You are on page 1of 6

TARIHIN

SHUGABAN WALIYAN ALLAH

JIKAN MA'AIKIN ALLAH

SHEHU AHMADU TIJJANI


Radiyallahu Anhu
Sayyidah Zahra Sadauki (Ummu Arifah)
NASABAR SHEHU TIJJANI R.T.A

Sunan sa Sayyadi Ahmad ɗan Muhammad, Sunan mahaifiyarsa kuma A’isha ‘yar Muhammadu
Sanusi. Kuma shahararren laƙabinsa shine "TIJJANI", Ana yi masa alkunya da "Abul-Abbas".

Shehu Ahmad Tijjani R.T.A cikakken sharifi ne (Jikan Annabi S.A.W) ta wurin mahaifin sa. Ga
Salsalar sa kamar haka: Sunan sa Ahmad Tijjani Ɗan Muhammad Ɗan Mukhtar Ɗan Ahmad Ɗan
Muhammad Ɗan Salim Ɗan Eid Ɗan Salim Ɗan Ahmad Ɗan Aliyu Ɗan Abdullah Ɗan Abbas Ɗan
Abduljabbar Ɗan Idris Ɗan Ishaq Ɗan Aliyu Zainul Abidin Ɗan Ahmad Ɗan Muhammad Ɗan
Hasanul Muthanna Ɗan Imam Hasan Ɗan Sayyidina Aliy da Nana Fadima Yar Annabi
Muhammad S.A.W

HAIHUWARSA DA NEMAN ILIMIN SA

An haifi Shehu Ahmadu Tijjani a garin Aini Mãdhi, cikin kasar Algeria a yanzu, a ranar 13 ga
watan Safar na shekara ta 1150 bayan hijira, kuma ya fito ne daga dangi da suka saba da
hidimar ilimin addini da karantarwa, lakabinsa na Tijjani jinginawa ne zuwa ga kabilar da
mahaifiyarsa ta fito wato TIJJANATA, kuma da yake dangin mahaifiyar tasa sun fi na mahaifinsa
shuhra, sai shehu ya fi jingina kansa zuwa garesu har lakabin Tijjani ya kama shi.

Shehu Tijjani ya rayu a tsakanin mahaifiyarsa da mahaifinsa har zuwa rasuwarsu, yayi neman
ilimi sosai tun a ƙuruciya cikin wata irin himma mai ban-mamaki, kuma ya bayyana cewa shi mai
albarka ne da Allah ya nufa da wata baiwa ta musamman, domin tun yana da shekaru bakwai
da haihuwa ya samu haddar alkur’ani mai girma da ruwayar warshu, a hannun malaminsa mai
suna shehu Muhammad bin Hamwu, sannan bayan ya haddace alkur’ani mai girma kuma sai ya
cigaba da karatun ilimin addini a wajen wannan malami, Shehu Tijjani ya karanta littattafan
sanin shari’ar muslinci a hannunsa, kamar Iziyya da Risala da Askari da sauransu, ya kuma
cigaba da karatu a hannun wasu malaman bayan shi, ance ya karance littafin Mukhtasar khalil a
hannun shehu Mabruku bin Bu’afiya, wanda kuma shi shehu Mabrukun nan ya rasu ne fa a
lokacin da shehu Tijjani yana dan shekara 16 da haihuwa, hakan na nufin shehu Tijjani ya kure
fannin fikhu tun bai wuce shekaru goma sha shida ba a duniya. Shehu Tijjani ya kure dukkan
malaman da ke kurkusa ta fuskar ilimi da karatu tun yana karami, kuma ya soma bada fatawa
tun wannan hali na kankanta.

RASUWAR IYAYEN SA DA AURENSA NA FARKO

Mahaifin shehu Tijjani da Mahaifiyarsa sun rasu ne a rana guda cikin wata annoba, a shekara ta
1166 bayan hijira, kuma a wannan shekara ne suka yiwa shehu Tijjani aure kafin rasuwar tasu,
shehu Tijjani ya cigaba da maida hankalinsa zuwa ga ilimin sufanci da neman sanin Allah tun
daga wannan lokaci, kuma daga bisani da ya soma samun bakin zaren, sai ya shauƙantu zuwa ga
haɗuwa da bayin Allah masana Allah waɗanda zasu sada shi da muradinsa, shi yasa bayan
shekarunsa sun kai 21 da haihuwa, sai ya nemi afuwar matarsa ya sauwake mata, har yana
cewa "Ita mace burinta matashin kai, shi kuwa Tijjani burin sa Ibada", ya kama hanya cikin
sahara don neman saduwa da muradin nasa, kamar yadda dama bayin Allah irinsa suka saba.

HAƊUWAR SA DA WALIYAI

A wannan fita, shehu Tijjani ya haɗu da waliyai da dama, waɗanda suke manya ne a walittaka
da sufanci, kuma dukkansu ya amfanu da su kuma suma sun amfanu da shi. Daga irin manyan
da ya haɗu dasu akwai Shehu Mahmudu al-kurdiy wanda ya sadu da shi a Misra, Egypt a yanzu,
kuma a wajensa Shehu Tijjani ya karbi Darikar khalwatiyya, sannan yayiwa shehu albishir da
cewa zai samu matsayi babba a cikin walittaka. Haka nan daga cikinsu akwai shehu Muhammad
bin Al-Hasan wanda yaiwa Shehu Tijjani Bushara da cewa zai taka muƙamin da shehu Aliyus
Shazali ya taka. Akwai shehu Ahmadus Sakali, da wasunsu da dama. Wani abin mamaki shi ne:
shehu Tijjani na zuwa wajen waɗannan waliyai ne domin neman ya amfanu da abin da suke da
shi na ilimi da ma’arifa, amma saɓanin haka da zarar sun soma tattaunawa da shi, sai sama ta
koma ƙasa, su zama su suke amfanuwa da shi saboda yawan baiwarsa ta ilimi da fahimta da
hikimar Magana.

ZUWAN SA AIKIN HAJJI

Himmar shehu Tijjani ta ja shi zuwa ga yin aikin hajji da kuma ziyarar kakansa Annabi
Muhammadu sallallahu alaihi wasallam a shekara ta 1196 kuma shehu Tijjani ya tafi yana mai
cigaba da abin da ya fara na bibiyar bayin Allah akan hanyar tafiyarsa zuwa makkah, ya shiga
makkah a shekara ta 1197 kuma yayi aikin hajji a wannan shekara, a nan ne kuma ya je ziyarar
shehu Abdullahil Hindiy, sai ya tarar ya shiga halwa, basu sadu ba, amma sun yi musayar wasiƙu
tsakaninsu, ya kuma tabbatarwa shehu Tijjani cewa shi ne magajin sirrikansa baki daya. Bayan
kammala hajji sai shehu Tijjani ya shiga madina inda ya ziyarci Annabi sallallahu alaihi wasallam,
Anan ne kuma ya sadu da shehu Abdulkarimus Sammani, sannan Shehu Tijjani ya kuma kamo
hanya ya biyo sahara don komawa gida bayan kammala hajji da ziyara.

SAMUWAR ƊARIQAR TIJJANIYA

A hanyarsa na komawa ɗin ne, ya ga Annabi SAW ido da ido ba a bacci ba, ya ce da shi "Ka bar
dukkan wani ɗariqa na kowani waliyyi, Daga yau nine shehin ka, Nine mai yi maka madadi",
Sannan ya umarce shi da karanta Istigfari 100 da salatin Annabi 100 kullum safe da yamma.
Wannan shine abu na farko da aka soma a Darikar Tijjaniyya, daga bisani a shekara ta 1200H,
Annabi Alaihi Wasallam ya cika masa da Hailala 100, sannan aka bashi wazifa da zikirin juma’a,
sannan aka umarce shi da ya bada wadannan wuridai ga wanda duk ya nema daga cikin jama’a,
sannan Annabi yayi masa alkawarin cewa shi zai zama kofar tsiran dukkan wanda yai riƙo da
Dariƙarsa.

IYALINSA DA WAFATIN SA

Bayan dawowar shehu Tijjani ya tare ne a garin Fas, babban birnin maroco a yanzu. Kuma Anan
ya cigaba da rayuwa har zuwa wa’adinsa ya cika. Shehu Tijjani daga bisani ya sayi bayi mata
guda biyu ya ƴanta su sannan ya auresu, sunan su: Sayyidah Mabruka da Sayyidah Mubaraka,
kuma da su ya rayu har suka Haifa masa ‘ya’ya, shehu Tijjani ya rasu ya bar waɗannan mata da
kuma ‘ya’yansa biyu: Sayyidi Muhammadul Kabir da Sayyidi Muhammadul Habib, ya kuma rasu
ne a shekara ta 1230H, yana da shekaru 80 a duniya, Allah ya bamu daga cikin albarkarsa.

BUSHARAR MAGABATA AKAN SHEHU TIJJANI RTA

Wannan saƙo mai Albarka wanda Sahibul Faidha Alhaji Ibrahim Niasse Alkaulakhiy RTA ya
rubuta, shi kuma ya samota ne daga kundin mahaifinsa Alhaji Abdullahi Inyass (Allah ya qara
masa Rahma).

Shehu Yana cewa "Ya kamata wannan saqon ya kasance a tareda duk wanda yake Darikar
Tijjaniya don samun Albarkar Quɗubil Maktum Shehu Ahmadu Tijjani RTA. Kuma Muqaddamai
su dinga karantawa a zawiyoyi ga muridan Shehu Tijjani RTA. Ga Allah ne muke godiya bisa
baiwarsa." Bayan haka, haqiqa an samu wannan wasiqa daga wurin Sahabban Shehu Tijjani RTA
daga Aini mãdi , Ga Abinda Saqon ya kunsa:

1. Shehu Abul wafã'i Al-bagdadiy Yana cewa “Akwai Kogi guda biyu wanda Allah bai sanar dani
su ba. Na farko kogin Maulanmu Shehu Tijjani RTA wanda babu ɗaya daga cikin waliyai baki
ɗaya wanda yasan shi sai Shugabanmu Annabi Muhammad SAW. Kogi na biyu shine kogin
Annabi SAW babu halittar da ta san ta sai shi Allah SWT.

(Abin nufi babu waliyin da yasan Shehu Tijjani Sai Annabi SAW).

2. Shehu Abdulqadir jilani RTA yana cewa “Kar ku daukaka/girmama ni fiye da Quɗubil maktum
domin waliyi baya sha da kwankwaɗa sai daga kogin Shehu Tijjani RTA. Haqiqa na shauqantu da
kasancewa a muqaminsa amma sai na tarar da muqaminsa da shamaki/katanga tsakaninsa da
dukkan waliyai baki daya.

(Wato Shehu Tijjani keyin madadi ga dukkan waliyai. Sannan Sidi Abdulqadir yaso ya samu
muqamin Quɗubil maktum amma sai yaga Allah ya haramta muqamin ga wanin Shehu Tijjani
RTA)
3. Shehu Muhammadul kurdi RTA yana cewa “Falalar Quɗubil Maktum a bisa dukkan waliyai
baki ɗaya kamar Falalar Illiyina ne akan sauran aljanna. Kamar yadda Annabi SAW yake faɗi cikin
hadisi cewa kaga su illiyina, babu wani abin nema bayan su”.

4. Abu yazidul basɗamiy RTA yana cewa “Duk wanda ya daukaka matsayin waliyai fiye da
matsayin Shehu Tijjani, toh haqiqa yazo da aikin ɓarna. Wanda yazo da ɓarna kuwa, Allah ya
la'ance shi.

5. Sayyadi Muhammadul kurdi ya qara cewa “Allah bai halicci daya daga cikin waliyai wanda ya
samu fifiko fiye da Shehu Tijjani ba, kai ko kwatankwacin sa ma babu".

6. Shehu Abdus-salam Al-mishisiy RTA yana cewa “Wani Waliyi zai bayyana Qarshen zamani ana
ce dashi Quɗubil Maktum, wanda yayi inkarinsa ko mabiyansa zai mutu kafiri sai dai in ya tuba".

7. Imamu Junaidu RTA yana cewa “Hasken waliyai baki ɗaya yayi sujjada ga Hasken Shehu
Tijjani kamar yadda hasken Annabawa baki daya yayi sujjada ga Hasken Annabi SAW”.

(Tun a alamil arwahi kafin ma a shigo darkil asfali)

8. Sayyadi Ilal ɗan Ahmad Al-mardiy yana cewa “Da Allah zai bani tsawon rai zuwa qarshen
zamani, da na kasance muridi/Almajiri ga Shehu Tijjani RTA".

9. Shehu Abdur-rahman Sa'a-libiy RTA yana cewa “Wani waliyi zai bayyana a qarshen zamani,
Falalar Sahabbansa kamar falalar sahabban Annabi SAW yake. Wasu daga cikin magabata sun
bamu labarin sunansa da alkunyarsa, Sunansa wanda yafi shahara shine Sayyadi Ahmadu ɗan
Muhammadu ɗan Mukhtar. Alkunyarsa/Laqabinsa shine Quɗbul Maktum".

10. Qudubul tuhamiyyu Al-wawazãniyyu RTA yana cewa “Dakin Allah yana kewaye gidajenmu a
shekara sau saba'in, saidai hakan yana faruwa ne cikin lamarin/bisa iznin Quɗubil Maktum
wanda akeyiwa laqabi da Abul-Abbas Batijjane. Babu mamaki cikin kyautar Allah”

11. Haka zalika Annabi SAW yana cewa “wanda yake son Quɗubil Maktum, ni yake so, haka
kuma wanda yake qinsa, ni yake qi”

12. Sayyadina Abubakar RTA yace “Wanda ya furta kalmar ɓatanci ga Quɗubil Maktum, zai
mutu kafiri sai in har ya tuba”

Sufaye suka ce in mutum ya qi Shehu tijjani koda ya tuba sai an yi shekara arba'in a zuri'arsa
babu mutumin kirki ballantana a samu waliyi. Wasu kuma suka ce sai anyi zuri'a bakwai a
gidansa babu waliyi.

13. Sayyadina Umar ɗan Khaɗɗabi RTA yana cewa “Sanin wanene Quɗubil Maktum abu ne mai
wuya akan sanin wanene Annabi SAW. Domin Shi Annabi SAW Sananne ne kuma ya shahara.
Amma kaga shi kuwa Quɗubil Maktum, Ko masana Allah basu sanshi ba ballantana mutane
gama-gari.

14. Sayyidina Usman ɗan Affan RTA yana cewa “Babu Wanda ya san martabar Quɗubil Maktum
har Mala’iku baki ɗaya.

15. Sayyidina Aliyu ɗan Abiy ɗalib KW yana cewa “Na tambayi Annabi SAW shin wanene
Quɗubil Maktum, yaya sunansa da laqabinsa? Sai Annabi SAW yace min Sunansa Ahmad kuma
Laqabinsa Tijjaniy, zai bayyana ne daga cikin zuri'arka can a qarshen zamani, zai bayyana ne da
zatin Waliyai da Qudubai kamar yadda na bayyana da zatin Annabawa da manzanni.

16. Sayyadi Mu'awuya RTA Yace “Annabi SAW yace wasu mutane daga cikin al'umma ta ba zasu
gushe ba sai ka same su cutar mai cuta bata cutansu, adalcin mai adalci baya amfanar su, zasu
bayyana ne daga magrib” . Wannan hadisin ya gangaro ne zuwa ga Mabiya Ɗarikar
Muhammadiya Ibrahimiyya Tijjaniya Allah ya qara musu yarda baki daya.

Alhamdulillah!

ZAN YI AMFANI DA WANNAN DAMA, IN KIRA DUKKAN YAN'UWA MUSULMAI, SU KARƁI


ƊARIQAR TIJJANIYA, WAYANDA SUKA KARƁA, SU KIYAYE DOKOKIN TA, HAQIQA RIBA
TABBATACCIYA CE GA DUK WANDA YAYI RIQO DA SHEHU TIJJAN R.T.A.

Daga yar'uwar ku

Sayyidah Zahra Sadauki

(Ummu Arifah)

You might also like