waya ƙarshe ma sai ya koma
chatting kawai ganin Yaseer ya zurfafa cikin tunani.

Bai tashi dawowa cikin hayyacin shi ba sai da muryar ta ya shiga cikin kunnen shi tana cewa "nine
mummy, nine mummy! ni zan bawa Junior nono tunda shine ɗa na, idan ya sha sai in bawa Zahira ma,
Abdallah kuma shine Daddy, zamu shiga ɗakinmu mu kwana tare a gadon mu...." Haka ta ci gaba da
tsara musu yanda wasan zai kasance.
*Saliha Ahmad Na'ibi (Seemahwrites ✨)*

*REINA 💍*

28......A hargitse Yaseer ya miƙe ya juya yana fuskantar yanda suke zaune suna sauraron huɗuban Reina.

Cikin ƙaraji yace "Hafsah!!!"

Har Jamal saida ya firgita domin yau ne karo na farko da ya taɓa jin Yaseer ya ɗaga murya.

Juyowa duka suka yi suna kallon shi banda ita hajiyar domin ta san abinda tayi ba dai-dai ba, bata yi
tunanin zai iya jiyo ta ba.

"Baki ji na kira ki bane?" Ya tambaya cikin kausasshiyar murya.

Ɗagowa tayi muryar ta na rawa tace "Na... Na'am"

"Sai na ce kizo?"
Jiki a sanyaye ta miƙe ta zaga mashigar rumfar sannan ta taka matakalar ƙafar ta na rawa ta ƙarasa wurin
shi idanun ta a ƙasa.

"Ka bita a hankali mana" cewar Jamal ganin yanda gabaki ɗaya ta firgice sai jikin shi yake bashi a cikin
wannan yanayin zata iya fallasa abinda ke tsakanin su ma Yaseer idan ya buƙata.

Banza yayi da shi yace "Maimaita abin da naji kina faɗa"

Haɗiyan miyau tayi kafin tace "wasan Mummy da Daddy ne zamu yi"

"Wani irin wasa ne haka?"

Ɗagowa tayi a hankali, amma yin arba da ɓacin ran dake kan fuskar shi yasa tayi saurin sadda kanta ƙasa
"kayi haƙuri Yaseer, ba zan sake ba" kalmar haƙurin kawai zamowa yayi daga harshen ta ba tare da ta
sani ba saboda bata saba da amfani da shi ba.

Laɓɓen bakin shi ya tauna yana ƙoƙarin dakatar da kanshi ya ɗauke idanun shi a kan koma menene
zatayi, amma sai yaji ya kasa.

"Get on your knees"

"Iye?!" Jamal yace cikin kaɗuwa. Ita kuwa hawaye ne suka shiga wanke mata fuska yayin da a hankali ta
zuba a kan guiwowin ta.

Ganin haka ya saka sauran yaran suka tattari komatsan su zasu gudu. Da hannu kawai ya yafato su suka
dawo don tunda ya iya saka Reina kneel down toh fa no nonsense ne.
"Miƙe bayan ki, ki ɗaga hannu sama kuma ki rufe ido"

Sheshsheƙar kuka take yi a fili yanzu amma bai hana ta yin kaman yanda yace ba, suma sauran ukun da
ƙarasowar su suka yi niyyar yin kaman yanda tayi amma sai ya dakatar da su tunda su bai ji maganar
banza a bakin su ba, ba zai bari laifin ta ya shafe su ba don haka yace su nemi wuri su zauna sannan ya
shiga duba shirmen Jamal ya barta a wurin.

Minti goma kacal amma jikin ta gabaki ɗaya rawa yake yi, hawaye da zufa sun wanke mata fuska babu
abinda bakin ta yake maimaitawa sai kalmar haƙuri.

Tausayi ta bashi yace ta miƙe ta buɗe idon ta.

Zaman dirshan tayi mishi a wurin tana maida numfashi idanun ta a cikin nashi. Lokaci ɗaya sai fushin ya
yaye tausayin ta ya maye gurbin shi.

"Ajin ki nawa a islamiyya?" Ya ajiye ainihin tambayar da yake son mata a gefe domin bayi da amfani
tunda ba komai zai iya yi a kai ba.

"Ajin farko" tace don har ga Allah bata san ma mai ake cewa ajin ba tunda ba damuwar ta bane.

"A wani Surah kike?"

"Wal Aadiyaati dabhan ne"

"Karanta min in ji"

Babu Bismillah ta fara karatun aya uku tayi ta fara kame-kame.


"Karanta min Suratul takaathur toh"

Rau-rau tayi da farin idanun ta da hawaye suke kwance a cikin su cike da tsoro tace "wanne ne kuma
shi?"

"Alhaakumuttakasur toh"

"Oh, na manta shi Allah"

Dogon numfashi ya shaƙa ya fesar domin kada ya sake hasala yace "Al-qaari'a kam kin san shi ko?"

Gyaɗa kai tayi "Eh"

"Toh idan baki karanta min Al-qaari'a har ƙarshe ba sai na zane ki. Kuma kiyi Bismillah kafin ki fara"

Zata cigaba da kuka ya daka mata tsawa a dole ta haɗiye shi ta fara karatun, burinta bai wuce wani ya
fito daga cikin gidan ya cece ta ba amma har tayi nisa da karatun babu wanda ya fito. duk inda tayi
kuskure sai ya gyara mata ko idan ta kakare ya ɗago ta har saida ta karance suran tsaff.

Dakatawa yayi domin ta maida nutsuwar ta, ya koma kan sauran yaran ma da tambayoyi.

Kaman yanda yayi tsammani suma ba wani abun arziki suka iya ba domin cikin su babu wanda ya wuce
izu biyu amma dai sun fita kuma ita ce babba.

Ya haɗa su duka ya tambaye su adduo'in da ya kamata yara irin su ace sun riƙe irin su na shiga ban ɗaki
da su kwanciya barci da sauran su, a nan kam ta bashi mamaki domin da daɗi da babu daɗi Hajiya
Fauziyya ta dage ta koya mata, sanin muhimmancin su.
Su hadisai, ƙawa'idi da ahlari kan ma ba'a magana bata ma taba yin su ba sai dai wanda ta tsinta a bakin
Aunty.

Don haka ya maida akalar tambayoyin shi zuwa fannin boko.

Shikam sauran yaran sun yi zarra, itama babu laifi don yanzu tana primary 4 amma shima babu abinda ta
iya domin kuɗin ubanta yasa take hayewa amma da ta sha repeating.

Har lokacin su da Jamal na karatun safe ya ƙare amma yana zaune dukda Yaseer ɗin ya sallame shi,
domin har yanzu bai gama nutsuwa de Reina ba zata fallasa shi ba.

Yaseer da a yanzu ya karyo reshen bishiya a matsayin bulala ya gwada yaran da shi yana faɗin "daga yau,
duk ranan da wani yaro yayi fashin makaranta ɗaya ko islamiyya ko boko sai ya kwanta a nan nayi mishi
bulala goma! Sannan har weekend zaku dinga zuwa islamiyya idan nazo na samu wani yaro yana wasa
lokacin makaranta ko? Hmm hmm hmm!" Ya jujjuya kai irin yana tausayin sun nan, baki ɗaya ya gama
tsorata su sai gyaɗa kai suke yi kaman ƙadangaru suna rantse-rantse.

"Kuyi min shiru!" Ɗiff kake ji kaman anyi ruwa an ɗauke, sai ƙifi-ƙifi kawai suke da idanu. "Kuma idan kun
dawo da islamiyyan safe duk asabar da lahadi zaku zo kuna bita mun karatun ku, zan duba idan kuna
class work da assignment kuma, duk wanda bai yi dai-dai ba hmm.. sorry ganda. Yanzu na baku minti
goma kacal ku wuce ku ɗauko jakar makaranta mu fara extra lesson, duk wanda ya ƙara minti ɗaya
bulala biyar!"

Bai rufe bakin shi ba suka ɗauki hanyar cikin gidan da mugun gudu har suna bangaje juna kuma babu
daɗewa suka dawo, Hajiya Hauwa na biye dasu ganin yanda suke a kiɗime tayi tunanin wani abun ne ya
faru.

Amma sai taga duk sun nemi wuri sun zauna sun fito da littafi da abun rubutu.

Gaishe ta Yaseer ya sake yi, ta amsa mishi da hannu kawai sannan tayi tsaye tana kallon gudun ruwan
shi.

Ko a jikin shi cikin Muryar umarni yace "baku iya gaisuwa ba ko?"
Jiki na rawa suka miƙe "good morning sir, we are happy to see you, may god bless you sir" murmushi
yaso kuɓce masa ganin Reina bata iya ba bin baki take yi amma ya fuske.

"Morning how are you"

"Fine thank you sir"

"Sit down"

Suka zauna. Har sai da ya fara musu karatu kafin Hajiya Hauwa ta koma ciki. Haka suka cigaba har saida
aka kira azahar kafin ya sallame su kuma dolensu su dawo.

Don haka suna gama cin abincin rana suka sake komawa wurin, Yaseer ma ya samu a wurin masu gadi
sun gayyace shi ya ci.

Don haka da ƙarfin su ya fara musu karatun Alkur'ani amma Reina tayi baya da yawa don haka dole ita
yayi mata nata daban. Sai da ya gama da su ya haɗa su da aikin aji kafin yace ya matso.

Ta taso ta dawo gaban shi ya ara mata ƙur'anin sauran yaran don ita bata da shi sannan ya fara bita mata
tana amsawa har saida ya tabbatar ta gaji kafin ya sallame su.

A daren Junior ya saka drama Hajiya Farida tazo ta ɗauki abinta ya rage sauran su uku kawai da zaman
gidan ya zama dolen su, sai a yau Reina fara kewar auntyn ta domin da itama daddynta yazo ya ɗauke ta
sun koma nasu gidan.

Tun daga wannan rana Reina ta shiga taitayin ta, kafin ace mata driver na jira har ta shirya ta fita kuma
da ta dawo take fito da assignment Hajiya hauwa ta taya ta sannan ko bata yi sallan la'asar ba zata yi
shirin islamiyya shima ta fita a kaita.
Wannan ya fara kawo sauyi a cikin hidimomin ta na yau da kullum, gajiyar jigilar makaranta ya saka ta
fara barci da wuri kuma da ta tashi sai shiri don haka yanzu bata da lokacin game ko kallace-kallace,
tsoron hukuncin Yaseer yayi mata diran mikiya a zuciya don gani take yi ma gwanda Aunty a kan shi.

Sati na zagowa kaman yanda Yaseer yayi alƙawari ya duba littattafan kowannen su, bai damu da tafiyar
junior ba daman Reina itace damuwar shi, sakaya sauran kawai yayi.

Hafsatu Reina ƴar Aunty, Auntyn da tayi wa iyayen shi Rana, Auntyn da ya ɗauka wa alƙawura masu
girma.

......

"Kin shirya zama ki fuskance ni Fauziyya?" Ummi ta tambaya.

Ɗago jemammun idanun ta tayi ta zuba mata don yanzu kukan ya fara gagaranta, tayi shi har ta gaji
gashi har yanzu babu abinda ya ragu a cikin laulayin da take fama kaman ta ajiye cikin ta huta.

Tayi kewar yaranta, babu kamar Maama ma wanda take ƙarama ga ƙuna a baki, sannan ko Reina bata
san ina Tahir ya kaita ba balle ita. shima Tahir ɗin tayi kewar shi, amma tun da ta dawo ko sau ɗaya bai
sake yarda ko kalmar baki ya shiga tsakanin su ba. Kullum a cikin kiran shi take yi, da tura mishi sakonnin
ban haƙuri amma bayi ɗauka bayi reply kuma shi bai yi blocking ɗin ta ba don haka bata fasa ba itama.
Ita ko ɗauka yayi ta tambaye shi jikin Maama da Reina ɗin ma amma har a text ta tambaye shi ya share.

Baki ɗaya ta gama fita hayyacin ta a yanzu, ta rame ta lalace fatar ta yayi duhu.

"Fauziyya magana nake yi"

"Ummi mai zan ce? Tahir ya raba ni da yara na" sai ta fashe da kuka da muryar ta dake a dishe.
"Ashe baki ga laifin da kika yi ya raba ki da su ɗin ba? Kina tunanin idan wani ne a matsayin shi ɗin barin
ki zai yi? Ni naga ƙoƙarin shi ma ai, domin da shi yayi wa ƴata haka wallahi sai nayi Shari'a da shi ko me
yake taƙama da shi kuwa".

"Ummi bayan shi kike bi?"

"Bayan gaskiya dai nake bi"

A lokacin Sajida ta shigo da sallama itama ta samu wuri a ƙasa ta rakuɓe, duk ta gama saka damuwar
Fauziyya a kanta.

Bata da wani shekaru aka yi auren yayar tata amma kowa ya shaida irin dramar da aka kwasa kafin
auren, idan haka ne tunda Alhaji Tahir ya iya sakin Fauzee toh ita waye da namiji ba zai iya wulaƙantata
ba?.

Ummi ta ɗaura ma Fauziyya daga inda ta tsaya "kina son yaran ki su tashi da tsanar juna ne Fauziyya?
Kina son su tashi basu shan inuwa ɗaya kaman masu ganin hanjin juna? Nace Kina son yaran ki su zamo
abokan gaban juna?! Toh ki ajiye banbancin da kike gwadawa a kan su tun kafin lokaci ya ƙure miki"

"Ummi duk yanda kayi ƙoƙarin jawo Reina a jiki wallahi sai haƙurin ka ya ƙare, kaman sheɗanu suna yiwa
yarinyar nan fitsari a kai. Ga taurin kai kaman jaka, ita ce rashin ji, rashin fasali, shegen son jiki da kyuya
ba'a magana, kanta yanda kika san ba ƙwaƙwalwa bane a ciki ba ko kunnen ƙashi gareta, kullum girma
take yi amma ƙasa take ƙara ci..."

Ganin kaman har yanzu bata gama ba Ummi ta dakatar da ita cikin takaici "ba sheɗanu bane suke mata
fitsari a kai ba Fauziyya, kalaman harshen ki ne suke dulmuyar da duniyar ta. Ta ina ɗan da uwar shi take
iya faɗan irin wannan kalaman a kan shi zai taɓa ganin dai-dai?."

Sauƙe ajiyar zuciya tayi bata iya amsawa ba.


"Fauziyya ke kika ɓata Hafsatu, da kunsan ba zaku iya mata tarbiyya ba da baku bata sunana ba don
baku min gwaninta ba."

Cikin matsanancin kuka da ya ƙwace ma Sajida ta fara magana "Ummi ki yafe ni amma me yasa a duk
lokacin da ɓaraka ya samu a gidan aure mace kawai ake bawa laifi? Ke kin san irin haƙurin da Yaya
Fauzee take da shi amma ace duk abinda ya faru iyayen mu ma sai ku take musu baya? Nima idan aka
zalunce ni na kawo kuka na haka za'a yi min?"

Gyaɗa kai Ummi tayi alamun ta fahimta sannan ta juya wurin ƴar uwar tan tace"Fauziyya kiyi min adalci,
sau nawa ina bin bayan ki a bayyane ko a ɓoye a duk lokacin da kike kan gaskiya ko dai-dai? Sau nawa
ina baki shawarwarin da baki nima ba ma a kan zaman aure da kuma tarbiyyar yara?."

Gyaɗa kai tayi alaman haka ne "Kiyi haƙuri Ummi in sha Allah daga yanzu zan gyara nayi alƙawari"

"Ba wa ni zaki faɗi kin gyara ba sai ma shi wanda kika yi wa laifi, ba'a kashe wuta da wuta Fauziyya na
sha faɗa miki zafi da ikon ki a kan Reina ba shi zai sauya ta ba.

Na san kinyi fama da ƙuruciya a lokacin da kika haife ta amma da haka kowa ya fara, ni lokacin da aka yi
min aure ma ban kai hakan ba kuma nima na kamanta irin kuskuren ki a kan Aina da Zeenat.

Yayun ku maza basu bani damuwa ba amma su sun tashi basu shaƙar inuwa ɗaya sai faɗa, ganin Aina ce
babba ko ita ta takalo Zeenat sai ba zan bincika abinda ya faru in bata gaskiyar ta ba har wasa-wasa abun
su ya ƙazanta suka koma kaman masu ganin hanjin juna. Ke kuma a lokacin da kike naki ƙuruciyar hankali
na yana kan shirya su bani da lokacin ki ga wasu yaran suna kan zuwa. Shi yasa kika tashi mun da mugun
riƙo, fushi da zurfin ciki dukda kina da sauƙin kai amma wannan halayen sun isa su wargaza ayyukan ki
har a wurin Allah ba zallan miji ba.

.....
A tsawon wata guda yaga sauyin da bai yi tsammani ba daga gare su, daga yaran har Jamal. daman
tsananin sake ne yasa suke nan kaman dolaye amma da ya matse musu lamba duk suna ƙoƙari
musamman ma Reina, bata da nauyin harshe a yanzu koyar da ita tajwidi ba zai yi wahala ba.

Suna tsaka da karatu Alhaji Tahir yayi parking ɗin mota sannan ya fito gani ma idanun shi sauyin da ya
fuskanta a tattare da ƴar shi a kwanakin nan. Ya fito hannun shi ɗauke da farin envelope fuskar shi ɗauke
da yalwataccen murmushin da ya ƙara girma lokacin da ya jiyo muryar Reina tana rera Al-ƙur'ani.

*Saliha Ahmad Na'ibi (seemahwrites ✨)*

*REINA 💍*

29........Har ya ƙaraso wurin bata lura da shi ba hankalin ta yana kan karatun ta sai mamaki ya kama shi,
anya wannan Hafsatun shi ne?

Yaseer ne ya fara hango shi, yayi mishi sannu da zuwa.

Jin yace Alhaji Tahir yasa Reina juyawa da sauri, ganin Daddynta tsaye yasa tayi firo da ƙur'anin izu biyar
da Yaseer ya siya mata, ta miƙe za ta nufi wurin mahaifinta da gudu amma tsawan da ya daka mata ya
saka ta daskarewa a hanya, ita bata je ba ita bata juyo ba ga hawaye har ya fara taruwa a idanun ta.

Shi kuwa Yaseer bai san ma yayi ba, wurgi da ƙur'anin da tayi shi ya razana shi, amma kwanannan yana
ƙoƙarin sake mata sosai don tausayi take bashi.
"Ƙaraso sarauniya ta" Alhaji Tahir ya yafato ta da hannu murmushin kan fuskar shi na bajewa.

A maimakon ta je ɗin kaman yanda yace sai ta juyo wurin Yaseer cikin karyayyen murya tace "yaya
Yaseer in je?"

Numfashi ya ja sannan ya gyaɗa mata kai. sai ta gyara nutsuwarta ta fara takawa a hankali taje ta
rungume mahaifin ta wanda ruwan mamaki ya shanye shi.

Daman bautar masa da ƴa ake yi?.

Hannun ta ya kama suka haura wurin yana kallon sauran yara biyu suna ta kwafan abinda ya rubuta
musu a allo, suka gaida shi sannan Yaseer ya saka mishi kujera ya zauna kana suka gaisa.

"Amma malam Yaseer ba za'a rage tsanantawa ba haka, idan ma wani abu ake buƙata da zai sanyaya ran
malam ko ya saka yaran karatu ai sai a faɗa a bayar"

Kaɗan ya rage yayi mishi kallon banza amma sai ya daure ya sauƙe idanun shi. yana ji a ran shi lallai ba
don Hajiya Fauziyya ba ko nawa wannan mutumin zai bashi bayi da lokacin ɓatawa a kan sakaltacciyar
ƴar shi, domin bayi jin zai taɓa mantawa da abubuwan da suka faru a kan idanun shi a shekarun baya har
abada.

"Babu abinda ake buƙata Alhaji, kuma suna karatun sosai" ya mayar mishi ganin ya tsare shi da idanu.
bayi raba ɗayan biyu mamakin yanda ya girma yake yi domin shima sun kwana biyu basu haɗu ba.

"Nima kawun ka ne ka ji?" Ya shafa kan ƴar shi dake rufe cikin baƙin hijabin da ta kamo ƙasan shi ta saka
a baki tana ci, murmushin alfahari na samuwa a kan fuskar shi "kuma ina son ganin Sarauniyata tana
karatu, idan ta samu ilimi mai yawa zan yi farin ciki"
Itama sai ta murmusa domin Daddyn ta kullum a cikin yabon ta yake komin kashin abinda zata yi kuwa,
amma Aunty ko tayi wani abu domin ta burge ta sai ta ɗauko kuskuren ta na baya tayi mata faɗa a kai,
sannan ko Maama ne zallah ta ɓata mata rai saita haɗa su duka biyu tayi ta faɗa.

"Nima buri na tayi karatun, kuma Insha Allah a tsawon lokacin da zan ɗauka a nan zan tabbatar da
hakan" ya ɗauki zancen shima kawun shi ne a matsayin sharrin kunne da ya jiyo mishi ba dai-dai ba.

"Zuwa Jamal ya rubuta Jamb ne ko?" Alhaji Tahir ya tambaya wani tunani na zuwa kan shi.

Gyaɗa kai Yaseer yayi "eh Alhaji"

Bai ji daɗin yanda ya sake kiran sa da Alhaji ba, alama ne na shi bai ɗauke shi a yanda yake so ba kenan.

"Toh idan kun kammala ɗin me zai hana sai ka ɗaura a namu gidan har zuwa itama lokacin da zata
kammala secondary ɗin ko bayan nan ɗin ma ai zai yiwu ku ci gaba"

"Yaseer ya ɗan waro ido"

Alhaji Tahir yayi saurin ɗaurawa da "zan iya ninka maka abinda suke baka, na san ko aikin gwamnati ka
samu idan ba gwaɓi gare shi sosai ba bazaka samu kamar hakan ba. Kuma ni nayi alƙawarin sama maka
aikin ma"

Duk ƙoƙarin shi saida sautin "Hmm" ya kuɓuce daga bakin shi.

Wato tunda morar shi zasu yi har alƙawarin aiki ake yi mishi tun ma bai gama karatun ba amma mahaifin
shi da yayi ta musu daako na tsawon shekaru sai matar shi ne ta iya rufa mishi asiri.

"Toh zan duba in gani Alhaji" yace don a bar maganan.


Ya miƙe cikin jin daɗi "yauwa, yanzu koda ta koma gidan ma zan saka ana kawo ta har ku gama da nan
ɗin"

Yaseer ya gyaɗa kai "toh"

Sai ya saka hannu a cikin aljihun shi a hanzarce ya dunƙulo sabbin ƴan dubu-dubu ya miƙa ma Yaseer.

Kallon yawan kuɗin yayi yana girgiza kai da hannu alamun ba zai karɓa ba.

Ƙwaƙwalwar shi ta tuna mishi skekaru tara baya, idanun shi ya hasko mishi mahaifin shi ya durƙushe
baya a gaban shi lokacin suna tare da Alhaji Salisu mahaifin Jamal a lokacin da shi kuma yake shirin shiga
Jss1, Ranar da aka haifi ita sarauniyar tashi.

Yana kallo ya ƙirgo kuɗi a aljihun shi wanda bai taka kara ya karya ba ya miƙa ma mahaifin shi amma bai
kai ga karɓa ba Alhaji Salisu ya amshe ya mayar cikin nashi aljihun.

Sai murmushin takaici ya suɓuce mishi "Allah ka barshi Alhaji" yace cikin sautin dariya-dariya.

Tunanin kunya da fulako yake yi don haka Alhaji Tahir ya mayar da kuɗin yana faɗin "toh ba haka za'a yi
ba" sai ya ciro katin shi ya miƙa masa.

"Gashi, kayi min text ɗin account number ɗin ka"

Sa hannu yayi ya karɓa, sannan Alhaji Tahir ya durƙusa ya sumbaci goshin Reina ya miƙa mata farin
envelope ɗin hannun shi.

Da sauri ta buɗe don ganin menene, ta ciro bundle ɗin 500 guda huɗu ta dube shi da alamun tambaya.
"Ban ce kuma ki koyi kashe kuɗi haka kawai ba. Ki bawa umman Jamal ta ajiye idan buƙatar wani abu ya
tashi sai ayi amfani da shi, Idan kuma wani abun kike so a siyo miki kawai ki faɗa ma driver zai siyo ya
kawo miki"

"Daddy har da su cake ɗin toh?"

"Komai ma idan kina buƙata kiyi magana kawai."

"Toh yaushe Aunty zata dawo?"

Ƙaramin murmushi yayi ya shafa fuskar ta "zata dawo soon idan kina karatu"

Ta gyaɗa kai cike da jin daɗi "thank you Daddy, zanyi da yawa kaji?sai ta dawo da wuri"

Ya lura yanzu ta rage tsalle-tsalle da garaje, girma ya fara kama Reina.

Ya so ta raka shi mota amma kaman tana tsoron hakan sai ya ɗaga mata hannu kawai itama ta ɗaga
mishi, suna kallo har driver ɗin shi yaja suka bar gidan ba tare da ya shiga ciki ba.

......

Har kwana biyu Yaseer bai nemi Alhaji Tahir ba, hasali ma katin da ya bashi neman wuri yayi ya ajiye bai
sake bi ta kan shi ba ya ci gaba da hidiman gaban shi. Ga shi yau sakamakon zagayen ƙarshe na aji biyu
zai fito su fara shirye-shiryen registration ɗin fara aji 3, kuma dake bai so zama haka nan ba a sauran
ranakun mako yana zuwa haddan su koyarwa shima ya ɗauki karatu don haka yanzu basu biyan shi.
Sakamakon shi na bana yayi kyau sosai, har Jama'are Saudat ta tura shi yaje ya gwada ma su goggo in
yaso bayan kwana biyu sai ya dawo.

Ranan Juma'a da hantsi ya sauƙa a tasha, mamaki ya kusan daskarar da shi ganin Meesha a tasha wai
tazo ɗaukan shi.

Itama bata wuce kwana biyu da dawowa ƙasar ba baki ɗaya wai sun je graduation ɗin Uncle ɗin su da ya
kammala karatun likitanci daga nan suka wuce yawon buɗe ido.

Tana yawan damun shi da kira don haka ya san da dawowar ta a cikin satin nan sai kuma yau da ya sanar
da ita shima zai dawo cikin gari shine fa dake hankali bai isheta ba ta tattaro mota tazo.

Haɗe gabas da yamma yayi kafin ya ƙarasa wurin ta, ta karɓi jakar shi tana mishi sannu da dawowa da
murmushi a kan fuskar ta gashi hutu ya karɓe ta sosai ta ƙara haske da kyau.

Saboda kar ya disga ta ga idanun jama'a a kanta ganin haɗuwar motar da tazo da shi da itama kanta ya
saka kawai ya shiga ta ja suka ɗau hanya. Amma a hanya tasha faɗa saida ta kusan zubda hawaye, har
dai suka isa bakin layin su Lafiya.

Yau ma yana fitowa suka yi ido huɗu da Saudat ta fito da shirin zuwa kasuwa don ta ɗauka sai can
maraice kafin ya dawo.

"Umma"

Ya kira ta cikin rasa abin cewa.

Sai Meesha ma tayi saurin fitowa daga motar ta durƙusa har ƙasa a kunyace ta gaida ta.
Babu yabo babu fallasa saudat ta amsa sannan ta gayyace su duka biyu su ƙarasa gida domin tana
buƙatar sanin wacece yarinyar da har take sauƙe ɗanta a mota bata sani ba.

Yanzu ƙofa ne mai kyau a jikin gidan su Yaseer, kuma gidan ya sha kwaskwarima sosai an lailaye ko ina
da siminti ga fenti, sai kuma shuke-shuken su da ya daɗa ƙawata wuri amma sai tausayin Yaseer ya
lulluɓe Meesha ganin irin gidan da yake rayuwa.

Ya shimfiɗa mata darduma ta zauna sannan ya kawo mata ruwa, sauran ƙannen shi duk sun tafi
makaranta.

"Baiwar Allah daga ina?" Umma ta tambaya cikin taushin murya

"Ita ce ƴar yayan umman Jamal da nake faɗa miki, wanda ta nima min lesson teaching ɗin nan??" Yaseer
ya amsa da rawar jiki.

Saudat ta haɗe fuska "kai na tambaya ne?!"

"A'a kiyi haƙuri" daga nan ya gimtse bakin shi.

Sai yau Meesha ta tabbatar ita ɗin cikakkiyar bafulatana ce domin kunyar Saudat ya kama ta sosai da
ƙyar ta iya buɗe bakin ta tayi magana, ita da ta ɗauka zasu fara wasan suruka tun yanzu.

Bata wani daɗe ba tayi musu sallama, Saudat ta saka shi yayi mata rakiya zuwa mota, ƴan unguwa sai
leƙowa suke yi suna hangen su ta katanga yara kuma suka yi cincirindo har jikin motar suna shafawa.

Sai da ta ɗan yi musu rabo kafin ta samu suka barta ta tafi, Yaseer kuwa kaman ya rufe su da duka, tsaki
yaja yana faɗin "matsalar ƴan ghetto Area kenan wallahi, baka isa ka kankaro aji ba sai sun kwaɓar
maka"
Da fargaba ya koma gida, kaman yanda yayi tsammani faɗan da yayi ma Meesha ɗazu saida Saudat ta
ninka masa shi da ƙyar ya samu ya rarrashe ta don ma ta riga da ta san me yake tsakanin su ne. Sai ta
rufe da mishi da nasiha da tuna mishi matsayin shi kaman ko yaushe, kada yaje ya jajiɓo musu abinda
yafi ƙarfin su.

Washegari sai gata a gidan Hajiya Hauwa wai tazo bashi haƙuri, tun daga nan ya fahimci Meesha ta zamo
mishi jarabawa.

A daren Lahadi yana cikin lissafin komawar shi makaranta sai ga alert ɗin Naira dubu ɗari biyu.

Bai sha wani mamaki ba ganin sunan account ɗin da ya turo Tahir Kamal.

Yaseer ya murmusa, shi da ya matsu ai gashi ya nimo account number ɗin sannan ma da personal
account ɗin shi ya turo masa, lallai Alhaji Tahir da gaske yake.

Yanzu yana da har dubu ɗari uku da ɗoriya na kan shi, kuma nan da sati biyu za'a sake biyan shi kuɗin
lesson ɗin Jamal.

Daman kuɗin makaranta yayi niyyan biya da dubu ɗarin farko, sai ya jinginar da komawa makarantar har
sai an biya shi na biyu kafin yayi siyayya ya biya kuɗin hostel ya tafi. Amma a yanzu ya canza ra'ayi.

POS yaje ya ciro dubu ɗari da Saba'in, yana dawowa ya damƙa dubu hamsin-hamsin ma iyayen shi su
biya bashin da ake bin su. Sannan sauran dubu saba'in ɗin yace ayi mishi siyayyan komawa makaranta da
shi da ƙannen sa, ayi musu sababbin uniform, jaka da litattafai da sandals, idan yayi canji a ƙara cefane.
kuma ya sanar ma Kamal kuɗin makaranta ma shi zai biya kayan shi.

Kowa ya zubda ƙolla wannan daren, har Saudat sai da ta sharara ma su Alhaji Tahir albarka. Babu
daɗewa kuma ya sake fita ya dawo da gasassun kaji da yoghurt suka yi kwanan ƙoshi da jin daɗi tare da
alfahari.
A washegarin bayan sun gama registration suka wuce kasuwa ya zaɓi yadi kala uku masu kyau
Muhammad ma ya zaɓi ɗaya ya bawa tailor a ɗinka musu sannan ya siya sabbon takalmi da turare, bai
dawo gida ba dai har saida kuɗin nan ya ƙare katt.

......

TV ne ke ɓaɓatu a parlourn dake a tattare yana fitar da ƙamshin turaren wutar da aka gama ƙonawa.

Tana kwance a ɓarin ta na dama hannun ta ɗaya a kan tumbin ta da ya fara fitowa, ɗayan kuma a kan
wayar da take ta rubuta saƙo tana gogewa.

Mai zata ce ma Tahir ne ya kula ta? Wani irin fushi yayi haka da har yanzu ya gagara hucewa? Bata da
burin da ya wuce yanzu ta koma ɗakin ta Saboda ba zata so ta haihu a gidan su ba.

Tambaya ta rubuta a kan lafiyar Maama da Reina da kuma ban haƙuri a tare da shi, tana nazari a kan
yiwuwar amsawar shi tunda ta saba tura masa irin wannan saƙonnin.

Sai kuma wani tunani yazo mata ta goge ta rubuta wani saƙon kamar haka.

"T ina kwana, yaya Jikin Reina? Tana zuwa makaranta? Tana yin assignment ɗin ta a kan lokaci?
Islamiyya fah? Don Allah a kula ana bata abinci saboda idan ta ƙoshi tana rage yame-yamen nan. Sannan
idan maghriba tayi don Allah a rufe mata kai a zaunar da ita a ɗaki tayi addu'a. Tana kuma Sallan asuba a
kan lokaci, banda fashin la'asar. Kada ta manta da addu'ar fita daga gida idan zata je makaranta"

Hannun ta na ƙaiƙayin tayi magana a kan Maama dai tayi jihadi ta tura, amma ji take yi kaman nan da
wani lokaci zata iya mutuwa idan bata saka ta a ido ba.

Ko minti biyar saƙon bai yi da tafiya ba sai ga kiran shi ya shigo wayar ta, Ai zumɓur ta miƙe zaune ƙirjin
ta na bugu kaman zuciyar ta zai faɗo daga kirjin ta.
*Saliha Ahmad Na'ibi (seemahwrites ✨)*

*REINA 💍*

30......Hello T?" Ta sake magana jin ta yi sallama babu amsa.

Furzar da numfashi yayi kafin ya amsa da "kina lafiya?"

Baki na rawa tace "da ƙyar nayi lafiya T, kaman ba zan rayu ba..." sai ta fashe da kuka.

Daga ɗaya bangaren ya rintse idanu yana sauraron kukan nata, Fauziyya ta azabtar da su duka, Allah
kaɗai ya san yanda aka yi ya iya jurewa har zuwa wannan lokacin ba tare da ya ji muryar ta ba. Da ita
yake kwanciya yake tashi idan ma ya samu barcin kenan tunda yanzu abubuwa sun haɗe masa goma da
ashirin ga yanda baki ɗaya rayuwar take ƙara rikice masa idan bata tare da shi.

"likita yana zuwa duba ki ina? Kuma kin fara zuwa asibiti?" Ya tambaya don tabbatarwa duk da yana bin
diddigin halin da take ciki.

Gyaɗa kai tayi kaman yana ganin ta kafin tace "T ina yara na? Ina ka kai Maama?"
"Ba zaki tambayi Reina ba ko? Ita kullum sai ta tambaye ki"

Hannu ta saka ta share hawayen fuskar ta tace "Na san kulawar da Reina zata samu ko a bayan idanu na
yana da yawa, amma Zainab baiwar Allah T, bata ma iya buɗe baki ta faɗi abinda take so balle wanda
bata so, sai ni kawai da na san buƙatun ta zan iya kula da ita"

Dariyar da bata haɗe da nishaɗi ya sake, dama ya san saƙon da ta turo mishi trick ne saboda ta samu ya
kula ta. "Fauzah wato ba zaki taɓa sauya zani ba ko? Ashe baki ɗauki darasi a abun da ya faru ba? Hmm.
Tunda haka ne ba matsala zan cigaba da kula da yarana duka, kowa zan yi mata abinda take so babu
bambanci. Kuma ki sani Idan kin haihu kin yaye abinda kika haifa zan karɓi abuna in nima musu wata
uwar da zata fiki son su"

Zamowa tayi daga kujerar ta samu wuri a ƙasa ta zauna daɓas, cikin muryar kaɗuwa tace "Mai kake nufi
T??"

"Ina nufin aure zan ƙara kwanan nan, ba zamu ƙare ni da yara a tsakanin gidaje ba kullum a tagayyare
ba. And for your information Maama tana Nijar, na bada ita ma Alaji Abdou"

Ya san shikkenan ya ƙare mata tanadi don haka ya datse kiran ba tare da ya saurari kururuwar da ta fara
kaman zautacciya ba, kuma yana da tabbacin zancen kishiyar da yayi mata bai kiɗima ta kaman zancen
kasancewar Maama a Nijar ba.

Abinda bata sani ba kuwa Rabon shi da Alaji Abdou tun fara rikicewar lamarin nan, gashi yanzu ya fara
shiga tsaka mai wuya babu abokin shawara balle mai taimako, yana daga cikin dalilin da ya saka bai nemi
sasantawa da Fauziyya ba don bayi son sai ta dawo kuma ya saka mata wani damuwar ga ciki.

Bai gama tunani ba aka yi knocking sau biyu tare da turo ƙofar a lokaci guda.

Hajiya Jummai ne ta shigo sai Maama biye da ita, da ɗan gudunta ta ƙaraso ta faɗa a jikin mahaifinta.
Shima rungumar ta yayi yana shafa bayan ta a hankali "gimbiya ta makarantar ne?"

Cigaba da riƙe shi tayi bata ɗago ba sai ya saka hannu ya tallafo fuskar ta da yanzu ya jiƙe sharƙaf da
hawaye.

"Yaya Jummai don Allah jira mu a waje" yace don ya san ba zata iya ce komai a gabanta ba.

Lokaci ɗaya ta fara rantse-rantse domin ta san babu abinda zai hana Maama faɗa mishi abinda yake
faruwa a yau dukda lallashin ta da ta gama yi, ta kawo ta wurin mahaifinta kaman yanda ta buƙata da
sharaɗin ba zata yi masa kuka ba.

"Wallahi Tahir ban sani ba! Amma yanzu ma na ɗauki mataki na hukunta su sosai kuma duk saida suka
bata haƙuri. Faɗa ne kawai irin na yara, ka san su da rashin hankali wai suna rama abinda Reina tayi
musu a kanta" ta fallasa kanta da kanta domin ta san itama yau ta ƙare mata kaman dai Hajiya lubabatu
wanda ko ga maciji yanzu bayi haɗa ta da Tahir.

Bayi son ya rikice a office yayi mata abinda zata sha mamaki, idanun shi a kan gefen collar farar rigar
Maama da fatar wurin ya tara jini yace "A shigo min da school bag ɗinta kawai ki wuce gida, na gode da
riƙon amana"

Zata ƙara magana ya ɗaga mata hannu "don Allah ki tafi"

Haka ta mayar da bakin ta rufe sannan ta juya cikin tashin hankali ta bar office ɗin.

Tana rufo ƙofar ya shiga ɓalle botiran rigan Maama sannan ya cire yana kallon jikin ta harda tabon cizo a
damtsen ta. "Tun yaushe suke miki haka?"

Shiru tayi daga farko kaman ba zata amsa ba sai kuma tace "Idan.... idan muka je school ne sai su duke ni
su saka friends ɗin su duka na wai ai Reina tana dukan yayun su suma. Ko kuma idan tayi musu wani abu
sai su rama a kai na, har lunch ɗina suke ƙwacewa kuma ko a gida sai su kai abinci na ma kare idan Hajiya
bata kusa"

"Kin faɗa ma teacher ɗin ku?" Ya tambaya cike da tausayin ta.

Ta gyaɗa kai "na faɗa mata ta saka su kneel down da picking amma basu daina ba"

"Ita Hajiyan fa? Kin faɗa mata?"

Sai ta girgiza gai wasu sabbin hawayen na zubo mata "Ina tsoro"

Ya sake kallon yanda ta ƙara ramewa ta lalace daman ita ba mai jiki bane kaman sarauniyar shi.

"Zan ɗauki tsatstsaurar mataki my princess, kada ki damu"

A ranar su biyu suka kwana a ɓangaren shi, daɗin ta ma Aina'u tana nan don haka ita ta shirya masa ita
ta bata abinci da kan shi ya kaita makarantar zuwa ofishin principal, yaje ya sauƙe musu buhun bala'i.

Har ƙasa saida principal ɗin ya kai yana bashi hakuri domin cewa yayi zai cire Maama da Reina a
makarantar. Gwanda ma Maama da take zuwan baya amma Reina da kuɗin makarantar ta aka kammala
ginin makarantar, saboda lokacin ɗoki ya saka Alhaji Tahir biyan school fees ɗinta baki ɗaya tun daga
farko har ta gama secondary.

Kuɗin uniform, abinci da litattafai duk ya biya a dunƙule saboda zumuɗi domin tsarin makarantar yayi
mishi, kaman na ƙasashen waje.

Da ƙyar manyan makarantar suka taru suka taushe shi, har mai makarantar sai da ya zo ya saka baki.
Kafin suka daidaita a kan bawa sauran yaran suspension na sati biyu sannan idan zasu dawo sai sunzo da
iyayen su dukda shi korar su yaso ayi harda yaran ƴan uwan shi duka, daga ƙarshe dai ya cire Maama a
makarantar ya bar musu Reinan tunda ita kam da bakin ta.

Haka dai ya tafi ya bar su da Mamakin shi nashi ƴar tana jibgar yaran jama'a ta kwana lafiya, a haɗu a
rufe maganar, amma an taɓa ƴar uwar ta ya ɗaga musu hankali.

......

Yau Yaseer ya samu kuɗin da yake jira daga wurin iyayen Jamal don haka ya biya kuɗin hostel ɗin da an
riga an kama mishi, sannan ya fara shirin tarewa a can sai dai dole zai dinga dawowa ko wani weekend
don zuwa koyar da Jamal da su Reina.

Ya karɓo sabbin ɗinkunan shi, Umma ta taya shi haɗa kayan yanzu gobe daga yayi wanka ya karya zai
wuce.

A sauran kuɗin ya cire har dubu ashirin pocket money sannan ya ɗauki ragowar ya damƙa ma umman shi
da take ta kalen inhaler alamun ya ƙare.

"Umma gashi a sake siyan numfashi" ya saka mata kuɗin a cikin tafin hannu.

Ɗayan hannun ta a kan ƙirji tana ƙoƙarin daidaita numfashin ta da tarin da tayi Saboda ƙuran waken da
take gyara mishi ya saka shi hawa, ta ɗago hannun tayi mishi danƙwale kafin ta mayar da shi kan ƙirjin.

Murya a shaƙe tace "ka ajiye kayan ka, ina da kuɗin siyan wani"

"Nima akwai kuɗi a wuri na, kawai ki riƙe" ya ajiye mata kuɗin a kan cinyar ta.
"Ba zaka yi ma kanka tanadi bane? Sai kashe kuɗi kawai Yaseer? Kaga bamu san mai gobe zata haifar ba,
ya kamata ace kana da wani shiri idan wanda kake da shi a yanzu bai ɓulle ba. Idan kana ajiye wani abu
duk wata zaka tara jari mai yawa zuwa ka gama karatun ka kaga sai ka kama sana'a mai gwaɓi"

"Umma Alhaji Tahir fa yayi min alƙawarin aiki idan na gama" yace don yaji bakin ta tare da karɓan tray
ɗin daga hannun ta yaci gaba da gyaran yana ɓoye dariyar shi.

"Kaci gidan ku! Alƙawarin Alhaji Tahir alƙawarin Allah ne? Ko baka ga abinda ya faru da mahaifin ka
bane? Ashe baka ɗaukan darasin rayuwa daga kuskuren wasu?"

Dariya kawai ya sake yi saboda daman tsokana ce, ya sauya hirar da "Umma yanzu ace da wata rana zan
yi kuɗi mai kike so inyi miki?"

Sauƙe numfashi tayi tace "ni idan ka kaini ɗakin Allah ka gama min komai Yaseer, ya Allah ka kira mu"

Da "ameen" ya amsa kana ya ɗaura da "in Sha Allah toh Umma Hajji duk shekara Umrah duk sati idan
nayi kuɗi"

Darawa tayi tace "toh Idan haka ne ai sai ka nima min gida a can kawai in tare"

"Shawara mai kyau, hakan ma kawai za'a yi. Idan baki son Abbah ma yana damun ki sai shi in bar shi a
nan in gina mishi makeken gida in bar shi yana hutawa kawai ya dawo Alhajin parlor har sai kin buƙati
ganin shi"

Shi karan kan shi saida ya dara jin abinda ya faɗa tace "kana magana Kaman Irfan wallahi, shi yace ma
wai jirgi baki ɗaya zai siya mu koma rayuwa a sararin samaniya"

"Tashin hankali, ashe namu burin kaɗan ne"


Sai da suka tsagaita dariya yace "amma da gaske Umma da ace Allah zai wadata ni ya bani dama kinga
matasa masu zaman hakan nan?! Sai na tattare mana su duka a Nigeria an dawo babu mai zaman banza.
amma bari kiga ma ba sai an je da nisa ba yaran da suke zube a unguwar nan kaman kiyashi, babu boko
islamiyya sai ɗaɗɗai ɗin nan kwanan nan duk zan biya musu PTA in ɗinka musu uniform in kai ƴan ƙaniya
makaranta, suna nan sai aikin cika mana kunne da zubar wa mutum aji a unguwa"

"Allah ya taimaka ya ida nufi"

Ya amsa da "ameen" suka ci gaba da hira har aka kira sallan maghriba sannan ya tattari ƙannen shi suka
wuce karatun dare da suke ɗauka a masallacin unguwa.

...

Sai da yayi attending lectures ɗin safe kafin ya koma ya shirya kayan shi a ɗakin, su Muhammad suka
taya shi. Daga nan kuma aka cigaba da fafatawa a fagen daga na karatu.

Abu ɗaya ne ya canza kuma ya fara damun shi, yanda Meesha yanzu ta dawo mishi wata mannani
katanga, har mutane sun fara gulman su gashi saboda alkhairin da tayi mishi ba zai iya wulaƙantata ba.

Yaran manya da masu ji da kansu dake binta tana wulaƙantawa kuma sai suka fara jin haushin shi, shima
yammatan dake ra'ayin shi yana gwada musu bayi da lokacin su sai suka shiga aibanta shi tunda gashi ya
makalewa ƴar masu kuɗi hala ma biyan shi take yi suna wani abun da bai dace ba, tunda shi bai yi ma
kowa ƙaryan shi ɗan wani bane.

Haka dai wannan semestern yazo masa a takure, ita kuma ta gagara fahimta ta rabu da shi.

.....

Sai yanzu ne Alhaji Tahir yayi ainihin lalacewa saboda kula da Maama da ya dawo wuyan shi, babu yanda
Hajiya Farida bata yi ba amma yana tsoron kada shima a sake cutar da ita. Daɗin abun ma bai ji wani
complain daga bakin Reina ba bayan ƙananun mitan da ta saba, gashi ta daɗa maida hankali a kan
karatun ta da Yaseer harma a makaranta yanzu tana cin tests fiye da average.

Sai dai fa Jamal bai sauya sheƙa ba, yana nan yana kan laluɓe ta a sirrance, sannan yana kan lallabar ta
da razana ta a kan kada ta faɗa ma kowa, dukda a yanzu tsoron hukuncin da zata fuskanta idan aka ji, da
kunyar da zata sha shi yafi damun ta fiye da wani abu saboda a yanzu ta fahimci munin abinda take
aikatawa musamman a irin nasihohin da Yaseer yake musu wanda burin shi ta rage sake jiki da maza
barkatai ne amma bai san abin har ya fi haka muni ba.

Taso ta faɗa mishi amma tana tsoron irin kallon da zai fara mata gashi yanzu suna mutunci sosai don
haka ta ja bakin ta ta gimtse shi.

Sai dai ta rage zuwa ɗakin Jamal a karan kanta. Wani lokacin idan ya kira ta sai tace tana zuwa har ya gaji
da jiran ta ba zata je ba. Ko kuma idan yace ta fara zuwa ta jira shi yana zuwa Saboda kada a lura da
shigewar su ɗakin a tare sai tace ya fara shiga tukunna. bayi son ya takurata ta bauɗe masa don haka sai
yayi kaman yanda yace ita kuma ta gudu.

Sannan yanzu tana ƙoƙarin sallah a kan lokaci saboda irin azaban da Yaseer ya sanar da ita za'a dinga
yiwa duk wanda bayi sallah a cikin kabarin shi da ma makomar mai wasa da Sallah.

Shi kuma Sallah tsari ne daga alfasha da munanan ayyuka. A hankali kallace-kallacen banzan nan ya fara
sane mata a rai, ta koma maida hankali a kan educational program wanda zai taimaka ma karatun ta da
ma wanda zata kalla saboda nishaɗi kawai tayi dariya.

*Saliha Ahmad Na'ibi (Seemahwrites ✨)*


*REINA 💍*

31......Tafiya ne ya taso ma Alhaji Tahir na sati biyu zuwa Abuja. Tunanin yanda zai yi da Maama ne ya
dame shi, ya rasa ya kai ta ma Hajiya Farida ne ya bi ya ja mata kunnen kada ya ji kada ya gani ko kuma?
Babu ma zancen su tafi tare saboda shima ba zama ya kaishi ba.

Da sallama suka shigo gidan, Reina na faman zungure ma Maaman kai amma bata ce komai ba kuma ta
saka ma ranta ba zata yi mata kuka ba, sai tafiya kawai take yi a hankali Reina kuma bata fasa ba.

Sauƙowar Alhaji Tahir daga saman bene ya saka Reina ƙarasawa da gudu ta rungume shi domin kwanan
nan bata wani samun ganin shi sosai.

Daman tayi mamakin ganin driver ɗaya ne ya ɗauko su daga school ita da Maama kuma sai yayo hanyar
gida da su.

"Daddy aunty ta dawo ne?" Ta tambaya cikin zaƙuwa.

Kai ya girgiza kafin ya miƙawa Maama hannu itama ta karaso.

Itama so take yi ta tambaye shi auntyn amma nauyin baki ya hana ta, don haka sai ta tsura mishi ido
tana jiran taji yace wani abu.
"Ku shirya zamu je bikin Aunty Sajida ne a gidan Ummi"

Duk sun fahimci dai waurin mahaifiyar su za'a je don haka suna rige-rige suka wuce sama suka kwabe
kayan su aka shirya su suka sauƙo.

Babu mai nutsuwar cin abinci a cikin su amma haka Alhaji Tahir yayi jan ido Saboda bayi son su je su ci
abincin biki.

Sama-sama suka ɗan taɓa sannan Reina ta saka masa rigima ko sallar la'asar bai kai ga yi ba suka fice.

Yau kam Maama tayi farin ciki da hakan.

Bayan mota ɗaya suka shiga da yaran sai kuma wani dake bin su a baya har cikin gidan su Hajiya
Fauziyya, yayi umarni da a fito da kayayyakin dake bayan motar da ta biyo su.

Babu ɓata lokaci aka yi masa iso zuwa parlourn abban su saboda ƴan biki dake ta shirin zuwa kamu a
babban parlour.

A hankali take takowa kaman bata son taka ƙasa, tayi siririyar sallama sannan ta shigo idanun ta a kan
shi.

Yau ga idanun ta cikin na Tahir, yau ga Tahir ya ga daman zuwa yaga lafiyar abin cikin ta.

Kafin ta ida tunani Reina ta ruga ta faɗa jikin ta har saida Fauziyya ta dafa garu saboda kada su kai kasa
domin jikin ta babu ƙarfi sosai.

Miƙewa Alhaji Tahir yayi shima yana kallon ta, kaman wanda suka shekara goma basu ga juna ba gabaki
ɗaya Fauziyya ta canza.
Ya daɗe yana danasani amma a yanzu yayi ya sake.

Ta shafa kan Reina tare da mayar da idanun ta kan Maama. Bata zo gare ta ba, tana tsaye jikin mahaifin
ta amma hawaye ke wanke mata fuska.

"Maama na ba zaki yiwa auntyn ki oyoyo ba? Ko kin manta da ni ne?"

"Kiyi haƙuri don Allah Fauzah"

Fauziyya ta mayar da duban ta gare shi jin raunin muryar da yayi amfani da ita.

Murmushin da yafi kuka ciwo tayi tace "Babu komai Tahir, dama na san wa na aura"

Tahir! Tahir! Bai taɓa jin sunan shi ya fito daga bakin ta ba sai yau. Mai kuma take nufi da ta san wa ta
aura?.

Miyau ya haɗiya bayi son ya saka ma ranshi tunanin wai ya fara sanewa a ran Fauziyya ne, don ya sha ji a
bakin masana soyayya wai mace bata iya faɗan sunan wanda take so take mutuntawa, bai tabbatar ko
hakan bane amma da ƙamshin gaskiya a zancen tunda gashi yana ganin abinda bai saba gani ba a cikin
idanun ta.

"Zauna mana, kada ki gaji da tsayuwa" ya ɗaga mata filallukan dake kan dogon kujera domin ta sake.
Haushin kanshi matuƙa ya kama shi na rashin zuwan shi ya ganta a tsawon watanni huɗu sai yau.

Mai ya sha kanshi?

Ya fara hauka ne?

Babu musu ta karasa ta zauna ɗin, sai kuma ta kishingiɗa ta kwantar da kanta a jikin hannun kujera.
"Yaya lafiya? Ko jikin ne?" Ya ƙarasa da nufin taɓa ta yaji zafin jikin ta, tayi saurin riƙe hannun shi tana
mishi wani irin kallo.

Basarwa yayi ya zauna tare da ɗago ta ya kwantar a jikin shi yana taɓa goshin ta da wuyan ta ga jikin ta
yayi rau kaman garwashi.

"Tun ƙarshen wancan watan nace ma Abba zamu koma gida yace na bari sai jikin ki ya ƙara kyau"

Samu tayi ta ƙwace daga riƙon shi ta matsa gefe tana dariyan yake wa yaran da suka kafe su da idanu.

Waya ta ɗaga ta kira a turo a ɗauke su a basu abinci.

Yanzu kam Alhaji Tahir bai damu ba indai zata saurare shi, don haka yayi shiru yana kallon ta tana kallon
yaran da tayi kewar su kaman zata cika har aka shigo aka tafi da su.

"Amma shine baka ga daman zuwa ba sai yau? Ko baka zo don ni ba Tahir ba zaka zo don abinda ke ciki
na ba?"

Bayi da amsar da zai bata, sai kawai ya canza zancen tunda ya san bayi da gaskiya.

"Ban kai Maama Nijar ba, ƙarya nayi miki" yana da yaƙinin hakan zai canza wani abu.

Taɓe baki tayi tace "idan ma ka kaita ba gashi ta dawo ba?"

"Fauzah kiyi haƙuri mana? Me yasa baki da haƙuri ne?"

Kallon shi tayi tare da sakin dariya mai sauti tana jin yanda fitar shi ya ƙona mata ƙirji.
Bani da haƙuri? Ni lokacin da nake baka haƙurin halan naka aika yaje. Shine kalaman da zuciyar ta ya
tanada mata ta faɗa mishi amma sai "Hmm" kawai bakin ta ya furta.

Duniyar ma da abin cikin ta baki ɗaya nawa yake?

"Toh ko zamu je asibiti ne?" Ya sake magana.

Girgiza kai tayi, ba don tana son magana dashi ba sai don ya ƙyale ta yasa tace "zazzaɓin yammaci ne
kawai nake fama dashi kwanan nan, anjima zai sauƙa"

"Amma kin fada ma doctorn da yake zuwa? Ya baki magani?"

Sai ta gyaɗa masa kai kawai.

"Allah ya sawaƙe. Yanzu kinga ba ma iya halartar bikin zaki yi ba, in dauke ku mu koma gida ne ko in bar
miki yaran idan kun gama ku dawo?"

"Kaje zamu dawo"

Bai gaji ba yace "akwai kuɗi a wurin ki ko ya ƙare?"

Ita ko kuɗin shin ma kwana biyu bata son taɓawa gashi duk sati sai taga alert, saidai kawai tayi ta alkhairi
da shi.

"Akwai"
"Kunga aika jiya?"

"Mun gani Allah ya saka da alkhairi ya ƙara buɗi"

Kusan shi ya ɗauki ɗawainiyar baki ɗaya bikin nan da za'a yi, tun daga ci da sha har kayan ɗakin amarya.

"Fauzah ki saki jiki kiyi min maga Please, bani son ganin ki so dull hakan nan. Kinga tafiya zanyi gobe don
Allah ki faranta min ko zan samu kwarin guiwar fuskantar abinda yake gaba na"

Yanzu kam ya fara damun ta don haka ta riƙe kai tare da rintse idanu kaman wanda take cikin tsananin
ciwo.

"Likita yace ina hutawa sosai T, kuma kada ana damu na da magana"

T ɗin da ta kira shi ya goge sauran kalmar don haka ya miƙe, yace "toh bari na tafi, ki kula da kan ki da
kuma yaran , in dawo inga canji a yanayin ki don Allah"

Ta gyaɗa masa kai tana leƙen fuskar damuwar shi ta ƙasan ido sai kuma ta ɗan ji daɗi a ranta har ta fara
jin kaman komai zai iya wucewa a yanzu.

"Ko zaki min rakiya ne?"

"T bani jin daɗi fa" tace cikin muryar shagwaɓa.

Murya a tausashe yace "Kiyi haƙuri don Allah, ban sani bane ko idan na tafi ba zan dawo ba, kinsan haali
na tafiya"

Sai ta saki kan sannan yayi gaba ta bishi a baya tana jan cikin da yayi girma yanzu, har zuwa jikin motocin
shi.
Kayan taɓe-taɓe irin wanda yaran shi suke ci kuma ya san ba za'a samu a nan ba shine aka zube ɗazun na
Reina da Maama.

Sai kuma aka fito mata da akwatunan kayan su daga booth.

A wurin ya saka mata kuɗi masu yawa na bukatun ta dama yaran kafin suka yi sallama ta bishi da addu'a
ya tafi.

.....

"Reina lafiya?" Hajiya Fauziyya ta riƙo kafaɗun ta don jin damuwar ta.

Rawan banjo take mata a wurin tana matse cinyoyi "Aunty fitsari nake ji"

Haɗe fuska tayi duk wani yunƙuri da zata yi na sauraron yarinyar nan sai ta bata haushi.

"A bakina ne zaki yi fitsarin? Ko sai na zo na kai ki?"

Fashewa tayi da kuka tace "yaƙi fitowa ne"

"Yaƙi fitowa kuma?"

Rage tsayin ta tayi ta ɗaga rigan da ya kai ma Reina zuwa cinya tare da saɓule pink ɗin leggings ɗin tare
da pant ɗinta har ƙasa sannan ta leƙa wurin, lokaci ɗaya kirjin ta ya fara bugu fat-fat!
Wurin yayi jaa ga ƙuraje sun feso mata sosai.

Ɗagowa Fauziyya tayi, tayi mata irin kallon da ta daɗe rabon ta da mata irin shi. "Reina akwai abinda
kike sakawa a private part ɗin ki ne?"

Da sauri ta girgiza kai.

"Toh zaki faɗa min waye yake taɓa miki wurin?"

"Wallahi tallahi babu" tsoro ma har ya saka ta bar rawar matsuwar.

Ƙwafa Fauziyya tayi ta ja hannun ta zuwa ɗakin su tace ma mai aikin da take gyaran ɗakin taje ta kira
mata Aina'u kuma kada ta dawo sai ta nime ta.

Daman Aina'un tana kusa don haka babu ɓata lokaci ta ƙaraso ta samu Reina mai rawan fitsari da
Fauziyya da ta kasa zaune ta kasa tsaye.

"Gani Aunty"

"Yauwa saka ta tayi fitsari don Allah " tace da ita tare da ficewa daga ɗakin.

Bata wuce ko ina ba sai kitchen ta zaro sharbeɓiyar wuƙan yanka nama sannan ta dawo lokacin sai
yunƙuri Reina take yi na fitsarin amma sai kaɗan-kaɗan yake fitowa kuma da tsananin zafi.

Shiga banɗakin tayi ta nufi Reina dake zaune a kan toilet seat gadan-gadan da wuƙar sannan ta cukumo
wuyar riganta ta kawo wuƙar kusa da fuskar ta tana zare idanun ta da sun kaɗa sun sauya kala.
"Innalillahi wa inna ilaihirrajiun! Aunty lafiya? Mai yake faruwa?" Aina'u tayi kokarin riƙo Fauziyya amma
sai ta fisge.

"Zaki faɗa min wanda yake taɓa ki a wurin ko sai na yanka ki?!!"

A razane ta saki ihu "wayyo Allah Aunty! kiyi haƙuri! na shiga uku!"

Ta jijjigata "ba zaki faɗa min ba sai yau kin mutu?!"

"Wallahi babu kowa Aunty!. Wallahi, tallahi, billahillazi la ila...,"

"Ba rantsuwa nace kiyi min ba, ki faɗa min ko in yanka wuyan ki da wukan nan!"

Idan ta ɓoye aunty ne kaɗai zata hukunta ta. Amma idan ta bayyana...

Idan ta bayyana aunty zata hukunta ta, daddyn ta ma hala yayi mata horo mai tsanani. Jamal zai ƙona ta,
yace mummyn shi ma idan taji zata yanka ta, sannan idan ta shiga kabari ma Allah zai yi mata azaba da
su macizai da wuta, haka Yaseer yace.

"Aunty don Allah abi komai a sannu." Aina'u ta shiga roƙon ta amma Fauziyya ta kurmance ta makance.

Ta sake wuyan rigan Reina ta ɗauke ta da zazzafan mari kafin ta sake mata ɗamƙar da yafi na da, amma
sai kawai ta biyo hannun ta yuuu kafin ta ankara ta zube a ƙasan bandakin sumammiya.
*Saliha Ahmad Na'ibi (Seemahwrites ✨)*

*REINA 💍*

32......RANAR WANKA

Zaune suke a harabar asibitin ita da Aina'u domin Fauziyya ji take yi duk iskan dake ciki ya kasa ma
huhun ta.

Ta rasa wani irin tunani zata yi, ta rasa mai yake mata ɗaɗi, idanun ta a bushe sai zuciyar ta dake zafi
kawai.

Motar yayan su ne yayi parking Ummi tayi saurin fitowa ta tunkaro su, "lafiya dai Fauziyya? Ina
Hafsatun? Mai ya same ta?" Ta tambaya cikin kaguwa saboda Aina'u ne tayi azancin kiran su ta sanar da
su an kwantar da Reina a asibiti, amma dalilin hakan yayi mata nauyi ta sanar da su don haka ta bari idan
sun zo suji daga bakin ɗiyar su.

Matsawa Aina'u tayi Ummi ta maye gurbin ta, yayan su ma ya zauna ta ɗaya ɓangaren yana bubbuga
kafaɗan ta cikin sigar lallashi, amma har yanzu idanun ta suna kafe a gaba kaman bata san da zuwan su
ba.

Ummi ta riƙo hannun ta na dama cikin nata duka biyu tana murzawa a hankali.

"Fauzeen Ummi, faɗa min abinda ya faru kinji? Cuta ba mutuwa bace Allah zai ɗaga kafaɗun Hafsah"
Sai ta juyo a hankali tana duban ta. "Ummi, na shiga uku!" Daga nan hawaye ya ɓalle mata kaman
saukan ruwan sama, ta damƙo hijabin Ummin sannan ta cusa kanta a cikin jikin ta tana kukan da ya jawo
musu hankalin sauran majinyata.

Babu wanda bai kawo cewa mutuwa aka yi mata ba.

"Innalillahi wa inna ilaihirrajiun" shine abinda Ummi ta shiga nanata mata.

Da ƙyar ta samu ta kama maimaitawa cikin muryar kuka har muryar ta na shaƙewa.

"Kai danna min kiran Abban ku ya bar abinda yake yi yazo wannan lamarin babba ne" Ummi tace da
yayan su.

Ciro waya yayi daga aljihu zai kira shi Fauziyya tayi saurin miƙewa ta riƙe wayan "A'a, kada ka kira shi don
Allah. Yana sani zai faɗa ma Tahir kuma ban san da wani ido zan dube shi ba wallahi, Tahir zai iya raba ni
da yara na har abada ku rufa min asiri"

"Shikkenan ba za'a kira shi ba" ya sake mata wayar ganin yanda ta kiɗime.

"Ummi muje ciki sai in faɗa miki" ta fara ƙoƙarin tsayar da hawayen da bai ma san tana yi ba, zuba yake
kan yi abin shi.

Babu musu Ummin ta miƙe, itama ta ja hannun ta ciki, fauziyya ta gwada mata ɗakin da aka kwantar da
Reina suka shiga.

Tana kwance tana barci ga drip ɗin da aka ɗaura mata, sai bakin ta dake fashe da gefen fuskar ta da yayi
jaa wurin da Fauziyya ta mare ta.

"Mai ya same ta?" Ummi ta sake tambaya.


Sai da ta riƙi gadon duka biyu ta sauƙe duban ta ƙasa kafin tace "Ummi wani mugun ne yake son ƙarar da
rayuwar yarinyar nan tun bata fara shi ba. I think she's being molested"

"Ya rabbal alameen! Wa kenan? A ina? Yaushe?"

Ta ɗago tana girgiza kai don gani take yi kaman ummin ma ganin laifin ta take yi "wallahi ban sani ba
Ummi, ta ƙi faɗa firr, ni kuma bani zargin kowa."

Ganin kukan ta ya dawo sabo Ummi ta sake jawo ta waje don kada su tada Reina.

"Yanzu mai likitan yace"

"Ta kamu ne da UTI, infection ɗin mafitsara, sai kuma rashes da suka feso mata a wurin. Ummi shekarar
ta tara kacal fah!"

Salati Ummi ta sake yi, ba don itace ƙarfin guiwar Fauziyya ba da itama kukan zata yi.

Sun daɗe zaune a wurin kowa na saƙa da warwara a tashi zuciyar kafin Ummi tace "toh yanzu yaushe
zaki sanar da mahaifin ta? Don ya kamata ya shigo cikin lamarin nan a bincika"

Girgiza kai ta shiga yi "na san waye Tahir wallahi Ummi, musamman ma a kan Reina, kafin ya bincika sai
ya ɗauki matakin da dukkan mu ba zai yi mana daɗi ba, zai ɗaura min laifin abinda bani da masaniya a
kai daga baya ya zo yayi nadamar da bashi da amfani. Gwamma ni in bincika in kamo koma waye kafin
nan"

Tunanin ta lokacin da take gida abin ya fara, don haka Ummi bata tuhumi Fauziyya ba da tace bata da
masaniya a kai.
Haka suka yi ta jinyar Reina har na sati guda, sa'ar ta ɗaya Alhaji Tahir ya ɗaga dawowar shi kuma kaman
bayi cikin mutsuwar da zai fahimci komai ba lafiya ba, don idan ya buƙaci zantawa da yaran kullum da
uzurin da Fauziyya take bashi, Maama ma yanzu tana wurin Ummi, tsakanin Reina da Fauziyya kuma sai
kallo don har yanzu da take bin ta da lalama ta ƙi faɗa mata, gashi likita ya gargaɗe ta sosai a kan tsorata
ta idan ba so suke yi su suka mata panic attack ba domin tsoron shi yake saka ta suma.

A rana na shida Yaseer ya kawo Saudat asibitin a mashin ɗin abban shi, don haka suka shigo tare.

A sanadin shi ma Saudat ta san Reina bata da lafiya domin ta kwana biyu bata zuwa lesson kuma ya ji a
bakin sauran yaran wai ai Auntyn ta ne ta dawo. shine ya matsa mata ta kira Hajiya Fauziyyan ta
tambaya domin bayi son shi da kanshi ya tambayi Alhaji Tahir balle Hajiya Hauwa, Alhaji Salisu kuma tare
suka yi tafiya Abuja.

Bayan sun gaisa da Saudat tana tambayar ta Reina ko lafiya Yaseer yace bata zuwa lesson. Mamaki ya
kamata jin wai ana yi musu lesson ashe, Alhaji Tahir bai faɗa mata ba, kuma itama Reina bata fada ba
duk da ranar zuwa lesson ɗin bai zago ba wannan abin ya faru.

A nan ne take faɗa mata ai an kwantar da Ita ne a asibiti shine a yammacin ranar suka zo duba ta.

Tana zaune da kwanon abincin da take ta juyawa tana kallon shi, shikkenan Aunty kuma ta dawo za'a ci
gaba da bata abinda bata so.

"Kici abincin mana" Fauziyya ta ajiye plate ɗin apple da ta fere ta yanka mata a gefe.

Ɗagowa Reina tayi ta kalle ta kaman zata fasa ihu amma bata ce komai ba. "Yanzu ta rage tsalle-tsalle da
rawar kai ɗinnan da surutun banza har abin naso ya damu Fauziyya amma sai ta saka ma ranta zaman
asibitin ne bata so.

"Hafsatu na" ɗagowa tayi tana kallon Fauziyya dake mata dariyar karfin hali, ta cigaba da cewa "kina son
cake? Zan baki chocolate cake mai daɗin tsiya idan kika faɗa min waye yake taɓa ki a nan"
Tayi ƙoƙarin ɗaga skirt ɗin ta amma sai tayi saurin jan baya tana hawaye.

"Wallahi ba kowa Aunty, Allah ba kowa"

Ta gane wayo kawai take son mata, tana buɗe bakin ta shikkenan zata ɗauki wukar da ta yanka apple
ɗinnan ta yanka ta.

Suna cikin haka aka kwanƙwasa kofar tare da turo shi, Saudat ta shigo ɗauke da sallama a baki.

Sauƙe ajiyar zuciya Fauziyya tayi ta aro karamin murmushi ta yafa domin ɓoye damuwar ta, kafin tayi
mata iso zuwa ciki.

itama sai lokacin ta juya tace ma Yaseer ya shigo ciki.

Sallama yayi da budaɗɗiyar murya ya ƙaraso ciki.

Reina na ganin shi tsugul ta mike zaune.

"Yaya Yaseer!!" Ta kira cikin muryar farin ciki haɗe da mamaki.

Har ƙasa ya kai a gaban Hajiya Fauziyya ya kwashi gaisuwa, saida ta amsa kafin ya ƙarasa gaban gadon
Reina yana mata yaya jiki.

"Yaya Yaseer kayi haƙuri gobe zan zo class ka ji?"

Idanun Fauziyya na kafe a kan su.

"Ba komai Ki bari sai kin samu lafiya"


Da toh kawai ta amsa sannan ta matsa mishi a gadon wai ya zauna.

Cigaba da tsayuwa kawai yayi yana rejecting kiran da Meesha ta dame shi da shi, saboda kawai ya dawo
gida ba tare da sanin ta ba.

Wannan ko uwar da ta haife shi albarka.

"Yaya mai jikin?" Saudat ta bukata.

"Ahh jiki da sauki alhamdulillah" Fauziyya ta amsa

"Allah ya ƙara sauƙi, amma mai yake damun ta?"

Ta so ta ɓoye mata amma sai take ganin kaman Saudat ɗin zata kawo mata mafita tunda ita da Ummi
duk sun gagara amma gashi tana sakewa da ɗan ta.

Bata son yin maganar a gaban ta don haka ta buƙaci su fita waje, amma bata iya barin Reina da Yaseer su
kaɗai ba saida ta tura musu Aina'u.

Aina'u ta shiga ta same shi zaune a bakin gadon yana fuskantar Reina. Ga abincin da ake buga daabi da
ita kafin ta ci yana ciyar da ita cikin sauƙi.

Reina ta so ta faɗa mishi abinda yake faruwa amma tsoron idon Aina'u ya hana ta kada taje ta faɗa ma
aunty, haka suka ƙarasa cin abincin cikin shiru.

.......

Fitowa yayi daga wanka sanye da jallabiya yana tsane kan shi da hand towel.

"Ai na ɗauka zan samu har kinyi barci tunda jirgin mun yayi dare sosai"
Rabon da ta samu barci cikin nutsuwa da walwala tun ranar da abin nan ya faru, balle yanzu da ya dawo,
tana da tabbacin ba zata iya cigaba da ɓoyewa na tsawon lokaci ba, dole zai sani amma sai ta gama
bincike tukunna.

Fauziyya dake kintsa ɗan shirgin da ya dawo da su don kawai ta guje ma idanun shi ta fitar da sautin
murmushi kawai.

tana tsoron ya gano abinda take boyewa a yanayin ta wanda shima a nashi ɓangaren haka ne, yana
tsoron ta gane abinda yake ɓoyewa a yanayin shi, amma tashi addu'ar bata karbu ba saboda hannun ta
ne ya sauka kan wata ƴar takarda na hotel dake ɗauke da sunan wani hotel a Germany.

Ta ɗago tana kallon shi da takardar a hannun ta.

Shi da yace mata Abuja zai je?

"Ba abinda kike tunani bane wallahi"

"Zan so ƙarin bayani"

Ya karaso ya karbi takardan da yayi mamakin yanda aka yi bai jefar da shi tun a can ba gashi yanzu dole
ya bayyana mata abinda yake faruwa don kar ta zarge shi.

Hannun ta ya riƙo suka zauna a bakin gadon suna fuskantar juna kafin ya dube ta da damuwar da ya
bayyana a kan fuskar shi.

"Ina cikin babban matsala ne Fauzah, bani son ɗaga miki hankali ya saka tun da ban sanar da ke ba"
"Subhanallahi, wani irin matsala kenan wannan?"

Numfashi ya ja ya furzar kafin yace "kuɗin kamfani na ɗauka na shiga wani project da shi a yanzu kuma
project ɗin yana ƙoƙarin crashing. Shine muka tafi da yaya Salisu daman shine ya gabatar min da project
ɗin, ganin na shiga daga farko na ci riba ya saka ni sake komawa, kuma a tsawon sati ukun nan ba
ƙaramin yawo mukayi ba Amma wallahi babu haske Fauzah "

"Amma har nawa ne kuɗin da zai ɗaga maka hankali har haka? Ba sai ka biya su ba tunda kullum dai
kasuwa daɗa bunƙasa take yi alhamdulillah"

Wani irin murmushi mai ciwo yayi yace "Hmm fiye da Biliyan ɗari biyu..."

"La haula wala ƙuwwata illa billah!" Ta rufe bakin ta da hannun ta jin yanda muryar ta ya tashi saboda
kaɗuwa.

"Wallahi. Yanzu kawai ki taya ni da addu'a Allah ya fitar da mu daga cikin wannan tsaka mai wuya. Amma
in sha Allah Reina sai ta gaji TK kingdom don haka yanzu niman taimako zamu bazama wurin malamai ko
Allah zai saka a dace"

Ambatan sunan Reina da yayi kawai sai da ya saka hanjin cikin ta kaɗawa, abin cikin ta ma sai da ya juya
babu shiri, ta fitar da ɗan ƙara ya shiga mata sannu.

Zuwa Safiya ta daɗa rasa nutsuwar ta tun Alhaji Tahir na tunanin abinda ya dame shi ne ya dame ta har
ya fahimci yafi hakan.

Ga sarauniyar shi tayi wani sanyi kaman ba ita ba.

"Fauzah, ke da yaran nan ina duk lafiya kuke da bana nan? Babu wani abinda ya faru ina?"
Kirjin ta ya buga dududum amma tayi yaƙin ƙaƙalo murmushi.

"A'a mai ka gani?"

"Don Allah idan akwai wani abun kada ki ɓoye min, zan saurare ki da zuciya ɗaya koma menene kaman
yanda kika min uzuri nima zan yi miki.

Kaman yanda Reina tayi tunanin wayo Aunty take mata haka itama tayi tunanin Tahir ya faɗi hakan ne
kawai a fatar baki.

Kaman yanda Reina taji tsoron hukuncin da zai biyo baya haka itama.

don haka sai ta girgiza masa kai.

"Wallahi babu komai!"

.......

"Yauwa Umma an sallami Reina daga asibiti ne?" Yaseer ya tambaya yana taje gashin kanshi da bayi
gajiya, a rana sai dai idan ba zai saka ƙafar shi a waje ba amma sai ya taje kai ko mace albarka.

"Eh, ai tun washe garin zuwan mu aka sallame su, kuma uwan tace ta warware sosai"

"Toh Allah ya ƙara sauƙi"

"Amma Yaseer kai babu wanda ka lura yana ruɗan yarinyar nan a gidan aikin ka? Ko da wayo ko da
razanarwa?"

Sauƙe comb din yayi ya juyo yana dubanta "bannn gane ba."
Bayanin abinda Hajiya Fauziyya ta sanar da ita tayi mishi sai kawai ya tsaya yana kallon ta kaman mutum
mutumi, zuciyar shi ke bugawa a cikin kunnuwan shi, ya kasa gaskata abinda yake ji daga bakin wanda ya
san ba zata masa karya ba.

Haka har ya ƙarasa shiri ya tafi gidan Alhaji Salisu jiki babu ƙwari.

Sai ya tsaya a filin gidan yana karewa masu hada-hada a cikin ta kallo. Toh waye? A ina? Tun yaushe?.

Juyowa yayi idanun shi suka shiga cikin na Jamal dake fitowa riƙe da littafi idanun shi sun ƙanƙance
alamun yanzu ya farka daga barci yana tafe yana tsaki.

Wuce Yaseer din yayi yana jan wani dogon tsakin don har yanzu bai fasa mishi ɗanyen kai ba, shi kuma
Yaseer yabi bayan shi da kallo ƙwaƙwalwar shi tana taryo mishi kusancin Jamal da Reina, alaƙar su da
kuma kusanci na musamman da ya lura akwai a tsakanin su a dan zuwan shi gidan.

Ya ga abubuwa da yawa da a da yayi ƙoƙarin kawar da su daga cikin ran shi da tunanin sharrin zuciya ne
kawai yake son raya mishi wani abun. Ga irin sunan da yake mata amfani da shi da kuma wasu
maganganu marasa ma'ana da wani lokacin idan ya faɗa mata sai Yaseer ya dago ya dube shi sai ya fara
kame-kame da bayanin da shi bai tambaye shi ba.

Yana da yakinin Jamal ne, abun da ya rage a yanzu shine tabbatarwa.

Ƙoƙarin jan ƙafar shi yayi ya ƙarasa suka yi karatun sama-sama, Jamal dai duk a tsarge yake da kallon da
Yaseer din ya ƙure shi da shi.

Har lokacin na su Reina yayi sauran yaran suka fito ita bata zo ba.
Yau kam ya damu, har ya fara tunanin ko dai ya koma zuwa nasu gidan ne yana mata a can tunda a nan
ɗin cutar da ita ake yi?

Bai ida tunani ba hancin motar gidan su ya danno kai cikin gidan.

Tsayawa yayi yana kallo ta fito daga cikin shi ta nufo su a ɗan hanzarce, sai ɗaya ɓangaren shima ya buɗe
Hajiya Fauziyya ta fito....

*Saliha Ahmad Na'ibi (Seemahwrites ✨)*

*REINA 💍*

33......Sauran yaran ma suka miƙe ta karaso suka rungume juna suna tambayar ta mai yake hana ta
zuwa, domin suma sunyi kewar ta.

Duk cikin su babu wanda ya san tayi rashin lafiya don ko iyayen su ma basu sani ba, maganar na shiga
kunnen su toh ya shiga kunnen Alhaji Tahir.

Rusunawa tayi har ƙasa ta gaida Yaseer, ya amsa idanun shi yana kan aunty dake takowa wurin a hankali
nata idanun a kan Reina, al'ajabi sosai yake kama ta na yanda Reina take behaving sosai a gaban Yaseer,
abinda ko iyayen ta basu sami darajar hakan ba.

Toh ko tsoron shi da take yi yana alaƙa da abinda ya faru da ita?.

Ta zurfafa cikin tunani sai ganin Yaseer tayi durƙushe a gaban ta a lokacin da zata taka matakala na
ƙarshe da zai sada ta da cikin wurin.

Takalman shi da na yaran ya matsar mata a hanya sannan ya miƙe da wadataccen murmushi a kan fuskar
shi yana mata iso.
"Bismillah Aunty, sannu da zuwa" sai kuma ta samu kanta da maida masa murmushin.

A yau bata shafa kan shi ba, Saboda wannan karon ba ƙaramin yaro ɗan shekara 12 bane a gaban ta,
wannan Yaseer ɗin har ya fita tsayi sosai.

Ta ƙarasa shiga tana tura ciki, yayi saurin jawo mata kujera ya riƙe shi da kyau har saida ta zauna tana
sakin ƙaramin nishi kafin ya sake.

ya dawo gabanta ya rusuna irin wanda Reina tayi a gaban shi da zata gaida shi kana shima ya gaida ta.

Ba zallan shekaru ya ƙara da tsayin ƙafa ba, harda kyawawan dabi'u da nagarta, shin tayi masa adalci
idan ta zarge shi?.

Amma shi mugu bayi da kama.

Kawar da dubanta tayi daga kallon da take mishi, gashi ya koma gefe ya tsaya sai fara'a yake yi ko zama
ya gagara.

ta maida hankalin ta tana duba tsaruwan wurin domin Alhaji Tahir ba ƙaramin shirya musu yayi ba, an
saka musu kayan karatun yara sosai a wurin, ga calenders da aka maƙala na multiplication table,
phonetics da sauran su, an maida shi kaman wani classroom.

Ganin shirun yayi yawa ya umarce su da su fara bitan AlQur'ani, Reina ta miƙe ta ɗauko ɗaya daga cikin
wa'inda ke ajiye sannan suka fara ƙira'a cikin kananun muryoyin su masu daɗi, Hajiya Fauziyya ta ka kasa
kunne tana sauraro.

"Aunty bari na kawo miki ruwa" yace da nufin shiga cikin gidan ya karɓo mata.

Saurin girgiza hannu tayi duk daɗi ya cika ta jin yanda muryar Reina har yafi na kowa tashi "A'a barshi,
yanzu zan shiga cikin kawai nace bari na tsaya duba ku ne"
Sai ya ƙara murmushi Aunty akwai sanin ya kamata.

"Allah sarki"

"Toh yaya karatun? bata wani rashin jin dai ko?"

Yayi saurin girgiza kai "A'a wallahi, da sauƙi" gaba ɗaya ma ya rasa a ina zai saka kan shi, kwarjinin da
Hajiya Fauziyya take mishi ko ita bata san tana da shi ba.

"Toh alhamdulillah, idan tana wani abun ma don Allah kada ka ɓoye min, zan hukunta ta yanda ya
kamata"

Yayi tunanin barin abinda yake zargi a zuciyar shi har sai ya tabbatar amma sai yake ga kaman hakan bai
dace ba, gwara ko ita ya faɗa mata tun da duk yanda ya damu da Reina yana da tabbacin mahaiyarta ta
fishi damuwa da ita, idan ma binciken ne zata fishi tsaurarawa gashi bayi da cikakken iko a gidan.

Ɗan matsowa kusa da ita yayi yace "Aunty daman ina son mu ɗan yi wata magana idan babu damuwa"

Sosai ta bashi hankalin ta tare da gyaɗa masa kai "go ahead, ina sauraron ka" fatan ta ya kasance abinda
take son ji shi yake son faɗa.

"Idan babu damuwa mu ɗan fita daga waje"

Wannan karon bata yi nauyin jiki ba ta miƙe ta fara gaba yana biye da ita a baya.

Gefe kaɗan suka koma tace "uhmm hmm, ina sauraron ka"

Sai yanzu kuma yaji maganar yayi mishi nauyi, ya haɗiyi miyau tare da ɗan ciza bakin shi.
"Kada kaji komai, koma menene idan ka faɗa min taimako na kayi. A kan Hafsatu ne ko?"

Ya gyaɗa kai a hankali sai ga ƙwalla sun fara taruwa a idanun ta, tana da tabbacin duk abinda zai fito
daga bakin shi a yanzu sai ya tarwatsa zuciyar ta.

Saida ya sake haɗiyan miyau kafin ya fara magana "Zargi ne kawai, amma ina ganin kaman...."

"Ah ah, Fauziyya barka da zuwa. Shine kuma kika tsaya a waje?"

Hajiya Hauwa ta tunkaro su tana washe haƙwaran dole ganin hajiya Fauziyya a gidan su da sammako
haka, ko lura da fitowar ta ma basu yi ba.

Sakwan biyar kawai, ji suka yi inama ace ta kara sakwan biyar kafin ta fito?!.

jinkirin sakwan biyar ya isheta taji komai ta yanke hukunci.

Jikirin sakwan biyar ya isa ya sauya rubutacciyar ƙaddara.

Jinkirin sakwan biyar ya isa ya tseratar da rayuka guda biyar.

"Zan jira idan kin fito" yace tare da juyawa ya koma wurin yaran tabi bayan shi da kallo.

Yanzu da anjima duk abu ɗaya ne. Ta ayyana a ranta sannan tayi ƙoƙarin sanya murmushin dole itama
ma Hajiya Hauwa suka wuce ciki a tare.
Zama yayi ya fara musu ƙari, suka koma gefe suka ci gaba da bita. zai yi amfani da wannan daman ya
tabbatar da zargin shi yanda zai faɗa ma Aunty abinda yake da tabbaci a kai.

Kiran Reina yayi ta ƙaraso gaban shi.

Hankalin shi a kan text book ɗin da yake koya musu saboda kada kallon cikin idanun shi ya sanya ta
tsorata ta gagara fayyace mishi komai.

"Yaya jikin ki? Yayi sauƙi?" Ya tambaye ta.

"Eh, yanzu bani jin ciwo sosai"

"Masha Allah. Ƙurajen fa? Suma sun warke?" Yayi mata tambayar yanda zata fahimci ya riga da yasan
komai ta saki jiki ta sanar dashi abinda yake son sani.

Da "Eh" kawai ta amsa lokaci ɗaya jikin ta na yin sanyi.

"Amma me ya saka miki ƙurajen?"

Yatsan ta takai baki ta saka farce a baki tana ci, alamun rashin gaskiya sun gama bayyana a tattare da ita.
"Haka kawai fa ya fito"

"A'a Reina, ƙuraje basu fitowa mutum haka kawai har su kwantar dashi a asibiti, Ko wasan da kuke yi da
Jamal ne ya saka miki?"

Suman tsaye tayi a wurin, ga idanun ta da suka firfito saboda tsoro kaman kace kyat ta zura a guje. Sai a
lokacin ya ɗago ya kalleta, suka yi ido huɗu, kuma bai taɓa ganin tashin hankali zunzurutun shi a cikin
idanun ta ba kaman na yau.
Daman ya sani! Jamal ne!.

Ba ƙaramin yaƙi da zuciyar shi yayi ba ya sanya murmushi a kan fuskar shi domin tayi tunanin abun ba
komai bane ya samu ya sha cikin ta.

Yaci gaba da cewa "ai ina ji wataran yana ce miki zaku yi wasa, shine ko?"

Sai kawai ta fashe da kuka tare da haɗe hannuwan ta cikin sigar roƙo.

"Don Allah yaya Yaseer kada ka faɗawa Aunty, wallahi yanka ni zata yi"

Lokaci ɗaya tafasan da zuciyar shi yake yi ya saka zufa fara yanko mishi duk da iska mai sanyi da yake
kaɗawa. Yana jin yanda tuƙuƙin baƙin ciki ya maƙure shi a wuya. Ji yake yi kaman ya shiga cikin gidan ya
fito da ɗan akuyan yayi masa dukan shan gishiri.

Ganin su Zaheera suna wurin gashi ta rikice yasa yace "shikkenan, je kici gaba da karatun ki, ba zan faɗa
mata ba"

Bata yarda ba tace "kayi alƙawari?"

Irin wannan alƙawarin bayi da tasiri don haka yace "nayi alƙawari"

"Toh kace wallahi"

Sai a yanzu ya bari ɓacin ran shi yazo cikin idanun shi ya watsa mata mugun kallon da ya sanya ta saurin
juyawa ta koma ta zauna amma gabaki ɗaya ta rasa nutsuwar ta ko zama mai kyau ta gagara.
Shima kan shi ya rike yana jin yanda yake tsananin sara masa. Jamal yayi illa ma rayuwar Reina amma
yana tsoron sanin girman shi, tun yaushe yake ta cutar ta babu wanda ya sani?. Yana taraddadin yanda
mahaifiyar ta zata ɗauki abun.

"Yaya Yaseer"

Ya ɗago rinannun idanun shi ya zuba mata, "don Allah kayi haƙuri"

"Idan na haƙura zaki faɗa min abinda yake miki?" Da kyar ya samu muryar shi yake fitowa.

"Ba zaka duke ni ba ina?"

"Kin san kinyi ba daidai ba kenan"

"Wallahi ba zan sake ba, kaji na rantse. Idan na sake Allah ya ƙona ni a..."

Yayi saurin saka yatsa ya ɗane mata baki.

"Shikkenan, ba zan dake ki ba, labari kawai zamu yi.

"Toh I want to ease myself"

Shi a yanzu ko cikin gidan ma bayi son ta shiga, shima daga yau ba zai sake taka kafar shi a nan ba ko
miliyan nawa za'a bashi, amma ganin a matse take tana haɗe cinyoyi yace "okay, na baki 5 minutes ki
dawo"

Da sauri ta bar wurin yayi mata rakiyan idanu.


Babban parlour babu kowa don haka ta wuce toilet ɗin ɗakin baƙi kasancewar shi mafi kusa.

Minti biyar, goma, har sha biyar Reina bata dawo ba.

Miƙewa yayi kai tsaye ya shiga gidan, hankalin shi bai kwanta ba duk da mahaifiyar ta tana cikin gidan,
ko da ɗinma ai masu gidan suna nan amma ake cutar da ita.

Har yanzu parlorn babu kowa, sai ya rasa a ina zai fara duba ta ɗaya. Ƙofar ɗakin Jamal yaje yana
kwanƙwasa shiru. ya tura ƙofar ya buɗe shi amma babu kowa, sai wani wari da yake fitowa daga ɗakin
ga tarkace a saman gadon shi, kayan shi kuma barbaje a ƙasa.

Har zai fita ya hango kwalba daga gefen gadon shi don haka ya ƙarasa ciki yaje ya ɗauki kwalban, bai kai
ga karanta abinda ke jiki ba warin abinda aka sha a cikin kwalban ya daki hancin shi. Yayi saurin ajiyewa
yana riƙe hanci cikin kaɗuwa, bai taɓa ganin giya zahiril ayni ba amma yana da tabbacin wannan shine,
Jamal har giya yake sha kuma a cikin gidan uban shi.

Ba zai iya ƙara second ɗaya cikin ɗakin ba don haka ya fito tare da rufo ƙofan. Ko babu komai yanzu
hankalin shi ya ɗan kwanta ya san cewa Reina bata tare da Jamal.

Neman wuri yayi ya zauna yana jiran yaga giftawar wanda zai tambaye su inda ta shiga.

Ko kuma ya kira umman shi ta kira Hajiya Fauziyya ne ta tambaye ta idan suna tare? Domin ya gagara
samun nutsuwa har yanzu.

Ciro wayan yayi daga aljihu zai danna kiran Saudat. Razanannen ƙaran da Reina ta sake ya karaɗe ilahirin
gidan.

Miƙewa yayi tare da sakin wayan a ƙasa ya ɗiba a guje zuwa direction ɗin da ya jiyo sautin.
Ya bankaɗe ƙofar ɗakin da yake da yaƙinin daga wurin saurin ya fito, idanun shi basu sauƙa a kan kowa
ba sai Reina dake zube a kan gadon ɗakin idanun ta a rufe bata motsi, sai kuma Jamal dake tsaye da
saɓulallen wando yana ƙoƙarin gyarawa cikin tashin hankali.

"Wallahi ban mata komai ba! Duba ka gani ma"

Hannu Yaseer ya dunƙule ya fara kai mishi naushi ba tare da ya shirya ba, ya kuwa same shi a fuska babu
ɓata lokaci jamal dake cikin maye ya zube a ƙasa.

Sai yanzu ya fara dawowa cikin hayyacin shi ya rarrafa zai bar ɗakin Yaseer ya ɗaga ƙafa zai tokare shi sai
Jamal ya riƙe kafar ya tura shi baya da iya sauran ƙarfin da ya rage mishi Yaseer ya bugu da bango
sannan Jamal ya mike yana tangaɗi ya bar ɗakin kafin Yaseer ya samu kan shi.

Yayi niyyar bin shi a baya ya ci gaba da dukan shi, yayi niyyar ya kama shi tsamo-tsamo ya tona mishi
asiri a idon iyayen shi da kuma mahaifiyar ta, amma ba zai iya tafiya ya bar Reina a cikin wannan yanayin
ba, don haka sai ya dawo ya tsuguna a gaban gadon yana girgiza ta shiru.

Fuskar ta ya shiga bubbugawa yana kiran sunan ta da ƙarfi ko zata dawo cikin hayyacin ta, ya miƙe da
nufin shiga toilet ya ɗibo ruwa ya shafa mata ta farfaɗo.

Juyawar da zai yi sai yayi gamo da katar.

Alhaji Tahir tsaye a bayan shi.

*Seemahwrites ✨*

*REINA 💍*
34.....koda ace yana fuskantar ƙalubale a kasuwanci, yanzu ya samu ya haɗa kan iyalan shi zai samu sauƙi
ta wani wurin.

"Likita babu matsala dai ko?" Alhaji Tahir ya tambaya ganin a yau ɗin sun ɗan riƙe shi ya daɗe. Shi bayi
da lokacin zuwa general checkup ma banda matsawar Hajiya Fauziyya, tun wata biyu da suka wuce ya
kamata ace ya zo.

"Eh toh, BP ɗin ka ne ya ɗan haura gaskiya, sikarin jinin ka ma ya faɗi sosai, amma idan sauran
sakamakon sun fito zan kawo maka gida a duba"

"Toh shikkenan, ni zan iya tafiya kenan"

"Zaka iya tafiya, amma Alhaji ka samawa jikin ka hutu ko yaya ne idan ba so kake yi ya baka kunya ba,
zuciyar ka ma haka, sannan ana samun abincin da ya kamata a kan lokaci. Muna rawa da bazar ku Alhaji
muna so kuyi ƙargo" ya karashe da raha Alhaji Tahir ya ɗan yi murmushin yaƙe sannan ya miƙe a kan
dugadugan sa da suka yi masa nauyi, yayi sallama wa doctor.

"Shikkenan sai nazo Alhaji, a ƙara gaida min ƴata da jiki"

Kallon rashin fahimta yayi masa. "Waye kuma babu lafiya a cikin su?"

"Ah ah, baka sani ba? Hafsatu ce har saida aka yi admitting ɗinta"

Babu ɓata lokaci ya koma ya zauna doctor ya shiga masa bayanin abinda ya samu Reina.
Kafin ya gama Alhaji Tahir ya rasa ina kan shi yake.

Shine kuma Fauziyya bata sanar dashi ba, wannan abu mai girma haka.

Miƙewa yayi a fusace zai bar ofishin, jirin da ya ɗibe shi ya saka shi ƙoƙarin faduwa, da azama doctor ya
riƙo shi ya saka shi komawa ya zauna dole.

Bai samu barin asibitin ba saida ya sha ruwa laida guda shima don ya samu ƙarfin zuwa ya sauke ma
Fauziyya buhun bala'i ne ya saka shi ya jure ya jira.

Daga Asibitin ya ɗauki hanyar gidan Alhaji Salisu, ba zai iya jira sai ta dawo gida ba.

Wurin karatun su Reina ya fara dubawa, bata nan haka ma malamin su, ya juya zai nufi cikin gidan
lokacin da ihun ta ya shiga cikin kunnen shi.

Tsoro ya kama shi, kada ace yau ma Fauziyya ƙoƙarin kashe masa ita take yi.

Jamal da ya fito a guje, ganin su Hajiya Fauziyya da mahaifiyar shi suna fitowa ya shige ɗaki mafi kusa
dashi ya rufo ƙofa.

Zarah dake kwance a gadon ta tana kallon series ta miƙe a firgice zata yi magana yayi saurin ƙarasawa ya
rufe mata baki ga idon shi ɗaya zuwa kumatun shi da ya tara jini.

A hanya Hajiya Fauziyya suka yi kiciɓus da Alhaji Tahir amma dake ba ita bace damuwar shi a lokacin ya
tunkari ƙofar da bai gama rufuwa ba sanadin kiran sunan Reina da yaji ana yi a ɗakin.
Ya ƙarasa ya wangale ƙofar, a nan yayi mummunan ganin da ya daskarar dashi a wurin ya gagara motsa
koda ɗan yatsan shi.

Ƴar shi ce kwance magashiyyan rigan jikin ta ya ɗage zuwa ƙirji sannan babu wando a jikin ta sai kuma
wanda ya gani a wurin yana taɓa ta.

Maganar da likita ya faɗa mishi ya shiga mishi yawo a kunne lokacin da Yaseer ya miƙe da niyyar guduwa
ko ɓuya yana da yaƙinin ɗayan biyun su tunda ya hallaka mishi yarinya.

cikin rashin Sa'a suka yi ido huɗu.

Daman wannan la'anannen yaron cutarwar da yake mishi kenan? Yana yi kuma yana biyan shi?.

Tsoro zahirin shi ya bayyana a cikin idanun Yaseer kaman ba shi bane ranar da yazo yana roƙon shi
alfarma a darajar Hafsatun yake masa kallon banza, ashe kashe masa ita zai yi.

Yaseer sai ya rasa da wani irin kalma ma zaiyi amfani ya kare kan shi.

Ya taka sawun ɓarawo, Allah kaɗai zai iya fidda shi.

Gwada Reina yayi yace "bata numfashi ne...." kamata yayi ya damu da kan shi ya nemi hanyar tsira.

"Ku taimaka mata Alhaji"

Su Hajiya Fauziyya da sauran mutanen gidan sun ƙaraso don ganin mai yake faruwa. Dukan su turus suka
yi a bayan Alhaji Tahir banda Hajiya Fauziyya da ta fashe da kuka haɗe da salati, ta bankaɗe Alhaji Tahir a
kan hanya tayi kan reina ta shiga jijjigawa.

Sai Yaseer ma ya juya zai shiga taya ta lokaci ɗaya yaji an finciko shi, bai sake ganin komai ba bayan
koriyar wutar da ta ɗauke ganin shi baki ɗaya sai duka kawai da ya shiga samun shi ta ko ina, hannun shi
kawai ya ɗaura a ka yana tare na wurin tare da yin baya-baya yana ƙoƙarin faɗawa a gadon shima, Alhaji
Tahir ya fisgo shi ya watsa shi a wajen ɗakin kaman kayan wanki sannan ya rufa mishi baya, yana ƙwala
kiran masu gadi.

Suna isowa babu tambayan ba'asi suka rufu a kan Yaseer da duka tun yana daurewa har ya fara ihu da
ƙoƙarin tserewa amma sun fi ƙarfin shi.

Da cikin jikin ta haka Hajiya Fauziyya ta cicciɓo Reina bayan ta suturta mata jikin ta tayi hanyar waje da
ita, bata lura da hajiya Hauwa bata nan ba a lokacin, hakama Alhaji Tahir ko lura da su bai yi ba burin sa
su kashe Yaseer kawai.

Sai da ta ƙarasa wurin mota drivern Alhaji Tahir ya ƙaraso da nufin karɓa mata ita tayi saurin ja da baya.

"Kada ka taɓa min ita! Kada ka kuskura ka taɓa min ita!!"

Komawa yayi ya buɗe mata bayan motan suka shiga suka bar gidan zuwa asibiti.

Su Alhaji Tahir ma sai da suka tabbatar sunyi ma Yaseer jina-jina bayi ko ƙwaƙƙwaran motsi kafin suka
miƙa shi ma folisawan dake jira a waje hankalin su a kwance, sun san ko gawar shi aka kawo musu za'a
biya su kuɗin da zasu binne shi babu wani matsala.

Haka suka tasa ƙeyar shi babu tausayi babu imani suka kai shi station suka rufe shi a cell.

Likitoci suka rufu a kan Reina, zuwa lokacin da Alhaji Tahir ya isa har ta farfaɗo anyi mata allurar bacci,
Amma sai da suka saka mata oxygen don ko da ta farka numfashin ta bai daidaita ba.

Saidai kuma naƙuda ne ya taso ma Hajiya Fauziyya gadan-gadan, ko da ta iso ita ta shigo da Reina har
emergency, taƙi yarda kowa ya karbe ta, tana ajiye ta ta zube itama aka rufu ceto rayuwar ta.

Zafi ya haɗu ma Alhaji Tahir goma da ashirin sai can jimawa Kafin Alhaji Salisu da Hajiya Hauwa suka
ƙaraso.
Abinda ya faru kuwa shine, Hajiya Hauwa da ta ga giftawar Jamal zuwa ɗakin Zahra da suka fito, sai ta
bari har sai da hankalin kowa ya karkata kan Yaseer da Reina kafin ta saɓule jiki taje ta buga musu ƙofa.

Zahra dake a tsorace tayi yunƙurin buɗe kofar Jamal ya hana ta, har saida Hajiya Hauwa tayi magana ta
umarce su su buɗe kafin ya barta.

Itama tana shiga ta turo zahran waje kana ta sake sakawa ƙofar key ta tunkari Jamal da shima ya miƙe ya
nufo ta jikin shi na kyarma.

"Wallahi Umma ban yi mata komai ba Allah" ɗauke shi da gigitaccen mari tayi, zai kai ƙasa ta riƙo shi ta
sake kai masa wani.

"Kai bunsuru ne?! Ba nace ka fita a harƙan yarinyar nan ba?! Sai ka jawo mana bala'i ko?!"

"Wallahi Umma ban yi mata komai ba." Kuka yake yi wiwi.

Yaci gaba da cewa

"Tsorata ta kawai nake son yi saboda ta fara fallasa ni ma wancan jakin yaron, na gwada mata zanyi
mata mai zafin shine kawai ta sume min shi kuma sai gashi ya shigo"

Wani ɓari na hankalin ta taji ya kwanta, tana da tabbacin Hajiya Fauziyya bata san da zancen ba har
yanzu balle Alhaji Tahir, kiran Alhaji Salisu ta fara yi yazo su san na yi kana ta umarce jamal da ya zauna a
ɗakin kada ya fito har sai ita ta dawo ta fito dashi da kanta, daga ƙarshe ma kawai sai ta cire key ɗin ta
rufe shi ta waje, hankalin ta zai fi kwanciya.

Lokacin kowa ya watse sai yara da suka haɗa kai suna kuka a parlour da kuma jinin Yaseer da ya ɓata
tiles inda suka buge shi.
Babu daɗewa Alhaji Salisu ya ƙaraso, bata bar shi ya fito daga mota ba ta shiga suka nufi asibiti a hanya
tayi mishi bayanin komai kuma hankalin shi ba ƙaramin tashi yayi ba saboda shi bayi da masaniya kwata-
kwata, yayi alƙawari Hajiya Hauwa ta kuskura ita da ɗan ta suka jawo masa matsala a business ɗin shi da
Tahir itama ba zata tsira ba, sai yaga bayan ta da duk dangin ta.

Likitoci sun tabbatar da Jamal bai yi nasarar cutar da Reina ba, yayi ƙoƙarin shigar ta da ƙarfi amma
suman da tayi shi ya ceceta, amma labarin da ya samu na Abinda ya faru ya saka shi ya ɗau alwashin ko
duniya zata tashi sai ya rufe Yaseer, Alhaji Salisu na daga gefe yana daɗa masa famfo domin daga an rufe
shi shikkenan asirin su ya rufu.

Hajiya Fauziyya har dare ya raba suna abu ɗaya, ga jinin ta yayi mummunan hawa, tsoron buɗe ta likitoci
suke ji domin za'a iya ɗaya babu idan ba duka biyu ba.

Karshe sai da suka gayyato wani babban likita yazo daga Abuja kafin suka shiga da ita tiyata.

......

Kasancewar a weekends kafin maghriba ko bayan ta Yaseer yake dawowa gida ya saka hankalin Saudat
tashi matuƙa.

Gashi bai kira ya faɗi uzurin shi ba don haka ta fara niman shi a waya sai dai kalma ɗaya matar cikin
na'urar take maimaita mata, 'the number you have dialled is switched off.'

Gashi Kamal ya tafi mata sari Jama'are da ganin gida sai yammacin Lahadi zai dawo.

Kiran shi tayi ta sanar dashi fa Yaseer bai dawo gida ba har yanzu kuma wayar shi a kashe. Yace ta
kwantar da hankalin ta wataƙil ya bi wani wurin ne kuma wayan ba caji, amma zuwa tara idan bai dawo
ba ta sanar da shi zai kira abokinsa ya tambaya.

Haka lokaci ya dinga tafiyar saiɓi bata kuma fasa kiran wayan Yaseer ba, tun takwas da rabi ta sake kiran
Kamal domin hankalin ta sam ya gagara kwanciya tunda bai taɓa irin hakan ba.
Kamal ya kira Muhammad ya tabbatar masa rabon shi da Yaseer tun safiyar juma'a kuma shikam ma
yana hostel amma zai binkica sauran course mates ɗin shi yaji.

Har goma da rabi ta wuce babu wani labari lokacin hankalin kowa a gidan ya gama tashi har na Kamal da
bayi nan. Kuma azancin kiran gidan Alhaji Salisu bai zo mishi ba sai daga baya.

Ƙarfe sha ɗaya da minti talatin da shida Saudat ta sake danƙara ma Kamal kira a karo na babu adadi.

Bai ɗauka ba har saida ya kusan tsinkewa saboda bai san me zai faɗa mata ba.

Masu gadin gidan Alhaji Salisu basu ɓoye mishi ba suka sanar dashi Yaseer yana police station Alhaji
Tahir ya saka an rufe shi a cell, amma ko suma basu san me yayi ba.

Ɗaukan kiran Saudat ɗin yayi kafin ya tsinke, ya daidaita muryar shi yace "Saudatu mun yi magana dashi
yana lafiya, wai assignment ɗin su ne a makarantar za'a karɓa da gaggawa shine ya tafi can don ya samu
ya ƙarasa nashi kuma wayan shi ba caji. Yanzu kiyi hakuri ki kwanta ki huta nima gobe da sassafe ina
hanya"

Ta yarda da abinda yace don haka ta samu nutsuwa tayi barci. Su kuwa a cikin daren goggo ta saka aka
ɗago wani maƙwafcin su direba suka kamo hanya.

.....

Tun kafin a fara ma Hajiya Fauziyya tiyata suka tabbatar da babu rai a jikin abun cikin ta daman bakwaini
ne kuma babu lafiya don haka babu yaƙini, amma duk yanda suka yi ƙoƙarin su ceto nata rayuwar abu ya
gagara.

~~~~~~~~~
Ga rayuka huɗu a cikin garari, wanne ne cikon na biyar?

*Saliha Ahmad Na'ibi (Seemahwrites ✨)*

*REINA 💍*
35......da ace a halin yanzu za'a samu wanda zai yi gigin yiwa Alhaji tambayar tsakanin Fauziyya da Reina
wa yafi so, to wannan mutumin ba zai bar ƙofar ɗakin tiyatar nan da ƙafafuwar sa ba.

Zama mai kyau ya gagare shi, yayi gaba yayi baya sai kuma ya sake gyara zama. Hannayen sa da ya
dunƙule a saman cinyoyin shi sai karkarwa suke, yana jin kaman ya ƙalubalanci ƙaddara; me yasa idan
zata zo ma ɗan adam sai ta taro muƙarraban ta? Ita kaɗai ma ai ta wadata ta danne mutum har sai ya ji
kaman numfashin sa zai ɗauke.

Idon shi ya ɗaga ya kalli mahaifiyar ta dake zaune da tasbhaha a hannu, bata fasa goge hawayen da ya
ɗauki awanni yana sintiri a kan fuskar ta da ɗan hankici ba. Wai itama kenan mai wasu yaran da yawa
kuma ga mahaifin su a tare da ita bai gaji da lallashi ba amma shi fa? Babu wani wuri da zai dafa ya ji
sanyi a halin yanzu.

"Tahir"

A hankali ya ɗago rinannun idanun shi ya zuba su ma Hajiya Hauwa.

Taci gaba da cewa "Bari naje na duba Reina ko ta farka"

Jinjina kai kawai yayi saboda shima yana so ya ji halin da take ciki. Ita kuwa a nata bangaren tsoron Reina
ta farka ta faɗa ma wani ainihin abinda ya faru take yi, idan hakan ya faru komai ya lalace.

Gwanda taje ta gargaɗe ta, domin a halin yanzu ƙoƙarin nima wa Jamal visa aka shiga yi faka-faka, koda
ace ba na ƙasar da suka so ya tafi ɗin ba idan an samu student visa ko na Sudan ne sai ya tafi tunda shi
ya jawo ma kan shi.
Murɗa ƙofar VIP room ɗin tayi ta shiga.

Reina na kwance har yanzu da oxygen mask a kan fuskar ta. Hajiya hauwa ba zata iya jira sai ta farka da
kanta ba don haka ta karasa gaban gadon ta jawo kujera ta zauna ta shiga bubbugata ta tashi.

Da ƙyar ta iya buɗe nannauyan idanun ta, tabi ta lumshe su. cikin muryar kukar da ta suma da shi tace
"yaya Jamal... ka yi haƙuri bana so.."

Zata cigaba da kukan Hajiya Hauwa ta miƙe tsaye ta miƙar da ita ta zaunar, tare da cire mata oxygen
mask. lokaci ɗaya Reina ta watstsake ganin yanda ta zaro mata idanu kaman zata ɗauki ran ta.

"Umman Jamal, kinga shine yake cire min wand..."

Bata san lokacin da ta shaƙo wuyar ta ba, tare da ɗaura yatsar ta a saman baki alamun tayi shiru.

"Ba yace idan kika faɗa zaki mutu ba? Kin ɗauka ƙarya ne?"

Idanun Reina zuru-zuru ta shiga girgiza kai da ƙyar tana ƙaƙari, ganin haka Hajiya Hauwa ta sake ta.

"Duk wanda kika faɗa mishi abinda yake miki shima sai ya mutu. Kinga kin faɗa ma Yaseer shima gashi
can zai mutu, shima ya faɗa ma Auntyn ki itama mutuwa zata yi kema kuma zaki mutu"

Cikin hargitsi ta fashe da kuka tana riƙo hannun Hajiya Hauwa.

"Don Allah umman Jamal ki yi haƙuri kada su mutu, wallahi ba zan sake faɗawa kowa ba na rantse, idan
na sake faɗa Allah ya tsine m..."

Kukan ta ne yake ƙaruwa muryar ta na tashi don haka Hajiya Hauwa ta saka tafin hannunta ta rufe mata
baki gudun tonon asiri.
"Shikkenan na ji. Amma idan baki so su mutu sai kin faɗa ma kowa Yaseer ne yake miki kin ji?"

"Toh shi yaya Yaseer ɗin ba zai mutu ba idan na faɗa haka?"

"Eh, yanzu haka ma ya kusan mutuwa har da ciwon mutuwa a jikin shi amma idan kika ce haka ba zai
mutu ba"

"Toh zan faɗa"

Ta murmusa tare da sauƙe ajiyan zuciya sannan ta mayar mata da oxygen mask ɗin ta, ta kwantar da ita.
"Yauwa ƴar albarka, yanzu daddyn ki zai ci gaba da son ki, amma duk ranar da kika ce ma wani Jamal na
yi miki wani abu toh har daddyn ki da kowa sai ya mutu."

Sai ta shiga girgiza kai hawaye na zubo mata, hajiya Hauwa ta saka ƙasan gyalenta ta share mata sosai.

"Ai yanzu babu wanda zai mutu har sai kin faɗa. Ki daina kuka kin ji Sarauniyar baban ta"

Ta shiga shafa kanta, Reina da bata son ganin fuskar ta sai ta rufe idanu a haka har barci ya sake awon
gaba da ita bayan tsawon lokaci don nurse sau biyu tana shigowa tana fita suna a haka har Hajiya Hauwa
tayi mata kyautar kuɗi saboda toshe ɓaraka sai zuba godiya take yi.

......

Dare ta raba, idanun masu ƙarancin damuwa ya fara nauyi amma akwai wa'inda duk halin sata irin na
barci bai isa ya tunkaro su ba.

Yana dafe da kansa idanun shi a kan ƙafar shi duk da zuciyar shi ba su yake kallo ba. Ɗauko mishi hoton
fuskar Fauziyya yake yi, da wasu moments a cikin tarayyar su da ba zai taɓa mantawa ba har duniya ta
naɗe, lokacin da idan ya zo ƙofar gidan su ta leƙo taga shi ne sai ta ɗiba da ɗan iskan gudu ta koma.
Murmushi mai sauti ne ya kuɓuce masa duk suka juyo suka dube shi amma bai san ma yayi ba. yana tuna
lokacin da ya ɗauki burin samun ta da kuma lokacin da ya same ta ɗin.

Lokacin da ta zamo kwanciyar hankali da nutsuwar shi, murmushin ta, kukan ta, sautin dariyar ta da
rabon da ya ji shi har ya manta, sai yanzu abun yake zuwa kan shi cewa tun da Fauziyya ta haifi Hafsah
yawan dariyar ta ya ragu, yawan kukan ta ya ƙaru, sai yanzu da lokaci yake niman ƙure masa ya fahimci
hakan.

Da buɗewar ƙofar da miƙewar shi a kan ƙafar shi bai san wanne ya riga wani ba.

Yanayin da ya gani a kan fuskar likitar kawai ya saka shi fara sarewa.

Ya dai yi juriyar buɗe baki yace "doctor anyi Nasara?"

Sai da ya ja dogon numfashi kana yace "ku yi haƙuri ɗan cikin ta bai zo da rai ba"

Namijin ne, namijin da yake buri, namijin da ya ƙwallafa rai, ya rasa shi, amma a yanzu shine ainihin
ƙarami daga cikin jerin gwanon damuwowin shi.

"Ita Fauzar fa? Tana lafiya ina?"

"Ku yi haƙuri..... Allah ya karɓi abun shi!"

Bai san cewa ya kai ƙasa ba sai da yaga Alhaji kalabu da Alhaji salisu a kan shi suna ƙoƙarin ɗago shi, haka
ma dangin Hajiya Fauziyya suka yi kan mahaifiyarta da duk yanda tayi domin ta jurewa tayi tawakkali
sautin kukan ta sai da ya suɓuce daga bakin ta.

Ƴan uwan ta ma kukan suke yi amma burinsu su tsayar da na mahaifiyar su.

A hankali aka gunguro musu gadon da aka rufe ta da bed sheet har kayi.
Sai aka rasa wanda zai buɗe a cikin su saboda tsoron ganin ita ɗin ce ya kama su, kaman idan basu buɗe
ɗin ba za'a ce musu wannan wani gawa ne daban, Fauziyyar su har yanzu tana numfashi.

Daddagewa yayi ya miƙe tsaye cikin dauriya ya ƙarasa gaban gadon ya riƙe bed sheet ɗin zai ja ya yaye,
sai kuma ya kasa, kukan dake danne a ƙirjin shi yana dambe da bugun zuciyar shi don shima ya samu ya
fito a saurare shi, amma ya ƙara jurewa yayi nasarar buɗewar sai ga fuskar Fauziyyar shi, matar aljanna.

Wani nishi yayi mai gunji kafin kukan ya biyo bayan shi, zuciyar shi yana maimaita innalillahi wa inna
ilaihiraji'un amma bakin shi ya gagara nanatawa, sai kawai ya rungume gawar da ta sake tayi sanyi babu
ɗumin rai a jikin ta.

Kan kace mene wuri ya koma ƙaramin makoki, babu ma wanda ya tuna da wani gawar jariri, har su
Hajiya Hauwa sai da suka zubda ƙwalla. amma mutuwar da suka gani yanzu a gaban idon su bai saka sun
ji tsoron zuwanta ta ɗauke su a duk lokacin da taga dama duk ikon su da dukiyar su ba. Basu ji kaman su
canza ra'ayi ba, ko dan goben yaran su idan basa nan.

.......

Tun da Saudat ta haifo Yaseer duniya bai taɓa kwanan tashin hankali ba irin na yau, ga azaban raunukan
dake jikin shi, ga tsamin da jikin shi yake masa, ga baƙar yunwa domin rabon shi da abinci tun karyawar
safiyar jiya, ga kuma sauro kaman zasu yanki naman jikin shi, ƙuda ma ba'a bar su a baya ba wajen
bidirin su a kan romon daɗin da suke samu.

Yayi tunanin yana da taurin zuciya amma sai ya samu kan shi yana kuka da roƙon su taimake shi ko
iyayen shi su kira mishi ko su bashi ruwa ya sha.

Amma gargaɗi ma suke mishi idan bai rufe musu baki ba zasu ƙara mishi gajiya a kan wanda yake fama
da ita.
~~~~~~~~~~

Cikin izinin Ubangiji mun kusa kammala littafi na ɗaya.

*Saliha Ahmad Na'ibi (Seemahwrites ✨)*

*REINA 💍*

36......da farar asuba Kamal suka iso, Saudat dake zaune saman darduma tana zikirin safiya tayi saurin
miƙewa a kiɗime ganin suna tafe har da goggo halime tabbas wani mummunan abu ne ya samu Yaseer.
A maimakon ta amsa sallamar su sai cewa tayi "Allah yasa ba mutuwa yayi ba" ƙoƙari take ta sanya ma
kanta dangana koma menene ya faru ta ɗau na annabawa, duk da haka burin ta bai wuce su ce mata A'a
abinda take tunani ba haka bane.

"Kinga kwantar da hankalin ki, yana raye kuma zai kasance cikin aminci da izinin Ubangiji, yanzu bari mu
samu muyi sallah sai muje mu duba shi ko?!". Goggo ta faɗi yayin da take ƙarasowa ciki, sai gaban
Saudat ya ƙara tsinkewa.

"Goggo hatsari yayi?" Daga jin muryar ta zaka san a shirye take ta fara kuka, tausayin ta ya hana goggo
cewa komai.

Kamal ya umarci Suhail da ya kawo masa ruwan alwala sannan ya tsuguna ya fara duk suka bar ta tsaye
da gudun zuciya, gashi Kamal yaƙi yarda ko haɗa ido suyi.

"Hatsari ne ko?" Ta sake tambaya da muryar da tafi na farko rauni.

"A'a ba hatsari yayi ba. Yana hannun folisawa aka ce amma komai lafiya, ki kwantar da hankalin ki"
Kamal ya amsa ta.

Ta kwantar da hankalin ta? Tun da suka maimaita har sau biyu dole abinda zata gani ya ɗaga mata
hankali.

Don haka a sukwane ta jira suka idar da Sallah lokacin gari ya fara haske.

bata basu damar addu'a ba tace "toh bari na je na tsare mana napep"

"A'a Saudatu, yayi wuri da yawa ba za'a samu abin hawa yanzu ba, sannan Yaseer ɗin zai buƙaci abin
karyawa, ki haɗa sai mu tafi masa da shi"
Ta amsa goggo da "toh" Cike da jin daɗin cewa zai iya cin abinci ta miƙe ta shiga kitchen. Akwai ajiyayyen
tuwon da tayi niyyar ɗumama musu da safiyar amma sai ta kwaɓa mishi ɗanwake na musamman ganin
tana da sauran flour.

Sai da ta gama ɗanwaken ta zuba a food flask ɗin shi kafin ta ɗaura musu ɗumamen tuwon.

haka dai kowa ya taɓa sama-sama, duk yanda yaran suka so bin su goggo ta hana don ko su basu san me
zasu je su ji a kan dalilin rufe Yaseer ɗin ba.

Tun daren jiya Kamal ya tambayi masu gadin gidan station ɗin da aka rufe Yaseer, don haka kai tsaye can
suka nufa ba tare da sun tuntuɓi Alhaji Tahir ɗin da ya saka aka rufe shi ba.

.....

Kaman jiya ne Alhaji Tahir ya ziyarci Alhaji Abdou a lokacin da ya rasa Malika, shima yau gashi ya ziyarce
shi a dalili makamancin sa.

Ya ɗauka Alhaji Abdou ya kiɗime a lokacin da ya rasa uwar Aicha, amma shi kuka yake da hawayen shi a
rashin majinginar zuciyar shi, ba ta Reina ko Maama yake ba.

Sosai ya bawa Alhaji Abdou tausayi, rashi har guda biyu a lokacin ɗaya ba wasa ba.

Amma ana buƙatar yayi ma Fauziyya gata ya sallace ta ya kai ta makwancin ta.

"Da ace na samu damar tunkarar ta a kan abinda ya sami Hafsatu, da ba zan taɓa yafewa kai na ba"
zaune yake a dandamalin ƙasa hannun shi riƙe da kai, yana ji kaman ya ajiye shi ya huta da tunanukan da
ƙwaƙwalwar shi yake faman kawo mishi.

Ya zalinci Fauziyya, ya ɓata mata, ya shiga hakkin ta, amma bai samu damar roƙonta ta yafe mishi ba,
gashi ta tafi lokaci ɗaya babu notice. yana tsoron Allah ya ɗaga su a ranar alƙiyama tana ƙullace da shi.
"Allah ya gafarta mata, ya yafe mana baki ɗaya. Amma sai ka jure Tahir, na sani akwai zafi, akwai ciwo
amma bata buƙatar komai a halin yanzu bayan ka sada ta da gidan ta na gaskiya sannan ka bita da
addu'a"

"Fauziyya na yafe miki, Allah ya yafe miki, Allah ya haɗa fuskokin mu a gidan aljannah."

"Ameen, In sha Allah "

.....

Bayan dogon roƙo da suka yi, da bayanin da aka musu wanda ya ɗaure musu kai, da ƙyar suka samu aka
basu daman ganin Yaseer. domin sai da suka ga alamun Saudat tana niman sume musu a wurin.

Da ƙyar yake iya takawa don ji yake yi kaman sunyi mishi targaɗe a ƙafa, yana tafe suna angiza ƙeyar shi
har idanun shi da suka kumbure suka shiga na iyayen shi da kakar shi, kamannin fuskar shi ya sauya baki
ɗaya.

Kukan da Saudat ta riƙo kayan ta tun daga gida sai yanzu ta samu damar sake shi ganin yanda ɗan nata
ya dawo a wuni ɗaya kawai.

Shi kuwa Yaseer ganin hawaye a idanun mahaifiyar shi ya tsotse nashi baki ɗaya, babban baƙin cikin shi a
duniya shine ya zamo silar kukan iyayen shi.

Kuka take yi tana sheshsheƙa har sai da numfashin ta ya fara sama-sama, dama Kamal a shirye yake ya
shiga shaƙa mata inhaler daman ya san hakan zai faru.

Yaseer da tsayuwa ya gagare shi saboda tsananin yunwa ya tsuguna a gaban Saudat ya riƙo ƙafar ta,
amma sai tayi saurin kwacewa tana maida numfashi.
"Ka ji tsoron Allah Yaseer, hukuncin duniya kenan ina ga wanda Ubangiji zai yi maka mai tabbatuwa a
ranar da muma ta kanmu muke yi? Idan ka ƙaryata zan yarda da kai amma ka sani ka ci amana ta irin cin
amanar da ba'a taɓa min irin shi ba, kuma ba zan taɓa yafe maka ba. ko da ban sani ba Allah ya sani
Yaseer, ko dan ban gani ba Allah ya gani, ko da ban ji ba Allah ya ji, kuma bayi barin hakkin wani a kan
wani komin kashin sa. Kayi ma kan ka gata ka faɗi gaskiya, mai ita bayi taɓa taɓewa, zata wahalar da kai
amma na ƙanƙanin lokaci ne, sai dai idan ka zaɓi kayi ƙarya wahala ta har abada ya tabbata a kan ka."
Kalaman ta ke harɗewa don haka ta tsaya ta ja dogon numfashi ta fesar da shi kafin ta ɗaura da.

"Ba don ni ba, sai don wanda ya isa da kai da zuciyar ka, mai hukunta wanda yayi zalunci kuma gatan
wanda aka zalunta..... Yaseer ka taɓa musu ƴa? Kana da laifi a kan abinda ake zargin ka da shi??"

Baki ɗaya bakin sa a fashe yake, don haka zafin tauna laɓɓan shi da yayi ya ratsa har cikin ƙwaƙwalwar
shi.

"Wallahi Umma, na rantse miki da sarkin da babu wani bayan shi, na rantse miki da wanda tsaron rai na
da lafiya ta yake hannun shi, Wallahi Wallahi ban yi ma Hafsatu komai ba, ban taɓa yunƙurin ketare
iyakokin da Ubangiji ya gindaya min a kan cikakkiyar mace ba ma balle yarinyar shekara tara Umma.
Hafsatu ƙanwata ce, na ɗauke ta yanda na ɗauki su Sabir da Irfan, ƙoƙari na a kullum shine in kare su
daga cutarwa, ta yaya za'ayi ni kuma da hannu na in cutar da su?"

Bata bari ya sauƙe numfashi ba tace "Na yarda da kai. Idan ka yi min ƙarya ka cuci kanka Yaseer."

Ɗagowa yayi ya kalle ta cikin ido, tabbas ya gani, yardar da tayi da shi ɗari bisa ɗari don haka ya dubi
mahaifinsa shima hakan ne, haka ma kakar shi, don haka zuciyar shi yayi mishi sanyi.

"Umma" ya kira Saudat.

"Na'am Yaseer" tayi ƙoƙarin saka murmushi a kan fuskar ta duk da hawaye bai daina mata zuba ba.

"Umma yunwa nake ji, amma ba zan iya saka komai a ciki na kina min kuka ba. Ina tsoron azabar Allah
Umma, soyayyar shi kawai nake so"
Sai ta murmusa tana share hawaye da ƙasar hijabin ta. "Allah ya so ka ɗana, Allah ya ƙaunace ka, Allah
ya ji ƙan ka yayi maka rahama ba sai ka mutu ba"

Da ameen ya amsa sannan suka fito mishi da food flask ɗin da suka zo da shi. Nan ma sai da aka yi daru
da police, Kamal ya ɗan miƙa musu wani abu kafin suka yarda suka bar shi ya fara cin abincin. Sun fi so
su luguiguita shi ne sosai yanda idan Alhaji Tahir ya zo zai ji daɗi yayi musu alheri.

A baki Saudat take bawa Yaseer abinci yana karɓa da wani zaƙuwa kamar zai cire mata yatsu, ita tsoron
fama masa ciwon bakin shi take ji.

Kamal ya bari har sai da ya tabbatar da ya fara dawowa cikin hayyacin shi kafin yayi masa tambayar ya
labarta musu ainihin abinda ya faru, yanda aka yi aka haihu a ragaya.

"..... Allah da bakinta ta amsa min. Jamal ne, Yaron gidan da nake zuwa in yi mishi lesson, kuma a
tambayi Aunty mahaifiyar ta, na fara mata zancen mahaifiyar Jamal ɗin ta fito ta katse mu, ko ita
Hafsatun ma a tambaye ta"

Kamal ya numfasa "Shikkenan, ni bari na je gidan Alhaji Tahir ɗin goggo, in same shi ko ita Hajiyar ma
idan bayi gida, idan abu ya gagara kuma sai ki zo amma bamu fatan hakan"

Babu daɗewa suka sake tasa ƙeyar Yaseer zuwa ciki, kamal ya bada kuɗin magani da kuma dressing ɗin
ciwon Yaseer ya dinga haɗa su da Allah su taimaka, dukkan su ƴan uwa ne kuskuren fahimta aka samu
sai dai zasu warware komai nan ba da jimawa ba.

Sun dai ji shi, amma suna tafiya suka raba kuɗin a tsakanin su.

Kamal ya fara saka goggo da Saudat a napep su tafi gida kafin ya tsari mashin ya ɗauki hanyar gidan
Alhaji Tahir, ya riski unguwar ma gabaki ɗaya bata shiguwa da abun hawa.
......

Da ƙyar Alhaji Abdou ya lallaɓa Alhaji Tahir ya ɗauro alwala ya fito, yana tafiya kaman zai kifa.

yana fitowa yawan mutanen da ya gani ya saka shi sake rushewa da kuka, Ciki da wajen gidan ya cika
maƙil.

Dandazon mutanen da ya gani sun zo su sallace Fauziyya ya ƙara narkar da zuciya da ruhin shi, karkarwa
yake yi a yayin da ake yin ƙabbara ma Ubangiji a Saboda wa'innan halittu guda biyu da ya busa musu rai
a lokacin da yaso kuma ya ɗauki ɗayan ba tare da ya shaƙi iskar duniya ba ma.

A cikin ƙanƙanin lokaci har sun kasance kamar ba'a yi ba, sun dawo tarihin da idan Reina ko Maama suka
shiga halin maraici za'a kalle su ace 'Allah Sarki, Allah ya jiƙar mahaifiyar ku da ta rasu yayin haihuwa'.

.....

Gidan Hajiya Hauwa Meesha taje duba Yaseer.

Tun jiya take niman layin shi a kashe baki ɗaya ta gagara samun nutsuwa, gashi tana jin kunya da kuma
tsoron zuwa gidan su, kada ya ƙara fushi da ita a kan wanda yake yi yanzu.

Tana da yaƙini koma tace tabbacin zai zo yiwa Jamal lesson yau kasancewar shi lahadi. Saidai da isar ta
aka sanar da ita gaba ɗaya masu gidan basu nan sun tafi gidan ƙanin mai gidan anyi rasuwa.

Tunanin ko ta kira Hajiya Hauwa ta tambaye ta Yaseer ya faɗo mata, amma ta lura itama ba son tarayyar
su take yi ba tunda gashi ta fara kai gulma wurin iyayen ta.

Toh ko taje gidan rasuwar ne ta tambayi Jamal ɗalibin shi?.

"Umm mai gadi nace Yaseer fa? Ya zo yau ɗin?"


Mutane da son gurmi wanda ba shi aka tambaya ba ya riƙe baki, "wani Yaseer ɗin? Yaron da yake zuwa
laluɓe ƴar masu gida? Ai tuni ƴan audu suka zo suka yi waje da shi" da safiyar yau ya ji raɗeraɗin abinda
yake faruwa shine shima yake son ayi da shi.

Yatsina fuska Meesha tayi cikin rashin fahimta tace "I don't understand, come again "

Ɗayan na ɗan tattaɓa shi don ya iya bakin sa amma ya share yace.

"Hajjaju! shi dai Yaseer abokin ki da yake zuwa yi ma yara karatu..."

"Uhm hmm?"

"Toh ashe zagawa yake yi yana laluɓe Hafsatu Rayina ƴar gidan Alhaji Tahir. Shine dubun shi ya cika Allah
ya kama shi uban ya kama shi da idon shi"

"Reina dai?!" Meesha ta maimaita da mamaki ganin to ko iskanci Yaseer yaso yi me zai yi da wata Reina
jaririyar da ko ƙirgen dangi da sauran ta?.

Amma shi sai ya ɗauka sunan da bai faɗa daidai bane take gyara mishi.

Yace "Ita dai" kana ya ɗaura da "ai ina faɗa miki Hajjaju mutane kina ganin su nan maha'inta ne ƴan
kutumar kaza. Ki ɗauko mutum a bushe ana bashi maiƙo har ya fara tada komaɗa yana tafiya da dogon
wuya zoƙai-zoƙai kaman jalbe amma shine duk cikin yaran duniya ya rasa wa zai taɓa sai ƴar alhajin
Alhazawa..."

Zai ci gaba da magana Meesha ta gwada shi da yatsa "in sha Allah duk ranar da na dawo cikin gidan nan
ka bar aiki. Wani station aka kai shi?"
A tsorace ya durƙusa yana ɗaga mata hannu kaman mai bara "dan girman Allah hajjaju a yafe ni, Wallahi
suɓul da baka ne, bakin ne ba'a farsa shi ba tun haihuwa"

Reverse tayi zata bar ƙofar gidan ɗaya mai gadin ya faɗa mata address ɗin wurin gudun kada idan tazo
tattarawa shima ta saka a haɗa da shi.

.....

Meesha bata yi musu kama da wanda zasu hana ta ganin Yaseer ba duk da suna tsoron Alhaji Tahir
kuwa.

Yana fitowa yaga ita ce ya juya zai koma, bai san kuma wata jarabar zata ƙara mishi ba yanzu, ta bar shi
ya ji da abu ɗaya.

Da gudu ta ƙarasa ta riƙo hannun shi amma saboda raunin shi ya saki ɗan ƙara sai a lokacin ta matsa
baya ta ƙare masa kallo da kyau.

"Yanzu shi Alhaji Tahir ɗin ne yayi maka haka? Wallahi ko duk duniya zasu taru a kai na ba zan taɓa yarda
da sharrin da suke son ƙulla maka ba, kai ba mutumin banza bane"

Wasa-wasa kukan da Meesha tayi sai da ya kusa zarce na mahaifiyar shi ma. Aka dawo shine mai rarrashi
da bada baki su kuma suka fita siyo mata ruwan gora mai sanyi saboda sun ganta da mota, gashi kana
kallon ta kaga rich kid.

Da ƙyar ta bar station ɗin zuwa tunkarar Hajiya Hauwa a gidan mutuwa. Ita ta ɗauke shi aiki don haka ita
ya kamata ta tsaya mishi tun da su suke morar shi.

.....
Yau ne gobe ne kamal zai dawo shiru. Har rana ya fara sanyi yana zaune cikin ƴan karɓar gaisuwa. Da
goggo taji shirun yayi yawa ta kira shi don jin ba'asi ya sanar da ita ai Hajiya Fauziyya ce ta rasu sai ta
ƙarfafa masa guiwar ya jinkirta da maganar suma gasu a hanya, don bata jin zata taɓa mantawa da kirki
da kuma halaccin Fauziyya ɗiyar albarka.

~~~~~~~~~~~~

Idan Allah ya bamu aron rai, littafi na biyu zai zo paid ne. 500 posting document kuma 1000, Zaku iya
fara payment yanzu ko zuwa lokacin da muka kammala littafi na ɗaya.

8021689184 Saliha Ahmad Na'ibi opay

Sai a turo shaidan biya ta wannan number 08021689184.

*Seemahwrites ✨*

*REINA 💍*

https://chat.whatsapp.com/Dn6MNAK5vgX3kRbwKwAPCv
37......A bakin hanya Meesha ta samu tayi parking, ganin yawan mutanen da ke sintiri a gidan ya saka ta
ɗauki sunglasses ta ƙwama saboda idanun ta da suka kumbura a dalilin kuka.

Da ƙyar ta samu wucewa cikin parlourn dake cike maƙil da mutane, bata fasa kiran Hajiya Hauwa a waya
ba ita kuma ta ƙi ɗauka.

Glasses ɗin ta cire ta fara baza idanu ko zata ga wanda ta sani ta tambaye su inda take yanzu su wuce
police station ɗin, don tana ji kaman idan Yaseer ya ƙara awa guda a cell zata iya haukacewa.

Can ta hango Zahra ta maƙale a wata ƴar kwana tana danne-danne a cikin wayar ta. Babu ɓata lokaci ta
ƙarasa wurin tare da ɗan shurin ta da ƙafa ta ɗago.

"Ke ina maman ki?" Ta tambaya.

Sai Zahra ta fara dube-dube, ita kaman ma tun kafin karyawan safe rabon ta da ita.

"Ban san inda take ba" ta bata amsa.

"Oya tashi kije ki dubo min ita, and ki hanzarta"

"Ni Wallahi ban san a ina zan same ta cikin wannan taron ba. Kije ki duba ta da kan ki"

A masife Meesha da ta manta a gidan mutuwa take tace "zaki je ki kira ta ne ko sai ɓaɓɓallaki mara
kunyar banza?"

Nan hankalin mutane ya dawo kan ta.

"Lafiya dai Meesha?" Hajiya Farida ta tambaya.


Juyawar da zata yi taga duk idanun mutanen parlourn ya dawo kan ta.

"Aunty Hauwa nake nima, ko kin san yanda take?"

"Gani. Mai zaki bani kike nima na?"

"Aunty Hauwa kin ci amana Wallahi " ta juya tana kallon Umman Jamal da yanzu shigowar ta gidan sun
raka Jamal airport kuma basu bar airport ba sai da suka ga tashin jirgin su.

hawaye na sake taruwa a idanun Meesha ta cigaba da cewa. "Kin ɗauko ɗan mutane zai taimaka muku
shine zaki bari ayi masa wannan wulaƙancin? Yaseer ɗin da ko kallo ban ishe shi ba mai zai yi da wata
Reina don Allah?"

Lokaci ɗaya hankalin Hajiya Hauwa ya ƙara tashi, kada Meesha ta since mata zani a gidan mutuwa.
Mutane kuwa an zuba kunnuwa aji gulma har masu jan tasbaha suna lazimi ma dakatawa suka yi su ji
rikicin duniya tukunna. Sai wata wata mai tunani ne aka samu ta tunasar da su cewa a gidan mutuwa
suke.

Meesha bata da niyyar fasa magana don haka ta karasa kusa da Hajiya Hauwa ta riƙo hannun ta tare da
sauƙe murya iya tsakanin su "Aunty Hauwa, don Allah ki taimaka ki yi magana a fito da shi. Wallahi yana
shan wahala sosai, kuma na tabbata ba shi bane, sharri aka yi mishi"

Hajiya Hauwa ta buɗe baki zata mayar da raddi suka jiyo hayaniya a waje. Alhaji Tahir da bayi iya buɗe
baki ya amsa gaisuwa amma muryar shi har cikin gidan yana hayagaga ma wasu.

Yanda kasan yara sun ji ana sadaka haka matan cikin parlon nan suka rige-rigen fita su ga abinda ke
faruwa.
......

Mutuwa ce, mutuwar ma na mace kamar Hajiya Fauziyya, matar kirki gaba da bai wanda babu fatan da
zasu yi mata da yayi ƙasa da Allah yayi mata rahama, ya kai haske makwancin ta.

Amma zuciyar uwa, Saudat ji take yi da wata ce ba zata je ba bayan Abinda suka yi ma gudan jinin ta.

Muhammad abokin Yaseer ya kira Kamal lokacin su goggo suna hanya ya bashi haƙurin sammakon zuwa
lectures yayi shiyasa bai kira ba tuntuni, sannan ya tambaye shi an ga Yaseer ɗin? Tunda ya san ba halin
shi bane fashin makaranta. department ɗin su ba ɗaya ba amma ɗakin su ɗaya kuma bai ga ya dawo ba.

Kasancewar mutum a cell koda bisa kuskure ne ba abin alfahari bane don haka sai Kamal ya sami kan shi
da mishi ƙaryar sun yi accident ne ya faɗi a mashin saboda idan sun gan shi ya dawo da raunuka su
fahimta.

Yayi musu Allah ya sawaƙe da alƙawarin zuwa yamma zai shigo ya duba shi.

Yana da yaƙinin zuwa lokacin an sake yaseer ya dawo gida, ya amsa da toh sai ya zo ɗin.

Cikin ƴan karɓan gaisuwan dake waje suka samu Kamal, ya ƙaraso wurin su don shima bai samu ganawa
da Alhaji Tahir ɗin ba sannan ya jagorance su suka shiga ciki a tare.

Suna haɗa idanu da Alhaji Tahir ya fara ɗaga mishi hannu ya koma inda ya fito daman yasan zasu biyo
sawu kuma ko duniya zata tashi a kan lamarin nan ba zai saurare su ba.

Kamal ya ja ya tsaya kawai yana kallon shi har Saudat ta shigo, goggo biye da ita.

Amma ko da yaga ƙanwar mahaifin shi, bai fasa musu alamun su koma ba, sai ma miƙewa da yayi a kan
ƙafafuwan shi.
Goggo ta karɓi jagorancin tayi gaba zuwa gare su sannan ta rage tsayin ta ta gaida su, Saudat ta mara
mata baya.

Ganin Alhaji Tahir ya ɗaga kai bai amsa ba yasa tayi mishi nashi gaisuwan na musamman.

Yaya haƙuri fa suke tambayar shi? Bayan ɗan su shi yayi sanadin da ya rasa Fauziyya! Bayan shi ya lalata
Hafsatun da duk burin shi na duniya ya gama ɗaurawa a kanta, amma shine basu ji kunyar gwada mishi
munanan fuskokin su ba?!

"Goggo! Kafin in yi miki abinda ba zaki iya ɗauka ba don Allah ku fice min a gida!"

Da ace bai ga wannan baƙar safiyar ba, da ace Fauziyya bata wurin, da ace bai danƙa amanar Hafsatu a
hannun la'anannen yaron nan ba, wataƙil da yanzu Fauziyya tana ɗan hidimomin ta na cikin gida da bata
gajiya da shi da cikin magajin shi a jikin ta, amma asarar da suka jawo mishi ba ɗaya ba har biyu, kar ma
aga laifin duk abinda zai yi musu.

"Ɗahiru komai rikicin Duniya mutuwa tafi ƙarfin shi. Kayi haƙuri ayi addu'a wa mamaci komai zai iya
zuwa daga baya"

"Goggo ki rufa ma tsufan ki asiri don Allah ki ɓace min da gani, darajar ki da ya rage a idanu na yasa ban
haɗa da sauran yaran ki na rufe ba, don haka ki tafi kawai na gargaɗe ki"

Miƙewa Alaji Abdou yayi ganin kaman mutuwa ya zautar da Tahir ɗin ya riƙo shi ya juyo da shi.

"Yaya kaman bakka da tunani Tahir, damuwa batta saka hauka fah, ka natsu!.

Cikin ɗaga murya don ya fusata ganin Abdou ya san komai amma laifin shi yake gani yace "Wallahi ko ku
fice min a gida ko in saka ku ma azo a fitar min da ku. Mutanen banza kawai wanda basu san halacci ba"

Goggo sai ta murmusa kawai don kalamin shi na ƙarshe ya bata dariya. Da ace Uban shi Kamalu zai iya
tasowa daga kabari ne toh zai sanar da shi wanene ainihin wanda basu san halacci ba.
Meesha da ta samu fitowa tare da sauran mutane ta ƙaraso gaban goggo ta tsaya ita a dole shamaki take
mata tsakanin ta da Alhaji Tahir domin tunda ta gan su tare da Saudat toh tabbas dangin Yaseer ne.

"Wani shaida kake da shi da zaka rufe ɗan mutane wanda bai ji ba bai gani ba? Don kawai zaka iya? Ko
don kana ganin bayi da gata?"

Alhaji Tahir yayi mata kallo ɗaya sannan ya ɗaga murya ya fara kiran security wanda suka nufo su da
hanzarin su.

"Kada ku kuskura ku taɓa su Wallahi" Alaji Abdou ya tsawatar tun kafin su ida ƙarasowa.

Ga su Alhaji kalabu da Alhaji salisu a wurin amma an rasa mai tsawatar ma Tahir, wannan wacce irin
rayuwa ce?!.

......

"Wallahi babu inda zan je. Ai ni na kawo muku shi" Meesha ta shiga tirjewa ta ƙwace kanta a hannun
Hajiya Hauwa dake ƙoƙarin fitar da ita daga parlourn da ƙarfi.

"Rabu da ita Hauwa, ai itama laifin ya shafe ta tunda haka ne" cewar Alhaji Salisu sannan Hajiya Hauwa
ta sake ta tana wurgin ta da harara.

Alaji Abdou ne ya miƙe bayan kowa ya zauna ya fuskance su yana tunatar dasu a irin yanayin da ake ciki
ganin kaman sun manta, Fauziyya ko kwana bata yi a cikin kabarin ta ba tukunna, addu'a ya kamata suke
mata ba rikici ba, ya ɗan yi musu wa'azi mai razanarwa a kan mutuwa don su farga, koma menene a
warware shi cikin lalama.

"Yanzu goggo mai yake tafe da ku?" Alhaji Kalabu ya tambaya bayan jikin kowa yayi sanyi.
Numfashi ta furzar sannan ta fara magana. "Taaziyyar muka zo yiwa Tahir kaman kowa a nan saboda
tabbas yayi babban rashi. Amma tunda abin har ya kawo haka bari kawai ayi ya wuce."

Sannan ta dubi Tahir "ka sani, ba zallan shekaru bane suka tsufar da ni. Haƙuri, sanin ya kamata da kuma
hangen nesa suna daga cikin abinda ya kawo mu har wannan lokacin nake zaune a gaban jikoki na. kuma
ni Halime ban yi ma tsatso na horo da ɗaure ma ƙarya gindi ba.

Saboda ka hukunta Yaseer a kan dai-dai da ba dai-dai ba ba zai saka na tako ƙafa na gidan ka har ka ga
dama na ba ɗahiru. Amma abinda kuke zargin shi da shi ba ƙaramin abu bane har a addinance, don haka
muna so mu san da wani hujjoji ka kama shi ka saka a kulle shi, don idan yana da laifi mu masu goya
maka baya ne ka saka doka ko wani iri ne tayi aiki a kan shi"

Cikin jin daɗi Meesha tace "yauwa! Tambaye shi kam goggo."

Hajiya Jummai dake ɗaya gefenta ta ɗane mata baki, Meesha ta ja mata Allah ya isa a ƙasan maƙoshi.

Tsoro ya so kama Hajiya Hauwa da Alhaji salisu amma da ikon Allah sun toshe ƙofar ko wani ɓaraka,
babu wani shaidar da zai gwada Yaseer ne yayi ƙoƙarin lalata Reina kaman yanda babu wanda zai gwada
ba shi ɗin bane Jamal ne.

Sannan har ita victim ɗin ma sun toshe bakin ta.

"Goggo kin gama?! Toh nayi miki rantsuwa da wanda yake busa min numfashi babu uban da ya isa ya
saka in sake la'anannen yaron nan. Da idona na gan shi ganin annabi musa da firauna."

"La'ananne kuma?" Saudat ta tambaya cikin ɗacin rai. "Mu bamu yi masa baki ba, sannan bai yi abinda
Allah zai la'ance shi ba"

"Ni zan yi ƙarya ma Yaseer kenan? Me ya kai shi ɗakin baƙi tare da ƴata Hafsah? Mai yake yi a ɗakin tana
cikin mummunan yanayi? Wa yayi mata hakan bayan shi da yake tsaye a wurin?" Ɓata bakin shi ma yake
yi da har ya tsaya yana bayani ma mutannen nan.
Kamal ya girgiza kai. "Baka ga dai-dai ba dai, duk da na shiga ban ɗauka ba bayi fidda ɓarawo amma ko
ita yarinyar da kun tuntuɓi abin da ya faru zata faɗa muku tunda ita ce babban shaida, zata faɗa muku
Jamal ɗin Alhaji Salisu ne da bakin ta, Yaseer yayi ƙoƙarin kare mata cutarwa ne"

Dududum!! Zuciyar Hajiya Hauwa da Alhaji Salisu suka haɗa baki wurin bugawa.

Kallon ta yayi tunda ita take da alhakin rufe ɓarakan da suka jawo. Ɓarakan da ta lura da samun shi tun
bai yi girma ba amma taƙi sanar da shi. Saboda ta kama Jamal tun wurin shekara guda da ya wuce
sanadiyyar mantawa da yayi bai rufe ƙofar ɗakin ba, suna kallace kallacen banza hannun shi cikin rigan
Reina.

Ranan ta buge shi sai da yayi zazzaɓi amma bata faɗa ma uban ba Saboda tana tsoron abinda zai biyo
baya. Yanzu idan ya zuciya sai ya ƙi cika burikan da suke da shi a kan Jamal ɗin ya saka masa ido da
takunkumi.

Ashe ita da kanta ta ƙara ma barakar girma.

Tun da yana ganin yayi ya sha, toh yanzu bayi tsoron abinda zai biyo baya tunda mahaifiyar shi ta sani.
kuma yayi Gaskiya domin daga baya ma lokacin da ya fara shan gida aka kawo shi ma mahaifin shi shima
ɗan dukan shi yayi ya shiga bayan uwan ya ɓuya tana kan guiwowin ta tana roƙon shi ya rabu da shi.

Shikkenan kuma ya sha, don haka ya fara shan kayan shi har a cikin gidan.

"Wani Jamal kamalu? Jamal ɗin da bayi ƙasa?. Tun ranar juma'a ya tafi Ghana makaranta, abinka da
Allah ya so wanke bawan shi, da yanzu sai ku ɗaura masa ko?"

Suka kalleta da mamaki don sun san Yaseer ba zai yi musu ƙarya har da kama suna ba. Tun da yace shi ne
toh shi ɗin ne.

"Yanzu abun da yafi kawai a kawo ita Hafsatun ta faɗi abinda ya faru tunda ita kaɗai ta sani".
"Hakan yayi, amma shima Yaseer ɗin a kawo shi saboda aji ta bakin shi a fita hakkin shi."

Alhaji Tahir ya shiga girgiza kai.

"A'a za'a firgita ƙaramar yarinya ta kasa magana daman tsoron shi take ji ni na gani"

Goggo ta amshe da "idan haka ne suma iyayen Jamal sai dai su fita saboda zasu iya firgitata ta amsa
abinda ba shi bane.

....

Sun rasa haƙuri ko rashin shi ya saka su zama ba tare da sun ƙosa ba har police suka fara kawo Yaseer
kafin ala kawo Reina daga gidan Ummi tazo ta shige jikin mahaifin ta.

Sai tabi mutanen ɗakin da kallo a tsorace, ita fa har yanzu bata ga Auntyn ta bane shine damuwar ta.

Idanun ta da suka sauƙa cikin na Yaseer ya saka ta miƙewa tsugul zata yi kan shi. hawaye na cika a
idanun ta ganin jikin shi da ciwon mutuwa kaman yanda Hajiya Hauwa tace.

~~~~~~~~~~~~~

Please To be clear document sai an kammala haɗa labarin kafin a same shi, wanda basu samu a lokacin
da ake posting bane idan an haɗa document kuɗin shi daban. Amma mai son sai an gama zai iya biya ya
jira.
Zaku sami littafi na biyu a kan 500 posting. Document kuma 1k. Ta wannan account 8021689184 Saliha
Ahmad Na'ibi opay, sai a turo shaidan biya ta wannan number 08021689184.

*Seemahwrites ✨*

*REINA 💍*

38..... Jamal ne!.

Jamal ɗin da ta bada amanar Yaseer a hannun iyayen shi, ashe su ke da alhakin duk abinda yake faruwa.
Meesha ta ayyana a ranta.

Da sauri Alhaji Tahir ya riƙo Reina ta dawo jikin sa sai kawai ta fashe da kukan tausayin Yaseer.

"Yaya Yaseer, wa ya ji maka ciwo?"

Ɗaga ido yayi ya kalleta.

Abun mamaki, yana cikin halin ha'ula'i amma tausayin ta yake ji. Yaya zata fara rayuwa babu mahaifiya?
Da ƙananun shekaru?.
Bai furta komai ba don bayi da ƙarfin magana yanzu.

Mahaifiyar shi, Meesha da goggo kuka suke yi sosai, har mahaifin shi a yanzu sai da ya zubar da hawaye.

"Yanzu idan a kan gaskiyar shi kuka mishi haka fah? Sai kuce yayi haƙuri?" Kamal ke magana.

Alhaji Tahir ya kalle shi sheƙeƙe. Yanzu wannan mabaracin har ya kai ya kalli idanun shi ya gaya masa
magana? Yo ko da gaske bai kama Yaseer da kan shi ba ko kuma ace bai aikata abinda yake da tabbaci a
kai ba zargi ba ma ai Yaseer be kai wanda zai buɗi baki ya bashi haƙuri ba, da girman shi da darajar shi a
tsakanin al'umma. ko iyayen shi basu isa ba, kai ko ita goggon ma.

"Toh ai gata nan, zamu ji daga bakin ta, idan ba hakan bane za'a san abun yi" Alhaji Kalabu ya mayar ma
Kamal, ya kuwa yi sa'ar dawo da duban shi garesa yana masa wani irin wulaƙantaccen kallo, bai taɓa
sanin ƙananun mutane bane su sai yau.

Babu wanda ya sake magana, babu abinda yayi saura a faɗa, shaidar Reina kawai ya rage. Gaskiyar ta
kawai zai warware wannan rikicin da kuma barazanar farawar gaba ta har abada a tsakanin ƴan uwan da
suka haɗa jini. Amsar ta shi zai tantance makomar tarihin da ba a yanzu aka fara rubuta shi ba, da
daidaitaccen alƙalami, a littafi mai daraja da kyakkyawar rubutu.

Sai dai farkon tarihin ne kawai yayi kyau, tsakiyar rubutun yazo da gargada, gashi ƙarshen sa na neman
dagulewa yanda ba zai yi daɗin karatu ma ƴan baya ba.

Alhaji Tahir ya kwantar da ita a jikin shi kafin cikin ƙasa da murya yanda ba zai razana ta ba ya kira ainihin
sunan ta na yanka a karo na farko.

"Hafsatu na." Sai dai saboda yanda wurin yayi shiru ko allura aka jefar za'a iya jin karar haɗuwar shi da
ƙasa, ba don hayaniyar ƴan gaisuwa dake shigowa sama-sama ba.
Reina ta ɗago ta kalle shi da idanun ta dake zubar da hawaye, ya saka hannun shi yana share mata, yana
auna tambayar da zai yi mata, yanda zai yi daidai da tunanin ta.

"Sarauniya ta... A gidan Umman Jamal da su wa kike wasa?"

Sai ta fara tunani a ranta, Wani irin wasa yake nufi kenan? Wasan da suke yi da su Zaheera da Abdallah?
Ko wanda suke yi da Jamal?

"Ina yi da su Zaheera da Abdallah sai kuma yaya Jamal"

"Yauwa kun ji ba?!" Saudat ta furta tare da ɗan jin sanyi a ran ta. Daman ta san idan yarinyar tazo
gaskiya zai fito.

Caraf Hajiya Hauwa tace "Ai wasa aka ce? Ɗan uwan ta bayi da ikon wasa da kanwar shi iye? Ko baku ji
ta ambaci sauran ƴan uwan ta bane?"

"Mun ji mun fahimta ɗan uwanta ne. Amma a tambaye ta wani irin wasa suke yi mana?" Yanzu abun ya
koma tsakanin Saudat da hajiya hauwa.

Ɗaga musu hannu Alhaji Tahir yayi ganin Reina ta fara tsorata. Suka yi shiru zuciyar Hajiya Hauwa ya
tsananta bugu kaman wacce take filin tsere na Olympics, Saudat kam ta samu nutsuwa zuwa yanzu,
ƙarƙare shirin kawai ya rage.

"Yaseer fa?" Ya cigaba da tambayar ta cikin kulawa.

"Yaya Yaseer dai ko?" Ta gyara masa, Saboda itama shi Yaseer ɗin ne ya haramta mata kiran sunan
babba gatsau.

"Eh shi ɗin. Baku wasa da shi?"


Sai ta girgiza kai "karatu yake mana ni da su Zaheera, bayi min wasa"

Yaseer ya saki numfashi, haƙiƙa ya tsorata da lamarin amma komai ya zo ƙarshe. Yayi kyan kai da ya
yanke shawarar koyar da su duka ba ita kaɗai ba.

Alhaji Salisu da Hajiya hauwa kam kaman a buɗe musu ƙofar nan su fice da ɗan iskan gudun da ba za su
tsaya ba sai sun isa birnin sin.

Ganin kaman Reina bata fahimci yanda tambayar tashi ya dosa ba, ya saka shi canza shawarar fito mata
a mutum kawai.

"Reina. Waye ya taɓa ki lokacin da kuka je asibiti da Aunty aka baki gado? Waye yake cire miki kaya da
wando a gidan Umman Jamal?"

"Wallahi Alhaji bayan gaisuwa babu abinda yake shigar da ni cikin gidan. Tsakani na da su duka a waje ne
Wallahi" Yaseer yayi maganar a wahalce.

Yanzu shine kawai dama ɗaya da yake da shi ya kare kan shi, dama ɗaya ne kawai aka bawa gaskiyar shi
ya cece shi.

Idan hakan ne ta yaya aka yi ya kama shi a cikin ɗaki a tare da ita?.

"... Yaya Yaseer ne!"

Reina ta katse maganar Alhaji Tahir da ma duk wanda ke da niyyar tsoma baki a wannan gaɓar, suka juyo
suna kallon ta, ita kuwa shi take kallo. Ceton shi ne kawai burin ta, ba zata juri rasa Auntyn ta ko shi ba,
bata son ya mutu, don ta tseratar da shi daga mutuwa zata yi ƙarya ɗari ba ɗaya kawai ba.
Shima ita yake kallo, cikin wani irin yanayin da bai sani ba. Wani abu yake ji a cikin zuciyar shi mai zafi,
zafin da yake ƙona tsokar jikin shi yana tsinka jinin jikin shi ya ƙara gudu. Wani abu mai kaifi ya taso tun
daga yatsar ƙafar shi yazo ya tokare shi a ƙirji kaman mashi. Ɗacin da yake ji a maƙogwaron shi kaman
bai taɓa ɗanɗana wani abu mai zaƙi ba a rayuwar shi.

"Hafsatu kiji tsoron Allah, ki san zaki mutu, dan Allah ki faɗi gaskiya kin ji?" goggo ke roƙon ta Saudat
kam fama take yi da numfashi.

"Ai daman na faɗa. Idan bata ji tsoron Allah ba naki zata ji? Ko kun fi son ta ƙala ma wanda bai ji ba bai
gani ba?" Hajiya Hauwa ta miƙe hannun ta a ƙugu tana girgiza. Gani take yi kaman zaƙewar ta shi zai
daɗa aza ƙasa a kan komai ya bisine shi yanda har abada babu wanda zai iya tonowa.

Zancen mutuwan da aka yi shi ya ƙara firgita Reina ta saka kuka "Wallahi shine. Wallahi yaya Yaseer ne!"

A lokaci ɗaya wuri ya hautsine, ɗaki ɗaya ya karkasu da rikici daban-daban.

A ɓangare ɗaya, fifita goggo ke yiwa Saudat kamal na ƙoƙarin sheƙa mata inhaler kada suyi har biyu
babu, domin Yaseer kam suna da tabbacin a yanzu ta ƙare masa.

A wani ɓangaren kuwa kururuwa Meesha tayi zata yi kan Reina Hajiya Farida ta riƙo ta don babu abinda
zai hana Alhaji Tahir kutubol da ita ta kuskura ta nufe su a halin da ake ciki.

"Wallahi ƙarya kike yi! Munafukar yarinya, an kitsa miki munafurci don a ga bayan shi ko?"

Lafiyayyar mari Hajiya Hauwa ta ajiye mata a kunci tana gwada ta da yatsa. "Ki shiga taitayin ki Wallahi,
kema bari muje gida sai mun duba ki mun gani idan bai gama da ke ba wannan zaƙewa haka.

Ɓangare na ƙarshe, mafi tasiri, wanda a wannan gaɓa, a wannan lokaci, a wannan yanayi, alƙalamin
ƙaddara ta fara rubuta babi na ƙarshe a cikin littafin tarihin nan.
"Wallahi sai na wulaƙanta ka, sai na tozarta ka, sai na ga bayan ka, sai na saka iyayen ka sun yi danasanin
haihuwar ka, la'anannen yaro, sai ka gagara gwada fuskar ka a ko ina saboda ƙasƙanci, sai na ga bayan ka
matsiyaci ɗan matsiyata!!"

Ba don riƙon da yayi ma Reina dake kuka a hannun shi ba da babu abinda zai hana shi sake yi ma Yaseer
lilis.

Laɓɓen bakin Yaseer ke sake zubar da jini saboda yanda ya datsa ta da haƙorin shi, burin shi zafin zai
dishashe azabar wutar dake cin zuciyar shi, amma bayi jin kaman gangar jikin shi na fahimtar wani yanayi
a yanzun.

Kan shi ya sauƙar ganin yanda ake fama da mahaifiyar shi da ta rasa numfashin ta ga yanda suke kuka
kaman ran su zai fita.

Duk shi ya jawo.

Da bai fara ba da ba'a zo wannan gaɓar ba.

Ashe zuciyar taimako na iya kawo maka cutarwa?

Ashe ba ko wani alƙawari ke buƙatar sai an cika shi ba?

Yayi danasanin sanin Hafsatu a rayuwar shi!.

Sauƙe kan shi ƙasa yayi hawaye na bin kuncin shi, yayin da ɗan sandan dake tsaron shi ya ƙara tsananta
riƙon da yayi mishi. Sun cire mishi ankwa ne saboda shiga cikin mutane amma yanzu babu amfanin
hakan sai ya sake cirowa daga aljihun shi ya haɗa hannun Yaseer guda biyu ya garƙame su.
Yana tsaye kawai sai yanda aka yi da shi, kunnen shi na jiyo masa ɗiban albarkar da Alhaji Tahir da ƴan
uwan shi ke masa.

"Ku tashi ku bar min gida matsiyata wa'inda basu gaji arziƙi ba, kotu ne zai raba ni da ku Wallahi. Idan
kuka ga ban rufe shi ba toh wallahi sai idan bani raye, amma sai naga bayan ka" Alhaji Tahir ya gwada
Yaseer da yatsa, kana ɗora ma sauran "mutanen Banza mutanen wofi" shima kukan zuci yake yi, domin
ya tabbata an cutar mishi da Reina, an raba shi da Fauziyya.

Kalaman shi sun yi ma goggo zafi

"Ka san wacece Halime a wurin Kamalu ɗahiru? Hannun mahaifin ka cikin nawa Allah ya karɓi ran shi,
ciwon ajali da ya kama shi bai iya ba sai da ya dawo Jama'are yaga gida yaga Halime, Halime da ƙauyanci
da jahilcin ta ita ta tsaya a kan rabon gadon ku ta tabbatar an fitar da hakkin kowa yanda ya dace. Amma
koran kare kake min saboda an jarrabi ƙarfin zumuncin mu?"

"Kai, ko ke kika haifi ubana albarka! Haba! Sai kace maita?"

A zuciye Kamal yayi kan Alhaji Tahir, su Alhaji Salisu suka shiga tsakani zasu buge shi.

Amma kukan Fauziyya yake ji a cikin kunnen shi, kuka take yi sosai a cikin kan shi.

"Ku fice min a gida kafin in saka a fitar min da ku!" Hayaniyar wurin sai da ya ragu saboda ihun da Alhaji
Tahir yayi, Reina dake jikin shi ta ƙanƙame jikin ta cikin firgici.

"Na faɗa a kunnen shi ya shaida, Allah ya shaida, ina so kuma ku shaida na yafewa Kamalu duniya da
lahira. Idan hakki na ke bibiyan zumuncin yaran shi har suke cutar da junan su ta ƙarƙashin ƙasa na yafe,
Wallahi na yafe har abada"
Ta riƙo Saudat dake kuka Kamal ya taya ta suka bar gidan, ba zasu iya tsayawa su ga yaya za'ayi da
Yaseer ba. Sun bar musu shi suyi yanda suka ga dama, amma sun bada amanar shi ma Ubangiji Azza wa
Jalla.

A wulaƙance suka ja Yaseer bayan iyayen shi sun yi tafiyar su. Meesha tayi yunƙurin bin shi a baya Hajiya
Hauwa ta saka nauyinta ta danne ta.

......

Sai da ya tashi mutuwa musu a cell ranan kafin suka kai shi asibiti aka kula da raunukan shi suka bashi
abinci.

Tun da ya samu kan shi kuma ya duƙufa ma yin taimama yayi sallolin nafila da tilawar Alkur'ani da
addu'o'i kaman yanda iyayen shi suke yi a gida suma ba dare ba rana, Allah ne kawai zai iya fitar da shi
daga wannan gadar zaren.

Kan kace mene har magana ya fara yawo, tunda burin Alhaji Tahir kenan ya tozarta shi. Ya mayar da
hankali a kan biyan mutane a yayata Yaseer a social media a maimakon ya mayar da hankali ga lafiyar
ƙwaƙwalar Reina kaman yanda likita ya shawarce shi.

Tana tsakanin buƙatar ganin likitan ƙwaƙwalwa saboda kada a gaba abinda ya faru yayi mata sanadin
trauma, har yawan suman da take fama ɗinnan ma yana da alaƙa da hakan sosai.

Sai dai suna zuwa sau ɗaya ta gwada mishi bata so ya ajiye zancen a gefe, domin yanzu lallaɓa ta yake yi
kamar ƙawai shiyasa ya bar Maama a wurin ummi na wani lokaci.

A ranar da za'a fara shiga Shari'a kuwa yan jarida sun yi cincirindo don haska fuskar Yaseer a kafofin sada
zumunta . Yawanci Alhaji Tahir ne ya biya su duk da cewa case ɗin ya jawo hankalin mutane sosai a
kafofin sada zumunta , mutane nata tofa albarkacin bakin su jin alaƙar su da yarinyar da ya lalatawa
rayuwa da kuma ƙarancin shekarun ta, kowa na mararin ganin yaya lamarin zai kaya.
Aka shiga zama na farko bayan an gabatar da shari'a guda biyu a gaban su sannan aka gabatar da
Shari'ar su a gaban alƙali, lauyoyin da aka ɗauka ma Reina har guda uku, da ƙyar su Saudat suka haɗa
suka ɗauki lauya guda ɗaya. Sannan sun buƙaci a ɓoye information ɗin Reina daga sunan ta da komai,
haka ma babu buƙatar gabatar da ita a gaban kotu saboda karenta daga idon Duniya da kuma tattalin
goben ta. bayan shi Yaseer mara gata an gama tagayyara shi.

A kan halin da Yaseer ya shiga sun kashe kuɗaɗe har sun ji babu daɗi, ƙarshe har gidan da Kamal ya
samu ya mallaka bayan zaman haya a cikin ta na tsawon shekaru sai da ya ɗaga shi ya siyar, don kawai ya
kuɓutar da ɗan shi.

Dabbobi da gona a ƙauye ma an haɗa an siyar saboda da gangan ake wahalar da su kuma sun riga sun
fahimci a wannan ƙasar kuɗi ke magana ba baki ba, kudi ke aiki ba hannu ba, kuɗi ke bada gaskiya, kuɗi
ke bada ƴanci, amma su nasu kuɗin ya kasa, ƴan canji ne a gaban wanda suke karawa da shi.

Alƙalin da aka gama cikawa aljihu da kuɗaɗe ya daga shari'ar nan da sati biyu, sannan ya buƙaci lauyoyin
ko wanne bangare su kawo shaidu domin kare wanda suke wakilta.

......

Test ya kai ta makarantar kawai amma sai da tayi danasanin zuwa.

Yau har an samu masu tsayawa a gaban ta su gaya mata magana saboda Yaseer. Mutanen da a da ko
cikin ido wasu basu iya kallon ta, amma dan yau kawai Allah ya ga daman jarrabar bawan sa shine ya
dawo musu abun jin daɗi abun izgili?

Ko sallama bata yi ba, da shigowar ta parlon tayi wurgi da hand bag ɗinta zata wuce sama ɗakinta,
mahaifiyarta ta kirawo sunan ta tare da miƙa mata waya.

"Waye ne?" Ta tambaya tana turo baki. Idan mahaifinta ne ma ba zata karɓa ba don bata jin zata iya
jurewa sauraron masifan shi a yanzu.

"Bilal ne."
Har tana tuntube ta ƙaraso ta karɓi wayan ta ƙara a kunne.

"Uncle B" ta kira cikin muryar kukan dake taso mata tun kafin yayi mata magana.

"Ameesha haka zamu yi da ke?" Wata murya mai sanyi ya amsa ta ɗaya ɓangaren.

"Wallahi Uncle B he's innocent. Yaseer is not a horrible person"

"Wannan kuma court ne zata yanke wether he's innocent or not ba ke ba."

"Uncle B na san waye Yaseer, ba zai taɓa yin abinda suke zargin shi ba. Sun fi ƙarfin shi ne kawai Uncle B
don Allah ka taimaka min"

"Shikkenan Meesha, amma kin san everything comes with a price right?"

"Idan ka taimaka mishi ko me kake so zanyi Uncle B."

"That's great. Then I'll get him a good lawyer amma da sharaɗin!... Babu ke babu yaron nan Ameesha,
and ina nufin har abada"

Kukan ta ne ya karu "Don Allah Uncle B!. Zan iya canza course ko wani abun amma banda wannan. Ina
son shi Allah."

"Shikkenan, sai ki bari idan ya gama serving time ɗin shi a jail ya fito ku cigaba da soyayya ko?"
Hakan ma shawara ne. Amma tayi ma Yaseer adalci? Koda ace ta shirya ma zaman jiran shi amma goben
shi fah?.

Yana shirin katse kiran tace "naji, ka sama mishi lawyern zan rabu da shi"

"Good girl" shine Abinda yace kana ya kashe wayan daga ɓangaren shi.

......

“Wannan kotu, bayan ta saurari kwararan bayanai daga bangarorin biyu, da shaidu da rahotannin lafiya,
ta tabbatar da cewa Yaseer Kamal, wanda ke ɗan uwan jini ga wanda abin ya shafa, ya aikata ƙoƙarin
fyade ga yarinya ‘yar shekara tara.

Wannan kotu tana ɗaukar wannan laifi a matsayin wani abu mai matuƙar muni, wanda ya keta doka,
zumunci, da kariyar da yara suke da ita a bisa doka.

Bisa la’akari da sashe na Penal Code da kuma dokar VAPP da Jihar Bauchi ta amince da ita, wannan kotu
tana yanke maka hukuncin shekaru sha biyar a gidan gyaran hali, ba tare da yuwuwar beli ba.”

"Alhamdulillah" shine kawai kalmar da bakin shi ya samu daman furtawa. Idanun shi a rintse har Yan
sanda suka ɗauke shi daga gaban kotu, cikin sanyin jiki yake bin su. Ihu da kuka daga bangaren iyayen shi
da ƴan Jama'are da suka zo mara masa baya ya kankama, har suka wuce da shi idanun shi na kallon ƙasa,
ba zai iya haɗa idanu da ɗaya daga cikin iyayen shi ba.

......
"Daddy... Daddy Wallahi ba yaya Yaseer bane, ƙarya nayi daddy....."

......

"Wannan expulsion letter ne, sun kori Yaseer daga makarantar.

~~~~~~~~~~

Hmm... Sannun mu.

Zaku sami littafi na biyu a kan 500 posting. Document kuma 1k. Ta wannan account 8021689184 Saliha
Ahmad Na'ibi opay, sai a turo shaidan biya ta wannan number 08021689184.

*Seemahwrites ✨*

*REINA 💍*
39..... WAIWAYE.

"Ah ah, Halime ta Kamalu, yanzu ɗaukar ɗanwaken kika yi kika ba shi?" Dattijuwar da ta shigo ɗauke da
kunu mai zafi a cikin kwanon sha ta tambaya, kana ta dire shi a gaban Halimen dake kishingiɗe a kan
shinfiɗin da aka yi mata saman tabarma hannun ta na ɗama a daure.

Kariya ce ta samu a sanadin ƙwatar Kalabu da taje yi a hannun kamalu lokacin da ya ɗauko tabarya zai
rotsa ma yaron saboda yanzu kuntalancin sa har ya kai yana saka hannu cikin aljihun uban shi yana masa
laluɓe.

Shine aka rasa mai shiga ukun da zata shiga tsakani sai ita dai Halime tsugudidi kaman yanda suka laƙaba
mata a gidan, don ita komai da ruwan ta.

ta kuwa yi Sa'a ya sauƙe mata taɓaryar a hannu, a take ya raba mata ƙashin wurin gida biyu. Sannan
yanzu a tare suke jinyar, ba wai raba zafi ko taya ta ɗawainiya yake yi ba A'a, duk abinda ta samu ne dai
nasu ne su biyun, duk abinda aka kawo mata na taɓawa tare zasu ci.

Koda ace bayi kusa ta samu abin daɗi zata rage masa, a dalilin haka bayi fashi kullum sai ya zo dubata a
ƙalla sau biyu zuwa uku a rana, ita kuma a tunanin ta ƙauna da yan'uwantaka ne hakan, har yake barin
iyalan shi da kasuwan shi ya zo ya kasance tare da ita saboda danasanin abinda ya faru da ita da ya kasa
barin shi.

Da wuya ka taɓa jin Halime ta ƙyalƙyala maka da dariya. Ko tatsuniyoyin nishaɗi ake yi haka zata yi ɗan
dariya kaman nishaɗin bai kai zuciyar ta ba, tayuyu tafi kowa jin daɗin ta kuwa saboda ita mutum ne mai
son ko yaushe ta kasance cikin nishaɗi bata son taga wani yana ƙunci a kusa da ita balle ita da kanta.
Amma kunya, kawaici da sanyin hali su suka yi mata ƙawanya, har aiki idan kana son kaga saurin shi toh
gwanda kayi kayan ka da ka haɗa Halime da shi, duk da cewa bata da ƙyuya kuwa.
A yanzun ma murmusawa tayi irin nata ita kaɗai, "Inna wai bayi son ɗumame ne yau ɗin, ya gaji da cin ta
kullum"

Kuma shine ya haɗa iyalan shi da ɗumamen? Yazo yana cinye wa mai jinya abinci?.

Amma dake duk jirgi ɗaya ya ɗibo Halime da mahaifiyarta sai cewa tayi "Allah sarki, to ga wannan kunun
ki sha da ɗumin sa, zai riƙe miki ciki"

A lokacin Salisu yayi Sallama da ƙullin sugar a hannun shi ya miƙa ma Innan Halime.

Kallon ƙullin sikarin Naira ashirin tayi, tana mamakin ko har ya sake tashi ne haka? Wannan tsadan
rayuwa dai Allah yayi mana maganin shi.

Karɓan sikarin tayi lokacin da idanun ta ya sauƙa a kan Naira biyar ɗin dake gaban aljihun rigan Salisu da
ya sha mandaƙo.

Sai ta murmusa Kawai, ta manta ne shi bayi zuwa aika sai za'a biya shi, idan kuma baka bashi ba toh zai
ɗauka a cikin kuɗin aikan ka.

"Nagode" tace da Salisu alaman yayi tafiyar shi amma hankalin shi a kan mahaifin shi dake suɗe kwanon
ɗanwake kaman yana son ya ga maƙerin ta.

Halime ma kallon shi take yi, sun yi da shi a kan zai ci rabi ne ya bar mata rabi saboda tana jin yunwa,
kuma ta san mantawa yayi ya cinye don akwai shi da yawan mantuwa.

"Baba sammun" Salisu ya miƙo masa hannu daga nesa yana tsoron ƙarasawa kusa Kamal ya riƙo shi ya
lakkaɗa masa na jaki. duk da ya gani babu komai a cikin kwanon samiran amma ko ɗan maiƙon ne shima
a ɗan bashi ya lasa.
Mummunan harara ya watsa mishi wanda ya saka Salisu ɗibawa a guje, kafin Kamalu ya fara jan baki
saboda yajin da aka baɗa a cikin ɗanwaken ya fi ƙarfin harshen shi.

Cikin hanzari ya sunkumi kwanon kunun da Inna ta gama zuba ma Halime sugar ko gaurayawa bata yi ba,
ya saka ludayin ya gauraya da sauri-sauri sannan ya fara sha ba ƙaƙƙautawa.

Taɓe baki Inna tayi tace "Ku kuka fi kusa" sannan ta fita waje ƙarasa wankin da kullum Safiya Halimen ne
ke musu tare don ita kaɗai Inna wacce take amarya a gidan ta samu ta haifa kafin mahaifin su ya kwanta
rashin lafiya, shi yasa Halime ta tashi da son sauran ƴan uwan ta a ranta, kasancewar ta ita kaɗai a nasu
ɗakin.

Bai fi ludayi biyu ya rage mata ba shima don kada ta ga zalaman shi ne, ya ajiye kwanon yana goge bakin
shi da bayan hannu, sannan kunun da ya shafu masa a bayan hannun ya goge a jikin afaferan ɗin jikin
shi, yana fitar da kakkaurar gyatsa mara daɗin sauraro.

Sai dai idanun Halime dake kan Kamalu babu komai a cikin su bayan so da ƙauna irin wanda Allah ke
sanyawa a cikin jini ɗaya.

Kallon babban wa majingina take mishi, kallon shi take yi a matsayin gatan ta, wanda idan yaji daɗi ya
samu wadata itama tana da tabbacin zata ji daɗin rayuwa cikin wadata.

"Gaskiya kin ciyar da ni ƴar ƙanwata Allah ya biya ki" yace tare da miƙewa zai tafi kasuwa, tana mishi
addu'ar Allah ya tsare ya bada kasuwa mai albarka, ba don raunin ta ba ma da rakiya zata yi mishi har
ƙofar gida kaman matan da ya ajiye har guda biyu basu isa ba.

......

Gidan su yana da girma sosai, domin mahaifin su babban manomi ne kuma ya ɗan taɓa tashen kuɗi a
lokacin su, don haka ya yanki ƙaton fili ya zagaye shi, a hankali ya dinga tada gini sashe-sashe sai ya saka
ƙannen shi ko ƴan uwa a ciki idan kayi naka sai ka tashi wani ya shiga.
Haka har yaran shi suka tasa suka fara aure wurin zama bai zamo musu matsala ba, sai dai yanzun da
mahaifin ƙarfin shi ya ƙare ɗan abinda ya tara ma yana niman ƙarewa a kan jinyar shi, sai aka ɗauki
manyan gonakin da yake da su aka yanka mo kowa fili ya shuka abinda zai ci da iyalan sa ya siyar da
saura.

Kasancewar Jama'are suna daga cikin wuraren da Allah yayi ma ƙasan su albarka, girbi tana yin kyau
sosai musamman ta shinkafa.

Sai dai cikin masu noman nan babu Kamalu, wanda shi kaɗai ne mai zalaman mata biyu duk cikin ƴan
uwan shi duk da bayi da halin riƙe su kuwa. Ya nemi wanda ya karɓi hayan gonan kana da kuɗin ya je ya
kama shago a bakin kasuwa don shi yana ji a jikin sa arziƙin shi na cikin kasuwanci ba noma ba.

.....

A sannu lokaci yake tafiya ma Halime mai karaya tana zaune a gida sauran sa'annin ta suna zuwa
makaranta har aka zo zana jarabawar gama primary bata koma ba, haka suka zana suka bar ta, kuma
daga nan shikkenan babu ƙarawa gaba sai dai aure. daman kuma karatun ba daga farko ta fara shi ba,
don sai da mahaifin ta ya kwanta jinya kafin mahaifiyarta ta rufe Ido ta saka ta a primary 2 lokacin, ta
kasance mace ta farko a gidan da ta fara zuwa makarantar boko.

Yanzu tana da shekaru 14, tsarar ta sun fara tsaida mazajen aure amma ta so ko da certificate ɗinta na
primary ta riƙe, tunda ci gaban da take so ba mai yiwuwa bane. Shima yanzu Kamalu yayi mata sanadi sai
ta maimaita ajin ƙarshe.

Da ita da mahaifiyar ta masu lura ne da sun fahimci tun fara jinyar ta sau ɗaya Kamalu ya kawo mata
kaza guda ɗaya aka yi mata farfesu ya zo suka shanye tare, amma ko Naira 10 ya fahimci halime tana da
shi sai ya roƙeta ta bashi aro zuwa ya fita yayi ciniki, kuma ba zai taɓa biya ba idan ba ta cire kunya bane
ta tambaye shi.

Ba wai don tafiyar tayi daidai ba, sai don kawai ɓangare ɗaya ke nuna ƙauna Saboda Allah, ɓangare ɗaya
ke bada yarda, ta aminta ana tauye ta don kawai tana tsoron warwarewar alaƙar da ɓangare ɗaya ne
kawai ta ƙulla ta, don tana jiyar da ɗaya bangaren daɗi shi kaɗai.
Amma ƙaunar dake tsakanin Halime da Kamalu ta zama gaban kwatance ma duk wasu ƴan uwa dake
Jama'are, mutanen da ke zagaye da su kuma gani suke yi babu mai moran Kamalu sai Halime shiyasa
take son shi haka. A wannan dalili ta fita kan matan shi masu ganin su da hakkin su yake wuyan shi fama
suke yi amma ya je ya buɗe bakin aljihu ma wata Halime, shiyasa da ta karye ko ita uwar kalabun bata
iya zuwa ta duba ta ba, sai aikan shinkafa da mai can ƙasan roba da tayi mata sau biyu.

Bata fita daga wannan jarabawar ba rana ɗaya suka wayi gari Allah yayi ma mahaifin su rasuwa.
Mutuwar sosai ya taɓa Halime kasancewar ita da mahaifiyar ta ne a jikin jinyar mahaifin su, ta saba da
shi sosai.

A kwana na huɗu da rasuwa rikici ya tashi a kan gado. Ƙannen Kamalu suka tashi zasu dake shi sai da aka
shiga tsakani saboda umartan su yayi da zasu bar gona an samu wanda zai siya har da shukan su dake
cikin ƙasa sai a raba kuɗin.

Aka yi ƙoƙarin danne shi dole ya haƙura zuwa lokacin da suka girbe hatsin su sai a raba gado mai niyyan
siyarwa ya siyar.

Washegari sai gashi da masu ganin gona, ya ɗaura aniyar sai ya siyar duk abinda zai faru ya faru tun da
takardan su na hannun shi. Ganin za'a yi biyu babu aka yi rabon gado a take, sannan aka ce mai siyan
gona sai ya bi masu ra'ayin siyar masa idan zai iya haƙurin sai sun yi girbi kafin ya karɓa.

Duk cikin su babu wanda yake da ra'ayin siyarwa tun da yana biya musu buƙatun su na yau da kullum har
da ƙari, sai Kamalu kawai da kuma Halime da ya lallaɓata ta bashi nata kason ya haɗa ya siyar.

Ta sha mamakin ganin zunzurutun kuɗi har dubu ɗari uku a gaban ta, Kamalu ya ajiye. Dubu ɗari uku da
hamsin aka siya amma ya riƙe hamsin ɗin lada.

Haka suka ɗauki wani dubu goma suka damƙa mishi kuma babu kunya ya saka hannu ya karɓa.
Ƴan uwan Mahaifiyar Halime suka shawarce ta a kan ta fara yiwa halime kiwo da dukiyar ta ko ta bayar
ana juya mata saboda ajiyan kuɗi haka hatsari ne. Ta kuwa aminta da shawarar nan aka siyo shanu har
da raguna da kaji aka saka a ɓangaren da ya shiga gadon su biyun a cikin gidan.

Shi kuwa Alhajiji Kamalu kwanan mahaifin shi 50 a cikin ƙasa ya ƙaro aure a karo na uku, yarinya
kyakkyawa har halime ta bata shekara guda. Sannan sauran kuɗin ya shiga wani kasuwancin da shi,
yanzu har cikin Bauchi yake kai bandan kifi.

A can ne ya haɗu da wasu da suka yi masa alƙawari zasu dinga karɓan kaya a wurin shi suna fitarwa
ƙasashen da muke maƙwaftaka da su Amma kuma wanda yake kawowa yayi kaɗan sai ya ƙaro.

A fujajan ya koma gida ya saka ɓangaren da iyalan shi ke zaune a kasuwa, ganin yana matse aka mishi
tayin wulaƙanci, bai damu ba saboda ya san arziƙin shi ne yake kusa, don haka ya zuba kuɗi ya sayi kaya
ya bawa mutane suka yi tafiyar su.

Daman shi kaɗai yake hidiman sa, don haka ko da asarar ta hau shi Allah sarki kawai suka yi mishi. Gashi
ya rasa muhalli don lokaci ɗaya mai wuri zai iya buƙatar ya tattara ya tashi, gashi ba kuɗi babu kadara ga
amarya dake da ciki haihuwa yau ko gobe.

Kamalu sai da yayi ciwo kaman ba zai tashi ba.

Babu daɗewa amarya ta sintimo ɗan ta namiji aka raɗa mishi Ɗahiru da ragon da Kamalu ya ara cikin
garken Halime, ta bashi ba tare da wata damuwa ba duk da ta sani ba Lallai ya biya ba amma cikin ranta
ta saka ta bar mishi kyauta domin idan yayi kuɗin da yake faɗan nan zasu ji daɗi dukkan su.

A koda yaushe idan suka zauna labarin irin kuɗin da zai yi yake bata ita kuwa bata gajiya da sauraron shi
cike da alfahari.

A yanzu ma suna zaune ne yana cin alalen da ta siyo masa da zata zo duba shi, hannu baka hannu
ƙwarya yake magana, ko tauna alalen baya yi yanda sulɓin ta yasa wucewa kawai yake yi, ga yajin ya ji
farin maggi.
"Hmm ..shh... Halime Kinga masu kuɗin nan daga kiji ɗan tata sai ɗan gwate, toh nima ɗan ƙanzo ko ɗan
alale zan zama"

Santin alale ne Halime ta sani, don haka ta murmusa kawai.

Ƙanwar shi talatu da ta ɗaga labule ta shigo tace "ko ɗan yaji ba! Ji yanda kake faman jan baki kamar
mace Yaya"

Ta ɗaga labulen yanda haske zai daɗa wadatan ɗakin kafin ta nemi wuri ta zauna tana share mummunan
kallon da yake watsa mata ta dubi Halime.

"Wato Halime tsugudidi ya zauna yana lallaɓaki ki bashi gadon ki ko?"

~~~~~~~~~~~

Please To be clear document sai an kammala haɗa labarin kafin a same shi, wanda basu samu a lokacin
da ake posting bane idan an haɗa document kuɗin shi daban. Amma mai son sai an gama zai iya biya ya
jira.

Zaku sami littafi na biyu a kan 500 posting. Document kuma 1k. Ta wannan account 8021689184 Saliha
Ahmad Na'ibi opay, sai a turo shaidan biya ta wannan number 08021689184.

Ƴan Niger kuma zaku turo katin Airtel na 300fcfa posting, document kuma 600fcfa.
*Seemahwrites ✨*

*REINA 💍*

Book 1

Saliha A. Na'ibi (seemahwrites)

_Women of words writers association_

40(End)...... Kaman ta san abinda ke zuciyar kamalu kenan, kuma yana da niyyar tunkarar Halime da
zancen amma ya rasa ta inda zai fara don haka shi hanya tayi mishi.

"Ta bani gadon ta kaman yaya? Ni ban kare mata dukiyar ta ba sai in karɓe?" Ya kintime fuska yana
watsa ma Talatu harara, Halime sai faman murmushi take kawai.

"Au, wai na san hali ne shiyasa."


"Ni bani son haɗa wuri, haka zaku ganni ku barni da ƙanwata, idan tayi niyyar ara min dukiyar ta don in
nima na kaina laifi ne?" Shanya baki kawai talatu tayi tana kallon shi, na sakwan guda ta ɗauka Kamalu
sauya hali yayi.

Sai ya juyo ya dubi Halime "Ko bari na zaki yi in yi ta fama bayan jarabawar da ya faɗa min Halime na?"
Ɗago idanun ta tayi ta zuba mishi, tun kafin ya isa wurin da yake son zuwa ta harbo jirgin shi, amma
kaman buƙatar tashi tayi wa sikelin kyautatawar ta nauyi.

Sai ya saka fuskar tausayi ƙwalla na taruwa a idanun shi, ya riƙo hannun ta biyu cikin nashi ya ɗan matse
su yanda zai yi saurin narka mata zuciya.

Talatu dai tana zaune tana kallon ikon Allah, ƙarshen sakarcin Halime take son gani a yau, idan har zata
iya saka rayuwar ta a kwale-kwale saboda son zuciyar Kamalu.

Ya ci gaba da cewa "Ga mata da yara ko sana'ar riƙe su bani da shi, ki taimake ni ƴar ƙanwa ta kin ji? nayi
alƙawarin zan dawo miki da abinda na karɓa harda riba a kai wallahi, kuma ba zan yi miki wasa da gado
ba, wannan da ya faru ma tsautsayi ne."

"Toh zan faɗawa Inna" ba ƙaramin tausayi ya bata ba .

"Innalillahi wa inna ilaihirrajiun!" Talatu ta tafa hannuwa cike da al'ajabin jin yanda ta amsa kai tsaye.

"Halime! Hankali wala ko?"

Murmushi mai sauti tayi tace "toh Addah meye amfanin kana da shi idan ɗan uwan ka na cikin wahala?
Ko rayuwata yaya ya buƙata zan bashi bare abin duniya mai ƙarewa"

Ta jinjina kai. "Allah ya kyauta" kana ta zaro kuɗi bandir ɗin ƴan ɗari biyar-biyar ta zare guda biyu ta miƙa
ma Halime, ta karɓa tana nanata godiya.
sannan ta zari wani biyun ta miƙawa Kamalu.

"Haba ke kuwa talatuwa na? Yi haƙuri ki ƙaro wasu biyun ko ki bani aron ko dubu biyar ne, Allah zan
maida miki cikin ƙanƙanin lokaci" ya yunƙuro kaman zai fisgi sauran daga hannun ta.

Tusa kuɗin ta tayi cikin jaka ta maƙale shi a hammata domin idan bata yi da gaske ba bazata fita da su
daga ɗakin nan Lafiya ba tunda Kamalu ya gani.

"Ka gani kuɗin hayan gona ne aka biya ni bana ban samu damar yin noma ba shiyasa ba wasu kuɗaɗe
bane a wuri na. ka samu ma tunda kai duk shekara ko abin naira 50 baka iya yiwa kowa a cikin mu" ta
harare shi.

"Allah ɗawainiya ne yayi min yawa abinda nake samu ko nima bayi isa na, amma na samu mai yawa
kema kin san duk zaku ji daɗi"

Haka yayi ta mata magiya bata bar ɗakin ba sai da ta samu kanta da ƙara masa wani dubun.

Ta miƙe tana yatsina fuska "Sai kace wani ne ya ɗaura maka! Ka san ba zaka iya ba ka auro su?"

Bai ce da ita komai ba tunda dai ta bayar, tayi masa sallama da Allah ya ƙara sauƙi ta bar ɗakin sannan ya
koma lallaɓa Halime, a ƙarshe dai bata bar ɗakin ba sai da ya karɓe dubun wurin ta kafin nan.

Ta ji nauyi sosai kafin ta tunkari Inna da buƙatar Kamalu, bata ƙi tata ba tunda yace aro ne kuma juyawa
zai yi amma tace ta bari ta shawarci ƴan uwanta tukunna.

Ko da wasa basu amince da zancen ba, yarinya marainiyar Allah gashi a ko wani lokaci Allah ya kawo
mata miji zata yi aure shine zasu ɗauki sauran abinda ya rage mata su bawa wani gardin banza?.

Halime ta samu Kamalu ta faɗa mishi yanda aka yi, Bai tsammaci hakan ba domin har kasafin yanda zai
yi da kuɗin yayi, har ya samu masu siyan dabbobin Halime da ɓangaren su da take kiwon ma.
Kamalu ya shiga tashin hankali sosai, ya dinga jigila ma Inna da Halime har wurin yayun innan sai da yaje
suka fatattake shi amma bai haƙura ba.

Sai gashi da wasu mutane wanda ya samu zasu dinga sarin shinkafa a hannun shi suna fitarwa kudu ga
uban riban da zasu samu saboda kayan abinci ya fi tsada ta can.

Babu yanda Inna da Halime suka iya haka Kamalu ya danne su suna gani aka fice da dabbobin Halime ko
ƴar kaza ba'a bari ba. Wurin da aka yi kiwon ma ya je aka yi mishi takarda ya zo ya tursasa su suka saka
hannu wani sabon ango ya bashi kuɗin sannan ya shiga kwaskwarima ma amaryar shi.

Ya dawo babu Abinda suka tsira da shi bayan ɗakin da suke kwana a cikin ta, ga hanyar samu lokaci ɗaya
ya tsaya musu, don ma ƴan uwan Inna masu ƙoƙari ne, su suke ciyar da su shiyasa Halime ke tsammanin
nata ƴan uwan ma zasu kasance haka.

Kamalu aka shiga business ɗin shinkafa fakafaka kuma da gaske ana samu ɗin. Domin ba zallan nashi
mutanen suke karɓa ba, tireloli suke cikawa suna kaiwa kamfani a gyare su a siyar a farashi mai kyau.

A hankali ya dinga taro musu mutane ana bashi kwamisho, kusan duk manoman shinkafa a Jama'are
dama masu zuwa garin su hayi gona suyi shuka duk suka koma bawa kamalu amfanin gonan su saboda
lokaci ɗaya za'a biya ka kuɗi a dunƙule kuma suna kamanta siya da daraja, kan kace mene farashin abinci
ya fara hauhawa a Jama'are saboda kowa ma siyarwa yake yi wa masu kuɗi, don haka suka bunƙasa
kasuwar su zuwa sauran ƙauyuka da suke makwaftaka suma ana saye nasu.

Da suka fara aminta da shi sai ya buƙaci yana bin su, da alƙawarin zai yi musu hanyar bandan kifi shima.

Allah mai azurta wanda yaso ba tare da hisabi ba, sai ya saka ma niman Kamalu albarka wanda ya fara
shi da dukiyar marainiya da niyyar zalunci, domin har a cikin zuciyar shi bai ji cewa zai biya Halime
kwanan nan ba, hala sai ya zamo wani hamshaƙin mai kuɗin tukunna.

Halime na cika shekara 15 wani ɗan makwafcin su ya turo tambaya. Basu bada rana ba sai da suka
tambayi Kamalu da yanzu zaman Jama'are ya fara gagaran shi. Ya faɗa musu a saka babu matsala zai yi
ma Halime duk wani abun buƙata, shi da kan shi ma ya bada lokaci aka saka tunda a yanzu shine waliyyin
ta, sannan bayan kwana biyu ya ƙada bujen shi yayi garin plateu, domin wani sabon kasuwancin
ma'adanai ma ya buɗe musu ta can.

Lokacin biki ya ƙarato, samun Kamalu a waya yayi wuya ma Inna, ko da ta tuntuɓi iyalan shi ma suma
shaida mata suka yi rabon su da shi tun tafiyar shi sai dai ta samu Maman ɗahiru hala.

Haka ta ci gaba da haƙurin jira har sai da biki ya kasance sauran sati guda Halime ko buta ba'a siya mata
ba kafin Inna tayi ƙarfin halin tunkarar Amaryar shi ƴar cikin ta, ta roƙe ta da ta kira mata Kamalu, cikin
Sa'a kuwa ta same shi saboda da ya canza layi ma ita kaɗai ya bada lamba, harƙan tonan kuza ya shiga
sosai a jos kuma yana gane mishi don haka shi ko ranar dawowa gida ma bayi da shi.

Ya dinga rantse-rantse ma Inna da ta tuhume shi da alƙawarin shi da kan shi zai ɗauki halime suje shagon
kayan ɗaki a Kano ta zaɓi wanda take so tunda akwai kuɗi yanzu ba sai an yi wahalar jiran kafintoci ba.

Inna ta yarda da shi, cike da jin daɗi taje ta sanar ma ƴan uwan ta suma suka yarda har da taya ta
murnan za'a yi ma Halime kayan ƴan gata. Itama Halime ba ƙaramin daɗi taji ba sai ta sami kanta da taɗa
ma ƙawaye don haka kowa ya zuba idanun gulma a kan bikin ta.

Sai dai har an fara shagulgula babu Kyallin Kamalu ko wani aika daga gare shi. Har kiran maman ɗahiru
ya daina ɗauka, ya ce dai ta faɗa ma Inna ko a ranar bikin ne dai zo musu da komai ayyuka ne suka yi
mishi yawa a yanzu.

Sun fara sarewa don haka aka haɗa abinda ya samu daga gudumawan ƴan uwa aka siya ma halime
abinda ya samu da fatan Kamalu zai cika alƙawari.

Ƙarshe dai ƙanin shi mai bin shi ne ya bada auren Halime kuma har yamma basu fidda tsammanin ganin
Kamalu ba har saida aka zo tafiya da ita ɗakin ta.

Ƴan gulma sunyi har sun gaji, Halime da mahaifiyar ta sun yi kuka har sun gode ma Allah. Haka aka kai ta
ɗakin miji daga katifa sai laidar tsakar ɗaki da ƴan robobin aiki.
Tukwanen girki ma ba'a iya siya mata saiti ba saboda gudumawar ƴan uwan inna da shi aka ciyar da ƴan
biki.

Wannan ya wuce, Kamalu da ya tashi dawowa bayan shekara guda bai zo ma halime dake ɗauke da cikin
wata tara da komai ba bayan kalmar haƙuri a kan harshen shi, sai kuma alƙawuran da ya rubuta su a kan
ruwa, bai sani ba dai ko Halime tayi ma ruwan kallon tawada ne don ya gani a cikin idanunta ta yarda da
shi.

Bai samu barin garin ba ta suntumo ɗanta namiji, sai tsintar zance na yawo Kamalu yayi wai tayi mishi
takwara. Ana gobe suna ya cire naira dubu biyar ya bawa maman ɗahiru ta bata ya tattara ya gudu.

Amma duk wanda yazo sunan Kamal sai da Halime ta gwada masa dubu biyar ɗinnan da sunan yaya
Kamalu ne ya bawa takwaran shi, sai kuma zani da Maman ɗahirun ta bata, amma sauran matan shi ko
biyar.

Ba'a ɗauki lokaci ba yazo da sunan ɗaukan iyalan shi su bar Jama'are baki ɗaya, ya gama ginin shi a cikin
Bauchi. Ƴan uwa aka tattaru zuwa mishi murna, kawunan su sai da ya kusan tarwatsewa ganin irin girma
da kyawun ginin da Kamalu ya ɗaga.

Amma tun daga wannan Ranar ganin shi a idanun su ya ƙara musu wuya. Domin yakan yi shekaru biyu
ko fi bai leƙo ba, sannan sai ka tattari ƙafa tun daga Jama'are kaje gidan ace maka basu nan haka dole
zaka juyo, koda Halime ce kuwa.

Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya, Kamalu na daɗa arziƙi da hakkin Halime a kan shi wanda bayi da niyyan
sauƙewa, yaran shi ma suka tashi da zafin nema ta ko wacce irin hanya amma babu kaman ɗahiru domin
shi tun da ƙananun shekarun shi ya san yanda ake juya biyar ya koma goma, gashi yana da ɗan maƙo irin
na uban ba kaman su kalabu da idan suka saka kuɗi a gaban su sai sunga bayan shi ba.

Kamalu bai tashi waiwayan Halime ba sai da mutuwa ta ƙwanƙwasa mishi kofa, a wannan lokacin
tausayin shi yasa yafe mishi duk abinda yake tsakanin su. Kaman yanda tayi tsammani yana mutuwa
rikici ya tashi a kan gadon shi kasancewar yaran shi 7 sun raba uwaye.
Yayi aurarraki bayan komawan shi Bauchi amma duk babu wanda sauran matan suka bari yayi lasting,
kuma ko kin samu ciki da boka da taggu sai sun zubar da shi, har Maman ɗahiru ma basu barta ta sake
haihuwa ba. amma duk da haka sai da suka tada tarzoma a kan gadon yaran su.

Saboda wasiyyar da kamalu ya bari aka ɗaura Halime a kan komai kuma tayi iya ƙoƙarin ta wajen ganin
an yi adalci ba'a tauye ma ɗahiru hakkin shi ba domin shine mai ƙasa da shekaru 18 a lokacin.

Kuma Ɗahirun shine Allah ya zaɓa domin da ya tashi yin dukiya sai da ya ninninka mahaifin shi ya dawo
shine ƙarfin sauran ƴan uwan sa baki ɗaya, har suka yi ƙwarin suna a baki ɗaya Nigeria da kewayen ta.

~~~~~~~~~~~

Halime ta yafe hakkin ta amma Yaseer fah?

Ina makomar rayuwar shi da aka gurɓata?

Ina makomar goben shi?

Ina makomar goben Hafsatu Reina?

Shin mummunar ƙaddaran da ta shiga tsakanin su zata ci gaba da bibiyar su kokuwa?

Waye uncle B?

Yana da wani tasiri a cikin rayuwar su?

Mu haɗu da ku a littafi na biyu domin cakwakiyar yanzu aka fara. It will be available on arewabooks by
12/07 and on WhatsApp by 14/07.
Ina miƙa saƙon godiya da jinjina ma Aunty Nafisa usman tafida @Maman Maama⁩

Alkhairin Allah ya kai miki a duk inda kike. You're such an amazing woman with a heart of gold. I wish
you all the good things in this world and hereafter ❤️.

Zaku sami littafi na biyu a kan 500 posting. Document kuma 1k. Ta wannan account 8021689184 Saliha
Ahmad Na'ibi opay, sai a turo shaidan biya ta wannan number 08021689184.

Ƴan Niger kuma zaku turo katin Airtel na 300fcfa posting, document kuma 600fcfa.

*Seemahwrites ✨*

You might also like