You are on page 1of 286

SADAUKARWA

Na sadaukar da wannan xan littafi ga iyaye na kuma iyayen qasa,


waxanda suka jagoranci jama’ar wannan gari cikin sha’anin siyasarta da
addininta :

1- Sarkin yaqi Usmanu Babale


2- Sarkin Kudu Salmanu
3- Sarkin Kudu Muhammadu
4- Sarkin yaqi Muhammadu Maidawa
5- Liman M. Idrisu
6- Liman Malam Ali Dawa
7- Liman Malam Garba Xandibi
8- Liman Malam Gero

Da fatan Allah ya gafarta masa, ya haskaka makwancinsa. Ya yi wa


zuriyya ta sa Albarka, amin.

1
GABATARWA

A ran wata litinin ce, cikin shekarar 2013, harkar kasuwanci na ya rufe
ni a shago, don ranar kasuwar garinmu kenan. Sai ga wasu ’yan aike, daga
cikin dattijan gari, daga fadar sarkin yaqi Muhammadu Maidawa xan
Usmanu, suna min albishir cewa, an sanya ni xaya daga cikin limaman
babban masallacin jumma’ah na sarkin yaqi. Sai kuma lokacin ya dace da
tuve wani daga cikin limaman masallacin, saboda larurar tavuwar hankali.
Na ce ni a gani na, zai fi kyau a gyara masa kura-kuransa, a barshi a
matsayinsa. Suka ce, na yi haquri da wannan magana kurum, wannan
hukunci an riga an yanke shi cewa ba zai dawo ba. Suka tilasta sai dai na
bar abin da na ke yi na bi su mu je wajen liman, daga can mu isa wajen
hakimi. Da muka je, a ran nan ya xora min nauyi biyu : nauyin limanci da
karantarwa a masallaci, kana yana son na rubuta wani littafi dangane da
tarihinsa, da tarihin wani abu da ya shafi wannan gari na mu, mai albarka.
Na buxe baki zan yi magana, aka hana ni, aka ce ayi addu’ah, aka watse.
To, bayan na je na yi dogon tunani, tare da shawara da manya na. Sai na
dawo, na ce, don rubutu dai in an nemi na yi, sai na yi. Amma in zavin rai
na ne, ina ganin zai fi kyau a samu wani wanda ya yi zurfi cikin ilimin
boko ya gabatar da wannan muhimmin aiki, ba iri na wanda bai yi zurfi
cikin ilimin boko sosai ba. Kuma ina ganin ban yi qarfin da za’a xora min
nauyi irin na limancin gari ba, saboda dalilai biyu. Dalili na farko ga ni
yaro, ga wauta irin ta quruciya wacce ba ta gama sake ni ba. Babbansu
kuma a gani na, ban yi zurfi cikin ilimin da zan iya riqe gari ba. To, idan na
yarda na karva, waxanda ba su san iyakar matsayi na ba, sai su xauki
rawanin girma, su sa min, duk abin da duk na yi, ba za su duba quruciya ta
ba, sai nan da nan a gane ajizanci na, kuma ayi ta yayata kura-kurai na
komai qanqantarsu, ayi ta cewa kun ga irin aikin limamin Sarkin yaqi.
Dalili na biyu kuma, shi wannan masallaci, an bar shi ’yan Shi’ah sun yi
kaka-gida a cikinsa. Yanzu idan na zo na kafa karatu, karatu na zai riqa cin
karo da na su. Na su kuma na cin karo da nawa. Qarshe za mu koma suna
zagi na, ina zaginsu. Suna mayar min da martani, ni ma ina mayar musu,
wannan fa ko na sani, ko ban sani ba. Su ma ko sun sani ko ba su sani ba.
Domin mavuvvugar littattafan su na Shi’ah da na mu na Ahlus Sunnah sun

2
sava da juna tun daga tushe. Wanda bai fahimta ba kuma, zai ce ka ga da
wurin nan na zaune lafiya, amma tun da malam wane ya zo, zaman lafiya a
wurin ya gagara. Kuma ina da sanin halin mutane duk lokacin da suka xora
ka a sama, to, su ke fara hango tsiraicinka, su yi maka terere. Sai na ga in
har na yarda na karvi wannan aiki, to, na ruxi kaina kenan. Na sa rigar da
ba tawa ba. Kuma na kai kai na kenan inda Allah bai kai ni ba. To, tun
daga lokacin da na yarda zan yi rubutu, daga san nan ne na fara cin karo
wahalhalun samun littattafai, ko wasu maqaloli, ko wasu dattijai da suka
san tarihi ko wani bayani game da tarihin wannan gari. A taqaice dai duk
wani dattijo da na nemi bayani a wajensa, ba na samun cikakken bayani,
mai gamsarwa. Domin riqe abubuwan tarihi, ba ga shekaru ya ke ba.
Wannan kuma shi ya qara min qarfin gwiwar in tashi a tsaye in yi wani
gagarumin bincike, in sadu da manya ma’abuta shekaru, da masana ilimin
addini da na zamani, don samun sahihin tarihin faruwar wannan gari. Don
tattara bayanan da ’yan baya za su zo su amfana da shi. To, alhamdu
lillahi! Ina farin cikin gabatar da wannan xan littafi wanda na raxawa suna
‘Taqaitaccen Tarihin Gumau, Guma Ladde Ta Sarkin Yaqi’ ga masu
karatu. Kuma ina fatan masanan yau da gobe su karanta shi, duk inda aka
samu gyara ko taqaitawa ko naqastawa ko kambamawa, sai a aikok min
domin na gyara na kuma qaru. Da fatan Allah ya taimaki dukkan waxanda
suka taimaka don wallafar wannan littafi a duniya da lahira amin.

Magajin Malam Babba


Ibrahim Sabo Gumau
08067304063
08079131914

3
MUHIMMANCIN ILIMIN TARIHI

Tarihi shi ne ilimin sanin wasu al’umma, garuruwansu, al’adunsu,


sana’o’insu, laqubbansu lokacin mutuwarsu, da sauransu.

SHIMFIXAR KOWANNE ILIMI

Kowanne fanni na ilimi yana da shimfixu aqalla goma. Kamar haka nan
ma ilimin tarihi ya ke :
SUNANSA

Ilimin tarihin al’amuran da suka shuxe da waxanda suke faruwa.

MA’ANARSA

Shi ne sanin labarin wasu al’ummomi, garuruwan su, rubuce-rubucensu,


al’adarsu da sana’o’insu, sunayensu da laqubbansu, abincinsu,
bukukuwansu, tsawon ransu mutuwarsu da wanin wannan.

MANUFARSA

Fahimtar halayen mutanen da, da yadda duniya ta ke a zamaninsu.

FA’IDARSA

Lura da halayen mutan da, gwamawa da mutanen yanzu, da abin da zai


zo nan gaba, wato dai lura da jujjuyawar zamani. Ilimin tarihi yana qarawa
ma’abucinsa shekaru, kamar yadda ya ke tsinkayar da ma’abucinsa – alhali
yana zaune a garinsu - ilimin da ba kowa ke samunsa ba sai matafiya. Har
Imam Shafi’iy yana cewa,
‫من علم التاريخ زاد عقله‬
“Wanda ya san tarihi hankalinsa ya daxu.”1

1
Aljabruti : (Ajã’ibul Ãthãr) : 1/2
4
Wanda kuwa bai san tarihi ba to wannan kamar yadda wani malami Hãjiy
Khalifa ya siffanta shi da cewa,

‫ليس بإنسان وال شبهه * من ال يعي التاريخ يف صدره‬


‫أضاف أعامرا إىل عمره‬ * ‫ومن روى أخبار من قد مىض‬
Ba mutum ba ne, bai ma yi kama da mutane ba. “Wanda bai haddace
tarihi a qirjinsa ba. Wanda ko ya karanta tarihin mutanen da suka
gabata, to, kamar ya qara wa kansa shekaru ne bisa shekarun da ya ke
da shi.”2

DANGANTAKARSA DA SAURAN ILMUMMUKA

Reshe ne na ilimin Alqur’ani da hadisi.

WANDA YA QAGO SHI

Allahu (SWT) ya qirqiro shi, kuma ya sanar da shi a cikin littafinsa.

MADOGARARSA

Rubutun littattafai da abin da ake gani na guraban ayyukan mutanen da


shuxe, kamar gine-ginensu da ayyukansu da aka tarar, na shekaru aru-aru
da suka shuxe.
HUKUNCIN NEMANSA

Faralu kifaya ne, idan wasu suka tsayu da nemansa, to, sun xaukewa
saura.
MATSAYINSA

Sanin halayen xaixaikun mutanen da suka shuxe, kama daga Annabawa,


waliyyai, malamai, sarakuna, mawaqa, masu sana’a da sauransu.

2
Hãjiy Khalifah : (Kashfuz Zunun) : 1/271
5
FALALARSA

Ilimin tarihi yana daga cikin ilmummuka masu fifiko, alqadari da


amfani a cikin kowace al’umma. Domin yana nuna mana yadda duniya ta
ke ci gaba da wayewa da ilimi, ayyuka da ciniki, da yadda mutane ke
qoqari su daidaita zamansu da juyawar zamani. Kuma yana bayyana yadda
rayuwar wasu mutane ta ke, tun shekaru da yawa da suka wuce, tun sadda
ake cikin duhun kai, har zuwa lokacin da suka fara farkawa, suka riqa
himmatuwa ga kyautata zamantakewarsu, don qara jin daxin zamasu a
duniya. Wannan ma ya sa Allah (SWT) ya cika littafinsa Alqur’ani da shi,

‫ﯫﯬ ﯭﯮﯯﯰﯱ‬
“Lalle ne haqiqa, abin lura ya kasance a cikin tarihinsu ga masu hankali.” 3

Kuma Allah maxaukakin sarki ya qalubalanci malaman Ahlul kitabi


masu murguxa gaskiya, su cuxanya qarya da gaskiya da ilimin tarihi inda
ya ce,
‫ﮋ ﮌ ﮍ ﮎ ﮏ ﮐ ﮑ ﮒﮓ ﮔ ﮕ ﮖ ﮗﮘ ﮙ ﮚ‬
“Ya ku mutanen littafi! Don me kuke jayayya a cikin sha’anin Ibrahima,
alhali kuwa ba a saukar da Attaura da Linjila ba face daga bayansa? Shin
ba ku hankalta?”4

Abdullahi bin Abbas (RA) ya ce, “Allah ya ambaci muhimmancin ilimin


tarihi a cikin Alqur’ani. Inda ya ce,

‫ﭯ ﭰ ﭱ ﭲ ﭳ ﭴ ﭵ ﭶ ﭷ ﭸﭺ ﭻ ﭼ ﭽ ﭾ ﭿ ﮀ ﮁ‬
“Kuma muna ba da labari a gare ka daga labarun Manzanni, abin da Mu ke
tabbatar da zuciyarka da shi. Kuma gaskiya ta zo maka a cikin wannan, da
wa’azi da tunatarwa ga masu imani.”5
3
Suratu Yusuf : 111
4
Suratu Ãli Imran : 65
5
Suratu Hud : 120
6
A cikin hadisi Ma’aiki (SAW) ya ce,

‫بلغوا عني ولو آية وحدثوا عن بني إرسائيل وال حرج ومن كذب عيل متعمدا فاليتبوأ مقعده من النار‬
“Ku isar gare ni ko da zance guda ne. Kuma ku ba da tarihin Banu Isra’ila
ba laifi ba ne. Kuma wanda ya yi min qarya da gangan6 to, ya nemi
matsuguninsa a cikin wuta.”7

Yahya bin Uyainatu (RA) cewa ya ke yi, “Idan ana ambaton tarihin
waliyyai, rahamar Allah tana sauka.” To, sai manyan shugabannin mu
biyu : Abu Hanifata da Shafi’iy suka ce, “Malamai ya ke nufi, domin idan
ba malamai ne waliyyai ba, to, fa Allah ba shi da waliyyi.” Malam xan
Abdulbarri kuwa ya faxa a cikin littafinsa Al’istizkar : “Sanin tarihin
rayuwar malamai, da shekarar mutuwarsu, na daga cikin kevantaccen
ilimin musulunci, kuma bai kamata ga wanda ya siffantu da ilimi ya jahilci
wannan ba.” Hassan bin Yazid shi ma yana cewa, “Babu abin da ake
tunkuxe qaryar masu qarya da shi kamar ilimin tarihi.”8 Hăjiy Khalifah ya
ambata cewa, Ma’aiki (SAW) ya ce,“Wanda ya tsare tarihin wani
mummuni, tamkar ya raya shi ne.”9 Malam Nawawi yana cewa, “Yana
daga muhimmin al’amari ga malami da xalibi su san ilimin tarihi,
musamman na malamansu, waxanda suka karantar dasu ilimin da shi ne
igiyar da ta sada su da Allah ubangijinsu.”10 Shaikh Ahmad Baba ya ce,
“Jahiltar tarihi tamkar hawan makauniyar dabba ce, domin za’a iya jingina
labarin ’yan baya ga magabata, ko kishiyar haka, ba tare da mutum ya gane
ba.”11
Karanta littattafan tarihi, a gani na, babu abin da ya fi shi amfani. Don
kuwa duk abin da ka gani a yau, mutane suna yi ko suna faxi, xan tarihi ne.
Da za’a yanke dangantaka tsakanin jiya da yau, da sai a ga xan adam bai
san komai ba, kuma ba komai ba ne shi.
6
Ashe rubuta littafin tarihi, da karatun tarihi, ba laifi bane, laifi shi ne yin qarya a cikinsa.
7
Jalaluddin Suyuxi (Jãmi’us saghir) : 1/126
8
Muhammad Makhluf (Shajaratun nûruz zakiyyah) : 1/14
9
Hãjî Khalifah : (Kashfuz zunun) (Muqaddimah) : 1/3
10
Muhammad Makhluf (Shajaratun nûruz zakiyyah) : 1/15
11
Ahmad Bãba (Kifãyatul Muhtãj) : 1/14
7
MAVUVVUGAR ILIMIN TARIHI
Tarihi na vuvvugowa daga mavuvvuga uku :
1- Rubutu
2- Guraban al’ummomin da suka shuxe, kamar zane-zanensu a jikin
duwatsu, ko shuke-shukensu ko gine-ginensu kamar ganuwar Bauci
3- Tarihin baka
DALILAN DA SUKA SA AKE KAFA GARURUWA
Lokacin da Allah ya saukar da Annabi Adam a bayan qasa, sai ya sanya
shi ba zai iya rayuwa shi kaxai ba, kamar yadda sauran dabbobi ke rayuwa.
Dole yana da buqatuwar xan’uwansa, don samun cikar burinsa na samun
abinci da tufafi da sauransu. Su kuma abubuwa ne da ake bin matakai da
yawa kafin a same su, babu wanda shi kaxai ya isa ya samarwa da kansa
su. Ta qaqa mutum shi kaxai zai jivintarwa kansa noma? Alhali noma na
buqatar kayan aiki, fatanya garma da sauransu, su kuma suna buqatar
maqeri da zai qera su, maqeri na buqatar masassaqi mai sassaqo masa
qota. To, yaushe kuma zai samu damar yin tufafi alhali ya shagaltu da
noma? Alhali tufafi suna buqatar saqa da kaxi da xinki. To, sai Allah ya
kimsa wa kowanne mutum irin sana’arsa, maqeri ya qera kayan noma,
masassaqi ya sassaqa qota, manomi ya yi noma, xan kasuwa ya saya ya
sayar, mai tuwon sayarwa ta tuqa tuwo. Mai niqa ya niqa gari, Mai ginin
tukwane ta gina tukunya. Kamar haka nan kowacce sana’a sai ka ga ta
xamfaru da ’yar’uwarta. Sai kuma Allah cikin hikimarsa ya tara su a gari
guda don kowa ya amfana da basirar kowa. Idan mun juya wajen tufafi ma
haka abin ya ke. To, duk sadda aka samu haxuwar waxannan ma’abuta
sana’o’i daban-daban shi kenan sai ka ga gari ya kafu. Kuma duk sadda aka
rasa xaya daga cikinsu, to, kamar jiki ne a rasa sashin wasu gavovi, to fa
naqasa ta samu. To, san nan kuma kowanne gari ya sha bamban da wani,
saboda savanin ruwa, da qasa, da bugawar iskarsa, da irin abin da yanayin
kowanne ke haifarwa na nau’ukan ma’adanai, da tsirrai, da dabbobi wanda
ba’a samu a wani. Da irin ginin da qasar kowanne gari ke karva, wanda
wani garin ba lallai ya karva ba. Da irin azanci da basira da kyawawan
xabi’u da ruwan wani gari ke haifarwa, wanda na wani garin baya yi.

8
TASIRIN QASAR GARI AKAN MAZAUNANSA

Masana sun ce, Allah ya halicci qasa da jihohi huxu ; gabas da yamma,
kudu da arewa. Maqurar gabashinta tsananin zafi ne dashi, ta yadda har
halittu ba su iya rayuwa, kuma tsirrai ba su iya fitowa a wajen, saboda
kusacinsa da mahudar rana. To, kamar yadda maqurar gabashinta ya ke,
haka ma maqurar yammacinta ya ke, tsananin zafi, saboda kusacinta da
mafaxar rana. Maqurar arewacinta kuwa babu komai sai tsananin xari, ta
yadda har halittu ba za su iya rayuwa ba, tsirrai kuma ba za su iya tsirowa
ba. To, kamar yadda maqurar arewacinta ya ke, haka ma maqurar
kudancinta ya ke, babu komai sai tsananin xari, don irin xeshin ranar da
suke samu iri xaya ne. Inda ake iya rayuwa a bayan qasa xan wuri ne
qanqani. Duk inda ba nan ba mutanen wurin azaba kurum suke sha, ko
kuma ace wahala ta zama xabi’arsu.

TASIRIN QASAR GARI AKAN MA’ADANAI DA TSIRRAI

Cikin tasirin da qasar gari ya ke yi akan ma’adanai da tsirrai kuwa ; ga


misali zinariya ba ta yaxo sai a qasa mai rairayi, da jigawa mai
tsakwankwani. Azurfa da tama kuma su a jigawar qasa mai haxe da
duwatsu suke yaxo. Kanwa da gishiri ba su yaxo sai a qasar kanwa da
gishiri. To haka kowanne ma’adani da irin qasar da ya fi yin yaxo a
cikinta, sai nadiran. Amma tsirrai kamar auduga, dabino da ayaba, da
lemon tsami da tanjirin da rumman ba su yi sai a qasa mai zafi. Ita kuwa
alkama ba ta yi sai a qasa mai tsananin sanyi. Irinsu rake kuwa su sai a
fadama ko bakin rafi ko qorama suke yi. Idan ka koma wajen dabbobi,
vauna ba ta haihuwa sai a qasa mai zafi, mai kuma wadataccen ruwa,
amma ba ta rayuwa a qasa mai sanyi. Shi kuwa raqumin dawa a qasa mai
zafi ya fi rayuwa. Tsuntsaye irinsu mikiya, shaho da shirwa, ba su fafa sai
akan qololuwar dutse. Amma jimina a rairayi ta ke qwai ta yi fafanta.
Irinsu agwagwa kuwa a bakin tafki ko wuri mai ruwa ta fi yin qwai. Ita
kuwa kanari a dogon gini ta ke qwai ta yi fafanta.

9
AL’AJUBAN GARURUWA

Daga cikin labaran abubuwan al’ajuba da muka samu, wannan labari da


za mu kawo muku. Sadda aka tambayi Khidir (AS) wanne abu ne mafi ban
mamaki da ka tava gani a cikin yawace-yawacenka na zagaya duniya? Sai
ya ce, “Mafi girman abin mamaki da na tava gani shi ne, wataran na shuxe
ta cikin wata babbar alqarya, wacce tun da nake ban tava ganin alqarya
mai kyanta ba. Ga jama’a nan danqam ana ta kai kawo. Ga gine-gine
tantsai-tantsai. Sai na tambayi wasu mutanen garin na ce, “ko yaushi aka
gina wannan alqarya? Sai suka ce, “Subhanallahi! Ko ga iyayemmu da
kakannimmu ba mu tava ji sun ambaci lokacin da aka gina wannan gari ba.
Wannan gari inda ka ganshi xin nan haka ya ke, tun bayan xaukewar
ruwan xufana.” Ya ce, sai na wuce, na ci gaba da tafiya ta cikin duniya,
ban sake dawowa ta wurin da wannan alqarya ta ke ba, sai bayan shekaru
xari biyar. Ina zuwa sai na tarar da ita rusasshiya, ta zama kufai. Babu
kowa a cikinta, ballantana na tambaye shi. Sai rusassun gini, nan da can.
Sai wasu ragowar kayayyakin mutan da da aka barsu, a warwatse, kamar
duwatsun niqa, da tsofin rijiyoyi da kuma wasu shuke-shuke. Can daga
nesa sai na hango wasu masu kiwon tumaki. Sai na kusance su, na ce ni
kuwa ina labarin alqaryan nan da da ta ke nan? Sai suka ce, “Subhanallahi!
Ko iyayemmu da kakannimmu, ba mu tava jin sun ambaci cewa da can
akwai wata alqarya a wannan wuri ba.” Ya ce, sai na wuce ta cikinta, na
qara kutsawa cikin duniya. Ban kewayo ta wajen ba sai bayan shekara xari
biyar. Ina zuwa sai na ga daidai inda garin ya ke ya zamo teku. Ga mutane
nan suna ta nutsawa qarqashinsa suna fito da wani abu kamar murjani ko
lu’ulu’u. Sai na matsa kusa da su na ce, tun yaushe teku ya ke a wannan
wurin ? sai suka ce, “Subhanallahi! Ko ga iyayemmu da kakannimmu, ba
mu tava ji sun ambaci lokacin da aka haqa wannan teku ba. Wannan kogi
inda ka ganshi xin nan haka ya ke, tun bayan xaukewar ruwan xufana. Ya
ce sai na kuma fakuwa shekara xari biyar, san nan na kewayo ta wajen. Sai
na tarar da ruwan wannan teku ya qafe, amma ya bar babban tafki,
tsakankanin wani kurmi, mai dogayen bishiyoyi sun kewaye shi. Ga
mutane nan wasu na ta kamun kifi a cikin qananan kwale-kwale. Sai na
dubi wasu na ce, ina labarin tekun nan da da ya ke nan? Sai suka yi min

10
wani irin kallo, suka ce, “ ba mu tava ji, ko ga iyayemmu da kakannimmu
cewa da nan wurin teku ne ba.” Shi kenan sai na wuce na ci gaba da tafiya
ta. Ban komo wannan wuri ba, sai bayan shekara xari biyar. Ina zuwa sai
na tarar da alqaryar nan, bisa yadda na tava shuxe ta shekaru dubu biyu da
suka shuxe. Ga jama’a nan danqam a cikinta. Ana ta kai-kawo. Ga
ginannun benaye tanqama-tanqama. Ga tituna kyawawa, ga kasuwanni ana
ta ciniki, kowa dai na ta hidimar gabansa. Sai na matsa kusa da wasu
tsofaffi a cikin wata rumfa na ce, ni kuwa ina labarin tafki mai kurmin nan
da da ya ke nan, kuma yaushe aka gina wannan alqarya? Sai suka ce,
Subhanallahi! “ ba mu tava ji, ko ga iyayemmu da kakannimmu cewa da
nan wurin akwai wani kurmi ko tafki ba. Inda ka ga wannan alqarya, tun da
ma can haka ta ke tun bayan xaukewar ruwan xufana ” sai na sake wucewa
na yi gaba, ban sake dawowa ba, sai bayan shekara xari biyar. Ina zuwa sai
tarar da ita rusasshiya, babu kowa, sai hayaqi ke tashi a ko ta ina a cikinta.
Na duba gabas da yamma, kudu da arewa ko zan ga wani mutum na
tambaye shi, sai ban ga kowa ba. Na yi gaba kaxan sai naga wani
makiyayi, sai na ce masa, ni kuwa ina labarin alqaryan nan da da ta ke
nan? Sai ya ce, “Subhanallahi! Ba mu tava jin iyayemmu da kakannimmu
sun ambaci cewa da akwai wata alqarya a wannan wuri ba. Wannan wuri
haka Allah ya yi shi tun fil azal.”12Tsarki ya tabbata ga Allah mai rusa
garuruwa, ya qarar da bayi, ya gaje duk abin da suka mallaka.
ASALIN GUMAU
Akwai wasu garuruwa da da can babu su kafin zuwan Turawa, amma
zuwan turawa suka kafa su, kamar Kaduna, Mina, Kafancan, Makurxi,
Pingel da sauransu. Akwai wasu garuruwa kuma waxanda koda dai turawa
sun same su, amma duk da haka sun qara musu suna, kamar su Jos haka
nan Gumau ta ke. Tun kafin zuwan turawa akwai ta, amma da turawa suka
dawo da hakimi da masarauta cikinta, aka gina barikin bature (Rehawus)
da makaranta da fulotin auduga, nan da nan sai mutane suka yi ta taruwa,
fatauci ya yi ta qaruwa, aka ba da himma ga noma, sana’o’i kuma suka
bunqasa.

12
Shihabuddin, Abul Fatahil Abshîhî (Almustaxraf Fi Kulli Fannin Mustazraf) : 2/502
11
MAZAUNA GARIN NA ASALI

Mazauna garin na asali su ne rimadan Kaurare. Su kuma iyayen gidansu


fulani ne suka ajiye su, a gefen labin wucewarsu tun shekaru masu yawa,
suka raxawa wurin suna Kaurare, saboda su fulani ba mazauna wuri xaya
ne ba. In da kuma ake kira Kaurare a san nan yana farawa tun daga dutsen
nan da ke yamma -maso arewa da makarantar Gumau Sanga, ya yo gabas
har inda unguwar mishan ta ke. Ya yi kudu har zuwa labi, daga nan ya yi
yamma har zuwa kogin Dawarde, wanda ya gangaro daga dutsen sanga, ya
ratsa kan hanyar zuwa Kutuku, ya je ya faxa Dilimi. Kodayake tun daxewa
ana kiran wurin da suna Kahawa, amma inda suka ajiye sun a cikinsa
sunansa Kaurare.13 To suna nan zaune haka shekara da shekaru sai wasu
gungun mahauta, da suka taso daga Lillingyal, wani tsohon gari da ke
gabas da Ririwai, a qarqashin shugabancin wani babbansu, suka kafa
gidaje, amma shi babban sun sai ya zakuxa gefe xaya can ta yamma ya
kafa na sa gidan. To, sai rimadan nan suna cewa sabuwar unguwar da aka
kafa unguwar mahauta. Suna cewa ‘Za mu unguwar mahauta’ ko ‘mun fito
unguwar mahauta.’ Kuma sai suna kiran gidan babban na su Maiwuro, bisa
yadda suka ga mutanensa suna girmama shi. Ma’anar Maiwuro, maigida
kenan da harshen fillanci, tun da su rimadan suna magana da fillanci. To,
ana nan haka, sai wani Bugushi wanda Allah ya yi masa abin hannu, kuma
mai alheri ana kiransa Gumau, da ya tava kafa kasuwa a Tantaroki,14 amma
ba ta yi kirki ba. Ya dawo Koruno15 ya kafa nan ma ba ta yi kirki ba. To,
sai yana sayen saniya a wajen fulani, amma bai san yadda zai yi da ita ba.
Sai ya kai wa mahauta su yanka, ya kan ce musu su cire masa cinya xaya,

13
Kuma kodayake an ce su ne farko, amma fa can kudu da labi, inda gidan bulo xin
Alhaji Musxafa (project) ya ke akwai gidan wani bafulatani mazauni ana kiransa
Dawarde. Shi ma ya samo sunan ne daga sunan kogin Dawarde. Shi ne ma wanda sarkin
yaqi Usmanu Babale sadda ya dawo Gumau ya yi masa sarautar mai unguwa, wacce ita ce
ma yanzu ta juye littafin Dawarde. Kuma akwai wasu a can hayin babban rafi na arewa
maso gabas da inda kwalejin koyon sana’a ta ke, ana kiran wurin da suna Babbar riga. San
nan akwai mutane a unguwar Kanya.
14
Wani tsohon gari a kan hanyar Wonu. An matsa wa mutanen garin akan biyan haraji, sai
suka yi qaura suka koma qasar kuza, inda sarkin Bauci bas hi da hannu a kansu.
15
Wani tsohon gari a tsakanin Babajayi da Farfaru. Babu kowa yanzu a wajen sai kufai.
12
“Wannan na mutane na ne a unguwarmu.” Sai ya bar musu ragowar naman
saniyar, idan sun sayar sai su haxa masa kuxinsa. To sai su mahautan suka
ce, “Wannan mutum gara mu jawo shi kusa da mu.” Suka ce masa ai
gidanshi ya yi jeji, gara ya dawo kusa da su, sai suka taimaka masa aka yi
rumfunan kasuwa a bakin titin Badiko daidai Rehawus,16ko gidan Alhaji
Hamisu Na’iya. Sai ana ce kasuwar Gumau. Duk masu wucewa nan suka
tsaya su yi sayayya. Har aka sa mata rana tana ci duk ranar alhamis.
Wataran Madakin Riruwai ya ce wa sarkin Riruwai, “Mu fa je mu qone
kasuwar nan, kadan ba haka ba za ta kashe mana (kasuwar mu ta)
Riruwai.”17 Shi kuma Gumau da ya samu labari, sai ya riqa zuwa Ririwai,
yana kai wa Malam Jubo Babarbare18 kuxi, akan ya yi masa addu’ah kada
wannan suna na sa ya mutu. Sai malam Jubo ya yi ta roqon Allah, shi da
almajiransa. Saboda yawan alherin da ya ke yi wa malam Jubo akan
wannan buqata ta sa, sai shi kuma malam yana ce masa, “Wannan suna na
ka, (In Allah ya yarda) har a Makkah sai an ji shi.” Sai kuwa Allah ya amsa
wannan addu’ah ta sa. Da farko turawa sunan Kahawar suka fara xauka,
har ma takardun aikin gwamnati na farko-farko sunan Kahawar za ka gani.
Abin ikon Allah, sai matafiya kan ce mun wuce ta kasuwar Gumau’ ‘mun
fito kasuwar Gumau’ ‘za mu kasuwar Gumau.’ Shi kenan sai sunan Gumau
ya yi rinjaye akan na Kahawa har yau xin nan. To, da gari ya fara ci gaba a
dalilin kasuwarsa, abin duniya ya fara zaqi, kwanci tashi sai fulanin da
suka zaunar da rimada a filayensu na Kauraren nan suka zo suka karve
abinsu, suka tashe su. Sai xan kaxan suka bar musu wanda za su riqa
nomawa suna samun abinci. Sai su rimadan suka tattaru suka kafa wata
sabuwar unguwa arewa maso gabas da Kaurare suka raxa mata suna Sabon
-gida. Kuma a nan suke zaune har yau xin nan.

16
Nan ne sadda bature Di’o ya zo aka yi masa masauki day a ke hutawa. Wato Rest house.
17
Kasuwar Riruwai a da tana ci ranar lahadi
18
Malam Jubo Babarbare, babban malami masanin Alqur’ani. Ya zauna a Riruwai. Shi ne
kakan Sama’ila Bala Gumau.
13
SUNAYEN GARIN

Mun dai ji yadda tun farko ake kiranta KAHAWA, wannan suna ko
rimadan Kaurare ma haka suka same shi. Wasu kuma na kiranta da sunan
kasuwarta GUMAU.
IYAKOKINTA A 1940

An shata garin Gumau a shekarun 1940 a tsakanin iyaka na rafuka kam


ban da qusurwa xaya. Ta arewa dai ya yi iyaka da rafin da ke gangarowa
daga dutsen Ririwai, wanda aka yi gada akansa. Ta gabas ma ya yi iyaka da
inda wannan rafin ya gangara, inda ake ce masa rafin Unguwar Kanya. Ta
kudu ya yi iyaka da rafin Kwalliya, wanda ya gangarowa daga makarantar
Gumau Sanga. Ta yamma ma ya yi iyaka da dutsen Kaurare. Wanda ya ke
yamma maso gabas da makarantar Gumau Sanga.

IYAKOKINTA A 2021

Amma a yanzu (2021) garin Gumau ya bunqasa ya wuce duk iyakokin


da aka shata masa a 1940’s. Yanzu ta gabas ya yi iyaka da rafin Sauke,
wanda ya ke gangarowa daga dutsen Jawando. Ta yamma kuwa ya
dangana da dutsen Sanga, ya game da Gagati. Ta arewa ya kai har unguwar
tsamiya. Kamar yadda ta kudu ya zarta Dawarde (Project).

MAZAUNINTA A TASWIRAR DUNIYA

A jikin taswirar duniya, masana sun ce garin yana kan layi na 9 a tsaye, a
kwance kuma yana kan layi na 10. Nisan garin ta hanyar mota zuwa Bauci
da ke gabas dashi, ya kai nisan Kilo mita 111, nisansa ta hanyar mota zuwa
Jos kuma da ke kudu maso yamma dashi ya kai Kilo mita 65. Nisan garin
tahanyar mota zuwa Kano da ke arewa dashi ya kai Kilo mita, yayin da
nisansa ta hanyar mota zuwa Kaduna da ke yamma maso arewa dashi Kilo
mita. Nisansa daga Abuja ta hanyar mota ya kai Kilo mita

14
SHURUQI DA GURUBINTA
Galibin shuruqin rana a garin Gumau a lokacin bazara yana kamawa
daga qarfe bakwai da minti bakwai zuwa da minti goma (7:07 - 7:10am). A
lokacin xari kuwa galibi da misalin qarfe shida da rabi (6:30am). Gurubi
kuwa galibi a lokacin xari ya kan fara da misalin qarfe bakwai saura
ashirin da biyar (6:35pm), amma a lokacin bazara yana kai wa qarfe
bakwai saura minti takwas (6:52).
KIRARIN GUMAU
“Gumau guma ladde,19
Garin gum da magana.
Ta sarkin Yaqi kasuwa duk mako.
Gari tarmani ciji wanda ya zaune ka.
Gari mai farin jini ga wanda ya zo shi,
Garin da wanda ke cikinsa ke qawazucinsa.
Garin da ’yan’uwa ba su morar mai samunsu
Garin da baqo ya fi xan gari kafin a jima.”

FASHIN BAQIN KIRARIN

Ba kamar wasu garuruwa waxanda ba sa karvar baqi ba, irinsu Toro,


Bauci, Maiduguri da sauran su ba. Daga jin kirarin Gumau, ka san gari ne
da ke karvar baki. Kuma wannan na daga cikin abin da ya kawo wa garin
ci gaba a cikin xan qanqanin lokaci. Har ya fi wasu garuruwa da suka
rigaye shi. Ko daga ina ka fito sai ka zo ka yi ta sana’ar da iya kuma ka
samu ci gaba, babu wanda ya sa idonsa a kanka. Kai hasali ma duk wanda
ya zo garin a farkon zuwansa, mutane kan nuna masa soyayya fiye da
wanda tun can ake tare da shi. Kafin daga baya idan wani ya zo bayansa,
sai a riqa rabuwa dashi kaxan-kaxan, har a rabu dashi baki xaya, a kama
baqon da ya zo a bayansa, shi kuma san nan ya ji daxin garin ba zai iya
barinsa ba. Wannan ya sa mutane da yawa da wani dalili ya kawo su,

19
Guma-ladde : shi ne qungurmin daji da fillanci.
15
kamar neman karatu, ko neman kuxi, ko aikin gwamnati, ba su iya barin
garin, saboda soyayyar da suke gani ana nuna musu a farkon zuwansu. Ko
da kuwa an yi musu canjin wurin aiki, za ka ga sai dai su riqa zuwa su
dawo. Sun mai da Gumau ita ce garinsu. Akwai waxanda har ma sarauta ce
da su a garuruwansu, sarautar nan kuwa mai daraja, amma suka gujewa
sarautar, suka yi zamansu a Gumau. Shi kuwa xan asalin garin, haifaffen
cikinsa, wanda ya sha ruwan garin kuma aka yi masa wanka das hi, ba
kasafai yak e iya barinsa ya je wani gari neman karatu ko neman kuxi ba,
ko da kuwa me ya ke samu samu a can. Kuma ko da zai zauna garin na sa
ba ya aikin komai.
SABABINSA

An ce sababin haka roqon Allahn da xaya daga cikin sarakunan garin,


wato sarki Usmanu Babale ya sa malamai suka yi ta yi ne, lokacin da
turawa suka tilasta sai ya dawo garin da zama, ko kuwa ya yi zamansa a
inda ya ke amma za su naxa wani. Sai shi kuma ya gayyato malamai suka
yi ta roqon Allah akan abubuwa huxu :
1- Allah ya kawowa garin zaman lafiya madauwami
2- Allah ya tsare garin daga dukkan sharri
3- Allah ya kawo jama’ah da qaruwar arziqi
4- Allah ya sanyawa duk wanda ya shige ta qawazucinta.
Kuma duk bakin abubuwan da aka roqi Allah a kansu, Allahn ya amsa.
Babu garin da ya fi Gumau zaman lafiya, don ba’a tava samun wani
mummunan tashin hankali a cikinta ba, har yau xin nan. Batun Arziqi
kuwa duk garuruwan da ke yammacin Bauci, babu garin da ke da masu
arziqinta da ’yan bokonta da kasuwancinta. Kuma ba kasafai mazaunin
cikinta ke son fita daga cikinta ba.
TASIRIN RUWAN GUMAU AKAN MAZAUNANSA
Kamar yadda bayani ya gabata na yadda qasar gari ke tasiri akan
mazaunansa, to haka ma ruwan gari ke da irin wannan tasiri ga halayen
mazauna wuri. To, garin Gumau ma kamar sauran garuruwa haka ruwansa
ya ke da tasiri ga mazaunansa har ma ya ke haifar musu da halaye kamar
haka :
16
i- Wanda duk ya tashi a garin, duk inda zai je a cikin duniya ba
shi rabuwa da qawazucinsa.
ii- Wanda duk ya yi arziqi a garin sai ya gujewa masoyansa –
’yan’uwansa da abokansa- ba su morarsa, sai dai wasu can
daban ’yan duniya ta yi daxi.
iii- Wanda duk kuma ya yi arziqi a garin ya ce zai yi wa masoyansa
-’yan’uwansa da abokansa- alheri, to, da su zai fara samun
matsala.
iv- Duk abin da ka yi wa mutanen garin za su saka ma, amma ban
da alheri.

QABILUN CIKINTA

Manyan qabilun cikinta dai galibinsu lamawa ne da Ririwawa. Ko da ya


ke lamawa ko ririwawa ba sunayen qabilu ba ne, amma dai mutanen
garuruwan ne suka yi hijira suka cika garin har ma suka rinjayi kowa.
Alhali idan aka ce lamawa, ko su cikin mutanen da suka yo hijira daga
lamen akwai Wuntawa (fulani), Guddirawa, Gyamawa, Rimada, Shawawa,
Gwawawa da sauransu. Haka ma cikin Ririwawa akwai Katsinawa,
Kanawa, Zage-zagi, Zamfarawa da sauransu. Amma idan muka taqaita
abin daga cikin mazauna Gumau akwai ; Hausawa (Kanawa, Katsinawa da
Zage-zagi), Fulani, Rimada, Sangawa, Bambarai, Gurawa, Inyamurai,
Yarbawa, Narkutawa da Sayawa. Akwai abubuwa da dama waxanda suka
haxa waxannan qabilu, babbansu shi ne fatar jiki, don duka baqaqe ne,
kuma dukkaninsu suna jin Hausa. San nan auratayya ya yi ta shiga tsakanin
musulman cikinsu.

HARSHEN MUTANEN GARIN

Babban harshen mutanen wannan gari duk da bambance-bambancen


qabilarsu, aqidarsu da addininsu shi ne harshen Hausa.

17
YANAYIN GUMAU

Gumau gari ne da ya ke da matsakaicin yanayi na zafi da sanyi. Amma


yanayi na shekara akwai kamar guda biyu, na rani da damina. Galibi
damina ta kan fara tun a tsakiyar watan Yuni. Kuma ta kan fara da iskar
hadari mai qarfi kodayaushe. Tun daga lokacin nan har tsakiyar watan
Oktoba duk damina ce. Yadda daminar ta kan fara, za ka ji zufa ya
tsananta, iska ta tsaya cik, mutane su yi ta kokawa da yawan zufa, har wasu
su riqa kwana a waje. Ita iskar damina daga kudu maso yamma ta ke
busowa, wato wajen teku, duk ranar da iska ta juya zuwa gabas, can sai ka
ga iska mai qarfi ta taso, sai walqiya ta biyo baya, sai kuma ruwa ya zubo.
Daga ce ruwa ya xauke, to, an shiga rani kenan. Sai kuma iskar hunturu ta
tashi, tana farawa tun daga farkon watan Disamba, har zuwa qarshen watan
Fabrairu. ita kuma tana busowa daga arewa maso gabas ne, ta ratso
Hamada. Da cewa wannan iska ta fara busowa, nan dan yanayin garin sai
ya sake. Ciyawa ta kan bushe, itatuwa su kan kakkave ganyayensu, rafuka
su kan qone nan da nan. Da ya ke iskar nan ta ratso Hamada ne, akwai
garin rairayi da ta kan kwaso, wanda ke dushe hasken rana. Galibi xarin ya
kan tsananta a cikin watan Janairu, idan ya tsananta ya kan kai har digiri 22
na ma’aunin salshiyus. Saboda haka kullum akwai garin hazo da kan riqa
sauka yana xamfarewa mutane a jiki. Wannan ya sa mutane musamman
talakawa ba su son sa, don jikinsu ya kan riqa kaushi, fatar jiki kuma ta kan
bushe, leven baki ya kan riqa tsagewa, idanu ya kan riqa zubar da hawaye.
Amma a wurin mawadata, waxanda galibinsu suna da qiba, kuma kullum
su kan yi wanka, don suna da wadatattun tufafin canzawa, sanyin hunturu
ya fi musu zafin bazara daxi. Idan ciyawa ta bushe, mutane su kan riqa sa
wuta a daji. Da rani mutane su kan riqa qona daji, idan an qona daji sai ka
ga sabbin ciyawa suna tsirowa. Daga qarshen watan Maris wuri ya kan
juye da zafi. Zuwa qarshen watan Afrilu zafin ya kan tsananta har ya kai
digiri 38 na ma’unin salshiyas, wannan lokacin shi ake kira lokacin bazara.

18
NAU’IN ABINCIN MUTANENTA
1- Tuwon dawa ko masara ko shinkafa.
2- Masa
3- Koko da Qosai
4- Xanwake
5- Fura
6- Guzguz
7- Alale
8- Dambu

NAU’IN RIGUNAN MUTANEN GARIN A DA

1- Malum-malum
2- Aganiya
3- Shafka20
4- Windiya21
5- Sace
6- Tsamiya
7- Mai asake
8- Aska biyu
9- Aska huxu
10- Aska tara
11- Shakwara
12- Gare
13- ’yar shara
14- Jamfa
15- Kufta
16- Shirt
17- T-shirt
18- Coat
19- Jallabiyya

20
Ana yi mata aiki har qasa gaba da baya
21
Tana da aljihu guda biyu a dama da hagu a gicciye
19
NAU’O’IN WANDUNAN MUTANENTA A DA

1- Tsala
2- Tumazagi
3- Tarangoma
4- Jambarebari
5- Turoza
6- Kabi shanu
7- Buje
8- Jins
9- Baggae
10- Fantalo

NAU’O’IN HULUNAN MUTANENTA

1- Havar kada
2- Damanga
3- Zita
4- Hana salla
5- Zanna-bukar
6- Bakwala

YAWAN JAMA’ARTA

Qiyasin mutanen da ke zaune cikin Gumau a shekarar 2021, mutum dubu


goma sha shida (16,000) ne.

YAWAN GIDAJENTA A 2021

Yawan gidajen Gumau a shekarar 2020, waxanda aka gama gininsu


mutane ke zaune a ciki, da waxanda an gama amma ba kowa a ciki, da ma
waxanda ba’a gama ba gidaje dubu xaya da xari biyar (1,500) ne.

20
YAWAN ADDINANTA

Akwai mabiya addinai iri huxu a garin. Ga sunayensu da kasonsu ;

1- Ahlus Sunnah
2- Salafiyya
3- Shi’ah
4- Kirista
CUTAR ZUCIYA DA KE DAMUN GARIN
Sai dai wannan gari ya samu wasu cututtuka guda huxu :
1- rarrabuwar kai tsakanin tudu da kwari. Abin da ke mai da garin
baya.
i- Su ’yan kwari su ne jama’ar sarkin yaqi, waxanda ya taso
da su daga Lame, ko kuwa suka biyo shi daga baya, ana
kiransu ko suna kiran kansu Lamawa. Ko da ya ke babu
wata qabila mai suna haka. Ko dai su kasance Rimada ne ko
Fulani ko Hausawa. Galibinsu da karatun boko da aikin
gwamnati aka sansu, kuma da shi kurum suka dogara. Suna
xaukan duk wanda ba na su ba to, xan tudu ne. Wannan
qa’ida ta su ya sa suka ragewa kansu yawa.
ii- Su kuwa ’yan tudu, waxanda galibinsu kanawa, katsinawa,
zage-zagi ne da wasunsu, ’yan kasuwa ne da masu sana’ar
hannu, waxanda suka zo daga Ririwan –Dalma, ana kiransu
ko suna kiran kansu Ririwawa, Saboda haka sun fi yawa,
kuma sun fi arziqi da yawa, don kullum cikin samun
qaruwar ’yan’uwa (baqi) su ke.
2- Rarrabuwa tsakanin aqidodin addini. Musulmi da kirista. Kai
musulmin ma su-isu tsakaninsu, rarrabuwar ta su ta yi yawa;
Xariqa, izala (i), izala (ii), Salafiyyah, Shi’ah.
3- Lokacin rabuwar masallacin Izala a shekarar 1996, jama’ar
masallaci ba su rabu ba, said a aka yi amfani da Kalmar xan gari da
baqo. Wato shugabannin da ke son a rabun, (waxanda galibinsu
Fulani ne da rimada) sun gayawa mabiyansu daga cikin qabilu
21
cewa, su (da suka kira kansu baqi) ne masu ilimin gari. ’Yan asalin
gari (mutan Ririwai da Lame) ba su qaunarsu. Da wannan salon
qabilanci, sai kusan dukkan Rimada, Bambarai, Gurawa suka yarda
da wannan magana.22 Gaba ke ta ruruwa har yau xin nan. Alhali
kuma bah aka ba ne, shi wannan gari bas hi da wasu mutanensa na
asali. Kai hasali ma duk wanda ya zo garin yana baqo, garin ya fi
qaunarsa fiye da wanda ya daxe a cikinsa. To, shi ma wannan yana
daga cikin abin da ke mai da wannan gari baya.
4- Dukkan wanda wani mugun abu ya same shi a cikin jama’ar
wannan gari, mutane sukan riqa yawo da maganar, ayi ta mata
qarin gishiri, ana dariyar qeta, ana cewa tukunna ma. Gwargwadon
yawan danginka a garin, gwargwadon yadda za’a yi ta tseguminka.
MAGANIN CUTAR ZUCIYAR DA KE DAMUN GARIN
Da dai ace mutanen wannan gari za su watsar da hasada wa juna, su
rabu qiyayya ta bambance-bambancen aqidodi da ra’ayi, kuma su haxa
kansu, don ganinci gaban garinsu, to, da ba za’a sami garin da zai yi kusa
dashi wajen ci gaba da bunqasa a nanm kusa ba.

CUTUTTUKAN JIKI DA KE DAMUN MUTANEN GARIN

1- Atini
2- Basur
3- Zazzavin maleriya da taifod
4- Shawara
5- Baqon dauro
6- Sanqarau
7- Hanta
8- Hawan jinni
9- Sukari
22
Alhali kuma ba haka ba ne, har yanzu Gumau gari ne ya fi son baqo fiye da xan garin
da ya daxe a cikinsa. Ko su waxanda suka qirqiro wannan gaba, babu abin da ba’a yi
musu ba na kyautata wa, irin wanda ba’a yi wa waninsu das u ke ganin xan garin ne shi
ba.
22
ABUBUWAN DA AKE MAGANI DA SU ADA DA YANZU

1- Xaura layu
2- Shan sassaqen ararravi
3- Surace
4- Turace23
5- Qaho
6- Sassaqen Qirya
7- Sassaqen Taura
8- Saiwar Rai-rai (rai xore)24
9- Minjirya25
10- Ganyen kajinjiri
11- Saiwar runhu26
12- Sassaqen tunar (maxacin fadama)27
13- Sassaqen tawatsa28
14- Ruwan kwakwa29
15- Goga-masu
16- Garin kuka (madarar kuka)
17- Sabbin fitowar ganyen baushe30

23
Yadda ake yinsa, sai a share qasa, a zuba garwashin wuta mai yawa, sai a kakkaryo
ganyaye xanyu a shimfixa, sai mara lafiya yah au kai ya kwanta, sai a lulluve shi da
mayafi duk jikinsa, san nan sai a malala ruwa cikin garwashin. Sai tururi mai zafi ya tashi
sama ta cikin ganyayen nan zuwa jikin mara lafiyan. In tururin ya qare, wutar kuma ta
mutu, sai a buxe shi. Sai a ga kamar ya yi wanka ne. zufa na ta keto masa ko ta ina ajiki
24
Maganin kumallo (rawayan amai saboda matsanancin zazzavi)
25
Ana haxa ganyen kajinjiri da sassaqen minjirya a dafa a riqa sha don maganin cutar
shawara.
26
A dafa da qwai, a cinye qwan, a shanye rowan don maganin shawara
27
Ana dafa shi da jar kanwa a riqa sha don maganin cutar Basur
28
A jiqa a riqa sha don maganin atini
29
Yana maganin kowacce irin guba idan an sha. Alamar da ake gani an sha guba it ace,
za’ ga baki na kumfa ga mutum, doki, kare da kyanwa.
30
Akan riqa tauna su, ana haxiye rowan don maganin atini.
23
MANYAN TITUNANTA

Manayan titunanta guda biyar ne :


1- Titin Sarkin Yaqi Usman Babale31
2- Titin Pingel32
3- Titin Maqabarta33
4- Titin Waziri Xanwunti34
5- Titin Bauci35
6- Titin Saminaka36

LITTATTAFAN SARAUTARTA 2021

Amma littattafan sarautar da suke cikinta guda goma sha biyar ne :


Sunan littafin Mai sarautar littafin
1 Littafin qwaryar Gumau Malam Sambo Muhammadu
2 Littafin sarkin Gabas Malam Umar Adamu
3 Littafin sarkin Yamma Malam Isa Bala
4 Littafin sarkin Kudu Alhaji Sidi Audu
5 Littafin sarkin Arewa Malam Umar Adamu
6 Littafin ’Yankwana Malam Ladan Salisu
7 Littafin Gakuyel Ibrahim Usman
8 Littafin Dawarde Malam Amadu Ali
9 Littafin Barandawa37 Wakili Haruna38
10 Littafin Shenu Malam Iliya Amadu39

31
Shi ne wanda ya tashi daga masallacin Xanzalau ya nufi qofar fada.
32
Shi ne wanda ya tashi daga masallacin Izala ya nufi unguwar Kanya.
33
Shi ne wanda ya tashi daga masallacin Salafiyya ya nufi gabas, hanyar maqabarta.
34
Shi ne wanda ya tashi daga qofar Marafa ya nufi asibiti, kuma ya faxa kan titin
Saminaka.
35
Shi ne wanda ya tashi daga masallacin Xanzalau ya nufi kudu.
36
Shi ne wanda ya tashi daga masallacin Xanzalau ya nufi arewa
37
Yakanaji An kafa masarautar Barandawa Harxo Babale (17 Kuri), xan qaninsa Audi (8
Kolodi), sai qaninsa Abdulqadir (28 Wul), sai Muhammadu Abdulqadir (20 Barandawa),
38
An haife shi a 1964, a Wul, amma ya tashi a Barandawa. Ya yi karatun Muhammadiyya
a wajen baffansa M. Ibrahim Dembo. Ya yi karatun ilimi a wajen M. Sabo Ibrahim
Barandawa. Ya yi makarantar qaramar firamare a Ririwan Dalma 1977-1980.
24
11 Littafin Unguwar tsamiya Malam Lawal Muhammad
12 Littafin Sanga Malam Garba Jauro
13 Littafin fulanin Kaba Malam Adamu Abdulhamid
14 Littafin Nabaka Mista Luka Damina
15 Littafin Unguwar Sako Mista Babangida Kaka

UNGUWANNINTA 2021

Amma unguwanninta guda casa’in da biyar ne. Ga su kamar haka bisa


tsarin kowanne mai littafi, tare da sunan kowanne mai unguwa :

LITTAFIN QWARYAR GUMAU40

Sunan unguwa Mai unguwa


1 Unguwar Waziri Malam Tukur Waziri
2 Unguwar Sharaxa Malam Yusuf Gayya
3 Unguwar sarkin Riruwai Malam Xahiru Maishayi
4 Unguwar Mahauta Malam Adamu Kalo
5 Unguwar Maiwuro Malam Abdussalam Muhd
6 Unguwar Mishan Mista Sardauna Dogo
7 Unguwan Gusawa Mista Yohanna malamin gona

LITTAFIN ’YANKWANA 41

Sunan unguwa Mai unguwa


1 Unguwar Alhaji Abashe42 Malam Haruna M. Mudi

39
An haife shi a 1976, a Tashar M. Sale, inda da can ake kira unguwar Jaba. Ya yi
firamare a Ririwai 1984-1990. Yana da mata biyu da ’ya’ya goma sha bakwai maza da
mata.
40
Shi ne ragowar cikin gari + Ungwar Mishan+Unguwar Mahauta, Sharaxa, Dogon Layi,
Titin Bauci, titin sarkin yaqi Usman har zuwa kwalbatin gidan Sanata Lawal Yahaya.
41
Iyakar mulkinsa abin da ya kama daga Unguwar Gabas ya yi gabas har zuwa Unguwar
Mato-Soko.
42
Sunansa Abbas Shu’aibu, an haife shi a Zingiri da ke gundumar Rishi, a shekarar 1946,
kuma a cikinta ya tashi. Ya yi karatun allo a wajen mahaifinsa. San nan ya xora da na
ilimi a wajen M. Idi Zuku, da M. Garba Babaji Zuku. Ya dawo Gumau a shekarar 1966, in
day a qara karatun ilimi a wajen M. Idi Gumau, da M. Gero. Shi ne shugaban qungiyar
25
2 Unguwar Babaji Malam Babaji Mai kuka
3 Unguwar Malam Yakubu M. Malam Hasan Sulaiman
4 Unguwar Mato Soko M. Xan’azumi Sale (Lumes)
5 Unguwar Gakuyel Malam Manu Muhd

LITTAFIN GAKUYEL

Sunan unguwa Mai unguwa


1 Unguwar Kanya M. Idris Sama’ila (Idika)
2 Unguwar Pah Mista Jacob Nawaila
3 Unguwar Sauke Malam Yusuf Xahiru Riyo
4 Unguwar Qauna Mista Joshua G. Damau
5 Unguwar Gurum Malam Maidawa Shu’aibu
6 Tashar M. Saleh Alhaji Yunusa Saleh
7 Unguwar Yaya Hudu Malam Iliya Xantata

LITTAFIN SARKIN GABAS43

Unguwa Mai unguwa


1 Unguwar Kwari Malam Garba Abdullahi
2 Layin Xahiru Magaji Malam Usman Musa Zuku
3 Layin Malam Bugau Malam Adamu Xanjummai
4 Malam Usman Muhammed
5 Unguwar Tsamiyar Malam Malam Yusha’u Maikano
6 Layin Alaramma Maitatsine Malam Umar Shehu Malami
7 Layin Alhaji Musxafa Malam Abdullahi Umar Lame

‘Jama’atu Nasril Islam’ na qaramar hukumar Toro, tun daga shekarar 1983 har zuwa yau.
Yana da ’ya’ya da jikoki masu yawa, kuma yana daga cikin tsofin ’yan kasuwa na garin
Gumau.
43
Iyakar mulkinsa abinda ya kama daga gidan Sanata Lawal Yahaya ya yi arewa kan layin
’yan doka har qarshen gari ta arewa ya game gabas har maqabarta da masallacin Idi, iyaka
ta sa kudu da hanya Unguwar Kanya.
26
LITTAFIN SARKIN KUDU44

Unguwa Mai unguwa


1 Malam Ibrahim Hasan
2 Malam Labiru Sadi
3 Unguwar Fasa-kayi Malam Ali Wanzam
4 Malam Bala Kafinta
5 Malam Garba Kala-kuta
6 Malam Abubakar Muhammed

LITTAFIN SARKIN YAMMA

Unguwa Mai unguwa


1 Unguwar Hayin M. Ahmadu M. Damina Ahmadu
2 Unguwar M. Abdulkarim Xanbugau Malam Musa Bawa
3 Unguwar Sabon gida M. Muhammed Isa
4 Malam Ali Caku

LITTAFIN SARKIN AREWA


(Sarkin Gurawa)45

Unguwa Mai unguwa


1 Malam Rabi’u Salisu
2 Malam Wada Nasarawa
3 Malam Muhammadu Shu’aibu
4 Malam Adamu Muhammed
5 Malam Xahiru Alhasan
6 Alhaji Sani Adanu
7 Mista Yohanna Waziri
8 Malam Yusuf Abdullahi

44
Iyakar mulkinsa abinda ya kama daga gidan Sule Baqi ya yi yamma har zuwa layin
Amadudu.
45
Iyakar mulkinsa abinda ya kama daga Transifoman Caji-ofis ya yi arewa har zuwa gada.
27
LITTAFIN SHENU46

Unguwa Mai unguwa


1 Unguwar Tudun makaranta Malam Yakubu Tanko
2 Unguwar Maqeri Malam Babaji Yakubu
3 Unguwar Shenun gabas Malam Adamu Adamu
4 Unguwar Jaba Malam Ibrahim Jaba
5 Unguwar Barde (Gagati) Malam Xankaka Barde

LITTAFIN UNGUWAR TSAMIYA

Unguwa Mai unguwa


1 Malam Bala Galadima
2 Malam Shitu Isa
3 Malam Adamu Liman
4 Malam Ciroma Xan’azumi
5 Malam Sulaimanu

LITTAFIN BARANDAWA

Unguwa Mai unguwa


1 Unuwar Gwaggo Malam Keke Yakubu
2 Tashar dutse Malam Baballo Abdullahi
3 Tashar Diddila Malam Bala Alhaji Mato
4 Sabon qaura Malam Likita
5 Babageru Malam Xantala Haruna
6 Unuwar Gwaggo Malam Keke Yakubu

46
Asalin wannan littafi na Sangawan gidan Jaba ne, ya samo sunansa daga sunan dutsen
Shenu, wanda ya ke gabas da Tashar Diddila. An kafa wannan littafi a cikin shekarun
1950. Da farko gundumar Ririwai suke kai wa haraji. Kana da mutuwar gundumar a 1956,
sai suka dawo kai wa Harxo Wonu. Waxanda suka sarauci littafin su ne ; Aleka, Gona,
Garba Gobe, sai qanin Gona Amadu Jaba da Iliya Amadu 2017 zuwa yau.
28
LITTAFIN SARKIN SANGA

Unguwa Mai Unguwa


1 Unguwar majanzu47 Mista Adamu Kuku
2 Unguwar Galma48 Mista Babaji Tinja
3 Unguwar Barku49 Mista Dogo Tamanka
4 Unguwar Shimba50 Mista Basangi Damisa
5 Unguwar Kahuwa51 Mista Gumau Mailatti
6 Mista John Garba Dede
7 Unguwar Masori-gana Mista Ashantu Boyi
8 Unguwar Je52 (Adada) Mista Tambaya Salingo
9 Unguwar Mista Garba Yakubu
10 Unguwar Kajanta53 Mista Turawa Adawa
11 Mista Kabe Xangabar
12 Unguwar Project Mista Inuwa Tantan
13 Unguwar Qauna54 Mista Joshua Gwangwan
14 Malam Yakubu Musa
15 Malam Usman Digabe

LITTAFIN FULANIN KABA

Unguwa Mai unguwa


1 Malam Ibrahim Barde
2 Malam Wada Bawa
3 Malam Bala Alhaji Makaka
4 Malam Sani Kudaxu

47
Kudu da fadar sarkin Sanga
48
Yamma maso arewa da gidan Adada. Kan hanyar Gagati idan tsallake rafi.
49
Kudu da Unguwar Jinkai
50
Yamma da unguwar Jinkai
51
Kudu da gadar Maigari
52
Yamma da Dam
53
Kudu da Kahuwa
54
Gabas da Unguwar Kanya, kan hanyar Didin.
29
LITTAFIN DAWARDE

Sunan unguwa Mai unguwa


1 Malam Lawal Baqoji
2 Unguwar Lule Mista Lule Boyi
3 Malam Yahaya Dauda
4 Unguwar Sumba Mista Sumba
5 Mista Sani Damashe
6 Unguwar Dawarde Malam Hamisu Mona’i
7 Unguwar Bakin kasuwa Malam Muhammadu Abdullahi
8 Unguwar Kwari Malam Jibrin
9 Unguwar Tati Mista Tati Maiqarfi
10 Mista Yohanna Fintau

LITTAFIN NABAKA55

Sunan unguwa Mai unguwa


1 Unguwar Nabaka Mista Yohana Tatu
2 Unguwar Kajole56 Mista Peter Barde
3 Malam Mu’azu Fate
4 Unguwar Magami Malam Adamu sadau
5 Unguwar Gawata Malam Magawata Jauro
6 Unguwar Narkutawa Malam Tanko Ibrahim

UNGUWAR SÃKÕ57

Sunan unguwa Mai unguwa


1 Unguwar Barko58 Mista Anthony Yakubu
2 Unguwar Dokkoro Mista Andrawus Musa

55
Tana gabas da Magami. Amma babu hanya sai an bi ta Laru, kan hanyar zuwa Wonu,
sai a sake ayi hagu.
56
Kudu da unguwar Kanya. Rafi ne ya raba su.
57
Tana kudu da unguwar Jinkai. Wanda ya fara sarautar littafin Basangi ne, amma
bayansa duk sarakunan da suka biyo bayansa Gusawa. Ga su Sãkó, Kaka (‫َك‬ َ ‫)ك‬, Babangida.
58
Ita ake fara isa kafin Dokkoro wacce ita ce ainihin unguwar Sako.
30
AL’ADAR KARVAR KUXIN SHARA

Kuxin Shara : Wata diyya ce da ake biya tsakanin xan mace da xan
namiji, don qarfafa dangantakar da ke tsakaninsu, mai kuma karvarsa shi
ne xan mace. Haka nan jika na karvarta daga wajen kakansa, da kuma mai
sunan kakansa.

AL’ADAR XIBAR RUWAN ALKAUSARA

Ranar goma ga watan Almuharram, ranar cika-ciki da daddare, bayan


manya da suka yi azumi sun yi buxa-baki, yara maza da mata za su fita
suna bi gida-gida suna rige-rigen xibar ruwa a randunar mata, kuma cewa
za’a ji xanxanonsa na zaqi. Kuma akan tafi rafi a je a xebi ruwa a sha, ana
cewa duk wanda ya fara xiba xan aljannah ne.

AL’ADAR KWANA ZAUNE

Ran azumin qarshe ake yinsa, a wayi gari sallah. ’Yan mata ne ke
taruwa a xakin wata qawarsu wacce ba ta daxe da yin aure ba. Ran nan za
su kwana suna hira da wasanni da tatsuniyoyi, da ciye-ciye da maqulashe
wanda samarinsu ke saya musu.

TARIHIN TASHAR MOTARTA

An sa harsashin gina tashar mota a Gumau ran litinin 2 Maris 1987.


Alhaji Adamu Husaini, kwamishinan qananan hukumomi na jihar Bauci
shi ya zo ya kafa harsashin, jama’a ta taru danqam domin murnar wannan
ci gaba da aka samu. Alhali kafin a gina tashar motoci na yin lodi ne a
bakin titi.
TARIHIN KUSHEWARTA (MAQABARTA)

Kafin a yi maqabarta, da a cikin gidaje ake binne waxanda suka mutu.


A cikin shekarar 1973 aka fara yunqurin yin maqabarta (Hurumi) a
Gumau. Sarkin kudu ya rubuta takarda ya aikawa hukumar L.A. a Bauci,

31
yana neman izini don yin kushewa a bayan gari. Saboda garin layi-layi ne,
babu yadda mutum zai yi qari don gidansa ya cika. Kuma gidajen a san nan
wasu sun riga sun cika da qaburbura da shaddodi (masai). Kuma har wayau
garin daxa girma ya ke yi. To, ana nan kan haka, umarni bai zo daga en’e
ba, sai a shekarar (1980) aka yi maqabarta a gabas maso arewa da gari, can
gangare, kusa da rafi. Sanadin yinta kuwa, Alhaji Yunusa ya yi wasiyyar
kada a binne shi a gida, da aka gaya wa sarkin kudu sai ya yi umarni a
nemi wurin yin kushewa, sai M. Gajeren Gada ya bad a wuri a yamma da
gari. San nan kuma Alhaji Umaru Xalladi Maute ya bad a wuri a gabas da
gari don yin kushewa.

WANDA AKA FARA BINNEWA A CIKINTA


Mutum na farko da aka fara binnewa a maqabartar gabas da gari wata
tsohuwa ce mai suna Tiyaye, asalin sunanta na gaskiya shi ne Maryamu, ita
ce kakar sarkin gabas Alhaji Adamu. Ita maqabartar yamma da gari ta cika
tun a wajejen shekarar 2005. Ita ma gabas da garin ta cika tun wajejen
shekarar 2009, sai Alhaji Musa Laska ya sayi gonakin da ke gefenta aka
qara faxaxa ta.
TARIHIN KASUWANTA
Kamar yadda muka gaya muku tun farkon kafa gari, cewa da kasuwa ya
fara, kuma ranar alhamis ta ke ci. To, dawowar Sarkin Yaqi Babale sai ya
kafa ranar litinin, amma dai ba’a daina cin kasuwar alhamis ba. Ko da dai
mutane sun xauka litinin ita ce babbar kasuwa, alhamis kuma qaramar
kasuwa. To, ana nan sai aka ba da dama a buxe masallacin jumma’ah daga
Bauci. Sai sarkin yaqi ya ga a shigo a ci kasuwa, gobe kuma a dawo
sallah? Ai gwamma a haxe, kasuwar alhamis ta dawo jumma’ah. Sai
manyan gari suka yi shawari da attajirai da malamai akan a mai da
kasuwar alhamis jumma’ah, nan da nan aka tara maroqa, Kwando Farin
Malam da Duna Nayayale suka yi shela a kasuwa da yamma cewa “Daga
yau duk mai son zuwa cin kasuwar Gumau alhamis, to, ya bari sai ran
jumma’ah, ya zo ya ci kasuwa, kuma ya yi sallar jumma’ah.” Tun daga ran
nan sai Gumau ta koma cin kasuwa ran jumma’ah da litinin, har kuwa yau
xin nan.
32
TARIHIN GININ RUMFUNAN KWANONTA

An fara gina rumfunan qasa tun cikin shekarun 1940. Amma rumfan
kwano sai a cikin shekarar 1958 aka gina su. Lokacin da baturen Dubagari
ya zo rangadin qasar Lame ran 18-11-1957, ya duba garuruwan Gumau,
Pingel, Rishi, da Dawa. To, bayan ya ga abin da ya gani, sai ya tsara
rahotonsa ya miqawa wa en’e kan yadda za’a qara kyautata su. Ga abin da
ya ce dangane da kasuwar Gumau :

“Kasuwar Gumau babu tsabta, nama da mahauta ke sayarwa a kasuwa ba


tsabta. Ya kamata kowanne mahauci ya sami tebur inda zai riqa saka nama,
ba a qasa kawai ba. To, saboda haka rumfunan kasuwa suna buqatar a sake
su. mayanka kuma da lambatun jikinsa yana da datti qwarai, kuma ya
rugurguje, ana buqatar a sake dave shi da siminti. Rijiyoyi na cikin gari
duka babu murfi, ana buqatar ayi musu duka.”

To, da ganin wannan rahoto, sai hukuma ta ba da aikin kwangilar gina


sabuwar rumfar kwanon mahauta. Kuma aka umarci sarakunan fawa da
sauran mahauta gaba xaya da su riqa bin dokoki da umarnin da ma’aikatan
lafiyar dabbobi za su riqa bas u. Kuma mafi muhimmancin abu da ake so a
gare su su kiyaye, shi ne, “Idan sun yi fixa, kada su tava huhu, hanta,
zuciya, kai, da hanji, sai bayan masu duba nama na sashin duba lafiyar
dabbobi sun ba su izini.” Kuma duk wanda aka samu ya sava wannan
doka, to, babu wata-wata za’a kais hi kotu, kuma shara’a bat a san jahilci
ba.

SHAGUNAN QARSHE DA GWAMNATI TA GINA

Shagon qarshe da gwamnati ta gina shi ne mai kallon gidan Alhaji


Badamasi da na arewa da shi, a shekarar 2001, zamanin shugabancin
Xanlami Garba Abubakar Tashar Durumi, kuma Alhaji Na’iya shi ya yi
kwangilar.

33
MASU GINANNUN SHAGUNA A KASUWAR GUMAU A 1970

1- Alhaji Yunusa Gumau


2- Alhaji Audu Safe
3- Alhaji Manaja
4- Alhaji Talle
5- Alhaji Sama’ila59

TARIHIN FULOTINTA
(Kasuwar Audugarta)
“Fuloti kasuwar sarki, wata uku ci, wata tara fashi”
Fuloti na farko yana daidai gidan Alhaji Na’iya da Alhaji Maiwada da
abinda ya yi bayansu, ya game da gidan Alhaji Talle har zuwa gidan mala
Muhammadu Yahaya.
XAKIN ANGURYANTA

An gina xakin angurya a Gumau cikin shekar 1965. An gina shi kusa da
asalin fulotin ta ke, gas hi nan har yanzu a tsaye da ginin kwano, arewa da
masallacin Alhaji Na’iya. Xan kwangilan da ya gina shi ne Malam Ibrahim
xan malam Ladan Gungura malamin gona.

SAYAR DA XAKIN ANGURYA


An sayar da xakin audugarta a shekarar 2013 ga Alhaji Yakubu Na’iya.

SAYAR DA FILIN FULOTI NA FARKO

An sayar da filin fulotin farko, ta bakin kasuwa a cikin watan Oktoba


1978. Aka yanka feguna shida a cikinsa, aka sayarwa mutum shida,
mutanen su ne ;

59
Shagonsa na yamma da shagon Fatakwal mai askin baba, amma fa yanzu babu ginin
shagon.
34
1- Alhaji Na’iya
2- Alhaji Maiwada Wundi
3- Alhaji Sarkin Ririwai
4- Alhaji Maikuxi Gumau60
5- Sarkin yaqin Bauci (M. Yakubu Lame)
6- Sarkin Noma Shehu Gumau

Shi filin Alhaji Na’iya sai ya gina abinsa, ya rayu a ciki. Shi ma filin
Alhaji Maiwada Wundi, ya gina abinsa, gabas da na Alhaji Na’iya, amma
shi bai rayu a ciki ba. A shekarar da aka bai wa Lame qaramar hukuma,
hedkwata Gumau, sai ya bayar das hi haya aka yi sakateriya. Da aka rushe
qaramar hukumar Lame kuma, wani xansa ya zauna a vangare xaya na
gidan, xaya vangaren kuma aka sa ’yan haya. Shi kuwa wanda sarkin
Riruwai Muhammadu Inuwa ya saya, ya gina abinsa gabas da gidan Alhaji
Maiwada Wundi, amma shi da kansa bai zauna a cikinsa ba, sai xansa Sani
ne ya xan zauna ciki. Hasali ma ya sayar dashi a shekarar 2000, ya saya wa
xansa Salisu motar haya yana tuqawa. A shekarar 2001 Salisu ya yi hatsari
da motar ya rasu, motar kuma an rasa ta. M. Ibrahim Qani, Xanburam
Wunti, shi ya sayi gidan, shi ma ya sayar wa Alhaji Iliya Garba a shekarar
2015. Shi kuwa wanda Alhaji Maikuxi ya saya, yana arewa da na Alhaji
Maiwada Wundi, sai ya sayarwa Alhaji Talle, in das hi Alhaji Tallen ya
gina abinsa ya yi rayuwarsa a ciki, har zuwa mutuwa, har ma iyalansa suka
gada daga gare shi.

TARIHIN FILIN FULOTI NA BIYU

Shi kuwa asalin filin sabuwar fuloti gonar M. Umaru ‘Mai miyar yanke
yatsu’ ne, uban Kãlakûta. To, lokacin da xansa Kalakuta ya samu auren
fari,61 har aka kai ga yanke masa sadaki, gashi kuma babu kuxi a hannu da
za’a biya. A lokacin kuma shi Kalakuta yana koyon xinki a wajen Dodo
Tela, sai uban ya ce shi kuwa ba zai sayarwa da kowa gona ba sai Dodo
60
Alhaji Maikuxi Gumau, shugaban jam’iyyar NPN (National Party Of Nigeria) na jihar
Bauci 1979-1984. Ya rasu ran 29 Disamba 1992
61
Uwar xansa Shehu
35
Tela, wanda ya ke koyawa xansa sana’a, sai dai fa idan shi ne ya ce ba zai
saya ba. To, sai ya je ya gaya wa Dodo Tela cewa yaronsa fa mai koyon
xinki ya samu aure, har an yanke masa sadaki, don kada ya ji a waje, kuma
yana so zai said a gonarsa ta wuri kaza don ya biya masa sadaki, shi ne ya
zo wurinsa akan ya biya. Dodo Tela ya biya kuxin gona, ya yi kamar
shekara biyar yana noma ta, To, cikin shekarar 1978, sadda aka tashi fuloti
daga bakin kasuwa, don tsoron tashin gobara, sai aka ce a duba wani wurin
da za’a yi sabon fuloti, to, sai aka ga babu inda ya dace kamar wannan
gona ta Dodo Tela. Aka auna, aka kafa qarafu, aka ce za’a biya shi
diyyarta. A biya yau, a biya gobe? Ba’a dai biya ba. Shi kuma dama duk
shekara idan lokacin damina ta yi bai daina yin nomansa a gonar ba. Idan
ya kwashe amfanin gonarsa kuma lokacin fuloti ya yi aci kasuwar auduga.
Su bas u hana shi noma tab a, shi kuma bai hana su cin kasuwar audugarsu
a gona ba. Har ma aka zo lokacin da noman audugar ya yi tasgaro, aka rufe
fulotin ma baki xaya. Alhaji Sani Xanhasan shi ya warware qarafan fulotin
ya sayar a shekarar 199. Su kuwa masu gona tun da dama ba’a biya sub a,
sai gonarsu ta dawo hannunsu baki xaya.

TARIHIN MAYANKANTA (KWATA)

Mayanka ta farko da aka gina tana daidai gidan Ibrahim Quli-quli da Mato
Direba. Bayan lalacewarta an gina sabuwar kwata a unguwar bariki, da ke
kan titin Badikko a qarshen shekarar 1977. Alhaji Sa’idu shi ya yi
kwangilar gininta. An gina ta a kan kuxi naira dubu goma sha xaya da xari
biyu da hamsin (N11,250) daidai, an yi aikin an gama a cikin wata shida.

TARIHIN XAKIN KARATUNTA (READING ROOM)

Ridaru kamar Hausawa ke cewa ko ‘Reading room’ kamar yadda bature


ya kira shi, xaki ne da hukumar en’e ke ginawa ana zuba littattafai a
cikinsa don qarfafawa da sauqaqawa masu son karatu, su je wajen su yi ta
karatu kyauta. Kuma akan aiko da jaridu, ga mai son sanin me duniya ta ke
ciki. Haka nan a wurin akan ajiye rediyo da za’a riqa kunnawa jama’a suna
jin labaran duniya. Akwai ma’aikaci na musamman da akan xauke shi aiki

36
,mai lura da wajen, shi ke buxewa kuma shi ke kullewa. An gina Ridaru na
Gumau a cikin shekarar 1955, a daidai inda ofishin malaman yaqi da
jahilci ya ke a yanzu. Yana kallon gidan Alhaji Saidu. Wanda ya yi
kwangilar ginawa shi ne Mista Hary. An sa tebur guda 2, da kujeru 3,
rediyo, kujeru kushin 2, tawada da alqalami, kananzir, da sabon littafin sa
hannu ga masu nufin yin aron littafi. An sabunta gyaransa a 1968 lokacin
da malaminsa ya rubuta takardar koke cewa tagogi uku, da filastar bangon
ginin sun lalace, kuma idan ba’a yi sauri an gyara ba, abin zai vaci. To, sai
hukumar en’e ta turo Malam Bala Kobi, shi ne xan kwangilar da ya yi
gyaransa a cikin watan Yunin 1968.

MALAMIN RIDINRUN

An nemi hakimi da ya nemi wani mutum malami, mai amana, wanda ba


ma’aikacin sarki ba, wanda zai riqa lura da wurin yana rufewa da buxewa
ana xan biyansa lada. To, sai aka xau M. Inuwa Ridaru ana biyansa fam
xaya da sule sha biyar (£1:15:00). Da en’e ta ga amana ta sa, bayan shekara
guda sai aka xauke shi aiki na sosai, kuma aka qara masa albashi. Bayan
M. Inuwa, sai aka xauki M. Isa Lame malamin Ridaru a 1958.

LOKACIN BUXE SHI

Ana buxe Ridaru da misalin qarfe na 3:00pm zuwa qarfe 6:30pm, a sake
buxewa da qarfe 7:30 na marece zuwa qarfe 10:00 na dare.

GIDAJEN HUKUMA A CIKINTA 1940-2021

1- Gidan hakimi
2- Gidan malamin hakimi62
3- Gidan malamin shanu63
4- Gidan malamin gona64

62
Gidan Ambasada na titin Waziri Xanwunti. Alhaji Muhammadu ya saye shi.
63
Sarkin kudu Muhammadu Maidawa ya saye shi a 1980.
64
Shi ne yanzu gidan M. Abdulkarim Kwabi. M. Umaru Abubakar ya saye shi.
37
5- Gidan malamin daji65
6- Gidan malamin lamba (duba-gari)66
7- Gidan baqi67
8- Gidan malamin asibiti68
9- Gidan Abasaya69
10- Gidan Alqali70
11- Gidan Magatakarda.71
12- Gidan Magatakarda72
13- Developmenta Area Office
14- Asibitin dabbobi
15- Asibitin primary health care
16- Qaramar kotun shari’ah
17- Babbar kotun shari’ah
18- Caji-ofis
19- Development Area

MUTANEN DA SUKA YI TSAWON RAI CIKINTA

1- Alhaji Sabo
2- Sarkin Yaqi Muhammadu Maidawa
3- Baba Julde
4- Iya rago-rago
5- M. Idi xan Muhammadu Jika
6- Gwaggon Talle

65
Shi ne yanzu gidan Murtala Yakubu (Majidaxin Wunti). Alqalin Gumau ya saye shi.
66
Shi ne gidan malamin lamba da ke tsakanin gidan Atamfa da gidan M. Yahya mai tebur.
M. Audu Ningi ya saye shi.
67
Yana arewa da gidan sarkin gabas. Tsakaninsa da gidan Ahmad Maigwaram kuwa yana
kudu ne, titi ne ya raba su. An sayarwa da Ambasada AG Abdullahi ran 13 Maris 2013, a
kan kuxi Naira dubu xari biyu (N200,000) daidai.
68
Matasan Salafiyya sun saye shi a 2016, Shi ne gidan marayu na ‘Almufidah’ a yanzu.
69
Gidan Xanladi Aljan haxe da gidan Ahmadu Audu Safe.
70
Alqalin Gumau M. Yakubu ya saye shi.
71
Alhaji Musa Umaru ya saye shi.
72
Shi ne gidan Ambasada mai kallon gidan Jarman Wunti.
38
7- Matar Mande (Inna)
8- M. Abdullahi Ubangida
9- Alhaji Audu Safe73

TARIHIN MAHAUKATANTA
1- Camfiyo
2- Yaramashushu
3- Tiri-tiri (motar ’yan gayu)
4- A-shiga-gari
5- Beru
6- Majidda
7- Camfiyo
8- Makuba (vata ruwa)
9- Ala -Kyauta -Alhaji74

TARIHIN BUKUKUWANTA

1- Bikin qaramar sallah


2- Bikin babbar sallah
3- Bikin cika-ciki

73
Ya rasu ran talata 01 Almuharram 1443 hijri, daidai da 10 Agusta 2021 miladi.
74
Asalin sunansa Aminu Baqi, mutumin Xanbatta ta qasar Kano. Qwararren mai aikin
jinya ne a asibiti, a ma’aikatar lafiya ta jihar Kano, a cikin shekarun 1980’s. daga bisani
sai ya rasa aikinsa, kuma aurensa ya mutu. Sai ya samu matsalar tavin hankali,
qwaqwalwarsa ta juye. Sai danginsa suka kais hi asibitin masu fama da matsalar
qwaqawlwa na Xanbatta. To, daga can ne ya gudu, amma sai ma’aikatan asibitin suka
cewa danginsa wai ya faxa a rafi, ruwa ya tafi dashi. Su kuma duk dab a su ga gawarsa ba,
sai suka sakankance ya mutu, kuma suka dangana. Ya zo Gumau tun wajen shekarar 1990.
Kuma bisa wasu alamomi da aka sha gani tattare dashi, ya yi karatun boko, kuma ko cikin
karatun bokon ma vangaren magani. Wani Xanjarida Sama’ila Bala Gumau ya yi ta bad a
cigiyarsa a gidan rediyon tatrayya na Kaduna. Ko za’a samu ’yan’uwansa su zo su xauke
shi, Allah bai sa an dace ba, sai a cikin watan Oktoban 2019 wasu mutanen garinsu masu
yawon neman wani xan’uwansu kuma day a vata, da suka zo Gumau sai suka ganshi.
Suka nemi a bas u shi, aka ce sai sun kawo sheda. Suka koma suka zo da shedu da takarda
suka nunawa hukuma, aka sallama musu shi ranar 24-10-2019. Mutanen Gumau sun yi
baqin cikin rabuwa dashi ranar da aka xauke shi.
39
4- Bikin Aure
5- Bikin Suna
6- Bikin saukan karatu
7- Bikin kaciya
8- Bikin Darero
9- Hawan Mamman Kusu75

YAWAN KOTUNANTA A 1957-2010

An buxe kotun farko Gumau a 1957. Amma yawan kotuna 2021 guda uku
ne :

1- Kotun eriya (Area Court), daga baya ta juye kotun Shari’ah.


2- Babbar kotun Shari’ah (Upper Shari’ah Court)
3- Kotun Majistare (Magistrate Court)

ALQALAN KOTUNAN SHARI’ARTA 1957-2020

1- M. Umar
2- Malam Nata’ala
3- Malam Jatau
4- Malam Shehu
5- M. Yakubu Umar
6- Malam Muhammadu Inuwa
7- Malam Adamu Aliyyu
8- Malam Yakubu Bauci (Reza)
9- M. Salihu Kangere
10- M. Qasimu Aliyyu
11- Abdullahi Manzo Atiku
12- Lawal A. Muhammed
13- Ahmad Wakili
14- M. Aminu Tukur
75
Ana yinsa da qaramar sallah. An fara shi a bayan qaramar sallar shekarar 2021. Sarkin
yaqi Aliyyu ya fara shi.
40
15- Ahmad Musa Wuro-Jamel
16- J. Aliyyu Duguri
17- M. Yakubu Xewu 2001-2020
18- Adamu Baba
19- Abubakar J. Alkas

TARIHIN TARON SHAWARA NA FARKO


DON RAYA GARIN GUMAU 1975

Tun cikin shekarar 1975, sakataren gwamnatin jihar Arewa maso gabas,
Alhaji Abubakar Umar ya jagoranci ’yan kwamitin ci gaban Gumau zuwa
Maiduguri wajen gwamnan jihar Arewa maso gabas Birgediya Musa
Usman76 da koken mutanen Gumau kamar haka ;

1- Neman sabuwar hanyar kwalta daga Magama zuwa Gumau.


2- Neman wutar lantarki a Gumau.
3- Neman babbar makarantar Sakandare.
4- Neman a yi ruwan famfo.
5- Neman yin madatsar ruwa (Dam).

Kuma gwamna ya yi murna da ganinsu, har ma ya yi musu


kyakkyawar tarba. Kuma ya yi alqawarin kadan Allah ya so duka za’a
yi su, har ma ya qara ya ce, ko shi bai yi ba wanda zai zo bayanshi zai

76
An haife shi ran 3 Fabrairu 1940, a Enugu, mahaifinsa Babarbare ne, mahaiyarsa kuma
Igala ce. Mafi yawan rayuwarsa ya yi ta a Ibadan ne, tare da mahaifiyarsa, a lokacin da
mahaifinsa ke can a filin daga, na WAFF ( West African Frontier Force) da ke yaqi a
Burma. Bayan dawowar mahaifinsa, ya koma Zariya da zama, in day a sanya Musa a
makarantar sojoji. Kafin nan kuwa an tava sa shi a makarantar ‘ Goodbye School’ da ‘St
Michael’ duka a Kaduna. Musa ya bi hanyar mahaifinsa, in da aka xauke shi aikin soja a
1958, har ma aka tura shi kwas a qasar Ghana. Shi ne Gwamnan mulkin soja na farko na
jihar arewa maso gabas, 1967-1975. Yana daga cikin sojojin da suka juyin mulkin day a
kifar da Janaral Aguiyi Ironsi a watan Yulin 1966. Shi ne wanda ya rubuta ya ajiye shirin
kafa kamfanin siminti na Ashaka, wanda aka buxe a 1979. Kuma shi ya rubuta ya ajiye
dukkan abubuwan ci gaba da mutanen Gumau suka roqa a wajensa. Ya rasu a asibitin
Jamus ran 14 Satumba 1991.
41
yi. To, a farkon 1976 sai aka raba jihar Arewa maso gabas gida uku,
Borno, Bauchi, da Gongola. A farkon 1977, sai sabon gwamnan jihar
Bauci na farko, Birgediya Bello Khaliel ya kawo ziyara Gumau, sai
manya suka kuma roqonsa waxancan buqatu. Shi ma ya yi alqawarin
zai tabbatar das hi a rubuce, kuma -kadan Allah ya so- wanda zai zo a
bayansa zai yi.

TARON SHAWARA NA BIYU


DON RAYA GARIN GUMAU 1978

Ana nan zaune kan haka, ranar 22 ga watan Maris 1978, shugaban
qaramar hukumar Toro ya da sarkin kudun Bauci hakimin qasar Lame
suka gayyaci manyan mutane dattijai, suka taru a Gumau ran Alhamis
30 ga wannan wata na Afrilu, 1978 suka yi shawara kan yadda za’a
kawo ci gaba ga cikin garin Gumau, don raya tat a sami shiga cikin
matsayin da ya dace da zamani, waxannan mutanen su ne :

1- Alhaji Sa’idu Gumau


2- Alhaji Uba Gumau
3- Alhaji Inuwa Ririwai
4- Alhaji Na’iya Gumau
5- Alhaji Talle Gumau
6- Alhaji Maikuxi Gumau
7- Alhaji Mamman Kilaki
8- Alhaji Inuwa sarkin Riruwai
9- Alhaji Abubakar Manaja
10- Alhaji Bala Direba
11- Alhaji Abubakar Tambuwal
12- Alhaji Badamasi Gumau
13- Alhaji Ibrahim Zalau
14- Alhaji Galadima Babban-Gura
15- Alhaji Iro sarkin Rishi
16- Alhaji Itatu
17- Alhaji Sabo Wundi

42
18- Alhaji Husaini Wundi
19- Alhaji Bala Makanike
20- Alhaji Maiwada Wundi
21- Alhaji Salmanu Maiwada Wundi
22- Alhaji Sunusi Rahama
23- Sarkin Fawa Rahama
24- Alhaji Alhasan Rahama
25- Alhaji Badamasi Rahama
26- Umarun Tulu
27- Majidaxin Tulu
28- Sarkin kudun Sabon gari
29- Alhaji Idi Tulu
30- Adamu Bahausa Barayan Wunti
31- Tare da sakataren qaramar hukuma : Alhaji Ahmed Baqon-dare

Jama’a ta taru danqam, kuma an yi taro, bayan qare taro, sai aka
shirya hanyoyin da za’a bi, don tunawa sabon gwamna Garba Duba77
irin alqawarin da magabacinsa ya yi. Ana samunsa kuwa, nan da nan
kuwa ya bad a kwangilar yin sabuwar hanyar kwalta tare da gadojinta
daga Magama zuwa Gumau, da gina makarantar babbar Sakandare ta
GSS Gumau, da sanya wutar lantarki, da sanya famfo. Dam ne kaxai a
san nan bai samu ba.

77
Tafidan Kwantagora, an hafe shi a Mariga, Kwantagora cikin jihar Neja, a 1942. Ya yi
makarantar firamare ta Kwantagora 1950-1956. Kana ya zarce Niger Provincial
Secondary School’ 1957- 1962. Daga nan sai ya tafi kwalejin horon sojoji ta ‘Nigerian
Military Training College’ Kaduna. Ya yi kwasa-kwasai da yawa, a qasashe daban –
daban. Ya zama gwamnan jihar Bauci a 1977-1979. Shi ne wanda ya bad a kwangiloli
masu yawa don raya jihar Bauci, shi ya gina sakatariyar qananan hukumomin jihar Bauci
guda 16. Ya kawo kamfanin Steyr, Bauchi State Polytechnic, ya qara yawan makarantun
horon malamai, da ‘BACAS da makarantun firamare masu yawa, a ko’ina cikin faxin
jihar Bauci.
43
TARIHIN SANYA WUTAR LANTARKI

An fara aikin sanya wutar lantarki a Gumau a farkon watan Satumbar 1980. An
fara da sassare bishiyoyi a duk inda ake buqatar kafa falwaya. Bayan nan an
kakkafa falwaya a kowanne layi na cikin gari, har ma inda gidaje ba su kai ba. Sai
dai layuka uku su kam ba’a sa ba ; layin liman, layin Atamfa bakin kasuwa, titin
Alqali da titin Harxo Abubakar. Ran 28-10-1980 wakilan kamfanin da aka ba su
kwangilar kai wutar lantarki Gumau, wato ‘Nigerlec’ suka zo Gumau don biyan
diyyar dukkan wanda aka sare masa bishiya, don kafa falwaya a wurin, aka
buqaci kowa ya tsaya a daidai in dad a bishiyarsa ta ke.

SHAHARARRUN MUTANE DA AKA YI A CIKINTA

A dukkan zamani akan samu wasu mutane waxanda Allah maxaukakin sarki ke
yi wa baiwa da abin da ya so. Wasu ya basu kuxi, wasu sarauta, wasu ilimi. Wasu
kuma wata fasahar daban. Wasu kuma ya yi musu tagomashi da abubuwa da
dama. Kamar haka Allah ya yi wa mutane masu yawa a cikin Gumau da baiwa iri-
iri kamar haka :

WAXANDA SUKA SHAHARA DA ILIMIN MUHAMMADIYYA

Na kasa malamanta gida bakwai kamar haka ;


1- Alarammomi masu tsangayar Alqur’ani
2- Alarammomi marasa tsangayar Alqur’ani
3- Malaman Alqur’ani masu tsangayar Alqur’ani
4- Malaman ilimi masu zauren karantarwa
5- Malaman ilimi marasa zauren karantarwa
6- Malaman Arabiyya masu wa’azi
7- Ladanai waxanda suka shahara da kiran sallah
8- Limamai

ALARAMMOMI MASU TSANGAYAR ALQUR’ANI


Alarammomi marubuta Alqur’ani da aka tava yinsu a wannan gari, daga da can
har zuwa yanzu su ne ;
1- M. Yahya
44
2- M. Mudi
3- M. Yusufu Mahmudu78
4- M. Umar Kawu79
5- M. Walidu Mu’azu
ALARAMMOMI MARASA TSANGAYAR ALQUR’ANI
1- M. Abdulkarim Xanbugau
2- M. Idris Tawakkalna
3- M. Hafizu Alaramma
4- M. Shu’aibu Ibrahim80
5- M. Iliya Kadage81

78
Alaramma, kuma shugaban masu darasu na garin Gumau. An haife shi a Unguwar
Alhaji Abashe a shekar 1980, ya sauke Alqur’ani a wajen mahaifinsa, kana ya fita neman
Alqur’ani. Ya zauna a garuruwa da, a gaban Alarammomi daban-daban, har said a ya
haddace, kuma ya rubuta. Yana da iyali kuma yana da ’ya’ya.
79
Umar Yakubu Muhammad, shi Yakubun shi ake cewa M. Kawu. An haife shi a
Unguwar Tsamiya cikin gundumar Wonu, a shekarar 1980. Ya yi karatun Muhammadiyya
a wajen mahaifinsa, har zuwa sauka. Kana ya fita neman karatu, inda ya yi karatu a
tsangayar Alaramma Doguwa, da kuma tsangayar Alaramma M. Muhtari da ke Mil tara
Kano ya fara rubuta Alqur’ani a shekarar 2003. Ya yi karatun ilimi a wajen M.
Muhammadu Yahya Gumau. Yanzu haka yana ci gaba da karantarwarsa kuma shi ne
na’ibi na biyu na babban masallacin Jumma’an Sarki.
80
Shu’aibu Ibrahim Adamu, an haife shi a 1933 a Bakin-Kogin Dulumi, kuma a cikinta ya
tashi. Ya yi karatun Muhammadiyya a wajen M. Jamau na Dalam, da M. Mahmudu na
Tukutu. Sai mijin mahaifiyarsa ana cewa da shi Baffa Xanmalam, wani mutumin Xewu da
aka kawo shi Bakin Kogi yana yi wa mutane fito, sai ya xauke shi zuwa Xewu in da ya
xora karatu a gidan limamin Xewu, har ya yi sauka cikin shekara uku. Daga nan sai ya
dawo Zingir in da mahaifiyarsa ta koma da aure, bayan mutuwar tsohon mijinta, ya xora
karatu na shekara biyu a wajen Alaramma M. Hamza, wani mutumin Barmaguwa cikin
qasar Haxeja, wanda Alhaji Xan Wudil Maigoro -babban mai kuxin Zingir a zamaninsa-
ya ajiye shi, in da ya samu tilawar Alqur’ani. Ya yi karatun ilimi a wajen M. Na’iya na
birnin Zazzau. Daga nan ya tafi Gwambe ya yi auren fari, ya auri Maryam ’yar malaminsa
M. Dauda, ita ce uwar babbar ’yarsa A’ishatu matar ‘Bammali Gumau’. Kana ya koma
Kafanchan in da ya auri matarsa Hajara, bafulatana, ta haifa masa Azumi Tanko da
sauransu. Malam ya koma Unguwar Mai lafiya a 1988, sadda aikin ma’adanai ya bunqasa
a wajen, har ya yi limanci na shekaru 33, kana ya dawo Gumau da zama.
81
Ya rasu ran Laraba da daddare 3 ga Ramadan 1442 daidai da 14 Afrilu 2021, bayan
gajeruwar jinya.
45
MAKARANTA ALQUR’ANI MASU TSANGAYA

1- M. Garba Xandibi
2- M. Yakubu Alaramma
3- M. Mahmudu Bugau
4- M. Abdulhamid Xanhasan
5- M. Abdullahi Ubangida
6- M. Salisu Maje-haji
7- M. Garba Dede
8- M. Haruna Didin
9- M. Ahmadu Jira
10- M. Babarere Laru
11- M. Babarere Unguwar Mahauta
12- M Musa Tsari82
13- M. Ibrahim Sabo83

82
Musa Muhammad ahmad, an haife shi a Kawo cikin gundumar Tama a 1996, kuma
cikinta ya tashi. Ya yi karatun allo a wajen baffanshi, M. Abbas Galadima Kawo, sai M.
Abdulhamid Xanhasan Gumau, da M. Salisu Majihaji, su biyu duka Gumau. Ya yi karatun
ilimi a wajen M. Abdulmumin Adamu, da Alhaji Sharu Lawal Jos. Ya yi karatun Firamare
a Sabon garin tulu a 1973-1982. Ya tafi makarantar koyon ilimin addinin musulunci mai
zurfi (School For Higher Islamic Studies) da ke layin sarkin Mangu Jos 1986-1990. Daga
nan sai ya tafi makarantar koyon aikin shari’ah da ke (School For Shari’ah & Legal
Studies) Misau 1991-1993. Kana sai jami’ar Abuja in day a karanci larabci 1998-2002.
Yana zaune a Gumau tare da iyalansa, kuma yana ciga bad a karatu da karantarwa.
83
An haifi Alhaji Ibrahim Sabo (Magajin malam Babba) a tsakiyar shekarun 1970, a gidan
Falaliyawa, da ke kan titin Sarkin Yaqi Usmanu Babale, a Unguwar Malamai, wacce aka
fi sani da Dogon layi Gumau, ta qaramar hukumar Toro cikin jihar Bauchi- Nijeriya. Ya
halarci makarantar Firamare ta Unguwar Waziri daga 1980-1985. A 1986 ya ci jarabawar
zuwa makaranta ta gaba, wato GSS Gumau, in da ya gama a 1989. A 1993 ya koma
wannan makaranta, wacce daga baya ta juye kolejin koyon sana’a (Government Technical
College), ya karanci sarrafa wayoyin lantarki ( Electrical Installation), ya gama a 1996. A
tun tashinsa, ya tashi da karatun allo. Har zuwa sadda ya sauka, ya kama hadda, kuma ya
xora karatun ilimi, duka a wajen mahaifinsa, da M. Abdulhamid Xanhasan, Alaramma Isa
Gezawa da Alaramma Muhammadu Hafizu. San nan ya yi karatu a wajen liman M. Garba
Xanbaqi, da liman M. Muhammadu Yahya wanda su duka almajiran kakansa ne. M.
Adamu Ibrahim Tilden Fulani, da sanannen malamin furû’an nan liman M. Abdulmumin
Adamu, in da ya sauke littattafai masu yawa a wajensa. Da dai malamai masu yawa wanda
46
14- M. Xanladi Ustaz
15- M. Ali
16- M. Dauda
17- M. Shafi’u

MALAMAN ILIMI MASU TSANGAYA

1- M. Idi xan Muhammadu Jika


2- M. Adamu Gwandu (Lazina)
3- M. Muhammadu Yahya
4- M. Abdulmumin Adamu84

ya yi karatu a gabansu, a garuruwa daban-daban. A 1996, ya tafi kolejin larabci da koyon


ilimin Alqur’ani mai zurfi da ke Kura-Kano (School of The Holy Qur’an & Islamic
Studies). Wacce wani vangare ne na jami’ar musulunci ta duniya (International University
of Africa) da ke Khartum-Sudan. Mashahuriyar qungiyar nan mai yaxa ilmummukan
addinin musulunci a duniya, wadda cibiyarta ke Khartum-Sudan suka buxe reshenta a
Nijeriya, wato Munazzamat El Da’awa El Islamiyyayyah. Ya gama a 1999, in da ya samu
shahadar qwarewa a ilimin kimiyyar Alqur’ani (Qur’an & Qur’anic Sciences). Ilimin da
ya tattaro qira’o’in Alqur’ani da bambance-bambancensu, ilimin tafsiri da yadda ake kira
zuwa ga addini (DA’AWA), fiqihun musulunci mai zurfi da bambance- bambancensa,
kana da ilimin hadisi da larabci. Yanzu haka shi ne limamin sarkin yaqin Bauchi, hakimin
qasar Lame. Kuma daraktan makarantun Ma’ahad Gwani Idrisu College For Qur’an &
Qur’anic Sciences. Kuma yana da tsangayar ilimi da ake xaukar karatu a cikinta. Yana da
iyalai, kuma ya tava yin aikin hajji da umrah. Ya wallafi littattafai da dama cikin Hausa da
larabci.
84
Abdulmumin Adamu Isa. Na asalin Bebeji ta qasar Kano. An haife shi a shekarar
miladiyya ta 1952. A wani qauye da ake kira Yalwan –Bage, wasu na kiransa Yalwan –
Tsakani, da ke gundumar Geji, ta qasar Jama'ah. A qaramar hukumar Toro da ke Jihar
Bauchi ta Nijeriya. Mahaifinsa ya rasu tun yana qarami. Amma kafin rasuwa ta sa ya
danqa shi don ya yi karatu a hannun babban wansa M. Isa Adamu Isa. Wanda shi malami
ne mai karantarwa a garin, kuma shi almajirin M. Na'iya ne, na birnin Zaria. Bayan ya yi
sauka a wajensa, sai ya tafi wajen shahararren malamin nan Fulata –Borno, da ake kira M.
Umaru, limamin Zaranda na farko. Wanda shi kuma almajirin M. Yahuza na Zaria ne. In
da ya karanci ilimi, tun daga qawa'idi, Ahlari, Qurxubi da sauran littattafai. Daga nan sai
ya tafi cikin birnin Bauchi. Tsangayar ilimi ta M. Sa'idu. In da ya karanci Ishimawi, Iziyya
da wasunsu. Daga nan sai ya koma Tsangayar Ilimi ta M. Garba Mai Karatu na unguwar
Kobi, duk dai a Baucin. Shi ma wani shahararren malami ne a zamaninsa. In da ya karanci
Lugga : Waqen Badamasi, Zuhudu, Alburdah, Ishriniyyah, Deliya, Xanxarani da
47
5- M. Salisu Ta’an
6- M. Mahmud Adamu85
7- M. Haruna Aliyyu

MALAMAN ILIMI MARASA TSANGAYA

1- M. Garba Xanbaqi86
2- M. Adamu Idris
3- M. Ibrahim Mai kemis
4- M. Xallami Audu Safe
5- M. Habibu Liman Abubakar
6- M. Alhasan Sadi
7- M. Mahmud Adam
8- M. Haruna Aliyyu

sauransu. Kana daga nan har an yi masa auren fari ma, sai malam ya dawo Gumau, in da
malam ya yi karatu a wajen M. Adamu Gwandu, wanda aka fi sani da Malam Lazîna. Inda
ya karanci Lawwali da Sani (Mukhtasar), Muwaxxa da sauran littatafai. Kuma a nan
Gumau Allah ya yi zamansa. Ya buxe Tsangayar koyar da ilimi, in da ya ke ta haifar da
malamai da limamai. Xalibai kuwa Allah kaxai ya san iyakarsu. A kan ce malami uba! Ni
ma xan qaramin almajiri, da ya yi wannan rubutu, ina godewa Allah, kasancewa ta xaya
daga cikin qyanqyasar makarantarsa. Inda na sauke har littafin Risala a wajensa, ba tare
da iyaye na sun biya ko anini ba. A yanzu haka da na ke rubuta wannan littafi, malam
yana da mata da 'ya'ya goma sha biyu. Kuma a yanzu limami ne na jumma'ah. Kuma har
yanzu bai daina karantarwa ba. Muna roqon Allah ya qara masa lafiya da xorewa a kan
gaskiya, ya albarkaci zuriyya ta sa amin.
85
An haife shi a 1957 a Kudenu, amma ya tashi a Gindin akwati, cikin qasar Filato saboda
mutuwar mahaifinsa tun yana xan shekara huxu. Ya yi makarantar Muhammadiyya a
wajen xan baffansa M. Umaru Saya, da malam Hammam Dalam wanda ya yi sauka a
wajensa. Ya yi karatun ilimi a wajen malam Hashimu xan limamin Dalam. Daga nan sai
makarantar firamare Islamiyya Saya. Daga nan sai Jkwalejin Jama’atu Jos inda ya samu
shahadar ‘Grade II’ inda ya ci gaba da karatun ilimi a wajen malam Ibrahim Bagobiri, da
limamin Zallaki M. Gajere, da M. Sharu Lawal Jos. Yana da mata biyu, da ’ya’ya takwas.
86
Malamin Arabiyya, kuma limamin farko na Izala. Ya rasu a Bauci ran laraba 3 ga Maris
1993, bayan sallar Magriba, kuma a can aka binne shi.
48
MALAMAN ARABIYYA MASU WA’AZI

1- M. Haruna Muhammad87
2- M. Xahiru Abubakar88
3- M. Abdullahi Kutubi
4- M. Mahmud Isa Wambai

WAXANDA SUKA SHAHARA DA LADANCI

Waxanda suka shahara da kiran sallah (ladanci) :


1- Waziri Makaho
2- M. Shehu heluman hanya
3- M. Ya’u Ibrahim89

87
Haruna Muhammad Ahmad, an haife shi a 1954 a qauyen Kwaftara cikin qaramar
hukumar Lere. Iyayensa sun yi qaura dashi zuwa unguwar Harxo Kaba, da ke unguwar
Sangatu Gumau. Ya fara karatun Muhammadiyya a makarantar M. Mahmud Bugau daga
1971 har ya sauke, kana ya tava ilimi a wajensa. San nan ya yi karatun ilimi a wajen
limamin Zingir M. Abubakar Aliyyu, tun daga Izziyyah har zuwa Askari. Kana ya xora a
wajen limamin Karambana M. Ya’u a 1976. Daga nan sai ya samu shiga makarantar horon
malamai ta larabci (Arabic Teacher’s College) Gwambe, a 1977. Ya qare a 1980. Ya tafi
kwalejin koyon alqalanci (Legal) Misau 1983-1986 in day a samu shahadar ‘Diploma.’ Ya
yi kwas na koyon ilimin tajwidi na shekara guda a Sakkwato. A 1993-1995 ya yi karatun
digiri a jami’ar Xan Fodiyo Sakkwato. Ya farad a aikin malamin makarantar firamare, ya
yi limanci, kuma yana cikin malamai masu wa’azi. Bayan ritayarsa daga aikin gwamnati,
ya yi kwamishina a hukumar shari’ah ta jiha, kuma shi ne sakataren majalisar malamai na
qungiyar Izalar Jos na jihar Bauci. Yana aure da mata huxu, kuma yana da ’ya’ya 28.
88
Muhammad Xahiru Abubakar Sambo. An haife shi a 1967, a Unguwar Mai alewa
(Tudun wadan Zalau), kuma a cikinta ya tashi. Ya yi karatun Muhammadiyya a
makarantar xan baffansa M. Abdulkarim Muhammad Ahmad da M. Ali Maigora Rishi.
Kuma a wurinsa ya fara karatun ilimi, da malam Sulaiman Zigau. Daga nan ya yi
makarantar yaqi da jahilci, sai ya tafi kwalejin Jama’atun ta Jos a 1984-1985. Sai ya tafi
ATC Gwambe daga 1986-1989. Sai ya tafi Legal Misau 1989-1993. Sai FCE Zaria 2000-
2004 inda ya samu shahadar NCE. Yana da mata biyu da ’ya’ya goma sha biyu.
89
Asalin sunansa (Zakari)ya’u Ibrahim. An haife shi a shekarar 1942, a Sumaila ta jihar
Kano. Kasancewar iyayensa Fulani ne ‘Gorkayi’ masu tashi daga wannan wuri zuwa
wancan, don nema wa dabbobinsu wuri dausayi, in da tun yana qarami suka taso da shi
zuwa qasar Bauci. Ko kafin su iso Bauci, sun yi zango a Domawa, wani gari cikin qasar
49
4- M. Lawal Xangulili
5- M. Salisu Maje-haji90
6- Baba Julde
7- Dodo Tela
8- M. Zakarai
9- Xanturai
10- M. Garba Dede
11- M. Mudi
LIMAMAI

1- M. Burai91

Lere ta Zazzau. In da a nan ya yi wayo, har ya yi karatun allo da na ilimi a tsangayar M.


Usman Labi, da M. Ahmadu Domawa, da M. Sule Bafulatani shi ma a Domawa. Mutum
ne mai yawan lizimtar masallaci, da yawan karatun Alqur’ani. Yana da ’ya’ya da jikoki
masu tarin yawa, kuma da yawansu sun bi hanya irin ta sa, su ma almajirai ne.
90
Muhammad Salisu Hamza Maje-haji. An raxa masa sunan kakansa Maje-haji, saboda
kakansa ga asali bakano ne, ya kan je hajji a qafa, akan hanya yana tsayawa a Sudan ya yi
noma, kana ya wuce. To, wata shekara ya fito da ’ya’yansa mata guda huxu; Ramatu,
A’ishatu, Gambo da Binta zai yi irin wancan tafiya, sai ya biyo ta Ririwan Dalma, da
mutanen Ririwai suka ji abin da ya fito dashi, sai suka roqi ya tsaya ya yi wa garinsu
addu’ar alheri, don su amfana da albarkacinsa. Ka san mutan da suna girmama wanda ya
tava zuwa hajji. Bayan tsayuwarsa don yin addu’ah, sai kuma sarkin garin ya xauki mata
ya ba shi, sai ta haifi xa aka raxa masa suna Hamza. An haife shi a 1940 a Bakin-kogin –
Jarmai, yanzu cikin qasar Filato. Ya yi karatun Muhammadiyya a wajen Alaramma M.
Yahya Gumau, da xansa M. Muhammadu Yahya. Ya yi karatun ilimi a wajen M. Idi, M.
Garba Xanbaqi, M. Muhammadu Yahya, M. Lazina da liman M. Abdulmumin Gumau.
Ya yi makarantar horon malaman arabiyya ta (Arabic Teachers College) Gwambe. Ya yi
aikin malamin arabiyya 1976-2006. Ya fara kiran sallah tun bai yi auren fari ba, kuma har
yanzu bai daina ba. Yanzu haka shi mai kiran sallah ne, kuma liman, san nan mai karantar
da almajirai.
91
Muhammadu Inuwa Burai. Shi Burai suna ne na kakanni. An haife shi a 1940 a qauyen
Mundu. Ko da yake asali iyayensa mutanen Zaranda ne, sai suka komo Mundu da zama.
Ya tashi a a wajen wan ubansa (baffansa) Malam Umaru, san nan yana malamin sarki a
Lame. Shi kuwa M. Umaru ya yi malamin sarkin Riruwai, har ma ya yi aurensa na farko a
can, sai aka dawo dashi Lame, a lokacin ne kuma ya xauko malam daga gaban mahaifinsa.
Daga nan kuma sai aka mai dashi Rauta, wanda tare kuma ya tafi dashi can, kuma a can
aka yi masa kaciya. Mahaifinsa ya fara xaura masa xan –ba na karatun Muhammadiyya,
daga nan kuma sai ya haxa shi da wani maqwabcinsa, ana cewa das hi M. Adamu Javvo.
50
2- M. Muhammadu Yahaya
3- M. Haruna Muhammad
4- M. Babangida Umaru Qwaino
5- M. Shehu Umar Malami92
6- M. Shagari
7- M. Aminu Kadiri93
8- M. Walidu Mu’azu
9- M. Aminu Sani
10- M. Mahmud Adam
11- M. Adamun Lumes94

Daga sai makarantar ta watse, sai aka mai dashi makarantar M. Musa wanda aka fi sani da
M. Kawu na unguwar Hunture. Daga nan sai ya koma makarantar M. Adamu Yayan –
Dudu, in day a sauke Alqur’ani a wurin. Daga nan sai makarantar M. Haruna Mai dogon
sanda, in daya fara karatun ilimi. Bayan rasuwarsa, sai ya koma wajen M. Shehu Na-bindi.
Ya dawo Gumau a shekarar 1979, inda ya xora katunsa na ilimi a wajen M. Adamu
Gwandu. Bayan rasuwarsa ya tava a wajen M. Garba Xanbaqi da M. Haruna a daidai
lokacin da qungiyar Izala ta bayyana, kuma ta ke ganiyar kafirta duk wanda bay a tare da
ita, sai karatunsa a wurinsu bai tsawo ba. Ya yi makarantar yaqi da jahilci, amma bai yi
zurfi har ya samu satifiket ba. Ya yi limanci bayan tuve liman M. Gero, har zuwa sadda ya
yi murabus da karan –kansa a shekarar 2014 saboda larurar rashin lafiya da ta same shi.
Ya auri ’yammata biyu a rana xaya, kuma yana da ’ya’ya.
92
An haife shi a shekara 1960, a garin Gingim ta gundumar Mara da ke yankin Jama’ah
da ke qaramar hukumar Toro. Ya yi karatu a wajen malam Inuwa Muhammad na Gau, in
da sauke Alqur’ani, kana ya xora da karatun ilimi, duka wajensa ya karanci Qawa’idi da
Ahlari da Tauhidi da sauran littattafai. Ya yi aikin gwamnati a ma’aikatar ruwa ta jihar
Bauci, in da ya yi ritaya a shekara 2013. Yanzu haka yana da mata uku da ’ya’ya bakwai.
93
Aminu Musa, an haife shi a 1956, a Tudun makaranta Unguwar Kadiri. Kuma a cikinta
ya tashi. Ya yi karatun allo a wajen kakansa M. Nuhu limamin Unguwar Kadiri, da M.
Ahmadu Unguwar Kadiri, da M. Shehu Lemari cikin qasar Guddiri. Ya yi karatun ilimi a
wajen M. Gero, da M. Amiru Kaduna, da M. Salisu Ta’an. Ya yi karatun nizamiyyah a
makarantar (School for Higher Islamic Studies) da ke Unguwar sarkin Mangu a Jos 1991-
1996. Ya yi Diploma a jami’ar Bayero (Bayero University) Kano. Ya yi aikin koyarwa a
ma’aiktar ilimi ta qaramar hukuma, in day a yi ritaya a 2018. Yana da mata da ’ya’ya
goma sha xaya, maza, ragowar mata.
94
An haifi M. Adamu Umar a shekarar 1966, a Rinjin–Gura ta gundumar, a cikinta ya
tashi, kuma cikinta ya fara karatun addini, a makarantar malam Husaini, wanda aka fi sani
da M. Damina. A cikinta ya yi karatunsa na Firamare, in day a gama a shekarar . Daga nan
ya tafi GSS (Government Secondary School) Gumau, ya gama a 1987. Sai kuma ya
51
12- M. Yusuf Mahmud
13- M. Saleh Xangwari95
14- M. Salisu Ta’an96
15- M. Xalladi Ustaz
16- M. Haruna Aliyyu97
17- M. Babaji
18- M. Alhasan Sadi98
19- Alqali Ahmad Wakili
20- M. Lawal Ali
21- M. Salisu Majehaji

tafi kwalejin ilimi ta (College Of Education) Kafancan. Sannan ya ci gaba da karatu a


zaurukan malamai danan-daban a Kafancan da Gwantu, da kuma wurin liman
Muhammadu Yahaya a Gumau. Yanzu haka malam yana zaune tare da iyalansa a Gumau,
in day a ke qoqarin qara karatu, kumu yana karantarwa.
95
Saleh Yusuf, an haife shi a Unguwar Yawa a shekarar 1954, kuma a cikinta ya tashi. Ya
fara karatu a tsangayar M. Yusuf har zuwa sauka. San nan ya yi karatun ilimi a wajen M.
Nata’ala na titin Wunti Bauci, da liman M. Muhammadu Yahaya, da M. Alhasan Sadi su
biyu duka a Gumau. In day a karanci tun daga ‘Qawa’idi, lahlari, Ishmawi da sauransu.
Yanzu haka malam yana da iyali da zuriyya a cikin garin Gumau, kuma yana kasuwanci
da noma don tsare mutuncin karatu.
96
Asalin sunansa Muhammad Salisu Hasan, an haife shi a 1953 a Gumau, kuma cikinta ya
tashi. Ya yi karatun Muhammadiyya a wajen liman M. Muhammadu Yahaya. Ya yi
karatun ilimi a wajen M. Idi da babban almajirinsa M. Garba Xanbaqi da kuma M. Lazina.
Yana da mata da ’ya’ya masu yawa.
97
An haife shi a Zallaki cikin jihar Filato a 1960, ya tashi a Saya. Ya yi karatun
Muhammadiyya a wajen mahaifinsa M. Aliyyu. Ya yi karatun ilimi a wajen M. Mahmud
Adamu, liman M. Muhammadu Yahya da M. Umar Abubakar Zabolo, M. Sharu Jos da M.
Ahmad Wakili Gumau. Ya yi makarantat firamare ta Zabolo 1980-1984. Ya yi makarantar
firamaren arabiyya 1989-1993, san nan ya yi makarantar horon malamai ta ‘Jama’atu
Arabic Teachers College’ Jos 2001-2004. Yana da mata biyu da ’ya’ya tara, maza bakwai
mata biyu.
98
Alhasan Sadi, an haife shi a 1964 a Zingiri cikin gundumar Rishi, amma ya tashi a
Gumau. Ya yi karatun Muhammadiyya a makarantar M. Mudi Alaramma. Ya yi karatun
ilimi a wajen M. Mahmud Alqalin Dajin a unguwar Bakin-kura Bauci, da limamin Zallaki
M. Yusuf (Gajere) da M. Aliyyu Usman Tilden –Fulani. Sai ya ATC (Arabic Teachers
College) Jos 1991-1997. San nan ya yi Diploma a wajen 2000-2004. Har yanzumalami ne
mai karantarwa, kuma yana aikin malamin yaqi da jahilci. Yana da mata da ’ya’ya goma
sha biyu, mata huxu, maza takwas.
52
22- M. Haruna Mahmud99
23- M. Auwal Adamu
24- M. Audu Waje100
25- M. Ibrahim Mai Kemis101
26- M. Armiya’u
27- M. Sulaiman Barista
28- M. Bala Muhd Inuwa
29- Yusuf Ibrahim102
30- M. Yakubu Xan’anko
31- M. Bawa
32- M. Nuru Ali
33- Sulaiman Abdullahi103

99
An haife shi a 1948, a Taura cikin gundumar Tama. Kuma a cikinta ya tashi. Ya yi
karatun Muhammadiyya a wajen M. Tahir da Abdu Dila Taura, da M. Ya’u Makanike
Tulu. Ya sauke Alqur’ani a Ningi tsangayar M. Garba Abubakar. Ya yi karatun ilimi a
wajen M. Xantabakko a Ningi, kana ya xora a wajen M. Ilimin Abdulmumin Gumau. Ya
yi firamare a Tulu daga 1959-1966. Daga nan sai School for Higher Islamic Jos 1986-
1990. Yana da mata biyu da ’ya’ya, kuma duk suna zaune a Gumau. Shi ne limamin
masallacin sarkin Lame.
100
Abdullahi Abdulkarim, an haife shi a 1940 a Rinjin-Gura. Ya tashi a Gumau, don a
cikinta ma aka yi masa kaciya. Ya yi karatun Muhammadiyya a wajen M. Audu wan
Saleh tsohon soja. Ya yi karatun ilimi a wajen M. Lazina, M. Gero, M. Bugau.
101
M. Ibrahim Dauda. An haife shi a shekarar 1939, a garin Maqera, qaramar hukumar
Dutsin-Ma, ta jihar Katsina. A cikinta ya tashi, kuma a cikinta ya fara karatun Alqur’ani, a
tsangayar Alhaji Isa Ibrahim. San nan ya yi karatun ilimi a gaban liman M. Ibrahim, da M.
Shu’aibu, da M. Lazina, M. Muhammadu Yahya da sauransu. Yana da iyalai da zuriyya
masu yawa.
102
Yusuf Ibrahim Maixorawa, an haife shi a 1990 a Tsakani. Ya yi karatu a wajen M.
Yakubu Kawu. Ya yi karatun ilimi wajen M. Abdulmumin Adamu, da M. Musa Tsari da
M. Abdullahi Kutubi. Ya yi makarantar ‘Sunnah Junior Secondary School’ Gumau.
103
An haife shi a 1979 a Tulu, kuma a cikinta ya tashi. Ya yi karatun Muhammadiyya a
wajen M. Garba Xantama, da M. Ahmadu Jibrin Hayin –Kanawa da M. Xalhatu Salihu
Tulu. Ya yi karatun ilimi a wajen M. Abdulmumin Adamu, M. Salisu Maje-haji da M.
Abdullahi Kutubi. Ya yi makarantar firamaren Tulu 1989- 1994. Ya yi ‘Islamic Secondary
School’ Gumau 1994-2000. Ya yi Diploma a makarantar kiwon lafiya (School Of Health
Technology) Ningi 2004-2007. Ya yi babbar Diploma HND (Higher National Diloma) a
53
34- M. Haruna Usman104
35- M. Iliya Kadage
36- M. Shu’aibu Bala Kanya105
37- M. Idi Kanya
38- Sulaiman Abdulhamid Ahmad106

WAXANDA SUKA YI LIMANCIN JUMMA’ARTA

Suna Asali Gari


1 M. Voyi daga Bauci Ung. Doya Bauci
2 M. Ballo Gwallaga Bauci
3 M. Idi Muhammad Jika Riruwai Gumau (limamin riqo)
4 M. Ali Dawa Dawa
5 M. Garba Xandibi Riruwai Gumau
6 Liman M. Gero Dokayel Gumau
7 Liman M. Burai Lame Gumau

Jami’ar Benin 2015-2017. Yana aiki aiki tare da qaramar hukumar Toro a vangaren kiwon
lafiya. Yana da mata da ’ya’ya, kuma har yanzu bai rabu da karatu da karantarwa ba.
104
An haife shi a a shekarar 1981 a Unguwar Kaba, Gumau. Ya yi makarantar Firamare ta
Unguwar Waziri daga shekarar 1988-1994, san nan ya tafi makarantar ilimin arabiyya mai
zurfi (School For Arabic & Islamic Studies) da ke layin sarkin Mangu Jos. Daga nan sai
tafi kwalejin ilimi ta (Sunnah College Of Education) Bauchi. San nan ya yi karatun ilimi a
wajen M. Mahmud Adam Gumau. A yanzu haka yana da mata da ’ya’ya, kuma har yanzu
bai rabu da karatu da karantarwa ba.
105
An haife shi a 1990 a Unguwar Kanya, kuma a cikinta ya tashi. Ya yi karatun
Muhammadiyya a wajen kakansa M. Idi Kanya, da M. Mika’ilu Kanya. Ya yi karatun
ilimi a wajen liman M. Muhammadu Yahaya, M. Abu Hanifa da M. Yunusa Cexiya. Ya yi
makarantar firamare ta Unguwar Kanya 1996-2003. Ya yi qaramar sakandaren al’umma ta
Gumau-Sanga 2004-2007. Ya yi babbar sakandaren al’umma ta Islamic Secondary School
Gumau 2007-2009. Kana ya tafi kwalejin ilimi (COE) ta Azare, in day a karanci lissafi da
kimiyyar Kwamfuta (Maths/Computer Science) ya samu shahadar malanta ta Nijeriya
(NCE) 2012-2015.
106
An haife shi a 1986, a Danqaro, ya tashi a unguwar Sauke. Ya yi karatun
Muhammadiyya har zuwa a wajen M. Babaji na Zingiri, cikin gundumar Rishi. Ya yi
karastun ilimi a wajen M. Yusha’u Zallaki. Yana da mata uku da ’ya’ya goma sha uku
maza da mata. Shi ne limamin masallacin unguwar Sauke.
54
YAWAN MASALLATAN DA KE CIKINTA

Masallatai sun kasu kashi uku :


1- Masallatan jumma’ah
2- Masallatan unguwanni (na khamsus salawat)
3- Masallatan idi
Amma masallatan unguwanni na sallolin yau da kullum ‘khamsus salawat’ su
kam guda 55 ne, ga su:

MASALLATAN UNGUWANNI

Masallaci Unguwa
1 Qofar Umaru Qwaino Layin Alh Musxafa
2 Qofar Kande Masifa107 Layin Alaramma Maitatsine
3 Masallacin Bala Umaru Layin Xahiru Magaji
4 Masallacin Kadirawa Titin Unguwar Kanya
5 Masallacin M. Yakubu Ung M. Yakubu
6 Masallacin Hajiya Gaya108 Ung Alu
7 Masallacin Alh. Na’iya Titin Sarkin Yaqi
8 Masallacin Hajiya Uwani109
9 Masallacin Alhaji Abashe Ung Alh Abashe
10 Masallacin Mato Soko
11 Masallacin Rahinah Layin Adamu Sanga
12 Masallacin Hamisu Hasan Layin Harxo
13 Masallacin Xalladi Ustaz
14 Masallacin Injiniya Shu’aibu Titin waziri Xanwunti

107
Wanda ya fara gina shi shi ne Alaramma M. Ya’u, wani mutumin Dutse Gadabur ta
qasar Jigawa, shi ne mutumin da ya fara zama a unguwar.
108
Asalin sunanta Hajiya Hansatu, mutuniyar Lame. Ta auri wani mutum wais hi Alhaji
Maxi, amma Allah bai bas u haihuwa ba, sai kuma aure ya mutu, tun daga nan bat a sake
aure ba. Saboda haka bat a da xa, ba jika, tana da gida, sai wasu suka bat a shawarar ta
sayar ta gina masallaci. Sai maqwabcinta Alhaji Wada na Alhaji Talley a sai gidan, ya
gina masallaci da kuxin dominta. Kuma ya bar tat a ci gaba da zama a gidan, har said a ta
koma ga Allah. Kafin rasuwarta ta kai kimanin shekaru 80 a duniya.
109
Asalin sunanta Hajiya A’ishatu Yahya Umar. An haife ta a Gumau, ta tashi a Rishi. Ta
yi karatun Muhammadiyya a makarantar M. Xanhasan. Ta yi karatun ilimi a wajen M.
Abdulmajid Bakin-kogi. A yanzu tana auren Alhaji Kabirun Xanzalau Gumau. Allah bai
bat a haihuwa ba.
55
15 Masallacin Hajiya Barirah Layin Tankon Alqali
16 Masallacin M. Idi Dogon Layi
17 Masallacin Baba Maikeke Dogon Layi
18 Masallacin Sarkin Lame Titin waziri Xanwunti
19 Masallacin Wambai Layin Alh. Sidi
20 Masallacin Kai-kaso-kaje Ung kai-kaso-kaje
21 Masallacin Yahya Mai tebur Layin malamin Lamba
22 Masallacin Wada Gayu Ung Kwari
23 Masallacin Ambasada Unguwar Kwari
24 Masallacin Babban Gida Titin Barde Sallau
25 Masallacin M. Ya’u Vilijo Titin Saminaka
26 Masallacin M. Yaro Ung Sharaxa
27 Masallacin Xankaka Unguwar Kaurare
28 Masallacin Mai Unguwa Ung Sarkin Ririwai
29 Masallacin Unguwar Mahauta Unguwar Mahauta
30 Masallacin Durumi ”
31 Masallacin Abdussalam ”
32 Masallacin Babaru Layin Babarere
33 Masallacin M. Ahmadu Jira Hayin M. Ahmadu
34 Masallacin Ibrahim Auta Unguwar Rehawus
35 Masallacin Alh Maikuxi Titin Bauci
36 Masallacin Tasha Tashar Motoci
37 Masallacin M. Nadabo Layin Xantululu
38 Masallacin Alin Ballo Layin Xantululu
39 Masallacin Abdul’aziz Unguwar Gurawa
40 Masallacin Caji –ofis Unguwar Gurawa
41 Masallacin Ahmadu Atamfa Kan –kwana
42 Masallacin Sale Nasko Layin Isyaku Fiqe
43 Masallacin Xanzalau Bakin kasuwa
44 Masallacin Musa Laska Gidan Man cikin gari
45 Masallacin Babangida Doka Gidan Man Titin Bauci
46 Masallacin Usman Pingel Gidan Man Hayin-gada
47 Masallacin Muhammadu Kure Hayin Gada
48 Masallacin M. Iliya Unguwar
49 Masallacin titin Sauke Unguwar Kanya
50 Masallacin Jeji Unguwar Kanya
51 Masallacin Gurum Unguwar Gurum
52 Masallacin M. Sale Tashar M. Saleh
53 Masallacin Waziri Sambo ’Yankwana

56
54 Masallacin Barandawa Barandawa
55 Masallacin Yaya Hudu Tashar A’i
56 Masallacin Sauke Unguwar Sauke
57 Masallacin M.

MASALLATAN JUMMA’ANTA DA TARIHINSU

Amma masallatan jumma’arta guda uku ne, ga su :

i- Masallacin sarkin Yaqi


ii- Masallacin Izala
iii- Masallacin Salafiyya

Ga bayanin kowanne da tarihin kafuwarsa nan tafe :

MASALLACIN SARKIN YAQI

Tarihin ginin wannan masallaci ya faro ne daga tasowar sarkin Yaqi


Usmanu Babale xan Umaru Alkammu, daga Lame zuwa Gumau, wannan
ya faru a cikin shekarun 1940. Domin a farkon al’amari, ba’a buxe
jumma’ah said a izini daga masarautar Bauci. Kai ko sabunta masallaci za
ku yi sai kun sanar, kum sai an ba ku izini. Kuma idan an yarda a buxe,
za’a turo muku da liman, mai karantarwa kuma yana jan sallah. Qungiyar
Jama’atu Nasril Islam ta zo Gumau ran 06 June, 1969. Kuma daga fadar
mai martaba sarkin Bauci aka fara turo su wajen Sarkin kudun Bauchi. Tun
da aka kafa wannan masallaci aka fara sallar jumma’a a cikinsa, wani dalili
bai tava sa an fasa ba, sai fa a cikin shekarar 1441 hijiri, daidai da 2020
miladi lokacin da aka samu varkewar annobar sarqewar numfashi dangin
‘Corona Virus’ da aka yi wa suna ‘Covid 19’. Cutar da ke tashi daga
mutum zuwa mutum, idan an haxa jiki. Wannan cuta ta sa duk harkokin
duniya sun tsaya cak. A ko’ina an rufe dukkan gidajen baxala, cin abinci,
rawa, sinima, qwallo, kasuwanni, da dku wani taron jama’a har ma da
tafiye-tafiye. Sai malaman duniya, suka yi ijima’in daina jam’in salloli a
masallatai, tun daga masallacin Ka’aba har wannan masallacin jumma’a na
Gumau. Sai da aka jera sati uku ba’a yi sallar jumma’a ba. Tun daga ran 1
57
Ramadan 1441 24 Afrilu 2020 har zuwa ran 29 Ramadan 1441, 22 Afrilu
2020, amma ana ci gaba da sallolin yau da kullum. Ko ran jumma’ar ma
ana yin azahar. Da kafin shekarar 1980 cikin qasar Lame baki xaya duk
inda ka je ka samu ana sallah, sai ka yi niyyah ka bi, idan dai kai musulmi
ne. Sai a wajejen shekarar 1978, wata qungiyar matasa mai suna ‘Izalatul
bid’ah wa iqamatus sunnah’ ta bayyana. Tun daga san nan sai abubuwa
suka fara canzawa. Wannan qungiya ta zo Gumau a 1980, kuma ta zo da
wasu sauye-sauye kamar haka :
i- Hana taron suna
ii- Hana xaura guru da laya
iii- Hana shan rubutu
iv- Yin sallama biyu. Alhali da duk inda ka je cikin rewacin
Nijeriyar nan sallama xaya ake yi idan za’a fita daga sallah.
Shi wannan masallaci ana kiransa :
i- Masallacin ’yan xariqa110
ii- Masallacin Jama’atu111
iii- Masallacin Fada
iv- Masallacin sarki

KWAMITOCIN SABUNTA GININ MASALLACIN JUMMA’A NA GUMAU

Sun rabu kashi biyu. Da da farko ba’a san masallaci da wasu ’yan
kwamiti ba. Iyaka masallaci na hannun liman ne da na’ibansa. To, maganar
kwamiti ya faro ne daga maganar taron sabunta masallaci, kwanci-tashi har
ya zamo ana yi wa masallaci kwamiti a qarqashin shugabancin liman. Har
kuma yau da gobe aka zo ana son a cire hannun liman xin ma baki xaya,
sai dai wasu daban su yi abin da suka ga dama a masallaci, shi kuwa liman
ya zama xan kallo.

110
Su ’yan izalar ne ke kiransa masallacin xariqa. Duk da cewa babu ’yan xariqa a
Gumau, kowacce iri ce kuwa. Kuma ko da ma akwai su, bas u ke iko, ko jan ragamar
masallaci ba.
111
Wato Jama’atu Nasril Islam
58
SABUNTAWA NA FARKO 1964
(’Yan Kwamitin 1964)

Tarihin ginin wannan masallaci ya faro ne daga tasowar sarkin Yaqi na


Usmanu Babale xan Umaru Alkammu daga Lame zuwa Gumau, a shekarar
1947. Da farko ana kiransa masallacin Zana. domin da zanan aka yi shi.
Kuma an yi shi ne a matsayin masallacin sallolin yau da kullum, amma ba
na jumma’a ba. Har ma a cikinsa ’yandoka ke xaure masu laifi. Domin a
san na ba’a fara sallar jumma’ sai in an yarje muku daga Bauci, bisa yadda
aka ga cancantar yin hakan. To ana nan sai aka gina na qasa, ginin bani-
bani, aka yi masa jinkan ciyawa. Cikinsa ba ko sumunti, rairayi ne. Kana
daga baya aka yi masa jinkar kwano. Ba da daxewa ba kuma, sai aka ba da
jumma’a daga Bauchi, sai aka turo da liman M. Voyi, shi ya fara jan
jumma’ah a wannan masallaci. To, sadda sarkin Yaqi Usmanu Babale ya
rasu a Bauchi a shekarar 1964, sai shi limamin ya koma gida. Sai aka naxa
sarkin kudu Salmanu xan Sarkin Yaqi Ade ya zamo Hakimi, kuma uban
qasa. Shi ne ya roqi Malam Idi ya zamo sabon liman. Shi kuma sai ya yi
kawaici da cewa, karvar zai shagaltar da shi daga karantarwarsa da kuma
kasuwancinsa da ya ke yi. Amma sai ya yi masa ishara da wani almajirinsa
da ake kira Malam Ali, wani mutumin Dawa. Aka ce ya aika masa. Da ya
zo sai malam ya yi masa wasiyya da yin haquri bisa wannan nauyi da za’a
xora masa. Kwamitin da aka yi don sabunta ginin masallacin nan daga na
zana zuwa qasa su ne :

1- M.Voyi – liman
2- Sarkin kudu Salamanu
3- Malamin sarki
4- Harxo wonu
5- Alqalin Gumau
6- M. Idi
7- Alhaji Sabo Gumau

59
SABUNTAWA NA BIYU 1972
(’Yan Kwamitin 1972)

A 1972 zamanin sarkin kudu Salmanu jama’ah ta yi yawa, arziqi ya


qasaita. Masu tasowa daga garuruwansu, su dawo Gumau da zama suka
daxu. Masallacin jumma’a ya yi kaxan. Sai ya tara masu faxi aji na cikin
gari, attajirai, malamai da sauransu, aka yi zama akan yadda yadda za’a
sabunta tare da faxaxa masallacin jumma’ah. Bayan xakin taro ya yi
ittifaqi a gina sabon masallaci na zamani. Kuma wannan shi ake kira
sabuntawa na biyu. Sai aka kafa kwamiti, ga su :

1- Shugaba Sarkin kudun Bauci


2- Sakatare M. Ahmadu Kafi Sakatare
3- Ma’aji - Alhaji Sa’idu
4- Sakataren Kuxi M. Ahmadu
5- Mai tara kuxi Harxo Wonu
6- ” ” ” Alhaji Baba Toro
7- ” ” ” Alhaji Inuwa
1- Odita Alhaji Inuwa Alqalin Gumau
8- ” Alhaji Jibrin Kaita
9- ” Alhaji Audu Safe
10- ” Alhaji Amadudu
11- ” Alhaji Sabo Gumau
12- ” Sarkin fawa Shehu
13- ” M. Hasan Mai gishiri
14- ” ’Yan kwana
15- ” Alhaji Musa Mai Kwabbai
16- ” M. Aliyyu limamin Gumau
17- ” Waziri Nababa
18- ” Alhaji Inuwa

60
SABUNTA HARABARSA A 1983

A shekarar 1983, maganar sabunta harabar masallaci ya taso. Kuma


kwamitin masallaci sun yi ittifaqi akan :

1- za mu sake ginin haraba da bulo na sumunti.


2- Da murafan qofofi guda biyar masu kyau.
3- Za’a sayi tankin ruwa
4- Za’a sayi shimfixu

A wannan lokacin mai girma sarkin yaqin Bauci ya ba da taimakon fam


xari biyu (£200:0:) daidai. Da kuxinsa ma aka fara aiki har aka gama gini.

’YAN KWAMITIN 1988

A 1988 aka yi sabbin ’yan kwamiti. Su ne :

1- Liman M. Isma’ila
2- M. Garba - liman
3- M. Muhammadu Burai - Na’ibi
4- M. Ali – Tshohon liman
5- M. Ashiru
6- M. Ya’u Alaramma
7- M. Ya’u Fulani
8- M. Mudi Alaramma

’YAN KWAMITIN 1990

An naxa wannan kwamiti ran 23 Mayu 1990

1- Alhaji Yakubu Maigari - Shugaba


2- M. Ali Laru – Mataimakin Shugaba
3- M. Bala Ibrahim – Sakatare
4- M. Muhammadu Xorawa – mataimakin Sakatare
5- Alhaji Alhasan Mai Awu – Ma’aji
61
6- Alhaji Umaru Lame – Mataimakin ma’aji
7- Alhaji Adamu Baraya – Mai binciken kuxi
8- M. Ashiru – mataimakinsa
9- M. Ladan Ahmed –
10- Alhaji Ya’u Vilijo - mamba
11- Baba Shehu Zalau - mamba
12- Barden Wunti - mamba
13- Liman M. Gero - mamba
14- Alhaji Mamman - mamba
15- Alhaji Umaru Dauda - mamba
16- Alhaji Umaru Xanladi Maute - mamba
17- M. Isa Lame - mamba
18- Alhaji Xanladi Tasha - mamba
19- M. Bala Makanike Laru - mamba
20- Alhaji Usman Gakuyel - mamba
21- Alhaji Bala Sama’ila - mamba
22- M. Ahmadu Jira - mamba
23- Harxon Wonu – Uban kwamiti

’YAN KWAMITIN 2000

Batun sabunta ginin masallacin Jumma’ah na Gumau bai sake tasowa ba


sai a farkon shekarun 2000 na miladiyya. Waxanda suka fara wannan
yunquri su ne :

1- M. Mairiga Lame
2- M. Yalwa Buba
3- Muqaddashin Wunti
4- Alh Yakubu Bula Wambai
5- Alh Umaru Xalladi Maute
6- Alqali M. Yakubu Umar
7- Alhaji Abashe
8- Alhaji Muhammadu Dallatu
9- M. Ahmad Iro
10- M. Ashiru

62
Da sauransu, jama’ah masu yawa. Amma hanyar tara kuxi da suka bi a
lokacin, na cewa sai an gama tara kuxi, kana a fara gini, a gani na shi ya
hana aikin tasiri. Domin kuwa halin mutane, sun fi so su ga duk abinda
suka bayar an yi aiki da shi. Kuma duk aiki na alheri, shexan yana shiga ya
nemi vatawa. To, sai ya raxawa mutane shakku cewa abin da suka bayar fa
cinyewa ake yi. Sai mutane su ji kasalar aikin. Da farko har an buga bulo,
ya kuma daxe a ajiye ruwa na dukansa. Qarshe dai aka sayar dashi, don ko
an yi gini das hi, ba zai yi qarfi ba. Aka ajiye kuxin a banki, a asusun
masallaci. A nan dai maganar ta mutu.

’YAN KWAMITIN 2002

Batun sabunta ginin masallacin Jumma’ah na Gumau karo na uku ya sake


tasowa ne a shekarar 2002 na miladiyya. An kafa wannan kwamiti ran 26
Disamba 2002. Ga su :

1- Baqo Abdullahi - Tarayya


2- Dr Lame - Tarayya
3- Ambasada AG Abdullahi - Tarayya
4- Alhaji Ahmed B. Yakubu - Jiha
5- M. Usman Mairiga Lame - Jiha
6- Yakubu Dembo Abdullahi (Sarkin shanu) - Jiha
7- M. Aminu Dauda - Jiha
8- Alhaji Ibrahim Musa Lame - Jiha
9- Alhaji Usman Muhd Tama - Jiha
10- M. Yalwa Buba - Jiha
11- Muqaddashin Wunti - Jiha
12- Alh Yakubu Bula Wambai – Xan kwamitin gida
13- Alh Umaru Xalladi Maute - Xan kwamitin gida
14- Alqali M. Yakubu Umar - Xan kwamitin gida
15- Alhaji Abashe - Xan kwamitin gida
16- Alhaji Muhammadu Dallatu - Xan kwamitin gida
17- M. Ahmad Iro - Xan kwamitin gida
18- M. Ashiru - Xan kwamitin gida

63
’YAN KWAMITIN 2013

A qarshen shekarar 2013, maganar ta sake tasowa. aka rushe tsohon


masallaci ran litinin 24/10/2014, aka share filin. Ko kafin a rushes hi, an
gyara wani wuri da ake xaure dawakai, an mai dashi masallaci na wucin
gadi. Aka zo da sabon zanen masallaci na zamani. Wanda ake ganin idan
an yi shi, zai dace da zamani mai tsawo. Wanda ya zana shi shi ne injiniya
Sunusi Waziri Gumau. An fara gini ran laraba 02 Zul hijjah 1436
(16/09/2015). An fara shi ran laraba don neman sa’a a wajen Allah
maxaukakin sarki. Kuma wannan shib ake kira sabuntawa na huxu. Ga
kwamitocinsa :

1- Ahmed Lame (Baba Ahmadu) – Ciyaman


2- Muhd Mai Xorawa Ajiyan Wunti – Mataimaki
3- Umar Adamu Umar (Babajin Sarkin Gabas) - Ma’aji
4- Adamu Muhammed (Ladan Xantiye) – Mataimakin ma’aji
5- Auwal Zakarya’u Vilijo – sakataren kuxi
6- Bawa Adamu – P.R.O
7- Rufa’I Muhd – mamba
8- Adamu Musa (Lifidi) – mamba
9- Sunusi Umar Maute - Sakatare
10- M. Ibrahim Sabo – Na’ibi
11- Ahmed Abdullahi – Ciyaman
12- Ajiyan Wunti – mataimaki
13- Alhaji Sunusi Maute – Sakatare
14- M. Babaji sarkin Gabas – Ma’aji
15- Rufain sarkin yaqi -mamba
16- Lifidin Wunti – mamba
17- Alhaji Abashe
18- Sarkin Gabas Alh Dindima

’YAN KWAMITIN 2021

Su ’yan kwamitin masallaci ne, masu taimakon liman wajen aiwatar da aikin da
ya dace don ci gaban masallaci bisa mahangar littafin Allah da sunnar ma’aiki
(SAW). An naxa su ran asabar 16 Jumadas Sani 1442 daidai da 30/01/2021.

64
SHARAXIN ZAMOWA XAN KWAMITI

i- Sai wanda ya yarda da masallacin kuma ya ke sallah a cikinsa.


ii- Ya zamo ba ya cikin tsohon kwamitin da aka rushe.
iii- Za’a riqa sabuntawa, a shigo da wasu ko a rage waxanda suka
gajiya duk bayan shekara biyu.

1- Liman M. Burai - Liman


2- Ibrahim Sabo – Na’ibi
3- Alarammam Umar Kawu – Na’ibi II
4- M. Yau Ibrahim – Ladan
5- M. Ibrahim Mai Kemis – limamin masallacin M. Yaro
6- M. Yusuf Mahmud – Limamin masallacin Alh. Abashe
7- M. Mahmud Adam – limamin masallacin Alh Na’iya
8- M. Armiya’u – limamin masallacin M. Ya’u Vilijo
9- M. Haruna Aliyu – limamin masallacin Eng. Shu’aibu
10- M. Bala Ibrahim – Magatakardan Wunti
11- M. Ado – Wakilin qasa da qasa na Wunti
12- Alh. Muhd – Dallatun Wunti
13- M. Mai Jama’a Waziri – daga gidan M. Gero
14- M. Idris Abdullahi –
15- Alh. Balan Sama’ila – Daga gidan M. Idi
16- Muhd Tukur Waziri – matasa
17- Sani Babba – matasa
18- Alh. Shagari Abbas – matasa
19- Xanlami Hasan (Mami) – Xan Agaji
20- Basiru Adamu – Xan Agaji
21- Hudu Mailalle - mamba
22- Sha’aban Maikuxi – Social media
23- Kamaluddin KMC – Social media

65
MASALLACIN IZALA 1982-yau

Izala sun buxe sallarsu ta jumma’ah a masallacin malam Idi da ke


Dogon Layi, ran 9 Yuli 1982. Liman na farko day a jagoranci sallar shi
ne M. Garba Xanbaqi.112 Kana daga baya suka gina sabon masallaci a a
gonar M. Abdulhamid Xanhasan, da ke kan titin Saminaka. Shi da
kansa ya ba da sadaqar gonar. To tun daga ran nan sai masallatan
jumma’ah suka zamo guda biyu. Na sarki da na Izala. To, haka aka yi
tafiya, har zuwa shekarar 1991. Sai qungiyar ta rabu gida biyu : ’yan
Jos da ’yan Kaduna, amma rabuwar ta kasance a shugabacinta ne a
sama kaxai. A qauyuka da sauran garuruwa ana ci gaba sallah wuri
xaya, ko da dai zuciyarsu su ma xin a rabe ta ke. To, ana nan kan haka,
cikin shekarar 1996, sai faxan ya qara tsananta, har shugabannin suka
sanya su dole sai sun raba masallatai, To, shi raba masallacin da ya taso
cikin shekarar ba kamar yadda aka yi sadda za su bar masallacin sarki
ba ne, da dutse hannun riga aka rabu, in da ’yan Jos suka fi qarfi, sai su
kori ’yan Kaduna. In da kuma ’yan Kaduna suka fi qarfi, sai su kori
’yan Jos. To, a Gumau ’yan Kaduna ne suka kori ’yan Jos. Sai ’yan Jos
suka buxe sallarsu ta jumma’ah a masallacin Alhaji Yunusa xan
Gauraka da ke bakin kasuwa. Kana daga baya ma suka rushe shi, suka
gina na zamani bene (gidan sama). Ana kiran masallacinsu da
masallacin ’yan Jos, ko masallacin sallama xaya. Akan :
i- Sai an bai wa shugabanci da yin biyayya ga shugaba
muhimmanci.

112
Waxanda suka kawo izala Gumau su ne ; M. Garba Xanbaqi, Musa Laska, Alhaji
Garba Badikko. Amma ba ta karvu sosai ba, sai da Alhaji Saidu ya shiga. Don shi mutum
ne ne mai kwarjini, tamkar gwamna ya ke a cikin jama’arsa, duk inda ya tsaya sai mutane
su taru a wajen. Domin duk cikin zuriyar gidan Muhammadu Jika ba’a yi mutum wanda
ya haxa kuxi da karatu kama ta sa ba. Ranar da ya shiga Izala, ran nan ya shigar da
babban abokinsa Malam Abdulhamid Xanhasan da Alhaji Musa Mai -wasa- da- kwabo
(Kansila)112 da M. Muhammadu Yahya da Alhaji Maikuxi Riruwai. Ragowar jama’arsu na
‘Lame District’ kuma su ne M. Ahmadu Idda Taura, Garba Tama Rishi, M. Garba Xan
arewa, M. Garba Shagayya, Dodo Tela, Basharu Gumau, Alhaji Idi Wundi, Maton Tulu,
limamin Matawai, M. Musa Sunkuye, Galadiman Zuku, Xan Gulili Pingel, M. Dungu
Laru, M. Ali Pingel, Umaru Lame, M. Sale Lame.
66
ii- sallamar fita daga sallah. ’Yan vangaren Jos na cewa, sai dai a
koma yin sallama xaya, kamar yadda ya keg a asali a cikin
mazhabar Malikiyyah. Suka qara kusantar da kansu ga
mazhabar Malikiyyah.
iii- Muhimmancin xaura rawani

MASALLACIN SALAFIYYA 2014-yau

A yayin da vangaren Kaduna ke cewa, sai dai a ci gaba da tafiya bisa


abin ake kai tun farko, wato sallama biyu. Kuma suka qara nesanta kansu
da duk mazhaba ma baki xaya. Qarshe ma suka juye suka kira kansu
da’yan salafiyya. Suka yi watsi da mazhaba da mabiyanta. Sai ana kiransa
da masallacin ’yan Kaduna, ko masallacin sallama biyu, ko masallacin ’yan
salafiyya. To, lokacin da qungiyoyin biyu suka haxe a cikin shekarun
2013/2014, sai shugabannin vangaren Kaduna, suka yi mubayi’a ga
vangaren Jos. Sai maganar vangaren Kaduna ya mutu. Shekara guda
kurum aka yi a haxe sai aka sake rabewa biyu akan :

i- Salafiyya ba su yarda da xaura rawani a matsayin addini ba


ii- Kuma ba su yarda bin wata mazhaba ba
iii- Kuma ba su yarda da biyayya muqlaqa ga wani shugaba ba.
Amma sun yarda a yi biyayya muxlaqa ga qasar Sa’udiyya
cewa duk abinda suke kai daidai ne. To sai ana kiran
masallacinsu da masallacin ’yan Abuja, ko masallacin sallama
biyu, ko masallacin salafiyya.

TARIHIN MASALLATAN IDINTA

Masallacin idi na farko da aka fara kafawa, tun shekarar farko da sarkin
yaqi ya dawo Gumau shi ne na tsallaken rafin malam Gardi, akan titin
Waziri Xanwunti, gabas da titin, amma fa tun ma ba’a tsaga hanyar ba,
wato inda dai asibiti ya ke a yanzu. An yi sallar Idi ta qarshe a wajen a
1978, a dalilin asibiti da aka gina. A shekarar 1979 an yi sallar Idi a gonar
Wangida, da ke kan titin Pingel, kusa da unguwar Mato-soko, sau xaya

67
kurum aka yi sallah a wurin sai aka fahimci bai dace da zamowa
masallacin Idi ba, saboda cavalvali da ke hanyan zuwa wajen lokacin
damina, sai Alhaji Umaru Xalladi Maute ya bad a wurare biyu a arewa
maso gabas da gari, aka turo gireda daga Toro ran 14-10-1980 ta share
filaye biyu, xaya don sallar idi, xaya kuma don yin kushewa, sarkin kudu
ya sa aka yi dashen itatuwa a cikinsa. A shekarar 1980 aka fara sallar Idi a
wajen, kuma a shekarar aka fara binne mutane a kushewar. Amma
qungiyar Izala yayin da suka raba masallaci a shekarar 1982, da sallah ta
zo sai suka buxe masallacin idinsu daban a can filin Alhaji Badamasi da ke
Kan- kwana, vangaren gabas ta hanyar zuwa Bauci. Amma bayan
mutuwarsa, iyalansa sun karva sun raba gadonsa, don da ma ba kyauta ya
bayar ba. Bayan rabuwarsu a shekarar 1996, sai Izala Jos suka buxe sabon
masallacin idinsu a tsohon masallacin idin farko na garin, wato can gabas
da asibiti, akan titin Waziri Xanwunti. Amma lokacin da qungiyoyin biyu
suka haxe a shekarar 2013, sai suka ci gaba da sallar idi a inda da ma can
suke yi tare kafin rabuwarsu. Bayan sake rabewarsu a 2014 kuma sai
waxanda suka juye Salafiyyah suka buxe na su masallacin a filin Alhaji
Musa Laska da ke kan kwana. A yayin da izala suka koma sallah a inda
muka bayyana da farko.

YAWAN MAJAMI’UNTA 2020

An fara gina coci a Gumau a shekarar 1965. Sai da aka kai ruwa rana ma
tsakanin sarkin kudu da Harxo Wonu a vangare guda da Jola Sanga, har ta
kai Jola Sanga ya yi qarar sarkin Kudu wajen sarkin Bauci. Ran 27-05-
1965 sarkin Bauci Adamu Jumva (1955-1982) da ’yan majalisar En’e suka
zo Gumau, don nuna wa Sangawa inda za su gina cocinsu. Bayan Jola
Sanga da Yakubu Dangana sun kai qarar sarkin kudu Salmanu da Harxon
Wonu Bauci akan sun hana su ginawa. Zuwa yanzu akwai cocuna kamar
haka :

Suna Wuri Shekara


1 Cocin ECWA Ung. Mishan 1965
2 ” ” Ung. Gurawa

68
3 ” ” Ung. Fa
4 ” ” Ung. Project
5 ” ” Ung. Magami
6 Cocin Baptist Ung. Gurawa
7 ” ” Ung. Mishan
8 ” ” Ung. Magami
9 Cocin Assembly Of God Ung. Mishan
10 Cocin Roman Catholic ” ”
11 Cocin Anglican ” ”
12 Cocin Cochin ” ”
13 Cocin Deeper Life ” ”
14 Cocin Living Faith ” ”

ASIBITOCINTA

1- Asibitin Malam Xan’inna113


2- Asibitin Mataniti : An gina shi a shekarar 1977/78. A shekarar 2008
aka gina sabo, aka katange shi, aka xauko asibitin M. Xan’inna aka
haxe su, aka xaga darajarsa zuwa qaramar cibiyar kiwon lafiya
(Primary Health Care Centre).

YAWAN MAKARANTUN ALLO - 1963

1 M. Mahmudu Bugau
2 M. Idi
3 M. Xanhasan
4 M. Umaru Mai almajirai114

113
An ba da kwangilar gina shi a 1977 akan N10, 029. Alhaji Uba Gumau ya yi kwangilar
gina shi. An buxe shi a 1978. Malamin asibiti na farko day a buxe shi, shi ne M.
Xan’inna, to, sai ake kiran asibitin da sunansa har yau. Kafin a buxe shi komai kasawar
jinya sai an tafi asibitin Zingir, Zabolo ko Pingel. An daina amfani dashi a 2008, aka haxe
shi da asibitin haihuwa (mataniti) aka haifar da qaramar cibiyar kiwon lafiya (Primary
Health Care Centre). Yanzu an mai da tsohon asibitin na kudu da masallacin M. Salisu
Ta’an, wurin koyar da yara ilimin kwamfuta.
69
5 M. Gardi
6 M. Babarere Mahauci
7 M. Yakubu
8 M. Xan’azumi
9 M. Yahya

YAWAN MAKARANTUN ALLO A 2021

1 M. Mudi
2 M. Yakubu
3 M. Xanhasan
4 M. Shafi’u
5 M. Dauda
6 M. Umaru Alaramma
7 M. Bugau
8 Yakubu

YAWAN ISLAMIYYOYINTA A 2021

1- Islamiyyar Izala Jos


2- Islamiyyar Izala Abuja
3- Islamiyyar Tahfizul Qur’an (MIMIS)
4- Islamiyyar Hamisu Na’iya
5- Islamiyyar Gwani Idrisu
6- Islamiyyar JNI – Asabar da lahadi
7- Islamiyyar M. Muhtari Bala
8- Islamiyyar Gidan Aminu Pele (Matan aure zalla)
9- Islamiyyar Gidan Tafida (Matan aure zalla)
10- Islamiyyar tashar Diddila

114
Wani mutumin Ningi, ya zauna a daidai gidan Alhaji Audu Safe na yanzu
70
MAKARANTUN FIRAMARE
1- Gumau Sanga
2- Unguwar Waziri
3- Sarkin Yaqi
4- Maiwuro
5- Shenu
6- Unguwar Pa
7- Gagati
8- Sangatu
QARAMAR SAKANDARE (MUTAWASSIXAH)
1- Junior Secondary School Lame 115
2- Sarkin Yaqi Upper Basic
3- Maiwuro Upper Basic
4- Gumau Sanga Upper Basic
5- Unguwar Waziri Upper Basic
6- Shenu Upper Basic
BABBAR SAKANDARE

1- Government Technical College116


2- Government Day Senior Secondary School

115
Qaramar hukumar Lame ta buxe ta a 1982, sadda sojoji suka yi juyin mulki kuma, sai
suka kasha Qaramar hukumar Lame, tare da rufe makarantar baki xaya. An rufe ta a
farkon watan Yuli 1984, a san nan tana da xalibai 344. Principal xinta na farko, kuma na
qarshe shi ne Mohammed Tsoho Gumau. An sabunta buxe ta a da sunan ‘Unguwar Waziri
Upper Basic’ a watan Oktoban 2019.
116
Ran talata 22 Fabrairu 1977, manyan ma’aikatan gwamnati, tare da Sakatare da
Ciyaman na qaramar hukumar Toro suka haxu a Gumau don tattauna inda za’a gina ta.
Manyan mutanen da suka halarta sun haxa da M. Usman Mairiga - Ciyaman qaramar
hukumar Toro, Alhaji Yarima Abba – Sakataren qaramar hukumar Toro, Alhaji Aliyu
Bununu – Sakataren ilimi Bauchi/Dass LEA, M. Umaru Saleh Tiffi – (Divisional
Inspector Of Education) Bauchi, M. Umaru Lame – Wakilin qasar Lame, M. Shu’aibu
Toro – Wakilin Sarkin Ayyukan Toro LGA. an xebi sabbin xalibai a farkon shekarar
karatu na 1978, suka fara karatu a inda aka fara ginawa na kudu da gari, har lokacin da aka
gama gini, suka tare karatu da kwana a 1979. Ta fara GSS har zuwa 1987, kana ta juye
GTC har yau.
71
QUNGIYOYIN CIKINTA

Qungiyoyi sun rabu kashi uku ; qungiyoyin addini, qungiyoyin masu


sana’a, da qungiyoyin ci gaban gari.

QUNGIYOYIN ADDINI

Daga cikin qungiyoyin addini da ake das u a wannan gari, akwai :


1- Qungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI)
2- Qungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ati Wa Iqamatis Sunnati (JIBWIS)
3- Qungiyar ‘Islamic Movement’ ta Shi’ah
4- Qungiyar Salafiyya
5- Qungiyar Christian Association Of Nigeria (CAN)
6- Qungiyar samarin Fityanu
7- Qungiyar ‘Almufidah’ masu lura da marayu

QUNGIYOYIN MASU SANA’A

1- Qungiyar Mafarauta/’Yan -tauri Tsintsiya Maxaurinki Xaya.117


2- Qungiyar ’yan dako
3- Qungiyar direbobi ta qasa (NURTW)
4- Qungiyar direbobi ’yan gada-gada (RTEAN)
5- qungiyar ’yan qwallo (Gumau United FC)
6- Qungiyar masu maganin gargajiya (BARMAGADA)
7- Qungiyar ’yan banga118
8- Qungiyar ’yan kasuwa (Gumau Co-operative Union)

117
Mambobin qungiyar su ne ; Maidawa Kanwa Lilo, Ali Chafta, Wake Garkuwa, da Sani
Duna.
118
An fara kafa qungiyar ’yan banga a Gumau ran 10 Maris 1989. Shugabanninta su ne :
Bature Ririwai (ya rasu ran Talata 4 Mayu 2004), M. Bikto, M. Isa Gado, M. Waje Xanye,
Ubale Babaji, M. Ali Dindima, Dogo Gumau, Shekarau Gumau, M. Sabo Maroqi, Fataye
Boda, Sarkin Arna, Gwadabe, Alhaji Adamu Badamasi, M. Audu Haladu, M. Idi Amadu,
Rabi’u Mai kayan zaqi, M. Ali Wanzami, GNT Gumau, Ginsau Mahauci, Isa Fawa
Gumau da M. Gani.
72
9- Qungiyar masu kamun kifi (Fishermen Co-operative
Society).119

QUNGIYOYIN CI GABAN GARI

Daga ciki qungiyoyin ci gaban gari kuma akwai :


1- Qungiyar Lame ‘Progressive Union’ (LPU)120
2- ‘Himma Matasa Social Club’ Gumau da kewaye121
3- Qungiyar aikin gayya122

SANA’O’INTA

i- Na gargajiya
ii- Na zamani

1- Noman damina : ‘Noma na duqe tsohon ciniki, Kowa ya zo duniya


kai ya tarar. Gadon gida alala ga rago’ Kowa ya bar gida, gida ya
bar shi.’123 Babban noman mutanen Gumau lokacin damina a

119
An yi zaven shugabanninta ran 17-08-1990. Shugabannin su ne ; Garba Lame, Audu
Kumanba Pingel, Yusufu Barden Wunti, Garba Ubandoma, Sarki Bala Jira, Ladan Bunu,
Damina Bukkuxu, Xankaka Ruhu, Shafi’i Bukkuxu, Yusufu Malam, Ladan Ya’u Jange,
Mato Nahari Lame Lame, Muhammed Dakan Wonu, Gargada Gumau da Maulud
Muhammed
120
An kafa wannan qungiya a shekar 1990, tana da mammbobi 50. An rantsar da
shugabanninta ran lahadi 13 Oktoba 1991 da misalin qarfe takwas na safe, a view Centre
da ke qofar fada.
121
An kafa wannan qungiya a farkon shekarar 1994. Sakatarenta shi ne Audu
Saleh
122
’yan kwamitinta su ne : Hakimi, dagaci ko mai unguwa, Magatakardar hakimi, Jami’in
gwamnati mai kula da aikin ci gaban jama’a, Xan majalisar hakimi, Sarkin samari,
Wakiliyar mata, Malamin gona, Malamin tsafta, Liman ko wani malamin addini, Principal
ko Hedimasta ko wani fitaccen malamin makaranta, Ma’abuta sana’ar hannu (Kafinta),
Magini, Latrisha, da mai walda, Wani mai unguwa, Wani attajiri da Fitaccen manomi
123
Haka ne kuwa. Allah ya halicci qasa, kuma ya halicci irin shuka da tsirrai daban-daban,
san nan ya saukar da ruwan sama. Da yawan mutanen wannan gari bas u zauna ba. Wasu
ma sai suka maid a noma sana’arsu.
73
zamanin da itace dawa, don ita ce abincin yau da kullum da mutane
ke rayuwa da shi. Akan noma farin dankali xan asali, da farin wake,
da dauro, galibi don cid a taimakon ’yan’uwa, ba don sayarwa ba.
Sai auduga da gyaxa da ake yi galibi don sayarwa da samun abin
biyan buqata da biyan haraji. Amma a zamanin yanzu an fi noman
masara, sai dawa, da shinkafa don abinci. Waken Soya, waken
Soya, shinkafa, dankali (lawur), da gyaxa. Ga asali, mutanen
Gumau bas u shahara da noman kwari ba, wato noman lambu.
Amma da ya ke kanawa’yan ci rani na yawan zuwa garin a ’yan
shekarun baya-bayan nan, ana noman tumatir, attaruhu, shamba,
lausur, latar, kabeji, alayyaho, gauta, yalo, karas da sauransu,
waxanda galibi ana noma su ne don neman kuxi, ba don hatsi ba.
Waxanda suka shahara da noma su ne : Sarkin noma Dindima,
Sarkin fawa shehu uban xankande

2- Kasuwanci : Shi ne saye da sayarwa na ko menene.

ATTAJIRANTA 1950-2021

1- Alhaji Sa’idu124
2- Alhaji Yunusa
3- Alhaji Na’iya
4- Alhaji Alhasan Sabo
5- Alhaji Alhasan Wan Manaja
6- Alhaji Alhasan Naramma
7- Alhaji musa Laska
8- Alhaji Voyi Tobbacco
9- Alhaji Kabiru Xanzalau
10- Alhaji Audu Safe
11- Alhaji Sabo125
12- M. Idrisu Wangida

124
Na Gwaggo, uban Tsalha, Bajimin gidan Jika, Xan Idrisu. Ya rasu ran Jumma’ah 21
Rabi’ul awwal 1413 hijri (16 Satumba 1992)
125
Ya rasu daren litinin 18 Yuli 1994, bayan ya yi fama da rashin lafiya.
74
13- M. Yunusa Wangida
14- M. Hasan Mai gishiri
15- Alhaji Uba
16- Alhaji Abashe
17- M. Audu Xandilimi
18- Alhaji Musa Mai kwabbai
19- Alhaji Musa Marmara
20- Alhaji M. Yaro
21- Harxo Wambai
22- Alhaji Ibrahim Xanjida
23- Alhaji Audu Ningi (Malamin Lamba)
24- Alhaji Hamisu Na’iya126
25- Alhaji Sunusi Alhasan
26- Alhaji Hasan Alhasan
27- Alhaji Alin Shehu
28- Alhaji Shehu Yusufu
29- Alhaji Saleh Nasko
30- Alhaji Hasan Laushi
31- Alhaji Maikuxi Nagadanya
32- Alhaji Ibrahim Auta
33- Alhaji Salisu Kasuwa
34- Alhaji Abdurrahman Nagadanya
35- Alhaji Isyaku Galadi
36- Alhaji Yunusa Gwanjo
37- Alhaji Muhammadu Mai gaskiya
38- Alhaji Ibrahim Jirgi
39- Alhaji Babawo
40- Alhaji Abbas Jafaru

126
An haifi Alhaji Hamisu Na’iya a 1979 a Gumau, kuma a cikinta ya tashi. Ya yi karatun
Muhammadiyya a makarantar M. Abdulhamid Xanhasan. Ya yi makarantar firamare
Unguwar Waziri 1993-1999. Ya yi makarantar GSSS Toro 2000-2006. San nan ya yi
Diploma a jami’ar Bayero ya karanci aikin banki da shige-da-ficen kuxi (Banking &
Finance). Duk cikin attajiran Gumau a yau (2020) babu mai qarancin shekaru irin na shi
day a mallaki irin abin da ya mallaka.
75
3- Xinki : xinkin tufafi, kwaxo da linzami, surfani da sauransu.
4- Kaxi : sana’ar kaxi itace tushen saqa, galibi sana’ar mata tsofaffi ne
a cikin gida. Da auduga ake yinta. Ita kuma auduga daga hannun
manoma ake samunta. Idan ta zo hannunsu, sais u gurje ta, su raba
tad a angurya. San nan su save tad a masavi tare da
makallaciya.127idan ya savu sosai sais u nemi mazare da makallatai
su kaxe shi ya zamo zare. Kowanne dunqulen mazari an ace masa
tangori. San nan sais u yi tariyar zaren nan, su sulance shi. Daga
nan ya zamo zare, sai su kai kasuwa, masaqa su zo su sara.
5- Saqa (Gwado, majanyi, tabarmi) : saqa muhimmiyar sana’a ce ga
dukkan talikai. Hasali ma idan ka xebe nomad a qira, babu sana’ar
da tafi taimakon mutum kamar ta. Domin ba don saqa bad a mutane
da yawa sun sha wahala. Tun da farko abinda masaqi ke buqata ga
saqa shi ne zare. Zare kuwa daga hannun mata ake samunsa. Akwai
masaqa iri biyu, saqar maza da saqar mata. Ta maza it ace ta fari da
saqi. Ta mata kuwa ta gwado, majanyi da tabarmi. Kayan aikin
saqa na maza ya fin a mata yawa. Akwai shika-shikai na itace, da
xan jifa, da allera, da akwasa, wannan na mata kenan. Na maza
kuwa, bayan waxanda aka zayyana, akwai qoshiya, da matsefi, kai-
ka-zo. Amma kowannensu sai ya nemi jakin saqa. Su ne gwafa
guda biyu na kwangwala da zai kafa dama da hauni. Da yawa akan
yi saqa da farin zare kaxai. Amma in ana son ado, akan yi turi iri-
iri. Idan da baqin zare ake so a yi, sai a kai wa marina shi baqi. Idan
kuma ja ne, sais u tura shi da galura. Idan rawaye ne, sai a sa zabibi.
Idan masaqi ya qare saqa, sai a kai kasuwa, maxinka su saya.
6- Qira : Qira tana cikin manyan sana’o’i na duniya. Sana’a ce da
dukkan mutane suna da buqatar wani abu daga gar eta. Kusan
kowacce sana’a a duniya, said a qira ya shige ta. Amfaninta ba ya
lasaftuwa. Har ma akan ce, “Ba don maqeri ba da ado ya naqasa,
tun ba wajen mata ba.” To, haka ma hawan dawaki, dab a zai yiwu
ba. Sai fa in hawan barde za’a yi. Maqera sun kasu kashi biyu :
maqeran farfaru da maqeran babbaqu. Dukkansu suna yin qira da

127
Makallaciya : it ace gavar dawa ta sama. Ta takanxa kuma an ace mata ‘sulle.’
76
qarafa daban-daban, kamar zinariya, azurfa, gaci, farin qarfe, baqin
qarfe, dalma, sanfalwa (goran ruwa)128 da sauransu. Maqeran
farfaru su ke aiki da farin qarfe, su qera zobe, munduwa, xankunne,
sarqa da sauransu. Maqeran babbaqu su ke qira da baqin qarfe, su
qera kayan yaqi, da na farauta, da kayan aikin gona da na sauran
sana’o’i, kamar su rowan garma, fatanya, gatari, masassabi, dagi,
dundurusu, takobi, barandami da sauransu. Dukkan maqera suna
kafa uwar maqera, wacce a kan ta ake qira. sais u nemi hantsaki,
wanda shi ake zura qarfe a cikin wuta, in ya yi ja kuma dashi ake
ciro shi, ya riqe ya buga shi, wasu n ace masa awartaki, har ana yi
masa kirari, “Awartaki makamar zafi!” sai babbar guduma da ake
kira masaba don dukan qarfe ya yi faxi. Qaramarta kuma mai qotar
itace ita ake kira muntalaga, in y agama aiki da masaba da ita yak e
qarasawa. Sai zuga-zugi don zuga wuta. Galibi maqeri za ka ganshi
qaqqarfa isasshe, ba kumama ba. Babbar xabi’arsu it ace zumunci.
Ko ina suka haxu da xan’uwansu maqeri, ko bas u sanshi ba, bas u
ma tava ganinsa ba, sais u xauke shi kamar xan’uwansu. In bikinsu
ya tashi, sais u sanar da dukkan maqeran da ke kusa, su zo ayi bikin
da su. Maqera suna da jimirin zafin wuta, har ba su kulawa da ita
idan suna cikin aikinsu. Kuma da za ka gansu sadda su ke biki, ko
ana yi musu kixansu na maqera, in ka ga yadda suke wasan wuta,
sai ka zaci jikinsu na dutse ne ba fata ba. Ana yi wa maqera kirari
da cewa, “Baqi dodon qarfe, mai amana da maharba. Na kaka
gwani, wanda ya iya don kansa. Da ba don taya ba da yai mota. Ba
don shi ba da qasa tai saura. Kai ba don shi bad a maza sun yi gizo.
Na Ali gatan kaka mai abin mamaki. Qarya ku ke magauta. Sai ya
gaji ya bari don kansa. Amma zuwa shekarar 2021 babu sauran
maqeri a Gumau. Duka sun qare, ’yan baya sun daina, kuma ba’a
samu da suka zo suke yi ba, sai dai masu kawowa sayarwa.
7- Wanzanci : Wanzamai su ne masu yin aski da gyaran fuska, da
kaciya, da qaho da fitar da ’yar wuya129 da zanen gado.130 Kowanne

128
Aluminium
129
Belu
130
Shaushawa
77
wanzami yana da asake, da qaho da ’yar qaramar aska mai tsini ta
yin zane, da mawashi na fata, ko na dutse. Duka yana rataye das u
cikin zabira yana yana yawo. Saboda muhimmancin wannan sana’a
akan ce, “Gari ba ya kafuwa sai da Wanzami.”
8- Ginin –Bani-Bani
9- Fawa
SARAKUNAN FAWANTA 1940-2020

i- Sarkin Fawa Naladan131


ii- Sarkin Fawa Ya’u132
iii- Sarkin Fawa Xanyaro133
iv- Sarkin Fawa Nayawo134
v- Sarkin Fawa Abubakar Nayawo
10- Kitso
11- Ginin tukwane : idan mace na son gina tukunyar sayarwa ko na
amfanin kanta, za ta je ta saro yumvu, ta kwaso zuwa gida ta
shanya. Idan ya bushe sarai, sai ta yi ta bugunsa ta kulki, har sai ya
yi livis. Sai kuma ta riqa xebowa kaxan –kaxan tana tankaxewa,
tana rairayewa tana zubar da ’yan tsakuwoyi. San nan sai ta kwava
ta cuxa da ruwa, har sai ta cuxu. San nan a xauko wata tukunyar da
aka qare ta, sai a kifa ta, a barbaxa toka a bayanta. Sai a xebo
yumvun nan a yave bayan tukunyar nan, ana bi ana bubbugawa da
xan makoxi. Idan yumvun ya rufe kamar rabin tukunyar, sai a bar
tat a sha iska kaxan, ta yi tauri. Kana sai a cire tukunyar da ke qasa.
A samu wani xan ice santsi, xaya daga ciki, xaya daga waje ana yi
ana tava ruwa, ana shafewa. San nan sai gina bakin, duka ana yi ana
tava ruwa ana shafewa. Idan tukunya ta gamu, za ka ganta sumul-
sumul mai kyau. Idan aka gina su da yawa, sai akai matoya, a
jejjera. A kawo qaiqayi da qirare a zuba bisansu, sai kuma a qyasta
wuta. Sai su toyu, su yi qwari, sai a kai wajen sayarwa.

131
’Ya’yansa su ne Xan’ayi, Tagumau, Injori.
132
’Ya’yansa su ne Lawandi (Xan chanis) da Muhammadu.
133
Xan Xan’ayi, jikan sarkin Fawa Yau, shi da shaqiqinsa Sabo.
134
Asalinsa mutumin Badikko ne. Ya samu sarautar sarkin Fawa ne a dalilin siyasa.
78
12- Tsibbu
13- Bokanci
14- Bori
15- Su
16- Xorin karaya
17- Farauta
18- Jinka
19- Karatu
20- Roqo

SHAHARARRUN MAROQANTA

1- Xankule
2- Busa Mai kakaki
3- Kwando Farin Malam
4- Kwando Xambana : mutumin Gukka
5- Duna Nayayale
6- Linsa
7- Sabo Mai garaya
8- Alhaji Maikano
9- Babaru
SANA’O’INTA NA ZAMANI

1- Karatun boko
2- Gonar kaji
3- Kafinta
4- Ginin zamani
5- Kanikanci
6- Walda
7- Dukancin zamani : (Yin takalma, Xinkinsu da wankinsu)
8- Wayarin
9- Dillanci
10- Tuqi
11- Buga bulo

79
WASANNI :

WASANNIN MOTSA JIKI NA MANYA

1- Dambe
2- Kokawa
3- Shaxi

WASANNIN MOTSA JIKI NA YARA MAZA

i- KAMA TAMUNGU TAMUNGU


(Yadda ake yin wannan was an sai a yi da’ira a kama hannuwan
juna da kyau. Sai xaya ya yi yunquri ya juya ya dire, a lokacin
da mutum biyu na gefensa ke riqe da hannayensa da kyau. Idan
ya dir, sai na damanshi ma ya yi haka, ayi ta kewaya wa, har a
dawo kan na farko).
BAYARWA : Kama tamungu tamungu
AMSHI : Mungule
BAYARWA : Kama tamungule gwaja
AMSHI : Mungule
BAYARWA : Mungule juyin waina
AMSHI : Mungule
BAYARWA : Xan gwauro ya kasa
AMSHI : Mungule
BAYARWA : Ni ko ba xan gwauro ba
AMSHI : Mungule
BAYARWA : Ni b azan kasa ba
AMSHI : Mungule
BAYARWA : Ka ga juyi –juyi
AMSHI : Mungule
BAYARWA : Ka ga juyin waina
AMSHI : Mungule
BAYARWA : Wancan xan gwauro ne
AMSHI : Mungule

80
BAYARWA : Ya kasa juyi-juyi
AMSHI : Mungule
BAYARWA : Ya kasa juyin waina
AMSHI : Mungule
BAYARWA : Maci tuwo a sakaina
AMSHI : Mungule
BAYARWA :Masha furar xan kiwo
AMSHI : Mungule
BAYARWA : Masha kunun xan kiwo
AMSHI : Mungule
BAYARWA : Masha kunu fal buta
AMSHI : Mungule
BAYARWA : Masha fura a sakaina
AMSHI : Mungule
BAYARWA : Mungule juyi xai-xai
AMSHI : Mungule
BAYARWA : Kai kama tamungu –tamungu
AMSHI : Mungule
BAYARWA :Kama tamungule gwada.

ii- IN GERO YA NUNA


(Yadda ake yi, za’a yi layi, mai bayarwa yana gaba, yana ba da
waqar ana amsawa. In ya zauna mabiyansa su zauna. In ya
kwanta su kwanta. Wato dai duk abin da ya yi na bayansa shi za
su yi).
BAYARWA : In gero ya nuna
AMSHI : In gero ya nuna
BAYARWA : Yara ku karya ku tuma shi
AMSHI : Yara ku karya ku tuma shi
BAYARWA : In dawa ta nuna
AMSHI : In dawa ta nuna
BAYARWA : Yara ku karya ku dafa ta
AMSHI : Yara ku karya kudafa ta
BAYARWA : Kadan masara ta nuna

81
AMSHI : Yara ku karya ku gasa ta
BAYARWA : Idan maiwa ta nuna
AMSHI : Yara ku karya ku tuma ta
BAYARWA : Idan gyaxa ta nuna
AMSHI : Yara da qoqonsu na kale
BAYARWA : Manya da qoqonsu na kale
AMSHI : Na yi haka ban a yi hakan ba
BAYARWA : Na yi haka Allahu akubar
AMSHI : Na yi haka kwanciyar kare
BAYARWA : Na yi haka kwanta ka ci wake
AMSHI : Na yi haka kwanta ka ci wake
iii- XAN AKUYA NA
(za’ yi da’ira a rirriqe hannaye da kyau. Xaya ya shiga cikin
da’irar yana bad a waqa, yana zagayawa, har sai ya ga waxanda
suka yi sako-sako da hannayensu, sai ya yi wubub ya ratsa
tsakaninsu ya wuce waje)
BAYARWA : Xan akuya na
AMSHI : Damusherere
BAYARWA : Ya shiga rumbu
AMSHI : Damusherere
BAYARWA : Za su kasha shi
AMSHI : Damusherere
BAYARWA : Har da wuqaqe
AMSHI : Damusherere
BAYARWA : Har da takobi
AMSHI : Damusherere
BAYARWA : Har das u adda
AMSHI : Damusherere
BAYARWA : Har das u lauje
AMSHI : Damusherere
BAYARWA : Wubub na wuce nan
AMSHI : Wubub na buge ka
BAYARWA : Wubub na wuce can
AMSHI : Wubub na buge ka

82
iv- JEMAGE :
(Yadda ake yi : za’a yi da’ira hannaye a sake ko a riqe. Mutum
xaya zai shiga cikin da’irar yana bad a waqar, ragowa suna
amsawa, yana yi yana duba sa’ansa. Idan ya samu sa’ansa, sai
ya xale shi, ya saki kansa da hannayensa suna reto, yana ci gaba
dab a da waqar. Idan y agama sai ya sauka, wani kum ya shiga
cikin fage, ya yi tamkar yadda na farko ya yi. Haka za’a yi ta yi,
har sai an zagayo kan kowa).

Bayarwa : kai na qolin qoli


Amshi : jemage
Bayarwa : Kai na kangali kangal
Amshi : jemage
Bayarwa : Yaro duba duba
Amshi : jemage
Bayarwa : Yaro dubi sa’anka
Amshi : jemage
Bayarwa : Xan jilon jilo qoqi
Amshi : jemage
Bayarwa : Kar ka hau shi ya faxi
Amshi : jemage
Bayarwa : Kar ka kama ruvago
Amshi : jemage
Bayarwa : Ruvago ba qarfi ba
Amshi : jemage
Bayarwa : Ba shi qwarin gwiwa
Amshi : jemage
Bayarwa : Sai ka faxi ka karye
Amshi : jemage
Bayarwa : Kar ka hau mai gemu
Amshi : jemage
Bayarwa : Kar ka hau babanka
Amshi : jemage

83
Bayarwa : Yaro dubi sa’anka
Amshi : jemage
Bayarwa : Na yi nitso na kamo kifi ko ruwa ban sha ba
Amshi : jemage
Bayarwa : Na yi nitso na kamo tarwaxa ko ruwa ban sha ba
Amshi : jemage

v- ASHA RUWAN TSUNTSAYE


(yara uku waxanda qarfinsu ya zo xaya, su ke yin wannan was
an , sai biyu su goya hannunsu a baya, su harxe’yanyatsunsu.
Shi kuma ukun sai ya sa xaya qafarsa a kwarmin xaya, ya sa
xayar kuma a kwarmin xayan, ana yin waqar).
Bayarwa : A sha rowan tsuntsaye
Daga sama
Bayarwa : Ba daga saman ba
Daga sama
Bayarwa : Shar na qoshi
Daga sama
Bayarwa : A sha rowan tsuntsaye
Daga sama

vi- WIWI NI KURA


(yadda ake yinsa : yara kamar shida zuwa goma za su jeru,
wannan a bayan wannan, su rusuna, kowa ya kama qugun na
gabansa. A samu qaqqarfa ya zama uba, ya tsaya a gabansu,
don ya riqa kare’ya’yansa in kura ta zo za ta kama su. wani
kuma a can zai ware, ya zamo kura, ya tafi nesa kaxan da uban
yara, suna kallon juna. Kura za ta riqa yin waqa, uba
da’ya’yansa suna amsawa).
Kura : Wiwi ni kura
Uba : ba kya ci ba
Kura : Ni kurar sarki
Uba : ba kya ci ba
Kura : ni ta galadima

84
Uba : ba kya ci ba
Kura : wancan da mai ya ke
Uba : ba kya ci ba
Kura : wancann lugui-lugui
Uba : ba kya ci ba
Kura : wancan sumul-sumul
Uba : ba kya ci ba
Kura : wiwi ni kura
Uba : ba kya ci ba
Kura : allura ta faxi
Uba : ba kya ci ba
Kura : ku duba mata
(idan uban ya ce ‘ku duba mata’ sai ’ya’yan su saki hannu
xaixai, su riqa sharer qasa da su. ita kuma kura, sai ta yi
qoqarin kama na bayansu. Su kuma suna kokkomawa wajen
uba, don yak are su. idan ta kama na baya, sai ta ajiye shi a
gidanta ta je neman wani. Idan ta sake kama na baya ta kais hi
gidanta, ta ajiye ta koma neman wani. Har sai ta kames u baki
xaya. Duk sadda ta je neman wani sai kura ta zamo uban yara.
Uban kuma ya zamo kura).

Ga kuma wasu wasannin masu buqatar saurare cikin natsuwa. Duk


wanda ya kai hankalinsa nesa ya vata wajen bad a amsa, to, za’a bi shi da
duka har sai ya sha)

vii- AWU AWU


Bayarwa : awu awu
Amshi : awu
Bayarwa : Na je Barno awu
Amshi : awu
Bayarwa : Na auno gero
Amshi : awu
Bayarwa : Na auno maiwa
Amshi : awu

85
Bayarwa : Na auno dawa
Amshi : awu
Bayarwa : Na auno acca
Amshi : awu
Bayarwa : Na auno ibiro
Amshi : awu
Bayarwa : Na auno shinkafa
Amshi : awu
Bayarwa : Na auno alkama
Amshi : awu
Bayarwa : Na auno masara
Amshi : awu
Bayarwa : Na auno su gyxa
Amshi : awu
Bayarwa : Na auno wake
Amshi : awu
Bayarwa : Na auno yashi
(shiru. Duk wanda y ace awo, za’a bi shi da duka)

viii- JINI JINI


Bayarwa : jini da jini
Amshi : janjan
Akuya da jinni
Amshi : janjan
Bayarwa : Rago da jini
Amshi : janjan
Bayarwa : Saniya da jini
Amshi : janjan
Bayarwa : Kaza da jini
Amshi : janjan
Bayarwa : Vera da jini
Amshi : janjan
Bayarwa : Giwa da jini
Amshi : janjan

86
Bayarwa : Raqumi da jini
Amshi : janjan
Bayarwa : Doki da jini
Amshi : janjan
Bayarwa : Shirwa da jini
Amshi : janjan
Bayarwa : Zaki da jinni
Bayarwa : Gafiya da jini
Amshi : janjan
Bayarwa : Alade da jini
Amshi : janjan
Bayarwa : Maraqi da jini
Amshi : janjan
Bayarwa : Tsako da jini
Amshi : janjan
Bayarwa : Tsakuwa
(shiru)

ix- ’YAR KUCCIYA


’Yar kucciya’yar kucciya
’yar kucciya qanwar Amina
Tashi mu je dawa itace
Ba zan je dawa ice ba
Menene yak an hanani?
Firfito yak e hanani
Firfito irin na wane?
Firfito irin na kaza
Fit, fit tafi sosai
Ina tsoron abin qasa maci
(Duk wanda ya ce ‘ji’ sai a bi shi da duka, har sai ya sha)

x- DUQUMA DUQUMAYE
Bayarwa : Duquma duqumaye
Amshi : Ho duqumi

87
Xan Sa duqumi ne, bas hi qaho balle ya yi suka
Amshi : Ho duqumi
Rago duqumi ne bas hi qaho balle ya yi tunkuya
Amshi : Ho duqumi
Akuya duquma ce bat a qaho balle ta yi tunkuya
Amshi : Ho duqumi
Barewa duquma ce, ba ta qaho balle ta yi tunkuya
Amshi : Ho duqumi
Mariri duqumi ne, bas hi qaho balle ya yi tunkuya
Amshi : Ho duqumi
Karsana duquma ce, bat a qaho balle ta yi tunkuya
Amshi : Ho duqumi
Kanki duqumi ne bas hi qaho balle ya yi tunkuya
Amshi : Ho duqumi
Gwambaza duquma ce, ba ta qaho balle ta yi tunkuya
Amshi : Ho duqumi
Gada duquma ce, ba ta qaho balle ta yi tunkuya
Amshi : Ho duqumi
Gwanki duqumi ne ba shi qaho balle ya yi tunkuya
Amshi : Ho duqumi
Guzuma duquma ce, ba ta qaho balle ta yi tunkuya
Amshi : Ho duqumi
Kaza duquma ce, ba ta qaho balle ta yi tunkuya
Amshi : (Shiru. Duk wanda y ace ‘ho duqumi’ ya vata kenan)

xi- Kulli kucciya


(Yadda ake yi : za’a yi da’ira a rirriqe hannaye. Sai xaya ya saki
hannunsa ya fita daga da’irar, yana tafiyar tsutsa a tsakanin
waxanda suka rirriqe hannayensu, ya shiga tan an ya fita tan an,
har sai ya zo daidai inda yak e kafin ya saki layin ana wannan
waqar)
Bayarwa : kulli kucciya
Amshi : kulli
Bayarwa : Kowa ya vata

88
Amshi : Kulli
Bayarwa : Zai sha duka
Amshi : Kulli
Bayarwa : Har da mangari
Amshi : Kulli
Bayarwa : Har da muntsuni
Amshi : Kulli
Bayarwa : Har da taxiya
Amshi : Kulli
Kowa : Ga gidanki nan shaya
(Sai wanda ya ke kewayawa ya koma cikin da’ira ya kama
hannu daidai inda ya ke da. Sai ace da shi ‘ga gidanki nan
shaya’ idan ba a nan ya ke ba ya vata kenan. Sai a bi shi da
duka da mangari da taxiya, har sai ya sha)

xii- BODARA ’YAR MUHAMMAN


(Yadda ake yi : za’a yi da’ira a zaune. Wani ya shiga tsakiyarsa.
A zavi shugaba wanda zai riqa bad a waqar tashin ’yar
(bodara). A samu wani dutse ko kasko, ko kwabo a ba shugaban
ya yi’ya das hi. Shugaba zai riqa faxin abinda zai batar da na
tsakiya, har na tsakiyan ya ka sa gane wanda’yar ke
hannunsa.’Yar kuwa tana ta zagayawa cikin rigunansu ko
gwadonsu.
Shugaba : ’Yar Muhamman
Yara : Bodara
Shugaba : Za ta tashi
Yara : Bodara
Shugaba : ’Yar Muhamman
Yara : Bodara
(tana ta tafiya)
Shugaba : Ta zo rimin Dada
Yara : Bodara
Shugaba : Ta kusa qofar fada
Yara : Bodara

89
Shugaba : Bodara ta zo dogon layi
Yara : Bodara
Shugaba : Ta zo qofar fada
Yara : Bodara

WASANNIN MOTSA JIKI NA YARA MATA

1- Gaxa
2- Darero
3- Tafa-tafa
4- Tashe
5- Wasan -kamu

i- Xan maliyo maliyo maliyo :


Bayarwa : Xan maliyo maliyo
Amshi : Maliyo
Bayarwa :Xan maliyo nawa
Amshi : Maliyo
Bayarwa :Ya tafi ina ne?
Amshi : Maliyo
Bayarwa :Ya tafi Ilori
Amshi : Maliyo
Bayarwa : Ba zai dawo ba
Amshi : Maliyo
Bayarwa : Sai a watan gobe
Amshi : Maliyo
Bayarwa : Gobe da labara
Amshi : Maliyo
Bayarwa : Jibi da labarai
Amshi : Maliyo
Bayarwa : Taka rawa mu gani, na Aliko gwaxas gwaxas. Amshi :
Na Aliko gwaxas gwaxas.

ii- Carmandudu carmanduduwa

90
Bayarwa : Carmandudu carmanduduwa
Amshi : carmande
Bayarwa : Akwai wani baqo a gidan mai gari
Amshi : carmande
Bayarwa : Ba ya bashi bay a lamuni
Amshi : carmande
Bayarwa : Ba ya neman’yam matan gari
Amshi : carmande
Bayarwa : Ko ya nema wa zai bas hi ma?
Amshi : carmande
Bayarwa : Yayata landiyo mana
Amshi : carmande
Bayarwa : Qanwata landiyo mana
Amshi : carmande
Bayarwa : Sa’ata landiyo mana
Amshi : carmande
Bayarwa : Shegiya mai tsiwar tsiya
Amshi : carmande
Bayarwa : Sa’ata me zan baki ne?
Amshi : carmande
Bayarwa : Carman dudu mu ci kaza da qwai
Carmande
Amshi : carmande

iii- IYE NANAYE


Bayarwa : Iye nanaye
Ayye yaraye
Ayye yaraye nanaye
Carmama
Amshi : Iye nanaye
Ayye yaraye
Ayye yaraye nanaye
Carmama
Bayarwa : jirgin goro lula-lula

91
Jirgin goro za ya kaxe ni
Jirgin goro kul ka kaxe ni
Jirgin goro zan maka saqo
Ba saqon sayen tasa ba
Ba saqon sayen kwano ba
In ka je ka gai da masoyi
In ka je ka sa masa riga
In ka je ka sa masa wando
In ka je ka sa masa hula
In ka je ka sa masa takalmin girma
Amshi : Iye nanaye
Ayye yaraye
Ayye yaraye nanaye
Carmama

iv- TAMA –YA-KI-TAMA :


Bayarwa : Tama ya ki tama
Amshi : Galadima
Bayarwa : Wasa ba faxa ba
Amshi : Arerere
Bayarwa : Ni nawa xan mashaxi
Amshi : Ya shaxe ki,
Bayarwa : ku ci shaxi, ku kwana shaxi.
Gadon gidanku ne bulala Xari da hamsin
ta shafe ki
Amshi : Gaba tsundum Baya tsundum a aljannah
Bayarwa : Ni nawa xan maxinka
Amshi : Ya xinke ki
Bayarwa : ku ci xinki, ku kwana xinki. Gadon gidanku ne
bulala Xari da hamsin ta shafe ki
Amshi : Gaba tsundum Baya tsundum a aljannah
Bayarwa : Ni nawa xan maharba
amshi : ya harbe ki

92
Bayarwa : ku ci harbi ku kwana harbi. Gadon gidanku ne bulala
Xari da hamsin ta shafe ki
Amshi : Gaba tsundum Baya tsundum a aljannah

v- WAYYO LILON TAYALO :


Bayarwa : wayyo lilon tayalo
Amshi : Tayalo
Bayarwa : An tayalo tayalo
Amshi : Tayalo
Bayarwa : An tayalon baba
Amshi : Tayalo
Bayarwa : An tayalon gwaggo
Amshi : Tayalo
Bayarwa : Ba qawata ce ba
Amshi : Tayalo
Bayarwa : Sai qawar qanwa ta
Amshi : Tayalo
Bayarwa : Ban wuri in yi wasa
Amshi : Tayalo
Bayarwa : In ba za ki iya ba
Amshi : Tayalo
Bayarwa : Ki je gida ki yi kwance
Amshi : Tayalo
Bayarwa : Ke ma tawo mu yi wasa
Amshi : Tayalo
Bayarwa : In ba za ki iya ba
Amshi : Tayalo
Bayarwa : Kira qawarki ta koya
Amshi : Tayalo
Bayarwa : Ni ma da qyar na koya
Amshi : Tayalo

vi- ARERE :
Bayarwa : ku ce kwalla

93
Amshi : kwalla
Bayarwa : Ku qara faxa
Amshi : kwalla
Bayarwa : Ban jib a dai
Amshi : kwalla
Bayarwa : Ashe kwalla tana maganin xakin budurwa
Amshi : Arerere im baa ram ba ba za ta zo ba
Bayarwa : Ku ci tsire
Amshi : tsire
Bayarwa : Ku qara faxa
Amshi : tsire
Bayarwa : Ban jib a dai
Amshi : tsire
Bayarwa : Ashe tsire yana maganin kwaxayin budurwa
Amshi : Arerere im baa ram ba ba za ta zo ba
Bayarwa : Ku ce mota
Amshi : mota
Bayarwa : Ku qara faxa
Amshi : mota
Bayarwa : Ban jib a dai
Amshi : mota
Bayarwa : Ashe mota tana maganin tafiya da sauri
Amshi : Arerere im baa ram ba ba za ta zo ba
Bayarwa : Ku ce nomau
Bayarwa : Ku qara faxa
Amshi : nomau
Bayarwa : Ban jib a dai
Amshi : nomau
Bayarwa : Ashe nomau na maganin aiki da sauri
Amshi : Arerere im baa ram ba ba za ta zo ba
Bayarwa : Ku ce kumbo
Amshi : kumbo
Bayarwa : ku qara faxa
Amshi : kumbo

94
Bayarwa : Ban jib a dai
Amshi : kumbo
Bayarwa : Ashe kumbo yana maganin xakin budurwa
Amshi : Arerere im baa ram ba ba za ta zo ba

vii- GAXA :
viii- DARERO :
Darero na daga cikin kevantaccen wasannin yara mata da
Hausawa ke yi, lokacin da duniya ke kwance lafiya, saboda
murnar azumi ya zo qarshe. Mahauta bas a yi, Lamawa bas a yi.
Ranar saba’ar watan watan azumi ake yinsa. Biki ne da ba’a
yanka kaji, ba’a kuma sayan naman miya a wajen mahauta, kai
ko an je don saya ma mahauta, ba za su sayar ba, domin su ne
abokan yi, sai dai tattabaru, za’a yanka a yi miya tun da
daddare. Ranar ashirin da bakwai, tun da asussuba za’a dafa
shinkafa da miya, ayi ta zubawa a kwano ana aikawa gidan
qawaye, yau idan kin kai wa qawa, gobe kuma ita ta kawo miki.
Shi ya sa masu zauren qofar gida ke kullewa, su sa sakata, don
kada qawa ta riga ki kawowa, don idan ta riga ki kawowa yau,
to, lalle gobe ki kai mata, to, gas hi kuma kin riga kin dafa ta ki
yau. Hantsi na xagawa sai a cikawa kowacce yarinya tuwo da
miya da kofin shan ruwa, su xauka a nufi rafi. Idan an je rafi sai
kowacce ta tona rijiya bakwai a cikin yashi, ta riqa xiba daga
kowanne tana sha. A nan za su yini suna ci, suna sha, suna
wasanninsu har la’asariyya sakaliya, kana su dawo gida, washe
gari ma haka. Tun wata shekara da wata yarinya mai suna Indo,
’yar gidan Xandilimi ta xauko cuta a rafi, suna dawowa gida ta
mutu, sai sarkin yaqi ya hana zuwa rafi yin darero. Sai aka
sauya musu wuri, zuwa ‘bauxa’ daidai in da rehawus ya ke. to,
sadda ake tafiya wurin dareron nan, akan riqa rera waqar
tsokanan mahauta, ana cewa :
Uwa ku na fawa,
ubanku na fawa,
idan ba ku jib a ne,

95
sarkin fawanku ya xora muku.
Idan ba ku jib a ne,
Mai unguwarku ya xorar muku
Mu taka na fawa
Mu murje na fawa
Na fawa da tsoro su ke,
Na fawa da tsoron faxa.
Mu na malam da tono su ke
Na malam da tonon faxa
Haba ’yan fawa ko a jejin gaba
Albasa na tsoron fashi.

Su kuma a vangarensu, ’yan matan mahauta su ma maid a


martani, suna cewa,
Uwa ku na malam
Ubanku na malam

Lokacin da duniya ke zaune lafiya, ’yan mata ne ziryan ke zuwa


rafi yin darero, babu ko namiji tare das u, sai fa ’yan qannensu
maza da za su riqa binsu suna rera waqar tashe, saura na
amsawa, su kuma ’yan matan suna zuba musu abinci. Ga abinda
su ke cewa :
Bayarwa : Maula ta sidi, maula ta balarabe.
Amshi : Maula
Bayarwa : Wannan gida da daxin bara ya ke.
Amshi : Maula
Bayarwa : Wannan ya ba ka, wannan ya daxa maka.
Amshi : Maula.

WASANNIN ZAUNE NA ’YAM MATA

a- TAFA-TAFA
i- Tafa tafa tafiyar nan da za mu tare
Da wa muka fara? Sai xan yaro sai masoyi

96
Kai xan yaro ka tsaya nan mu dama gari
Mu dama mu dama kar kura ta ci mu tare
Ta ci mu ta ci mu Allah ne abin yabawa. Annabi ne abin
yabawa
Da dala da goron dutse sun yi kuxinsu sun azurfa
’Yam matan qwaile samarin qwaile
Sun haxa kai suna koko ciko, suna ingirici
Ke kaza da tone-tone kada ki tono mana abin duniya da
rana tsaka gagal
’Yar mai dogon wuya saval
Haqorinki savi tara rivis
Haqorinki savi tara gagal
Ke xanxano mana gishiri, ko da muka je baqon gari
muka sha lami

ii- Na xauko ruwa daga Bebeji za ni in kai Yalwa


Na ci karo da shege xan maye yace, “Ke sauke”
Na ce, “La’ilaha illallahu b azan sauke ba.
Ko tulun rowan mai nauyi ne ko da daro ne
’Yam matan gidammu guda biyu ne sun qi jinin wasa
In aure ku ke so kun samu gobe a kama ku
Na sai taskira da mazarenta sun isa kama ku
Na sai tsintsiya ta sule goma ta isa share ku
Na sai goxiya ta sule goma ta isa xora ku.

iii- Ina da ciki da ciki na


Ina da cikin xan fari
Wata xaya ban haifa ba
Wata biyu ban haifa ba
Wata uku ban haifa ba
Wata huxu ban haifa ba
Wata biyar ban haifa ba
Wata shida ban haifa ba
Wata bakwai ban haifa ba

97
Wata takwas ban haifa ba
Wata tara ban haifa ba
A ran na goma na haife
Na je ni karyar runhu
Iskar gabar ta danno
Ta arewa ma ta danno
Ta yammaci ta danno
Na je gidammu da goyo
Na tad da baba a azure
Yana cinike-cinikensa
Yana cinikin goronsa
Ya ce, “Mu ga jikan na mu
Jikan na mu har ya girma?”
Na bas hi jikan na su
Ya rarrawa shi ya juyar
Ya bas hi goro goma
Biyar a wannan hannu
Ka ji biyar a wancan hannu
Ashe xaya yai tsalle
Na sunkuya zan xauka
Ya ce, “Ku ga’ya ba kunya”
Na ce, “Uhm, ba komai”
Na je gidammu da goyo
Na tad da iya a azure
Tana cinike-cinikenta
Tana cinkin yin qosai
Ta ce, “Mu ga jikan namu
Jikan na mu har ya girma?”
Jikan na mu ya isa yaye?
Na bat a jikan na su
Ta rarrawa shit a juyar
Ta bas hi goro goma
Biyar a wannan hannu
Ka ji biyar a wancan nhannu

98
Guda xaya ya faxi
Na sunkuya zan xauka
Ta ce, “Ku ga’ya ba kunya”
Na ce, “Uhm, ba komai”
Na je gidammu da goyo
Na tadda kishiyar iya Wawa
Tana cinike-cinikenta
Tana ta jibgar saqa
Ta ce, “Mu ga jikan na mu”
Jikan na mu har ya girma?
Jikan na mu ya isa yaye?
Na bat a jikan na su
Ta rarrawa shit a juyar
Ta muntsune shi a baya
Ta muntsune shi a ciki
Ta muntsune shi a qirji
Ta muntsune shi a hanci
Ta muntsine shi a cinya
Ta muntsune shi a kayi
Na tad da na ta a salga
Yana cinike-cinikensa
Yana cinikin yin kashi
Na muntsine shi a hanci
Na muntsine shi a qeya
Na muntsine shi a mama
Na dangwala shi a toka
Na muntsine shi a wuya
Ta ce, “Ku ga’ya ba kunya”
Na ce, “A lokacin ba kunyan ne
Ki ka muntsine min nawa?
Garin kallon xan fari
Dawa ta gudu ta bar turmi
Maiwa ta gudu ta bar turmi
Ga quad daga Barno

99
Ya rangaxa min guxa,
marangaxi, marangaxi
Wai na haifi xa kyakkyawa
Kunkuru daga Barno
Ya rangaxa min guxa
Marangaxi, marangaxi
Wai na haifi xa kyakkyawa

WASANNIN ZAUNE NA MAZA KO MATA

i- Na jajje na jajje
Na jajje ni gidan gwauro
Gwauro ya bani tuwon dusa
Ban karva ba ina tsro
Tsoron me, tsoron wani abu jan baki
Jan baki sari qoto
Qoton wa?
Qoton gidan Baraje
Barajen da way a ke
Miqo hanu mu je mu
Mu je mu wacce rana
Ranan yaqin qwalele
Qwalele qwaya ta fashe a bayan xaki tagararas
(wanda aka yi tangararas a kan gwiwarsa. Sai ya fid da
wannan qafar).

WAQOQI DA WAQE :

WAQEN IYAYE MATA IDAN SUNA NIQA

(Iyayemmu mata da a dutse suke niqa dawa, ko gero ko gyaxa da sauran


hatsi. Domin a san nan babu injin niqa, kamar yadda mu ke da shi a yanzu.
To, idan suna niqan nan su kan riqa rera waqar da za ta xebe musu kewa,

100
kuma su riqa jin daxin aiki. Yawanci kuma waqe ne na addini suka fi
rerawa).

i- BABU KOKWANTO

Ya rabba! na roqe ka ka ba ni ta’arifi,


Tsarin yabo ga Muhamman, babu kokwanto.

Farkon yabo Muhamman a gurin riqon suna,


Aka bayyane da kamatar, babu kokwanto.

An bayyane da kamatar can ga Alqur’an,


Gurin yabo na sa tari, babu kokwanto

Wanzala da ya kama kalimatus shahadah,


Huxuba da Attahiyatu babu kokwanto.

Xaukacin musulmin Allah duka wanda ke sallah,


Yana batu ga Muhamman babu kokwanto.

Idan kana yin sallah yai kira amsa,


Sallarka ba ta vaci, babu kokwanto.

Idan ka amsa waninsa in kana sallah,


Sai dai ka sake sallah, babu kokwanto.
In ka ji ambaton sunansa, sai ka ce, sallalla,
Sallarka ba ta vaci, babu kokwanto.

Maqyanqyamar al’arshi an rubuce ta,


Aka sa cikin Linjila babu kokwanto.

Ya rabbana ga Muhamman Jalla mai lema,


Ka taimake mu Muhamman, babu kokwanto.

101
Amina ce ta yi niyya za ta gun aiki,
Ya ce, “ki tuba da aiki” babu kokwanto.

Ta waiwaya bayanta ba ta ga kowa ba,


Ta waiwaya a gabanta ba ta ga kowa ba.

Ya ce, “Ga ma ni cikinki.” babu kokwanto.


Ta je gidansu ta zauna babu ta Magana.

Da nan da nan fa ta rame tai kamar jinya.


Uwar mijinta ta qare har ta tambaye ta.

“Ke ’yar nan ya kamarki ta sake?” babu kokwanto.


Tai kurum ta qyale babu ta magana

Shi ma uban mijinta ya qare har ya tambaye ta,


“Ke ’yar nan, ya kamarki ta sake?” babu kokwanto.

Shi ma mijinta ya qare, har ya tambaye ta,


“Ke ya kamarki ta sake?” babu kokwanto.

Ta ce, ”Ya niqa riqa saka na ga al’ajuba,


Yaron ciki da wa’azu.” babu kokwanto.

Ya ce, “Tun kina qaramarki ba ki yi haife ba.


Yau me ya sa ki ka aika.” babu kokwanto.

Ya ce, “Jiye jiye mini kaka ta, ni na ke magana.


Iya ba ta yi qarya ba. babu kokwanto.

Jiye jiye mini kakana ni na ke magana.


Iya ba ta yi qarya, ba babu kokwanto
Jiye jiye mini baba na ni na ke magana.
Iya ba ta yi qarya ba babu kokwanto.”

102
Daren lilitinin aka haifi Muhamman 12 ga wata,
Wata na sallar mata babu kokwanto.

Ranan ana goyonsa yai batun magana,


An al’ajab ga Muhamman babu kokwanto.

Ranan ana goyonsa aka yi fari a Makkah,


Har ya tsananta da kyawu babu kokwanto.

Halima ta xauke shi ta cane, “Allah !


Ka sauko ruwa don wannan babu kokwanto.

A sauko ruwa a garinsu har ya shashata,


Albarkacinka Muhamman babu kokwanto.

Soron garinsu ya yanke, ya zube a qasa.


Batunsu alfasha ne babu kokwanto.

Ran nan a sau tauraro sai ka ce mashi,


Aka kori shexanunsu babu kokwanto.

Ran nan abin da ke wuta ka ce salkuna ka zuba.


Abin da ke ruwa quna babu kokwanto.

Idan ba kai ba Muhamman wa ke mutum da haka?


Ishidun –shidun ishiduna babu kokwanto

Halima ce an nono za’a yaye shi,


Ta ce, “Amina ki ba ni.” babu kokwanto

Ta ce, “Ki je da shi naba ki babu rarauka.


Ki je da shi na ba ki.” babu kokwanto.

103
Halima ce ta ya yi Muhamman har ya taka qi.
Tana batu ga Muhamman babu kokwanto.

Ya ce, “Iya na ki bar ni nai bibiko,


In bi ’yanuwa na mu saba babu kokwanto.

Ta ce, “Ina tsoronka Muhamman bakin duniya,


Baki abin tsoro ne babu kokwanto

Ya ce, “Iya na ki bar ni nai bibiko,


In bi ’yan’uwa na mu saba babu kokwanto

Ta ce, “Ina tsoronka Muhamman kada su cuce ka,


Bisa qishirwa da yunwa babu kokwanto.”

Ya ce, “Iya na ki bar ni, ba su cuta ta.


Ya Khaliqu ya tsare ni babu kokwanto.”

Ya je wajen ’yan kiwo da rijiya a wurin,


Can saniyarsu ta faxa,

manyan garin suka taru, garin su xauko ta.


sukai sukai suka kasa babu kokwanto
Muhamman ya zo ya miqa hannunsa shi ya xauko ta
Xan shekara huxu haqqan babu kokwanto
Labari ya tadda Halima, tai ka yin murna
ta taho wajen ’yan kiwo
ta rungume shi da murna babu kokwanto
Washegari ya ka koma can wajen kiwo,
Ya tarar mutum uku sun zo.

104
sukai caraf ga Muhamman sai su bushe shi
suka sa wuqa suka yanka babu kokwanto
Zuciya ta Muhamman sun ka fisshe ta
Suka sa wuqa suka yanka babu kokwanto
Akwai jini a cikinta sun ka fisshe shi,
Suka sa ruwa suka wanke babu kokwanto
Suka ciccika ta da Hikamu du da annuri,
Abin da kai duka wannan bai ji komai ba.
Ba shi ya kan ci Muhamman babu kokwanto

Labari ya tadda Halima tai ka yin kuka,


Ta taho wajen ’yan kiwo ta taras da shi a sama
Ta ce da shi, ”Ha barka.” babu kokwanto
Ya ce, “Iya na bar yin kuka, Jibrilu ne Mikaila
An ka aiko su zo su taimaki Manzo babu kokwanto

Makarviya wanzami sabulun wanka,


Ba su aikata ba Muhamman babu kokwanto

Da Sha da yankan cibi ga shi tsattsarka,


Ba su aikata ba Muhamman babu kokwanto

Mutum da saurin girma, ko fa wanene,


Koyi ya ke ga Muhamman babu kokwanto.

Mutum da zafin hannu ko fa wanene,


Koyi ya ke ga Muhamman babu kokwanto.
Allahummaf tahna abwabil ilmi,
waballigna abwabil khairi
Da ma mu ganka Rasulullahi ranar tsanani.

105
ii- WAQEN IMFIRAJI IMFIRAJI

WAQOQIN TATSUNIYA

i- DASKIN-DA-RIXI :
Dawa : Assalam salam xan yaro
Assalam salam
Saurayi : Wanene nan ya ke mana
Assalam salam
Dawa : Dawarku ce ta ke maka
Assalam salam
Mai tuwo da daxi ni dawa
Mai tuwo da daxi
Saurayi : Na ji na ki suna yarinya,
Ba ni nawa suna
Dawa : Ban san ka ba xan yaro
Ban san ka ba
Saurayi : Da ba ki san ni ba yarinya
Koma da baya ki sha kuka
Burtuntuna : Assalam salam xan yaro
Assalam salam
Saurayi : Wanene nan ya ke mana
Assalam salam
Burtuntuna : Burtuntunarku ce ta ke maka
Assalam salam
Burtuntuna ai ni ce
mai vata kaya
Saurayi : Na ji na ki suna yarinya,
Ba ni nawa suna
Burtuntuna : Daskin-da-rixi xan yaro
Daskin-da-rixi
Saurayi : buxe ki shigo yarinya
Buxe ki shigo

106
ii- MUSA XAN MAKARANTA :
Kai musa kai musa
Musan Gayya
Musa xan makaranta
Musa xan saraki
Ka qaunaci Allah
Musa ban nbante na
Ka qaunaci Allah
Musa ban riga ta
Ka qaunaci Allah
Musa ba ni zani na
Xankwali na
Musa Musan Gayya

Kai wane kai wane


Wanen Gayya
Wane xan makaranta
Wane xan saraki
Ka qaunaci Allah
Wane ban bante na
Ka qaunaci Allah
Wane ban riga ta
Ka qaunaci Allah
Wane ba ni zani na
Xankwali na
Wane Wanen Gayya

iii- RUWAN BAGAJA :


Kogi, kogi ko kai ne ruwan Bagaja?
Bagajar gayya ta ’yan sarki?
Domin qirgi aka aiko ni,
In zo in wanke a ruwan Bagaja.

iv- ALA-GIDI-GO :

107
Ai yara iye ala gidigo
Ala gidigo ala gidigo ’yan yara na
Ku ’yan yara mu je wanka
Ba dai wankan ba,
kar aci rogon mutane
Rogo da kuxi
saiwa xaya sule talatin.
Wayyo Allah zaqi na jiyo
Zaqi na jiyo
in ji varawon takanxa
Tilas ka biya
in ka qi a xaure ka gobe

Inda ni ce matar gyartai


In na yi tuwo
sai in fasa qwaryar da gangan
In ya xinke mu yo aure,
In bai xinke ba
a bakin aurensa kenan
In da ni ce matar kuturu
In baya nan
sai in cika xakin da tsidau
In ya taka mu yo aure,
In bai taka ba
a bakin aurensa kenan
In da ni ce matar kurma
Sai yai nuni,
sai in gwada ban san kwatance
In yai magana mu yo aure,
In bai magana ba
a bakin aurensa kenan
In da gurgu ke aure na,
Sai babu ruwa gidanmu
In ce xauki tulu.

108
In ya xauka mu yo aure
In bai xauka ba
a bakin aurensa kenan.
In makaho ya ka aure ni
Sai za shi bara in ce masa,
Kai ba ni sanda
In ya damqan mu yo aure
In bai damqan ba
a bakin aurensa kenan
Ke yarinya zavi dogo
Zavi dogo na xanwara dokin iyali
Ita mai wada turmi ta tuno
Turmi ta tuno zuwa gaba ta xau kujera

WASANNIN MAZA DA MATA :

TASHE LOKACIN AZUMI

Tashe na daga cikin al’adun Hausawan asali, kuma ana yinsa ne lokacin
azumi, idan azumi ya kai goma sha biyar. Tashe ya samo asali ne daga
tashi don yin sahur yayin xaukar azumi. Was an tashe kuwa ya samo asali
ne daga Nalako, wanda sarki ke naxawa sarkin gwagware. Wato waxanda
suka daxe bas u yi aure ba. Nalako shi ke riqa kewaya gari yana wasanni
don tashin gwagware daga bacci, saboda bas u da matan da za su riqa
tashinsu. Bayan Nalako ya buxe na sa, sai samari da’yammata su ma su yi
ta aiwatar da na su bayan sallar asham. Masu was an tashe sukan yi
qoqarin kwaikwayon wata xabi’a, mai kyau ko mara kyau da wasu ke yi a
cikin al’umma, wacce ake son su gyara saboda muninta, ko kuma su xore
saboda kyawunta don ci gaban al’umma. Kuma akwai hannunka mai sanda
ga shugabanni, magidanta da malamai kan yadda suka ratse hanya. A cikin
waqoqin tashe akan yi amfani da ban dariya, wajen isar da saqo ta hanyar
was an nishaxi. Masu was an tashe kan yi shiga da adon duk wanda suke so
su kwaikwaya, don su isar da saqo ga al’umma. Sukan riqa bi gida-gida, ko
kasuwanni da wuraren taruwar jama’a. wani lokacin ma har sukan haxa da

109
kixa da rawa. A yayin das u kuma masu kaloo da saurare kan riqa bad a
kyautattukar kuxi, hatsi ko wani abin marmari.
Tashe ya kasu kasha-kashi : akwai tashen’yammata da kuma samari.
Wato yara samari su ware tawagar sa’o’insu su gabatar dashi, ba tare da
cuxanya da’yammata ba. Haka ma’yammatan sukan yi nasu, ba tare da sun
cuxanya da samari ba. Kuma irin wasannin tashesu ya sha bamban. Akwai
kuma wani nau’in tashe da manya ke gabatarwa, galibi a fadar sarakuna da
gidajen masu kuxi. Dukkan masu was an tashe sukan samu tarba mai kyau
a wajen jama’a. Daga cikin waqoqin tashe na ’yam mata akwai :

i- Waqar Asha ruwa -ruwa


Bayarwa : Asha ruwa-ruwa asha ruwa lafiya
Amshi : Asha ruwa
Bayarwa : Masu gidan nan bacci ku ke ko sallah?
Amshi : Asha ruwa
Bayarwa : In bacci ne in kun idar kwa ba mu
Amshi : Asha ruwa
Bayarwa : In sallah ne in kun idar kwa ba mu
Amshi : Asha ruwa
Bayarwa : Asha ruwa-ruwa asha ruwa lafiya
Amshi : Asha ruwa

ii- Waqar Samodara


Bayarwa : Iya duba-duba
Amshi : Samodara
Bayarwa : Iya dubi ido na
Amshi : Samodara
Bayarwa : Jam –baki da gazal
Amshi : Samodara
Bayarwa : Baba ne ya saya min
Amshi : Samodara
Bayarwa : Ya ce in yi yanga
Amshi : Samodara
Bayarwa : Ya ce in yi yanga in yo rawa

110
Amshi : Samodara
Bayarwa : Iya duba-duba
Amshi : Samodara
Bayarwa : Iya dubi idona
Amshi : Samodara
Bayarwa : Jambaki da hoda
Amshi : Samodara
Bayarwa : Malam ya saya min
Amshi : Samodara
Bayarwa : Don in mishi yanga
Amshi : Samodara
Bayarwa : Don in mishi yanga in yo rawa
Amshi : Samodara

Bayarwa : Iya duba-duba


Amshi : Samodara
Bayarwa : Iya dubi idona
Amshi : Samodara
Bayarwa : Fankeke da gazal
Amshi : Samodara
Bayarwa : Baba ne ya saya min
Amshi : Samodara
Bayarwa : Ya ce in yi yanga
Amshi : Samodara
Bayarwa : Ya ce na yi yanga na yo rawa
Amshi : Samodara
Bayarwa : Iya duba –duba
Amshi : Samodara
Bayarwa : Iya dubi cikina
Amshi : Samodara
Bayarwa : Baba ne ya saya min
Amshi : Samodara
Bayarwa : Ya ce in yi yanga
Amshi : Samodara

111
Bayarwa : Ni ko yangar zan yi
Amshi : Samodara
Bayarwa : Ni ko yangar zan yi in wo rawa.
Amshi : Samodara
Bayarwa : Iya duba-duba
Amshi : Samodara
Bayarwa : Iya dubi zani na
Amshi : Samodara
Bayarwa : Malam ya saya min
Amshi : Samodara
Bayarwa : Ya ce in yi yanga
Amshi : Samodara
Bayarwa : Ni ko yangar zan yi
Amshi : Samodara
Bayarwa : Ai ai samo-samo, ai samodara!!!
Amshi : Samodara

iii- WASAN –KAMU :


Mai gudu ya gudu
Mara gudu ya tsaya
Ga tan an za ta zo
Mai idanun kare
Mai idon mujiya

MAGANGANUN FASAHA

a- Wasar Ka cinci-Ka cinci : Wasa ne tambayoyi da Amsoshi. Gas hi


kamar haka tsakanin Kandela da Ladi :

Kandela : Qulin qulifita?


Ladi : Gauta
Kandela : Shirim ba ci ba?
Ladi : Baba
Kandela :Taqanda ba Qashi ba

112
Ladi : Kanwa
Kandela : A fake a fake ba kya shigo ba xakin na uwa ki ne?
Ladi : Tufaniya
Kandela :Baba na zaka gemu na waje?
Ladi : Hayaqi
Kandela : faifai na xinkin marido?
Ladi : Zuma
Kandela : kuntukurin varin vas?
Ladi : kabewa
Kandela : Makaranta a dokar daji?
Ladi : Gidan tururuwa
Kandela : Tsohuwar gidammu ta takwarkwashe tana roqon Allah?
Ladi : Rumfa
Kandela :’yam matan gidammu kullum za su fita sai sun raba mana
goro?
Ladi : Kashin awaki
Kandela : kututture uku gagara xauri?
Ladi : Qwai
Kandela : shanuna dubu-dubu maxaurinsu xaya?
Ladi : Tsintsiya
Kandela : Iya ta zaga baba ya zaga bas u haxu ba?
Ladi : Kunne
Kandela : gaya xaya dama duniya?
Ladi : Farin wata
Kandela : kogi nay a kai ya kawo sai a gefe na ke wanka?
Ladi : Gwate
Kandela : kogi nay a kai ya kawo ba mai tsallake shi sai Bello mai
xan warki?
Ladi : Kwaxo
Kandela : Na je jeji, jeji na yi mini dariya?
Ladi : Auduga
Kandela : Rub-rub kushewar bayi?
Ladi : Qaiqayi

113
Kandela : Na wanke qwara tat as –tas na je makka da madinah na
dawo bas u bushe ba?
Ladi : Hancin kare
Kandela : Xan baka a bayan shuri?
Ladi : Farce
Kandela : Abu xil ya sa maigari kuka?
Ladi : Barkono
Kandela : Abu xil ya sauko da sarki daga kan doki?
Ladi : Fitsari
Kandela : Ke wannan shegiyar da ki ka tsefe kanki wa zai yi miki
kitso?
Ladi : Bishiya
Kandela : Daga nesa na jiyo muryar qawa ta?
Ladi : Ganga
Kandela : abu siriri abu zarara, abu tufkar Allah?
Ladi : Gashi
Tsumangiyar kan hanya fyaxe yaro, fyaxe babba?
Ladi : Yunwa
Kandela : Xillin bari xillin xillin na kallonki?
Ladi : Kaza bari tono, shaho na kallonki
Kandela : Yadda xillin ta kan yi xillin, haka ma xillin yak an yi
xillin?
Ladi : Yadda kaza ta kan yi qoyi, haka ma qoyi yak an yi kaza
Kandela : ’Yar baqa jakar mata?
Ladi : Kujera
Kandela : samarin gidammu masu fararen kayuwa?
Ladi : Tavare
Kandela : kurkucif kucif?
Ladi : Kwanciyar kare
Kandela : Gwamma lili da liyo?
Ladi : Gwamma noma da awu

114
b- WANI SALON KA-CIN-CI -KA-CIN-CI :

Alti : Da wuta nan?


Dije : Cici ta kashe
Alti : Wacce Cicin?
Dije : Cicin Barde
Alti : Wanne Barde?
Dije : Barde Lanqaya
Alti : Wanne Lanqaya?
Dije : Lanqaya kogi
Alti : Wanne kogi?
Dije : Kogin sharvo
Alti : Wanne Sharvo
Dije : Sharvo tuwo na
Alti : Wanne tuwon?
Dije : Tuwon aduwa
Alti : Wacce aduwar?
Dije : Aduwar wuya
Alti : Wacce wuyar?
Dije : Wuyar yaqi
Alti : Wanne yaqin?
Dije : Yaqin gwano
Alti : Wanne gwano?
Dije : Gwano ka-ci-ci
Alti : Wanne Cicin?
Dije : Cicin Udu
Alti : Wanne Udun?
Dije : Udun Baka
Alti : Wanne baka?
Dije : Bakace kuxa
Alti : Wacce kuxa?
Dije : Kuxar Nomau
Alti : Wanne Nomau?
Dije : Noma ciyawa

115
Alti : Wacce ciyawa?
Dije : Ciyawar rago
Alti : Wanne rago?
Dije : Ragon sarki
Alti : Wanne sarki?
Dije : Sarki Allah
Alti : Dagan nan fa?
Dije : Ta kashe baki

c- SANNU SANNU

Idi : sannu sannu


Habu : ina ciwo ne?
Idi : Da kana ciwo da ba ka hau gado ba?
Habu : In hau gado ni sarki ne?
Idi : Da kai sarki ne da ba’a kaxa maka tambari ba?
Habu : A kaxa mini tambari ni amale ne?
Idi : Da kai amale ne da ba’a aza maka kaya ba?
Habu : A aza mini kaya ni jaki ne?
Idi : Da kai jaki ne da ba’a doke ka ba?
Habu : A doke ni ni nama ne?
Idi : Da kai nama ne da ba’a yanka ka ba?
Habu : A yanka ni ni rago ne ?
Idi : Da kai rago ne da ba’a ci ka ba?
Habu : A ci ni ni kasuwa ne?
Idi : Da kai kasuwa ne da ba ka tashi ba?
Habu : In ta shi ni shirwa ne?
Idi : Da kai shirwa ne da ba ka zari xan tsako ba?
Habu : In zari xan tsako ni muzuru ne?
Idi : Da kai muzuru ne da ba ka shiga daji ba?
Habu : In shiga daji ni kwaxo ne?
Idi : Da kai kwaxo ne da ba ka shiga ruwa ba?
Habu : In shiga ruwa ni kifi ne?
Idi : Da kai kifi ne da ba ka yi santsin baya ba?

116
Habu : In yi santsin baya ni karkashi ne?
Idi : Da kai karkashi ne da ba’a tausaka ba?
Habu : A tausa ni ni bante ne?
Idi : Da kai bante ne da ba’a xaura ka ba?
Habu : A xaura ni ni aure ne?
Idi : Da kai aure ne da ba’a tara maka shedu ba?
Habu : A tara mini shedu ni mai shedar zur ne?
Idi : Da kai mai shedar zur ne da ba ka fita gari ba?
Habu : In fita gari ni xan hari ne?
Idi : Da kai xan hari ne da ba ka taimaki jama’ar musulmi ba?
Habu : In taimaki jama’ar musulmi ni Annabi ne?

WASA DA WAQOQIN DODO

Wasan Dodo wasa ne na al’adun gargajiya. Asalin masu yinsa maroqa


ne, da ke haxa roqonsu da tsafi da rawa, don xebe kewa ga mutane. Shi ya
sa da yawa-yawan waqoqinsu habaici ne da zambo ga mutane, cikin
mutanen ma musamman malamai da maroqa da maharba ke yi wa kallon
marowata. Da kuma yabon duk wani mai miqa musu abin duniya, kuma
mai qoqarin kyautata musu.

DODON MANA

Daga cikin dodannin da suka yi wasa a wannan gari, dodon da ya fi


shahara a cikinsu, har ma da qasar Lame da qasar Bauci baki xaya, babu
kamar ‘Dodon Mana’ Manawa asalinsu mutanen Kwandon-qaya ne, da
suka yi hijira suka dawo in da duwatsun Mana suke a yanzu, lokacin da
Kwandon Qaya ta watse. A shekarun baya can, sun shahara da tsafin da har
ya kai suka kafa qungiyar wasan dodo, da su da maqwabtansu Shawawa da
Kwankwanawa. Su mutanen Shau, asalinsu Bare-bari ne, da su ma gudun
hijira ya kawo su zama inda suke a yanzu. Su kuwa Kwankwanawa,
mutanen Kwankwan, taron wasu qabilu ne, kuma mazaunan wurin na asali.
Duk da cewa taron waxannan mutane ne ya kafa qungiyar wasan dodo,
kuma da ‘Dodon Mana’ aka fara, amma fa daga zamani zuwa wani zamani

117
an yi dodon Kwankwan’ da ‘Dodon Gyamawa’ amma sunan dodon ya fi
shahara da Dodon Mana. 135 Ba’a san lokacin da aka fara wasan dodo ba.
Amma dai an fara saninsa ne lokacin da qasa ta zauna lafiya aka daina
yaqe-yaqe. Mutanen da suke zaune bisa duwatsu suka fara saukowa qasa
suna kafa garuruwa da gonaki, a kan riqa wasanni don xebe kewa da
annashuwa.
Masu wasan Dodo suna da sunaye iri daban-daban, gwargwadon rawar
da kowa ke takawa a cikin wasa. Wasu kixa suke yi, wasu kuwa. Mai
shigar ‘Babban Dodo’ sunansa Gamji. Mai bi masa sai ‘Tauraro yaron
Maidawa’ shi ma yana shigar dodo, kuma yana rikixa siffa daban-daban.
Sai Jami shi ne mai xaukar zabirar tsafi. Akwai Najûme shi ne mai tiqa
rawa. Akwai Xan kacake, da Zabiya. Daga cikin ’yan baya –bayan nan da
suka shahara da wasan Dodo su ne ;

1- Magawata Mana
2- Babangida Wariyo
3- Audu Barun kudu
4- Audu Safe Mana
5- Saleh Mana
6- Garahunu –gama-danga
7- Ulu
8- Tauraro
9- Goro (mai goga qwarya)
10- Idi Unguwar Dogo
11- Muhammadu Unguwar Dogo
12- Sabo Mai garaya Gumau (Xan kacake)
13- Mato Makaxi Gwa (Baba mai kixa yayan Mato)
14- Hamza Magaji Danka
15- Xangazagin Mato Gwa
16- Kande Matar Audu Bauci
17- Tabawa Gwa

135
Na qarshensu shi ne Barun kudu
118
MISALAN WAQOQIN DODON MANA

Kamar yadda ka san al’adar maroqa duka, mai ba su abin hannunsa, shi ne
abin yabo a wajensu, to, haka ma Dodanni su ke. Dodon Mana ya bi wasu
mutane, saboda yawan kyautarsu gare shi.

1- Kamar yadda ya faxa yana mai yabon ga :

i- Sarkin Muhammadu Maidawa:

Sarkin kudu kyakkyawan yaro


Kyakkyawa abin cika aljannah

Da na fito a budurwa ne
wallahi da na aure ka

ii- Marka matar sarkin Maidawa, saboda yawan kyautarta gare


shi :

A faxa wa Muhammadu Maidawa


Shafa tozalinka na menene?

Ga farin ido kuma ga kyawu


Marka ta riga ta qwace ka.

iii- Tsohon malamin makaranta, M. Garba Xan’arewa, saboda


yawan kyautarsa gare shi :

Garba Xan’arewa ne siti-gemu


Ga malami mai koyarwa

Abin da kai mani na gode


Dodo ba zai ce komai ba.

119
iv- Hajiya Suma mai abincin sayarwa, saboda idan sun ci abinci
a wajenta, za su biya sai ta ce su bar kuxinsu :

Suma mai miyar kwana goma


Kwana xari ba jin yunwa

v- Ladi mai tuwon sayarwa

Ladi masu tuwon gado


Du wanda ya ci tuwon Ladi
Har jibi ba ya jin yunwa

vi- Wani arne mai suna Sabulu Xan Dabo,136 saboda yawan
alherinsa gare shi.

Zan gai da Sabulu Xan Dabo


Wutsiyar biri kere tukunya.137

vii- Sarkin fawan Shau

Zan gai da sarki baban Mato


Na Ta-awaki138 masu gwaten nama

viii- Yana yaba abotar wasu mutanen Rimi ta Zayam guda biyu:

Bala Gazin da Bala Roka


Qaryar zumunci ya qare.

136
Sabulu xan Dabo wani arne ne mai abin hannunsa, da Allah ya yi masa yawan kyauta.
Gidansa na can kusa da wata gada, kan tsohuwar hanyar da ta tashi daga Magama Gumau
ta nufi Rinjin Gaini, ana kiranta gadar Sabulu.
137
Abin nufi da wutsiyar biri, wato arne. Abin nufinsa da ‘kere tukunya’ mai alheri.
138
Ta –Awaki sunan matar sarkin fawan kenan.
120
ix- Yana yabon Baba Julde:
Baba Julde tsohon dakare
Shafa tozalinka na alfanu,
Na san ba ka bar mata ba

Quruciya ya zama gado


Wanda bai yi ba ba labari

Gaya mini wanda ya zage ka


In ja masa ’yar Aya kima

Kayau-kayau a cikin dawa


Dodon Gori ya buge shege
A kwarin kunya muka tsince shi

x- Yana yabon kansa:

A Bauci wa ya ci qwallo ne?


Zuwanmu Bauci taron durbar?

Dodon Muhammadu Maidawa


Zan gaida dodon Maidawa.

2- Wani sa’in kuma sukan yabi mutum ta hanyar tsoratar dashi Dodo,
bisa yadda ya ke ga al’ada. Kamar yadda ya yi yabo tare da
tsoratarwa ga :

i- Kilishi xiyar uban qasa sarkin kudu Maidawa:

Kilishi jikar Usmanu


Ba don kina tsoro na ba,
Ko kin qi da na aure ki.139
139
Bisa alama wanda ya faxi wannan a cikin masu shigar Dodon bashawi ne, saboda wasa
dake tsakaninsu da Wuntawa.
121
ii- Kwando farin malam :

Kwando farin malam


Ba don kana tsoro na ba
Da na riga na cinye ka

3- Kamar yadda suke yabon mai ba su abin hannunsa, to, haka kuma
suke yin zambo ga duk wani mai dunqule hannu. Kamar yadda ya
faxa yana mai zambo ga :

i- Duk wani mai rowa da cewa :


Da qulu a qeya kamar maye
Marowaci ya ci kayansa
Dodo ba zai ce komai ba
ii- Ga ’yan boko, wai su masu wayo ba sa kyauta :
Gari duka ’yam boko
Qaqa za’a qulla abin kirki
Saboda ba za su yi kyauta ba
To sai su je su ci kayansu
Dodo ba zai ce komai ba
iii- Barden Wunti Muhammadu zambo inda ya siffanta shi da
cewa mutum ne hali, amma kuma mai tsumulmula :

Qilu-qilu ya fi makanta
Kyautar sulen Barden Wunti
iv- Ga malamai, domin abokan wasansu ne :

Wani malamin ma mala ne,

122
Malan-kwari140 ma ya fi shi.
v- Mutanen Mana :

Ba za ni Mana da kwana ba
Shegu varayin takalma.

Na ce kunu suka ce, babu,


Ka-dawo sun ce, babu.
Shegu varayin takalma

vi- Makaxinsa Baba baban Mato:

Baba mai kixa Baban Mato


Me ya sa ka ke mana sherere141

4- To, wani sa’in kuma roqon suke bayyanawa a fili na irin abinda
suke nema. Ga misali:

i- Wata shekara an je Bauci an yi wasa, abinda Dodon Mana


ya yi ya qayatar da sarkin Bauci sosai. To, sai ya tambayi
sarkin kudu Salmanu cewa, me za mu yi musu ne, ko na ba
su mota ne? Sai sarkin kudu ya ce, waxannan mutanen
qauye, ai garinsu ma ko hanyar mota babu. Ka dai ba su
kyautar doki kawai. Sai wani ya kwashe duk suka yi ya
gayawa Dodo. Washe gari da aka fara wasa sai Dodo ya ke
cewa :

Ku gaya Mai kudu Salmanu


Dodo ba zai hau doki ba,
doki ba zai xau dodo ba.

ii- Wani salon roqo ga uban qasa sarkin kudu Salmanu :


140
Malan- kwari : Abin da maharba ke ratayawa a bayansu don zuba naman da suka kama.
141
Sherere wato shiririta.
123
Sarkin Kudu Sule Salmanu
Dodo yana kwaxayin nama
Sarkin kudu zan gaishe ka
Dodonka na kwaxayin nama
Har yanzu bai san komai ba.

iii- Ya tava yin irin wannan roqo msa ga sarkin kudu Maidawa:

Yanzu Bauci sai dai Maidawa


Sarkin Kudu zan gaisheka
Dodonka na kwaxayin nama
Bai samu ragon yanka ba.142

iv- Ya kuma tava yin irin wannan roqo ma ga sarkin Lame


Balarabe :

A Bauci wa ya ci qwallo ne?


Sarkin Lame jikan Goro.

Dodonka na kwaxayin nama


Bai samu ragon yanka ba.

v- Ga Jika’aya sarkin ruwan mashigin Bangwale :

Zan gai da kai Jika-Aya


Kar ka bar ni kogi zai ci ni

vi- Ya faxa ga Naduni mahauci:

Naduni bai wa gari nama

142
Nan da nan sai sarkin kudu ya sa aka kawo masa bunsuru, aka xaure a jikin turke aka ci
gaba wasa. Ana kixan ‘yanzu mutum, yanzu ba mutum ba.’ Can kawai sai aka ga bunsuru
ya faxi, aka yanka ko jini babu. Dodo ya tsotse jininsa.
124
Ka raba ka ba dodo na sa.
5- Wani sa’in kuma Dodo har wa’azi da nasiha ke fitowa daga
bakinsa, tamkar dai al’adar sauran maroqa. Kamar inda ya ke :

i- Nasiha ga faxin alheri ko yin shiru:

A duniya iya bakinka


In ka qi ungulu ta nuna ka.

ii- Tsoratarwa ga mai kwaikwayonsu :

Mai kwaikwayon dodon Kwano


Wata rana Ungulu ta nuna shi.143

iii- Tsoratarwa akan yin addini rabi da rabi :

Kowa ya sha giya ya ci mushe


Naman biri masa rago ne.

iv- Na siha akan ba’a halicce mu ba, sai don mu yi bauta:

Ba ka shan giya ba ka sallah


Zaman duniya na ka menene?

v- Nasiha akan ka xau rayuwa daidai da samunka:

Idan ruwanka bai isa wanka ba


Yi kwalliya ka wanke idanunka

vi- Yana yi wa kansa nasiha a qarshen rayuwarsa da cewa:

Dodo yana son ya yi sallah,


143
Dodo ya faxi wannan lokacin da Bala-bade ya ce, “la ga qafan dodo, ashe dodo mutum
ne.” Nan dodo ya riqa rimi zai cinye Bala-bade, sai da sarkin kudu ya shiga tsakani.
125
Wannan qaho ya dame shi.
vii- Har ma ya qare ya ce:

Dodo yana maganar Allah


Wataran karatu zai buxe.

Akan ce babu abin da ya ke dauwama cikin kayan duniya. Sai ga shi


abin mamaki, mutanen da a da ko sallah ba su kula da ita ba, balle sauran
ibadu, yau ’ya’yansu ba su da aiki sai karatu. Har su ne ma suke yi wa
wasu ganin wai ba musulmin kirki ne ba. Babban xan Dodon Mana yanzu
xan agaji ne a cikin izala. Ko hiran cewa iyayensu Dodanni ba su son a yi
yanzu.

MANYAN ZURIYOYIN DA SUKE ZAUNE CIKINTA

Abin nufi manyan zuriyoyinta su ne zuriyoyi mazaunan cikinta waxanda


suka fi yawan jama’a, ko masu kuxi da ’yan boko, ko muqamin sarauta ko
ma’aikatan gwamnati. Bincike ya nuna manyan zuriyyoyin da suka fikowa
yawa, kuma mutanenta suke zaune a cikin garin Gumau a yau (2021) su ne
:

1- Zuriyar gidan Muhammadu Jika (Wangarawa)


2- Zuriyar gidan Gaman
3- Zuriyar Alhaji Audu Safe
4- Zuriyar Kilaki
5- Zuriyar Rimadan Kaurare
6- Zuriyar falaliyawa
7- Zuriyar Rimadan Babban gida

MA’AUNIN DA AKA YI AMFANI DA SHI

i- Wajen yawa kada su kasa mutum xari biyar.


ii- Wajen boko shi ne shahadar Diploma, NCE da sama da haka.

126
iii- Wajen kuxi shi ne mallakar Naira miliyan xaya da sama da
haka.
iv- Wajen yawan ma’aikatan gwamnati ko kamfanoni da sauransu
samun mutum
v- Wajen masu sarauta waxanda su ka mallaki saurautu biyar
zuwa abin da ya fi haka.

ZURIYAR DA TA FI YAWA

Zuriyar da ta fi kowacce yawa a cikin garin Gumau a yau (2021), ita ce


zuriyar gidan M. Muhammadu Jika, wato zuriyar Wangarawa. Yawansu ya
fi mutum dubu.

ZURIYAR DA TA FI YAWAN MASU KUXI

Zuriyar da ta fi kowacce yawan masu kuxi a yau (2021) a cikin garin


Gumau ita ce zuriyar gidan M. Muhammadu Jika, wato zuriyar
Wangarawa. Yawan waxanda suka mallaki naira miliyan a cikinsu ya fi
mutum ashirin.

ZURIYAR DA TA FI YAWAN ’YAN BOKO

Zuriyar da ta fi kowacce yawan masu karatun boko a yau (2021) a cikin


garin Gumau ita ce zuriyar gidan M. Muhammadu Jika, wato zuriyar
Wangarawa. Yawan waxanda suka mallaki shahadar Diploma, NCE da
digiri a cikinsu sun fi mutum sittin.

ZURIYYAR DA TA FI YAWAN MA’AIKATAN GWAMNATI

ZURIYYAR DA TA FI YAWAN MASU SARAUTA

Zuriyar da ta fi kowacce yawan masu sarauta a yau (2021) a cikin garin


Gumau zuriyyar Kilaki. Yawan masu sarautar masarautar Wunti a cikinsu
mutum goma :

127
1- Alhaji Muhammadu - Dallatu
2- Musa Damba - Xan ruwata
3- Nasiru Adamu – Baraya
4- Ahmadu Adamu – Dujuma
5- Lawal Sabana – Barden Gabas
6- Xahiru Muhammed _ Barade
7- Basiru Adamu – Ubandawaki
8- Muhammadu Inuwa – Kaigama
9- Buhari Adamu – Xanjika
10- Bello Adamu - Sallama

ZURIYAR DA TA FI DAXEWA A GARIN

1- Zuriyar rimadan Kaurare

TARIHIN MANYAN ZURIYOYIN CIKINTA

ASALIN WANGARAWA

Asalin Wangarawa fulanin qasar Malle (Mali) ne, waxanda suka shahara
da kasuwancin zinariya a tsohuwar daular Ghana. Har wayau kuma ana
kiransu ‘Wăkŏre.’ ’Yan’uwansu da suka fito daga tsatso xaya ana kiransu
‘Mălinke,’ kuma dukkaninsu biyun sun fito ne daga tsatson ‘Soninke.’144Su
Malinke su ke riqe da sarautar qasar, domin da ma su maharba ne jarumai,
kuma mayaqa a fagen fama. Su kuwa Wăkŏre (Wangarawa) sun shahara da
yaxa ilimin addinin musulunci, da alqalanci tare da kasuwanci, musamman
ma na zinariya, a tsohuwar daular Ghana, don qasarsu qasar zinariya ce.
Suna xaukar kayan kasuwanci daga cikin garuruwansu zuwa sassan duniya
daban-daban. Daga can kuma sai su sayo hajjar qasar su dawo da ita

144
Soninke : Su ne waxanda suka kafa tsohuwar daular Ghana, AD 750-1240, sun karvi
musulunci daga ’yan kasuwa Al murabixun tun wajen AD 1066 su ake cewa Sarawulli,
harshensu shi ne babban harshen da ake Magana dashi a qasar Mali. Har wayau akwai
masu magana dashi a qasashen : Senegal, Mauritaniya, Guinea, Guinea –bissau, Gambiya
da Kwadebuwa.
128
qasarsu. Daga cikin manyan garuruwansu akwai ; Tadmakka, 145 Kumbi
saleh,146 Tambutu da sauransu, kamar yadda Al’idrisi malamin tarihi ya
bayyana.

SHEDAR MALAMAN TARIHI


KAN QWAREWARSU A KASUWANCI

Ga abin da matafiyin qasar Turai Mungo Park ya ke cewa game da su,


sadda ya ziyarci qasarsu, a qarshen qarni na takwas miladiyya : “Su
Sarawulli (Wangarawa), babban cinikinsu shi ne fatauci. Suna da ilimi mai
yawa na sha’anin saye da sayarwa. Suna cinikin bayi da zinariya da
Faransai, suna kuma sayarwa da Ingilishi da ke zaune a Gambiya bayi da
hauren giwa. An ce su masu gaskiya ne wajen ciniki, ba rikici, ba kuma cin
kura. Im mutum ya dawo daga fatauci, ’yan’uwansa da abokansa sukan
taru su ga irin ribar da ya ciwo. In an ga ya zo da dukiya, an san ya iya
ciniki kenan, sai a maishe shi mutumin kirki, a ba shi girma. Amma in
kasuwa ta bashe shi, bai komo gida da kome ba, sai zagi da zambo. Sukan
ce wai Wane bai komo da kome ba sai gashin kansa!”147

ZUWAN MALAMAN WANGARAWA QASAR HAUSA

A cikin yawace-yawacen kasuwancinsu da yaxa addinin musulunci da suke


yi , malaman Wangarawa su wajen mutum xari da sittin, sun zo qasar
Hausa, da isowarsu sai suka rabu biyu, wasu suka nufi Gobir, wasu kuma a
qarqashin shugabancin Abdurrahman Zaiti suka nufi Kano, zuwansu a
zamanin sarkin Kano Yaji (1349-1385). Suka zo da zancen musulunci.
Babbansu Abdurrahman Zaiti da kuma Yakubu. Da Mandawari da Famure
da Bilqasim, Kanaji da Dukure. Da Sheshe da Kebe da Mutuku da limamin

145
Wani barikin ma’adanai day a juye babbar cibiyar kasuwancin zinariya a tsohuwar
daular Ghana. Yanzu yana gundumar Kidal ta qasar Mali.
146
Gari ne a kudu maso gabashin qasar Murtaniya. ita ce babban birnin tsohuwar daular
Ghana. Hedkwatar cinikin zinariya tun daga qarni na takwas har zuwa qarni na goma sha
uku miladiyyah.
147
Nuhu Bamalli (Mungo Park Mabuxin Kwara) : Shafi 21
129
jujin’yan Labu, uban sarkin fawa. Da Gurdumasa da Auta, Lawal da
limamin Maxatai, da waxansunsu na cikon arba’in. yayin da suka zo suka
umarci sarki da sallah, sai ya yi. Suka sanya Gurdumasa limaminsa. Lawal
ladaninsa. Auta kuma mai yankan dukkan naman da ake ci. Mandawari
limamin gari. Abdurrahman Zaiti kuma shi ne alqalinsu. Sarki ya umarci
dukkan kanawa su yi sallah, kuma suka yi.

FANTSAMARSU DAGA KANO ZUWA SASSAN HAUSA

Dalilin fantsamar Wangarawa daga Kano zuwa wasu garuruwa shi ne


Basasar Kano. Me ya sanar da kai Basasar Kano? Wani al’amari wanda
Allah (SWT) ya qadarta babu makawa sai ya faru. Ga sababinta “Tun kafin
sarkin Kano Bello148 ya rasu, sarkin musulmi Abdurrahman149 ya yi
alqawari zai bai wa Galadiman Kano Tukur, xan sarkin Kano Bello,
sarautar Kano bayan rasuwar mahaifinsa. Dalili kuwa domin a wani yaqi
da aka yi tsakanin sarkin musulmi da Argungu, Galadima Tukur ya nuna
jarunta, wacce ta hana Argungu samun nasara a kan Sakkwato. Galadima
Tukur ya kora mutan Argungu har qofan garinsu, yana cewa sarkin
musulmi, “Zauna daidai, a gidanka ka ke.” Argungu suka sake kawo hari,
ya sake dafar qeyarsu, said a ya mai dasu. To, wannan jaruntaka ita ta
qayatar da sarkin musulmi, har y ace Tukur shine sarkin yaqinsa, ya kawo
takobi da garkuwa ya bas hi. Wannan shine dalilin day a sa ake yi wa duk
sarkin Kano kirari, ana cewa, “sarkin yaqin sarkin musulmi.” Shi wannan
mashin har yanzu shi Kilishi ke riqewa in sarki ya yi hawa a Kano.
To, sadda sarkin Kano Bello ya ya kamu da ciwon ajali, wazirin
Sakkwato Mu’azu ya zo Kano, bayan ’yan kwanaki sai sarkin Kano Bello
ya rasu. Waziri Mu’azu ya koma da takardar naxa Tukur kamar yadda
sarkin musulmi ya yi alqawari. Sai waxansu manyan Hakimai irinsu
madaki, suka ce dashi, “Wannan naxi da sarkin musulmi ya yi bai dace ba,

148
Sarkin Kano Bello (AD 1883- 1892), shi ne sarkin Kano na shida a cikin jerin Fulani,
kuma na arba’in da bakwai a cikin jerin sarakunan Kano.
149
Sarkin musulmi Abdurrahman xan Abubakar Atiku xan Muhammad Bello (AD 1891-
1902), shi ne sarkin musulmi na goma sha xaya. Hula biyu ke tsakaninsa da Shehu xan
Hodiyo mujaddadi.
130
domin Galadima Yusufu150 shi ne jama’a ke so, don ya fi dacewa da
sarauta. Suka ce ya kamata waziri ya maid a waiwaye gun sarkin musulmi.
Waziri yace shi kam ba zai kasa zartar da umarnin sarkin musulmi ba,
amma dai zai sheda masa wannan magana. Sai ya aike aka shaidawa sarkin
musulmi cewa akwai haxari wajen wannan shiri. Sarkin musulmi ya maid a
jawabin cewa ko me zai faru shi ba zai warware wannan abu da ya yi ba.
Don haka sai waxansu manyan mutane suka qi zuwa masallaci inda ake
naxa sarakuna. Suka cewa waziri sai dai ya naxa sarautar a masaukinsa,
wato sabon gida Tukur ya shiga gidan sarki da ’yan mutane tsiraru. Da
Yusufu yayi mubaya’a ya fito, sai ’yan sarki suka biyo bayansa zuwa
gidansa, in da suka tsai da shawara a kan su bar garin xungum, don kada
kada sarki ya qarasa su. Sai suka fita, su da gayyarsu duka zuwa Dawakin
kudu, daga nan sai Takai. Ya sauka a gidan sarki, ya riqa aikewa dagatai
takardun kira, duk dagacin day a yi taurin kai sai a tura mayaqa su ci garin.
Jama’ah masu yawa suka goyi bayansa qarfi da yaji. Suka tara dawaki da
kaya, suka ci garuruwa da yawa. A can birnin Kano kuma, sarki Tukur da
ya ke ya san kwanan was an, sai ya shiga shiri.
Yusufawa suka gayyaci Gumalawa, Ningawa da mutanen Misau, suka
kawowa Kano hari, sarkin Gaya Dabo ya maid a su. Suka koma Takai suka
yi wata uku suna shiri. Sai suka tsai da shawarar su fara cin Gaya tukuna
sannnan su nufo Kano. Su kai yaqi mai tsanani, suka ci garin, sarkin Gaya
ya gudu Kano. To, sadda suka ci Gaya, Yusufu bas hi da lafiya, day a sami
sauqi sai y ace a isa Kano, da suka iso Garko sai ciwonsa ya tsananta. Sai
ya tara manyan bayin sarki da ’ya’yan sarki ya yi musu wasiyya y ace su bi
Malam Babba, wato Alu,151 idan bah aka ba Sakkwatawa ba za su qyale
sub a, amma saboda darajar Alu, za su yafe su. Washegari sai Yusufu ya
rasu. Da rasuwar Yusufu sai suka cika wasiyyar day a bar musu, suka naxa
Alu, suka riqa aikewa’ya’yan sarki. Kowane xan sarki idan ya zo ya yi
ta’aziyyar Yusufu sai ya zo wajen Alu yayi mubaya’a. Ga takubba sun

150
Xan sarkin Kano Abdullahi Maikano, wan sarkin Kano Bello.
151
Sarkin Kano Alu, sarki na bakwai cikin jerin sarakunan Fulani. Kuma sarki na arba’in
da tara cikin jerin sarakunan Kano. Yayi sarauta daga (1894- 1903), shi Jikan sarkin
musulmi na huxu wato Aliyyu Babba ne, wanda yayi sarautar sarkin musulmi a shekarun
(AD 1842- 1859)
131
zazzare, ko wani zai yi taurin kai, su sareshi. Da qare wannan mubaya’a,
sai Alu ya tara su ya gargaxesu das u haxa kai, don kada Tukurawa su
rinjayesu. Kuma ya yi musu alqawarin zai cika shirin Yusufu na yi musu
sarautu idan an ci Kano. Sai suka taso daga Takai, suka yi zango a
Dawakin kudu. Labari kuma ya iso kunnen sarki Tukur, shi kuma ya yi wa
jama’arsa gargaxin kada su yarda Yusufawa su karyasu. To, a wannan
karawa dai Alu ya ci Kano, ya kuma cika duk alqawarin naxa sarautun da
Yusufa yayi niyyar naxawa idan an ci Kano. Shi kuwa sarki Tukur, da dai
ya fita daga Kano, bai zame ba sai Kamri, cikin qasar Katsina tare da
hakimansa. Jama’arsa kuwa ta fashe, wasu suka yi gabas, wasu suka yi
yamma. Ana cikin haka sai sarkin musulmi ya umarci sarakunan Katsina,
Kazaure da Zazzau ya ce su taimaki Tukur ya koma kan gadonsa. Sai suka
ce ba za su shiga wannan zarafi na 'yan'uba ba. Sai wazirin Sakkwato ya
aike wa Tukur cewa ya taso ya zo Tafashiya. Duk in da Tukur ya kwana
sai 'yan rahoton Alu su kai masa labari. A qarshe an kara a Tafashiya,
kuma a wannan karawar aka kash sarki Tukur. Jama'ar Tukur ta watse, ta
nufi Sakkwato, in da daga qarshe aka haxo su da waziri da takardar sarkin
musulmi cewa a bas u gidajensu. Wannan ita ce alamar sarkin musulmi ya
amince da naxin Alu. To, wannan Basasar ita ce sanadiyyar watsuwar
Wangarawa cikin garuruwan Hausa, qasar Katsina da qasashen Zazzau da
Sakkwato, daga cikin jama'ar Tukur. Wasu kuma suka yi zamansu a Takai,
Dawakin kudu da Ningi daga cikin jama'ar Yusufu. To, daga cikin
waxanda suka zauna Takai aka samu Malam Muhammadu Jika, attajirin
bayi, kuma malami mai yaxa addinin musulunci. Ya kan sari bayi yana
fataucinsu yak an bi ta qasar kuza zuwa qasar Bauci. Suna bi ta tsohuwar
hanyan nan mai tarihi wacce ta taso daga Takai ta bi ta Sumaila, ta gangaro
Ya-da-gungume, sai su ci zango a Sabon garin Tulu. Daga nan idan suka
tashi sais u kuma cin zango a Wundi, sai Riruwan Dalma, sai waxanda
suka nufi Bauci su ci zango a Badiko. Waxanda suka nufi qasar kuza
kuma, daga Riruwan Dalma, sai su ci zango Maciya, kusa da Zallaki, sai
Narkuta sai Jos. Kuma duk inda suka saba cin zango a waxannan
garuruwa da muka lasafta, su kan kafa unguwa da suke raxa mata suna
Unguwar Shaura.

132
ZUWAN MUHAMMADU JIKA BAWANGARE RIRUWAI
DA DALILIN TSAYUWARSA

Mutanen Riruwai sun gaya wa sarkinsu cewa zai yi kyau ya rarrashi


wannan mutumin ya yi zamansa a nan. Domin mai arziqi ne, kuma mai
kyauta da ake buqatar irinsu ga ci gaban gari. Kuma sarkin ya fahimce su,
ya nuna masa wuri shararre, y ace, “Ga wurin zama nan yalwatacce, yadda
zai ishe ka kai da jama’arka. Mu dai burinmu ka yi zamanka a nan.” Sai ya
koma gida gida ya taho da ragowar iyalinsa, ya yi zamansa nan,
arziqinsaya yi ta qaruwa, kuma ya yi ta hayayyafa, har zuriyarsa suka
yawaita, kuma suka gaje shi a wajen arziqi da ilimi. Kuma da yawansu
suka dawo Gumau, ta yadda tarihin Gumau ba zai cika ba idan ba’a
ambace su ba. Wangarawa jama’ar Malam Idi Sun taso daga Riruwai zuwa
Gumau a shekarar 1948. Muhammadu Jika yana da ’ya’ya :

1- Umaru (Baban Ayashe)


2- Idrisu
3- Musa
4- Ramatu
5- Umaru
6- Bitan

Waxannan’ya’ya da’ya’yansu sun kai mutum dubu a cikin Gumau.

ZURIYAR KATSINAWA NA GIDAN GAMAN

ZURIYAR ZAGE-ZAGI TA MALAM SIDI

Asalinsa mutumin Ancau ta qasar Zazzau ne sunansa Sidi. Mai arziqi


ne, wanda a kan ce ‘ko a kwara ya sai da ruwa’ Komai ya saya, za’a saya a
wajensa. Yana fatauci daga wannan gari zuwa wancan, san nan yana
cinikin bayi, a kawo bawa ya saya, a zo nema ya sayar. To, ka san an ce
’yawan mutane shi ne kasuwa’ sai ya ji labarin yadda jama’a ke tururuwan
zuwa Riruwan Kano, saboda kuza da ake samu a garin, da harkokin

133
kasuwanci da ke akwai a garin a san nan. Mutanen garin sun iya narkar da
kuza su yi dalma da ita, kuma daga nisan duniya ana zuwa saya. Tun yana
zuwa ya dawo, har sai ya tare a garin, ya yi gidansa a cikinta, don ya ga
wurin kasuwanci. Arziqinsa ya yi ta qara bunqasa, har aka ji labarinsa
cikin birni. To, ran nan sai sarkin Kano (Alu Mai Sango (1894-1903)152 ya
aikowa hakimin Riruwai cewa, mun ji labari akwai babban attajiri a
qasarka da ya bunqasa. Ina sanar da kai cewa, ran cikar kwana uku, zan
turo dogarai na su yi wa gidansa wasoso. Abin da ake cewa wasoso shi ne
mutane da yawa kowa ya kawo wa kayanka sura, su tsiyata ka cikin dare
guda. To, sadda aka zo wa da hakimi wannan labari, akwai wani bafade
yana kwance gefe guda yana ji. Can sai miqe ya xan fita kamar mai nufin
zagawa. Sai ya rankaya, sai gidan Sidi attajiri. Ya ce masa kaji-kaji abin da
aka aikowa hakimi, saboda haka ka san ta yi. Shi kenan sai attajiri nan ya
kawo wani abin hasafi ya ba shi, kuma ya yi masa godiya bisa wannan
karimci da ya nuna masa da kuma soyayya. Nan da nan sai ya sa aka ta yi
ta xaure kaya, ana yi wa jakuna da raquma labtu. Kwana uku ba su cika ba,
face sai da ya bar garin. Ya nufo wajen kudu don dai ya fita daga mulkin
sarkin Kano cikin sauri. Sai ya zauna a wani gari da ake kira Jûra, (Juran
masaqa). A nan ya yi rayuwarsa tare da iyalansa, har ya koma ga Allah.
To, bayan rasuwarsa, sai babban xansa Aliyyu, ana masa laqabi da Ali
Gero, ya ci gaba da jan ragamar kasuwancin uban, yana sarin bayi, yana
sayarwa. To, cikin yawace-yawacen kasuwancinsa, har ya zo Riruwai.
Saboda a san nan karabka ce, kuma zango ce, matattarar fatake da ’yan
kasuwa. Kuma gari ne cike da danginsa na wajen uwa. Sai ya ga zai fi kyau
ya taso daga inda ya ke zuwa cikinta. Saboda haka sai ya taso daga Jura, ya
komo Ririwai. Sadda zai taso, sai ya xebo qaninsa li’abi da ake kira
Tanimu, uban Alhaji Maikuxi Yaro, da qanwarsa li’abiya da ake ce mata
Barakah, uwar Hajiya Darki, ya zo da su Ririwai, domin a san nan uwar
kowannensu ta rasu. A Ririwai ya haifi Sidi da Jummai da Hajo,153 su duka

152
Sarkin Kano na hamsin. Aliyyu xan Abdullahi Dabo. Shi ne wanda ya ci sarauta bayan
an yi yaqin basasa mai tsanani a Kano, sai ya sa aka yi ta shiga gidan mutane ana wasoso,
kuma ya riqa kama duk wanda ya goyi bayan sarki Tukur.
153
Ta rasu tun tana qarama, ko aure bat a yi ba.
134
cikinsu xaya, sunan mahaifiya ta su Maimunatu. Jubo,154 Yargida (Binta),
Lami155 da Shehu su ma cikinsu xaya, sunan mahaifiya ta su Hama. San
nan Sule,156 Laraba,157 Inuwa,158 Babayo159 da Abdullahi su ma cikinsu
xaya, sunan mahaifiya ta su Adama. Waxannan ’ya’ya da ’ya’yan su sun
kai mutum xari shida a cikin garin Gumau.

ZURIYAR FALALIYAWA
JAMA’AR ALHAJI SABO

Asalinsu Kanawa ne, mutanen Falali. Babbar sana’arsu tajirci, sai karatu
da karantarwa. Kasancewarsu masu arziqi, sai sarakunan qasarsu suka
dame su da maganar harajin attajirai. Sai suka yi hijira suka koma
qarqashin mulkin sarkin Ningi. A san nan Ningi suna yaqi da duk
maqwabtansu Kano, Bauci, Zazzau da Shira. Saboda haka duk wanda ya
bar qasar Kano idan yana son ya samu mafakar siyasa, sai ya koma Ningi.
To, sai suka ga kuma ba za su iya zama cikin qasar ba, saboda yawan
yaqinsu ga jama’ar musulmi. Sai suka biyo tsohuwar hanyar fataken nan,
mai tarihi, suka shigo qasar Bauci. Suka zauna a unguwar Shaura a Sabon
garin Tulu, wasu suka tsaya nan. Kana wasu suka iso Wundi suka kafa
unguwa mai irin wancan suna, wasu suka tsaya nan. Wasu suka wuce zuwa
tafi Liman Katagum, suka zauna can. San nan Yusufu xan malam Xahiru
da jama’a ta sa, suka zauna a Badikko. Malam Yusufu xan malam Xahiru
na gidan Madakin Falali yana da ’ya’ya kamar haka :

1- Adama (Baba Ada)


2- Usman (Babandãdã)
3- Jibrin (Na Antau)
4- Yakubu (Babale)

154
Bai ko yi auren fari ba, yana saurayi ya rasu.
155
Uwar Saleh wan Makanike
156
Uban Alhaji Talle
157
Uwar Zubairu, uban Mamuda Kuskus
158
Uban Xankaka, Isyaku Ustaz, da su M. Salmanu da sauransu.
159
Kurma ne, ya rasu bai yi ko aure ba.
135
5- Adamu (Sabo)
6- Idris (Wangida)
7- Mu’azu
8- Hasana
9- Nuhu

A shekarar 1949 Alhaji Sabo ya dawo da wasunsu Gumau. Waxannan


’ya’ya da ’ya’yansu sun kai mutum xari biyar a cikin garin Gumau.

ZURIYAR BARE-BARI TA KILAKI

Asalinsa babarbare ne, mazaunin qasar Guddiri. Kuma xan kasuwa ne


da ke tajirci daga wannan wuri zuwa wancan. To, sai ya ji labarin barikin
Fakuru da yadda irin hajjarsa ke tafiya a wajen. Tun yana zuwa ya koma ya
dawo, har sai Allah ya yi zamansa a wajen, a dalilin kuxi da aka riqe masa.
Dalilin yi masa laqabi da kilaki, shi mutum ne mai son ado da kwalliya.
To, sai manya na cewa, “yaro da son ado sai kace kilaki?” to, sai ana wane
kilaki. Kamar wasa kuma sai abin ya bi shi. Ya zauna a Lame shekaru
masu yawa, har ma ya xauko iyalansa daga can garinsu ya dawo da su
Lame, kuma a cikinta ya haifi wasu, kuma a cikinta ya rasu. Kwanci-tashi
bayan turawa sun taso da sarkin yaqi daga Lame zuwa Gumau. Sai ’ya’yan
suka biyo shi suka dawo Gumau. Daga cikinsu akwai Adamu, Muhamman,
Baban Gwaggo, Aliyyu (Sabana), Kande, Musa, Lami, Xalhatu, Atu,
Talata mato, Goma, Balange, Hasana, Husaina, Gambo, Shu’aibu, Yunusa,
Gwamma, Ladi, Gyatun, Ayya da Jummai. Waxannan ’ya’ya da ’ya’yansu
sun kai mutum xari shida a cikin garin Gumau.

ZURIYAR RIMADAN KAURARE

ZURIYAR RIMADAN BABBAN GIDA

WANDA YA FARA

1- Wanda ya fara dawowa Gumau daga Riruwai shi ne Alhaji Saidu.

136
2- Wanda ya fara buga kwanon rufi a gidansa shi ne Alhaji Saidu.
Kafin bugawarsa ko gine-ginen gwamnati guda uku ne kaxai masu
bugun kwano ; bariki (rehawus), gidan jojin rafi, ofishin huji.
3- Wanda ya fara buxe gidan burodi M. Dadaye uban Soni Rock
4- Wanda ya fara kantin provision Xanjuma uban Ado Sparker
5- Wanda ya fara sana’ar xaukan hoto M. Tsoho (MT Gumau)
6- Wanda ya fara zuwa hajji a qafa shi ne Alhaji Mato Ririwai
7- Wacce ta fara zuwa hajji a mota itace Hajiya Maryamu ’Yar
magwalle, matar M. Hasan Mai gishiri
8- Wanda ya fara zuwa hajji a jirgi shi ne Alhaji Saidu.
9- Wanda ya fara sayan mashin ‘Super zaki’ shi ne Isyaku Fiqe.
10- Wanda ya fara sayan motar neman kuxi a Gumau shi ne Alhaji
Yunusa da Alhaji Saidu, da suka haxa kuxi suka saya.
11- Wanda ya fara sayen mota tirela shi ne Alhaji Na’iya Gumau
12- Wanda ya fara iya tuqa mota shi ne Ali Chambe. Bayan shi sai
Shamakin Wunti
13- Macen farko da ta fara sayen mota ita ce Hajiya Safiyyah matar
Alhaji Sai’idu.
14- Wanda uwarsa ta fara saya masa mota yana yaro qarami shi ne
Alhaji Ibrahim Sa’idu (Jirgi).
15- Wanda ubansa ya fara saya masa mota yana yaro qarami shi ne
Alhaji Yahuza Alhasan.
16- Wacce ta fara kai ’yarta aikin hajji ita ce Hajiya Safiyya, matar
Alhaji Sa’idu.
17- Wacce uwarta ta fara kai ta aikin hajji ita ce Hajiya Alti Sa’idu
matar Muhammadu Mai gaskiya.
18- Wanda aka fara fara ajiye ‘Sef’ na ajiyan kuxi a gidansa shi ne
Alhaji Saidu.
19- Wanda aka fara ganin rediyo a wajensa shi ne sarkin yaqi Usmanu
Babale. En’e ce ta saya masa.
20- Wanda ya fara sayen rediyo mai waini irin na agogo shi ne Alhaji
Saidu.
21- Wanda ya fara sayen rediyo mai batir shi ne Alhaji Jibrin Kaita.

137
22- Wanda ya fara zuwa da rediyo rikoda mai kaset shi ne Malam
Ladan Gungura, malamin gona.
23- Wanda ya fara sayen garmaho mai waini shi ne Alhaji Saidu
24- Wanda ya fara yin digiri Ambasada AG Abdullahi
25- Wanda ya fara yin digiri a xaliban makarantar firamaren Unguwar
Waziri shi ne Xalladi Yakubu Umar.
26- Wanda ya fara zamowa kansila shi ne Alhaji Audu Safe
27- Wanda ya fara zamowa xan majalisar jiha shi ne Audu Saleh daga
jam’iyyar APP (All People’s Party) (1999-2003).
28- Wanda ya fara zamowa xan majalisar dattijai shi ne Sanata Lawal
Yahaya Gumau daga jam’iyyar APC (All People’s Congress) daga
2018-2023.
29- Wanda ya fara cin musabaqar Alqur’ani na qasa na qungiyar Izala
mai Hedkwata a jos shi ne M. Yakubu Idris
30- Wacce ta fara cin musabaqar Alqur’ani na qasa na qungiyar Izala
mai Hedkwata a jos ita ce Khadijatu Muhammad
31- Wanda ya fara yin gonar kaji shi ne Alhaji Voyi Tabako (Madakin
Wunti).
32- Wanda ya fara yin gidan gyaran kuza shi ne Alhaji Yahaya
Nagadanya.
33- Wanda ya fara yin gidan bulo shi ne Alhaji Sale Sa’idu (Nasco).
34- Wanda ya fara sana’ar gyaran keke shi ne Alhaji Badamasi.160
35- Wanda ya fa sayen Bidiyo shi ne Alhaji Maikuxi Gumau.
36- Wanda ya fara gina shago a kasuwar Gumau shi ne Alhaji Audu
Safe.
37- Wanda ya fara gina bene shi ne Alhaji Maikuxi Gumau
38- Wanda ya fara gina shaguna benaye shi ne Alhaji Mamman Kilaki.
39- Wanda ya fara gina makarantar boko ta karan-kansa shi ne
Abubakar Sadiq Abdullahi (Baba Habu), sunan makarantar
‘Abdullahi Memorial Academy’

160
Kafin farawarsa, masu gyarar keke daga wasu garuruwa suke zuwa, kuma sai ran
kasuwa, idan ta watse kowa ya koma garinsa. Kamar M. Sale daga Tashar M. Sale, Burai
Unguwar Kanya, M. Bala da Gawata daga Laru, M. Bala Wonu da M. Yahaya Pingel.
138
40- Makarantar Islamiyya mallakar mutum guda da aka fara ginawa ita
ce ta Alhaji Ibrahim Sabo mai suna ‘Tsangayar Ma’ahad Gwani
Idrisu for Qur’an & Qur’anic Sciences’ da ke Unguwar malamai
(Dogon-Layi).
41- Makarantar haxakar al’umma da aka fara kafawa ita ce ‘Islamic
Secondary School Gumau’161
42- Makarantar Islamiyya ta qungiya da aka fara yi ita ce ta Izala da ke
qofar M. Haruna limamin izala.
43- Wanda ya fara sayen injin niqa shi ne sarkin Ririwai Hudu.
44- Wanda ya fara sana’ar facin taya mota shi ne Isa Maski
45- Wanda ya fara sana’ar sai da fetur a duro shi ne Alhaji Badamasi
46- Wanda ya fara kafa injin tsaga katako shi ne Alhaji Musa Laska.
47- Wanda ya fara sana’ar kamisho shi ne sarkin Tasha Galaru.
48- Wanda ya fara sana’ar sai da siminti shi ne Alhaji Musa Laska
49- Wanda ya fara gina gidan mai shi ne Alhaji Musa Laska
50- Wanda ya fara sana’ar sai da lemon kwalba shi ne Alhaji Musa
Laska.
51- Wanda ya fara sana’ar cajin baturan mota shi ne Alhaji Musa Laska
52- Wanda ya fara sana’ar cajin baturan wayar salula shi ne Adamu
Musa Bawa.
53- Wanda ya fara buxe kantin sai da wayoyin salula shi ne Alhaji Ado
Kabiru.
54- Wanda ya fara aikin xaura Satellite da gyaranta shi ne tafidan
Wunti Abubakar Gixaxo.
55- Wanda ya fara sai da kayan wutar Solar shi ne Alhaji Ado Kabiru
56- Wanda ya fara sana’ar latirisha shi ne Imran Sanin sarkin Riruwai
57- Wanda ya fara sana’ar naxa ‘Coil’ shi ne Abdullahi Sabo
(Tambaya).
58- Wanda ya fara sana’ar sayen firji shi ne Alhaji Musa Laska
59- Wanda ya fara sayen injin Photocopier machine’ shi ne Alhaji Bala
(Galadiman Wunti)

161
Amma an kashe ta a 2012, a dalilin tarwatsa malamanta da baturen ilimi ya yi, domin
dama yawancin malaman ’yan ‘secondement’ ne.
139
60- Wanda ya fara sana’ar sai da kayan gini shi ne Alhaji Salisu
Kasuwa
61- Wanda ya fara sana’ar sai da bututun wayarin xin ruwa shi ne
Alhaji Ibrahim Sabo.
62- Wanda ya fara sana’ar wallafar littattafai shi ne Alhaji Ibrahim
Sabo.
63- Wanda ya fara sayen keken ‘Zigzag’ shi ne Xanturai.
64- Wanda ya fara xinkin ‘Barnina’ shi ne Alhaji Sani Xanhasan.
65- Wanda ya fara sana’ar Wayarin shi ne Abdullahi Sabo (Tambaya).
66- Wanda ya fara yin bautar qasa (NYSC) Alhaji Hasan Mai dabino
1973, a Inugu.
67- Wanda ya fara zama farfesa shi ne Haruna Yahaya.
68- Wacce ta fara digiri cikin mata ita ce Saudatu Muhammed (Islamic
Studies).
69- Wanda ya fara zama likitan mutane shi ne Dakta Shagari Abdullahi
70- Wanda aka fara yi masa wayarin xin wuta a gidansa shi ne Alhaji
Sa’idu.
71- Wanda ya fara zama likitan dabbobi (Veterenery) shi ne Dakta
Muhammed Abdullahi.
72- Wanda ya fara auren ’yan mata biyu, aka kawo masa su a rana xaya
shi ne Abubakar Sadiq Abdullahi (Baba Habu). Ya auri Nauwaratu
Abdullahi Darazo da Aminan Alhaji Sani Xanhasan.
73- Wanda ya fara sallar qablu shi ne M. Abba mai littattafai.162
74- Wanda ya fara waldar lantarki shi ne Mato Walda a 1983. Ya fara
yi wa Malam Adamu Idris a giyar mashin xinsa.
75- Wanda ya fara waldar Gas shi ne Jibrin Saleh.
76- Wanda aka fara saya wa motar shiga shi ne sarkin yaqi Babale,
Bauci En’e ta saya masa a 1953.

162
Uban Ali kwanyo. Gidanshi na kallon gidan man Alhaji Musa Laska. A san nan
gidanshi ne qarshen gari ta kudu. Mutane har sukan riqa yi dashi wai ya zo da sabon
addini. Alhali kuwa shi almajiri ne, yana zuwa Kano sarin littattafai, sai ya shiga
Tijjaniyya. A san nan kuma a qasar nan ’yan tijjaniyya ne kaxai ke yin qablu, har ma a
Kano ana yawaita rikici tsakanin ’yan tijjaniyya masu yin qablu, da ’yan qadiriyya masu
yin sadlu. Sai su ’yan qadiriyya na kiran ’yan tijjaniyya da sunan ’yan qabalu.
140
77- Wanda ya fara zamowa shugaban kwalejin gwamnatin tarayya
‘rector’ shi ne Sunusi Waziri.
78- Wanda ya fara sana’ar sai da goro shi ne Harxo Wambai Mahmud.
79- Wanda ya fara sayen talabijin shi ne Alhaji Saidu
80- Wanda ya fara buxe shagon Kwamfuta shi ne Yusuf Musa Laska
81- Wanda ya fara buxe kantin sai da magungunan dabbobi shi ne
Alhaji Audu Ningi (malamin lamba).
82- Wanda ya fara sana’ar kafinta shi ne Saleh Kafinta.
83- Wanda ya fara buxe asibitin dabbobi shi ne Sabi’u Bala Umar163
84- Wanda ya fara yin gida mai falo a qarqashin qasa shi ne Ambasada
AG Abdullahi.
85- Wanda ya fara sayan motar shiga da kuxinsa shi ne
86- Wanda ya fara aikin keken ‘Design’ shi ne Rabi’u Hasan Maigishiri
(Tururu).
87- Wanda ya fara aiki a gidan rediyo ba tare da an ji muryarsa ba shi
ne Alhaji Idi Jibrin.
88- Wanda ya fara magana a gidan rediyo ana jin muryarsa shi ne
Sama’ila Bala.
89- Wanda ya fara tallata sunan Gumau da bakinsa a gidajen rediyo shi
ne Sama’ila Bala.
90- Wanda ya tallata sunan Gumau da ayyukansa shi ne Alhaji Maikuxi
Gumau.
91- Wanda ya fara sai da hajja (turamen atamfa da yadi) shi ne Alhaji
Sabo.
92- Wanda sana’ar kafintan qasa na kayan xakin mata shi ne M. Sule
Kafinta.
93- Wanda ya fara sana’ar kafintan sama shi ne Sale Kafinta.
94- Wanda ya fara shiga aikin xan sanda shi ne
95- Wanda ya fara shiga aikin soja shi ne

163
An haife shi a 1992, a Gumau, kuma a cikinta ya tashi. Ya yi karatun Muhammadiyya
a makarantar M. Abdulhamid Xanhasan. Kana ya yi firamaren Unguwar Waziri 1999-
2005. San nan ya tafi Federal Government College, Azare 2005-2012. Sai Bauchi State
College of Agriculture 2012-2014, inda ya karanci Animal Health & Production
Technology. Daga nan sai ATBU 2017-yau. Inda ya karantar Animal Science.
141
96- Wanda ya fara sayen injin dakan shinkafa shi ne

FARARRUN AL’AMURA NA GARIN GUMAU

1- A cikin watan Yuni 1953 hukumar en’e ta saya wa sarkin yaqi


motar shiga, kuma aka lamunce masa tafiyar mil 300 gwamnati ce
mai biya masa kuxin mai.
2- Ran 15-07-1955 baturen qudan tsando (Sleeping sickness
superintendent) Mista J. Bradley-Turner ya zo Gumau don duba
wuraren da qudan tsando masu hana shanu sakewa su ke.
3- Ran laraba 09-11-1955 mataimakin Di’o Mista Dent da baturiya
mai kula da jarirai suka zo Gumau suna tambayar ko za su sami
mata masu ilimi da za’a xauke su aikin kula da jarirai
4- Ran 08-06-1958 har zuwa ran 12-06-1956 baturen ciwon bacci
yana rangadi a Gumau, yana duba halin da mutanen qasa ke ciki.
Kuma ya sa aka ajiye M. Garba Mashi malamin ciwon bacci yana
bad a maganin ciwon bacci a asibitin Pingel.
5- Ran 26-09-1956 Gumau ta cika maqil da dagatai da masu littafi da
sauran talakawan qasa. Aka yi ta kaxe-kaxe da bushe-bushe da
sukuwan dawakai, don taryan mataimakin Di’o (A.D.O.) Mr
Dupays. Ya zo ya yi bayanin zave ran 27-09-1956 da safe.
6- Ran 02-01-1958 aka kawo wata mata ungozoma mai suna Martha
Dimka aikin ungozoma a Gumau.
7- A ran 31-05-1958 aka ba da kwangilar gina rumfar kwano a
Gumau. Wacce ita ce ta farko a dukkan kasuwannin qasar Lame.
8- A cikin watan Janairu 1961 aka yi aikin lalume na qasar Lame a
Gumau, daga cikin mutum 50,800 an duba mutane 46,418, an samu
marasa lafiya 50, kuma nan da nan aka shirya yi musu magani.
9- A cikin watan Mayu 1964 aka sa harsashin gina gidan baqi na
Gumau. Zuwa qarshen watan Oktoba har an gama shi. Aka aiko da
gadaje da katifa da matashin kai daga Bauci. An sayarwa da
Ambasada AG Abdullahi ran 13 Maris 2013, a kan kuxi Naira dubu
xari biyu (N200,000) daidai.

142
10- Ran talata 20-01-1966 da misalin sha biyun dare, mota ta faxi a
gadar Gumau. Har direban ya qure hawa, kawai sai motar ta xauke
wuta, sai ta dawo da baya, ta faxa a cikin ruwa da duwatsu, ta
vangaren gabas. Mutum biyar suka karye, nan da aka aika Pingel
aka xauko malamin asibiti, ya zo ya ba da gudummawar taimakon
farko, kafin aka xauke su tare da xandoka zuwa asibitin turawan
Mishan a Saya.
11- A ran 28-08-1966 da misalin qarfe tara na safe, motar fasinja ta
faxi a gadar Gumau, har mutum guda ya rasu, wata mata kuma ta ji
mummunan rauni.
12- Ran 25-01-1968 aka yi gobara a gidan sarkin kudun Bauci, a
Gumau, da misalin qarfe shida na safe. Gidan ya qone kaf, sai
adada guda da zauren girki. Hasarar da aka yi ta kai ta kimanin fam
xari biyu da hamsin (£250:00:0).
13- Allah ya yi wa malam Hamza Harxawa, malamin auduga rasuwa,
ran laraba 27-02-1968 a Gumau
14- Allah ya yi wa Marafa Ahmadu Maiwunti rasuwa ran alhamis 31-
12-1971, da qarfe shida na almuru.
15- Ran 13-02-1962 Bawa Sanga ya rataye kansa, saboda an kore shi
daga makaranta a dalilin ciwon sanyi.
16- Ran 15-05-1972 sarkin Bauci ya fito rangadi zuwa qasar Lame. Ya
ziyarci Gumau ya wuce zuwa Dawa kamfani, in da ake haqar kuza.
17- Ran 24-25 Fabrairu 1974 aka yi was an gona a Gumau. Manoma
suka yi tat a kawo amfanin gona suna nunawa.
18- Ran talata da laraba 24-25 ga watan Fabrairu 1974 aka yi bikin
nunin amfanin gona a garin Gumau in da manyan malaman gona na
lardin Bauci suka halarta. Mutane kuma suka yi ta kawo amfanin
gonarsu da fasaharsu suna nunawa.
19- A ranar 21 Disamba na shekarar 1976, Allah ya yi wa sarkin kudu
Salmanu xan Ade rasuwa.
20- A cikin watan Satumbar 1977 qaramar hukuma ta aiko da buhunan
dawa 30, na masara 29 garin Gumau don sayarwa talakawan
gundumar Wonu cikin rahusa, kowanne buhu N16:0:0.

143
21- A qarshen shekar 1978 aka bad a kwangilar yin sabuwar hanya mai
kwalta tare da gadojinta daga Magama zuwa Gumau. Tifofi masi
xiban qasa sun ture bishiyoyi da yawa, a Marmara kaxai sun ture,
xorawa 40, mangwaro 50, dabino 4, da gwaiba 4. Kuma kowacce
said a aka biya diyyarta.
22- Ran 28-10-1980 wakilan kamfanin da aka ba su kwangilar kai
wutar lantarki Gumau, wato ‘Nigerlec’ suka zo Gumau don biyan
diyyar dukkan wanda aka sare masa bishiya, don kafa falwaya a
wurin, aka buqaci kowa ya tsaya a daidai in da da bishiyarsa ta ke.
23- Ran 19-11-1981 qaramar hukumar Lame ta buxe ajin koyar da
sana’o’i da girke-girke ga mata a gidan baqi na garin Gumau. Aka
xauki malama Laraba matar muqaddashin sakataren ilimi na
qaramar hukuma ita ce mai koyarwa.
24- A shekarar 1978 kuma aka kawo dawa, masara da shinkafa na
gwamnati masu rahusa, don sayarwa talakawa. Buhun dawa N20,
buhun masara N21, buhun shinkafa N24.
25- A qarshen watan Oktoba na 1977 aka samu qanfan ruwan sama.
Gonakin shinkafa, da auduga, da gyaxa, da wake masu yawa suka
bushe. Mutane suka yi hasara mai yawa.
26- A cikin watan Oktoba 1978, aka xauke kasuwar auduga (fuloti) ta
farko daga in da ta ke aka yanka feguna shida aka sayarwa mutum
shida, saboda gidajen mutane da kasuwa sun matse ta, ana tsoron
gobara, aka mai da ita can gaba da rehawus kan hanyar Badikko,
aka yi ta zamani a wurin.
27- Ran 04-03-1978 kamfanin ‘WIMPEY’ da suka gina hanyar
Magama-Gumau zuwa Gumau suka biya waxanda suka rasa
amfanin gonakinsu da gidajensu da itatuwansu yin moriya diyyar
abinda aikin hanyar ya shafa. An yi biyan a sakateriyar qaramar
hukumar Toro da qarfe goma na safe.
28- Ran 30-04-1978 aka yi babban taron shawara don taimakawa a raya
cikin garin Gumau. Jama’a da dama suka taru.
29- A cikin watan Afrilu 1978 aka yi safiyon sabuwar hanya daga
Magama-Gumau zuwa Gumau. Hanyar da ta bi ta gidajen mutane

144
da yawa a garuruwan kan hanya, said a aka biya su diyyar
gidajensu da bishiyoyinsu.
30- A ranar litinin da safe, 23-06- 1979, mota (tifa) ta xebi leburori
masu aikin ginin makarantar sakandiren Gumau ta yi hatsari a gadar
Gumau. Ta dawo da baya, ta faxi ta gefen yamma, mutum shida
suka mutu.
31- A cikin watan Maris 1980 mutanen Sanga suka haxu a wuri guda
kusa da makaranta. Kuma suka nemi hukuma ta zo ta yi musu layi-
layi ta gina musu rijiya a wurin.
32- A farkon shekarar 1982 aka tsaga hanyar mota daga mahaxar titin
zuwa maqabarta da ke titin waziri Xanwunti zuwa mataniti zuwa
kan titin Saminaka. Kuma ’yan bautan qasa suka fara yin kwalabati
a rafin M. Gardi don haxewar hanyar.
33- Ran 06-05-1981 aka yi wata guguwa da ta xauke rufin makarantar
Unguwar Waziri da kan titin Waziri Xanwunti a Gumau.
34- Ran asabar 03 Oktoba 1981. Jama’a ta taru danqam daga sassan
gundumomin qasar Lame baki xaya, aka yi ta wasanni iri-iri na
gargajiya. Aka yi bikin kafa sabuwar qaramar hukumar Lame mai
hedkwata a Gumau a qofar fadan hakimi.
35- Ran lahadi 29-03-1981 zaki ya zo rugar Harxo Mamudu da ke
Sanga, ta gundumar Wonu, ya hana mutane da shanunsu bacci.
36- A cikin watan Maris 1983 aka samu masifar karnuka suka riqa
kasha tumakin mutane a garin Gumau, said a aka tashi tsaye da
roqon Allah, har ma aka yi dokar duk in da aka ga kare a kashe shi.
37- Ran 31 Disamba 1984 aka yi juyin mulkin sojoji a Nijeriya, kuma
aka rushe qaramar hukumar Lame mai hedkwata a Gumau.
38- Ran 12 Maris 1987 kiristoci mabiya majami’ar ECWA Bishara
No.1 Sanga suka valle daga bin majami’ar ‘ECWA Plateau District
Church Council’ kuma waxanda aka valle daga cikinsu suka umarci
waxanda suka valle daga cikinsu, su bar yin sujada a cikin
majami’arsu da gaggawa, in da su kuma suka kafa nasu a gefen
wancan.
39- A cikin watan Oktoban 1987, Allah ya yi wa Munkaila sarkin
kasuwan Gumau rasuwa.

145
40- Ran 6 Satumba 1988 farin xango masu vata amfanin gona suka
vulla gonakin mutanen Gumau da kewaye. An fara ganinsu a gonar
Isa Mai Manja Gumau.
41- Ran 05-12-1991 aka bude makarantar Firamare ta sarkin yaqi.
42- Ran talata 16-10-1990 aka yi wata mummunar gobara a gidan M.
Salisu Ta’an a Gumau da misalin qarfe bakwai da rabi na safe, ta
qone xakuna biyu da kayan cikinsu, har ma da wani yaro mai suna
Abubakar Salisu.
43- Ran 16 zuwa 18-11-1990 haxaxxiyar qungiyar kiristoci ta ‘ECWA
ZONE D ZABOLO, SANGA DA JENGRE’ suka yi babban taro a
babbar majami’ar ECWA BISHARA No 1 Gumau. Irin abinda ba’a
tava yinsa a cikin garin Gumau ba sai san nan.
44- Ran 25-11-1991 aka rantsar da shugabannin kwamitin fara aikin
tara kuxi don tafiya Lagos, neman qaramar hukumar Lame mai
hedkwata a Gumau. Kowanne mutum ana so ya bad a gudummawar
naira biyar (N5), mai hali yana iya bad a fiye da haka. Aka yanke
wa kowacce gunduma ta kawo naira dubu goma (N10,000) su kawo
ran laraba 04-12-1991
45- Ran 28 Janairu 1994 ma’aikatan wutar lantarki ta qasa NEPA suka
cire rumbun wutar lantarkin (transformer) kwalejin koyon sana’a
(Government Technical College) Gumau suka je suka sayar, ba tare
da sun gamu da wani turjiya daga mutanen gari ba.
46- Ran 10-05-1994 sarkin Bauci ya aiko da wata addu’a da limaminsa
ya rubuta da ake buqatar a karanta ta qafa dubu saba’in ( 70,000) a
dukkan masallatan qasar Lame, a gurbin kowacce sallar farilla,
saboda tsoron fitinar da ake ganin za ta iya tasowa a wannan lokaci,
saboda soke zaven Abiyola, da kuma karve mulki da Janar Sani
Abaca ya yi daga hannun Shonekan, da yadda qasashen duniya
suka juyawa shugabannin Nijeriya baya, kuma su ke mata mugun
fata. Ga addu’ar kamar haka : “Kullama auqadu naral lilharbi
axfa’ahallah”
47- Ranar jumma’ah 22-06-1994 aka tabbatarwa da sarkin kudu
Muhammadu Maidawa samun sarautar sarkin yaqi. Ranar lahadi
26-06-1994 kuma aka xaura masa rawani.

146
48- Ran jumma’a 03-02-1995 wasu Fulani ’yanuwan juna suka yi faxa
har xaya ya ya kasha xaya. Bafulatani Adamu Gambo ya kasha
Hamidu Caccava a Gumau akan rikicin gonad a gida. Sun fara
shari’a tun daga kotun Gumau, suka koma Toro, suka je har Bauci,
irin abin da ba’a tava ganin irinsa a wannan gari ba.
49- Ran 15-05-1995 da yamma Hasan yaron Audu na Barandawa ya
kasha M. Musa Baduku Ririwai, akan wata mata mai zaman kanta,
mai suna Jummai.
50- A ran 29-05-1995 aka xauke babban asusun ajiyar qaramar
hukumar Toro (Toro Local Government Main Account) daga reshen
Gumau na bankin arewa (Bank Of The North) zuwa reshen bankin
na Toro. Abin day a jawo mutuwar reshen Gumau baki xaya.
51- Ran Asabar 31-10-2020 sarkin yaqi Aliyu xan Abubakar ya auri
Hafsatu xiyar Yakubu Bisingini.
52- Ran 27-05-2021 aka wayi gari da tashin gobara a gidan Shehun
Laru da ke Dogon Layi, in da wuta cinye gidan qurmus, ba abinda
aka fita dashi. Sai dai Allah ya kiyaye ba’a yi hasarar rai ko xaya
ba. Abin da ake ganin tartsatsin wutar lantarki ne ya haddasa ta.
53- Ran 01-06-2021 aka samu ruwan sama a Gumau, alhali kafin
zuwansa an yi dogon rani na wata takwas, abin da ba’a tava ganin
irinsa ba a tarihi, don ruwan sama ya xauke tun satin farko na watan
Oktoban 2020. Dukkan rafuka da tafuka da rijiyoyi sun qone, masu
noman rani sun yi babbar hasara, shanu sun marmace. Dusa ta yi
tsadar da ba’a tava jin irinsa ba, don sai da mudunta ya kai N75,
duk da haka ba ta samuwa. Masu kiwon dabbobi sun wahala. Kuma
an yi zafi mai tsanani mutane suka yi ta rashin lafiya. Kana ga
tsananin fatara da talauci da ya riqa damun jama’a. Kana ga tsadar
kayan masarufi. Muna fata dai kada Allah ya maimaita mana irin
wannan shekara.
54- Ran 02-12-1974 raqumin sarkin Bauci ya vace, aka aiko da
cigiyarsa har Gumau.
55- Ran 27-05-1965 sarkin Bauci da ’yan majalisar En’e suka zo
Gumau, don nuna wa Sangawa inda za su gina cocinsu. Bayan Jola

147
Sanga da Yakubu Dangana sun kai qarar sarkin kudu Salmanu da
Harxon Wonu Bauci akan sun hana su ginawa.
56- Ran 06-04-1963 aka wata rigima akan rikicin aure tsakanin
Kungusu Sanga da surukansa Mato da Alti, sun xaura aure akan
auren matarsa, bas u bas hi dukiyarsa ba. Asabe it ace matar
Kungusu, ta je gida ne kawai, sai iyayen suka hanata komawa
gidansa. Ya je biko sau shida, bas u bar tat a dawo ba. Qarshe ma
sai suka xaura mata aure akan aurensa.
57- Ran 14-05-1963 daren laraba varayi suka fasa tagar ‘Reader room’(
Ridaru) na Gumau suka sace rediyo. Kuma ran 16 ga wata suka
sace kujeran qarfe a bariki (resthouse), abinda ya xaga hankalin
mahukunta.
58- Ran 6-2-2021 aka naxa Malam Umar Adamu Umar (Babaji) mai
littafin sarkin Gabas na Wunti.



148
GUNDUMARTA

1- Gundumar Wonu/Ririwai

GUNDUMAR WONU

Asalin sarautar gundumar Wonu ta qabilar fulanin Yakanaji ce


(Fulve Yakanaji), waxanda asalinsu mutanen Bebeji ne, cikin qasar
Kano. A cikin qarni na 19 miladi, wajejen shekarun 1828-1830,
suka yo hijira zuwa qasar Bauci, don neman dausayin kiwo, mafi
dacewa da dabbobinsu. Suka zauna wani daji, yamma da wani dutse
da ake kira ‘Wonure’ suka kafa gari a wajen suka kira shi da suna
Wonu.
IYAKOKIN GUNDUMAR WONU

Gundumar Wonu ta gabas ta yi iyaka da gundumar Lame a


dutsen Sagere. Idan ka yi gabas da dutsen kana cikin gundumar
Lame, idan ka yi yamma da shi kana cikin gundumar Wonu. Ta
kudu ta yi da ta yi iyaka da gundumar Ribina idan ka gota dutsen
farko da ke kudu da Geljaule, daidai wata ’yar wuriya. Ta yamma ta
yi iyaka da qasar Filato a qarshen dutsen Sanga ta yamma. Ta
arewa ta yi iyaka da gundumar Zalau a daidai kwalbatin da ke daf
da Tashar-Dugu, daga nan abin da ya yi gabas har zuwa dutsen
Jawandu.

SHIGOWAR RIRIWAWA CIKIN SARAUTAR GUNDUMAR WONU

Dalilin shigowar mutanen Riruwai cikin sarautar shi ne, wani


kisan kai da wasu ’yan fashi suka yi wa masu dakon haraji za su kai
Bauci a kusa da Ririwai, a zamanin Harxo Mainasara. Nan da nan
sarkin Ririwai da sarkin Sanga suka riqa sangaraftu da dawakai ana
neman ’yan fashin. Sai kuma aka samu sakaci shi Harxo Mainasara
bai zo da wuri ba, har bayan kwana uku, har sai da Di’o (bature) da
sarkin Bauci, suka samu labari suka riga shi zuwa. Abinda mai

149
martaba sarki da majalisa suka tuhumce shi da sakaci da aiki, suka
ce tun da shi bai damu da hidimar sarauta ba, to, ya zauna ya huta.
Sai aka tuve shi aka naxa M. Musa Gaman Ririwai wanda turawa
suka ga qoqarinsa a san nan. Bayan shuxewar M. Musa Gaman, sai
rikicin sarauta ya vullo a cikin magadansa, har said a sarautar ta bar
gidansa baki xaya, ta koma gidan Kafakawa, kuma unguwanninsu
daban-daban ne. Abin da kuma ya qara rura wutar gabar unguwa da
unguwa tsakanin Ririwai cikin gari da Hayin sarki. Da ta bar gidan
Kafakawa, sai ta koma gidan Kanawa waxanda su ma mazauna
cikin gari ne, sai wutar gabar ta kuma qaruwa tsakanin Hayin sarki
da cikin gari, tsakanin Katsinawa, Kafakawa da Kanawa. Abin da
kuma ya janyo kuvucewar sarautar daga Ririwawa baki xaya, ta
koma gidan Fulani inda nan ne mavuvvugarta na asali.

LABARIN ASALIN RIRUWAN DALMA

Asalin mutanen da suka kafa Riruwan Dalma, mutanen Riruwan Kano


ne. Lokacin da Xanmaje,164 sarkin Ningi ya sanya qasashen da ke kewaye
da shi, yana yaqinsu. Bai bar wani da ke kewaye dashi ba, sai da ya yaqe
shi. Ya yaqi Bauci ya ci garuruwa masu yawa. Ya yaqi Kano ya ci
garuruwa masu yawa. Ya yaqi qasar Zazzau da qasar Shira. Ya kwashe
dukiya mai yawa, har al’amarinsa ya bayyana, sunansa ya xaukaka. Ya kan
tara gayyan yaqi mai yawa kamar mutum dubu huxu, ya sauko daga cikin
duwatsunsa, ya sa fuskarsa inda ya yi nufi. To, Riruwai na daga cikin
garuruwan qasar Kano da ya fi sa su a gaba . Su kuma Ningawa, ba wai

164
Xanmaje sarkin Ningi na III (1855-1870), ya gamu da ajalinsa sadda ya yaqi Toro,
mutanen garin suka fito suka yi yaqi dashi a jikin wata qorama da ake kira Salarma.
Mutanen Toro, ba su yi masa da daxi, mutanensa da yawa suka halaka, shi ma xan yaro ne
qarami ya harbe shi da kibiya guda biyu, sai ya mutu. jama’a ta sa suka watse. Waxanda
suka qetara wannan qorama su kamar masu dawaki xari uku, suna cewa juna ‘A mazgaya
akai gida, don kada iri ya qare’ da qyar suka sha. Da suka koma gida sai suka naxa
Haruna sarkinsu. Ya ci gaba da yaqin qasar Bauci da Zazzau har ya mutu. Sai suka sarauta
Gajigi, sai Xanyaya ya kashe shi ya karve sarautar bisa tilas. Ya zauna cikin sarautarsa
yana yaqin jama’ar musulmi, har lokacin da bature, Mr Temple da sojojinsa suka rinjaye
shi, ya ximauce ya gudu, aka kashe shi a wani wuri ana ce masa Sãma.
150
tsananin yaqi na gaba da gaba, ko jaruntaka ne suke dashi wanda ya fi na
saura ba, a’a, amma dai wata dabarar yaqi gare su. Dabarar nan kuwa itace
ba su kai yaqi gari sai dare ya tsala. Sai su kewaye garin su bunka masa
wuta ko ta ina. To, duk wanda ya fito cikin dare a gigice, mace ko namiji,
sai su kashe na kashewa, su kame na kamawa, su kwashe dukiyarsu da
matansu da ’ya’yansu, su kai matattara. Idan suka gama tarawa, sai su tasa
su a gaba su tafi da su Ningi su yi ta sayarwa attajirai da fatake, wasu kuma
su je da su gida su yi musu bauta. To, ita Riruwai ta Kano, gari ne na
ma’adani. Ma’adanin nan kuwa shi ne kuza. Kuma mutanen garin qwararru
ne wajen iya sarrafa ta, su tankaxe ta, su rarrabe qarfe da kuza da
kalambaye, ba tare da amfani da inji irin na zamani ba. Sukan kuma narkar
da kowanne, su zuba shi a mazubinsa. Ana zuwa daga nesa ana sari, ana
tafiya da ita wasu qasashe, ana sayarwa. To, gari irin wannan bai cika
rabuwa da leburori da fatake da masu sana’o’i daban daban. To, da
al’amarin Ningawa ya tsananta gare su, sai wasu gungun ’yan kasuwa daga
cikinsu, suka yi shawarar su yi hijira, su bar garin, su koma cikin mulkin
sarkin yaqin Bauci, in da ke da zaman lafiya. Domin shi arziqi bai cika son
wurin da babu zaman lafiya. Da suka shigo qasar Bauci, sai suka kafa garin
Babajayi 165da Koruno da garuruwan gefensu. Amma da suka kafa
rahoniyar narka dalmarsu, suka yi mazubai, sai suka ga wurin bai karve su
ba. Sai suka yi shawarar a sauya wuri.166 Domin ma’abucin sana’a, duk
inda sana’arsa za ta samu tasgaro, to, ba wurin zamansa ba ne. Cikin
neman inda za su zauna ya dace da sana’arsu ne, suka zo inda Riruwai ta
ke yanzu. Da suka gwada kafa rahoniya da mazubai suka ga sun yi musu
yadda suke so, sai suka zauna a wurin suka sanya masa suna Riruwan
Dalma, don su bambance ta da wancan Riruwai da suka baro ta qasar
Kano. Cikin xan lokaci qanqani malam, sai ga wuri ya bunqasa, Ta zamo cibiyar
kasuwanci na wancan zamani. Kuma sai garin ya dace da kasancewarsa a kan
hanyar fatake, kuma maciya da fatake ke yin zango da kayan kasuwancinsu.

165
Yanzu haka, akwai dutse a jikin Babajayi da ake kiransa dutsen Riruwai.
166
Bayan tashinsu daga Babajayi, sai Gusawa suka zauna a wajen. Da ya ke su kuma ba
mazauna waje xaya ne ba, su ma suka tashi, har wasu suka mamaye gun. Amma har yanzu
mutanen Riruwai na da saura a wajen. Kamar Koruno har yanzu shuke-shuken mutan
Riruwai ne za ka riqa gani, har da duwatsun niqansu da suka bari, har yanzu suna nan.
151
ZUWAN TURAWA

Ana cikin wannan hali, suna gyaran kuzarsu zuwa dalma, suna zuba ta
a mazubai, fatake ’yan kasuwa zuwa daga nisan duniya suna saye suna
tafiya da ita qasar kuza har zuwa Kwatan-qarfe, kwatsam sai turawa suka
bayyana, suka qwace mulkin dukkan qasa ya dawo hannunsu a 1906. Cikin
bibiyar qasa da suke yi har suka zo Ririwai, suka ga wata irin fasaha da
Allah ya yi wa baqar fata a cikin dajin Afirka. Na iya sarrafa qasar da aka
tono, a ware kuza daban, da kalambaye, da teli, da qarfe da sauran
ma’adanai, ba tare da inji ba, alhali ko shi bature a lokacin bay a iya
rarrabe sub a tare da inji da ake kira ‘Safureta’ ba. To, shi kuma bature ya
fito daga qasarsa ya shiga duniya ne da manufofin yaxa addininsa na
Kirista, da mallake kasuwancin duniya, da kwashe tattalin arziqin
al’ummomin duniya. To, a bisa waxannan qa’idodi da ya xauka wa kansa,
ba zai yarda da wata sana’a da ta fit a sa inganci ta ci gaba da wanzuwa ba.
Saboda wannan sai suka hana mutanen Ririuwai sarrafa kuza da mulmula
ta zuwa dalma. Sai kuma suka xaukarwa kansu biyan duk waxanda suka
hana yin wannan sana’ar kuxin fansho duk shekara, har zuwa qarshen
rayuwarsu, da sharaxin ba za su qara yi ba, kuma ba za su koya wa wani
don ya iya ba. Kuma turawa sun yi bakin qoqarinsu wajen cika wannan
alqawari, wani sa’in a aiko da kuxin ta ofishin hakimi, wani lokacin a yi
kiransu su je Bauci su karvo da kansu a ofishin en’e. idan sun je da kansu
sun karvo, su kan biyo ta Katsinawa su saro kayan koli da kuxin su dawo
dashi gida su yi ta sayarwa. Haka aka yi ta yi, har zuwa kan mutane huxun
qarshe da suka karvi wannan kuxi ran 20 Mayu 1954 kamar haka ;
1- Madugu : ya karvi fam uku (£3:0:0) daidai.
2- Lãsan :167 ya karvi fam uku (£3:0:0) daidai.
3- Dangana : ya karvi sule goma sha biyar (15:0)
4- Turai : ta karvi sule goma sha biyar (15:0)
Jimilla = £7:10:0

167
Uban Xanlami Xangulili Pingel. Shi ya sa ma ake masa kirari ‘Alhasan xan Aka, mai
tuwon dami uban Xanlami’
152
5- Maigyalan ba’a faxi abin da ya karva ba. Shi kuwa Dangana, wannan
ne karvar kuxinsa na qarshe, domin ya rasu a 1954. Zuwa 1958
dukkansu sun mutu, kam ban da Lasan, shi ne wanda ya karvi kuxinsa
na qarshe a 1959, kuma a wannan shekarar ya rasu. Ko kafin ya rasu,
yana faxa da kansa yace, ya karvo kuxinsa na qarshe kenan.

GUNDUMAR RIRIWAI

Ta tava zama gunduma a 1909 zamanin sarkin Bauci Yakubu II


Usmanu Maigari (1907-1941) har zuwa zamanin sarkin Bauci Adamu
Jumva (1956). Sai rikicin cikin gida ya janyo sulmuyar gundumar, in da ta
koma mavuvvugarta na farko, wato gidan fulanin Wonu. An yi yunqurin
samun sabuwar gundumar Ririwai a shekarar 1999 amma yunqurin bai
samu nasara ba. Sai a shekarar 2010? aka samu sabuwar gundumar Ririwai
wacce aka yage ta daga gundumar Wonu mai littattafai goma sha uku ;
1- Ririwai ‘A’
2- Ririwai ‘B’
3- Unguwar Tsamiya
4- Shenu
5- Barandawa
6- Sanga ‘A’
7- Sanga ‘B’
8- Dawarde
9- Kudenu
10- Yamman Kadage
11- Unguwar sarkin Yamma
12- Unguwar Maiwuro
13- Unguwar Sako

Amma ba ta daxe ba, cikin shekarar 2017? sai aka rushe ta, ungulu ta
koma gidanta na tsamiya. Ga jadawalin sarakunan Ririwai nan tafe :

153
JADAWALIN SARAKUNAN RIRUWAI

Suna Asalinsa Nau’in Sarauta Daga


1 Gaman Bakatsine Mai littafi
2 Abdu Gaman ” ” 1909
3 (Madugu) Ibrahim Gaman ” ”
4 M. Musa Gaman ” Mai Gunduma
5 M. Baqo Kafakawa ”
5 Hurde ubanbbn umma Kafakawa ”
6 Hudu168 ubn alhuba Bakano ”
7 Abdu ” 1932-1956169
170
8 Barde (Gago) Mai Littafi 1956-1970
9 Muhammadu Inuwa Bakatsine ” 1970-2010171
10 Abubkr Garba Badamasi ” ” 2011-Yau172
Yawan shekarun da Ririwawa suka yi suna sarautar gunduma 1909-1956 =47

SARAKUNAN GUNDUMAR WONU

Suna Daxewa Shekara Qabila


1 Harxo Muhd Bebeji 1830- Fulani
2 Harxo Fate 7 ”
3 Harxo Wari ”
4 Harxo Ade (Maikayi) ”

168
Ya yi murabus da qashin kansa.
169
An cire shi ran 25 Yuli 1956
170
An naxa shi sarauta ran 10 Oktoba 1956, ya rasu ran 9 Maris 1970. Ya bar ’ya’yansu
uku duka mata ne ; Hadiza, Laraba da Ladi. Ita Hadiza ta haifi Sale Agambo, Xanlami
Nauyi da Shu’aibun Sarki. Ita kuwa Laraba ta auri Ako, ta haifi Mu’azu Timba, da
Auwalu Sule. Ladi ta auri Bula, ta haifi Hamar Xan’azumi Mai shayi, Titi, Zulai matar
Xanyaro ‘Lafiyan gari.’
171
Sarkin Ririwai M. Muhammadu Inuwa an naxa shi sarauta ran 30 Maris 1970, ya rasu
ran litinin 12 ga Afrilu 2010 a babban asibitin Bauci. An binne shi a Gumau.
172
An haife shi a 1965 a Ririwai, amma ya tashi a Gumau. Ya yi karatun Muhammadiyya
a makarantar M. Audu Xanturai, da kuma wurin mahaifinsa M. Adamu. Ya yi karatun
ilimi a wajen liman M. Aminu limamin Ririwai, da liman M. Abdulmumin Gumau. Ya yi
makarantar firamare a Ririwai 1979-1985. Ya yi sakandaren JSS Lame. Ya zamo mai
littafin Riruwai a 2011-yau.
154
5 Harxo Barandawa ”
6 Harxo Halilu 36 ”
7 Mainasara ”
8 M. Musa Gaman Bakatsine
9 M. Baqo Bakafake
10 Hurdi173 ”
11 Hudu174 Bakano
12 Abdu 1932-1956175 25 ”
13 Harxo Abubakar Buhari 1956-1996176 41
14 Harxo Abubakar Buhari 1997-Yau177
Yawan shekarun da Fulani suka yi suna sarautar gundumar Wonu 2021-
1830 =191

LITTATTAFAN DA KE BIN GUNDUMAR WONU :

Gundumar Wonu tana littattafai 44, ga su :


1- Littafin Wonu “A”
2- Littafin Wonu “B”
3- Littafin Riruwan -Dalma
4- Littafin sarkin Sanga
5- Littafin Barandawa
6- Littafin Shenu
7- Littafin Gakuyel178
8- Littafin Unguwar Tsamiya
9- Littafin Mana179

173
Kakan Alhaji Baban Umma Rishi
174
Kakan Alhaji Na’iya Gumau
175
An tuve shi daga sarauta ran 25 Yuli 1956.
176
Ya rasu ran 28 Oktoba 1996
177
An haife shi a 1958 a Gumau, kuma a cikinta ya tashi. Ya yi makarantar
Muhammadiyya ta M. Mahmudu Bugau, kana ya yi karatun ilimi a wajen liman M.
Abdulmumini Adamu. Ya shiga makarantar elementare da firamare duka a Gumau-Sanga
a shekarar 1966-1973. An zave shi ran talata 19 Agusta 1997, an naxa shi ran Jumma’ah
14 Nuwamba 1997.
178
Iyakar mulkinsa abin da ya kama daga Unguwar Kanya har Tashar A’i (Ko Tashar
mangwaro).
155
10- Littafin Tenuwa
11- Littafin Pingel
12- Littafin Dawarde
13- Littafin Izar
14- Littafin Badikko
15- Littafin Harxon Babajayi
16- Littafin Kwacchaho
17- Littafin Harxon Kwacchaho
18- Littafin Harxon Badikko
19- Littafin Lullungwal
20- Littafin Jallakoji
21- Littafin Unguwar Yarima
22- Littafin Buri
23- Littafin Katafaje
24- Littafin Tantaroki
25- Littafin Nabaka
26- Unguwar Garkuwa
27- Unguwar Mahmudu
28- Littafin Tudun Wada
29- Littafin Sarkin kudun Badikko
30- Littafin Unguwar Labari
31- Littafin Unguwar Kadiri180
179
Asalin Manawa mutanen Kwandon –Qaya ne, daga can suka yi qaura suka zo in da
Mana ta ke yanzu, suka voye a tsakanin duwarwatsu. Sunan sarkinsu na yanzu M. Dauda
Idris, an haife shi a 1950, a Mana, kuma a cikinta ya tashi. Ya yi karatun Muhammadiyya
a wajen M. Jauro wani bafulatani, mutumin Fakuru da ya dawo Mana da zama. Ya yi
karatun yaqi da jahilci a Mana. Yana daga cikin ’yan ajin M. Maikanti Unguwar Kadiri da
M. Adamu Voyi Madakin Wunti. An naxa shi mai littafin Mana ran 11 Nuwamba 1977.
Waxanda suka rigaye shi yin sarautarta, su ne Tauxo, Muhammadu, Idris, Usman ya yi
shekara 15 (1962-1977). Daga jikin littafin Mana aka cire littafin Pingel da littafin
Tenuwa. Saboda haka yanzu littafin Mana ya yi iyaka da littafin Durugu cikin gundumar
Lame ta gabas a shrgiyar dutse. Ta arewa ma ya yi iyaka da littafin Fakuru a shirgiyar
dutse. Ta yamma ma ta yi iyaka da littafin Kulfana cikin gundumar Zalau a shirgiyar
dutse. Ta kudu ma ta yi iyaka littafin Unguwar Baduku duka dutse.
180
Asalin M. Aliyyu, kakan mutanen Unguwar Kadiri fulanin Sulluvawa ne, suka yi hijira
daga qasar Zamfara zuwa Bauci, zamanin sarkin Bauci Umar Salmanu, Maje-wase 1883-
156
32- Littafin Didin
33- Littafin Unguwar Baduku
34- Littafin Unguwar Sako
35- Littafin Unguwar Garkuwa
36- Littafin Unguwar Isma
37- Littafin Sarkin Bauxa
38- Littafin Fulanin Kaba181

1902, suka yi masa caffa, sai ya naxa M. Aliyyu sarautar Uban dawaki. Da suna zaune a
Bauci, yana taya sarkin Bauci yaqin jihadi, to, da sarki ya fahimci cewa jarumi ne, sai ya
yi masa sarautar gunduma, ya turo shi Sabon-Qaura kimanin kilo mita guda gabas da
Sauke, don ya kafa gari a wajen, ya tsare masa Ningawa. Bayan sun yi hijira, sun bar
wajen wasu sun zauna sun kira wajen da suna Bindari. Ita gundumar Uban Dawaki, ta
gabas- maso- kudu ta yi iyaka da Harxo Wonu a rafin ‘Didin’ ta yamma maso arewa kuwa
mulkinsa ya kai har Zalau, kam ban da Riruwai. Wani malami bafulatani, sunansa Ibrahim
ya zo daga Katsina, sai ya yi baranta a gidan Uban Dawaki, da suka ga mutumin kirki ne,
sai suka aurar masa da ’yarsu. Sai suna tura shi Zalau yana karvo jangali yana kawowa
daga wajen ’yan’uwansu Fulani mazauna yankin. Ta wannan hanya ya tara shanu masu
yawa, ya yi qarfi sosai. To, ana nan kan haka, har Allah ya yi wa Uban Dawaki Aliyyu
rasuwa. Ba’a daxe ba kuma sai turawa suka dawo da sarkin yaqi, da Harxo Wonu Gumau.
Suka kuma yi sabuwar gunduma a Zalau. Sai turawa suka nemi malam Sule Baguri da
maganar sarauta, shi kuwa ya qi. Sai Kawu Maina, qanin Uban Dawaki Aliyyu, da M.
Ibrahim mai karvo jangalin yankin Zalau, suka fito takara. Sai M. Ibrahim ya yi nasara, ya
zamo mai gundumar Zalau na farko. Kuma tun daga ran nan sarautar gundumarsu ta koma
hannun baran gida, in da kuma ta ci gaba da wanzuwa a hannun ’ya’yan mace. Faruwar
wannan ya sa waxannan Fulani yin fushi, har suka tashi baki xayansu da shanunsu, suka
koma ‘Dokar Bawa Sha-kunu’ (Gana) can kusa da Wundi. To, sai wani babbansu M.
Abdulqadir xan Muhammadu xan Aliyyu ya ba su shawarin su koma in da suka fito, su
kafa sabon gari, da suka dawo in da suka bari, sai suka tarar da wurin ya zama kufai, sai
suka qara gaba, in da suka samu wuri wanda suka ga zai dace da shanunsu. Sai suka kafa
gari a wajen, suka kira shi da sunan babbansu ‘Unguwar Malam Abdulqadiri’ daga baya
aka riqa taqaita sunan ana cewa ‘Unguwar Kadiri’ a shekarar 1947. Sai aka yi musu littafi
a qarqashin gundumar Harxo Wonu, kuma aka kira ta ‘littafin Unguwar Kadiri’
maimakon na Ubandawaki. Shi Malam Abdulqadiri ya fara sarautar, da ya rasu a shekarar
1966, sai qaninsa Jauro (Ahmadu), sai Mu’azu xan Abdulqadir, sai Babaji xan
Abdulqadir, sai Garba Maikanti xan Ahmadu mai ci a yau.
181
Asalinsu fulanin Bebeji ce, ta qasar Kano, sai babansu ya yi hijira ya koma Gamawa,
kana daga can ya dawo Gumau, ya sauka a Sangatu, yamma da Unguwar Jinkai.
Masarautar ta samo suna saboda ciyawar kaba da ya tarar da ita a inda ya sauka da
shanunsa. Harxonta na farko sunansa Harxo Mahmudu Matunkuyel, abin nufi da
157
39- Littafin Sarkin Kudu :182Alhaji Sidi183
40- Littafin Sarkin Arewa (Sarkin Gurawa)184 :
41- Littafin Sarkin Yamma :185Isa Bala
42- Littafin Sarkin Gabas186 : Alhaji Adamu Dindima187
43- Littafin ’Yan kwana :188
44- Littafin Gumau (Wazirin Wunti) :189

‘Matunkuyel’suna ne na launin saniya. Sai Harxo Husaini, sai Harxo Ciga, sai Harxo
Mahmudu, sai Harxo Alfanda, sai Harxo (Abubakar) Gunda, sai Harxo (Adamu) Shagari.
182
Iyakar mulkinsa abin da ya kama daga gidan Sule Baqi ya yi yamma har zuwa layin
Amadudu.
183
Muhammadu Sidi, an haife shi a Ririwai a 1930, kuma a cikinta ya tashi, ya yi karatun
allo a tsangayar M. Audu Jibrin a Riruwai. Ya yi karatun ilimi a wajen M. Garba Xanbaqi,
da M. Muhammadu Yahya. Ya dawo Gumau a shekarar 1949. Maxinki ne qwararren
maxinki. Yana da ’ya’ya da jikoki aqalla xari. Shi ne sarkin kudun Wunti na farko, an
naxa shi ran alhamis 13 Disamba 2012.
184
Iyakar mulkinsa abinda ya kama daga Transifoman Caji-ofis ya yi arewa har zuwa
gada.
185
Iyakar mulkinsa abinda ya kama daga gidan Sanata Lawal Yahaya ya yi arewa kan
layin ’yan doka har qarshen gari ta arewa ya game gabas har maqabarta da masallacin Idi,
iyaka ta sa kudu hanya Unguwar Kanya.
186
Iyakar mulkinsa abinda ya kama daga gidan Sule Baqi ya yi yamma har zuwa layin
Amadudu.
187
Sunansa Adamu Umaru, an haife shi a Lame a shekarar 1922, kuma a cikinta ya tashi,
ya yi makarantar Elementare (Junior Primary School) a Lame a shekarar 1940-1944.
Daga cikin malamansa na makarantar Lame akwai M. Muhammadu Duguri, wanda aka
naxa Hakimin Duguri ran 22/12/1963, shi ne uban gwamnan Bauci na yanzu Bala Qaura,
da M. Burra. Daga cikin abokan karatunsa akwai Alhaji Uba Riruwai, da sarkin Riruwai
Muhammadu Inuwa da mutane masu yawa. Ajiyan Bauci Adamu Tafawa Valewa yana
ajin gaba da su. San nan ya yi karatun allo a wajen M. Tata Babarbare, da M. Magatakarda
Lame, da M. Maidoki. Sai kuma ya shiga neman karatun ilimi, in da ya yi karatu a wajen
M. Garba, wani mutumin Tsakuwa, da M. Haruna mai Dogon sanda. Ya yi aikin malamin
yaqi da jahilci, da gidan gona, inda daga baya, ya komo Gumau ya riqe noma da kiwo, har
aka naxa shi sarkin noma. Asalin iyayensa dama fulanin qasar Adamawa ne, daga Toro
mahaifinsu ya dawo Zigau-manga, kana ya dawo Lame. Yanzu xaya ne daga cikin ’yan
kwamitin babban masallacin jumma’a na sarki, kuma xaya daga cikin iyaye masu bad a
shawara na qungiyar ‘Jama’atu Nasril Islam’ reshen gundumar Wonu.
188
Iyakar mulkinsa abinda ya kama daga Unguwar Gabas ya yi gabas har zuwa Unguwar
Mato-Soko.
158
MALAMAN MAI GUNDUMAR WONU

1- M. Muhammadu Xa 1963
2- M. Bala Ibrahim Lame 1963-1967
3- M. Baba Alqali 1967
4- M. Baba Bakunawa
5- M. Sule Beni (sarkin Beni)
6- M. Haruna Kangere
7- M. Shehu Ahmed Laru 1978-2010
8- M. Bello Umar 2010-

YAWAN MAZAVUN GUNDUMAR WONU 1956

1- Gumau
2- Gakuyal
3- Nabaka
4- Katafaje
5- Mana
6- Ririwan-dalma
7- Dawarde
8- Barandawa
9- Shenu
10- Unguwar sako
11- Unguwar Isma
12- Unguwar Garkuwa
13- Unguwar Baduku
14- Unguwar Kadiri
15- Unguwar Tsamiya
16- Kamfanin kuza
17- Sanga
18- Tantaroki
19- Badikko
189
Shi ne ragowar cikin gari + Ungwar Mishan + Unguwar Mahauta, Sharaxa, Dogon
Layi, Titin Bauci har zuwa kwalbatin gidan Sanata Lawal Yahaya.
159
20- Izar
21- Jallakoji
22- Buri
23- Kwaccaho
24- lullungwal

YAWAN MAZAVUN GUNDUMAR WONU 2019

Daga 1956-2019 gundumar Wonu qarin mazava xaya kurum ta samu,


abinda ke nuna koma baya da rashin ci gaba da gundumar ke samu. Amma
gundumomin Toro/Tulai/ Tilden Fulani a zaven 1956 suna da mazavu 27,
amma a zaven 2019, Tilden Fulani ita kaxai ma tana da mazavu 25,
Toro/Tulai kuwa suna da 39, ka ga idan ka tara (25+39) =64, ya zama sun
ninka gundumar Wonu, su sun ci gaba, Wonu ta ci baya.

’YAN MAJALISAR GUNDUMAR WONU190 – 1960s

1- M. Dabo Dawarde
2- Ali Ririwai
3- Gauza
4- M. Diddila
5- Galadiman Izar191
6- Nadabo Badikko192
7- Aliyyu Lullungwal193
8- Wakili Buba Buri194

190
Irin ayyukan da majalisar gunduma za ta riqa yi shi ne ba da shawara ga majalisar
hakimi a kan yaqi da jahilci, aikin kashe biroyi da gwaggwani, gyaran majalisar gunduma
da ajin yaqi da jahilci, maqabarta, tashoshin motoci, shuke-shuken da aka yi don amfanin
jama’a, aikin gayya, wurin bada magani da haihuwa, urin shan iska, hanya da lambatu,
aikin tsabta, fitilun tituna, ruwan sha, zaven mai gunduma, zaven mai littafi da sauran
abubuwan da suka shafi gunduma baki xaya.
191
Asalinsa Barunje, shekarunsa 52, sana’arsa noma.
192
Asalinsa Bakano, shekarunsa 50, sana’arsa qira.
193
Asalinsa Bakano, shekarunsa 50, sana’arsa noma.
194
Asalinsa Bafulatani, shekarunsa 56, sana’arsa noma.
160
9- Muhammadu Unguwar Tsamiya195-1967
10- Xan Gwami Tantaroki
11- Mato Wonu196-1967
12- Maigishiri Katafaje 197-1967
13- Audi Barandawa 198- 1967
14- Daniya Pingel199-1967
15- Samu Unguwar Isma 200-1967
16- Garba Unguwar Sidi201-1967
17- Hudu Unguwar Gakuyel202 -1967
18- Xahiru Ririwai 203- 1967
19- Maiwayo Sanga204- 1967
20- Mijinyawa Kudenu205-1967
21- Hasan Kwacchaho206-1967

WASU NASARORI
DA MAJALISAR TA SAMU A SHEKARUN 1960-1970

1- Gina mayankan shanu a Gumau207 (£60) (Harxo Wonu ya kawo


shawarar) – 21-07-1962
2- Xaukar nauyin wani yaro ya je ya koyo sana’ar gini (mason) daga
28-04-62 – 30-11-63 an kashe masa (£98) – 1962

195
Asalinsa Barunje, shekarunsa 40, sana’arsa noma.
196
Asalinsa Bafulatani, shekarunsa 50, sana’arsa noma.
197
Asalinsa Bakano, shekarunsa 60, sana’arsa noma.
198
Asalinsa Bafulatani, shekarunsa 45, sana’arsa noma.
199
Asalinsa Bakano, shekarunsa 50, sana’arsa noma.
200
Asalinsa Balimari, shekarunsa 48, sana’arsa noma.
201
Asalinsa Bagushi, shekarunsa 45, sana’arsa noma.
202
Asalinsa Barunje, shekarunsa 50, sana’arsa noma.
203
Asalinsa Bakano, shekarunsa 35, sana’arsa noma.
204
Asalinsa Basangi, shekarunsa 35, sana’arsa noma.
205
Asalinsa Bafulatani, shekarunsa 58, sana’arsa noma.
206
Asalinsa Barunje, shekarunsa 40, sana’arsa noma.
207
Saboda Gumau it ace masarautar hakimi, saboda haka bai kamata ace ba mayanka mai
kyau ba.
161
3- Tona lambatun layukan Gumau208 (£25) (Waziri Adamu Nababa ya
kawo shawarar) – 31-05-1963
4- Gina xakin shawara a gundumar Wonu (£100) - 31-05-1963
5- Tonon shadda a kotun Gumau don masu jiran shari’ah209 (£8)
(Waziri Adamu Nababa ya kawo shawarar) – 31-05-1963
6- Gina gidan baqi a Gumau210 (£280) – 06-03-1964
7- qara yin lambatun layukan Gumau (£60) (M. Ladan Lame) -19-06-
1965
8- Gina rumfunan kasuwa huxu a kasuwar Pingel211 kowacce akan
(£6×4 =£24) (Wakili Liba Mana ya kawo shawarar) – 1965
9- Gyaran hanyar qafa daga Gumau zuwa Sauke (£10) (Alhaji Yunusa
ya kawo shawarar) – 1965
10- Tonon rijiyar hannu a unguwar Liba212 (£3) (Muhammad Arab
Lame) – 22-03-1965
11- Gyaran cikin garin Gumau saboda ya yi duhu, (sharve ciyawa, sare
itatuwan cikin gari), (£10), (Harxon Wonu ya kawo shawarar) –
1966
12- Sayan Kabot na qarfe (Sef)213 don ajiye takardu, da gindin rasit, da
fayilolin asiri a ofishin hakimi (£45) (M. Ladan Lame ya kawo
shawarar) -1968

208
Saboda na da sun cike, sun lalace, ruwa na kwanciya akan hanya, yana kawo cavi da
rima a gidajen mutane. Yanzu ana buqatar ayi mai zurfin qafa biyu, faxin qafa uku.
209
Dalilin yinta shi ne saboda mata masu qara sai sun shiga gidajen jama’a barkatai kafin
su kama ruwa, haka ma mazan.
210
Saboda bai kamata ace inda hakimi yak e babu gidan baqi ba. Za’a gina adada guda
biyu, ciki da falo (10ft×20ft), da xakuna biyu masu faxin qafa 13, shadda biyu da rijiya, a
kewaye gidan da katanga, gadajen bono 2, da katifunsu, matashin kai 4, jar tabarma 4, da
karauno 6. Dukkan xakunan gidan za’a yi musu fandisho na dutse da siminti da rufin
kwano
211
Kasuwar Pingel tana ci ranar lahadi.
212
Saboda mutanen garin suna fama da wahalar ruwan sha, domin sai sun xebo a rafi,
saboda haka mutanen ke fama da ciwon kurkunu, saboda ruwan rafinsu duk kurkunu ce a
ciki, kuma ciwon sai qara yaxuwa ya ke yi yana cinye matansu da ’ya’yansu.
213
Don tsoron kada wataran hakimi ya tafi rangadi a shiga ayi ta’adi a gidansa.
162
13- Majalisa ta nemi en’e ta dawo da asibitin Pingel ya dawo Gumau,
don Pingel ta zama suna, amma Gumau kullum sai qara havaka ta
ke yi, kuma a Gumau en’e ba za ta wahala ba wajen neman inda
za’a riqa bad a magani, saboda akwai xakin bariki (resthouse)
wanda yanzu ba’a amfani da shi.
14- Sayan kayan gidan baqi na Gumau don sun qone214(£43) (Harxo
Wonu ya kawo shawarar) -1968
15- Gyaran rumfunan kasuwar Gumau (dave na rumfuna biyu da rufin
kwano na rumfuna biyu) (£30) (Alhaji Yunusa Gumau ya kawo
shawarar) - 1968.
16- Yin gadar katako a hanyar Badikko zuwa Jallakoji (£20) (M. Ladan
Lame ya kawo shawarar) - 1968.
17- Sassaben itatuwan cikin garin Gumau da suka yi duhu215 (£8)
(Waziri Nababa ya kawo shawarar) – 1968
18- Gina rumfar kwano a kasuwar Badikko (£200) – 1969
19- Tona shadda a kasuwar Gumau, don rage yawan qazanta (£5) –
1969
20- Gyara shaddar Caji-ofis xin Gumau (£2:10:0) – 1969

KANSILOLIN GUNDUMAR WONU 1976-2021

1- Alhaji Audu Safe


2- Alhaji Musa Mai kwabbai
3- Yohanna Bala
4- Maigari Sanga (care taker)
5- Adamu Xanhasan
6- Xanqasim Maikuxi DPN (Democratic Party of Nigeria)
7- Alhaji Yakubu Bula (care taker)
8- Ladan Ahmed (care taker)

214
Duk kayan gidan baqi sun qone a dalilin gobara da aka yi a gidan sarkin kudu. Nan
shawara ya tsayu akan tun da zakuna biyu ne a gidan a sayi kaya iri biyu, kuma bambance
kayan da za’a sayo, kayan xaki na farko don qananan baqi (baqin yau da gobe). Kayan
xaki na biyu don manyan baqi idan sun zo
215
Domin lokacin garin ya yi kurmi, ya yi sunkuru.
163
9- Ahmad Danka (march 1996-june 1997) caretaker
10- Dauda Dakama 1999-2003
11- Musa Audu 2003-2007
12- Maitala Sama’ila 2007-
13- Maijama’a Bojuwa APP (All Peoples Party)
14- Yusuf Xankaka Hoxa APC
15- Umar Zakariyya’u 2020-yau PDP

FARARRUN AL’AMURAN GUNDUMAR WONU

1- A ran 14-01-1955 Bature da ke lura da barikin kuza na Pingel, ya


nemi Hausawan garin su tashi, su bar wa leburorinsa garin domin
duk garin kamfaninsa ne. Hausawan Pingel suka ce sun gina
gidajensu tun turawa bas u sayi filaye ba.
2- Ran 14-12-1955 wani bature da ke aikin hanyar Magama (Gari)
zuwa Gumau ya harbi kansa da bindiga ya mutu a Badikko, cikin
gundumar Wonu. Abin day a tsai da aikin wannan hanya, ba’a sake
taso shi ba sai a shekarar 1978. Ranar faruwar abin said a sarkin
yaqi, hakimin qasar Lame, da Di’o, da Razdan da likita daga Jos
duk said a suka zo Badikko.
3- Ran 06-09-60 kura tax auke gawar wani, kafin ayi mata sutura a
Zingiri, da ke gundumar Rishi.
4- Ran 25-04-60 kogin Dulumi ya ci mutum tara a mashigin Tukutu.
5- Ran 09-02-62 wani mutum sunansa Afolo, ya huda cikinsa da wuqa
a Luggugol, amma bai mutu ba. An tambaye shi dalili, y ace,
zuciyarshi c eke vaci. Ya hau bishiya ya faxo, bai mutu ba, sai ya sa
wuqa ya huda cikinsa. Wuqar ta huda fata, amma bat a huda hanji
ba.
6- Ran 21-09-1963 aka yi wata tsawa a Mana da gundumar Wonu,
wacce ta kasha shanu 7, tumaki 10 na Alhaji Ciroma xan Tumbaxi,
wanda rugarsa ke Mana.
7- Ran 15-02-1964 Allah ya yi wa sarkin yaqi Usmanu Babale rasuwa
a Bauci.

164
8- Ran jumma’ah 10-04-1964, kogin Dulumi ya ci wasu ’yammata
guda biyu, a Izar. Sun je itace ne, sai suka rates, za su yi wanka. Sai
Fatu ta cewa Sahura da Hairanatu, “kada ku shiga ruwan nan.” Sai
suka ce, “ai sun saba wanka a rowan.” Sahura da Hairanatu suka
faxa wajen zurfi, nan take suka mutu. Ita Fatu ta sa hannu ta jawo
Asabe da Lami. An yi musu sutura a Bakin kogi.
9- Ran 15-08-1964 sabon hakimin qasar Lame, sarkin kudu Salmanu
ya fita rangadi zuwa garuruwan Tulu, Rishi, Wundi, Zalau, da
Pingel don ganin jama’ar qasarsa, da gaisawa das u.
10- Ran 07-03-1967 majalisar sarkin Bauci ta buxe aikin kisan
gwaggo,216 da jan biri, da gadi, da kura da ake yi shekara-shekara a
qasar Lame. Shugaban aikin kisan gwaggo na qasar Lame na
wannan shekarar shi ne Malam Garba Xanbaqi.
11- Ran 12-11-71 aka aiko da dokar hana yawo tsirara, da xaur ganye
da wasu qabilu ke yi, lalle su daina. Daga cikin qabilun da ke xaura
ganye asan nan, akwai Ribinawa da Sangawa, Zulawa da
Zarandawa.
12- Ran litinin 18 Fabrairu 1979 da misalin qarfe 2:30 na rana aka wata
mummunar gobara a Ririwai cikin gundumar Wonu, bayan galibin
mazaje bas a gida, sun tafi cin kasuwar Gumau. Ta qona gidaje
bakwai, xakuna 25, katakon dawa 27 da dami 32, takardun kuxi
N1,535, da kayayyaki masu yawa.
13- Ran lahadi 29-03-1981 zaki ya zo rugar Harxo Mamudu da ke
Sanga, ta gundumar Wonu, ya hana mutane da shanunsu bacci.
14- Ranar 24-03-1985 aka yi zaven mai littafin Unguwar Kadiri inda
mutane suka taru suka zavi Muhammadu Babaji a matsayin

216
Asali qasar Lame qasa ce mai yalwar itatuwa da dabbobi iri-iri a cikinsu. To, duk
shekara sai gwaggwani da biroyi sukan yi wa mutane ta’adi a gonakinsu. Kuma day a keg
alibi lokacin tafiyar qafa ake yi. Gwaggwani sukan tare mutane a hanya, musamman ma
mata, kura da gadi kan far ma al’umma da dabbobinsu, abin da ke damun jama’a matuqa.
To, duk shekara sai hukuma ta ke b a da aikin kwangilar kisansu. Kuma har shela ake yi
cewa duk wanda ya harbi kura, gadi, ko biri mai wutsiya to, ya kai fatar kura da gadi da
wutsiyar biri Bauci, ‘Central Office’ za’a biya shi fam xaya na kowanne fata day a harba.
A kan buxe aikin ne da kaka sadda amfanin gona ya nuna, da kuma lokacin farkon
damina.
165
sarkinsu. Waxanda suka yi zaven sune ; Mai Unguwa Sabo, Mai
Unguwa Husaini, Yero Nuhu, Garba Maikanti, Liman Sani, da
Ahmadu Maiwunti.
15- Ran lahadi 09-09-1995 Allah ya yi wa mai lttafin Badikko M.
Sa’idu cikin gundumar Wonu rasuwa.
16- A ran 31-08-1956 aka sauke Mai Gundumar Ririwai sarki Abdu
daga sarautarsa. Bayan ya shekara ashirin da biyar da wata bakwai
yana sarauta (1932-1956).
17- Ranar 07-08-1964 sarkin kudu Salmanu ya tafi rangadi gundumar
Tilden Fulani, saboda takardar da sarkin Tilde ya aiko masa cewa
wani mai littafinsa da ake cewa sarkin Jimfi, ya shaidawa sarkin
Tilde cewa shi ya gaji da sarauta bay a so, ya ba xansa. Sarkin Tilde
ya kais hi ga hakimi, ya sheda masa haka da bakinsa. Hakimi ya sa
aka zo da manyan garinsu, ya tambaye su, ko akwai wani dalili da
suka sani wanda ya sa bay a son sarauta? Ya ce shi dai ya gaji ne
kurum, yana buqatar ya huta, ya bar wa yara su ma su tava.
18- Ranar 17 Nuwamba 1964 da sassafe Mai littafin Buri ya aiko
yaronsa wajen Harxo Wonu cewa a gaya masa ya bar sarautarsa,
don ba zai iya ci gaba ba, saboda tsufa ya kama shi, kuma bay a
gani, ga kuma ciwo, san nan bas hi da mai taimako. Bayan aikawa
Bauci, sai suka yardar masa ya sauka, kuma aka yarda a zavi sabon
mai littafi.
19- Ranar 6 Janairu 1974 Jauro mai littafin Uban Dawaki (Unguwar
Kadiri) cikin gundumar Wonu ya sanar da murabus xinsa daga
sarauta. Kuma hukuma ta amince masa ran 13 Mayu 1974.
20- Ran 10 ga Janairu 1976 sarkin kudu Salmanu ya yi murabus ga
barin kujerarsa ta hakinci.
21- Ran 10-10-1956 mutanen Ririwai cikin gundumar Wonu suka zavi
Barde a matsayin mai littafinsu, bayan tuve mai gunduma sarki
Abdu.
22- Ran Jumma’a da sassafe 1 Fabrairu 2019 Allah ya yi wa Sarkin
yaqin Bauci, hakimi qasar Lame M. Muhammadu Maidawa
rasuwa.

166
23- Ran 20 ga Mayu 1962 mutanen Mana cikin gundumar Wonu suka
zavi Ciroman Mana M. Usman ya yi musu sarautar littafinsu.
Manyan garin da suka zave shi su ne ; Galadiman Mana, Sarkin
noma, Ubandoman Mana, Sarkin Hausawan Pingel, Ajiyan Mana.
An yi zaven bisa sa idon ’yan majalisar gundumar Wonu, da kuma
’yan majalisar Hakimi.
24- Ran 26 Yuli 2015 Allah ya yi wa M. Umar Dangana mai littafin
sarkin yamma cikin gundumar Wonu rasuwa rasuwa.
25- Ran 15 Fabrairi 1965 mutanen Buri cikin gundumar Wonu suka
zavi Galadima Abdu ya yi musu sarautar littafinsu, bayan saukar
magabacinsa saboda tsufa. Manyan garin da suka zave shi su ne ;
Wakili Buba, Baya, Soba, Audu, Boka, Maimako, Dabo, Bala, Mai
Unguwa Yakubu. An yi zaven a gaban wakilan gunduma da na
hakimi.
26- Ran 25 Afrilu 1970 mutanen Unguwar Kadiri cikin gundumar
Wonu suka zavi M. Jauro ya yi musu sarautar littafinsu. Kuma
majalisar gunduma ta yarda da zavensu
27- Ran 30 Maris 1970 mutanen Ririwai cikin gundumar Wonu suka
zavi M. Muhammadu Inuwa ya sarauci littafinsu. An yi zaven bisa
sa idon wakilan majalisar gunduma da ta hakimi.
28- Ran 5 Mayu 1973 mutanen Gakuyel cikin gundumar Wonu suka
zavi ’Yan kwana ya yi musu sarautar littafinsu. Kuma majalisar
hakimi ta amince da zavensa. Da farko an tura su a naxa shi, sarki
bai samu naxa shi ba, sai a zuwa na biyu ran 24 Mayu 1973.
29- Ran 20 Mayu 1974 mutanen Kwacchaho cikin gundumar Wonu
suka zavi M. Gero ya yi musu sarautar littafinsu. Kuma majalisar
hakimi ta amince da zavensa.
30- Ran 20 Mayu 1974 mutanen Unguwar Isma cikin gundumar Wonu
suka zavi Gwamne ya yi musu sarautar littafinsu. Kuma majalisar
hakimi ta amince da zavensa.
31- Ran 6 Yuni 1974 mutanen Unguwar Kadiri cikin gundumar Wonu
suka zavi M. Mu’azu ya yi musu sarautar littafinsu, bayan barin
magabacinsa. Kuma majalisar hakimi ta yarda da ingancin zaven.

167
32- Ran 11 Nuwamba1977 mutanen Buri cikin gundumar Wonu suka
zavi Wakili Buba Buri ya yi musu sarautar littafinsu, ba tare da
muhawara ba.
33- Ran 11 Nuwamba1977 mutanen Mana cikin gundumar Wonu suka
zavi Ciroma Bawa (M. Dauda Idris) ya yi musu sarautar littafinsu,
ba tare da muhawara ba.
34- Ran 1 Mayu 1979 mutanen Unguwar Tsamiya cikin gundumar
Wonu suka zavi M. Adamu xan sarkin day a mutu ya yi musu
sarautan littafinsu, bayan mutuwar sarkinsu na da. Ya ci zave ba
tare da hamayya ba, kuma majalisar hakimi ta yarda da zaven da
aka yi.
35- Ran 25 Oktoba 1984 mutanen Unguwar Tsamiya, cikin gundumar
Wonu Galadima da liman, da sauran manyansu suka zavi M. Inuwa
ya yi musu sarautar littafinsu.
36- Ran 16 Afrilu mutanen Buri cikin gundumar Wonu suka zavi M.
Abdulqadiri ya yi musu sarautar littafinsu
37- Ran 6-2-2021 aka naxa Malam Umar Adamu Umar (Babaji) mai
littafin sarkin Gabas na Wunti.
38- A ranar 23-04-1985 mutanen Unguwar Kadiri da ke gundumar
Wonu suka zavi Muhammadu Babaji ya zamo sarkinsu (Mai
littafi), waxanda suka yi zaven su ne ; Mai unguwa Sabo, Mai
unguwa Husaini, da Yaro Nuhu, da Garba Maikanti, da liman Sani,
da Ahmadu Maiwunti.



168
LAME

Domin fahimtar tarihin qasar Lame da kyau, zai yi kyau mai karatu ya
fahimci wannan shimfixa.

SHIMFIXA

1- Turawan mulkin mallakan Ingila sun qwace mulkin qasar nan daga
hannun sarakunamu daga 1900-1903.
2- Gwamnati ita ce muqaman da turawa ko ’yan siyasa ko sojoji ke
riqe da su, kuma kuxi, ikon zartarwa a hannunsu ya ke.
3- En’e (N.A.) ita ce hukumar mulkin mallakar turawa da ke mulkin
qasa ta hannun sarkin qasar, gwamnati ta yarda da ita, kuma suna
cikin tsarin mulki. Sarki shi ne shugabansa. Manufarsa rage ikon
sarakuna a cikin mulkin qasa, don babu kuxi da ikon zartarwa a
hannunsu.
4- An fara mulkin En’e (mulkin turawa ta hannun ’yan qasa) a 1914,
kuma sojoji sun rushe shi ran 27 Mayu 1967.
5- Ran 27 Mayu 1967 aka maye samfurin mulkin En’e (N.A.) da zai
ba sarki dama ya yi mulki ‘wahdahu la sharika lahu’ (Sole Native
Authority System) da L.A. (Local Authority). Manufarsa shi ne qara
rage ikon sarakuna a cikin mulkin qasa.
6- Qaramar hukuma ko L.G. (Local Government) ita ce hawa na qasa
na gwamnati. ’Yan majalisunta su ne Kansiloli, Ciyaman shi ne
shugabansu. Manufarsa zare hannun sarakuna baki xaya daga
kundin tsarin mulkin qasa.
7- Qasar Lame daga 1812-1927 ita ce ;
i- Jos ta Arewa.
ii- Jos ta Kudu (Vukur), mai gundumomi huxu; Du, Gyel, Kuru
da Vwang.

169
iii- Jos ta gabas217 (Jarawa) mai gundumomi biyar ; Fedare,
Fobur, Fursum, Maigemu da Shere.
iv- Gundumomin Jama’a, Zaranda, Mara, Palama daga Jama’a
District.
v- Toro District mai gundumomi biyar ; Toro, Tulai, Tilden-
Fulani, Ribina da Jarawa
vi- Lame District mai gundumomi shida ; Wonu, Lame, Zalau,
Rishi, Tama da Rahama.
8- Qasar Lame daga 1927-1950 ita ce
i- Jarawa District mai gundumomi biyar ; Fedare, Fobur,
Fursum, Maigemu, Shere.
ii- Toro District mai gundumomi biyar ; Toro, Tulai, Tilden-
Fulani, Ribina.
iii- Lame District mai gundumomi shida ; Wonu, Lame, Zalau,
Rishi, Tama da Rahama.
9- Qasar Lame daga 1950-1976 ita ce;
i- Toro District mai gundumomi biyar ; Toro, Tulai, Tilden-
Fulani, Ribina.
ii- Lame District mai gundumomi shida ; Wonu, Lame, Zalau,
Rishi, Tama da Rahama.
10- Qasar Lame daga 1976 -2021 ita ce;
i- Lame District mai gundumomi shida ; Wonu, Lame, Zalau,
Rishi, Tama da Rahama.

LAMAWAN ASALI BA SU CIN NAMAN AKUYA

Lamawa ko ka ce Wuntawa na asali bas u cin akuya, saboda wasu


dalilai na qashin kansu, ko kuma wata al’ada da ta shafi gidansu ko
danginsu ko qabilarsu, ko kuma don camfi da jahiltar asalin addini. Haka
ma Lamawa saboda zamantakewarsu da Wuntawa, da kuma cewa al’adar

217
mai karatu kada ka ruxe, idan na ce ‘Jos ta gabas’ ina nufin qasar Jarawa, haka idan n
ace ‘Qasar Jarawa’ ina nufin Jos ta kudu. Bambancin shi ne qasar Jarawa ko ‘Jarawa
District’ wannan san nan tana bin qasar Lame ne. Amma sadda aka maid a ita Jihar Filato
sadda Janar Murtala Muhammed ya qirqiro jihohi a 1976, sai ake kiranta Jos ta gabas.
170
mutane kullum masu kwaikwayo ne ga sarakunansu, wasunsu bas u cin
naman akuya, wannan al’amari kuwa ya daxe, duk da cewa an samu
raguwar lamarin. Wasu camfawa suka yi cewa idan sun ci namanta za su
riqa yin halayya da xabi’u irin na ta, kamar yadda wani ya ce min, “Ka da
ka mance, akuya a kowanne lokaci tana kuka da damun mutane, sai na ke
ganin idan naci namanta zan yi hali irin na ta.” Dukkan gidajen sarautar
sarkin yaqi, fulaninsu da Bare-barinsu, bas u cin naman akuya. Su Bare-
barin wai suna tsoron ciwon kuturta ke hana musu cin naman akuya. Su
kuwa fulanin (Wuntawan) dalilinsu shi ne wai saboda wanda ya kafa
daular Sakkwato, Shehu Usmanu xan Hodiyo ba ya cin naman akuya, su
kuma jininsa ne, shi ya sa su ma ba za su ci ba. Duk da cewa cikin duk
littattafan da Shehu ya rubuta ba’a ga inda ya haramta cin naman akuya ba,
amma su duk da haka sun zavi su kafe a kan wannan. Amma ko su
wuntawan ba dukkansu ne bas u cin naman na akuya ba, don wani mai xan
sani cikinsu ya ce min, “Ba ni ganin ba mu cin akuya ne don Shehu bay a
ci, sai don kare lafiyarmu, domin a bayanin da na samu, babu naman da
Shehu xan Hodiyo ke so kamar naman akuya da nononta. Ya bar cin
naman ne kan alwashin day a yi wa Allah, dangane da wani yaqi day a fita,
y ace in ya samu nasara zai bar cin abinda ya fi so a rayuwarsa. Hakan ya
say a bar cin naman akuya. Wani dattijo day a daxe da rabuwa da wannan
camfi yace, “Ni kam Bawunte ne amma ina cin naman akuya, a shekarun
baya duk sadda na ci naman sai quraje su fito min, amma na qi dain awa,
gas hi yanzu ko na ci babu abinda zai same ni.” Wani kuma ya ce, “Mu da
muka yi imani da haka, ba mu cin naman akuya don tsoron cutar kuturta,
kuma da mun ci sai ka ga quraje sun bayyana a jikimmu, amma yanzu ga
yarammu nan dab a su yi imani cewa idan sun ci wani abu zai same sub a,
suna ci kuma ba mu ga wani abu ya same sun ba.” A kan ce tsafi gaskiyar
mai yi, wani yace, “Su duk gidansu ba su cin naman akuya, saboda wani
dalili na su. Bayan na girma an fara aikena yin cefane, mahaifina kan
gargaxe ni cewa kada na kuskura na sayo naman akuya. “Ni a zato nab a
komai a naman, wata rana na tafi yin cefane nag a naman akuya, na sayo.
Da aka dafa shi a gidammu mahaifina ya ci nan ta key a rikice mana.
Quraje suka firfito ko’ina a jikinsa, kuma jikinsa ya riqa rawa. Muka yi
sauri dashi zuwa asibiti, a can aka gano naman akuya ya ci. Tun daga nan

171
ban qara karambanin sayo naman akuya ba, kuma ni ba ni ci.” M. Bala
malamin sarki sadda na tambaye shi, ko yana cin naman akuya? Ya ce, “Ni
mutumin Lame ne, amma ba Bawunte ba ne, ko da dai na tashi a cikinsu,
saboda haka ba ni cin naman akuya, amma dukkan iyalaina suna ci. Ni ne
ma ke saya musu.” Da na tambaye shi ko in ya ci naman akuya akwai abin
da zai same shi? Sai y ace, “Qwarai kuwa, don na tava ci sau xaya a Lame,
da dare ya yi sai ciki nay a kumbura, sai ta hanci, ta baki na ke numfashi.”
Shi kuwa M. Xan Usmanu da na tambaye shi, ganin shi mutumin Lame ne
ko yana cin naman akuya? cewa ya yi, “Ni kam lalle xan Lame ne, amma
ni ina ci, iyalaina ma suna ci.” Da na tambaye shi ko ya san wasu a Lame
da su bas u ci, kuma ko me ya sa bas u ci? Ya ce, “Jingim ma kuwa, wasu
ko warinta suka ji ma sais u yi amai, wasu kuma idan suka ci sai cikinsu ya
yi ta ciwo. Wasu kuma sukan ce idan sun ci za su yi ta amai ne, har ya kai
su ga mutuwa.” Da na tambaye shi wannan abu a littafi aka ganshi, ko
kuwa camfi ne? sai y ace, “ To, shi dai kam bai sani ba.” Da kuma na
tambaye shi ko akwai waxanda ya san da gidansu ba’a ci, amma yanzu
yaransu suna ci? Sai y ace, “Lalle kuwa, su ma ya sansu da yawa, kuma
babu abinda ya samu yaran.” Wani mai sana’ar fawa y ace, “Idan ma
naman yana da matsala a gare su, to, can baya ne, yanzu bai yi musu
komai, don kuwa yanzu muna yanka akuya, kuma muna ganinsu waxanda
da can bas u ci, yanzu kuma suna saye.”

QASAR LAME

Qasar Lame qasa ce da ke gabas maso kudancin qasar Zazzau, amma ba


qasar Zazzau ce ba, don ita tana cikin qasar Bauci ce.

YAWAN MUTANEN QASAR LAME A 1979

Qiyasin jimillar mutanen da ke zaune a qasar Lame a shekarun 1979,


qasar Lame a 1979 ita ce abinda ake kira ‘Lame district’ a yau, su mutum
dubu sittin da biyar da xari shida da talatin da bakwai (65,637). Ga su bisa
tsarin gunduma kamar haka :

172
Gunduma Yawan mutane
1 Lame 6,670
2 Tama 11,173
3 Zalau 11,626
4 Wonu 14,138
5 Rishi 10,657
6 Rahama 11,053
Ma’aikata 320
Masu biyan haraji 9,757

YAWAN MUTANEN QASAR LAME A 2021

Amma a yau da muke rubutun littafin nan 2021, qasar Lame na da


qiyasin jimillar mutane dubu xari da saba’in da biyar, da xari bakwai da
biyu (175,702).

IYAKOKIN QASAR LAME 1812-1927

Qasar Lame ta gabas ta yi iyaka da tsohuwar qasar jama’a, in da sarkin


yamma ke mulki. Shi kuwa sarkin yamma, xaya daga cikin ’ya’yan
sarautar Bauci ake naxowa ya yi sarauta a wajen. ta arewa maso gabas ta yi
iyaka da qasar Ningi. Ta arewa sak ta yi iyaka da qasar Kano. Ta yamma
maso arewa ta yi iyaka da qasar Zazzau, a yayin da yamma da ta kudu ta yi
iyaka da Mangu.

IYAKOKIN QASAR LAME 1927-1950


(CIRE JOS DAGA QASAR LAME)

Turawan mulkin mallaka sun cire lardin Jos daga qasar Bauci a 1927.
Sun kuma yi wa qabilar Birom sarki mai suna ‘Bongom’ a 1935, saboda a
san nan sune qabilu mafi rinjaye da ke zaune a wannan yanki na tsakiyar
Nijeriya. Tun daga nan (1927) sai ya zamo ana maganar qasar Lame ba
tare da ambaton qaramar hukumar Jos ta arewa da ta kudu ba.

173
IYAKOKIN QASAR LAME 1950-1976
(CIRE GUNDUMAR JARAWA DAGA QASAR LAME)

Turawan mulkin mallaka sun cire qasar jarawa218 daga qasar lame a
shekarar 1950, dalili kuwa duk abin da Allah ya yi nufin aukuwarsa, idan
ajalinsa ya zo sai wani sanadi ya faru don abin ya kasance tamkar yadda
Allah ya nufa. Wani Razdan na Bauci ne ya tafi rangadi qasar jarawa a
shekarar 1948 - san nan kuwa tuni an yi wa maqwabtansu Birom sarki a
Jos, tun cikin shekarar 1935- cikin jawabi da ya ke musu sai ya ce, “Ko
kuna so a yi muku sarkinku na jarawa, kamar yadda aka yi wa Birom?” sai
suka amsa baki xaya cewa, “I, muna so! Muna so!!” An ce a lokacin da
Razdan ya yi wannan magana, har Di’on gundumar Toro sai da ya ce lallai
Razdan ya yi kuskure da ya tsokano wannan zance. Sai Razdan ya ci gaba
ya ce, “Amma fa ba yanzu ba, sai mun fara kafa muku kotun gargajiya
tukuna, wacce idan ta yi shari’ah, ba za’a zartar ba, sai kotun Toro ta duba,
ta tabbatar.” Suka ce sun yarda. To, ana nan kan haka, a shekarar 1950, sai
suka ce ba zasu bai wa sarkin kudu Muhammadu Sani haraji ba, don kuwa
an ce za’a yi musu qasar kansu, har yanzu ba’a yi ba. Idan sun ci gaba da

218
Jarawa ko Afizere, Afusari, Afizarek, Fezere, Fezerek, Fizere, Izere, Jarawa, Jarawan
dutse, Jari, duka wannan suna ne da suka yardarwa kansu a kira su dashi, ko da yadda ake
lanqwasa harshe ake kiran sunayensu ya sha bamban, amma dai duk yadda ka kira yana
komawa ga ma’ana guda ce, wata qabila dake zaune a tsakiyar Nijeriya da ake kira
jarawa. Qabilun Fulani, Anaguta, Irigwe, da Birom su ne maqwabtansu na kusa-kusa.
Asalinsu suna zaune a duwatsun Cawai da ke kudancin Zazzau ne, sai suka yi hijira suka
qara nausawa kudu, suka zauni tsaunukan kudu maso yammacin yankin qasar Lame in da
ake kira yau (qaramar hukumar Jos ta gabas, da ta arewa, da Mangu da Toro). Sun
gwammace wa kansu zama akan duwatsu ne, don su zamo kariya garesu daga harin Fulani
musulmi masu jihadi. Suna da tsarin sarauta irin ta su, sunan babban sarkin su Agwom,
kuma yana da hakimai biyar masu yi masa biyayya a garuruwa daban-daban, garuruwan
su ne Fobur, Forsum, Maigemu, Shere da Federe. Addinin musulunci shi ne addinin farko
day a fara zuwa gare su, tun da suna qarqashin sarakunan musulmi ne, sai kuma addinin
kirista ya je gare su daga bisani, ta hannun wata qungiyar mishan da ake kira ‘Sudan
Interior Mission’ Jarawa mutane da suka surka addini da al’adu, kowanne irin addini suke
bi, idan lokacin bikin al’adarsu na shekara ya yi sukan haxu su yi bukukuwa, har ma da
wani irin rawan al’ada da su ke kira ‘Asha ruwa’ wanda idan aka tashi yi musulmi da
kirista kowa sai ya taka shi.
174
bai wa wani sarki dab a na sub a haraji, to, babu ranar yi musu sarauta
kenan. Shi kenan sai aka yi musu hakinci, sarkin Bauci ya naxa musu
hakimi, wanda ake kira sarkin yamma, ko sarkin jarawa, maimakon sarkin
kudun da gidan sarautar sarkin yaqi ke naxa musu. Shi kuwa sarkin
yamma, ga asali yana sarauta a tsohuwar jama’a ne, sai aka xauke cibiyar
mulkinsa daga tsohuwar jama’a aka mayar da ita Unguware cikin qasar
jarawa. To, da ma qasar jarawa tana haxe da gundumar Toro ne, saboda
haka da jin jarawa sun sami mulkin kansu, sai mutanen gundumar Toro,
suka ce, su kam faufau ba za su bi jarawa ba, amma sun yarda su ci gaba da
bin ’yan’uwansu Lame. To, sai aka maid a Toro, Ribina da Tilde qarqashin
mulkin sarkin yaqi. Tun daga nan (1950) sai ya zamo ana maganar qasar
Lame ba tare da qasar Jarawa ba.

IYAKOKIN QASAR LAME 1976-2021

To, ana nan kan ran 3 ga watan Fabrairu 1976, aka cire qasar jarawa
daga masarautar Bauci baki xaya, aka mai dasu qarqashin masarautar
Birom, suna bin sarki Bongom Jos. Kuma a ran nan aka raba jihar Arewa
maso gabas, aka raba ta gida uku; Barno, Bauci da Gongola. Aka cire
Bauci daga bin Barno zuwa jiha mai cin gashin kanta, aka sanya cibiyar
mulkinta birnin Bauci. Kuma dai a ran nan aka cire gundumar Toro, Ribina
da Tilden Fulani daga qasar Lame. Aka sanya Toro xaya daga cikin
qananan hukumomi 16 da sabuwar jihar Bauci ke qunshe dasu, kuma
ma’abuciyar gundumomi uku ; Toro (ta qunshi Ribina da Tilde), Jama’ah
(ta qunshi gundumar RAUTA, da GEJI da aka gutsuro daga ZUNGUR
qasar Galadiman Bauci. Da MARA da ZARANDA da aka gutsuro daga
LAME qasar sarkin yaqi) Aka yi musu cibiya garin ZARANDA. Amma ba
ta daxe ba a Zarandan saboda wasu matsalolin da aka samu da asalin masu
mulkin wurin, to, sai aka mai da ita NABARDO. Sai aka ci gaba da turo
’ya’yan sarkin Bauci suna sarautar hakinci a wurin. Kuma tun daga nan
(1976) sai ya zamo ana maganar qasar Lame ba tare da ambaton gundumar
Toro, Ribina da Tilde ba. Da Lame mai qunshe da gundumomi shida,
Wonu, Zalau, Rishi, Tama, Rahama da Lame. Ta arewa maso yamma ta yi
iyaka da qasar Zazzau akan iyakar gadar Rahama. Idan ka yi arewa kashiga

175
jihar Kaduna. Ta yamma ta yi iyaka da qasar Filato a dutsen Sanga. Idan ka
haura dutsen ka fita daga qasar Bauci. Ta gabas maso kudu ta yi iyaka da
gundumar Mara ta qasar Jama’a a rafin Gyam, idan ka yi gabas da rafin
kana cikin gundumar Mara, idan ka yi yamma da shi kana cikin qasar
Lame. Ta kudu ta yi da ta yi iyaka da dutsen Fanshanu, gari na qarshe cikin
qasar Lame shi ne Dabo, kana shuxe shi sai dutsen Fanshanu. Ta kudu
maso yamma ta yi iyaka da gundumar Ribina idan ka gota dutsen farko da
ke kudu da Geljaule, daidai wata ’yar wuriya. Ta arewa sak, da ta arewa
maso gabas ta yi iyaka da Ningi.

QARAMAR HUKUMAR LAME

An yi bikin kafa sabuwar qaramar hukumar Lame mai hedkwata a Gumau


a qofar fadan hakimi, ranar asabar 03 Oktoba 1981. Jama’a ta taru danqam
daga sassan gundumomin qasar Lame baki xaya, aka yi ta wasanni iri-iri
na gargajiya. Kuma an rushe ta ran 31 Disamba 1984 bayan juyin mulkin
sojoji.
YARE DA QABILUN QASAR LAME 1976

Yaren da qabilun qasar Lame a 1976 su goma sha shida ne. Akwai
abubuwa da dama waxanda suka haxa waxannan qabilu, babbansu shi ne
fatar jiki, don duka baqaqe ne, kuma dukkansu suna jin Hausa. Yanayin
zamansu duka xaya ne, haka fasalin garinsu da na gidajensu. Sai dai
musulminsu suna zagaye gidansu da danga ko katanga, waxanda ba
musulmi ba kuma bas u damu da yi ba. Akwai masu qabilanci cikinsu,
akwai marasa shi. Akwai masu son mutane, akwai marasa so.
1- Fillanci
2- Sanganci
3- Guranci
4- Bambaranci
5- Yaren mutan Gwa
6- ” Shau
7- ” Kyare
8- ” Kurama

176
9- ” Gananci
10- ” Shakobo
11- ” Zirya
12- ” Gusawa
13- ” Limoro
14- ” Jere
15- ” Narkutawa
16- ” Miyango

YARE DA QABILUN QASAR LAME 2021

Amma ya zuwa shekarar 2021, duk harshen Hausa ya lanqwame


waxannan yare, waxanda ma bai lanqwame baki xaya ba, to, ya raunana
su. Yarukan da suka yi ragowa cikinsu su ne :
1- Fillanci
2- Sanganci
3- Guranci
4- ” Zirya
5- ” Gusawa
6- ” Limoro
7- ” Narkutawa
8- Gyamawa

HAULOLIN FULANI DA AKE SAMU A QASAR LAME

1- Gorkayi : Galibinsu farare ne, masu madaidaitan jiki. Suna da


kyawun hali kuma suna da kunya. Su xin ma xaki –xaki ne, akwai :
a- Yãmadãwa219
b- Bardãwa
c- Gayãkuma
d- Kêrãwa
e- Buxãwa
219
Su ne masu siraran uku-uku dogaye a gefen fuskarsu. Suna da qoqarin yanka saniya
lokacin suna. Sai dai a yanzu sun shahara da satar satar shanu da garkuwa da mutane.
177
f- Sawanko’e
g- Hadãwa
h- Lumbudãwa220
i- Fãramãwa
j- Jafûnu
k- Kontãwa
l- Tubãrãwa
m- Yarkãwa221
n- Kãyãwa
o- Barbãwa
p- Dabãwa
q- Ravãwa
r- Mûsãwa
s- Jaurãwa
t- Labawa (Labankwai)
u- Gauxãwa
v- Gamãwa222
2- Yãvãje : A da su ne asalin bararoji mutanen daji, da ba su san
komai ba sai kiwo. Amma yanzu suna haxa noma da kiwo, suna
shiga gari su yi gini su zauna a ciki. Kuma sun fi yawancin qabilun
fulani shiga Izala, kam ban da Kacaccare. Sun shahara da yawan
shaxi, kuma suna yi ne tare da ’yan’uwansu Rãhãje. Daga cikinsu
akwai :
i- Kollãwa (Kollonko’e)223
i- Dexãwa

220
Hadawa da Lumbudawa asalin iyayensu Lumbudu da Hado wa da qani ne, uwarsu
xaya ubansu xaya. Sai kowa ya kafa gidansa daban da na xan’uwansa, rafi ne ya raba su.
Sai waxannan suna ce za mu gidan Lumbudu, waxancan kuma suna cewa za mu gidan
Hado. To, tsawon zamani sai ya sa aka taqaita ana cewa waxannan Lumbudawa,
waxancan kuma Hadawa.
221
Su ne masu zane n bibbiyu gajejjeru a qasar idaniyarsu.
222
Su ne mazauna qasar Filato da wani yankin qasar Bauci (qasar Lame) da Nasarawa.
Galibinsu baqaqe ne. Suna noma suna kiwo, kuma suna zama a gari. Suna da qoqarin
karatun addini.
223
Su ne mutanen Tamfol (Ladduga).
178
ii- Gojãwa
iii- Wãnãwa
iv- Shalvãwa
v- Dovvãwa
vi- Durbãwa
vii- Baikãwa
viii- Dùrãwa
ix- Lùmãwa
3- Rãhãje : sun fi duk qabilar fulani siririntaka. Kuma kyawawa ne
farare. Sun fita daga Yavaje, sai suka zamo abokan wasansu.
4- Bóxi
a- Yogomãwa224
5- Kûmãwa
6- Tûbãwã
7- Jãjãwa
8- Ûdãwa (Ûdãji)225
9- Vokoloji226
10- Ba’aãji227
11- Kacaccare : Suna zama a gari, suna haxa noma da kiwo kuma sun
shahara da auren qabilu.
a- Kirgiji
b- Fiktoji
c- Kofoji
d- Boxi
e- Gijiyanko’in
f- Bonsankin (Bonsanko’in)
g- Wuntankin (Wuntanko’in)
224
Su ne mazauna qasar Kafin Xanyamusa. Suna kiwo, amma ba su bin labi, kuma ba su
zama a babban gari sai a qauyuka, a cikin ginannun gidaje. Kuma ba su cika jin fillanci
ba, sai in sun koya.
225
Asalinsu mazauna qasar Ningi ne. Sun fi shahara da kiwon tumakin Uda, ba kasafai
suke kiwon shanu ba.
226
Su ne mazauna dajin Falgore. Sun shahara da fashi da satar shanu.
227
Suna noma suna kiwo. Hasali ma matansu sun qware a tatsar nono. Suna da qoqarin
yanka saniya yayin bikin aure.
179
h- Dallaje (Dallanko’in)
i- Gayaje (Gayajiko’in)
j- Buli (Bulanko’in)
k- Boronko’in

Dukkan waxannan haula na fulani a yanzu akwai su ko danginsu a qasar


Lame. Amma da can kafin rikici ya yi yawa tsakanin qabilu, fulanin da aka
sani mazauna qasar Lame ba su kai haka yawa ba.

LABARIN ASALIN SANGAWA


Asalin Sangawa suna daga cikin qabilar Zûmãwa ne, ’yan’uwan su da
suka fito gindi xaya su ne, Miyango, Rukuba, Jarawa, Gurawa, Bambarai,
Kurama da Manawa. Asalinsu duka daga qasar Barno suka yo hijira zuwa
yamma, tun cikin qarni na goma sha shida miladi, saboda qyamatarsu ga
sallah da addinin musulunci, suka zauni yankin yammacin Bauci, wanda a
lokacin duka arna ne. Lokacin da Malam Yakubu ya karvo tutar jihadi daga
wajen Shehu Xanhodiyo, ya kuma fara jihadi a qasar Bauci, sai waxannan
qabilu suka haye kan duwatsu, suka kafa garin Kwandon qaya a kan dutsen
Fanshanu saboda tsoron kada masu jihadi su ribace su. Lokacin da aka
tarwatsa ta, sai wasu qabilunta suka yi yamma wasu kuma suka yi wajen
arewa. To su Sangawa sai ba su yi nisa da dutsen ba. Sai dai suna sauya
wurin zama daga wannan dutse zuwa wancan, har a qarshe suka zauni
dutsen da ake danganta shi zuwa gare su, wato dutsen Sanga wanda ya ke
kudu da Ririwan Dalma, wanda kuma ba su gushe ba a kanshi har bature
ya zo ya same su. Qabilar Sangawa gida-gida suke, kuma kowanne gida
suna da sarautarsu, amma sarkin sanga shi ne babbansu. Sai gidan Madaki,
sai gidan Galadima, sai gidan Ciroma. Sarkinsu na farko shi ne Bashar, sai
Karfi, Munasane, Gizau, Donde, Mayaqi, Bayaro, Takafu, Jauru, Ciga,
Anyam. Ukun farko daga cikinsu Hausawa da fulani ba su same su ba.

180
LABARIN ASALIN GURAWA

Asalin Gurawa mutanen Kwandon Qaya ne, sun fito gindi xaya da
Vankalawa da Bambarai, har ma yarensu yana kama da juna. Shahararrun
duwatsunsu waxanda su ne kamar garuruwa gare su, su ne dutsen Saya,
dutsen Mato da dutsen Babban –Gura. Koda yake mazauna kowanne dutse
suna da sarkinsu, da kuma sarkin tsafinsu da ake kira Baliba, amma
Babban-Gura ita ce babban birninsu, ma’anarta kuma fadar Gurawa da ke
bisa dutse. Masarautar dutsen Saya wanda ke arewa maso yamma da qasar
Gura suna da gidaje kamar haka; Magagau –sura,228 Magagau –yatata,229
Makundûlî, Makubiya, Masomi da Makenu. Masarautar dutsen Mato kuwa
wacce ke kudu maso yammacin qasar Gura, suna da gidaje kamar haka;
Magaran –tanna,230 Magaran –kititi,231 Magaran –tongolo, Ma -magaji-
sawa, Ma –magaji –lintin, Makuri –bãkã, Makuri –fini232 da Mazimi. Ita
kuwa masarautar dutsen Babban –Gura, wacce ke tsakiyar qasar Gura tana
da gidaje kamar haka; Makwili, Malabazu ma’azu gwimpi, Ma’azu kankai
da Mauzun gwini dai. Kuma akwai alqawari tsakaninsu kowanne gida na
da irin sarautarsa ta musamman. Akwai gidajen da su ke cin sarautar sarki
daban. Akwai kuma masu cin sarautar Galadima da Madaki da sarkin
noma, da sarkin daji da sauransu. Dukkan sarakunan Gurawa a kan
waxannan duwatsu suka yi mulki, har zuwa kan malam Bature (1829-
1848). Wanda Gurawa ke yi wa kallon daidai ya ke da gwamna Lugga
(Lord Lugard) a wajensu, shi ne wanda ya kawo musu fikirar sauko da
fadarsu daga dutse, ya kuma haxa su zama a waje xaya a Izadai har suka yi
qarfi. Dalilin sauko da fadar ta sa qasa kuwa, wata rana ne ya sauko yana
farauta, sai maharan Ningawa suka kama shi, suka tafi da shi Kano, suka
sayar da shi ga wani malami. Sai malamin ya karantar da shi Alqur’ani da
ilimi. Tun da suka xauke shi, mahaifinsa Zauno ke ta cikiyarsa, har ga
fatake matafiya, har ya koma ga Allah bai ko ji labarin wanda ma ya ce ya

228
A yaren guranci Sura =manya.
229
A yaren guranci yatata =qanana
230
A yaren guranci tanna =sama
231
A yaren guranci Kititi =tsakiya
232
A yaren guranci Fini =baqaqe
181
ganshi ba. Sai ran nan wasu fatake suka kawo labarin cewa sun ga Bature,
yana ta karatu a gidan wani malami a birnin Kano. Sai mutanen gari,
’yan’uwa da dangi suka ce a je a fanso shi, a dawo da shi gida don ya gaji
mahaifinsa. Sai suka tara kuxi, aka tura wakilai don su je su fanso shi, su
dawo da shi gida. Da dawo ta sa, sai suka naxa shi sarkinsu, shi kuwa sai
ya qi zaman kan dutse, ya sauko qasa, don kuwa musulunci ya qarfafa a
zuciyarsa, saboda ba zai yarda da bin al’ada ba. Shi ne sanadiyyar yaxuwar
addinin musulunci da karatunsa a cikin ’yan qabilar Gurawa, kuma shi ne
sarkin Gurawa na farko da kushewarsa ke bisa dandanin qasa. Daga nan
kuma sai dukkan sarakunan Gurawa da suka biyo bayansa suka ci gaba da
mulkinsu a qasa (Babban -Gura), har zuwa zamanin sarkinsu Babale
wanda ya yi mulkin Gura yana zaune a Tashar-Sule, haka ma sarakunan da
suka biyo bayansa. Akan yi musu kirari da cewa Gurawa fulanin have.
Domin mutane da suka shahara da noma, farauta da jaruntaka, don kare
kansu daga abokan gaban zamaninsu wato Ningawa. Har ma an yi wasu
shahararrun jarumai cikinsu waxanda tarihin qasar Bauci ba zai tava
mantawa da su ba, saboda irin gudunmawar da suka bayar wajen karya
Ningawa, kamar Chawai, Fasamaza, Goldo, Baba Pogolo, Jibir da sarkin
Lali da jama’a masu yawa da suka taimakawa harxon Toro su da abokan
wasansu Ribinawa, wajen kashe Xanmaje sarkin Ningi na III (1855-1870),
a kusa da Salarma cikin gundumar Ribina. Abin da ya sa sarkin Bauci
Ibrahim Yakubu233 ya yi musu tukuici da ajiye rimadan Gaini wa sarkin
Ribina, domin su yi masa bauta. Ya kuma ajiye rimadan Gura wa sarkin
Babban –Gura domin su yi masa bauta. An tava yi musu gundumar
Gurawa a shekarar 2011, inda suka zavi M. Ya’u Muhammadu Soye,234
amma zuwa shekarar 2013 sai sabuwar gwamnati ta rushe ta. Daga cikin
garuruwansu akwai Babban Gura, Riga, Mato, Saya, Jawando, Tudun

233
Ya yi sarauta daga 1845-1877. Ya rasu a qauyen Rauta, lokacin da ya je kafa garin
ribaxi na Kafin Rauta, domin tsare birnin Bauci daga maharan Ningawa. An binne shi a
cikin xakin da ya rasu a cikinsa. An ce da kansa ya tona qabarinsa a cikin xakin. Ya kuma
bar wasiyyar idan ya mutu su binne shi ba cikinsa. Kuma suka aikata hakan.
234
An haife shi a Bishiwai, ya yi makarantar firamare a Wundi 1975-1981. Kana ya yi
sakandare a Bununu 1981-1986.
182
wada, Dawa, Dinga, Cexiya, Kulfana, Wa’ere, Fishere, Rafin ciyo da
sauransu. Ga jerin sarakunansu kamar haka :

Suna Daxewa Shekaru


1 Bulama 1719-1740 21
2 Tatiya 1740-1773 33
3 Gimba 1773-1814 41
4 Zauno 1814-1829 15
5 M. Bature 1829-1848 19
6 Sulaimanu 1848-1912 64
7 Marabun Allade 1912-1915 3
8 M. Xanladi 1915-1961 46
9 Babale 1961-1977 16
10 Yakubu Dabara 1977-1997 20
11 Yunusa Ibrahim 1997-2010 13
12 Salihu Yakubu Dabara235 2010- Yau 10

LABARIN ASALIN BAMBARAI

Bambarai asalinsu maguzawa ne da suka yi gudun yin sallah, daga qasar


Kano suka shigo qasar Bauci da ke maqwabtaka da su, suka fara zama a
dutsen Zuna. Sakamakon yawan kawo hari da Ningawa ke kawo wa suna
ribatar ’ya’yansu, sai suka yanke shawarar zakuxawa zuwa wani tsohon
gari da ke bisa dutsen Fanshanu da ake kira Kwandon –Qaya. To, lokacin
kuma da Kwandon qaya ta fashe, sai suka yi qaura kuma suka rabu gida
biyu, wasu suka yi kudu, wasu kuma suka yi arewa. To, waxanda suka yi ta
wajen kudun nan, sai suka yi maqwabtaka da Jarawa a cikin garuruwansu,
kamar Tulai, Kufai da sauransu, suka zamo tamkar ’yan’uwa, har ma suna
jin yaren juna, waxannan galibinsu ko day a ke daga baya sun musulunta,
amma fa bas u riqe musuluncin da qarfi sosai ba. Su kuwa waxanda suka

235
Sarkin Babban –Gura na yanzu M. Salihu Yakubu Dabara an hafe shi a Tashar-Sule a
1974, ya yi makarantar firamaren Zalau 1982-1987. Kana ya yi makarantar yaqi da jahilci,
kamar yadda ya yi karatun muhammadiyya. Babbar sana’arsa noma da farauta, amma ya
iya sana’ar mahaifinsa na gyaran keke, san nan kuma qwararren kafintan sama da qasa ne.
An naxa shi sarkin Gurawan Babban-Gura ran 12 Oktoba 2010. Kafin naxa shi, an
tavanaxa shi Ciroma. Ya kuma tava zama shugaban ’yan banga na gundumar Zalau.
183
yi ta wajen arewa, sai suka zauni Kulfana, Zingiri (Zuku) har zuwa wani
yanki na qasar Tama suka mamaye ta. Kuma su ko da yake daga baya sun
yi sallah, lallai an ga sun fi ’yan’uwansu ’yan’uwansu waxancan da suka yi
kudu riqe addinin musulunci da qarfi. Babbar sana’arsu it ace noma, kiwo
da kasuwanci. Manyan haulan Bambarai guda bakwai ne; Bindar Di, su ne
zuriyar sarakunan Tama na yanzu. Sai Bindar Gwam, su ne masu sarautar
Galadima a qasar Tama. Sai Bindar Bãtu su ne zuriyar sarkin yaqin Tama.
Sai Zûnãwa, Azumãwa, Zukãwa, Zungirãwa da Mukãfana. Da can Zunawa
ke sarautar, amma daga baya cikin qarni goma sha takwas miladi, sai
sarautar ta koma gidan Bindar Di. Waxanda suka yi sarautarsu su; Makixi,
Gimba, Saldu, Zango, Kakaki, Usman Gimba, Yakubu Gimba,
Muhammadu Gimba, Umaru Muhammadu Gimba,236Yakubu Jibrin
Usman237 da Adamu Yakubu Jibrin.

YAWAN MAKARANTUN QASAR LAME 1914-1960

Yawan makarantun Elementare da firamare na qasar Lame, wato J.P.S.


(Junior Primary School) da S.P.S. (Senior Primary School) a shekarar
1963 su takwas ne, ga inda suke ;
1- Lame
2- Tulu
3- Rishi
4- Rahama
5- Gumau Sanga
6- Tilden Fulani
7- Toro
8- Ribina

Na Sakandare kuwa guda xaya ce itace kwalejin horon malamai ta TC


(Teacher’s College) Toro, wacce aka buxe ta tun cikin 1929.

236
An zave shi ran 29 Fabrairu 1972
237
An zave shi ran 14 Afrilu 1984
184
YAWAN MAKARANTUN QASAR LAME A 1976

Duk qasar Lame babu makarantar sakandare, a shekarar 1976’s ko na


Firamaren ma guda shida ne kaxai. Ga su :

Makaranta Buxe ta Gunduma


1 Lame 1914 Lame
2 Tulu 1959 Tama
3 Gumau Sanga 1952 Wonu
4 Rahama 1952 Rahama
5 Rishi 1952 Rishi
6 Unguwar Waziri238 1976 Wonu

SABBBIN MAKARANTUN DA AKA BUXE A QASAR LAME A 1977


A cikin watan Satumbar 1976, gwamnatin mulkin soja ta Janar Olusegun
Obasanjo ta qirqiro shirin bai wa kowanne yaro day a kai shekara shida
ilimi kyauta, da ake kira UPE (Universal Primary Education). San nan
Birgediya Garba Duba, shi ne gwamnan Bauci, sai ya karvi wannan shiri
da muhimmanci, in da shekara xaya da fara shirin a 1977 hukumar ilimi ta
‘Bauchi Dass Local Education Authority’239 ta buxe sabbin makarantun

238
Tun ran 13 Oktoba 1975, sarkin kudu Sulaimanu ya rubuta wa Bauchi Local Authority
neman qarin makaranta a cikin Gumau, har ma an samu yara 40. To, ba’a aiko da izinin
buxewa ba, sai a qarshen shekarar 1976, domin ta zamo makarantar gwaji, bayan qirqiro
shrin UPE na bai wa yara ilimi kyauta. Zangon karatu xaya kurum aka ci a shekarar, sai ta
qare, aka sake xiban xalibai ’yan aji biyu. An fara karatu a bargar dawakai na qofar
hakimi, in da ake aka mai da shi masallaci yanzu. Daidai bishiyar kanyar nan nan xalibai
ke taruwa ayi musu jawabi. A shekarar 1980 aka maid a ita matsuguninta na dindindin,
aka gina tamfararen kwano a gonar M. Idi inda makarantar firamaren ta Sarkin yaqi ta ke
a yanzu. Xalibai ’yan aji biyar da aji huxu ne kurum suka samu aji, ragowar duk a gindin
bishiyoyin xorayin wurin ake biya musu karatu. A shekarar 1984 sadda aka rufe qaramar
makarantar sakandare ta JSS (Junior Secondary School) Lame, sai aka maid a xaliban
makarantar Unguwar Waziri matsuguninsu da sunan aro, inda bas u gushe ba har yanzu a
wajen su ke. Ita kuwa unguwar waziri ta asali da aka qaurace mata, sai aka buxe sabuwar
makarantar firamare a wajen, aka kira ta ‘firamaren Sarkin yaqi.’
239
A lokacin hukumar ilimin Bauci na haxe da Dass, Toro kuma na qarqashin Bauci.
185
firamare, lokaci guda sai ga yawan makarantun firamare cikin qasar Lame
ya qaru sun kai 38. Ga su :

Makaranta Gunduma
1 Ririwan Dalma Wonu
2 Turkunyan Beru Tama
3 Unguwar Sako
4 Turmusawa
5 Gau Lame
6 Bangwale Lame
7 Sagere Lame
8 Sunkuye
9 Dawarde Wonu
10 Gukka Lame
11 Zuna Rishi
12 Cexiya Zalau
13 Pingel Wonu
14 Dini Rahama
15 Gana Rishi
16 Matawai Rahama
17 Sabon garin tulu Tama
18 Nasarawa Tama
19 Unguwar Arewa Tama
20 Kari Tama
21 Kyare Rahama
22 Shibi Tama
23 Dinga Tama
24 Badikko Wonu
25 Ruhu Lame
26 Gwa/Bakin Kasuwa Lame
27 Shau Lame
28 Davave Rishi
29 Kadaxe Rahama
30 Zuku Rishi
31 Zalau Zalau
32 Wundi Rishi

186
YAWAN ASIBITOCIN QASAR LAME A 1960-1979

Yawan asibitocin qasar Lame a shekar 1963 guda uku ne kacal, biyu na
en’e, xaya na gwamnati ;

1- Asbitin Toro – En’e


2- Asibitin Pingel – En’e
3- Asibitin Rishi - Gwamnati

YAWAN ASIBITOCIN QASAR LAME A 2021

Yawan asibitocin qaramar cibiyar kula da kiwon lafiya (Primary Health


Care Centre) na qasar Lame a shekarar 2020, guda takwas ne ;

1- Gumau
2- Zalau
3- Rishi
4- Tulu
5- Sabon gari
6- Rahama
7- Lame
8- Geljaule

MANYAN KASUWANNIN QASAR LAME 1930-1940

1- Tulu Alhamis
2- Ririwai Lahadi
3- Ganye Talata
4- Zalau Jumma’a

MANYAN KASUWANNIN QASAR LAME 1950-1960

Manyan kasuwannin qasar Lame a shekarun 1950 su ne :

187
1- Ganye Lahadi
2- Rishi Lahadi
3- Gumau Litinin
4- Tilden Fulani Talata
5- Tulu Alhamis

MANYAN KASUWANNIN QASAR LAME 2021

Manyan kasuwannin qasar Lame a shekarun 2021 su ne :


1- Gumau Litinin
2- Kwabi Litinin
3- Saminakan-Gwa Laraba
4- Tulu Alhamis

QANANAN KASUWANNIN QASAR LAME A 2021

5- Rishi Lahadi
6- Shau Lahadi
7- Zalau Jumma’a

MASALLATAN JUMMA’AR NA QASAR LAME


DA SHEKARAR BUXE SU

Gari Buxewa
1 Gumau 1948
2 Rishi 1966
3 Sabon Garin Tulu240 02-04-65
4 Dawa 21-06-1969
5 Wundi 1970
6 Lame 03-06-1971
7 Badikko 18-05-1973
8 Zalau 5/9/1980
9 Gukka241 19-2-1988

240
M. Mahmudu limamin Bauci ya buxe shi
241
Sarkin Bauci Sulaimanu Adamu ya buxe shi
188
10 Bakin kasuwa-Gwa242 21/12/1988
11 Dini243 13/01/1989
12 Dinga 20/01/1989
13 Rinjin Gura244 23 Maris 1990
14 Baradawo245 30 maris 1990
15 Nahuta246 04/01/1991
16 Zuna247 16/02/1991
17 Lau248 23/02/1991
18 Zirya 1996
19 Wurno249 16-05-1996
20 Guraka250 10 Afrilu 1997
21 Kulfana251 2013

YAWAN MASAUKAN TURAWA NA QASAR LAME 1940-1960


A shekarun 1940 akwai barikoki (resthouse) na saukar turawa guda goma
sha uku, abinda ke alamta qasar na da yalwar arziqin da turawa ke kai-
kawo a cikinta ;
1- Barikin Lame
2- Barkin Mukur
3- Barikin Ofisa
4- Barikin Sabon –gari
5- Barikin Nasarawa
6- Barikin Rahama
7- Barikin Zalau
8- Barikin Majalisa
9- Barikin Riruwai

242
Na’ibin limamin Bauci ya zo ya buxe shi
243
Na’ibin limamin Bauci ya zo ya buxe shi
244
Na’ibin limamin Bauci ya zo ya buxe shi
245
Na’ibin limamin Bauci ya zo ya buxe shi
246
Limamin Bauci ya zo ya buxe shi
247
Limamin Bauci ya buxe shi
248
Limamin Bauci ya buxe shi
249
Limamin Bauci ya buxe shi
250
Limamin Bauci ya buxe shi
251
Na’ibin limamin Gumau ya buxe shi
189
10- Barikin Badikko
11- Barikin Magama (gari)
12- Barikin Zaranda
13- Barikin Nabardo
14- Barikin Gumau

KAYAYYAKI MASU DARAJA


DA AKE SAMU A QASAR LAME

Tun shekaru masu yawa sunan qasar Lame ya shahara a duniya, wajen
samun kuza da iya sarrafa ta, abin da ake ce ma dalma. Su duka kuwa
abubuwa ne masu daraja qwarai da gaske. Kusan duk inda aka tona a qasar
Lame, za’a samu kuza. Qasar Lame qasa ce wacce ke cike da arziqi, amma
galibin kayan amfanin da ke cikinta, har yanzu mutanen qasar bas u san su
ba. Bayan kuza da dalma, akwai su zuma da kakinta. Da qirgi, da fata, da
qaro, da baba, irin wanda ko a qasar Hindu, ko Sin ko turai ba’a samun
wanda ya fi shi. Da bishiyoyin xorayi, da manyan filayen noman damina,
da fadamun noman rani. Waxannan ga su nan ko’ina a qasar, kuma a
yalwace. Akwai kuma da manyan dazuzzuka da rafuka, da yashi iri-iri.
Amma mutanen yankin hajja iri uku kaxai suka fi sayarwa; kuza, dalma,
kalwa, itacen girki, to, sai dai fa kayan noma wanda wannan guminsu ne.
Babbar sana’ar mutanen qasar Lame itace noma, mata kuwa sun fi yin
saqar gwado da tabarma. Amma bai kyautu mutum ya ba da labarin halin
zaman mutanen qasar Lame, ba tare da ya tava maganar cinikin bayi ba,
wanda aka yi a garuruwa irinsu Badikko da Ririwai da Sabon Garin Tulu
da Lame, Shau da ma wasu garuruwa ba. Lalle an sani a zaman xan Adam
bas hi yiwuwa kowa da kowa a zama daidai, lalle ne wani ya fi wani daraja
ko arziqi. Amma in fifikon nan ya hana mutum ikon yin komai said a
yardar wani , al’amarin ya zama bauta kenan. Su bayi ba’a buqatar komai
das u sai aiki, shi ake sa su kullum, komai xari, komai rana, komai ruwa.
Ba su da ikon zaven lokacin farawa, balle na tashi. In sun duqa, sun duqa
kenan, sai an ce su bari, kuma duk abin da suka yi sun yi wa bauta ne, bas
u da ikon tambayar lada ko biya. Amma duk da haka a shari’ar qasa akwai
abubuwa na wahalarwa da ubangiji ba shi da ikon yi wa bawansa. In ya yi

190
tilas za’a sayar da bawan. Kafin mu wuce wannan wuri, yana da kyau mu
yi bayanin cewa akwai nau’ukan bayi iri huxu :
i- Bayin yaqi : Su ne waxanda aka ribace su a fagen fama, ko aka
ci garuruwansu da yaqi.
ii- ’Ya’yan da bayi suka haifa a gidan bauta, don xan bawa shi ma
bawa ne.
iii- Bayin bashi : Su ne waxanda suka ci bashi suka kasa biya. Ga
al’ada kuwa mabarci na iya kama wanda ya ci bashinsa. In bai
same shi ba ya kama xansa. In ba xa ya kama wani daga cikin
danginsa, har ma in ba dangi ya kama wani mutumin garinsu.
iv- Bayin yunwa : Su ne waxanda yunwa kan sa su sayar kansu
bayi bisa tilas. Su kan tafi wurin wani mai abinci su sayar masa
da ’yancinsu, don su sami abin da za su ci, koda yake sun san
bauta mugun abu ne, amma sun fi tsoron mutuwa da ita.

BABBAN MA’ADANIN QASAR LAME

Babban ma’adani da aka fi samunsa a qasar Lame, ita ce kuza. Duk faxin
Nijeriya babu inda ake samun kuza fiye da qasar Lame. Koda yake ana xan
samun kuza a Ilori, Zariya da Kano. Amma duk babu kamar ta qasar Lame.
Babu wani rafi da za ka tona a qasar Lame ba ka samu kuza ba. Kuzan ita
ta janyo wa qasar yawan mutane. Yanzu a nan Nijeriya, kusan kowanne
mai aikin kuza, ya san xan garin nan da ake kira Pingel, ko ya tava jin
sunansa. Mutane daban daban cikin Nijeriya ke taruwa cikinsa. Da can
kafin zuwan turawa, mutanen qasar na suna haqo kuza, amma ’yar kaxan.
Sai su sayar wa maqera. Maqera sukan narka ta su shafe kayan adon da
suka qera, don su riqa qyalqyali. Cikin shekarar 1885 ne baturen kamfani,
Captain Wallace ya zo qasar Lame (Jos252 da kewayenta), ya yi zagayen
duk inda ake samun kuza a yankin ya kai labari Ingila. Bayan wasu
shekaru, sai turawa suka zo qasar Lame, suka kafa kamfanonin haqar kuza
da gyaranta guda 57.253 Ga su :

252
Domin ba’a cire Jos daga cikin qasar Lame ba sai a shekarar 1927.
253
A lokacin da turawan aikin kuza suka buxe waxannan kamfanoni ake aikin sosai da
sosai, babu rashin aikin yi, ko rashin kuxi a cikin wannan qasa. A lokacin har neman
191
BARIKOKIN TONON KUZA

A gundumar Wonu sun buxe kamfanoni goma sha uku :


1- Pingel
2- Wul254
3- Kogon Gandu255
4- Maisaje256
5- Kuratandu
6- Danka
7- Gula257
8- Gawo
9- Kamfanin Isubu
10- Tsika
11- Hawan Liba258
12- Bundum
13- Kamfanin Buri

leburori da ma’aikata ake yi ta hannun sarakuna. Idan na kalli yadda yaranmu yanzu
danqam suka gama makaranta babu aikin yi, da yadda wasu lafiyayyu kan wayi gari ba su
san inda za su ba, sai na kan tuna takardar da turawan kuza na Kalatau da Mailamba wato
‘Nigerian Tin & Exploration Company’ wata shekara 1951 suka kawo kuka cewa suna
neman ma’aikata mutum 500 saboda aikin kuza. Mutum xari biyar malam! Wannan fa a
kamfanoni biyu kenan. To ina ga kamfanoni hamsin da bakwai? To, sai da sarkin yaqi ya
sa aka yi ta shelar neman ma’aikata. Amma duk da haka ba su cike gurbin da ake bukata
ba, said a aka nemo mutane daga wajen qasar Bauci, har daga Nijar da Chadi. A dalilin
zuwansu kuma aka samu varkewar cutar ‘guinea worm’saboda a cikin tafkin da mutane ke
shan ruwa suke wanka, su yi amai duk a ciki.
254
Ana xaukar hanyarta daga Danka, hanyar ta yi hannun dama. Nisanta daga Danka kilo
mita 4. Kuma har yanzu akwai mutane da ke zaune a cikinta.
255
Tana kan hanyar Sagere daga Pingel, tafiyar kilo mita 2, da zarar ka haura rafin Mana,
sai Gawo. Kuma har yanzu akwai mutane da ke zaune a cikinta.
256
Tana kudu da Wul. Ana xaukar hanyarta daga makarantar Unguwar Kadiri, hanyar ta
miqa gabas ta hannun dama. Nisan tafiyar daga makaranta ya kai kilo mita 3, ko kusa.
Kuma har yanzu akwai mutane da ke zaune a cikinta.
257
Da an haura rafin ‘Sauke’ kufayin Gula shi ake fara isa. Babu kowa a wajen da ke
rayuwa.
258
Yana arewa da Mana, kamar kilo mita 3. Babu kowa a wajen, yazu kufai ne.
192
A gundumar Tama sun buxe kamfanoni takwas :
1- Kamfanin Buba
2- Jama’ah
3- Kalatau259
4- Marmara
5- Doka
6- Mailamban Tudu
7- Mailamban Kwari
8- Kamfanin Dogo

A gundumar Rishi sun buxe kamfanoni goma :


1- Yalwan Rishi
2- Rafin Tavo
3- Sabon Qaura
4- Saminaka
5- Kamfanin Kistoba
6- Kamfanin Wundi
7- Sisin Kwabo
8- Dakatsalle
9- Bishiwai
10- Qaguwa
11- Aladeni

A gunduman Lame sun buxe kamfanoni goma sha xaya :


1- Bangole260
2- Dabo
3- Maje
4- Fakuru
5- Turmusawa
6- Dabon Sarari
7- Dogon Sanga

259
Sunan baturen da buxe aiki a Kalatau a cikin shekarun 1940 shi ne J.P. Rodier.
Leburori na cewa da shi Bahausa.
260
Asalin sunan baturen Mr Bongwelli
193
8- Faranshi
9- Tsararo
10- ’Yar Harxo
11- Lange

A gundumar Rahama sun buxe kamfanoni biyu :


1- Yagi
2- Maraku

A gundumar Zalau sun buxe kamfanoni goma sha shida :


1- Dawa
2- Ankwakusa
3- Katakau
4- Mahanga
5- Ja-ta-ka-xima
6- Akawu
7- Garwa
8- Dankashari
9- Jawandun Gurawa
10- Jawandun Gindin dutse
11- Kulfana
12- Doka
13- Gada
14- Faranshi
15- Maje-uku
16- Kamfanin M. Ango

Tun da turawa suka koma qasarsu, sai aikin kuza ya yi kamar ya mutu.
Yanzu kusan kowa na yin na kansa ne. Ya sayi gona, ya biya a haqe masa,
ya xebi leburori su wanke, ya kai inji ya gyara ya sayar, ya sallami
ma’aikata.

194
ABIN DA QASAR LAME TA AMFANA DA SHI
A DALILIN AIKIN KUZA

Babu abin da Qasar lame ta amfana da shi a dalilin aikin kuza da ake yi a
cikinta, kam ban da qaruwar masu biyan haraji, to, sai dai kuma hanyoyin
mota da turawan kuza suka yi a shekar 1949 don su ji daxin kwashe arziqin
wannan qasa cikin sauqi. Misali ;
1- Kamfanin turawan Pingel da Kulfana ‘Minerals Research
Syndicate’ na Mista Renouf da Mista Spooner sun yi hanyar mota
da gadoji daga Gumau zuwa Pingel, da kuma daga Zalau zuwa
Kulfana.
2- Baturen kuza na Garwa Mista Schaer shi ya yi aikin hanyar mota
daga Gumau-Rishi zuwa Tulu da Rahama.
3- Kamfanin turawan kuza na Rishi ‘Gold & Base Metals’ na mista
Swabey, da turawan kamfanin Dawa ‘Mista Hanvey, na Filani (N)
Tin-Mining Company’ da baturen kamfanin Zalau Mista Benzies, su
suka faxaxa hanyar mota, suka yi gadoji daga Zalau zuwa Rishi.

Haka an yi hanyoyin mota zuwa duk inda ake samun kuza, amma fa duk
waxannan hanyoyi ne shararra, ba wai masu kwalta ba. Kuma ba’a yi su
sun haxa mu da wata jiha ko wasu al’ummomi waxanda ba mu ba. Iyaka
an yi su ne kurum don a samu sauqin kwashe arziqin qasarmu. Kuma
bayan haka ba’a samu wata gwamnati da ta inganta su, ta sadar dasu da
wasu jihohi ba, wanda sanadin hakan ya jawowa qasar lame iyakar koma
baya. Wanda yau kimanin shekaru casa’in kenan ana xibar arziqi a yankin,
amma har yanzu yankin a kulle yak e ruf saboda rashin hanya. Kuma ko ita
hanyar da turawan kuzan suka yi, ba kowacce irin motac e ake bari ta bi ba.
Saboda ba kowacce irin mota za ta iya xauka ba.

ABIN DA YA DAQUSHE CI GABAN QASAR LAME

1- Rashin hanyoyin zirga-zirga


2- Rashin manyan makarantun gwamnati
3- Rashin ma’aikatun gwamnati

195
4- Rashin haxin kan mutanen qasar
5- Rikice-rikicen siyasa261
6- Rashin hanyoyin zirga-zirga
7- Rashin manyan makarantun gwamnati
8- Rashin ma’aikatun gwamnati
9- Rashin haxin kan mutanen qasar262

AIKIN DOKA

Aikin doka aiki ne turawan mulkin mallaka suka bai wa hukumomin


En’e na kowanne lardi damar xibar masu yinsa domin samar da tsaro a
cikin qasa. Tun da ya ke ’yan mulkin mallaka sun yi mulki ne ta hannun
sarakunammu na gargajiya, sai suka maye gurbin dogarai da aka sani a da
da ’yandoka, shi ya sa ma asalin sunansu da turaci shi ne ‘Native Authority
Police’.

261
Ga misali a shekarar 1983 lokacin da za’a yi sabon zave, Abubakar Umar daga
gundumar Zalau ya fito neman takarar kujerar gwamna tare da gwamna mai ci Tatari Ali,
alhali a lokaccin Tatari Ali ya ba da kwangilar aikin hanyar da ta taso daga Kafin Madaki
ta bi Burra ta vullo Zalau ta yi fuskar Mata ta faxa babban hanyar motar da ta taso daga
Zariya zuwa Jos. To kuma shugabannin kamfen xinsu duka gaba xaya ’yan Gumau ne.
Alhaji Maikuxi Ririwai shiu ne shugaban jam’iyyar NPN na jihar Bauci, kuma shugaban
kamfen xin Tatari Ali, a xaya vangaren kuma Alhaji Yakubu Bula Gumau, shi ne
shugaban kamfen xin Abubakar Umar. Kuma dukkaninsu sukan shiga gidan rediyo suna
muhawara suna sukar juna. Abin da kenan ya fusatar da gwamna Tatari Ali ya soke
wannan aikin hanyar, ya ce idan Abubakar Umar ya ci zave ya yi muku. Hanyar da har
yau ga shi ba’a yi ta ba.
262
Ga misali mutanen Rishi suna tsananin gaba da mutanen Gumau, har ta kai idan
mutanen Gumau sun rubuta takardar neman qaramar hukuma, hedkwata a Gumau
mutanen Rishi za su rubuta takardar ‘Petition’ su aika cewa ba sa so a bayar. Ko lokacin
da aka bai wa Gumau ‘Federal Constituency’ a shekarar ? mutanen Rishi sun aika da
takardar ‘Petition’ cewa ba su so. Dalilin da ya jawo aka xauke ta aka mayar Bajoga. To,
lokacin da shugaban qasa Ibrahim Babangida zai qara qananan hukumomi, sai ya yi
amfani da dokar cewa ‘duk waxanda suke da Federal Constituency’ sun zama qaramar
hukuma. Shi kenan sai aka raba Bajoga da Nafaxa, alhali da a haxe su ke.
196
YAWAN ’YANDOKAN QASAR LAME 1963

Dududu ’yandoka goma sha biyu ne a qasar Lame baki xaya a shekarun
1960’s, amma tsaron da ake dashi a wancan lokaci, babu kama tasa a yau.

1- Gumau - 3
2- Rinjin Gaini - 2
3- Tilden Fulani - 1
4- Pingel -1
5- Doka- 1
6- Tulu - 2
7- Rishi – 1
8- Rahama -1

HEDKWATATOCIN ’YANDOKA 1940-1967

Manyan cibiyoyin da aka ajiye ’yandoka cikin qasar Lame a shekarun


1940 an kasa su reshe uku ne :

RESHEN ZALAU :
Su na duba garuruwan da aka rubuta, da wasu na kusa da
su waxanda ba’a rubuta ba.
Gari Nisanta daga Zalau km
1 Rishi 7
2 Garwa 3
3 Ririwai 7
4 Gumau 10
5 Danka 6
6 Bindari 5
7 Pingel 8
8 Kulfana 3
9 Barikin 9

197
RESHEN RAHAMA :
Su na duba garuruwan da aka rubuta, da wasu na
kusa da su waxanda ba’a rubuta ba.
Gari Nisanta daga Rahama Km
1 Jirya 13
2 Gana 13
3 Matawai 5
4 Davave 5
5 Xankande 8
6 Gurbin- kawo 15
7 Wundi 10
8 Zuku 8
9 Bishiwai 8
10 Yagi 7

RESHEN TULU :
Su na duba garuruwan da aka rubuta, da wasu na
kusa da su waxanda ba’a rubuta ba.
Gari Nisanta daga Tulu Km
1 Kalatau 15
2 Mailamba 15
3 Turkunyan- Beru 16
4 Burku 8
5 Kari 8
6 Shibi 10
7 Zuna 12
8 Gurungu 11
9 Dinya 13
10 Gulbi 3

Ga wasu kasuwanni da barikokin ma’adanai da ake tura ’yandoka aiki


cikin kayan sarki a kowacce ranar kasuwa, ko a kullum su je su yi aiki su
dawo hedkwata.

198
RESHEN RINJIN GAINI :
Su na duba garuruwan da aka rubuta, da na kusa da su waxanda ba’a rubuta ba
Gari Nisanta daga Rinjin Gaini Km
1 Ganye (Lahadi) 7
2 Badikko (Alhamis) 10
3 Toro (Jumma’a) 2
4 Dole (Laraba) 15
5 Tilde (Talata) 8
6 Narabi 10
7 Diriko 17
8 Kamfanin Baro 2
9 Kwadon 10
10 Barikin Gangala 10
11 Panshanu kamfanin Wurwa 8
12 Barikin Jubga 13
13 Makarantar Zangam 7
14 Unguwar sarkin kudu 6
15 Miciyan Magama 5
16 Asibitin kutare Yalwa 4

DAWOWA DA OFISHIN ’YANDOKA GUMAU


To, sadda sarkin yaqi ya dawo Gumau, ta zamo cibiyar mulkin qasar
Lame baki xaya, sai aka kashe matsugunan cibiyar aikin ’yandoka baki
xaya zuwa Gumau da Rishi kaxai. To su na Gumau :

Su na duba garuruwan da aka rubuta, da na kusa da su


Gari Rana Km
1 Pingel Asabar-litinin
2 Kasuwan Gwa Kowacce Laraba
3 Kasuwan Lame Jumma’a kowanne wata ×1
4 Fakuru Kowanne sati ×2
5 Kulfana Jumma’a-lahadi
6 Akawu Kowanne sati ×2
7 Tsararo Jumma’a-lahadi
8 Faranshi Kowanne sati ×2

199
RESHEN RISHI :
Su na duba garuruwan da aka rubuta, da na kusa da su
Gari Rana Km
1 Dawa Kowanne sati ×1 4
2 Faranshi Bariki Kowanne sati ×1 4
3 Tabo Kowanne sati ×1 4
4 Yalwan Rishi Kowanne sati ×1 4
5 Rahama Kowacce lahadi 15
6 Tulu Kowacce alhamis 12
7 Wundi Kowanne sati ×1 12
8 Aladeni Kowanne sati ×1 12
9 Bishiwai Kowanne sati ×1 12
10 Sabon Kauru Kowanne sati ×1 2
11 Jama’ar Amadu Kowanne sati ×1 3
12 Siyayel Kowanne sati ×1 3
13 Kasuwan Zalau Kowace jumma’a 8
14 Xankushiri Sabuwa Kowanne sati ×1 11
15 Mailamba Tudu Kowanne sati ×1 7 daga S/gari
16 Mailamba Kwari Kowanne sati ×1 9 daga S/gari
17 Kalatau Kowanne sati ×1 7 daga S/gari

KAWO QARSHEN AIKIN XANDOKA


A da lokacin da ’yandoka a qarqashin sarakuna su ke, har a kan naxa
wakilin doka, shi ne babbansu, kuma shi ke rarraba su zuwa wuraren
ayyukansu. Amma lokacin da sojoji suka karvi jan ragamar mulkin
Nijeriya 1967-1975, sun yi alqawarin za su sake fasalta tsarin zaman
Nijeriya don samun canji mai fa’ida. A jihar arewa a san nan kotuna
(alqalai), ’yandoka da gidajen yari duka suna qarqashin hukumar En’e ne,
sai sojoji suka soke tsarin hukumar En’e (N.A.) Native Authority suka
maye madadinta da L.A. (Local Administrative) a 1970, a 1976 kuma aka
musanya L.A. da L.G.A. (Local Government Administrative). To, da rusa
tsarin En’e sai duk abin da ke qarqashinsa ya rushe, ’yandoka suka juye
’yan sanda ‘Nigeria Police Force, aka maid a gidajen yari qarqashin
hukumar kula da gidajen yari ta qasa ‘Nigerian Prisons Service’ aka
qirqiro jihohi da qananan hukumomi a madadin hukumar En’e.
200
YAWAN CAJI-OFIS XIN QASAR LAME 2021

Yawan caji-ofis xin ’yansanda na qasar Lame a shekarar 2021, guda


bakwai ne, amma DPO (Divisional Police Officer) yana zaune a hedkwata
ne wato Gumau. Caji-ofis xin sune ne :

1- Gumau
2- Zalau
3- Rishi
4- Tulu
5- Sabon Gari
6- Rahama
7- Geljaule

YAWAN KOTUNAN QASAR LAME 2021

1- Lower shari’ah court Gumau


2- Upper shari’a court Gumau
3- Magistrate court Gumau
4- Lower shari’ah court Tulu
5- Lower shari’ah court Rishi
6- Lower shari’ah court Lame

SARAUTA

Asalin sarauta ta fara ne, tun sadda Allah (SWT) ya halicci Annabi
Adamu (AS) kuma ya saukar das hi ya zuwa qasa, don ya zamo halifansa a
cikinta. Kuma duk Annabawa da Allah yak e aikowa, ya aiko su ne
tabbatar da shari’arsa, su shiryar su yi bushara kuma su yi gargaxi. Kuma
abinda suka zo dashi shine tushen sarauta. Ga asali da sarauta da addini
’yan’uwan juna ne. xaya baya tafiya, ba tare da xayan ba. Addini shine
tushe, sarauta ce mai tsaronsa. Shi kuma al’amarin mai sarauta bay a
daidaituwa matauqar ana sava masa. Kuma duk mai sarautar da
talakawansa ke tsoronsa, shi ya fi akan wanda yak e tsoron talakawansa.

201
Duk mai mulkin day a zamo mai tausayin talakawansa, to, ya zamo inuwar
Allah a bayan qasa. Addinin musulunci bai yarda al’umma su zauna kara-
zube, ba tare da shugaba ba. Ko da kuwa kamar su uku ne za su yi tafiya,
to, lallai su naxa xayansu ya zamo shugabansu. Ma’aiki (SAW) ya cewa,
“Zamantakewar mutane ba ya daidaituwa, idan suna zaune kara-zube.
Haka nan ko an yi sarautar, al’amarinsu ba zai daidaitu ba, matuqar jahilai
(marasa asali) ne shuwagabanni.”263 Duk shugaban da ya ke so ya ci nasara
a mulkinsa, sai ya zamo mai jaruntaka, mai cika alqawari, mai kyauta, mai
yafewa kana mai kau da kai. Wani malami Abu Tamam Axxa’iy yana
cewa : “Wawa ba zai tava zamowa shugaban mutanensa ba. Sai dai
shugaban mutane dole sai ya zamo kamar wawa.”264

HALAYEN DA MULKI YA KE DAUWAMA DA SU

Mulki yana dauwama ne da halaye shida :


1- Barin yin alqawari na qarya
2- Barin yin uquba da fushin kanka, sai da gwargwadon zunubi265
3- Shugabantar da masu kaifin hankali
4- Shugabantar da mutane masu asali266
5- Shugabantar da dattijai bisa matasa
6- Barin yin sako-sako cikin al’amarin umarni ko hani

BIYAYYA WA SHUWAGABANNI

Yi wa sarakuna xa’a wajibi ne. Allah ya yi umarni a yi wa sarakuna


biyayya. Ya ce, “Ya ku waxanda suka yi imani ku yi biyayya ga Allah, ku
yi xa’a ga manzonsa da waxanda aka jivintar da su al’amarinku.” Ma’aiki

263
Almawardi (Al’ahkamus sulxaniyyah) : 1/3
264
Arraghibul Asfahani (Muhadharatul Udaba’u) :1/6
265
Shugabanci ba ya yiwuwa ga marowaci ko mai tsananin fushi. Idan shugaba ya zamo
marowaci, to ba wanda zai yi masa biyayya. Idan kuma ya zamo mai tsananin fushi, kuma
ga iko a hannunsa, to, zai halakar da al’umma.
266
Duk sadda aka rasa mutane masu asali a cikin shugabanci, to, al’umma za ta halaka.
Domin mutane ba su gyaruwa sai da shugabanni masu asali.
202
(SAW) ya ce, “Wanda ya yi min biyayya, to, ya yi wa Allah biyayya.
Wanda ya yi sarki na biyayya, to, ya yi min biyayya. Wanda kuwa ya sava
min, to ya savawa Allah. Wanda ya savawa sarki na, to, ya sava min.”267

TSARIN SARAUTA A QASAR BAUCI


KAFIN ZUWAN TURAWA

A tsarin sarautun gargajiya na qasar Bauci sarki shi ne gaba da kowa. Shi
ne shugaba mai iko da qasa baki xayanta. daga shi sai Waziri, ko Madaki
da sauran mataimakansa na cikin gari da na qauyuka. Waxannan mutane su
ne hakimai. A cikin gari akan samu Makama, da Ciroma, da Iya, da Turaki
da sauransu. A qauyuka kuwa ana samun hakimai , da masu gunduma,
waxanda kowa ke riqe da yankinsa. Sai kuma masu binsu su ne masu
littafi, ko masu unguwanni, ko masu gari. Bayansu sai magidanta manya da
qanana. Shi mai gida gwargwadon girma da yawan jama’ar gidansa,
gwargwadon mulkinsa. Ga yadda jerinsu ya ke a masarautar Bauci kamar
haka: Sarki – Hakimi - Mai gunduma - Mai littafi - Mai unguwa - Mai gida

TAFIYA YAQI

Idan za’a je yaqi, sarkin dogarai shi ke kan gaba, san nan madaki.
Waxannan su ne kamar masu tsokano faxa. Su ne kuma kan kai hari domin
gane ainihin wurin da abokin gaba ya yi kwanto, da kuma irin qarfinsa.
Idan sun yi nasara, sai gayya duka ta yunqura ta aukawa abokan gaba. Idan
kuma aka juyo das u. to, sai jarumawan da ke baya su kawo xauki. A
kewaye da sarki kuma akwai ’yan lifida, da ’yan sulke da’yan bindiga. Idan
an je sansani, sai a bar yara da mata tare da masu jiransu. Waxannan su ke
taimakon waxanda suka ji rauni. Su ke dafa abinci. Su kuma ke gyara
makamai. A wurin karawa, akan yi wa sarki shimfixa, ya zauna. Jarumawa
kuma suna kai hari suna dawowa. Sai su zo gaban sarki su tsaya su yi
kirari. Haka za’a yi ta yi, har a yi nasara. Ko kuma in yaqi ya vaci a juyo
da baya. A da lokacin yaqi, martaba da samun alfarma wajen sarki ta

267

203
dogara da jarumtaka ne. Don haka kowa yak an yi qoqari ya nuna
bajintarsa. Misali wasu kan je fagen Daga su zauna ayi ta harbinsu a wofi.
Waxansu kuwa qwalwar kansu su ke tuvewa, ayi ta sara da takobi yana
lauyewa. Ta haka idan sarki ya ji daxin bajintar wani bawansa a wajen
yaqi, sai ya bas hi kyauta mai yawa. Ko kuma ma ya yi masa sarauta.
Kuma ta irin wannan hanyar na ma aka yi ta sarautu na bayi, waxanda suka
zamo na qasaita a yanzu.

FITA RANGADI

Sarkin Yaqi na fita rangadi duk shekara sau xaya, don ya gana da
talakawansa ya gansu, su kuma su ga sarkinsu, a yi hidima ta arziqi. A
wannan fita ya kan karvi harajin waxanda bas u gama biya ba, ko ma bas u
biya gaba xaya ba. Wanda ya yi taurin biya a kan said a awakansa da
dabbobinsa idan yana da su, ko a fasa rumbun dawarsa a xebi na kuxin
haraji a biya. Cikin fitar nan a kan yi kimanin wata biyu ko fiye daga fita
zuwa dawowa. Yana fita da kimanin mahaya dawaki sittin, ko fiye galibi
ga kowanne qauye kwana xaya ake yi, sai dai idan buqatar a yi kwanaki
fiye da haka ya kama, kamar idan an zo Kafin-Dilimi inda ake tsayawa
kwana biyu, sarkin yaqi ya ba da kuxi a yi man gyaxa, mutane su yi ta
shiga ruwa suna kamo kifi, suna kawo gaisuwarsu gare shi, sai a soye shi
da man gyaxar nan a yi kamar kwando goma ko fiye, da shi sarki zai yi
tsaraba zuwa gida. To, sai kuma idan ya sauka a garin Mai gunduma, nan
kam sai ya yi kwana bakwai kana ya wuce. Kuma a lokacin Rahama kaxai
ita ce gunduma. Idan qauye ba zai iya xauke jama’ar da sarki ke tafe da su
ba, sai a raba qauyen biyu, ko ma uku. Duk mai masauki, dole ya tanadi
abu biyu; kazar wanda zai saukar, da damin dawar dokin sa. Masaukin
sarki kuwa shi ne xakin mai sabon aure, saboda tsaftarsa da kyawun
ganinsa. Idan sarki ya shuxe sai amarya da ango su dawo xakinsu.
Mutanen qauye suna sanin zuwan sarki garinsu ne tun kafin sarkin ya isa
garin, ta hanyar jakada da kan yi gaba, ya isar musu cewa ga sarki nan tafe.
San nan ana tafiya ne ana buga jauje, haka ma idan an baro gari na qarshe
wanda daga shi sai Lame, a kan tsaya a yi ta buga jauje tun cikin dare har
gari ya waye, don mata su kikkintsa, idan akwai wata mai yawon lalata ma

204
da ta tafi yawon kwartanci sai ta yi sauri ta dawo gida, ko akwai wata
wacce ta jawo kwarto gidanta, sai ta yi saurin sallamarsa ya fita. Kana sai a
shiga gari da hantsi. Hakan da ake yi kuma shi ne abin day a dace da
shari’a, don Ma’aiki –mai tsira da aminci- ya hana magidanci ya auko wa
iyalansa da daddare don kada ya ga abin da zai gurvata ransa. Kamar yadda
ya tava faruwa a wata shekara a Lame xin, wata mata ta tafi yawon
kwartanci ganin mijinta bay a gida, da jin kixan jauje, sai ta rugo zuwa
gida don mijinta ya same ta a gida, amma sai garin saurin xaukar zanenta,
sai tax au wandon kwartonta ta yafa a kayi ta koma gida, da shiga xaki
kuma ta rataye shi a ragaya, bat a san cewa wando ta xauko ba, har mijinta
ya dawo ya tarar da wandon a rataye, kuma ya san mai wandon, abin da
qarshe ya yi sanadiyyar rabuwar aurensu. Garin Lame a da can tana da
qofofi uku da sarki ke fita rangadi ta xayarsu ; Qofar Nasarawa, qofar Toji
da qofar Shifa. Kuma kowacce idan ya fita ta cikinta akwai garuruwan da
ta ke isarwa gare su. Ga misalan jerin garuruwan da aka ci zango, a wani
fita da ya yi ta qofar Nasarawa a shekarun 1940 kamar haka ;

1- Lame-Shau
2- Shau-Ruhu
3- Ruhu-Jira268
4- Jira-Sabon Gari
5- Sabon Gari-Gamãmai
6- Gamamai-Zuna
7- Zuna-Burku
8- Burku-Zomo
9- Zomo-Makana
10- Makana-Davave
11- Xavave-Kyare
12- Kyare-Rahama (Nan ya ke hutawa sati guda)
13- Rahama –Davave
14- Davave-Wundi
15- Wundi-Rishi

268
Iyakar qasar Bauci da qasar Ningi
205
16- Rishi-Zalau
17- Zalau-Ririwai
18- Ririwai-Jajuwal
19- Jajuwal-Tilde
20- Tilde-Toro
21- Toro-Magama Gari
22- Magama Gari-Rimin Zayam
23- Rimin Zayam-Nabardo
24- Nabardo-Zaranda
25- Zaranda-Tashar Durumi
26- Tashar Durumi-Biciki
27- Biciki-Zaranda
28- Zaranda-Kwamvo
29- Kwamvo-Maqera
30- Maqera-Kafin Dulumi
31- Kafin Dulumi-Mundu (kwana biyu ake yi a garin)
32- Mundu-Lame
Wata shekara kuma da ya fita ta qofar Toji, ga garuruwan da aka ci
zango cikinsu kamar haka ;
1- Lame-Shau
2- Shau-Toji
3- Toji-Nasarawa
4- Nasarawa-Tauran -baki
5- Tauran Baki-Zuku
6- Zuku-?
7- ?-Davave
8- Davave-Makana
9- Makana-Matawai
10- Matawai-Kyare
11- Kyare-Rahama (Nan ya ke hutawa sati guda)
12- Rahama-Gana
13- Gana –kamfanin kuza? Sauke?
14- -Rishi
15- Rishi-Yalwa

206
16- Yalwa-Zalau
17- Zalau-Rinjin Gura
18- Rinjin Gura-Ririwai
19- Ririwai-Marmara
20- Marmara-Jajuwal
21- Jajuwal-Tilde
22- Tilde-Toro
23- Toro-Magama Gari
24- Magama Gari-Rimin Zayam
25- Rimin Zayam-Nabardo
26- Nabardo-Zaranda
27- Zaranda-Tashar Durumi
28- Tashar Durumi-Biciki
29- Biciki-Zaranda
30- Zaranda-Kwamvo
31- Kwamvo-Maqera
32- Maqera-Kafin Dulumi
33- Kafin Dulumi-Mundu (kwana biyu ake yi a garin)
34- Mundu-Lame
Shekarar da ya fita ta qofar Shifa kuma, ga garuruwan da aka ci zango a
cikinsu kamar haka ;
1- Lame-Shifa
2- Shifa-Tama
3- Tama-Tulu
4- Tulu-Tauran baki
5- Tauran Baki-Sunkuye
6- Sunkuye-Xandanshi
7- Xandanshi-Kwabi
8- Kwabi-Rahama (Nan ya ke hutawa sati guda, don ita kaxai ce
gunduma a san nan)
9- Rahama-
10-
11- -Jajuwal
12- Jajuwal-Tilde

207
13- Tilde-Toro
14- Toro-Magama Gari
15- Magama Gari-Rimin Zayam
16- Rimin Zayam-Nabardo
17- Nabardo-Zaranda
18- Zaranda-Tashar Durumi
19- Tashar Durumi-Biciki
20- Biciki-Zaranda
21- Zaranda-Kwamvo
22- Kwamvo-Maqera
23- Maqera-Kafin Dulumi
24- Kafin Dulumi-Mundu (kwana biyu ake yi a garin)
25- Mundu-Lame

TSARIN SARAUTA A QASAR BAUCI


BAYAN ZUWAN TURAWA

TSARIN MULKIN EN’E : Lokacin da turawan mulkin mallaka na Ingila


suka karvi jan ragamar mulkin qasar Bauci a 1902, da kuma lokacin da
suka arewaci da kudancin Nijeriya a 1914, a san nan duk sun gwada tsarin
mulkin da suka zo das hi daga turai, don su mulki qasar nan da karan-
kansu, amma bas u ci nasara ba, tsarin mulkin farko da suka fara vullowa
das hi shine tsarin En’e wato mulkin qasa ta hannun sarakunan qasa, suka
ragewa sarakunanmu qarfin mulki, suka xora kansu akan sarakunan,
saboda wai a wurinsu sarakuna naxa su ake yi, ba zavarsu aka yi ta hanyar
zaven dimokaraxiyya ba, saboda haka sub a wakilan al’ummar qasa ba ne,
su dai wakilan gwamnatin mulkin mallaka ne. a farkon shekarar 1950
akwai hukumomin En’e 246 a qasa baki xaya, jihar arewa tana da 144,
jihar yamma na da 55, jihar gabas na da 47. Bisa sabon tsarin da suka zo
dashi sai suka tsara jerantuwar girman sarauta kamar haka ;

Razdan 269 - Sarki 270- Di’o271- Hakimi272 - Ma’aji273- Alqali274


269
Babban jami’in gwamnati mai qarfin mulki bature, mai lura da qasar sarki, kuma shi ke
riqe da kuxin qasa.
208
Wato dai sai suka zo da tsarin mulki mai qarfi uku ; legislative, Zavavvu
da Shari’a. Babbar manufarsu baki xaya it ace tabbatar da doka da oda, da
tara wa ’yan mulkin mallaka haraji. Daga 1967-1975 sadda sojoji suka
karvi jan ragamar mulkin Nijeriya sun rushe samfurin mulkin En’e, sun
kawo samfurin jihohi da qananan hukumomi, suka zo da tsarin mulki mai
hawa uku ;
Gwamnatin tarayya - Gwamnatin jiha - Gwamnatin qaramar hukuma275
(Shugaban qasa) (Gwamna) (Ciyaman)

SARAUTUN QASAR LAME A MASARAUTAR BAUCI

Ga asali yawan sarautun qasar Lame a masarautar Bauci, guda biyu ne ;


1- Sarautar sarkin yaqi
2- Sarautar sarkin kudu

ASALIN SARAUTAR SARKIN KUDU

Asalin sarautar sarkin kudu a masarautar Bauci, sarauta ce ta gidan


sarautan sarkin yaqi. Dalili kuwa a wajejen shekarar 1906, akwai wani
Bafulatani Yakanaji da ke zaune a Fedare, cikin qasar jarawa da ke
gundumar Toro, ana kiransa Jauro Kadiri, sai jarawa suka Sassari shanunsa
da adda, suka kashe wasu, to, shi wannan bafulatani, bai kai qara wajen

270
Babban jami’in mulkin mallaka mai qarfin mulki xan qasa, mai lura da baki xayan
masarauta.
271
Babban jami’in gwamnati mai qarfin mulki bature mai lura da qasar Hakimi, kuma shi
ke riqe da kuxin qasar.
272
Babban jami’in mulkin mallaka mai qarfin mulki xan qasa, mai lura da qasar
hakincinsa.
273
Babban jami’i mai lura da gidajen yari
274
Babban jami’I mai lura da vangaren shari’ah
275
A cikin sabon tsarin qaramar hukuma da sojoji suka zo dashi ; aikin qaramar hukuma
shi ne lura da tashoshin mota, aikin tsaftace gari, maqabartu da kusheyi, yin rajistar
haihuwa, mutuwa da aure, lura da lambuna, da xakunan taruwar jama’a, lura da labi da
burtali, da wuraren dashen itatuwa, sa ido a kasuwanni dab a da takardar kasuwa. Tara
harajin saran daji, da lura da gandun daji da sauransu.
209
Harxon Toro ba -zamanin Harxo Jika- bai kai qara wajen sarkin Bauci ba -
zamanin sarkin Bauci Hasan Mahmud - sai ya tafi wajen Razdan,276 ya kai
qarar cewa Jarawa suna kashe musu shanu. A san nan kuwa turawa suna da
qarfi, don ba su daxe da biyar qasar nan ba, sai Razdan ya sa aka kira
sarkin Bauci ya ce, “Qaqa zai bar wuri kamar Fedare, bai sa wakilinsa ba?”
Sai sarkin Bauci ya umarci sarkin yaqi da ya sa wakili a wurin, sai sarkin
yaqi ya umarci Harxon Toro, wanda wanda wannan rikici ya taso a cikin
gundumarsa, da ya tura wakili can. Da Harxon Toro ya tuntuvi
’yan’uwansa, ko akwai wanda zai yarda a tura shi wakilci a can? Duk sai
suka qi, saboda suna ganin yana son ya yi musu wayo ne, ya tura su daji,277
nesa da gida, don kada su ma su gaji gida, wataran su yi sarautan Harxo.
Da sarkin yaqi ya samu labarin halin da ake ciki, sai shi da kansa yana
naxa Aliyyu Mai Gunduma, yana tura shi babban cibiyar qasar Jarawa da
ake kira Unguware. To, da ya ke tana kudu da Lame sai ana kiran wanda
duk aka tura can da Sarkin Kudu. Bayan mutuwarsa sai aka naxa Usman
xan Harxo Bello, uban sarkin yaqi Muhammadu Maidawa, ya shekara
ashirin da biyar yana Mai gunduma a can 1920-1929. Kana sai batun
sarautar hakinci ya taso, sai ya bar wannan sarauta ta Mai gunduma, in da
ya koma Lame ya gaji Sarkin yaqi Abubakar, ya kuma yin shekara tara
yana sarautar sarkin yaqi 1929-1938. Bayan barinsa sarautar gunduma, sai
masarautar Bauci ta qwace sarautar sarkin kudu daga gidan sarkin yaqi, ta
mayar da shi na ta. yadda ta yi kuwa shi ne sai ta haxewa sarkin yamma,
mai mulkin tsohuwar qasar jama’a, gundumar jarawa, aka xauke
hedkwatar daga tsohuwar jama’a aka mayar Kwacciyel, cikin qasar jarawa.
Shi kuma sarkin yamma ga asali, xaya daga cikin ’ya’yan sarkin Bauci ake
naxawa. Wato dai an qwace sarautar sarkin kudu daga gidan sarkin yaqi,
an mai da shi na ’ya’yan sarkin Bauci. Sarautar da ba ta sake dawowa
mavuvvugarta na asali ba, sai bayan da aka bai wa Yakubu xan Abubakar
sarautar sarkin yaqi Bauci 1964-1994, shi kuma lokacin yana kwamishina
a lardin Neja, Sai aka yi wa Malam Salmanu xan sarkin yaqi Ade, wanda
aka fi sani da ‘Baba Buye’ hakincin qasar Lame 1964-1976. Bayan
murabus xinsa aka naxa sarkin kudu Muhammadu Goge 1976-1976, kana
276
Mista Oliver Howard
277
Don a san nan wurin jeji ne, ba kowa sai qabilu. Ba wanda yak e so ya zauna a gun.
210
sai Muhammad Maidawa, wanda shi ma ya fara da sarautar sarkin kudu
1976-1994, kana ya cike da sarautan sarkin yaqi, bayan mutuwar sarkin
yaqi Yakubu a shekarar 1994. Sai aka naxa Ciroman Bauci sabon sarkin
Kudu ya gaji Harxo Bello, bayanshi sai Sarkin Kudu Ahmadu xan sarkin
Bauci, sai kuma sarkin kudu Sani. Daga nan sai aka yi wa jarawa qasar
kansu a 1950. A taqaice dai masarautar Bauci sun qwace sarautar sarkin
Kudu na asali, wacce ake tura xan sarki Wase sun mai da ita na’ya’yan
gidansu. An dawowa da gidan sarki ita zamanin hakimin qasar Lame
Salmanu da Muhammadu Maigoge da Muhammadu Maidawa (1964-
1994). Kana aka sake qwacewa bayan haxewa Muhammadu Maidawa
sarautar sarkin Yaqi.

JIMILLAR WAXANDA SUKA YI SARAUTAR


SARKIN KUDU A QASAR JARAWA

Suna Shekara Daxewa


1 Sarkin Kudu Aliyyu
Harxo Bello xan sarkin yaqi Hasan 1920-1929 9
2 Ciroman Bauci
3 Ahmadu Xan Hasan Mahmud
4 Sarki Sani 1941-1950 9

Shi ma sarkin yamman daga qarshe aka daina tura shi, a 1950 aka yi wa
jarawa qasar kansu, da hakiminsu na musamman.

ASALIN SARAUTAR SARKIN YAQIN BAUCI


Asalin sarautar sarkin Yaqi a masarautar Bauci, ta faro ne tun sadda
sarkin Bauci malam Yakubu ya karvo tutar jihadi daga wajen Shehu Xan
Hodiyo, shi ma sai ya naxa masu taimaka masa cikin isar da saqon Allah.
Daga cikin waxanda ya naxa, akwai sarkin yaqi Muhamman Kusu.
ASALIN GIDAJEN DA SUKE SARAUTAR SARKIN YAQI
1- Gidan bare-bari
2- Gidan fulanin Wunti
211
ASALIN FULANIN WUNTI

Wunti tsintsiya maxaurinki xaya


Wunti gidan da munafiki bas hi zama
In ka ga munafiki ya shigo baqo ne

Asalin fulanin wunti, ko ‘Wuntankin’ kamar yadda ’yan’uwansu Fulani


ke kiransu, wasu qabilu ne na larabawan Sinhaja, da suka zauna a wani
yanki da ake kira Tukrur, a qasar Murtaniya. Sun yi hijira zuwa gavar
tekun Senigal, wasu zuwa Tambutu tun cikin qarni na takwas bayan hijira.
A Tambutu sun taka rawar gani wajen tabbatar da Askiya Muhammad a
matsayin sarkin daular Songai a qarni na 15 miladi, har ya ba su mulkin
gwamnan Tambutu, kuma aka samu gwamnoni cikin gidansu da dama, har
zuwa kan Muhammad Aqix a 1591 miladi. Bayan rushewar daularsu, sai
suka yi hijira daga Tambutu a qarni na 17, suna tafiya suna kafa garuruwa,
suka ratso ta kudancin Nijar suka shigo arewacin Nijeriya. Sun fara ya da
zango a Zamfara, a wani wuri da ake kira Tsohon Banaga. A cikin
shekarun 1750 sun yi hijira suka bar yankin Zamfara, suka shigo qasar
Zazzau, a qarqashin jagorancin shugabansu Muhammadu Sambo, da
qaninsa Muhammadu Dabo, shi ake ce masa ‘Titi’ ko ‘Titiye’ ma’ana ta sa
da fillanci ‘makiyayi,’ da qaninsu M. Yunusa da mutane masu yawa. Suka
bar xan’uwansu a Zamfara mai suna malam Muhammadu Daxi. Shi
Muhammadu Sambo sai ya bar ’yan’uwansa a Zariya ya tafi Kaciya, Shi
ma Muhammadu Dabo, sai ya bar xan’uwansa Yunusa a Jaji ya zauna wani
gari can kudu maso gabashin Zariya, da ake ce masa ‘Xan’alhajin gabas.’
Daga baya kuma ya kafa wani gari, ya raxa masa suna Lere, sarakunan
Zazzau suka tabbatar masa da sarautarsa a 1808. Waxannan Fulani, sun san
sauka a yankin Bauci, a wani wuri da ake kira Zaranda, a qarshen qarni na
18, wato tun kafin jihadin Shehu Xan Hodiyo. Daga nan M. Muhammad
Dabo Titi ya zakuxa, zuwa Toro, in day a gina gidansa a wani wuri da ake
kira Gyamzo, sai ana kiran wurin ‘Wunti-Gyamzo’ To, a cikin jama’ar
fulanin nan ne, wasu jama’a qarqashin jagorancin Usman Biri suka tashi
suka nufi kudancin Bauci, suka yaqi qabilar Sayawa, a kusa da Tafawa
Valewa suka gina zagayayyen gari suka raxa wa suna Leren Zage-zagi a

212
1790. Suna kai wa sarkin Zazzau gaisuwa, saboda a lokacin duk qasar
Bauci babu wani babban sarki, kam ban da sarkin Zazzau, har sai lokacin
da M. Yakubu ya fara yaqin jihadi a 1806, in day a samu nasarar haxe
garuruwa masu yawa, cikinsu hard a Leren a qarqashin masarautarsa, daga
nan aka maid a sunanta Leren Bauci. Bayan Shehu Xan Hodiyo ya
qaddamar da jihadi a 1804, sai Muhammadu Dabo Titi ya taimakawa M.
Yakubu, wanda ya karvo tutar jihadin qasar Bauci. Sai M. Yakubu ya naxa
shi sarkin yaqi, daga baya kuma ya bar wa surukinsa Fulata-Barno mai
suna Muhamman Kusu. Zuriyyar waxannan mutane biyu su ke sarautar
sarkin yaqi, hakiman qasar Lame a masarautar Bauci, har yau xin nan.

DANGATAKAR GIDAJEN SARAUTUN BIYU

1- Abotar Muhamman Kusu da M. Jibir


2- Faximatu uwar sarkin yaqi Abubakar da sarkin yaqi Usman xan
Harxo Bello (uban sarkin yaqi Maidawa) uwarsu xaya ubansu
xaya.

SARKIN YAQI NA I
MUHAMMAN KUSU
(1812-1822)

Lokacin da Malam Yakubu Daxi ya yi karatu a wajen Shehu xan


Hodiyo, har Shehu ya aura masa ’yar wani abokinsa bazamfare. To, a san
nan mutane da yawa sun yi ta zuwa wajen Shehu suna taruwa. Sai
sarakunan Hausa suka fusata. Suka zama suna fitinar jama’arsa, suna kama
su, suna sai da su. Da abin ya tsananta, sai ya kira mubaya’a, domin su
yaqi abokan gaba. Suka gina ramin ganuwa, suka xaura tuta. Sai Shehu ya
umarci Yakubu da ya koma wajen mutanensa (Gerawa) ya kiraye su. sai ya
koma gida ya kiraye su, amma ba su amsa ba. Amma sai waxansu mutane
daban waxanda ba ’yan qabilarsa ba suka amsa masa. Daga cikinsu akwai

213
malam Adamu, da Ibrahim. Abdun Dumi da Hasan da Faruqu da
Muhamman Kusu. Muhammadu Yaro da Hammadan da malam Badara da
waxansu daban. Suka karvi abin da ya gaya musu. Sai ya tafi da su wajen
Shehu, suka yi masa mubaya’a. Shehu ya kawo tuta ya ba su. Kuma ya yi
musu addu’ar Allah ya ba su taimako da nasara. Da suka dawo, sai Malam
Yakubu zauna a wani wuri da ake ce masa Warunje. Bayan haka ya tashi
ya koma Inkil ya zauna. Mutane suka yi ta zuwa daga kowacce fuska, suna
yi masa mubaya’a, suna zaunawa wurinsa. Sai ya naxa malam Faruqu
Galadima. Ya kuma naxa Muhammadu Kusu sarkin yaqi. Kuma Yakubu
ya aiki Muhammadu Kusu, da Dawaki Hammada Muhammadu Yaro zuwa
Zaranda, da Felu, da Geji da Bulu suka yaqe su, suka karkashe su. suka
kamo ’ya’yansu suka komo wurin Yakubu amintattu, masu samun ganima.
To, sai savani ya shiga tsakanin Yakubu da Buba Yaro sarkin Gwambe,
akan sha’anin kan iyaka. Suka yi yaqi har da kashe-kashe. Aka yi kare jini,
biri jini. Ko da ya ke akan ce Yakubu ne ya yi rinjaye, don an kasha
mutanen Gwambe da yawa. Amma fa a wannan yaqi Sulaimanu xan sarki
Buba Yaro ya kashe masa sarkin yaqinsa Muhammadu Kusu. Yakubu ya
qetare kogi ya cim musu. Da suka ga haka suka ruga. Sai suka yi sulhu,
kuma suka yi wa junansu alqawari cewa ba za su sake ta da fitina irin
wannan ba har abada. Shi Muhamman Kusu asalinsa babarbare ne, amma
da ya ke ba a qasar bare-barin ya tashi ba ko barbarcin ma ba ya ji. Ya tashi
ne a wajen fulani wuntawa. Yana ma;lanta gare su. Shi ya sa ma ko da
maganar sarauta ya taso, suka tura shi don su a lokacin kula da hidimar
shanunsu ya fiye musu komai.

SARKIN YAQI NA II
M. JIBRIL
(1822-1842)

Sarkin yaqi malam Jibir aminin Muhammadu Kusu ne na qut da qut,


sadda aka kasha Muhammadu Kusu, sai sarkin Bauci ya naxa shi, sarkin
yaqinsa. Shi bawunte ne, bafulatanin Toro. Kuma a nan Toron ya yi
sarautarsa, har ya mutu Allah bai ba shi haihuwa ba.

214
SARKIN YAQI NA III
ABDULQADIR XAN MUHAMMAN KUSU
(1842-1852)

SARKIN YAQI NA IV
HAKIMIN QASAR LAME NA I
USMANU I XAN HARXO SAMBO
(1852-1867)

Sarkin yaqi Usmanu qanin sarkin yaqi Jibril ne. Amma irin riqon da ya
yi masa, sai mafiya yawan mutane suka xauka qaninsa ne. An naxa shi
sarautar sarkin yaqi yana zaune a Toro. Amma daga baya sai ya bar Toro
ya koma ‘Gau’da zama. Lokacin da Ningawa suka ci Gau da yaqi, don ya
ji daxin gudanar da mulkinsa cikin sauqi, sai ya shawarci ’yan’uwansa
fulanin Lame ta farko, da da ta ke arewa da kogin Dilimi kan cewa su dawo
tsallaken kudu da kogi. Domin ko ba komai kogin zai zamo kariya gare su
daga magauta, musamman lokacin damina, kadan bah aka ba kuma
Ningawa su lamushe su. Sai suka amsa kiransa, suka dawo suka taya shi
kafa sabuwar Lame. Aka shata ganuwa da gidan sarki da masallaci. Sai ya
gina gidan sarkin Mara, da sarkin Gwa, da sarkin Shau duka a cikinta.
Shekara ta sa huxu yana zaune cikinta. Sai sarkin Bauci Ibrahim Yakubu278
ya umarce shi ya roqi Harxon Zaranda wani wuri a cikin qasarsa, ya kafa
garin Ribaxi. Cikin yawon nema sai suka ga wasu wurare guda biyu, xaya
ana kiransa ’Yolawari,279 xayan kuma ’Yolawai wai sai aka ce masa idan
ya kafa gari a wurin na farkon, mutanensa za su yi arziqi, amma za’a ci su
da yaqi. Idan kuma ya kafa ana biyun, to, dukiyarsu za ta qare, amma ba
za’a ci su da yaqi ba. To, sai ya zavi na biyun, inda ba za’a ci su da yaqi
ba. Sai ya sauya sunan wurin, ya raxa masa Kafin Dilimi. Sai kuma ya
dawo da hedkwatar mulkinsa cikinta. To, ana nan sai rikici ya auku

278
Ya yi sarauta daga 1845-1877. Ya rasu a qauyen Rauta, lokacin da ya je kafa garin
ribaxi na Kafin Rauta, domin tsare birnin Bauci daga maharan Ningawa. An binne shi a
cikin xakin da ya rasu a cikinsa. An ce da kansa ya tona qabarinsa a cikin xakin. Ya kuma
bar wasiyyar idan ya mutu su binne shi ba cikinsa. Kuma suka aikata hakan.
279
Ita ce aka canza sunanta ya koma Mundu
215
tsakaninsa da Harxon Zaranda. Abu kamar wasa sai rikicin ya tsananta. Sai
sarkin Bauci ya umarci sarkin yaqi ya bar garin, ya koma wajensa a Rauta.
To, sai ya koma Rauta, bayan wata shida, Allah ya yi qarar kwanansa a
can, kuma a can aka binne shi.

SARKIN YAQI NA V
HAKIMIN QASAR LAME NA II
AHMADU XAN MUHAMMAN KUSU
(1867-1896)

SARKIN YAQI NA VI
HAKIMIN QASAR LAME NA III
IYA XAN SARKIN SARKIN YAQI JIBRILLA
(1896-1897)

SARKIN YAQI NA VII


HAKIMIN QASAR LAME NA IV
MUHAMMADU MAIKAYI XAN AHMADU
(1897-1901)

Shi ne wanda ya yi sarauta har sau biyu. Ya yi na farko aka tuve shi,
kuma dalilin tuve : ya tafi rangadi, bai sanar da sarkin Bauci ba. Ga kuma
qasar Lame da yawa, kafin ya kewaye qasar Lame ya dawo, yak an xauke
shi kimanin watanni masu yawa. Na farko dai ga wuyar tafiyar a lokacin,
ga kuma rashin yalwatattun hanyoyin tafiya da na sadarwa. Tafiyarsa ked a
wuya sai sarkin Bauci ya zo rangadi qasar Lame, ba tare da sanin sarkin
yaqi ba ya nan ba. Wannan abu ya vata ran sarkin Bauci ainun, yadda
mutum zai bar gun aikinsa ba ta tare da sanar da na gaba das hi ba. To, an
ce shexanu kuma sun shiga al’amarin suka qara vata shi. Sai sarkin Bauci
ya tuve shi, ya naxa wani a madadinsa. Shi kuma sadda ya dawo ya samu
labarin abinda ya faru, sai ya koma gidansu a Bauci, ya yi zamansa a can.
To, yana can ne zaune, sai wanda aka naxa xin shi kuma ya rasu bayan
shekara huxu. Kuma shi wancan sarkin Baucin day a tuve shi, shi ma ya

216
mutu. Sai magajinsa, sarkin Bauci Hasan Mahmudu280 ya mayar das hi
karagar mulki, inda ya shekara biyu, kana ya rasu a shekarar 1907. Idan ka
tara kwanakin sarautarsa shekaru huxu ne cif, biyu kafin a tuve shi, biyu
bayan an dawo da shi.

SARKIN YAQI NA VIII


HAKIMIN QASAR LAME NA V
UMARU ALKAMMU XAN SARKIN YAQI USMANU I
(1901-1905)

SARKIN YAQI NA IX
HAKIMIN QASAR LAME NA VI
MUHAMMADU MAIKAYI XAN AHMADU
(1905-1907)

SARKIN YAQI NA X
HAKIMIN QASAR LAME NA VII
ADE XAN SARKIN YAQI AHMADU
(1907-1909)
Ga shi sarki ga shi malam, kyauta kuwa wajensa sai ka ce ruwan sama.
Aminin sarkin Bauci Maigari ne, wanda ya yi sarauta daga 1907-1941.
Wata shekara ya fita rangadi kafin ya dawo, sai aka yi kisan kai a qasar
Lame. Mai karatu ka san fa yadda sarakunanmu na da su ke xaukar kisan
kai babban al’amari ne. to, gas hi kuma an yi, kuma sarki bay a nan, babu
wata kafar sadarwa kuma a wancan lokaci da za’a iya isar masa da halin da
baya ke ciki. Di’o na zamanin ya yi jira yau ne gobe ne, hakimi zai dawo
ya sanar das hi halin da ake ciki, don shi ma ya sanar da Razdan, shi kuma
Razdan ya sanar da sarki, amma har ga abu zai ja lokaci, shi kan shi ma
ba’a sanar dashi ta hanyar day a kamata ba tukuna balle ya kai maganar ga
magabatansa don a fara bincike. Sai ya ga cewa shi ma idan ya daxe bai kai
labarin gaba ba, laifin zai iya shafar aikinsa. Saboda haka sai ya sanarwa da

280
Ya yi sarauta daga 1903-1907. Ya rasu a Bauci, kuma qabarinsa na maqabartar
sarakuna ta Dajin.
217
Razdan duk halin da ake ciki. Shi kuma ya xauke shi tare suka sanarwa da
sarkin Bauci cewa, “Mun zo ne mu sanar maka cewa an yi kisa a wani
lungu cikin qasar Lame, amma sarkin yaqi bai zo ya sanar mana ba, na zo
ne na gaya maka cewa na tuve shi.” Ba su daxe da fita daga fadar sarki ba,
sai ga sarkin yaqi Abubakar ya dawo, ya tarar da sarkin Bauci Maigari na
karatu, sai ya shiga, da ganinsa sai sarki ya ce, “Sarkin yaqi? Ya amsa ya
ce, “Allah ya daxe da ranka.” Ya ce, “Ba ka gamu da Razdan da Di’o ba?”
y ace, “Na gamu da su.” Ya ce, “To, ya zo y ace an yi kisa ba ka zo ka
sanar dashi ba, ya tuve ka. Amma ina roqonka, kada ka xaga hankalinka,
ka bar ni ka ga yadda za mu qare dashi” Washe gari sai aka samu gawar
Razdan ta yi tim, ya wuce daga bacci.281 Qabarinsa na nan a kan titin ‘Sir
Kashim Ibrahim’ kusa da ‘Bauchi Club’ an kewaye shi da dangar waya.
To, kasancewar idan an tuve sarki ba’a barinsa a garnish, sai aka xaga shi
daga Wunti aka mai dashi Unguwar Karofin Madaki, in day a qarasa
rayuwarsa yana karantar da ilmai na shari’ah, don ko dama can shi malami
ne.

SARKIN YAQI NA XI
HAKIMIN QASAR LAME NA VIII
HASAN XAN HARXO BELLO
(1909-1924)

SARKIN YAQI NA XII


HAKIMIN QASAR LAME NA IX
ABUBAKAR XAN IBRAHIM
(1924-1929)

SARKIN YAQI NA XIII


HAKIMIN QASAR LAME NA X
USMANU II XAN HARXO BELLO
(1929-1938)

281
Razdan xin Bauci da ya rasu aka binne shi a Bauci sunansa Mista Oliver Howard. An
haife shi ran 14 Maris 1875, ya rasu ran 20 Satumba 1908
218
SARKIN YAQI NA XIV
HAKIMIN QASAR LAME NA XI
SARKIN YAQI USMANU BABALE
(1938-1964)

Usmanu Babale xan sarkin yaqi Umaru Alkammu xan sarkin yaqi
Usmanu xan Harxo Sambo na asalin Fulata-Borno. Shi ne sarkin yaqin
Bauci, hakimin qasar Lame na goma sha huxu. Shekara ta sa 27 yana
sarauta. Shekara takwas a Lame, shekaru goma sha tara a Gumau. Yana
daya daga cikin mutum huxu da suka raka mai girma sarkin Bauci zuwa
Ikko wajen bikin karvan mulkin kai a shekarar 1960. Shi da Ajiya, da
sarkin Jarawa, da Bunu.

TASOWA ZUWA GUMAU

Sababin tasowa daga Lame zuwa Gumau dai saboda :


1- Lame ta yi gefe daga inda mu’amalar turawa ta ke.
2- Kuma ta yi gefe a zamanta hedkwatar qasar Lame
3- Kuma babu hanyar mota mai kai wa zuwa garte ta, musamman
a lokacin damina. Ga shi kuma lokacin mu;lkin En’e ake yi, duk
abin da turawa za su yi sai sun haxa da sarakunan qasa. Sai
turawa suka ce wa sarkin yaqi, ko dai ya tashi daga Lame ya
komo sabon garin da su turawa suka kafa (Gumau), ko kuwa su
naxa wani hakimin a Gumau, shi kuma su bar shi ya yi zamansa
a Lame. Da mutanen Lame suka ji haka fa sai suka shiga sauke
alqur’ani suna yanke-yanke suna sadaqa da addu’o’i, kada
wannan shiri na turawa ya tabbata. Shi kuwa sarkin yaqi sai ya
aika wa wani abokinsa malami masanin furu’a, wato malam Idi
xan Muhammadu Jika a kan ya duba masa wannan al’amari. Sai
malam ya ce masa, dawowa Gumau shi ne ya fi, idan ma ya qi
dawowa, garin dai zai samu ci gaba da bunqasa. Sai sarkin yaqi
ya ce, “To ya yarda zai dawo, amma sai in za su dawo tare da
shi malam xin.” Da jin malam ya yarda zai komo Gumau, su
kuma mutanen Riruwai su ma sai suka shiga yanke-yanke da

219
sadaqa da addu’o’i kada malam ya bar gari, domin sun san
tashin mutane irinsu daga gari, zai tafi da jama’ah masu yawa.
Kuma suna tuna abin da wani malami ya tava gaya wa sarkinsu
cewa kafa wannan gari na Gumau, har in ya tabbata shi zai
zamo sanadiyyar mutuwar garinsa, ko za ta dawo sai bayan
tsawon zamani. Mutanen Ririwai sun yi ta kafe-kafe akan duk
wata hanya ta zuwa Gumau akan wanda ya yi niyyar barin
garinsu ba zai wuce wurin da kaya akan jakinsa, sai jakin ya yi
tutsu ya zubar da kayan a wurin. Kuma har yanzu wurin yana
nan, kuma haka ya ke, duk xan shekara sittin a Ririwai yana
sane da wannan. Kuma ko ga mutanen Lame, kafa Gumau da
barin cikinsu da sarkin yaqi ya yi bai yi musu ciwo irin yadda
ya yi wa mutanen Ririwai ciwo ba. Domin tun ana raba feguna
kyauta ake so da su su zo su karva fir sun qi. Kuma har gobe
sun fi tsanar zuriyar ’yan asalin can da iyayensu suka yarda
suka dawo Gumau. Kuma har gobe suna Alla-allan ranar da
wani arziqi zai bayyana a garinsu zuriyoyin waxannan su ce za
su koma su ga wulaqanci. A kan ce qaddara ta riga fata. Komai
qwazo abin da Allah ya hukunta shi ke aukuwa. Ana nan sai
aka sa rana sarkin yaqi da malam suka zo aka nuna wa malam
fulotinsa, inda zai gina gida, ba nesa ba da gidan sarauta. Abin
da ya sa bai yarda an gina masa ba ma, kamar yadda aka gina na
sauran malamai da aka xauko su daga garuruwasu, domin ya ce
ya fi son ya gina abinsa da kansa. Don yana tsoron kada
wataran ko bayan ranshi a zo a fid da ’ya’yansa daga ciki, a ce
na hukuma ne.

Ana nan kwanci-tashi turawa suka matsa sai sarkin yaqi ya dawo daga
Lame zuwa Gumau, har suka sa masa ranar tasowa tun ma kafin a gama
gina gidan sarauta. Ya taso ran takwas ga watan Nuwambar 1946 tare da
jama’ah ta sa. Sai ya fara sauka a unguwar Kanya. Sai da ya kusan shekara
aka qare aikin gidansa sannan ya shigo cikin Gumau. Qaninsa Baba Audu
da Madakin Wunti sun sauka a Kaurare. Barden Wunti ya sauka Babbar
Riga. Da jin ya dawo cikin Gumau sai shi ma malam ya taso daga Riruwai

220
zuwa Gumau bayan dawowar sarkin yaqi da ’yan kwanaki qalilan. Sai ya
zamo kowannensu ya cika wa xan’uwansa alqawarin da ya xauka masa.

JAMA’AR DA SARKIN YAQI YA TASO DA SU

Da ranar tasowa ta zo sarkin yaqi Usmanu Babale ya taso daga Lame


zuwa Gumau, da umarnin turawan mulkin mallaka, ran 08-11-1946 da
magidanta 55. Yara da matasa kuma 36. Magidanta cikinsu su ne Abdu
Mahe, Barden Wunti Muhammadu282Marafa Sambo, Habu Nannake, M.
Balarabe, Umaru xan Tafida283Liman M. Bello, Haruna Nabintus, Baba
Buye284Bunun Fuloti285 Dunqule mawaqi286 Kwando Farin- malam287 M.
Aliyyu, Cigari, Xanbage288 Qanqara, Duna Nayayale289 Garba Zagi, Sarkin
Zagi Ahmadu, Sarkin Zagi Rabo, Sarkin Zagi Basai, Nababa, Harxon
Wonu Abubakar, Waziri Xanwunti290 Madakin Wunti, Wazirin Jauje, M.
Shekarau, Masu, Sambon Wonu, Baba Xandukushi, M. Gixaxo xan
Ciroman Rafi, M. Abdussamadi, Ciroma Habu, Balla, M. Bawa, M.
Mande, Waziri Kadai291 Gashi Mai takalmi, Dumfama, Gare, Maina Nuhu,
Inuwa Mahe, Garba Barema, M. Dabo, M. Shehu Manden tadi, Xanlawal

282
A tarihin sarautar Barde a masarautar Wunti shi ne na biyu. Kafin shi an yi Barden
Wunti Badau, wanda shi ne ma ya fara. Bayan shi kuma an yi Barden Wunti Yaro. Sai
Barden Wunti Garba Muhammadu.
283
Uban ’Ya’ya mahaifiyar Xan’atta.
284
Shi ne sarkin Kudu Salmanu (1964-1976)
285
Uban Ladan mai hoto.
286
Xan barden Wunti Muhammadu ne.
287
Xaya daga cikin maroqan masarautar Wunti
288
Amintaccen yaron sarki Yaqi Babale ne. Gidansa ne a daidai inda gidan M. Ladan
Xantiye ya ke a yanzu.
289
Shi ma maroqi ne. Gidansa ne a daidai sabon gidan Ambasada AG Abdullahi
290
Uban waziri M. Muhammadu Sambo. Shi ne wanda ake jingina makarantar Unguwar
Waziri da sunansa. A cikin gonarsa ne aka fid da titi daga qofar waziri Gadanga zuwa
asibiti, har zuwa b=titin hanyar Saminaka.
291
Wazirin Lame. Uban Xanladi Maute da Ambasada AG Abdullahi. A cikin gonakinsa
ne ma aka yi maqabarta da masallacin idin garin nan.
221
Mai bedi, Makama Dembo, Julde292 M. Nagura, Shamaki293 Gidibidi,
Shu’aibu Have, Galadima Bawa294da Jarumi Guddi. Matasan cikinsu kuma
su ne Waziri Musa, Ahmadu Kola, M. Isa, Musa Na Mailara, Badaqoshi,
Musa Maidawa295 Sani, Umaru, Voyi Tabako, Sale Xan Bagadaza,
Maiwunti, Sambo, Gyamzo, M. Badagari, Nata’ala, Lakatu, Munkaila
Ibrahim, Duni Mai igiya, Bala, Wada Xan bature, Ahmadun Kwas, Sango,
Ladan Ahmed, Maigoge, Barde yaro, Garba Xan’azumi, Xalladi Maute,
Ahmadu Xanbaba, Xannot, Xankule, Ibro, Bishek, Mamuda Bugau,
Maimato da Boyi Ariyas.

RASUWARSA

Ya bar Gumau ya ta fi Bauci yin sallar azumi da shirin hawan daushe ran
13 ga watan Fabrairu 1964, an kuma yi hawan sallah ran 15 ga Fabrairu.
Ranar qaramar sallah da daddare yana hutawa a masaukinsa, sai ga xan
aiken sarkin Bauci cewa a gaya masa ana buqatar shi da jama’arsa gobe su
fito qofar fada da sassafe kafin qarfe bakwai, don za’a je a yi wa
kwamishinan lardin Bauci gaisuwar sallah. Kuma aka ce ya gaya wa
jama’arsa duk wani mai abin hawa, doki, mota, babur, ko keke ya hawo ya
zo qofar fada a lokacin da aka faxa. Bayan an gama wasan sallah ya koma
gida, sai ya fita rangadi Lame. Ya fito yana zagaya dawakai a tikensu, yana
shasshafa su sai wani doki ya taka shi a sawu, sai ya dawo Gumau ya sa
aka xauko masa wani malamin asibiti ana ce masa Malam Garba Mashi, ya
zo yana masa jinya a gida. Da aka ga ciwo bai warke ba, sai aka xauke shi
aka kai shi asibitin Bauci. Da ya ke abu ya zama na ajali, bai kwanta a
asibiti ba, sai ya bar asibitin ya koma gidansa a Bauci yana jinya a can, tare
da wani baransa da ake kira Dabo. Sai ciwo na ta ci gaba, har ya kai ga ba
ya iya cin abinci. Wata ran M. Baqon dare ya shiga gare shi yana masa

292
Sa’in Wunti. Da shi aka zana garin nan tare da turawa, su na riqe musu igiya. Ya yi
tsawon rai. Don bai rasu ba sai cikin 2017. Amma Allah bai ba shi haihuwa ba.
293
Uban Sule Shamaki. Kuma direban sarkin yaqi Maidawa. Shi ne mutum na biyu da ya
fara iya tuqa mota a garin nan.
294
Uban su Xanlami Galadima da AGG
295
Uban lifidin Wunti
222
faxa ya ce, “Sarkin Yaqi, wallahi ka kula da cin abinci, idan fa ba ka cin
abinci za ka mutu.” Rashin cin abincin nan na sa, ba ya rasa nasaba da wata
magana da wani malami mai bugun qasa ya tava gaya masa, cewa doki ne
zai yi sanadiyyarsa. Domin da ma shi mutumin malamai ne. Bisa dukkan
alamu kuma ya yarda da wannan magana, kuma ya riqe ta sosai, kuma ita
ta yi tasiri a zuciyarsa. Allahu Akbar ! duniya ba gidan dauwama ga kowa
ba. Sarkin yaqi Babale ya rasu, bayan shekaru masu yawa yana aikin Ala
sambarka, da taimakon bayin Allah. Ko da ya ke Allah bai ba shi haihuwar
xa namiji ba, amma Allah ya ba shi haihuwar ’ya’ya mata biyu masu
albarka; Yalwa da Zariya. Ita Yalwa ta auri sarkin Lame Muhammadu
Gixaxo ta haifi Alhaji Ahmadu marafan Wunti, da Dawai. Ita kuwa Zariya
ta auri Adamu Barayan Wunti, ta haifi Jummai matar Ubandoma, da Ladi
matar Ali Dutse.

SUNANSA AKA YI WA GARIN BABALE

Sunansa ne aka raxawa garin Babale na gundumar Tilden Fulani, a can


kan iyaka tsakanin Bauci da Filato. Domin a zamanin da, idan ya tafi
rangadin tattara haraji a gundumar Tilde, Ribina da Toro, nan inda Babale
ta ke ya ke zama, sai duk mai son ganinsa ya zo ya gun. Sukan ce, “Za mu
wajen (sarki) Babale, mun fito wajen (sarki) Babale.” Yau da gobe sai ya
zamo ana taqaitawa ‘Za mu Babale. Mun fito wajen Babale.’ shi ken an
kuma sai sunansa ya bi garin har bayan ransa, har yau. Wanda aka turo ya
wakilci qasar Lame kafin a naxa sabon sarki shi ne M. Ibrahim Bauci.

SARKIN YAQI NA XV
YAKUBU XAN ABUBAKAR
(1964-1994)

‘Dodon Gwari
Irin gidan Muhamman Kusu’

An haife Alhaji Yakubu OFR, a shekarar 1925 a cikin garin Lame, san
nan lardin Bauci, yanzu kuwa qaramar hukumar Toro. Sunan mahaifiya ta

223
sa Faximatu. Cikin duk sarakunan yaqin da aka yi, ba’ayi mai ilimin
zamani kama ta sa ba. Ya yi makarantar Elementare ta Lame 1934-1937.
Ya shiga Midil 1938-1943. An xauke shi aiki a ofishin mulki na lardi
‘Central Office’ 1943-1948. Ya yi makarantar koyon aikin akawu ta
lardunan arewa (Northern Provinces Clerical College) da ke Zariya 1948-
1949. In da daga dawowarsa aka yi masa qarin girma ya zamo mataimakin
magatakardan ofishin lardi a 1950-1954. A 1952 ya halarci wani kwas na
qungiyar xalibai ‘Man ‘O’ War’ a qasar Kamaru. Bayan dawowarsa daga
wannan kwas, sai aka naxa shi sarautar ‘Sarkin Dawakin Bauchi’ in da ya
zamo xan majalisar hakimin birni, mai lura da tsaron cikinsa, ’yan doka da
gidajen yari duk suna qarqashinsa tun daga 1954-1955. Daga baya aka
naxa shi kansilar ma’adanai da ilimi duka 1955. Kuma a shekarar ne ma
aka tura shi Ingila, ya yi kwas in da ya koyo ilimin dabarun mulki a
qaramar hukuma. An zave shi xan majalisar wakilai na jihohin arewa a
1956. Kuma a shekarar aka naxa shi sarautar ‘Magajin Gari’, kuma
Kansilan kuxi da ayyuka, har zuwa 1962. Yana daga cikin ’yan kwamitin
lardin Bauci da suka marabci sarauniyar Ingila, sadda ta kawo ziyara a
1956, kamar yadda yana daga cikin mutane ’yan qalilan da suka tsara
yadda za’a gudanar da bukukuwan karvar ’yancin kai a 1959. An naxa shi
shugaban ofishin mulkin lardi a 1961-1962. Kana aka sake zavarsa xan
majalisar wakilan jihar arewa a 1961, in da aka tura shi kwamishina a
lardin Neja 1962-1964.
An naxa shi sarautar Sarkin Yaqin Bauci, babban Kansila, kuma Xan-
Majalisar mai martaba Sarki, kana xaya daga cikin mutum shida masu
zaven sabon sarki, idan ya faxi a 1964. Da kamar ba zai karvi sarautar ba
ma, saboda ayyukan da suke gabansa a gwamnatin jihar arewa, amma sai
Sardauna ya bas hi shawarar ya karva, saboda dalilai biyu, na farko domin
abinda yake hange na muqamin gwamnati, a rana xaya ana iya raba shi
dashi, wancan kuwa gadon gidansu ne. na biyu saboda fitowar Alhaji Audu
Magori neman wannan sarauta, da yadda ya riqa kamun qafa a wajen
Firaminista Abubakar Tafawa-Valewa. Shi kuwa Alhaji Audu Magori xan
Sabo ne, shi kuwa Sabo asalinsa basakkwace ne, amma daga Darazo ya zo
Wunti. Sai ya yi baranta a gidan sarkin yaqi Iya, sarkin yaqi Iya kuma ya
riqe shi irin yadda uba ke riqe xansa, ta yadda wanda bai san yadda su ke

224
ba ma, sai ya xauka cewa xansa ne na cikinsa. Domin har ma ya aura masa
Zainabu, ’yar sarkin yaqi Muhammadu Maikayi xan Ahmadu. A taqaice
dai ta wajen ubansa bara ne, ta wajen uwa xan mace ce, wanda ga al’ada ta
kowacce fuska ba ya sarauta. Sardauna ya tsoratar da shi hatsarin qin
nemansa, har ma ya ce masa, “To, idan kai xan gida ba ka nema ba,
’ya’yan waje sa gaje sarautar, nan gaba ta zamo ta gidansu.” Wannan
magana da Sardauna ya gaya wa Magajin Gari lallai ta yi tasiri a cikin
zuciyarsa, kuma ita ce dalilin nemansa sarautar mahaifinsa. A kansa aka
fara raba sarautar sarkin yaqi da hakimin qasar Lame. A dã dukkan Sarkin
Yaqi, to, shi ne Hakimin qasar Lame. To, shi saboda manyan ayyuka da su
ke gabansa a gwamnatin jihar arewa, sai aka nemi ya kawo wanda za’a
naxa hakimin qasar Lame, wanda zai wakilce shi a cikinta. 296 To, da farko
sai ya kawo wannan mutumin da suka nemi sarautar sarkin yaqi tare, wato
Alhaji Audu Magori.297 Saura kwana biyu a naxa shi, har an yi dafe-dafen
kayan abincin biki, sai Hajiya Baba mahaifiyar ajiyan Bauci, Alhaji Adamu
Tafawa Valewa, wacce ita kuma ’yar sarkin yaqi Ade ce, ta isa wajen
sarkin Bauci da kuka, akan ba ta yarda a naxa baran gidansu sarautar
gidansu ba. Nan da nan majalisar sarki, ta sa aka kira Alhaji Audu Magori,
ya zo ya faxi nasabarsa. Daga faxin nasabarsa, sai majalisar sarki ta cire
sunansa daga wanda za’a naxa sarautar sarkin Kudu. Aka nemi Magajin
Gari ya kawo wani, sai ita Hajiya Baba ta ce, akwai li’abbinta Salmanu a
Gumau shi ta ke so a naxa, kuma Magajin Gari ya yarda da hakan. To, sai
ba’a xaga naxi bisa ranar da aka sa ba, sai batun naxi ya koma kan
Salmanu a ranar da aka sa tun farko,298 aka aiko masa ya tafi Bauci da
gaggawa. An naxa sarkin yaqi Yakubu ran Asabar 2 ga watan Mayu 1964.
An rako shi Gumau tare da Sarkin Kudu Sulaimanu, Hakimin qasar Lame,
ran talata 5 ga watan Mayu. Kuma a wannan shekarar ya wakilci ministan
cikin gida, in da ya jagoranci alhazan Nijeriya, da manyan ma’aikatan

296
Wannan shi ke tabbatar da cewa sarautar Sarkin Kudu tana qarqashin sarautar Sarkin
yaqi ce, amma dukkansu sarautun Wuntawa ne.
297
Zuriyar Alhaji Audu Magori su ne ; Ibrahim Qani Xanburam, Abubakar, M.
Maijama’a, M. Zailani, Ahmadu, Jibir, Labaran, Ladan da’yan’uwansu mata masu yawa.
298
To wannan shiga maganar da Hajiya Baba ta yi kuma shi ya haifar da rashin shiri
tsakaninta da Alhaji Audu Magori da zuriya ta sa har yau.
225
gwamnati a aikin hajji na qasa. Ya ma tava riqe muqaddashin ministan
harkokin qasashen waje, duk a 1964, da muqaddashin ministan sadarwa a
1965, kuma a shekarar ne ma ya samu lambar girmamawa ta OFR. 299 Wato
‘Gwarzo mai kare daular Nijeriya.’ An naxa shi kwamishinan lardin
Zazzau 1965-1966. Bayan juyin mulkin da sojoji suka yi, suka kifar da
gwamnatin farar hula, ya dawo Bauci da zama, in da aka naxa shi kansila
mai sa ido kan ayyukan hukuma na lardin Bauci. Sadda aka qirqiro jihar
arewa maso gabas, a 1968 an naxa shi kwamishina mai lura da harkokin
kuxi. Ya rasu ran 3 ga Yuli 1994. A lokacin rayuwatrsa ya auri mata biyar
a lokuta daban-daban, ya rabu da xaya, xaya kuma ta mutu a hannunsa,
uku ne cikinsu ne suka yi masa takaba, su ne; Hajiya Uwani (Amina),
Hajiya Kananatu (Faximatu) da Hajiya Halimatu. Ya kuma bar garken
’ya’ya 33, maza 22, mata 11.

HAKIMIN QASAR LAME NA XII


SARKIN KUDU NA I
SALMANU XAN SARKIN YAQI ADE
(1964-1976)

To, bayan rasuwar sarkin yaqi Usmanu Babale sai qasa ta zauna
qarqashin wakilin qasar Lame, Malam Ibrahim Bauci tsawon kwanaki 75.
To, sai kuma Allah ya danqa ta ga sabon hakimi, ba tare da zawarci ba.
Wanda ya nema daban, amma sai mai bayarwa ya bai wa Salmanu. Amma
a wannan karon an samu wani sauyi wanda ba’a tava ganin irinsa ba cikin
sarakunan da suka gabata, shi ne sai aka raba sarautar hakinci da sarautar
sarkin yaqi. Sarautar sarkin yaqi aka bai wa M. Yakubu xan Abubakar.
Hakincin qasar Lame kuma aka bai wa Sulaimanu. An naxa shi ran
jumma’a 1 ga watan Mayu 1964. An rako shi Gumau tare da sarkin yaqi
Yakubu ran talata 5 ga watan Mayu. Sarkin Kudu Salmanu ya yi sarauta

299
Lambar girmamawa ta OFR (Commander Of The Order Of The Federal Republic)
‘Gwarzo mai kare daular Nijeriya’, xaya ce daga lambobin girmamawa guda biyu, da
gwamnatin tarayyar Nijeriya ta qirqiro a 1963 don girmama ’yan qasa nagari, da suka
bautawa qasa tsakaninsu da Allah ita. Xayar ita ce GCFR (Grand Commander Of The
Order Of The Fedral Republic) ma’arsa : ‘Babban Gwarzo mai kare Daular Nijeriya.’.
226
shekara goma sha xaya da wata takwas da kwana goma sha shida daidai.
San nan ya yi murabus a dalilin tsufa. Ya yi murabus ran 10 Janairu 1976.
Wanda aka ba shi riqo da wakilcin qasar Lame kafin a naxa sabon sarki shi
ne magatakardansa Malam Umaru Lame.

HAKIMIN QASAR LAME NA XIII


SARKIN KUDU NA II
MUHAMMADU GOGE XAN SARKIN LAME AHMADU
(11/1/1976-25/12/1976)

Sunan mahaifiya ta sa Hadiza, ana mata laqabi da ‘Maman Jira’ ba’a


daxe da haihuwa ta sa ba sai mahaifinsu sarkin Lame Ahmadu, ya rasu ya
bar su tun suna qanana qwarai, su biyu da xan’uwansa Ladan. Ba dukansu
uwarsu xaya ce ba, amma dai Hadiza ce duka ta shayar da su. domin uwar
Ladan na ciwon mama, sai Hadiza ta xauko shi ta shayar da su baki xaya
da qaninsa. Bayan mutuwar mahaifinsu Sarkin Yaqi Usmanu Babale ya
xebo su -saboda shi baffan ubansu ne- ya yi renonsu a gidansa. A san nan
Ladan shi yana tafiya, shi kuwa Muhammadu ko zama ma bai iya ba. To,
Muhammadu shi ne qaraminsu, yana da raunin jiki, don kafin ma ya yi
tafiya sai da aka riqa sa shi a kwando ana jansa tukuna.

DALILIN KIRANSA DA ‘MAI GOGE’

To, sadda ya ke qarami yana da yawan kuka, idan ya fara ba ya yin shiru,
sai in an yi ta yi masa rawa, ana jijjiga shi, ana yi masa waqa tukuna. To,
sarkin yaqi yana da garmaho, sai ana kunna masa waqar Xantiti mai goge,
idan yana ji sai ya riqa yin shiru. To, sai mata na kiransa ‘Kai mai goge’
kwanci-tashi har Muhammadun ya vata sai Maigoge. Sunan da bai qara
dawowa ba sai da ya ci sarauta tukuna. Matashin malamin makaranta ne,
fari kyakkyawa, da ka ganshi dai ka ga bafulatanin asali. Yana aikin
Hedimasta a makarantar Tulu, sarkin Bauci ya aika a xauko shi, ya naxa
shi sarautar sarkin kudu, ba tare da an yi zave ba, ba tare da ya tuntuvi
jama’ar Wuntawa ba, abin da kuma ya qona wa ’ya’yan sarautan Wunti rai,
bai yi musu daxi ba. San nan bayan an naxa shi, sai aka yi masa masauki a
gidan Alhaji Baqon -Dare, abin da kuma bai yi wa Magatakarda
227
Muhammadu Maidawa, wanda baffansa ne, kuma shi ke aure da
mahaifiyarsa, tun bayan rasuwar ubansu daxi ba, har ma ya ce, “Yanzu ina
baffansa, kuma ina da rai sai a naxa shi sarauta, amma ba’a kawo shi gida
na ba, sai a kai shi gidan wani bare? Wannan ai ci gaban gidammu ne.” Ya
kuma yi murna da xan -xan’uwansa ya samu. Ba’a daxe da naxa shi ba, sai
Allah ya saukar masa da ciwon mutuwar sashin jiki ‘Stroke’ har aka rako
shi Gumau bai san ma in da kanshi ya ke ba. Abin da mutanen gari ke
ganin ’yan’uwansa ’ya’yan sarauta ne suka yi masa sammu, suka jefe shi
da asiri. Wanda irin wannan tunani, ni mai rubutu ban isa cirewa
al’ummarmu shi ba, don al’umma ce wacce ta yi imani da tasirin sihiri.300
Tun da aka kawo shi Gumau ko gidan sarauta ba’a shigar da shi ba, saboda
rashin lafiya, sai aka wuce da shi gidansa, nan ya yi ta jinya. Da jiki ya
tsananta sai baffansa Magatakarda Muhammadu Maidawa ya sa aka xauko
shi daga Gumau, aka dawo dashi gidansa a Bauci, a nan ya yi ta jinyarsa
har ya koma ga Allah. Ya rasu a Bauci, kuma a can aka binne shi, ran 25 ga
watan Disamba 1976. Watansa goma sha xaya da kwana ashirin, wato Sati
(mako) hamsin ya yi a kan gadon sarauta. Ya rasu ya bar mata biyu;
uwargidansa Jummai wacce asalin sunanta Hamamatu, da amaryarsa
Yalwa, wacce asalin sunanta Faximatu. Ita Jummai ta haifi Ahmadu,
Usman, Yahaya, Mahmud, Mairo da Adamu. Ita kuwa Yalwa ta haifi
Bara’atu, ya kuma bar ta da cikin (Muhammad) Tukur.

HAKIMIN QASAR LAME NA XIV


SARKIN YAQI NA XIV
SARKIN KUDU NA II
MUHAMMADU MAIDAWA XAN USMANU II

“Sarki Muhammadu Maidawa xan Usmanu,


sarki da rabin sarki, da kuma wani sarkin a xora bisa”

300
Abu biyu da ya ke wajibi ga al’umma su sani shi ne, ba’a mutuwa sai da cikar ajali, shi
kuma sihiri ba shi da tasirin komai, wurin sa wa ko hanawa, sai fa abin da Allah ya yi
nufin ya same ka. Har Ma’aiki –mai tsira da aminci- yana cewa, “Mutane uku ba su shiga
gidan aljannah; mashayin giya, da mai yanke zumunci, da mai gaskata sihiri.” SAHIH :
Azzahabi (Alkaba’ir) Bab Assihir.
228
An haife shi a 1920 a Unguware cikin gundumar Jarawa, yanzu kuma
qaramar hukumar Jos ta gabas. A lokacin mahaifinsa shi ne Sarkin kudun
Bauci, 301 fadarsa na Unguware. Ya yi sarautar sarkin kudu daga 1929-
1938. Ya yi karatun Muhammadiyya a makarantar allo ta M. Gajere Tilden
–Fulani. Yana wajen karatun ne ma, mahaifinsa ya samu sarautar sarkin
yaqi a 1929. Sadda mahaifinsa samu sarautar sarkin yaqin Bauci, hakimin
qasar Lame, sai aka xauke shi daga qasar Jarawa aka mai da shi Lame,
cibiyar mulkin qasar Lame. A 1932 sai ya xauko Maidawa daga Tilde,
bayan ya yi ido a karatun Alqur’ani, ya sanya shi a makarantar elementare
ta Lame a 1932-1936. Domin a lokacin turawa sun sanya dokar dole ne
sarakunan qasa su sanya ’ya’yansu a makarantar boko. Daga nan ya tafi
makarantar Midil ta unguwar Kobi cikin garin Bauci 1936-1939. Kuma ya
yi kwasa-kwasai masu yawa. Ya fara aikin gwamnati a matsayin malamin
auduga, a ma’aikatar aikin gona ta lardin Bauci, ran 1 Nuwamba 1951. Sai
aka yi masa canjin wajen aiki daga lardi zuwa tarayya, in da ya yi aikin
akawun kotu a gwamnatin tarayya daga ran 1 Nuwamba 1967, in da ya yi
ritaya a 1973. Sai aka kuma ba shi wani sabon aikin a sabuwar jihar Bauci,
har ran da ya kuma yin ritaya ran 31 Maris 1976. Bayan gama karvan
makokin tsohon sarki Muhammadu Maigoge. Da abu ya kwanta, sai
rigimar wa zai gaje shi ta taso, ’ya’yan sarki mutum takwas suka fito
neman sarauta. Cikinsu akwai M. Ahmed Lame (Ladan Oganeza), Ahmadu
xan Ciroman Wunti Muhammadu Mairawa302Ahmadu Risku xan sarkin
yaqi Yakubu Lame, Babaji Mai Jaddoji303 Sarkin Lame Balarabe, Shehu
Nagado, Ladan Baban –Fulani da Alhaji Umaru Dawaki (Ubandoman
Wunti). To, saboda ganin irin abin da ya faru a naxin wancan sarki da ba
zavenshi aka yi ba, masarautar Bauci ce dai ta naxo shi, yanzu da maganar
sarauta ya taso, sai aka nemi a bi hanyar da ta dace, wacce dama can ita ake
bi a al’ada, shi ne a bar masu zaven hakimi su zava da karan-kansu, ba wai
a zava musu ba. Aka ba masu zaven sarki na gargajiya sharuxxa na irin

301
wasu na ce masa sarkin Jarawa.
302
Jikan sarkin Yaqi Ade
303
Direban Xankyarana. Ubansa da uban Gwaggo Ladi matar Shehu Nagado, da Marafa
Ahmadu Maiwunti (Xan Yakwalle), uwarsu xaya ubansu xaya. Asalinsu mutanen Rauta
ne.
229
mutumin da za su zava ya zama hakimi, ya zamo gogagge a cikin sha’anin
mulki. Kuma ya zama gaskiyarsa da riqon amanarsa da kyawawan
halayensa ba voyayyu ba ne ga kowa. Kuma ya zamo wanda zai karvu ga
jama’ar qasar Lame. Daga nan sai masu son sarauta suka fara shige da fice,
da tsuguni-tashi. Shi Muhammadu Maidawa ba ya cikinsu, saboda tun da
aka bai wa xansa Muhammadu Maigoge sarauta, shi har ya fid da rai da
samunta. To, ashe bai sani ba sadda aka nemi mai riqon qasar Lame na
lokacin (M. Umar Lame) ya kai sunayen ’yan sarautar Wunti, ya sa har da
sunansa a ciki. Da ranar zave ta kusa, sai aka ce malamin sarkin ya kira
’yan takara, ya sanar da su ranar zave. A san nan shi Maidawa yana zaune
a gidansa a Bauci, labari bai gare shi ba sai ranar da za’a yi zave cewa ya
yi maza ya je Toro dandalin da za’a kaxa quri’a. Ya je ya samu an kafe
akwatin zave a Toro, Hedkwatar qaramar hukuma, masu zave suka ce babu
wanda ya dace da halayen da aka zana sai Magatakarda Muhammadu
Maidawa. Aka buga aka busa! Mai rabo ya samu! Mugun madambaci yai
kaye! Komai muqaddari ne daga sarki Allah tun ba mu zo duniya ba.
Magatakarda ya ci zave da mafi rinjayen quri’u. Hasali ma duk cikin
waxanda suka yi takara tare dashi babu wanda ya samu quri’a ko xaya, sai
fa M. Ladan Oganeza da ya samu quri’u biyu, ta sa da ta sarkin Shau,
sauran kuwa duk Magatakarda ya lashe su.

“Mamman tun da ka yi Sarkin Yaqi,


Rungumi danginka ba su haqqinsu.”

Ko da ma can, shi ya kamata a naxa shi sarautar sarkin kudun, domin


talakawa suna qaunarsa, amma matsalarsa da sarakunan qasa ne abin da
suke zarginsa da rashin kamun kai. Don ko ranar naxinsa ma sadda suka
shiga fada, sai da sarkin Bauci Adamu Jumva ya goranta masa, kuma ya yi
masa faxa a kan rashin kamewa, kuma ya umarce shi da ya gyara
halayyarsa tun da yanzu girma ya zo. An naxa shi sarkin kudun Bauci,
Hakimin qasar Lame bayan wata guda da zavensa, ran 5 ga Mayu 1977.
Hasali ma shi ne mutum na 17 cikin waxanda suka yi hakincin qasar Lame,
kuma na uku cikin waxanda suka yi sarautar Sarkin Kudu. Bayan naxa shi
sai aka xebo iyalansa daga Bauci, aka dawo da su Gumau. To, saboda

230
gaskiya da riqon amanarsa da aka gani kuma, bayan mutuwar sarkin yaqi
Yakubu Ibrahim Lame, sai sarkin Bauci Dakta Sulaimanu Adamu ya naxa
shi sarautar Sarkin Yaqin Bauci, kuma hakimin qasar Lame ran 26 ga Yuni
1994. Tun daga ran nan sai ya zamo sarqin yaqin Bauci na 17, da suka yi
wannan sarauta. Kuma babban kansila, kuma xan majalisar mai martaba
sarki, kana xaya daga cikin mutum shida masu zaven 304 sabon sarki a
masarautar Bauci. San nan mutum na biyu a jerin manyan hakimai da ke
gaba idan sarki ya yi hawa, bayan tawagar Madaki sai ta sa. Shaqiqansa su
ne Sarkin Lame Ahmadu, Sarkin Lame Balarabe, Kumbo da A’ishatu.
Daga cikin fadawansa akwai Adamu Xantiye,305 Malam Bala,306
Xan’azumi Gukka, Xan’atta, Xallami Ajayi, Sarkin Bariki, 307Marafa
304
Mutum shida masu zaven sarki a masarautar Bauci su ne ; Madaki : Hakimin Ganjuwa.
Galadima : Hakimin Zungur. Sarkin Yaqi : Hakimin qasar Lame, Ajiya da liman.
305
Adamu Lame, an haife shi a 1944, a gidan sarkin yaqi a Lame. Ya yi karatun
Muhammadiyya da na ilimi a wajen M. Yayan Dudu Lame. Ya yi makarantar elementare
ta Lame 1951-1955. Ya yi aikin malamin kutare, kana ya koma Duba-gari tun daga 1976
har zuwa sadda ya yi ritaya a 2011.
306
Asalin sunansa Bala Ibrahim, an haife shi a Lame a shekarar 1944, kuma a cikinta ya
tashi. Ya yi karatun allo a wajen limamin Lame M. Haruna. Ya yi karatun ilimi a wajen
limamin Gumau M. Ali. Ya shiga makarantar elementare Lame a 1954- 1957. Sai aka
xauke shi aikin malamin gunduma a 1963. Ya koma makarantar ya yi babbar firamare ya
qare a 1966. Ya yi aikin malamin gunduma 1963-66, sai aka mai da shi malamin
gundumar Wonu 1966-1969. Daga nan sai ya koma aiki a masaqar buhu na (Fiber
Factory) Jos, wata shida kurum ya yi, sai ya bari ya shiga aikin soja. Shekara ta sa xaya
sai ya bari, domin sadda ya shiga a gida ba’a sani ba, sai ana ta roqon Allah ya dawo dashi
gida. Da ya dawo gida a 1970, sai kuma ya tafi Bauci a 1972, sai sarkin Dawakin Bauci ya
mai da shi aikin malamin gundumar Yautare, cikin qasar Darazo. A 1974 sai aka dawo da
shi malamin gundumar Lame. A 1977 sai aka mai da shi malamin gundumar Rahama,
zamanin sarkin Rahama Abdulkarimi. A 1982 sai aka mai dashi akawu a sakateriyar
qaramar hukuma. A 1985 sai sarkin yaqi Muhammadu Maidawa ya xauko shi a matsayin
malaminsa. Ya yi ritaya a 1996, kuma ’yan’uwanshi sun so su mai dashi gida, sai sarkin
yaqi ya ce, a’a, su barshi ya zauna kusa dashi, domin shi ne idonsa. A yanzu haka yana
zaune a Gumau, yana da iyalai da ’ya’ya, har ma da jikoki.
307
LABBA SARKIN BARIKI Asalin sunansa saleh sarkin bariki. Abin nufi da bariki
masaukin bature da ake kira rehawus (resthouse) a turanci. An haife shi a Tulu ta
gundumar Tama a shekarar 1930. Ya yi karatun allo a wajen M. Umaru Tafida na babban
gida Tulu. Yana daga cikin matasa majiya qarfin da suka yi hijira da qafafunsu daga Lame
zuwa Gumau tare da sarkin yaqi Usmanu Babale. Wato su ba sai da aka xora su akan doki
231
(Damari), Malam Lawal. Dogaransa su ne sarkin Dogarai Adamun
Julde308Babaji, Waziri Gadanga, Shehu, Inuwa Adamu Zalau309Wakili
Mairiga, Xallami Xankwana, Abdulkarim (Ubale). 310 majayin sandarsa
bayan naqasar makanta da ta same shi shi ne Sa’idu Lawal Alaramma.
Direbobinsa kuwa su ne ; Alhajin Balan Sama’ila311 Shamakin Wunti da
Baqo. Matansa kuwa akwai ; Hadiza (Maman Jira)312 ta haifi Ibrahim.

ba. Shi da Barden Wunti, da sarkin Jakadu, da Umaru xan Tafida da sauransu mutane
masu yawa. Dalilin haxuwarsa da sarki Usmanu Babale tun wata shekara da sarki Babale
ya ke rangadi a gundumar Rahama, akan hanyarsa zai wuce ta Tulu, sai ya ganshi, sun fito
kallon sarki, a san nan yana yaro matashi, wanda mahaifinsa bai daxe da rasuwa ba. Sai
sarki Babale ya tsawaita kallo gare shi ya ce, “Wannan yaro kuwa ina sonka, da za ka
yarda, da ka bi ni ka zauna da ni.” Sai shi ma ya ce, “Ranka ya daxe ni ma ina sonka,
kuma in ka yarda sai na bi ka.” Sai ya bi shi suka je Rahama suka dawo. Da za su wuce,
sai ya tambayi qannensa, ko za su yarda su bar shi ya tafi da xan’uwansu. Da suka yarda
sai ya tafi dashi Lame. To, suna nan a Lame, bas u daxe ba, sai turawa suka matsawa
sarkin yaqi lalle sai ya dawo Gumau.
308
An naxa shi Sarkin Dogarai ran Jumma’ah 16 Mayu 1980.
309
An xauke shi aikin dogari a shekarar 1994.
310
Asalin sunansa Abdulkarim Saleh, an haife shi a garin Shau ta gundumar Lame a
shekarar 1952. Kuma a cikinta ya tashi, ya yi karatu a wajen limamin Shau M. Yakubu.
Sanadin komowarsa Gumau, tun yana zuwa Gumau yin aikin gona, ya yi kunyaryaki, ya
koma gida, sai sarkin kudu muhammadu goge ya ji daxin aikinsa, ya ce yana son zama da
shi idan ya yarda, sai ya dawo da shi Gumau, to, bai daxe a kujerar mulki ba sai ya rasu.
To, da aka naxa sabon sarki Muhammadu Maidawa, sai ya ci gaba da riqe shi fiye da
sarkin day a gabace shi. Ya samu shiga fada sosai, har ma duk wanda ya gagara kamuwa,
shi ake aikawa ya je ya taso qeyarsa.
311
Asalin sunansa Isyaku Abubakar, an haife shi a Riruwai, a 1948, amma ya tashi a
Gumau. Ya yi karatun Muhammadiyya a wajen M. Muhammadu limamin Fuskan-Mata,
da M. Idrisu Gumau. Ya yi karatun ilimi a wajen M. Tsoho Ririwai, da M. Gero Gumau.
Ya kuma yi karatun zamani na yaqi da jahilci a ajin M. Barau. Ya koyi tuqin mota a wajen
Isa na Harirah, wani mutumin Gwambe. Alqalin Gumau M. Shehu ya fara xaukarsa aiki
ya riqa tuqa shi, har ranar da aka naxo sarkin kudu Muhammadu Maidawa a 1977, to, sai
yana tuqa su baki xaya. Asalin sana’arsa gyaran keke ne, Alhaji Badamasi ya koya masa.
Sai Allah ya yi masa nasibi ya sayi ta sa motar, kuma it ace sanadiyyar arziqinsa.
Mazaunin Gumau ne, ya tava yin aikin hajji, kuma yana da zuriyya ’ya’ya da jikoki masu
yawa.
312
Ta fara auren wansa sarkin Lame Ahmadu ta haifi Muhammadu Maigoge da Ladan
Oganeza. Bayan mutuwarsa sai Magatakarda Muhammadu Maidawa ya aure ta, ta haifi
Ibro babban xansa.
232
Marka ta haifi Korau, Abubakar Garba (’Yandoton Bauci), Lantana,
Jamila, Musa. Alo ta haifi Zubairu, Amina, Ruqayyah, Gambo. Azumi ta
haifi Rufa’i qarami, Muhammad Ballo, Hadiza (Bara’atu). Lami : ta haifi
Umar (Ali). Salamatu : ta haifi Rufa’i babba. Hajara (Hajo) : ta haifi
Yakubu (Yariman Wunti). Amma waxanda suka yi masa takaba cikinsu, su
ne Azumi da Lami kaxai. Waxanda suka yi sarauta cikin ’ya’yansa su ne;
Abubakar Garba (’Yandoton Bauci)313Yakubu (Yariman Wunti)314 Aliyyu
(Xan MadaminWunti) 315da Ahmad Rufa’i316 (Iyan Wunti).

313
An haife shi a 1948 a Gumau, kuma a cikinta ya tashi. Ya yi karatun Muhammadiyya
da ilimi a wajen M. Idi. Ya yi makarantar elementare da firamare ta Kobi-Bauci 1959-
1964. A 1966 sai xan’uwan mahaifinsa M. Yakubu Lame ya sama masa aiki da hukumar
kula da jiragen qasa ta qasa (Nigerian Railway Corporation) a Bauci.
314
An haife shi a 26 Disamba 1963 a Bauci, Ya yi karatun Muhammadiyya a wajen M.
Buba Bayan Bata Bauci. Ya yi karatun ilimi a wajen M. Inuwa Bauci. Ya yi karatun
firamare a Sheka 1968-1974. Sai ya tafi makarantar sakandare ta GSS Numan (SAKATO)
1974-1979. Sai jami’ar Bayero in day a karanci watsa labarai (Mass Communication)
1991-1994. Yana aiki tare da gwamnatin jihar Bauci, yanzu shi ne Sakataren qungiyar
’yan jarida ta qasa reshen jihar Bauci.
315
Aliyyu Muhammad Maidawa, an haife shi a 1982 a Bauci, ya tashi a Gumau. Ya yi
makarantar Muhammadiyya a wajen M. Bugau, da liman M. Garba Xandibi inda ya yi
sauka a wajensa, kuma ya xora da karatun ilimi. Ya yi makarantar firamare ta Unguwar
Waziri 1987-1993. Ya yi ISS Gumau 1993-1996. Sai kuma ya kwalejin koyon sana’a ta
GTC Gumau 1996-1999. Ya tafi babbar makarantar koyon qere-qere ta gwamnatin
tarayya (Federal Polytechnic) Bauchi ya yi Diploma a injiniyar wutar lantarki (Electrical
Engineering) 2001-2004. Ya ci gaba a wannan makaranta in day a yi babbar Diploma a
dai wannan kwas 2005-2007. Ya xora karatu a jami’ar ATBU Bauchi a fannin ilimin
kimiyyar komfuta ‘Computer Science’ A shekarar 2010 ya fara aiki da kamfanin wutar
lantarki ta qasa a Maiduguri, sai rikicin Boko-Haram ya vullo, sai ya bar waqnnan aikin
inda ya koma malamin wucin gadi a ATAP. Yanzu yana aiki da gidan rediyon Nijeriya na
‘Globe FM’ Bauci. Yana da ta da ’ya’ya. Kuma shi ne Xanmadamin Wunti, an naxa shi a
2000.
316
An haife shi a 1970 a Bauci, yana da shekara bakwai sai aka naxa mahaifinsa Sarkin
Kudu, hakimin qasar Lame a 1977, to, sai ya dawo das u Gumau. Ya yi karatun
Muhammadiyya a wajen limamin Gumau M. Garba Xandibi, har ya sauke Alqur’ani. Ya
yi karatun ilimi a wajen M. Abdulmumin Adamu. Ya yi makarantar firamare ta Unguwar
Waziri 1977-1983. San nan ya tafi GSS Gumau 1983-1986. Kana ya tafi GSSS Dass
1986-1988. A 1989 ya yi ‘Remedial’ a makarantar ‘BACAS’ a Bauci. An xauke shi aikin
akawu a qaramar hukumar Toro, sai kuma ya tafi jami’ar Jos ya yi karatun satifiket a
233
A zamaninsa wannan gari ya samu ci gaba, da bunqasar da ba’a tava
ganin irinta ba cikin waxanda suka gabace shi. A zamaninsa aka tsago
hanyar kwalta daga Magama Gumau, zuwa Gumau. Aka yi babbar gada ta
zamani a rafin Badikko, da rafin Dilimi a shekarar 1978-79. 317 Aka kawo
wutar lantarki a 1980. Aka gina randar famfo a qofar gidan Alhaji Tsalha,
aka yi qaramar madatsar ruwa (Dam) a can yamma da gari. Makiyaya suka
samu wurin shayar da dabbobinsu. Noman rani ya qara bunqasa. Aka samu
bunqasar makarantu. Aka gina makarantar Sakandare GSS (Government
secondary school) Gumau da JSS (Junior secondary school) Lame, su biyu
duka a Gumau. Ita GSS Gumau daga baya ta juye kwalejin koyon sana’a,
wato GTC (Government Technical College). Ita kuma JSS Lame, daga
baya ta juye GDSS (Government Day Secondary School) Gumau. San nan
aka buxe qananan makarantun sakandare na Upper Basic guda huxu. Xaya
a makarantar Firamaren sarkin yaqi. Xayar kuma a makarantar Gumau
Sanga Firamare, ta ukunsu a firamaren Unguwar Waziri, ta huxunsu a
makarantar Maiwuro. Waxannan vangaren makarantun gwamnati kenan, ta
vangaren makarantu masu zaman kansu kuwa, an yi makarantu masu yawa
tsakanin Nursery, firamare, mutawassixah, sakandare da kwaleji na
arabiyya da na boko Allah kaxai ya san iyakarsu. A cikin zamaninsa aka
kafa eriyar sadarwar kamfanin MTN da GLO, kana kwance a kan gadonka,
sai ka yi magana da duniya. Aka gine kasuwar Gumau, har ta yi kaxan,
tsakanin ginin gwamnati da na ’yan kasuwa. Samun rumfa ya zamo sai
mutum ya yi da gaske kafin ya samu. Aka yi gadar zamani a rafin Gumau,

fannin shige-da-ficen kuxi (Accounting). Ya zurfafa wannan karatu zuwa Diploma a


BACAS 1994-1996. Ya qara zurfafawa ya yi babbar Diploma a makarantar kimiyya da
fasaha ta jihar Filato ‘Plateau State Polytechnic’ 1999-2001. An ba shi sarautar ‘Iyan
Wunti’ a 2015.
317
Kafin zamaninsa daga Gumau idan mutum zai je Bauci, sai ya bi ta hanyar Fuskar
Mata, ya vulla Jos, kana ya gangara ya tafi Bauci, mota kuma guda xaya ce. Haka ma
wanda ya ke son zuwa daga Bauci, sai ya yi wannan zagaye. Amma da yin wannan hanya
ta Magama Gumau, sai aka samu sauqin tafiya. Kuma sai Magama Gumau ta rayu, alhali
da ’yan gidaje ne nan da can a unguwar Gwaljarandi. Kuma yin wannan hanya shi ya
sabbaba mutuwar Magama Gari, alhali da idan aka ce Magama, to, Magama Gari ake nufi
ba Magama ta Gumau ba. Har wa yau sai tsohuwar hanyar da ake bi idan za’a je Jos a da,
wato hanyar Fuskar Mata ita ma sai ta mutu, mabiyanta suka zama sai nadiran.
234
wanda da duk shekara sai ya ci rai. A dai zamanin na sa kuma aka yi hanya
mai kwalta daga Gumau zuwa Rahama, dake kan iyakar qasar Bauci da
qasar Kaduna. Wacce ta kawo sauqin tafiya ga wanda ya fito gabashin
Nijeriya yak e son zuwa Kaduna ko gaba. A zamaninsa aka bai wa Gumau
cibiyar qaramar hukumar mulki ta qaramar hukumar Lame. Jama’ah da
ma’aikata suka yi ta tururuwan zuwa. Gari ya qara havaka. Kasuwa ta
bunqasa. Kwatsam sai Buhari ya yi juyin mulki ran 31 Disamba 1983 ya
rushe ta.318 Ya rasu ran jumma’ah 16 Jumada Sani 1440 Hijiriyya, daidai
da (01-02-2019) bayan sallar asuba, bayan fama da gajeruyar jinya. An
sallace shi bayan sallar jumma’ah. Limaminsa almajirin da ke wannan
rubutu shi ya sallaci gawarsa. Xaruruwan jama’ah daga ciki da wajen gari
ne suka sallaci gawarsa. Ya rasu yana da shekaru 99 a duniya (1920-2019).
Wanda aka bas hi riqon wakilcin gari bayan rasuwarsa shi ne
magatakardarsa M. Adamu Muhammadu Goge. Ya yi riqo tun daga ran 01
Fabrairu har zuwa Disamba ran 8 ga watan Disamba 2019. Ya yi riqo na
kwana 308, sati 44, wata 10 da rabi daidai.

HAKIMIN QASAR LAME NA XIX


SARKIN YAQI NA XV
ALI XAN YAKUBU XAN ABUBAKAR
(2019- Yau)

An haife shi a Bauci, ran 19 Maris 1969. Ya halarci makarantar firamare


ta Bakaro 1974-1980. Kana ya yi makarantar Sakandare ta GSS Gumau
1981-1986. Kana ya yi kwasa-kwasai masu yawa. In da ya samu satifiket a
kan xaukar hoto mai motsi da majigi (Film Projection/ Cinematography),
wanda ma’aikatar sadarwa da al’adu ta jihar Bauci ta shirya 1987-1988.
San nan ya samu satifiket daga tsangayar koyon aikin ’yan jarida ta duniya
(International Institute Of Journalism) a shekarar 1997. Yana da satifiket
xin ‘Diploma’ a fannin sarrafa kwamfuta don aikin yaxa labarai

318
kuma tun daga ran nan sai baqin ma’aikata da suka zo suka gina gidaje daga wasu
garuruwa, suka yi ta tashi, Gumau ta yi ta komawa baya har yau. Sai fax an abinda ba’a
rasa ba.
235
(Journalism & Mass Communication In Microsoft Office XP & Internet
Skills). Da kuma wani satifiket xin mai nuna qwarewarsa a fannin yaxa
labarai ta kafar sadarwar zamani. Ya yi aiki da gidan talabijin na jihar
Bauci, ya fara da aikin xaukar hoto mai motsi, san nan ya zama mai aiko
da labarai, san nan ya zama mai fassara labarai. Ya zamo shugaban
vangaren kasuwanci, kana yanzu ya zamo sarkin yaqi. An naxa shi sarautar
sarkin yaqi hakimin qasar Lame ran asabar 8 ga Rabi’us sani 1441, daidai
da 7 ga Disamba 2019. Mai martaba sarkin Bauci ya rako shi masarautarsa
ran litinin 10 Rabi’us sani 1441, daidai da 9 ga Disamba 2019. Sallarsa ta
farko day a fara sallata a babban masallacin qofar fada it ace sallar la’asar.
Sallar jumma’a ta farko day a fara sallata a Gumau kuwa ita ce ran
jumma’a 12 ga Rabi’us Sani 1441, daidai da 13 Disamba 2019. A ranar da
aka rako shi, a ran nan ya shiga gidan sarauta, kuma ya tara malamai suka
sauke masa Alqur’ani don ‘tafã’uli’ da fatan alherin Allah ya sa ya shiga
gidan sarautar a sa’a. Sadda ya ci sarauta, mutum na farko da aka fara
naxawa sarauta shi ne Mairiga sarkin dogarai.319 Da ma an bashi sarautar
tun zamanin sarki marigayi, amma dai naxi ne ba’a yi ba.

319
Muhammadu Mairiga, asalin sunansa M. Hasan. An haife shi a shekarar 1943, an naxa
shi sarkin dogarai a shekarar 2020, a san nan yan da shekaru 77 a duniya. Ya daxe yana
bautawa masarautar Wunti, tun daga Lame har tasowa Gumau. Ya yi aiki tare da sarkin
Lame Gixaxo, Balarabe, sarkin yaqi Babale, sarkin kudu Salmanu da sarkin yaqi Yakubu,
da sarkin yaqi Mahammadu Maidawa. A zamanin sarkin sarkin Lame Gixaxo har zuwa
sarkin Lame Balarabe shi ne mai kai wa sarkin Lame saqon sarkin yaqi, shi ko
Muhammadu Mairawa. A zamanin sarkin kudu Salmanu (1964-1976) ya yi aikin karvar
haraji. Ya zauna tare da sarkin yaqi Muhammadu Maidawa yana masa bauta a Bauci, tun
kan shi sarkin yaqi ya ci sarauta. Sadda ya ci sarautar sarkin kudu, sai ya dawo Gumau das
hi, yana kula masa da dawakai. Babbar kyautar da wani sarki ya tava yi masa wacce har
mutuwarsa ba zai manta da ita ba it ace kyautar sule biyar da aka tava bashi. Amma duk
da haka ranar naxa shi sarautar sarkin dogarai ta fi wancan rana farin ciki a wajensa. A
yanzu haka (2020) yana aure da mata 3, da ’ya’ya 4. Mutum mai hali irin wannan, na
biyayya ga masarauta, a ra’ayi irin nawa ya kamata ayi masa laqani da ‘Xan Qwarai.’
236
SALSALAR SARAUTAR
SARKIN YAQIN BAUCHI (GIDAN MUHAMMAN KUSU)
I. Sarkin Yaqi Muhamman Kusu
1812 – 1822

V. Sarkin Yaqi Ahmadu III. Sarkin Yaqi Abdulqadir Ibrahim


1867-1896 1842-1852
XII. Sarkin Yaqi Abubakar
VII. Sarkin Yaqi Muhd Ahmadu X. Sarkin Yaqi Ade S. Lame Sani320 1924 – 1929
1897-1901 1907 -1909
IX. 1905-1907 XV. Sarkin Yaqi Yakubu Lame
Muhd Mairawa I. Sarkin Kudu Salmanu 1964 -1994
(Ciroman Wunti) XVI. Hakimin Qasar Lame
1964-1976 XVII. Sarkin Yaqi Aliyyu
Ahmadu Ciroman Wunti XIX. Hakimin Qasar Lame
Babangida Xanlawal Wunti Adamu Ganzo 7/12/2019 - Yau
Sarkin Lame Muhd Gixaxo

Marafan Wunti Ahmadu Tafidan Wunti Abubakar

320
’Ya’yansa biyu ne mace da namiji. Macen sunanta Dudu uwar Musale. Sai Xanbaji wanda ’ya’yansa duka mata ne.
237
SALSALAR SARAUTAR
SARKIN YAQIN BAUCHI GIDAN BAKONGO (FULANIN WUNTI)
BAKONGO

Harxo Sambo II. Sarkin Yaqi Jibir


1822-1842
IV. Sarkin Yaqi Usmanu I
1852-1867 VI. Sarkin Yaqi Iya
1896-1897
Harxo Bello VIII. Sarkin Yaqi Umaru Alkammu
1901-1905
XI. Sarkin Yaqi Hasan XIII. Sarkin Yaqi Usmanu II XIV. Sarkin Yaqi Usman III Babale Abdullahi
1909- 1924 1929-1938 1938-1964 S. Lame Baffa321
Muhd Mahe Babayo Manja
XVII. Sarkin Yaqi Muhd Maidawa S. Lame Balarabe S. Lame Ahmadu
XVIII. Hakimin Qasar Lame
1977-2019 Anas Shagari Ladan Oganeza II. Sarkin Kudu Muhd Goge
Sama’ila XIII. Hakimin Qasar Lame
(10/1/1976-25/12/1976)

321
’Ya’yansa duka mata ne Magama, Gwaggoji, Laraba, Talatu, Kilishi.
238
JIMILLAR WAXANDA SUKA YI SARAUTAR SARKIN YAQI
KO HAKINCIN QASAR LAME (1812-2019)

Wannan kuwa na raba su gida goma sha uku :

1- Waxanda suka yi sarauta daga gidajen sarautar sarkin yaqi


2- Ya yi sarkin yaqi ya yi hakinci.
3- Ya yi sarkin yaqi, bai yi hakinci ba.
4- Ya yi sarkin kudu ya yi hakinci, bai yi sarkin yaqi ba.
5- Ya yi sarkin yaqi, ya yi sarkin kudu, ya yi hakinci
6- Ya yi sarauta a Bauci
7- Ya yi sarauta a Toro
8- Ya yi sarauta a Gau-Lame-Kafin Dilimi
9- Ya yi sarauta a Lame
10- Ya yi sarauta a Lame -Gumau
11- Ya yi sarauta a Gumau
12- Jimillar sarakunan gidan Barebari
13- Jimillar sarakunan gidan fulani
14- Waxanda ba su haihu ba daga cikinsu
15- Waxanda suka yi murabus

WAXANDA SUKA YI SARAUTA DAGA GIDAJEN BIYU

Suna Shekaru Daga Sarauta


1 M. Muhammad Kusu 10 1812-1822 S/yaqi
2 M. Jibrilla 20 1822-1842 S/yaqi
3 M. Abdulqadir xan Muhd Kusu 10 1842-1852 S/yaqi
4 M. Usman Harxo Sambo 15 1852-1867 S/yaqi
5 M. Ahmadu xan Muhd Kusu 29 1867-1896 S/yaqi
6 M. Iya Jibrilla 1 1896-1897 S/yaqi
7 Muhamman Maikayi xan Ahmad 4 1897-1901 S/yaqi
8 Umaru Alkammu xan Usman 4 1901-1905 S/yaqi
9 Muhd Ahmadu xan Muhd Kusu 2 1905-1907 S/yaqi
10 Ade xan Ahmadu 2 1907-1909 S/yaqi

239
11 Hasan xan Ballo xan Usman 15 1909-1924 S/yaqi
12 Abubakar Ibrahim xan Muhd Kusu 5 1924-1929 S/yaqi
13 Usman xan Harxo Ballo 9 1929-1938 S/yaqi
14 Usman Babale xan Umaru Alkammu 26 1938-1964 S/yaqi
15 Yakubu xan Abubakar 29 1964-1993 S/yaqi
16 Salmanu xan Ade 13 1964-76322 S/kudu
17 Muhd xan Ahmadu Wata 6323 1976-1976 S/kudu
18 Muhd Maidawa xan Usman Ballo 16 1977-1993324 S/kudu
26 42
1993-2019 S/Yaqi
19 Ali Yakubu xan Abubakar 7/12/2019- S/Yaqi

Waxannan sun wuce sai ambatonsu * Sai tunanin arziqinsu


Kyan adonsu da kyan hawansu * Ba ka koma ganin xayansu
Kam ba zuri’ar da sun bari ba

YA YI SARKIN YAQI YA YI HAKINCI

Suna Shekaru Daga Sarauta


1 M. Abdulqadir xan Muhd Kusu 10 1842-1852 S/yaqi
2 M. Usman Harxo Sambo 15 1852-1867 S/yaqi
3 M. Ahmadu xan Muhd Kusu 29 1867-1896 S/yaqi
4 M. Iya Jibrilla 1 1896-1897 S/yaqi
5 Muhamman Maikayi xan Ahmad 4 1897-1901 S/yaqi
6 Umaru Alkammu xan Usman 4 1901-1905 S/yaqi
7 Muhd Ahmadu xan Muhd Kusu 2 1905-1907 S/yaqi
8 Ade xan Ahmadu 2 1907-1909 S/yaqi
9 Hasan xan Ballo xan Usman 15 1909-1924 S/yaqi

322
Ya yi murabus ran 10 Janairu 1976
323
An naxa shi ran 11 Janairu 1976, ya rasu ran 25 Disamba 1976 bayan doguwar
jinya.
324
Hukuma ta tabbatar da shi sarkin Kudu ran 27 Afrilu 1977. An kuma naxa shi a
Bauci, ran lahadi 8 Mayu 1977. An rako shi Gumau ran litinin 09 Mayu 1977. An
naxa shi sarautar sarkin yaqi ran 26 Yuni 1994. Ya rasu ran jumma’ah 16 Jumada
Sani 1440 Hijiriyya, daidai da 01 Fabrairu 2019, bayan sallar asuba.

240
10 Abubakar Ibrahim xan Muhd Kusu 5 1924-1929 S/yaqi
11 Usman xan Harxo Ballo 9 1929-1938 S/yaqi
12 Usman Babale xan Umaru Alkammu 26 1938-1964 S/yaqi
13 Muhammadu Maidawa xan Usmanu 26 1993-2019 S/Yaqi
14 Ali Yakubu xan Abubakar 7/12/2019- S/Yaqi

Zahiri ga zatonta yaqi * Ko wuta ko ko ga biqi


Ta taras da mutum masaqi * Ya zage ya tara miqi
Ya mace bai jefa qoshiya ba

Sanadi ga waxansu doki * Wasu ko sanadinsu zaki


Wasu su mace a tafki * Wasu ma sanadinsu xaki
Ya zubo musu ba cikin shiri ba

YA YI SARKIN YAQI, BAI YI HAKINCI BA

Suna Shekaru Daga


1 Muhamman Kusu 10 1812-1822
2 Malam Jibrilla 20 1822-1842
3 Yakubu xan Abubakar 29 1964-1993

YA YI SARKIN KUDU, YA YI HAKINCI


BAI YI SARKIN YAQI BA

Suna Shekaru Daga


1 Salman xan Sarki Ade 12 1964-1976
2 Muhd Ahmadu Maigoge Wata 6 1977-1976

Dubi dai ga sarakunammu * Wanda sun ka riqe qasarmu


Masu ko daraja gare mu * Dubi Shehu mujaddadinmu
Ka tuna ba za mu dauwama ba

241
YA YI SARKIN YAQI, YA YI SARKIN KUDU, YA YI HAKINCI

Suna Sarkin kudu Sarkin yaqi


1 Muhd Maidawa xan Usman 1977-1993 1993-2019
*Yawan kwanakin Bare-bari a sarautar sarkin kudu = 13½
#Yawan kwanakin Bare-bari a sarautar sarkin kudu =41½

Kar ka ba mutuwa aminci * Don wada ko don talauci


Don yawa ko don kaxaici * Ta taras da waxansu gun ci
Ba su tauna abinda sun haxe ba

Ta taho ta xauki sarki * Mai hawa da dubun dawaki


Ga dubun matsara a xaki * In da ma ta fi qara auki
Ba ta bar fanko maras kwabo ba

YA YI SARAUTA A BAUCI 1812-1822

Suna Inda ya yi sarauta


1 M. Muhammadu Kusu Bauchi

Dubi dai manyan mazaje * Masu shan kotso da jauje


Sun wuce manyan gwaraje * Soba mai baya da qauje
Ka cane ba za ka lahira ba.

YA YI SARAUTA A TORO 1822-1842

Suna Inda ya yi sarauta


1 M. Jibirilla Toro

YA YI SARAUTA A GAU-LAME-KAFIN DILIMI 1852-1867

1- Usman xan Harxo Sambo : Shi ne wanda ya kafa sabuwar


Lame, ya xauke ta daga arewa da kogin Dilimi, ya mai da ita
arewa da kogi saboda kare kai daga harin Ningawa. Ya zauna

242
cikinta shekara huxu, kana ya bar ta da izinin mai martaba
sarki ya je ya kafa wani garin ribaxi na Kafin Dilimi. cikin
qasar harxon Zaranda, ya kuma mai da hedkwatar mulkinsa
cikinta, duka don tsare kafa da Ningawa ke biyowa suna
kawowa Bauci hari.325 Har lokacin da rikici ya auku tsakaninsa
da Harxon Zaranda. Sarkin Bauci ya umarce da ya canza gari,
sai ya koma Rauta, kuma ya rasu bayan wata shida, aka binne
shi a can. Abin mamaki an naxa shi sarautar sarkin yaqi yana
zaune a Toro, ya koma Gau, kana Lame san nan Kafin Dilimi,
san nan makwancinsa a Rauta.

YA YI SARAUTA A LAME 1842-1929

Suna Inda ya yi sarauta


1 Abdulqadir Muhamman Kusu Lame
2 Usman Harxo Sambo Lame
3 Ahmadu Muhamman Kusu Lame
4 Muhamman Maikayi xan Ahmadu Lame
5 Umaru Alkammu xan Usman Lame
6 Muhammadu xan Ahmadu Lame
7 Ade xan Ahmadu xan Muhd Kusu Lame
8 Hasan xan Ballo xan Usman Lame
9 Abubakar Ibrahim xan Muhd Kusu Lame

325
...Su Ningawa, ba wai tsananin yaqi na gaba da gaba, ko jaruntaka ne suke dashi
wanda ya fi na saura ba, a’a, amma dai wata dabarar yaqi gare su. Dabarar nan kuwa
itace ba su kai yaqi gari sai dare ya tsala. Sai su kewaye garin su bunka masa wuta ta
ko’ina. To, duk wanda ya fito cikin dare a gigice, mace ko namiji, sai su kashe na
kashewa, su kame na kamawa, su kwashe dukiyarsu da matansu da ’ya’yansu, su kai
matattara. Idan suka gama tarawa, sai su tasa su a gaba su tafi da su Ningi su yi ta
sayarwa attajirai da fatake, wasu kuma su je da su gida su yi musu bauta. sanya
qasashen da ke kewaye da shi, yana yaqinsu. Ba su bar qasar wani sarki da ke
kewaye da su ba, sai da suka yaqe shi. Sun yaqi Bauci da Kano da Zazzau da qasar
Shira.

243
YA YI SARAUTA A LAME-GUMAU 1938-1947

Suna Inda ya yi sarauta


1 Usmanu Babale xan Umaru Alkammu Lame : shekaru 9
Gumau : shekaru 17

YA YI SARAUTA A GUMAU 1947-yau

Suna Daga
1 Salmanu xan Ade 1964-1976
2 Muhammadu Maigoge xan Ahmadu 1976-1976
3 Muhammadu Maidawa xan Usman 1977-2019
4 Aliyyu Yakubu xan Abubakar 2019-yau

JIMILLAR SARAKUNAN GIDAN BARE-BARI

Suna Shekaru Daga


1 M. Muhammad Kusu 10 1812-1822
2 M. Abdulqadir xan Muhd Kusu 10 1842-1852
3 M. Ahmadu xan Muhd Kusu 29 1867-1896
4 Muhd Ahmadu xan Muhd Kusu 4 1897-1901
5 Muhd Ahmadu xan Muhd Kusu 2 1905-1907
6 Ade xan Ahmadu xan Muhd Kusu 2 1907-1909
7 Abubakar Ibrahim xan Muhd Kusu 5 1924-1929
8 Yakubu xan Abubakar OFR 29 1964-1993
9 Salman xan Sarki Ade 12 1964-1976
10 Ali Yakubu xan Abubakar 7/12/2019-
Kwanakin shekarunsu a mulki = 103

Soya tattabaru da kaji * Ko miyar taushe da goji


Ko hawan Rali da Roji * Ke yawan tura ku rami
Ba ku san mutuwa tana zuwa ba.

244
JIMILLAR SARAKUNAN GIDAN FULANI

Suna Shekaru Daga


1 M. Jibrilla 20 1822-1842
2 M. Usman Harxo Sambo 15 1855-1867
3 M. Iya Jibrilla 1 1896-1897
4 Umaru Alkammu xan Usman 4 1901-1905
5 Hasan xan Ballo xan Usman 15 1909-1924
6 Usman xan Harxo Ballo xan Usmanu 9 1929-1938
7 Usman Babale xan Umaru Alkammu 26 1938-1964
8 Muhd Ahmadu Maigoge Wata 6 1976-1976
9 Muhd Maidawa xan Usman xan Ballo 42 1977-2019
Kwanakin shekarunsu a mulki = 132

Tun da dai manyan Halifa * Larabawa masu iffa


Sun wuce wa ke da qofa * Cewa ba za shi lahira ba.

WAXANDA BA SU HAIHU BA

Suna Daxewa Sarauta


1 Sarkin yaqi Jibril 20 1822-1842
2 Abduqadir xan Muhamman Kusu 10 1842-1852

WAXANDA SUKA YI MURABUS

Suna Daxewa Sarauta


1 Muhd Ahmadu xan Muhd Kusu 4 1897-1901
2 Ade xan Ahmadu xan Muhd Kusu 2 1907-1909
3 Salman xan Sarki Ade 12 1964-1976

245
SARAUTUN DA KE AKWAI
A MASARAUTAR QASAR LAME

Ga asali a qasar Bauci, kafin bayyanar turawa wasu sarautun ana


gadonsu ne, wasu kuma ana samu a dalilin ’yan’uwantaka da sarki.
Wasu kuma na bayin sarki ne, shi ke naxa su kyauta, saboda wata
bajinta da suka nuna a fagen yaqi. Sai kuma ’ya’yansu da jikokinsu su
gada daga gare su. San nan wani lokacin idan wani mutum ya qasaita,
har ya zama shugaban jama’arsa, to, akan bar shi da sarautarsa. Wani
ma har sarki kan aurar masa da ’yarsa don shigar da shi cikin
danginsa.

SARAUTUN DA WASU KE AKAI

1- Tafida : Abubakar Sadiq


2- Ciroma : Ahmad Muhd Lame326
3- Bunu : Ibrahim Umar
4- Xanburam : Labaran Abdullahi
5- San turaki : Ango Mato Lame
6- Marafa : Alhaji Ahmadu
7- Iya : Ahmad Rufa’i Muhammed
8- Xallawal : Babangida Sulaiman327
9- Xangaladima : Lawal Mamido
10- Darman : Adamu Muhammadu Goge
11- Xandarman : Aliyu Muhammed Lame

326
Ya rasu a asibitin Kano ran lahadi 19-10-2016. An sallaci gawarsa da qarfe biyu
na ranar litinin a masallacin Federal Low cost Bauchi.
327
Asalin sunansa Adamu, amma ana sakayewa ana cewa Babangida, saboda sunan
kakansa sarkin yaqi Ade aka raxa masa. An haife shi a Gumau a shekarar 1970. A
shekarar 1976 sadda mahaifinsa ya yi murabus daga sarauta, sai ya koma dasu
Bauci, inda ya tashi a cikinta. Ya yi makarantar Firamare ta Rariya 1977-1983. Kana
daga nan ya tafi makarantar horon malamai (Teachers College) Toro 1983-1989. Sai
kuma ya tafi kwalejin ilimi ta (Aminu Saleh College Of Education) Azare 1989-
1992.

246
12- Xan’amar : Aloma Ibrahim
13- Yarima : Yakubu Muhammed
14- Sardauna :328 Babayo Sa’idu
15- Ubandoma : Umar Dawaki
16- Xan’iya : Alhaji Ibrahim adamawa?
17- ’Yankwana : Yusufu Waziri (Xan’atta)329
18- Shamaki :330 Mudi malam Maidoki
19- Xanrimi :331 Alhaji Babangida Nasarawa
20- Sallama :332 Bello Adamu
21- Sarkin gida : Shehu Dogari
22- Lifidi :333 Adamu Musa
23- Sarkin dogarai : 334

328
Kafin shi an yi Sardauna Haruna Adamu
329
Yusuf Waziri, An haife shi a Gumau ran 15 ga Yuli 1966. Ya yi karatun
Muhammadiyya a makarantar M. Bugau. Ya yi karatun ilimi a wajen M. liman M.
Muhammadu Yahya da M. Gero. Ya yi makarantar firamare ta Gumau Sanga 1973-
1979. Sai ya tafi kwalejin koyon sana’a ta GTC Gumau 1982-1989. Yanzu yana aiki
da ma’aikatar lafiya a matsayin Dubagari. Kuma yana zaune a Gumau tare da
iyalansa.
330
Shamaki : Asalinta sarauta c eta bayin sarki. Shi ne babban bawan sarki. Har ma
ana yi masa kirari cewa, “Korau kan bayi.” Aikinsa shi ne isar da harkar Hakimai ga
sarki. Ko harkar Dagatai ga Hakimi. Ta wajensa Hakimai duka ke ganin sarki. Ko
Dagatai duka ke ganin Hakimi. Idan sarki ko Hakimi ya zauna a fada, shi ke fara
gaisuwa, san nan sauran jama’a su yi. Daga shamaki sai sarkin Dogarai.
331
Xan rimi : asalinta sarauta ce ta bayin sarki. Sarautar Xanrimi a zamanin zuwan
turawa aka qirqirota, kuma aikinsa shi ne mai zirga-zirga tsakanin sarki da Razdan,
ko tsakanin Hakimi da Di’o. da zarar sarki ya yi hawa shi yak an tafi ya gayawa
Razdan cewa ga sarki nan tafe. Ko ya gayawa Di’o cewa ga Hakimi nan tafe.
332
Sallama : Asalinta sarauta ce ta bayin sarki. Hasali ma shi ne mai daraja ta uku a
cikinsu. Shi ne mai kula da harkar Shari’ah da kuma malamai. Shi ke wa Waziri da
Alqalai Magana da sarki a kan harkokin da suka shafe su.
333
Kafin shi an yi lifidi Xanduqushi
334
Sarkin Dogarai : Asalinta sarauta ce ta bayin sarki. Shi ne mai bin Shamaki cikin
fara gaisuwa ga sarki, idan ya zauna a fada. Kuma shi ne wakilin Doka. Yana da
Dogarai da yawa a qarqashinsa, waxanda alhakinsu ne su kamo varawo, ko wani
wanda ya faskara. A zamanin das hi ke xora sarki akan doki, in za’a yi hawa. Daga
sarkin dogarai kuma sai Sallama.

247
24- Sarkin Samari : Salisu Na’iya (Kurfo)
25- Sarkin Dawaki :
26- Kilishi :335 Xan china
27- Wambai : Abubakar Jumva
28- Babban Zagi (Sarkin zagi) : 336 Waje Xanye
29- Sarkin kakaki :
30- Kwandon gari : Babaru
31- Garkuwa : Sabo Isa
32- Masu :337 Sani Sulaiman Kaita
33- Makama338 : Musa Jibrin
34- Barde : Abubakar Garba Muhammed
35- Jarmai : Sale Garba Kuna339

335
Kilishi : shi ne mai kula da shimfixar sarki, kuma jakada ne tsakanin sarki da
masu qara mata. Bayan an naxa shi, sai a damqa shi a hannun Baraya. wanda aka
haife shi bayan mahaifinsa ya ci sarauta. Saboda haka sarauta ce da ta ke faxawa kan
namiji ko mace?
336
Babban Zagi ko sarkin Zagi : Shi ne ke kusa da dokin sarki. Shi kuma ke zama
daf da shimfixa ta sa, idan yana zaune a majalisa.
337
Shi ne wanda dukkan masun yaqi ke hannunsa. Kuma bayan an dawo daga yaqi
sai ya tsaya a baya, akan hanyar garin da aka yaqa, ya kafa bariki, ko da mutanen da
aka yaqa za su biyo sawu, sais u murqushe su. kamar yadda ya faru lokacin sarkin
Bauci Umaru, sadda ya ci Gwaram da yaqi, sai ya tura Masu gabar da gari ya kafa
garinsa, don ko wata fitina za ta biyo baya ya tsar eta. Sai garin ya qasaita, ana
kiransa ‘Masuri.’
338
Asali Makama a hannunsa ake tara ganimar yaqi. Kuma shi ke raba ta
gwargwadon cancantar kowa, bisa qa’idodin shari’ah. Wato sarauta ce ta ilimi. Har
akan yi masa ba’a akan ce, “Makama mai rabo, mu ga na ka.” Domin daga baya
wasu idan sun yi rabo, sukan fifita kansu, ko idan wani abu ya yio ragowa, sai su
kwashe shi gaba xaya. Shi makama kullum a cikin birni yak e zaune, bas hi da qasa
ta kansa.
339
An hafe shi a 1967 a Gumau, kuma cikinta ya tashi. Ya yi karatun
Muhammadiyya a makarantar M. Bugau. Ya yi karatun ilimi a wajen M. Alhasan
Sadi, M. Ibrahim Sabo da M. Mai jama’a (Muhammad Tukur). Ya yi makarantar
firamaren Gumau-Sanga 1974-1978. Kana ya qarasa a makarantar firamare ta
Gyamzo 1978-1980. Ya fara JSS Lame a 1982, sadda aka kashe ta a 1984, sai aka
mai da su GSS Gumau, in da ya gama a 1987. Ya yi Diploma a makarantar horon
aikin gona (School Of Agriculture) Bauci 1989-1990. Kana ya yi digirinsa a

248
36- Barden Gabas : Lawal Aliyyu Sabana
37- Barden Yamma : Abubakar Badamasi (Sarkin Ririwai)
38- Barade : Xahiru (Maigana) Muhammed340
39- Sarkin/Magajin Aska : Ali
40- Galadima : 341 Alhaji Bala342
41- Madaki : Abdullahi Adamu343

fannin ilimin kimiyyar qasa (Soil Science Technology) a Kuru, ya a 1995. San
nan ya yi bautar qasa a jihar Ekiti. Ya koma jami’ar ATBU Bauchi ya yi ‘Post
Graduate Diploma’ a fannin ilimin ‘Environmental Technology’ 2001. Yanzu
2020 yana da digiri na biyu a fannin ilimin ‘Environmental Management
Technology’ ya fara aikin gwamnati tun shekara 1988. Yana da mata huxu, ’ya’ya
goma sha huxu. An naxa shi sarautar Jarman Wunti ran 13 Satumba 1993.
340
An haife shi a 1983 a Gumau, kuma a cikinta ya tashi. Ya yi karatun
Muhammadiyya da na ilimi a makarantar M. Xanjimmai Gumau. Ya yi makarantar
firamare ta Unguwar Waziri1990-1996. Ya yi makarantar sakandare ta ‘Islamic
Secondary School’ Gumau 1996-2003. Ya tafi kwalejin ilimi (College Of
Education) Kangere 2012-2014, in day a samu satifiket xin Diploma a kan Ci
gaban al’ummar qasa (Social Development). Yanzu yana aikin malamin yaqi da
jahilci, kuma qwararren direba ne.
341
Dukkan mai sarautar Galadima, ana yi masa laqabi da Gwauron giwa. Saboda
Galadima Gwauron giwa da aka tava yi a Kano.
342
Asalin sunansa Yusuf Abubakar. An haife shi a 1960 a Gumau, kuma a cikinta ya
tashi. Ya yi makarantar Muhammadiyya ta M. Mahmud Bugau. Ya yi makarantar
elementare da firamare ta Gumau-Sanga 1967-1974. Ya tafi mmakarantar horon
malamai TC (Teachers College) Shuwa a tsohuwar jihar Gongola 1975-1978. San
nan ya tafi ‘Social Development Institute’ Kumo-Gombe 1981-1982. Kana ya shuxe
zuwa ‘Kaduna Polytechnic Cabs’ 1987-1988. Ya yi ‘ADPA’ a jani’ar Jos. Ya yi
aikin malamin makaranta a 1978 a Tulu. Ya zamo Hedimastan Lame 1979-1981. Ya
yi aikin ‘Community Development’ har ya kai matsayin ‘Supervisor’ a qananan
hukumomin Toro da Dass a 1995. Ya kuma zamo darektan ilimi da walwalar jama’a
(Education & Social Develpoment) na qaramar hukumar Toro 2005-2013. Kana ya
yi ritaya ya kkama sana’ar noman rani da na damina. Kuma yana tava harkar siyasa.
343
An haife shi ran 10-08-1968 a Gumau, ya yi makarantar allo a tsangayar M.
Bugau, da tsangayar M. Ahmadu Tilden Fulani. San nan ya shiga makarantar
Firamare ta Gumau Sanga a shekara 1975- 1981. Daga nan ya makarantar horon
malamai ta TC (Teacher’s College) Toro 1983-1988. San nan ya yi NCE (National
Certificate Of Education) daga shekarar 2004-2007. Yanzu shi ne Hedimastan
makarantar Cexiya.

249
42- Ajiya : Muhammadu Xorawa344
43- Liman : M. Muhammadu Burai
44- Waziri : 345 Sambo Muhammadu346
45- Barwa : Ahmad Abdullahi347
46- Shatima : Xan’azumi Zalau

344
Xan M. Ibrahim Fakuru, an haife shi a 1943 a Fakuru, cikin gundumar Lame,
kuma a cikinta ya tashi, har ya yi aure ya haifi ’ya’ya biyu. Ana kiransa da ‘Xorawa’
saboda haihuwa ta sad a aka yi lokacin aikin xorawa, wanda ya fara kiransa das hi
shi ne wani dattijo maqwabcin gidansu, mai yi wa turawa hidima, an ace masa
‘Sarkin Ara’. Ya yi karatun muhammadiyya a tsangayar M. Adamu limamin Shau.
Ya yi karatun ilimi a tsangayar M. Ibrahim a Kano, da M. Mahmud Babban Dodo
Zariya. Ya yi makarantar ‘Evening Class’ a Bauci, in da ya samu shahada mai
darajar JPS (Junior Primary School). An xauke shi aikin malamin shanu a 1973, aka
tura shi Maiduguri, daga baya aka dawo dashi Darazo. In da ya yi aiki da LIBC
(Livestock Investigation Breeding Centre). A 1977 an dawo da shi kamfanin nama
‘Meat Factory’ Bauci. Daga nan sai ya yi ritaya daga aikin gwamnati, ya zama
akawun auduga a gidan Alhaji Usman Xankyarana, yana sayo masa auduga daga
lungunan jihar Bauci. A 1978 sai Alhaji Baba Saleh, wani shahararren xan kwangila,
abokin Chanchangi, ya yi cigiyar a nema masa wani yaro natsattse, wanda ya iya
rubutu, ya kuma san lissafi, kuma ya fito daga yankin Gumau, domin an bashi
kwangilar gina makarantar Sakandare a Gumau. Sai aka haxa su das hi, ya xauke shi
aikin ‘Site Manager’ yana lura masa da aiki har aka gama. Abinda ya yi sanadiyyar
zuwansa Gumau, da zama a cikinta. Yanzu haka yana zaune da iyalansa da jikoki,
kuma jigo ne a siyasar gunduma.
345
Sarauta ce da ba’a gadonta. Duk wanda sarki ko hakimi suka amince dashi, shi su
ke naxawa. Aikinsa shi ne bai wa sarki shawara ta gari. Sarki kaxai ke gaba dashi.
346
Waziri Muhammadu Sambo xan wazirin Xanwunti. Ya rasu ran jumma’ah 3 ga
Ramadan 1442 daidai da 16 Afrilu 2021, bayan doguwar jinya da ta kais hi ga
makancewa.
347
An haife shi a 1976, a layin Babarere, Gumau, kuma a cikinta ya tashi. Ya yi
karatun Muhammadiyya a makarantar M. Salisu Babarere, da makarantar M.
Xanjimmai, duka Gumau. Ya yi karatun ilimi a wajen mahaifinsa M. Abdullahi,
sarkin malamai. Ya yi karatun firamare a makarantar Unguwar Waziri 1982-1988.
Ya ta fi GSS Darazo 1996-2001. San nan ya ta fi kwalejin horon alqalai ta Legal
Misau 2003-2005, in day a karanci harshen Hausa da darussan addinin musulunci
(Hausa & Islamic Studies). Yanzu yana makarantar kimiyya da fasaha ta ‘Abubakar
Tatari Polytechnic’ Bauchi, in day a ke karantar yadda ake tarbiyyar yara ’yan
makarantar firamare (Primary Education).

250
47- Xanruwata : Musa Dembo
48- Durvi : Musa Audu Safe
49- Wali : Shehu Maqeri
50- Sintili348 : Ali Dutse349
51- Cigari : Nuru Lame
52- Majidaxi : Murtala Jibrin350

348
Sintili : asalin Sintili sunan wata buta ce mai murfi da ake zubawa sarki ruwan
zuma wacce aka dama ta da nakiyar dandaqwarya. Sintili shi ke riqe da ita. To, duk
shekara sarakuna suna zagaya qasarsu inda su ke mulki. To, duk inda sarki ya ji’yar
yunwa ta kama shi, sai ya k an ce, “ina sintili?” sais u rates gefen hanya, sai a zuba
wa sarki daga wannan buta a cikin qoqo, ya sha, ya share baki. Kana su bi sauran
jama’ah. To, shine sai sunan wannan buta ya bi mai riqe ta, ta kuma zama sarauta
mai zaman kanta.
349
An haife shi a Fakuru, a 1933, ya tashi a Lame a hannun sarkin Yaqi Usmanu
Balale. Dalilin haka kuwa wata rana ne shi sarkin yaqi da sarkin Bauci Maigari
(1907-1941) sun je Shau, cikin gundumar Lame, don halartar taron lalube na ciwon
bacci. Bayan gamawa sai aka shiga wasannin nishaxi, su kuwa suna zaune suna
kallon wasanni iri-iri, sai sarkin yaqi ya hango shi, cikin yara wane talatin? Suna
wasa, yana yaro qarami, ko kaciya ba’a yi masa ba, sai ya tura qaninsa Baba Audu
ya je ya zo masa dashi. Ya xauko ya zo das hi gabansa. Sai ya yi tambaya, ko
wanene uban wannan yaro. Ba’a samu wanda y ace ya sani ba. Sai aka tambayi yaro,
sai y ace tsohonsa na Fakuru, tafiyar mil biyu tsakaninta da Shau, sai aka tad a
jakada ya je ya kira shi. Da aka zo das hi bayan sun gaisa, ya ce, “Abin day a san a
yi kiranka, wannan yaro ina so ka ba ni shi.” Tsoho y ace, “Ranka ya daxe! Ai ni da
abin da na haifa duk na ka ne, ko ni ka ce na tashi na komo wurinka, ai sai na
komo.” Da zai dawo Lame sai ya dawo das hi, ya yi masa kaciya, ya riqe shi
kyakyawar riqo, ko wanda ya haife shi, ya sanya shi a makarantar elementare a
1940, lokacin ’ya’yan sarakuna kaxai ake saw a. Rana xaya aka sa shi a makaranta
tare da Abubakar Umar, Alqali M. Yakubu Umar, su biyu ’ya’yan alqali M. Umaru,
da Alhaji Uba xan sarkin Riruwai. To, saboda gatan da sarkin yaqi ya nuna masa,
sai ya zamo duk sadda aka koma makaranta, shi bay a dawowa sai an yi da gaske, a
daddafe ya gama a 1944. Sai ya koma barikin Fakuru, ya shiga shiririta, ya bi wani
shexanin mutum bamaguje, mai sihiri, wais hi ‘Mai ragajaniya’ saboda shexancinsa,
yak an harba kibiya, ta tafi ta dawo y ace ta kafe a jikin bishiya. Ko ya miqa maka
hannunsa ka yi ta ja kamar alewa. Kai yak an iya cire kansa ma ya ajiya a kan tebur.
Sai ya bi shi ya tafi das hi Sumaila, cikin qasar Kano, shekara ta sa biyar yana koyon
sihiri.

251
53- Magajin Malam na Wunti :
54- Magajin Malam Babba : Alhaji Ibrahim Sabo
55- Uban Dawaki : Basiru Adamu
56- Tafarki : 351Hasan Sama’ila
57- Wakilin Wunti : Abdullahi Yakubu Lame
58- Maidala : Yakubu Hamidu
59- Dattuwa –Manga : Garba Aliyyu Maigamo
60- Baura : Alhaji Yakubu Na’iya
61- Sarkin Dawaki mai tuta : Sunusi Dauda
62- Sarkin Dawakin Tsakar Gida : Ali Yakubu
63- Gimbiya : Hajara Abdullahi Jibrin352

350
Murtala Yakubu Abdullahi, an haife shi ran litinin 2 ga Fabrairu 1972 a gidan
Sarkin shanun Bauci, da ke kan titin Aminu, Unguwar Wunti Bauci. Ya yi karatun
Muhammadiyya a makarantar M. Babba ‘Madrasatun Nurul Huda’ da ke kan titin
Yakubu Lame. San nan da suka dawo Gumau da aiki ya xora karatun a makarantar
M. Mahmud Bugau cikin Gumau. Ya kuma fara makarantar Firamare ta
Shadawanka Bauci, har ya yi aji biyu, sai aka yi mahaifinsa sauyin wurin aiki daga
Bauci zuwa Toro, ya shiga Gyamzo, in da ya qarasa karatunsa a makarantar firamare
ta Unguwar Waziri Gumau a 1982. A shekarar kuma ya tafi kwalejin horon
malaman larabci ATC (Arabic Teacher’s College) Gwambe 1982-1987. Har ya fara
aikin koyarwa, sai kuma ya tafi kwas xin samun Satifiket a cibiyar horon ma’aikata
(Staff Training Centre) Azare 1990-1991. Sai ya koma qaramar hukuma da aiki.
Kana sai ya tafi makarantar Cibiyar zurfafa ilimi (Centre For Continuos Education)
da ke gangaren Jos ya yi Diploma a wajen a 1992-1994. Ya tafi Jami’ar
(University Of Abuja) Abuja 1994-1997. Yanzu haka yana da gidansa day a ke
zaune tare da iyalansa a Gumau. Kuma yana ci gaba da aikinsa a sakatariyar
qaramar hukuma.
351
Ga asali idan sarki zai yi tafaiya zuwa wani gari. Tafarki shi zai fara zuwa ya
duba inda aka tanadar na saukar sarki, da inda aka tanadar zai zauna, Sai idan ya
amince da su tukuna kana sarki zai zauna a wurin. Hatta hanyar da sarki zai bi ya je
garin said an ya amince da ita tukuna, kana sarki zai bar gari. Kadan bai amince da
ita ba, sarki ba zai ko xaga qafa ba.
352
An haife ta a 1966 a Gwambe. Amma ta tashi a Toro, inda ta halarci makarantar
firamaren Gyamzo 1971-1977. Ta tafi makarantar sakandaren ’yan mata ta (GGSS)
Doma 1978-1983. Kana ta halarci makarantar koyon harshen larabci mai zurfi
(School for Higher Islamic Studies) Jos 1991-1994. Ta zarce zuwa jami’ar Abubakar
Tafawa Valewa (ATBU) Bauci 1998-1999, kana ta cike da jami’ar Jos 2004-2008.

252
64- Sarkin Malamai : Barista Shu’aibu Rahama
65- Sarkin Ladanai : M. Ya’u Ibrahim
66- Saraki :353 Mudi Musa Jahun
67- Sarkin Yamman Wunti : Sadisu Tama
68- Sarkin Hawa : Yakubu Ibrahim
69- Sarkin Sudan : Sule Shamaki
70- Sarkin jakadu :354 Murtala Ibrahim
71- Sarkin itatuwa : Idris Ibrahim
72- Wakilin doka : Hasan Muhammad
73- Wakilin makaranta : Xallami Badamasi
74- Kaigama : Muhammadu Inuwa Adamu
75- Dallatu : Alhaji Muhammadu355
76- Mutawalli :356 Musa Abdullahi Fakuru357

Ta yi aiki a wurare da dama. Kamar yadda ta yi aure, kuma tana da ’ya’ya shida. Ita
ce shugabar qungiyar mata musulmi (FOMWAN) reshen qaramar hukumar Toro
353
Shi ne wanda kere-keren makamai ke hannunsa
354
A zamanin da, Hakimai duka su ke riqe da garuruwansu. Amma day a ke
wasunsu a cikin birni suke zaune, bas u da qasa ta kansu. To, jakadu ne ke kai-kawo
tsakaninsu da talakawansu. Jakadu su ke karvar zakka, jangali da kuxin gandu.
355
Asalin kakansa mutumin Garko ne, ta qasar Kano. Karatu ya kawo shi qasar
Guddiri, sai ya yi zamansa a gun. Sai xansa ya taso da kasuwanci da fatauci, tun
yana zuwa Lame da kayan sayarwa, har ya yi zamansa a cikinta. Alhaji
Muhammadu Kilaki, ana yi wa mahaifinsa laqabi da Kilaki ne saboda da can mutum
ne mai samun abin duniya, kuma mai yawan ado, har manya kan ce ‘Yaro da yawan
ado kamar kilaki?’ shi kenan kuwa sai sunan ya bi shi. An haife shi a Lame cikin
shekarar 1933, kuma a cikinta ya tashi. Shekara ta sa bakwai yana karatun
Muhammadiyya a tsangayar M. Adamu limamin Shau, har ya yi sauka ya fara
tilawa. Bayan dawowarsa gida ya yi karatun yaqi da jahilci, kana ya yi karatun ilimi
tun daga Qawa’idi har zuwa littafin Izziyya duka wajen M. Ibrahim qanin limamin
Shau, da kuma M. Garba Xanbaqi a Gumau. Ya dawo Gumau tun bai yi auren fari
ba, tun yana leburanci, har ya fara kasuwanci. Allah kuma ya yi masa nasibin arziqin
kuxi da na ’ya’ya. Yanzu haka dashi da ’yan’uwansa suna da ’ya’ya fiye da xari
biyu, ban da jikoki.
356
Shi ne mai kula da aikin dukkan alqalai.
357
An haife shi a 1950, a Fakuru da ke gundumar Lame. Ya yi karatun allo a gidan
limamin Fakuru, uban malam Haruna. Ya shiga Firamaren Lame a shekarar 1960-
1967. Daga nan sai aka xauke shi aikin malamin shanu a Bauci,har sun tava tura

253
77- Majikira : Bashiru Muhammed Xorawa
78- Yari : Idris Sulaiman Kaita358
79- Dikko : Husaini Idris
80- Gado-da-Masu : Babaji Musxafa
81- Sarkin kasuwa359 : Sabo Isa
82- Sarkin Fada : Alhasan Atamfa360

shi kwas Vom. Daga baya sai ya koma ‘Bauchi Central Office’ sai aka tura shi
Fataskum ‘Clerical Course’ da ya gama sai ya yi qaramar Sakandare ‘Intermediate.’
ya gama a 1976. Ya dawo da aiki Toro a shekarar 1977 a matsayin ‘Senior
Clerical Officer’ a 1979 ya tafi Kaduna ya yi karatun ‘Diploma’ a fannin shige da
ficen kuxi ‘Local Government Finance & Administration’ a Kaduna Polytechnic.
Ya riqe mataimakin sakatare na qaramar hukumar Lame 1982-1984. Ya yi babbar
Diploma ‘HND’ a jami’ar Ahmadu Bello Zaria. Ya tava riqe ma’ajin sashin ilimi na
‘Toro LEA’ da kuma mataimakin ma’aji na qaramar hukuma. Ya yi ritaya a 1990 ya
shiga siyasa. ya yi shugabancin qaramar hukumar Toro har sau biyu na farko daga
1991-1994. Na biyu daga 2003-2007. Ya riqe matsayin kwamishinan dindindin a
ma’aikatar xaukar ma’aikata na qananan hukumomi (Local Government Service
Commission) a 2000-2003. An naxa shi ‘Member Governing Council’ na jami’ar
Ahmadu Bello. Bayan haka jihar Bauchi ta naxa shi kwamishinan dindindin a
vangaren majalisa 2009-2016.
358
An haife shi ran Talata a Unguwar Dogon Layi Gumau, a shekarar 1974, kuma a
cikinta ya tashi. Ya yi makarantar Muhammadiyya ta M. Abdulhamid Xanhasan. Ya
kuma yi makarantar Firamare ta Unguwar Waziri 1981-1987. San nan ya tafi
kwalejin (Unity College) Bauci 1988-1994. Sai ya tafi (Tatari Ali Polytechnic)
2000-2002. San nan ya tafi jami’ar Bayero (Bayero University) Kano 2009-2014. A
yanzu haka yana zaune a Gumau tare da iyalansa, kuma shi ne shugaban makarantar
‘Upper Basic’ ta Maiwuro a cikin Gumau. Kuma babban malami mai darasu a
tsangayar tarbiyya a kwalejin tarbiyya ta Sunnah (Sunnah College Of Education)
zauren Gumau.
359
Shi ne wanda dukkan ’yan kasuwa su ke hannunsa. Aikinsa yana kasuwa ne
kaxai.
360
Alhasan Shehu, an haife shi a 1980 a Gumau. Ya yi makarantar Muhammadiya ta
M. Xanhasan Gumau, a wajen M. Salisu Maje-haji. Ya yi karatun ilimi a wajen M.
Mahmud Adam da M. Ibrahim Sam Sabo duka a Gumau. Ya yi makarantar firamare
ta Unguwar Waziri 1986-1992. San nan ya yi qaramar sakandare makarantar horon
malamai ta TC Toro 11993-1995. Kana ya tafi kwalejin Janar Hasan Usman Katsina
Bauci 1996-1999. Yana zaune a cikin garin Gumau, ya riqe noma, kasuwancin
magunguna da kiwon kaji, kuma yana da iyalansa da ’ya’yansa.

254
83- Xan’isa : Misbahun Oganeza
84- Salanke : Abdulhamid Garba361
85- Baraya :362 Nasiru Adamu
86- Cika Soro : Abubakar Adamu
87- Katuka : Xayyabu Garba
88- Magatakarda : M. Bala Ibrahim
89- Magajin Rafi : Sale muhammed Jange
90- Muqaddas : Alhaji Ahmed B. Yakubu
91- Xanmoyi : Isiyaka Salisu Ta’an
92- Sarkin Fawa :363 Abubakar Nayawo
93- Mai babban xaki : 364 Hajiya Maryamu365
94- ’Yan kwana : Yusuf Waziri
95- Wakilin qasa- da-qasa : Ado Ibrahim Pingel366
96- Jagaban : Joshua Titus Sanga
97- Zinariyar Wunti : Hadiza Babayo
98- Uwar Soro :367 Hajiya Hasanah (Larai)
99- Ciroman Uwar Soro :368 Hajiya Safiyyah
100- Madakin Uwar Soro369 : Hajiya Fati

361
An haife shi a 1974 a Ririwan –Dalma, kuma a cikinta ya tashi. Ya yi karatun
Muhammadiyya a wajen M. Audu Ririwai. Ya yi marantar firamaren Ririwai 1980-
1986. Yana gidansa a Gumau, kuma a cikinta yak e zaune. An naxa shi sarautar
Salanke a shekarar 2008. Yana da mata uku da ’ya’ya biyar. Kuma yana sana’ar
aune-aune a cikin kasuwar Gumau.
362
Shi ne jakada mai sadarwa tsakanin wani gari, ko wasu manyan baqi da sarkinsa.
363
Shi ne shugaban mahauta. Aikinsa na farawa tun daga mayanka har zuwa
mahauta, tare da abokan aikinsa.
364
Ita ce Uwar Sarki
365
Ita ce mahaifiyar Sarkin Yaqi Ali xan Yakubu
366
An haife shi a 1962 a Pingel, kuma a cikinta ya tashi. Ya yi karatun
Muhammadiyya a wajen M. Audu Mai Unguwar Hausawa Pingel. Ya yi karatun
ilimi a wajen limamin Ningi M. Sanda. Ya yi makarantar elementare da Midil a
Maiturare da ke qofar Fadar Sarkin Ningi. Yanzu shi ne shugaban masu aikin
ma’adanai na qaramar hukumar Toro. Yana da mata 3 da ’ya’ya 18.
367
Ita ce Uwargidan Sarki
368
Ita ce matar sarki ta biyu
369
Ita ce matar sarki ta uku

255
101- Sha lelen Uwar Soro :370
102- Xan Adalar Wunti : Yakubu Aliyyu Yakubu

SARAUTUN DA BABU KOWA A KAI

1- Xankade :
2- Xan’iya :
3- Xan makwayo :
4- Xanmaliki :
5- Mabuxi :
6- Sarkin dafe :
7- Sarkin rumbu :
8- Sarkin soro :
9- Sarkin sulke :
10- Mahaukata :
11- Chuchana :
12- Sarkin qwarbai :
13- Maja Sirdi :371
14- Makaman Xanrimi :372
15- Tukura :
16- Ganxoki :
17- Galadiman Zagi :
18- Makaman Zagi :
19- Masun Zagi :
20- Xan Isan Zagi :
21- Sarkin Tambura :
22- Sarkin kixa :
23- Sarkin jauje :
24- Sarkin busa :373

370
Ita ce amaryar sarki.
371
Maja Sirdi : Shi ne mai kula da dawakin sarki.
372
Makaman Xanrimi : Aikinsa shi ne kula da harkar masu qara maza, idan ana
shari’ah.

256
25- Turaki : 374
26- Qaura :
27- Madawaki : 375
28- Barden Kudu :
29- Barden Arewa :
30- Adon Gari :
31- Fasa-maza :
32- Maza-waje :
33- Ma’aji :
34- Talba : 376
35- Wakilin Tarihin Wunti :
36- Sa’i :
37- Jakadiya :
38- Fagaci :
39- Sarkin Gabas na Wunti :
40- Sarkin kudun Wunti :
41- Sarkin Arewan Wunti :
42- Sarkin Fulani :
43- Idaya (Qidaya) : 377
44- Dokaji :
45- Magayaqi : 378

373
Da zarar sarki ya fito, sarkin busa shi ke fara busa qahonsa, san nan sauran
maroqa duka su xauka. Shi kuma ke busa wa wanda aka naxa sabuwar sarauta, san
nan maroqa su faxi sunan sarautar.
374
Shi ne mai naxa rawanin duk wanda aka bai wa sarauta. Kuma yana daga cikin
jaruman sarki, na kusa dashi idan ya yi hawa.
375
Shi ne mai biyo ayari a baya idan ana dawowa daga yaqi, don in sun yard a wani
kaya ya tsinto ya taho dashi.
376
Shi ne wanda alqalai ke qarqashinsa, kuma ta hannunsa su ke ganin sarki.
Sallama shi ke yi musu iso.
377
shi ne mai qirga bayin da aka kamo bayan dawowa daga yaqi, kuma shi ke sanar
da sarki yawansu.
378
Shi ne wanda ake turawa ya je ya sanar wani sarki cewa ga rundunar yaqin
sarkinsa nan zuwa gare shi. San nan ya dawo ya gaya wa sarkinsa amsar yadda ta

257
46- Xanmaje :
47- Kacalla :

MALAMAN HAKIMIN QASAR LAME 1940-2021

1- M. Abubakar Saleh Kuna


2- M. Maijama’a Rimin Zayam
3- M. Umaru Lame
4- Jibros
5- Shehu Laru
6- M. Bala Lame
7- Nadawa
8- M. Adamu
9- Sarkin Hawa

JAKADUN GUNDUMOMI A 1960

1- M. Umaru (Iyan Wunti ) - jakadan Tama379


2- Galadima Bawa - jakadan Rishi380
3- Xanwunti - jakadan Rahama381
4- Waziri Nababa - jakadan Zalau
5- Bunun Fuloti - jakadan Wonu
6- Xan Lawal - jakadan Lame
7- Atamfa – jakadan Ribina

JAKADUN GUNDUMOMI 2021

1- Shehu Dogari – jakadan Tama/Rishi


2- Xan’azumi Gukka – jakadan Rahama

kasance. Wani da ya faxi saqon da aka aike shi, sai sarkin da aka kai wa saqon ya sa
ayi tag aura masa mari. Wani kuma ya sa ma a kasha shi.
379
An naxa shi jakadan Tama a 21 Disamba 1967
380
An mai dashi na Wonu a 21 Disamba 1967
381
A 21 Disamba 1967 an maid a shin a Zalau

258
3- M. Bala Ibrahim – jakadan Zalau
4- Adamu Xantiye – jakadan Wonu
5- Xanlami Ajayi – jakadan Lame (Babban jakada)
6- Sarkin jakadu – Murtala Ibra

FARARRUN AL’AMURAN QASAR LAME

1- Ran alhamis 24 Yuni 1954 Allah ya yi wa mai M.


Abubakar littafin Rishi cikin gundumar Rishi rasuwa.
2- Ran 23 Agusta 1962 Harxo Bawa na cikin gundumar
Rahama ya yi murabus, ya mayarwa da sarkin Rahama
littafinsa, y ace shi yanzu qarfinsa ya qare, kuma bas hi da
wanda zai riqe masa aikin, shekarunsa na haihuwa kuma
sun kai 70. Nan dan aka aika aikawa sarkin Bauci, y ace an
yarda masa ya huta, kuma an yarda masa ya zauna a garin,
ba tare da tad a tsoma bakinsa cikin sha’anin sarauta ba,
amma idan a gidan hukuma yak e sai ya fita, ya koma na
sa. Kuma an yarda mutanen garin su zavi sabon Mai littafi.
3- Ran 27-03-1963 sarkin Rafin-gora cikin gundumar
Rahama ya gaya wa sarkin Rahama cewa yana son a bashi
izinin barin sarauta saboda tsufa, kuma bas hi da mai
taimako. A lokacin shekarunsa 78, kuma ya shekara 33
yana sarauta. Kuma yana son sarkin Wurno ya riqe littafin.
Domin yana da xan’uwansa Voyi y ace shi bay a son
sarauta don baya son ya vata da’yan’uwansa. Shi kuma
sarkin Rahama nan da nan ya aika gaba. Nan da nan aka
aika Bauci, suka aiko da cewa an yardar masa ya yi
murabus, kuma ya ci gaba da zama a garinsa, sai dai gidan
day a ke ciki, idan na gwamnati ne, sai ya fita daga ciki.
To, daga baya kuma sai Boyi ya sake shawara yace yana
son sarauta. Sai suka kasu kasha biyu; mutanen Wurno su
43 suna son sarkin Wurno. Mutan Rafin-gora su 33 suna
son Voyi. Qarshe dai said a wazirin Bauci ya zo Gumau
aka tara su ran 24 Agusta 1963 aka yi wa kowa littafinsa.

259
4- Ranar 08-05-1963 sarkin Gyem cikin gundumar Lame ya
sanar da barin sarauta, ba tare day a faxi dalili ba. Sarkin
yaqi ya tambaye shi dalili, y ace babu wani dalili shi ya
bari ne kurum. Aka yi ta rarrashinsa y ace shi fa bay a so.
Aka aikawa sarkin Bauci, ya ce a gaya masa ya je Bauci.
Sarkin Lame ya aiko cewa bas hi da lafiya, domin ya vata
tsafinsu, tsafi kuma ya kama shi. Aka ce to in ya warke dai
ana nemansa a Bauci.
5- Ranar 14-04-1964 sarkin Davave cikin gundumar Rishi ya
haqura da sarauta saboda tsufa da ruxewa.
6- Ranar 19-05-1964 sarkin Gurungu cikin gundumar Tama
ya bad a sanarwar barin sarauta saboda tsufa da
makancewa, sai da sanda ya ke tafiya.
7- Ran 23 Satumba 1964 aka samu rahoton mai littafin
Nannake cikin gundumar Rishi ya bar sarauta, saboda cutar
kuturta da ta same shi, kuma ta ci qarfinsa, sai ya tashi ya
koma Dutsen Dass da zama, da kuma neman magani.
Amma kafin ya tafi ya bar garin a hannun Galadima. To,
da Galadima ya tabbatar sarki ba zai dawo ba, sai ya sanar
da magabatansa.
8- Ran 20 Maris 1965 mai gundumar Ribina ya aiko wa
sarkin kudu cewa mutanen Salarma cikin gundumar Ribina
sun ce bas u son mai littafinsu Jauro, kuma in ya zamo shi
ne mai sarautan wannan gari, to, wasu sun ce sai dai a
rubuta su a wani littafi, wasu kuma sun ce za su tashi su
koma wani littafin. Dalili kuwa da suka bayar shekara biyu
kenan ba halartar idi ran sallah, kuma lafiyarsa lau. Kuma
bad a daxewa ba yaran garin suka yi xan rikici a kan
xorawa, maimakon ya sasanta, ya gyara tsakaninsu, sai ya
xauko ’yan doka, aka tafi das u xakin shari’ah, aka yi musu
tarar fam talatin (£30). To, sai sarkin kudu ya aika Bauci,
aka nemi sarkin Salarma ya je Bauci, En’e tana nemansa,
sai ya qi zuwa. Mai gundumar Ribina ya tafi Salarma da
kan sa, ya karanta musu takardar sarkin Bauci. Sai Jauro y

260
ace shi fa ya ma haqura da sarautar. Sarkin kudu ya neme
shi da in ba zai je Bauci ba, to, ya zo wajensa a Gumau, ko
kuwa ya bayar a rubuce cewa ya bar sarauta. Da saqo ya
ishe shin an ma y ace ba zai je ba. Sai aka aka sanar dashi
cewa an yarda da barin sarautarsa, amma ya zavi garin da
zai zauna. In kuwa ya zavi zama Salarma, to, fa ya kiyayi
sa bakinsa cikin harkokin sarauta, ballantana ya aikata
wani abinda zai jawo tashin hankali. Sai ya zavi zama a
gonarsa da ke kusa da Salarma, kuma ya xau alqawarin ba
zai sa baki cikin sha’anin mulki ba. Sai aka naxa wakili a
garin kafin ayi zaven sabon mai littafi.
9- Ran 19 Afrilu 1966 M. Musa mai littafin Zigau-Danga
cikin gundumar Ribina ya sheda wa sarkin Ribina cewa ya
bar sarauta. Sarkin Ribina ya tambaye shi ko an yi masa
wani laifi ne y ace a’a, shi dai ya gaji ne kurum.
10- Ran 11 Yuni 1966 mai gunduman Ribina ya roqi ya huta
ga barin sarauta, saboda tsufa da qyar yak e tafiya akan
doki. Sai aka tura Goje ya yi wakilcin qasar kafin a yi
zaven sabon sarki.
11- Ran 26 Nuwamba 1966 hukumar En’e ta yarda da barin
sarautar mai gundumar Ribina, bayan daxewa ana doguwar
muhawara yana cewa ya bar sarauta saboda tsufa da rashin
lafiya, da kuma tun lokacin da mota ta yi hatsari dashi yana
jin kamar kansa ya juye, amma ya yarda a bai wa xansa.
Manyan qasarsa na cewa bas u yarda a naxa xansa ba, sai
dai a yi sabon zave, En’e na cewa bat a yarda da barin
sarautarsa ba tukuna, sai ya ba ta qwararan hujjoji. Bayan
murabus xinsa ya sauko daga dutse, ya koma gidan
gonarsa.
12- Ran 2 Maris 1977 mai littafin Lau cikin gundumar Tama
ya roqi sarkin Tama akan ya huta ga barin sarauta, saboda
tsufa, kuma bas hi da xa, balle yaro wanda zai aike shi.
13- Ran litinin 15 Yuni 1987 Alla ya yi wa mai littafin Wonu,
M. Sulaimanu Abdullahi rasuwa.

261
14- Ran litinin 6 Afrilu 1986 da misalin qarfe 1:25 na dare,
Allah ya yi M. Umaru mai gundumar Tama rasuwa, bayan
ya yi rashin lafiya na kwana 12. Tafidan Tama ya sanarwa
hakimi da rasuwar, Galadima kuma shi aka bai wa riqon
gari.
15- Ran lahadi 7 Disamba 1986 Allah ya yi wa mai littafin
Saya M. Isubu cikin gundumar Zalau rasuwa, bayan
shekara ashirin yana sarauta.
16- Ran Jumma’a 28 Janairu 1996 da misalin qarfe 4:00 na
yamma, Allah ya yi wa M. Muhammadu mai littafin Taura
cikin gundumar Tama rasuwa, bayan dogon rashin lafiya
na kimanin watanni goma.
17- Ran 11 Janairu 2014 Allah ya yi wa Harxo Adamu
Makawu cikin gundumar Lame rasuwa.
18- Ran 1 Nuwamba 2014 Allah ya yi wa mai littafin
Saminakan Gwa Madakin –Gwa Haruna Mahe cikin
gundumar Lame rasuwa.
19- Ran 6 Satumba 2017 allah ya yi wa Aliyyu Muhammed
mai gundumar Lame rasuwa.
20- Ran lahadi 17 Yuni 2018 Allah ya yi wa Alhaji Iro mai
littafin Rishi cikin gundumar Rishi rasuwa.
21- Ran laraba 10 Maris 2019 da misalin qarfe 2:00 na dare
wasu mutane da ake kira ’yan bula suka xauke Harxo Idris
cikin gundumar Rishi, ran jumma’ah 22 Maris 2019 aka
tsinci gawarsa a Shau cikin gundumar Lame.
22- Ran jumma’ah 27 Disamba 2019 da misalin qarfe 2:00 na
dare, wasu mutane da cewa das u ’yan ba beli sun xauke
Adamu Muhammed mai littafin Xandanshi cikin gundumar
Rishi sun tafi dashi, an tsinci gawarsa a bayan dutsen
Gwalbanya.
23- Ran 16 Afrilu 1970 majalisar gundumar Zalau suka zavi
M. Dabo xan marigayi sarkin Zalau Ibrahim wanda zai
sarauci gundumarsu, bayan rasuwar sarkinsu na da.’yan
majalisar gundumar Zalau mutum 16 ne, mutane 9 suka

262
zavi Dabo, idan an haxa dashi sun zama 10, don shi ma
wakili ne a majalisar. Sai mutum 3 ba su zave shi ba, kuma
bas u zavi wani xan sarki ba. Mutum 3 kuma bas u samu
dammar halartar zaven ba. An yi zaven bisa sa idon
Sakataren mulkin En’e (Administrative Secretary), Malam
Aliyyu Wulumba Daxi, da kuma wakilan ’yan majalisar
qasar Lame.
24- Ran 29 Fabrairu 1972 masu zaven sarautar gundumar
Tama suka taru suka zavi Ciroman Tama Malam Umaru,
xan marigayi sarkin Tama M. Muhammadu wanda zai
sarauci gundumarsu, bayan rasuwar sarkinsu na da. ’yan
majalisar qasar Lame sun yi taro domin duba zaven, bayan
da aka faxi dukkan halayensa, da iliminsa na ajin yaqi da
jahilci, da kuma shekarunsa na haihuwa 40. Kuma an ce ya
daxe yana riqe da aikin ubansa, ba’a tava samunsa da wani
hali mai muni ba. Kuma an ce yana da qwazo qwarai
wajen aikin hukuma. Shi ken an sai majalisa ta yarda da
zavensu.
25- Ran 1 Satumba 1975 majalisar gundumar Zalau ta zavi M.
Adamu xan marigayi sarkin Zalau Ibrahim ya yi musu
sarautar gundumar Zalau. Kuma majalisar hakimi ta yi
zama ta tabbatar da ingancin wannan zave. An zave shi
yana da shekaru 40, musulmi ne ga addini, Bafulatani ga
qabila, kuma yana da ilimin yaqi da jahilci. Ranar 3 ga
Oktoba an nemi hakimi idan zai shiga Bauci sallah, day a
tafi da M. Adamu da dukkan masu littafin gundumar
Zalau, don mai martaba sarki ya tabbatar ,masa da
sarautarsa a gabansu.
26- Ran 25 Mayu 1975 wakilan gundumar Rishi da masu
littafinsu suka zavi M. Muhammadu Wali xan Magajin
Rishi M. Umaru ya yi sarautar gundumarsu. Ya yi rinjaye
da quri’u 16, ta wakilai 4, ta masu littafi 12. Kuma
majalisar hakimi ta amince da ingancin zaven. An naxa shi
ran 4 Agusta 1975.

263
27- Ran 2 Nuwamba 1976 masu littafin gundumar Rahama da
manyanta suka taru suka zavi M. Muhammadu Inuwa xan
sarkin Rahama M. Usman ya yi musu sarautar
gundumarsu. Musulmi ne ga addini, Bagobiri ne ga haula,
xan shekara 40, ya yi karatun yaqi da jahilci. Ya yi takara
tsakaninsa da M. Goma. Majalisar qasar Lame ta yi zama
ran 15 Nuwamba 1976 akan wannan zave kuma sun yarda
da zave. Ya ci sarauta ya ci sarauta yana da shekaru 35,
sana’arsa kuma noma. An kuma naxa shi ran jumma’ah 15
Afrilu 1977
28- A qarshen watan Disambar 1992 Allah ya yi wa tarkunyar
Gundumar Rahama M. Muhammadu Inuwa Abdurrahman
rasuwa.
29- Ran 14 Afrilu 1984 masu littafin gundumar Tama 22 duk
da Galadiman Tama suka taru suka zavi Alhaji Yakubu
Tama mai quri’u 16,382 ya kada M. Musa Tama mai quri’u
4,383 da Ciroman Tama mai quri’u 2,384 da Alhaji Yakubu
Sunkuye385 wanda bai samu ko quri’a xaya ba, ya yi musu
sarautar gundumarsu, bayan mutuwar na da. Mai littafi
xaya bai yi zave ba, saboda rashin lafiya. An yi zave
lafiya, babu tashin hankali, waxanda aka kayar sun yarda

382
Ga sunayen waxanda suka zave shi haxe da littafinsu ; M. Hudu Ubandoma Kari,
mai littafin Tauran Baki, M. Isa Nasarawa, M. Adamu Dinga, M. Musa Shibi, M.
Ahmadu Hamidu Jama’ar Ahmadu, M. Abdulmumin Guraka, M. Adamu Tarkunyan
Beru, M. Idrisu Baqarfa, M. Garba Arewan Rinji, M. Musa Shifa, M. Shu’aibu
Kayarda, M. Badamasi Lau, M. Salihu Shim, da M. Adamu Yunusa Burku.
383
Musa Tama shekarunsa 35, yana da ilimin Elementare (qaramar Firamare) J.P.S.
(Junior Primary School), kuma ma’aikacin gwamnati ne. Ga sunayen waxanda suka
zave shi haxe da littafinsu ; M. Muhammadu Sabon gari, M. Muhammadu Sani
Gurungu, M. Haladu Ubandoma Bangon Tama, da M. Muhammadu Taura.
384
Ciroman Tama shekarunsa 46, yana da ilimin Alqur’ani, kuma sana’arsa noma.
Ga sunayen waxanda suka zave shi haxe da littafinsu ; M. Umaru Kuri, da
Galadiman Tama.
385
Alhaji Yakubu Sunkuye, shekarunsa 36, yana da ilimin Arabiyya, kuma sana’arsa
noma.

264
da abin da aka zava. Ya ci sarauta ya ci sarauta yana da
shekaru 36, ya yi ilimin yaqi da jahilci da na arabiyya,
sana’arsa kuma noma.
30- Ran 5 Mayu 2018 aka naxa M. Ahmad Aliyyu Muhammed
sarautar mai gundumar Lame.
31- A ranar 24 Satumba 1964 aka kama sarkin Jeren Bauci,
cikin gundumar Tilden Fulani, aka tsare shi a kurkuku a
Bauci. Aka aiko cewa mutanen garin su zavi wanda zai
riqe garin kafin ayi musu sarki. Sai suka zavi wani mutum
wais hi Gashiri ranar 28 Satumba 1964. An yi zaven bisa
halartan ’yan malisar gunduma da Atamfa wakilin hakimi.
32- Ran 7 ga Mayu 1963 mutanen Unguwar Magaji cikin
gundumar Tama suka zavi Karimu Ciroman Lau ya yi
musu sarautar littafinsu. Manyan garin da suka zave shi su
ne ; Galadima, sarkin yaqi, Majidaxi, Baraya, Sarkin
Noma, Audu Xanjaba, M. Nuhu, Sarkin Fawa, Xanmarwa,
Mai agogo, Bala, Mijinyawa, Maisamari, Gagarau, Yakubu
Bula, Magaji, Waziri Karo, Badamasi, Bala, Babuwa,
Mantau. An yi zaven bisa bisa sa idon wakilan gunduma da
na hakimi.
33- Ran 12 Agusta 1962 aka tuve Mai littafin Zuna cikin
gundumar Tama, bayan xaure shi a kurkuku. Kuma aka
umarci manyan garin das u zavi sabon mai littafi. Sai suka
zavi Ubandoma Jibrin, kuma an yi zaven a gaban ’yan
malisar qasar Lame.
34- Ran 24 Agusta 1963 mutanen Wurno cikin gundumar
Rahama suka zavi Sa’idu sarkin Cakobo, suka ce bas u son
a kirashi sarkin Wurno. Manyan garin da suka zave shi su
ne Mai Unguwa Qoshi, Dodo, Abai, Sodari, M. Adamu
Kunnuwa, Barau, Ticcha, Kwando, Sati, Kombo, Gandu,
Gungun, Baqoshi, Haji. An yi wannan zave a gaban’yan
majalisar gunduma da ’yan majalisar hakimi, saboda yadda
sarautar ta zo da rikici.

265
35- Ran 6 Satumba 1963 arnan Diriko cikin gundumar Tilden
Fulani, suka zavi Mai Unguwa Yamma ya yi musu sarautar
sabon littafinsu, bayan rabuwarsu da littafin Diriko, sun
raxawa unguwar suna ‘Jeren Bauci’ manyan garin da suka
yi zave sune ; Adamu, Maqeri, Wakili Gishiri, Kokon,
Shagayya, Mawanki, Amaza, Adaji, Jatau, Alaji. An yi
zaven bisa sa idon wakilan hakimi da na gunduma.
36- Ran 21 Satumba 1963 qabilun Chikobo cikin gundumar
Rahama, suka zavi M. Sa’idu ya yi musu sarautar sabon
littafinsu, bayan rabuwarsu da littafin Rafin-Gora (Zage-
zagi), sun raxawa unguwar suna ‘Chokobon Bauci’
manyan garin da suka yi zave sune ; Mai Unguwa Qoshi,
Dodo, Abai, Sodari, M. Adamu Kunnuwa, Barau, Ticcha,
Kwando, Sati, Kwambo, Gandu, Gungun, Baqoshi, Haji.
An yi zaven bisa sa idon wakilan hakimi da na gunduma.
37- Ran 8 Fabrairu 1964 mutanen Kuri cikin gundumar Tama
suka zavi Bunun Kuri Xanmgaji a matsayin sabon mai
littafinsu. Manyan gari da suka zave shi su ne; Galadiman
Kuri, Isyaku, Daudu, Gagarau, Mazadu, Ubandoma,
Zailani, Musa, Alewa, Lawal, Baba Maqeri, Maishera,
Agara, Agwale, da Marafa. An yi zaven bisa sa idon ’yan
majalisar gunduma da na hakimi. Ran 25—05-1964
mutanen Saya cikin gundumar Zalau suka zavi Ciroma
Yusufu a matsayin sarkinsu
38- Ran 12-06-1964 mutanen Unguwan Ta cikin gundumar
Lame suka zavi Majidaxi Tamilo a matsayin sarkinsu.
Manyan garin da suka zave shi su ne ;Mailau, Garba,
Ango, Mai Unguwa, Maijaki, Wawa, Tafida, Sarkin yaqi,
Baban Basa, da Sallau.
39- Ranar 17-06-1964 mutanen Gurungu cikin gundumar
Tama suka zavi Ubandoma a matsayin sarkinsu. Sun yi
takara su uku, Ubandoma ya samu quri’u 20, Xanburam ya
samu6, Mamuda ya samu 5.

266
40- Ranar 17-06-1964 mutanen Turkunyan Beru cikin
gundumar Tama suka zavi M. Muhammadu a matsayin
sarkinsu
41- Ran 10-07-1964 mutanen Gyem cikin gundumar Lame
suka zavi Ciroma Yarda ya zamo sarkin Gyamawa.
Manyan garin da suka zave shi su ne ; Galadiman Gyem,
sarkin yaqin Gyem, Marafan Gyem, Babangida, Barno,
Dodo, Sadau, Ajiya.
42- Ranar 1-09-1964 mutanen Davave cikin gundumar Rishi
suka zavi M. Jibri Davave ya zamo sabon sarkinsu.
Manyan garin da suka zave shi su ne ; Muhammadu Mai
Unguwa Doka, Bala Mai Unguwa Gezawa, Liman Qarami,
Kasada, M. Nahama, Zakarai, Tanko, Xangaladima,
Xanjuma, Almajiri.
43- Ran 23 Oktoba 1964 mutanen Nannake cikin gundumar
Rishi suka zavi M. Usmanu ya yi musu sarautar littafinsu.
Manyan garin da suka zave shi su ne ; Galadiman gari,
Madaki, Sarkin noma, Bage, Musa, Adamu, Isa. An yi
zaven a gaban ’yan malisar gunduma da ta hakimi.
44- Ran 9 Nuwamba 1964 mutanen Jikai cikin gundumar
Zalau suka zavi Tafida Mato ya yi musu sarautar littafinsu.
Manyan garin da suka zave shi su ne; Magaji Burra, Gito,
Hasan, Dugu, Barammi, Maisaje, Maganda. An yi zaven a
gaban ’yan majalisun gunduma da ta hakimi.
45- Ran 1 ga Mayu 1965 mutanen Zuna cikin gundumar Tama
suka zavi Karimu ya yi sarautan littafinsu. Manyan garin
da suka zave shi su ne; Galadima, Haquri, Sabongari,
Yakubu, Ibrahim, Adamu, Xankaka, Algai, Audu,
Muhammadu. An yi zaven bisa sa idon ’yan majalisar
qasar Lame.
46- Ran 1 Mayu 1965 kuma mutanen Baradawo cikin
gundumar Lame suka zavi Ahmadu Bala ya yi musu
sarautar littafinsu, bayan mutuwar na da. Manyan garin da
suka zave shi su ne ; Baraya, Bunu, Madaki, Ciroma,

267
Galadima, Abarshi, Buba, Idi, M. Sule. An yi zaven a
gaban ‘’yan majalisar qasar Lame.
47- Ranar 15 ga Mayu 1965 mutanen Faka cikin gundumar
Lame suka zavi M. Xanladi ya yi musu sarautar littafinsu.
Manyan garin da suka zave shi su ne ; Galadima, Ma’aji,
Ciroma, Sarkin Faka tsoho, Barde Shuni, M. Baw, Mijin
Mata, Barde Gero, M. Bala. An yi zave a gaban ‘’yan
malisar hakimi. Bayan zave da kwana biyu, sai wasu suka
tafi Bauci ofishin En’e suka yi qara cewa sub a su yarda da
zaven da aka yi ba. Domin akwai wasu unguwanni biyu ;
unguwar Galadima da unguwar Ciroma suna nesa da cikin
garin Faka, to, sai wasu suka ce Xalladi suke so, wasu
kuma suka ce in dai Xalladi ne, su gwamma su koma bin
littafin Fakuru. Sai En’e suka aiko a nemi Galadima da
Ciroma, tare da dattijai biyu daga unguwar Galadima,
dattijo xaya daga unguwar Ciroma da ke wajen gari. Kuma
daga cikin Faka (unguwar ma’aji) a samu shi ma’aji da
dattawa huxu, duka-duka su goma kenan, sai suka sake
zaven Xanladi ran 19 Mayu 1965. Mutanen da suka yi
zaven sune ; Galadima, sarkin Faka tsoho, Yusufu, Ciroma
Kemo, Wali, Ma’aji, Buba, Liman, M. Isa, Audu.
48- Ran 5 Afrilu 1966 mutanen Yalwa cikin gundumar Ribina
suka zavi M. Tukur ya yi musu sarautar littafinsu. Manyan
garin da suka zave shi su ne; Yari Ganau Yalwa, Alhaji
Gambo, M. Muhammadu, Barde Saleh, M. Yakubu, Alhaji
Isyaku, Dogari, Jahuno, Dindin, Agara. An yi zaven bisa sa
idon ’yan majalisar qasar Lame.
49- Ran 29 Janairu 1967 mutanen gundumar Ribina suka taru
suka zavi Waziri Auta ya yi musu sarautan gundumarsu,
bayan murabus xin sarkinsu. Manyan qasar Ribina da suka
yi zaven su ne Xanrimi, Ma’aji, Waziri, Sarkin Dawaki,
Madaki, Turaki, Wakili, Ciroma. An yi zaven bisa sa idon
Wakilin qasar Ribina da ’yan majalisar qasar Lame.

268
50- Ran 14 Fabrairu 1967 mutanen Unguwar Magaji cikin
gundumar Tama suka zavi Babuwa ya yi musu sarautar
littafinsu. Manyan garin da suka zave shi su ne; Galadiman
Lau, sarkin yaqi, Baraya, Majidaxi, Sarkin noma. An yi
zaven bisa halartan ‘’yan majalisar qasar Lame.
51- Ran 29 Mayu 1967 mutanen Loro cikin gundumar Toro,
suka kawo wa sarkin kudu kukansu cewa suna son a yi
musu sarkinsu Bajari. Asalin mai littafin mutan Loro tsufa
ya kama shi , bay a aiki. To, sai ya damqa littafin a hannun
waikilin Loro, to, sais u bakin jarawa suka ce bas u son aiki
da wakili, don bas u daidaita wad a shi. Kuma a cikin
littafin Su jarawa mutum 45 ne, waxanda bas u ba kuma
mutum 10 ne. nan da nan aka Bauci, aka nemi wakilin
Loro da wasu manya mutum biyu. Bayan an saurari
kokensu aka bas u izinin su yi zave, ran 6 ga Yuni suka
zavi sabon mai littafi, wanda ya sanya wa littafinsa suna
‘littafin Mongol’
52- Ran 17 Yuni 1967 aka xinka sabon littafin Galadima, aka
fitar dashi daga littafin Laro cikin gundumar Toro. Aka ce
akwai wasu jarawa, waxanda su ke kan iyaka, wato Wakili
Azim, M. Jatau da sarkin yara Azuk, suna cikin littafin
Unguwar Fada ne, na littafin Laro, amma jarawa da ke
yamma duka suna cikin littafin Galadima ne, haxe da
sauran gidaje da ke Unguwar Galadima.
53- Ran 28 Yuni 1967 mutanen Tilel Jarawa suka zavi Sarkin
yaqin Tilel ya yi musu sarautar littafinsu, bayan mutuwar
na da tun cikin shekara 1965, sai wakili ke riqe da garin.
Manyan garin da suka zave shi su ne ; Ciroman Tilel,
Galadima, sarkin yamma, Gimba Kaze, Magaji, Mai
unguwa. An yi zaven bisa sa idon ’yan majalisar qasar
Lame, kuma sun tabbatar da ingancinsa.
54- Ran 21 Agusta 1967 mutanen Wa’ere cikin gundumar
Zalau suka zavi M. Zailani ya yi musu sarautar littafinsu.
Manyan gari da suka zave shi su ne ; Galadiman Wa’ere

269
Xanladi, Marafa Bodewa, Sambo, Waziri Sakainu, Ciroma,
Tsoho Wanzami. An yi zaven bisa sa idon wakilan hakimi.
55- Ran 25 Agusta 1967 mutanen Bangwale cikin gundumar
Lame suka taru suka zavi Ciroman Bangwale ya yi musu
sarautan littafinsu. Manyan gari da suka zave shi su ne;
Sarkin noma Bidi, Gandai, Gambo, Baraya, Tahiru. Kuma
’yan majalisar hakimi sun sheda zave ya yi kyau.
56- Ran 31 Oktoba 1967 mutanen Yalwa cikin gundumar Toro
suka zavi M. Tela ya yi musu sarautar littafinsu. Manyan
garin da suka zave shi su ne; Ciroma Dembo, Dillali,
Daudu, Idrisa. An yi a gaban ’yan majalisar qasar Lame
kuma sun inganta shi.
57- Ran 20 Afrilu 1968 mutanen Kuri cikin gundumar Tama
suka taru suka zavi Magaji Adamu ya yi musu sarautar
littafinsu, bayan mutuwar sarkinsu na da. Kuma majalisar
qasar Lame ta amince da zaven.
58- Ran 21 Yuli 1968 Fulanin gundumar Tilde suka zavi Jauro
Gixaxo Na Yola ya yi musu sarautar harxonsu. Manyan
Fulanin da suka zave shi su ne ; Ciroma, Wakili, Madaki
Ila, Siddi. An yi zave bisa sa idon wakilcin ’yan majalisar
qasar Lame.
59- Ran 21 Oktoba 1968 mutanen Wa’ere cikin gundumar
Zalau suka zavi M. Mai Daro ya yi musu sarautar
littafinsu, bayan barin sarautar mai littafinsu na da.
Manyan garin Wa’ere da suka zave shi su ne; Galadiman
Wa’ere Xanladi, Marafa Bodewa, Wakili Sambo,
Ubandoma Xankaka, Waziri Sakainu. An yi zaven bisa sa
idon wakilan majalisar gunduma da ta hakimi.
60- Ran 30 Oktoba 1968 mutanen Bangwale cikin gundumar
Lame suka zavi M. Baba Ibrahim ya yi musu sarautar
littafinsu, bayan tuve386 na da. Manyan garin Bangwale da

386
Asali tun 1964, wasu Gusawa mutum 50 daga Bangwale suka yi qara cewa bas u
sonsa ko da qanqani. Aka turo sarkin Dawakin Bauci, ya haxu da sarkin kudu da

270
suka zave shi su ne; Galadiman Bangwale, Dodo, Bidi,
Mai Unguwa Buya, Kadunga Sanga. An yi zaven bisa sa
idon wakilan majalisar gunduma da ta hakimi.
61- Ran 29 Janairu 1969 mutanen Ruhu cikin gundumar Lame
suka zavi M. Muhammadu Rabo Ruhu ya sarauci
littafinsu. Manyan garin Ruhu da suka zave shi su ne;
Galadima, Liman M. Adamu, Barden baka, Madaki Goje,
Ubandoma, Ciroman Baka, M. Babba. An yi zaven bisa sa
idon wakilan majalisar gunduma da ta hakimi.
62- Ran 20 Fabrairu 1969 mutanen Zingiri cikin gundumar
Rishi suka zavi Majidaxi Zubairu ya sarauci littafinsu. An
yi zaven bisa sa idon wakilan majalisar gunduma da ta
hakimi.
63- Ran 11 Maris 1970 mutanen Kere cikin gundumar Rahama
suka zavi M. Idi ya sarauci littafinsu. An yi zaven bisa sa
idon wakilan majalisar gunduma da ta hakimi.
64- Ran 11 Maris 1969 mutanen Unguwar Waziri cikin
gundumar Tama suka zavi Ubandoma ya sarauci littafinsu.
An yi zaven tsakanin mutum biyu, Ciroma da Ubandoma,
Ubandoma ya samu quri’u 55, a yayin da Ciroma ya samu
quri’u 52. An yi zave bisa sa idon wakilan majalisar
gunduma da ta hakimi.
65- Ran 17 Afrilu 1970 mutanen Taura Babba cikin gundumar
Tama suka zavi M. Jano ya yi musu sarautar littafinsu. An
yi zaven kamar yadda aka saba zaven mai littafi, kuma
majalisar hakimi ta yarda.
66- Ran 15 Mayu 1970 mutanen ’Yola cikin gundumar Tilden
Fulani suka zavi M. Muhammadu ya sarauci littafinsu. An
yi zaven bisa sa idon wakilan majalisar gunduma da ta
hakimi.

sarkin Lame suka sasanta su. cikin shekarar 1966, sai Ciroman Bangwale ya fara
neman a raba Bangwale gida biyu, shi ma a yi masa littafi. Sarkin kudu ya gargaxe
shi ya hana shi. To, cikin shekarar 1968 sai fitintinun Bangwale suka tsananta,
qarshe dai aka dakatar dashi daga sarauta ranar 9 ga Agusta 1968.

271
67- Ran 13 Mayu 1970 mutanen Makana cikin gundumar
Rahama? suka zavi M. Husaini ya sarauci littafinsu. An yi
zaven bisa sa idon wakilan majalisar gunduma da ta
hakimi.
68- Ran 31 Yuni 1970 mutanen Shau cikin gundumar Lame
suka zavi M. Mato ya sarauci littafinsu. An yi zaven bisa
sa idon wakilan majalisar gunduma da ta hakimi. Ran 24
Nuwamba 1970 mutanen Kadaxe cikin gundumar Rahama
suka zavi M. Ibrahim ya yi musu sarautar littafinsu, kuma
majalisar gundumarsu ta yarda da zaven.
69- Ran 2 Nuwamba 1971 mutanen Magajin Kanawa cikin
gundumar Rahama suka zavi M. Mas’udu Dauda xan
wanda ya rasu ya yi musu sarautar littafinsu. Kuma an yi
zave kamar yadda aka saba.
70- Ran 08-01-1972 aka buxe sabon asbitin ‘Dispensary’ a
Sabon garin Tulu. Babban likitan asibitin Bauci, da
Magajin rafin Bauci da jama’a masu yawa suka zo don
buxewa.
71- Ran 19 Yuli 1972 majalisar LA. Central Office Bauchi
suka yarda bisa tilas a raba littafin sarautan Kerawa da
Kuramawa littattafansu daban-daban. Sarkin Kere ya riqe
Kyarawa kaxai, Kuramawa a yi musu na su littafi.
72- Ran 29 Janairu 1972 mutanen Riga cikin gundumar Zalau
suka zavi Marafa Nuhu ya yi musu sarautar littafinsu. Ya
ka da abokin hamayyarsa Ciroma da quri’u biyu. Manyan
gari suka yi zaven bisa sa idon majalisar gunduma.
73- Ran 2 Agusta 1972 aka naxa Xankaka mai littafin
Kuraman Bauci na farko.
74- Ran 30 Mayu 1973 mutanen Chokobon Bauci cikin
gundumar Rahama suka zavi Ciroma ya yi musu sarautar
littafinsu. Kuma majalisar hakimi ta amince da zavensa.
75- Ran 1 Mayu 1974 mutanen Cako cikin gundumar Zalau
suka zavi Marafan Cako ya yi musu sarautar littafinsu.
Kuma majalisar hakimi ta amince da zavensa.

272
76- Ran 25 Oktoba 1974 mutanen Sabon gari cikin gundumar
Tama suka zavi M. Muhammadu Sani ya yi musu sarautar
littafinsu. Kuma majalisar hakimi ta yarda da ingancin
zaven.
77- Ran 17 Nuwamba 1975 majalisar gundumar Zalau da
manyan Arewan Runji suka zavi M. Umaru sabon mai
littafin Arewan Runji, ba tare da hamayya ba. Kuma
majalisar hakimi ta amince da zaven.
78- Ran 26 Nuwamba 1975 mutanen Rishi cikin gundumar
Rishi suka zavi Alhaji Iro ya yi musu sarautar littafinsu na
Rishi Babba. Manyan gari suka zave shi, kuma an yi zave
ba tare da hamayya ba, kuma majalisar hakimi ta yarda da
wannan zave.
79- Ran 5 Satumba 1977 manyan mutanen Gana cikin
gundumar Rishi, cikinsu akwai liman, Galadima, da masu
Unguwanni da mutanen Gana gaba xaya suka zavi Wazirin
Gana ba tare da hamayya ba. Kuma majalisar hakimi ta
sheda kuma ta yarda.
80- Ran 27 Afrilu 1977 mutanen Wa’ere cikin gundumar suka
zavi M. Nuhu ya yi musu sarautar littafinsu. Kuma
majalisar hakimi ta amince da zaven.
81- Ran 1 Mayu 1977 mutanen Matawai cikin gundumar
Rahama suka zavi M. Tanko ya yi musu sarautar littafinsu.
An yi zave ba tare da muhawara ba. Kuma majalisar
hakimi ta amince da zaven.
82- Ran 2 Janairu 1978 mutanen Limoron Bauci cikin
gundumar Rahama suka zavi Ashu ya yi musu sarautar
littafinsu ba tare da hamayya ba. Kuma majalisar hakimi ta
yarda da zaven.
83- Ran 11 Afrilu 1978 mutanen littafin Harxo Bawa suka zavi
M. Sulaimanu Xanladi ya yi musu sarautan littafinsu.
Manyan gari da suka zave shi su ne ;Alhaji Abdu, Musa
Kallamu, Alhaji Abdu Bala, Waziri Harxo, M. Umaru,

273
Sa’adu Mai unguwa, Muhammadu Dandalo. Kuma
majalisar hakimi ta yarda da zaven.
84- Ran 14 Afrilu 1979 aka naxa Nagwaggo Direba sarkin
Hausawan Zalau.
85- Ran 1 Mayu 1979 mutanen Kuraman Bauci cikin
gundumar Rahama suka zavi Bawa Xankaka xan sarkin
day a mutu ya yi musu sarautan littafinsu, bayan mutuwar
sarkinsu na da. Ya ci zave ba tare da hamayya ba, kuma
majalisar hakimi ta yarda da zaven da aka yi.
86- Ran 18 Oktoba 1979 mutanen Tulu cikin gundumar Tama
suka zavi Bunu Adamu qanin sarkin day a mutu ya yi
musu sarautan littafinsu, bayan mutuwar sarkinsu na da.
Ya ci zave ba tare da hamayya ba. Manyan garin da suka
zave shi su ne; Mai Unguwa, M. Xan’azumi Tulu, Ciroma,
Ubandoma, M. Umaru, M. Mato, Alhaji Risku, Mai
Unguwa Juma. Kuma majalisar hakimi ta yarda da zaven
da aka yi.
87- Ran 5 Maris 1980 mutanen Gaferxe-Kulfana cikin
gundumar Zalau suka zavi Galadima Audu ya yi musu
sarautar littafinsu. Kuma majalisar hakimi ta yarda da
zaven.
88- Ran 27 Maris 1980 mutanen Mato cikin gundumar Zalau
suka zavi M. Sale xan sarkin day a mutu ya yi musu
sarautar littafinsu. Kuma majalisar hakimi ta yarda da
zaven.
89- Ran 6 Mayu 1980 mutanen Unguwar Sarkin Noma Dini
cikin gundumar Rahama suka zavi Umaru Haure mai
quri’u 32 ya yi musu sarautar littafinsu. Ya kada abokin
hamayyarsa Wakili Mantuwa mai quri’u 30. Manyan garin
da suka yi zave su ne ; Liman M. Lawal, M. Rabi’u, Mai
Unguwa Xan’azumi, Mai Unguwa Abuga, Mai Unguwa
Daminma, Chaya Samanja, Mai Unguwa Indari, Mai
Unguwa Kisalla, kuma majalisar hakimi ta yarda da zaven.

274
90- Ran 2 Nuwamba 1980 mutanen Gukka cikin gundumar
Lame suka taru suka zavi M. Ciroma Sallau Sulaimanu
mai quri’u 9, ya ka da M. Waziri mai quri’u 5, ya yi musu
sarautar littafinsu. Manyan gari da suka zave shi su ne ;
Galadima Haruna, Madaki Sama’ila, Mai Unguwar Tudun
Wada, Mai Unguwa Mato Gyam, Mai Unguwa Kurmi,
Galadima Mai gero, Mai Unguwa Tsoho Diga, Sarkin
Aska, Sarkin Noma Mato.
91- Ran 24 Nuwamba 1980 mutanen Gurbin –Kawo cikin
gundumar Rahama suka zavi M. Ya’u mai quri’u 84 ya yi
musu sarautar littafinsu. Ya kada abokin hamayyarsa
Yakubumai quri’u 52. Manyan garin da suka yi zave su ne
; Galadima, Waziri, Mai Unguwa Yusufu. Kuma majalisar
hakimi ta yarda da zaven.
92- Ran 23 Satumba 1982 mutanen Dawa cikin gundumar
Zalau suka zavi Alhaji Adamu Juji ya yi musu sarautar
littafinsu.
93- Ran 14 Maris 1983 mutanen Libazu cikin gundumar Rishi
suka zavi Wazirin Libazu ya yi musu sarautar littafinsu.
94- Ran 7 Yuni 1983 mutanen Taura, Unguwar Galadima,
cikin gundumar Rahama suka zavi M. Shu’aibu ya yi
musu sarautar littafinsu, da suka raxa wa suna ‘Littafin
Kayarda.’
95- Ran 21 Nuwamba 1983 mutanen Gau cikin gundumar
Lame suka zavi M. Wada ya yi musu sarautar littafinsu.
96- Ran 20 Nuwamba 1984 mutanen Yadabango cikin
gundumar suka zavi Badagari ya yi musu sarautar
littafinsu. Manyan gari da samari gaba xaya suka taru suka
zave shi.
97- Ran 8 Yuli 1986 mutanen Kuri cikin gundumar Zalau suka
zavi M. Ya’u Marafan Kuri xan sarkin Kuri na da mai
quri’u 19, ya ka da abokin hamayyarsa Voyi mai quri’u
14, ya yi musu sarautar littafinsu. Manyan gari da samari
gaba xaya suka taru suka yi zave. Ran 30 Disamba 1986

275
mutanen Unguwar Ta cikin gundumar Tama suka zavi M.
Abubakar Unguwar Ta ya yi musu sarautar littafinsu.
Manyan gari da samari gaba xaya suka taru suka zave shi
ba tare da hamayya ba.
98- Ran 14 Yuli 1986 fulanin Kaba cikin gundumar Zalau suka
zavi Alhaji Julele ya yi musu sarautar harxonsu. Manyan
Fulani da suka taru suka zave shi su ne ; Alhaji Jauro
Moto, M. Isa, Abdu Waje, Sule, Muhammadu Waliba tare
da hamayya ba.
99- Ran 18 Yuni 1987 mutanen Davave cikin gundumar
Rahama suka zavi Labiru Mato mai quri’u 77 ya yi musu
sarautar littafinsu, ya ka da Muqaddas Mato mai quri’u 40.
Manyan gari da samari gaba xaya suka taru suka zave shi.
100- Ran 26 Afrilu 1987 mutanen Sagere cikin gundumar Lame
suka zavi M. Usman Barde ya yi musu sarautar littafinsu.
Manyan gari da samari gaba xaya suka taru suka zave shi.
101- Ran 10 Maris 1987 mutanen Saya cikin gundumar Zalau
suka zavi Ciroman Saya mai quri’u 73, ya kada Alhaji
Muhammadu Soyawa mai quri’u 51, da Majidaxi 16 ya yi
musu sarautar littafinsu. Manyan gari da samari gaba xaya
suka taru suka zave shi. To, bayan kamar sati guda da yin
zave, sai xan sarkin Saya Alhaji Muhammadu Soyawa ya
rubuta takarda zuwa ga mai gundumar Zalau cewa shi da
jama’arsa ba su yarda da zaven da aka yi ba, saboda wanda
aka zava bay a sallah. Da sarkin Zalau ya sanar da hakimi,
sai hakimi ya rubuta a sanar da shi cewa, bisa qa’idar zave
wanda ya fi yawan quri’u shi ya ci zave, kuma babu
maganar addini a sha’anin sarauta, arne zai shugabanci
musulmi, musulmi zai shugabanci arne. Kuma Yakubu
Gowon ya shugabanci Nijeriya, saboda haka abin da Allah
ya yi a kansa za’a zauna. Kuma dole mutum xaya dai mai
yin wannan satrauta.

276
102- Ran 23 Maris 1987 mutanen Libazu cikin gundumar suka
zavi Maigari Xanrisga ya yi musu sarautar littafinsu.
Manyan gari da samari gaba xaya suka taru suka zave shi.
103- Ran 3 Maris 1987 mutanen Jama’ar Ahmadu cikin
gundumar Tama suka zavi Alhaji Abdulhamidi ya yi musu
sarautar littafinsu. Manyan gari da samari gaba xaya suka
taru suka zave shi ba tare da hamayya ba.
104- Ran 18 Nuwamba 1995 mutanen Gyautawa/ Hayin Bawa
cikin gundumar Rahama suka zavi Muhammadu Rabi’u
xan marigayi sarki Xanladi, ya yi musu sarautar littafinsu.
Masu Unguwanni da suka zave shi su ne; Alhaji Tata
Kwabi, Alhaji Iliya Gyautawa, Waziri Yahaya, Abdu
Ibrahim, M. Mas’udu Muntsira da M. ’Yan biyu.
105- Ran 22 Maris 1990 aka samu rahoton vullar wata qungiyar
addini mai suna ‘Nurul Islam’ daga cikin ‘Jama’atu Nasril
Islam reshen Rishi’ a garin Rishi cikin gundumar Rishi, har
sun samu mabiya (almajirai) 60. Suna karantar da littafin
Qawa’idi ran litinin, Ajami ranar talata da jumma’a,
Tarihin Annabawa ranar laraba, Ahlari da Risala ranar
alhamis, Alqur’ani ranar asabar.
106- Ran 21 Yuni 1946 alqalin Zalau M. Bello ya rubuto cewa
“jiya cikin daren asabar varayi sun shiga cikin Zalau, babu
gidan da ba su shiga ba, kam ban da guda xaya. Har ma a
gidan magatakarda sun xauke littattafan shari’a da rasit,
wata tsohuwa matar Dada xan Maixorawa ta tsinci gindin
rasit xaya a zauren girkin gidansu.
107- Ran Alhamis 20 ga Mayu 1948 sarkin Bauci Yakubu ya zo
Rimin Zayam, ko kafin ya zo gayyato sarkin Yaqi da
sarkin Kudu (Sarkin Jarawa), da masu gundumar Lame,
Zaranda, Tulai, Jama’a da Palama tun ran Laraba don buxe
sabuwar kotu da naxa sabon Alqali a garin Rimin Zayam,
kuma bai kwana ba a ran nan ya gama ya koma. An gina
Majalisar shari’a, adadan masu jiran shari’a, gidan alqali
xakuna 3, zaure 3, gidan magatakarda xakuna 2, zaure 2 a

277
kan kuxi fam talatin da biyu da sule goma sha biyar
(£32:15:00) daidai.
108- A ran 10-08-1950 wani baturen Mishan Mista J.F. Herbert
ya sa harsashin gina makarantar Mishan a Rishi. Nan da
nan mutanen gari suka nuna rashin goyon bayansu. Suka
aikowa sarkin yaqi, shi kuma ya aikawa sarkin Bauci
Yakubu na uku. Ya aiko da umarnin da dakatar da aikin.
Mutanen suka ce su makarantar Elementare su ke so. Sai
gwamnati ta gina musu ita aka buxe a 1952.
109- A ran 14-11-1952 wata qungiyar ’yan Mishan mai suna
‘Sudan Interior Mission’ qarqashin Mista B.N Dorth ta
aiko da takardar neman izinin gina coci a Rinjin Gaini.
Wani mutum wais hi Auta ya bad a filin gonarsa, kuma
sarkin yamma, wato sarkin Rinjin Gaini ya yarda. Suka
nemi idan sarkin yaqi ya yarda, to, ya rubutawa Di’o
takardar nuna yarda, shi kuma ya qi.
110- Ran 3 Janairu 1961 aka yi wa qabilun qasar Lame wakilci
a kotun lardi kamar haka ; Xankaka yana wakiltan Kurama,
Goje Damina yana wakiltan Ribinawa, Bujiyal da Loro.
Barayan Gyam yana wakiltar Gyamawa, Ciroma Binkilbe
yana wakiltar Sangawa, Gusawa da Limoro. Ciroma Dawa
yana wakiltar Gurawa.
111- Ran 29-05-1961 da daddare aka yi faxa a Makana, cikin
gundumar Rahama. Xan salanke da qaninsa sun yi wa wani
mai suna Audu duka, suka farfasa masa kai, suka gudu
suka barshi a kwance cikin jini, suna tsammani ya mutu.
Alqali ya sa xan doka ya kama mutum ashirin da biyu,
waxanda aka yi faxan a jikin gidajensu ba su kawo
gudummawa ba sadda Audu ke kururuwan neman taimako.
Ya ce ko dai su kamo Xan salanke, ko kuwa ya ci su tarar
fam tara-tara.
112- Ran 02-12-1963 sarkin Tama da mutanensa suka yi qaura
daga Tama, suka koma bakin kasuwar Tulu, suka gina

278
gidaje a vangaren gabas maso kudu da kasuwan Tulu, kan
hanyan zuwa Taura.
113- Ran 12-04-1964 aka samu rahoton vullar annobar baqon
dauro, a gundumar Zalau. A Rinjin –Gura kaxai mutum 12
ne suka mutu, mutum 15, suna kwance.
114- Ran 30-03-1964 motar nuna majigi ta fara zuwa Rishi don
nuna majigin wayar da kan jama’a. Kuma ta je Zaranda ran
03-11-1964, kana ta wuce zuwa Gumau ta nuna majigin
ran 06-11-1965 in da jama’a ta taru danqam don kallo.
115- Ran 14 Agusta 1964 aka samu rahoton ta’adin kuraye a
gundumar Ribina, har ma ana tsoron fulanin da ke zaune a
Varga, Gwaskayi da Xanbaqo za su iya tashi su bar
wajajen idan hukuma bat a xauki matakin gaggawa ba.
116- A ran 10-10-1964 aka samu rahoton yawan tashin gobara a
gundumar Ribina a garuruwa daban-daban, yau in ta tashi a
wannan qauye gobe ta tashi a wancan qauyen a jejjere,
kuma kowacce tana ta’adi sosai, garuruwan su ne
Gwalfada, Zigau, Bakin kasuwar Ganye da sauransu. ’Yan
doka sun bincika an samu wani tsohon varawo wai shi
Qwai ke cinnawa.
117- Ran 18-05-1964 turawan suka sayi gonakin mutanen
Wa’ere dab akin rafi, inda za su yi aikin kuza akan kuxi
fam xari uku (£300:00:00).
118- Ran 19-07-1965 baturen kamfanin tonon kuza da ke
barikin yalwan Rishi ya nemi izinin sarkin kudu Salmanu
da En’e ta Bauci, akan shi da shugabannin barikokin kuzan
na wannan yanki, suna son su sabunta ginin gadar Maigari
Sanga, yadda ba za ta sake lalacewa ba.
119- Ran 01-07-1966 wasu ’yan mata da shekarunsu na haihuwa
bai wuce sha tara tara ba. ’Yar gidan Alhaji Namayango da
’yar gidan Amina, suka yi faxa, a kasuwa, ’yar gidan
Namiyango ta bugi ’yar gidan Amina da kujera a kayi. Ta
yi jinya kwana 18, kana ta mutu.

279
120- A cikin watan Oktoba 1966 aka samu rahoton vullar wata
annoba da ba’a san irinta ba, ta bushewan gonakin dawa a
garin Riga ta gundumar Zalau. Wurin da ake samun dami
300 da qyar aka samu dami 50.
121- Ran 30-4-1967Allah ya yi wa wani Xandoka Dan goma
Fobur rasuwa a Tulu.
122- Ran talata 21-05-1968 Allah ya yi wa Harxon Fulanin
Tilden Fulani Harxo Yako rasuwa a gundumar Tilden
Fulani
123- A ran 26-03-1969 ruwa ya ci Gwanki Bafulatani, a
gundumar Zalau. Yadda abin ya faru kuwa, shi Gwanki
yana da ’ya Maimunah, tana da goyo, sai ta sayo xan
kunne, tana sa wa ’yar. To, shi sai ya ji yarinya tana kuka.
Sai ya yi wa Maimunah tsawa, amma’ya bat a daina kuka
ba. Sai ya taso da fushi zai bug eta, sai ta tashi ta faxa wata
tabga. A lokacin kuma akwai xansa yana bin shanu, sai y
ace ya faxa ya fiddo ta. To, sai ya ga nawan xan, shi ma sai
ya faxa. Sadda xan ke fiddo ta sai ya ga uban na nutsewa.
Sai ya sake faxawa, ko kafin ya ciro shi rai ya yi halinsa.
124- Ran 28-11-1969 aka yi shelar cewa jirgin sama mai yin
safiyo, zai zo kusa-kusa da qasa, don kada mutane su ji
tsoro.
125- Ran 11 Afrilu 1970 Allah ya yi wa sarkin Zalau M.
Ibrahim rasuwa.
126- Ran 06-05-1970 aka samu rahoton vullar annobar qudan
tsando a gundumar Lame da Tama, har Fulani na tashi da
shanunsu.
127- Ran 12-06-1970 aka wasu giwaye bakwai da’ya’yansu
biyu suka vulla a karkarar gundumar Tama, suka yi ta
cinye kunyaryakin doyar mutane.
128- Ran 16 Yuni 1970 aka raba littafin Tilde gida biyu, wato
littafin Hausawa daban, na Fulani daban, bayan wani
dogon rikici da aka daxe ana yi tsakanin mai gundumar
Tilde Abubakar da xan’uwansa Shakuwari, kuma domin a

280
samu sauqin aiki a garin, tun a da dukkan garin yana
hannun mai gunduma ne, saboda haka aikinsu ba ya sauri.
Kuma an ga bai kamata mai gunduma ta riqe aikin mai
littafi ba. An yi zaven raba gardama an samu mai unguwar
Hausawa yana da mutane 191 masu biyan haraji. Mai
unguwar Fulani kuma yana da mutane 92 masu biyan
haraji.
129- Ran 19-06-1970 hukuma ta maid a jejin Lame gandun daji,
tamkar Yankari. Nan da nan kuma aka haramtawa mutane
da ke kewayen jejin yin abubuwan dad a aka yardar musu,
kamar yin ciyawar jinka, itacen girki, shan zuma, xiban
’ya’yan itatuwa masu amfani, kamar xorawa, tsamiya,
kanya, kaxanya da sauransu. Qauykan da ke kewaye da
dajin Lame su ne ; Jangu, Yuga, Fukki, Dulumin Have,
Mundu, Jange, Lame, Toji, Shim, Shifa, Ruhu da Jira.
130- Ran 22-06-1970 aka aiko daga Bauci cewa ana buqatar
waxannan namun daji da ransu, don a saya ; vauna,
damisa, kura, gwanki, kwanta-rafi, gwambaza, mariya,
tunkun juda, batsiya, gada da barewa. Maharba suka yi ta
samun kuxi.
131- Ran 27-06-1970 a Lame aka samu vullar annobar wasu
giwaye masu ta’adi, da aka ce wai an koro su ne daga qasar
Kano, giwayen su takwas ne, kuma har xaya daga cikinsu
ta haihu a wurin. Bayan korarsu daga qasar Lame, sai suka
vulla dajin Tama, sai da aka yi gayyar maharba da makaxa
san nan aka kore su.
132- Ran 24-08-1970 Allah ya yi wa wata yarinya mai shekaru
12 rasuwa a ruwa a Ribina. Sun zo za su tsallake rafi da
mahaifiyarta, sai suka tarar babu ruwa sosai. Sai uwar ta
riqo hannunta suka shiga. Da shigarsu sai ruwa ya raba su
da uwan. An yi nema, an yi nema ba’a ganta ba.
133- Ran laraba 24-11-1971 aka yi wa wani Inyamiri mai suna
K.E. Abu Williams wata gagarumar sata a Rishi. An xauke

281
masa kuxi fam xari da ashirin (£120:00:00) da radiyon fam
goma (£10:00:00).
134- Ran talata 9 Nuwamba 1971 (daidai da 21 Ramadan 1393)
Allah ya yi wa sarkin Tama M. Muhammadu rasuwa.
135- Ran 30-11-1972 wasu giwaye guda uku suka vulla a Zuku
ta gundumar Rishi, sun cinye dawa ta fi dami sittin. Doya
kuwa kunya-kunya su ke bi suna tonewa. Mutane sun taru
domin su kore su, duk da haka bas u gudu ba, kuma bas u
tsoron jama’a.
136- Ran 19-04-1975 giwaye uku da vauna suka vulla tsakanin
Shibi da Guraka da ke gundumar Tama, suka ta ta’adi a
gonar rogo, kuma suna koran mutane masu sharer gona har
cikin gidajensu.
137- A cikin watan Agusta na shekarar 1976 aka yi tsadar dawa
a qasar Bauci, har said a sarkin Bauci ya aiko neman dawa
a kasuwannin qasar Lame akan kowanne buhu N26, amma
bat a samuwa. Irin tsadar da ba’a tava gani ba. Da
gwamnati ta ga al’amari ya shaddada sai ta qayyade kuxin
dawa akan N12 akan kowanne buhu, kuma ta buxe
rumbunta, aka aiko da dawa buhu ashirin daga Bauci ana
sayarwa talakawa mai kwano xaya, mai kwano biyu akan
kwabo sha biyar –biyar.
138- A wannan shekara ta 1976 dai aka kuma samun vullar
annobar wasu tsuntsaye ana kiransu ‘Jira’ suna tafiya
garke-garke, idan sun sauka a fagen acca, sai su cinye ta
gaba xaya. Da suka gama da gonakin acca sai suka koma
gonakin dawa.
139- A cikin watan Janairun shekarar 1976 aka yi zaven
sarauniyar kyau a Rishi wanda qungiyar Red Cross ke
shiryawa duk shekara a garuruwa daban-daban, duk mai
son shiga said a ya biya kuxin rasit kwabo 20 da su
qungiyar ke sayarwa. Ba’a samu waxanda suka shiga
takarar ba sai karuwai, wacce ta yin a xaya da na biyu daga
Rishi, wacce ta yin a uku daga Sabon gari.

282
140- A cikin watan Fabrairun 1979 mutanen Faka cikin
gundumar Lame suka gamu da wata masifa, a dalilin kama
wani gwaggo da suka yi suka kasha shi, saboda yana musu
varna, kuma yana kasha musu tumaki, da masu aikin daji
suka samu labari, suka kama mutanen garin masu yawa,
suka yi ta dukansu, suka sa su a mota zuwa Nabardo, alqali
ya yi musu tarar N160.
141- Ran 29-09-1979 wasu giwaye suka vulla a Sabon garin
Tulu suka yi ta cin amfanin gona.
142- Ran 01-05-1980 aka samu rahoton vullar fari a yankin
Baradawo zuwa Jira, da ke gundumar Lame. Suna cinye
ganyen bishiya baki xaya, duk bishiyar da suka sauka a
kanta, sai itacen ya karye.
143- A cikin watan Fabrairun 1980 aka sabunta ginin asibitin
Rishi, kuma aka ciyar da shi gaba ya zama ‘Health Centre’
144- Ranar 29-09-1980 mutanen Riga da ke gundumar Zalau
suka kawo koken a taimaka yaransu su koma zuwa
makarantar Zalau maimakon ta Dawa saboda tsoron zaki a
tsakaninsu da Dawa.
145- Ran 14-03-1982 wani bafulatani mai suna Ja’o ya kashe
zaki a Lame. Zakin ya kasha masa shanu tara bara, bana
kuma ya kasha bakwai.
146- A ran 03-04-1982 aka zaki ya kashe shanu tara a rugar
wani bafulatani mai suna Jarma a qauyen Jange cikin
gundumar Lame.
147- Ran 26-04-1982 aka ga wani abin mamaki a garin Tulu ta
gundumar Tama in da wasu karnuka suka kasha tumaki
wajen 100.
148- Ran 22 Fabrairu 1989 aka samu rahoto daga sarkin Lame
cewa, zaki ya kasha yaru a Ruhu. Zakin har cikin xaki ya
kutsa kai ya kasha shi, kuma ya kasha dabbobi masu yawa.
149- Ran 28 Yuli 1989 Alhaji Wada Wayo Rishi ya ba da aron
gidansa na shekara biyu, don buxe kotun shari’a ta farko a
Rishi. Waxanda suka tsayin daka don samuwar wannan

283
kotu su ne; magajin Rishi, Tarkunyan Rahama, Alhaji
Saleh Mai allo, Alhaji Sabo Rishi, Alhaji Itatu da Tanko
Rahama.
150- Ran 25 Satumba 1989 ’yan sanda suka kama sarkin
kasuwan Rishi Xahiru Abdu, xan tsohon sarkin kasuwa
Sarki Xanjatau, kuma sun yi binciken gidansa, saboda
samunsa da bindigar sata tare da harsashai 40.
151- Ran 27-08-1994 shugaban qaramar hukumar Toro ya bai
wa Ya’u Garba da Alhaji Voyi kwangilar gina sabon gidan
sarautar mai gundumar Zalau
152- Ran litinin 09-01-1995 wasu varayi suka kashe wani
bafulatani mai suna Bammi, suka rufe gawarsa da ciyawa,
kuma suka kwashe shanunsa guda arba’in suka gudu da su,
a Tama. Nan da nan sarkin Tama ya aika da rahoto ko’ina,
kuma aka baza maharba da ’yan banga suka shiga cikin
daji, ran 17-01-1995 aka samu rahoton an kama Alhaji
Oria garin Marke ta qasar Ningi da shanu ya nufi Gadar-
maiwa.
153- Ran 26-05-1995 wani rikici ya tahsi a garin Zalau tsakanin
Gurawa da wani bakano mai sai da shayi mai suna
Xantala.387 Gurawa suka bubbuge gidan Xantala da
shagonsa, da tagogin ofishin ’yan sanda, da qofar gidan
sarki, kuma suka tsaga wuyar rigan Adamu, dogarin sarkin
Zalau. Asalin faxan ya ya fara ne da Adamu xan gidan
sarkin Saya, da shi Xantala, inda shi Adamu ya ce wa
Xantala ubansa ya yi mutuwar tsiya. Shi kuma Xantala ya
ce masa, “Ai kai ma ubanka kafiri ne, don yana hawa
dutse.” Shi kenan sai faxa ya zama na Gurawa baki xaya.
Suka tasamma Xantala za su kasha shi, sai ’yansandan
Zalau suka tsare shi a Caji-Ofis, Gurawa suka ce idan ba’a
fito dashi an bas u shi ba za su qona caji-ofis xin. Sai suka
maid a shi caji-ofis na Gumau. Washegari aka kais hi kotu,

387
Ya rasu a Gumau a shekarar 2020 a dalilin ciwon sukari da ya yi fama da shi.

284
suka tura shi umara na sati biyu, kwana xaya da tafiyarsa,
sai aka yi belinsa. Nan da nan sai Gurawa suka yi taro a
gidan Alhaji Bala Babban –Gura, bakinsu ya haxu akan su
kasha shi. To, dab a su same shi a gida ba, shi ne suka
abinda suka yi.
154- Ran 24 Agusta 1994 aka ba da kwangilar gina asibitin
haihuwa (mataniti) a Saminakan Gwa.
155- Ran 31 Yuli 1995 da misalin qarfe biyar na yamma, aka yi
wata tsawa wacce ta faxa rugar Muhammadu Rabi’u cikin
gundumar Zalau ta kashe shanu goma sha xaya, duk suka
yi mushe.
156- Ran 12-12-1995 Allah ya yi wa wani Inyamuri wanda ya
buxe Kemis a unguwar Maji rasuwa a asibitin Saminaka,
kuma ba’a samu wani xan’uwansa ba, sauran inyamuran
da suke garin kuma sun ce shi ba xan’uwansu ba ne, abin
da ya yi ta bai wa mutane mamaki.

285
LITTATTAFA DA AKA YI NAZARI CIKINSU

1- Muhammad bin Muhammad Makhluf : Shajaratun nûruz


zakiyyah fî xabaqãtil mãlikiyyah
2- Alhaji Abubakar Dokaji : Kano Ta Dabo Cigari
3- Sarkin Musulmi Muhammad Ballo bin Shaikh Usman bin
Fodiyo : Infãqul maisûr fî tãrikh bilãdit tukrur
4- JAHUN, Ibrahim Sa’id : The roles & the challenges of
traditional rulers in land conflict resolution & management in
Nigeria : A case study of Bauchi State, Nigeria.
5- R.M. East : Hausawa Da Maqwabtansu
6- Z.O. Apata (Department of History University of Ilorin) :
Lugard & The Creation Of Provincial Administration In
Northern Nigeria 1900-1918
7- Tukur Muhammad Mukhtar (Department of History
Xanfodiyo University Sokoto- Nigeria) : Colonialism &
Mazãlîm Court System In Sokoto Province 1903-1960
8- Enyi John Egbe, Ph.D (Department of political science, Benue
State University, Makurxi -Nigeria) : Native Authorities &
Local Government Reforms In Nigeria Since 1914
9- Muhammad bin Abdulkarim Almaghîlî Attilmisãni: Tãjuddin
fî mã yajibu alal mulûki wassalãxîn

286

You might also like