You are on page 1of 224

LITTAFIN TARIHIN

ANNABI ‫ﷺ‬
MATAKI NA FARKO

SHIRYAWA:
SASHIN ILMANTARWA NA TSANGAYAR AFRICA,
WANDA AKA RUBUTA DOMIN ƊALIBAN TSANGAYAR
AFRICA TARE DA HAƊIN GWIWAR TASHAR
AFRICA TV3.

ƘARƘASHIN KULAWAR:

HUKUMAR GUDANARWA TA AFRICA TV3

Bugu Na Ɗaya
1445H-2023

1
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINƙAI

2
Jawabin shugaba:
Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, Salati da
aminci su ƙara tabbata ga mafi ɗaukakar Annabawa da Manzanni,
Annabinmu Muhammad ‫ ﷺ‬da iyalan gidansa, da Sahabbansa baki
ɗaya, bayan haka.
Haƙiƙa ilimin shari’a yana ɗaya daga cikin mafiya
muhimmancin ilimi na dole da Musulmi yake buƙata a cikin
rayuwarsa, kuma al’umma gabaɗaya tana buƙatar shi wajen tafiyar
da cigabanta, saboda hakan ne nassoshin shari’a suka zo domin su
ɗaukaka darajar wannan ilimi da kuma waɗanda suke ɗauke da shi,
Allah Maɗaukakin Sarki Ya ce:

‫ﱡﭐ ﱔﱕﱖﱗﱘﱙﱚﱛﱜﱝﱞﱟﱠ ﱡﱢﱣﱤﱥ‬

١٨ :‫ﱦﱧﱠ آل عمران‬
{Allah Ya sheda cewa: Lalle ne babu abin bautawa bisa
cancanta face Shi, haka ma Mala’iku da Ma’abuta ilimi, alhali Yana
tsaye a kan adalci, babu abin bautawa face Shi, mabuwayi Mai
hikima} [Ali Imran: 17].
Imam Asshaukani ya ce: “Abin da ake nufi da ma’abota ilimi
a nan, Shi ne masana littafin Allah, da Sunnar Manzon Allah”.

3
Allah l Ya ce:

١١٤ :‫ﱡﭐﱏﱐﱑﱒﱓﱔﱠ طه‬


{kuma kace ya Ubangiji Ka ƙara mini ilimi} [Suratu: Ɗaha: 114].
Kuma a cikin Hadisi -Manzon Allah ‫ ﷺ‬- ya ce: “Duk wanda
ya bi wata hanya yana mai neman ilimi a cikinta, Alalh zai sauƙaƙe
masa hanya zuwa Aljanna da shi”. Muslim ne ya ruwaito shi.
Kuma tun da ya kasance isar da ilimi zuwa ga mutane ta
mabambantan hanyoyi tana daga cikin manyan manufofin (Afica
TV3) da kuma sauƙaƙa hanyar samun shi, hakan ya sa su tunanin
samar da shirin sadar da ilimi ta hanyar (Tsangayar Africa) wacce
take kan tsari na ilimantarwa, kuma take nufin kusanto da ilimin
addini ga masu kwaɗayin samun shi ta hanyar internet, da kuma
hanyar keɓantacciyar tashar talabijin, duk saboda ƙoƙarin tabbatar
da manufa ta tushe wadda ita ce yaɗa ilimi da kuma tabbatar da
ilimin Addini mai ƙarfi wanda aka gina shi a kan ginshiƙi na ilimi
ingantacce, a kan ingantacciyar aƙida da ta dogara a kan littafin
Allah da Sunnar ManzonSa ‫ﷺ‬, a salo na zamani mai sauƙi, don haka
ina roƙon Allah Maɗaukakin Sarki; da ya ba wa kowa ilimi mai
amfani da kuma aiki nagari, da kuma dacewa da kuma yin abu
domin Allah.
DR. HABEEB TIJJANI TAHIR.

4
ƘUNSHIYA
1. Muhimmancin (karanta) tarihin Manzon Allah ‫ﷺ‬.
2. Annabi Muhammad ‫ ﷺ‬- Nasabarsa zuwa haihuwarsa.
3. Waɗanda suka shayar da Annabi ‫ﷺ‬.
4. Tasowar Annabi ‫ﷺ‬.
5. Matan Annabi ‫ﷺ‬.
6. Ƴaƴan Annabi ‫ﷺ‬.
7. Manzancin Annabi ‫ﷺ‬.
8. Lokacin zaman Makka.
9. Rabe-Raben Wahayi.
10.Matakan kira zuwa ga Allah a ɓoye.
11.Kira zuwa ga Allah a bayyane.
12.Ƙaurar (Hijirar) musulmai guda biyu.
13.Kira zuwa ga Musulunci a wajen garin Makka.
14.Mubaya’ar Aƙaba ta farko.
15.Mubaya’ar Aƙaba ta biyu.
16.Lokacin zaman Madina.
17.Yaƙe-yaƙen da suka faru kafin yaƙin Badar.
18.Yaƙe-yaƙen da Annabi ‫ ﷺ‬ya halarta.
19.Yaƙin Badar babba.
20.Yaƙin Uhud.
21.Yaƙin Gwalalo (Ahzabi).
22.Yaƙin Khaibar.
23.Yaƙin Mu’uta.
24.Buɗe garin Makka.
25.Rushe gumaka.
5
26.Yaƙin Hunainu.
27.Yaƙin Tabuka.
28.Shekarar Tawagogi.
29.Hajjin Annabi ‫ﷺ‬.
30.Umarorin Annabi ‫ﷺ‬.
31.Wafatin Manzon Allah ‫ﷺ‬.
32.Muhimmancin karantar ɗabi’un Manzon Allah ‫ﷺ‬.
33.Kamannin Manzon Allah ‫ﷺ‬.
34.Fuskarsa da Jikinsa da Tambarin Annabta.
35.Tufafinsa ‫ﷺ‬.
36.Tafiyarsa da zamansa.
37.Guminsa da Turarensa ‫ﷺ‬.
38.Sunayensa ‫ﷺ‬.
39.Yadda yake ci da sha.
40.Yadda yake Magana, da kuma dariyarsa, da murmushinsa, da karsashinsa ‫ﷺ‬.
41.Yadda yake bacci da kuma farkawarsa.
42.Ibadarsa, karatunsa, da kuma kukansa.
43.ƘanƘan-da-Kansa (tawali’u), da ɗabi’unsa, da yawan shekarunsa, da
wafatinsa, da kuma gadonsa.

6
KASHI NA ƊAYA:

MUHIMMANCIN (KARANTA)
TARIHIN ANNABI ‫ﷺ‬

DA KUMA MATSAYINSA

7
A WANNAN ZANGON NA FARKO ZAMU KARANTAR DA:

 Muhimmancin karanta tarihin Annabi ‫ﷺ‬, da kuma matsayinsa.


 Gargaɗi game da wasu littattafan tarihi da sira.

MUHIMMANCIN KARANTA TARIHIN ANNABI ‫ﷺ‬

DA KUMA MATSAYINSA:

Muhimmancin karanta tarihin Annabi ‫ﷺ‬, zai bayyana a ƙarƙashin waɗannan


batutuwa masu zuwa:

 Haƙiƙa tarihin Annabi ‫ ﷺ‬shi ne ma’auni da za a auna ayyuka da shi, abin da


ya yi daidai da shiriyarsa da salonsa ya zama karɓaɓɓe a cikin Shari’a. Abin
da kuma bai yi daidai da shiriyarsa da salonsa ba, zai zama abin mayarwa (ba
za a karɓa ba).
 Tarihi yana siffantawa mutum hoton abin koyi mai kyau, cikin sura
maɗaukakiya ga mutane, Annabi ‫ ﷺ‬mai karamci ne, saboda haka ne Allah ya
yi umarni da a riƙe shi a matsayin abin koyi, Allah Maɗaukakin Sarki Ya ce:

‫ﱡﭐﲾﲿﳀﳁﳂﳃﳄﳅﳆﳇﳈﳉﳊﳋﳌﳍﳎﳏﱠ‬
٢١
“Lalle, abin koyi mai kyau ya kasance gare ku daga Manzon Allah ga wanda
ya kasance yana fatan rahamar Allah da ranar Lahira, kuma ya ambaci Allah
da yawa”. [Ahzab:21].

8
 Karatun tarihin Annabi ‫ ﷺ‬zai taimaka wajen fahimtar littafin Allah, da kuma
aiki da shi. Domin shi (Manzon Allah) ‫ ﷺ‬Alƙur’ani ne ɗabi’unsa, rayuwarsa
kuma gabaɗaya ta kasance koyi da Alƙur’ani ce da kuma aiki da shi.
 Da karatun tarihi ne son Annabi ‫ ﷺ‬yake ƙaruwa, hakan yana faruwa yayin
tsinkaye da duba zuwa ga wasu ɓangarori masu girma na rayuwarsa. Haƙiƙa
Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya ce: “Imanin ɗayanku ba ya cika har sai na kasance ni na
fi soyuwa gare shi fiye da iyayensa, da ƴaƴansa, da mutane bakiɗaya”.
Bukhari da Muslim sun haɗu wajen ruwaito wannan Hadisi.
 Haƙiƙa ɗabi’un Annabi ‫ﷺ‬, da kuma tarihinsa su ne hanya mafi girma, da
Musulmi zai bi ga wanda yake son alheri, da kuma rayuwa ta karamci a duniya
da lahira.
 Mutum zai san zamani mai girma wato zamanin Sahabbai yardar Allah ta ƙara
tabbata a gare su, da kuma matsayarsu tare da Manzon Allah ‫ﷺ‬, da hidimtawa
Shari’arsa, da kuma fansarsa da suka yi da rayukansu, da ƴaƴansu, da
dukiyarsu, da kuma yadda suka kai matuƙa wajen kwaɗayin koyi da shi, cikin
duk wata magana, ko aiki, ko umarni, ko hani, sai hakan ya zama hanyar da
za a yi koyi da su.
 Haƙiƙa karanta tarihin Manzon Allah ‫ ﷺ‬zai taimaka wajen fahimtar addini
bakiɗaya tun daga Aƙida, da Ibada har zuwa ilimin Fiƙihu. Saboda rayuwarsa
‫ ﷺ‬addini ce gabaɗayanta.

9
GARGAƊI GAME DA WASU LITTATTAFAI.

Wannan wani jan hankali game da wasu littattafai da ake sanin wani sashe na
tarihin Annabi ‫ ﷺ‬daga ciki, tare da abin da yake ciki na hatsari da manya-manya
kusakurai, daga cikin waɗannan littafai akwai:

Litattafan adabi, da diwanai na waƙoƙi, kamar littafin AL’AGANI NA ABUL


FARAJ AL-ASBAHANI) ko littafin AL-IƘDUL FARID NA IBN ABDU-RABBHI
AL-ANDALUSI.

Haƙiƙa waɗannan littattafai sun ƙunshi labarai masu yawa game da Annabi
‫ﷺ‬, da Sahabbansa, kuma labarai ne na ƙarya marasa iganci, ga kuma abin da yake
ciki na tadlisi (wato shigar da abin da babu shi) da lalata abin da yake mai kyau, da
kuma ƙire ga tarihi.

Waɗannan littattafai bai dace a ce su zama maɓuɓɓugar da za a dinga samo


labarai da tarihi ba, musamman wanda da ya shafi Annabi ‫ﷺ‬, da tarihin Musulunci
da labaran sahabbai yardar Allah ta ƙara tabbata a gare su ba.

10
Auna Fahimta

1- Ka rubuta taƙaitaccen bayani game da muhimmancin tarahin Annabi ‫ﷺ‬

__________________________________________________________________
__________________________________________________________________
__________________________________________________________________
__________________________________________________________________

2- A baya an yi maka bayani game da littattafan da ya kamata a nesanta game


da tarihin Annabi. Faɗi wasu biyun daban.
_____________________________________________________________
_____________________________________________________________
_____________________________________________________________
_____________________________________________________________

11
KASHI NA BIYU:
Annabi Muhammad ‫ﷺ‬

12
A wannan darasin za mu karanci:

- Dangantakarsa ‫ﷺ‬.

- Haihuwarsa ‫ﷺ‬.

- Waɗanda suka shayar da shi ‫ ﷺ‬.

- Tasowarsa da rayuwarsa ‫ﷺ‬.

- Mu’ujizar tsaga ƙirjinsa ‫ﷺ‬.

13
DANGANTAKARSA ‫ﷺ‬:

Shi ne Muhammad ɗan Abdullahi ɗan Abdulmuɗɗallib ɗan Hashimu, ɗan


Abdumanafi, ɗan Ƙusayyu, ɗan Kilabi, ɗan Murratu, ɗan Lu’ayyu, ɗan Ghalibu, ɗan
Fihru, ɗan Maliku, ɗan Nadaru, ɗan Kinanata, ɗan Khuzaimata, ɗan Mudrikata, ɗan
Ilyasu, ɗan Mudaru, ɗan Nizaru, ɗan Ma’ad, ɗan Adnan. Bukhari ya rawaito.

Adnanu yana daga cikin tsatson Annabi Isma’il Azzabihi (wato wanda aka so
yankawa), ɗan Ibrahim e.

Manzon Allah ‫ ﷺ‬zaɓaɓɓe ne daga zaɓaɓɓe daga zaɓaɓɓe.

Muhimmiyar Fa’ida

Daga Wasilatu ɗan Asƙa’i Allah ya ƙara yadda a gare shi ya ce: Manzon Allah ‫ﷺ‬
ya ce: “Haƙiƙa Allah Ya zaɓi Kinanatu daga ƴaƴan Isma’il, kuma Ya zaɓi
Ƙuraishawa daga cikin Kinanatu, kuma ya zaɓi banu Hashim daga cikin
Ƙuraishawa, kuma sai Ya zaɓe ni daga cikin banu Hashim”. Muslim ya ruwaito shi.

Mahaifinsa: Shi ne Abdullahi ɗan Abdulmuɗɗallib. Ya kasance mafi kyawun


samarin Ƙuraishawa.

Mahaifiyarsa: Ita ce Aminatu ƴar Wahab. Mahaifinta ya kasance shugaban banu


Zuhrata mafi karamci, ɗaukaka da nasaba mai kyau.

Kakansa: Shi ne Abdulmuɗɗalib ɗan Hashim, shi ne shugaban ƙabilar Ƙuraishawa,


yana da ɗabi’u na karamci, ya shahara da tona rijiyar Zamzam.

14
Haihuwarsa ‫ﷺ‬:

An haifi Annabi ‫ ﷺ‬a daren Litinin, sha biyu ga watan Rabi’ul awwal. An ce tara
ga wata, haka kuma a wata ruwayar an ce takwas, a wata ruwayar an faɗi wanin haka
a shekarar giwaye. Ƙissar ma’abota giwaye sananniya ce. Alƙur’ani Mai Girma ya
ambace ta. Yadda ƙissar take shi ne: Abrahata Sarkin Yamen ya so ya rushe Ka’aba,
sai ya zo mata da runduna mai girma da giwaye a tare da su, sai Allah Ya mayar
musu da kaidinsu, Ya kiyaye Ka’aba. A wannan lokaci Manzo Allah ‫ ﷺ‬yana cikin
Mahaifiyarsa, Mahaifiyarsa ta ga wani haske ya fito daga jikinta, yayin da ta haife
shi, hasken kuma ya haskaka fadar mulki ta Basara a ƙasar Sham.

Mahaifinsa ya yi wafati yayin da Manzon Allah ya ke cikin mahaifiyarsa – a


zance mafi inganci – yayin da aka haife shi, ya kasance a ƙarƙashin kulawar kakansa
Abdulmuɗɗalib, yana lura da buƙatunsa, da na Mahaifiyarsa.

Muhimmiyar fa’ida

Yin taro domin zagayowar ranar haihuwar Manzon Allah ‫ ;ﷺ‬ba shi da asali a
cikin Shari’a, mauludi yana cikin abin da ƴan Faɗimiyya ƴan shi’a ne rafidawa suka
ƙirƙiro, babu wani daga cikin Sahabban Manzon Allah ‫ ﷺ‬da ya aikata, ko kuma wani
daga cikin waɗanda suke cikin ƙarnunka ukun farko masu falala da ya yi, babu wani
daga cikin malaman Musulunci da ya yarda da yin mauludi.

Waɗanda Suka Shayar da shi ‫ﷺ‬

- Suwaiba Baiwar Abu Lahab.


- Halimatu ƴar Abu Zu’aibu.

Wacce ta fara shayar da shi ita ce Suwaiba baiwar Abu Lahab, kuma ta kasance
ta shayar da Hamza ɗan Abdulmuɗɗalibz kafin Manzon Allah ‫ﷺ‬.

15
Halimatus Sa’adiyya: Wasu mata daga cikin ƙabilar banu Sa’ad bin Bakr sun
zo suna neman yaran da zu shayar da su, sai ya zama wacce za ta shayar da Annabi
‫ ﷺ‬Mai Albarka, yana cikin rabon Halimatu ƴar Abu Zu’aibu Assa’adiyya, sunan
mijinta Abu Kabshata. Albarka ta sauka ga iyalin wannan gida da suka shayar da shi
tsawon lokacin da ya kasance a cikinsu.

Haƙiƙa ya zauna tare da su kusan fiye da shekara huɗu.

Masana tarihi sun ambaci cewa ta shayar da Hamza ɗan Abdulmuɗɗalib, sai ya
kasance an shayar da shi tare da Manzon Allah ‫ ﷺ‬ta fuskoki biyu.

Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya tashi yana maraya domin kuwa:

 Mahaifinsa ‫ ﷺ‬ya yi wafati yayin da ya ke cikin mahaifiyarsa.


 An ce yana dan wata biyu ko wata bakwai a cikin mahaifiyarsa.
 Kuma mahaifyarsa ta rasu yayin da yake ɗan shekara huɗu, wasu sun ce
shekara shida.
 Sai kakansa Abdulmuɗɗalib ya ɗauki ɗawainiyarsa, yayin da ya kai ɗan
shekara takwas, sai kakansa ya rasu, daga nan kawunsa Abu Ɗalib ya jiɓinci
lamarinsa.

Abin da ya faru na tsaga ƙirjin Manzon Allah ‫ﷺ‬:

Wannan mu’ujiza ta faru ga Annabi ‫ ﷺ‬sau biyu.

Na farko:

A ƙauyen Banu Sa’ad yayin da yake wajen wacce take shayar da shi, lokacin yana
ɗan shekara huɗu a duniya.

Na biyu:

Ya faru a daren Isra’i kamar yadda Bukhari da Muslim suka ruwaito.

16
Haƙiƙa Muslim ya ruwaito a cikin ingantaccen littafinsa, daga Anas ɗan Malik
zcewa: Mala’ika ya zo wajen Manzon Allah ‫ ﷺ‬yayin da yake wasa da yara, sai
ya kama shi, ya kwantar da shi, sannan ya tsaga ƙirjinsa ya fito da zuciyarsa, ya fitar
da gudan jini daga ciki, sai ya ce: “Wannan shi ne rabon Shaiɗan daga wajenka”,
sannan ya wanke ta da ruwan Zamzam a cikin wani mazubi na zinare, sannan ya
haɗe ta (wato ya haɗe sashenta da sashe), sannan ya mayar da ita inda ya ciro ta. Sai
yaran da yake wasa da su suka tafi wajen mahafiyarsa suna sauri (wato wacce take
shayar da shi) suka ce: “Haƙiƙa an kashe Muhammadu”, domin sun ga launinsa
(kamanninsa) sun sauya. Anas (R.A) ya ce: “Haƙiƙa na kasance ina ganin bigeren
wannan ɗinkin a ƙirjinsa ‫”ﷺ‬.

Komawarsa wajen Mahaifiyarsa:

Halima ta ji tsoron abin da zai same shi a nan gaba bayan wannan abin da ya
faru, hakan ya sa ta mayar da shi wajen mahaifiyarsa. Daga nan Annabi ‫ ﷺ‬ya kasance
a wajen mahaifiyarsa, har sai da ya kai ɗan shekara shida.

Amina: (Mahaifiyar Annabi ‫ )ﷺ‬ta fito domin ta je ta ziyarci kawunnansa dake Banu
Adiy bin Najjar, daga Makka ta yi wannan tafiya mai tsananin wuya tare da ɗanta
maraya Muhammad ‫ﷺ‬, ta zauna a wajensu tsawon wata guda, sannan ta dawo.

Wafatin Mahaifiyarsa ‫ﷺ‬:

Yayin da take halin dawowa kwatsam sai rashin lafiya ta riske ta a farko farkon
hanya, sannan rashin lafiyar ta tsananta har ta rasu a (garin) Abwa’i tsakanin Makka
da Madina.

17
Rayuwarsa da kakansa mai tausayi:
Abdulmuɗɗalib ya dawo da shi garin Makka, inda ya tausasa masa matuƙa fiye
da ƴaƴansa. Ya kasance ba ya son rabuwa da shi, yana ma fifita Annabi ‫ ﷺ‬a kan
ƴaƴansa.

18
Wafatin kakansa:
Kakan Annabi ‫ ﷺ‬ya yi wafati a Makka, yayin da Manzon Allah yake ɗan shekara
takwas kafin rasuwarsa, sai ya ga abin da zai fi shi ne, ya bayar da ɗaukar ɗawainiyar
jikan nasa kafin mutuwarsa; zuwa ga Abu Ɗalib Baffan Annabi ‫ﷺ‬, wanda ya zauna
da shi tsawon lokaci. Abu Ɗalib ya dinga ƙarfafa shi, kuma yana ba shi kariya, kuma
yana tausasa masa.

Haɗuwa da Bahira mai ibada (Malamin Nasara):

Yayin da Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya kai ɗan shekara goma sha biyu, sai Abu Ɗalib ya
tafi da shi kasuwanci zuwa garin Sham. Da isarsu garin Basara, dama a wannan gari
akwai wani malami da ake kira da suna Bahira. Lokacin da ayarin ya sauka, sai
Bahira ya zo wajensu, alhali a da can ya kasance ba ya fitowa zuwa wajensu. Sai ya
yi ta shisshiga cikinsu har sai da ya kamo hannun Manzon Allah ‫ﷺ‬, ya ce: “Wannan
shi ne shugaban talikai. Wannan shi ne ɗan aiken Ubangijin talikai, wannan Allah
zai aiko domin rahama ga talikai”.

Sai Abu Ɗalib da wasu manyan ƙuraishawa suka ce da shi: “Ta ya akai kasan
hakan?”, sai ya ce: “Domin lokacin da kuka dirfafo daga aƙaba, ba wani dutse ko
wata bishiya da ta tsaya face sai da ta faɗi tana yin sujjuda a gare shi, kuma ba sa yin
sujjada sai ga wanda yake Annabi, ni kam tabbas na san shi da alamar annabtaka da
ta ke daura da allon kafaɗarsa, kwatankwacin girman tufa, lallai mu mun sami hakan
a rubuce a cikin littafinmu. Bahira ya girmama su da liyafa, ya kuma nemi Abu ɗalib
da ya mayar da shi gida, kada ya je da shi garin Sham, saboda yana ji masa tsoron
Rumawa, da Yahudawa domin za su iya cutar da shi. Sai kuwa Baffansa ya mai da
shi Makka tare da shi da wasu bayinsa.

19
Rantsuwa da alƙawarin kare haƙƙin masu rauni:
Wannn rantsuwa da alƙawarin ya faru ne a watan Zulƙi’ida a wata mai alfarma.
Wasu daga cikin ƙabilun Ƙuraishawa suka yi kira da a yi hakan; Banu Hashim, Banu
Muɗɗallib, Asad bin Abdul’uzza, Zuhratu bin Kilabi, Taimu bin Murratu, sun taru
a gidan Abdullahi ɗan Jud’anu Attamimiy, saboda yawan shekarunsa da kuma
ɗaukakarsa, suka ƙulla alƙawari kan ba wani wanda za a zalunta ɗan garin Makka,
ko waninta daga sauran mutane, face sai sun tsaya ma sa. Za su haɗu a kan wanda
ya yi zaluncin har sai ya mayar da abin da ya zalunta. Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya halarci
wannan alƙawari na haɗin guiwa.

Muhimmiyar Fa’ida:

Imam Baihaƙi ya rawaito, kuma Albani ya inganta shi, daga Abdullahi ɗan Auf
cewa: Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya ce: “Haƙiƙa na halarci ɗaukan alƙawari a gidan Abdullahi
ɗan Jud’an, wadda ya fi soyuwa gare ni fiye da ace ina da jajayen raƙuma a
madadinsa, da a ce za a kira ni zuwa gare irinsa a lokacin Musulunci, da na amsa”.

Kiyayewar da Allah Maɗaukakin Sarki Ya yi wa Annabi ‫ ﷺ‬tun yarinta har


zuwa manzanci

Annabi ‫ ﷺ‬ya ta shi a cikin ɗabi’un kirki masu kyau. Allah Maɗaukakin Sarki Ya
kare shi daga dukkanin abin da ya saɓa wa ɗabi’u masu kyau. Ya kasance ba ya shan
giya, ba ya cin abin da aka yankawa gunki, ba ya zuwa idin bautar gumaka, ko
tarukansu, hasali ma ya kasance yana ƙyamatar irin wannan bautar tun tasowarsa,
har ya zama ba abin da yake ƙyamata fiye da wannan bauta, ga shi ya kasance ba ya
jurar jin an yi rantsuwa da Lata da Uzza.

Daga Jabir ɗan Abdullahi z ya ce: “yayin da ake sabunta gina ɗakin Ka’aba,
sai Annabi ‫ ﷺ‬da Abbas z suka tafi suna ɗaukar dutse, sai Abbas z ya ce da
Annabi ‫ﷺ‬: da za ka yagi kwarjallenka ka sanya a gefen wuyanka da ya fi kare ka

20
daga zafin ɗaukar dutsen, sai (Annabi ‫ ﷺ‬ya zame) ya faɗi a ƙasa sai ya ɗaga
idanuwansa zuwa sama, sannan ya farka (bayan ya suma), sai ya ce: Ina kwarjallena?
Ina kwarjallena?, sai aka ɗaura masa kwarjanllansa”. Bukhari ya da Muslim sun fitar
da wannan Hadisi. A cikin wata ruwayar ta su kuma: “sai ya faɗi a sume, amma ba
a ƙara ganinsa a yanayin da ba kaya a jikinsa ba banda wannan lokaci”

21
Auna Fahimta

1- Ta yaya Manzon Allah ` ya kasance daga mafificin tsatso daga cikin


Larabawa? Yi bayani game da hakan.

__________________________________________________________________
__________________________________________________________________
__________________________________________________________________
__________________________________________________________________

2- Yaya kake ganin abin da mutane suke ƙirƙira game da bikin murnar
zagayowar ranar da aka haifi Annabi ‫ ?ﷺ‬Mece ce matsayar shari’a game da
shi?

________________________________________________________________
________________________________________________________________
________________________________________________________________
_______________________________________________________________

3- Yi magana akan mu’ujizar tsaga ƙirji. Kuma ka ambaci abin da ya zo game


da hakan?

__________________________________________________________________
__________________________________________________________________
__________________________________________________________________

4- Me ka sani game da rantsuwa, da alƙawarin kare haƙƙin masu rauni?

__________________________________________________________________
__________________________________________________________________
__________________________________________________________________
_________________________________________________________________

22
KASHI NA UKU:
Matansa da ƴaƴansa ‫ﷺ‬

23
A Wannan darasin za mu koyar da:

 Auren Annabi ‫ ﷺ‬tare da Nana Khadija d.


 Matan Annabi ‫ﷺ‬.
 Ƴaƴansa.

24
Auren Annabi ‫ ﷺ‬da Nana Khadija d:

Matar Annabi ‫ ﷺ‬ta farko:

Yayin da Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya kai ɗan shekara ashirin da biyar sai ya fita zuwa
garin Sham, domin ya yi kasuwanci da dukiyar Nana Khadija. Da ma can
Ƙuraishawa sun kasance mutane ne ƴan kasuwa. Nana Khadija ta ji labarin gaskiyar
Manzon Allah ‫ ﷺ‬da girman amanarsa da kyawawan ɗabi’unsa, sai ta aika masa da
saƙo, ta bijiro masa da maganar ya ɗauki dukiyarta ya fita kasuwanci zuwa garin
Sham. Ita kuma za ta ba shi lada mai yawa fiye da wanda take ba wasu ƴan kasuwar.
Annabi ‫ ﷺ‬ya fita tare da wani bawanta da ake kira da suna Maisara. Manzon Allah
‫ ﷺ‬ya yarda da hakan.

Yayin da ya dawo zuwa garin Makka, sai Nana Khadija ta ga amana da albarka a
cikin dukiyarta irin wacce bata taɓa gani ba kafin haka. Kuma Maisara ya ba ta
labarin abin da ya gani na ɗabi’u masu kyau, a lokacin kuma ya kasance manya da
shuwagabanni suna neman aurenta, amma ta ƙi, sai ta je ta zanta wa ƙawarta Nafisa
abin da ya ke cikin zuciyarta. Nafisa ta ta fi wajen Annabi ‫ ﷺ‬ta bijiro masa da
maganar, sai Annabi ‫ ﷺ‬ya yarda da hakan. A wannan lokacin Nana Khadija ta
kasance mace mafi girman nasaba, da dukiya, da hankali a cikin mutanenta.

Ita ce mace ta farko da Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya aura, kuma Manzon Allah ‫ ﷺ‬bai haɗa
ta da wata mace ba har Allah Ya karɓi rayuwarta.

Nana Khadija ita ce:

 Mace ta farko da Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya aura.


 Bai ƙara aurar wata ba yayin da yake tare da ita.

25
 Ita ta haifa masa ƴaƴansa gabaɗaya; in ban da Ibrahim. Ta haifi;
Alƙasim, da Abdullahi, da mata huɗu, su ne: Zainab, da Ummu
Kulsum, da Faɗima, da Ruƙayyag.

 Amma Ibrahim kuma; Mariyatul Ƙiɓɗiyya ce ta haife shi, wacce


Muƙauƙis na Misra ya ba shi ita kyauta.

Matansa ‫ ﷺ‬bayan Nana Khadija d:

 Saudatu ƴar Zam’ata d.

 A’isha ƴar Abubakar d.

 Hafsatu ƴar Umar d.

 Zainabu ƴar Kuzaima d.

 Ummu Salama Hindu ƴar Abu Umayya Makazumiya d.

 Ummu Habiba, Ramlatu ƴar Abu Sufyanu d.

 Juwairiyya ƴar Haris. Sunnanta Barratau sai Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya sanya
mata suna Juwairyya d.

 Maimunatu ƴar Haris Alhilaliyya d.

 Safiyyatu ƴar Huyayyi ɗan Akhɗab d.

 Zainab ƴar Jahshi d.

Ƴaƴansa ‫ﷺ‬:

 Alƙasim:

Ana yi wa Annabi ‫ ﷺ‬alkunya da sunan (Abul Ƙasim ko Baban Alƙasim). An haife


shi gabanin annabta. Ya rasu yana ɗan shekara biyu.

26
 Abdullahi:

Ana kiran shi da Ɗayyib da Ɗahir (wato tsarkakakke), saboda an haife shi bayan
Annabta.

 Ibrahim:

An haife shi a garin Madina a shekara ta takwas bayan hijira, shi ne na ƙarshe
cikin ƴaƴan Annabi ‫ﷺ‬.

 Zainab:

Ita ce babba cikin ƴaƴan Annabi ‫ﷺ‬.

 Ruƙayya.
 Ummu Kulsum.
 Faɗimatu.

Dukkansu sun rasu a lokacin da Manzon Allah ‫ ﷺ‬yake raye, in ban da Faɗima
ita ce ta yi wafati bayansa.

27
Auna Fahimta

1- Ta yaya Annabi ‫ ﷺ‬ya auri Nana Khadija d, kuma su wa ta Haifa masa?

----------------------------------------------------------------------------------------------------
----------------------------------------------------------------------------------------------------
----------------------------------------------------------------------------------------------------
----------------------------------------------------------------------------------------------------
----------------------------------------------------------------------------------------------------

2- Wacce mace ce mafi soyuwa ga Annabi ‫ ﷺ‬cikin matsansa. Yi bayani tare da


dalili?

----------------------------------------------------------------------------------------------------
----------------------------------------------------------------------------------------------------
----------------------------------------------------------------------------------------------------
---------------------------------------------------------------------------------------------------

3- Kawo dalilai kan matsayin Aisha d a wajen Manzon Allah ‫?ﷺ‬

----------------------------------------------------------------------------------------------------
----------------------------------------------------------------------------------------------------
----------------------------------------------------------------------------------------------------

4- Ta yaya zaka bayar da amsa ga wanda yake sukar A’isha d?

----------------------------------------------------------------------------------------------------
----------------------------------------------------------------------------------------------------
---------------------------------------------------------------------------------------------------

28
KASHI NA HUƊU:
Manzancin Annabi ‫ﷺ‬

29
A Wannan Darasin Za mu Karanci:

 Rabuwar Manzancin Annabi ‫ ﷺ‬zuwa:

Zamanin Makka, da zamanin Madina.

 Aiko Shi ‫ﷺ‬.

 Matakan da ya bi wajen kiran mutane zuwa Addini.

 Jarrabawar da suka fuskanta tare da Sahabbansa.

 Ƙaura/Hijira.

30
Manzanci a Makka:

 Aiko shi `.

 Mala’ika Jibril q da Wahayi.

 Shar’anta Salla.

 Ƙaurar musulmai ta farko zuwa ƙasar Habasha.

 Alƙawarin zalunci, da shingen Abu Ɗalib.

 Shekarar baƙin ciki – shekara ta goma bayan aiko shi `.

 Isra’i da Mi’iraji.

 Mubaya’ar Aƙaba ta farko, da da biyu.

 Gidan da ake taruwa don zartar da hukunci, da daɗuwa da suka yi kan kisan

Annabi ‫ﷺ‬.

 Hijirar Annabi ‫ﷺ‬.

31
Manzanci a Makka:

Bayan Allah Ya ɗaukaka Manzon Allah ‫ ﷺ‬da Annabta, rayuwarsa ta rabu zuwa

zamani biyu, su ne:

Manzanci A Makka: Shekara goma sha uku, da kuma zamanin Madina shekara

goma.

Sannan kowanne zamani yana ɗauke da matakai daban-daban. Kowanne mataki

yana da abin da ya yi fice da shi fiye da waninsa.

Kafin fara Magana akan zamanin Makka, da kuma farkon lokacin da aka aiko

Annabi ‫ﷺ‬, ga wasu abubuwa da suka bayyana dake nuna kariyar da Allah Ya ba wa

ManzonSa tun kafin Ya aiko shi:

 Ubangiji Maɗaukaki Ya kiyaye shi tun yana ɗan ƙarami, ta yadda ya zaɓo shi

daga cikin zaɓaɓɓen dangi, da kuma yadda aka haife shi ta hanyar ingantaccen

aure, ba wai ta abin da yake na ɓarna da ɓata ba.

 Ɗaukar ɗawainiyarsa da Abdulmuɗɗalib ya yi, daɗin-daɗawa kasancewarsa

shugaban Ƙuraishawa, tun yarinta har ya kai ɗan shekara takwas, sai kakan na

shi ya rasu, sai ya koma ƙarƙashin kulawar baffansa Abu ɗalib – shi ma

shugaban Ƙuraishawa ne – a cikin hakan akwai yanayi na bayar da kariya gare

shi ‫ﷺ‬.

32
 Allah Ya kiyaye shi yayin da yake saurayi game da faɗawa cikin abin da

samari suke afkawa na alfasha da batsa. Ya shahara da gaskiya, da amana, tun

yana saurayi.

 Allah Ya kiyaye zuciyarsa ‫ﷺ‬, bai taɓa bauta wa wani abin bauta ba; in ba

Allah ba. Bai taɓa yin sujjada ga gunki ba. Bai taɓa shafar gunki ba don neman

albarka. Bai taɓa rantsuwa da wanin Allah ba. Yana ƙyamar iyayengijinsu

kamar Lata da Uzza da waninsu.

 Allah Ya shirye shi da irin shiriyar wanda aka kuɓutar daga fizgar Shaiɗan,

da zugarsa, Ya kuma kiyaye baɗininsa. Hakan kuwa ya bayyana sarai cikin

abin da ya faru na tsaga ƙirjinsa ‫ﷺ‬.

33
Aiko shi ‫ ﷺ‬yayin da yake cikin kogon Hira:

Yayin da Annabi ‫ ﷺ‬ya kusanci shekara arba’in; sai aka saka masa son keɓewa,

ya kasance yana ɗaukar gari da kuma ruwa, ya tafi zuwa kogon Hira dake da

nisan mil biyu daga garin Makka, yakan zauna a ciki a watan azumi, yana bauta

da tun-tun-tuni game da abubuwan dake kewaye da shi na wannan duniya, da

abin da ke bayanta, saboda bai nutsu da abin da mutanensa suke kai na aƙidar

bautar gumaka ba. Sai dai duk da haka shi ma ba shi da wata hanya bayyananniya,

ko wani tafarki iyakantacce, ko kuma wata hanya mai manufa da zai iya nutsuwa

da yarda da ita.

Wannan keɓancewa da ya zaɓa wani yanki ne na tanadi da Allah Ya yi masa,

saboda abin da yake dakonsa na al’amari mai girma, don ya shirya domin ɗaukar

amana mafi girma, hakan ya faru ne kafin a ɗora masa nauyin manzanci da

shekara uku.

34
Mala’ika Jibril q da zuwan wahayi a gare shi:

Yayin da Annabi ‫ ﷺ‬ya kai shekara arba’in; sai Allah Ya aiko shi domin ya yi

bushara da gargaɗi ga talikai. Mala’ika Jibril ya zo masa da wahayi a kogon Hira

daga Ubangijin Talikai, sai ya ce da shi: “Yi karatu”, sai ya ce: “Ni ba mai karatu

ba ne”, sai Manzon Allah ` ya ce: “Sai ya kama ni, ya matse ni, har sai da na

sha matuƙar wahala, sannan sai ya sake ni, sai ya ce: Yi karatu, sai na ce: Ni ba

mai karatu ba ne, sai ya ce mini a karo na uku:

‫ﱡﭐﲅﲆﲇﲈﲉﲊﲋﲌﲍﲎﲏﲐﲑﲒﲓﲔﲕﲖ‬
٥ - ١ :‫ﲗﲘﲙﲚﲛﲜﲝﱠ ال علق‬
(Ka yi karatu da sunan UbangijinKa wanda Ya yi halitta. (1) Ya halitta mutum

daga gudan jini. (2) ka yi karatu, kuma UbangijinKa Shi ne Mafi karamci. (3)

wanda Ya koyar (ta hanyar) alƙalami. (4) Ya sanar da mutum abin da bai sani ba.

Bukhari da Muslim sun ruwaito wannan hadisi.

Jinkirin da mala’ika Jibril ya yi wajen saukar da wahayi:

An ambaci hakan cikin wata ƙissa da ta zo a cikin Sahihul Bukhari cewa:

“yayin da Mala’ika Jibril yi yi jinkiri wajen saukar da wahayi; a farko farkon

manzanci, sai Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya zauna wani ɗan lokaci, wahayi ya yanke,

Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya yi baƙin ciki – cikin labarin da ya zo mana – baƙin cikin da

ya bayyana ƙarara a tare da shi. Sau da yawa yakan wayi gari yana ƙoƙarin hawa

35
kan ƙololuwar duwatsu ya jeho kansa ƙasa, duk lokacin da ya kai ƙololuwar

dutsen domin ya jeho da kansa ƙasa; sai mala’ika Jibril ya bayyana a gare shi,

ya ce da shi: Ya kai Muhammad ‫ ﷺ‬haƙiƙa kai Manzon Allah ‫ ﷺ‬ne na gaskiya,

hakan kuwa ya sa zuciyarsa ta nutsu, kuma hankalinsa ya kwanta sai ya dawo.

Idan yankewar wahayin ta ƙara tsawaita gare shi, sai ya sake maimaita hakan,

idan ya kai ƙololuwar dutsen; sai Jibirl ya bayyana gare shi ya faɗa masa

kwatankwacin abin da ya saba faɗa masa.

Muhimmiyar fa’ida:

Magana mai inganci ita ce cewa wannan labarin; ba ya cikin abin da Bukhari ya

ruwaito. Wannan na daga cikin ruwayoyin da suka isa zuwa ga Imam Zuhuri. Ba

hadisi ne mausuli ba (ma’ana wanda ya sadu zuwa ga Manzon Allah `), Jingina

wannan Hadisi zuwa ga Annabi ‫ ﷺ‬bai inganta ba.

Jibril q yana sauko da wahayi karo na biyu:

Imam Ibn Hajar ya ce: “hakan ya faru – wato wannan yankewar wahayi –

saboda abin da yake ji na tsoro ya tafi. Ya fara jin kwaɗayin dawowar (wahayin)

yayin da hakan ya faru da shi, sai ya fara bibiyar zuwan wahayi. Sai Allah

Maɗaukaki Ya ƙara girmama shi da saukar wahayin a karo na biyu, Manzon

Allah ‫ ﷺ‬ya ce: “Na zauna cikin kogon Hira tsawon wata guda, yayin da na

kammala zamana, sai na sakko, yayin da na so na sauka doron ƙasa sai aka kira

36
ni, sai na yi duba zuwa ɓangaren damana, ban ga komai ba, sai na yi duba zuwa

ɓangaren haguna; ban ga komai ba, na duba gabana; ban ga komai ba, na duba

bayana; banga komai ba, na ɗaga kaina sai na ga ashe Mala’ikan da ya zo min a

kogon Hira ne. Yana zaune a kan wata kujera tsakanin sama da ƙasa. Sai na ji

tsoron shi, na sauka zuwa ƙasa na je wajen Nana Khadija dna ce:

“Ku lulluɓe ni, ku lulluɓe ni, ku lulluɓe ni da mayafi, ku zuba min ruwan sanyi a

kaina”, sai ya ce: sai suka lulluɓe ni suka zuba mini ruwa, sai waɗannan ayoyi

suka sauka:

٥ - ١ :‫ﱡﭐﲚﲛﲜﲝﲞﲟﲠﲡﲢﲣﲤﲥ ﲦﲧﲨﱠ المدث ر‬


Ma’ana: (Ya wanda ya lulluɓa da mayafi. (1) Ka tashi domin ka yi gargaɗi. (2)

Kuma UbangijinKa, sai ka girmama Shi. (3) Kuma tufafinka, sai ka tsarkake su.

(4) kuma gumaka, sai ka ƙaurace musu (5) (Suratu Mudassir: 1- 5). Hakan ya

faru ne kafin a wajabta yin Sallah, sannan sai wahayi yayi ta cigaba da sauka

bayan hakan) Bukhari da Muslim suka ruwaito wannan Hadisin.

Muhimmiyar fa’ida:

Wannan ayoyi su ne mafarin Manzancin Manzon Allah ‫ﷺ‬. Ayoyin sun ƙunshi

nau’i biyu na aiki da aka ɗora masa:

37
Nau’in farko:

Ɗora masa nauyin isar da saƙo da kuma gargaɗi cikin faɗinSa l:

‫ﭐ‬ ٢ :‫ﱡﭐﲝﲞﲟﱠ المدث ر‬


“Ka tashi domin ka yi gargaɗi”.

Nau’i na biyu:

Ɗora masa nauyin aiwatar da umarnin Allahl a karan kansa, hakan ya zo a cikin
sauran ayoyin, kamar faɗinSa l:

٣ :‫ﱡﭐﲠﲡﲢﱠ المدث ر‬
“Kuma Ubangijinka, sai ka girmama Shi.) da faɗinSa l:

٤ :‫ﭐﱡﭐﲣﲤﲥ ﱠ المدث ر‬
“Kuma tufafinka, sai ka tsarkake su”.

38
Auna fahimta:

Rubuta taƙaitaccen bayani game da Manzanci a Makka?

________________________________________________________________

________________________________________________________________

_______________________________________________________________

Wacce aya ce za a ɗauke ta a matsayin mafarin Manzanci? Mene ne mafi

muhimmancin abin da ta ƙunsa?

________________________________________________________________

_______________________________________________________________

39
Rabe–raben wahayi:

Wahayi ya rabu zuwa mataki shida:

1- Mafarki na gaske: wannan shi ne ya zama mafarin wahayinsa ‫ﷺ‬.

2- Mala’ika yana zuwa masa a siffar wani mutum, ya yi magana da shi har sai ya

haddace abin da yake gaya masa. A wannan mataki sahabbai ma sukan ga

Mala’ikan a wannan lokacin.

3- Abin da Mala’ika ya kan jefa shi cikin zuciyar Manzon Allah ‫ ﷺ‬ba tare da ya

ganshi ba, kamar yadda Annabi ‫ ﷺ‬ya ce: “Haƙiƙa Ruhi Mai tsarki (Mala’ika

Jibril) ya yi busa a cikin zuciyata, cewa wani rai ba zai mutu ba face ya cinye

arziƙinsa. Don haka ku ji tsoron Allah ku kyautata nemanku. Ka da jinkirin

zuwan arziƙi ya sa ku neme shi cikin saɓon Allah. Domin ba a samun abin da

ya ke wajen Allah; face sai da yi masa biyayya”. Baihaƙi ya ruwaito wannan

Hadisi, Albani kuma ya inganta shi.

4- Wahayin ya kan zo masa a yanayi kamar ƙarar ƙararrawa – shi ne sautin

faɗuwar ƙarfe - wannan shi ya fi tsanani gare shi. Har goshinsa ya kan yi zufa

a lokacin tsananin sanyi, har taguwarsa takan durƙusa ƙasa idan yana kanta.

5- Yana ganin Mala’ika a cikin sifarsa da aka halicce shi da ita. Sai ya yi masa

wahayin abin da Allah Ya so. Hakan ya faru da shi sau biyu, kamar yadda

Allah Ya ambaci hakan a cikin Suratun Najmi.

40
6- Abin da Allah ya yi masa wahayi yayin da yake sama; a daren da aka yi

Mi’raji, na daga wajabta sallah da sauransu.

41
Matakan kira zuwa ga Allah l:

Matakin farko: Kira zuwa ga Allah a ɓoye.

Mataki na biyu: Kira a bayyane.

Mataki na uku: Kira zuwa ga Musulunci a wajen garin Makka.

Matakin farko: kira zuwa ga Allah a ɓoye.

Bayan saukar abin da ya gabata na ayoyin dake cikin suratul Mudassir, sai

Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya fara kira zuwa ga Allah, domin mutanensa sun kasance masu

tsauri, kuma ba su da addini face bautar gumaka, ba su kuma da wata hujja sai

dai cewa sun sami iyayensu ne a kan hakan, kuma ba su da wasu ɗabi’u face sai

ƙwace da jiji da kai da taurin kai, ba su da wata hanya ta warware al’amari face

aiki da takobi. Duk da haka sun kasance su ne suke jan ragamar addini a yankin

Larabawa. Su suka mamaye babbar cibiyar yankin, kuma suka taru suke kare

gwadabenta. Don haka tabbas yana daga cikin hikima; kira zuwa ga Allah a

wannan yanayi a fara shi a ɓoye, domin kada Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya farwa mutanen

Makka da abin da zai sa su tayar da jijiyoyin wuya.

Kuma yana daga cikin abin da yafi dacewa; Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya bijiro wa da

waɗanda suka fi kusanci da shi wannan addini, kamar iyalan gidansa da

abokansa, zuwa Musulunci. Sai kuwa suka amsa masa kuma ba wani shakku da

42
ya taɓa shigar su game da annabtarsa. Mutane ne da aka sani a tarihin Musulunci

da Magabata na farko (a addinin musulunci), kuma daga na gaba-gabansu akwai:

 Matar Annabi ‫ ﷺ‬kuma Uwar Muminai, Nana Khadija bint Khuwailid d

 Babban Abokinsa masoyinsa Abubakar Assidiƙ z.

 Bawansa Zaidu bin Harisaz.

 Ɗan Baffansa, Aliyu bin Abi Ɗalib z.

Bayan bibiya da bin ƙwaƙƙwafi ya bayyana cewa, waɗanda ake siffantawa da

magabata na farko a Musulunci sun kai mutum ɗari da talatin, maza da mata. Sai dai

ba a sani ba ko sun musulunta ne lokacin da ake kira zuwa ga Allah a ɓoye, ko kuma

musuluntar wasu daga cikinsu ta ɗan yi jinkiri; har sai da aka bayyana kira zuwa ga

Allah.

Shar’anta salla:

Umarni da yin Sallah yana daga cikin hunkun-hukunce na farko da suka sauka.

Ita ce bautar da aka umarci muminai da ita, ba a san su da wasu ibadu, ko wasu

umarni da hani ba, saɓanin abin da yake da dangantaka da sallah. Kawai dai wahayi

yana yi musu bayani ne game da ɓangarorin Tauhidi daban daban. Yana kwaɗaitar

da su wajen tsarkake zukata, da kwaɗaitar da su game da ɗabi’u nagari, da

makamancin haka. Kira zuwa ga Allah bai gushe ba a kan iya wasu ɗai-ɗaikun

mutane har zuwa tsawon wani lokaci. Annabi ‫ ﷺ‬bai bayyana komai ba sai abin da

43
da yake sananne ne a wajen Ƙuraishawa, har sai da ambaton Musulunci ya fantsama

a garin Makka, mutane suka fara magana a kansa.

Mataki na biyu:

Kira zuwa ga Allah a bayyane.

Farkon abin da ya sauka na umarni shi ne faɗin Allah Maɗaukakin Sarki:

٢١٤ :‫ﭐﱡﭐﱯﱰﱱﱲﱠ الشعراء‬

“Kuma ka yi gargaɗi ga danginka mafiya kusanci”. (Shu’ara 214)


Hakan ya zo ne cikin jerin zance da aka ambaci Ƙissar Annabi Musa q,

tun daga farko annabtakarsa; har zuwa ƙaurar da ya yi tare da banu Isra’ila, da kuma

ƙissar tsira da kuɓuta da suka yi daga hannun Fir’auna, da kuma mutanensa, har

zuwa dulmiyar da Fir’auna, da mutanensa a ruwa.

Kai ka ce wannan bayani an zo da shi ne tare da umarnin da aka ba Manzon Allah

‫ ;ﷺ‬na ya bayyana kira zuwa ga Allah, domin ya zama izina gare shi; na misalin abin

da zai iya samun su, shi da mutanensa; na takurawa da ƙaryatawa; yayin da suka

bayyana kiransu zuwa ga Allah l.

A kan dutsen Safa:

Annabi ‫ ﷺ‬ya hau dutsen Safa, ya ƙwalla kira cewa: “Gari ya waye! ku zo zuwa

ga wani al’amari mai girma da muhimmanci”.

44
Sai ya dinga kiran ƙabilun Ƙuraishawa, yana kiransu Ƙabila bayan Ƙabila,

“ya ku Banu Fihir, ya ku Banu Adiy, Ya ku Banu wane, ya ku banu wane, ya ku

banu Abdu Manaf, ya ku Banu Abdulmuɗɗalib”.

Yayin da suka ji sai suka ce: “Waye wannan mai kiran?”. Sai suka ce:

“Muhammad ne”, mutanen kuwa suka yi sauri zuwa gare shi, har ya zama idan

mutum ba zai iya zuwa ba yakan aika wani domin ya gano masa abin da yake faruwa.

Yayin da suka taru sai ya ce: “Ya ku ke gani idan na ce muku akwai wasu mahara

a ƙasan wannan dutsen, suna so su kawo muku farmaki, shin za ku gasgata ni? Sai

suka ce: Eh mana! Ba mu taɓa gwada ka mun same ka da ƙarya ba, ba abin da muka

san ka da shi; sai gaskiya.

Sai ya ce: “To, ni mai gargaɗi ne gare ku game da wata azaba mai tsanani, misalina

da ku kamar misalin wani mutum ne da ya ga abokan gaba, sai ya fita ya hau wani

waje mai tsayi yana dubawa iyalansa wajen da abokan gaban suke, domin kada su

afko musu, sai kuma ya ji tsoron kada su riga shi, (su cimma iyalan nasa) sai ya

dinga ƙwala kira yana cewa: “gari ya waye ku farka!”.

Sannan sai ya kira su zuwa ga addinin gaskiya. Ya kuma yi musu gargaɗi game

da azabar Allah. Ya keɓance (bayaninsa) ya kuma ya game, sai Ya ce:

45
“Ya ku taron Ƙuraishawa. Ku fanshi kanku a wajen Allah. Ku tseratar da kanku

daga wuta. Domin ni ban mallaki wata cuta ko amfani a gare ku ba, kuma ba zan

wadatar da ku komai a wajen Allah ba.

Ya ku taron Banu Ka’ab bin Lu’ayyi, ku fanshi kanku a wajen Allah. Ku tseratar

da kanku daga wuta. Domin ni ban mallaki wata cuta ko amfani a gare ku ba.

Ya ku Banu Murrata. “Ku tseratar da kanku daga wuta”.

Ya ku taron Banu Ƙusayyi. “Ku tseratar da kanku daga wuta, domin ni ban

mallaki wata cuta ko amfani a gare ku ba”.

Ya ku taron banu Abdu Manafi ku tseratar da kanku daga wuta. Domin ni ban

mallaki wata cuta ko amfani a gare ku ba, kuma ba zan wadatar muku da komai ba

a wajen Allah.

Ya ku Banu Abdu Shamsi “ku tseratar da kanku daga wuta”.

Ya ku Banu Hashim, “ku tseratar da kanku daga wuta”.

Ya ku taron Banu Abdulmuɗɗalib “ku tseratar da kanku daga wuta. Domin Ni

ban mallaki wata cuta ko amfani a gare ku ba, kuma ba zan wadatar muku da komai

ba a wajen Allah. Ku tambaye ni duk abin da kuke so na dukiyata. Amma ban

mallaka muku komai a wajen Allah.

46
Ya Safiyya bint Abdulmuɗɗalib “ba zan wadatar miki da komai ba a wajen

Allah”.

Ya ke Faɗimatu ƴar Muhammad ki tambaye ni komai kike so na dukiyata, ki

tseratar da kanki daga wuta. Domin ni ban mallakar wata cuta ko amfani a gare ki.

Kuma ba zan wadatar da ke game da komai ba a wajen Allah. Sai dai tabbas kuna

da zumunta, ni kuma zan sadar da ita da gwargwadon yadda ta cancanta.

Ahmad da Tirmizi da Nasa’i ne suka fitar da wannan Hadisin, amma asalinsa

yana cikin Sahihu Muslim.

Yayin da ya kammala wannan gargaɗi, sai mutane suka watse suka rarrabu,

(Masana tarihi) ba su ambaci wata amsa da (Mushrikan) suka bayar ba, sai dai Abu

Lahabi ya fuskanci Annabi ‫ ﷺ‬da ɓatanci ya ce: “Halaka ta tabbata a gare ka tsawon

abin da ya yi saura na wannan rana! Da ma don haka ka tara mu?! Sai wannan aya

ta sauka:

١ :‫ﭐﱡﭐﱸﱹﱺﱻﱼﱽﱠ المسد‬
“Hannaye biyu na Abu Lahabi sun halaka, kuma shi ma ya halaka” [Masad: 1].

wannan sauti ba gushe ba yana ta amo a garin Makka; har sai da faɗin Allah ya

sauka:

47
٩٤ :‫ﱡﭐﱎﱏﱐﱑ ﱒﱓﱔﱠ الحج ر‬

“Ka tsage gaskiyar abin da aka umarce ka da shi, kuma ka kawar da kanka daga
mushirikai”. Hijir 94.

Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya tashi ya na kira zuwa ga Musulunci a bayyane a wajen

tarukan mushirikai, da dandulansu, yana karanta musu Littafin Allah, yana faɗa

musu abin da sauran Manzanni suke gaya wa mutanensu:

٥٩ ‫ﱡﭐﱛﱜﱝﱞﱟ ﱠﱡﱢ ﱠ‬
“Ya mutanena! Ku bauta wa Allah! Ba ku da wani abin bautawa da gaskiya sai Shi”.

[Suratul A’araf: 59].

Sai ya fara bauta wa Allah a gaban idanunsu, har ya kasance yana sallah a

farfajiyar Ka’aba; da rana a bayyyane, kuma a gaban jama’a.

Matsayar mushirikai game da Manzon Allah ‫ﷺ‬:

Cutarwar Ƙuraishawa ta tsananta ga Annabi ‫ ﷺ‬da Sahabbansa, bayan sun bayyana

kiransu zuwa ga Allah. Daga cikin irin nau’o’in cutarwar; akwai abin da Bukhari da

Muslim suka fitar daga cikin Hadisin Ibn Mas’udz ya ce: Yayin da Annabi yake

cikin Sallah a wajen Ka’aba, Abu Jahal da wasu mutanensa suna zaune, sai sashensu

ya ce da sashe: “Waye zai tashi ya je ya ɗakko mahaifar raƙumar banu wane, ya zo

ya ɗora a gadon bayan Muhammad?”. Sai wanda ya fi taɓewa cikin mutanen

48
ya tashi ya jira har sai da Annabi ‫ ﷺ‬ya yi sujjada, sai ya ɗora ta a kan bayan Manzon

Allah ‫ ﷺ‬tsakankanin kafaɗunsa. (Ibn Mas’ud) ya ce: “Ni kuma ina gani amma ba

zan iya komai ba, ko da kuwa ina da waɗanda zasu kare ni”. Ya ce: “Sai sukai ta

dariya, suna rangaji. Manzon Allah ‫ ﷺ‬kuma yana cikin sujjada bai ko ɗaga kansa ba

har sai da Faɗima ta zo, ta jefar da ita (mahaifar) daga bayansa. Sannan ya ce: “Ya

Allah ina kawo maka ƙarar Ƙuraishawa”. Ya faɗi haka har sau uku”.

Haƙiƙa Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya bi wasu sawu guda biyu na hikima, waɗanda suka

kasance sun yi matuƙar amfani da tasiri wajen da’awarsa.

Na farko:

Ya zaɓi gidan Al’Arƙam bin Abil Arƙam Almakhzumi; ya kasance wata cibiya ce

ta da’awa, Musulmi suna taruwa a ɓoye, sai ya karanta musu littafin Allah, kuma su

iya ibadunsu da ayyukansu.

Na biyu:

Ƙaurar musulumai ta farko zuwa ƙasar Habasha.

49
Hijirar farko:

Yayin da bala’i, da fitina, da cutarwa suka tsananta ga Musulmi a garin Makka,

sai Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya ce da su: “Lalle a ƙasar Habasha akwai wani sarki ba zai taɓa

bari a zalunci kowa a wajensa ba. Ku tafi zuwa garinsa, har Allah ya yi muku buɗi

da mafita daga cikin abin da kuke ciki”.

Sai Musulmi suka fita zuwa ƙasar Habasha. Sai Najashi ya girmama su ya ba su

kariya.

Daga cikin waɗanda suka yi hijirar farko a cikin Musulmai; akwai Usman bin

Affan (R.A), da matarsa Ruƙayya ƴar Manzon Allah ‫ﷺ‬, sai kuma wasu daga cikin

manyan Sahabbai suka bi su.

Hijirar farko ta faru a shekara ta biyar bayan aiko Manzon Allah ‫ﷺ‬. Adadin

waɗanda suka yi ƙaura zuwa can, maza goma sha ɗaya ne, da mata huɗu.

50
Hijira ta biyu:

Adadin waɗanda suka yi ƙaura zuwa can; maza tamanin da biyu, da kuma mata

goma sha takwas. Dalilin hakan kuwa shi ne, waɗanda suka yi ƙaurar farko sun ji

cewa, Ƙuraishawa sun musulunta, sai wasu daga ciki suka dawo, daga cikinsu akwai:

Usmaan bin Affan da matarsa d, amma kuma sai ya zama ba su sami Ƙuraishawan

sun Musulunta ba, hasali ma sun sami musulmai a cikin bala’i mai girma da tsanani.

Wannan ya sa suka ƙara yin hijira ta biyu, a tare da su akwai adadi mai yawa na

musulmai.

Haƙiƙa Ƙuraishawa sun aika Amru bin As, da Abdullahi bin Abi Rabi’a su bi

bayansu, suna ɗauke da kyaututuka masu yawa zuwa ga Najjashi, domin ya dawo

da Musulmai. Sai dai kuma hakan ya faskara, domin kuwa Najjashi ya karɓi

muslunci, don haka ya ƙi ya mayar da su. Hasali ma, sai ya ba su aminci a cikin

ƙasarsa. Ya tabbatar da su a kan addininsu. Ya kori ƴan aiken Ƙuraishawa, ba tare

da sun cimma burinsu ba.

Musuluntar Hamza da Umar bin Khaɗɗab

Ana tsaka da wannan yanayi na tsanani, sai wasu mutane biyu masu daraja suka

shiga cikin Muslunci, waɗanda suke da cikakken kwarjini a wurin Ƙuraishawa, wato

Hamza bin Abdulmuɗɗalib, da Umar bin Khaɗɗab c. Saboda hakan sai

Ƙuraishawa suka ɗauki hanyar tattaunawa tare da Manzon Allah ‫ﷺ‬.

51
Alƙawarin zalunci, da kuma shingen Abu Ɗalib:
Al’amari ya tsananta ga Mushirikai, sai suka haɗu suka yi rantsuwa a kan cewa

ba za su ƙara auratayya tsakaninsu da Banu Hashim, da Banu Muɗɗalib ba, ba za su

ƙara yin cinikayya da su ba, ba za su ƙara zamantakewa da su ba, ba za su ƙara

cuɗanya da su ba, ba za su ƙara magana da su ba, har sai idan sun miƙa musu Manzon

Allah ‫ ﷺ‬sun kashe shi, suka kuma rubuta takarda a kan hakan.

Suka tabbatar da wannan alƙawarin, suka kuma aka rataya takardar a cikin ɗakin

Ka’aba. Aka tsare musulmai a shingen Abu Ɗalib. Takunkumi ya tsananta ga dangin

Annabi ‫ﷺ‬, aka datse musu zuwan duk wani abinci, mushirikai ba sa barin wani

abinci, ko wata cinikayya ta shiga Makka, face sai sun yi sauri sun siye, har tsanani

ya kai tsanani suka koma cin ganyayyakin bishiyoyi da fatu, har ya kai ana jiwo

sautin kukan mata da yara tun daga bayan kwarin, saboda yunwa.

Warware alƙawrin wannan takardar ta zalunci:

Bayan wucewar Shekaru uku, wannan al’amari dai yana nan a haka. A cikin watan

Muharram shekara ta goma bayan annabta, sai aka warware wannan alƙawarin, aka

kuma cire musu wannan takunkumin, hakan ya faru ne saboda a cikin Ƙuraishawa

akwai waɗanda suka yarda da wannan alƙawari da aka ɗauka, da akwai kuma

waɗanda ba su yarda ba. Sai waɗanda ba su yarda da hakan ba, suka yi ƙoƙari wajen

warware wannan yarjejeniyar.

52
Muhimmiyar fa’ida:

Shekarar baƙin ciki:

Abin da ya shahara a wajen mutane; shi ne kiran wannan shekarar da: Shekarar

baƙin ciki, saboda ita ce shekarar da Nana Khadija ta rasu, tare da Abu Ɗalib. Amma

bai tabbata ba cewa Annabi ‫ﷺ‬, ko wani daga cikin Sahabbai, ko daga cikin Tabi’ai,

ya kira wannan shekara da wannan suna.

Shekara ta goma da turo Annabi ‫ﷺ‬:

Rasuwar Abu ɗalib Baffan Manzon Allah ‫ﷺ‬:

Cuta ta tsananta ga Abu ɗalib, bai jima ba ya rasu. Rasuwarsa ta kasance a watan

Rajab; shekara ta goma da turo Annabi ‫ﷺ‬, bayan ɗage musu takunkumi da wata

shida.

An kuma ce: Ya rasu ne a watan Ramadan gabanin rasuwar Nana Khadija d

da kwanaki uku.

Rasuwar Nana khadija d:

Rasuwar Nana Khadija d: d Bayan rasuwar Abu ɗalib da kusan wata biyu

da kwana uku, a bisa saɓanin maganganu biyu, sai Uwar Muminai Nana Khadija ta

rasu. Manzon Allah ‫ ﷺ‬yana ɗan shekara hamsin a wannan lokacin.

53
Auna fahimta:

1- Ambaci rabe-raben wahayi a dunƙule, kuma ka bayyana; wanne ne ya fi girma?

----------------------------------------------------------------------------------------------------

----------------------------------------------------------------------------------------------------

2- Ka yi bayani a taƙaice game da matakin farko na kira zuwa ga Allah?

----------------------------------------------------------------------------------------------------

----------------------------------------------------------------------------------------------------

3- Ka yi Magana a kan hijira guda biyu. Kuma mene ne abu mafi girma da ya faru

a cikinsu?

4- A farkon kira zuwa Musulunci, mece ce matsayar mushirika game da kiran

zuwa ga Musulunci?

------------------------------------------------------------------------------------------------

---------------------------------------------------------------------------------------

5- Me ka sani game da shingen Abu Ɗalib? Kuma ta yaya aka warware wannan

yarjejeniyar ta zalunci?

----------------------------------------------------------------------------------------------------

----------------------------------------------------------------------------------------------------

54
Mataki Na Uku:

Kira zuwa ga Musulunci a wajen garin Makka.

Tafiya zuwa garin Ɗa’if, a watan Shawwal – Shekara ta goma bayan annabta

A watan Shawwal shekara ta goma bayan Annabta Annabi ‫ ﷺ‬ya fita zuwa garin

Ɗa’if, Ɗa’if tana nesa da garin Makka kwatankwacin mil sittin. Annabi ‫ ﷺ‬ya tafi

zuwa can a ƙasa tare da shi akwai bararren bawansa Zaidu bin Harisa.

Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya fara da shugabannin mutanen Ɗa’if, ya yi musu magana

game da Musulunci, ya kuma kira su zuwa ga Allah. Mutanen Ɗa’if suka amsa masa

da amsa mara daɗi kuma suka ce da shi: “fice daga garinmu”. Mutanen ƊA’if ba ma

su tsaya da wannan lamari ba sai da suka ruɗi wawayen cikinsu da bayinsu, suka bi

shi suna zagin shi, suna yi masa tsawa da ihu suna jifan shi da duwatsu, har suka ji

masa rauni a digadigansa, Jini ya kwarara daga jikinsa. Baƙin ciki da damuwa da

gajiya suka rufe Manzon Allah ‫ﷺ‬, har hakan ya sa ya faɗi a kan fuskarsa

maɗaukakiya. Bai farka ba sai ga Jibril nan a tsaye a kansa yana ba shi labarin abin

da mala’ikan dake lura da duwatsu yake cewa: “Idan kana so ya Muhammad ‫ ﷺ‬sai

in yi jifa in kife su da duwatsu biyu manya”, Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya amsa da cewa: “Ina

fatan Allah Ya fitar da waɗanda zasu bauta wa Allah ba tare da sun haɗa shi da wani

a wajen bauta ba daga tsatsonsu”. Bukhari da Muslim sun haɗu wajen fitar da

wannan Hadisi.

55
Tallata Musulunci ga ƙabilu da ɗai-ɗaikun mutane:

A watan Zulƙada, a cikin wannan shekarar ɗin dai, Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya dawo

garin Makka domin ya ci gaba da tallata Musulunci ga ƙabilu, da ɗaiɗaikun mutane,

saboda kusantowar lokacin tarukansu na shekara (wato aikin hajji). Mutane suna

zuwa garin Makka domin su sauke farillar aikin Hajji, sai Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya yi

amfani da wannan damar, ya dinga zuwa wajensu ƙabila bayan ƙabila, yana tallata

musu Musulunci, yana kiransu zuwa gare shi, kamar yadda ya kasance yana kiransu

tun a shekara ta huɗu bayan aiko shi. A wannan shekara ta goma haƙiƙa ya fara ne

da neman su ba shi mafaka, su taimake shi, su kare shi, har ya isar da abin da Allah

ya aiko shi da shi.

Mazaje shida daga mutan Madina:

Cikin abubuwan da ke faranta rai, mutanen Madina sukan tattauna da abokan

burminsu Yahudawan Madina, a duk lokacin da ya kasance akwai wani abu

tsakaninsu na faɗa, Yahudawan na kurin cewa akwai wani Annabi daga cikin

Annabawa; da za a turo a wannan zamani zai fito, za mu bi shi, zamu yaƙe ku da shi,

kamar yadda aka yaƙi Adawa da ƙabilar Irama.

A lokacin da Annabi ‫ ﷺ‬ya haɗu da su (wato mazaje shidan nan) sai ya ce da su:

“ku su waye?” Sai suka ce: mu mutane ne daga ƙabilar Kazraj. Sai ya ce: daga cikin

abokan Yahudawa? Wato abokan zamansu, sai suka ce: eh, sai ya ce: “shin ba kwa

56
zauna na yi Magana da ku ba?” Sai suka ce: “zamu zauna”. Sai suka zauna tare da

shi, ya bayyana musu ainihin Musulunci, da abin da yake kira zuwa gare shi, kuma

ya kira su zuwa ga Allah Maɗaukakin Sarki. Kuma ya karanta musu Alƙur’ani, nan

da nan suka gayawa juna cewa: “kun sani wannan tabbas shi ne Annabin da

Yahudawa suke muku gargaɗi da shi, kada ku sake su riga ku zuwa wajensa, sai suka

yi gaggawa wajen amsa kiransa, suka musulunta, yayin da waɗannan mutane suka

dawo garin Madina sai suka kawo saƙon Musulunci zuwa garin Madina. Sai da aka

wayi gari ba wani gida daga cikin gidajen Madina face sai ka sami ambaton Manzon

Allah ‫ ﷺ‬a ciki.

Auren Manzon Allah ‫ ﷺ‬tare da Nana A’isha d:

A watan Shawwal goma sha ɗaya bayan annabta, Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya auri A’isha,

mai gaskiya (Siddiƙa) lokacin tana ƴar shekara shida, ya tare da ita a garin Madina

a watan Shawwal shekara ta farkon bayan hijira, yayin da take ƴar shekara tara.

Isra’i da Mi’iraji:

Ibn Ƙayyim ya ce: “An yi isra’i da Manzon Allah ‫ ﷺ‬tare da jikinsa daga Masallaci

mai alfarma zuwa Baitul-Maƙdis yana haye da Buraka tare da rakiyar Jibril q,,

, sai ya sauka a nan ya yi sallah tare da Annabawa a matsayin limami, ya ɗaure

Burakra a maratayin ƙofar masallacin, sannan aka hau da shi zuwa sama a wannan

daren daga Baitulmaƙdis. Sannan aka hau da shi zuwa ga Aljabbaru (Mai tilastawa)

57
girmanSa ya girmama. Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya kusance shi, har ya kasance gwargwadon

zira’i biyu, ko kuma abin da ya fi kusa da haka. Sa’annan ya yi wahayi zuwa ga

bawanSa (Muhammad ‫ )ﷺ‬da abin da ya faɗa masa. Ya farlanta masa salloli hamsin.

Annabi ‫ ﷺ‬ya roƙe shi da a sauƙaƙa adadin sallolin, bayan Annabi Musa q ya yi

masa nuni da ya nemi a sauƙi game da adadin sallar, har aka mayar da ita guda biyar,

sannan mai shela ya yi shela: “Haƙiƙa na zartar da farillata, kuma na sauƙaƙa wa

bayina”. Bukhari da muslim sun haɗu wajen ruwayar wannan Hadisi.

Mubaya’ar Aƙaba ta farko

Ya gabata cewa wasu mutum shida daga cikin Mutanen Yasriba (Madina) sun

musulunta a lokacin aikin Hajji, kuma suka yi wa Manzon Allah ‫ ﷺ‬alƙawarin za su

isar da saƙonsa zuwa ga mutanensu.

Sai ya zama daga cikin alkhairin waccan ganawar a lokacin aikin hajji. Kuma

hakan ya kasance ne shekara ta goma bayan annabta. Mutum goma sha biyu da suka

zo a cikinsu; akwai mutum biyar cikin shidan da suka haɗu da Manzon Allah ‫ ﷺ‬a

shekarar da ta wuce. Mutum na shidan da bai samu halarta ba shi ne Jabir bin

Abdullahi, da kuma wasu mutum bakwai bayansu na da.

Bukhari da Muslim sun ruwaito daga Ubadatu bin Samit cewa: Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya

ce: “Ku zo ku yi min mubaya’a a kan ba za ku haɗa wani da Allah ba a wajen bauta.

Ba za ku yi sata ba. Ba za ku yi zina ba. Ba za ku kashe ƴaƴanku ba. Ba za ku zo da

58
ƙarya da kuke ƙirƙira tsakanin hannuwanku da ƙafafunku ba. Ba za ku saɓa min ba

cikin abin da aka sani na shari’a ba. Duk wanda ya cika waɗannan abubuwa daga

cikinku toh ladansa yana wajen Allah. Wanda kuma ya yi wani abu daga cikin hakan

to za a yi masa uƙuba a nan gidan duniya zata zama kaffara gare shi. Wanda kuma

ya yi wani abu daga cikin hakan, sai kuma Allah ya rufa masa asiri, toh al’amarinsa

yana wajen Allah, idan Ya so ya yi masa uƙuba, idan kuma Ya so ya yi musa afuwa”.

Sai suka yi masa mubaya’a a kan hakan.

59
Mus’ab bin Umair (z):

Jakadan farko a Addinin Musulunci

Bayan an kammla Mubaya’a kuma taro ya ƙare, sai Annabi ‫ ﷺ‬ya tura jakada ɗin

farko tare da waɗannan da suka yi mubaya’a zuwa Yasrib, domin ya koyar da

Musulmi Addinin musulunci ya kuma fahimtar da su ibada. Sannan ya yaɗa

Musulunci ga waɗanda ba su gushe ba suna kan shirka.

Game da wannan jakadanci sai ya zaɓi wani saurayi daga cikin samarin Musulmi,

daga waɗanda suka rigayi shiga addinin Musulunci tun farko-farko, wato Mus’ab

bin Umair (z).

Mus’abu bin Umair ya sauka a wajen Asad bin Zurara. Su biyun sun yaɗa

Musulunci a cikin Mutanen garin Yasrib cikin ƙoƙari da hamasa har ya zama an san

Mus’ab da (laƙabin) Gwanin karatu (Al-muƙri’u), Mus’abu ya zauna a gidan As’ad

bin Zurarata yana kiran Mutane zuwa Musulunci, har sai da ya zama ba wani gida

daga gidajen Madina; face sai ka sami Musulmai maza da mata a ciki.

Mubaya’ar Aƙaba ta biyu:

A taron aikin hajji na shekara ta goma sha uku da annabta, sai mutane fiye da

Saba’in na Musulman Yasriba suka zo aikin hajji. Sun zo a cikin ayarin mutanesu

na Mushrikan Yasriba. Haƙiƙa waɗannan mutane sun yi ta tambaya a tsakaninsu

yayin da suke cikin garin Yasriba, ko kuma yayin da suke tsaka da tafiya: wai har
60
zuwa yaushe ne zamu bar Manzon Allah ‫ ﷺ‬yana kaikomo, ana korar shi cikin

duwatsun Makka yana cikin yanayin tsoro? Yayin da suka zo Makka sai suka yi wata

ganawa ta sirri tsakaninsu da Manzon Allah ‫ ﷺ‬, har ta bayu ga sun yi ittifaƙi a kan

zasu haɗu a cikin ranakun tashriƙi, a wannan kwarin dake kusa da Aƙaba (wato

hanya mai duwatsu), in da jamra ɗin farko take daga Mina, kuma wannan taron ya

faru a sirrance gabaɗaya a cikin duhun dare.

Yarjejeniyar da aka cimma a mubaya’ar:

Jabir ya ce: “Sai muka ce ya Manzon Allah ‫ﷺ‬, a kan me zamu yi maka mubaya’a?

Sai ya ce: “a kan ji, da kuma yin biyayya, a yanayin nishaɗi, da kuma akasin haka,

a kan ciyarwa a lokacin wahala da na wadata, a kan umarni da kyakkyawa, da kuma

hani da mummuna, kuma a kan ku yi magana game da lamarin Allah kada ku ji

tsoron zargin mai zargi, kuma ku taimake ni idan na zo wajenku, kuma ku kare ni

daga abin da kuke kare kawunanku da matayenku da ƴaƴayenku, da haka za ku sami

sakamakon Aljanna”.

Gidan ganawa (Darun Nadwa):

Yayin da Mushirikai suka ga cewa sahabban Manzon Allah ‫ﷺ‬, sun shirya sun fice

sun tafi da iyalansu, da yara, da dukiya zuwa ga ƙabilar Ausu da Kazraj. Sai fushi

da baƙin ciki ya kama su. Tsoro da firgici ya yi ta kai-komo gare su, a cikin yanayin

da ba su taɓa tsintar kansu a ciki ba a baya. Haƙiƙa wani hatsari mai girman gaske

61
ya bayyana gare su, wanda yake barazana ga gumakansu, da tattalin arziƙinsu. Yayin

da suka zo gidan tattaunawarsu kamar yadda suka yi alƙawari. Sai Iblis ya bayyana

gare su a siffar tsoho mai shekaru, ya tsaya a dokin ƙofa, sai suka ce: “wanne tsoho

ne wannan?” Sai ya ce: “Tsoho ne daga Najad ya ji abin da kuka yi alƙawari, sai ya

zo ya halarci wajen tare da ku, domin ya ji abin da zaku tattauna, ina fatan ba za ku

rasa samun wata nasiha ko ra’ayi ba daga wajensa”. Sai suka ce: “haka ne”. Toh ka

shigo, Sai ya shiga tare da su.

Ƙoƙarin halaka Annabi ‫ﷺ‬:

Tsare-tsaren Abu Jahal:

Wannan al’amari ya faru a Darun Nadwa, domin ƙulla makircin kashe Manzon

Allah ‫ﷺ‬. Haƙiƙa sun haɗu a kan ra’ayin Abu Jahal. Abu Jahal ya ce: “na rantse da

Allah, ina da wani ra’ayi da har yanzu ban ga kun tattauna a kansa ba”. Sai suka ce:

“Wene ra’ayi ne shi ya Abul Hakam? Sai Abu Jahal ya ce: “Ina ganin mu ɗauko

saurayi ƙaƙƙarfa mai nasaba, kuma tsara daga cikin kowacce ƙabila, sannan mu

bawa kowanne saurayi daga cikinsu takobi gayawa jini na wuce, sannan su fuskance

shi, su sare shi saran mutum ɗaya, su kashe shi. Sai mu huta da shi, domin idan suka

yi hakan to jininsa ya tarwatsu tsakanin ƙabilu gabaɗaya, Banu Abdu Manafi ba za

su iya yaƙar mutanensu gabaɗaya ba. Sai wannan tsohon Najadu ɗin ya ce: “Magana

62
kam ita ce maganar da wannan mutum ya faɗa, wannan shi ne ra’ayin da bana ganin

waninsa”.

Hijirar Annabi ‫ ﷺ‬- shekara ta goma sha huɗu bayan aiko Annabi ‫ﷺ‬.

Annabi ya tafi da tsakar rana zuwa wajen Abubakar, domin su tsara fita hijira tare

da shi, Nana A’isha x ta ce: “Yayin da muke zaune cikin gidan Abubakar (z),

a lokacin da rana ta take; sai wani mai magana ya ce wa Abubakar (z): ga Manzon

Allah ‫ ﷺ‬ya zo kansa a rufe, a wani lokaci da bai kasance yana zuwa mana a irinsa

ba. Sai Abubakar z ya ce: “Mahaifina da mahaifiyata fansa ne a gare shi. Na

rantse da Allah bai zo a wannan lokacin ba, face sai a kan wani al’amari mai girma.

Sai Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya nemi izini. Sai ya yi masa izini sai ya shigo. Sai Annabi ‫ﷺ‬

ya ce wa Abubakar:z “ka fitar da waɗanda suke wajenka”. sai Abubakar (z)

ya ce: Iyalanka ne kawai. Ina fansar ka da Mahaifina da mahaifiyata ya kai Manzon

Allah ‫ﷺ‬, sai Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya ce: “To haƙiƙa nifa an yi mini izinin ficewa”. Sai

Abubakar (z) ya ce: “Zan tafi tare da kai mahaifina fansa ne gare ka ya Manzon

Allah ‫ﷺ‬. Sai Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya ce: “Na’am. Sannan ya shirya yadda za a yi hijirar

tare da shi. Sai ya koma gidansa yana jiran dare yayi.

Amma su kafiran Ƙuraishawa sun tafiyar da ranarsu wajen shiri a ɓoye domin

zartar da wannan shiri da sukashirya, wanda suka ƙulla shi a Darun Nadwa.

63
Annabi ‫ ﷺ‬ya saba yin bacci a farko farkon dare bayan sallar Isha’i, sai ya fita zuwa

Masallaci mai alfarma a cikin tsakiyar dare, ya yi sallar dare, ya kuma umarci Aliyu

(z) a wannan daren da ya kwanta a shimfiɗarsa, kuma ya rufa da koren bargonsa

ɗan Hadaram. Ya kuma gaya masa cewa ba wani abin ƙi da zai same shi.

Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya yi ƙaura:

Ƙuraishawa sun faɗi warwas cikin abin da suka shirya. Tare da baza ido da kaiwa

da komowa. Tuni Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya fita daga gida. Ya ratsa ta tsakiyar sahunsu ya

cika tafin hannunsa da ƙasa, sai ya dinga zuba ta akansu, haƙiƙa kam Allah ya ɗauke

ganinsu ba za su iya ganin shi ba. Yana ta karanta wannan ayar:

:٩ ‫ﱡﭐﲉﲊﲋﲌﲍ ﲎﲏﲐﲑﲒﲓﲔﲕﱠ ي‬
:‫س‬
“Kuma Muka sanya wata toshiya a gaba gare su, da wata toshiya a bayansu , saboda

haka Muka rufe su, sai suka zama basa gani”. (Yasin :9).

Bai bar wani mutum ɗaya daga cikinsu ba; face ya sanya turɓaya a kansa. Annabi ‫ﷺ‬

ya tafi gidan Abubakar z, sannan suka fita ta wata taga ta cikin gidan Abubakar

z a cikin dare, har sai da suka je Kogon Saur wanda yake ta ɓangaren Yaman.

Yayin da Annabi ‫ ﷺ‬ya san cewa Ƙuraishawa za su neme shi da gaske, kuma ya san

hanyar farko da za a sanya wa ido a tashin farko ita ce babbar hanyar zuwa Madina

wacce take ɓangaren hagu. Kawai sai ya bi hanyar da ta saɓa mata gabaɗaya ita ce

hanyar da take yankin kudu da Makka wacce ta fiskanci garin Yaman. Annabi ‫ ﷺ‬ya

64
bi wannan hanya tafiyar tsawon mil biyar har sai da ya kai wani kogo da aka kira da

suna Dutsen Sauru. Dutse ne da yake mai girma me hanya mai wahalar bi mai

wahalar hawa mai bishiyu da duhuwa mai yawa. Yayin da ƙafafun Manzon Allah ‫ﷺ‬

suka yi nauyi, sai Abubakar (z) ya ɗauke shi (a kafaɗa) yayin da suka isa kan

ƙololuwar dutsen. Bai gushe ba yana ɗauke da shi, har sai da ya kai shi zuwa

tsororuwar dutsen, wanda aka fi sani a tarihi da Kogon Sauru. Suka zauna a wannan

kogo tsawon kwana uku. A daren Asabar da daren Lahadi Abdullahi bin Abubakar

ya kasance yana kwana a wajensu.

Amma Ƙuraishawa kuwa haukansu ya tashi da ta tabbata cewa Manzon Allah ‫ﷺ‬

ya kuɓuce musu a safiyar ranar da za su zartar da makircin kashe shi. Farkon abin

da suka fara kuwa a wannan yanayi sai suka farwa Aliyyu (z) da duka suka ja shi

zuwa Ka’aba suka riƙe shi na ɗan wani lokaci, suna fatan ko zasu jiyo labarinsu.

Ƙuraishawa kuwa sun tabbatar da za su yi amfani da duk wata hanya da zata ba

su damar, kama Manzon Allah ‫ ﷺ‬da Abubakar sun sanya duk wata hanya da za ta

fitar da mutum daga Makka cikin yanayi na kulawa mai tsanani. Kamar yadda suka

tabbatar da cewa za su bayar da tukuici mai ɗimbin yawa, da ya kai raƙuma ɗari a

duk wanda ya kawo Annabi ‫ ﷺ‬da Abubakar z, ya dawo da su zuwa wajen

Ƙuraishawa a raye ko a mace kuma ta kowane hali.

65
A kan hanya zuwa Madina:

Sai Manzon Allah ‫ ﷺ‬da Abubakar suka tashi, Amir bin Fuhairatu ya tafi tare da

su, Abdullahi bin Uraiƙiɗ mai nuna musu hanya ya bi da su ta ɓangaren hayin ruwa,

Shiga Madina:

Urwatu bin Zubair ya ce: “Musulmi a Madina sun ji labarin fitowar Manzon Allah

‫ ﷺ‬daga Makka, sai ya kasance duk safiya suna yin sammako zuwa Harra – wani waje

ne a mashigar Madina –su tsimayi zuwansa har sai zafin rana ya mayar da su gida.

Sai watarana suka dawo bayan sun jira shi lokaci mai tsayi. Yayin da suka isa

gidajensu sai wani Bayahude ya hau kan saman gini daga cikin gine – ginensu domin

ya duba wani lamari sai ya hango Manzon Allah ‫ﷺ‬. Wannnan Bayahude bai iya

kame kansa ba face ya ƙwalla ƙara ya ce: Ya ku taron larabawa wannan shi ne

tagomashinku – wato ɗaukakarku da buwayarku – wanda kuke jiransa, sai Musulmi

suka fito suka riski Manzon Allah ‫ ﷺ‬a bayan Harra.

Ibn Ƙayyim ya ce: Sai Musulmi suka yi ta kabbara saboda farin ciki da zuwansa,

duk suka fito domin su haɗu da shi kuma suka haɗu da shi suka gaishe shi da

gaisuwar Annabta suka kewashi suna kallonsa, nutsuwa ta lulluɓe shi, ana saukar

masa da wahayi,

٤ :‫ﱡﭐﲋﲌﲍﲎﲏﲐﲑﲒﲓ ﲔﲕﲖﲗﱠ ال تحريم‬

66
“To lallai Allah Shi ne Mataimakinsa, da Jibrulu da salihan Muminai. Kuma

mala’iku a bayan wancan mataimaka ne”. Tahrim 3

Sannan Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya ci gaba da tafiya har sai da ya shiga cikin garin

Madina. Tun daga wannan lokaci aka ambaci garin Yasrib da sunan Madina.

Wannan rana ta kasance rana da ake halarta kuma wacce take shahararriya. Haƙiƙa

hanyoyi da gidaje sun kauraye da sautin godiya ga Allah da tasbihi.

Manzon Allah ‫ ﷺ‬ba zai wuce gida daga cikin gidajen mutanen Madina ba, face

sai mai gidan ya kama linzamin taguwarsa ya kira shi da ya sauka a wajensa. Amma

wannan taguwa ba ta gushe ba tana tafiya, har sai da takai wajen masallacinsa, sai ta

durƙusa, sannan ta yunƙura ta tashi, ta ɗan yi tafiya kaɗan sannan ta dawo wajen

farko ta durƙusa. Sai Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya sauka a wajen kawunnansa daga cikin

Banun Najjar. Annabi ‫ ﷺ‬ya ce: “wanne gida ne ya fi kusa daga cikin gidan

ahalinmu?” sai Abu Ayyuba ya ce: “Ni ne” ya Manzon Allah ‫ﷺ‬. Sai Annabi ‫ ﷺ‬ya

sauka a wajen Abu Ayyuba Al’ansari. Bukhari ya ruwaito wannan Hadisi.

67
Auna Fahimta

Yi Magana game da mataki na uku na da’awa, (kira zuwa ga Addini) a waɗannan

batutuwa masu zuwa:

 Tafiya Zuwa Garin Ɗa’ifa

----------------------------------------------------------------------------------------------------

----------------------------------------------------------------------------------------------------

 Isara’i da Mi’iraji

----------------------------------------------------------------------------------------------------

----------------------------------------------------------------------------------------------------

 Mubaya’ar Aƙaba Ta Farko Da Ta Biyu

----------------------------------------------------------------------------------------------------

----------------------------------------------------------------------------------------------------

 Abin da ya faru a Darun Nadwa

----------------------------------------------------------------------------------------------------

--------------------------------------------------------------------------------------------------

Hijirar Annabi ‫ ﷺ‬Zuwa Madina

----------------------------------------------------------------------------------------------------

---------------------------------------------------------------------------------------------------
68
Manzanci A Madina
Gina Masallacin Annabi ‫ﷺ‬.

Haɗa ƴan-uwantaka Tsakanin Musulmi.

Umarni da a Yi yaƙi.

Annabi ‫ ﷺ‬A Garin Madina

 Ayyukan da Annabi ‫ ﷺ‬ya yi a lokacin da ya isa zuwa garin Madina.

 Saraya (wato tawagun yaƙin da Manzon Allah bai halarta ba) da kuma sauran

yaƙe-yaƙe.

 Wafatinsa .

Gina masallacin Annabi ‫ﷺ‬

Farkon abin da Annabi ‫ ﷺ‬ya fara da shi lokacin da ya isa Madina shi ne ginin

Masallacinsa. Annabi ‫ ﷺ‬ya zaɓi wurin da taguwarsa ta sauka, sai ya sayi wajen daga

wajen wasu yara biyu marayu masu filin, ya fara wannan ginin masallaci da kansa,

ya kasance yana ɗaukar tubali da duwatsu da kansa, yana cewa:

“Ya Allah ba wata rayuwa in ba rayuwar lahira ba # Ka gafarta wa Ansarawa da

Muhajirai”.

69
Haɗa ƴan-uwantaka Tsakanin Musulmi

Bayan ɓangaren ginin masallacinsa, sai Annabi ‫ ﷺ‬ya kama wani lamarin daban

wanda tarihi ya rubuta. Wannan shi ne batun haɗa ƴan-uwantaka tsakanin mutanen

Madina da mutanen Makka a kan taimakon juna, da kuma cin gadon juna bayan

mutuwa, duk da kasancewarsu ba ma’abota zumunta ba, yayin da Allah ya saukar

da faɗinsa:

: ٧٥ ‫ﱡﭐﳈﳉﳊﳋﳌﳍﳎﳏﳐﳑﳒﳓﳔﳕﳖﱠ‬
“Kuma ma’abuta zumunta, sashensu ne waliyyan sashe a cikin Littafin Allah. Lalle

Allah ne ga dukkan komai Masani”. (Anfal 75) sai aka mai da cin gado zuwa ga

zumunta, ba ga ƙulla ƴan uwantaka ba.

Yarjejeniyar Ƙawancen Musulunci:

Kamar yaddda Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya ƙulla ƴan uwantaka ta Musulunci tsakanin

Muminai, haka nan ya ƙulla wata yarjejeniya wadda ta kawar da abin da yake

tsakanin Larabawa na adawa, da ƙiyayya tun zamanin jahiliyya. Da irin abin da suke

kai na ƙabilanci da zalunci. Da haka ya samu damar gina haɗin kan Musulunci na

bai ɗaya.

Bayar Da Izinin Fita Yaƙi:

Ƙuraishawa ba su daina barazana ga Musulmai ba, duk da an yi hijira, Sai

al’amarin ya ƙara ƙamari. Kullum Ƙuraishawa na aika saƙo ga Mutan Madina cewa:
70
“Haƙiƙa kun bai wa abokin rigimarmu mafaka. To muna yi muku rantsuwa da Allah,

ko dai ku yaƙe shi, ko ku fitar da shi, ko kuma mu taho muku da tawaga gabaɗaya

mu kakkashe mayaƙanku mu ribace matanku”.

Ita kuma wasiƙarsu zuwa ga Muhaijirai tana cewa: “Kada ku ruɗu cewa wai kun

kuɓce mana zuwa garin Yasriba. Tabbas za mu zo mu kakkaɓe ku. Mu yi mu ku

kisan ƙare dangi a cikin ƙuryar gidanku”. Ana cikin wannan yanayi kawai sai aya ta

sauka tana bayar da izinin a fita a yi yaƙi, Allah Ya ce:

٣٩ :‫ﱡﭐﱁﱂﱃﱄﱅﱆﱇﱈﱉﱊﱋﱌﱠ الحج‬
“An yi izini ga waɗanda ake yaƙar su da cewa lalle an zalunce su, kuma lalle ne

Allah, haƙiƙa, Mai ikon yi ne a kan taimakonsu” (Hajji 39) Allah Ya ƙara cewa:

‫ﱡﭐ ﱴ ﱵ ﱶ ﱷ ﱸ ﱹ ﱺ ﱻ ﱼ ﱽ ﱾ ﱿ ﲀ‬

٤١ :‫ﲁﲂ ﲃﲄﲅﲆﱠ الحج‬


“Waɗanda suke idan Muka ba su iko a cikin ƙasa, sai su tsaida salla, kuma su bayar

da zakka kuma su yi umarni da abin da aka sani, kuma su hana abin da ba a sani ba.

Kuma aƙibar al’amura ga Allah take”. (Hajji 41).

71
Auna Fahimta

Yi magana a kan manyan ayyuka a Madina, tare da kawo hujjoji daga darusan da

ka koya a baya.

----------------------------------------------------------------------------------------------------

----------------------------------------------------------------------------------------------------

---------------------------------------------------------------------------------------------------

72
Ƙananan Rundunoni Da Kuma Yaƙe-yaƙe Kafin Badar.

Akwai jimillar waɗannan rundunoni (saraya) da yaƙe yaƙe gabanin yaƙin Badar,

kamar haka:

1- Sariyya mai suna Saiful bahar. An yi ta a shekara ta farko bayan hijira, Hamza

bin Abdulmuɗɗalib (z) shi ne wanda ya jagorance ta.

2- Sariyyar Rabig: An yi ta a shekara ta farko bayan hijira Ubaidatu bin Haris

bin Abdulmuɗɗalib shi ne wanda ya jagorance ta.

3- Sariyyar Kharra: A shekara ta farko bayan hijira Sa’ad bin Abi Waƙƙas (z)

shi ne wanda ya jagorance ta.

4- Yaƙin Abwa’i ko kuma Waddan: An yi shi a shekara ta biyu bayan hijira,

Manzon Allah ‫ ﷺ‬shi ne wanda ya jagoranci yaƙin da kansa. Shi ne yaƙi na

farko da Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya yi, Hamza bin Abdulmuɗɗalib shi ne wanda yake

ɗauke da tuta a wannan lokaci.

5- Yaƙin Buwaɗ: A shekara ta uku bayan hijira. Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya jagoranci

yaƙin da kansa.

6- Yaƙin Safwan: A shekara ta biyu bayan hijira Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya jagoranci

yaƙin da kansa.

7- Yaƙin Zul’ashira: A shekara ta biyu bayan hijira Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya jagoranci

yaƙin da kanshi.

73
8- Sariyyar Nakhla: A shekara ta biyu bayan hijira, Abdullahi bin Jahsh (z)

ya jagoranci yaƙin, tare da mutum goma sha biyu daga cikin muhajirai, su

kuma (kafirai) sun kashe Amru bin Ahadrami. Shi ne farkon wanda aka fara

kashewa a cikin Musulunci, aka kama Usman bin Abdullahi bin Mugira, da

Hakam bin Kaisan bararran bawan Mugira. Su biyun su ne ribatattun yaƙi na

farko a Musulunci.

Manufofin Ƙananan Tawagu da Sauran Yaƙe-yaƙe.

Game da wannan saraya da yaƙe – yaƙe akwai manufofi kamar haka:

1- Gano duk wasu hanyoyi dake kewaye da birnin Madina, da duk wasu hanyoyi

da za su kai mutum birnin Makka.

2- Ƙulla yarjejeniya tare da ƙabilun da suke zaune a kewayen waɗannan hanyoyi.

3- A sa Mushirikan Yasriba, da Yahudawa, da Larabawan ƙauye su gane ƙarfin

Musulmi.

4- A saka Ƙuraishawa su fahimci haɗarin dake fuskantar kasuwancinsu da kuma

buƙatunsu.

Wajabta Yin Yaƙi

A wannan lokaci bayan Sariyyar Abdullah bin Jahash sai Allah ya wajabta yin

yaƙi cikin faɗinSa kamar haka:

74
:‫ﱡﭐﲾﲿﳀﳁﳂﳃ ﳄﳅﳆﳇﳈﳉﳊﳋﳌﱠ ال بقرة‬
١٩٠
“Kuma ku yaƙi waɗanda suke yaƙinku, a cikin hanyar Allah, kuma kada ku yi

tsokana, lalle ne Allah ba Ya son masu tsakona” (Baƙara: 190)

75
Auna Fahimta

 An samu yaƙe yaƙe, da ƙananun rundunonin yaƙi (saraya) masu yawa kafin

yaƙin Badar. Ka ambaci manufa game da faruwar hakan.

------------------------------------------------------------------------------------------------

------------------------------------------------------------------------------------------------

-----------------------------------------------------------------------------------------------

-----------------------------------------------------------------------------------------------

 Me ka fahimta game da wannan aya?

 ‫ﳅ ﳇ ﳈﳉ ﳊ ﳋ ﳌ ﱠ‬
‫ﳆ‬ ‫ﱡﭐﲾﲿﳀﳁﳂﳃﳄ‬
١٩٠:‫ال بقرة‬
“Kuma ku yaƙi waɗanda suke yaƙinku, a cikin hanyar Allah, kuma kada ku yi

tsokana, lalle ne Allah ba Ya son masu tsakona” (Baƙara: 190)

------------------------------------------------------------------------------------------------

------------------------------------------------------------------------------------------------

----------------------------------------------------------------------------------------------

-----------------------------------------------------------------------------------------------

76
Manyan Yaƙe–yaƙen Annabi ‫ ﷺ‬Da Kuma Sulhun Hudaibiyya.

Yaƙin Badar babba.

Yaƙin Uhudu.

Yaƙin Gwalalo (Ahzab).

Sulhun Hudaibiyya.

Yaƙin Khaibar.

Yaƙin Mu’uta.

Yaƙin Hunaini.

Yaƙin Tabuka (Usurat).

Yaƙin Badar babba:

A Ramadan, shekara ta biyu bayan Hijira.

Dalilin Yaƙin:

Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya ji cewa ayarin Ƙuraishawa ya taho daga ƙasar Sham zuwa

Makka. Ayarin da Abu Sufyan bin Harb yake jagoranta, tare da mutanen da ba su

wuce mutum arba’in ba. Haƙiƙa Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya so ya kai farmaki ga wannan

ayari, ya ƙwace iko da ita dan ramuwa ga abin da Mushirikai suka yi wa Musulmai;

yayin da su suka tafi hijira zuwa Madina. Manzon Allah ya faɗa wa Sahabbansa:

77
“Wannan ayarin Ƙuraishawa ne. A cikinsa akwai dukiyarsu. Sai ku fita zuwa gare

ta”.

Abubuwan Da Suka Faru:

Hakan ya faru uku ga watan Ramadan, a shekara ta biyu bayan hijira. Adadin

Musulmai ya kai ɗari uku da goma sha uku. Tare da su akwai dawakai biyu da

raƙuma saba’in. Sai Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya bar Abdullahi bin Ummu Maktum (z) a

matsayin Magajin Garin Madina. Yayin da Abu Sufyan ya sanu labarin Annabi ‫ﷺ‬,

da sahabbansa, sai ya aika Damdam bin Amru Algifari zuwa mutan Makka, yana

neman taimakonsu. Damdam ya isa wajen mutan Makka, ya kwarmata ihu yana

cewa: “Ya ku taron Ƙuraishawa, Muhammad da Sahabbansa sun nufi dukiyarku,

bana ganin zaku iya risker ta”. Sai Mushirikai suka yi wani yunƙuri mai tsanani,

suka yi shirin yaƙi tare da mutum ɗari tara da hamsin. A tare da su akwai dawaki

ɗari, da raƙuma ɗari bakwai.

Labari ya iso wa Manzon Allah ‫ ﷺ‬cewa, ayarin Abu Sufyan ya sauya hanyar da

yake bi, kuma zai iya isa kashe gari, ko kuma bayan kashe gari. Sai Abu Sufiyan ya

aike wa mutan Makka cewa: “Allah Ya tseratar musu da ayarinsa, kuma ba wani

buƙatar taimako; Abu Jahal ransa ya ɓaci ya ce: “Na rantse da Allah ba za mu koma

ba har sai mun isa zuwa Badar”.

Manzon Allah ya tara sahabbansa ya ce da su: “Haƙiƙa Allah ya saukar da faɗinsa:

78
‫ﱡﭐﲖﲗﲘﲙﲚﲛﲜﲝﲞﲟﲠﲡﲢﲣﲤ‬

‫ﲥ ﲦ ﲧ ﲨ ﲩ ﲪ ﲫﲬ ﲭ ﱠ‬
٧ :‫األن فال‬
(Kuma a lokacin da Allah Yake yi muku alƙawari da ɗayan ƙungiya biyu, cewa lalle

ɗaya taku ce, kuma kuna gurin cewa lalle ƙungiya wadda bata da ƙaya ta kasance

gare ku, kuma Allah Yana nufin ya tabbatar da gaskiya da kalmominSa, kuma ya

katse ƙarshen kafirai.) (Anfal 7).

Sai Miƙdadu bin Aswad ya miƙe ya ce: “Ya Manzon Allah ‫ﷺ‬, ka zartar da abin

da Allah ya umarce ka da shi. Na rantse da Allah ba zamu faɗi irin abin da Banu

Isra’ila suka gaya wa Annabi Musa ba:

:‫ﱡﱃﱄﱅﱆﱇﱈﱉﱊﱋﱌﱍﱎﱏﱐﱑﱠ الم ائدة‬


٢٤
“Ba za mu shige ta ba har abada matuƙar sun dawwama a cikinta, sai ka tafi kai da

Ubangijinka domin ku yi yaƙi. Lalle mu, muna nan a zaune”. (Ma’ida 24), ka zartar

kawai tabbas mu muna tare da kai. Kai ka ce an yaye wa Manzon Allah ‫ ﷺ‬wani baƙin

ciki yayin da ya ji wannan magana.

Mushirikai sun iso Badar. Suka kuma sauka a gaɓa ta nesa, Amma Musulmi kuma

sai suka sauka a gaɓa ta kusa.

Sai Musulmai suka tashi suka kafa wa Manzon Allah tanti a kan wani ɗan tudu,

harshensa kuwa bai gushe ba yana motsi, da addu’a yana mai cewa: “Ya Allah ga

79
Ƙuraishawa nan. Haƙiƙa sun zo da jijidakai suna ƙaryata ManzonKa. Ya Allah ina

roƙon Ka nasarar da ka yi min alƙawari. Ya Allah idan har aka kashe wannan jama’a

a yau (wato Sahabbai) to ba za a bauta maka a ban ƙasa ba”. Har mayafinsa ya faɗi

daga kan kafaɗunsa. Abubakar yana mai cewa da shi: “Ya Manzon Allah ‫ ﷺ‬haƙiƙa

Allah zai zartar da abin da ya yi maka alƙawari”.

Sai Musulmai suka rusa rijiyar – bayan sun kama iko da ita, kuma sun sha daga

ruwan- domin kada Mushirikai su sami damar shan ruwan.

Kafin a fara gwabzawa, sai mutum uku daga cikin gwarazan Ƙuraishawa suka fito

su ne: Utuba bin Rabi’a da ɗan’uwansa Shaiba da ɗansa Walid, suna neman waye

zai yi fito-na-fito da su daga cikin Musulmai. Sai mutum uku daga cikin mutanen

Madina suka fito, sai waɗannan gwaraza suka yi ihu suna masu cewa: “Ya kai

Muhammad, ka fito mana da sa’anninmu, daga cikin mutanenmu, daga ƴaƴan

baffanmu, Sai Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya gabatar da Ubaidatu bin Haris da Hamza bin

Abdulmuɗɗalib da Aliyu bin Abi Ɗalib”.

Sai Hamza ya tunkari Shaiba ya kashe shi. Aliyu kuma ya tunkari Walid ya kashe

shi. Ubaidatu ya tunkari Utuba kowanne daga cikinsu ya ji ma ɗan’uwansa rauni, sai

Hamza da Aliyu suka farwa Utuba suka kashe shi.

Yaƙi ya tsananta aka yi gumurzu, haƙiƙa Allah ya taimaki Muslmai da saukar

Mala’iku suna yaƙi tare da su: Allah Ya ce:

80
‫ﱡﭐﱩﱪ ﱫ ﱬ ﱭ ﱮ ﱯ ﱰ ﱱ ﱲ ﱳ ﱴ ﱵ ﱶ ﱷ‬

١٢٥ :‫ﱸ ﱹﱠ آل عمران‬


“Na’am! Idan kun yi haƙuri, kuma kuka yi taƙawa, kuma suka zo muku da

gaggawarsu, irin wannan, Ubangijinku zai ƙare ku da dubu biyar daga mala’iku

masu alama”. (Ali Imaran 125)

Wannan yaƙi ya ƙare da samun nasarar Musulmai, da cin galabar Mushirikai, ta

yadda aka kashe mutum saba’in aka kama fursunonin yaƙi saba’in daga cikinsu.

Amma waɗanda suka yi shahada daga cikin Musulmai, mutum goma sha huɗu ne.

Haƙiƙa Musulmai sun jefa gawarwakin Mushirikai a cikin rijiya. Fursunonin yaƙi

kuma Manzon Allah ‫ﷺ‬, ya karɓi Dirhami dubu huɗu game da fansar kowanne ɗaya

daga cikinsu. Wanda kuwa bai mallaki abin da zai iya fansar kansa da shi ba, sai ya

ba su mutum goma goma daga cikin yaran Musulmai, domin su koyar da su rubutu

da karatu.

Yaƙin Uhudu.

Shekara ta uku bayan hijira.

81
Dalilin Yaƙin:

Ƙuraishawa sun ji ɗacin samun nasarar da Musulmai suka yi a kansu a yaƙin

Badar, sai suka so su ɗauki fansar galabar da aka yi a kansu. Sai suka yi tanadi domin

su ƙara haɗuwa da Musulmai, a wani lokacin domin su rama galabar da aka ci a

kansu.

Abubuwan da suka faru:

Safwan bin Umayya, da Ikrima bin Abu Jahal, da Abbdullahi bin Rabi’atu, sun

tafi wajen Abu Sufyna suna neman dukiyar wannnan ayarin da ake kasuwanci da ita,

domin su samu damar haɗa runduna. Ribar wannan ayari kuwa ta kai kusan Dinare

dubu hamsin, sai Abu Sufyan ya bi ra’ayinsu na yaƙar Musulmai, suka dawo suna

neman waɗanda zasu zuga mazaje a cikin ƙabilu (domin su fito yaƙi). Ƙuraishawa

suka tara mayaƙa dubu uku.

Sai wannan runduna ta fito har ta isa Zul hulaifa (sunan wani wuri ne) a kusa da

Uhud.

Yayin da Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya ji labarin zuwan Mushirikai, sai ya nemi shawarar

sahabbansa. Dattawan cikinsu suka ce: “Mu yi yaƙinmu a nan”. Samari suka ce: “Mu

fita mu haɗu da su a waje”. Sai Manzon Allah‫ ﷺ‬ya bi ra’ayin samari.

Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya sanya kayan yaƙinsa ya fita ya tunkari Mushirikai. Annabi ‫ﷺ‬

ya fita daga Madina tare da mutum dubu ɗaya, sai Abdullahi bin Ubayyu bin Salulu
82
ya sulale tare da ɗaya bisa ukun wannnan runduna yana cewa: “Mu ba mu san a kan

me za mu kashe kawunanmu ba”.

Musulmai suka ya-da-zango a wajen dutsen Uhudu. Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya shirya

yadda za a yi yaƙin cikin hikima. Ya sanya mutum hamsin a kan dutsen. Kuma ya

umarce su da ka da su motsa ko ina, ko da sun ci nasara, ko kuma an ci galaba a

kansu.

An fara gwabza yaƙi, Hamza ya yi yaƙi yaƙi irin na gwaraza. Jubairu bin Muɗ’im

ya yi wa bawansa Wahashi alwaƙarin zai ƴanta shi; idan har ya kashe Hamza, ai

kuwa tabbas ya kashe shi ɗin.

Maharba daga kan dutse suka ga anci nasara a kan Mushirikai. Sai sashensu ya

ce: “Ba wata buƙatar mu tsaya fa”. Suka manta da wasiyyar da Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya

yi musu, lallai kuwa wanda yake jagorantarsu ya tunasantar da su game da ita. Amma

ba su ji maganarsa ba, suka yi gaggawa wajen tattara ganima.

Khalid ya hango saukar waɗannan maharba daga kan dutsen, take kuwa ya taso

tare da wani sashe na Mushirikai, suka kewayo ta bayan dutsen suka afka wa

Musulmai ta baya, sai kuwa Muslmai suka kama gudu. Tutar Mushirikai ta ɗaga a

wannan karon, yayin da rundunar Mushirikan suka ga haka sai suka dawo da

farmakinsu.

83
Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya yi kira cikin Sahabbansa, sai mutum talatin daga cikin

Sahabbansa suka taru, sai ya ƙara tayar da rundunar ya tsara ta, ya nufi Mushirikan

domin ya mayar da nasararsu zuwa faɗuwa, yayin da suka yi nisa suka ƙara

nisa……sai ya bar su ya dawo Madina.

84
Yaƙin Gwalalo (Ahzab):

Shekara ta biyar bayan hijira.

Yahudawan Banu Nadir sun so su ɗauki fansa daga Annabi ‫ﷺ‬, da sahabbansa

waɗanda suka fitar da su daga gidajensu daga Madina, suka sanya babban abin da

ya dame su; shi ne su ta da tawaga mai yawa, mai ƙarfi da zata taka birki ga Manzon

Allah ‫ﷺ‬, da sahabbansa.

Shuwagabannin Banun Nadir suka fita zuwa wajen Ƙuraishawa; suka kira su

zuwa ƙara yaƙar Musulmai, sun kuwa ci nasara wajen ƙulla yarjejeniya da su, Banu

Nadir ba su wadatu da wannan yarjejeniya ba kaɗai, sai da suka ƙara tafiya zuwa ga

Banu Gaɗafan, suka kwaɗaitar da su a kan su zo su haɗe tare da su, da Ƙuraishawa,

suka ruɗe su da cewa; zasu ba su ƴaƴan itacen wannan shekara na dabinon Khaibar

idan har sun ci nasara.

Yaƙin Gwalalo:

Haka wannan runduna ta tara mayaƙa kimanin dubu goma inda Abu Sufyan bin

Harb ya jagoranta. Hakan ya faru a shekara ta biyar bayan Hijira, a watan Shawwal.

Sai Salman Alfarisi ya ba wa Manzon Allah ‫ ﷺ‬shawara, da a haƙa rami a kewayen

Madina, sai Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya gamsu da ra’ayinsa, kuma ya yi aiki da shi.

85
(Ana cikin tsaka da aikin haƙa), Sai Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya sami wani dutse mai girma

da ya tare gaban Salman har gatura na ƙarfe suna kakkaryewa. Sai Manzon Allah ‫ﷺ‬

Ya zo wajen dutsen. Ya ce: “Bismillahi”. Ya doki dutsen take dutsen ya tsatstsage

ya yi walƙiya mai haske. Ya ce: “Allahu Akbar…..ga fadar Ƙasar Sham can! Na

rantse da Ubangijin ka’aba”, sannan ya ƙara wani dukan daban, sai ya ƙara yin

walƙiya sai ya ce: Allahu Akbar…….ga fadar Farisa can! Na rantse da Ubangijin

Ka’aba”.

Mushirikai basu sami wata hanya da zasu shiga Madina ba (Saboda wannan

rami), Har sai da Huyyi bin Akhaɗab ya zo wanda ya je wajen Banu Ƙuraiza a ɓoye,

ya gamsar da su a kan su ɓata yarjejeniyar da banu Ƙurazai suka yi da Musulmai.

Ikrimatu bin Abi Jahal, da wani ɗan adadi na Mushirikai suka sami damar shiga

garin Madina amma sai dai Aliyyu ya tsaya musu a madakata aka kashe wanda aka

kashe, wanda ya gudu ya gudu. Ikrima na daga cikin waɗanda suka gudu.

Daga ƙarshe dai Muminai suka ci nasara. Haƙiƙa duk wani abu da zai haɗa kan

Mushirikai ya lalace, ya zama babu aminci da yarda a tsakanin ƙabilu. Kuma Allah

ya aiko da wata iska mai ƙarfi, ta tsittsige bukkokinsu. Ta lalata guzirinsu, ta

karkashe wutarsu. Tsoro ya shiga zuƙatan Mushirikai suka gudu zuwa garin Makka

a firgice.

86
Yaƙin Ahzab ba wani gumurzu da aka yi a fagen yaƙi ba, sai dai gumurzun

ƙwaƙalwa ne, da jarraba mutane da kuma duba abin da ke cikin zuciyoyi. Allah

Maɗaukakin Sarki Ya saukar da ayoyi:

‫ﱡﭐ ﱁ ﱂ ﱃ ﱄ ﱅ ﱆ ﱇ ﱈﱉ ﱊ ﱋ ﱌ ﱍ ﱎ ﱏ ﱐﱑ ﱒ ﱓ‬

‫ﱔ ﱕ ﱖ ﱗ ﱘ ﱙ ﱚ ﱛ ﱜ ﱝ ﱞ ﱟ ﱠﱡ ﱢ ﱣ ﱤ‬

‫ﱥﱦﱧﱨﱩﱪﱫﱬﱭﱮﱯﱰﱱﱲﱳﱴﱵﱶ‬

٢٥ - ٢٣ ‫ﱷ ﱸﱹ ﱺ ﱠ‬
“Daga Muminai akwai waɗansu mazaje da suka gasgata abin da suka yi wa Allah

alƙawari a kansa, sa’annan a cikinsu, akwai wanda ya biya buƙatarsa, kuma daga

cikinsu kwai wanda ke jira. Kuma basu musanya ba, musanyawa. (23) Domin Allah

Ya saka wa masu gaskiya da gaskiyarsu, kuma Ya azabtar da munafikai idan ya so,

ko Ya karɓi tuba a kansu, lalle Allah Ya kasance Mai gafara Mai jinƙai. (24) Kuma

Allah Ya mayar da waɗanda suka kafirta da fushinsu, ba su sami wani alheri ba.

Allah Ya isar wa Muminai daga barin yaƙi. Kuma Allah Ya kasance Mai ƙarfi

Mabuwayi (25)” Al’ahab: 23- 25).

87
Sulhun Hudaibiyya:

Sulhun Hudaibiyya wata yarjejeniya da ta afku tsakanin Musulmai, da

Ƙuraishawa a watan Zul ƙi’ida a shekara ta shida bayan hijira, kusa da wani waje da

ake kira Hudaibiya, kafin shiga Makka. A wannan shekarar Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya yi

mafarki cewa, shi da sahabbansa sun shiga Masallaci Mai Alfarma (Ka’aba), kuma

suna yin ɗawafi a Ɗakin Allah. Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya bai wa Sahabbansa labarin

hakan, sai suka yi farin ciki mai yawa.

Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya fita tare da matarsa Ummu Salama a cikin Musulmai dubu

ɗaya da ɗari huɗu, suka fuskanci garin Makka domin su yi aikin umra na farko, tun

bayan da suka yi hijira suka ɗauki makamai domin kare kansu daga sharrin

Ƙuraishawa.

Yayin da suka iso Zulhulaifa, sai suka ɗauki harama, da waɗanda suke tare. Sai

Annabi ‫ ﷺ‬ya aika Busur bin Sufyan zuwa garin Makka, domin ya jiyo masa labarin

Ƙuraishawa, da kuma abin da zasu aikata.

Yayin da Musulmai suka isa garin Usfan (wani waje ne tsakanin Makka da

Madina), sai Busur ya zo musu da labaran shirin Mushirikai na dakatar da Musulmai,

da hana su shiga garin Makka.

Sai Annabi ‫ ﷺ‬ya nemi shawarar sahabbansa. Abubakar a ya bayar da shawarar

a tafi kawai zuwa Makkan, domin a yi umra a yi ɗawafi a ɗakin Ka’aba. Ya ce: “duk

88
wanda ya dakatar da mu, sai mu yaƙe shi” sai Annabi ‫ ﷺ‬ya ce: “Toh mu tafi da sunan

Allah”.

Sai Annabi ‫ ﷺ‬ya tafi tare da sahabbansa suka nufi Makka. Annabi ‫ ﷺ‬ya ce: “na

rantse da wanda raina ke hannunsa; ba zasu roƙe ni wani abu ba; da za a girmama

iyakokin Allah a ciki face sai na ba su shi”.

Yayin da Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya sauka a Hudaibiyya, sai ya aika Usman zuwa ga

Ƙuraishawa, ya ce da shi: “Ka ba su labarin cewa; mu ba yaƙi muka zo ba, mun zo

ne mu yi umra, kuma ka kira su zuwa Musulunci”.

Sai Usman ya tafi, sai ya gamu da wasu Ƙuraishawa. Sai suka ce da shi: “Ina

zuwa haka?” Sai ya ce: “Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya aiko ni wajenku, da in kira ku zuwa ga

Allah, da Musulunci. Kuma in gaya muku cewa ba yaƙi ya zo ba, kawai dai mun zo

mu yi umara ne”.

89
Bai’atur Ridwan (Wato Mubaya’ar Da Allah Ya Tabbatar Da YardarSa Ga

Muminai)

Ƙuraishawa sun riƙe Usman domin ya yi jinkirin dawowa wajen Musulmi.

Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya ji tsoron abin da zai same shi. Musamman ma bayan labarin

cewa an kashe shi ya yaɗu. Annabi ‫ ﷺ‬ya kira da a zo a yi mubaya’a. Sai kuwa suka

yi gaggawa zuwa wajensa yayin da yake ƙasan wata bishiya. Musulmi suka yi masa

mubaya’a a kan ba zasu gudu ba. Wannan ita ake kira da Bai’atur Ridwan, wacce

faɗin Allah Ya saukar da ayar nan a kanta:

‫ﱡﭐ ﱾ ﱿ ﲀ ﲁ ﲂ ﲃ ﲄ ﲅ ﲆ ﲇ ﲈ ﲉ ﲊ ﲋ ﲌ ﲍ‬

١٨ :‫ﲎﲏﲐﲑﲒﱠ ال فتح‬
“Lalle ne, haƙiƙa, Allah Ya yarda da Muminai a lokacin da suke yi maka mubaya’a

a ƙarƙashin itaciyar nan, domin Ya san abin da ke cikin zuƙatansu, sai Ya saukar da

nutsuwa a kansu, kuma Ya saka musu da wani cin nasara makusanci”. (fatahi 18)

Sai Ƙuraishawa suka aika Urwatu bin Mas’ud, domin ya tattauna da Manzon

Allah ‫ﷺ‬. Shi kuma Suhail bin Amru domin ya ƙulla sulhu. Yayin da Annabi ‫ ﷺ‬ya

gan shi sai ya ce: “Haƙiƙa al’amarinku ya sauƙaƙa”. Mutanen suna son sulhu tun da

suka aiko wannan mutumin. Sai Suhail ya yi magana mai tsayi daga bi-sani suka

haɗu a kan dokokin sulhun.

90
Wannan tattaunawa da suka yi ittifaƙi a kai ita ake kira wajen malaman tarihi da

Sulhu. Ga abin da aka yanke kamar haka:

 Ya kasance za a daina yaƙi tsakanin ɓangarorin biyu tsawon shekara goma.

Musulmi su koma Madina a wannan shekarar; ba za su yi umara ba har zuwa shekara

mai zuwa.

Muhammad ‫ ﷺ‬ya mayar da duk wanda ya zo wajensa daga cikin ƙuraishawa;

wanda ya musulunta ba tare da sanin ahalinsa ba, kuma Ƙuraishawa ba za su mayar

da duk wanda ya koma wajensu ba bayan ya yi ridda.

Duk wanda ya so ya shiga yarjejeniyar Ƙuraishawa zai iya shiga (ya amfana.),

Wanda ya so ya shiga ƙarƙashin yarjejeniyar Muhammad ‫ ﷺ‬zai iya shiga, sharaɗi

kada ya zama daga cikin Ƙuraishawa.

Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya yarda da sharruɗan wannan yarjejeniya, wacce wasu suka

ga akwai tauye haƙƙi, da ƙasƙantar da Musulmai a ciki. A cikin masu wannan ra’ayi

akwai Umar a wanda ya ce da Manzon Allah ‫ﷺ‬: “Shin ba a kan gaskiya muke ba?

Kuma maƙiyanmu ba a kan ɓata suke ba?”. Sai ya ce: “Na’am”. Umar a ya ce:

“To a kan me zamu fifita duniya cikin Addininmu? Haka zamu koma ba ba tare da

mun tsaya Allah ya hukunta abin da zai faru tsakaninmu da su ba?” Sai Annabi ya

ba shi amsa ya ce: “Ya kai ɗan Khaɗɗab. Lalle ni Manzon Allah ‫ ﷺ‬ne, kuma Allah

ba zai taɓa taɓar da ni ba”.

91
Yayin da mutane suka san cewa wannan umarnin Allah ‫ ﷺ‬ne, ba wani abu da za

su yi face su miƙa wuya, Musulmai suka dawo zuwa garin Madina bayan sun soke

abin hadayarsu, kuma suka warware haramin umararsu, suka tsaya a Hudaibiya

tsawon kwana ashirin.

Yaƙin Khaibar:

Shekara ta bakwai bayan hijira.

Bayan Sulhun Hudaibiyya da waɗancan abubuwa da suka faru, Manzon Allah ‫ﷺ‬

bai huta a Madina na tsawon wata guda ba. Sai ya yi umarni da a fita zuwa Khaibar,

domin haƙiƙa Yahudawan Khaibar sun kasance suna nuna ƙiyayya ga Musulmi,

kuma sun yi ƙoƙari sosai wajen haɗa rundunoni domin a yaƙi Musulmai a yaƙin

Ahzab.

Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya fito a farkon shekara ta bakwai bayan hijira, a cikin rundunar

da yawansu ya kai mutun dubu ɗaya da ɗari bakwai. Garin Khaibar ya kasance a

gine da katanga, Katanga mai ƙwari. A cikin garin akwai katanga har takwas,

kowacce tana zaman kanta. Yahudawan Khaibar sun kasance Yahudawan da suka fi

sauran ƙungiyoyin iya yaƙi mai tsanani, kuma sun fi su yawan makamai.

Rundunar Musulmai da Yahudawan Khaibar suka haɗu, suka yi yaƙi mai tsanani.

Ɗebe ƙauna, game da cin nasara ya dabaibaye Yahudawa, sai suka nemi yin sulhu

da Manzon Allah ‫ ﷺ‬a kan ya kiyaye jininsu. Sai Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya yarda da hakan.

92
Gonakinsu suka zama na Allah, da Manzonsa, da Musulmai bakiɗaya. A haka

Musulmai suka karɓi ikon mallakar Khaibar.

Daga cikin abin da Musulmai suka samu ganima a Khaibar, akwai wasu takardu

na Attaura, Yahudawa suka nemi Musulmai su mayar musu da su, Musulmin suka

mayar musu, Manzon Allah ‫ ﷺ‬bai yi irin abin da Rumawa suka yi ba lokacin da suka

buɗe garin Arshalima, suka ƙona litattafan nasara da suka samu a ciki, suka tattaka

su da ƙafafunsu, bai yi irin abin da Tatar suka yi na ƙona litattafai a garin Bagdada,

da waninsa ba.

Ramakon Umara:

Zul Ƙa’ada – shekara ta bakwai bayan hijira

Musulmai sun yi ramakon umara a watan Zulƙa’ada shekara ta bakwai bayan

hijira. Bayan Annabi ‫ ﷺ‬ya dawo daga Khaibar da ƴan watanni, yayin da ya fita zuwa

Makka – kamar yadda ya yi yarjejeniyar da ƙuraishawa a Hudaibiyya – Adadin

waɗanda suka halacci wannan umara ya kai mutum dubu biyu, banda mata da

ƙananan yara.

Musulmai suka yi ɗawafi a Ka’aba, suka bayyana ƙarfinsu da ya sa ƙuraishawa

suka yi ta mamakin bunƙasarsu. Sai Allah ya saukar da faɗinSa game da wannan

umara:

93
‫ﲥﲧﲨ ﲩﲪﲫﲬﲭﲮ‬
‫ﲦ‬ ‫ﱡﭐ ﲠ ﲡ ﲢ ﲣ ﲤ‬

:‫ال فتح‬ ‫ﲲ ﲴﲵ ﲶﲷﲸ ﲹﲺﲻ ﲼ ﲽﲾ ﱠ‬


‫ﲳ‬ ‫ﲯﲰ ﲱ‬
٢٧
“Lalle ne, haƙiƙa, Allah ya gaskata wa ManzonSa markinsa da gaskiya: lalle za ku

shiga masallacin Harami, in Allah ya so, kuna masu nutusuwa, masu aske

kawunanku da masu saisaye, ba ku jin tsoro, domin (Allah) Ya san abin da baku sani

ba, sa’an nan Ya sanya wani cin nasara makusanci bayan wannan”. (Fatahi 27)

Ana kiranta da Umarar sakayya. Domin Ƙuraishawa sun dakatar da Manzon

Allah ‫ ﷺ‬a watan Zulƙa’ada a shekara ta shida. Don haka yanzu ya yi ramuwa, sai ya

shiga Makka a watan zulƙa’ada a shekara ta bakwai.

Yaƙin Mu’uta:

Jumada‘ula – shekara ta takwas bayan hijira.

A cikin watan Jumada Ula a shekara ta takwasa bayan Hijira, sai Manzon Allah

‫ ﷺ‬ya haɗa runduna domin su yi ramuwa game da waɗanda suka kashe Haris bin

Umair. Wanda Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya aika wajen sarkin garin Busra, yana kiransa

zuwa Musulunci. Zaidu bin Harisata ne shugaban wannan runduna. Manzon Allah

‫ ﷺ‬ya ce: “Idan an raunata Zaidu toh Ja’afar bin Abi Ɗalib ne shugaba, idan kuma

aka raunata Ja’afar toh sai Abdullahi bin Rawaha (g).

94
Sai wannan runduna ta fita, yawansu ya kai mutum dubu uku daga cikin

Muhajirai da Ansarawa. Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya yi musu wasiyya da kada su kashe

mace, ko yaro, ko tsoho tukuf, kada kuma su yanke bishiya ko su rushe gini.

Wannnan runduna har ta isa zuwa wani wuri da ake kira da suna (Ma’an) a ƙasar

Sham.

Shi kuma Hiraƙil ya tanadi runduna da ta haɗa mutum dubu ɗari biyu domin su

yaƙi Musulmai.

Sai waɗannan ruduna biyu suka haɗu, waɗanda ba dai-dai suke ba wajen adadi,

da kuma tanadi. Musulmai suka yi yaƙin irin na gwaraza, suka tsaya a gaban wannan

runduna mai girma. Zaidu bin Harisatu wanda ke ɗauke da tuta ya yi yaƙi har sai da

aka kashe shi. Sai Ja’afar bin Abu Ɗalib ya ci gaba da jagoranci, ya riƙe tutar da

hannun damansa har aka sare hannun daman nasa, sannan sai ya riƙe ta da hagunsa,

shima aka sare shi, haka ya rungume ta da dungulminsa, har sai da wani mutum daga

cikin rumawa ya sare shi, ya kashe shi. Shi ya sa aka kira shi da suna: mai fuka-fukai

biyu, domin kuwa Allah ya musanya masa da fuka–fukai biyu, yana tashi da su a

cikin Aljanna ya je duk in da ya so.

Sannan sai Abdullahi bin Rawaha ya ɗauki tutar, shi ma ya yi ta yaƙi har sai da

ya yi shahada.

95
Sai Khalid bin Walid ya ɗauki tutar. sai ya yi amfani da ƙwarewarsa ta yaƙi ya

tafi da wannan runduna, ya tseratar da ita daga cin galaba da takusa faruwa a kansu.

Khalid a ya jira zuwa dare, sai ya sauya tsarin rundunar. Ya sanya daman rundunar

a hagu, sannan ya sanya hagunta a dama, kamar yadda ya sanya farkon rundunar ta

koma ƙarshe, ya mayar da ƙarshen zuwa farko.

Yayin da gari ya fara wayewa, sai Rumawa suka ga tutocin MusulmAi sun sauya,

ba kamar yadda suka sani ba, suka jiyo karafkiya da ƙarar takkuba, suka yi zaton ko

taimako ne ya zo musu. Nan suka ji tsoro suka tarwatse, Khalid bai gushe ba yana

ta kai-komo yana jan su, su kuma MusulmAi suna ta kashe su, yayin da suke ƙoƙarin

ficewa a tsawan waɗannan ranaku; har sai da Rumawa suka ji tsoron ko wannan

wani wayo ne da yake jan su zuwa sahara. Sai yaƙin ya tsaya. Sai galabar da za a ci

a kan rundunar MusulmAi ta sauya zuwa nasara da falalar Allah Maɗaukakin Sarki.

96
Auna Fahimta

Yi Magana game da yaƙin Badar babba, tare da la’akari da: Lokacin da aka yi,

sababin da ya sa aka gwabza, da abubuwan da suka faru a ciki da sakamakon yaƙin?

----------------------------------------------------------------------------------------------------

----------------------------------------------------------------------------------------------------

--------------------------------------------------------------------------------------------------

Mene ne babban dalilin da ya sa aka ci galabar Musulmi a yaƙin Uhudu?

----------------------------------------------------------------------------------------------------

----------------------------------------------------------------------------------------------------

--------------------------------------------------------------------------------------------------

Tattauna game da Sulhun Hudaibiyya. Waɗanne sharruɗa ne suka fi bayyana,

waɗanda aka yi ittifaƙi akansu?

----------------------------------------------------------------------------------------------------

----------------------------------------------------------------------------------------------------

--------------------------------------------------------------------------------------------------

97
Ka yi taƙaitaccen bayani game da yaƙin Khaibar da Mu’uta, dai dai da abin da ka

fahimta a darasin da ya gabata?

----------------------------------------------------------------------------------------------------

----------------------------------------------------------------------------------------------------

--------------------------------------------------------------------------------------------------

98
Buɗe Makka (Fathu Makka):

Ramadan – shekara ta takwasa bayan hijira.

Bayan Sulhun Hudaibiyya sai ƙabilar Bakar ta haɗe da Ƙuraishawa. Ita kuma

ƙabilar Khuza’a ta shiga cikin ƙawancen Musulmai, dama kuma ya kasance tsakanin

Bakar da Khuza’a akwai ɗaukar fansa, da jinane tun zamanin Jahilyya. Wata rana

kawai sai ƙabilar Khuza’a ta fuskanci harin ta’addanci daga ƙabilar Bakar, suka

kashe musu kusan mutum ashirin.

Sai ƙabilar Khuza’a ta shiga Harami domin ta tseratar da kanta. Amma sai da

Banu Bakar suka bi su har ciki suka kashe wasu daga cikinsu a Haramin. Sai Amru

bin Salim Alkhuza’i ya je wajen Manzon Allah ‫ﷺ‬, ya ba shi labarin ta’addancin da

Ƙabilar Bakar ta yi musu. Har ya rerawa Manzon Allah ‫ ﷺ‬wata waƙa kamar haka:

Ya Ubangijin lalle ni ina shelanta wa Muhammadu…

Ƙawancen babanmu da babansa (tsohon ƙawance)

Haƙiƙa kun kasance ƴaƴamu, kuma iyaye (ya faɗi haka saboda mahaifiyar Banu

Abdumanaf daga ƙabilar Khuza’a take, haka ma Ƙusayyu mahaifiyarsa ita ce Fatima

bin Sa’ad Alkuza’iyya)

Tun lokacin da muka miƙa wuya ba mu ɗaga hannu ba,

Ka taimake mu, Allah ya yi maka buɗi taimakon da aka saba,

99
Ka kira bayin Allah su zo da yawa su taimaka.

Sai Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya fara haɗa runduna, domin su fita zuwa Makka, ilai kuwa

Ƙabilu masu yawa suka halarta.

Sai Rundunar Musulmai ta fita a ƙarƙashin jagorancin Manzon Allah ‫ﷺ‬, a

tsakiyar watan Ramadan a shekara ta takwasa bayan hijira, yawansu ya kai mayaƙa

dubu goma.

Suka isa (Marruz Zahran), Annabi ‫ ﷺ‬ya haɗu da Abu Sufyan ya kira shi zuwa

Musulunci sai ya Musulunta. Sai Abbas ya ce: “Haƙiƙa Abu Sufyan mutum ne mai

son Alfahari, don haka a ba shi wani abu (na matsayi)”, Sai Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya ce:

“To duk wanda ya shiga gidan Abu Sufyan ya tsira. Duk wanda ya shiga gida ya

tsira. Wanda ya kulle ƙofar gidansa ya tsira”.

Sannan sai Abu sufyan ya dawo garin Makka cikin gaggawa, ya yi shela da murya

mai ƙarfi ya ce: “Ya ku taron Ƙuraishawa, haƙiƙa wannan Muhammad ne ya zo

muku da abin da ba yadda kuka iya da shi. Duk wanda ya shiga gidana ya tsira,

wanda ya kulle ƙofar gidansa ya tsira. Wanda ya shiga masallaci ya tsira”. Sai

mutane suka yi sauri zuwa masallaci, da gidajensu suka kukkule ƙofofin gidajensu,

suna leƙowa ta ƴar kafar hudar ƙofa, su kalli rundunar musulamai. Rundunar ta shiga

garin Makka a safiyar ranar Juma’a, wadda ta yi daidai da ashirin ga watan Ramadan

a shekara ta takwasa bayan hijira.

100
Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya shigo Makka ta tudunta yana karanta faɗin Allah:

١ :‫ﱡﭐﱁﱂﱃﱄﱅﱆﱠ ال فتح‬
“Lalle Mu, Mun yi maka buɗi, buɗi bayyananne”. (Fatahi: 1)

Makka ta miƙa wuya, Musulmai kuwa suka kewaye ɗakin Ka’aba suna ɗaga

sautinsu zuwa sama suna kabarbari: Allahu Akbar! Allahu Akbar!!

Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya fuskanci Harami, ya yi umarni da a rurrusa gumakan da suke

ciki, ya kasance yana nuna su yana cewa:

٨١ ‫ﱡﭐﲉﲊﲋﲌﲍﲎﲏﲐﲑﲒﲓﱠ‬
“Kuma ka ce, gaskiya ta zo, kuma ƙarya ta lalace. Lalle ne ƙarya ta kasance

lalatacciya”. (Isra’i: 81)

Bayan kuma an tsaftace Ka’aba daga gumakan dake ciki, sai Annabi ‫ ﷺ‬ya umarci

Bilal da ya kira Salla.

Amru binul As ya rusa gunkin Suwa’a

An aika Amru bin As a watan Ramadan zuwa Suwa’a – gunkin ƙabilar Huzail ne

– ya ce: “Na je sai na sami mai yi wa gunkin hidima. Sai ya ce: “Me kake so?” Sai

na ce: zan rusa shi ne, sai ya ce: “ba zaka iya ba”, sai na ce saboda me? Sai ya ce:

“za a hana ka”, sai na ce kaiconka har yanzu kana kan ɓata? Kaiconka shin yana ji

101
ko yana gani? Sai na kusance shi, na ɓalla shi, na ce da mai hidimta wa gunkin ya

ka gani? Sai ya ce: “na miƙa wuyana ga Allah Maɗaukakin Sarki”.

An tura Sa’ad Bin Zaid ya ruguza gunkin Manata.

Sannan aka tura Sa’ad bin Zaidu Al’ansari zuwa gunkin Manata a cikin watan

Ramadan, domin ya ruguza shi. Sa’ad ya fita tare da shi akwai mayaƙa mutum

ashirin, sannan har ya isa wajen, sai ya sami mai hidimta wa gunkin, sai ya ce: “Me

kake so?” Sai ya ce: ruguza shi nake so na yi, sai ya ce: “to gaka ga shi nan” sai

Sa’ad ya nufi gunkin, sai kawai wata mata ta fito daga ciki tsirara kanta butu-butu

tana addu’ar kaico, da bone na azaba, tana dukan ƙirjinta. Sai mai yi wa gunki hidima

ya ce: “Manata ga wasu masu saɓa miki nan”. Sai Sa’ad ya sareta ya kashe ta. Sannan

ya tafi ga gunkin ya rusa shi.

Haka tutar musulunci ta yi sama a Makka da kewayenta, mutane suka koma cikin

ni’imar kaɗaita Allah.

102
Auna Fahimta

 Ka ambaci abubuwan da suka faru yayin buɗe Makka, da mafi girman darasin

da ke ciki, ka kuma yi bayanin yadda aka share guraben shirka a Makka?

----------------------------------------------------------------------------------------------------

----------------------------------------------------------------------------------------------------

----------------------------------------------------------------------------------------------------

---------------------------------------------------------------------------------------------------

103
Yaƙin Hunainu:

Shawwal – shekara ta takwas bayan hijira

Bayan Musulmai sun buɗe garin Makka, sai ƙabilun da ke maƙwabtaka da

Ƙuraishawa suka tsorata da nasarar da Musulmai suka yi a akan Ƙuraishawa.

Ƙabilar Hawazin da Saƙif suka ji tsoron su zama su ne duka na gaba. Sai suka ce:

“Bari mu yaƙi Muhammad kafin ya yaƙe mu”. Waɗannan ƙabilu biyu suka nemi

taimakon ƙabilun dake maƙwabtaka da su,

Suka haɗu a kan cewa Malik bin Auf shugaban ƙabilar Hawazin; shi ne wanda

zai jagoranci wannan runduna da zata yaƙi Musulmai. Sai ya umarci mutanensa da

su taho da matansu, da yara, da dabbobi, da dukiyoyisu, su sanya su a ƙarshen

rundunar, ta yadda hakan zai zaunar da mazan domin su kare dukiyoyinsu, da

ƴaƴansu da matansu.

Yayin da Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya fahimci haka, sai ya fito zuwa gare su, tare da

sahabbansa. Hakan ya faru ne a watan Shawwal na shekara ta takwas bayan hijira.

Yawan Musulmai ya kai mayaƙa dubu goma sha biyu. Yawan kafirai kuma dubu

ashirin

Sai Musulmai suka kalli rundunarsu mai girma, da yawa suka ruɗu da yawansu,

suka ce: “Yau kam ba za a ci galabarmu ba saboda rashin yawa”.

104
Labarin fitowar Musulmai ya isa gare su, suka yi wa Musulmi kwanton-ɓauna a

kwarin Auɗas kusa da Ɗai’fa.

Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya taho cikin sahabbansa, suka ya-da-zango a wannan kwari.

Lokacin gabanin ketowar alfijir ne. Duhu kuma ya rufe kwarin Hunainu. Kawai sai

Musulmai suka ji ruwan kibbau suna sauka akansu ta kowanne ɓangare, sai al’mari

ya rikice musu, sahunsu ya girgiza. Wasu daga cikinsu suka gudu. Yayin da Manzon

Allah ‫ ﷺ‬ya ga an tarwatsa Musulmai, sai ya yi shela a cikinsu ya ce: “Ni ne Annabi

ba ƙarya ba, ni ne ɗan Abdulmuɗɗalib”. Ba wanda ya iya fitowa zuwa gare shi daga

cikin kafirai, duk da shi ne wanda ake nema. Sai Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya umarci Abbas

a da ya yi shela da cewa: “Ya ku taron mutanen Madina! Ya ku taron Muhajirai!

Ya ku waɗanda kuka yi mubaya’a a ƙasan bishiya”. Sai suka amasa masa da cewa:

Mun amsa maka ya Manzon Allah ‫ﷺ‬.

Sai rundunar ta ƙara haɗuwa yaƙin ya tsananta. Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya yi gaba cikin

wannan gumurzu. Ba a wani jima ba sai da aka tarwatsa Mushirikai suka juya baya

a guje, suka bar mata, da dukiyoyi da ƴaƴa.

Hadisi ya zo a Sahihu Muslim cewa: Sai Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya ɗebi tsakuwoyi ya

watsa wa fuskar mutanen, sannan ya ce: “Na rantse da Ubangijin Muhammad an

tarwatsa su” Abbas ya ce: “Ba a ɗau wani lokaci ba bayan ya jefe su; na ga sun

tarwatse, ƙasƙanci ya kama su”.

105
Yaƙin Hunainu wani darasi ne da Musulmai suka samu, Musulmai suka gane

cewa; samun nasara ba daga adadi mai yawa ba ne, ko tanadi.

106
Auna Fahimta

 Tattauna yaƙin Hunain tare da la’akari da fayyace:

 Lokacin da aka yi.

----------------------------------------------------------------------------------------------------

----------------------------------------------------------------------------------------------------

----------------------------------------------------------------------------------------------------

---------------------------------------------------------------------------------------------------

 Abubuwan da suka faru.

----------------------------------------------------------------------------------------------------

----------------------------------------------------------------------------------------------------

----------------------------------------------------------------------------------------------------

---------------------------------------------------------------------------------------------------

 Manyan darusa da fa’idojin yaƙin.

----------------------------------------------------------------------------------------------------

----------------------------------------------------------------------------------------------------

----------------------------------------------------------------------------------------------------

---------------------------------------------------------------------------------------------------

107
Yaƙin Tabuka:

Rajab – Shekara ta tara bayan hijira

Bayan buɗe garin Makka, da kuma shigar yankin Larabawa gabaɗaya cikin

Musulunci, sai Larabawan da suke bin Rumawa a ƙasar Sham suka ji tsoron ƙarfin

Musulmi. Rumawa suka yanke hukuncin zasu yaƙi Musulmai, suka haɗa runduna

mai yawan gaske, suka ya-da-zango a kudancin Sham.

Labarai sun isa wajen Manzon Allah ‫ﷺ‬, sai ya yi kira da a tashi runduna mai ƙarfi

da zata dakatar da yaƙin Rumawa, ya kwaɗaitar da masu kuɗi, da su bayar da

taimako da dukiyoyinsu, sai Usman bin Affan (z) ya bayar da kyautar Dinare

dubu goma, da raƙuma ɗari tara, da dawakai ɗari.

Kamar yadda Abubakar (z) ya bayar da dukiyarsa gabaɗaya.

Abdurrahaman bin Auf (z) ya bayar da Dinare dubu arba’in, mata suka bayar

da kayan adonsu na zinare.

Rundunar Musulmai ta tashi zuwa Tabuka a watan Rajab a shekara ta tara, a

ƙarƙarshin jagorancin Manzon Allah ‫ﷺ‬. Adadin mayaƙan Musulmai ya kai kusan

dubu talatin.

Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya ya-da-zango a wani waje da ake kira Sanniyatul wada’i,

Musulmai sun sha wahalar rashin ruwa, da guziri, har sai da ta kai suna yanka

108
raƙumansu suna fito da abin da yake ciki suna matsewa suna shan ruwan. Saboda

haka ake kiran wannan yaƙi da suna yaƙin wahala.

Musulmai sun zauna a Tabuka kusan kwana ashirin. Sai dai ba a samu ko mutum

ɗaya daga cikin Rumawa ba. Domin kuwa sun koma ta inda suka fito, yayin da suka

ji fitowar rundunar Musulamai, waɗanda suke fifita mutuwa a kan rayuwa.

Sai Annabi ‫ ﷺ‬da Musulmai suka koma Madina.

Lokacin Shigar Mutane Cikin Addinin Allah Ƙungiya Ƙungiya:

Shekara ta takwas zuwa ta goma sha ɗaya bayan hijira.

An kammala buɗe Makka, Ƙuraishawa sun zama mallakin Manzon Allah ‫ﷺ‬. Da

Larabawa suka fahimci ba yadda za su iya da Manzon Allah ‫ﷺ‬, ba za su iya adawa

da shi ba, sai suka shiga cikin Addinin Allah ƙungiya ƙungiya, musamman ma bayan

yaƙin da aka yi bayan buɗe Makka.

109
Auna Fahimta

 Ka yi magana game da yaƙin Tabuka tare da la’akari da:

 Lokacin da aka yi.

----------------------------------------------------------------------------------------------------

----------------------------------------------------------------------------------------------------

----------------------------------------------------------------------------------------------------

---------------------------------------------------------------------------------------------------

 Abubuwan da suka faru.

----------------------------------------------------------------------------------------------------

----------------------------------------------------------------------------------------------------

----------------------------------------------------------------------------------------------------

---------------------------------------------------------------------------------------------------

 Manyan darusa da fa’idojin yaƙin.

----------------------------------------------------------------------------------------------------

----------------------------------------------------------------------------------------------------

----------------------------------------------------------------------------------------------------

---------------------------------------------------------------------------------------------------

110
Shekarar Tawaga:

Shekara ta tara bayan hijira.

Ana kiran wannan shekara ta tara bayan hijira da shekarar tawaga ne, saboda

yadda ƙabilun Larabawa suka fara gangami suna zuwa Madina, suna bayyana

Musuluncinsu, da kuma yi wa Manzon Allah ‫ ﷺ‬mubaya’a. Haƙiƙa marubuta tarihi

sun ambaci cewa; yawan tawagar ya kai guda sittin, Bukhari ya ambaci wasu daga

ciki misali akwai: tawagar Tamim, da tawagar Abdulƙais, da tawagar Banu Hanifa,

da tawagar Najran waɗanda ba su Musulunta ba, amma sun yadda za su bayar da

jiziya, sai tawagar Ash’ariyyawa, da tawagar mutanen Yaman, da tawagar Dausu,

da tawagar Ɗayyi’u, da Adiy bin Hatim Aɗɗa’i da sauransu.

Hajjin Da Abubakar Ya yi Da Mutane

Shekara ta tara bayan hijira.

Manzon Allah ‫ ﷺ‬bai yi aikin hajji ba a shekarar da aka buɗe Makka, sai dai kawai

ya yi umara ne. Sai ya naɗa Abubakar jagoran aikin hajji, ya fita a cikin watan Zul-

hijja zuwa garin Makka, tare da Mutum ɗari uku daga cikin Sahabbai, a tare da su

akwai raƙuma ashirin, sai Surar Bara’a (Tauba) ta sauka a ranar soke hadaya, Sai

Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya aika Aliyyu da saƙo. Ga abin da saƙon ya ƙunsa:

“Ba wani rai da zai shiga Aljanna face sai ran da ta yi Imani. Kada wanda ya yi

ɗawafi tsirara. Ka da wani mushiriki ya ƙara yin aikin hajji bayan wannan shekarar.
111
Duk wanda yake da wata yarjejeniya/alƙawari tsakaninsa da Manzon Allah ‫ ﷺ‬to

yana nan har zuwa lokacinsa”.

Wannan raba gari da aka yi da Mushirikai, lokacinsa ya zo ne bayan shekara

ashirin da biyu da annabta, da kuma saukar wahayi.

Akin Hajjinsa ‫ﷺ‬:

Shekara goma bayan hijira (Hajjin bankwana).

Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya fita aikin Hajjin bankwana da rana, bayan ya taje kansa ya

sanya turare, sai ya kwana a Zulhulaifa ya ce: “Wani mai zuwa ya zo mini daga

wajen Ubangijina, ya ce: “Ka yi sallah a wannan kwari mai albarka, ka ce: umara a

cikin hajji”. Sai ya yi haramar ƙirani (wato haɗa aikin hajji da umara a tare).

Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya shiga Makka a ranar Lahadi da wuri, ta wajen Kuda’u, ta

hanyar Sanniyatul Ulya, ya yi ɗawafin isowa, ya yi sassarfa sau uku, sannan ya yi

tafiya sau huɗu. Sannan ya tafi zuwa dutsen Safa ya yi tafiya yana haye a kan abin

hawa, sannan ya umarci duk wanda bai koro abin hadayarsa ba, da ya warware aikin

hajjin ya mayar da shi umara.

A ranar Tarwiya sai ya tafi zuwa Mina, ya yi sallar Azahar da La’asar da

Magariba, da Isha’i, ya kwana a can ya yi sallar Asuba a can.

112
Yayin da rana ta hudo, sai ya tafi Arfa, an kafa masa tantinsa a wani waje da ake

kira Namira. Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya zauna a ciki har sai da rana ta yi zawali, sannan ya

yi wa mutane huɗuba, ya yi sallar Azahar, da La’asar tare da su, da kiran sallah ɗaya

da iƙama biyu, sannan ya tafi wajen tsayawa. Bai gushe ba yana ta addu’a, yana

tahalili, da kabarbari, har sai da rana ta kusa faɗuwa. Sannan ya tafi zuwa Muzdalifa

bayan rana ta faɗi, ya kwana a can ya yi sallar Asubahi.

Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya tsaya a Mash’aril Haram har gari ya waye, sannan ya tafi

zuwa garin Mina kafin hudowar rana, ya yi jifan Jamratul aƙaba da tsakuwoyi

bakwai a cikin kwanaki uku na salla. Ya kasance yana jifan Jamrorin nan guda uku,

yana tafiya a ƙasa. Ya yi jifan da tsakuwa bakwai, yana farawa da wacce take kusa

da Khaifu, sannan ta tsakiya, sannan kuma sai ta ƙarshe, yana tsawaita addu’a a

wajen ta ɗaya da ta biyu.

Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya soke abin hadayarsa a ranar da ya sauka a Mina, sannan ya

tafi zuwa Ka’aba, ya je yi ɗawafi sau bakwai, sannan ya je wajen shan ruwa, ya nemi

a ba shi ya sha, sannan ya koma Mina. Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya tafi a rana ta uku, ya

sauka a wani waje mai suna Muhassibi ya sanya A’isha ta yi haramar Umara a wani

gari da ake kira Tan’im, sannan ya yi umarni da ta tafi. Ya yi ɗawafin bankwana ya

fiskanci Madina (ya koma).

113
Wannan Hajji ana kiran ta da Hajjin bankwana, saboda Manzon Allah ‫ ﷺ‬bai ƙara

yin wani aikin Hajji ba bayanta.

Umararsa ‫ ﷺ‬da ya yi:

Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya yi Umara sau huɗu bayan Hijira, dakkansu a cikin watan

Zulƙi’ida, sai dai ɗayar da ya yi tare da aikin Hajji.

Ta ɗaya: Umarar Hudaibiyya ita ce ta farko. Ya yi ta ne a shekara ta shida bayan

Hijira, yayin da Mushirikai suka hana shi shiga Ka’aba.

Ta biyu: Umarar Ramako wacce ya rama a shekara ta gaba, ya shiga Makka ya

zauna tsawon kwana uku, sannan ya fito bayan ya kammala umararsa.

Ta uku: umarar da ya haɗa ta da aikin hajjinsa.

Ta huɗu: Umararsa da ya yi daga Ji’irrana yayin da ya fita zuwa Hunain, sannan

sai ya dawo Makka, ya yi Umara daga Ji’irrana.

Ya zo a cikin Littafin Bukhari da Muslim, daga Anas bin Malik (z) ya ce:

“Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya yi umara guda huɗu, dukkansu a cikin watan Zulƙi’ida, sai

wacce ya yi tare da hajjinsa, da umarar da ya yi daga Hudaibiyya, da umarar da ya

yi a shekara ta gaba a watan Zulƙi’ida, da umararsa daga Ji’irrana; yayin da ya raba

ganimar Hunain a watan zulƙi’ida, ya yi Umara tare da aikin hajji.

114
Bayan ya dawo daga hajji:

Haɗa Rundunar Usama (z):

Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya fara ta da rundunar Usama da za taje ƙasar Sham, bayan ya

dawo daga aikin hajji da wata biyu, ko fiye da haka. Ya sanya Usama bin Zaid (z)

ya zama jagoran rundunar. Ya umarce shi da ya nufi Balƙa, da Falasɗin, sai mutane

suka shirya a cikinsu akwai Ansarawa, da Muhajirai, da Abubakar, da Umar

gYawansu ya kai mutum dubu uku. Sai dai wannan hari da za a kai ya yi jinkiri,

saboda rashin lafiyar Manzon Allah ‫ﷺ‬.

115
Auna Fahimta

 Daga cikin abin da ka koya; mene ne abu mafi muhimmanci da ya faru a

shekara ta tara bayan hijira?

----------------------------------------------------------------------------------------------------

----------------------------------------------------------------------------------------------------

----------------------------------------------------------------------------------------------------

---------------------------------------------------------------------------------------------------

 Nawa ne adadin Umarar da Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya yi?

----------------------------------------------------------------------------------------------------

----------------------------------------------------------------------------------------------------

----------------------------------------------------------------------------------------------------

---------------------------------------------------------------------------------------------------

 Da wanne suna aka kira hajjinsa ‫ﷺ‬, kuma saboda me?

----------------------------------------------------------------------------------------------------

----------------------------------------------------------------------------------------------------

----------------------------------------------------------------------------------------------------

---------------------------------------------------------------------------------------------------

116
 Menene abin da ya kawo jinkirin fitar rundunar Usama?

----------------------------------------------------------------------------------------------------

----------------------------------------------------------------------------------------------------

----------------------------------------------------------------------------------------------------

---------------------------------------------------------------------------------------------------

117
Wafatin Manzon Allah ‫ﷺ‬

Goma sha biyu ga watan Rabi’ul Auwal – shekara ta goma sha ɗaya bayan Hijira.

Rashin lafiyar Manzon Allah ‫ ﷺ‬ta yi tsanani, bayan ya dawo daga Hajjin

bankwana, da kusan wata uku. Ya fara kokawa da rashin lafiyar yayin da yake gidan

matarsa Maimuna.

Ya inganta a cikin Sahihul Bukhari cewa; ya fara kokawa da rashin lafiyar tun a

shekara ta bakwai; bayan buɗe garin Khaibar, bayan ya ci naman wata akuya da aka

sanya wa guba, da wata Bayahudiya matar Sallam bin Mishkam ta kawo masa.

Matansa sun nemi da ya yi jinya a gidan Aisha (z). Haƙiƙa ta kasance tana karanta

masa ƙul’a’uzai, sai ta shafa masa da hannunsa, saboda albarkarsu.

Yayin da rashin lafiya ya kwantar da shi; bai iya fita zuwa masallaci domin ya yi

sallah da mutane, sai ya Umarci Abubakar da ya yi wa mutane Sallah, sai A’isha ta

bayar da uzuri, don kada mutane su camfa mahaifinta. Ta ce: “Haƙiƙa mahaifina

mutum ne mai sanyin hali, sautinsa mai rauni ne, ga yawan kuka idan yana karanta

ƙur’ani. Sai Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya dage a kan Abubakar ne zai ja Sallar. Abubakar ya

je ya yi musu salla.

Wannan ita ce babbar alamar da zata tabbatar da cewa shi ne zai zama halifa

bayan Manzon Allah ‫ﷺ‬. Domin kuwa Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya yarda da shi a kan

118
al’umarsa game da addininsu da sallarsu, to saboda me ba zaka yarda da shi ba kuma

a kan sha’anin duniyarsu?

Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya fita yana dogarawa da jikin Abbas, da Aliyu. Sai ya yi wa

mutane salla, ya yi musu huɗuba, ya yabi Abubakar a cikin huɗubarsa, ya bayyana

falalarsa, ya bayyana wa mutane zaɓin da Allah ya ba shi; tsakanin duniya da lahira,

da kuma zaɓar lahira da ya yi, ya ce: “Haƙiƙa wani bawa Allah Ya ba shi zaɓi

tsakanin furen rayuwar duniya, gwargwadon abin da ya so, sai ya zaɓi abin da yake

wajenSa (Allah)…sai Abubakar ya gane cewa fa yana nufin kansa. Sai ya fashe da

kuka sai mutane suka kama mamaki, domin kuwa su basu fahimci abin da ya fahimta

ba.

Yayin da mutuwa ta zo masa, ya kasance a jingine a ƙirjin Aisha (z), ya kasance

yana sanya hannunsa cikin ƙwaryar ruwa yana shafawa fuskarsa, saboda tsananin

zazzaɓi, yana cewa: “La’ilaha illallahu, haƙiƙa mutuwa tana da maye”. sai kuma

muryarsa ta canza, sai na ji yana cewa: “Tare da waɗanda Allah ya yi wa ni’ima”,

yana ce wa: “Tare da abokan tafiya maɗaukaka”, sai A’isha ta gane ashe an ba shi

zaɓi ne, shi kuma sai ya zaɓi abokan tafiya maɗaukaka (wato Annabawa, da Siddiƙai

da Shahidai).

119
Sai Fatima ta shiga wajensa, ta ce: “Ya baƙin cikin mahafina”. Sai ya ce da ita:

“Mahaifikin ba zai ƙara baƙin ciki ba bayan wannan rana”, ya ba ta labarin cewa ita

ce ta farko da zata fara haɗuwa da shi.

An karɓi ran Manzon Allah ‫ﷺ‬, ya yin da gari ya yi hantsi, kansa yana ƙafafun

A’isha (c), a ranar litinin, sha biyu ga watan Rabi’ul Auwal, a shekara ta goma

sha ɗaya bayan hijira.

Ya yi wafati a gidan A’isha, yana jingine a ƙirjinta, da wuyanta. Abu na ƙarshe

da ya ɗanɗana, shi ne yawunta a jikin asuwakin da ta tattauna masa. Ta ba shi domin

ya goge bakinsa da shi ‫ﷺ‬. Wannan kam ita ce mace da martabarta ta ɗaukaka,

matsayinta ya girmama.

Abubakar (z) ya shiga wajensa bayan ya dawo, ya yaye fuskar Manzon Allah

‫ﷺ‬, ya sumbace shi, sannan ya fita wajen mutane cikinsu akwai wanda yake musanta

wafatin Manzon Allah ‫ﷺ‬, da wanda yake gasgatawa, saboda yanayin na firgici da

suka tsinci kansu a ciki.

Sai ya ce: “Ku saurara! Duk wanda ya kasance yana bauta wa Muhammad, to

haƙiƙa Muhammad ya yi wafati. Wanda kuma a cikinku Allah yake bauta wa, to

Allah Rayyaye ne, ba Ya mutuwa, Allah l Ya ce:

120
‫ﱡﭐ ﱣ ﱤ ﱥ ﱦ ﱧ ﱨ ﱩ ﱪ ﱫﱬ ﱭ ﱮ ﱯ ﱰ ﱱ ﱲ ﱳﱴ ﱵ‬

١٤٤ :‫ﱶﱷﱸﱹﱺ ﱻﱼﱽﱾﱿﲀﲁﱠ آل عمران‬


(Kuma Muhammad bai zama ba face Manzo, Lalle ne Manzonni sun shuɗe a

gabaninsa. Ashe idan ya mutu ko aka kashe shi, za ku jiuya a dugaduganku. To

wanda ya juya a dugadugansa ba zai cuci Allah da komai ba, kuma Allah zai saka

wa masu godiya”. (Ali Imran: 144)

Sai mutane suka nutsu. Umar ya zauna a ƙasa, domin kuwa kafafunsa sun kasa

ɗaukar shi, kai ka ce basu taɓa jin wannan ayar ba sai a wannan lokacin.

Fatima ta yi kukan rashin mahaifinta tana cewa:

Ya babana! Ubangiji ya amsa addu’arsa,

Ya Babana! Wanda Aljannar Firdausi ce makomarsa

Ya babana! Muna sanar da wafatinsa zuwa ga Jibrilu.

Rayuwar Manzon Allah ‫ ﷺ‬ta zo ƙarshe; amma saƙonsa bai zo ƙarshe ba. Saƙonsa

wanzajje ne har izuwa ranar Lahira, Al’ummarsa ba zata taɓa yankewa ba, alheri

yana cikin wannan al’uma har izuwa ranar da za a tashi kowa, Allah Ka yi salati da

aminci da albarka a kan AnnabinKa mai gaskiyar zance amintacce, Dukan godiya ta

tabbata ga Ubangijin talikai.

121
Auna Fahimta

 Bayyana wafatin Annabi ‫ ﷺ‬abu ne mai girma, da ya faru. Ka yi bayani a kan

waɗannan batutuwa masu zuwa:

 Girman matsayin Aisha (c) a wajen Allah da Manzonsa.

 Matsayin Abubakar da Umar (x).

Falalar yi wa Annabi salati:

Allah l ya ce:

‫ﱡﭐﱢﱣﱤﱥﱦﱧﱨﱩﱪﱫﱬﱭﱮﱯﱰﱠ‬
٥٦ :‫األح زاب‬
(Lalle, Allah da mala’ikunSa suna Salati ga Annabi. Ya ku waɗanda suka yi Imani!

Ku yi salati a gare shi, kuma ku yi sallama domin amintarwa a gare shi) (Ahzab: 56).

Muslim ya fitar da Hadisi daga Abdullahi bin Amru bin As (z), cewa shi ya

ji Manzon Allah ‫ ﷺ‬yana cewa: “Duk wanda ya yi mini Salati ɗaya; to Allah zai yi

masa salati goma”.

Daga cikin siga mafi falala a cikin salatan Annabi ‫ﷺ‬, ita ce abin da ya zo cikin

Hadisin Bukhari da Muslim, daga Abu Huraira(z): “Ya Allah ka yi salati ga

Annabi Muhammad, da alayen Muhammad, kamar yadda ka yi Salati ga Ibrahim,

da kuma alayen Ibrahim. Ka yi albarka ga Muhammad, kamar yadda ka yi albarka

ga Alayen Ibrahim a cikin talikai, domin kai ne abin godewa Mai Girma”.

122
Kashi Na Biyu:
Da sunan Allah Mai rahama Mai jinƘai.

Dukkan godiya ta tabbata ga Allah. Muna gode masa, muna neman taimakonSa,
muna neman gafararSa, muna neman tsarin Allah daga sharrin kawunanmu, da
munananan ayyukanmu. Duk wanda Allah Ya shiryar; ba wanda zai iya ɓatar da shi.
Haka kuma duk wanda Allah Ya ɓatar; to babu mai iya shiryar da shi. Ina shedawa
babu abin bauta na gaskiya sai Allah, shi kaɗai ya ke ba Shi da abokin tarayya, kuma
ina shaidawa Annabi Muhammad ‫ ﷺ‬bawanSa ne, kuma ManzonSa ne.

Bayan haka, wannan shi ne darasin sharhin ɗabi’un Annabi ‫ ﷺ‬ga ɗaliban matak
na farko. Wajibi ɗalibin ilimi ya kasance cikin cikakken sani game da siffa, da kuma
halayen Annabi mai karamci ‫ﷺ‬. Hakan zai sa Musulmi ya kasance mai koyi da
Manzon Allah ‫ﷺ‬, wajen tsarki, da kyawawan ɗabi’u, don haka mutum ya samu shiga
cikin sahun manyan ɗabi’u, da zuƘata managarta.

Idan aka ce: (Shama’il) a harshen Larabci jam’i ne na kalamar (Shimal ko


Shamila) wato ana nufin ɗabi’a, da halayya.

Abin da ake nufi da ilimin ɗabi’un Manzon Allah ‫ﷺ‬, shi ne sanin abin da ya zo na
sanin ilimin siffar Manzon Allah ‫ﷺ‬, da kuma adonsa na waje, wanda shi ne mafi
kyawu, da Ƙayatar da idanu. Tare da sanin abin da ya zo na kyawawan halayensa
masu tsafta. Waɗannan su ne ɗabi’u mafiya girma. Kuma tafarkinsa ne wanda yake
da matuƘar kyau ‫ﷺ‬.

Zai iya yiwuwa mafi shaharar littafin da aka rubutua a wannan fanni shi ne:
Littafin Imam Tirmizi (Asshama’ilul Muhammadiyya), wannan shi ne littafi da ya
yi fice a wannan babi. Littafin ya ba da kulawa game da siffar Manzon Allah ‫ﷺ‬, da

123
kyawawan al’adunsa, da ɗabi’unsa na karamci, da adonsa, sai kuma tafarkinsa a
cikin mafi yawan al’amuransa na rayuwar yau da gobe.

Alhafiz ibnu Kasir a cikin littafin Albidayah wan-nihayah ya ce: “haƘiƘa mutane
a da can da yanzu, sun wallafa littattafai masu yawa game da ɗabi’un Manzon Allah
‫ ﷺ‬ɗaiɗaiku, da waɗanda ba ɗaiɗaiku ba. Daga cikin mafi kyawun abin da aka
wallafa a wannan babi, wanda ya yi kyau, kuma ya fa’idantar shi ne littafin Abu Isa,
Muhammad bin Isa bin Suratu At-tirmizi, wanda ya wallafa wannan shaharrarren
littafi game da ɗabi’un Manzon Allah, wato littafin “Ash-shama’il”

124
Muhimmanci Sanin Ɗabi’u Da Halayyar Manzon Allah ‫ﷺ‬.

Sanin ɗabi’u, da sanin siffar Annabi ‫ ﷺ‬yana da fa’idoji masu yawa, na daga ciki:

Na farko: ita ce cikakken hanyar sanin Manzon Allah ‫ﷺ‬. Wajibi ne a kan kowanne
Musulmi ya san Annabinsa. Domin mutum yana Imani da abu ne gwargwadon yadda
ya san abun, waɗanda suka fi kowa yaƘini game da Manzon Allah ‫ﷺ‬, su ne waɗanda
suka fi sanin shi. HaƘiƘa Allah Ya yi nuni ga hakan, ta yadda a cikin kowacce al’uma
ya zaɓi mutum ɗaya (manzo), wanda mutanensa suka san nasabarsa, da girmansa,
da tarihinsa, da ɗabi’unsa. Allah Ya ce:

٦٥ ‫ﱡﭐﲩﲪﲫﲬﲭﱠ‬
(Kuma zuwa ga Adawa ɗan’uwansu Hud) (A’raf 65) Allah ya Ƙara cewa:

(٧٣ ‫ﱡﭐﲤﲥﲦﲧﱠ‬
(Kuma zuwa ga Samudawa ɗan’uwansu Salihu) (A’raf 73)

Na biyu: HaƘiƘa sanin ɗabi’un Manzon Allah ‫ ﷺ‬yana Ƙara wa Musulmi son Manzon
Allah ‫ﷺ‬, da jin shauƘin rayuwa tare da shi, da gabatar da shi a kan komai, hakan na
daga tushen Imani. Duk wanda ya yi duba na tsanaki cikin tarihin Manzon Allah ‫ﷺ‬,
zai ga ya sami rabo mai girma na soyayya, da Ƙaunar Annabinsa ‫ﷺ‬.

Na uku: Yana Ƙara Ƙarfin biyayya, da kuma ko yi da Manzon Allah ‫ﷺ‬. Wannan shi
ne abin da mutanen farko (Sahabbai) suka kai matuƘa cikinsa, har sai da suka sami
shaidar Allah a kai a cikin Ƙur’ani, da za a yi ta karantawa zuwa tsawon shekaru.
Allah Ya ce:

125
‫ﱡﭐ ﱁ ﱂ ﱃ ﱄ ﱅ ﱆ ﱇ ﱈ ﱉ ﱊ ﱋ‬

‫ﱌﱍﱎ ﱏﱐﱑﱒﱓﱔﱕﱖﱗ ﱘﱙﱚﱛﱠ‬


١٠٠ :‫ال توبة‬

“Kuma masu tserewa na farko daga Muhajiruna, da Ansar, da waɗanda suka bi su


da kyautatawa, Allah ya karɓa daga gare su, su kuma sun karɓa daga gare Shi, kuma
Ya yi musu tattalin gidajen Aljanna, Ƙoramu suna gudana a ƘarƘashinsu, suna
madawwama a cikinsu har abada. Wancan ne babban rabo mai girma”. (Tauba: 100)

Na huɗu: Sanin ɗabi’un Manzon Allah ‫ ﷺ‬zai tabbatar da mumini cikin imaninsa,
kuma ya yi raddi game da masu taurin kai, da Ƙin karɓar gaskiya. Waɗannan ɗabi’u,
da siffofi, su ne matsayin hasken rana da ke haskaka hanyar da salihan bayi suke bi,
kuma take haskaka tafarkin masu tsoron Allah. Game da raddi ga shubuhar masu
taurin kan karɓar gaskiya kuma; ɗabi’u na Manzon Allah ‫ ﷺ‬sukan sanya manyan
malaman addinin Kirista, masu adalci, su faɗi Ƙasa su yi sujjada ga Allah, suna masu
tabbatarwa cewa wannan Annabi matsayinsa.

Wasu daga Iƙirarinsu:

Goethe (wani malamin Adabi ne ɗan Ƙasar Jamani) ya ce: “HaƘiƘa mu mutanen
Turai, tare da dukkanin abin da muka sani, kuma muka fahimta (na rayuwa), har
yanzu ba mu kai zuwa inda Muhammad ya kai ba. Kuma nan gaba ba wanda zai fi
shi. HaƘiƘa na yi bincike sosai cikin litattafan tarihi domin gano siffa maɗaukakiya,
da daraja ga ɗan’Adam. Sai na same ta a cikin Annabi Muhammad ‫ﷺ‬.

Bernard show ya faɗa a cikin littafinsa da ya wallafa ya sanya masa suna


(Muhammad). Littafin da shuwagabannin Birtaniya suka Ƙona, yake cewa: “HaƘiƘa
duniya tana cikin matuƘar buƘatar mutum mai tunani irin na Muhammad. Kuma

126
haƘiƘa ma’abota addini a Ƙarnukan tsakiya (wato daga Ƙarni na biyar zuwa na sha
biyar), saboda Jahilci da ta’assubanci, sai suka suranta Manzon Allah ‫ ﷺ‬a cikin baƘar
sura, suka ɗauke shi a matsayin maƘiyin addinin Nasara. Ashe al’amarin ba haka
yake ba, ya ma zama wajibi a kira shi da cewa: shi ne mai ceton ɗan’Adam. Kuma
a ra’ayina lalle da zai jiɓinci lamarin wannan duniya a yau, da ya warware dukkan
matsalolinmu ,da abin da zai kawo na aminci, da jin daɗi, da duk wani mutum yake
kuka a kansa.

Michel Hert a cikin littafinsa (The 100: A Ranking of the Most Influential Persons
in History) (wato fitattun mutane guda ɗari a tarihi), wanda ya sanya Muhammad ‫ﷺ‬
na farkon mutane ɗarin. Ya ce: “haƘiƘa na zaɓi sanya Muahammad ‫ ﷺ‬a farkon jerin
waɗannan mutane ɗari….saboda Muhammad shi ne mutum ɗaya tilo da ya ci
nasara; cikakkiyar nasara a matakin addini, da na duniya. Shi ɗin tabbas ya yi kira
zuwa ga Musulunci, kuma ya yaɗa shi, yar ya zama ɗaya daga cikin manyan addinai,
kuma ya zama shi ne jagoran siyasa, da sojoji, da kuma addini. Bayan Ƙarni goma
sha uku da wafatinsa, haƘiƘa abin da ya bari bai gushe ba yana da Ƙarfi, kuma ana
sabunta shi.

Anne Birzeit ya ce: “Abu ne da hankali ba zai ɗauka ba; ga duk mutumin da ya
karanci rayuwa da yanayin wannan Annabin Larabawan mai martaba, kuma ya san
yadda wannan Annabi ya rayu, ya san yadda ya ilimantar da mutane, face sai ya ji
girmansa cikin ransa, ya kuma san cewa shi ɗaya ne daga cikin Manzonnin Allah
masu girma.

Dakta Nazmi Luke: (Ɗaya daga cikin Ƙibɗawan Misra), yana da litattafai biyu a
kan tarihin Annabi ‫( ﷺ‬Muhammad, Arrisaltu, war-rasul) da (Muhammad fi hayatihil
– Khassa) yana faɗa a cikin littafinsa: (Muhammad, Arrisaltu, war-rasul): “haƘiƘa
Muhammad ‫ ﷺ‬ba kamar ɗaiɗaikun mutane ba ne a yanayin rayuwarsa, da kuma abin

127
da ya yi fice da su, shi ne wanda dukkkanin ni’imomi, da aka yi wa manzanni ta
tattaru a gare shi, da himmar gwaraza. To ya zama tilas ga duk wani mai adalci ya
girmama wannan abin koyin, kuma ya yi rayuwa da ɗabi’unsa.

Kuma yana cewa: “HaƘiƘa mutuwa ta ɗauke ƴaƴan Manzon Allah ‫ﷺ‬, domin
hakan ya zama wata izina ce dake nuna cewa; haƘiƘa Manzo Mutum ne. Ba shi da
wani abu da ya keɓanta da shi; fiye da sauran mutane. Domin haka, duk wata da’awa
dazata ƙi bin shi, to ta gaza.

128
Siffar Jikin Manzon Allah ‫ﷺ‬:

Siffar jiki: Anan abin da ake nufi shi ne, mabayyanin gangar jiki, da zubinsa,
kamar tsayi, da gajarta, fari, ko baƘi, ko Ƙiba, da makamantansu.

Amma kuma ɗabi’u su ne: ɓoyayyiyar surar mutum kamar haƘuri, tausasayi,
ƘanƘan-da-kai, ilimi, da dai makamantansu.

HaƘiƘa mun zaɓi gabatar da magana a kan siffofinsa na zahiri, wato waɗanda su
ne siffofin jikinsa ‫ﷺ‬. Siffofinsa na ɓoye sun fi ɗaukaka, kuma a kansu dukkan tsira
yake. Siffofi na zahiri su ne abu na farko da yake bayyana na mutum, kuma su ne
suke nuni ga suffofin mutum na ɓoye. Domin abin da ya bayyana shi ne yake nuni
ga wanda ya ɓuya.

Yanayin Fuskar Annabi ‫ﷺ‬:

Farkon abin da za a fara kwaɗayin saninsa, kuma mai kallo zai nemi ya gani, shi
ne fuskar Manzon Allah ‫ﷺ‬.

Daga Jabir bin Samuratu (a) ya ce: “Na ga Manzon Allah ‫ ﷺ‬a wani dare mai
hasken farin wata, sai na dinga kallon watan, kuma ina kallon fuskar Manzon Allah
‫ﷺ‬. Sai na ga ya fi watan kyau a wajena”. (Tirmuzi ya ruwaito wannan Hadisi kuma
ya ce: Mai kyau ne)

A cikin Sahihul Bukhari kuma: wani mutum ya tambayi Barra’u a: “Shin fuskar
kamar takobi take (wato wajen walƘiya da haske)? Sai ya ce: a a, kamar wata
take(wajen kyau da haske)”.

Daga Ka’ab bin Malik ya ce: “Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya kasance idan aka faranta masa
rai; sai fuskarsa dinga yin sheƘi, da annuri kamar yankin wata”.

Wannan ta bangaren hasken fuska Kenan.

129
Haka ma kamar rana, da wata yake wajen haskakawa, da wajen fuska
madaidaiciya.

Daga Jabir bin Samuratu (a) ya ce yayin da wani mutum ya tambaye shi game
da yanayin fuskar Manzon Allah ‫ﷺ‬, shin fuskar Manzon Allah ‫ ﷺ‬kamar takobi take
(wato wajen walƘiya, da haske)? Sai ya ce: a’a kamar rana, da wata take a zagaye”.

Daga Aliyu (a) ya ce: “Manzon Allah ‫ ﷺ‬ba mai faffaɗar fuska ba ne, kuma ba
mai kumburarriyar fuska ba ne. (fusakarsa ba doguwa ba ce, ba kuma takurarriya ba
ce).

Yanayin gashinsa:

HaƘiƘa ya kasance yana da yawan gashi, har yana zuwa daf kunnuwansa. Ta baya
kuma yana sauka har kan kafaɗunsa. Ba bu furfura a gashinsa, sai a ƴan
Ƙididdigangun gashi.

Daga Anas (a) ya ce: “Gashin Manzon Allah ‫ ﷺ‬ba cukurkuɗaɗɗe ba ne, kuma
ba sakakke ba ne, kuma Allah ya karɓi ransa babu farin gashi da ya kai guda ashirin
a kansa, ko gemunsa”. Bukahri da Muslim sun ruwaito wannan Hadisi.

Daga A’isha (a) ta ce: (Gashin Manzon Allah ‫( ﷺ‬ya kai ) saman fatun kunnensa,
(ta baya kuma) ya sauka kan kafaɗunsa)

Ƙarancin furfura a gashinsa:

Furfura kaɗan ce a gashin kan Manzon Allah ‫ﷺ‬, saboda Ƙarancin furfurar dake
kansa; ba a iya ganinta idan ya yi lalle. An karɓo daga Jabir bin Samurata, an
tambaye shi game da furfurar Manzon Allah ‫ﷺ‬, sai ya ce: “ya kasance idan har ya yi
lalle, to ba a ganin wani abu (na furfurar), idan kuma bai yi lalle ba ana gani”. Muslim
ya ruwaito wannan Hadisi.

130
Wannan furfurar tana wajen saman sajensa, da mararrabar gashin kansa, da kuma
Ƙasan leɓensa na Ƙasa.

Dalili a kan haka kuwa shi ne, Hadisin Anas (a): An tambaye shi game da lallen
Manzon Allah ‫ﷺ‬, sai ya ce: “Kawai yana ɗan yi ne a saman sajensa”.

Daga Jabir bin Samuratu (a) ya ce: “Babu furfura a kan Manzon Allah ‫ ;ﷺ‬sai
ƴan Ƙididdigaggun gashi a mararrabar gashin kansa. Idan ya yi lalle sai su ɓuya”.
Ahmad ya ruwaito wannan Hadisi.

Daga Wahab Abu Juhaifa Assuwa’iy (a) ya ce: “Na ga Annabi ‫ ﷺ‬sai naga farin
gashi a Ƙasan leɓansa na Ƙasa”.

Daga Ibn Abbas (a) ya ce: “Abubakar ya ce: “Ya Manzon Allah ‫ﷺ‬, haƘiƘa ka
yi furfura, sai ya ce: Suratu Hudu da WaƘi’a da Amma yatasa’aluna da Izash-
shamsu kuwwirat ne suka sa ni yin furfura”. Tirmuzi ya ruwaito wannan Hadisi,
Imam Albani kuma ya inganta shi.

Malamai suka ce: Sirrin da ya sa waɗannan surori suka sa Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya yi
furfura shi ne, saboda abin da waɗannan surori suka Ƙunsa na ambaton wahal-halun
da za a shiga a ranar AlƘiyama, da musibun da suka sauka a kan al’ummomin da
suka gabata, sai hakan ya kama Manzon Allah ‫ﷺ‬, har sai da yasa shi yin furfura kafin
lokacinta ya yi.

Manzon Allah ‫ ﷺ‬yana sakin gashinsa:

A farkon lamari (wato farkon zuwan addinin Musulunci), Manzon Allah ‫ ﷺ‬yana
son yaga yana yin abubuwa daidai da yadda Ahlul-kitbi suke yi, yana ƘoƘarin ya
saɓawa Mushirikai, sai ya zama yana sakin gashinsa ya sauka bayansa.

131
Sannan sai mutane suka fara shiga Addinin Allah Ƙungiya–Ƙungiya, kuma
Ƙiyayyar da Ahlul-kitabi suke masa ta bayyana gare shi, sai ya koma kan al’adar
Larabawa, wato shi ne mutum ya rarraba gashi zuwa ɓangare biyu.

Daga Ibn Abbas (a) ya ce: “HaƘiƘa Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya kasance yana sakin
gashinsa, su kuma Mushirikai suna raba gashi (ya sauka zuwa ɓangare biyu), su
kuma Ahlul-kitabi suna sakar gashi (yayi baya), Manzon Allah ‫ ﷺ‬yana so ya ga yana
yin abubuwa dai-dai da na Ahlul-kitabi, cikin abin da wani umarni bai zo a kai ba.
Daga baya sai Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya dinga raba gashin kan nasa (wato kamar yadda
al’adar Larabwan take)

Malamai suka ce: “Maganar da take da a kwai kuma zaɓaɓɓiya ingantacciya, shi
ne halaccin mutum ya saki gashin kansa, ko kuma ya raba shi zuwa ɓangare biyu.
Amma rabawa shi ya fi”. Allah Shi ne masani

Shaikhul Islam Ibn Taimiya ya ce: “Da hakan ne raba gashin kai (zuwa ɓangare
biyu ya sauka a gefen fuska) ya zama wata alama ce ta Musulmai, kuma ya zama na
daga cikin sharaɗin da aka saka wa kafiran amana shi ne; ba za su raba gashin kansu
ba (domin kada su yi kama da Musulmai).

Askin Manzon Allah ‫ﷺ‬.

Game da aske gashin kansa ‫ﷺ‬:

Al’imamun Nawawi ya ce: “Wannan ya tabbata cewa Manzon Allah ‫ ﷺ‬bai taɓa
aske gashin kansa ba; a shekarun da ya yi na hijira, sai a shekarar da aka yi sulhun
Hudaibiyya. Sannan sai shekarar da suka yi Umarar ramako, sai kuma shekarar
Hajjin bankwana”.

132
Aske wani sashi na gashin kai (Al-Ƙaz’u)

Ya tabbata a cikin Sahihul Bukhari da Muslim, daga Abdullahi bin Umar (a)
cewa: Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya yi hani game da yin Al-Ƙaz’u. Ma’ana aske wani sashe
na gashin kai, a bar wani sashen. Shi kuwa hani yana bayuwa ne zuwa ga haramci.

Ma’abota ilimi suka ce: “zai shiga cikin wannan aski da aka hana (Al-Ƙaz’u),
mutum ya aske wani wajen a gashin kansa, ko ya aske tsakiyar gashin, ya bar sauran
ɓagarorin kamar dai yadda yawancin Nasara (Kiristoci) suke yi, ko kuma mutum ya
aske gefen gashin, ya bar tsakiyarsa, kamar yadda yawancin wawaye suke yi, ko ya
aske gaban gashin ya bar bayansa.

Yin lalle a gashin Manzon Allah ‫ﷺ‬:

Malamai ma’abota ilimi sun yi saɓani; wajen tabbacin shin ko Manzon Allah ‫ﷺ‬
ya yi wa gashinsa lalle? A cikinsu akwai waɗanda suka kore hakan. Akwai kuma
waɗanda suka tabbatarwa. Sai dai abin da ya fi inganci shi ne cewa; Manzon Allah
‫ ﷺ‬ya yi lalle.

HaƘiƘa an tambayi Abu Huraira (a) shin Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya yi wa gashinsa
lalle? Sai ya ce: (Ƙwarai kuwa.) Imam Tirmuzi ya ruwaito wannan Hadisi, a cikin
littafinsa (Ash-shama’il), kuma Imam Albani ya inganta Hadisin.

Kamar yadda Bukhari ya ruwaito daga Hadisin Abdullahi bin Wahab ya ce: “Na
shiga wajen Ummu Salama (a), sai ta fito mana da gashi daga cikin gashin Manzon
Allah ‫ ﷺ‬wanda aka yi wa lalle”.

Daga ibn Umar (a) cewa: Annabi ‫ ﷺ‬ya kasance yana sanya takalmin
jemammiyar fatar Saniya, kuma yana rina gemunsa da warsu ,da za’afaran, Ibnu
Umar a ya kasance shi ma yana aikata haka. Abu Dawud da Nasa’i sun fitar da
wannan Hadisi, kuma Imam Albani ya inganta shi.

133
Tsokaci:
Babu laifi maza su rina kansu da lalle. Saboda abin da malaman Hadisi suka
ruwaito daga Abu Zarrin (a) daga Annabi ‫ ﷺ‬ya ce: “HaƘiƘa lalle da katamu su ne
mafi kyawun abin da zaku sauya gashinku da shi”. Imam Albani ya inganta wannan
Hadisi.

Sai dai rina kai da baƘin lalle tsantsa; bai halatta ba ga maza da mata. Saboda
faɗin Annabi ‫ ﷺ‬cewa: “Ku sauya wannan furfura, amma ku nisanci (baƘin) lalle”.
Muslim ya ruwaito wannan Hadisi.

Kamar yadda Abu Dawud ya ruwaito, daga Ibn Abbas (a) cewa: Manzon Allah
‫ ﷺ‬ya ce: “Akwai wasu mutane da za a yi a Ƙarshen zamani, suna sa baƘin lalle (a
gashinsu), kamar gashin Ƙirjin tantabaru, ba zasu taɓa jin Ƙanshin Aljanna ba”.

Abin da yake wajibi shi ne, an hana duk wani irin rini, ko lalle da zai zama mutum
yana kama da mata, saboda hanin da Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya yi game da kamanceceniya
da mata, da kumaa tsinuwar da ya yi ga wanda yake hakan.

Umarni da a cika gemu:

Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya yi umarni da a cika gemu. An karɓo daga Abdullahi bin Umar
(a) ya ce: Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya ce: “Ku aske gashin baki, ku cika gemu”. Bukhari
da Muslim ne suka ruwaito wannan hadisin.

A cikin wata ruwayar ta Bukhari da Muslim ya ce: “Ku saɓa wa Mushirikai, ku


kai matuƘa wajen aske gashin baki, kuma ku cika gemu”.

Abin da wasu mutane suke yi na aske gemu, ko kuma rage tsayinsa, ko faɗinsa
hakan bai halatta ba. Saboda hakan ya saɓa wa tafarkin Manzon Allah ‫ﷺ‬, da ya yi
umarni da a yawaita gemu.

134
Sheik bin Baz ya ce: “Duk wanda ya kafa hujja da maganar Ibn Umar (a) cewa
ai ya rage gemunsa, na abin da ya Ƙaru da kamu ɗaya, to mutum ba shi da wata hujja
a cikin hakan. Domin wannan ijthadi ne daga wajen Ibn Umar (a). Ita kuma hujja
tana cikin abin da ya ruwaito, ba cikin ijtihadinsa ba.

Gemun Manzon Allah ‫ﷺ‬:


Gemun Manzon Allah ‫ ﷺ‬cikakke ne, mai kauri. HaƘiƘa Nasa’i ya ruwaito daga
Barra’u bin Azib (a) ya ce: “Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya kasance mutum…mai yawan
gemu, kuma gemunsa mai kauri ne”.

An karɓo daga Aliyu bin Abi Ɗalib (a) cewa, Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya kasence yana
da gemu mai yalwa. Ahmad ya ruwato shi, Albani ya ce: “Hadisin mai kyau ne”.

135
Auna Fahimta

 Rubuta taƘaitaccen bayani a kan Muhimmancin karanta halayen Manzon


Allah ‫ﷺ‬.

--------------------------------------------------------------------------------------------------

--------------------------------------------------------------------------------------------------

--------------------------------------------------------------------------------------------------

 Yaya Turawan yamma suka nuna gamsuwarsu da Manzon Allah ‫ ?ﷺ‬Kuma


hakan me yake nuni a kai?

--------------------------------------------------------------------------------------------------

--------------------------------------------------------------------------------------------------

--------------------------------------------------------------------------------------------------

 Siffanta kamannin fuskar Manzon Allah ‫ﷺ‬, da gashin kansa, da gemunsa ‫ﷺ‬.

--------------------------------------------------------------------------------------------------

--------------------------------------------------------------------------------------------------

--------------------------------------------------------------------------------------------------

 Shin Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya yi wa gashinsa lalle? Kawo hujjoji cikin abin da zaka
faɗa, kuma mene ne hukunci yin baƘin lalle?

--------------------------------------------------------------------------------------------------

--------------------------------------------------------------------------------------------------

--------------------------------------------------------------------------------------------------

136
 Cikin abin da ka karanta a wannan babi, bayyana yadda aka hana
kamanceceniya da kafirai.

--------------------------------------------------------------------------------------------------

--------------------------------------------------------------------------------------------------

--------------------------------------------------------------------------------------------------

Ta yaya zaka bayar da amsa ga wanda yake cewa, cika gemu ba wajibi ba ne?

--------------------------------------------------------------------------------------------------

--------------------------------------------------------------------------------------------------

--------------------------------------------------------------------------------------------------

137
Zubin halittar jikin Manzon Allahn ‫ﷺ‬:

Anas bin Malik (a) ya faɗi wata Magana cikakkiya game da jikin Manzon Allah
‫ ﷺ‬ya ce: “Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya kasance mai kyakykyawan jiki” Tirmuzi ya ruwaito
Hadisin Albani kuma ya inganta shi.

Barra’u bin Azib (a) ya ce: “Ban taɓa ganin wani abu da ya kai Manzon Allah
‫ ﷺ‬kyau ba”. Bukhari da Muslim sun ruwaito wannan Asari.

Tirmuzi ya ruwaito a cikin littafinsa (Ash-shama’il) da isnadi ingantacce, daga


Aliyu bin Abi Ɗalib (a). ya ce: “Manzon Allah ba dogo ba ne, kuma ba gajere ba
ne. Yana da kauraran tafikan hannaye, da kuma digadigai. Yana da yalwataccen kai,
yana da Ƙasusuwa manya, yana da dogon gashin Ƙirji”.

A cikin Hadisin Anas (a), yana Siffanta Annabi ‫ ﷺ‬ya ce: “Ya kasance tsaka-
tsakin mutane, shi ba dogo ba ne, kuma ba gajere ba”. Bukhari da Muslim sun haɗu
wajen ruwaito wannan Hadisi. Amma wannan lafaizin Bukhari ne.

Barra’u (a) ya ce: “Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya kasance tsakatsakin mutane. Akwai
tazara tsakanin kafaɗunsa”. Faɗinsa (kuma da tazara tsakanin kafaɗunsa) wato
saman bayansa.

An ruwaito daga Al-jariri cewa, (wata rana) yana yin ɗawafi tare da Abuɗ Ɗufail,
sai ya ce: “Na ga Manzon Allah ‫ﷺ‬, kuma babu wanda ya yi saura a ban Ƙasa cikin
waɗanda suka gan shi in ba ni ba. Sai na ce: “Siffanta mini kamanninsa” sai ya ce:
“Ya kasance fari kyakkyawa madaidaici”.

Faɗinsa: madaidaici, wato wanda ba mai Ƙiba ba, kuma ba ramamme ba. Ba dogo
ba kuma ba gajere ba.

Faɗinsa: kuma babu wanda ya yi saura a ban Ƙasa cikin waɗanda suka gan shi in
ba ni ba. Hakane saboda Abuɗ Ɗufail, shi ne Amiru bin Wasila Al-laisi (a), shi ne
138
Ƙarshen mutuwa cikin Sahabbai. An haife shi a shekarar da aka yi hijira, da mutuwar
shi ne aka rufe sashin Sahabbai masu girma da karamci.

Ibnul Ƙayyim ya ce: “Allah ya cika duk wani matakin kyawu na fili da na ɓoye ga
Manzon Allah ‫ﷺ‬. Annabi ‫ ﷺ‬ya kasance shi ne mafi kyawu cikin halittun Allah.
Kyawun hallita da na halaye, kuma mafi kyawun sura da ma’ana”.

HaƘiƘa (Ibnul Ƙayyim) ya ambaci cewa, wani daga cikin sahabbai ya haɗu da
wani malamin Nasara, sai ya ce da shi: “siffanta mini kamannin Manzon Allah ‫ﷺ‬,
kamar ina ganinsa, domin haƘiƘa na ga siffofinsaa cikin Attaura, da Injila, sai kuwa
wannan Sahabi ya yi ta ambaton kamanninsa. Ya ce: “Bai kasance dogo sosai ba,
kuma ba gajere ba ne”. Ya dai ambaci wasu daga cikin siffofinsa, ya ce: “sai wannan
Malamin Nasara ya musulunta”.

Launin fatar Manzon Allah ‫ﷺ‬:

Manzon Allah ‫ ﷺ‬fari ne da yake haɗe da ja, wanda ya yi kama da sirki da duhu.

Bukhari da Muslim sun ruwaito daga Anas bin Malik (a) ya ce: “Manzon Allah ‫ﷺ‬
ya kasance ba fari fat ne, ba kuma baƘi ba ne).

A cikin wata ruwayar ta su: “Ya kasance mafi kyawun launi. Shi ba fari fat ba ne,
kuma ba baƘi ba ne”.

Al’amhaƘ: Shi ne fari fat irin launin zabiya.

Al’adamu: Kuma shi ne jan da ya yi baƘi, ko duhu sosai

Azhar: Kuma shi ne farin da yake haɗe da ja, (shi ne kalar launi fatar Manzon Allah
‫)ﷺ‬.

139
Tambarin annabta:

Akwai alamar annbtaka a jikin Annabi ‫ ﷺ‬mai daraja. Wato hakan wata alama ce
daga cikin alamomin annabtakarsa.

Ga alamar da wani malamin Nasara da Salman Al-farisi ya rayu tare da shi ya ce


da shi: “Yanzu me zaka umarce ni da shi?” Sai ya ce: “Ya kai ɗana. HaƘiƘa zamanin
wani Annabi da za a aiko da addinin Ibrahim ya zo, zai fito a Ƙasar Larabawa. Zai
yi hijira zuwa wata Ƙasa tsakanin baƘaƘen duwatsu biyu. Garin yana da bishiyun
dabino a tsakaninsu. Yana da wasu alamomi da basa ɓuya. Yana cin kyauta, amma
ba ya cin sadaka. A tsakanin kafaɗunsa akwai tambarin annabta. Idan har zaka iya
zuwa wannan garin; to ka tafi”. Ahamad ya fitar da Hadisin, Albani ya inganta shi.

Wannan ita ce alamar da Bahira Malamin Nasara ya gane Manzon Allah ‫ ﷺ‬da ita.
Har ya ce: “Wannan shi ne shugaban talikai. Wannan shi ne ɗan aiken Ubangijin
talikai. Wanda Allah zai aiko domin rahama ga talika”.

Sai Abu Ɗalib da wasu manyan Ƙuraishawa suka ce da shi: “Ta ya akai kasan
hakan?” Sai ya ce: “Domin lokacin da kuka taho daga hanyar dutsen can, ba wani
dutse, ko wata bishiya da ta tsaya, face sai da ta faɗi tana yin sujjuda, kuma su ɗin
ba sa yin sujjada sai ga wanda yake annabi. Ni kam tabbas na gane shi da alamar
Annabtaka da take daura da allon kafaɗarsa, kwatankwacin tuffa”. Tirmuzi ya
ruwaito wannan Hadisi. kuma ya inganta shi.

Daga Jabir bin Samura ya ce: “Alamar Manzon Allah ‫ ﷺ‬-wato wacce take
tsakankanin kafaɗunsa – wata ƴar tsokar nama ce, tsakanin naman jikinsa, da kuma
fatar jikinsa, da jaja-jaja a jiki”.

A wata ruwayar ta Muslim ya ce: “Na ga wannan alamar a wajen kafaɗarsa,


kwatankwacin Ƙwan tantabara, kuma ta saje da jikinsa”.

140
Al’imamul Ƙurɗubi ya ce: “HaƘiƘa Tabbatattun Hadisai sun haɗu a kan cewa,
alamar annabtaka wani abu ne da yake bayyananne a kafaɗarsa ta dama. Girmanta
kwatankwacin Ƙwan tantabara”. Bai inganta ba cewa a wannan alama an rubuta
sunan Allah, ko Muhammad, ko dai wasu kalmomi.

Tufafin Manzon Allah ‫ﷺ‬

An karɓo daga Ummu Salama (a) ta ce: “Mafi soyuwar tufafi a wajen Manzon
Allah ‫ ﷺ‬ita ce riga”. Abu Dawud, da Tirmuzi, da Nasa’i suka ruwaito wannan Hadisi,
Albani kuma ya inganta shi.

Sheikh Ibnu Usaimin ya ce: “Sun kasance a zamanin Manzon Allah ‫ ﷺ‬suna sanya
kwarjalle, da mayafi. Wani lokacin kuma su sanya riga. Manzon Allah ‫ ﷺ‬kuma ya
kasance ya fi son riga, domin ta fi suturce mutum, kuma da yake ita abu guda ce
kawai da mutum zai saka a lokaci ɗaya. Ta fi sauƘi a kan mutum ya sanya kwarjalle
da farko, sannan ya ɗaura mayafi daga baya”.

Daga Mu’awiya bin Ƙurra daga babansa (a) ya ce: “Na je wajen Manzon Allah
‫ ﷺ‬a cikin wasu mutane; daga Ƙabilar Muzaina, domin mu yi masa Mubaya’a. Tabbas
rigarsa a sake take (wato kwarjallensa a kwance yake ba a ɗaure ba)”. Ahmad ya
fitar da wannan Hadisi, Arna’uɗ kuma ya inganta shi.

Daga Anas bin Malik (a): “HaƘiƘa Annabi ‫ ﷺ‬ya fito yana dogara a jikin Usama
bin Zaid (a), yana sanye da tufafin Ƙiɗiriy yana mai yin yafe da shi, sannan ya yi
musu Salla”.

Tufafin Ƙiɗiriy; wani irin tufafi ne da ake yin shi a Ƙasar Yaman, ana yin shi
da auduga, yana da jaja-jaja da layi-layi yana da kaushi.

Daga Anas bin Malik (a) ya ce: “Mafi soyuwar tufafin da Manzon Allah ‫ﷺ‬
yake sakawa, shi ne mayafin Ƙasar Yaman”.
141
Ibn Baɗɗal ya ce: “Abin da ake nufi da Kalmar Alhibra da tazo cikin hadisin,
Ita ce: Wani mayafi ne daga cikin mayafan Ƙasar Yaman, da ake yi da auduga. Shi
ne tufafi mafi ƙima a wajensu.

Me sunna ta koyar yayin saka sabon tufafi?

Daga Abu Sa’id Al-khudri (a) ya ce: “Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya kasance idan ya
yi sabon tufafi; yana ambaton sunansa – misali rawani ko riga ko mayafi – sannan
sai ya ce: “Ya Allah dukkan godiya ta tabbata gare Ka kamar yadda ka tufarar da ni
shi, ina roƘonKa aherinsa, da alherin abin da aka yi domin shi, ina kuma neman
tsarinka daga sharrinsa, da sharrin abin da aka yi domin shi”. Tirmuzi, da Abu
Dawud suka ruwaito wannan Hadisi, Imam Albani kuma ya inganta shi.

Sanya farin tufafi:

Mafi yawan tufafin da Manzon Allah ‫ ﷺ‬yake sakawa shi ne fari. Saboda
Hadisin Ibn Abbas (a) ya ce: Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya ce: “Ina horan ku da sanya farin
tufafi. Rayayyun cikinku su sanya, kuma ku yi wa matattun cikinku likafani da shi,
domin yana daga cikin mafi alherin tufafinku”.

Siffar yadda Manzon Allah ‫ ﷺ‬yake sanya tufafi:

Tufafin Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya kasance zuwa rabin Ƙwaurinsa. Shi kuma hannun
riga zuwa wuyan hannu.

Hadisi ya zo a cikin Sahihu Muslim. HaƘiƘa Annabi ‫ ﷺ‬ya fito cikin jan tufafi,
Abu Juhaifa ya ce: “Kamar ina hango farin Ƙwaurinsa”.

Ya zo a cikin wani Hadisi mai kyau da Tirmuzi ya ruwaito, daga Asma’u ƴar Yazid
bin Sakan ta ce: “Hannun rigar Manzon Allah ‫ ﷺ‬zuwa wuyan hannu ne”.

142
Waɗannan Hadisai suna yi mana nuni a kan cewa, Manzon Allah ‫ ﷺ‬yana da Ƙan-
Ƙan-da-kai (Tawali’u) a cikin abin da yake sanyawa na tufafi. Ya kasance yana son
riga, kuma yana sanya wanin hakan. Kamar kwarjalle, ya kasance yana yafa mayafi
a wani lokacin, wani lokacin kuma ya ɗaura kwarjalle (Zani). Ba ya hana kansa
sanya tufafi mai kyau. Ya kasance yana son farin tufafi da aka yi masa zane-zane da
ja, ko da wani launin daban.

Sanya jan tufafi da hukuncin hakan:

Daga Aunu bin Abi Juhaifa, daga Babansa (a) ya ce: “Na ga Manzon Allah
‫ ﷺ‬sanye da jan tufafi. Kamar ina hango farin Ƙwaurinsa (a yanzu). Sufyan ya ce:
“ina ganin Hibra ce”.

Maganar Sufyan da ya ce: “ina ganin Hibra ce” wato ba wai zallar ja ba ne,
yana nufin akwai zane- zanen ja a jiki. Wannan shi ne zance mafi inganci.

Kalmar Hulla da ta zo a cikin Hadisin. Malaman harshe suka ce: “Tufafi ne


guda biyu ba ɗaya ba, su ne: Kwarjalle da Mayafi”.

Sheikh Ibnu Usaimin ya ce: “Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya yi hani game da sanya jan
tufafi, idan ja ne zalla. Amma idan fari ne haɗe da ja; to babu laifi game da hakan.

Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya sanya huffi:

Mugira bin Shu’uba (a) ya ce: “Dihyatul-Kalbi ya bai wa Manzon Allah ‫ﷺ‬
kyautar huffi, sai (manzon Allah ‫ ) ﷺ‬ya sanya su”.

143
Takalmin Manzon Allah ‫ﷺ‬:

Daga Ƙatada ya ce: “Na ce wa Anas bin Malik (a): yaya takalmin Manzon
Allah ‫ ﷺ‬ya ke? Sai ya ce: “suna da igiya biyu”.

Wato igiyar da take a tsakankanin ƴanyatsu biyu.

Hadisi ya zo a Sahihul Bukhari da Muslim, daga Ubaid bin Juraih cewa, shi
ya ce wa Ibnu Umar a: “Na gan ka kana sanya takalmin jemammiyar fata! Sai ya
ce: HaƘiƘa na ga Manzon Allah ‫ ﷺ‬yana sanya takalman da babu gashi a jikinsu,
kuma yana yin al’wala da su. To nima ina son in saka su”.

Daga Amru bin Hurais (a) ya ce: “Na ga Manzon Allah ‫ ﷺ‬yana salla a sanye
da wasu takalma biyu da suka huhhuje”.

Wannan yana nuni a kan ƘanƘan-da-kai irin na Manzon Allah ‫ﷺ‬. Ya kasance
wajen tawali’u kamar yadda A’isha (d) ta siffanta shi: “Yana saka takalmi har ya
huje. Yana ɗinke tufafinsa (idan ya yage), yana aiki a gidansa kamar yadda ɗayanku
yake aiki a gidansa. Ahmad ne ya ruwaito wannan Hadisi, da Bukhari kuma a cikin
littafin (Al-adabul Mufard).

Yin tafiya da warin takalmi ɗaya:

Daga Abu Huraira (a), haƘiƘa Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya ce: “Kada ɗayanku ya yi
tafiya da warin takalmi ɗaya, ko dai ya sa su gabaɗaya, ko kuma ya cire su
gabaɗaya”. Bukhari da Muslim ne suka ruwaito wannan Hadisi.

Daga Jabir a: HaƘiƘa Annabi ‫ ﷺ‬ya yi hani ga mutum ya ci abinci da hannun


hagunsa, ko kuma ya yi tafiya da takalmi wari ɗaya”. Muslmi ya ruwaito wannan
Hadisi.

Abin da yake a Sunna wajen sanya takalmi; shi ne farawa da Ƙafar dama.

144
Daga Abu Huraira (a): HaƘiƘa Annabi ‫ ﷺ‬ya ce: “Idan ɗayanku zai sanya
takalmi; to ya fara da damansa, idan kuma zai cire; to ya fara da hagunsa. Dama ta
zama ita ake fara sakawa, kuma ita ce a Ƙarshe wajen cirewa” Albani ya inganta
wannan Hadisi.

An sunnanta yin salla da takalmi, amma idan ba a kan shimfiɗa ba ne:

Hadisi ya zo a Sahihul Bukhari, da Muslim, an tambayi Anas bin Malik (a),


shin Manzon Allah ‫ ﷺ‬yana salla a sanye da takalmansa? Sai ya ce: “Ƙwarai kuwa”.

Hadisi ya zo a Sunanu Abi Dawud, daga Shaddadu bin Aus (a), daga Annabi
‫ ﷺ‬ya ce: “Ku saɓa wa Yahudawa, domin ba sa yin Salla a sanye da takalmansu, ko
kuma a sanye da huffinsu”. Albani ya inganta wannan Hadisin.

Malaman tarihi sun ambaci cewa: HaƘiƘa Abdullahi bin Mas’ud (a) ya
kasance shi ne ma’abocin takalman Manzon Allah ‫ﷺ‬. Ya kasance idan Annabi ‫ ﷺ‬ya
miƘe; sai ya sanya masa takalmansa, idan kuma ya zauna; sai ya ɗauka ya riƘe su a
hannunsa.

Abul-Abbas Al-maƘari ya ce: “Ya tabbata cewa Abdullahi bin Mas’ud (a)
ya kasance ma’abocin takalma, da asiwaki, da sirri, da kuma ruwan tsarkin Manzon
Allah ‫”ﷺ‬. Kamar yadda ya zo a cikin Bukhari.

ZOBEN MANZON ALLAH ‫ﷺ‬:

Daga Anas bin Malik (a) ya ce: “Zoben Annabi ‫ ﷺ‬ya kasance na azurfa ne,
kuma dutsen shi na habasha ne”. (wato adon da ake sanyawa a saman zoben).

Annawawi ya ce: HaƘiƘa Musulmai sun yi ijma’i a kan halaccin sanya zoben
azurfa, sai dai wasu malaman Sham na wannan Zamani sun karahanta sanya shi ga
wanda ba shi da sarauta. Kuma suka ruwaito asari a kan hakan, sai dai hakan ya saɓa
wa ingantattun hadisai, kuma wannan magana ba karɓaɓɓiya ba ce.
145
Al-Baji ya ce: “Amma game da sanya zoben azurfa, ga abin da Sa’idu binul
Musayyab ya ce wa SadƘatu bin Yasar: “Ka je ka sanya shi, kuma ka bai wa mutane
labarin cewa ni na ba ka fatawar hakan”.

Daga Anas bin Malik (a) ya ce: “Yayin da Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya so aika saƘon
rubutu zuwa ga Ajamawa. Sai aka ce da shi, haƘiƘa ajamawa ba sa karɓar wani
rubutu face sai dai idan da akwai sitamfi a kansa, sai ya haɗa sitamfi, kamar ni ɗin
nan ina hango farinsa a tafin hannunsa”. Bukhari da Muslim ne suka haɗu a ruwayar
wannan Hadisi.

Zanen dake jikin zoben Manzon Allah ‫ﷺ‬:

Daga Anas bin Malik (a) ya ce: “Rubutun dake jinkin zoben Manzon Allah
‫ ﷺ‬ya kasance kamar haka: Muhammad a layi ɗaya. Rasul a layi ɗaya, Allah a layi
ɗaya (waton an rubuta Muhammadun Rasulullahi a jiki)”. Bukhari ya ruwaito
wannan Hadisi.

Daga Ibn Umar (a) ya ce: “Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya riƘi zoben azurfa, ya kasance
a hannunsa. Sannan ya kasance a hannun Abubakar. (a) Sannan a hannun Umar.
(a) Sannan ya kasance a Hannun Usman (a), har sai da ya faɗa cikin rijiyar Aris
An rubuta Muhammdun Rasulullahi a jikisa)”. Bukhari da Muslim ne suka haɗu a
ruwayar wannan Hadisi.

Daga Aliyu bin Abi Ɗalib, haƘiƘa Annabi ‫ ﷺ‬ya kasance yana sanya zobensa
a hannunsa na dama. Nasa’i, da Ibnu Majah ne suka ruwaito Hadisin, Albani kuma
ya inaganta shi.

Mene ne hukuncin sanya zoben azurfa ga maza?

Maganar da take ingantacciya ita ce cewa ya halatta. Amma ba wai Sunna ba


ne. Dalili kuwa shi ne Manzon Allah ‫ ﷺ‬bai riƘi zobe ba har; sai da aka ce da shi

146
tabbas sarakuna ba sa karɓar wani rubutu har sai idan da akwai sitamfi akai, sai ya
yi riƘi zobe (wanda da shi ne yake buga sitamfi).

Kamar yadda hadisi ya zo a Sahihul Bukhari da Muslim, daga cikin Hadisin


Anas (a) cewa: Annabi ‫ ﷺ‬ya so ya aika wasiƘa zuwa ga Kisra, da Ƙaisar, da
Najashi, sai aka ce da shi: “HaƘiƘa su ba sa karɓan rubutun da babu sitamfi akai. Sai
Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya yi zobe, a zagaye da azurfa, aka rubuta Muhammadun
Rasulullahi a jiki”.

Manzon Allah ‫ ﷺ‬bai sanya zoben da nufin aikin ibada ba, wacce har da za a
nemi kusancin Allah da ita, balle ya zama mustahhabi (wato abin da aka so mutum
ya yi, kuma ya sami lada idan ya aikata), Saboda haka ne sai ya zama halak ne kawai,
in ka sa ba lada, in ka bari ba alhaki.

Rawanin Manzon Allah ‫ﷺ‬:

Daga Jabir (a) ya ce: “Annabi ‫ ﷺ‬ya shiga Makka ranar da aka buɗe ta, yana
sanye da rawani baƘi”. Muslim ya ruwaito wannan Hadisi.

Daga Ja’afar bin Huraisu (a), daga Babansa cewa: “Annabi ‫ ﷺ‬ya yi wa
mutane huɗuba yana sanye da baƘin rawani”. Muslim ya ruwaito wannan Hadisi.

Annawawi ya ce: “A cikin wannan Hadisi akwai nuna halaccin saka baƘin
tufafi, da sanya shi yayin huɗuba, ko da kuwa fari ya fi shi falala. Kamar yadda ya
tabbata a ingantaccen Hadisi, Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya ce: “Mafi alherin tufafinku shi ne
fari”. Abu Dawud, da Tirmizi ne suka ruwaito hadisin, Albani ya inganta shi.

Daga Ibn Umar (a) ya ce: “Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya kasance idan ya yi rawani
yana sakin shi zuwa kan kafaɗunsa”. Tirmuzi ya ruwaito hadisin kuma ya kyautata
shi.

147
Ba Sunna ba ne saka rawani. Sunna ce ta al’ada, ba sunnar ibada ba ce.
Manzon Allah ‫ ﷺ‬bai sanya rawani domin bauta ba, kuma bai umarci al’umarsa da
sanyawa ba.

Kwarjallen Manzon Allah ‫ﷺ‬

Daga Ubaidu bin Khalid Al-muharibi (a) ya ce: “Yayin da nake cikin tafiya
a Madina kawai sai na ji mutum a bayana yana cewa: “Ka ɗage kwarjallenka, domin
hakan shi yafi taƘawa (jin tsoron Allah), kuma ya fi wanzar da tufafinka, sai ya ce:
“Ai baƘin mayafi ne, (mai zane baƘi da fari, wanda baya cikin tufafin Larabawa, da
suke sakawa domin alfahari), sai Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya ce: “Shin ba zaka yi koyi da ni
ba? Sai na duba sai naga kwarjallensa zuwa rabin Ƙwaurinsa ne”.

Daga Huzaifa Binul Yamani (a) ya ce: “Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya kama guiwar
Ƙwaurina, ko Ƙwaurinsa, sai ya ce: “Wannan shi ne bigiren kwarjallenka, idan ka Ƙi
kuma; to zuwa Ƙasan haka, amma kada kwarjallenka ya rufe idon sawunka”. Tirmuzi
ya ruwaito wannan Hadisi, kuma ya inganta shi.

Hukuncin Jan Tufafi A Ƙasa

Jan tufafi a Ƙasa haramun ne. HaƘiƘa Muslim ya ruwaito daga Abu Zarrin,
haƘiƘa Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya ce: “Mutum ukun nan Allah ba zai yi magana da su ba,
kuma bai zai yi duba zuwa gare su ba, kuma ba zai tsarkake su ba. Sai na ce: “Su
waye ya Manzon Allah ‫ ?ﷺ‬Sun taɓe, sun yi asara. Sai ya maimaita har sau uku. Na
ce: “su waye? sun taɓe sun yi asara”. Sai ya ce: “Wanda yake jan tufafinsa a Ƙasa,
da annamimi, da mai siyar da kadararsa da rantsuwar Ƙarya, ko Fajiri”.

Hadisi ya zo a cikin Sahihul Bukhari, daga Abu Huraira(a) , ya ce: Manzon


Allah ‫ ﷺ‬ya ce: “Abin da ya yi Ƙasa da idon sawu na kwarjalle to yana wuta”.

148
Daga Abu Sa’id Alkhudri (a) ya ce: Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya ce: “Kwarjallen
Musulmi zuwa rabin Ƙwaurinsa ne. Amma babu lafi cikin abin da yake tsakanin
rabin Ƙwaurin zuwa idon sawu. Abin da ya yi Ƙasa da idon sawu kuwa; to yana wuta”
Abu Dawud ne ya ruwaito hadisin, Albani kuma ya inganta shi.

A cikin waɗannan nassoshin akwai bayanin cewa jan tufafi a Ƙasa gabaɗaya
haramun ne. Sai dai haramcin yana Ƙaruwa idan an yi don jiji da kai, da alfahari.
Domin haka sai uƘuba ta Ƙaru. Amma kawai saukar da tufafi zuwa Ƙasa da idon
sawu ba tare da jiji da kai ba, shi ma yana tabbatar wa da mutum uƘuba, da wuta.

Ibnul Arabi ya ce: “Bai halatta ba tufafi ya Ƙetare idon sawun mutum, ko ya
ce: ai ba ina jan shi ba ne don jiji da kai. Domin lafazin hanin ya nuna hakan, domin
haka, bai halatta mutum ya saɓa wa abin da lafazi ya yi nuni a kai ba”.

149
Auna Fahimta

 Ka yi rubutu game da siffar jikin Manzon Allah ‫ﷺ‬, tare da amfani da sabbin
kalmomi.

--------------------------------------------------------------------------------------------------

--------------------------------------------------------------------------------------------------

--------------------------------------------------------------------------------------------------

 Me ake nufi da tambarin Annabta? Yaya kamarsa take? A ina yake? Mene ne
dalili a kan samuwarsa?

--------------------------------------------------------------------------------------------------

--------------------------------------------------------------------------------------------------

--------------------------------------------------------------------------------------------------

 Me aka sunnanta yayin saka sabon tufafi?. Ambato dalilin yin hakan?

--------------------------------------------------------------------------------------------------

--------------------------------------------------------------------------------------------------

--------------------------------------------------------------------------------------------------

 Mene ne hukuncin sanya jan tufafi zalla? Waɗanne ire–iren launuka shari’a
ta yi kira da a yi amfani da su na tufafi?

--------------------------------------------------------------------------------------------------

--------------------------------------------------------------------------------------------------

--------------------------------------------------------------------------------------------------

150
 Mene ne hukuncin tafiya da warin takalmi ɗaya? A cikin karance-karancen
da ka yi, banda wannan littafin, rubuta illar da ta sa aka yi hani game da hakan.

--------------------------------------------------------------------------------------------------

--------------------------------------------------------------------------------------------------

--------------------------------------------------------------------------------------------------

 Rubuta ɗan Ƙaramin bayani game da zoben azurfa, ko zinare ga maza. Ya


Ƙa’idar saka rawani ta ke?

--------------------------------------------------------------------------------------------------

--------------------------------------------------------------------------------------------------

--------------------------------------------------------------------------------------------------

 Rubuta dalilai game da haramcin jan tufafi a Ƙasa, tare da tattauna maganar
masu cewa ya halatta.

--------------------------------------------------------------------------------------------------

--------------------------------------------------------------------------------------------------

-------------------------------------------------------------------------------------------------

151
Yanayin Tafiyar Manzon Allah ‫ﷺ‬

Daga Anas (a) ya ce: “Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya kasance tsakatsakin mutane. Shi
ba dogo ba, kuma ba gajere ba. Idan yana tafiya yana ɗaga Ƙafafunsa, (wato ba jan
Ƙafa yake ba, idan yana tafiya)”. Tirmuzi ne ya ruwaito wannan Hadisi, Albani kuma
ya inganta shi.

Daga Ibnu Abbas (a) ya ce: “HaƘiƘa Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya kasance idan yana
tafiya, yana tafiya da gabaɗayan jikinsa, ba tare da wata kasala ba”. Ahmad ne ya
ruwaito Hadisin, Arna’uɗ kuma ya inganta shi.

A ruwayar wajen Ahmad kuma Aliyu ya ce: “Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya kasance
idan yana tafiya (yana sauri) kamar yana gangarowa daga kan tudu”. Arna’uɗ ya
kyautata wannan Hadisi.

Cewar kamar yana gangarowa daga kan tudu. Hakan yana nuna yadda yake
sauri a cikin tafiyarsa.

Ibnul Ƙayyim ya ce: “Amma kuma yanayin tafiyarsa tare da sahabbansa, sun
kasance suna tafiya ne a gabansa, shi kuma yana bayansu. Yana cewa: “Ku barwa
Mala’iku bayana…..Ya kasance yana tafiya ba takalmi a Ƙafarsa, wani lokacin kuma
da takalmi a Ƙafarsa”.

Yanayin Zaman Manzon Allah ‫ﷺ‬:

Daga Ƙailatu binti Makhrama (d) cewa tabbas ta ga Manzon Allah ‫ ﷺ‬a
masallaci, yayin zaman Ƙurfasa’u. Abu Dawud ya fitar da wannan Hadisi Albani
kuma ya ce: “Hadisi ne mai kyau”.

Zaman Ƙurfasa’u shi ne mutum ya zauna a kan mazaunansa, sai ya haɗa


cikinsa da cinyoyinsa, ya sanya hannayensa a kan Ƙwaurinsa.

152
Daga Abbad bin Tamim, daga Baffansa (a), cewa shi ya ga Manzon Allah
‫ ﷺ‬yana kishingiɗe a masallaci, ya ɗora Ƙafarsa a kan ɗayar. Bukhari da Muslim ne
suka ruwaito shi.

Amma game da abin da Muslim ya ruwaito, daga Jabir bin Abdullahi cewa
lalle Annabi ‫ ﷺ‬ya ce: “Kada ɗayanku ya kishingiɗa, sannan ya ɗora Ƙafarsa a kan
ɗaya”.

Al’imamun Nawawi ya bayar da amsa ya ce: “Malamai sun ce: Hadisan da


suka yi hani game da kishingiɗa tare da ɗora Ƙafa a kan wata, za a ɗauki hakan ne
ga yanayin da al’aurar mutum zata iya bayyana, idan ya yi. Ko wani abu na daga
al’aurar. Amma kuma abin da Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya yi, ya yi ne ta fuskar da ba wani
abu da zai bayyana na al’aurarsa. To wannan babu laifi, kuma ba a karhanta wanna
sifar ba.

Yanayin zaman cin abincinsa ‫ﷺ‬:

Game da yadda zaman wanda zai ci abinci yake, to Muslim ya ruwato a


littafinsa daga Anas bin Malik ya ce: “Na ga Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya yi zaman iƘa’i yana
cin dabino”

Sheik Ibnu Usaimin ya ce: “Zaman IƘa’i, shi ne mutum ya cake Ƙafafunsa, ya
zauna a kan diga-digansa, Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya zauna ne a hakan; domin kada ya jima
a zaune, kuma domin kada ya ci abincin da yawa. Domin mafi yawanci idan mutum
cake Ƙafafunsa ya zauna; to ba ya samun nutsuwa sosai a zaman. To ba zai ci da
yawa ba. Idan mutum ba a nutse yake ba; to ba zai ci abinci da yawa ba, idan kuwa
a nutse yake, to zai ci abincin da yawa. Wannan shi ne abin da ya fi yawa.

153
Al-hafiz Ibnu Hajar ya ce: “Abin da aka fi so game da siffar zaman cin abinci,
shi ne mutum ya gurfana a kan guyawun Ƙafarsa, ya zauna a bayan Ƙafafunsa, ko
kuma ya cake Ƙafar dama ya zauna a ta hagu…

Daga Abu Juhaifa ya ce: Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya ce: “Bana cin abinci a
kishingiɗe”.

Kisihingiɗe: Shi ne mutum ya zauna ya karkata a ɓarin jikinsa.

Annawawi ya ce: “Ma’anar Hadisin shi ne: Wato ba na zaman cin abinci irin cin
wanda zai ci da yawa, ya zauna zaman dirshan. A’a ina zama ne kamar zaman wanda
zai tashi, sai na ci abincin kaɗan.

Zaman ittaka’in Manzon Allah ‫( ﷺ‬kashingiɗa)

Ana amfani da kalmar ittika’i, a harshen Larabci, da ma’ana biyu:

Ta farko: Ita ce: Mutum ya zauna ya karkata a wani ɓarin, ya dogara da ɗaya daga
cikin ɓarin jikinsa (wato abin da aka fi sani a Hausa da suna kashingiɗa), wannan
shi ne abin da ya fi shahara. Ibn Asir ya ce: “Gama garin mutane ba su san kalmar
ittika’i da wata ma’ana ba; sai ga wanda ya ɗan karkata a zamansa, kuma ya dogara
da ɓarin jikinsa (kamar hannu)”.

Na biyu kuma Ita ce: Mutum ya yi zaman dirshan, yana daga cikin wannan
ma’anar faɗin Allah: ٣٤:‫( ﱡﭐﱃﱄﱅﱆﱠ ال زخرف‬da gadaje a kansu
suke kashingiɗa) (Zukhruf: 34), wato ana zama a kai, da kuma faɗinsa:
٣١ :‫ﭐﱡﭐﱆﱇﱈﱠ يو سف‬
(Ta yi tattalin abincin da ake dogara wajen cinsa) (Yusuf: 31), wato ta samar musu
abin zama da zasu zauna a kai zaman dirshan.

154
Daga Jabir bin Samuratu (a) ya ce: “Na ga Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya zauna, ya
dogara da filo, da hannunsa na hagu”. Abu Dawud, da tirmuzi ne suka fitar da
wannan Hadisi, kuma Albani ya inganta shi.

Daga Abdurrahman bin Abi Bukrata daga babansa (a), ya ce: “Manzon
Allah ‫ ﷺ‬ya ce: “Shin ba na ba ku labarin mafi girman laifi ba? Sai suka ce: Na’am
Ya Manzon Allah ‫ﷺ‬, Sai ya ce: Haɗa wani da Allah a wajen bauata (shirka), da saɓa
wa iyaye, ya ce: sai Manzon Allah ‫( ﷺ‬ya gyara) zama, da ya kasance a kashingiɗe,
sai ya tashi, sai ya ce: “Da shaidar Ƙarya, da maganar Ƙire, ya ce: Manzon Allah ‫ﷺ‬
bai gushe ba yana ta nanatawa, har sai da muka ce: ina ma dai ya yi shiru”. Bukhari,
da Muslim ne suka ruwaito shi.

Hadisin Abu Juhaifa ya gabata cewa: “haƘiƘa Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya ce: (Bana
cin abin ci a kishingiɗe l”

Daga Abdullahi bin Busur (a), ya ce: “Na bai wa Manzon Allah ‫ ﷺ‬kyautar
(naman) akuya, sai Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya gurfana a kan guyawun Ƙafarsa yana ci, sai
wani balaraben Ƙauye ya ce: wannan wanne irin zama ne? sai (Manzon Allah ‫ )ﷺ‬ya
ce: “HaƘiƘa Allah ya sanya ni bawa mai karamci, bai sanya ni bawa mai girman kai
da tsaurin rai ba”. Abu Dawud, da Ibnu Majah ne suka ruwaito Hadisin, Kuma albani
ya inganta shi.

Yanayin guminsa ‫ﷺ‬

Bukhari da Maslim sun ruwaito daga Anas (a) ya ce: “Ban taɓa taɓa wani
alhariri, ko dibaji da ya fi tafukan hannun Manzon Allah ‫ ﷺ‬laushi ba. Kuma ban taɓa
shaƘar wani turare, ko wani Ƙamshi da ya fi Ƙamshin jikin Manzon allah ‫ ﷺ‬Ƙamshi
ba”.

155
Bukhari ya ruwaito daga Abu Juhaifa (a) ya ce: Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya fita
cikin tsananin rana, zuwa bayan garin Makka, sai ya yi alwala, sannan ya yi Sallar
Azahar raka’a biyu (Ƙasaru), ya yi La’asar ma raka’a biyu. A gabansa akwai wata
sanda (wato ya yi sitira da sandar), sai ya wuce ta bayan sandar. Sai mutane suka
miƘe, suka kama hannayan Manzon Allah ‫ ﷺ‬suna shafar fuskokinsu da su. Ya ce:
Sai nima na kama hannunsa na sanya a kan fuska ta. Sai na ji sun fi ƘanƘara sanyi,
kuma sun fi turaren almiski Ƙamshi”.

Muslim ya ruwaito daga Jabir bin Samurata ya ce: “Na yi salla tare da Manzon
Allah ‫ … ﷺ‬sai ya fito zuwa wajen iyalinsa, sai nima na fito tare da shi. Sai wasu yara
suka zo wajensa, sai ya dinga shafar kumatunsu ɗaya bayan ɗaya, ya ce: Nima sai
ya shafi kumatuna, ya ce: sai na ji sanyi a hannunsa, ko Ƙamshi kamar ya fito da
hannayensa daga cikin mazubin turare”.

Muslim ya ruwaito daga Anas (a) ya ce: “Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya kasance mai
kyakkyawan launi, guminsa kai ka ce lu’u lu’u ne … kuma ban taɓa shaƘar wani
almiski, ko turaren anbar da ya fi Ƙamshin Manzon Allah ‫ ﷺ‬ba”.

Ana gane zuwan Manzon Allah ‫ ﷺ‬daga Ƙamshin turarensa; da ake shaƘa tun
daga nesa. Darimi ya ruwaito daga Jabir bin Abdullahi cewa: haƘiƘa Annabi ‫ ﷺ‬ba
zai bi wata hanya ba, kuma wani ya bi wannan hanyar; face sai ya gane cewa Manzon
allah ‫ ﷺ‬ya bi wannan hanyar, saboda Ƙamshin guminsa.

Kai haƘiƘa (sahhabai) sun kasance suna ɗibar guminsa a matsayin turare.
Domin Muslim ya Ƙara ruwaitowa daga Anas bin Malik (a), ya ce: “Manzon Allah
‫ ﷺ‬ya shigo mana, sai ya yi baccin rana a wajenmu. Sai ya yi gumi, sai mahaifiyata
ta zo da kwalba, sai ta dinga matsar gumin tana zubawa a cikin kwalbar, sai Annabi
‫ ﷺ‬ya farka, sai ya ce: “Ya ke Ummu Sulaimd,,, ,me kike yi haka ne?” sai ta ce:
“wannan guminka ne, muna zu ba shi a cikin turarenmu domin ya fi turare Ƙamshi”.
156
Turaren Manzon Allah ‫ﷺ‬:

Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya kasance yana son turare har ma yana cewa: “Abin da aka
saka mini son su a cikin wannan duniya su ne mata, da kuma turare. Kuma an saka
mini sanyin idanuwana a cikin Salla”. (wato abin da yake faranta misa rai). Ahmad,
da Abu Dawud ne suka ruwaito wannan Hadisi, kuma Albani ya inganta shi.

Ƙamshi mai daɗi na daga cikin siffofin Manzon Allah ‫ﷺ‬, ko da kuwa bai sanya
turare ba. Daga Anas bin Malik (a) ya ce: “Ban taɓa taɓa wani alhariri, ko dibaji
da ya fi tafukan hannun Manzon Allah ‫ ﷺ‬laushi ba, kuma ban taɓa shaƘar wani turare
da ya fi Ƙamshin jikin Manzon Allah ba ‫”ﷺ‬. Hadisin ya gabata.

Ya kasance ana gane zuwansa, ko tafiyarsa, da Ƙamshin jikinsa. Abu Ya’ala


da Bazzar sun ruwato, kuma Ibnu Hajar ya inganta Isnadin hadisin daga Anas (a)
ya ce: “Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya kasance idan ya wuce ta wata hanya, daga cikin hanyoyin
Madina, sai a dinga jin Ƙamshin almiski, sai a dinga cewa: Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya
wuce”.

Saboda haka ne yake Ƙyamatar duk wani abu da zai sa aji wari daga wajensa,
hakan yasa ya bar cin abubuwa da yawa da suka halatta, kamar tafarnuwa, da albasa,
da lawashi, da makamancinsu, saboda warinsu.

Sanya turare, da kuma son turare da Manzon Allah ‫ ﷺ‬yake yi, ya nuna kenan
saka turare ba girman kai ba ne, kai hakan ma zai iya zama abin da za a sami lada a
kai. Kamar cin ado yayin da za a yi salla, ko kuma wajen taruwar jama’a da
makamanacin haka. Kuma abu ne mai kyau mace ta saka turare domin mijinta, haka
mijin ma ya saka domin matarsa. HaƘƘin malami ne ya saka turare domin sanya
girman ilimi a cikin zuƘatan mutane da sauransu.

157
Lokutan da aka fi ƙarfafa wa mutum ya sanya turare:

An Ƙarfafa cewa maza su sanya turare a ranar Juma’a, da idin Ƙarama, da babbar
Sallah. Da wajen ɗaukar haramar aikin hajji, da wajen halartar sallar jam’i, haka ma
yayin karatun AlƘur’ani, ko wajen bayar da ilimi, ko yayin zikiri.

An Ƙarfafa wa maza, da mata su sanya turare yayin rungumar juna. Domin


hakan na daga cikin kyakkyawar zamantakewa.

Bai halatta ba mace ta sanya turare ta fito kan waje ba, ko ta shiga tsakankanin
maza. HaƘiƘa alƘawarin narkon azaba mai raɗaɗi ya zo a kan haka. Annabi ‫ ﷺ‬ya ce:
“Duk matar da ta sanya turare ta wuce mutane domin su ji Ƙamshinta, to mazinaciya
ce”.

Nasa’i ya ruwaito wannan Hadisi, kuma Albani ya ce Hadisin mai kyau ne.

158
Sunayen Manzon Allah ‫ﷺ‬

Daga Jabir bin Muɗ’im, ya ce: Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya ce: “HaƘiƘa ina da sunaye,
Ni ne: Ahmad, kuma ni ne Mahi, wanda Allah Ya share kafirci da shi. Ni ne Hashir
wanda za a tashe shi kafin sauran mutane (ranar AlƘiyama). Ni ne AƘibu, wanda
babu wani Annabi a bayansa”.

Muhammad: Saboda yana da ɗabi’u masu kyau, da ake yawan yabon shi a kansu,
saboda haka suna Muhammad ya fi nuna kaiwa matuƘa wajen yabo, fiye da suna
Mahmud.

Ahmad: Suna ne a ma’aunin Af’ala domin ya nuna fifiko a cikin sunan. An ciro
sunan daga Alhamdu, (wato yabo, ko godiya).

Ɗaya daga cikin sunayen ya yi nuni ga cewa Shi Muhammad ne, saboda
kasancewarsa Mahmud (wato Sha Yabo), ɗaya sunan kuma ya nuna Shi ne Ahmad,
saboda kasancewarsa mafi godiya ga Ubangijinsa Mai Girma da Ɗaukaka.

Mahi: Shi ne wanda Allah Ya share kafirci da shi a ban Ƙasa, Allah bai share kafirci
da wani daga cikin halittunsa ba; fiye da yadda ya share kafirci da (aiko) Annabi ‫ﷺ‬.

Domin kuwa Allah ya aiko shi yayin da mutanen duniya bakiɗaya suke kan
kafirci, sai kaɗan daga cikin Ahlul kitabi da suka rage. Mutane daga masu bautar
gumaka, sai Yahudawan da aka yi fushi da su, sai kuma ɓatattun Nasara, da kuma
Sabi’abawa masu bauta wa zamani, basu san wani Ubangiji, ko wata makoma ba,
sai kuma masu bautar taurari, da masu bautar wuta, da sauransu. HaƘiƘa Allah l
Ya yi duba zuwa ga mutanen duniya a wannan lokaci, sai Ya yi fushi da su,
Larabawansu, da Ajamawansu, sai kaɗan ɗin da suka rage a kan abin da ya yi saura
na addinin Ƙwarai, Sai Allah Ya (aiko shi) ya taimaki garuruwa, da da mutane. Ya
yaye wannan duhun da ake ciki. Ya rayar da halittu bayan mutuwa. Ya shiryar da

159
mutane bayan ɓata, ya ilimantar da su bayan jahilicin da suke ciki. Ya buɗe
idanuwan mutane da shi; bayan makancewarsu, da kunnuwansu bayan
kurmancewarsu, da zukata bayan rafkanarsu, har sai da Addinin Allah ya ɗaukaka a
kan sauran Addinai. Ya isar da wannan Addinin nasa zuwa inda rana, da dare suka
isa. Kira zuwa ga wannan Addini ya tafi tafiya irin ta rana, zuwa ga dukkanin sassan
duniya.

Hashir: Saboda shi za a fara tayarwa daga Ƙabarinsa, kafin a tashi sauran mutane.
Kamar yadda ya zo a cikin wani Hadisi: “Ni ne farkon wanda Ƙasa zata tsage da shi)
(wato za a tashi mutane bayansa, ko kuma za su bi shi bayan tashinsa daga Ƙabari”.
Bukhari ne ya ruwaito shi.

AƘibu: Wato Annabin da ya zo a Ƙarshen Annabawa, shi ne na Ƙarshe cikamakon


Annabawa, ba wani Annabi bayansa.

an karɓo daga Huzaifatu (a) ya ce: “Na haɗu da Annabi ‫ ﷺ‬a wani sashe na
hanyoyin Madina. Sai ya ce: “Ni ne Muhammad. Ni ne Ahmad. Ni ne Nabiyyur-
Rahma. Ni ne MuƘaffi. Ni ne Hashir. Ni ne Nabiyyul-Malahimu”.

Tirmuzi ne ya ruwaito wannan hadisin a cikin Shama’il, kuma Albani ya ce: “Hadisi
ne mai kyau”.

Nabiyyur-Rahma: Wato wanda Allah l ya aiko shi domin jin Ƙai, Allah l Ya
ce:

١٠٧ ‫ﱡﭐﲀﲁﲂﲃﲄﲅﱠ‬
“Kuma ba Mu aike ka ba face domin rahama ga talikai” (Anbiya: 107), haƘiƘa Allah
ya jiƘan halittu bakiɗaya da aiko shi. An aiko shi domin rahama ga al’umarsa, kuma
rahama ga talikai.

160
Nabiyyut-Tauba: Wato wanda da shiriyarsa ne za a karɓi tuban mutum, kuma
mutum zai koma ga Ubangijnsa.

MuƘaffi: Wato wanda yake bin gwadaben Annabawan da suka zo gabaninsa, sai ya
zama shi ne na Ƙarshe, kuma cikamakonsu, ana iya cewa: MuƘaffi ko MuƘaffa).

Nabiyyul-Malahimi: Wato wanda aka aiko domin ya yaƘi maƘiyan Allah. Kuma
yaƘe–yaƘen da suka faru tsakanin al’umarsa, da kafirai ba a taɓa samun irunsu ba;
ga al’umomin da suka shuɗe.

Ɗaha, ko Yasin: Basa cikin sunayen Annabi ‫ﷺ‬, ba a taɓa samun wani asari
ingantacce ba; a kan haka. Ko daga wani cikin magabata nagari, madogarar wannan
Maganar wani Hadisi ne mai rauni da yake cewa: “Ina da sunaye goma a wajen
Ubangijina, sai ya ambaci cewa a cikin sunayen akwai Ɗaha da Yasin”.

Ibnul Ƙayyim ya ce: “Amma abin da gama-garin mutane suke faɗa cewa:
Ɗaha, da Yasin suna cikin sunayen Manzon Allah ‫ﷺ‬, to babu wani ingantaccen
Hadisi, ko hadisi mai kyau, ko Mursalin hadisi, kai ko ma wata magana daga wani
Sahabi, wanɗannan kawai harrufa ne irinsu: A L M, da H M, da A L M R. da
makamantansu”.

161
Auna Fahimta

 Siffanta yanayin tafiya, da kuma yanayin zaman Manzon Allah ‫ﷺ‬, tare da
bayanin ire-iren zaman da aka hana.

--------------------------------------------------------------------------------------------------

--------------------------------------------------------------------------------------------------

--------------------------------------------------------------------------------------------------

 Me ake nufi da zaman kishingiɗa?, Tare da ambaton siffar yadda ake yin shi,
ka ambaci dalilin ka?

--------------------------------------------------------------------------------------------------

--------------------------------------------------------------------------------------------------

--------------------------------------------------------------------------------------------------

 Ka yi Ƙwarya-Ƙwaryan bincike a kan tabarruki da kabarin Annabi ‫ ﷺ‬wanda


aka hana, kuma mene ne hukuncin tabarruki da salihan bayi, tare da ambaton
dalili.

--------------------------------------------------------------------------------------------------

--------------------------------------------------------------------------------------------------

--------------------------------------------------------------------------------------------------

 Ka ambaci suna biyar daga cikin sunayen Annabi ‫ﷺ‬. tare da sharhin
ma’anarsu, wanne irin kuskure gama-garin mutane suke tafkawa a ciki a
wannan babi?

--------------------------------------------------------------------------------------------------

--------------------------------------------------------------------------------------------------
162
--------------------------------------------------------------------------------------------------

Yadda Manzon Allah ‫ ﷺ‬yake cin abinci:

Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya tabbatar da wani asali mai girma game da cin abinci, shi
ne faɗinsa: (Ɗan’adam ba zai cika wani burgami ma sharri ba; fiye da cikinsa. ƴan
lomomi kaɗan da zai ci sun ishe shi, su tsayar da ƙashin bayansa da su (su ba shi
kuzarin rayuwa) Idan ba makawa sai ya ci (da yawa, to ya raba cikinsa gida uku),
ɗaya na abincinsa, ɗaya na abin shansa, ɗaya na numfashinsa”. Ahmad, da Tirmuzi
ne suka ruwaito Hadisin, kuma suka inganta shi.

Daga Abu Huraira (a), ya ce: Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya ce: “Musulmi yana cin
abinci cikin uwar hanji guda ɗaya, shi kuma kafiri yana ci cikin uwar hanji guda
bakwai”. Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi.

Ambaton sunan Allah yayin fara cin abinci (Bismillah) da kuma yin godiya
bayan kammalawa (Alhamdulillah).

An karɓo daga A’isha (a) ta ce: “HaƘiƘa Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya ce: Idan
ɗayanku zai ci abinci; to ya ambaci sunan Allah (Ya ce: Bismillah), idan kuma ya
manta bai ambata ba, to sai ya ce: Da sunan Allah a farko da Ƙarshe”. Abu Dawud
ne ya ruwaito Hadisin, kuma Albani ya inganta shi.

Daga Umar bin Abi Salama (a) ya ce: Na ci abinci tare da Annabi ‫ﷺ‬, sai ya
ce: “Ka Ambaci sunan Allah, kuma ka ci abin da ke gabanka”. Bukhari da Muslim
ne suka ruwaito shi.

Yayin kuma da ya gama cin abincin; sai ya ce: “Godiya ta tabbata ga Allahl,
godiya mai kyau, kuma karɓaɓɓiya. Godiyar da bawa ba zai wadatu daga barin ta
ba, kuma ba zai bar ta ba. Kuma ba zai wadatu daga ita ba ya Ubangijinmu (Ma’ana

163
wacce dole ɗan’Adam yana cikin buƘatar ya yi godiya mai yawa ga Allah
Maɗaukakin Sarki). Bukhari ne ya ruwaito wannan hadisin.

Ya zo a wata ruwayar yana cewa: “Godiya ta tabbata ga Allah wanda Ya ciyar


da mu, Ya shayar da mu. Godiyar da ba zamu iya wadatuwa da barin ta ba, kuma ba
za mu yi inkarin ni’imar Allah ba a kanmu ba”.

An karɓo daga Anas (a), haƘiƘa Annabi ‫ ﷺ‬ya ce: HaƘiƘa Allah l Yana
yarda da bawa idan ya ci abinci, ya yi godiya gare shi a kan wannan abincin, ko
kuma ya sha abin sha, sannan ya gode wa Allah a kan hakan) Muslim ne ya ruwaito
wannan hadisin.

Yana daga cikin Sunnar Manzon Allah ‫ﷺ‬: Cin abinci da hannun dama, da
kuma cin abin dake gabansa. HaƘiƘa hadisi ya zo daga Annabi ‫ ﷺ‬yana cewa: “Idan
ɗayanku zai ci abinci; to ya ci da hannun damansa, idan kuma zai sha; to ya sha da
hannun damansa, domin Shaiɗan ne yake ci da hannun hagunsa, kuma yake sha da
hannun hagunsa”. Muslim ne ya ruwaito wannan hadisin.

An karɓo daga Anas bin Malik (a), ya ce: “Annabi ‫ ﷺ‬ya kasance idan ya ci
abinci yana siɗe ƴan yatsunsa guda uku”. Muslim ne ya ruwaito wannan hadisin.

Bayani game da yanayin zaman cin abincinsa ya gabata.

Annabi ‫ ﷺ‬ba ya cin wasu ire-iren abincin:

Annabi ya kasance ba ya cin naman damo. Ya bayar da dalilin hakan da


faɗinsa; (...saboda bai kasance a Ƙasar mutanena ba, shi ya sa na sami kaina ina
Ƙyamatar naman). Bukhari da Muslim ne suka ruwaito wannan hadisin.

Haka nan Manzon Allah ‫ ﷺ‬ba ya son tafarnuwa, saboda warinta. Daga Abu
Ayyuba Al’ansari (a): “HaƘiƘa Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya kasance idan ya ci abinci yana
aika wa Abu Ayyuba ragowar abincin, sai wata rana aka kawo masa akushin abinci
164
da tafarnuwa a ciki, sai ya aike da shi (zuwa ga Abu Ayyuba) sai ya ce: “Ya Manzon
Allah ‫ ﷺ‬cin ta haramun ne?” sai ya ce: “a’a, sai dai ni ba na son warinta”

Ahamad ne ya ruwaito shi, Al’arna’uɗ ya inganta shi.

Shiryarwarsa /Sunnarsa game da abin da aka kawo masa na abinci:

Manzon Allah ‫ ﷺ‬bai kasance yana mayar da abin da aka samu na abinci ba,
kuma ba a taɓa kawo masa abinci ba face sai ya ci. Sai dai idan ransa ba ya so; sai
ya bar shi. Daga Abu Huraira (a) ya ce: “Annabi ‫ ﷺ‬bai taɓa kushe abinci ba. Idan
ya ji yana son abinci; sai ya ci, idan kuma baya son abinci; sai ya bar shi”. Bukhari
da Muslim ne suka ruwaito wannan hadisin.

Yanayin Shan Ruwan Annabi ‫ﷺ‬

Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya kasance yana shan ruwa sau uku. Daga Anas bin Malik
(a) “HaƘiƘa Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya kasance yana yin numfashi sau uku idan ya sha
ruwa”. Bukhari da Muslim ne suka ruwaito wannan hadisin.

A wata ruwayar ta Muslim yana cewa: “Domin hakan ya fi tafiyar da Ƙishirwa,


kuma ya fi lafiya, kuma ya fi rashin nauyaya hanji).

Kuma ya yi hani da ayi nufmashi a cikin mazubin ruwa, ya ce: (Idan ɗayanku
yana shan ruwa kada ya yi nunfashi a cikin mazubin ruwan”. Bukhari da Muslim ne
suka ruwaito wannan hadisin.

Ibnul Ƙayyim ya ce: “Ma’anar yin numfashi yayin shan ruwa; shi ne mutum
ya nesantar da Ƙwarysa (abin shan ruwansa) daga bakinsa. Ya yi numfashin a waje.
sannan sai ya Ƙara komawa ya ci gaba da sha”.

165
Malamai suka ce: “Hani da aka yi game da yin numfashi a cikin abin shan
ruwa. An yi hakan ne saboda ladabi. Don tsoron kada a sanya Ƙazanta a ciki, ko wari,
ko wani abin ya faɗa cikin ruwan daga baki, ko hanci, da makamantan haka.

Ibnu Hajar ya ce: “Wannan ita ce hanya mafi kyau, da lafiya, za abi wajen
kauce wa cututtuka”.

Kamar yadda Hadisai suka zo game da hani a kan shan ruwa ta bakin salka,

Akwai hadisin da Bukhari ya ruwaito daga Abu Huraira (a) ya ce: “Manzon Allah
‫ ﷺ‬ya yi hani game da shan ruwa daga bakin salka”.

A cikin Sahihul Bukhari, da Sahihu Muslim, daga Hadisin Abu Sa’id ya ce:
“Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya yi hani da shan ruwa daga bakin salka”.

Al’iraƘi ya ce: “Abin da zai iya kasancewa na uziri kamar ace salkar ruwan a
rataye take, ko kuma wanda ya zo shan ruwan bai samu wani mazubi ba; da zai iya
zuba ruwan a ciki. Kuma ba zai iya shan ruwan da tafukan hannayensa ba, to babu
karahanci a wannan lokacin, a kan wannan ma’anar ne za a ɗauki waɗannan Hadisai
da aka ambata”.

Shan ruwa a tsaye:

Haka kuma Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya yi hani game da shan ruwa a tsaye. Manzon
Allah ‫ ﷺ‬ya ce: “Ka da ɗayanku ya sake ya sha ruwa a tsaye”. Muslimne ya ruwaito
wannan hadisin.

Sai dai kuma Hadisi ya tabbata cewa: Annabi ‫ ﷺ‬ya sha ruwa a tsaye. Daga
Ibnu Abbas (a) ya ce: “Na shayar da Manzon Allah ‫ ﷺ‬ruwan zamzam, sai ya sha
alhalin yana tsaye”. Bukhari da Muslim ne suka ruwaito wannan hadisin.

166
HaƘiƘa Malamai sun haɗa tsakanin wannan hani a wannan Hadisi kan cewa:
wancan hani da ya zo a cikin hadisi za a ɗauke shi a matsayin hani ne na karhanci.
Hadisin kuma da ya zo game da cewa ya sha ruwa a tsaye; a matsayin halaccin haka.

Tambaya

Shin wancan hadisin da ya yi hani game da shan ruwa daga bakin salka; zai
hau kan shan ruwa irin na roba, da leman kwalba iri-iri na wannan zamani? Shin
dole sai mutum ya zuba a wata moɗa, ko wani mazubin sannan zai sha?

Amsa: Idan muka yi duba zuwa ga illar da ta sa aka yi hani game da shan ruwa kai
tsaye daga bakin salka, zamu ga babu wannan illar game da ruwan roba, ko
waɗannan kwalabe. Domin mutum ɗaya ne yake sha, ba wani da zai Ƙara zuwa ya
sha daga kwalbar, ko robar. Ballantana mutum ya Ƙyamaci shan. Mas’alar Ƙwarewa
kuma, ko jiƘewar jiki, duk an kuɓuta daga ita, kuma an tsira daga samun Ƙwari ko
datti daga cikin kwalbar ruwan.

Daga cikin dalilan da ya sa aka yi hani game da shan ruwan kai tsaye daga
bakin salka:

Na farko: Saboda ba a aminta ba daga shigar Ƙwari cikin ruwan. Ƙwaro zai iya shiga
ta bakin gorar ba tare da an sani ba.

Na biyu: wanda yake shan ruwa kai tsaye daga Ƙwarya/ko wani mazubin ruwan; zai
iya rinjayar shi ya zubo da yawa fiye da buƘatarsa. Hakan zai iya sawa ya Ƙware.

Mahaɗin gurasar Manzon Allah ‫ﷺ‬:

Al’idamu a harshen Larabci ana nufin: Duk wani abu da ake haɗa shi da
gurasa a ci, ko da kuwa da me aka yi wannan abu.

167
Daga A’isha (a) ta ce: “HaƘiƘa Annabi ‫ ﷺ‬ya ce: “Madalla da a matsayin
Khallu, mahaɗin cin gurasa”.

Khallu: Ruwan Inibi ne, ko dabino, da ake matse shi, sai a dinga haɗa shi da gurasa,
ana ci.

Daga Ummu Hani Bintu Abi Ɗalib (a) ta ce: “Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya shigo
wajena, sai ya ce: “Shin akwai wani abu a wajenki (Abinci), sai na ce: a’a, sai dai
gurasa, da kuma khallu, sai Annabi ‫ ﷺ‬ya ce: Ka wo su. Ai gida ba ya talauta idan a
cikinsa akwai miya da mahaɗinta”. Tirmuzi ne ya ruwaito shi, kuma ya ce: “Hadisin
ne mai kyau”.

Muslim ya fitar da Hadisi daga Jabir (a) cewa: Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya tambayi
iyalinsa ko suna da (Idamu), mahaɗin gurasa? Sai suka ce: babu komai a wajenmu
sai dai Khallu, sai ya nemi a kawo misa, sai ya dinga ci yana cewa: “madallah da
Khallu mahaɗin cin gurasa, madallah da Khallu mahaɗin cin gurasa”. Jabir (a) ya
ce: “Ban gushe ba ina son Khallu tun da na ji ambaton shi daga bakin Manzon Allah
‫”ﷺ‬.

Daga Abu Sa’id (a) ya ce: Annabi ‫ ﷺ‬ya ce: “Ku ci zaitun (wato ku haɗa shi
tare da gurasa), kuma ku shafa shi, domin daga itaciya mai albarka yake”. Tirmuzi
ne ya ruwaito shi, Albani ya ce: “Hadisin ne mai kyau”.

Daga Anas bin Malik (a) ya ce: “HaƘiƘa wani maɗinki ya gayyaci Manzon
Allah ‫ ﷺ‬cin abinci da ya yi a (gidansa), Anas (a) ya ce: “Sai na tafi tare da Manzon
Allah ‫ ﷺ‬zuwa wajen wannan abinci, sai ya kawo wa Manzon Allah ‫ ﷺ‬gurasa, da aka
yi ta da sha’ir, da kuma room, a ciki akwai kabewa da busasshen nama”. Anas (a)
ya ce: “Na ga Manzon Allah ‫ ﷺ‬yana bibiyar kabewar a gefen akushin, (yana ci), tun
daga wannan lokacin ban gushe ba ina son kabewa”. Bukhari da Muslim ne suka
ruwaito wannan hadisin.
168
Kayan marmarin Manzon Allah ‫ﷺ‬:

Daga Abdullahi bin Ja’afar ya ce: “Annabi ‫ ﷺ‬ya kasance yana cin gurji, da
ɗanyen dabino”. Bukhari da Muslim ne suka ruwaito wannan hadisin.

Cewa yana cin gurji da ɗanyan dabino: abin da ake nufi yana cin su tare a
lokaci ɗaya.

Daga A’isha (x): “HaƘiƘa Annabi ‫ ﷺ‬ya kasance yana cin kankana, da
ɗanyan dabino”. Abu Dawud, da Tirmuzi ne suka ruwaito shi. Albani kuma ya
inganta Hadisin.

HaƘiƘa bayanin ma’anar hakan ta zo a cikin littafin Abu Dawud, Annabi ‫ ﷺ‬ya
ce: “Muna karya wannan (wato ɗanyan dabino, da sanyin wannan (wato kankana),
mu karya sanyin wannan kuma (wato kankana) da zafin wannan (ɗanyan dabino)”.
Mu kawar da zafin wannan da sanyin wancan. Ma’ana ɗanyan dabino da kankana
suna sassaita yanayin jiki.

Abubuwan da Manzon Allah ‫ ﷺ‬yake sha:

Daga A’isha (a) ta ce: “Abin da Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya fi so; na daga abubuwan
sha, shi ne ruwan kayan marmari mai sanyi”. Ahamd, da Nasa’i ne suka fitar da
Hadisin cikin Sunanul Kubra, Albani kuma ya inganta shi.

Ibn Ƙayyim ya ce: “Shi abin sha idan har ya haɗa siffofin ruwan kayan
marmari, ga kuma sanyi, to ya fi amfanar jikin mutum. Na daga cikin sababi mai
girma na kare lafiya, da ruhi, da Ƙarfin jiki, da hanta, da zuciya, akwai matuƘar
buƘatar shan kayan marmari, idan har aka same su a hakan; to zai Ƙara gina jikin
mutum, kuma ya isar da abincin da mutum ya ci zuwa ga gaɓɓansa.

169
Yanayin maganar Manzon Allah ‫ﷺ‬:

Daga A’isha (a) ta ce: “Manzon Allah ‫ ﷺ‬ba ya zubo zance kamar yadda
kuke zubowa. Sai dai shi yana yin magana a bayyane, kuma a rarrabe. Wanda yake
zaune tare da shi ma; yana iya haddace maganarsa”. Tirmuzi ne ya ruwaito shi, kuma
ya inganta shi.

Ma’ana: Manzon Allah baya yin gaggawa cikin zance, wani bayan wani,
kamar dai yadda kuka san gaggawarku a cikin zance.

Abin da ake nufi: Yana yin magana a hankali, kuma yana kaiwa matuƙa wajen
ya fahimtar da mutum. Saboda rashin saurinsa cikin zance, har wanda yake zaune
tare da shi, ko yake jin shi yana iya haddace maganarsa, saboda Ƙarancin zancen, da
kuma bayanin da yake.

Daga Anas bin Malik (a) ya ce: “Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya kasance yana maimaita
Magana sau uku, domin a fahimci abin da yake faɗa”. Tirmuzi ne ya ruwaito
Hadisin, Albani kuma ya inganta shi.

Wannan ita ce sunnar Manzon allah ‫ ﷺ‬a Sallama, da neman izini, da wanin
haka.

Maganar Manzon Allah ‫ ﷺ‬game da waƙa:

Daga MiƘdam bin Shuraihin daga babansa daga A’isha (a) ya ce: “An ce
wa A’isha (a), Shin Manzon Allah yana rera wani abu na waƘa? Sai ta ce: Ya
kasance yana rera waƘar Ibnu Rawaha, yana rera faɗinsa: “(Zamani) zai zo maka da
labarin wanda baka ba yi guzirinsa ba”. Tirmuzi ne ya ruwaito hadisin, kuma ya
inganta shi.

Amma faɗin Allahl:

170
٦٩ ‫ﱡﭐﲺﲻﲼﲽﲾﲿﳀﳁﳂﳃﳄﳅﳆ ﳇﱠ ي‬
:‫س‬
(Ba Mu sanar da shi (Annabi) waƘa ba, kuma waƘa ba ta kamata da shi (Annabi) ba)
(YS: 79), Ibnu Kasir ya ce: “Abin da ake nufi shi ne, waƘa bata cikin ɗabi’unsa ba,
kuma bai iya yi ba”.

Daga Abu Huraira (a) ya ce: Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya ce: “Mafi gaskiyar Magana
da mawaƘi ya faɗa, ita ce maganar Labid da ya ke cewa: “Ku saurara, duk wani abu
da ba Allah a cikinsa; to mai gushewa ne”. Bukhari da Muslim ne suka ruwaito

Labid, shi ne ibnu Rabi’ah Al-amiri, ya zo wajen Annabi ‫ ﷺ‬yayin da


mutanensa suka zo. Ya kasance yana da girma, da Ƙima a zamanin jahiliyya, da kuma
zuwan Musulunci. Ya zauna a garin Kufa. Ya rasu shekara ta 41 bayan hijira, yana
daga cikin fasihan Larabawa, da mawaƘansu. shi.

Daga Amru bin Sharid daga babansa ya ce: “Na kasance muna haye a kan
dabba tare da Manzon Allah ‫ﷺ‬, sai na rera masa waƙo baiti ɗari daga cikin waƘar
Umayyatu bin Salt As-saƘafi. Duk lokacin da na rera masa baiti; sai Annabin ya ce:
Ƙara mini, wato ka Ƙaro mini wani baitin, sai Annabi ‫ ﷺ‬ya ce: “MawaƘin ya kusa ya
karɓi Musulunci (amma kuma Allah bai datar da shi ba”. Muslim ne ya ruwaito shi.

Bukhari da Muslim sun ruwaito hadisi daga Jundub bin Sufyan Al-bajali, ya
ce: Dutse ya ji wa ɗan yatsan Manzon Allah ‫ ﷺ‬rauni sai ya ce:

“Kai ba komai ba ne face ɗan yatsa da ya yi jinni # Kuma duk abin da ya same ka
a tafarkin Allah ne”.

Hadisi ya zo a Sahihul Bukhari, daga Barra’u bin Azib (a), ya ce: “Wani
mutum ya tambaye shi. Shin kun gudu kun bar Manzon Allah ‫ﷺ‬, ya kai Abu
Umarah? Sai ya ce: “Na rantse da Allah a a, Manzon Allah bai tsere ba, sai dai
mutanen masu gaggawa daga cikin mutane ne suka juya baya lokacin da suka haɗu
171
da Ƙabilar Hawazin, suka dinga yi masu ruwan kibbau. Manzon Allah ‫ ﷺ‬kuma yana
kan raƘumarsa, Abu Sufyan bin Haris bin Abdulmuɗɗalib (a) yana riƘe da
linzaminta, Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya na cewa:

“Ni ne Annabi ba Ƙarya ba *** Ni ne ɗan Abdulmuɗɗalib”

Muhimmiyar fa’ida:

Danganta kansa zuwa ga Abdulmuɗɗalib da ya yi a wannan Magana, ya yi


hakan ne saboda labari ya shahara a tsakanin mutane tun da can, cewa wani mutum
zai fito daga cikin tsatson Abdulmuɗɗalib, wanda zai dinga kira zuwa ga Allah l.
Kuma Allah zai shirya bayi a hannunsa, zai kasance cikamakon Annabawa. Shi ya
sa ya danganta kansa zuwa gare shi, domin wanda ya san shi; ya tuna hakan. Domin
tabbas hakan ya shahara a cikinsu.

Daga Anas (a): “HaƘiƘa Annabi ‫ ﷺ‬ya shiga Makka lokacin da zai yi umarar
ramako Ibnu Rawaha kuma yana gabansa, yana tafiya, yana rera waƘa yana cewa:

“Ya ku ƴaƴan kafirai ku ba wa (Manzon Allah) hanya *** Yau zamu yaƘe ku
kan abin da ya sauka (na Ƙur’ani).

YaƘin da zamu cire kawunanku daga bigirensu *** Badaɗi ya gudu daga
wajen badaɗinsa (saboda wahala)”.

Sai Umar (a) ya ce da shi: “Ya Ibnu Rawaha a gaban Manzon Allah ‫ﷺ‬,
kuma a cikin Haramin Allah kake rera waƘa? Sai Annabi ‫ ﷺ‬ya ce: “Ƙyale shi ya kai
Umar, wannan waƘa tafi gaggawar shiga jikinsu fiye da ruwan kibbau”. Tirmuzi ne
ya ruwaito hadisin, kuma ya inganta shi.

A cikin wannan Ƙissa zamu fahimci cewa waƘa wani makami ce mai Ƙarfi,
idan an kyautata amfani da ita. Tana cikin jihadi da harshe, kuma tabbas Manzon

172
Allah ‫ ﷺ‬ya ce: “Ku yi Jihadi ga mushirkai da dukiyoyinku, da hannayenku, da kuma
harasanku”. Annasa’i ne ya ruwaito shi, Albani kuma ya inganta shi.

Daga cikin yanayin jihadi a wannan zamani:

Yin jihadi da Magana, da rubutun maƘala, da fatawoyi, da yaɗa ilimi, da yaɗa


tauhidi, da ingantaccen fiƘihu, da kuma bayar da kariya ga janibin Manzon Allah ‫ﷺ‬,
da sanar da mutane (tarihinsa), da koyar da littafin Allah Mabuwayin sarki, duka
nau’i ne na jihadi a wannan zamani.

Daga Jabir bin Samurah (a) ya ce: “Na zauna da Manzon Allah ‫ ﷺ‬fiye da
sau ɗari, sahabbansa sun kasance suna rera waƘa, suna tuna abubwan da suka faru
na zamanin Jahiliyya, shi kuma ya kan yi shiru (yana jin su), sau da yawa ma yana
murmushi tare da su”. Tirmuzu ne ya ruwaitoshi, kuma ya inganta shi.

173
Auna Fahimta

 Rubuta taƘaitaccen bayani game da ladubba, da sunnoni wajen cin abinci, da


shan abin sha.

----------------------------------------------------------------------------------------------------

----------------------------------------------------------------------------------------------------

----------------------------------------------------------------------------------------------------

 Mene ne hukunci cin abinci da hannun hagu? Kawo dalili game abin da zaka
faɗa.

----------------------------------------------------------------------------------------------------

----------------------------------------------------------------------------------------------------

----------------------------------------------------------------------------------------------------

 Mene ne hukuncin cin naman damo? Me sunna ta koyar idan baka son cin
wani abinci?

----------------------------------------------------------------------------------------------------

----------------------------------------------------------------------------------------------------

----------------------------------------------------------------------------------------------------

 Mene ne hunkuncin shan abin sha daga bakin salka (mazubi)? kuma shin
hukuncin zai hau kan kwalba, ko roba da ake yi a wannan zamani?

----------------------------------------------------------------------------------------------------

----------------------------------------------------------------------------------------------------

----------------------------------------------------------------------------------------------------

174
 Yi rubutu taƘaitacce game da mahaɗin gurasa, da kuma kayan marmari, da
abubuwan da Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya ke son sha.

----------------------------------------------------------------------------------------------------

----------------------------------------------------------------------------------------------------

----------------------------------------------------------------------------------------------------

 Mece,ce matsayar Annabi ‫ ﷺ‬game da waƘa?

----------------------------------------------------------------------------------------------------

----------------------------------------------------------------------------------------------------

----------------------------------------------------------------------------------------------------

 Yi bayanin yadda za a iya amfani da internet, da na’ura mai ƘwaƘwalwa, da


tashoshin talabijin, a matsayin wasu hanyoyi na yin jihadi a wannan zamani
da muke ciki?

----------------------------------------------------------------------------------------------------

----------------------------------------------------------------------------------------------------

----------------------------------------------------------------------------------------------------

175
Dariya da murmushin Manzon Allah ‫ﷺ‬:
Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya yi umarni da a dinga yin murmushi, kuma ya sanya hakan
a matsayin wata hanya da za a sami lada da ita, Annabi ‫ ﷺ‬ya ce: “Murmushin da za
ka yi a fuskar ɗan’uwanka sadaka ne”. Tirmuzi ne ya ruwaito shi, kuma ya ce:
“hadisi ne mai kyau”.

Daga Abu Zarrin ya ce: Annabi ‫ ﷺ‬ya gaya mini cewa: “Kada ka raina wani
abu na aikin lada, ko da kuwa ka haɗu da ɗan’uwanka da sakakkiyar fuska ne”.
Muslim ne ya ruwaito shi.

Daga Abdullahi bin Haris bin Jaz’in, ya ce: “Ban taɓa ganin wanda ya fi
Manzon Allah ‫ ﷺ‬yawan murmushi ba”. Ahmad, da Tirmuzi ne suka fitar da hadisin,
Albani kuma ya inganta shi.

Daga Abdullahi bin Haris, ya ce: “Dariyar Manzon Allah ba komai bace face
murmushi”. Ahmad, da Tirmuzi ne suka fitar da hadisin, Albani kuma ya inganta
shi.

Daga Jarir ya ce: “Manzon Allah bai taɓa hana ni shiga wajensa ba, kuma ba
zai taɓa kallo na ba face sai ya yi murmushi”. Bukhari da Muslim ne suka ruwaito
shi.

Ahmad ya fitar da Hadisi daga Jabir bin Samurah ya ce: An tambaye shi,
cewa: Shin kana zama tare da Manzon Allah ‫ ?ﷺ‬Sai ya ce: “Ƙwarai kuwa. Ya kasance
yana yin shiru mai tsayi. Sahabbansa sun kasance suna rera waƘoƘi. Kuma su
tattauna abin da ya kasance na zamanin Jahiliyya. Sai su yi ta dariya, shi kuma
Manzon Allah ‫ ﷺ‬sai ya yi murmushi, idan sun yi dariya”. Albani ya inganta wannan
Hadisin.

176
Ibnu Hajar ya ce: “Abin da zai bayyana idan aka tara waɗannan Hadisai
gabaɗaya, za a ga Manzon Allah ‫ ﷺ‬ba ya ƙarawa a kan murmushi a mafi yawan
al’amuransa. Wani lokacin kuma yana ɗan Ƙarawa sai ya yi dariya , abin da ba a so
shi ne mutum ya yawaita dariya, ya zarce gona da iri. Domin hakan yana tafiyar da
nutsuwar mutum.

Murmushin Manzon Allah ‫ ﷺ‬har ga wanda ya munana masa:

Bukhari da Muslim sun ruwato adisi daga Anas bin Malik (a) ya ce: “Na
kasance ina tafiya tare da Manzon Allah ‫ﷺ‬, yana sanye da mayafi ɗan garin Najarana
da gefen mayafin yake da kauri, sai wani balaraben Ƙauye ya haɗu da shi, ya jawo
mayafin nasa, janyowa mai tsanani, sai na duba jikin wuyan Manzon allah ‫ﷺ‬, sai na
ga alamun (shaƘewa) a wuyansa saboda janyo shin da ya yi da Ƙarfi, sannan ya ce:
ya kai Muhammad, ka yi umarni da aba ni dokiyar Allah da ke tare a wajenka. Sai
Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya waiga ya kalle shi, sai ya yi dariya. Sannan ya yi umarni da a ba
shi kyauta.

Rahar Manzon Allah ‫ﷺ‬:

Annabi ‫ ﷺ‬ya kasance yana yi wa sahabbansa raha, amma baya faɗar Magana
sai gaskiya. Daga Abu Huraira (a) ya ce: Su ka ce: Ya Manzon Allah ‫ ﷺ‬kana mana
(raha) sai ya ce: “Ƙwarai kuwa, sai dai ni bana faɗar Magana sai gaskiya”. Tirmuzi
ne ya ruwaito hadisin a cikin littafin shama’il, kuma ya inganta shi.

Daga Anas bin Malik (a) ya ce: “Tabbas Manzon Allah ‫ ﷺ‬yana yi mana
raha, har yakan ce wa Ƙaramin ɗan’uwana. Ya kai Abu Umair ina labarin ɗan
tsuntsu”. Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi.

177
Daga shi ɗin dai: HaƘiƘa wani mutum daga cikin mutanen Ƙauye sunasa
Zahir, ya kasance yana kawo wa Manzon Allah ‫ ﷺ‬kyauta daga Ƙauye, Manzon Allah
‫ ﷺ‬yana fita tare da shi idan zai fita, sai Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya ce: Zahiru shi ne mutumin
Ƙauyenmu, mu kuma ƴan birninsu, Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya kasance yana sonsa, shi
kuma ya kasance mutum ne mummuna. Sai Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya je masa (wata rana)
tsaka da ciniki. Sai Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya rungume shi ta baya shi kuma baya ganinsa,
sai (balaraban Ƙaunyen) ya ce: waye wannan? Ka sake ni, sai ya waiga sai ya gane
Annabi ‫ ﷺ‬ne. Sai ya Ƙara matse bayanshi da Ƙirjin Manzon Allah ‫ ﷺ‬lokacin da ya
gane Annabi ‫ ﷺ‬ne. Sai Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya kama cewa: “Wa zai sayi wannan
bawan”. Sai ya ce: “Ya Manzon Allah ‫ ﷺ‬ai kuwa na rantse da Allah, da ka same ni
da araha. Sai Annabi ‫ ﷺ‬ya ce: “Amma kai baka da araha a wajen Allah, ko kuma ya
ce: “Kana da tsada a wajen Allah”. Ahmad ne ya ruwaito, kuma Arna’uɗ ya inganta
Isnadin Hadisin.

Daga Alhasan ya ce: Wata tsohuwa ta zo wajen Annabi ‫ ﷺ‬sai ta ce: Ya

Manzon Allah ‫ﷺ‬, ka roƘa mini Allah ya shigar da ni Aljanna. sai ya ce: “Ya ke

Mahaifiyar wane, tsofaffi basa shiga Aljanna”. ya ce: sai ta juya ta fashe da kuka.

Sai Annabi ‫ ﷺ‬ya ce: “Ku gaya mata ba zata shiga ba tana halin tsufa.

Allah lyana cewa: ‫ﱡﭐﲑﲒﲓﲔﲕ ﲖﲗﲘﲙﲚ‬


٣٧ - ٣٥ :‫الواقعة‬
“Lalle Mu mun Ƙaga halittarsu Ƙagawa (35) Sai Muka sanya su budurwai (36) Masu
son mazansu a cikin tsara ɗaya”. (WaƘi’a: 35-37). Albani ya kautata shi a cikin
littafin Mukhtasarus Shama’il.

178
Raha aba ce mai muhimmanci. Yar sararawa ce da take sauƘaƘa wa rai
nauyaye-nauyayen wannan rayuwa. Da sharaɗin kada ya zama da Ƙarya a cikin
wannan raha, ko tsoratarwa, ko kuma yi wa Addini izgilanci. Kamar yadda Abu
Salamata bin Abdurrahman yake faɗa cewa: Basa karkacewa cikin raharsu, sun
kasance suna rera waƘoƘi, suna tattauna lamarin zamanin Jahiliyyarsu, amma idan
aka nufi yin izgilanci ga wani daga cikinsu; a lamarin addininsa, sai ka ga Ƙwayar
idonsa ta sauya, kai ka ce hankalinsa ya gushe (saboda ɓacin rai). Bukhari ne ya fitar
da hadisin cikin Adabul-mufrad, Kuma Albani ya kyautata Hadisin.

An tambayi Ibnu Umar (a) shin Sahabban Manzon Allah ‫ ﷺ‬suna yin dariya?
Sai ya ce: “Ƙwarai kuwa, kuma Imani ya cika zuƘatansu, ya fi girman dutse”.
AbdurrazzaƘ ne ya fitar da Hadisin cikin Almusannaf.

Bilal bin Sa’ad ya ce: “Na riske su, sashensu na dariya ga sashe, idan kuma
dare ya yi, zaka same su masu yawan bauta”. Ibnu Abi Shaiba ne ya fitar da Hadisin
cikin Almusannaf.

Muhimmiyar Fa’ida:

Ƙarya bata halatta ba domin saka mutane dariya, kamar yadda ya yaɗu a
wannan zamani. HaƘiƘa Annabi ‫ ﷺ‬ya ce: “Bone ya tabbata ga wanda yake ba wa
mutane labari ya yi Ƙarya, domin mutane su yi dariya, bone ya tabbata gare shi, bone
ya tabbata gare shi”. Ahmad, da Abu dawud ne suka fitar da hadisin, kuma Albani
ya kyautata shi.

Yanayin baccin Manzon Allah ‫ﷺ‬:

Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya kan yi bacci a kan shimfiɗar da aka yi da jemammiyar


fata. Wataran kuma a kan tabarma, wataran kuma a kan dandagaryar Ƙasa, wataran

179
kuma a kan gado. Katifarsa an yi ta da jemammiyar fata, da aka cusa mata
busasshiyar ciyawa, haka ma matsashin kansa ya ke.

Ya kasance ba ya yin bacci fiye da buƘata. Kuma ba ya hana kansa bacci


gwargwadon buƘata. Ya kasance idan yana bacci ba sa tashin shi, har sai dai shi ya
farka da kansa.

Daga Barra’u bin Azib cewa: HaƘiƘa Annabi ‫ ﷺ‬ya kasance idan ya kwanta
yana sanya tafin hannunsa a Ƙasan kuncinsa na tsagin dama. Sai ya ce: “Ya Ubangiji
ina neman tsarinKa daga azabarKa ranar da zaka tashi bayinKa”. A wata ruwayar
kuma (ranar da zaka tara bayinKa). Tirmuzi ne ya ruwaito Hadisin, kuma ya inaganta
shi.

Daga Abu Ƙatada, HaƘiƘa Annabi ‫ ﷺ‬ya kasance idan zai ya-da-zango cikin
dare, yana kishingiɗa a tsaginsa na dama. Idan kuma zai ya-da-zango gabanin sallar
Asuba, sai ya shimfiɗa hannunsa, ya sanya kansa a kan tafin hannunsa. Muslim ne
ya ruwaito shi.

Daga Huzaifa a ya ce: Annabi ‫ ﷺ‬ya kasance idan ya tafi shinmfiɗarsa yana
cewa: “Godiya ta tabbata ga Allah Wanda ya ciyar da mu, kuma Ya shayar da mu,
kuma Ya Ƙosar da mu, Ya ba mu makwanci, da yawa daga cikin mutane ba su da
abin da zai Ƙosar da su, ba su da makwanci”. Muslim ne ya ruwaito shi.

Daga A’isha (x): HaƘiƘa Manzon Allah ‫ ﷺ‬idan ya tafi makwancinsa a


kowanne dare, yana haɗa tafukan hannunsa, sai ya yi tofi a ciki. Sai ya karanta:

(Ƙul Huwallahu Ahad, da١ ‫ﱡﭐﱁﱂﱃﱄﱅﱠ‬

(Ƙul A’uzu bi rabbil falaƘ, da ١ :‫ﱡﭐﱔﱕﱖﱗﱘﱠ ال فلق‬

180
(Ƙul A’uzu bi rabbin nasa):‫ناس‬
١ ‫ﱡﭐﱰﱱﱲﱳﱴﱠ ال‬
Sannan sai ya shafi duk inda zai iya a jikinsa. Yana farawa da shafar kansa, da
fuskarsa, da duk abin da yake daga jikinsa, yana yin hakan sau uku”. Bukhari ne ya
ruwaito shi.

Daga Ibnu Abbas (a): “HaƘiƘa Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya yi bacci, har sai da ya
ɗan yi munshari. Ya kasance yana yin munshari idan yana bacci. Sai Bilal ya zo
wajensa, ya sanar da shi lokacin Sallah ya yi. Sai ya tashi ya yi Sallah ba tare da ya
sake al’wala ba”. Bukhar da Muslim ne suka ruwaito shi.

Al’imamun Nawawi ya ce: “Wannan na daga cikin abubuwan da Manzon Allah ‫ﷺ‬
ya keɓanta da su. Baccin da ya yi a kwance ba ya warware alwalarsa, domin
idanunwansa ne kawai suke bacci, amma zuciyarsa ba ta bacci, da wani kari zai fita,
to da zai ji. Saɓanin waninsa daga cikin mutane.

Sufyan bin Uyaina ya ce: “Wannan ya keɓanta ne kawai ga Annabi ‫ﷺ‬. Domin
Hadisi ya iso gare mu cewa, idanunsa ne suke bacci, amma zuciyarshi ba ta bacci”.

Bacci a tsagin dama (a mahangar malaman lafiya):

Malaman lafiya na wannan zamanin sun tabbatar da cewa, bacci a ɓarayin


dama shi ya fi wanzar da nutsatstsiyar lafiya a jiki ga mai bacci. Shi bacci a tsagin
dama shi ne abu mafi inganci, domin kuwa huhun ɓangaren hagu yafi na ɓangaren
dama ƘanƘanta. Hakan zai sa zuciya ta zama ba nauyi sosai a kan ta. Ita kuma hanta
zata kasance cikin daidaitaccen yanayi, hakan zai sa ta narkar da abin da aka ci ta
narkar da shi cikin sauƘi.

Kamar yadda ake ganin bacci a tsagin dama yana taimakawa hanyar fitar
nunfashi, wajen samar da sinadarin dake hana datti shiga cikin hunhu.

181
Kuma hakan yana taimakawa wajen gudin jini zuwa cikin jiki daga gefen
hagu, na saman cuciya, wanda hakan yakan sa zuciya ta huta. Saboda dukkanin
sassan jiki suna sama, ko kuma suna mataki ɗaya.

Ladubban bacci:

A karkaɗe shimfiɗa kafin bacci, saboda Hadisin Abu Huraira (a) ya ce:
Annabi ‫ ﷺ‬ya ce: “Idan ɗayanku ya tafi zuwa shimfiɗarsa; to ya karkaɗe ta da gefen
kwarjallensa. Domin bai san meye ya zo wa shimfiɗar ba a bayansa. Sannan sai ya
ce: “Da sunanKa Ubangijina nake sanya jikina a shimfiɗa, da kuma sunanKa ne nake
ɗaga shi. Idan Ka riƘe raina to Ka jiƘan shi, Idan kuma Ka sake shi; to ka kare shi
da abin da Kake kare nagartattun bayinKa) Bukhari ne ya ruwaito shi.

Malam Ɗayyibi ya ce: “Domin mutum bai san abin da ya faɗa kan shimfiɗarsa ba,
kamar Ƙasa, ko wani datti, ko Ƙwari bayan ya bar shimfiɗar tasa”.

An son yin alwala yayin bacci: Saboda faɗin Manzon Allah ‫ ﷺ‬ga Barra’u bin Azib
(a): “Idan ka je wa makwancinka, sai ka yi alwalarka irin ta sallah”. Bukhari da
Muslim ne suka ruwaito shi.

Ya yi bacci a tsaginsa na dama: Ya yi matashi da hannunsa na dama, kamar yadda


bayanin hakan ya gabata.

Kada ya yi rub-da-ciki yayin bacci, na dare ne, ko na rana: Saboda abin da ya


zo daga Annabi ‫ ﷺ‬ya ce: “Domin kwanciyar ƴan wuta ce”. Ahmad ne ya fitar da
Hadisin, Arna’uɗ ya ce: “Hadisi ne mai kyau, idan aka yi la’akar da waninsa.

Ya yi zikirin bacci kafin ya yi bacci: Wani sashe na waɗannan zakiran ya gabata.


Amma ga wasu daga cikin abin da ake faɗa yayin bacci:

Faɗin Subhanalli da Alhamdulillahi, da Allahu Akbar. Domin Annabi ‫ ﷺ‬ya


ce wa Faɗima, da Aliyu (a), bayan sun nemi a ba su ɗan aiki da zai taimaka musu
182
a kan aikin gida. Sai Annabi ‫ ﷺ‬ya ce: “Shin ba na nusar da ku ba i zuwa abin da ya
fi alheri, fiye da abin da kuka roƘa? Idan kuka je wajen baccinku, ku ce: Subhanalli
sau talatin da uku, ku ce Alhamdulillahi sau talatin da uku, ku ce: Allah Akbar sau
talatin da huɗu. Wannan ya fi muku alheri fiye da aba ku ɗan aiki”. Muslim ne ya
ruwaito shi.

Hadisi ya zo a kan za a karanta Suratul Kafiruna kafin a yi bacci, daga Farwatu


bin Naufal (a) cewa: Ya je wajen Annabi ‫ﷺ‬, sai ya ce: Ya Manzon Allah ‫ﷺ‬, ka
sanar da ni wani abu da zan dinga faɗa idan na je shimfiɗata? Sai ya ce: Ka karanta:
Ƙulya Ayyuhal Kafirun domin (karanta ta) kuɓuta ne daga shirka. Ahmad, da Tirmuzi
ne suka ruwaito shi, Albani kuma ya inganta shi.

Daga Jabir (a): “HaƘiƘa Annabi ‫ ﷺ‬ba ya yin bacci, har sai ya karanta A.L.M
Tanzil (Suratus Sajada), da kuma Tabarakallazi bi yadihil Mulku”. Ahmad, da
Tirmuzi ne suka ruwaito shi, Albani kuma ya inganta shi.

Idan kuma ya farka yana tsaka da baccinsa, to abin da ya zo na Sunna shi ne


ya ce: “Ina neman tsarin Allah da kalmominSa cikakku daga fushinSa, da kuma
uƘubarSa, da kuma sharrin bayinSa, kuma ina neman tsari da Kai daga fizge–fizgen
Shaiɗanu, Kuma ina neman tsari da Kai, da ka da su zo inda nake”. Ahmad, da
Tirmuzi ne suka ruwaito shi, Kuma Tirmizi ya kyautata hadisin.

Falalar Karanta Tabaraka (Suratul Mulk):

Tirmuzi ya ruwaito, kuma ya ce hadisi ne mai kyau, daga Abu Huraira (a)
daga Annabi ‫ ﷺ‬ya ce: “HaƘiƘa wata sura a cikin Ƙur’ani da take da ayoyi talatin, ta
nemi ceton wani mutum, har sai da aka gafarta masa. Ita ce surar: (Tabarakallazi
biyadihil Mulk)”.

183
Yanayin farkawar Annabi ‫ ﷺ‬daga bacci:

Ibnul Ƙayyim ya ce: “Duk wanda ya lura da bacci, da kuma farkarwar Manzon
Allah ‫ﷺ‬, zai ga hakan shi ne daidaitaccen bacci, kuma wanda ya fi amfanar jiki, da
gaɓɓai, da Ƙarfin jiki, domin ya kasance yana yin bacci a farkon dare. Sai ya farka a
farkon rabin dare na biyu. Sai ya tashi ya yi asuwaki. Ya yi alwala, ya sallaci abin
da Allah ya Ƙaddara zai sallata. Sai jiki, da gaɓɓai, da Ƙwarin jiki su yi bacci, kuma
su huta, tashin da ya yi; hakan yana sa su su motsa. Daɗin daɗawa ga lada mai yawa
da zai samu. Wannan shi ne Ƙarshe wajen gyran zuciya, da jiki, da duniya, da lahira”.

Hadisi ya zo daga Tirmuzi, kuma ya ce Hadisin mai kyau ne. Daga Abu
Huraira (a)……ya ce: Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya ce: “Idan (mutum) ya farka to ya ce:
“Godiya ta tabbata ga Allah da Ya ba ni lafiya a jikina, kuma Ya dawo mini da raina,
kuma Ya yi mini izini da ambatonSa”.

Yin asuwaki:

Daga Huzaifa (a) ya ce: “Annabi ‫ ﷺ‬ya kasance idan ya tashi cikin dare yana
wanke bakinsa da asuwaki”. Bukari da Muslim ne suka ruwaito shi.

184
Wanke hannuwa, da kuma fyace hanci sau uku:

Daga Abu Huraira (a): HaƘiƘa Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya ce: “Idan ɗayanku ya
farka daga baccinsa, to ya wanke hannunsa kafin ya shigar da su cikin ruwan alwala,
domin ɗayanku bai san inda hannunsa ya kwana ba”. Bukari da Muslim ne suka
ruwaito shi.

Annabi ‫ ﷺ‬ya ce: “Idan ɗayanku ya farka daga baccinsa, to ya fyace hancinsa
sau uku, domin Shaiɗan yana kwana a cikin karan hancinsa”. Bukari da Muslim ne
suka ruwaito shi.

Shafe alamun bacci daga fuska da hannu:

Saboda hadisin Ibnu Abbas (a) ya ce: “Sai ya farka- wato Annabi ‫ﷺ‬- sai ya
dinga shafe alamun baccin daga fuskarsa. Sannan ya karanta ayoyi goma na cikin
Ali Imaran”. Bukari da Muslim ne suka ruwaito shi.

Wani hadisin ya zo a Bukahri da Muslim, daga Abu Huraira (a): Tabbas


Annabi ‫ ﷺ‬ya ce: “Shaiɗan yana yin Ƙulli uku a Ƙeyar kan mutum yayin da yake
bacci. Yana dukan kowanne Ƙulli (yana cewa): kana fa da dare mai tsayi, ka yi
kwanciyarka kawai. Idan kuma ya farka ya ambaci Allah, sai Ƙulli ɗaya ya warware,
idan kuma ya yi alwala, sai wani Ƙullin ya Ƙara warwarewa. Idan kuma ya yi salla
sai ɗaya Ƙullin ya kwance. Sai ya wayi gari cikin nisaɗi, cikin farin ciki. Idan kuma
ba haka ba sai ya wayi gari cikin ɓacin rai da kasala”.

185
Auna Fahimta

 Mene ne hukuncin dariya a Musulunci? Mene ne tasirin murmushi a fuskar


ɗan’uwanka?

---------------------------------------------------------------------------------------------------

---------------------------------------------------------------------------------------------------

 Kawo misalai na yanayin rahar Manzon Allah ‫ﷺ‬, kuma ta ya ya hakan ya yi


daidai da gaskiya?

---------------------------------------------------------------------------------------------------

---------------------------------------------------------------------------------------------------

 Ana samun wasu mutane daga cikin Musulmai; suna zuwa wajen mutane
domin su bayar da labarin ban dariya na Ƙarya. Mene ne hukuncin hakan?
Kuma dame zaka yi musu nasiha a Musulunci?

---------------------------------------------------------------------------------------------------

---------------------------------------------------------------------------------------------------

 Rubuta jimillar ladubban bacci, da farkawa, sannan ka bayyana hukuncin


bacci, a ruf-da-ciki?

---------------------------------------------------------------------------------------------------

---------------------------------------------------------------------------------------------------

186
Yanayi ibadar Manzon Allah ‫ﷺ‬:

Bautar da Manzon Allah ‫ ﷺ‬yake yi wa Ubangijinsa; ita ce mafi girman abin

da aka siffanta shi da ita, Mafi girman abin da aka yabe shi a kai. HaƘiƘa ya tabbatar

da wannan matsayi mafi girma, Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya kasance wanda ya fi kowa yi

wa Allah biyayya, da bautarSa. Ya kasance yana yi masa cikakkiyar biyayya, babu

gajiyawa, ko kuma wuce gona da iri a ciki. Ibadarsa ita ce mafi cika. Ya tabbatar da

faɗin Allah Maɗaukakin Sarki da ya ce:

٥٦:‫ﱡﭐ ﱣﱤﱥﱦﱧﱨﱩﱠ ال ذاريات‬

“Ban halicci aljani da mutum ba, face sai domin su bauta Mini" (Zariyat: 56).

Babu wani lokaci a rayuwarsa da yake wucewa, ba tare da yana bautar Allah
a ciki ba. Idonsa biyu, ko yana bacci, a zaune yake, ko a tsaye, fushinsa ma don Allah
yake yi. Kowane lokaci yana tsaye kan abin da Allah ya umarta, kuma yana hakan
daidai misali, tare da bai wa duk wani mai haƘƘi haƘƘinsa. A’isha (x) ta ce:
“Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya kasance yana yin azumi, har sai mun ce ba ya shan ruwa, kuma
wata ran yana shan ruwa, har sai munce: ba ya azumi” Bukhari ne ya ruwaito shi.

A wani Hadisin ya ce: “Tabbas ni ina yin azumi, kuma ina sha ruwa, ina Sallar
dare, kuma ina bacci, kuma ina aurar mata. To duk wanda ya Ƙyamaci sunnata; to ba
ya tare da ni”. Bukari da Muslim ne suka ruwaito shi.

Wannan shi ne daidaito a cikin ibada. Da kuma tsayawa a kan haƘƘin Allah
ta cikakkiyar fuska. Tare da bai wa duk wani mai haƘƘi haƘƘinsa.

187
Dawwama a kan aikin alheri, da kuma rama abin da ya kuɓuce:

Ya kasance yana dawwama a cikin Ibada. An tambayi A’isha (x): Yaya


aikin Manzon Allah yake? Shin yana ware wasu ranaku domin wasu abubuwa? Sai
ta ce: “A’a, dawwama yake a cikin dukkanin ayyukansa. A cikinku kam waye zai
iya abin da Manzon Allah ‫ ﷺ‬zai iya?” Bukari da Muslim ne suka ruwaito shi.

Ya kasance yana dawwama cikin aikin ɗa’a, har ya kasance idan wani abu ya
kuɓuce masa na daga nafilfili sai ya rama.

Daga A’isha (x) ta ce: “HaƘiƘa Annabi ‫ ﷺ‬ya kasance idan bai yi salla da
daddare ba bacci ya hana shi, ko idanunsa suka rinjaye shi, sai ya yi salla raka’a
goma sha biyu da rana” Muslim ne ya ruwaito shi.

Daga Umar (a) ya ce: Annabi ‫ ﷺ‬ya ce: “Duk wanda ya yi bacci game da
karantunsa na Ƙur’ani, da yake yi cikin dare, sai ya karanta shi tsakanin sallar
Asubahi, da La’asar, to za a rubuta masa kamar ya karanta shi da daddare ne”.
Muslim ne ya ruwaito shi.

Daga A’isha (x) ta ce: Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya shigo wajena, ina tare da wata
mata, sai ya ce: “Wace ce wannan? Sai na ce: Wance ce, ba ta bacci da daddare, sai
Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya ce: Ina horonku da ayyukan da zaku iya, na rantse da Allah,
Allah ba zai yanke (bayar da lada ba), har sai kun yanke (ayyukanku), abin da
Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya fi so, shi ne aikin da mai shi zai dawwama yana yi”. Bukari da
Muslim ne suka ruwaito shi.

An tambayi A’isha da Ummu Salama (h): Wanne irin aiki Manzon allah ‫ﷺ‬
ya fi so? Sai su biyun suka ce: “Abin da aka dawwama ana yi, komai ƘanƘantarsa”.
Tirmuzi ne ya ruwaito shi, kuma ya inganta shi.

188
Daɗewa a tsaye a cikin salla:

Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya kasance yana daɗewa a tsaye. Daga Aufu bin Malik (a)
ya ce: “Na tashi (salla) tare da Manzon Allah ‫ﷺ‬, sai ya fara da asuwaki, ya yi alwala,
ya tashi ya fara salla. Sai ya buɗe da suratul BaƘara. Ba ya wuce wata Aya ta rahama,
ba face sai ya tsaya ya roƘi Allah, kuma ba zai wuce wata Aya ta azaba ba, face sai
ya tsaya ya nemi tsari. Sannan sai ya yi ruku’u, ya daɗe a ruku’unsa gwargwadon
lokacin da yake a tsaye. Yana cewa a cikin ruku’unsa: Subhana zal jabaruti wal
malakuti wal kibriya’i wal azamati, sannan ya karanta Ali Imran, sannan wata surar
sannan wata surar”. Nasa’i ne ya ruwaito shi, Albani kuma ya inganta shi.

Daga Mugiratu bin Shu’ubah (a) ya ce: “Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya yi Salla, har
sai da Ƙafafunsa suka kumbura, sai aka ce da shi: yanzu ka ɗorawa kanka haka?
Kuma bayan Allah ya gafarta maka abin da ya gabata na zunubanka, da abin da zai
zo? Sai ya ce: “Shin ba na kasance bawa mai godiya ba”. Bukhari da Muslim ne suka
ruwaito shi.

Daga Abu Salama bin Abdurrahman cewa ya tambayi A’isha (x): Yaya
Sallar Manzon Allah ‫ ﷺ‬take a watan Ramadan? Sai ta ce: “Manzon Allah ‫ ﷺ‬bai
kasance yana Ƙarawa a watan Azumi, ko a waninsa ba fiye da raka’a goma sha ɗaya,
yana yin raka’a huɗu kada ma ku tambaye ni game da kyawunsu, da tsayinsu, sannan
ya Ƙara sallatar raka’a huɗu, kada ma ku tambaye ni game da kyawunsu, da tsayinsu.
Sannan ya yi raka’a uku, A’isha (x) ta ce: Na ce: Ya Manzon Allah ‫ﷺ‬, shin kana
bacci kafin ka yi wutiri? Sai ya ce: “Ya A’isha haƘiƘa idanuwana suna bacci, amma
zuciyata ba ta bacci”. Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi.

Daga Abdullahi bin Mas’ud (z) ya ce: “Na yi Salla tare da Manzon Allah
‫ ﷺ‬a wani dare. Bai gushe ba yana tsaye – wato ya jima sosai a tsaye- har sai da na

189
ayyana ba daidai ba. Sai aka ce da shi: to me ka so ka yi? Sai ya ce: na so na zauna
na Ƙyale Annabin ‫( ﷺ‬a tsaye)” Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi.

Al’imamun Nawawi ya ce: “Malamai sun haɗu a kan cewa, idan wanda yake bin
limami sallar nafila ya ga zai takura sosai; game da tsayuwa asallar, kuma ya gaji a
tsaye, to ya halatta ya zauna. Shima Ibn Mas’ud (z) ya Ƙi zama ne kawai; saboda
da ladabi ga Annabi ‫”ﷺ‬.

Sallar da Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya yi a zaune yayin da ya manyanta:

Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya kasance yana salla a zaune yayin da girma ya fara kama
shi, Bukhari ya ruwaito daga A’isha (x) cewa: “Ba ta taɓa ganin Manzon Allah
‫ ﷺ‬ya yi Salla a zaune ba, har sai da ya yi shekaru da yawa”.

Muslim ya ruwaito daga A’isha (x) ta ce: “Na ga Manzon Allah ‫ ﷺ‬yayin
da jikinsa ya yi nauyi, mafi yawancin sallarsa a zaune yake yi”.

Daga Hafsatu (x) ta ce: “Ban taɓa ganin Manzon Allah ‫ ﷺ‬yana nafilarsa a
zaune ba, har sai ya zama saura shekara ɗaya da wafatinsa. Ya kasance yana sallar
nafilarsa a zaune”. Muslim ne ya ruwaito shi.

Shi zama a cikin Salla ba shi da wata keɓantacciyar siffa, kowanne irin zama
ya na isarwa, kamar mutum ya zauna a kan mazaunansa, ko ya tanƘashe Ƙafafunsa
a zaune, ko kuma ya lanƘwashe kafar dama, ya zauna a kan mazaunansa (wato
zaman tahiya ta biyu), da sauransu. Amma ban da irin zaman da aka hana…kamar
zaman da mutum zai cake Ƙafafunsa ya zauna a kansu.

AlƘali Abdulwahhab ya ce: “Zaman da ya fi; shi ne na tanƘwashe Ƙafa, domin


ya fi saka nutsuwa”.

Hadisi ya zo a Bukhari daga hadisin Imran bin Husain ya ce: Manzon Allah
‫ ﷺ‬ya ce: “Duk wanda ya yi salla a tsaye; to shi ya fi falala. Wanda kuma ya yi salla
190
a zaune to yana da rabin ladan wanda ya yi a tsaye. Wanda kuma ya yi salla yana
kwance; to yana da rabin ladan wanda ya yi a zaune”.

Wannan Hadisin za a ɗauke shi ne a kan sallar nafila. Mutum zai iya sallar
nafila a zaune idan ya so, ko da kuwa zai iya yi a tsaye, yana da rabin lada. Amma
ita sallar farilla bai halatta a yi a zaune ba. Sai dai wanda ba zai iya tsayawa ba, sai
ya yi a zaune, kuma zai samu cikakken lada.

Yanayin azumin Manzon Allah ‫ﷺ‬:

Daga Abdullahi bin ShaƘiƘa daga A’isha (x) ta ce: “Ban taɓa ganinsa ba –
wato Manzon Allah ‫ ﷺ‬- ya azumci wani wata gabaɗaya ba, tun da muka zo Madina,
sai dai a watan Ramadan”. Muslim ne ya ruwaito shi.

Daga Anas bin Malik (z) cewa: An tambaye shi game da azumin Manzon
Allah ‫ﷺ‬, sai ya ce: “Ya kasance yana yin azumi a cikin wata, har mu ga kamar ba ya
son shan ruwa. Kuma yana buɗe-bakinsa (wato ba ya azumi), har sai muga kamar
ba ya a zumtar wani abu a watan. Ba zaka so ka gan shi yana salla da daddare ba,
face sai ka gan shi yana sallar, kuma ba zaka so ka gan shi yana bacci ba, face sai ka
gan shi yana baccin”. Hadisin ya gabata.

Daga A’isha (x) ta ce: “Manzon Allah ‫ ﷺ‬ba ya azumi a wani wata fiye da
yadda yake azumi a cikin watan Sha’aban”.

Daga Abdullahi bin Mas’ud (z) ya ce: “Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya kasance yana
yin azumi a farkon wata, kwanaki uku”. Tirmuzi ne ya ruwaito hadisin, kuma ya ce:
mai kyau ne.

Daga Mua’azatu (x) ta ce: “Annabi ‫ ﷺ‬ya kasance yana azumtar Asabar, da
Lahadi, da Litini, a cikin wata. A wani watan kuma yana azumtar Talata, da laraba,
da Alhamis”. Tirmuzi ya ruwaito hadisin, kuma ya ce: mai kyau ne.

191
A cikin wannan Hadisin zamu ga, an so mutum ya dinga sassauya ranakun da
yake azumta, da waɗanda yake bari.

Ibn Ƙudama ya ce: “Jimallar abin da hakan yake nufi; an so a dinga yin azumi
guda uku a kowanne wata. Ba mu san wani saɓani da aka yi ba a kan wannan
maganar”.

Kuma wannan ita ce wasiyyar Manzon Allah ‫ﷺ‬, Hadisi ya zo daga Abu
Huraira (z) ya ce: “Badaɗina Babban abin Ƙaunata ya yi min wasiyya da abu uku:
Azumin kwana uku a kowanne wata, da kuma sallar walaha, da kuma na yi wutiri
gabanin na yi bacci”. Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi.

Daga A’isha (x) ta ce: “Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya kasance yana dagewa wajen
yin azumin Litinin da Alhamis”. Tirmuzi ne ya ruwaito hadisin, kuma ya ce: mai
kyau ne.

Ya zama wajibi ga mai yin azumi, ya kiyaye azuminsa, da harshensa. Kada ya


yi musu. Ya kiyaye harshensa, (Bayin Allah nagari) sun kasance idan suna azumi;
suna zamansu a cikin masallaci, suna cewa: “Muna kare azuminmu ne”. Mutum kada
ya ci naman wani, kuma kada ya yi wani aiki da zai raunata azuminsa.

Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya ce: “Duk wanda bai bar maganar Ƙire ba, da aiki da ita.
To Aallah ba ya buƘatar barin cinsa, da shansa da ya yi”. Bukhari ne ya ruwaito shi.

192
ƘanƘan-da-kan Annabi ‫ ﷺ‬ga Ubangijnsa, duk da waɗannan ibadu da yake yi:

Muslim ya fitar a cikin ingantaccen littafinsa daga Agarru Almuzanni (z)


cewa: HaƘiƘa Annabi ‫ ﷺ‬ya ce: “Tabbas akan yi rufi a zuciyata, domin hakan nakan
yi Istigfari fiye da sau ɗari a kwowacce rana”.

HaƘiƘa Annabi ‫ ﷺ‬ya kasance ko yaushe cikin ambaton Allah, da lazimtar


haka. Idan kuwa ya ɗan rafkana kaɗan da wani abu da ya saba yi (bai yi ba); sai ya
Ƙirga hakan a matsayin laifi, sai ya koma da yin istigfari (nan take).

Karatun Manzon Allah ‫ﷺ‬:

Daga Ummu Salama (ɗ) ta ce: “Annabi ‫ ﷺ‬ya kasance yana rarraba

karatunsa, yana cewa: ٢ :‫ﱡﭐﱆﱇﱈﱉﱊﱠ الف اتحة‬

“Godiya ta tabbata ga Ubangijin halittu”, sai ya tsaya, sannan ya ce:

: ٣ :‫“ ﱡﭐﱋﱌﱍﱠ الف اتحة‬Mai rahama Mai jin Ƙai” sai ya tsaya, ya kasance

yana karanta: ٤ :‫“ ﱡﭐﱎﱏﱐﱑ ﱠ الف اتحة‬Mai nuna mulikin ranar

sakamako”. Tirmuzi ne ya ruwaito hadisin, kuma ya inganta shi.


A wata ruwayar ta Ahmad wacce Arna’uɗ ya ingantata: “Yana tsayawa a kan
kowacce a ya”.

Daga Abdullahi bin Ƙaisu ya ce: Na tambayi A’isha (x) game da karatun
Annabi ‫ﷺ‬: Shin yana karatu ne a fili ko a ɓoye? Ta ce: “Yana yin hakan dukkaninsu,
sau da yawa yakan yi karatu a ɓoye, wasu lokutan kuma yakan yi karatu a bayyane.
Sai na ce: na gode wa Allah da ya sanya yalwa cikin lamarin”. Tirmuzi ne ya ruwaito
hadisin, Albani kuma inganta shi.

193
Daga Ummu Hani (x) ta ce: “Ina ji yo karatun Manzon Allah ‫ ﷺ‬da daddare,
alhali kuma ina cikin ɗakina”. Ahmad ne ya ruwaito hadisin, Albani kuma ya inganta
shi.

Daga Ibn Abbas (z) ya ce: “Karatun Annabi ‫ ﷺ‬ya kasance sau da yawa,
wanda ma yake tsakar gida yana jiyo wa, alhali kuma shi yana ɗaki”. Ahmad, da
Abu Dawud ne Suka ruwaito hadisin, Albani kuma ya inganta shi.

Ibnu Hajar ya ce: “Abin da ake nufi shi ne, karatunsa tsakatsaki ne. Ba can
Ƙarshe ba wajen bayyanawa, kuma ba Ƙarshe ba wajen ɓoyewa”.

Kuma haƘiƘa Hadisi ya yi nuni kan cewa: Karatun Annabi ‫ ﷺ‬ba wai ɗaga
murya yake ba ɗagawa mai yawa, ba kuma Ƙasa yake ba, da har wani ba zai ji karatun
ba.

A ciki akwai aiki da faɗin Allah l:

١١٠ ‫ﱡﭐﲋﲌﲍﲎﲏﲐﲑﲒﲓﲔﲕﱠ‬
:‫اإلسراء‬
“Kuma ka da ka bayyana ga sallarka, kuma kada ka ɓoye ta, ka nemi hanya tsakanin
wancan” (Isra’i: 110)

Ya dace a yi koyi da Manzon Allah ‫ ﷺ‬a karatunsa, wajen bayyanawa, da


ɓoyewa, da rarewarsa, da bayyanawarsa. Domin Ƙur’ani an saukar da shi ne domin
a yi tun-tun-tuni, da kuma aiki da shi. Kamar yadda Allah lya ce:

٢٩ :‫ﱡﭐﱢﱣﱤﱥﱦﱧﱨﱩﱪﱫﱠ ص‬
“ “(Wannan) Ƙur’ani mun saukar da shi zuwa gare ka, yana mai albarka domin lura
da ayoyinsa, kuma saboda masu hanakli su riƘa yin tunani” (Sad: 29).

Tadabburi da gane saƘon ayoyi ba ya samuwa idan ana karatu da sauri, sai dai
a hankali, da kuma rera karatu da murya mai daɗi. HaƘiƘa malamai sun yi ittifaƘi a
194
kan cewa: An so a dinga rarewa a hankali, suna masu dogara da Hadisai ingantattu
da suka zo, kuma karatun Annabi ‫ ﷺ‬rerawa ne a bayyane.

Wani mutum ya zo wajen Ibnu Abbas (z), sai ya ce: “HaƘiƘa ina da saurin
karatu, ina karance AlƘur’in a cikin kwana uku, sai ya ce: “In karanta BaƘara ina
mai lura da abin dake ciki, ina mai rera ta, ya fi soyuwa a gare ni, fiye da in yi irin
karantun da kake faɗa”. BaihaƘi ne ya ruwaito Hadisin.

Al’ajuri ya ce: “Karatu kaɗan na Ƙur’ani tare da tunani ayoyin ciki, da lura da su, ya
fi soyuwa a gare ni, fiye da yawaita karatunsa, ba tare da tadabburi, da tunani a ciki
ba, Zahirin AlƘur’ani, da Hadisai, da Zantuttukan Musulmai sun yi nuni ga hakan”.

Daga Mu’awiyatu bin Ƙurrah ya ce: Na ji Abdullahi bin Mugaffal yana cewa:
“Na ga Annabi ‫ ﷺ‬a kan taguwarsa a ranar da aka buɗe Makka, yana karanta:

٢ - ١ :‫ﱡﭐﱁﱂﱃﱄﱅﱆﱇﱈﱉﱊﱋﱌﱍ ﱎﱏﱠ ال فتح‬


“Lalle Mu Mun yi maka buɗi (a kan maƘiyanka) buɗi bayyananne (1) Domin Allah
ya shafe abin da ya gabata na laifinka da wanda ya jinkirta (2)” (Alfathi: 1-2), ya
ce: “Sai ya karanta, ya Ƙara maimaitawa, sai Mu’awiya ya yi karatu yana hakaito
musu karatun Ibnu Mugaffal, ya ce: “Ba don mutane kada su taru a kanku ba, nima
da na ɗaga sauti, na maimaita karatun kamar yadda Ibnu Mugaffal ya yi shi, yayin
da yake haikaito karatun Annabi ‫ﷺ‬. Sai na ce da Mu’awiya: yaya yake maimai a
cikin karatun: sai ya ce: Sau uku”.

Wanda yake rera AlƘur’ani; ya zama wajibi a kansa ya yi iya ƘoƘarinsa wajen
kyautata muryarsa da karatun. Ya sanya hakan ya zama al’adarsa, da kuma koyi da
sunnar Annabi ‫ﷺ‬, da kuma aiki da umarninsa”.

195
Ibnu Abi Hamza ya ce: “Abin da ake nufi da maimaita murya shi ne: Mutum
ya rera Ƙur’ani da kyau, ba wai ya yi masa rerawar waƘa ba. Domin yin karatu kamar
ana waƘa; hakan yana cire nutsuwa, wanda ita ce maƘasudi a cikin karatun.

Malam Alƙari ya ce: “Yana daga cikin abin da zai Ƙarfafi hakan, abin da aka
ruwaito cewa: Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya saurari karatun Abu Musa Al-Asha’ari, yayin da
ya gaya masa hakan. Sai ya ce: “Ai da a ce na san kana saurara ta; da na tsara maka
karatun da murya mafi daɗi...amma abin da wasu suke yi a wannan zamani na
wahalar da kai, da tsayawa a nazarci yanayin wasu sautin waƘoƘi, da karya harshe,
wannan shi ne abin da magabata nagari suka karahanta, da kuma ji musu tsoron
fushin Allah l.

HaƘiƘa Ibnu Ƙayyim ya tattara hakan, inda yake cewa: “Ya kasance Manzon
Allah ‫ ﷺ‬yana da hizbi iyakantacce da yake karantawa a kullum, ba ya sakaci da shi.
Karatunsa ya kasance yana rera shi rerawa mai daɗi, ba ya gaggawa. Karatu yake yi
a bayyane, harafi bayan harafi. Ya kasance yana raba karatunsa aya bayan aya. Ya
kasance yana jan harka idan ya zo wajen da yake da harafin madda, yana jan Kalmar
Arrahman, kuma ya ja kalmar Arrahim. Yana neman tsarin Allah daga Shaiɗan a
farkon karatunsa. Sai ya ce: Ina neman tsarin Allah daga Shaiɗan korarre daga
rahamar Allah. Sau da yawa yana cewa: “Ya Allah ina neman tsarinka daga Shaiɗan
korarre daga rahama, daga zungurinsa, da hurarsa, da busarsa. Ya kasance yana
neman tsari kafin ya fara karatu. Ya kasance yana son ya ji Ƙur’ani daga waninsa.
Ya umarci Abdullahi bin Mas’ud (a) da ya karanta masa AlƘur’ani, sai ya karanta
masa, yana saurara, ya nutsu yayin jin karatun nasa. Har sai da idanunsa suka zubar
da hawaye….Ya kasance yana karatun Ƙur’ani a tsaye, ko a zaune, ko a kishingiɗe,
yana da alwala, ko ba shi da alwala, ba abin da yake hana shi karatun alƘur’ani sai

196
dai janaba…Ya kasance yana rera shi, yana maimaita sautinsa da karatun wani
lokacin. Kamar yadda ya yi a ranar buɗe Makka, yayin da yake karanta:

١ :‫ﱡﭐﱁﱂﱃﱄﱅﱆﱠ ال فتح‬
(Lalle Mu Mun yi maka buɗi (a kan maƘiyanka) buɗi bayyananne) (Fatahi: -1)

Kukan Manzon Allah ‫ﷺ‬:

Duk da abin da aka ruwaito na Ƙarfin zuciya, da Ƙarfin jiki, da kwarjini, da


tabbatuwa a kan abu, sai dai yana da zuciya mai taushi sosai, da haƘuri. Manzon
Allah ‫ ﷺ‬yana tasirantuwa da duk wani abu na baƘin ciki, yana kuka har waɗanda
suke kewaye da shi suma su yi. Daga cikin waɗannan wurare da ya yi kuka akwai:

Kukansa a salla:

Daga Abdullahi bin Shakir (z) ya ce: “Na je wajen Manzon Allah ‫ ﷺ‬yayin
da yake salla, ana jin gunji a Ƙirjinsa kamar sautin tafasar ruwa, saboda kuka”.
Ahmad, da Abu Dawud ne suka ruwaito wannan Hadisin, kuma Albani ya inganta
shi.

Wannan Hadisi dalili ne a kan halaccin kuka a cikin salla, kuma hakan ba ya
ɓata Salla a cikin zancen malamai mafi inganci, musamman ma kuka yayin da aka
ambaci Aljanna, da Wuta.

Daga Aliyu ya ce (z): “Babu wanda yake haye a kan doki a ranar yaƘin
Badar in ba MiƘdad ba. HaƘiƘa na gan mu duk muna bacci, sai Manzon Allah ‫ﷺ‬
kaɗai yana Ƙasan wata itaciya yana salla, yana kuka, har sai da gari ya waye”. Ahmad
ne ya fitar da wannan Hadisi, Arna’uɗ kuma ya inganta shi.

197
Kukansa yayin da yake sauraron AlƘur’ani:

Daga Abdullahi bin Mas’ud (z) ya ce: Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya ce da ni:
“karanta mini Ƙur’ani. Sai na ce: Ya Manzon Allah ‫ﷺ‬, ya zan karanta maka Ƙur’ani
bayan kai aka saukarwa? Sai ya ce: Ni kam ina son in ji shi daga wajen wani na.
Sai na karanta misa Suratun Nisa’i, har sai dai na kai kan faɗinSa:

٤١:‫ﱡﭐﱾﱿﲀﲁﲂﲃﱠ ال نس اء‬
(Kuma muka zo dai kai a kan waɗannan kana mai shaida) (Nasa’i: 41), sai ya ce: Ya
isa haka yanzu. Sai na waiga na kalle shi, sai na ga idanuwansa suna zubar da
hawaye”. Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi.

Ibn Baɗɗal ya ce: “Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya yi kuka ne yayin karanta wannan aya,
domin ya suranta wa kansa wahalhalun da za a shiga a ranar lahira, da wahalar da
mai kira yake sha wajen shaidawa, da gasgatawar mutanensa, da kuma roƘon ceto
da zai yi ga waɗanda suke wannan wuri. Wannan lamari ne da ya cancanci ayi kuka
mai tsayi a kansa”

Ibnu Hajar ya ce: “Abin da yake bayyana shi ne: Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya yi kuka
ne, domin jinƘai, da rahama ga al’umarsa. Domin ya san dole ne ya yi shaida ga
al’umarsa game da aikinsu. Shi kuma aikinsu na iya yiwuwa ba miƘaƘƘe ba ne,
wanda hakan zai iya bayuwa zuwa ga azabtar da su”.

Kukansa a wajen mutuwa:

Daga Usama bin Zaid (z) ya ce: “Wani yaro daga cikin jikokin Annabi ‫ﷺ‬
yana gargarar mutuwa, sai (mahaifiyar) yaron ta aika cewa Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya zo.
Sai ya aika mata da cewa: HaƘiƘa abin da Allah l ya karɓa daga Allah yake, haka
kuma ga Allah abin da ya bayar yake, kowa yana da wani lokaci da aka ambata masa.

198
Don haka ki yi haƘuri, ku nemi lada da haƘurin. Sai ta aika masa tana
rantsuwa a kan sai ya zo. Sai Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya tashi, sai nima na bi shi, da Mu’azu
bin Jabal, da Ubayyu bin Ka’ab, da Usama bin Samit. Yayin da muka shiga, sai suka
miƘa wa Manzon Allah ‫ ﷺ‬yaron, ransa yana kaikawo a Ƙirjinsa. Sai Manzon Allah
‫ ﷺ‬ya fashe da kuka. Sai Sa’ad bin Ubadah (z) ya ce: kai ma kana kuka? Sai ya
ce: “Allah yana jin Ƙan bayinsa masu jin tausayi”. Bukhari da Muslim ne suka
ruwaito shi.

Daga Anas bin Malik (z) ya ce: Mun halarci jana’izar wata ƴar Manzon
Allah ‫ﷺ‬, Manzon Allah ‫ ﷺ‬yana zaune kusa da kabarin. Sai na ga idanuwansa suna
zubar da hawaye. Sai ya ce: a cikinku akwai wanda bai kusanci iyalinsa ba da
daddare? Sai Abu Ɗalha ya ce: ga ni, sai ya ce: ka sauko, sai ya sauka cikin
Ƙabarinta”. Bukhari ne ya ruwaito shi.

Daga Abu Huraira (z) ya ce: “Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya ziyarci kabarin
mahaifiyarsa, sai ya yi kuka. Sai hakan ya saka waɗanda suke kewaye da shi kuka.
Sai ya ce: “Na nemi izinin Ubangiji a kan in nema wa mahaifiyata gafara, amma bai
yi mini izini ba. Sai na nemi izininsa a kan na ziyarci kabarinta, sai ya yi mini izini.
Don haka ku ziyarci kaburbura, domin kuwa suna tuna wa mutum mutuwa”. Muslim
ne ya ruwaito shi.

A cikin wannan Hadisi zamu ga cewa: Mahaifiyar Annabi ‫ ﷺ‬ta mutu tana kan
shirka, kuma ba ta cikin waɗanda saƘo ya yankewa, waɗanda za a jarraba a ranar
lahira, bai tabbata ba cewa Allah ya rayar da su suka yi Imani da Annabi ‫ﷺ‬, sannan
suka Ƙara rasuwa ba, duk hakan kawai guluwwi ne da wuce gona da iri game da
iyayen Manzon Allah ‫ﷺ‬, da iyalinsa.

199
Daga Barra’u bin Azib (z) ya ce: “Mun kasance tare da Manzon Allah ‫ ﷺ‬a
wajen wata jana’iza, sai ya zauna kusa da gefen kabarin, sai ya yi kuka har sai da ya
jiƘa turɓaya, sannan ya ce: “Ya ku ƴan’uwana game da irin wannan rana sai ku yi
tanadi”. Ahmad ,da Ibnu Majah ne suka ruwaito Hadisin, Albani kuma ya kyautata
shi.

200
Kukansa saboda mutuwar sahabbansa:

Daga A’isha (x) ta ce: “HakiƘa Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya sunbaci Usman bin
Maz’un (z) yayin da ya rasu, ko kuma ta ce: idanuwansa suna zubar da hawaye,
suna kwarara” Ahmad ne ya ruwaito shi, Albani kuma ya inganta shi.

Shi Usman bin Maz’un (z) ɗan’uwan Manzon Allah ‫ ﷺ‬ta ɓangaren
shayarwa.

Wannan yana nuna mana cewa: Manzon Allah ‫ ﷺ‬yana da tausayi, da jinƘai,
yana kuka saboda rabuwa da ƴaƴansa, da kuma Sahabbahnsa.

Kukan da yake ba wai na tsoro ba ne, a’a kukan tausayi ne.

Daga Ibnu Abbas (z) ya ce: “Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya ɗauki ƴarsa yayin da take
gargarar mutuwa, sai ya rungume ta, sai ya ajiye ta a gabansa. Ta mutu tana gabansa.
Sai Ummu Aiman ta kwarmata ihu, sai Annabi ‫ ﷺ‬ya ce: “Au zaki yi kuka haka a
gaban Manzon Allah ‫ ?ﷺ‬sai ta ce: kaima ba na ga kana kuka ba? Sai ya ce: “ni ba
kuka nake ba, kawai (hawayen) tausayi ne. Shi Mumini yana cikin alheri a kowanne
hali yake. Ana fitar da ransa daga geffensa, yana godiya ga Allah Maɗaukakin Sarki.
Tirmuzi ne ya fitar da Hadisin a ckin Shama’il, kuma Albani ya inganta shi.

HaƘiƘa ya gaya wa Ummu Aiman (x) wannan Magana ne, saboda kukanta
na kwarmata ihu ne, da ɗaga sauti tare da raki. Sai ya yi mata inkarin haka. Sannan
ya ce: (Ni ba kuka na ke ba) wato bana kukan raki da na rashin hakuri, ba za a ji abin
da Allah ya haramta ba daga wajena na yin kukan kaico da ihu da makamancin haka
ba, (kawai rahama ce) wato kukan jinƘai ne. Ahmad ne ya ruwaito wannan Hadisi,
Albani kuma ya inganta shi.

201
Auna Fahimta

 Yaya Annabi ‫ ﷺ‬yake ta fannin ibada? Dame ake kafa hujja wajen yawan
ibadarsa?

----------------------------------------------------------------------------------------------------

----------------------------------------------------------------------------------------------------

 Ta ɓangaren fiƘihu, mene ne hukuncin wanda ya yi bacci bai yi wutiri ba?


Kuma mene ne hukuncin salla a zaune tare da ikon yi a tsaye?

----------------------------------------------------------------------------------------------------

----------------------------------------------------------------------------------------------------

 Mene ne tafarkin Annabi ‫ ﷺ‬game da karatun Ƙur’ani? Kuma mene ne


hukuncin kuka a cikin Salla? Kuma ya zaka tabbatar da tadabburin abin da
kake karantawa?

----------------------------------------------------------------------------------------------------

----------------------------------------------------------------------------------------------------

 Ambaci misalai na kukan Annabi ‫ﷺ‬, kuma mene ne hukuncin yin kuka a cikin
salla? Shin yana ɓata ta?

----------------------------------------------------------------------------------------------------

----------------------------------------------------------------------------------------------------

 Ta ya zaka bayar da amsa ga wanda yake wuce gona da iri a kan iyayen
Annabi ‫?ﷺ‬

----------------------------------------------------------------------------------------------------

----------------------------------------------------------------------------------------------------
202
ƘanƘan da kan Annabi (Tawali’u) (‫)ﷺ‬:

Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya haɗa dukkanin sifar tawali’u. Ba ya jin girman kai ko
kaɗan, ballantana ya yi taƘama saboda girman matsayinsa, yana ƙanƙan-da-kansa
ga Muminai. Ba ya jin fifiko a kansu, yana zama a tsakaninsu, kamar ɗaya daga
cikinsu. Ba a gane wajen zamansa a cikin wajen zaman sahabbansa, domin yana
zama ne inda wuri ya samu, yana zama a tsakaninsu, har idan baƘo ya zo ba ya iya
gane waye Manzon Allah ‫ ﷺ‬a cikinsu, har sai ya tambaya.

AlƘali Iyadh ya ce: “Amma game da ƘanƘan-da-kai na Manzon Allah ‫ﷺ‬, duk
da girman matsayinsa, da ɗaukakarsa, ya fi kowa ƘanƘan-da-kansa, kuma ya fi kowa
rashin girman kai”.

Ya ishe mu misali, a lokacin da aka ba shi zaɓi a kan ya zama sarki, ko kuma
Annabi, ko Annabi kuma bawa, sai ya zaɓi ya zama bawa kuma Annabi.

HaƘiƘa wani mutum ya shiga wajensa, sai kwarjinin Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya kama
shi, ya kama karkarwa. Sai Annabi ‫ ﷺ‬ya ce: “Kwantar da hankalinki, ni ba sarki ba
ne, ni ɗan wata mata ne, daga Ƙabilar Ƙuraishawa, da take cin busasshen nama”. Ibnu
Majah ne ya ruwaito Hadisin, kuma Albani ya inganta shi.

Daga cikin misalan ƙanƙan-da-kansa akwai waɗannan abubuwa masu zuwa:

ƘanƘan-da-kansa wajen makwancinsa:

Daga A’isha (x) ta ce: Manzon yana yin bacci a kan shimfiɗar da aka yi ta
da jemammiyar fata, an cusa mata cikinta da bushasshiyar ciyawa”. Bukhari da
Muslim ne suka ruwaito shi.

203
Daga dai Nana A’isha (x) ta ce: “Matashin kan Manzon Allah ‫ ﷺ‬da yake
baccin dare a kai; an yi shi daga jemammiyar fata, an susa mata basasshiyar ciyawa
a ciki. Abu Dawud ne ya ruwaito shi, kuma Albani ya inganta shi.

Al’imamun Nawawi ya ce: “A cikin Hadisin akwai halascin mutum ya riƘi abin da
zai dinga kwana a kai, da kuma matsashin kai domin kishingiɗa a kai”.

Malam Alƙari ya ce: “Abin da ya fi fitowa fili shi ne a ce mustahabbi ne hakan,


saboda dawwamar da ya yi a kan hakan, kuma hakan shi zai fi samar wa mutum
hutun da ake yin bacci domin shi. Kuma hakan zai fi ba wa mutum nishaɗi wajen
tashi yin ibada”.

Daga Abdullahi bin Mas’ud (z) ya ce: “Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya kwanta a kan
tabarma, sai ta yi masa alamu a jikinsa, yayin da ya tashi; sai na dinga share masa
jiki, sai na ce: “Ya Manzon Allah ‫ ﷺ‬shin ba zaka umarce mu da mu ɗan shimfiɗa
maka wani abu ba a kan tabarmar? Sai Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya ce: Ina ni ina duniya,
misalina fa da misalin duniya, kamar matafiyi ne da ya huta a Ƙasan bishiya, sannan
ya tashi ya bar ta”. Ahmad ne ya ruwaito shi, Kuma Arna’uɗ ya inganta shi.

Ibnul Ƙayyim ya ce: “Manzon Allah ‫ ﷺ‬kan yi bacci a kan shimfiɗa, wataran
kuma a kan shimfiɗar jemammiyar fata, wataran kuma a kan dandagaryar Ƙasa,
wataran kuma a kan gado, wataran a kan rairayin Ƙasa , wataran kuma a kan baƘin
bargo.

ƘanƘan Da Kansa A Wajen Zama:

Daga Abu Zarrin (z), da Abu Huraira (z) sun ce: “Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya
kasance yana zama a cikin sahabbansa, har baƘo ya zo amma ba zai san waye shi ba,
har sai ya tambaya. Sai muka nemi mu yi wa Manzon Allah ‫ ﷺ‬wajen zaman da baƘo
zai gane shi idan ya zo, sai ya ce: sai muka gina masa dakali da taɓo, sai yake zauna

204
a kai, mu kuma muna zama a gefensa”. Abu Dawud ne ya ruwaito shi, Albani kuma
ya inganta shi.

Ba ya sa wa a miƙe masa domin girmamawa:

Daga Anas bin Malik (z) ya ce: “Ba su da wanda da suke tsananin Ƙauna
fiye da Manzon Allah ‫ﷺ‬, Duk da haka sun kasance idan sun gan shi; basa miƘewa,
saboda ba ya son hakan”. Tirmuzi ne ya ruwaito shi, Albani kuma ya inganta shi.

Ibnu Usaimin ya ambaci ire-iren miƙewa da suka rabu zuwa gida uku,

miƙe wa mutum, da tsayawa a kan mutum, da miƙewa zuwa ga mutum.

MiƘe wa mutum: Wato miƘewa idan mutum ya shigo waje domin girmamawa,
wannan ba laifi a kansa.

MiƘewa zuwa mutum: Shi ne mutum ya miƘe ya ɗan taka ya tafi wajen wanda
yake shigowa, wannan ma ya halatta. Yayin da Sa’ad bin Mu’az (a) ya zo domin
yin alƘalanci, sai Annabi ‫ ﷺ‬ya ce: “Ku miƘe (ku je) zuwa ga shugabanku”. Sai ya yi
umarni da a miƘe aje masa domin girmama shi. Bukhari da Muslim ne suka ruwaito
shi.

Tsayawa a kan mutum: Wannan bai halatta ba. Sai dai idan akwai fusata
Mushirikai idan an yi hakan. Domin Annabi ‫ ﷺ‬ya hana mu tsaya a kan waninmu,
kamar yadda Ajamawa suke yi wa sarakunansu. Abu Dawud ne ya ruwaito shi,
Albani kuma ya raunana Hadisin.

Kai har ma a cikin salla, domin kuwa yayin da ya yi salla a zaune, su kuma
suka yi salla a tsaye a bayansa, sai ya umarce su da su zauna, domin kada
kamanceceniya da (Ajamawa) ta bayyyana a cikin salla.

205
Amma kuma idan akwai fusata Mushirikai idan an yi hakan; to babu laifi.
Kamar yadda Mugiratu bin Shu’uba (z) ya tsaya a kan Manzon Allah ‫ ;ﷺ‬a lokacin
da Ƙuraishawa suke tattaunawa da shi a Sulhun Hudaibiyya.

Wannan babu kokwanto abu ne da za a yaba da shi. Domin a bayyana wa


kafirai cewa Musulmai suna girmama shuwagabanninsu, da manyan cikinsu.

Hani da ya yi game da wuce-gona-da-iri wajen yabonsa:

Daga Umar bin Khaɗɗab (z) ya ce: Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya ce: “Kada ku wuce-
gona-da-iri wejen yabona, kamar yadda Nasara suke yi ga Ɗan Maryama. Ni ba
kowa ba ne face bawan Allah, ku ce bawan Allah, kuma ManzonSa”. Bukhari ne ya
ruwaito shi.

“Kamar yadda Nasara suka yi ga Ɗan Maryama”: Saboda sun wuce-gona-da-iri


wajen yabonsa, suka zarce iyaka, har suka sanya shi ɗa ga Allah maɗaukakin Sarki.

Ƙanƙan-da-kansa wajen amsa gayyata:

Daga Anas bin Malik (z) ya ce: “Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya kasance ana gayyatar
shi zuwa ga gurasar alkama, da kakidin da ya jima, kuma ya amsa gayyatar”. Tirmuzi
ne ya ruwaito shi a Shama’il, Albani kuma ya inganta shi.

Daga Anas bin Malik (z) ya ce: Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya ce: “Da za a ba ni
kyautar Ƙafar akuya, da na amsa, kuma da za a gayyace ni; da na amsa gayyatar”.
Bukhari ne ya ruwaito shi.

A cikin Hadisin akwai dalili kan kyawun ɗabi’unsa ‫ﷺ‬, da kuma Ƙanƙan-da-
kansa, da kuma Ƙarfafa zuƘatan mutane da yake; wajen karɓar kyautarsu, da kuma
amsa gayyatar da yake yi, ko da kuwa ya san abin da aka gayyace shi akansa ;abu
ne ƘanƘani.

206
ƘanƘan Da Kansa A Cikin Gidansa

Daga Umaratu (x) ta ce: “An ce wa A’isha (x): Me Manzon Allah ‫ﷺ‬
yake yi a cikin gidansa? Sai ta ce: Shi dai Mutum ne daga cikin mutane, yana caje
tufafinsa (domin ya cire Ƙaya, ko wani abu da ya maƘale a jiki), kuma yana tatsar
(nonon) akuyarsa, kuma yana hidimta wa kansa”. Ahmad ne ya ruwaito shi, Arna’uɗ
kuma ya inganta shi.

Bukhari ya ruwaito daga Aswad ya ce: “Na tambayi A’isha (x): Me


Manzon Allah ‫ ﷺ‬yake aikatawa a gidansa? Sai ta ce: Yana kasancewa cikin hidimar
iyalinsa. Idan lokacin salla ya yi sai ya fita zuwa Salla”.

ƘanKan-da-kansa ga Ƙananan yara:

Bukhari da Muslim sun ruwaito hadisi daga Anas (z): Cewa ya wuce wasu
Ƙananun yara, sai ya yi musu sallama, sai ya ce: “Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya kasance yana
yin hakan”.

Daga Anas (z) ya ce: “Annabi ‫ ﷺ‬ya kasance yana ziyartar Ansarawa, yana
yi wa yaransu sallama, yana shafar kawunansu”. Ibnu Hibban ne ya ruwaito shi,
Albani kuma ya inganta shi.

Daga wajen Anas (z) ɗin dai ya ce: “Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya kasance yana yi
mana raha, har yakan ce wa Ƙaramin ɗan’uwana: “Ya kai Baban Umair meye labarin
ɗan tsuntsun?”. Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi.

Annabi ‫ ﷺ‬ya kasance mai-ƘanƘan-da-kai ba tare da ƘasƘanci ba. Mai kyauta


ba tare da ɓarna ba. Mai taushin zuciya mai jinƘai ga kowanne Musulmi. Yana
ƙanƙan-da-kansa ga Muminai, ga shi mai sauƘin kai.

207
Ɗabi’un Manzon Allah ‫ﷺ‬:

Wato halayensa, abin nufi surarsa ta ɓoye:

Abin da ake nufi da kyawun ɗabi’a, shi ne yin abu na falala, da ƙima, da kuma
barin abubuwa marasa kyawu, da Ƙima.

HaƘiƘa An tambayi A’isha (x) game da halayen Manzon Allah ‫ﷺ‬, sai ta
ce: “Ƙur’ani ne ya a kasance ɗabi’unsa”. Muslim ne ya ruwaito shi.

HaƘiƘa ya siffantu da dukkanin suffofin da aka yaba, da kuma aka ambata a


cikin Ƙur’ani. Yana nesantar duk wani hali mai muni, da aka san shi. Allah
Maɗaukakin Sarki Ya yi gaskiya da Yake bayyana Annabi ‫ ﷺ‬ya ce:

٤ :‫ﱡﭐﲋﲌﲍﲎﲏﱠ ال قلم‬

“Kuma, lalle, haƘiƘa kana kan halayen kirki manya”. (Ƙalam: 4)


Ibnu Kasir ya ce: “Abin nufi a nan, Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya kasance yana bin duk
umarnin da ya zo cikin Ƙur’ani. An umarce shi ne, ko an hane shi wani abu. Har
hakan ya zama halayyarsa, komai Allah Ya yi umarni a kai, to zai yi shi. Kuma
komai Ya hana shi; to yana barin shi. Wannan shi ne abin da Allah ya ɗora shi a kai
na halayen kirki manya, kamar su: Kunya, karamci, gwarzantaka, yafiya, haƘuri
juriya, da duk wani hali mai girma.

A’isha (x))) ta ce: “Manzon Allah ‫ ﷺ‬ba mai alfasha ba ne, kuma ba ya aikata
ta, kuma ba mai hayaniya ba ne a kasuwanni, kuma ba ya saka mummuna da
mummuna. Sai dai ya yi afuwa ya yafe”. Tirmuzi ne ya ruwaito shi, Albani kuma ya
inganta shi.

Ibnu Usamin ya ce: “Halayen kirki, wato halin mutum game da Allah. Da
kuma halayensa game da bayin Allah”.

208
Amma kyawun hali game da Allah, shi ne mutum ya yadda ya miƘa wuya ga
dukkanin hukunce–hukunce da Allah Ya shar’anta. Kada mutum ya ji wata takura,
ko Ƙunci a ransa, idan Allah Ya umarce shi da yin salla, da bayar da Zakka, da yin
azumi, da wanin haka. Mutum ya karɓi hakan da yalwataccen Ƙirji.

Shi kuma kyawun hali game da Mutane: Shi ne rashin cutar da su, da kuma
yin haƘuri game da cutarwarsu, da sakin fuska, da sauransu.

Halinsa nagari game da hadimai.

Anas bin Malik (z) ya ce: “Na yi wa Manzon Allah ‫ ﷺ‬hidima tsawon
shekara goma, bai taɓa cewa da ni uffan ba. Ban taɓa yin wani abu ya ce da ni: don
me ka yi? Ko na bar wani abu ya ce: don me ka bari ba?” Bukhari da Muslim suka
ruwaito shi, wannan lafazin Tirmuzi ne.

Daga Anas (z) ya ce: “Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya kasance mafi kyawun halaye a
cikin mutane, kuma ban taɓa taɓa wani Kazzi, ko akharri, ko dai wani abu da ya fi
tafin hannun Manzon Allah ‫ ﷺ‬laushi ba, ban kuma taɓa shaƘar wani almiski, ko wani
turare da yafi gumin Manzon Allah ‫ ﷺ‬Ƙamshi ba”. Bukhari da Muslim suka ruwaito
shi.

Tausasawarsa da kuma rashin tsaurinsa:

Daga A’isha (x) ta ce: “Yahudawa sun kasance suna yi wa Annabi Sallama
suna cewa: (Assamu alaika) Mutuwa ta tabbata a gareka. Sai A’isha ta fahimci abin
da suke faɗa, sai ta ce: “kuma mutuwa, da tsinuwa su tabbata a kanku”. Sai Annabi
ya ce: “a’a dai A’isha. HaƘiƘa Allah yana son tausasawa a cikin lamari gabaɓaya”.

Sai ta ce: ya Annabin Allah ‫ﷺ‬, shin ba ka ji abin da suke faɗa ba? Sai ya ce: “Shin
kema baki ji me nake amsa musu da shi ba? Ina cewa: kuma ta tabbata a kanku”.
Bukhari da Muslim suka ruwaito shi.

209
Daga wajen ta ɗin dai ta ce: “Bai taɓa ɗaukar fansa ba a kan abin da aka yi
masa ba, sai dai idan an taka iyakokin Allah, sai ya ɗauki fansar domin Allah”.

Daga Abu Huraira (z): HaƘiƘa wani balaraban Ƙauye ya yi fitsari a cikin
masallaci, sai mutane suka taso zasu afka masa, sai Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya ce da su:
“Ku Ƙyale shi, ku kwara gugan ruwa, ko likidirin ruwa a kan fitsarin, haƘiƘa mu an
aiko mu ne domin mu sauƘaƘa, ba a aiko mu don tsaurarawa ba”. Bukhari ne ya
ruwaito shi.

Yanayin Kyautarsa ‫ﷺ‬:

Daga Muhammad Al-munkadir, ya ce: Na ji Jabir bin Abdullahi (z) yana


cewa: “Ba a taɓa tambayar Manzon Allah ‫ ﷺ‬wani abu ba, ya ce: a’a ba”. Bukhari da
Muslim suka ruwaito shi.

Daga Ibnu Abbas (z) ya ce: “Manzon Allah ‫ ﷺ‬shi ne mafi kyautar mutane.
Ya kasance lokacin da ya fi kyauta shi ne a watan Ramadan, har sai ya wuce. Jibril
(q) yakan zo masa, ya bijiro masa da Ƙur’ani, idan Jibril ya zo masa yakan fi
sakakkiyar iska kyauta”. Bukhari da Muslim suka ruwaito shi.

A cikin wannan Hadisi akwai bayanin girman kyautarsa, da kuma yawanta.

Daga Anas bin Malik (z) ya ce: “Annabi ‫ ﷺ‬ya kasance ba ya ajiye komai
domin gobe”. Tirmuzi ne ya ruwaito Hadisin, Albani kuma ya inganta shi.

Wannan hadisi yana nuna Ƙarfin tawakkalin Manzon Allah ‫ﷺ‬.

Amma abin da ya zo a cikin Sahihul Bukhari da Muslim cewa: Yana ajiye


abincin shekara guda ga iyalinsa. Ibnu Hajar ya ce: “Wannan ya faru ne game da
abin da ya zama dole. Domin abin da yake ajiyewa, abin da ba a samun shi ne sai
shekara bayan shekara, domin ba ya ajiye komai in ba dabino ba, ko Alkama. Da ace

210
ya zama abin da yake aijyewa ba a samu sai bayan shekara biyu–biyu, da hakan da
ya bayu zuwa ga halaccin taskace abinci saboda haka”. Allah shi ne masani.

Kunyar Manzon Allah ‫ﷺ‬:

Daga Abu Sa’id Al-khudri (z) ya ce: “Manzon allah ‫ ﷺ‬yana da tsananin jin
kunya, fiye da budurwar da take cikin gidanta. Ya kasance idan ba ya son wani abu
sai dai a gane hakan a fuskarsa”.

“Ya kasance idan ba ya son wani abu ana gane hakan a fuskarsa”: Wato
fuskarsa tana canzawa, sai sahabbansa su gane ba ya son hakan.

Al’imamul Ƙari ya ce: “Budurwar da take gidanta, mafi yawanci ba ta magana


a gaban mutane, sai dai ana gane yardarta, ko rashin yardarta a kan abu a fuskarta.
Da hakan ne za ga alaƘar maganar Ƙarshe, da wacce ta gabata”.

A hadisin da ya zo a Sahihul Bukhari da Muslim, daga Anas (z) a cikin


Ƙissar auren Annabi ‫ﷺ‬, da zainab bint Jahashin, bayan sahabbai sun ci abinci, sai
suka yi tafiyarsu, sai uku daga cikinsu suka tsaya suna ta hira, alhali kuma Manzon
Allah ‫ ﷺ‬yana son su fita, sai Anas (z) ya ce: “Manzon Allah ‫ ﷺ‬yana da tsananin
jin kunya”.

A wata ruwayar kuma, sai Annabi ya dinga jin kunyar ya yi musu magana.

Wannan Hadisi na daga cikin manyan dalilai dake nuna tsananin jin kunyar
Manzon Allah ‫ﷺ‬, saboda kunyarsa ne ya sa ya kasa fuskantar waɗannan mutane, da
kan cewa su fita, har sai da Allah ya jiɓinci bayar da wannan labara, domin girmama
haƘƘin Annabinsa ‫ ﷺ‬.

Allah z ya ce:

211
‫ﱡﭐ ﲅ ﲆ ﲇ ﲈ ﲉ ﲊ ﲋ ﲌ ﲍ ﲎ ﲏ ﲐ ﲑ ﲒ ﲓ ﲔﲕ‬

‫ﲖ ﲗ ﲘ ﲙ ﲚ ﲛ ﲜ ﲝ ﲞﲟ ﲠ ﲡ ﲢ ﲣ ﲤ‬

‫ﲥﲦﲧﲨﲩﲪﲫﲬﲭﲮﲯﲰﲱﲲﲳﲴﲵﲶ‬

‫ﲷﲸﲹﲺﲻﲼ ﲽﲾﲿﳀﳁﳂﳃﳄﳅ ﳆﳇﳈﳉ‬

٥٣ ‫ﳊ ﳋ ﳌﳍ ﳎ ﳏ ﳐ ﱠ‬
“Ya ku waɗanda suka yi Imani! Ka da ku shiga gidajen Annabi face ba idan an yi
izini a gare ku zuwa ga wani abinci, ba da kun tsaya jiran nunarsa ba, kuma amma
idan an kira ku, to ku shiga, sa’an nan idan kun ci, to ku tafi, kuma ba da kun tsaya
kuna masu hira, da wani labari ba. Lalle wannan yana cutar da Annabi, to, yana jin
kunyarku, alhali kuwa Allah ba ya jin kunya daga gaskiya”. (Ahzab: 53)
Shekarun Manzon Allah ‫ﷺ‬

Daga Ibnu Abbas (z) ya ce: “Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya zauna a garin Makka
tsawon shekara goma sha uku ana yi masa wahayi, ya kuma zauna a Madina tsawon
shekara goma, ya yi wafati yana da shekaru sittin da uku. Bukhari da Muslim ne
suka ruwaito shi..

212
Wafatin Manzon Allah ‫ﷺ‬:

Yayin da mutuwa ta zama abar Ƙi ta gaske, saboda abin da yake cikinta na


tsanani, da wahala mai yawa, ba wani Annabi daga cikin Annabawa da ya rasu, face
sai yana sallamawa game da Ƙarewar rayuwa, da mutuwa, game da ɗaukar ransa,
kuma domin ya sadu da abokan tafiya maɗaukaka. Haka Annabi bai gushe ba yana
kusantar ajalinsa a Ƙarshen rayuwarsa, ya faɗa wa mutane yayin Hajjin bankwana:
“Ku koyi ibadar aikin hajjinku daga wajena, domin ban sani ba la’alla ba zan Ƙara
yin aikin hajji ba bayan wannan”. Muslim ne ya ruwaito shi.

Daga Anas bin Malik (z) ya ce: “Ganina na Ƙarshe da Manzon Allah ‫ ﷺ‬shi
ne ranar Litinin, ya buɗe labule, sai na ga fuskarsa cikin annuri, da walala, kai ka ce
takarda (Ƙur’ani) – mutane kuma suna bayan Abubakar (z) yana jan su salla –
wato a sallar Asubahi – mutane sun kusa su yanke sallarsu (saboda ganin Annabi ‫)ﷺ‬,
sai ya yi musu nuni da ya su ci gaba. Sai ya yaye labulen. Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya yi
wafati a Ƙarshen wannan ranar – wato ranar Litinin – Ahmad, da Ibn Majah ne suka
ruwaito shi, Albani kuma ya inganta shi.

A wata ruwayar kuma ta Muslim, “Sai Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya yi murmushi yana
mai dariya”.

Al’imamun Nawawi ya ce: “Dalilin da ya sa Annabi ‫ ﷺ‬ya yi murmushi shi ne:


Saboda da farin cikin ya ga sun taru a salla, kuma sun bi limaminsu, sun tsayar da
shari’ar Allah, kalmarsu ta tsayu, da kuma haɗuwar zuciyarsu, saboda haka fuskar
Annabi ta yi annuri, kamar yadda al’adarsa take, idan ya ga, ko ya ji abin da ya
faranta masa”.

Wato har sun kusa su katse sallarsu, saboda farin ciki saboda ganinsa.

213
Abubakar (z) kuma yana jan su salla, saboda umarnin da Annabi ‫ ﷺ‬ya yi
da ya ce: “Ku umarci Abubakar ya yi wa mutane salla”. Bukhari da Muslim ne suka
ruwaito shi.

A cikin wannan Hadisi a akwai nuni game da cewa Abubakar (z) shi ne
halifa bayan Manzon Allah ‫ﷺ‬.

Daga A’isha (x) ta ce: “Na jinginar da Manzon Allah ‫ ﷺ‬Ƙirjina, ko a cinyata, sai
ya nemi a kawo masa tasa domin ya yi fitsari a ciki, sannan sai ya yi fitsarin. Sai
Allah ya karɓi ransa. Tirmuzi ne ya ruwaito Hadisin a cikin Shama’il, Albani kuma
ya inganta shi.

A cikin wata ruwayar kuma: “Annabi ya yi wafati a cikin gidana, a kwanana,


yana tsakanin Ƙirjina, da wuyana, Allah Ya haɗa yawuna da yawunsa”. Bukhari ne
ya ruwaito shi.

Abin nufi wato ta saka yawunta, ta tattauna asuwaki ya yi laushi, sannan


Annabi ‫ ﷺ‬ya yi amfani da shi.

Kuma ya rasu alhali kansa yana tsakanin wuyanta, da Ƙirjinta. Allah Ya Ƙara
yarda da ita.

A cikin hakan gabaɗaya akwai nuni ga girman matsayin A’isha (x) a wajen
Allah, ta yadda Annabi ‫ ﷺ‬ya rasu a gidanta, tsakankanin Ƙirjinta, da wuyanta, kuma
ya zama yawunta shi ne Ƙarshen abin da ya ɗanɗana a duniya.

Daga A’isha (x), ta ce: “Na ga Manzon Allah ‫ ﷺ‬yayin da zai rasu, akwai
moɗa, da ruwa a tare da shi, yana shigar da hannunsa cikin mazubin, sannan ya shafi
fuskarsa da ruwan, sannan ya ce: “Ya Allah ka taimake ni a kan magagin mutuwa”.

Tirmuzi ne ya ruwaito Hadisin, Ibnu hajar ya ce: “Hadisi ne mai kyau”.

214
Bukhari, da Muslim sun fitar da Hadisi daga A’isha da Abdullahi bin Abbas
(z) su biyun sun ce: “Yayin da rashin lafiya ta tsananta ga Manzon Allah ‫ﷺ‬, sai
ya dinga yaye tufafin dake fuskarsa, idan numfashinsa ya tsananta, sai ya yaye
mayafin daga fuskarsa, sai yake faɗa yana cikin wannan hali: “Tsinuwar Allah ta
tabbata ga Yahudu, da Nasara, sun riƘi Ƙaburburan Annabawansu wurin salla”. yana
gargaɗin Al’ummarsa ga abin da suka aikata.

Ƙurɗubi ya ce: “Game da tsananin mutuwa ga Annabawa, akwai fa’ida guda


biyu:

Ta farko: Saboda hakan cikar falalarsu ne, da ɗaga darajarsu. Hakan ba tawaya
ba ce, ba kuma azaba ba ce. Kawai dai kamar yadda ya zo a cikin Hadisi cewa:
“Mafiya shiga tsananin bala’i; su ne Annabawa, sannan waɗanda suka yi kama da
su (wato salihan bayi, sannan waɗanda suka yi kama da su (wato salihan bayi)”.

Ta biyu: Saboda mutane su san girman raɗaɗin mutuwa. Domin mutum yakan
ga wasu suna gaɓar mutuwa, amma ba zai ga wani motsi, ko firgici ba a tare da shi,
ya ga sauƘin fitar ruhinsa, sai ya yi zaton sauƘin lamari, bai san halin da mamacin
yake ciki ba.

Ibn Rajab ya ce: “Wafatinsa ya kasance ranar Litinin a watan Rabi’ul Auwal
ba tare da wani saɓani ba”.

Faɗinsa: “Tsinuwar Allah ta tabbata a kan Yahudu, da Nasara, sun riƘi


Ƙaburburan Annabawansu wajen salla”, yana gargaɗi a kan abin da suka yi.

A ciki akwai gargaɗi mai girma da ya yi a Ƙarshen rayuwarsa, na riƘar


Ƙaburburan Annabawa wajen bauta, kuma hakan yana tabbatar da tsinuwa a kan
mutum. To yaya kake gani ga waɗanda suka riƘi Ƙaburburan bayi nagari, da waninsu
waɗanda ba su kai Annabawa ba wajen bauta?! Wannan gargaɗi da ya yi a wannan

215
lokaci babban dalili ne dake nuna haramci, da girman laifin aikata haka, da kuma
girman saɓa wa shari’a miƘaƘƘiya, da ya yi, da kuma saɓa wa Tauhidi, da kaɗaita
Allah Ta’ala.

216
Wajen da aka binne shi ‫ﷺ‬:

Daga A’isha (x) ta ce: “An karɓi ran Manzon Allah ‫ ﷺ‬sai (sahabbai) suka
yi saɓani game da wajen da za a binne shi. Sai Abubakar (z) ya ce: “Na ji wani
abu daga wajen Annabi ‫ ﷺ‬da ban manta ba, ya ce: “Allah ba zai karɓi ran wani
Annabi ba; face sai a wajen da yake son a binne shi a ciki”. Ku binne shi a wajen
shimfiɗarsa”. Tirmuzi ne ya ruwaito shi, kuma Albani ya inganta shi.

Alhafiz Ibnu Kasir ya ce: “An sani cikin labarai da hankali ba zai taɓa yi yuwa
ya zama labarin Ƙarya ba cewa: An binne Manzon Allah ‫ ﷺ‬a ɗakin A’isha (x),
ɗakin da ta keɓanta da shi, a gabas da Masallacinsa, a zawiyar yamma da alƘibla,
sannan aka binne Abubakar, sannan Umar (z)”.

Tabarrukin da aka hana da ƙabarin Annabi ‫ﷺ‬:

An shara’anta ziyartar Ƙabarin Annabi ‫ ﷺ‬ba tare da tsananta tafiya zuwa can
ba, duk wanda ya yi hakan zai sami lada, kamar yadda da ake samun lada idan an
ziyarci Ƙaburbura a jumlace. Sai dai kuma wasu daga cikin masu zuwa ziyarar
Ƙabarin Annabi ,‫ ﷺ‬sun farar da wasu bidi’o’i, da abubuwa masu girma, da suka saɓa
wa Shari’a. Hakan haramun ne, an hana shi a Shari’a, domin a yanke duk abin da zai
bayu zuwa ga shirka, kuma a tabbatar da Tauhidi. A yi ikhlasi kaɗai ga Allah
Maɗaukakin Sarki.

Na daga cikin surarin abin da aka haramta:

Neman Addu’a, ko ceto daga wajen Manzon Allah ‫ﷺ‬.

Sanya wa Ƙabarin Ƙubba, da yin salla ana fuskantar kabarin.

Shafar Ƙabarin, ko sumbatar shi.

217
Gadon da Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya bari:

Daga Abu Huraira (z) ya ce: Fatima (x) ta zo wajen Abubakar (z),
sai ta ce: “waye zai ci gadonka”? Sai ya ce: “iyalina, da ƴaƴana”. Sai ta ce: “to ni me
ya sa ba zan ci gadon mahaifina ba?” Sai Abubakar (z) ya ce: “na ji Manzon Allah
‫ ﷺ‬yana cewa: “Mu ba a cin gadonmu” amma ni zan ɗauki nauyin wanda Manzon
Allah ‫ ﷺ‬yake ɗaukar nauyinsa, kuma zan ciyar da duk wanda Manzon allah ‫ ﷺ‬ya
kasance yana ciyarwa”. Ahmad, da Tirmuzi ne suka ruwaito Hadisin, Albani kuma
ya inganta shi.

A cikin Sahihul Bukari, da Muslim, daga A’isha (x): HaƘiƘa Fatima (x)
ƴar Manzon Allah ‫ ﷺ‬ta tambayi Abubakar (z), da ya raba gadonta, bayan wafatin
Manzon Allah ‫ ﷺ‬, sai Abubakar (z) ya ce: “HaƘiƘa Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya ce: “mu
ba a cin gadonmu, abin da muka bari ya zama sadaka”.

Daga Abu Huraira (z) daga Annabi ‫ ﷺ‬ya ce: “Kada magadana su raba wani
dinari, ko dirhami, abin da na bari bayan abincin matana, da ɗaukar nauyin masu
lura, da al’muran Musulmai (wato halifansa) to sadaka ne”. Bukhari da Muslim ne
suka ruwaito shi.

Sheik Albani ya faɗa game da rashin bai wa Fatima (x) gado da Abubakar
(z) ya yi, wannan shi ne abin da ƴan shi’a suka yi wa Abubakar (z) inkarinsa,
suka soke shi da shi, da abin da suka so na son zuciyarsu, da kuma ɓatansu, domin
wai bai ba wa Sayyada Fatima (x) gado ba. Saboda ya yi amfani da wannan
ingantaccen Hadisi wanda da yawa daga cikin Sahabbai sun ruwaito wannan Hadisi,
kamar: Umar, Usman, Sa’ad, Ɗalha, Zubari, Abdurrahaman bin Auf, da A’isha
(g), da waninsu ma.

218
Auna Fahimta:

 Bayyana ta yaya Manzon Allah ‫ ﷺ‬ya zama mai ƘanƘan-da-kai, ta ɓangarori


masu yawa?

--------------------------------------------------------------------------------------------------

--------------------------------------------------------------------------------------------------

 Mene ne hukuncin tsayawa a kan mutum, ko kuma ga mutum? Rarrabe


Magana a cikin hakan, tare da ambaton dalili.

--------------------------------------------------------------------------------------------------

--------------------------------------------------------------------------------------------------

 Ta yaya Annabi ‫ ﷺ‬ya kare Tauhidi, kuma ya hana wuce-gona-da-iri?

--------------------------------------------------------------------------------------------------

--------------------------------------------------------------------------------------------------

 Manzon Allah ‫ ﷺ‬a cikin gidansa ya kasance babban abin kwatance ne ga duk
wani namiji, yi cikakken bayani a kan hakan.

--------------------------------------------------------------------------------------------------

--------------------------------------------------------------------------------------------------

 Bayyana kyawun halayen Annabi ‫ ﷺ‬ta kowanne ɓangare?

--------------------------------------------------------------------------------------------------

--------------------------------------------------------------------------------------------------

 Mene ne Ƙarshen abin da Annabi ‫ ﷺ‬ya faɗa a cikin rayuwarsa? Kuma me


hakan yake nunawa?

219
--------------------------------------------------------------------------------------------------

--------------------------------------------------------------------------------------------------

 Ta yaya zaka bayar da amsa ga ƴan shi’a a kan sukar da suke yi wa Abubakar
(z), saboda bai ba wa Sayyada Fatima (x) gadon Manzon Allah ‫ ﷺ‬ba?

--------------------------------------------------------------------------------------------------

--------------------------------------------------------------------------------------------------

Allah Ya sa mu dace

220
Manazarta:

Assiratun nabawiyya na Ibnu Hisham.

Tahzibu sirati Ibnu Hisham.

Albidayatu wan nihayatu na Ibnu Kasir.

Zadul Ma’ad fi Hadyi khairil ibad, na Ibnul Ƙayyim Al-jauziyya.

Arraudul Al-anf, na Suhaili.

Uyunul Asar – Ibnu Sayyidin-Nas.

Sublul Hadyir-Rashad fi sirati Khairil Mi’ad – Muhammad Yusuf Salih Ash-shami.

Mukhtasaru siratin nabawiyya, na Muhammad bin Abdulwahhab.

Arrahiƙul Makhtum, na Mubarakfuri, a kan wannan littafi aka dogara sosai cikin.

maudu’ai mafiya yawa (a cikin wannan littafi).

Muƙaddimatus Sira, na Sheik Abdurrahaman Salih Al-mahmud.

221
SHIRIN TSANGAYAR AFRICA:

An samar da Tsangayar Africa ne, da nufin taimaka wa


al’umar Africa, wajen samun ingantacciyar fahimtar Musulunci, ta
hanyar Alƙur’ani Mai Girma, da Sunnar Annabi (‫ )ﷺ‬.

Dandali ne shakundum wanda ke gabatar da shirin


ilimantarwa da nufin kusantar da ilimi zuwa ga masu sha'awar
shi, ta hanyarInternet, da kafofin sada zumunta, da kuma kan
akwatin talabijin na Africa tv3.

Dandalin ya dogara da samar da ilimi mai zurfi akan tsarin:


MassiveOpen Online Course wanda ake taƙaita shi da kalmar
(MOOCs) Tsangayar tana aiki ne 100% ta Internet, ɗalibai inda
za su iya shiga darussa ta hanyar kwamfuta da na'urori masu
ƙwaƙwalwa, kuma suna iya halartar bitoci ta hanyar darussan da
aka ɗauke su ta hanyar bidiyo da kuma littattafan amfanin na’ura
mai ƙwaƙwalwa, da kuma amsa tambayoyin auna fahimta.

Kuma ta dogara da fitattun malamai masu wa'azi na Ahlus


Sunna Wal Jama’a masu magana da harshen Hausa.

222
Littafin tarihin Annabi ‫ﷺ‬

A maddar Sira: ɗalibi zai nazarci Sirar Annabi ‫ ﷺ‬bakiɗayanta, a


taƙaice, sannan kuma zai karanci ɗabi’un Annabi ‫ﷺ‬, sannan kuma zai tsaya
akan wasu daga cikin abubuwa da yanayin da suka faru a rayuwar Annabi
‫ﷺ‬, a mataki na ƙarshe kuma zai nazarci yanayin ma’amalar Annabi ‫ ﷺ‬tare
da mutane a taƙaice, sannan kuma a kawo kyawawan maganganun malamai
game da abin da ya gabata.

223

You might also like