You are on page 1of 15

(1) ILIMIN DARIKAR TIJJANIYA (Kashi na daya)

**

***

A'uzu billahi minash-shaɗanir rajim

Bismillahir Rahmanir Raheem

Nayi wannan rubutu ne dan yan'uwa su san Darikar Tijjaniya da abinda ta qunsa dan su fahimci abinda
suke yi ba abun wasa bane.

1. WAYE SUFI?

Mutum ne musulmi Mumini Wanda Babu Abinda Yake Bukata A Duniya Sai Yardar Allah Da Neman
Kusanci Da Manzon Allah SAW. Haka Kuma Baya Kwadayin Aljanna Ko Kuma Tsoron Jahannama, Yana
Ibada Ne Dan Godiya Ga Allah Bisa Ni’imominsa Gareshi. Sufi Waliyyi Ne, Amma Ba Dukkan Waliyyi Bane
Sufi.

2. MENENE SUFANTAKA?

Shine “Aikata Dukkan Abinda Allah Yakeso A Yadda Yakeso Ba Yadda Kakeso Ba, Da Barin Dukkan Abinda
Allah Bayaso Koda Kai Kanaso Tareda Kyautata Zato Ga Allah Da Halittunsa.

3. MENENE DARIQUN SUFAYE?

Farko ƊARIQA Kalma ce Wacce Take Nufin “HANYA” Ko “TAFARKI” A Harshen larabci.

Darika a musulunci yana nufin tafarkin da za a bi dan Samun Kusanci da Allah da yardarsa cikin sauqi bisa
qamun qafa da waliyan Allah.

Allah S.W.T shi yayi umurni garemu akan mubi tafarkin Sufaye inda yake cewa “Wattabi’i Sabila Man
Anaba Ilayya” Wato Kubi Tafarkin Wanda Zai Taho Gareni.
Darikun Sufaye guda 313 Yana Da Tushe A Musulunci Kuma Hanyace Ta Samun Shiga Aljanna A Saukake.
Annabi SAW Yace “Lallai Shari’ata (musulunci) Tazo Ne Bisa Dariku Guda 313, Duk Wanda Yayi Riko Da
Ita (daya daga ciki) Ubangiji Zai Shigar Dashi Aljanna” (Dabarani ya ruwaito hadisin).

4. DARIKAR TIJJANIYA

Tijjaniya itace ɗarika ta qarshe a jerin Ɗariku guda 313 ɗin nan kuma Wanda Allah yaba ragamarta shine
Sidi Ahmad bin Muhammad Attijaniy RTA. Cikakken Sharifi, shugaban waliyan Allah baki daya daga
farkon duniya zuwa qarshe. Kuma shine cikamakin su baki daya. Annabi SAW ne ya bashi komai na
darikar tijjaniya ido da ido ba a bacci ba.

5. ABINDA TA QUNSA DA HUJJOJI

Shehu Ibrahim RTA Yana Cewa: “Darikace Mai Tsantsar Falala Da Samun Yardar Allah Wanda Aka Gina
Bisa Sunnar Annabi S.A.W Da Kur’ani”.

Darikar Tijjaniya Babu Komai A Cikinta Sai Abubuwa Guda Uku Kamar Haka:

A. ISTIGFARI: Allah Yana Cewa “Kayi Tasbihi Ka Godewa Allah Ka Nemi Gafararsa Lallai Shi Allah Mai
Karbar Tuba Ne” (Suratun Nasri Aya Na 3). Duk Da Kasancewar Annabi SAW Wanda Baya Laifi Amma A
Kullum Shima Yana Istigfari Sau 70 Inji Abu Huraira RA.

B. SALATIN ANNABI: Allah Yana Cewa “Lallai Allah Da Mala’ikunsa Suna Salati Ga Annabi SAW, Ya Ku
Wayanda Kukayi Imani Kuyi Salati A Gareshi Da Aminci” (suratul ahzab aya na 56). Annabi SAW Yace
“Mutanen Da Suka Fi Kowa A Wurina Sune Mutanen Da Suka Fi Yi Min Salati” tirmizi ya ruwaito shi.

C. LA ILAHA ILLALLAHU: Allah Yana Cewa “Ku Ambace Ni Zan Ambace Ku, Ku Gode Min Kar Ku Kafurce
Min” Sannan Annabi SAW Yace “Mafificin Kalma Shine La Ilaha Illallahu”.

6. AYYUKANTA DA HUJJOJI
A. LAZUMIN SAFE DA YAMMA: Allah yana cewa “Kuma Ka Ambaci Ubangijinka Cikin Ranka Kana Mai
Kaskantar Da Kai Da Nuna Tsoro Kuma Kana Mai Kas-Kas Da Murya Bada Karfi Ba, Safe Da Yamma Kada
Ka Zama Mai Gafala” (Suratul A’araf Aya Na 205)

B. WAZIFA: Itace Hilakuz-Zikiri Wato Da’irar Zikiri. Anas RA Ya Ruwaito Cewa Annabi SAW Yace “Idan
Kuka Zo Dausayin Aljanna Ku Tsaya Kuyi Kiwo A Ciki, Aka Tambaye Shi Ina Ne Dausayin Aljanna? Sai Yace
Da’irar Zikiri” (tirmizi)

C. ZIKIRIN JUMA’A: Allah yana cewa “Sannan In Kuka Idar Da Sallah Sai Ku Watsu A Kasa Kuna Masu
Nema Daga Falalar Allah Sannan Ku Ambaci Allah Ambato Mai Yawa Sai Ku Iya Tsira” (Suratul Juma’ati
Aya Na 10.

Anan zan tsaya Insha Allah sai a gaba zamu kawo Sharuddan shiga darikar Tijjaniya da sauransu Insha
Allah.

️DAGA TASKAR NAZIRIYYA SIRRIN YABO FOUNDATION ️

Don NEMAN QARIN BAYANI 🤝🤝🤝

07018171482

Please faward this

‫الدال على الخير‬........


(2) ILIMIN TIJJANIYA (kashi na biyu)

**

***

QA'IDOJIN DARIKAR TIJJANIYA

***

A'udhu Billahi minash-shaɗanir rajim

Bismillahir Rahmanir Rahim

Wa sallallahu alal fatihil khatimil Nasiril Hadiy wa alihi wa sahabihi haqqa qadrihi wa miqadarihil Azim.

7. QA'IDAR SHIGA DARIKA

Wayannan sune qa'idojin da suke wajibi ne mutum ya aminta dasu kafin ayi masa iznin shiga Ɗarikar
Tijjaniya.

A. BA A DAINAWA IN AKA KARƁA.

Ma'ana in ka karɓa babu ranar da zakace kai ka gaji ko ka fasa dan haka ba zakayi lazumin da wazifar da
zikirin juma'ar ba. Ba a gajiya, ba a fasawa ba a dainawa domin Alqawari ne. Alqawari kuwa abin
tambaya ne kuma saɓata suffar munafukai ne.

B. BA A HAƊA TIJJANIYA DA WATA ƊARIKAR.

Wato kamar yadda naga wasu suna yi sai suce su QADIRAWA ne kuma TIJJANAWA ne. A'a sam ba a haɗa
ta da wata ɗarikar. Shehu Tijjani a lokacin da Annabi SAW zai bashi wannan darikar, yana riqe da dariku
kusan 40 akace amma Annabi SAW yace duk ya ajiye su ya riqi wannan shi kaɗai. Annabi yace masa NINE
SHEHINKA NINE MAI YI MAKA MADADI.
C. BA A ZIYARTAR WANI WALIYYI WANDA BA BATIJJANE BANE DAN NEMAN ALBARKA

Misali kaji ance waliyin Darika kaza yazo gari ko A'a Qabarinsa na wuri kaza bari kuje neman albarkarsa,
A'a haka haramun ne. Amma kana iya zumunci da yan'uwanka wayanda suke wata darikar.

HUKUNCI

Duk wanda ya aikata daya daga cikin sharudda guda uku ɗin nan, ya yanke alaqarsa da tijjaniya sai in har
ya sake komawa wurin muqaddami an sake yi masa izni.

8. QA'IDOJIN DAKE INGANTA AIKIN DARIKA

Bayan ka karbi darika ka kiyaye sharuddan karbarta, toh lazumi da wazifa da zikirin juma'a akwai
sharudda guda biyar akan su kamar haka

A. Niyya: dole kayi niyya yayin da zakayi lazumi ko wazifa ko zikirin juma'a.

B. Tsarkin Jiki: tsarkake jiki daga fitsari da bayan gida da maniyyi da sauransu

C. Tsarkin Tufafi: sanya tufafi masu tsarki ba wayanda shari'a ta haramta ba

D. Suturta Al'aura: Ba a yarda Batijjane ko Batijjaniya suyi lazumi ko wazifa ko zikirin juma'a da tsiraici a
waje ba, dole namiji ya rufe cibiyarsa zuwa gwiwar sa, mace ta rufe dukkan jikin ta sai kawai hannayenta
da sawayenta da fuska.

E. Rashin magana: yayin da kake lazumi ko wazifa ko zikirin juma'a, ba a son kayi magana da kowa sai dai
in da larura waccw shari'a ta yarda da ita.

HUKUNCI

Duk wanda yayi watsi da ɗaya daga cikin sharuddan nan toh lazumin sa ko wazifarsa ko zikirin juma'ar sa
ta lalace. Wajibi ne kuma ya sake yin su cikin kiyaye wayancan sharuddan.
9. QA'IDOJIN DAKE CIKA AIKIN BATIJJANE

Idan ka kiyaye sharuɗɗa biyar din can na baya da suke iya rusa aikin ka, toh ga wasu masu ɗumbin yawa
wayanda zasu sanya aikin naka ya zama karɓaɓɓe har ka samu abubuwan da ake samu na riba. Daga ciki
akwai:

A. Fuskantar Alqibla yayin da zakayi lazumi (ko wazifa da zikirin juma'a in kai kaɗai ne ba a jam'i ba).

B. Zama irin na tahiya yayin wuridi. Wato zama da gefen ka na hagu ba zaman harɗe (zaman sarakuna)
ba.

C. Da kiyaye salloli biyar cikin jam'i

D. Da biyayya ga iyaye da miji (ga matar aure)

E. Da aikata mai kyau da barin mara kyau

F. Da dawwama cikin son Shehu Tijjani so mai tsanani da son yan'uwanka tijjanawa.

G. Da yawan nasiha ga yan'uwa

H. Da hadarto surar Annabi SAW ko Shehu Tijjani ko shehinka yayin da kake wuridin tijjaniya.

I. Da kakkabe duniya da abinda ke cikinta daga zuciyar ka yayin da kake wuridin tijjaniya.

J. Da fahimtar ma'anar abinda kake fadi yayin wuridi.

Da sauransu...
QARIN BAYANI

1. Sharuɗɗa uku na farko su kaɗai suke iya fitar da mutum daga tijjaniya ba wani abu ba. Ballantana wani
yayi maka barazana yace zai qwace darikar daga gareka in bakayi masa kaza da kaza ba. Saidai akwai
manyan waliyai a cikin tijjaniya wayanda in ka taɓa su, tamkar ka taɓa Shehu Tijjani ne, taɓa Shehu
Tijjani kuwa, yanke alaqa ne da tijjaniya. Wannan shi ake kira SALBU.

Watarana Shehu Dahiru Bauchi RTA yaje ziyara wurin Shehu Gibrima. Da ya juya zai wuce sai Shehu
Gibrima yake cewa mutanen wurin, kunga wannan yaron? Nan gaba za a yiwa manyan shehunnai SALBU
in suka taɓa shi.

Haka zalika Shan taba, Zina, ca-ca da sauran laifuka basa fitar da mutum daga tijjaniya amma babu kyau
Batijjane ya aikata su.

2. Sharuɗɗa na biyu kuma su lalata aikin Batijjane suke yi.

3. Na uku kuma rashin aikata su baya lalata aikin Batijjane amma yana rage masa tibar aikin.

IN KAGA SUNNA A YAU HASKENTA NA ZAHRA, ZIKIRI SALATI SUNA JERANTUWA KU JIYA

TALLAHI KA GANSU SUNE SUNKA RAYA WAJEN, BAYAN MACEWASSA SHEKARU TILI KU BIYA

DAGA TASKAR NAZIRIYYA SIRRIN YABO FOUNDATION 🤝

️0000. Baba njawai ️

DON NEMAN QARIN BAYANI


07018171482

(4) ILIMIN ƊARIKAR TIJJANIYA

(kashi na huɗu)

**

***

HUKUNCE HUKUNCEN LAZUMI DA WAZIFA DA ZIKIRIN JUMA'A DA SAURANSU

****

1. HUKUNCIN DA SUKA RATAYA AKAN LAZUMI KAWAI SUNE:

a. RASHIN DAGA MURYA: A Lazumi Ba Aso Mutum Ya Daga Muryarsa Amma Zai Motsa Harshensa Ta
Yadda Shi Kadai Zaiji Abinda Yake Fada.

b. RASHIN JAM’I: Shi Lazumi Mutum Shi Kadai Yakeyi Ba A Jam’i Ba Kamar Yadda Ake Zikirin Juma’a Ko
Wazifa Ba.

c. LOKACI: Ana iya Lazumin Safe kafin sallar Asubahi daga kashin qarshe na dare. Amma Lazumin yamma
ba a yin shi sai bayan sallar la'asar. Kuma lokacin yinsu sun rabu kashi uku kamar haka:

i. LOKACIN DA AKAFI SO: Anfiso Kayi Lazumin Safe Daga Bayan Sallar Asubahi Zuwa Fitowar Rana Sannan
Lazumin Yamma Kayi Shi Daga Bayan Sallar La’asar Zuwa Isha'i.

ii. LOKACIN LARURI: In Bakayi Lazumin Safe A Lokacin Da Akafiso Ba To Kana Iya Yinta Daga Fitowar Rana
Har Zuwa Sallar La’asar. In Bakayi Lazumin Yamma A Lokacin Da Aka Fiso Ba Kana Iya Yinta Daga Bayan
Sallar Isha'i Har Zuwa Asubahi.

iii. LOKACIN RAMUWA: In Akayi Sallar La’asar Bakayi Lazumin Safe Ba To Zakayi Shi Da Niyyar Ramuwa.
In Akayi Sallar Asubahi Bakayi Lazumin Yamma Na Jiya Ba To Da Niyyar Ramuwa Zakayi Shi.

2. HUKUNCIN DA SUKA RATAYA AKAN WAZIFA KAWAI:


a. JAM’I: Yin Wazifa A Cikin Jam’i Dolene Sai In Da Larura .

b. DA’IRA: Zaman Wazifa Dole Sai Anyi Da’ira Wato Circle A Turance.

c. DAGA MURYA: Dole Ne A Cikin Wazifa A Daga Murya Yayin Karantawa.

d. DAIDAITUWA: Dole Ne A Daidaita Karatu Kada Wani Ya Wuce Wani Da Sauri.

e. LOKACI: Kana Iya Yin Wazifa Ko Yaushe Daga Bayan Sallar Asubahi Zuwa Wani Asubahin, Sannan Ne In
Bakayi Ba Zai Zama Ramuwa. Amma An fiso Ayi Wazifa Bayan Sallar Magariba Kafin Ayi Isha’i Domin
Shehu Ibrahim RTA Yana Cewa “Yin Salatil Fatihi Guda Daya A Tsakanin Sallar Magariba Da Isha’i Daidai
Yake Da Salatil Fatihi 500 Wanda Akayi Ba A Wannan Lokacin Ba”

Duka Wayannan Abubuwan (daga a zuwa c) Basu Rataya A Kan Mace Ba (wato zatayi wazifarta ita kadai
a dakinta kamar yadda take sallah a dakinta) Ko Namiji Mai Uzuri (Uzuri Shine Larurar Da Zai Hana
Mutum Halartar Jam’i).

Wanda Yaki yin Wazifa Cikin Jam’i Da Gangan Har Tsawon Kwanan Uku A Jere Toh Ya Yanke Igiyar
Madadinsa Tsakaninsa Da Shehu Tijjani RTA. Dole Sai Ya Je An Sake Yi Masa Tajdidi Wurin MuKaddami.

Idan Akayi Wazifa A Jam’i Ba Tareda Daya Daga Cikin Sharuddan Nan Uku Ba (daga b zuwa d) Toh
Wazifar Ta Lalace Kuma Dole A Sake Ta.

3. HUKUNCIN DA SUKA RATAYA AKAN ZIKIRIN JUMA’A

a. LOKACI: Ba Ayin Zikirin Juma’a Sai Ranar Juma’a Bayan Sallar La’asar Da Misalin Awa Daya da rabi
Zuwa Faduwar Rana.
b. RAMUWA: Wanda Baiyi Zikirin Juma’a Ba Saboda Wata Larura Ta Shari’a Toh Bazai Rankata Ba. In
Akayi Magariba Shikenan Lokacin Zikirin Juma’a Ya Wuce.

4. WANDA YAYI RAGI KO YAYI KARI: Wanda Ya Rage Adadi Toh cika abinda ya rage sannan Zaiyi Istigifari
100 Bayan Ya Gama Aikin Da Niyyar Gyara Kuskuren Nasa. Misali, Idan Kayi Salatin Annabi 90 Maimakon
100 A Lazumi Toh Zaka Cika Salati Goman Da Ka Rage Bayan Ka Gama Lazumin Naka Sannan Kayi
Istigifari 100. Idan Kuwa Kayi Kari Ne Misali Maimakon Kayi Hailala 100 Sai Kayi 120 Toh Zakayi Istigifari
100 Ne Kawai Bayan Ka Gama Aikin Naka.

5. GABATAR DA WANI ABU BA MUHALLINSA BA: Wanda Yayi Mantuwa Ya Gabatar Da Wani Abu A Inda
Ba Muhallinsa Bane, Misali Cikin Wazifa Maimakon Da Kayi Salatil Fathi 50 Ka Shiga Hailala Sai Ka Manta
Ka Fara Jauharatul Kamali, Toh Zakayi Hailala 100 Da Ka Tsallake Sannan Kayi Jauharatul Kamali ɗin.
Bayan ka gama sai Kayi Istigifari 100 Da Niyyar Gyara Kuskurenka. Amma In Da Gan-Gan Kayi Haka Toh
Aikinka Ya Lalace Kuma Dole Sai Ka Sake.

6. WANDA YA RISKI JAM’I: Wanda Yaje Wazifa Sai Ya Tarar An Rigashi Farawa Toh Zai Ci Gaba Dasu Daga
Inda Ya Same Su Har Zuwa Karshe Amma Bazai Shafa Addu’a Dasu Ba, Ana Gama Jauhara Na 12 Sai Ya
Sauke Hannunsa Ya Cika Abinda Bai Samu Ba Sannan Yayi Nasa Addu’ar Ya Shafa. Idan Kuma Jam’in
Zikirin Juma’a Ne Toh Zai Cigaba Dasu Har Karshe Sannan Yayi Addu’a Tareda Su Kuma Babu Abinda Zai
Cika Na Daga Hailalan Daya Rasa.

7. WANDA BAI IYA JAUHARA BA: Idan Baka Iya Jauharatul Kamali Ba To Idan Aka Fara Karantawa A
Wazifa Sai Kayi Shiru Ka Karanta Salatil Fathi 20 A Sirrance A Maimakon Jauhara 12. Sai Kayi Addu’a
Tareda Su Ka Shafa.

8. MARA ALWALLA: Wanda Babu Ruwan Da Zaiyi Alwalla Toh Yana Iya Taimama Yayi Lazuminsa Ko
Wazifa Ko Zikirin Juma’a Saidai A Wazifa Bazaiyi Jauhara Ba Saboda Ita Jauhara Dole Sai Mai Alwalla Yake
Iya Karanta Ta. Dan Haka Saidai Yayi Salatil Fathi 20 A Maimakon Jauhara 12 Din.

9. MACE MAI HAILA: Kamar Yadda Ba Zata Rama Sallah Ba Idan Tana Haila Haka Zalika Ba Zata Rama
Wazifa Ko Lazumi Ba Ballantana Zikirin Juma’a Wanda Shi Daman In Ya Wuce Ba A Rama Shi.
10. MATAFIYI: Idan Uzurin Tafiya Ya Kamaka Kana Iya Yin Lazuminka Ko Wazifa Ko Zikirin Juma’a Amma
In Wazifa Ne Kuma Kana Kan Abin Hawa Ko Kana Tafiya Da Kafa Toh Bazaka Yi Jauhara Ba Sai Dai Ka
Zauna Ko Kayi Salatil Fathi 20 A Maimakon Jauhara.

A rubutu na gaba zamu kawo bayani a taqaice akan tarbiyatul Azkar da hukunce hukuncen ta Insha Allah

️DAGA TASKAR NAZIRIYYA SIRRIN YABO FOUNDATION ️

O,,oh BABA NJAWAI IKON ALLAH.


(5) ILIMIN ƊARIKAR TIJJANIYA

(Kashi Na Qarshe)

**

***

MENENE TARBIYATUL AZKAR, WURIN WA ZA A YI, YAYA LADABIN TSAKANIN MURIDI DA SHEHINSA?

****

TARBIYATUL AZKAR A MUSULUNCI

Allah Yana Cewa "Ku sanni Kafin ku bauta min, idan baku sanni ba tayaya zaku bauta min" Annabi SAW
kuma yace Abinda Allah yake nufi shine "Ku Bautawa Allah kamar kuna ganinsa, idan baku ganinsa shi
yana ganin ku".

Toh tayaya zaka iya bautawa Allah tamkar kana ganinsa?

Allah yana cewa “Faktulu Anfusakum Zalikum Khairun Lakum” Wato Ku Kashe Kanku Shine Mafi Alheri
Gareku. Shin Wani Irin Laifi Mutum Zaiyi Da Allah Zai Ce Ya Kashe Kanshi?

Annabi SAW Yace “Mutu Kabla Anta Mutu” Shin Ta Yaya Zakayi Irin Wannan Mutuwar?

BAKU SANI BA?

Allah sai yace "Ku tambayi ma'abota zikiri in ya kasance baku da sani"
Wannan Shine Manufar Tarbiyatul Azkar A Darikar Shehu Tijjani RTA. Ka Yaki Zuciyarka Ka San Kanka
Kamar Yadda Annabi SAW Yace “Man Arafa Nafsahu Fakad Arafa Rabbahu” ka zama matacce Alhalin
kana raye ta hanyar yanke Alaqarka da wanin Allah da duniya karan-kanta da abinda ke cikinta.

Dan Haka Ba Zaka San Kanka Ba Har Sai Ka Kashe Zuciyarka Daga Ganin Kanka Da Ganin Waninka Ta
Hanyar Imani Da Kai Babu Ne ALLAH Ne Akwai, Shine Farkon Komai Shine Karshen Komai, Shine A Zahiri
Shine A Boye.

SHEHUN DA YA KAMATA YAYI MAKA TARBIYATUL AZKAR

Wanene Shehu? Shine Waliyyin Malami Wanda Kayi RiKo Dashi Dan Ya Zama Jagoranka Cikin Lamarin
Allah Da Kuma Samun Tsarkin Zuciya.

A tijjaniya, Shehu Shine muqaddami wanda yake da cikakken Iznin Gabatar da dukkan lamarin tijjaniya
ba wai iya bayar da darikar kawai ba.

Shehinka Shine Tsaninka Zuwa Ga Allah Kuma Indararon Madadinka Daga Kogin Soyayyar Manzon Allah
SAW. “Duk wanda bashi da shehun da ya riKe, toh shaidan shine zai zama shehinsa”.

Shehu Ibrahim RTA Ya Bada Siffofin Wanda Zaka Rike Ya Zama Shehinka. Suffofin Guda Biyar Ne Kuma
Gasu Kamar Haka:

1. KHABEERAN: Wato Ya Kasance Masanin Sharia (Kur’ani Da Hadisi) Da Ilimin Ma’arifa (Ilimin Sanin
Allah SWT).

2. NAASIHAN: Ya Zamanto Mai Nasiha Ne Ba Mai Tilastawa Ba Domin Allah SWT Yana Cewa “Babu
Tilastawa A Addini”. Dan Haka Anaso Ya Kasance Mai Jan Hankalin Mutum Cikin Hikima.

3. KAMILA IRFANIN: Ya Kasance Cikakken Masanin Allah. Masanin Allah Shine Wanda Yake Rungumar
Kaddara Mai Kyau Da Mara Kyau Bisa Aminta Da Cewar Allah Ne Ya Jarabce Shi. Mai Nema Da Kai
Kukansa Zuwa Ga Allah. Mai Godiya Ga Allah Ko Da Yaushe Cikin Ko Wani Irin Hali.
4. IMAMAN: Ya Kasance Shugaba Mai Nuni Da Aiki Mai Kyau Kuma Mai Hani Da Mummunan Aiki.

5. SALIHAN: Ya Kasance Salihi Ma’aboci Kyawawan Halaye Da Mutunci.

Muddin Yana Da Wayannan Siffofin Duka Toh Kayi Masa Biyayya Ka Mallaka Masa Kanka Tamkar Gawa A
Hannun Mai Wanketa. Kayi Gaggawan Yin Abinda Ya Umarce Ka Sannan Ka Gaggauta Daina Abinda Yace
Ka Daina Koda Kuwa Dainawar Zata Sanyaka Kuka Saboda Shi Shehin Naka Mai Daura Ka Ne Akan Hanya
Madaidaiciya.

LADABI TSAKANIN MURIDI DA SHEHINSA

Wanene Muridi? Shine Wanda Yayi Riko Da Shehun Malamin Darika Dan Samun Tsarkin Zuciya Da Sanin
Allah Da Neman Kusanci Da Annabi SAW.

Kafin Muridi Ya Samu Wayannan Abubuwan Dole Akwai Wasu Halaye Da Zai Daurawa Kansa Dan Cikar
Burinsa. Su Wayannan Halaye Sune Ladabi Da Biyayya Da Fahimtar Girman Shehin Naka Kamar Haka:

1. Aikata Abinda Yake So Ka Aikata Da Barin Abinda Bayaso Ka Aikata.

2. Aminta Dashi Akan Zantukansa Da Ayyukansa Wato Ka Gaskata Abinda Ya Fada Sannan Ka Yarda Da
Abinda Ya Aikata.

3. Kaso Shi So Mai Tsanani Domin Gwargwadon Yadda Kake Son Shi Haka Zaka Dinga Samun Albarkarsa.

4. Girmama Ahalin Sa Misali Matansa Da Danginsa Kai Hatta Abokansa Da Makwabtansa.

5. Hidimta Masa Da Jikin Ka Da Dukiyarka.


6. Rashin Kallon Waninsa Wato Kar Ka Bar Naka Shehin Ka Tafi Wurin Wani Shehin Dan Neman Wani
Abu.

7. Babu Jayayya Tsakanin Ka Da Iyalan Shehinka Ko Abokanansa Ballantana Kayi Jayaya Dashi Shehin
Naka.

Da Sauransu A Cikin Ruhul Adab Da Yakutatil Fareeda Da Kuma Khashiful Ilbas

YA SAHIBI KAMA TARBIYA KA SAMU RABO, WAUTAR GARIQAI CIKINTA KAR TASA KA QIYA

ALHAMDULILLAHI HAMDAZZATI MINHU LAHU SUBHANAHU JALLA AN MASLIN ILAHU ƊAYA

YU'UƊI LIMAN SHA'A MIN IN'AMIHI FADLAN MA SHA'A YAS'ALU BA MAI TAMBAYASSA SHIYA

Nayi Hadiyyar duk wani Alherin da posts din nan suka qunsa daga na daya zuwa na qarshe ga AHALIN
SHEHU BABA NJAWAI R.T.A baki dayan su. Ina fatan hakan ya zama katanga tsakanina da saɓa musu
cikin ko wani irin hali alfarmar jinin dake yawo a jikinsu.

Alhamdulillahi alhamdulillahi alhamdulillahi

️DAGA TASKAR NAZIRIYYA SIRRIN YABO FOUNDATION ️

MAI BUQATAR QARIN BAYANI 🤝🤝07018171482

You might also like