You are on page 1of 13

An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.

ng ku ziyarci shafin na
www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na
yake yake dana soyayya

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu
kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama
sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana
magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490

A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci,
duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna
neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman
munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai
fi kyau ku riga dauko PDF da DOC

Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai
wayarku

This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng


You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to
download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography
including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490
its free we do not charge for our services

Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted
biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not
blame us

Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we
are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day,
any time you can visits our site and download it

Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF
or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
MATSATSUBI 1Complete bookNa Abdul Aziz Sani madakin gini.Typing #MBRMATRIX
Whatsapp.. 08100767577Sarki Dujalu yayi gyaran murya sannan yace to sai ku kimtsa,
kai mai rubutu ka aza alkalamin ka akan tkrd domin wannan hikayar da zan baku na
dauke da matukar abubuwan al-ajabi.Ni kai na ko tunowa nayi da lbrn sai nayi
kuka.Hikaya ce ta wani kyakykyawan saurayi kuma jarumi wanda ake kira nazmir bin
halad da gimbiya luzaiya yar sarki fahalul bahafus.A wani zamani can mai tsawo da
ya shude anyi wata babbar Qasa wadda ake kira duhamul.Wannan kasa ta bunkasa da
girma karfi da kuma mayaka.A bisa wannan dalili ne kasar duhamul ta shahara kuma ta
zama gagara badau a ckn dukkanin kasashen kewayenta.Ya zamana ana matuakar
tsoranta.Sarkin da ke mulkin a wannan kasa ta duhamun wani azzalumin sarki ne ana
kiransa Bashakur.Sarki bashakur ba tsoho bane kuma ba yaro bane domin shekarunsa ba
zasu gaza ar'ba'in da hudu ba. Zuwa da biyar.Sbd zalunci irin na bashakur ko a ckn
garin nasa indai mutum bai shafi jinin sarauta ba ko kuma bai zamo daya daga ckn
attajirai ba to yana ckn tashin hankali.Domin ba ka da yancin kan ka. Dukiyarka da
matanka zasu iya zama ba sarki a koda yaushe.Haka kuma ana dorawa talakawa haraki
mai yawa ta yadda ko kadan basa morar arzikin su baya ga wannan idan sarki bashakur
ya bushi iska sai ya tura mayaka izuwa wata kasar ya basu izinin murkushe kasar a
kamo masa bayi kuma a debo dukiya mai yawa.Bisa wannan haliya ne ya tara dukiya mai
tsananin yawa wacce shi kansa bai san abin da zai yi da ita ba.A wannan zamanin na
sarki bashakur tsafi baiyi shahara ba a ckn al'umma babu abinda ke tasiri face
karfin damtse da yaki.Sarkin yakin wannan birni na duhamul wani tsoho ne dan
kimanin shekara saba'in da shida wanda yayi suna a duniya db tsagwaran jarumtarsa.
Da kuma iya yakinsa a tarihin rayuwarsa bai taba jagorantar yaki an rasa nasara
ba.Ana kiran sa da suna Halufa
Matsatsubi part 2Whatsapp 08100767577 Posting #mbrmatrixJafar ya kare nazarin kayan
cikin kifin tsaf sannan yace "yau kuma a tsakiyar shuke-shuken teku aka watsamu
Yanzu ta yaya zamu iya fita daga wajen nan nikam banga alamar akwai wata hanya
ba.Koda jin haka sai Gulzum ya bushe da dariyar karfin hali sannan yace amma dai ka
cika dakiki kuma kidahumi, wa ya gaya maka cewa nan a cikin kifi muke tabbas
rayuwarmu na ckn mugun hali domin ko zafin dake ckn kifin nan bai kashemu ba to
kuwa yunwa da kishirwa sa kashemu. Nan da kwanaki da ba zasu gaza biyu ba.Koda jin
wannan batu sai gaba dayansu hankalinsu ya dugunzuma kowa ya rasa abinda ke masa
dadi.Daga can sai Yelisa ta dubi Mazalish tace waike ina takamarki ta tsafi take?
Me yasa baza ki cece mu ba daga ckn wannan masifa da muke ciki?Mazalish tace ai kin
san cewa gaba da gabanta ko? Inda tsafina zai iya cetonmu da tun kafin guguwar nan
ta jefo mu cikin tekun zamu kubuta.Jafar ya mike tsaye ya duba gaba da baya ya
jinjina kai yace kai amma fa ubangijin da ya halicci wanna kifi ya cika
tsoro.....koda labari ya riski sarkina sai ya tura aka kirani ya rufe ni da fada
kuma yace lallai ynz a daren nan na zo na yanke kawunanku na kai masa.Maimakon nayi
hakan ne na yanke hukuncin na kubutar da ku.Yakai wannan sarki kayi sani cewa ban
kubutar da kai don komai ba sai dan na ga kana da Qarama kuma kyakykyawar yarinya
wadda kake matukar so itama kuma na fuskanci ta shaku da kai dan haka ba zan so na
zama sanadin raba wannan soyayya ba ta da da mahaifi domin nima ina da da wanda
nake matukar so fiye da komai a rayuwata.Ba zan so a ce ya zama maraya tun yana
Qarami ba."koda halufa yazo nan a zancensa sai kaunarsa ta mamaye zuciyar wannan
sarki da jama'arsa.Dukkaninsu basu san sa'adda idanunsu ya ciko da kwallah ba.Nan
take suka yiwa halufa gdy sannan suka yi bankwana dashi.Halufa ya kamo musu dawakai
suka haye suka kama gabansu.Tafiyarsu keda wuya yayi sauri ya sauya kayan jknsa
sannan yayi wa kansa raunuka a jiki ya koma gidan sarki.Koda sarki bashakur yaga
jini na zuba a jkn halufa sai ya mike zumbur ya tareshi cikin firgici yana mai cewa
ya kai sarkin jarumai me ya faru gare ka?Halufa yace" ya shugabana ai lokacin da na
isa kurkukun sai na iske mayaka dubu biyu sun afkawa masu gadi har sun bude dakin
da aka kulle fursunoninka sun fito dasu.Koda nayi kokarina akan na hana su tfy da
fursunoninka amma sai abu ya gagara don kasan sarkin yawa yafi sarkin karfi.
Da kyar ma na kubuta da kaina.Kafin na dawo cikin gari na nemi mataimako tuni sunyi
mana nisa."koda jin wannan mummunan lbr sai zuciyar sarki bashkur tayi bakirkirin
ya cika da bakin ciki kawai sai ta sallami halufa ya shiga tunani mai zurfi.Daga
can sai ya mike ya yi hawa ya tafi can kurkukun da kansa.Da zuwa ya iske masu gadin
a kwankwance cikin jini magashiyan.Da kyar ya samu mutum daya wanda bai raunata ba
sosai.Sarki ya durkusa gabansa ya cakumi wuyan rigarsa cikin tsawa yace " wane ne
ya zo yayi muku wannan dayan aiki?Mai gadin ya bude baki da kyar.....mai gadin ya
bude baki da kyar yace" ai wani mutm ne shi kadai ckn shigar bakaken kaya ya zo ya
tarwatsamu ya fito da fursunoninka ya kubutar dasu.Koda jin haka sai sarki bashkur
yayi jifa da mai gadin yace wannan zancen banza ne duk fadin kasar mahazus babu
wani sadauki mai irin wannan jarumtarkar. Lallai ka tabbata makaryaci.Kawai sai
sarki bashkur ya zare takobi ya fille kan wannan mai gadin. Nan take ya sake hawa
dokinsa ya sukwane shi ckn fushi ya koma ckn gari.Da zuwa bi zame ko'ina ba sai
gdjn manya mayankan garin yana tmbyr su ko jarumi halufa yazo neman taimako su a
ckn wannan daren bisa farmakin sumame da aka kaiwa kurkukunsa?Kowa sai yace shi ba
a neme shiba hasalima yanzu yake jin lbrn abinda ya faru.Yayin sarki bashkur ya
gaji da yawan tmby sai ya koma gd ya kwanta ckn tsananin bakin ciki kashe gari da
safe sarki bashkur ya tara dukkan yan majalisar sa ya sanar dasu duk abind ya faru
jiya da daddare kuma ya tabbatar musu da cewa shi kam yayi tunani kuma ya tabbatar
musu da cewa shi kam yayi tunani kuma yayi bincikeya gano cewa ba kowanne ya aikata
wannan mummunan aiki ba face jarumi hakufa.Nan take ya kawo hujjojinsa guda biyu
hujja ta farko itace babu wani sadauki a gaba daya wannan hahiya wanda zai iya
tarwatsa barade dubu face jarumi halufa.Hujja ta biyu itace halufa yayi masa karyar
cewa ya dawo ckn gari ya nemi taimakon wasu mayakan amma da aka tmy su sai suaka ce
ba wanda ya nemi taimakonsu.Duk wannan bayani da sarki bashkur yake halufa na zaune
gefe guda yana saurari kawai sai yayi shiru bai ce komai ba yana muzurai
kawai.Sarki bashkur ya dubi fadawansa yace to kunji laifin halufa ya aikata don
haka sai ku yanke masa hukunci da kan ku.Gaba daya yan majalisar suka yi tsit aka
rasa wanda zai ce wani abu. Daga can sai waziri yace ya sarkin sarakuna ai ni a
ganina wannan hukuncin ba zai yanku ba yanzu muna bktr muyi zama na musamman.Sai da
aka shafe arba'in ana mahawara a majalisa akan irin hukuncin da za.a yankewa
halufa.A karshe dai aka yanke masa hukunci cewa an dakatar dashi daga kan matsayin
sa na sarkin yaki har tsawon shekara ashirin masu zuwa nan gaba.Kuma dukiyarsa aka
raba ta kaso biyu aka dauki kaso guda aka ravawa masu gadin gidan kurkukun aka bar
masa guda.
Daga wannan rana halufa ya cire hankalinsa daga harkokin fada gaba daya ya maida
nutsuwarsa akan dansa guda daya wanda suka haifa tare da matarsa zuwaisa.Wannan da
an rada masa suna Nazmir.Nazmir ya taso yaro mai kwarjini kwazo da basira ya zamana
mahaifinsa na koyar dashi kyawawan dabi'u kuma yana koya masa juriya jarumta da
dabarun yaki.Yayin da Nazmir ya cika shekara 14 sai ya zamo jarumin gsk kuma farin
jininsa ya yawaita tsakanin mutane garin.Sbd irin kyawawan halayensa na tausayi da
jin kai da kuma biyayya ga na gaba dashi.A bangren jarumta kuwa sai da yabar abin
tarihi a kasar duhamul domin shi kadai yake shg daji ya yi farautar manyan dabbobin
dawa masu hadari.Sai dai aga yazo da gawarsu.Tun yana jarraba jarumtarsa a tsakanin
sa'anninsa har ta kai cewa yana tunkarar mayna baraden kasar daya bayan daya.Duk
wanda suka gwada yar kashi ko tsagwaron yaki sai ya sami galaba akan sa.Ckn
kankanin lokaci lbrn jarumi nazmir ya yadu ko'ina a fadin kasar ya zamana ana zuwa
ganinsa daga gari-gari.Lokacin da nazmir ya cika shekara 20 a duniya sai kyawunsa
ya kara bayyana a fili karara.Jarumtakarsa ta linka ta da ya zamana bashi da abokai
sai yayan sarautar kasa amma da yake shi mutum ne na mutane mai saukin kai bai yar
da wasu abokansa ba su shida wadanda suka taso tun yarinta.Wandannan abokai gaba
daya yayan talakawa ne.Kuma dare da rana suna tare da nazmir duk da cewa mahaifinsa
yafi iyayensu arziki da daukaka.Daga cikinsu akwai Sharhil, Bagwan, Hasuf, Iklam,
Bardil da kuma Huzaik...Al'amarin su jafar kuwa lokacin da suka shige Qarkashin
Qasa inda birnin Qira yake. Suka zube Qasa suna haki cikin mugun tashin hankali sai
kawai suka ga sarki Azbir na tare dau.Koda ya hada idanu da Mashrila sai yace" yake
ma'abociyar hikima ynz dai kinga irin dabarar da muatanen galbasa suka zo da ita
ma.ana sun zo da Qatuwar garkuwa da majaujawa wadanda ke lalata kibiyoyinmu ynz
mene ne abinyi ? Wace hikima za ki sanar da mu hanzarta amfani da ita domin nan da
rabin sa.a kacal za su gama da mu gaba daya."yayin da mashrila ta ji wannan tmby
sai tayi shiru tswan dakika biyar tana tunani daga bisani ta dubi sarki azbir tace"
ya kai wannan sarki ka yi sani cewa babu wata dabara face abu daya abin kuwa shine
indai muna san mu sami galaba mu kwaci majaujawar dake hannayensu mu yake su da
ita."koda jin haka sai ran Azbir ya baci yace "haba yarinya wannan wace irin mgn ce
kike ta rashin hankali ta yaya zamu iya kwatar makami a hannun mutanen galbasa
alhalin sun fi mu karfi kuma sun linkamu girma sau 10."Cikin fushi mashrila ta nuna
Azbir da hannu tace" wacece yarinya shin kana tsammanin za ka girme nine? Dube kafa
kamar a kife da kwando."koda jin haka sai Azbir ya yi murmushin karfin hali yace"
au dan kin ganni dan guntu shine kike tsammanin ke sa.a ta ce. Ko kuwa dan kinga
fuskata irinta yara? To tsaya kiji a wannan watan da muke ciki na cika shekara dubu
daya da dari da hamsin.Duk wannan nahiyar tamu Galbasa ne kawai ya girme ni.Koda
jin wannan batu sai jkn mashrila yai sanyi ta kasa cewa komai.Gulzum ya dubi azbir
ya ce kaga ku bar musun shekaru dan nasan a shekaruna baka dauki kaso daya ba.Abin
da nake so dakai shine mu yi amfani da shawarar yarinyar nan domin itace kadai
mafita.Ku sani cewa a barin tayi akan bar arha, kuma damu zauna a zo a ci mu da
yaki gwara mu jaraba iya kokarinmu dan wani lkcn sai an gwada ake dacewa. Dan haka
zan yi amfani da damata da kuma dabarun yakin da na koya irin namu na aljanu na
kwato majajjawa daCikin Hanzari Jafar, Yelisa, Mashrila da azbir suka daka tsalle
suka dane bayan aljani Gulzum.
Koda sauran mutanen Galbasa suka ga irin barnar da Gulzum ya soma yi muru sai
dayawa suka yi kukan kura suka afka masa, amma kafin su cim masa tuni sun makara
domin har ya sami damar finciko wadansu majajjawun guda biyu. Kawai sai ya mikawa
su Jafar Guda sannan ya rike guda a hannunsa ya zamana yana amfani da guda biyu shi
kadai.
Koda Jafar, Yelisa, da Mashrila suka kama majaujawar da niyyar riketa sai nauyinta
ya rinjaye su, suka subuto daga kan aljani Gulzum za su fado Qasa.
Cikin tsananin zafin nama Azbir ya ruko jikin majaujawar da hannu daya sai ga su
jafar suna rito a jikin majaujawar.
Azbir ya dawo da su kan gulzum kowannensu ya zauna daram sannan shi kuma ya kama
majaujawar da hannu biyu ya fara kaiwa mutanen Galbasa farmaki kamar yadda aljani
Gulzum ke yi.
Al'amarin da ya jefa su Jafar cikin matuqar mamaki kenan jafar ya dubi mashrila
yace" ke kin ga wannan mutumin da kike rainawa ashe ma duk ya fi mu Qarfi ba mu
sani ba. Lallai sai miya ta Qare ake sanin maci tuwo.
Yelisa tayi ajiyar zuciya sannan tace"Tab dijan daga yau na daina raina Qananan
mutane ni kam ban taba tsammanin cewa wannan mutum zai iya daukar koda abu mai
nauyi mutum ba. Sai ga shi yana sarrafa wannan Qatuwar majaujawar wadda nauyinta ya
wuce gawarwakin bil'adama guda dubu, kuma manyan Qarata ababan kwatance.
cikin Qankanin lokaci gulzum da sarki Azbir suka tashi hankalin mutanen Galbasa
suka Quntata musu, suka hana su sakat, duk da cewa kuwa suma ba su fa sa barna ba
domin sun sha jinin sama da mutum miliyan uku da doriya.
Yayin da masifa tayi masifa,artabu,dauki ba dadi da tsananin turnuku ya yawaita,
sai Dauduf ya Sake yin sama cikin tsananin gudu ya isa inda su sarki Galbasa suke
wannan karan sai gashi ya zo cikin mugun tashin hankali yana ta haki ya risina
gaban galbasa yace"Ya shugabana wani bakon aljani tare da Azbir da wadannan bakin
bil'adama sun sami nasarar qwatar majaujawa guda uku daga hannun jama.ar mu har sun
yi mana gagarumar barna.
Gaba dayanmu mun rasa yadda zamu yi da su lallai muna bukatar taimakonka cikin
hanzari in ba haka ba kuwa nan da Qankanin lokaci za su iya Qarar da mu.
Koda jin wannan batu sai Galbasa ya bude fukafukansa yayi cikin Qasa cikin tsananin
gudu tamkar tauraruwa mai wutsiya koda ganin haka sai kowa ya bi bayan su a wannan
lokacin ne galbasa ya rinka Qwala ihu mai tsananin firgitarwa wanda amonsa ya
haifar da faruwa wani irin rugugi a sararin sama tamkar tsawa. Wuta ta rinka fita
daga bakinsa.
Lokacin da Mazalish ta ga kowa ya bi mahaifinta sai ta noke ta tsaya ita kadai shi
kuwa dauduf sai ya noke a bayanta yana mai buya dan kar tasan da shi.
Abin da bai sani ba shine tuntuni ta gane manufarsa kuma har tayi tunanin hanyar da
za ta yi maganinsa.
Sai da ya rage saura su kadai a wajen sannan mazalish ta yunkura ta juya ta soki
idanuwan dauduf da faratan hannayenta. Take idanunsa sua fashe ya zama makaho.
Bai san sadda ya kwalla ihu ba sbd tsananin radadi da yake ji.
Kafin yayi wani yunkuri tuni mazalish ta fiddo wata igiyar tsafi ta daure shi
tamau.
Nan ta bar shi a sararin sama iska na ta kulin kubura dashi sai ka ga yayi gaba
yayi baya amma ya kasa yin sama ko Qasa sai Qara yake yi.
Cikin tsananin mugun gudu tamkar an harba tauraruwa mai wutsiya mazalish ta bi
bayan su sarki Galbasa amma kafin ta isa tuni Galbasa ya riski su Gulzum.
Da zuwa yayi wani tsafi sai ga shi ya fincike majaujawar hannunsu tamkar mayan
Qarfe ya zuke guntun Qarfe da ke ajiye a gefe guda nan take ya sake yin wani tsafin
sai ga igiyar tsafi ta daddaure su tamau suka kasa motsi.
Anan ne Yelisa ta tuna cewa ita ma fa matsafiya ce yar babban matsafi kawai sai ta
rufe ido tayi kiraye-kiraye da yan tsatsube-tsatsube amma sai ta ji shiru kamar
maye yaci shirwa sarki Galbasa ya dube ta ya tuntsire da dariya yace"Ke yarinya
daina bata lokacin ki babu wani irin tsafi da zai yi aiki anan in ba irin namu ba.
Lallai zan tafi da ku izuwa fadata dan nayi muku mugun kisa sanadiyar barnar da
kuka yi mini.
sarki galbasa na gama fadin haka ya bada umarni a cgb da shan jinin mutanen gari
nan aka sa musu wawa tamkar an ajiyewa karnuka yankan nama guda faya kacal.
Nan fa gari ya sake hargitsewa da iface-iface sai dai ka ga jini na ambaliya da
famtsamuwa tamkar teku ta balle.
Ana cikin haka mazalish ta iso tamkar walkiya cikin abinda bai wuce dakika guda ba
ta tsitstsinka igiyar da ta daure su jafar da karfin tsafi sannan ta sure su ta
dora su a gadan bayanta ta kuma suri kibiya guda irin wacce mazalish tasa aka kera
tare da na'urar harbata duk da hannu daya ta sake cillawa da gudu ta bace a ckn
sararin samaniya tamkar walkiya.
"kar ku yi zatan mun tsira da ni da ku daga yanzu zuwa kowane lokaci za ku iya
ganin mahaifina sarki Galbasa domin shi kadai ne zai iya cim mani. Amma dai ckn
baradansa babu wanda zai iya suwa nan ya riske mu.
Ai kuwa bata gama rufe bakinta ba sai suka ga Galbasa biye da su.Aikuwa mazalish
bata gama rufe bakinta ba sai suka ga sarki Galbasa biye da su cikin tsananin gudu
tamkar an harbo kibiya.
Jikinsu jafar na karkarwa suka shiga saita shi da kibiyar.
Amma da sun saita shi sai ya bace ko kuma ya zama haske.
Shi kuma sai ya dunga harbo musu kibiyoyin tsafi da wutar tsafi ba dan mazalish na
zilliya da gocewa ba da tuni sun hallaka gaba dayansu.
Kai in da a ce mutum na ganin wannan artabu sai ka yi zatan kare ne ya biyo kyanwa
a tsiyace tana neman tsira da rayuwarta.
Sai da aka shafe sa'a biyar cur ana wannan gumurzu Sarki Galbasa bai cin musu ba
suma ba su sami damar harbinsa da kibiya ba.
Ba zato ba tsammani sai wutar tsafin Galbasa ta fara Qona su Jafar.
Yayin sa ya zamana babu wanda bai kone ba daga cikin su.
Yayin da mazalish ta tabbatar da cewa in dai aka cgb da wannan gumurzu a haka
Galbasa zai samu nasarar hallakasu sai ta juyo cikin shammace da zafin nama ta kama
bakin kunamar harba kibiyoyin nan da hannunta ta saita mahaifinta ta sakar masa
harbi a tsakiyar Qirjinsa.
Nan take kibiyar ta huda Qirjinsa ta bullo gadan bayansa sai suka ji ya kurma uban
ihu, sannan ya yi Qasa luuuuuu..............
Tun suna hango shi har ya bace musu da gani dama a wannan lokacin mazalish ta tsaya
cak a sararin samaniya.
Nan take idanunta suka ciko da Qwalla ta fara zubar da hawaye kafin waninsu yace
wani abu ta she da kuka tana mai nadamar abinda ta aikata a wannan lokacin ne suka
ga sarki azbir ya fashe da kuka jafar ya dafa kafadarsa yace " ya kai wannan sarki
ina dalilin kukan ka ?
Azbir yayi ajiyar zuciya sannan yace " ba komai ne ya sani kuka ba face sanin cewa
a halin yanzu gaba dayan mutanen Qasa ta sun zama mayu domin a tabbata babu wanda
zai tsira daga sharrin mutanen Galbasa ni kam na san bani ba komawa Qasata har
abada shi kenan na rasa iyalina dangina mutanena da mulkina da Qasata
Yayin da Azbir ya zo nan a zancen sa sai tausayi ya kama su jafar gaba daya ita
kuwa mazalish sai da taci kukanta ta koshi sannan ta ci gaba da tafiya a sararin
samaniya, tana dauke da su jafar a gadan bayanta.
Bata gushe tana tafiya ba sai bayan sun shude sa'a bakwai,
sannan ta sauko Qasa suka dire a tsakiyar wani irin jeji mai ababan al'ajabi kala-
kala.
Bayan su jafar sun sauka daga kanta sai ta girgiza ta dawo cikakkiyar siffa irinta
mutane sosai.
Mazalish ta dubi su jafar har yanzu hawaye na zuba a idanunta tace " yanzu na dawo
cikin ainihin halittata siffar da kuka ganni da ita dazu ba komai ba ce face sirrin
tsafi."
yayin da mzalish ta zo nan a zancenta sai jafar ya dubeta yace" yake yar.uwa ya
akai kika zama mutum kamar mu alhalin kin kasance jinsin mayu ?"
nan take mazalish ta basu lbrn yadda aka yi mahaifinta ya cire mata maita da kuma
yadda ya raba rabin karfin damtsensa da rabin tsafinsa.
Jafar ya sake dubanta ya to mene ne dalilin da yasa kika ceci rayuwarmu har kika
harbi mahaifin ki da hannunki ?"
Zidane kd
Nan take jafar ya kwashe labarin su kaf tun daga farko har Qarshe ya sanar da
mazalish.
Bayan ya gama ne ta cika da tsananin mamaki kuma ta dauki alkawarin tafiya tare da
su har a gama karanta shafukan kundin tsatsuba dan ta hadu da masoyinta Hubairu bin
mas'ud wanda ba ta taba ganinsa ba sai a mudubin tsafi.
Bayan jafar ya gama baiwa mazalish labarinsu sai suka mike gaba daya suka nausa ckn
wannan jeji suka yi ta tafiya ba tare da sanin inda suka dosa ba.
Kwatsam sai suka ga wata rijiya dama kishirwa suke ji.
Ita dai wannan rijiya tsohuwa ce ainun kuma an rufe ta da Qatan murfi karfe a
bakinta an yi rubutu kamar haka" babu mai bude wannan rijiya yasha ruwan cikinta
sai bakin da suka zo daga wata duniyar."
koda gama krnt wannan jawabi sai Jafar ya dubi Yelisa da Gulzum yayi murmushi
yace"ai domin mu aka yi rijiyar nan. Yakai gulzum maza ka bude mana mu sha ruwa ko
ma huta da kishirwa."
cikin fushi gulzum yace waye bawanka har da za ka bani umarni?
Koda jin haka sai yelisa tace...ba zato ba tsammani kuma sai ga sarki lu'umanu bisa
dardumar tsafi ta sauke shi daf da jarumi hubairu suka fuskanci juna sai ya murtuke
fuska yace" ya kai babban makiyina kayi sani cewa babu inda zaka shiga a ckn duniya
nan ka boye mini, ka tuna cewa munyi gagarumin fada ni da kai har sau 2 ko kuma
nace sau uku munyi kare jini biri jini, ina tabbatar maka da cewa wannan karan na
zo da cikakken shirin irin wanda bantaba yi ba don haka dolee ne naga bayanka.
Tabbas yau sai nayi gunduwa-gunduwa da sassan jikinka.
Ita kuwa masoyiyar taka dole na mallaketa ko tana so ko bata so.
Jarumi hubairu ya dakawa lu'umanu tsawa yace" kai tsohon makiyin ALLAH babban
mushiriki ma.abocin fasikanci domin ina tare da ubangijin musulunci addinin gsky.
Duk wanda ya rukeshi yafi karfin masu yin waninsa da izinin allah zan samu rinjaye
akanka kuma da sannu zamu Qarar da ire-irenku a doran kasa mu kawar da kafirci mu
shimfida musulunci ya baibaye duniya gaba daya.
Koda jin wannan batu sai sarki lu.umanu ya...
kafin su jarumi hubairu suyi wani yunkuri tuni sarki lu'umanu dun bace kuma sun
bacene tare da gimbiya sima.
Cikin hanzari jarumi hubairu ya krnt wata addu'a sai wannan duhu ya yaye haske ya
baibaye tamkar ba'a taba yin duhuba.
Koda hubairu yaga babu su lu'umanu kuma babu gimbiya sima sai hankalinsa ya tashi
ckn sauri ya bada umarni abi sawun su.
Ai kamar an harba kibiyoyi dakarun musuluncin suka harba jukkunansu suka luluka ckn
gajimare suna masu tsananin gudu ckn sahu sahu abin gwanin ban sha'awa kaikace
tsuntsaye ne ke bikin gsar gwada tsere,
wannan shine abina ya faru tsakanin su jarumi hubairu da su sarki lu'umanu yayin da
aka fafata bakin gumurzu a gdn bokanya samaratu don daukar gimbiya sima.
* * *
tun sa'adda aljani durfus ya tafi ya barsu a ckn kejin tsafi bisa sharadin cewa
idan sun amince ya zama shugabansu zai dawo ya kubutar dasu.
Sai suka kasance ckn halin damuwa da shawarwari. Markahus sabus ya dubi ummansa
bokanya samaratu yace yake ummina tun dazu boka jinshan da boka sulbaini sunata
fadin albarkacin bakinsu bisa shawarar da ya kamata mu yanke akan sharadin da
aljani durfus ya gindaya mana. Amma ke kinyi shiru ba kice komai ba ko kina da
dalili?
Samaratu tayi murmushi tace" yakai dana kayi sani cewa shifa aljani durfus bawa ne
ga boka sulbaini don haka ya fi saninsa shi ya kamata ya bamu shawara abin da ya
dace muyi.
Koda jin haka sai sulbaini yayi farat yace haba samaratu ai in ki ka fadi haka baki
yi mini adalci ba. Ki tuna fa cewa wannan durfus din na ynz ba shine na da ba wanda
na sani ma.ana ina nufin cewa a halin ynz aljani durfus ya taka matsayin da ban
sani ba. NI ina ganin kawai mu amince da zama bayinsa in yaso bayan ya kubutar damu
sai muyi masa tawaye ta hanyar yaudararsa har mu kai ga samun nasara akan shamharu.
Yayin da sulbaini yazo nan a zancen sa sai boka jinshan ya tuntsire da dry yace wai
shin kai ina ka kai tunaninka ne ka ajiye...yayin da sulbaini ya zo nan a zancensa
sai boka jinshan ya tuntsire da dariya yace" wai shin kai ina ka kai tunaninka ne
ka ajiye shi har ka manta dashi.
Tsaya na gaya muku gsky na gaba yayi gaba na baya sai lbr.
Ai dama wanda duk ya rigaka barci dole ya rigaka tashi idan har muna so mu sami
nasara akan shamharu dole ne muma mubi irin hanyar da yabi ta neman zama
matsatsubi.
"Ta yaya zamu zama matsatsubai kai ma ka zo da zancen banza abinda ba zai yiwu ba."
markahus sabus ne yayi wannan furuci.
Jinshan ya ce" to shi shamharu ya aka yi ya shahara har ma yake bin hanyar zama
matsatsubin? Duk abin da yayi ya shahara muma shi zamu yi domin ance sannu ba ta
hana zuwa sai dai a dade ba.a jeba.
Koda jin haka sai samaratu ta sake tuntsirewa da dariya a karo na biyu tace"hakika
na fuskanci kuna neman zautuwa shin kun manta ne cewa shi shamharu aljanine ba
mutum kamar ku ba. Ku tuna fa sai da shafe daruruwan shekaru yana tara ilmun tsafi
sannan ya shahara.
A cikinku nan waye zai iya dadewa,,,,,pls matsala page.
A can fadar sarki dujalu kuwa bayan kuyanga ta kawo shayi an zubawa kowa ya sha.
Sai ruziyal da boka harjrul makurus suka yi gyatsa tamkar wadanda suka ci nama suka
koshi.
Hajarul makarus ya dubi sarki dujalu yace yaka wannan sarki mai tarin hikima ka
sani cewa hakika ynz ma mun sake jagije gajiyar jikinmu.
Kuma babu yunwa ko kishirwa a tare da mu ko kadan don haka sai ka fara bamu lbrn
hikaya ta uku muji abin al'ajabi dake cikinta.
Sarki dujalu yayi murmushi sannan ya dubi tsoho rafkanagu ya girgiza kai cikin
alamun gamsuwa yace ranka ya dade ai kamar yadda suka ji a jikinsu nima haka na
kasance.
Dujalu yayi gyaran murya sannan yace to ku kimtsa kai mai rubutu ka za alkalamin ka
akan tkrd domin hikayar da zan baku na dauke da matukatr abubuwan tausayi da
jarumta da kuma al'ajabi.
Ni kaina ko tunowa nayi da lbrn sai nayi kuka.
Hikayar ce ta wani saurayi kuma jarumi wanda ake kira Nazmir bin halufa. Da gimbiya
luzaiya yar sarki fahalul bahafus.
A wani zamani can mai tsawo da ya wuce anyi wata babbar kasa wadda ake kira
duhamul.
Wannan kasa ta bunkasa da girma da kuma arziki da karfin mayaka.
Abisa wannan dalili ne kasar dahamul ta shahara kuma ta zama gagara badau a ckn
dukkan kasashen da ke kewayenta.
Ya zamana ana matukar tsoranta.
Sarkin da yake mulki a wannan kasa ta dahamul wani azzalumin sarki ne na kiransa
bashkur ba tsoho bane kuma ba za.a kirawo shi yaro ba.
Domin shekarunsa ba zasu gaza arba'in da hudu ba.
Sbd zalunci irin na bashkur ko a ckn garin nasa in dai mutum bai shafi jinin
sarauta ba ko kuma bai zamo daya daga ckn attajirai ba to yana ckn tashin hankali
domin ba ka yancin kan ka dukiyarka da matanka za su iya zama na kasa a koda
yaushe.
Haka kuma ana dorawa talakawa haraji mai yawa ta yadda ko kadan basa morar arzikin
su.
Baya ga wannan idan sarki bashkur ya huri iska sai ya tura mayaka izuwa wata kasar
ya basu izinin murkushe kasar a kamo masa bayi kuma a debo dukiya mai yawa.
Bisa wannan halaiya ne ya tara dukiya mai tsananinA ranar da Nazmir ya cika shekaru
20 cif a duniya sai halufa ya shirya masa walima.
A wannan rana zawisa tasha dawainiyar girke-girke.
Gaba daya yayan sarakan garin sai da suka halarci wannan walima.
Kai daga wasu kasashen ma haka yayan sarakai suka yi ta shigowa ckn birnin dahamul
duk da cewa kuwa da yawansu ba gayyatarsu aka yi ba.
Kawai sunzo ne don du ga jarumin da lbrn sa ya cika duniya Nazmir bin halufa.
Yayin da taro yayi taro sai jarumi Nazmir tare da abokanansa suka yi ta gaisawa da
baki ana bashi kyaututtuka ya wakilta su huzaik suka cgb da karba.
Nan take aka shigo da kayan ciye-ciye da shaye-shaye.
Makada da mawaka kuwa suka hau aikinsu.
Nazmir ya koma inda iyayensa ke zaune ckn farin ck suma abokansa suka koma gefe
guda ana kallon masu yin rawa.
Anan cikin wannan shagali ne aka hangi sarkin dogarai ya shigo wajen kai tsaye rike
da takarda a hannunsa.
Nan take wuri yayi tsit kowa ya kame tamkar babu mai numfashi a wurin kai kace
mutuwa ce ta giftayayin da nazmir ya gama karanta wannan wasika sai ransa ya
harzuka.
Har ya yunkura zai yayyaga tkrdr sai halufa yayi masa wani irin kallo.
Nazmir ya ajiye tkrdr a gefe guda shi kuwa halufa sai ya dubi sarkin dogarai yace
kaje ka sanar da majalisa cewa sako ya zo mini kuma gobe da safe zan hallara a
fada.
Sarkin dogarai yayi gdy ya fita ckn farin ciki.
Shi kuwa halufa sai ya bayar da izinin a cgb da walima.
Take wuri ya sake hautsinewa da hayaniyar kade-kade da raye-raye ba.a gama walimar
ba sai da duhu ya fara sannan baki suka fara yin sallama suna bankwana daya bayan
daya.
A haka dai wuri ya dade aka bar su halufa kadai.
Nan take halufa ya koma kan kujera ya zauna sannan ya umarci su nazmir da su zauna.
Dama zuwaisa na can gefe daya azaune. Halufa ya dubi Nazmir yace ya kai dana hakika
na fuskanci zuciyarka ta sosu sa'adda sako yazo mini daga majalisa. Lallai ina son
ka yayyafawa zuciyarka ruwan sanyi.
Yayin da Nazmir yaji wannan batu sai yace ya abbana ai dole ne ta sosu ban ga
dalilin da zai sa majalisa ta bukace ka ba ynz. Alhalin ta wulakantaka a lokacin da
kake ganiyar sharafinka wace gwaninta zaka iya yi mata a halin ynz da tsufa ya
riske ka wacece ba ka yi kamarta ba abaya.
Halufa yayi ajiyar zuciya yace yakai dana hakika kayi tunani mai kyau nima kuma
jikina ya bani cewa lallai akwai babbar bukata da ta tasowa sarki wadda dole sai da
taimakona za ta biya shi yasa aka neme ni.
Huzaik yayi murmushi yace abba ni kam ina ganin babu wata bukata kawai ana so a
yaudare ka ne a tura ka wani wurin inda zaka hallaka don bayar da sarautar ga wani.
Halufa yayi murmushi yace a'a ina ganin ba haka bane koma dai mene ne nayi mku
izini gobe da safe ku zo ku duka kuyi mini rakiya zuwa fadar domin ku gani kuma ku
ji komai da kunnanku.
Washe gari fadar sarki bashkur ta cika makil da jama.ar gari domin tuni lbr ya bazu
cewa yau ne sarkin yaki jarumi halufa zai dawo kan kujerarsa ta fada.
Sarki bashkur na zaune fadawa sun kewaye shi yana mai tunkaho da karfiHuzaik ya
risina yace "ya sarkin sarakai ina son na roki waya alfarma da yawun abokan Nazmir.
Sarki bashkur yayi murmushi yace fadi bukatarku naji.
"muna son idan zaka tura nazmir tfy biyan bukatarka ayi mana izini muyi masa
rakiya.
Koda jin haka sai sarki bashkur ya kyalkyale da dariya yace an yi muku izinin.
Ynz na sallame ku amma ku dawo nan fada gobe war haka cikin shirin barin kasarnan
don aiwatar da bukatata.
Da wannan furuci ne aka sallami kowa fada ta watse.Daga wannan rana su Nazmir suka
kama hanya suka yi tafiya suna ratsawa ta ckn dazuzzuka gari-gari kasa-kasa.
Duk da inda suka iske yan fashi ko namun daji sai sun tarwatsa su sun kashe na
kashewa amma duk inda suka riski gari basa yiwa mutane komai kuma basa taba
dukiyarsu sai dai tambayi hanyar zuwa birnin mahazus a nuna musu.
Tafiya kwanci tashi harr suka shafe wata bakwai da kwana tara kwatsam suka hango
ganuwar birnin mahazus acan gaba nesa da su nan yake farin ck ya lullubesu.
Kawai sai shugaban tawaga jarumi Nazmir ya bada umarnin a sauka nan fa aka sassauko
aka kafa tantina kowa ya bude guzurinsa aka ci aka sha aka shiga hutawa.
Acan ckn birnin mahazus kuwa tunani lbr ya riski sarki fahalul bahafus cewa ga wata
tawaga can ta rundunar mayaka ta sauka a bayan gari ba'asan da wacce suka zoba.
Cikin kwanciyar hankali da takama sarki fahalul bahafus ya subi bafadensa mai suna
jambu yace maza kayi hawa ka tafi ga wannan runduna ka tmbye su abinda ke tafe
dasu.
Jambu ya risina....
Kowa ya kama gabansa tunda su nazmir suka dawo gd ya kasance cikin tsananin damuwa
har ma ya rufe su huzaik da fada yana mai cewa don me zai jefa kan su cikin wannna
masifa.
Ya sani cewa aikin da za.a tura shi ba karamin bala'i bane duk da cewar bai san
mene ne ba duk zasu iya hallaka.
Koda jin wannan batu sai huzaik,sharhil,
bagwan,husuf,iklam,da bardil suka hada hannayensu waje suka bude baki lkc guda suka
ce mun kasance abokan juna tun kuruciya mun shaku da junanmu kuma bama rabuwa koai
ruwa komai iska ya kai nazmir gamu mu shida da kai ne cikon na bakwai shin kana
tare damu ko kuwa zaka ware daga cikin mu ne?
Yayin da nazmir yaji wannan jawabi daga bakin abokansa sai zuciyarsa ta karaya
idanunsa akan nasu yace ina tare da ku har abada zumuncinmu da soyayarmu ga juna ta
ratsa jini da tsoka.
Take suka rungume juna gaba daya ckn kukan farin ciki.
A wannan rana su Nazmir suka gama kimtsa kayansu don yin tafiyar da basu san inda
zasu je ba bayan sun tanadi dawakai da guzuri gami da kayan yaki sai suka dunguma
suka tf gidan su huzaik don yin sallama da mahaifinsa tsoho marnush.
Da shigarsu inda yake sai suka iske shi a zaune yana sharbar kuka gaba dayansu sai
hankalinsu ya tashi suka durkusa a gabansa huzaik ya kama hannayensa ya rike yana
mai zubda hawaye yace yakai abbana ina dalilin wannan kuka naka?
Tsoho marnush yace yakai dana kayi sani cewa kai kadai nake dashi a duniya gashi
har tsufa ya riskeni banga auren kaba.
Yau dare daya lbr ya zo mini cewa zaku yi tfy mai hadari.Koda jin haka sai luzaiya
tayi murmushi tace ai koma dame suka zo daidai muke dasu ya kai abbana ni kam nasan
cewa a halin ynz yadda kake da tarin gwarazan mayaka babu wata runduna da zata iya
cin mu da yaki.
Sarki ya kyalkyale da dariya yace tabbas haka zancenki yake yata domin inda na
kasance azzalumi da tuni yanzu na mallaki duk kasashen dake makwabtaka damu.
Sarki na gama fadin haka kenan sai ga jambu ya dawo dauke da wasika sai ya mika
tkrdr ga sarki shi kuma ya baiwa magatakarda ya umarceshi daya karanta.
Take magatakarda ta warware ya fara bayani kamar haka...
Daga jarumi Nazmir bin halufa zuwa ga sarki fahalul bahafus na biirnin mahazus.
Gaisuwa tare da biyayyaka a gareka yakai wannan sarki.
Kayi sani cewa ni manzone daga sarki bashkur na birnin duhamul kuma bai turoni gare
ka dan komai ba sai don na yanke kanka na kai masa kuma na tafi da kyakykyawar
yarka gimbiya luzaiya don ta zama sa dakarsa ina mai shawartarka da kasa a yanko
mini kan naka a hado tare da yarka a kawo mini domin tsirar da rayukan jama.arka na
tafi salin alin idan kuma kaki bin wannan umarni ni da baradena zamu shigo cikin
birninka da karfin tsiya mu cika umarnin sarkinmu.
Tun sa'adda jama'a suka ji ma.anar wannan wasika fadar ta yamutse da surutu da kuma
al'ajabi sai da sarki fahalul bahafus ya rinka daka tsawa sannan magatakarda ya
sami damar kammala karantawa yana gamawa ne sarki ya bushe da mahaukaciyar dariya.
Itama gimbiya Luzaiya tare da sauran manyan fadawa suka yi tsit.
Luzaiya ta dubi mahaifinta tace ashe mahaukata marasa lissafi da tunani basa karewa
a ckn duniyarnan.
Ynz in banda batan basira yaushe wasu mutane zasu yi tunanin cewa zasu iya shigowa
har cikin garin nan suyi mana wannan wulakanci.
Sarki fahalul bahafus yai gyaran murya yace yake yata ai kinsan shi makiyi har
abada baya fitar da ran samun nasara akan makiyinsa ki sani cewa fiye da shukaru 20
baya sarki bashkur yayi iya yinsa akan yaga bayana amma abu ya faskara...
Umar Faruq Madabo sarari.Sai yanzu kuma yake ganin yayi cikakken shiri da zai iya
samun nasara akaina bai san cewa jiya ba yau bace nima nawa shirin ya linka nasa.
Sarki fahalul bahafus ya dubi jambu yace mene ne adadin wadannan dakaru ?
Jambu yace ya sarkin sarakai ai gaba dayansu ba zasu wuce dubu goma da doriya ba
domin shi shugaban tawagar matashine ba zai fi shekara 20 ba shine jarumi nazmir
din sai kuma wadansu mutum shida wadanda su kadaine suke da kirar jarumta ma a
cikin dakarun.
Koda jin wannan batu sai sarki ya bushe da dariya yace maza a rbt tkrdr raddi
akaiwa wannan mara kunyanr jarumi kuma a shirya mayaka dubu dari suje su maishe da
su abincin tsutsa. Nan da nan kuwa aka cika umarni daga nan fada ta watse....Kashe
gari tun kafin su jarumi Nazmir su aiwatar da nufinsu suka ga an bude kofar birnin
mahazus sai ga rundunar mayaka ta fara fitowa suna jeruwa sahu-sahu.
Koda suka gama jeruwa su nazmir suka ga yawansu sai zuciyoyinsu suka karaya.
Huzaik ya matso kusa da jarumi nazmir yace kai anya kuwa mayi wannan yaki? dubi
yawan dakarun nan fa na rantse da darajar mahaifina sun linkamu sau 10.
Nazmir ya dubi huzaik ya daka masa tsawa yace ka zamo namiji mai kwarin zuciya ai
faduwar gaba asarar namiji ce. In dai muka daure zamu iya gamawa dasu a ckn sa.a
biyar.
Kafin wani ya kara cewa wani abu tuni jarumi nazmir yayi kukan kura ya sakarwa
dokinsa linzami.
Dokin kuwa sai ya nufi tawagar dakarun sarki fahalul bahafus a sukwane ckn mugun
gudu.
Koda ganin haka sai huzaik, sharhil, bagwan,husuf,iklam da bardil suma suka sakarwa
nasu dawakan linzami suka bi bayansa suna masu kokarin su riske shi kafin ya karasa
ckn abokan gaba don kasa su yi masa sarkin yawa su halaka shi amma tuni jarumi
nazmir ya basu rata mai yawa.
Kafin kace me tuni ya kutsa ckn baradan sarki fahalul bahafus ya hausu da sara ba
sassauci su kuwa suka yanyame shi kmr an sa kyanwa a tsakiyar karnuka.
Sai dai wannan kyanwar ta zamewa karnukan alakakai domin sun gaza cin mata duk inda
jarumi nazmir ya kai sara sai ka ga kawuna na zubewa kuma duk inda ya durfafa dole
a dare hanya ta samu a gare shi bisa dole.
Kafin su huzaik su karaso tuni nazmir yayiwa rundunar mummunan barna.
Ai kuwa sa.adda su huzaik suka karaso sai wuri ya kara hautsinewa mummuna yaki ya
rincabe banda karajin mazaje da na karafa babu abinda mutm ke ji.
Kafin dakaru nan guda dubu10 masu taimakawa su nazmir su iso tuni an gama da
dakarun sarki fahalul bahafus gaba dayansu. Sun zama gawa.
Ana gamawa dasu ne aka ga huzaik ya dafe kirjinsa yana sunkuyawa kasa. Cikin
yanayin jiri kafin wani ya karasa gare shi tuni ya fada kasa koda ganin haka sai
nazmir ya kwarara uban ihu mai firgitarwa ya ruga inda yake...Koda ganin haka sai
jarumi nazmir ya kwala ihu mai firgitarwa ya ruga inda yake ya tashe shi zaune ya
dora shi akan cinyarsa sai ga jini na bulbula daga cikin kirjin huzaik.
Cikin dimaucewa nazmir ya yaga rigar huzaik yana mai cewa abokina tashi muje ckn
tantina in sa maka magani. Lallai zaka sami lfy.
A wannan lokacine su sharhil suka karaso gabansu ckn tsananin tashin hankali da
matukar damuwa.
Ckn karfin hali huzaik ya rike hannun nazmir idanunsa na lumshewa hannunsa na
karkarwa yace ya kai abokina ka gafarce ni bazan iya tashi ba kuma ka da ka bata
lokacinka akan yi mini mgni.
Tabbas tawa ta kare mutuwa zan yi ku yi hkrnrashina idan ka samu ikon komawa gida
ka danar mahaifina cewa ga yadda tawa ta kasnce ya rungumi kaddarar rashin cika
alkawarina na zuwa masa da sirikarsa. Lallai ka yi mini wannan aiki amanace na
baka.
Koda jin haka sai nazmir ya fashe da kuka yana cewa huzaik na karbi amanarka kuma
tabbas zan dankata ga mahaifinka.
Rufe bkinsa ke da wuya idanun huzaik suka kafe ko'ina jikinsa ya daina motsi kawai
sai suma su sharhil suka durkusa gaban gawar suka fashe da kuka wannan shine abinda
ya faru tsakanin dakarun sarki fahalul bahafus sa su jarumi nazmir.
Sarki fahalul bahafus na tare da matarsa munaiya wato mahaifiyar gimbiya luzaiya
suna hira ckn nishadi sai ga gimbiya luzaiya ta fado cikin yanayin tashin hankali
koda ganin haka sai sarki ya mike zumbur ya tare ta yana mai cewa yake rabin jikina
me ya fr kika zo gare mu a ckn siffar mara dadin gani haka?
Luzaiya tayi ajiyar zuciya tace yakai abbana ga daya dg ckn masu tsaran kofar gati
yazo da mummunan lbr cewa dakarunka daka tura guda dubu 100 don su yaki makiyanmu
mutum bakwai kacal sun gama dasu.
Cikin firgici fahalul bahafus ya saki luzaiya ya ja da baya kadan yace wace irin
mgnr banza kike fada mini haka? Ya za.a yi mutum 7 su kasge mutum dubu 100 a ckn
kankanin lokaci ai kuwa koda mutm bakwan aljanune su aikin yafi karfinsu.
.....A wannan yaki ne sarki fahalul bahafus tare da yan majalisar suka zo kan
ganuwa suka tsaya suna ganin abinda e faruwa a filin yakin.
Sai da aka kwana uku ana fafatawa ya zamana an yi fata-fata da mutanen sarki
fahalul bahafus alokacin ne fahalul bahafus ya hango fuskar Jarumi Nazmir kawai sai
ya tuna da fuskar mahaifinsa. Wato sadauki Halufa nan take ya tuna lkcn da halufa
ya kubutar da shi daga kurkuku sai hankalinsa ya dugunzuma gumi ya tsatstsafo masa.
Ba zato ba tsammani sai aka ga fahalul bahafus ya sauko daga kan ganuwa aguje ya
hau dokinsa ya nufin bakin kofar gari.
Da zuwa sai ya dakawa masu tsaron tsawa yace su bude masa kofar.
Jikinsu na rawa suka bude masa kofar ya sukwani dokinsa ya nufi inda jarumi nazmir
ke gumurzu alokacin sauran yan tsirarun barade a fili. Koda aka hango tahowar sarki
bahalul fahafus bisa kan doki sai kowa ya tsaya da yakin aka zuba masa idanu ckn
mamaki yayin da sarki bahalul fahafus yazo gaban jarumi Nazmir sai yaja da tunga ya
sauko daga kan dokin
Kashe gari tun kafin alfijir ya keto suka fara jin haniniyar dawaki a can kofar
gari.
Ckn hanzari su Nazmir suka mike suka hau dawakansu ckn shirin yaki suka nufi kofar
garin.
Da zuwa kuwa suka iske gaba daya an kwashe gawarwakin dakarun jiya.
Tsaitsaiye akan dawakai dakrun dubu dari uku ne ckn mugun shirin yaki shi kansa
Nazmir sai da zuciyarsa ta buga ya dubi abokansa guda 6 sannan ya dubi dakarun nan
mataimaka su dubu 10.
"yau fa abin nayi ne. Maza mu afka musu mu ga abinda hali zaiyi daga nan zuwa
magriba.
Ai kuwa nan take kowa ya saki linzamin dokinsa kura ta tashi dawakai suka yi kaimi
kai ka ce gasar tsere ake yi Suka nufi kofar birnin.
Koda mayakan Fahalul bahafus suka ga wadannan tsirarun dakaru sun taso musu sai
suma suka ruga gare su don su tare su kafin su iso ai kuwa sai aka gamu a tsakiya
gamuwar da kowa ta zamo mastiyaciya domin tafi karron batta turnuku da ko
rugumtsimi sai dai a kira ta annoba.
Tabbas a wannan rana Nazmir da abokansa sun nuna tsantsar jarumta.Cikin Fushi
Yelisa tace To naji ni matsoraciya ce tunda ke jaruma ce ai sai ki bude mana
rijiyar ko.
Wannan kuma aikin sarkin Qarfin ne Gulzum. Inji Jafar
Gulzum ya murtuke fuska duk da cewa an yabeshi Nan take yasa hannu daya da nufin
dauke murfin rijiyara amma sai ya kasa mamaki ya kama shi ya saka hannayensa biyu
ya takarkare iya karfinsa ya dago murfin amma sai ya kasa dago shi gaba daya nan fa
su Jafar suka cika da mamaki domin basu taba ganin aikin karfin da ya gagari Gulzum
ba sai yau tun sa'adda suka shigo ckn kundun tsatsuba.
Koda ganin abinda ya faru sai Mazalish tace Gulzum gafara nan ka bani wuri tunda ka
kasa budewa.
Gulzum yace to yar sarkin mayu ai sai ki jarraba karfin maitarki anan mu gani.
Mazalish ta daka masa tsawa tace kar ka sake kirana maiya tunda ni ba maiyya vace
kuma na baro maitar a can mahallinta.
Kawai sai Mazalish ta nuna murfin rijiyar nan da danyatsanta guda take wata
siririyar iska ta fito daga ckn danyatsan ta daga murfin rijiyar nan
sama......Cikin firgici su Jafar suka juya da baya suka runtuma da gudu suka bar
Mazalish nan tsaye gaban Ifritin ta kasa gudu don tsananin razana sai ihu take
faman yi kawai.
Ifritun nan ya sake takarkarewa ya wangame katon bakinsa sai da ya amayar da kusan
mutum dubu sannan hankalinsa ya dawo kan Mazalish wacce har yanzu tana nan tsaye a
gabansa tana ihu cikin zafin nama ya kawo mata wafta don ya dauke ta ita kuwa ta
goce ckn zafin nama sannan ta ruga da gudu ta nufi inda su jafar suka yi.
Ifiritun nan kuwa ya bita a guje suka kasa tsere idan tayi gudu tayi gudu ta waiga
bayanta sai taga ifrintun nan daf da ita yana jeho harshensa waje don ya lasota
kawai sai ta kara kwala ihu ta kara kaimin gudu haka dai ya cgb da binta har suka
riski su jafar koda su jafar suka waiga suka ga katon ifritun ya kusa cimma
mazalish sai suka kara kaimin gudunsu kawai sai wasu fukafukai guda biyu suka fitar
da kansu a jkn ifritun nan ya tashi sama ya riski mazalish ya lasota da harshensa
sannan ya hadiyeta.
Daga nan yabi su jafar daya bayab daya duk ya hadiye su.
A gaban kundun tsatsuba su jafar suka tsinci kansu.
Har yanzu jini na zuba a jikinsu sakamakon raunukan nan da yan mini-mini aljanu
sukai musu.
Kuma shafi na goma sha hudu ne a bude jkn littafin kundin tsatsuba nan take su
jafar suka yanke jiki suka fadi kasa sumammu.
Sai bayan sa'a guda sannan kowannansu ya dawo ckn haiyacinsa.
Yelisa ce ta fara mikewa zaune ta dubi kowa tace tab dijam amma fa wannan karon mun
sha bakar wuya.
Mashrila tayi tsaki tace ai in dama wahalarce zalla babu tashin hankali ai da
sauki.
Shi kuwa jafar sai ya dubi mazalish yace wai ke ina karfin tsafin naki ya tafi me
yasa baki cece mu dg wannan ifritun ba.
Mazalish tayi murmshi tace lallai ynz na tabbatr da cewa kai yaro ne ai idan kaji
ana cewa Ki gudu sa gudu bai zo ba.
Jafar yace wai ina ruwan filfiluwa ai ban san cewa Gulzum na da gudu ba sai sadda
ifritun nan ya biyo mu kafn na waiga bayana tuni Gulzum ya wuce mu..
Lokacin da su Jafar suka fada cikin shafi na goma sha shida a kundin tsatsuba wato
bayan iskar cikin kundin ta zuke su sai suka tsinci kansu a cikin sararin samaniyar
wata sabuwar duniyar kuma a kudundune cikin wata irin gugarumar guguwa sai da ya
zamana cewa ta tale hannayensu da kafafunsu gashin kansu ya tsefe sama kamar taron
tsintsiya.
Idanuwansu suka gwale kofofin hancinsu da bakunansu suka kara girma Ban da ihun
azaba babu abinda suke yi.
Kwatsam sai suka ga wata surar fuskar bil'adama a samansu wacce ta saje da kalar
gajimare bakin surar ya wangame yana mai kyakyata musu dariya. Al'amarin da ya kara
jefa su ckn razana kenan Mazalish ta fara kokarin hade hannayenta biyu waje guda
don yin tsafi amma sai abu ya gagara domin ta kasa hade hannayen nata.
Fuskar ta sake wangame baki a karo na biyu ta barke da mahaukaciyar dariya mai
tsananin firgitarwa sannan tace.
" Nice guguwar masifa kuma nice guguwar bala'i duk wanda ya ziyarce ni sai na
kaishi mahallaka dubu kaicon ku da kuka zama daga cikin rafkanannu......
👍👍😀😀💁
Last post
#mbrmatrixhttp://zamaniweb.com/administrator/files/19/05/56/kundin_tsatsua_matsatsu
bi_miftahul_zarbil_n.jpg

An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na


www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na
yake yake dana soyayya

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu
kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama
sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana
magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490

A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci,
duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna
neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman
munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai
fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai
wayarku

This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng


You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to
download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography
including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490
its free we do not charge for our services

Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted
biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not
blame us

Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we
are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day,
any time you can visits our site and download it

Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF
or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT

You might also like