0% found this document useful (0 votes)
2K views290 pages

KUTKULE

The document is a promotional piece for a novel titled 'Kutkale' by Sajida, which explores themes of prison life and personal struggles. It includes a narrative excerpt that depicts intense and dramatic scenes involving characters in a prison setting. The author invites readers to purchase the novel and join a group for further engagement.
Copyright
© © All Rights Reserved
We take content rights seriously. If you suspect this is your content, claim it here.
Available Formats
Download as DOC, PDF, TXT or read online on Scribd
0% found this document useful (0 votes)
2K views290 pages

KUTKULE

The document is a promotional piece for a novel titled 'Kutkale' by Sajida, which explores themes of prison life and personal struggles. It includes a narrative excerpt that depicts intense and dramatic scenes involving characters in a prison setting. The author invites readers to purchase the novel and join a group for further engagement.
Copyright
© © All Rights Reserved
We take content rights seriously. If you suspect this is your content, claim it here.
Available Formats
Download as DOC, PDF, TXT or read online on Scribd

*KUTKALE*

*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct
NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan
number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA, ZAKU
YI MIN ENVOI NA DALA DARI BISA NUMERO KAMAR HAKA 92777744 AMAN FA TA ORANGE
MONEY.....* taku ce, Sajida😍😍😍😍

1️⃣

*Free page*

Kwonce take, inda aka gama jibgarta dan ta yiwa Eliz gardama, wani bacin wahala ne ya kwashe ta,
kamar a mafarki take ji ana damkarta, a hankali abin ya fara shigarta har ta gane da gaske ne, lalubarta ake,
hannu ne..sanda ce...kafa ce? Kai koma menene wannan mai tauri ne, kuma so yake sai ya shige cikin
jikinta da ko yar karamar yatsarta bata shiga dan tsabar matsewa da rufewa,
Kara cusa abin aka yi cikin dadaudan kuma tsantsaman bujenta dake kankabare tsabar dati wanda shi kadai
ne jikinta ko pant bata da shi , wato dai hanya ba kofa a bude ham ,
Idannuwanta ta bude da kyar, wulik wulik ta yi da su inda ta sauke su saman mai kokarin sai ya kai mata,
Cinyoyinta ta gama ta hade da dukan karfinta, sannan ta budi bakinta dake rawa ta kwala wani kara ln da ya
saka sojan dake gadinsu ji aman kememe bashi da jiyar kitsawa bale ya leko ya ga abinda ke faruwa har ta
saka ran za.a ceceta,
Ihun take yi tana kokarin kwatar kanta, inda idannuwanta suka sauka kan abinda yake so ya tura mata,
Baka kirin, bata da wata sadawa a tare da ita, bata da wani kyan da zai ja ra.ayin mutun, dunkuleliya ce yar
lukuta, kanta kansa baki kirin da shi bale sauran jikin, wani irin cukurkuraran dadaudan hashi ne jikinta
wanda ya saka ta jin amai ya zo mata,
Kafarta ta saka ta hambare shi, Ba kowa bane sai Usman! USMAN dake gidan kason dalilin kashe
kanwarsa da ya yi ta hanyar yi mata fyade,
Hantsilawa ta yi kafin ta warto wani ice dake ajiye nan yashe a wajen ta nuna masa tana ihu tana magana
kamar haka" walahi ka matso inda nake sai na ilata ka, sai na caka maka a jikin wannan abin, ka matso ni
sai na huda maka makoshi,

Mikewa ya yi, gaba dayansa bashida wani tsayin kirki ya dubeta ya girgije irin tashin balagar iskancin nan,
ya kuwa nufota da karfinsa,

Icen hannunta ya fara damka ya rike, ya fizge shi suka aniya kokowa inda ya kai hannunsa ya matsi
mamanta dake cikin farar rigar da tsabar dati ya sa ta koma maroon mai duhu,
Ai kuwa zafin ya saka ta bura ta makalkale masa wuya ta kai cizo wajen kunnensa ta rike taf ,
Ihu ya saka ya bugata da garu, ya damko cukwuikuyayen gashin kanta da kitson ya tsufa har ya dadake ya
ja da karfin tsiya ko zata saki,
Aman karfin hali da zuciya ya sa ta ki saki saima ji da ta yi kamar ta suma , suda haka ta kara damke shi
suna ta hajijiya a wajen inda ihunsa ya sa matan wajen firfitowa dan kuwa wajen mata ne, cikin gidan mata
ne, ba.a hada maza da mata ko wajen cin abinci, jin muryar gardi yana ihu ya saka du suka fito suna kallon
ikon Allah sai dambatuwa suke aman ba wanda ya gigin zuwa bale har ya raba, saima ihun da suke suna
murna an samu abun nishadi,

Jin hayaniyar na kara yawa, wajen na kara daukan harama ya mike ya yiwa yan uwansa magana dake dora
shayi biyu suka taso suka bi bayansa suka shiga ciki wajen matan dan gannin abinda ke faruwa,

Gaba dayansu tsayuwa suka yi da mamakin wannan yarinya,


Ko su yi kiranta jarababiya, gari bai taba wayewa dare ya yi ba.a dambatu da ita a gidan yarin ba,
Ta kasance mai yawan kuka da zama waje daya ita daya, su kuwa yan zaman gidan yarin suce ba zasu
dauki haka ba sai sun shiga huruminta, ai kuwa a kama cin kan juna tamkar za.a kashe juna,

Banban cikin sojawan ne ya je ya daga abin dukan dake hannunsa na karfe wanda ake dannawa ya kara
tsayi ya shiga tafka masu ba ji ba gani, inda masu kallon suka fara fita a guje sakamakon suma biyun suka
rufta masu da dukan suka kora su ciki ,

Ai ba shiri ta diro daga wuyansa tana sosa bayanta tana tsalen azaba,
Shima da gudu ya so tserewa sai dai sukai raf da shi suka rike shi,
Sojan nan ne ya ce" kai, uban me ka zo yi wannan wajen a wannan lokacin? Mtsss ba wannan bama ta ina
ka shigo? Shi ne damuwana, dan kuwa ko me ka zo yi can ta matse maku, mai yiwuwa karuwarka ce ta
rincabe maku ana tsakar harka,

Kafin ya bashi amsa ta dago daga tsalen da take ta daga kafarta mai sanye da takalmin fulani irin kafa cikin
nan ya kasance ya rufe mata kafar wanda ba dare ba rana shi ne a kafarta ta rufe ido ta kaiwa wannan sojan
duka a wajen al.aurarsa,
Ihu ya saka ya rike wajen ya kai kasa yana ihu, inda ta budi baki ta ce" ba karuwarsa ba dai, sai ubanka!

Wai wai masifa, ido suka zaro baki dayansu, harda Usman din, a fili ya ce" wannan kin fi karfina, yau zaki
ci ubanki,
Bai kai ga rufe bakinsa ba ya ga mazan nan biyu sun rufa mata sun shiga kwalo da ita ba ji ba gani, inda
abokinsu ke yashe cikin mumunan hali, kuka yake yi da girmansa yana rike da wajen da ta daka yana juya
kai , a hankali ya fara fita daga hayacinsa har ya sume domin ciwon hauhawa yake har ya tainke masa
numfashinsa,
Dukanta suke tun tana tarewa har ta kai kasa, suka kara rufar mata ba ji ba gani, sai da suka tabatar da ba
zata anfanu ba suka barta nan yashe wajen tarin shirgin datin wajen sannan suka ankara da halin da abokin
aikinsu ya shiga,
Ba shiri suka kinkeme shi suna ihun a tada mota suka nufi *MAIKILAGO* dan su kaishi asibitin sojoji a
duba shi,

Sume take , har wajen karfe biyar na asuba,

Kakayatun mutane har ya karade gidan, wasu sun farka dan gabatar da sallar asuba ne, wasu dan su lalaba
daidai lokacin da masun salar suka tafi yi su sace dan abinda sukai sake suka bari, wasu hatsaniyar suka
tashi kallo dan kuwa a ajiye take sai an dambatu da wani, wasu sun farka ne dan su yi mankas abinsu da
kwayoyin mayen da ake shigo masu ta hanyar boye suna siyar da kayansu, kai abubuwan dai kowa da
wanda ya karbe shi,
A haka Eliz ta samu wani dan gora ta duka ta yi fitsari a ciki, ta zo ta tsirara mata a fuska da jikinta,

A kidime ta farka tana zaro ido tana kale kale, idannuwanta suka sabka saman Eliz dake tsaye kanta,
Eliz ta yarda goron tana dubanta ta ce" ke *AISHA, SA.ADATU, FATIMATA, RUKAYA, AMINA,* ke dai
kika san sunnanki mai sunnaye diyawa kamar karuwar Lybia, tashi banza safiya ta yi za.a shiga surfe!

Sai da ta daidaita lumfarfashin da take kafin ta bi jikinta da kallo, du sun ji mata ciwo, bama fuskarta du
sun kumbura mata gefen ido ne, baki ne, ita dai halitarta suka canza mata a dan kankannin lokaci,

Rarafawa ta yi ta karasa kusan tsohuwar dake taimaka mata da ruwa ,


Tana zuwa kuwa tsohuwar ta kare mata kallo,
Kanta kawai ta girgiza ta mike daga alwalar da take ta kwonce canji a bakin zaninta ta je wajen wanda ya
siyar mata da ruwan ta karbo wani ruwan ta kawo ta mikwa mata sannan ta juya ta tafi dan gabatar da
sallah,

Jikinta na rawa ta fara kuskure bakinta ta sha ruwan sannan ta dadarwaye jikinta, nan wajen dai ta samu ta
kare gabanta ta yi tsarki, ta kara wanwanke inda fitsarin Eliz ya taba sannan da dan sauran ruwan ta yi
alwallah ta fito ta nufi ciki inda kowa ke binta da kallo sunai mata dariyar shakiyanci da nunata suna
kiranta jaka dan kuwa ta zama jakar zama daketa ne a kulun ya fi a kirga,

Salla ta gabatar a nitse, duda suturar jikinta bata da nutsuwar,


Tana gamawa ta daga hannunta sama ta shiga karanta rabanoni,
Ba ruwanta da yanda wasu ke kallonta , ba ruwanta da kyamar da suke nunawa adininta, domin diyawa
basu da adini ma ,
Sai da ta gama a fili sannan ta shiga adu.a a zuciyarta kamar haka" Allah, ka yafe min, ya Allah ka yafe
min, ya Allah ka wanke ni, Allah ka rufa min asiri kar na komawa iyayena da tabon gidan kaso, ya Allah
kar ka basu ikon cin mini, ya Allah ka shiryar da du wani mai irin halina, kar ya tsinci kansa a irin rayuwar
da na tsonci kaina a ciki,
KUTKALE ko fita ka yi dan guduwa baka da hanyar bi bale ka kai kanka gida, Kutkale gidan kason masu
mumunan laifi, yai gani cikinsa, ban kashe ba, ban birne ba, ban ci kudin wani ba, na tainci kaina ciki
sanadiyar rashin jin maganar iyayena,
Sai da ta nisa kafin ta ce *Mijin da suka aura mini*, Ya Allah ka..........
Bata karasa adu.ar ba ta ji an doke hannunta, cikin hargagi ta ce" dan ubanki jiya ki rasa wanda zaki bi sai
Usman? Du mazan gidan nan ki rasa wanda zai zaga da ke sai saurayina? Shigiya mai fata kamar ta
bunsurun dan akuya! Usman ya fi karfin uwarkima ba ke ba!

Hannunta ta kuma dagawa ta karasa adu.arta da gagawa ta shafa, daidai lokacin ta fincike mata dan rufar
kan nata da ta yi salar da shi,

Mikewa ta yi da sauri ta warce abin, domin shi kadai ne da ita da shi take sallah,
Wurgawa tsohuwar nan dake girgiza mata kai ta yi , bata tsaya wata wata ba, bata dubi irin raunin jikinta
ba, bata karya ba, daman jiya ta kwonta bata ji ba, ta ja tirjiya kafin ta yi ciki da abokiyar fadan nata suka je
kiiiii suka fada cikin tabo da kwatar dake wajen......
*WACECE WANNAN?*
*ME YA KAWOTA PRISON?*

MENENE MAKOMARTA?

KU BIYO NI, DAN JIN ME KUTKALE YA KUMSA?


*KUTKALE*

*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct
NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan
number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA, ZAKU
YI MIN ENVOI NA DALA DARI BISA NUMERO KAMAR HAKA 92777744 AMAN FA TA ORANGE
MONEY.....* taku ce, Sajida😍😍😍😍

2️⃣

*Free page*
Ita ce *HASANA, HUSAINA, NADIA, AMINA, FATUMA, MARDIYA, AISHA, LAURATU,
HINDATU,......ETC* an haifeta a shekarar januarry ranar da aka yiwa shugaban kasa cou d'eta (wato aka
sauke shi daga saman kujerarsa ta karfi da yaji ta hanyar kashe shi), a tsakiyar dare aka haifeta, daidai
lokacin da kasuwar garin ta kama da wuta du wasu manya manyan shaguna suka kama da wuta,
Gari ya hargitse da iface iface, da rudu, da tsoro, da tashin hankali, a lokacin mahaifiyarta ta kama kafar
gado ta duka tana girgiza kai bayan ta sha rubutun da mijinta maman malami, mai daraja, mai amana kuma
gagarumin dan kasuwa, mai neman na kansa, mai kudi atajiri daidai gwargwado, mai tarin mutane ya
rubuta mata ya bata yana kokarin saka babar rigarsa dan ya sadata da asibitin da take aiki a karbi
haihuwarta sai dai ji ya yi ta ce " Malan, kai fa ya bado,

Ido ya zaro yana duban yannayin tsugunnin da ta yi, jikinsa ne ya dauki rawa yana dubanta, matansa hudu,
sai dai an samu akasin ba wace ke gidan a daidai lokacin du sun tafi wajen rasuwa can garin iyayen
amaryarsa sun je da niyar kwana ne, sai uta da bata bi su ba dalilin cikinta haihuwa yau ko gobe,

Diriricewa ya yi, du kuwa da irin tarin iliminsa da nutsuwarsa,


Sai da ta rintse ido ta figi magana da kyar ta ce da shi" malan ka nutsu dan Allah, ka bani fillow ka kama ni
na dora gwuiwoyina, ka tare min abinda ke cikina kar ya fadi a kasa,

Da sauri ya juya ya dauko, ya yi mata yanda ta ce, sannan ya koma daga bayanta yana ta tofa mata adu.a, a
hankali ya rike yarinyar tana nisawa har kafadunta suka fito bayan badowar kan sannan gaba daya ta yo
waje tare da uwar gaba daya suka fito,
Zaren cibi ya nanade mata wuya sosai, dan haka cikin hikima ya samu ya warware mata sannan ya auna da
yatsarsa ya yanke cibin inda ya mike ya ajiyeta bakin bed yana mai duban yanda bata yi kuka ba, kuma
idanjuwanta ruf a rufe tamkar makauniya,
Bai fadawa mahaifiyarta ba ya kamata ya rakata bayi kafin ya dawo yana duban wajen yanda ya yi kaca
kaca da jini da kuma ruqan haihuwa ga karni baki daya ya cika dakin,

A hankali ta zauna cikin katon bahon wankan mijin nata ta nutsu cikin ruwan masu mugun zafi ta daure ta
cije ta lume ciki ta gasa kanta da kyau da kyau, sannan ta samu dan karfi ta kwararar da ruwan ta tara wani
ta zubo a roba, inda ta zauna ta saka hannunta na dama dan daidaita ruwan wankan kar ya kone jaririyar,
domin hannun hagu nada juriya a zafi fiye da hannun dama shi yasa ake aunawa da na daman , idan har
hannunka ya zauna to ba wani aibu ana iya saka yaro a wankeshi tsaf,
Fitowa ta yi da ruwan, nan ta saki murmushi sanadiyar gannin mijin nata na ta kokarin tatara wajen da ya
zama uwa dakin haihuwa dan kuwa haihuwa ai ba abin wasa ba, aman bawan Allah ya kasa,

Ruwan ta ajiye tana dubansa kafin ta dago yarinyar,


Tsura mata ido ta yi, gata dai tamkar gawa, lumfashin da take ne kawai zai hana a kirata da gawa,
idannuwanta rufe ruf suke, hannayanta jimke kafafuwanta na yawo,
Dubanta ta kai wajen mijin nata, gannin haka ya saka shi ajiye abinda yake ya karaso wajenta ,

Kallon rarashi ya yi mata kafin ya karbi yar jaririyar ya danata cikin ruwan zafin,
Wato reaction din da ta yi kadan ya saketa ta sha ruwan nan , sai dai kasancewarsa namiji, kuma mai adu.a
sai ya tsurawa halitar Allah ido,
Firit ta bude idannuwanta sannan ta kwala wani ihun kuka, wai du wannan shagalin da aka sha ta shigo
duniya ita baci take, iskar duniya bata tasheta ba, kakainiyar iyayenta bai tashe ta ba, sai fatar jikinta da ta
dandani zafin ruwa ya farkar da ita a firgice, yar jaririya haihuwar yanzu ta kwala kukan wahala ,

Ido suka tsura mata, tsagar idannuwanta radau da kwali, tamkar a lokacin aka zana mata kwali a idon,
gashin idannuwanta kuwa har sun lalakwasa baya sannan bakake sidik,
Fatar jikinta haske tau irin na jarirai sabuwar haihuwa, yan lubunanta jajaye da su sai hadewa suke
sanadiyar kukan da take, hancinta kuwa, koda jaririya ce tsaf da karan hanci da tsayinsa,
Tabarikkalah, Alhamdulilah, masha Allah, Allah ya yi maku albarka, Allah ya raya *Uwata*
Shi ne abinda malan ya fada kafin ya mika mata ita ta ci gaba da wanketa,

Malan ya fada da babar murya cewa *bai taba haihuwar yaro ko yarinyar da ta yi goshi kamar UWATA ba,
hasalima arzikinsa kara bunkasa ya yi a daidai lokacin da ta fado duniya, dan kuwa kafin gari ya waye kira
uku ya samu na kwongila na hanyar halal, kuma wutar kasuwa ta ci shagon gefe da gefensa aman bata taba
ko zaren cikin shagwonsa ba*

Ta tashi da wani irin kuka, ba dare ba rana makokiya ce, tun tana yar jaririyarta tsayayiya ce, kaya sai
wanda ya yi mata take yarda a saka mata,
Sai kuma wata baiwa ta Allah, shekara goma ta sauke alkur.ani mai girma, ta yi harda a sha daya,
Karatun boko tsalaketa kawai ake, dan kuwa ilimi kamar me, kulun mahaifinta hankalinsa tashe yake kanta
dan kaf gidan ba mai irin wannan baiwa, har gari an dauka, musabaka du shekara sai ta je yar yarinya da ita
ta kayar da manya,
Mahaifinta tsaye kanta kan adu.o.i na tsari, tsaye kanta kan tarbiyarta, mahaifiyarta kuwa tsoron lamarinta
take, dan bata taba barin ta kwana ba, koda yan uwanta ciki guda bale na waje, idan ta fita a ajiye take sai
an kawo kararta , an dasa mata mujiya a anguwa da irin girman idannuwanta da tsagerancinta,
A haka ta kai shekara goma sha shida,
Gidansu ba.a fita sai ta kama, aman ita ko ta katanga ne sai ta haura ta fece abinta, walahi ko yan anguwa
dadaya suka san asalin sunnanta domin fatiyar masalaci ya yi, sai karfe goma ya yo taron aminnan arziki da
yan kasuwa da yan siyasa,
*UWATA* du yawanci haka ake kiranta, domin Uwar Malan, Uwar kowa ce, sunnan uwar malan din kuwa
ba kowa ya sani ba sai na jikin malan, wa.inda ko bayan ran malan ba zasu yi garajen kama sunnan ba,

Tana tafka tsiyarta, tana shagalinta , du irin tsaron mahaifinta a haka ta fara soyaya da yaro nan cikin
anguwar mai suna Abdul Karim, ,
Abdul Karim kam dan baba da rai ne, motarsa biyu, yaro karami da shi aman idan ka ga abubuwan da yake
yi sai hankalinka ya tashi kai mai hankalin fa nake nufi, domin marar hangen nesa lamarin birge shi zai yi,
Yarinya yar dagwas, tunda ya ganta sai da ya koya mata son sa, suke soyayrsu a haka har ya koya mata
zuwa gidan rawa, a hankali ya kara fetsarar da ita, yar maganar mahaifiyar tata da take ji ta fasa ji, ya koya
mata fada tamkar karya, bata ji bata gani, ga kirtawa samari rashin mutunci, ko kai dan waye zata zabga
maka rashin mutunci ta yi gaba, haka idan aka ce yau ana marche ( fitowar da dalibai ke yi su yi ta kone
kone a gari, ko mutanen gari dan nunawa gwamnati wani abinda ta yi bai yi masu ba) zaka ganta tsamo
tsamo a ciki, an sha a kwashe su harda ita a kai a rufe sai dai bata taba kwana ba za.a dake su a sake su,

Mahaifinta ya yi dukan tamkar gangan dan gannin ya tsoratar da ita, aman ina, hakan ya sa ya ci gaba da
adu.a da nema mata miji, dan kuwa har sadaka ya gwada badata aman sai a silibe masa,

A haka wani lokaci suna gidan su saurayin nata suna hira kanwar mahaifiyarsa ta zagi mahaifiyarta, ita
kuwa du tsakaninka da ita du abinda take yiwa iyayenta bata lamunci wani ya taba mata su, dan haka ta
tsinkawa matar mari, da yayanta da girmanta da komai, inda shima ya nuna ai ita ta jata suka kusan karyata
a gidan da kyar ya kwaceta ya yi fushi yace sai an je an aura masa ita zai dawo gidan,

Kwonci tashi, kara shekaru take, aman kara baudewa take,


Gaba dayanta ta zama wata iri, haka idan suna magana da mamanta tanai mata nasiha kan ta kimtsu, ta
nutsu, ta daina abinda take yi ko zara samu mai aurenta, sai ta ce" mama, ni fa ba.a yi namijin da zai iya da
ni kamar Abdul karim ba, zai zo neman aurena da kansa idan iyayensa basu zo ba, mu yi auren mu mu fi
tafiarmu mu huta,

Takan fashewa malan da kuka kan halayar yar, sai malan ya rarasheta ya ce da ita" tabas ana cewa idan
kyau ya yi yawa yana jan fitintunun rayuwa, ban san ba ko soyaya na nunawa uwata mai yawa? Abinda dai
na sani wannan ikon Alllah ne, muguwar kuruciya ne da uwata, fatana Allah ya tsare min ita, ya shirye ta,
ya bata miji na gari,

Haka suka ci gaba da yi mata adu.a,


Wani lokaci ya je taro garin adarawa dan amininsa ya nemi iri a wajensa,.

Bai boye masa komai ba ya sanar masa dukan halayen ta, nan ya nunawa abokin mahaifinsa da ya ji ya
gani, a aura masa,
Kai na takaice maku bai bar garin Dogon dutsi ba sai da suka tsayar da magana ya karbi sadaki dan daidai
kaya kuwa yace idan ta je gidanta zai yi mata idan yana da halin hakan,
Yana zuwa ya shiga shirye shirye, ya fada masu aurenta sati guda kawai ya tsaida,

Kowa murna yake, da masu murnar zata tafi su huta , da masu taya mahaifiyarta murnar ta samu miji duda
basu ganshi ba, basu san ko waye shi ba,

A ranar da ta ji, ta kyarta rashin mutunci, domin wuka ta dauka ta yi tsaye ta kyarta saman tiles din
dankareren gidansu dari kal ta yi masa katuwar shaida ta kawo rantsuwa ta ratsa ta ce" in dai kuka ga an
daura min aure da wannan mutumin to sai na yanka shi na kawo kansa har gidan nan!

Ba wanda ya kulata, kowa ya yi ta kansa , suka yo gum, domin ko yayunta basa haye mata, mahaifiyarta
kuwa ta girgiza kai ta ci gaba da sha.anin gabanta,

Ita du a wai take dauka, hakan ya sa ta ci gaba da wadakarta a gari da anguwa, tare da Abdul Karim dinta,
Ana jibi aurenta suna zaune a restaurant suna cin abinci ya dubeta da kyau ya ce" bab, dan Allah ki fada
min sunanki na gaskiya mana?

Murmuahi ta yi ta ce" to wai menene a sunan nawa? Ba na fada maka ka kirani da du wanda ya yi maka
ba? Ka tambayi babanka mana idan har ya samu chance din zuwa fatiyar haihuwana,

Kansa ya girgiza yana tabe baki, kai yana son yarinyar nan dan walahi ba daren banza da baya mafarkinta,
du irin yanda ya so rudarta dan ya cin mata aman ta kiya, kai ko gidan rawa da take zuwa fa bata shigar
banza, sai dai ta saka doguwat riga har kasa kuma ta daure kanta cikin hula yar das das,
Kansa ya juyar ya ce" ina son ma ci jarabawar nan da zamu yi bab, ko.na yi karatu baya zama,

Murmushi ta yi kafin ta zabga masa harara ta ce" a ina kake yin karatun? Ka yi karatu Aladji, sannan ka
lazumci Nasurun minalaho wa fatahun kariba,

Kallonta yake, shi a kulun yana mamakinta, ko abu ta saka gaba zata lashe shi ba wani dar, ga karatu, ga
adu.o.i, kai ko irin rubutun alo idan ta zauna sai ta rubuce walahaula dubu ta wanke ta shanye, takan yi
dariya idan ta gama sha ta dubi kishiyoyin mamanta ta ce" Walahaula dubu tsakaninka da mugu, ah to wa
ya san zuciyar wani? Ana maka allah ya isa da mugun fata a gaban ido a zuciya wa ya san me ake maka
fata? To li.ilafi kuraish!

Haka suka wuni tare, sai da yama ta nufo gida ta je dakinta ta sha barcinta domin fashin sallah take,

Baya bikon bidi.a, yakan yi walima hakama iyalansa, dan haka ne ba wani kakatsamniya sai shiri a
adinance da kuma gayance,

Ana gobe daurin aurentama wuni ta yi tana barci, daga ita sai sket dinta na atamfa da pant dinta mai dauke
da audugarta, sai farar rigarta kalkalkal,

Tana tsaka da baci ta ringa jin hayaniya, ana kafin a hankali warin barkonon tsohuwa ya farkar da ita a
gigice,

Ohun mutane da dirufkiya ya shaida mata ana tashin hankali a gari ana dauki ba dadi da iko da mutanen
gari kennan, ya yi tsamarin da har ya shigo cikin gari,
Dan haka aka bata dauki komai ba ta dirko daga saman lafiyayan gadonta ta fito da sanda, gannin ba kowa
tsakar gidan ya sakata dariya ta fece domin du sun labe kowa na neman lumfashin kirki dan shakar
barkonon taohuwa ba dadi,

A haka ta fice a gidan, bata san wace irin rigima ake yi ba, bata san da wa da wa ta hado ba, ta kirmu ta
shiga cikin kartin da ake bi da gudu suna jefa dutsi suna ihun haukan kwatar yanci,
A haka aka radada su aka matse su aka sakar masu barkonon tsohuwa mai yawa, wanda du aka kwashe su a
sume aka yi police station da su.......
*Menene sanadiyar karasawarta prison? Ya maganar aurenta? Iyayenta basu da labarin halin da take
ciki ne ko me?*

Naira dari biyu ne, ko dara dari ta orange money


*KUTKALE*

*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct
NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan
number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA, ZAKU
YI MIN ENVOI NA DALA DARI BISA NUMERO KAMAR HAKA 92777744 AMAN FA TA ORANGE
MONEY.....* taku ce, Sajida😍😍😍😍

3️⃣

*Free page*
Koda suka dawo hayacinsu, du sun jigata, domin duka kai sun sha shi, haka suka zuba idon a
sake su? Aman shiru,

Wasa wasa suka kwana a gidan nan, nan fa hanali ya fara tashi, cikin gari iyaye na cigiya, cikin police
station yaya na zuba ido,

Ba.a wani dauki lokaci ba aka shiga kwasarsu zuwa kotu da su,
Tabas sun ga ikon Allah, ashe sojawa sun biyo wasu yan fashi ne suka fantsama gari, au kuwa yan gari
masu zaman banza da neman fitina suka fara jifansu, hakan ya hadasa fada da tashin hankalin da ya si kuwa
du suka kwaso su suka zuba gidan kason,

Hankali bai gama tashi ba sai da ta ganta sanye da ancor, an tiso keyarta an sakata a mota,
An gabatar da ita gaban alkali a matsayin daya daga cikin yan fashin,
Bata gama tsurewa da mamaki ba sai da ta ji lauyan nan ya mike ya lauyo karyar wai itace budurwar
shugaban yan fashin, dan haka kotu mai adalci ta yanke mata hukunci daidai da laifinta na zama yar fashi a
kasa, sanann ta fito da saurayinta,
Gabanta bai buga ba sai da ta yi ido hudu da alkalin da ya dage yana zazago hujojin karya, da nadidiya
karyayaki kan ita din muguwa ce ta ga ai mijin kanwar maman Abdul karim ne, innalihi wa ina ilaihi
raj.une, mutumen da ta dudurawa ashar dan ya tareta ya tambayeta dan me ta mari matarsa ita da take
sarakuwarta? Mutumen da ta yiwa ihun kwarto dan zai wanka mata mari hakan ya saka shi guduwa bai
shirya ba, sam ya ki jinnin ganninta ko jin labarinta, yau shi ne tsaye a matsayin wanda zai dulmiyar da ita,

(Bincikena ya nunan cewa tabas kana iya samun kanka a irin wannan prison da ba.a kai kowa sai manyan
yan fashi, wa.inda suka kashe mutane, ko wa.inda suke kaso suna karawa cikin babar prison mai cike da
rashin tausayi, rashin imani, tsaro na gangariya, rayuwar kunci, irinta ba sai idan mutun ya aikata laifin nan
mai muni, ko kuwa wajen sharia *LAUYAN DA ZAI YI JA SHARI.AR YA KASANCE YA YI YANDA
YA YI YA NUNAWA ALKALI KAI DIN NAN HAKAN TAKE MAI LAIFIN DA YA CANCANCI
WANNAN HUKUNCIN NE* dan haka kana iya riskar kanka a ciki),

Sosai ya saka dukan wata hanyar da zai bi, a matsayinsa na lauyan da ya kware a harkar, ya nunata a
matsayin budurwar baban yan fashin, inda aka nemi da ko tana da magana?
Cikin ikon Allah ta budi baki ta nuna shi da yatsa ta ce" ni zaka yiwa shari Kadre? Walahi sai na rama, sai
na fadawa Malan, sai na ja maka yaseen!,

Tsawatar mata alkali ya yi, kafin a yanke mata hukucin zaman gidan yari, gidan yarinma *KUTKALE* na
tsayin shelara goma, aman idan har ta fido da saurayin nata zata samu sasaucin shekarun, a lokacin
shekarunta ashirin,

Wannan shi ne mafarin shigarta gidan yari, wannan shi ne dalilin da ta tsinci kanta a gidan yari,
Gidan yarin da mahifanta basu san tana can ba, domin sun yi cigiyar, su ne har asibiti wajen da ake ajiye
gawarwakin mutanen da ba.a ga yan uwansu ba, su ne kauyuka, su ne gidan yarin dake xikin gari, su ne
jarda kai karar Abdul karim aman ga dukan bincike bashi da masaniya a lamarin, haka mahaifinta ya daura
aurenta domin bai fasa ba, aka ci gaba da nemanta, inda yaron na dagawa a ranar da aka daura auren
uwarsa ta saka shi sakin auren domin ba zata aminta a yi mata wannan gangancin ba a aura masa yar da
bata san darajar iyayenta ba, dan kuwa du ta samu labarun irin abubuwan da take, a ranar ne wajen daurin
aurenta du yan unguwar suka ji ainahin sunanta wato ...............

Ci gaba

Fadan nan bai mutu da dadi ba har sai da aka kuma kiran sojojin nan suka shiga tsakani,
Surfe aka zuba masu na abincin ranar da za.a yi, dawa ce, dan haka du wanda bashi da galihu a gidan yarin
ya shiga dukan sirfen ba ji ba gani, ciki harda ita cikin yannayin galabaita aman tana yi dan du wanda ya
bari za.a zabga masa bulala ne,

Cikin prison din nan, du wanda ya saki kansa, ko nace du wanda bashi da daurin ginda zai zama tamkar
gida, du wani kato na iya shigarsa ya fita son ransa, du wanda ya yarda da haka zai samu kariya da kuma
shiryawa da kowa a gidan,
Sannan mata ma tsakaninsu suna watsewarsu son ransu,
Watanta takwas kennan da shigowa gidan, a kulun kiyayarta kara daukaka take domin za.a yi du masifar da
za.a yi da ita kan jikinta da kuma zagin iyayenta,

Suna tsakar dakan nan aka shigo aka kirayi sunnanta kamar haka *ZAHRA* ta fito,

Shiru gurin ya yi, wata mai sunnan zahra ta mike dan tafia aman sai aka ce ba ita ba,
Dakan da take ta dakatar ta hanyar cire tabaryar ta daga cikin turmin, hade fuskarta ta yi kafin ta dauki
hanyar fita waje dan tafia,

Eliz ce ta ce" yau na ga jaraba gannin idona, yau kuma sunnanki ZAHRA? Ke wai wace irin masiface ta
fado mana gidan yari rana tsaka? Ni kam na fara tunanin bakya baiwa yan nan sai yan can, shegiya karuwar
sojoji,

Juyowa ta yi ta nuno yatsarta, saka yatsar ta yi a bakinta kafin ta fitar ta ce" kin san bilahilazi, kika kuma ce
min karuwa sai na kwakwalo idannuwanki kina barci, kin dai san na san lokacin barcin kowa, kuma ina
rigayen kowa tashi ko? To mu zuba , ba sarkin matan prison kike ba, koda kuwa uwar me sai na mayar da
ke makauniya!

Ido du suka zaro da mamaki, Eliz dai bagwariya ce da ta fito daga kudu, bata da adini, bata da haramun, ta
kasance fitinaniya, masifafiya, ya jaraba, shekarunta uku yanzu a gidan yarin sanadiyar kisan kai da ta yi na
mutun biyu a cikin tafiarsu ta hijira dan dauke kudinsu na guzuri inda polisan hanya suka kama su suka
kamata da laifin aka so mayar da ita garinta su mata hukunci a can sai dai gwamnatinta ta ce idan an
kawotama harbeta ne za.a yi, a niger babu Loi din harbe mutun koda ya yi kisa hakan ya saka suka sakata
kaso daurin rai da rai,

Tunda ta zo kason sai da ta san yanda ta yi ta zama shugaba, kowa tsoronta yake tamkar rai, basa haye
mata, dan ta fada ta kara kashe wani ba damuwarta bane dama ta shigo ne da niyar a fitar da gawarta bata
da matsala da hakan!

Haka aka fitar da ita, aka nufi inda ake son gannin nata, nan ta bar su kowa jikinsa mace dan sun san yau ba
su ba barci, za.a sha masifa ta bugu da kari!

Turata ya yi dan dakin sannan ya ja ya tsaya yana muzurai,

Daman ta san shi ne, bata san tambayoyin me yake mata ba, bata san me yake nufi da ita ba,

Tana shiga ta kara kallon yannayinsa, a ranta ta ayana ban taba gannin fuska marar annuri irin taka ba,

Shima dake zaune fuska hade ya mike ya dauki abin auna tsayin mutun ya auna tsayinta,
Hannunsa ya daga a lokacin da take tsaye ya zabga mata wani wawan mari wanda ya sa ta daku da jikin
bangon wajen,
Da sauri ta taro kanta sannan ta mike tsaye tana dubansa ido cikin ido,

Dakin take bi da kallo, ba komai ciki sai bindiga daya kwal dake ajiye saman table din da ya tashi daga
sama,
Da gudu ta nufi wajen bindigar ta dauka ta saita shi ta firfito da idannuwanta ta daga muryarta da kyau ta
ce" kai mahaukaci! Me na maka? Me na maka? Uban me kake zuwa nema wajena? Ko jira kake kaima na
daga maka jiki? Kan haka zan iya harbeka dan Walahi malan ba zai yi kukan na rasa mutuncina a waje ba!
Koda kuwa gawata zama fitar daga wannan bakin gidan!

Da sauri guard din dake waje ya shigo ya nufeta dan karbe bindigar, ai kuwa ta dana ta kara dana kunamar
bindigar, sai dai ba alburushi a ciki,
A haka ya karbe yana mai jin zuciyarsa na bugawa dan kuwa shima bai san ba alburushi a ciki ba, ya dauka
ya gama mutuwa kennan,

Datijo ne mutumen da ya gannin nata dan haka ya zagaya ya koma wajen zamansa,

Wayarsa ya ciro ya canza harshe zuwa yaren french ya ce" na yarda da taurin zuciyarta, girman mutun,
yannayin fuskarsa, ko karfin mulkinsa ba zai sakata yin dar ba idan ta hado su, tsayinta ya kai daidai a
dauketa , bata da kakauran jikin da zai hanata daukan formation, zan saka rana a sakata cikin wa.inda aka
dauka,

Shiru ya yi yana gannin yanda take waiwayensa bayan an fitar da ita sannan ya ci gaba da fadin" tabas idan
ta samu mugun horo, zata kara tsayuwa saman kafafuwanta, zamu dauketa mu bata horo na wata biyar, zata
fito a matsayin *BODYGUARD SECRET* zamu bata horo kala daban daban, zamu bata horo na tausasa
murya, zamu bata horo na kalolin yaudara, zamu bata horo na jure azaba komai girmanta, sannan zamu
horata da yin biyaya,

Shiru ya kuma yi inda ake masa bayanin an gamsu da kyanta? An gamsu da girman gayunta? An gamsu da
girman iliminta? An tabatar tana jin yare biyar *HAUSA, FRENCH, TURANCI, LARABCI, DA
ZABARMANCI?*

murmushi ya yi ya ce sunnanta na gaskiya shi ne *HAFSAT MUHAMAD SA.IT*, yare tara take ji, gaba
daya kwaya biyu ne na iyayenta, sayran ta koye su ruwa ruwa je a makaranta zama da masu iya yaren,
yarinyar kamar computer take, tana dauke abu nan da nan ba tare da ta sha wahala ba, tun da ta shiga
makaranta itace ta fari har zuwa faruwar kadararta, gasa ta school da islamiya sai dai idan ra.ayi ya hanata
shiga, in dai ta shiga sai ta lashe,
Tana da kakarfar zuciyar da na yi na.am da ita,
Shekara ashirin kennan ina horon sojoji, polisai, guard, Body guards, ban taba tsayuwa gaban mutun mace
ko namiji muka kali juna ido cikin ido ba tare da ya sada kansa ba sai wannan yarinyar, zuwan da nake dan
duba yannayin mutanen kason dan zaban wanda zan dauka har na isheta yau ta nuna min bindiga danma
bana ajiye bindiga da alburushi da ta dana ta harbe Guard dina,

Haka suka gama magana kafin ya fito ya nufi motarsa inda suka sara masa aka ja shi aka fice da shi .......

Wannan kennan .
..

Ku biyo ni ku sha labari....😍


😍😍😍😍
*KUTKALE*

*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*
Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct
NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan
number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA, ZAKU
YI MIN ENVOI NA DALA DARI BISA NUMERO KAMAR HAKA 92777744 AMAN FA TA ORANGE
MONEY.....* taku ce, Sajida😍😍😍😍

4️⃣

*Free page*

Ana mayar da ita cikin kurkukun dakinsu ta ja ta tsaya sanadiyar ganninsu da ta yi fada suke mata kowace
na rantsuwar a barya da ita ta koya mata hankali,

Ganninta ya saka suka fara nufota da yannayin izgilanci suna rantsuwar yau sai dai gawarta, bale masu
zaune a wajen da nufin daurin rai da rai,

Da gudu ta warci tabaryar da ake dakan da ita, daidai saratu ta karaso wace ta fi kowa rawar kafa dan
samun gidin zama wajen Eliz, sai dai me, batai wata wata ba ta daga tabaryar nan ta sheka mata ita a goshi,
sannan ta aniya tarban wa.inda basu rigai sun karaso din ba, ja suka fara yi suna tsayawa, kai danma zaman
balaki ne zaman kurkuku? Da me zai saka ka tarban gabanta? Mai zai kaika yin wannan kasadar? Bata ji
bata gani, idan ta rufe ido kawai a fado a mutu ne,

Cikin hargagi da iface iface suka shiga dankarawa da gudu, wasu na zagayawa suna nufar wajen sojojin
gidan,

Sojojin du mikewa suka yi tsakaninsu suna magana, ba wani abu ba suke cewa sai canko cewa da Aljanar
prison ne ake fada, harda masu saka kudi, sannan bakin zuwa sun cika da mamakin wai ita haka take?
Da gudu suka shigo da shirin ko ta kwana, gaba daya suka rufta masu suka shiga dukansu, ba ji ba gani,
duka kawai suke sha, sai da suka yi laushi sannan aka barsu, aka tiso keyarsu dan dora garin da suka surfa
ba wankewa sai fecewa da suka yo suka kuma daka shi ya zama gari suka dora tuwonsa, inda masu tuka
tuwon du suka tafi wanke helunan da zasu tuka tuwon da shi,
Can gefe kuwa Eliz ta hasa wuta da itacen mainan da mazan ke yowa a wajen su hura wutar ta dora
tankamemiyar tukunya ta kawo tunjumemen ruwa ta maka ta zuba yan kayan miyan da suka samu, ta afka
gishiri, sai dakakiyar miyar da suka dakata da kansu bayan miyar ta tashi sosai ta kawo ta kada da katuwar
sanda ba ruwanta da wani burkakewa ta kawo dan mai kadan ta afka abinta ta juya ta zauna tana jira ta yi
dan kauri a shiga rabo, yau ta yi niya dan ubanta ba zata samu tuwo ba! Zata nuna mata wanda ke iko a
gidan!

Sai lokacin rabo ya yi kowa ya zo da robarsa, dominfa wajen nan ba.a kawo masu ziyara bale ka ci abincin
gidanki, abincin da kowa ya ci ne zaka ci ko ka mutu,

Nan kowa ya kawo yar robarsa ana zuba masa abincin da daga shi sai kuma gobe, basu da abincin dare ko
na kari, aman suma samun isashen da idan sun adana zai masu anfani.

Tana ji tana gani aka hambarar da robarta, aka zubawa ta bayanta,


Hakan ya sa ta mike ta dauke robar ta kai ta adana, dan indai ta harta a nan wani na iya taketa dan kawai ta
rasa yar robar cin abincinma,

Waje ta samu ta rakube tana mai jin wata irin juwa, idannuwanta ta rufe ruf kafin wani hawaye mai zafi ya
shiga bin gefen fuskarta,
Innalilahi wa.ina ilaihi raj.une, Allahuna ajurni fi masibati, wa khalifuni khairan mine ha, ya Allah na tuba,
Allah na tuba Allah,

Allah mamana, Abana Allah, ka sa su yafe min, idan har nan karshena yake Allah ka sa su ga gawata, su yi
min adu.a, Allah kar ka basu ikon cin mani, Allah ka wankeni koda kuwa gawata ce, Allah ka yafe min,

Abinda ta yi ta maimaitawa kennan tana istghfari, ita kam ta ga rayuwa, ta ga ilar tsalake maganar iyaye,
bata san haka lamarin yake ba, niyarta lokaci ya yi ta tuba wa Allah, niyarta ta tuba idan ta kara girma ta
dawo ta shirya da iyayenta, sai gashi, tana raye, suna raye, ta wayi gari, nesa kadan da garin da suke, aman
basu san a duniyar take ko ta mutu ba, tana tausayawa mahaifiyarta, tana tuna dumbin kaina da take yi
mata koda kuwa tana kokarin boyewa, yau gata a raye tamkar mataciya,
Bata da wani anfani,
Ana yakin kwace mata martabarta, ana yakin raba gangae jikinta da numfashin da take shaka, adininta ya
tabu, walwalarta ta gushe, bata da tunanin da ya fi ta budi ido ta ga iyayenta, ta ga farkon wannan ukuba
bata san karshenta ba,

Tana nan zaune du suka ci abincinsu, ba wanda ya damu da irin halin da take ciki, kai ba itaba, akoy
wa.inda suka fita jigata, suka fita shiga wani halin rayuwa, ba wanda ya damu da su bale ita da ba zaman
lafia suke da junna ba,

Sai da tsohuwar nan ta lura da sahun kafa ya dauke, ta lalaba ta ajiye mata abincin nan ta gefen damarta
inda zata iya ci ba tare da wani ya kula da ita ba,

Da kallo ta bi matar da kallo,


Tunda ta zo gidan, zata iya cewa wannan matar na bakin kokarinta a kanta, akoy lokacin da ta kwatanta yi
mata nasiha kan ta bar kula mutanen nan haka, ta yi hakuri ta daina, aman cikin ikon Allah ta fada mata
itafa kan abu biyu ne ba zata iya kawar da kanta ba, darajar mahaifanta, da ita tata darajar dake tare da ita,
dan haka indai a kansu ta ga tana fada , karma ta daga dan yatsanta ba zata saurareta ba,

Abincin ta wawura daga gefen nata ta shiga ahawa ba ji ba gani,


Tuwon bashi da wani dandano a harshen bawa, yana gangarawa ne ya je ya dunkule maka a cikin ciki,
Bata damu ba sai da ta cinye shi kakaf sannan ta shiga maida numfashi tana duban yanda ganninta ya fara
dawowa,

Godiya ta yiwa Allah da bai barta cikin yinwa ba, ta labe robar tsohuwar sai da ta mike dan gabatar da
sallah ta kai mata ta ajiye a boye ba wanda ya kula da an tiso tsohuwar a gaba danme zata hana a yi mata
horon yinwa.

Sai da ta zo tsakiyar wajen ta yi tsaye , ta saki murmushin godiya ga Allah, sannan ta bi kowa da kallo, bata
da dar, du wace ke jin kanta wata shegiya ce kuwa jiranta take, dan haka a gadarance ta nufi wajen ruwa ta
dauka, ruwan da na siyarwa ne ta dawo ta shiga alwallah bayan ta kwonkwada,

Ke ina kudin ruwana?


Muryar mai siyar da ruwan ya daki kunnenta,
Namiji ne , aman kuma dan daudu ne, zamansa cikin prison din ba irin sana.ar da baya yi, shi ke samo
ruwansa ta hanyar da masu tsaro suka yarje masa, ba wai babu panpo bane a wajen, da ruwa fa, kawai ana
hana su zuwa wajen ruwan ne, sai idan dare ya tsala ake bari, su kuwa da ba abubuwan cika ruwan garesu
ba wa zai basu? (Ya Allah ka rufa mana asiri, ka rabamu da kadara muguwar kadara, tabas zaman gidan
yari wani nufi ne na Allah wanda idan ya nufi bawansa ba wanda ya isa ya hana, kadarra ce, ya Allah ka
kare mu da rayuwar rashin yanci ),

Da sauri ta karasa alwalarta, sosai ta didiki ruwan, sannan tamike tsaye tana dubansa cikin ido yanda yake
wani laudi, du fuskarsa ta jeme tsabar shafe shafe da yake dan jaraba a gidan yarinma, sannan fuskar wani
tafkekiya da ita da dogayen lebuna da aka kara fitar da su dan dole dan kuwa lankwasa sun da ake ta hanyar
sai an yi maganar mata dan dole,

Murmushi ta sakar masa sannan ta ce" kai ko kema sunnan yake, kali sama, rana ta raba, tsuntsaye sun yi
shiru, sararin samaniya ya kara haske, wanda ya yika, ya kuma baka ruwan ne zan gaisar, in kuwa baka
yafe ba fadi mu ji....

Ta karashe tana harde hannayenta biyu tana dubansa ,

Baki ya tabe kafin ya ce" jarababiya mai bakin uwa (zaginsa kennan sai yace da kai mai bakin uwa, wai
nufinsa in ba bakin uwa ba me zai kawo mutun kutkale),

Wartar butarsa ya yi kafin ya zabga mata harara tamkar wata mace, ya ja tsaki ya kuma buga cinya ya juya
ya bar mata wajen yana mitar ke kika sani, ah ina dalili ga zafin prison ga na yinwa ga kuma na dambe?,
bara in je in yi neman kudina in huta, neman fada ai sai matsiyaci!

Ita dai tunda ya juya itama ta juya dan zuwa ta yi sallah, domin malaman cikin prison din sun yi kiran
sallah tun dazu, ( kar ku sha mamaki, kamar yanda na fada, ba abinda babu a gidan yari, )

Gidan Malan Muhammad Sa.it

Sadakar damamiyar madara da kuma abinci dafafe ne ake yau juma.a,

Ko a masalaci da aka gama sallah kamar yanda ya saba, sadaka ya yi sosai, inda shima manyan elhazan nan
ke kawonasu gudunmuwar , wasu da sunnan masalaci, wasu kuwa da sunnan malan din da kansa, duda
kuwa ya fi karfin hakan, aman ba karamin dadi yake masa ba domin kuwa mutuntawa ne,

Sai da aka watse, ya mike ya gyara salayarsa a ma.ajiyarta yana duba agogo dan karfe hudu yana da wa.azi
da gidan tv Tele Sahel,

Abokin shawararsa ne, wato Malan Laminu ya shigo masalacin,


Cikin raha suka gaisa kafin su fito daga wajen sallar suka yada zango a balbalin masalacin wajen shuke
shuke na gazon macha Allah,

Dubansa ya yi a tsanake sannan ya ce" yaya karin hakuri? Ya juriya, ya hakurin Matar arziki?

Shiru ya yi kafin ya sauke ajiyar zuciya yana dubansa ya ce" ka san na shaku da yarinyar,
Kai shaida ne komai nata daban ne,
Inada vidioyinmu inda take tatata, tana yi tana fadin Baba..baba tatata,

Malan laminu ya sauke ajiyar zuciya ya ce" ba kai kadai ba malan, ko ni da ta yi karatun alkur.ani hanuna
na sha mamakin lamarinta,
Wai ka san tun kafin ta yi sauka ta taba kamo bata a cikin rubutun litafi da malan salisu yake koyon nan da
tadawa? A nan na kara dubanta,
Ka duba ka ga a kusan tare ta yi hardar ahlari, kawa.idi, da alkur.ani, tana gamawa ta shiga damkar litatafan
adinin nan, kuma ya shiga kwajwaluwar cikin ikon Allah ya zauna,
*UWATA* raye ko mace?

Malan Muhammad ya ce" na so gannin gawarta, na tabata da na hakura na samu nutsuwar zuciya, man
laminu, mutuwa bata boyuwa, gani nake koda a ketare da niger ta mutu zamanin android za.a haskota,
Ina ji a jikina *UWATA* na raye, ina ji a jikina tana wani yannayin rayuwa, mahaifiyarta ke bani labarin
mafarkinta, takan yi mafarki *HAFSATU* na miko mata hannu, ko ta yi mafarkinta ta dora kanta saman
cinyarta tana shasheka tamkar wace ta yi tsere,
Ya Allah ka kare min UWATA du inda take, idan da kafarta ta gudu dan zan mata auren da bata so, Allah ka
shiryeta ka dawo da ita gida, idan kuwa fitar da ita aka yi, Allah ka kare min ita,

Shiru ya yi yana duban Malan laminu daje amsawa cike da girmamawa sannan ya ce" idan kuwa Uwata ta
rigamu gidan gaskiya, ya Allah ka jikanta, ka sa tana cikin rahamarka, Allah ka hada mu da wanda koda
hoton mutuwarta ne ya gani ya fada mana ko hankali uwar daukan cikinta zai tsaya waje guda, ko zata rage
yawan fado mani a cikin zuciya ya Arahaman rahimine

Amsa masa adu.arsa yake, inda suka mike suka rankaya gidan Malan Muhammad din, somin yau juma.a
ce, gidan malan na cika ne tun da asuba har wata asubar ana raya ranar sosai,,

Bayan sati biyu

Murkashi take na ciwon ciki, ita daya yashe a rana sai juyi take , abin ne ya hadun mata ha yunwa da take
ji, ga rashin bacin kirki , ga damuwa, ga kuma al.adarta da ta risketa cikin wannan halin,
Adu.a take so ta yi aman ina, sosai cikinta ke ciwo tamkar ranta zai fita...................

*Domin Samun kutkale, naira dari biyu ne, Niger kuwa 500 franc ta orang money*
*KUTKALE*

*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar
DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct
NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan
number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA, ZAKU
YI MIN ENVOI NA DALA DARI BISA NUMERO KAMAR HAKA 92777744 AMAN FA TA ORANGE
MONEY.....* taku ce, Sajida😍😍😍😍

5️⃣

*Free page*

Wasu kartin sojoji ne hudu suka shigo wajen, nan hankalin kowa ya yi kansu,
Neme neme suka fara yi, kafin dayansu ya je ya birkitata ,
Da yaren french ya ce" c'est elle, la voila chef (ita ce, gatanan sir)

A tare suka nufo wajen, basu yiwa kowa magana ba suka kinkimi Hafsat suka fita da ita ,

Jigum jigum wajen ya yi, Eliz ce ta ce" ko ratayeta dai za.a yi? Wadinnnan mutannan mararsa annuri?

Baba fsohuwa ce ta kaleta da sauri ta ce" kin taba jin an rataye wani a Niger? Ai ba.a hukuncin rataya,

Eliz ta daga kafadarta ta ce" to , an taba yarki ko? To ina fatan su je su yagalhalata sannan su maido mana
honkon!

Shiru tsohuwar ta yi, dan ba zata iya ba kam, aman kasan zuciyarya tana adu.ar ba amen ba, haka kuma ta
nemi waje ta zauna tana duban hanya

Tafiya ce suka yi ta mamaki, a cikin wata bakar mota wuluk,


Cikin jejin suka kara dafaruwa,
Sai da suka shige wajen da sai dai GPS zai nuna maka nan ne gabas yama kudu ko arewa sannan suka
karaso wajen wata bakar kofa,

Basu tsaya wata wata ba suka danna horn,


Nan aka bude masu kofar suka shiga da ita,

Wani irin waje ne mai gine gine, da wajajen gudu, da wajen tatakawa a hau, da 2ajen tsalake igiya, da
wajen haura katangu,
Kai gurin dai wani irin tsari ne da shi mai wuyar fasara,

Basu zame da ita ko.ina ba sai wani bangare, nanma get ne, dan haka sai da suka kuma yin wani Horn din
aka bude masu suka shiga daga bakibaki suka fitar da ita suka dauketa cimak suka kaita cikin wani daki,

Dan daki ne dan dogo madaidaici, mai dauke da katifa kwonciyar mutun guda, da wani dan table karami,
sai sutura wando da riga bakake sakaku sannan na auduga,(kada), sai fankar sama karama ba baba ba, sai
fitila daya doguwa, da kuma wasu irin fitilu cike zagaye da fankar nan, sai kuma wajen dake huro zafi ,

Fita suka yi, ba wanda ya yiwa dan uwansa magana, inda tana ji, tana gani, tana son ta mike aman ta kasa,

Daga jikin kofar aka bude yar kofa aka turo mata wani faranti mai dauke da magani d goran ruwa da
audugar mata , da pant, da kuma wani sabulu dan karami mai kyau,

Ta jima tana hangen abin da juwa juwa, a hankali ta ringa jan jiki har ta karasa wajen da suke ta dauko
farantin,
Zama ta yi ta karanta sunnan maganin, bata san shi ba, aman ta ga bayanin na sauke ciwon mara ne,
Bata tsaya wata wata ba ta sha maganin nan sannan ta kwonta nan tana kara cikwuikuye sket dinta tana tare
jikinta dan kar ya bata mata jiki,

Ta samu kamar minti talatin, tana barci barawon da ya dauketa, kafin ta farka a firgice,

Dakin ta shiga bi da kallo, sannan ta mike tsaye tana duban wajen, harda su auduga da pant din da aka miko
mata,

Kanta ta kara dagawa tana dubam dakin, ba camera, bata ga camera ba, dan haka ta nemi waje ta zauna
tana duban waje guda cike da fargabar ina ne nan? Ta san dai ba prison bane,
Innalilahi wa.ina ilaihi raj.une, ya Allah in dai dan a keta min hadi aka satoni aka kawoni wajen nan Allah
ka kasheni kafin su zo su fi karfina, Allah kar ka bari su cinma burinsu 👏🏻👏🏻

Haka ta zauna, idonta biyu, bata san karfe nawa bane, bata gane lokacin sallah, bata gane dare ne ko rana,
sai dai idan ta gaji da zama ta canza waje ko ta mike tsaye ta kama kofar nan ta yi ta jinjigawa aman bata
ko dar bale har ta bude,

Magannin nan da alama yana saka baci, domin wani bacin ya kara fuzgarta sai goshin asuba ta farka dalilin
bude kofar tata da ta ji ana yi,

Da sauri ta dauki farantin nan ta labe daga gefe, ana budewa ta daga zata kwadawa wanda ta shigo, sai dai
ta ji an yi raf da hannunta,

Dubanta matar yar dagwas take da mamaki, wannan kazamar kuma? Ya aka yi aka kawota wannan aikin da
sai yayan masu gata, masu gatanma masu hanya, masu hanyar ma sai sun hau table sun zana jarabawa har
kala biyar,?

Hannunta da ta tare ta sake mata a hankali, sannan gurds din dake tare da ita ya karbe farantin,
Abincin da aka miko mata ta ga bata ci ba,
Dan haka ta dauko abincin tana dubanta ta kawo mata kusa da ita, inda take tsayen ta mika mata ,
Murmushi ta yi mata ta ce" ciki da yinwa, ko fada ne, bashida wani armashi Hafsat
Ido ta zaro cike da mamakin ya aka yi ta san sunnanta?

Matar ta dafa kafadarta ta ce" kar ki yi mamaki, ba sunnanki kawai na sani ba, harta Malan, da Ummi
magaifiyarki na sani,
Ki kwontar da hankalinki, ki ci abinci cikin gagawa mu je ki yi wanka domin yau za.a fara,

Hafsat ta yi dandaja tana dubanta, yau za.a fara? Za.a fara me?

Jiki a sanyaye ta dubeta ta ce" aman dan Allah ina ne nan? Me aka kawo ni yi nan?Allah dai ya sa ba
karuwanci kuka kawoni yi nan ba, domin bani da ra.ayin hakan!

Murmushi matar ta yi tana dubanta, eh gaskiya ne, bata da tsoron abu, kuma tana da ra.ayinta, dan haka a
fili ta ce da ita" ko daya, ba abinda muke yi kennan ba,
Kin shigo nan gidan ne wajen horon Manyan sojoji ba sojojin dake cikin gari ba, aa , irin wa.inda sai fitina
ta ki mutuwa ake kaisu, wa.inda cikin gari kuke kiransu da kurame, wa.inda idan sun je waje dan kashe
tarzoma basa bambanci suke hadawa su kashe tarzomar ba ji ba gani,
Sai kuma *BODYGUARD* bodyguards mata da maza, manyan bodyguards masu baiwa shugaban kasa
tsaro, da manyan yan siyasan da suke iya biyansu, da manyan bakin da suke shigowa kasa suke iya biyansu,
da banban jujun kotu, da sarakan ketare dake iya faukan nauyinsu, ana tura takardunsu ne kasa kasa domin
aikinsu bai tsaya iya nan ba, suna da damar fita waje su yi aiki idan ta kama, ana iya daukansu aiki mai
takaitacen lokaci kamar sati biyu, ko uku, ko wata, ko wata biyu, ko biyar,
Haka kuma ana iya daukansu aiki na dindindin ana biyansu kudi masu matukar yawa,

Bata tsamaci tambayar da ta cilo mata ba cewa" kennan dai rayuwarsu zata kare a bautawa wasu ba
maganar aure?

Sai da ta yi shiru tana dubanta kafin tace" akoy damar yin aure,

Da yannayin izgili Hafsat ta ce" wace iri ce damar? Sannan na ji kin kama sunana kai tsaye, bayan na
kasance mai boye sunana, na ji kin kureni ta hanyar kama sunan mahaifina da kiranyen da ake yiwa
mahaifiyata, dama dan gari haka yana zama fitacen dan ta.adan da ya cancanci zama gidan yarin
*KUTKALE?*

Matsowa ta yi kusa da ita ta ce" daman sai dan jeji ke zama dan ta.ada?

Hafsat ta girgiza kai ta yi murmushin yake ta ce" aman a sanina , kafin a rufe ni, niger kasa ce ta incin kai,
kasa ce da mutun keda damar zaban abinda zai yi na aiki a rayuwa, koda kuwa an dora min laifin ta.adanci
me yasa ba za.a bani damata na kasancewata yar kasa mai cike da shaidar hakan na zabi aikina? Ko a
zaman wata takwas da sati biyu da na yi a gidan yari an canza hakan?

Kallonta ta kara yi tana kara mamakin yarinyar, kuma ba komai ya sa ta biye mata tana bata amsa ba, sai
dan ta kara tabatarwa da girman iliminta ta hanyar tambayoyinta, da yannayin da take yin tambayar, dan
haka ta ce" eh, haka, Niger kasa ce ta inci,
Anman ke da kika fito a matsayin mai babar laifi a kasa, kika cancanci mugun hukunci ta hanyar rataya ko
harbe ki, aman kasa mai adalci ta barki ci gaba da numfashi, harma aka baki opportunity na zama babar
Bodyguard da kuma kunada masu tsaronku idan har kuka gama cinye jarabawar nan, me kike nema na
kari??

Hafsat ta tsayar da cin abincin da take ta dubeta da kyau, shigarta wando da riga ne, sai dan siriin belt,
tsarin yannayinta zai tabatar maka da a cikin hutu take,
Hafsat ta ce" da farko, ba wani ya bani damar ci gaba da numfashi ba face Allah,
Na biyu, kowa da bikin zuciyarsa, kowa da irin salon takun rayuwarsa,
Abinda yake opportunity a wajenki, sai ki ga ni tashin hankali ne, burina bai fi na koma gaban iyayena a
karo na biyu, na samu wannan opportunity na kasancewata da su, na yi masu biyaya,
Shiru ta yi na dan lokaci sannan ta mike ta taka ta ajiye farantin fari kal da shi ta kuma dubanta inda ta yi
mata nuni da ta dauki sabulun da kayan da aka ajiye mata,

Sai da ta dauka ta zo zata shiga gabanta ta ja ta tsaya daidai ita tana dubanta ta ce" wannan shi ne
opportunity mai ma.ana, mai dadi, mai daraja , wanda nake kwadayi a ruhina, ba zamana mai gadin lafiar
wani kato ko wata katuwa ba wanda hakan na nufin daga bakin lokacin da zan fara karbar koyarwarku *NA
SAIDA RAINA*

Tana gama fada fada ta juya ta yi gaba, nan guards din suka rabu biyu suka saka su a tsakiya,

Tafe suke tana kallon yanda karti ke tafka gudu da duhu duhun asubar nan, sannan kowane kansa a aske tall
tall suna ta gudu,
Da wasu na biye da su a mota das a zaune,

Haka suka yi yar tafia suka shiga wani batiment (gini)


Nan ta ga mutane, yan mata tsala tsala suna shigi da fici da tawul a jikinsu, ana iya yi,

Da mamaki suke kallon wace aka shigo da ita, duda basu jima sosai da zuwa wajen ba, aman basu taba
gannin mace mai dati irin wannan ba,
Gaba dayanta tamkar an tonota, sannan sket din jikinta du ya yi datin balaki ga karni da take yi, kai ba kyan
gani dai,

Haka ta mata jagowa har zuwa wani bangare, nan aka umarceta da ta zauna,
Suka kama kitson kanta suka shiga tsefe mata,
Sai da suka gama tsefe mata shi tas sannan aka bata damar ta shiga ta yi wanka,

Mikewa ta yi tana dari dari ta shiga wajen da aka nuna mata,


Tsayuwa ta yi tana kallon shower, ga soson wanka, ga sabon brosh da makiline, ga abin wanke kai,
Gaba daya ta sansu, domin gudansu ba baya ba, mahaifinsu na kula da komai nasu ,

Har gagawa take , bata cire kayan jikinta ba ta kunna ruwan ya shiga bin jikinta tun daga kanta , aman dati
baya fita domin kuwa datin jar ya zama mai maiko ne a jikinta,

Haka ta cire kayan ta sake su nan cikin ruwan ta dauko sabulun ta shiga dirzar jikinta,
Soson ta dauko ta aniya dirzar jikinta da shi , fuskarta ne, wuyanta ne, kunnayenta ne, jikinta ne, hamatarta
ne, kafafuwanta ne, ita kanta da ta ga bakin ruwan dake sauka daga fatar jikinta sai da tsikar jikinta ta tashi,

Haka ta yi ta yi ruwa na darwaye mata sannan ta debo abin wanke kan nan ta matso da yawa ta laftawa
gashinta da ita bata yi tunanin idan an zo kwonce shi zai tsaya a kanta bama,
Tana laftana tana saka faratunanta tana dirzar kan, ruwa na zuba yana kara darwaye mata, ta yi haka ya kai
sau hudu har sai da ta ji wani irin sakayau sannan ta dauki demelin ta kara a kan ta darwaye,
Sai da ta kara wanke soson nan fes ta kara saba masa sabulu ta kara bin jikinta da dirza sannan ta duka ta
dauki kayanta ta shiga wankewa tana jin har zuciyarta na tashi,
Du yanda ta so su yi fes ki suka yi, sai dai sun wanku ba laifi,
Abin aski ta dauka ta gyara jikinta gaban madubin bayin, hakama hamatarta tas sannan ta dauki tawul din
dake rataye tana mai jin dadin kamshin sabulan da ta yi anfani fa su, ta daura a jikinta bayan ta rataye
kayanta da ta wanke ta fito,

Tana fitowa aka shiga dan wanke bayan dakin,

Wajensu ta zo, suma ita din suke jira, dan haka tana zuwa ta zauna , duda jikinta du a tsatsamce saboda bata
saba fitowa daga ita sai tawul ba,

Kayanta aka mika mata da bras,

Kallonta ta yi ta ce " bana anfani da bras,


Matar ta ce" zaki fara anfani da ita daga yanzu, domin gudu za.a fara daga yanzu, idan kina gudu ba bras
nononki zai zube ne, mu kuwa du wani abinda zai kawo mana cikas bama so,

Ita dai da ido take binta, nan aka busar da gashinta aka daura mata ribom baki dan siriri sannan aka daure
gashin da kyau yanda ba zai hanata komai ba,

Wasu mayuka biyu suka bata, dayan suka ce da ita na fatar jikinta ne, dan gyaran fatar jikinta, dayan kuwa
ta ringa shafa shi a tafin hannayenta, gwuiwar hannayenta da na kafafuwanta, da kuma tafin kafafuwanta
dalin tausi da suka yi, kafafuwan harda dan ysatsagewa suka yi wato faso,

Karba ta yi tana dubawa

Kallonta ta yo ta ce" ba wannan zaki yi ba, tashi ki saka kayanki maza ki bi inda kika ga yan matan nan na
bi,

Mikewa ta yi ta saka kayan harda audugarta yar karama wace kamarma baka saka ba dan baka jinta a
jikinka, ta saka kayan ta nufi inda ta ga yan matan na bi suna fita bayan ta daura takalmi kafa ciki na gudu
kamfanin Gucci

Sai da gabanta ya fadi da ta ga wanda ke tsaye ya hade girar sama da ta kasa,


Wannan datijon ne, da wani a gefensa shima bakin ne kamarsa shima ya hade fuska tamkar an zage shi,

Kanta take sadawa wai kar ya ganeta inda ta je ta ja layi wajen da suka tsatsaya su wajen goma yan mata
cikinsu ba ta yardawa, kowace yar dagwas da ita , gashi basuda wani jiki mai girma, sai dai wata ta fi wata
tsayi sosai

Fuska tamke yaron ya shigo gabansu ya fara magana kamar haka inda kolon kansa ba gashi ko dis , murya
hade ya ce".....

*Domin samun Kutkale naira dari biyu ne, yan niger kuwa 500franc ta Orang Money*
*KUTKALE*

*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE


BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct
NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan
number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA, ZAKU
YI MIN ENVOI NA DALA DARI BISA NUMERO KAMAR HAKA 92777744 AMAN FA TA ORANGE
MONEY.....* taku ce, Sajida😍😍😍😍

6️⃣

*Free page*

*SALAM, ZAKU GA WASU ABUBUWA CIKIN WANNAN RUBUTU NAWA, KAMAWA TA YI, WANI
ABIN YA ZAMA DOLE NA SAKA SHI, DAN HAKA KU BIYO NI👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻😢*

Cikin dakakiyar murya ya ce" kafin ku shigo gidan nan kun yi gudu na kilometa 4 a minti talatin, to yau
zaku yi 6 a minti ashirin, ba tserere bane, domin so muke ku zo gaba dayanku a tare, kar wani ya rigayi
wani zuwa, kar kuma a bar wani a baya, akoy mai tambaya ne?

Shiru du suka yi domin kuwa kida sunada tambayar ba zasu iya yinta a wannan mutumen marar annurin ba,
taf idannuwansa kansu wasu jajajir ne kamar an watsa masa barkono, kai ko da hakoran bakinsa ya cikeja
ya tada ka tsaye domin dogaye ne, dan haka du suka yi shiru suna tunanin abin,

Kara maimaita tambayar ba mai magana ya yi?

Tsagal ta ce" wani irin mu zo a tare? A tare zamu yi aiki ne? Ko akoy aikin da za.a iya tura mu tare da
sharadin sai mun dawo a tare daya ta kula da ran daya?

Datijon nan ne ya saki murmushi yana dubanta kafin ya gyada kansa,


Sai a lokacin ya matso inda saurayin ya dan matsa masa gefe,

Datijon ya dube su ya ce" ya zaku tsaya gaban mutun ya zayano maku maganganu kuna sauraronsa kuma
kuna kallonsa, cikin hankalinku, ba maye kuka yi ba, ba duka kuka sha ba, bayan kun san abinda kuka zo yi
, horon aikin zama Bodyguard wanda a kaf cikinku za.a dauki mutun uku zuwa hudu, sauran sai dai a yi
wani wajen da su, bayan kun zana jarabawa an tabatar maku da abubuwa na wannan aiki, aiki ne na
individual (mutun daya), shi ne za.a ce da ku wajen gudu ku karaso tare tamkar tayar mota da aka daidaita
wajen hakan sai kawai ku hafiye?
Murmushi ya yi irin na mugunta kafin ya dubi saurayin nan ya daga murya a hade ya ce" Bg soldier
(Bodyguard soldat ), ka fitar da wace ta yi tambayar ma.ana gefe, sauran ka horar min da su ta hanyar yin
tsalen kwado dari kafin su yi gudu,

Haka ta ja gefe tana kallon yanda yake tsaye kansu da zabgegiyar bulala suna tsalan kwado suna karawa du
wance ta yi da sanya ba wata wata yake dada mata bulala ciki harda wata mai dan kakauran jiki baiwar
Allah yar baba da rai ce, ta samu shiga wajen da mahaifinta wani ne, dan haka baki dayansu suka jigata
sosai , sannan aka laya su aka sake su gudun kilometer hudu, wanda ta jigata ta ji kamar zuciyarya zata
tsaya, domin rabonta da wani gudu mai dan tsayima tun wanda ya kawota gidan yari, hakan ya sa sai da
suka rigayeta isawa kafin ta karaso, aman bata yarda ta zauna ko ta fadi ba, jurewa ta yi a du kuwa da irin
yanda take jinta zata kife kas ta ki bari sai da ta karasa,
Ai kuwa da gudu take neman ruwa, nan ya dakatar da ita ya hana mata ruwan kafin ya firfito mata da micik
micik din idannuwansa ya zazaro mata ya ce" du lokacin da kika yi gudu kar ki yarda ki sha ruwa daga kin
tsaya, hakan na tsayar da zuciya, ki bari sai kin jima sannan ki sha ruwa!

Kai kawai take gyadawa inda baki daya jikinta ya jike da ruwan zufa

Basu gama mayar da numfashinsu ba aka nuna masu wajen da zasu shiga dan jim, (dakin motsa jiki),
A cikin dakin ba abinda babu, sai dai su aka yi masu iyaka da duk wani abinda zai saka jikinsu ya yi tauri
ko hannayensu su mumurde, abinda ake so a nan shi ne, du mai wata yar guntuwar tebarsa, mai wani
lumkilumki a bayansa, da wani mai mundil mundil din hannu du su sabe su zube, slim, su zubar da du wani
teba, ko wace ya kasance bayanta ya fice girman musali akoy itama mashine din dake rage masu tudu ko
fadi, dan haka cikin gagawa aka shiga horar da su, wanda wasunsu har hawaye suke na wahala, basu saba
ba, ba.a saba masu da haka ba,

Haka suka jure sukai ta motsa jiki, ba su su baro wajen nan ba sai kusan takwas, ya rage minti talatin
takwas ta yi aka fito da su,

Tsaye ya yi yana kallon yanda suke haki ya ce " daga yau, kulun, karfe shida ta maku a wajen da muka fita
gudu yau, zan salameku bayan mun gama karfe bakwai da rabi, kunada minti goma na cin abinci, minti
ashirin ku tabatar da kun shirya kowace da kayanta a dakinta ku fito daukan darasi,

Amsawa suka yi a tare sannan kowace ta nufi dakinta cikin gagawa

Tana zuwa ta tarar da abinci sannan da wasu fararan kaya wando da riga suma, sai dai su wandon ne kawai
sake aman rigar daidai take da mutun cicif kuma fara tas,
Ajiyewa ta yi da gagawa ta fita ta je ta kara yin wanka ta dawo dakin cikin sauri ta zurma kayan sannan ta
dauki abincin tana jujuyawa, irin abincin nan ne da bashi da mai cikinsa, sannan ba wani mai nauyi bane,
Kanta ta gyada kafin ta yi bismillah ta shiga ci cikin nutsuwa,
Sai da ta gama ta dubi yar agogon baka dake ajiye saman litafi da byron da aka ajiyewa kowace, nan ta ga
takwas har da minti biyar,

Mikewa ta yi cikin sauri ta fita ta nufi wajen da take da tabacin nan ne wajen karatun,

Sai da ta shige kafin ya juyo wajen ya je office dinsa,


Bakuwar da aka kawo ce ta shigo ta zauna,
Mace ce mai shekaru, dan zata kai shekara hamsin a duniya,
Cikin yannayin kamala da girma ta ce" kamar yanda na fada maka, yarona ne, mahaifinsa ya rasu ya bara
masa dukiya ta mamaki,
Abin dubawar shine, maahaifin nasa kansa kashe shi aka yi,
Mun jima a kasar Misrah, yana karatun kasuwanci da alkur.ani,
Maganar da nake maka a yanzu, a Africa yana daya daga cikin mutane goma sha hudu da za.a zana
sunanyensu a matsayin masu kudin fari,
Damuwata shi ne, ya cika sanyin hali, sanyin hali ne da shi wanda inai masa nuni da abinda nake tsoro shi
baya gani, aurensa biyar, ukun sai dai a wayi gari a ga sun mutu, dayar cikinsu ce mutuwarta ta tsaya min a
rai domin kuwa a lokacin da muke mata wankan gawa wajen wuyanta birdadai ne, sannan cikin akaifunta
abin fatar mutun ne tamkar ta yayagi wani,
Ina cike da damuwa, gashi nima girma sai zuwa yake,
Kanwata ke auren General, ita ta yi masa bayani, shi ne ya saka a kawo ni nan, an ce na zo kawai na bada
bayanin komai ,

Kansa yake gyadawa kafin ya ce" hajia, muna hora Bodyguard maza da mata, sannan muna hora soldiers,
Gwamnati bata biyansu, sai wanda ya daukesu aiki ke biyansu,
Kina da damar zaban wanda ya yi maki , idan macen, namijin , ko kuwa soldier din,

Kanta take gyadawa kafin ta karbi takardar da ya miko mata dan duba kowane adadin farashin daukansa,
sannan ta mike, ta koma wajen motar da aka kawota wace sai da aka saka mata hula aka rufe mata ido
sannan aka ja motar aka fitar da ita har wajen gari kafin take shiga cikin motar da masu tsaronta suka kwasa
suka shiga cikin gari, ta kuma daukan jirgi sai Kanya,

Kenia,

Basu gama mayar da numfashinsu ba aka nuna masu wajen da zasu shiga dan jim, (dakin motsa jiki),
A cikin dakin ba abinda babu, sai dai su aka yi masu iyaka da duk wani abinda zai saka jikinsu ya yi tauri
ko hannayensu su mumurde, abinda ake so a nan shi ne, du mai wata yar guntuwar tebarsa, mai wani
lumkilumki a bayansa, da wani mai mundil mundil din hannu du su sabe su zube, slim, su zubar da du wani
teba, ko wace ya kasance bayanta ya fice girman musali akoy itama mashine din dake rage masu tudu ko
fadi, dan haka cikin gagawa aka shiga horar da su, wanda wasunsu har hawaye suke na wahala, basu saba
ba, ba.a saba masu da haka ba,

Haka suka jure sukai ta motsa jiki, ba su su baro wajen nan ba sai kusan takwas, ya rage minti talatin
takwas ta yi aka fito da su,

Tsaye ya yi yana kallon yanda suke haki ya ce " daga yau, kulun, karfe shida ta maku a wajen da muka fita
gudu yau, zan salameku bayan mun gama karfe bakwai da rabi, kunada minti goma na cin abinci, minti
ashirin ku tabatar da kun shirya kowace da kayanta a dakinta ku fito daukan darasi,

Amsawa suka yi a tare sannan kowace ta nufi dakinta cikin gagawa

Tana zuwa ta tarar da abinci sannan da wasu fararan kaya wando da riga suma, sai dai su wandon ne kawai
sake aman rigar daidai take da mutun cicif kuma fara tas,
Ajiyewa ta yi da gagawa ta fita ta je ta kara yin wanka ta dawo dakin cikin sauri ta zurma kayan sannan ta
dauki abincin tana jujuyawa, irin abincin nan ne da bashi da mai cikinsa, sannan ba wani mai nauyi bane,
Kanta ta gyada kafin ta yi bismillah ta shiga ci cikin nutsuwa,
Sai da ta gama ta dubi yar agogon baka dake ajiye saman litafi da byron da aka ajiyewa kowace, nan ta ga
takwas har da minti biyar,

Mikewa ta yi cikin sauri ta fita ta nufi wajen da take da tabacin nan ne wajen karatun,

Sai da ta shige kafin ya juyo wajen ya je office dinsa,


Bakuwar da aka kawo ce ta shigo ta zauna,
Mace ce mai shekaru, dan zata kai shekara hamsin a duniya,
Cikin yannayin kamala da girma ta ce" kamar yanda na fada maka, yarona ne, mahaifinsa ya rasu ya bara
masa dukiya ta mamaki,
Abin dubawar shine, maahaifin nasa kansa kashe shi aka yi,
Mun jima a kasar Misrah, yana karatun kasuwanci da alkur.ani,
Maganar da nake maka a yanzu, a Africa yana daya daga cikin mutane goma sha hudu da za.a zana
sunanyensu a matsayin masu kudin fari,
Damuwata shi ne, ya cika sanyin hali, sanyin hali ne da shi wanda inai masa nuni da abinda nake tsoro shi
baya gani, aurensa biyar, ukun sai dai a wayi gari a ga sun mutu, dayar cikinsu ce mutuwarta ta tsaya min a
rai domin kuwa a lokacin da muke mata wankan gawa wajen wuyanta birdadai ne, sannan cikin akaifunta
abin fatar mutun ne tamkar ta yayagi wani,
Ina cike da damuwa, gashi nima girma sai zuwa yake,
Kanwata ke auren General, ita ta yi masa bayani, shi ne ya saka a kawo ni nan, an ce na zo kawai na bada
bayanin komai ,
Kansa yake gyadawa kafin ya ce" hajia, muna hora Bodyguard maza da mata, sannan muna hora soldiers,
Gwamnati bata biyansu, sai wanda ya daukesu aiki ke biyansu,
Kina da damar zaban wanda ya yi maki , idan macen, namijin , ko kuwa soldier din,

Kanta take gyadawa kafin ta karbi takardar da ya miko mata dan duba kowane adadin farashin daukansa,
sannan ta mike, ta koma wajen motar da aka kawota wace sai da aka saka mata hula aka rufe mata ido
sannan aka ja motar aka fitar da ita har wajen gari kafin take shiga cikin motar da masu tsaronta suka kwasa
suka shiga cikin gari, ta kuma daukan jirgi sai Kanya,

Kenia,

Zaune yake bakin ruwa, daga shi sai dan gajeran wando , kansa dage , fuskarsa sanye da gilashi,
Yana kallon wajen nan ta yi zumbul zumbul ta nitse cikin ruwan kafin ta dago tana dariya tana watsa masa
ruwan

Shima murmushi yake mata hankalinsa a kanta,

Fitowa ta yi daga ruwan daga ita sai kayan shiga ruwa, ta nufo inda yake tana tafe tana kada jikinta tana
rawar shegantaka, gaba daya bras din dake rataye da mamanta bata wani rufe su da kyau ba,

Haka ta karasa inda yake zaune, ta raba kafafuwanta ta haye saman jikinsa,
Cike da kwarewa da rashin kunya ta shiga rikita masa jiki,
Shi kuwa ya daga kansa ya lumshe idannuwansa yana sauraronta,
Kasa kasa ta yi ta shiga yi masa abinda ya fi so, nan ya bata dama ya saki jikinsa sosai ya takarkare yana
mai karbar sakonta,

Tun tana yi da marmari har ta fara sarewa, ya ki ya saki ya samu nutsuwa ko itama zata huta, gashi dai ita
kawai ke fama , shi bai tabata ba, ba kuma zai shigeta ba!

Sai da ta gama sharholiyarta, dan kansa ya yi niya ya saki abinda take so ya sakin, sai da ta yi ajiyar zuciya
gannin ya samu nutsuwa kafin ta zauna da tissu tana goge masa da kanta,

Idannuwanta take lumshewa tamkar maya ta ce" Man, ka bari mana mu haura katanga plz👏🏻

Dubanta ya yi shima idannuwan nasa lumshe,


Wandonsa ya ja ya saka ya mike daga zaunen da yake ya dauki byro ya rubuta mata chek ya ajiye mata ya
juya ya kara gaba,

Da kallo ta bishi tana ayyana lale ko gobe zata dawo, wannan uwar kyautar a wannan kawai? To da
zagayawa yake da yaya kennan?

Direct dakinsa ya shiga ya zarce bayan dakin nasa,


Yana shiga ya shiga kasan pampo ya sakarwa kansa ruwa,
Wani irin kuna ya ji zuciyarsa na yi, shi dai ba zai yi zina da kowace mace ba, (zinar ta nawa kuma?) Shi
kuma ba zai kara aure ba, domin dai aurensa biyar, mace uku sun mutu, biyun sun guje shi wanda bai san
dalili ba,

Idannuwansa lumshe yana mai jin ciwon yanda yake hayar mata suna zuwa a banza suna kale masa wajen
da ya fi daraja a jikinsa su side da bakinsu ya biya su, yana mai jin kunya idan ya gama wannan lamari,
yana mai jin kunyar Allah, yana mai jin kunyar idan mahaifiyarsa ta kama shi fa? Yana mai jin kunyar a
tayar da mahaifinsa a nuna masa abinda yake yi da kudin da ya tara a duniya, sannan yana mai jin kunyar
kara hada ido da macen da ta gama wannan lamari da ahi tamkar wani mijinta!

Haka ya gama wankan ya fito ransa sai kuna yake, aman mararsa sakai,
Bakin mirroir ya je ya tsaya yana kallon kansa,
Dogo ne shi, mai zubin karfi, baki ne shi dan bashida haske ko kadan,
Kansa koda yaushe cikin askin kolo talll yake, wato zamani na matan dake fadin cewa namiji mai yin kolo
tall is so sexy😢 ,
Bashi da kiba sosai, sannan bashi da tumbi, haka kuma baya daukan karfe
Asalinsama shi mutun ne mai sanyin hali, in ka cire halayarsa na mata shima baya haurawa wai ba zai yi
zina ba , bashi da saje, sai dan gemun da ya bari dan gayu wanda ke shan gyara , fuskarsa mai dan fadi ce,
ya fi kama da mahaifinsa,

Haka ya gama ya fito, nan ya tarar da kiran mahaifiyarsa a waya,

Kiranta ya yi suka gaisa, shiru ya yi yana sauraronta kafin ya dubi agogo ya ce" Ummih, zan zo, aman sai
na yi nafila,

Wai nafilar nan yaushe da yaushe ne kake yinta Abdul?

Cikin sanyin murya ya ce" zan roki Allah ya yafe min ne,

Shiru ta yi, bata san me hakan ke nufi ba, dan haka ta kashe wayar inda shi kuwa ya mike ya gabatar da
sallar nafila bayan isha ya daga hannunsa yana adu.ar Alah ya yafe masa, Allah ya hane shi aikata zina
*KUTKALE*

*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct
NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan
number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, AKOY WA.INDA BASU DA ACCNT, TOH
ZAKU IYA TURO DA KATIN KU TA NAIRA DARI BIYU, MUTANENA NA NIGER KUWA, ZAKU YI
MIN ENVOI NA DALA DARI BISA NUMERO KAMAR HAKA 92777744 AMAN FA TA ORANGE
MONEY.....* taku ce, Sajida😍😍😍😍
7️⃣

*Free page*

Ire iren abinda ke faruwa da rayuwar Abdul kennan, baya iya kwana biyu ba tare da mace ta zo ta sauke
masa nauyin dake kansa ba , idan kuwa ya yi toh zai shiga wani hali ne na takura da rashin lafia, shi kuwa
yaki ya yi aure, shi ke gudun matan, dan kuwa matansa biyu bai san inda suke ba, iyayensu kansu sun
tabatar masa da suna son saki aman kuma basu fadi dalili da kuma inda suke ba, zamani na daurewa yaya,
zamani na soyayar yaya, bai ga laifinsu ba, ya yi masu uzuri ne, rayuwace....

Sai da ya gama abinda zai yi ya mike ya dauki hula ya dorawa kansa ya fito ya nufi motarsa,
Direba ke jansa ya dauki hanya,
Doguwar tafia ce sosai suka yi kafin su karaso inda take,

Suna zuwa ya sauka ya shiga ya samu waje ya zauna yana sauraronta bayan ya gaisheta,
Cikin sanyin murya ya ce" aa, bana so, na yi me da Bodyguard bayan wa.inda ke bibiye da ni a nan gasu
nan har mutun biyar dake karkashina dan kare lafiata? Me yasa kike tsoro har haka ne Ummi? Ki daina , ki
cire tunanin wani na jikina ke kashe min mata, lokacinsu ne ya yi,

Kanta ta dafe, gardama ce yake mata aman cikib sanyin murya tamkar mai fadin maganar dadi, sai da ya yi
shiru ta ce" ban yarda da su ba, mutanen da ka dauka a haka shanshakai? Mutanen da kake biyansu dan
kudin da ba zai yiwu su sadaukar da yaruwarsu dan taka ba? Mutanen da ana iya siyansu ta hanyar basu
kudin da ya fi yawa su ilata ka? Wai kai baka gannin hankali ya fara juyowa kanka dalilin kudadan dake
bankina da sunnanka? Ba niger ba, ba nigeria ba, har saudiya kudinka dake cikin banki sai da ya saka
prince Muhamad ya nemeka kuka gaisa?

Bakinsa ya tabe ya ce" Ummih, Kudi, Kudi, Kudi, Ummi ba kowa kuddi ya rufewa ido ba, eh ana kisa
dalilin kudi, ana abubuwa dalilin kudi, aman ummi dukanama nawa nake? Ban tafasa bama bale na kone,
ba zai yiwu da kananun shekaruna 31 na zauna du inda na saka kafata wani gardi ko wata gardiya na tsaye
kaina wai kareni, adu.o.in da nake basu isa su kareni ba? Ummih, ina da sirri, inada rayuwa tawa, ina yawo
kasashe, ni ba zan zauna da gardi yana tsarona ba sai kace wani soko, haka kuma ba zan wani zauna
sarkacecen kato da ni mace ta yi gadina ba sai kace dan daudu,

Tsura masa ido kawai ta yi, ta san an rina, muryarta ta sanyayar ta ce" aman ka san doguwar tafiar da na yi
dan samo wannan solution din? Ka san yanda nake gagara rintsa ido du lokacin da ka fita da sunnan wai kai
ka tafi nema? Ka nemo me? Ka samo me? Du wanda ka tara ko jikokin jikokinka ne zasu yi wadaka daidai
da zamaninsu, aman sai kace wani kogima na son kari, kuma du abinda dibansa ake kawai ba.a kara masa
watarana zai zama babu,
Shiru ta yi kafin ta kara tausasa murya tamkar itace yar (kun san mutanenmu na yanzu da shegen son yaya
bale yan gayu) ta ci gaba da fadin" kai daya na malaka gidan duniya, yayarka ta mutu, mahaifinka an kashe
min, ya hankalina zai kwonta idan na ga kana rayuwar garari? ABDUL a cikin mota zaku je diner, ka fita
amsa waya ka dawo ka tarar da gawar mace tamkar tana barci,
Tafia ta biyu washe garin aurenka ta tashi da ciwon ciki, itama ta tafi,
Ta uku a cikin gidana, na tarar da gawar yarinyar da an daura aurenku muna saka ran zuwanka cikin satin ,
ni na mata wanka, da idona na ga shaidar jan jan abu wajen wuyanta na kamar an shaketa da wani abu mai
kauri ne,
Mata biyu sun gudu ba tare sa kun yi zaman auren ba domin sun tsinci labarin komai!
Abdul, duka matan nan ba wace ka yi ainahin rayuwar aure da ita, kowace hakan baya tabatuwa ake katse
lamarin, har yanzu shekara 31 baka san aure ba, ka yi aure har biyar, why ba zan damu ba? Danme ba zan
kawo abubuwa a raina ba? Da idonka muka kalli vidon da jirgin da mahaifinka ya watse ciki, yana zaune
kamar an lika shi ne a saman kujerar, da ido yake magana sannan yanda ya zaro ido kamar yana kallon
wani ne ya tsare shi, kamar an sakawa mahaifinfa glue ne an dafke shi, har vidion ya dauke,
Abdul, ka yarda ka ji? Ka amsani

Fuskarsa ya shagwabe, daga inda yake zaune ya tashi ya karasa kusa da ita ya zauna ya kara yin takwaf
takwaf da fuska ya ce" Ummih, ki yi hakuri, ba zan iya yawo da kowa ba, ni rayuwar yanci nake so, bana
son rayuwar shiga hanci da kudundune, ki bar magnar nan kin ji?

Da kallo ta bishi a kasan zuciyarta tana fadin" zaka sauko ne, sai ka yarda in sha Allah, zan yi ta lalabaka
(toh fa🤔 wollah da oo ne, cewa kawai za.a yo kai maza an daukar maka bodyguard, zai amsa da to mama, ba
maganar ehyane😌)

Gidan horo

Sannu a hankali ta gama fahimtar eh lale wannan aiki da aka kawota aka hadata da mutane aiki ne mai
mahinmanci, mai girma, mai hatsari, wanda cikin su su goma sha biyar dan an karo wasu, duka duka mutun
hudu ake so, idan har bata ci wannan Jarabawa ba, to fa zata koma rayuwar KuTkale ne , rayuwar da abinda
ya fi damunta a cikinta irin yanda ko adinninta yake da rauni, sannan ake harin mutuncinta!
Hakan ya sa ta tatara hankalinta, ta maida baki daya hankalinta kan wannan aiki,
Bata ji , kuma bata gani,
Abu mai mutunci a wajenta a wurin nan shi ne!
Suna yin excercise kala kala kamar : Gudu, gymnastic, karin koyon espanol, larabci, inglish, hausa, wanda
shi ke ajiye su class, iya tafia, iya magana cikin sanyi da kyakyawan yannayi, iya saka kaya, kare rayuwar
abokin aiki fiye da taka, iya girki, kai du wani abu na rayuwa ana koya masu cikin kwarewa da hikima,

A haka suka dauki wata uku, wanda zuwa lokacin su bakwai kawai suka rage,
Sai ya zama wata irin rayuwa ta ba mutunci, ba tausayawa dan uwa, uwa uba harin rai, somin kuwa a
bakwai din nan ba wace ke so a cireta, gogagu ne, fitatu ne, a haka aka fara sama masu mission dan kara
tabatar da hazakarsu, mission din da idan sun fita ana biye da dukan wani motsinsu,

A haka wata mata ba za.a kirata datijuwa ba, ba kuma za.a kirata da yarinya ba, ta dauki Hafsat a matsayin
wace zata bata kariya na tsayin wata biyar sakamakon wata shari.a da ta dauka, domin lauya ce mai zaman
kanta, kuma gagarumar yar kasuwa ce, hakama gidansu an tara, tana aikin lauyanci ne dan ya kasance
passion dinta,
Matar bata da aure, aman kuma yayanta biyu wa.inda ta yi adopted,
Tana zaune da su a gida guda inda su kansu sun girma sun zama baban saurayi da budurwa sosai, sannan
suna karatu ne a kasar,

A lokacin da aka gama bata labarin irin aikin fa zata yi, aka bata damar yin tambaya, ta jima tana rubuta
dalilin aikin nata sannan ta dago da kanta ta ce" wace irin shari.a ce ta zata gabatar? Da wa da wa shari.ar ta
hada?

Sai an fada maki sirin shari.ar ko me? Da kike son sannin sirrin shari.at bisa wani dalili?

Hannayenta ta hade waje guda , dogon wando sakake ne jikinta sai riga mai hannaye daidai gwuiwar
hannu, sai hula irin ta mazan nan wace ta yar kofar bayanta ta fitar da gashinta dake daure da dan karamin
ribom, ba wani abin kwaliya a fuskarta ko dis, aman wani sirririn sirin kyau ne a tatare da ita, ita kanta idan
ta mike din zaka yi mamakin wannan yar abar har zara iya kare lafiar wani?
Aman kuma mu je zuwa dai,

Cikin nutsuwa ta fitar da harshenta ta lashi lebenta na kasa, sannan ta fitar da hakoranta na sama ta dantse
leben nata,
Sai da ta yi wal wal da idannuwanta sannan ta ce" wannan bai shafeka ba!
Da mamaki yake dubanta, shi ne bai shafa ba? Shi zata rainawa wayo? Karamar yarinya dan tana ganninsa
a bagas? Dan tana tunanin zama Bodyguard din fake kila wa kala shine har zata fara maida masa magana
haka gatsal? A me ta dauki kanta? Bayan ga mutanen da suka fitar da ita suna jiranta su daga?

Muryarsa ya daga ya ce" ni zaki maidawa magana a haka tamkar wani sa.anki ko wani class dinki? Ko yau
kika fara aiki baki isa ki kamo ni a dukiya ba sai kin yi aikin shekara ashirin na rayuwarki! Shi ne zaki
kalleni ki ce da ni ina ruwana? Kin manta ni ke hora ki?

Datijon da ya daukota daga kutkale, wanda shi ne mai gidansu baki daya ne hankalinsa ya kawo wajen
hayaniyar da SB yake yi, dan haka ya mike ya nufo wajen ba tare da ya yi ma masu jiran nasa magana ba,
Nan matar ta mike itama da dan sauri ta bi bayansa, dan kuwa ba mai hana shiga a kofar,

Cikin nutsuwa daga zaunen da take ta ce" aman ai na ga nan ba filin horo bane bare in bi du abinfa ka ce
ko?

Me ke faruwa? Ya jefo tambayar a dake, sannan fuskarsa ba alamar sasauci

Gaba dayansu suka mike suka sara masa,


Nan ya shiga kora masu bayannin abinda ya faru,

Dubanta ya yi ya ce" baki dauki lesson din ladabi da biyaya bane na maida ke baya ko me?

Kanta ta girgiza tana dubansa ta ce" GN, an yi mana lessin din ladabi da biyaya, kuma an yi mana ta
mahinmancin lokaci da maida amsa wajen da aka yi tambaya da kuma kiyaye yin tambayoyin da basu da
ma.ana!

Ido suka zari su duka, sun gama sarewar shikenan ba za.a dauketa ba, tana zubawa wanda ya horata irin
wannan fitsarar wa zai dauketa? Bayan wannan ai sai ta bata image din wajen, dan kuwa an sansu da bin na
gaba da su ido rufe,

Bai so haka ba, sam bai so haka ba, irin abubuwan da ya take ya kutsa ya tarba dan gannin ya cirota daga
cikin gidan yari, bai so haka lokaci daya ta tarwatsa komai ba, dan kuwa a lokacin da aka yi shari.arta yana
wajen, yana zaune a wajen, shi da shi aka kama dan ta.adar, ya san waye shi, sannan a lokacin da aka bata
damar ta yi magana a kotu magangannun da ta jefowa lauyan suka kara saka shi shakun abinda ake
tuhumarta da shi du kuwa da irin yanda lauyan ya tafi da imanin du wanda ke wajen,
A haka ya ringa bibiyar zamanta a gidan yarin, a hankali ya ringa samun amsoshin wasi wasin da ya ringa
yi kanta, sai dai baban tashin hankali maganar dake dakatar da shi wace kaf anguwar su yarinyar ba wanda
ke mata shaidar arziki, wani idan ya buda baki ceqa yake wa wai Khadija? Ai sunnayenta da yawa
muguwar yar daba ce....
Su sunai haka fasara daban ta irin mugun rashin jin maganarta, da mugunta wajen fadanta,
Iko kuwa zai yiwa maganar fasara daban duba da irin halin da aka kamata aka ce itace da hakan,
Suturar da aka kamata da ita, ba wani dan kwali, ba hijabma sun taimaka wajen bada gudunmuwar rashin
samun tudun dafawa,
Hakan ya saka shi jin tausayin irin hidimar da mahaifinta ke yi, da irin hirarsa dadaya da ya tsinta a
masalaci da aminansa kan yarinyar, ya saka masa tausayi da son yin ceto,
Shi ya saka shi ya kasa zaune ya kasa tsaye, ya hana kansa baci sai da ya samu ya yi convaincre (ya ci
galaba) din wanda ya yanke mata hukunci aka yarda da zata iya wannan aiki, aka bata dama dan karancin
shekarunta da tarin iliminta ana hasashen zata kawowa kasa ci gaba, aka kawota sai gashi du ta shanye
wahalhalun da jarabawar da yawa sai yanzu da za.a fita da ita take faman farke komai a gaban wannan
lauyar da tana iya ja da kowa bata da dar, wanda hakan na iya ja, a yau a yanzu a mayar da ita gidan kason
da bata taka ba, bata karya ba!
Hakan ya saka shi tafka mata tsawa ta hanyar fadin" *LA FERME SOLDAT* (CHUTUP SOLDIER)

Shiru ta yi da maganarta sannan ta kame ta sara masa,


A hankali matar ta karasa shigowa tana dubanta da kyau, sai da ta gama karantarta ta ce" menene dalilinki
na son shiga hurumin shari.ar bayan ke kariya kawai aka ce ki bani?

Shiru ta yi kanta a sade, jikinta kam ya mutu dan karara ya fada mata cewar ta maida hankali, wannan aikin
shi ne tikitin fitarta daga *KUTKALE*,

Hankalinsa ya maida wajen lauyan ya ce" MADAME BILKISSU, ki yi hakuri, zamu maida ita baya mu
bata horo,

Kanta tsaye ta ce " ina son na ji amsar tambayata,

Kallonta ya yi da yannayin takaici ya ce" ki bada amsa!

A hankali ta dago da dubanta ta saka dara daran idannuwanta cikin na matar ta ce" na yi wannan tambayar
ne dan ina son na yi bincike a tsanake kan wanda ya dace na fi saka idona a kansa a harkar aikina,
Shin wa.inda kuke shari.a da su ne? Abokin shari.arki da su ne? Ko kuwa a cikin gidan da kike rayuwa ne?
Ki yi hakuri aman an koya mana cewa mu kasance komai ba jikinmu ya zama idannuwa, kwakwaluwarmu
ta kasance tana aiki kowani lokaci, aman kuma mu tabatar da muna da abinda zamu fi sakawa ido,
Ba nan na nufa ba, ta yiwu wa.inda kuke shari.a da su, kaurin sunansu ya sa aka kalubalance su cewar
menace din da kike samu na za.a kashe ki su ne, mai yiwuwa wani ya fake da haka ne dan ya cinma wani
burinsa,
Makashi, baya bada damar a gyara ko ya yi kisa, makashi na yin kisa ne sai dai kowace wace, an kwana da
sannin cewa ba zaki ja da baya kan ra.ayinki na shari.ar da ta tunkaroki ba, kokonto ne ya darsun mani na
cewa, wanda kike shari.a da shi....anya kuwa mai laifi ne kamar yanda ake hasashen yana iya bi ta kasa ya
tsorataki dan ki bar shari.ar da kike? Ko dai kaurin sunnansa ne ya jaza masa jafa.i?????
Ta karashe tana mai duban GN wanda ta yi maganar kaurin sunna ya jazawa mutun balaki da biyu.....

Gaba dayansu ita suke kallo,


Lokaci guda Madame Bilkissu ta kara shigowa face to face da Hafsat ta ce.......
*KUTKALE*

*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........
*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct
NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan
number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA, ZAKU
YI MIN ENVOI NA DALA DARI BISA NUMERO KAMAR HAKA 92777744 AMAN FA TA ORANGE
MONEY.....* taku ce, Sajida😍😍😍😍

8️⃣

*Free page*

Gaba dayansu ita suke kallo,


Lokaci guda Madame Bilkissu ta kara shigowa face to face da hafsat ta ce" wani diplom gare ki kafin ki
shigo nan?

Zata bada amsa GN ya yi gagawar matsowa ya ce" Confidential ne Madame,

Dubansa ta yi da kyau kafin ta dubi Hafsat ,


Agogon hannunta ta kalla ta ce" ta mini, na fasa cinikin farashin daukan nata, a bani ita a kudin da aka
yanke min,

Ba karamin mamaki hakan ya basu ba, sai dai ba mamaki kadai ba, harda tsoron kar aje da biyu ta yi haka?
Ya kama GN, shi kuwa SB shiga kimtsata yayi yana fadin Allah ya sa kar ta je ta tafka iya yin nata ta
hanyar bada labari har ta tona asirin gidannan!

Haka aka hada mata abubuwan da ya dace, sannan aka bata wani dan abu dan karami aka ce ya kasance
koda yaushe cikin kunnenta, banda wanda da shi dan baya son ruwa, ta kiyaye ruwa ya shige shi,

Karba ta yi ta saka a kunnen nata, wanda zai ringa basu damar jinta da kuma yi mata magana ne, sannan zai
basu damar gyara mata abin gyarawa har dai lokacin da za.a magance menace din dake tunkaro wace zata
kare lafiyarta,

Haka ta je suka shiga mota, nan su duka aka rufe idannunsu suka dauki hanya,
Sai da suka jima sunna tafia sannan aka tsaya,

Cire mata abin idon, hasken ranar da ya tandi idonta da fatar jikinta ya sakata saurin rintse ido sannan ta
kare da hannunta,
A hankali take jin ranar a jikin fatar jikinta har ra iya supportg dinta, yaushe rabonta da rana haka? Yaushe
rabonta da su hade haduwa irin haka da rana? An jima, a gaskiya an jima, sai tace tun da aka daukota daga
*KUTKALE* ,

Lauyar na kallonta ta ce da ita " mu je,

Bin bayanta ta yi suka nufi motar da ta zo da ita,

Har zata saka ky ta bude motar su shiga, Hafsat ta yi gagawar dakatar da ita,
Ky din motar ta karba tana dubanta kafin ta ce" duniya ta ci gaba fiye da tunaninki,
Ana saka yar karamar Bomb wace zata daki wajen gidan mai ta tayar da mota cikin kankannin lokacin da
damar da gareka kawai ta ka saka kys din motar ka juya kys din ne,
Ki matsa,
Da mamaki take kallon yarinyar da ta tabata ta haifeta da cikinta, aman wama ya san da ta zo wajen nan
imba gidan Oga da ta fito ba wanda ya sakata zuwa nan ta tsaya za.a dauketa?
Ko daga gidanta danta kawai ya farka, da ta shiga dakin Joli tana ta magana aman ina nauyin bacin nata ya
yi nisa haka ta fito ta yiwa Kader salama ta tafi,

Kai, anya kuwa? Ta yaya? Ta ina? Muna dai samun bindigogi a kasa, irin wadinnan miyagun kayan aikin ai
sai wajen manyan miyagun mutanen,
Sai dai ba zata hanata ba, ba zata yi mata katsalandan a sha.annin aikinta ba, zata bata dama ta warware
basirarta .....

Cikin jakar bayanta ta ciro wata yar sanda karama wace ta danna wasu butons jikinta sai ga abin ya dan
kara tsayi,

Zuwa ta yi ta kara shi daga kasa wajen gidan man,


Wani dan kara abin ya fara yi tsut.tsut.tsut....

Dakatawa ta yi tsai tana jin irin ihun da GN ya yi na fadin" Yes, Yes, Yes,

Tsayar da murnar gannin abinda ta samo ya yi dan har yaren sun fara taruwa wajensa,

A hankali ya ce" ki jata ku nemi motar haya ku karasa inda zaku, zan turo a cire,

Bata bada amsa ba ta je wajenta ta damki damtsen hannunta na hagu ta shiga tafia da ita,
Da yake itama mai ilimi ce, kuma ta san da ganganci hakan ba zai faru ba sai da kwakwaran huja, dan haka
sai ta bata haddin kai suka shiga tafiar gagawa har ta tsayar da motar da ta yarda da ita suka shiga suka
dauki hanya,

Sai da suka fara tafia ta samu kira daga wajen danta, tana dagawa ya ce" Mam kuna ina ne? Ni yinwa nake
ji,

Amsa ta bashi da gatanan zuwa gida ya dan yi hakuri kadan, ina yar uwarsa ne? Ta farka?

Cikin shagwaba ya ce" ta farka gatanan sai kumburi take wai kin tafi baki tasheta ba,

Murmushi ta yi ta ce" ganinan, sai na zo,

Haka suka kashe wayar, kiran GN ya shigo wayarta ta daga,


Tana dagawa ya ce" Madame, za.a kai maki motarki cikin gari sai ku karasa da ita gidan, an cire bomb din

Cikin mamaki ta ce" da gaske an samun kuwa?

Amsata ya yi da" eh, bayan fitarki a motar aka sakata,

Doguwar ajiyar zuciya ta sauke, ta saci kallon Hafsat ta ga tsai kale kale take ta ce" to aman ya aka yi ka
san gida muka nufa?

A nitse ya ce" ki yi hakuri, zamuna jin du maganarki ta waya da du wanda ya yi kiranki, haka itama mai
baki tsaron zatana jin komai,

Kanta ta gyada ta kashe wayar,


Sai da ta ajiye wayar Hafsat ta ce" daga yanzu har zuwa lokacin da asirin mai bibiyarki zai tonu kar ki
kuma fadawa kowa inda kike, ko abinda kike shirin yi,
Da kallo ta bita, ita kam yanzu ta kara tsorata da lamarin mai bin bayan nan nata, harda Bomb? Me ya yi
zafi har haka? Idan kuwa shari.ar nan ce gwarama ya yi da aniya dan ba zan barta ba!

A hankali ta ce" y'ayana ne,

Eh na sani, Muhamad kike kiransa da boy, yaro saurayi dan shekara ashirin da takwas sai wace keda suna
Mardiya kina kiranta da Joli mai shekara ashirin da tara, kin dauko su a gidan marayu na Garin dutsi,
dukansu farare ne , yarinyar bata da jiki sosai, namijin ya fita jikin girma duda ta girme masu,

Dan tsagaitawa ta yi ta juyo tana duban yanda ta cika da mamakinta ta ce" kina yi masu so na hakika, bakya
hada su da kowa,
Da kyau ta kara saka idannuwanta cikin nata ta ce" *harda su nake nufi*

Lauya take, babar lauyar da ko lauyoyi suna tsoron karo da ita, saboda nacinta kan gaskiyarta, tsayuwarta
kan kafafuwanta,
Aman a yau sai da gabanta ya fadi yannayin yanda yarinya karama irin wannan take tsaye kan abu, sannan
ta iya duban idan mutun ta nanata gaskiyarya,
Ina, ta ji wani shayin yarinyar, da son sannin wacece ita ya darsun mata,
A haka har suka zo inda tace zasu sauka,

Da suka sauka wani lamari ya so ya shagaltar da ita, ba komai bane sai ganninta a waje, gata a filin Allah,
da kafafuwanta, da ranta, tana shakar numfashi,
Inama inama, inama zata iya gannin koda wulgin mahaifinta da tawagarsa ne? Inama zai bilo ta gabanta a
daidai wannan lokaci?
Sai dai ta sani karfin jini da haihuwa ne zai saka ya gane wada ke gabansa, a yanzu haka idan ka ganta zaka
yi tunanin irin fararan fatar nan ne wato nasaru,
Kanta ra saka hular gashi mai ruwan fara kar wace tamkar gashinta dan kuwa baba ce mai tsada kuma an yi
mata baban dinki,
Idannuwanta sanye da bakin gilas,
Lebenta sanye da jan baki ja mai haske,
Tana sanye da suit bakake sai farar riga a ciki,
Hannunta rike da jakar aikinta,
Daga ciki jikin wandonta da yar karamar bindigarta a hade da bel din wandon jikinta

Sau hudu kennan GN na kama sunnanta, kafin ya daki table din gabansa da hargagi ya ce" BD O1 ki bani
amsa!

Da sauri ta zabura ta amsa shi,

Nan ya ce" ki nutsu, kina cikin tafe ne a hadari, ki tabatar kin sadata da gidanta lafia,

Sai a lokacin ta farfado da kyau kafin ta juya wajen Madame ta je da sauri ta shiga motar ta yi mata ky,

Bismillah ta yi a ranta kafin ta dubi JPS ta fara neman gidan matar da kanta sannan tukinta ne na fari a
cikin gari dan haka ta tafi a hankali har suka karaso...

Tana tsaye wasu jibga jibgan y'aya suka fito a sangarce dan tarbanta,

Dakatar da su Hafsat ta yi ta hanyar su gaisa nesa da nesa

Da mamaki gaba daya suke kallonta,


Uwar ta ce" ah no, ba zai yiwu ba, y'ayana ne fa, kice ba zan rungume su a jikina ba?

Maganar da aki mata ne ya sakata dan ja baya tana kare masu kallo irin yanda du suka rufeta da
tambayoyin me hakan ke nufi? Wacece wannan? Me ya kawota gidansu,
Reaction dinsu ba wata bace sai nuna tashin hankalinsu na ana bibiyar rayuwar mahaifiyarsu, daga nan
suka rankaya baki daya ciki,

Sosai ta cancanzawa yannayin dakin Madame Bilkiss zama, kwata kwata ta canzawa du abinda zai sadata
da tagar dakin yannayi, karshema ta rufe tagar da bakin zannin da zai hana maka damar gannin na ciki ko
abinda ke faruwa,

Ita dai kallonta take, tana karantarta, har ta gama komai ta gama caje dakin da komai sannan ko abincin da
zata ci ita ta dafa ta kawo mata kafin take yi mata salama ta fita,

Ko da ta fita ba wani inda ta je sai nan kusa da dakin da ta tsaya,

Kwonci tashi, haka suke rayuwa, du zaman da za.a yi a kotu tare da ita ake yi, inda take shige da arniya
domin kuwa sam ba.a bari ta yi shigar da wani zai ganeta ba,
Sosai take takatsantsan kan lamarin aikinta,
A haka ta shiga jikin mutumen da ake karar ya yiwa yar yarinyar fyade, ahi kuwa mai kudi ne dan haka
yake son batar da shari.ar,
A hankali ta ringa gane abubuwa, ta ringa taro abubuwa,

Wani dare Sahun kafa ya dauke,


Shiru kake ji sai dan kukan tsuntsayen tsakar gidan,

Gilmawar da ta gani daga can lungun dakin baby ya sakata sakawa wajen ido,
Shiru ne ya dauka na lokaci mai dan tsayi, dan haka cikin nutsuwa ta duduba inda take tsayen ta kara duba
eh lale dakin Madame a rufe,
Dan haka ta jakuda daga kofar a hankali ta bi hanyar da ta ga motsi,

A hanlai take tafe cikin sanda tana dudubawa, har ta karaso kusan dakin Boy,

Ja ta yi ta tsaya jin alamar motsi ,

A hankali ta kara abin jin maganar mutun ko daga bayan kyaure ko daga nesa ne a jikin kofar dakin ta kasa
kunnenta,

Magangannu ne kamar haka........


Ba ita ta haife mu ba, ba uwarmu daya ba ubanmu daya ba da kai, dan me zata hana mu rayuwa tare?
Dan me zata hana mu rayuwar soyaya? Ni ina son ka, da soyayarka na tashi, kaf duniya du wanda yace zai
rabani da kai, koda kuwa kai ne, na rantse da wanda lumfashina ke hannunsa sai inda karfina ya kare!

Ya zaki ringa magana irin haka a kan macen da ta dauke mu daga gidan marayu, ta bamu tarbiya, ta kawo
mu jikinta, ta ririta mu, ta daga martabarmu, ta nuna mana soyaya daya da ba hadi? Ya zaki yi kokarin
bijirewa maganar macen da take tamkar mahaifiyarki?

Ta dauko mu ne dan bata haihuwa! Da tana haihuwa kana tunanin kafarta zata je inda muke ne? Da tana
haihuwa tsakaninmu da ita sai dai ta bamu sadaka a titi!

Aman nawa basa haihuwar basu nemi talafawa marayun ba? Saurara, ni fa ba butulu bane, tunda muka
nuna mata muna son juna ta kiya ni fa na daina wani son ki, daman ke kika koya mani taba sashin jikinki,
kika koya mani abubuwa, ki barni na yi mata biyaya dan ni uwata ce!

Cikin dan daga murya ta ce" ni bata haife ni ba! Kuma bana sonta dan tana son raba ni da nake so! Shi
yasa ka daina taba ni? Shi yasa ka fara yan mata? Kar ka tsoma kanka abinda zaka yi dana sani, dan kuwa
nan ba da jimawa ba zaka zama nawa!
Tana gama fadar haka ta nufo fita da mugun sauri.............

Kallonta yake yanda take rawa da jigidar dake daure a kugunta,


Cikin kwarewa da iya juya kugu take taka rawarta tana bada cas cas cas, haka kuma na kafarta suma suke
bada kida,

Sau uku kennan sai ta zo kusa da fuskarsa ya shaki kamshin jikinta ya miko hannu zai cire bras dinta sai ta
ja baya ta kuma dauki rawar jan ra.ayinsa zuwa aikata alfasha

Wannan dawowar da ta yi, cikin kwarewa a barikanci ta saka hannunta ta kunce dan yololon abin da ya
kasance wanda ya hade bakin dan pant din dake jikinta ta yar sannan ta karasa ta haye jikinsa tana rawar
iskanci,

Cikin sanyin murya bayan ya riko hannunta ya ce" shuiiiit, ki bar mani hayaniya kar ki saka ta kwonta!
Kamar ba shi ya yi mata maganar ba ya yi mata wani mahaukacin riko, da wani irin karfin da a yannayin
maganarsa ba zaka taba sakowa ranka shi din nan Allah ya hore masa wannan karfin ba, duba da yannayin
hutu dake sakashi magana a yangance da kuma sanyi, wai kuma yannayin rikon bai nuna alamar ya saka
wani karfin a zo a gani bane

Bras din dake jikinta ya bale sai dai me ciko ne ya fado,


Ashe tudun nan na sama da ya saka saman cika ya batse gaba daya ciko ne ta yi daga kasan ta turo saman,

A hankali ya sasauta mata rikon, harma ya saketa baki daya,


Cikin salon karuwanci ta nemi komawa jikinsa tana wani laudi ita ga zata jashi koda ya ga sirrin cikonta,

Riketa ya yi ya zaunar da ita suna kallon juna ya ce" ke musulma ce??

Tana kane ido daya tana turo yan berayan kirjinta ta girgiza masa kai , amsar eh ita musulma ce,

Habarsa ya talabe da hannayensa ya ce" yanzu karuwancinma ba zaki yi da gaskiya ba? Ai musulmi an
sanshi da gaskiya ko? Ya zaki cika taunman pant a nono ki ja ra.ayin maza? Haba cutar ai ta yi yawa, kina
tunanin idan kasanki nake so zan zauna kina min rawa ne?
Ni bana zina....aman ina son mata,
Mata ababaden so ne,
Kin san me idan na ga mace wace ta amsa sunnanta nan da nan wannan take mikewa, idan kuwa muna
mata ne lafewa take kara yi ta yi kwonciyarta,
Mata duka suna da kyau, sai dai wace ta iya gyara ta fi kowace kyau,
Kin ga bariki ta shaida ki, ji yanda nononki ya dawo dan Allah in dai ba dan da kika haifa ba ya sha dan kar
ya mutu ubanwa zai sha wannan yangom din?

Shiru ya yi yana duban irin yanda ta saki baki tana dubansa,


Murmushi ya yi cikin sanyinsa ya ci gaba da fadin.....

(Ku fa gane, ya fito a wani irin mutun marar sirin baki, sam sam bakinsa bashi da birki, magana zai saketa
ne son ransa )
*KUTKALE*

*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*
Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct
NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan
number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA
SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN
SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN,
.....* taku ce, Sajida😍😍😍😍

9️⃣

*Free page* daga page 10 an gama free

Cikin sanyinsa ya ci gaba da fadin" dan Allah ku yiwa kanku adalci, yanzu ke kin je kin yo shafe shafenki,
kin cika hoda ta kara janye fuskarki, kin zagaye lebe ya zama dan dagwas, da a duhu zaki zo mini shikenan
kin ribace ni?
Duba ki ki ganni, fatar jikinki ta fara janyewa irin alamun shekaru sun tarun nan aman dai har yanzu
wannan bata isheki ba?
Ya fada yana mai nuna .....dinsa,
Manyan idannuwansa ya daga sama kafin ya maido kanta ya ce" da yarintata yanzu ni hariki ta yiwa
wulakanci na kale tsohuwa tas har ina shirin mika mata abuna ta yi wasa!
Gaskiya baki yiwa bariki adalci ba,
Ki saka kayanki kin ji? Ba zan iya rike wannan takalman ba,
Ya fada yana mai nuna kirjinta,

Gaba dayanta ji ta yi ta muzanta, so take a hakanma ta kara jan ramayinsa, sai dai ina, ba wani hayanniya
ya yi mata ba, aman tana tsoron ta ga hayanniyar tasa,
Dan haka ta mike jikinta na dan rawa ta saka bras dinta, ta nufi wajen kayanta tana faman du ta maida , ta
tsinci muryarsa ya ce" menene kika zuba cikin kofin maltina na?

Gaba daya jikinta ya dauki rawa, inda ta juyo a firgice, gabanta ya yanke ya fadi, gaba daya ta rasa bakalin
kwarewa a barikin da ta yi, gaba daya ya wani hautsina mata lisafi ita dake dakon wannan ranar bisa
biyanta da aka yi kan ta cin masa, sai gashi kamar da wasa gawo na son juyewa da mujiya, yana son karfi
da yaji sai ya ladaftar da haukanta a nitse,

Inda inda ta fara, kafi ta sakar masa murmushi ta nufi wajen kofin ta dauka ta ce" oga, abin karin karfi ne
na zuba maka dan mu ji dadin rayuwa, tunda ka fasa shikennan,

Murmushi ya yi yana shafa gemun gayun da ya ajiye yana dubanta a takaice ya ce" to shanye,

Me? Ta fada tare da zaro ido a lokaci daya kuma ta saki kofin gaba daya maltinar ta zube kasa,

Da ido ya bi farin tiles din dakin nasa da kumfar Maltina ke ta yi kafin ta farfashe sai ruwan maltinar, a
hankali ruwan ya dan gangara hakan ya sa ake gannin color din maltinar daga maroon mai duhu ya dawo
wani jajaja ,

Kallonsa ya kai kanta, ya girgiza kai, ya ce" dauko abin gogewa a wancen wajen,

Wajen da ya nuna mata ta je da sauri ta dauko abin gogewar,


Karba ya yi a hannunsa kafin ya duka da wani dan kofi ya dibi kadan, sai kuma yace goge,

A tsorace ta goge tana hankalce da na hannun nasa,

A hankali, cikin sanyin murya ya ce" ki goge da kyau, bana son kazamta ni, ki kwontar da hankalinki, ji ba
zan iya kisan kai ba, wannan laifin bana so na tafka shi gaskiya,
Ke yanzu dan rashin imani kashe ni ne kika zo yi, da maganin da ake zubawa bera? Ina laifin ki kasheni da
abu mai tsada tunfa dai kin ga mai tsada ne ni, kuma fisabililahi dan rashin tausayi mutuwarma a gabanki
kike so na yi? Wannan fuskar taki mai shige da ta dan iskan bunsuru kike so ina kallo har raina ya fita? Ina
wa laifin ki turo yar yarinya wace komai ya ji, na more idan na gama sai in mutu ina kallon jan lebe da gira
mai kyakyawan gashi? Aman kuri da ido ya na yan shaina kike so ina kallonki har na daina motsi? To ta
Allah ba taki ba, tashi ga kudinki ki tafi kin ji? Ki canza sa.a tun kafin ki karasa zama karyar yan bariki.

Ita kam zuwa wannan lokaci lamarinsa ya girmami tunaninta, da sauri ta gama gogewa da hannunta ,
sannan ta dauki takardar da ya ajiye mata na kudin da zata dauka, jikinta na bari sannan sanyi kalau ta fice
daga gidan wannan bawan Allah mai cike da abin mamaki, tabas da wuya a cin masa, ya kasance wani irin
mutun mai wasu halaya masu wuyar fasara, ingarma ne, tsayaye ne mai sanyin magana, hutu ya saka shi
abin tashin hankalima shi a shanshakai yake dubansa, ashe du haukan da take ya ganta?

Wayar da aka kirata da ita dan bata kwongilar kashe shi ce ta shiga kara,
Sai da gabanta ya fadi a lokacin da ta ga kiran,
Sun bata rabin kudin aikin zasu cika mata rabi idan ta gama, da sharadin ta kuka da kanta idan sunnansu ya
fito ko ta kasa cika aikinta,

Jikinta na rawa ta wurga wayar cikin kwondon shara ta canza hanya tana yi tana dudubawa kar a cin
mata..... wannan kennan

Ya jima tsaye jikin window din dakinsa na baci,


Tsakar gidan kawai ya tsurawa ido yana hangen mai baiwa fulawowin gidan ruwa da kuma daidaita su,
A ransa yake ayyana shi kam wannan hankalinsa kwonce, ba zai kwonta da tunanin kudi ya kuma tashi da
tsoron fita ba, bashi da wata damuwar da ta fi ya samu yan na kashewarsa ya kashe ya baiwa matarsa ,
burinsa na gaba daya tsayin rayuwarsa basu fi adadin sadakar da yake badawa ba,
Gashi saboda *Kudi* yana haduwa da abubuwan rayuwa kala kala,
Menene na gagawar? Dan adam, menene na zakuwar?
Ya aka yi baya iya hadiye zalamarsa?
Mutuwa ai mai zuwa ce, idan ka yi hakuri zan mutu....koda kai baka ci ba sai ka yi iya yinka iyalinka su ci
ko? Tunda ka rantse sai ka ci haram,
Idan ka yi hakuri, shekara talatin ai an raraka, me ya yi saura? Idan na jima na kara saba.in a kai...
Wani murmushi ne ya saki kafi ya shafa kolon dake kansa tal tal ba digon gashi a sama ya yi baya baya ya
fada saman bed dinsa ya lalubo wayarsa ya shiga duba hotunna a Instagram, ua ga wace ta masa, ya tura
mata adireshinsa kawai, koda ba yar kasar bace ta biyo jirgi, dan kuwa ba zai iya rintsa idannuwansa
mararsa da wannan nauyin ba, shi kuwa ba zayana didikar mqgani ba har ya je ya bata mararsa! ......
(ALLAH YA SHIRYE MU)

Da wani irin gudun da ta jima bata yi ba, gudun ceton rai ta bar wajen,
Tana zuwa kofar dakin Madame Bilkiss ta ja ta tsaya tana maifa ajiyar zuciya,

Kyam ta yi tana duban waje guda, gaba daya du wani huja dake tatare da ita ne take hadawa kafin ta bi Joli
da kallo har ta shigewa ganninta

Ajiyar zuciya ta sauke , ta ci gaba da aikinta kafin lokacin da ya dace ta kwonta ya buga, sai dai ina , bata
tunanin zata iya rintsawa a wannan lamarin!

Washe gari bayan Madame bilkiss ta shiga office dinta ta gama caje komai ta fito ta nufi bakar motar dake
jiranta,

Tana shiga bata yi magana ba sai takarda daya da ta mika masa,

Ya jima yana duba takardar sannan ya dago da wanni yannayi ya ce" menene hujarki ta fadin wannan
gagarumin abin? Kin san da idan har ba haka bane, hakan na nufi da ja da kungiyar lauyoyin garinnnan? Da
masu kare mutuncin su, da dukan wani mai nuna tausayinsa kansu? Kin san da bamu da karfin ja da su a
haka?

Kai tsaye ta ce" huja kake so? Bani da ita GN, bani da hujar da zan daki kirji na nunota a fili, sai dai ina so
ka taimaka kamar yanda na roka, wannan number, itace ta karamar wayar da na samu a dakinsa boye cikin
karamin wandonsa,
A saka a cire layi daga cikin layin layikan da ba za.a iya jin hirarsu ba, sannan a saurari abinda suke fada,
Zuciyata ta bani amanar hakan, na yarda da hakan, kuma in sha Allah gaskiyar lamari na cikin nan,

Number dake saman takarda rubuce ya bi da kallo, kafin ya bi bayanta da kallo har ta bacewa ganninsa, ta
koma bakin aikinta,

Jujuya takardar yake a hannunsa, cikin zuciyarsa ya kasa yarda da irin girman abin da ta kawo,
Sai dai me, ba zai yar ba, zai saka a bi a boye , idan har hakan ne shikenan, duniya ai ba abinda bata gada
ba.

Bayan kamar kwana biyu,


A lokacin , a lokacin har an gama shari.ar an yanke hukunci daidai laifi,
Suna zaune a fallo suna shirin cin abincin da Joli ta girka da kanta, sai zumudi uwar take cikin murnar
jolinta ta fara shiga kicin da kyau,

Har an zuba abincin za.a fara ci , Hafsat dake tsaye tana kallonsu Joli ta duba ta ce" wai Mam, ba kun gama
shara.ar ba, me kuma wannan abin ke yi tare da ke gar yanzu?

Uwar ta kai dubanta wajen Hafsat, ta ga tsaye kawai take, yau ba gilas din, aman duda haka wani sirri ke
tatare da yarinyar, wanda tana so ta san menene shi, tana son sannin wacece yarinyar da du abin shagalta
baya dadata da kasa, menene duhun da ya mamaye mata ranta bayan gata yar yarinya, yar karamar attajira ,
domin a wannan aikin kadai da ta yi ta tara kudi na mamaki, idan aka cire percentage din ma.aikata wanda
zai zama nata ba kadan bane, ko tunanin wannan baya sakata irin ka ganta tana ta murna,
A hankali hafsat ta matso sosai kusa da Madame bilki dake son kai abincin nan bakinta ta ce" ashe shi mai
bincike, idan ya tashi idonsa na kasa gannin amsar da yake nema a gaban idonsa?

Dago da kanta ta yi tana duban Hafsat, ta sani ne, farin sannin cewa, bata maganar da bata da ma.ana ko
wace bata shafi aikinta ba, tunda suka hadu, kusan wata hudu kennan, bata taba koda wasa shiga hurumin
abinda bai shafeta ba, du irin cin kashin da joli ke mata kuwa bata taba koda nuna ta san da ita a wajen ba,
aikinta ta zo yi, tana kamanta yinsa da dukan gaskiyarta, dan haka maganar da ta fada ya saka madame
Bilkiss cikin dan gajeran tunani,

Kasa gane komai ta yi, ta kuma dauka da niyar kara kai abincin bakinta,

Da sauri ta ce" idan kika ci abincin nan, zaki tashi normal ki je dakinki, harma zaki yi wankan minti goma,
shafa.i da wuturin minti goma sha biyar , shirin bacin minti biyar, ki kwonta ki fara baci, cikin bacin da bai
fi na minti ashirin ba zaki ji gaba daya an hade hanjin cikinki,
Zaki farka da sauri domin takurewar ba ta wasa bace, zaki nemi mikewa ki sha ruwa,
A lokacin da kika sha ruwa, dan lokacin karasawarsa cikin cikinki wajen wannan shinkafa da kika hadiya
zai dauki second biyar *kacal*, daga bakin wannan lokacin numfashinki zai nemi gagararki, a hankali a
hankali zaki fara fitar da wata kumfa mai kalar shudiya, a haka zaki ringa kaiwa kasa har ki zube kina ihun
kiran Bodyguard, aman muryarki bata fita dan ya ci karfinta, cikin haka zaki tafi ta hanyar birkidodoniyar
da zata goge kumfar da kika zubar da kashin da za.a dauka du na zafin fitar rai ne, a haka zan shigo na tarar
da gawarki, wanda zata nuna min maganin hawan jinin da likita ya rubuta maki a kasar faranc me kika sha
mai yawan da ya hadasa maki haka har kika rasa ranki a lokacin da ni sauna nake kofa tsaye dan zama mai
kare lafiyarki..........

Gaba daya wajen, su su uku ne dama, domin Boy bai fito ba tukunnan yana daki, wajen gaba daya tsit ya yi
kafin cikin matsanancin faduwar gaba madame bilkissu ta saki cokalin tana dubanta ta mike tsaye ta ce" ke,
me kike nufi haka? Me menene wannan din kuma?

Hafsat ta yi murmushin da har cikin ranta yannayin da ta nuna ya bata dariya, bata son mutuwa wai ita
wannan? Ikon Allah, yanzu ita bata so ta mutu, so take ta yi ta rayuwa cikin jin dadin nan har yaushe? Har a
busa kaho ko me?

Murmushi ta kuma yi ta ce" aa, bafa mutuwar bace Madame,


Wai yanda aka tsara lamarin karshenki ne na baki a takaice,

Wata irin tsawa ce ta daki kunnayensu daka wajen matatakala, ashe Boy ya sauko yana sauraro,
Jikinsa na rawa ya karaso yana dubanta ya ce" kashe mini uwa zaki yi? Wannan wani irin banzan zance ne?
Tunda kika zo gidannan dai abincin oder ake ci dan kin kori yan aiki na odernma ke ke kawowa dan baki
yarda da kowa ba, idan kika fadi haka, wannanma na yau ke kika kawo shi, kennan kece zaki kashe min
uwa ko me?

A nitse ta ce" aa dan jaririn mamansa, ba.a kai ga wanda na kawo din ba kennan,

Ni ne jaririn? Ni ne jaririn? Ya fada da hargowa yana dubanta yana matsowa da niyar kai mata duka

Da sauri madame bilkissu ta tare shi ta riko hannunsa ta maido shi kusa da ita tana duban yannayin Hafsat
ta ce" ki bani haske kan maganarki , a kan aikinki kike kar ki manta,

Hafsat dake sauraron maganar su BS da suka karaso da police ta kai dubanta wajen Joli dake tsaye itama
gaba dayanta, du wani alama na rashin gaskiya ya bayana a tatare da ita ta ce" bomb da aka saka a motarki,
ta sayeta ne da makudan kudin da kike sakar masu a acct, ta hanyar kawarta dake da yaya dan fashin boye,
wanda yake harkar miyagun makamai a boye ,
Bata cinma burinta ba na kashe ki ta hanyar bomb, ta siyi dan sholisho kan ya soka maki wuka, wanda mun
fito daga alimentation ya shigo mu da gudu da wuka na karbe, wannan ma bai mata ba, ta so ta buga
zuciyarki ta hanyar kiranki tsakiyar dare ta fasa maki kuka dan ta san kinada mugun hawan jinnnin da tabas
damuwarta na iya tada maki ita.......
Wannanma ba.a samu galaba ba, shi ne aka gwada ta jus jus, shima du na canza su, yau aka gwada ta
hanyar yin Fride rice, abincin da kika fi so,

Wai wai wa kike nufi? Ya zaki ringa magana kina duban Joli? Me kike nufi?

Karan laluwar da ya karade anguwar harma dake nuni da cikin gidan yake nufowa ya saka Joli sakin marfin
glass na kwannon cin abinci ta juya da gudu ta nufi waje da niyar neman inda ta tsere,
Wata irin juwa ce ke neman kayar da ita, nan da nan boy ya tareta a jikinsa, jikinsa na rawa da mamakin
wai da da gaske da take cewa zai zama nata niyarta ta kashe matar da ta dauketa ta mayar da ita mutun?

Magani ta balo wanda dama ta san a rina ta mika masa ya saka mata a baki , aka bata ruwa sannan aka
jinginar da ita inda gidan ya rikice da hayaniyar kama Joli,

Idannuwanta da sukai mata nauyi ta daga ta dubi boy, muryarta na rawa ta ce" Boy, kace min karya ne ka
ji? Kace min ba haka bane, me me ya sa ? Me yayi zafi Boy? Ashe dama makashina na tare da ni? Me na yi
da zafi haka boy?

Boy ya sada kansa yana kuka kamar yaro gannin yanda mam dinsu abu ke cinta har zuciyarta,

Wani abu Hafsat ta ji a ranta, tausayin matar, tabas ita fa a matsayin yayanta na cikinta ta dauke su, idan
kuwa har haka ne dole ta ji mugun mikin da zai yi barazana wa numfashinta,
A hankali ta matso kusa da ita ta tsaya ta ce" ke fa lauya ce hajia, kin yi shara.ar da ta fi haka gigita, dan
yau ya zo a kanki idan har kika yi hakuri zaki bada exampl wa duniya,
Ke kika bani kalmar dan adam mugun ice ne,
Ni kuwa zan kara maki kalmar Allah na jarabtar bawa da abubuwa da yawa, ciki kuwa harda raba bawa da
abu mafi soyuwa a ransa, yaya ne, iyaye ne, kudi ne, mata ce, ko miji ne...da dai sauran su,
Da ciwo, aman kar hakan ya zama sanadiyar rugugewar tsayayiyar lauya mai kare yancin matan garina👏🏻

Kallonta kawai suke gaba dayansu, har BS ya shigo falon,


Nan ta mike ta sara masa tana dubansa har ya bata izinin tana iya sauke hannunta,

Likitan da aka zo da shi ne ya karaso aka kama Madame bilikiss aka dora gado na turawa aka fita da ita,.a
takaice dai kafin su bar gidan sai da suka daidaita komai, suka kwashe komai na dakin joli dan karin
bincike suka bar gidan tare da Hafsat

Sai da ta yi wanka ta mike saman gadon dakinta da aka maida su masu gadaje ta lumshe idannuwanta,
Maganar BS ke dawo mata, ashe zasu shirya da shi? Lale duniya, .........

Ummih, bafa zan zauna kato na take min baya a dukan motsina ba, haba ummih ba zaki bar maganar nan
bane?

Zama ta yi kusa da shi tana dubansa ta ce" kana so na mutu?

Da sauri ya dago da dubansa kanta shima yana dubanta , murmushi ya sakar mata, sak yanda take masa
yana yaro idan ya ki yarda abu, tsoron hakan ke saka shi amincewa da koma menene, shine yanzuma zata
yi masa,

Hannayenta ya riko yana dubanta , ya ce" idan kin amince da abu daya, zamu je tare da ke, a bani na zaba,
aman fa mace, a bisa sharadin zamu baro wajen da sunnan matata take, dan kin ga zata zame min karfen
kafa, du inda na shiga zata ce sai ta shige itama, zamu ringa kwana gida guda.......
Ni ban ce zan yi wani rayuwar aure da gardi irina ba, dan kuwa du macen da ta san ciwon kanta ba zata
dauki kafa wai ita ta je ta yi gudu ta shiga duniyar mazajen daga tace itama yar dagan ce na iya kallonta ba,
aman saboda irin rayuwar da ake a nan, da irin yanda aka cakulu ake cakuda abubuwa, ga auren nan da
kika saka a yi na yarinyar nan, kin ga zan so ta bata tsaron, aman wai ba ni ba, aman kuma a matsayin wace
zata fito a Bodyguard kuma matata

*Wannan cakwakiyar fa? Mai yiwuwa ce? Yan matan Bodyguard, damar au yi auren ana nufin irin
wannan ko me? Idan irin wannan ne daman ana iya aure haka? Aure dai ai aure ne, ana iya rayuwar aure da
su normal ko yaya? Irin matarka ce idan ta raya maka matarka ce?..............mu je zuwa karatun Kutkale*
*KUTKALE*

*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct
NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan
number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA
SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN
SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN,
.....* taku ce, Sajida😍😍😍😍

*Free page*
*Alhamdulilah, nan na kawo karshen free page...du mai son ci gaban Kutkale ya garzayo ta hanyar biyan
nasa ya samu shiga cikin grup din*

Ta jima tana auna maganarsa, kafin ta janye hannunta tana harararsa,

A dan kufule ta ce" a ina aka taba yi? Dama an tana haka? Wace za.a dauko dan ta tsare lafiarka kace sai an
daura maku aure? To danme ma za.a wani aura maka yarinyar? Ka yi yaya da ita?

Kansa ya shafa yana kallon maman basa har ta gama kafin ya ce" an samu ci gaba kala daban daban a
duniya Ummih,
Sun buda wannan wajen dan a dauka a kuma biya su,
Akoy damar ka auri mace na adadin lokacin da ka dauketa aiki, su zasu san yanda zasu yi tsarinsu, sannan
ni fa ba wani abu nake nufi dan nace a yi hakan ba, halin rayuwa nake dubawa,

Kanta ta dafe da hannunta na dama,


Da na hagu ta yi masa nuni da ya tafi,
Dan haka a hankali ya mike yana mai adu.ar Allah yasa ta ki amincewa, shi fa a gaskiya baya so, baya
ra.ayi, haba, ko dan bata san shi nasa aikin da yake yi na biye bane ya saka take takurar kanta haka? Da zata
san menene ainahin aikinsa, da bata damu kanta haka ba, somin ya baro saudiya ne bisa dalili kwakwara na
kasancewarsa agent mai aiki a boye, ya baro ne dan shima da nasa aikin, kasuwanci da ya karanta shi
duniya ta sanshi da aikinsa, idan ba wannan ba ta yaya zai ringa gane abubuwan dake faruwa a tatare da
shi? Shi ba aljani ba? Horon da ya samu, ya yi imanin ba zasu taba samun irinsa ba!

A haka ya baro gidan mahaifiyarsa, cikin motar da yake ja da kansa,


Ya yi tuki mai nisa ya ja gefe ya tsaya sakamakon sarawa da kansa ya yi,
Idannuwansa ya lumshe ya shiga karanta du wata ayar da ta zo bakinsa dan neman tsari,
Kansa ya jinginar jikin kujerar da yake tuki samanta,
Gabansa ne ya yanke ya fadi, ya kara yankewa ya fadi,
Da sauri ya dafe daidai zuciyarsa yana mai jin wata irin zufa na karyo masa,
Innalilahi wa.ina ilaihi raj.une!
Shi ne abinda ya shiga maimaitawa ba ji ba gani,

Wani irin ribos ya yi da motar ya dauki hanyar gidan mahaifiyarsa, gaba daya jikinsa rawa yake,
Gaba dayansa ya fice a hayacinsa, irin wannan abin ne ya faru da shi, a shekarun da suka shige, shekarun
da ya rasa babansa, shekarun da ya rasa kanwarsa, shi ba mahaukaci bane, kudi gata basu saka ya zauce
ba.... yana rayuwar sakalci ne bisa dalilai,

Horn din da ya dane ya saka mai gadi mikewa da gudu gudu ya bude masa kofa yana mamakin abinda ya
dawo da shi,

Yana shiga gidan abinda ya hango ya saka shi sakin sitiyarin motar ya dora hannayensa biyu saman kansa
tare da fasa wani ihu mai taratsin mai fitar da innalilahi wa.ina ilaihi raj.une
Hannayensa saman kansa motar ta je ta daki karfen rumfar ajiye motoci, nan rumfar ta rufto ta rufe motar
baki daya, inda da wuta ka yi tunanin idan har za.a iya ciro mutun da rai daga wannan accident

Wannan shi ne farko,


Wannan shi ne mafarin sabuwar rayuwar da zata budewa *ABDUL JABAR*, wannan shi ne duhu, kunci,
rayuwar gimgim, rayuwar gimtsewar da zata samu Abdul Jabar, daga wannan lokaci, wannan dan saurayi
mai rayuwa cike da sangarta, da garari, ya dawo tamkar kurma, ya dawo wani bahagumen mutun mai
wuyar zama,
Ya kai sati kwonce cikin halin rashin sannin inda kansa yake a babar asibitin garin, inda sojoji ke gadinsa ,
A ranar da ya farka ya kai dubansa saman agendar dake dakin makekiya ta shekarar da ake,
Bai gane ranar da ake ba, sai dai awar ta bashi damar gannin kamar ya kwana a wajen kennan?
A lokacin da likita ke cike da murnar farfadowarsa bayan sati daya da sumarsaa ya saka shi jin wani irin
bugawar zuciya,
Da kyar ya iya buda bakinsa ya ce" ina Ummih? Ina Ummih?

Gargadin da yarima Muhammad ya yi kan kar wanda ya bashi amsar nan ya saka su kokarin gannin sun
masa alurar da zata saka shi baci,
Sai dai ina, a hankali karfin zuciyarsa ya hayo inda ya shiga kokowa da su yana ihun ina Umminsa?

Ta mutu ko? Ta mutu? Ku kai ni wajen gawarta, ku kai ni na ga gawarta, sun kasheta? Ummih, kina fadi sai
da suka rufe maki baki?
Daneshi suke son yo aman sun kasa dan haka suka baiwa sojoji biyun da suka shigo waje suka kai shi kasa
suka dane kafin ya tsira masa allurar baci,
Shiru dakin ya dauka, dan kuwa sai da ta kashe masa jiki idannuwansa kekashe kafin ta yi masarar
daukansa,
........................................

Haushi yarinyar ke bata walahi, bata san yaya zata yi ta taro yarinyar da a haife ta girmeta aman take hauka
irin haka,
Dama haka mutanen dake kallonta tana tafka tsiya har wa iyayenta suke jin haushinta? A gaskiya da tana da
yancin cewa ita a mayar da ita camp da ta fada domin du wani kokarin nunawa yarinyar shirmenta ya jaza
mata tiwa saurayi rashin mutuncin da ya wanka mata mari da ikirarin sai ya tozartata, ta kasa fahimta,

Ko yanzu da suke tsaye, Hafsat din na tsaye bayanta , ita kuma sai hauka take na fadan ita gaskiya dad a
rabata da wannan mai biye da bayan nata, haba sai kace jela, wai kayan da ta yi niyar sakawa Hafsat din ta
hanata, dama haka ne? Aikinta fa ta bata tsaro a biyata, to na me zata ringa shiga hurumin irin suturar da
zata saka?

Maimakun ya tsawatar mata ya nuna mata hanata saka kayan nan damamu shi ne daidai ko dan gudun
janyo hankalin mugayen samari kanta, sai ya shiga rarashinta da fada mata ta yi hakuri ya je ya samo
wannan Bodyguard din ne dan a samu a kamo yaron da ya daga hannu ya mareta , da barazana kala kala, ko
so take sai ya kona mata fuskar?

Jin maganar kona fuska ya sakata girgiza kai a hankali tana mai jin gabanta na dokawa, ina idan aka taba
mata lafiyar fuska an gama da rayuwarta, ita dake takama da kyan fuskarta? Ita dake ji du duniya babu
abinda ba zata iya sakawa ba dan gannin fuskarta ta kara kyau? Lale wannan saurayin ya aika, gashi tunda
hakan ya faru da su tama daina ganninsa a makarantar ko a gida, du ya dauke kafarsa ya yi kwontan bauna ,
jira yake sa.a ta kama shi ya damketa

Kara tsoratar da ita ya yi cikin hikima , kafin ta hakura ta fita da shigar abaya kamar yanda Hafsat din ta
saka itama suka fita tare suka nufi university wajen daukan karatun yar budurwar .....wannan itace mission
din Hafsat ta biyu da ta samu, inda take baiwa budurwa tsaro mai shekaru ashirin da biyu a duniya, wace ke
bata wahala sosai don kuwa sam bata bata damar da zata yi aikinta yanda ya kamata, tana nuna halin
yarinta da sangarta, tana matukar wahalar da aikin, hakan na konawa Hafsat rai, domin irin tsayayar da
yarinyar ke nunawa na tuna mata muguwar rayuwar da ta yi har ta taka san barawo, gashi kuma mahaifinta
da mahaifiyarta sun daure mata , basa gannin matsalar dake tare da su,

Bayan sun dawo, dare ya tsala,


Daren alhamis ne, wato wayewar juma.a, daren da yawancin bayi masu nema wajen Allah suke raya shi,
Tun karfe goma mutuniyar tata ta yi baci, hakan ya sakata gyara du abinda zata gyara, ta cire abin kunnen
nata ta ajiye shi ta fito cikin shiga ta abaya tare da yane kanta da mayafi baki,

Tafiar kafa ne ta ci ta mamaki, wace ta sha mamakin yanda aka yi ta gane hanyar kanta,

A hankali, ta rabe kofa tana kallon yanda ake dan raragewa, sai muryar malan dake tashi yana ta wa.azi,
Sai da ta jima nan tsaye kafin ta yi wuf ta shiga, ta baya ta yi sando ta shake mutumen dake tsaye nan ya
tafi duniyar suma, dama daga shi sai malan, ya fito sake alwallah ta yi wuf da shi,..

A hankali ta shiga masalacin,


Bayansa take hange, ta rakube tana dubansa,
Wasu zafafan hawaye ne suka shiga siraro mata, tana kallonsa ta saka kafarta bayan ta cire takalminta da
safarta ta dan fara takawa da niyar karasawa wajensa sai dai ji ta yi an rufe mata idonta da bakinta an
dauketa cimak an fita da ita inda take wutsil wutsil da kafafuwanta........

Malan dake zaune tsai ya yi da wa.azin da yake ya dan waiwayo bayansa,


Wani abu ya ji kamar uwata ta ziyarci wajen,
Wata irin ajiyar zuciya ya sauke, idannuwansa ya lunshe ubda ya shafi gemun fuskarsa,
Hawaye ne ya ji sun cika masa ido, walahi ya san da ta mutu da Allah ya saka masa dangana a kanta, tana
raye, innalilahi wa.ina ilaihi raj.une,
Haka kawai sai ya cire wa.azin ya shiga wata irin kira.a ta hanyar daukan suratul Yusufa ya lumshe ido
yana yi yana mai tuna irin tarihin yusufa zuciyarsa na kara tsumuwa tana kara kusanta shi da
ubangijinsa........

Basu direta ko.ina ba sai cikin bakar motarsu, suka ja da mugun gudu suka nufi anguwar da take aikin,
Nesa da gidan kadan suka yi parking kafin a saketa,

A yanda ta hayayako da sun yi sanya wajen kare kansu tabas da ta jiwa wani,

Ido cikin ido suke kallon juna ita da BS, tsaye su dukansu cikin motar inda ya saka mutun ukun da suka
kamota fita aka batsu daga shi sai ita,

Tamkar wasu zakaru irin yanda kowa ke kallon kowa da tarin haushin dan uwansa,

San me kike saka kanki a uku, danme kike son saka mini zuciya cikin tunani da hargitsi? Me yasa ke du
motsinki na wanda zaki tarwatsa min tunani ne? Ke dake bakin aiki ashe kina faman tarwatsa komai? Idan
har kika je ya ganki a yanzu koda zaki saka masa glue kin isa ki hana shi yada cigiyar nemanki, a tv, a
redio? Ku ku goma sha shida na hora, ban taba zuwa gado dan yin baci baki fado mini a idannuna ba! Zan
so ki kiyaye dokokin gidan nan ki yi doguwar rayuwar da zan iya rayuwa da ke !

Idannuwanta da ta ruruko dan masifar dake cinta na son ta ga mahaifanta, gata ga mahaifinta ya saka aka
kamota ta matso sosai kusa da shi cikin murya kakausa ta ce" mahaifana? A raye? A cikin kasa daya da ni?
Zaka hana ni ganin su?

Shima muryar tasa ya kausasa ya ce" du lokacin da kika yi kokarin guduwa harbe ki shi ne abinda aka ce na
yi!

To ka harbe ni mana! Ka harbe ni na huta da wannan rayuwar! Ka harbe ni su tabatar da na mutu da


rayuwar da suke a matsayin wada na gudu dan gudun auren dole ko me?

Ki fice!
Ya daka mata tsawa yana kara kusancinsa da ita,
Idonsa ya saka cikin nata har jijiyar goshinsa na kara tsayawa dan neman balaki ya ce" ki fice a nan!

Idannuwanta ta lumshe dan kokarin mayar da hawayen dake son kubce mata sannan ta karbi abin kunnenta
ta mayar ta juya ta fita a motar ta shiga gidan dake zagaye da masu tsaro ta katanga ba tare da sun san da
shigarta ba,

Tana zuwa waje ta samu ta tsaya ta sada kanta kasa,


Wasu irin hawaye masu zafi ne suka shiga bin kumatunta, ta sani ne, in dai wannan maganar ta fita zuwa
manyansu to fa za.a iya mayar da ita *KUTKALE*.
Gaba dayansu ya tara su su ukun ya tsare su cikin yannayin da ba zasu taba gigin tunanin da wasa a
lamarinsa ba ya ce" koda wasa, na tsinci maganar cewa mun kamo BD 01 ta je gannin mahaifinta sai na
bibiyi daga inda maganar ta fito na hana mutun zaman lafia! Da hanuna zan shakewa mutun wuyansa har
ya daina numfashi!

Haka ya gama da su ya koma motar ya zauna ya kai hannayensa saman kansa yana shafa kan cike da
yannayin rashin karfin jiki,
A cikin zuciyarsa ya ayyana *Sonki nake, kuma ni ne mai rabin samun ki* (ko?)

Bai wani jima sosai ba maganin bacin ya sake shi, nan ya ga an dadaure jikinsa jikin bed din da yake
kwonce magani na shiga cikin jikinsa,

A hankali ya ringa gani da kyau har ya sauke idannuwansa kan sojojin kasar saudiya tsaye kusa da prince
Muhammad,
Gefe daya kuma kanwar mahaifiyarsa da ta yi saura a family dinsu ce zaune da dogon hijab dinta blue mai
ruwan byro, dakin shiru kowane cikinsu na jan carbin dake hannunsa, yannayinsa zai nuna maka halin da
zuciyarsa ke ciki,

A hankali ya maida idannuwansa ya lumshe dan basu san da ya farka ba,


Wani zazafan hawaye, mai mugun zafi da radadi a kwarmin ido ne ya samu damar tsinke masa,

Abinda ya hango a lokacin da ya shiga gidan mahaifinyarsa, mamansa ce yashe saman tiles din tsakar
gidanta, hasken motar da ya dala ya nuna masa harbin bulet din da aka dana mata a gaban goshinta,
Zai iya tuna cikin al.adarta ne idab ta kore shi, tana biyowa tace da mai gadi idan ya dawo yace da shi ta yi
tafia, dan ya dauki maganar da suke da mahinmanci,
A dalilina, aka kashe uwata? Ni na kashe ki Ummih.....

Bugun zuciyarsa ne ya tsananta hakan ya sa injin dake jikinsa mai shaida yannayin hawan jinninsa ko
saukarsa ya shiga shaida jinninsa ya fara hawa,

Da sauri Muhammad ya nufo wajen gadon yana kiran sunnansa a hankali,


Kanwar mahaifiyarsa kuwa ta fita da gudu dan kiran docters,

A hankali ya buda idanjuwansa da sukai masa nauyi ya kai dubansa kan Prince Muhammad,
A hankali ya buda bakinsa da muryarsa da ta canza amo ya ce" Muhammad, ya haka aka kule ni tamkar
mahaukaci?

Muhammada na son fada masa dalilin daure shin da aka yi ya ji ya daga murya da karfin amo ya ce".......

Alhamdulilah, an gama freee


Du mai son ci gaban labarin naira dari biyu ne ga yan Nigeria,
Yan niger kuwa dala dari ne sahelcom ta numberna kamar haka 91466605
*Taku ce, yar mutan niger*
*KUTKALE*

*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar
DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct
NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan
number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA
SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN
SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN,
.....* taku ce, Sajida😍😍😍😍

1️⃣1️⃣

Cikin tashin hankali a yannayinsa da yannayin muryarsa ya ce " ku kunce ni, ni ba mahaukaci bane! Ku
kunce ni!

Likitan da ya shigo da sauri da abin auna bugun zuciya rataye a wuyansa da takarda a hannunsa, bayansa
nurse tana tura dan abin dake dauke da magungunna ta auka karaso wajen gadon da Abdul ke faman kuma
tayar da wata tarzomar ya yi gagawar zuwa kusan gadon yana daidaita alurar barcin da ya tsira cikin
seringe da niyar zubata cikin karin ruwan dake tafia,

Muryarsa cikin yannayi na jigata ya ce" haba docter, kar ka kara min alurar barci mana, sai yaushe zaka
barni na je na gana da mahaifiyata? Ka barni haka docter ka ji?

Tsai ya yi yana subansa,


A hankali kanwar mamansa ta matso kusa da shi , hannunta ta dora dake rawa saman hannunsa tana
dubansa ta ce" Abdul, idan kana irin haka, ba za.a iya barinka ba, kar ka jiwa kanka ciwo ta hanyar fada a
haka ko ka tayar da hawan jinninka, Abdul shin kowani mai rai ba mamaci bane? Dan Allah ka rufa mana
asiri ka dawo da tunaninka, ka kwontar daa hankalinka haka Abdul, musulmi ne fa kai, da ciwo Abdul, da
firgita, da gigita, sai dai imanin dake tare da kai na kasancewarka musulmi zai hanaka wasu abubuwan, ka
nutsu Abdul, ta rasu, ta rasu, ba zata dawo ba, ka farka Abdul, kai da ya dace ace kana tsaye kan
kafafuwanka , ka ciri jarumta ka arawa kanka, ka daina haka Abdul, bani da kowa yanzu, daga kai sai
Ni.ima, bani da kowa Abdul........
Ita dake bashi baki, sai ta fashe da kuka tana dukewa kasa,
Idannuwansa ya lumshe, bai ci gaba da kokowar da yake yi ba, bai ci gaba da wani hayaniya ba, sai dai
fuskarta da irin rayuwar da ya yi a kusa da ita kafin ta amsa kiran Allah, shi, ya yi dandaja da maganarta na
daukan mai tsaro ne dan a tunaninsa shi kadai ake iya neman rayuwarsa, ahi kuwa ya san me ya taka, ashe
ashe abin zai haura har haka? Ashe za.a cin masa a daidai lokacin da bai yi tunani ba, bai kawowa ransa ba?
Shikenan yanzu babu Ummih? Ta tafi, shin ka yi mata adu.a dayama kuwa Abdul?

Da sauri ya bude idannuwansa ya sauke kan fuskar Muhammad,


Da hannunsa ya nuna masa carbin hannunsa, hakan ya saka Muhammad karasowa kusansa yana mika masa
carbin,

Karba ya yi yana dubansa ya ce" Muhammad, a kunce ni ka ji?

Muhammad ya gyada kansa ya shiga kwonce belt din da aka daure shi inda docter ya so hannawa aman ya
nuna masa ba komai,

Ana kwonce shi ya roki da a kama shi,


Bayi ya shiga ya yi abinda zai yi ya dauro alwallah ya fito,
Zama ya yo saman salaya ya shiga ramuwar salolin dake kansa, ba zai iya yi a tsaye ba domin kuwa juwa
yake yi sosai, dan haka ya yi a zaune wanda ya daukan masa lokacin sosai,
Yana gamawa ya dukufa yana ta jan kulhuwa lahu wa mahaifiyarsa, harma da sauran iyayensa, da kuluhin
musulmai,
Yi yake ba ji ba gani, har ya dago ya tsurawa waje daya ido yana mai tuna yanda ake sakawa mutun
likafani, a hada yatsutsansa a daure , a toshe hancinsa da kunnayensa da kada, a nade shi da likafani yayan
an daure kafafuwansa,
(Dan adam kennan a macema daure shi ake), a haka ya yi tunanin irin matsewar rami, a doraka saman
hannunka na dama,
a jera itatuwa a rufa kasa kanka,
Shikennan an baroka, kana ji zaka ringa jin takun yan uwanka da iyayenka har su baro makabarta,
Yanzu haka aka kai mahaifiyarsa ba tare da rakiyarsa ba? Haka aka sakata ba tare da sannin shin ana bi a
laluma ana ta adu.a ko sakatan kawai aka yi? Shi yaya amsar cikin kabari ta zo mata? A yanzu da take
kwana goma da rasuwa, shin tana cikin rahamar ubangiji a cikin wannan daki dan kurkuku wanda yana iya
zame mata yalwatace ko akasin haka? Ya Allah ka jikan iyayen mu, Ya Allah ka jikan magabatan mu, Alla
ka jikan kuluhin musulmai, ya Allah ka bamu guzurin tarda su na alkhairi.....
Haka ya yi ta zubar da hawayen da yake kukan zuci sosai,
.
......................

Washe gari da ta tashi, sai wajen karfe goma ta shirya dan zuwa makaranta,
Ita dai kallonta kawai take, dan ta yi mata magana ta saka wani damamen wando da yar riga ta dora hula a
kanta,
Sai dai ga mamakinta, ko ta nuna mata kar ta saka, saima jakarta da ta miko mata wace ta hada mata kayan
bukatarta na makaranta suka fito suka shiga mota,

Dirwba na jan su , Hafsat na kallon titi, ita kuwa ta tsurawa Hafsat ido,

Murmushi ta yi ta ce" hala kin yi fushi?

Hafsat da ta san da ita take sai ta yi kamar bata san da ita take ba,

Hannunta ta miko zata taba cinyar Hafsat da niyar yi mata magana, sai dai hafsat ta janye kafarta ta zabga
mata harara ta ce" kar ki yarda ki taba min kafa,

Murmushi ta yi tana janye hannunta irin ta yi hakuri ba tabata zata yi da wata niya ba,
Tana kallonta ta ce" kin san da na girme ki?

Hafsat ta juyo da manyan idannuwanta ta sauke saman fuskarta,


Tsai ta yi da dubanta tana kallonata, tabas ta girme ta,
Kanta ta juyar bata bata amsa ba dai,
Bata gaji ba ta ce" idan har na bata maki rai ne ki yi hakuri kin ji? Kin ga na saka kayan nan ko ki hana ni?

Hafsat ta juya tana kallonta again, ko na hanata? Ita mahaukaciya ce? Ko me?

Kanta ta girgiza kafin a hankali ta ce" ki rike damarki, tun kina da damar hakan, kar wauta, baci, sangarta
ya saka ki aikata aikin dana sani, ke naki mai sauki ne, ki fita harkar samarin zamani, idan wani ya hadiye
ya kawar da kai, wani zai bilo maki ta inda baki taba zato ko tsamani ba,

Ina iyayenki suke suka barki kike aikinnan? Bauta ce a gayance fa? Bakya baci sai kin tabatar da ina cikin
kariya tamkar mahaifiyata? Iyayena kansu suna gefensu suna hutawa ke kuwa kina tsaye kan kafafuwanki?
Ke baki da gata ne? Fatar jikinki bata nuna ke din wahala ta kai ki zama mai tsaron lafiar wani ba, baki da
dad da mom ne? Ina nufin sun wula ne????
Ta fada da yannayin shakiyanci du dan ta kulata,

Murmushi ta yi na zuci, ta kawar da kanta,


Motar da ta gani tunda suka hau bakin baba layi ce dai bata daina binsu ba, kuma gashi suna faman su shiga
ta wani lungu,

Juyowa ta yi wajen direban zata yi masa magana aman ga mamakinta, hular da ta baiwa direban dake tuka
su ba itace a kanta ba,
Gabanta ne ya fadi, tabas ta shagala yau, tunanin iyayenta da ta kwana yi da kuncin zuciya ya sakata a
duniyar shagalta, wannan du inda ya fito ba direban da yake tukasu bane,

Abayar dake saman wando da rigarta ta anniya kwabewa cikin hikima, kafin ta samu da dabara ta haska
madubin dake cikin pos din wayar dake hannunta,
Tabatarwa da ta yi cewar ba shi bane ya sakata saka rigar nan tata ta shako wuyansa,

Ihu yarinyar ta saka inda shima abin ya diro masa a bazata dan haka ya shiga kokarin kwatar kansa da
kuma gannin morar bata fadi ta kashe su ba,

Ihu take tana fadin" zaki kashe mu, ke zaki kashe mu,

Kafarta ta saka ta hambara mata kutufo a wajen da ta san koda bata suma ba, tofa zata tafi duniyar jigatar
da zai hanata magana,

Suma ya yi, inda ya dora kansa saman sitiyarin motar, da sauri ta tsalaka ta mayar da shi gefe sannan ta
warci motar dake tangal tangal tana fama maka su da garu,

Atach din dake saman kanta ta cire da hannunta na hagu ta yar saman direban da ya tafi duniyar summa,

Sai da ta gama tare jinnin hancinta ta dago du a firgice tana ta zarar ido gannin sun canza hanya su da zasu
dauki hanyar da zata kaisu university sun canza sun durfafi police station din da ta fi kusa

Ta gama sarewa, inda Hafsat ke wani irin tuki cike da kwarewa da kuma garari har ta samu ta karaso , nan
ta ga suna faman juyawa, da gudu ta tsayar da motar kusa da wani police da ya mike ya nuno motarta da
bindiga kan ta tsaya ko ya harbeta kar ta shigo masu police station a irin tukin nan,

Tana tsayar da motar ta fito da gudu ,


Takardar dake aljihunta ko mace kati ta nuna masa shaidar ita din ko wacece sannan ta warci babur dinsa ta
yi masa nuni da ya tsare mutanen dake cikin motar,

Wani irin tuki take yiwa babur din, inda take magana da BS kan hanyar da ta ga motar dake binsu ta bi,
sannan tana biye da motar saman babur

Cikin azama da wani irin gudu suka dauki hanya , nan Allah ya basu sa.ar cafko mutanen cikin kwarewa da
aikinsu suka kama su, sannan suka koma police station,
Kallonta kawai yarinyar ke yi da muguwar sha.awar aikinta a yanzun kam,
Ta birge ta, irin yanda ta tuka motar dake faman juyewa da su, irin yanda yarinya karama da ita ta warci
babur ta yi masa irin tukinnan, kai da zata samu wannan aikin, ta zama irin wannan baiwar Allah da ta so,
ta gama tafia da ita,

A lokacin da ta mayar da Abayarta ta fito cikin nutsuwa tana goge jinnin dake zuba a hannunta wanda ta ji a
lokacin da ta daki gilas din motar, ta dubi yarinyar da ta gama baiwa tsaro,
Murmushi ta sakar mata, ta mika mata hannu kan su yi salama

Itama cikin murmushin ta bata hannun suka yi musabaha,


Murya kasa kasa Hafsat ta ce" bawa na tsintar kansa a rayuwa kala kala, idan yana da dabara zai dauketa
yanda ta zo,
Babar dabarar da bawa zai yiwa rayuwarsa shi ne, ya iya rike opportunity.....bata fiya zuwa sau biyu ba,
*FREIND*

Da haka ta saki hannunta ta juya cikin tafia ta yanga irin ta yar budurwar da ta cika ta batse take takama da
sura mai kyau, Hafsat ta gama hardace abubuwan d aka koya mata hakan ya sa ba zaka taba tunanin tana
iya juyewa ta daki fada na mamaki

Tunda ta taho ya shagalta da kallonta, yannayin yanda take shawagi, ga sansanyar iskar safiya na kadata,

Murmushin da bai shirya ba ya saki yana kara kallonta, kafin ya waiga inda aka saka mutanen da aka kama
da direban cikin motarsu,

Tana zuwa ta zagaya ta shiga motar ta zauna mazaunin direba,


Idannuwanta ta lumshe tana mai jin yanda mitar ta dauki shiru,
A hankali ta mika hannunta wajen kuna redion motar ta kuna, sai waka ta shiga tashi ta hayaniya irin
wannan,

Hannunsa ya kai ya kashe, da hannu ya yi mata nuni da GN na sauraronsu fa,

Dan karamin lebenta ta tabe sannan ta shiga bin garin da kallo, tana mai tunanin abinda zai kara fitar da ita,
wata mission din?

Ko da suka karasa computernta ta dauka ta shiga yanar gizo tana bincijen abinda ya shafi aikinta hankali
kwonce, idan ta motsa daga inda take dan ta gabatar da ibadarta ne,

A cikin wannan daren suka tashi da tashin hankali, daya dake cikinsu da ta tafi kasar Span dan baiwa wani
atajirin saurayi tsaro, an cin mata, an zo harbe shi rana kusa aka hada da ita, inda shi bai mutu ba, aman ita
a lokacin ta amsa kiran Allah,
Wannan lamari ya girgiza su, domin yarinyar bata da damuwa, bata da dagin kai, duda yar wani ce bata da
wata damuwa da hakan,
Haka suna ji suna gani aka shirya gawarta cikin sanduki hayan an yi mata likafani aka kuma nadeta da
drapo din niger ana sakata a sanduki aka tafi da ita inda za.a yi mata sutura tare da iyayenta wa.inda sai dai
su ga sandukin, ba zasu ga gawarta ba,

A wannan ranar wajen mutun uku suka ce sun fasa aikin, inda wajen ya rikice da rigima da koke kokensu,
sun tsorata, harbi a kai? Ta tafi shikenan? Sun matukar girgiza, kowace so take ta samu mahaifinta , bata so,
ta fasa wannan aikin mai cike da gadari.....su sun dauki hakan a matsayin gayu da nunawa duniya su din
jarumai ne, aman haka kawai sai a kawo gawar daya? Aa......

......................................................

Bayan kwana arba.in


Du wani na nesa da na kusa, qminan arziki dama yan uwan yan uwa du sun tatara sun koma daga gaisuwar
rasuwar mahaifiyarsa,

Kanwar mahaifiyarsa da Muhammad kawai suka rage, shima Muhammad ya yi zuwa uku kasarsa ya dawo
ne,

Abdul Jabar ya zana wani silent man


Askin nan da yake yi kwalkwal ya aske kai, rabonsa da shi tun kafin rasuwar mahaifiyarsa hakan ya saka
suma ta fito sosai kansa, suma mai yawa mai kuma tauri tauri hakan ya saka kan ya cika da gashi irin yanda
samari ke tarawa ,
Sajensa da a da yake askewa baya barin ko kadan, yanzu ya fito sosai ko.ina ya zagaye fuskarsa,
Gemunsa ya kara cika, lebensa suna da dan girma, dan ba zaka taba kiransa da mai kananun lebe ba, aman
kuma ba dambatsa dambatsa bane,
Idannuwansa sun fi komai girma a fuskar tasa idan ka cire karan hancinsa mai tsini, idannuwansa jajajir
suke, rabonsu da su yi haske tun a lokacin da yake tataunawa da mahaifiyarsa yana mata murmushi itama
haka,

Zaune suke su su uku,


Su biyun suna dan taba hira, ba ta komai ba sai ta zaman duniya da jimamin yau da gobe wanda bai bar
talaka ko mai kudi ba,

Tunda suke magangannun shi dai kansa a kasa yana sauraron su, bai ce da su komai ba, haka kuma bai hana
su maganarsu ba,

A hankali ya bude bakinsa, muryarsa da ta zama wata iri mai amon irin muryar nan ta kakarfan maza ko
wa.inda giya ta kashe masu zakin murya ya ce" aure nake so.

Muhammad dake magana da aunty Firdausi ya juyo da sauri yana kallon Abduk Jabar,
Itama auntyn hankalinta ta maido kansa,

Dago da idannuwansa da a yanzu in dai ba dole ba , mutun ba zai so su kurewa juna kallo ba, ya sauke
saman kansu,
Lebensa na kasa ya kamo da harshensa ya shiga dan tsotsa yana kallonsu bai ce da su komai ba,

Kai aunty ta kawar daga dubansa ta ce" Aure?

A hankali ya saki bakin nasa ya ce" eh, aunty na san kin san na yi rayuwar rashin jin magana,
To bana so na sake , dan ba zan so a tayar da mahaifiyata a nuna mata abinda nake daga kabarinta ba, kuma
gashi ina son mace a kusa da ni, dan haka zan yi aure.....

Muhammad ya shiga jinjina kai yana mamakin jaraba irinta abokinsa,


Aman kuma ba laifi tunda yanzu ya nemi ya kara wani auren.....aman kuma wani abu ya tsaye masa a rai,
ba irin maganar da ba.a fada masa kan ya daina harkar mata ko dan mahaifinsa idan baya tsoron sauran
abubuwan, ya ji kunyar Allah, ya kuma kaucewa mahaifinsa shiga halaka ta dalilin sabon Allahn da yake,
Yakan ci gaba da shagalinsa , aman yanzu ya nuna zai fasa dan mahaifiyarsa? Me abansa ya yi masa haka?
Ko dai da wata a kasa? Irin rayuwar rashin sannin ciwon kan da ya ringa tafkawa?

Dubanta ta kawo saman kansa bayan ta yi dogon nazarin maganarsa, a hankali, a nitse, da yannayi na
rarashi, da neman cin galaba kan maganarta ta ce" aure ba laifi, za.a nema maka auren ko yar gidan wa
kake so,
Sai dai da sharadi Abdul,....
Maganar *BODYGUARD* da mahaifiyarka har ta rasu tana fama yana nan daram bai canza ba,
Za.a je a dauko kwararun bodyguard biyar,
Daya zata baiwa matar da zaka aura tsaro.....
Hudu zasu kasance da kai idan maza kake so ko mata, a dukan motsinka,
Abdul kar ka yi min gardamar haka, dan na rantse maka da Allah sai dai ka ja na ja....idan kuwa nima so
kake mu yi ta jayayar har a dauken kai da alburushin shikenan.............

Ku yi hakuri, i.m sick ne,😊, na gode da adu.o.inku, Allah ya saka da mafificin alkhairi
*KUTKALE*

*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct
NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan
number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA
SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN
SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN,
.....* taku ce, Sajida😍😍😍😍

1️⃣2️⃣

Tsura mata ido ya yi, yana gannin mugun kamanin mahaifiyarsa a tatare da ita,
Tunda aka yi rasuwar suke nan ita da yarta kwal da ta malaka a duniya mai sunna Ni.ima wace ta bi ta
makalkalewa du wani motsinsa,
Tabas shi ba zai ce ga halayen matar ba, aman ta kasance mai fatan alkhairi a gare shi,
Bai wani yi zama na sosai da ita ba, tunda du yawancin zamansa a saudiya ne, sai idan mahaifinsa ya tada
balin maza ya zo yake zuwa ya dan yi kwanaki ya juya,

Idannuwansa ya lumshe , ba tare da yace komai ba ya mike ya fice a wajen,


Dubanta ta maida kan Muhammad kafin ta dafe goshinta ta ce" ni bana gane yarensa,
Muhammad ya yi murmushi ya ce" ai ya amince kennan, da bai amince ba, zai fada ne kwaro kwaro ....

Kanta take gyadawa sannan ta mike ta shiga ainahin dakin da suke kwana,

Kwonce ta tarar da ita tana hawaye,


Ni.ima, yarinya ce nutsatsiya, domin bata da hayaniya,
Tana da kamun kai daidai gwargwado,
Kudin mahaifinta bai saka ta zama sangartaciyar yarinya ba,
Tana da baci a gaban mahaifanta, baci irin tsaftatacen nan,
Bata da hayewa,....sannan ta iya zama inda ake da muradinta.

Tsayuwa mahaifiyarta ta yi a kanta tana dubanta,


A hankali ta ce" lamarin har ya girmama haka??

Mikewa ta yi da sauri dan bata san tana kanta ba, da kallon tambaya ta bi maman nata, kafin ta ce" wami
lamari Mama?

Kanta ta girgiza ta zauna tana dubanta ta ce" bari ki ji Ni.ima, ba zan iya tirsasa yaron nan kan komai ba, ke
ni inada fargabar hakanma na fada maki gaskiya, dan ko mahaifiyarsa nada rai ba zata yarda da haka da
gagawa ba dan kuwa akoy kuli, mugun kulin dake tare da shi, hatsari baba,
Bayana haka, namiji ne mai zaune da ra.ayin kansa,
Ni bana tunanin Abdul zai iya yin soyaya, sai dai ya yi aure dan wata manufar....., yau da ace zai so ki, bani
da damuwa a hakan, da ace zai iya rayuwar soyaya da ke , da zan fi kowa farin cikin ganninku tare,
Ki sani, Abdul rayuwar Saudiya ya yi,
Mata na bibiyarsa, sun saka shi daukan kansa tamkar wani sarki,
Baya iya bautawa mace da zuciyarsa idan dai ba kamuwa ya yi da sonta ba, yana iya rayuwa da mace dan
kawai ta zama abin marmarinsa, Abdul, atajirin saudiya ne, dan jin dadinsa yana iya kashe ko nawa ne,
aman kuma zuciyarsa daban...

Gaba daya ta tsure, duda ta sha mamakin irin yanda mamanta ta gane halin da zuciyarta ke ciki, sai dai
tashin hankalin abinda ta fada ya hana mamakin yin wani tasiri a tare da ita,

Kanta ta dago ta saukewa maman nata kallo tamkar marainiya,


A hankali ta sauko kafafuwanta ta dora kanta saman kafar maman nata cikin shashekar kuka ta ce " mama,
ni ban ce sai ya so ni ba, ni ina son sa, ba damuwana bane dan ana kashe matansa, lokacinau ne ya yi,
mama , in dai zai bani gurbi a rayuwarsa, zan zauna da shi....

Sai da gabanta ya tsinke dan tarin tausayin yar tata, sai dai ba zata taba kaiwa dan yar uwar tata tayin auren
Ni.ima ba, koda kuwa zata mutu ne!

Ranar ba zata

Suna tsaka da cin abincin dare, bayan kwana uku da maganarsa da kanwar mahaifiyarsa, mijinta ya yi
kiranta cewa yanzu jirgi ya sauke shi garin, gashinan zuwa gidan,

Kallonta ta kai wajen Abdul, ta ce" Abdul, aban Ni.ima ne ke tafe wai yanzun, ko lafia?

Abdul da tunda ya zauna a dinning din bisa tursasawar auntyn tasa, yake dan surbar jus din kankana da aka
yi ya gyada kansa ba tare da yace komai ba,

Kanta ta girgiza kawai, ta ci gaba da cin abincin tana aikawa Ni.ima hararar irin yanda take kure shi da
kallo bama ta tsoron ya ankara da ita ya yaba mata maganar da zata kwana tana kuka!

A lokacin da ya zo sai da Muhammad ya fita sannan ya samu shigowa, duda kuwa powernsa na kasancewa
baban sojan da ake ji da shi, aman yana zuwa wajen sai suka hane ahi shiga,
Da yake bakin aikinsu suke, shima sai bai wani ja ba, ya tabo mai gidansu ya zo ya saka shi,

Yana zuwa matarsa da yarsa suka mike suka rungume ahi cike da farin ciki,

Aa haka ya lakaci hancin Ni.ima ya ce" auta, wato ke kin zo kennan ko? Shikennan daga nan ma ai bama
zamu koma da ke ba,

Da mamaki suke masa kallon tambaya kan abinda ya ce,


Bai yi kasa da gwuiwa ba , ya basu labarin da ya basu matukar mamaki,

Da sauri mahaifiyar ni.imar ta kai dubanta wajensa, hankalinsa na kansu shima, so yake su gama gaisawar
ya gaishe da mutumen aman sun kasa sakinsa,
Kaunar dake tsakannin famillyn ya tsaya kallo cike da tuno abubuwan da suka faru a da,
Shi bai san kauna irin wannan tsakaninsa da mahaifinsa ba, aman mahaifiyarsa da girmansa da komai kulun
cikin kula da lamarinsa da bibiyar lamarinsa take, har hakan ya siyo rayuwarta,

Aman Elhaj, yaushe aka yi haka? Ni nan bai fada min maganar nan ba, aman ta yaya haka zai faru?

A hankali ya mike ya karasa inda suke tsaye su duka,


Hannunsa ya baiwa Elhajin suka gaisa domin shi ya fara bashi,
Cikin nutsuwa ya ce" to yanzu dai bani da mama bale baba,
Ke ce kika rage min, shi kuwa mijinki ne , kin ga shi ne babana,
Na yi kiransa na fada masa muradina dan na san mata basa zuwa neman aure, a zagaya a zagayo dai shi zai
nema min auren koma wacece, idan ita ta nuna bata iya zama da ni .....fine, sai a nemo min na wata,

Yana gama fadar haka ya juya ya nufi dakinsa,


Daga elhaj, da aunty, da Ni.ima, da Muhammad gaba daya binsa suka yi da kallo,

Aunty ta juya ta koma wajen table din cin abincin ta zauna,

Jiki sabule suka bi bayanta, ciki kuwa harda Muhammad dake son tausar su,

Yannayinta na nuna tsantsar damuwa ta dube su gaba dayansu ta ce" ba zan yarda da irin wannan rayuwar
rashin incin da take son saka kanta a ciki ba,

Wannan wani irin bahagumen rayuwa ce?

So fa ba hauka bane,
Ke yaushema aka haife ki? Baki tafasa bama bale ki kone, ki rufawa kanki asiri da Abdul, kin ga irinta ko?
Har ya fahimci kina sonsa, gashi tun ba.a je ko.ina ba yace idan mahaifinki ya taso ya zo, kuma ya ce idan
za.a bashi fine idan ba za.a bashi ba kuma ba laifi yana da kudi ya tara ya san ko dan yan canjinsa ba za.a
hana shi auren ko yar gidan waye ba, tabas ina cike da tausayin rayuwar dan yar uwata uwa daya uba daya,
aman baya bani damar na fuskanci waye shi bale har a nema masa sanyin rayuwa,

Elhaj dake kallonta ya zauna da kyau saman kujera,


Tabas shima irin yanda ya nuna a bashi ko kar a bashi ba damuwarsa bane ya taba ransa, aman yana yi
masa uzuri da yannayin kadaicin da ya tsinci kansa , duba da irin shakuwar da ya yi da mahaifiyarsa,

Murya tausashe ya ce" uzuri ya dace mu yi masa,


Wannan rashi na lokaci daya na iya taba wasu lamuran da suka danganci dangantakarsa da mu.amalarsa da
mutane,
Ki yi hakuri Fannata,

Elhaj, ba maganar rashi bane, halayen abdul ne, tunda har ya nuna idan ba.a bashi Ni.ima ba wata damuwa
ba a barshi kawai, ya nemo watan ya aura,
Wato kin nuna son kanki? Ke ki kilace taki ki shige gaba a kawo yar wani ko me kike nufi? Elhaj ya fada
yana mai dan nuna jayayar ta ishe shi haka,
Kafin ya kara tausasa muryarsa, du dan kar a kauce hanya ko a bata zumunci ya ce" ba tashi zamu bi ba,
Zamu yi masa uzuri, kuma ni da ya kiraye ni ya nunan na zo a yi maganar aurensa da Ni.ima, koda baya
sonta, shi ya nemi aurenta, koda ya lura da tana sonsa kamar yanda kika fada , shi ya nemi aurenta ba
tirsasa shi aka yi ba,

Dubansa ya maida wajen Ni.ima dake zaune hankalinta tashe sai bin iyayen nata da kallo take ya ce" ke
auta, kina son sa ko bakya son sa?

Da sauri ta kai dubanta wajen mahaifiyarta,


Da sada kanta inda gabanta ke dokawa ta kasa magana sai jikinta da ya kwashi rawa,

Muhammad ya kara matsawa a hankali ya ce" mama, Baba...., dan Allah, ina mai rokar masa yafiya,
Tabas yana da murdadan hali, sai dai wannan lamari da ya riske shi ya kara taurara abubuwa da dama a tare
da shi,
Ko ba komai dai Ni.ima yar uwarsa ce, ba zai wulakanta ta ba,
Dan Allah, ku yi hakuri idan da dama a yin...

Ajiyar zuciya kawai Aunty ke saukewa, bata da ta cewa, domin Ni.ima bata nuna bata son Abdul ba, saima
wani kallon munafurci da take na tsoro, ba laifi, ba ita tace zata iya ba? Ta iya!

Mikewa ta yi ta nufi dakinta ranta na suya,

Elhaj kuwa hakan da ta yi ya bashi kunya, domin koda Muhammad na yaro a shekaru, baban mutun ne mai
daraja, idanma abinta zata yi , ta yi iya su mana? Ya zata nuna hali irin haka?
Dan haka ya sakarwa Muhammad murmushi ya ce" ka yi hakuri, ka san wani lokacin cikin jinsin maza da
mata , idan rai ya tabu, muna kawar da mahinmanci abu, mu dauki abinda zuciya ta yanke, in sha Allah za.a
daura aurennan a gobe sannan ku shirya daga wajen daurin auren zamu dawo mu dauke su mu je dauko
*BODYGUARDS* din, domin kuwa komai matsayina sai na taka da kaina zan iya daukan su.

tana shiga dakin nata ta zauna bakin gado tana mai jin haushin wannan abu, ta kai ruwa , ta kai mari, ta
rasa yaya zata yi, dan haka ta budewa mijinta daki da ya hauro inda take, nan yake shaida mata ya bada
kudin sadakinsa za.a daura aurensa da safe!

Wannan shi ne tabatuwar Ni.ima a matsayin Matar Abdul Jabar ta shida............


*KUTKALE*

*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI
IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct
NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan
number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA
SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN
SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN,
.....* taku ce, Sajida😍😍😍😍

1️⃣3️⃣

Yannayin shigarsa , ba zai tabatar maka da shi din ko wanene ba koda kuwa ka saba gannin jalabiyoyi masu
tsada,
A yau , ranar da aka daura aurensa, suka dauki hanyar zuwa dauko mutanen da zasu kasance masu basu
tsaro, cikin tawagarsu, da mutanen Muhammad amininsa, da mutanen Elhaj, da auntynsa da amaryar tasa
kanta wace ta sha abaya sai walwali take goshin amare na kara haskata, sai shi,
Jalabiya mai shigen milk ce ya saka,
Bai wani gyara kasumbar da ya ajiye ba, tana nan yanda take, saima kara cajeta da ya yi ya dora hirami
saman kansa,
Sai takalmi da ya zura mai shige da silifas inda Muhammad ya sha farar shada ta karbe shi sai annuri yake
bazawa tamkar shi ne angon,
Dubansa ya yi a lokacin da ya gama shirin ya ce da shi" daurin aurenka ne zamu je fa Abdul?

Abdul ya dage girarsa guda yana dubansa sannan ya ce" na *Shida* ba, ina cike da zumudin ku gama jana
a kasa ku bani macen ta sakar min mara!

Kansa kawai ya girgiza, domin kuwa lamarij na abdul tamkar wanda akaiwa asirin da mace? Baya iya boye
bukatuwarsa da harkar mace ko a gaban waye, wannan abin ba da shi aka haife shi ba, domin ya san shi ba
yau ba, sun yi karatu tare sun yi yawo tar, wannan lamari ya same shi ne daga baya, yana mai binsa da
kyakyawar adu.a......yana mai cike da tausayin Ni.ima da ya fahimci irin yanda take rawar kai da murnar
samunsa a matsayin miji, bai san yaya zata iya da tashin hankalin jarabar mijin nata ba bale idan suka daga
baki daya suka kara yin nesa da iyayenta, wato suka juya saudiya

GN ne da kansa ya laya Bodyguard din da yake ji da su maza da matan biyu rak dake iya tafia, domin kuwa
biyun suna asibiti wannan rigimar sai da ta kaisu da shan matsiyacin dukan da aka kwontar da su!

Da kansa Elhajin ya bi layin mazan dake tsatsaye, cikin sannin aikinsa da irin kwazonsu ya zakulo maza
biyu da BS cikon na ukun domin kuwa har shi ya nemi da a laya duda irin tsadar aikinsa,

A haka ya dawo wajen yan matan, dayar ta fi Hafsat tsayi, da yannayin alamun karfi, Hafsat a yannayin
jikinta ba zaka taba tunaninma wai zata saka kafa a wajen nan,
Dan haka ya juyo wajen GN ya maida shi gefe cikin yannayin damuwa ya ce" GN, wannan yarinyar ba zata
iya aikinmu ba, ana son yarinya daya da namiji daya su baiwa Ni.ima tsaro, yarinya daya da maza biyu
kuwa su baiwa mijinta tsaro ne, dayar da alamun karfi a tatare da ita, aman wannan bana jin zata wani iya
wanu abu,

GN cikin yannayin son a yarda da maganarsa ya ce" na yarda da formation din yarinyar, na matukar yarda
da ta tsaya saman kaina a lokacin da ba bace cikin jeji, in sha Allah kwakwaluwarta mai ja ce,

Yar gidan waye?

Sai da gaban GN ya fadi, domin Elhaj na daya daga cikin wa.inda suka so bashi wahala sosai kan a fitar da
ita a sakata wannan aikin,
Aman ya ya iya, ya fada masa gaskiyar ita ce wace aka fitar daga *KUTKALE*

kana nufin, matar dan ta.adan zaka bamu a matsayin wace zamu je da ita da yarda ta baiwa iyalina tsaro?,

GN ya sada kansa, domin mai gidansa ne, bashi da bakin wani daga murya ko wani abin,
A tausashe ya ce" *a bakin raina*

Sosai abin ya bashi mamaki, a bakin ransa fa ya ce? Idan ta aikata wani abin a kama shi , idan ta kashe a
kashe shi? Ya yarda ya daukarwa kansa wannan baban hatsarin a kan dan adam mai iya canzawa saboda
kudi? Ko wani ra.ayi nasa mai girma ko marar girma?

Kansa ya jinjina kafin ya kai hannunsa ya daki kafadar GN ya ce" zamu yo signed kan ran ka! Aman kuma
ba ita zata baiwa Ni.ima tsaro ba, sai dai ta hadu da baban yaronka su baiwa Oga Abdul Jabar tsaro! Ka ga
a wajen namijin mun dauki wanda ya kware mun hada da Abdul, a wajen macen mun dauki wace ta kware
mun hada da Ni.ima,

Murmushi GN ya yi a fili mai cike da ma.anoni, kafin su tatara su je a yi du abinda za.a yi, a tarkata su su
dauki hanya , suna zuwa cikin gari suka dauki jirgi suka juya inda suka bar Aunty da mijinta,

Suna dira baban gidansa suka zarce,

Kowa na neman hutu banda masu tsaron su, da kuma shi kansa uban tafian,

A lokacin da ya ga Hafsat tsaye a bayansa matsayin wace du inda ya kutsa ta kutsa sai da ya rike kugu ya
dafe habarsa ya kare mata kallo tun daga kafarta hat kanta sannan ya yi kwafa a ransa ya ayyana....yanzu
wannan ai almubazaranci da sakani a uku ne, toh mana, maimakun na yi ta raina kadai sai na hada da ta
jaririyar nan, idan ba son banza irin na iyayenta ba, ya zasu dauketa su kaita irin wannan aikin da sai mazan
wajen sun gama kwakule masu yaya sannan a koya masu abubuwa irin na karti, su juye su dawo bawa karti
tsaro? Wai yanzu wannan yar jaririyar ce zata kare wani abu ya same ni, ni wannan uban da ni, da na yi
imanin da na yi aure da wuri da na zubawa matar cikin yan hudu irinta?

Haka ya juya ya shige inda Hafsat ta sha mamakin ashe wannan bakin mutumen mai sifar samudawan ne
za.a baiwa tsaron? Ita walahi du ji take wancen balaraben mai sifar yayan gatan ne za.a baiwa tsaron,
domin sam ba.a basu fuskar wata tambaya ko wani cikaken bayani a kan wannan aikin ba, dan kuwa Oga
ne da kansa a tsaye a wajen wanda ita saima a ranar ta fara ganninsa da sannin matsayinsa a Niger.

Biye take da shi a lokacin da ya fito daga dakinsa, inda BS ya bita da kallo, ya so ace shi aka baiwa wannan
aikin mai hatsari na ko menene sai ta fara duba zai iya anfani da shi, ko zai ci kai koma menene, ya so ace
shi ne da wannan abin ba dan komai ba sai dan a yannayin aikin, wannan mutumen na cikin hadari sosai,
wanda sai an yi da gaske, an baza ido, an baza komai kafin idan da rabo a samu galaba....

Kansa ya sada ya sauke ajiyar zuciya sannan ya juya ya ja dayan suka ci gaba da bincikar gidan lungu
lungu da kayan aikinsu......

Shi dai bai ce da ita ta koma, ko ta tsaya ba, har suka karaso kofar dakin Ni.ima, wanda suka tarar da
Bodyguards dinta tsaye bayin Allah kowanne a kame waje guda,
Sai da ya tsaya ya kara kama tsatso, wanda yake kamar sabonsa ne, ya kare masu kallo,
Murmushi ya yi a fili, shi walahi an kawo masa nishadi, yo nishadi mana, wanna lamari kamar gunkina? Ba
um bare umum, du sun kame suna jiran uwar gidansu, shi ko a million goma a wuni ba zai iya irin wannan
aikin ba!

Bude masa namijin ya yi ya shiga, sai dai ga mamakinsa, yarinyar dake biye da shi itama ta shigo,

Tsayuwa ya yi ya juyo ya dubeta, sannan ya kai dubansa wajen Ni.ima da ta mike da sauri daga ringeshen
da ta yi cikin riga da wandonta na barci ,

Sai da ya ciro harshen sa , ya lashi lebensa na kasa sannan ya kara dubansu a tare,

Wani murmushin yan duniya ya yi, ya rike tsatsonsa ya dubeta da kyau kafin ya ragewa idannuwansa girma
su dawo kalar baci ya ce" ni dai a sanina mace daya aka daura min aure da ita a yau, kuma wajenta na zo
dan ta kama wannan abin ta rage masa nauyi ( 😭ni dai wannan labari a hargitse yake dan sakin
magangannun ciki),
Da hannunsa ya nuna inda yake nufin a ragewa nauyi, wanda hakan ya saka su a tare rintse ido daga Hafsat
din har Ni.imar, dan kuwa ba warda ta yi tunanin, ko a tsuman ranta cewa abinda zai aikata kennan,
Ci gaba ya yi da magana bayan ya wani rausayar da kai ya ce" zuwa na yi na kwonta da matata, ko yar biyu
za.a yi?

Ya fada yana mai fitarwa da Hafsat gaba daya idannuwansa, sai kuma ya ja wani yaji yaji ya ce" ko a zina
ba kyai hada biyu, bale yanzu na bar zina, kin ga ki dan fita na gama sai ki maida ni daki ko?

Hafsat kam, yau ta ga ubanta a rashin kunya, yau ta ga ikom Allah, da hasken gari ba wai dare ya yi ba, kiri
kiri, ra.aine da ra.aine, kunne da kunne, ya dubi tsabar idannuwanta, da na wace a tunaninta a yau aka daura
aurensu, ya gangantsaro wadinnan gantsara gantsaran magangannun?

Sai da ta lumshe idannuwanta ta hadiye wani yawu makwat, sannan ta daga kafafuwanta ta shiga kara saka
kanta cikin dakin tana mai nufar.......

Comment plz👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻
*KUTKALE*

*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE


BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct
NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan
number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA
SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN
SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN,
.....* taku ce, Sajida😍😍😍😍

1️⃣4️⃣

Nufar gadon da Ni.ima ke zaune tana zarar ido ta yi,


Irin yanda kirjinta ke dokawa da a lokacin ya yi gigin cewa da ita kekek...ba abinda zai hanata yin dayan
biyu, au ta zura da gudu , au ta kwala ihu, domin wannan lamari ba jarumta ya aro mata ba , sai tarin tsoro
da fargaba, ko a abubuwan da aka koya mata ba.a koya mata irin wannan ba.

Tsaye ta yi gaban gadon tamkar an dasata , ta tsurawa Ni.ima ido tanai mata kallon da ita kanta bata san na
menene ba,
Can kamar an tsikareta ta dan farfado ta karasa da kyau wajen bed din ,
Sai da ta saka hannun mai dauke da abin aikinta na caje abubuwa ta caje gadon nan har kasan sa,
Sannan ta dawo tsaye gaban Ni.ima, wace da ba aikinta ne ya kama da hakan ba, ba zata taba gigin cajeta
ba, domin yannayinta bai nuna alamar muguwa ce ba, sai dai a aikinsu babu innocent face da ake ignored,
kowama damka ake a bashi kyakyawan kulawan da ya dace....

Hannunta na dan rawa ta shiga bin du wani yaken da ake iya adana abin cutarwa a jikin Ni.ima har ta gama,
ita kanta Ni.imar ta cika da mamakinta ta zura mata ido ne tana kallonta,

Haka ta gama ta kuma bi dakin da bincikenta sannan ta juya kanta a kasa ta lalubu hanyar fita tana mai jin
zuciyarta na gudun da bata taba yi ba,....namiji?

Duk abinda take yana tsaye ne a wajen da ta barshi yana kallonta,


Shi gaba daya ta zame masa wani abin nishadi, ikon Allah..wai ita nan caje matar da zai yi mu.amala da ita
ta yi kennan? Kar ta kashe shi,

Kafadunsa ya daga, kafin ya juyo da dubansa wajen Ni.ima,


Yannayin da ya ga ta nuna ya jara bashi nishadi,
Gadin ya tunkara kai tsaye, wanda hakan da ta gani ya sakata kara gyara zama tana kara sada kanta kasa
tamkar ta zo gaban sarki,
Tsayuwa ya yi yana mai bin ko.ina na jikinta da kallo,
Zama ya yi bakin bed din, wanda ya bashi damar dora gaba daya kafafuwansa saman bed din aman kuma
ya tankwashe su yana kallonta ya ce" aman ai kin san zaki yi wani abu dan birge ni ba wai kawai ki zauna
min da wadinnan manyan kayan tamkar kin zo gaban liman ba ko?

Gabanta ya yanke ya fadi, abinda zata birge shi? Shi ne abinda ta ayanna a ranta, to aman amarya ai daraja
gareta ko bazawara ana shigo mata da fuskar kamala ana ririta ta, duk kuwa da ta san romonta za.a
sha ...aman ana mai nuna mata da tafiar ba ta hakan bace,
Sai gata, ita Ni.ima, ya Dadynta da momynta, ya daya kwal a wajensu, mai kananun shekaru domin bata fi
ashirin da biyar ba , ta tare gaban namiji ingarma da zuciyarta ta rayu da soyayarsa, darensu na farko, tana
hasashen tarairaya ko dan ramin da yake yiwa....sai gata ita zata tarairaye shi?,

Kokarin mikewar da ta fahimci yana yi ya sakata saka hannunta na fama dake rawa ta rike hannunsa na
hagu,
Ba zata yi gangancin nan ba, ba zata yarda tana kallo ya fice a wajen nan ba, ba zata manta waye shi ba,
dan haka mace ce ita ba zata yi wasa da damarta ba....

Hafsat na fita bata tsaya wajen bodyguards din Ni.ima ba kamar yanda ya dace har ya fito daga
dakin..takim takim takim ta nufi tsakar gidan,

Tana fita bata lura da BS dake tsaye yana gadin wajen ba ta yi gagawar dukewa wajen tana mai dafe wajen
zuciyarta dan ta tsayar da bugawar da take mata,

Riko damatsunan hannayenta da ya yi ya sakata firgita ta mike da sauri da kuma karfi da nihar kaiwa bugo,

Tarewar da ya yi sannan ya bude bakinsa ya ce " hei Bab, menene haka ? Lafia?

Tsai ta yi da yannayinta ta tsurawa fuskarsa ido,


A *KUTKALE* an sha kokarin haye mata,
Sai dai bata taba gannin ainahin abin, tudunsa ko yannayinsa ba, domin za.a shigo mata tsakiyar dare ne su
sha dambe da mai tsautsayin,
Aman yau, dan tudunsa ne ta gani ba wani abu ba, ta tsorata,
Dan me maza fitsararu ne?
Ba sai ya nunawa duniya shi din dan duniya bane za.a yarda, ya bar abinsa a shi kadai mana, ki Allah ya yi
hani ga bawa tonon asiri idan ya rufa maka,

Da sauri ta janye kafadunta da ya rike yana son ta dawo hayacinta,


Sai da ta janye ya tuna cewar a duniya ta tsani lamari irinnan a taba mata kafadarta,
Koda wasa bata son hakan,
A hankali ya dan ja baya ya bata spac, hakan ya saka ta sauke ajiyar zuciya ta tsurawa waje daya ido tana
mai sauraron yanda BS ke faman kwontar mata da hankali duda bai san abinda ya firgitata ba,
Sun dauki lokacin mai tsayi, domin har duhu ya shigo sosai,
Ita kam tana cikin halin rashin sallah hakan ya saka bata nemi zuwa sallar magariba ba, BS kuwa bai je ya
yin bane,
Suna hira tana dan kai dubanta wajen windows din dakin, zuciyarta na cike da tambayoyin da ta san ba zata
taba samun amsar su ba..........

Kanta ta kuma dagawa ta kai dubanta wajen windows din, idannuwanta ne suka sauka a kan irin jar fitilar
nan da ake daidaitawa jikin garu, wace ke hade da bindigar seti, ana daidaita wajen windows din dakin
Ni.ima,

Da idannuwanta ta yi masa nuni, wanda hakan na cikin aikinsa,


Da wani irin matsiyacin gudu ya juya ya fita waje inda ita kuwa ta juya da mugun gudu ta afka cikin dakin
ba tare da damuwar wani abin ba kuma,

Tsaye ta tarar da shi wajen windows daga shi sai gajeran wandon dake cikin jalabiyarsa yana tsaye kikam
ya lumshe idannuwansa iska, sansanyar iska, mai cike da ni.ima na hura shi, yana jin kansa sakayau,

Wani irin ihu ta yi tana mai cewa" ka kwonta!

Juyowa ya yi da sauri, da kuma mamakin me ya dawo da yarinyar nan a wannan lokacin da bai nemeta ba?
Sai ganninta ya yi a kiftawa da bismillah ta masa wani irin afkowa gaba dayanta a jikinsa wanda hakan ya
saka shi zubewa kasa, domin kuwa ba wani shiryawa ya yi ba, ba wani tunanin haka zai faru ya yi ba a
ransa,
Suna faduwa kuwa karan harbi mai boyayen kara ya fasa gilas din dakin ya tafi ya huda labulen ya shiga
jikin garun domin kuwa bai samu wanda aka daidaita dominsa ba,

Gannin hakan ya saka mai harbin gane cewar an gane zai yi harbin, dan haka da sauri ya tatare ya nemi
hanyar tsira.....

BS ba inda bai duba ba, haka abokin aikinsa ya kasa ya tsare a bakin titin yana gannin shige da fitar kowa,
ya zubawa ko.ina ido , inda gaba daya sauran masu tsaron gidan aka shiga haya haya ana ta duduba masu
shiga da fita, hakama cikin gidan du sun rikice bodyguards din sun fitar da du wani soja daga wajen da ya
shafi Abdul da matarsa sai hayaniya ake,

A lokacin da abdul ya gane abinda ya faru,


Ya ganshi yashe kasa, yar yarinyar nan dare dare saman kirjinsa ta saka hannunta ta rufe bakinsa,
Ya rintse idannuwansa yana sauraron yanda zuciyarta ke dokawa,.....
Tabas jaruma ce, sai dai boyayiyar jaruma,

Da sauri ya yinkura ya cireta a jikinsa da niyar mikewa sai dai ta kara damke hannunsa da yannayin tashin
hankali ta ce " ka daina yannayin masu kudi ko sangartatu ka gane rayuwarka ke hatsari ka duka, kar ka
mike, domin ba.a ga wanda ya yi harbin nan ba!

Yannayin yanda ta yi magana murya a kausashe, da irin yanda ta bashi ordre ya saka shi yin dan tsai yana
kallon fuskarta, kafin ya bi hannunta da kallo,

Da sauri ta cika hannun nasa tana mai kara tamke fuskarta , tana kallo ya mika hannu ya dauki jalabiyarsa,
ya dan tsurawa Ni.ima ido sannan ya juya ya fice,

Kuka Ni.ima dake dukunkune waje daya ta fashe da shi tana mai bin hanyar da ya fice da kallo,
Shikenan , ta shigo rayuwar hadari, ashe da gaske dai neman ransa da du wani wanda ke tare da shi ake?
Yanzu da an same shi, da shikenan har an mayar da ita karamar bazawara?

Da sauri Hafsat ta kawar da kallonta saga kan Ni.imar ta bi bayansa,

Dakinsa ya je, kai tsaye ta ratsa ta shiga inda ya shiga,

Tsayuwa ta ja ta yi dan ta gane wankama shi ya shiga,

Tana nan tsaye ya fito da tawul daure a kugunsa hakan ya saka ta kawar da dubanta daga wajensa,
Ikon Allah ita bata taba gannin bakin namiji mai cikar gashi a fatar jiki irin wannan ba, dama ba sai
larabawa, buzaye , fulani, da dai sauransu keda irin wannan izgar gashin?

Hankali kwonce ya cire tawul din, ba tare da damuwar tana dakin ba, ya saka wandonsa na ciki, sannan ya
dora wani wandon baki,

Rigarsa ya saka irin mai lafewa a jikin mutun din nan du tana kallon wajen da ba wajensa ba,

Bata tashi juyowa da sauri ba sai da ta ji wani kara yannayi na gyaran bindiga,

Da sauri ta juyo tana mai zaro ido tana kallon irin yanda ya saka kartushi a yar karamar bindiga ya ja ta ya
gyarata da kyau sannan ya yi mata kyakyawan ajiya a kugunsa, irin ajiyar da idan ba karantun hakan aka
koya maka ba , ba zaka taba iyawa ba,
Bata gama mamaki ba sai da ta ga ya dauko computernsa ya kunna ya ajiye saman table din dake dauke da
turaruka shi kuwa ya dora hannunsa na hagu dake jimke saman table din, na daman kuwa ya shiga dadana
computern kamar wanda shi ya kirkiri abinsa,

Bakinta da hancinta gaba daya a bude suke tana mai binsa da kallo, har ya gama nuno waje waje a jikin
computern dake nuna ciki da wajen gidan, abin mamaki har benen da aka yi harbin daga shi gashinan waje
waje radau ya fito a sama

Sai da ya yi wani recherche sannan ya dora wata hanya, wace ke nuna wani mutun tsaye yana ta waige
waige bayansa goye da wata jaka sannan kunnensa yana waya da alama wayar a hanzarce yake yinta,

A tare suke kallon mutumen, kafin ya dago da dubansa ya dora saman kanta, irin yanda ta matse masa waje
ita kanta bata kula ba, ta raja.a tunaninta da hankalinta kan mutumen nan,

Yannayin kallonsa ya shaida mata yana nufin wannan shi ne, dan haka da sauri ta je dora hannunta saman
computern dan gannin hawa na nawa ne, da yannayin da zai kara tabatar mata da wajen,

Da sauri ya tare hannunta, domin gaba daya computern na anfani da emprinte din yatsutsansa ne, dora
hannun wani na iya tayar da karan laluwar da ya saka gaba daya a cikin gidan,

Fitar mata da abinda ya tabata take son gani ya yi, yana mai dan kara yarda da yannayin aikinta , domin da
wanda bai san aikinsa bane yana iya fita da gudu ya shaidawa mutane ai yana nan, a fantsama a yi ta hauka
ba.a samu mutumen ba,

Maimakun ya ga ta fice da gudu sai ya ga ta kara dan abin hannunta ta ce" BS, suspect din mu na hawa na
biyu wajen matatakala yana kokarin saukowa, sanye da bakin jeans da riga baka mai dogon hannu, fari ne
kar bayansa dauke da jaka baka mai dauke da bindigar,
Yana waya, ku kula yana waya, kar ya jefar da wayar .....

Shiru ta yi ta tsurawa screen din ido , inda shi kuwa ya tsura mata ido yana kallonta,

A sakalce ya ce" ke, yo ke bakya zuwa ne? Kin wani sakani gaba kina kale min na.ura?

Bata daina kallon computern ba ta bashi amsa a takaice cewar" eh!

Murmushi ya yi ya juya ya zauna saman kujera ya daga hannayensa ya dora bayan sumar kansa ya dan
daga kujerar daga gaba ya watsa kafafuwansa yana kai kawo yana duban yarinyar,
Bakinsa ya tabe , ya so ta bara masa dakin, shima ya fice ta inda zai gyara shi ko zai damki wannan wannan
mai harbin, aman ta wani zauna , shi kuwa ba zai yarda saboda haka wannan yar yarinyar ta gane menene
aikinsa har ta falasa shi ba!

A hargitse mutumen yake doka waya wa wanda ya bashi wannan mission din,
Ana daga wayar aka ce da shi" ka tabatar ka yarda layin nan ko ka hadiye shi, sannan ka san yanda zaka
kubuce masu, idan kuwa aka kama ka, ka san ko rayuwar wa ka saka a hatsari!

To fa........., shin za.a kama wannan mutumen kuwa?


Yaya tafiar wannan aiki tsakanin Hafsat da Abdul?
Ni.ima fa?
Bs Fa?

Na ji dadin comment din ku sosai wollah,


Ban bayar da amsa ba domin ban zauna ba,
Ina biye da ku kamar yanda kuke biye da ni makaranta *KUTKALE*
*KUTKALE*

*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct
NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan
number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA
SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN
SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN,
.....* taku ce, Sajida😍😍😍😍

1️⃣5️⃣

*DUNIYA MAKARANTA,*

ASALAMU ALAIKUM

A lokacin da su BS suka cinma wannan mutun, sun tarar da shi yana zubar da wata irin kumfa , wato ya
hadiyi poison,

Ba yanda basu yi ba dan gannin bai auna barzahu ba, sai dai ina poison din mai karfi ne,
Wayarshi dake yashe dan nesa da shi suka dauka da sauri,
Bayanta BS ya buda dan cire layin, sai dai wayam ba layi a ciki, ba alamunsa,
Cike da jin haushi ya doka wayar da kasa yana fadin shiiit!
Kafin ya kai dubansa wajen yaren dake tare da shi ya basu umarnin maza maza su duduba layin inda ya
jefar da shi,

Hafsat dake tsaye tana kallo ta yi saurin maido baya kadan,


Inda ya yi kamar ya labe fuskarsa ta yi zooming,
Nan ta ga yanda ya yi da layin, wato a bakinsa ya saka shi ya taune shi sannan ya ya hadiye,

Bata san lokacin da ta dora hannayenta biyu saman kanta ba, ta janye atach mai ruwan blue din dake kanta
dan bada kama, ta yar ta dan ja da baya irin desespoir din nan,
A hankali jiki a sanyaye ta ce" BS, kar ku ba kanku wahala, ya taune layin kafin ya hadiye shi

Sai a lokacin ta tuna da yana zaune a dakin, sai a lokacin ta kai dubanta inda yake zaune,

Kuri ita yake kallo, tun da ya hadiye layin shi ya gani, kuma ya gane nufinsa, aman kuma ya barsu su yi
aikinsu,
Yannayin da ta nuna na tashin hankalin echec din abinda ta saka a gaba ya matukar bashi mamaki,
Menene damuwarta haka a kasan zuciyarta? Ko kashe shi aka yi ita fa bata da asara domin kudin aikinta
cas sai an cashe mata su,
Abu biyu ke iya saka ta a wannan yannayi, tana da damuwar kanta,
Ko kuwa ta matukar dauki aikinta da mahinmanci,

Ido cikin ido suke kallon junna,


Kafin ya ga ta mike ta tunkaro inda yake zaune,

Sai da ta zo kusa da shi, irin kusan da babu wani space a tsakaninsu ta saka idannuwanta cikin nasa ta ce"
ka bamu damar yin aikinmu yanda ya dace,
Ya za.a dauke mu aiki, ba.a bamu wani cikeken bayani a kan aikin ba, ba.a fada mana girman risk din da
muke ciki ba, bamu san komai ba, kuma a ce zamu iya yin wani abin kirki? Ya dace kafin mu hau filin aiki
mu san ko kai waye, meye sana.arka, meye tarihinka, me ke yawo da kai haka da za.a farauci rayuwarka
daga zuwanmu, kafin mu zo an farauce ka har haka? Kana da wanda kake hasashen shi ke neman
rayuwarka?

Duka magangannun nan da take masa , cikin yannayi na daure fuska, da kuma iya gaskiyar abinda take son
sani kennan take yi, sannan idannuwanta tsai cikin nasa, ba tare da ta ji wani dar ko wani nauyin saka
idannuwanta cikin nasa ba, haka ta kare zanenta sannan ta yi shiru tana mai dubansa , hakan na nufin
amsarsa take jira.

Kijerar ya ajiye daga lilon da yake mata, sannan ya mike tsaye, wanda mikewa ta saka kirjinsu kusan
goguwa da juna har sai da ta dan ja baya,

Tsayuwar da ya yi ya sakata dan daga kanta fan kar ya ga wasa a tatare da ita ko gazawa a idannuwanta ta
ci gaba da kallon nasa wanda hakan shima ya so din,

Idannuwansa ya bude mata baki daya yana dubanta ya ce" wacece ke? Su waye mahaifanki?

Kanta ta dafe da yannayin irin wannan tambayar ta isheta , kafin ta kuma dubansa ta ce" ba shi ne abinda ya
kawo ni gifanka ba! Dan me kai ba zaka iya bamu information din da muke so ba?

Idannuwansa ya kankance ya matso kusa da ita domin ta kara ja baya irin suna jin har bugun zuciyar juna
ya ce" ban ga dalilin da zai saka na dauki karti biyar na tinga biyansu kudin aiki masu tsokar da ba a gine
nake ba sai na girgije dan an wawushe ni, sannan kuma na masu rabin aikin!
Me aikin ki ya kumsa? Bincike, shige shige, dan samun amsoshin da suke cikin hadari, mutu ko rai!
Sai ki zauna, ki auna, ki yi aikin ki yanda ya dace, ba wai ni kamar wani sauna na zauna ba kwashe komai
na fada maki, na ciyar da ke , kuma na biya ki kudin aiki ba!
Yana gama fada ya juya ya fice a dakin, inda ya nudi dakin Muhammad da sojoji suka kasa suka tsare sai
muzurai suke,
Yana zuwa suka bar shi ya shiga....

Mutuwar tsaye ne ta yi, na dalilin irin amsoshin da ya bata, *KARTI BIYAR* , kennan mu duka karti ne?
Wannan mutumen akoy dan wulakanci na bugawa a jarida! Wannan mutumen yana neman fitina da ni!
Yana son tashin hankali da ni! Zan kuwa gwada maka na san aikina....
Dubanta ta kai kan computersa, wace ko a dazu da ta dano dan yin zooming din vidion wanda ya zo harbe
shi da ta taba ba tare da ta tsaya ya yi mata ba sai da gaba daya gidan ya dauki wata laluwar da ta kara
hargitsa masu tsaron, wanda da sauri ta dana buton din dake kashe kukan,
Ta san a cikin wannan computern ba za.a rasa wani abin ba,
Sai dai ba damar tabawa dan yanzu zata jawa kanta taruwa a kai, shi kuma ya tirke ta da tuhumar me ta
koma yi.masa cikin computer

Nauyi kanta ya mata, nauyi da zafi, a hankali ta juya ta fice ta shuga fafutukar yanda zata yi

Wannan aikin na bani tsoro Abdul,


Ka duba ka ga yanda wannan abin ya jaza mana balakin da ya taba rayuwar Ummih?

Ka bar wannan binciken mu koma gida Abdul, wanda ke bibiyar rayuwarka, ko kiyar bera ya sha ba zai
taka kafarsa saudiya da nufin hakan ba, dan ya san gaba da gabanta,
Aman a kasar nan, tamkar gidan dake bude ne, hayam, baka da wani kariya Abdul, dan Allah ka bari ya
dace ka fuskanci rayuwa ka rungumi matarka ku hayayafa ka samu farin cikin rayuwa,

Abdul dake dubansa ya yatsina fuskarsa ya ce" farin ciki? Farin ciki?
Rabona da farin ciki, tun daga lokacin da na kama shi yana dukan mahaifiyata a gaban kanwata,
Rabona da farin ciki tun daga lokacin da na gane ba kowa ne ke dirawa dakin kanwata ba sai shi,
Rabona da farin ciki tun daga lokacin da na nemi mahaifiyarsa ido rufe aman na rasa har ta mutu, ni, na
tashi da kudurin bayan ya mutu ma, zan tabatarwa iko cewa shi da wannan marar imanin ne suka tagayara
rayuwata,
Duka a kan me?
Dan yana da wannan dukiyar,
Duka dan me?
Dan rayuwar gayu da ta saki, ta sakankance ta bara masa tarbiyar kanwata , wankanta, saka mata sutura,
pampos , bata abinci saman cinyarsa, ana dariya ana dauka a waya ana yadawa a duniyar gizo gizo, mutane
na yabawa suna tura lyk dan kawai a fada, a dauka, duniya ta yayata,
Duka dan me, dan a yi tunkaho, a nunawa duniya, a kuma daki kirji da akoy kusanci tsakanin dan da
uban....
Ba.a ankara da komai ba, aka ci gaba da rike wannan relation din har ta kai idan zai yi tafia da ita yake yi,
Ta fara girma wajen shekara biyar aman baya jin kunyar saka kaya ko tubewa a gabanta ba, domin shi fa
yar jaririyar yarsa ce mai tatata marar wayo,
A hankali ta horu da gannin al.aurarsa ba wani abin bane,
Bayan ta tasa har ta kai shekara bakwai , takwasma yakan dorata saman cinyarsa yanai mata cakulkuli
domin nishadinsu, idan uwar na kisa ta yi ta kakaba dariya,
Dalilin nisantani daga kusa da su dan na kasance mai nuna ba za kyau irin haka, a islamiya ana fadin hakan,
Tafia ta yi tafia na gane cewar rayuwar da ta zama baka a tare da shi a tsakaninsa da yarsa, wanda
mahaifiyarta bata sani ba, sai dankon soyayar dake tsakani, sannan ya cire du wani kuntatawa da yake mata
da, ya sakar mata mara ta yi fitsari son ranta, cewar cutar yarta ne ake, kuma hakan ba shi daya keda irin
mu.amala kazamar mu.amala a gidansa ba, harda aminansa su suka kwadaita masa wannan lamari, wato
gida bai koshi ba ba za.a kaiwa daji ba!

Muhammad da ya rintse ido dan yannayin abubuwan nan na girgiza masa zuciyarsa ya ce" shut up plz man!

Abdul Jabar ya karasa kusa da shi sosai ya ce" Na yi wannan karatun mai cike da hatsari bayan nunawa
duniya kasuwanci nake ne dan na bi didigin su,
Ni na san makashina,
Abinda ban sani ba shi ne...waye makashin, waye mataimakin, kuma waye ya kashe Ummih?
Abinda ban sani ba shi ne...waye ya hada ni da jarabar mata? Idan na ga mace, yanda ka ga bindin kare na
kadawa ko bunsuru na tabe lebe haka nake,

Baka da tabas Abdul, daga jin maganarsu ka hau haka ka zauna, dan Allah ka daina,

Abdul ya daki karfen bed din da aka yi runfa da shi irin an saki labulayen nan ya daga muryarsa wanda da
ace irin ginninmu ne da tabsa du sai an ji abinda yake fadi ya ce" ka ci gaba da boye min kennan?
Baka yarda ba da daya daga cikinsu ne ya kada jirgin da Abdul Basid ke ciki wanda sai da aka bashi damar
yiwa mahaifiyata vidion ban kwana?
Baka yarda ba da , qn harbe shi ne sanadiyar arzuzumin wandonsa da baya iya daurewa sai da ya afkawa
matar amininsa?
Baka yarda ba da *Ubana* mijin Ummih ya rayu bisa fuska biyu a gaban matarsa salihi a waje dan duniya
ba?
Ba zaka yarda cewa idan nace da kai Abdul Basid may be bai mutu ba, yana raye ina iya yin gaskiya?

Yaushe zaka yarda cewa aminan Abdul Basid ke bibiyar rayuwata bisa dumbin arziki da kuma daukan
fansar amininsu wanda suke gannin sun kashe maciji ne basu sare kansa kuma suka dandatse kansa ba?

Kai Muhammad Auwal Bin Muhammad yaushe zaka yarda da aikin da nake ba cira na yi daga sama ba, na
cancanci zama zakara kuma kwararan mai.......

Dan suuu din da ya ji dalilin kawo hannunsa kusan wuyan rigar dake jikinda ne ya saka shi datse
maganarsa tare da bugun zuciya,
A lokaci daya ya kai hannunsa na dama wajen ya lalubo dankaramin speaken da ta makala masa a lokacin
da suke tsaye jiki da jikin juna sunaiwa juna kallon doya da man ja, wanda ya lumshe a idannuwanta bai
ankara ba, sai yanzu da agogon hannunsa ta shaida masa da haka,

Da hannunsa na hagu ya nunawa Muhammad abin, sannan ya juya da wani mahaukacin gudu ya koma
dakin da ya barta,
Sai dai ina bata nan,
Ba ita ba alamarta

Da wani irin sauri har yana hardewa ya kuma fitowa ya daga hannunsa yana yafito du wani ikon dake cikin
gidan fuskarsa tamkar na bakin kumurci ya kare masu kallo

Bai ganta ba, babu ita a wajen ba alamunta,

Cikin yannayin damuwa ya kara bin su da kallo baki daya, inda dubansa ya tsaya kan BS,

Takawa ya yi ya karasa gabansa, du girman jiki, da yannayin karfi na BS ashe cika ido ne, a yanzu da
Abdul ke sanye da wannan body din sai gaba daya ya dame BS ya shanye,
A tsayima ya fi shi nesa ba kusa ba, dan haka yana tsayawa gabansa ya saka idannuwansa da sukai ja cikin
nasa yana dubansa, kafin ya sauke ajiyar zuciya kamar zai yi rada sai kuma ya bude muryarsa ya ce" ina
take?

BS da ya fara kokonton yannayin Abdul, cewa du inda ya fito wannan ba kawai elhaj mai kudi zaune da
bakin duwaiwai ciki cike da sangarta bane, ya dube shi shima da yannayin kulawa sannan ya ce" wa ce?

Shi kam haushin tambayar ya ji, hakan ya saka shi takawa ya yi gaba kadan, ya kuma dawowa ya ce"
yarinyar dake biye da ni!

Sai a lokacin BS ya lura da Hafsat bata wajen, gabansa ne ya fadi tare da tsoron kar a je an dauketa ne?
Da yannayin tashin hankali ya kai dubansa wajen Abdul, sai dai bai tsaya jin amsarsa ba ya juya da sauri ya
fita da niyar nemota da kansa, inda su BS suka bi bayansa da abu biyu, bashi tsaro, da kuma neman
Hafsat........

*Shin ta ji du abbin nan?Wai waye Abdul? Ina Hafsat ta shiga? Idan Abdul ya ganta, me zai faru da ita?
Duba da ta saurari sirinsa, duda kadan daga cikin sirrin ne, wato tsunguye tsunguye.....*
Toh fa

😌
*KUTKALE*

*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct
NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan
number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA
SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN
SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN,
.....* taku ce, Sajida😍😍😍😍

1️⃣6️⃣
A lokacin da suka fito gaba dayansu da yannayin na zakunna, kowane na jefa kafarsa inda ta je, suka tsaya
gaba dayansu a tare sakamakon ganninta tsaye ta zuba masu ido su duka,

Sai da gabansa ya yanke ya bada wani irin sautin da kunnayensa suka jiyo masa,
Tsaye take kawai, hannayenta gaba daya a sake, wandon dake jikinta irin mai lafewa a jiki ne aman kuma
sakake wajen mazaunanta kawai ya rike , sai riga mai botura da wata a ciki wada dalilin bale boturan da ta
yi ya saka ake ganninta, kanta dauke da asalin gashinta ba wancen atach din ba,
Fuskarta babu ko digon kwali bale a yi hangen hoda ko wani abin,
Aman wani fayau da shiga ido da take sai a hankali, dole ta girgizawa namiji lafiyaye zuciya sai dai idan
zuciyar taka na hangen wata sai ka kyasa a ranka ka huce wajen,

Hannayensa ya daga ya cusa cikin gashin kansa da ya bar suma ta taru sannan baya gyarawa,

Sai da ya dan waiwaya ya ga tsayuwar me kuma suke a bayansa? Sannan ya daga kafarsa ya tunkareta,
Hannunta na dama ya damka ya jata tamkar rakumi da kala haka ta bi shi ba tare da ta warci hannun nata
ba, ba kuma ta yi masa gardama ba,

Da kallo suka bi su, inda BS ya daga kafarsa ya bi bayan su da saurin gaske, sai dai yana karasawa Abdul
na banko kofar da wani irin karan sautin dake nuna halin bacin ran da yake ciki,

Wani irin hankadata ya yi cikin dakin dake mamaye da duhu, wanda yake daya daga cikin dakunan gidan,
shi kansa bai san ainahin inda zai je ya kuna fitila ba, sannan tun da ya hankadata yama rasa inda ya
hankadata,

Garu ya yi nufin kaiwa naushi, wanda sai da ya naushi iska sau uku kafin ya samu hannunsa ya naushi
garun da wani irin karfin da da normal ne sai ya ji jiki ainun, aman da yake ransa bace ne sai ihun bacin rai
da ya saki murya kausashe ya ce" me kika ji? Me ki ka ji nace?

Inda yake kallo daban, inda muryarta ta fito daban, domin ita a bayansa take, a hankali, cikin mutuwar jiki
ta ce" ina bayanka,

Juyowa ya yi ya yi shiru, inda ya dauke numfashinsa, yana so dole ya lalubota ta habyar numfashin da take
saukewa,

Fahimtar hakan da ta yi ya sakata tsayar da numfashinta sannan ta canza waje da sauri ta saisaita ajiyar
zuciyar da take yi, ta dan labe wajen labulen wajen ta ce" a wajen formation din zama gagarimin sojan dake
aiki wa kasashen duniya baki daya, wanda yana da damar yin operation inda ya ga dama, yana da takardun
shaidar shi dan kasar da du ya yada zango ne, shi dai wannan mutun ko shugaban kasa na mangarinsa
domin ba.a bayar da formation dinsa a kananun kasashe sai irin su chaina, dubai, ko su Saudiya. Japan...da
dai sauransu....
Wanda a cikin mutun hamsin bai fi biyar su fita ba, kai ana iya goge kowa a hanawa duka hamsin din!
Sai kuma bodyguard , ana koya masa irin wannan abin a sama sama ba a zufafe ba saboda halin rayuwa......

Labulen da ya damka ne ya sakata saurin matsawa ta canza waje ,

Sai da ta sauke ajiyar zuciya ta ce" a ciki.... *WANENE KAI ABDUL JABAR ABDUL BASID?*

Gabansa ne ya wani irin bugawa sakamakon irin yanda ta ja sunnansa lokaci daya take neman sannin waye
shi, a iya yau, a iya hafuwar yau, awowin da ba zasu fi goma sha biyu ba , wanda da yawa da suke tare
shekara da shekaru.basu san hakan ba?

Jikinsa ne ya yi la.asar, sanyi ya yi sosai da sosai, dan haka sai ya daina neman lalubo infa take ya saki abin
sauraron da ta laka masa nan ya juya ya lalubi kowa ya bude ya fice a dakin,

Bai yiwa kowa magana ba, sai dakinsa da ya je ya shige ya rufe ,


Bakin bed dinsa ya zauna ya dora kafarsa daya kan daya ya daga kansa sama,

Wasu zafafan hawaye ne suka shiga bin gefen kumatunsa a lokacin da ya tuna mahaifiyarsa da irin rayuwar
da ta yi cikin duhu, haka kuma irin mutuwar da kanwarsa ta yi, da irin rayuwar da mahaifinsa ya yi ,
Shi kansa irin tasa rayuwar ta yanzu, wace yake tantiri fitinane a idon mutane da yawa,
Kai innalilahi wa.ina ilaihi raj.une, shi kam bai ga ranar kudi ba,
Kudi sun saka familynsa a halaka,
Shi da kudin nan na haramun ne, ba zai zauna a cikinsu ko na second daya ba,
Sai dai kudin irin gadon nan ne na iyaye da kakani,
Irin kudin nan na da, manyan kudade da kadarori masu albarka, shi shi daya,

A hankali ya kai idannuwansa kan wandon dake jikinsa,


Jikinsa ya ga ya canza yannayi kamar yanda ya ji a jikinsa.... *mace* yake bukata, mace yake so a yanzun!
Wannan lamari ya saka shi dora hannauensa gaba daya saman kansa, wannan wace irin masifa ce aka hada
shi da shi? Shi kennan za yana jin bukatar mace kamar yanda yake da bukatar cin abinci a kowani lokaci?
Ni.ima ce ta fado masa a rai,
Ya yi mata zuwan biji biji, wanda bata taba sannin.harkar nan ba aman sai da ya mata zuwa biyu, wai a
hakanma ya mike yana shan iska ya koma ne yarinyar nan ta fado masa daki,

Juyawa ya yi ya kurawa waje guda ido, kafin kuma ya saki murmushi, a fili ya ce" makashi, baka da
mutunci, wato so ka yi ina ciki ka kashe ni, na jibgunma yarinyar mutane sannan kowama ya ga tsiraicina
ko? Harda wannan piciciyar yarinyar domin sai an zare ni daga jikin Ni.ima....
Murmushi ya yi ya juyar da kansa yana mai hangen maganin da ya saya da niyar fara sha, domin ba zai
koma harkar da yake a da ba, baya son komawa, ya gwamace ya yi ta kawo matan a matsayin na aurensa
yana bin dakin kowace kowani dare har ruwan jikinsa ya kare idan ya mutu ai shikenan kowama ya huta!

Haka ya yi ta abu, bayan ya sha maganinma shi dai ya ji ya dan rage nauyi, aman ba wai wani sakayau ya ji
shi ba,
Dan haka alwallah ya dauro ya zo ya hau darduma ya shiga gabatar da sallah.

Ta jima tsaye wajen da ya fice, idannuwanta lumshe, gaba daya ta raja.a tunaninta kansa , yannayinsa, irin
abubuwan da yake yi tamkar mai aljannu, kai harma da irin yanda ya shigo da ita da niyar kowace wace,
aman kuma da ta tabata ta tabo gaskiya cikin lamarinsa sai kawai ya fice a dakin,
He's a brave man? Or Bodyguard?

A wannan tunnanin ta silale jikin karfen ta jinginar da kanta,


Zurfafa ta yi a tunanin da kulawa da kuncewa,
A fili, kuma muryarta na rawa tamkar zata fashe da kuka ta ce" *shi, nasa iyayen basama duniyar*,

Hawaye ne suka shiga bin kumatunta, hawayen tausayin kanta, da kuma kulaliyar maganar da ta tsinta tasa,
innalilahi-wa-ina-ilaihi-raj.une.
Lamarinka, lamarinka ya fi nawa hargitsi..........zan san ko kai waye!

Washe gari karfe tara na safiya ya fito daga dakinsa da ya sakawa kys ya gama ibadarsa ya huta ,
Tun da ya bude ya fito, su su uku dake tsaye suka dan juyo dan gannin wanda ya bude dakin,

Su duka sun sha mamakin a yanda ya bayana yau kuma,


Hashin kansa da ya taran nan ya zauna ya bashi lokaci wajen yi masa gyara irin na samarin america , wato
askin nan na yan basket ball mai salo da kyan kallo a ido, sai dai sak irin na yan duniya ne!
Ya rage bajewar sajen fuskarsa ya siririnta shi a fuskar tasa, haka kuma gemunsa ya rage shi sosai ya bar
dan kadan da ya yiwa fuskar das da ita ta bada kala,
Lebensa na kasa ya fi na sama girma, yau wajen broshing ya sha garzar da ya saka ya dawo fresh yanda
yake da, wato kalar pink mai dan duhu duhu da shi na kasan na saman kuwa baki,
Kamar wanda ya caje gashin idonsa, yannayin kulawar da ya bashi da kayan kulawar ya saka harta da
gashin idon nasa ya yi tsai kamar barkonon tsohuwa kirikiri ba tsoro ba kunya yana kallon mutane, haka
kuma dara daran idannuwansa sun kara fitowa suna kallon du wanda ya kale su ido cikin ido,

BS da jibrin suka juyar da kansu daga dubansa inda Hafsat gabanta ya yanke ya bada wani irin sautin da
bata shirya ba, hakan ya sa ta lumshe idannuwanta tana adu.ar da ta bata karfin gwuiwar controling din
abinda take ji wanda ta baiwa kanta amsar hakan ya faru ne dan jiya ta ji wani yanki na sirrinsa , yau da
take tunanin ba zai iya mikewa bisa kafafuwansa ba sai gashi ya fito a ba zata, cikin yannayi na karfi,.....eh
ta yarda da abinda Ni.ima ta fada a yanzu da safe da ta je gannin ko can ya kwana dan ta dora masa break
fast ta tarar da ita zaune bakin bed ta fito a wanka daure da tawul tana gyara fuskarta cikin yannayi na
kamar ba abinda ya dame ta,
Da ta tambayeta sir fa?
Sai ta tsura mata ido, can kuma ta girgiza kai ta ce" bai shigo ba tukunnan,

Har hafsat din zata juya ta ji ta ce" Bodyguard,

Juyowa Hafsat din ta yi tana kallonta, nan Ni.ima ta mike daga zaunen da take, ta nufota da wata irin tafia
ta tatata ta tsaya gabanta ta ce" ki kular min da tashinsa, zaman sa, motsin sa, cin abincin sa, komaima,
hakin kula da shi a wuyan ki, idan har suka cin masa....ke kika kashe shi, ni kuwa ina numfashi ne da
numfashin sa, kin ga kin kashe rai biyu! *Ina son mijina, komai irin halayensa*

tunaninta ne ya katse, sanadiyar jin an dauke hular gashin da ta dora ta yau mai shigan blonde,
Da sauri ta zaro ido sakamakon farar rigar dake cikin Costume din jikinsa da ta hanga domin ya matse mata
waje irin sosai din nan,

Da sauri ta saka hannayenta ta tare hular gashin wace a lokacin da tana kanta tamtar irin fararan americain
din nan, aman yana cirewa ta dawo kamaninta irin filanin nan masu dukan ido da zuciyar mai kallon su.

Da wani irin yannayi ta dago da dubanta ta kai wajen hular gashin, ya riketa taf ya ki sakar mata abinta,
Dubanta ta maido kansa,
Sai da gabanta ya yanke ya fadi sanadiyar idannuwanta da ta saka cikin nasa,
Wani nauyi ta ji idannuwanta na neman yi mata , sai dai ta ki ta cire dubanta a kansa danma kar ya dauka
wani tsoronsa ko wani abin ne,
Tana kallonsa shi ya lumshe nasa idannuwan, sannan ya fuzge hular gashin ya jefawa BS da ya kuma
juyowa jin shirun ya yi yawa,

A gimtse ya ce" ni da ba arne ba, yaya za.a ringa bina da gashin arnawan!

Shi dai BS tarewa ya yi ya mikawa dayan abokin aikinsa, shi kuwa ya juya da gudu ya koma ya ajiyeta ya
dawo,

Gaba yake, tafiya yake hankalinsa kwonce, takalman kafarsa sau ciki bakake sidik sababi fil sai bada kala
suke a cikin yannayin tafiarsa,
Bayansa Hafsat ce itama sanye da bakaken kayan wando da riga, sai bakin gashin kanta dake fili ba dan
kwali, sai gilas baki da ta saka dan madaidaici tana lure da dukan wani motsins, wanda gilass din na aiki
ne.

Motocin da aka janyo ne ya saka shi dubansu, wasu motoci ne da ba nasa ba,
Aman bai yi tambayar ko na waye ba, dan ya san ba zai fice su suka kawo su ba,
Maduban motar da aka bude masa ya shiga ya duba,
Bayan ya zauna Hafsat na zaune facing dinsa, BS na gaba kusa da direban da su suka kawo abinsu, ya mika
hannu ya daki madubin motar wanda hakan ya saka su kallon shi gaba dayan su,

Murmushi ya sakar masu ya dage girarsa guda ya ce" dan na kara yarda idan har wanda bulet din baya
ratsawa ne,
Kunfa fara jan attention dina, ba laifi kuna kokari..m
Ba wanda ya bashi amsa, saima hankulansu da suka maida bakin titi ana jan motar,
Irin kallon da yake binta da shi, irin tsareta da idannuwansa da yake ne ke sakata tsarguwa walahi,
Banzan kallo ne da shi, irin kallon nan na kurewa mutun waje,
A hankali ta sosa keyarta ,
Ta kale shi a sace ta ga dai shi ko.ina na jikinta ne yake bi da kallo,
Gashin kanta ta saka hannunta sosa, ta kara sosawa irin ta samu kwarin gwuiwa ko zai gane ya daina yi
mata wannan kallon,
Aman tana kuma dubansa ta ga ita din dai yake kallo,

Gilashin idonta ta cire, ta wara kafafuwanta, ta dora hannayenta saman gwuiwoyin kafafuwanta ta tsura
masa idon itama tare da cuno bakinta da kuro idannuwanta irin kale ni da kyau din nan🙄

Murmushi ya saki shima ya yi exactly yanda ta yi , hannunsa ya dago ya ka8 wajen hancinta da nufin
shafawa, sai dai ta kauce tana hada fuska,
Sai da ya kara sakar mata murmushi ya ce" idan ba Allah ba, ba wanda ya isa ya zana mutun ya fito das da
shi, ke wollah kina da kyau, wa kika biyo? Maman ki ko baban ki?

Da mamaki ta dawo da dubanta wajensa, sai dai bata gama mamakin hakan ba ya ci gaba da magana
hankali kwonce, wanda du abinda yake fadi kowa na jin sa, ya ce" kin ga, kyakyawar halita da ke, yar
caras, ga kugu...
Ya saki murmushi , ya ci gaba da fadin...ga gashi, ga ido, ga dogon hanci, ga dan baki mai dadin tsotsa🙁.....
Murmushi ya kuma yi, ya ce" ke karantar jikinki da kasancewarki gardi kawai ya bata, kin ga jikin ki
karami ne sosai, haba namiji na son ya ringa damka, ba wai ya ringa tsakura ba, kuma yana son ya ji lema
ba wai kamas ba,
Kin ga yawo jiki a bude, na busar da mace, ruwan jikinki yanzu haka ba komai , du ya tafi, haka kuma
Shut up!
Ta fada ranta bace, fuskarta har ta yi ja dan masifa....
Sai fai kafin ta yi shiru da hakan muryarsa ta daukaki tata, ta fi tata nuna masifa ta hanyar fadin" *u
shurrrp!*

Karya na maki ne? Uban me ya kawo ki harkar aikin da maza ke yi kuma ki ce sai an kiyaye harshe wajen
yi maki maganar da ake yiwa maza?
Na fada maki Ke gardi Bodyguard nonsense! Ni zaki biwa rayuwa? Aikin ki, ki tare min harbi, ba wai ki
min bincike ba,
Na maki alkawarin sai na binciki taki rayuwar nima!

Mu je zuwa ni da ke!

Cikin yannayin bacin rai Hafsat ta kara matsowa kusa da shi, bayan ta janye kafarta da ya take da
takalminsa sako kafafuwanta suka shige takankannin nasa , ta yi zama irin na neman fitinan nan ta dago
idannuwanta da suka cika da hawaye dan jin haushi tana kallinsa yana kallonta ta maida hawayenta gaba
daya ta ce"

*SUNNAN KA ABDUL JABAR ABDUL BASID* , AN haifeka a cikin niger garin Niamey,
Ka kasance jikan Buraima mai cefa, dan Hajia Mariama Kabir!
Shekara goma sha daya ka yi tare da iyayenka mahaifinka ya tura ka kasar Saudiya dan larantar kasuwanci,
wanda kake basaja da shi cewar kai dan kasuwa ne,
Kanwarka ta rasu a shekaru goma sha shida,
Mahaifinka a shekara hamsin da bakwai,
Mahaifiyarka a shekara hamsin da uku,
Kai a yanzu shekarunka talatin da uku da sati hudu da kwana biyar da awa tara da minti arba.in da
sakwani........
😌😌😌😌😌😌😌😌😌 anuna ko😌
*KUTKALE*

*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct
NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan
number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA
SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN
SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN,
.....* taku ce, Sajida😍😍😍😍

1️⃣7️⃣

Shiru ta dan yi tana kallon yanda ya tsurawa bakinta ido,


Ta ci gaba da fadin" babu kalar abincin da baka ci, du irin arzikinka kana iya cin du abinda ka samu,
Baka da dar da kwonciya a duk inda ya kama , irin gado, katifa, tabarma, dandar kasa,
Baka da damuwar irin suturar da zaka saka a duk halin sakawar ya kama,

Idannuwanta ta lumshe, jin irin yanda sukai mata nauyi, ta bude ta dube shi ta hada babar yatsarta da ta
tsakiya ta ri tap tap biyi da su ta ce" kadan,
Kadan ya rage min na baka labarin rayuwarka Sire!

Abdul Jabar ya lumshe idannuwansa ya dan ja baya ya jinginar da bayansa jikin kujerar da yake kai still
idannuwansa a lumshe,
Yana matukar girmama kwazon yarinyar,
Tana auna abubuwa, tana da zurfafa bincike kan abinda ke gabanta,

A haka suka karaso tafkeken ma.aikatar da suka fito dominta,

Fita ya yi a lokacin da ya hangi mutumen na tsaye, wato shi yake jira,

Su BS fitowa suka yi suna ta aikin duba wajen, inda ya yi gaba Hafsat ta bi bayansa,

Maimakun su shiga cikin ma.aikatar sai suka ja suka tsaya gaban mutumen,

Kalon kallo sukaiwa juna shi da Abdul,


Kafin mutumen ya bude hannayensa yana dariya irinta ka ga abin farin ciki kafin ya ce" yarona, zo gare ni,

Abdul sai da ya dane zuciyarsa ya nufe shi ya shige jikinsa duda katon tumbinsa bai bari sun yi gaisuwar
yanda ya dace ba, nan sukai gaisuwar larabawa kafi su saki juna,

Mutumen ya ce" ai tunda kace da ni gaka nan tafe na kasa zama sai da na fito tarbanka yarona,
Mu je office din mana

Abdul ya gyada kai yana murmushin yake kafin ya ce" aa, ba sai mun shiga ba ai elhaj, nan ma ya isa,

Dubansa ya yi, eh tabas du yawanci da Elhaj ake kiransa, kai harma matansa, sai dai kuma a yau Shi Abdul
da ya fadi kalmar sai ya ga kamar da nufin wulakanci ya fada ko da niyar zagi, domin dai *bako* shi ake
kira da Elhaj a saudiya, a dan yana kiransa dad, ne ko yace da shi Uba, ko dan tsakaninsa da mahaifinsa,
aman a yau ya kire shi *Elhaj*,

Murmushin yake ya saki ya ce" aman ya kana mai guri, ka zo kuma ka tsaya a kofa?

Abdulma ya sakar masa murmushin ya ce" ka san, bawa na iya malakar guri, sai dai ya zamo masa
fage....wato fili,
Yaya maganar kayan nan, an saka su du inda ya dace?

Elhaj ya gyada kai tare da bashi gamsashiyar amsa,

Abdul ya mika masa hannu da niyar yi masa salama,

Har sun juya sun fara tafiya ya juyo ya ce" *ni ina mutuniyar, Baby kennan sarkin son dadi, koda yake,
dadin ce*

Wata dariyar Elhajin ya saki yana sosai keyarsa har Abdul ya shige motar suka zo suka tashi motar Elhaj na
tsaye suka bar wajen,

Hankici ya ciro ya goge zufar dake goshinsa, kafin ya danna kira a wayar dake hannunsa,

Ana dagawa ya ce" bafa zan iya wannan lamari da yaron nan ba, kamarma ya san me ya shiga tsakanina
da baby ka ji maganar da ya fada min?

Shiru dai ba amsa kamarma an kashe kiran,

Sauraronsa da yake ya saka shi yin tsitt, sai dai maganar da Hafsat ta fada ya saka shi saurin kallonta,
A nitse ta ce" in dai munafukan ne, ba zasu yarda su ja maganar a waya ba Sire,

Da sauri ya dube ta, abin kunnenta ta nuna masa,


Kan uba, yaushe ta lika masa abin sauraro, wato shi ya yarda ya shige jikinsa ya laka masa abin sauraro ta
haka, ita kuwa ta saka masa a lokacin da ya cika shi ymta matso tana yin kamar tana kakabe masa jikinsa,

Murmushi ya sakar mata, jin wani irin birge shi da ta yi, yana son ya ga mutumen da ya san ciwon kansa
walahi, hakan na masa dadi sosai a rai,
Wani irin attention dinsa yarinyar nan ke kara ja du haduwarsa da ita daga jiya zuwa yau,
Yana kallonta tana kallonsa har aka kai shi wajen da zai sha caputulo,

Fita ta yi ta saka aka ajiye masa saman table bayan ta yarda da hakan ta kimtsa wajen shan ta fada BS ya
fada masa suka fito suka shiga wajen,

Zama ya yi ya dauki jarida ya shiga karantawa, hakan ya bata damar karasawa kusa da BS suna dan dube
duben yannayin wajen da mutanen dake dan shawagi a wajen,

A hankali ya ce" kar ki mance karkashinsa kike, kar ki manta uban gidanki ne a yanzu, yana da damar yi
maki tsawa, wulakanta ki, ya taka ki, du abinda yake so, ke kuwa dole ki yi hakuri,
Bana son abinda zai jaza maki matsala a wannan mission din, bana son dalilin haka a taba lafiarki ko kudin
da za.a biya ki, fatan kin fahimta,

Sai da ta dan waiwaya ta hango shi, ya kare fuskarsa dai da jaridar hannunsa yanda suka bar shi haka yake
ta juyo wajen BS ta ce" damuwarka kennan? Ni damuwana na yi na gama na samu liberty din fita kamar
kowa,

Idan har kika bata mission din nan kin san da baya za.a maida ke, jiya me ya hada ki da shi ya fito nemanki
haka? Kar ki yarda kuma ya yaudare ki, domin kin san aiki ya hada ku, daga shi babu wani, koda ya
yaudare ki toh ya kare da ke ne,

Tsai ta yi tana dubansa, shifa du wani waje ya nufa, shi fa tarin kishi ke dawainiya da shi,, dan haka ta
girgiza kai ta kuma duban cikin cafetaria din dan gannin ko ya fara shan caputulon?

Sai dai abinda ya bata mamaki, irin zaman nan dai da yannayin rike jaridar da ya yi tun na farko bai gyara
ba, bai canza ba,
A hankali ta matso ta kurawa hannayen ido, ba damar gannin kafafuwan domin table din rufafe ne kuma
mai girma,

Hannun ta kara kurawa ido kafin gabanta ya fadi,


Da gudu ta nufi cikin ta shiga da sauri ta karasa ta warce jaridar dake hannun wanda ke zaune a wajen da ya
dace ace Sire Abdul ne ke wajen,
Gabanta ne ya fadi wannin wani dan kyakyawan saurayin da ba shi ba zuru sai zarar ido yake,
Irin juyowar da ta yi ta dubi BS ne ya saka shi zaro ido domin ya fahimci me hakan ke nufi,

Da sauri ya bude yar karamar computer ya danna abin localization dan samun inda yake dan kuwa jikin
rigarsa suka laka masa abin,

Sai dai abin haushin yana karasowa inda ta dora kafa daya tana bin saurayin da kallon takaici ta dago ta
dube shi ta ce" mutumen da ya iya guduwa a irin tsare shin nan da muke, idan har ya yi gigin bari mu gane
inda yake ta hanyar barin abin localization a jikinsa ai da ya zama lusari,
Rigar ya yiwa wannan saurayin kyautarta da sharadin ya zauna ya kame da jaridar nan na wasu yan lokuta,
Shi kuwa da yake banza ne ya zaunan kuwa!
Ta karashe tana mai dukan table din da karfi yannayinta na nuna tsantsar bacin rai na rainin hankalin da
Abdul ya yi masu,
BS kam dubanta ya yi cike da kulawa, gannin ranta ya kai kololuwar baci ya saka shi yin gaba yana mai
cewa" ki hanzarto mu je nemansa

Sai da ra mike ta bi wajen da kallo, haka kawai zuciyarta ke fada mata yana wajen, sai dai bata ganshi ba,
bata ga alamunsa ba, dan haka ta juya ta bi bayan BS ta bude bayan motar ta shiga suka daga suka nufi
gidansa ko can ya koma,

Zuru ta yiwa waje daya cike da jin haushin kanta, yama aka yi ta fito ta bar masa wajen bayan ta gama
fahimtar mutumen lale na cikin hadari kuma shi da kansa yana mai kara saka kansa a hadarin? Yama aka yi
ta yi saken yin hira a lokacin da ana iya harbe kan wanda suke baiwa tsaro?

Kanta ta girgiza ta jinginar da jikinta jikin motar ta lumshe idannuwanta,


Murmushi ta saki a fili kafin ta dubi BS dake bin du wani motsinta da kallon mamak8n yanda take
abubuwanta, ta ce" ka san me? Shi din, bayan sannin abinda yake yi da ya yi, ya kuma kware a aikinsa,
tabas jarumi ne!

BS ya kauda dubansa daga kanta ya mayar bakin titi har suka karasa gidansa,

Du inda suka san zasu same shi a cikin gidan sun duba, aman ba shi ba alamarsa,
Sai a lokacin kuma suka fara afkawa cikin tsoro, tsoron da suka shiga ba na komai bane sai na tunanin idan
fa dauke shi aka yi aka raina masu hankali da wannan saurayin?
A lokacin da ta yi wannan tunanin sai da hanjin cikinta ya motsa tsabar kaduwa da ta yi,
Ba shiri suka juya wajen, sai dai saurayin na nan bai wani tafi ba, da alama wajen nasu ne, nan yake wuni
idan ya zo, yana ta aikinsa da mutanen wajen,

Jiki sanyaye suka koma gidan nasa, du sun yi wujiga wujiga a tsakar gidan, har sun yi kiran GN sun sanar
masa inda cikin tashin hankali ya nemi layin ogansa ya fada masa.......

Muhammad kansa tsaye yake cike da tsoron fitowarsa , shi fa ya zama na daki, baya zuwa komina, hakama
Ni.ima sun tsatsareta sun canza mata yannayin gadon dakinta, kai windows din gaba daya sun rufe shi ruf
irin yanda ba za.a iya hango na ciki ba du jarabar mutun,
Tun da ta ji hayaniyar ana neman mijinta hankalinta ya gama tashi, gashi babu waya kaf gidan du an cicire
sai tasa da ta masu tsaronsa kawai, ta rasa ina zata tsoma ranta ta ji sanyi dan kuwa tana son fita sun bi sun
tsare sun hanata fitowama bale ta nemi yanda zata yi ta samu labarin inda yake,

Hafsat kam, haka ranar nan ta daketa, yama ta yi ta kasa tsaye ta kasa zaune, ita fadan da GN ke yi tamkar
zai ci namansu danye ba shine damuwarta ba, wani irin abu take ji mai shige da matsannanciyar damuwa
kan rayuwarsa,
Tun a jiya da ta ji kadan daga cikin labarinsa take jin wani irin tausayi da jinkai a gare shi, tsaye take, ta yi
shiga ciki da fitowa ya fi a kirga,
Bata kai ko ruwa bakinta ba bale cikinta ya tsamaci wani abin,
Ta gama fita a hayacinta ga GN fada kamar ya shako su ta computer da ya yi vidio call ya yanyanka su ya
huta,

Wasa wasa har aka fara kiran sallar magariba, aka gabatar da sallah aka gama, inda duhun magariba ya fara
sanyo kai

Wani babur ne aka budewa gidan ya shigo, wani irin hayaki babur din ke yi da wani shegen kuka irin ya
tsufan nan har yana faman bugawa dan kansa,

Gaba dayansu ido suka bi babur din da shi da mamakin ya aka yi aka budewa wannan babur haka gida ya
shigo?

Tsayar da babur din ya yi ya sauka,


Kayan dake jikinsa kansu ba da su ya fita ba, du ya yi wani budu budu da shi haka yannayinsa na nuna a
matukar gajiye yake,
Basu gama yarda da shi bane sai da ya karaso inda suke tsatsaye da shirin ko ta kwana ya ja ya tsaya ya rike
kugu yana mai bin su da kallon nan na son kure mutun kafin ya sakar masu murmushin nan na raini ya ce"
hi!

Dankari, gaba dayansu da mamaki suke binsa, kafin du a nufe shi masu bashi tsaro suka fara tunkararsa
inda BS ne shugabansu shi ya dube shi da girmamawa da yannyi na son jin gaskiya ya ce" sire, aman ina ka
shiga? Me ya same ka haka? Wannan suturar fa? Wannan yannayin fa? Bamu ga fitarka ba sai nemanka
muke tun da safe?

Abdul ya gama sauraronsa da kyau, kafin ya kai dubansa wajen Muhammad dake saurin karasowa shima da
yannayin murnar gannin shi da aka yi,

A hankali ya ce" kana zance a wajen aiki yaya zaka gane na fita? *baka san aikin ka ba Bodyguard soldier*

Yana kokarin ratse su sai ga Ni.ima da gudunta ta fito, inda macen dake bata tsaro ke biye da ita tana mai
son dakatar da ita kar ta karasa wajen nan aman ina

Tana zuwa jikinsa ta shige ta fashe da kuka,

Sororo ya yi yana dubanta, basu gama gannin hakan ba ta cika shi da jin haushi ta juya ta dale mai bata
tsaron nan da kallo inda gaba dayansu sai da suka zaro ido, tunbama Hafsat dake cike gefe tana kallon du
abubuwan dake faruwa,

Cikin muryar kuka ta ce " ya zaki hana ni fitowa na ganshi? Ke din banza ke din wofi? Aikin ki bani tsaro
ba bani umarni ba, dan me zaki hana ni fita kuma yanzu da ya zo ki hana ni fitowa ganninsa? Mai kashe
mun ya jima bai kashe ni ba a kansa!

Gaba dayansu kallonta kawai suke, inda Hafsat har wani sarawa kanta ke yi na irin abubuwan dake faruwa
a yau din nan,
Haushi bai kara kumeta ba sai marin da aka wankawa abokiyar aikinta sannan aka wulakanta ta dan kawai
ta yi hani da kar ta fito wajen da ake iya daukan ranta a banza?

Idannuwanta ta rintse , gannin ya cika hannun Ni.imar kuma ya nufi wajen Muhammad da abinda Ni.ima ta
yi ya kashe masa jiki yana dubansa,

Yana zuwa sukai gaisuwar larabawa kamar yanda suka saba,


Muhammad ya rike hannunsa da kyau ya ce"ka je ka yi wanka,

Murmushi ya sakar masa kafin cikin dabara ya sinar masa da abin hannunsa , da ido ya yi masa signal din
yana zuwa,

Dubawa ya yi ya ga du sai kallonsa suke , da hannunsa ya yafito Hafsat dake tsaye fuskarta tamkar ta fashe
da kuka dan haushi ya ce" uzurina na je, wanda bana son bindina na biye da ni....ku gane man, yanzu na
dawo gidan farautana, zo mu je ke mai kula da ji ki duba dakina, na wuni bana ciki kar a je wani ya yi ajiya
😌
Ya karashe yana mai kane ido daya ya juya ya yi gaba ba tare da ya baiwa BS amsar tarin tambayoyinsa ba,
ba kuma tare da ya kula irin abinda Ni.ima ta yi ba,
Haka suka juya suka bi bayansa, sauran suka koma bakin aikinsu,
Haka mai tsaron ni.ima ta kuma bin bayanta tare da namijin cikin yannayin nuna halin ko.in kula da abinda
ya faru da ita domin qn hore da hakan na iya faruwa da su,

Idan Hafsat ta tankawa abubuwan da ya yi, to tabas rigar jikintama ta yi magana,


Haka ta fara shiga dakin , ta nufi wajen bed dinsa ta fara bincikawa, ta koma dakinsa na baci ta bincika, ta
dawo ta shiga bayi ta hada ruwan wankan bayan ta bincika ta kuma gyara komai, ta fito da niyar barin
dakin ta ganshi tsaye daure da tawul, jikinsa sai warin rana yake da alama fitar nan da ya yi ba karamar
wahala ya sha ba,

Murmushi ya sakar mata ya ce" yau ba fada ne my Bodyguard *budurwar dan ta.ada?*

Dan tsai ta yi, kafin ta girgiza kai ta kara daga kafa zata fita ya ce" *Nadia abdallah* (wato sunnan da aka
basu kennan na Hafsat a can gidan formation)
Ya dan taka ya bude bayin yana mai cire tawul din jikinsa gaba daya sannan ya ce or *Hafsat
Muhammad* , ba zaki ban muryarki na ji ba?

Da wani irin sauri ta juyo , juyowar da ta tsorata ta, ta.......

.............comment nah?.......
*KUTKALE*

*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct
NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan
number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA
SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN
SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN,
.....* taku ce, Sajida😍😍😍😍

1️⃣8️⃣
*HELLO READERS, DAN ALLAH KAR KU DAMU DA YAWAN PAGES, DU RANAR DA NA GA DA
HALI ZAN KAWO MAKU 2, AMAN A HAKANMA KUN GA AI DA YAWA🤣*

Irin dirar da ya yi ya kare ainahin wajen da ba.a son gannin da tawul dinsa kafin ya dafe goshinsa ya leko
gaba dayansa yana daura tawul din ya dubeta irin yanda ta rintse ido, bata ga ainahin abinda ba.a son a
gannin ba, aman ta ga cinyoyinsa, kai harma da kusan cibinsa ta gani, ga kirjinsa dake dauke da wani gashi
tsakiya har zuwa cikin tawul dinsa, wanda da gangan yake aske sauran ya bar iya nan su wani bada kala,

Kansa ya dafe da hannunsa ya fito daga bayin ya karaso inda take tsaye ya tsaya sosai daf da ita, ba abinda
ya dame shi da irin yanda jikinsa ke bugawa sanadiyar wuni cir a wajen da sai shi kawai ya sani, ba wanka
ba iska, gashi garjejen kato me zai hana shi bugawa? Ya dubeta da kyau ya ce" yanzu, fisabililahi, banda
soyaya da dan ta.ada da kike wai harda neman gannin ogana? To me kike son ganni in ba fitina ba, Hafsat
shekarunki duka duka 21 fa, kin shiga ta da biyu yau da wata hudu da kwana ashirin da biyu da awa ashirin
da minti goma sha hudu da second tik tak tik tak tik tak......., yaushe kika san dadin namiji haka? A gidan
yarin *KUTKALE* , ko a yawon neman fada lungu lungu? Ko dai da saurayin naki ne dan gidan abansa?
Ko mijin da aka baiwa ke sadaka ya dana ne can dama a biye ba.a sani ba?

Da sauri ta dube shi, duba irinnan tsoro, da fargaba,


A hankali ta ce" kaka je neman labarina ne? Dama fitar da ka yi tawa ce?

Wata dariyar da ya jima bai yi bace ta kubuce masa, kafin ya dubeta da kyau ya ce" du na rasa aikin yi, na
tashi na fita zuwa neman labarin ki? Kin manta wanda ya dauko ki daga gidan yarin gaba dayansa a tafin
hannu na yake? Kin manta yanzu duniya ta zama ta yanar gizo?
Ina zaune sai da na gama hutawa, na shiga yanar gizo na bincika wacece ke, nan aka bani labarin da na kasa
hadiyewa, dan haka ina zaunen nan ina shan shayi hankalina kwonce na danna kira aka bani cikaken
wacece ke, duka a yan mintunan da basu cika sitin ba, wato awa! Yaya zaki yi tunanin darajar ki, ko haye
min da kike zai saka har na yi irin fitar nan da na yi dan sannin ke ko wacece?

Ba ke ce yar gidan malan ba? Wace kika ci sunnan mahaifiyarsa, kin taso cike da abubuwan mamaki, kin
kare a soyaya da dan ta.ada da dan gidan dad? Abinda ya fi tsaye min a rai shine dan ta.ada, ta yaya? A ina
kika gan shi? Na kasa yarda da hakan, ni ba sakarai bane da za.a bani wannan labarin na hadiye, ki sani
wani labarin duniyar medias, da bakunnan mutane basu isa su baka ba, kamar yanda kika ji wasu abubuwan
a kaina, baki isa a duniyar bincike ki san wasun ba sai dai idan ni na fda maki, haka naki labarin rayuwar
ban isa na san wasu abubuwan ba, du irin fitinata da neme neme na, du karfina da dukiyata sai idan mai
labarin ta fada da bakinta, meye sirrin rayuwar ki? Me ke damun ki? Me ya kai ki gidan yari da tsauri haka?
Wace ratuwa kika yi a gidan yari? Yaya aka yi daga zama budurwar dan ta.ada kika dire a gagarumar
bodyguard da kasa da mutan wajen kasa ke rububi? Kin zama karamar hamshakiya daga yar caskale,
Hafsat, wacece ke?

Idannuwanta ta bude daga lumshe sun da ta yi, ta zuba masa su, sun kara wani girma, sun cika da ruwan
hawaye, haka kuma bakin na ciki ya kara girma,

Sai da ta hadiyi yawu ya kai sau uku kafin ta dube shi da kyau ta kuma lumshe idannuwan nata ta bude a
hankali ta ce" *ina ka je? Ka saka mu a balaki, ka bamu damar kawo maka talafi Abdul, ka taimake ni mu
yi mu bar maka gidanka Abdul*
Ta karashe maganar sosai tana mai sauke ajiyar zuciya,

Gabansa ne ke ta faduwa, shi kam ya rasa wannan jarabar da me ta yi kama, du in zai kadaice ya yi koda
maganar minti daya da yarinyar sai gabansa ya fadi, baya son faduwar gaba dan kuwa saka shi take jikinsa
ya yi sanyi, komaima nasa ya yi sanyi,
Haka ta juya ta fice a dakin ta jingina da kofar ta sada kanta kasa, a rayuwa daga bakin lokacin da ta tsinci
kanta a gidan ladaftar da shege wato *Kutkale* ta gane mecece rayuwa da mahinmancin iyayenta, daga
wannan ranar idan kana son ka ga ka ruguzata ..to ka yi maganar iyayenta, ka takalo maganar su, a nan har
kuka sai ta yi maka, tana son Malan da mama, tana son su sosai, tana son komawa gare su ta yi masu
biyaya, tana cikin duhu, shin malan ya daura aurenta? Idan ya daura da auren wani kennan a kanta? Ita din
matar aure ce ko me? Idan har matar aure ce, shi ne take irin wannan rayuwar? Ita dake neman sauki wajen
Allah kuma take irin wannan sakacin? Yaya take tunanin gannin haske bayan idan har da aure a kanta tana
wasa da sunnar ma.aiki?

Idannuwanta ta lumshe, hawayen da take rikewa ya yi nasarar zubo mata a kumatunta, ta bude idannuwanta
a kasan zuciyarta ta ayyana Malan idan na dawo, walahi koda mahaukaci, ko wani irin mutun ne ka aura
min zan zauna da shi, na yi masa biyaya, malan in sha Allah zan rike mutuncina komai rintsi, malan ka yafe
min👏🏻

Abdul kuwa yana tsaye yana kallonta har ta fice a dakin,


Shima wani iri ya ji , sosai ya ji ba dadi,
Shi bai yi fitar nan dan ita ba, ya yi fitar nan dan zuwa gannin yar Elhaj da ya kama ya boye a can yankin
ghana cikin wata rigar fulaninsu wace ya saka yan tsaro tsareta wanda ita hakan ya yi mata dadi dan kuwa
cike take da bakin cikin ubanta ya shiga dakin uwarta ya kuma shiga nata! Gashi kiri kiri ba wata magana
dake hadata da uwar tata, uan uwanta maza du an yi nesa da su basa kasar, kai ko suna nan du daga wanda
ya mayar da giya ruwan shan sa, sai wanda ya mayar da mata lumfashinsa, ba wanda zata tarba ta yiwa
maganar ya fahimta bale har ya ji ciwo,
Tana faman kashe kanta , tana tunanin hakan a tafiarta da ta yi wanda abanta ya sakar mata kudade dan yin
yanda take so ta dawo su dora daga inda suka tsaya (wa iyazubillah) , har ta shiga neman abinda zai dauke
numfashinta ya shigo rayuwarta ya sace ta, bai san alfarma ya yi mata ba, bai san taimakonta ya yi ba, bai
san ya cire mata masifar da ta fi damunta ba, dan kuwa har ta fara bushe bushe, wajen da ya boye ta nan
akai mata magani dan ta dawo clean,
Baki dayansu jira suke, jiran ranar kin dilaci suke,

Ya gudu ya je gareta a yau ne dan yana son yi mata wasu tambayoyi a kan aminin abanta wanda ya yi
imanin ta sani dan kuwa akoy sakin baki a wajen uban idan yana cikin farin ciki,

Nan ta nemi bashi wuya, dama baya shiga rigar sai ya yi shiri irin nasu, hakan ya saka shi neman yi mata
tijara da kyar dai ta sanar masa labarin , ta boye ne dan ya shafi mahaifiyarta ita kuwa har ga Allah tana jin
son mamanta a ranta, harma tana fatan idan ta ga bayan wannan lamari da ranta ta je wajen mamanta ta
rungume ta.

Daga rigar ma wajen yan sholishon cikin garin ya koma, saman babur din nan na aro, ya saje da su, ya
burmu inda suke burmuwa, dan tabatarwa kansa labarin dan aminin Elhaj, shi ne diler din wato mai siyar
masu da kwayar wanda suka haifa da matar Elhaj a lokacin da ya yi doguwar tafia wace ta faukan masa
shekara biyu harda yan watani......wannan masifa na tafe da su duka bisa tafkeken laifin da suka aikata,
harma sula gayaci wani!

Juyawa ya yi a hankali ya shige wankan,


Wankan da ya daukan masa lokaci, kafin ya fito yana tsane jikinsa

Sai gashi fess ya fito da shi cikin dan kankannin lokaci

Doguwar riga ya saka , ya bude frijj dinsa, nan ya ga an cancanza madarar holondia dake ciki, daukowa ya
yi yana dubawa,
Bai sha ba ya mayar cikin frij din ya taka ya fita

Yana fitowa ya ganta tsaye, ba wata walwala a fuskarta irin dai a shirye take shirin aikinta,

Dakin matarsa ya nufa, wanda ya saka mata bugawar zuciya na tsoron kar a je ya kuma abinda ya yi jiya?
Sai dai bata iya cewa komai ba ta bi bayansa suka shiga, suna shiga bata tsaya jiran wani abin ba ta je du ta
yi binciken da zata yi kafin ta juya ta fita ta ja ta tsaya kusa da abokannan aikinta,

Yana kallonta ya zo wajen kujera ya zauna, ya dora kafa daya kan daya

Saukowa ta yi daga saman bed, gabanta na dukan tara tara tana adu.ar Allah dai ya sa ba abin nan na jiya ya
dawo da shi ba, dan yau da ba dan ta wuni gasa jikinta ba, toh da tabas ba zata iya takawa rasss da
kafafuwanta ba,

Zaman da ya yi, yana duban du motsinta har ta karaso kusa da shi ta tsuguna ta gaisar da shi,

Bai amsa gaisuwarta ba ta mike ta zauna a kujerar dake facing dinsa tana sinne kai irin kunyar nan,

Hannunsa ya nuno wajenta ya ce" menene wannan kike yi? Irin wannan sada kan haka?

Daina sada kan ta yi aman bata dago ta dube shi ba, dan haka ya ci gaba da fadin" kin san a tarihin matan
da na aura ke ce ta farkon da ta kai warhaka bata mutu ko ta gudu ta bar ni ba? Ke ce wace bayan kin ga
girmana har na so sakar maki shi sai dai kika kasa dauka sai hakura na yi dan kina ta ihun da ya saka na ji
na daina muradi? Kin san da lale masu baki tsaro sun bada kyakyawar gudunmuwa wajen gannin rass har
yanzu kina takawa yanda kike so?

Shiru ya yi gannin ta nutsu harma tana dagowa ta dube shi sannan ta sada kanta, ya ci gaba da fadin" bani
da time din da zan auri mace kuma na bata tarbiya! Ki gane bana wulakanta dan adam mai daraja, kar ki
yarda ki saba da haka domin kuwa idan har na gane haka ko da cikina a jikin ki na wata tara ina iya
salamarki, can ki je ki karata da abinki ki bani lafia ni ba zan so ina ji ina ganni mace ta mayar da ni wawa
ba!

Ajiyar zuciya take saukewa na dan kukan da ta fara, dan a fada ta dauki magangannunsa, duda bai yi su a
lalama ba, bata wani saurari abinda ya dace ta tsinta ba, sai tsayar da hakan na faruwa ne dan ba soyayarta a
ransa, dan haka sai ta ji ta muzanta,

Sai da ya gama ya maida dubansa wajenta, sarai ya lura da yannayinta aman ya basar ya mike ya ja rigar
jikinsa ya cire kafin ya koma saman kujerar ya yi wani zaman rashin kunya yana dubanta ya ce" yau fa, sai
na shiga, zo ki ja ra.ayina😌

Ya karashe yana mai lumshe idannuwansa ,


Sai da gabanta ya fadi a lokacin da ta dube shi, jibgin uwannan kai, haka yake a haske sosai? Haka yake?
Waima ya shiga ina? Ta yaya? Yau ta shiga yku ta ga abinda ya fi karfinta, gashi ya yi wani ringeshe wato
jira yake ta zo ta yi masa abubuwan nan wanda ta dauka na jar fata ne, sai dai ya yi mata nuni da sunna ce
kafin ya nemi darara mata ? Kai ita dai tsakaninta da matan da yake daukowa har suka saba masa da irin
wannan rayuwar sai Allah ya isa (😳 to fa, ke, shi da ya dauko sun fa? Fans kar ku yi mamakin irin yanda
zai mikewa mace amarya santaleliya irin Ni.ima cewar ta ja ra.ayinsa, idan baku manta ba Abdul fa namiji
ne da ya yi mu.amalar jan ra.ayi da mata kala daban daban, wa.inda suka isa da wa.inda basu isan bama duk
suka zube suka ririta shi ya wanke su da dala....hakan ya saka shi gannin wanima ya yi rawa balatana dan
makadi, kennan wanima ya ja ra.ayinsa ina ga ta sunna?)

Sai da ta cire rigar tata ta sama ta baci, sannan ta duka gabansa irin yanda ya nuna mata a jiya ta yi tsuru
tana kallon sa,

Bude idannuwansa ya yi a hankali ya kai kanta, shi take kallo abinta, kallo irin na san gane abu...
Dagowa ya yi da yannayinsa mai nuni da jarabar ta gama motsawa yana dubanta, a hankali ya ce" yaya
sunnan ki na gaskiya banda Baby? (Sunnan da yake ji kennan shi tun da ya santa, ko wajen daurin aurensu
shi fa sai ya rantse bai ji sunnanta da kyau ba bai rike ba, 🙄🙄🙄, zaka fada ne Abdul)

Idannuwanta ta bude da kyau tana dubansa,


Sunana kuma? Wai dama bai san sunana ba?
Jiki sanyaye ta ce" NNNi.uma,

Hannayensa ya saka ya dagota ya dorata saman cinyarsa, a hankali ya matso da ita zuwa jikinsa , cikin
yannayin rada ya ce" Ni.ima, Allah ya sa Ni.ima na tare da ke, ki daina langewa ki bani kulawa kin ji?

Kanta ta shiga gyadawa a hankali, tana jin wani irin yannayi na shigarta na sababin abubuwan da ya shiga
yi mata ta hanyar anfani da hannunsa da kuma sajen fuskarsa.......

A yau kam abin ya ja daga, dan kuwa ba shi ya fito a dakin Ni.ima ba sai kusan karfe daya, sai da ya gama
mayar da ita cikakiyar mace, wanda shi da kansa ya tausayawa yannayin da ta shiga , ta sha wahala ta kirki
wace sai da ya talafa mata lumfashinta ya dawo jikinta, tabas ya san dole sai ta ji jiki, shi din bai taba yi ba,
ya bita a hankali aman ya girmeta sosai, shi ya sa ya kasance mai tunanin zama da mace biyu, dan a
ganninsa irin wannan fitinar da wuya mace daya ta iya dauka,

Bayan ya gama bai tsaya wani gashe gashe ba, da ta farka, kayanta kawai ya iya zura mata ya kwontar da
ita ya ba dakin baya, yo shi ina ya san ana wani gashi? Inama ya san ana wani ririta? Shi fa a sanninsa
shikennan kafin safe ta ware, dan haka ya fice yana mai jinsa sakayau kam, (wayo Ni.imana, ashe ke wuni
da gashinma ba na dalili bane? Yau kam zaki yi gashi)

Yana fitowa ya tarar da ita dai tsaye,

Gaba ya yi tana biye da shi a baya har suka shiga dakinsa,


Suna zuwa ta kakabe shinfidarsa, ta bude frij ta ciro hollondiar nan biyu da ruwan gora ta ajiye ta juya ta
fice a dakin inda ya rakata da kallo kafin ya zarce bayi dan yin wanka........

Kwonci tashi, yau har kwannan su Hafsat goma a gidan Abdul, sun ga fitintunnu da abubuwan mamaki da
tarin takaici a tare da wannan bawan Allah,
Abdul, bai taba yin wani yinkuri dan nuna masu yana son kare lafiarsa da ransa ba, bai taba basu damar su
fuskanci inda zasu kare ba,
Ya sha dan iya shege su fita ya zile masu du tsaron su, du kulawar su ya dawo gida kawai dan ya saka
Hafsat ta yi ta balaki kamar ta kai masa mazga yana zaune yana dubanta yana murmushi, kuma du fitar da
zasu yi, Hafsat na kula da takunsa basu taba fitar da ba wani abin mahinmanci na lamarin aikinsa ya fitar da
shi ba, cikin dabara take hada abinda ta samu itama har ya zile masu!

Kamar yau ma da karfe biyar na yama ,


Abdul ne ya fito daga dakinsa cikin shiga ta kayan gudu, wato yau dole su yi sports dai?

Yana fitowa bai yiwa kowa magana ba ya dauki hanya ya falla da gudu,
Sai da Hafsat ta dora hannu a ka gannin wani balakin kuma, sannan ta cire rigarta ta sama ta fala da gudu
ta bi bayansa hakama su BS gaba dayansu sunna biye da shi da wani irin gudu ,

Sunna shan kwana, kamar daga sama wata bakar mota ta shanyo kwanar a guje ta ........... . ........

*Toh fa, lamarin na Abdul ba saukiK,*

Ku yi hakuri da yannayin rubutuna, ina iya yina dan baku pages mai yawan gaske a hakan, ku min uzuri
plz👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻,
*KUTKALE*
*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct
NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan
number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA
SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN
SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN,
.....* taku ce, Sajida😍😍😍😍

1️⃣9️⃣

Tun da suka hangi motar, da irin gudun da ta shanyo kwanar da shi ya saka su BS ihun fadin su Abdul su
duke!

Hafsat dake kusa da Abdul da wani irin sauri ta saka hannunta na hagu ta janyo damki damtsen hannunsa,
da dayan hannun nata kuwa ta dafe kansa ta aniyar dukar da shi kasa,

Wuta ce su BS suka budewa motar domin suma daga ciki hakan suka yi kokarin yi masu, cikin rashin sa.a
aka samu Hafsat a damtsen hannu sannan aka samu abokin aikin nasu a kafada,
Gannin zasu cin masu ya saki hafsat dake kasa ya janye bindigarta ya mike,
Irin yanda yake harbi, harbi ne na neman hana su motsi domin kuwa wajen tayoyinsu yake ta nema
Hakan da suka gane ya saka su wani irin jan motar suka aniyar guduwa wanda Abdul ya ki basu wannan
damar ya dankara da wani irin gudu yana harbin su, nan ya samu direban nasu wanda motar ta yi masa nida
sosai

Yana kokarin ci gaba da harbin bulet ya kare,


Wani irin ihu ya yi ya soke bindigar a jikinsa ya aniya kara gudunsa ko zai cin masu,
Sai dai kafin ya isa sun samu sun canza direba sun ja motar da gudun balaki

Sai a lokacin BS ya karaso da gudun shima yana dubansa kafin ya mika masa hannu kan ya bashi bindigar,

Bindigar ya ciro ya mika masa sannan ya juya yana wani irin jefa kafarsa ya nufo inda suke yashe kowane
na jin abinda bai taba ji ba

Hafsat kam ita a ranta ta yi tunanin shikennan mutuwarta ce ta zo, irin yanda gaba daya a lokaci daya ta ji
wata irin azaba sannan hannun ya zame mata tamkar dutse ya gagari motsin kirki ya mutun mata ya saka ta
sarewa, nan da nan wani irin tsoro da take yawan ji idan ta yi fadan da take da gaskiya a gaban iyayenta ya
kamata,

Daidai wannan lokacin Mama dake zaune tare da babar yarta, ta yi tsai ta kurawa waje daya ido

Gannin yannayin da mama ta shiga ya saka asiya zaunawa maimakun ta je ta karo ruwa a saman ruwan
kankarar da zata sha ta zubawa maman ido,
Jiki a sanyaye ta kai hannunta ta dafa maman ta ce" Mamanmu, lafia??

Manyan idannun nan masu kama da na Hafsat ta dago ta tsurawa Asiya, sak irin duban Hafsat ne,
A hankali ta nazarci asiyar kafin ta buda baki ta ce" tabas malan ya yi gaskiya, tana raye,

Wani tausayin mahaifiyar nata ne ya darsun mata, a hankali ta kai dubanta kan dan jaririnta da ta haifa yana
dan wutsil wutsil din wasansa gwanin sha.awa, ta kuma kai dubanta kan mamanta, kai lale ta jinjinnawa
iyayen da suke rayuwa ras ras ras bayan batan yayansu, kai baka ga gawar dan ba, kai baka san ina ya shige
ba, tabas da mutuwa ce ya yi da ka dangana ka sakawa kan ka hakurin rashinsa ka fuskanci rayuwa,
Aman a haka, du irin rashin ji irin na maman malan ba ranar banza da ba zai jajanta rashinta ba da fadin shi
ya san tana raye,
Gashi yau maman dake bashi bakin ai kawai a bita da adu.a, idan tana raye ina ta shige? Ita din ce ke fadin
tana raye kuma?

Yaron mama ta kara rikewa da kyau tana duban Asiya ta ce" a jikina nake jin farin cikinta ko akasinsa, idan
tana cikin hali na tsoro...a jikina nake ji sosai sosai,
Tabas Maman malan na raye kuma du inda take a yanzu tana cikin hali na tsoro,
Maza ki saka hijabin ki, ki haya sama wajen malan ki shaida masa cewa adu.ar da za.a fita yanzu inji ni
nace a rokarwa mamansa sauki!

Ajiyar zuciya ta sauke ta dauki hijabin nata ta fita dan kaiwa sakon mahaifiyarta, domin kuwa ba.a koya
masu musu da iyayensu ba, ko Hafsat ta fita daban ne a cikinsu dan idan Hafsat ce har Malan ta sha hayawa
dakinsa tace da shi Babana, kan abinda ka yanke a gidannan ni bai min, ba zan bi ba! Sai dai ko wace wace

Da kyar ta samu ganninsa, domin sai samun baki yake masu zuwa karbar adu.a a yamacin nan,

Sakon na isa kunnayensa kansa ya gyada yana murmushi,


Ba komai ya saka shi murmushin ba sai gannin yau ta yarda da maganar cewa mamansa a raye, shi kam ya
jima da yarda da hakan, karin tabacin hakan shi ne irin yanda ya jita a jikinsa amasalaci ranar juma.a,
sannan aka sumar masa da malan,
Dan haka ya sakawa Asiya albarka ta mike ta fito tana mai taya iyayenta adu.ar baiyanuwar daya daga cikin
yayansu, wace ta tabata soyayarta ta darsu a ran malan tun da ya amshi haihuwarta, ta ci sunnan
mahaifiyarsa, kuma ta yi kama sosai da mahaifiyar tasa sai yan abubuwan da ta dauka na mamanta irin ido
da yannayin kallo da kafarta da yan yatsuntsanta, aman har miskilanci na mamansa ne, ta zo ta sauke
alkur.ani a kananun shekarunta, ta hadace ta dandamki litatafan adini take shigarsu a guje, ta zo harkar
boko ta ce kauce ban wuri, kai wani lamarin harda baki dan kowa dai kowa dai maman malan, maman
malan, hakama mahaifiyarsu du irin yanda take nunawa maman malan sun tabata da ace wata mai bin
sahun iyayen ce, da ba zata iya boyo soyayarta ba, ko dan irin baiwar da Allah ya yi mata na abubuwa da
yawa....

Kallonta ta kai kan Abdul majid, yayansu ne baki daya yana shirin haurawa sama wajen malan ta gaishe shi
ta yi gaba aman sam ba kamar yanda can da baya suke yar ganewa juna ba, da kallo ya bita yana mamakin
tana fushi da shi dan ya fadi gaskiya a kan kanwarta ne? Dan kuwa tun lokacin da ya ce su daina damun
kansu kan wata maman malan, dan kuwa shi a irin iya shegen yarinyar nan in dai ba mutuwa ta yi ba, to
kawai ta shiga yawon duniyarta ne aman malan ya kasa ganewa sai asarar kudinsa da lokacinsa yake a kan
yarinyar dake kokarin hadasa masa ciwon hawan jinni!....................................................................
*KUTKALE*

*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct
NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan
number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA
SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN
SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN,
.....* taku ce, Sajida😍😍😍😍

2️⃣0️⃣

Kafadunsa ya daga ya ci gaba da haurawa sama wajen malan.

Wannan kennan

Abdul na zuwa wajen da suke bai tsaya wata wata ba ya kinkimi hafsat ya dora a kafadarsa ya nufi gidansa
da wani irin sauri bamashi da niyar kula maganar da BS ke yi masa ya shige gidansa inda BS ya shiga
neman layin asibiti dan a zo a dauki Hafsat da Jibrin din yana mai mamakin inda kuma Abdul zai kai
Hafsat

Yana shiga bai zarce ko.ina da ita ba sai dakinsa na baci,


Yana zuwa ya shinfideta saman bed dinsa ,

Juyawa ya yi ya dauko yar akwatin aikinsa ya bude ya zauna ya ciro kayan aikinsa,

Sai da ya zuba alcohol ya yi disinfect wajen kafin ya dauko wani sixo ya dubi yanda Hafsat ke lumshe ido
ya dago ya yi mata rumfa kadan ya saka hannunsa na haku ya rike hannun nata da kyau yanda ba zata iya
motsawa ba ya saka sixo din nan cikin ramin harbin ya shiga kokarin jan bullet din,
Wata irin zufa da wani dan ihu ne ta saki tana mai rike hannunsa tana kwalkwacewa, aman ina ta kasa cire
hannunsa bale har ya cikata ta kwace nata hannun, har sai da ya ciro ya gama wanke wajen ya gyara ya rufe
mata sannan ya cikata ya juya yana tatara kayan ya mayar baki daya inda ya dace sannan ya juyo inda take
idannuwanta rufe ruf sai sauke ajiyar zuciya take irin ta wahala sosai din nan,

Kujera ya janyo ya maida bayanta kusan gadon ya hau ya dora kansa saman bayan kujerar yana dubanta,

Murmushi ya saki ya ce" yanzu da a kanki ne suka harbe ki da wannan karin gashin da kike kakabawa
kulun ina keacewa da sai dai ki mutu ido daya a bude daya a rufe kina gannin yanda malakiri ke nuna maki
zaki fada ne idan kika je da wannan karin gashin mai mayar da ke irin yan iskan nan na turai,

Shiru ya yi yana gannin yanda take marmarmar da idannuwanta kafin ya ci gaba da fadin" ni, ban san wata
irin marar jin magana bace ke Hafsatu!

Ido ta bude cike da mamakin sunnanta gatsal da ya kama eai harda wata tu ya kara,

Bakinsa ya tabe ya mike daga saman kujerar yana dubanta ya ce" a tashin min a bed, sai wani bankaro min
kike kina nuno min abinda ba tayawa zan ba bare na siya malama mike harbin bullet a hannu ba zai saka ki
kuka bama bale har ya kashe ki! Kin wani yi min dare dare a bed an samu laushi ko?

Kanta ta girgiza daga kwoncen da take kafin ta shiga kokarin mikewa , sai a lokacin ta ga rigar jikinta,
sannan ta tuna irin yanda ta ringa bankarewa dan zafin ciwo ashe wannan dan sharin yana kallonta har ya yi
mata wata fasara daban,

A lokacin da ta zauna, gashin kanta gaba daya ya yo gaba ya rufe mata fuskarta ,
Daidai lokacin ya dawo a hankali ya zauna,
Hannunsa ya kai wajen gashin kan nata ya janye a hankali, wanda hakan ya sakata dago da idannuwanta ta
sauke saman fuskarsa,

Lumshe idannuwan nata ta yi ta kuma budewa, yatsina fuskarta ta yi hakan ya baiwa gefen kumatunta
damar lotsawa gaba dayansu haka kuma saman goshinta ya yi wani dan limki limkin da ya fitar da yarintar
fuskarta da kuma tsantsar shagwaba,

Murmushi ya saki ya kai hannunsa wajen fuskar tata da gangan dan yana so ta cike abin na karshe dake
bashi dariya, wato harare,
Ai kuwa ta dala masa harare ta kawar da fuskarta cike da tsiwa da nunin ita kar ya taba mata fuska!

Sai da ya talabe kumatunsa yana kallonta sannan ya ce" kina da kyau Hafsatu

Kara kallonsa ta yi da kyau, ya ilahi, wannan mutumen kamar aljanni? Hafsatun ya kara fada, ba ko dar?
Sunnan maman malan ne fa? Yo ko ita bata fadin sunnan dan kunyar malan take ta kama sunnan
mamansa...haba du rashin jinta tana kunyar wannan, idan ta kai ga kama sunnan maman malan ai ta idasa
rikicewa ba damar tarota.

Tana cikin wannan tunanin ta ji ya ce


Sunnana *ABDUL JABAR ABDUL BASID BINE IBRAHIM*
kamar yanda kika ji an haife ni a wannan garin, a karkashin inuwar wannan gida da kike ciki,
Na kasance dan Abdul Basid da Mamana ...ba zan kama sunnan mahaifiyata ba ki gane dai 😌,
Mahaifina ya taso cikin dukiya, gaba da baya ya gaji arziki na iyaye da kakani, sannan ya taso cikin
sangarta dan kuwa du abinda yake so afkawa yake kansa tsaye ba ruwansa, iyayensa basa kwaba basa nuna
masa bacin rai sai dai su yi ta rarashi dan ya kasance shi daya suka malaka duniya basu da wani sai shi,
Haka ya yi ta yin mugayen abokanni, wanda a irin haka ya bata rayuwar makarantarsa, ya lalata karatunsa
na islamiya ya dawo ya zauna a gida inda iyayen suka rungumi abinsu ba abinda ya dame su da matsa masa
kan ya koma ya nemi karatu a ganninsu dan ya yi neman kudi ne ko? To ya huta abinsa kudi an tara masa
wanda zai shana harma jikokin jikokinsa su shana ba ruwansa!
Ya yi rayuwa, kafin aurensa ya haihu da wata mata wace ke masu aiki, aman iyayensa suka daure masa a
lokacin da ya nuna baya so a sani kar a hana masa auren budurwarsa da yake so kamar rai sai suka kori
yarinyar da dan danta ta shiga duniya wace har yau ban san inda suke ba,
Bayan aurensu, da shekara uku ta haife ni, dan baki na fado abina irin fatar babana, dan jariri baki da ni,
hakan ya sa banyi wani farin jini wajen mahaifina ba du kuwa da irin yanda nake kama da shi,
Babu wata shakuwa, ko soyayar gaskiya tsakanina da mahaifina, tun ina yaro na gane yana kiyaye
lamarina, dan haka na ringa wayo da abubuwa a zuciyata cewar mahaifiyata ita ce duniyata, shi kuwa
*dayan* ya dace na saka masa ido!

Shiru ya yi yana kallon yanda ta zaro ido da ya ce dayan,


Murmushi ya yi ya kai hannunsa wajen kumatunta ya ce" wai ke komai kika yi sai kumatun ki sun loba?

Kanta ta girgiza kafin ta ce" Abdul ci gaba,

Fuskarsa ya yatsina ya ci gaba da fadin" ina da shekara shida aka haifi kanwata, mai sunna Humaira,
Humaira na da wani irin kyau, da shiga rai, ga girma ga gashi, yar fara da ita kamar ke, dan bakinta ciwat
abinda ba irin lebena ba😌

Shiru ya yi yana kallon kasa kafin ya ci gaba da fadin" Humaira da Abanna, suna da shakuwa ta mamaki,
shakuwar dake bani tsoro, sai dai ta zama abin ado a wajen Ummihna,
Abahna ya rasa iyayensa a daidai wannan lokacin hakan ya sa kudi ya karu komai ya sakar masa ya zama
wani hamshakin da kowa ke son sanni bale har ya yi abota da su,
Daidai nan ya lalubo manyan abokanansa da sukai karatu a turai kafin a kore shi, ya kirawo su ya mayar da
su aminnan shawara, sannan ya basu aiki a wajaje da dama domin su su uku ne, ya raba masu mukami ya
sakar masu dukiya, hakan ya sa suka shiga damawa suna cin karansu babu babaka,

Hafsat, sun kasance wasu irin mutane masu wasu irin dabi.u mugaye, dabi.unsu babu tsafta ko tsari a ciki,
Suna shaye shaye abinsu wato mayen yan gayu, suna baja kolinsu inda biyun suka auri masu jan kunne
mararsa adinni dayan kuwa ya auri yar uwarsa wace itama muguwar yar hannu ce

Hafsat mahaifina ya mayar da su abokanai na kud da kud sannan ya cire masu iyaka da gidansa,
Koda yaushe sukan zo gidannan su baja kolinsu sannan su tatara su watse,
Abinda zai baki mamaki, du irin zaman da zasu yi, du irin jimawar da zasu yi da shi ba zaki ga sun tashi
sun yi sallah ba,
Tun yana yi idan suna nan har ta kai ya koma biye masu ba zai yi sallah ba sai sun tafi ki ga yana ta maida
salloli yana ta ramuwa,

Sun kara koya masa kara damkon zumunci tsakaninsa da Humaira,


Mamanta bata gannin komai tana sakin baki tana dariya zai dauki yar ya je bayi da ita ya yi wanka a
gabanta , ya yi mata ya nadota ya maido ta,

Irin kusancin dake tsakaninsa da yar ko da uwar, ke abin ya huce gona da iri, a cikin gidan ni aminin
mamana Humaira ta abanta,
Nakan yi magana idan na ga wasu mugayen wasan nakan jawo ayar da malan ya fada min na nunawa abana
ba kyau fa, ya daina wasu abubuwan domin mu musulmai ne, akoy irin shakuwar da adinnin mu ya kawo
mana tsakaninmu da iyayenmu tsaftataciya,
Nakan saka Ummih gaba ina son nuna mata wasu abubuwan, aman sai ta dauki hakan a matsayin ina jin
kishin kanwata ne, da irin yanda Abanna ke son ta fiye da ni,
Ke karshe a daren da na ga wani mugun ganni Abanna ya fito daga saka Humaira baci, a lokacin mamanku
ta jima da yin baci , da na shiga dakin na tarar da ita bakinta sai tanda take, hakan ya saka ni zuwa na kai
bakina dan jin kanshin me take ci cikin baci? Dan ba zan boye maki ba ina son kanwata tamkar raina, kuma
Allah ya yi ni mutun mai shegen shige shige, shegen karambanina ya jiyo kanshin sperm wanda na san
sperm ne sanadiyar irin hirar da abokin abanna ke yi a gabana, harma wani lokaci na ga condom a dakin
bakin mu bayan abokin Abanna sun zo tare da matar dayan abokin sun shige dakin sun dan jima sun fito, a
nan ne na shinshinna harma na rike mugun warinsa a hancina,

Tsoro ya saka ni kwana a tsaye, har lokacin da Banna ya fito, nan na tarbe shi nake fada masa me ya kai
wannan abin bakin joli?

A ranar na sha duka da zagi, kan dalilin da bashi da dalili,

Kwana biyu tsakani aka daga da ni garin saudiya karatun kasuwanci

Na tafi da burika a rai na, na tafi da abubuwa a rai na, na tafi da bakin cikin rayuwar gidan mu,
Ban tashi dawowa ba sai da na shekara takwas,
A lokacin da na dawo baro baro na ga komai, irin yanda Mahaifina ya mayar da kanwata matarsa ta biyu,

Shiru ya yi, idannuwansa na kallon kasa, cike da wata irin kunya, a hankali ya dago da dubansa ya ce" ni ni
Abdul na ga bakar rana, na ga ranar da ba zan iya mantawa da ita ba, na kasa gane girman bakin kadarata,
gani a tsaye, bakin balaraben da ya sauke alkur.ani, ya zurfafa a karatun islamiya, na fito shar da ni dan
saurayi mai zamani, mai boyayiyar rayuwa ta fannin aiki, gani tsaye na kasance dan fasiki mai neman yar
sa ,

Ki ji fa sharin zina, ki ga sakamakon zina,


Daga lokacin na daina gannin kima da girman wanda ya haife ni, daga ranar na dawo na zama wani tantiri a
gaban ubana, nakan kirashi da kai babanmu da wata irin murya ta zan bashi umarni, nakan yi masa duban
kaskanci wanda hakan ke tayar da hankali mahaifiyar da ta yi sake da ragamar tarbiyar yarta ta dawo kukan
irin yanda bama shiri da ubana da kanwata, dan kuwa harta ita kafin na gane cewar an bata tarbiya ne da
horen sex, sex da mahaifinta, ba.a kula da makarantarta ba bale ta gane ba kyau, bata da kawa bale wataran
ta gane ba kyau, bata da wasu shekarun da zasu fahimtar da ita, gashi ba da karfi aka koya mata ba, an koya
mata ne ta silar soyaya da ja a jiki da tarairaya , har ta zama wata irin harijar karfi da yaji wace na takaice
maki sanadiyar mutuwarta dare biyu ya kaurace mata bisa dalilin da ban san ko na meye ba hakan ya sakata
a tashin hankali, ta yi kiransa ta fada masa a waya idan bai yi mata ba zata fadawa Ummih ta saka ya yi
mata,
Daga nan bamu tashi da komai ba sai gawarta, wace nake kan binciken cikin shi da aminan nasa wanda ya
kashe ta,

Kin san tarayar da ba Allah a ciki, Allah na tarwatsata cikin hikima da ruwan sanyi,

Haka ce ta faru da tarayar su,


Sun juya masa da wasu gigitatun kudi, hakan ya sa ya dauke masu kafa, harma ya shiga dora du wani
abinda ya malaka da sunana, wanda a lokacin na kai shekara ashirin da biyar a duniya,
Wani irin fada ne suka yi a cikin wani gidan mu dake bayan gari, wanda suka yi tone tonen asirinsu , nan
suka gane suna bin matan junnansu aman shi ba.a taba bin tasa ba? Wato ummihna,

A nan daya ya ce" ka kwonta da matata, aman ni ban taba kwontawa da taka ba? To ka sani, kan na mutu
sai na ga daya, ko na kwonta da matarka ta kowani hali, ko na mayar maka da dan naka da sai yanzu kake
son sa kare shi ya kwonta da matarka!
Wannan lamari ya batawa mahaifina rai, ya kai dubansa inda nake zaune cikin mota, a tunaninsa bana jin
abinda suke fada domin bayan nisa dake tsakanin mu, cikin mota nake a rufe ruf, bai san ya turani aikin
kasuwanci ne, ni kuwa na yo nawa karatun dan kawai na tona masa asirin irin rayuwar da yake yi da
kanwata wajen mahaifiyata ko zata farka ta raba, sai gashi tun ba.a je ko.ina ba an kashe ta, wanda na likun
masa dan gane shi ya kashe min Humaira? Ko kuwa wani ya saka ya kashe ta?
Gannin kamar hankalina baya kansu ya saka Abana wankawa Elhaj mari ya ce" kai sakarai, *RAMATU*
kamila ce, yanda na bareta a leda, ni daya na san hanyarta, mace ce dake zaune a karkashina ba wai fin
karfina ta yi ba, in sha Allah sai dai ka mutu da bukatar gannin haka, ni kuwa ni zan nuna maka na fi ka iya
shegantaka dan irin yanda kuka kwadaita min y'ata, kuka kai ni kuka baro, sai na gwada maka gannin
idonka sauran aminnan naka ba iya matanka suka tsaya ba, har yarka suna bi wace kake kishi kamar ranka!

Shiru ya yi na dan lokaci,


Kafin ya dago ya dube ta,
Yannayin idannuwansa suka kara sakata a halin tashin hankalin wannan lamari, kafin ya ce" na yi kuka da
idannuna, barci ya gagare ni, naa yi nesa da iyayena domin a lokacin suka koma wani gidan ni kuwa na
zauna a nan,
Tsakani shekara biyu Mahaifina ya shirya tafia,
A cikin jirgin da ya shiga aka nuno shi anai masa vidio, inda ya nemi yafiyar mahaifiyata a baibai, sannan a
lokacin sai da ya gama komansa a tsare, aka dauke maganar a tv aka nuno faduwar jirgin da yake ciki, wai
ya mutu, ta hanyar shahada

Hawayen dake bin kuncinta ya bi da kallo, sannan ya ci gaba da muryarsa dake fita da sanyi ya ce" kennan
a sakarkaru aka dauke mu? Ni da uwata!

Da mamaki ta yi masa wani duba,


Zamansa ya gyara ya ce" an taba mutuwa haka? Irin a dauke shi sai da ya gama komai sannan ya mutu!
Abdul Basid bai mutu ba saboda dalilaina kamar haka,
A cikin jirgin da ya fadi, dukan wasu abubuwan da suka shafi Abdul Basid an gan su banda agogon karfen
da ya gada wajen babansa wanda wuta bata narkar da shi tono shi ake a cikin kasa, wanda baya yawo ba
shi, bale tafia mai nisa, yana ji da agogon nan fiye da komai dan ji yake kamar yana tare da babansa ne!

An cire kudi, cefa milliard dari a cikin acc mai sunnansa dake kasar misrah a daidai wannan tashin hankalin
wanda shi bai san ba ni ina da damar sannin hakanta dalilin girman aikina da darajarsa ina da damar sannin
manyan sirrikan da suka shafi ahugaban kasama bale Abdul Basid,
Sai abu na uku, bayan gama takabarsa da Ummih ta yi, dif sama ko kasa ba manema, ba alamun su, gata
yar dagwas, ga cefa, wanda duniyar nan ta zama ko baki da kyau idan kina da kudi za.a yi rububun ki,
aman ko kare bai yi shayin giftar uwata ba,
Wannan aikin jinnin Ibrahima ne bama bari mu so abu wani ya so shi sai dai idan mun mutuK

Abdul Basid na raye, ya mayar da du wata dukiya tasa da sunana ya juyo da abokanan gabarsa kaina,
Ana farautar rayuwata dan a ci wannan arzikin ne, ni na tabata masu son kashe ni basu fi aminan mahaifina
ba dan kuwa duka kaf arzikin da suke takama da shi din har yanzu sunna aiki ne a karkashina, wanda na
tabata suna tsoron na tsige su rana tsaka, du cin da zasu yi basu tara na ci gaba da wadaka ba, gashi sun
dogara da kudin, an hada ni da harkar mata, wanda da na ga abin ya yi yawa na shiga asibiti aka yi ta
bincike ba.a samu wata malatin da zata hadasa min haka ba,
Hakan ya sa aminina ya dafe da nema min a cikin saudiya, har ya hadu da wanda ya fadi maganar da ta tino
min da maganar da aka yi cewar za.a mayar da ni tamkar kare....
Shaidata ta biyu kennan,

Sai kashe min uwa da aka yi, ummih ta rayu da tsoron ko wasu abokannan harkar mahaifina ke bin mu da
shari? Dan ban taba yarda, koda wasa na kara kokarin nuna mata wani lamarin da zai sakata zuciyarta
bugawa, ta kasance jarumar mace, ta rungumi gawar yarta, ta rungumi ta mijinta da bata gani ba, sai take
cike da tsoron rasa ni,
Ni kuwa ina mai kauce mata shiga dagar abinda nake ciki na irin hare haren da ake kawo min, aman cikin
ikon Allah ta shige ta yi kane kane,
Tanbayoyina shi ne.......
Shin cikin aminnan Abdul basid ne?
Aa , Abdul Basid din ne da kansa ya ga na ki sakar masa arzikinsa kuma na ki mutuwa zai fara kasheta dan
ya san idan ta mutu ta mutu da ni ne? Ko a sangartar tawa na janyo wanda ya harbe min uwata? Ni na kashe
uwata?

Hafsat dake zaune ta dora kanta saman cinyarta ta fashe da kuka, kai, ina, dole ta yi kuka walahi, dama
abinda ya gani, kuma ya rayu da shi kennan? Duda haka yakan yi murmushi, shin idan ya yi murmushi har
zuciyarsa ne kuwa? Innalilahi wa.ina ilaihi raj.une, wayo harta da lamarin matan nan an hada shi da shi ne?

Gyaran muryar da ya yi ne ya sakata tsagaita kukan, a hankali har ta yi shiru ta kuma dago da kanta ta tsura
masa ido kamar yanda yake kallonta,

Sai da ya jima a haka sannan ya kawar da dubansa ya ce" *ke ce mutun ta biyu da ta san komai a kaina
bayan Muhammad, na baki kadan daga cikin labarin rayuwata, wanda ya dace ki sani wato a
dunkule....idan kina so ki fita ki fadawa kowa, idan kina so ki rike min sirrina dan ban yarda na baki
labarina ba sai da na yarda da irin gwaje gwajen da na yi maki, ke ko dalilin daukan bullet din da ya dace
na dauka da kika yi kin ci ki san ko ni waye dan haka ke nake son sannin labarin ki dala dala daga bakin
ki*

Hafsat ta sauke ajiyar zuciya , ta dan motsa kafadarta ta lumshe idannuwanta kafin ta nisa ta shiga bashi
labarin ko ita wacece,
Irin rayuwar da ta yi,
Irin hatsabibancin da ta yi,
Jarabar fada, kiriricew, rashin tsoro, neman fitina, rashin gudun bacin ran iyayenta har kawo abinda ya faru
da ita da taintar kanta da ta yi a cikin *KUTKALE* , kawo inda take zaune a gabansa,

Ga mamakinta sai ta ga yana dariya, kamar ba shi ne ya gama bata labarin irin mumunar rayuwar da ya yi,
da kuma irin yanda ake harinsa,
Hannunsa ya daga da jinjina ya ce" ashe ni da kauriya nake tare?

Idannuwanta ta fitar tana dubansa kafin ta girgiza kanta ta ciciba ta mike ta dauki magannin da ya ajiye
mata nan ta juya a hankali ta fice a dakin,

Idannuwansa ya lumshe ya mike ya haye bed din da ta tashi ya kuma lumshe idannuwansa a fili ya furta"
malan ka fa iya haihuwa Walahi....ina son mace marar jin magana😌

Hafsat kam na fita dakinta ta nufa,


Tana shiga ta nemi waje ta zauna nan kasa ta fashe da kuka, kana tunanin kana cikin tashin hankali da
muguwar rayuwa sai ka hadu da wanda ya dame ka ya shanye,
Gashi dai bawan Allah, yana ji yana ganni abubuwan nan suka ringa faruwa da shi, kuma yana ci gaba da
walwala da tunanin samun sauki nan gaba da fama kan ya ga haske ya gurfanar da wa.inda suka kashe
masa kanwa da mamansa ?

Shiru ta yi ta kurawa waje daya ido, a fili ta ce" kana baban ma.aikacin da baka fada min ko aikin menene
ba aman kuma kake takaita zarginka da binciken ka?
Shin ina *MAI AIKIN DA AKA KORA DA CIKIN YAYAN KA?* su baka ma san inda suke ba a duniya,
baka neme su ba, baka bincike su ba! Su waye su? A ina suke? Ba lale ne zarginka ya zo gaskiya ba
Abdul...

BS ne ke tsaye da waya a hannunsa a cikin asibiti da kyar ya samu GN cikin yannayin gajiyawa ya shiga
zayanno masa irin yanda wannan mutumen da suke yuwa aiki wato Abdul ke mayar masu da rayuwa marar
dadi, su kam ya isa haka, gashi yana faman rasa mutun biyu du a sakacinsa,
GN ne ya sauke ajiyar zuciya kafin ya ce" BS ka san da wa kuke tare?
Kana tare da GNB na saudiya baki daya wanda shi daya ya fita a shekarar horonsa , kana tare da uban
gidanmu ne,...ina mai tabatar maka du abinda yake yi, ya sani, yana sane, ka bi shi kawai, ka sada kanka ka
koyi aiki, sannan ka sani kar ka yarda ka nuna masa da ka sani, nima na sani ne da na matsa kan tambayar
shi din ko wanene, kuma na fada maka ne dan ka kula, kar ka janyowa kanka dama mu duka abinda ya fi
karfin mu,!

*To fa readers ga Abdul, ga Hafsat*


*KUTKALE*

*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct
NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan
number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA
SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN
SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN,
.....* taku ce, Sajida😍😍😍😍

2️⃣1️⃣

Mamaki ne ya cika zuciyar BS, haskiya ne, shifa ya ga abubuwan da suke da girman da isa da iza ba zata
saka a koya ba , sai dai idan an ginaka da abin,

Wayar ya kashe ya koma ya dauki jibrin da aka gama yiwa dinki suka nufi gidan Abdul dan ba zai yiwu ya
bar shi ya yi jinya a asibiti ba,
A lokacin da suka karaso, ya jima tsakanin dakin da aka baiwa Hafsat da nasu, yana ta kai kawo kafin da
kyar ya iya bugawa yana saurare da bugawar zuciyar Allah ya sa ta bashi damar shiga, dan wani irin
kwarjini take masa kamar ba yarinya karama ba.

Amsawa hafsar dake zaune kasa bayanta jingine da gadon dakin , laptop gabanta ta yi shiru tana duban
screen din cike da rashin kwarin gwuiwa domin kuwa lale Abdul ya bata labarinsa aman ba wai ya bata
sunaye bane, komai a dunkule a baibai ya bata, ta tabata ya yi haka ne dan karta ce zata shiga lamarin da ba
nata ba, ya yi haka ne dan kar wani ya kutsa kai cikin abinda bai shafe shi ba,
Gashi dai tun da ta shigo sallah kawai ta iya yi ta samu waje ta zauna tana ta binciken abubuwan da ba
amsa, sai canke canke take ko zata dace har BS ya shigo dakin nata,

Waje ya samu ya zauna a kasa kamar yanda ta zauna yana kallonta,

A hankali ya ce" yaya jikin ki?

Hafsat ta dube shi da kyau tana mai rufe laptop din,


Hannun ta kalla, sannan kuma ta dubi BS , kafadarta ta daga kadan kafin a hankali ta ce" Alhamdulilah,

BS ya kureta da kallo, a nitse ya dan muzkuta yana dubanta sannan ya ce" wa ya cire maki bullet din?

Itama wannan karron tsura masa idon ta yi, sannan ta ce" Abdul ne,

Abdul? Ya maimaita yana mai nuni da wata manufa, sannan ya kawar da kansa gefe yana dan murmushin
yake ya kuma dubanta ya ce" da sunnansa kike kiransa haka?

Dan sasaucin dake saman fuskarta ta yi kokarin kwashewa, inda ta dora yannayin rashin walwala sannan ta
kawar da dubanta daga kansa,

BS ya juyo da nasa duban jin ta yi shiru, ya dago hannunsa yana dubanta ya ce" kar ki yaudari kan ki, kar
ki sakawa kanki wani tunanin abinda ba zai taba yiwuwa ba, kin san shi kuwa? Kin san ko shi waye? Kina
kokarin yin wasa da wuta, kina son saka kanki a halaka ne? Ki sauko daga inda kika hau, aiki ya kawo ki,
ki yi shi kawai, ki duba ki ga yanzu da harbin nan a wani wajen da zaki mutu aka yi shi da shikenan kin
mace wajen kokarin gannin kin birge shi ko me?

Da sauri ta juyo da dubanta wajensa,


Ta jima tanai masa wani kallo kafin ta sada idannuwanta , ranta ne take jin yana wani irin tafarfasar da ba
zata so yin wani furuci a gabansa a wannan yannayin ba,
Me yake tunani da ita, au shi ba zai cire wannan shirmen dake dawainiya da shi a kanta ba? Dan ita bata ga
dalilin da zai saka shi duban kwayar idannuwanta ya jefeta da magangannun dake nuni a sakarai ya dauketa
ba, an fada masa tana neman kai ko ta zo dan haka ne?

Sasauta yannayin muryarsa daga bacin rai zuwa rarashi ya yi ya ce" ba ina miki haka dan na tsaneki bane,
ina so ne ki farga tun kafin ya zame maki matsala

Hafsat ta dube shi da idannuwanta ta ce" kar wani yannayi naka da ka kasa daidaitawa ko tsayarwa ya kai
ka aikata baban kuskure a rayuwarka BS! Kar ka mayar da abokiyar hamayarka....
Shiru ta yi na dan seconni kafin ta dago da idannuwanta da yannayin she's vry serious da abinda take fada
kafin ta taune lebenta da hakorinta ta ce" *dan walahi sai na bika har gawarka sai na yi kokowa da ita!*

Idannuwansa ya zaro yana dubanta, inda gabansa ke tsannanta faduwa kan irin lamarinta,
A dan hargitse ya ce" saboda shi din ne zaki mayar da ni abokin gabanki ko me kike nufi?

Hafsat ta kankance idannuwanta dan jaraba hannunta na ciwo aman bakinta ya ki mutuwa ta ce" dan me
saboda shi? Me kake tunani tsakanina da shi? Ina jin da ni fasika ce, da na jima da bayar da kaina kafin na
shiga *kutkale!*
Aman ai dan na yi maganar nan ne kika bata rai haka ko?
Ya fada yana dubanta da kyau yana dan matsawa kusa da ita kafin ya dakata yana dubanta , sasauta murya
ya yi ya ce" bana daukan ki a fasika, bana miki kallon wawuya, hasalima idan har ya kai ki wajen da zaki
sha wahala zamu sha ta tare ne,

Shiru ya yi gannin ta kura masa ido, daya daga cikin sunnayenta ya zaba dan kiranta domin ta hana shi
kama na asalin, a hankali ya ce" Ummi, ina son ki, kin jima da sannin haka aman kike wasa da zuciyata?
Bayan kin san da daya daga cikin sauran na so, da da gudu zata amince min harma ta bini inda zan je ko?
Ki bari haka, ki daina haka, ya karashe yana mai dubanta kamar yanda take dubansa,
Sai da ta lumshe idannuwanta ta ce" BS, ka yi hakuri ka ji? A yanzu, babar damuwata shine na fita a aikin
nan lafia na samu incina na yawo inda nake so a lokacin da nake so, na sadu da iyayena mu sansanta
tsakanin mu, walahi na fada maka gaskiya rabona da na ji wai ina iya soyaya tun wace ta kai ni
*KUTKALE* me ta anfana min ne soyaya? Ita ta saka na kara zama fitsarariya, dalilin soyaya na tarbi
gaban malan gaban yayansa masu jin kunyarsa na yi tsalen albarka na ce" *Malan, ba aure zaka min ba? To
sai na yanka mijin!*

Haka ya bini da kallo da adu.a, na sha na tashi tsakiyar dare na ga mamana na tofa min adu.a, cikin ikon
Allah sai na je na yi wanka wai na wanke adu.ar dan ta dankwafar da ni ne take min tofi salon a min auren
ko yana wulakanta ni na zauna ko? To kar ta kuma min tofi!
Dalilin soyayar nake duban du wani yayana da ya yi garajen tsawata min na lalaya masa maganar da zai ji
ya tsane ni har karshen rayuwarsa,
Dalilin soyayar na ringa kirta rashin mutunci da nake jin daidai ne, kaina daidai yake da na kowa idan dai
za.a taba min abin so na! Wata alfarma ta yi min soyayar dake saka ni fita tsakiyar dare tare da kato mu je
gidan rawa ni ba karuwa ba, ni ba arniya ba, ina kallo ana abubuwan da ba daidai ba aman a gobema na
koma dan bacin ransa na nufin tashin hankalina?
Ita soyayar nace dan ubanta me ta tsinana min bayan *bakin jini, hau, tabewa, shiga uku, rayuwar da ko a
mafarki ban taba tunanin ganina ciki ba, wato rayuwa irin ta dakarun sojoji?*

Tsagaitawa ta yi da maganar da take yi jin kanta na sarawa ta dube shi ta ce" ban ce bana son ka ba, ban
kuma ce ina son ka ba, hasalima na mance kalar soyaya ne...ko nace na rasa sunnan da zan bata, *fara, ko
bak'a* aa, *zaki ko madaci ce?* , *rayuwa ko mutuwa ce?*, a yanzu burina shi ne *ABDUL* ya rayu, ya
fita a damuwarsa ko zai salame mu mu koma gaban GN ya bani inci cikake na arta a guje sai gaban Malan

Shi kam du kallonta ne yake, wai bata soyaya? Wai ta daina so take son fadi? Shi kam ya kasa yarda, yana
tsoron irin yanda kusancinsu yake da girma tsakaninta da uban gidansu ya girmami tunaninsa ya zarce
mizanin dan bashi tsaro ne kawai

Kansa ya kawar gefe, har tsakar ransa yana jin haushin irin yanda yake wareta ita kadai yana bata kulawa,
du sun lura ba shi kadai ba irin yanda yake sakar mata murmushi ko idan ita ta yi masa tambaya zai tsaya
ne ya bata amsa yanda take so , yana bata lokacinsa , har tsayuwa yake ya cire mata hular gashin dokin da
take dorawa, yakan dora kujera idan sun biyo bayansa in ya zile masu ya zauna dangagal a matsayin da
gare shi a dukiyarsa ya ringa binta da kallo tana faman kuftayar a saketa ta yi masa kashedin kar ya kuma yi
masu haka, da an harbe shi fa? Me yasa hannayin damuwar da take nunawa ke birge shi? Ko meye hakan
ke nufi? Ita kanta takan nuna bacin ranta da dukan karfinta tamkar an taba rayuwar wani na jikinta wanda
take matukar so? Eh lale haka ake koya masu, ana koya masu cewar rayuwar wanda zasu je baiwa kariya ta
fi tasu mahinmanci, su baiwa rayuwar girma su kareta da dukan karfin su, aman ita ta zurma da yawa, ta
shiga da yawa, haka ake yi?

Har ya mike, ya dawo ya tsugunna yana dubanta kafin ya ce" ki kwana lafia, ki kwontar da hankalin ki, in
dai gidan nan ne za.a turo wa.inda zasu canje ku, domin kun ji ciwo ba zai yiwu ku ci gaba da aiki ba, a
gobe gobe GN zai turo masu canzarku ke da Jibrin, a mayar da ke camps, hankalina zai fi kwonciya, ki je
can ki yi jinyar hannun ki, idan kika warke sai a sama maki wata mission din mai sauki ki yi ki gama a baki
damar fita inda kike so, a lokacin da kike so!
Yana gama fada ya juya ya bar mata dakin cike da yannayin damuwa, da tsoron rasata, dan shi sonta yake ,
koma mecece ita sonta yake

Da kallo ta bi shi,
Ya Allah, hakane fa, za.a iya mayar da ita fa, shikennan yanzu ta sha bulley din banza kennan? Eh mana
tunda dai wata mission din za.a kuma fitar da ita, bayan ta shiga wannan? Bayan ta sha wahalar nan
maimakun idan an mayar da itanma a ajiyeta a matsayin ta gama fita mission da sunnan camps din sai dai a
turata wata?

Idannuwanta ta rintse tare da shiga tashin hankali, ita fa so take daga nan ta je camp a matsayin wace ta ci
nasara ta samu incinta!

A hankali ta buda idannuwanta ta shiga kokarin mikewa bayan ta kashe laptop din

Fitowa ta yi ta nufi dakinsa kanta tsaye,


Tana zuwa ta shiga bugawa, jin shiry ya sakata kara kunnenta, sai dai abinda ta dan fara jiyowa ne ya sakata
saurin matsawa gefe tana mai jin gabanta na faduwa,
Sai a lokacin ta dafe kanta da hannun da bashi da ciwo ta ayyanawa kanta cewa....kema baki da kai, a
wannan lokacin kike tsamanin samunsa a hayacinsa?

Zama ta yi a wajen, inda BS ya yi kai kawo ya fi a kirga yana aikinsa bai ce da ita komai ba, ya ajiyeta a
zata yi ta gama ne,

A kadan sun kwashe awa uku a wajem, daga masu baiwa Ni.ima tsaro, da BS da ita kanta,
Suna kallon juna lokaci zuwa lokaci, suna jiran fitowar Ni.ima , kowa na kallon kowa da ido , basu da abin
cewa, sunna zaune ne, kowa kuma ya san me ake yi a cikin dakin, basu da katabus sai ido, dan kuwa
rabonsa da ya je dakinta tun da ya mayar da ita cikakiyar mace, ya kasance ita ke zuwa kowani lokaci ya
bukaci hakan bisa abinda ya dora mata

A lokacin da suka ji karan buda kofar kowa ya kawar da kansa sannan ya kimtsa kansa,

BS kuwa murmushi ya sakarwa Hafsat yana mai yi mata nuni da ba ta gani ba?

A lokacin da Ni.ima ta fito daga dakin ta yi gaba suka bi bayanta Hafsat ta mike ta nufi dakin da niyar
shiga,.

Damtsen hannunta BS ya rike ya saka idannuwansa cikin nata ya ce" zaki je ki wanke abinda baki saka
bane ko zaki je ya gama koshi? Ki farka, ko aure yake ba zai aure ki ba!

Hannunta ta fuzge daga rikon da ya yi mata, ta zabga masa wani harar tsana zata yi magana kennan
idannuwanta suka sauka saman Abdul dake tsaye yana hangen su,

Kwafa ta yi ta nufi dakin da niyar idan ta fito zata kirta masa rashin mutuncin da ba zai taba mantawa da ita
ba

Tana shiga ta rufe dakin ta yi tsaye gabansa,


Da alama bai jima da fitowa daga wanka ba dan kuwa jalabiyar jikinsa na like masa a jikin,

Kawar da fuskarta ta yi dan ita ta tsani wannan kallon rashin kunyar da yake yiwa mutane, sam bai iya
kallon adini ba!

Ba wani kwane kwane ta ce" *Abdul, ka hana a tafi da ni gobe, dan Allah👏🏻*

Dan karamin tawul din da yake tsane kansa ya dan yarfe ya matso kusa da ita a hankali ya ce" kin shaku
da dan baiwa Abdul ne kema? Wai ya aka yi mata basa son yin nesa da ni ne?
Bata san lokacin da ta dawo da dubanta wajensa ba, kai wannan mutun idan da asirima to walahi da hali,
Kanta kawai ta iya girgiza masa kafin ta yiwa fuskarta kalar kaucona ni Hafsat,

Abdul ya dora mata tawul din mai dan lema lema wanda ya gama gogo ruwan kansa a kafadarta ya yi
gaba ,

Janye tawul din ta yi ta ajiye nan tana yatsina fuska ta juya inda ya nufa ,
Gani ta yi ya ciro karamin wando yana kokarin saka abinsa bayan ya san tana dakin
Da sauri ta juya gaba dayanta, inda ya saci kallonta ya yi murmushi tare da girgiza kansa,
Wandon ya saka sannan ya mike da kyau ya nufi wajen bed dinsa ya zauna,
Fuskarsa ya talabe da hannu daya yana kallonta kafin ya yi gyaran murya

Idannuwanta ta bude a hankali, ganninsa zaune ya sakata sauke ajiyar zuciya,


Wajensa ta nufa, ta samu waje ta zauna tana dubansa a sace sannan ta ce " dan Allah, ka yi min alfarmar
nan,

Abdul ya saki talabe fuskar tasa da ya yi ya ce" dalili?

Hafsat ta tsayar da dubanta kansa ta ce" savoda ina son na gama aikina daga nan lafia, ina son inci,

Abdul ya tabe bakinsa sannan ya kuma dubanta ya ce" ke yanzu kina mace har wani inci kike tunanin
samu? Tafia ta yi tafia fa aure za.a maki, ki je ki yiwa mijin bauta, yi na yi bari na bari, ki masa girki, ki yi
shara, ya maki ciki ki haihu ki shayar da su daga shi har yaron ki rin.....

Dan Allah ya isa, wai kai da kowama haka kake magana marar da.a ko nice kake yiwa kallo mn yar bariki?
Ka je ka yiwa matarka mana? Sai ka 2ani saki baki kanai min magangannu mararsa da.a? An gaya maka ni
yar iska ce?

Kallon da yake mata ne ya sakata tunawa da a gaban wa take,


Hakan ya sakata yin sororo, tsawa fa ta daka masa, ta yi masa tsawa , bayan yana mai gidanta kuma ta zo
neman alfarmarsa ne?

Nan da nan idannuwanta suka ciko da kwala,


Juyawa ta yi ta shiga tafia a hankali tamkar kazar da kwai ya fashewa a ciki,
Har ta kusa fita ta ja ta tsaya tare da juyawa ta dube shi , a hankali ta ce" ka manta abinda na zo nema, dan
ban ga anfanin karasa aiki a cikin irin wannan rayuwar ba,

Hawayen idannuwanta ne suka zubo daga kwarmin idon, muryarta ta shiga rawa ta bude dakin ta dago da
idannuwanta ta dube shi ta ce" *ni ba yar iska bace Abdul*

Sakin kofar ta yi ta fice a dakin da saurin gaske, inda ya mike da sauri ya sauko daga saman bed din da
niyar bin bayanta, sai dai me ya tuna, me ya hana shi? Ya dakata ya dafe goshinsa da yake jin ya wani irin
sara masa,
Hannunsa ya kai wajen madubin dakin nasa ya daka da mugun karfi kafin ya saki ihu mai cin rai

Idannuwansa ya dago ya kai dubansa wajen madubin, yana mai jin zuciyarsa na wani irin tafarfasa, jajayen
idannuwansa ya kai wajen da ta tsaya a hankali ya ce" ba zan kuma yarda na saka rayuwar wani a hatsari ba
Hafsat, ki gane.....ni kuma ba mahaukaci bane soyaya aka hana min yi karfi da yaji..............

Wani murmushi mai kama da na yake ya yi mai ciwo sannan ya ce"


*kWANA goma sha uku kacal, kwana goma sha uku kacal kina faman tarwatsa ni? Ba zan baki wannan
damar ba, na fi kowa sannin ke ba yar iska bace Hafsat! Aman zan je da ke a yar iskana 😔*
[6/24, 4:04 PM] BAK'A CE: *KUTKALE*

*(PRISON)*
NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct
NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan
number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA
SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN
SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN,
.....* taku ce, Sajida😍😍😍😍

2️⃣2️⃣

Koda Hafsat ta koma dakinta wanka ta shiga ta yi ta fito ta saka wata riga fara dake cikin kayanta ta zauna
tana kallon waje guda,
Kwata kwata wani lokacin idan ya yi irin abubuwan nan sai ta ji ta tsani kanta,
Mikewa ta yi ta dubi madubi,
Tabas yannayinta tamkar ba yar musulmai ba, suturar jikinta a kulun ba kamilaliya bace irin ta yayan
musulmai,
Gashin kanta rabon sa da dan kwali ya zauna daram a kanta ba lokacin sallah ba tun tana gidan mahaifanta,
Sam aikin zama bodyguard ba aiki ne da zai ja maka mutunci da girmama ba a kasar Musulmai,
Kai dai kulun ka kare a saka wando, da rigar da ba zasu iya hanaka gabza fada ko dankarawa da gudu ba ?
Kai dai haka zaka kare a bushe?

Zama ta yi tana mai jin haushin irin yanda yake nuna mata iya shege a fili duda ba shi ne na fari ba, aman
nasa na yi mata ciwo, bata san dalili ba, bata san me yasa du idan ya ambaceta da gardi, ko yace da ita a
bushe sai abin ya yi ta yi mata yawo a kwonya!

Tsaki ta ja tana zabgawa bed din da zata kwonta harara a fili ta ce" ba dai na shayar da uban ba, aa shima na
mayar da shi cikina na haifo shi! Kuma gwarama na bar aikin naka dan banda neman kai ni barzahu ba
abinda yake, ga wulakanci! In sha Allah zan tafiata gobe ka je ka zama abinda zaka zama sai me? Idan ban
samu incin daga wannan aikin ba sai me? Na yi hakurin duka wannan lokacin dan wannan ba zai kashe ni
ba!

Haka ta yi ta magangannun bacin rai, har ta raba dare kafin ta yi kwonciyarta a nan kasa ta nemi rintsawa,

Du irin yanda ta cika dare, kiran sallar farko a kunnenta, dan haka ta ciciba ta mike tana mai jin hannun ya
dan yi mata nauyi dan kuwa ko ba komai ciwo ne da ya kwana ya yi tsami bale harbin bindiga

Zuwa ta yi ta yi wanka, ta kiyaye wajen bata jika ba, haka ta gama du wani uzurinta ta dauro alwallah ta
fito,
A daidai lokacin da take kokarin tayar da sallah ta ji shigowar mota,
A hankali ta daga labulen dakin tana hange,
Bakar mota ce ta shigo , gannin BS tsaye a wajen motar ya sakata juyawa ta tayar da sallarta, sai da ta gama
a nitse sannan ta dauki dogon wandonta baki da riga baka ta saka, rigar mai karamin hannu ce bata dora ta
samanta ba dalilin ciwon hannunta,
Bata shafawa fuskarta komai ba, sai harhada kayanta da ta yi cikin yar akeatinta dama kayan ba wasu masu
yawa bane sai bindigarta da ta daura a tsatsonta ta ja rigarta ta rufe bindigar,
Wajen madubin dakin ta je ta tsaya, tsurawa madubin ido ta yi, a hankali ta furta" shikennan, haka zaki bar
shi tsakiyar wannan tashin hankalin?

Fuskarta ta yatsina ta dubi madubin da kyau ta ce" kwarai, mutuncina, da son haduwa da iyayena ya fi mani
aikin nan da kowama, dan haka zan kara gaba!

Murmushi ta yi ta duka ta dauki akwatin ta shiga janta a hankali, kanta bude ba dan kwali sai gashin kanta
da ta daure da dan karamin ribom,

A lokacin da ta fito katon falon gidan, BS ne kawai tsaye ,


Ido ya tsura mata, kai yarinyar ta hadu ne, du irin gudun da aka sakata bai saka mazaunanta rage fadi da
tudu ba, cikinta kiwa tamkar babu hanji a ciki, fatar jikinta wani urin fresh da ita, domin kuwa mayukan da
sabulansu na wanka ba jagaliya bane, sun karbeta sosai, haka kuma gashin kanta baki ne sidik ba yambo ba
komai, haka yake halitarsa ce, ga cika ga madaidaicin tsayi, gaban goshinta ya fi cika da suma luflufluf
haka yake, girar fuskarta har cajeta take ta daidaita ta yanda take so, hancinta ya ja ya tafi tsuwait har kusan
dan karamin madaidaicin bakinta mai dauke da lebunna kalar pink, idannuwanta manya manya ne masu
hasken fari bakin cikinsu mai girma ne sannan ko ranta ya baci sai dai su cicika da kwala,

Shi kansa bai san da ya zuba mata ido ba sai da ta zauna saman kujerar zaman mutun daya bayan ta mayar
da jakarta gefe ta dan jingina suka shiga zaman jiran fitowar Abdul da ya san da zuwansu tun jiya da sare

A hankali ya karasa inda take zaune ya zauna shima,

Sai da ya hadiyi yawun neman kwarin gwuiwa ya ce" fuahi ake da ni ne?

Bata buda gazar gazar din gashin idannuwanta ba ta girgiza masa kai kawai,

Kyakyawan dogon hannunta fari kal wanda baya dauke da gashi ko dis , damtsen hannun shar da shi du irin
formation din da ta samu bai saka ya yi mundil mundil da shi ba, ya dan kara girma aman bai zama wannan
kigi kigi din irin na maza ba ya bi da kallo,
Sai da ya karewa wajen kallo sannan ya kai dubansa kan fuskarta, da son samunsa ne, ya watsa mata selfi a
ajiye a gaban wayarsa ya ringa kallo idan ya samu lokaci sai dai ya san bama zai samu hakan ba dan haka a
hankalin dai ya ce" yaya jikin ki?

A hankali ta buda bakinta ta dane zuciyarta dan kar ta dankara masa magana ta ce" alhamdulilah

Shiru ya yi shima, bai matsa a kusa da itan ba, bai kuma kara yi mata magana ba, yana mamakin irin yanda
sam baya gabanta, ba wani ziga kai ba, ba komai ba irin yanda manyan yan matan cikin gari ke binsa yana
jan su a kasa yana tafka masu iya shege da yaudarar soyaya sai gashi yana bin yar yarinyar nan tana faman
jan sa a kasa, ko yanzu wace aka kawo ta canjeta babar bodyguard ce, kuma ta yi kudi sosai yanzu haka
daga america aka daukota aka yo nan da ita, yar kwalisa , yar cakwas da ita, ita kanta soyaya suka yi ya
yarda ita daga baya , ko yanzu yace su koma zata yarda da gudu ne, aman ita ga damarta a hannunta tana
wasa da ita.

Wasa wasa a nan a zaune sai da suka kai wajen karfe tara da mintuna, suna yi suna kallon agogo, aman ba
Abdul ba alamunsa,
Shi dai BS yana zaube bai yi gigin zuwa taso shi ba, hakama ba wanda ya yi gigin hakan domin dai su BS
ne mai gidansu, umarnin da ya bada shi za.a bi dole, shi kuwa an fada masa waye Abdul din, dan haka yake
kiyayewa

Goma saura kadan alamun bude dakinsa suka bayanna , dan Haka da sauri BS ya mike ya koma wajen
kofar ya tsaya hakama Hafsat ta mike tana jiran fitowarsa, inda BS ya shaidawa na wajen cewa zai fito dan
haka kowa ya kama kansa

Sai da Abdul ya gama wana kys din kofar sannan ya bude ya fito,
A lokacin da ya fito maimakun ya tsaya ya bi abinda ake juransa dominsa, sai ya shiga dayan lungun da zai
sada shi da dakin Muhammad,

BS juyowa ya yi ya dubi Hafsat dake tsaye itama,


Ai kuwa yannayin da ya nuna ita sai ya bata dariya ma, dan haka ta murmusa tana dubansa sannan ta kauda
kanta, a ranta kuwa tana ayyana baka san rainin hankalin Abdul har inda ya kai ba kennan, muna iya wuni a
wajen nan idan ya yi niya!

Abdul na zuwa ya samu Muhammad ya gama shiryawa, shima cikin shirin manyan kaya kamar yanda
Abdul din ya saka irin dinkin yan nigeria , shada har da hula kuma du sun karbe su sun fito da su das
gwannin sha.awa,

Muhammad ya dube shi da kyau bayan sun gaisa ya ce" yanzu sai ka je daurin auren nan Abdul? Kai wai
ina ruwanka ne ma da shiga wannan lamarin? Shi mahaifin nata ba ya san daga inda ya daukota ba? Kuma
dai ya san ba zikiri ake a wajen ba abinda ya kaita take yi ba wata damuwa, to yanzu dan zai mata aure
fisabililahi Abdul sai ka wani saka mu shiga ta mutunci tamkar zamu je yin abib kirki ?

Abdul ya zauna saman kujera yana dubansa ya ce" Muhammad, Muhammad ya rab, Muhammad kana so
kennan mu zuba ido a daura mata aure bayan da dati a jikinta? Ina laifin ta kilace kanta har datin dake
jikinta ya barta? Shi kennan dan son kai sai ya rufe ya baiwa wani? Ka ga idan zaka bi ni aikin Allah tashi
mu je, idan kuwa tsoron mutanen dubiya ya fiye maka aikin ubangijinka kuma Fine, ai yana kallon ka

Muhammad kam ya shiga cikin tsaka mai wuya, ya dirmiya shi a cikin lamarin shaku kuma ya hada shi da
Allah, shi bai san yaya zai yi ba, walahi yana son barin garin aman irin hadarin da Abdul ke shiga ya hana
shi motsawa, yanzu mai gaba daya zai dulmiya su a wani lamarin

Turarensa ya kara fesawa, ya gyara zaman hularsa, wato ya kafeta a kansa sannan ya dubi Abdul ya yi gaba
ya fara tafia

Murmushi Abdul ya yi ya mike shima ya bi bayansa suka fito gaba dayansu,

Sai da suka fito farfajiyar gidan ya tsaya yana sauraron BS dake masa bayannin an kawo wa.inda zasu
dauki wajen bodyguards dinsa da aka harba

Juyawa Abdul ya yi da bakin gilas din idannuwansa ya shiga bin su da kallo,


Wanda aka kawo namijin sosai ya girm8 jibrin, alamun karfi da jajircewa sun bayana a tare da shi, sai
macen wata yar dagwas da ita yar kwalisa, duda uban ramar dake jikinta dan kuwa bata da jiki ko kadan
gaba daya ta gama horuwa ko.inanta ya sabe ya zube aman kyakyawa ce dan lebenta harda dan jan bakinta
kalar ja, haka ya kai dubansa wajen jibrin ya ga sai da aka talabe shi du kuwa yanda yake son ya tsaya da
kansa ya kasa dan a ciki aka same shi, sai ko Hafsat dake tsaye kikam, ba wata fara.a, ba alamun komai a
tare da ita ba zaka gane hallin da take ciki ba, ita dai a tsaye take,
Bin suturar jikinta ya yi da kallo har takalmi sau cikin da ta saka kafin ya maida dubansa wajen BS,
Kai tsaye ya ce" suna iya juyawa da Namijin, aman a bar matan biyu da wanda aka kawo
yanzu............................... ya karashe yana mai kara hade girar sama da ta kasa , ya ci wata irin fuska da ta
saka bakin gilashin kansa kara fitar da mazakuntar fuskar yana duban BS tsai a gabansa!
[6/24, 4:04 PM] BAK'A CE: *KUTKALE*

*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct
NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan
number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA
SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN
SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN,
.....* taku ce, Sajida😍😍😍😍

2️⃣3️⃣

Sai da BS ya dago da dubansa da sauri ya dora saman fuskar Abdul, sai dai kuma da wani saurin ya kara
kawar da dubansa ya juya dan cika umarnin da aka bashi,

Yana zuwa, fuskarsa tamkar an wanka masa mari ya basu umarnin su juya da Jibrin, a bar Hafsat,
Da mamaki bakuwar da aka kawo wace zata hau wajen Hafsat ta dan matso ta ce" aman, ai GN ya bada
umarnin a koma da ita na hau wajenta ko?

Cikin daurewar fuska ya dubeta da kyau ya ce" yaushe aka koya maki yin gardama da mai baki umarni a
wajen aiki?
Da sauri ta girgiza kanta wato ba.a koya mata ba, dan haka ya ce" idan mun dawo zaki yi tsalen kwado
hamsin punishment din kokarin yi min gardama,

Hafsat sai da ta zaro ido gannin yanda ya ringa bada umarni, daga wannan yar tambayar wannan hukuncin
ya hau kanta? Lale ta yarda yana son ta, to haka mana, ita wani irin iskanci ne bata yi masa, har lda kashedi
ta sha yi masa ido cikin ido, sai kawai ya yi murmushi ko ya zuciya ya bar mata waje, kai ita yanzu da yake
hakama sai ta ji ya birgeta,

Maimakun a mayar da ita daki ita dake jinya, sai tsintar muryarsa ta yi yana fada masu inda za.a je da irin
ysaron da za.a baiwa Abdul da Muhammad baki daya,
Sai da ya gama ya kara dubansu ya ce" ku sani, ku rike, ka saka a kwakwaluwarku, rayuwarsu ta fi taku
mahinmanci, aman kuma takuma ana so ta ci gaba da wanzuwa, ku saka duk wani kokari naku, sannin aikin
ku, wajen gannin kun kare lafiar uban gidan ku! Ba maganar rashin lafia , rashin shiri, a shirye muke baki
daya!

Gaba dayansu suka amsa,


Wata doguwar mota mai gilas bakikirin ce aka karaso da ita,

BS na kokarin gyara yanda za.a yi zaman sai tsintar muryar Abdul ya yi yana fadin Hafsat ta zagaya ta
shiga ta dayan barin, shi ya shiga tsakiya Bakuwar mai sunna Hasana ta shiga dayan barin wato dai suka
saka shi tsakiya, sai Muhammad ya shiga ya zauna a kujerar dake facing din su, su Abdul suka shiga gaba
sai sabon Bodyguard din ya hau wani katon mashin sannan sojojin Muhammad suka shiga wasu motocin
suka daga,

Tafe suke da gudun gaske, aman daga cikin motar sai ka yi zaton ba.a wani gudu ana dai dan motsawa
kadan, dan kuwa ba.a jin komai dake wakana a waje sai a ciki

Zamansa ya gyara yana kada kafarsa da ya dora saman daya, idannuwansa a kan Muhammad wanda ke
kallonsa shima da yannayin tambaya, sai dai ya kasa yin tambayar duba da irin yanda Hasana ta tsare su da
kallo tsuru ta hana shi motsi, shi sai ma ya fara tsarguwa ko ji take shi ne makashin?

Hasfat kam zaman da ta yi a takure take, domin wannan zaman da Abdul ya yi du irin fadin wajen da tsayin
kujerar sai ya wani gaje wajen, haka take samu ta dan matsa aman daga ta matsa sai ta ji ya matso ya kara
matse mata waje, wannan dan matsawar da suke nema ya saka Muhammad tsura masa ido yana dubansa,

Abdul ya tabe bakinsa bai ce komai ba, har suka karaso anguwar da ta cika makil maza ne ko.ina manyan
mutane ana ta haya haya ana shirin daura auren Elhaj Moctar wato daya daga cikin aminan Mahaifin
Abdul, wanda ya je ya dauko yar tasa daga kasar chaina da karfin balaki ya yi mata miji zai aurar da ita
bayan ita a chainar zaman kanta ne take , tana tsaka da rayuwar ya kawota ba abinda ya dame shi da
tsarkinta ya shiga hada hadar daura mata aure

Abdul na zaune a cikin motar ya ji an fara sanarwar a matso zama daura aure,
Baban dan ministern man fetur ne zai aureta, dan haka wajen sai kara daukan harama yake ana ta cuwa
cuwa, mahaifin amarya sai baza babar riga yake hakama mahaifin ango an hadu za.a hada

Sai da ya hango motar da angon ke ciki, a lokacin har sun zazauna saman lafiyayir tabarmar da aka shinfida
dominsu alwalin kowane ya matso za.a fara gabatar da daurin auren Abdul ya samu ya bude motar ya fita
inda Muhammad ya bi bayansa gabansa na faduwa, su Hafsat kuwa suka mara masa baya suna ta dube
dube inda Su BS ma suka kafa suka tsare idannuwansu a kan du wani mai giftawa, haka na kan mashin sai
zagaye yake yana kara dubawa, sannan na sojojin Muhammad du sun kafa sun tsare suna sakar masu hanya
har suka karasa wajen motar da ya tabata angon le ciki,

Kwonkwasawa ya yi, aka bude masa ya shiga ya zauna,

Ido ya tsura masa kafin su yiwa juna murmushi,


Abdul ya mika masa hannu yana kallonsa ya ce" ango ango, yau aurwnta aman sai cika fuska kake?

Wanda aka kira da angon ya yi murmushin yake bai ce komai ba,

Abdul ya ce" kar ka yarda a daura maka aure da yarinyar da bata yi tsarki ba Almustapha

Almustapha ya dube shi da sauri ya ce" me kake nufi?

Abdul ya ce" koda an daura ba kyau, kai ka san abinda nake nufi, na tunatar da kai ne, kuma ni ba mace
bane sa zan zauna baka komai a tsare, kai dai ka yiwa kanka karatun ta natsu, ka tina Allah zaka sabawa
wajen yiwa mahaifinka biyaya ko zaka bi Allah ka sabawa mahaifinka?

Tamkar wanda Abdul ya yi masa allurar dawowa daga duniyar summa ya wani zabura inda ya cire hular
dake kansa wani shegen aski irin na yan gala ya bayanna a kansa,

Kana gannin lebensa ka ga rikeken dan giya, hakama muryarsa ta shaida shi, aman dan iya shege ya cire
babar rigar da aka saka shi sakawa ya dubi Abdul ya ce" ai aikin Allah na gaba da komai Elhaj, kai dai yi
jirana a nan na je can na dawo
Ya karasa fadi yana mai nuna masa kafin ya bude motar ya fice da sauri sauri yana washe baki

Abdul kam bude motar ya yi shima ya fito, tsaye ya yo ya bi shi da kallo shi da Muhammad kafin ya yi
dariya yana girgiza kai,
Dubansa ya maida wajen Muhammad dake dan waige waige du a firgice yannayinsa yake ya ce" ka san ana
iya shege ko alhaji, ka ga ya yi tilif fa, qman da yake neman kubucewa aurwn yake ya tafi da gudunsa wai
zai je ya yi aikin Allah

Muhammad kansa sai da ya saki dariyar da bai shirya ba sannan ya ce" Abdul , kai mugu ne

Abdul ya yi murmushi sannan ya gimtse fuskarsa yana mai jin gabansa ya wani irin faduwa,
Da sauri ya shiga waige waige, da hannu ya yi alamun a tafi da Muhammad

Muhammad na gannin haka shima hankalinsa ya fara tashi dan ya san kawai ba zai ce a kai shi mota ba ,
dan haka ya damko hannunsa ya ce" mu je tare,

Abdul ya girgiza masa kai, sannan ya dubi Hafsat da ta fi kusa da shi ya daka mata wata tsawar da sai da
gabanta ya fadi ta hanyar fadin" me kike jira da ba zaki kai shi motar ba??

Da sauri ta saka hannunta da ya fi aikatuwa ta ja Muhammad dake tirje mata kan a taho da Abdul da kyar ta
samu ta ja shi suka dauki hanya dan kai shi cikin mota, sai dai karon da suka ci da wani mutun sanye da
manyan kaya, ya yi rawani ya dan dakatar da su, inda Hafsat ta dan dubeshi ba sosai ba, sai dai bibdigar da
ta ganni a hannunsa ya sakata kwala ihun kowa ya kwonta
Gaba daya wajen ya kwashi kururuwa, masu afkawa gidajen mutane na afkawa, masu shigewa mota na
shigewa, masu ihu su antaya a guje suna antayawa, masu kwonciyar suna kwonciyar, su BS ma sun shigo a
guje suna nemman kare lafiar Abdul,

Maimakun mutumen ya fice da gudu, sai tsayawa ya yi ya damki hannun Hafsat wanda take faman daukar
bindigarta da shi, gashi mai ciwon ne bata jinsa sosai a jikinta sai ciwon da yake mata, gashi ya damke shi
da wani irin karfin da ta ji ta kasa katabus dan haka ta saki Muhammad da ya kai kwonce ya dora
hannayensa saman kansa,

Damko hannunta da mutumen ya yi ya sakata kallon cikin idannuwansa,


Bata ga komai ba sai wata muguwar tsana da ishirwar balaki, baki ne kirin, cikin idonsa ya kwonta da jini
jini alamun baya cikin yannayi na dadi,
Ido cikin ido suka kalli junna kafin a hankali ya motsa bakinsa dake cikin rawani ya ce" Abd........
Bai kai ga karasa fadin sunnan ba, ko tace kunnayenta basu idasa jin me ya yi niyar fadi ba ya cikata ya
shige cikin mutanen dake gudun neman tsira hakan ya sa bat lokaci guda ta juyo da niyar ganninsa aman ta
neme shi ta rasa, hakan ya sakata durfafar cikin mutane rana ra juyo du wanda ta gani da shigen irin rigarsa
tana son ganninsa,

Daga wajen su Abdul kuwa BS na zuwa da sauri ya rike hannunsa ya shiga jan sa
Bai yi gardama ba har sai da suka karasa wajen motar sannan ya saki hannunsa ya bude masa
Shiga ya yi ya zauna, du a tunaninsa su Muhammad na ciki, sai dai yana juyowa ya ga basa nan

Da sauri ya kama zai bude, sai dai BS ya rufe daga waje da KY ya yi gaba,

Aljihun rigarsa ya shiga laluba, aman wayam babu abin budewar, nan ya tuna dinkin sabon dinki ne da
Muhammad ya yi masu,
Hannayensa ya dora saman kansa ya shiga bin yanda su BS suka tatare mutane tuni Ministerma an fita da
shi da yaronsa inda yaron har an daura aure ya dankara saki kan ai bata da tsarki🙁

Du mutanen dake wajen, ko nace yawanci sai da su BS suka zagaye anguwar aka rufe aka shiga bincike, sai
dai ina basu ga alamun wani mai alamun shi ne Hafsat ta nuna da ihun a kwonta ba, domin abin kunnensu
du ya saka kowa juyowa ya ga mutumen a lokacin da ta fada shi yasa kowa daga wajensa ya shiga ihun a
kwonta a kwonta,

Sai da suka kusan awa , Hasana na tsaye kusa da motar da Abdul.ke ciki kikam ta tare gaba ta tare baya,

Daga inda yake zaune ya rasa katabus, jikinsa du ya yi sanyi, sai zuciyarsa dake tafarfasa,

Faduwarnan da gabansa ya yi ya samu irinta ne du idan wani abin ya kusanto rayuwarsa, tabas akoy abinda
aka so a yi, ko aka yi a wajen nan, gashi ya rufe shi bale ya fita ya bashi taimako ko zasu gane wani abin

Sai da suka gama sannan suka kama Muhammad aka kai shi cikin motar, wanda yana shiga ya shiga Abdul
da fada,
Fada yake tun karfinsa cewar" ka bar wannan abin Abdul Jabar, ka bar shi haka, wasa da ran ya isa haka,
kai kulun idan ka fita sai an samu matsala?

Yana cikin fadan su Hafsat suka shigo cikin motar, aka kunna motar inda yanzu har BS a saman mashin
suke raka motar cikin tukin garari su yi gaba su yi baya

Muhammad fada yake tun karfinsa har ya saka tissu ya share hawaye ne ko zufa ce? Aman a yannayin da
yake dole ya baka tausayi, sam sam baya so a taba lafiar aminin nasa, abin na bashi tsoro, shi so yake ya bi
shi su juya gida ya koma bakin aikinsa aman firr ya mayar da wannan mission tasa karfi da yaji har kiranta
yake mission din da aka turo shi yi.

Shi dai direba na tukinsa cikin kwarewa har suka iso gidan Abdul Jabar,

A daidai lokacin da aka tsayar da mota, du wani bodyguards da sojan cikin motar ya fice, ya kasance Hafsat
da Hasana sun bude gefe da gefen motar sunna jira Muhammad ya gama fadan da tamkar aku ya kasa
gajiya kuma Abdul din ya ki ya tanka sa gashi da yaren larabci zallah yake yi wanda bai san ba ruwa ruwa
haka hafsat ke jin sa ya saka Abdul dago da kansa,
A lokacin da ya bude idannuwansa sai da gaban Hafsat ya fadi, domin daga cikin idon har wani abu tamkar
jini jini gefe da gefe ya kwonta,
Saurin kawar da kanta ta yi tana laluben ina ta ga haka?

Muryar Abdul ce ta daki kunnenta cikin yaren larabci ya ce" *ba nace maka yana raye ba? Abdul bas....*

Kafin ya yi karasa ya saka hannayensa gaba daya ya rike kansa, wani irin yamutsa masa kan nasa ya shiga
yi nan da nan sai ga habo ya bale ta hancinsa tamkar wanda jijiyar wajen yanketa ne aka yi ba dan
jakudawa ne ta yi ba,
Idannuwansa ne suke tafia a hankali, Muhammad da ya rukunkeme shi ne ya basu damar gane Abdul ya
rufe idannuwansa, lumfashin sa ya rabu da gangar jikinsa

Lahaula wala kuwata illa billah,

Wani irin tuma BS ya yi ya janye Hasana dake faman kama shi ya kamo shi ya samu da kyar ya ciro shi
daga motar,
Sabon Bodyguard dinsa ne ya zo ya kama shi suka ciciba shi sukai ciki da shi inda du aka rufa masu baya
banda Hasana da Hafsat,

Hasana kam ta tsaya rurufe kofar motar ne tana tunanin me ke faruwa da wannan gys din da suke baiwa
tsaro ne? Larabcin nasa ya yi gagawa da yawa gaskiya bata fahimci komai ba , aman kamar ransa ne ya
baci ko me? Waima *ya mutu ne ko da ransa?*

Sai da ta gama gyara komai na cikin motar ta baiwa direban kys sannan ta ga Hafsat na tsaye cikin ranar
nan ta kurawa hanyar da aka bi da Abdul ido,

Mamaki ne ya so kasheta, kai, me yarinyar nan ke nufi ne? Dama ta ga an barta ya hana a tafi da ita, to wai
wacece ita? Waye shi da har ya isa ya zabar masu wanda za.a je da shi ko aa? Yanzu haka maimakun ta ga
an fita da shi zuwa asibiti sai dai suka shiga da shi ciki doctern familly za.a kira masa ko me? Me ke faruwa
ne haka?

Cikin izgili ta nufi Hafsat ta yi tsaye kikam gabanta ta shiga binta da kallo kafin ta tafa hannunta tana gyada
kanta ta ce""""

😹😹😹😹😹😹😹😹😹 comment plz plz plz plz comment masu zafi zafi😌
[6/26, 4:45 PM] BAK'A CE: *KUTKALE*

*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE
INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct
NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan
number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA
SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN
SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN,
.....* taku ce, Sajida😍😍😍😍

2️⃣4️⃣

Hasana ta ce" hala, menene tsakanin ki da wannan Elhaj?

Hafsat kuwa tamkar mai koyon gane yaren Hasanat ta tsurawa lebenta ido tana kallon yanda yake motsawa
tana fitar da harufa, tamkar da gaske tana fahimtar abinda take fada, ashe ita bata ma san me take cewa ba,

Zagayeta ta yi ta nufi ciki tamkar ta kifa,


Tana zuwa ta tarar an rufe dakin, bodyguard din nan sabo ya tsare kofar ya caka fuska,

Shi kansa uban gidansu ne, dan haka ba zai yiwu Hafsat ta kawo masa wargi ko wani gatsali ba, kusa da
kofar ta je ta tsaya ta tsura masa ido tana kallon sa

Shima ita din ya kala, mamaki ne ya kama shi irin yanda ta tsura masa ido, dan haka da girarsa ya yi mata
alamun tambayar lafia?

Kanta ta sada ta kasa bashi amsa,


Suna wajen nan wasa wasa har docter ya zo,
Cikin wani irin sauri bodyguard din nan ya caje shi sannan ya bashi hanya ya shige,
Abin ya baiwa docter tsoro, domin wannan jinnin da yake fitarwa ta hancinsa dole ya fitar da shi a
hayacinsa, kuma a iya binciken da ya yi da abubuwan da ya dauko da aka fada masa cewa habo ne bai ga
wani dalili ba, kuma ya bayar da du abinda ya dace a yi an yi dan ya tsaya aman ina, haka suka talaba shi
suka yi ta bubuga goshin , shima dai sai ya yi kamar ya tsaya aman daga sun kwontar da shi sai ya dawo,
gashi dai tamkar gawa dan ya fice a hayacinsa tuni

Doctern ne cikin wani yannayi ya ce " sai fa mun je asibiti da shi, idan ba haka ba kuwa za.a iya rasa shi a
kowani lokaci

Cikin tashin Hankali Muhammad ya dube shi kafin ya yo gaba ya fito a sukwane ya nufi dakinsa

Cikin hanzari ta mike ta bi bayansa sai dai nan ma an hana ta shiga sanadiyar sojojin dake wajen

Me ya yi? Oho sai fitowa ya sake yi tamkar ya tashi sama , fuskarsa jaga jaga da hawaye nan Hafsat ta tare
shi tana tambayarsa jikin Abdul din

Sai da ya dan dubeta, sannan ya girgiza mata kai ya rabata ya shige

Hannayenta duka biyu ta dora saman kanta a fili ta furta" shikennan, sun cin maka Abdul,
Hannunta mai ciwo ne ta ji kamar wani abin ya kara sukarta, dan haka ta dan ajiye shi a ranta tana tunanin
harbin ne ke hadasa mata haka, aman a hankali sai ta dan juyo hannun dan dubawa

Sai da gabanta ya fadi irin abinda ta gani, rubutu ne, da larabci a bayan hannun nata,
Da sauri ta juya ta fada dakinta ta kunna wutar dakin ta je gaban madubi ta ja ta tsaya tana kallon hannun,

A hankali ta karanta abinda aka rubutan kafin ta fasarce da kalmar hausa cewa *maganin ruwan zamzam da
dabino ta hanyar da jinnin ya yawaita*

Ta karanta ta maimaita ya fi a kirga kafin kamar a mafarki abinda mutumen da ya damki hannunta a wajen
taron nan ya dawo mata,
Tabas wannan mutun shi ne ya damki hannunta daidai wajen nan wanda ta gani rike da bindiga har ta yi
ihun mutun da bindiga,

Da sauri ta ruko idannuwanta domin kuwa ba zata manta ba da ya fadi haka sai da ya kure mata waje kafin
ya furta mata sunnan *ABDUL*

Baya baya ta yi dabas ta zauna a kasa,


Tsoro da rudu ne suka shigeta a lokaci daya,
Ta shiga rudanni tsakanin amsoshi biyu ta fanni biyu,

To waye shi? Me zai saka shi ceton Abdul? Idan fa ba cetonsa bane zai yi aa karasa shi ne zai yi ta wannan
hanyar? Aman kuma ruwan zamzam waraka ne, tsaftacen ruwa ne, zai cutar da bawa ne?
Eh to ana iya hada shi da wani abin ya cutar din mana,
To aman da dabino ne aka hada shin fa, dabinoma ai warakar ne,
Yannayin mutumen bai bata kalar mai tausayi ba,
Yannayinsa bai yi mata nuni da zai iya ceto ba, idannuwansa sun tsoratar da ita, irin rikon da ya yi mata ya
tsoratar da ita,

Tana nan zaune tana sakawa tana warwarewa har ta ji alamar kukan ambulance

Mikewa ta yi cike da mamakin ambulance kuma? Ina kwakwaluwar BS zai bari a kai shi asibiti a
ambulance? Idan fa an yi haka ne dan a tarbi motar a karasa shi?? Baya tsoron daga ambulance din wani
mugun abin ya same shi??

Da sauri ta nufi hanyar fita ta fice a dakin ta tunkari dakin Abdul din

Tana zuwa yanzun tsaye ta yi gaban Bodyguard din ta bashi bayannin ita ke kula da ci shan Abdul, ya dace
ace tana kusa idan za.a saka masa karin ruwa da du wani abu, idan ya hanata shiga Abdul ya tashi zata kai
karansa wajensa dan kuwa ya hanna mata yin aikinta yanda ya kamata

Sai da ya yi mata kallon baki da wayo, sannan ya yiw BS magana da abinda Hafsat ta fada,

Jimm BS ya yi na dan lokaci kafin ya ce" barta ta shigo

Hanya ya kauce mata ta shiga ya bi bayanta da kallo yana mamakin to idan ta fadawa Abdul din sai me?
Shi ya san kan aikinsu ne? Kuma yayama aka yi take kama sunnansa kai tsaye tace *ABDUL?*

Tana shiga wajen BS ta zarce tana kallon yanda Abdul ke kwonce shame shame an cire masa rigar jikinsa
daga shi sai wandon rigar , likita da Muhammad na kusa da kusa da shi
Haka kawai ta ji zuciyarta ta karye, ya salam, mutun, mutun ba komai bane, mutun ba komai bane, yanzu
Abdul ne lokaci kankani ya dawo haka? Mutun shi ya dauki kansa wata tsiya!

Sai da ta yi da gaske ta hana idannuwanta zubar da hawaye, a haka ta karasa gaban BS dake tsaye ta dago
da idannuwanta ta lunshesu sosai ta bada kalar tausayi da son ya saurareta ta ce" BS, ya zaka yarda a tafi
asibiti da shi?
BS ya tabe baki yana kawar da idannuwansa daga yannayin fuskarta fanma kar zuciyarsa ta karye ya ce"
kin san dai a haka ba za.a iya tafia da shi asibiti a motarsa ba ko? Dole sai an jona masa abin taimakon da
dole sai an saka shi a ambulance domin a ciki ne za.a iya samu!

Hafsat ta kara matsawa kusa da shi sosai , ta rage karfin muryarta ta ce" mutumen da ya rike hannuna, dubi
abinda ya rubuta min a bayan hannu, idanfa an saka masa poison ne sai wannan ne makarinsa?

Wani duba ya yi mata kafin ya ce" ta ina aka kai gareshi? Marabinku da shi shigarsu cikin motar dan
minister, jikin ku jikinsa fa, a iska aka saka? Idan a iska ne yaya aka yi mu bamu shaka ba?
A abin sha aka bashi? Sannin kanki ne ko abinci bai yarda da shi ba , shi ke girkawa ya ci da kansa ko
*abincin ki* bai yarda da shi ba!

Da sauri ta dube shi, wai ko abincinta, dan me za tana wareta da su?


Kanta ta kawar tana dubansa ta ce" wannan likitan, baban likita ne da ake takama da shi a garin nan, tun da
na shigo ni banda kame kame da desespoir din dake nuna bai san kan abinda ya hadasawa Sire wannan
rashin lafia ba bana gannin komai,
Yana maimaita ko ya shaki wata iska ne? Ko wani abin?
Yace a kai shi asibiti dan su shiga bincike su ga abinda ya same shi ya hadasa masa haka, binciken da kan
iya daukan awowi domin inji ke bada amsoshin ba mutun ba,

Shiru ta yi kafin ta kara dubansa da idannuwanta da suka ciciko da kwallah cikin wani irin sanyi da murya
mai rawa rawa ta ce" *idan fa ya mutu kafin lokacin?* jinni ne fa ke zuba daga hancinsa *Bashir*

Tsai ya tsayar da idannuwansa cikin nata jin yau na farko kennan da ta taba kiran sunnansa kai tsaye, ashe
ta san sunnan? Ashe ta san sunnansa?
A gaskiya maimakun yannayinta ya saka shi cikin shaukinta sai ya saka shi cikin halin damuwa, shi fa ko
me za.a ce ba za.a iya saka shi yarda da wai Hafsa na haka dan samun yanci bane! Dan haka shima cikin
dakewa ya ce" idan ya mutu, ai lokacinsa ne ya yi, akoy wanda ya isa ya hana shi tafia ne?

Mamaki, tsoro, duka suka daketa tana duban BS yana dubanta ya furta mata haka?
A hankali ta hadiyi yawun dake bakinta dan kadan wanda da shi da babu kusan daya, ta lumshe
idannuwanta hakan ya saka hawayenta zubowa bisan kumatunta,

Wannan karron muryarta ta daga ta ce" na rantse da wanda raina ke hannunsa idan akoy wanda zai fita da
wannan mutumen yau sai dai idan harbe ni zaka yi kafin a fice da shi! Ban ga wani dan adam din da zai
kara nisan kusancina da Malan ba!

Juyawa ta yi da sauri tana kokarin ciro karamar bindigar dake kugunta BS ya yi saurin damko hannunta ya
juyo da ida inda du su Muhammad da docter suka juyo wajen da suke dan kuwa da gaske ta tayar da
kukuma gata tsurut a gabansa

BS na kallonta da takaici ya ce" kin san ba ke daya ke anfani da bindiga a wajen nan ba ko? Kuma kin san
gaba dayanmu manyanki ne ko? Ke ko kunya bakya ji saboda shi zaki yi haka?

Hannunta ta fizge ta ruruko idannuwanta, wato dai masifar ta motsa ta ce" me ya kai kudi daraja a
wajenka? Kai saboda kudi kana iya yin komai ko? A tsaka mai wuya muke daga ni har kai! Ka harbe ni
kawai ka huta da ni, idan ka harbe ni me za.a yi? Ba abinda za.a yi kana iya cewa kan aikinka kake na tare
maka hanya BS!

Hannunta ta kara fuzgewa daidai lokacin Hasana ta shigo domin dai sabon Bodyguard dinma na casan
kokowa da Ni.ima wace sai zuwa lokacin da ta ji kukan Ambulance ake fada mata mijinta ne ba lafia dan
haka ta fito da rigimar sai ta je inda yake
Hasana na shigowa ta kai dubanta wajen BS tana jiran umarnin yanda za.a yi da Hafsat, sai dai ga
mamakinta sai ta ga ya saki hannun na Hafsat din ya barta sai da ta fara tafia wai kamar BS ya sandeta ya
buga mata hannunsa dake mike a bayan keyarta hakan ya hadasa mata zuwa duniyar summa

Bata gama jin tsanar Hafsat ta darsun mata ba sai da ta ga BS ya kinkimeta ya dorata saman kujera mai cin
gurin mutun hudu ya mikar da ita ya gyara mata kwonciya sannan ya mike yana kallon Muhammad dake
jefo masa kausasun tambayoyi kan abinda ke faruwa,

Muryar docter ce ta katse masa hanzarinsa inda ya furta cewa maza a shirya shi a dora shi kan gadon
mararsa lafia a fita da shi a saka shi Ambulance

A lokaci guda BS ya mike ya zuba masu ido su duka ya kalli wannan , ya kalli wancen, ya kalli Hafsat dake
kwonce filat da ita,

Ya shiga rudu, gashi a tsaka mai wuya........

Sai da ya fara tafia ya ce"""

*shin, za.a yarda a fita da Abdul bayan tabas gaskiyar Hafsat ne komai na iya faruwa, dan kuwa ko doctern
kansa ana iya sayensa irin wannan naci na a fita da Abdul? Waye wannan bawan Allah da ya damki hannun
Hafsat? Zai bada taimako ko zai cutar ne? Meye dalilinsa na yin daya cikin biyun? Me ya faru a wajen
daurin auren da Abdul ya tarwatsa? Hafsat, me ke damunta? Idan wannan magani da ta fada na cutarwa ne
fa? Idan aka ki yi masa kuma a je shi din ne magannin da zai bashi taimakon? Ku biyo ni mu je zuwa daga
alkalamin yar mutan Niger........*

Dan Allah ki yi hakuri da rashin yawansa, ina jinyar yar muleka😔😔😔😔

😎😹😹😹😹😹😹

*KUTKALE*

*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE


BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct
NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan
number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA
SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN
SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN,
.....* taku ce, Sajida😍😍😍😍

2️⃣5️⃣

*wannan nvl na kudi ne, idan kin biya kin shiga na roki alfarmar dan girman Allah ba dan ni ba kar ki fitar
min da shi ki yi hakurin har na gama shi sai ki fitar da abinki ki yi yanda kike so da shi bani da matsala da
hakan, dan Allah idan kin san dan fitina, ko dan ki wulakanta min kika shigo ki min magana pc daga ni sai
ke na biya ki kudinki wato naira 200 ta hanyar accnt din ki ko kati, dan alfarmar soyayarku da annabi
muhammad kar ku fitar min da novel, ku bari na gama shi, in sha Allah ba mai tsayin da zai saka ku gajiya
da jira bane👏🏻 na gode*

Sai da ya fara tafia ya nufi wajen gadon da Abdul.ke kwonce kafin ya juyo cikin tsawa ya dubi Hasana ya
ce" zaki je ki saka matarnan ta daina mana ihun batancii a wajen nan ko sai na wanka maki marin da zai
dauke jin ki ne BD?

Da sauri ta kame masa sannan ta juya ta fice dan fitar da Ni.ima a wajen nan

Bayan fitarta tsayuwa ya yi gabansu yana dubansu daya bayan daya,

Shi bai ga wani allamu na rashin gaskiya a tatare da su ba, aman du da haka sai ya ce" bafa za.a shiga
ambulance da shi ba, zan tuka motarsa na kai shi asibitin naku , ku ban kwatance

Muhammad ya dafe kansa cike da takaicin wannan lamari ya ce" wani irin kai zaka kai shi? Kai a wa? Ni
na fi kusanci da shi a wannan lokacin, rayuwarsa ita ta fi min komai mahinmanci , dan me zaka ce kai zaka
fita da shi? Bayan ka ji bayanin likita cewa dole sai an bashi taimakon oxcygene a tsayin tafiarsa?

Kansa ya girgiza ya matso sosai kusan Muhammad ya dube shi ya ce" kai ka san ko waye shi, nima na san
hakan, an bashi horon nitsewa cikin ruwa tsayin minti ashirin tare da rike numfashinsa, ya yi kuma ya ci,
An saka shi a rami an rufe irin na gawa sai dai fa ransa kuma a zaune, sannan ramin mai dan fadi ne aman
ba oxygene, haka yana shakar oxygene dinsa har ya kare a hankali ya silale ya tafi duniyar suma

Kai ka san me da me da me ya gani wanda mu fada mana ne ake cewar idan muna son zama irinsa sai mun
je mun ga wannan rayuwa,
*Mutuwa* ina jin ba yau ba yake gwadata, idan har ya mutu a yanzu a hannuna, toh fa ba wanda ya isa ya
tado shi, aman ba zan yarda a fita da shi a wancen motar mai kuka ba! A matsayin na shugaban masu bashi
tsaro ina da dama da ikon yanda za.a yi da shi, kai harta likitan da zai ganshi ina da damar zaba, dan haka
na yanke hukunci!
Muhammad ya girgiza kansa cike da tashin hankali ya ce" to sai dai idan da ni zamu je, ba zan yarda a yi
wasa da rayuwarsa ba, !

BS ya daga kafadunsa sannan ya juya wajen da Abdul yake, sai da ya saki wani nishi dan walahi a dazuma
da bai idasa fita a hayacinsa ba sqi da suka kama sannan suka iya shigowa da shi, to ina da yanzu da ya
gama ficewa a hayacinsa lumfashi kawai yake ja aman jikinsa du ya mace sai bin mutane yake da ido
kuri .......Abdul an ji jiki.

gannin docter bai ce komai ba ya daka shi janyo gadon mararsa lafian ya kama Abdul ya dora shi da kyar
ya gyara kafafuwansa ya kare masu kallo ya ce" kar wanda ya fito sai nan da minti biyar, Muhammad ka
same ni cikin motar

Shi kam Muhammad bai san me zai ce ba, hankalinsa du ya dagu, kar dai a je likitan nan da ya kirawo mai
cutarwa wa lafiar Abdul ne? To aman ai likitan mahaifin Abdul din ne, wannan shi ya ci gaba da duba lafiar
Ummih wato mahaifiyar Abdul har ta rasu, shi bai san wani likita dabana da zai iya kirawowa Abdul, aman
gashi yana tsaye sai wani abu ke faruwa,
Dubansa ya kai wajen Hafsat dake summe, hakan ya saka shi bufar frijj neman ruwa ya watsa mata ko zata
dawo hayacinta ta fada masa abinda ke faruwa? Gasbi BS ya fice tun tuni, docter kuwa sai duba agogo
yake

BS na fita da gadon nan maimakun ya bi hanyar da zata fitar da shi tsai sai kawai ya juya ya canza hanya ya
shige ta kicin ya tafi,
Ya jima yana ta fama dan hanyar sai da ya yi da gaske gadon ya ratsa domin kuwa dan lungu ne ke raba shi
da hanyar ya shige ya samu ya fitar da gadon ya isa har bakin titi ta wata hanyar daban ba hanyar da kowa
ka iya ganninsa ba sannan ya dakata ya samu ya ciciba Abdul ya riko kafadunsa ya sauke shi a saman
gadon ya dora hannunsa na dama saman kafadarsa ya talabe tsatsonsa sannan ya shiga dan tafia da shi a
haka har ya kawo bakin titin da ya tsayar da taxi ya shige ya umarce shi da fara biyawa islamic kems kafin
yaa sada shi da dan karamin asibiti habo dan uwansa ke yi

Shi dai dan taxi tukinsa ya yi normal, yana gannin yanda BS ke ta faman gyara Abdul, aman bai wani yi
jayaya da hakan ba har ya kai shi bakin kasuwa,

Bs kam da kokari kara ciciba Abdul ya yi ya je ya siyo abin bukatarsa ya dawo cikin motar da shi, sai sakin
nishi yake, haka kuma kafadunsa jinsu yake wani iri, sun kage tun ba.a je ko.ina ba

Tuka shi ya yi ya sada shi da asibitin gwamnati , suna zuwa kudin da BS ya bashi ya bashi mamaki, domin
kuwa a aljihun Abdul na wandon dake jikinsa dan gajere ya laluba cikin sa.a ya samu kudinmu jika goma
goma ya ciri daya ya mikawa dan taxi ya fice ba tare da ya kula da canjinsa da dan taxin ke kokarin bashi
shi dai yana tunanin me Abdul zai yi da kudi ya saka su a kanfai? Kanfai mana har cikin karamin wando?

Sunna shiga BS ya zarce Urgence,


Yana zuwa ya ajiye Abdul nan dandar kasa ya je da sauri wsjen likitocin cikin yannayin hadewar fuska ya
tambayi docter
Kun san halayar manyan, sai sukai kuri sunna kallonsa, wasu har suna kokarin zilewa dan kiran masu
tsaron kofa a fitar da shi dan sam yannayinsa ya basu tsoro, tun bama kansa dake aske tall yake kyali
tamkar wanda ya shirbine shi da man gyada na goma

Ciro baje dinsa ya yi ya mikawa wanda da alama shi ne responsable dinsu yana kokarin karantawa ya shiga
kara masa haske da nuna Abdul da fada masu cewar yana daf da mutuwa!

Da sauri ya mike ya shiga fada masu abubuwan da zasu kawo , shi kuwa ya saka aka kawo gadon asibiti
mutun hudu suka ciciba Abdul suka dora saman gadon aka tura shi aka shiga dakin aiki da shi inda BS ya
kasa ya tsare a cikin dakin, su kuwa suka kasa fitar da shi dan kuwa shima a kan aikinsa yake
Gannin mutumen dan gajere fari na kokarin fara duba Abdul BS ya matso ya ce" bawan Allah bafa kai zaka
duba shi ba, docter nace a kira min

Hannayensa ya dan watsa kafin ya ce" ai ni din ne, ban yi magana bane dan ana iya zuwa nemana dan
cutarwa,

BS ya dubi gaban rigarsa, sai yanzuma ya ga rubutun sunnan mutumen sannan ya ja baya yana jin haushin
tsoro irin na mutumen, to sai me? Idan an zo nemanka ba sai ka kwaci kanka ba?

Du abinda suka san zasu yi sun masa,

Ya kawo hankali, ya dawo daga duniyar suman, aman wata irin juwa yake tamkar zai koma duniyar
summan domin komai kankantar jinni ya fita daga jikin mutun sai ya juyaka bale fa Abdul ya zubar da jinni
sosai, dan kuwa jikinsa ba riga haka BD ya bi duniyar nan da shi gaban kirjinsa du abin jinnin ne, shi kansa
BS din jikinsa ya taba bale kuma Abdul din

Sun shiga rudu, dan har haskawa aka yi aka duba ba.a ga wani lamarin da zai mayar da jijiyar wajenta,

Docten ne ya dubi BS ya ce" daman yana irin wannan abin ne? Me kuke masa ya tsaya? Wani abin ake saka
masa bayan wa.inda muka yi? Ana iya bamu traitement din sai mu yi masa mu ga ko za.a samu galaba

BS ya shiga matsowa gabansa na faduwa da irin abinda zai fadawa Abdul din, yana tsoron hakan ya jaza
masa matsala, eh matsala mana , Abdul dai an fada masa uban gidansa ne, wannan kuma magana ce ake ta
rayuwar Abdul dake cikin hadari😔

Yana zuwa ya zauna sosai kusa da Abdul, hannunsa ya kama ya rike inda Abdul ke binsa da kallo

BS ya sada kansa, sannan ya kuma daga kansa yana jin wani iri, wani tausayin Abdul ne ya ji na lokaci
daya bayan aikinsa da yake yi, hakan ya saka ya juye harshe zuwa yaren Hausa , tsagwaronta hausa ta yan
garin Damagaran,
Hausa ya yi masa ya bashi maganar du abubuwan da Hafsat ta ce,
Yanzu tambayarsa shi ne, yana gannin wannan magana mai mahinmanci ce ? Sannan ta ina za.a saka masa?
Yayanene za.a yi? Shi da ya so ya je a samo rubutu da ake yi, somin ana rubutun hakan, aman kuma ga
abinda Hafsat din ta ce

BS ya kirayi Hafsat da sunnan da ta zo da shi na aiki ne, dan bai san cewa Abdul ya san sunnanta harma
yake kiran sunnan gatsal ba,
Shi dai da ido yake bin Abdul a lokacin da ya nuna masa ruwan zamzam dake cikin gora gangariyarsa da
kuma dabino dake cikin gidansa direct daga saudiya

Baya iya magana, ba zai iya rubutawa ba, dan haka da hannunsa ya yi nuni aka karbo kwanon aikin dake
hannun Nurse din dake tsaye da likitan sunna kallon abinda zasu yi, ba damar su dakatar da su, ko au hana
su, du kuwa irin yanda aka san likitoci da hana magannin hausa, sai dai takarda BS ta saka ba zasu shiga
hurumin nan ba, ba zasu hana ba, dan sunna iya hanawar idan wani abu ya faru sunnansu ya shiga ciki dole
dole.

Da hannunsa, ya iya da kyar motsawa ya yiwa Abdul kwatancen cewa ya zuba ruwan sannan ya saka
dabino a ciki,

Haka ya yi , sai da ya dan jima kadan Abdul ya yi nuni da a zuba masa a hancin

Jim BS ya yi yana duban Abdul, kowa ya sani, irin yanda ruwa a hanci ke gigida mutun, gashi wannan
harda wani abu a ciki kuma da dan yawansa
Gannin Abdul na kara galabaita ya saka BS zuwa ya talafi kansa, bai taba jin wani irin tsoron Allah da son
ambatonsa irin na wannan lokacin ba, sai kace bai taba gannin mutuwa ko gawa ba, yannayin da Abdul ke
kokowa da numfashinsa ya tsoratar da shi, gadhi dai Abdul ya riki sallah, dan baya wasa da sallah, yana
nafila, wace sun sha gani da idannuwansu dan idan suka ji motsi dole su leka, du irin danyen kansa ya
kiyaye wadinnan, ga bautar Allah daga boye, baya sadaka ya shaidawa duniya zai yi, bai taba bayar da
kyauta ya yarda wani ya san shi ne, yana iya yinsa dan gannin ya kare abubuwa da yawa, yana irin wannan
jijiga tamkar mai fitan rai, to ina da shi idan ya fadi rashin lafia? Allah fa zai ce ya kiraya shi marar kunya,
Allah zai nema shi mai mantap alkhairi, sai daga baya zai nemi Allah ko me? (Ka tashi bawa, ka tuba,
domin kuwa baka san zaka kai goben ba? )

Hannunsa na bari, zufa ta wanke masa fuska haka ya samu ya dildilawa Abdul ruwan zamzam din bayan ya
yi bismillah

A hannunsa Abdul ya dage idannuwansa, bakin ya bace sai farin ya sake zuwa duniyar summa ko
mutuwace? Wace ta tsoratar da shi har ya ajiye kan Abdul ya diro ya dora hannyensa saman kai ya shiga kai
kawo cikin tashin hankali.............

..........comment comment commemt


*KUTKALE*

*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct
NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan
number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA
SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN
SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN,
.....* taku ce, Sajida😍😍😍😍
2️⃣6️⃣

*wannan nvl na kudi ne, idan kin biya kin shiga na roki alfarmar dan girman Allah ba dan ni ba kar ki fitar
min da shi ki yi hakurin har na gama shi sai ki fitar da abinki ki yi yanda kike so da shi bani da matsala da
hakan, dan Allah idan kin san dan fitina, ko dan ki wulakanta min kika shigo ki min magana pc daga ni sai
ke na biya ki kudinki wato naira 200 ta hanyar accnt din ki ko kati, dan alfarmar soyayarku da annabi
muhammad kar ku fitar min da novel, ku bari na gama shi, in sha Allah ba mai tsayin da zai saka ku gajiya
da jira bane👏🏻 na gode*

Likita ne ke ta kokarin danna kirjinsa,


Kin dawowar da ya yi ne ya saka fa sauri aka kawo abin dannar kirji

Aka mikawa likita aka matso likid din nan aka goga a sama sannan aka shiga kokarin kara tayar da shi ta
hanyar murza abubuwan nan biyu aka dora saman kirjinsa,

Sai da ya dago baki dayansa sannan ya koma yarab tamkar matace

Wani ihu BS ya saka a fili ya furta" shikenan, ya mutu, mun karasa masu aikin su, mun kashe shi!

Kallon da docter ya yi masa ne ya saka daya daga cikin nurse kokarin fitar da shi yanzu kam, sai dai
tirjewar da ya yi ya sakata sakinsa ya kara dawowa yana kallo za.a dora masa a karo na biyu

Sai da aka kara jonawa aka dora masa,

Wannan karron kam alhamdulilah, yana yin saman da kirjinsa sai ko injin ya shiga bada wani kukan dake
nuni da ya dawo duniyar masu rai,
Da sauri Doctern ya shiga gyagyara du abinda zai gyara nurse na daimaka masa tana bashi du abinda ya
ambaci sunnansa,

A haka suka gama komai sannan du suka tsaya sunna kallonsa,

Nurse di Docter ya umarta da su je, bayan ya cire safar hannun ya rage daga doctet sai BS tsaye kuri sunna
duban Abdull

Ya jima, ya jima sosai, domin a kadan ya dauki minti talatin a wannan yannayin ,
Sai can ya shiga kokarin bude idsanuwansa, sannan bakinsa ya shiga motsawa yana mai adu.ar tashi a barci

Kamar kuma wani hadin baki sai wani bakin jinni bulbul ya bulbulo daga hancin wanda ya sanya Docter
zabura ya nufe shi ya saka abu yana dauke jinnin, inda Abdul ya ringa jin wani sanyi sanyi wani sakayau, a
hankali abinda ya rike gansa da wani irin nauyi da duhu ya ringa barinsa har ya sake shi baki daya,
A hankali ya bude idannuwansa da suka kara girma sukai jajajir ya sauke a kan BS da docter, sai da ya
gama yi masu kallo, sannan ya juya ya shiga bin dakin da yake kwonce da kallo

Shi dai bai ce komai ba, har aka jima sosai domin Docter ya fice da jinnin dan aunawa gannin abinda ya
hadasa masa haka, ya rage daga shi sai BS sun yi shiru su duka ba wanda ya ce wani abu, ba wai dan
muryar Abdul bata dawo ba, aa kawai bin BS da kallo yake yana tunna wasu abubuwan da ya gani da
wanda yake tine, saima suturar dake jikinsa wato daga shi sai gajeran wando

Docter ya jima da fita kafin ya dawo, sai da ya dawo yake tambayar ya shi ko sha wani abu?

BS ya ce" ai bai fara magana ba har yanzu bare na ji abinda yake son ci
Docter ya juya wajen Abdul dake dubansu ya ce " to ka kwatanta masa mana, idan baya magana na san
abin wahalar da ya sha ne kafin muryarsa ta saki,

Matsowa suka yi su duka biyun sunna duban Abdul, nan fa suka shiga kokarin yi masa yaren kurumci
sunna kwatanta masa abin ci ko na sha wane yake so, kuma wani kalla?

Sai da ya kare kalle su baki dayansu sannan ya yi murmushi yana kokarin mikewa zaune

Kama shi suka yi suka zaunar da shi, nan ya dube su kuma, sannan ya ce" bana jin yinwa

A tare suka dubi junnansu, kai dama yana magana ka ce bai fara magana ba? Docter ya tambayi BS

BS kam mamaki ya hana shi magana bale ya baiwa docter amsa, sai kawai ya shiga murmushin shima yana
duban Abdul na kokarin cire allurar dake bashi karin ruwa da kansa,

Docter ne ya ce " aa kar ka cire, wannan na karin ruwaa ne ko zaka ji dadin jikinka

Abdul ya dubi docter da kyau ya ce " likita, ina jin jikina da wani irin karfi walahi, ban jigata ba, hancina
ne ya dan zubar da jinni, ba.a dake ni ba,

Docter kam zuwa wannan lokacin baima san abinda zai cewa bayin Allahn biyu ba,

Abdul ne ya dago yana kallon yanda Docter ke kwonce masa yan abubuwan allurar da ya saka ya sasaka
masa a jiki ya yi kamar ya daure shi ya ce" likita, bana son ana daure ni, du sai na ji na rikice , in dai ba
mutuwa na yi ba, kar a daure ni

Docter kansa kawai ya gyada ya karasa kunce Abdul yana son fada masa sai gobe za.a salame su, domin
yama ta yi an fara kiraye kirayen la.asar sai gannin Abdul ya mike ya yi yana kallon dakin bai ga ko irin
rigar mararsa lafia ba bale ya dauka ya saia

Dubansa ya kai kan BS dake tsaye ya ce" ina rigar asibiti ne??

Docter ya dube shi da kyau kafin ya yi murmushi ya ce" ai oga bamu da shi a nan mu, wannan dakinma
mun tanadeshi dan irinku, ba kowa ake sakawa a ciki ba,

Da mamaki ya dube shi, ya ce" ku su wa? Wace asibiti ce?

BS ya dan zaro ido , kafin ya tari numfashin Doctern ya ce" am, am sire mu je kawai, ga rigata da wandona
bara na je cire sai na je na tsayar da taxi,

Abdul kara zaro ido ya yi, taxi? Taxi fa yace? Me ya hada shi da taxi? Shi ko a saudiya bai shiga taxi ba,
yana kallo BS ke kokarin cire kayansa, bai hana shi ba, dan walahi ba zai yarda ya ratsa gari ba kaya ba,
idan fa ya hadu da wanda ya sani? (Abdul, a taxin? A dazu da ka ratso ko dan kana duniyar summa ne?

Bawan Allah BS haka ya cire kayansa, Allah ya taimake shi, shi wandon na ciki ya kai har gwuwarsa
sannan sakake ne, dan haka da mamaki ya bi Abdul da kallo har ya saka kayansa inda sukai masa wani
kabe kabe rigar ta wani irin tamke shi dan sun masa kadan, wandon kansa ya tsalake masa sosai tamkar dan
izala aman kuma da damamiyar riga,

Ido ido sukai da doctern sannan ya fice ya nemi taxi ya tsayar

Nan fa Abdul ya shiga taxin gidan baya ya hakimce inda BS ya shiga gaba ya fadawa mai taxi cewar sun yi
shata har inda za.a kai su
Shi dai Abdul yana kallon gari, da irin yanda motar ke sama da kasa da shi, da irin yanda suke kutsawa
sunna wani rin gudu, a haka suka zo suka wuce danjar da ta bayar da jar wuta a guje inda Abdul sai da ya
dora hannunsa samman kansa ya leka da kyau ya dubi mai taxi din ya ga ba yaro bane datijo ne sosai aman
yake wannan tukin
Sai,da suka zo danja wace polisai ke tsaye ya ja ya tsaya kafin ya lailayo wata ashar ya dura ya ce" mutanen
banza ido yay masu kuri, ka fice ka janyowa kanka balaki, to ba dai aljihuna ba!

Abdul kam komawa ya yi ya zauna yana mamakin ashe bai ga komai ba? Shi bai taba shiga taxi ba, yana
hawan tsofafin mashin ya shiga wurare masu hatsarin gaske, aman yau gashi a taxi zata kashe shi!

Tafiar da idan a motocinsa nene bai fi su yi minti ashirin ba, sai gasu a minti kusan arba.in

Ko tsayuwar da direban motar zai yi sai da ya wani irin ja ya yi wani kuuuu motar ta fitar fa hayaki sannan
ya tsaya ya fitar da kansa ya ce" ikon Allah, jama.a ku ga ginnin gida tamkar ba za.a mutu ba? Yanzu mai
gidan nan haka zai mutu yana ji yana ganni a nutsa shi a kabari? Han gaskiyar mabaraci da yace a baku a
nan mu a can mu samu

BS tamkar ya mangare mutumen haka yake ji, gashi tsaf sai da Abdul ya gama sauraronsa ya bude ya fita
daga motar yana duban yanda BS ke hararn mutumen, aman cikin ikon Allah sai mutumen ya ce" kai yanzu
bawan Allah shaye shaye ka yi ka tunkaro gidan nan mai zagaye da arnawan sojoji ko rigar kirki baka da ita
, ka dauko wannan shi kuwa da wata riga a dame a jiki tamkar bazawarin kwarto da wani wando ko sauka
kasa bai yi ba yana lumshe ido uwa ya hadiyi jinjirar tinkiya?

Tsayuwa ya yi ya dafe tsatsonsa sai da mutumen ya gama ya shiga kokarin tayar da mota yana mika hannu
BS ya bashi kudinsa motar sai tayar da hayaki take abinta Abdul ya dubi BS da du ya daburce ya kankance
ido ya ce" ni, ni din ne dai bazawarin kwarto? Bama saurayi ba ko *Bashi*?
Ni dai ne mai tsangalalen wando ko? Na gode!

Yana gama fda ya kara gaba abinsa yana tafia da sauri da sauri dan da tazara sosai dan kuwa ta kofar bayan
ya saka a ajiye su , to shi wannan direban da ta gaban kofar ya je yaya kennan?

Wai bama wannan ba, a ina sire ya san sunnansa Bashir? Ita mana! Ya huci ita zata fada masa du
sunnayenmu na gaskiya?
Wata zuciyar ta bashi amsa inda nan da nan ya ji haushi ya turnike shi, nan kuwa datijon nan ya ce" kai
yaro ya haka? Cinye min kudin zaka yi ne ko me? Ka bani kudina ko na fito mu yi wace zamu yi da kai a
wajen nan dan bari gannina tsoho, na fi ka iya shegantaka

BS ya ciro jika goma ya dankawa tsohon yana dubansa ya shiga neman canji, nan ya duko ya ce" bab, ai
duka na baka, ka dan ban adireshinka mana na kawo maka hira?

Tsohon ya dube shi da kyau ya kalli kudin hannunsa, sai kuma ya yi shiru, can ya ce" yanzu yaro, tsakani
da Allah dan ka bani wannan zaka biyo ni ka yi kudin kaina? Kudin kaina mana yaro, da ganninka ai ba.a
ga yannayin mutumen kirki ba ko?

BS kam gannin wannan mutumen komai ma yana iya fada kai tsaye idan ya so kowace wace ya saka shi
saurin dage kafarsa ya bi bayan motar da kallo ya dauki number motar dan walahi sai ya tarda shi ya ci
masa abinda ba za.a fadi ba, gashi kiri kiri zai hada masa masifa da wannan mutumen

Ya jima yana shawagi dan ba zai shiga kai tsaye su hade da Abdul ba, dan kuwa ya ga alamar ya gode din
nan yana iya yi masa komai

Abdul kam na shiga, bai zame ko.ina ba sai dakinsa,

Ya jima cikin ruwa masu dumi, ya lumshe idannuwansa ya afka duniyar tunani,
Waye ta ganni? Yaya sifarsa take? Yaya aka yi ya san da wannan abin da zai same shi? Sihiri ne, wannan
magannin makarin sihiri ne ba na poison ba, ko likita bai ga guba a cikin bakin jinnin da ya fitar,
Waye kuma ya neme shi da sihiri? Wanda ya fadi makarin a gabansa aka yi ko yaya aka yi ya sani har ya
bada makari?

Sai da ya kusan kwashe minti ashirin yana gasa jikinsa, sannan ya wanke jikinsa sosai da sosai ya fito ya
zauna bakin gadonsa,

Dakin ya bi da kallo, daga nan aka fitar da shi ko daga ina? A halin summa, yanzu da ya zama marigayi
kennan?

Murmushi ya yi kafin ya daga kansa sama yana shafar gemun fuskarsa,


Ni.ima, Ni.ima toh wace irin mace ce? Tana ina? Idan tana zayanno irin son da take masa har mamakinta
yake, aman shi baya gannin kulawa irin ta son? Bata taba nuna yi masa girki ba, bata taba idan sun gama
abinda suke ta gyara shinfidarsu ba, ita dai barta da yarinta,
Shi yasa yake zaune da niyar aure aure idan komai ya lafa,
Sai ya auri hudu, ya jera su daki daki, tsala tsala, su ringa yi masa juyi suna kashe masa ido, ya wuni a daki
abinsa (yanzu marar lafiar ne?😳)

Haka ya yi ta zancen zuci, har aka yi kiran magarib nan ya ajiye komai ya mike ya nemi sallah

Bayan sallar magariba, sai a lokacin BS ya nufi ainahin bangaren nasu,


A lokacin da ya karaso Abdul har ya shige daka wanda ya gama zance da Muhammad da mahaifin
Muhammad din a waya

A lokacin da ya hangota tsaye sai da gabansa ya fadi, ita da Hasana ne tsaye a kofar dakin Abdul sai
bodyguard din Ni.ima rigar sojan da ya amsa ya kara ja ya gyara a jikinsa kafin ya karasa inda suke
tsatsaye,

Dubansa ya kai wajen Hasana cikin daurewar fuska ya ce" ki yi abinda na saka ki yanzu, tsalan kwado kai
ka irga mata

Fuska hade ya juya ya nemi dakinsu shi da abokin aikinsa ya watsa ruwa , har zai fito ya tsaya ya dauro
alwallah sannan ya saka wasu kayan ya dauki salayar abokin aikinsa ya shinfida ya hau ya yi tsaye yana
mai kallon alkibla, rabonsa da sallah har ya manta ranar (wa.iyazubillah) , haka ya gabatar da sallar
magariba ya yi nafila sannan ya mike ya fice yana tunanin karbar adu.o.im shiriya👏🏻

Abdul bai nemi sakewa da kowa ba har sai da ya kara kwana biyu ya warware sosai ya kara samun lafia

A yamacin yau ya fito da wandonsa wanda tsayinsa ba zai fi gwuiwarsa ba sai riga mai hannu kananu
fuskarsa dauke da gilashi

A lokacin da ya fito du suka shiga hada hadar shirin fita, inda Hafsat da Hasana suka take masa baya,

Sai da ya fito tsakar gidan ya tsaya ya shaki iskar yamar dake kadawa, sannan ya juya cikin nutsuwa abinsa
ya nufi bangaren ruwan dake gidan inda ruu suka kuma biyo shi su hudu harda BS

A lokacin da ya zo wajen ruwan ya yi tsaye, can ya hango runfarsa ta shanawa, wace a nan yake holewa da
yan matansa,
Kansa ya girgiza yana murmushi ya kai dubansa wajen Hafsat dake kallon yanda ruwan ke garairai da shi
sai daukan hankalinta yake, ya ce" shiga mana,

Ta san da ita yake, ta share shi ta kawar da dubanta daga wajen ruwan

Hakan ya saka shi juyawa ya koma wajen kujera ya zauna, su kuwa suka tsaya a bayansa wato Hafsat da
Hasana
Kaffafiwansa ya daga ya fora saman kujerar sannan ya dago fuskarsa ya tsura mata ido ta cikin gilashi
wanda hakan da ya yi ya saka ta kawar da fuskarta inda hasana kuwa ta kale shi ta kauda kanta dan kar ya
ga ta kura masa ido,

Rigar jikin nasa fara ce mai digo digo blue sannan mai boturai, boturan saman du sun bude har uku hakan
ya saka gashin kirjinsa bayana kadan, harda pecto dinsa na gefen hagu ana iya hanga idan aka kure shi da
kallo

Harshen larabci ya dauko, da sak irin larabcin larabawa wanda idan ba kwarewa ka yi sosai din nan ba ba
zaka gane komai ba ya ce" na yi marmarin gannin gashin kanki kauriyata, ya aka yi kika tsori yafa dan
kwali kamar wace akai maki aure? Ko a summar da na yi kafin na dawo akai maki aure?

Du abinda yake fada tana jinsa, tana kuma biye da dukan kalmominsa, aman yannayin da ta nuna sai ka
rantse da Allah da ba da ita ake ba, koma bata jin yaren da ake yi,

Kansa ya gyada ya ci gaba da fadin" kin san rayuwa ashe abu ce mai mahinmanci? Hafsat Malan ina son na
rayu mai dan tsayi, kin ga na yi aure aure du na masu ciki abina!

Ikon Allah, shi ne abinda ta fada a ranta, ashe dai bai yi sauki ba? Ta kara fada aman kuma bata nuna da ta
san yanai ba koda kuwa ta gane ya kama sunnanta da na malan ne dan ta kula magangannunsa

Abdul dake lure da ita ya ci gaba da fadin" ashe dai kauriyata banda zama kauriya harda magannin karya
sihiri ta samu? To dan kwatanta min sak fuskar macecin nawa mana?

Sai a lokacin Hafsat ta juyo da dubanta ta dube shi da kyau, sak fuskar tata tamkar ta balarabiyar dan
kwalin da ta yane kanta da shi yay mata das masha Allah

Yaren da bata taba yi ya ji ba, wace sai da ya mike zaune da ta fara dan walahi shi baima yarda da ba
yarenta bane wai koya ta yi, wato larabci wace ta saka hasana juyowa itama da mamaki tana kallonta harda
sakin baki, inda hafsat ta gyara tsayuwarta da harshen larabci ta ce" *Rayuwa, lumfashi, shakar iska zan
iya ce maka mun fi jin dadinsu da komai, to ai dole ne Abdul, mutun ba zai san darajarsu ba sai a lokacin da
ciwo ko wani abin ya tunkaro shi, yah Abdul*

Bata damu da irin kallon da suke mata ba ta juyar da kanta, gefe ta kara rage muryarta ta ce " *Abdullah*

Hannayensa ya dora gaba daya ya rungume a kirjinsa yana dubanta yana kuma sauraronta,
Hafsat ta numfasa ta juyo wannan karron ta saka idannuwanta cikin nasa ta dan rage tsayinta tamkar zata
afka saman kujerar da yake zaune ta ce" *Abdel*

Idannuwansa ya lumshe daga kallon cikin idannuwanta yana tunanin me take son fada da mahinmanci
haka? Sai sunnayen da ta kiraye shi da su, wato Abdullah, da kuma Abdel

Katse shi ta yi da fadin" *bayan tafiarta bayan korar ta da kakanin ka suka yi, ta yaya ka samu labarin ta
haihu? Menene tabacinka na namiji ta haifa? Wanda yake yayanka ko yayarka, shin zumunci kake yi da su
ko taimaka masu kake da wani abin? Ka san inda suke a duniya? Ko baka taba nemansu ba? Suna da
bukata ko sun fi karfin hakan? Abdel........ina suke?*

Sai da Abdul ya zauna da kyau saman kujerar da a da kwonce yake yana dubanta,
Idan ya gane tana son sannin wani abu dangance da labarin da ya bata na rayuwarsa cewar yana da dan uwa
ko? Aman me ya sa? Menene dalilinta?

Ya jima da zama, tamkarma ba zai amsata ba, ya kai dubanda wajen su BS dake shawahi sunna aikinsu, ya
kuma duban bakuwar Bodyguard dinsa mai nacin kallo wato Hasana da ta yi kuri so take dole sai ta gane
me suke fada ko meye? Kafin ya maida dubansa wajen Hafsat da ta yi shiru tana kallonsa, kallon fuskarsa
sak take tana sauraronsa dan ta san a yanda ya kasance mutun mai taka tsan tsan ba zai yarda kamar sakarai
ba a yi masa tambaya irin wannan ta fice ba tare da ya bada amsa ko ya ji dalili ba,
Fuskarsa ya hade kafin ya ce""""
*KUTKALE*

*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct
NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan
number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA
SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN
SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN,
.....* taku ce, Sajida😍😍😍😍

2️⃣7️⃣

Fuskarsa ya hade sosai kafin ya ce" wa kike magana kanta?

Hafsat ta sauke lumfashi, ta dube shi da kyau, ta san fa ya gane wanda take nufi aman zai wani tambayeta!
Dan haka ta ce" mai aiki mana

Abdul ya lumshe idannuwansa ya ce" ki ce dai budurwar ubana!

Ido ta zaro tare da dora hannunta saman bakinta tana dubansa, bata san lokacin da ta ce" Abdul!

Idannuwansa ya bude daga lumshen ya kalleta da su kafin ya mike gaba dayansa ya shiga kokarin bin
hanyar cikin gidan
Bayansa suke bi daidai da takun tafiarsa,

Bata gajiya ba a lokacin da zai shiga dakinsa ta yi saurin fadin sunnansa ta hanyar kafe shi da ido

Tsayawa ya yi yana dubanta , ido cikin ido suke kallon juna sai kuma ya yi kasa da idannuwansa ya mayar
wajen lebenta da shi baima san nan ya kurawa ido ba a hankali ya ce " Hafsat, sunna zan raya, kin san bata
jira dai ko?

Da sauri ta rintse idannuwanta sanadiyar kunyar abinda ya fada, gashi ya fada ne da yaren da kowa zai iya
ganewa ga Hasana itama a kusa da su take sosai dan kuwa ita zata shiga ta gyara dakinsa kamar yanda aka
saba,

Juyawa ta yi gaba dayanta ta koma gefe ta tsaya, ta kasa daga idannuwanta bale har ta yi ido hudu da daya a
cikinsu, gaba dayansu kunyarsu ta ji ta mamayeta a haka har bata san lokacin da ya shige ba, sai takun
takalman sarauniya ya shaida mata har ta karaso,

A hankali ta dago da dubanta ta sauke saman Ni.ima,.ta sha wani danyen lesh mai ruwan madara, ta sha
kwaliya fuskarta tamkar ka saceta ka gudu,
Ni.ima ba ramama bace, sam bata da rama, sannan ba sakaken jiki ne da ita ba gashi ya hadu da kulawa dan
akoyta kwaliya sosai, budurwa ce mai zamani wace dubai ke son malaka a wannan karni

Yannayin takunta ke tafiar da isarta, Ni.ima ta jiki, jika irin ta naira, dan kuwa bata nema ta rasa ba, ga
kuma daidai gwargwado iyayenta sun bata tarbiya, so ne kawai ya sakata sangarta da shiga sabgar Abdul

Kanta ta sada dan kuwa du macen dake wajen a tsaye sai da Ni.ima ta kwasheta da kallo ta yarfata kasa da
idannuwanta sannan ta tsayar da masu bin bayanta da hannunta ta juya ta buda dakin Abdul ta shige abinta
ba tare da damuwar komai ba a fuskarta

Tana shiga gabanta ya fadi, dan kuwa ta san abinda ya kawota dakin, wai ita, yaushe zai zauna ya yi hira da
ita irin na soyaya? Yaushe xai dubeta da duba na darajanta dan adam a matsayinta na matarsa?

Inda yake zaune ta je, tana zuwa ta haye saman cinyarsa ta zauna tana kallon yanda yake lunshe ido

Abdul dake binta da kallo ta kasan idannuwansa ya saka hannayensa ya janyota a hankali jikinsa sosai
sannan ya shiga kokarin sarafata dan samun nutsuwar damuwar dake damunsa

Binsa kawai take, du yanda ya jirgata sai ta bi ba tare da ta nuna wani yannayi na shauki ko murafin hakan
ba,
Tun yana yi da nuni a yannayinsa na muradin gannin shaukinta har ya cire a ransa ya shiga kokarin zuwa
duniyar ma.aurata

Da sauri ta rike damtsen hannunsa wanda du girman hannunta sai ya kasance ko rabin damtsen bata cika ba
bale har ta cike wajen da hannun nata,
Muryarta na rawa ta ce" ka...ka bari na birgeka mana?
Yakan ce da ita birge ni, a duk ranar da baya son zuwa waje mai kakant din , takan yi ta fama kafin ta samu
ya samu kansa, har bata son yace da ita ta birge shi dan haushi take ji lamarin na wahalar da ita, sai gashi
yanzu da kanta ta nemi ta birge shi?

Tsai ya yi da niyar shigar nata ya tsurawa yannayinta ido,


Tabas bata cikin ra.ayin hakan, sam babu muradin hakan a tatare da ita,
Aman rabonsa da ita fa yau 2 days, shi ne batama daukinsa?

A hankali ya janye hannayensa ya rage nauyinsa a jikinta sannan ya mike gaba dayansa,

Maimakun ta ga ya juyo ya bata damar birge shin sai ta ga ya nufi bayi


Da sauri ta mike zaune tana raraba ido, gabanta ne ke ta faduwa lokaci guda kuma ta ji wani haushin kanta
wanda har ya hadasa mata zubar da hawaye, ya salam, ya yi fushi? Fushi ya yi ko me?

Nan take zaune tana ta sharar hawaye har Abdul ya fito da tawul yana goge jikinsa

Turus ya ja ya tsaya da mamaki yana kallonta tana kuka,


Yana son ya budi baki ya tambayeta abinda ke damunta aman bai san me yasa yake da nauyin baki a kan
lamarin mata ba, shi dai zai maki surutu ne idan ya yi niyar dizga ki, shi banda Kauriyama wace mace ce
yake sakewa ya yi ta surutu da ita?

Kallonta da yake ya sakata mikewa gaba dayanta ta nufo inda yake tsaye ta mika hannu zata taba shi ta ce"
dan Allah ka yi hakuri kar ka yi fuahi da ni

Abdul ya dan ja baya yana dubanta kafin ya fahimci inda ta nufa,

Wajen ajiye tawul din ya nufa ya sarkafe shi ya juyo inda take tsaye ya ce" bana takurawa mace dan zuwa
duniyarnan, ina son koda yaushe duniyar nan ta zama a kawace, ba fushi na yi ba, ki saka kayanki kinje ki
tsaftace jikinki

Yana gama fada ya bude wajen suturunsa ya kurawa wajen ido,


Kaya ne kala daban daban, na manyan manyan kudade sannan masu kyan gaske,
Du a cikinsu ya janyo wata riga fara ya zura ba tare da ya saka komai ba ya dawo saman bed din ya zauna,
Har ta fice a dakin, da kuma kuka ta fita,
Bakinsa ya tabe yana mai kallon wajen windows din da ba damar ya shaki iskan wajen an rufe ruf

Karamar wayarsa ya mika hannu ya dauko ya kunnata,

Kara wayar ya yi a kunnensa bayan ya danna kira a wata bakuwar number

Bai jima yana wayar ba ya ajiye ya mike ya shiga shiryawa sannan ya saka akaiwa masu tsaron kofa
maganar zai yi bako a bar shi ya shigo

A lokacin da bakon ya zo , Abdul ya nemi Hafsat da ta shigo wajen da zai gana da bakonsa dan ta kula da
lafiarsa,

Bakon wani mutun ne da ba za.a kiraye shi yaro ba, magidanci ne ya kwana biyu sosai sai dai ba tsoho
bane,

Irin mutanen nan ne wayayu, masu shegen wayo da son da bakinsu su sayi du wani gara,
Suna siyen kuwa dan idan ka yi wasa lokacin da zasu tafi da kai kai kanka sai ka laluba ka ga babu kai

Tunda ya zauna suka gaisa Hafsat ke tsaye gefe tana aikinta ba tare da ta bada hankalinta kansu ba

Tambayar da Abdul ya jefa masa ne ya sakata maido hankalinta inda suke zaune ta raja.a dukan wani
nutsuwarta a kansu da rataunawar tasu, sannan sai a lokacin ta gane ya saka ta shigo ne dan wannan dalilin

Mutumen ne ya dago hannunsa na dama ya shafi gaban goshinsa kafin ya maida hannuj bayan keyarsa ya
dan sosa sau biyu ya ce" eh Elhaj, tabas marabina da su na ga dan nata , sosai saurayi ne kakarfa sai dai
sam baya kama da kai, kuma shi fari ne,

Abdul dake kallonsa ya ce" kuma yaya sunnansa ne? Yanzu a ina suke ne? Ko nace marabinka da su a ina?

Dan zakutowa mutumen ya yi ya saka hannayensa ya ja rigarsa ta kara yin sama hakan ya baiwa dogon
wandon rigar damar kara bayanuwa,
Agogon hannunsa ya murza da babar yatsarsa, ya zagaye ya kuma zagayewa, sai da ya rintse ido na
sakonni sannan ya budi baki ya shiga bada labarin marabinsa da matar da kakaninsa suka koreta da cikin
mahaifinsa, wanda ya tabatar masa cewa namiji ta haifa harma ya ga mutumen da idannuwansa, ya tabatar
masa cewa makudan kudadan da kakaninsa suka bata dan ta kula da rayuwar dan da zata haifa sun isheta
rayuwa suna cikin wadata suna rayuwa cikin jin dadi,

Abdul ya sauke kafa daya daga saman cinyarsa ya ce" ta musulunta ne?

Sai da ya kurawa Abdul ido sannan ya ce" ae, eh eh mana Elhaj ta musulunta mana,

Abdul ya gyada kansa, kafin ya maida dubansa wajen Hafsat ya ga kawai mutumen take kallo da sexy eys
dinta,
Komawa ya yi ya jingina da jikin kujerar ya ce" wane da wane kika yarda a cikin magangannun nan?

Hafsat da ta yi firgigit ta maida dubanta wajen Abdul, ta kasa cewa komai, dan ita dai ba sannin mutumen
ta yi ba, duda yannayinsa na nuni da rashin gaskiya da son dole dole sai ya yi cinvaincre din Abdul din, ba
zata iya cewa komai a kan hakan ba,

Abdul ya lumshe idannuwansa ya ce" wato idab mutun baya son gannin abu a zahiri ba zai gansa ba?

Mutumen ne ya ce" Elhaj ban gane inda ka nufa ba

Abdul ya bude idannuwansa aman bai basu damar budewa baki daya ba ya ce" karya kake min Murtala,
gaba daya magangannun nan da ka fada ba daya dake gaskiya,
Kai hasalima baka ga wannan matar ba, dan kuwa da ka ganta da ba zaka ce ta musulunta ba dan can dama
musulmar ce

Saukin mikewa tsaye ya yi yana zarar ido, hakan ya bashi damar tsayawa kerere gaban Abdul

Ya buda baki zai yi magana sai jinsa ya yi an dangwarar da shi zaune saman kujerar da ya miken,
Mamaki ne ya kama shi gannin yar budurwar an ce ta mayar da shi haka da zafi sannan ta yi tsaye a
gabansa wanda yannayin kyakyawar fuskarta da ya nuna hadewa sam ba alamar annuri ya saka shi jin
gabansa ya fadi,

Abdul dake zaune a hankali ya bi hannun Hafsat da ta saka ta mayar da Murtala zaune da kallo,
Wandon dake jikinta ne ya kuma bi da kallo , ya dameta sai dai na roba ne hakan ya saka take motsawa son
ranta aman du wata halita mai rawa ko mai motsi a wajen tana iya mitsawa in dai Hafsat din ta motsa,
Sannan rigar dake jikinta mai siririn hannaye ce, dan kuwa tun harbin da akai mata ta daina saka mai dogon
hannu ko fita zasu yi dan hannun ya warke kar ya danyace
Rigar ta yi mata caras a jikinta, kanta da dan karamin dan kwali baki sidik wanda ta yane kan da shi,
fuskarta ba ko digon kwali aman lebenta haka yake jan idon wanda ya kale shi dan tamkar ta goga masa jan
baki ne

Lebensa ya hade gaba daya sannan ya tabe bakinsa yana kallonta, irin tsayuwar da ta yi a kan Murtala,

Kansa ya girgiza sannan ya mike tsaye,


Hannunsa ya saka ya mayar da ita gefe hakan ya saka ta zama yar tsuwat a gefensa tana huci dan neman
fadan dama take

Abdul sai da ya daura agogon hannunsa da kyau sannan ba zato ba zamani ya saka hannunsa na dama ya
dago wuyan Murtala ya ja shi ta wajen kujerar hakan ya saka wandon dake rige da kugunsa janyewa dan
kuwa arzunzumi ne harka da yan gayu bai wani daure shi da kyau ba,
Kiiii ya ja shi sai da ya dangana shi da bangon dakin sannan ya saka dayan hannun nasa ya daga shi gaba
daya ya raba shi da dandar kasa ya rike masa wuya sosai yana dubanda ido cikin ido ya ce" yaushe na zama
bolar da har zaka daga muryarka a kan tawa? Bayan karya da cin amanar har raini zai shiga tsakanina da
kai? Ka manta a gidan iskancin da na hadu da kai a irin halin da kuka hadu? Ko dan kana tunanin kai lauya
ne sannan ka girme ni zaka raina ni?

Murtala dake harhaba kafafuwansa dan neman a sake shi, du idannuwansa sun ruruko yana ta kokarin yin
magana a hakan ko zai sake shi sai rike hannayensa yake aman Abdul ya kasa sakinsa sai kara matsar masa
wuya yake

Da sauri Hafsat ta matso ta tsaya ta ce" Abdul, ka sake shi, kar ka kashe shi Abdul👏🏻

Idan ya kulata to lale dakin ya amsata,


Gannin yana neman yin kisa ya sakata dan kokari matsawa ta saka hannayenta dan kwaljwace wuyan
Murtalan a hannun Abdul

Hannayen nata ya yarfe da hannunsa na hagu, bai saki murtalan ba ya hankadata da hannun nasa hakan ya
saka ta yi tagal tagal ta hadu da kujerar wajen ta ja ta tsaya tana sauke ajiyar zuciya kafin ta tsinci muryarsa
a kausashe ya ce" *Ke, bilahilazi kika yarda kika kara taba wannan jemagen sai na karya maki wuya!*

Yana gama fadi ya sake shi nan ya fadi yana kakarin tari , shi kuwa ya duka ya lalubi wayoyinsa ya juya da
su ya fice ya nufi dakinsa ya rarumi computernsa ya zauna ya jona wayar ya shiga aiki yana mai jin shi
bashi da abinda zai iya yiwa wannan mutumen ya huce sai dai idan zai kwakule masa idannu ne ya soye ya
huta!

Hafsat kam sai da ta sha jinnin jikinta a lokacin da ta ga ya nufo kamar ita zai damka , sai kuma ta ga ya
fice a dakin,

Ajiyar zuciya ta sauke a fili ta zabgawa hanyar harara a ranta kuwa ta ce" dama na bari ya hayeka a
mikewar da ya yi dazun, ni na ga jaraba! Malan ana kare ka kana hana mutun aikinsa!

Juyawa ta yi ta fice a dakin ba tare da ta kuma bi ta kan Murtala dake yashe a nan ba ta fice gaba dayanta ta
zagaya wajen sojojin dake gadin bayan gidan ta samu daya ta amshi aron mashin dinsa ta haye ta harba titi

Gudu take tamkar ba zata karasa inda ta nufa ba,


A haka man mashin dinta ya kare ta tsaya ta zuba harma ta yi guzurin wani, sannan ta dauki wayar da ta
gama bincike ta kare a sunnan wani gagarumin malamin islamiya dake raye a kauyen garin Minna din,
wanda ke rayuwa daga shi sai almajiransa, aman kuma mutumen har ya iya hawa social media, ba komai ya
ja hanlalinta yau tsayun kwana biyar a kansa ba sai sunnansa,

Sunnansa *Muhammad bine Abdul Basid Abdallah*

Ta zama wata irin mutun ce mai kurmuwa dukan wani abinda zai bata damar samun gaskiyar abinda ke
boye a tatare da Abdul, ba ruwanta da me zata tarar? Waye shi mutumen? Burinta ya kasance shi ne!

A lokacin da ta shiga cikin jejin, a bakin wata rijiya ta ga mutun zaune yana rubutun allo,

Babur din ta tsayar tana son saka jak ta ajiye mashin din mutumen ya dago da kansa daga saman allon
karfen da yake rubutu samansa

A tare gabansu ya yanke ya fadi, a wannan lokacin a wannan wajen ya mike ya durfafa cikin jejin wanda
kafin hafsat ta sauka a mashin din tuni ya bace mata bat ta nema ta laluba kamar ta yi hauka ba shi ba
alamarsa

Wajen allon ta je ta tsugunna ta dauki allon da tawadar,


Yatsarta ta saka ta lashi tadawar, ta daga idannuwanta ta kai wajen rijiyar,
Ba komai ake rubutawa a jikin allon ba sai astagafari,
Mutumen ba wani yaro ba aman irin yanda lokaci daya ya bace mata ya tsoratar da ita
*Wannan mutumen shi ne ya damki hannunta a wajen daurin auren dan minister da yar Elhaj,*

Ta shiga rudu, waye shi? Ko shi ne mai wannan sunna? Me ya sa a page din da yake yawan rubutu baya
saka komai sai jawabi da gargadi a kan zina? gashi dare na kokarin yi mata a jejin da ta daina gannin ko
wulgawar tsuntsu ne bare na mutun.

Zuciyarta na son gaskata mata hasashenta, runguntsumin tashin hankalin Abdul na ture komai,

Idan haka ta kasance ina zai shiga da ransa?

*Wai wa ke neman ranka Ya Abdel?* hafsat ta mike ta kuga haka wanda gaba daya sai da wajen ya amsa
da amon muryarta ......

Allon nan ta dauke ta juya wajen mashin din tana kokarin hawa ta tayar ta hang...........

Comment , comment, comment


*KUTKALE*

*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct
NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan
number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA
SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN
SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN,
.....* taku ce, Sajida😍😍😍😍
2️⃣8️⃣

Tana kokarin tayar da mashin din ta hango wani irin mutun,


Mutun ne zabaya namiji kuma wada ,
Kai ba dan ba dan ba sai tace ko ta yi gamo ne? Dan kuwa mutumen tsayawa ya yi yana kallonta kamar ya
ga bakuwar halita

Adu.a ta yi sosai ta tofa masa yana kallonta tana kallonsa,


Gannin ya ki motsawa ya kuma kin yi mata magana ya sakata saukowa a hankali ta nufe shi inda gabanta
ke luguden kida

Tsayawa ta yi dan nesa da shi ta yi salama,

Ga mamakinta sai ta ga ya matso kusa da ita sosai

Sai da ya daga kansa ya kaleta domin ya matso kusa da ita kafin cikin muryarsa dake nuni da
manyantakarsa ya ce" ke kuwa, kin ari musulunci ne ko musulmar ce ke?

Kanta ta sada dan kallonsa da kyau itama kafin ta ce" kama gare su ne musulmai ko salamana ne bai cika
ba?

Kansa ya gyada kafin ya juya da niyar tafiyarsa ,


Gane hakan da ta yi ya sakata matsawa da sauri ta ce" dan Allah, ka taimake ni, ina son sannin waye
Muhammad bine Abdul Basid Abdallah? Ko zaka iya kai ni inda yake?

Sai da ya kare mata kallo sannan ya ce" ki je dare ya yi, ki dawo zan kai ki wajensa, aman yanzu akoy nisa
ga kuma dare

Ta so ta yi magiya ko zai saurareta, sai dai gannin bashi da niyar hakan ya saka ta juyawa ta hau mashin din
ta tayar ta dauki hanya wanda a lokacin tuni isha ta kawo kai, a kadan zata iya kaiwa awa uku ko zata isa

Gudu kawai take yi, gashi a lokacin da zata bar gidan Abdul sai da ta ajiye du wani abin aikinta da zai bada
damar a san inda ta nufa, ta tabata yanzu an farga da bata nan, fatanta kar ta kai BS bango ya dauki mataki
a kanta ya kawar da wani gudun bacin ranta ya saba mata!

Ta jima, ba karamar wahala ta sha a hanyar ba kafin ta karasa anguwar, a haka har ta karasa kofar gidan

Tun daga irin kallon da sojojin ke binta da shi ta dan sha Jinnin jikinta, sai dai bata saka komai a ranta ba ta
samu ta shigar da mashin din ta karamar kofar sannan ta sauka ta shiga tura shi ta ci uwar tafia kafin ta
karasa farfajiyar gidan

Dare ne, aman ko.ina ya dauka da hasken fitila , hakan ya saka du wani mai motsi ana iya ganninsa da
dukan abinda ke tare da shi

Tun da ta shigo gabanta ya yanke ya fadi, dan kuwa du wani bodyguard da ya kwana ya tashi a gidan yana
tsaye cirko cirko , BS sai doka waya yake haka kuma sai duba agogo yake, gefe kuwa Abdul ne tsaye
hannayensa cikin aljihun wandonsa ya zubawa hanyar da ta fito ido
Turus ta yi da babur din gannin yanda BS ya nufo inda take tsaye gadan gadan ta tsura masa ido sannan ta
sadakar cewa idan ya zo yana iya dauketa da mari

BS na karasowa hannunta dake rike da mashin din ya damka yana dubanta ya ce " ina kika je? Ke da wa
kuka je? Me kika je yi? Bakya tsoron wata fitina ta same ki?

Idannuwanta ta kikifta tana kallonsa,


A hankali ya sasauta damkar da ya yiwa hannunta ya rage ihun muryarsa ya ce" baki damu da damuwata
ba? Ya dace ki damu da aikin ki, dan wanda ya dauke mu ya san takun mu

Yawun bakinta ta hadiye a lokaci guda kuma ta dan leka bayansa,


Ido hudu suka yi da Abdul sannan ya juya ya shige ciki ba tare da ya ce da kowa komai ba

Sai a lokacin ta jinginar da mashin din dake kauri ta ce" BS, ka yi hakuri, na gaji da zaman waje dayan ne,
shi yasa na fita na sha iska

Hasana dake tsaye ido ta zaro tare da fadin" me? Ke kina da hankali kuwa? Ke Bodyguard har wani
lokacinki gare ki bale muradinki? Ki dubi idannuwan mutane ki ce wai kin tafi shan iska? Ba laifi, tunda
kin shawo iska sai ki zo ki zagaye balbalin gidan nan sau hamsin!

A tare suka dubeta, daga BS har Hafsat,

Hafsat kam dukawa ta yi ta kara gyara takalmanta sau ciki sannan ta cira da gudu da daren nan ga tarin
gajiya , ga yinwa, ga bukatar yin wanka ta shiga gudun punishment domin kuwa Hasana dai ta isa ta sakata
ko ta hanata a bangaren aikinta dan gaba take da ita ya zama wajibi ta yi mata biyaya

Hannun Hasana ya damka ya juya da ita da wani irin karfi ya hankadata gefe inda ba za.a iya hangosu ko a
ji maganarsu ba ya ce" ke a wa zaki shiga hurumin da ba.a saka ki ba? Ina ruwanki da amsar da ta bani? Ke
idan a halayanki zan bi ki kina tunanin zan bar ki ki numfasa ne?

Bayanta da ya buga da bango ta dafe kafin ta ce" BS , saboda na hora yarinyar dake kokarin rainaka a
gabana ne kake wulakanta ni haka? Menene tsakaninka da ita? Wacece ita? Me ya sa na ga du kuna wani
rawar kai a gabanta? Idan tana zagayawa da wancen da muke yiwa aiki kaima kwoncin kake da ita ko?

Cikin daga murya ya ce" ki rufe min baki da fadin magangannun da ba tsari a nan,
Kin ga yarinyar can da kika raina? Ni ita nake so, kuma ki daina kokarin zaginta dan ko daya , ba irinki
bace, yanda take jana a kas ya saka nake kara mutuwa kanta, ta san ina sonta, har yanzu ta kasa so na, dan
haka ki girmamata kar ki yarda ki mayar da ita abokiyar gabanki , dan na rantse maki ta ishe ki tuwo da
miya

Sosai magangannun nan sukai mata zafi, tana dafe da bayanta ta ce" aman ka san da ni kake soyaya ko?
Kuma ka san aikinka ya haramta maka soyaya da dalibar da ba.a yaye ba ko?

Sai da ya shafa gaban goshinsa da sankon kansa sannan ya ce" to ki tona, ke bari ki ji, abinda zai hana ni
samunta daya ne, idan ta ce da ni Bashir ka barni haka, bana son ka!

Yana gama fada ya juya ya fice ya tsaya can gefe yana hangen yanda Hafsat ke gudu tana raba hanya,
Kwarai yana da damar hanawa, ya isa ya hana dan shima yana matsayin gaban Hasana, sai dai ba zai shiga
ba ko dan ya kori tsargi sannan ya rike girmansa a wajen yarensa, tausayinta yake ji, kaunarta yake yi, ji
yake dama zai karbar mata gudun!
Abdul dake tsaye kusan windows din dakin Muhammad ya rike dan labulen ya tsura mata ido yanda take
gudu, Muhammad na yi masa magana shi walahi kwata kwatama bai san me yake cewa ba, a haka ya juyo
ya ce" *daga ina take?*

Muhammad dake dana waya yana nuna masa sabuwar motar da kanfanin Helix suka kera wace ke da
tsananin tsada ya dago yana dubansa
Sai da ya matso inda yake tsaye ya ce" wa kake tambayar inda ta je?

Sai a lokacin Abdul ya farka, tamkar an dan tsikare shi ya dubi Muhammad da kyau, sai kuma ya shiga
takawa ya ce " ina zuwa.......

A wannan dare haka kowa ya yi barci zuciyarsa a cinkushe, tun daga Abdul, Ni.ima, Hafsat, BS , Hasana,
da du wani ikon dake gidan wanda sanadiyar rashin gannin Hafsat da tabatar masa cewar ta fita a mashin ya
saka tayar masu da hankali da rantsuwar su saurari du irin abinda zai sameta walahi da hannunsa zai masu!
Hakan ya saka du suka firgice suna masu jin haushin juna da jin haushin wanda ya ara mata mashin din

Ko da safe ba wanda ya shiga sabgar wani, kowa bakin aikinsa yake tun safe har yama,

Ko da yama ta yi , yauma fitowar ya yi , sai dai yau wani bakin yadi sidik ne ya saka ya fito ya nufi wajen
shakatarwarsa

A lokacin da ya zauna ya mike kafarsa ya kali BS dake kai kawo ya ce" ka ce da dayar nan ta fita can baya
ku kuwa ku zo kai da wancen ina son gannin ku

A nunin da ya yi, yana nufin a cewa Hasana ta fita, su kuwa ya nuna su zo saman kujerar dake kusa da shi
yana son gannin su

Abinda ya bukata BS ya aiwatar, inda suka zauna a kujerar dake gabansa su duka suna kallon yanda ya
tsura masu ido ya kalli wannan ya kalli wancen

Sai da Abdul ya gama kallon su sannan ya ce" *wai ku yaushe kuke zance ne? Wace irin soyaya ce kuke
haka bakwa bata kulawa? To yau ku yi zance!*

Sai da suka kalli junna sannan suka kale shi a tare tamkar hadin baki,
BS ya dan gyara zamansa yana kallon Abdul,

Abdul ya girgiza kai ya ce" kai yanzu, katoto da kai, kake jin tsoron wannan yar yarinyar? Bashir maza ka
rako duniya ko me? Ka fito kace da Hafsat cewa kana son ta aman sai ka ringa hauka har kowa ya gane
kana sonta ita ka kasa fada mata kiri kiri?

Sai da BS ya mike tsaye, sai kuma ya koma ya zauna tamkar an dangwarar da shi yana zare ido yana kallon
yanda Abdul ke kada kafarsa dake wanke tas tamkar a side,
A haka ya bi shi da kallo har fuskarsa, kai shi ko a lakuru bai ga kwalon dan duniya irin Abdul ba,

Dubansa ya maida wajen Hafsat ya ga ta tabe bakinta ta dafe gaban goshinta, kuma abinda ya bashi
mamaki bai ji ta yiwa Abdul ihun kar ya yarda ya kama sunnanta sunnan mahaifiyar malan ce, ohk wato sai
su da aka raina ko?

Katse masa tunaninsa ta yi ta hanyar fadin" *ABDUL*

idannuwansa ya dauke daga duban gefen da yake , ya saka cikin idannuwanta har da takabe kumatunsa
yana kallon yanda ta kankance idannuwanta wai kennan zata yi jaraba ko?
Dubansa ya kai wajen BS ya ce" Bashir, ko jaraba zata yi kyau take mata, bara ka ga yanzu ta ce" Abdul,
menene haka? Ka bar mu mu koma bakin aikin mu....
Sai ta wurgan harara, sai ta mike ta tabe baki kuncinta ya lotsa , sai ta koma bayana ta yi tsaye ta hade rai
dan Hafsat bata son raini!
Kallon junna suka kuma yi ,
Nan Hafsat ta lumshe idannuwanta tana son tunanin girman rainin hankalin Abdul,
Sai dai bai bata wannan damar ba ya katse mata tunani da fadin" kina tunanin zan baiwa soja mashin na
kasa saka masa abinda zai nunan inda yake shiga?
Hafsat me kika je yi cikin jejin da ba wani mahaluki dake rayuwa a cikinsa a sanina? Kina son na saka
maki ido a motsinki ne?

Shiru ya yi, kafin ya ci gaba da fadin" BS nah? Ka tambayi wajen wanda ta je dan ba zan lamunci hakan
ba!

Mikewa ya yi ya mayar da bakin gilas dinsa ya juya da niyar tafia,


Sai dai sunnan da Hafsat ta ambata ya kusan tainke masa lumfashi,

Wani irin ja ya yi ya tsaya sannan ya juyo a haukace ya.......


*KUTKALE*

*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct
NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan
number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA
SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN
SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN,
.....* taku ce, Sajida😍😍😍😍

2️⃣9️⃣
A haukace Abdul ya dawo gaban Hafsat, gaba daya ya kai gwuiwiyinsa kasa ya zubasu
Bai san lokacin da ya saka hannayensa ya damki hannayenta ba kafin ya ce" kin ganshi? Hafsat ke kin
yarda cewar yana raye? Hafsat, kin yarda da maganana kennan? Ke bakya ja da hakan ne?

Hafsat dake kallonsa wani tausayinsa ne ta ji a ranta,


A hankali ta zame hannayenta ta ce" Abdul, me kake nufi? Wa ke raye? Abdul, hatsarin jirgin sama fa,
kuma dubai sun shaida ya shiga, Abdul dan me ba zaka daina maganar cewa yana raye ba?

Hannunta na dama ya yarfe yana kallon yanda idannuwanta suka cicika da hawaye ya ce" a lokacin da
muke magana irin ta fahimta da shi ya taba ce min" Abdallah, du ranar da halin rayuwa zai sakani canza
sunna, ba sunna na zan canza ba , sai dai na jirga sunana,

Juyowa ya yi ya dubeta ya ce" *MUHAMMAD BINE ABDUL BASID ABDALLAH*


Hafsat, sunnan kakana ne Muhammad,
Abdallah sunana ne,
Hafsat,

Mikewa Hafsat ta yi da sauri ta juya ta bar wajen,


Abdulma bin bayanta ya yi yana kugin kiran sunnanta aman har ta shige ciki, hakan ya saka shi shigewa
cikin dakin nata kai tsaye

Tsugune ya ganta ta hada kanta da gwuiwarta tana rizgar kuka,

Wajenta ya karasa ya tsuguna infa take tsugunen ya rike damatsunnan hannayenta ya ce" kuka kuma?
Kukan me kike? Me ya taba zuciyarki? Hafsat, maimakun ki tsaya ki bani haske a kan gannin macuci kuma
azalumin mutumen da yake neman rayuwana shine sai ki gudu ki shiga kuka ? Ni ya dace na zubar da
hawaye Hafsat, da zan samu kuka, walahi da na rusa, da zan samu kuka, ni kam da na rera, ki dube ni,
waye ni? Banza ne dan fasiki Hafsat!

Abdelah,
Hafsat ta fada da wata irin murya mai fitar da numfashi hadi da kuka,
Hannunsa ta saka hannunta ta riko ta ce" Abdellah,
*zato zunubi ne,....koda ya kasance gaskiya ne*

*Abdul, jinni, mahaifinka Ya haifeka, ya maka sunna, ya tarbiyantar da kai, ya baka ci sha sutura muhali,
ya baka sunnansa kake anfani da shi, ya daure maka, ya tare maka, ya tsare maka, Wani irin rudin duniya ,
ko zigar shaidan ne zai saka shi neman rayuwarka?*

Abdul ya kankance idannuwansa yana dubanta ya ce" ashe baki da hankali? Ashe duban mai nazari ne nake
maki ke baki kai can ba? Baki san a duniya babu halitar dake tafe da hadari mai tare da guba irin dan adam
ba? Wai dan Adam din zaki yiwa shaida? Shi kuwa keda abubuwan da zai kashe ni, kin manta wace irin
rayuwa ya yi gaban iyayensa? Rana tsaka ya mayar da dukiyarsa a sunana komai da komai, *KUDI
HAFSAT?* ai masifa ne, kudi dauda ne, kan su yana iya halaka ni,
Baya cutar da gudan jinninsa ya ringa kwonciya da yar da ya haifa?

Da sauri Hafsat ta saka hannunta wajen bakinsa ta rufe tana girgiza masa,
Hannunsa ya saka ya cire nata ya watsa mata idannuwansa da sukai jajajir ya ce" ko a lahira kar Allah ya
tsaida ni gabansa, dan ba zan maki rantsuwa ba, aman idan ana iya cakumar mutun sai na shaki kwalarsa!

Abdul Mahaifinka ne fa!


Sai me Hafsat? Na ce sai me? Ubana ne, kuma na tsane shi, idan bai mutu ba, ya shiga uku, dan yanda yake
bibiyata sai na bibiye shi!, ko a cikin kaya sai na shiga na mamana masa ita a jikinsa, Hafsat sai na hana shi
zaman lafia har mu hadiye zuciya mu mutu mu duka!

Hafsat kam gaba daya abin ya girmami tunaninta, tsana, muguwar tsana Abdul ke yiwa mahaifinsa, wanda
take tunanin har ta kwadaitawa kanta idan har za.a samu sasauci ko itama iyayenta zasu dubeta?

A hankali bata saki hannun nasa ba ta ce" Abdul, zuciya mugun nama ce mai saka dan adam ya yi ta tafia
har sai ta kai shi ga halaka,
Gagawar yanke hukunci baya haifar da komai sai dana sani,
Tafia cikin zargi, halaka me Abdul,
*Ya Abdul Jabar* baka son kaima ka haihu yayanka su yi maka biyaya?
Shi Abdellah, idan har ka samu yaron da ya yi maka irin haka yaya zaka ji? Komai girman laifin
mahaifinka baka isa ka hukuntashi ba Abdul, kai zaka ji dadin zaman duniya idan kana hamaya da d'an
cikin ka?

Abdul ya lumshe idannuwansa yana kallon yanda yarinyar da bai hada komai da ita ke son kwontar masa
da hankali ta hanyar nasiha,
Mahaifiyarsa ce ta fado masa a ransa,
Ummih bata taba daga muryarta dan yi masa nasiha ba, takan bi shi ta laluma da dabara, ko dan shi kadai ta
malaka?

A hankali ya zauna, ya mike kafarsa daya ta je har kusa da gwuiwar Hafsat, ya dage dayar ya lankwasheta
ya dora hannunsa na dama a samanta,
Sai da ya ja numfashi, sannan ya sasauta murya ya ce" wace irin rayuwa ce kike hasaso min mai cike da
ni.ima haka bayan na mayar da ita mafarki?

Da yatsitsansa ya nuna ya ce" Hafsat, mace , mace mace, sai da na auri biyar a kananun shekaruna aure irin
na gata na fadawa duniya, aure irin na garari aman ba wace na yi kwonciyar aure da ita, sai da na birne uku
da hannuna biyun suka gudu suka shige duniya,
Ya lumshe idannuwansa ya bude ya ce" Hafsat, mahaifiyata na kokarin hana alburushi taba fatar jikina ya
ratsa gaban goshinta ya kaita lahira, firgicin hakan ya saka har aka yi mata sutura ba da ni ba, aka ajiyeta a
makwoncinta ba da ni ba, aka rufa mata kasa ba da ni ba,

Hafsat, na bi matan banza, yarinya , baba, harda tsohuwa, in dai zata iya kama jikina ta sakani samun
saukin tashin hankalin dake damuna wanda idan ya motsa yanda kika san mahaukaci bana ji bana gani har
sai na aikata iskanci nake samun nutsuwa Hafsat,

Shiru ya yi yana kallon yanda take kallonsa kafin ya lumshe idannuwansa ,


Wani hawaye ne ya fito ta gurbin idonsa dan gajere dan kuwa bai idasa sauka daga fuskarsa ba ya tsaya
yana dubanta da manyan idannuwansa ya ce" na zama dodo mai shanye jinnin matansa a cikin gari, na
zama fasiki mai bin matan banza a idannun kowa, nine atajirin da ya daukowa kansa harka da yan shan
jinni har aka kashe min uwa a cikin gari,
Hafsat, a yaya kike son na haihun? Ke idan na yarda na yiwa mace ciki ta haihun mun na yiwa yaro ko
yarinyar da zata sama min adalci kennan? A ina nake son su rayu bayan abinda ke faruwa a kasata du inda
na saka kafa ya yadu dan ni din cele ne?
So kike na rayu cikin kuncin da yayan cikina su girma duniya ta wulakansu, idan sun gaji kudin ubansu a
so su dominsa, idan kuwa basu gada ba su zama yan ta.ada? Hafsat, a haka kike so na haifi y'a mace na
haifawa karti? Hafsat na bi yayan wasu, mai yiwuwa harda matan aure, duniya ta lalace inda matan aure ke
neman mazaje dan abin duniya, ban taba kwonciya da mace ba aman du daya ne Hafsat,
Ya zan kali idon matar da na aura a lokacin da muka zama daya ta hanyar hayayafa yayan suka ringa tona
abinda na birne?

Ban zo duniya dan na ji dadinta ba Hafsat, a hakan kike min hangen rayuwa mai dadi bayan na yi imanin
ko yarinyar da aka aura min da tantirin dan iska ne marar sisi daga ita har iyayenta ba zasu dube ni ba bale
har su aminta da ta zauna da ni? A halayana , babu macen da zata so ni bani da sisi,
Hafsat ta lumshe idannuwanta ta mike tsaye a hankali ta juyo inda yake sosai ta rage tsayinta ta ce" kar
bawa ya fida rai da rahamar ubangijinsa,
*Idan kana numfashi, kana da sauran dama*

Abdul, ka yawaita istghfari, ka kara kadaice kanka da Allah,


Ka sani ko hana haihuwar da kake yiwa kanka idan Allah ya yi sai ka haihun wani sabon ne,
Ka ringa kalamai irin na musulmai Abdel,

Idannuwansa ya zaro sosai ya ce" ke, kina nufin ni arne ne? Oh kalamainama na arnawa ne? Ni ni Hafsat
ko?

Hafsat ta hade bakinta ta yatsine ta dan ja baya dan a yada ya ruruko mata idon kamar ya dauketa da su,

Goshinta ta dafe ta ce" malan ya muna magana a nitse zaka rikita? Wai me damunka haka ne? Ba zaka
canza maganar ba fa, magana nake maka kan ka nutsu sai ka wani ce kaine ma?

Abdul ya koma ya jingina yana girgiza kai irin ta yi halin , sannan ya ce" ba zan nutsun ba,

Kai walahi sai ka nutsu!


Hafsat ta fada tana galawa bayansa harara ta shiga kokarin bara masa dakin

Muryarsa ya dan daga kadan ya ce" an ki a nutsun Hafsat, nace an ki a nutsun, zan tata yin abubuwan
arnawan ki yanka ni! Kuma ki dawo dakin ki ne ni na bara maki, kai na shiga uku yarinyar nan idan na
tashi aurar da ke ban san ya zan ba

Da mamaki ta tsaya ta juyo tana dubansa, ya kuwa yi mata tsuru yana kallonta, kamar ba shi ba , yanzu ya
yi kalar serius , yanzu ya shiga abubuwa,

Dawowa ta yi tana kallonsa ya mike, cike take da mamakin wai idan ya tashi aurar da ita,
Kasa rikewa ta yi sai da ta ce" bayan ga malan, ga yayuna, ga komai kamar wata wace aka kora sai na zo ka
yi min aure, Kai da ba dan uwanmu bama!
Ta karashe tana kebe bakinta gefe tamkar sangartatun yaren nan

Cike da nishadi yake kallon yanda take jajen zai mata aure, dama ya fadi haka ne dan ta bar maganar
abinda yake gannin ba mai yiwuwa bane, shi baima san me yasa yake iya zama ya fayacewa yarinyar nan
karama abinda yake ji a ransa na game da damuwarsa kai harma da wasu sirikansa, yanzu dai ba wanda ya
taba fadawa cewar yana anfani da maganin da zai hanawa mace daukan ciki idan ya yi mu.amala da uta, sai
gashi ya saki baki ya zayane mata komai bayan ita batama taba yin auren ba,
Wani sashi na zuciyarsa ne ya ce da shi, ai dan bata fiya hayaniya ba, bata da maganar da zata yada maka
sirinka, dan ko na farko ka fada mata dan ka gwadata ne, aman baka tsinci alamun wani ya sani ba, Abdul,
ko dai ka rasa abokin yiwa jaje ne?

Murmushi ya yi ya juya da sigar tsokana ya ce" koda yake da Bashari ne zan maki auren ai, shi kuwa zan
fada masa idan kikai fushi ya rarasar min ke, dan kuwa Hafsana , ni kawai keda ikon muzguna maki!

Ficewa ya yi a dakin yana mai neman layin yaron da zai tuka shi a tsakiyar daren nan zai je jejin nan, ya
tabata Hafsat ta ga wani abin da ya sakata yin gim da bakinta ta shiga yi masa wa.azi, xai tafka masu tsiyar
ne a yanzu da ya san su BS sun shiga sallah ita kuwa ya barota a dakinta kafin ta ankara ta biyo bayansa ya
daga, dan baya jin hasana, ta gabanta ya yi shigar basaja ya fice bata gane shi ba dan kawai ya saka kayan
daya daga cikin sojojin muhammad, zai je wajen nan, ya tarar da mai anfani da sunnan nan, koda fatalwa
ne ya kara kashe shi kowama ya huta!

Nan ya bar Hafsat tsaye baki bude, magangannunsa na wahalar da ita, abubuwan da suka tatauna na mata
yawo a kwonya, sannan zolayarsa ta yau ta tsaye mata a rai shi koda yaushe yana tafe da sabon salo ne? Ya
kuwa iya zolaya,
Murmushi ta saki, wanda bata shirya ba ta ce" Abdel zan so ka gyara idan har mahaifinka na raye ka gane
ba kai ya dace ka hukunta shi ba, laifinsa da ya yiwa ubangijinsa ba ruwanka, fatana , baban fatana shi ne
ace ba hannunsa a kisan kanwarka da kuma mahaifiyarka👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻😔

Hafsat hafsat farka fa😢

Sisters, comment comment, comment plz😊

*KUTKALE*

*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct
NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan
number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA
SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN
SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN,
.....* taku ce, Sajida😍😍😍😍

3️⃣0️⃣

*KU YI HAKURI DA PAGE DIN YAU DAN ALLAH, KU MIN UZURI, INA CIKIN SHIRIN TAFIA
NE, KU MIN UZURI KKK, zan fanshi kaina in sha Allah ta hanyar sambado maku pages biyu zuwa gaba*
A lokacin da ya fito, ya fita a gidan a matsayin kuku mai dafa abinci,
Ta gaban hasanar kuwa ya bi ya fice, bata yi tunanin tun da ta zo bata ga wani mai dafa abinci ba, bata
tsaya ta kula da kyau dan gannin ko waye ba, bata ga shigarsa dakinsa ba , aman ta zura ido ya fice ta
gabanta da plat din abincin da ya dafawa kansa ya fice a falon

Hanyar baya ya sanda, wace ya kwashi minti talatin yana gadinsu har sai da sallah ta tayar da su ya fice a
gidan

A lokacin da ya zo bakin gari tuni kusan karfe shida na yama ne, ba wani haske sosai sai na Allah, wato
wata dan kuwa idan ka yanki cikin gari duhu ne sai fitilun da aka kukuna a gidajen mutane

Mashin din ya karewa kallo, sannan ya duba yar karamar wayarsa wace BS ke kiransa , ya samu numbersa
ya privet ce a jiya da suka nemi Hafsat,
Tsaki ya ja, ya rasa ko ya gane baya nan ne ko me? Yana ta kiran wayar dai dan haka sai ya kasheta ya saka
aljihunsa ya haye mashin din

Tuki yake na garari, wani irin gudu yake yana duba JPS din dake hannunsa sannan yana duba agogo ya
mika hannunsa ya laluba yar karamar bindigarsa da ya sakawa abin hana a ji karan harbi ya mayar da
hannun ya ci gaba da gudu tamkar zai tashi sama

Kai da ba dan muguwar wutar dake cin zuciyarsa ba da ya juya da wannan tafiar mai mahaukacin wahala
dan kuwa wani rami da ya afka sai da mashin din ya yi cili da shi, Allah ya taimake shi kwakwaljewa ne
kawai ya yi, haka ya mike ya tayar da mashin din ya kuma daukan hanya

A lokacin da GPS din ke nuna masa cewar ya zo wajen, a lokacin ya kashe babur din ya nemi waje ya ajiye
shi da adu.ar Allah ya sa ya tardo shi, dan kuwa jejin nan ba za.a rasa barayi ba

A hankali yake tafe yana sandar wajen bakinsa dauke da adu.a, hannunsa kuwa dauke da yar karamar fitila
ta haskawa mai duhun haske,

Wajen shiru, shiru ne gaba daya wajen a haka yake kara shiga cikin jejin yana mai baza kunne yana
sauraron du wani motsi

Motsin da ya ji a bayansa ne ya saka shi dukewa cikin ciyayin dake wajen ya tsurawa wajen da ya ji motsin
bayan ya dane hasken fitilar

A hankali mitsin ke kara matsowa kusansa, har ya kasance an matso sosai kusan shi

Ido ne ya zaro a lokacin da ya ga mai motsin,


Kai, me?

Mikewa ya yi da sauri ya fito ya karaso wajenta, wada itama motsin da ta ji ya sakata aniyar labewa

Hannunta ya damko ya juyo da ita da karfi , hakan ya sakata zazaro ido tare da jan a.uziya ta kurawa wanda
ya damki hannunta ido da taimakon hasken watan da ya raba tsakiya ya haske wajen tar,
mutun mai sanye da wani gajetan wando da riga marar hannun kirki da hular kuku, sai dai kuma fuskar
Abdul ne,
Gabanta ne ya fadi a lokacin da ya ce" ke, baki da hankali ne? Me ya kuma fitar da ke a wannan tsohon
daren? Bayana kika biyo dama? Ke bakya gudun wannan jejin? Wai wa ya saka ki a sha.anin rayuwata ne
da kike daukan irin wannan garajen?

Ajiyar zuciya ta sauke, dan kuwa ta yarda ba aljani nane ya yi kama da shi, shi din dai ne, kennan da ya fito
nan ya yo? Au , kennan ya dilmiyar da ita ne? Haba gaske a lokacin da ta so bara masa dakin ya yi gagawar
dawo da ita? Ikon Allah zuwa ya yi kennan ya kashe mutumen ko me? Wani haushinsa ne ta ji lokaci guda,
shi kennan baya jin bari? Ba zai daina wannan banzan kudurin ba?

Hannunta ta yarfe wanda ya rike mata ta ce" ni ba kai na biyo ba malan, tafiata daban, kuma kar ka kuma
rike min hannu, a kan aikina nake

Wani takaicinta ne shima ya ji ya rufe shi, wai aikinta, to ubanwa ya dauketa aiki irin wannan?
Haba sai yanzu ya gane kiran da BS ke masa, wato dan ya fada masa ne ta kara fita ko? Lale yanzu ya
yarda da irin taurin kanta, yanzu ya yarda lamarinta sai ita, idan ba kasada ba , mace, ita daya kwal da
ranta, ta tashi ta wani dadame da wani shegen wando ta daure gaban goshinta da wani dan siririn gyale ta
dunkule gashinta ta shigl jejo yamkar zaTa yi farauta?

Tsaki ya ja a fili ya ce" to sai ki kama hanya ki koma inda kika fito

Hafsat ta dube shi da kyau ta ce" mu juya dai

Ke ni sa.an ki ne wai? Ya ina baki umarni kina kokarin takewa who are u? Umarni na baki ki juya ki koma
gida

Hafsat ma ta yi tsaye gabansa, ya kasance suna facing din juna ta ce" idan muka yi fita ta ni da kai, na zama
a karkashin, ina matsayin malakar ikonka, a yanzu ka bar uwar malan a daki tana baci!

Takaici ne ya saka shi dafe goshinsa ya nufi Hafsat da niyar nuna mata ya fita iya tsayaya, sai dai wata
murya ce ta ce da shi" *kul Abdallah* dukan mace kuma ka koma?

Wani irin tsayawa ya yi, lokaci guda gabansa ya fadi,


Da wani irin sauri ya juyo dan gannin wanda ya yi maganar,

Innalilahi wa.ina ilaihi raj.une,

Tsaye mutumen yake, ya ja rawanin da ya yiwa kansa ya sauka hakan ya bada damar gannin fuskarsa dake
dauke da gemu da saje mai tsayi tamkar tun da ya fara fitar da gemu bai taba askewa ko ya gyara fuska ba
Du irin karancin hasken wajen ba zai taba bace masa ba, du irin yanda ya fito a gabansa ba zai bace masa
ba,

Gaba daya jikinsa ne ya kwashi rawa, da sauri ya saka hannunsa jikin wandonsa ya janyo bindigarsa da
niyar karasawa wajen mutumen dake tsaye kikam ya ki motsawa ko ya gudu kamar yanda ya yi wamcen
karron

Da wani irin gudu ta sha gabansa, ta yi tsaye a gabansa sannan ta nuna masa bindigar dake hannunta gaban
goshinsa, cikin karaji ta ce" *walahil azim kafin ka yi harbi zan harbeka Abdul Jabar!*

Sai da ya fan dakata yana kallonta sannan ya yi wani murmushin gefen kunci ya ce" *a kan wannan
kudurina kashe ki ba wani abu bane, idan har kin yarda kar ki kauce ki ban hanya!*

Gadan gadan Abdul ya nufo Hafsat dake tsaye tsakaninsa da wannan mutumen dake tsaye shima ya harde
hannayensa
Yana zuwa ya danna alburushin bindigarsa ya........

*Ya Allah, shin wa Abdul ya gani haka? Kar kuyi gagawar yanke hukunci fa? Kar ku manta Abdul na
tsakiyar makiya kala daban daban,*

*Ya Allah Shin Abdul harbe Hafsat din ya yi?*

Ina muka dosa ne?

*KUTKALE.....KUTKALE...KUTKALE*
*KUTKALE*

*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct
NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan
number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA
SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN
SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN,
.....* taku ce, Sajida😍😍😍😍

3️⃣1️⃣

*GA MAKATSIN SHIRU*


Tabas Abdul ya yi harbi, sai dai a lokacin da zai saki kunamar harbin nasa aka wani irin doke hannunsa
hakan ya saka harbin ya bi iska ta gefe,

Bai gama gane abinda ya faru da bindigar hannunsa ba aka yi masa wani bugu a keyarsa wanda ya saka shi
faduwa ya sume a wajen

Wani irin ihu ne Hafsat ta saka ta nufe shi ta duke tana girgiza shi hankali tashe,

Muryarta na rawa ta dago ta kali mutumen da ya doke shi, wani mutun ne baki dogo, sannan wadan nan ya
dauko bindigar ya mikawa mutumen suka zagaye su

Gabanta ne ta ji ya fadi dan kuwa ta gama sarewa cewar tasu ta kare,

Bindigarta ta wawura ta mike daga girgiza abdul din ta saita bindigar wajen ogan nasu tana kule da na
bayanta kar itama ya sumar da ita , cikin karaji ta ce" kai, waye kai?

Datijon nan shima da yannayin tambayar ya ce" ke wacece ke a rayuwar Abdallah da har ya kasa karasowa
kai tsaye ya aiwatar da kudirinsa bayan wannan shi ne baban burinsa na duniya??

Hafsat ta saka hannunta ta cire dan kwalin nan ta yar ta ce" waye kai a cikin masu neman ransa? Me ya
maku? Me kuke so da shi? Ku barshi haka mana, ku barshi!

Yawun bakinsa ya hadiye sannan ya ce" ba.a koya maki baki amsa idan an maki tambaya a gidanku ba?

Hafsat kam ranta ya gama baci, dan haka ta daga bindigar ta yi harbi a sama ta ce" walahi walahi idan baka
ban amsa yanzu ba, to kuwa zan sauke na gaba a kanka, sai dai ku kashe mu ku duka,

Jim ya yi, kafin ya ce" aman ai kin ga jeji ne nan ko? Harbin nan da kika yi kina iya gayato mana ko wani
irin mugu ko?

Hafsat kam tunkararsa ta yi ta dangwala bindigarta a gaban goshinsa dan kuwa da kadan ya fita tsayi, bata
damu da ta Abdul dake hannunsa ba, cikin kakausar murya ta ce" Qui est tu bordel!
?(who are u?)

Sai da ya saka idannuwansa cikin nata exactly yanda Abdul yake yi idan zai kirta rashin mutunci ya ce" i.m
*ABDUL BASID BINE MUHAMMAD*

Ba duka akaiwa Hafsat ba, ba mugun zagi ba, qman sai gata dabas a kasa tana kallon wannan mutumen,

Innalilahi wa.ina ilaihi raj.une,


Shi ne, mahaifin Abdul ne

Bata gama dimaucewa ba ta ga an karaso da wata mota ana kokarin daukan abdul a saka ciki,

Da gudu ta rike shi tana tambayar inda za.a kai shi?


Amsa ya bata cewa....gidansa za.a mayar da shi, muma zamu tashi daga nan dan kuwa harbin nan ya
shaidawa na nesa da na kusa cewar da mutane a wajen, cikin harda sojoji

Tana rike da Badul an saka shi a motar aman ba.a rufe ba cikin sanyin murya ta ce" me ya sa kake son
kashe dan cikin ka???

Ido ya zaro da kyau, kamar yanda abdul ke yi idan abu ya bashi mamaki, tabas mamakin yake ciki, wani
irin alaka ke tsakaninsa da yarinyar nan mai karfi wace har ya fada mata sirrin ban bayan ya san Abdul da
mugun zurfin ciki?

Gannin har ta san haka ya saka shi shima bata amsa daidai da tambayarta cewa" *Ba ni ke son kashe shi
ba*

To aman waye? Wa ya kashe kanwarsa? Wa ya kashe mahaifiyarsa? Wa ke bin rayuwarsa? Dan me ake bin
rayuwarsa?

Sai da ya waiga, gannin cikin sauri sai harhada komansu suke cikin wasu motocin biyu, ya saka hannunsa a
gaban aljihunsa ya ciro wata yar takarda mai dauke da lambar waya ya kama hannunta ya damka mata a
hannunta , cikin gagawa ya ce" ki yi ta gwada kiran number nan, du lokacin da na dauka zan baki amsoshin
tambayoyin ki, yanzun ba lokaci dan kuwa tuni mai tsare hanyar nan ya shaida cewa miyagu sun fara nufo
nan,

Har ya juya zai koma motar ya dawo da sauri ya tsaya kusan Hafsat da ta haye motar tana kallon sa ya ce"
*NI ALMAJIRI NE, NA GANE CEWA DUNIYA GIDAN DADI NE GA KAFURI, TUN DAGA
LOKACIN DA NA WAYI GARI A CIKIN MUGUWAR KADARA WACE ALLAH YA ANKARAR DA
NI KAFIN NA KOMA GA UBANGIJINA NA DAWO NA DUKUFA NAKE AIKIN ALLAH, DU
TAKUN YARONA INA SANE, ALLAH YA JIKAN MATATA DA Y'A TA*

Motar ya rufe da sauri ya daki marfin hakan ya saka mai jan motar ya tayar da sauri ya warceta ya durfafa
cikin jejin inda aka bar mashin din da hafsat ta sato na yan aikin gidan Abdul din, da kuma na wajensa da
ya karba a wajen yaronsa

Sosai ya fafala gudu da su suna ta fafadawa ramuka aman bai rage ba sai da ya fitar da su bakin titi baban
ya taka wani irin birki tamkar an dunguri keyarsa,

Kallonta ta sauke daga fuskar Abdul dake wani irin numfashi ta kai kan mai tukansun,
Haba gaske tuki da cin karfi haka ashe wadan nan ne ya ja su ya fitar da su daga jeji, gaba daya tukin a
bakin kujerar ya zauna kafin kafarsa ta taba su ambrillage da freins din motar sai yan hannayensa da suke
ajiye saman guidon din motar,

Bai ce da ita komai ba ya sauka ya yi gaba sai wani fadin rai yake abinsa

Gaba ta koma ta shiga ta tayar ta harba bakin titi ta shiga tuki cikin kwarewa har ta karasa gidan Abdul

Wannan karron ita kanta ta san ta tabo BS , dan haka da ladabi da biyaya sosai take tsaye gefensa a lokacin
da suka shimfide Abdul suka shiga bashi taimakon gagawa har ya dawo hayacinsa ta hanyar sauke ajiyar
zuciya ya bude idannuwansa

A fuskokin dake zagaye da shi ya sauke dubansa, daya bayan daya ya bi su da kallo kafin ya kafe
idannuwansa a fuskar Hafsat wace da farko ita din ma shi ta kafe da ido tana kallo

Wani irin kallon da bai taba yi mata irinsa ba ya yi mata, kallo mai shige da na tsana, kamar yana jin wani
mugun haushinta, hakan ya saka ta sada kanta tana sauke ajiyar zuciya gabanta na faduwa
Cikin kakausar murya ya ce" ku koma bakin aikin ku

Da sauri ta dago kanta tana kallonsa, har suka fice baki daya aka barta tsaye da Muhammad suna kallon sa

Da wata irin tsawa mai firgitarwa ya ce" ke ba zaki koma bakin aikin naki ba ko me kike jira tsaye a kaina?

Da sauri ta juya tana jin gaba daya gaban jikinta na risgarta , wata irin zufa da tsoro ne suka mamayeta,

Tsanata? Garin shiga abinda ba.a sakani ba na jawa kaina tsana daga wajen mutumen da ya bude min
sirrinsa??

Idannuwanta ta daga sama ta furta *INNALILAHI WA INA ILAIHI RAJ.UNE*

ABDUL kam tana fita ya maida dubansa wajen Muhammad ya ce"


*KUTKALE*

*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct
NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan
number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA
SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN
SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN,
.....* taku ce, Sajida😍😍😍😍

3️⃣2️⃣
Sai da ya gama yi masa wani kallo sannan ya ce" kai, banma taba sannin irin girman rainin hankalin da ka
yi min ba sai yau da na tabatar da abinda na dauki shekaru ina fada maka baka yarda ba!

Muhammad ya nemi waje ya zauna yana dubansa, da irin duban da yake masa a kulun idan ya yi maganar
cewa mahaifinsa na raye, ya tabata yau din ma maganar ne dan haka ya yi masa wani zuru yana kallonsa
irin kai nake sauraron nan

Abdul ya gyada kansa yana kallonsa,

Girgiza kai ya yi ya Mike ya gyara rigarsa da ta yakune sanadiyar daukansa da aka yi har sau biyu,

Tsaki ya ja a fili mai mugun karfi ya juya ya fita shima a dakin ya bar Muhamad zaune yana mai binsa da
kallo

Sai da ya tabatar da ya fita ya dauko wayarsa ya kara shiga dakin ya danna wata number ya shiga waya
cikin rage murya sosai yanda idan ba kai ne yake yiwa maganar ba zaka yi ba, hakan ya saka ban fahimci
abinda yake fada ba

Abdul, yanda ya ga dare haka ya ga rana, zuciyarsa ciwo take masa, yana mai jin wani irin tsananin haushin
Hafsat da ta tare masa gaba ta tsayar da shi wa aikata abinda ya fi buri a rayuwa, bai taba tunanin wata
halita zata shiga gabansa , ta tare masa aiwatar da harbe Abdul basid, muten da ya yi sanadiyar mutuwar
mahaifiyarsa, da kanwarsa, sannan yake neman rayuwarsa, sai gashi, yarinyar karama da zai yi kanwa ta
biyar da ita, yarinyar da bai hada komai da ita ba ta zo ta shiga gaban mutumen da yake nema ruwa a jalo
aman ya ji gabansa ya yanke ya fadi, hannunsa ya kwashi rawa?

Saman bed din daya daga cikin sauran dakunnansa ya kwonta ya mike kafafuwansa ya lumshe
idannuwansa,

Tamkar an dake shi ya zabura ya zauna, dan kuwa hasko masa ita ne aka yi a lokacin da ta yi tsaye da
bindigarta ta yi rantsuwar sai dai ya kasheta kafin ya kashe mutumen nan,
Hannunsa ya saka ya mari gefen fuskarsa ya ce" ABDUL me ya hana ka harbeta kafin ta yi shiru a
maganarta? Abdul me ke damunka har haka? Abdul kana ji kana gani ya kubuce maka bayan ka gansa a
raye? Ba zaman jeji ba ko zaman cikin rami ko rijiya zaka koma sai na kara samo inda kake , kuma ba wai
wannan yarinyar ba, ko wa ya shiga tsakanin bindigata da kwakwaluwarka sai na harbe shi kafin na harbe
ka!

Idannuwansa ya kuma lunshewa yana sakar zuci, shi dai a tambaya daya ya tsaya wace ya rasa amsarta
gamsashiyar da zata saka shi kawar da kai ya manta komai hakan ya saka shi kwana zaune, yanda ya ga
dare haka ya ga rana

Washe gari wajen karfe tara na safe, hayaniyar da ya ringa jiyowa kasa kasa ce ta saka shi mikewa daga
saman salayar da ya keana kaiwa Allah subahanahu wata.ala kukansa

Labulen dakin ya dan ja ya leka kansa,

Ikon Allah, shi ne kalmar da ta fara fitowa da bakinsa zubewa lebensa

Ido ya kurawa yan mata biyun da yake hange daga dakinsa,

Wannan matarsa ce Bahija, wace ta gudu ita da Mariam, kwarai wannan bahija ce, dayar da ta bayar da
kanta gefe ce bai fahimta ba,
Aa, yaya aka yi bakin fuska suka samu damar shigowa har tsakar gidansa? Yaya aka yi haka?
Tsayuwa ya yi ya harde hannayensa yana kallo da kyau

BS ne ya yi tsaye a gabansu ya ce" dan kina tsohuwar matarsa bai bamu damar dan kina haka ki zo kai
tsaye ki shiga har inda yake ba, ki juya wanda ya baki damar shigowar da ya sanki ya shigo ya hau wajen
Sire ya tambayo shi ya kuma sako ki ciki, aman daga inda nake tsayen nan ba zaki shiga ba

Kallonta ta sauke saman kansa a yatsine, ta mayar da dubanta wajrn daidaikun sojojin dake yawo a tsakar
gidan, haka kuma ta mayar da dubanta kan BS da kuna abokin aikinsa dake tsaye wanda BS ne kawai ya
bata amsa kan ba zata shiga wajen Abdul ba, hakan ya saka take ta hayaniya tana karawa kan sai an barta ta
shiga, domin gidan mijinta ne, tana da ikon zuwa a lokacin da ta ga dama, harma ta gayaci wanda ta ga
dama

Dubansa ya maida wajen abokin aikinsa, yana tunanin sakawa a fitar masa da wadinnan yan matan yan
rainin hankali

Abdul ne ya bude kofar dakinsa ya fito cikin takunsa na kakarfan namiji

Jikinsa sanye da doguwar riga ta sallah baka mai dan adon goldin

Fuskarsa ba fara.a ko ta naira biyar, ya hade fuska tamkar zai kai duka

Wata irin firgita Hafsat ta yi a lokacin da ta ga fitowarsa domin bata shirta hakan ba, sam bata yi tsamaninsa
a irin wannan lokacin ba

Sai da ya ja ya tsaya kamar yanda ya saba, ya kai dubansa wajen Hasana dake tsaye ta shiga taitayinta jira
kawai suke ya yi gaba su bi bayansa,
Haka kuma ya kai duban nasa wajen Hafsat,
Irin kallon dake bata wahalan nan dai ya yi mata, wani kallo mai kama da tsana tsana mai shige da harare
hararenta,
Tsai itama idannuwanta ke cikin nasa kafin a hankali saman lebent ta furta" *ABDELLAH* ta karasa ta
lumshe dara daran idannuwanta ta kuma budewa hakan ya saka ta tara masu ruwan kwallah a cikinsu

Gabansa ne ya ji ya rikida ya fadin masa, hakan ya saka shi kawar da dubansa yana mai jin wani ruwa ruwa
kadan a goshinsa

Hannunsa ya kai wajen goshin ya dan shafo, ya kalla da idannuwansa, *ZUFA* ZUfa ce yake yi dan ya yi
ido hudu da yarinyar nan?

Juyawa ya yi da sauki ya nufi kofa hakan ya saka su mara masa baya da sauri

Yana fitowa BS na gama rufe bakinsa cewar a fitar da su

Yarinyar da ta baiwa wajen su BS baya kan ba zata iya yin cacar baki da su bane ta juyo da sauri jin an ce
wai a fitar da ita

Sai da ta yi masu kallon sama da kasa kafin ta ce" *GIDAN UBAN NAWA ZAKU CE A FITAR DA NI?*

Abdul da ya sanyo kai ya fito da sauri ya kai dubansa saman kanta,


Itama idannuwan nata ta zuba masa cikin wani kallo na rainin wayo irin na ka.ide tabas shi ne,

Gyaram murya ya yi, hakan ya saka su Abdul ja gefe sannan suka sara masa

Kallon su ya yi a fakaice sai kuma ya kai dubansa wajen matar da ta gudu da igiyar aurensa kan wai yana
cikin hatsari da kuma yar farar yarinyar da suke tare
Bai yi magana ba sai idannuwansa da ya jefa masu tambaya da su ta hanyar buda masu su baki daya ya
dadage masu giraransa sannan ya dan gumtse bakinsa

Bahija ce ta shiga dan kara jan abayar dake jikinta tana kara rufe jikinta sannan du rawar kan nan da take yi
nan da nan ta nutsu, ta sada kanta ta kasa kuma dago da kanta ma bale har ta dubi idannuwansa dake
firgitata

Wace suke tare ce ta kalli yannayinta, murmushi ta yi a ranta tana ayyana lale na yarda matansa na tsoronsa
tamkar rai, kamar ba Bahija ba ta wani nutsu nan da nan daga gannin mutun tsaye a gabanta,

Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta mika hannunta irin su yi musabahan nan ta ce" *hi kanina, sunana Furaira
ana kirana da Fulawa, wato fleur, ni yayarka ce wace aka fara haifa kafin a haifi mamanka*

Hannun nata ya bi da kallo, nan ya ga baki bakin hannayen nata irin na kana shafe shafen nan sosai ya
kasance jikinka ne farin banda hannun naka, sosai ya kone mata hannun du irin kinshin da akai mata dan
boye shi kuwa tsaf ana ganninsa

A haka ya kuma binta da kallo ita din kanta,


Wata irin farar hoda ce akai mata mak up da ita ta yi mata bau da ita, sai gashin idon nan manyan wato na
karshen tsayin nan an sakawa idannuwanta da suka fara dan jemewa irin man shafe shafe ya ci fatar idon du
ya yamutseta,

Wani irin kwali ne aka saka mata mai mugun baki sannan aka ja shi saman idonta sosai kafin a dora mata
far bau mai ruwan ja ya yi mata wani irin bau a fuskar, sai jan baki da aka saka mata a leben wanda ya saka
bakin yin wani irin dambarere da shi , kai kana gannin fuskarta ka ga rikakiyar yar bariki

Abdul kam kallon tsaf yake mata tun daga kanta har kafarta, hakan ya saka hannun da ta miko da gatsali da
iya yi ya fara gajiya har ta fara jin wani iri hakan ya saka ta bude bakinta da niyar yin magana tana dan
satar kallon yan matan dake bayansa wa.inda ta tabata bodygurads dinsa ne ta yannayin shigarsu wato su
Hafsat, da Bahija da su BS sai shi kansa wanda ta zo dominsa ta ji muryarsa a tsakiyar kanta inda ta yi
gagawar kallonsa da yannayin mamaki Abdul ya ce"

*Dan girman Allah, ku yi hakuri yan uwana, walahi doguwar tafia ce na yi tun karfe biyar na suba sai karfe
biyu na dare muka karaso, zaman mota hakan ya saka ina tare da gajiya sosai gabaina na ciwo 😌, ku yi
hakuri da kadan dinsa, kun san hannuna zaku ji da yawa daga na ji garai*
*KUTKALE*

*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA
BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct
NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan
number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA
SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN
SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN,
.....* taku ce, Sajida😍😍😍😍

3️⃣3️⃣

Cikin murmushi, da yannayin raini Abdul ya dora yatsarsa saman lebensa ya ce" shiiiiiiit,
Sai da ya kikifta ido sannan ya ci gaba da fadin" Huraira? Not Furaira, u.r wlcm yar uwa, ku ware mata
daki, wannan da kuke ganni an sameta ne ta hanyar kauna, ita din yar kauna ce

Wani dan murmushi ta saki , a hankali ta janye hannunta ta ce" thanx

Kafadunsa ya daga yana tsaye ya ga soja biyu sun nufi dayan bangaren dan ware mata dakin da zara zauna

Juyawa suka yi ita da Bahija dan zuwa wajen, yana kallon su

Sai da ya ga Bahija ta kusa shiga ya kalli gefen da Hafsat ke ciki, cikin yannayin basarwa ya ce" kirawota

Nunatan da ya yi ya saka ta gane wace yake nufi, juyawa ta yi ta nufi wajen su ta kirawotan saannan ta
dawo ta tsaya inda take tana mai satar kallonsa

S lokacin da ta zo daf da shi, hannunsa ya mika mata yana kallonta

Hannunta na rawa ta saka cikin nasa, da yannayin nunin soyaya ya janyota a hankali jikinsa yana mai daga
kansa ya hangi window din Ni.ima dake tsaye tana kallon du abinda ke faruwa, ya kuma maida dubansa
wajen masu tsaron ba tare da wani dar ba ya dan saki wani dan karamin murmushi ya sakata cikin jikinsa
ya bata kyakyawar runguma

Ajiyar zuciya ta sauke ta yi luf a kirjinsa tana shakar kanshin turaransa mai dadin gaske,

Bakinsa ya kai daidai kunnenta, wanda du bawan da ya ga haka zai dauka wani kalaman soyaya ne yake
shirin rataba mata dan har dan rausayawa kadan yake da ita a cikin kirjinsa

A hankali ya ce" me kika zo yi gidana ne Bahija?


Bahija da ta lumshe ido tana jin wani irin mugun kaunarsa a ranta a hankali ta amsa shi da" na yi missing
dinka ne, ka yi hakuri

Abdul ya dan saki murmushi ya ce" kin min laifi ne?

Kanta take gyadawa a hankali a jikinsa sannan ta ce" ban gujeka da son raina ba, na gudu ne dan tsoro
Abdul Jabar

Abdul ya lumshe idannuwansa irin kalamanta sun masa dadin nan, sannan ya ce" ba laifi, *Bahija, ni Abdul
Jabar mijinki, na tsinke igiyoyin auren da aka daura min da ke saki uku bisa dalilina na bin maza da kike,
daga yanzu idan kika samu miji zaki iya aure, ban lamunce maki zaman minti daya a gidana ba, sannan
idan na sake ki abu daya zai hana ni damun rayuwarki, ina nufin bin rayuwarki na tagayara ki shi ne ki
mana min kiss a kuncina ki juya da niyar kin tafi ki dawo, idan kika kuskure da nu kike magana!*

Gaba daya jikinta ne ya kwashi rawa, tana so ta dago da mugun firgicin da ya daketa sai dai ta kasa hakan
ya sakata yin wani irin lakwas tana limshe idannuwanta da suka cicika da kwallah,

A hankali ta ce" Abdul,

Abdul ya ce" shuiiiiiiiiiiiiiiit

Idannuwanta ta lumshe ta kuma budewa ta ce" *ABDUL, MAKASHINKA NA TA...*

ABDUL ya kuma wani irin matseta a jikinsa ya kara cewa" i said .....Shuittttttttttttttt

A hankali ya sasauta rikon da ya yi mata ya saketa baki daya yana sakar mata murmushi, sannan ya saka
hannayensa ya share hawayenta a fili murya a dan dage ya ce" to meye na kukan? Ba gashi kin dawo ba?
Ki je gidan zan zo
Ya karashe yana kashe mata ido daya

Murmushi ta kakaro itama ta matso jikinsa sosai ta yi dadage saman dogon takalmin dake kafarta ta mana
masa kisss a kuncinsa kamar yanda ya umarta mata ta juya ta nufi motar da suka zo da ita cike da faduwar
gaba da fatan Allah ya fidata lafia daga gidan

Hafsat dake tsaye a hankali ta jinginar da bayanta jikin garun wajen ta lumshe idannuwanta tana mai jin
zuciyarta na wani irin dokawa tamkar zata ballo kirjinta ta fito

Abdul dake tsaye ya kuma mayar da dubansa dakin da aka kai yarinyar wace ta yi ikirarin ita yayarsa ce
wato yar Abdul Basid, a hankali ya kara satar saitin tagar dakin Ni.ima, nan ya ga bata wajen, dubansa ya
dan saci kallon dakin Muhammad,
Tsai ya tsayar da idannuwansa wajen, kallon wajen yake sosai inda kansa ya sara,
Dubansa ya kara maidawa dakin Huraira,

Juyawa ya yi ya koma cikin dakin inda su Hafsat suka bi bayansa gaba dayansu

Sai da ya kama kofar zai shiga ya juyo ya yafito Hafsat da hannunsa guda sannan ya juya ya shiga dakin

Hafsat sai da gabanta ya yanke ya wani irin faduwa kafin ta daga kafarta da kyar ta kawar da dubanta daga
hararan da Hasana ta gala mata ta juya ta shiga dakin itama

A lokacin da ta shiga dakin yana zaune saman kujera ya janye jalabiyar nan sosai ta yi sama hakan ya
bayanar da cinyoyinsa fili cike da gargasar gashi kwonce lufluf a jikinsa, hannunsa dauke da waya da kuma
irin abin sauraron nan dake bada damar a ji inda mutun yake din nan
Takunta ta kara daukakawa ta karasa inda yake zaune,

Bakinta ta buda da niyar yin magana sai dai saurin kallonta da ya yi , ta kuma nuna mata abin hannunsa ya
sakata yin gum, haka kuma ta ki yin wani motsin da zai saka a gane ko da mutun ko babu

Wayar dake hannunsa ya mika mata


Tana dubawa ta ga message ne rubuce saman screen din kamar haka " meye dalilin ki, una son sannin
hujarki na cewa ba Abdul basid ke neman rayuwana ba,

Sai da ta kalli fuskarsa sannan ta saki murmushi hadi da ajiyar zuciya,


Waje ta samu ta zauna ta rubuta masa message kamar haka" *SHI NE DA KANSA YA FADA MIN*

Cikin sauri ya yi mata typing din cewa" ya dauki shekaru yana zaune da Ummih cikin karya da ha.inci, ina
son sannin a matsayin girman aikin ki, kin yarda da maganar da ya fada ne?

Da sauri ta gyada kanta a lokacin da ta karanta tana kallon cikin idannueansa

Shima wani irin tsai ya yi ya zubawa kwayar idannuwanta ido,


Su kansu basu san sun jima sunna kallon cikin idon juna ba har sai da ta ji idannuwanta na neman bushewa
da ruwan cikin ido ya sakata lumshe idannuwanta tare da dan gumtse bakinta kadan

Hannunsa ya dora saman screen din ya fara typing din message kamar haka" *kina da kyau Hafsat, ina
sha.awar kasancewa a haka da ke*

Hannunsa ya tsurawa ido gannin yana ta rawa rawa , a hankali ya shiga bin harufan daya bayan daya da
kallo kafin ya saka hannunsa ya shiga gogewa cikin sauri,
Sai da ya gama gogewar ya kuma kallonta ya ga ta kawar da kallonta kwata kwata daga kansama, haka
kawai ya ji ba dadi, ta daina kallonsa dan me?

Message ya rubuta cewa " *Budurwar BS, na kara shiga duhu, tsohuwar matata ta dauko kalmar cewa
Makashina na tare da ni, hakan na iya nufin ke ce, bs ne, Mubarack ne, Hasana ce, Ni.ima ce, bakuwar da
ta zo yanzu ce, ko cikin sojojin dake gadin gidana?*

Da maimaita maganar ya fi a kirga sannan ta dago ta dube shi,

Mayar da yatsunta ta yi , jiki a mace ta saka" *INA TA JE NE? A ZANEN DA KA YI KA MANTA


MUHAMMAD.*

da sauri ya dago ya dubeta, mikewa ya yi ya nufi bayi da sauri ya nitsa abin cikin ruwan wanka hakan ya
saka ya daina aiki, fitowa ya yi ya yi tsaye gaban Hafsat yana kallonta tana kallonsa,

Sai da ya hadiyi wani irin yawu ya ce" kina tunanin, Muhammad, dan uwana, yaron da muka girma tare,
muka yi karatu tare, muke kwana muke tashi tare, zai nemi dukan wannan lamari da ni ne Hafsat?

Hafsat ta girgiza kai tana kallonsa sannan ta ce" ban ce ba, na ga kana zane ne ya saka ni tina maka
sunnansa dan kar ka maanta kowa,

Abdul ya gyada kai yana kallonta , dan sam bai karanci abinda take nufin nan da gaske bane, dan haka ya
dan kankance idannuwansa yana kallonta

Murmushi ta sakar masa sannan ta dan matso kadan kusa da shi ta ce" *ka bani dama mana, dan Allah ka
bani dama na shiga cikin lamarin, ina son binciken nan a kusa da ku, ina son binciken kowa ciki harda ni
kaina*
Fuskarta ya karewa kallo yana jin yanda wata irin zufa ke son keto.masa, tamkar wanda ya yi gudu,

A hankali ya kai dubansa wajen kafadarta inda aka harbeta,

Hannunsa ya kai da niyar taba wajen sai dai tuna cewar hakan na iya bata mata rai ya saka shi jimke
hannunsa a hankali ya tsura mata ido,

Hannunsa dai ya kuma dagawa ya kai wajen goshinta ya dan dora yatsar wajen gashin gaban goshin da ya
yi luf luf da shi a hankali ya fan shafa shi sai kuma ya janye hannunsa,

Tsura mata ido ya yi yana kallon yanda take kallonsa tana jira ya bata amanar shiga dumu dumu cikin
harkar hargitsin dake tare da rayuwarsa,
A hankali, cikin wata irin murya ya ce" wanda kika yi na jiya da shekaran jiya, ban so ba,
Sai dai na yafe maki Hafsat,
Ifan kika kuma saka kanki cikin wannan lamarin, Ba zan iya yafe maki ba Hafsat,
Ba zan iya kuma shakar numfashi ba idan har ya kasance wani abu ya same ki,

Idannuwanta da ta lumshe tana kallon cikin idonsa ne ya saka shi cewa" ba zan iya kuma walwalaba idan
har wani abu ya kuma samun wani ta dalilina ba ke kadai ba Hafsat!

Hafsat ba zan iya jura ba a ce wa......

Ihun da suka jiyo daga tsakar gidan ne ya saka su gaba daya kallon kofar,

Da wani irin sauri ya daga kafarsa da niyar zuwa hakan ya yi daidai da itama ta damko hannunsa tana
girgiza masa kai ta ce"""""""""

Comment jama.ata na tuba🤣🤣🤣


*KUTKALE*

*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........
*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct
NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan
number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA
SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN
SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN,
.....* taku ce, Sajida😍😍😍😍

3️⃣4️⃣

Hannun suka kalla a tare,


Da sauri ya janye hannun dan wani irin tsam gaba daya jikinsa ya ji, dan kuwa ba tsintsiyar hannunsa ne ta
damko ba, aa damtsen hannun ne

Basarwa ta yi ta shige gaba da niyar fitan itama,


Abinda kunnensa ya jiyo masa na muryar Hasana tana fadin" sire kar ka fito, domin an harbe Matar da ta
fita yanzu ne, yanzu haka gatanan su BS sun shigo da ita ana duba ta

Da sauri Hafsat ta juyo da dubanta wajensa, aman sam bata fahimci halin da yake ciki ba dan kuwa
fuskarsa bata nuna mata ba, sai ma juyawa da ya yi da wayar dake hannunsa ya nemi waje ya zauna ya
shiga dadana wayar

Tagar dakin ta duba da kyau ta ga a rufenta take dan haka ta juya da sauri ta fita itama ta nufi wajen su BS
dake ta haya hayar aikinsu suna bata taimakon gagawa kar ta tafi dan samun labarin abinda ya faru, dan
kuwa sojojin nan ne suka kawota da gudu suna fadin tana tuki bata idasa fita a anguwar ba aka harbeta, su
kam sun hadu da wani irin aiki mai gardama, sun rasa gane abinda ke faruwa,
Mubarack, abokin aikin su BS ne ya dago daga kokarin tsayar da jinnin ya ce" oga, wannan dole a yi
gagawar zuwa asibiti, tana zubar da jinni kar ta kai inda zata kasa daukan hakan

BS ya gyada kai ya juya wajen Hasana ya ce" zaki shiga da ita gari ta hanyar baya, ki samu wanda zai duba
lafiyarta, ki kula fa

Hasana ta yi gagawar amsa masa, nan suka kamata suka fice da ita da niyar kai ta asibiti dan kuwa sam bai
ji ransa ya amsa da barinta a gidan nan ba

Hafsat biye take da bayan BS tana sauraron irin yanda yake kara shirya shirin kare Abdul, du irin tsare
tsaren tana sauraronsa da kyau tana kuma shanyewa a cikin kwakwaluwarta,

Suna haka har suka shige tsakiyar dakin inda ya juyo yana gyara bindigar dake hannunsa ya kalleta zai ci
gaba da maganar ya yi shiru yana kallon yannayinta

Muryarsa ya sasauta ya ce" me ke damun ki?

Saurin girgiza kai Hafsat ta yi, tana nufin ba komai ba

BS ya yi murmushi yana kallonta ya ce" kina tsoron wani abu ya same shi ne?
Da sauri ta kara kallon sa tana kikifta idannuwanta sak yannayin wace ke firgice na tare da ita, sai dai bata
bashi amsa ba

Kansa ya gyada ya kara rage muryarsa ya ce" kar ki manta waye shi, ko daukan mu da ya yi ba dan zamu
iya yi masa wani abu ba sai dan ya rufe ko shi waye wa duniya

Kara zuba masa ido ta yi tamkar tana son karantar wani abu a fuskarsa,
Tana son BS ya shiga lamarin binciken nan na cikin gida, ita ta san waye BS, mutun ne mai shegen naci da
shiga waje mai hatsari, da ace yana cikin wannan lamarin ta tabata komai na iya faruwa, ta tabata kai da
tuni ya kara mata haske a wajen da take gannin duhu,
Sai dai ina, ba zai yiwu ta fito fili ta fada masa ainahin sirrin Abdul din ba, domin kuwa ko ba komai sirri
ne

Kansa ya girgiza ya juya ya nufi dakin da bakuwa mai sunna Furaira ta zo, ita kuwa ta koma wajen dakin
Abdul

Dakin Abdul din ta tura ta shiga bayan ta bubuga an bata damar shigowar

Zaunen dai inda ta fita ta bar shi, nan ta hango shi,


A hankali ta karasa tana kallonsa ta tsaya dan kusa da shi sannan ta ce" BS ya ce na ringa dafa maka abinci
daga yanzu, idan da hali ka daina fitowa har mu ga tafiar Bakuwar nan

Sai da ta gama Abdul ya gyada kansa , a hankali ya ce" ba zan iya ba

Hafsat ta gyada kan itama ta ce" dama na san ba zaka yarda ba

Abdul ya ce" Hafsat, ni mai taurin kai ko? Ni mai gardama ko Hafsat? Kin ga dai ina cikin damuwar an
harban min abar kaunana, kar ki karan wata damuwar!

Bakinta ta yatsina ta daga kafadunta tana kallinsa sannan ta juya ta fice a dakin

Murmushi ya saki bayan fitarta yana girgiza kansa,


Wayar dake hannunsa ya danna kira

Ana dagawa cikin mutunci da girmamawa suka gaisa da shehin malamin sannan ya shiga kora masa
bayannin wani rudun da ya tashi da shi a yau

Cikin nutsuwa Malan Muhammad mahaifin Hafsat da Abdul ya saka aka samo masa numbersa na whatsupp
suke magana har suka yi mugun sabo yake karbar adu.o.i na neman tsari , a hankali har ya aminta ya yi
masa voice cewar yana cikin duhu mai tsanani, yana son adu.ar da zai lazumta ko Allah ya warware masa
haske a duhu
Shi ne ya ringa taimaka masa da adu.o.i da shawarwari, a wadinnan lokutan har ya bashi kadan daga cikin
labarin rayuwarsa ya boye masa wasu, ya dai shaida masa ana harin rayuwarsa ne,
Cikin muryar datako ya ce" Abdul Jabar kana ji? Ba wanda ya isa ya saka , ko ya hana sai Allah, tabas
Allahn da ya ankarar da kai cewa ana harin rayuwarka, shi ke tsare ka, ina so ka farga cewa da ya yi niyar
baiwa mai bin sahunka sa.a a kanka da tuni mai faruwa da kai ta faru,
Mai runfar na sama yana kallo Abdul,
Kuma wannan magana da ka ce an fada maka cewa makashinka na tare da kai, kar ya baka damar zargin
kowa, wannan ma kuskure ne, ka dai ci gaba da adu.ar in sha Allahu Allah zai kawar da mai son kawar da
kai da kansa

Kansa yake gyadawa har ya gama sauraron muryar datijon mai magana cikin nutsuwa, wanda ke amsa
kiransa bayan bai taba haduwa da shi ba, bai san ko shi waye ba, bai san ko mai niyar cutar da shi bane ko
na kirki ne? Wato su dai malamanmu Allah ya saka masu da alkhairi, suna aikin Allah tare da dogaro da shi
da zuciya daya da imanin du abinda ya same su daga shi ne,
Ajiye wayar ya yi yana lankwasa yatsutsansa,
Ya yi mata magana kan kar ta saka kanta a wannan lamari, lale zai ji dadi idan ta bi maganarsa, shi ya sa bai
mata maganar da wata hayaniya ba , ya bita a laluma ya kwatanta mata wannan sako daga cikin ransa yake

Wani digon tsaki ya ja ya mike ya shiga cire kayansa dan kara shiga ya yi wanka ya je bangaren bakuwarsa
mai rawar kai, wace ya dasawa hajia😌, a fili ya ce" Hafsat, bakya jin magana! Mai taurin kai kawai! Uwar
gardama,,😌mai kyauna😌

Hafsat na fita a dakin Abdul zuwa ta yi ta dauki abubuwan aikinta ta fito cikin tafiar basarwa irin tana cikin
aikinta ne na kare lafiar Abdul ta nufi garden ,

Tana zuwa wajen abin shilawar wajen ta je cikin sando ta makala abin hannunta sannan ta bar wajen ta
kuma dauki hanyar dakin Furaira

Tana zuwa sojan dake kofar tsaye ya hanata shiga, ya ce oga ya hana kowa shiga

Bakinta ta yatsina ta juya tana kallon yannayin wajen da fatan abinda ta wurga a lokacin da ta daga
hannunta da niyar shafa gashinta ya makalu a labulen dakin,

Bangaren su Abdul ta koma cikin nutsuwa take takunta ta nufi dakin Ni.ima

Tana zuwa ta shige dan a nan ba wanda zai hanata shiga

Tana shiga ta tarar da Ni.ima na zaune gaban madubin dakinta ta dira kanta saman table din madubin
hannunta rike da tamfatsetsiyar wayarta

Bata ji shigowar mutun ba hakan ya sa bata motsa ba, wannan ya baiwa Hafsat damar aiwatar da du abinda
ya kaita dakin sannan ta juya ta fice ba tare da ta san ta shigo dakinta bama ta lula duniyar tunanin
damuwar dake damunta

Haka Hafsat ta kara sadadawa ta shige dakin Muhammad domin sojojin dake gadin kofarsa sunna tsakar
gida sai zagaye suke tun da aka yi harbin nan,

Sadadawa ta yi ta shige dakin, abinda ya kaita ta aiwayar ta zo fita kennan ya fito daga bayi daidai kuma
Abdul ya shigo dakin

Da mamaki Abdul ya kaleta, inda Muhammad ya ce" aa, yau harda yar rakiyar taka kake tafe har cikin
dakin nawa?

Abdul ya tsurawa hafsat ido, ita kuwa ta sada kanta kasa ta raba shi ta fice a dakin hakan ya baiwa Abdul
damar shigewa ciki yana mai jin ransa na suya,
Me ta zo yi dakin nan? Me ya kawota? Ba dai abinda ya hanata ne take kokarin daura aniyar yi ba?

Haka ya je suka tatauna da amininsa, dan uwansa kafin ya mike ya zarce dakin Furaira

Gaba daya hirar da ya yi da matar bai fahimci komai ba sai tsabar bariki dake dawainiya da ita,
Karara ya fahimci cewa abin duniya ya rufe mata ido, kuma shi ke janye da ragamar rayuwarta
Dan haka ya biyewa sallon kidanta suka doka gangar iya iyawarta ya bari bangarenta bayan ya nuna mata
kudi akoysu, wanfa hakan ya sakata kara share waje ta baza tabarmarta

Kwonci tashi, har an kara sati biyu cikin wannan hali,


A cikin gidan Abdul, an ci gaba da fuskantar hatsaririka kala kala,
Du wani wanda ke gidan ya koyi sannin mahinmancin lumfashinsa, irin hare haren da aka ringa kawowa ya
saka kowa ya gane cewa rai ba karamin abu mai daraja bane da Allah ya arawa bawa wanda yake iya
karbarsa a kowani lokaci, hakan ya saka musulman ciki suka kara mayar da kansa wa Allah, christocinma
suka kara rike adinnin su,

Har yanzu Furaira na gidan, wanda take son fitarsa ido rufe aman cikin ikon allah Allah hakan ya gagara ta
rasa dalilin da ya sa du irin iya barikinta da wayonta ta kasa samo kalaman da zasu saka shi barinta tafiarta
dan kuwa tana son fita a gidan

Hafsat na nan har ta fada ina nufin ta rame tsabar irin yanda ta sakawa kanta damuwar wani a ranta, dan
kuwa ta zama tamkar fatalwa wajen iya leken asiri da daukan rahiranni tana hadawa a cikin kundin
bincikenta dan samun amsa gamsashiya wa hasashen da take wanda ke nukurkusarta ita kanta yana bata
tsoro, dan kuwa amsar da take hangowa bata tunanin idan ta fito fili za.a wanye lafia

A tsakiyar daren talata, a wannan rana ce Hafsat ta saurari wayar da ta firgitata,


A wannan rana ne ta fito da niyar zuwa dakin Abdul a talatainin dare,
A wannan rana ne aka wayi gari ba Hafsat ba labarinta,

A lokacin da BS ya shiga dakinta gannin har karfe tara da rabi ta fice bata fito ba bayan hakan ba sabonta
bane yana shiga ya tarar ba computenta, ba wayarta, ba du wani abin aikinta an kwashe babu ita babu
alamunta,
Hakan ya saka kansa sarawa ya fito da gudu yana harhada du wani ma.aikacinsa suka rarabu suka shiga
nemanta ilahirin gidan

A haka ya je dakin Abdul da ya gama ganawa da Ni.ima ya shiga a firgice yana mai tambayar a yau ko ya
ga Hafsat?

Abdul dake zaune saman salaua ya dago a hankali tare da rintse ido dan irin yanda gabansa ya yanke ta fadi
ya kali BS ba tare da ya yi masa tambaya ba, yana jiran karin bayani

BS ya ce" mun nemeta bata nan, wannan batan ba irin wanda ta saba ficewa bane domin ba kayanta a
dakinta

Wata irin mikewa Abdul ya yi tsaye, lokaci guda kuma ya dafe kujerar dake kusa da shi domin wani irin jiri
ne ya ji ya zo ya rufe idannuwansa,

Da wani irin ihu ya ce" ina take? Ina ta shiga?

A hankali kuma ya shiga rage muryarsa yana magana tamkar wanda ya zauce cewa" sai da na hana ki, sai
da na hana ki, kin gano ne? Kin gono ko waye? Kin gano an ganki kafin ki fada ne? Ina kike? Kina ina? Ki
zo gare ni?????

...........saura kirisssssss
*KUTKALE*

*(PRISON)*
NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct
NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan
number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA
SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN
SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN,
.....* taku ce, Sajida😍😍😍😍

3️⃣5️⃣

Ki zzo gare ni Hafsat,


Ya karashe yana mai dafe kansa da dukannin hannayensa kafin yake mikewa kuma da wani irin sauri

Fita ya yi ya nufi dakin da computersa ke girke,


Yana shiga ya kunna ya kamo ya shiga bi yana kallo daya bayan daya

Ba abinda ya gani sai duhu ridim , wato wanda ya dauki Hafsat ko waye ya san inda camerorin suke dan
kuwa baki daya sai da aka rufe su aka hana gannin abinda zai wakana

Gaba daya Abdul ya fita a hayacinsa, du wani abinda zai tunkara dan gannin ya sameta, ya ganta ya duba ,
ya bincika aman babu, babu ita babu alamunta

A hankali ya ringa jin wani irin zazabi na son rufe shi, hakan ya saka shi neman magani ya hadiya kafin ya
juyo inda ya tara gaba daya mutanen dake cikin gidan, wato du wanda ya kwana ya tashi a gidan nan in dai
mutun ne dan adam yana halarce a tankamemen falon Abdul du suna zazaune kamar yanda ya umarta shi
kuwa yana tsaye dafe da kansa, ciki kuwa harda matarsa ta sunna da kuma Furaira

Sai da ya gama saisaita kansa sannan ya shiga bin kowa da kallo,


Sai fa ya gama kare masu kallo kafin ya hadr hannayensa cikin wata murya mai nuna tsantsar tashin
hankali ya ce" koma wanene a wannan waje, na roke shi da ya saketa ya kama ni,

Na yarda, ya gane menene lagona ya kuma dakan harbi a lokacin da nake barci,
Ina mai rokarsa, idan har da dan sauran imani da kuma sannin zai yi kwonciyar kabari ya sakar min ita ta yi
tafiarta nesa da ni, nesa da hargitsin rayuwata,

Ya karashe yana mai kara bin su da kallo,


Gaba daya, yana iya cewa gaba daya sun nuna fuskar basu san abinda yake nufi ba, kai ko wa yake nufi
gaba dayama, dan haka ya kara gyara tsayuwa ya ce" daya daga cikin ma.aikatan gidan nan aka dauke,
wace ke gadina mai sunna Hafsat, mun wayi gari babu ita ba labarinta, ba kayanta sama ko kasa,
Sasauta muryarsa ya yi irin na wanda ke azabtuwa da lamarin ya dube su duba irin na neman agaji ya ce"
shin , da wanda ya ga Hafsat?

Kallon kallo suke yiwa junna, aka dauke wata? Mai bashi tsaro? Aa, kuma? Hankali nan ya fara tashi, da
yawa suka shiga mikewa ana mayar da su zaune, inda Ni.ima ta kure shi da kallo, Furaira ta dafe kunci cike
da mamakin wannan gida, Muhammad kuwa ya karasa kusa da amininsa ya shiga tausar sa yana bashi
hakuri

Abdul ya gyada kansa sannan ya ce" ban so mu shiga fannin neman juna ido rufe ba, ban so mu shiga
fannin da zan fita farautar mai farautana ba, walahil azim idan ban kashe shi da hannuna ba sai dai karfin
ikon Allah, *tunda ya yi gigin taba min ita* nima sai na taba shi!

Abdul na gama fadar haka ya juya ya shige dogon lungun daka iya kai shi dakinsa yana mai jin wata irin
juwa na neman dibansa ta kayar

Da sauri Muhammad cike da tausayin aminin nasa ya dafa kafadarsa hakan ya saka Abdul rage saurin tafiar
da yake

Muhammad ya ce" Abdul, menene kuma? Me ke damunka haka da yarinyar kuma? Eh tabas dole
hankalinka zai tashi da wannan sabon lamarin, to aman sai na ga abin na taba ka sosai, ko da wani abu
tsakaninka da ita ne?

Abdul ya tako da sauri inda Muhammad ke tsaye ya kama hannunsa da karfi kafin Muhammad ya ankara
ya dora hannun daidai wajen zuciyarsa,
Sai da ya furzar da huci ya ce" ta bani tsaro fiye da tsaron kanta ne? Dalilin ta dauki harbina ne? Ta iya
zama da ni ne? Ko dan na ga tausayina na zahirin gaskiya a fuskarta ne? Tun da abokin aikinta ya fado
dakina gudun zuciyata ya ki komawa yanda yake da, kuma yana yi gabana na faduwa ne,
Muhammad, nawa suka kashe? Nawa suke son kara kashewa? Ni na san ba son kashe ni suke yi ba, dan
walahi da son kashe ni suke son yi na san da tuni sun cin min, Muhammad so suke su haukata ni? So suke
na zama dan gidan su? Ko takarduna suke bukata? basu da wasa Muhammad, basu da wasa......

Ya karashe yana mai dora hannunsa ya share zufar da ta zubo masa

Muhammad dake kallon sa da yannayin tsoron yannayinsa ya ce" Abdul, soyaya kake da ita ko kwonci?

Abdul ya saki hannunsa ya ce" ba zaka fahimta ba,


Ita din ba zata kwonta da dan iska ba, bata taba yarda na rike hannunta a yannayin lafia ba bale har a zarfe
wani waje da ita ba,

Shiru ya yi yana kallon kasa , sai kuma ya yi murmushi ya ce" so? Soyaya? Ina na ga halin yin soyaya ni?
Ta ina zan soma? Ko daya , ba wannan wasan tsakanina da ita, soyaya suke da mai gidan su, wato BS
Ya karashe yana mai duban gefensa sannan ya saki murmushi ya daki kirjin Muhammad ya ce" zan iya
hakurin rashin da aka rigaya akai min, bana jin zan kuma iya rintsa ido idan bamu yi fada yau ba

Nan ya bar Muhammad tsaye ya shige ya saka suturar kirki ya fito ya haye mashin ya bar gidan

Wasa wasa haka ake neman Hafsat tamkar ana neman zinari, ba inda basa dubawa, ba wanda ke zaune, du
wanda ke gidan nan hankalinsa a tashe, GN da kansa ya tako ya zo ya kuma bada gudunmuwar neman
Hafsat,

Abdul du ya wani firgice, harda lokacin da Muhammad ya tirke shi kan wai me yake haka? Ya fita lokacin
da ya yi niya ba tare da an san fitarsa ba , a yi ta nemansa a rasa, baya tsoron masu farautarsa su samu
galaba a kansa, baya gudun wani mugun abin ya same shi,?
Sai kawai ya karewa Muhammad kallo ya ce" da sun kasheta, da sun kawo gawarta kamar yanda suka saba,
tana raye, yau kwananta hudu tana raye a hannun makiyana

Muhammad ya ce" ka tabata makiyan naka suka dauketa? Yarinyar da ta saba guduwa abinta ta yi tafiarta?
Yau aka fara tsayuwa nemanta? Shaidar basu kasheta ba zai nuna maka cewa kawai ta yi tafiarta ne

Abdul ya kare masa kallo kawai ya sa kai ya barshi wajen tsaye

Yau an tashi lahadi, kwanan hafsat biyar kennan rabonta da gidan Abdul, ko yau tsaye ya kwana yana
kaiwa Allah kukansa

Safiya na yi Ni.ima ta fara shigo masa daki, cikin shiga ta abaya a jikinta
Waje ta samu ya zauna bayan ta gaisar da shi tana kallon sa,
Sai da ya shafa fatihar azkhar dinsa ya kai dubansa wajenta sannan ya amsa gaisuwar tata ,
Yana kallonta ta ce" me ke faruwa haka ne? Kwana biyar kennan baka waiwayi inda nake ba, baka neme ni
a komai ba, wani abin ne?

Tsuru ya yi yana kallonta cike da mamaki, kai kwanansa biyar bai nemi mace ba? Ikon Allah, dama akoy
damuwar da zata gigita wannan bukatar har ta daina hayo masa a lokacin da ta yi niya?

Yawun bakinsa ya hadiya kafin ya yi mata nuni da ba komai

Kukan dake cin ranta ta hadiye sannan ta mike da niyar yi masa salama,
Har ta fara tafia ta kuma dawo ta duka tana kallon zara zaran yatsutsan kafafuwansa masu dauke da gashi
baki sidik sun kwonta luf luf a yatsar ta ce" Abdul, ina son ka, sonka ya saka ni makancewa na bi ka, bani
da jiyar gudun ka komai wuya Abdul, kar ka juyan baya dan kuwa a irin take take da kuma yannayinka da
na karanta na girgiza na kasa baci, ni ban hanaka kara aure ba, dan kuwa ina son abinda kake so

Tana gamawa ta mike ta fice a dakin, inda Abdul ya bita da kallo a wajen a zaune tamkar mutun mutuni

Mikewa ya yi ya shiga wanka ,


Yana fitowa ya saka manyan kaya harda hirami saman kansa ya fito ya nufi dakin Ni.ima

A lokacin da ya shiga tana kwonce saman bed tana aikin, wato kuka

A hankali ya karasa inda take da irin kwonciyar da ta yi ya saka hannunsa ya dagota zaune,

Ido ya dan tsura mata kafin ya ce" ba kyau kwonciya saman ciki,

Kanta ta gyada tana kallonsa tamkar ta dauke abinta ta mayar cikin cikinta ko zata ji sasaucin zafin kaunar
da kishinsa da take

Sai da ya sauke ajiyar zuciya sannan ya ce" kin san wani abu? Kyautatawa na saka so koda babu shi,
Ki lalubi sauran kyautatawar zaman aure, ki rike a hannun ki, ina mai baki albishir din tabas zan maki hira
Shiru ya yi cikin jan aji da jan maganar da ya yi sannan ya ce" ban san me yasa kowa ke gannin nuna
damuwata wa batar yarinyar da ta damu da ni *So ne*, shi dama ba.a shakuwa sai soyaya? Na shaku da ita,
ina walwala da ita, ta iya hira da ni
Wannan shi ne kawai tsakanina da ita,

Yana gama fada ya mike ya mikar da Ni.ima dake jin wani irin kaunarsa da kara shiga ranta da yake da irin
yanda yannayin jan ajinsa da kwaliyarsa ke kasheta ,
Cikin yannayin nutsuwa ya kai lalausan lebensa wajen goshinta ya mana mata kiss, sannan a hankali ya ce"
Allah ya maki albarka

Bai tsaya ya kuma kara wani zama ba ya fice a dakin ya fice tare da masu bashi tsaro ba tare da ya fada
masu ga inda zasu je ba, haka kuma bai yiwa Muhammad salama ba suka dauki hanya cikin tukin garari
kamar yanda suka saba har suka dangana da aeroport

Jirgi na daukan su sai da ya kawo su Niger, ya sauka a Niamey

Suna sauka wasu motocin suka shiga wa.inda BS ua tanada ,

Tafia suka yi mai tsyain gaske, dan a kadan sun yi awa daya da minti talatin sunna tafe a cikin banban
birnin kafin su karaso anguwar

A lokacin da suka karaso masalacin da akai masa kwatance da shi ya saka su karasawa direct har kofar
tankamemen gidan

A lokacin da Abdul ya fito ya yi tsaye yana bin anguwar da kallo haka kawai murmushi ya kubce masa,

Salamar da ta doki dodon kunnensa ta saka shi saurin juyowa,

Yau gashi ga kamilin datijon, datijon da yake jin muryar sa a waya,

A lokacin da malan ya karaso inda Abdul ke tsaye kasa tsayawa kikam ya yi a gabansa kamar yanda ya
saba, dan kuwa wani irin ni.imtacen kanshi ne yake bazawa gashi cikin wata farar shada an yi mata baban
dinki gari da yar ciki, kansa da hula da carbinsa madaidaici a hannunsa mai kyan gaske, sai walwali yake
na annuri yana karawa

Gaba daya Abdul ya kai kasa dan gaisar da Malan, hakan ya sa sauranma zuba masa ido da mamaki, dan
basu taba gannin haka ba, du girmanka har sai ya wani karkace zai maka gaisuwar raini sai gashi yau ya
dukawa wani datijo

Malan kam da ido ya bi shi yana murmushi, sai da ya amsa gaisuwarsa sannan ya mika masa hannu ya taso
su kai musabaha ta kirki kafin Malan ya ce"
*KUTKALE*

*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA
DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct
NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan
number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA
SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN
SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN,
.....* taku ce, Sajida😍😍😍😍

3️⃣6️⃣

Tunda Malan ya saka Abdul a gaba da ido yana kallonsa cike da al.ajabin labarin da ya bashi nasa na
ainahin waye shi dala dala har ya dire malan kallonsa kawai yake

Mikewa ya yi ya dauko goron ruwa ya mika masa tare da fadin " Sha

Bismillah Abdul ya yi ya sha ruwan nan sannan ya kokarta ya mayar da damuwar dake tare da shi ya dubi
malan dake kallonsa zuru, sak irin idannuwan Yar malan

Malan ya lumshe idannuwansa sak irin na Hafsat kafin ya dan gumtse bakinsa sai kuma ya saki ya ce da
Abdul" Sannu

Abdul ya yi murmushi ya sada kansa, dan shi wani irin nauyin Malan yake ji sosai,

Malan ya ce" bawa na haduwa da jarabawa kala kala yaro,


Tabas jarabawarka mai girma ce, ba kamar gannin gawar mahaifiyarka da harbi a goshinta,
Tabas Allah ya san da zamanka dan ka rayu cikin jarabawa Alhamdulilah,

Sai dai maganar da batai min dadi irin yanda kake magana da sunnan mahaifinka a cikin lamarin nan, ba
zan so ka yanke hukunci a kansa ba, ba zan so ka zama mai fushi da iyayenka ba, ko mai ya yi zan so ka
saurare shi sannan ka yi maza uzuri, jarabawar rayuwa ce shi kansa ta same shi, muguwar jarabawa ce mai
saka bawa kauracewa mutane, kai wannan mahaifin naka yana da zuciya mai kyau da abi saka rayuwarsa a
hatsari ba, ina nufin ya kashe kansa, ko ya idasa lalacewa ya shiga wata muguwar hanyar daban

Abdul ya sauke ajiyar zuciya yana sauraron Malan,

Malan ya ci gaba da fadin" sai maganar da muka yi da kai cewa an ce da kai makashinka na tare da kai,
gashi an harbi tsohuwar matarka kuma an sace mai baka tsaro ko?
Andul ya tsura masa ido yana kallonsa,

Malan ya ce" in sha Allah, tunda har suka kai haka, zan iya ce da kai wata hanyar ce ta samun nasara, tabas
ka sakawa ranka cewa za.a iya dacewa a kowani lokaci gaskiya na iya bayana,

A hankali Abdul ya ce" ta kasance mai kwana da tashi da sunnanka,


A kan dalilinta na ta dawo wajen iyayenta ta tarbi harbin da zai same ni ya sameta, fama take, ta shure
makudan kudadan da take iya samu dalilin aikin da aka bata ,

Tsai malan ya yi da jan carbin da yake ya tsurawa Abdul ido

Abdul dake zaune saman abin salaya mai laushin gaske , ya kara tankwasa kafarsa yana kallon malan ya
ce" ba zata gudu ba, ba kuma ta wulakanta kanta ba, rayuwar tsayaya da ta yi halitarta ce, iko ne daga
Allah,
Ta kasance mai tsare kanta, mai tsare mutuncinta, mai hanawa a kama sunnanta kai tsaye dan malan, mai
kuka da hawayenta tana kitan sunnan malan,

Carbin hannun malan ne ya kubuce ya fadi daga hannunsa yana kallon Abdul, unda hannunsa ya shiga rawa
rawa haka kuma ya kasa magana ya kuma kasa motsawa

Mikewa Abdul ya yi daga inda yake ya matsa kusa da shi ya zauna sosai kusa da malan ya ce" na taso daga
kasar Minna a irin wannan lokaci dan na kasa dangana,halayanta na gari sun saka na shaku da ita, na zo da
kokon barana a kama mana da adu.a, Allah ya kuma fitar da ita da hannun da ta shiga, dan kuwa wasu na
zargin ta tafi da kanta ne, ni na san ba zata tafi da kanta ba, dan kuwa tun fitar higar da ta yiwa gidan nan ta
yi alkawarin za.a san da tafiarta in dai mai daukan lokaci ce

Idannuwa Malan ya lumshe a hankali, wasu hawaye ne suka zubo daga gurbin idannuwansa, kafin ya budi
baki a hankali ya ce" *Uwata*

Abdul ya kali malan, sai da ya ji tsigar jikinsa ta mike gaba daya, dan kuwa karara tsantsar tsabar soyayar
Hafsat ne ta bayana a fuskar mahaifinta, ya bashi magana a baibai bai shaida masa ko da wa yake ba, dan
kuwa duniya ce mai cike da girma da kuma fadi, tabas ana iya samun masu halayenta birjik, sai gashi daga
jin yannayin, makamancin halayenta ya zubar da hawaye, tsabar ya yi missing din gudan jinninsa, hakan na
nuni da du irin wahalar da ta gana masu suna kwana suna kuma tashi da ita a ransu a tare da su ko?

Ji ya yi ba zai iya boye masa kamar yanda ya zo da niya ba, ya zo ne da niyar saduwa da shi ya bashi
labarin kansa ya kuma roki alfarmar a kama masa da adu.a a taya shi kan Allah ya bayana Hafsat dan kuwa
idannuwansa sun rufe, ya kasa gannin komai, ya kasa fahimtar du wa.inda yake tare da su bare har ya ware
daya ya bibiye shi, sai gashi datijon ya canza masa abinda ya yi niya

A hankali Abdul ya fuskance shi ya ce" a lokacin fa ta fita daga gidan nan, ta hadu da kadara wace ta yi
sanadiyar zamanta a gidan yari na tsayin watani, kusan shekara,
Bayan wannan gwamnati ta dauketa ta horeta zama cikakiyar mai baiwa mutane tsaro wato Bodyguard, sai
dai mutanen manyan mutane wasun bama a cikin kasar niger ba, ta haka na dauketa aiki, ita ce wace muka
baiwa juna labarin juna

Malan ya miko hannunsa ya riko na Abdul, wanda hakan da ya yi ya saka Abdul bin hannayen nasu da
kallo,
Malan ya ce" yaro, kana nufin...UWATA na raye a doron kasa? Uwata na tine da mu har tana faman zuwa
garemu? Yaro kana nufin Uwata ta nutsu har tana yi mana adu.a? Yaro wai Uwata ce ta zama mai baiwa
mutane tsaro? Yaro ita fa? Uwata mace ce, Uwata yarinya ce, ita ce ta yi kaso? Innalilahi wa.ina ilaihi
raj.une,

Abdul ya jimke hannun Malan yana kallonsa sai dai bai ce da shi komai ba
Malan ya sauke ajiyar zuciya sai kuma ya saki wani murmushi ya ce" tun da na ga na kasa dangana cewa ta
mutu na yi hakuri na bar tunaninta zuciyata ta aminta da tana raye,
Sai dai sake sake ba wanda ban yi ba, dan Uwata ta nuna cewa idan ta bale ba zat yi mana da dadi ba,

Abdul ya saki murmushin shima a hankali ya ce" bata jin magana

Malan ya kale shi da kyau ya ce" Uwata? Bata san mene jin magana ba, Alhamdulilah, Allah ya kara
shiryar min da ita,

Abdul ya amsa da amen,

Malan ya ce" ka san meye? In sha Allahu zata fito, ba abinda adu.a ta bari, hakuri da adu.a su ne makamin
bawa

Abdul ya gyada kansa har zuwa wannan lokacin hannunsa da na malan na cikin juna,

Malan ya kali hannayen shima sai kuma ya kara yin murmushi, wato da ka karanci datijon zaka gane yana
cikin wani irin farin ciki dan kuwa sai sakin murmushi yake duda an bashi abin a dunkule an kuma bashi
labarin tana wani hannun mai hatsari, aman da yake mutun be mai tawakali, sai ya saki du wata damuwa ya
ringa barin zuciyarsa na turo masa da sakon murmushi yana karba yana yi yana karawa,

Malan ya ce" ka san da sai da na daurawa Uwata aure?

Abdul ya kafe malan da ido, dan kuwa ya san da maganar an daura mata aure, aman ce masa aka yi mijin
ya saketa, kar dai malan ya fadi abinda ba haka ba, kai lale da ba.a kyauta ba, da aurenta tana irin aikin
nan?

Muryar malan ce ta katse masa tunani inda ya ce" sai dai yarin ya ki yin hakuri, da yake Allah bai yi ba sai
zigar mutane ta yi tasiri a kansa ya haye ya zauna ya mayar min da Uwa bazawara

Wani murmushi ne Abdul ya sake saki sai kuma ya yi gagawar rufe bakin nasa ya daina murmushin, aman
a ransa hasasowa yake inama inama tana nan aka fadi maganar nan, yana kuma nan, da zai mike ne ya kali
tsakiyar idonta ya ce da ita" *kauriyata, bazawara!*

Wata zuciyar ce ta ce da shi" kai Abdul, tana fa iya baka kunya ta ki tankaka, ta yi tafiarta abinta ta bara
maka wajen,

Sai wata ta kuma fadin" kai ina, ba zata iya ba, sai ta tsaya ta kama tsatso ta ce" *kai🙄, ni ce Bazawarar?
Ka daina bana so Abdellah*

Haka Abdul ya roki Alfarma wajen malan cewa, ya rike bakinsa, dan kuwa yana son koda Allah ya yi an
ganta a wanketa a wajen gwamnati na irin wahalar rayuwar da ta gani har ta rayu a *KUTKALE*

malan sai da ya zabura ya saki hannun Abdul ya ce" bawan Allah, *KUTKALE?* gidan kason nan da ake
fadi a gari,? Gidan yarin da sai ka giga ake kai ka? Me Uwata ta yi da zafi haka ta shiga gidan yarin nan da
ake fada a cikin gari? Wanda baki da yawa ke fadin irin hatsarinsa? Wani irin rike mutunci neza.a iya yi a
wajen da ba mai hanawa ko mai sakawa? Mai karfi shi ke mulki, ga Uwata yarinya? Wace kake nufi a tsare
mutuncin?

Abdul ya sauke ajiyar zuciya yana kallon yanda datijon ke jefo masa tambayoyi, a ransa ya ce" ku ji fa, shi
da ya dace ya yi ta murna, aman da yake ya shafi Mamansa du ya rikice abinsa, dan Haka Abdul ya ce" ai
ina ga a yi murna kawai tunda ta fito a raye,
Jikin malan kam ya yi kalau da shi, a haka har Mama ta zo da kulolin abincin da aka dafa dan kuwa sun
tarbi Abdul yanda ya kamata ya fado ranar aikinta ne, ita da kanta ta yi girkin ta hada komai ta shigo da
zumbulelen hijabinta wanda ya rufe mata kafafuwanta ba.a ganninsu ko kadan sai fuskarta da hannunta

Gaisawa suka yi da Abdul cikin mutunci kafin ta juya ta tafi bayan ta ajiye komai da komai bata tsaya
zubawa ba dan kuwa malan da kansa yake zubawa baya so matansa su tsaya wajen da ya yi baki , sam baya
son matansa su kasance a wajen da maza ke wajen, hankalinsa baya kwonciya da
hakan....................................................................................
*KUTKALE*

*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct
NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan
number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA
SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN
SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN,
.....* taku ce, Sajida😍😍😍😍

3️⃣7️⃣

*DUNIYA, ABAR TSORO CE, KANA TAFE KANA YIWA KANKA MAKIYA A LOKACIN DA KAI
KANKA BAKA SANI BA, FATAN RABIH YA SA MU GAMA DA DUNIYA LAFIA👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏
🏻👏🏻*
A wannan rana Sun wuni tare da Malan da Abdul, dan kuwa sallah kawai ke fitar da su, sun tatauna sosai,
hankali malan ya kwonta ya kuma fada kan adu.ar Allah ya kubutar da ita,
A haka suka yi masa salama da yama suka kama hanyar garin Minna

Tun da ta ji motsin an shigo dakin ta yi tsai tana sauraro


kamar yanda aka saba aka so aka bude wajen da zata ci abinci aka saka mata mesa aka dudura mata
abincin da sam babu dadin dandano sannan aka barta aka rufe mata bakin aka fita

Idannuwanta dake rufe cikin bakin kyale ta lunshe wasu irin hawaye suka bi tsuman suka jika, nan ta shiga
buga hanci dan kuwa muguwar mura ke damunta na irin azabar da ake gana mata

Mamake take, irin yanda ba.a fita da ita a mota ba an fai ja ta an yi tafia mai nisa da ita a lokacin da aka
rufe mata idannuwanta da bakinta aka kuma daureta aka durfafi wajen da ba zata ce ko ina ne ba aka
kawota aka daureta saman kujera ake gana mata azaba kala daban daban dan kuwa namiji daya ne ke
azabatar da ita sai ta fadi inda ta saka wayar da ta hada da computernta take sharing du wasu informations
dan kuwa wannan dalikin kawai ya hana a kawar da ita aman mirsisi ta ki fadi, du ta fice a hayacinta ta
zama wata iri sai karbar azaba take ko abinci sau daya ake bata wani irin damun da bata san ko meye ba a
bata ba wani da yawa ba shikennan sai kuma gobe, ta yi ta yi ta kwonce daurin da sukai mata aman ta kasa
san ba komai a jikinta wanda zai saka ta iya kwoncewar, so take a mayar da ita azabar tsoma kanta a cikin
ruwan da aka yi ko zata samu ta damki wani abin da zai bata damar kubuta

Tarin tashin hankalinta shi ne


Bayan masu son ran Abdul ma tare da shi, tayi imanin kuma *A CIKIN GIDANSA NE AKA DAURETA*
dan kuwa ta ina za.a bi a fita da ita a irin mugun tsaron da gidan ke samu? Idan sun jirge camera ai ba zasu
jirge sojoji da su BS ba, ba zai yiwu duda dare ne a fita da ita a kafa a yi nisa da ita ba, in dai an fitan da ita
to fah ana kusa!
Kai, irin girma da lungu lungu sako sakon gidan nan, ta fara tunanin ko dakin horon Abdul ne?

Motsin da ta ji an buda dakin da wani irin karfi ya saka gabanta yankewa ya fadi

Muryar da ta ji sama sama ana fadin magana kamar haka" *banzan sonta yake! Sonta yake, kuma ya iya
fita da bada sau! Ka san irin yanda yake da mugun naci a kan abu, ina jin wannan yarinyar idan muka
kasheta mun idasa tunzura shi! Damuwarta ya hana shi bin matan da wadincan sakarkarun suka hada shi
da shi fa? Dan haka ka bude mani idonta idan har bata fada min a inda ta saka wayar nan na harbe banza a
kai masa dakinsa a ajiye masa ya dawo daga inda ya je din ya tarar da gawarta mu ga abinda zai yi* !

Das das das das das shi ne abinda gaban Hafsat ke yi,

Wani irin mugun tausayin Abdul, da tata rayuwar ne suka kamata,


Shikenan,
Shi ne abinda ta iya fadawa zuciyarta

A hankali ta shiga neman taimakon Allah har ta ji an kama abin bakinta an vire shi da mugunta hakan ua
sakata jin wani irin zafi

Bata gama jin zafin ba aka cire abin da ya rufe idannuwanta


Tar hasken wajen ya sakata saurin rufe idannuwanta dan wani irin dukanta abin ya yi a idannuwanta

A hankali ta ringa buda idannuwanta tana gannin dishi dishi da kumburariyar fuskarta har ta idasa buda
idannuwanta saman fuskarsa
Ido cikin ido suke kallon junna, a hankali ta buda baki ta ce" *WHY? WHY? Kai ne wanda ya fi kowa
kusanci da shi, kai ne wanda ya fi kowa sannin sirrin sa, kai ne wanda ke yi masa fada kan ya bar desir na
vengeance ku juya gida, kai ne wanda a duk lokacin da aka kawo masa hari ka fi kowa rikicewa da shiga
tashin hankali, aman ka san kai ne ka shaka masa abu da kanka a wajen auren yar gidan aminin mahaifinsa?
Bashi da baban abokin shawara sama da kai, ka kasance mai yi masa fada a kan banzan burin daukan fansa
da nacin zama a wajen da ake son gannin bayansa! ME YA AIKATA DA GIRMA DA KUMA ZAFI HAKA
DA HAR KA ZABI ZAMA MAKUSANCINSA MAFI KUSANCI SANNAN MAKIYINSA MAFI
GIRMA A DORON KASA? KA MIN ALFARMAR SANAR DA NI WANNAN DALILI NAKA KAFIN
KA KASHE NI👏🏻*

Gashin kansa ya shafa cike da dumbin mamakin yanda aka yi a kankanin lokaci, kwanakin da basu fi wata
uku ba yarinyar karama ta shigo ta gane abubuwan da sauran mutanen basu gane ba, wato cewar banda bin
bayan Abdul na son kashe shi da yake shi ne ya kashe mahaifiyarsa da hannunsa, ya kuma saka aka kashe
kanwarsa? Kai wannan yarinyar dole a yau a yanzu ya kasheta dan kuwa yana gannin take takensa da
dukan jama.ar dake tare da shi, a kowani lokaci suna iya gane wanda ke saka su a rudun rayuwa su kashe
shi kafin shi ya kashe shi!

Kafarsa ya dora daya saman abin kujerar yana kallonta ya ce" dalilinsa hukuncin sare kai ya hau budurwata
wace tun da aka haifeta nake son ta tamkar raina, ina ji ina gani ta afka soyayarsa a lokacin da muka tasa
dan ya fito a matsayin zakaran da ya zarce kowa ya ci aikin baban bodyguard na kasar *SAUDIYA*

Mun kasance mun fi karfin a kiraye mu aminai , sai dai yan uwa
Ni ke zuwa gidansu hutu a lokacin da ya je aikin da take takamar shi rikeken dan bincike da kuma gane mai
laifi ne,

Tabas na san dukan abubuwan dake faruwa tsakanin mahaifinsa da yar da ya haifa, na kuma san du wani
shirye shiryen uban ,

Mahaifinsa ya dauke ni kamar yanda ya dauke shi, dan kuwa har shi kansa bai san ainahin waye ni ba , bai
kuma san na yi alkawarin karar da danginsa ba!

*Hasina* ta kasance mai son bakin namiji jarumi dan kuwa muguwar harija ce a tana kananun shekarunta
ma na san da haka dan wani lokacin sai na taimaka mata nake samun lafiarta,
Tun da ta yada ido ta ga Abdul, ta shiga tarda shi ni tana kewaye ni,

Abin ya zama jaraba ta tsane ni tamkar ranta, shi kuwa ya tsane ta tamkar mutuwarsa!

Takan tarda shi du inda ta san zai je, ya wulakanta ta ko a gaban waye ya taketa ya yi tafiarsa,
Gana da kanai ciki akoy wace sak irin halayanta ne da ita dan kuwa itama nunawa ta yi tana son sa,

A lokacin shi harkar mata bata gabansa, ni kuwa ina bibiyar kanwarsa jira kawai nake ya yarda ya so
Hasina ni kuwa na bi kanwarsa dan kuwa cikin ma.aikatan gidan na samu mai bin mani du wani motsinta

Ke bara na takaice maki, dan ya kori Hasina sai ya fara kula kanwarta a lokacin ya dawo ya zama cikeken
sojan boye, yana shirye shiryen zuwa gida wajen iyayensa wani lokaci aka wayi gari Hasina ta Kashe
kanwarta da hannunta , binciken da ya yi ya gano ita ce ya fakasata aka kawot tsakiyar gari aka gile kan
Hasina ina tsaye ina kuka ina magiya ina kallo ya gurgura gangar jikinta ta fadi gefe

Daga wannan ranar na zama makiyin Abdallah, ke ko raina zai shiga sai na ga Abdallah na kukan jini yana
magiyar a yi hakuri a kashe shi dalilin bakin cikin rayuwar da yake gani kala daban daban kafin na kashe
shi da hanuna

Hafsat kyam shi take kallo, kafin ta ce" *tabas, mutuwarsa zata fi zuwan masa da sauki da jin mumunan
labarin cewa kai MUHAMMAD kai ne bakin kumurcin dake bibiyar rayuwarsa cikin innuwa yana kasara
shi, na baka albishir din a lokacin da zai san da hak, abinda zai hana zuciyarsa bugawa to fa lale baban abu
ne mai girman sauran kwanakinsa a duniya, kuma tabas na yarda da maganar cewA......makashinka yana
tare da kai, ko ba komai na gane cewa duniya sai Allah*

Irin yanda take hawaye yake kallo kafin ya yi wata yar karamar dariya yana kallonta ya ce" na kasa gane
shin son ki ne ya saka shi a wannan halin ko shakuwar ce da yake fada? Dan kuwa a yanzu ina cikin
tsakiyar abu biyu, ban taba gannin ya yi rikicewar da ya yi sai da na dauke ki! Shi kashe ki zai idasa
haukata shi ko kuwa cire maki kayan jikinki nake, na mayar da ke matata na tsayin wata guda, gefe guda
shi kuwa ina kara tunzura shi, sai na maki ciki , cikin ya fara fitowa sannan na cire maki kai na dora masa a
kofar dakinsa a lokacin da zai fito ya yi tozali da ke? Kin ga an yi dai dai,
Taya ni gannin shawarar da ta fi dacewa?

Ido Hafsat ta rintse tana adu.a a cikin zuciyar, ba wata adu.a take ba sai rokon Allah kan kar Allah ya bashi
damar taba jikinta da mugun nufinsa,

A firgice ta buda idannuwanta sanadiyar jin ya.......

Comment comment commetn😭😭😭😭😭😭😭😭


*KUTKALE*

*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct
NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan
number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA
SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN
SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN,
.....* taku ce, Sajida😍😍😍😍
3️⃣8️⃣

Wani irin shake gashin kanta dake baje ne ya yi, hakan ya sakata buda idannuwanta ba shiri sai kuma ta
mayar ta rintse,
Walahi da za.a tona zuciyarta da an ga rubutacen abu cewa taba fatar jikinta da ya yi a yanzu ya fi mata
ciwo fiye da azabar dukan da yake gana mata,

Murya na shake mata ta ce" Ta yaya zaka yi tunanin muna soyaya da shi bayan ba wani abu makamancin
haka da ya taba hada ni da shi?

Kara matsa fuskarsa kusa da tata ya yi sosai sannan ya ce" irin alwashin da ya ci a kan du wanda ya dauke
ki na shi ne ajalinsa da hannunsa kadai ya isa ya shaida cewa kina zuciyarsa,

A kan ya ci alwashin kake son halakani?

Yana shirin bata amsa wayarsa ta dauki ruri,

Da sauri ya rarumo abin rufe bakin ya rufe bakinta sannan ya saita kansa ya daga wayar

Yana dagawa ya ce" Abdul, ina ka je kuma? Ina ka je? Kana ina ne? Shin yaushe zaka daina tayar min da
hankali idan kana fita? Yaushe zaka san ciwon abubuwan dake faruwa ka daina fitar nan da kake har sai
wani abu ya same ka? Sai da na tashi na neme ka ban same ka ba shin yaya kake so hankalina ya kwonta?

Abdul ya yi murmushi ya ce" Muhammad, gani fa na dawo kai ne nake nema ban gani ba, ka yi hakuri
nima kana raina, na je wani uzuri ne

Muhammad ya yi gagawar kashe wayar ya koma wajen Hafsat dake binsa da kallo , da yatsarsa ya yi mata
nuni da zasu sake haduwa ne, sannan ya juya da sauri ya fice ya bar mata dakin, wanda yana fita mai tsaron
nata ya dawo ya rufe mata idon ya ci gaba da gadinta

A lokacin da Muhammad ya koma ya tarar da Abdul zaune a falonsa,

Sai da ya kimtsa yannayinsa sannan ya karasa wajen Abdul fuskarsa na nuna tsantsar damuwar halin da
yake ciki,

Yana zama ya kura masa ido kafin ya ce" yaushe zaka cire damuwar yarinyar nan a ranka ne? Kana abu
cikin yannayin da kai kanka baka sani ba, nace da kai kaunarta kake ka kamu da son macen dake baka
tsaro, wace aka bata horo irin na gardawa aman ka musa min?

Abdul ya girgiza kansa ya mika masa hannu ya ce" kai kuwa yaushe zaka daina dirowa wajen mutun ka
rufe shi da fada da accusation ne? Asalamu alaika

Muhammad ya mika masa hannun da ya shaki gashin kan Hafsat sukai musabaha kafin su ci gaba da
tataunawa suna musun da suka saba a haka har ya mike ya ce da shi zai je ya watsa ruwa

Da ido Muhammad ya raka shi har ya shige kafin ya bi masu bashi tsaro sai shawagi suke a wajen,

Murmushi ya yi kasa kasa sannan ya mike shima ya nufi dakinsa


A lokacin da Abdul ya shiga dakinsa tubewa ya yi ya dauki tawul ya nufi bayi da niyar yin wanka
Tsayuwa ya yi kasan shower rufa na sauka jikinsa ba tare da ya goga sabulu a jikin nasa ba,

A hankali ya kawo hannun da sukai musabaha da Muhammad da shi ya saka wajen fuskarsa yana share
ruwan dake rubar masa a fuskar

Tsai ya yi da hannun, inda gabansa ya wani irin bugawa,


A hankali ya maida hannun wajen hancinsa da kyau dan kara shakar kanshin turaran gashin matan da ya
shaka wanda ya tabata da turaran gashin mata ne dan kuwa a da mamansa ke anfani da shi sai kuma da ya ji
shi wajen Hafsat dan kuwa irin yanda ake zama na matsewa junna waje dole a ji iskar kamshi ko warin da
jikin mutun ke iya fitarwa, dan shinema ya saka GN basu kulawa dan kiyaye fitar da warin jiki

Tsai ya kurawa pampon ido kafin ya mika hannunsa ya dauko sabulu ya shiga gogawa,

Wankan ya yi ya gama ya dauro tawul ya fito ya tsaya gaban gadonsa yana kallo,
A fili ya furta" aa, Ni.ima da na shiga dakinta bata kanshinnan, hasalima ban taba jin kanta na kanshi ba sai
dai abin ruwa ko kanshi kanshin man gashi hade da warin ruwa,

Tawul din ya yar ya mika hannunsa ya dauko jalabiyarsa zai saka ya kuma juyowa ya ce" aman, malan
kawai na yi musabaha da shi a fitan da na yi, me zai hada hannun malan da kanshin turaran ruwa na gashin
mata?

Yarfe hannunsa ya yi kafin ya kara kai hannun wajen hancinsa ya sinsina, wankan da ya yi da sabulu ya
saka babu kanshin,

Dan tsaki ya ja ya shinfida salaya ya tsaftace tunaninsa ya gabatar da sallah

Yana gamawa ya shiga jan carbi yana mai kallon waje daya, ya jima yana adu.a kafin ya shafa ya mike ya
cire rigar daga shi sai wandon cikin ya kwonta saman bed dinsa

Shiru ya yi yana mai jin tunanin turaran nan na dawo masa,

Mikewa ya yi ya zauna, a ransa yake ayanna bayan malan sai Muhammad da muka yi musabaha da shi,

Muhammad? Ya Salam, me ya hada Muhammad da turaran gashin mace wanda hakan na nunin ya taba
gashin ne? Shin Muhammad ya saka kansa a harkar bin mata ko meye?

Saurin rintse idannuwansa ya yi, dan ba zai yarda yana ji yana gani ya kyale Muhammad ya saka kansa a
muguwa kuma lalataciyar rayuwa irin ta bin mata ba, rayuwar da idan kana yi baka da mutunci a idannun
al.uma? Ita kanta abokiyar watsewar naka ba mutuncinka take gani ba, a wajen Allah baka da rabo, haka a
duniyar du abinda ka taba sai dai ya ringa yin baya? Ina ba zai bari amininsa ya saka kansa a
wulakantaciyar rayuwa irin wannan ba

Waje ya samu ya kwonta aman fir baci ya ki zo masa, haka ya yi ta juyi yana tunane tunane ga tarin gajiya,
karshe dai ya mike ya kara dangana kansa da darduma dan kara fadawa Allah ya kare mutuniyarsa a samu
yar mutane lafia ya shige gaba kan matsalarta na kaso a wanketa tsaf ya mayar da ita wajen iyayenta lafia
idan ya so ya daga ya yi tafiarsa shima saudiya tare da amininsa!

A lokacin da ya gama shafa fatiya wayarsa message ya shigo,

Hannunsa ya saka ya shiga message din dan kuwa yanzu baya sake da du wani abinda zai shigo masa dan
gudun ya taka kaya ya bar abinda zai kai shi ga Hafsat

Yana dubawa message ne kamar haka" *Ba.a gane mahinmancin abu sai yana nesa da kai, yanda kake ji,
haka nake ji ba dare ba rana tun daga bakin lokacin da na shiga jirgi da niyar yiwa yarona daya kwal da
matata karyar na mutu, Abdallah damuwa ta hana ka baci ne? Rabona da baci tun lokacin da aka kashe min
yarinya,.........BA NI BANE*

Tsaki ya ja ya jefa wayar saman bed dinsa ya mike ya fice a dakin a lokacin karfe hudu ne na dare dan
kuwa ko kiran sallar farko ba.a yi ba

Ky din wajen sa ya saka ya buda dakin ya shiga, yana shiga ya zarce inda yake kwonce ya saka hannunsa
ya dada masa wani duka mai karfi wanda ya saka shi mikewa tsaye a firgice yana kallon Abdul

Abdul ya kura masa ido kafin ya nuna shi da yatsa ya ce" kai, wace irin rayuwa kake son shiga? Daga ina
kake dazu? Ina ka hadu da ita? Ina ka kai ta?

Wani irin faduwar gaba da ta ziyarci zuciyar Muhammad, lokaci guda kafafuwansa suka kwashi rawa ,
wata irin zufa ta shiga zubo masa a fuskarsa,

Da sauri ya kalli bayan Abdul ya ga shi daya ya shigo a wannan lokacin, gaba dayansa a hargitse, yannayin
Abdul ya mugun tsorata shi dan kuwa a lokaci daya abinda ya fado masa a rai shi ne asirinsa ya tonu,
lokaci daya ya fara jin wani abu na bi masa kafa kamar wanda fitsari ya kufce masa fan ya sani, ya fi uban
kowa sani in dai har asirinsa ya tonu ne walahi sai dai a banbare gawarsa ko yace abinda ya yi saura a
gangar jikinsa daga hannunsa,

Hannayensa ya hade yana son yin magana, lokaci daya kuma yake son amayar wa da abdul cewa eh shi ya
yi, shima dan ya raba shi da budurwarsa

(Allah kennan, wato shi mugun abu , ita mugunta idan kana aikata ta du dadin da kake ji bai kai fargabarka
da tashin hankalinka ba, dan kuwa kai kulun jininka a akaifa yake, baka da nutsuwa a komai! Cin amana?
Du mai yi bashi da nutsuwar zuciya, haka kuma ka mace ka je ka tarar da Allah)

Kafin ya yi magana Abdul ya sasauta muryarsa ya ce " Haba, Haba , Haba Muhammad, me ya yi zafi da
zaka saka rayuwarka a kazamar rayuwa irin wannan , kar ka manta fa, kai ke min fada kan rayuwar zina,
kar ka manta tashin hankalinka ka ganni ina rabawa mata ruwan jikina, ka fi kowa sannin ba shigar mace
nake ba aman a wancen din ma adu.arka Allah ya shirye ni, sai yanzu da na shiryu na canza na daina kai
zaka afka? A inama ka ga yarinyar da har ka yi kusancin da ya hada hannunka da gashin kanta?

Wata wawuyar ajiyar Zuciya Muhammad ya sauke yana mai matse kafafuwansa tare da neman zama saman
bed din dan kar Abdul ya fahinci abinda ya aikata a jikinsa,
Sai da ya zauna sosai sannan ya saka hannun nasa cikin gashin kansa yana shafawa a hankali kafin a ransa
ya ayanna' tabas zan yi gagawar kawar da ke a doron kasa kafin sanadiyarki asirina ya tonu, idan na mutu a
yanzu yanzu ban ga anfanin rayukan da na yi ta dauka ba, dan kuwa du irin mutuwar da akai masa kala
daban daban bai saka shi ya rasa imaninsa ba, haka kuma bai zauce ba! Burina na ga Abdul na sakin
magangannun haukacewa, kafin na kai shi gidan mahaukata a ringa tsira masa alurar mahaukata mai karfi
tana cinsa a hankali tana azabtar da shi har lumfashinsa ya bar gangar jikinsa, daga nan na tabata na ci
galaba a kansa!

Abdul ma ya zauna irin zaman fa ya yi ya ce" mazinaci, mazinaci, bashi da wata daraja da ta rage masa a
duniya, karshensa ya mutu babu ido, ba abin hannu, ba iyalin da zasu talafe shi, ba mutunci a idannun
kowa, dan kuwa yaro karamima zai taka shi ya fice idan bai tuba ba wa Allah ba.......wannan shi ne
nasiharka gare ni

Muhammad ya gala masa harara ya ce" yanzu saboda wannan abin ne ka biyo bayana kai jarababe da
tsakiyar daren nan Abdul kake kokarin sakawa jinina ya hau? Ni ba tsoro na ji ba kar a je mugayen
anamiman masu biyar bayan naka ne suka kuma kawo mana farmaki da tsakar dare haka? Gaba daya ka
saka na firgice na fita a hayacina bayan ni na sayi abin gashin dan ya birge ni?
Sai a lokacin Abdul ya yi tsai yana mai karewa yannayinsa kallo,
Dariya ce ke son kubuce masa dan kuwa walahi ya bashi dariya du ya yi tsuru tsuru da shi,
Hannunsa ya matso kusan sa ya ce" Muhammad, wai tsoron mutuwa kake?

Muhammad ya tsura masa ido bai bashi amsa ba, ya nuna yannayin irin ya kufilan nan

Abdul ya yi murmushi ya dan daki kafadarsa ya ce" to dan me ba zaka juya saudiya abinka ba Muhammad?
Ka koma gida ka huta zan biyo bayanka in sha Allah

Muhammad ya sauke hannun Abdul a kafadarsa ya ce" kana tunanin zan iya barinka kai daya tsakanin
masu harin rayuwarka? Rana tsaka fa wata aljanar yarinya ta zo wai yayarka ce, kai kuwa ka bata wajen
zama , idan fa ita ke harin rayuwarka? Abdul bana samun isashen baci dan yawan tunani, a ina tare da kai
idan na koma yaya kake so na samu nutsuwa?

Abdul ya koma ya zauna a hankali yana kallon sa ya ce" *MUHAMMAD, MAKASHIN MAZA AI MAZA
KE KASHE SHI*
Na yi imanin ko irin yanda mai bibiyar rayuwana ke hana aminina sukuni Allah ba zai barshi ba,

Muhammad, hakurin da nake yi, ahi zan ci gaba da yi, na tabata Adu.a bata faduwa kas,
Ban san tsayin lokacin da zan kara dauka ina cikin wannan rayuwar ba, aman na san lokacin da Allah ya
diban mata zai zo zata kare,

Muhammad....mai bibiyar rayuwana na kusa da ni, tunda Allah ya saka hijabi tsakanina da shi na kasa gane
shi du irin yanda na kware a harkar bincike, nasa ya zame min a cikin duhu ..... to kawai na barama Allahn,
na tabata ya bashi dama ne ya gama rawarsa kafin ya daga shi sama ya kuma dada shi da kasa,

*MUHAMMAD, IN SHA ALLAH, ALLAH SAI YA SAKA MIN KAFIN YA BAYANA SHI KOMA
WANENE*

Muhammad dake binsa da wani irin kallon da ba zan iya gane ko na meye ba, cikin wata irin murya mai
rawa rawa ya ce"......
*KUTKALE*

*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct
NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan
number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA
SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN
SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN,
.....* taku ce, Sajida😍😍😍😍

3️⃣9️⃣

*ALHAMDULILAH, NA GODE DA UZURIN DA KUKAI MIN NA RASUWA DA AKAI MANA, NA


GODE DA ADU..O.IN KU, SANNAN NA GODE DA KULAWA, IN SHA ALLAH ZAMU CI GABA
HAR MU GAMA ALLAH YA BANI IKON GAMA SHI LAFIA*

Cikin rawar Murya Muhammad ya ce" ai ai haka ne, ita rayuwa hakuri ke da wahala Abdul, kuma an ce
rana dubu ta barawo, rana daya ta mai kaya ne

Murmushi Abdul ya yi ya mike ya ce" bara na shiga bayinka na yi alwallah sai na fice masalaci daga nan

Muhammad kam bai kara magana ba daga maganar nan da ya yi dan kuwa gumm ya yi yana tunanin
maganar da ya fadawa kansa da kansa

Abdul bayin ya shiga ya zarce wajen alwallah,

Ya dukufa ya yi alwallar ya gama cikin nutsuwa, yana mikewa idannuwansa suka sauka wajen kayan
wankan Muhammad din

Har ya kawar da kansa dan tafiarsa sai ya kara duban wajen,

Dan tsai ya yi dan kuwa bai ga shampoo din nan ba bai ma ga mai shigensa ba, ba zai yiwu ya manta
sunnansa ba ko dan irin yanda shi ke sayowa mahaifiyarsa da kansa dan faranta mata,

Kansa ya girgiza dan kuwa karara ya fahimci cewa Muhammad ya boye masa wannan lamari, ya gane cewa
idan har ya zuba masa ido sai abin ya shiga jikinsa , dan haka ya dauki damarar bin bayansa cikin sando
dan ya gane da warda ya fara fita ya katse abin tun bai yi nisa ba!

Fitowa ya yi ya kuma yi masa wani kallo, kamar ba shi ne yanzu ya shige sun fahimci juna ba hakan ya
kara sakawa Muhammad dar dinsa yana kallonsa ya fice a dakin ya nufi masalaci

Wata irin zabura ya yi tsaye ya bi bayansa ya ga ya tafi bai labe masa a bayan kofa kamar yanda ya saba
taka tsantsan ya dawo ya dauki wani wandon yana mai jan wani uban tsaki a fili ya ce" mu zuba ni da kai,
zan koya maka aikinka banza kawai!

Abdul na gama sallah sai da ya hantse tare da su BS

Suna fitowa ya shiga shawagi tsakar gidan, inda BS ke biye da du wani takunsa hakama Hasanna dake jiran
shigowarsu daga masalacin,
Waje waje suka shiga bi a cikin gidan nasa kama daga lambu, wajen motsa jikinsa kai du wajajen da ya san
yana zuwa ya zauna da Hafsat dan kawai ya tsokaneta ya bibi karshe ya tsaya a kasa shukar mangwaron
dake shuke a tsakiyar gidan ya kurawa inda take yawan tsayuwa ido sai kuma ya saki murmushi ya girgiza
kai dan kuwa har irin hararar da take binsa da shi idan ya yi wani abin yana hankalce da ita kawai yi yake
tamkar bai ganta ba

Yana murmushin sai kuma ya gimtse fuska yana satar kallon su BS, tabas BS na cikin muguwar damuwar
rashinta, yana hankalce da shi sai dai bashi da damar nunawa ko zakewa a lamarin dan a karkashinsa yake a
yanzun

Kansa ya girgiza ya kai hannunsa na dama ya shafa uwar sumar da ya tara a kansa da sajen da ya tara tsabar
damuwar da yake ciki sai kuma ya saki hannun nasa ya dantse lebensa na kasa yana kallon wajen dai bai
kawar da idannuwansa ba yana mai ayanna ya Allah ya bayana masa wanda ya dauketa da ransa ido da ido!

Muryar BS ne ta dawo da shi hayacinsa, sanyin safiya dalbeji sai kadawa suke da shuke shuken cikin gidan,
A hankali ya kai dubansa wajen wada BS ya dakatar kar ta karaso wajen Abdul

Ido ya tsura mata,


Du ta fita hayacinta tamkar ba ita ce ta shigo da iya yi da kisisina da tarin iskanci a tare da ita ba,
A yanzu haka fitowar da ta yi doguwar bakar riga ce jikinta, gaba daya jikin nata sai rawa yake, hannayenta
ta dago ta maraoraice fuskarta ta budi baki da kyar ta ce" ka taimake ni, kashe ni zai yi👏🏻

Idannuwansa ya zaro, inda yana wulaga ido ya ga jan hasken abin harbi a jikin bishiyar dake kusa da shi, da
sauri ya maida hankalinsa kanta sai dai me, BS da ya zabura da hanzari dan riketa ya yi wata irin juyowa da
gudu yana ihun su tare Abdul su kare Abdul,

Wata irin girgije Hasana da ta je da niyar jan sa da karfi ta kai shi maboya ya yi kafin ya karasa da gudu
inda aka harbeta a baya daidai kahon zuciya wanda ya sakata take wani irin abu tana zubar da jini ta
bakinta idannuwanta na yin sama sama tana hahakewa ,

Mikewa ya yi shima da gudun balaki ya rufawa BS baya dan zuwa inda suke tsamanin an yi harbin, sai dai
abinda suka tarar mutun yashe da shigar masu harbin nesa da alama an shamace shi a lokacin da ya yi
harbin shima an harbe shi kuma duka kaf haka ba tare da an ji karar harbin ba

Lokaci guda kuma aanguwar ta kwashi kukan laluwa dan kuwa BS ya shaidawa polisai an kuma yin wani
harbin, nan da nan maganar har ta hau sama wayoyi sun shiga kuka suna neman maganar Abdul,

Abdul ya jinginar da bayansa jikin garun wajen yana mai kallon gawar nan,
Dubansa ya maida tsakar gidansa inda aka yi harbin nan ya ga har an sakata cikin wata bakar jaka irin ta
rufe gawa an dora gawarta saman gadon asibiti an shigar da ita cikin ambulance

Yana nan tsaye sai ga baban sojoji wanda yake aboki a gare shi ya hayo da kansa inda suke tsaitsaye,

Sai da ya dan ja ya kale shi kafin ya sara masa dan kuwa du girman sa girman aikin Abdul ya zarce nasa,

Wajen BS ya je inda BS kuwa ya sara masa, ya karbi bindigar yana jujuyata sannan ya kali BS ya ce" shi
kadai ka samu a tare da shi?

BS ya gyada kansa yana kallonsa,

Mikewa ya yi ya dawo wajen Abdul ya tsaya ya ce" kar ka tayar da hankalinka abokina, zamu je da
gawarwakin nan asibiti likitoci su bincika dan gane shi wannan sabuwar gawa ce ko tsohuwa?

Abdul dake bin bakinsa dake magana da kallo ya lumshe idannuwansa ya kuma bude yana kallon sa,
A hankali ya daga kafarsa ya taka ya je inda gawar ke kwonce wace aka hayo itama da niyar a rufe ta a tafi
da ita ya duka wajen gawar ya saka yatsarsa mai bin banar yatsar a dan ramin harbin inda ya dangwalo
jinnin dake baki baki wanda bai yi tauri ba gayanan shar a hannunsa ya dago da yatsar ya nunawa Baban
sojojin mai suna Ahmad ya ce" wannan sabon harbi ne, domin jinnin da duminsa sannan bai yi kauri ko ya
dunkule ba,

Ahmad ya kale shi da kyau kafin ya ce" aman, me hakan ke nufi?

Abdul ya karasa bakin windows din da daga nan aka harbi matar ya tsaya a hankali ya ce" hakan na nufin
*Makashina na kusa sosai da ni, hakan na nufin makashina na cikin wannan benen a wannan lokacin*

Da sauri Ahmad ya matsa kusa da shi ya ce" ga polisai da sojoji du sun cika wajen sai bincike suke, gashi
du mutane sai kaura suke daga anguwar babu wasu mutane da yawa bale har ya shige cikin mutane ya bace
mana, ko cikin benen nan mutanen basu fi hudu ba du irin girman hotel din nan, kuwa, kar ka damu zamu
same......

Kafin ya karasa muryar Muhamad ta karaso wajen, ya shigo da sauri hankalinsa a tashe ya nufo Abdul,

Ba wanda ya dakatar da shi sai dai binsa da kallo da mugun tausayin irin yanda ya damu da lamarin aminin
nasa

Shi kansa Abdul ido ya kura mada har ya karaso ya rungume shi a jikinsa ( kun san ai larabawa saka mutun
a jiki a wani abu bane, hakan gaisuwa ne ko nuna an damu da mutun), yana rungume shi ya ce" innalilahi
wa.ina ilaihi raj.une, ya Abdellah, kana gannin bakin cikin rayuwa, irin haka sai ya saka mutun ya haukace
ko zuciyarsa ta buga

Abdul ya lumshe idannuwansa ya damki hannunsa sannan ya cire shi daga jikinsa ya kuma lumshe
idannuwansa ya bude, sai kuma ya yi wani dan malalacin murmushi ya ce" Muhammad, ka daina
tsawalawa kanka damuwar nan, ji yanda zuciyarka ke bugawa, yannayin numfashinka na sauka da sauri
sauri tamkar wanda ka yi gudu, haka kuma jikinka ya dauki dumi, sannan bana so kana zuwa inda nake a
irin lokacin da ake harin rayuwana, Muhammad idan wani abu ya same ka zuciyata zata tsaya, bana tunanin
zan iya ci gaba da tafia a matsayin mai hankali

Idannuwansa ya rintse da karfin gaske ya bude su inda suka kara rikidewa ya jimke hannayensa ya kaiwa
garun wajen naushi da karfin murya ya ce"""
*KUTKALE*

*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI
IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct
NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan
number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA
SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN
SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN,
.....* taku ce, Sajida😍😍😍😍

4️⃣0️⃣

Cikin karfin murya ya ce" *INNALILAHI WA INA ILAIHI RAJ.UNE, ALLAHUMA AJURNI FI
MASIBATI, WA KHALIFUNI KHAIRAN MINE HA!*

Muhammad da sauri ya karasa inda yake tsayen ya riko hannun nasa da ya daki garun da shi yana kallo da
yannayin mugun tausayawa ya ce" ka bari mana, dan Allah ka bari

Abdul ya rike hannun nasa shima ya ce" me ake so da ni? So ake a taba imanina ne? Muhammad za.a saka
ni na fara zance a titi, zan iya fita da gudu a kowani lokaci

Muhammad ya kara shiga kirjinsa irin ya hana shi maganar nan, aman a kasan zuciyarsa murna yake na lale
lale bukatarsa ta kusa biya, burinsa zai cika na gannin Abdul ua wulalance kafin ya aika shi lahira,

A haka shima aka nade shi aka fita da shi, inda su BS ne, sojoji da polisai ne, sai kwaya dayan sojan
Muhammad da ya bari dan kuwa ya salami sauran dayan nan kwal shi ke biye da shi

Sai da kowa ya watse sannan suka fito tare suna tafia du da yannayin rashin karfin jiki da rashin laka,

Muhammad ya kale shi ya ce" ka yi hakuri, na san da ciwo Abdul a kashe maka lanwarka, a kashe maka
mahaifinka, a kashe maka mahaifiyarka, a zo a kashe maka kuma yar uwarka daya da ta rage maka?

Abdul ya ja ya tsaya , sai da ya dan dafe kansa sannan ya ce" ba yar uwata bace

Muhammad ya tsura masa ido yana kallon sa ya ce kamar yaya?

Abdul ya daga kafadunsa ya ce" ba yar Abdul Basid ba ce,

Aman ya aka yi ka gane haka? Muhammad ya fada cike da mamaki

Abdul ya waiwayo shi sai kuma ya saki murmushi ya ce" tana zaman kanta a saudiya kusan shekara goma
sha bakwai, ita din haifafiyar maradi ce, iyayenta du sun mutu, ta fita neman na kanta da kanta ne,

Muhammad ya yi saurin cewa" to me ya kawota nan, me ya hadata da tsohuwar matarka?


Abdul ya shafa sajen fuskarsa sannan ya daga kafadunsa ,

Muhammad ya kasa sammun nutsuwa suka ci gaba da tafia da Abdul har suka shiga baban falonsa,
Muhammad ya ce" Abdul, sai nake gannin hankalinka a kwonce, wannan matar ta zo da niyar cutarka fa,
domin ta zo a matsayin wai yayarka, hakan kuma harda tsohuwar katarka, ta zo dan dukiyarka ko dan
rayuwarka?

Abdul ya ce" eh, aman ai ka ga Allah ya tsayar da lamarin da kansa

Muhammad ya kura masa ido ya ce" to aman ita matar taka ina take? Ina ta shiga?

Sai da Abdul ya fara tafia dan kuwa jirri yake ji sosai dan hankalinsa ba a karamin tashe yake ba , gaba
daya ya sare , tsoro ya lulube masa zuciya na tunanin a wani hali Hafsat take ciki? Ko har an kashe ta ne?

Da kyar ya iya tsayawa ya juyo ya ce" tana boye , ni kaina ban san inda suke bata soin ba!

Haka Muhammad ya yi shiru yana kallon sa har ya shige dakinsa na baci,

Yana shiga nan ya fadi ya rintse idannuwansa yana jin yanda kansa ke sarawa, ya Allah, ya Allah shi ya fi
maimaitawa yana mai neman hawaye su zubo masa aman shiru basu zubo ba

Wayarsa ce ta dauki kuka dan haka ya mika hannu ya lalubo ba tare da ya duba mai kiransa ba ya kara a
kunnensa yana sauraro

A takaice aka ce" *jarumi ne kai, cikin da ta fita da shi barinsa ta yi bata haife shi ba, zubar da shi ta yi
Abdellah, tashi kar a cin maka a lokacin da kake halin kaka naka yi*

Ihu ya yi da haushi ya nausa wayar a kasa

A cikin wannan rayuwar kunci aka ci gaba da tafia da Abdul da Muhammad da mutanen dake tare da shi,

Wa.adin da malan ya dauka na sati daya cir suna wata nafila tsakiyar dare daga shi har Abdul dan neman
haske da bayanar Hafsat a wajen Allah ya zo ya cika aman shiru

Hankalin Abdul ya kara tashi, shi dai du ya daburce abinsa aman yana yin bakin kokarinsa yana boyewa
dan gudun hargitsa lamarin Muhammad dake tare da shi ba dare ba rana

A rana ta tara , ya tashi da matsananciyar faduwar gaba,


Tazbaharsa ya lalubo ya shiga lazumi zaune saman salayarsa, har lokacin komawarsa baci ya yi na wajen
karfe goma aman shiru baya jin bacin ko kadan,

Yana zaunen nan ya ji zafi , ko nace kunci wajen ya yi masa hakan ya saka shi mikewa ya je bakin windows
ya ja ya tsaya ya dage labule yana kallon yannayin garin

Idannuwansa ne suka sauka a kan Muhammad dake tafiar sauri sauri ya nufi can wajen bangaren dakinsa na
sirri na horo, domin daga dakinsa tsayin ginnin na bashi damar hango du wani abinda ke nesa dake cikin
gidan

Har ya juya dan komawa bakin gadonsa ko zai samu baci, sai kuma ya maida dubansa wajen yana kallo,
Gani ya yi wannan sojan daya kwal da ya ragewa Muhamad ya tarbo shi sun tsaya suna yar magana sai
kuma suka juya a tare bayan Muhammad din ya amshi wani abu a hannunsa tamkar igiya

Kansa ya girgiza a fili ya ce" Muhammad, me kuma ya kai ka har wancen wajen kai da na maka hani da fita
nesa in dai ba zuwa daukan jirgi dan tafia Saudiya zaka yi ba?
Komawa ya yi bakin gadon ya zauna,

Haka kawai ya ji hankalinsa ya kasa kwonciya da nisan da Muhammad ya yi, sannan zuciyarsa sai
tambayar me ya je nema nan take masa?

Mikewa ya yi da sauri ya je dakin computernsa,

Yana kunnanwa ya hasko wajen dan gannin me yake a nan, sai dai ya ga duhu ya mamaye screen din,
kamar an cire camerar ko an rufeta da wani abu mai duhu dan kar a ga abinda ake a wajen

Gabansa ne ya yanke ya fadi, lokaci guda jikinsa ya dauki rawa, ya salam, kar dai a je yau kuma
Muhammad dinsa za.a kashe masa?

Ai zuciyarsa na gama fada masa haka ya wani irin dirkowa daga saman kujerar da ya zauna dan gannin
camerar ya fita da wani irin gudun balaki yana mai gyara karamar bindigarsa da ya warto

Yana fitowa su BS suka rufa masa baya suna masu tambayarsa lafia? Aman ina bakinsa ya kasa basu amsa
haka kuma ya kasa tsayawa, su kuwa sun kasa cin masa

Da gudu suka karasa wajen, sai dai me, mai tsaron kofar na ganninsu ya ciro bindigar jikinsa da niyar
harbin su, sai dai ya makaro dan kuwa kafin ya saki kunamar harbin nasa BS ya dauke shi da bindiga hakan
ya saka shi faduwa wajen

Tabas da Muhammad na cikin hayacinsa, da karar faduwar sojansa ta saka shi lekowa dan gannin abinda ya
yi kara haka, sai dai ina yana can ya tube zindir hahuwar uwarsa haka kuma ya cirewa Hafsat rigar dake
cikinta kokarinsa shi ne ya karasa cire mata wandon jikinta ya idasa nufinsa a kanta aman saman kirjinta ba
komai ko bras babu bale a yi tunanin riga, albartun kirjinta gaba daya sun bayana suna kiririta da fitsara
abinsu........

Abdul da yannayin tashin hankali ya kali solda din nan sannan ya kalli BS, sarai ya gane niyar soldier din
ya harbe shi, aman kuma rudu ya hana shi yarda sai ma komawa da ya yi ya shaki kwalar BS ya buga shi da
garu daga baya baya ya rage muryarsa cikin bacin rai ya ce" ya zaka kashe mutun tamkar kiyashi kai
mahaukacin ina ne? Ka sani idan na fitar da Muhammad daga dakin nan sai na rufe ka da kai da azalumana
dake biye da bayana!

Yana sakin BS ya juya ya wankawa su Hafsat wani wawan harara sannan ya tunkari dakin kai tsaye inda su
Hafsat suka bi bayanya

Yana zuwa ya buda dakin gaba daya ya afka bindigarsa a hannunsa a shirye da shirin harbi a kowani lokaci

Wani irin ja ya yi ya tsaya, domin wajen haske ne tar ya haske dakin

A hankali shashekar kukanta ya fara shiga kunnansa da kalma kamar haka" *MUHAMMAD KAR KA
KETA MIN HADI, NA ROKE KA KA KASHE NI BA TARE DA KA HADA NI DA KAZANTA BA*

Muhammad da ya bada baya yana hada kwaya cikin jus din maltina dan so yake sai hankalinta ya gushe zai
yi bidirinsa a kanta , sam bai ji an buda kofar ba dan kuwa kofar ba mai kara bace sai a bude a rufe bata yi
kukan an bude ta ba, sannan kafar Abdul ba ko takalmi bale a jiyo takun tafia, gashi sun yi shigowar da ba
za.a jiyo su da sauki ba

Idannuwansa ne suka sauka kanta,


Gefen fuskarta a kumbure kadan dan kuwa ya tasa irin marin da yake wanka mata idan ta bata masa rai,
Lebenta ya yi wani irin jajajir tsabar dantse shi da kukan da take ci na iftila.in rayuwar da ta afka ita ba a
duniya ba ita ba a lahira ba,
Gashin kanta gaba daya ya zubo mata ya kare wajen da ya kumburan a fuskarta a hankali ya kai
idannuwansa a jikinta, kirjinta gasu nan a bayane kiri kiri jajajir da su sun kumbura sun batse suna rawar
nanaye daga ta motsa,
An yi mata wani irin dauri ana shirin rapping dinta!

Kansa ne ya mugun sarawa, ya wani irin sarawa,

Bindigar hannunsa ce ta kubuce ta fadi a daidai lokacin da Muhammad ya juyo daga shi sai dan pant na
maza jikinsa ya yi shirin kwasar gara ya sha kwayoyin maza dan niyarsa ya yi mata kaca kacan da ba za.a
iya ganeta ba!

Sai da ya rintse idannuwansa sannan ya kuma budewa, Hafsat dake kallonsa tana lumshe idannuwanta tana
mai jin wani irin ciwo , muryarta ciki ciki baya fita da kyau ta ce" *Abdallah*

Abdul ya lumshe idannuwansa dan du kalma daya da ta fito daga bakinta dirrect zuwa ta yi ta samu
matsugunni a zuciyarsa, ta mata wata irin duka sannan zufa ta keto masa

A hankali ya daga kafarsa daya ya yi taku daya zuwa ga Muhammad da ya ruruko ido, ya daga hannayensa
ya dora saman kansa, gaba daya jikinsa yake bari, haka kuma wandon dake jikinsa sai ga fitsari ya biyo
yana gudu nan da nan zarni ya fara tashi

Muryarta ta kara budawa ta ce" *ABDALLAH SHI NE*

Da sauri ya juyo dan kara kallonta a lokaci daya kuma ya ringa gannin duhu na karade wajen baki daya

Lumfashinsa ya ji yana sama, da karfin gaske ya ja numfashin ya sauke, ya kuma ja ya kara saukewa,
Zuciyarsa ce ya ji tamkar ana zuba masa ruwan zafi,
Adu.a ya nema ya rasa ,

Da wani irin karfi ya daki kirjinsa da hannunsa na dama ya kara daga kafarsa ya nufi inda Muhammad din
ke tsaye , sai dai ina gaba daya lumfashin nasa ya dauke idannuwansa sukai tsaye tsaye kafin su rufe,

Tun daga tsaye sai ji kake yimmmmmmmmmmm Muhamad ya fadi kasa

Hafsat dake daure Hasana nafamar kunceta bayan ta kare mata kirjinta inda BS da abokin aikinsa suka nufi
wajen Muhammad sunna tsaye sunna jiran jin abinda Hafsat ke nufi da bayaninta Hafsat ta kwala kara ta
ce" Abdl............

Bata karasa kiran sunnansa ba ta fashe da wani irin kuka jikinta na rawa daidai nan hasana ta kunce ta

Mikewa ta yi ta rukunkume hasana jikinta na rawa ta ce" dama ina gudun wannan ranar, ku duba shi kar ya
mutu!

BS dake cikin wani yannayi, na murnar gannin hafsat da kuma katon rudanin da ya hane shi nuna farin
cikin nasa na gannin aminin mutumen koma ya ce dan uwansa a tsaye a irin wannan shiga da kuma
kalaman da suka fito a bakin hafsat da irin yanda suna kallon abdul din ya sume sun kasa motsawa dan
karasawa inda yake dan kuwa sun saka Muhammad din tsakiya BS ya ce" Bodyguard H, wa ya sato ki ya
kawo ki nan? Me kike nufi sa maganarki na *Shi ne?* shi ne me?

Hafsat da jikinta zafi rau ta saki Hasana tana kare kirjinta da rigarta ta kai dubanta wajen Abdul sannan ta
maida wajen BS ta ce"
Alhamdulilah........comment yan uwa
*KUTKALE*

*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct
NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan
number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA
SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN
SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN,
.....* taku ce, Sajida😍😍😍😍

4️⃣1️⃣

Cikin yannayin rashin tsoro da kyama take duban keayar idannuwan Muhammad dake dan langi
sakamakon kwayoyin da ya hadiya ta shiga mayar da zancen duka kaf da ta gano wajen bincikenta, da irin
sato tan da suka yi shi da sojansa mai bashi goyon baya, da komai da komai

Sai da ta ja numfashi ta kai dubanta wajen BS da har jikinda bari yake tsabar firgita da ikon Allahn nan, ya
ga lamari da yawa, ya ga gaba da yawa, aman bai taba gannin ci amana irin wannan ba

Idannuwanta cike da hawaye ta ce" wannan da kake gani, wanda ba zan iya kiransa da madaukakin sunna
irin MUHAMMAD ba, domin ya kasance azalumi, mai izgili da rashin tsoron Allah, wannan aljanin
mutumen wanda ban ga sunnan da ya dace da shi a musulunce ba!

Ta kuma rinyse idannuwanta sannan ta ce" *shi ne mai kashe kashen nan baki daya ban cire maka ko daya
ba, kuma yana yi ne dan vengeance*
Sai da BS ya dafe gaban kirjinsa dan luguden kidan da yake masa,

Dubansa ya kai wajen algungumin a daidai lokacin da ya daga hannunsa ya nuna Hafsat ya ce" karya ne!

Gindin bindigarsa ya saka ya daki keyarsa hakan ya katse masa fitsarar da ya dauko a bakinsa ya silale
wajen a sume

Da kallo ya bi shi sannan ya bada umarnin a nufi asibiti da Abdul da Hafsat


Shi kuwa ya dadaure Muhammad dauri irin na huhun goro sannan ya shiga bincike da harhada du
abubuwan da zasu isa cikaken shaida haka kuma ya tabo ikon garin wa.inda bai isa ya aiwatarwa da
Muhammad wani abu ba sai abinda aka yanke masa a kotu

A lokacin da aka saka masa ankwa bayan sun dankara masa wata gigitaciyar allura mai taba kwakwaluwa
aminin Abdul mai sunna Ahmad ya yi tsai yana kallon motar da aka shigar da shi baima san inda kansa
yake ba,
Tabas shima ya girgiza, sai dai da wuri ya kwabi kansa a lokacin da ya tuna cewa Muhammad fa mutun ne,
dan adam ba, dukan abubuwan da ya ringa yi ke dawo masa a idannuwansa,
Sai da ya kalli BS dake kokarin tayar da mota dan bin bayan su Abdul sannan shima ya buda motar da shiga
wace ke dauke da gagan sojoji wa.inda ba alamar sun taba sannin wani abu mai sunna dariya a rayuwarsu
sannan ya gyada kai a ransa ya ayyana........shara.ar Muhammad ya dace a barwa Allah, bai ga hukuncin da
za.a yiwa wannan bawa a nan cikin duniya ba, bai ga irin abinda za.a iya yiwa wannan bawa ba a huce ko a
rama irin abubuwan da ya shuka, tabas zasu tura shi kasarsa a hukuntashi a can, ya tabata kisa ne ta hanya
mafi muni ya je can kuma ya fuskanci wanda ya halice shi!

A asibiti kuwa tun a hanya BS ya samu ya kirayi number Malan, domin tun ranar da Abdul ya je BS ya
gane akoy fahimta tsakanin datijon da Abdul, a irin yanda Abdul ya zame kasa ya duka ya gaishe shi wanda
hakan shi ne gannin farko da ya yi ya mutunta mutun

Bayanin da ya yiwa malan ya saka shi jin zufa ta keto masa, cikin nutsuwa ya nuna masa cewa da zai samu
jirgi a lokacin tabas da ya zo da kansa domin kuwa dole Abdul na bukatar mutun a kusa da shi

BS na jin haka ya ce da shi ya kasance cikin shiri koda yaushe ana iya zuwa daukansa in sha Allah za.a
kawo shi

BS ma karasawa ya tarar likitoci na kan Abdul , famansu shi ne su dawo da numfashinsa da bugawar
zuciyarsa daidai,

Hafsat kuwa na zaune saman kujera an saka mata magana a fuskarta an gyara mata an yi an yi ta kwonta ta
huta aman ta kasa tana zaune ta saka wata riga baka mai dogon hannu aman bata canza wandon jikinta ba ta
faure kanta da dan kwali baki ta yi zuru da ita tana kallon waje daya, a kasan zuciyarta kuwa sai adu.a take
kan Allah ya sa ya yi hakuri ya dauki komai da sauki

Sun dauki kusan awa kafin a fitar da shi a kai shi dakin hutu sai a lokacin ta mike ta koma dakin da ya dace
a kwontar da ita ta shiga bayi ta yi wani irin wanka sannan ta fito ta dauki wani wandon da rigar baka da
hijab da Hasana ta kawo mata ta saka ta kabarta sallah a nitse

Ta jima tana ramuwar salolin dake kanta, ta dauki lokaci tana sallah kafin ta salamce ta shiga adu.a da
godiya ga Allah

Jaka kawai ta tsinci kanta da yi masa adu.a mai nauyin gaske, ta jima tana rokon Allah ya taimaketa ya ji
kanta duda baya barin wani dan wani ya ji dadi ita kam bata tunanin zata ci gaba da walwala idan bai mike
ya samu kansa ba
Tana ta jero adu.o.in ta ji wata kamilaliyar murya, nitsatsiyar murya, muryar da ta kasance mai yi mata
nasiha da lalaba ta, muryar dake tsananin girmamata ta hanyar kiranta *UWATA* muryar da ta kasance
daya daga cikin adu.o.inta na Allah ya nuna mata ranar da zata kara jin muryar a duniya

Kasa kunne ta yi tana mai jin zuciyarya na bugawa a lokacin da ta ji BS ya yi magana sai kuma ta ji muryar
ta ce" Allahu ya tashi kafadar bawan Allah, ya bashi lada da juriyar wannan jarabawa, domin Abdallah
mutumen kirki ne

Wata irin mikewa ta yi ta doshi kofar, sai dai me, Hasana ce ta riko hannunta da karfin gaske ta ce" ki koma
ki zauna H, kar ki jazawa kanki kin san kina cikin mission ne

Wani kallo ta yiwa hannunta da ta riketa da shi sannan ta ce" ki cika ni

Hasana ta saketa ta ce" zaki lalata aikin ne

Hafsat bata ce da ita komai ba ta buda dakin da saurin gaske ta fita

Tsayuwa ta yi ta shaki kamshin turaransa, bai canza shi ba shi dai ne har yanzu,

Da sauri ta shiga raraba ido tana neman inda zata gan shi, ina zata ga hasken idanniyarta,

Kyalkyalin tazbaha da ta gani a daidai kofar dakin da aka saka Abdul ya sakata nufar wajen har tana
hardewa , muryarta ta buda ta ce" *ABANA*

Da sauri ya saki kofar da ya buda da jiyar shiga domin likita ya ce ana iya shiga Abdul ya farka ya juyo
inda ya ji muryar

Ita ce tsaye gabansa


A hankali ya furta" Alhamdulilah.... *UWATA*

AI kuwa Hafsat ta fashe da kuka sannan ta arta a guje , tana zuwa ba wata wata ta fada jikin mahaifinta ta
kankame hannunsa tana wani irin kuka , bata wani damu da tunawa ya hana su fadawa jikinsa ba, ko jikin
wani namijin haka kawai ba, shi kansa sai da ya ji kwala ta cika idannuwansa sannan ya yi mamakin yanda
mamansa ta girma a dan lokacin nan fuskarta ta nuna alamun ta nutsu.

A hankali ya cirata a jikinsa yana kallonta ya ce" ya isa haka ko Uwata?

Tana haki da komai ta ce" Aba, ba guduwa na yi ba Abana, Abana ka min auren da du wanda ka zaba min
na maka alkawarin da zauna da shi koda kuwa yankan naman jikina yake, Abana ka yafe min, ina mamana?
Abana ka san inda aka kai ni? Ka san me aka min? Abana gidan yarin *KUTKALE* aka kai ni a matsayin
wace ta yi laifi na zama budurwar dan ta.ada, Abana daga nan aka kai ni .....

*UWATA* ya fada cikin nutsuwa yana kallonta,

Hannunsa ya saka ya share hawayenta sannan ya ce" Abdallah ya je ya fada min,

Shiru ta yi tana kallonsa, sai a lokacin mamaki ya kamata na jin wai Abdallah ya je wajen mahaifinya ya
fada masa wannan maganar,
Ikon Allah, sai yanzu tunanin me ya zo yi asibitin ya dirar mata,

Dubanta ta kai cikin dakin marar lafiar nan ta hango Abdul kuri su yake kallo
Gabanta ne ta ji ya yanke ya fadi lokaci daya kuma ta damki hannun mahaifinta a hankali ta ce" Abana, ya
farka
Malan ya kai dubansa wajen Abdul din, ya ga gaba daya hankalinsa a kansu dan haka ya ja hannunta da
niyar shiga da ita, sai dai ga mamakinsa hannun ne ya fara rawa ta kasa motsawa harma ta iya furta cewa"
Aba

Tsayawa ya kuma yi da mamaki ya kalli yannayinta, a hankali ya cika hannun nata sannan ya juya ya shiga
dakin , sai dai ya kasa rufe kofar dan du ji yake idan ya rufe ba zai bude ya kuma ganninta a wajen ba

BS ne ya zo ya yi mata magana fuskarsa a tamke hakan ya sakata bin bayansa suka je suka tsaya nesa da
dakin, bai ce da ita komai ba sai dai shirun da ya yi shima yana kallon waje daya kamar yanda ya ga
hankalinta ya raja.a dakin da mahaifinta da kuma Abdul ke ciki

Tun da malan ya shiga ya nemi waje ya zauna, ba abinda yake karantawa Abdul sai girman hakuri
mahinmancinsa da sakamakon da ake samu mai kyau idan an yi shi,
Jarabawar da ya shiga mai girma da duhu ya ringa bashi baki da musalai da kuma ribar da zai samu idan ya
yi hakuri da ita a hakan,

Shiru ya yi yana kallon yanda Abdul ke kallon kasa bai ce da shi komai ba
Ci gaba ya yi da bashi baki, da nuna masa kar ya dauki maganar cewa zai dauki fansa shima, hakan ba zai
kai shi ga ci ba, ba zai samu wata nasara ba

Abdul ya dago idannuwansa da suka yi jajajir da mugun nauyin da sukai masa ya sauke a kan malan
Sai da ya hadiyi yawu mai daci da kuma yauki a hankali ya ce" ba komai *ABA, ALLAH YA JIKAN DU
WA.INDA SUKA MUTU*
Sai da ya ji zuciyarsa ta girgiza, ba komai fa yace? Tabas yana iya karbar abin aman ba komai din na lokaci
daya ya bashi mamaki, ko dan yana cikin hali na rashin dadin yannayi shi sai ya ce kamar yau baya cikin
yan magana ma,

Ajiyar zuciya ya sauke ya mike da niyar fita, sai dai muryar Abdul ta dawo da shi cewa" Aba,
Dama amini na zama makiyi? Aba dama alkhairi na jazawa mutun kiyaya? Aba, shin a gabanan zan iya
yarda da wani dan adam komai kusancina da shi kuwa?

Aba ashe aminina ya kashe min kanwata? Ya kashe min mahaifiyata? Ya kashe mutanen dake tare da ni?
Du dan ya kai ni ga ciwon hauka kafin na bar duniya? Aba........zuciyata sai nake jin tamkar ba zata kuma
gannin haske ba, ji nake tamkar na gama da farin ciki, idannuwana na gannin kowa da fuska biyu, *ABA,
shin me zai saka na yarda da kai kanka?*

Halin rudani na rudar da zukatanmu a likacin da wani lamari ya dake mu😔, sauki na Allah ne
*KUTKALE*

*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA


NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct
NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan
number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA
SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN
SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN,
.....* taku ce, Sajida😍😍😍😍

4️⃣2️⃣

A hankali malan ya koma ya zauna ,


Sai da ya sauke ajiyar zuciya sannan ya ce" da baka yi magana irin haka ba, da na bar wajenka cike da tsoro
da tunani dan kuwa idan ba mahaukaci ba sai mai kishirwar ramuwa zai hadiye irin wannan lamari lokaci
daya
Abdallah , imani da Allah da yarda cewa a cikin mutane akoy masu cuta akoy masu tsoron Allah,

Imani, hakuri ne kawai zasu saka ka yarda da wani mahalukin a nan duniya
Zan so ka kasance mai hakuri ka cinye jarabawar nan Abdallah

Kansa ya sada yana mai jin yanda zuciyarsa take cinkushe bata da wani yannayi na wanda zai iya samun
nutsuwa,

Kansa ya kuma dagowa ya kalli malan ya ce" da idona, da kunnena na jiyo shawarar aminan mahaifina na
zasu hada ni da bin mata, duda bata fadi komai ba idannuwanta sun karantar min komai
Zan so a ce ba daga bakinta haka ya fito ba ko na samu damar musawa har na fuskanci dan uwana

Malan ya kara matsa kujerarsa kusa da gadon yana kallonsa ya ce" ka rage zurfafa kauna , haka kuma ka
rage zurfafa kiyaya
Tsananin kaunar da kake masa da yardar da ka bashi dari bisa dari ne ya rufe maka ido ka kasa gannin
ainahin wanene shi, sannan wacece ta fada maka? Kar ka yarda ka hau kan abu ba da kwakwaran shaida ba

Idannuwansa ya dago yana kallon Malan,


Sai da gabansa ya yanke ya fadi, a lokaci daya kuma irin yannayin da ya tarda ta ya fado a idannuwansa,
Shikenan, ta dalilinsa rayuwarta ta bace ko me? Anfani ya ringa yi da ita? Shi kam me ya yiwa
Muhammadu a duniyar nan? Me ya yi masa da zafi haka? Da sauri ya kali malan, tausayin malan da na
Hafsat ne ya ji sun mamaye zuciyarsa, ta jure gwagwarmayar rayuwar nan, ta shiga Kutkale ta fito lafia, ta
shiga gidan horon maza ta fito lafia, du bata rasa mutuncinta ba sai a dalilin bashi tsaro? Bashi tsaroma ya
dace ya mayar da ita tun harbin da akai mata aman ya kasa hakan ya riketa a wajensa gashi ya jaza mata
wannan balaki?
Muryar malan ce ta dawo da shi daga dogon tunanin da ya saka shi mayar da ido ya rintse dan jin wani irin
kyankyamin Aminin nasa,
Bai taba jin kyankyamin zina, kallon matan wasu ba irin na yau....sai a wannan lokacin ya ringa hasko
dubunnan matan da ya ganni tsirara dan kawai ya samu biyan bukatarsa,
Sai a lokacin ya yi tunanin wa.innan mutanen fa y'ayan wasu ne, iyayen wasu ne, yayun wasu ne, kuma
kannun wasu ne, duda su suka kawo masa kansu aman shi dan rashin tsoron Allah da rashin kunya ya mike
ya mika masu abinda ya fi sirri a jikinsa suka lumda suka bashi nutsuwa ta hanyoyi daban daban....sai gashi
shi ya ki ya haihu dan kar a yiwa abinda ya haifan aman cikin ikon Allah,
Allah ya saka masa muguwar shakuwa da yarinyar da basu hada komai ba, shekarunsu ba daya ba , fatarsu
ba daya ba, shakuwa irin ta yan uwantaka wace yake jinta har cikin jinninsa, yake yi mata so daya da ba
hadi... an yi mata abinda yake gudun a yiwa yayan nasa? Dama ba.a isa a zagaye ikon Allah ko a yiwa
Allah dabara ba ko? Dama lokaci Allah ya ara masa na ya gama zagaye zagayensa kafin ya rike shi?
Kai, ya san ba zai iya ja da amininsa kan maganar kisan kan da ya ringa yi....wannan Allah zai saka masa!
Cin amanar aminta da ya yi ..shima ba zai wani hukunta shi ba,
Aman baya jin zuciyarsa zata iya amince masa ya hadu da mutumen da ya tsaga jikin Hafsansa ba tare da
igiyar aure ba dan kawai cin mutunci da wulakanci ba tare da ya gile shegiyar da ta kai shi aikata hakan ba,
tabas sai ya yi masa kaciya da faratunansa zai tsinke abinda ya kasa rikewa a wandonsa sai da ya ketawa
Hafsat hadi!

Shiru Malan ya yi gannin wasu guntayen hawaye na biyowa gefen fuskarsa , carbinsa ya ci gaba da ja yana
mai dubansa a kasan zuciyarsa kuwa yana nema masa sauki a wajen ubangiji

A haka BS ya shiga dakin ya ja ya tsaya,

Ya jima a yannayin da yake na sarawa Abdul na kallonsa kafin ya iya daga masa hannu ya sauke hannunsa

Yana saukewa a hankali ya ce" takarda ce daga saudiya, suna bukatar a mika masu mai laifi dan an karanta
masu komai an kuma tura masu dukan hujoji ta hanyar computer shine suka turo da sakon a mika masu shi
can

Kafarsa dake ajiye yana karkadawa a hankali ya ce" idan aka basu shi me zasu iya yi masa?

BS ya yi shiru domin ya tabata tambayar ba ta neman amsa bace

Abdul ya dago jajayen idannuwansa ya ce" zasu saka masq fararan tufafi ne, su dauko shi su shigo tsakiyar
gari da shi, su saka masa bakin yadi su rufe masa fuskarsa su dauki doguwar takarda su karanto laifinsa
sannan su saka doguwar wuka sun gile kansa.....

Sai da ya tsaida idannuwansa cikin na BS ya ce" an bashi mutuwa mai sauki, bai ga duniya ba an tafi da shi
lahira.....

Malan dake kallonsa sai da ya ji dar din Abdul din, dan kuwa gaba dayansa ya mike zaune ya kara kallonsa
da kyau ya ce" ka bani wayoyina

Da sauri ya juya ya yafito su Hafsat dake tsatsaye

Suna shigowa ya karbi wayoyin Abdul din dake hannun su Hafsat ya mika masa su kuwa du suka juya suka
layu daga kan Bs Har su Hafsat din kusan garu inda malan ya bi Hafsat da kallo dan kuwa yanzu ba hijab
din a jikinta cikin damararta na aiki da ta saba

Abdul kam mikewa ya yi tsaye kan kafafuwansa da kayan asibiti a jikinsa ya danna kira,

Ana dagawa ya canza harshe ya shiga magana cikin yannayin zafi zafi , yana yaran larabawa wanda Hafsat
da Malan suna fahimtar duka kaf abinda yake fada
Cikin yannayin tsoronsa ta kafe shi da dara daran idannuwanta, dan kuwa ya fito sak a baban mutun
ma.aikaci mai zaman kansa mai iko da kansa wanda ya san hakokinsa da wa.inda ba.a isa a take masa ba

Maganar da ya karasa da uta shi ne" *in dai ba za.a sake shi a saki amininsa a fili a basu damar kashe kansu
ba, to fa ba.a isa a tura shi saudiya ba, a barshi a Minna su yanke masa hukunci....a kai shi Niger a saka shi
a cikin gidan kason KUTKALE*

Yana gama fada ya ajiye wayar ya daga manyan damatsunansa ya cusa hannayen nasa a cikin gashin kansa

Ya jima a haka ba wanda ya ce komai a cikinsu har ya yi niya da kansa kuma ya juyo a hankali

Yana juyowa ya kurawa Hafsat dake kusa da BS ido,


A hankali ya kai dubansa wajen BS din, da kuma Hasana....
Haka kawai ya tsinci zuciyarsa na cewa" ba abinda basu gani ba

Rigar asibitin ya shiga cirewa hakan ya saka Hafsat saurin sada kanta daga dubansa da take, ba ita daya ba
du wanda ke wajenma sai ya kawar da dubansa a kansa , wasu na mamakin shi bashi da kunyar cire kaya
ne? Wa.inda suka san ko shi waye kuwa basu wani yi mamaki ba

Wando da riga ya saka bakake lut, sannan ya saka gilas a fuskar tasa ya juyo wajen Malan dake tsaye,

Zuwa ya yi sosai kusa da shi sannan ya duka har kasa, a hankali ya ce" na gode da mutuntani, da adu.o.i da
nasihohi, in sha Allah zaka juya da Hafsat a yau yau.....zan zo nima domin zaman kasar nan ya fice min a
rai

Malan kam kansa kawai yake gyadawa yana kallonsa, haka ya mike ya fice inda suka mara masa baya gaba
dayansu

Suna fita daga asibitin ya mikawa BS waya,

BS na gama sauraron maganar ya kalli Hafsat da sauri, sannan ya kali Abdul,

Ganni ya yi Abdul din ba wani alamar fara.a a tare da shi, dan haka ya mika masa wayar ya je kusa da
Hafsat ya yi mata bayanin abinda aka ce

Ji ta yi kamar tsokanarta yake, dan haka da wani irin gudu ta karasa inda Abdul yake tsaye,

Haki ne ya hanata magana sai nuni da take masa,

Abdul ya lumshe idannuwansa yana mai jin nauyinta har cikin ransa ya ce" ki je

Hawayen idannuwanta ne suka bale, cikin yannayin kuka ta ce" kana nufin..shikenan? Kana nufin na zama
mai cikeken yanci? A yanzu ta waya ka saka aka sake ni daga kason da na shiga? Kana nufin zan ga
mahaifiyata

Dariyar da take ua saka shi tsurawa fuskarta ido,

Hannunsa ya dago a hankali, hakan ya saka hannun nasa dake bari bari ya dora yar yatsarsa a gurbin
kumcinta da ya lotsa sosai , sannan ya kama dan mayafin nata da ya fadi a kafadunta ya dora saman gashin
kanta sosai ya rufe,
Idannuwansa ne ya sauke saman kirjinta, lokaci daya gabansa ya buga da mugun karfi, lokaci daya kuma ya
rintse idannuwansa a hankali ya ce" *zan waiwaye ki*

Suna tsaye suna kallo ya shige wata mahaukaciyar bakar mota ya tayar ya harba bakin titi inda su hasana
suka mara masa baya
Gaba daya jikinta ne ya mace mata, bata son tafia ta barshi du irin zumudin gannin wannan ranar,
Gata dai ga mahaifinta, sannan an tabatar mata da ta bi mahaifinta ta je gida ta huta ba tare da an tsara mata
tsarin rayuwarta ba,
Sai dai kash, yau ta tabata sabo tirken wawa ne, ita kuwa ta yaya zata iya sabawa da rashinsa bayan ya saba
mata da shi a ko wani motsi nata?

Dubanta ta kai wajen BD dake tsaye yana yi mata murmushi, sai a lokacin ta waiwaya sai ta ga mahaifinta
baya nan,

Da sauri ta ce" ina Abih?

BS ya saki murmushi yana kallonta ya ce" sun tafi da Abdul, daga can za.a kai shi aeroport ne, akoy abinda
zasu yi, mu je a can zamu hadu

Ajiyar zuciya ta sauke ta daga kafarta ta shiga motar da ya nuna mata ya tayar suka kama hanya

Ko a hanya hira ne BS ya cikata da shi, wanda dadaya take tsinta sai dai ta yi masa murmushi

Cikin nutsuwa ya ce" kin taka sa.a, babar sa.ar rayuwa, wace ba kowa ke samun irinta ba,
A yau na ga abubuwa da yawa, na ga ribar zuciya daya da girman adu.a, tabas a baya na yi sake da na ringa
wasa da Sallah, ashe dai wanda ya rike Allah ba zai ji kunya ko ya wualakanta ba?

Hafsat ta sakar masa murmushi tana mai kallon gari, itafa walahi har wata iska mai sanyi ce take ji tana
ratsa gabanta.....

Muryar BS ce ta tsinke tunaninta a lokacin da ya ce" *me zai hana ki cika min nawa burin nima? 1ki karbi
tayin soyayata ki so ni tamkar yanda nake son ki Uman Malan?*

Tsurawa fuskarsa ido ta yi tana kallonsa,


Menene aibunsa? Dama sallah ce, a yanzu yana yin sallah tun karfinsa,
Idan ta kai warhaka da karfinta a sha.anin kutakale tabas harda taimakon BS

Yana biye da ita ne dan yana matsanancin son ta,


Ita kuwa isan bata so shi wa zata so? Mutun ne shi mai daraja da daukaka, ya kasance mai kaunarta tun bata
zama Bodyguard ba, ya kasance mai kawar da kai a irin halayanta na yau da kulun, ya jure iskancinta kala
kala, baya hukunta ta, baya sakata kwana cikin maza.......yana kishinta, to ita kuwa wa zata samu ya yi mata
irin wannan son?

Kanta ta sada cikin yannayin kunya, abinda bata taba nuna masa ba a hankali ta budi bakinta ta ce"........
*KUTKALE*

*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA
BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct
NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan
number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA
SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN
SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN,
.....* taku ce, Sajida😍😍😍😍

4️⃣3️⃣

Jiki a sanyaye ta ce" idan zaka iya aurena a yanda nake, ka zauna da ni a haka, ni me zai hana na amince da
soyayarka?

Daidai sun karaso aeroprt kennan ya ja ya tsaya yana kallonta,


Wani murmushi ya sakar mata kafin ya ce" da Sire ya salame mu, zaki gan ni, zan zo neman aurenki, zan
koya maki so na domin kuwa a yanzu ba sai an fada min ba, ba soyayata a tare da ke, bana son ki amince
min dan kina tunanin na cancanci haka, ina so ki so ni dan na cika namiji

Shanyayun idannuwanta ta lumshe sannan ta bude motar ta fita

Nan wajen motar suka zauna har aka kawo malan cikin wata motar harda masu yi masa rakiya

Suna sauka basu jima sosai ba jirgi ya sauka , man ya kara kwasar yan Niger suka daga

Malan da Hafsat sai dai su sakarwa junna murmushi lokaci zuwa lokaci

A lokacin da jirgi ya sauka motoci ne suka zo daukan su wa.inda ta yi mamakin hakan,


Sai dai a lokacin da suka zo shiga ta gane daga abdul ne domin mai jagorar motocin ya shaidawa Malan
daga wajen Oga Abdul Jabar ne

Shiru sukai cikin motar mai sanyi ga kamshi su duka,

A lokacin da aka shigo anguwarsu sai ta ringa jin gabanta na matsananciyar faduwa,
Du masu zazaune da ido suka ringa bin motoci ukun dake shigewa da matsiyacin gudu har suka ja suka
tsaya kofar gidan malan

Dubansa ya kai kan Hafsat da ta yi tsuru da ita, gashi wando dogo ne a jikinta sai dan kwalin da ta yane
kanta da riga mai dan dogon hannu aman kuma bata da wani tsayin a zo a gani
A hankali ya ce" bakya murna ne???

Da sauri ta kai dubanta kansa, sai kuma ta sada kanta,


Tunaninta idan ta fita a irin wannan shigar da wannan yannayin me mutanen anguwar nan zasu kaleta da
shi? Ta tabata koda za ta bi layin da ihun rantsuwar ba daga yawon bariki take ba, ba wanda zai yarda sai
dai ma a kara tsanarta

A hankali malan ya ce" menene mamana?

Idannuwanta da suka cika da kwallah ta dago ta kali mahaifinta,


Sai da ta ja hanci sannan ta ce" Abana, idan na fita a haka, zan kara jaza maku zagi ne da kai da mamana

Murmushi ya saki wanda daga zuciyarsa ya fito, a cikin ransa ya furta alhamdulilah, ko ba komai duniya ta
ladaftar masa da yarinyarsa, yo da da ne ko shigar da ta fi haka muni zata saka kafa ta fice abinta ba abinda
ya dame ta da wai kar a zageta ko ta ji kunyar wani ba, a haka kuma idan mai tsautsayi ya yarda ya yi mata
wani kallo su cashi junna

Hannayenta malan ya riko yana kallon yanda du ta takure kanta, cikin nutsuwa ya ce" ki ji tsoron Allah
Uwata ba wani ba, kin ji? Mu tafi

Ajiyar zuciya ta sauke tana kallon yanda Almajirai suka tataru suna masu nuna murnar gannin malan ne ya
dawo harda yan rakiya a yau tsal , da yake yama ta yi sosai mutane du sun dadawo daga nema

Malan ya fara fitowa , nan ya shiga mikawa jama.ar hannu suna gaisawa cikin harda baban dansa

A hankali ta sako kafarta mai sanye da takalmi sau ciki mai dan tudu baki kirin na aiki

Gaba daya hankalin mutanen ne ya fara yowa wajen, a haka har ta fito gaba dayanta

Ai kuwa magangannu ne kasa kasa suka fara tashi, ba dan ba.a saba ganninta da shigar wando da riga ba,
ba dan ba.a saba ganninta da takalmi , kai kanta ko fan kwali bata sakawa a da aman a yanzu da dan
kwalinta a rufe a kan hakan bai hana mutane mamakin ganninta harda fadin ta dawo daga yawon kennan
Wasu kuwa kasa kasa su ce ita kuwa ba zata shiryu ba jiya i yau? Duniya ta horata kennan?
Kiri kiri wajen ya nemi hautsinewa da dan hayaniya dan kuwa har matan anguwar sun fara lekowa ganewa
idannuwansu wai da gaske UWAR malan ce ta dawo?

A hankali ta zagaya mazan nan da suka tare hanya ta shiga cikin gidansu

Tana shiga ta tarar da wata bakuwa bakin baban fanfon tsakar gidan ta tara abin wanke shinkafa tana tarar
ruwa da alama girki take yi

Tsayuwa ta yi tana bin gidan da kallo, dan kwata kwata ta shagala da shaukin ganninta a gidan ko salamar
ma ta kasa yi

Matar ce ta tsura mata ido tana kallonta dan bata santa ba, batama taba ganninta ba kanwa take a wajen
daya daga cikin matan malan ta zo hutun makaranta ne

A dan kiririce ta ce" ke, ke kuwa wacece malama zaki shigo gidan mutane da irin wannan shigar tamkar
arniya ko an fada maki gidan nan yana daukan arnawa ne??

Da sauri ta kai dubanta kan matar, dai dai nan matan gifan suka fara fitowa jin hayaniyar nan, haka kuma
daidai lokacin malan ya shigo cikin gidan

Gannin Hafsat tsaye ya ce" aa, Uwata me kike tsaye nan sai kace baki san waje ba?

A daidai lokacin da ta juyo dan kallon malan kunnayenta suka jiyo murya a hankali cikin zazakar muryar
nan irin nata an ce" *ANMIH*

Da sauri ta juyo haka kuma lokaci daya ta damko hannun mahaifinta


Shima tsayuwa ya yi suna kallon mahaifiyarta dake sanye da wani zumbulelen hijab mai ruwan milk wanda
ya rufe mata ilahirin jikinta sai hannunta da fuskarta dake waje,
Tsaf tsaf da ita sai yar ramar da ta yi aman fatar jikinta lufluf daga fuskar da kuma hannayen

Sai da ta lumshe idannuwanta, hawayen dake ciki suka fito sannan ta dago mata hannayenta irin ta zo din
nan

Hannayen malan ta saki ta daga kafarta da mugun gudu ta je ta fada jikin mahaifiyarta lokaci daya kuma ta
fashe da kuka.....
Tana kukan ta ce" baki yi fushi da ni ba? Ashe ba zaki juya min baya ba? Du laifin nan da na yi maki
Ummana?

Bayanta take taping a hankali, sai a lokacin ta tuna a tsakar gida suke kuma ta tabata abokanan zamanta na
wajen,

A hankali ta zame jikinta a nata dan a duniya irin mugun kawaicinta da kunyarta? Tana zamewa ta sada
kanta bata kuma kallon kowa ba ta shige ciki tana share hawayen kukan farin cikin da ta yi,

Tana shiga Malan ya saki murmushi, yana matsayin girmama lamarin matar nan tasa a nan gidan duniya,
sam bai bata labarin inda mamansa take ba, rana tsaka ta shigo gidan da shiga irin ta wada ba.a so, aman
bata mike ta shiga jaye jayen jafa.i da mugayen magangannu ba sai nuna tsantsar farin cikinta da ta yi har ta
kasa boyewa, bata yi mumunar magana kamar cewa daga yawon duniyarta take ko makamancin hakan ba,
sai riketa da ta yi ta nuna mata ta yi missing dinta haka kuma halayanta ba zasu saka ta gujeta ba,

Yana kallo Hafsat ta gaisar da sauran matayen nasa da suka yi cirko cirko wasu na tsoron jarababiya ta
dawo, wasu na mamakin wani abin sai a gidan malan yarinya ta je ta yi yawon duniya ta dawo gida anai
mata oyoyo

Basu iya amsata ba, sai saurin kauce mata suka bata waje ta shige wajen mahaifiyarta

Juyawa ya yi ya fice a gidan bai ko amsa gaisuwar da suke yi masa na sannu da zuwa ba, dan ba zai iya
rufe ido a irin lamarinsu ba

Babar dake cikin matansu ce ta kama habarta ta ce " to fa, uwar masu gidan ta dawo mun shiga uku da
ranmu kowace ta yi ta kanta domin a kanta malan sai ya saki mace ko ya tsinewa d'a

Nan fa suka shiga cicira maganar wanda hakan ke iske har inda su Hafsat suke , tana zaune mahaifiyarya
sai kwararo adu.o.i take tana godewa Allah

A wannan rana mahaifiyarta ta kai mata ruwan wanka masu dumin gaske, ta tsaya ta yi wanka sun dawo
daki, ta bata man zafi ta shafe jikinta haka kuma ta saka abin gasa jiki ta ringa gasa mata gefen fuskarta, ta
bata madara hade da maltina ta shanye sannan ta yi mata shinfida saman gadonta dakinta ta kwonta saman
lalausan bargonta kafin ta rufa mata lalausan bargonta ta kuna mata panka

Ajiyar zuciya ta ringa saukewa tana hangen mahaifiyarta ta tsura mata ido, bata tambayeta daga ina take ba
har yanzu, du dai wani takunta tana biye da shi , sai dai abu daya da maman nata ta yi mata shi ne a lokacin
da ta fito a wanka ta dawo daki ta umarceta da ta kwonta zata dubata,
Bata wani damu da hakan ba, hasalima bata san me hakan ke nufi ba dan kuwa ta jima tana mata irin haka
ko can baya, irin idan ta cika daren nan da safe sai ta duba ta,

A lokacin da ta gama dubanta kuwa sai ta ga murmushi kan leben mahaifiyar nata, tabas mama ta yi farin
cikin abinda ta gani hakan ya sakata kwonciya itama a lokacin da ta fahimci Hafsat ta yi baci itama ta
kwontar da hakarkarinta
A washe gari ba ita ta farka ba sai wajen karfe tara dan kuwa tsakiyar dare al.adarta ne ya tasheta ta kimtsa
kanta ta koma

Wanka ta fito ta yi cikin nutsuwa sanann ta koma dakin mahaifiyarta

Har kasa ta duka tana gaishe da mamanta hakan ya sakata tsayawa tsai cike da mamaki tana kallonta,

Kasa rike tambayarta ta yi, dan haka ta ce" *ANMIH, INA KIKA JE? ME YA SAME KI? ME AKAI
MAKI?*

HAFSAT ta dago da dubanta, ko a yanzun doguwar rigarta ce cikin kayanta na da ta saka, rigar bata
matseta ba dan bata kara jiki ba saima daidaituwar halitarta da ta yi sai dai rigar bayanta gaba daya a bude
yake, ahigar sam batai mata dadi a ranta ba,

Jiki a sanyaye, muryarma a sanyaye ta buda baki zata yi magana ta kasa, ta kara budawa zata yi sai kawai ta
shiga inda indar da bata saba ba, haka kuma jikinta ya dauki rawa, muryarta ne take rawa sosai a lokaci
daya ta ce" *MAMA*

muryar mahaifinta da ya kasa hakurin jiran har su je gaishe shi ne ta katseta a lokacin da ya ce" *UWATA?
*

A tare suka juya , shi kuwa ya tako ya shiga cikin dakin a nitse, sai da ya kali Hafsat din sannan ya kalli
mahaifiyarta ,

Da hannunsa ya yi mata nuni da ta zauna,

Cikin nutsuwa ta zauna jikinta a sanyaye dan ta tsorata da abinda ya tsoratar da yarinyar nata har haka
harma ta kasa magana,

Sai da malan ya kara dakin sannan ya zauna cikin nutsuwa ya ce"""


*KUTKALE*

*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct
NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan
number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA
SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN
SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN,
.....* taku ce, Sajida😍😍😍😍

4️⃣4️⃣

Cikin nutsuwa malan ya yi gyaran murya ya shiga labartawa mama duka kaf abubuwan da Abdul ya fada
masa, da kuma gannin idonsa da ya yi, harma ya tina mata lokacin da ya zo ya fada mata a yau mamansa ta
ziyarce shi, mamansa na raye dan kuwa a masalaci ya ji a jikinsa ita din ce

Idannuwanta cike da hawaye ta kai dubanta wajen da Hafsat ke zaune a saman cafet ta sada kanta sai zubar
da hawaye take,
A hankali ta ce" Allah ya kara shiryar da ke, ya maki albarka, ya baki miji na gari

Hafsat ta dago kanta da sauri ta saka idannuwanta cikin na mahaifiyarta, gaba daya maman nata ta yi wani
irin sanyi bata zaci zata zama haka ba, tana shashekar kuka ta ce" mama, uncle din Abdul aziz ne, shi ne ya
kai ni gidan kason gagan yan daba dan kawai na mari matarsa, mama ba zan taba yafe masa ba, ya
wulakanta ni, ya tozarta ni, ya kai ni gidan halaka wanda Allah kawai ya fitar da ni

Mama ce ta gala mata harara ta ce" ko komawa zaki yi ki kara daukan fansa?
*UNMIH* ba zan so ki koma irin rayuwarki ta da can baya ba, kin ga taurin kai, jayaya, masifa, raina
maganar manya sun bada gudunmuwa wajen saka ki a wannan jarabawa, shiga gidan kaso na abin kunya
bane dan kuwa kadarar bawa ne baka isa ka kauce masa ba, sai dai abin lura me kika koyo a can? Yaya kike
son tafiar da rayuwarki a yanzu? Mace kike, rayuwarki kadan ce, kar ki yi tsamanin kyan nan naki zai yi ta
karuwa ne, daidai da gashin kankin nan zai ringa ja baya a hankali a hankali ne har ya dawo kadan, fatar
jikinki zata janye, idannuwanki zasu jeme, furfura zata yi maki salama idan har kin dace! Ki rufa bakin ki,
babu rufin asirin da ya kai na kariyar da Allah ya baki, Allah ya baki kariya Unmih ke kin sani...nima na
sani...nan gaba kowa zai sani, kar ki yi garajen da Allah zai barki ya ga yanda zaki yin! Tashi malama ki
fice min a daki ga kys din dakinki an gyara , je ki zan neme ki!

Jiki a sabule ta mike ta karbi kys din dakin a hankali ta shiga takawa tana kuma waiwayen malan aman ga
mamakinta bai daka tsawar kar a yi mata fada ba, saima kawar da kai da ya yi tamkar baya wajen
Bakinta ta zumburo ta daga kafa ta fice a dakin tana fadin lale malan ya daina son ta

Tana fita malan ya kurawa mama ido yana kallonta,

Kanta ta sada kafin take kamo dan yatsarta ta shiga dan ja,

Malan ya ce" to a huce a kaina mana da za.a saka min uwa gaba daga dawowarta a fara yi mata ihu ana fitar
mata da ido? Ni madame me ya sa karfinki kike nuna shi a kan UWATA NE?

murmushi ta saki a hankali, ta dago da idannuwanta da sukai jajajir,


Sai da ta sauke ajiyar zuciya sai kuma ta fashe masa da kuka marar sauti
Murmushi malan ya yi yana kallonta ya ce" menene na kukan kuma?

Sai da mama ta yi dan kukanta wanda tamkar na shagwaba kafin ta sasauta tana kallonsa ta ce" tsoro nake
ji, du wannan rayuwar da Anmih ta gani bai saka ta daina fada ba, ji fa ita nan har tana gannin ramuwar da
zata yi ta huce? Ramuwa ta fi ta barwa Allah ya saka mata?

Sai da ya lakaci hancinta yana kallonta ya ce" shekarun ki arba.in da bakwai da wata hudu da kuma kwana
ashirin da biyar yau maman Uwata, aman har yanzu akoy rigima.........
Ki kwontar da hankalin ki, adu.ar nan dai da muke yi in sha Allah ba zata kuma ba, ai yanzunma Allah ya
dawo mana da ita lafia ba karfinmu ko dabararmu ba ko?

Kanta ta gyara a hankali sai kuma ta shiga sauke ajiyar zuciya

A kadan dai sai da Malan ya jima dakin mama yana ta yi mata nasiha sai da hankalinta ya idasa kwontawa
sosai sannan ya mike ya kalli agogon hannunsa ya ce" yau ban ga ana shirin zuwa turakata ba

Murmushi ta yi tana rufe idannuwanta irin ta ji kunyar nan, hakan ya saka malan kara sakar mata murmushi
ya juya ya fice a dakin, har tsakiyar ransa yana so ya je ya ga kar a je fadan da mamanta ta yi mata tana can
tana kuka, kai a duniya da ake cewa ko cikin yaya Allah na saka maka kaunar wani ta fi ta wani, haka yake
jin kaunar mai sunnan mamansa har baya iya boyewa, dalilin wannan ne ya saka shi daukan damarar
boyewa ko a gaban mahaifiyarta ne bale a cikin yan uwanta da sauran matansa ko za.a shafa mata lafia

Bayan kwana hudu.....

Hafsat a kilace take cikin gidansu, an yi gumurzun an kare an yi rigimar da tashin hankalin an kare, an yi
yawan maganar da tsegumin du an lafa, masu jiran su ga ta tsiro da dabanci kala daban daban sun ga shiru,
Abdul aziz ya yi sau ya fi a kirga bai ga ko kalar mai kama da ita ba bale ya ganta, kai hasalima ta zama
kawar mamanta da kuma yayarta

A yanzu du zama da tashinta tana lure da kyawawan dabi.un mahaifiyarta, idan aikin mamanta ne takan
shiga ta zabga masu girki na ji na gani mai dadin dandano a zuba kowa ya ci da sabon taste wa.inda ta koya
a wajen Formation na zama bodyguard

Bata da waya, bata damu da rikewa ba , ita ta kanta take sai a yamacin yau mahaifiyarta ta mika mata
wayarta ta da wace masoyinta na da wanda sanadiyarsa ta afka tashin hankalin rayuwa

Ta jima tana juya wayar kafin ta kai ta saka a caji ta ci gaba da sha.aninta

A rana ta shida mai dinki wato hajia Farida ta kawo dinkunnan da mama ta bata ,
Ai kuwa dinkuna ne masu shegen kyau rufafu tsararu sannan na gayu masu tsadar gaske,
Ba karamin farin cikin kayan nan ta yi ba, haka ta hau sama wajen mahaifinta dan yin godiya, tana zuwa ya
kara mata abayoyi kala biyar masu shegen kyau na yayi dukansu masu botira da mayafansu bakake masu
tsari

Kanta kawai ta sada ta rasa bakin magana, a hankali ta dago da idannuwanta sai ta ga mahaifin nata na
kallonta yanai mata murmushi, ba komai yake jin dadinsa ba sai yannayinta na yanzu, wai mamansa ce ke
nuna farin ciki dan an saya mata sutura, yarinyar da a da hayowa zata yi, ba ruwanta da neman izini sai dai
ta afka idan a gaban wa sai dai ta fadi muradinta na kudi ta karashe da fadin" kuma a bani ko na je
saurayina ya bani!
Sai gashi yanzu a gidan duniya Allah ya nuna masa ita tana godiya harma ta rasa bakin godiyar

Hannunsa ya daga mata dan ya tabata tana iya yi masa kuka a gurin , shi kuwa baya so , dan haka ta mike
har ta kusa fita ta tsinkayo muryarsa ya ce" su ABDALLAH zasu dawo gari da zama karshen satin nan,
kwana biyu ina tsaye kan saukar alkur.ani a gidan da zai zauna , kulun muna zuwa a sauke a yi sadaka dan
gudun fitinar zamani
Sai da gabanta ya fadi, a ranta ta ayanna me kuma zai dawo da shi kasar Niger?

Kafadunta ta daga a lokacin da ta tuna asalin dan niger din ne shima fa, haifafan garin ne, haka kuma
dangin da suka rage masa yan nan ne wato matarsa da kanwar mamansa

Bata baiwa Malan amsa ba sai karasawa da ta yi da murnarta suka dadaga kayan da mahaifiyarta kafin su
shiga yi masu turaran wuta da adu.ar Allah ya sa a mora lafia

Bayan kwana goma

Kwonce take tsakar dakinta wajen karfe biyar na yama, juyi kawai take tana tunanin wai yau zata yi zance,
zancen ma da BS, zuwansa biyu sai yau Malan ya bashi damar ya zi su gana

Mikewa ta yi zaune tana kallon madubin dakinta mai tsayi, kanta ta girgiza ta koma ta kwonta gashi har
karfe bakwai din ta kusa,

Tana nan kwoncen har karfe shida ta buga, buda kofar da aka yi ne ya sakata mikewa zaune tana kallon
yayarta da ta shigo da yaronta da ya fara rarafe yana yawonsa ko.ina

Bayan sun gaisa ne yayar tata ta bita da kallo,


Can ta ce" Maman malan, ni ba bako aka ce zaki yi yau ba?

Hafsat ta dubeta ta ce " eh

Yayarta ta ce" to ya haka baki shirya ba

Hafsat ta kaleta da mamaki ta ce" shiryawar me kuma auntu ? BS ne fa??

Sai da ta rike habarta sannan ta yi dariya ta girgiza kai ta ce" dan BS ne shine ba zaki kimtsa jikinki ba?
Oya tashi tashi malama

Mikewa Hafsat ta yi tana kallonta kafin ta shige ciki ta dauko abaya daya daga cikin abayoyin Aba ta saka
abinta a nan sannan ta shiga saka turarukan wutar da ta miko mata

Tana kokarin yana mayafin dan kwalin ta tsayar da ita ta zauna ta dan gyara mata fuska da kwalinta sannan
ta yana mata dan kwalin a kanta

Tsaf hafsat ta fito tamkar ba ita ba, wani irin kyau ne ya bayanna a tare da ita wanda ita kanta sai da ta shafa
gefen fuskarta sannan ta yi murmushi

Ana fitowa sallar magariba aka suka zauna tsakar gida inda malan ya basu minti talatin su gana

A zancen nan Hafsat banda tambayoyi a kan aiki ba abinda ta tsare BS da shi, shi kansa sai ya kasa wani yi
mata zancen soyaya sai da ya tashi tafia ne ya ce da ita" Hafsat, ina son na turo a yi komai da wuri a gama,
dan kin ga malan baya son dogon zance

Sai da ta ji gabanta ya fadi, ta dan tsura masa ido aman sai ta kasa ce da shi komai,

Murmushi ta sakar masa sannan ta shige ciki da dan gudu gudu hakan ya saka shi sauke ajiyar zuciya ya
juya ya tafi ya shiga galeliyar motarsa yana tunanin sai dai a waya ya mata maganar aikinta da kuma
dukiyarta
Can wajen karfe biyun dare, dare ya tsala Hafsat na zaune tsakiyar gadonta daga ita sai dan gajeran
wandonta da yar rigarta na barci ta yi zuru da wayarta a hannunta tana dannawa tana game

Message ne ya shigo mata kamar haka " *KAURIYATA, NA KASA BACI*

kurawa harufan ido ta yi tana kallo, bugun zuciyarta ne ya canza lokaci daya hannunta ya fara rawa,
Du duniya ba wanda ke haye mata irinsa, shi ne, walahi shi ne

Wayar ta ajiye tana kallon rubutun tamkar wanda ya yi da hannunsa idan hasken wayar zai dauke sai ta
danna ta kara kallo

A hankali ta rubuta " *ME YA HANA KA BACI?*

mikewa ya yi zaune daga kwoncen da yake yana mai hararar wayar, kafin ya rubuto " *ke, gida kika je kika
tara samari haka? Bakya dan jan aji daga yi maki magana har ki bani amsa ko kin sanma da wa kike
magana ne?*

A lokacin da ta karanta sai da ta saki murmushi, sannan ta rubuto" *na san ko kasuwa na yi a tsakiyar dare
irin na barawo? Dole bazawara ta ringa damka da karfi karfinta mana*

Wani uban tsaki ya ja a lokacin da ya karanta message din,

Zama ya gyara ya shiga dandankara magana son ransa, har ya so saki sai kuma ya koma da baya ya zauna
ya jinginar da kansa jikin bed din, ajiyar zuciya ya sauke yana kallon waje daya sai kuma ya rubuta
message kamar haka" *Na yi missing din ki amaryar BS*

Numfashinta ne ta fara ji yanai mata sama sama, lokaci daya kuma ta koma ta mike kafafuwanta saman bed
din , sai da ta yi mika nitsatsiya sannan ta rubuta message kamar haka.........
*KUTKALE*

*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........
*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct
NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan
number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA
SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN
SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN,
.....* taku ce, Sajida😍😍😍😍

4️⃣5️⃣

Sai da ta yiwa kanta fada kan irin rikicewar da ta yi dan kawai ya rubuto mata haka sannan ta rubuta" *NI
KUWA, BANA JIN KEWAR KA*

murmushi ya saki , sannan ya ki bata amsa ya dai kurawa magangannun su ido yana kallo haka kuma
Na.ima dake gefensa tana kallonsa bata dai san me yake yi a waya ba, aman kuma ta ga ya bada hankalinsa
sosai hasalima bai san ta farka daga bacin gajiyar da ya tara mata ba

Hafsat dake jiran gannin amsarsa na ya rama da fada fada ta ji shiru sai abin ya dameta,
Tunani ta yi kan yanzu fa ba aiki take masa ba, mutun ya nuna damuwarsa a kanka bai dace ka yi masa
abinda zai iya taba ransa

A hankali ta rubuta message kamar haka" *Yaya jikin ka?*

Mikewa ya yi zaune yana murmushi mai sauti, sannan ya bata amsa da" bani da lafia ne?

Hafsat ta yi shiru da wayar a hannunta, ajiyar zuciya ta sauke sannan ta rubuta" *malan meye wai? Zakana
wani neman bani wahala ka manta da maman malan kake magana?*

Wannan karron har sai da ya buda hakoransa wajen murmushi, a fili ya ce" come on, relache toi, i really
miss yannayinki,

Na.ima dake kallonsa ce ta yi motsi irin wanda zai saka shi gane ta farka

A hankali ya kai dubansa kanta, bata sanye da riga sai gajeran wando baki mai santsi
Yan berayan mamanta ya kalla haka kawai lokaci daya siffar Hafsat ta fado a ransa

Wani irin mikewa ya yi tsaye ya rintse ido lokaci daya, a hankali ya yi baya baya ya jingijar da bayansa
jikin garun wajen,

Sai da ya jima a jaka kafij ya buda idannuwansa ya ga dai kuri shi take kallo

Takowa ya yi inda take ya tsaya mata kerere yana kallonta ya ce" ki daina zamarmin ba riga dan Allah, idan
nemanki na yi ina gamawa ki saka rigarki....hakan zai sama min kwonciyar hankali

Yana gama fada ya juya ya nufi bayi ,


Da kallo ta raka shi tana mamaki halayarsa,
Mikewa ta yi ta shiga saka rigar a kasan zuciyarta kuwa ayyanawa take cewa.... ban san yaushe zan
fahimceka ba, tanzun kuma wane zan yi? Nan ka ce da ni na ringa zama ba kaya, nicema nake saka wandon
nan dan ba zan iya zama haka ba, kuma yanzu kaine da cewa na ringa saka kaya hankalinka zai fi
kwonciya?

Tana gama sakawa wayarsa ta dauko ta ajiye masa gefen gado ta yi tsuru tana kallon wayar, da wa yake
magana? Da wa yake nishadi har haka? Wacece ita? Wata dabara, wani irin kyau, ko wani irin iya girki ta
iya wanda ya saka shi sakewa da ita har haka?
Gabanta ne ta ji ya fadin mata lokaci daya, ta sani ba tun yau ba ko ba dade ko ba jima Abdul sai ya kara
aure dan kuwa a da can ma ta san da ba mijin mace daya bane bare a yanzu da yake jajan wai dama haka
take da son jiki?
Tsoro ne ta ji ya rufe mata zuciya lokaci daya, in dai wannan da yake magana da ita budurwarsa ce kuma
aurenta zai yi ai kuwa da zaune bata sameta ba, tabas da ta hadu da tsayuwa kennan, dan tana tunanin auren
so kennan, ganninsa ma zai iya yi mata wahala

Tana cikin tunanin ta ji ya janyota baya, wato saman bed din, gaba dayanta ta tafi jikinsa a hankali ya saka
hannunsa cikin rigarta sannan ya ja hannunta ya kai wani sashe na jikinsa daban wanda ya sakata jin
gabanta ya kwonci kwonci ya fadi, aman da yake yanzu ta gama daukarwa kanta niyar gwada juriyar sai ta
rintse ido ta shiga bashi hadin kai du da irin tarin tsoron kasancewarsu abu daya,

Hafsat dake jiran amsa shiru shiru haushi ne ya isheta, cike da jin haushi ta ajiye wayar kasa ba saman bed
dinta ba dan kuwa an hanata ajiye waya kusa da kai dan babu kyau yana hadasa rashin lafia

Kwonciya ta yi saman hannunta na dama bayan ta gama adu.ar baci ta yi shiru tana kallon waje daya

Wani uban tsaki ta ja ta mike ta zauna saman gadon tana kallon waje daya

A fili ta saki wata yar karamar dariya kafin ta tafa hannayenta, hannun nata ta dago ta zunguri kanta a fili ta
ce" Hafsat baki da mutunci, ke da zaki yi baci kina mai yabon ma.aiki aa sai kawai ki je duniyar baci kina
hangen rayuwarki ta Bodyguard? Rayuwar ta hatsari? Wace har harbi akai maki a can? Wajen da kika hadu
da dan rainin hankalin nan wato Abdul?

Kanta ta girgiza ta ce" to ki yiwa kanki fada, ki yi aurenki ki tafi abinki, ki je ki yiwa BS biyaya, .....

A daren nan ta jima tana kokowa kafin baci ya dauketa , hakan ya sa da asuba sai da mama ta shigo dakinta
da kanta ta tasheta tana yi mata fadan cika dare dan kar ta fara makara a sallah kuma!

Ranar Lahadi da yama wajen karfe biyar Hafsat ta gama shirinta tsaf cikin sabin suturunta sannan sabin
shiga a wajenta wanda ta mayar shigarta na yanzu wato Abaya

Ta yane kanta, fuskarta ta gyarata daidai misali ba abinda ta saka mai yawa ko mai daukan hankali sosai
aman a banza dan kuwa irin yanda hankali ke kaiwa kanta abin ba.a cewa komai

Ta jima duke dakin malan tana shafa fatiyar adu.ar tsarin da yake ta binta da ita, shi kam dan an fito masa
da cewa haka zata yi ta zama a gida sannan aka daure shi cewa ai Allah ke tsarewa da shi aka bi, da ba zai
taba yarda ta fita ba sai dai idan za.a kaita dakin mijinta

Sai da ya gama sannan ya dauki kudi jika biyu ya bata tare da cewa ta shiga taxi idan ta gaji

Mama dake tsaye murmushi kawai take zubawa, a ranta kuwa fadi take wai a nan malan gani yake yana
mugun kokari na boye soyayar yar tasa, yanzu ba fita bane zata yi? Ta tabata ta siyarwa kanta jaje kennan,
idan kuwa maman malan ta yarda ta kai magariba to fa tabas zata ga malan a bayanta ya je nemanta

Sai da ta rakata har tsakar gida, kiri.kiri mai dakin tsakiya ta yi dariya a bayane sannan ta ce" wani lamarin
sai a gidan mu, yaro ya je bariki ya dawo a ci gaba da ririta shi ana kara tura shi wani barikin

Ikon Allah ko kallonta Hafsat bata yi ba bale ta nuna ta ji me ta ce ko ta tankata, wannan abin shi ke kara
basu haushi dan irin ta tanka mutun din nan irin na da a yi ta masifa har yayansu su kai mata duka su ce ta
yiwa masu rashin kunya basa samu, du inda ta je din nan ya kware su dan magana ba irin wada basa yaba
mata aman sai ta zama tamkar dutse ta ki motsi ta ki nuna ta ji bare har a yi fitinar da zata fitar da malan ! A
haka basa tunanin zasu ci galaba a burin sakawa uban ya tsaneta harma ya koreta, wau shi malan karfin
imani da daukan kadara ko? Yarinya ta je yawon ta zubar ta dawo masa aman ba wanda ya ji inda ya yi
mata fada da daga murya ma bale a yi tunanin duka da kora, aa sau nasiha da nuna soyaya!

Tsaki ta ja masu mai karfi sannan ta ja gefe ta tsaya tana kallonsu tana son jin me za.a cewa Hafsat

Mama ta kali Hafsar fuska a hade ta ce" *ANMIH,* ki tabata magariba ta yi maki a gida in sha Allah, Allah
ya tsare ki da dukan sharin abin shari, Allah ya kare ki ya shirye ki

A hankali Hafsat ta amsata da amen Mamana, sannan ta juya ta sa kai ta fice tana dariya cikin ranta, sarai ta
gane nufin matar babanta so take ta tankata a dawo kada mata rashin mutuncin, bata san Kutkale da horon
zama Bodyguard ya horeta zama kurma sannan makauniya gaban du wani abinda ta yi niya, sai ta yi niya
zata tanka koma menene, idan ta ki ba zata tanka komai ba walahi!

A hankali take tafia da pos fara kal a hannunta har ta isa bakin titi
Tana tsayar da taxi ta fada masa Butik din da zai kaita sannan ta shiga gidan gaba ta daura belt ya ja suka
kama hanya

Kanta ta sada dan irin yanda fuska da yawa ke binta da kallo irin kugun kallon nan mai sakawa a fadi,
Ta san kallonta suke dan su gane wai ita ce ko ba ita ba?

A haka mai taxin ya tsaya ta cire kudinsa ta bashi ya bata canji a cikin kudin da Malan ya bata

Sai da ta daga kanta ta karanta tankamemen rubutun dake jikin Boutik din kafin ta zagaya a hankali ta je
hanyar shigar

Matar dake tsaye da abin caje mutun ce ta cajeta sannan ta shiga


Sai da ta yi tafia mai dan tsayi kafin ta tura madubin wajen ta shige
Zuwa ta yi wajen accenseur ta shiga domin inda zara yi siyayar dole shi zai kaita ki ta yi ta hawan
matatakala har sai ta hau hawa tara!

Tana fitowa a nitse ta taka ta je wajen da ake siyar da liptom din, lipton din malan kennan, wanda yake
anfani da shi

Gidan Lipton din kansa abin kallo ne, kwaya daya ne ta siyo aka saka mata a jakar Butik din, sannan ta fita
ta nufi ainafin aiken da akai mata wato siyen shada gizner ta babar sallar dake karasowa tata da kuma ta
yayarta wace yayar tata ce da kanta ta kawo mata kudin kan ta je ta siyo masu ta kai masu wajen mai
dinkinta

Tana shiga wajen mai tsaron wajen wani bature ne jajajir da shi da gilas dinsa na karin ganni yana zaune da
jaridarsa a hannunsa yana karantawa da ganninsa saurayi ne mai jinni a jika hutu ya kwonta masa

Wajen shadojin ta je tana dubawa cikin nutsuwa ba tare fa ta yi kwaramniya ko ta tsaya a cito mata ba

Tun fa ta shigo yake kallonta, dan da yawa wasun idan suka shigo sai su wani zarto wajensa su shiga
tambayarsa inda zasu je su dauko abinda suka zo nema bayan ga komai a ajiye idan ka zo zaka kala ne a
katon screnn din kana dudubawa har ka samu wace ta yi maka sai ka nuna a ciro maka ka biya kudin ka
juya abinka aman sai an yi ta basu wahala

Mai ruwan maroon mai manyan zane ta tafi da ita, dan haka sai kawai ta danna daidai ita sannan ta juya ta
je wajen biyan ta ciro kudin a pos dinta ta mika ta tsaya tana jira mai gidan nasu ya bata canjinya ta juya
abinta

Canjin ya taso sa kansa ya miko mata yana kallonta, da yannayin gimshewa ya miko mata makekiyar
wayarsa ba tare da ya yi wani dogon magana ba ya ce" No
Wayar ta kala, sannan ta bi hannayen nasa da kallo masu dauke da gashin jiki sosai kalar fatarsa dan ba
bakake bane gashin a haka har ta kai fuskarsa dake dauke da dan karanmin saje dan siriri
Sai da ta wana idannuwanta tana kallon yanda yake wani tsarewa yana wani kamewa abinsa
A hankali ta yarfe shi da idannuwan nata da suka dauki bakin kwali suka kara fitowa radau da su sannan ta
buda labanta cikin wani yannayi na shegantakar da ta koya wajen Abdul a wani irin hankali ta ce" *Baka da
saje da gemu*

Tana gama fada ta karbi jakar kayan ta juta da canjinta tana sakawa cikin pos dinta

Idannuwansa ya firfitar da matsanancin mamaki sannan ya kali madubin wajen da ya zagaye ko.ina,
Na farko a rayuwarsa an fizga shi, wai bashi da saje, saje kuma a me?
Ina ba zai barta ta tafi haka ba bayan ta zama ta farko da ta ki shi fan saje

Juyawa ya yi wajen yaran nasa ya ga du sun kawar da dubansu a kansa wato suna kallon du abinda ya faru?

Juyawa ya yi ya shiga bin bayanta a hankali jar suka fito bakin inda zata dauki taxi

Shi dai bai gane taxi ne zata dauka ba sai da ya ga ta tsayar da daya yace ba can ya nufa ba mamaki ya kara
kashe shi,
Bama ta da motar kanta? Aman ta iya dizga namiji kamarsa? Ko dai dan ya biyota ne? Aa, ko dai tana da
aure? Ko kuma mata take so?

Shi daya ya yiwa kansa tambayoyin da sun kai biyar aman ba amsa dan haka yake tsaye yana magana ko
zata saurare shi har ta amsa kiran wayar da ajau ta yi mata inda ta fadi sunnan Boutik din fa take sannan ta
ci gaba da neman taxi domin lokacin saukar aikin yama ya yi taxi na wahala sosai bare anguwar yan gayu
taxi na wahala sosai.......
*KUTKALE*

*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........
*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct
NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan
number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA
SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN
SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN,
.....* taku ce, Sajida😍😍😍😍

4️⃣6️⃣

Suna nan tsaye kusan minti ashirin har ta fara kitan layin Malan dan ta fada a zo a dauketa sai ga wata
mahaukaciyar hamer baka wulik ta tsaya a gabansu sai maskin sabuntaka take tana dana ashar din rashin
mutunci ita kadai sai lillon iskanci take tsabar an murxata an yi gudu da ita, bakaken gilas ne a jikinta gaba
da baya hakan ya sa koda wasa ba.a gannin na ciki komai kwakwarka dan sabuwa ce , komanta sabo ne

Daga cikin motar ya kare masu kallo lafin ya sauke gilashin yana jinjina rainin hankalin Hafsat, ta sab sarai
ko waye a motar aman ta wani kawar da kanta tana kallon wannan jajir fin uwa gwonda,

Dariya ya yi a lokacin da yake sauke gilashin ya rage sautin cikin motar ya kali na tsayen
Muryarsa ya dan daga dan zuwa lokacin ta ga dama ta kallo infa yake ya ce" tsakaninka da Allah da
wannan tsatson tamkar zaka karye da kuma wannnan jar fatar taka uwa yumatir ne zaka zo ka tsaya gaban
wannan yarinyar kanai mata bunsuranci kaima ga namiji ko? Yanzu kaima dan iska ne?

Daga Hafsat har mutumen kallonsa suke baki da ido bude,....


Hafsat har sai da ta murje idannuwanta tana kallonsa, dama kiran da ya yi mata dan ya tardota infa take ne?

Kanta ta girgixa ta kara dagawa mai taxi hannu aman ya fice ba tare da ya tsaya ba

Abdul ya sasauta murya ya ce" Kauriyata mu je mana

Dai da ta galawa motar harara sannan ta ce" wai kai haka Malan ya yanka min ragon sunna?

Abdul ya kikifta ido yana kallonta sannan ya girgiza kai ya ce" aa

Ta kebe bakinta gefe sannan ta kawar da kai

Mai jan kunnen nan da wani mamakin kuma ya kalli Hafsat, gannun kamar fitsara ce ta yiwa wannan
fitsararan aman ya bata amsa a sanyaye

Ki shigo mu tafi kin ji?


Abduk ya fada cikin muryar rarashi da kwontar da murya

Motar ta karewa kallo, sannan ta shagwabe fuskarta ta ce" ni aa, ka je kawai

Fuskar ya kurawa ido dan ta yi hakan ita kanta bata san ta yi ba aman ba karamin kashe shi abin ya yi ba,

Motar ya shiga citewa a ky sannan ya ce" idan baku shigo ba, na rantse zan fito na dauke ki na saka ki a
motar nan bayan na fafala maki mari
Hafsat ra kale shi da kyau ta ce" Malan fa? Ya hana ni shiga motar karti!

Sai da ya zazaro ido sannnan ya yi murmushi ya ce" daga wajen malan din nake Maman malan

A hankali ta faga kafarta ta nufi mitar cikin nutsuwa ta bude ta shiga ta zauna
Mai siyar da shadojin nan na tsaye yana kallon ikon Allah yau ya hadu da tantiran da suka fi shi iya
shegantaka har Abdul ya tayar da motar ya harbata bakin titi
Ajiyar zuciya ya sauke ya ce" gaske kike dizga maza!

Abdul na fara tafia ya juyo ya kali Hafsat, bata ankara ba ta ji ya saka yatsarsa ya lakaci man leben da ta
goga a bakinta,

Kansa ya girgiza ya ja tsaki ya ce" kema yanzu sai kwaliya da saka kaya masu maki kyau dan ki yi samari
ko? Samarinma maimakun ki sami jarumi ingarma aa sai wannan lange langen tamkar igiyar leko? Hafsat
kin ji kunya, kin ji kunya kin kara jin kunya!

Hafsat ta lumshe idannuwanta tana jin yannayin wani iri, Abdul ne ya dawo niger da zama? Shine da
walwalarsa? To aman yaya ya yi da damuwar Muhammad? Yaya ya yi da Muhammad?

Abdul ya kaleta ya ga shi ke haukansa ita batama san yana yi ba ya girgiza kai daidai sun tsaya a danja ya
yi shiru

Hafsat ta karkato ta kale shi a hankali ta ce" me ya sa jiya ka min magana kuma ka min banza a waya?
Sannan wama ya baka number wayana ne?

Abdul ya juyo yana kallonta ya ce" number wayarki satowa na yi a wayar malan a lokacin da zai ja salar
juma.a ya banu komai ajiya ni kuwa na koma gefe na sata!
A jiya kuma a daidai lokacin da muke magana da ke madame ta farka, tana farkawa ta jefo min kallon
kauna, lokaci daya na rikice na fita a hayacina, kin san lafia idan ta yi yawa , ga na koshi, a hankali na
kamo matata na kwontar na.....
Niyar Abdul fayace mata abinda ya yin sai horn din mutane ya saka shi waiwayawa ya ja tsaki ya tayar da
motar ya kara daukan titi a nitse yana tafia a hankali

Cikin nutsuwa Hafsat ta ce" sai mun biya ta chateau 9 na kai dinkin Aunty

Kansa ya gyada mata ya dauki hanyar chateau noeuf din, aman yana tafe yana neman fitina yana takalarta
rigima ita kuwa ta yi malakas tamkar ba ita ba

Sai da suka tsaya wajen dinkin ta sauka ta nufi ciki a ranta tana girmama girman masifar Abdul, wai
yaushema ya zama haka ne? Wato duka kaf masifar da yake era mata ne yake sauke mata a yanzu, to wai
inama tuwansa ne? Ita kam ta ga ta kanta

A lokacin da ta bayar , Nadiar ta umarci daya daga cikin yarenta fa ya dauki awon yannayin jikin Hafsat,

Dan kwalinta ta warware dan ta ce a yi mata baban wuya sosai

Daukan abin awon ya yi da litafin rubutawa ya zo da nuyar dauka sai ji suka yi Nadia na gaishe shi ta mike
da kanta tana tambayar dinki aka kawo ne?

Kallonta ya yi yanda man shafe shafe ya bi ya kokona mata fuska, shagon cike da karti sai dinki suke da
wasu irin manyan yan mata irin yan dunuyan nan kowace sai fama take da atach cike a kai ya kada kansa
sannan ya kaleta ya ce" ke baki iya aunawar bane zaki saka wannan ya dauki awonta ko ita tace sai namiji?
Kallonta ta kai wajen da ya nuna, da sauri ta ce" yi hakuti oga,
Sannan ta karasa ta karbi abin awon ta shuga auna Hafsat da kanta

Sai da ta gama Hafsat ta tambayi kudin, nan ta yanka mata tsada sosai na dinkin nasu ita da auntynta , dan
haka ta buda jakarta ta ciro kudin ciki baki daya ta mika mata ta ce zata kawo sauran idan an gama

Yana tsaye yana kallonta har ta gana ta fice ta shiga motar kamar ta zabga masa mari dan haushinsa take ji
sosai,

Daya daga cikin yaran ya yafito ya juya shima ya buda motar ya shiga,

Cofre ya ja ya janyo yan jika goma goma har kwaya takwas ya mika masa ya rufe motar ya kana hanya

Yana kama hanya Hafsat ta kale shi ta ce" Abdul, ya isheka haka ka ji ko? Mme ya shafe ka da dinkina ne?
Makan da zaja ringa yi min ihu a ka wai yarka ce ni? Haba haba, kuma walahi idan ba.a yi min wuyan da
na zaba ba ba zan saka shadar ba, kuma sai ka mayar da ni ma karbi canjina dan ban iya almubazaranci ba!

Satar kallonta yake yanda take daga murya tana dukan cinyarta wai ita nan tsakaninta da Allah masifa take
masa?
Bakinsa ya hade sannan a hankali ya ce" kin zama fitsarara kin gama! Hafsat ba dai ni ba ko? Ni dai ne ko?
Na ji

Shiry ta yi tana kikifta ido tana kallon hanya har suka shigo anguwarsu,

Suna shigowa ta sasauta muryarta ta ce" Abdul, dan Allah ka ajiye ni a nesa da gida na karada gidanmu a
kafa kar a je wani ya ga an ajiye ni a wannan motar a ci gaba da jifana da munana kalmomi fa munanan
furuci ka ji?

Kallonta ya kara yi, yanda ta marairaice, wani tausayinta ne ya ji ya tsirga masa, dan haka ya fage gudun
aman bai tsaya ajiyetan ba

Tun tana kallon kamar zai ajiyeta har ta ga ya iso lusan gidansu,

Sai da ya tsaya kofar gidansu ya danna horn

Wangame get din gidansu aka yi dan ana tunanin malan ne zai sako motarsa, sai dai gannin wannan
wuleliyar mota ta saka mai budewar kansa yayansu tsayawa yana kallo

A hankali ya ja motar ya shige cikin gida da ita,

Motar ya tsayar yana kallon yanda du ake lekowa ra taga ana kallon abinda ke faruwa

Tsoro ne karara ya bayana a fuskarta, harma wata kwallah ta tarun mata a idannuwanta, kallonta ta kai
wajensa a hankali ta ce" ka san a zaginsu wanda ke tayar min hankali har nake tsoron wataran su kaini
bango? Bama son suna saka mahaifiyata a shirmen su, idan sun yi kirana da karuwa shin du lalacewar uwa
zata aiki danta ya je ya yi karuwanci ne? Abdul me ka yi haka? Yaya zaka sako ni har cikin gidanmu da irin
wannan motar? Wa zai ki yarda cewa ni karuwa ce?

Sai fa ya rintse idannuwansa sannan ya bude, bai taba tunanin hannunsa zai kai jikinta ba sai yau, dan kuwa
hannunsa ya daga ya tsinka mata marin da ya sakata saurin saka hannayenta bibiyu ta rufe fuskar cike da
tsoro tana kallonsa

Sai da ya daki kujerar motar hakan ya sa mitar ta dan motsa dan gaba dayansa ya girgiza
Yatsarsa ya nuno mata da kakausar murya ya ce" ba zan lamunce wani ya kiraye ki da wannan sunnan ba
tare da na halaka shi ba kafin ya gama furta kalmar karshe!
Kin ci sa.ar ke ce, kema kuma na farko ne! Walahi Hafsat Muhamadu kika kuma kiran kanki da wannan
kalmar sai na cire harshen daje cikin bakin ki na cinye, idan kika kuma sai na lalata maki rayuwa ta hanyar
hana ki farin ciki, Hafsat Allah ya isa idan kika kuma kiran kanki da wannan kalmar, na tsani wannan
kalmar ga makiyina bale wace na fi a duniya!

Motar ya bude ya saka kafarsa waje daya, har jikinsa rawa yake dinkin kaya blu fin shada ce a jikinsa harda
hula ta mugun karbarsa
Har ya juya zai fita ya dawo yana kallonta ya ce" dama motar malan ce da aka kawo, idan kin yi niya ki fito
ki shiga ciki, iran baki yi niya ba ki zauna ki dawama a nan!

Da kallo ta bi shi har sau da ya fice yayansu na kallonsa sannan ta lumshe idannuwanta hawayrn suka shiga
bin kuncinta,

A hankali ta waiga nan gabanta ya kara bugawa dan gannin du sun firfito sunna tsaitsaye ba wanda babu
cikin matan gudan da yayansu ciki kuwa harda bakuwar kanwar aunty amarya

Jikina ne ya dauki rawa gannin mamanta na nufo motar.....


*KUTKALE*

*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct
NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan
number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA
SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN
SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN,
.....* taku ce, Sajida😍😍😍😍
4️⃣7️⃣

Jikinta ne ya dauki rawa gannin mamanta ta nufo motar,


Kanta ta sada da sauri ta shiga murza yatsutsanta, ta saka a ranta ne tata ta kare, sai da ta yi mata nasiha,
sannan tun da ta dawo kulun famanta nuna mata ta karyata abinda ake fadi a gidansu da kuma anguwarsu

Shirun da ta ji ne ya sakata dan dago da kanta,


Tsai ta tsayar da dubanta ga al.ajabin da take hange,
Malan ne da amininsa ladan, da kuma mama a gefe tana amsa gaisuwar Abdul da ya duka har kasa kansa a
kas yana gaisheta,
Malan ne da kansa ya yi kiranta ta fito su gaisa da mutumen da Hafsat ta yiwa aiki

Ita kanta tamkar wani sirikinta sai kara gyara zumbulelen hijabin jikinta take tana amsa masa cikin nutsuwa
inda kunyarsa ta lulubeta dan ba karya abdul akoy cika ido da siffar kamilin mutun

Sai da suka gama gaisawar Mama ta yi ciki kusa da yan uwanta, nan malan ya fara shiga ya ga kowace da
shigar kamala ba wace ta yi shigar da zai ji kunyar nunata dan haka ya kara yiwa Abdallah iso ya shige
suka shiga saman malan
Gannin har an fito a sallar magariba sun kasa bata waje ko zata fito ya sakata ziro kafarta a hankali ta fita a
motar da lipton din malan sai yar pos dinta

Bata kula kowa ba ta shige bangarenta ta nufi dakinta

Tana shiga ta fada bayi ta zauna ta shiga kuka, ita kanta bata san kukan me take ba, mari dai a gidan duniya
ba kalar wanda bata sha ba, ta sha dukan balakima bare wani mari can?

Sai da ta ji muryarta na shakewa sannan ta sasauta ta kunna ruwa ta wanke fuskarta ta dauro alwallah ta fito
a dakin

Sallah ta tayar cikin nutsuwa ta gabatar sannan ta mike saman bed ta kashe wayarta gaba daya ta shiga
neman hutu

Abdul kam sai da matan malan suka hau da kansu daya bayan daya suka gaisa, ya gabatar da shi a matsayin
wanda Hafsat ke gidansu
Ido ido suka ringa yi kowace na ciki na ciki har malan ya salame su suka fito a dakin

Sai da Abdul ya kusan raba dare dan kuwa sun jima da malan suna tataunawa kan lamarin duniya, kafin ya
mike ya sauko bayan sun yi salama da malan ya roki da ya yi zamansa ba sai ya raka shi ba

A lokacin da ya sauko ya dan jima yana kallon kofar da ya tabata ita ce ta mama, kuma a ciki dakin Hafsat
yake,

Sai da ya ga daren na kara yi sannan ya juya ya fice a gidan ya tarda direban da ya kawo masa wata motar
har ya fara baci bawan Allah ya tashe shi suka tafi

Ko da suka karasa gida wanka kawai ya yi, ya gabatar da shafa.i da wuturi, ya gama adu.o.insa, har ya zo
shafawa ya lumshe idannuwansa, wata adu.ar ya yi kamar haka" ya Allah, ka kare ni da mugayen mutane,
Allah ka bani amini mai tsoronka wanda zan shiga aljanah dalilin zumuntar mu, Allah ka raba ni da
mugayen mutane

Bugun zuciyarsa ne ya ji na neman canzawa sakamakon kokarin tuno irin abinda ya faru tsakaninsa da
Muhammad da kuma irin hukuncin da ya yi masa, da sauri ya dauki carbinsa ya shiga jan salatin annabi
*MUHAMAD SALALAHU ALAIHI WA SALAM*, yi yake ba kakautawa, a hankali ya ringa jin nutsuwa
na ratsa masa zuciyarsa har ya nemi damuwarsa ya rasa
Bai tashi a wajen ba sai da ya rokawa malan gamawa da duniya lafia, domin shi ya bashi sirrin salatin
annabi, da ba dan ya riki sirrin nan ba da bai san idan ransa ya baci ina zai tsoma ransa ya ji dadi ba

Sai da ya kwonta saman bed dinsa, yana rintse ido ya ji passsssss


Karar marin da ya sakar mata,
Da sauri ya buda idannuwan nasa,
Hannunsa ya daga yana kallo, hannunsa na dama wanda da shi ya mareta,
A hankali ya mayar da hannun ya ajiye a fili ya ce" aman me ke damun zuciyarki Hafsana? Me ya sa kika
zuran ido baki ce da ni komai ba? Na mare ki, na yi maki ihu a kai duka kina kallona baki bani amsa daidai
da ni ba? Da gaske sunna mugun takura ki a gidan nan? In dai dalilinsu kike cikin yannayi na rashin
walwala zan saka a yi maza a yi aurenki ko na maido ki nan a matsayin bodyguard dina har a maki aure ki
yi tafiarki gidanki,

Wayarsa ya dauko yana kallo, sunnan BS dake cikin wayar ya kurawa ido,
Ya so ya rubuta masa message sai kuma ya fasa,
Juyawa ya yi ya gyara kwonciyarsa da niyar idan ya kai gobe lafia zai nemi BS, zasu yi da wajewa idan ya
auri Hafsat ya wulakanta masa ita walahi sai ya yi shara.a da shi! Dan rainin hankalin banza dan rainin
hankalin wofi, dalilin wulakantata da Muhamad ya yi ba zai yarda kowani kato ya wulakantata a gidan aure
ba, idan da hali zai saka camera dan gannin irin zaman da suke dan kar ya je ana cutarta a yanda ta zama
lusarar nan yanzu ta rufe ta kasa fadi!!!!!!!!! (Sannu baba)

Sai da mama ta gama salolinta ta shiga dakin Hafsat, nan ta tarar da ita ta yi wani kwonci a takure tana baci
sai sauke ajiyar zuciya take

A hankali ta shafi gefen fuskarya da ya tasa kadan, ya kumbura irin an daketan nan, kura mata ido ta yi cike
da tausayawa , ko wa ya dake ta? Me ya hada su?

Ledar Boutik din da ta je ta buda ta ga Lipton din da ta siyo,


Murmushi ta yi ta mayar mata da kayanta ta mike ta fita a dakin tana mai yi mata fatan alkhairi a kasan
zuciyarta

Bayan Hafsat ta yi sallar asuba wanka ta kuma yi ta canza kayan jikinta na baci, ta saka hijab dinta na
sallah ta dauki ledar lipton din malan da canjin jika biyun da ya bata na taxi ta fito

Daya daya cikin yaran gidansu ke wulgawa jifa jifa domin safiya ce karfe bakwai da wani abu gashi ba
makaranta,
Da ido suke binta, ba wanda ya gaisheta cikinsu dan kuwa iyayensu sun fada masu daga yawon banza ta
dawo kar wanda ya girmamata, gashi dama ta girma fiye da yanda malan ke barin yayansa mata su kai bai
masu aure ba, hakan ya sa du suke mata wani gani gani sannan suka yarda da maganar iyayensu

A hankali ta karasa kofar dakin mahaifinta, hannunta ta saka ta tura kofar da salama a bakinta
Tana shiga ta ringa jin maganar hajia, uwar gida kennan ran gida , matar malan ta farko tana magana kamar
haka" aman malan yaya zaka ringa nuna rashin adalci a tsakanin yayanka kiri kiri? Nan Zakari tafia ce ya
yi neman kudi dan ka hana shi da ya dawo ba irin abinda bai gani ba da ni kansa mahaifiyarsa,
Aman malan ita yar gwal din shekararta nawa bata gida ba aure akai mata ba ba karatu aka kaita ba ba
dawan makaranta aka kaita ba? Rana tsaka a dawo da ita cikin yayanmu kananu a shigo da ita cikin gida
gaban kowa a ringa yi mata oyoyo ana murnar dawowarta ana rungumarta ana nuna mata farin cikin
ganninta , malan baka tsawata ba, baka tara yayanmu baki daya ka yi fada ka hukuntata ba, baka nuna wani
bacin ranka ba, hasalima kilaceta ka yi ka yi mata dinkuna, bata yi mana aikin fari bare na baki a cikin gida
tana nade a daki tana cin abinda ta yi muradi, tana shan abinda ta ga dama, karshe malan da girmanta
shekara kusan ashirin da biyu har damar ta zauna tanai maka zance a cikin gidanka da wani kato wanda ba
tsaresu ake bare a san me suke yi ko suke cewa ba, malan a jiya a kawo mana wani gabjejen katon da bashi
da fara.a ya zo ya tsaya a gabanmu kikam yana harararmu wai a gidansu ta zauna, a fadi haka a gaban
yayanmu warwararu da kananu, malan kwakwaluwar yara me ake so su dauka? Me zai hana su suma gobe
su tafka tsiyar da ta tafka su kuma dawo mana gida kai tsaye? Koda yake su sun san ba yayan so bane ba
zasu yi hakan ba, aman gaskiya malan korafinmu kawai a san abin yi, idan da hali a fitar da ita a kaita can
wajen dangi har a yi mata aure, ko a maida ta gidan su yaron da ya zo jiyan muga idan shi iyayansa zasu
aminta anai masu irin haka a cikin gida ba aure ba komai!

Malan dake zaune, tun da ya bata damar magana shiru ya yi yana sauraronta har ta gama,
A hankali ya shiga bin sauran matan da kallo, kowace na zaune kusa da ita da alama shawara aka yi na
abinda za.a fada masa , sai aka baiwa wace ta fi kowace tsaurin ido da rashin tsoron zuciya ta fada masa,
Dubansa ya kai kan matarsa, mahaifiyar Hafsat, kanta a sade yake, ko daya ba.a gannin fuskarta bare a
gane yannayin da take ciki, sai yatsutsanta da take ta murzawa tana karawa tamkar wa.inda take son canza
masu kalar fatarsu dake jikin hannun nata,

Dubansa ya kara kaiwa kan matarsa, wace ita ce ya dace ta zama mai datako, mai tsawatarwa mai tausasa
muryarta mai nasiha gare su da shi kansa, aman kananun sun turota ita ce yau ta buda baki, ta daga
muryarta sama da tashi, ta gaigaya masa magangannu irin haka a kan *Uwa*, shi da yake rayuwa a takure ,
yana boye nuna soyayar mamansa a gaban yan uwanta dan a zauna lafia ashe bai tsita ba? Shi da yake nuna
kowani da da ya haifa daya ne a wajensa ashe ba tsira ya yi ba? Me ya ragi yayansa da shi? Bukatunsu,
tarbiya, ilimi, ko walwalarsa? Ba wada ya hana masu, kowane ya basu wadatace kuwa,
Me suke so da shi ne? So suke ya rufe Mamansa da duka kan laifin da bata aikata ba? Ko a kan zarginsu
suke so su dawama harma suke ikirarin ya fitar da ita daga gidansa ? Mamansa? Mamansa ce suke so ya
wulakanta haka?

Ajiyar zuciya ya sauke mai karfi wace ta saka mama dago da kanta a hankali ta saci kallonsa idannuwansa
sun kada sun yi jajir, tausayinsa ne ta ji ya kama ta, haka kuma sai ta ji haushin Hafsat din, tun tana karama
ake irin haka a kanta, a da yana da karfi da yarinta a yanzu da ya fara manyanta ma ba zai huta ba? A bar
mata mijinta ya huta haka, in dai a kan Hafsat ne in sha Allah idan bata samu miji bama ita zata kaita inda
ta kaita, in sha Allah zata samu ya yarje mata ta kaita nesa da gidan ko kowa zai kwontar da hankalinsa a
kan kishin zamanta a gidan da suke, kallonta ta kawar, idannuwanta je suka sauka kan kwalin lipton din
nasa da ta ajiye ta juya,
Gabanta ne ta ji ya fadi, kar dai a je ta ji? Dama akoyta sabkon zuwa wajensa su yi karatu kafin su yi ta
hirar duniya, yakan yi mata labarai su sha dariya, yakan yi mata bayanin dukiyarsa , kai harma da shawara,

Kanta ta sada, sai kuma jin muryar malan ta yi ya ce"


*KUTKALE*

*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE


BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct
NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan
number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA
SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN
SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN,
.....* taku ce, Sajida😍😍😍😍

4️⃣8️⃣

Cikin kakausar murya aba ya ce" ku tashi ku tafi

Kowace sai da ta kale shi, baki mama uwar gida ta kebe kafin ta fara mikewa da sauri ta yi gaba kasa kasa
kuwa sai guna guni take

Bayanta suka rufa baya , sai mama kawai a zaune kanta a sade
Aba ya kawo dubansa wajenta, cikin kakausar murya ya ce" ba nace ku tafi baki dayanku ku bani waje ba?

Da sauri ta mike tsaye tana maida kukan dake cin zuciyarta,


Juyawa ta yi har ta kusa fita a dakin ya ce" daga yau a fara shirya Uwata, in sha Allah zan karbi kudin
aurenta karshen makon nan!

Mama kam kanta kawai ta gyada ta fice a dakin, wannan shine a dakeka a hanaka kuka, shi dama malan
idan ransa ya baci kowama hadawa yake ya hukunta ba ruwansa abinsa,
Yanzu dai sun jaza masu fada da fushin malan, a kan mamansa ransa na kololuwar baci fa!

Sai da suka fita baki dayansu Malan ya dauki katuwar wayarsa irin rakani bayi din nan mai hasken tsiya ya
latsa numbobin ya samo sunnan da yake nema ya danna kira

Abdul dake zaune yana shan lipton dan safiar yanzu ta waye a wajensa ya daga kiran cikin nutsuwa ya yi
salama

Sai da suka gaisa a mutunce sannan malan ya sauke ajiyar zuciya cikin yannayin nutsuwa ya ce " ka yi
hakuri na yi maka kiran samako ko?

Abdul ya ajiye dan abin shan lipton din dake hannunsa ya gyara zama tamkar malan din na gabanshi ya ce"
aa, ai na jima da farkawa malan

Malan ya ce" masha Allah, dama ina so ne na fada maka, ka fadawa wannan yaro mai neman auren Uwata,
idan har da gaske yake ya turo da magabatansa, sannan ina so ka taimaka min wajen bincike kamar yanda
ake yi

Shiru Abdul ya yi, har sai da malan ya dubi wayar yana fadin ko dai bai ji ba network din nan da bashi da
tabs
Abduk ya sauke ajiyar zuciya ya ce" in sha Allah malan zan shigo idan na sauka a aiki

Salama suka yi Abdul da malan, nan Abdul ya mike ya nufi dakinsa dan kimtsawa ya tafi wajen aiki

A lokacin da ya fito suka hadu da Na.ima, ta sha doguwar riga ja mai duwatsu, rigar ta bi dan jikinta mai
tsari, kokarin karasawa dakinsa take suka hadu a nan falo

Hannunsa ya saka ya kamota jikinsa, goshinta ya sakarea kiss ya shafi gefen fuskarta kafin a hankali ya ce"
zan tafi wajen aiki

Idannuwanta ta lumshe kafin ta ce" zan yi missing dinka

Murmushi ya yi mata sai kuma ya juya daga shi sai ky din motarsa ya dauki hanya

Ya yi aikin awa uku, a kampaninsa na atampa daga nan ya dauki hanyar doguwar tafia,
Hankali kwonce yake ratsa jejin har ya karaso dan nesa kadan da wajen sannan ya sauka ya daga
hannayensa sama sakamakon mai tsaron da ya kurma ihun ya daga hannayensa sama sannan aka shiga
tambayarsa waye shi, wa ya zo nema, wa ya gwada masa wajen?

Shi dai a tsaye yake har suka karaso inda yake suka shiga da shi wajen horon bodyguards din suna masu
taka tsantsan da mamakin waye shi kuma daga ina ya zo masu wajen sirrin nan?

Sai da aka yi jiran GN ya zo sannan suka sake shi bayan ya bada umarni

A hankali suke takawa GN da shi, cikin yannayin mamaki GN ya ce" yaya aka yi ka kawo kanka wajen
nan?

Abdul ya kale shi ya ce" a ranar da aka maida mu tare da mahaifiyata, tun a ranar na saka maku abinda zai
nunan inda kuke dan tsaro,
A ranar na san inda kuke ba.a dai yi falilin da zan zo bane sai yanzu

GN ya jinjina kai yana kallonsa, wato dai shi bai yarda da kowa ba?

Abdul ya ce" waye BS? A ina iyayensa? Ta yaya ya zo base? Menene halayensa?

GN gabansa ne ya ji ya fadi yana kallon Abdul,


Tsoro ne ya ji ya kama shi kar a je BS ya janyowa kansa wani balakin?

Abdul ya juya ya fuskanci GN da kyau , ya yi masa wani kallon dake nufin shi yake sauraro

GN ya sauke ajiyar zuciya ya ce" BS, bazabarme ne, domin ni ne mahaifinsa, mun same shi ne da
mahaifiyarsa a lokacin muna soyaya, Allah bai yi zan aureta ba aka aura min wata

Abdul ya kafe shi da ido cike da mamakin wai ashe BS dansa ne? Aman yaya aka yi bai amsa sunnansa ba?
Duda ya ji ya ce ba da aure ya same shi ba,
Kansa ya girgiza ya furzar da wata iska daga bakinsa, shi kam bai san me ke damun mutane ba, ya sani
akoy kadara aman wai har wata kunya yake ji a yanzu ko me?

Tsaki ya ja a fili ya ce" yaya aka yi ya ci jarabawar zuwa wajen nan, harma ya zama Bodyguard soldier?
Shin takardubsa suka bashi dama ko babansa?

GN ya kali Abdul ido cikin ido, sam bai ga tsoro ko alamun zai risina masa ko dan ya girme shi, dan haka
gwara ya fito a mutun ya bashi du wasu informations kan questions dinsa, fatansa dai ba wani laifi ya yi ba
Bakinsa ya buda ya zayanewa Abdul du wata tambaya tasa a nan a inda suke tsaye dan GN ya so su karasa
su zauna abdul ya ce sauri yake

Sai da ya gama Abdul ya gyada kansa ya ce" masha Allah

GN ya ce" aman, sire wani laifi ya aikata ne?

Abdul ya kale shi, sai da ya gama nazartarsa sannan ya daga kafadunsa duka biyu ya ce" bai aikata ba
tukunnan, ka bashi sako yarinyar da yake neman aurenta idan har da agske yake mahaifinta ya ce ya fito a
cikin satin nan a yi komai a gama, idan kuma ba da gaske yake ba, abinda nake so da shi shine ya janye a
hankali, ba tare da ta zubar da hawaye dalilin hakan ba, dan na tabata zata samu wani idan shi baya yi

Yana gama fada ya mikawa GN hannu suka gaisa sannan ya sakar masa fuska suka yi salama tare da
mutunta junna suka rabu

Abdul bai koma gidansa ba masalaci ya je, yana zuwa ya tarar da Malan zaune da jama.a ana ta karatu dan
haka ya gaishe su kawai ya juya ya koma gidansa

Da dare bayan salar isha.i suka shigo da malan, sai da suka zauna Abdul ya fadawa malan cewa ya je, ya
binciko, in sha Allah ya fadawa mahaifin yaron idan har sun tashi auren da gaske to su fito

Malan kam godiya ya ringa yiwa Abdul, wace har sai da ya gaji da amsawa

Sun jima zaune suna hira jefi jefi, sai malan ya ji Abdul ya ce" wani abu ya faru da ita ne?

Malan ya kale shi, sam bai gane wa yake nufi ba, aman gannin ya yi jim ya saka shi cewa" wa fa?

Abdul ya dago yana kallon malan, shi fa gaskiya ba zai cewa Hafsat wai mama ba, shi kuma ba zai kama
sunnanta kiri kiri gaban malan har a je ya daina gannin mutuncinsa ba, dan haka sai ya ce" ita wace za.a
yiwa auren

Malan ya kada kansa yana murmushi ya ce" Abdallah, bana son yaro ya ringa yi min dogon zance a gida, ai
kawai idan yi yake ya fito a yi a gama, idan kuwa ba shi ne rabon ba sai ya bada waje ko zata sami wani ya
aureta itama ta je ta raya sunnar ma.aiki

Abdul ya gyada kai sannan ya kawar da dubansa, wani haushi ne ya ji yana ji, wai ko ta samu mai aurenta,
Hafsat din rasa mai sonta zata yi ne? Yarinyar mai daraja mai hankali mai ilimi mai kyau? Me ta rasa a
jikinta na mace har da malan ke son saka gagawa a lamarinta?

Yau bai cika dare ba ya yiwa malan salama,

Yana saukowa ya hadu fa ita tana shanya saman igiya, ita daya ce kwal a tsakar gidan da yake lokacin
kamar da sanyi sanyi kowa yana daki ya labe, itama wankin kayanta irin dogon wando ne ya sakata yi da
dare sannan ta kwashe da wuri dan basa barin kananun kayansu na shawagi a tsakar gidan, wannan
mahaifiyarta ce ta yi mata wannan horon

Tsayawa ya yi ya harde hannayensa duka biyu yana kallon yanda take dukawa ta matse kayan sannan ta
mike ta shanya saman igiya, har dira take dan ta gyara shanyar da kyau

Idannuwansa ya lumshe a hankali ya furta" ANGEL

Hafsat dake shanyarta bata ma san yana wajen ba, sai da ya ga hakan ba gyara shi zata yi ba da sauri ya
matso inda take ya tsaya a gabanta tana shanya kayan tana juyowa suka kusan hada kirji

Da sauri ta ja baya tana kallon sa


Murmushi ya sakar mata a hankali ya ce" wanki kike ne? Ina mai wankin ki?

Kin bashi amsa ta yi , saima juyawa da ta yi ta dauko wata shanyar zata shanya

Kara matsawa kusa da ita ya yi ya ce " wai fushi ake da ni ne?

Hafsat ta tsaya da shanyar tana kallonsa,


Abdul ya saki murmushi ya ce" yi min murmushi kin ji?

Hafsat ta zabga masa harara tana kallonsa sannan ta shanya kayanta

Zuwa ta yi ta dauki bokicin karfen ta zubar da dan sauran ruwan cikin bokicin sannan ta juyo da niyar
tafiarta

Da sauri ya kama kunnayensa ya ce" na tuba, dan Allah ki min magana ko daya ce Hafsat

Hafsat ta kale shi sama da kasa sannan ta juya ta yi shigewarta cikin dakinta

Ji yayi gaba daya hankalinsa ya tashi, a hankali ya lalubi kofar ya fita ya shiga motarsa ya ja,

Tukin dai kawai yake, aman gaba daya kunnayensa sun rikice, bukatarsu shi ne su ji muryarta,
idannuwansa kuwa su ga murmushinta,

Hannun nasa da ya mareta da su ya kara kallo, sai kawai ya kai yatsarsa guda wajen bakinsa da niyar
cizawa
Ko me ya tuna, ya fasa ya ci gaba da wani irin tuki har ya karasa gida

Yana shiga gidan wayarsa ya dauka a cikin motar ya shiga kiranta,


Tun yana kirga kiran da yake mata tana reject har ya daina irgawa ya zauna kawai bakin bed dinsa ya cire
belt din wandonsa ya bale mabalin rigar ya dan sasauta wandon kasa ya dafe gaban goshinsa da hannunsa
yana kara gwada kiranta hankalinsa a kanta gaba daya

Can ta daga, cikin wata irin murya mai cike da kasala da sangarta ta ce" Abdul, ka barni na yi hira da mijina
mana, yaya ina waya da shi kana kirana sai titit yake ya kasa jina yanda yake so

Idannuwansa ne ya lumshe, a hankali yake jin maganar na girmama a zuciyarsa, kamar da wasa ya ringa jin
maganar tamkar ta zagi mahaifiyarsa , wani irin dacin maganar yake ji,
A kasan ransa ya maimaita" *tana hira da mijinta?*

Zuciyarsa ce ya ji ta wani irin bugawa, a hankali ya ce" ki yi hakuri kin ji? Ki daina fushi da ni Hafsana

Ita kanta yannayin yanda muryarsa ta fito sai da ta ji gabanta ya fadi, a hankali ta janye wayar a kunnenta ta
duba shi dai ne,
Mayar da wayar ta yi a kunnenta ta yi shiru tana sauraronsa, sai wata irin ajiyar zuciya take saukewa wace
ke sauka da lumfashinta tana dirar masa har kahon zuciyarsa

Ji ya yi idannuwansa sun yi masa wani irin nauyi, a hankali ya ce" ba zan kuma marinki ba, kar ki hora ni
da fushin ki Hafsat

Sai da ta ja numfashi kamar wanda ya toshe mata lumfashin nata ta ce" ba dukan da ka yi min ya tsorata ni
da kai ba Abdul

Abdul ya yi saurin cewa" menene?


Hafsat ta ce" irin yanda ka nuna rashin damuwarka a halin da zan shiga da kuma mamana bayan na fada
maka bana jin dadin hakan,
Abdallah, ka san girman matsayinka a wajena? Kai yayana ne, abokin sirina, aminina, Abokina,
Abdallah ina jinka a raina sosai, ni ba zan yarda na saka ka a damuwa ba, aman kai sai ka saka ni ka yi
tafiarka, ka san halin da nake ciki a gidanmu ne?

Ji yake harta gaban jikinsa sun yi masa nauyi, du wani furuci nata sai ya kayar masa da gaba, wai me ya sa
ne ta kasance mai karfin ruguza shi, sannan mai karfin saka shi risinawa? Shin me ya sa take da
madaukakin iko a kan muradinsa da akasinsa?

A hankali ya buda bakinsa ya ce........

Hapoy sallah yan uwana,

Allah ya karbi ibadun mu, ya maimaita mana

*KUTKALE*

*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct
NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan
number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA
SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN
SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN,
.....* taku ce, Sajida😍😍😍😍
*KUTKALE*

*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct
NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan
number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA
SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN
SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN,
.....* taku ce, Sajida😍😍😍😍

4️⃣9️⃣

A hankali ya kuma iya daga bakinsa ya ce" Hafsat... ..

Wani irin jan sunnan ya yi, ya karasa shi da ajiyar zuciya wanda ya hakan ya saka Hafsat rungume fillow
din dake kusa da ita ta lumshe idannuwanta baki daya ta shiga neman saisaita lumfashinta, domin gagarar
buda bakinta bale har ta iya amsawa ta yi

A hankali ya ce" bani da uwa, mahaifina yana jin kunyata da ba zai iya kuma rayuwa tare da ni ba,
Na tara dukiyar da ni kaina ban san adadinta ba,
Ina kwana da sannin ni ba kowa bane dare daya mala.ikan mutuwa zai zare raina na zama gawa

Shiru ya yi kafin ya ce" a da na zauna zaman ni sai na ga mace an min asiri, ko wata rana sai na ga wani
kalar tsiraicin daban bayan na kwana da sannin mai kallon tsiraici baya tsufa da ido, tun a gidan duniya
bare irin girman hukuncin da zan tarar aman haka nake tafe watara na hadu da yarinyar da na haifa da
cikina, wata rana na hadu da wace ta haife ni da cikinta aman da yake aikin shedan ne haka zan zauna na
bita da kallo har ta gama karanta min karatun nata na zubar da najasar tawa a kasa kusa da abin wankana!
Hafsat, sai da kika zo rayuwata na fara fahimtar eh lale idan da asirima to ni kaina na baiwa abin gaskiya,
Hafsat ke ce ta biyu bayan mahaifiyata da nake jin kunyar ki kama ni ko ki san irin halin da nake ciki daga
bakin lokacin da na fahimci kina tare da ni da zuciya daya da niyar gama aikin ki lafia ki yi gaba abinki
Hafsat ba irin kalar iskancin da ban nuna maki ba aman sai ki juya abinki ko idan abin ya yi maki tsauri
take kike wanke ni tas bakya raga min harma ki zubar da hawayenki dan takaicina
Ina sane, ina sane da dukan motsin ki,
Hafsat, ba zan iya hadiye abu a kanki ba, ba zan iya kawar da kai a dukan wani wanda zai cutar da ke ba,
Ban san dalili ba, har ji nake lumfashina zai tsaya idan na ji ki a damuwa,
Abin haushinma sai kawai kike son canzawa daga matakin mai kare yancin kanta ki koma wata mau tsoron
mutun, ban kai hanuna fuskarki ba sai tukukin haushin kin kirayi kanki da muguwar kalma, Hafsat, koda a
ce haka kike ina nufin kalmar nan ke din ita ce ta haramta ga kowani mutun ya fade ta, ina iya soya masa
idannuwa dan ubansa!

Wani irin tsam tsam tsam ta ringa ji a gaba daya jikinta, lale ta yarda da maganar nan cewa a duniya ka ji a
damu da kai ba karamin jin dadi bane bare ka gani da idannuwanka,

A hankali ta ce" kai mafadaci ne Abdallah

Murmushi ya yi, wanda bai yi shirin yinsa ba, wai Hafsat ce ke cewa wani yana da fada

Sai da ya gama murmushin ya ce" takura maki ake a gidan nan ko? Me suke maki ne? Wa da wa ke maki?

Ta so sakin baki dan fada masa , sai dai a likaci daya kwakwaluwarta ta tina mata wanene shi, da kuma
magangannunsa ba cika baki bane yana iya aiwatar da alkawarinsa ko furucinsa,
Dan haka sai kawai ta ce da shi" ba wani abu ni dai ka taya ni da adu.a samun saukin rayuwa

Haka suka yi ta tautaunawa har kusan raba dare, sai da ya ji yannayin saukar numfashinta ya canza, a
hankali ya ce" baci ki ka yi?

Shirun da ya ji ne ya saka shi sakin murmushi a fili ya kai dubansa agogo, karfe biyu har da rabi, adu.ar
baci ya yi mata wato ta tsari daga wayar da niyar Allah ya kai mata domin suna tsakar hirar bacin ya yi
awon gaba da ita ta gaji ainun gashi ya tsareta har wannan lokacin

Da duku duku, da duhu duhu kamar yanda ya saba jiransa har ya karaso yau har tarbo shi ya yi

Tun da ya hango shi ya tabata akoy abinda ke faruwa dan kuwa mahaifinsa nasa na kiyaye a ganshi tare da
shi ko dan kar a san a yanda ya same shi ya jaza masa matsala a ma.aikatarsa

Motarsa ya bude ya shiga , kafinma ya gaishe shi sai ya ji ya balbale shi da fada kamar haka" lale lale
Bashir kana wasa da wuta! Tun lokacin da ka je yi masa aiki na gargadeka cewa wannan mutumin da kake
gani basaja yake dan kar a gane meye asalin aikinsa, na bayana maka ko waye shi mai gidan mai gidanka
kuma ubanka ne shi! Aman da yake cikin kwakwaluwarka majina ne cike shine har kake son sako shi a
lamarinka? Har ya kasance shi zai yi bincike kan yarinyar da kake so kuma? Yaushe zaka daina zuwa
gidajen yan mata kana nuna kana so ? Nawa ka saka har muka je tambaya ka dawo ka fasa? Nan yarinyar
nan har ciki kuka zubar kuna soyaya daga baya ka watsar da ita da ka gama samun abinda kake so, shine
yanzu tsautsayin tozarci ya kai ka ga afkawa wajen da zaka tonawa kanka asiri ka tona min? Waima yar
gidan wa ka je ka saka kanka a ciki da har ya saka shi tasowa da kansa da niyar yin bincike a kanka?

Haushi, takaici hadi da kishin lamarin abdul ne ya turnike BS, haka kuma haushin mahaifinsa ya kama shi,
shi ya san du abinda ya saka babansa a taro a taro din nan dan baya so duniya ta san ya haifi dan gaba da
fatiya ne, aman ba komai zai nuna masa shi din ya iya iskanci
A dake ya ce" yarinyar nan ce da ka kawo daga prison *KUTKALE* na horata ta zama bodyguard

Da sauri ya kale shi,


Kansa ya girgiza sannan ya ce" lale a mahaukatanma kai baba ne, ka san da shugaban kasar nan ya yi kira
cewa a kurce sunnanta a matsayin mai laifi ko mai bashin kasa a kanta? Yarinyar da ta gagari yan ta.adar
Kutkale? Yarinyar da ta fito lafia daga kutkale? Ta zo nan ta zama zakararsu? Yarinyar da ta tsare mutuncin
kanta take adu.ar Allah ya tsareta?

BS ya ce" wannan abinda take nuna mana kennan! Ni kaina da farko na dauka hakan ne, aman daga bakin
lokacin da ta fara yiwa Abdul aiki na gane cewa itama watsatsar ce sai dai bata haraka sai da manya,
yarinyar da ta bi Abdul kuma ta kare da abokinsa? Idan ba aikinta ba ta ya ta gane shi ne mai neman
rayuwar Abdallah? Idan ba kwaratanta ba ta yaya muka tarda ita a yannayin da muka tarda ita? Ta raina
arzikina ne, bata san ba wanda ta gama watsewar da shi ba aurentan zai yi ba! Eh na je gidansu, kuma ina
son aurenta dan haka a aura min ita ba ruwan kowa

Ikon Allah kawai yake kallo kafin ya ce" ka sani, ni kaina mai tsayawa shara.a da kai ne idan ka cutar da
rayuwar yarinyar nan, bare na tabata ba za.a rasa mai iya wujijiga namanka ba, dan ka sani *yar kamilin
datijo yar kuma baban gida ce*, yanzu fice min a motar nan tun kafin ka hadasa min wani ciwo!

Bakinsa ya tabe, sannan ya fice a motar, yana kallo babansa ya shige cikin gidan horon da motarsa sannan
ya kara tabe baki a fili ya ce" idanma iskanci ne ai gado na yi, kuma yan mata yanzu na fara haye ruwan
cikin du wanda ta dagan buje! Itama wancen tunda na lura ba zan samu dan arzikina ba zan aureta na haye
ruwan cikinta na ga meye banbancin sa da na sauran da har ake min iskanci a kansa, dama dama ni na
zubar da cikin ban bari ta haifo min dan ba! Kai da ka haife nin sai na saka ka a uku!

A haka ya gama magangannunsa na rashin kunya sannan ya aro fuskar jarumin namijin ya kutsa kansa cikin
wajen da yana shiga du suka shiga bashi girma suna kauce masa har ya isa inda zai hori yaren

Bangaren Hafsat bata ga wani canji daga wajen BS ba, yakan kirayeta su sha hirarsu, hirar soyaya, bai taba
kauce hanya wajen yi mata hira ba, yakan nuna mata soyayarsa tsakani da Allah ne, tsantsar tausayinta da
nuna mata so ya saka ta ita kanta fara shakuwa da shi,
A haka har ya yi sauran kwana uku a kwanakin da Malan ya diban masa kan ya turo da magabatansa su zo
neman aurenta da komai sai dai shiru ba.a irin daya daga cikin manyansa ya zo dan jin karin haske a batun

Abdul kuwa, ya zamewa dangin Hasfat tashin hankali, bashi da lokacin shiga gidan malan, kowani lokaci ta
raya masa zai zo gidan malan ne ya dauki kujeru ya ajiye kasan katon dalbejiyar gidan mai sanyin ni.ima
wace da yawancin lokuta matan sukan zauna a nan aman kirikiri wajen ya haramta wa su sai dai su hade a
daki hajia uwar gudan malan su yi abinda suke yi a labe, abin na basu mamaki, na basu takaici irin yanda
malan ko yayan cikinsa bai sake masun da zasu ringa shiga gidansa a lokacin da suka yi ra.ayi ba ko dan
yayansa mata aman sai gashi wani garjejen kato dan kawai hannunsa na rike da hatimin nasara ya mayar
masa da gida wajen zama sannan ya saka wannan tsaura idon a gaba har ka ringa hango hakoranta tana
washkala dariya , dariyar da ba.a san me yake ce da ita ba, duda rabonta da ta yi wata shiga ta ba daidai ba
tun da ta dawo aman ai ba daga shigar mutun abin yake ba!

Fitowa ta yi daga dakinta cikin nutsuwa ta shiga dakin mahaifiyarta,


Yayarta ce zaune tana ninke kayan da aka wanke kafin a kaisu guga , yaronta kuwa yana can cikin kuryar
dakin da mahaifiyarsu tana neman kaeanfanin da ta saka aka siyo mata mai yawa ta raba biyu fan baiwa
yarinyar nata rabi dan anfaninta sai wasansa yake ita kuwa tana taro shi

Da murmushi ta karasa kusa da yayar tata ta zauna itana ta dauka ta kade ta shiga ninkewa,

Kallonta yayar tata ta yi tana murmushi ta ce" amarya amarya


Itama kallonta ta yi, ta kawar da kanta a hankali ta ce" aunty gabana na yawon faduwa a duk lokacin da
kika kirayeni da wannan sunnan, wai dama nima zan yi aure? Na auri mai sona haka? Harma na yi tunanin
samun yanci?

Murmushi ta yi, ta ce" bawa baya cire rai da rahamar Allah, koda ace zaman kanki kikai kika hayayafa
Allah zai baki malamuncinki bale yanda kowace y'a take haka kike? Ina so a kaiki gidanki da raina da
lafiata auta, zan so na ga takun rayuwae aurenki na tafia cikin salama

Murmushi ta yi har hakoranta suka bayana fili , sai kuma ta sada kanta irin ta ji kunyar nan

Shigarta yayar tata ta kala, sabuwar abaya ce mai ruwan ja mai duhu ta yane kanta da dan kwalin abayar, ta
yi kyau karshen kyau a haka bata shafa komai ba koda kwali ne

Tana shirin yi mata magana sai ga mahaifiyar tasu ta fito, kallonsu ta yi kafin a hankali ta ce" Anmih, yaya
haka? Wancen bawan Allahn ba ke yake jiraba?

Bakinta ta dan cuno gaba ta ce" mama, fada fa mukai da shi jiya a eaya shine yau zai wani zo min haka
kawai mutun sai neman fitina bayan na fada masa ya fita a harkar yan gidanmu, cewa fa ya yi zai zane yaya
fa, kuma a gabansa da gaban hajia, kuma ya fadawa Aba cewa wai shi ya girmi yaya aman ya shigo gida
bai gaishe shi ba shi zai xane shi idan ya ci gaba da yi masa rashin kunya, yanzu mama tsakani da Allah
abdallahh ba zai shiryu ba? Yayanmu mu duka gidan zai zane? To mu mu shiga ina da ranmu? Baya gudun
rigima sam, sai kace gidansu wai ya shigo gida bai gaishe shi ba
Ta karashe tana turo baki

Dariya auntynta ta saka sosai har tana rike cikinta, ta nunata da yatsarta ta ce" zan so na ga idannuwan
hajiar gidannan, wai wai wai za.a zane mata elhaji a gabanta, kuma a cikin gidan ubansa

Mama ta harareta ta ce" ke ba zaki girma ba ko? Bana so


Ki ce da Abdallahn ni nace dan Allah ya yi hakuri ya daina biyewa kowa a gidan nan, idan kuwa dukan ne
ya daki anmih dan kuwa ke ce bakya jin magana, maza tashi ki je ku zauna dan na tabata zaman nan da
bawan Allahn nan ke yi a wajen nan dan kawai ya tare maki rigimarsu ce, kin ga kuwa da sauki dan ni
kaina an jima ba.a zage ni ba bare ke.................

5️⃣0️⃣

Aunty kam murmushi take ita kuwa ta karasa ninke na hannunta ta juya tana tura baki gaba waima kar ya
ga damarta ta fice a dakin

Murmushi aunty ta yi tana duban mamansu ta ce" ina mamakin shakuwarsu, mutun baban mutun irin
wannan, da farko aban Fahad na fada min ko shi waye a kasar nan na ji tsoro ko wani abin yake kawo shi
gidannan? Sai dai irin yanda mu.amalarsa da malan da kuma ita kanta Maman malan abin sai ya fara yi min
haske, a hankali na gane shi din ne mai saukin hali domin kuwa da akama shi ya saka maman malan
nutsuwa

Tun da ta tunkaro inda yake zaune ya tsayar da danna wayar da yake ya tsura mata ido,
Yanda ka san ta zauna ta tsara yanda halitarta zata kasance mata ,
Daga sama ba wani mugun tudu aman daga kasa ko batai niya ba sai sun shaida kansu

Kawar da kansa ya yi, dan baya so ya ringa irin wannan tunanin, yau dai alhamiss ce in sha Allah a gobe
za.a zo tambayar aurenta a yi a gama shikenan
A haka ta karaso ta zauna bayan ta yi salama ciki ciki

Shareta ya yi ya ki amsa salamar a bayane saima ya fitar da wayar ya ci gaba da dadanawa

Ta kai dubanta kansa ya fi a irga , sai da ta gaji ta ce" meye?

Shiru ya yi mata ya ki kallonta

Hafsat ta ce" Abdallah, menene wai?

Dago da kansa ya yi, ya zuba mata manyan idannuwansa masu zama da launin ja kusan koda yaushe
sannan ya ce" Hafsat, kin yi kyau

Bakinta ta turo ta ce" ba mun yi fada ba, shine ba zaka bani hakuri ba?

Abdul ya tabe bakinsa ya ce" shikenan kulun sai na ringa baki hakuri bayan nine yayanki ke kuwa
kanwata?

Kanta ta juyar gefe sai kuma ta sauke ajiyar zuciya ta shiga dan jefa kafarta daya tanai mata gaba da baya a
hankali
Kafar ya kaiwa idannuwansa kallo, yatsotsin kafar sun sha jan lale faratunan kansu sun sha jan lale sun yi
tsaf da su, Hafsat ba dai tsafta ba

A hankali ya dan daga kansa har zuwa fuskarta, ya ga utama shi take kallo irin kallon kurullahn nan

Girarsa ya daga mata a hankali ya dan kane idonsa guda ya ce" kallon fa? Ko na maki ne yarinya?

Bakinta ta tabe a hankali itama ta ce" kallon fuskarka ne nake, cike da kamala kamar ba kai ba idan ka tafka
tsiya wai Abdul ni zaka zane yayana? Kuma ka fadawa malan kiri kiri

Baya ya yi ya jijgina da kujerar da yake sama ya ce" ai kece yayanki, ni kuwa na girme shi, kuma ni ba
soyaya nake da ke ba bale na kama kafarsa kar ya hana min , ke kanki dan bana iya dukanki aman da ina
iyawa na fara kwalo da ke Hafsat sai na kwonce maki kusoshin kai kwaila kawai!

Idannuwanta ta zaro waje ta ce" ni ce kwailar?

Abdul ya ce" eh ke din,

Haushi ya kama ta, zata rama wayarta t shiga kuka,

Tana gannin sunnan BS ne ta gyara zamanta ta daga kiran

Sosai ta sanyayar da muryarta ta amsa masa,


Cikin nutsuwa ta shiga baiwa kowace kalma tasa mahinmanci tana sauraronsa

Irin yanda take wasa da idannuwanta da kuma lebenta ya kurawa ido,


Mamaki yake irin yanda take zance da Bashir,

Mikewa ya yi a hankali ya duka ya dauki kys din motarsa da ya yar wajen mikewar ,
Bai kuma koda kallonta sau daya ba ya juya da niyar tafia

Tana nan zaune tana kallonsa har ya bar wajen kafib ta sauke wata nanauyar ajiyar zuciya, ita kam a kulun
tana tausayawa matarsa, zama da abdul wani gagarumin hore ne da za.a baiwa bawa kafin ya mutu bisa
laifukansa , shi bakinsa ya kunshi abubuwan haushi da takaici!
Ranar juma.a,
Yau ne ranar da ya dace a karbi auren Hafsat, wace malan ya yi nuyar idan sun zi zai fada masu a yi abin a
kusa kusa, kai shifa idan da hali sai ya daura mata aure a yau din nan dan bai ga me zai ci gaba da jira ba
shi kam a shirye yake dukan abubuwan da za.a yiwa yar gata ya tanadarwa mamansa sai dai idan fangin
mijin nata ne basu shiryawa hakan ba........

Bayan sallar juma.a, sanye suke cikin shiga ta alfarma, a yau shi kansa Abdallahn ya saka manyan kaya na
gani na fada hakama malan ya saka fararan kaya sai murmushi yake cikin nutsuwa
Manya manyan tabarmi aka shinfida a kofar gida, aka ajiye kujeru inda anguwa ta dauka cewa Malan zai
bayar Da Uwar malan a karo na biyu, hakan ya sa du wani mai jin kwakwaf ya hakarta a wajen mata kuwa
suka ringa shiga cikin gidan, masu zuwa dan zumuncin Allah da taya murna ma du sun halara sai gashi
kamar da wasa gidan malan da kifar gidansa yana neman mugun cikar da ba za.a iya saka tsinke ba

Zaune suke Malan sai Abdul a gefensa na hagu sai aminan malan a na dama, a kan tabarma daya, sai sauran
tabarmin du mutane ne a zazaune ana ta zaman jiran zuwan angwaye

Ana zazaunen nan awa daya ta shige, ta biyu ta shige,


Abdul da malan na yawan duban hanya,

A haka lokacin sallar isha.i ta yi, aka ringa fitar da butoci kofa dan yin sallah wa mutane, nan suka ringa
dauka suna alwallah karshe dai aka gyara tabarmin malan ya ja sallah

Ana salame sallah malan na kallon waje daya, idan ka bincika zuciyarsa zaka ga tana dokawa fiye da yanda
ya dace ta doka

Abdallah ya mike ya fita daga cikin mutane ya ci gaba da neman layin BS, dokawa yake, layin na ringin
sosai sai ya kusan tsinkewa sai a latse shi a kashe kiran,

Zuciyarsa ce ya ji ta fara daukan zafi, a haka ya nemi number GN, shima ya yi ta kira aman shiru tasa bata
shigama bare har a daga

Dawowa ya yi yana gannin yanda ake binsa da kallo, ya ratsa ya shige cikin gidan malan

Yana zuwa ba ruwansa da yanda ake binsa da kallo ya samu ya ratsa matan nan da suka cika tsakar gifan ya
shige bangaren mama

Yana zuwa bai tsaya wata wata ba ya shige ya karasa inda mama take zaune saman kujera, gefenta Hafsat
ce nanade da lafaya ruwan maroon ta dukunkune kanta sai sauke ajiyar zuciya take, sai yan uwanta mata
uku ciki harda aunty suna zaune jigum jigum

Karasawa ya yi inda mama a


Ke zaune ya tsuguna a gabanta hakan ya saka du suka juyi suna kallonsa banda Hafsat da ta kara labe kanta
a ranta tana fadin yau Abdul har a dakin mamana ya shigi ne ya mun jan ran ko? Na shiga uku kar dai da
gaske malan har ya daura min aure?

Kafin Abdul ya yi magana , muryar hajia mama uwar gidan aba ce ta karade gidan da budar da sai da ta
baiwa mutane mamaki,

Mikewa ta yi tsaye ta daga murya ta ce" kowa sai ya kama gabansa, ai ba yau aka fara ba a tara jama.ar da
ba.a taba tarawa ba dan yar gwal aman a kwashi kunya,
Daurin auren da aka so a yi daidai salar juma.a dan a samawa yar albarkar juma.ar sai dai Allah ai ba lale
ya yi maka abinda ranka ke so ba dan kai ka bambanta abu kana so na daya ya fi na kowa ai Allah ba zai
yarda a yi haka ba, mata ku watse kowace ta je gidanta ta dora sanwa an fasa auren uwar malan yar gwal
domin da za.a daura da an daura shi! Hehehe dadina da gobe saurin zuwa, ba zaka je ka gama yawon ta
zubar dinka ba kuma ka dawo a rurufe a yi maka gata duka Allah na kallonka ba!

Nan da nan yar hayaniya ta ringa tashi, kowace na tofa albarkacin bakinta wasu na tambayar da gaske an
daina? Dama wai wa zai kwashi saura? Abubuwa dai babu dadin ji

Da sauri ta bude lulubar da ta yiwa kanta, yar rigar cikin lafayar ce kawai ta yi saura sai na tsatsonta dake
nanade,

Dubanta ta fara ajiye kan mahaifiyarta dake kokarin jan hijabinta da kyau ta kara rufe fuskarta dan bata so a
fahimci halin da take ciki

Da sauri ta kai dubanta wajen agogon bangon dakinsu, har magariba ce ke neman yi,

Dubanta ta kai wajen Abdul ta ga ya kama hannun mahaifiyarta yana magana kasa kasa sannan ira kuwa
tana gyada kanta a hankali,

Wajen yan uwanta da suka nufota ta kai dubanta , da sauri ta diro daga saman bed din ta kali auntynta ta ce"
aunty, ina wayana? Bani wayana dan Allah

Auntyn tata ta bita da kallo sai dai bata bata wayar ba

Muryarta ta daga ta ce" aunty wayana nake tambayarki aman kin zura min ido? Ki bani wayana

Cikin daga murya mama ta ce" uban me zaki yi da waya?

Da sauri ta juyi wajen maman nata, kafarta ta daga ta karasa wajenta Abdul ya dan ja gefe daya, tana zuwa
ta kama hannun maman ta ce" mama, zan yi kiran Bashir ne, na tambaye shi lafia suka yi dare haka? Mama
kin ji abinda hajia ke fada wai an fasa aurena? Mama bani na kitaye shi ya zo a daura min auren nan ko zata
ji kunya ta shafa min lafia, mama na rantse da Allah ba karuwanci na je ba, ni ba yar bariki bace, ban yarda
na zubar da mutuncina ba, kuma Allah bai basu ikon zubar min ta karfi ba

Dubanta ta kai wajen Abdul da sauri ta damko hannunsa na dama ta rike gam a hannunta ta ce" Abdellah,
ka saka su bani wayata na yi kiran shi, maza ya zo da sauri kar dare ya yi, ya zo a dauran aurena , kai ka san
yana so na ko? Kai ka san ya fada min shi koma me ake kirana ko ake kalona da shi yana sona a haka,
kuma a dazu muka gama waya da shi da sasafe, da sasafe sai da ya fadan yau zai kawo kudin aurena Abdul,
ko bashi da lafia ne? Ko bashi da kudin ne? Ka bashi ya aure ni ka ji? Idan bashi da lafia ne a kai ni
wajensa ka ji?

Hannunta da ta rike shi ya bi da kallo, kafin ya kai kallon nasa wajenta, irin yanda ta rikice take sakin zance
na bata cikin hayacinta

Aunty ya kala hakan ya sanar mata fa yana so ta kamata ne,

Mikewa aunty ta yi ta riko hannunta sai dai maimakun ta sake shi sai gaba dayanta ta afka kirjinsa ta
rukunkume shi tana wani irin jijiga shi gaba daya ta yakune masa gaban rigar tasa shadarsa mai ruwan
sararin samaniya du ta aniya yakuneta tana jijiga a kirjinsa tana maimaita ya kira mata Bashir tana son
magana da bashir!

Da wani irin karfi ya cireta a jikinsa ya dauketa cimak ya direta saman bed din da take a dazu kafin ya juyo
ya kali yan uwanta irin yanda du suka fita a hayacinsu tsabar tashin hankali sai mahaifiyarsu dake zaune
kanta a kasa bata dago bama bare a fahimci halin da take ciki
Bakinsa ya buda da kyar ya ce.......
*KUTKALE*

*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct
NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan
number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA
SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN
SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN,
.....* taku ce, Sajida😍😍😍😍

5️⃣1️⃣

*Yan uwa😭😭😭 ya bakwa comment zaffaafa ne? Ko labarin ba siger ne? Haba kuma na fns, ina mugun
yi da ku, ku kuwa kun daina bani comment zafafa? Idan har yanzu cikin sallah muke na dakatar idan aka
gama shagulgulan sallah sai mu ci gaba 😔😔😔😔😔*

Bakinsa ya buda da kyar ya ce" menene haka? Haba aunty, ku yi hakuri, zamu yi jiransa daga nan har karfe
goman dare

Yana gama fada ya juya ya fice , nan Hafsat ta kara mikewa da niyar dirowa daga bed din, sai dai kafin ta
karasa hanzarin nan nata ta ji saukar wani gigitacen mari,

Kuncinta ta dafe da sauri ta kali fuskar mahaifiyarta, sai da gabanta ya yanke ya fadi domin kuka mamanta
ke yi hawaye ne sosai ke zuba daga gurbin idannuwanta
Yatsarta ta nuna mata ta ce" binsa zaki yi? Kuma bace mana zaki yi? To ki je ANMIH! na ce sai ki tashi ki
kara fita a irin wannan halin, ke dama zagin mutane ko magangannunsu ba damunki ya yi ba, sai ki mike ki
je ki raba abin fadan kin ji? Zaki nuna min rashin hankali da rashin da.a ne? Ko kuwa tarbiyarki ce ta koma
haka? Ke idanma wahainiya kike mai canza kala a dukan wani lokacin da ta yi niya dan ubanki a yau ba
zaki je neman namiji ba, meye? Me kike tsoro? Me kike gudu? Menene baki gani ba?

Shiru ta yi sakamakon kukan da babar yarta ta fashe da shi tana rike mahaifiyar tasu,

Dubanta ta mayar wajenta, tanai mata kallon nan na abin tausayi

Tana hawayen ta ce" baki koya mana daga murya ba, ki sasauta muryarki ummah,
Menene bamu gani ba muka kashe muka birne tsakanin mu? Daga muryarki na iya tona sirrin mu,
Ummah, rayuwa ce, jarabawa ba irin yanda bata zuwa, na sani , uma na san kina cike da tashin hankali
yannayin rayuwar maman malan, sai dai kuma ina so mu zauna mu zubawa sarautar Allah ido, malan kanda
ya yanke hukunci yi mata aure ne dan ya fitar da ita a gidan nan ko zata ji sanyi da ranta,
A wajenmu ne take samu sanyi, ba zan yarda wajen namu ya koma ya zame mata gidan kurkuku ba!
Ummah, ai maman malan ta yi sauki, a ganina an samu ci gaba a halayar maman malan

Hannunta ta janye a hankali ta juya ta shige bayin dakinta ta dauro alwallah

Tana fitowa ta dube su muryarta sanyi kalau ta ce" ku tashi ku yi alwallah, sallar magariba ake kira, kar ta
shige

Daya bayan daya suka ringa shiga ciki suna dauro alwallah suna fitowa domin sun kasa fita waje bale har
su yi anfani da bayin wajen

Ita kanta Hafsat alwallar ta dauko ta zo kusa da yan uwanta ta tayar da sallar magariba,
Gaba daya ta cire du wani abu mai iya sakata kyalkyali ko annuri,
Bayan ta gama sallah a hankali ta ja jikinta ta jingina da jikin gado ta kurawa waje daya ido,
Tana jan carbinta tana tana kaiwa wayarta dake saman gado kallo, idonta na kara lumshewa tamkar zata
fasa ihun kuka sai dai ba hali

A haka aka yi kiran sallar isha.i, cikin gidan sai kakayatu ake magangannu sai isko su suke da shewa kala
daban daban, sai dariya ake shekaya ana kashewa kowace ta sha ado ana buga waya ana fadin yau malan ke
aurar da yar gwal aman ana jiran angwayen tun rana har yanzu basu karaso ba

Dakin mama sun yi shiru, ba mai yiwa dan uwansa magana, suna lazumi dai kowa na neman sauki a wajen
Allah

Mama ce ta dubi yayanta baki daya, cikin murya a shake ta ce" dare fa na yi, ku tashi ku lalubi gidajenku
mana Mariam?

Nana Mariama ta dubeta, ta kai dubanta wajen agogon dakin , karfe tara da rabi ce ta yi,

Mikewa ta yi a hankali ta matsa kusa da maman nasu da niyar yin magana

Wata irin buda ce aka saki a tsakar gidan, buda mai karfin tsiya, buda ce irin ta harshen buzaye wace ake
kada harhen ana ajiyewa ana kuma dauka ba tare da an sauke lumfashi ba

Matar da ta shigo daga waje, wace take marokiyar anguwar ce, macen da ta zo tun da rana dalilin daurin
auren aman gannin an fasa kamar yanda hajia mama tace kowa ya watse sai yan tsegumi dake lekowa jifa
jifa suna jin kwaf suna fita

A yanzu haka ta dawo ne sakamakon mai yar lasifikar da ya shaida za.a daura aure,
Za.a daura auren Hafsat a irin wannan lokacin
Ba wanda bai yi mamakin irin lokacin da angon ya saka ba, du mutanen dake kusa sun halarci daurin auren
da ya gigita su,

Hafsat? Yar gidan malan, yarinyar da ta kwashe tsayin shekarun rayuwarta tana rayuwa mai hatsari, rayuwa
marar tsari, rayuwa tamkar wace ta fito a tsatson arnawan da basu san kalmar musulunci ba, yarinyar da
baki da yawa a dazu sun ambaci cewa su sun zo ne dan ubanta mutumin mutane ne, sun zo ne dan kawai su
amsa gayatar mai zuwa gayar mutane, aman kowa ya sani ko sadaka zai bayar da yar nan tasa sai ya hada
da bada hakuri da jari harma da wajen zama, dan a yi hakuri a zauna masa da ita, yarinyar da ta sha marin
saurayi? Daidaiku ne suka yi mamaki rashin zuwan ango a kan lokaci, sai dai daurin auren da aka kusan
karfe goma na dare ya saka mutane da yawa mikewa tsaye daga zaunen da suke......

Dubansu du suka kai wajen mutumen da aka ce shi ne mijin Hafsat, nan yan kananun magangannu suka
fara tashi, sai dai a lokacin da ya yi bayanin kyautar uwa da ta uba sai baki ya mutu, ya kasance du wanda
suka yi ido hudu da shi sai dai ka ga ya sakar masa murmushi ko yana kokarin karasawa dan ya samu shiga
a hankali aka fara canza salon zagi zuwa yabo, a hankali aka fara dan yaba magana cewa" ai ita uwar malan
barta da fadanta, aman yarinya ce mai mutunci da mutunta wanda ya girmeta

Malan dake zaune, zuwa wannan lokacin ajiyar zuciya kawai yake saukewa sannan yana bin mutane da
kallo, a yau ya ga rana ta mamaki, rana wace a yau kawai Allah ya nuna masa mai zaune da shi dan rufin
asiri da mai zaune da shi dan moriyar wani abin,

Ashe dan adam yake?

Marokiyar nan sai da ta ja ta tsaya ta kara rangada buda,

Wani tsaki ne yayar su Hafsat ta ja, kafin ta ce" wai Ummah, ba za.a tsawatarwa mutanen waje idan na
cikin gida sun zame mana dole ai banda na waje

Maganar da marokiyar ta fara fada ne ya sakata katse maganarta, lokaci daya kuma ta zabura ta mike da
niyar fita

Hafsat da ta dago kanta da sauri, lokaci daya ta hango wayarta ta bada wani haske,

Mikewa ta yi ta lumshe idannuwanta sai kuma ta bude tana dariya dariya hadi da kuka, irin emotion din
nan,
A hankali ta buda bakinta ta ce" ni na san wani abu mai girma ya tike shi, mama, na san zai zo komai dare,
mutumen da ya gama min rantsuwar irin soyayar da yake min?

Sai da ta gama maganar ta nufi wayarta,


Dai dai nan marokiyar ta ce" *lale komai nata daban ne, tauraruwa ce yar malan, mai sa.a ce maman malan,
uwar masu gida wanke ki bamu ko jikokinmu sa dauko wannan farin jini da farar sa.a, yau ku zo ku duka
ku gaisar da masu garin, ta auru, uwar malan ta auru, sai da ta dandanje ta zabo dalele kakarfa, sai da ta
gyagije ta dauko zakara mai takun zaki, to yaya zata yarda yan bukulu su gane mata shi bayan tanai masa
takun kura wace safiya maraicenta ce? Ba fa dan iska bane dan baiwa ne, maman malan ki je da ni na zauna
a gidan gilas domin ko a aljanna in sha Allah muna fatan Allah ya yi mana domin*

Daidai nan du matan da suka rarage du sun halarta suna kallonta, kowace jira take, sauraro take ta fada
mata sunnan mijin da take yiwa wannan uban kirarin sai kace wace ta auri dan shugaban kasa ko wani
gagarumin dan kasuwa?

Da sauri Nana mariama ta ratsa su, bata iya yiwa kowa magana ba famanta ta karasa wajen marokiyar nan,

Tana zuwa ta ce " ladiyo, me nake ji kina fada kamar an dara auren maman malan?

Bakinta ta buda ta ce" aure kuwa gangariyarsa, sanadiyar na rangada gidar daurin auren nan kin ga damin
da ya bani angon da kansa
Hajia mama da gabanta ke tsale yana wani irin dokawa, hankalinta a tashe ji take tamkar ta matse wuyan
ladiyo ta matso ta ce" ke dallah rufe min baki, waye mijin wa sunnansa, waye shi a garin nan da zai iya
daukan kyauta irin haka ya maki dan kawai kin yi murnar daurin aurensa da yar da ta gama yawo?

Du kallonta mutanen wajen suke, dan sam bata iya ta rufe abinda ke ranta ba a irin wannan lokacin

Sai da ladiyo ta rangada guda ta matso sosai kusa da Hajia mama ta ce"

A daidai lokacin ne Hafsat ta dauki wayar andoid dinta kirar samsung ta duba message ne akai mata

Buda message din ta yi tana murmushi dan ta tabata albishir zai mata ko ya yi mata barka

Message ne kamar haka

*zaki rayu kuwa da ni? Tsoronki nake, ina tsoron haduwata da ke, sai dai na ceci jin kunya da kuma kwana
da zulumin malan, mama, su aunty da ke kanki, ki gafarce ni da kalmar da zan fada, aman daga yau
igiyoyin aurena sun rataya a wuyanki, Hafsat U.R MINE*

Wayar dake hannunta ta daki, lokaci daya ta kwala ihu ta silale nan kasa

Su mama da basu bi aunty Mariama ba suna zaune suna sauraron abinda ake fada daka dakin ne suka
zabura a tsorace suka yi infa Hafsat take yashe a sume

A daidai wannan lokacin Ladiyo ta ce" mijin da aka aurawa uwar malan lale shi ne uban masu gida

Sunnansa *ABDUL JABAR ABDUL BASID* wannan da NURU WALAM ke talar shagunansa a dukan
kafofin talabijin dake niger, wa.inda du abinda aka saka idan aka cire za.a saka wani sai an hasko daya daga
cikin shagonsa an yi talarsa ,
Wannan yaro karamin mai tashen....

Ke ki rufe mana baki , mu zaki kawowa zancen banza a nan? A ina? A ina zata ganshi? Wacece ita? A irin
wannan anguwar? Kin san da wa kike magana?

Amaryar malan, jinnin sarauta, yar shuwa ta fada da wata irin tsawa tana katse ladiyo, daidai nan baban dan
hajia mama ya shigo gidan a wani irin haukace, wanda yake adawa da yayan Maman su Hafsat, bale Hafsat
din

Yana shigowa ya ce"....


*KUTKALE*

*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA


NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct
NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan
number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA
SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN
SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN,
.....* taku ce, Sajida😍😍😍😍

5️⃣2️⃣

Yana shigowa hankalinsa tashe, karara fuskarsa take hargitse har ya kasa zama ya taya mahaifinsa salamar
mutanen da suka rage ya afko gidansu a orin wannan lokacin da yan uwansa da iyayensa da bakin fuska ke
tsaitsaye ya ce" ummah, ummah kin san waye wannan Abdallahn? Wannan yaron gayen dake zuwa gidan
nan ne, wanda ke da iko da cikin gidan nan fiye da mu yayan da Malan ya haifa,

Hankalinta ne ya kara tashi ta ce" kana nufin dama shi ne mai wannan dukiyar? Wannnan yaron mai shige
da yan daba mai magana ba risinawa mai yi mana kalon sa.aninsa shi ko wa?

Harde hannayensa ya yi ya ce" shi fa, shi da kansa

Wani wawan tsaki ta ja tana waskewa ta ce" dama wa zai kwasa idan ba abokin yi ba?

Da sauri nana Mariama ta kaleta, tana yin shiru amaryar malan ta ce" ai dama sai abokin aiki ya san kan
aiki, wa zai dauki saura? Ai shi dai da ya saba shi zai kwashi abinsa

Nana mariama ta kaleta da kyau, wani abu ne ta ji ya kasa ficewa a kirjinta, a yau ta ji ba zata iya yin shiru
ba dan haka ta ce" eh ai ba laifi bane, idan kika ga har ya kara nacewa mota tabata ya ji dadin tukinta, wata
mitar dan ubanta komai gyaran da za.ai mata ba zata tashi ba sai dai ta ja kara ta zubar da bakin hayaki!

Guda matar nan marokiya ta kara saki tana dariya, domin kamar an saka su buda baki a tare abinka da
ko.ina haske na haska dakin sai ya kasance du ana kallon su

Wace ke bima mama ce ta ce" ikon Allah, Mariama dama kema baki da kunya? Dan kanwarki ta auri mai
kudi har bakin ki ya bude? To a yi dai mu gani ku tsaya ku ga zaman kafin ku fara takun kasaitar

Sai da ta juya dan nufar dakinsu ta ce" zama daram Uwar karuwa a cikin wuta!
Du da kallon mamaki suka rakata, domin kaf a cikin yayan mama ita ce mai lafia , koda an tabota takan
labe ta sha kuka ne bata tankawa bata kula kowa haka har Allah ya rabata da rayuwar gidan malan

Sai bayan ta shiga cakartun magana ya bi bayanta, bata damu da juyowa ba ta yi shigewarta falo ta shige
cikin dakin mama

Tana shiga ta tarar mama na shafa goshin Hafsat sun shinfideta saman bed sun gyarata sauran na tofa mata
adu.a

Yannayinsu ya shaida mata da suma ta yi, da sauri ta karasa tana tambayar me aka yi? Menene?

Mama ta ce" wayar ce ta yi kara , sako ne tana dubawa sai kawai ta ihu ta fadi, mun shafa mata ruwa
kamar ta farka aman kuma kin ga idannuwan a rufe mu dai munai mata adu.a

Zama itama ta yi tana gyarawa yarinyarta hijab din jikinta sannan ta dauki wayar ta duba message din

Bakinta ta tabe ta ajiye tana hararn Hafsat din a kasan zuciyarta kuwa fadi take banza ba suma ba sai dai ki
mutu muna nan ma ga irin lokacin da zaki dauka baki farfado ba!

Suna nan zaune su Mama sai tofi suke mata suna tofa mata adu.a aunty nana mariama kuwa na zaune gefe
tana baiwa yarda madarar da ta kada mata

Gidan ne ya dauki shiru, shirun lokaci daya haka marokiyar kanta ta yi dif tamkar ta fita a gidan

Dan lokaci aka dauka sai ga Malan ya bayana a kofar dakin yana salama

Mama ce ta mike da sauri ta nufi kofar tana goge fuskarta tana gyarawa dan ba zata so ya ga yannayin da
take ciki ba

Cikin nutsuwa ya shigo dakin,


A hankali yake bin su da kallo, kafin ya amsa gaisuwar da suka jero masa sunai mata su duka

Sai da ya gama amsawar ya ce" Alhamdulilah, zaku iya tashi mazajenku na waje suna jiran ku

Ba wace ta tsaya tsaye tsaye du suka mike suna daukan abubuwan da suka san nasu ne, sukaiwa mamansu
salama

A hankali malan ya karasa bakin bed din da mamansa ke kwonce

Ido ya tsura mata na dan lokaci, a hankali ya ce" mamana, tashi mana, ba kyau fa irin haka

Idannuwanta ne suka dan yi rawa jin muryar babanta, tana son buda idannuwanta tana tsoron ta bude ta ji
wannan labari mai kama da almara, ita bata san da me zata kwatanta wai wai tap, ina ba zai yiwu ba, ba zai
taba yiwuwa ba! Ita ta rayu da Abdul a matsayin mijinta? Mutumen da suka raina juna? Mutumen da karara
ta san waye shi a harkar mata? Mutumen da macen dake gidansa kanta sai dai ta isko shi? Abdul bai iya
yiwa mace yar murya ba bale ya rarasheta, bai iya bin mace ba, bai iya yabawa mace ba, ta rasa wani
banzan tunani na kar ya bar malan cikin zulumi ya saka shi wasa da maganar aure, shi kennan a wasa da
komai rayuwarsa zata kare? Haba dan Allah! Bama zai taba yiwuwa ba

Murmushi malan ya yi gannin bakinta na murgudawa da alamomin tsaf ta farka , kansa ya girgiza yana
girmama rigimarta, wato a haka take a sankame du sun zagayeta bayin Allah

Juyawa ya yi ya yafito mama da hannunsa ya yi gaba


Sai fa mama ta dan kara waigawa tana mamakin malan hala bai san a sume take ba yake mata magana? Ko
ji yake da gangan ne?

Da sauri ta taka ta cin masa ta karbi kys din hannunsa

Sai da suka haue sama ta ga matan gidan a tsaitsaye da alama kowace ya kiraya

Bude dakin ta yi sannan ta koma karshe ta tsaya, sai da malan ya shiga, suka shige sannan ta bi bayansu

Zama malan ya yi a babar kujerar da yake zama wace ba mai hawa sai shi

Su duka a kasa suka zazauna suka tankwashe kafafuwansu

Sai da malan ya sauke ajiyar zuciya sannan ya ce" tsarki ya tabata ga Allah ubangiji subahanahu wata.ala,
Alhamdulilah,
Kamar yanda kuka ji, an daura auren mamana yau bisa sadaki mafi kankanci jika goma , sai kyautar uwa da
ta uba mota kirar Ferari daya daya, sai motar jigilar kaya wato babar mota ta uba, sai kujerar haji in sha
Allah ta uwa uba da yan uwanta da iyayenta wato ku

A tare suka kalli juna sannan suka kale shi

Malan ya ci gaba da fadin" za.a kawo lefenta jibi idan Allah ya nuna mana sannan za.a saka bikin kusa
kamar yanda kuka sani bana taron wunin biki a gidana, ba.ai min kade kade bale wata diner, almajirai nake
tarawa a wuni ana sabkar alkur.ani mai girma da neman zaman lafia a wajen Allah

Shiru ya yi yana kallon yannayin kowace, shirun da ya biyo baya daga garesu ne ya saka shi guara babar
rigarsa yana sauraron su

Hajia mama ce ta muzguta ta ce" uhum

Malan ya saki murmushi yana kada kai, sauraron su kawai yake yana jiran jin fatan alkhairi daga bakin
dayarsu, aman cikin ikon Allah shiru ba wace ta yi fatan alkhairi

Dubansa ya kai wajen mama ya ce" Ramatu

Da sauri ta dago da dubanta ta kali malan

Malan ya gyara zama ya ce" daga yau, na umarce ki da ki nuna kulawa wa yayan da kika haifa, na soke
maganar jin kunya kawar da kai ko kara, na umarce ki da ki buda baki ki yiwa yarki adu.a, ina so ki kula da
shirye shiryen tarewar yarki!

A karo na biyu ta kuma kallonsa, kwarai ba wasa da gaske malan yake, da gaske yake ba wasa a maganarsa

Hannayenta ta hade ta shiga murzawa a hankali ,


Cikin nutsuwarta ta ce" Alhamdulilah, Allah ya basu zaman lafia

Malan ya gyada kansa yana murmushi ya mike ya shige ba tare da ya kuma tankawa kowace ba

A hankali ta mike itama dan ficewa a dakin dan gaba dayanta hankalinta a tashe yake , bata taba irin haka
ba, ba.a taba haka da ita ba, hasbunallahu wani.imal wakim

Tana fita a dakin ta kama sauri, aman cikin ikon Allah sai da hajia mama ta cin mata, matar sosai
dajikantaka ta fara bayana a jikinta aman dan tsabar fitina ta riko hijabin mama ta ce"malan ya yi haka dan
ya nunawa duniya daban take da sauran ko? To kudinsa baya damuna! Sannan bana son kujerar makar
domin ni ba zan je bautar Allah da kudin haram ba!
Ita dai mama tsayuwa ta yi sai da ta gama ta sakar mata hijab ta shiga daki

Tana shiga ta ga wayam ba Hafsat,


Da sauri ta daga kafarta ta shiga dakinta

Tarar da ita ta yi tsaye, daga ita sai dan dogon wando da rigarsa sai kai kawo take,
Yannayin fitina da neman balaki ya bayana a tare da ita

Kallon tsaf ta yi mata kafin ta tabe baki, lale Hafsat ta raina mata hankali, kuma ta yarda da ake cewa likita
ya fi kowa rikicewa idan abin ya shafe shi.

Sai da ta gama kallonta sannan ta ce" ki lulube jikin ki, daga yanzu bana son na kuma ganninki ba da lulubi
ba kafin a kawo magungunnan ki

Da kallo ta raka maman nata, iyeah? Shi ne abinda ta fada

Da sauri ta warto wayar nata, karfe goma sha biyun dare ne fa aman da yake ranar ta zo masu wani iri du
gidan malan yara kananu kawai suka samu rintsa idannuwansu

Wayar ta danna ta danna masa kira

Ta yi ya kai sau hudu kafin ya daga da wata irin murya

Sai da gaban Hafsat ya fadi domin muryar wani irin kasa kasa, sannan bata fita da kyau

A hankali ya ce" Hafsat

Hafsat ta kara rintse idannuwanta ta kai zaune saman bed din dakinta
Niyarta ta daga murya ta darza rashin mutunci sai gata da sasauta murya ta ce" Abdul, dan me zaka min
haka? Me na maka ne wai ni? Dan me zaka saka a aura maka ni bayan ka san da wanda ke so na yake shirin
zuwa ya aure ni? Yanzu idan ya zo sakina zaka yi a kara aura min shi ko me?

Abdul ya kara lumshe idannuwansa yana sauraronta , a nitse ya ce" *ni ban aure ki dan na sake ki ba*

Me kake nufi da baka aure ni dan ka sake ni ba? Wani irin aure kake jiran yi da ni haka? Baka so na Abdul,
bana son ka!, dan me ka min haka? Ta fada muryarta a sanyaye haka kuma tana rawa rawa

Abdul ya sauke ajiyar zuciya, a hankali ya ce" *na san bakya so na, ban roki ki so ni ba, Hafsat baki ga
lokaci ba ne ni? Lokacin neman nutsuwa ne, idan kuwa zaki iya....ina nufin idan har kin san kina bukata, a
yau kin saka haka a ran ki .... sai na sauka daga nan na zo in hau naki bed din*

Abdul ya karashe yana mai duban Na.ima dake kwonce kusa da shi

Shiru ya ji wayar, ba magana dan haka ya dubi screen din,


An kashe, murmushi ya yi yana girgiza kansa, dubansa ya kai wajen Na.ima, baci take kashirban, baiwar
Allah, a gaskiya yana tausayinta, shi baima taba tunanin ta yanda zai fadi abu sai wannan lokacin

Kwonciyarsa ya gyara yana mika, a hankali ya furta" *na san bakya so na Hafsat, na jima da sani....sai dai
ba zan iya sakin ki ba, ke na yiwa rabon wani garaje dan Allah ya kashe ni kafin ya fito daga tsatson
ki ....Hafsat idan na rabu da ke ni kuwa na rayu a yaya?*

Bayan kwana biyu aka kawo lefen Hafsat


Lefen da ya kara kashe bakin mutanen gidan malan kowa sai dai ya labe daga daki yana leke ba um ba
umum,
Anguwa du an dauka, maganar uwar malan kawai ake, da yawa na fadin alkhairin da yawa na kushewa

Kwana biyar kennan da maman malan ke zaune da auren Abddallah a kanta,


Bata kuma jin duriyar BS ba, haka kuma shi kansa abdul din daga daren da ta yi kiran nan nasa da ta kashe
bata kuma nemansa ba

A yau ta tashi ta gama shiri da sanyin safiya cikin nikaf da abin hannun da mama ta bata, shima an ce dole
sai ta je da kanta gidan mai dinki ne, hakan ya saka mama ta ce maza ta je ta dawo su yi dilkar safe domin
ko dilkar basu yi ba

Har ta yiwa mama salama mama ta dawo da ita

A hankali ta ce" kin nemi izininsa ne?

Da sauri ta kalli mama cike da mamakinta, izini? Wai izinin wa?

Mama ta daure fuska ta mika mata wayarta da aka karbe du idan za.ai mata dilka ake amshewar

Amsar wayar ta yi ta kuma kallon mama gani ta yi ta tsareta da kallo dan haka ta danna wayar ta shiga
kiran numbersa

Sabon wulakancin da take gani ya dauka yanzu ne ya yi mata dan sai a kira na biyu ya daga sannan ya ki
yin magana

A hankali ta yi salama domin mama na kallonta ido cikin ido

Amsawa ya yi yana mamakin salamar daidai ya tsaya wajen danja

A hankali ta ce" an aike ni wajen mai dinki zan je na dawo

Ajiyar zuciya ya sauke kamar wanda ya yi tsere, a hankali ya ce" ki jira

Bai karasa ba ya kashe kiran , ta bi wayar da kallo


Sarai mama ta fahimci abinda ya ce dan haka sai ta dauko kujera ta zauna a kofar dakin mama

Ta kusan minti ashirin a zaunen nan, tana yi tana duba agogon wayarta tana kuma kallon hanyar fita

Kanshin turaran da ta jiyo ne ya sakata yin shiru ta ki motsi

A hankali yake takowa har ya iso inda take zaune


Bai yi mata magana ba sai tura kofar da ya yi ya yi salama

Da mamaki ta dago tana kallon wai da gaske dakin maman zai shiga? Yau ta ga ikon Allah, mazan yayunta
basu taba shiga dakin mama ba sai yau shi bakon jiya zai shige har dakin mamanta

Mikewa ta yi ta yi gaba dan har an fara leke, bata son a bata mata rai da safiyar nan

Sai da ya gama gaishe su ya fito ya fita wajen

Ganninta waje tsaye ya sosa ransa, aman bai nuna a nan ba ya bude ya shiga itama ta bude ta shigan

A hankali ya tayar da motar ya dauki hanya

Batai masa magana ba sai murza yan yatsunta da take,


A hankali a hankali har suka karasa wajen da bata fada masa ba sai dai gani ta yi ya kaita ta tabata mama ya
tambaya

Fita ta yi ta shiga akai mata aune aunen da za.ai mata baki daya ta fito ta dawo motar

Dagawa ya yi suka fara tafia,


Suna tafiar ya canza hanya a hankali ya ce" bana so kina fita Hafsat,

A hankali ta dan kale shi sai kuma ta kawar da kan nata

Hafsat talk to me;

Dubanta ta kai wajensa, sai kuma ta shiga shashekar kuka,


Kuka take a hankali a hankali wanda ya saka shi ja ya tsaya a cikin kwanar da suka shigo sabuwar
anguwar yan gayu ba wasu mutane a waje da yake safia ce sai jefi jefi du suna gida suna baci

Mitar ya tsayar kasan wata shuka,


A hankali ya karkata yana kallonta,
Rufar fuskar nata ya dage ya cire mata baki daya yana kallonta

Gashin idannuwanta sun yi gazar gazar da su, sun shiga idannuwansa har sun zarta

A hankali ya fora yatsarsa saman girarta ya dan shafa kafin ya lumshe idannuwansa,
Muryarsa ya sanyayar ya ce" menene?

Hafsat ta dago da dubanta a hankali ta dube shi,


Muryarta ta sanyayar ita din ma ta ce" Abdul, ina BS ya shiga?

Abdul ya tsura mata ido, gabansa ne ya ji ya fadi lokaci guda,


Bai yi shishigi ba kuwa? Bai sako kansa wajen da zai zauce ba kuwa? BS? Tare fa ka gansu Abdul, shin
wannan damuwa da shi ka san da tana son sa, idan fa bayan so din Hafsan ka ta yarda da BS ne?
Gabansa ne ya kara faduwa, hankalinsa ya ji ya tashi a hankali ya saka hannayensa bibiyu ya kamo
fuskarta,

Matso da fuskar tata ya yi ya samu da kyar ya hada ido da ita,


A hankali ya ce".......

🙂🙂🙂🙂🙂🙂🙂🙂🙂🙂🙂🙂🙂🙂
*KUTKALE*

*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA


NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct
NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan
number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA
SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN
SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN,
.....* taku ce, Sajida😍😍😍😍

5️⃣3️⃣

A hankali ya ce" kin kasance mai fadin gaskiya Hafsana,


Ki fada min, a cikin mazan da suka ringa kawo maki hari shin shi ya samu galaba a kanki ko menene
wannan damuwar da shi?

Sai da ta wanna idannuwanta a cikin nasa sannan ta saka hannnayenta biyu ta janye hannunsa

Sakar mata fuskar ya yi yana kallonta, a hankali ta ce" haba Abdallah, me zan yi kwadayi da zaman yau da
kulun? Na zauna da kai Abdallah! Bana son irin rayuwar nan, rayuwar da ba kula ba yanci? Ni wa na fi da
zan yi tunani ai ni ce zaka waiwayeni? Ni ta nawa ce? Abdul shin ka taba so a rayuwarka?
So wani abu ne mai nauyi mai wahala, Abdul ni na taba so, so yakan saka mutun tsalake maganar
manyansa, Abdul Bashir ya nunan so, ya bi ni sau da kafa...ya waka min, ya yi hakuri har na samu kaina
sannan ya zo har gidanmu ya nemi soyayata da aurena
Shin me ya tsayar da shi? Ina cike da zulumin abinda ya tsayar da shi mai girma ne, Abdul du irin zagina da
ake a kulun sai ya furtan kalmar so

Idannuwansa ya lumshe ya kuma budewa yana kallonta

Sai da ta sauke ajiyar zuciya ta kale shi ta ce" ban san kansu mazan ba bale har na ware shi dan hakan! Ka
kaini nesa Abdul, ka yi yawo da ni sama a zuciyarka ka ajiye ni malan kar ka saka na kasa sauka🙄
Ta karashe tana mai turo masa bakinta sannan ta gyara zama a cikin motar

Murmushi ya yi kawai ya girgiza kansa ya tayar da motar ya harba hanya

Ashe wajen da zasu je din babu ma nisa da inda ya tsaya dan kawai ta kwasan masa kukan rigima ne ya
rikice ya ja ya tsaya kar ta halaka shi, da zata san irin abinda yake ji da bata yi haka ba

Kofar gidan ta karewa kallo, tamfatsetsiyen get ne da sojoji biyu a kofa

Buda kofar kawai suka yi ba tare da sun tsaya binciken wanda ya zo ba hakan ya tabatar mata da sun san ko
waye a cikin motar
Sai da ya isa ciki sosai ya yi parking

Fita ya yi ya tsaya yana kallon kofar falon

A hankali ta fito bayan ta saki nikaf din fuskarta


Takawa suka yi tana biye da shi har suka shiga falon

Gabanta ne ta ji ya fadi sakamakon hango kanwar mamansa, kuma mahaifiyar matarsa hakimce saman
kujerar falon tana amsa waya

Tana ganinsa ta kashe kiran tanai masa oyoyo

Murmushi ya yi ya karasa har inda take zaune ya dan duka ya bata peck a goshinta itin gaisuwar larabawa
sannan ya zauna sosai kusa da ita ya rike hannayenta suna gaisawa

Itama cike da kulawa take amsa gaisuwarsa kafin ta tambayi wajen su na.ima

Sai da suka gama gaisawar ya dan waigo sai ya ga Hafsat na tsaye a bakin capet din bata shiga ba ta zauna

Mikewa ya yi ya karasa inda take tsaye ya kamo hannayenta ya janyota a hankali har wajen zama ya zaunar
da ita

Dubansa ya kai wajen kanwar mamansa ya ce" ummi, matata na kawo ta gaishe ki

Daga ummin har Hafsat a tare suka dafo kai suka sauke dubansu a kansa

Cikin dakewa ya ce" Hafsat, ga mamana, kanwar mahaifiyata wace ta rage min kadai a duniya

A tare kuma suka kalli junna Hafsat din da maman Na.ima

Bata taba jin zufa ta karyo mata tashi daya sai yau, kan uba, shi ne abinda ta ayanna a kasan zuciyarta, a
duniya bata taba haduwa da mutun dan rainin hankali irin Abdul ba,

A hankali ta sada kallonta daga duban mahaifiyar Na.ima,


Ita kam maman na.ima bata ma san me zata yi tunani ba,
Dan haka ta kali Abdul dake zaune yana kallonsu, bin kowace yake da kallo dan ya gane hallin da suka
shiga

A nitse ta ce" ban fahimci abinda kake nufi ba, kana nufin aure ka yi?

Keyarsa ya dan sosa irin ya dan ji nauyin nan ya ce" eh moms, yau kwana shida da daura auren, auren ne ya
zo kai tsaye hakan ya sa ban shaida maku ba, ita kanta bata tare ba ana shirye shiryen tarewar nata ne

Kanta ta gyada tana kallonsa kafin ta mike ta ce" Abdul mu je ciki ina son gannin ka

Mikewa ya yi ya bi bayanta ,
Suna shiga ta juyo da dubanta ranta a bace ta ce" aman Abdallah ni zaka wulakanta a cikin garin niger ka
nunawa duniya ni ba kowa bace haka kuma ka nuna kai ka isa da kanka kai mai kudi ko? Aure ne zaka kara
baka sanar da ni ba sai dai ka zo min da yarinya kai tsaye ka wani ce ga matarka? Ka manta y'a ta kake aure
idanma baka dauke ni a uwa ba ai zaka sasauta ko dan yar da na baka take zaune a gidanka ko?

Habarsa ya rike da mamaki ya ce" moms aman me ya yi zafi haka?

Tambayana kake abinda ya yi zafi? Du abinda na fada wanene baka fahimta ba na baka haske!
Ajiyar zuciya ya sauke ya ce" auren ne damuwar ko kishiyar da aka yiwa yar ki?

Idannuwanta cike da bacin rai ta ce" eh dan me zaka yiwa yarinya kishiya ko haihuwar fari bata yi ba?

Kansa kawai ya girgiza kafin ya dan matsa kusa da ita dan ya ga ta soma daga muryarta shi kuwa baya so
wata baraka ta fito daga wajenta, ko ba komai fa kanwar mamansa ce

A hankali ya ce" aman ai na fada auren kai tsaye ne ko Moms? Kuma kin dai san ina aure aure ai bai dace
hakan ya bata maki rai ba, moms kawai sai dai idan zaki nuna kin fi son Na.ima a kai na ne, ni da na zo dan
ki lalaba min ita kar ta daga hankalinta? Kin dai san tana so na bana son abinda zai hanata sukuni

Tsareshi kawai ta yi da ido, a gaskiya dan yar uwarta ne na jini, sai dai rashin mutuncinsa na wahalar da ita,
ta rasa a ina ya dauki dabi.ar wulakanta mace haka? Wulakanta mace mana dan mace na sonka sai ka mayar
da ita banza? Ai kuwa larabawa akoysu da ririra mace, rayuwar balaraben mutun da matarsa duda shi ba
balarabe bane aman ai a can aka raine shi

Shiru ta yi masa hakan ya saka shi sasauta murya ya ce" ki yi hakuri momy, a matsayinki na uwa q wajena
ban kyauta ba, aman ki yarda da ni ban aureta dan na wulakanta yar uwata ba, su duka zan hada na zauna
da su daga su bani da ra.ayin kara wasu sai dai idan sun gaza da ni ne

Kawar da duban da take masa ta yi, a hankali ta ce" idan ka je ka kawota nan mahaifinta ya rarashe ta,
Abdallah ka yi adalci tsakanin su

Kansa ya ringa gyadawa har ta gama sannan ya riko hannunta yana kallonta
Murmushi ya sakar mata a hankali ya ce" ki dauke mu mu duka tamkar yayanki momy, na roke ki...yin
hakan zai bani kwarin gwuiwar risinawa koda bana so👏

Murmushin ta sakar masa ita din ma sannan suka fito daga dakin

A lokacin da suka fito tana zaune inda suka barta kanta a sade kasa tana dan kada kafarta

Muryar momy ce ta sakata dago da kanta, momy ta ce" yarinya kina zaune ko ruwa ba.a kawo maki ba?

Abdul ya karasa kusa da Hafsat ya zauna saman kujerar , da kafarsa ya dan mintsinota hakan ya saka ta dan
matsa kadan tana kallon kasa bata ce komai ba

Daidai nan aka kawo jus, sai dai bata kai ga dauka ba Abdul ya mike ya ce" momy tafia zamu yi

Mikewar ta yi itama ta rako su har wajen mota, bata ce su ci kansu kuma ba sukai salama suka fito a gidan

Sai da ta ga sun fito ta dage nikaf dinta cikin yanayin tashin fitsara ta ce" Abdul wannan wani irin
wulakanci ne? Ya zaka dauko ni ka......
Wani wawan birki ne ya taka wanda ya saka taratsun maganar da ta dauka tana zazaro mai ido ta hadiye
lokaci guda ta dan yi gaba Allah ya taimaketa da belt a jikinta ya mayar da ita kujerar

Yana tsayawa, bai bari ta dawo a doguwar rikicewar da ta yi ba ya kara daukan hanyar kara rikitata,
Lokaci daya Abdul ya janyo Hafsat jikinsa bayan ya kunce belt din jikinta ya janyota sosai jikinsa ,
Cikin kankanin lokaci ya hade bakinsa da nata....a hankali ya lashi lebenta na kasa,
Idannuwansa dake lumshe ya dan daga gani ya yi ta zazaro ido haka kuma kofofin hancinta kansu sun
bubude da mugun mamaki da tsoro

Idannuwan nasa ya lumshe ya fitar da harshensa kadan ya kara lashe lebunanta baki daya, a hanakli ya saka
harshen nasa a bakinta yana dan zagayawa hakan ya sa ta kara daga bakin cike da mamakin girman
fitsararsa da kallon abinda yake mata wani iri
Abdul ya yi haka ne dan ya kashe bakinta wajen yi masa ihu, ba zai iya daga mata murya ba zai so ta gane
haka itama ta daina daga masa murya

A hankali ya karasa damkar harshenta ya shiga kissing passionately, wani irin hucin numfashi ya fara
fitarwa lokaci daya hannunsa da ya ririke hannayenta ya sake au ya shiga hayowa da daya har wajen kanta
ya talabe bayan keyarta yana kara tsotsor bakinta tamkar ya samu alewar kara

Dayan hannun nasa dake rawa rawa ne ya saka a hankali ya shiga lalubar hanyar da zata bashi damar saka
hannun cikin rigarta...lokaci daya kuma yake kokari kara dorata saman cinyarsayana shafa bayanta a
hankali yana sama da hannun yana neman zif din rigar tata

Lumfashin da yake saukewa ne ke shiga ilahirin jikinta yana sauka a fuskarta mai wani irin dumi da
kanshin maclean na ananas mai sanyi

Ajiyar zuciya yake saukewa a kai a kai, lokaci daya yannayin yanda ya samesu da Muhammad ya fado
masa a cikin idannuwansa,
Da sauri ya cika leben nata, q haka kuma ya ririketa a jikinsa da wani irin karfi
Kansa ya cusa cikin dokin wuyanta , muryarsa na rawa ya ce " *HaHafsssssssat, me ya maki a ranar nan?*

Wannan karon damkar da ya yi mata ya fi gigitata fiye da taba mata jikin da ya gama yanzu yanzu, lokaci
daya ya birkice mata kamaninsa suka canza mata,
Gaba daya ya hade ya zame mata tamkar kumurci sannan ya yi mata tambaya ya tsareta da wani mugun
kallo

Gabanta ne ya shiga dokawa,


Lokaci daya ta shiga tambayar kanta wa? Wa yake tambaya? Me ya yi mata a wace rana????

Hafsat baki fahimci wanda yake nufi ba ko?🤔🤔🤔


*KUTKALE*

*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct
NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan
number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA
SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN
SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN,
.....* taku ce, Sajida😍😍😍😍

5️⃣4️⃣

Cikin bacin rai ya dago da dubansa yana kallonta ya ce" ki bani amsa ke nake sauraro Hafsat, me ya maki?
Me da me ya maki?

Wai wa kake nufi Abdul?


Hafsat ta fada tana dan matsawa daga irin maysewa juna wajen da suka yi

A hankali ya maida bayansa jikin kujerar ya jinginar


Ya jima a haka dan a kadan ya dauki minti goma sha biyar inda Hafsat ta takure jikinta tana kallon kasa
tana murza hannayenta a kasan zuciyarta kuwa sai yawo take mata, tsoro ne ke faman halakata, a gaskiya ta
tsorata da yannayinsa gashi ya yi mata tambayar da bata fahimta ba

Hannayensa gaba daya ya dora saman kansa, gashin kansa da ya caje ya yi tsaf da shi ne ya saka yatsunsa
ya cakule tsarin gashin

Yatsun nasa ya yi ta cusawa cikin kan kafin yake samu ya dan saisaita kansa

A hankali ya kai dubansa jikin rigarsa , wajen wandonsa


Ajiyar zuciya ya sauke ya kali agogon hannunsa sannan ya tayar da motar ya kama hanya

Tuki yake ba tare da ya kuma yi mata magana ba a haka har suka isa kofar gidan malan

Ja ya yi ya tsayar da motar, bai kaleta ba bai kuma yin magana ba sai dan sada idannuwansa da ya yi dan
baya son ta san waye shi a fagen bacin rai, zuciyarsa idan ta kai makura suma yake , hakan kuwa shi ya fi
zama alkhairi domin da bai suman ba sai dai kuwa shi ya summar dan riko yake yiwa mutun wanda sai dai
idan ya fadi mutun ya gudu hakan kuwa komai girmanka raf yake yi da kai sai dai a yi abinda za.a yi, baya
gudun ya kama mutun du shekarunsa

Kallonsa ta kara yi, jikinta ne ta ji ya yi mata mugun sanyi, eh lale ta san waye shi, tana iya fadin kadan
daga halayarsa da ta sani , ta san rigimame ne shi mai mugun fada aman kuma bata san shi da hadiye bacin
ransa a kanta ba hakan ya saka jikinta yin mugu mugun sanyin

A hankali ta saka hannunta ta bude motar

Kafarta daya ta fitar tana kokarin fitar da dayar ya riko hannunta na hagu dake kusa da shi

Murya can ciki ya ce " ban lamunce fitarki ko kofar gida ba

Yana gama fada ya sakar mata hannun, a hankali ta juyo da dubanta ta tsayar a ka fuskarsa
Dan tsai ta yi sannan ta fice gaba dayanta ta bara masa motar

Daga wannan lokacin, Abdul bai kuma kiran layinta ba , ya san ita ba zata kiraye shi ba dan haka bai
kankara hakori a hakan ba, bai kuma zuwa gidan malan dan su hadu ba daga karshe tafiama ya yi bayan
kuma an saka ranar da za.a kaita gidanta wace bata fi sati daya ba domin malan ba.ai masa kowani sabgar
aure da ta fi saukar alkur.ani

Sosai abin nan ya tsaye mata a rai, takan zauna a dakinta idan yan uwanta sun bata sarari ta dan huta ta
zurfafa a tunanin me kuma hakan ke nufi? Me abdul ke nufi da ita ne?
Ta sha ta dauki waya dan yi masa message sai kuma ta ajiye ta yatsina fuska a fili ta ambata koma me kake
nufi da ni daidai nake da kai malan, nima ba sonka nake ba bare abin ya dame ni

Abinda ya fi madaukakin bata mamaki shi ne message din bank da ta samu da makudan kudi a ciki, sai
bakuwar lambar kasar waje da ta yi mata message cewa kudin aikinta da ta yi a matsayin bodyguard ne,
Sai kuma wasu kudadan da suka shigo mata bankin ne dai, accmpte din da bata san lokacin da ta bude ba
dan ita dai bata taba budawa ba aka kuma shaida mata da kudi sun shigo wayarta da sabon message da
number dai an saka mata
Idan kina da wata bukata ki min message

Kanta ta girgiza ta ajiye wayar, bata ma fadawa kowa ba dan ta fahimci cewa Abdul ne ke wannan aikin,
shi mai kudi ko? Ita zai hau ta haka ko? Itama ta shiga layin matan nasa kennan, ya aura ya wulakanta so
yake ya ga tana biye da shi tamkar jela, yo ita da ba dan ta san idan ta tsiro da maganar bata sonsa da aure
ba mahaifiyarta zata fita hankalinta ba da ta nuna masa ita zata fara neman sakin a wajensa, ba zata taba
bari ya wulakantata ba a haka, bata nemi ya rufa mata asiri ya aureta ba bale har ya mata iza!

Abdul kam ya sadar da kansa garin Minna,

Gidan horon da ya kai Muhammad ya yiwa tsinke, nan ya tarar da shi tamkar ba shi abinka ga farin mutun
da ya saba rayuwar hutu,

Tsayuwa ya yi gabansa bai furta masa A ba yana kallonsa yana so ya dago su yi ido cikin ido sai dai ina ya
kasa dago da kansa bale har ya yi ido hudu da shi dan kuwa wani mugun tsoronsa yake ji, yanzu haka da
aka barshi daga shi sai shi gaba daya jikinsa bati yake, da haka azabar wahala take? Da haka duniyar da ba
dadi ba sanyin ac ba abinci ba barcin kirki bare wajen kirki yake? Da haka matsatsatsin gidan duniya yake
bama na kiyama ba? Shi da yake daukan kansa wani shege har yake tunanin a kan soyayarsa ba abinda ba
zai iya ba, ba irin wahalar ba zai jura ba sai gashi wahalar duniya kawai ta saka shi ya fara zarewa dan a
yanzu daga ya ga duhun magariba ya fara yowa ya fara ihu tun karfinsa yana neman ceto, wai hakan a
duniyar kennan, shi da ya kashe rayuka tamkar kiyashi ashe ko karfin jinnin su ba zai masa adalci ya saka
shi zama fitacen masifafe ba? Shi kam ya ga rayuwa, yana cikin ganninta....
Yana so ya buda bakinsa ya duka gaban Abdallah, sai dai ya sani ne mai yiwuwa ya matso da zuwansa
kabari!

Sai da Abdul ya gama kallonsa sannan ya juya ya fice a wajen, nan aka ja shi kiiiii aka jefar cikin gagan
yan kurkukun dake jiran ko ta kwana!

Ya jima cikin mota, kansa hade da sitiyarin motar ya rintse idannuwansa,


Zuciyarsa yake ji ba dadi, abubuwan da zuciyarsa ke raya masa a kan rayuwa da rayuwar amininsa ya saka
shi dagawa zuwa saudiya
Ya kusanta kansa da Allah ko zai samu sasaucin sake saken da ruhinsa ke masa... wannan shi ne mafarin
dagawarsa zuwa saudiya
Yan uwa sun je gidan da Abdallah ya fada dan gyarawa Hafsat daki wanda ba yanda bai yi ba kan ba sai an
kai komai ba aman malan ya ce ya jima yana shirin kayan dakin mamansa

Sun gigita da gannin wai a wannan gidan ne Hafsat zata yi zaman aure, Hafsat dai maman malan? Ita ce da
daukaka haka? (Yanzu mutanen mu idan ka yi aure ba.a wani tunani sai na sharetan gidan da aka kai ka🤣
🤣🤣, )
Lale yar malan ta samu waje

Har suka yi suka gama basu ji alamun da wata halita a gidan ba, basu ma san mijin na da wata matar ba,
haka suka dawo gida a lokacin an rufe daki anaiwa Hafsat kunshin tukunya ga dumin dakin kadai wani
tashin hankalin ne, suka zo suna ta santin gidan da tsare tsaren gidan da irin abincin da aka kawo masu wai
daga gidan mamansa sai dai basu ga maman nasa ba

Ita dai mama bata ce komai ba, sai su aunty dake amsawa a haka har aka gama aka watse da niyar gobe
wajen yama za.a dawo a raka amarya dan kowa ya sani gidan malan ba.ai masa bidi.a

Tsakiyar dare wajen karfe uku mama ta tasota daga dakinta ta kamo hannunta ta hau da ita dakin malan

A lokacin yana zaune saman salayarsa yana jan carbi, suna shigowa ya daga hannayensa ya shafa fatiya
sannan ya mike ya dawo saman kafet din kamar yanda suka zauna suka tankwashe kafafuwansu shi dinma
hakan ya yi

Sai da ya sauke ajiyar zuciya sannan ya ce" Alhamdulilah, yau dai Allah ya nuna min ranar da zan sada
mamana da dakin aurenta,
Mama?

Da sauri ta dago da dubanta domin kanta a sade jikinta kuwa sai rawa yake,
Subahannallah shi ne abinda na fada, domin wani irin goshin amare da ake cewa da na hanga a fuskar
Hafsat yana wani irin kyali, gaba dayanta ta canza, gyaran amare ya mugun karbanta, ga jan kunshin da
akai mata na zamani na amare abin ba.a cewa komai

Idannuwanta kuwa tamkar sun kumbura, da alama kuka maman maman malan ta yi, yannayinta da ya gani
ya dan karyar masa da zuciya sai dai ina a yau ita ce ranar karshe, baya so safiya ta waye bai yi magana da
ita ba, dan haka ya ci gaba da fadin" shin zaki zauna a dakin mijinki ki yi biyaya ki girmama sunnar
ma.aiki? Mamana, zaki je ki rayu da niyar sai dai a fitar da gawarki daga dakin ki? Ummana zaki je zaman
bauta, gwagwarmaya da zuciya daya da niyar neman sakamako a wajen Allah?

Gabanta ne ya shiga dokawa, irin yanda mahaifinta ke mata magana a yanzu

A hankali kuma ya sasauta muryarsa ya ce" kowani uba burinsa ya yiwa yayansa aure, Allah ya cikan
burina, zan so y'ata ta zauna dakin aure,
Mamana rayuwar aure wata sabuwar rayuwa ce da zaki shiga mai wuyar fasara,
Hakuri, hakuri, umana hakuri,
Ko wa kike aure, komai girman son da yake maki to fa lale sai kin juri wannan kalma ta hakuri sannan zaki
ga haske a rayuwar zaman auren ku,
Ki yi masa biyaya, sai ku wanye lafia
Mamana, Abdallah dai mai aure ne, kin san da yana da aure, kema kin tashi gidan da mahaifinki ba daya ya
ajiye ba, ke koda mamanki daya nake aure idan kin auri mai mata sai ku zauna lafia!
Na hane ki fitina, na hane ki taurin kai, rashin kunya ko gardama,
Mamana ki kasance........ kukan da ta rushe da shi ne ya saka mahaifinta sada kansa, har cikin ransa yake
jin irin yanda take kuka, da ba dan mamanta na kusa ba ya tabata zai yi shiru ne da nasihar ko zara daina
kuka,
Allah ya saka masa kaunar yarsa mai girma a ransa, yana rokon Allah ya sa rashin jin maganarta shi ne iya
jarabawar da zai yi masa da ita, Allah ya sa mijinta ya zauna lafia da ita, kar ya wulakanta masa mamansa
Duban da mama ta yi masa ya bashi kwarin gwuiwa, dan haka ya rintse ido ya ci gaba da yi mata mata
nasiha mai ratsa dukan gabai har ya saka ka yi sanyi tamkar ruwan sama ya dake ka

Tun tana kuka muryarta na fita har ta kwontar da kanta a cinyar mamanta take gurnani gaba daya muryarta
ta disashe ta daina fita
Sai da aka fara kiraye kirayen salar farko ya saka shi mikewa bayan ya yi mata wata irin doguwar adu.a, ya
yafe mata dukan abinda ta yi masa wanda ya sani da wanda bai sani ba, mahaifiyarta ma haka, sannan ya
umarta da a kaita kowani daki ta nemi gafara, ya mike yana mai shaida masu Abdallahnma zai shigo nan da
sati domin yana saudiya har yanzu bai gama ba

Kamar a lokacin za.a tafi da ita gidanta, gaba daya mama ta kasa mikar da ita, a hankali muryarta na wata
irin magana take furta" Abanna, ni ba zan je ko.ina ba, ni a barni a wajen Abanna, wayo Abanna

Mama kam ta san za.a rina, shi kansa ta san fama ne yake ya gudu ya zubar da hawayen zai rabu da
mamansa, murmushi ta yi ta cicibata da kyar ta kamata a jikinta ta fito daga dakin malan din ta nufi dakinta
da ita,

Suna shiga ta cire mata hijabin jikinta ta zaunar da ita,


Wata dilkar ta zo ta shiga cude jikinta da ita, ba abinda ya dameta da irin kukan da take ta san za.a rina
kuma dole ta yi hakuri ta je domin kowama da haka ya saba

Sai da ta gama filketa ta shiga ta dauro alwallah

Tana gama sallah har sai da rana ta fito ta tashi ta kamata daga saman salayar da take zaune ta kasa tashi ta
dauketa ta kaita can kurya

Ba.a jima ba aunty mariama ta zo

Tana zuwa ta tube hijabin ta kawo garwashi ta mikar da Hafsat ta saka turare a cikin bokicin karfe ta sakata
zama bisa

Hafsat na zama ta ji yanda hayakin ke ratsa jikinta, a hankali ta lumshe idannuwanta sai wasu hawayen ke
zubo mata, karo na biyu kennan, karo na biyu zata bar gidan mahaifinta ta je gidan wani ba da son ranta ba,
eh lale ba da son ranta ba domin bata son sa kuma baya son ta

Aunty ce ta kaleta ta ce" Maman malan, menene??

Idannuwanta da ta ci kuka da su har sukai mata hadari hadari bata iya daga su da kyau ta dago ta zuba mata,

A hankali ta ce" Aunty

*Ni BANA SON SA, KU SHIMA YA TSANE NI!*

ido Auntyn ta tsura mata tana kallonta kafin ta mike ta bude humurar da ta zo da ita katuwar kwalba guda ta
bude ta debo mai yawa ta zo kusa da ita a hankali ta ja zip din rigarta ta yi kasa da ita sosai ta shiga murza
mata shi a hankali a wuyanta sannan ta daga hannayenta ta ce" du saurin ki, ki kasance cikin kanshi Maman
malan,
Ki ringa shafa turare a gurbi gurbi na jikin ki, kin ga daga kasan wuyan ki, bayan kunnen ki, hamatar ki,
kasan maman ki, tsakakanin cinyoyin ki, cibiyar ki, du inda ya dace wannan humura ta zamo ita ce ta sirrin
jikin ki kafin turaran wuta,
Idan kina haka zaki kasance daban, bata da daci bale hakan ya damu abokin zaman ki, bata da karfi bale ta
dame ki ko ta dame shi,
Hannunta Hafsat ta rike ta shagwabe fuska sai ga hawaye ta ce" yanzu aunty kai ni zaku yi? Aunty yaya ina
magana bama zaki kula ni ba??????

Comment zafafa ke saka ni rubutu bilahi🤭


*KUTKALE*

*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct
NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan
number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA
SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN
SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN,
.....* taku ce, Sajida😍😍😍😍

*KUTKALE*

*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA
DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct
NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan
number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA
SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN
SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN,
.....* taku ce, Sajida😍😍😍😍

5️⃣5️⃣

Tsayar da abinda aunty take ta yi, sannan ta duka gaban Hafsat domin so take su yi ido cikin ido da ita

Ai kuwa suka hada idon, hakan ya saka Hafsat dan kawar da dubanta a hankali

Aunty ta yi murmushi tana girgiza kanta ta ce" kar ki damu maman malan, zaki so shin ne

Hafsat ta zumburi bakinta gaba, ita kai ji take da ta je gidan Abdul a yau gwarama ta yi ta zama a
gwauruwarta a yi ta yi mata gorin in dai zatana gannin mamanta da malan sai me?

Daina kulata suka yi, kowa yake hidindimunsa na shirye shiryen kaurar da ita gidanta, domin yan uwanta
mata baki daya kulewa suka yi a dakin mama suna ta kimtsa dukan abin kimtsawa

Sai da magariba ta yi sannan aka samu fitowa da Amarya


Abin mamaki ga kowa mama da kanta ke janye da Hafsat, wace ke cikin lulubi cikin farin abin rufa ba.a
gannin komai nata, yan uwanta sun zagayeta kamshi kam sai rabawa take

A hankali aka shiga dakin Hajia mama da ita,

Suka da ita mama ta yi, cikin nutsuwa ta kalli hajia mama ta ce" mamanta, ta zo yin salama da neman
gafara, a yafe mata zaman yau da kulun

Hajia mama dake zaune da sauran matan a dakinta ana ta cicira maganar irin motocin da suka zo daukar
Hafsat motar ba wasu masu yawa ba aman hameur biyar ce cif dukansu bakake wulik sai haska wajen suke,
suna tsaka da tautaunawar aka shigo da hafsat din hakan ya saka suka bi su mama da kallo da mamaki
Hajia mama ce ta tabe baki ta ce" a yafe

Murmushi mama ta yi ta kama Hafsat ta mikar da ita daga tsugunnin da akai mata

Kama hannunta ta yi suka juya har sun kusa fita amarya kasa kasa ta ce" ba girin girin din ba, ta yi mai, ai
shi matsalar irin haka ba ridi ba daraja sai dai a je a dawo

Aunty nana mariam ce ta ja ta tsaya, sai dai kallon da mama ta yi mata ya sakata juyawa suka fice a dakin
Sai da suka zo kusan kofar gidan mama ta ja ta tsaya ta damka hannun Hafsat a cikin hannun Aunty ,

Da sauri ta juya domin raf Hafsat ta rike hannun taki saki sai da mama ta janye da karfi ta yi ciki tana jiyo
irin yanda Hafsat ke kuka , ita kanta sai da ta labe ta yi hawaye kafin ta saku ta shiga sha.aninta tanaiwa
yarta fatan alkhairi

Su Aunty kansu sun yi adu.a da fatan alkhairi a irin gidan da Hafsat ta samu, sun yi fatan Allah ya sa mai
hakuri da datako ne mijin , hakan zai sa su jima zaman nasu ya yi karko

Tamkar zata suma a lokacin da zasu tafi su barta


Sai dai aure ne, daga shi sai mutuwa su ke rabaka da iyayenka, da danginka , su canza maka muhali,
yannayin rayuwa,
Haka suka rabu da yar uwarsu bayan dogon jawabi da rarashi,
Sun yi mamakin gannin ba wanda ya leko su ko ya aiko masu da sakon su ci kansu, sun kuwa lura da gidan
akoy mutun domin fitila a kunne take kuma da dan hayaniya

Suna tafiya ta nemi waje ta zauna kasa saman kafet dinta ta saka hannayenta bibiyu ta yi tagumi tana bin
dakin da kallo
Jin abin da gannin abin take a wai, wai ita ce matar Abdul? Mutumen da ta hadu da shi dan kawai ta zama
bodyguard dinsa sai gata yau ta zo gidansa a matsayin katarsa?
Rabonsa da ya yi mata wata maganar arziki tun da suka fita zuwa gidan dinki,
Gaba dayansa ya canza mata tamkar ba shi ba, ba wata magana bale kulawa, wai yau ake kawota gidan miji
ba danginsa ba wani nasa shi kansa baya nan bare har ta ji kanta tamkar amarya ko ta rufe fuskarta anai
mata oyoyo ana zolayarta ana jan rufarta,
Gata dai zaune a dakin da mahaifinta ya wani irin kashe kudi ya zuba mata kaya, kayan alatu, kayayaki
masu kyau da gayu, an tafi an barta daga ita sai halinta!

Rufar da ta aka lulubo mata ta yaye baki daya,


Mikewa ta yi tana jin kanta har yanzu da zafi irin kitson nan da aka yaryara mata kananu har haka, kitson
tamkar da alura aka yi su, sun yi cas sun cika sun yi tsayo sun kuma zanu

Hannayenta ta bi da kallo,
Ita kanta kunshin jan lalen hannunta na birgeta sosai

Cire rufar ta yi baki daya ta nufi wajen kular abincin da aka kawota da shi
Budawa ta yi hankali kwonce ta zauna ta ci abincinta,
Kanta ta baiwa hakuri cewar zamanta da abdul ba wani zama bane dan ba zai iya da halayanta ba itama ba
zata iya da wulakancinsa ba, dan haka kar ta wani saka damuwa a ranta ta tsamure ta lalace a wofi, zata
koma kusa da iyayenta soon

Sosai Hafsat ta saki jikinta ta saki ranta a tankamemen bangarenta , bata rasa ci, sha , sutura, kayan kwalam
da makulashe, bata rasa abin kallo ba, ga Ac da take sha kowani lokaci,
Sangartarta take zubawa da barna kala kala,
Takan hada fruits ta markade ta juye peak da kananfari da dabino ta zauna ta yi ta sha abinta
Karshema da yawa ta yi ta saka a frij ya zama ruwanta, koda yaushe zata didika ta je ta mike abinta
Karshen neman magana Hafsat na farkawa daga baci ta yi ra.ayin buda facebook, tana budawa ta dora
hotonta a dp dinta ba tare da dar ba, sannan ta saka sunnanta tsaf Hafsat maman malan, ta koma Whatsupp
ta buda
Sai da ta budar ne ta shiga neman numbobin yan uwanta du ta saka ai kuwa ta shiga takura su sun ki lekota
sun kawota har sun kare da ita kennan?

Su kam suna bata amsa suna rarashinta su a tunaninsu ta kwontar da hankalinta har mijinta ya bata damar
hawa whatsup da facebook

Saukowarsa kennan daga masalaci


Ya nemi waje ya zauna, balarabiyar dake masa girki ta kawo masa tea da dan abinci kadan wanda salak
nema kawai aka gyara da kayan lambu da mayonaise ta juya

Cikin nutsuwa ya sha tea din, yana gamawa ya mike ya dauki wayarsa ya shige can kuryar dakinsa ya dauki
wayarsa katuwa kirar iphone 11 pro ya zauna bakin kujera baba ya danna kiran number Na.ima

Na.ima dake kwonce saman bed doguwar kujerar falonta ta daga kiran

Tana dagawa ta sauke ajiyar zuciya sannan ta shiga shasheka tamkar wace zata fashe da kuka

Idannuwansa ya lumshe, a hankali ya ce" menene?

Sai da ta sauke ajiyar zuciya jin muryar muradin ranta sannan ta ce" ka dawo gida

Abdul da idannuwansa ke lumshe ya ce" kin daina fushin?

Na.ima ta yi shiru, sai kuma ta saki wani dan marayan kuka irin na shagwababun yara, tana yi tana jan
majina sosai hawaye na bin kumatunta

A hankali ya ce" zan kashe fa

Da sauri ta ce" ka yi hakuri, Abdul dan me mani kishiya? Me na gaza Abdul? Abdul haka zaka ci gaba da
aure aure ko fada min ba zakana yi ba bale har na yi tunanin zan samu rarashi?

Idannuwansa ya bude sosai , a hankali ya kuma fadin" Na.ima, tun yaushe kike so na? Wani irin so kike
min?

Na.ima ta gyara kwonciyarta ta ce " ina son ka da dukan karfin jikina, ina jin kaunarka har bargona

Abdul ya lumshe ido yana mai jin tausayinta har cikin ransa, a hankali ya kuma cewa" dan me zaki yi fushi
dan na sako mace cikin gidana dan na kara raya sunnar ma.aiki da ita? Na.ima, a tunanina ko kura na kawo
maki zaki kulata ki ciyar da ita

Zaune na.ima ta mike, a hankali ta ce" Abdul, ko zaki ka kawo min, zan bashi nama, aman idan macen da
zata rabarmin ni.imatacen kuma tsadadan jikinka ne, ina kishinta, Abdul.kishiya ka min ba yar uwa ba, ban
iya boye abu ba bale na yi munafurcin zan so ta, ban taba ganninta ba, bana so na hadu da ita, Abdul bana
son ta!

Abdul dake sauraronta da mamaki ya kali wayar, murmushi kawai ya sakar mata a wayar ya datse kiran

Mikewa ya yi ya bale agogo hannunsa ya ajiye, kansa ya daga ya kali agogon dakin, karfe biyar ne na
yama, ya yi daidai da karfe goma sha daya a Niger,
Doguwar fara kar din jalabiyar jikinsa ya cire ya kwonta saman bed,

A hankali ya lumshe idannuwansa,


Murmushi ya saki, a fili ya ce" kina ina? Kina me? Ke da wa? Shin kin saki ranki a bakon waje? Har yanzu
kin tsane ni? Na san ba zaki taba so na ba, Hafsat kin raina ni sanadiyar sannin na kayar da zina abin yi a
da, da wahala ki ga girmana bayan na sha yin izgili kala kala a gabanki, kin dauke ni mai wulakanta mata
dan kin ga rayuwar taka tsantsan da na yi da matata kin dauki hakan a matsayin ni mai kudi ne, mai halayar
wasu masu kudin

Murmushi ya yi yana dauko wayarsa ya kunna ya shiga whatsupp dan kiran kampaninsa, a fili ya ce" ba
dole ba ki raina ni, ke da kike zuwa ki kakabe min kurar dakin mata kafin na raya sunna? Ke da kike gannin
ke ke bani tsaro?

Yana shiga ya yi kiran su, aka hasko masa kayan da ya yi oder,

Yana kashewa haka kawai ya shiga bin sunnayen wayar yana ware wa.inda zai goge daga wayar

Sunnan Kauriyata ya kurawa ido,


Hotonta ne daga ita sai hulaa a kanta ba ko dan karamin hijab bale baba a saman dp

Da sauri ya shiga cikin sunnan yana kallon yaushe rabonta da hawa ko tsohon whatsup ne bai taba sannin
tana da shi ba??

Ga mamakinsa a lokacin ma tana online

Lokaci daya ya ji gabansa ya yanke ya fadi, a hankali ya fara share zufa yana kallon wayar,

Ya rubuta message ya fi a kirga yana gogewa,


Ina bata isa na mata message ba, bata isa ba!

Shi ne abinda ya fada

Mikewa ya yi ya dauki wayar tafi da gidanka ya yi kira fada

Ana dagawa ya yi maganar yana bukatar su hadu da wuri yana son juyawa gida

A wannan ranar sai da ya fasa wayarsa sannan ya daina kokarin yi mata magana ta whatsup din

Mamaki kawai yake, whatup?

A washe gari yana fitowa daga meeting din da suka yi, ya zauna a wata yar cafetaria

Ya fara shan cafe din kennan ya dauki sabuwar wayar da ya saka layinsa kirar samsung ya yi gagawar shiga
facebook

Tunani ya fada, sunnayenta sun fi million a duniyar nan, idanfa ta shiga da wani sunna daban?

Wata zuciyar ta ce da shi" kai yanzu gani kake rashin jin maganarta har zai sakata ta shiga Facebook? Ba
zata aikata haka ba mana Abdul

Wata kuma ta ce da shi" kai rubuta maman malan!


Ai kuwa har hannunsa rawa yake ya shiga dora maman malan

Maman da suka hayo ba kadan bane, a hankali ya shiga bi yana jin zuciyarsa na dokawa

Sai da idannuwansa sukai masa arba da Hafsat maman malan, ya duba da kyau yar ina ce da komai ya
tabatar masa Kauriya ce ya ajiye wayar hannunsa

Bakinsa ya hade waje daya ya cije lebensa, lale kauriya ta gama raina masa wayo a gidan duniya, yanzu shi
shi shi? Shi zata wulakanta? Talar kanta take ko me? Ko wani rikeken dan iskan take so ya ankara da tsarin
kayatuwar halitarta na fulawer da Allah ya kagota irin Mamuda take so? Ni ko? Ya fada a fili wanda hakan
ya saka daidaikun laravawan dake wajen dan kallonsa

Mikewa ya yi ya saka bakin gilashinsa ya fice a wajen

Yana zuwa gida ya dauki passport dinsa dake ajiye gaban sif din dakinsa na baci ya shiga dubawa, yana
gamawa ya danna kira dan tambayar shin zai samu jirgi ne????????

A ranar bai samu tafia ba ba jirgi, sai an saka shi a tafiar gaba

Bayan kwana uku ta kama lahadi da safe

Hafsat na zaune da aunty Mariam da ta zo kawo mata sauran turarukanta wace bata so zama ba aman
Hafsat fir ta boye waren takalminta sai zaunawa ta yi du a takure tana kallon Hafsat da mamaki gannin ta
sha wando da riga abinta tana shagalinta ga tamfatsetsiyar tvn gidan na hasko indiyawa suna rawa

Jus din da ta mayar ruwanta shi ta kawowa aunty ta bata

Aunty na sha ta kaleta , jus din ya hadu kauri kitib da shi haka kuma ua sha kananfari, a ranta ta ayanna wa
ya koyawa maman malan wannan hadi? Ta san anfaninsa ne?

Gidan ta bi da kallo, ba dati ko daya gidan tsaf tsaf tsaf da shi, ga kanshin turare dake tashi

Da kyar auntu ta samu ta gudu bayan ta kara yi mata nasiha

Ita dai murmushi kawai take har ta tafi ta barta

Dawowa ta yi ta sake wani wanka ta saka doguwar riga marar nauyi fara kal wace sosai ta hade da jikinta
dan rigar bata da wani girma bakinta gwuiwarta ta kwonta saman kafet tana kallon fim har baci ya yi gaba
da ita

Da kansa ya tuko kansa har cikin gidan nasa

Daga cikin motar ya gyara zama yana hangen bangarorin biyu


Masu yi kasu aiki na ta shawagi, mata ne mazan kwaya hudu ne wa.inda ke tsaron kofa kawai, aman daidai
da masu baiwa fulawowi ruwa mata ne, kowace kuma a ma.aikatarta ya daukota, gidan du yan gayu ne
ma.aikatan, girki kansa mata uku ke yi, idan wannan ta yi break fast, wancen ta yi na rana, wancen ta yi na
dare , sai dai du yin nan da ake basu taba shiga bangarenta ba, hasalima bakinsu bautar bangaren Na.ima
domin ko shara basu taba shiga sukai mata ba, yo mai gidan baya nan bai bada umarnin hakan ba, matarsa
kuwa bata saka su ba.

Sai da ya jima sannan ya bude ya fito a motar, daga katon kwadon dake kofar Na.ima ya gane bata nan, a
hankali ya shiga takawa yana gannin sai a lokacin suka gane shi ne a motar dan sai zubar da abubuwan
aikin suke suna risinawa sunai masa sannu da zuwa
Amsa su kawai yake da hannu har ya fice ciki ya karasa dakinsa

Wanka ya yi na kirki da ruwan dumi, sannan ya canza kaya zuwa kananun kaya

Saukowa ya yi ya nufi bangarenta yana ayana irin abinda zai mata na hukuncin buda Facebood da
whatsupp ba da izininsa ba ya tura kofar ya shiga ta coridor din dake sada ka da dakinsa domin kowani dagi
da hanyar da zata kai shi dakin matan ba sai ya fito ta fili an ga ya shiga dakin matansa ba

Hafsat dake dukunkune saman cafet tana baci bata san da an buda kofarta ba bale har ta yi wani abu,

A hankali ya ringa takawa ya shiga, kamshin turaran wutar dakin ne ke ratsa kofofin hancinsa

Tsayuwa ya yi ya kama tsatsonsa ya buda baki ya ce" *Kauriya* da karfi karfinsa

Wata irin zabura ta yi daga kwoncen da take ta mike tsaye cirrr tana kallon inda ta ji amon murya gaba
dayanta a zabure hakan ya saka hannun rigarta ya fado kasa bayin Allahn da ba.a saka masu bra ba suka
dan bayana sosai daga sama sannan gaba daya gashin kanta ribom din ya fadi kasa haka kuma rigarta a
sama daga kasan har pant din ya dan leko daga baya domin mikewar dama rigar ba mai tsayi bace ta dage
mata sosai sai kawai ta yi sama ta haye mazaunanta masu tudu da su

Galala ya yi da bakin da hancin yana kallonta, ba ko kifyawa bale kawai da kai

Hafsat kuwa da ta tsorata kallonsa kawai itama take gana tunanin shi din ne ko kuwa aljani ne? Kun san
abin baci da zabura tsoratar cikin baci

A hankali ya ringa takawa yana nufar inda take tsaye....

Sai da ya karaso dan kusa da ita kadan, kamshin humurarta ya yi masa salama sanyaya mai nutsuwa,

Hannayensa ya miko ya....

5️⃣6️⃣

Hannayensa ya miko a hankali ya janye gashin da ya zubo ya kare masa ganninta da kyau

A hankali ya mayar da gashin saman kanta , fuskarta ta bayana sosai da sosai

Idannuwansa ya sauke a hankali wajen jan lebenta , jajajir da shi yana kallonsa ko ya ce yana harararsa

Idannuwansa ya lumshe kuma lokaci daya ya saka duka kaf hannayen nasa ya janyota

Da yake a firgicen dirowar da ya yi mata ya sameta sai kawai ta tafi gaba dayanta luuuu cikin kirjinsa

Da sauri ya rintse idannuwansa sakamakon jin wani shok da ya yi tun daga kafarsa har cikin idannuwansa

Kara tintse idannuwan nasa ya yi yana jin wani irin kanshi sansanya da take fitarwa

A hankali ya dora hancinsa a dokin wuyanta,


Idannuwansa ya lumshe dan abin ratsa shi kawai yake, jinsa yake har saman kansa

Caji ne ya fara hawa lokaci daya,


Caji mai karfin gaske kuwa
A hankali ya fara jin jikinsa ya fara dan daukan rawa,
Wata tafia tafia ce ya fara ci a cikin sumar kansa tamkar wata kusa ce a kan nasa ta kunce

Idannuwansa ya buda sanadiyar jin tana jan jikinta daga gare shi

A hankali Hafsat ta zare jikinta daga nasa, rungumetan da ya yi ya saka gaban rigar ya kara saukowa sosai,
aman kuma bayan sai ya rufe wato pant dinta ya rufe

Idannuwansa ya kai saman gabar rigar nata,


Sun yi luhu luhu da su daga sama, daga yannayin rigar da ta saka yana iya hangen jajayen kawunansu, sun
yi wani bulbul da su sun bada kalar pomme

Wani irin yawu ne ya hadiye, wanda ya saka dabinon makogwaronsa yin sama da kasa tare da yin wani
makot da su

Baya son kifta ido, baya son wani motsi a irin wannan lokacin

Da sauri ta juya bayanta daga tsayen da take a gabansa

Kafafuwanta ta daga da sauri da niyar barin wajen sai dai meh, jin muryarsa ta yi ya ce" Kauriyata

Muryar a wani irin kurya ta fito, a shake sosai ya yi amanta hakan ya saka Hafsat juyowa ta dube shi

Bakinta ta dan yatsine sai kuma ta juya, ita fama take ta je ta suturta jikinta domin wata irin kunyarsa take
ji, Abdul ne ke kallonta a irin wannan shigar? Harma ta fada cikin jikinsa a haka? Kai gaskiya an yi sakara
itama!

Yana ji yana gani take kokarin shigewa dakinta hakan ya saka shi daga kafarsa ya matsa kusa da ita sosai ya
ce" malama meye haka inai maki magana zaki bani baya?

Gannin ya kusa cin mata ya sakata daga kafarta ta fada dakinta da sauri ta saka kys

Ido Abdul ya zaro daga inda yake tsaye,


Muryarsa ya daga ya ce" ke, meye haka ne? Ya zaki min irin haka ne? Ba zaki tarbeni ba? Ba zaki bani
ruwa ki yi farin cikin ganina ba?

Daga inda take tsaye ta tabe baki itama ta ce" Abdul aikenka na yi ne??

Idannuwansa gaba daya tamkar zasu fado ya fifido, meh? Shine abinda ya fada a zuciyarsa a fili kuwa ya
ce" kin isa ki aike ni ne? Meye kike yiwa sauri ki rufe? Wannan berayen abubuwan naki da basu nuna ba?
Ke Hafsat kin san karamar bab ce ke! Ki fito ki fada min wanda ya baki izinin buda facebood da whatsup a
gidan nan!

Bakinta ta kara tabewa ta haye saman bed dinta ta ki yin magana

Hannunsa ya saka ya shiga dukan kofar, tun yana jijigawa har ya tsaya yana huci ya ce" Hafsat magana
nake maki fa, ki kiyayi ranar da zan rike ki da niyar hukuntaki fa, ni ba sakaran namiji bane da matata zata
shiga yanar gizo fan tsabar wulakanci harda doro hoto? Kowani banza ya kale ki kennan, ciki harda sakaran
tsohon saurayinki ko?

Daga daki Hafsat ta mike ta karaso kusan kofar ta tsaya ta ce" Abdul, ka daina zaginsa, dan ba abinda ya yi
maka, kuma Facebook ni ba wanda na tambaya ni na saka kaina
Wani irin ihu Abdul ya yi daga kofar da yake ya kaiwa kofar wani mahaukacin duka ya ce" ma zage shin,
shege Allah tsine masa mai kallon matan mutane! Ke zaki jaza masa har ubansa na rufe shi ba shi ba
sannan ke kuwa na kakarya ki, Hafsat kika kuma saka wani kato a ranki ban yafe ba, Allah ya mana shara.a
da ke, kuma ba karya wuyanki kowama ya huta

Shiru Hafsat ta yi a hankali ta zauna kusa da kofar, murmushi ta yi a hankali a ranta ta ayanna ashe irin
kofar nan nada rana? Gashi dai ya kasa budeta da karfi ko motsi ta kasa yi

Abdul kam ji yake tamkar ya kona kofar,


Dukan kofar kuwa ya yi ya fi a kirga har hannunsa da kafarsa zafi suke

A hankali ya dora kansa jikin kofar daga tsayen da yake, muryarsa a shake ya ce" Hafsat, so kike ki kashe
ni ne?

Hafsat dake zaune, muryarta ta sanyayar ta ce" aa

Abdul ya ce" to bude min kofar kin ji?

Hafsat ta dan zaro idonta sannan ta ce" ba zan iya bude maka ba ka kashe ni Abdul

Abdul ya ce" kin san dai gidana ne ina iya na shigo maki ta wani wajen ko??

Murmushi ta yi sannan ta ce" da zaka shigo ta wani wajen , da ka shigo tun dazu *Abdallahna*

A hankali ya ce" ba zan iya koda taba gashin kanki da niyar cutar da ke ba, ki bude min kauriyata

Murmushi ta yi, ta ki budewar

Abdul ya kara sanyaya muryarsa ya ce" ki bude min, wayarki zaki bani kin ji?

Hafsat ta mike jiki a sanyaye ta dauko wayar

Tana zuwa ta yi tsaye da hijab a jikinta ta rasa ta ina zata fara?

A hankali ta bude kofar

Tana budewa yana tsaye a waje guda

Ido cikin ido suke kallon juna

A hankali ya mika hannunsa na dama dake masa rawa ya damko hannunta

Janyota ya yi a nitse ya kawota wajen kujera ya zaunar da ita

Zama shima ya yi , ya karbi wayar nata ya shiga

Yana nan zaune ya goge komai da ta yi a facebook bayan ya duba da wa da wa take abota sannan da wanda
ta yi magana

Yana gamawa ya fita ya shuga whatsup, shima sai da ya goge komai sannan ya fita ya goge su a wayar

Daidai da opera mini dinta sai da ya goge sannan ya tsurawa wayar ido

A hankali ya dago da dubansa ya kaleta

Yanda gabansa ya doka masa sai da ya ji tamkar ya saki wayar, irin yanda ya ga ta yi masa a idannuwansa
A hankali ya mike daga inda yake ya matsa kisa da ita, ita kuwa ta dan hade jikinta dan du ta tsorata kar ya
kai mata duka ta san halinsa sarai

Yana zama ya kuma tsurawa fuskarta ido,

Dan yatsina fuskar ta yi , hakn ya saka shi dago da yatsarsa karama ya shafa girar fuskar tata

A hankali ya ce" *KINA DA KYAU HAFSAT*

Hafsat da ta rintse ido na tsoro da sauri ta bude ta tsurawa fuskarsa ido

Saje ya mugun gyara masa fuskar, ta zama wata mai ni.ima, gashin girarsa a cike hakama na dara daran
idannuwansa
Idonsa bai taba yin fari ba, kulun cikin jajaja kadan yake, kwayar ciki kuwa baki kirin da ita sannan mai
girma ce
Lebensa basu da kananta, haka kuma ba manya sosai bane, hancinsa mai dan girma ne sai dogon karan
hanci da ya kawata fuskar

Gashin kansa kuwa ya sha gyata, ba mai santsi bane aman akoy cika
Kanshin turaran Xmen ke tashi a jikinsa mai gida blue wanda ya ciza

Tana kallon nan nasa, yake matsowa inda take zaune.......


A hankali ya dora lebensa saman nata,
Idannuwansa ya lumshe yya shiga bata wani irin kisss mai laushi

Hannunta ne ta jimke sakamakon jin jikinta ya fara rawa,

A hankali ya ja hijabin fake jikinta ya cire mata shi baki daya


Yana fitarwa rigar nan ta jikinta ta bayana, a yanzunma hannayenta du sun fadi

Saman doguwar kujera ne suke a zaune, dan haka sai ya ja ta da kyau saman kujerar shi kuwa ya dora
kafarsa saman kujerar daya, dayar kuwa ya sauketa kasa

A hankali ya dorata jikinsa ......romancing dinta yake cikin nutsuwa, gaba daya jikinsa kuwa rawa yake
haka kuma tun da ya fara taba jikinta bai buda idannuwansa ba

Rawa jikinsa yake sosai da sosai, haka itama nata jikin , sannan tana zubar da hawayen da bata san ko na
meye ba haka kuma ta kasa koda daga hannunta ne bale har ta kwaci kanta

Rigar jikinta yake kawo hannunsa, sai ya kama kamar zai cire mata sai ya bari

Gaba daya yannayin jikinsa ne ya canza hakan ya saka shi sakadukan hannayenta ya dago rigar jikin nata
ya cire mata ita baki daya

Fari kal din pant ne a jikin manyan mazaunanta, sai fara kal din rigar mama dake jikinta irin rigar mamar
nan ce mai rufe iya rabin mama sauran kuwa su ciciko daga sama

Cikinta ya wani irin shafewa, aman cinyoyinta ne ya bi da kallo, ba gashin jiki ko kadan sannan sun tafi
sambal da su sai sheki suke
Gaba daya jikinta kala daya ne, sannan wani irin santsi da kamshi mai dadi dake dukansa

Kansa ne ya kwashi wani irin ciwo lokaci daya ,

Da sauri ya saketa ya mike


Wani irin taka kafafuwansa yake har ya bar dakin

Da sauri Hafsat ta mike daga yannayin da ya yi mata ya haye kanta

Sai kuma ta koma da sauri ta duka ta rufe fuskarta da tafunan hannayenta,


Ajiyar zuciya take saukewa cike da tsoron menene wannan? Abubuwan da ta ringa ji a lokacin da yake raba
jikinta ya girmami tunaninta.....wai dama haka ne abin??????

Abdul na fita ya fada dakinsa bai zame ko.ina ba sai cikin bayin dakinsa

Yana zuwa ya shiga kasan pampo ya kunawa kansa ruwa masu sanyi

Hannayensa gaba daya ya daga ya dora saman garun, idannuwansa ya rintse , sai ga halitarta ta bayana a
idannuwan nasa

A hankali yake jimkar wajen da ya rike da hannayensa

Innalilahi wa.ina ilaihi raj.une, ka cuce ni, ka cuci rayuwata, mema ya kai ni zuwa na dauko ki? Gashi kin
shiga rayuwata kuma sanadiyata an maki balshe, ashe gudun na haihun da nake a banza ne? Ina gudun na
haihu a taba min yayana ni a tunanina wayo na yi na kaurace tunda ban haihun ba ba wanda zai lalata min
y'a bale aya ta kasance a kaina ashe ashe ban tsira ba???

Allah, kai ka saka min mugun shakuwa da yarinyar nan, ni kaina ban san irin girman yanda nake kare
mutuncinta ba, sai gashi wani ya keta min hadinta? Ina son kusantar iyalina ina tsoron zuciyata ta tsaya
idan na je na ji yanda ya mayar min da abina, yanzu mamuda a haka ka kallar min halitar Hafsana? A haka
ka wulakanta min ita da nakasashiyar halitar jikinka? Ashe idan ba.a rabar min yar da na haifa ba za.a rabar
min Hafsat? Ashe ciwon abin nan zai hana ni kadaicewa da ita? Yaya zan yi? Ta ina zan fara? Yaya zan yi
na iya zuwa inda ya dace da ita? Shin bana sonta ne? Aman ai ina girmana lamarinta, kuma ni ba kishi nake
ba! Sannan ba kyamarta nake ba, ban tsaneta ba, hasalima birge ni take sosai da sosai

Abdul kam ya jima cikin bayin nan kafin ya fito

Daga shi sai tawuk ya dauki wasu kayan ya saka ya shinfida darduma dan gabatar da sallah

Bayan ya gama ne ya tsurawa waje daya ido,


Jikinta laushi, komai nata santsi ga kamshin jikinta har yanzu jinsa yake a hancinsa
Halitar jikin Hafsat, bai san akoy irinta a africa ba
Jikinta tamkar na jariri sabuwar haihuwa

Wani murmushi ya yi yana shafar kansa, a fili ya ce" *Kina da kyau Kauriyata*.......
*KUTKALE*

*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA
DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct
NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan
number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA
SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN
SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN,
.....* taku ce, Sajida😍😍😍😍

5️⃣7️⃣

Haka Abdul ya kai har wajen karfe goma na dare kafin ya mike ya sadar da kansa dakin Na.ima domin ba
zai iya yin baci a irin halin da ya shiga ba
Ko a lokacin da yake tarr da Na.ima yakan lumshe idannuwansa ne yana ambaton sunnan Kauriyarsa a
cikin ransa, inda na.ima ta karbe shi suka raya ranar nan domin ita kanta a yanzu ta fara zama jarababiyar
sai dai rashin juriya dake damunta, ta sha maganin , ta saka a ran nata kamar yanda aka umarta aman hakan
ya kasa samuwa, a kulun lamarin sai a hankali

Sai da dare ya ratsa yana lafe da jikinta, ji yake tamkar miya ce aka lasa masa a gaba ya samu abincin,
kallonta yake ta yi fayau da ita bacin wahala ya kama ta

A hankali ya mike ya leka wajen maganin da ya bata ya umarceta idan dai ya kusanceta ta tabata ta sha

Tsurawa maganin ido ya yi, dubansa ya kai wajenta ,

Har sai da ya dauko maganin da niyar zubarwa sai kuma ya mayar ya ajiye
Sosai gabansa ke faduwa yana tunanin abinda yake aikatawa, shin yana kuwa tuna da Allah ke yin komai??
Wata zuciyar ce ta ce da shi, idan ka mata cikin ta haifi ya macen duniya ta mayar da ita dokin hawanta fa?
Mayarwa ya kara yi da kyau wajensa ya juya da sauri ya nufi dakinsa ta dayar hanyar,
Kokarin yakice tunanin dake nuna masa rashin dacewar maganin dake narkar da abinda ya zubawa Na.ima
a cikinta dan jar ya zama halita ba daidai bane yake, a haka har ya shige dakinsa ya nufi bayi

Bai kwonta ba sai da ya kimtsa kansa sannan ya kwonta ya nemi samun baci

Ya jima, ya matukar jimawa yana tunanin rayuwa kafin ya samu baci ya yi awon gaba da shi, Hafsat na
cikin gidansa, na kwonce, Hafsat? Maman malan ....
Wani murmushi ya yi ya juya yana hangota,
A fili ya furta" na san dama ke jarababiya ce😉
Washe gari wajen karfe goma , Abdul ne ya shigo falon Hafsat

Zaune ya sameta saman cafet dinta , ta yi zaman makaranta ta tankwashe kafafuwanta


Salak ne gabanta cikin dan plate tana kara yi masa gutsigutsi,
Gefe guda kuwa ta yanyanka su tumatir da kwai da kayan hadi dai

Tun da ya shigo da salama a hankali da ta daga kanta ta kale shi gabanta ya yanke ya mugun fadi,
Da sauri ta sada kan nata ta ci gana da yanyankawa bayan ta amsa salamarsa

Kujerar da ta fi kusanci da ita ya hau ya zauna, kafafuwansa ya dora daya kan daya yana kallon yanda gaba
daya ta haske dakin,
Ba dakin ne ya hasketa ba, ita ce ta haske dakin gaba daya

Bakar doguwar riga ce ta saka a jikinta mai karamin hannu sosai, tigar daga gaba wani sange sange ne mai
haske wanda ya bayanar da saman halitun jikinta
Gashin kanta gaba dayansa ta hade shi ta saka masa dan siririn bakin ribom
Hannunta da yar karamar agogo baka sidik mai dan zagaye baki mai haske

Bata shafa komai a fuskarta ba sai kanshin turaran jiya da ya shaka a jikinta

Zaman da ya yi kallon yannayinta ne kawai yake,


Sai cacaka wukar hannunta take cikin kwanon, ta ki ta dago da dubanta ta kuma ki ta saki jikinta

Murmushi ya yi, domin karara kunya ce take karanta a tatare da ita aman tana so ta ci karfinta

Mikewa ya yi ya kai dubansa wajen hijabin dake ajiye saman kujerar

Dauko shi ya yi ya karaso kusa da ita, tana zaunen nan ya saka hannayensa ya dagota gaba dayanta tsaye

Hijabin ya zira mata mai hannu sannan ya kama hannunta

Kin tafiar ta yi kamar yanda yake so dan haka ya dubeta da kyau, a hankali ya ce " mu je mu karya ko?

Ajiyar zuciya ta sauke ta shiga bin bayansa suna tafia

Bangarensa baban falonsa nan suka nufa gaba dayansu

Suna shiga sai da gabanta ya yanke ya fadi


Na.ima ce zaune saman table ta hade cikin wani danyen boyel
Gaba dayanta ta sha wani mahaukacin mak up, sai walwali take

Gaba daya Hafsat ta ji ta raina kanta, hakan ya saka ta rage hanzarin tafiar da take

Sai da ya danganata da wajen zama ya zauna shima

Yana zama ya dana abin karaurawa hakan ya saka nan da nan mai dafa abincin ta bayana

Ita kanta abin kalo ce, irin matan nan ne na yare masu shegen kyau, ta iya shafa man shafe shafe hakan ya
saka ya dauki fatarta take fitar da wani shegen haske sai dai karni karni domin kuwa turaren da ta saka
daban haka kuma karnin jikinta daban

Ita dai Hafsat daga salamar da ta yi bata kuma magana ba, salamar da Abdul kadai ne ya amsata, Na.ima ko
kallonta bata yi ba bare har ta amsa salamarta, hasalima waya ce a kunnenta tana amsawa cikin murya kasa
kasa sosai
Gyaran muryar da Abdul ya yi ne saka mai dafa abincin budewa, ta shiga zuzuba masu su duka

Hakan kuma ya saka Na.ima ajiye wayar hannunta

Sai da ta gama zubawa kowa tana wani irin yauki ga manya manyan bonbon ta ajiye sai juyi take da
doguwar riga jikinta sannan ta juya ta tafi

Hafsat kam da kallo ta bi ta har ta shige cikin wajen da take da yakinin kicin ne sannan ta juyo da dubanta

Ido hudu suka yi da Abdul dake rike dariya a cikin cikinsa, dan kuwa irin kallon da Hafsat din ke yi a gaban
kowa ne bata wani rufe ba ko ta boye, sam bata iya munafurci ba

Abincin su Abdul suka fara ci, hakan ya saka Hafsat daukan cokali mai yatsu

Kallon abincin take, crevette ce zallah irin manyan nan an yi mata yar dagargarar miya,
Ina, ba zata iya cik tsutsu ba, tsutsur ruwa ce fa haka kiri kiri ta ci?

Dan juya abin take a hankali tana jin zuciyarta na tashi tashi a hankali
su kuwa sosai suka ci abincin su, basu wani damu ba

Sai da Na.ima ta zo daukan jus ne idannuwanta suka sauka a fuskar Hafsat

Tsai ta yi tana kallonta, so take ta tuna inda ta santa aman shigarta ta batar mata ko wacece aman yannayin
sanyayan kyan fuskarta ya saka mata mutuwar jiki da faduwar gaba
Ashe yarinyar kyakyawa ce? Ashe da aka ce mata yar wani tsohon malami ce ba haka bane? Yaya aka yi ta
samu irin wannan tsararun akaifun da sukai mata das a hannunta

Haka kawai ta ji ta koshi, ji ta yi gaba daya wajen ya cika mata ido komai ya tsaya mata, so take ta ga
tsarin halitar yarinyar sai dai hijab ne a jikinta kuma a zaune take

Tissu ta ja ta goge bakinta, ko ruwan bata samu ta sha ba ta mike tsaye


A hankali ta kali Abdul ta ce" excuse me

Abdul dake dan kurbar jus ya bita da kallo ta juya a hankali ta bi ta baya ta tafi

Bayan ya surbi jus din ya ajiye ya kuma daukan cokalinsa


Dubansa ya kai kanta ya ga har yanzu bata ci komai ba
A hankali ya mika kafarsa ta kasan table din

Hafsat na kokarin kurbar dan ruwan dake hannunta ta ji wani irin abu mai laushi na sosa mata kafarta kuma
a hankali yana yin sama

Da sauri ta ajiye ruwan ta kai dubanta wajen Abdul,


Ido hudu suka yi suna kallon juna , da sauri ta kawar da kanta ta janye kafafuwanta

Biyo kafafuwan ya yi ya kuma shiga sosa mata jiki

Gaba daya jikinta ne ya dauki rawa rawa a hankali a hankali, gaba daya wani irin yamyamyam jikin yake
mata

A hankali ta kuma dubansa ta ga ita din yake kallo,


Lebenta kawai ta iya budawa ta ce" Bari mana

Abdul ya yi mata nuni da ya kiya


Hakan ya saka ta mike tsaye ta gyara hijabinta ta juya da niyar tafia
Bata ga mikewarsa ba, haka kuma bata ji takunsa ba, sai ji ta yi ya dauketa gaba dayanta a hannunsa

A hankali yake takawa da ita har ya je tsakiyar dakinta,


Kallon fuskarsa da take ya saka shi dakatawa,

A hankali ya duko da fuskarsa ya sumbaci saman idannuwanta,

Idannuwan ta jujuya a hankali sannan ta ce" Abdul, ka qjiye ni, ka daina haka mana

Sai da ya idasa shiga tsakiyar cafet din mai taushin gaske ya kara tsaya, fuskarta ya taurawa ido yana
kallonta,

Muryarsa ya rage ya ce" ba zan iya sakin ki ba, ba zan iya dainawa ba Hafsat, so nake na bi du wani sashi
na jikin ki da harshena ina sidewa

Idannuwanta ta yi gagawar rufewa domin irin yanda ya yi maganar gatsaigatsai abin ya dake ta, shin
yaushe Abdul zai daina magana kai tsaye? Yaushe zai koyi al.adun bahaushe ne na kunya?

Tana wannan tunanin ta ji gaba dayanta ya cire hijabin jikinta

Bata ankara da komai ba ya shiga bata kyakyawar kulawa, mai tsuma bawa bale sabon shiga, mai rikita
kwakwaluwa......
Sai dai a lokacin da ya gaba hawa caji sai kawai ya rukunkumeta a jikinta ya rufe idannuwansa ruf, sannan
ya hanata mikewa ta saka rigarta daga ita sai pant mai dan tsayi tamkar gajeran wando da rigar mama
bakake masu kyan gaske

Kwonci tashi, wajen satin Abdul biyu a gidansa tare da matansa

Kowace safiya yakan yi kokarin hada su waje guda su ci abinci tare, cin abincin da ba.a taba gama shi a
tare ba
Bai taba yi masu maganar hada kai ko raba kwana ba,
Bai taba rokar alfarmar su ringa gaisawa ba
Shi dai yakan je ya zo da kowace harda Na.imar kuwa

A kowace rana wani sabon kayan ne Na.ima zata kashe tana walwali abinta,
Bata taba maimaita kaya idan har zasu hadu da Hafsat ba,
A kulun burinta ta ga yannayin Hafsat a tsaye, sai dai hakan ya gagara
Sannan tana mamakin irin yanda kowani lokaci Hafsat din ke zuwa da hijab, kulun ita dai sabon hijab ne
zata saka mai shegen kyau wani kalar dinkin hijab din ita kanta takan kara kallonsa

Wata irin shakuwa ce Abdul ya saka a tsakaninsa da Hafsat,


Ya mayar da lebenta wajen wasansa,
Yakan kai masu cafka ko a wani lokaci ya yi kuradin hakan, yakan zauna a kasa saman kacef ya wara
kafafuwansa ya cire mata manyan suturunta ya zaunar da ita a tsakiyar kafafuwansa su yi ta buga gem a
wayarsa
Sukan yi baci a haka,
Wani lokacin zai saka kudi ya ce idan ta kayar da shi, haka zasu yi ta kokowa suna karawa yana kilkila
dariya yana karawa

Tun tana kawar da lebenta daga bakinsa har ta koyi rikewa da kanta,
Ita kanta ta koyi tsotsar lebensa tamkar ta samu halewa

Sai dai wani lamari fake bata mamaki.....


Abdul bai taba zarce haka da ita ba,
Bata taba yi ba, bata taba maganar haka ake yi da wani ba hasalima a makarantar islamiya ta fahimci miji
na zuwarma mace ,
Zaune take da Abdul, tana gannin irin yanda yake da mugun son mu.amalar taba jikin mace
Abubuwa da dama ke shigo mata kwakwaluwa
Me ke faruwa ne?
Shin haka yake da Na.imarma?
Me yasa da dama lokuta sai ya rikice ya damki jikinta sai kawai ya jirkice ko ya mike ya fita?
Me yasa wani sa.in yake saurin sada kansa idan ya kali halitar jikinta?
Shin auren bakin nan ya tsaya ko kala kala ne?

Ta fara yiwa kanta tambayoyin abinda ke faruwa tsakaninta da Abdul

Basu taba furtawa juna kalmar so ba,


Aman shakuwar dake tsakanin su ta kara girmama ta yi nisan da su kansu basu ankara ba

Basu taba kawo maganar BS ba, basu taba maganar wani bayansa ba ,
Bata taba yi masa maganar matarsa ba,
Bai taba kwana a dakinta ba hasalima bai taba hawa shinfidarta ba

Bangaren Abdul kuwa yana cikin wata irin rayuwa ta matsi,


Bukatarta yake , so yake jininsa da nata ya gwaurayu su zamo abu daya so yake ya buda ido ya ganta a
matsayin wace ya mayar tasa shi nata
Ya rasa yaya zai yi da abinda yake ji a kanta
Hafsat dai ya gama salamarwa cewa, ya yi zaman kareta , hanata zama da Bs, tsayuwa a duk lokacin da
zasu iya yin hira dan ya hana su! Ne kawai bisa dalili kwaya daya tak
Wannan dalilin shi ne ya saka ya kasa mayar da Hafsat mace irin na kowa, shi ya saka masa mugun jin
abinda yake ji a tatare da ita
Yana wuni idannuwansa bude idan ya tina cewa waninsa ya wulakanta masa ita!

Yaya zai yi? Yaya zai yi ne?

Yau ta kama daren Laraba

Wajen karfe biyu ya mije da kyar yana layi ya tafi dakin Na.ima

Tarar da maganin ciwon mara ajiye kusa da bed dinta ya yi ,


Audugar mata kuwa ajiye dan nesa da bed din nata ita kuwa ta samu baci

Tsuru ya tsura mata ido, haka kuma audugar, gaba daya jikinsa rawa yake, hankalinsa ne ya ji yana kara
tashi fiye da yanda yake tunani

A hankali ya kai zaune yana kallon yanda jikinsa ke rawa sosai da sosai
Zuciyarsa ce ya ji tana wani irin gudu

A hankali yake saka lebensa na kasa cikin bakinsa ya shigo tsotsa

So yake ya saka kanshi hakuri a haka sai dai abin ya kasa samuwa

Da sauri ya mike tsaye yana jin gabansa na faduwa


Juyawa ya yi yana wani irin takun sauri ya nufi dakinta

Idannuwansa har rufewa suke son yi tsabar balakin da ya kuno shi

Yana zuwa ya.......

*KUTKALE*
*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct
NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan
number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA
SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN
SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN,
.....* taku ce, Sajida😍😍😍😍

5️⃣9️⃣

A hankali ya ce" Hafsat

Hafsat dake lunshe idannuwanta da ta ji sun yi mata mugun nauyi ta amsa can kasan makoshi tana
sauraronsa

Abdul ya ce" na gode

Shiru ta yi, bata san godiyar ko ta meye ba, ita dai da son samu ta yi ya yi shiru ta yi baci

Abdul ya kuma cewa" Hafsat?

Da kagauta ta dago idannuwanta, da irin duban ba zaka barni na huta ba?

Abdul ya sakar mata murmushi ya ce" Allah ya yi maki albarka


Idannuwanta ta lumshe a hankali sannan can kasan makoshinta ta amsa da amen ta rufe idannuwanta ta
shiga fafutukar neman baci ido rufe

Sai da ya ji lumfashinta ya sauya da na dazu sannan ya mike a hankali ya gyara mata kwonciya

Zuwa ya yi ya kuma dauro alwallah ya dawo ya hau salayarsa,

Sai da ya yi raka.a biyu kawai sannan ya zauna ya shiga jan carbinsa

Ya jima yana jan carbin, kafin yake kai dubansa wajen wayarsa dake ta haske tun dazu

Daukota ya yi ya duba,
Message ne daga number mahaifinsa

Message din ya shiga ya ga kamar haka" Allah ya kara budi Abdallah, mun gode

Bakinsa ya tabe ya ajiye wayar ya koma ya ci gaba da jan carbinsa

Sai da ya kai har kusan karfe biyar sannan ya ajiye ya mike ya dauko maganin dake cikin kayansa

Zama ya yi saman salayar, kansa ya tsayar waje daya yana tunani


Zako ta yarda ta sha?
Zata yarda ta sha wannan maganin kuwa?
Idan Na.ima ta yi masa biyaya ya tabata dan tana yi masa mugun son da ba zata iya musa masa komai
girman bukatarsa ba
Aman Hafsat fa? Ya sani sarai ba zata yarda kawai ya balo mata magani ya ce ta sha ta yarda ta sha ba tare
da ta san ko na meye ba,
Abincin mai aikinsu bata taba ci ba a kulun sai dai ta cacaka ta mike sam ya rasa me ya sa bale har ya
sameta ta nan
Idannuwansa ya rintse,
Shi kam bai san yanda zai yi da lamarin nan ba,

Mayar da maganin ya yi ya koma saman bed din ya kwonta ya rungumeta a jikinsa

Bacinta take hankali kwonce, lumfashinta da dumi dumi sosai yake sauka hakan na nuni da zazabi ke son
zubo mata

A takaice dai wannan dare Abdul ya raya shi idonsa biyu, ya raya shi yana begen fulawar dake gabansa
kwonce, ya raya shi yana mai neman mafitar yanda zai yi da ita ta sha maganin da yake baiwa yar uwarta,
yana son haihuwa fa, yana son samun yaya, da zai samu maza ......sai dai ya san ayya sai ta tabata a kansa,
irin yanda ya yi wasa da yayan mutane yana tsoron hakan ta kasance a kansa!

Sai bayan ya gama sallah ya tasheta,

A hankali ta iya mikewa ta sauko daga saman bed din nasa

Kanta na kallon kasa ta samu ta yayumi abin rufar tasa ta nemi hanyar ficewa dan zuwa dakinta

Da sauri ya rike hannunta yana kallonta ya ce" ki zauna a nan Kauriyata plz

Hafsat ta kale shi da kyau sannan ta ce" nan bangarenka ne Abdul, wanda ba ni daya nake da kai ba,
matarka na iya shiga du lokacin da muradin hakan ya taso mata, inma tambayeka na taba kwana a nan ne?
Ni dakina zan je
Murmushi ya yi yana kallon bakin tsiwar nata, ita dai bata sasautawa kennan dai, du irin halin nan da take
ciki na wahalar da ta sha a jiya da dare bai hanata buda dan bakinta ta dan juya shi ba

Murmushi kawai ya yi sannan ya bita da kallo har ta fice a dakin

Wani murmushin ya yi a ransa yana godewa Allah da ni.ima da ya yi masa, du irin abubuwan da ya ringa
aikatawa sai Allah ua bashi matayen auren dake rufe ruf abinsa, shi dai haihuwa ne kawai ba zai yi na, ya
hakura da haihuwa.

Hafsat na komawa dakinta wayarta ta dauka ta yi kiran number auntynta


Kuka ta fashe mata da shi kafin ta ce" aunty ciwo nake ji

Shiru aunty ta yi, ta dan jima sannan ta ce" Hafsat, kina ina ne? Mijin ki ya zo ne??

Hafsat ta turo bakinta ta ce" eh ya zo, yama jima da dawowa ai, aunty ni ki zo dan Allah ba zan iya tafia ba,
ki zo ki kaini wajen Malan!

Aunty ta sauke ajiyar zuciya tana mamakin yaya aka yi Hafsat ke barambarama haka? Koda yake ba sai ta
yi kawayen da zasu koya mata yanda zata yi ba sannan zata gane me yaren ke nufi

Cikin hikima aunty ta kwatantawa Hafsat cewa hakan ba wani abu bane zai fice, sannan ta koya mata yanda
zata kula da kanta
Sai da ta kwadaita mata ladan hakan sosai sannan sukai salama

Yanda Aunty ta koyar da ita haka ta yi, ta tatare zannin gadon ta kai mashine din wanki,
Sallah ta gabatar

a hankali ta samu ta yi shinfida sannan ta haye gadonta ta nade

Can wajen karfe biyu na rana ya shigo dakin, kwonce take tana ta bacinta hankali kwonce

Abincin da ya shigo da shi ya ajiye sannan ya karasa kusa da ita

A hankali yake shafar gefen fuskarta har ta buda idannuwanta

Murmushi ya sakar mata yana kallonta

Mikewa Hafsat ta yi daga kwoncen tana kallon agogo

Idannuwanta ta zaro tana kallon agogo

Bata yi magana ba ta sauka daga saman gadon ta je ta yi brushing

Tana fitowa ta karasa inda yake zaune

Hannunsa ya mika ya janyoya jikinsa yana kallonta, yanda take sasada kanta abin na matukar birgeshi, ita
kam komqi ta yi na jan ra.ayinsa sosai

Abincin da ya shigo mata da shi ne ya miko mata ,

Zaunar da ita ya yi ya shiga kokarin ciyar da ita

Sai da ta kusan rabi ta ji cikinta ya dan daure


Dafe cikin ta yi kadan, sai kuma ta ji ya saki
Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta kai dubanta wajensa
Gani ta yi madaukakiyar damuwa a tare da fuskarsa, gannin ta saki cikin nata har sai da ya sauke ajiyar
zuciya

Bata nuna komai ba sai ci da ta yi cikin nutsuwa har ta gama

Tana gamawa ya fice da abincin,

Sai da ya ajiye abincin a kicin ya jinginar da bayansa, ajiyar zuciya ya ringa saukewa domin irin rike cikin
da ta yi gabansa ba karamin faduwa ya yi ba, me hakan ke nufi?
Tsoro ya ji kar a je maganin da ya zuba mata a abincin dan dabara ya saka mata rikewar cikin

Watsar da abin ya yi ya nemi walwalarsa, karshema fita ya yi ya tafi gidan malan cike da nishadi

A kwanaki bakwai da Abdul ya yiwa Hafsat sun matukar shakuwa


Shakuwa fiye da ta da, domin kwana daya rak ya saka mata ta huta kafin ya shiga horar da halitarta irin tasa

A hankali ta ringa koyon al.amuransa, bata da sanya a abinda ya shafe shi, tana kafa kafa da komai nasa, sai
dai abinda ke damunta mararta na yawan yi mata ciwo bayan ba al.adarta ke kusantota ba, sam al.adarta na
nesa dan bata ana jibi kawota gidanta ta gama

Bayan wata mu.alar aure da suka yi, Abdul ya kawo mata jus

Hafsat na sha ba.a dauki lokaci mai tsayi ba cikinta ya kule

Wata irin zabura ta yi jin mararta na kara rikice mata,


Da sauri ta nemi sauka a gadon gannin abin na kara hawar mata
Abdul da fitowarsa kennan daga bayi ya tarar da ita tsugune wajen bed din tana mitsitsiya

Da sauri ya ajiye kum din hannunsa ya nufeta gabansa na wani irin mugun faduwa..........yana zuwa ya........

Ku gane, situation din rayuwa na saka mutun da yawa zama wasu iri, zaka ga mutun na rayuwa irin ta
bayahude, wanin na canzawa, wani kuwa haka yake tafia har ya tsufa ya koma ga mahalicinsa
Abdul na gudun haihuwa ne dan baya so ya sami mace ya wayi gari ya riski wani ya wulakanta masa ita,
Bai san cewa Allah mai gafartawa bayinsa ne, sannan idan ayyar ce zata kqsance a kansa bai isa ya hana ba,
ba.aiwa Allah wayo
Dan haka zan so ku fahimci labarina....ku gane me ya kunsa.....godiya nake🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰
*KUTKALE*

*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA
DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct
NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan
number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA
SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN
SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN,
.....* taku ce, Sajida😍😍😍😍

6️⃣0️⃣

Da sauri Abdul ya nufeta, irin yanda take damkar cikinta sai da gabansa ya yanke ya fadi

Da sauri ya cicibata ya dagata ya dorata saman bed din dakin


Du ya bi ya rude, danna inda take rikewar kawai yake hankalinsa tashe

Hafsat dake neman ficewa a hayacinta ta yi saurin damke hannunsa, muryarta na wani irin rawa ta ce"
Abdul zan mutu

Da sauri ya mike tsaye ba tare da ya yi wata wata ba ya wawureta daga saman bed din

Sai da ya nufi hanyar bayi da ita sai kuma ya juyo da wani irin sauri sauri gudu gudu ya nufi kofar fita da
ita, daidai lokacin tuni Hafsat ta sume, ta fita a hayacinta

Gaba daya Abdul ya rikice, yana zuwa motar da ya bude ya sakata a nan ya lura da ta sume,
Innalilahi wa.ina ilaihi raj.une...shi ne abinda ya fada da dan karfi yana kallon fuskarta da ta yi fayau da ita,
Bai wani lura da bai dauko mata hijab ba, haka kuma bai lura da rigar jikin nata doguwar riga ce mai siririn
hannu rigar da ta bi ta fitar mata da surar jikinta sosai

Wata irin rufewa ya yi ya zagaya ya shiga mazaunin direva ya tayar da motar

Tuki yake na garari, yana yi yana take dokokin tukin,


A haka har ya karasa clinik
Yana zuwa ya fita a sitin ya kuma daukanta ya nufi cikin dakin likitocin

Tarbansa nourse din ta yi da sauri aka gurguro gadon mararsa lafia aka dorata

Da sauri wata daga cikin nurse din ta danna number docter dan fada masa an kawo urgence
Wani irin zama abdul ya yi kan kujerar dake wajen,
Idannuwansa ya rintse da sauri sakamakon wani irin dokawa da zuciyarsa ke yi,
Walahi rabonsa da ya ji irin haka tun lokacin da ya ga gawar kanwarsa, ya ga ta mahaifiyarsa, sai wanda ya
ji a lokacin da ya gane amininsa ne bakin kumurcin da ya hana shi zaman lafiya

Yana nan zaune mutumen da yake docter ya zo ya shige dakin

Nurse din ce ta zo wajensa ta ce" asalamu alaikum

Da sauri ya dago ya sauke dubansa a kanta

Dan gyara tsayuwarta ta yi ta ce" docter ne ya ce a tambayo, shin wani abu ta ci? Sannan tana da ciki? Ta
saba irin haka?

Tamkar wanda ke karantar bakinta dan tsai kawai ya yi yana dubanta,


Sai da ta ce" Malan are u ok?

Da sauri ya kawar da dubansa daga kanta, fuskarsa a yannayin hadewa ya ce" ban sani ba

Kara dubansa ta yi daga sama har kasa, yannayin shigarsa ya sakata yin gum da bakinta ta juya da sauri

Tana shiga ta tarar ta farfado aman sai birkidadoniya take ana tareta

Likitan ya gama sauraron abinda aka ce,


Da yake mai hakuri ne sai ya matsa kusa da Hafsat din ya shiga yi mata tambaya a hankali

Kanta kawai take juyawa idan eh ne ko aa ne

Kina da aure?

Hafsat ta gyada masa kanta


Yaushe rabon ki da al.ada?

Hafsar ta nuna masa hannunta wato yatsarta biyu


Tambayarta ya kuma yi kwana?
Ta girgiza kai,
Sati?
Ta gyada masa kai

Shin kin ci wani abin da baki saba ci ba??

Hafsat ta juya masa kai

Ya ce" dama kina irin haka??

Hafsar ta kuma juya masa kai alamar aa

Wajen da ta fi rikewa ya kurawa ido,


A hankali ya ce" kin sha wani magani ne???

Hafsat ta girgiza kanta tana ta mikewa tamkar zata kara sumewa

Dubansa ya kai wajen nurse din ya umarta da a yi mata hoton cikin da na.urar haskawar

Yana gefe yana kallo yanda suka ja rigar,


Sai da aka shafa mata wani ruwa ruwa mai mai sannan aka dora abin haskawar,
A hankali suka ringa bin shafafiyar mararta suna haskawa, lokaci daya kuma suna daykan hoton wajen da
ya dace, doctern kuwa yana tsaye yana ganni da kyau

Sai da suka gama sannan ya amsa ,

Sai a lokacin ya tsira ruwan allura ya tsira mata

A hankali a hankali ta fara sauke ajiyar zuciya, a haka har ta saku ta ji ya lafa mata sosai da sosai

Sai a lokacin ta bi dakin da kallo, nurse daya ce can gefe kusa da docter, sai ita dake kwonce saman gado an
rufa mata wani abin rufa wajen kirjinta

A hankali ta sauke kafarta daya, dayar ra miko ta sauko cikin nutsuwa baki dayanta ta sauka daga saman
bed din
Mararta take ji ta yi mata wani mugun daurewa da nauyi,
Bata yi kasa da gwuiwa ba ta tunkari wajen doctern, shima lokacin ya ga ta sauko

Nurse din ce ta kamata ta zauna a wajen da ya nuna mata

Sai da ta yamutsa fuska domin yana kara murda mata kadan kadan sannan ta fuskanci doctern da kawai
yake binta da kallo

Sai da ya dan sosa kansa sannan ya shiga yi mata tambayoyin da suka shafi aikinta ko karatu, shekarunta,
shekarunta nawa da aure,

Tambayarta ya yi cewa, shin kafin ta yi aure ta ringa shan maganin hana daukan ciki? Jin cewa auren nata
gaba daya bai fi wata biyu ba

Ido ta tsura masa, cike da mamaki,


Kanta ta girgiza

Ajiye biron hannunsa ya yi ya ce" look, zan so ki bani gamsashiyar amsar da zata bani damar dora ki
abinda ya dace, mararki na cinkushe ne da maganin hana daukan ciki, na.urar da muka yi anfani da ita ta
bamu damar fahimtar hakan

Ajiyar zuciya ta sauke, a hankali ta ce" ban taba sannin kalarsa ba

Docter ya dubeta da yannayin mamaki, aikinsa ne ya zama wajibi ya bi didigi, dan haka ya ce" ko dai kin
sayi magani a bakin titi na mura ko wani abin a rashin sani an baki wannan?
Shi kansa sai da ya fadi hakan ya ga abin wani baibai, a bakin titi?

Hafsat ta dago da dubanta, zuwa lokacin hankalinta ya fara tashi,


Idannuwanta ta saka cikin na docter ta ce" bana shan magani na fi kaunar a min allura da na hadiyi magani!
Rabona da na hadiyi magani na kusan shekara hudu! Bana sha, bana bukatar shan magani docter!

Kansa ya daure, dan haka ya ce" magani ne mai hatsari kika ringa sha, ba sai kin sha shi a gudajinsa zai
tarun maki a mara ba, koda a narke kike shan sa idan ya fi karfin ki zai je ya tarun maki ya zame maki
matsala, magani ne mai narkar da sperm, muna samun irin cas din nan sosai, bamu bata a hakan, aikina ne
fannin mata, yanzu haka zamu dauki fitsarinki dan mu ko ahigar cikin kika samu yake faman barewa ya
saka haka?

Hannayenta gaba daya biyun ta dora saman table din, a hankali ta dora su saman yalwatacen gashin kanta
dake fitar da ni.imtacen kamshi
Gabanta ne ke faduwa, lokaci daya rigimarsu ta baya son haihuwa ba zai daina baiwa matarsa maganin
rashin daukan ciki ba ta shiga fado mata a rai, tun tana matsayin bodyguard dinsa, tun a lokacin da yake yi
mata maganar matsalarsa a ranar da ta yi fushi ta shige dakinta ya bi bayanta yake mata bayani, har ta yi
masa nunin yana tunanin ya isa ya zagaye abinda Allah ya hukunta a kansa?

Da sauri ta dago da dubanta ta ce" docter, ko a cikin abinci, ko a jus ana iya narkar da shi?

Docter ya bata amsar kwarai kuwa

Gabanta ne ya kara faduwa, lokaci daya kuma ta samu ta mike daga zaunen da take,
Lale yau ta yarda cewa rayuwar da suke da shi ana yinta ne bisa tafarkin sha.awar jikinta, ta sani mace bata
daraja a wajen Abdul, rashin nuna mata soyayarsa bai dameta ba gannin suna zaman lafia, sai dai a yau ta
gane yana zaune da ita ne da zuciya biyu, suna zaune gida daya karkashin innuwa daya suna wasa da dariya
suna raba shinfida daya yana tatalinta yana rungumeta ba dan so ba sai dan albarkatun jikinta, ita kuwa me
ya rufe idannuwanta har haka? Me ya yi mata dadi haka? A yau a duniya ba zata iya zama da mutumen da
baya tsoron Allah har haka! Da ta mutu fa? Da ta samu mugun ciwo fa? Yanzu haka wa ya san me ya samu
mahaifarta? Sam, bata ma fara yi masa son da idannuwanta zasu rufe ta zauna da shi yana bata maganin da
zai cutar da ita a duniya sannan ta je ta tarda Allah, yo ita wani dadi ta ji na duniya da har zata ki mararin
samun dan jaririn da zai debe mata kewa? Namiji? Zara yi ta zama da shi kulun a dadi zuma ne? Watarana
sai ya nuna mata halin, wata rana sai ya yi mata abin, idan ya mayar mata da wuninta tamkar tana prison
din KUTKALE wani sanyin idanniya zata kalla ta ji sanyi? Yau du wanfa baya son haihuwa da kai baya
son ka, koda mutuwa ce zai maka fata

Likitan ne ke kiran madame, ji mana? Nurse din ma ta biyo bayanta sai dai ina, gashin kanta ya yi mata
male male a jikinta, rigar ta mugun karbarta du kuwa da jigatar da ta yi ta fito a dakin

Abdul dake tsaye yana kallon kofar dakin urgence din ya tako da sauri yana kallonta da mamakin har ta
mike likitan bai fito ya kiraye ahi ba??

Hannunsa ya mika wajen fuskarta, murna, mamaki, da fargaba ya dan dago habarta yana kallonta, a hankali
ya ce" Kauriyata, kin tashi? Ni na san sai kin fi karfin wannan ciwon! Me aka ce ke damun ki? Mu koma na
ji bayanin likitan

A hankali ta saka hannunta ta cire nasa daga habarta,


Idannuwanta da suka canza mata ta dago ta saka cikin nasa cikin wani irin kallo na kakausa,

A hankali ta ce" Abdul, dama haka ne rayuwa? Ashe ki ba zai tana zama so ba? Abdul na godewa Allah da
bana jin ko digon son ka a raina!

Gabansa ne ya kwonci kwonci ya fadi, da sauri ya kara buda idannuwansa yana kallonta, a hankali ya ce"
Hafsat, kwakwaluwarki ta tabu ko.me? Me aka baki a cikin dakin can???

Hafsat ta yi murmushi tana kallonsa, a hankali ta ce" Alhamdulilah, ban haukace ba, hasalima na fi kowani
lokaci nutsuwa, Abdul dan Allah na roke ka, ka je gida ko ka tsaya a hanya ka rubuto min takardata, na
hakura zama da kai!

Da karfi ya ce" *KE*

Hafsat ma ta ce" *KAI!*


Na tsane ka Abdul! Na tsane ka! Ka sake ni, in sha Allah koda ka bata min mahaifa ba zan rasa mai
kwasana a haka ba!

Hannunta da ya rike ba da karfi ba ta fizge daga rikon ta juya da sauri ta fice a haka

Summar seconni ne Abdul ya yi a tsaye sakamakon jin cewa ta farga da abinda ya ringa bata cikin jus ko
abinci,
Kalamanta suka kasance ruwan farfadowarsa,
Lokaci daya ya daga kafarsa da gudu ya bi bayanta,

Har ya kusan fita ya dawo doctern dake tsaye ya ciro baje dinsa ya nuna masa, a gagauce, murya cike da
jaraba da tashin hankali ya ce" walahi sai na tagayaraka! Na rantse ba zan barka haka ba!

Doctern ya bi rubutun da kallo lokaci daya kuma Abdul ya fice daga wajen, Doctern ya kalli nurse din
itama shi take kallo,

Muryarta na rawa ta ce" docter dama ana haka? Ba aikin ka ka yi ba???

Doctern ya juya da sauri ya shige Office yana danna wayarsa

Abdul da ya fito a kafarsa da mugun gudu, sai dai me...adaidaita ya hangi ta dauki Hafsat har sun falfala da
gudu

Wani irin ihu ya saki a wajen ya ce" Hafsat! HAFSAT!


Burbudin hayakin adaidaitar kawai ya bade shi, lokaci daya ya ringa jin duniyar ta yi masa zafi,
Hankalinsa ne ya ringa jin ya gama tashi, a hankali ya ringa jin numfashinsa tamkar na mai ciwon huka sai
sama yake yana kasa,
Hafsat ce zata bar shi?
Hafsat din sa ce zata bar shi?
Ky din motarsa ya laaluba ya ji baya jikinsa,
Ya tataba ita ta lalube dan kar ya bi ta da gagawa!

A hankali ya ce" Hafsat, kar ki bar ni....na tuba

Idannuwansa ya rintse yana jiran wani adaidaitan, dan ya san kawai gidan malan zata je, zai kai kansa da
kansa , a yi masa du hukuncin da ya dace aman walahi ba mai raba shi da matarsa!

A lokacin daa Adaidaitan ya tsaya ya shiga, sunnan anguwar kaawai ya fada masa, bai damu da yau ya taba
shiga adaidaita ba, hankalinsa a tashe kawai yake!
A hankali ya kuma fadin" ko hijab babu a jikin ki Hafsat, na san darajar du wata halita taki Hafsat, yaya
zaki fita cikin garin dake cike da kuraye a haka? Hafsat, ina *Kishin ki😔*, ..............

😩😩😩😩😩😩😔😔😔😔😔😔
*KUTKALE*

*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA
DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct
NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan
number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA
SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN
SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN,
.....* taku ce, Sajida😍😍😍😍

6️⃣1️⃣

Direct bakin makaranta Abdul ya nufa, dan ya tabatar cewa Hafsat ba zata koma gidansa ba, sai dai ta yi
gidan su

Sosai malan ya yi mamakin ganninsa an sauke shi a adaidaita sahu,


Bai gama mamakin ba wani mamakin ya sake kama shi jin Abdul ya bukaci da a biya mai adaidaitan

Shi dai malan cirewa ya yi ya biya sannan suka zauna tare da almajirai ana ta karatu

Abdul ya yi tsuru tsuru yana bin malan da kallo, shi kuwa malan ya maida hankali tun bayan da suka gama
gaisawa da Abdul din kan dalibansa

Sai da ya gama yiwa wa.inda zai yiwa kari, ya kuma karbi harda wajen wa.inda zasu kawo sannan ya
takaita dogon zaman karantun ya yi masu salama

A hankali suke takawa shi da malan har suka samu wata sansanyar innuwa suka zauna

Malan ya fuskanci Abdul, sai da ya dan kara kallon yannayin shigarsa, lale mutun ne mai son saka jalabiya,
sai dai shirin abin kallo ne

A hankali ya ce" Abdallah, yannayinka bai kwontar da hankalina ba

Abdul dake ta kale kale ya dubi malan, a hankali ya sauke boyayiyar ajiyar zuciya sannan ya ce" Malan, a
gafarta min, ni din mai laifi ne

Malan ya kara fuskantarsa da kyau, a hankali ya ce" me ke faruwa ne??


Abdul ya sada kansa da kyau, can ya ce" dama ta taba nuna min bata son irin haka tun a lokacin da muka yi
zaman aiki da ita, tsoron irin rayuwar da na gani, na kuma aikata a da can baya kafin na shiryu ya kasa
barin zuciyata har nake daukan mataki, hakan ne ya hasalata har ta min fushi da munanan kalamai, Malan
har cewa ta yi wai ta tsane ni

Malan dake sauraronsa ya dube shi da kyau, duda bai fahinci laifin da ya aikata ba, domin kuwa Abdul din
sam bai fadi laifin nasa ba, sai dai ya ji mamakin mugun furucin da ta yiwa mijinta, miji fa? Miji mai
daraja? Ashe du irin nasiha da gargadin da ya bata lokaci mai tsayi yanai mata a banza ne? Bai taba jin ya
mugun ji haushin mamansa irin na yau ba, ashe ba zata saduda da duniya ta gane ba gidan zama bace
Malan bai iya cewa Abdul komai ba, sai da ya sauke ajiyar zuciya na bacin ya fi a kirga sannan ya ce" a ina
take ne maman??

Abdul dake sasada kai cike da kunya ya dan dago jin kamar ton din voice din malan ya canza , a hankali ya
ce" na san ta zo gidan ne dan ranta a bace ta shiga adaidaita

Malan ya gyada kansa, nan ya kara tabatarwa kansa cewa lale bata san ciwon kanta da na mahaifiyarta ba,
yanzu ko dan gudun gorin yan gidansu ba zata yi hakuri ta zauna gidan mijinta ba? Mutumen da shi bai
gujeta ba , a irin yanda aka so wulakanta ta, ya dauka ya ce shi a daura da shi, shine zata furtawa ta tsane
shi,
Sai.ma ya ringa jin haushin Abdul din kansa dan ya nuna muguwar damuwa da shi, a nan take kuma ya
shiga tambayar kansa....shin ya mugun sangartata ne ya saka ta irin wannan lamari ko me?
Bai iya cewa komai ba sai shiru da ya yi da bakinsa ya mike ya yi gaba

Abdul ya mike da sauri yana dan sosa kansa ya bi bayan malan

Wajen mitar suka nufa malan ya masa bismillah, wato yana nufin ua shiga

Abdul ya bude ya shiga motar ya yi shiru yana kallon waje guda

Sai da Malan ya tayar da motar ya fara tafia kadan kadan sai kuma ya take birkin, kallon Abdul ya yi ya ce"
kai, dan me ka zuba mata ido ta yi maka rashin kunya baka lakada mata duka ba? Kai zaka bari ta ringa
haka ne? Mamana fa idan ta samu haka ba zata taba jin magana ba, mamana ce, ni na haifi abina, na san
wacece ita !

Abdul ya tsurawa malan kawai ido, duka, wai ya daki Hafsat, hm

Malan ya kuma tayar da motar ya dauki hanyar gidan

Abdul na lure da yannayinsa, kamar ransa ya baci sosai, sai dai ya kasa yin wani abin yana dai biye da shi

Malan na zuwa ya ja ya tsaya kofar gidan

Sauka ya yi ya nufi cikin gidan bayan ya umarci Abdul da ya tsaya

Bai jima da shiga ba ya fito,


Tsaye ya yi yana kallon yannayin garin,
Hankalinsa ne ya fara tashi bata gidan, bata zo ba
Juyawa ya yi ya karbi waya a hannun baban yaronsa ya lalubo number yayarsu

Amsar da ta bashi bai ji dadinta ba, domin rabonta da Hafsat tun da suka rakata gidanta wai

A haka ya ringa kiran yayan nasa har ya fada kan Mariama

Inda infa ta fara a lokacin da ya tambayeta Hafsat,


Kashe kiran kawai ya yi, ko hular kansa bai cire ba ya koma motar ya tayar

Tun da yake bai taba zuwa gidan yar tasa ba, bai taba zuwa ba ko da wasa, ko bata da lafia yana jira har ta
zo da kanta sannan sai gashi yau bai jira an yi masa iso ba bai sanar da zai zo ba ya yiwa gidan tsinke
bayan ya umarci sirikin nasa da ya biyo bayansa su shiga

Nana mariama dake tsaye bakin Pamp ta dago da sauri jin muryar mahaifinta da kuma kamshin turaransa

Idannuwanta ta kwalalo waje baki daya, lokaci daya kuma ta gyara zaman hijab din jikinta ta ce" Aba???

Malan ya gala mata wani mugun harara, ransa bace ya ce" ina take??

Marima ta yi gagawar juwaya ta tafi dakin, bata jima ba sai ga Hafsat ta fito, a kan rigar nata dan kwali
kawai ta dora ba abinda ya shafeta ,

Tana fitowa ta nufi malan da yannayin rigima

Bata san da haka ba, bata taba tunanin haka ba, bata taba zaton hakan zai faru ba, sai ji ta yi na farko a
rayuwarta mahaifinta ya wanka mata mari

Daga Abdul, har Nana mariama idannuwa suka zaro a fili a tare kuma suka Furta Aba😳
Ba.a taba yi ba, hakan bai taba faruwa ba, malan bai taba daga hannunsa a kan mamansa ba, bai taba taba
lafiar jikinta ba, hakan ya saka lokaci daya Hafsat ta duke a wajen a kan kafafuwanta
Kanta ta sada kasa, gaba daya jikinta ne ya dauki rawa

Hankali tashe Abdul ya nufeta, yanda ta dukan shima ya duka, gaba daya jikinsa ne ya kwashi rawa, lokaci
daya kuma ya kuma dago da dubansa ya kali malan, muryarsa har rawa take ya ce" Aba, nine da laifi fa,
walahil azim nine da laifi ba ita ba, Aba ka san me na mata? Aba magani fa.............
Da sauri ta dago , duban da ta yi masa bai hana shi son karasa maganar tasa ba, gannin da gaske fadi zai yi
ta saka hannunta da sauri ta rufe bakinsa, lokaci daya kuma hawaye na zuba a idannuwanta tamkar an bude
fanfo

Aunty nana mariama dai jikinta ne ke bari tana kallon mahaifinsu,


Bata taba tunanin zai saka hannunsa ya mari mamansa ba

Mamaki ne ke neman kashe malan gannin wai Abdul haushi ya ji dan an daki mamansa bayan yanzu ta
gama rashin da.ar ce masa ta tsane shi! Ita kanta maman nasa kuma bata so mijin nata ya fadi laifinsa

Daina cewa abinda ya yi niyar cewa ya yi, sai kawai ya ce" ki tashi ki koma dakin ki, shi ne tabatuwar
kwonciyar hankalinki mamana

Yana gamawa ya juya ya fita,


Yana fita Hafsat ta saki hannunta daga bakin Abdul ta mike

Da sauri ya mike ya bi bayanta sunna shiga dakin nana Mariama ta ja yan yayanta ta hana su shiga ta zauna
sai zarar ido take

Abdul na bun bayanta ya ja ya tsaya , a hankali ya ce" Hafsat....

Hafsat kamar jira take ta juyo da sauri , cikin bambami ta ce" me kuma kake so? Mahaifina ka je ka tiso?
Me yasa ba zan yi daraja a idannuwanka ba Abdul ka dake ni kuma ka hana ni kuka?

A hankali yake binta da kallo, sam baya sonta da irin haka,


A hankali ya ce" ki daina daga min murya Hafsat, ba kyau..nine mijinki, ke kuma matata, ba kyau kina
daga min murya komai bacin rai
Hafsat ta yatsina fuskarta ta juya dan cikinta ba wai gaba daya ya daina murda mata ba,
Juyawar da ta yi a hankali ta durkusa tana kara damke mararta

Da sauri ya je wajenta ya duka shi din ma ya dora hannunsa a saman cikin nata,
Shafawa yake yana adu.a a hankali a hankali har ya lafa mata,
Muryarsa ce ta kara rikicewa a lokacin da ya ce" ki yi hakuri, ban yi haka dan bana son ki ba, hasalima ban
san idan zan kwatanta maki kalmar nan ta inda zan bi ba
Hafsat, ki yi hakuri, ki rufa min asiri mu koma gidanmu, ba zan kuma ba, ita kanta Na.imar zan hana ta sha
Hafsat kar ki guje ni dan na kasance mai laifi, kiyi min nasiha ki dawo ki cancane ni,
Fada fa kike min ki tirsasa ni abinda na kauce, dan me yanzu zaki guje ni?
Dan Allah, na tuba...kin ji?

Hafsat da idannuwanta ke lumshe, tana sauke ajiyar zuciya tana sauraronsa


Abdul ya tsurawa fuskarta ido yana kallonta shima,
Sai kuma ya ce" ba ki yi karya ba da kika ce zan so ki dan albarkatun jikin ki, kin san me....nutsatsu ne,
wuta suke badawa, suna lasa mon zuma a baki...dan Allah ni da lafiyaye ne dan me zan munafurci kaina?
Hafsat, kina da ni.ima, kina bada kala....bakya shaye shayen komai ko cushe cushe...aman kuma tun da na
bi hanyar kulum shinfide take da ni.ima😔, ina son jikin ki sosai kauriyata

Yana fada ne yatsarsa mai bima baba na bin dogon hannunta a hankali yana shafawa,

Sai kuma ya ce" a haka kika bi layi, dan kawai kina fushi da ni ko??

Hafsat ta dan buda idannuwanta ta dago da duban nata kadan, a hankali ta ce" ba fushi nake da kai ba,
tsoron zama nake da kai....ba zaka iya rayuwa irin na mutane bane Abdul? Muna zaune a gidanka mata
biyu, ba abinda ya dame ka da muna zumunci ko bama yi, hasalima mu kanmu bamu san yau kwanan
wancen ko na wannan bane da wace ka yi ra.ayi kake gayata! Kana zaune da mu muna tafiar da rayuwa
tamkar rainon yahudu ko dan ka tsara ba zaka haihu ba bale ka gyara gidanka ko dan tarbiyar yayanka??

A hankali ya kai bakinsa kan nata,


Rufe bakin nata ya yi ta hanyar shiga kissing dinta a hankali a hankali

Sai da ya yi iya yi sannan ya dan saki bakin nata, muryarsa can kasa ya ce" ba zan kuma ba nace, ina son
haihuwar yanzu, a min hakuri na daina, zan ta yi maku ciki kuna haife min du shekara...walahi ko hutu ba
zan baku ba, Hafsat ina son yaya sosai fa, tsananin jin son yayan da ban haifa ba tukunnan ya saka ni tsoron
kar a cutar min da su

Tunaninka sai ta yaya Allah zai kama ka idan har baka tuba ba?
Mu ba matayenka bane? Ohk kana tunanin ka kilace mu ka rufe mu a gida baka barinmu fita , baka barin
maza zuwa inda muke ka tsiratar da mu kennan ko? Idan Allahn ya jarabeka da mu fa??

Idannuwansa ya kura mata ido, ji yake tamkar ya make bakinta kai lahaula wala kuwata illah billah
Falyakul khairan auliyasmut! Ya fada muryarsa na kausasa....

Mikewa ya yi a hankali ya kamata ya tayar da ita tsaye,


Hijab din auntynta ya saka mata ya kama hannunta

Du irin yanda ta so ya saketa a gaban aunty kiyawa ya yi sai auntyn ce ke kakauda fuskarta irin tana jin
kunya , haka sukai mata salama suka fice ita dai sai fa suka fita sannan ta sauke ajiyar zuciya a ranta tana
girmama eh lale tauri da tauri ne

Suna fita Abduk ya tsayar da adaidaita sahu,


Dan adaidaitan na tsayawa ya karewa motar adaidaitan kallo, kallon Hafsat ya yi yana murmushi ya ce" ita
wannan ai kungurguma ce
Hafsat dake wani shasha masa kamshi bata san lokacin da ta saki murmushi ba, sai kuma ta hade fuskar
tana kallon dan adaidaitan dake jiran su shiga ya kaisu inda zai kai su

Abdul ya dube shi ya ce""""


*KUTKALE*

*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct
NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan
number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA
SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN
SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN,
.....* taku ce, Sajida😍😍😍😍

6️⃣2️⃣

Abdul ya dube shi ya ce" malan zaka dan saki wannan abin dan ya rufe mana iskar gari??

Mai adaidaitan ya juyo ya kali Abdul da kyau, bai ce da shi komai ba ya saki labulen adaidaitan sannan
suka shiga suka zauna

Ko a cikin adaidaitan yana ja ne hannun Abdul na rike da na Hafsat, suna tafe ne a hankali domin ya hana
mai adaidaitan yin gudu da su
A hankali yake murza yan yatsun nata, yana yi yana sauke ajiyar zuciya,
Bai taba tunanin idan wai mace tace zata barshi na dukan rayuwa zai ji ciwon kai bama bale wai har ya
firgice, sai gashi wuni daya tak da ta dan nuna tana fushi harma ta yi gaba abinta du ya fice a hayacinsa

Hafsat kuwa dake jin irin yanda yake murza mata yan yatsunta bata iya hana shi ba, hasalima shiru ta yi
tana sauraronsa, sai kuma a hankali ta ringa jin hankalinta na tashi, ba komai ke tada mata hankalin ba sai
irin yanda Abdul ya biyota ya rungumeta a jikinsa, ta ji mugun dadin dadadan kalamansa, sai dai kaf cikin
bayaninsa babu inda ke nuni da ya kamu da soyayarta, ita tama fi fahimtar yana girmama wajen hutunsa ne

Daidai adaidaita sahun ya tsaya kofar tamkamemen gidansu Abdul ya fito daga ciki sannan ya fitar da
Hafsat a hankali

Masu tsaron kofar da suka zaburo da korar mai adaidaita daga kofar gidan ogansu ne suka yi azamar zuwa
dan salamar mai adaidaitan a lokacin da suka fahimci ai ogan nasu ne a adaidaita

Shi dai murtuke fuska ya yi ya kama jan hannun Hafsat suka shige cikin gidan

Tafia mai tsayin gaske suka yi dan sosai akoy tsayi tsakanin kofar shigowa da kuma bangaren Hafsat din,
sannan a tsakannin tafiar sun hadu da ma.aikaran gidan jefi jefi, su kuwa gannin Abdul din ne da kansa
suke tsayawa su mika gaisuwarsu cike da girmamawa, sannan su bi su da kallo har sai sun fice a gabansu

Suna shiga bangaren Hafsat Abdul ya saki hannunta ya karasa tsakiyar fallon ya zauna ya dafe kansa da
hannayensa bibiyu

Tsayuwa Hafsat ta yi daga dan nesa da shi tana kallonsa, a ranta kuwa tambayar kanta take meye kuma??

A hankali ya dago da dubansa ya sauke saman fuskarta


, idannuwansa ya lumshe sakamakon jin yanda zuciyarsa ta buga,
Hijab na yiwa Hafsat kyau fiye da tunanin mai karatu.

Hannunsa na dama ya dago ya mika mata, yana nufin ta zo gareshi

Sai da ra kalli hannun da kyau, sannan ta shiga takawa a hankali har ta karasa kusa da shi din

A hankali ya zaunar da ita sosai daf da shi, sannan ya juya yana kallonta

Bakinta ta tabe tana dan yamutsa fuskarta jin har yanzu ba wai daina ciwon cikin nata ya yi ba, yana yi
yana lafawa ne

A hankali Abdul ya ce" na shiga tashin hankali Hafsat, da kika ce kin tsane ni,
Shiru ya yi na dan lokaci sannan ya kamo hannayenta yana murzawa a hankali yana massaging yana
kallonta
Hannun ta kalla, sannan ta kali fuskarsa da manyan idannuwansa suka kara girma suka yi mata wani irin
nauyi a cikin nata idannuwan,

A hankali ya lumshe idannuwansa ya kuma budewa ya sanyayar da muryarsa ya ce" *tell me, da gaske kin
tsane ni?*

Zuciyarta ce ta ji ta buga mata lokaci daya, a haka kuma ta ji jikinta ya fara daukan dumi harma cikin
tafukan hannayenta ta fara jin sunna fitar da zufa mai zafi

Cire idannuwanta ta yi daga cikin nasa, a hankali take son ya sake mata hannu dan gaba daya ji ta ringa yi
wani irin abu na shiga jikinta daga jikinsa

Abdul ya ki ya saki hannun, saima kara kusanta kansa da ita da ya yi,


Muryarsa ta nuna mugun raunin da yake ciki ya ce" dan Allah, idan na kasance mai laifi ki yi min nasiha ba
ko guje ni ba Hafsat, baki san me na ji ba, baki san irin halin da na tainci kaina a ciki ba.....
Hannun nata ya kai daidai kahon zuciyarsa ya kara tausasa muryarsa
A hankali ya ce" kin ji , har yanzu dokawa take...

Gabanta ne ya kara faduwa, wasu irin kwallah suka cika mata ido lokaci daya

Hannun nasa ta kaiwa kallo da hannunta, tabas zuciyarsa ta canza salon bugu, tana bugawa da mugun sauri
ba kamar da ba
A hankali ta lumshe idannuwanta hawayen nan suka samu damar zubowa,
Tana kallon fuskarsa irin yanda du ya matse mata waje sai kawai ta ringa jin ta kasa kwakwaran lumfashi
idan ba da nasa na taimaka mata ba

A hankali ta buda bakinta tamkar ba zata yi magana ba, sai kuma ta ce" bugun zuciyar yayi min kama da
idan kana da bukatar mace Abdallah
Idannuwanta ta lumshe tana kokarin dane mugun kukan dake tukota wanda bata san ko na meye ba ta yi ta
kuma ce" wacece ni? Wa na fi ko halitata aka daukaka fiye da ta sauran? Abdul, dan Allah ka taimaka ka
fada min dala dalan abinda ya faru aurena ya juya a wannan ranar

Kallonta kawai yake, hankalinsa gaba daya ya dugunzuma ya tashi, kennan tana nufin bugawar zuciyarsa
na nufin dan yana da bukatar mace ne ko? Sai kace wani bunsuru?
Sannan bata bar maganar BS ba kennan?

Kusancinsu da ya matse sosai ya dan sasauta ta hanyar dan ja baya kadan

Hannunta ya sasautama rikon da ya yi mata, a hankali ya ce" Malan ya tura ni binciko masa waye shi
kamar yanda adini ya tanada
Na binciko, sai dai na boye masa hasalin waye shi din, ke din kanki ba zan iya fada maki ba dan ban
kasance mai tona asirin bawa ba, sannan kowa na da tabo a rayuwarsa sai dai na wani ya girmi na wani

Dan shiru ya yi, sannan ya ce" maganar auren ki, eh ya daina ne dan an bashi zabi, kuma ya zaba
Wani shirun ya yi kafin ya fuskanceta da kyau ya ce" sai malan ya daura da ni

Kallonsa kawai take,


Bata iya cewa komai ba,
Abdul ya karsa sakin hannayen nata ya kara sasauta muryarsa ya ce" na ga mata da yawa, na gan su a
matsayin da suka diro duniya..... *sai dai na shigi biyu kacal*
Eh ina da jarabar mace, sai dai ina da kyankyami! Idan min ga na raba shinfida da mace Hafsat ki tabata
dan na fita hakinta na igiyar aurena dake kanta ne ko dan ina rayi... *wato ina son abinda ke cikin bujenta!*

Yana gama fada ya mike ya juya ya shige can cikin dakinta ya barta nan zaune, cike da dana sannin tsokano
zancen nan haka gashi ya yi tafiarsa bayan ya fada mata magana mai tsayea a rai da saka tunanin dole!
Ita yake zuwarma dan fita hakinta na aure? Kennan ita ke gannin ita har mace ce ko? Yana zuwa ne dan ya
fita hakinta na aure

Gaba daya ji ta yi tamkar an lakada mata duka, sosai take ji zuciyarta na kuna na wani irin zafi! Dan me zai
wulakanta ta ta hanyar kwatanta mata karara yana zuwar mata ne dan ya fita hakinta? Shi mai wata matar
ko?
Ciwon abin ya sakata dage kafafuwanta a hankali ta dora saman doguwar kujerar sannan ta jinginar da
kanta ta limshe idannuwanta tana jin yanda ranta ke kara daukaka abin
Adu.a ta shiga yi tana kara lumshe idannuwan nata tana neman sauki wajen Allah.

Ba shi ya fito ba sai bayan salar magarib, daga nesa ya tsaya yana kallonta,
Sam baya gajiya da kallonta dan birge shi take a koda yaushe, sannan jikinta sai kara daukan haske da
ma.ana yake
A hankali ya taka ya buda dakin ya fice, buda dakin ya shaida mata da an fita

Kofar ta tsurawa ido dan ko ya wuni a daki ba zata rasa kanshinsa ba

A hankali ta mike ta nufi dakinta tana jin kanta tamkar wata marainiya, sam bata da sukuni bata da wani
kwonciyar hankali sosai magangannunsa ke tsaye a ranta, sannan sharetan da yayima haka, fushi yake da
ita ne? Ko menene?

Wanka ta fara yi na kirki domin ta wuni ba wankan tun safe rabonta da ruwa,

Tana fitowa ta shiga tsane gashin kanta , sannan ta saka turaran wuta ta rufa ya kama jikinta sosai

Pad ta saka domin kadan kadan take zubar da jinni, wanda ke murda mata cikinta , ba karamin daurewa ne
take yi ba

Tana gamawa ta ciro doguwar rigarta na atamfa cikin kayanta ta saka , atamfar ja ce mai adon manyan
shuka farare da baki baki

Dan kwali ta daura saman kayan sannan ta balo ubiprophene ta hadiya dan ciwon marar

A hankali ta taka ta fita ta shiga kicin dinta, madara ta kada da siga ta sha dan har jiri take ji na yinwar da ta
hana kanta ci

Tana nan zaune har ta ji kiran wayarta na ta zo cin abinci, dama shi take jira ko zata samu ta kwonta

A hankali ta mike ta saka hijab dinta har kasa ta shiga ta kara feshe jikinta da turare sannan ta fito ta nufi
bangarensa

A hankali ta tura ta shiga, dariyar Na.ima ta fara jiyowa kasa kasa sannan ta ji muryarta tana magana cike
da nishadi

Ita dai bata yi kasa da gwuiwa ba ta yi salama sannan ta nufe su cikin nutsuwa

Tana tafe ne tana jin zuciyarta zata tsinke,


Kallon da ya saba taryota da shi bai wani kulata ba, ko daya bai kaleta ba kamar yanda ya saba tsura mata
lumsasun shanyayun idannuwansa masu tafe da wani irin baiwa wa.inda ke sakata jin yanai mata susa a jiki
tsabar yanda suke da tasiri a tare da ita ,
Tana kallonsa ko kiftawa babu har ta karasa wajen table din ta zauna

Gaishe shi ta yi a hankali, ya amsa mata kamar wata bakuwarsa sannan ya ci gaba da kokarin zuba
abincinsa

Dago da dubanta ta yi ta kale shi, sai dai baima kaleta ba bale har ya gane yarenta

A haka Na.ima da Abdul ke cin abincinsu cikin nutsuwa, inda Hafsat ke dan jujuya spoon din tana jin
zuciyarta na tashi

Basu jima suna yi ba suka gama, nan ya mike ya yi masu duba daya ya ce" ina son magana da ku

Su duka da kallo suka bi shi har ya nufi fallonsa, hakan ya sa Na.ima mikewa ta bi bayansa

Hafsatma mikewar ta yi jiki sanyaye ta bi su, suna zuwa suka zazauna saman kujera sannan kowace ta bada
hankalinta kan mijinta mai aji!

Abdul dake daura agogon hannunsa kampanin Gucci na farin azurfa ya yi gyaran murya kafin ya fara
magana
Magana ce yake cikin daurewa da cikakiken iko wanda gaba dayansu lokaci daya suka ji darr dar dinsa

Hafsat kallon lebensa da fuskarsa take tamkar bakonta, bata taba ganninsa a yannayi na serius irin yau ba,
hakan ya saka ta hangi girman darajarsa harma take tunanin irin su Abdul ne sanninsuma riba ne

A hankali ta saci kallon Na.ima, gani ta yi ta bada hankalinta gaba daya da nutsuwarta tana sauraronsa, sai a
lokacin ta ga eh tabas idanma Na.ima ta yi kishin mijinta ba laifi bane dan ya isa ya kai a yin,

Ajiyar zuciya ta sauke tana jin tsare tsaren da ya canzawa gidansa,


Ya raba masu kwana, sannan ya tsara tsarin zumunci, ya yi kwakwaran kashedi a gaba, haka kuma ya yi jan
ido a fada, ya masu nuni da zaman aure suka zo ba wata wada zata fi yar uwarta a wajensa , idan kwanan
mace ne ya soke mai zuwa gyra masa bangarensa da kula da cinsa da shan sa idan ba ita ba har ta fita
aikinta, kys din bangarensa ya mikawa Na.ima kafin ya yi nuni da zata fara aiki a ranar,
Daga karshe ya rufe maganar cikin sansanyar murya sannan ya mike ya fara bara masu wajen ya fita

Wani tsadaden murmushi Na.ima ta saki sannan ta mike a hankali cikin shigar nan tata mai razana zuciya ta
shige uwar dakan Abdul....danma ba abubuwan jujuyawa da sai ta jujuyasu son ranta, ita yau bata san me
ke damun Abdul ba, ga0ba dayansa ya bata lokacinsa , wai Abdul ne harda bata labarin abin dariyarsu a
saudiya? Ita dai tana son mijinta kuma batun kishiya kishiya ce idan har kishin take so su yi!

A hankali Hafsat dake ji zuciyarta na tsintsinkewa na irin halin ko in kulan da Abdul ya nuna mata ta mike
ta fita ta nufi bangarenta tana ji tamkar zata kife dan wahala

Da kallo ya bi ta daga inda yake tsaye har ta shige bangarenta,


Ajiyar zuciya ya sauke yana mai jin radadin irin yanda sam bata damu da damuwarsa ba, yana cikin
yannayi na rokon kulawarta da kasanceewa tare da ita ta yi masa tambaya kan tsohon saurayinta, karshema
ta yi masa nuni da idan dai mace ne kowace ya bi, bugun zuciyarsa da ya canza wanda har yanzu idan ya
tina maganarta cewa ta tsane shi sai ya ji zuciyarsa ta buga , ta dora hakan kan jarabarsa ce ta motso......
Tabas yana girmama lamarinta a rayuwarsa, ta kasance mai dukan tunaninsa , tana dukan lamuransa , tana
hana masa sukuni, tana saka shi jin muradinta a saman kirjinsa, tana motsa masa jinin jikinsa dama
zuciyarsa har ya ji muguwar zufa ta wanke masa jikinsa.....sai dai hakan ba zai hana ya hukuntata ba, !

Juyawa ya yi ya shiga motarsa ya tayar ya fice a gidan,


Tuki yake na iskanci a saman titin har ya iso kofar gidansa.... ina, ba zai iya rintsawa ba idan bai jijiga shi
ya ci ubansa ba! Yau sai ya gane me ya fi shi ne? Yau sai ya bambance girman iskancinsa bilahi!
*KUTKALE*

*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA
BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct
NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan
number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA
SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN
SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN,
.....* taku ce, Sajida😍😍😍😍

6️⃣3️⃣

Sauka ya yi daga cikin motarsa ya je wajen mai gadi

Salama ya yi masa a mutunce harma sukai musabaha kafin ya tambayar shi ko mai gidan na nan? Wato BS

Gannin irin motar da ya fito, irin yannayinsa, da kuma zuwan mutuncin da ya yi masa bai tsaya wani tsaye
tsaye ko tambaye tambaye ba ya budewa Abdul gida bayan ya tabatar masa da BS na gida yanama bayan
gidansa wajen hutawarsa

Sai da ya karewa yannayin gidan kallo kafin ya tabe bakinsa ya shiga nema hankali kwonce

Da kyar ya gane yannayin gidan dan tamkar gidan barawo sai lunguna lunguna

Hango shi ya yi zaune saman tapi mai fadi, gefensa budurwar nan ce da suka bashi tsaro tare , cikin shiga
mafi muni sannan sun mayar da hankali kan begen juna a irin wannan yannayi

Kansa ya gyada kafin ya yi murmushi ya karasa inda suke

Bai yi masu salama ba, haka ya ya karasa infa suke, sosai ya matse masu waje ya yi masu kerere a ka a
tsaye

Da wani irin sauri suka zabura du suka mike suna kallonsa,


Kallo daya ta yi masa ta gane shi, du kuwa da irin yanda ya gyaru ba uwar kasumbar nan, ba hadewar
fuskar nan, du yannayinsa da sauki sosai,
Murmushi ta yi ta daga hannunta ta sara masa tana kallonsa, bata damu da wanda take tare da shi ba ta
kashe murya ta ce" sire ne da kanshi?

Abdul ya zuba mata ido yana karantarta na dan kankannin lokaci,


Murmushi ya yi kafin ya kada kai,
Hannunsa na dama ya daga ya shafi gaban goshinsa, a fili ya ce" kai, bariki, bariki ba sana.a ba, idan kana
son ka zama sakarai wanda bai san ciwon kansa ba sannan baya kishin kansa...to fa biyewa bariki,
Kallon BS da ya hade rai ya yi kafin ya kara kallonta ya ce" ke yanzu tsakaninki da Allah da aikin ki,
iyayenki da rai, kina musulma, ba laifi da dan kyanki sannan yannayin jikin ki wanni zai iya kwasa a haka
dan shi abin ra.ayi ne, ki rasa abinda zaki yi a rayuwa sai bariki? Ke kuwa hau din bai miki adalci ba ki
duba ki ga yanda kika make wata garjejiyar muryarki kina gaishe ni bayan da na shigo hannun wannan
shegen a cikin rigarki yana laguda wannan shanyayun abubuwan tamkar slifas tsofi kuma nima kike kashe
min wadinan tsofafin idannuwan naki so kike mu hadu mu uku ko me?

BS dake kallonsa da mamaki, ga dumbin haushinsa na auren Hafsat da ya yi dan kawai ya ce ya zabi
aikinsa a kanta baima tsaya ya ga daga baya idan bai auretan ba kamar can dama son ta yake, kamar mai
jira ya aureta a ranar ya kale shi da kyau ya ce" *ABDULLLLL......*
bai bar shi ya kai karshen maganarsa ba ya dauki lafiyayen hannunsa, ido da odo , gaba da gaba, ya dauke
BS da wani irin gigitacen marin da sai ya rantse bai bai taba jin mari mai sakawa a ji shiru irinsa irinsa ba

Daga shi har Budurwar tasa ido suka zaro suna kallon Abdul, wanda a yannayi na ko in kula ya daga masa
hannunsa sannan ya nuna masa yatsarsa daya ya ce" ai ka yi hakuri na gama da ita sai mu yi dan dan kai na
zo nan din ko?

Kallonsa ya mayar wajen budurwar ya ce" yanzu tsakani da Allah gajen hakuri dai ai bashi da kyau ko?

BS da ransa ya gama bacewa ya data hargagi yana daga murya ya ce" ni ka mara? Ni ka mara a cikin
gidana? Kai waye? Takamarka kai banbana ne a wajen aiki? Shi ne zaka shigo har cikin gidana ka mare ni?
Abdul Jabar idan kana tunanin ko na kai kararka za.a bani hakuri ne a min wasa da hankali dan kana baba a
niger ni zan nuna maka nima shege ne, da wajen da baka isa ka ja da ni ba! Wannan marin da ka yi mini sai
na yi maka dubunsa! Sai ka gane ka shiga gonar da bata dace da kai ba!

Hannunsa ya kuma dagawa ya wanka masa wani lafiyayen marin, wanda ya harzuka BS ya nufi Abdul da
mugun bacin rai ya cakume shi

Daga daga sukai a wajen kamar zai kai shi kasa daga baya baya dan tura shi baya ne yake da dukan
karfinsa, sai dai kafin ya karasa aiwata hakan Abdul ya ja tunga, ya tura ya tura ya yi kokarinsa tabe shi ya
kayar sai dai ina ya kasa yin hakan

Sai da suka riki hannun juna da kyau kafin Abdul ya saki hannun nasa da zafin nama ya warci kafar BS ya
nausa shi da kasa
Bai yi kasa da gwuiwa ba ya bi shi ya bashi kyawawan naushi hagu da dama har sau hudu hannunsa a
dunkule a fuska

Sosai gefen bakinsa ya fashe ya fara jini, daidai mai gadi ya samo mutane dan tun hargowar BS ta farko ta
fargar da shi ba lafia ba nan suka hadu suka dage Abdul daga kansa mai gadi sai dora hannu yake a kansa
yana tunanin tasa ta kare a gidan yana kallon Abdul irin kallon nan na ashe baka da kirki?

Da sauri Abdul ya warce hannunsa daga rikon da wani kakauran saurayi ya yi masa ya kara durfafar BS da
aka mikar ana bashi baki

Da gudu suka tare kowa na kokarin gannin ya raba fadan da mamakin zaratan samari masu kudi da kyau
suna fada a irin wannan lokacin? Me zai hada su haka?

Hannun ya kuma kwacewa kafin ya yiwa BS mugun kallo , da wata murya mai nuna bacin rai ya ce" kai
karami ne a duniyar bariki! Aunawa na yi na ga ba sana.a bace! Bashir na baka dama kaf garin niger
kwararo kwararo du wani dan iska, dan kwaya, dan tasa, barawo, ko dan ta.ada ka kawo ku farauci
rayuwata! Zaka gane kai wawa ne!

Hannunsa ya kuma kufcewa daga hannun mai gadi dake dunkule hannayensa yana magiyar ya tafi dan
Allah
Har ya fara tafia ya juyo da wani yannayi tamkar zai kuma kara rukunkumar BS din wanda shi kansa sai da
ya ji gabansa ya fadi yana kokarin mikewa tsaye dan ji yake bayansa tamkar ya bala masa shi

Abdul ya nuno shi da yatsa ya ce" dan ubanka da lalatatu ake neman yin bariki ba da kyakyawar kadara ba!
Na ji bakin cikin horo da ka bata na tsayin shekara kana kaleta, na yi bakin cikin sannin da ka yi mata, na
maka rantsuwa da Wanda ya busan numfashi ka kara koda mafarkinta ne sai na kwakulo maka ido na soye
na baka ka cinye! Shege mai zalama

Kallo ya bi mutanen da kallo ya juya ya fice a gidan baki daya

Mai gadi kam sifsifsif ya fice, da kansa ya kori kansa aiki a gifan BS dan ya san idan har ya yarda BS ya
wartsake daga rikitar da ya shiga sai ya wulakanta shi fiye da tunaninsa, dan kuwa a yana binsa sau da kafar
nan ma yaya aka kare bale yau ya buda kofa an shigo har gida an ci ubansa?

Abdul da ya koma motarsa sai da ya ciro tissu ya goge gefen hannunsa da ya yi masa mugun yago wanda
ya saka jini fitowa
Tsaki ya ja yana kallon yanda ya yaga masa rigar jikinsa ya tabe baki a fili ya ce" mai fada irin na mata

Tada motar ya yi ya nufi cikin gari dan bashi da jiyar komawa gidan nasa a irin wannan lokacin

Hafsar kam ta wuni cikin zulumi da tunani, daga baya ta baiwa kanta hakuri ta nemi bed ta mike dan wani
irin baci ke damun idannuwanta

A kwana biyun nan da Na.ima ta yi kwata kwata bata samu fuskar Abdul ba,
Idan ba lokacin cin abinci ne ya yi bama sam bata ganninsa, ko wajen cin abincin sai ta yi dagowa goma
sam bata tsintar idannuwansa a kanta kamar yanda ya saba binta da kallon nan mai sakata jin wani irin
shauki

Ba wani cin abincin take ba, dan gata gabanta hasalima ita bata sha.awar cinsa har a gama, sam baya ce
mata ta ci ko ya dameta da murmushi, baya taba jikinta ko ya rakota ya rungumeta a jikinsa, ita kam ta rasa
gane kanta, ba zata boye ba tana missing din hakan
Tana jinsa da matarsa suna magana a hankali, harma ta ji tana dariya

Ba wani abu tsakaninta da kishiyarta, basa fada sam, basa yade yaden magana, aman kuma basa shiga
harkar juna,
Idan sun zauna cin abinci zasu gaishe da juna a gaisuwa mai gajarta,
Ba wani dake shiga harkar wani, idan daya na magana da miji ba mai tankawa, ba ruwansu da junansu,
basuma shiga sabgar juna ba bale idan wata ba lafia su yiwa juna ya jiki, ko idan abin dadi ya samu a yi
maka murna ko na jaje a yi maka jaje.....wani kishi suke na shiru wanda kowace a zuciyarta kadai ta san
irin abinda take ji kan yar uwarta

Suna ciki da cin abinci a yau da ta kama aikin Hafsat, Hafsat da ta fi kusa da Abdul, tun da ta shigo yau din
ma da wani zumbulelen hijab har kasa a jikinta, ra samu waje ta zauna

Bayan gaisuwar nan ba abinta ya hada ta da su duka mai tsayi ko mai zurfi,
A lokacin ta lura da ciwon dake hannunsa wanda ya yi kama da an yayage shi sosai din nan dan kuwa sosai
wajen yana da girma

A ranta ta afka duniyar tunanin me ya same shi? Me ke damunsa? A ina ya ji ciwo haka?

Sai da ya gama cin abincin ya kale su baki daya,


A hankali ya ce" Hafsat?

Dago da kanta ta yi da sauri ta sauke idannuwanta a cikin nasa, wanda ta ga ya yi saurin kawar da duban
tsakiyar idon da ya yi mata na yan sakwani
A hankali ya ce" tafiar, yau ne da yama...zan yi kwana biyu ne, Na.ima tafia ta taso min dazu da safe
HAfsat ta tsura masa ido sosai, sam ba gaskiya a kan lebensa hakama furucinsa
Lokaci daya ta ji ta muzanta, du irin sanyin ac din dakin sai ta ji ta fara hada gumi, gaba daya lamarin yana
sukar nutsuwarta

A hankali ta yi murmushi tana kallonsa, murmushi irib mai fitar da sauti sannan ta ce" eh, ai ka ce daga
mun gama cin abinci zaku tafi jiya da ka yi kirana da dadare, shi ya sa nake son mu yi salama na koma
kaina ke dan min ciwo me amor

Daga shi, Har Na.ima kallo suka bita da shi, shi yana kallon mamakin gila masa karyar wai ya yi kiranta
jiya da irin yanda ta nuna halin ko.in kular da ta nuna na zai yi tafia a irin wannan lokacin da yake ranar
aikinta, kennan ita ko a kwalar rigarta ko? Yana so ta gane kurenta na kiea masa sunnan wani kato ua horata
sai dai yana gannin kamar ya yi hakan da wuri dan sam ba soyayarsa a zuciyarta bale har hakan ya hanata
sukuni

Ita kuwa tana dubanta da mamakin yaya aka yi tun jiya ya sanar da ita yana da tafia bayan ba aikinta
bane, wani faduwar gaba ne ta ji ta ziyarceta da tsoro, tashin hankali wanda ba.a saka masa rana ......kar
dai a je wannan ita ce wace ta sacewa mijinta zuciya??

*Na san ni mai laifi ce, dan Allah ku min uzuri...idan fa wa.inda suka saba min novel dina sun san bana
wasa da typing ko jan rai, idan haka ta kasance a yanzu ina mai fatan a yi min uzuri......lafia uwar jiki😊
na gode*

[9/12, 8:06 PM] BAK'A CE: *KUTKALE*

*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA
DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number
+22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR
RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO
NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce,
Sajida😍😍😍😍

6️⃣4️⃣

A hankali ta katasa maganarta tana dubansa kasa kasa irin duban nan na kasan ido, kafin ta mike cikin
nutsuwa ta zagaya kusa da shi
Rankwafawa ta yi a hankali inda kamshin turarenta ya shiga hancinsa, kanshi mai saka nutsuwar zuciya
Ita kanta nata idannuwan ta lumshe jin nasa kamshin ya jara cika mata zuciya

A hankali ra mana masa kiss a kuncinsa, ta rage murya sosai da sosai ta ce" Allah ya tsare

Tana gamawa ta mike ta tafi , har ta fice a falon nasa da kallo suke binta su duka kafin a hankali ya mayar
da dubansa wajen Na.ima
Gaba daya fuskarta ta canza yannayi, yannayi na bacin rai da tashin hankali da wani kallo irin na ka ci
amanata!

Mikewa ya yi da tissu a hannunsa ya fice a wajen ba tare da ya furta kalma daya ba

Yana shiga dakinsa ya je ya shiga canza kayan jikinsa,


Ya zo daidai bala mabalin ya rintse idannuwansa da sauri dan kuwa zafin kiss dinta da karansa ne ya daki
kunnayensa lokaci daya kuma ya buda idannuwan nasa ,
Sun kade tamkar ba nasa ba, yana jin lamarinta da dukan karfin jikinsa da tunaninsa, yana jin du wani
abinda ya shafeta a gangar jikinsa,
Bai san yaya aka yi ya yi sake har haka ta same shi ba, yana kallon ina? Dan me ya yarda har irin wannan
abin ke kokarin cin karfinsa? Ya sani ita ce ra farkon da ta yi masa musu, ta farko da ta yi masa tsayaya, ta
farko da ta yi masa fada, ta farko da ta fashe da kuka dan abinda ya shafe shi shi ba wani ba, ta farko da ta
tsaya kai da fata take nuna masa hanya, mahaifinta ne na farko da ya dube shi ba tare da ya san shi ba, na
farko dake dubansa da tarin dukiyar tasa da takamarsa ba ruwansa ya saka shi a hanya mai bilewa ha
wani dar ko tsoron kar ya kubuce masa tunma kafin ya zama sirikinsa,
Tabas ta taka mahinmiyar a rayuwarsa, ta girgiza tunaninsa, aman kuma shi kansa ya yi mugun saken da
ta cin masa a lokacin da vai shirya ba,
Wai shi maman malan zata nuna bai isa ba? Ba zata nuna ta damu da shi ba? Kennan ba zai taba samun
matsayi a zuciyarta ba du kuwa da irin yanda yake kokarin yi mata biyaya a bukatunta?
Shi ke binta ba ita ke binsa ba, ashe haka ne idan kai ke son mutun dole kai zaka ringa binsa du abinda ya
yi niya? Ba laifi ta je din!

Ya karashe yana mai daukan wayarsa da makulin motarsa

Fitowa ya yi ya fice a dakin ba tare da ya rufe ba ya yi gaba abinsa

A motarsa ya shiga ya kama hanyar tuki, bai dauko komai ba sai katinsa ta banki sai takardunsa na zuba
mai a stations
A irin lokacin nan ya shiga tukinsa ya dauki hanya mai tsayi dan niyarsa zai yada zango a garin maradi,
garin da yake son buda reshe na kampaninsa mai tatar mai

Ya wuni cir yana tuki da kansa dan kwata kwata baya jin dadin yannayin da yake ciki, yakan yi murmushi
ya girgiza kansa, dan bai taba tunanin zai kamu irin wannan kamuwar haka ba, sai dai ya tabata ba wani
abinda zai bashi wahalar da ta fi wada ya sha na tsayin rayuwarsa , ya ga rayuwar da baya tunanin da
mace ta ki shi zai mutu, tunda har yanzu zuciyarsa ke harbawa yanda ya kamata baya tunanin soyayar
mace zai tsayar da ita sai dai idan lokacinsa ne ya yi
Yana zuwa hotel ya sauka,
Wanka ya yi ya dauro alwallah ya gabatar da sallar shafa.i da wuturi sannan ya zauna bakin bed din dakin

Hannayensa ya saka saman kansa yana dan yin gaba da baya da hannun nasa

Mikewa ya kuma yi ya dauki jakar goyon fa ya zo da ita ya zuge zip din jiki

Takardu ya shiga fitarwa sannan ya ciro laptop wani dan karami ya bude ya kunna shi

Da wifi din hotel din ya shiga internet,


Sai da ya gama aikin da zai yi sannan ya shiga tarin messages din da ake turo masa wa.inda ba kowa bane
sai mahaifinsa

Du messages din magangannu ne na rayuwar yau da kulun, baki daya nasiha ne na zamantakewar rayuwa,

Ajiyar zuciya ya sauke bai kashe laptop din ba ya samu waje ya kwonta ya lumshe idannuwansa

Wani irin yarr ya ji tun daga cikin kwakwaluwarsa har zuwa dan yatsansa sakamakon tuno irin zazafan
kisss din da ta mana masa a lokacin da ta mike dan ficewa a dakin
Da sauri ya kama fillon dake gefensa ya rungume shi sosai a jikinsa , a hankali ya fara tunanin yanzu da
yana gida, da tabas a irin wannan lokacin tana cikin dakinsa,
Koda kuwa bai yi yinkurin zuwa duniya mai nisa da ita ba da ya tabata harshenta na cikin bakinsa yana
baiwa lokacin mahinmanci ta hanyar side du waji loga na jikinta

Idannuwansa ya buda da suke kara yi masa nauyi, lokaci daya ya mike ya zauna yana kallon wayarsa dake
ajiye gefe

Hannunsa ya mika ya dauko yana kallon messafe din da ya samu du daga Na.ima ne, message ne da suka
kunshi kalaman yabo, adu.a, fatan alkhairi sai zafafan kalaman soyaya a ciki

Idannuwansa ya lumshe ya jinginar da jikinsa jikin bed din


Sai a wannan lokacin ya fara dan bambance tsakanin rayuwar da ya gani da irin karfin rugurguzar soyaya
Baya so ta so shi dan tana tausaya masa ko dan dole,
Baya so ta yi masa son jeka na yika
Da ace zata iya gane menene farin cikinsa ta bashi? Da kau ya huta

A hankali ya buda idannuwan nasa ya shiga wajen message

Bai taba bata rspons a kan irin kalamanta ba


Tabas ya yarda da yau ta cancanci amsa

Cikin nutsuwa ya rubuta amsa kamar haka" *ki huta lafia matar Abdul, i miss u*

Tura message din ya yi sannan ya kuma lumshe idannuwansa

Ji yake zuciyarsa na yi masa wani irin mugun nauyi


Why? Why? Hafsat me na rasa? Me na rasa na namiji?

Wata zuciyar ta ce da shi....ko bata gane yarenka na abinda ke damun zuciyarka da ita ba?

Idannuwansa ya lumshe ya kuma budewa....eh lale ban furta mata ba


Ya baiwa kansa amsa a fili
Sai kuma ya kuma cewa....aman ban taba furtawa kowa ba hasalima yannayina ya cancanci nuna mata me
nake ciki
Wara idannuwansa ya yi sosai yana jin ba zai iya rintsawa ba, me take ciki? Yaya jikinta? Ko ta daina jin
tsamkin dake damunta?

Wasa wasa sai da ya mike dan daukan laptop dinsa sai ya ga har kusan karfe biyun dare

Daukowa ya yi ya zauna yana jin kirjinsa na yi masa zafi,

Buda wajen message din da ya yi masa ya yi ya kuma karantawa a tsanake

Kansa ya girgiza kafin ya rubuta message kamar haka" *na yi nesa da ita ko zan samu sauki halin da nake
ciki a kanta, sai dai na kasa samun hakan sai ma cushewar tunani da nata da ya same ni, shin akoy ayar
da zata ciren abinda nake ji ne na lazumta??*

Turawa ya yi kafin ya rufe laptop din baki daya ya koma ya kwonta ya ci gaba da yabon nata

Bangaren Hafsatma wuni ta yi tana al.amuranta kamar yanda ta saba, kama daga girkinta, gyaran
bangarenta dan zagaya tsakar falonta dan jikinta ya sake domin sam bata wani jin dadin jikinta sosai

Sai da ta gama cin kayan kwadayinta son ranta ta je ta yi wanka hankali kwonce ta fito ta kwonta domin a
hali na rashin sallah take

A lokacin da ta rufe idannuwanta kamar an hasko mata hotonsa sai kuwa ta yi saurin budewa
Lokaci daya abinda ke damunta ya shiga bijiro mata,
Abinka da mace sai kawai Hafsat ta janyo hijabinta da kyau ta rufe kanta ta fashe da kuka

Kuka take hankali kwonce tana rerawa,


Gani take zuciyarta batai mata adalci ba, shin auren cushe ya taba yin daraja ne? Lale da da ake ce mata
so bai san ciwon kansa ba, mugun dan shishigi ne da saka bawa a uku bata yarda sai yanzu da ya mike ya
shiri shiri ya lulukata a kasa sannan ya bita a guje ya dane kanta

Dan me yake wulakanta ni? Dan me yake da son kansa da yawa?


Take tambayar kanta da kanta,
Tafia? Bai tashi tafiar ba sai da ranar girkina ta zagayo bayan ya kwana biyu cirrr yana min fushin da ban
san laifin da na aikata ba? Abdul, ni ko? Ni?
Tamkar wata sabon kamu ta girgiza kanta ta ce" a kanka malan ya taba daga hannunsa a kaina, kai kake
min laifin dan ka tsane ni kuma ka fi ni zuciya? Da wace kake so din ce ai da baka yi mata laifi ba!

Kukanta ta ci na arziki kafin ta shiga shashaka a hankali tana rage karfin kukan

Sai kuma ta kankame jikinta a hankali ta ce" me ya ji maka ciwo Abdellah? Hannunka da ciwo wa ya taba
min kai?????

😆😆😆 i.m back😆


[9/13, 10:43 PM] BAK'A CE: *KUTKALE*

*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar
DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA
DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number
+22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR
RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO
NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce,
Sajida😍😍😍😍

6️⃣5️⃣

Wasa wasa haka ta yi ta juyi, sai barci barawo ne ya yi awon gaba da ita a irin wannan halin,

A washe gari Abdul na daukan wayarsa ya duba call din da ya yi missing

Bai bi ta kai ba dan da wuya su samu abinda suke so, domin aiki ne ake nemansa ya gabatar a kasar
maroco, binciken sirri na wani ahli da daga an haifi jariri a gidan sai a wayi gari a nemesa sama ko kasa,
gasu da samari sai aute suke suna hayayafa mace daga wata ta barsuma wata zama take ko dan dukiyarsu,
Shi ne baban dan gidan ya nemi da a bashi kwararen malamin sirri, dan sam bai yarda da cikin gidansu
ba, hakan ya saka kasar da ta hore shi nemansa dan ta tura shi gidan a matsayin dan aikin giran har ya
gabatar da bincikensa

Laptop dinsa ya kuma kunnawa,


Message din amail dake nuno masa ya danna

Ba wani hayaniya akai masa ba sai amsa da aka bashi kamar haka *da zata dawo min, ko cikin ramin
ginnin rijiya take sai na je na zauna da ita*

Ajiyar zuciya kawai ya sauke dan ya fahimci wada mahaifinsa ke nufi, wato matarsa mahaifiyarsa

Rufe komai ya yi ya fice ya tafi cikin gari dan karasa abubuwan da suka kawo shi garin

Sosai ya wuni yana zirga zirga da kansa, sai da ya tabata ya ga wajen da ya dace da shi sannan ya karbi
number mai wajen ya fice hotel din
A lokacin tuni wani daren ya kara zagayowa dan haka sai kawai ya nemi waje ya yi ibadarsa sannan ya
nemi kwonciya

Ko yau hakan take a bangarensa, domin ya kasance mai tunani a kanta, daren ya yi masa tsayi ga gajiya,
ya matukar wahala wanda tun karfe shida bayan ya gama sallar asuba da adu.o.insa ya dauki hanyar
garin shugaban kasa , a cen take, ya yarda koda yanai mata fushi to fa yiwa kansa adalci shine zama a
inda take, idan har ya yarda ya yi nesa da ita to fa ya tabata wannan shafa ruwa ne a alwallar dake
gabansa dan haka ya baiwa kansa baki ya shiga murza sitiyarin motarsa ya dauku tafiar mai tsayi

Zaune take da yarinyar da auntynta ta turo mata dan ta yi mata kunshin zamani, wanda da iya ja kawai
ake zana shi ana na kafar dama an gama na hagu

Katuwar wayar dake hannunta take dan jujuyawa,


Idan bata mance ba yau kwanansa uku kennan da tafia, tun da ya tafi bai kirayeta ba bai nemeta ba, a
ganninta ai ita ya yiwa laifi ko?

Whatsupl dinta fa ya buda ta shiga , kan sunnansa ta shiga ta kirawa ido


Nan ta ga rabonsa da whatsup din jiya wajen karfe goman dare

Fita ta yi ta ajiye ta mikawa yarinyar hannunta na hagu ta shiga zana mata kunshin kadan ba mai yawa ba
a hannun

A lokacin da aka gama mata ta salami yarinyar sannan ta mike ta shige daki dan yin wanka

Sosai ta gasa jikinta dan a yanzu hakan kawai take kafin ta samu ta ji dadin jikin nata

Fitowarta daga wanka ta ji tsayuwar mota

Da sauri ta mike ta je wajen windows din dakin jata ta dan leka

Daga motar ya fito, yana fitowa ya yi tsaye ya daga hannayensa ya wara kafafiwansa ya yi wata irin mika
daga inda yake yana salati a hankali

Ido ta tsura masa tana kallonsa, wani irin farin ciki ne ta ji na ziyartarta lokaci daya, a hankali ta lumshe
idannuwanta ta kuma budewa a kansa,
Juyawa ya yi ya dauko jakar laptop dinsa ya maida kofar ya rufe sannan ya kuma juyowa a hankali ya
shiga takawa

Kamar daga sama ta ga Na.ima ta fito da gudu ta fada jikinsa

Gabanta ne ya kwonci kwonci ya fadi ,


Rungumeta ya yi a jikinsa kafin ya dan dagata ya shiga juyi da ita a hankali

Da sauri ta saki labulen ta yi gagawar fadawa saman bed dinta

Zuciyarta ne ta ringa ji tamkar ta faso kirjinta ta fito, kamar da wasa sai ji ta yi hawaye na neman zubo
mata

Abdul kuwa na dan juyawa da Na.ima idannuwansa na kan kofar Hafsat

Ya san ba zata taba fitowa a irin wannan lokacin ba, sai dai ya kasa kwadaituwa da son ganninta
Duda magariba ta kawo kai gashi basa haduwa cin abincin dare, baya son kara rintsawa bai ganta ba
Haka suka juya suka shige bangarensa da Na.ima wace ta maida hankali sosai ta kula da mijinta cikin
nutsuwa, abinda da jarababe daman ya kunso lamarinsa suna shigewa daka shiru kake ji bai kuma fitowa
ba sai da lokacin sallar asubahi ta yi

Hafsat kam kuka ta kwana yi wanda ya matukar hadasa mata ciwon kai, gani take cin fuska ne, wulakanci
ne , nuna mata ne zai yi ita ba kowa bace!

Wajen karfe shiga ya dan buga kofar dakinta ita kuwa a lokacin ta shiga wanka bayan ta gama sallah

Jin shiru ya saka shi zuwa bangarensa da kudurin daukan wayarsa ya yi kiranta haka kuma lokaci daya ya
ringa jin gabansa na wani irin dokawa tamkar zuciyarsa zata fito ta balo ta bar jikinsa

Da sauri ya shige ya zarce kuryar dakinsa,


Na.ima dake zaune tana busar da gashin kanta ta yi gagawar juyowa tana kallonsa gannin kamar
hankalinsa a tashe

Da sauri ya zauna saman bed dinsa hannunsa har rawa rawa yake ya shiga danna kiran numberta

Da sauri itama ta mike ta je kusa da shi ta zauna tana kallonsa, muryarta har rawa take ta ce" lallalafia?
Me ke faruwa???

Abdallah dake kara danna kiran numberta aman ana ce masa wai a rufe ya kaleta da sauri ya ce" a a rufe
numberta, bana samun numberta, kar dai a je ta kuma yi min fushi? Tun da na zo ban ji motsinta ba,
Na.ima ina yar uwarki ta je??

Gabanta ne ya fadi, lokaci daya kuma ta hi zuciyarta ta yi mata bakinkirin


Ba zata manta ba a jiya a lokacin da yake kokarin shigarta a hankali ya furta sunnan kishiyarta kafin ko
ankara ne ya yi ko me sai kuma ya yi shiru
Ita kennan du yanda zata nuna masa soyaya a banza ne?
Kennan ba zata taba yin daraja a wajensa ba dan ta kasance wace ta fara nuna masa tana son sa? Ji
yanda hankalinsa ya tashi bayan ta ji dawowarsa aman bata fito ta gaishe shi a maysayinsa na mijinta ba,
sai shine zai fito a yanzu a haka??

A hankali ta shiga sauke kafafuwanta kafin ta mike ta kama hanyar fita

Mikewa Abdul ya yo yana kallonta da mamaki,


Me aka yi? Kukan me take? Dan ya tambayeta yar uwarta ne zata yi fushi ta wani fice? Shi kam wai dama
haka auren mata biyun yake da saka ciwon kai? Daga wace ke yin halin ko in kula da shi sai wace ke son
fitar da sabon halaya?

Komawa ya yi ya zauna ransa na kuna


Bai gama tunanin ba ya ga ta dawo dakin

Yana kallonta ta zo har inda yake ta tsugunna gwuiwoyinta a kasa

Fashewa ta yi da kuka bayan ta kamo hannayensa

Tana kukan ta ce" dan Allah ka so ni, ka so ni Abdellah koda kwayar zara ne, dan Allah ka so ni, ka ga ni
ba kudinka nake so ba, ba burina zama wata ba, Abdellah ni yar uwarka ce ta jini ko dan wannan na samu
soyayarka ka ji??

Ta karashe tana kara fashewa da kuka tana dora kanta saman cinyarsa

Wani irin tausayinta ne ya ji ya tsarga masa


Fuskarta ya tsurawa ido yana kallonta, menene makusarta? Ita dai zuciya sakarai ce wace bata san ciwon
kanta ba ko kadan, ita wace kake yiwa haukan ta nemeka ne?

A hankali ya dakar mata murmushi yana kallonta ya ce" wa ya ce maki bana son ki Na.ima?
Shin za.a iya hada shinfida ba.a son mutun?
Kin kasance mai hakuri da ni da kuma daukan nauyina
Tabas ina son ki Na.ima, ki daina saka damuwa a ranki haka kin ji?

Wata irin ajiyar zuciya take saukewa a kai a kai, tana kuma kallon fuskarsa kafin ta mike da sauri tana
dariya ta tsere

Ajiyar zuciya shima ya sauke, a ransa kuwa ya yiwa kansa fadan cewa daga yau komai halin da zai shiga a
kanta zai kiyaye nunawa a gaban yar uwarta

Can wajen karfe biyu na rana suna zaune suna niyar fara cin abinci inda hankalinsa kacokam na kam
kofar falonsa, tunaninsa da dukan abinda ya shafi zuciyarsa na hangen kofa,
Yakan sauke ajiyar zuciya, kai sai ya rantse cewa har ya rame walahi!

Bayan ta zuba masa abincin ya gama haduwa ya saka cokali zai fara ci odannuwansa suka hango wani
irin kyali

Bai san lokacin da ya yi sakala da baki yana kalonta,


Tun da suke, bai taba ganninta da mak up da shiga irin ta yau ba
Wani irin dogon takalmi mai tsini ne a kasan kafarta tana tafe yana dan bada wani sauti a hankali mai
dadin sauraro

Ajiyar zuciya ya kuma saki yana son kawar da fuskarsa inda hancinsu ya shiga sanar masu da zuwanta
inda wani dadadan kamshi ya yi masu salama

A hankali ya kai cokalin wajen bakinsa, sai dai gudun bugun zuciyarsa ya hana shi samun damar saka
abincin a bakin bale har ya iya hadiyar abincin

To fa, shin xai kuwa iya??????🤣🤣🤣🤣


[9/14, 10:53 PM] BAK'A CE: *KUTKALE*

*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA


NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA
DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number
+22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR
RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO
NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce,
Sajida😍😍😍😍

6️⃣6️⃣

Kokarin kaucewa tsareta da kallo yake, sai dai abin na neman faskara

Wayarsa ya dauka da sauri ya danna kira ya kara a kunnensa

Yana amsa wayar da sam baya fahimtar abinda ake fada masa har ta karasa ta zauna wajen zamanta

Bayan salamar da ta yi bata kuma tofa komai ba sai hannunta da ya sha jan lale ta mika ta dauko zug din
jus ta zuba a hankali ta shiga surba hankalinta kwonce

Tun da ta zo ta zauna Na.ima ta kasa katabus, nan take ta raina tata kwaliyar sannan ta cika da mamakin
dama haka take take fama da hijab? Dama ta iya saka kaya? Dama tana da wannan tsadaden lesh din?
Dama ta iya tafia da takalmi mai tsini aman bata sakawa?

Abincin ne ta ji ya fice mata a ranta, du sai take gannin kayan da ita ta saka basu kamo na Hafsat din ba,

Gannin ya kasa gama wayar gashi kuma ita gaskiya ba kuma zata iya ci gaba da zama dan du jinta take a
takure ya sakata mikewa a hankali da niyar tafia

Hannunsa ya nuno mata alamar ta koma ta zauna dan haka sai ta koma cikin nutsuwa ta zauna tana
sauraronsa har ya gama wayar

Yana gamawa ya dauki jus dinsa dake cikin gilas cop ya kai bakinsa a hankali
Lafiyayen sajensa dake kwonce luf luf luf ke kyalin gyara da yannayin nutsuwa a tare da shi ne ke nunowa
da ka kale shi,

Bakinta ta tabe tana girgima ganta cikin dabara

Kunnayenta ne suka jiyo mata magana kamar haka" zata karasa kwanakinta da bata yi ba, sai ku dauki
kwanan jiya a matsayin sadaka da kuma karbar kyauta daga hannun wace ta fi yinkurin badawa
Daga Na.ima har Hafsat ransu ne ya baci lokaci daya
Hafsat mamakin an daketa kuma an bi ta da mugayen magangannu suka sakata jin wani irin haushi
Na.ima kuwa haushin zai je ya kwana da matarsa ne ta ji, kai ita kam sai ta yi da gaske kafin soyayar
jarumon mijinta ta yi mata ilah

A hankali Hafsat ta ce" , eyah, ai ba wani abu na bar mata na yau din ma

NA.ima ta kaleta da sauri, sai kuma ta ce" aa, ki rike abinki ...
Tana gama fada ta mike ta yi gaba
Shiru ne ys ratsa wajen na yan dakiku, shiru irin baban shirun nan baka jin karan komai sai na pamka

A hankali ta dan saci kallonsa, hakan ya hadasa mata faduwar gaba

Da sauri ta janye idannuwanta daga nasa da suka kada suka yi jajir yana kallonta

A hankali ta gyara kafafuwanta dan har wasu dan tawa rawa suka kwasa na tsoron yannayinsa

Da sauri ta ajiye kopin hannunta ta shiga kokarin mikewa daga saman kujerar

Bai hanata tashin ba, har sai da ta mike ta ajiye tissu din da ta goge bakinta sannan ta juya a hankali da
niyar barin dakin tana mai jin matsanancin faduwar gaba

Bata kai ga fita ba ta ji gaba daya ta yi baya,


Ifannuwanta ta rintse dan ji ta yi an fizgota tsoron tikuwa a kas ya sakata razana da saurin kankame
abinda ta ji ta jingunu da shi

Matsar da ya yi mata a jikinsa ya sakata fahimtar inda ta samu masauki,


Lokaci daya ta shiga ja da karfi dan kwatar kanta

Kin bata damar nan ya yi ta hanyar rungumeta sosai a jikinsa yana sauke ajiyar zuciya tamkar ya yi tsere

Dukan kirjinsa ta shiga yi kafin ta kece da kuka mai zafi,


Tana dukan nasa tana fadin" ka sake ni, ka sake ni Abdul, ba wulakanci bane? Ka ci gaba da nunawa
duniya ko ni wacece a wajenka! Ka yi tafia ranar kwanana , a yanzu da ka dawo ka daukan min kwanana
ka bata sai wani yanzu zaka wani ce na karashe ni da ba yar mai kudi ba ko? Ni da ba yar uwarka ba?
Abdul me na tsare maka?

Jin bugun zuciyarta yake da karfin gaske , ashe ta ji ciwo? Kamar tana kishinsa? Shin kishinsa ne take ?

A hankali ya lalumi bakinsa


A sanu sanu ya kama lebenta, idannuwansa lumshe ya shiga tsotsarsu yana mai binta da tafiar tsutsa
hankali kwonce

Hannunsa na dama ne ya samu ya zura cikin rigarta ta kasa , a hankali ya ringa yin sama da hannun har
ya ji ya kai wajen da yake muradi.....
Cikin nutsuwa ya kamo kan da ya ji ya yi tauri sosai ba irin na da ba,
Dan mulmula shi ya shiga yi a hankali cikin wani yannayi na bukatuwa da nuni tamkar rayuwarsa na tafe
ne da wannan muradi

Kafafuwansu suka gagara daukansu,


Aun manta inda suke,
A irin lokacin da suke
Irin halin fada da gabar da suke
Lokaci daya Abdallah ya shiga kokarin noma gonar da aka halata masa mai cike da kayan alatu,
A nan a irin wannan lokacin ya yi fatali da rigar dake jikinta, jikinsa na kyarma ya dage zanin da ta daura
domin ya kasa samo zaren daurin gashi jininsa a akaifa ,
Bai iya gane kan yanda zai cire pant din jikinta ba sai gefe da ya matsar da shi gaba daya jikinsa na wani
irin kyarma ya shiga baiwa wannan gefe wani irin kulawa mai zafi cike da ma.ana
Ita kanta, bata taba jinsa har cikin ranta irin na yau ba,
Sam bata ji mugun zafin da takan ji a da ba, sai wani irin hauhawa da jininta ke yi ta hanyar karbar
zafafan sakwonnin Bawan Allah
A hankali ta kamo kansa ido cikin ido tana kallonsa ta hade bakinta da nasa....
Abinda bata taba yi masa ba, bata taba taimaka masa ko bashi gudunmuwa ko nuna masa cewa yes shi din
wajen hutunta ne sai yau....
Hakan ya kara gigita shi, ya rikita shi, sai da ya cire bakinsa da dan karfi ya ce" *wayo, wayo, wayo
Allahna....yar malan zaki kashe ni*...kafin ya ci gaba da....

Kai na fa yi rashin munya yau


[9/24, 11:12 AM] BAK'A CE: *KUTKALE*

*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA
DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number
+22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR
RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO
NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce,
Sajida😍😍😍😍

*KUTKALE*

*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*
Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA
DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number
+22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR
RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO
NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce,
Sajida😍😍😍😍

6️⃣7️⃣

Sun matukar gurzar junansu wanda Hafsat ta mugun bashi mamaki,


Ta dauke shi, ta jure shi, ta sakar masa jiki yanda yake so

Bayan komai ya lafa, lake yake da jikinta nan saman tils din, sanyin wajen na ratsa su aman ko daya basu
da niyar gane cewa wajen nan akoy sanyi

Ajiyar zuciya suke saukewa a kai a kai, gaba dayansu idannuwansu a lumshe suke,
A hankali ya kai hannunsa kan cikinta yana shafawa, da zata kara masa da ya kara....bai taba jin irin
wannan lamari ba, ko dan a yau ta bashi hadin kai? Ba wani baban abu ta yi masa na a zo a gani ba , sai
dai sam batai masa gardama ba, sannan du inda ya kai hannunta zata aminta ta lalubi wajen cikin
nutsuwa, wani irin ni.imar da bai san mace nada ita ba ya tsinta a eajen yar malan, a wajen Bodyguard,
yar da ta yi prison, ta yi formation, ta yi zaman saka kananun kaya dan aikinta, ashe suma irinsu nada
ni.ima haka?

Wata ajiyar zuciyar ta sauke a bangarenta, haushin kanta take ji na irin yanda ta mugu mugun jin dadin
kasancewa da shi a irin wannan lokacin harma ta manta irin wulakancin da ya yi mata,

A hankali ta saka hannunta dan cire nasa, sai dai ji ta yi ya kara matseta ya kankameta a jikinsa
Wata irin kunya ce ta ji ta rufeta jin a yanda yake har yanzu, ita kanta a irin halin take dan haka ta shiga
kiciniyar kwace kanta
Da sauri ya dora habarsa saman kanta, murya can kasa ya ce" shuiiiiiiiiiiit *Amatullah*

irin yanda ya ja sunnan sai da ta ji gaba daya jikinta ya amsa, lokaci daya tsoro ya darsun mata , tsoro ne
ya shigeta da fargabar menene wannan kuma ke damunta? Yaya abin dake bakon lamari a wajenta ke
neman zame mata wani banban muradi na zuciya?

*kar ki raba jikina da ni.imtacen dumin jikin ki da kanshi mai dauken nazarina*

Ajiyar zuciya ta sauke mai karfi kafin ta kara jan jikinta tana mai jin haushin kanta, domin maganar tasa
ta kara birgeta fiye da fushin da take

Mikewa ya yi zaune dangalgal, ba wata kunya ko tunanin rufe yannayinsa ya kamo hannunta ya ce"
menene???

Da sauri ta rintse idannuwanta zuciyarta ta shiga dokawa fiye da da, muryarta ne ta shiga rawa rawa a
lokacin da ta buda bakinta ta ce" i.m tired, zan je dakina

Murmushi ya saki gannin yanda take kakaucewa kamar ba mijinta ke gabanta ba, salon kunyar tata kuma
sai ta bashi sha.awa,
Lebenta ya kurawa ido irin yanda ya yi jajajir tsabar ya sha wahala yau a hannunsa, sai rawa rawa yake
A hankali ya duka sosai kusa da ita ya damki leben nata ya shiga tsotsa
Bata san daga ina ba, bata san ta yaya ba, ita dai ta tsinci kanta da daukan hannunta na dama ta talabo
shi da kyau ta shiga bashi taimako domin zuciyarta bata da muradin da ya fi a koma abinda aka dauki
lokaci ana yi

Abinka da kwarare a fannin sai kawai Abdul ya karbi tayin maman malan ya kara lulawa duniya mai cike
da lada yana hako du wasu arnawa yana kashe au cikin sauki

Shi kansa ya tausaya mata a lokacin da komai ya lafa , cikinta ta damke tana hawayen wai yinwa take ji

Taimaka mata ya yi da niyar ta fara wanka kafin ta ci? Sai dai ruf ta rufe ido kan sai ta ci

Ido kawai ya tsura mata a lokacin da take kai loma bakinta , wato tana yin hannu baka hannu kwarya ba
sasautawa
Ba ita ta dan dakata ba sai da ta ji wajen da kamar an mata sata ua cike sannan ta dawo hayacinta harma
ta fara jin mugun zogin da jikinta ke mata
Sai a lokacin kuma ta tuna cewar ta rushe tsarin jan ajin da ta yi niyar yi in dai tana gabansa na cin
abinci, wato sam ba zata yarda ya gane irin yannayin cin abincinta ba, sai gashi rashin lafiar da take son
kai kanta asibiti wace ta sameta a kwana biyun nan na cin abinci ta tona mata asiri a gabansa

Fuskarta ta tsuke,
Ta mugun hafe girar sama da ta kasa ,
Ta hade gabas da yama
Irin ba zata saki fuskar da za
a kawo mata wargin bama

Murmushi ne ya subuce masa yana kallonta


Hannayensa duka biyu ya saka ya talabe habarsa,

A hankali ya ce" ban taba hora kaina irin na jiya da yau ba

Dara daran idannuwanta da suka sha wahala suka wani lumshe da su ta maido kansa,
Bata yi masa tambaya ba, sannan bata daina kallon kyakyawar fuskarsa mai sakata jin yana fuzgarta
Hannayenta ya kamo, du da kuwa ta so kin bashi, sai dai ta kasa hakan sakamakon babu wani karfi a tare
da ita, tunanin bata da lafia ya fara damunta

A hankali ya ce" Hafsat?

Idannuwanta da suka fara cika da kwallah ta zuba masa tana kallonsa

A hankali ya kuma cewa" ban iya karya ba, ban iya tsokana ba, ban iya wasa da wannan lamarin ba.....ni
dai na samu kaina a ciki tun lokacin da kika kasance mai shiga lamarina, kikai min fada dan ina aikata
masha.a
Hafsat, shi ne damuwata, tashin hankalina, Hafsat du yanda na yi dan kar wani ya birge ki, sai da ya tashi
ya wani shiga rayuwarki, ina ji ina kuma ganni harma zai aure ki
Shiru ya yi yana dan murza hannayenta,

Muryarsa ce ta kara yin wani irin sanyi ya ce" sai dai wani baya auren matar wani, can can dama Allah
bai yi ba shine mijin ki,

Idannuwansa ya dago ya sauke a fuskar tata, a hankali ya ce" zaki taimaka ki rufa min asiri, ki daina
maganarsa ko tunaninsa? Walahi idan kika ci gaba lumfashina zai iya barin gangar jikina domin hakan na
kai ni tunanin cewa har abada ba zaki tana so na ba dan kina da wanda kike so,

Jikinta ne take ji yana amsawa da dukan kalamansa,


Jikinta ne ya yi sanyi,
A hankali ita din ma ta ce" Abdallah, tambayar da na yi maka a ranar nan ce ta saka ka daukan fushi da
ni?

Idannuwa kawai ya tsura mata ya kasa amsata

Hannayen nasa ta dan jimke kafin ta ce" ban san dadin so da har zai kai ni haka ba, ban san muguntarsa
da har zai kai ni tunanin wani da kalmar so bayan da aurena
Koda makiyina na aura a duniya ina fatan daga bakin da na amsa kira da sunnansa zan girmama igiyarsa
dake kaina
Wacece ni?
Me na aikata na tarin ladan da zan yi tunanin koda na kauce hanya haka zan ci riba wa wajen?
Na yi maka tambayar nan ne da ina cikin damuwa, na yi maka ne dan ina cikin tunani mai zurfi, mamakin
dan adam ne ya kashe ni na irin kalaman dan adam da suka zama na yaudara

Abdallah ban san yanda zan kwatanta maka lamarina da Bashir ba, aman ka sani babu *kalmar so* a tare
da lamarin

Idannuwansa ya sada yana jin nauyin da kirjinsa ya yi masa ya ragu,


Dadi ne ya ji na irin yanda har ta iya fahimtar da shi abinda ke ranta, ashe zata yi saukin kai da dadin
zaman gidan aure haka? Ashe du irin taurin kanta da rigimarta da tsayayarta idan aka zauna magana ta
fahimta da ita za.a ga laushinta?

Ajiyar zuciya ya ringa saukewa kafin ya dago ya saka idannuwansa cikin nata, a yau ya kara gane wani
lamari cewa Hafsansa baiwa ce da Allah ya bashi domin kuwa a wasan da ya buga da ita a yau ya nuna
masa idan ta gama zama kwarariya idan ya shige daka sai safe🤣

A hankali yana kallon kwayar idannuwanta wa.inda ta ki cire nata dan tana son ya yarda da maganarta ,
sam ita bata wani saka maganar son Bashir ba , ta yi tambayarta ne dan gane dalilinsa na wulakantata a
ranar aurensu
Bata tsamaci kalmar da zai yi mata kennan ba, bata tsamaci zai yi mata wannan tambayar ba hakan ya
saka ta shagalta da kallonsa tana jin dadin yannayinsa a ranta, rigarsa mai botira ce kawai ya dora saman
gajeran wandonsa baki , bai baka botiran ba hakan ya bashi kalar black American din nan
A hankali ya ce " *Hafsat? Dan Alllah, ni zaki so ni? Watarana zaki so ni? Kina tunanin na saka hakuri da
juriya na tsayin lokaci watarana zaki so ni nima? Hafsat Ni Ina son ki*

Ji ta yi tamkar za.a jefota daga kujerar da take zaune


Dakin ne ta ji ya yi masu kadan su su biyu rak,
A hankali ta fara jin lumfashinta na gudu ba kamar da ba,
Ita dai bata da cutar athsma, sai gashi lokaci daya ta shiga huka da tari tamkar mai ciwon Athsma,
Sama da kasa kirjinta yake nan da nan ta mike ta shiga neman wajen da zata je ta tsere ta labe kar ya
kashe ta,
Jikinta na rawa tama faman kaucewa rikotan da yake kokarin yi
Kuka ne ta ji zai kwace mata, wani irin dadi da kuma tsoro ne suka haifar mata da emotions din da ta
sakata tarin mai huka, zubewa ta yi jikinsa tana kallon tashin hankali karara a fuskarsa,

Zata so shi?
Shin watarana zata so shi?
Shi yana son ta?
Ita kanta sai ta tsinci kanta da yiwa kanta tambayar shin menene ke saka ta a irin wannan yannayin a duk
lokacin da take tare da shi tun farkom lokacin da ta ganshi tare da mace na neman tubewa dan ta bashi
kulawa irin wace bata cancanta ba a matsayinta na baligar da ba muharamarsa ba
A hankali ta ringa tariyo irin yannayin da takan shiga a duk lokacin da ta je kakabe masa shinfidar da ta
tabata ya je dakin matar nasa ne dan sqnub nutsuwa da ita duda ba hutuminta bane sannan ita Na.ima din
ta kasance matarsa ta sunna sai ta wuni cikin kasala da bacin rai
Tana tune da lokacin da aaka so harbinsa harbin ya sameta ajiyar zuciyar da ta sauke ba na ta samu kare
mutun a kan aikinta take bane, aa, ta sauke nanauyan ajiyar zuciyar dake nunin ta ji dadin da ba shi ba
aka harba abin ya sauka a kanta?
Murnar aurenta da Bashir da ya taya ta sai ta tsinke waya ta ringa jin haushinsa? Shin na menene?
A hankali ta ringa jin lumfashinta na daidaita a lokacin da ta fahimci idan ba da kyar ba tama rigaye shi
fadawa a tarkom da ya fada na soyayarta, ashe itama zuciyar tata lusara ce? Har take jin haushin yan
matan dake nuna masa suna son sa ashe itama halin da tata zuciyar take kennan? Har take mugun jin
haushin matarsa irin yanda so ya sakata zama tana jurar kayan haushinsa ashe du jirgi daya ya kwaso su?
Bambancin su kawai ita bata fito da maitarta ba, bambacinsu ita bata nuna ba,
Ashe ashe tashin balagar tsararan shegantakarsa itama ya haukata tunaninta?

A hankali ta saka hannunta ta bayansa ta rungume shi,


Bakinta ta kai daidai kunnensa ta ce" is ok Abdellah

Shima rungumeta ya yi a jikinsa yana mai jin tashin hankalin kar dai ba zata taba son nasa bane har ya
sakata cikin wannan yannayin? Dan haka ya ce" i....i.m sorry,

Hafsat ta lumshe idannuwanta tana mai jin yannayinnan fiye da kowani yannayi, dama haka ake ji? Kamar
ya kunna wani abu ne a jikinta dake mace a da, can kasan zuciyarta ta masa shi da I love u too, aman a fili
sai ta ce"""""""

Saura kiris....eh saura kirisss in sha Allah

6️⃣8️⃣

Aman a fili sai ta ce" kar ka bani hakuri, baka yi min laifin komai ba
Shiru ya yi yana sauke ajiyar zuciya cike da mamakin irin jan ajinta, ya tabata da wata ce da tuni ya samu
amsar zata so shi ko aa, aman ita ta bar shi a duhu ya kasa gane gabas din maganarta tamkar tandun
kwali.

Basu su tashi a wajen ba sai da kiraye kirauen sallah ya fargar da su,


Nan ya taimaka mata suka mike suka nufi dakinsa

A keana biyun nan sun kasance cikin aminci, shakuwa, kulawa, madaukakiyar soyaya

Hafsat cancara kwaliyarta take kafin ta koma bangarensa idan ya fita,


Eh lale bai ji da bakinta ta furta masa kalmar so ba, aman yannayinta , ayyukanta a gare shi, irin yanda a
yanzu take bashi hafin kai a bed, harma ta neme shi dan kanta wanda shi kansa yana mamakin dama
harijar mace ce ita? Irin yanda idan yanai mata hira take bashi hankalinta baki daya harma ta dara na
darawar, na jimami fuskarta ta nuna, komai na zaman lafia sai dai ya godewa Allah
A haka har lokacin fitarta a aiki ya yi sukai wata irin rabuwa tamkar zata bar gari, tamkar ba zasu kuma
haduwa ba dan kawai zasu raba kwana na kwana biyu kacal, hakan ya sakata hawaye da ta koma
bangarenta sannan ta tashi da azumi domin a gaskiya ita ta san wannan lamari na bukatar mijinta dake
damunta ya fice misali, sarai take cikin damuwar rashin mijinta, sai dai ta kwana da sanin ba na ita kadai
bane dan haka sai ta gayato hakuri ta yafawa kanta ta tura masa sakon tana azumi danma kar su yi
tsamaninta wajen kari da kuma cin abincin dare

Sarai tausayinta da tausayin kansa ya kama shi, a hankali ya mike bayan ya salami Na.ima daga cin
abincin safe ya nufi bangarenta kafin ya fita aiki

Dakatawa ya yi daga bakin kofa tun da ya shigo yana kallonta,


Tana yannayin mutun mai sanyi, tana yannayin damuwa

A hankali ya karasa inda take kwonce


Hannunsa ya dora saman mararta ba da nufin wani abu ba sai dai taurin da ya ji wajen ya yi ne ya saka
shi sauke idannuwansa a kan fuskarta da sauri

Itama jin ya tabata da kuma jin zafin dana mararta da ya yi ya sakata saurin zabura tana kallonsa

Da yannayin damuwa yake kallonta, a hankali ya saka hannayensa ya janyota jikinsa, cikin nutsuwa ya ce"
bab, me ke damun ki??

Murmushi ta kakalo tana kallonsa a hankali ta ce" ba komai, ina azumi ne

Idannuwansa ya lumshe yana kallonta ya ce" me ya sa mararki take da tauri haka?

Kallonsa take, ita kam bara san mararta na da tauri ba dan bata taba ganewa ba, takan ji dau marar tata
ta yi mata nauyi sosai, sai dai sam bata taba jin taurinta ba

Kallonta ta kawar daga fuskarsa a hankali ta ce" ban san tana da tauri ba

Mikewa ya yi ya ce" kwonta na ga?

Irin kwoncin da ya tarar da ita ta yi ta kuma yi tana kallonsa


Tamkar wani likita ya kara yaye rigarta ya shiga dana cikin nata a hankali yana kallon yannayinta

Rike hannun nasa ta yi tana yatsina fuskarta dan walahi ita zafi take ji sosai

Daina danawar ya yi ya shiga shafawa a hankali yana kallonta ya ce" yaushe rabonki da al.ada?

Hafsat ta amsa shi a cikin sanyin murya cewa" wannan watan ma na yi


To me ke damun ki?

Hafsat ta daga kafadarta

Abdul kam ji ya yi hankalinsa ya kasa kwonciya, gashi tana jini da sai ya ce cikin ne bai fita ba, mai ke
damunta?

Agogo ya kalla ya ga takwas har ta yi dan haka sai kawai ya mikar da ita ya bata hijab dinta ya ce" saka
mu.je asibiti

Kallonsa take bayan ta saka din ta ce" aman ni ai lafiata kalau, bana jin wani ciwo fa

Abdul ya gyada kansa ba tare da ya bata wata amsar ba ya kama hannunta ya jata a hankali suka fice

Suna fita motarsa suka zarce


Kys ya yiwa motar kafin su kama hanya

Ita dai kawai kallon hanya take, bata san na me zai kaita asibiti haka ba ita lafiarta kalau
Gabanta ne ya fadi na tunanin ko dai shima yana tsantsamin bata da lafiya ne sakamakon wannan yanayi
Harhade fuskarta ta yi tana jin kamar ta dadage ta zunduma ihu ko zai mayar da ita gida tun kafin ya kaita
a fadi wani abinda zata ji kunya

A haka suka karasa cikin clinik din

Wannan karon kin ya riko mata hannun ta yi ta dai bi bayansa har suka shige wajen gannin likitan matan

Sun taki sa.a mace biyu ce kawai zaune dan haka suka zauna suma yana mai binta da kallo sai ta ga ya
sakar mata murmushi aman kuma bai yi mata magana ba

A haka har zuwansu ya zo suka mike suka shiga tare

Tun da ya shiga ya ga wani jikeken namiji mai kalar fatarsa zaune yana aikin duba matan mutane gabansa
ya fadi, ransa ya yi masa bakikirin ,
Bai aune ba sai gani ya yi har ta zauna a farar kujerar duba mararsa lafia ta bada hankalinta wajen
likitan

Sai da ya gama rububuce rubucensa ya dago ya zuba masu kallo,


Fuska Abdallah ya yatsina yana kallonsa, a zuciyarsa kuwa fadi yake mumuna ne kai, sam baka da kyau

Daga kafa ya yi da sauri ya karasa shima ya samu waje ya zauna sai muzurai yake

Likitan da ya gama kallonsa ya ga bai bashi hannu a matsayin wanda ya tarar suka yi musabaha ba kuma
dai a yannayinsa bai ga yannayin mai duhun kai ba sai shima ya ki bashi

Sai da ya buda katon litafinsa sannan ya dube su ya yi masu tambayar waye ba lafiar? Yaya sunnansa?
Shekarun haihuwarsa?

Tana shirin yin magana ta ji Abdul ya ce" Hafsat , Madame Abdul Jabar, shekarunta ashirin da uku

Kallonsa ta yi, inda shima likitan ya kaleta yana tunanin to ko kurma ce ita din??

Rubutawa ya yi sannan ya basu hankalinsa kacokam ya ce" menene damuwarta? Wace irin rashin lafia ke
damunta?

Abdul ya hadiye abin haushin da ya tsaya masa a makogwaro sannan cikin isa shima ya ce" mararta ke da
tauri, tana daukan zafi, bayan as nrmal marar mutun bata haka
Kansa ya gyada ya kara yi masu tambayoyin da ya dace kafin ya mike ya nuna mata bed din da zata
kwonta kusa da wani allon haskawa wato wata yar karamar tv

Irin kwonciyar da ta yi kanta sai da cikinsa ya juya, wannan a haka din idan ba shi zai haye ruwan cikinta
ba gaskiya wani garjeje ba zai kale masa yannayi mace ba ehe!

Bai gama fahimta ba sai da ya ga ya kai hannu zai yaye hijab din jikinta ya kai wajen mararta, waje mai
daraja da daukaka a idannuwansa, waje mai tarin sirrinsa

Hannunsa ya kai da sauri ya tare nasa hannun,


Dago da idannuwansa dake cikin gilas ya yi sukai ido hudu,

Abdul ya lumshe idannuwansa ya kuma budewa yana kallonsa bai ce da shi komai ba

Doctern ya saki murmushi kafin ya janye hannunsa a hankali ya juya ya fice a office din

Hade fuska ya yi tamkar bai san meye daria ko fara.a ba inda Hafsat mamaki tamkar ya kasheta

Kanta ta girgiza tana kokarin mikewa da niyar sai su tafi ai tunda likitan ya bara masu office din baki
daya!

Bata kai ga tashi ba sai ga likitan ya dawo tare da wata likitar mata

Zuwa ta yi cikin fara.a suka gaisa ta gabatar da kanta ita din ma doctern mata ce

Waje Abdallah ya matsa ya bata ya tsaya gefe kusa da kan Hafsat dake binsa da kallon ga irinta

Shi dai ko a ransa saima maida hankalinsa a wani ruwa ruwan da likitar ta matso ta shafa a marar Hafsat
din

Dora abin ta yi ta shiga yawo da shi a hankali tana kallon allon wannan karamar tv din

A hankali ta ce" haka ne doctern, gayanan dan jaririn foetus

Da sauri Hafsat ta rintse idannuwanta tare da jin gabanta ya fadi, Foetus? Aman ai tana al.ada, kennan
cikinta bai fice ba? Cikinta yana nan? Gabanta ne ya fadi cike da tsoron me mijin nata zai yi shi da baya
wannan ra.ayi a yanzu?

Sai dai yannayin da ya shiga a lokacin da likitar ta tsayar masa wajen da dan karamin halitar da ba.a
gama ba aman ana iya gannin abin tamkar wani kadangare sai ya ji gaba daya jikinsa ya dauka

Tsurawa abin ido ya yi, ba.a gama halitarsa ba, bai san kalar da zai bada ba, aman ya ji gaba daya jikinsa
ya dauka da kaunar abin,
Ji yayi dama kar ta daina haska masa, ji ya yi dama a janyo wata biyar din da suka rage ya taka duniya ya
ganshi,
Kaunar abin, wani irin yamyam ya ringa ji inda ya duka yana shafa wajen
Cikin nata ya dan tada , sai dai ba zaka yi tunanin dan mutun bane a ciki sai dai ma ka yi tunanin nrmal
haka cikinta yake

Wata kwala ce ya ji ta tarar masa a cikin idannuwan nasa, a hankali ya karasa kusa da fuskarta ya duka
sosai ya kama lebenta
Idannuwansa ya lumshe ya tsotsi na kasan cikin wani irin sanyi sannaj ya saki yana kallonta
A hankali ya ce" ina son ki Hafsat, plz ki so ni? Ki so ni tun kafin yarinyar mu ko yaron mu ya taka kasa?
Hafsat zaki bani baby
Idannuwanta dake kallonsa ta ji sun mata nauyi cike da hawaye
A hankali ta ce" Abdallah *I LOVE U*

gaba dayansa ya ji kafafuwansa zasu gagara daukansa, hakan ya saka shi zama saman kujerar dake ajiye
kusa

Idannuwansa ya lumshe, sai ga wasu hawaye masu dumi


Yau babar rana ce a gare shi, yau ya tashi cike da ni.ima , Alhamdulilah shi ne abinda ya iya fada

Sai kuma tunanin mahaifinsa ya diro masa a zuciyarsa


Dama haka ya ji a lokacin da ya san matarsa na dauke da cikin dansa na farko? Kai, wannan
madaukakiyar soyaya ita uba ke ji idan ka ji zaka samu yaro?

Ajiyar zuciya ya sauke suka mike ya kama hannunta dan du yanda ta ki sai da ya riko gam a hannunsa
suka fito

Murmushi kawai yake saki, sai ya kaleta, ita kuwa kunya ta cikata dan likitocin nan sun sha dariyar irin
yanda ya zaburo ya ringa bata muah du inda bakinsa ya kai cike da murna da farin ciki gabansu ba wani
kunya , harma suka yi sabo da doctern inda ya kara fahimtar inda ya nufa harma ya ji ya birge shi

A hankali ya karasa anguwar da malan ke zama ,


Farin ciki ne ya mamaye zuciyarta a lokacin da ta hangi mahaifinta zaune cikin shigarsa ta kamala

Tana kallon yanda Abdul ya duka yana gaishe shi aman Malan ya mikar da shi yana ta doka masa
murmushi

Tana kallonsu har suka karaso wajen motar aka bude nan Malan ya yi tozali da yarsa da yake ji tamkar
nama daya kwal a cikin miya

Murmushi ta yi hannunta cikin na malan, shima yana kallonta yana mai jin farin ciki a ransa, ko ba.a fada
masa ba shi ba yaro bane, koda basu sani ba shi ya fahimta, yarsa ce fa, shi ya raini abinsa, ya gane me ke
tare da mamansa, lale ya godewa Allah, murna ce cike da ransa wace ya salame su bakinsa kamar ya kai
kunne

Gidan mama ya ajiye Hafsat inda ya ki shiga ya ce da ita zai je wani waje ya dawo

Bai zame ko.ina ba sai kasan wata bishiya mai cike da innuwa sanyayen waje ne mai cike da ni.ima

Zama ya yi waje guda ya dauki wayarsa ya danna kira

Kiran na shiga aka daga

Shiru ne ya dan ratsa kafin a hankali ya ce" ka dawo cikin Gari Abu Abdellah

Da sauri mahaifinsa ya cire wayar ya kali sunnan, ya kuma mayarwa a kunnensa


Bakinsa na rawa rawa a hanklai ya ce""""
[9/26, 5:28 PM] BAK'A CE: *KUTKALE*

*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*
Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA
DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number
+22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR
RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO
NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce,
Sajida😍😍😍😍

6️⃣9️⃣

A hankali ya ce" Abdu?

Abdul ya yi murmushi mai sauti ya ce" Abih

Ajiyar zuciya ya sauke, da sauri ya ce" dama zan kuma jin sunnan da murmushi a lebenka?

Abdul ya kuma yin murmushi bai dai ce komai ba

Abdul Basitt ya ce" ko yanzu Allah ya amshi raina na cika burina Abdallah, na gode, na gode, baka san
irin farin cikin da ka saka ni a yau a yanzu ba, baka san irin yanda na ji a zuciyata ba

Abdul ya ringa sauke ajiyar zuciya shima jinsa yake sakayau, ashe ka riki mutun kanai masa fushi da
gabama ba wai wani jin dadi bane sai tarin nauyin fake azuwa saman zuciyarka da faduwar gaba idan ka
ji sunnansa? Mahaifinsa ya tafka kuskure a rayuwa, ya aikata laifi mumuna na hanyar saduwa da yar da
ya haifa, sai dai hakan ya faru bisa sharin magabata, sharin abokan zama , banzayen abokai masu kai
mutun ga halaka,
An kasheta dan a dora masa laifi
Ya yi nesa da su dan tarin kunyarsu, yana jin kunyar haduwa da mahalincinsa a irin wannan rayuwa hakan
ya saka shi kauracewa kowa ya kadaice kansa da neman gafarar ubangijinsa da neman zabinsa
Dansa cilo ya rayu cikin kunci da tunanin bayan bata rayuwar yar cikinsa shi ya kasheta haka kuma ya
kashe mahaifiyarsa sannan yake bibiyar rayuwarsa dan dukiyarsa

Du irin abubuwan nan suka taru suka saka gaba mai tsanani da rashin fahimta tsakanin dan da uban
Aman da yake buwayi gagara misali ya kaiwa kukansa
Ya duka ya zubar da komai nasa
Ya kasance babu wani abu tsakaninsa da Allahnsa wanda bai fito ya fada ba,
Ya yi kukan jin kunyar ubangijinsa da irin abubuwan da ya aikata
Ya nemawa yarsa da matarsa gafara
Ya kuma roki da ya tausasa zuciyar dansa cilo ya kasance koda shi daya zai wanki gawarsa ya yisa yana
mai bi a hankali yana yi masa shinfidar kabari mai ma.ana,
Sai gashi sarkin sarakuna
Mai mulkin da ba algus
Wanda zaka roka ya baka in ka kuma roka ya kara maka ya yi ta baka ba tare da ya gotanta maka ba
Wanda zaka yiwa laifi mai tsanani idan ka tuba ya karbi tubanka harma ya daukaka ka? Mai annabi aban
fati ya nuna masa ranar da dansa na cikinsa ya nemi da ya dawo kusa da shi bama a ya mutu ba
Bashi da bakin magana,
Bashi da abin mamaki
Burinsa ya kafaice ya kai sujada
Idan goshinsa a kas yakan ji kansa sakayau ne, yana jinsa a cikin nishadi kasancewa a fadar Allah, zai je
ya tsaftace wajen salarsa, ya kara saka turare ya kai goshinsa kasa ya yiwa Allah kirari, ya yabi
manzanninsa da sahabansa
Zai rubar da hawayen farin ciki kafin ya tatara ya kaura kusa da shi

Cikin muryar farin ciki ya ce" Abdallah, Alhamdulilah

Abdul kansa dake jin dadi har ransa ya ce" Abih, zan so ka zauna cikin gidana, kusa da mu duka , Abih zan
so matana su yi zumunci da soyayar junansu, zan so su zauna da ni da zuciya daya
Abih, basa fada, basa gaba, sai dai basa shiga harkar junna kuma daya bata damu da halin da yar uwarta
ke ciki ba

Shiru Abih ya yi , tun da ya ce ya koma cikin gidansa da zama da ta fado masa a rai,
Da gaske ya huce harma zai yarda ya zauna tare da matansa bayan ya afkawa yarsa ta cikinsa????

Abdul ne ya katse masa tunaninsa ta hanyar fadin" yanzu ita Kauriyata dake cikin wannan yannayin idan
aka yi katarin tana da wani bukatar ni kuwa bana nan sai dai ta yi hakuri? An ce ba.a son mai ciki ta nemi
abu ta rasa, idanma haihuwa ta kamata bana nan yaya za.a yi kennan? Ko hali na rashin lafia?

Wani murmushin ya saki a fili ya ce" inyeh, zan zama papy? Ita maman malan din?

Shiru abdul ya yi, sai kuma ya ji wani yannayi mai shige da kunya ya kama shi,
A hankali ya kashe kiran yana sosa bayan keyarsa yana murmushi,

Message ya shigo masa mai tsayi , budawa ya yi ya karanta kamar haka" kai zaka zama jajirtacen namiji a
cikin gidanka Abdu, kai zaka hada kan matanka, sannan ka yi ta adu.a
Zan dawo cikin gari kusa da kai aman ba zan zauna da tsufana da komai a cikin gidanka ba , aa ba zan
sakawa yara ido ba, zan dai kama wani gidan da ya fi kusa da kai, sannan ka sani ba zan lamunce su
dorawa dana daya cilo hawan jini ba, koma waye zan dauki tsatsauran mataki a kansa ehe!

Murmushi Abdul ya saki, sai kuma ya rubuta


"HARDA KAURIYATA ABIH?

murmushin shima ya yi ya ce" *Eh harda maman malan, kai koda kai da kanka ne*

Jinsa yake cikin nishadi, karshe dai hirar haka ta kare ya dauki hudubar Abansa cewa ya yi masu jan ido
idan suka ki shirya kansu, zaman kishi ai ba hauka bane, kuma aure sunnan ma.aiki ce

Hafsat dake gidansu yau ta yi matukar mamakin irin yanda mamanta ta ringa nan nan da ita,
Bata gama mamakin ba aka shigo da kayan kwadayi wai malan ya ce a kawowa mamansa
Ai kuwa ta hau tande tande tana murna dan kuwa azumi tun a wajen likita ya fice domin sai da ta cika
cikinta da ruwa kafin a yi mata aikin da farko ta so kiyawa Abdallah ya ce shi ai dama ba da izininsa ta
dauki azumi ba, ita dai bata ce da su ga abinda ta kunso ba, kuma bata fahimci sun fahimci hakan ba sai ta
dauka dan ta jima basu hadu bane ya saka su yin nan nan da ita
Halayen matan mahaifinta na nan yanda suke, amarya ce ta yi yaji wai malan ya kwashe kayan abinci kaf
da dukiyarsa ya aikawa yarsa sai kace ita daya ya malaka wai gara bayan mijinta ya ce ya hutashe shi
aman ya cika motoci aka kaiwa maman malan abinda bai taba yiwa wata yar ba dan rashin adalci irin
nata bayan malan din bai yiwa mamansa kayan daki ba, wannan din ma fin karfin abdallah ya yi!

Ita dai sha.aninta ta wuni yi hankali kwonce,, nan kafarta ta mike jikintama haka ta samu ta samu
walwallah sosai domin kadaici mugun ciwo ne

Sai yama Abdallah ya je daukanta nan ya shiga ya gaishe da su mama cikin jin kunya da girmamawa kafin
suke mikewa su fice

Sai da ya yi yawo da ita a garin Niamey har kiraye kirayen sallar magarib ya fara kafin ya dakata wani
waje su gabatar da sallah baki dayansu domin nesa suke da gida

Sai bayan sun gama ya dauki hanyar gidansu ,

Yana tafe yana yi mata hira cikin nutsuwa da birgewa suna cikin nishadi har suka karasa gidansu

Yanzunma fitowa ya yi ya bude mata sannan ya kamo hannunta ta sauka daga motar

Rufewa ya yi yana rike da hannunta ya nufi bangaren Na.ima da ita

Ja ta yi da sauri ta tsaya tana kallonsa

Juyowa ya yi shima yana mai jin dar dar dan bai san yanda zai iya tankwasa kansa gaban maman malan
ba!

Kallonta ya yi cikin ido ya ce" ya dai??

Hafsat ta kale shi da kyau sannan ta kalli inda zai kaita, a hankali ta ce" nan ba bangarena bane ba fa

Abdul ya lumahe idannuwansa shima cikin nutsuwar ya ce" eh na sani, zamu je ne mu yi zumunci sannan
kin ga bata san fitarmu ba

Hafsat ta kara kallonsa da kyau kafin ta ce" aman ai sai ka fada mata ko? Sannan ai zamu hadu
bangarenka ba sai mu yi zumuncin ba??

Tana maganar tana kokarin hadiye sauran ne sakamakon wani irin yanda fuskarsa ta fara hadewa tana
hade kanta tamkar kashin safe

Takead ya yiwa fuskarsa irin bai taba dariyar nan ba,


Bai bata amsar maganarta ba ya kara jan hannunta suka je kofar fallon Na.ima

Ja ya yi ya tsaya ya danna abinda zai shaida mata da bako bangarenta

Na.ima dake zaune tana jiran lokacin zuwa bangarensa ya yi ta sha kwaliyarta daidai misali ta mike cike
da mamakin waye ya zo gidanta a irin wannan lokacin? Yan aiki dai ba shiga wajensu suke a irin wannan
lokacin ba, mijinta kuwa bai taba zuwa bangarenta ba bale ta kawo shi a tunanin ko shi ne

A wannan yannayin mamakin ta je ta buda kofar


Sai dai mamakin ganninsa tsaye ne ya kasheta
Murmushin da bata shirya yi bane ya kubuce mata saman fuskarta ganninsa tsaye
Sai dai gannin hannunsa rike da na mace a hankali murmushin nata ya ringa ragewa har ya bace fuskarta
ta kasance babu yabo babu falasa a lokacin da ta ga wace ke tare da shi din

Gannin ta yi bake bake a bakin kofar ya saka shi cikin yannayin laushi ya ce" hajia mun zo ziyara ne ko
mu juya wannan tsare hanya haka?

Na.ima ta kale shi da kyau, ta kuma kallon Hafsat


Ja ta yi gefe wanda ba haka ya dace ta yi ba a matsayin wace aka zo gidanta

Sai da suka shiga sannan ta bi bayansu jikinta du a mace tana jinsa yana waya da mai kula da harkar
girkin gidan

Zama suka yi su duka, ba wace ta gaishe da yar uwarta, shi kuma bai damu ba ya dai shiga jan kowace da
hira cikin hikima yake sako daya cikin hirar daya a haka har aka gabatar masu da abinci suka ci a nan
bangaren nata

Sai da dare ya kara tsalawa Hafsat ta mike,


Dan murmushin iya lebe ta sakar masu kafin ta ce" Allah ya tashe mu lafia

Na.ima ta kalleta itama murmushin ta sakar mata ta amsa da " asuba ta gari

Abdul ya mike ya kashewa na.ima ido ya ce" Ina zuwa

Fita ya yi ya bi bayan Hafsat ya rakata har kofar dakinta

Gannin zata shige bata ko kale shi ba ya saka shi riko hannunta da yannayin shagwaba irin ta maza ya ce"
ko dan muah babu Madame??

Hafsat ta juyo da idannuwanta da sula cika da kwallah ta jin haushinsa ta sauke su a kan fuskarsa
Haka kawai sai ta fashe da kuka ta janye hannunta ta shige bangarenta,
Ita fa kawai ya wulakantata ta, dan me zai fara kaita bayan ita bata taba takowa inda take ba? Me take
takama da shi da ita bata da shi? Kallon raini da wulakanci? Dan me zai wani kwasheta ya kaita bangaren
macen da bata damu da ita ba?

Abdul dake tsaye ya daburce sai dora hannunsa yake yana shafa kansa,
Tamkar ya fada dakin ya duka ya bata hakuri, sai dai ina, hadewar kansu ya fi masa komai, ya fi masa
fushin su su duka

Juyawa ya yi ransa a jagule ya koma bangarensa

Yana zuwa ya tarar da Na.ima ta zo,


Tana ganninsa ta tabe baki a fili ta ce" an bi matar so kennan

Na.ima, bata san dawan garin ba da bata yarda ta yi furucinta ba, bata san a kan tsani yake ba, bata san
kiris yake jira ya fashe ba, bata san ta tabo tsuliyal dodo ba sai da ya budi baki bayan ya ja ya toge ya dafe
tsatsonsa da hannunsa na hagu ya nunota da manuniyar hannunsa na dama ya kankance idannuwansa ya
ce"
[9/26, 5:29 PM] BAK'A CE: *KUTKALE*

*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*
Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA
DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number
+22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR
RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO
NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce,
Sajida😍😍😍😍

7️⃣0️⃣

Wato ga sakarai wawa marar hankali


Ga dan iskan nan ya dawo
Ga danki da kika tsana bara ki sauke masa kwondon rashin kutunci
Wato ga shegen nan ya dawo
To Na.ima sai ki mike ki ciro wayar jikin bangon dakinki ki ki lakada min dukan jaki kin ji?

Au, girmama kin da na yi na dauke ta na kaita bangarenki dan ku yi zumunci ne laifina ko me?
Shin ku dukanku marainin ku nine?
To bara ku ji baki dayanku, bilahilazi karya kuke! Ni ba sakaran namiji bane au ku hade kanku au na
dauko rigar rashin mutunci na yafa na yarfa maku kalar nawa takun sai a auna a ma.auni idan naku ya fi
rinjaye zan sadako! Kan muradina ba abinda ba zan iya yi ba, muradina a wajenku kuwa shi ne ku hade
kanku ku yi zumunci! Abdaul jabar nake haihuwar Mina girman maka ni da ku shege ka fasa!

Yana gama fada ya ja tsaki ya juya dan komawa bangaren Hafsar domin ya ga alamun idan har ya yi
sanya zasu mayar da shi wani sauna ne zancen ya tafi a shashance

Yana zuwa turawa ya yi ya shige uwar dakanta ba tare da ya nemi izini ko wani lako lako ba
A lokacin Hafsat na tsaye gaban gadonta zintir haihuwar mamanta tana shafe jikinta da man zafi ko zata ji
damar ciwon da yake mata domin ita cikinta bai zo mata da wani ciwace ciwace ba sai dai taunar jiki da
abubuwan da ba za.a rasa ba

Turus ya yi yana kallon bayanta da ta baiwa kofa,


Dukawar da ta yi dan lakato Victago din ta kuma bin jikinta da shi ne ya kusan dauke numfashinsa
Da sauri ya rintse idannuwansa sai dai yana rintsewar ya ji idannuwan sun kuma budewa suna kara
waruwa kan abincin su

Shi da ya shigo da niyar yi mata wankin banban bargo sai kawai ya ji ta shiga bulale shi da taimingiyar
dukan rakumi!

A hankali ya taka ya karasa bayanta


Rungumeta ya yi a jikinsa tare da lumshe idannuwansa
Ta so tsorata dan bata ji shigowarsa ba ta raja.a a abinda ke gabanta sai dai jin kamshin jikinsa ya sakata
sauke ajiyar zuciya ta lumshe nata idannuwan itama tana jin yanda yake bin jikinta da shafa cikin nutsuwa
yana jan numfashi

A hankali ya dora hannunsa a kugunta pamkameme da shi kafin ya shafa kasan mararta
Murya can kasa tamkar ba muryar da ya gama kirta fada da ita ba ya ce" cikin ki a shafe yake sosai, a
haka akoy ajiyata na wata hudu? Ki ringa cin abinci Kauriyata kar ki haifa min yaro da tamowa

Hafsat ta saki murmushi tana jin wai yaro da tamowa, ita kanta mamakin cikinta take a haka wai da mutun
a ciki?

A hankali ya kuma shafota ya ce" na kai ki bangaren Na.ima a farko.ne dan tana matata ta farko kafin ke,
ita ce uwar gidana ke kuwa amaryata, ina so ki girmamata itama ta girmama ki, ban fi son wata fiye da
wata a cikin ku ba, dukanku zabina ne Hafsat ba na kowa ba, dan Allah, ku taimake ni ku hada kanku ku yi
zumunci tsakaninku hakan zai haifar min da kwonciyar hankali harma na samu karfin gwuiwar fita nema
cikin nutsuwa

Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta juyo jikinta na dan rawa rawa ta kama lebensa na kasa ta shiga tsotsa
idannuwanta a lumshe

Ya fita haukacewa , jin zai zarme ya sakata dakatar da shi a hankali ta rada masa a kunnensa cewa yau
ranar auntyna ne,

Sakinta ya yi shima yana janyo numfashinsa ya sauke mata manyan idannuwansa da suka canza kalla yana
kallonta

Murmushi ta yi ta mana masa kiss a kuncinsa a hankali ta furta" i love u

Hannunsa ya kara mikowa dan ya damkota ta saki karamar dariya ta zile da sauri sauri gudu gudu da
gaya ta afka bayin dakinta tana juya jikinta wanda hakan ya saka shi yin sakalau da baki ya bita fa kallo

Sai da ta bacewa ganninsa sannan ya saki murmushi ya ce" Yar malan, bakya jin magana walahi.

Juyawa ya yi ya fice a dakin tun kafin ta karasa shi dan ya lura hanyarta ta hukunta shi kennan

Sai da ya fita ya tsaya ya dafe bishiyar wajen cike da mamakin abinda ya faru, aa, ya zo ne da niyar itama
ya sauke mata abinda ya saukewa yar uwarta, aman yaya aka yi ya bige da yar murya? Yaya aka yi bai
balbaleta da balaki ba?
Wato da ake cewa akoy matan da suke da kwarjini shi ne wannan? Matar Abdallah maman malan ta fi
karfin ya kirta mara rashin mutunci?
Murmushi ya yi ya girgiza kansa ya daga kafarsa ya nufi bangarensa yana ayanna bara ya koma itama ya
rarasheta ko dan kwatanta adalci a tsakaninsu, bale a yau yana bukatar taimakonta ko dan kunosa da
maman malan da ta yi
[9/26, 9:56 PM] BAK'A CE: *KUTKALE*

*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA
DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number
+22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR
RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO
NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce,
Sajida😍😍😍😍

7️⃣1️⃣

Nd
Nd
Nd
Nd
Nd
Nd
Nd
*Alhamdilah*

Ba karamar jajircewa Abdul ya yi dan gannin iyalansa sun hada kansu, yakan hada su ya sake a cikinsu ya
yi ta jan su da hira da wasa da dariya
Idan sun kadaice daga su sai shi yakan yi nasiha da nuna irin yanda yake son su hade kan nan nasu
Sam baya nuna wata ta fi wata tsakanin su,
Yana bakin kokarinsa dan kamanta adalci tsakanin su, baya baiwa wata fuskar kawo maganar wata idan
ba alkhairi zata fada ba, shi baya daukan sirrin wata ya fadawa wata, baya yaba wata gaban yar uwarta
dan ya bata mata rai

Ba laifi ya samu abinda yake so , domin a cikin watani hudu da suka karu ya yi tafia sau uku kan harkar
shagunan da zai bude a maradi, kowace tafia yakan saka ido sosai dan gannin shin daya zata nemi daya?
Abin farin ciki shine ba.a wuni dare ya yi daya bata leka yar uwarta sun gaisa ba, duda ba wani hira can
can ba ko wani sakin jiki irin wannan , aman haduwa a yi zumunci suna yi, idan kuma daya ba lafia dayar
na tsayawa kamar yana nan ba wani abinda zai ragu
Sukan dan zagaya a tsakar gidan tun da docter ya bada umarnin zagayawar

Sosai Hafsar ke samun kulawa bangaren mijinta, iyayenta, mahaifin mijinta da abokiyar zamanta

A haka har watan haihuwarta ya tsaya inda Abdul ya murje ido kan ba inda zai motsa, sam ba zai je ko.ina
ba yana tare da ita , harma ya baiwa saudiya amsar zai je bincike aman da sharadin idan matarsa ta haihu
zasu je tare

Wani yamacin juma.a, Hafsat na gidan malan ta je gaishe su du kuwa da irin nauyin da ta yi, Abdul ne ya
kaita da kansa ya ce bayan salar magariba zai zo ya dauketa dan ta shiga yan uwanta ko zata warware dan
kuwa kwanakin nan haka kurum ta cika fushi, abin fushi da ba na fushin ba tanzu zata fashe da kuka ta
samu da kyar ta mike ta barawa mutun waje, an ce da shi idan cikin mace ya tsufa takan fitar da sirfa kala
kala

Zaune take zugum tun da ya ajiyeta wajen karfe goma na safe


Ciwo take ji na fitar hankali bayanta cinyoyinta kai harta da idannuwanta bata so ta daga su da karfi dan
ji take har su ciwon suke

Mahaifiyarta na lure da rashin walwalarta, sai ta ringa kokarin gannin ta sakata walwalar domin cen
dama maman Hafsat ba mai basu damar yawon kawo korafin gidansu bane bale har ta saurare su ta basu
kofar shirme

Ita dai Hafsat daga zaune ta kasa yiwa abin dariyar mamanta dariya, a haka har aka kawo abincin rana

A lokacin da ta muzguta dan wanke hannunta ne ta ji wani irin bulbul ruwa mai yawan gaske ya zubo daga
pant dinta daga zaunen da take
Di kira ta yi ta sanar da ubangiji kafin ta kai dubanta wajen kafafuwanta inda ruwan gayannan har ya fara
gudu

Gabanta ne ya fadi, irin gargadin mamansu na tsafta ne ya fado mata inda take fadin ba ruwanta da
iskancin matan zamani wai dan kina da ciki shikennan ke an tara kazamta a tare da ke, ki zubar da wannan
ki ci ki bari ba ruwanki da wanki wanka ko wanke waje, ke ga mai ciki kina wari kina karni fuska ba kwali
a yi magana a ce ciki to ba a kanki aka fara ba bare a gama a kanki, yau ta shiga uku fitsari ne ta yi zaune
a dakin mama? Mama da tsantseni ba mai hanata cewa a gidanta ma haka take,gashi duka duka yanzu
karfe uku ta yi bale ta sa ran Bawan Allah zai zo ya dauketa su yi tafiarsu, yau ta san mai rabata da mama
sai Allah dan haka a hankali ta dago suka hada ido da mama da ta yi sokoko tana kallonta da yannayin
mamaki da tsoro a fuskarta

Da Sauri Hafsat ta daga dan yatsarta manuniya sama ta ce" mama, na rantse da girman Allah ban taba
yin fitsari a jikina ba , komin dare sai na sauka na saka takalmina zan je bayi na yi na dawo, kuma ki
tambaye shi, itama auntyn ki tambayeta, sannan shi wannan fitsarin ban ji ina jinsa ba ban san zai fito ba
sai fitowarsa da na gani mama, wly shi kadai ke zuba

Da sauri mama ta koma ta rufe dakinta ta karasa kusan Hafsat ta duka ta ce" maman malan kina jin ciwo
wani waje ne? Tun yaushe kika fara jin ciwon? A asibiti sati nawa suka baki?
Hafsat na kallonta ta ce" mama tun da watan nan ya kama nake fama da ciwon baya da cinyoyi sai na ji
marata ta kara nauyi sannan ta sauki dumi, ban fadi ba dan kin hana ni yawan korafi

Mama ta gyada kanta kafin ta kamata ta ce" mu je saman bed, cire zanin nan ya jike

Hafsat ta cire tana mamakin mama batai mata fada ba, sai dai tana kokarin mikewa gaba dayanta ta ji
wani irin ras ras ras wanda bashi da misali

Da sauri ta so durkushewa mama ta riketa gam ta taimaka mata ta dorata saman bed dinta

Nan da nan mama ta saka safar likitoci ta hannu ta gyara Hafsat da kamar jira ake ta motsa a gagabo
mata ciwo ta dubata

Tabas Hafsat nakuda take har nakudar ta kankama domin a 3 take hakan ya saka mama saurin kallon
agogo ta dauki wayarta ta shiga neman layin Malan

Malan dake tare da jama.a yau juma.a sam bai ji wayarsa na kuwa ba, a wajen kuwa Harda Abdul suna ta
hira da jama.a wanda shi kuwa ya baro tashi wayar a cikin mota

Gannin ta yi ta doka wayoyinsu ba.a dagawa sai ta nemi ta babar yarta wato Aunty ta doka kira

Aunty dake kicin tana gyara abincin mijinta da bakinsa sam bata ji kira ba hakan ya saka natama har ya yi
ya tsinke shiru a lokacin kuma har karfe gudu ta zarce sosai

Da sauri mama ta ahiga safa da marwa tana kallon Hafsat wace idan ciwon ya lafa sai ta dafe goshinta
saman hannunta tana sauke ajiyar zuciya

Bata taba fita ba da izinin mijinta ba koda halin rashin lafia ne, bata san yaya zata yi ita dai likitar mata
ce mai karbar haihiwa aman ba zata so Hafsat ta haihu a gida ba hakan ya sa ta dauki hijab dinta ta fita
tsakar gidan tana bin dakunan samarin gidan ko zata samu wanda zai taimaka ya kira mata malan

Da kyar ta samu ta aiki salihu bayan ta fada masa a gagauce ne

Tsaye ta tana yarde zufa, ta kasa komawa dan tsoro, haka kuma ta kasa fita ta tarbo malan din da kanta

Ya kai minti arba.in tana safa da marwa sai ga malan da Abdul sun shigo a tare domin gannin irin misscal
din da mama ta yi sai hankalinsu ya tashi

Da sauri ta tarbe shi, bayan ta yi masa sannu a gagauce ta ce" UMMA ce ke kan gwuiwa

Da sauri malan ya ce" Me? Kuma kuke gida baku je asibiti ba ?

Abdallah da ya kwararo ido ai bai san lokacin da ya shige kai tsaye ya nufi dakin mama ba

Yana zuwa ya tura kansa ya shiga


Muryarta ya jiyo a hankali tana fadin" ALLAHUMA LA SAHLA, ILAMA JA.ALTAHU SAHLA, WA ANTA
TAJ.ANUL HAZNA IZA SHI.ITA SAHLA

Da sauri ya karasa ya tsuguna inda take kwonce kanta na kallon sama


Hannayenta ya kama cikin nasa hakan ya sakata rintse ido ta damki hannun nasa da wani irin karfi kafin
ta saki wani mugun nishin da ya saka mama afkowa da gudun tsiya ta karasa shiga cikin dakin

Gaba daya jikinsa da nata rawa suke, wani irin hawaye ke taruwa a idannuwansa yana gogewa yana
kallon yanda take jijiga sannan adu.a a bakinta ta kasa dainawa
A haka maman malan ta haifo danta, dan jaririnta wanda yana saukowa a hannun kakarsa ya calara
kukan da ya saka malan kaiwa kasa a nan kofar dakin yana tazbihi ga ubangiji

Abdallah kuwa muryarsa sama sama yake fadin" Alhamdulilah

Mama na gyara yaron ta dora mata shi kan cikinta bayan ta janye farar rigar dake jikinta mai girman
gaske sannan ta zagine ta cire kunya ta shiga kiciniyar gyarata haihuwa mai gayar dati gashi yau an mata
ita a kan gadonta🤣

Gannin ya ki fita ya saka mama ce masa" yawa ka je daga waje na kimtsata

Kallon mama ya yi, kai da ba dan ita bace gaskiya da ba inda zashi, haka ya dauki yaron yana ta kallo ya
nade a zannin mama mai kyau sabo fill abinsa ya fice waje

Yana fitowa malan ya mike a zabure yana kallon yaron, sai kawai ya ji hawaye ya zubo masa, a fili ya ce"
ya Allah, ka baiwa mamana ladan nakuda da haihuwa, ya Allah ka baiwa mamana lafiar shayarwa da
ladan shayarwa, Allah kar ba baiwa wannan yaro damar saka mamana hawaye, ka shiryar mata zuriyarta
, ya Allah kar ka jarabi mamana da yaya masu rashin ji, domin ni na yafe mata duniya da kiyama hakama
mamanta, Allah ka ja da kwanakin mamana su zauna lafia da mijinta da kuma abokiyar zamanta ka basu
zuri.a dayiba

Abdul amsawa yake, dan ya tabata wannan adu.ar malan ce ta zuci ya kasa rikewa, kai yana jinjina
soyayar da da uba ba kamar ta malan da mamansa

Alhamdulilah maman malan ta sauka lafia a gidansu, Na.ima sai dai gannin mutane ta yi sun dawo mata
da yaro da kuma mai taya wankan jego, hakan ya sakata wata irin murna da nan nan da yaron, ta rike shi
a hannunta sai kallo take, jinsa take har cikin ranta, sonsa take tamkar ita ta haife shi
Sanadiyar haihuwar yaron nan ta kara kusanci tsakaninsu domin idan ta fito tun safe sai kwonciya ke
mayar da ita bangaren oga, wanda take mugun jin ya matsa mata da cinada dan kuwa da Hafsat da sauki
sauki sai a kwana biyu bai hau ba yanzu kuwa ita daya ce keken tuki kawai yake!
An yi sunna mai sunna sunna, yaro ya ci sunnan *FAHAD* , an sha shagalin sunna kamar ba gobe, an
dagargaje an more an yi gatsa

Maman yaro wato Na.ima ta yi kaya akwati uku manya shake da kayan jariri ba abinda ta manta
Mahaifinsa ya yi masa kaya shi da mamansa daki guda
Kakaninsa sun yi masa kaya wanda Hafsat ta gyada kai a fili ta ce" Fahad haihuwarka na karyar kafar
baya😉

Jinni bai wani dauki lokaci ba ya dauke mata, nan fa suka shiga wasan buya da mai gidan dan kar ya gane
ta samu kanta, domin a hakanma da yaya ta kare kulun yana nanuke da ita ya tsotsewa Fahad milk dinsa
ya barshi da darwAyar kwano ina da ya ji lamari ya koma yanda yake

Mama kuwa daga bangarenta ta zage tana ta aiko mata da kayan gyara masu inganci, ita ce kaza mai
nonon rakumi, an mayar da icen gongoli ruwanta, du abinda zai karkaro mata mutunci ta yi tsaye jina tana
gyara maman malan inda aljihun malan ya yi kuka domin da ta fada masa abinda za.a yi sai kawai ya cire
zif sin jaka ya bar mata a bude take diba tana taka rawa da liki

Harda hadin shananak, da sa buzu ihu akai mata ta shanye kora guda hakan ya saka ita kanta sai ta ji
tamkar tana fitsari tsabar yoyo

A haka har ta yi arba.in da kwana biyar cif, kafin ta shirya dan kanta ta kai Fahad wajen mamansa da
nononta a fida uku aka saka a firij da pampos dinsa da komai ta yi masu salama ta kada abinda ba wani
shaku ko dar dan ta yarda da soyayar Na.ima dama halayenta domin sai da ta karanceta ta gane ita mutun
ce marar munafurci mai fitar da abinda ke ranta komai dacinsa idan tana sonka zara fada maka ne idan
kuwa bata sonka ko waye kai zata fada maka dan haka itama ta lamunce mata suke zaune lafia
A hankali ta karasa bangarensa, tana zuwa ta tarar da shi zaune gaban laptop yana dane dane,
Abayar jikinta ta cire ta yar daga inda take kafin ta karasa ta haye bed hakan ya saka shi amsa wannan
gayata....a wannan dare ba.a ji motsinsu ba har wajen karfe taran dare, inda suka raya daren suna ibada,
lada lodi lodi wanda Abdul ya kasa gane yaya aka yi ya ji wajen tsammmmmmm, matarsa duniyarsa

FAHAD na da shekara daya da wata biyu maganar tafiarsu ta tashi gadan gadan wanda akai masu
alkawarin albashi mai mugun tsoka

Sun shirya a matsayin almajirai masu neman wankau zasu je gidan inda Na.ima ta karbe yaronta ta yi
masu fatan alkairi

Sun fito da shiri, zasu je su aiwatar da aikinsu na *BODYGUARD* YAN BINCIKEN DA HORON GIDAN
YARI YA ZAME MASU ALKHAIRI.............

ALKHAIRI ALKHAIRI

ALHAMDULILAH..

ALHAMDULILAH

ALHAMDULILAH

MU HADE A SABON NOVEL DINA MAI TAKEN" *MAKAUNIYA* DA KUMA KARASHEN *AURE
YAKIN MATA* IN SHA ALLAH

ya Allah, du abinda na yi ba daidai ba ka yafe min, abinda na yi daidai ka sa ma anfana ko bayan raina,
Allah ka sa mu sace ka sa mu cika da imani.........taku ce, yar mutan Niger SAJIDA

You might also like