You are on page 1of 2

ASHE DAN AREWA ZAI IYA MANTA WANCAN LOKACIN?

Lokacin da aka bindige Janar Mamman Shuwa na jihar Borno

Lokacin da aka kaiwa Sheikh Sani Yahya Jingir hari da bomb a wajen tafsir a birnin Jos

Lokacin da aka kashe manyan Malaman addinin Musulunci a Borno da sauran garuruwa

Lokacin da Musulmai suke dena shirya duk wani taro na yada addinin Musulunci da zuwa da'awar don
musuluntar da maguzawa

Lokacin da duk wata tsangayar koyon Qur'ani da tayi shekaru daruruwa sai da aka rufeta a birnin
Maiduguri

Lokacin da aka tashi bomb a Masallacin Sarkin Kano na lokacin Malam Muhammadu Sunusi II

Lokacin da tsaron yafi na yanzu muni har aka kaiwa babban sufeta janar na 'yan sandan Nigeria dan
arewa hari a cikin tawagar shi

Lokacin da tsohon shugaban kungiyar mabiya addinin nasara Ayo Oritse Jafor yake abinda yaga dama da
jirgin shugaban kasa, har a Kasar South-Africa an taba kamashi da Jirgi ya siyo makamai alhali shi ba
Jami'in tsaro ba

Lokacin da akayi harin bomb na farko da ya faru a Nigeria wanda tsagerun Niger Delta wato MEND
karkashin jagorancin Henry Okah suka kaddamar a Abuja a gurin bikin murnan Nigeria shekaru 50 da
samun 'yan cin kai, Jonathan ya ya fito ya karesu, sukace sune sukayi harin

Lokacin da gwamnonin Plateau da 'yan uwansu Birom suke cin naman mutane Musulmai a Masallacin idi
a Jos

Lokacin da a jihar kaduna mafi yawan 'yan jihar Musulmai ne sun zama second class citizens wato
kaskantattu, daga abu ya faru a tare hanya ayi ta shan jinin mutane Musulmai kafin Allah Ya kifar da
Patrick Yakowa a jirgi aka samu sauki

Lokacin da tsohon mai bawa shugaban kasa shawara a kan tsaro Janar Andrew Azazi yace masu tsara
ta'addanci ana shan shayi dasu a fadar shugaban kasa Jonathan, kwana uku da fadin haka Jonathan ya
tsiio agaji ba

A lokacin da sata a gurin maciya amanar Nigeria ba laifi bane

A lokacin da basu fara yaki da Boko Haram ba da gaske sai bayan da suka dage zaben 2015 na tsawon
sati shida, sannan suka maida hankali wajen yaki da Boko Haram don su yaudari talakawan Arewa da ake
kashewa a lokacin
A lokacin da suka turo karnukan farautarsu 'yan Boko Haram suka shigo har cikin garin Gombe suka ajiye
mana sakon takarda cewa kada mu kuskura mu fita rumfar zabe don basa son a zabi shugaba
Muhammadu Buhari

A lokacin da tsohon gwamnan Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya kama wani Jirgi makare da
Makamai a Kano, amma tsohon shugaban kasa Jonathan ya sa aka sake jirgin

A lokacin da shingen duba ababen hawa na jami'an tsaro ya yawaita, amma sun zama na banza saboda
Boko Haram suna wucewa tare da zugarsu su je duk inda suka ga dama

A lokacin da sai mun sauka daga kan mashin kafin mu wuce gurin duba ababen hawa na jami'an tsaro

A lokacinda tafiya awa daya ta koma awa biyar saboda bala'in duba ababen hawa

A lokacin da ake shiga dakunan matan aure na sunnah wai ana lalubar bomb har karkashin gado

A lokacin da Musulmai suka dena ajiye gemu da bayyana da siffa irin na musulmi saboda kar su siffantu
da Boko Haram, sai da aka koma shiga irin ta arna

Lokacin da idan aka zo daukan aiki sai an fifita 'yan kudu kafin 'yan Arewa, ba ma za ka san an dauka ba

Akwai Ma'aikatun da dan Arewa bai isa ya leka ba balle a ce ya samu aiki a wurin, misali sai da shugaba
Buhari ya zo aka ta6a samun 'dan arewa da ya taba rike hukumar NITDA ya shugabantar da Dr Isa Ali
Pantami da yawan 'yan Arewa ba san da wata hukuma da ake kira NITDA ba, sai da Baba Buhari ya
dauko Malam Isah Ali Pantami daga Saudi Arabia ya danka masa.

Yau Allah Ya kawo mana saukin wadannan masifa sun gushe ta sanadin shugaba Buhari, amma an
manta, wai har ana cewa gwanda Allah Ya mayar damu lokacin Jonathan, akwai wadanda na ga suna
cewa Jonathan kayi hakuri ka dawo Buhari ya ishe mu, hakika wannan butulci ne wa ni'imar Allah

Muna rokon Allah Ya karemu daga butulcewa ni'imarSa, Ya taimaka wa shugaba Buhari, Ya magance
mana dukkan matsala dake faruwa a Kasar Amin

You might also like