You are on page 1of 42

Salisu Abdulrazak

CIKAKKIYAR KARIYA
NA
KUNGIYAR “AREWA COMPUTER LIBRARY”

WANDA YA RUBUTA

SALISU ABDULRAZAK
(SHUGABAN KUNGIYAR NA KASA)
EMAIL: abdulrazaksalisu1@gmail.com

Cikakkiyar Kariya Page i


Salisu Abdulrazak

Juhaifah Ventures
NO. 57 FCE Kano Business Village,
Kano State.

©Haqqin Mallaka (M), Arewa Computer Library (ACL) 2022

Ba’a yarda a juyi wannan littafai ta kowacce hanya, ko sarrafa shi,


ko sake buga shi ba saida izinin kungiyar ACL.

An fara bugawa a shekarar 2022/1443 A.H.

Kamfanin da ya yi Xab’i
Juhaifah Ventures FCE Kano
07037131142, 08086889983
Email: juhaifahcafe@gmail.com

Cikakkiyar Kariya Page ii


Salisu Abdulrazak

GODIYA
Bissimillahi Rahmanirrahim.
ALHAMDULILLAH.
Godiya ta tabbata ga ubangijin tsira kuma ubangijin rahma da ya
bani iko da damar kammala rubuta wannan littafi mai suna
CIKAKKIYAR KARIYA salati da daukaka su kara tabbata ga
annabin daraja, fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW).
Wannan littafi ya samu kammaluwa tareda taimakon wasu
yan’uwa da abokan arziki wanda zan iya lissafo kadan daga
cikinsu kamar haka:
Ameer salisu yaro, Isma’il aliyu ubale, Abubakar Ibrahim, Datti
Assalafy, Iliyasu Sunna, Inusa khamal ladan, buhari yunusa
Muhammad, Bin danladi mai littafi, Mohiddeen Ahmad da
sauransu.
Sannan ina jinjina ga daukacin daliban makarantar AREWA
COMPUTER LIBRARY da malaman makarantar da
shugabannin makarantar baki daya da irin gudumuwar da suka
bani wurin ganin littafin ya samu shiga lungu da sako na arewa cin
kasar mu Nigeria.

Cikakkiyar Kariya Page iii


Salisu Abdulrazak

BUDEWA

A yanzu ilimin fasaha ya zama ruwan dare ya shiga lungu da sako


na duniya, idan muka duba kasashen da suka samu cigaba ta
hanyar amfani da ilimin fasaha zamu ga cewa haryanzu kasar mu
tana baya sosai ta bangaren fasaha, idan kuma aka shigo kasar mu
Nigeria za’aga cewa yankin Arewa shine koma baya ta bangaren
shiga ilimin fasaha wanda hakan ba karamin koma baya da rashin
aikinyi hakan ya haifar ba, wanda ina mai tabbatar mana cewa nan
gaba kadan aikin gadi ma idan za’a dauki mutum sai yanada ilmin
computer ko bayawa saboda yanzu ilimin ya shiga lungu da sako
na duniya.

Abu na biyu babban abin takaici shine idan muka duba irin yadda
akeyi wa yan Arewa kutse (hacking) na accounts dinsu na social
media abin yanzu har ya zama abin tsokana ga yan kudancin
kasar,yadda ake mana hacking na accounts din mu na banki da
social media baki daya yakamata ace Arewa mundade da wayewa
akan yadda zamu kula da accounts din mu ko wane iri ne.

Na rubuta wannan littafi domin ya zama cikakkiyar kariya ga yan


Arewa da irin wannan Al’amari da yake faruwa na kutsen asusun
bankunan su da social media accounts dinsu.

Ban rubuta wannan littafi domin komai ba sai domin a karanta a


koyi yadda za’a iya kare kai daga masu kutse.

Cikakkiyar Kariya Page iv


Salisu Abdulrazak

ABUBAWAN DAKE CIKI

GODIYA........................................................................................ iii

ABUBAWAN DAKE CIKI ........................................................... v

MENENE HACKING .................................................................... 1

KARIYA DAGA KO WANE IRIN HACKING NA SOCIAL


MEDIA ......................................................................................... 11

KARE KAI DAGA MASU KUTSEN ASUSUN BANKI (BANK-


ACCOUNT) .................................................................................. 12

YADDA ZAKA BI DIDDIGIN BARAWO BAYAN YA SACE


MAKA WAYARKA .................................................................... 15

YADDA ZANBI DIDDIGIN WAYATA TA HANYAR AMFANI


DA IMEI DIN WAYATA ............................................................ 19

YADDA ZAKAGA HOTON BARAWON DA YA SACE MAKA


WAYARKA BAYAN YA SACETA ........................................... 22

DAME AKEYIN HACKING. ...................................................... 26

ILIMIN HACKING (KUTSE) ..................................................... 31

RUFEWA ..................................................................................... 37

Cikakkiyar Kariya Page v


Salisu Abdulrazak

MENENE HACKING
Hacking shine yin kutse domin shiga rumbun adana bayanai na
wani ko shiga cikin na’urar wani ko Accounts din wani domin yin
bincike ko domin samun wata dama da za’a gudanar da wani abu
acikin rumbun adana bayanan wanda akeso ayi ma kutsen.

Su kansu masuyin Hacking din sun kasu kashi-kashi, akwai Grey


Hat hackers, White Hat hackers da Black Hat hackers.

Kuma dukkansu ko wane da irin salon yadda yake gudanar da


nashi hacking da dalilinsa na hacking da sauransu, shi Grey Hat
Hacker yana hacking ne domin nishadi shi kuma White Hat hacker
yana hacking ne domin bincike tareda jami’an tsaro badan cutarwa
ba shi kuwa Black Hat hacker yana yi ne domin cuta da mugunta
da sata.

Hacking Na Facebook Da Whatsapp Na Iyalinka Domin Bincike


(ba don cutarwa ba)..

Zanyi wannan bayani amma badan kaje ko kije ki kulle wa wani


account dinsa ba Zanyi shine domin iyaye su san halin da yaransu
suke.

Cikakkiyar Kariya Page 1


Salisu Abdulrazak

Kamar yadda na fada tun farko su masu yin hacking din ma sun
kasu kashi-kashi, amma wadanda akafi sani aciki kuma suka yi
fice sune:

1. Grey hat hackers


2. White hat hackers
3. Black hat hackers

Wato akwai dabaru gida biyu zuwa ukku da hackers suke amfani
dasu wajen kulle wa mutane Facebook dinsu ma'ana (Hacking).

Wadannan dabaru sune kamarhaka:

1. Hasashen "Password Guessing" da kuma "Social


Engineering". Da kuma ta hanyar yaudara. "Password
Guessing:
Wato yanzu da yawan hackers sun gano cewa mutane da
dama suna amfani da numbers din wayarsu, shekarun
haihuwar su, da kuma sunayen su wajens anya password
dinsu na Facebook, Wannan shine yabaiwa Hackers babbar
dama wadda a duk lokacin da suka bukaci kwace maka
account sai suyi hasashen amfani da number wayarka ko
kuma sunan ka da sauransu, Domin kaucewa irin wannan

Cikakkiyar Kariya Page 2


Salisu Abdulrazak

hadari sai ka kiyayi sanya Password dinka da yake da sauki


ko yake da alaka da number ka ko sunanka. (iyaye zasu iya
amfani da wannan dabarar domin binciken account din
yaransu)
2. Social Engineering:
Wato hanya ce mai zaman kanta wadda Hackers suke
amfani da ita domin suyi hacking din Computer dinka
kokuma account dinka, ita ake kira da "Zamba Cikin
Aminci" wato zasuyi amfani da ku sanci da ke tsakanin ku
kai kana ganin kayarda da mutum bari kabude password
dinka agaban shi sai shi kuma ya kyalla ido a lokacin da
kake sanya password din account dinka, shi ake kira da
(eaves dropping) da zaran yaga me ka rubuta shikenan sai
yayi amfani dashi ta hanyar (Password Recovery) ko kuma
ta hanyar yin Installing wani Application wacce zata dinga
yin leken asiri ne tare da tura bayanai zuwa wurin hacker
din. (wannan ma iyaye suna amfani da ita wurin binciken
iyalin su)
3. Yaudara:
Shi kuma wannan mutum zai karbi number wayarka ne sai
yaje yasanya yayi "Password Recovery" daganan zasu turo

Cikakkiyar Kariya Page 3


Salisu Abdulrazak

maka wani Code a wayarka sai shi kuma Hacker din sa


iyayi sauri ya kira ka ta waya yace maka dan Allah an turo
maka wani Code? Idan kace: "Eh" sai yace to dan turo min
su ina jaraba cike wani File ne ko kuma wata register ko
kuma wani abun samun kudi domin dai kawai ya samu ya
yaudare ka, to kai kuma da zaran katura mishi shikenan sai
yayi hacking din sa ya cigaba da abinda yakeso yayi dashi.

Whatsapp Monitoring Hack

Wato bawai zanyi wannan bayanin bane dan kaje kayi wa mutane
hacking di nwhatssp din su ba, sai dai kawai zany ishine saboda
zai taimaka ma iyaye don binciken whatssp din iyalansu ko kuma
kannen ku domin kuga abinda sukeyi, Matakin farko Kaje "Play
Store" ka dauko wani Application mai suna; "WhatsWeb" Bayan
ka dauko shi sai ka bude shi, kana bude shi, Zai bayyanar maka da
abubuwa da yawa to sai ka danna wurin da aka rubuta;
"WhatsWeb"

Kana dannawa zakaga yana Loading, to sai ka dan jira shi


yagama.. (Wani lokaci zakaga yana sakar maka talla haka, kuma

Cikakkiyar Kariya Page 4


Salisu Abdulrazak

yana Loading, to kana iya Exit din tallar) bayan ya gama Loading
zai bayyanar maka da wani shafi da alamar Scanner, to anan zaka
samu wayarshi wanda kakeso kayi wa binciken sai ka hau
Whatsaap din shi ka bude wan iwajen da zaka ga yana da alamar
Scanner..(QR- Code) Sai kayi Scanning din wannan alamar
Scanner din na wayarka..

Daman kuma Data din ka abude take Daganan zakaga wayar ka


tafara Loading, zuwa wani lokaci kawai zaka ga gabadaya
Whatssp din shi ya bayyana awayarka, Zakaga chatting din shi da
komai, zaka dinga la'akari da duk lokacin da ka lura ya hau
whatssp to kaima a lokacin sai ka hau, kana hawa komai na
whatssp dinshi zai sauka a wayarka zaka ga komai na saman
whatssp dinshi, ba zai taba gane ka hau mishi whatssapp ba.

Allah yatai maka..

GIDAN YANAR BOGI (Phishing)

Shin kasancewa ana amfani da gidan yanar bogi don sace maka
"password" dinka cikin sauki..? wannan mummunar dabarar

Cikakkiyar Kariya Page 5


Salisu Abdulrazak

sunanta (Phishing) a ilimin kimiyyar sadarwa na zamani, Kuma fa


hakan yana yiwuwa ne wajen hanyar kirkirar shafin yanar gizo na
karya da hasashen kimiyyar sadarwa na zamani da tsaron bayanai
da ake kira da "Website Cloning" wannan tsarin na su yana da
wasu shaharrarun hanyoyin sace password guda biyu wanda kuma
ina mai tabbatar maka da kadanne daga cikin Al'umma suka san
dasu .

✓ Hanya ta farko:
Itace gina shafin internet sananne wanda yayi fice ansanshi
sosai, wanda jama'a suke hada hadar kasuwanci ko kuma
suke ziyartar sa akai-akai, irin wadannan internet din sune
kamar gidajen yanar sadarwa na bankuna, da na makarantu
wadanda ake biyan kudaden makaranta (School fees) da
wasu shahararrun shagunan saye da sayarwa to wannan
shine ake kira da "WebCloning" da zaran sun gina shafi
mai kama da na wani kamfanin da suka tabbatar ana
ziyartar shi sosai wanda zasu jawo hankalin jama'a to daga
nan sai suyi masa Register da address mai kama da wanda
akasani...

Cikakkiyar Kariya Page 6


Salisu Abdulrazak

Misali: Bari kaji; suna iya gina shafin yanar sadarwa na


"Starling Bank" kuma su hada komai iri daya dana bankin,
idan kai kuma baka haddace address din gidan yanar
sadarwar bankin ba, kana shiga nasu kawai zasu zarce dakai
na Bogin.

Babban abinda suke bukata daman sune: Bayanan ka kamar


haka: Sunanka, Kalmar izinin shiga wato password din ka
kenan, idan banki ne da zaran kashigar da wadannan
bayananan a wannan shafin na Bogi to daganan zasu zarce
ne zuwa rumbun adana bayanan barawon wato (Database),
acikin computer dinshi dake dauke da gidan yanar sadarwa,
a maimakon na bankin da kai ka ke zato ko kake da
tabbacin a shafin su kake, daganan zasu kwashe bayanan ka
cikin sauki don cin ma manufarsu ta mugunta (Shiyasa
acikin wannan littafi mai taken "Cikakkiyar Kariya" nayi
maku bayani sosai akan yadda zaku tantance shafin gaskiya
da na Bogi)

Cikakkiyar Kariya Page 7


Salisu Abdulrazak

✓ Hanya ta biyu:
Itace wadda zakaga ana aiko maka da sakonnin Bogi wato
(Spam Mails) ta "ImeI" din su masu
Dauke da"Web Link" to wannan web link din yana dauke
da wasu bayanai masu jan hankali..

Misali: a sakon zasu iya turo maka da wani abu mai


matikar muhimmanci sai suce maka idan kanaso kasameshi
to sai kabi wannan Link din, sai su ajiye maka link din kai
kuma kana Danna wa zaka tsinci kanka a shafin nasu na
Bogi (Cloned site) wurin da zaka shigar da bayanan naka,
Da yawan mutane masu mu'amulla da ImeI har ma masu
Facebook nasan wasu da yawa a cikin ku kunsha samun irin
wadannan messages din na Bogi, wadanda za'ayi maka
bayani wata garabasa ta kudi ko kuma wani message na
tausayi ko na neman taimako, ko bahaka ba..?
Masu wannan dabarar ta karshe wato asalin mugayen sukan
ajiye Link akasan message din nasu wanda kana dannawa
to akwai wata Fasaha mummunar fasaha dake makale a
jikin bayanan da ka matsa.

Cikakkiyar Kariya Page 8


Salisu Abdulrazak

Yar karamar Manhaja ce (Software) da aka gina ta da


dabarun gina manhajar Computer mai suna: "JavaScript"
wato bayanan dake cikin wannan Fasahar aikin su shine; da
zaran ka danna wannan Link din sai su shige dakai cikin
manhajar ("Browser") da kake amfani da ita kait saye.

Shafin da zai bude maka babu wani abun kirki aciki tunda
daman sun budeshi ne domin yaudara.. Duk shafin da ka
shiga ka bayar da sunanka, (Username) da Kalmar izinin
shiga (Password) ko kuma number sirrin ka na ATM, nan
take wannan fasahar zata rika aikawa wanda ya ginata
(Developer dinta) wadannan bayanan da ka rubuta, kai
tsaye wannan Manhaja ita ake kira da "KeyLogger" saboda
tana aika bayanan ne dai dai lokacin da kake shigar dasu
wanda da zaran ka latsaa wayar ka ko kuma Computer
dinka shikenan ka samu gaggarumar matsala, daga lokacin
zasu iya kwashe shekaru masu yawa suna cin Karen su
babu babbaka acikin na'urarka, suna ganin duk wasu
surikan ka da password dinka...

Cikakkiyar Kariya Page 9


Salisu Abdulrazak

Wannan hanyar itace wadda tafi kowace irin kwayar cutar


computer hadari aduniyar kimiyya da fasahar bayanai na
zamani.

Domin kaucewa irin wadannan hadarirrika na hacking din


Facebook dasauransu, sai ka kiyayi sanya password dinka
da kasan ba mai karfi bane (Strong Password) password din
ka ya kasance wanda ba kowa zai iya hasashen shi ba,
kuma ka boye number ka da gmail dinka a Facebook su
zama kai kadai zaka iya ganin abin ka wato kamayar dasu
(Only Me) idan kashiga Setting din ka na Facebook zakaga
Privacy&Security nan zakashiga ka se ta komai.
Sannan ka seta Facebook dinka da whatssp dinka "Two
Factor Authentication" hakan zai kara baka tsaro matika a
Accounts din ka na social media.

Cikakkiyar Kariya Page 10


Salisu Abdulrazak

KARIYA DAGA KO WANE IRIN HACKING NA SOCIAL


MEDIA

Yan kwanakin nan ina ta jin korafi wajen jama'a cewa ana ta masu
hacking accounts din su na shafin Facebook, kuma duk yawanci
idan suka min bayani sai na fahimci bama irin Black hack dinnan
bane, Simple hack ne wato "Social Engineering".

Hakan yakara min kwarin guiwa wurin rubuta wannan littafin


domin jama’a su iya kare accounts dinsu.

Da farko idan FACEBOOK dinka ne akayi hacking wanda ya


kasance a duk sanda kaje hawa Account din naka a "Facebook
Lite" idan kasanya number, kuma ka sanya Password, sai ya nuna
maka "Wrong Pin" kaga kenan wani ne yayi awon gaba da
password din naka saboda mugunta..

To kaikuma idan kaga haka, sai ka natsu ka kwantar da hankalinka


,Kaje kai tsaye a browser dinka ka rubuta; facebook.com

Idan ya bude aka sa zakaga "Forgot Password" kai kuma kawai sai
kashiga, kasa Lambarka Wanda kabude Account din da ita,
daganan zaka ga ya nuna maka sunanka, zasu turo maka "6/5"

Cikakkiyar Kariya Page 11


Salisu Abdulrazak

"Digit Confirmation Code" sai kasa a wurin, shikenan sai kasa


sabon "Password" din da kakeso, Insha Allah shikenan Account
din ka zai dawo Mallakinka..

Allah yasa adace..

KARE KAI DAGA MASU KUTSEN ASUSUN BANKI


(BANK-ACCOUNT)

Wannan lokaci da muke ciki ana samun mutane mararsa imani da


tsoron Allah, wadanda ba za suyi amfani da basirar su da ilimin su
wajen neman halak ba sai dai wajen neman haramun din da bazai
amfane su da komai ba duniya da lahira, Sune wadanda zaku ga
suna sacewa mutane kudaden su daga banki ta hanyar amfani da
BVN ko Account Number din mutum, kana kwance daki sai dai
kaji wayar ka tana aleart kudade sai fita suke, da yake kasan idan
zasu yi maka irin wannan datsen (Hacking )to akwai ka'idar yadda
zasu dinga cire kudaden, zata iya yiwuwa kaga suna ta Cire dubu
goma-goma, kai kuma gashi kana da nisa da banki bare kayi gudu
ka sanar dasu a haka dai kafin ka yunkura sai kaga kudaden
account dinka sunkare, kuma idan kaje banki kayi Complain su
kasa dawo maka da kudadenka..

Cikakkiyar Kariya Page 12


Salisu Abdulrazak

To insha Allah zanyi maku bayanin wasu Codes da ake amfani


dasu da zaran kaji kudaden ka suna fita bakasan dalilin fitar su ba,
zakayi sauri kayi Block din account din aka, wanda hakan zai
tsayar da transfer din account din idan kuma ma da ATM dinka
ake cire kudin to zasu daina fita har sai da cikakken izininka, daga
baya sai kaje Banki kayi masu Complain sai su gyara maka komai
sai su bude maka account dinka! Hakan lallai babban tsaro ne
domin idan babu wannan Codes din sai dai fa kaje bankin kuma
kafin kaje zasu iya kwashe kudaden sannan ma idan kaje bankin
sai sun baka wani Form ka cike kafin ma suyi Blocking Account
din naka, kaga kuwa ai zuwa lokacin kudaden ka sun canza
mazauni..

1. Zenith Bank
Da zaran kaga fitar kudi daga account dinka, ko an sace
maka ATM kuma ansan Lambobin ka na sirri, ko kuma an
sace maka wayar ka kuma layin da yake cikin wayar da
shine kake harkokin ka na banki, to sai ka nemi wata wayar
idan an sace maka taka wayar ne, idan kuma ba wayarka a
ka sace ba to zaka iya yi da wayarka, Sai ka danna
wadannan numbers din; *966*911# sai ka danna wurin

Cikakkiyar Kariya Page 13


Salisu Abdulrazak

kira, Bayan ka danna wadannan numbers din to zasu bukaci


da ka saka Account number din ka da kake son ka dakatar
da Transaction din nata, daganan zasu bukaci kasaka
lambobin sirrin ka (Pin).
Kana saka wa shikenan, zasu dakatar da fidda kudi daga
wannan asusun naka harm sai kaje bankin naka ka bada
izinin a bari kudi ya dinga fita.
2. FirstBank; kaje wajen message dinka katura "Block" zuwa
ga 30012, shikenan zasu rufe account din.
Note: Amma shi First Bank dole sai dai kayi da number
dinka da ka bude account din da ita..
3. UBA BANK; *919*9#
4. ACCESS BANK; *901*911#
5. STERLING BANK; *822*911#
6. FEDILITY BANK; *770*911#
7. GT BANK; *737*51*74#
8. UNION BANK; Sai kaje wurin rubuta message sai ka
rubuta BLOCK CARD NUBAN zuwa ga wadannan
lambobin 20123.

Cikakkiyar Kariya Page 14


Salisu Abdulrazak

9. FCMB; Zaka kira wannan number a waya


+2342798800 kai tsaye zasu dauka suyi directing dinka
yadda zaka rufe.
10. WEMA BANK; *945*911#

YADDA ZAKA BI DIDDIGIN BARAWO BAYAN YA SACE


MAKA WAYARKA

Irin wannan lokacin ba sai na fada maku ba kunsan cewa tabbas


akwai mutane yan zaman banza wadanda burinsu bai wuce suga
wani yayi sakaki da kayan sa ba su kuma su dauke, ma'ana dai da
kayi sakaki da wani abu naka sai suzo suyi gaba dashi su barka a
hoto, Akwai lokutta da dama da idan barawo ya sace maka
wayarka baya zuwa yasiyar da ita sai dai kawai zai cire layikan ka
(Simcards) sannan yaci gaba da amfani da wayar, kokuma kawai
watarana sai ka ajiye wayar ka wani wuri kuma ka dawo Kaman ta
wurin da ka ajiye ta, kaduba-kaduba amma baka ganta ba, kokuma
dai wani ya dauketa yaboye ta domin ya razana ka ko kuma yaga
yadda zakayi ,To insha Allah acikin littafin nan zana bayyana
maku wata hanya da na gano wadda zata nuna maku Location din

Cikakkiyar Kariya Page 15


Salisu Abdulrazak

inda wayar ka take insha Allah, Sannan kuma ta wannan hanyar


zaka iya saka wayar ka Security bayan wani ya karbeta, misali;
kunje taro haka wani wuri ko kuma a makaranta sai malamin ku ya
kwace wayar ka kuma gashi ya karbeta a lokacin babu security a
jikinta kuma kai baka son ya duba maka abubuwan dake cikin
wayar to ta wannan hanyar zaka iya saka wayar security ta wayar
abokinka, Da farko dai inaso ka tabbatar Email dinka yana akan
wayarka, idan kuma baka sanya shi ba to lallai kayi sauri kasanya
saboda yanada matikar amfani kuma dashi ne zaka samu damar
nemo wurin da wayar ka take..

❖ Matakin farko:

Kaje playstore ka dauko wannan application din: "Google Find


My Device" kawai ka rubuta "Google find My device" zakaga ya
bayyana a sama.

To misali: sai muce ai yanzu haka an sace maka wayar naka!

To kaga kenan wannan Application din zakayi download din sa ne


a wayar abokin ka domin gano wurin da wayarka take.. Ina fatan
an fahimta..? To bayan ka dauko application din sai kashiga kai
tsaye cikinsa, bayan ya bude maka zaka ga ya bayyana maka da;

Cikakkiyar Kariya Page 16


Salisu Abdulrazak

"Sign in as guest" To sai ka danna wurin, kana danna wa zai bude


maka wani wuri da zakaga ya baka space ka rubuta Email dinka,
To anan wane Email kenan zaka rubuta..?

To sai ka natsu sosai kasanya Email din wayarka da a ka sace ko


kuma da kake neman location dinta, shiyasa nace maka ka tabbatar
akwai Email akan wayar naka..

To bayan kasaka Email din wayar naka daka ke nema, sai ka


danna Next, Bayan ka danna next zai kawo ka wani box da zaka
sanya"Password".

Wane password kenan?

Password din wayar naka da aka sace na Email dinka.

Meyasa zata nemi password?

Saboda tana so ta tabbatar da cewa shin dagaske ne mai wayar ne


yakeso ya gano wurin da wayar nasa take kokuwa ,saboda ai kaga
kai kadaine kasan password din, Bayan kasanya Password din
shikenan, zakaga alamar "Next" sai ka dannashi, Kai tsaye bayan
ka danna zai nuno maka taswira (Map) din wurin da wayar taka
take, idan ka lura sosai acikin taswirar zakaga wata alama ,to sai

Cikakkiyar Kariya Page 17


Salisu Abdulrazak

kadinga zooming dinta har sai ta matso kusa da i donka domin


kasamu ganin wurin da wayar taka take sosai, idan kuma daman
kasanya Email din ka a wata wayar bayan asalin wayarka to zata
bayyanar maka da Location din waya biyu kenan kuma kowa ce
da sunanta, to a ciki tunda taka kake nema sai kaje kai tsaye wurin
takan, Daga lokacin zakaga wata alama wadda zakabi takai ka har
wurin da wayar naka take, kuma kana zuwa wurin da wayar naka
take, zakaga alamar ta tsaya daidai wurin, Idan kuma ya kasance
shi wanda ya dauki wayar ya bude data din wayar yana amfani da
ita ko kuma ya bude Wifi din wayar, to acikin wannan app din
zakaga ta bayyanar maka har charging dake cikin wayar naka da
aka sace tare da sunan wayar, Daga cikin abubuwan da wannan
application din yake yi shine: kamar yadda na fada maku misali
idan wayar naka ba sace ta akayi ba kawai ka manta wurin da ka
jiye ta ne kuma kana nemen ta, to a cikin wannan app din bayan ya
bude ka sai ta Email din wayar da password dinka, to zakaga zabi
(options) guda ukku to sai ka dauki zabin farko da zakaga ya
rubuta "Play Ringtone" to a lokacin ita wayar naka daka manta
inda ka a jiyeta zata fara kara tana ringing koda kuwa tana silent
ne.

Cikakkiyar Kariya Page 18


Salisu Abdulrazak

Abu na biyu shine:"Secure Device" misali ace lokacin da barawon


ya sace maka wayar naka sai ya kasance daman acikin wayar
babu password babu wani security to kai kuma kanaso kasanya ta
security yadda bazai iya amfani da ita ba, to kai tsaye a cikin
wannan Application din zakaga "Secure Device" sai kashiga
cikinsa kai tsaye zakaga ya bayyanar maka da "Set password" to
sai ka shiga ka saita password din da kakeso, kana sanya wa
shikenan wayar naka da aka sace zata shiga password!

Allah yatai maka.

YADDA ZANBI DIDDIGIN WAYATA TA HANYAR


AMFANI DA IMEI DIN WAYATA

Kamar yadda nace wasu basa sanya Gmail akan wayar su wasu
kuma koda sun sanya a kan cire Gmail din idan aka sace wayar,
wato kenan yanzu barayin wayar sun karo wula kanci kenan, sun
gane ana bin diddigin su ta Gmail shiyasa suka koyi Cire Gmail
din, To ni kuma kullun burina nasamu hanyar da duk wani barawo
na na'ura zai kasance a fargaba a duk sanda yayi satar wata na'ura
daba tashi ba, haka yasa na kawo maku hanyar bindiddigin wayar
taka ta hanyar IMEI wanda shi kuma wannan IMEI yana zuwa da

Cikakkiyar Kariya Page 19


Salisu Abdulrazak

wayar ne tun tana sabuwa dashi aka kirkire ta kai idan ma sabuwa
kasiyi wayar ka to zakaga wadannan IMEI Numbers a jikin kwalin
wayar naka, zakagan su guda biyu, da Sim1, da Sim2, Idan kuma
ba sabuwa kasiya ba, taka Second hand kasiye ta shima cikin sauki
zakaga IMEI Number dinka idan ka danna wadannan Numbobin
*#06#.. Ina fatan kowa zai danna wadannan Numbobi yanzu, Idan
ka danna ka gansu, to kayi sauri kasamu biro da takarda ka kwashe
su ka ajiye su cikin a kwatin ka saboda gaba zasu iya maka amfani
idan barawo ya sace maka wayar, (Bama Fatan Faruwar Hakan)
To matakin farko, mu kaddara yanzu an dauke maka wayar taka,
to kuma daman ka kwashe wadannan IMEI Numbers, to abinda
zakayi anan shine, sai kaje ka samu wayar Abokin ka ko baban ka
ko kanwarka Ko wani naka dai, To ka tabbatar wayar abokin naka
akwai Data, sai kaje kai tsaye kashiga Chrome browser dinshi,
bayan ta bude sai ka natsu sosai ka duba daga can sama gefen
damar ka zakaga wasu digo guda ukku (...)
Sai ka taba shi, bayan ya bude zai baka wasu Options da yawa to
sai kadinga Scrolling dinsa zuwa kasa har ya kawo ka wurin da
aka rubuta "Desktop Site" a gaban shi zaka ga alamar akwaiti
(box) to idan kaga alamar ticking (Good) a cikin box din to sai
kabarshi, idan kuma kaga babu alamar to sai ka danna akwatin

Cikakkiyar Kariya Page 20


Salisu Abdulrazak

domin alamar ta fito, to daganan sai ka fito daga wannan layin, ka


dawo wajen da ake rubuta "Web address" sai ka rubuta wannan;
https//my-phonefinder.com/ Bayan ka gama rubuta wannan
address din sai kaje ka danna Alamar searching..
Kana danna wa zai fara Searching bayan ya gama zai nuno maka
abubuwa a ciki, A farko zakaga akwati guda biyu, Daya an rubuta;
"Phone Number Or IMEI" dayan kuma zakaga an rubuta "Find"
To a wurin da a ka rubuta; Phone Number or IMEI to anan wurin
ne za ka rubuta wadannan numbobin naka dana fada maku wato
(IMEI Number) dinka, bayan ka gama rubuta su kuma ka tabbatar
ka rubuta su daidai a wurin, Bayan ka gama sanya su sai kaje
wajen alamar "Find" sai ka danna, Kana danna wa kai tsaye zata
bude maka, zata fara bayyano maka bayanan wayar da duk abinda
ke cikinta da sunan wayar da hoton wayar, da sunan kamfanin
wayar, idan ka dinga yin kasa (Scrolling) zakaga tana bayyano
maka irin layin dake cikin wayar,da duk wasu abubuwa da suka
shafi wayar, A hankali kana Scrolling zakazo daidai wurin da aka
rubuta "VIEW IN MAP" to a nan zaka shiga, sai ka duba kaga
ainahin location din inda wayar taka take, Koda kuwa ya karya
layukan wayar ya zu ba nashi sai ka ganoshi, sannan tabbas a na
canza IMEI to amma canza IMEI din yana da daukarl okaci dan

Cikakkiyar Kariya Page 21


Salisu Abdulrazak

haka kafin su canza kagano su..(Naso nayi bayanin yadda ake


canza IMEI din, to amma saboda barayin zasu iya amfani da hakan
don cuta) Daganan zaka iya bin wannan barawo har gidan su ka
karbo wayarka tunda ba tashi bace (Barawon banza).
Allah yakara tsare mu baki daya..

YADDA ZAKAGA HOTON BARAWON DA YA SACE


MAKA WAYARKA BAYAN YA SACETA

Nasan kila kuna gama karanta Heading din wannan rubutun


zakuce; "Kamarya kuma naga hoton wanda ya sace min waya
bayan kuma ya tafi da wayar, ta wace wayar zanga hoton nasa,
kuma tayaya..? To kunsan yanzu lokaci ne naTechnology duk
abinda ka ke tunanin bazai yiwu ba to a wajen kimiyya da fasaha
mai sauki ne, Daga lokacin da barawo ya sace maka waya

To idan wayar taka tana cikin wannan tsarin da zan fada maka
yanzu to lallai zaka ga hoton sa duk da ba wayar ah annunka.

Nasan tambayar da zakayi itace; "Wai ta yaya zanga hoton nasa


ne..??

Cikakkiyar Kariya Page 22


Salisu Abdulrazak

To amsar itace: ta Email dinka, bayan barawon ya sace wayar ya


tafi da ita, kasan matakin farko zaiso ya cire wayar daga Security
din da kabarta ,to da zaran ya fara kokarin cire security din, tun
da baisan asalin security din ba to yana sanya wa zata nuna
"Wrong Pin" to da zaran taba shi wrong pin zata dauki hoton sa
zuwa Email dinka..Ta a jiye maka shi acen, Kaga kenan duk
wanda yayi kokarin cire security din zata dauki hotonsa zuwa
Email dinka Kana dawowa kaga babu wayar, to sai ka nemi
wayar Abokin ka kawai sai kayi login din Email dinka, kana
hawa zata bayyanar maka da hoton barawon idan har yayi
attempting bude security din. Matakan da zakabi sune kamar
haka: kai tsaye kaje Play Store ka dauko wannan App din "App
Lock-Finger Print" ka natsu sosai domin kasan akwai irin
wadannan apps din wadanda kuma ba duka suke aikin da a keso
ba dan haka ita wannan app din da zaka dauko zakaga sunan
kamfanin da sukayi ta akasa shine; "Sp soft" Bayan kafara dauko
shi zai iya nuna maka to ya kamata ka sauke manhajar Helper-
(Applock), to kawai karka bata lokaci sai shima kayi installing
dinsa bayawani dadewa zakaga shima ya gama installing a
wayarka, amma kuma wasu zakaga baya nuna masu hakan to
idan bai nuna maka ba kawai shikenan sai kayi download din app

Cikakkiyar Kariya Page 23


Salisu Abdulrazak

din kayi installing dinta, Bayan yayi installing ka bude shi kai
tsaye zai bayyanar maka da bangaren sanya password, ma'ana
kasanya Kalmar sirrin da kakeso ka seta shi da ita, to ba tareda
bata lokaci ba sai ka zabi password din da kakeso kasanya mishi,
kana sanya wa zakaga ya rubuta maka "Confirm password" sai
kasa ke sanya wa, daganan zai bude zai tambayeka, shin kanaso a
hada shi da "Finger Print"..? kawai sai kace Eh.. Dan haka sai
kadanna "Yes". To bayan kagama zai bude maka, A cikinsa
bayan ya bude zakaga wata alamar plus + Sai ka dannata
Zakaga "Password Setting" sai ka dannashi, bayan ka danna
zakaga "Lock type" sai ka danna shi..To anan zai baka zabi,
kamar haka; "Password (pin)" "Pattern" "Password character"
"Gesture" To anan kai kuma sai ka zabi wanda kake so a ciki, to
idan na farko ka dauka wato "Password"

Sai ka danna shi daganan zai kawo ka wurin da idan kanaso ka


seta shi da Finger print, to bayan ka seta shi sai ka dawo ac ikin
Menu din app lock din sai kaje ka shiga setting shi kuma zaka seta
Yare (Language) haka da dai abinda ya kamata wanda kana ganin
su zaka gane me nake nufi ba sai nayi maka bayani ba yanzu,
Bayan ka gama da wannan, sai ka duba wani wuri da zaka ga an

Cikakkiyar Kariya Page 24


Salisu Abdulrazak

rubuta "Observer" kana shiga cikin sa zaka ga hoton drawing na


kai din mutum, a kasan hoton zakaga an rubuta maka: "Zan dauki
hoton duk wanda yayi kokarin bude security din wayar kuma bai
samu damar bude wa ba har na san ya mishi "Wrong pin" Ma'ana
yasanya Password din ba dai dai ba, to zakaga wata alama a sama
sai ka danna ta alamar yarda da abinda manhajar ta fada maka
kenan, kana danna wa zaka seta komai daganan zakaga ya nuna
maka komai yayi daidai, Kana koma wa baya zakaga yayi ma
"Observer" alamar good.. Yayi marking dinta.

Ma'ana yanzu" Observer" ya fara aiki, to bayan kagama sai ka


sake shiga ciki zakaga alamar Setting a saman observer, sai ka
danna shi kashiga cikin sa, zai bayyana maka da:

"Taking Picture" da "Recording Vedio" da kuma "Do Not Touch


My Phone" to sai ka zabi wanda yayi maka idan ka dauki na video
din to har video din mutumin zai yi maka kaji maganganun da
yake cewa bayan ya saci wayar, idan kuma hoton nashi ne to sai
kasanya "Taking Picture" shikenan zai daukar maka hoton ya tura
maka a Email dinka, idan kuma na ukkun ka dauka wato "Do Not
Touch My Phone" to shi kuma wannan aikin sa shine duk wanda

Cikakkiyar Kariya Page 25


Salisu Abdulrazak

ya dauki wayar naka yasanya password din ba daidai ba to zata ce


mishi; "Karka Daukar Min Waya Ta" da yaren turanci.

Allah yataimaka..

DAME AKEYIN HACKING.

Mutane da dama suna mamakin irin basirar da Allah yayi wa


Hackers, wasu ma su kanyi mamakin shin wai su hackers dinnan
Dame Sukeyin Hacking.? Shima hacking ilimi ne mai zaman
kanshi wanda sai ka nema zaka sanshi, Sannan yin hacking dole
akwai buqatar saika mallaki kayan aiki, wato kamar idan zakaje
makaranta sai ka nemi biro da takarda, haka shima hacking sai ka
nemi kayan aiki idan babu kayan aiki haka zalika babu hacking..

Acikin wannan littafi Zan lissafo maku wasu kayan aikin da


akeyin Hacking dasu guda 8 da kuma kalan aikin da sukeyi awurin
hacking din inshaAllah! (Gargadi: sanin su kadai bazai baka
damar yin hacking ba)

Gargadi: Nasan da yawa zasu ji tsoron meyasa zanyi wannan


bayanin ai zan iya budewa gurbatattun mutane kofar neman

Cikakkiyar Kariya Page 26


Salisu Abdulrazak

wadannan Tools da zan bayyana kuma suyi amfani da ita wajen


gurbatattiyar hanya.

To inaso kusani cewa kamar yadda na fada maku da farko shi


hacking ilimi ne dole sai ka koya zaka iya, misali yanzu kanada
biro da takarda amma kuma baka zuwa makaranta babu kuma mai
koya maka karatu shin zaka iya karatu..? Haka zalika shima
hacking koda ka mallaki kayan aikinshi idan har ba'a koyar dakai
ba, to lallai wadannan Tools din sun zama kamar hoto a wurinka..

Dan haka bari mufara:

1. Angry IP Scanner (ipscan):

Wannan Tool ne mai zaman kanshi wanda yake taimaka wa


hacker wurin gano ainahin IP Address na abinda akeso ayi
hacking, misali kamar IP Address din wani banki haka,idan
kanason ka shiga cikin rumbun adana bayanan su da sauransu,
kuma ana hacking din computer ta sanin IP Address din computer
din dashi.

Cikakkiyar Kariya Page 27


Salisu Abdulrazak

1. Kali Linux:

Wannan gama gari ce kusan kowa yasanta anyi lunching din ta


ashekarar 2015, wannan tool din

Itace tool din da yawancin hackers suke jin dadin ta sosai saboda
irin Features din dake cikinta, sannan da ita zaka samu damar
running dinta da CD ko USB batareda sai kayi wani Installation
ba, Wato wannan Tool din tana da duk irin abubuwan da kake
buqata wurin yin hacking, wanda acikinsu akwai; Kirkirar Fake
Network, Spoof Messages, da samun damar Cracking din WIFI
Password.

2. Cain &ABEL

Suma wadannan suna cikin manyan kayan aikin hackers , wanda


suke aiki wajen ruguza Microsoft Operating System, wato su
wadannan zasu taimaka maka wajen Recover din wireless network
password, user account, sannan zaka iya amfani dasu wajen
gudanar da Bruteforce method idan kanason kayi Cracking wani
password, haka zalika zaka iya amfani da su wurin record din
VoIP conversation sessions. Ana dai amfani dasu wajen kwace
Accounts dinka ko wane iri ne.

Cikakkiyar Kariya Page 28


Salisu Abdulrazak

3. Burp Suite:

Wato wannan tool din bala'ine, yana burgeni sosai, wurin aiki
dashi zaka iya amfani dahi wajen gano Must Vulnerable Website
(Ma'ana Websites din da aka bude su ba'a saka masu tsaro mai
kyau ba,) to zakayi amfani da wannan kayan aikin ka gano ire-iren
wadannan sites din kuma ka iya kwacesu ko ka rufesu.

4. Ettercap:
Kun ga wannanTool din.. Ina tsoron shi kwarai dagaske, domin
dashi ake kwashewa jama'a kudin dake cikin akwatin bankin
su,wlh inajin takaicin barawo marar zuciya da bazai iya amfani da
wannan fasahar tashi ba wajen kawo tsaro da cigaba ba sai cuta,
Zaka iya amfani da wannan Tool din wurin transferring kudade
zuwa account dinka kokuma kayi transferring wasu Data zuwa
inda kakeso , kokuma ka saurari wasu maganganu da kakeson
saurara a inda kakeso shine muke kira (Eavesdrop on a
Conversation).

6. John the riper;


Wannan tana cikin manyan kayan aikin Brute Force password
Cracker wacce take amfani da DictionaryAttack, wato yawancin

Cikakkiyar Kariya Page 29


Salisu Abdulrazak

hackers suna wahala wurin password cracker wato su lalata


password din wani tsaro na banki ko na wani kamfani domin
ashiga ayi sata, yawancin su basu san "John the riper" itace Tool
din da ake amfani da ita cikin sauki ayi hakan ba. Idan har
Encrypted password ne to babu kamar "John The riper" a yanzu
kam.

7. Metasploit:
Ita ma dai kamar "Angry IP Scanner" ce, tana kokari wurin search
din location da kuma must Vulnerable website haka...

8. Wireshark and Aircraft-Ng:


Wannan ita ma bala' ice wurin aiki, tana amfani wajen detecting
wireless connections da hacking din User da password ita Aircraft-
ng da ita ake monitoring Wifi security, kaga ita tana da amfani
sosa iwajen saka tsaro da lalata shi…

Yawancin mutanen mu basusan wadannan Tools din ba amma sai


kaji mutum yana cika baki shi ala dole Hacker ne, Idan har
bakasan wadannan Latest Tools din ba, to haryanzu da sauran ka
kadaina kiran kanka Hacker. Kuma sanin su da kayi yanzu bazai
baka damar da zaka iya amfani dasu ba.

Cikakkiyar Kariya Page 30


Salisu Abdulrazak

Kayi kokarin zama Cryptology wanda su basa cutarwa..


Allah yasa mu dace.

ILIMIN HACKING (KUTSE)

Kamar yadda nake fada maku shima fa hacking ilimi ne wanda sai
ka koya zaka iya, ba wai cika baki da hacking din Facebook
account din bayin Allah ba shine hacking ba, wannan kawai dai
kana shirme ne tare da daukar alhakin mutane amma ba shine ai
na hin duniyar hacking ba.

Barikuji; idan kanaso ka zama shahararren white hat hacker wanda


har jami’an farin kaya da yansanda zasu dinga aiki dakai domin
binciken mugaye da azzalumai na internet to fa sai ka tsunduma
wajen karantar bangaren dan'uwa, kuma idan ka koya ka iya to ya
zama hanyar da zaka dinga taimakon Addininka , basai na maku
dogon bayani ba kungane abinda nake nufi, Wato kwarewa a
Hacking yana bukatar ka maida hankali bangaren koyon wadannan
abubuwan da zan lissafo guda 10 yanzu inshaAllah…

Cikakkiyar Kariya Page 31


Salisu Abdulrazak

1. Intermediate Computer Skills:

Wato yana da kyau ace ka iya kirkirar Word documents kokuma


kana iya surf din web, sannan

Dole ya kasance kasan yadda zaka dinga amfani da mabanbantan


Commands Lines na Windows, ka iya seta network, sannan ka iya
Editing din Registry din Computer dinka..

2. Good Networking Skills:

Wato yawancin hackers sunfi yin ta'adi a Online sunfi yin barna a
saman yanar gizo dan haka dole ka koyi ilimin Networking
daTerms dinsa kamar irin su;

• WEP versus WPS password


• NAT
• MAC Addresses
• Routers
• Ports
• VPN
• IPv6
• DNS

Cikakkiyar Kariya Page 32


Salisu Abdulrazak

• Subnetting
• DHCP
• Private and public IPs
• Ipv4
• OS IModelling
• Packets
• TCP/IP

3. Using a Linux operating system:

Yawancin hackers sunfi amfani da "Linux OS" saboda tana barin


programs da tweaks a windows da kuma Mac operating system.
Yawancin hacking tools din sunfi aiki acikin wannan operating
system din..

4. Virtualization:

Kafin kafara kokarin yin hacking farko kafara sanin menene


zakayi kuma ka tabbatar komai kanayin shi akan tsari ba tareda
kuskure ba, kwararren hacker baya barin kuskuren da za'a
kamashi, idan kasamu kwarewa kana so ka jaraba baiwar naka to
karkace zaka fara da babban aiki, kafara jaraba Hacking din ka ga
karamin abu haka, kamar "Virtualization Software package"
Cikakkiyar Kariya Page 33
Salisu Abdulrazak

kamar irin su; VMWare Workstation. Wajen amfani da Virtual


Workstation hakan zai baka damar kayi gwajin fikirar ka ta
hacking ba tare da wani hadari ba kuma batare da kajawo wa
computer dinka wata matsalar ba ko lalacewa, saboda idan kana
koyo kace zakayi hacking din wani abun bayan baka kware ba to
Ido zai raina fata domin kana iya lalata computer dinka.

5. Tc dump or Wireshark:

shi dai Tc dump anfi sanin sa da Command Line Protocol analyser


ko kuma kace Sniffer duk sunansa ne Tool ne na hacking mai dan
bala'in sata. Shi kuma Wire shark yawanci mutane sun san shi
shima aikin shi iri daya da Tc dump..

6. Knowledge of security Technologies and concepts:

Lallai duk hacker yana da bukatar mafi muhimmanci a cikin


Concept and technologies wanda

Yake da alaka da information technology. Saboda haka yana da


kyau kasan Wireless Technology And Concepts irinsu; "Secure
Sockets Layer" (SSL) Firewalls, Intrusion Detection System
(IDS), Public Key Infrastructure (PK) da sauransu.

Cikakkiyar Kariya Page 34


Salisu Abdulrazak

7. Scripting Skills:

Kasamu damar iya kirkira da editing din Scripts hakan zai baka
damar ka iya kirkirar naka Tool din, ta yadda zaka zama
Independent! Kana harkar ka ba ruwan ka da amfani da tools din
wasu, zaka kirkiri kayan aikin da ba kowa yasanta ba kayi amfani
da abin ka wurin kai hari, to idan kanaso ka kware wajen hakan
dole ka maida hankali wajen karantar Scripting language kamar
irinsu; Ruby on rails, kokuma Python.

8. Database Skills:

Idan kanason kasan yadda hackers suke kutse su fada cikin


rumbun adana bayanan mutane ko kuma kanaso ka iya hakan to
yana dakyau ka sanshi yaya ma database din take aiki da sauransu,
dan haka yana da kyau kasamu kwarewa a "Database management
system" kamar irinsu; Oracle, ko MySQL.

9. Reverse Engineering:

Shi wannan zai baka damar ka iya converting piece na malware


kokuma mai kama da Exploit in to more advanced hacking tool.

Cikakkiyar Kariya Page 35


Salisu Abdulrazak

Daga lokacin da ka fahimci yadda "Malware da Exploit features


suke aiki to tabbas kasamu damar gane yadda ake cikakken
hacking din computer.

10. Cryptography:

Wannan skill din yana baka damar kasan yadda hackers suke
samun damar boye kan su idan zasuyi barna ko ta'asa awani wuri
to zaka iya gane yadda suke batar da sawu kaima kuma zaka iya
koya , sannan zai baka damar gane mabanbantan Weakness
Algorithm wadanda ake amfani dasu wajen Decrypting Personal
Information kamar irinsu; Stored Password.

Allah yatsare mu da shairinsu.

Cikakkiyar Kariya Page 36


Salisu Abdulrazak

HAKKIN MALLAKA

Gargadi: ni Salisu Abdulrazak marubucin wannan littafi mai suna


cikakkiyar kariya, ban yarda wani ko wata ya dauki wani sashi na
littafin ba yayi wani abu dashi ko makamancin haka batareda
izinina ba kuma wannan littafi an bugashi ne domin amfanuwar
yan Arewa domin sanin muhimman hanyoyin kula da kai ba domin
cutarwa ba.

RUFEWA

Ina mai jawo hankalin matasan mu yara da manya mata da maza da


lallai su kula sosai da duk wasu lambobin sirri da za’a basu a banki
da kuma lambobin sirrin Accounts din su na Social media, karka
yarda wani ya kiraka a waya yace katuro min shi su zaiyi maka
wani abu ko zai cike maka wani abu ko yace maka daga banki
yake, kaje bankin da kanka domin tabbatar da gaskiyar sa.

Dole matasan mu su mike suzo mu hada kai domin ganin mun


ciyar da yankinmu gaba game da abinda ya shafi ilimin fasaha idan
muka kwanta wasu zasu dinga cin moriyar mu muna zaune muna
kallo.

Cikakkiyar Kariya Page 37

You might also like