You are on page 1of 42

MATSAYIN AURE A MUSULUNCI (A TAKAICE) – NA DANDABARA

MATSAYIN AURE
A
MUSULUNCI =

NA
MUHAMMAD M. MUSA (DANDABARA)
Ya gabatar a lokacin Seminar da Kungiyar Jama’atu
Izalatil Bid’ah Wa Ikamatis Sunnah (JIBWIS)
ta shirya a garin Pupule daga ran
11 – November, 2020 zuwa 15th – November, 2020
th

Contacts:
1. dandabaraislam78@gmail.com
2. 08031934282 / 09078771442

ABU MARYAM, MUHAMMAD M. MUSA (DANDABARA)08031934282 1


‫‪MATSAYIN AURE A MUSULUNCI (A TAKAICE) – NA DANDABARA‬‬

‫املقدمة‬
‫إن الحمد هلل نحمده ونستعينه ونستغفره‪ ،‬ونعوذ باهلل من شرور أنفسنا‬
‫ومن س يئات أعمالن ا‪ ،‬من يه ده هللا فال مض ل ل ه‪ ،‬ومن يض لل فال ه ادي ل ه‪،‬‬
‫ً‬
‫وأشهد أن ال إله إال هللا وحده ال شريك له وأشهد أن محمدا عبده ورسوله‪.‬‬
‫َ‬ ‫َأ ْ ُ‬ ‫َ ُ‬ ‫َُ‬ ‫َّ‬ ‫ُ َّ ُ‬ ‫َ{ياَأ ُّي َها َّالذ َ‬
‫ين َء َامنوا اتقوا الل َه َح َّق تقا ِت ِه َوال ت ُموت َّن ِإ ال َو نت ْم ُم ْس ِل ُمون}‬ ‫ِ‬
‫َّ‬ ‫َ‬ ‫ََ‬ ‫اس َّات ُق وا َر َّب ُك ُم َّالذي َخ َل َق ُك ْم م ْن َن ْف َ‬ ‫َ َأ ُّ َ َّ‬
‫اح َد ٍة َوخل َق ِم ْن َه ا ز ْو َج َه ا َو َبث‬ ‫سو ِ‬ ‫ٍ‬ ‫ِ‬ ‫ِ‬ ‫الن ُ‬ ‫{يا يه ا‬
‫َ َأل ْ َ َ َّ َّ َ َ َ‬ ‫َّ َ َّ َ َ َ ُ َ‬ ‫ْ ُ َ َ َ ً َ َ ً َ َّ ُ‬
‫ِمنهم ا ِرج اال ك ِث يرا و ِنس اء واتق وا الله ال ِذي تس اءلون ِب ِه وا رح ام ِإ ن الله ك ان‬
‫َ ُ‬
‫َعل ْيك ْم َر ِق ًيبا}‬
‫ْ‬ ‫َّ َ َ ُ ُ َ ْ َ ً ُ ْ َ ُ َأ َ ُ‬ ‫ُ َّ ُ‬ ‫َ{ياَأ ُّي َه ا َّالذ َ‬
‫ص ِل ْح لك ْم ْع َم الك ْم َو َيغ ِف ْر‬ ‫ين َء َامن وا اتق وا الله وقول وا ق وال س ِديدا ي‬ ‫ِ‬
‫َ‬ ‫ً‬ ‫ْ‬ ‫َ‬ ‫َ‬ ‫َ‬ ‫ْ‬ ‫َ‬ ‫َ‬ ‫ُ‬ ‫َ‬ ‫ُ‬ ‫َ‬
‫وبكم ومن ي ِطع الله ورسوله فقد فاز فوزا ع ِظ ً‬ ‫َ‬ ‫َ‬ ‫َّ‬ ‫ُ‬ ‫ْ‬ ‫َ‬ ‫َ‬ ‫ْ‬ ‫ُ‬ ‫َل ُك ْم ُذ ُن َ‬
‫يما}‬ ‫ِ‬
‫أما بعد‪،،،‬‬
‫ف إن أص دق الح ديث كت اب هللا‪ ،‬وأحس ن اله دي ه دي محم د ‪ -‬ص لى هللا علي ه‬
‫اللة‪ ،‬وك ل‬
‫وس لم ‪ ،-‬وش ر األم ور مح دثاتها‪ ،‬وك ل محدث ٍة بدع ٍة‪ ،‬وك ل بدع ٍة ض ٍ‬
‫ضاللة في النار‪ ،‬وبعد‪.‬‬
‫ٍ‬
‫‪Godiya ta tabbata ga Allah, muna gode masa, muna neman‬‬
‫‪taimakonsa, muna neman gafararsa, kuma muna rokon Allah ya tsare‬‬
‫‪mu daga sharrorin kawunanmu da munanan ayyukanmu. Wanda Allah‬‬
‫‪Shiryar babu mai ɓatar da shi, wanda kuma ya ɓatar babu mai Shiryar‬‬
‫‪dashi sai Shi kaɗai.‬‬
‫‪Na shaida babu abin bautawa da gaskiya bisa cancanta sai‬‬
‫‪Allah, ba shi da abokin tarayya, kuma na shaida lallai Annabi‬‬
‫‪Muhammad (SAW) bawansa ne kuma Manzonsa ne.‬‬
‫‪ABU MARYAM, MUHAMMAD M. MUSA (DANDABARA)08031934282‬‬ ‫‪2‬‬
MATSAYIN AURE A MUSULUNCI (A TAKAICE) – NA DANDABARA

ABUBUWAN DA LITTAFIN YA KUNSA:

1. Ma’anar Aure

2. Dalilan yin Aure

3. Fa’idodin yin Aure

4. Hikimomin yin Aure

5. Hukuncin yin Aure

6. Shekarun da za a kai kafin a yi Aure

7. Wa za a Aura? (Zaɓin Abokin zama)

8. Hakkokin Miji a kan Matarsa

9. Hakkokin Mace a kan Mijinta

10. Kammalawa

ABU MARYAM, MUHAMMAD M. MUSA (DANDABARA)08031934282 3


MATSAYIN AURE A MUSULUNCI (A TAKAICE) – NA DANDABARA

MA’ANAR AURE:
Aure a harshen Hausa shi ne abinda a Larabci ake kira An-Nikaahu ko
kuma Az-zawaaju. Kuma ma’anarsa a cikin harshen shi ne: Haɗuwa ko
Tarawa. A wani kauli kuwa shine shigar da wani abu cikin wani abu,
misali idan tsakuwa ta shiga kofaton doki sai a ce kofaton doki ya auri
tsakuwa. Wannan fasara ana bayar da shi a yare saboda a bayan aure
miji da mata suna haɗuwa ko saduwa ko tarawa da juna a cikinsa.
Amma a wurin Malaman shari’ar Musulunci, sun fasara aure da cewa
wani kulli ne a tsakanin namiji da mace wanda yake da manufar halatta
musu jin daɗi da junansu, kuma da manufar samar da inganttacen gida
mai kai wa ga samar da ingantaccen gari da al’umma.
Har ila yau, Aure shine haɗa wata irin alaka tsakanin mace da namiji,
wannan yana nufin haɗe rayuwarsu ta zama ɗaya haka nan kuma
makomarsu ta kasance guda ɗaya. Kowace irin al’umma akwai irin
matsayin da ta ba wa aure. Auri a Musulunci wani ɗauri ne da yake
halatta wa ma’aurata (Mace da Miji) jin daɗi da junansu ta hanyar
saduwa irin ta Jima’i da sauran Mu’amala. Allah (SWT) ya halicci mace
daga kashin hakarkarin namiji ya kuma sanya soyayya da tausayi a
tsakaninsu.
Wannan yana nuna mana cewa alaka tsakanin mace da namiji, Allah ne
ya kulla tun fil azal. Abin da kuwa Allah ya haɗa, wallahi babu wanda ya
isa ya raba shi, duk iya kokarinsa.
Wannan shi ya sa a ɗabi ’ance kowane namiji yana bukatar mace, haka
kowace mace tana bukatan namiji. Idan har hakan bai samu ba, to, lallai
tawaya ne a rayuwar ɗan Adam. Wato Kowane ɗaya ba zai iya
ABU MARYAM, MUHAMMAD M. MUSA (DANDABARA)08031934282 4
MATSAYIN AURE A MUSULUNCI (A TAKAICE) – NA DANDABARA

wadatuwa da kansa ba, ya rayu shi kaɗai, dole sai dai haɗe da
waninsa.
Kula da wanna fasara za mu fahimci cewa: Kulla aure a Musulunci yana
da manyan manufofi kamar haka:
i. Jin daɗin juna a tsakanin ma’aurata
ii. Samar da natsuwa tsakanin ma’aurata da kwanciyar hankali;
iii. Samun nagartattun ‘ya’ya domin samar da nagartattun al’umma
wajen kafa gida kyakkyawa
iv. Samun zaman lafiya mai ɗorewa
v. Soyayya da kauna da sauransu
A takaice mun fahimci aure yana nufin kulli da ake yi tsakanin namiji da
mace domin halattar da jin daɗi a tsakaninsu, da kiyaye cigaban zuriya
da tabbatar da jinsin ɗan Adam har zuwa cikar adadin da Allah ya
kaddara zuwan sa wannan duniya. Bayan ga haka shi aure Ibada ne da
Ubangiji ya sanya ma wasu daga cikin bayaninsa. Shi yasa;
 Akwai wadda aure ke wajibi a gare shi
 Akwai wadda aure ke Sunnah a gareshi,
 Akwai wadda aure ke Mustahabbi a gareshi,
 Akwai wadda Aure ke haramun a gareshi
HIKIMOMIN AURE A MUSULUNCI:
Ka da a manta waɗannan bayanai muna yin su ne a takaice, idan
muna bukatar karin bayani kuwa sai mu dubi wasu litattafai da zamu
bayar a karshen littafi domin samun bayani. Ga kaɗan daga cikin
Hikimomin Aure a Musulunci:

ABU MARYAM, MUHAMMAD M. MUSA (DANDABARA)08031934282 5


MATSAYIN AURE A MUSULUNCI (A TAKAICE) – NA DANDABARA

i. Yaɗuwa da ɗorewar jinsin ɗan Adam: Shi Allah Maɗaukakin


tsarki ya yi ɗan Adam a duniya domin ya ɗore ne zuwa
wa’adin da Allah ya sanya masa, don haka hanyar da za’a
samar da hakan shine ta hanyar aure. Domin Allah
Maɗaukakin tsarki yana cewa:
ّ َّ ّ ُ ّ
‫واحدة وخلق منها زوجها وبث منهما‬
ٍ ‫نفس‬
ٍ ‫يا أيها الناس اتقوا ربكم الذى خلقكم من‬
1 ‫ سورة الناسء‬.‫رجاال كثيرا ونساء‬

“Ya ku mutane! Ku ji tsoron Ubangijinku wanda ya halicce ku daga


rai guda ɗaya, ya kuma halitta muku mata, daga nan ya watsa muku
mazaje da mata masu yawa” Suratul Nisa’i aya ta 1
ً َ َ ُ َ ْ ‫َ َ َ َ ُ ّ ْ َأ ْ ُ ْ َأ ْ ً َ َ َ َ َ ُ ْ ّ ْ َأ‬
‫ سورة النحل‬.‫اجكم َب ِنين َو َحف َدة‬
ِ ‫وهللا جعل لكم ِمن ن ِس كم زواج ا وجع ل لكم ِمن زو‬
َ

72

“Allah ya sanya daga kayukanku mata, ya sanya muku daga


matanku ‘ya’ya da jikoki” Suratul Nahl 72
ii. Biyan bukatar sha’awa ta ɗabi’a: Shi ɗan Adam, Allah ya yi
shi yana da bukata na sha’awa musamman na wasu
abubuwa kamar yadda Allah ya faɗa a cikin Suratul Al Imrana
aya ta 14. Idan muka koma wannan ayan, zamu samu abinda
Allah ya fara ambatawa shine Sha’awar mace. Don haka ne
yana daga cikin hikimar aure domin bukatar sha’awa ta
ɗabi’a. Manzon Allah yana cewa:
ٌ ‫أياتي أحدنا شهوته ويكون له فيها‬
‫أجر؟ رواه مسلم‬

ABU MARYAM, MUHAMMAD M. MUSA (DANDABARA)08031934282 6


MATSAYIN AURE A MUSULUNCI (A TAKAICE) – NA DANDABARA

“Yanzu ɗayanmu zai zo ya biya sha’awarsa (lokacin jima’i) sannan


kuma ace yana da lada”? Muslim ne ya ruwaito
iii. Jin daɗin duniya: Shi ɗan Adam yana samu natsuwa da jin
daɗin duniya ne idan akwai mace kusa dashi, shiyasa a
lokacin da Allah ya sanya Annabi Adamu cikin aljanna bai
samu cikakken natsuwa ba duk da abubuwan da aka tanada
masa cikin aljanna na more rayuwa, bai samu natsuwa ba
sanda aka halitta masa nana Hauwa’u daga kashin
hakarkarinsa na hagu, wanda ya fi lankwasa. Annabi (SAW)
yana cewa:
‫ رواه مسلم‬.‫الدنيا متاع وخير متاعها املرأة الصالحة‬

“Duniya jin daɗin ce, mafificin jin daɗinta shine samun mace ta gari”
iv. Samun natsuwa da kwanciyar hankali: Allah Ta’alah ya ce:
ّ ‫واج ا ل َت ْس ُك ُنوا َإل ْي َه ا وجعل بينكم‬
‫مودة ورحمة‬ ْ ‫ومن آياته َأ ْن َخ َل َق لكم‬
ً ‫من أنفس كم ْأز‬
ِ ِ
21 ‫ سورة الروم‬.‫لقوم يؤمنون‬ َّ
ٍ ‫إن فى ذالك االية‬

“Yana daga cikin ayoyin sanin Allah ya halitta muku mata daga
kayukanku domin ku sami natsuwa daga gareta (ita ma ta samu
daga gareka), sannan ya sanya Soyayya da kauna a tsakaninku, a
cikin haka akwai ayoyi ga mutane da suke da Imani” Suratul Rum
21.
v. Muhimmanci a cikin al’umma: Wadda yake da mata, a
gaskiya yana da muhimmanci cikin al’umma kuma ana
mutunta shi. Wannan ne ma yasa Imam Ahmad yake cewa:

ABU MARYAM, MUHAMMAD M. MUSA (DANDABARA)08031934282 7


‫‪MATSAYIN AURE A MUSULUNCI (A TAKAICE) – NA DANDABARA‬‬

‫ولو تزوج بشر كان قد تم أمره‬

‫”‪“Da dai Mutum zai yi aure, hakika da al’amarin ya cika‬‬


‫‪FA’IDODIN AURE A MUSULUNCI:‬‬
‫‪Shi aure yana fa’idodin da ake mora masu yawan gaske, amma ga‬‬
‫‪kaɗan daga cikin su:‬‬
‫‪i.‬‬ ‫‪Da’a ce ga Allah da Manzo: Duk mutumin da ya yi aure‬‬
‫‪hakika ya bi umarnin Allah ne da Manzon Allah domin Allah‬‬
‫‪Maɗaukakin tsarki ya faɗa a wurare daban – daban domin‬‬
‫‪umurtan ɗan Adam da yin aure kamar Suratul Nisa’i aya ta 3.‬‬
‫ْ َ ُاَل َ‬ ‫ُ َ َ َ َُ ّ َ ّ‬ ‫ََْ َ َ‬ ‫َ ْ ْ ُ ْ َأ اَّل ُ ْ ُ‬
‫الن َس ِاء َمثن ٰى َوث ث‬
‫انكحوا م ا ط اب لكم ِمن ِ‬ ‫وِإ ن ِخفتم تق ِس طوا ِفي اليت ام ٰى ف ِ‬
‫َ َ ْ َأ ُ ُ َٰ َأ َ َأ اَّل َ ُ‬ ‫ً َأ‬ ‫َ ُ َ َ َ ْ ْ ُ ْ َأ اَّل َ ْ ُ َ َ‬
‫اح َدة ْو َما َملكت ْي َمانك ْم ۚ ذ ِل َك ْدن ٰى ت ُعولوا‬
‫ورباع ۖ فِإ ن ِخفتم تع ِدلوا فو ِ‬
‫ُ ً‬ ‫اًل ‪ ‬م ْن‪َ  ‬ق ْبل َك‪َ  ‬و َج َع ْل َن ا‪َ  ‬ل ُه ْم‪َ ‬أ ْز َو ً‬
‫اج ا‪َ  ‬وذ ّ ِر َّية‪َ ۚ ‬و َما‬
‫َْ‬ ‫َ َ َأ‬
‫َولق ْد‪ْ  ‬ر َس لنا‪ُ  ‬ر ُس‬
‫ِ‬ ‫ِ‬
‫َ‬ ‫َ‬ ‫َأ‬ ‫ّ‬ ‫ُ‬ ‫َّ‬ ‫ْ‬ ‫اَّل‬ ‫َ‬ ‫ْأ‬ ‫َأ ْ‬ ‫َ َ َ ُ‬
‫ٌ‬
‫ِت َي‪ِ  ‬بآي ٍة‪ِ ‬إ ‪ِ  ‬ب ِإ ذ ِن‪ ‬الل ِه‪ِ ۗ ‬لك ِل ج ٍل‪ِ  ‬كت اب‪﴾٣٨﴿ ‬‬ ‫ول‪  ‬ن‪َ  ‬ي‬ ‫ك ان‪ِ  ‬لرس ٍ‬
‫ُ‬ ‫ُ‬ ‫َ‬ ‫َام ٰى م ْن ُك ْم‪َ  ‬و َّ‬ ‫َأْل‬ ‫َأ ْ‬
‫اِئ ك ْم‪ۚ ‬‬ ‫ِادك ْم‪َ  ‬وِإ َم‬ ‫ِال ِحين‪ِ  ‬م ْن‪ِ  ‬ع َب‬ ‫الص‬ ‫ِ‬ ‫وا ا َي‬ ‫َو ن ِك ُح‬
‫الل ُه‪َ  ‬واس ٌع‪َ  ‬عل ٌ‬‫ْ َ ُ ُ ُ َ َ َ ُ ْ ُ َّ ُ ْ َ ْ َ َّ‬
‫يم‪٣٢﴿ ‬‬ ‫ِ ِ‬ ‫﴾ِإ ن‪ ‬يكونوا‪ ‬فقراء‪ ‬يغ ِن ِهم‪ ‬الله‪ِ  ‬من‪ ‬فض ِل ِهۗ‪ ‬و‬
‫ُ ُّ‬ ‫ٌ‬ ‫ٌ‬ ‫ٌ‬ ‫ُ‬ ‫َّ‬
‫الخلق والتكوين‪ ،‬وهى عامة مطردة‪ ،‬ال يش ذ عنها‬ ‫ِ‬ ‫الز ْو ِج َّية سنة من سنن هللا في‬
‫ات‪ ،‬ق ال تع الى‪َ :‬و ِم ْن‬ ‫الم النب ِ‬ ‫ع الم اإلنس ان‪ ،‬أو ع الم الحي وان‪ ،‬أو ع ُ‬
‫ِ‬
‫ْ َ َ‬ ‫َ َّ ُ َ‬ ‫َ َّ ُ َ‬ ‫َََْ َ‬ ‫َ‬ ‫ُ‬
‫ْي ٍء‪ ‬خلقنا‪ ‬ز ْو َج ْي ِن‪ ‬ل َعلك ْم ت ذكرون‪ .﴾٤٩﴿ ‬وق ال‪ :‬س بحان‬
‫ُ‬ ‫ِ ّل‪ ‬ش‬ ‫ك‬
‫َ‬ ‫اَل َ‬ ‫َأ ْ ُ‬ ‫اج‪ُ  ‬ك َّل َه ا م َّما‪ُ  ‬ت ْنب ُت‪ ‬اَأْل ْر ُ‬
‫َّالذي‪َ  ‬خ َل َق‪ ‬اَأْل ْز َو َ‬
‫ض‪َ  ‬و ِم ْن‪  ‬نف ِس ِه ْم‪َ  ‬و ِم َّما َي ْعل ُم ون‪﴾٣٦﴿ ‬‬ ‫ِ‬ ‫ِ‬ ‫ِ‬
‫َ ْ َ َأ ْ َ َ َ َ ُ ْ ْ َأ ْ ُ ُ ْ َأ ْ َ ً َ ْ ُ ُ َ ْ َ َ َ َ َ َ ْ َ ُ ْ َ َ َّ ً َ َ ْ َ ً‬
‫و ِمن‪ ‬آيا ِت ِه‪  ‬ن‪ ‬خلق‪ ‬لكم ِمن‪  ‬نف ِسكم‪  ‬زواجا‪ِ  ‬لتسكنوا‪ِ ‬إ ليها‪ ‬وجعل‪ ‬بينكم‪ ‬مودة‪ ‬ورحم ةۚ‪ ‬‬
‫َ َ َّ َ‬
‫ات‪ِ  ‬لق ْو ٍم‪َ  ‬يتفك ُرون‪ ﴾٢١﴿ ‬وما أشبهه‬
‫َ‬ ‫َّ َٰ َ آَل َ‬
‫‪ِ.‬إ ن ِفي ذ ِلك ي ٍ‬

‫‪ABU MARYAM, MUHAMMAD M. MUSA (DANDABARA)08031934282‬‬ ‫‪8‬‬


MATSAYIN AURE A MUSULUNCI (A TAKAICE) – NA DANDABARA

َّ ّ
‫ فمن‬،‫ النكاح من ُس نتى‬:‫ قال رسول هللا صلى هللا عليه وسلم‬:‫ قالت‬،‫وعن عائشة‬
َ ّ
‫ ومن ك ان ذا ط ْو ٍل‬،‫األم َم‬
َ ‫اثر بكم‬ ّ ،‫منى‬
ٌ ‫ ف إنى مك‬،‫وتزوج وا‬ ‫لم يعم ل بس نتى فليس‬
‫حس ن ص حيح س نن‬.‫وج ٌاء‬ َ ‫الص ْوم ل ه‬ ّ
َّ ‫ ف إن‬،‫بالص يام‬ ْ
ِ ‫ ومن لم يج د فعلي ه‬،‫فلينكح‬
1508 ‫ابن ماجه‬

ii. Samun rabin addini ne: Lallai kuwa duk wanda yayi aure
kuma ya dace da auren, hakika ya sami rabin addini domin
Annabi (SAW) yana cewa:
(‫الطبرانى و )من رزقه هللا امرأة صالحة فقد أعنه على شطر فليتق هللا فى الشطر الباقى‬
‫الحاكم‬

“Duk wanda Allah ya azurta shi da mace ta gari hakika ya sami rabin
addini, ya ji tsoron Allah a ɗayan rabin da ya saura.
Ɗabaraani/Hakim
‫ البيحق‬.‫ فليتق هللا في النصف الباق‬،‫إذا تزوج العبد فقد استكمل نصف دينه‬

“Idan mutum ya yi aure, hakika ya cika rabin addininsa, ya ji tsoron


Allah a ɗayan rabin da ya saura” Baihaki ne ya ruwaito
iii. Ladan jima’i da ciyarwa: Akwai lada mai yawa ga wanda ya
sadu da iyalinsa, kuma idan ya zo yin wankan janaba kowace
ɗigon ruwa ana rubuta masa lada ko kankare masa zunubi.
Domin Annabi (SAW) yana cewa:
‫ رواه مسلم‬.‫وفى بضع أحدكم صدقة‬

“A cikin saduwar ɗayanku da Iyalinsa akwai sadaka” Muslim

ABU MARYAM, MUHAMMAD M. MUSA (DANDABARA)08031934282 9


MATSAYIN AURE A MUSULUNCI (A TAKAICE) – NA DANDABARA

Haka kuma wajen ciyarwa: domin yace: Dukiyar da ka ciyar


domin ɗaukaka kalmar Allah da wanda ka ciyar domin Sadaka da
wanda ka ciyar da Iyalanka, wanda ka ciyar da iyalanka yafi lada. A
wani kauli Mala’iku suna yin addu’a kullum ga magidanci da ya ke son
ciyar da iyalinsa, sannan wanda ya ke kuntatawa iyalinsa, shima
Mala’iku suna masa mummunar addu’a
iv. Yana samun taimako daga Allah: Ko shakka wanda yake da
aure yana samun taimakon Allah domin Annabi (SAW) yana
cewa:
َّ
‫ والناكح‬،‫ واملك ا ِت ُب ال ذى ُيري ُد األداء‬،‫ املجاه ُد فى س بيل هللا‬:‫هللا ع ْو ُن ُهم‬ ٌ ٌ
ِ ‫ثالث ة ح ق على‬
‫ رواه الترمذ‬.‫الذى يريد العفاف‬

“Mutane uku, Allah ya yi alkawarin taimaka musu. Mai


gwagwarmaya domin ɗaukaka maganar Allah (Mujahidi), da
Mukaatibi da ya ke son biya, da kuma magidanci da yake bukatar
sauki (ciyarwa da sauke nauyin da ke kansa).
v. Kariya ce daga Zina: Wanda ya yi aure tana kare shi ko ita
daga yin zina, domin zina haramun ne kuma ana samun
zunubi mai yawa. Annabi yana cewa:
(‫ فإنه أغض للبصر وأحصن‬،‫يا معشر الشباب من استطاع منكم الباءة فليتزوج‬
‫ ومن لم يستطع فعليه بالصوم فإنه له وجاء (أى وقاية) البخاري ومسلم‬،‫للفرج‬

vi. Rayar da Sunnah ce: Duk wanda yayi aure hakika yana rayar
da Sunnar Manzon Allah (SAW).
َ َّ
‫ رواه النساء‬.‫الصال ِة‬
ُ ّ
‫والط ْي ُب َو ُج ِع َل ق َّر ِني ِفي‬ ُّ ‫ُح ّب َب َل َّي م َن‬
ُ َ ّ ‫الد ْن َيا‬
ِ ‫النساء‬ِ ِ ‫ِ ِإ‬
1
ABU MARYAM, MUHAMMAD M. MUSA (DANDABARA)08031934282
0
MATSAYIN AURE A MUSULUNCI (A TAKAICE) – NA DANDABARA

vii. Hanyar shiga Aljanna ce: Tabbas ta hanyar yin aure ana
samun Guzurin da za’a shiga aljanna da ita.
((‫ املرأة‬:‫ من سعادة ابن آدم‬،‫ ومن شقاوة ابن آدم ثالثة‬،‫من سعادة ابن آدم ثالثة‬
‫ املرأة‬:‫ ومن ش قاوة ابن آدم‬،‫ واملركب الص الح‬،‫ واملس كن الص الح‬،‫الص الحة‬
‫ واملركب السوء‬،‫ واملسكن السوء‬،‫))السوء‬
ً ً ً ً :‫أرب ع من أعطيهن فق د أعطى خ ير ال دنيا واآلخ رة‬
((،‫ ولس انا ذاك را‬،‫قلب ا ش اكرا‬
ً ً ً
‫ وزوج ة ال تبغي ه ُحوب ا (ظلم) فى نفس ها وماله‬،‫رواه ))وب دنا على البالء ص ابرا‬
‫الطبرانى‬

viii. Ana samun addu’ar ‘ya’ya da kuma ceton wanda ba a haifa


ba: Tabbas wanda yayi aure yana samun wannan fa’ida
domin Annabi (SAW) yana cewa:
‫ رواه مسلم‬.‫ وولد صالح يدعو له‬............ ‫إذا مات ابن آدم انقطع عمله إال من ثالث‬
‫ صحيح‬.‫ باستغفار ولدك لك‬:‫ أني لي هذا؟ فيقال‬:‫إن الرجل لترفع درجة في الجنة فيقول‬
ْ َْ ‫ُأ‬ َ َ َّ
‫ ابن ماجع‬.‫احت َس َبته‬ ‫السقط ل َي ُج ُّر َّم ُه ِب َس َر ِره إلى الجنة إذا‬ ‫والذي نفسي بيده إن‬
TSOKACI: Na’am idan muka yi la’akari da waɗannan hujjoji, ya ishi ɗan
Adam mai hankali ya gane cewa akwai fa’idodi masu yawa da ake samu
cikin aure, idan haka ne lallai kuwa za’a sami jarrabawa. Kenan abinda
ake bukata shi ne hakuri, domin shaiɗan ba zai taɓa yarda ɗan Adam
ya shiga aljanna ba sai in abin ya fi karfinsa.
HUKUNCIN AURE
Aure wajibi ne, amma wasu suna ganin ba wajibi bane Mustahabbi ne.

1
ABU MARYAM, MUHAMMAD M. MUSA (DANDABARA)08031934282
1
MATSAYIN AURE A MUSULUNCI (A TAKAICE) – NA DANDABARA

Hukuncin yin aure a Musulunci: Aure ya tattara dukkan hukunce-


hukunce guda biyar da sharia ta tanadar, sune kamar haka: Wajibci,
Hallacci, Haramci, Sunnah da Zaɓi. Ga kaɗan daga cikin dalilan da
suka sa aure ya tattara waɗannan hukunce-hukunce kamar haka:
1. Aure wata hanya ce ta yaɗuwar zuri’a.
2. Aure abu ne wanda yake haɗa Jinsi guda biyu wato mace da
namiji.
3. Aure abu ne wanda ya kunshi hakkoki na dukkan ma’auratan
su biyu.
4. Aure abu ne da ya kunshi soyayya da amincewar juna su
rayu tare a waje daya.
Kasancewar aure ya kunshi manufofi da hikimomi ne ya sa shari’ar
Musulunci ba ta ba shi takamaiman hukunci guda daya daga cikin
hukunce hukuncen da ta tanadar ba, har sai bayan an yi bincike a
tsakanin ma’aurata. Yin bincike ko duban yanayin ma’aurata ne ke bada
damar sanin hukunci da ya dace da daya daga cikin ma’aurata.
SHEKARUN AURE:
Babu wata Nassi cikin Alkur’ani ko Hadisi da ta nuna takamammen
shekara da namiji zai kai kafin ya yi aure ko ita mace. Kawai babban
abin da ake la’akari dasu sun haɗa da
i. Balaga: Lallai kuwa abin da aka fi kulawa dashi shi ne
balaga, domin Annabi (SAW) ya yi nasa auren yana ɗan
Shekara ashirin da biyar (25) ya balaga, haka kuma a dubi
matan da ya aura akwai mai shekara kasa da goma, akwai

1
ABU MARYAM, MUHAMMAD M. MUSA (DANDABARA)08031934282
2
MATSAYIN AURE A MUSULUNCI (A TAKAICE) – NA DANDABARA

mai sama da sittin. Nana Fatima (‘yar Manzon Allah, RA) ta yi


aurenta a lokacin da ta cika shekara goma sha takwas.
ii. Hankali: Duk balagan da yaro zai yi, ba zai yi aure ba sai ya
zamanto mai cikakken hankali, haka abin yake a ɓangaren
mace. Da hankali ne ake rarrabe mai kyau da mara kyau, dai-
dai da kuma kuskure. A karkashin wannan ne ilimi ke
shigowa domin sanin abubuwan da ya kamata.
iii. Iko: Dole mai yin aure ya zamanto yana da iko kamar na
lafiya, ciyarwa da kuma ɗaukan wasu ɗawainiya. Anan ne
ma ake son miji ya fi matar da zai aura da wasu abubuwa,
son samu kamar shekaru, dukiya da sauransu.
TSOKACI: Babban abin kulawa shine Musulunci baya bukatar cutarwa,
don haka idan an yi cikakken bincike na ilimi an fahimci tabbas mace ta
kai aure sai ayi mata, babu cewa sai ta kai shekara kaza. Kaddara ace
shekarunta ya kai arba’in amma idan an yi mata aure akwai cutarwa a
hankalinta ko gangan jikinta, dole a yi la’akari da hakan, a kuma dakatar
da auren.
Sannan babu wata nassi da ta tabbata daga kowace ɓangare cewa sai
mace ta kammala makaranta kafin ta yi aure, ko saurayi sai ya yi
Diploma ko Degree ko sai ya gina babban gida da sauransu. Abin
kulawa muhimmi sune wadda muka kawo, shin ya balaga, shin yana da
cikakken hankali, shin zai iya ɗaukan nauyin matarsa da sauransu?
Anan ana samin kura – kurai masu yawa, sai matashi ya ki yin aure,
sannan kuma yana ɓarna da fasikanci a waje, iyaye ba za su hana shi
ba, amma sun hana shi yin aure. Idan kuma yana gudun ɗaukan nauyi
ne, sai ka samu yana yin wa budurwarsa duk abin da take bukata
1
ABU MARYAM, MUHAMMAD M. MUSA (DANDABARA)08031934282
3
MATSAYIN AURE A MUSULUNCI (A TAKAICE) – NA DANDABARA

gwargwardon iko, amma na aure ne zai bashi wahala. Allah ya


sawwaka mana wahala.
WA ZA A AURA?
Idan kana neman matar aure ko kina neman mijin aure, akwai
muhimman abubuwa da ya kamata, ku kula da su matuka. Rashin
zaɓar matar da ta dace ko mijin da ya dace dake ko da kai da kuma
addininka, shine mafarin samun matsalarka a duniya da lahira. Kula da
hadisin Manzon Allah (SAW) da ya gabata. Manzon Allah (SAW) ya yi
maganganu a kan irin matar da ya kamata namiji ya aura, ga kaɗan
daga cikin hadisan:
i. Mace, Musulma, Mumina: Akwai abubuwa guda huɗu da ake iya
dubawa wajen auren mace kamar yadda Manzon Allah (SAW)
yace, sannan ya fi karkata zuwa ga mafi dacewa domin jin daɗin
da ake bukata cikin aure. A ɓangaren mace wajibi ne Musulmi ya
zamanto mijinta, domin babu aure tsakaninki da Kafuri ko
Mushirki
 Abu Huraira (RA) ya ruwaito hadisi cewa Manzon Allah (SAW)
yace: Ana aurar mace don abubuwa guda huɗu; ko don
dukiyarta, ko matsayinta (dangi), ko don kyawun ta ko kuma don
addinin ta (tsoron Allah). Don haka ku auri mace don addininta
sai ka ribaci hannunka. (Bukhari da Muslim ne suka ruwaito).
Kula da wannan hadisi ba a haramta wa Musulmi auran kyakkyawa ko
mai dukiya ko mai dangi ba, sai dai abin da Annabi (SAW) yake nufi shi
ne a fara duba addini domin shine jigon rayuwa kafin duk wani abu ya

1
ABU MARYAM, MUHAMMAD M. MUSA (DANDABARA)08031934282
4
MATSAYIN AURE A MUSULUNCI (A TAKAICE) – NA DANDABARA

biyo bayansa. Shi addini ba ya gucewa komen jimawansa, amma kyau


da dukiya da dangi suna karewa, watan watarana.
 A wata hadisi Manzon Allah yace: mafi girman abinda bawa zai
iya mallaka shine harshe mai ambaton Allah, zuciya mai godiyar
Allah da kuma mace ta gari (Mai Imani) wadda take taimaka
masa a kan tsoron Allah.
 Sa’ad bn Abi Waqas ya ruwaito hadisi, Manzon Allah (SAW)
yace: Akwai abubuwa guda huɗu da suke sanya farin ciki da
kuma abubuwa huɗu da suke sanya wa ɗan Adam bakin cikin
rayuwa. Abubuwan da suke sanya farin ciki sune:
 Mace ta gari wadda take faranta maka rai, idan ka kalle
ta, wadda ka aminta da ita idan ka fita (ka bar ta),
 Abin hawa mai sauki, wadda baya wahalar da kai,
 Yalwataccen gida da akwai komai na more rayuwa,
 Makwabci na kwarai,
Abubuwan da ke sanya bakin ciki da kunci sune:
 Muguwar mace wadda take bakanta maka rai, idan ka
kalle ta, wadda take munana maka da harshen ta, wadda
ba ka aminrta da ita idan ka fita ka bar ta a gida.
 Abin hawa mai wahalarwa, wadda ba ya biya maka
bukata.
 Kuntaccen gida, wadda bai wadatar da kai ba,
 Mugun makwabci

1
ABU MARYAM, MUHAMMAD M. MUSA (DANDABARA)08031934282
5
MATSAYIN AURE A MUSULUNCI (A TAKAICE) – NA DANDABARA

 Ka nisanci mace wadda take cutar da kai: Abu Musa al-Ash’ari


(RA) ya ce Manzon Allah yace: Akwai mutane uku, idan sun yi
addu’a, Allah ba ya karɓa, sune:
o Mutum da yake da mace mai munanan ɗabi’u, sannan
kuma bai sake ta ba,
o Mutum da ya bayar da bashin kuɗi ba tare da shaida ba,
o Da mutumin da ya bayar da kuɗi ga mai almobazaranci.
Hakim ne ya ruwaito
ii. Budurwa: Siffa ta biyu da ake son namiji ya duba shi ne budurci
irin na fahimtar Musulunci. Budurwa a Musulunci ita ce wadda
bata taɓa sanin ɗa namiji ba ta kowace hali, sannan kuma ita ce
wadda take mace cikakkiya wajen halittan ta na ‘ya mace
(ma’ana aikin wahala bai sa ta zubar da budurcin ta ba).
Budurwa a al’ada kuwa shine wanda ba ta taɓa yin aure ba, ko
da kuwa ta yi fasikanci da mazaje masu yawa, ko da kuwa ta
haifu a waje ko ta zubar da ciki. Gaskiyar magana ba budurwa ba
ce. Abdullahi bn Mas’ud (R.A) ya ruwaito cewa Manzon Allah
(SAW) yace: Ka auri budurwa, domin ita iya daɗaɗan kalaman
soyayya, kuma tana da kuɓutacciyar mahaifa (mai haifuwa),
kuma ana iya wadatar da su da dukiya ɗan kaɗan (Ɗabaraani ne
ya ruwaito).
haka kuma akwai hadisin Jabir bn Abdallah yace: Watarana
muna dawowa daga tafiya tare da Manzon Allah, a lokacin da
muka yi kusa da Madina, sai yana sauri, sai Annabi yace me ya
sa kake sauri ne yaa kai Jabir? Sai yace yaa Rasulullah kwanan
nan na yi aure. Sai Annabi yace Budurwa ko Bazawara ka aura?

1
ABU MARYAM, MUHAMMAD M. MUSA (DANDABARA)08031934282
6
MATSAYIN AURE A MUSULUNCI (A TAKAICE) – NA DANDABARA

Sai yace Bazawara. Sai Annabi yace: Me yasa ba ka aure


budurwa ba wadda zaka yi masa da ita, ita ma ta yi maka wasa,
za ta saka dariya kai ma ka sata dariya ba?
iii. Mace mai nuna maka so da kauna: Tabbas wannan shima jigo
ne wajen zaɓan matan aure ko mijin aure. Domin duk auren da
za a yi babu soyayya akwai matsala kwarai da gaske. Kafin
zuwan Musulunci ana wa mata auren dole, sai Musulunci ya zo
haramta auren dole ta fuskoki uku, ya hallata guda ɗaya. Ga su
kamar haka
 Idan miji na so, mace ba ta so auren haramun ne,
 Idan mace na so, miji ba ya so auren haramun ne,
 Idan miji da mace ba sa so, iyaye ne suke so, auren
haramun ne,
Wadda Muusulunci ya yarda da shi, shine a samu miji na so,
mace ma tana so, wannan auren ya halatta ko da kuwa iyaye ba sa so.
Sai dai akwai bukatan nazari kan dalilian da ya sa iyaye ba sa so.
Sannan kuma kafin a sami miji na so, mace na so, sai an sami wasu
abubuwa kamar haka:
 Su ga juna har da abubuwan da zai sa su burge juna,
 Su yi hira da juna,
 A sami wadda zai fara furta kalman so,
 Sannan su gamsu da ɗabi’an junansu da sauransu
Ga wasu misalai na dalilai kan dole a sami so da kauna kafin a yi aure
domin tabbatar da manufofin yin aure:

1
ABU MARYAM, MUHAMMAD M. MUSA (DANDABARA)08031934282
7
MATSAYIN AURE A MUSULUNCI (A TAKAICE) – NA DANDABARA

 Abu Uthaynah as-Sadafi (RA) yace, Manzo Allah (SAW) yace:


Matan ku da suka fi alkhairi sune masu haifuwa, masu nuna so
da kauna, masu tausayawa da kuma mutuntawa, sannan kuma a
tabbatar suna da tsoron Allah. Sai ya kara cewa ma fi munin
matan ku sune waɗanda suke sihiri, sannan suna tafiya da
takama, waɗannan Munafikai ne, sune waɗanda za su shiga
wutan Jahannama (Bayhaqi ne ya ruwaito).
 Ibn Abbas (RA) yace, Manzon Allah (SAW) yace: Matanku da za
su zamanto ’yan aljanna sune waɗanda suka iya soyayya kuma
masu haifan ‘ya’ya masu yawa, sannan suna kulawa da mazajen
su (Tammam ar-Razi da wasu ne suka ruwaito).
iv. Kyau: Yana daga cikin abin da ake dubawa idan za a yi aure shi
ne kyau, sai dai ka da ya zamanto shi ne abin da ake baiwa
muhimmanci. Sayyidina Umar yace Allah yana iya baiwa mace
kyau ko baya son ta, amma Allah ba ya bayar da Imani wa bawa
har sai in yana son sa. Kyau a wajen mace ribar kafa ce ga
mijinta, idan ta haɗa da kyawawan ɗabi’u kamar yadda Manzon
Allah (SAW) yace, an karɓo daga Ibn Abbas: Mace da ta fi
alkhairi itace wadda in mijinta ya kalle ta, sai ta faranta masa rai,
idan ya ba ta umarni, tana biyayya, sannan kuma ba ta saɓa
mishi, ko kuma kashe dukiyarsa a kan abin da ba ya so.
v. Kafaa’a: Abinda ake nufi da wannan shine tsaran juna wajen
daraja da ɗaukaka, wato abin da Bahaushe ke cewa kwarya ta bi
kwarya. Wannan yana taimaka wa zaman aure matuka domin
akwai illa babba idan har miji ya ga matar da ta fi shi daraja
kamar ‘yar Sarki da sauransu, sannan yace ita yake so. Idan har
tana son sa babu matsala. Ga wasu dalilai a kan wannan:
1
ABU MARYAM, MUHAMMAD M. MUSA (DANDABARA)08031934282
8
MATSAYIN AURE A MUSULUNCI (A TAKAICE) – NA DANDABARA

 An karɓo hadisi daga nana Aisha tace, Manzon Allah (SAW)


yace: Ku nema wa ‘ya’yanku uwa ta gari, ku auri waɗanda suke
tsararku (wajen daraja), sannan ku aurar da ‘ya’yanku mata ga
tsararku (Ibn Majah, Hakim da wasu ne suka ruwaito), sannan
akwai:
ABUBUWAN DA AKE SO NAMIJI YAFI MATARSA DA SU:-
1. Ilmi.
2. Arziki.
3. Karfi.
ABUBUWAN DA AKE SO MACE TAFI MAI GIDANTA DA SU: -
1. Kunya.
2. Hakuri.
3. Kyau
4. Nasaba.

vi. Mai girmama iyayenta: Duk macen da take girmama iyayenta,


idan ka aure ta, za ka sami sauki matuka, musamman idan
iyayen sun zamanto na Allah.
vii. Mai nutsuwa:
viii. Mara almubazzaranci.
ix. Mara yawan Surutu babu dalili.
x. Mai Sanin ya kamata.
A karshe babban abubuwa da ake kula wa da su, sune addini da kuma
kyawawan ɗabi’u, don haka mata da miji duka ana bukatar duba
waɗannan a lokacin neman aboki ko abokiyar zama.
1
ABU MARYAM, MUHAMMAD M. MUSA (DANDABARA)08031934282
9
MATSAYIN AURE A MUSULUNCI (A TAKAICE) – NA DANDABARA

HAKKOKIN MIJI A KAN MATARSA:


Lallai kuwa miji yana da matsayi mai girma a wajen mace mai
hankali kamar yadda Musulunci ya bashi domin shi ne mai kulawa da
dukan lamuranta, azanci ne da rashin wayewa mace ta ɗauki kanta
kamar na miji, har maganganun Turawa makiya addinin Musulunci ya yi
tasiri a rayuwanta na Gender Equality.
Don haka idan mace tana son ingantaccen zamantakewa da
mijinta, ta ringa jin yana alfahari da ita a kullum, lallai kuwa ga wasu
muhimman abubuwan da Malamai suka tattara bisa bincike cikin ayoyin
alkur’ani da hadisai wadda sune hakkokin da ake bukata ta bayar domin
ya zamanto, ta samu kyakkyawar sakamako a wajen Allah.
1. Faranta masa rai: Duk wani ɗan Adam yana bukata a faranta
masa rai shi yasa ma, ita zuciya tana karkata ne zuwa ga mai
kyautata mata, kamar yadda Manzon Allah (SAW) yace:
َ ‫أحس َن إليها و ُب ْغض َم ْن‬ ُ ‫الق ُل‬
َ ‫وب على ُح ّب َم ْن‬ ُ َ
 ‫أساء‬ ِ ِ ‫ُج ِبل ِت‬
‫إليها‬

“An halicci zuciya tana son mai kyautata mata, sannan tana kin wadda
yake munana mata”
Lallai ko shakka babu kowane mutum yana bukatar a kyautata masa, ko
da kuwa wannan ba shi ne nasa ɗabi’an ba. Don haka ana bukatar
mace ta faranta wa mijinta rai, domin girman hakkin da yake da shi
akanta. Sannan kuma Malamai suka ce akwai abubuwa masu yawa da
mace zata yi domin farantawa mijinta rai, amma ga muhimmai daga
cikinsu:
2
ABU MARYAM, MUHAMMAD M. MUSA (DANDABARA)08031934282
0
MATSAYIN AURE A MUSULUNCI (A TAKAICE) – NA DANDABARA

 Iya abinci: Abinci wani sinadari ne na soyayya wadda


yake sa mutum ya ringa tunawa da matarsa, shiyasa in
miji ya saba cin abinci a waje kuma tana gamsar da shi
sama da na gida, kullum hankalinsa zai koma wajen. Don
haka idan ki ka iya abinci, a wannan fagen kin gama da
gogan. Kada ki yarda ki bar mijinki da yunwa, ki kula da
lokacin da yake dawowa da kuma lokacin da yake fita.
Idan mace ta iya abinci, komen kankantan cefani da aka
bata zai isheta yin abinci. Agaskiya ki tabbata a kalla kin
iya sarrafa abinci kala – kala har guda arba’in mafi
karanci, musamman a gidan da ake yin abinci sau uku a
rana ko huɗu.
 Iya magana: Ana bukatar mace ta iya magana da mijinta,
ta kula da lokacin da yake bukatar magana, musamman
ka da ta bijiro masa da matsaloli lokacin da yake biyan
nasa bukata kamar bacci, fitan waje da sauransu. Idan
tana son ta nemi izinin fita, ta bi hanyoyin da ya dace da
kuma kalmomin da suka dace. Misali, Your Eminence,
idan har ba zan shiga hakkin ka ba, ina son na yi kyautar
tsohuwar rigata ga kanwata wance ko kanwarka wance.
Ranka daɗe, wacece ta dace na baiwa takalmi na nan?
Ko kuma Abu Rumaisa, ina neman alfarman Ziyartan
kawata wance, domin na sami labarin an yi mata tiyata,
amma ka zaɓa mini ranar da ya kamata na je, da dai
sauran hanyoyin da ya kamata. Rashin iya magana yana
haifar da matsaloli masu yawa a zamantakewa na aure.

2
ABU MARYAM, MUHAMMAD M. MUSA (DANDABARA)08031934282
1
MATSAYIN AURE A MUSULUNCI (A TAKAICE) – NA DANDABARA

Kada ta yi anfani da harshenta har ta cutar da shi, ta hanyar


gaya masa maganganu masu ɗaaci da sauransu. Annabi (SAW) yace:
ٌ
((‫ ال تؤذه قاتلك‬:‫ال تؤذى امرأة زوجها فى الدنيا إال قالت زوجته من الحور العين‬
‫ يوشك أن ُيفارقك إلينا‬،‫ فإنما هو عندك دخيل‬،‫))هللا‬

“Babu matar da za ta cutar da Mijinta a nan duniya, face matarsa na


Huru ini (Aljanna) tace: ka da ki cutar da shi, Allah ya tsine miki, ya yi
kusa ya rabu dake ya dawo zuwa garemu (don mu kyautata masa)”
 Iya kallo: Ana bukatar mace ta ringa kallon mijinta da ido
na mutunci da girmamawa, ka da mace ta zamanto mai
zura masa ido, musamman idan wacce take fama da
aljannu sai tsoro ya kamaci ya sammaci, aljannun ne suka
bayyana. Ibn Qayyim yace kallo ya kasu kashi – kashi har
kashi goma sha bakwai, akwai na reni, akwai na
girmamawa, akwai na sha’awa, akwai na neman izini,
akwai na tashin hankali da sauransu, kuma duka da idanu
ake yin su, don haka ki sansu sosai domin mijinki. Idan
har ki ka kiyaye, za ki sha mamaki, domin sai ya rikice
don natsuwa.
 Iya kwalliya: Hasali ma, mace ba ta cika siffarta na ‘ya
mace sai da kwalliya, don haka koyon kwalliya wajibi ne
ga ‘ya mace. Musamman ma, ta kula wace kwalliya ce
idan ta yi, mijinta ya na satar ta da kallo (Musamman irin
mazajen da ba zasu iya buɗe baki suke wannan kwalliyan
ta yi ba). Ta kiyaye dukan kayan kwalliya da ransa ba ya
so, ko da kuwa ranta na so kamar yaya. Domin babu

2
ABU MARYAM, MUHAMMAD M. MUSA (DANDABARA)08031934282
2
MATSAYIN AURE A MUSULUNCI (A TAKAICE) – NA DANDABARA

wanda za ki burge shi da kwalliya sai mijinki, tunda ba ya


so ki yi hakuri, idan kuwa ya yi tafiya sai ki yi wadda ki ke
so, tunda ba haramun bane.
 Iya tsafta: Ita tsafta rabin addini ce kamar yadda muka
sani, don haka mace ta tabbata tana da tsafta, sai mijinta
ya ji babu kamar ta. Dole ne mace ta fi na miji tsafta,
domin itace a gida kuma itace kyawunta na cika da
kwalliya. Don haka ki kula da tsaftar randa, kitchen,
ɗakuna, cikin gida, banɗaki, tufafi da sauransu. Ka da ki
yarda mijinki ya ga kazanta, musammam ma in akwai
yara kanana a cikin gidanku, haka kuma idan kuna yawan
samun baki suna ziyartanku. Shi tsafta yana kawo arziki
da cigaba mai ɗorewa a ko’ina. Tsafta shi ne mace.
2. Yin masa biyayya: Wannan shi ne muhimmin abin da miji ya fi
bukata a wajen matarsa sama da kome, idan mace ta zamanto
mai biyayya dole kawai mijinta zai so ta, domin shi namiji yana
son a yi masa biyayya.
Miji ya cancanci a yi masa biyayya domin girman hakkin da yake da shi.
Manzon Allah (SAW) yace:
َ ُ ‫َأل‬ ُ
ً ‫كنت آم ًرا‬
((‫ َم ْرت املرأة أن تسجد لزوجها‬،‫أحدا أن َي ْسجد ألحد‬ ِ ‫))لو‬

“Da na kasance zan iya umurtan wani ya yi ma wani sujjada, da na


umarci mace ta yi wa mijinta sujjada (domin girman hakkin da yake
dashi)”
Wannan hakkin ne ma yasa Allah Maɗaukakin Tsarki yake cewa
a cikin Littafinsa mai Tsarki cewa:
2
ABU MARYAM, MUHAMMAD M. MUSA (DANDABARA)08031934282
3
MATSAYIN AURE A MUSULUNCI (A TAKAICE) – NA DANDABARA

‫َأ‬ ُ َ ْ ‫َأ‬ ْ َ ٰ َ َ ْ ُ َ ْ َ ُ َّ َ َّ َ َ َ ّ  ‫ َع َلى‬ ‫ون‬


َ ُ َّ َ ُ َ ّ
‫ ْم َو ِال ِه‬ ‫ ِم ْن‬ ‫ نفقوا‬ ‫ َو ِب َما‬ ‫ض‬
ٍ ‫بع‬ ‫على‬ ‫بعضهم‬ ‫الله‬ ‫فضل‬ ‫ ِبما‬ ‫النس ِاء‬ ِ ‫قوام‬ ‫الرجال‬
ِ
‫ْم‬

“Maza masu tsayuwa (girman hakki) ne a kan mata, saboda abin da


Allah Ya fifita sashensu da shi a kan sashe kuma saboda abin da suka
ciyar daga dukiyoyinsu” sai dai duk da wannan ba’a son biyayya akan
saɓon Allah
((‫ إنما الطاعة فى املعروف‬،‫))ال طاعة فى معصية هللا‬

“Babu biyayya cikin saɓon Allah, Ana biyayya ne cikin kyawawan


ayyuka”
Ba karamin kuskure bane mace ta zamanto mai taurin kai wajen
mijinta, yana sa mijin ya sane ta, duk lokacin da aka rabu zai wahala ya
so dawo da ita, domin ya san abin da ya ɗanɗana na rashin biyayya.
Ka da mace ta yarda ta saɓawa mijinta musamman wajen kin
saduwa da shi, domin hakkin saduwa yana daga cikin jigo na aure. Asali
ma, ana bukatar mace ce a kullum ta mika kanta ga mijinta, sai dai shi
ne yace a’a, kar ta damu.
Dubi waɗannan hadisai, da kuma wasu dalilai na daban.
َ
((‫ فب ات غض بان عليه ا‬،)‫إذا دع ا الرج ل امرأت ه إلى فراش ه فلم تأت ه (غ ير ع ذر‬
ً
‫ ((ما استفاد املؤمن بعد تقوى هللا عز وجل خيرا ))لعنتها املالئكة حتى تصبح‬:‫وقال أيضا‬
‫ وإن‬،‫ وإن أقسم عليها أبرته‬،‫ وإن نظر إليها سرته‬،‫ إن أمرها أطاعته‬،‫له من زوجة صالحة‬
))‫غاب عنها نصحته فى نفسه وماله‬

2
ABU MARYAM, MUHAMMAD M. MUSA (DANDABARA)08031934282
4
MATSAYIN AURE A MUSULUNCI (A TAKAICE) – NA DANDABARA

3. Ɗaukaka shi sama da kowa: Yana daga cikin hakkin da miji yake
da shi akan matarsa, shi ne ta ɗaukaka shi, sama da kowa a
duniya, domin wanda suka fi shi girman hakki akan ta sune Allah
da Manzonsa (SAW). Amma iyaye da kowa su na bayansa ne.
wannan magana zai yi ma wasu zafi, amma hakan abin yake,
domin matsayin iyaye daban, sannan kuma akwai abin da miji ke
iya yi wadda iyaye basa iya yi, amma babu abinda iyaye za su
yiwa ‘ya’ya wadda miji ba zai iya ba. Girman hakkin miji ne ya sa
idan Miji ya mutu, mace zata yi masa takaba, amma da
Mahaifinta zai mutu, babu takaba akan ta. Miji ne kaɗai yake iya
auren mace kuma ya sadu da ita, duk soyayyar da uba yake wa
‘yarsa dole ya hakuri da aurenta. Don haka ki sani Miji shi ne oga
a cikin dukan lamuranki.
ْ َ َ ُ َْ
‫رأة ال تشكر لزوجها وهى ال ت ْستغنى عنه‬ ْ
ٍ ‫))ال ينظر هللا تبارك وتعالى إلى ام‬

“Allah ba ya dubi zuwa ga matar da ba ta nuna godiyarta ga


Mijinta, ba ta wadatuwa da shi” haka kuma Annabi ya kara cewa:
ّ ّ
((‫ وال ت أذن فى بيت ه إال بإذنه‬،‫))ال يح ّل للم رأة أن تص وم وزوجه ا ش اهد إال بإذن ه‬

“Ba ya halatta ga mace ta yi azumin Nafila alhali mijinta yana gari har
sai da izininsa, kuma ka da ta yi ma wani izini a gidansa sai da
yardansa”
Don haka akwai bukatan ɗaukan miji da daraja sosai, ka da ki
fita har sai da izninsa, ka da ki cutar da shi da wasu munanan ɗabi’u, a
maimakon haka ki daraja shi. Yau abin mamaki mace tana kiran wasu a
ma’aikatansu oga, domin suna gaba da ita, ta baiwa wasu girma da
2
ABU MARYAM, MUHAMMAD M. MUSA (DANDABARA)08031934282
5
MATSAYIN AURE A MUSULUNCI (A TAKAICE) – NA DANDABARA

cewa Your Highness, Your Excellency, Akramakallah da sauransu. Me


za su anfanar da ke sama da shi mai gida? Kar ki manta shi ne fa
aljannarki kuma wutarki kamar yadda Annabi (SAW) ya faɗi cikin wasu
hadisai. A kiyaye
4. Kare masa Mutuncinsa da dukiyarsa: Yana daga cikin hakkin da
miji yake da shi akan matarsa ta kare masa mutuncinsa da
dukiyarsa kamar yadda ya dace. Ka da mace ta shiga cikin
waɗanda suke zagin mijinta don yau sun sami saɓani, ka da ta
yarda in an sami matsala ta sanar da waɗanda daman tun can
basa bukatar aure, kuma ka da ta yarda ta bayyanar da sirrinsa
ga waɗanda basa da sirrin, idan an tozarta shi kema kin shiga
ciki. Misali, sai aka ce wa mijinki Mazinaci, ke nan kema kin auri
Mazinaci. Kuma Allah yace Mutumin banza sai da mutumiyar
banza, haka kuma yace Mazinaci baya auran kowa sai
‘yar’uwansa mazinaciya. Don haka a kiyaye. Annabi (SAW) yana
bayanin mace ta gari sai yace:
َْ َ َ
((‫ وتحفظه فى نفسها وماله‬،‫وتسر إذا نظ َر‬
ّ ،‫))التى تطيع إذا أمر‬

“Ita ce wadda ta ke biyayya idan an Umarceta, ta ke gamsar da


shi idan ya kalleta, take tsare masa kanta (mutuncinsa) da dukiyarsa”
5. Kulawa da iyayensa da kuma ‘ya’yansa: Yana daga cikin abin da
Miji yake so a rayuwarsa ya ga ana mutunta iyayensa da kuma
kyautatawa ‘ya’yansa, sai ya ji ya natsu, hankalinsa ya kwanta.
Don haka ne ma, ya zamanto hakki ne a kan mace ta tabbata ta
sauke wannan nauyin. Idan tana da hikima da dabara sai ta nuna

2
ABU MARYAM, MUHAMMAD M. MUSA (DANDABARA)08031934282
6
MATSAYIN AURE A MUSULUNCI (A TAKAICE) – NA DANDABARA

masa ta fishi son iyayensa, ta hanyar kyautata musu da kuma


mutunta su, domin su ma iyayenta ne.
Idan mace tana bukatar zaman lafiya da mijinta kuma ta ringa
samun albarkansa a kullum ta kula da abinda yake so, sannan ta ninka
kaunarta akan wannan abun sama da shi, Wallahi za ta sha mamaki
matuka na irin kaunar da zai nuna mata. Misali, ya zo da maganar aure,
ka da ta nuna ɓacin rai, kawai ta ji a ranta ta fi shi so, idan kuma ta yi
haka ka da kuma ta yi guna guni da zai ji, ta ringa fatan alkhairi. Sannan
ta meyar da dukan lamuranta ga Allah. Idan kuma a cikin gida ya
karkatar da ransa ga wani yaro ko ‘ya, ta nuna ita ma tana son wannan
ɗan, amma in tace za ta bayyana kiyayyanta ga abinda yake so, lallai
kuwa za’a sami matsala, musammam ma idan ba ita ce ta haifi ɗan ba
ma. Wannan a takaice kenan, sai kuma
HAKKOKIN MACE AKAN MIJINTA:
Kamar yadda muke ta maimaitawa, hakkoki da ake zayyanawa
domin a kyautata ne, shi Ubangijin Allah yana son a yawaita kyautatawa
halittunsa, shi yasa yake umarni da adalci a kullum. Don haka zamu
kawo hakkokin mace akan miji ba tare da tsawaitawa ba, idan ana
bukata sai a nemi littafi na da ke magana kan hakkokin ma’aurata na
musamman, wadda zai zo nan gaba kaɗan Insha Allah. Ga Hakkokin da
kowace mace take da su akan mijinta:
1. Sadaki: Kowace mace tana da hakkin Sadaki a wajen mijinta,
idan har bai bata Sadaki ba, kuma bai zayyana abinda zai ba ta
na Sadaki ba, aure bai yi ba a Musulunci. Domin Allah yace:

2
ABU MARYAM, MUHAMMAD M. MUSA (DANDABARA)08031934282
7
MATSAYIN AURE A MUSULUNCI (A TAKAICE) – NA DANDABARA

ُ ‫ َف ُك ُل‬ ‫ َن ْف ًسا‬ ‫م ْن ُه‬ ‫ َش ْيء‬ ‫ َل ُك ْم َع ْن‬ ‫ط ْب َن‬ ‫ۚ َف ْن‬ ‫ن ْح َل ًة‬ ‫ص ُد َقاته َّن‬
‫ َم ِريًئ ا‬ ‫ َه ِنيًئ ا‬ ‫وه‬
ّ
َ  ‫الن َس َاء‬ ُ َ
ِ ٍ ِ ‫ِإ‬ ِ ِِ ِ  ‫وآتوا‬

“Kuma ku bai wa mata sadakokinsu da saukin bayarwa. Sannan


idan suka yafe muku wani abu daga gare shi, da daɗin rai, to, ku ci da
jin daɗin da kuma saukin haɗiya”
Sadaki hakkin mace ce, dole kuma a ba ta, sannan ana iya bayar
da sadaki da duk abin da ya halatta Musulmi ya yi mu’amala da shi. Ana
iya bayar da Sadaki kafin aure, ana iya bayarwa a ranar aure, ana iya
bayarwa bayan aure. Duka babu laifi. Babban abinda ake bukata a
kiyaye shi ne ka da a tsananta. Domin tsanantawa yana ɗebe albarkan
aure. Haka kuma babu laifi a kula da hali da ake ciki, idan miji yana da
hali ya kyautatawa gidan matarsa domin samar musu da sauki. Ka sani
kyakkyawar sakamako yana tare da kyautatawa.
2. Wurin zama: Samar da inda za’a zauna (wato gida), yana kan
miji ne kuma dole ne. domin Allah yace:
َ ُ َ ُ ُ ُّ َ ُ ‫َأ ْ ُ ُ َّ ْ َ ْ ُ َ َ ْ ُ ْ ْ ُ ْ ُ ْ َ اَل‬
‫ َعل ْي ِه َّن‬ ‫ ِلتض ِّيقوا‬ ‫وه َّن‬ ‫تضار‬  ‫و‬ ‫وج ِدكم‬ ‫ ِمن‬ ‫سكنتم‬ ‫ۚ س ِكنوهن ِمن حيث‬
“Ku zaunar da su daga inda kuka zauna na gwargwadon
samunku. Kuma kada ku cuce su domin ku kuntata musu.
Abin da aka fi so, shi ne a tabbata gidan yana da banɗaki da
kitchen da kuma ɗakin karɓan baki (faalo), idan kuma babu duk abin da
ya saukaka ya yi. Ba haramun bane zama a gidan haya, amma don
Allah a dubi gidan mutunci, kai ma ka zamanto mai mutunci, ka ringa
biya a kan lokaci, domin tsare mutuncinka da na Iyalanka.
3. Ciyarwa: Ciyarwa yana daga cikin hakkin da mace take dashi
akan mijinta, aure yana iya mutuwa a Shari’ance a dalilin rashin

2
ABU MARYAM, MUHAMMAD M. MUSA (DANDABARA)08031934282
8
MATSAYIN AURE A MUSULUNCI (A TAKAICE) – NA DANDABARA

ciyarwa. Hasali ma, ba’a ba mace hakuri cewa ta cigaba da


zama da yunwa, idan mijinta ya gagara ciyar da ita. Ciyarwa
hakki ne da yake dole, domin Allah Maɗaukakin Tsarki yace:
‫ُ ْ ْ ُ َ َ ْ َ َ َ َ ْ ُ َ َ َ ْ ْ ُ ُ َ ْ ُ ْ ْ َّ َ ُ َّ ُ اَل ُ َ ّ ُ َّ ُ َ ْ ً اَّل‬
‫ِإ‬ ‫نفس ا‬ ‫الله‬ ‫يك ِل ف‬  ۚ ‫الله‬ ‫آت اه‬ ‫ ِمما‬ ‫فلين ِف ق‬ ‫ ِرزق ه‬ ‫علي ِه‬ ‫ق ِدر‬ ‫ۖ ومن‬ ‫س ع ِت ِه‬ ‫ ِمن‬ ‫س ع ٍة‬ ‫ِلين ِف ق ذو‬
َّ َ
‫ ُي ْس ًرا‬ ‫ ُع ْس ٍر‬ ‫ َب ْع َد‬ ‫الل ُه‬ ‫ َس َي ْج َع ُل‬ ۚ‫آت َاها‬ ‫َما‬
“Sai Mawadaci ya ciyar daga wadatarsa kuma wanda aka
kuntata masa arzikinsa, to, sai ya ciyar daga abin da Allah Ya ba shi.
Allah ba ya kallafa wa wani rai face abin da Ya ba shi. Allah zai sanya
sauki a bayan tsanani.”
ّ ‫ يا رسول هللا ما‬:‫قلت‬ ُ
‫حق زوجة أحدنا عليه؟‬ :‫فعن معاوية القشيرى رضى هللا عنه قال‬
ّ ‫ وال‬،‫ وال تض رب الوج ه‬،‫وتكس وها إذا اكتس ْي َت‬ َ َ ْ ُ ‫َأ‬
‫ وال‬،‫تقبح‬ ِ
ُ ،‫ (( ن تط َعمه ا إذا طعمت‬:‫ق ال‬
ّ َ
‫ سنن أبي داود‬:‫ت ْه ُج ْر إال فى البيت)) حسن صحيح‬

“Mu’awiya Qushairiy yace: Na tambayi Manzon Allah, menene hakkin


matan ɗayanmu akansa? Sai yace: Ka ciyar da ita idan ka ci, ka tufatar
da ita idan ka tufatar da kanka, ka da ka duki fuskarta, ka da ka munana
ta, ka da ka kaurace mata sai a ɗaki”
Malaman Musulunci sun yi ittifaki cewa ciyar da mace dole sai
dai idan ta kauracewa mijinta a shinfiɗa, nan kam babu ciyarwa akansa.
Har ila yau, idan muka kula da wannan hadisin zamu ga ba
ciyarwa kawai ya kawo ba, don haka a karkashin ciyarwa akwai
tufatarwa, akwai jinya, akwai sayan kayan kwalliya, sannan ka da a
cutar da ita da sauran abubuwan da ke tabbatar da zaman lafiya cikin
gidan aure.

2
ABU MARYAM, MUHAMMAD M. MUSA (DANDABARA)08031934282
9
MATSAYIN AURE A MUSULUNCI (A TAKAICE) – NA DANDABARA

Bayan haka ciyarwa ba zaɓin miji bane, misali yace za’a ringa
yin abinci a gidana sau uku ko biyu ko ɗaya, a’a, iya bukatuwanta ga
abinci, za ka iya kokarinka ka kawo abin da ya sawwaka, ba kai ne za
ka tsara mata ba, ko zaɓa mata abin da za ta ci ba. Abin da za ka lura
da shi sosai shi ne abincin da ke gina jiki. Allah ya siffanta Muminai a
wajen ciyarwa yace:
“Kuma waɗanda suke idan sun ciyar, ba su yin ɓarna, kuma ba su yin
kwauro, kuma (ciyarwarsu) sai ta kasance a tsakanin wancan da
tsakaitawa.”
4. Kyakkyawar Zamantakewa (Husnul Ma’ashara): Wannan gaɓa
yana taimakawa zaman aure sosai. Kamar yadda muka yi ta
nanatawa, babu wanda baya bukatan kyautatawa, wannan ne
ma yasa a alakar miji da mace sai Allah Ta’alah yace:
َ ّ ُ َ ْ ‫َ ُ َأ‬ ‫اَل‬ ُ َ َّ ‫َأ‬
 ۖ‫ك ْر ًها‬ ‫َاء‬ ‫الن َس‬ ِ  ‫وا‬ ‫ت ِرث‬ ‫لك ْم ن‬ ‫ُّل‬ ‫ َي ِح‬   ‫وا‬ ‫ َآمن‬ ‫ين‬ ‫ا ال ِذ‬ ‫ا ُّي َه‬ ‫َي‬
‫ُ َّ اَّل‬ ُ َ
‫آت ْيت ُم‬ ‫ا‬ ‫ َم‬ ‫ض‬ ْ َ َُ ْ َ ُ ُ
‫ ِلت‬ ‫وه َّن‬ ُ ‫ َت ْع‬  ‫َواَل‬
‫ِإ‬ ‫وهن‬ ِ ‫ ِببع‬ ‫ذهبوا‬ ‫ل‬ ‫ض‬
َ ُ ُ َ ْ َ ْ َ ‫مْل‬ ََُّ َ َ َ ‫َأ ْ َ ْأ‬
‫ف َع َس ٰى‬ ‫وه َّن‬ ‫ك ِر ْهت ُم‬ ‫وف ف ِإ ن‬ ِ ‫ ِب ا ع ُر‬ ‫اش ُروهن‬
َّ ُ َ َ
ِ ‫وع‬  ۚ‫مب ِين ٍة‬ ‫احش ٍة‬ ِ ‫ ِبف‬ ‫ي ِتين‬ ‫ن‬
َ َ َّ َ ْ َ ْ ‫َأ‬
‫ك ِث ًيرا‬ ‫خ ْي ًرا‬ ‫الل ُه ِف ِيه‬ ‫ َو َي ْج َع َل‬ ‫شيًْئ ا‬ ‫تك َر ُهوا‬ ‫ن‬
“Ya Ku waɗanda suka yi imani! Ba ya halatta a gare ku, ku gaji
mata a kan tilas kuma ka da ku hana su aure domin ku tafi da sashen
abin da kuka ba su, face idan suka zo da wata alfasha bayyananniya
kuma ku yi zamantakewa da su da alheri sa´an nan idan kun ki su, to
akwai tsammanin ku ki wani abu alhali kuwa Allah Ya sanya wani alheri
mai yawa cikinsa.
Kyakkyawar zamantakewa da mata abu ne da Musulunci yake
kira a kai kullum domin Manzon Allah (SAW) yace:
3
ABU MARYAM, MUHAMMAD M. MUSA (DANDABARA)08031934282
0
MATSAYIN AURE A MUSULUNCI (A TAKAICE) – NA DANDABARA

ًُُ َ ْ
ٌ
((‫ إن ك ِره منها خلقا َر ِضى منها آخر‬،‫مؤمن مؤمنة‬ )‫))ال َيف َر ْك (ال يبغض‬

“Kada Mumini ya kaurace wa yar ‘uwarsa (Matarsa) Mumina,


idan ya ki wata ɗabi’a a wajenta zai yarda da wani ɗabi’an”
Kula da waɗannan dalilai, ana bukatar miji ya yi kyakkyawar
mu’amala da matarsa domin ita mace abu biyu ta fi son mijinta ya yi
mata, wato ya nuna mata soyayya da kuma tausayi. Malamai suka ce
alama da yake nuna miji yana son matarsa shi ne ya samar mata duk
abinda suka dace da ita a Musulunce, ka da ta koka kan wani abu
alhalin ka na da hali. alama kuwa ta tausayawa shi ne damuwa da halin
da take ciki, kuma ka kyautata mata ko iyayenta ko ‘ya’yanta ko
yan’uwanta da sauransu.
Daga cikin kyawawan mu’amala (zamantakewa) akwai wasu
abubuwa kamar haka:
i. Yin hakuri da ita: Lallai kuwa yana cikin kyakkyawar zama
tsakanin miji da matarsa, ya ringa yin hakuri da ita. Kuma ana
son hakurinsa ya fi nata matuka har sai abin ya gagara.
An karɓo Hadisi daga Anas yace: Manzon Allah (SAW) ya kasance
kowace dare matansa suna haɗuwa a ɗakin wadda kwana ke kanta.
Zainab (RA) ta shiga ɗakin Aisha wadda a ranan kwanan ta ne, sai ta yi
sallama sai Annabi ya ba ta hannu (don su gaisa), sai Aisha (RA) tace
Zainab ce fa….; surutu ya ɗan tashi har sayyidina Abubakar wadda
yake wucewa a bayan gida ya ji su, hankalinsa ya tashi, har ya ji kamar
ya shiga cikin gidan, ………………..…

3
ABU MARYAM, MUHAMMAD M. MUSA (DANDABARA)08031934282
1
MATSAYIN AURE A MUSULUNCI (A TAKAICE) – NA DANDABARA

Sannan akwai hadisi daga Urwah, yana cikin Sahihul Bukhari wadda
yake bayani cewa matan Annabi sun kasu gida biyu: Akwai group na
Aisha tare da Hafsat, Safiyah da Saudah. Sannan akwai group na Umm
Salamah tare da Zainab bnt Khuzaymah, Zainab bn Jahsh, Juwairiyah
bnt Alharith, Maimuna da sauransu. Musulmai kuma sun san kaunar da
Annabi yake wa Aisha ya fi na sauran matan, don haka idan suna son
su bayar da wani kyauta, za su jira sai ranar kwanar Aisha sai su bayar.
Sai group na Ummu Salamah suka tattauna wannan matsala, sai su ka
tura ita Shugabansu domin ta sami Annabi, ta gaya masa cewa suma
matansa ne, bayan ita sai nana Fatimah, bayan ita sai suka tura Zainab
bnt Jahsh wadda ta yi masa maganganu marasa daɗin
ji………………………
Sannan akwai hadisi da yake bayani kan ɗaga murya da Aisha (RA)
ta yi wa Manzon Allah, har Mahaifinta ya shigo gidan, ya kamata, ya ce
yake ‘yar Umm Ruuman! Me yasa kike ɗaga murya sama da na Manzon
Allah? Annabi ne ya ba shi hakuri domin ka da ya duke ta……….
Haka ma Hafsat bnt Umar. Shima sai da Mahaifinta Umar bn
Khattab ya shigo domin ɗaukan mataki sai Annabi ya ba shi hakuri.
Idan ka dubi waɗannan misalai za ka fahimci, Annabi yana hakuri da
matansa. Watarana Annabi yana ɗakin Aisha sai aka kawo masa abinci
sai Aisha ta buge abincin ya zuɓe don kishi, Annabi ya nemi yan
gidanta su ɗebi abincin…………….
ii. Nuna mata tsantsar kauna: Yana daga cikin kyakkyawar
zamantakewa tsakanin miji da matarsa ya nuna mata soyayya da
kauna. Idan muka dubi gidan Annabi zamu ga haka babu iyaka,
3
ABU MARYAM, MUHAMMAD M. MUSA (DANDABARA)08031934282
2
MATSAYIN AURE A MUSULUNCI (A TAKAICE) – NA DANDABARA

domin ba ya kiranta da sunanta kai tsaye. Ya zo cikin hadisi,


nana Aisha tace: Manzon Allah yana kira na Ayesh, tace:
Watarana Manzon Allah ya shigo gida sai yace: Ya ke Ayesh, ga
Mala’ika Jibril yana miki Sallama, sai tace shima amincin Allah ya
tabbata a gareshi”
iii. Yin wasa da ita: Lallai kuwa mace tana bukatan mijinta ya yi
wasa da ita, don haka yana daga cikin zama mai kyau yin wasa
wadda babu raini tsakanin miji da matarsa. Nana Aisha ta
ruwaito hadisi cewa: watarana tana cikin tawagan Annabi (SAW)
sai yace wa mutane su yi gaba, su barsu a baya, sai aka barsu a
baya, sai Annabi yace, su yi tsere – tsere, sai na tsere masa.
Watarana kuma na sake kasancewa cikin tawagansa na tafiya,
muka sake yi sai ya tsere mini.
Aisha (RA) tace watarana Saudat ta kawo mana ziyara sai ta zauna
da kafa ɗaya a ɗaki na, ni kuma na shirya wata abinci da ake kira
Khazeerah sai na ce ma ta ki ci. Sai ta ki ci, sai na ɗauki abinci ina
kokarin saka mata a baki, ita kuma tana nunawa ba ta so (don yin
wasa), sai na kwaɓa ma ta baki dashi, Annabi ya yi mana dariyan abin
da muka yi
Haka kuma nana Aisha ta ruwaito hadisi wannan ita da wasu
kawayenta guda biyu suna wasa na buga kwarya da waka a ranar Mina,
sai Mahaifinta ya zo ya hana ta, sai Annabi yace masa, ka bar yan mata
su yi wasan su, ai yau ranar murna ne ……………..
Kula da waɗannan misalai, lallai su na nuna irin saukin kai da
Manzon Allah yake dashi ga iyalansa.

3
ABU MARYAM, MUHAMMAD M. MUSA (DANDABARA)08031934282
3
MATSAYIN AURE A MUSULUNCI (A TAKAICE) – NA DANDABARA

iv. Yin tafiya tare da ita: Yana da muhimmancin gaske miji ya yi


tafiya da iyalinsa, Wallahi yana sa ta kara son shi sosai kuma su
kara fahimtar juna. Domin tana ji a ranta ka ɗauke ta da
muhimmanci, kuma za ta kara wayewa da sanin irin abubuwan
da kake yi. Dubi hadisin da muka kawo wadda Annabi yana
tafiya da matansa, yau zai yi da wance gobe kuma wata ce
daban.
Amma yau mu kam sai a hankali, har ya kai mutum ya bar matansa
ta zamanto ‘yar kauye, fadar jihansu ma mace bata sani ba. Haba
Mallam! Wannan shi yake sawa idan Allah ya yi ma ta dalilin fita, ta
ɗauka ka cuce ta a rayuwa. Ba ka tunanin watarana Allah zai ɗaukaka
ka zamanto wani abu, yaya kake son matarka ta fara shigan cikin
mutane?
v. Neman Shawaranta: Ko shakka babu mace tana jin daɗi, idan
mijinta yana neman shawaranta akan wasu lamura da suka
shafe shi. Don haka yana da kyau sosai, kuma yana samar da
kyakkyawar zamantakewa idan miji yana neman shawaran
matarsa. Wannan ne ma yasa akwai abubuwan da Musulunci
yake son mace su tattauna da mijinta kamar lokacin cire yaro a
nono, tarbiya, tura shi karatu da sauransu. Dubi abinda ya faru a
Sulhun Hudaibiyya. Shawaran Ummu Salma shi ya kuɓutar da
al’umma daga fushin Allah (A lokacin da ya yi tafiya da ita).
vi. Yin Adalci a tsakaninsu. Kowa yana bukata ayi masa adalci, wato
a bashi abin da ya dace da shi ko ita. Don haka idan aka sami
wannan lallai miji zai yi zaman lafiya da matansa. Dubi lokacin
rashin lafiyar Manzon Allah (SAW), hadisi yana cikin Bukhari

3
ABU MARYAM, MUHAMMAD M. MUSA (DANDABARA)08031934282
4
MATSAYIN AURE A MUSULUNCI (A TAKAICE) – NA DANDABARA

babin Yaki 8/144. Haka ma mu dubi inda Aisha ta fasa wa Umm


Salamah (RA) kwanun abinci ya sa ta biya, duk da irin so da
yake mata.
Haka kuma lokacin da Aisha ta kuuce Safiyah cewa: Yaa
Ma’aikin Allah ka ga yadda gajercin Safiyah yake kuwa? Ya
meyar da martini yace abinda ta faɗa da za’a jefa a cikin ruwan
teku sai ya lalata shi.
vii. Kulawa da Tausaya ma ta: Kowace mace tana bukatar mijinta ya
ba ta lokaci domin ganinsa ko tattaunawa da shi, musammam
ma idan tana son ta gaya masa wani abinda yake damun ta, ka
da ya ringa haɗa ma ta fuska ba. Kuma ka ringa tausaya ma ta,
ta hanyar ta ya ta wasu ayyuka a cikin gida kamar wanke –
wanke, share, dafa abinci da sauransu, sannan kuma idan tana
da jariri ka rike ma ta, domin ta samu daman yin aiki babu takura
da dai sauransu. Tirmizi ya ruwaito hadisi daga Anas dan Malik
cewa Hafsat ta zagi Safiyah tace ke sabon tuba (Bayahudiya),
Manzon Allah ya tsawatarwa Hafsat yace ki ji tsoron Allah, ya
nuna ɓacin rai mai tsanani, har ya meyar da martanin da Hafsat
ta yi nadama sosai, domin yace wa Hafsat, Safiya fa ta fi ku
daraja domin ita yar’uwan Annabi Musa ne kuma, Matan Annabi
ce ita.
Wata rana Annabi suna cikin tafiya da matansa sai Rakumin Safiyah
ya sami Matsala, sai ya cewa Zainab ta taimakawa Safiyah da Rakumi
guda, ta ce ni in taimakawa Bayahudiya? Annabi ya bar ta ya koma
wajen Safiyah domin ya ba ta hakuri ransa a ɓace.

3
ABU MARYAM, MUHAMMAD M. MUSA (DANDABARA)08031934282
5
MATSAYIN AURE A MUSULUNCI (A TAKAICE) – NA DANDABARA

Dubi bayanin auren Annabi da Aisha tana yaranta ‘yar shekara


shida, tana wasan kasa bai taɓa tsawatar mata ba. Idan ta gan shi tana
jin kunya, shi kuma sai ya bar ta da kawayenta suna wasan da suka
saba cikin al’adarsu da Larabawa, bai taɓa hana ta ba.
Haka ma mu dubi lokacin da ya tsayar da rundunan yaki baki ɗaya
domin neman abin wuyan Asma bnt Abubakar wadda Aisha bnt
Abubakar ta ɓatar.
5. Jima’i (Saduwa): Hakkin saduwa (jima’i) yana ɗaya daga cikin
hakkin mace akan miji wadda idan ya gaza bayarwa, aure yana
mutuwa. Shiyasa ma mace tana samun tsinuwa idan ta ki baiwa
mijinta haɗin kai a lokacin jima’i. Allah Ta’alah yace:
َ ْ َ َ َّ ُ َّ ُ ُ ْ ‫َأِل‬ َ ُ ‫َ ُ َأ َّ ْئ‬ ُ ‫ٌ َ ُ َ ْأ‬ ُ ‫ُؤ‬
‫اعل ُمو‬ ‫و‬ ‫الله‬ ‫ َواتق وا‬  ۚ‫ نف ِس ك ْم‬ ‫ َوق ِّد ُموا‬ ۖ ‫ ِش ت ْم‬ ‫ ن ٰى‬ ‫ َح ْرثك ْم‬ ‫ف توا‬ ‫لك ْم‬ ‫ َح ْرث‬ ‫ِن َسا ك ْم‬
َ ‫َأ َّ ُ ْ ُ اَل ُ ُ ّ مْل ُْؤ‬
‫ا ِم ِنين‬ ‫ َو َب ِش ِر‬ ۗ‫وه‬ ‫م ق‬ ‫ نكم‬ ‫ا‬
“Matanku gonaki ne a gare ku, saboda haka ku je wa gonakinku
yadda kuka so. Kuma ku gabatar (da alheri) saboda kanku, ku bi Allah
da takawa. Kuma ku sani cewa lalle ne ku masu haɗuwa da Shi ne.
Kuma ka bayar da bushara ga muminai. “
َ ٌ ُ ْ ‫ٌ َ ُ َأ‬ ُ َ ُ َ ّ  ‫ َل ْي َل َة‬ ‫ُأ ح َّل َل ُك ْم‬
‫ل ُه َّن‬ ‫اس‬ ‫ ِل َب‬ ‫لك ْم َو نت ْم‬ ‫اس‬ ‫ ِل َب‬ ‫ ُه َّن‬.‫ ِن َس اِئ ك ْم‬ ‫ِإ ل ٰى‬ ‫ال َّرفث‬ ‫الص َي ِام‬ِ ِ
ْۖ ‫ َع ْن ُكم‬ ‫ َو َع َفا‬ ‫ َع َل ْي ُك ْم‬ ‫اب‬ َ ََ ْ ُ َ ُ ْ ‫ُ َ َأ‬ َ ْ َ ْ ُ ْ ُ ْ ُ َّ ‫َ َ َّ ُ َأ‬
‫فت‬ ‫كم‬ ‫ نفس‬ ‫انون‬ ‫كنتم تخت‬ ‫ نكم‬ ‫الله‬ ‫ۗ ع ِلم‬ 
ُْ َ ُ َّ َ َ َ َ ُ َ ْ َ َّ ُ ُ َ َ ‫َ آْل‬
‫لكم‬ ‫الله‬ ‫كتب‬ ‫ما‬ ‫وابتغوا‬ ‫اشروهن‬ ِ ‫ب‬ ‫فا ن‬

“An halatta a gare ku, a daren azumi, yin jima´i zuwa ga matanku, su
tufa ne a gare ku, kuma ku tufa ne a gare su, Allah Ya sani lalle ne ku
kun kasance kuna yaudarar kanku. Saboda haka Ya karɓi tubarku,

3
ABU MARYAM, MUHAMMAD M. MUSA (DANDABARA)08031934282
6
MATSAYIN AURE A MUSULUNCI (A TAKAICE) – NA DANDABARA

kuma Ya yafe muku. To, yanzu ku rungume su kuma ku nemi abin da


Allah ya rubuta muku…………….”
Lallai kuwa jima’i hakki ne da miji da mace suka yi tarayya a kai,
kuma narko na azaba yana kan kowanne idan ya cutar da ɗan’uwansa
akan wannan hakkin. Akwai maganganun Malamai akan tsawon lokaci
da miji zai ɗauka, in bai sadu da matarsa ba sai ya zamanto ya yi laifi
da za’a rubuta masa zunubi. A takaice kawai ya biya ma ta bukata da
yadda ba za ta faɗa zina ba, kuma ya gamsar da ita.
Matsala ta jima’i babu wasa ciki, dole ne miji ya san karfin sha’awar
matarsa, haka ita ma dole ta san karfin sha’awan mijinta, babu maganar
kunya anan. A ɓangaren sha’awa na jima’i maza da mata sun kasu
kashi uku. Don haka kowa ya sani a wane mataki yake ko take? A yau
rashin fahimtar juna da kuma rashin sanin ilimin jima’i yana kawo wa
aure matsala, mutane ba su sani ba. Shi jima’i tasirinsa yana kaiwa ga
kwakwalwan mutum da kuma zuciyarsa.
6. Samar mata da ilimi: Wannan wajibi ne akan miji ya samarwa
matarsa da ilimi, musammam ma na abubuwan da take
bukatarsu kamar sanin Allah da addininsa. Dole mace ta sami
ilimin zaman aure, ilimin tarbiyan ‘ya’ya da sauransu.
Musammam ma, abinda wannan littafi ya kunsa na hakkoki, ta
haka ne za ta zauna lafiya da kowa. Annabi yace:
‫طلب العلم فريضة عل كل مسلم‬

Baya ga haka, miji ya samarwa matarsa ilimin zamani na wayewa,


domin addinin Musulunci ba addinin kauyanci ba ne, Musulunci ya zo da

3
ABU MARYAM, MUHAMMAD M. MUSA (DANDABARA)08031934282
7
MATSAYIN AURE A MUSULUNCI (A TAKAICE) – NA DANDABARA

wayewa. Ta wannan hanya ne za ta kara sanin abubuwa na zamani


yadda ake anfani da su kamar gas cooker, firiji, heater da sauransu.
Dole ka tarbiyantar da matarka bisa Sunna, ta yi karatun da za ta
anfanar da al’umma ko kuma ta yi sana’a bisa tsari na Musulunci domin
taimakon al’umma. Kasancewa ita baiwa ce na Allah, Allah yana
bukatan gudumawa daga gareta wadda dole harkan kuɗi zai iya shiga
ciki. Ita ma za ta yi koyi da magabata.
7. Kishinta: Wannan hakki ne da kowace mace take dashi akan
mijinta, ya zamanto yana Kishinta, ka da ya yarda ya barta kowa
yana ganinta, yana mu’amala da ita sai waɗanda Musulunci ya
yarda masu kamar yadda yazo a cikin Suratul Nur aya ta 31.
Agaskiya ba wayewar Musulunci bane, mutum ya kasance ba ya
kishin matarsa, ya bar ta kowa na ɗaukan ta a babur, kowa na
shigan gidansa babu hijabi, kowa na zama kujerar ɗaya da ita, tana
fitan waje a duk lokacin da take so, kuma ta yi mu’amala ko da na
kasuwanci ne da kowa, wannan halaka ne matuka domin Annabi
(SAW) yace:
ّ ‫وث َوامْل َ ْرَأ ُة امْل ُ َت َر ّج َل ُة َت َش َّب ُه ب‬
‫الر َج ِال‬
ُ ُّ َّ َ ُّ َ ْ َ َ ْ َ ْ َ ْ ْ َ ُ َّ ُ ُ ْ َ ٌ َ َ
‫ العاق والدي‬:‫ثالثة ال ينظر الله ِإ لي ِهم يوم ال ِقيام ِة‬
ِ ِ ِ
“Mutane uku ba za su shiga aljanna ba: Wanda ya guji iyayensa, da
wanda ba ya kishin matansa (ko kuma matan da ba ta kishin mijinta), da
kuma mace me kamanceceniya da na miji (wajen sanya sutura)”

3
ABU MARYAM, MUHAMMAD M. MUSA (DANDABARA)08031934282
8
MATSAYIN AURE A MUSULUNCI (A TAKAICE) – NA DANDABARA

َ ْ ّ َ ُ َ ُ َّ َ َ ّ َ ُ ُّ َّ
‫ َو ُم ْد ِم ُن الخ ْم ِر‬،‫الن َس ِاء‬
ِ ‫الرج ِال والرجل ة ِمن‬ ِ ‫ ال ديوث ِمن‬:‫ثالث ة ال ي دخلون الجن ة أب دا‬
َ ‫ َق‬،‫الر َج ال ؟‬ ّ ‫وث ِم َن‬ُ ُّ َّ َ ‫ َف‬،‫ول هللا َأ َّما ُم ْدم ُن ْال َخ ْم ر َف َق ْد َع َر ْف َن ُاه‬ ُ َ َ ُ ََ
" :‫ال‬ ِ ِ ‫ي‬ ‫د‬ ‫ال‬  ‫ا‬ ‫م‬ ِ ِ ِ َ ‫ ي ا رس‬:‫فق الوا‬
‫الر َجال‬ ّ ُ َّ َ َ َّ َ َ َ ّ ‫الر ُج َل ُة م َن‬ َّ ‫ َف‬:‫ ُق ْل َنا‬. " ‫َّال ِذي اَل ُي َبالي َم ْن َد َخ َل َع َلى َأ ْه ِل ِه‬
ِ ‫ " ال ِتي تشبه ِب‬:‫ قال‬،‫النس ِاء ؟‬ ِ ِ ِ

“Mutane uku ba za su shiga aljanna ba har abada: Wanda ba ya kishin


iyalinsa daga cikin maza da mata. Da wanda ya dawwama yana shan
giya, sai Sahabba suka ce: Ya Ma’aikin Allah, mun san mashayin giya,
wanene addayuth cikin maza? Sai Manzon Allah yace: Shi ne wanda ba
ya damuwa da duk wanda ya shiga wajen iyalansa, sai muka ce cikin
mata kuma fa? Sai yace: ita ce me kamanceceniya da ɗa namiji”

((‫ ل و رأيت رجال م ع ام رأتي لض ربته بالس يف غ ير مص فح عن ه‬:‫ق ال س عد بن عب ادة ق ال‬


‫فبلغ ذلك رس ول هللا ﷺ فقال أتعجبون من غيرة سعد؟ فوهللا ألنا أغير منه وهللا أغير‬
‫))مني من أجل غيرة هللا حرم الفواحش ما ظهر منها وما بطن‬

“Sa’ad ɗan Ubbadata yace: Da zan ga mutum da matata, zan yi masa


duka da takobi ba na kisa ba, sai labari ya isa wajen Manzon Allah
(SAW) sai yace: Yanzu ku na mamakin kishin Sa’ad ne? Wallahi ni na fi
shi Kishi, Allah kuma ya fi ni Kishi, sai dai kishin Allah shi ne ya Haramta
Alfasha abinda ya bayyana da kuma abinda ya ɓuya”
8. Kare mata mutunci: Ana bukatan miji ya tsare wa matarsa
mutuncin ta, ka da ya zage iyayenta, ka da ya ringa aibanta ta
cikin mutane domin a ga bakin ta ko rashin kyautatawanta. Allah
yace:
َ ٌ َ ْ ُ ْ ‫ُ َّ َ ٌ َ ُ ْ َ َأ‬
‫ل ُه َّن‬ ‫اس‬ ‫ ِلب‬ ‫لكم و نتم‬ ‫ ِلباس‬ ‫هن‬

3
ABU MARYAM, MUHAMMAD M. MUSA (DANDABARA)08031934282
9
MATSAYIN AURE A MUSULUNCI (A TAKAICE) – NA DANDABARA

“Su tufafi ne a gareku, kuma tufafi ne a garesu.” Kowa ya san aikin tufafi
shi ne rufe tsiraici domin haka, mu kiyaye. Ba daidai ba ne mutum ya
faɗi komai a kan matarsa, sai in ya zama dole ne.
Yana daga cikin tsare mata mutunci, miji ya kewaye gidansa da
kuma ɗaukan nauyin da ke kansa kamar yin shefani, ɗeba ruwa da
sauransu. Rashin kishin mace ne da kuma zubar mata da mutunci, a ga
matan Musulmi a Bohol ko rijiya ko famfo alhali miji yana gari kuma
yana cikin halin lafiya. Gaskiya mutunci ya zube, komen matsayinka.
9. Yin musu adalci: Yana daga cikin hakkin kowace mace mijinta ya
yi mata adalci tsakaninta da abokan zamanto. Shi adalci kuwa
shi ne a baiwa kowacce hakkinta daidai da ita, ka da a musguna
mata ko a zalunce ta, domin ba’a son ta. Annabi (SAW) yace:
ّ
((‫))من كان له إمرأتان فمال إلى إحداهما دون األخرى جاء يوم القيامة وشقه مائل‬

“Wanda ya kasance yana da mata biyu, sai ya karkata zuwa ga


ɗaya, zai zo ranar Kiyama ɓarin jikin ya ruɓe yana waari”
Ya kamata mu kara fahimta, raba daidai ba shi ne adalci ba, wannan
zalunci ne, misali mutum yana da mata biyu, sai wannan tana da yara
biyu, wannan kuma ba ta haifu ba, sai ka sayi sabulun wanki, sai ka ba
su sanda ɗaɗɗaya, bai yi ba a Musulunci, sai dai da sharaɗin wanda na
ta ya riga karewa (wadda take da ‘ya’ya), za ka sake saya mata kafin na
wancan ita ya kare. Haka kuma wannan doguwa ce yadi biyar zai yi
mata, wannan kuma gajeruwa ce, yadi huɗu zai yi mata, sai ka saya
musu yadi biyar – biyar, bai yi ba wannan zalunci ne, domin doguwa
biyar zai yi mata daidai, gajeruwa kuwa, yadi ɗaya zai saura.

4
ABU MARYAM, MUHAMMAD M. MUSA (DANDABARA)08031934282
0
MATSAYIN AURE A MUSULUNCI (A TAKAICE) – NA DANDABARA

A takaice ana bukata miji ya yi iya iyawarsa, ka da ya ji a ransa yana


fifita wata akan wata bisa zalunci. So na cikin zuciya babu adalci anan,
ba zai yu ɗan Adam ya iya ba, domin Allah ma yace wa Manzon Allah
(SAW):
َ ‫ص ُت ْم َفاَل َتم ُيل وا ُك َّل امْل َ ْي ل َف َت َذ ُر‬ ّ َ ْ َ ُ ْ َ ْ ‫َ َ ْ َ ْ َ ُ َأ‬
ْ ‫الن َس اء َو َل ْو َح َر‬
‫وها‬ ِ ِ ِ ِ ‫ولن تس ت ِطيعوا ن تع ِدلوا بين‬
ً ‫ان َغ ُف‬
ً ‫ورا َر ِح‬ َ َ َ َّ َّ َ ُ َّ َ َ ُ ْ ُ ْ َ َ َّ َ ُ ‫َ مْل‬
‫يما‬ ‫كا علق ِة وِإ ن تص ِلحوا وتتقوا فِإ ن الله ك‬

“Kuma ba za ku iya yin adalci ba a tsakanin mata (na soyayyar


zuciya) ko da kun yi kwaɗayin yi. Saboda haka ka da ku karkata, dukan
karkata, har ku bar ta 9wanda ba ku sonta) kamar wadda aka rataye.
Kuma idan kun yi sulhu, kuma kuka yi takawa, to, lalle ne Allah Ya
kasance Mai gafara, Mai jin kai.” 
10. Bin ka’idojin kaurace mata a shimfiɗa ko kuma rabuwa (Saki):
Yana daga cikin hakkin mace a kan mijinta ya bi tsarin dokoki da
Matakan da Allah ya sanya wa miji ya kauracewa matarsa. Haka
kuma ake bukata ya bi wannan tsari wajen rabuwa da ita kamar
yadda yake a cikin Suratul Talaq.
Dukan waɗannan hakkoki, an sanya su ne domin kyautatawa wa juna.
Kenan duk abin da miji zai iya yi wa matarsa domin ya faranta mata rai,
matukar bai saɓawa Shari’ah ba, ya yi iya kokarinsa domin su sami
kyakkyawar fahimtar juna.
KAMMALAWA:
Ina kara roko da cewa don Allah duk wanda ya ga kuskure ya gyara
mini a take ta hanyar lambobin waya na ko kuma e-mail address na wato
dandabaraislam78@gmail.com. Sannan kuma kafin yin gyaran ka/ki tabbata

4
ABU MARYAM, MUHAMMAD M. MUSA (DANDABARA)08031934282
1
MATSAYIN AURE A MUSULUNCI (A TAKAICE) – NA DANDABARA

cewa ka fahimci hujja ta mai rauni ne matuka. Idan ka ga kuskure sai ka ki yin
gyara, kana guna-guni, ka sani kana karawa kanka zunubi ne.
Ina kara roko kowa ya karanta littafin da kyakkyawar manufa sai ya
dace da dalilin rubuta wannan darasin.
Abu Maryam,
Muhammad M. Musa (Dandabara)
08031934282, 09078771442

4
ABU MARYAM, MUHAMMAD M. MUSA (DANDABARA)08031934282
2

You might also like