Professional Documents
Culture Documents
1, Gabatarwa
2, Sadaukarwa
3, Godiya
4,Technical analysis
5,Candlestick
6,Tarihin candlestick
7,Rabe-raben-candlestick
8,Market structures
10,Time Frame
12, Kammalawa
Gabatarwa
Assalamu alaikum
2
Wannan littafi karatune da mukai a class namu na Fx & crypto market, kasancewar karatun yayi
tasiri sosai wajen wayar da kan mutane game da ilimin technical analysis shiyasa muka ga ya
dace ace mun mai dashi PDF saboda al’ummar mu masu tasowa su amfana, sannan mun danyi
gyare-gyare akan yadda kukai karatun hadi da karin wasu abubuwa masu muhimmanci da bamu
kawo su a asalin karatun da kukai ba.
amma saidai wannan ba wai sha-kundum bane game da ilimin technical analysis, a’a mun dan
tsakuro wasu ilimomine da suke tushe na shi technical analysis ɗin, don haka idan ka karanta
wannan kana da bukatar kara fadada bincike domin samun ilimi mai yawa akai.
Rubutawa :
Msky✍️
SADAUKARWA
Na sadaukar da wannan rubutu ga mahaifiyata da fatan Allah ya kai mata ladan, sannan da
bukatar yi mata addu’a daga bakin duk wanda ya karanta wannan littafi Mai albarka.
GODIYA
Godiya ta tabbata ga Allah maɗaukakin sarki mai kowa mai komai da ya bani ikon kammala
wannan rubutu lafiya,
Sannan ina godiya da jinjina ga abokan gwagwarmaya kuma admins namu na Fx& crypto Market
bisa jajircewa da mukai akan jagorancin wannan gida namu mai albarka,
Khamisu Musa
3
Mas’ud King
Oga Rabilu.
Muna fatan Allah ya sanyawa wannan littafi albarka ya zama sanadin wayar da kan al’umar mu
Hausa Fulani game da wannan ilimi na technical analysis
Technical analysis wani ilimi ne da traders kanyi anfani dashi ta hanyar lura da yanayin motsin
farashi a kasuwa,
Ilimin kan bawa mutum dama yai duba ga motsin da kasuwa tai a baya sannan yai lura ga abin da
kasuwa take a halin yanzu, sai yai hasashen me kasuwa zatai a gaba ta hanyar amfani da wasu
ƴan dabaru.
4
CANDLESTICK
Kamar yadda sunansa ya baiyana, Candlstick hotone mai kama da icen kendir wadda ke da
gangar jiki da kuma inuwa, wadda ke haduwa ya bada labarin yanayin halinda da kasuwa take ciki,
Idan nace kasuwa ina nufin kasuwar *Currencys, Coins, commodities, Stock…. And many more*
A sanda aka kirkiri candlestick asalin kalarsa shine fari da baƙi , fari shike kaiwa kasuwa sama,
baki kuma shike kaiwa kasuwa ƙasa.
Daga baya da aka samu cigaba an samar da kala wa candlestick, inda yake Kore da ja, Kore ke
kai kasuwa sama, ja ke kai kasuwa ƙasa,
Duk da cewa a yanzu software na trading musamman Meter trader tana bada dama mutum ya iya
zansa kalar candlestick zuwa kalar da yakeso.
TARIHIN CANDLESTICK
An ƙiƙireshine a japan shekaru daruwa-ruwa da suka gabata, inda suka ƙirƙireshi domin gane
salon cinikayyar shinkafa, wannan tasa ake masa laƙabi da Japanes candlstick patterns.
5
Bayan wani lokaci sai wani mutumin kasashen yamma mai suna *Steve Nison* ya gano sirrin
wannan ilimi da ake kira japanes candlatick, saboda haka ya tsaya ya koyeshi daga wani broker
na japan sannan ya ƙara faɗaɗa bincike akai yai masa kyakkyawar fahimta ya zama ƙwararre akai,
sannan sai ya fara rubuce-rubuce akansa, wanda a sanadiyyar haka wannan ilimi ya bazu a
duniya a 90s, hakan tasa akewa Steve Nison lakabi da Mr candlstick .
RABE-RABEN CANDLSTICK
1, Singe (TILO)
2, Double (TAGWAYE)
Spinning tops
Doji
Marubuzo
Hammer
Hanging Man
Inverted Hammer
Shooting Star
6
Double, ya ƙunshi kendira kamar haka👇
Bullish engulfing
Beariah engulfing
Tweezer topa
Tweezer bottom
Morning stars
Evening stars
Three inside up
Spinning tops
Kendir ne wanda ke da ƙaramin gangar jiki sannan yana da madaidaiciyar inuwa ta sama da kasa
ma’ana ya fidda kai ta sama sannan ya fidda jela ta ƙasa, sannan zakaga da inuwar sama data
ƙasa duk kusan tsawonsu ɗaya.
Spinning tops yana nuni da cewa a halin yanzu kasuwa bata da tabbas ba’asan suwaye keda
rinjaye ba tsakanin masaya da masu siyarwa,
Gangar jikin nasa walau ja ne ko kore na nuni da cewa an samu motsi kaɗan daga sanda kendir
ɗin ya buɗe zuwa sanda ya kulle, wadda inuwoyinsa ke nuni da cewa masaya da masu sayarwa
na gumurzu a tsakaninsu amma ba’a samu wanda yai rinjaye akan ɗaya ba.
7
Ga misalin spinning tops👇
DOJI
Doji kendir ne dake kullewa a wurin da ya buɗe sannan yana da ɗan ƙaramin jiki matuƙa wanda
bai wuce zanen lai ba.
8
Doji yana nuni da cewa an samu artabu sosai tsakanin masaya da masu sayarwa inda masaya
suka turashi sama daga inda ya buɗe amma kuma masu sayarwa suka jawoshi ƙasa da inda ya
buɗe sannan masaya suka sake turashi sama ya dawo ya kulle a inda ya buɗe.
Dan’uwa idan kaga doji ya bayyana to ka kula sosai da abinda ya faru kafinsa, idan doji ya
bayyana bayan jerin kendira da suke nuna kasuwa sama take kamar *White Marubuzo* to dojin
nan na nuna maka cewa masaya sun fara gajiya ana buƙatar agajin gaggawa domin masu
sayarwa na shirin ƙwace kasuwa.
Hakanan idan doji ya bayyana bayan jerin gwanon kendira da suke kai kasuwa ƙasa, kamar *Black
Marubuzo* to wannan dojin nuna maka cewa masu sayarwa sun fara gajiya ana buƙatar agajin
gaggawa domin masaya na shirin ƙwatar kasuwa.
RABE-RABEN DOJI
Gravestone doji
Doji ne da kan iya aukuwa a ko ina walau sama ko ƙasa, wanda keda doguwar inuwa ta sama da
doguwar inuwa ta ƙasa, gangar jikinsa a tsakiya.Wanda yake nuni da irin artabu da akai tsakanin
masaya da masu sayarwa amma duk ƙarfinsu yazo daidai.
9
Wannan shine hoton Long legged doji 👆
Doji ne da yake da ƙaramin kai ta sama da doguwar inuwa ko kuma kace jela a ƙasa shima doji ne
dakan iya aukuwa a ko ina amma yafi bayyana a ƙasa bayan an samu doguwar tafiyar jirgi dake
kai kasuwa ƙasa,
Yana nuni da cewa masu sayarwa sun tura kasuwa ƙasa amma masaya sun turota ta dawo ta
kulle a daidai inda ta buɗe, Hakan na nuni da cewa a halin yanzu masaya na shirin rinjayar masu
saidawa don haka ana kyautata zaton kasuwa zata koma sama.
10
Ga hoton dragon fly doji 👆
GRAVESTONE DOJI
Doji ne da yake da ƙaramin kai ta ƙasa da doguwar inuwa a sama shima yakan iya bayyana a ko
ina amma yafi zuwa a sama bayan an samu doguwar tafiyar jirgi dake kai kasuwa sama, inda yake
nuni da cewa masaya sun tura kasuwa tayi sama amma masu saidawa sun dawo da ita ƙasa ta
kulle a daidai inda ta buɗe.
Hakan na nuni da cewa ƙarfin masaya ya fara ƙarewa yanzu kuma masu saidawa ne zasu karɓi
kasuwa.
11
MARUBUZO
Marubuzo dogon kendir ne mai cikakken gangar jiki, baida inuwa ko kuma da ƴar ƙaramar inuwa.
1, White marubuzu
2, Black marubuzu
12
Ga misalin hoton marubuzu 👇
1 WHITE MARUBUZO
13
White marubuzo wani dogon farin kendir ne mai cikakken gangar jiki wanda ke kai kasuwa sama
amma a yanzu kalarsa korene, inda ya buɗe yana daidai ko kusa da ƙarshen kasan sa, inda ya
kulle yana daidai ko kusa da ƙarshen samansa.
White marubuzo yana budewa ne ta ƙasa ya kulle a sama.Idan kaga white marubuzo ya baiyana
bayan doguwar tafiyar jirgi dake kai kasuwa ƙasa to lallai yana nuna maka cewa a halin yanzu
kasuwa juyawa zatai domin masaya sun ƙwace kasuwa.
2 BLACK MARUBUZO
14
Black marubuzu wani dogon baƙin kendir mai cikakken jiki dake kai kasuwa ƙasa amma a yanzu
kalarsa ja ce, inda ya buɗe yana daidai ko kusa da ƙarshen samansa, inda ya kulle yana daidai ko
kosa da ƙarshen kasansa,
Black marubuzo na budewa ta sama ya kulle a ƙasa, wadda yake nunu da cewa masu sayarwa
sun rinjayi masaya,
Idan kaga black marubuzo ya baiyana bayan doguwar tafiyar jirgi dake kai kasuwa sama to lallai
yana nuna maka cewa a halin yanzu kasuwa juyawa zatai.
HAMMER
15
Hammer wani kendir ne mai matuƙar ƙarfi a kasuwa da yake nuna alamar juyawar kasuwar bayan
doguwar tafiyar jirgi dake kaita ƙasa,
Hammer na da matsakaicin gangar jiki a sama da doguwar jela a ƙasa, walau fari ko ja, indai ya
bayyana a ƙasan doguwar tafiyar jirgi dake kai kasuwa ƙasa ko a a waiwaye (retracement) to lallai
yana nuna maka cewa yanzu kasuwa juyawa zatai, sbd masu sayarwa sun tura kasuwa ƙasane
inda masaya suka dawo da ita ta kulle a sama ko ƙasa kadan da inda ta buɗe.
HANGING MAN
Hanging man wani kendir ne mai kama da hammer amma shi kuma yana baiyyana ne sama,
shima yana bayyana alamun juyawar kasuwa musamman idan ya baiyyana bayan doguwar tafiyar
jirgi dake kai kasuwa sama ko kuma ya bayyana a waiwaye (retracement)..
16
Shima na nuni da cewa bayan kasuwa tai sama masu sayarwa sunyi kokawa da masu saya wajen
ganin sun dawo da kasuwa ƙasa amma masaya suka maida ta sama domin su fita a sama ko ƙasa
kaɗan da inda kendir ɗin ya buɗe,
INVERTED HAMMER
17
Wani kendir ne mai matsakaicin kai a ƙasa da doguwar jela a sama wadda ke bayyana a ƙasa,
yana nuna alamun juyawar kasuwa musamman idan an samu doguwar tafiyar jirgi dake kai
kasuwa ƙasa ko kuma ya bayyana a waiwaye (retracement).
Inverted hammer na nuni da cewa masaya sunyi ƙoƙarin ƙwace kasuwa inda suka turata sama da
inda ta buɗe, amma kuma wani dalili yasa masu sayarwa suka sake dawo da ita ƙasa da inda ta
buɗe, amma duk da haka masaya suka sake jan ɗamara suka turata ta kulle a sama kaɗan da
inda ta buɗe
Shooting star
Shooting star shima kendir ne mai ƙarfi dake nuna alamun juyawar kasuwa, yana bayyana ne a
sama,
18
Shooting star nada matsakaicin kai a ƙasa da doguwar jela a sama wadda ke nuni da cewa
masaya sun tura kasuwa tai sama da inda ta buɗe amma masu sayarwa suka dawo da ita ta kulle
a kasa ko sama kaɗan da inda ta buɗe.
Idan kaga shooting star ya bayyana musamman bayan doguwar tafiyar jirgi dake kai kasuwa sama
to yana nuna maka cewa tafiyar ta ƙare haka yanzu kuma juyawa za’ai.
19
DOUBLE CANDLESTICK (TAGWAYEN KENDIRA)
1, *Bullish engulfing*
2, *Bearish engulfing*
3, *Tweezer tops*
4, *Tweezer bottom*
Bullish engulfing
Bullish engulfing wasu tagwayen kendira ne dake bayyana a ƙasa wadda suke bada alamun
yiwuwar juyawar kasuwa daga ƙasa zuwa sama,
Bullish engulfing yana da matukar tasiri a kasuwa musamman idan ya bayyana bayan doguwar
tafiyar jirgi dake kai kasuwa ƙasa,
Akan sumu karamin jan kendir ne ya fara bayyana a karshen tafiyar jirgi dake kai kasuwa ƙasa,
Sannan sai a samu dogon koren kendir ya bayyana wadda tsawonsa yakai kusan biyun wannan
jan da ya fara bayyana, hakan tasa ake kiransa da bullish engulfing saboda wannan dogon koren
kendir din yayi engulfing din (Rufe) wannan karamin jan kendir din,
Hakan na faruwa ne kasancewar masu sayarwa sun samu riba a kasuwa sosai wadda tasa kowa
ke ɗebe ribarsa ya fita daga kasuwa hakan zai sa masaya su kuma su samu damar shiga kasuwa
da karfin gaske su maida kasuwa ta koma Long position
20
Bearish engulfing
Shi kuma sabanin bullish engulfing yana bayyana ne a sama inda yake nuna yiwuwar juyawar
kasuwa zuwa ƙasa,
Bearish engulfing yana da matukar tasiri shima kamar ɗan’uwansa musamman idan ta bayyana
bayan doguwar tafiyar jirgi dake kai kasuwa sama,
Inda yake nuni da cewa masaya sun fara tattare kayansu tunda su samu riba yayinda masu
sayarwa su kuma zasu shigo kasuwar da ƙarfi su maida ta ta koma short position.
21
Ga misalin bearish engulfing 👇
Tweezer bottom
Wasu tagwayen kendira ne ja da Kore da suke bayyana ya zamanto kansu ɗaya yanayin girman
jikinsu ɗaya sannan wutsiyar suma daya idan masu wutsiyar ne,
Tweezer bottom basa bayyana mafi yawanci sai bayan doguwar tafiyar jirgi sosai dake kai kasuwa
ƙasa,
Idan suka bayyana suna nufin tafiyar da ake yanzu ta ƙare za kuma a juyane.
22
Ga misalin twizzeer bottom 👇
Tweezer tops
Wasu tagwayen kendira ne Kore da ja da suke bayyana a sama ya zamanto kansu ɗaya yanayin
girman jikinsu ɗaya sannan wutsiyar suma daya idan masu wutsiyar ne,
Tweezer tops basa bayyana mafi yawanci sai bayan doguwar tafiyar jirgi sosai dake kai kasuwa
sama,
Idan suka bayyana suna nufin tafiyar da ake yanzu ta ƙare haka za kuma a juyane.
23
TRIPLE CANDLESTICK (YAN'UKU)
Morning stars
Morning stars wasu kendira ne guda uku da suke bayyana a ƙarshen tafiyar jirgi dake kai kasuwa
kasa ko a karshen waiwaye (retracement), wadda ke nuna cewa yanzu kasuwa zata juya,
24
1, kendir ɗin farko ya zamanto jan kendir ne wadda yana daga cikin jerangiyar tafiyar jirgi zuwa
ƙasa,
2, kendir na biyu ya zamanto mai ƙaramin gangar jiki walau ja ne ko kore, wadda yake nuna rashin
tabbas na kasuwa
3, kendir na uku ya zamanto koren kendir wadda tsawonsa yakai ko kusa da daidai inda kendir ɗin
farko ya bude, wadda yake nuna cewa yanzu kasuwa ta koma hannun masaya.
Evening stars
Evening stars shima kamar dan’uwansa wasu kendira ne guda uku da suke bayyana a ƙarshen
tafiyar jirgi dake kai kasuwa sama ko a karshen waiwaye (retracement), wadda ke nuna cewa
yanzu kasuwa zata juya,
1, kendir ɗin farko ya zamanto koren kendir ne wadda yana daga cikin jerangiyar tafiyar jirgi zuwa
samaa,
25
2, kendir na biyu ya zamanto mai ƙaramin gangar jiki walau ja ne ko kore, wadda yake nuna rashin
tabbas na kasuwa
3, kendir na uku ya zamanto jan kendir wadda tsawonsa yakai ko kusa da daidai inda kendir ɗin
farko ya bude, wadda yake nuna cewa yanzu kasuwa ta koma hannun masu sayarwa.
Three white soldiers wasu kendira ne yan uku dake bayyana a karshen tafiyar jirgi dake kai
kasuwa ƙasa, wadda ke nuni da cewa tabbas yanzu kasuwa ta juya sama,
Three white soldiers suna daga cikin alamu mafiya ƙarfi dake tabbatar da cewa yanzu fa kasuwa
ta juya, musamman idan sun bayyana bayan doguwar tafiyar jirgi dake kai kasuwa ƙasa Sannan
aka samu consolidation kaɗan, Sannan kuma yafi bayyana a reversal.
Three white soldiers ba zasu zama abin luraba sai ya kasance sun bayyana alamomi kamar haka
26
1, kendir din farko ya zama Kore mai cikakken gangar jiki, wadda baida wutsiya, ko kuma akwai
amma yar karama matuka,
2 kendir na biyu shima ya zamo Kore sannan ya zamto yafi kendir din farko tsawo kuma ya
zamanto baida wutsiya ko kuma akwai amma ƙarama matuka.
3, kendir na uku ya zamanto Kore shima, sannan tsawonsa yakai ko yafi kendir na biyu, sannan ya
zamo baida ko kuma yar karamar wutsiya.
27
Three black crows wasu kendira ne yan uku dake bayyana a karshen tafiyar jirgi dake kai kasuwa
sama, wadda ke nuni da cewa tabbas yanzu kasuwa ta juya kasaa,
Three black crows suna daga cikin alamu mafiya ƙarfi dake tabbatar da cewa yanzu fa kasuwa ta
juya, musamman idan sun bayyana bayan doguwar tafiyar jirgi dake kai kasuwa sama Sannan aka
samu consolidation kaɗan, sannan kuma yafi bayyana a reversal.
Three black crows ba zasu zama abin luraba sai ya kasance sun bayyana alamomi kamar haka
1, kendir din farko ya zama ja mai jikakken gangar jiki, wadda baida wutsiya, ko kuma akwai amma
yar karama matuka,
2 kendir na biyu shima ya zamo ja sannan ya zamto yafi kendir din farko tsawo kuma ya zamanto
baida wutsiya ko kuma akwai amma ƙarama matuka.
3, kendir na uku ya zamanto ja shima, sannan tsawonsa yakai ko yafi kendir na biyu, sannan ya
zamo baida ko kuma yar karama wutsiya.
28
Ga misalin Three Black crows👇
Three inside down wasu kendira ne guda Uku da suke bayyana a kasa, bayan anyi tafiyar jirgi
dake kai kasuwa ƙasa,
Three inside down na nuna cewa tafiyar da ake a yanzu ta ƙare za kuma a juyane.
Three inside up, bazai zama abin luraba sai ya samar da abubuwa kamar haka.
29
2, sannan na biyu ya zama koren marubuzo matsakaici wadda dole ya zamo tsawonsa ya kai
tsakiyar kendir din farko.
3, kendir na uku ya zamanto koren marubuzo ne wadda dole ya zamto mai tsawo da ya kasance
ya kulle a ƙasa da inda kendir din farko ya buɗe.
Three inside up
Three inside up wasu kendira ne guda Uku da suke bayyana a sama, bayan anyi tafiyar jirgi dake
kai kasuwa sama,
Three inside up na nuna cewa tafiyar da ake a yanzu ta ƙare za kuma a juyane.
Three inside up, bazai zama abin luraba sai ya samar da abubuwa kamar haka.
30
2, sannan na biyu ya zama jan marubuzo matsakaici wadda dole ya zamo tsawonsa ya kai
tsakiyar kendir din farko.
3, kendir na uku ya zamanto jan marubuzo ne wadda dole ya zamto mai tsawo da ya kasance ya
kulle a sama da inda kendir din farko ya buɗe.
MARKET STRUCTURE*
Ma’ana ilimi da zai baka dama ka fahimci wanne irin motsi kasuwa ke gudanarwa.
31
Ranging market (Jeka-ka-dawo)
Trending market
Idan akace kasuwa na trending, ana nufin cewa kasuwa na tafiya a bigere daya, ma’ana tana
tafiya zuwa inda tasa gaba.
Uptrend
Downtrend
Uptrend
32
Uptrend shi ake nufi da upward, ana nufin idan kasuwa na tafiya zuwa sama a wani irin salo da
zamuyi bayani
Kasuwa na yin impulsive sannan sai ta dawo tai retracement sannan ta sake impulsive, ma’ana
zatai sama (impulsive) saita dan dawo kasa kadan (retracement)
Haka zatai tayi har tai doguwar tafiya, iya inda masu juya kasuwar suka ga damar Kaita.
Downtrend
Downtrend shi ake nufi da Downward, ana nufin idan kasuwa na tafiya zuwa kasa.
Kasuwa na yin impulsive sannan sai ta dawo tai retracement sannan ta sake impulsive, ma’ana
zatai ƙasa (impulsive) sai ta dawo sama kadan (impulsive) sai ta cigaba da yin ƙasa (impulsive)
Haka zatai tayi har tai doguwar tafiya, iya inda masu juya kasuwar suka ga damar Kaita.
https://youtu.be/SI6aRacoflU
33
Ranging Market (Jeka-ka-dawo)
Ranging Market shi ake kira da Sideway Market ma’ana wani yanayin motsine na kasuwa wadda
take yawo a tsakanin wani support da Resistance.
Kasuwa kan je kasa ta taɓa ko ta kusa taɓa wani support sannan ta tashi zuwa sama taje jikin
wani resistance ko kusa da shi sannan ta sake dawowa ƙasa,
Idan aka samu kasuwa tayi irin wannan motsin na tsawon lokaci to shi ake kira da Ranging
Market.
Ga link da zai kaika video totorial da yake karin bayani akan Ranging Market 👇
https://youtu.be/p5GWel7CPvE
Choppy market na faruwa saboda karanci volume ko kace liquidity a kasuwa, kasancewar babu
mutane da yawa sun zare kudinsu basa trading a wannan Lokacin, sai kaga kasuwa na yawo a
wuri guda tana fidda wasu kananun kendira, wadda ko ka shiga trading saidai ka bata lokaci baka
samu wata riba ba, shiyasa masana suka ce ba’a trading a indecision market.
34
Ga Link na video totorial da yake bayani akan choppy Market 👇
https://youtu.be/sgrxqJ1urus
Support
Support wani bigire ne a ƙasa wadda kasuwa ke girmamawa, wurine da idan kasuwa tazo ko tai
kusa dashi take juyawa ta koma sama, zatai ta yin haka har a samu lokacin da zata karya support
din kuma tai ƙasa dashi.
Support ya zama wurine dake juya akalar kasuwa saboda kamar yadda mukai bayani a baya
cewa Kasuwa na maimaita abinda take shiyasa idan kasuwa tazo wuri ta juya; traders kai ko Ni ko
shi ke zuba ido muga kasuwa ta sake dawowa wurin domin mu shiga trade din a daidai wannan
wurin sbd mun san cewa _tarihi na maimaita kansa_ hakan tasa dole kasuwa indai tazo wurin
saita sake tashi.
35
Ga misalin support da resistance 👇
Resistance
Resistance shi kuma kishiya ne na support, wani bigire ne a sama wadda kasuwa ke girmamawa,
wurine da idan kasuwa tazo ko tai kusa dashi take juyawa ta koma ƙasa, zatai ta yin haka har a
samu lokacin da zata karya Resistance din kuma tai sama dashi.
Resistance ya zama wurine dake juya akalar kasuwa saboda kamar yadda mukai bayani a baya
cewa _Kasuwa na maimaita abinda take_ shiyasa idan kasuwa tazo wuri ta juya traders kai ko Ni
ko shi ke zuba ido muga kasuwa ta sake dawowa wurin domin mu siyar da abin da muke rike
dashi a daidai wannan wurin sbd mun san cewa _tarihi na maimaita kansa_ hakan tasa dole
kasuwa indai tazo wurin saita sake faduwa.
Sannan akan iya samun support ko Resistance mai ƙarfi da mai rauni
36
Ga misalin support da resistance 👇
Horizontal support
Horizontal Resistance
Dynamic support
Dynamic Resistance
37
Horizontal support
Shine mikakken support wanda zaka iya zana layinsa a kwance, a mike
Horizontal Resistance
Shine mikakken Resistance wanda zaka iya zana layinsa a kwance, a mike
Dynamic support
Shi kuma shine wanda ke samuwa a jirkiɗe, ma’ana zaka zana layinsa a jirkiɗe ne
Dynamic Resistance
Shi kuma shine wanda ke samuwa a jirkiɗe, ma’ana zaka zana layinsa a jirkiɗe ne
Ga link na video totorial da yake karin bayani akan support and resistance 👇
38
https://youtu.be/xDHLGuWoSkI
Time Frame
A kasuwar kudi (financial Market) an tsara yanayin bayyanar kendir gorgodon time Frame da
mutum ya saita, ya danganta da wanne irin trader ne Mutum.
Time Frame yana da matukar muhimmanci saninsa saboda hakan zai baka kyakkyawar fahimtar a
wanne yanayi kasuwa take ciki sannan wanne yanayin zata iya shiga nan gaba.
*Longer time frame* sune time frame masu tsawo, wadda idan aka haifi kendir yakan dade kafin
ya kulle,
MN1 (Monthly)
W1 (Weekly)
D1 (Daily)
MN1 shine time Frame da idan kendir ya bayyana saiya kai wata guda kafin ya kulle.
W1 shine wadda idan ya fito sai ya kai sati guda kafin ya kulle
39
D1 shine wadda idan ya fito sai yayi 24 hours sannan ya kulle.
Shine tsaka-tsaki wadda idan kendir ya fito baya dadewa sosai zai kulle a sake haifar wani,
H8
H4
H1
H8 ba a kowanne platform ake samun sa ba amma shima time frame ne da idan kendir ya fito sai
yayi awa takwas yake kullewa
H4 shi kuma idan kendir ya fito sai yayi awa hudu yake kullewa.
Mafiya yawancin swing traders da day traders suna amfani da wadannan time frame ne
*Shorter time frame* sune idan kendir ya fito baya dadewa zai kulle a sake haifar wani
15M
5M
1M
15M shine wadda idan kendir ya fito daga yayi minti sha biyar sai ya kulle
40
1M shine wadda daga yayi minti ɗaya wato second sittin zai kulle a sake haifar wani.
https://youtu.be/_SKWrDFxC5Q
Wannan shine karshen karatun da mukai alkawarin koyarwa a wannan gida mai albarka
A wannan babi zan bada wasu shawarwari masu matukar karfi a kasuwa wadda idan ka bishi sau
da Kafa inshallah 85% na trading naka zai zama cikin Nasara, muddin kana amfani da money and
risk management mai kyau.
Da farko abinda zaka fara yi shine ka samarwar kanka trading style (salon trading) da ya dace da
kai gwargwadon yanayin opportunity naka da kuma irin emotions da kake dashi,
Ma’ana kasan cewa kai wanne irin trader ne, shin scalper ne kai ko a day trader ko swing trader ne
ko kuwa kai position trader ne,
1, Idan ka tashi analysis ya kasance zakai analysis a time frame na sama da wadda kake trading
(entery da exit).
2, ka duba salon tafiyar da kasuwa take a time frame din sama da wadda kake trading dashi, shin
trending take koko Ranging koko choppy take.
3, shin tafiya take zuwa inda ta nufa (impulsive) koko waiwaye take (Retracement).
4, shin taje jikin support ko resistance, koko tana demand zone ko supply ne.
5, idan kasuwa na uptrend ne to ka jirata tai retracement wadda dole zata dan dawo jikin wani
support, bayan ta dawo jikin support saika koma karamin time frame kaga wanne irin candlestick ta
fitar, idan aka samu wani candle da yake nuna cewa kasuwa sama zatai kamar Hammer ko bullish
engulfing ko morning stars kawai ka shiga trade ɗin,
41
Hakan kuma idan kasuwa tana downtrend ne vise-versa.
6, idan kuma kasuwa tana Ranging ne to ka jira kasuwa taje jikin support ko resistance a babban
time frame sannan saika dawo karamin time frame ka duba candlestick pattern ka jira ka samu
confirmation candle saika shiga trade ɗin,
7, ana sanya SL a kasa da candlestick pattern da aka shiga da kamar tazarar pips goma ko
ashirin,
8, Zan baka shawara, ya kasance kake shiga trading yayin da ka samu confirmation na Hammer
ida kasuwa faduwa tai da shooting star idan kasuwa tashi tai ko bullish engulfing da bearish
engulfing ko morning stars and evening Stars. Wadannan pattern 3 suna da tasiri sosai.
9, idan kai position trader ne zakai Analysis naka a monthly time frame, ka dawo weekly ko daily
ka nemi entery, idan kuma swing trader ne zakai Analysis naka a weekly TF ka dawo daily ko H4
ka nemi entery, idan kai a day trader ne zakai Analysis naka a daily TF ka dawo H4 ko H1 ka nemi
entery idan kai scalper ne zakai Analysis naka a H4 ka dawo 15 minute ko 5 minute ka nemi
entery.
10, ka tabbata kana da target a kowanne trading da ka shiga; sannan idan ka kai target naka ka
fita a trade ɗin.
12, ka tabbata kana trading ne yayin da ka samu confirmation, ba’a gaggawa a trading,
13, ka tabbatar kana trading da abinda bazai tada hankalin ba yayin da ka samu wata asara a ciki.
Kammalawa
Ina sake sanar da kai dan’uwacewa wannan littafin ya ɗan tsakura kadan daga ilimin tantance
kasuwa ne bal ma zan iya cewa abin da ya kunsa bazai wuce 25% na ilimin financial Market ba
42
don haka duk wanda yake son ya shiga makarantar da muke koyarwa Ga ko yake son magana
dani zai iya tuntuɓata ta wannan hanyar da zan aje a ƙasa.
Idan ka shiga makarantar anan ne zamu fara maka karatu tun daga tushe har zuwa sama hadi da
baka shawararwarin da dabarun trading, yadda kaina zaka zama trader mai cikakken yanci
inshallah. Amma saidai kafin ka shiga don zaka biya kudin registration.
MbrSky01@gmail.com
+2349032721310
Muna rokon Allah ya bamu Lada ya kuma taimake mu a wannan harka ya kara fahimtar damu da
hanyoyin samun nasara a cikin ta.
Sannan ina batar addu’aga duk wadda ya karanta littafin nan yai wa mahaifiyata addu’a,
Allah Ubangiji ya kara kai haske kabarinta ya sanya farin ciki da jindadi a kabarin sannan ya sanya
ta a gidan aljanna, muma idan tamu mutuwar yazo yasa muyi mutuwa mai sauki da dadi irin Tata
yasa kuma mu cika da imani 🤲
Msky ✍️
43