You are on page 1of 256

💝KYAUTAR KODA💝

(It's about love, sacrifice, hatred, and destiny)

*First edition*

_by Noor Eemaan_

Wattpad
@NoorEemaan

ELEGANT ONLINE WRITER'S📚🖊

In the name of Allah, most glorious, most


merciful.

Allah ya bani ikon rubuta d'aidai, ya hane ni da rubuta akasin haka...👏

*Wanna labarin k'irk'irarren labari ne, nawa ne, mallaki nane.., ban yarda a juya min shi ta kowace siga ba,
ko karanta shi a wata manhaja ba tare da sani na ba, idan kunne yaji...*

Alhamdulillah dukkanin yabo sun tabbata ga ubangiji mai sammai da kassai, am back again da wasu novels
har biyu KYAUTAR KODA da PAPI NE! Ni Bazance komai ba, Amma ina tabbatar muku zaku so novels din💯 in
sha Allah...

This whole book is dedicated to my love (Aaban)❤

*_wanna book din ba sabo bane, tsofaffin fans dina sun san da hakan, ina kara reposting ne wa new fans
da ma wanda yake so ya sake karantawa_*🥰

_idan kina/kana da ra'ayin karanta kyautar kod'a dan Allah ku fara bi yanzu, ba sai na yi nisa a dinga cewa
daga farko, ku yi ta sani sub akai-akai_😫

Editing is not allowed❌

https://facebook.com/groups/943534712916776/

Masu amfani da Facebook sai kuyi join wan nan link din

In the name of Allah, most gracious, most merciful...

Page 1-2

*LAGOS*
_Victoria island_
"RSVP restaurant" shine sunan dak'e rubuce baro baro a had'add'en restaurant di'n, duk da k'asancewa
babban wuri ne, amma talaka kan iya zuwa suma su kashe d'aid'ai aljihun su.

Yammanci ne da misali karfe biyar, mai cike da ni'ima da sanyin d'ad'i daga rabbul samawwati, wata
K'yak'yyawar matashiyar buɗurwa ce mai k'imanin shekaru22 zaune kan d'aya daga cikin kujerun wajen,
fara ce sosai, mai zagayayyen fuska, mai dauk'e da dogon hancin, fararen oily eyes, da karamin baki, tana
da cikar gira haka zalika gashi idanunta masu yalwa ne, bata da jiki ko kadan domin kai tsaye za'a kira ta da
siririya, saidai structure din jikinta mai kyau da tsari ne....

A hankali take sipping smoothie din dake gaban ta, yayinda hankalin ta gaba daya ke kan tsadaddiyar
wayar hannunta kirar *iphone 3G Kings button Wanda kudin shi zai kai $2.5 million*, ba ma wayar ƙaɗai
ba, komai na jikinta daga sama har zuwa kasa tsad'add'en ne....

Dan bata fuska tayi ganin kusan rabin awa tana zaune amma har yanzu Mr Daniel Paul, bai karaso ba
wanda ya k'asance business partner dinsu, kuma sun yi kan cewa anan zasu hadu domin su tattauna wata
muhimmiyar magana wanda na cigaban companies din su ne....
Number mr Daniel ta kira yana daga wa ta fara yi masa magana kan rashin zuwan sa da wuri....

Yayinda wani k'yak'yawan saurayi daya bata baya ya yi saurin juyowa jin wata zazzak'ar muryar tamk'ar
busar sarewa, take zuciyar sa ta bugu domin ta, kana wani mugun sonta ya tsoki kirjin sa a lokaci daya, zai
iya rantsuwa bai taba ganin mai dadin murya hadi da kyawun fuska kamar wanna matashiyar ba, take ya
zaro wani babban cardboard paper irin na masu zanen mutum wato (artist)daga cikin katuwar jakar sa ta
goyo, cikin kwarewa yake zana wanna matashiyar budurwa idanun sa kafe kan fuskar ta, a ransa yana
d'ad'a yaba sihirtaccen kyawunta, yayin da cute bakin ta dake magana ya fi komai tafiya da shi...

D'aidai loƙacin daya gama zanen, wani waiter or nace ma'aikacin restaurant din yazo wujewa, ciƙin muryan
sa mai sanyi yace "hey! can you please give this to that young lady over there"
Ya fada yana nuna d'aidai inda budurwar ke zaune.

"yes! Sure" waiter'n ya fada yana amsar cardboard paper d'in daga hannun sa, hannu wanna saurayin ya
bashi suƙa yi musabaha ƙana ya furta "Thanks" murmushi waiter yayi kawai yana barin wajen...

D'aidai inda taƙe zaune waiter ya nufa, cikin girmamawa yace "ma'am waccen saurayi yace na baki wanna"
ya fada yana nuna sautin inda saurayin ke zaune, dago idanunta tayi ta bi inda ya nuna da k'allo, Sai dai
wayam babu wanna saurayin babu alamar sa....

Dan zaro ido waiter nan yayi yana mamakin ta yaya ya bar wajen ba tare da ya ko lura ba, cikin dan rudewa
yace "sorry please, yana zaune yanzu nan, kafin na karaso, shi yace na kawo miki".... Ya fada still cikin
girmamawa...

Murmushi ta saki wanda ya loɓar da wani dimple daƙe tsaƙiyar habar ta


"okay no problem" tace tana karban cardboard paper'n a hannun shi, shi ma waiter din murmushi yayi ya
bar wajen yana yaba kirkin ta a ransa...
A hankali ta fara warware takardan cardboard paper'n tana tunanin ko waye wanna? Wani zaro ido tayi
cikin zallan mamaki, ganin tamkar photo copy dinta ne a jikin paper'n "who is he?" ta fada tana kallon
zanen, wani mugun kyau zanen yayi mata , rungume paper'n tayi domin zanen ya burgeta matuk'ar
burgewa...

Take ta k'wadaitu da son ganin wanda ya iya zane ta tsaf haka, babu ko digon k'usk'ure, tana cikin wanna
zurfin tunanin ne mr Daniel Paul ya karaso hadi da bata uzurin abun da ya rikeshi, "babu damuwa" ta ce
kawai suka tattauna abinda ya kawo su duk da rabi da rabin hankalin ta baya wajen...

Ɓayan sun yi sallama da Mr Paul ta fito daga cikin wajen, sosai tafiyar ta ke da daukar hanƙali, duk da bata
da kiba amma jikinta har wani girgizan ɓirgewa yake daya yi matukar amsar ta ainun, za a iya tunanin da
gangan take yin hak'an, Sai dai sam ba haka bane, halittar ta ce a hak'an...
wasu motoci ne ke fake Masu kyau da tsari har guda shida jera reras, motar dake tsak'iyan sauran motocin
shidan ta nufa, wanda ya k'asance kirar *Ferrari Monza* red color, take wani bodyguard dinta mai sanye
cikin suit baki kamar yanda sauran suma kalar shigar su kenan, yayinda wani bak'in glass ke manne kan
fuskar ko wannensu, sam babu alamun fara'a a fuskar su, hannu ya mika domin karban cardboard paper'n
hannun ta, daga masa hannu tayi alamun ya barshi, take ya bata hanya cikin girmamawa, wani daga cikin
bodyguard dinta ne ya bud'e mata motar ta shige kana cikin k'warewa suka bawa motocin wuta....

_In cigaba ko in tsaya??? ku sani cewa comment dinku kadai ne zai sa na cigaba da rubuta novel
dinnan..._🤸

Banason stickers ko
emojis, sai zallan comment🥺🥰

share ✔
Comment✔
vote✔

Noor Eemaan ce🌟


07082281566

*Dan Allah duk wacce ta karanta, Please share as much as you can, as you share jazakallahu khair.*

I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or
*460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*


Whatsapp OR
Call 0806626851

💝KYAUTAR KODA💝
(Its all about love, sacrifice, hatred and destiny)

_by Noor Eemaan_✍️

Wattpad
@NoorEemaan

https://facebook.com/groups/943534712916776/

Masu amfani da Facebook sai kuyi join wan nan link din

Page 3-4

A nutse suke tafiya kan shimfud'ad'iyyar kwalta reras gwanin sha'awa, yayinda wasu mutanen ki bin
had'add'u kuma tsad'add'un motocin da kallo.... yayinda budurwar nan take kallon titi ta cikin glass din
motar, amma a zahiri ba kallon motocin dake ta wucewa a kan titi take ba, tunani mai zurfi take, tana
tunanin waye wanna daya iya zana fusk'ar ta haka tsaf, abin ya kasa barin zuciyar ta da ma k'wak'walwar
ta....

★ Unguwar *ikoyi* suka nufa, unguwa ne masu hannu da shuni domin babu gidan marasa hali a unguwar,
domin talaka bazai iya siyan ko hayan muhalli a unguwar ba.

Babban estate din motoci ke ta shiga, duk yanda baki zai kwantata estate din abin zai faskara, sai dai
wanda ya ganewa idanun sa kawai. Domin girman estate din zai iya yin girman wani karamin unguwa,
Had'add'en gine ne tamk'ar a turai, domin a turan ma ba ko ina bane za'a samu irin wanna estate din...
Bayan sun gama d'aidaita parking motocin kana dukkanin su suka fito, daya daga ciki ya buɗe mata mota
cikin girmamawa,... har kofar da zai sada ta da bangaren mahaifiyar ta suka rakota kana suka juya cikin
girmamawa suka koma.

Shigar ta cikin had'add'en falon, yayi d'aidai da tahowar wata K'yak'yyawar mata da zata yi shekaru arba'in
da biyar a duniya, wanda idan ka ganta zaka dauka cewa bata fi shekaru talatin da biyar ba saboda kyawun
jikinta, tana matsakaicin jiki, yayinda take da tsayi babu laifi, kallo daya zaka yiwa matar ka hango jindadi,
Hutu, hadi da kwanciyar hankali a tare da ita.

Murmushi matar ta sakar mata kana tace "welcome back sweetheart, ya gajiya?"

Martani murmushi ta mayar wa matar kana tace "Thank you Mommah na" hadi da bata kisses a kumatun
ta biyun.

Riko ta matar ta yi tamk'ar wata yarinya karama ta zaunar da ita kan daya daga Cikin had'add'un royal
chair kana tace "bari na zuba miki juice ki sha" murmushi kawai tayi tana bin Mommah'n ta da kallo, bayan
Mommah ta dawo ta zauna ta sanya mata juice din a baki bata wani sha da yawa ba ta janye bak'inta,
"sweetheart!" Mummy ta kira ta, dago kanta tayi ta kafe su kan Mommah ba tare da ta amsa ba.

Cikin serious tune tace "fadeelah meye damuwar ki, you re not looking okay?"

Budurwar nan mai suna fadeelah tace "ba komai Mommah, ina son hutawa ne kawai" ta fad'a tana sakar
wa Mommah murmushin k'arfin hali.

Ita ma Mommah murmushin tayi ta riko hannunta, har part dinta ta rakata sai da ta tabbatar ta kwanta
kana ta fito, tana ganin fitar Mommah ta sake bud'e cardboard paper'n nan, take zanen ya bayyana,
kurawa zanen hoton ido tayi, tunani masu yawa na zuwar mata, ta gyara kwanciyar yafi sau ba adadi,
domin babban burinta a yanzu ta ga waye wanna daya iya zane fusk'ar ta tar tar babu ko mistake, ta duba
ta ga ko akwai sunan sa ko number'n sa a kasan zanen kamar yadda masu zanen kan saka, amma babu...

*** *** *** ***

Kwance matashin nan mai zane yake kan cinyar wata mata mai kimanin shekaru hamsin a duniya, sosai
take da k'yau domin bazaka yi tunanin ita ce mahaifiyar wanna saurayin ba, saboda bambamcin kalar fatar
su, domin baki ne shi irin black beauty din nan yayinda matar ta k'asance fara sosai duk da cewa kalar fatar
ta ta dan dishashe sak'amak'on halin babu da suke fama dashi, domin kallo daya zaka yiwa gidan ka
tabbatar da hak'an...

"Fadeel my son, lafiyar ka kuwa tun jiya na kasa gane kanka, na kuma tambayeka kace babu komai, shin
kana da kowa a duniyar nan da zaka iya raba damuwar ka da shi baya ga ni ummin ka?"
Ta tambayeshi cikin tsananin kulawa yayind'a hannun ke kan gashin sa tana shafawa har yanzu.

Cikin son mahaifiyar sa yace "Mahmah... na fada soyaayyar wata yarinyar" ya karasa yana sauk'e
numfashin idanu sa a lumshe yana tuno kyakyyawar fusk'ar ta, murmushin ta, tsarin jikinta da ma
dukkanin wani abu daya dangance ta.
"Oohh ya rabb! Fadeel da gaske kake? Yau da kanka kace kana son wata? Gaya min ka sanar da ita? A wani
unguwa take?" Mahmah ta yi masa tambayar cikin zallan farinciki da zumudi.

"Ooh Mahmah relax, shiyasa bana son baki labari sometimes fa" ya karasa yana murmushi.

"Bazaka gane ba son, tun yaushe nake cewa ka samo budurwar ka ki, yau kuma ka sanar dani kace bazan yi
farinciki ba?" sai k'uma yanayin ta ya sauya a take
Cikin damuwa yace

"lafiya Mahmah?"

Hawaye ne suka ciko idanun ta tace "ina son ganin kayi aure ka tara zuri'a, inason ganin jikokina daga
tsatson ka, kai kadai na haifa, kuma ina alfahari da kai, domin daya kake tamkar da dubu, damuwa ta shine
idan ma auren ya taso ina muka ga kudin da za a yi hidimomin biki? Ni da kai mun sani cewa kullum cikin
babu muke sai godiyar Allah"

Jikinsa ne yayi sanyi d'omin baya kaunar ganin Mahmah cikin damuwa sam, da yana da iko daya cire
wanna damuwar, sai dai babu yanda zai yi, ƙaddarar su ce hakan, cikin sanyin muryar sa yace "Mahmah
wanna dalilin ne yasa na kasa kowa miki suruka d'omin bazan iya tukarar kowacce mace a haka ta saurare
ni ba, d'omin yawancin yanmmatan yanzu are after Money not Love, sannan ita wanna yarinyar ban ma
san sunan ta ba, balle gidan"....

SHARE✔
VOTE✔
COMMENT✔
EDIT❌

shhhh!🤫 Ƙarku ce update yayi kadan🤒 just manage 😘

NoorEemaan
07082281566

I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or
*460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*


Whatsapp OR
Call 0806626851

💝KYAUTAR KODA💝
(Its all about love, sacrifice, destiny and hatred)

*First edition*

_by Noor Eemaan_✍️

Wattpad
@NoorEemaan

https://facebook.com/groups/943534712916776/

Masu amfani da facebook su yi join ta wanna link din.

ELEGANT ONLINE WRITER'S✍️

Page 5-6

Cikin mamaki Mahmah tace "baka san gidan su ba kace fadeel?"

Jinjina kai yayi, yace "eh ban san gidan su ba, a restaurant din nan da nake zuwa wasu lokutan nan na hadu
da ita"
"Ikon Allah, toh Allah ya zaba maka abinda yafi Alkhairi son, addu'a ta na tare da kai a kullum"

K'amk'ame ta yayi yace "nagode Mahmah nah"

Haka suka cigaba da hirar su irin ta d'a na uwa, har suka tafi makwancinsu.

★★★

Katafaren masana'anta ne wanda ake sarrafa abubuwa da dama.

Fadeelah ce ta kasance CEO din masana'antar, duk da tana da karanci shekaru amma ta san kan business
ba kadan ba, hak'an ya sa Daddy'n ta bar mata ragamar company gaba daya, ba tare da ya ji ko d'ar ba, ya
mayar da hankalin sa kan wasu business din sa.

Kamar kullum a jere motocin suka shigo cikin masana'antar, bayan an sun d'aid'aita parking duk suka fito
cikin sauri, kana daya daga cikin bodyguard din ta yayi saurin bud'e mata kofar wata tsad'add'iyar mota
blue kirar *pagani zonda HP barchetta* wanda tsadar sa ya kai $17,000,000.

A hankali ta fito da Santala santalan fararen k'afafun ta masu sanye cikin tsad'add'un takalma na kamfanin
*PASSION JORDAN SHOES* bak'ak'e, a nutse ta fito daga motar gaba-daya cikin wasu had'add'un English
wears da basu kama jikinta ba, na company *Giorgio Armani*.
Wandon palazzo ne, sai riga blue color tayi stocking da rigar sai bakin dankwali data dan yane kanta da
dashi, yayin da ta sanya glass mai dan fadi da yayi matuk'ar amsar ta sai agoga kamfanin Gucci a hannunta,
jikin ta banda kamshin turaren Company'n *DOLCE & GABBANA* babu abinda yake, cikin takun daukar
hankali ta fara takawa yayinda bodyguard's dinta suka shiga bin ta domin bata tsaro har izuwa kofar zallan
glass din da zai sada mutum da ainihin cikin masana'antar.... cak ta tsaya, su ma take suka tsaya basu ko
motsa ba, a hank'ali ta motsa tattausan labb'anta tace "Thanks all, kuna iya komawa daga nan"

"You are welcome ma'am" suka fad'a cikin girmamawa, domin sosai suke jin dadin aiki da ita.

Tana tsaye kofar glass din ya buɗe kan sa ta shige ciki, nan ma'aikatan suka mike domin nuna girmamawa a
gareta, daga wa ma'aikatan hannu tayi fuskar ta d'auke da murmushi, haka suka shiga gaishe ta tana
amsa wa kana ta shige had'add'en office d'inta...

Ganin ta shiga office din yasa wasu ma'aikata biyu mata dake zaune gaf da juna suka fara gulma "wallahi
yarinyar boss tana burgeni, ga kyau ga wanka, amma sam bata wulakantawa mutane"

D'ayar tace "ke dai bari, ai kusan kowa yabon ta yake a company din nan, amma kinga wanna uban nata
mai kwala-kwalan idanun, wulakanta mutane da rashin fara'a a cikin sa kamar me"

Tafa wa suka yi, wacce ta fara magana tace "wallahi baki da dama kawata, wai kwala-kwalan idanu"

"Atoh ai gaskiya na fada" haka suka cigaba da maganganun su...


Zaune take tana ta aikin shigar da wasu bayanai a laptop dinta kirar Apple, gaba daya hankalin ta naga
aikin da take da alama aikin mai muhimmanci ne.

Bayan ta gama, ta kwantar da k'anta jikin kujera irin mai juyin nan, gaba d'aya hankali da tunanin ta ya tafi
kan mai zanen ta, saboda tsananin son da take wa hoton yasa ta manna shi a bangon dak'in ta...

Sai karfe biyar na yamma ta tashi daga Company'n, aka bude mata mota ta shiga suka dauki hanyar gida,
babu jimawa suka isa unguwar tasu ta *ikoyi* bayan an bude mata mota ta fito, ta fara takawa, kamar
kullum bodyguard dinta na take mata baya har bakin kofar da zai sadata da part dinta, kana ta dakatar
dasu suka koma.....

Glass din idon ta kadai ta cire, a hankali ta nufi wajen da ta manna zanen hoton a bango, shafa fuskar ta
take, ta sauke numfashi kana tace "where on earth are you? zan sake ganin ka? shin zan ma gane ka idan
mun hadu? You left, without even showing me your self, ya rabb ka taimake ni" ta karasa wasu zafaffan
hawaye na zubo mata, domin ta rasa me take ji game da mai zanen ta domin d'aid'ai da second daya
tunani sa yaki barin zuciyar ta ya huta.

A sanyaye ta shiga bathroom din ta, ta fada cikin jacuzzi bayan ta tari ruwa mai dumi, a hankali ta shiga
goga hada'dd'en shower gel dinta mai suna *Molton brown orange*...

Bayan ta gama wankan ta fito sanye cikin bathrobe, lotion mai saukin zafi ta shafa kana ta dauko wani
high-waist skirt fari da jan top, sai hula fari data sanya, sannan ta dauki wayar ta wanna karon kirar
*huawei mate 30 pro* ne.

Bangaren Mommah ta nufa, tana shiga ta tarar da wani mutum a zaune kan daya daga cikin royal chair din
falon, K'yak'yawan gaske ne, domin kamanin su daya da fadeelah, duk inda ake neman mutum mai ji da
kudi, hutu, hadi da jindadi toh *Professor Imran mai naira* ya kai, a zahiri zaka dauka irin mai shekarun 35
din nan ne, saboda kyawun jikin sa, sai dai shekarun sa na ainihi 55 ne.

Cikin waro ido da farincikin d'aya kasa buya a fuskar ta tace


"Daddy!"

Daga kansa yayi daga kan fask'ek'iyyar wayar sa, fuskarsa dauk'e da murmushi... zare medicated glass din
idanun sa yayi kana ya ware hannayen sa cikin muryansa mai dan kauri yace "come, come my princess, my
lovely beautiful daughter" Ya fada yana bin ta da kallon kauna hadi da alfaharin kasancewar ta yar sa.

Cikin saurin ta fada jikin sa tace "Daddy daman ka dawo, how comes you didn't tell me? Nayi kewar ka
sosai Dad"

Bubbuga bayanta yayi yace "I so much miss you too my little princess, ya kokari?".

Raba jikin su tayi tana cewa "Alhamdulillah Daddy"


"That's very good of you my princess"

"Eh lallai yayi kyau sweetheart, dan kinga Daddy ko ta ni ba a yi ko? zamu gauraya ne"
Mommah tace tana jifan ta da hararan wasa.

"Wayyo Mommah na kiyi haku'ri"


fadeelah ta fada cikin shagwa'ba tana k'arasa wajen ta hadi da rungume ta.

"Don't mind her my princess, kishi take" daddy' ya fada cikin zolaya

Dariya suka sanya gaba-daya, kana suka cigaba da hirar su gwanin sha'awa wanda hakan ya rage mata kaso
saba'in daga cikin damuwar ta...

★★★

_Victoria island_
*RSVP restaurant*

A yau ma fadeelah ta sake zuwa restaurant din nan, saboda burin ta da fatan ta mai zanen ta ya bayyana a
gareta, soft drink hadi da table water tayi ordering, yayinda bodyguard dinta ke can gefe ta basu daman
shigowa, suka zabi duk abinda suke so, duk da haka, duk wani motsin ta na kan idanun su ne, saboda bata
tsaro...

Babban glass da ake wa lakabi da "no respect" sanye kan fuskar ta, wanda hak'an yasa mutum ba zai taba
fahimtar yanayin da kwayar idanunta ke ciki ba...

Tayi zurfi a tunani taji magana daga bayanta kamar haka "excuse me ma'am, ance in baki wanna" ya fada
yana mika mata cardboard paper kalar na ranan, take gabanta ya fadi cikin sauri ta mike hadi da cewa
waiter'n "ina yake? Where is he?"

Take dukkanin bodyguard dinta suka yo wajen suna saita bindigogin su, cikin rudewa waiter yace "ya fita
yan...zu nan"

A take ta ce "guards! ku duba min inda yake"...

Cikin sauri suka fita tare da waiter'n domin ya nuna musu shi... Ware paper'n tayi, wanna karon tayi mugun
kyau fiye da na baya, kuma tsaf kayan jikin ta da glass din fusk'ar ta da komai ya zana...

Tana cikin kallon zanen ne suka dawo hadi da cewa " he is no where to be found ma'am"

Dafe kanta tayi, ta ji wani irin daci a bakin ta, kana ta fara tafiya cikin sauri- sauri ta fita daga restaurant din,
ko jira a bud'e mata kofar mota bata yi ba ta fad'a ciki....
Cikin rawar jiki bodyguards din ta suka shige motocin kana suka dauki hanyar gida....

Ajiyar zuciya ya sauke kana ya fito daga maboyar sa, zuciyar sa ce ta karye, daman ba sa'ar yin sa bace bai
sani ba? Hannu ya d'ora kan saitin zuciyar sa ya cigaba da cewa "hak'ik'a zuciya baki min adalci ba, ta ya ya
ka kamu da son wanna attajirar? Ya ya zan yi da soyaayyar ta d'aya yiwa zuciya ta da'bai'bayi?"
Lumshe idanun sa yayi, tunani barkatai na kai kawo a zuciyar sa, daga karshe dai ya tari mai keke napep ya
shiga, yana tunanin dole ya yakice ta a zuciyar sa ko ta halin ka ka ne......

_i most confess this... nayi farinciki sosai da yanda kuka karbi littafin kyautar koda, i do really appreciate,
duk wani book dana yi kuna kaunar sa, i love You all fans_

Comment✔️

Share fisabilillah✔️

Vote✔️

Editing is not allowed❌

07082281566
NoorEemaan

I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or
*460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*


Whatsapp OR
Call 0806626851
💝KYAUTAR KODA💝
(It's all about love, sacrifice, hatred and destiny)

*First edition*

Story and written by


Noor Eemaan

Wattpad
@NoorEemaan

https://facebook.com/groups/943534712916776/

Masu amfani da facebook su yi join ta wanna link din.

_if you see any typing error, avoid it please_

Page 7-8

Yana isa gida ya zauna kan tabarma ko lura da Mahmah bai yi ba, jikin ta a sanyaye ta karaso wajen sa ta
zauna hannun sa ta kamo cikin muryar tausayawa tace "fadeel what's it, lafiya kake?"

Kallon mahmah yayi da jajayen idanunsa, kana ya fada jikinta tamkar wani yaro karami yana sauke wani
irin numfashi... Ya dauki mintuna goma masu kyau kana ya fara bawa mahmah labarin abinda ya faru
yau..... Domin tun yana karami baya da wani abokin shawara sama da ita, idan ka gansu tamkar ya da kani.

Ta tausayawa fadeel sosai, tilon danta, domin ta gani baro-baro cewa ya faɗa tarkon son yarinyar, cikin
tausasawa tace " 'Dana Fadeel, meyasa ka sare? Meyasa ka sare da wuri haka? Kai namiji ne, namijin ma
jarumi, bai kamata wani abu ya baka tsoro ba, dan muna matsayin talaka ba hakan ke nuni da cewa ba
zaka iya auren wacce ta fi ka arziki ba, ina me baka umarni daka bayyana kanka a gareta, domin tun kafin
na ganta na ji na fara son ta, duk abinda kake so dole nima in so shi, da gwaji akan san na kwarai, ka ji ko?"

Jinjina kai yayi, maganganun mahaifiyar sa na kara masa k'arfin guiwa, nan ya dan saki jiki ya fara bata
labarin irin kyau da haduwar fadeelah, mahmah kuwa sai murmushi take tana fatan danta ya samu
soyaayyar budurwar daya gama mutuwa akan son ta....

ASALINSA

Fadeel Abdul-basit dane ga Abdul-basit Muzakkir, tun yana da shekaru 7 mahaifin sa ya rasu. Asalin su yan
jahar kebbi ne, aiki ne ya dawo dasu nan lagos, toh bayan rasuwar mahaifin fadeel suka fara shiga halin
matsin rayuwa, ga yan'uwan baban fadeel basa ko taimaka musu, kasancewar mahmah mai zuciyar nema
ce yasa ta fara sana'ar siyar da biredi akan titin layinsu, da wanna kudin ta cigaba da biyawa fadeel danta
kudin school har ya samu kwalin degree a bangaren artist.

k'wararren mai zane ne domin a mintuna ƙalilan zai zana mutum tsaf... Duk da haka bai yi girman kai ba,
domin shi ke zama wajen sana'ar ta ya siyar mata da biredi, A cewar sa ta hutu a gida, amma wani zubin
Mahmah bata yarda sai tace su tafi su biyu, har mamaki take domin ta dauka tunda yana da degree bazai
iya siyar da biredi a bakin titi ba... har tambayar sa tayi domin ta kasa hakuri ya kuwa bata amsar cewa
"mahmah idan naji kunya ko nuna girma kai banyi miki adalci ba, domin da biredin kika siyar har kika biya
min kudin makaranta har na gama, dan haka ko da na samu aiki mai kyau da za a biya ni millions ne, toh
zan iya cigaba da siyar miki da bread matuk'ar kina so kin kuma bani umarnin yin haka"

Sosai jikin Mahmah yayi sanyi domin kalaman sa sun ratsa zuciyar sa, hakan yasa take alfahari da shi...

Haka suka cigaba da rayuwar su gwanin sha'awa, sai dai Mahmah na boyewa Fadeel wani abu, wanda nan
gaba zamu ji ko ma menene...

*CIGABAN LABARI*

Tsaye take cikin shigar sleeping wear's dan guntu da alama tashin ta daga bacci kenan, gaba daya hankalin
ta na ga zanen dake manne a bangon dakin, ta rasa wanne yafi kyau cikin zane biyun, hawaye suka wanke
mata fuska tuno cewa bata san wanda yake zana ta ba, wanda shine babban burin ta a yanzu...

Kwankwasa kofa da ta ji ana yi ne yasa ta yi sauri share hawayenta hadi da bada umarnin shigowa, Daddy'n
ta ne ya bayyana, sallama dauke a bakin sa, murmushin k'arfin hali tayi ta isa garesa hadi da rungumesa
tana cewa "good morning Dad"
Shafa bayanta yayi yana cewa "morning my beautiful princess, how was your night?" Daddy ya tambayeta
cikin tsananin kulawa hadi da son yarsa.

"It pass great my hero Daddy" murmushi yayi kana yace "sai yanzu hankali na ya kwanta princess, domin
kwana biyu na k'asa gane miki"

Raba jikinsu yayi yace "kiyi freshing up, kizo muyi breakfast ok, ni da Mommah na jiran ki" ya kare maganar
yana bata light kiss a hagu da daman na kumatun ta kana ya fice...

Ajiyar zuciya ta sauke, tana yaba kulawa da son da Daddy'nta ke mata, kara kallon zanen ta yi kana ta fada
bathroom.

*1 MONTH LATER*
(BAYAN WATA DAYA)

Motocin fadeelah ke sharara gudu kan kwalta kamar kullum, har sun wuce wanna restaurant din kawai taji
gabanta ya fadi, taji hankali da tunanin ta ya kasa barin wajen, magana tayi wa driver'n dake tuka ta, take
ya juya alakar motar zuwa restaurant din, ba bata lokaci suma sauran motocin suka biyo bayan motar da
Fadeelah take ciki zuwa restaurant din,,,, bayan sun daidaita parking motocin, aka bude mata kofa ta fito
cikin shigar suit na mata mai riga da wando hadi da karamin mafayi data yi rolling sai dan hand bag daya
dace da kayan, duka brand din *HUGO BOSS* wanda yake cikin tsadaddun companies...
Wanna karon ma ta bawa bodyguards din ta umarnin shigowa tare da ita, bayan waiter yayi serving din ta
da juice kadai kamar yadda ta bukata... Hankalin ta naga wayar ta kirar *Samsung Galaxy Fold2*
wanda ya dace da kalar kayanta, domin duk shigar da ta yi toh fa da wayar da take dauka, sannan mafi
yawan lokuta wayar na kasancewa kalar shigar ta ne.

Lokaci zuwa lokaci ta kan kalli wajen a tunanin ta ko zata iya ganin mai zanen ta, sosai ta dukufa kan lissafin
da take a wayar, da alama Mai Muhimmanci ne, kamar a mafarki, amma kuma ta san ba mafarki bane,
kawai ta ga hannu dauke da cardboard paper irin na kullum yana miko mata, gaban ta ne ya fadi take ta
fara bin hannun da kallo har ta sauke kan Kyakyawan fuskar sa, gabanta ya sake bugawa da karfi, mikewa
tayi ta nuna shi da yatsa, cikin rawar murya tace "it's you, bana ko tantama Kaine! Kaine mai zana ni......"

_In sha Allah gobe ma zanyi k'ok'arin baku update, nasan na barku kuna ta jira, amma sai kun mun hakuri
cos two book nake rubutawa at once, so ina buk'atar hutu a brain dina...._
Ina muku pure love

07082281566
Noor

I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or
*460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*


Whatsapp OR
Call 0806626851

💝KYAUTAR KODA💝
(It's all about love, sacrifices hatred and destiny)

_by Noor Eemaan_✍️


07082281566

https://facebook.com/groups/943534712916776/
Masu amfani da facebook su yi join ta wanna link din.

Page 9-10

Dan shiru yayi, yana ƙoƙarin tara courage, at last ya Jinjina kai kawai alamun "eh" yayinda murmushin
karfin hali ke dauke a fuskarsa, domin bai san a yanda zata karbe shi ba.

Tana shirin yin magana, bodyguards dinta suka zagaye Fadeel, sai karan saita bindigogin su kake ji, ko daya
bai ji tsoro ba, sai bin su da kallo yake, cikin bacin rai Fadeelah tace "drop your guns and go away"

Cikin girmamawa suka ce "we are sorry ma'am" kana suka kalli Fadeel suka ce "sorry sir" jinjina musu kai
yayi alamun ba komai.

Bayan barin su wajen fadeelah tace "da gaske Kaine mai zana fuskata? oh my God! Yau ina cikin farincikin"

Tace tana kallonsa idanunta sun kasa boye tsananin farincikin da take ciki, wanda hakan ya sanya Fadeel
cikin tsananin surprise, yet happy deep down inside his heart "zauna dan Allah, na cika ka da surutu"
Fadeelah tace tana nuna masa wajen zama.

Zama yayi yana sauke boyayyen ajiyar zuciya, yayinda fargaban rasa ta ke barin zuciyar sa a hankali "Me
zaka ci ko sha, a kawo maka"

"A'a ki barshi nagode"

Shagwa6e fuska tayi tace "Allah bana jin dadi idan nayi niyyar yin abu wa mutum yace baya so"

Murmushi ya saki yana karantar halayen ta daga yanayin maganar ta, kana yace "kiyi hakuri amma bana jin
ci ko shan komai"

"Ok fine, ba matsala" Fadeelah tace domin ita din ba mai son takurawa mutum bace.

Ruwa ta dan kurba tace "shin zan iya tambayar ka?"

"Kwarai kuwa ina jinki" ya amsa yana jin bugun zuciyar sa na karuwa.

Gyara zama tayi tace "meyasa kake boye kanka?"

Numfashi ya sauke, domin abinda yayi tunanin zata ce daban, sai da ya hadiye wani yawu, kana ya tuno
yanda Mahmah ta karfafa masa guiwa akan ta yace "saboda ina tsoron rasa ki, domin a ranar dana fara
ganin ki a daidai wanna wajen na kamu da tsananin son ki, naji tsoran bayyana kaine ganin cewa ke ba aji
na bace..."

Fadeelah bata bari ya karasa ba, ta katse shi da cewa "Kai rago ne! da har ka kasa bayyana soyaayyar ka a
gareni, ka azabatar da zuciyoyin mu, dame na wuce ajin ka? A rayuwar nan babu wanda ya wuce wani sai
wanda yafi tsoron Allah, komai kudi da dukiyar da yake da shi kuwa, wanna dalilin naka be min ba, baka yi
tunanin nima ina sonka ba, lemme say this ina sonka, ina kaunar ka mai zana ni" ta karasa maganar tana
jifan sa da wani kallo daya sanya Fadeel jin sa on top, kana ya mike zumbur saboda farinciki yace "da gaske
kina sona, zaki iya aure na?"

"Yes! Ina sonka kuma zan rayu da kai a ko wani hali"....

Sosai suke cikin farincikin ganin dukkanin su na son juna, hira suka sha har karfe bakwai da rabi kana suka
farga cewa dare yayi.

Har bakin inda aka faka motocin ta suka karasa tare, bodyguards dinta kuma na tsaye dan nesa dasu.

"Zamu rabu bamu san sunan juna ba" Fadeel ya fada yana dage girar sa daya, murmushi tayi tace
"I'm Fadeelah" shima yace
"I'm Fadeel" sai suka saka dariya a tare ganin sun kira sunan su a lokacin daya.

"Fadeel da Fadeelah masu tagwayen suna, kin sani an hallace mu ne domin mu so juna, Kisa a ranki cewa
har abada ni mai sonki ne, please ki kulamin da kanki, domin ke din ta musamman ce a cikin dubban mata"

Wani zallan farinciki ne ya sake bayyana a fuskar ta, she loves admiration, ta kuma lura yaba mutum da
bashi kulawa is one of Fadeel's attitude, ba kuma tare da ta san zancen zuci ya fito fili ba tace "dama haka
so yake da dadi?"

"Yeah darling, musamman in tare dake ne" Fadeel ya bata amsa.

Kunya taji ya saukar mata, domin bata yi tunanin ya ji taba.

"ki taimaki bawan Allah da number, domin idan ba haka ba zan iya zaucewa kafin gobe matukar ban ji
wanna d'ad'addan muryar ki tamkar busar sarewa ba"

Wani tsadadden murmushi na zallan farinciki ta saki, kana tace ya bata waya ta sanya masa number'n,
take ya sanya mata wayar sa kirar *itel* mai madannai wanda kudin sa ba zai haura dubu uku da dari biyar
ba, wanda da kyar ya hada kudin ya siya, a hakan ma second hand ce.

Bayan ta sanya masa ya ga lambar special ce, bai taba ganin tsararren lamba Irin wanna ba, Fadeelah ta
nemi ya shiga mota su fara sauke shi, amma yaki, dole ta shige mota tana waiwayon sa, hannu suke
dagawa juna har motocin suka bace a idon Fadeel....

Shi ma Fadeel keke-napep ya tara ya shige, wayarsa manne a hancinsa yana shakan dadaddan kamshin
turaren ta, da kamshin ya kama wayar sa...
Isar sa gida ya fara rawa tun daga tsakar gida yana kiran "mahmah! Mahmah!! Mahmah!!! Where are
you?"
Sai ya fara waka kamar haka

🎻🎻 _soyyaya da dadi, amma in ku aminta da juna, zuciya ta samu soyaayyar wacce take kauna_
Sai ya ɗora da cewa still cikin amon sautin waka
_Mahmah ki tayi ni murna_
_na samu mahadin rayuwata da ni da Fadeelah a Soyyaya_ 🎻🎻

Ya kara sa wakar ta sa da rungume mahmah data fito tun dazu tana taya shi rawar.

Hannun shi ta kamo suka zauna tace "my son Fadeel ka bani labari"

Nan kuwa ya fara bata labarin komai, ba tare da ya boye mata komai ba, sosai mahmah taji dadi ta kuma yi
musu addu'ar fatan Alkhairi, har 12 na dare suna zaune suna hira wanda zallan labarin Fadeelah yake
bata...

★★

Ɓangaren fadeelah kuwa tana kwance kan gadon ta yi ruf da ciki, yayinda ta kurawa hotunan dake manne
a bango ido, wanda yanzu sun dawo uku har da wanda yayi mata yau, wani murmushi take saki lokaci
zuwa lokaci bata taba tsintar kanta cikin annushuwa kamar yau ba, tun tana kallon har ta fara jin bacci,
duvet ta rufawa kanta, babu jimawa bacci ya dauke ta cike da mafarkin Fadeel...

*** *** *** ***

Babban asibiti ne a lagos wanda yawanci masu hannu da shuni ke zuwa. mahmah ce zaune a office din
doctor Gabriel yana mata bayani kamar haka "madam condition dinki kara gaba yake, domin tun farko ya
kamata a tari wanna cuta ayi miki maganin sa, maganar gaskiya yanzu baza a iya komai a kai ba, sai dai ki
cigaba da shan maganin ki domin samu sauki kawai, duk da kin gaya min rashin kudi ne yasa baki yi saurin
taran ciwon ba, kuma kamar yadda nayi alkawari zan cigaba da duba ki kyauta, kawai siyan magani ne naki,
Allah ya baki lafiya"
doctor Gabriel ya karasa maganar hadi da mayar da medicated glass din sa ido

Hawaye Mahmah ta share tace "nagode sosai doctor Gabriel, Allah ya biya maka dukkanin bukatun ka na
Alkhairi, i do really appreciate"

"Ameen madam" doctor ya amsa yana cigaba da aikinsa

A sanyaye Mahmah ta fito daga office din sa ta nufi pharmacy din hospital, kudi hadi da takardan da doctor
Gabriel ya bata ta mika wa wata nurse, amsa nurse din tayi a wulakance kana ta cilla kudin hadi da
takardan jikin Mahmah tace "ke dallah bar wajen nan, wanna asibiti yayi miki kama da na talakawa? Da
zaki wani miki wata tsohuwar dubu da dari biyar dinki, ki bar wajen nan ko..."

"Ke! Baki da hankali ne?wanna matar sa'ar ki ce, baza ta iya haifar ki ba, hakika baki cancanci zama nurse
ba, domin su da tausayi aka san su"

Fadeela da ta zo wucewa ke wanna maganar cikin tsananin bacin rai, yayinda bodyguards dinta ke tsaye
da ita kamar kullum.
Kan Mahmah a kasa tana hawaye, ganin yanda wasu mutanen basa ganin mutuncin talaka, maganar
Fadeelah ne ya katse mata tunanin ta...

"Akan me kike mata wanna fadan kamar sa'ar ki?"

Kan nurse a kasa domin ta san wacece fadeelah da irin arzikin su

"magani zata siya shine ta miko dubu daya da dari biyar"

"Nawa ne kudin maganin" inji Fadeelah.

Nurse tace "Dubu goma ne"

"Daman akan wasu dubu goma kike gaya mata wadannan maganganun? Toh ki bata maganin" Cewar
fadeelah tana hararan nurse kana tace
"Guards! Ku bani jakar kudi" Cikin sauri daya daga cikin bodyguard dinta ya miko jaka mai cike da kuka, fiye
da dubu goma ta bawa nurse hadi da cewa "be careful, kina daf da rasa aikin ki matuƙar kika cigaba a
haka" Fadeelah tace tana sake hararan nurse din domin ba karamin haushi ta bata ba.

Juyowa tayi ga Mahmah tace "kiyi hakuri dan Allah Mama"

Murmushin karfi hali Mahmah tayi tace "nagode sosai yata, Allah ya biya ki da Alkhairin sa ya baki miji na
gari"

Da ameen fadeelah ta amsa kana tace "Mama ga wanna ba yawa Ko dan zuwa asibiti" ta fada tana miko
mata rafa biyu na 1k.

"A'a yata ki barshi" inji mama har cikin ranta.

"Dan Allah Mama ki karba, idan ba haka ba bazan ji dadi ba" Fadeelah tace tana sanya kudin cikin ledar
maganin hadi da ficewa daga asibitin....

Addu'a Mahmah ke bin ta dashi har ta bace wa ganinta, dama akwai sauran masu kudi wadanda suka san
darajar talakawa a duniya? take taji son yarinyar a ranta, tana fatan danta Fadeel ya samu mai Kyakyyawar
zuciya kamar wanda yarinyar.

Fita Mahmah tayi daga asibitin ta tari keke- napep, a ranta tana cewa dole zan bawa Fadeel labarin wanna
yarinyar....

_Idan kunga typing error kuyi hkr ban tace ba (editing) saboda na gajiya..._

Kuyi manage wallahi nayi typing, yau ma ya goge, dan dai nayi alkawari yi muku yau da bazan yi ba,
sai gobe, saboda haushi wlh...
Ku cigaba da bina domin labari bai soma ba😎
Noor na muku sahihiyar kauna

Vote and follow me on wattpad


@NoorEemaan

Share fisabilillah

Comment domin kara


min k'arfin guiwar typing

Editing is not allowed❌

I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*

💝KYAUTAR KODA💝
(Its all about love, sacrifices hatred and destiny)

_by Noor Eemaan_✍️

07082281566

Saboda Allah da manzon sa (s.a.w) vote and follow me on👇


Wattpad
@NoorEemaan🤒
ELEGANT ONLINE WRITER'S📚🖊

Congratulations once again sweetheart (nimcyluv) Allah ya kara daukaka. Alkhairi Allah ya kai muku writers
da readers a kokarin ku na nuna wa the famous writer na'imah sulaiman(nimcyluv) kauna👏💖

https://facebook.com/groups/943534712916776/
Masu amfani da facebook su yi join ta wanna link din.

Page 11-12

............Cikin adaidaita sahun ma tunanin Fadeelah na nan daram a ranta sa, babu abinda yafi daukar
hankalinsa gami da Fadeelah kamar nutsuwa, mutunci da sanin daraja dan Adam...

★★

Daidai kan layin su mai adaidaita sahu ya sauke ta, ta mika masa dari biyar yace babu canji, babu ko dar
tace ya rike sauran canjin(su mahmah an samu kudi yau lolz).
Godiya mai adaidaita sahu ya dinga zuba mata, ji tayi wani yanayi mai dadi na shigarta, wai yau ita ce da
bawa wani kyautar kudi, ina ma ta yi arziki data yi farinciki domin zata cigaba da tallafawa marasa shi, ba
shakka a duniya ka fi wani, wani ya fika, duk yanda ka kai ga cewa kai talaka ne, sai ka ga Kai mai arziki ne
akan wani ko wata...

Wani babban store da ake siyar da dukkanin kayan abinci ta nufa dake daidai kan layin na su, da dubu dari
da ashirin tayi siyayyar kayan abinci data san zai dade musu, zuciyar ta fall da saka wa Fadeelah albarka,
yan shagon suka bada akori-kura aka zuba kayan sannan ta shige gaban akori-kuran suka nufi cikin layin su
yan shagon na ta zuba godiya, a ranta tace "talaka bawan Allah" dama haka masu kudi ke jin wanna
alfaharin musamman idan ana zuba godiyar nan, a fili kana a sanyaye tace "Allah ya iya mana" direban
akori-kura ya kuwa amsa da "ameen Hajiya" murmushi ya subuce mata jin an kirata da hajiya lallai idan
baka dashi ka sha kallo...

Daidai kan kofar gidansu mai akori-kura ya tsaya kana ya fito ya shiga sauke mata kayan, sai daya sauke
duka kana ya fara shigar su cikin gidan, ya kuwa samu Fadeel zaune gaban murhu yana fifita wuta da alama
girki yake... Da kallon mamaki Fadeel yabi mai akori-kura, ba tare da ya iya furta koda kalma daya ba,
domin ya gama bayar wa batan gida mai akori-kuran yayi, ajiye muficin yayi ya bi bayan mai akori-kuran...
Wani zallan mamakin ne ya sake kama shi ganin Mahmah a tsaye. "Mahmah" ya kira sunan ta muryar sa na
bayyana mamakin da yake ciki..

Murmushi mahmah ta sakar masa ba tare da tace komai ba, kallon ta kawai yake kamar yaga sabuwar
halitta, ganin idon mai akori-kura ya hana shi yin magana
Bayan mai akori-kura ya gama shigar da kayan, Mahmah ta zaro dubu biyu ta bashi, da wani mamakin
dauke a fuskar sa ya sake bin Mahmah da kallo ko ina ta samu kudi? godiya sosai mai akori-kura ya dinga
zuba wa yayin da Mahmah ta ja hannu shi suka shiga gidan, kan tabarma ta zaunar da shi ita ma ta zauna
kana tace "nasan damuwar ka Fadeel, na kuma san tambayar dake bakin ka...."
Nan ta shiga bashi labarin haduwar su da Fadeelah, amma ta biyo abinda doctor Gabriel yace, shima yayi
mamaki ya kuma ji haushi da tsanar nurse din, domin babu abinda ya tsana kamar a wulakanta masa uwa
koda kallon banza ne, baya so.

Ajiyar zuciya ya sauke a fili kana yace "amma Mahmah da baki karbi kudin ta ba, ni bana so wani ya miki
abu matukar bani bane, ina kuma fatan Allah yasa na kai minzanin da za kiji dadi har ki bawa wasu, sai
wani yaba ta kike dan baki ga fadeelah ta bane, na tabbata ta fi wanna komai da kika lissafo" ya karasa
cikin yanayi na shagwa'ba...

Dariyar Farincikin mahmah ta saki, saboda Kalmarsa ta karshe.


Ta san shi sarai yana da zuciyar nema sannan baya dogara da mutum, wanna karsashin nasa na burgeta
sannan tana alfahari da hakan, kuma zata cigaba da alfahari da hakan ko da bayan ranta ne.

"Fadeel my son kamar yadda na gaya maka banso karban kudin ba, kai ma kasan halin mahmah'nka, sanya
wa tayi cikin ledar maganina batare da ta jira ba ta tafi, kuma a duniyar nan kana ganin akwai macen da
zan yaba ko zan so da zata wuce Fadeelah'n Fadeel dina?" Ta karasa cikin sigar tambaya kana ta cigaba
"kawai yarinyar na da girmama na gaba da ita hadi da sanin mutuncin dan Adam, hakan yasa maganar ta
ya shiga zuciyata matuka, amma duk da haka na fi jin Fadeelar Fadeel dina a zuciyata"

Murmushin farinciki ya saki kana ya rungumeta cikin kaunar ta yace. "Muga maganin ki Mahmah, har yau
kin ki gaya min wani irin ciwo kike" Fadeel ya fada da damuwa saman fusk'ar sa.
Ledan maganin ta boye domin sam bata son ya sani, ta rufe zancen da cewa "wai me dan albarka ke dafa
wa Mahmah'n sa ne?"

Murmushi yayi yace "taliya zan dafa miki kada ki dawo kina jin yunwa, gashi wutar ma taki kamawa sosai"

"sannu dan albarka, ai sauke wanna girkin zanyi, tunda har kalanzir(kerosene) na siyo galan daya, sai inyi
mana jar miya da naman kazar nan, ai Allah ya yayi wa wanna yarinyar albarka, yaushe rabon mu da miyar
stew (dage dage)" ta kai ayar maganar tana shiga daki domin boye maganin kamar kullum gudun kada
Fadeel ya gani, kana ta fito ta fara kokarin dora musu girki....

*** *** *** ***

A dan gagauce ta fito daga bathroom sanye da bathrobe fari kal, tsadaden lotion daya dace da kalar skin
dinta ta fara murzawa a lallausan farar fatar ta, bayan ta gama ta sanya inner wears farare kal, ta bud'e
closet dinta mai murfin glass gaba dayan sa, take uban kayan sawar ta ya bayyana wanda koda shekaru
ashirin nan gaba zasu ishe ta a wadace, hannu ta dora a kugu tana bin kayan da kallo, karshe dai ta ciro
wani pencil trouser hadi da wani fashion riga mai hannun armless, sai kimono mai shara shara hadadde
black color, sai dan mafayin rolling karami duka na company *PRADA* bayan duk ta sanya kayan tayi rolling
batare da ko digon makeup a fuskar ta ba, amma tayi kyau sosai mai jan hankali kuwa, bangaren da take
ajiye zallan takalma ta nufa, wasu hills masu tsini ta sanya kirar *HELLS STUART WERITZMAN* wanda
tsadar sa zai kai *$104,765* da ganin takalmin ma ba sai an fada ba kasan tsadadde ne, turaren *Majesty*
mai dadin kamshi ta fesa sama sama hadi da daura agogon zallan zinari kana ta ɗauki wayar ta wanna
karon kirar *Gold striker iPhone 3Gs supreme da kudin sa yakai $3.2million*, dan hand bag ta dauko kalar
takalmin kana ta fice cikin sauri kamar ba takalmi mai tsini bane a kafarta, wanda hakan zai tabbatar wa
mutum cewa ta saba da saka su...
Ɓangaren Mommah ta nufa ta same ta tare da Daddy zaune suna dan taba hira, sallama tayi duk suka
amsa cikin kaunar ta fuskar su dauke da murmushi kana ta nufi Daddy ta bashi sumbata a kumatu haka
zalika Mommah... Babu bata lokaci Daddy ya mike yana gyara zaman tsadaddiyar rigar shaddar jikinsa da
aka yiwa ɗinkin zamani, sai shekarun sa suka sake buya, hannu Fadeelah ya kama suka fice bayan sun yi
sallama da Mommah...

Suna fitowa farfajiyar gidan suka tarar bodyguard's dinta dama na Daddy tsaye jikin tsadaddun motoci jere
reras har guda goma, cikin sauri bodyguards biyu suka bud'e masu kofofin wata mota kirar *FERRARI LA
FERRARI* fari, kana bodyguards suka shiga sauran motocin taran suka fara fita daga gidan a jere, motar da
su Fadeelah ke ciki shine a tsakiyar motocin taran domin tabbatar da tsaro.

Babban hall din da sukan yi meeting ko wani sanarwa wa ma'aikatansu da kuma sauran bushiness partners
suka nufa... gaba daya kowa ya hallara su kadai ake jira, zama suka yi nan aka gaisa cikin wayewa kana suka
fara tattauna abinda ya kawo su.
(Kasancewar duk meeting ko wani abu daya shafi dukiyar Daddy to da fadeelah yake zuwa domin a
dukkanin kadarorinsa sunan ta ne)
WANNA KENAN

*** *** *** ***

Zaune suke a *ORIENTAL HOTEL* gaba d'aya sun manta kowa a duniya saboda hirar soyaayyar da suke
babu kama hannun yaro, hakan yasa suke jin kansu tamkar su kadai ne a duniyar, kallo daya zaka musu
kasan cewa su di'n masoyan asali ne masu so da tattalin junan su.
Cikin zakin muryar ta tace "har yanzu baka zo gidanmu ba, ban san meyasa ba, kuma Mommah da Daddy
na basu da matsala" ta karasa a yangance, wanna mutum zai yi tunanin kirkirowa tayi, sam ba haka bane
dabi'ar ta ce hakan.

Murmushin ƙarfin hali ya sakar mata, har ga Allah yana fargaban zuwa gidan su Fadeelah domin bai san a
wani yanayi iyayenta zasu karbe shi ba. Kullum da kalar waya, kayan sawa, mota da zata yi amfanin da shi,
duk da kasancewar sa talaka amma yasan tsadaddun abubuwa, domin a makaranta yayi rayuwa da
mutane kala kala hakan yasa yake da sani kan abubuwan rayuwa da dama, duk da hakan yana fatan
halayen iyayen Fadeelah ya zama irin na yarsu, saboda ba zai taba juran rasa ta ba, da kyawawan idanun sa
ya tsare ta domin kwantar mata da hankali yace "Darling am sorry, in sha Allah zan zo gaida su Daddy
soon"

Murmushi farinciki ta saki kana tace "da kuwa ranar nayi farinciki"
Martanin murmushin ya mayar mata zafaffan soyaayyar ta na ratsa shi, yana kallonta ta bud'e handbag
dinta, waya ta miko masa tana kallonsa da murmushi, da kallo yabi wayar dake sanye a tafin hannunta
banda daukar ido babu abinda take yi wanda ya kasance kirar *SUPERNOVA IPHONE 6* "ka rike ka dinga
amfani dashi, kaga idan ma muna son ganin junan mu sai muyi video call ko?"

Bakin ta dake motsi kawai yake bi da kallo kana ya girgiza kansa alamun "a'a" bata fuska tayi kamar zata yi
kuka tace "baka son abun hannuna ko?"

Girgiza kai yayi yace "ta ya ya zan ki abinda ya fito daga hannun abra kaunata? Kiyi hakuri kin ji bazan iya
karba bane, I prefer na cigaba da amfani da wanna" ya fad'a yana daga dan itel d'insa.
Kallonsa take with much respect, ba kadan ba take matukar son wanna halin nasa, sam bashi da mataciyar
zuciya kamar na wasu samari da suke son mace ta dinga yi musu hidima, tabbas ta ga Samari da yawa da
suke son ta dan dukiyar ta, hakan yasa bata soyaayya amma daga haduwar ta da Fadeel ta fuskanci cewa
ba duka aka taru aka zama daya ba. Duk da bata so yanda yaki karba ba amma ta jinjina masa kai kawai
hadi da cewa "ok ba matsala"

Murmushi ya saki kana ya yi tunanin yin abinda zai faranta ranta, take ya fito da cardboard paper ya fara
zana fuskar ta kamar yadda yake a duk lokacin da suka hadu.

Gyara zama tayi fuskar ta dauke da murmushi yayinda ya cigaba da zana ta.

Sai misalin karfe takwas na dare suka yi sallama... bakin mota ya rako ta ta shige tana daga masa hannu,
kasancewar daga company ɗin su tace bodyguards dinta su wuce gida, duk da sun san sun karya dokar
daddy, amma kuma basu yi jayayya da Fadeelah ba...

Daidai tangamemmen gate din estate dinsu ta danna horn mai gadi ya bud'e mata, babu bata lokaci ta
danna hancin motar ciki, sai da ta daidaita parking ta fito hannun ta dauke da cardboard paper, gabanta ne
ya dan fadi ganin bodyguards dinta tsaye cirko cirko kansu a kasa yayinda Daddy ke tsaye gaban su fuskar
sa daura tamau da alama balbale su da fada yake...

(Not edited)

In sha Allah zanyi kokarin baku update gobe, nagode sosai da kaunar da kuke nunawa books dina😍

Share fisabilillah
Comment comment comment

Saboda Allah vote and follow me on wattpad @NoorEemaan

Editing is not allowed❌

I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*

💝ƘƳAUTAR ƘOƊA💝
(Its all about love, scracife, hatred and destiny)

*First edition*

_by NoorEemaan_✍️

Wattpad
@NoorEemaan

ELEGANT ONLINE WRITER'S📚🖊

Juma'at Mubarak to all Muslims ummah,


Allah ya sa damu da Alkhairi cikinta, yasa muyi kyakyyawar karshe, mu kuma cika da kyau da imani.
NoorEemaan na kaunar ku my fans❤

_I must say this....😃 What a coincidence! a ranar da nayi typing wanna page din Friday ne, which is last
year, ikon rabbi kuma Gashi nayi reposting again still that Friday_😻

https://facebook.com/groups/943534712916776/
Masu amfani da facebook su yi join ta wanna link din.

Page 13-14

............A sanyaye ta karaso gaban su, daidai lokacin Daddy ya dagawa bodyguards dinta hannu alamun su
tafi, ba musu suka fice kasan su a kasa alamun girmamawa, yayinda suka ji relief na ganin Fadeelah, akasin
hakan kuma da sunan su gawa a hannun Alhaji Imran.

Bin bayan Daddy Fadeelah tayi har main parlour, hannun sa goye a bayan sa ya juyo gareta kana ya jefa
mata tambaya kamar haka " a iya sanina 'yata mai bin umarni na ce, sannan bata da wurin zuwa daga
company sai gida, sannan yaushe kika fara fita ke kadai ba tare da bodyguard ba princess? Did you know
thousands of enemy we have out there? (Kin san dubanin makiyan da muke dashi a gari?)" Ya karasa a
dame, yana nuni da yatsa, duk yanda yaso yi mata fada abin ya gagara, matsanancin soyaayyar 'yarsa ta
hana shi yi mata fada domin sam baya son ganin bacin ranta koda na sakan daya ne.

Ajiyar zuciya ta sauke, domin abinda tayi tunani daban, tabbas ta san cewa kaunar da yake mata yasa yake
bata tsaro domin kula da lafiyar ta. Cikin zallan son mahaifin ta kana murya a sanyaye tace "am so sorry
Daddy, bazan sake fita ba tare da bodyguard ba, na fita shakatawa ne, ganin ba nisa nayi sosai da gida ba
yasa nace su taho gida" ta karasa cikin shagwaba da marairaita ta yadda zai fi tausaya mata.

Murmushi mai taushi ya sakar mata, wanna maganar da ta yi ya wanke masa dukkanin damuwar daya
dauki awanni cikin sa, "its ok my princess, sannan ki dinga barin wayar ki a bude saboda irin haka, domin
dana samu wayar ki da hankalina bai tashi haka ba"

Murmushi tayi, domin soyaayya ta dauke mata hankali har ta manta da wata aba wai waya "in sha Allah
Daddy zan kiyaye, ina Mommah nah?"

"Tana part d'inta tun rana kanta ke ciwo, ita ma hankalin ta gaba daya ya tashi da rashin dawowarki... ni
nace taje ta kwanta ta samu huta, yanzu zanje part dinta domin sanar da ita kin dawo saboda hankalinta
ya kwanta, ke ma je ki huta good night" ya fad'a yana bata sumbata a goshinta....

Handbag dinta kadai ta ajiye kana ta dauki gum(gam) data siya takanas domin manna hotunan da yakan
zana na fuskarta a duk haduwar su.

Tsaye tayi tana bin zanen da kallo wanda yanzu sun dawo shida reras, har yau ta kasa gane wanne yafi kyau
cikin zanen domin dukkansu ba baya wurin kyau, murmushi take saki akai- akai hirar da suka tayi dazu ke
dawo k'wak'walwarta, daga karshe ta cire kayanta ta fada wanka bayan ta kunna wayoyinta, ta jima sosai a
toilet duk cikin sunan wanka kana ta fito daure da towel, lotion mai k'amshin gaske ta shafa kana ta sanya
pajamas masu kyau pitch color na company *NIKE* dan karamin hijab fari half sunnah ta sanya, wata
yalwataccen jallabiya kirar saudiya ta dora kan pajamas din kana ta tayar da sallah...

Bayan ta iddar ta cire jallabiyan ta haye gado, take wayarta ta dauki kara, lumshe ido tayi kana ta bud'e a
nutse murmushi dauke kan fuskarta domin tasan Fadeel ne, domin shi kadai ta sanyawa wanna ringing
tone din, latsa Kore tayi ta kara wayar a kunnenta hadi da furta "Assalama alaykum" cikin zazzakar
muryarta.

"Wa'alaikumu salam" ya amsa yana kara curewa kan 'yar yololuwar katifarsa da alama muryar tace ta
haddasa masa shiga wanna yanayin

"My darling yakike, ya gajiya, Fatan kin je gida lafiya?"duka ya jero mata tambayar a lokacin daya.
A shagwa6e tace "Alhamdulillah, wallahi my one na gaji sosai, amma yanzu na fara warwarewa
sak'amak'on jin muryar muradina, muradin raina, Yes my heart desire".
Murmushi ya saki cikin wani sabon shauki yasake k'amk'ame jikinsa kana yace "I hope ina tare dake, I hope
yanzu mu ma'aurata ne dana yi miki tausa" ya karasa cikin rada.
Murmushi mai sauti ta saki, tana ji ina ma Ina ma su din ma'aurata ne, da hakika sun gina rayuwar aure
mai cike da so hadi da birgewa.

"Darling kaunar ki zata haukata ni, kinsan har mafarkin nake akan ki kullum, jiya da asuba Mahmah tazo
tashina Saboda na makara taji ina ta kiran Fadeelah cikin bacci, dan Allah ki rike mun amanar kanki bazan
iya juran rasa ki ba a rayuwa, ji nake tamkar dan soyaayyar ki kadai aka halicce ni" ya karasa cikin iyakar
gaskiyar sa.

Pillow ta k'amk'ame a kirjinta, maganganun sa na shiga jini da tsokar jikinta har wani tashi sigar jikinta ke yi
alamun maganganun na shigar ta sosai.

Cikin wani salon so tace "my one, kasani cewa babu kowa a birnin zuciyar Fadeelah fiye da Fadeel dinta,
sannan Abadan da'iman muna tare, mutuwa ce zata raba mu in sha Allah"

Ajiyar zuciya mai karfi ya sauk'e daya sanya taji wani sabon so da tausayin sa, cikin muryar rada yace
"Darling mutuwar ma nafison ta d'auke mu a lokaci daya, ko kuma ni na fara mutuwa domin bazan juri
rasa ki a rayuwa ta ba..."

Katse shi tayi da cewa"gwara ta dauke mu a lokaci daya, mu tafi tare, nima bazan juri rasa ka ba my one,
we are made for each other I love you"

"I love you so much too my Darling, ki kwanta kiyi bacci, ki yi mafarkina bye muaaahh" ya karasa da sakar
mata sumbata ta wayar

Wani sanyi dadi ke ratsa ta hakika babu abinda ya kai kasamu masoyi mai son ka tsakani da Allah. "love is
sweet when it's new, sweeter when its you fadeel, and sweetest when it's pure" ta fada a bayyane fuskarta
d'auke da murmushi, addu'ar kwanciya bacci tayi kana ta rufe jikinta da duvet babu jimawa bacci mai
dadin gaske masu cike da mafarkin Fadeel ya d'auke ta...

*WASHEGARI*
suna zaune a dinning table suna breakfast, Fadeelah sai murmushi take ita kadai har Daddy ya farga yayi
gyaran murya hadi da cewa "My beautiful princess, wanna murmushi fa ke kadai? kwanan nan na kasa
gane miki fa, You seems over happy" ya fada shi ma da murmushi kan fuskarsa alamun farincikin daya
tsinci 'yarsa a ciki yayi masa dadi...

"Atoh professor nah, taya ni tambayar ta, domin yanzu hardly kaga fuskar sweetheart ba murmushi, ya dai
kamata ki gaya mana what's the secret behind" Mommah tace tana kai Irish omelette bakinta.

Dariya tayi cikin jin kunya, kana tace "babu komai Daddy, Mommah"

"Haka dai kika ce, amma bari idan tayi tsami zamuji koma menene, ko professor nah?" Ta fada tana kallon
Daddy.
"Haka yake my first Lady" Daddy yace cikin salon su na manya.

Fadeelah kanta a kasa tana cin chips dinta daya bayan daya, yayinda take tunanin shin ta gayawa Daddy'n
ta cewa ta samu mahadin rayuwar ta, a life partner ko a'a?....✍️

_In sha Allah gobe ma zan sake baku sabon update da sannu zamu shiga cikin labarin..._
_Amma two pages as promise tunda reposting muke_

*Thanks my people da kulawar ku gareni a sakamakon jina shiru da kuka yi jiya, i was damn busy ko data
ban kunna ba jiya, wadanda suka yi min mgn private dama groups, ina godiya sosai*

Share

Comment

Vote

Editing is not allowed❌

I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*

💝ƘYAUTAR ƘOƊA💝
(It's all about love, scracife, hatred and destiny)

_by Noor Eemaan_✍️


Wattpad
@NoorEemaan

ELEGANT ONLINE WRITER'S📚🖊

Page 15-16

Sau ba adadi ta budi baki da niyyar yin magana, sai taji wani abu mai nauyi ya rufe akinta, karshe dai ta
yanke hukunci bari zuwa nan gaba sai ta sanar da shi komai...

Bayan ta gama breakfast ta koma bangaren ta, da tunanin idan ta dawo zata leka part din kakanin ta da
sauran ahalin gidan su gaisa domin yau kwana hudu kenan bata leka su ba, kasancewar akwai tazara mai
yawa tsakanin parts din... Da wanna ta shiga toilet, cikin jaku'zzie ta fada, lumshe ido tayi ruwan dumin na
ratsa ta, *L'occitane verbena shower* ta fara murzawa a farar fatar ta, kasancewar ta kusan yin latti yasa
tayi wankan a gurguje ta fito daure da pink towel, lotion take shafawa idanunta kafe kan hotunan zanenta
dake manne a bango, murmushi take saki ba tare da tasan tana yin hakan ba.

Inner wears ta saka, kana ta dauko wata hadaddiyar gown na company *Giorgio Armani* banda walwali
babu abinda rigar ke yi, dan veil din rigar ta yana a kanta kana ta dauko takalmi wage da handbag duka na
company Giorgio Armani din.

Duk da bata son yin make-up sosai, amma haka nan ta ji yau tana sha'awar yi, a tsayen ta fara goga
hada'dd'en powder dinta daya dace da skin color d'inta sannan ta sanya k'walli hadi da goga pink lip gloss,
fadin kyau da haduwar fadeelah bata baki ne, ita kanta sai data yaba duk da ta san ita din mai kyau ce,
amma tabbas *idan kana da k'yau ka kara da wanka* inji malam bahaushe.

*DKNY(golden delicious millions dollars fragrance)* shine turaren da Daddy ya kawo mata tsaraba daga
USA wanda kudin sa 1 million ne, sannan shine turaren mai mafi tsadar gaske wanda babu kamar sa a
yanzu. Fesawa tayi Sama_sama tana yaba kamshin turaren mai sa nutsuwa, hakika DKNY yaci kudin sa,
glass ta sanya a fuskarta brown kana ta fito bayan ta dauki wayar ta kirar *falcon supernova*
Ganin tayi latti sosai yasa bata koma part din su Daddy ba, direct ta nufi inda motoci ke fake suna jiran ta,
kamar kullum motar da ake tanada domin ita kadai ne, wanna karon *Bugatti La voiture Noire* aka bud'e
Mata kalan fara, yayinda duk suke gaishe ta cikin girmamawa, fuskarta a sake kana da murmushi ta amsa,
zama tayi aka rufe mata kofar, gate man ya wangale masu gate suka fara ficewa dayan bayan daya....

Idanunta na kan wayarta tana danne-danne, da alama chatting take kamar ance ta dago kanta ta ga wani
kamar Fadeel ya taho a kafa, zare glass din idanunta tayi, "tabbas my one ne" ta aiyana a ranta idanunta
kan Fadeel din tace wa driver "stop the car!" ba musu mai tuka ta ya tsaya, take sauran suma suka tsaya...
Bata jira ba, ta balle murfin motar ta fito, har ya dan gota su domin sam bai lura da ita ba...

Tana jikin motar ta hard'e hannunta kan kirjinta ta kira shi a shagwa'be
"my one"
cak! ya tsaya, kana ya juyo murmushi d'auke kan fuskar sa. Takowa yayi ya dawo gabanta yace "my
darling?"
Bata rai tayi cikin wasa tace "Shine kayi fuska ko, bayan ka ganni"
Murmushi ya kara saki shagwa'bar ta na tafiya da shi matuk'a "my Darling afuwan, sam ban ganki ba" ya
fada cikin yanayin na dan ji nauyi, domin har kokarin boye kafarsa data yi butu-butu da kasa yake alamun
ya sha tafiya sosai....

Dariya ce ta so kamata domin ta fahimce shi sarai, shi bai san duka wanna bai dameta ba, shi takeso, ba
wai kyau, qualities ko wani abu daya shafe shi ba.

Kura masa ido tayi tana yaba kyawun sa, sam bashi da haske ko kadan, amma yana da mugun kyau da
wasu fararen ma basu da shi, kallon kafar tasa ta sake yi kana ta dawo da kallonta kan fuskar sa tace "ina
kaje haka?"
Shafa kansa yayi yace "Mahmah ce ta aike ni kai kudi gidan biredi, fatan sauraniyar Kyawawa ta tashi
lafiya?"

Murmushi tayi, tausayin sa fall zuciyar ta tace "alhamdulillah, kai fa?"


"Same" yace a tak'aice.

Murmushi tayi wani lokacin tana son wanna halin sa na rashin son dagon magana, sannan tasan idan tace
ya hau mota su ajiye shi gida ko bashi kudin mota tofah bazai yarda ba, ta rasa wani irin mutum ne dashi
daya dau duniya da matukar saukin gaske, a fili tace "my one akwai maganar da nake so muyi da kai, it's
very important"

"Ok ba matsala zamu yi waya, then muyi fixing wurin haduwa ko?"

"Toh shikenan bye na makara office" tace tana daga masa hannun ta.

"Zan yi kewar ki sosai darling, take care I love you"

"I love you too" tace tana shiga motar ta.

Yanda bud'e murya yanda zata ji yace "Darling kinyi kyau sosai, karki bari kowa ya kalli min Kyakyyawar
fuskar ki fa..."

Dariya tayi domin yadda ya bata rai sai ya dawo mata kamar wani yaro karami.

Kamar kullum a nutse ta shiga cikin company, duk suka gaisa da ma'aikata(staff) d'inta, kana ta wuce office

"wallahi abokina yarinyar boss na matukar tafiya da ni, naso ace tazo a matsayin wacce bata fi karfina ba,
da ba shakka zan gabatar mata da kaina a matsayin masoyinta, domin sosai nake sonta" Cewar wani
matashi dake sanye da kaya mai dauke da tambarin company.

Abokin nasa yace "kasan Allah, ina jin na fika son yarinyar nan, kowa a company nan maganar ta yake,
mutane da dama sun ce matukar cutar dake damunta ya kai minzanin da ya gaza, to zasu iya Sadaukar
mata da nasu ciki har dani, ban taba ganin mai son jama'a hadi da talakawa kamar yar boss ba".
Haka suka cigaba da hira duka dai kan Fadeelah, haka kullum yawanci ma'aikatanta suke hira a kanta, a
duniya babu inda za a ce mutum bai da makiya, amma a company'n din su Fadeelah za a iya cewa kaf
dinsu masoyan ta ne.

Please follow and vote me on wattpad👏🥺


@NoorEemaan

Share✔

Comment✔

Vote✔

Edit❌❌❌

I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*

https://facebook.com/groups/943534712916776/
Masu amfani da facebook su yi join ta wanna link din.

💝ƘƳAUTAR ƘOƊA💝
(It's all about love, scracife, hatred and destiny)

_byNoor Eemaan_✍️
07082281566
Wattpad
@NoorEemaan

https://facebook.com/groups/943534712916776/
Masu amfani da facebook su yi join ta wanna link din.

Page 17-18

Bayan sun dawo daga company, wanka kawai tayi ta nufi part di'n family'n babanta, kasancewar da yar
tafiya hakan yasa tayi amfani da mota.

Da Abba Yusuf ta fara cin karo wanda ya kasance yaya ga Daddy'n ta, kyakyyawan farin mutum ne mai
yawan fara'a sabanin Daddy'n Fadeelah da bai cika fara'a ba.

Gaban sa ta tsugunna cikin girmamawa tace


"AbbaYusuf ina wuni"

Murmushi yayi har farin hokarin Makkah sa ya bayyana sai walwali yake yace "A'a Fadeelah kina lafiya,
kinyi wuyar gani, ko nayi surukine ya boye min ke?"

Dariya tayi cikin jin kunya tace " Abba Yusuf, aiki ne wallahi, amma nazo kwanaki mama(matar Abba Yusuf)
tace min baka dade da fita ba"

"Kwarai kuwa, anyi haka, ya aikin? Toh Allah ya taimaka 'yar albarka"

"Alhamdulillah Abba Yusuf, Ameen nagode"

Bai kara cewa komai ba ya fada motar sa ya bar gidan.

Da kallo ta bi Abba Yusuf, sosai take kaunar sa, domin ya fita daban cikin yan'uwan Daddy'n ta.

Bangaren kakarta ta fara zuwa, sallama tayi aka amsa hadi da bata izinin shigowa. Zaune dattijuwar matar
dake kan wasu had'add'un kujera daya kara kawata falon, duk da kasancewar matar tsohuwa ce domin
zata kai irin shekaru 79.

Fara ce sosai bata da yawan fara'a, yar gayu ce sosai, domin duk da shekarun nan nata sanye take da riga
da skirt na tsadaddiyar atamfa daya sha dinkin zamanin fuskar ta kuwa ya sha make-up irin na wayayyun
mata, yayinda take sanye da medicated glass, tun kafin Fadeelah ta karaso take cewa "my beautiful grand-
daughter"

Murmushi Fadeelah tayi tace " Grandma" hadi da rungume ta kana ta gaisheta, a sake grandma ta amsa
gaisuwar ta domin kaf cikin jikokinta tana matuk'ar ji da Fadeelah.
"Ai Daddy'n ki bai jima da barin nan ba, har Ina cewa kin guje ni kwana biyu ashe yar halak kina tafe"

"Murmushi tayi hadi da cewa " Grandma wallahi naso zuwa abubuwa ne suka min yawa, akwai wani
branch da Daddy zai bud'e a Kaduna ya sa abubuwa suka kara min yawa yanzu"

"Eh kwarai ya gaya min haka, toh sannu Allah yayi miki albarka, ya Samira(Mommah)?"

"Alhamdulillah, tana lafiya. Grandma yau baki yi kunun aya ba?"

Murmushi grandma tayi tace "grand-daughter kenan, ke da kunun ayar nan, toh yana fridge dazu nayi wani
domin na shanye na safe"

"Ai a wajen ki na gado son kunun aya, tunda Daddy baya sha" Fadeelah ta fada cikin tsokana tana bude
fridge.

Murmushi kawai Grandma tayi tana bin jikarta mafi soyuwa a ranta da kallo. Dawowa tayi ta zauna da mug
hadi da glass cup ta siyayi kunun aya mai sanyi domin har wani rabar sanyi jikin glass cup d'in yake, a nutse
take shan kunun yayinda suke hira da grandma har ta shanye suka yi sallama.
Part din sauran yan'uwan taje ta gaishe su kana ta fada motarta ta koma part di'n su.

Bangaren Mommah ta koma, ta tarar da ita a zaune tana kallon tashar Bollywood, jikinta ta fada tace "
Mommah nah sannu da gida"

Shafa lallausan gashinta Mommah tayi tace "Sweetheart yakike yau kam kin dade"

"Mommah na dade da dawowa fa, part dinsu Grandma naje"

"Kin kyauta kam, kin same su lafiya?"

"Lafiya lou suke, sun ma ce suna gaishe ki"

"Ina amsawa, nima na kwana biyu ban leka ba, amma idan professor ya dawo zan nemi izini naje, tashi ki ci
abincin gashi can cikin warmers, yau girki kala uku nayi miki da kaina ba da taimakon chef's ba, kuma duka
favorite dinki"

"Awwwwnn my sweet Mommah, nagode sosai muaaahh" ta bata sumbata a kumatu tana nufar dinning
table.
Dan daga murya Mommah tayi tace "kuma duka zaki cinye domin nasan ki da rashin cin abinci shiyasa gaki
bakya hauki kullum"
Mommah ta karasa a zolaye.

Dariya Fadeelah tayi ta zauna tana cin abincin daga dinning table din suke dan taba hira.

★★★

*Bayan sati daya*

"Ohh Mahmah har na haddace labarin yarinyar da kuka hadu a asibiti, kullum sai kin yi min hirar ta, ni
wallahi dama labarin Fadeelah kike min kullum" Fadeel dake zaune kusa da mahmah ya fada a ɗan
shagwabe

Dariya Mahmah tayi ita kanta tana mamakin so da kauna da take yiwa yarinyar data hadu da ita a asibiti da
ko sunanta bata sani ba. Kullum sai ta yi hirar ta, maganar ta ya kasa barin baki da zuciyar ta. A fili tace
"Fadeel my son Ina mai tabbatar maka da cewa da zaka ga yarinyar nan data kwanta maka a rai ko dan
Saboda nutsuwa da sanin mutuncin dan Adam"

Shiru kawai yayi domin yasan matukar Mahmah na son abu tofah ta dinga maganar abin kenan...

Ana haka wayar sa ta fara ringing yana dubawa yaga "my Darling" murmushi ya saki kana ya mike yana
kara wayar a kunnen sa,
"ok gani nan zuwa yanzu nan Darling" shine amsar da Fadeel ya bawa Fadeelah

Dan shafa kansa yayi alamun jin kunya yace "Mahmah zan fita"

Dariya tayi tace "yaushe Fadeel dina ya fara jin kunya ta, toh ka gaishe ta, idan ka dawo zamuyi wata
magana"

"A'a Mahmah zan iya tsaya muyi maganar dake"

"A'a ban amince ba, ka bar min suruka da jira jeka dai ka dawo, Allah ya kiyaye hanya sai ka dawo"

"Toh Mahmah na ameen, I love you"

"Love you too son" tace tana cigaba da jajjaga attaruhun dake gaban ta.

*Banana Island*
shine inda fadeelah tace su hadu, wanda ya kasance hadadden wurin shakatawa ne.
Tun daga kofar wajen ya ga bodyguards dinta reras jikin motocin ta, shi kanshi a wasu lokutan yana
mamaki yanda ya iya kamuwa da son diyar miloniya haka, dan dai so daban yake babu ruwan sa da kudi,
kyau, ko wani abu na mutum amma yasan Fadeelah ba sa'ar yin sa bace domin wusiyar rakumi tayi nesa da
kasa.

Sai dai ko kadan baya jin zai karaya har abada har sai ya mallake ta...

gaisheshi suka yi, domin sun gane shi yanzu sosai, amsawa yayi a mutunce ya nufi cikin wajen.

Tun daga nesa suke jefan juna da kallo mai dauke da tsantsar so hadi da kauna.

Bayan sun yi gaisuwa irin ta masoya.Ta gabatar masa da abinci, lemo hadi da ruwa gora data yi musu
ordering.
Saboda kada ta ji ba dadi ya sa shi shan ruwa kadai kana ya kalleta a tausashe yace "my Darling kince akwai
magana mai muhimmanci da zamuyi"

Diamond ring di'n hannunta take murzawa yayinda k'lanta ke kasa, a sanyaye ta dago hadi da cewa "eh"
wanda yayi daidai da zubar wasu hawaye masu zafin gaske a idanunta.

"Subhanallah! My Darling meya faru haka, mai yayi zafi? Please ki gayamin kafin zuciyata ta buga, bana son
ganin damuwa a tare dake ko kadan, hazantar gaya min damuwar ki dan Allah" Ya fada cikin zallar damuwa
yayinda ya dawo gabanta ya tsugunna.

_comment ɗinku na kadan fa, ko in ajiye labarin ne_🤒

Share✔

Comment✔

Vote✔

Edit❌

I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*

💝KƳAUTAR ƘOƊA💝
(It's all about love, scracife, hatred and destiny)

*Wattpad*
@NoorEemaan

ELEGANT ONLINE WRITER'S📚🖊

https://facebook.com/groups/943534712916776/
Masu amfani da facebook su yi join ta wanna link din.

The destiny has begin

Page 19-20

(Not edited)

Cikin tashin hankali mara mitsaltuwa Fadeel ke wanna maganar.

Wasu hawaye ne suka sake zubowa a idanun Fadeelah tamkar an balle famfo. A karo na barkatai take son
furta masa damuwar ta, damuwar da bata son tuno dashi, haka zalika duk wani family'n nata basa son
tada maganar cutar ta saboda muninsa....

A karo na biyar ya sake cewa "please Darling say something, kada kisa zuciyata ta buga saboda damuwar
da kike ciki, ki gaya min ko akwai wani abu dazan iya taimaka miki dashi please" ya kai karshen maganar
tamkar zai rusa mata da kuka.

Hannu tasa tana goge hawayen fuskar ta, amma kara zubowa suke, a sanyaye kana cikin muryar kuka tace
"ina...In...ina... d'auke da cutar *Koda* Yes kidney tsawon shekaru masu yawa, karshen zuwa na asibiti
likitana yace bazan kara watanin biyu masu kyau ba zan mutu, zan mutu matuk'ar ba a samu wanda zai
siyar min da kodar sa ba domin tawa tayi chronic, tayi muni sosai.... Shiru tayi tana jan numfashi kamar
zata shide kana ta cigaba

Abu ne mai matuk'ar wahala a samu, domin shekaru masu yawa kenan da ake neman wanda zai siyar min
da kodar sa amma...amma..." Shiru tayi saboda wani kuka daya sake taho mata, ajiyar zuciya ta sauk'e
kana ta sake cewa "Ban sanar da kowa a gida abinda likitana yace karshe ba, not even Daddy, na kuma yi
hakan ne domin kada hankalin su ya tashi, kaine mutum na farko dana fada wa...."
Sauran maganar ya makale sak'amak'on wani mugun kuka daya sake taho mata. har wani biyu biyu take
gani saboda wani mugun ciwon kai daya saukar mata lokaci d'aya.

Kan Fadeel na kasa yayinda wasu hawaye masu zafin gaske ke bin kuncin sa suna diga kan tiles dake
shimfud'e a kasan wajen.

Bai taba jin maganar dake barazanar tarwatsa zuciya da kwakwalwarsa kamar wanna ba. Fadeelah'nsa na
dauke da cutar koda Sannan bazata kara watanin biyu masu kyau ba.

Ji yayi duniyar na juya masa baya, mikewa yayi da kyar yana dafe kansa kana a haukace ya fara takawa
domin barin wajen yayinda zuciyarsa ke bugu tamkar zata fasa kirjinsa ta fito...

Wani sabon kuka ne ya sake zuwar wa Fadeelah zubewa tayi a kasa, cikin fitar hayyaci take cewa "Fadeel!
Fadeel!! Fadeeeeeeeel!!! Please kada ka juyamin baya" sam bashi da alamar juyowa haka ta cigaba da
kiran sunan shi tana kuka har ya bace wa ganinta.

Tamkar Fadeel d'in a gabanta tace "abinda nake gudu kenan, shiyasa na boye maka wanna ciwon nawa, ina
tsoron kada ka juyamin baya, kamar yadda *Jameel* ya yi min, duk da ba shi da wani muhalli a zuciya ta
amma naji ba dadi matuk'a, dan Allah my one come back to me bazan jure rashin ka ba, ka dawo muyi
kyakyyawar sallama domin ina daf da mutuwa". Ta kai karshe maganar tana sake sakin kuka mai ratsa
zuciya, kanta ta dora kan table din wajen ta cigaba da kukanta har idanun ta ya fara yaji kana ta tsagaita
tana sauke ajiyar zuciya...

Ta kai awa daya a zaune, sannan ta mike domin barin wajen.


Babban glass baki ta kafa a fuskar ta, domin sam bata son kowa ya ga ta yi kuka, domin ta kasance mutum
ce da bata son idan tana cikin damuwa ta sanya wani.

Sai dai ta makaro domin duk Wanda yaga fuskarta zai san tayi kuka Saboda wani mugun ja da yayi...

*** *** *** *** ***

Ikon Allah kadai ne ya kai Fadeel gida lafiya, domin a kafa ya taka har gidan. Saboda tashin hankalin da
yake ciki sam bai ji wahalar tafiyar ba.

Mahmah na zaune a kujera tana shan ruwa taji ya shigo a haukace bako sallama, dakinsa ya nufa ya rufe
da sakata. Kan kafitar sa ya fada, ya fashe da wani mugun kuka tamkar mace, kuka yake yana surutai shi
d'aya, cikin damuwa Mahmah ta ajiye cup din hannunta ta nufi kofar dakinsa.
k'wank'wasawa take tana fadin "Fadeel my son, ka bud'e, meya sameka? Wani ya mutu ne ko wani abu ya
faru? Ka bud'e ka gaya wa Mahmah'nka damuwarka kaji"

Ko motsi bai yi ba, domin bai san mahmah na nayi ba, kuka yake mai tada zuciya, kuka yake jin cewar
fadeelah'nsa na daf da barin duniya, shi kam ya zai yi da rayuwar sa, idan Fadeelah ta bar duniya meye
amfanin zaman sa babu ita???

*** *** *** ***

Bangaren fadeelah kuwa, koda isar su gida bata jira sun bud'e mata kofar mota ba, ta fita hadi da daga
musu hannu alamun bata bukatar rakiyar su.
Cikin bin umarnin ta suka tsaya cak! A guje tayi bangaren ta tana kuka.

Yar aikin Fadeelah mai suna Elizabeth kadai ce a hada'dd'en falon d'aya kasance mallakin Fadeelah tana
goge centre table, bata ko ji gaisuwar da Elizabeth d'in ke mata ba, Saboda halin tashin hankali da take
ciki, bedroom d'inta ta shige hadi da murza key.

Da mamaki Elizabeth tabi Fadeelah ta da kallo, tayi matuk'ar mamakin ganin ta a wanna yanayi, domin
sanin kowa ne cewa Fadeelah yar gata ce sannan mai yawan fara'a .

A fili ta furta "what's wrong with ma'am?" Sanin cewa bata da bai Mata amsa yasa ta cigaba da
goge_gogen ta tana jin ba dadi domin har ranta tana kaunar fadeelah...

Da misalin 8:00pm kukun Fadeelah tsaye a bangarenta yayi bugun duniya shiru bata bud'e ba, ya kuma
san tana ciki domin Elizabeth ta bashi tabbacin tana nan..

ƙarshe dai ya ajiye tsad'add'en tray di'n mai d'auke da aɓincin ta akai ya fita.
(kasancewar shi ke mata girki, Emmanuel sunan sa, ƙwararren chef ne d'aya iya girƙe_girƙen zamanin
ɗana nan namu na Nigeria da ma k'asashen ketare. Amma akwai ranakun da take warewa da a bangaren
Mommah take cin abinci) wanna kenan.

Zaunen Elizabeth da Emmanuel suke a boy's quarters, tattaunawa suke kan fadeelah, cikin damuwa da
tsoro Elizabeth tace "Emma anya bazamu gaya wa boss abinda ke damun ma'am ba, kasan halin boss ko,
wani abu na samunta, kama mu zai yi fa, kasan yana ji da 'yar sa ko ehen"

Jinjina kai Emmanuel yayi cikin pidgin English yace "Eli na true you talk ooh, I swear boss no get joy at all,
he fit shot us with that his big gun, stand up let's go and meet him" ya karasa cikin turanci mai k'yau.
A jere suka nufi bangaren daddy, suka tarar dashi zaune tare da Mommah data zo sanar dashi bata ji
shigowar Fadeelah ba, ganin su Elizabeth ya hana mommah magana.
A dan tsorace su Elizabeth suka hada baki wurin fadin "Good evening boss"

Sai d'aya debi mintuna biyar idanunsa kafe kan jarida kana ya dago yace "Evening, how may I help you?"
Murya na rawa suka sanar dashi, domin sosai suke jin tsoron sa, muryar sa mai dan kauri da tarin kwarjini
ma ya isa ya sanya mutum a firgici.

"What!?" Yace yana mik'ewa da hanzari kana ya nufi side dinta cikin gudu-gudu Mommah na biye dashi
cikin tashin hankali, fatan su kada su ji wani abu ko su ga Fadeelah'n cikin mayuwancin hali...

Ƙwanƙwasa kofar su Mommah keyi da iya karfi, sai dai ko motsin Fadeelah'n basu ji ba.

Can suka fara jin sautin k'ukan ta na tashi ƙasa_ƙasa, kara rudewa Daddy yayi yace "my princess, ki bud'e
mana ƙinji, it's me your Daddy, and your Mommah too is here" ya kai karshen maganar yana kallon
Mommah da idanunta har sun fara kowa ruwan hawaye.

A sanyaye Fadeelah ta zuro kyawawwan ƙafafunta ƙasa, ba ma ta ganin gabanta sosai saboda wani jiri da
take ji, bud'e kofar tayi ta basu hanyar shigowa, cikin damuwa duk suka shiga jero mata tambayoyin akan
meke damunta?

Kuka ta fashe dashi d'aya kara tayar musu da hankali, kan hadadden gadonta suka zaunar da ita yayinda
suka zauna a gefe da gefen ta, ya zamana tana tsakiyar su.

Ganin har Mommah ta fara kuka yasa tayi shiru tana kokarin daina kukan. Sai da ta dauki mintuna goma
masu kyau sannan muryar ta a shake tace "doctor Mahfouz said bazan kara watanin biyu masu kyau ba zan
mutu domin kidney dina yayi failing, the last time dana je check up, sai tayi shiru na yan mintuna kana ta
cigaba ya sanar dani cewa dayan kodar ma ta fara tabuwa, kuma har yanzu ba'a samu wanda zai siyar min
da kodar sa ba"

_"innalillahi wa innah ilaihi raju'un"_

Mommah da Daddy suka hada baki wurin fad'in hakan. Kuka Mommah ta fashe dashi, yayinda wasu
zafaffan hawaye suka biyo kuncin Daddy, tabbas da ba dan yayi namijin kokari ba, ba shakka kukan shima
zai fashe dashi...
Sun dauki tsahon lokaci a wanna mayuwancin hali kana daddy yace "when last kika je asibitin?".

Cikin muryar kuka Fadeelah tace "Wancan watan ne " shiru Daddy yayi, gaba d'aya ya rasa abin yi, kenan a
lissafi saura wata daya. Wasu hawayen ne suka biyo kuncin sa, tabbas yasan cewar cutar Fadeelah nada
muni amma bai yi tunanin munin ya kai har da za a ce ga sauran watanin da zata kara nan gaba a duniya
ba.

Tabbas bai ga amfanin tarin dukiyar sa matuk'ar yana kallo tilon 'yarsa na mutuwa a hankali ba tare da zai
iya yin wani abu a kai ba. miliyoyin kudade ya saka kan wanna zai siyar da kodar sa wa tilon yarsa, daga nan
gida Nigeria har kasan waje amma, har yau ba a samu ba.... (Ba komai kudi ke siya wa mutum ba)

*BAYAN SATI D'AYA*

Har yau Fadeel bai fito daga dakin sa ba, tun ranar, k'asancewar akwai dan karamin toilet a dakin sa yasa
yake alwala a ciki yayi sallar sa a nan, gaba d'aya ya rame ya fita hayyacin sa.

Yana kwance kamar kullum idanunsa na siyayyar da ruwan hawaye yaji Mahmah na sake buga kofa.

Lumshe idanunsa yayi yace "Mahmah ki gafarceni, bazan bud'e miki ba, ki je Mahmah, mutuwa zan yi
banga amfanin tawa rayuwar ba"

Mahmah dake tsaye bakin kofa ta dan ji sanyi a ranta, domin tun ranar d'aya rufe dakin sai yau taji muryar
sa, cikin dan fada_fada tace "Fadeel ni Mahmah'nka ce, shin akwai wanda zaka raba damuwar ka dashi kaf
duniya sama dani? Gaba daya ka sauya hali, yanzu umarnin nake baka ka bud'e kofar nan, ko nayi nesa da
garin lagos na barka tunda baka bukatata a rayuwarka..."

Cikin sauri ya mike jin furucin Mahmah na karshe, bud'e mata kofar yayi kana ya tsaya kansa a kasa,
kallonsa mahmah take yayinda idanunta ke zubar da hawaye ganin yadda yayi rama.
Jikinta ya fada yana sakar mata kuka tamkar wani yaron goye, wani dan sanyin _sanyin yake ji a ransa
adalilin runguman d'aya yiwa mahaifiyar sa

Mahmah bata hana shi kukan ba, kanshi kawai take shafawa, sai daya yi mai isar sa kana ta riko hannunsa
har kan tabarma suka zauna. A nutse ta shiga kwantar masa da hank'ali kana tace
"meya sanyaka cikin wanna halin tsawon sati daya yau Fadeel?"

Bai boye mata komai na cutar Fadeelah ba ya sanar mata... shiru tayi yayinda zuciyarta ta karye, taji
tausayin Fadeelah matuk'a.
ta kuma sake tabbatar da cewa Fadeel, so mai zafin gaske yake wa Fadeelah'n tunda har ya shiga wanna
damuwar mai yawa, zata iya cewa halin ta ya gado matukar tana son abu bata mai son wasa, haka zalika
Fadeel...
A kuma daidai lokacin ne Fadeelah ta shigo layin gidan su Fadeel, kallon mutanen unguwar take cikin
tausayawa, domin unguwar talakawa ne sosai, sai dai hakan bai hana su hada_hadar su cikin farinciki ba.

Tausayin masoyinta Fadeel ya sake kamata, daidai lokacin motar ya tsaya a kofar gidansu. Bin gidan take
da kallon tana aiyana cewa yanzu Fadeel dinta na iya rayuwa cikin wanna gidan? Hawaye suka zubo mata,
tunda tasan cewa kwanakin mutuwar ta na kara matsowa sai gabadaya ta sake dawowa wata shiru_shiru
mara son hayaniya, bud'e mata kofa bodyguard dinta yayi ta fito a sanyaye ta tunkari cikin gidan yayinda
gabanta ke bugawa domin bata san a wani yanayi Fadeel zai karbe ta ba...

_Gobe ma zanyi k'ok'arin yi muku update, nagode muku kwarai da add'uar da kuka yiwa yar kanwata da
bata da lafiya, alhamdulillah jikin da sauki Allah ya bar kauna da zumunci my beautiful people_😍

#Share fisabilillah
#Comment
#vote

Editing is not allowed❌

I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*

💝KYAUTAR ƘOƊA💝
(its all about love, scracife, hatred and destiny)

*wattpad*
@NoorEemaan
ELEGANT ONLINE WRITER'S📚🖊

https://facebook.com/groups/943534712916776/
Masu amfani da facebook su yi join ta wanna link din.

Page 21-22

Sai da ta zo daidai soron gidan ta tsaya, gabanta na matsanancin bugawa... Tana iya hango Fadeel dinta da
wata mata zaune kusa dashi wanda bata tantama mahaifiyar sa ce. A Kallo dayan da ta musu ta hango
tarin damuwa a fuskokinsu.

Wasu hawaye ne suka sake zubo mata sakamakon mugun ramar da ta ga Fadeel yayi, jitayi tayi zuciyar ta
ya karye, juyawa tayi domin barin gidan hakan yayi daidai da dago kan da Mahmah tayi...

"Wacece nan?"

Fadeelah taji saukar muryar Mahmah. Cak! ta tsaya yayinda gabanta ya fadi.

"Shigo mana" ta sake juyo muryar mahmah.

Waro ido tayi kana ta juyo a hankali, nufo su tayi bakinta dauke da sallama.

Waro ido Mahmah tayi idanunta kafe kan fuskar Fadeelah, har abada bazata taba manta wanna
kamilaliyyar fuskar ba. Kallon_kallo aka shiga yi tsakanin su ukun.
ita Fadeelah, kallonta da Mahmah keyi ya dan tsorata ta yayinda Mahmah ke mamakin menene ya kawo
Fadeelah gidansu? Fadeel kuwa mamaki yake ta yadda aka yi Fadeelah tasan gidan su.

"Fadeelah!" Suka tsinci muryar Fadeel ya kira ta, cikin wani amo mai wuyar fassaruwa.

Wasu hawayen farincikin ne suka zubo wa Mahmah, dama wanna ce Fadeelah'n fadeel dinta, wanna
yarinyar mai Kyakkyawar zuciyar ce? ita ce kwanakin mutuwar ta saura wata daya? Hakika bata cancanci
mutuwa a yanzu ba, domin rasa irin su a al'ummah babban rashi ne....

Durkusawa fadeelah tayi a kokarin ta na son gaishe da Mahmah, cikin sauri mahmah ta dago ta, ta
rungumeta hadi da cewa "yata" sai kuma Mahmah ta fashe da kuka, wanda na zallan tausayin Fadeelah'n
ne.

Shiru Fadeelah tayi itama hawaye na zuba a idanunta, duk da tayi mamakin ganin Mahmah na kuka, Fadeel
kuwa mamaki yake a ina Mahmah ta san Fadeelah har haka? Domin yanayin ta ya nuna ta san ta din.

Riko hannun ta mahmah tayi suka zauna kan tabarma bayan ta shimfud'a wani zanin ta mai kyau akan
tabarman Fadeelah ta zauna.
Da ido Fadeel ke binsu ya kasa ko da furta kalma daya ce, da hannu Mahmah ta kira shi alamun yazo ya
zauna kusa da su.
Bai yi musu ba ya zauna gefen Mahmah. Cikin sanyi da muryar ta mai dadi tace "Ina wuni Mahmah"
Murmushi dauke a fuskar Mahmah tace
"lafiya lau 'yata, kina lafiya?"
"Lafiya alhamdulillah" ta amsa cikin girmamawa.

Wani murmushin mahmah ta saki, domin sosai take jin dadi a ranta, ganin cewa Fadeel d'inta ya samu
mace mai sanin ya kamata, yarinyar da take so sosai, ashe itace muradin ran danta.

" 'yata kin manta ni ko?" Mahmah ta tambaya.

Dan satar kallonta Fadeelah tayi a kunyace kana tace "eh Mahmah ban shaida ki ba"

Wani murmushi Mahmah tayi kana ta fara bata labari ko ince ta basu, saboda taga kamar fadeel yana cikin
rudu.

Jinjina kai Fadeelah tayi, ba shakka alkhairi danko ne, gashi ita ta manta fuskar Mahmah amma, ita ta tuna
ta ta,
tabbas ta tuna ranar sai dai Mahmah'n ce ta manta, domin ranar tana cikin matsanancin damuwa, Saboda
a ranar ne doctor Mahfouz ya sanar da ita sauran kwananinta a duniya.

Bangaren fadeel kuwa, sai yanzu ya gane inda Mahmah tasan Fadeelah, yayi mamaki ya kuma yi farinciki
jin cewa duk yabon hadi da kauna da Mahmah take yiwa yarinyar da suka hadu a asibiti Fadeelah'nsa ce.
Sai dai murnan sa ragagge ne idan ya tuna cewa kwanakin mutuwar abar kaunarsa saura kwanaki kalilan a
duniya.

Dan janta da hira Mahmah keyi domin ta saki jikinta, hadi da yi mata nasiha kan ta fawwalawa Allah komai,
yana sane yana kuma ji, Sannan damuwa bata maganin komai. Da wanda zuciyoyin su ya dan yi sanyi.

Mik'ewa Mahmah tayi tace " 'yata me zan dafa miki?"

Murmushin k'arfin hali ta saki kana tace "ba komai Mahmah nagode"

"A'a A'a dole kici fa, ko kin bani zabi na girki miki duk abinda nayi niyya?"

Kasancewar bata son musu yasa tace "toh Mahmah"

Wajen madafa mahmah ta nufa ta fara kiciniyar dora musu girkin...

Ajiyar zuciya ta ji kusa da ita, hakan yasa ta kalli gefen ta, Fadeel taga ya matso kusa da ita, bata ce komai
ba tayi kasa da kanta.

"My Darling" ya kira ta, shiru bata amsa ba.


"My Darling" ya sake kira nan ma shiru
'My Darling pleaseee" ya kira a karo na uku cikin magiya.

Idanun ta suka ciko da kwalla, a sanyaye kana a hankali tace "meye laifina? Me nayi maka daka zabi ka
hore ni ta wanna hanyar? Ka tafi ka barni ba tare da ka tsaya munyi Kyakyyawar sallama ba, bayan kasan
kwanaki mutuwa ta na kusanto ni, a haka kake cewa kana sona? Gashi ni na kasa jurewa nazo domin inyi
sallama da kai ko hakan zai sa na samu salama a kabarina" Ta karashe maganar cikin wani mugun kuka
daya taho mata. Saurin toshe bakinta tayi, domin bata son Mahmah taji sautin kukan nata..

Hawaye ke bin fuskar sa, ba kadan ba kalaman ta suka shige sa, bazata fahimci halin da yake ciki ba, shi
kadai yasan halin tashin hankali da yake ciki right now.

Cikin murya kuka yace "am so sorry Darling, is not what you think, I swear you have no idea akan irin
tashin hankalin da nake ciki, Fadeelah ban taba shiga tashin hankali irin wanna ba, duk minti daya da
agogo zai buga, toh da zuciya ta yake bugawa, domin kwanakin mutuwar abar kauna ta, muradin raina
yana kusanto wa" kasa karasa wa yayi Saboda wani mugun kuka d'aya taho masa mai karfin gaske, amma
ya danne.

Sosai Fadeelah ta yarda da maganganun sa, domin cikin iyakar gaskiyar sa yayi ta, ita kanta ta rasa wa yafi
son juna cikin su biyun???

Gaba d'aya kukan suke babu mai rarrashin wani, karshe dai Fadeel yayi k'arfin hali fara lallashin Fadeelah
da kalamai masu sa nutsuwa da ratsa zuciya.

Shiru tayi sai ajiyar zuciya da take saukewa, abinda zai sanya ta farinciki yayi tunanin yi, mikewa yayi ya nufi
dakinsa, ya dauko kayan zanan sa... Tun kafin ya fara zanen ta fara sakin murmushi, kasa da minti goma ya
zana ta tsaf, hakan ya sanya ta cikin farinciki.

Kallonta yayi yace "my Darling ta ya ya kika gane gidanmu?"

"My one, kana tunanin garin masoyi yana nisa ne? Kana tunanin bazan iya bincikan inda kake ba? Kasani
cewa inda so da kauna, komai zai iya faruwa, sannan komai zai yu, dan haka ka daina mamaki"

Cikin gamsuwa ya jinjina kansa kana ya sake cewa "Amma me yasa kika boye min wanna cutar taki har
tsawon wanna lokacin?"

Murmushi mai ciwo tayi kana tace " dalilina shine, babu abinda hakan zai kara, na kuma boye maka ne
saboda hankalin ka zai tashi, sannan ina tsoron kada ka guje ni, wanna cutar tawa ya kai shekaru masu
yawa, haka na taso na ganni dashi, a lokacin da cutar yayi muni ne aka fara neman wanda zai siyar min da
kodar sa amma ban samu ba. Haka dai doctor na Mahfouz ya cigaba da dora ni kan magani hakan yasa
nake samun saukin cutar, sai dana je last check up result dina ya nuna cewa kodar ta lalace sosai haka
zalika dayan ya fara tabuwa, ban sanar da kowa ba, domin dukkanin wani dangin nawa basa son tada
maganar cutar koda na. Sannan Saboda tashin hankali da zan sanya mutane yasa ban sanar da kowa
abinda Doctor Mahfouz yace ba. Ganin cewa kwanaki na na daf da karewa ne shiyasa nayi tunanin sanar
da kai..." Ta kai karshe tana sauk'e wasu tagwayen numfashi.

Iska mai zafi Fadeel ya furzar tausayin Fadeelah fal ransa.

Haka dai suka dinga hirar su ta soyaaya, yayinda damuwar su ke raguwa a hankali, ana haka Mahmah ta
dawo da dauke da kwanuka biyu masu d'auke da tuwo hadi da miyar kubewa, ajiyewa tayi gaban su tana
cewa
"Allah yasa 'yata ta iya cin wanna abinci"

Murmushi Fadeelah tayi, tana kallon abincin, matsanancin tausayin su na ratsa ta, dama mutane na iya cin
irin wanna cimmar kuma su rayu? Zata iya cewa bata taba ganin abinci irin wanna ba, a fili
tace "zan iya ci Mahmah nagode"
ita kanta kawai fada tayi, za dai ta gwada ci domin faranta ran Mahmah, domin taga kaunar ta mai tarin
yawa a idanun mahmah'n, haka ita ma sosai matar da kwanta mata arai tana kuma sonta.

Murmushin farinciki Mahmah tayi, Allah kadai yasan tarin kaunar da take yiwa Fadeelah'n, kallon Fadeel
tayi tace " My son kai mata abincin dakin ka domin ta samu taci abincin a sake"

"Toh Mahmah" ya mike hadi da kai mata abincin dakin.


Dawo da kallon ta tayi ga Fadeelah dake zaune kai a kasa tace "tashi 'yata kije ki ci abinci ko"

A kunyace ta mike ta nufi dakin sa.


Tsaye tayi cikin mamaki tana bin dakinsa da kallo, gaba d'aya zanen hotunan tane manne a bangon dakin
duka.

Murmushi take yi yayinda idanun ta ke kafe kan nashi, daya bayan d'aya, ko wani bango take bi tana kallon
hotunan ta, tama rasa wanne yafi kyau, farinciki ya cika zuciyar ta. Muryar sa taji yace "my Darling taho kici
abincin".
Ba musu ta dawo ta zauna fuskar ta d'auke da murmushi.

" Thank you" tace masa

"Kin cancanci fiye da hakan my darling" ya bata amsa.

Bata kara cewa komai ba sai murmushi da ta yi...


A karo na biyu ta kai hannu da niyyar gutsiro tuwon domin taci ta kasa, saboda zafin sa.

Murmushi ya saki, kana ya wanke hannunsa ya gutsiro tuwon hadi da dangwalo miya, sai ya shiga hura
iskan bakin sa cikin tuwon na yan seconds kana ya nufi bakin ta dashi... A hankali kana a kunyace ta bude
bakinta ya sanya mata tuwon.

Dan lumshe ido tayi domin ta yi tunanin zata ji daci, sai ta ji tsabanin haka, domin duk da babu komai cikin
miyar daga Maggi sai yaji domin ko mai babu, amma mutum zai iya ci... Haka ya cigaba da bata, har tayi
loma biyar kana ta kauda kai alamun ta koshi. Bai ce komai ba, domin yaga mugun k'ok'arin ta, domin bai
yi tunanin zata iya cin ko da loma d'aya na abincin ba.

" kai ma kaci?" Tace dashi.


Ba musu ya fara ci, shi ma bai wani ci da yawa ba ya rufe, saboda har yanzu ba wai hankalin sa ya kwanta
bane, amma ganin ta ya rage masa wani kaso na daga cikin matsanancin damuwar da yake ciki.

Har shidan yamma Fadeelah na gidansu Fadeel, sosai wata shakuwa mai yawan gaske ya shiga tsakanin
Mahmah da Fadeelah cikin wuni daya.
Sannan Mahmah ta debewa Fadeelah kewa, har take jin tamkar kada ta bar gidan...

Da zata tafi ta kawo kudi masu yawa ta bawa Mahmah amma sam taki karba, duk yanda Fadeelah tayi,
Mahmah taki karban kudin.
Haka suka yi sallama cikin mutunta juna, sai a lokacin kukan Fadeelah ya dawo sabo domin ji take kamar
sallamar karshe take yi dasu Fadeel, gani take kamar bazata kai sauran kwanakin daya rage mata ba.

Suna tsaye a kofar gidan su Fadeel, suna sallama cike da kewar juna, kuka mai suna kuka suke gaba daya,
an rasa wa zai lallashi wani cikin su, karshe dai Fadeel ya bude mata murfin mota ta shige, kana ya kalleta
murya a shake yace "zan kira ki idan kinje gida, I love you" yana fadin haka ya koma cikin gidan da mugun
sauri.
Haka dukkanin gidajen biyun suka k'asance cikin damuwa, har garin Allah ya waye...

***★ ***★ ***★

Washegari Fadeel na zaune yayinda Mahmah tace "son ina so ka kwantar da hankalin ka, in sha Allah zaku
rayu tare da Fadeelah har ku haifo min jikoki, bana son kayi wani abu akai hakan umarni nake baka, addu'a
zaka cigaba da yi mata kaji?"

Jinjina kai yayi alamun gamsuwa


Shiru na yan mintuna Mahmah tayi kana ta sake cewa "ina son sake zuwa asibiti cikin satin nan, domin
bana jin dadin jikina" wani shiru tayi kana ta cigaba
"ka kira 'yata kuwa?"

Ajiyar zuciya ya sauke kana yace "eh na kirata, amma number ta baya zuwa tun jiya, amma bari na sake
gwada wa"

Kara dialing number yayi har ya tsinke ba a daga ba, kara kira yayi a karo na biyu, yaji an daga.
amsar da aka bashi yasa shi mikewa zumbur gaban sa na wata mahaukaciyar bugawa....

_Gobe ma zanyi k'ok'arin baku sabon update matukar naga comments dinku, yeah two pages as promise, i
love my fans_...

#share
#Edit
#vote

Editing is not allowed❌

I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*
#NoorEemaan.

ƘƳAUTAR ƘOƊA💝
(It's all about love, scracife, hatred and destiny)

*Wattpad*
@NoorEemaan

ELEGANT ONLINE WRITER'S📚🖊

*EDITING IS NOT ALLOWED*❌

https://facebook.com/groups/943534712916776/
Masu amfani da facebook su yi join ta wanna link din.

_akwai complete din labarin nan a Wattpad, ƙarku manta da following dina Please_

Page 23_24

(Not edited)

Cikin wata murya da amon sa ke fidda zallan tashin hankali da yake ciki yace "mekika ce?" domin sam
kunnuwansa basu yarda da abinda yaji ba.

Daga dayan ɓangaren Elizabeth ta sake cewa


"Nace Jikin ma'am ya tashi sosai, suna asibiti, tun uku na daren yau" ta karasa cikin gurbataciyyar hausar
ta, yayinda Muryar ta ke bayyana halin damuwar da take ciki.

Ba tare da ya sani ba ya saki wayar kasa, kana shima ya sulale kasan, wani mugun kuka ya saki, tamkar ba
namiji ba, itama Mahmah kuka take, kukan tausayin danta domin taji abinda Elizabeth tace.

Ganin kukan kara gaba yake ya sa Mahmah ta samu ta rungume shi da kyar tana cewa "my son, Fadeel!
Stop all this, ka nutsu kaji me zan ce maka"
Cikin kuka yace "A'a Mahmah, bazan iya nutsuwa ba, muradin raina na k'ok'arin mutuwa, ta yaya
hankalina zai kwanta, mahmah ki barni, ki barni na bawa Fadeelah *koda* ta, domin ta rayu, zan kasance
cikin farinciki koda a kabarina ne idan Fadeelah na raye...."

"I said stop Fadeel! Bazaka mutu yanzu ba in sha Allah, haka ita ma Fadeelah baza ta mutu ba, baku
cancanci mutuwa yanzu ba, ku duka biyun zaku rayu cikin farinciki"

"Ta ya ya hakan zai yu Mahmah? dole idan ban bawa Fadeelah *koda* ta ba, mutuwa zata yi, idan kuma
hakan ya kasance zan kashe kaina, sannan bazan taba yafe wa kaina ba har abada"

"Son kasani cewa ni Mahmah'n ka bazan cutar da kai ba, umarnin nake baka kada ka bayar da kodar ka,
shin kana tunanin fadeelah zata ji dadi ne matuk'ar tasan cewa kai ka bada kodar ka? ita ta rayu, kai ka
mutu"
Sam bazata ji dadi ba, domin ta na buk'atar ka a rayuwar ta"....

Share hawaye tayi kana tace "zan je asibiti domin a duba ni, ina kara maimaita maka, kada ka bada kodar
ka wa Fadeelah, Allah zai kawo mafita in Sha Allahu".

Tana gama fadin haka ta mike hadi da daukar hijab d'inta ta fice...

Kansa ya shiga bugawa da bango da k'arfin gaske, har jini ya fara bin gefen fuskar sa, sai dai ko daya bai ji
zafi ba k'amar yanda zuciyarsa ke masa matsanancin zafi tamk'ar an watsa masa narkakkiyar dalma. Gaba
daya ya fita hayyacin sa, tamkar wani sabon kamu...

★★
Zaune Mahmah take cikin adaidaita sahu, ji take kamar tayi tsalle ta ganta a asbitin. Duk gudun da matukin
keke napep din keyi sam bata gani.
Bayan wasu mintuna suka iso, sauka tayi hadi da mika masa kudin sa, ta nufi cikin asibitin...

Tun daga hospital din ta ga canji mai tarin yawa, domin security's, bodyguards, hadi da sojoji ke zagaye
cikin asibitin. Take jikinta ya bata cewa Fadeelah na asibitin. A ranta tace " ikon Allah, ashe asibiti daya
muke zuwa checkup tare da Fadeelah"

Tana shiga cikin asibitin taga wasu mutane masu yawan gaske fuskokin su cike da damuwa, kallo daya ta
musu ta fahimci cewa su din dangin Fadeelah ne, sai wani magidancin mutum dake tsaye idanun sa na
zubar da hawaye wani baturen likita nayi masa magana wanda bata jin me suke cewa, take jikinta ya bata
cewa mahaifin Fadeelah ne domin ga kamanin nan baro-baro.

Direct office din doctor Gabriel ta nufa, yana zaune kuwa, yana wasu rubuce _rubuce a littafin kundin
marasa lafiya, dago kansa yayi kana ya amsa sallamar hadi da cewa "a'a madam, ya kika zo yau? Ai ranar
checkup dinki jibi ne, have a sit please"

Murmushin k'arfin hali Mahmah ta saki, kana ta zauna Kamar yadda yace, ajiye biron hannunshi yayi hadi
hade hannunsa cikin na juna, alamar ita yake saurare.

Ajiyar zuciya ta sauke kana tace "likita meye amfanin zuwa na checkup? Bayan lokacin mutuwa ta na daf
da zuwa, idan ban manta ba, kwanaki dana zo ka sanar dani cewa cancer da nake fama dashi a lungs dina
ya dawo so chronic, har ya fara taba wani sashen, sannan zan kuma iya rasa raina a ko wani lokaci, haka ne
doctor?"

cikin tabbaci hadi da tausayi likitan yace "tabbas hakane" dan jan numfashi tayi kana ta cigaba "duk da ina
jin ciwo mai tsanani gaske a yan kwananin nan, amma sam ban nuna wa dana ba, kuma har in koma ga
Allah banason yasani. Likita bana iya bacci har gari ya waye a yan kwananin nan, ina ji a jikina kwana kin
mutuwa ta yazo daf"... wasu hawaye ne suka zubo mata kana ta cigaba "wata alfarma nazo kayi min"

Sosai jikin doctor Gabriel yayi sanyi, duk da kasancewar sa ba muslumi ba, amma yasan kaddara, sosai
yake jinjinawa Mahmah domin tana da tawwakali, ya kuma yaba mata, domin tsananin son da take yiwa
danta ne ya hanata sanar dashi cutar da take fama dashi tsawon shekaru masu yawa.

Ajiyar zuciya ya sauke cikin tausayawa yace "ina jinki, wani alfarma kike so nayi miki matukar bai fi karfina
ba zan yi miki shi"

"Nagode doctor Gabriel, nasan cewa Fadeelah na asibitin nan ko?"

"Cikin zallan mamaki likita yace "Fadeelah! Fadeelah dai mai dauke da cutar koda? diyar professor Imran
mai naira, ina kika Santa?"

Duk da Mahmah bata san sunan mahaifin ta ba, amma tana da tabbacin ita ce, a fili tace "kwarai ita nake
nufi"

"Eh kwarai tana nan asibitin tun cikin dare aka kawo ta" doctor Gabriel ya fada.
"Toh alhamdulillah, alfamar da nake so ka min shine, matukar Allah ya dauki raina, ina son a cire *kodata*
a sanyawa Fadeelah"

Azabure likita ya mike daga kan kujerar yace "What!!!?"


"Madam kin san mikike cewa kuwa? Duk da cewa kina daf da barin duniya Kamar yadda result dinki ya
nuna, ba wai hakan na nufin ki cire kidney dinki ki bayar ba, meye dalilin ki na yin hakan? Allah na iya canza
komai idan yaso" Doctor Gabriel ya karasa cikin tashin hankali daya bayyana a fuskar sa karara.

Wani murmushin karfin hali Mahmah ta kara saki kana tace "kwarai nasan me nake yi, zan sadaukar da
koda ta wa fadeelah saboda kauna hadi da tausayi da nake mata, yes I will scracife my kidney to her, domin
ita din farinciki dana ce, zan kuma iya bata *kodata* ko da ace lafiya ta lau bana tare da lung's cancer
dinan (cutar daji ta makwogaro) ina kara neman alfarman ka please doctor" ...

Wani gumi doctor ya share, sosai yake mamakin matar, zuciyar ta mai kyau ce, Saboda farincikin danta zata
sadaukar da *kodar ta* wa Fadeelah, wanda har yau ba a samu kodar ba, kuma sosai take cikin halin ciwo
mai munin gaske domin bata san waye a kanta ba.

Muryar Mahmah ce ta katse masa tunanin sa cikin kuka tace, "doctor! ka tabbatar da cewa Fadeelah bata
mutu ba, ita din farincikin dana fadeel ce. Bata cancanci mutuwa yanzu ba Saboda halayenta masu
nagarta, bata cancanci mutuwa yanzu ba, domin rasa irinsu al'ummah babban rashi ne. Ni nayi niyya, tun
daga ranar dana ji sauran kwanakin ta a duniya, a ranar naga tashin hankali a idanun dana, tun daga ranar
na sadaukar mata da koda ta"

Ajiyar zuciya ta sauke kana ta cigaba da cewa

"Doctor! Inaso hakan ya zama sirri tsakanin na da kai, har a gama dashen kodar, kada ka sanar da kowa dan
Allah" Mahmah tace tana hade hannun ta alamun roko.

Shiru doctor yayi, a kafatanin rayuwar sa zai iya cewa bai taba ganin mace mai kyawun zuciya irin Mahmah
ba, Saboda farincikin wasu zata iya Sadaukar da komai nata, kodar da ake nema ido rufe, shi take rokon sa
akai? Sannan bata bukaci ko sisi ba, tabbas matar nan ta cancanci yabo mai girman gaske...

Wani nannauyan ajiyar zuciya ya sauke kana yace "madam na amince da abinda kika ce, zan kuma rike miki
wanna sirrin, bazan gaya wa kowa ba, har a gama aikin" ya kai karshe wasu kwalla suka zuba masa, wanda
na tsantsar tausayin Mahmah ne, ga ramar ta ya fito fili sosai, alamun cutar na cinta from the inside.
A matsayin sa na likita yaga cases da yawa na patients, amma babu wanda ya daga masa hankali hadi sa
shi kuka Kamar na Mahmah, hankici ( handkerchief) yasa yayi saurin share hawayen sa.

Murmushi fall fuskar Mahmah tace "nagode sosai doctor Gabriel"

"Mu ke da godiya madam, Allah ya saka miki da aljanna, amma yanzu zamu je wajen likitan Fadeelah'n
wato doctor Mahfouz domin mu tattauna maganar dashi. Ya karasa cikin sanyin jiki.

Ba musu ta mike suka nufi office din doctor Mahfouz di'n.

Zaune suka tadda doctor Mahfouz cikin zurfin tunani, domin cutar Fadeelah bai taba daga masa hankali
irin daga daran jiya zuwa safiyar yau ba. Tun fadeelah na da kananun shekaru yake a matsayin likitan ta.
Har rashin yana jin zafi, yana kuma tsoran ta rasa ranta, gabadaya ya gama sarewa yana jiran ta Allah ta
kasance, domin yayi iya k'ok'arin sa.

Shigowar su Mahmah ne ya katse masa tunanin sa, babu bata lokaci doctor Gabriel ya sanar dashi komai,
sosai yayi mamaki da murna ya kuma ji tausayin Mahmah kwarai, duk da burin sa kenan *a samu kodar da
za a datsa wa Fadeelah*
Amma sai ya samu kansa da jin ba dadi wanda hakan baya rasa nasaba da kyawun halin mahmah wata
zuciyar ta bashi tabbacin hakan.
ya kuma yi musu alkawarin har a gama aikin shi ma ba zai fadawa kowa ba, kamar yadda Mahmah ta
bukata.

Mahmah ta bukace ganin fadeelah, duk da ba mai shiga saboda ba a son hayaniya a kusa da ita amma ba
musu ya amince duk suka shiga hadadden dakin da aka kwantar da ita. Sosai Mahmah ta tausayawa
Fadeelah, domin ta fita hayyacin ta sosai, banda na'uran nan dake Reading cewa tana da sauran numfashi
tabbas za a dauka ta mutu ne.

Hannunta Mahmah ta riko tace "Allah ya baki lafiya 'yata, Allah ya tashi kafadunki, Allah ya kara muku
kaunar juna ke da dana abun sona Fadeel, nasan ina daf da mutuwa, amma zan kasance cikin farinciki a
gidana na gaskiya matuk'ar kuna raye cikin farinciki, ki kulamin da Fadeel, na baki amanar shi, domin ke
kadai ce zaki bashi farinciki idan na mutu, ki min alkawarin zaku haifa min jikoki..." Kuka ne ya ci karfinta,
haka zalika doctor Gabriel da doctor Mahfouz sai da suka share hawayen tausayin ta...

Daga baya ta bar asibitin ta koma gida, halin data ga Fadeel a ciki yayi matuk'ar daga mata hankalin ta, take
ta rike shi, suka nufi chemist aka yi treating ciwon kansa...
★★
Bangaren Daddy kuwa zaune yake yana kuka sosai, tamkar karamin yaro, bai taba tunanin akwai abinda
kudi baya iya siya ba sai yau, domin duk mahaukatan kud'add'en sa basu yi masa rana ba, tunda ga yarsa
na kwance a gadon asibiti cikin mayuwancin hali domin bata san wanda yake kanta ba, da taimako na'urori
take numfashi.

Wani matashi ne ya fito daga wani daki, ya kalli Daddy cikin girmamawa yace " yallabai kana iya shigowa"
Mik'ewa yayi cikin sauri ya nufi dakin gabatar da shirye_shiryen, kasancewar yazo gidan TV ne.

Zaune yayi idanunsa na zub da kwalla yana fadin "a taimaka min, wani ya siyar wa 'yata da *kodarsa* ko
daya ce, tana cikin matsanancin halin ciwo, banda wata 'yar sai ita, jama'a ku taimaka min, ku taimaka
min, ku taimaka min dan Allah!!!" Ganin kuka yaci k'arfin sa, yasa aka katse daukan, hadi da watsa shi
duniya... Domin bukatar Daddy kenan.

kudi masu zunzurutun yawa ya saka, daga million hamsin, zuwa ko nawa mutumin ke so ya fada zai bayar,
ko da duka dukiyar sa ne zai bayar.
Su kansu yan gidan TV sun zub da hawayen tausayin sa, domin duk fadin lagos kowa yasan tarin dukiyar
*professor Imran mai naira* sannan an sa izzar sa hadi da jin kansa, amma yau shi da kansa yazo gidan TV
neman taimako.

Abin da matuk'ar mamakin ba shakka son da yake yiwa yarsa mai yawan gaske ne.

Sosai aka watsa daddy duniya har wasu gidajen Tv da radio, gari ya dauka ko ina maganar ake, sai dai har
bayan kwana biyar ba'a samu wanda ya zo da niyyar zai siyar da kodar sa ba.

Wanna kenan.

*** *** ***

Yau kwanan Mahmah biyar a kwance jikin ya matsa mata sosai, domin har tashi bata iya yi, Fadeel ya dawo
tamk'ar wani zararre, uwar sa mafi soyuwa agareshi na Cikin wani hali, ga Fadeelah'nsa a gadon asibiti,
sosai yayi rama, domin baya iya cin komai, haka zalika Mahmah sai abu mai ruwa take iya kai baki, shima
da kyar take hadiya...

da daddare ta dan samu sauki har ta dan yi hira da Fadeel, ya kuma ji dadi domin tunda ta kwanta bata iya
magana. Sai dai wasu maganganun da take yi, mai kama da wasiyya, sai dai sam bai kowa komai a ransa
ba.

"Mahmah please ki bari na kai ki asibiti, zan fita ko ina ne domin neman kudi"
Murmushi mai ciwo tayi, ita a jikinta tana jin lokacin mutuwar ta yazo, cutar dake damunta yayi mugun cin
karfinta, domin yazo gabar da ba za a iya yin komai akai ba. Toh meye amfanin zuwa asibiti???

A fili tace "my son Fadeel, kada ka damu sannan bana so ka fita nema saboda ka kai ni asibiti, babu bukatar
hakan, ina maka so mai tarin yawa dana farincikina. Allah ya dauwamar da farincikin a rayuwar ku, kai da
'yata Fadeelah, I love you son" ta kai karshen maganar cikin murmushi irin na marasa lafiya.

Wasu hawaye ne suka zubo masa, duk da ba a cikin nutsuwar sa yake ba, amma yaji kalaman ta har Cikin
kashin sa, ya ma kasa magana sai sumbatar hannunta hadi da goshinta da yayi, itama kuma ta daga
hannunta ta shafa tarin sumbar sa d'aya kara yawa hadi da hargitsewa saboda gyaran da baya samu...

Ta kara cewa
"ka bani labarin soyaayyar ka kai da 'yata"

Duk da baya cikin farinciki amma sai daya yi murmushi daya taho da zubar hawayen sa, Kamar yadda ta
bukata, ya fara bata labari so da tarin kaunar da yake mata, hadi da labarin irin soyaayyar da suka gudanar.

Kallonsa Mahmah take tana murmushi, har ranta soyaayyar fadeel dinta da Fadeelah na burgeta, tana
musu fatan Alkhairi a rayuwa...

*** *** *** ***

Washegari har tara na safe fadeel yaga Mahmah bata tashi ba, domin da asuba bayan ya d'ora Mata alwala
tayi sallah, tace zata yi bacci ya taimaka mata ta kwanta.

Kunu daya dama mata ya nufi dakinta da niyyar tashinta ta sha.

Gabanta ya tsugunna ya kira sunan ta shiru, "Mahmah!!!" Ya sake kira a karo na uku nan ma shiru. Ga dai
fuskar ta d'auke da murmushi Kamar ka kirata ta amsa.

Hannunta ya rike, take yaga ta saki, gaban sa ya fadi, sake rike dayan hannun yayi yaga ta kuma saki,
hannunsa ya d'ora a k'irjinta yaga bata bugawa.

"_innalillahi wa innah ilaihi raju'un, mahmah!!!_" yace cikin karaji yana jijjjiga ta, sai dai shiru bata ko
motsa ba, sam k'wak'walwa hadi da zuciyar sa taki yarda da abinda take gaya masa, hakan yasa shi daukar
ta zuwa asibiti domin a duba ta.
Cikin tashin hankali ya shigo asibitin, Mahmah dauke a kafadar sa yana kuka sosai, daidai lokacin doctor
Gabriel ke k'ok'arin shiga motar sa domin aikin dare yayi jiya yana son tafiya gida, kallon daya yayi wa
fadeel, take yaga Mahmah a kafadar sa, gabansa ne ya fadi, fasa shiga motar yayi ya nufi wajen Fadeel
kana ya kwala wa wasu nurses kira, aka dora Mahmah cikin gadon nan na asibiti aka turo ta cikin sauri
zuwa emergency...

Hannu Fadeel doctor Gabriel ya kamo zuwa office d'insa yace ya zauna yana zuwa,
Kana Cikin sauri doctor Gabriel ya nufi dakin da aka shigar da Mahmah...
Nan ya shiga dubata cikin kwarewa, sai dai ina rai yayi halin sa, Mahmah is gone forever, Mahmah ta tafi,
tafiya ta har abada.

_kullin nafsin za'ikatul maut_ (dukkan mai rai sai ya dandani zafin mutuwa) domin babu alamun numfashi
a tare da ita.

Kansa ya dafa, yace "Jesus Christ! is innocent woman is dead!!!" Sosai kuwa yaji mutuwar ta, duk da
kasancewar sa ba Musulmi ba, amma yaji wani tsoran Allah na shigar sa.

A sanyaye ya koma office d'insa ya tarar da Fadeel zaune abin tausayi, zama yayi yana kallon Fadeel cikin
tausayawa, duk da bai taba ganin sa ba sai yau, amma suna yanayin kama da Mahmah ya aiyana aransa
afili kuwa hannu Fadeel ya riko yace "my friend sai haku'ri domin...."
Ai kafin ya karasa Fadeel ya katse shi da cewa "don't tell that my Mahmah is dead doctor, because I will
squeeze your Bone's like an Orange (kada ka kuskura kace Mahmah nah ta mutu, domin zan ma_matse
kasusuwanka tamkar na lemon bawo" Fadeel yace cikin fitar hayyaci kana cikin kuka har wani shidewa
yake.

Girgiza kai doctor yayi cikin tausayawa yace "the truth is that..." sai ya dan shiru kana ya cigaba "your
mother is dead!"

Afirgice Fadeel ya mik'e yana kokarin furta wata kalma, amma ina sai ya tafi luuuuuuu sakamakon wani irin
jiri daya debe shi, take ya fadi tsumamme....

Cikin wani sabon tashin hankali doctor ya dauke shi zuwa emergency aka fara bashi taimako gaggawa...

Bayan yayi masa komai harda alluran bacci sai da ya nufi office din doctor Mahfouz, sai dai sam baya nan.
Fita ya sake yi ya nufi dakin da aka kwantar da Fadeelah, gaba d'aya ta sake fita kamanin ta, maganar
Daddy yaji yana cewa cikin kuka "doctor tayaya zaka ce idan ba a samu *koda* nan da minti talatin ba zan
rasa 'yata, bazan juri kallon 'yata ta mutu ba, ka cire duka nawa kodar ka sa mata, banda wata 'ya sai ita
Mahfouz!"
"Professor sai hakuri fa, kalli abinda na'uran ke fada, nayi iya k'ok'ari na..." Suna cikin wanna halin, kirjin
Fadeelah ya fara sama da kasa har wani jijjiga gadon yake. Yayinda na'uran ya tsawaita kara...

Cikin saurayi doctor Gabriel dake tsaye yace "an samu kodar, a shirya shiga da ita aiki yanzu"

Gaba daya suka juyo gare shi, take murmushi ya wad'atu kan fuskokinsu, tsabanin dazu da wasu ke kuka
wasu na cikin damuwa, domin Mommah har bata iya bud'e idanun ta saboda zafi ".

Wani kallo da doctor Gabriel yayi wa doctor Mahfouz take ya fuskanci Mahmah ta mutu, duk da yaji dadi
Fadeelah zata rayu, amma yaji mutuwar Mahmah matuka.

Babu bata lokaci aka shigar da Fadeelah aiki, cikin gaggawa domin mintunan daya rage mata sauran kadan.

Bangaren doctor Gabriel kuwa, bayan an cire kodar Mahmah, ya nemo wasu dattijai mata da maza
wadanda suka yi zurfi a ilimin addini, suka nufi gidan Mahmah, yayinda gawar mahmah ke cikin ambulance
din asibitin.
Domin ayi mata wanka, duk da kasancewar shi ba muslumi ba amma, yasan duk wani muslumi idan ya
mutu ba a son ajiye shi, an fi so ayi gaggawar kai shi gidan sa na gaskiya. Wanna kadai zai iya yiwa
Mahmah, tunda danta yana gadon asibiti a kwance.

Kasancewar lokacin da Mahmah ke zuwa asibiti, adreshin gidan ta na rubuce a file dinta hakan yasa bai sha
wahalar gano gidan ba.

Babu bata lokaci aka shigar da ita ciki, take yan unguwar suka fara shiga gidan musamman da suka ji jiniyar
motar asibiti.

Bayan anyi wa Mahmah wanka an shirya ta cikin liƙƙafani kana aka fito da ita hadi da yi mata sallah, duka
doctor Gabriel na cikin motar sa, wani tsoron Allah na shigar sa, yayinda hirar da suka yi da Mahmah ya
shiga dawo masa a fili ya furta " hakika madam kinyi Sadaukarwa mai girman gaske". Sai ga Hawaye a
idanun sa.

Bayan an dawo daga kai ta mutanen da suka hallaci jana'izar ta suna da yawan gaske, sai dai fatan mu ce
Allah ya jikan ta.

Doctor Gabriel ya bawa dattijan nan daya samo kudi masu yawa, suka ki karba, domin suma imani da
tsoron Allah ya kara shigar su.

Amma mamakin take yaji addinin musulunci ya burge shi sosai.


Inda mutanen ke zaman makokin ya nufa, take yace yana son shiga musulunci, kabbara mutanen wurin
suka sa, yayinda limamun unguwar tasu ya musuluntar da doctor Gabriel, aka ce wani suna yake so a sanja
masa take yace *Aleeyu haidar* domin a sunan muslimai yana kaunar sunan sosai...

Take doctor Gabriel yaji kamar an yaye masa wani zunzurutun nauyi akansa, wani yanayi mai dadi kana
marar mitsaltuwa na shigar sa, nan liman ya kara wayar da kan shi game da addini musulunci ya kuma ce
masa dole ya nemi islamiyya na manya domin ya kara sanin menene addini musulunci. Take ya amsa da in
sha Allah domin ko liman bai fada ba, yana da niyyar hakan, domin shi mutum ne mai riko da addini, ko da
a lokacin da yake cikin addinin su na kirista ne(Christian), haka zalika yanzu ma daya shiga addinin
muslunci, addini mai haske, zai dage da ibada.

Haka yayi sallama dasu ya tafi cikin yanayi mai dadi da yake jin kansa a ciki, duk da murnan sa ragagge ne,
saboda mutuwar Mahmah.

Asibiti ya koma domin yana son kula da Fadeel, hakika bai cancanci a bar shi ba kowa tare da shi ba...

*_(Kusani cewa, a rayuwa wani kaddara baya samuwa sai da wata kaddaran, toh hakan ke faruwa a novel
din kyautar koda ku dai cigaba da bin alkalamina...)_*

_Yau nayi typing mai yawa, billahi banga comment dinku na k'ok'arin tarwatsa waya ta ba, zan dauki hutu😹
ina jiran ra'ayinku akan page din yau, Mahmah is dead_.😫

#share
#comment
#vote

Noor Eemaan loves you all my beautiful fans

'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*
#Nurrr

💝ƘƳAUTAR ƘOƊA💝
(it's all about love, scracife, hatred and destiny)

Story/written by
NoorEemaan
07082281566

https://facebook.com/groups/943534712916776/
Masu amfani da facebook su yi join ta wanna link din.

*Wattpad*
@NoorEemaan

ELEGANT ONLINE WRITER'S✍️

EDITING IS NOT ALLOWED❌

*(Assalama alaykum my lovely fans, nasan wasun ku baku ji dadi da Mahmah ta mutu ba, domin wasu sun
gaya min, wasu ma sun ce sai da suka zub da hawaye, ni Noor a lokacin da nake typing wajen sai dana yi
kuka domin wajen is very heart touching I know. Amma littafi na riga ma tsara shi, rubutuwa ya rage min
kawai, domin haka labarin yake, soyayya ce, sadaukarwa, tsana/kiyayye hadi da kaddara. A rayuwa ba a
taba samun farinciki kullum, haka ke faruwa a *kyautar koda*.
*Da sannu zaku fahimci darassin dake cikin labarin, ina godiya sosai da add'uar ku gareni hadi da
comments dinku masu sugar*😹
*Allah ya bar kauna da zumunci*)
Noor Eemaan loves you all

Page 25-26

(Not edited)

Kwanan Fadeel hudu a gadon asibiti ya farka da sunan Mahmah ɗauƙe a bakinsa, yayinda idanunsa ke a
rufe.

doctor Aleeyu(Gabriel) dake tsaye yana kokarin cire masa karin ruwa yayi saurin dawowa gaban gadon
yana fadin "sannu ka tashi?"
A hankali fara bud'e idanunsa, saurin mayarwa yayi ya rufe sakamakon wani haske d'aya cika idanun sa...
Ya d'auki mintuna goma kana ya fara ware idanun sa a hankali ya sauke su kan doctor Aleeyu...

Take k'wak'walwarsa ta tariyo masa komai, wani ihu ya saki kana ya fara buga kansa da karfen gadon yana
fadin "Mahmah don't do this to me, please Mahmah ki dawo gareni, banda kawo sai ke, ki dawo please,
doctor kace Mahmah na ta dawo gareniiiiiiiii" ya ja Kalmar karshen gwanin tausayi.

Cikin sauri doctor Aleeyu ya rike shi hadi rungume shi yana bubbuga bayansa alamun rarrashi...
"Shikenan Mahmah ta mutu, shikenan Mahmah ta mutu, shikenan bani da uwa a duniya likita? "

Haka ya dinga maimaitawa yana kuka sosai gwanin tausayi. Doctor ya dauki tsawon lokaci yana rarrashin
Fadeel kana yace masa ya yi sallah dake kansa domin yau kwanan sa hudu a kwance.

Ba musu ya miki, sai dai ya kasa tsayuwa kan kafafunsa Saboda rashin kwarin jiki hakan yasa doctor Aleeyu
taimaka masa har zuwa toilet.

Bayan duk ya iddar da sallar dake kanshi ya shiga yiwa mahaifiyar sa add'ua, yana kuka sosai, shima doctor
Aleeyu sai ya kama kuka domin duk wanda ya kalli Fadeel dole ya tausaya masa.

Hankici(handkerchief) doctor Aleeyu yasa ya share hawayen fuskar sa, kana a fili yace "abokina kayi hakuri,
tabbas mutuwa na da daci musamman ga wanda aka yi wa, nima da kake ganina banda uwa banda uba a
duniya, duk sun mutu kuma a rana d'aya sak'amak'on hatsarin da suka yi. Hakika ban taba ganin mutum
mai kyawun zuciya hadi da tawakkali da yarda da kaddara Kamar mahaifiyar ka ba, hakan ya janyo
hankalina na shiga musulunci a ranar da ta rasu..."

Fadeel ya dago jajayen idanunsa ya kalli doctor Aleeyu, jinjina masa kai doctor'n yayi alamun "Haka ne"

tabbas idan yace bai ji dadin cewa wani ya shiga musulunci ta silar Mahmah ba yayi karya, sai dai bazai iya
nuna jin dadin sa a fili ba Saboda matsanancin damuwar da yake ciki

A hankali ya budi baki yace "dan girman Allah doctor ka gaya min wani irin cuta ke damun Mahmah
tsawon shekarun nan bata taba gayamin ba" Fadeel ya kai karshe yana sauke wasu tagwayen ajiyar zuciya
gwanin tausayi.

Furzar da iska doctor yayi daga bakinsa kana yace " hakika mahaifiyar ka bata son ka san da cutar ta , kuma
duka Saboda kada hankalin ka ya tashi ta boye maka, a yanzu dai babu bukatar boye maka"

Numfashi ya sauke kana ya cigaba "mahaifiyar ka na dauke da *cutar daji ta makwogwaro* (lung's cancer)
tsahon shekaru kenan, a lokacin data fara zuwa asibitin nan cutar ya fara cin karfin ta. Sai dai ba kudin yi
mata aiki a lokacin domin kudin aikin ya kai million biyu da rabi. Rashin kudin aiki yasa cutar ta ci karfin ta
sosai......" nan dai ya cigaba da bawa Fadeel labarin abinda ya sani gami da cutar Mahmah, hadi da
Sadaukar da *kodar ta* da ta yi.
Babu Abinda ke fita a idanun Fadeel sai hawaye masu zafin gaske, dama haka mahaifiyar sa ta sha wahalar
rayuwa? Haka ta boye masa ciwo duk don farincikin sa? Ta Sadaukar da kodar ta just because ya zama cikin
farinciki, ya rayu da abar son sa fadeelah.

Kuka ya ci sosai, har ya fara ganin biyu_biyu sakamakon wani mugun ciwon kai da ya saukar masa, jajaye
kuma kumburarrun idanun sa ya dago ya kalli doctor yace "please wani kabari aka binne Mahmah na? Ina
son zuwa, ina son yi mata add'ua, ina son zuwa please doctor!!!!" Ya kai karshe cikin wani kukan daya ci
karfin sa.

Wasu hawaye doctor Aleeyu ya share na zallan tausayin Fadeel. Cikin dauriya yace " a gaskiya bansan wani
makabarta bane, kasancewar lokacin ban karbi musulunci ba, hakan yasa ban bisu ba, amma bari na kira
wani a nan asibiti yake aiki tare suka je" ya fada yana kara wayar sa a kunne.....

Babu jimawa matashin yaron yazo, ya fadi sunan makabartan da unguwar da yake, ya kuma ce zai iya raka
Fadeel d'in.

Da kyar fadeel ya budi baki yace "nagode zan iya zuwa da kaina"

Ba musu matashin ya koma bakin aikinsa, Mikewa Fadeel yayi da kyar yace "thank you doctor for
everything" kana yana hada hanya, haka ya fita daga asibitin a haukace.... Doctor Aleeyu (Gabriel) nayi
masa magana kan cewa zan iya tafiya kuwa? amma ina yayi nisa bazai ji kira ba....

Tafiya yake cikin makabartan tamkar wanda yake kirga kasa dake shimfud'e a kasan wajen, hawaye ke zuba
a idanunsa, wani tsoron Allah hadi da imani na kara shigar sa, wanda ya sanya kofofin gargasan jikinsa bu-
budewa yanayin daya sanya wani sanyi sanyi ke shiga jikinsa. Aransa yake aiyana cewa shima wata rana
haka zai kasance anan, haka zai tafi, tafiya ta har abada, kamar yadda Mahmah ta tafi ta barshi.

Tun daga nesa ya hango signboard mai d'auke da sunan Mahmah. Gaban kabarin ya tsugunna, wanda aka
mulmule da siminti dake da sauran sabonta har yanzu, domin duk wanda ya gani zai san cewa mamacin
bai dade ba.

Wani kuka ne ya taho masa mai karfin gaske daya kasa rike shi, sosai yake kukan mai taba zuciya, kana ya
rarrashi kansa tuna cewa ba a son ayi wa mamaci kuka.

A fili ya fara furta cewa "Mahmah you re gone, gone forever, kin tafi kin barni, ki tafi kin barni a wanna
duniya mai cike da kalubale, kin tafi kin barni bana da sauran kowa daya rage min" . ajiyar zuciya ya sauke
tamkar yaron goyon daya ci kuka ya koshi kana ya cigaba " ina sonki Mahmah, ina matuk'ar kaunar ki, your
son fadeel loves you.
Ina fatan kina cikin farinciki da salama a yanzu, har abada kina cikin k'irjina da dukkanin wani sassa na
jikina, kin yi Sadaukarwa mai girman gaske saboda farincikina, ina kaunar ki uwar da babu tamkar ki a
duniya, Allah ya jikan ki Mahmah nah..." Nan ya shiga yi mata add'uo'i kana yaja wata alama da wani dan
karfe daya gani a kasa, kan siminti, domin iska zai iya d'auke signboard din. Wanna alamar daya zana zai
taimaka masa wurin gane kabarin Mahmah....

Mikewa yayi ya nufi gida. Sosai gidan yayi masa girma da fadi ainun, haka ya kudundine kan yar katifar
mahmah matsanancin kewar ta na ratsa zuciya da jinin jikinsa......

*** *** ***

*BAYAN WATANIN BIYAR*

A haka rayuwa ke tafiya. Kwanaki na juyewa zuwa satittika, satittika na juyewa izuwa watanni, haka zalika
watannin na juyewa izuwa shekara.

Yanzu babu laifi Fadeel ya dau dangana, tun ranar daya bar makabartan nan baya zuwa ko ina daga
masallaci sai gida, haka zalika baya iya cin komai daga ya tafasa ruwan black tea (bunu) shikenan, shi ma
sai ya ji Cikin sa na kugin yunwa zai sha, gaba daya ya dawo wani mara son hayaniya ko magana baya son
yi, kuma har yanzu bai san a wani hali Fadeelah ke ciki ba, duk da sonta na nan daram a ransa...

A yau yayi tunanin gyara gidan, domin tunda Mahmah ta rasu gidan bai ga tsintsiya ba. Tsakar gida, da
toilet ya gyara, kana ya nufi dakinsa ya fara gyarawa, bayan ya gama ya dawo dakin mahmah ya gyara mata
tsaf, jakar kayanta dake a hargitse ya nufa da niyyar gyarawa wasu takardu suka fado.....

Rubutun Mahmah ya fara tozali dashi, sai wasu takardun asibitin. Ajiye takardun asibitin yayi a gefe, ya
dauki na rubutun nata ya fara karantawa Kamar haka:

_my lovely son Fadeel_

_ina fatan kana cikin koshin lafiya, nasan bayan raina zaka ji komai. Ina fatan zaka yafe wa Mahmah'n ka a
dalilin boye maka ciwon da nake fama dashi tsahon shekaru, na boye maka ne saboda bana son ka kasance
cikin damuwa. Ina fatan dana abin sona baya fushi da Mahmah'n sa?_

Share hawaye yayi kana cikin muryar kuka yace "bana fushi dake mahmah bazan taba fushi dake ba, ina
son ki sosai Mahmah na" kara share hawayen yayi, sai dai wani na koran wani, hakan yasa ya cigaba da
karantawa bai damu da zubar hawayen ba.

_na hana ka bayar da kodar ka wa yata Fadeelah ba dan komai ba, sai dai ku rayu cikin lafiya da farinciki.
Shin idan ban Sadaukar da koda ta ga abar son dana ba wa zai Sadaukarwa mata? Ka sani cewa ina cikin
farinciki a lokacin da na bayar da koda ta ga fadeelah. Ina yi muku so mai yawan gaske. Kada ka karaya kan
soyaayyar fadeelah ya kai jarumin dana, ka jajirce da dukkanin iyawarka har ta zama mallakin ka, nasan ku
biyun zaku zamo the best couple ever da za a yi alfahari da ku a duniya... Ka kasance cikin farinciki dana,
ka kula da fadeelah, ku kula da junan ku, ina farinciki da taraiyyar ku, sannan ina muku fatan alkhairi, ka
gaida min yan jikokina idan sun zo in sha Allahu. Ina kaunar ka Fadeel, Mahmah loves you, fatan alkhairi._

Kurawa takardan ido yayi hawaye masu dumin gaske na sake zubo masa, shafa wani sashe na rubutun yayi,
da ya dan yi jurwaye wanda da alama hawayen Mahmah ne ya diga kan takardan a lokacin da take
rubutun..

Kan kayan Mahmah dake hargitse ya dora kansa, lumshe idanun sa yayi hadi da kamkame takardan a
k'irjinsa, waka ya fara rera mata kamar haka:

🎻🎻_wanna naki ne Mahmah_.....

_Rayuwa nayi nazari duk wanda ya zamto a raye, wata ran sai ya rasu ko yana so ko zai zubda hawaye.
Duniya ba wajen zama ne ba, aro aka bamu ba jaye-jaye, mu rike Allah gwani mafita ne ga mazon na
fiyayyye_.......

_Rayuwa ta sai a hankali, na rashin mahaifiyata. Na zama kamar banda hankali ku dubeni bani da gata.
Hakuri ya zama faralli ya Allah jikan mahaifiyata_....

_wayyo! wayyo!! Ya Allah jikan mahaifiyata. Innalillahi wa innah ilaihi raju'un, Allah ya jikan ki Mahmah
dan ki tafi wayyo ya zanyi_...........

_innalillahi wa innah ilaihi raju'un Allah ya jikan ki Mahmah dan ki tafi wayyo ya zanyi_......

_Allah nagode. Kullin nafsi za'ikatul mautu, duk mai rai tilas ne ya mutu . Sai dai ni du'a'in neman hutu
Allah ya yafe mata_........

_kuka ka daina ka share hawaye abokina. Dani da kai zata zo kanmu watan wata rana, ka zo mu roki Allah,
in muyi sallah nasan zaya kalla ya Allah! Mutuwa nazan tana da zafi, hakuri dazaka yi shi ya fi. Wanda ya
mutu bazai dawo ba, add'ua zamuyi shi zaya je gareta....ya Allah!_

_innalillahi wa innah ilaihi raju'un Allah ya ji kanki Mahmah dan ki tafi wayyo ya zanyi. Wayyo! Mahmah,
wayyo!! Mahmah, wayyo!!! Mahmah nah, wayyo Mahmah nah, wayyo Mahmah nah_....

_duk abinda nakeso cikin duniyar nan Mahmah tana bani, yanzu bata nan na lalace dare da rana kullum
tunani. Burin rayuwa in zauna da mahaifiya dan ita ce garkuwa mai share duka damuwa. Wayyo! Mahmah,
wayyo!! Mahmah, wayyo!!! mahmah nah, wayyo Mahmah nah!!!! Innalillahi wa innah ilaihi raju'un Allah
ya jikan ki Mahmah dan ki tafi wayyo ya zanyi_.......🎻🎻

Haka ya gama wakar hawaye masu zafi na zubo masa, suna bin gefen da gefen fuskar sa suna shiga
kunnuwan sa, dumin na ratsa kwanyar sa.
Da haka wani wahalallan bacci ya yi gaba dashi...
Bai jima da yin baccin ba, motocin fadeelah da body guard dinta suka tsaya kofar gidan.
Kofa aka bud'e mata ta fita kana ta shiga cikin gidan bakin ta dauke da sallama... Sai dai shiru babu amsa,
hakan yasa ta nufi cikin dakin da ta gani a bud'e.....

#Share fisabilillah
#comment
#Vote

Please Vote and follow me on wattpad @NoorEemaan

I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*

💝KYAUTAR ƘOƊA💝
(It's all about love, sacrifice, hatred and destiny)

_by Noor Eemaan_✍️

*Wattpad*
@NoorEemaan

ELEGANT ONLINE WRITER'S📚🖊


EDITING IS NOT ALLOWED❌

*(Please&please kuyi following nawa a Wattpad👏 @NoorEemaan)*

Page 27-28

(Not edited)

Dai-dai 6akin ƙofar ɗakin ta tsaya, ta sake sallama cikin zazzak'ar muryarta. Amma shiru, hakan yasa ta leƙo
da ƙanta cikin dakin.

A ƙwance ta hango fadeel, ya rame sosai ya sake yin ɗuhu, cikin sauri ta cire tsaɗaɗɗen takalmin kafarta na
company *GUCCI* ta shige dakin.

Gabansa ta tsugunna da nufin tashin sa, sai ta tsaya caƙ! saƙamaƙon ganin takarda rungume a ƙirjinsa. A
Hankali ta kai hannu ta zari taƙardan, haka kawai taji zuciyar ta na azalzalarta ta karanta ko ganin abin cikin
taƙardan.

Mikar da takardan tayi sak'amak'on dan cuƙurƙuɗewan da yayi ta fara karantawa...... Tun kafin tayi nisa da
karatun ta fara hawaye tamkar an balle famfo. Sai da ta zo karshen karatun ta kasa rike kukan da ya kufce
mata, dama Mahmah ce ta Sadaukarwa mata da *kodar ta?* Saboda su kasancewa a raye cikin farinciki?
Kaunar da Mahmah ke mata ko tace take musu ya kai haka? Meyasa doctor Mahfouz bai sanar mata?
Surutai ta dinga yi a ranta, yayinda kukan ta ke karuwa domin abin ya taba zuciyar ta matuka.

A hankali Fadeel ya Fara bud'e jajaye kuma ƙumɓurarrun idanun sa sakamakon kukan ta da ya ji ya sauke
su kanta, Kallonta yayi na yan mintuna ya maida idanunsa ya lumshe.....

Bakinta ne ya fara rawa, so take ta furta masa wata kalma ta kasa, kallon sa take yayinda zuciyar ta ke kara
karyewa. Ya dawo kamar bashi ba, ya fita a kamanin sa ainun. Gashi yaki kulata, sai dai hakan bai mata
ciwo ba, domin mutuwar uwa ba karamar abu bane...

Cikin sauri ta bar gidan ta fada mota hadi da bawa driver umarnin ya kaita asibiti. sanin cewa asibiti daya
take zuwa ya sa shi cewa "yes ma'am" Cikin sauri hadi da girmamawa. Haka motocin suka bar unguwar a
jare kamar ko yaushe.
Bangaren fadeel kuwa, yana jin fitar ta ya bude idanunsa ya bi kofar da ta fita da kallo. Wasu hawaye masu
dumi suka biyo kuncin sa, idan yace bai yi kewar ta ba yayi karya, amma baya son kowa ya rabe shi a halin
da yake ciki, yana bukatar privacy, yes yana bukatar kebancewa.

A hankali ya mike ya dauko kayan zanen sa, ya fara zana Mahmah kana ya zana fadeelah cikin mintuna
ashirin. Hotunan biyun ya ajiye kan cinyoyin sa bayan ya gama zanen, ya kafe su da ido hawaye na zuba
daga idanunsa, daya kalli zanen mahmah sai ya fashe da kuka, idan kuma ya kalli zanen fadeelah sai ya sa
dariya, haka ya dauki tsawon lokaci yana yi tamkar wani mai tabin k'wak'walwa.
Hakika yana farincikin Fadeelah ta rayu, yana kuncin Mahmah ta mutu.

***

Tun cikin mota ta kira doctor Mahfouz ta sanar dashi tana tafe. Bayan isar su asibitin direct office d'insa ta
nufa. Ta kuwa tarar dashi a ciki. Bata tsaya bata lokaci ba ta fara jero masa tambayoyi...

Doctor Mahfouz bai yi kasa a guiwa ba ya shiga sanar mata da komai da komai. Har wani sama _sama
numfashin ta keyi saboda kukan da take. Cikin kukan tace "doctor meyasa ka boye min? Ka boye mana? da
ban samu wasikar nan na karanta ba ta ya ya zan sani? I know fadeel won't tell me, Kwanan Mahmah nawa
da mutuwa?" Duk ta jiro masa tambayoyi cikin matsanancin damuwa da mamakin irin tarin kaunar da
Mahmah ke mata, domin sam abin yaki bace wa a zuciyar ta.

Ajiyar zuciya doctor Mahfouz ya sauke kana yace "yau watanta biyar da rasuwa. Wato Fadeelah ni kaina
abin yayi matukar taba ni, a lokacin da aka rasa wanda zai siyar miki da kodar sa hankali na ya tashi sosai, a
ranar da matan nan(mahmah) tazo da maganar a sanya miki kodar ta kyauta bayan ranta". Shiru yayi kana
ya cigaba... "Maimakon nayi farinciki samun kodar da aka yi sai naji ba dadi sak'amak'on matsanancin
tausayin matar daya kama ni, domin ban taba ganin Sadaukarwa hadi da kyawun zuciya irin na baiwar
Allah nan ba"

Hawaye masu zafi ke sauka a kuncin Fadeelah, matsanancin tausayi hadi da zafaffan soyaayya Mahmah na
ratsa ta. Ashe tayi watanin da mutuwa? (Kasancewar yau kwana fadeelah biyar da farfadowa, sam bata
zaci ta dauki watanin kwance a gadon asibiti ba)

Ba tare da ta sake cewa komai ba ta bar asibitin, hadi da bawa driver umarnin su koma gidan su Fadeel.

★★

Tsabanin dazu da ta tarar dashi a kwance, yanzu a zaune ta tarar dashi, ya kimtsa jakar kayan mahmah
dake a hargitse dazu.

Gabansa ta tsugunna cikin muryar kuka tace "my one" sai kuma kuka, sauran maganar ya makale,
idanunsa a kasa, yana jin kukan ta har zuciyarsa...
A karo na biyu ta budi baki tace "ya... Ka... Karin haku'rin mu?"

Ya dauki mintuna biyu kana cikin shakakken murya yace "Alhamdulillah"

Wasu hawayen ta share ta sake cewa "Allah ya jikan mahmah, Allah ya sa aljanan ta zama makoma a
gareta, Allah yasa kin huta mahmah"

Har ƙahon zuciyarsa ya ji dadin aɗɗuar ta ga mahaifiyar sa, a fili ya furta "Ameen"

"Nagode sosai my one, Mahmah ta bani kodar ta domin na rayu, bansan da wani baki zanyi godiya ba, sai
yau na sani, Mahmah Allah ya sanya haske da salama a kabarin ki, ina kaunar ki sosai Mahmah, nagode
nagode...." haka dai ta cigaba da maganganun kala kala abin tausayi.

Idanunsa ya bud'e ya sauke su kanta, yan sirarran lips din ta ya kurawa wa ido na second hamsin kana yace
" shhhhhhhhh! Kiyi shiru, Mahmah is gone, tafiya ta har abada, add'ua kadai take bukata" yana gama fadin
haka ya mayar da idanunsa ya lumshe.

Fadeelah kuwa jinjina masa kai kawai alamun gamsuwa tamkar yar yarinya. Ta kai mintuna goma a dakin,
babu mai magana, Mikewa tayi cikin sanyin jiki tace "ni...z...zan tafi, Allah ya jadadda rahamarsa ga
Mahmah" tama rasa wani irin godiya da ƙalar aɗɗuar ɗaƴa dace tayi, domin gani taƙe ɗuk ƙalmar ɗata yi
amfani da shi yayi kaɗan.

Shiru yayi na yan mintuna kana a takaice yace "Ameen Bye"

Idanunta taf da kwalla ta bar dakin, duk bata ji dadin halin shariyar d'aya nuna mata ba, amma sam bata ga
laifin sa ba, domin rasa uwa a duniya abu ne mai matukar ciwo, uwar ma irin Mahmah mai tarin kyawawan
halaiyya.

A ranar Fadeelah ta sha kuka sosai, irin wanda bata taba yi ba, irin wanda ko lokacin da take shirin ɓarin
ɗuniya bata yi k'watank'wancin sa ba, a daren ranar ta yi sallah'n dare, tayi add'ua sosai kan Allah haskaka
makwancin Mahmah, ta jima sosai tana addu'o'i har aka kira sallar asuba...

*** *** ***

*BAYAN SHEKARA DAYA*


Alhamdulillah zuwa yanzu Fadeel har ma da Fadeelah sun dawo da zafaffan soyaayyar da suke wa juna.
Duk da cewa kowace rana, ko wani seconds tunanin Mahmah na maƙale a zuciyoyin su, bare ma fadeelah
da take jin mahmah a zuciyar ta irin sosai dinnan domin duk wani motsin ta, mahmah na nan makale a
ranta. Hakika mahmah bata cancanci a manta da ita ba...

Kamar yau zaune suke a bakin beach suna shan hirar soyaayyar su, gwanin burgewa, dago kyakyyawan
idanunsa yayi ya kafe su kan Fadeelah dake waya tana fadin kalar cake da yanayin design da take so ayi wa
cake din. (Kasancewar gobe birthday dinta)

Bayan ta sauke wayar suka hada ido dashi, wani murmushi ta sakar masa hadi da cewa "kallon fa?"

Ajiyar zuciya ya sauke kana yace "kullum kara kyau kike, kullum da irin sabon salon yanayin maganar ki,
tafiyar ki, murmushin ki, in fact komai naki kara kyau suke kullum, gaya min menene sirrin?"

Tattausan murmushi ta sakar masa, Wanda na zallan jin dadi ne kana tace "kaine sirrin duk wani canjin
nawa my one, you re the reason behind" sai kuma ta shagwa'be fuska kana tace "yakamata ku hadu da
Daddy fa".
Ajiyar zuciya ya sauke kana yace " in sha Allah, kwana biyu da gama birthday dinki zan zo har gidan in gaida
Daddy"

"Yeeeeeeeehhh amma naji dadi sosai, Allah ya nuna mana jibin"

Murmushi ya sakar mata kawai, wasu lokutan yana matukar son yanayin yarintar ta hadi da shagwa'bar ta,
domin idan bai manta ba, gobe ne zata cika shekaru ashirin da uku a duniya, amma idan tayi wani abun
kamar yar shekara goma, kuma sosai hakan ke yi mata kyau.

Haka dai suka cigaba da hirar su kana suka yi sallama cike da kewar juna, tana sake jaɗaɗɗa masa ya zo
wajen birthday partyn nata da wuri, ɗomin shi kaɗai take bukatar gani, jinjina mata kai yayi murmushi
d'auke a fuskar sa...

*WASHEGARI*

Misalin karfe 4:00pm had'add'un motocin fadeelah ke shiga cikin tsad'add'en hall din da daddy ya kama
musamman domin shalelen sa (fadeelah). Bayan motocin duk sun gama daidaita parking, cikin sauri daya
daga cikin bodyguard dinta ya bud'e ƙofar wata rantsatsiyar mota fara kirar *PININFARINA BATTISTA*. A
hankali ta ziro farar kafarta mai sanye da tsad'add'en takalmi kirar *VALENTINO GARVANI*. Fitowa da
dayar kafar tayi, kana ta fito gaba d'ayan ta. "Wow!" yawancin mutanen dake haraban hall din suka ce, a
dalilin ganin Fadeelah.

Domin wasu had'add'un English wears ne a jikin ta kirar *DOLCE AND GABBANA*. Kayan basu fidda
siraicin ta ba, amma ya dace da yanayin jikinta matuka, Duk da light makeup ne a fusk'ar ta amma, tayi
wani irin sihirtacen kyau mai burgewa haka zalika agogo, sarka da dankunne ta duka na company D&G ne.

Gaba daya wadanda aka gayyata babu talaka, masu hannu da shuni ne bana wasa ba, In ka dauke Fadeel
bawan Allah dake can gefe, cikin wasu kananun kaya masu saukin kudi, da flat takalmi na fata, kirar sa hadi
da iya daukar wankan sa ya sanya kayan suka yi matukar dacewa da jikin sa.
Manyan masu kudi hadi da kusoshin gwamnati ke ta taya ta murnan zagayowar ranar haihuwar ta, amsawa
take yayinda hankalin ta ke kan dube-duben ta inda zata ga Fadeel.
Sai dai sam bata gan shi ba, hawaye ne ya ciko idanun ta. Daidai lokacin daddy ya karaso da manyan
abokan sa , ya sumbaceta kana suka nufi cikin hall din gabadaya.

Ajiyar zuciya fadeel ya sauke, sam bayason abinda za a yi masa kallon kaskanci, amma baya da zabi daya
wuce ya shiga din, kodan farinciki Darling d'insa (Fadeelah) fitowa yayi daga maboyar sa ya nufi cikin hall
din.

Babu abinda ke tashi sai zazzakar muryar wata matashiyar budurwa dake ƴiwa fadeelah wakar HAPPY
BIRTHDAY TO YOU. Yayinda wasu yan mata suka shiga fesa mata wanna abin mai Kamar kumfa fari mai
flavour din vanilla. Wani lumshe ido Fadeelah tayi domin kamshin abin yayi mata dadi sosai domin duk
wani abu mai vanilla tana son shi.

Fadin tsaruwa hadi da haduwar cikin hall din bata lokaci ne, kalar kayanta, kalar cake, hadi decoration din
wajen duk iri daya ne.

Nan aka shiga gabatar da shirye_shirye masu kayatar wa, sannan iyayenta, family, da abokan arziki suka
shiga kawo mata kyaututtuka masu tsadar gaske. Amsa take tana murmushin karfin hali saboda rashin
ganin Fadeel.

Fadeel dake tsaye kam a baya yana ganin duk yanayin ta, a hankali ya fara ratsa mutane yana son isa
gareta, daidai lokacin wani babban dan kasuwar kasar AMERICA ya kira Daddy a waya, hakan yasa ya dan
yi nesa daga wajen taron.

Daidai lokacin Fadeel ya karaso yana jefan ta da wani murmushi mai burgewa, take fuskar ta ya wad'atu da
fara'a, a hankali ya mika mata kyautar wata pure silver ring mai jan stone (zoben azurfa) Wanda kudinsa
bazai haura dubu biyu ba. Cikin tsantsar farinciki ta amsa, kana ta mikawa bodyguard dinta dake gefe
wayar ta kirar *GOLDVISH REVOLUTION DE MILLION* tace ya kyasta musu selfie, duk da cewa masu
camera na ta daukar hotona hadi da videos amma tafi son ta samu hoton sa a wayar ta.

Bayan ta Fadeel ya dawo ya dan ranƙwafo yayinda bodyguard din ya dauke su hoto kala uku. sosai hotunan
suka yi kyau bana wasa ba, komawa yayi ya tsaya daga dan gaba domin ya lura idan bata ganinsa kusa
hankalin ta yana rabuwa.

Sosai fadeelah taji dadin hakan, da yawa daga cikin mutanen da idanunsu ke kan fadeelah sun yi mamakin
ganin tace ayi musu hoto da Fadeel mutumin da kallo daya suka masa suka hango talauci daga yanayin
shigar sa, haka dai wasun su suka yi ta mamaki a ransu hadi da son sanin waye ma wanna matashin daya
samu wanna matsayin a wurin Fadeelah, domin yanda tayi murnan ƙaramar kyautar daya bata, sam ba
haka tayi murnan manyan kyaututtukan da aka bata ba, does that mean tafi farinciki da son karamar
kyautar sa?
Daidai lokacin *JAMEEL* ya shigo tare da tagawar sa, farin matashi ne sosai, in ka d'auke red cute lips
d'insa babu wani abun burgewa a tare dashi duk da uban farin sa kuwa.

A lokacin Daddy ya gama wayar sa ya juyo suka hada ido da Jameel. Rungume Daddy yayi cikin wayewa
kana yace "Good day Dad"
"Good day too son, ka buya?"
Dan murmushi Jameel ya saki ya ce "Dad bana kasar shekaru biyu kenan, jiya na dawo"...

"ohh yes! Minister Sa'id ya gayamin kaje wani course, welcome back" Daddy ya ƙarasa murmushi ɗauƙe a
fuskar sa.

"Thank you Dad" Jameel yace yana dan ruguman daddy kana ya nufi wajen fadeelah.

Gaban Fadeelah ne ya fadi lokacin da ta yi arba da Jameel, bata manta kalaman sa na karshe a gareta ba.

_I guess we should break up the relationship, domin kina da cutar koda. A tsarina bazan iya auran mace
mai wata cuta ko nakasa ba, bazan iya da jinya ba, domin auren hutu da jindadi nayi planing a rayuwa ta_

Kalaman kan yi mata zafi a duƙ sa'ilin data tuna, duk da cewa bata son shi, Daddy ke son tarayyar su hakan
yasa ta daure take kulashi a da. Isowar sa wajen ya katse mata tunanin ta.

"Hey my beautiful fiancy, am happy for you"

Cikin ɗauriya tace "Thanks"

Wani hada'dd'en mukulin mota kirar *BUGATTI CHIRON PUR SPORT* hadi da dan kunnen da sarka na
zallan gwal(gold) Wanda kudinsa ya kai *MILLION 20* ya bata hadi da cewa "here is your birthday gift"
babu abinda sarkar nan keyi sai daukar ido duk da yana cikin wani kyakkyawan box din sa.
Kasancewar ita din ba mai wulakanta mutane bane yasa ta karba kana ta furta "Thank you" domin har
ranta kyautar bai burgeta ba.

Daddy kuwa wani madaukakin murmushin farinciki ne ya wad'atu a fusk'ar sa, haka zalika wasu daga cikin
mutanen wajen kyautar ta birgesu, dama haka rayuwa take idan kana tunanin ka fi wani, tofah akwai
Wanda ya fika tabbas! Domin kowa ji yake ya bada kyauta ta kece raini, sai da Jameel ya gabatar da kyautar
sa suka ga nasu bai kai na Jameel tsada ba.

Gaban speaker Jameel ya tsaya yace "am so happy today is my girl birthday, and also my wife to be"

Ihun murna hadi da tafi irin nasu na wayayyu wajen ya dauka, kana aka saki wani romantic waka irin ta
masoya.

Take zuciyoyin Fadeel dana fadeelah suka buga da k'arfin gaske a tare, kallon sa fadeelah take tana
mamakin rashin Hankali irin ta sa, yayinda Fadeel ya ji wani yanayi mai wuyar fassaruwa, take kansa ya
shiga tsara masa, ya fara jin juwa, a haukace ya bar cikin hall din idanunsa jajir tamkar an watsa masa
barkono

_poor fadeel_😫💔

(Assalama alayk'um habibtie's am so sorry jiya kun jini Shiru, wutar ta lalace sai da magariba aka gyara.
Naga texts dinku, ina godiya da kauna.
Gobe ma zanyi kokarin Baku sabon updates, Noor loves you all💞)

#Share fisabilillah
#Comment
#vote

'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*

💝KYAUTAR ƘOƊA💝
(It's all about love, sacrifice, hatred and destiny)

_by Noor Eemaan_✍️

*Wattpad*
@NoorEemaan

ELEGANT ONLINE WRITER'S📚🖊

EDITING IS NOT ALLOWED❌

*(Please&please kuyi following nawa a Wattpad👏 @NoorEemaan)*

Page 27-28

(Not edited)

Dai-dai 6akin ƙofar ɗakin ta tsaya, ta sake sallama cikin zazzak'ar muryarta. Amma shiru, hakan yasa ta leƙo
da ƙanta cikin dakin.

A ƙwance ta hango fadeel, ya rame sosai ya sake yin ɗuhu, cikin sauri ta cire tsaɗaɗɗen takalmin kafarta na
company *GUCCI* ta shige dakin.

Gabansa ta tsugunna da nufin tashin sa, sai ta tsaya caƙ! saƙamaƙon ganin takarda rungume a ƙirjinsa. A
Hankali ta kai hannu ta zari taƙardan, haka kawai taji zuciyar ta na azalzalarta ta karanta ko ganin abin cikin
taƙardan.

Mikar da takardan tayi sak'amak'on dan cuƙurƙuɗewan da yayi ta fara karantawa...... Tun kafin tayi nisa da
karatun ta fara hawaye tamkar an balle famfo. Sai da ta zo karshen karatun ta kasa rike kukan da ya kufce
mata, dama Mahmah ce ta Sadaukarwa mata da *kodar ta?* Saboda su kasancewa a raye cikin farinciki?
Kaunar da Mahmah ke mata ko tace take musu ya kai haka? Meyasa doctor Mahfouz bai sanar mata?
Surutai ta dinga yi a ranta, yayinda kukan ta ke karuwa domin abin ya taba zuciyar ta matuka.
A hankali Fadeel ya Fara bud'e jajaye kuma ƙumɓurarrun idanun sa sakamakon kukan ta da ya ji ya sauke
su kanta, Kallonta yayi na yan mintuna ya maida idanunsa ya lumshe.....

Bakinta ne ya fara rawa, so take ta furta masa wata kalma ta kasa, kallon sa take yayinda zuciyar ta ke kara
karyewa. Ya dawo kamar bashi ba, ya fita a kamanin sa ainun. Gashi yaki kulata, sai dai hakan bai mata
ciwo ba, domin mutuwar uwa ba karamar abu bane...

Cikin sauri ta bar gidan ta fada mota hadi da bawa driver umarnin ya kaita asibiti. sanin cewa asibiti daya
take zuwa ya sa shi cewa "yes ma'am" Cikin sauri hadi da girmamawa. Haka motocin suka bar unguwar a
jare kamar ko yaushe.

Bangaren fadeel kuwa, yana jin fitar ta ya bude idanunsa ya bi kofar da ta fita da kallo. Wasu hawaye masu
dumi suka biyo kuncin sa, idan yace bai yi kewar ta ba yayi karya, amma baya son kowa ya rabe shi a halin
da yake ciki, yana bukatar privacy, yes yana bukatar kebancewa.

A hankali ya mike ya dauko kayan zanen sa, ya fara zana Mahmah kana ya zana fadeelah cikin mintuna
ashirin. Hotunan biyun ya ajiye kan cinyoyin sa bayan ya gama zanen, ya kafe su da ido hawaye na zuba
daga idanunsa, daya kalli zanen mahmah sai ya fashe da kuka, idan kuma ya kalli zanen fadeelah sai ya sa
dariya, haka ya dauki tsawon lokaci yana yi tamkar wani mai tabin k'wak'walwa.
Hakika yana farincikin Fadeelah ta rayu, yana kuncin Mahmah ta mutu.

***

Tun cikin mota ta kira doctor Mahfouz ta sanar dashi tana tafe. Bayan isar su asibitin direct office d'insa ta
nufa. Ta kuwa tarar dashi a ciki. Bata tsaya bata lokaci ba ta fara jero masa tambayoyi...

Doctor Mahfouz bai yi kasa a guiwa ba ya shiga sanar mata da komai da komai. Har wani sama _sama
numfashin ta keyi saboda kukan da take. Cikin kukan tace "doctor meyasa ka boye min? Ka boye mana? da
ban samu wasikar nan na karanta ba ta ya ya zan sani? I know fadeel won't tell me, Kwanan Mahmah nawa
da mutuwa?" Duk ta jiro masa tambayoyi cikin matsanancin damuwa da mamakin irin tarin kaunar da
Mahmah ke mata, domin sam abin yaki bace wa a zuciyar ta.

Ajiyar zuciya doctor Mahfouz ya sauke kana yace "yau watanta biyar da rasuwa. Wato Fadeelah ni kaina
abin yayi matukar taba ni, a lokacin da aka rasa wanda zai siyar miki da kodar sa hankali na ya tashi sosai, a
ranar da matan nan(mahmah) tazo da maganar a sanya miki kodar ta kyauta bayan ranta". Shiru yayi kana
ya cigaba... "Maimakon nayi farinciki samun kodar da aka yi sai naji ba dadi sak'amak'on matsanancin
tausayin matar daya kama ni, domin ban taba ganin Sadaukarwa hadi da kyawun zuciya irin na baiwar
Allah nan ba"
Hawaye masu zafi ke sauka a kuncin Fadeelah, matsanancin tausayi hadi da zafaffan soyaayya Mahmah na
ratsa ta. Ashe tayi watanin da mutuwa? (Kasancewar yau kwana fadeelah biyar da farfadowa, sam bata
zaci ta dauki watanin kwance a gadon asibiti ba)

Ba tare da ta sake cewa komai ba ta bar asibitin, hadi da bawa driver umarnin su koma gidan su Fadeel.

★★

Tsabanin dazu da ta tarar dashi a kwance, yanzu a zaune ta tarar dashi, ya kimtsa jakar kayan mahmah
dake a hargitse dazu.

Gabansa ta tsugunna cikin muryar kuka tace "my one" sai kuma kuka, sauran maganar ya makale,
idanunsa a kasa, yana jin kukan ta har zuciyarsa...

A karo na biyu ta budi baki tace "ya... Ka... Karin haku'rin mu?"

Ya dauki mintuna biyu kana cikin shakakken murya yace "Alhamdulillah"

Wasu hawayen ta share ta sake cewa "Allah ya jikan mahmah, Allah ya sa aljanan ta zama makoma a
gareta, Allah yasa kin huta mahmah"

Har ƙahon zuciyarsa ya ji dadin aɗɗuar ta ga mahaifiyar sa, a fili ya furta "Ameen"

"Nagode sosai my one, Mahmah ta bani kodar ta domin na rayu, bansan da wani baki zanyi godiya ba, sai
yau na sani, Mahmah Allah ya sanya haske da salama a kabarin ki, ina kaunar ki sosai Mahmah, nagode
nagode...." haka dai ta cigaba da maganganun kala kala abin tausayi.

Idanunsa ya bud'e ya sauke su kanta, yan sirarran lips din ta ya kurawa wa ido na second hamsin kana yace
" shhhhhhhhh! Kiyi shiru, Mahmah is gone, tafiya ta har abada, add'ua kadai take bukata" yana gama fadin
haka ya mayar da idanunsa ya lumshe.

Fadeelah kuwa jinjina masa kai kawai alamun gamsuwa tamkar yar yarinya. Ta kai mintuna goma a dakin,
babu mai magana, Mikewa tayi cikin sanyin jiki tace "ni...z...zan tafi, Allah ya jadadda rahamarsa ga
Mahmah" tama rasa wani irin godiya da ƙalar aɗɗuar ɗaƴa dace tayi, domin gani taƙe ɗuk ƙalmar ɗata yi
amfani da shi yayi kaɗan.

Shiru yayi na yan mintuna kana a takaice yace "Ameen Bye"


Idanunta taf da kwalla ta bar dakin, duk bata ji dadin halin shariyar d'aya nuna mata ba, amma sam bata ga
laifin sa ba, domin rasa uwa a duniya abu ne mai matukar ciwo, uwar ma irin Mahmah mai tarin kyawawan
halaiyya.

A ranar Fadeelah ta sha kuka sosai, irin wanda bata taba yi ba, irin wanda ko lokacin da take shirin ɓarin
ɗuniya bata yi k'watank'wancin sa ba, a daren ranar ta yi sallah'n dare, tayi add'ua sosai kan Allah haskaka
makwancin Mahmah, ta jima sosai tana addu'o'i har aka kira sallar asuba...

*** *** ***

*BAYAN SHEKARA DAYA*

Alhamdulillah zuwa yanzu Fadeel har ma da Fadeelah sun dawo da zafaffan soyaayyar da suke wa juna.
Duk da cewa kowace rana, ko wani seconds tunanin Mahmah na maƙale a zuciyoyin su, bare ma fadeelah
da take jin mahmah a zuciyar ta irin sosai dinnan domin duk wani motsin ta, mahmah na nan makale a
ranta. Hakika mahmah bata cancanci a manta da ita ba...

Kamar yau zaune suke a bakin beach suna shan hirar soyaayyar su, gwanin burgewa, dago kyakyyawan
idanunsa yayi ya kafe su kan Fadeelah dake waya tana fadin kalar cake da yanayin design da take so ayi wa
cake din. (Kasancewar gobe birthday dinta)

Bayan ta sauke wayar suka hada ido dashi, wani murmushi ta sakar masa hadi da cewa "kallon fa?"

Ajiyar zuciya ya sauke kana yace "kullum kara kyau kike, kullum da irin sabon salon yanayin maganar ki,
tafiyar ki, murmushin ki, in fact komai naki kara kyau suke kullum, gaya min menene sirrin?"

Tattausan murmushi ta sakar masa, Wanda na zallan jin dadi ne kana tace "kaine sirrin duk wani canjin
nawa my one, you re the reason behind" sai kuma ta shagwa'be fuska kana tace "yakamata ku hadu da
Daddy fa".
Ajiyar zuciya ya sauke kana yace " in sha Allah, kwana biyu da gama birthday dinki zan zo har gidan in gaida
Daddy"

"Yeeeeeeeehhh amma naji dadi sosai, Allah ya nuna mana jibin"

Murmushi ya sakar mata kawai, wasu lokutan yana matukar son yanayin yarintar ta hadi da shagwa'bar ta,
domin idan bai manta ba, gobe ne zata cika shekaru ashirin da uku a duniya, amma idan tayi wani abun
kamar yar shekara goma, kuma sosai hakan ke yi mata kyau.

Haka dai suka cigaba da hirar su kana suka yi sallama cike da kewar juna, tana sake jaɗaɗɗa masa ya zo
wajen birthday partyn nata da wuri, ɗomin shi kaɗai take bukatar gani, jinjina mata kai yayi murmushi
d'auke a fuskar sa...

*WASHEGARI*
Misalin karfe 4:00pm had'add'un motocin fadeelah ke shiga cikin tsad'add'en hall din da daddy ya kama
musamman domin shalelen sa (fadeelah). Bayan motocin duk sun gama daidaita parking, cikin sauri daya
daga cikin bodyguard dinta ya bud'e ƙofar wata rantsatsiyar mota fara kirar *PININFARINA BATTISTA*. A
hankali ta ziro farar kafarta mai sanye da tsad'add'en takalmi kirar *VALENTINO GARVANI*. Fitowa da
dayar kafar tayi, kana ta fito gaba d'ayan ta. "Wow!" yawancin mutanen dake haraban hall din suka ce, a
dalilin ganin Fadeelah.

Domin wasu had'add'un English wears ne a jikin ta kirar *DOLCE AND GABBANA*. Kayan basu fidda
siraicin ta ba, amma ya dace da yanayin jikinta matuka, Duk da light makeup ne a fusk'ar ta amma, tayi
wani irin sihirtacen kyau mai burgewa haka zalika agogo, sarka da dankunne ta duka na company D&G ne.

Gaba daya wadanda aka gayyata babu talaka, masu hannu da shuni ne bana wasa ba, In ka dauke Fadeel
bawan Allah dake can gefe, cikin wasu kananun kaya masu saukin kudi, da flat takalmi na fata, kirar sa hadi
da iya daukar wankan sa ya sanya kayan suka yi matukar dacewa da jikin sa.

Manyan masu kudi hadi da kusoshin gwamnati ke ta taya ta murnan zagayowar ranar haihuwar ta, amsawa
take yayinda hankalin ta ke kan dube-duben ta inda zata ga Fadeel.
Sai dai sam bata gan shi ba, hawaye ne ya ciko idanun ta. Daidai lokacin daddy ya karaso da manyan
abokan sa , ya sumbaceta kana suka nufi cikin hall din gabadaya.

Ajiyar zuciya fadeel ya sauke, sam bayason abinda za a yi masa kallon kaskanci, amma baya da zabi daya
wuce ya shiga din, kodan farinciki Darling d'insa (Fadeelah) fitowa yayi daga maboyar sa ya nufi cikin hall
din.

Babu abinda ke tashi sai zazzakar muryar wata matashiyar budurwa dake ƴiwa fadeelah wakar HAPPY
BIRTHDAY TO YOU. Yayinda wasu yan mata suka shiga fesa mata wanna abin mai Kamar kumfa fari mai
flavour din vanilla. Wani lumshe ido Fadeelah tayi domin kamshin abin yayi mata dadi sosai domin duk
wani abu mai vanilla tana son shi.

Fadin tsaruwa hadi da haduwar cikin hall din bata lokaci ne, kalar kayanta, kalar cake, hadi decoration din
wajen duk iri daya ne.

Nan aka shiga gabatar da shirye_shirye masu kayatar wa, sannan iyayenta, family, da abokan arziki suka
shiga kawo mata kyaututtuka masu tsadar gaske. Amsa take tana murmushin karfin hali saboda rashin
ganin Fadeel.

Fadeel dake tsaye kam a baya yana ganin duk yanayin ta, a hankali ya fara ratsa mutane yana son isa
gareta, daidai lokacin wani babban dan kasuwar kasar AMERICA ya kira Daddy a waya, hakan yasa ya dan
yi nesa daga wajen taron.
Daidai lokacin Fadeel ya karaso yana jefan ta da wani murmushi mai burgewa, take fuskar ta ya wad'atu da
fara'a, a hankali ya mika mata kyautar wata pure silver ring mai jan stone (zoben azurfa) Wanda kudinsa
bazai haura dubu biyu ba. Cikin tsantsar farinciki ta amsa, kana ta mikawa bodyguard dinta dake gefe
wayar ta kirar *GOLDVISH REVOLUTION DE MILLION* tace ya kyasta musu selfie, duk da cewa masu
camera na ta daukar hotona hadi da videos amma tafi son ta samu hoton sa a wayar ta.

Bayan ta Fadeel ya dawo ya dan ranƙwafo yayinda bodyguard din ya dauke su hoto kala uku. sosai hotunan
suka yi kyau bana wasa ba, komawa yayi ya tsaya daga dan gaba domin ya lura idan bata ganinsa kusa
hankalin ta yana rabuwa.

Sosai fadeelah taji dadin hakan, da yawa daga cikin mutanen da idanunsu ke kan fadeelah sun yi mamakin
ganin tace ayi musu hoto da Fadeel mutumin da kallo daya suka masa suka hango talauci daga yanayin
shigar sa, haka dai wasun su suka yi ta mamaki a ransu hadi da son sanin waye ma wanna matashin daya
samu wanna matsayin a wurin Fadeelah, domin yanda tayi murnan ƙaramar kyautar daya bata, sam ba
haka tayi murnan manyan kyaututtukan da aka bata ba, does that mean tafi farinciki da son karamar
kyautar sa?

Daidai lokacin *JAMEEL* ya shigo tare da tagawar sa, farin matashi ne sosai, in ka d'auke red cute lips
d'insa babu wani abun burgewa a tare dashi duk da uban farin sa kuwa.

A lokacin Daddy ya gama wayar sa ya juyo suka hada ido da Jameel. Rungume Daddy yayi cikin wayewa
kana yace "Good day Dad"
"Good day too son, ka buya?"
Dan murmushi Jameel ya saki ya ce "Dad bana kasar shekaru biyu kenan, jiya na dawo"...

"ohh yes! Minister Sa'id ya gayamin kaje wani course, welcome back" Daddy ya ƙarasa murmushi ɗauƙe a
fuskar sa.

"Thank you Dad" Jameel yace yana dan ruguman daddy kana ya nufi wajen fadeelah.

Gaban Fadeelah ne ya fadi lokacin da ta yi arba da Jameel, bata manta kalaman sa na karshe a gareta ba.

_I guess we should break up the relationship, domin kina da cutar koda. A tsarina bazan iya auran mace
mai wata cuta ko nakasa ba, bazan iya da jinya ba, domin auren hutu da jindadi nayi planing a rayuwa ta_
Kalaman kan yi mata zafi a duƙ sa'ilin data tuna, duk da cewa bata son shi, Daddy ke son tarayyar su hakan
yasa ta daure take kulashi a da. Isowar sa wajen ya katse mata tunanin ta.

"Hey my beautiful fiancy, am happy for you"

Cikin ɗauriya tace "Thanks"

Wani hada'dd'en mukulin mota kirar *BUGATTI CHIRON PUR SPORT* hadi da dan kunnen da sarka na
zallan gwal(gold) Wanda kudinsa ya kai *MILLION 20* ya bata hadi da cewa "here is your birthday gift"
babu abinda sarkar nan keyi sai daukar ido duk da yana cikin wani kyakkyawan box din sa.
Kasancewar ita din ba mai wulakanta mutane bane yasa ta karba kana ta furta "Thank you" domin har
ranta kyautar bai burgeta ba.

Daddy kuwa wani madaukakin murmushin farinciki ne ya wad'atu a fusk'ar sa, haka zalika wasu daga cikin
mutanen wajen kyautar ta birgesu, dama haka rayuwa take idan kana tunanin ka fi wani, tofah akwai
Wanda ya fika tabbas! Domin kowa ji yake ya bada kyauta ta kece raini, sai da Jameel ya gabatar da kyautar
sa suka ga nasu bai kai na Jameel tsada ba.

Gaban speaker Jameel ya tsaya yace "am so happy today is my girl birthday, and also my wife to be"

Ihun murna hadi da tafi irin nasu na wayayyu wajen ya dauka, kana aka saki wani romantic waka irin ta
masoya.

Take zuciyoyin Fadeel dana fadeelah suka buga da k'arfin gaske a tare, kallon sa fadeelah take tana
mamakin rashin Hankali irin ta sa, yayinda Fadeel ya ji wani yanayi mai wuyar fassaruwa, take kansa ya
shiga tsara masa, ya fara jin juwa, a haukace ya bar cikin hall din idanunsa jajir tamkar an watsa masa
barkono

_poor fadeel_😫💔

(Assalama alayk'um habibtie's am so sorry jiya kun jini Shiru, wutar ta lalace sai da magariba aka gyara.
Naga texts dinku, ina godiya da kauna.
Gobe ma zanyi kokarin Baku sabon updates, Noor loves you all💞)
#Share fisabilillah
#Comment
#vote

'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*

💝ƘƳAUTAR ƘOƊA💝
(It's all about love, scracife, hatred and destiny)

Written by
Noor Eemaan

Wattpad
@NoorEemaan

https://facebook.com/groups/943534712916776/
Masu amfani da facebook su yi join ta wanna link din.

ELEGANT ONLINE WRITER'S📚🖊

EDITING IS NOT
ALLOWED❌

Page 29-30
(Not edited)

Da kallo Fadeelah ta bishi yayinda idanunta suka ciko da kwalla, sai dai bata basu damar zubo wa ba. Ta
sani cewa fushi yayi, domin ta hango kishi mai zafin gaske a idanunsa....

Wani haushi Jameel din ne ya kamata, haka dai aka cigaba da gudanar da birthday party cikin farinciki da
annushuwa, banda fadeelah da hankalin ta ke tashe, sai dai mutum ba zai gane hakan kai tsaye ba, domin
ita sam bata son damuwar ta ya shafi wasu.

Sai karfe takwas aka tashi daga birthday party'n, suka dawo gida, har karfe tara manyan masu hannu da
shuni wandanda basu samu zuwa birthday party ba na zuwa har gida domin taya Fadeelah murnan
zagayowar ranar haihuwar ta.

Sai karfe goma ta koma part dinta cike da gajiya, kasancewar tayi sallah a part din Daddy ya sanya ta fada
Wanka, ruwan zafi ta shiga watsa wa fresh skin dinta domin gajiyar jikin ta ya warware. *LAURA MERCIER
ALMOND COCONUT MILK shower gel* ta sha murzawa a farar kana lallausan fatar ta, bayan ta gama ta fito
daure da towel sabanin yawan lokutan da ta fi amfanin da bathrobe.

Wani lotion mai kamshi ta fara shafawa a jikinta in a slow motion, kallo daya zaka mata ka hango zallan
damuwa Cikin idanunta. Bayan ta gama ta bude closet dinta na zallan glass, ta ciro wata T-shirt na
company *Hermés* wine color, ya sauko Mata har saman cinyarta.

Wani black hula ta sanya a kanta ba tare da ta damu da taje gashinta mai tsayi da bai fiye cika ba. domin
bata da kuzarin taje kan Saboda halin damuwar da take ciki.

Dad'add'an turaren *TOMFORD OUD WOOD* ta fesa sama_sama kana ta fada kan gado tana sauke ajiyar
zuciya. Kurawa hoton da suke manne a bango ido tayi, Wanda ya kusa mamaye bango gaba-daya saboda
yawan sa, tsayar da idon ta tayi kan zanen hotunan Mahmah kala biyu data sa Fadeel ya zana mata, sosai
take jin soyaayya, kauna, girma, hadi da darajar Mahmah duk da bata raye kuwa. Numfashi ta sauke a fili
tace "Allah yasa kin huta Mahmah" hoton zanan Fadeel ta kurawa ido, fuskar sa dauke da murmushi,
idanunta suka ciko da kwalla tuno yanayin daya fita daga cikin hall din dazu.

Number Fadeel ta kira, har ya fara ringing ta katse sak'amak'on knocking data ji a bakin kofa
"Yes come in" tace idanunta kafe kan kofar shigowa.
Daddy dake sanye cikin jallabiya kirar Cairo ya shiga bakinsa d'auke da sallama. Amsawa Fadeelah tayi a
sanyaye. Kan gadon ta ya zauna hadi da cewa "birthday girl ya gajiya?"

Murmushin karfin hali tayi "wallahi Dad, am so tired" ta fada a shagwa'be. tana dora kanta kan kafadar
Daddy'n.

Shafa kanta yake kana yace "kinyi sallama da Jameel kuwa kafin ya tafi?"

Dan bata rai tayi, domin ko sunan sa bata son ji "eh Dad" tayi karya.

"That's Good my princess" cewar Daddy yana kokarin yin magana idanun sa suka sauka kan zanen hotunan
fadeelah, Fadeel, hadi da Mahmah.

Cikin mamaki, domin bai taba lura ba yace " my princess hotunan zanen ki sunyi matuk'ar kyau, hakika
wanda ya zana ya kware matuka. Amma waye wanna matashin da matar dake gefensa?"

Gabanta ne ya dan fadi, duk da taji dadin yabon da fadeel ya samu daga wajen dad, abin ya dan mata
mamaki domin dad ba komai yake yabawa ba. a fili tace "suna da matukar muhimmanci a gareni Dad"

Dan shiru Daddy yayi kana yace "but ya akayi ban san su ba?"

A shagwa'be tace "please Dad!" alamun su bar maganar.

Sarai ya fahimci abinda 'yar tasa ke nufi dan haka yace "it's alright, dama na shigo ne domin duba lafiyar ki
good night I love you".

Murmushi tayi, ita kanta tasan kaunar da Daddy ke mata bana wasa bane, a fili tace " love you too Dad"
hadi da bashi sumbata a kumatu.
Shi kuma Daddy ya bata a goshi kana ya bar dakin cike da kaunar 'yar tasa.

A karo na hudu kenan ta cigaba da k'iran Fadeel sai dai har wayar ta katse baya daga kiran. Bata hakura ba,
ta sake dialing number shi...
Daga bangaren Fadeel kuwa a fusace ya daga wayar, Cikin murya da amon sa ke fidda zallan tashin hankali
hadi da halin matsanancin kishi da yake ciki yace "what!?"

Kuka fadeelah ta fashe da shi sak'amak'on kakkausar muryar daya yi amfani da shi.
"Ka...yi haku'ri please"
Daga bangaren Fadeel kuwa lumshe idanun sa yayi yana jin kukan ta har cikin zuciyar sa, ajiyar zuciya ya
fara saukewa a dalilin sa na son daidai ta fushin sa.
Furzar da wani huci mai zafi yayi "waye shi?" Ya fada cikin zallan kishin Jameel din.

"Please my one ka bar maganar shi, sam bashi da wani muhalli a zuciyata, dan abokin Daddy ne." Ta fada
wasu hawaye na sake bin kuncin ta.

"Kenan saurayin ki ne?" Ya sake jefo mata tambaya yana kokarin controlling kishin sa.

"A'a ni ba saurayi na bane, ko da can bana kula shi, kai nake so my one, kuma har abada kai zan so"

Lumshe idanun sa yayi yana jin wani sanyi dadi na ratsa shi, ko ba komai ta nuna tafi son shi kan Jameel.

Wasu tagwayen ajiyar zuciya ya sauke kana yace "am sorry da fadan da nayi miki, I...i can't just control my
self, ina kishin ki sosai fadeelah, i love you"

Wani dadi ne ya ratsa zuciyar fadeelah, Cikin muryar ta mai dadi tace "baka min komai ba my one, I love
you too"

"Baka manta bako? jibi zaku hadu da Daddy"


Murmushi yayi hadi da cewa " my Darling kenan, ina sane amma, yakamata ki sanar dashi zuwan nawa
ko?"

"Toh in sha Allah, zamuyi magana gobe" ta fada still da murmushi kan fuskar ta, haka dai suka cigaba da
hirar su irin ta masoya masu yiwa junan su kauna domin Allah.

*WASHEGARI*
Bayan sun gama having breakfast a part din Mommah Kamar yadda suka fi yi a yawan lokuta.

parlour'n ta suka dawo suka zaune, Fadeelah na shirin yi masa maganar Fadeel ta ji saukar muryar Daddy
kamar haka "princess alhaji Sa'eed ya kira ni jiya bayan na bar dakin ki, akan Jameel yana son ayi auren ku
nan bada jimawa ba, ban wani bashi wata gamshashiyyar amsa ba, domin har yanzu ke yarinya ce karama,
bana jin zaki iya d'aukar responsibility na aure" Daddy ya fada Cikin iyakar gaskiyar sa, domin shi kullum
ganin fadeelah yake tamkar yar 15years.
Duk da gabanta dake faduwa hakan bai hanata yin murmushi ba, hannun Daddy ta riko tace "Dad ta yaya
kake tunanin na yi kankanta da daukar ragamar rayuwar aure ? Dad ka tun ina da shekaru 19 kabar min
ragamar kula company din ka. Na taba failing dinka Daddy? I have ever failed you dad? Na taba yin wani
abu daya dakusar da company'n? An taba rasa wani abu, ko wasu kudade sun bata, tunda ka bar
company'n a karkashin kulawa ta?" Ta karasa a ladabce.

Numfashi Daddy ya sauka hakika babu karya cikin abinda 'yarsa tace "ba ko daya my princess, ina matuk'ar
alfahari dake domin kin kawo ababen cigaba a company'n sosai, zan bawa mahaifi Jameel damar turowa"

Gaban ta ne ya sake faduwa, kuka ta fashe dashi daya tayar da hankalin shi, dama Mommah da ta karaso
falon yanzu, cikin damuwa daya bayyana a fuskokin su suka shiga tambayar ta meya sata kuka.

Cikin shesheka tace "ni bana son Jameel, akwai wanda muke tare da shi".

Maganar ta ya soki Daddy matuk'a, amma farincik'in diyar sa ta fiye masa komai, don haka yace " yi shiru
my princess, ki daina kuka kar kiyi fever, zaki auri Wanda kike so kinji, a ina yake, dan waye shi a kasar
nan?"

Cikin muryar kuka tace "gobe Dad zai zo ya gaida ku"

"Alright, Allah ya kaimu" Dad ya fada yana share mata hawaye.

Mommah ce ta janyo ta jikin ta, cikin rarrashi ta shiga debe mata kewa haka dai har ta sake suka cigaba da
hirar su gwanin burgewa...

★★★

WASHEGARI

4:00pm

Tsaye Fadeel yake a dan nesa da tafkekken gate din su Fadeelah, kamar yadda fadeelah tayi masa
kwantance, ga sojoji da Daddy yayi hayan su birjik zagaye da katafaren estate din. Girma estate din ya
tsorata shi, domin duk wanda yaga estate din yasan ba kananun kudi aka kashe wurin gina shi ba. Duk da
jikinsa yayi sanyi amma sam baza ka fahimci hakan ba Saboda jarumta da dakiyar sa. Maganar Mahmah
kan soyaayar Fadeelah na karfafa masa guiwa...

Unguwar shiru baka jin motsin komai, babu kananun gida ko daya a unguwar, wayar sa kirar ITEL daya sa
aka gyara masa, ya yi dialing number fadeelah ya sanar da ita yana waje, saurin kashe wayar yayi
sak'amak'on wani ihun murnar Fadeelah daya cika dodon kunnen sa.. Mayar da wayar aljihu yayi yana
sakin murmushi daya sanya beauty point (dimple) din sa lo'bawa.

Shakka babu Fadeel yana da mugun kyau, duk da kasancewar shi baki, domin bashi da haske ko kodan,
dogo ne mai faffadar k'irji, idanunsa manya fararen kal, lips d'insa karami ne ja masu dan tudu kadan, yana
da kwantaceccen saje daya Kara kawata fusk'ar tasa, dukkanin jikinsa gargasa ne daya kwanta luf_luf
gwanin burgewa... (Kadan daga cikin kyau da haduwar Fadeel kenan)

Cikin girmamawa daya daga cikin masu tsaron gidan ya bud'e wa fadeelah gate. Yayinda bodyguard dinta
shida suka biyo bayanta domin yi mata rakiya, kamar yadda Daddy ya basu umarnin Kula da lafiyar ta.
Tsayawa tayi cak! Hadi da ce musu "ku koma, ba nisa zan yi ba"

Cikin girmamawa suka koma cikin, tun daga nesa suke jifan juna da murmushi na zallan kauna.
Shima Fadeel ganinta ya sa shi fara tako wa domin cin mata, kallonsa take, domin wani mugun kyau ya kara
mata, wata shadda ce a jikinsa mai saukin kudi dark blue anyi masa dinkin zamani daidai rufin asiri,
yayinda kafarsa ke sanye cikin wani takalmi na fata shi ma mai arahar gaske, sumar sa da bai fiye laushi ba,
tamkar dai na wasu mazan mu yan Nigeria, ya taje shi.
Duk da duka kayan jikin sa masu araha ne, amma kayan yayi masa kyau, domin iya daukan Wanka a jini
yake, kana iyawa ce, duk arahar kaya kuwa.

Sai da suka bata mintuna biyar duk suna hirar su kana tayi masa jagora suka nufi cikin gidan.
A fakaice Fadeel ke bin motocin da ke parking space sun fi hamsin da kallo, kuma duka babu karamin
mota, gidan kanshi abin kallo ne, idan wani attajiri ya shigo gidan zai sarawa ginin, hadi da tsaruwar gidan,
balle shi talaka.

Su kansu ma'aikatan gidan sun yi mamakin ganin fadeel, domin tunda suka fara aiki basu taba ganin wani
talaka ya rabe gidan ba, amma gashi yau sun ga talaka da diya mafi soyuwa a ran professor Imran mai
naira.

A falon Daddy ta sauke shi kamar yadda Daddy'n ya bukata.


Abubuwa kala_ kala na ci dana sha fadeelah ta sa aka kawo masa, snacks, drinks, abinci, fruits, da dai
sauran su, amma bai taba ko daya ba
"My one please kaci kafin Daddy ya sauko, yana sama"

Murmushi yayi, duk da baya jin zai iya cin komai, amma Saboda kar taji ba dadi yace "don't worry Darling
zan ci"

Murmushi tayi tace " toh, bari na kira Mommah nah ku gaisa "
Tana fadin haka ta fita da dan saurin ta, da kallon so ya bita kana ya sauke ajiyar zuciya.

Babu jimawa suka shigo tare da Mommah, cikin girmamawa ya gaida ita, Mommah ta amsa a sake, ta
danyi mintuna biyu kana ta basu waje tana ganin dacewar fadeelah da wanna matashin... Domin sam bata
lura da kayan jikin sa ba, kasancewar ta mace da bata fiye yiwa mutum kallo mai yawa ba.

Ganin babu wani expression mara dadi daga Mommah ya sanya Fadeel jin relief a ransa, yana fatan kada
ya samu matsala daga wajen dad ma.
Hirar soyaaya suka cigaba da yi, bayan mintuna talatin suka fara jin karar takun takalmin Daddy na
saukowa daga saman upstairs (bene)...

_may be ku jini gobe, may be not_😚

Vote and follow me on wattpad fisabilillah @NoorEemaan

#Share
#Comment
#Vote

'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*
💝ƘƳAUTAR ƘOƊA💝
(It's all about love, scracife, hatred and destiny)

*First edition*

Story/written by
*Noor Eemaan*

*wattpad*
@NoorEemaan

ELEGANT ONLINE WRITER'S📚🖊

https://facebook.com/groups/943534712916776/
Masu amfani da facebook su yi join ta wanna link din.

TO MY LOVELY AND BEAUTIFUL FANS💫📿


May Allah protect us all from bad calamities, disease and guide us all in the right path.
AMEEN.

EDITING IS NOT ALLOWED❌

Page 31-32

Haka kawai Fadeel yaji gaban sa ya fadi, duk taku daya da Daddy zai yi da bugun zuciyar sa yake fita, amma
bai dago k'ansa ba.
Bayan Daddy ya gama saukowa, yayi wa kansa mazauni kan ɗaya ɗaga cikin had'add'un kujerun falon yana
gyaran murya idanunsa kafe kan Fadeel.

"Barka da saukowa Daddy, ina wuni?"


Fadeel ya fada cikin calm and cool voice dake nuni ɗa girmamawa ga Daddy.

Shiru wajen ya d'auka, Daddy bai amsa gaisuwar ba, sai idanunsa ɗake ƙafe kan na fadeel. Tun daga
yanayin shigar Fadeel din, ya ji bai yi masa ba, tun dazu yana tsaye bakin window part d'insa, yaga
shigowar Fadeelah da Fadeel. Ya kasa yarda cewa wanda ke shirin zama suruƙinsa, mijin diyar sa mafi
soyuwa aran sa ne, ya shigo cikin ƙatafaran estate din sa a kafa? Yake
Kuma sanye da wata shadda dako masu gadin gidansa zasu iya bawa wani kyautar sa. "impossible" ya
aiyana a ransa.
Domin ya sake tabbatarwa yace "my Princess dan bamu waje"

Fadeelah da idanunta suka ciko da kwalla ganin Daddy bai amsa gaisuwar fadeel ba ta jinjina k'anta hadi da
Mik'ewa ta bar falon tana waigensu...

Wani kallo dake nuni da kaskanci yayi wa fadeel, kana cikin murya a dan kausashe yace "Waye kai? Waye
mahaifin ka a kasar nan?"

Wani abu mara dadi Fadeel ya hadiya, cikin girmamawa yace "Sunana Fadeel Muzakir, ni dan asalin....."

"Ba wanna nake son ji ba, waye mahaifin ka, wani mukami yake dashi a kasar nan? Ban tambaye ka asalin
ka ba" Daddy ya katse shi a zafaffe.

Take idanun Fadeel suka sanja launi zuwa ja, duk da haka yace "iyayena duka sun mutu, sannan su din ba
kowa bane a kasar nan ina......."
Saurin katse shi Daddy yayi da cewa "what!? Kana nufin kai din talaka ne fakiri? kuma kace kana son 'yata,
wait a minute! wanna katafaran estate din yayi maka kama dana talakawa irin ka, ko ma'aikatan gidana
babu talaka, domin bana hada inuwa dasu, kayi babban kuskuren zuwa estate din nan, 'yata ba sa'ar yin ka
bace, ina so kasani daga yau sai yau, kada na kara ganin ka rabi 'yata domin baka ko kama kafar ma'aikatan
ta ba. Wai meyasa ku talakawa kuke da kwadayi ne? kai a ganin farko daka mata tayi maka kama da mai
arahar da za ka iya aure? Kasani cewa ni PROFESSOR IMRAN MAI NAIRA bazan iya bawa talaka fakiri auren
ƴata ba, ka fita daga harkan ta, kayi nesa da rayuwar ta, idan ba haka ba. Hmmmm zan batar da kai ta
yanda ko sunan ka baza ka iya tunawa ba, zan batar da kai ta yanda ko hanyar garin Lagos aka ambata zaka
girgiza, idan kuma kudi kake so ko million nawa zan baka ka fita daga rayuwar 'yata, kayi nesa da ita, tunda
ka siye zuciyar ta"

"Ba....bb...na...bukatar komai sai auren Fadeelah, ina son ta Daddy pl......."


Duk da halin da Fadeel yake ciki bai hana shi yin maganar ba.

Cikin hanzari Daddy ya katse shi


"Hey shut the hell up! Nayi maka kama da baban ka da zaka kirani Daddy? A karo na karshe ina maimaita
maka, ka fita a rayuwar ta, if not...." Sai yayi wani murmushi mai sauti irin na mugunta kana yace "zaka yi
nadama mai yawan gaske!" Yana gama fadin haka ya bar wajen fuuuuuuuuuuuu cikin bacin rai ya nufi
bangaren Mommah.
idanunsa suka yi ja kamar gauta yabi Daddy da shi, wasu hawaƴe masu azabar zafin gaske suka zubo masa,
a kafatanin rayuwar sa ba a taba zagin sa ba sai yau, not even Mahmah bare baban shi da duk suke
karkashin kasa. Zuciyarsa tafarfarsa take, ji yayi duniyar tayi masa zafi mai yawa, ga soyaayyar fadeelah
dake neman tarwatsa zuciyar sa. Ya zai yi da tarin kaunar ta? Ga Daddy yace ya rabu ta, ta ina zai fara? Ina
zai kai tarin so da kaunar ta? A hankali kalaman Mahmah suka amsa kuwa a kunnen sa.

_kada ka karaya kan soyaayyar Fadeelah ya kai jarumin dana, ka jajirce da dukkanin iyawarka har ta zama
mallakin ka_

Wasu hawaye masu zafi ya kara sharewa, haka ya mike yana ganin biyu-biyu ya bar gidan, yana zancen zuci
dole ya shiga duniya, dole ya nemo kudi da dukkanin iyawar sa, ko ta ina, ƙo a wani gari, bazai taba bari
fadeelah ta ƙubce masa ba, abu daya ya sani shine bazai taba neman kudin haram ba!

★★★

"Fadeelah!"

"Fadeelah!!"

"Fadeelah!!!"

Fadeelah dake bedroom din Mommah a kwance cikin mutuwar jiki ta mike cikin sauri, tun dazu take jin
wani yanayi mara ɗaɗi a jikin ta. Sai dai a yau da Daddy ya kira sunanta na ainahi yafi komai daga mata
hankali, tun tana karama har kawo girman ta Daddy bai taba kiranta da sunan ta ba sai yau, ɗan ɗai wasu
mutanen na k'iran sunan ta, ɗa ba zata taba sanin cewa sunanta FADEELAH ba.

Dafe saitin zuciyar ta tayi, tana ambatan sunan Allah, daidai lokacin Mommah ta fito daga toilet cikin sauri
sak'amak'on muryar Daddy data sake ji a kausashe ya ƙira faɗeelah.
Bata yi magana ba, kawai ta riko hannu Fadeelah suka fito.
Zaune suka tarar da Daddy yana faman girgiza kafarsa irin yadda maza keyi idan suna cikin fushin nan, kallo
daya fadeelah tayi masa taji gabanta ya tsananta bugu.

"Ni zaki kunya ta Fadeelah? ki rasa wa zaki so sai bakin talaka fakiri, mutumin da ko keken kansa bai
mallaka ba, mai yake dashi da har ya rude ki kika fada son sa? Tambayar ki nake!"

Daddy ya fada da k'arfi kana cikin matsanancin fushi daya sake bayyana karara a fuskar shi.

Kuka fadeelah ta fashe da shi, jiƙinta ya kama rawa sam bata san meƴe faɗa ba, ba a taɓa yi mata ba, a ƴau
da daddy'n ta ke mata fada sai ta gan shi tamƙar wani sabon halitta, cikin dauriya tace "Daddy, Fadeel
bashi da makusa yana da dukkanin qualities da nake so a tare ɗa mijin aurena, ba dukiyata yake so ba, ni
yake so. Daddy Fadeel ya cancanci fiye da na so shi" shiru tayi Saboda harshen ta daya sark'e kana ta
cigaba.
"Ka taba tambaya Daddy? Ka taba tambayar ta ina aka samu KODAR da aka samin a lokacin da numfashi na
ke daf da barin gangan jikina? Ka taba tambaya Daddy? Ka tambayi doctor mahfouz? A lokacin da kuke
farincikin an samu wanda ya bani kodar sa, a lokacin Fadeel ke bakin cikin rasa mahaifiyarsa mafi soyuwa
aransa. Daddy kasan waye bani kyautar kodar sa, batare da ta karbi ko sisi ba? toh Mahaifiyar Fadeel ce, ita
ta bani kodar ta, ita ce ta bani Daddy, ya rasa mahaifiyar sa, ba shida sauran farinciki daya rage masa sama
dani, kada ka raba mu Daddy please I beg of you"

Shiru Daddy yayi kamar ruwa ya cinye shi, yayi matuka wurin girgiza jin cewa Mahaifiyar baƙin ƴaron ɗaƴa
bari a falon sa ne ya bawa 'yar sa abar son sa kyautar koda ba tare da ta bukaci ko naira biyar ba, sannan
bata raye, dama aƙwai sauran talaka da zuciyar su bai mutu ba, da basu damu da duniya da abinda ke cikin
ta ba, shi kallon da yake wa talaka masu kwadayi ɗa matattaciyar zuciya ce. Ɗama akwai masu zuciya da
basu damu da arzikin mutum ba? Wani yanayi mai kama da nadama da tausayi ke kokarin ratsa zuciyar sa,
sai dai inaaaa.... kiyayyar da yake wa fadeel kasancewar sa talaka ya rinjaye wanna tausayin da nadama,
musamman tuna yanayi da shigar dake jiƙin Fadeel din. Shi ko ma'aikatan zai dauka baya taba daukar
talaka futuk, sannan ace surukin sa ya kasance talaka? wanna aɓin ƙunƴar har ina....

"Impossible!"

Ya fada da dan k'arfi kana ya cigaba.

"Sai me? Sai me dan ta baki kodar ta? Idan ɓiyan sa yaƙe so ayi sai a ɓiya shi ƙoɗar mahaifiƴarsa. idan kudi
yake so zan bashi ko million nawa yake so, idan in dollars yake so zan bashi, kai duk nau'o'in kan kuɗaɗen
da yake so, ko na wani kasa ne zan bashi, matuk'ar zai rabu da ke, ya fita hanyar ki, baku dace ba....."

Cikin wani mugun kuka fadeelah ta katse Daddy da cewa "Daddy please ina son shi a haka, ko da kuwa a
daji zamu rayu, y'ay'an itatuwa da ganyayeki su zama abin cin mu zan iya rayuwa dashi, a ƙo wani hali ne,
dan Allah Daddy shi kadai nake so"

"Shut up! princess yaushe kika girma da har kike maganar soyaaya? Saboda soyaaya kike son barin gatan
ki? namiji yana da taɓɓas ne? Namijin ma talaƙa da basu iƴa cin arziƙi ba, kaf zuri'ar mu babu mai rufin
asiri balle ma ace za a samu talaka, har abada wanna bakin yaron ba zai taba zama suruki na ba, ki....."

Mommah dake share hawayen tausayin su Fadeelah tace "haba my professor, be calming down please, a
ganina wanna yaron bai da wani aibu, he has duk wani quality da ake so ga namijin aure expect money
wanda zai yi idan lokacin sa yayi, domin arziki ta Allah ce, dan Allah ina taya su rokon ka, ka barsu suyi
aurensu. Kada fa ka manta Manson Allah S.A.W yace a duk lokacin da y'ay'anku suka kawo....."
"Ke! Shuhudah!(mommah) ni zaki yiwa wa'azi? Idan 'yar cikin ki ce zaki yarda ta auri talaka fakiri? Ooh
Saboda ba yar cikin ki bace shiyasa kike son ta auri talaka ko? Ta ki saurara da k'yau, 'yata FADEELAH
IMRAN MAI NAIRA bazata taba auran talaka ba!!!!"

Kuka Mommah ta fashe dashi, a dukkanin rayuwar ta bata taba bakin ciki da jin ciwon rashin haihuwa
kamar na yau ba, domin kallon fadeelah take tamkar ƴar cikin ta. Amma yau maganar professor ya fama
mata mikin data dade da binnewa a zuciyar ta.

A fili tace "professor, duk abinda ka fada ba haka bane, fadeelah 'ya na dauke ta, ban taba tunanin ko yin
abinda zai cuce ta ba. Amma ka gafarceni in sha Allah daga yau bazan sake yin magana ko saka baki a
maganar nan ba"

Tana gama fadin haka ta nufi dakin ta cikin sauri tana sharar hawaye...

( Tun jiya na so yi muku update amma Allah bai nufa ba. A next page zamu ji asalinsu fadeelah in sha
ALLAH)

#Share
#Comment
#Vote

'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*

💝ƘƳAUTAR ƘOƊA💝
(It's all about love, scracife, hatred and destiny)

*Written by*
Noor eemaan

*Wattpad*
@NoorEemaan

ELEGANT ONLINE WRITER'S 🖊

EDITING IS NOT ALLOWED❌

https://facebook.com/groups/943534712916776/
Masu amfani da facebook su yi join ta wanna link din.

(Ya jama'a pls&pls, dan kaunar ku da Manzon s.a.w ku garzaya manjahar WATTPAD kuyi following dina
@NoorEemaan ngd👏)

*Ngd sosai da kulawar ku gareni, jiki da sauki alhamdulillah, son so fisabilillah my fans*

Page 33-34

(kila ku ga typing error😎)

Kuka fadeelah ta sanya mai matuƙar ta6a zuciya, taji ba dadi matuƙa, da irin maganganun da Daddy ya
fadawa Mommah, da ba ɗan da wayonta mahaifiyarta ta rasu ba, zata iƴa rantsewa Mommah ce ta haife
ta, saboda tsananin so, kulawa, haɗi da ƙaunar da Mommah'n ke mata.

tana da tabbacin cewa Daddy ya gayawa fadeel maganganun marasa dadi, ita kam ina zata sa kanta taji
ɗaɗi?
Daddy daya bi mommah da kallo har ta shige dakin ta, ƴa ɗawo ɗa ƙallon sa ga fadeelah, taƙe wani
tausaƴin ƴarsa ya darsu a zuciƴarsa, domin duk fadan da yake mata dauriya yake, sai dai baya jin zai mata
abinɗa taƙe so wato ya rarrashe ta, ɗomin rarrashin ta na nufin ya amince da auren ta, da wanna bakin
talaƙa faƙiri a cewar shi...

Murƴa a ɗan ƙausashe yace " ƙi sani har ɗuniƴa ta nade bake ba auren shi, ke bama shi ba ɗuk wani fakiri
talaka bazai taba raba ta ba, kuma dole ki auri Jameel ɗomin shi yafi dacewa dake, period!!!"

yana gama fadin haka, ya bar part din Mommah, dama gidan gaba-daƴa, ƴaƴinɗa masu tsaronsa suƙa yi
saurin buɗe masa kofar mota ƙirar *RANGE ROVER* ya shiga kana sauran suka shiga motocin, a jere suka
bar gidan...

Fadeelah ta jima tana ruzar kuka, can ta mike zumbur ta nufi part din Daddy domin a tunanin ta Fadeel na
nan. Sai dai wayam ta gani, bayan isar ta had'add'en falon daddy.

Hannun ta na rawa ta fara dialing number shi, guiwarta ta sanyi kalau ta sulale kasa, sak'amak'on jin
muryar matan ma ta mtn tace *The MTN number you dialed is switched off please hold on or call back
later*
Tana jima zaune cikin mayuwancin hali kana ta koma part d'in ta tana hada hanya...

*ASALIN SU FADEELAH*

Professor Imran mai naira dan asalin garin Adamawa ne a garin jimeta, sai dai a lagos suke rayuwar su, sai
irin dangin su haka dake Adamawa suma a tamfatsetan estate dinsu. Sunan mai naira ya samo asali ne,
daga mahaifin professor Imran di'n wato professor Dalhat Abdul-mutalib mai naira wanda ya k'asance kaka
na wajen uba ga Fadeelah.

Gaba daya zuri'ar wanna gida yan boko ne na bugawa a jarida, sannan kaf dinsu Allah yayi musu arzikin
mai yawan gaske.

Tun daga kakan kakanin su suke da wanna arzikin mai dimbin yawa. Haka professor Imran ya taso ya ganshi
cikin arziki, zan iya cewa professor Imran bai san zafin nema ba, haka zalika sauran yan'uwan sa...

Yayinda Mahaifiyar professor Imran Nadia(Grandma) ta kasance yar asalin saudiya, sannan itama iyayenta
sun kasancewa masu kudi sosai, wanda a saudiyan an san dasu da ma wajen saudiyan. Nadia ɗa professor
Dalhat Abdul-mutalib (mahaifin Imran kenan) sun hadu a Canada lokacin daya je karo karatu har ya taka
matsayin PROFESSOR.
Nadia da professor Abdul-mutalib mai naira basu bata lokaci wurin bayyana soyaayyar da suke wa juna
kasancewar su wayayyu.
Ba'a dauki lokaci ba suka mallaki juna a matsayin ma'aurata ɗomin ba'a samu matsala daga bangarorin
biyun ba.

Bayan shekaru biyar Nadia(Grandma) ta haifi da namiji, ranar suna yaro yaci suna Yusuf (Abba Yusuf) sosai
iyayensa ke matuk'ar kaunar sa, bayan shekara biyar Nadia ta sake haifar da namiji ranar suna yaro yaci
suna IMRAN (Daddy) sosai suka yi murna, da sake samun wanna karuwar, bayan shekara uku Nadia ta sake
haifar Ya mace mai suna Widad (Anty Widad kamar yadda fadeelah ke kiranta)
Daga nan suka yi family planning a Cewar su sun gama haihuwa. Sosai yaran ke samun kulawa daga iyayen
su dama sauran ahalin gabadaya.

Tun professor Imran na k'arami ya tsani talaka, baya son hada inuwa dasu ko da wasa, sam bai yi la'akarin
cewa wanna arzikin ba dabara ko wayon su ne ya Samar musu ba. Sannan bai yi tunanin cewa ita arziki ta
Allah ce ba, sannan da talaka da mai kudi duk daya suke a wajen Allah, illa wanda yafi tsoron Allah ta ala.
Sannan baya samun k'waba daga wajen Nadia(grandma) domin ita ma ta tsani talaka, gwara mahaifinsa na
dan kwabar sa wani lokacin.

Sabanin wansa Yusuf(Abba Yusuf) dake haba-haba da ko wani irin mutum ne, komai kaskancin sa kuwa,
zan iya cewa halinsa fadeelah ta dauka.

Bayan duk sun gama karatu sun kai minzanin aure, professor Imran yaga wata daga dangin Nadia
(Grandma) yace yana so mai suna Waheedah(mahaifiyar fadeelah) itama waheedah bata wani ja da ƴawa
ba ta amince, domin tana son sa....
Abba Yusuf ma ya samu wacce yake so, yar garin bauchi, itama ba laifi za a k'ira su da masu kudi. Duk da
Nadia(Grandma) bata so ba, domin tana matuk'ar son zuri'ar ta su auri masu kudi na bugawa a jarida, irin
sosai ɗinan.
Amma professor Dalhat Abdul-mutalib ya rarrashe ta kan ta amince da auran, tunda Yusuf din na so...

Ba a dauki lokaci ba aka yi musu aure har da Widad, data auri Wani babban dan kasuwa, wanda a yanzu
suke zaune ne a California...

*SOME YEARS LATER*

Abba Yusuf na da y'ay'a biyu namijin da mace wanda suka kasance yan biyu masu shekaru shida_shida a
duniya

Bayan shekaru shidan da haihuwar matar abba yusuf, Waheedah ta haifi santaleliyar 'yarta, ranar suna
yarinya taci suna FADEELAH, fadin murnan wadanan ahalin bata lokaci ne.
Sosai Fadeelah ta samu kyatuttuka daga iyayen ta, kakanin ta, abokan arziki, kusoshin gwamnati da dai
sauran su, tun fadeelah na yar jaririya take da mugun arzikin ta.
Daga nan haihuwar ta tsaya mata, tun fadeelah na karama likita ya tabattar da ta cewa tana da cutar koda
wanda yayi mugun daga hankalin ahalin, domin da shi aka haife ta, sai dai likita ya kwantar musu da
hankali kan cewa za a dora ta kan medication.

Fadeelah na da shekaru goma a duniya Allah yayi wa Waheedah rasuwa, wato mahaifiya ga fadeelah.
Mutuwar ya matuk'ar girgiza ahalin biyun, domin Waheedah (Mommy kamar yadda fadeelah ki kiranta)
macece mai kirki da iya zama da jama'a.

Ranar data yi kwana arba'in da rasuwa professor Dalhat Abdul-mutalib mai naira ya rasu shi ma.
wayyo Allah! Wadannan ahalin sun shiga kuncin mai yawan gaske, daga baya suka fawwalawa Allah komai.

Bayan shekaru biyar da mutuwar su professor Imran ya hadu da Shuhudah(Mommah) a wani business trip
daya je Ghana, wanda Mommah ta kasance yar asalin Ghanian ce, Daddy bai bata lokaci wurin bayyana wa
Mommah ko shi waye ba, da irin son ta daya kamu da shi, domin Daddy irin mutanen nan ne da basa iya
boye abinda ke ransu.

Mommah ma bata wani ja da yawa ba ta amince masa, kasancewar professor'n yayi mata hundred
percent, Kuma tun kafin taga fadeelah ta kamu da son ta kasancewar Daddy ya gaya mata yana da 'ya.

*BAYAN WASU SHEKARU*

Fadeelah ta zama budurwa mai tsananin kyawun gaske, a kananun shekarunta ta kammala masters d'inta,
inda Daddy ya dora ta kan wasu company dinsa, daga na Nigeria har na kasar waje, domin ya yarda da
kwazon ɗiyar tasa, hadi da ƙaifin tunanin ta, hakan ya sanya Daddy bai yi shakkar Sakar mata wasu
company'n ba, domin fadeelah daya take tamkar da dubu.......

*JAMEEL*

Jameel ya k'asance dan abokin Daddy wanda mahaifin sa ya kasance MINISTER OF FINANCE, tun a
zamanin kuruciya suke abota da Daddy, kasancewar hali ya zo daya, yasa abotar su ta daure.

Jameel shine ɗa daya ɗa MINISTER SA'ID ya mallaka, ya kuma dora son duniya ga dan sa.
Wata rana Daddy'n jameel tare da Jameel ɗin sun kawo wa Daddy ziyara, inda anan Jameel ya ga Fadeelah
ya kamu da sonta, bai boye ba a gaban Daddy'n ya sanar, kasancewar boko ta ratsa Daddy sam bai damu
ba, sai ma farincikin sa ɗaya nuna.

Sama-sama Fadeelah ke kula shi, domin sam bata kaunar sa dai-dai da kwayar zarra, darajar Daddy yake ci
take ma kulasa, suna da shekara daya tare da Jameel, yasan cewa Fadeelah na dauke da cutar koda, bai
boye mata ba yace, bazai iya auran mace mai lalurar ƙo wata tawaya ba. Duk da kasancewa Fadeelah bata
son shi amma taji ciwon maganar matuk'a.
Jameel ya bar kasar, sai dai yana biyayar al'amuran fadeelah.

A lokacin da FADEELAH ta hadu da gwarzon masoyinta Fadeel, tayi farinciki sosai domin irin namijin da
take fatan wa k'anta kenan, wanda zai so ta da tsakani da Allah ba dan dukiya ko wani kyale-kyalen Rayuwa
ba, kuma alhamdulillah ta samu.(sai dai daddy ya kawo cikas😩)

lokacin da jameel ya samu labarin an bawa Fadeelah koda, ba karamin farinciki yayi ba, domin yana sonta
dama, dalilin sa mara tushe ya sa ya barta, take ya dawo Nigeria cike da burin mallakar ta...

Labarin su Fadeelah a tak'aice kenan.

*** *** **

Ƴau kwana hudu kenan bata samun Fadeel a waƴa, faɗin tashin hanƙali, ɗamuwa, da faɗeela tayi going
through a kwanakin nan ɓata loƙaci ne.

A ƴau ta ƙuɗirci niƴƴar zuwa gidan su Fadeel, ɗomin duba halin ɗa ƴaƙe ciki, ɗomin a ƙwanaƙin nan ita
ƙadai ta san azabar da taƙe sha na rashin jin murƴar sa....

Wanka ta fada, ta murza jikin ta da tsad'add'en kana hada'dden shower gel di'nta na *pink sugar* bayan
yan mintuna ta fito sanye da bathrobe, lotion ta shafa kana ta zura *Robber to Cavalli* jeans trouser hadi
da riga daya sauko mata har kasan cinyarta fara, sai tayi rolling da madaidaicin mayafi, hills shoe ta sanya
kirar Dubai, kana ta fesa turaren *Balade sauvage*
Bata yi makeup ba, amma sosai tayi kyau duk da halin matsanancin damuwar da take ciki....

Yalwataccen farfajiyar su ta fito, ga security da body guards nata kai wa da komowa... Suna ganinta suka
nufe ta cikin girmamawa da niyyar bude mata mota. A hankali ta motsa tattausan labb'anta tace "ni kadai
zan fita, ku bani mukullin *Ferrari Sergio* red din can"

Cikin sauri aka tuko shi zuwa gabanta, kana driver ya fito, ya mika mata key, amsa tayi ta fada cikin motar
ta bata wuta ta bar gidan...

Daddy dake tsaye a saman part dinshi ya hango fitar fadeelah, cije lebe yayi ganin ta fita ita kadai, take
kuma zuciyar sa ta raya masa kila wajen Fadeel zata, cikin sauri ya kira personal security d'insa ya ce ya bi
masa bayan fadeelah ya ga inda ta nufa...

Isar Fadeelah kofar gidan su Fadeel yasa gabanta ya yanke ya fadi sak'amak'on ganin kofar gidan datse da
mukulli, dafe zuciyar ta tayi tace "ya Allah"

Hawaye suka cika idanunta, a hankali ta shiga takawa domin isa bakin kofar, domin wata farar takarda ta
take gani a jikin kwadon da aka rufe gidan dashi, bama ta ganin gaban ta sosai saboda ruwan hawaye daya
cika idanunta, a hankali ta kai hannu ta zaro takardan ta fara warwarewa.......
Please👏follow and vote you sister a manjahar wattpad
*@NoorEemaan*

Share fisabilillah
Comment
Vote

I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*.

💝ƘƳAUTAR ƘOƊA💝
(It's all about love, scracife, hatred and destiny)

*Written by*
Noor eemaan

*Wattpad*
@NoorEemaan

ELEGANT ONLINE WRITER'S 🖊


EDITING IS NOT ALLOWED❌

https://facebook.com/groups/943534712916776/
Masu amfani da facebook su yi join ta wanna link din.

(Ya jama'a pls&pls, dan kaunar ku da Manzon s.a.w ku garzaya manjahar WATTPAD kuyi following dina
@NoorEemaan ngd👏)

*Ngd sosai da kulawar ku gareni, jiki da sauki alhamdulillah, son so fisabilillah my fans*

Page 33-34

(kila ku ga typing error😎)

Kuka fadeelah ta sanya mai matuƙar ta6a zuciya, taji ba dadi matuƙa, da irin maganganun da Daddy ya
fadawa Mommah, da ba ɗan da wayonta mahaifiyarta ta rasu ba, zata iƴa rantsewa Mommah ce ta haife
ta, saboda tsananin so, kulawa, haɗi da ƙaunar da Mommah'n ke mata.

tana da tabbacin cewa Daddy ya gayawa fadeel maganganun marasa dadi, ita kam ina zata sa kanta taji
ɗaɗi?

Daddy daya bi mommah da kallo har ta shige dakin ta, ƴa ɗawo ɗa ƙallon sa ga fadeelah, taƙe wani
tausaƴin ƴarsa ya darsu a zuciƴarsa, domin duk fadan da yake mata dauriya yake, sai dai baya jin zai mata
abinɗa taƙe so wato ya rarrashe ta, ɗomin rarrashin ta na nufin ya amince da auren ta, da wanna bakin
talaƙa faƙiri a cewar shi...

Murƴa a ɗan ƙausashe yace " ƙi sani har ɗuniƴa ta nade bake ba auren shi, ke bama shi ba ɗuk wani fakiri
talaka bazai taba raba ta ba, kuma dole ki auri Jameel ɗomin shi yafi dacewa dake, period!!!"

yana gama fadin haka, ya bar part din Mommah, dama gidan gaba-daƴa, ƴaƴinɗa masu tsaronsa suƙa yi
saurin buɗe masa kofar mota ƙirar *RANGE ROVER* ya shiga kana sauran suka shiga motocin, a jere suka
bar gidan...

Fadeelah ta jima tana ruzar kuka, can ta mike zumbur ta nufi part din Daddy domin a tunanin ta Fadeel na
nan. Sai dai wayam ta gani, bayan isar ta had'add'en falon daddy.
Hannun ta na rawa ta fara dialing number shi, guiwarta ta sanyi kalau ta sulale kasa, sak'amak'on jin
muryar matan ma ta mtn tace *The MTN number you dialed is switched off please hold on or call back
later*
Tana jima zaune cikin mayuwancin hali kana ta koma part d'in ta tana hada hanya...

*ASALIN SU FADEELAH*

Professor Imran mai naira dan asalin garin Adamawa ne a garin jimeta, sai dai a lagos suke rayuwar su, sai
irin dangin su haka dake Adamawa suma a tamfatsetan estate dinsu. Sunan mai naira ya samo asali ne,
daga mahaifin professor Imran di'n wato professor Dalhat Abdul-mutalib mai naira wanda ya k'asance kaka
na wajen uba ga Fadeelah.

Gaba daya zuri'ar wanna gida yan boko ne na bugawa a jarida, sannan kaf dinsu Allah yayi musu arzikin
mai yawan gaske.

Tun daga kakan kakanin su suke da wanna arzikin mai dimbin yawa. Haka professor Imran ya taso ya ganshi
cikin arziki, zan iya cewa professor Imran bai san zafin nema ba, haka zalika sauran yan'uwan sa...

Yayinda Mahaifiyar professor Imran Nadia(Grandma) ta kasance yar asalin saudiya, sannan itama iyayenta
sun kasancewa masu kudi sosai, wanda a saudiyan an san dasu da ma wajen saudiyan. Nadia ɗa professor
Dalhat Abdul-mutalib (mahaifin Imran kenan) sun hadu a Canada lokacin daya je karo karatu har ya taka
matsayin PROFESSOR.

Nadia da professor Abdul-mutalib mai naira basu bata lokaci wurin bayyana soyaayyar da suke wa juna
kasancewar su wayayyu.
Ba'a dauki lokaci ba suka mallaki juna a matsayin ma'aurata ɗomin ba'a samu matsala daga bangarorin
biyun ba.

Bayan shekaru biyar Nadia(Grandma) ta haifi da namiji, ranar suna yaro yaci suna Yusuf (Abba Yusuf) sosai
iyayensa ke matuk'ar kaunar sa, bayan shekara biyar Nadia ta sake haifar da namiji ranar suna yaro yaci
suna IMRAN (Daddy) sosai suka yi murna, da sake samun wanna karuwar, bayan shekara uku Nadia ta sake
haifar Ya mace mai suna Widad (Anty Widad kamar yadda fadeelah ke kiranta)
Daga nan suka yi family planning a Cewar su sun gama haihuwa. Sosai yaran ke samun kulawa daga iyayen
su dama sauran ahalin gabadaya.

Tun professor Imran na k'arami ya tsani talaka, baya son hada inuwa dasu ko da wasa, sam bai yi la'akarin
cewa wanna arzikin ba dabara ko wayon su ne ya Samar musu ba. Sannan bai yi tunanin cewa ita arziki ta
Allah ce ba, sannan da talaka da mai kudi duk daya suke a wajen Allah, illa wanda yafi tsoron Allah ta ala.
Sannan baya samun k'waba daga wajen Nadia(grandma) domin ita ma ta tsani talaka, gwara mahaifinsa na
dan kwabar sa wani lokacin.
Sabanin wansa Yusuf(Abba Yusuf) dake haba-haba da ko wani irin mutum ne, komai kaskancin sa kuwa,
zan iya cewa halinsa fadeelah ta dauka.

Bayan duk sun gama karatu sun kai minzanin aure, professor Imran yaga wata daga dangin Nadia
(Grandma) yace yana so mai suna Waheedah(mahaifiyar fadeelah) itama waheedah bata wani ja da ƴawa
ba ta amince, domin tana son sa....
Abba Yusuf ma ya samu wacce yake so, yar garin bauchi, itama ba laifi za a k'ira su da masu kudi. Duk da
Nadia(Grandma) bata so ba, domin tana matuk'ar son zuri'ar ta su auri masu kudi na bugawa a jarida, irin
sosai ɗinan.
Amma professor Dalhat Abdul-mutalib ya rarrashe ta kan ta amince da auran, tunda Yusuf din na so...

Ba a dauki lokaci ba aka yi musu aure har da Widad, data auri Wani babban dan kasuwa, wanda a yanzu
suke zaune ne a California...

*SOME YEARS LATER*

Abba Yusuf na da y'ay'a biyu namijin da mace wanda suka kasance yan biyu masu shekaru shida_shida a
duniya

Bayan shekaru shidan da haihuwar matar abba yusuf, Waheedah ta haifi santaleliyar 'yarta, ranar suna
yarinya taci suna FADEELAH, fadin murnan wadanan ahalin bata lokaci ne.
Sosai Fadeelah ta samu kyatuttuka daga iyayen ta, kakanin ta, abokan arziki, kusoshin gwamnati da dai
sauran su, tun fadeelah na yar jaririya take da mugun arzikin ta.

Daga nan haihuwar ta tsaya mata, tun fadeelah na karama likita ya tabattar da ta cewa tana da cutar koda
wanda yayi mugun daga hankalin ahalin, domin da shi aka haife ta, sai dai likita ya kwantar musu da
hankali kan cewa za a dora ta kan medication.

Fadeelah na da shekaru goma a duniya Allah yayi wa Waheedah rasuwa, wato mahaifiya ga fadeelah.
Mutuwar ya matuk'ar girgiza ahalin biyun, domin Waheedah (Mommy kamar yadda fadeelah ki kiranta)
macece mai kirki da iya zama da jama'a.

Ranar data yi kwana arba'in da rasuwa professor Dalhat Abdul-mutalib mai naira ya rasu shi ma.
wayyo Allah! Wadannan ahalin sun shiga kuncin mai yawan gaske, daga baya suka fawwalawa Allah komai.

Bayan shekaru biyar da mutuwar su professor Imran ya hadu da Shuhudah(Mommah) a wani business trip
daya je Ghana, wanda Mommah ta kasance yar asalin Ghanian ce, Daddy bai bata lokaci wurin bayyana wa
Mommah ko shi waye ba, da irin son ta daya kamu da shi, domin Daddy irin mutanen nan ne da basa iya
boye abinda ke ransu.
Mommah ma bata wani ja da yawa ba ta amince masa, kasancewar professor'n yayi mata hundred
percent, Kuma tun kafin taga fadeelah ta kamu da son ta kasancewar Daddy ya gaya mata yana da 'ya.

*BAYAN WASU SHEKARU*

Fadeelah ta zama budurwa mai tsananin kyawun gaske, a kananun shekarunta ta kammala masters d'inta,
inda Daddy ya dora ta kan wasu company dinsa, daga na Nigeria har na kasar waje, domin ya yarda da
kwazon ɗiyar tasa, hadi da ƙaifin tunanin ta, hakan ya sanya Daddy bai yi shakkar Sakar mata wasu
company'n ba, domin fadeelah daya take tamkar da dubu.......

*JAMEEL*

Jameel ya k'asance dan abokin Daddy wanda mahaifin sa ya kasance MINISTER OF FINANCE, tun a
zamanin kuruciya suke abota da Daddy, kasancewar hali ya zo daya, yasa abotar su ta daure.

Jameel shine ɗa daya ɗa MINISTER SA'ID ya mallaka, ya kuma dora son duniya ga dan sa.
Wata rana Daddy'n jameel tare da Jameel ɗin sun kawo wa Daddy ziyara, inda anan Jameel ya ga Fadeelah
ya kamu da sonta, bai boye ba a gaban Daddy'n ya sanar, kasancewar boko ta ratsa Daddy sam bai damu
ba, sai ma farincikin sa ɗaya nuna.

Sama-sama Fadeelah ke kula shi, domin sam bata kaunar sa dai-dai da kwayar zarra, darajar Daddy yake ci
take ma kulasa, suna da shekara daya tare da Jameel, yasan cewa Fadeelah na dauke da cutar koda, bai
boye mata ba yace, bazai iya auran mace mai lalurar ƙo wata tawaya ba. Duk da kasancewa Fadeelah bata
son shi amma taji ciwon maganar matuk'a.

Jameel ya bar kasar, sai dai yana biyayar al'amuran fadeelah.

A lokacin da FADEELAH ta hadu da gwarzon masoyinta Fadeel, tayi farinciki sosai domin irin namijin da
take fatan wa k'anta kenan, wanda zai so ta da tsakani da Allah ba dan dukiya ko wani kyale-kyalen Rayuwa
ba, kuma alhamdulillah ta samu.(sai dai daddy ya kawo cikas😩)

lokacin da jameel ya samu labarin an bawa Fadeelah koda, ba karamin farinciki yayi ba, domin yana sonta
dama, dalilin sa mara tushe ya sa ya barta, take ya dawo Nigeria cike da burin mallakar ta...

Labarin su Fadeelah a tak'aice kenan.

*** *** **

Ƴau kwana hudu kenan bata samun Fadeel a waƴa, faɗin tashin hanƙali, ɗamuwa, da faɗeela tayi going
through a kwanakin nan ɓata loƙaci ne.

A ƴau ta ƙuɗirci niƴƴar zuwa gidan su Fadeel, ɗomin duba halin ɗa ƴaƙe ciki, ɗomin a ƙwanaƙin nan ita
ƙadai ta san azabar da taƙe sha na rashin jin murƴar sa....
Wanka ta fada, ta murza jikin ta da tsad'add'en kana hada'dden shower gel di'nta na *pink sugar* bayan
yan mintuna ta fito sanye da bathrobe, lotion ta shafa kana ta zura *Robber to Cavalli* jeans trouser hadi
da riga daya sauko mata har kasan cinyarta fara, sai tayi rolling da madaidaicin mayafi, hills shoe ta sanya
kirar Dubai, kana ta fesa turaren *Balade sauvage*
Bata yi makeup ba, amma sosai tayi kyau duk da halin matsanancin damuwar da take ciki....

Yalwataccen farfajiyar su ta fito, ga security da body guards nata kai wa da komowa... Suna ganinta suka
nufe ta cikin girmamawa da niyyar bude mata mota. A hankali ta motsa tattausan labb'anta tace "ni kadai
zan fita, ku bani mukullin *Ferrari Sergio* red din can"

Cikin sauri aka tuko shi zuwa gabanta, kana driver ya fito, ya mika mata key, amsa tayi ta fada cikin motar
ta bata wuta ta bar gidan...

Daddy dake tsaye a saman part dinshi ya hango fitar fadeelah, cije lebe yayi ganin ta fita ita kadai, take
kuma zuciyar sa ta raya masa kila wajen Fadeel zata, cikin sauri ya kira personal security d'insa ya ce ya bi
masa bayan fadeelah ya ga inda ta nufa...

Isar Fadeelah kofar gidan su Fadeel yasa gabanta ya yanke ya fadi sak'amak'on ganin kofar gidan datse da
mukulli, dafe zuciyar ta tayi tace "ya Allah"

Hawaye suka cika idanunta, a hankali ta shiga takawa domin isa bakin kofar, domin wata farar takarda ta
take gani a jikin kwadon da aka rufe gidan dashi, bama ta ganin gaban ta sosai saboda ruwan hawaye daya
cika idanunta, a hankali ta kai hannu ta zaro takardan ta fara warwarewa.......

Please👏follow and vote you sister a manjahar wattpad


*@NoorEemaan*

Share fisabilillah
Comment
Vote

I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*

💝ƘƳAUTAR ƘOƊA💝
(It's all about love, scracife, hatred and destiny)

*Written by*
Noor eemaan

Wattpad
@NoorEemaan

ELEGANT ONLINE WRITER'S📚🖊

(Assalama alaykum, kamar yadda na fada a baya cewa wattpad dina yana ɗa matsala, domin nayi kuskure
wurin saka username din. Domin akwai masu cewa suna son following dina na basu Wattpad name dina,
alhamdulillah yanzu dai waccan tsahon acct din an goge shi, duk da mutanen sunyi following dina.
Ina rokon ku kada ku gajiya Ku sake following and voting dina dama wadanda basu taba yi ba, saboda Allah
da Manzon sa.
Ga sunan wattpad din👉 @NoorEemaan Nagode sosai da kauna da kuke nunawa novels dina💖 )

EDITING IS NOT ALLOWED❌

https://facebook.com/groups/943534712916776/
Masu amfani da facebook su yi join ta wanna link din.
Page 35-36

_Aminci Allah ya tabbata a gareki my Darling, nasan zaki samu takardan nan, ina da tabbacin haka, am so
sorry Darling ban tafi da niyyar bata ranki ba, na tafi ne kan wani dalili mai karfi, kuma duk dan mu samu
farinciki ne_

Kuka ta fashe dashi, kamar ta san abinda ke gaban rubutun tace "meyasa my one, Meyasa ka tafi, meyasa?
Wani dalili ne wanna!!!"

Sai data kai mintuna tana kukan, kana ta share hawayen ta ta cigaba da karanta takardan kamar haka.

_na tafi ne saboda na samu arzikin auren ki, domin ni talaka ne fakiri Daddy bazai bani auren ki ba, duk
inda arziki yake zan nemo da gumi na halak domin na mallake ki, in sha Allah zan cika wa Mahmah burinta,
zamu zama ma'auratan juna, abu daya nake so, ki rike min alkawari da amanar kanki. I swear matukar na
dawo na ga kin karya alkawari zan rasa raina, zan dawo gareki my Darling I love you muaaaaahh_

Nan ta durkusa tana kuka sosai, tamkar ranta zai fita, ta jima tana kuka hadi da sumbata kana ta mika
rungume da takardan, motar ta ta fada kana ta bata wuta....

Ikon Allah kadai ne ya kai ta gida, bayan ta faka motar a parking lot ta nufi hanyar bangaren ta, taji muryar
Daddy ya kwala Mata kira, a sanyaye ta nufe shi, gabanta na fadu'wa ganin irin kallon daya jefa mata, yana
tsaye bakin kofar part d'insa, hannun sa goye a bayan sa, ganin ta nufo shi, hakan yasa ya shiga falon sa
yana jiran isowar ta...

***

"Daga ina kike?" Ya jefo mata tambayar daidai shigowar ta kayataccen falon sa, haka zalika hakan yayi
daidai juyowa da yayi yana mai fuskantar ta.
Cikin diriricewa ta kasa magana, sai bakin ta dake rawa, domin kallon da Daddy ke jefa mata ne ya sanyata
cikin wanna halin. Sosai rauni ya bayyana a fusk'ar ta, domin bata saba da wanna yanayin ba, bata saba
ganin Daddy'nta haka ba. Bata san wani abu daure fusk'a, ko tsawa, da fada ba. Amma yau Daddy dake
matuk'ar son ta ne ke mata haƙa?

A fili tace "Daddy na fita ne...."

"Zuwa ina?" Ya katse ta a kausashe.

Cikin dauriya, domin kuka na daf da kubce mata tace "na....na...je...gi"

"Kinje kangon wanna talaka fakirin ko? Domin sam wanna ba gida bane" Daddy ya katse ta, hadi da mata
nuni da screen din tsad'add'iyar wayar sa mai dauke da hoton Fadeelah rike da wasikan Fadeel tana
karantawa...

Gabanta ne ya bada dam! Tayaya haka ta faru, ya akayi Daddy yasan gidan su Fadeel taje? Ta tambayi
k'anta, a fili tace

"Am sorry Dad" tace tana barin wajen da gudu yayinda ta fashe da kuka mai ban tausayi.

jikin Daddy yayi sanyi, domin yaga ta rame, komai cikin daurewa yake yinsa, amma baya jin zai iya barin ta
samu abinda take so wato Fadeel.

*** *** *** ***

Haka rayuwa ta cigaba da mikawa, kullum Fadeelah na cikin kuka hadi da damuwa, gabadaya Daddy hadi
da mommah basa jin dadi, amma iya part dinsu domin grandma da sauran yan'uwan basu san abinda ke
faruwa ba, hakika fadeelah ce farinciki su...
Mommah ce kullum sai tazo part di'n ta tana rarrashen ta hadi da gaya mata kalami masu dadi, domin bata
fiye zuwa part din su ba, tana kuma karfafa Mata guiwar cewa ta bar wa Allah komai kana ta cigaba da
add'ua matuk'ar Fadeel mijinta ne Zata mallakeshi komai rintsi, tana kuma mata nasihar kada ta bijirewa
wa Daddy, domin babu kyau bijirewa umarnin mahaifi, komai lalacewar sa kuwa, sai dai idan abinda yake
so ka bi umarnin din, ya kasance haram a musulunci. Da wadanda kalaman Fadeelah ke samun nutsuwa,
sannan ta dage yanzun da tashin dare, muradin ta yanzu bai fi taga fadeel ya dawo gareta ba, har ila yau
bata fasa kiran sa ba, sai dai a kashe take.

Sosai zafaffan kauna Fadeel din ke ratsa ta, bata da abinda ke debe mata kewa kamar hotunan sa dana
Mommah dake kafe a bangon dakin.

Kamar yau tana kwance tayi zurfi a tunani yayinda idanun ta ke kafe a zanen hoton su dake bango, amma
ba hotunan take kallo ba, tunani kawai take.

gaba daya zaman estate din ma ya ishe ta, ga Daddy kuma yace ta dan dakata da zuwa company, domin a
tunanin sa zasu dinga haduwa da fadeel.

Daddy dake tsaye a bakin kofa ya tura dakin ya shiga, sak'amak'on yayi knocking yaji Shiru... Inda yaga ta
kura ido nan ya kalla shima, sai yanzu ya lura ashe matashin nan na zanen hoton nan shine bakin talakan
nan ya aiyana a ransa, take kuma jikin sa yaga masa cewa matar dake gefensa itace Mahmah.

Dauke idanun sa yayi, ya maida kan fadeelah hadi da cewa "my princess!" A razane ta dago jin muryar
Daddy, domin sam bata ji shigowar sa ba.

"Daddy!" Tace cikin raunin murya.

Wani iri yaji a jikinsa, yana kara jin tsanar Fadeel din a ransa, ace 'yarsa da gatan ta da komai, amma kan
wani talaka can ta sanya damuwa a ranta.

Zama yayi kan gado yana rike hannun ta, a dan tausashe yace "my princess meyasa kike sanya kanki cikin
damuwa uhm?" Ya kamata kin san cewa ni mahaifi ki ne mai so da kaunar ki, ke yarinya ce karama baki san
yaudara da butulcin namiji ba, wasu mussaman ma talaka, Jameel shine yafi dacewa dake, yanzu ki shirya
Jameel yazo yana part din baki na farko, yace ya kira wayar ki a kashe, maza tashi my princess " ya fada
yana bubbuga bayanta kana cikin lallashi...
"Okay Daddy" tace cikin k'arfin hali, nasihar Mommah na amsa kuwa a kunnen ta.

Ba k'aramin dadi professor Imran mai naira yaji ba, a tunanin sa, ta fara cire Fadeel din a ranta.

A fili ya furta "that's my princess" hadi da bata K'yak'yyawar sumbata a kumatu kana ya bar dakin.

A sanyaye ta mike, sai yanzu hawayen da suka cika idanunta suka zubo, share su ta yi, dama sanye take da
wata roba gown na company *Balenciaga* wardrobe dinta na zallan glass ta zuge, wata haɗɗaɗiƴar
kimono ash color da dan veil din shi ta zaro domin ya rufe siraicinta, saɓoda rigar jiƙinta ta fidda duk wata
sura ta jikinta, Saka kimonon tayi, ta yafa veil din ta bar dakin...

Zaune yake a hada'dden falon baki na farko, ya dora kafa daya kan daya, sanye yake da suit blue color na
company *dolce and gabbana* daya yi matuk'ar haska farar fatar sa, kan nan ya sha gyara hadi da askin
zamani, farin Bluetooth na makale a kunnensa, komai na jikinsa tsad'add'en ne, a kallo daya mutum zai
fahimci hakan.

Sosai take jin haushin jameel d'in, sam baya burgeta ko daya, amma Saboda sanin darajar sallama yasa tayi
kasa_kasa, glass cup mai dauke da campaign dake hannun sa ya dire kan hada'ɗɗen glass table dake gaban
sa, kana ya amsa sallamar fusk'ar sa dauke da murmushi....

Daure fusk'a tayi, ta zauna nesa da shi, k'anta a kasa tana murza zoben azurfa hannun ta, wanda fadeel ya
bata ranar birthday dinta.

"My wife to be" Jameel ya fada cikin wani salo, Yana jefan ta ɗa wani shu'umin kallo.

Wani zallan haushin sa taji, jin ya kira ta da sunan matar shi, ta sani cewa Jameel din ba laifi domin za a iya
saka shi cikin sahun maza masu cikar halitta, amma farar fatar sa ce ta taimaka wurin fidda kyaun sa,
domin babu wani kyau a fusk'ar sa.

Wani mugun muninsa take gani, domin Fadeel yafi shi duk wani abu, kama daga kyau, nagarta, kyaun hali
da sauran su..

"Ok you okay babe?" ya sake tambayarta Yana mikewa izuwa gareta.

"Yeah!" ta amsa a tak'aice, domin muryar sa kadai ma bata son ji.


Daidai gabanta ya tsugunna, ya kamo lallausan hannun ta, saurin fisgewa tayi tana jefan sa da harara.

Bai damu ba, sai ma wani murmushi daya saki kana cikin hausar shi da ɓai gama kwari ɓa yace "haba babe
meyasa kike behaving like a local girl, gaki wayayya amma, bakya abin wayayyu, you know ina sonki, kuma
ni zan aure ki so menene a ciki uhm!" Ya karasa yana kawo labbansa bakinta da niyyar kissing di'n ta.

Wani tura tayi masa kana ta mike a fusace tace "if you think aikata abinda Allah ya haramta shine wayewa,
toh kayi kuskure, don't ever in your life ka sake ko da kawo yatsa jikina ne" Fadeelah ta karasa tana sauke
numfashi, domin bata saba daga murya ba, tasan cewa Jameel manemin mata ne, amma bata yi tunanin
abin nasa ya kai haka ba, take kuma tunanin Fadeel ya fado mata, idanunta suka ciko da kwalla, domin bai
taba kawo hannu jikinta ba, duk zaman da suke ƴi a waje daya always, ƙo da su biyu ƙadai ne kuwa.

Hakika tasan soyaayyar fadeel dinta tsaftataciyya ce da babu algus. Tana cikin wanna tunanin taji saukar
muryar sa.

"It's fine, amma idan na aure ki baki isa ki min Katanga da taba ko yin duk abinda nake so dake ba" ya
karasa a dan zafaffe domin yaji haushin yanda ta hana shi morar jikinta, ɗomin duk matan da yake tarayya
dasu basu taba hana shi ba....

Wani kallon ta watsa masa kana ta bar part din, ba tare da ta sake ƙula shi ba.

Sosai Jameel yaji haushin yanda fadeelah ta bar shi zaune, abinda babu macen data taba yi masa haka "me
kika dauki kanki?" Ƴa fada a bayyana idanunsa kan kofar data bi ta fita, ƙamar zai samu amsa.

Mikewa yayi shima ya bar falon bakin, inda masu tsaron sa suke ya nufa, fadawa yayi mota, suka bar gidan
a guje
Da tunanin dole ya samu Daddy'n sa akan yana son ayi aurensu da Fadeelah nan kusa, domin yaga tana
kokarin jefa shi wani hali.......✍️

Hakuri dai😩👏
kunyar ku ma nake ji fans, musamman yan group din kyautar koda da Papi ne! Kumin afuwa ban Baku
update jiya kamar yadda na ce ba, nasan kun sha jira nayi busy da yawa ne jiyan.
'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*

💝ƘƳAUTAR ƘOƊA💝
(it's all about love, scracife, hatred and destiny)

*Written by*
Noor eemaan

*Wattpad*
@NoorEemaan

ELEGANT ONLINE WRITER'S 📚🖊

EDITING IS NOT ALLOWED❌

(Don't forget to vote and follow me at Wattpad @NoorEemaan)

https://facebook.com/groups/943534712916776/
Masu amfani da facebook su yi join ta wanna link din.
Page 37-38

(Kila kuga typing error🤒)

Sosai motocin Jameel suke sharara guɗu kan kwalta, haƙan yasa cikin kasa da mintuna ashirin suka isa
giɗansu, buɗe masa mota akayi, bayan an faka motocin, cikin isa da gadara ya fito ya nufi bangaren daƴa
san zai samu Daddy'nsa.

Zaune ya tarar da iƴaƴensa manne da juna suna kallon a tashar *zeeworld*, ganin tilon dansu ya sanya
suka faɗaɗa murmushin su, ba tare ɗa ko sallama ba, ya zauna tsakiƴar su, sam iƴaƴen nasa basu damu ba,
sai ma bashi ɗuƙƙanin hankalin su suka yi hadi da tambaƴarsa me yake damunsa.

Cikin sangarta irin ta ƴaƴan wasu masu gidan rana yace "Mom! Dad! ina son a ɗaura mana aure da
fadeelah cikin satin nan"

Kafin Daddy'n jameel yayi magana, mummy'nsa tace "what! haɓa son sanin ƙanka ne cewa ƙoɗa a ƴau
ƙake son a daura maka auren da mata ɗari kasan muna arziƙin yin haka, amma bikin ka ne fa, bikin dan mu
abin son mu, kuma a yi shi cikin week dinan impossible, dole muyi biki da kaf cikin Nigeria da wajenta su
san da bikin dan minister" Mummy'n Jameel ta fada cikin alfahari da isa irin su ta wasu masu gidan rana.

Alhaji Sa'id da ya bi matar sa da kallon murmushi ganin yadda take magana tana fari hadi girgiza yace "my
son gaskiya ne abinda mummy'n ka ta fada, kuma fadeelah taka ce domin mun gama magana da professor
Imran, in sha Allah zan tafi Qatar amma da zaran na dawo za a yi bikin ku, domin bazai yu bikin dana ayi shi
bana kasar nan ba, tafiya Qatar ta zame min dole, amma da zaran na dawo komai za a yi shi fiye da yanda
kake so my son kaji ko?"

"Cikin gamsuwa da maganar iyayen sa ya jinjina kai, so da sha'awar fadeelah ne suka rufe idanun sa, har
yake so ayi bikin cikin gaggawa, domin shi kanshi zai so bikin sa ya zagaye duniya, ya zamana duk inda
mutum ya shiga aji zancen bikin ake tattaunawa akai, da wanna tunanin ya hakura.
*** *** ***

Zaune fadeelah take a bedroom d'in Mommah, yayin da ta dora k'anta akan kafadar Mommah, babu
abinda ke fita a fuskar ta sai zallan damuwa, Mommah dake shafa k'anta tace " sweetheart har yanzu dai
wayar Fadeel din baya shiga?"

An tabo mata inda yake mata kaikaiyi, kwallan da suka taru a oily eyes dinta ta yi saurin share, kana tace
"har yanzu bana samun sa Mommah, ya jefa ni cikin wani hali, meye laifina Mommah? Kila ma ya daina
sona" ta karasa tana rushewa da kuka hadi da rungume Mommah gam-gam a jikin ta.

Cikin tausayawa Mommah ta shiga bubbuga bayan fadeelah, hakika soyaayyar su tazo da wani irin salo mai
wuyar fassaruwa, amma zanen kaddarar su ce tazo da hakan, a tausashe kana cikin murya rarrashi tace
"stop crying fadeelah, ki bar komai a hannun Allah, ki cigaba da add'ua da karatun qur'ani domin shi
maganin damuwa da duk wata masifa, sannan ina da yakinin cewa duk in da Fadeel yake a halin yanzu kina
makale a ransa, daina damuwa domin baya maganin komai, gaba d'aya kin sanja, kin rame kamar ba diyata
ba yar gayu da, oya tashi ki je ki shirya mu fita outing" Mommah ta karasa tana mikar da ita tsaye.

Bata musa ba, ta nufi bangaren ta, toilet ta fada ta sakar wa k'anta ruwan dumi hadi da murzawa lallausan
fatar ta da shower gel na *Versace Pour Homme Dylan* ta d'auki mintuna talatin a bathroom kana ta fito
daure da pink towel da wani daure a k'anta, lotion mai k'amshi ta murza kana ta fito da wasu had'add'un
English wears na company *Valentino* riga ce mai digon hannu daya sauka har saman cinyar ta, a gaban
rigar zuwa kasa akwai botira(buttons) , sai wando dogon rigar mai bud'ed'en kasa duka yellow ne, wani
hill cover shoe ta saka baki, tayi parking gashin ta a tsakiya da yellow ribbon, sai mayafin rolling irin na
larabawa ta yana a k'anta shima baki, handbag karami baki mai walwali ta dauka sai glass golden color mai
dan fadi ta sanya, hannunta daure da agogo na kamfanin *Gucci* shima baki, sai perfume mai k'amshin
vanilla ta fesa, babu ko digon makeup a fusk'ar ta, amma tayi wani irin sihirtaccen kyawun mai tafiya da
hankalin dukkanin wani lafiyayyen namiji, cikin takun nutsuwa ta bar dakin bayan ta gama kallon zanen
hoton su fadeel da Mahmah kana ta bar dakin idanunta cike da kwalla sai dai bata bari ya zubo ba.
Zaune ta tarar da Mommah cikin shigar tsad'add'en leshi wanda kudinsa ya kai million daya da rabi, anyi
mata dinkin boubou irin na manyan mata, sosai tayi kyau itama ta sha make-up domin Mommah ba dai iya
daukar wanka ba, sannan ta na son makeup a fusk'a.

"Wow! My sweetheart kinyi kyau sosai" sai kuma ta jefa mata hararan wasa tace "ohh ni Shuhudah naga
ranar da zaki yi makeup"

Murmushi fadeelah ta saki kana tace "Mommah Allah bana son makeup, fusk'a ta nauyi take min"

Dariya ma ta bawa Mommah Wai fuskar ta d'auki yake, hannun ta ta kama suka fice, a jere motocin
bodyguard din fadeelah shida suke, Yayinda a tsakiyan shidan akwai wata rantsatsiyyar mota black color
kirar *Pagani huayra Bc roadster wanda kudinsa ya kai £3,764000*

Suna kokarin shiga motar, bodyguards din Mommah suka karaso wajen suna tambayar ta ko su dauko
mota? Tace a'a ana fadeelah zasu fita, cikin girmamawa suka ce toh, hadi da musu fatan dawowa lafiya,
bayan motocin sun fita, har sun hau babban kwalta Mommah ta kalleta tace "sweetheart akwai wani
wajen shakatawa da kike sha'awar mu je?"

"Yes! Mommah ina son muje VICTORIA ISLAND, RSVP RESTAURANT"

Dan kallonta Mommah tayi kana tace "akwai wajen shakatawa da suka fi RSVP restaurant amma meyasa
kika zabe shi?"

Lumshe ido tayi kana ta bude, kwalla taf Cikin su tace "Mommah ina son wajen, domin a nan na fara
haduwa da fadeel"

Jinjina kai Mommah tayi fusk'arta dauke da murmushi, Yayin da kasan zuciyar ta tausayin fadeelah ne fall
cikinsa, ko wani bawa ta tasa kaddara, Hakika ciwon so ciwo ne mai zafin gaske, musamman idan masoyan
sun kasance masu tsananin son juna kuma an samu matsala daga bangaren iyaye, misali ga fadeelah bata
da matsalan komai tun tana karama har ila yau babu abinda ta rasa a duniya, Sai dai Allah ya jarrabe ta da
son Fadeel wanda ya kasance talaka, ita kam tana yi wa fadeelah sha'awar auren Fadeel domin yaron ya
kwanta mata, ajiyar zuciya ta sauke tana musu fatan mallakar juna, matuk'ar akwai alkhairi a tarrayar
su ......

Bayan sun isa RSVP restaurant suka yi ordering abin sha kana Mommah ta shiga debe mata kewa, har karfe
biyar suna wajen kana suka komo gida....

Da isar su estate suka hango Daddy zaune a farfajiyar gidan rike da news paper Yayinda idanunsa ke sanye
da glass, lokaci zuwa lokaci yana dan kurban tsad'add'en campaign na mixed fruit.

Ganin su Mommah ya sanya shi rufe news paper yana murmushi, basarwa Mommah tayi kamar bata gan
shi ba ta nufi part d'in ta, murmushi professor yayi yasan cewa matar tasa tana da hakuri, amma wanna
karon tayi fushi da yawa, domin tun ranar da fadeel yazo estate din har yau basa shiga harkan juna.
fadeelah kuwa ta nufi wajen shi, domin ta gaishe shi...

Ku min haku'ri wallahi abubuwa sun min yawa kwana nan, wanna ma tsatsaye nayi muku shi domin
faranta ranku my lovely fans.💖

Thank you for reading kyautar koda💞

#Share
#Comment
#Vote
I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*

💝KƳAUTAR ƘOƊA💝

(It's all about love, scracife, hatred and destiny)

*Wattpad*
@NoorEemaan

ELEGANT ONLINE WRITER'S📚🖊

EDITING IS NOT ALLOWED❌

https://facebook.com/groups/943534712916776/
Masu amfani da facebook su yi join ta wanna link din.

Page 39-40
Ƙujerar ɗaƙe kallon wanda Yake Zaune ta zauna, kana tace
"Daddy barka da hutawa"

"Yawwa my princess, ina ƙu ka je ne ke da Mommah'n taki"

Murmushi tayi tace "mun fita outing ne"

"Yayi kyau, naji dadin ganin K'yak'yyawar 'yata cikin walwalwla"

Wani murmushin ta kara yi tana wasa da zoben hannunta, haka dai fadeelah tayi ƙoƙarin sake wa da Daddy
suka dan taba hira kana ta koma part di'n ta....

★★★

*JAMEEL*

Kwance yake a part dinshi, tare da wata K'yak'yyawar budurwa suna aikata laifi mai girma gaske ( *zina*
Allah ya tsare imanin mu) babu abinda kake ji sai saukar numfashin su, gabadaya sun birkita gadon.....

*Bayan yan mintuna*

Kwance suke manne da juna, Yayinda wanna budurwar ke sharar hawaye, kana cikin kuka ta fara cewa "my
Jameel me na rage ka dashi? Da har zaka auri wata, lokacin dana samu labarin 'yar gidan professor zaka
aura na shiga tashin hankali sosai, idan ƙudi da arziki ne nima kasan ba baya nake ba, dan Allah kada ka
barni, ina sonka sosai my Jameel, ka sani kai ka fara sani na a 'ya mace, amma meyasa zaka barni dan
Allah!!!!"

Cije leben sa masu kyau da taushi ƴayi, domin leben sa shine ƙawai abun burgewa da k'yau a fusk'ar sa, a
ransa yace ba zaki gane ba, duk da bansan yaya take ba, amma ina da yakinin ita din ta daban ce....
(Kalubale garemu yanmmata, shi namjin idan ya gama da rayuwar ki, sai ya je ya nemo wacce take
kamilaliyya mai daraja ya aura, Allah ya tsare imanin mu da mutuncin mu)
A fili yace " haba my haulat, kin san ina son ki nima, kuma auren Fadeelah ba shi ke nufin zamu rabu ba,
zamu ƙasance tare, Saboda haka daina mun asarar hawayen ki" ya fada cikin tsantsar murƴar yaudara yana
share mata hawaye....

Luf tayi a jikin shi tana sauke ajiyar zuciya, tsakanin ta da Allah take kaunar Jameel, haka dai ya cigaba da
kwantar mata da hankali, har suka sake aiƙata masha'ar su, sai karfe biyar na yamma ta bar gidan, har
bakin motar ta ya raka ta, kana ta tafi, ko dar babu, domin iyayen sa sun san duk abinda ke faruwa, domin
acewar su wayewa ce, hakan yasa Jameel ke cin karan sa babu babbaka, domin babu mai hanashi....

Sai da motar haulat ta gama barin haraban gidan, ya dauke idanun sa hadi da tabe baki kana ya nufi
bangaren mummy'n sa...

****** ****** *****

Bangaren Fadeelah kuwa har yanzu damuwa na nan daram a ranta, domin kullum cikin kuka da damuwa
take, saidai tana matuk'ar kokari wurin boye damuwar ta ta, sai dai kallon d'aya mutum zai mata ya fahimci
tana da damuwa mai tarin yawa....

Kullum tunani da damuwar ta Fadeel, ina yake? Wani hali yake ciki? Kullum tunanin ta kenan, kamar yau
tsaye take gaban hoton zanen Fadeel da ke bango tana zubar da ƙwalla masu zafin gask'e hadi da radaddi...

"My one, please ka dawo gareni, I have missed you a lot, can't you see am dying Saɓoɗa rashin ka" shiru
tayi tana sauke shesheka kana ta ɗora da cewa

"Ka barni cikin kewa da zafin son ka, dama kana da zuciya da juriyar yin nesa dani? Hakika ina cikin ciwo
mai yawan gaske dan Allah ka dawo! Ka dawo gareni ina buk'atar ka, dan Allah Fadeel!!!".

Ta karasa tana zubewa kasa, Yayinda hawayen ke zuba a fusk'ar ta kamar famfo...
Haka ta jima tana kuka kana ta shiga hada'dden bathroom dinta domin wanke fusk'ar ta.... Da wani mini
towel ta fito fari tana tsane ruwan fusk'ar ta.... Wayar ta ce ta fara ringing, a sanyaye ta kai hannu ta dauka,
ganin number'n mai kiran ne yasa ranta ya bace, duk da bata yi saving number shi ba, amma ta shaida
number'n...

Kamar ta kashe wayar, sai kuma ta barta ta cigaba da ringing kusan karo na biyar

Daga bangaren Jameel kuwa tsaki yayi ganin ya kira bata daga ba, shi da yanmmata ke rubibi amma yau shi
ke kiran wayar fadeelah har sau biyar tayi ignoring,
"meta dauki kanta ne?" Ya fada a bayyane.

Shi kam yasan bai yi mata laifi komai ba, sannan ya cika namiji toh meyasa bazata so shi ba?

Mikewa yayi ya nufi bangaren Daddy'n sa, yana fatan ya same shi domin ya gaya masa abinda ke ransa...

Ya kuwa same shi tsaye yana kokarin kafa hula. Murmushi minister sa'id ya saki ganin tilon dan sa.

"Lafiya dai my boy naga fuskar ka haka?"

Kara shan kunu Jameel yayi kana yace "Dad! A gaskiya ina son ayi mana engagement da Fadeelah, zuwa
lokacin da zaka dawo daga kasar Qatar din, hankali na zai fi kwanciya"

"Ohhhh! My son rigima, shiƙenan abinɗa ƙake so ayi?"

"Yes! Dad" Jameel ya amsa.

"Ok kwantar da hankalin ka, zan fita meeting, daga nan zan je wajen professor d'in, domin muyi maganar
dashi ko?"...
Dan murmushi ya saki na farinciki, burin shi ya mallaki fadeelah domin ya kwaɗaitu da kyawunta da kuma
Surar ta, ya kuma san ba zata taba amincewa dashi, ba aure ba....

A fili kuwa yace "thanks Dad" ya fada yana bashi sumbata a goshi hadi da rungume shi, kana ya fita yana
jin shi sakayau, domin hakan zai kara kwantar masa da hankali cewa Fadeelah zata zama mallakin shi.....

★★

Zaune minister Sa'id da professor Imran suke a garden din estate din shi, ga kwalaben tsad'add'un
Champaign da ke gaban su, gyaran murya alhaji Sa'id yayi yace "wato danka fa Jameel ya matsa lallai ayi
masa engagement da ƴata Fadeelah, domin ina son zuwa Qatar kan maganar nan da muka tattauna, da
zaran na dawo sai ayi bikin nasu" Alhaji Sa'id ya karasa yana kallon Daddy.

Dariya irin nasu na manya wanda boko da waye ta gama ratsa wa yayi kana yace "babu laifi ai, hakan yayi,
in sha Allah zamu yi fixing date".

Cikin jin dadi Alhaji Sa'id ya bawa Daddy hannu suka yi musabaha, haka dai suka cigaba da hiran su irin ta
abokai....

*WASHEGARI*

Washegari bayan ma'aikatan gidan sun gama hada breakfast sun jera a part di'n Mommah domin mafi
yawan lokuta anan suke breakfast, Daddy ne ya shigo sanye da wata shadda tsad'add'e sai maiko take,
Mommah da ke zaune a parlour ta dago k'anta, ganin shine sai ta dauke ƙai, murya a daure ta gaishe shi,
da murmushi a fuskar sa ya amsa, kana ya d'ora da tambayar ina Fadeelah, bata bashi amsa ba ta daga
tsadaddiyar wayarta ta dora a ƙunne hadi da cewa

"hello! sweetheart breakfast is ready, muna jiran ki"

"Mommah am ok, bana jin yunwa" daga dayan ɓangaren fadeelah ta karasa cikin damuwa, sanyin muryar,
hadi da shagwa'ba, har wani bata fuska take.
"I said ki zo muyi having breakfast, me kika ci da zaki ce you're ok?" Mommah na gama fadin haka ta yanke
kiran.

Professor da ya zuba wa Mommah ido baya ko kiftawa ya lumshe su, hakika yana matuk'ar son matar shi,
yana kuma son su dawo kamar da, amma ya rasa me zai ce mata, babban abin da yasa ta samu muhalli a
zuciyar sa shine tsananin son da kauna da take yiwa tilon 'yar sa.....

Daga bangaren Fadeelah kuwa, a hankali ta mike tana bata fusk'a, sanye take da wasu riga da wanɗo masu
taushi ash color, na company *NIKE* hular rigar ta rufe dogon gashinta ɗashi, kana ta tsaya gaban zanen
Fadeel, sumba mai tsayi ta manna masa a labb'ansa, kana ta maida duban ta ga zanen Mahmah, tuna
mahmah yasa hawaye zuba daga idanunta, Sumba itama ta manna mata a goshi da kumatun ta, kana ta
bar dakin tana daidaita nutsuwar ta hadi da share hawayen ta.

Elizabeth ta tarar tana gyaran hada'dde kuma yalwataccen falon ta, murmushin ƙarfin hali ta sakar wa
Elizabeth d'in, martani Elizabeth ta mayar mata kana cikin turanci tace

"ma'am good morning"

"Morning Elizabeth" fadeelah ta amsa kana ta bar part din.

Da kallo Elizabeth ta bi fadeelah ita dai


Allah ya d'ora mata kaunar fadeelah, ba kuma komai ya janyo hakan ba, sai rashin wulakanta mutane da
bata yi, tana ƙuma mata fatan Allah ya yaye mata damuwar ta, domin ta fahimci tana ɗa damuwa.
A fili kana a hanƙali tace

"ohh wanna rayuwar, kowa da kalar ƙaɗɗarar shi"

******

"Good morning Dad!"


" Good morning Mommah"
Fadeelah ta fada a tare, tana zama gefen su, amsawa suka yi fuskar ko wannen su dauke da murmushi...

Mommah ce ta fara mikewa ta isa dinning table din, sannan Daddy da Fadeelah suka Mike su ma...

A nutse suke jin abincin su, baka jin karan komai sai na spoons, fork, da knife. Sun yi nisa a cin abinci
amma, banda fadeelah da ke tsakura kadan-kadan, daman ita ba gwanar cin abinci bace, yanzu ƙuma
rashin cin abincin ta ya sake raguwa fiye dana da.

Gyaran murya Daddy yayi, idanunsa kan na mommah yace "Nan da jibi in sha Allah za a yi baikon
*FADEELAH DA JAMEEL* sannan bayan aminina Sa'id ya dawo daga Qatar za ayi bikin nasu, wanda ina jin
zai iya daukan shekaru d'aya ko wata goma kafin ya dawo".

Wani kwarewa fadeelah tayi, Yayinda k'irjinta ke bugawa da k'arfin gaske, cikin sauri daga Daddy har
Mommah suke kokarin sanya mata glass cup mai dauke da ruwa a baki, Daddy'n ne yayi nasaran bata,
sosai ta sha ruwan tana sauke numfashi Yayinda ta ji dakin na juya mata....

Sosai itama Mommah taji ba dadi, amma ya zasu yi kaddarar ce ta zo da hakan, kallon fadeelah tayi ɗa
hawaye ke daf da zuba a idanunta, girgiza mata kai tayi kana tayi mata alama da ido kan kar tayi magana
sannan kada ta bari Daddy ya fahimci halin da take ciki.....

_karku manta wanna novel din ba sabo bane, zaku iya samun complete din sa a Wattpad_😘

Manage pls

Afuwan habibtie's in sha Allah daga yanzu ranakun posting sun dawo sau uku a sati, domin wallahi busy da
nake ciki ya sanya hakan, bana da lokaci kwata kwata wallahi, ku tayani add'ua kan abinda nake yi yanzu,
Allah ya bani sa'a.
ina fatan zaku min haku'ri... Ranakun posting din sune kamar haka monday, Thursday, Sunday. Amma
matuk'ar na samu lokaci a sauran ranakun da ban ambata ba, toh zaku iya ganin update, amma kusa a
ranku cewa ranakun dana ambata wato litinin, alhamsi, da lahadi suna ranakun da tabbas zaku ga posting.
Ngd sosai da kauna da kuke nunawa books dina, ku sani a addu'oi'n ku👏 Noor na muku sahihiyar kauna💞

#Share
#Comment
#Vote

I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*

💝ƘƳAUTAR ƘOƊA💝
(It's all about love, scracife, hatred and destiny)

*First edition*

*Wattpad*
@NoorEemaan

ELEGANT ONLINE WRITER'S📚🖊


EDITING IS NOT ALLOWED❌

https://facebook.com/groups/943534712916776/
Masu amfani da facebook su yi join ta wanna link din.

*(Assalama alaykum ya jama'a ina gaida ku my fans a ko ina kuke a duniya da Wanda na sani da wanna ban
sani ba. Na fara posting din novel dina na farko mai suna RAYUWAR FAHEEMAH nasan wasu sun fara
karantawa, wasu kuma sun karanta... dalilin daya sa na sake reposting din labarin Saboda abubuwan daya
kunsa, Wanda zan so kowa ya karanta ya amfana, sannan a lokacin da nake littafin mijin Ammina ne sila
nayi posting dinshi, sai dai rashin lokaci yasa nake turowa da yawa wani har readmore goma, fiye da haka
ma nayi posting a lokaci d'aya, ma'ana complete din labarin na dawo dashi page 10 gaba daya kana a
kwana goma. Hakan yasa bakowa ya karanta ba, Saboda yana da yawa sosai, shiyasa yanzu na sake
reposting din shi, a yanda yake page by page. A cikin labarin akwai fadakarwa, wa'azantarwa, tsantsar
mugunta, soyaayya mai tsafta da babu algus a ciki, da dai sauran su. Dan haka ku biyo ni comment dinku
kadai nake bukata already ina da complete din novel din)*

Page 41-42

..........jinjina wa Mommah kai fadeelah tayi tana kokarin rarrashin k'anta.


Daddy ya kalli Fadeelah zai yi mata magana wayar sa ta fara ringing, hakan yasa ya mike ya fita ba tare da
yayi maganan ba, kasancewar yana da appointments da wani business partner din shi....

Fadeelah na ganin fitar Daddy ta fashe da kuka mai ban tausayi, taso wa Mommah tayi ta dawo kujerar
dake kusa da na fadeelah'n. cikin rarrashin ta shiga yi mata da kalamai masu kwantar da hankali, hadi da
nuna mata amfani da tasirin bin umarnin mahaifi....

******** ******** *******

*RANAR BAIKO*

Zaune fadeelah take fuskar ta ba walwala gaban wata kwarariyyar make up artist tana tsantsara mata
kwalliya...

Fadeelah kuwa daurewa damuwar ta take Saboda kada mutane su fuskanta, a yau daya kasance ranar
baikon ta da Jameel sai ta rasa k'arfin guiwar cewa ɗa saƙa ran Fadeel dinta zai dawo gareta....
A wani had'add'en hall da a masu hannu da shunin ma ba kowa zai iya kama wajen ba saboda tsananin
tsadar wajen...

Fadin kyau da haduwar wajen bata baki ne, haka zalika yawan mutanen da suka hallacin wajen bazai fadu
ba, kai kace bikin ake ba baiko ba.

Sosai fadeelah tayi kokari wurin jure damuwar ta, Yayinda Jameel dake gefen ta sai faman shige mata
yake....

Bata nuna komai ba, sai murmushi yake wanda na k'arfin hali ne. Domin sosai Mommah ta ja mata kunne
kan kada ta Nuna komai domin ƙaɗa jama'a su fahimta

Sai takwas na dare suka tashi daga taron, bayan anyi fixing date din biki shekara daya, wanda a dalilin
tafiyar minister Sa'id din yasa a kasa lokaci mai tsayi har haka.

Bangaren Daddy kuwa ya dan samu farinciki da nutsuwar zuci, ganin cewa anyi baikon Domin a tunanin sa
idan fadeelah ta auri Jameel din zata manta da fadeel din.

Domin sarai yana lura da walwalar ta ya ragu sosai. Amma ina bazai iya bata abinda take so ba, wato auren
wanna baƙin talaka fakiri a Cewar sa.

***** ****** ******

Fitowar ta daga wanka kenan sanye da bathrobe Yayinda k'anta ke sanye da *shower cap* lotion ta murza
kadan a farar fatar ta, wani tsad'add'en oil perfume ta shafa a jikinta, kana ta taje k'anta hadi haɗi da yi
masa oiling ta yi parking din shi ta gefe.
Closet dinta na zallan glass ta zuge ta ciro wasu had'add'un English wears na company *Armani* gown ne
mai tsukakken sama Yayinda kasan ya bud'e sosai white color.

Hada'dd'en Falon ta ta fito ta zauna tunani Fadeel dinta makale a ranta, tuno wasu lokuta da suka yi having
a baya yasa hawaye hadi da murmushi suka subuce mata a lok'aci daya...

"Shikenan my one ka tafi kenan, shikenan bazan kara ganin ka ba, shikenan bazamu mallaki juna ba,
shiƙenan bazamu cikawa Mahmah burinta ba...?" A fili take wadanan kalaman hawaye masu zafin gask'e
na zubo wa daga cikin su....

Wayar ta dake kan cinyar ta ya dauki kara, hawaye fusk'ar ta ta sharen ta, kana ta kai idanun ta kan fuskar
wayar, number'n jameel ta gani, wani bata rai tayi Yayinda zafin da zuciyar ta ke mata ya karu.

Kamar tayi rejecting call din, sai kuma tayi picking ba tare da tayi magana ba...

"Ina part din baki" abinda taji jameel din ya fada kenan.

Ta kai mintuna goma a zaune kana ta mike cikin dauriya ta yafa veil kana ta fice cikin sanyin murya jiki
domin sam bata da kasala ko daya a jikin ta.

Bayan yan mintuna ta isa part din, domin akwai dan nisa tsakanin part di'n ta da part din baki...

Kamar kullum yana Hakim ce kan daya daga cikin had'add'un kujerun falon. Kallon daya zaka masa ka
fahimci cewa shi din dan nasu kudin gaske ne.

Da wani mayen kallo yake binta dashi, Yayinda murmushi ke shimfud'e a fusk'ar sa. Sanin darajar Sallama
yasa fadeelah tayi masa, ya amsa still idanun sa kafe a kanta, mikewa Yayi ya isa gabanta daf da ita kamar
zai shige mata jiki, dan jan baya tayi tana daure fuska.
Cak ya tsaya, kana ya dan bata fusk'a yana cewa "come on! Babe kamar ba wayayya ba, miye a ciki, just
want to hug you.
kin manta an mana baiko yanzu?".

Hararar da bata san ta iya ba ta jefa masa kana tace " please and please na roke ka, bana so! Na sha gaya
maka bana son irin wanna wayewar mudin shine wayewa, dan anyi mana baiko ba shi ƙe nufin cewa kana
da right din taba wani sashe na jikina ba" ta karasa cikin fada, dama ranta a bace yake.

"Oh! Babe ni kam kina bani mamaki, wasu talakawan ma yan kauye suna da wayewa kan wanna fanin ɓare
ke, meye a ciki? Bafa wani abu zan yi miki ba, fine naji zan hakura har muyi aure, amma ki bari even kiss da
hug (sumbata da runguma) ki bari nayi miki mana meye a ciki uhm" ya karasa cikin sigar lallashi, hakika so
da sha'awar fadeelah na cin sa sosai, ta kuma ki bashi damar ya dan kashe kishiruwar sa ko kadan ne...

"Ba wani abu a ciki kace? Ko dai kana take sani ne wanda haƙan zunubi ne babba, kasan abu ba kyau still
kana aikata shi, Toh ni bazan iya ba, domin wanna zunubi ne, kai ma ina mai baka shawara ka daina aikata
hakan"

Wani murmushi ya saki yana shafa gemunsa, bawai maganganun ta sun shige shi bane, domin shi bai
yarɗa cewa akwai zunubi cikin kiss da hug ba. Shiru yayi na mintuna biyu kana yace "OK fine, ki zo mu fita
outing ko?"

"No Thanks! Bana bukata, if you don't mind I will take my leave now, Excuse me" tace bayan ta jefa shi da
wani kallo ta bar part din gabadaya....

Da kallo jameel ya bita, duk da yaji ba dadi yanda ta fice, bayan yau yazo da niyyar zai dan kashe
k'ishiruwar sa, a tunanin sa tunda anyi musu baiko zata dinga amince da shi.(kaluɓale ga yammata, ɓa wai
dan anyi muƙu baiƙo ko sa rana da saurayi ki amince ya dinga taba ki ba, haƙan zunubi ne, kuma taɓɓas
bazai ga darajar ki ba, Allah ya sa mudace ya tsare imaninmu, ya bamu ikon koyi da hali irin na fadeelah)

Bayan fadeelah ta koma part dinta, sosai ta sha k'uk'a, ɗomin tsaf ta fahimci Jameel din, Abinda fadeel
dinta bai taba gwada yi mata ba kenan. Ta ya ya ma zata iya son wani da namiji bayan Fadeel? Mutumin da
ke mata tsabtattaciyar kauna da babu algus, hakika samun irin su fadeel dinta a duniya yana da wahala.
Haka ta wuni kuka hadi da tunani barkatai.
*BAYAN WATANIN TAKWAS*

Haka rayuwa ta cigaba da juyawa, Wasu na farinciki, wasu na walwala, sai dai babu farinciki mai dorewa a
rayuwar ko wani bawa, dole Akwai ranar da mutum baya samun farinciki, ko ya tsinci kan shi a yanayi mara
ɗaɗi.

Ta bangaren Fadeelah kuwa babu abinda ya Sanja daga damuwar da take ciki sai ma abinda ya karu
musamman tuno cewa kwanakin aurenta da Jameel yana ta gab ɗa ciƙa, domin sauran watanin hudu
yanzu haka, ga har yanzu babu wani labari game da fadeel din, number'n sa ma baya zuwa, ta kuma ki
hakura da kira duk da tasan cewa number'n bata shiga.....

Gaba daya komai ya gama fice mata a rai musamman da babu gwarzon masoyinta Fadeel a kusa da ita......

Manage please🙏 a tsaye ina ciƙin tafiya nayi muku wanna din ba yawa.

In sha Allah ranar lahadi ma zan sake muku sabon update kamar yanda nace.

Thank for reading my novel


Kyautar koda

NOOREEMAAN
07082281566

Share fisabilillah

Comment
Vote

I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*

💝ƘƳAUTAR ƘOƊA💝
(It's all about love, scracife, hatred and destiny)

*First edition*

*WATTPAD*
@NoorEemaan

ELEGANT ONLINE WRITER'S📚🖊

EDITING IS NOT ALLOWED❌

https://facebook.com/groups/943534712916776/
Masu amfani da facebook su yi join ta wanna link din.

_ina ta ganin karin followers a Wattpad, which I'm very happy, jazakallahu khair masu following, wandanda
basu yi ba, Please do follow me on Wattpad, @NoorEemaan thanks.👍🥰

Page 43-44

Misalin ƙarfe takwas na safe ne, Fadeelah na kwance a dakin ta, kewa da zafaffan soyaayyar gwarzon
masoyinta Fadeel ke nuƙurƙusanta, ƴayinda hawaye masu zafin gasƙe ke zuba a cikin idanuna ta....
Take tunanin zuwa gidan su fadeel ya zo ranta, tana fatan iɗan ta je ta ganshi a bud'e, ta kuma samu fadeel
ɗinta a cikin gidan...

Cikin wani kuzari daya zo mata ta mike ta fada bathroom bata wani jima ba ta fito, lotion kadai ta murza
kana ta sanya wani palazzo trouser pink da riga black, wani hada'dd'en jacket kimono ta sanya kana ta rufe
kanta da wani siririn mayafi, tsad'add'un takalmi da agogo ta sanya, body spray mai sanyin k'amshi ta fesa
kana ta bar dakin......

Tana fitowa ta ga bodyguards dinta tsaye, ganinta ya sanya suka yi nufe ta, hada'ɗɗen mota silver color ta
nufa, waiwayewa tayi ta kallesu kana tace
"am karku damu yanzu zan dawo" A yanɗa ta ɗaure tayi magana zaka yi zaton ba taɗa ɗamuwar ƙomai.

Cikin girmamawa daya daga cikin su yace "please ma'am kiyi hakuri ki barmu muyi aikin mu, domin idan
boss ya samu labari ke kadai kika fita, toh zamu shiga matsala wanda zai iya kaimu ga rasa aikin mu"

Tausayin su taji ya kamata, ajiyar zuciya ta sauke, domin Daddy baya gari, amma taɓɓas zai san ita kadai ta
fita.

"Ok fine muje" Fadeelah tace musu haka, domin bazata so a dalilin ta su rasa aiƙin su ɓa.

"Mun gode ma'am" suka ce fuskar su dauke da murmushi.

Itama murmushi tayi kana ta fada motar bayan daya daga cikin su ya bud'e mata, a jere reras kamar ƙullum
motocin suka bar gidan...

*******

Abinda ya sanya gabanta matsanancin bugawa bayan isar su kofar gida shine ganin kofar gidan a kulle still
da kwado kamar waccen karon, hawaye masu zafi ta share, sosai ta daure bata yi kuka ba domin guards
dinta dake wajen....
Mota ta fada ta umarce su da cewa su tafi gida, haka ta dinga kallon titi tamkar mai ƙirgin motocin da suƙe
falfala gudu kan titi, sai dai sam ba motocin take kallo ba, tunani mai zurfi ta fada....

Bayan sun isa gida ta nufi part di'n Mommah domin a nan kadai zata samu nutsuwa, domin jin kanta take
tamkar zai rabe gida biyu Saboda tsananin ciwo....

Jiƙin Mommah ta faɗa ta shiga rera kuka sosai gwanin tausayi, buɓɓuga bayanta Mommah keyi ba tare da
tace komai ba, domin ta riga ta san damuwar Fadeelah'n baya taba wuce na Fadeel ɗinta, har yamma tana
part din, Mommah taki barinta ta tafi part din ta saɓoɗa ƙaɗa damuwar tayi mata yawa.

****** ***** ***** *****

Haka ta cigaba da jinyar zuciyar ta tana kokari matuk'a gurin yin tawwakali hadi da yarda da kaddarar daya
shigo rayuwar ta, add'ua kam kullum sai tayi shi kan Allah ya bayyana mata Fadeel domin bazata iya
rayuwar aure da Jameel ba, baza ta iya ba, domin shi mutum ne da bai da kyakyyawan halayya da duk
macen kwarai zata so......

*BAYAN WATA HUDU*

A Yau minister Sa'id ya d'ira a Murtala international airport ɗaƙe Lagos, gabadaya airport din cike yake da
mutane masu hannu da shuni wadan da suka zo taryar sa, cikin su kuwa akwai Jameel da Mummy'n sa sai
wasu yan yan'uwansa na jiki, bayan yan gaishe gaishe daya wakana tsakanin mutanen da suka zo taran sa,
da yi masa barka da dawowa ya fada daya daga cikin motocin dake jere reras, haka zalika Jameel da
Mummy duk cikin motar ta minister ya shiga suma suka shiga inda sosai jameel da Mummy suka nuna jin
dadin ganin sa, bare ma Jameel daya san cewa tabbas yana gab da mallakar Fadeelah tunda dai shekaran
dayan da Daddy yace ya cika gashi har ya dawo.....
Bayan duk yan sannu da zuwa su tafi, Jameel ya samu Daddy da maganar auran Fadeelah dariya irin nasu
na manya minister sa'id yayi yace "my son kenan, zumudi yayi maka yawa, toh ina sane da kai, kuma ko
sati biyu bazaka kara ba, zaka mallaki fadeelah"...

Cikin farinciki daya kasa boyuwa a fuskar Jameel ya rungume dad yace " wow! Dad thank you so much "

Har hangowa kansa yake yana making love da Fadeelah bayan anyi daurin auren su, domin ba kadan ba
yake azabtuwa da matsanancin sha'awar fadeelah'n. shekara dayan nan daƴa wuce tamkar shekaru goma
haka suka huce a idanun sa, amma yanzu sakayau yake jin sa zai samu abinda yake so, domin ba shi da aufi
kan maganar Daddy'n sa...

Bangaren Fadeelah kuwa ta shiga tashin hankali mara iyaka, a ranar da Daddy'n jameel ya dawo daga
Qatar ta gani an hasko a plasma, sosai ta sake shiga tashin hankali domin ba makawa za a yi bikin su da
Jameel, ga Fadeel shiru har yanzu kusan shekara daya da watanin kenan.

Ta rame domin kallo daya mutum zai Mata zai hango zunzurutun damuwa a tare da ita, ko abinci bata iya
kaiwa bakin ta, kullum Mommah cikin rarrashi da nasiha take mata.

*Bayan kwana uku*

Yau kwana uku da dawowar Daddy'n jameel, hakan yayi daidai da ranar da yan gidan su jameel zasu kowa
lefe, gaba daya gidan ya cika da alhalin professor Imran mai naira har na Adamawa, ko ina security ne
domin yanzu an karo su, Saboda biki da za a gudanar, sosai Mommah ta daure tana shiga sha'anin biki
domin kada yan uwan Daddy sun fahimci bata son auran, domin har ga ranta bata son hadin Jameel da
Fadeelah sosai take tausayin halin kuncin da damuwar da fadeelah'n ke ciki...

Misalin karfe sha biyun rana wasu tsad'add'un motoci guda goma sha biyu suka shigo cikin estate din
professor Imran mai naira, tabbas duk wanda yaga motocin nan yasan ba k'ananun kudi aka narka wurin
mallakan su ba, daya ɓayan daya mutanen ciki suka fara fitowa wanda zallan mata ne, sai drivers din
motocin da suka kasance maza, nan mazan suka shiga fito da lefen ɗaga motocin wanda ya k'asance
akwati hamsin ne cif masu kyau da tsari...
Nan aka yi ta shigar da akwatun nan tareda taimakon ma'aikatan gidan. Bayan sun gama shigar da
akwatunan ciki ne sannan matan suka shiga ciki, nan aka yi gaishe-gaishe kana su Mommah suka gabatar
masu da snacks, abinci, da drink's iri daban -daban wanda aka tanada domin su kadai...

Bayan duk sunyi abinda ya kamata aka sanya sati biyu masu zuwa, kana suka tafi cike da mutun ta juna,
gabadaya yan'uwan professor da ma wadanda suka karbi lefe da ɗai sauran su babu abinda suke banda
yaba lefen, duk da kasancewar su masu hannu da shuni amma tabbas ba ko wani mai kudi bane zai iya
akwati har guda hamsin ba...

Bangaren Fadeelah kuwa kuka ta shiga rera wa sosai mai taba zuciya, domin taji hayaniyan yan kawo lefen,
duk da bata fito ɓa, kenan da gaske zata tabbata Matar Jameel, ba muradin ta Fadeel ɓa? Kenan da gaske
ta rasa masoyinta na gaske, mai so da kaunar ta domin Allah? Cikin karaji hadi da fitar hayyaci, a fili tace "
Fadeeeeeeeeeeeeeel please ka dawo gareni, kada ka bari Jameel ya aureni, ka dawo mu mallaki juna, ka
dawo mu cikawa Mahmah burinta, dan Allah ka dawoooo!" Ta karasa cikin kuka mai matuk'ar taba
zuciya....

Bayan awa d'aya da tafiyar yan kawo lefe, wasu had'add'un motoci guda takwas daga gidan minister suka
shigo cikin gida, dauke da lefe, bayan sun gama parking motocin aka shiga fito da lefen wanɗa ya k'asance
akwati talatin ne, suka fara shigar wa cikin gidan....

Kallon-kallo aka shiga shiga yi tsakanin yan gidan su jameel da su Mommah, zuciyar ko wanne da tunani da
yake, ba komai ya janyo hakan ba sai ganin akwatuna had'add'u guda hamsin dake zube a falon.

Kasa hakuri daya daga cikin yan'uwan professor Imran tayi tace

"bayin Allah shin ba ɗazu ƙuƙa kawo lefe ba?, ya muka ga an kawo wasu akwatunan?"

Sosai kan dangin minister Sa'id ya daure, wata tsohuwa daga cikin su tace "ai mu ma abinda ya daure
mana kai kenan, domin ba mu muka kawo wadanccan lefen ba" tsohuwar ta fada tana nuna akwatuna
d'azu....

Nan fa kai ya sake daurewa, aka shiga rudu, domin a tunanin su Mommah lefen da aka kawo dazu daga
gidan su jameel ne, amma sai aka samu tsabanin haka....
To kenan su waye suka kawo lefe?

Nan take Grandma ta fidda tsadaddiyar wayar ta ta bugawa professor Imran mai naira kira....

*_Afuwan habibtie's nasan kuna kokari wurin jirana, taɓɓas nasan hakan, ina godiya sosai da kauna, rashin
lokacin yasa bakwa jina kamar da, ma'ana bana posting k'ullum kamar da, da sannu zamu gama labarin,
yanzu kyautar koda ya soma_*🔥🔥🔥

Nooreemaan
07082281566

Share
Comment
Vote

I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*

💝ƘƳAUTAR ƘOƊA💝
(It's all about love, scracife, hatred and destiny)

*First edition*

*Wattpad*
@NoorEemaan
ELEGANT ONLINE WRITER'S📚🖊

EDITING IS NOT ALLOWED❌

*Ina matuk'ar jinjina kokarin ki wurin yi min comment mai yawa kullum, therefore I dedicated is page to
you my love(DARMA)*

https://facebook.com/groups/943534712916776/
Masu amfani da facebook su yi join ta wanna link din.

#Suprise

Page 45-46

Cikin daurewar kai Grandma tace "Imran where are you? Ka zo yanzu, there is something fishy here"

Professor Imran dake tare da minister Sa'id a wani had'add'en wurin shakatawa ga Champaign da snacks
zube a gabansu suna hira cikin wayewa irin ta aminan juna.
Cikin mamaki yace "mummy(Grandma) lafiya dai? toh gani nan yanzu, right away"

Idan sa na kan wayar yace "mummy na nema na yanzu, bara naje ma karasa maganar some other time"
cewar Daddy.

"Toh fa, Allah yasa lafiya, ko dai mu tafi tare ne?" Cewar minister.

"No karka damu bari naje, zamu yi waya dai" Daddy ya fada yana nufar motocin sa.....
Ƙasa ɗa mintuna hamsin suka iso ƙatafaran estate din. Bayan ya shiga falon ya tarar da jama'a masu yawan
gaske, ciki harda yan'uwan minister domin yayi musu farin sani.

Cikin mamaki ganin fuskokin su ba walwalwla yace "what's happening here? Mummy lafiya?"

"Ina fa lafiya Imran, kalli ka ga" Grandma ta fada tana nuna masa tarin akwatunan da aka kawo da farko, da
ma wanda yan gidan su minister suka kawo.

Take ya kai idanun sa kan aƙwatunan yana jinjina yawan su, a tunanin sa duka Jameel ne ya kawo, da dan
murmushi dauke a fusk'ar sa yace "mummy miye a ciki? I guess lefen princess ne" Daddy ya fada.

Girgiza kai Grandma tayi tace "Nooo! you're wrong Imran, wait bari na tambayeka maza biyu kaƙe son
auran Fadeelah'n ne banda labari?"

Cikin zallan mamaki Daddy yace "maza biyu kuma? Tayaya zan yi hakan Mummy please ki yi min bayani?"

"ɓasan ta ƴa ƴa zanyi maka bayani ba, domin kaina ya kulle, amma kalli can, kaga wadancan akwatunan
guda hamsin ɗin? toh wasu mata ne suka k'awo shi, bayan awa ɓiƴu ɓa jimawa dangin minister suka kawo
akwatunan talatin gasu nan" ta fada tana nuna masa.

Kana ta dora da cewa "mun dauka lefen farko daga gidan su minister aka k'awo, sanin kanka ne bawai mun
yiwa dangin abokin naka farin sani ba, hakan yasa muka dauka lefen farko da aka k'awo daga bangaren su
ne, tambayar nan shine WAYE YA KAWO LEFEN FARKO???
Take gabansa ya fadi, Kan shi ya kulle, to kenan waye ya kawo lefen farko? Ya budi baki zai yi magana, wata
mata cikin yan'uwa minister data kasance kanwar sa tace "mu fa baza a mayar damu k'ananun mutane ba
a toh, ina aka taba haka? Dama kuna sane so kuke ku tozar ta mu, toh bazai yu ba, I repeat bazai yu ba!" Ta
karasaà cikin daga murya da amon sa ke fidda zallan halin fushin da take ciki.

Nan hayaniya ya ƙaure tsakanin dangin biyun, sai dai cikin wayewa suka jifan juna da kalamai marasa dadi,
musamman dangina minister da suka dau fushi ada yawa, Mommah dake kallon su ta saki boyayyen ajiyar
zuciya, domin ba a'akadan ba taji dadin lefen wafarkon da aka kawo, sai dai murnan ta ragagge ne tunda
bata san lefen farkon daga hannun waye ya fito ba?

Nan dangin minister suka gama fadin maganganun su marasa dadi kana suka tafi rai a bace, abu dai bai yi
kyawun gani ba, ko akwatunan basu dauka ba.

Da kyar Daddy ya ja kafafun sa ya zube kan kujera, ya ma rasa tunanin yi, domin Kan sa ya kulle, ya ma rasa
a wani yanayi ya ke ciki yanzu haka, maganar Grandma ce ta dawo dashi tunanin sa.

"My Son Imran, bari na kira wayar ita fadeelah'n tazo muji ko akwai wanda ta bawa ɗama kawo lefe ba
tare da mun sani ba"

Bata jira amsar sa ba ta danna wa fadeelah....


Kwance take hawaƴe masu dumin gaske na zubo mata, kuka take sosai gwanin tausayi, kukan take domin
tasan burinta, muradi, hadi da fatan ta na son auren Fadeel dinta ya kau, tunda gashi yan gidansu Jameel
sun kawo lefe .

Ɗomin a lokacin ta iddar da sallah azahar kenan, ta ji shigowar dagin Jameel, har ta leke ta hango su daga
nesa ana sauke aƙwatunan da take ganin su kamar ledoji Saboda rashin son wanda akwatunan ya fito daga
hannun sa, duk k'yau da haduwar su kuwa.

Ringing din wayar ta ne ya dawo da ita nutsuwar ta, sunan *Grandma* ta gani yana yawo a jikin screen
din, hakan nan ta ji gabanta ya bada ras! Har dafa saitin zuciyar ta tayi tace "ya Allah!" Kana a sanyaye ta
latsa Kore hadi da d'aura wa kan kunnenta, cikin matsanancin dauriya, sai dai duk da haka muryar ta rawa
yake tace "Hello Grandma"

Grandma ƙuwa yau ko grand-daughter babu tace "fadeelah maza kazo yanzu your presence is needed
urgently" tana fadin haka ta katse kiran.

Da kallo ta bi wayar tana jin gabanta na tsananta bugu, saƙamaƙon jin murƴar Grandma cikin wani yanayi.

mikewa tayi a sanyaye ta nufi bathroom, wanke fusk'ar ta tayi kana ta dauki wani madaidaicin towel ta
goge fusk'ar ta, kana ta fito.

Duk da Grandma bata gaya mata a wani part din take ba, amma hakan nan taji jikinta ya bata taje part din
Mommah.

Cikin sanyin murya tayi sallama, wani faɗuwar gaban ne ya sake risketa sak'amak'on ganin tarin lefe zube a
kasan tiles, Yayinda tashin hankali ya saƙe bayyana karara a fusk'ar ta, ta tabbata cewa da doctor Mahfouz
zai auna BP dinta a yanzu, da tabbas sai jinin ta ƴa hau fiye da tunanin mai tunani, domin ganin lefen ƙusa
da ita ya fi ƙomai ɗaga hankalin ta.
Ganin yan falon gabadaya ita suke kallo hakan ya kara mata faɗuwar gaba.

Cikin dauriya ta karasa kusa da Mommah ta zauna, kana kasa² tace "Grandma gani"

Fuskantar ta sosai Grandma tayi tace "Fadeelah shin bayan Jameel akwai wanda ya kike so har ya riga su
jameel din kawo lefe? ko ƙuwa" Grandma ta faɗa tana nuna lefen.

Gaban ta ne ya sake bada dam! Cikin rawar murya tace "A'a" tana kokarin controlling hawayen dake daf da
zuba a fusk'ar ta.

Domin idan bata ce a'a ba, me zata ce? Bayan bata san a wani duniya Fadeel yake ba, bare tace shine, ba
ma wanna ba, ina Fadeel din ta zai iya kawo lefen da ko jameel din bai kawo irin sa ba?.

Cikin wani daurewan kai wata mata cikin ahalin professor tace "anya mutanen da suka kawo lefe da farko
ba batan kai suka yi ba?"

Nan fa hayaniya ya sake kaurewa wasu na cewa ta yaya zasu yi batan kai a irin wanna babban estate din da
kowa ya san dashi... Da dai sauran maganganu.

Fadeelah dai kanta na kasa cikin daurewar kai, ta wani bangaren ƙuma tana jin sanyi a ranta, sai dai
murnan ta ragagge ne domin bata da tabbas din za a fasa bikin ta da Jameel.
Tun da suka fara magana sai yanzu Mommah dake bubbuga bayan fadeelah tace "Akwai number'n daya
daga cikin matar da suka kawo lefen da na karba, ina tunanin ta haka ne komai zai warware"

Cikin zakuwa Daddy yace "please do call her now"

Bai samu amsa ba, sai ma wayar ta data fidda ta danna wa matar kira, bai wani jima da ringing ba ta dauka

"Assalama alaykum" cewar Mommah.

A tausashe wanna matar tace


" wa'alaikumu salam" ɗama na san zaki kira" matar tace tana sakin murmushi.

Dan zaro ido Mommah tayi tace "kin san ɗama zan kira? Kenan ba batan kai kuka yi ba, kamar yanda muƙe
tunani?"

Wani murmushi da har sautin sa ya fito matar ta sake yi tace "ko daya, am sure gidan da muka kawo lefen
FADEELAH gidan professor Imran mai naira ne, karki damu magabatan danmu zai so in Sha Allah domin ya
gana daku"

Cikin wani sabon rudani mommah tace "Toh wayeku? Sannan waye dan naku? meye sunan sa? Domin an
saƴar da ranar auren fadeelah ɗa dan gidan minister Sa......"
Da murmushi matar ta sake katse mommah tace "duk muna da masaniyar hakan, sannan sanin waye mu
da danmu zaku ji in Sha Allah, kiyi haku'ri da zaran iyayen sa maza sun zo zaku ji komai, sai anjima" kit
matar ta kashe wayar.

Da kallo Mommah tabi wayar kamar zata gano matar a Cikin sa, kana ta bi su da Daddy da kallo da suma
suka kafe ta da idanu domin tana da tabbacin sun ji abinda matar tace a hands free ta saƙawayar.

"Toh su waye su? Da uɓan me suke takama da basu fada ba yanzu?" Grandma tace cikin isa da fushi.

Shiru kowa yayi domin sun rasa abin cewa kasancewar kowa kansa ya kulle, Daddy shima ya zama
speechless ya rasa abin cewa, bama zai iya fassara yanayi da take ciki ba, amma bazai ce komai ba, sai
magabatan yaron nan sun zo kamar yadda matar tace.

Grandma ta koma part di'n ta, Daddy ma ya fita, haka sauran yan'uwan suka fara fita har falon ya rage
daga Mommah, sai fadeelah.

Dago ta Mommah tayi wanda zuwa lokacin hawayen ya gama wanke kyakyyawar fuskar ta daya yi fayau,
cikn tausayin ta Mommah tace "sweetheart ya isa haka! Kina jina?" Jinina kai fadeelah tayi alamun "eh".

" Good! Nasan 'yata bata karya, ki gayamin shin babu wanda kika yi dashi zai kawo lefe, duk da da kamar
wuya, amma kaina ya d'aure dole ne nayi miki wanna tamɓaƴar"

K'uk'a fadeelah ta rushe dashi tace "I swear, Allah Mommah babu wanda nake tare dashi, Fadeel ya tafi ya
bar ni, ya manta dani, ban san waye wanna ba, ban san waye shi ba, basan Shi ɓa".... Ta karasa tana
fadawa jikin Mommah, ta ci gaba da kuka, Mommah bata hana ta ba, ta kai awa daya tana kuka sosai kana
bacci ya dauke ta tana sauke shesheka duk da a cikin bacci ne, shafa bayanta Mommah keyi cikin tsananin
tausayin ta....

Haka duka ahalin professor Imran mai naira suka kwana cikin wani yanayi da suka kasa fassara shi,
musamman wadanda abin ya shafa, su basa murna, sannan basa bakin ciki gasu nan dai, yanayin bazai
fassaru ba...

★★★

*WASHEGARI*

LAGOS
*IKEJA GRA*

Hada'dden kuma babban gida ne, kai wanna ya wuce gida ko estate sai dai a kira shi da unguwa guda.
Girman sa, tsayin sa hadi da fadi'n sa bazai faɗu ɓa. Gini ne na zamani wanda mutum zai yi tunanin a turai
ne.

Fadin sassa da yawan sashe na gidan bazai fadu ba, Saboda yawan sa, waje da cikin gidan security's ne
masu kirar k'arfi cikin blue da white uniform, ma'aikatan gidan da yawan su bazai fadu ba, ko wanna
sanye da unform ja da fari.

*A wani sashe na gidan*

Kwance yake sambal sanye da dogon wando kirar Dolce and gabbana Yayinda bakin fatar sa ke ta shining
da glowing wanda kallo daya mutum zai masa ya fahimci ba k'ananun kudi yake narkawa wurin gyaran
fatar sa ba. Ga kwantance gashi dake kwance luf kuf a k'irjinsa, Yayinda kansa mai dan tauri irin na yan
Africa ke ta shining da kyalli, ya sha wani askin zamani daya fara fidda zallan kyawun sa.

Cikin matsanancin kewar ta, da zunzurutun sonta dake dawainiyya dashi kusan shekara daya da watanin
kenan.
Lumshe kyawawan idanun sa masu haske da kyau yayi, kana ya bud'e su,,, ya sauke kan zanen hoton ta
dake kafe a ko wani bango na dakin.....

Share

Comment

Vote

Noor Eemaan
07082281566

I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*

💝ƘƳAUTAR ƘOƊA💝
(It's all about love, scracife, hatred and destiny)

*WATTPAD*
@NoorEemaan

ELEGANT ONLINE WRITER'S📚🖊

EDITING IS NOT ALLOWED❌

https://facebook.com/groups/943534712916776/
Masu amfani da facebook su yi join ta wanna link din.

Page 47-48

Ɗan cije leɓen sa yayi, yana jin matsanancin kewar ta, na cigaba da ratsa jijiya, soƙa, da jinin jiƙin sa.

A hankali ya sauke black shining legs d'insa kasa ya mike, cikin tafiya mai cike da aji da kasaita ya karasa
gaban hoton ta ya kura mata idanun sa masu cike da tsantsar kaunar ta, a hankali ya dan ranƙwafo tamk'ar
ita ɗin ce a gaban sa ya bawa zanen wani hot kiss mai tafiya da hankali.

A hankali ya motsa bakin sa can kasan makoshi ya furta "I miss you badly!"

Zura hannuwan sa yayi cikin aljihu yana bin ko wani hoton ta da kallo ɗake manne a bangon. Ƴa jima sosai
yana kallon hoton kana ya nufi had'add'en bathroom d'in sa, ba dan ya gaji da kallon su ba...

Cikin nutsuwa ya sauke wandonsa kasa, ya jefa a washing machine kana ya nufi gaban shower ya kunna,
ruwan ya shiga dukan naked black shinning body d'insa, domin sam baya ra'ayin shiga jaku'zzie (jaccuzi)
yau.
Lumshe kyawawan idanun sa yayi yana jin dadin saukar ruwan a jikin sa, duk da ruwan sanyi ne, ga kuma
lokacin da sanyi a gari, amma sam bai damu ba, domin ruwan sanyi ba bakon sa bane...

Hada'dd'en bar soap ya fara murzawa a baki Kuma lafiyayyen fatar sa, domin bai fiye son shower gel ba a
yawan lokuta, ya dauki 30minutes yana wankan kana ya fito da bathrobe fari kal yayin da ruwa ke diga a
sumar sa mai yawa....

Lotion daya dace da black skin d'insa ya shafa a fatar sa, kana ya fito da boxer hadi da white singlet ya
sanya, perfume na company'n *black gem* mai suna *TRINITI MEN POUR HOMME* ya fesa kana ya
sanya wasu had'add'un English wears, wando jeans baki, sai wata riga daya kama shi red color ya sanya, sai
canvass black irin na maza duka dai na company'n *NIKE* .
Agogon *luxury brand* sliver color ya sanya, oiling din kan shi yayi ya taje. kana ya fesa hair spray.
Wani stylish sunglass brown color ya sanya a fuskar sa, komai cikin nutsuwa yake yi, tamkar yanda ya
kasance mai nutsuwar, sai dai a yanxu komai nasa ya Sanja ya zama cikin class yake yin sa.

Had'add'un wayoyin sa ya dauka kana ya fita, nan ma'aikatan sa suka shiga gaishe shi, a nutse kana a
mutunci yake amsa musu, cikin sauri motocin sa dake fake reras guda goma sha ɓiƴu ya nufi daya ɗaga ciƙi,
kafin ma ya karaso sun bud'e masa, shiga yayi kana bodyguard's ɗin sa suka fada sauran motocin. Sun yi
tafiya mai tsayi kana suka iso babban gate din da aka jima da wangala musu shi....

Still dai akwai tafiya mai tsayi kafin suka iso babban titi, kamar yadda rashin magana ya zama dabi'a a gare
shi yanzu, ya bud'e baki yace

"Abuja gidan alhajina muka nufa" ya fada a tak'aice.

"Noted sir!"

Driver ya fada cikin girmamawa, nan ya dauki hanyar, hakan yasa sauran motocin fahimtar cewa gidan
alhajin zasu...

Sunyi tafiya mai nisa, domin tsakanin Lagos da abuja akwai 'yar tafiya hakan yasa basu isa da wuri ba... Ba
kuma ya son hawa jirgi a Cewar sa.

Fadin kyau da tsaruwar gida alhajin bata lokaci ne, sanin waye shi da matsayin sa a gidan hakan yasa suka
wangale masa gate din. Take motocin sa mai dauke da sunan *FFM* a ɓaƴa suka shiga faka motocin su a
haraɓan giɗan kasancewar ba jimawa zasu yi ba.

Bud'e masa motar suka yi ya sauke kafar sa, kana ya fito gaba daya, Cikin tafiyar kasaita hadi da tsantsar
aji ya nufi general falo, inda anan yake sammanin alhajin yake.
Ya kuwa same su tare da yar tsohuwar matar sa, sai dai kasancewa suna da dukiya da su kansu basu san
hadadin sa ba ya boye shekarun su matuka.

Murmushi alhajin ya sakar masa haka ma matar sa, shima martani ya mayar su, Cikin tsokana kamar yadda
alhajin ke kiran sa yace "the great younger billionaire, har ka iso?"

Kujerar dake kallon nasu ya zauna kana ya dan rissina a zaunen cikin girmamawa yace "barka da rana
alhajina, barka da rana hajiya"

Hade baki suka yi wurin amsawa kana alhajin yace "yanzu zamu tafi lagos din, amma ta flight zamu,
already a can zamu hadu da su alhaji Aminu a airport din, ka sanar da guards dinka suyi gaba, ko angon
fadeelah?" Murmushi mai taushi ya saki yana jin farinciki mara mitsaltuwa da sunan karshen da alhajin
nasa ya kira sa.

Take ya fidda tsadaddiyar wayar sa ƙirar *Vertu Signature Cobra* ya sanar wa shugaban bodyguard's d'insa
cewa suyi gaba....

Take ma'aikatan gidan suka cika masa gaban sa da kayan snacks dana marmari, bai wani ci da yawa ba ya
ture, domin shi ba ma'abocin yawan cin abinci bane dama can.

Bayan awan sa ɓiƴu da zuwa gidan. Alhajin ya ƙoma part din sa ya sanja kaya zuwa shadda tsaɗaɗɗiƴa,
dinkin babban riga kasance cewa dama da kananun kaya yake zaune tun ɗazu.

Nan suka yi sallama da hajiya tayi musu fatan dawowa lafiya kana suka fita. Motocin alhajin ne suka kai su
airport babu jimawa jirgin su ya daga zuwa lagos...
Bayan sun sauka, nan suka tarar da alhaji Aminu da alhaji Abdallah. Take suka shige motocin sa wanda
already bodyguards din sun isa lagos ɗin.

Haka ya lumshe idanun sa Cikin tunani barkatai ɗa suƙa cika kwanyar sa, sai dai yana jin farinciki domin
yana ganin cewa zai mallaki muradin ransa soon.

Basu dauki tsawon lok'aci ba suka iso estate din professor Imran mai naira. Nan take motocin sukayi
parking a tsakiyar haraban gidan...

Har suka iso bai bud'e idanunsa ba, sai dai tsayuwar motocin ya tabbatar masa da cewa sun iso kenan.

A hankali ya ware idanun sa da suka fara Sanja launi. Tuno a yanda, da ƙuma yanayin daya bar gidan a
wasu loƙuta ɗaƴa shuɗe ya sanya kwalla ciko idanun sa, a hank'ali ya fito yana jin faduwar gaba na
abubuwa da dama, amma sam bazaka fahimci hakan ba Saboda jarumtar sa....

Wajen su alhajin ya karasa ya tsaya, ganin cewa babu dacewa su shiga kai tsaye hakan yasa alhajin kiran
wani security dake ta shawagi a farfajiyar gidan, Cikin girmamawa security ya karaso domin yaga
wadannan mutanen ba kananun mutane bane.

"Am... Is professor Imran around? I mean your boss" Alhajin yafada domin yaga siffar sa irin ta yare ce
wanda da alama ma baya jin Hausa...

"Yes! Yes Sir" security'n ya fada cike da girmamawa.

"Ok please sanar dashi yana da baki urgent"

"Ok sir" security ya amsawa alhajin.

Babu jimawa ya fito yace professor ya ce su shigo...


Gabadaya suka nufi inda suka ga security'n ya fito, hada'dd'en falon Daddy suka zauna suna jiran fitowar
sa, domin falon ba kowa suka same shi...

Bayan mintuna biyar takun takalmin daddy ya fara kusanto su, hakan yasa yaji gaban sa ya yanke, sai dai ba
kamar baya ba, domin tuna irin abinda ya faru a irin wanna yanayin ne ya dan daga hankalinsa, sai dai
kansa na kasa bai dago ba, hakan kuma mutum bazai fahimci yanayin sa ba ɗomin idanun sa na sanye da
sunglass ne.

Dan waro ido Daddy yayi a lokacin da yayi arba da Alhaji Sufyan Rufa'i mutumin da ko ina ake fadin arzikin
sa, yana da uban dukiya mai ban mamaki, sai dai bai d'aura wa kansa girman kai ko wulakanta mutum ba,
ya dan yi mamaki ainun ganin sa Cikin estate din nasa, kuma a falon sa....

Karasa yayi ya mika wa alhajin Sufyan Rufa'i hannu cike da girmamawa, haka ma sauran aminan sa suka
gaisa.

gaishe shi wanna saurayin yayi, Daddy ya amsa a sake cikin kulawa.

Nan Daddy ya zauna su ka dan taba hira irin na manyan mutane, kana alhaji Sufyan ya yi gyaran murya
yana kallon Daddy yace "hakika Imran na san munyi wani abu da bai dace ba, duk da ta wasu bangarorin
iɗan aka duba babu laifi, amma a gaskiya munyi nema cikin nema ne wanda a ka'idar addini musulunci
haramun ne, amma dana ya jima yana kaunar 'yarka, so bana wasa ba, ya rayu da kaunar ta, matuk'ar aka
bari fadeelah ta auri wani toh ba shakka zan iya rasa Dana, domin kaunar da yake mata. mune dai
magabatan yaron da aka fara kawo lefen sa. Ina fatan zaka yi wa magana ta duba ta fahimta" alhaji Sufyan
Rufa'i ya karasa yana kallon Daddy...

Shiru Daddy yayi, wani yanayi daya kasa fassara shi ya shiga ratsa shi, hak'ik'a ba zai iya kallon fuskar
alhajin yace bazai iya bawa dansa auran Fadeelah'n ba. Domin alhaji Sufyan Rufa'i mutum ne da wasu
masu arzikin ma ke fatan ya rabe su. Babban damuwar sa shine amminin sa minister Sa'id bai san yanda
zasu ƙarƙe ba.

Kallon sa ya kai ga dan Alhaji Sufyan dake zaune yana dan danna wayar sa a wanna karon, tabbas wanna
shine surukin nuna wa sa'a, Daddƴ ya aiyana a ransa...
Kallon alhajin yayi yace "ba matsala alhaji Sufyan, naji bayanin ka, sai dai akwai yaron minister Sa'id da aka
samu musu rana tare, amma zan tattauna da aminin nawa Sa'id, in Sha Allah babu wata matsala" Daddy ya
fada cikin taɓɓaci.

Saurayin nan kuwa cak! Ya tsaya a lokacin da Daddy ya ambaci dan minister, wani matsanancin kishi ya
dirar masa, sai dai sam mutum bazai fahimta kai tsaye ba.

Haƙa dai suka cigaba da tattaunawa akan maganar auren, inda suka yanke cewa ayi bikin nan da sati biyu
kamar yadda aƙa saka ɗa farƙo.

Bayan sun gama maganar ne, suka yi musabaha hadi da sallama cike da mutunta juna kana suka fice gaɓa
ɗaƴa har Daddy'n.

A haraban inda motocin su suke faƙe suka tsaya, shi kan shi Daddy ya jinjina yawa da tsadar motocin.

Bayan Daddy ya koma ciki ne alhaji Sufyan Rufa'i yace ƙalli saurayin cikin zolaya ƴace "toh angon two
weeks mu zamu koma kauyenmu(abuja), amma ƙa ɓamu aron motar ka daya zai ajiye mu a airport idan
babu damuwa yallabai" alhaji ya karasa a zolaye Yayinda alhaji Abdallah ɗa alhaji Aminu suka sanya musu
dariya...

Cikin wani haɗaɗden muryan sa, da amon ya sanja fiye dana baya yace "ni Alhajina kana sani kunya,
umarnin ya kamata ka bani, take zan aiwatar da abinda kake so, zan ma kai ku airport din da kaina"
saurayin nan ya fada.

"A'a a'a karka damu, driver daya ma zai ishe mu zuwa airport din, kaima ka wuce naka unguwar ka huta
(haka yake cewa gidan nasa saboda tsananin girman sa)"

Murmushi daya bayyana white teeth d'insa yayi, domin ya san alhajin nasa da zolaya, a fili kana murya
kasa-kasa yace "Alhajina ina son ganinta, kewar ta zai min illa idan na tafi ban ganta ba"
Jinjina kai alhaji yayi duk da sun yanke hukuncin sai bayan daurin aure zai bayyana Kan shi gare ta, amma
ya fahimci yanayin sa, hakika is not easy at all...

"So kenan ya zaka yi? Kasan dai yanda muka tsara komai, bana son a samu matsala, idan ma za a samu is
better ko bayan daurin auren ne duk abinda zai faru ya faru, yanzu kayi hakuri muje nan da sati biyu ne
ƙawai, she will be yours for ever in Sha Allahu"

Cikin gamsuwa ya jinjina kansa, kana suka shige motocin suka bar estate din.

Bangaren Daddy kuwa bayan ya raka su alhajin ya dawo cikin falon sa, ya ga kiran minister Sa'id, cikin dan
sanyin jiki ya dauka, yana shirin yin maganar ƴaji muryar minister "hello professor ya haka? Abinda kayi
yayi daidai kenan? Dama kasan cewa akwai wanɗa ka riga ka bawa auren 'yarka amma ka bari dana ya bata
lokacin sa a kanta...."

Taran numfashin sa daddy yayi da cewa "minister calm down ba haka bane, sam bana da masaniya kan
kawo lefen ko wani da na bawa auren fadeelah, bayan Jameel. ina taƙaice maka ƴanzu nan alhaji Sufyan
Rufa'i suka bar estate ɗina domin dan sa ne ke son Fadeelah'n"

Daga dayan bangaren dan zaro ido minister Sa'id yayi, domin indai alhaji Sufyan Rufa'i babban kasuwar da
Duk duniya tasan shine tofah akwai matsala...

Cikin basarwa yace "wani alhaji Sufyan Rufa'i din?"

Daddy yace "babban dan kasuwar nan dai shi nake nufi, a gaskiya na kasa ce masa a'a, sanin kanka ne
alhaji Sufyan Rufa'i ba irin mutanen nan bane da mutum zai ki mu'amala dashi bane, domin girma da
darajar sa a duniya ba kadan bane..."

Cikin fushi minister Sa'id ya katse Daddy ɗa cewa "yanzu professor Saboda ka ga wanda ya fi dana dukiya
shine zaka yi mana butulci? Toh ka sani wallahi tallahi ba za a yi haka dani ba, Jameel ɗai Fadeelah Yake so,
kuma dole ita zai aura, wanna ai tozarci ne, ko ta halin kaka ne ƙuwa, ka rubuta ka ajiye jameel sai ya
mallaki 'yarka!"

Ran Daddy ya baci, dama arziƙin abota minister Sa'id yake ci shiyasa yayi masa Shiru tun dazu

"Kaga minister ya ishe ka haka! Fadeelah 'yata ce, kuma yanzu nace ba zan bawa danka ba, dan alhajin zan
bawa, dama can Ni na lallashi princess ta amince da auran Jameel din, ɓa so taƙe ba, toh yanzu nace na...."

_i'm seeing a lot of msgs and comments, Amma ban san wanne zan yi reply ba saboda yawan su, but naji
dad'in addu'o'in ku da fatan alkhairin ku gareni, love You all_

Share

Comment

Vote

I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*

💝ƘƳAUTAR ƘOƊA💝
(It's all about love, scracife, hatred and destiny)
*WATTPAD
@NoorEemaan

ELEGANT ONLINE WRITER'S📚🖊

https://facebook.com/groups/943534712916776/
Masu amfani da facebook su yi join ta wanna link din.

EDITING IS NOT ALLOWED❌

Page 49-50

Cikin fushi shi ma minister ya katse Daddy da cewa "oho! Wato sai yanzu ka san cewa fadeelah bata son
auran Jameel din ko? Shi dan gidan alhajin son shi tace maka tana yi? Toh wallahi....."

Kit daddy ya katse kiran, domin baya son su yi batacciya da minister Sa'id din.
Babu jimawa ya nufi part din Grandma ya sanar da ita komai, bata ko yi masa fada ba, sai ma nuna
murnan ta a fili domin babu wanda bai san alhaji Sufyan Rufa'i ba kaf kasar nan dama wajenta, nan aka
cigaba da shirye_shirye gida na kara cika, yan'uwa da abokanan arziki na ta zuwa tun kafin ma satin bikin
ya kama...

******. ******. ******.

"Daddy wallahi bazan hakura da Fadeelah ba never! Ta ya ya ma professor zai mana haka, yanzu ɗan alhaji
Sufyan Rufa'i zai bawa fadeelah? Bayan na jima ina kaunar ta, gaba daya yanzu zai bata min budget,
matukar ya hana ni Fadeelah, toh sace ta zanyi mu bar kasar gaba daya ma kowa ya huta"... Jameel ke
wanna maganar tamkar zai fashe da kuka.
Murmushi mai ciwo minister yayi yace " kai yaro ne my son, ɗuƙ inda kake tunanin wayon professor ya
wuce nan, childhood friend dina ne, nasan shi in and out, bare yanzu daya kara security masu yawan gaske
Ta yaya za a iya sace ta? ka kuma san duk inda zata tana tare da bodyguard's dinta..... "

Mummy'n Jameel data cika tayi fam tace "yanzu minister haka zamu bari ya ci bulus, gaba daya ya kunyan
ta ni gaban kawayena, bama ni kadai ba, gabadaya mu abin kunya ne a garemu, gaskiya kayi wani abu kai,
akan wata can dana bazai shiga mayuwancin hali ba, ƙalli fa tun safe ƴa ƙasa cin abinci"

"Calm down! Calm down!! Dole zan yi wani abu a kai, domin duk na fi ku jin ciwon abinda ya faru, kamar ni
professor zai yi wa haka?" Ya fada cikin takaice, nan dai suka cigaba da tattaunawa kan maganar....

*WASHEGARI*

Yan'uwa da abokan arziki sun cika falon Mommah mai yalwa sai kallon lefen Fadeelah suke, fadin yawan su
bata lokaci ne, domin su kansu masu hannu da shuni sun yaba kwarai da akwatunan ɗa uɓan ƙayan ciƙin
sa.

Kaf kayan babu na kasa da dubu dari biyar, duka kayan masu tsadar gaske ne, duk nacin mutum da son
ganin duka kayan baya iya wa, domin akwati daya ma yawan kayan bazai fadu ba, bare in aka hada duka
guda hamsin din.

Sosai wani akwati Madaidaici ya ja hankali mommah, haƙan yasa ta bud'e, take zanen hotunan fadeelah
kala kala da aka yi masa kamar enlargement ne a cikin akwatin, ƴawan su zai ƙai ashirin, sosai hakan ya
birge jama'a abinda ba a taba samu ba, a ciƙin lefe kenan...

Nan mutane suka fara daukar akwatunan hoto ɗa video suna watsawa a social media, kafin dare comment,
like, da share kamar zai fasa wayoyin jama'a, abin gwanin burgewa, Grandma baki yafi rufuwa ganin jikarta
mafi soyuwa a ranta tayi goshi, ɗomin tasan bikin ya zo ɗa wani salo mai kayatarwa, ta kuma san biƙin zai
kafa tarihi wanda shekaru masu yawa anan gaba mutane zasu dinga tattaunawa akai...
Duk abinda da ake yi, fadeelah bata sani ba, tana kudundine a dakin ta, tana kuka, domin ta rasa madafa,
ita kam bata son wani d'a namiji idan ba Fadeel ba, duk da taji sauki ganin an fasa bikin da Jameel, amma
still hankalin ta bai kwanta ba, domin bata san waye wanna da zata aura ba, bata kuma damu da tambayar
kowa, ko magana yanzu bata son yi, amma tana kokari matuka wurin boye damuwar ta tunda yanzu gida
ya cika da jama'a...

Wanna kenan.

*******. ********. *******.

TWO WEEKS LATER

*RANAR DAURIN AURE*

Zaune take a dakin Mommah, tana sanye da wata tsadaddiyar material wanda fadin kudin sa bata lokaci
ne, a yau shine karo na farko data fara saka manyan kaya (in kun tuna shigar Fadeelah english wears ne,
amma ba matsatsu ba) wanda yayi mata kyau ainun, duk da cewa tayi rama sosai saboda damuwa da
fargaba da take kwana take tashi dashi, amma hakan bai boye kyawunta ba.

Light makeup ne a fuskar ta, kana hannu ɗa kafar ta ya sha jan Kunshi wanda duka sai da taga bacin ran
Mommah sannan ta yarda aka yi mata su.

Tunda aka fara event din bata ko saka ango nata a ido ba, domin an sanar cewa baya kasar, sai daurin aure
da zai hallata, duk inda ka shiga labarin bikin da event din ake Saboda uɓan dukiyar da aka narka wurin
gabatar da kala- kalan event din.
Wanda kaf ba a taba irin bikin ba a fadin Nigeria, abinda mutanen ke ta fada kenan.

Babu abinda take ji sai faduwar gaba mai tsanani, domin ta san cewa ta rasa masoyinta Fadeel har Abadan
kenan, hak'ik'a basu cikawa Mahmah burinta ta ba. Take wasu hawayen masu zafin gaske suka zubo mata.
Babu jimawa yan daurin aure suka fara dawowa, inda aka d'aura auren akan sadaki naira na gugan naira
har million biƴar, sosai gidan ya cika ɗa hayaniya, saboda yalwar jama'a.

A hankali ta mike ta zuge labulen Mommah, nan ta hango tarin jama'a da ba za su fadu ba cikin shigar
fararen kaya...

Ganin hayaniyan jama'a sun fara yawa a part din Mommah, hakan yasa ta bi ta kofar baya ta koma part din
ta, domin wani mugun ciwon kai ke barazanar tarwatsa kanta.

Tsaye yake tare da alhaji Sufyan Rufa'i cikin shigar tsadaddiyar shadda fari kal Yayi dinkin babban riga.
agogo, takalmi, hula, duka mai tsadar gaske ne, babu abinda ke tashi a jikin sa sai k'amshi, sosai yayi kyau
mai tarin yawa ya kuma fito saƙ a angon sa....

Cikin marairaicewa yace "Alhajina I want to see her, kaji yanda k'irjina ki dukawa Saboda da ita"

Murmushi alhaji Sufyan Rufa'i yayi, fuskar sa fes cikin annushuwa domin ya cika masa alkawari, kamar
ƴaɗɗa ƴayi wurin taimakon sa ɗomin mallakar muradin ransa, yanzu duk abinda zai biyo baya a shirye
suke...

Hannu sa ya kamo yace "for sure zaka je gareta, domin ita din taka ce yanzu, mallakin ka ce, Allah ya baku
zaman lafiya mai dorewa, ina tayaka murna sosai, mu ma anjima zamu koma abuja in Sha Allah"

Rungume alhajin yayi yana jin kwallan farincikin ya cika idanunsa, sai dai sam bai basu damar zubowa ba,
Saboda tarin jama'a dake wurin ...

A hankali ya motsa labb'ansa yace "Alhajina Kalmar godiya tayi kadan in yi amfani da shi wurin gode maka,
domin kaine silan wanna farincikin nawa na yau..."
"Shhhhh! Ka cancanci haka, babu godiya a tsakanin mu, maza je ka gareta kaji" alhajin ya fada yana raba
jikinsa da nasa.

Wani security daya zo gifta wa alhaji ya kira shi yace "ina ne part din amarya?"

Sanin cewa saurayin dake gefen alhajin shine mijin ma'am din su, hakan yasa cike da girmamawa yace
"muje zan nuna masa yallabai"

Jinjina kai alhajin Yayi, ya kalli dan nasa yace "all the best the young billionaire ku je"

Murmushi saurayin ya sakar wa alhajin kana suka tafi da security'n. Suna zuwa daidai kofar da zai sada
mutum da part din Fadeelah'n security ya tsaya cikin girmamawa yace
" nan ne kofar shiga part din ta"

Murmushi wanna saurayin ya sakar wa security kana ya murda kofar ya shige.....

Kwance fadeelah take tayi rub ta ciki tana kuka sosai, Idanunta sai yaji suke mata Saboda tsananin kuka ga
uban kumburin da suka yi, kuka taƙe tana surutu cikin fitar hayyaci, ga jikin ta daya dauki zafi da alama
zazzzabi na shirin saukar mata...

Cikin nutsuwa ya murda kofar bedroom din ya shiga, lumshe idanun sa yayi sak'amak'on dad'add'an
k'amshi turaren ta daya kama dakin, kana ya ware idanun sa da suka sanja launi zuwa ja a kanta...

Wani abu tamkar mashi ya soke masa k'irjin sa sakamakon jin kukan ta, da alama bata ma san ya shigo
dakin ba...
Ya jima yana kallon ta, ba tare da ya iya furta wata kalma ba, ganin bata daina kukan ba ya sanya shi ware
kyawawan labb'ansa ya furta

"my darling Fadeeeeeeeeeelerh"

Cak! Kukan ta ya dauke sakamakon jin muryar da ko a wani hali take zata gane, sai dai sam bata yarda shi
din bane, tafi yarda cewa gizon da kunnewan ta suka saba yi mata ne.

Cigaba tayi da rera kukan ta, wani murmushi daya taho da hawaye ya saki kana ya kara cewa

"Fadeeeeeeeeeelerh! It's me your Fadeel"

Wata zabura tayi ta sauko daga kan gadon kasancewar ta bawa kofar baya ne ɗama, waro ido tayi cikin
mamaki.... Shin da gaske fadeel abin kaunar ta ne ke tsaye a gabanta ko a'a? Shin ba gizo ko mafarki data
saba yi bane?
Murza idanun ta tayi da dukkanin hannun ta, still yana tsaye a gabanta, hawaye da murmushi dauke a
fuskar sa...

Ganin kamar tana tamtama ya sa shi ƙara cewa "my Darling nine! your Fadeel da gaske ni ne a gabanki"
Fadeel ya fada yana ware mata hannuwan sa, kana ya kare maganar cikin muryar sa da amon sa ke fidda
aji, so, kauna, kewa, hadi da matsanancin tausayin ta.

"Fadeeeeeeeeeeeeeeeeel"

tace cikin zunzurutun mamaki hadi da zallan farinciki kana ta buga tsalle ta rungume shi, a karon farƙo tun
da suka fara soƴaaƴƴa, ta fashe da kuka sosai harɗa shesheƙa...

Cikin wani zafin nama ya taro ta, domin da ba dan yayi namijin kokari ba, da sun zube a kasa domin babu
kwari a jikin sa, Saboda da dukkanin k'arfin ta ta rungume shi.

Hugging dinta so tight shi ma yayi, ya kasa controlling hawayen dake zuba a idanunsa, yalwataccen
gashinta ɗa ya rufe fuskar ta ya mayar baya, kana ya dora lips d'insa cikin kunnen ta yace......
*Team fadeel and Fadeelah, Fadeel is back! I know you guys are happy, dan haka ina son jin ra'ayinku akan
page din yau*

Shin Ta yaya Fadeel yayi arziki?

Daddy zai amince ɗa auren kuwa idan ya san cewa Fadeel daya dauka dan alhaji Sufyan Rufa'i ne, ba kowa
bane face wanna talaka fakirin daya raina?

Sannan Jameel zai hakura kuwa?

ƴa ƴa Mommah zata ji, idan ta san cewa Fadeel din fadeelah'n ta ne angon? Da dai sauran su....

Muje zuwa fans😚

Thank you for reading my Novel *Kyautar koda*

NoorEemaan ce
07082281566

#Share fisabilillah

#Comment

#Vote
show me love😍
please vote and follow me on wattpad @NoorEemaan

I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*

💝ƘƳAUTAR ƘOƊA💝
(it's all about love, scarife, hatred, and destiny)

*WATTPAD*
@NoorEemaan

ELEGANT ONLINE WRITER'S📚🖊

EDITING IS NOT ALLOWED❌

https://facebook.com/groups/943534712916776/
Masu amfani da facebook su yi join ta wanna link din.

Page 51-52

"Shhhhhhhhhhhh! It's okay, my Darling stop crying, am so sorry ok?"


Kara k'ank'ame shi tayi tamkar zata shige cikinsa, ta kasa yarda cewa Fadeel din ta ne, ta kasa yarda cewa
shine tsaye a gabanta tana rungume dashi a karon farko, ta kasa yarda cewa a lokacin data fidda tsamanin
ganin sa, amma finally ta ganshi, a lokacin da hakan bai da amfani, a lokacin da ta zama matar wani, ta sani
cewa a lokacin da ma bata yi aure ba, Daddy bai amince dashi ba, bare yanzu da aka d'aura Mata aure, Ga
samu ga rashi, ta aiƴana a ranta...

Tuno hakan ne yasa gabanta faduwa sosai, kara k'amk'ame shi tayi sosai, duk da tasan cewa haramun ne
rungume shi data yi, musamman yanzu da take da aure, amma bata da zabi daya wuje tayi hakan, domin
ba k'aramin kewar sa ke dawainiyya da ita ba, kana tana jin farinciki sosai hadi da sanyi a ranta a
sak'amak'on ganin sa ɗa ta yi, sai dai murnan ta ragagge ne domin yanzu ta zama matar wani, wanin ma da
bata sani ba.

Tuno hakan da ta saƙe yi ne yasa ta ture shi da k'arfi, ta zube kasa tana kuka....

Taga-taga yayi kamar zai fadi, kana ya ja tunga ƴa tsaya, domin da dukkanin k'arfin ta ta ture shi, ga ba
kwari a jikin sa, cikin mamaki yake binta da kallo, miyesa ta sanja all of a sudden?

Sosai hawaye ke zuba a Idanunta, numfashin ta har wani seizing yake Saboda uban kukan take "go, go, go
away, bana son ganin ka, so kake in mutum dama, shiƴasa ƙa zo ƴanzu, idan na mutu ƙa huta, domin banga
amfanin rayuwa babu muradina a tare Dani ba, ashe kana da zuciya da zaka iya rabu da ni tsawon lokaci
haka? Baka san halin da zan shiga ba, ka tafi without even a second thought, ka ɗawo a lokacin da nake
bukatar ka, amma zuwan ka babu abinda zai tsinana min, banda damuwa da zaka kara min, domin ni
matar aure ce yanzu, an d'aura min aure da waniiiiiiiiiiii" ta karasa tana kuka sosai har wani buga hannunta
take a kasan tiles....

Tsad'add'en murmushin sa ya saki, duk da kalaman ta sun taba shi matuka, ya ƙuma tausaƴa mata, amma
kalaman ta na karshe ya yi sanadin wanna murmushi nasa.

A hankali kana cikin takunsa mai ban sha'awa ya iso gaban ta ya tsaya, a hankali ya tsugunna gaban ta,
hannayenta ya riko, ta kwace, da karfi ya sake riko hannaƴen ta wanna karon, sak'amak'on haƙan ya sa ta
kasa kwacewa, "look at me" ya fada yana kokarin sanya Idanunsa cikin nata...

Shiru tayi masa tana cigaba da kukan, ba zato taji ya rungumeta da kyar, tana zillewa, dukan bayansa take
tana cewa ya sake ta, Yayinda har yanzu kukan take...
"Shhhhh! Ki daina dukan mijin ki, ɓaɓu kyau fa"

Cak! ƙukan ta ya dauke jin Kalmar *MIJIN* daya ambata...

Cikin sauri ta dago tace "miji? Yana ina" ta fada tana kallon dakin, ko zata ga mijin.

Dariya ta bashi, hakan yasa shi sakin murmushi yana cewa


"look at me! nine mijin ki, ni zaki kalla"

Waro ido tayi, cikin rashin yarda tace " ni ɓan ƴarɗa ɓa, ka saƙe ni, ta yaya hakan ta faru?"

"Zaki ji komai Darling, tafiyar mai tsawo ce, haka ma labarin, ina so ki yarda dani ki bani nutsuwar ki, you
know fadeel dinki bai taba miki Karya ba ko?"

Wata nutsuwa hadi da farinciki ke ratsa sassan jikinta, cikin sauri ta daga masa kai alamun

"eh"

Kara kamkame ta yayi a jikinsa, haka ita ma, tagwayen ajiyar zuciya ya sauke kana yace....

*WAIWAYE ADON TAFIYA*

(Yanda akayi fadeel yayi arziki)

Cikin kunnen Fadeelah ya dora bakin sa, kana ya fara bata labari kamar haka...

"A lokacin dana bar estate ɗin nan, ban zame ko ina ba sai gida, cikin tashin hankali da bazai mitsaltu ba.

Fadeelah I cried! Nayi kuka da ban san tsawon kwanakin dana dauka ina yi ba.
kalamai marasa dadi da Daddy yayi min ke ta amsa kuwa a kunnewa na, ɓan taɓa damuwa da talaucina ba
sai ranar.

Sosai hankalina ya tashi, na fara tunani ta yadda zan samu arziki domin in cika mana burin mu, sannan in
cikawa Mahmah alkawarin ta, sannan sunan bakin talaka fakiri ya kau....."

Kuka fadeelah ta saka daya fadi kalaman karshen nan, dago ta Yayi, ya kura wa hawayen dake zuba daga
Idanunta ido, cikin damuwa yace

" idan kuka zaki yi, toh bazan cigaba da baki labarin ba"

Dif kukan nata ya dauke, rungume shi tayi, tana fadin "na daina" cikin muryar kuka.

"Kwana na hudu a daki, ban san ina kaina yake ɓa, even ruwa bana iya hadiya Saboda tsananin dacin da
yake min, a kwana na biyar na fita da kyar duk da uban jirin dake diba na, garin lagos ya min zafi sosai,
tunanin yin nesa da garin nayi, ko zan samu abin yi domin Daddy ya bani auren ki, cikin k'arfin guiwar
hakan na fice daga gidan, bayan na rubuta wasika na soka jikin kwado Saboda nasan zaki zo duba ni idan
kika jini Shiru kwana biyu, sai....."

Katse shi tayi da cewa "meyasa baka kira ni ka fadamin ba, kasan halin ciwon dana kasance a ciki my one?"

Tsad'add'en murmushin sa mai cike da aji yayi mata, kana yace "I know cewa kin kasance cikin
mayuwancin hali, like wise nima, ranar dana zo gidan ku wayar dama chajin sauran kadan, so a daran ranar
ma ta mutu, Saboda halin matsanancin damuwar da nake ciki ya sanya ko tunanin wayar bai zo min ba,
balle na kai caji"

Jinjina kai fadeelah tayi cikin gamsuwa.

Gyaran murya yayi, domin bayan lokuta masu tsayi, sai yau yayi magana mai yawa.

"Ban san ina nake jefa kafana ɓa, kawai tafiya nake cikin fitar hayyaci da kuma rashin gwarin jiki, nayi tafiya
mai nisa sosai, kana na fara jin horn na motoci a bayana, sai dai halin fitar hayyaci da nake ciki ya hanani
motsawa, nama rasa ta ina zan bi in kauce, abu na karshe dana ji, shine buge ni da mota tayi kana sallatin
jama'a daga nan ban kara sanin inda kaina yake ba.....
Wata na daya a asibiti, kana na bud'e idanuna, na ganni daure da na'urori hadi da Oxygen domin taimaka
min wurin numfashi, hakan ya tabbatar min da a asibiti nake, abu na farko da idona ya fara sauka a kan shi
shine wani mutum tare da matar sa, fusk'arsu dauke da alamun damuwa...

Kokarin cire Oxygen din nake, mutumin ya lura, cikin sauri suka yi kaina suna murmushi, domin watana
daya cur bana motsi, hakan yasa su farinciki yanzu.

"sannu! Sannu!! Yaro" suka fada a tare, kana alhajin ya cire hannun na daga kan oxygen din.

Wasu mutanen masu sanye da suits tsaye da alama escort d'in wanna mutum ne. Daya daga ciki ya danna
wani madanni dake manne a bango, hakan ya bada kara, kasa da mintuna biyar wani doctor da nurse suka
shigo fusk'ar su dauke da murmushi, cire min Oxygen din doctor yayi, hadi da na'urorin dake jikina, kana ya
hada wasu allurai ya min.
Nan naji doctor yana fadawa wanna mutumin cewa idan na farka daga baccin alluran nan da suka min
komai zai yi normal, sannan yace wai ina karfi, Allah ya nufa ina sauran kwanaki a duniya, domin mutane
da suke k'asancewa cikin irin wanna halin nawa suna jimawa a kwance, wasu ma suna mutuwa iɗan ƙwana
ƴa ƙare......

Ban Kara jin cigaban maganganun sa ba, sak'amak'on baccin da yayi gaba dani.

Sai ɓaƴan awanin biyar na tashi, na tsinci mutumin nan yana fadawa matar dake kusa dashi wanda bana
tamtama matar sa ce cewa ya saka gasa (competition) na manyan masu Zane na duniya domin a zana
masa katafaran company dazai gina, domin so yake ginin ya zama special, sannan ya saka zunzurutun kudi
masu yawa-yawan gaske...

Karon farko dana bude baki cikin rawar murya nace "zan shiga gasar alhaji"

A mamakance suka juyo gareni domin basu san na farka ba, cikin mamaki alhajin yace "zaka shiga kace?
Kasan wadanda zasu yi zanen kuwa? Ba kananun masu Zane bane, manyan architecture's ne"

Alhajin yafada cikin iyakar gaskiyar sa, domin bai yi tunanin na kware a zane ba.
Cikin k'arfin guiwa na bud'e baki nace "alhaji banyi alkawari, ko nace nawa zanen zai fi na kowa ba, amma
ina mai tabbatar maka nawa zanen daban zai k'asance fiye da na sauran"

na fada masa cikin dakewa, domin wanna shine hanyar kadai da nake saka ran samun kudi domin na
mallaki ki, ban damu da ko nawa bane, muddin zan samu kudi da zan fara business ko wani abu da zai bani
riba mai yawa domin nayi gaggawar mallakar ki...

Murmushi alhajin ya min domin karsashina ya birge shi, matar tasa ta kalleshi, kana tace "alhaji a bashi
dama ya gwada bajintar sa" cikin gamsuwa ya jinjina Kai, dama ko bata fada ba, yana da niyyar bashi
daman.

Nan alhajin ya bani hakurin cewa motocin escort d'insa ne suka bige ni, sosai nayi mamakin saukin kai irin
nasa, domin kallo daya nayi masa na fahimci cewa shi din mai arziki ne irin sosai dinnan...

Bayan sati daya aka sallameni a asibiti, alhajin yace na fada masa ina ne giɗan mu ko na kira wani nawa
domin yasan halin da nake ciki...

Sosai rauni ƴa bayyana akan fuska ta, domin ya tuna min da miki dake binne a zuciyata, cikin k'arfin hali
nace "banda kowa, iyayena sun rasu"

Sosai alhajin ya tausayi min, nan yace yana neman alfarma na bi su gidan shi, tunda an sallame ni, na kasa
yi masa musu, domin haka kawai naji mutumin ya kwanta min, kana ina ganin girman sa sosai....

Haka na koma gidan sa, mai girman gaske, nan na kara tabbatar da arzikin alhajin, sosai kuma dabi'arsa ta
saukin kai da daraja dan Adam ke burge ni, ina ji ina ma haƙa sauran masu kuɗi ƙe ɗa halin ƙwarai irin
nasa...."

_to be continue after sallar isha, ngd sosai da comments ɗinku masu sugar_😚

Share
Comment

Vote

NoorEemaan
07082281566

I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*

💝KYAUTAR KODA💝
(Its all about love, scracife, hatred and destiny)

*WATTPAD*
@NoorEemaan

ELEGANT ONLINE WRITER'S✍️

EDITING IS NOT ALLOWED❌

https://facebook.com/groups/943534712916776/
Masu amfani da facebook su yi join ta wanna link din.
Page 53-54

Sosai Alhajin yake ja na a jikinsa, hatta idan zasu ci abinci sai ya kira ni mun ci tare, tunda nazo gidan ban
ga wani d'a ko 'ya tasa ba, daga shi sai matar sa, su kadai ke rayuwa a cikin gidan...

Sati daya a gidan, da yamma alhajin ya kira cewa, na shirya gobe ne zamu yi gasar zane. Da toh na amsa
kana na koma part din da suka bani, ƙarƙi manta kullum tunanin ki, hadi da matsanancin kaunar ki na nan
daram a raina, bana iya bacci, Saboda tunanin ki da fargaban rasa ki, sosai nayi add'ua kan Allah ya bani
sa'an wanna gasar.

*WASHEGARI*

Muka fita da alhajin zuwa inda za'a yi zanen, Hada'dd'en waje ne, mai dauke da duk wani abun bukata na
zane, abokan gasan nawa babu wani talaka a cikinsu, domin hudu daga ciki ma turawa ne, amma still ban
karaya ba, awanin shida aka bamu domin mu gama.....

Bayan awanin hudu na gama na saka suna na daga dan kasa in a fashionable way, sai dai ban rubuta full
ba, *FFM* haka na saka sunana kana na miƙe.

Taƙe na ga abokan gasar tawa suna min dariya, ganin nine mutum na farkon gamawa, a tunanin su ban iya
komai ba, Domin babu wanda ya sanni a duniya a matsayin architecture...

Bayan awanin biyu naga sauran masu zanen suka fito, Wani wajen mai kyau aka ƙai mu haɗi ɗa bamu
hada'ɗɗen abinci da abin sha, suƙa ce mu jira har a kira result din wanda ya zo na daya.

Sam na kasa ko da shan ruwa ne, burina ƙawai a kira result na ji ko na ci, sabanin sauran dake cin abincin
su cikin raha da farinciki, ni kuma ina gefe, ban shiga cikin su ba, domin irin kallon kaskancin da suke min,
abinda na tsana ƙenan raini da wulakanci, duk da kasancewa na talaka bana daukar raini, komai arzikin
mutum kuwa, domin sam bana son zuciyata ta mutu kan abun duniya.
*Da Misalin Karfe Shida Ɗa Rabi Na Ƴamma*

Muna zaune a wanna wajen ɗai da aka bamu, muna jiran jin sak'amak'o, bayan sallar bana ko motsi....

babu zato ɓaɓu tsammani muka ji muryar wata mace ta wani loudspeaker domin maganar ta karade
ila'irin wajen kamar haka "The winner is FFM, congratulations to you"

Take na zube kasa nayi sujjadul-shukur, Yayin da hawaye masu dauke da abubuwa da dama suka zubo min,
Sosai nayi farincikin hakan, finally ni na ci.

Abokan gasar zanen nawa kuwa, mutuwar zaune suka yi, domin basu taba tunanin cewa zan zo ana karshe
ba ma, domin a dakin da muka yi zanen babban ne, sannan akwai tazara mai dan yawa tsakanin mu, babu
mai ganin zanen wani...

Mutum daya ne daya kasance baƙin fata dan garin Ibadan ya min murna, kana ya fada min cewa "na maka
murna sosai bro, congratulations! tabbas a rayuwa kada ka taba raina ko wulakantawa mutum komai
kaskanci shi kuwa, hakika na koyi wani darasi daga gareka.." Yana fadamin haka yana ficewa daga wajen...

Nan sauran suma suka tafi cike da jin haushina ko nace tsana ta, domin naga hakan ta idanun su.

Bayan awa d'aya Alhajin ya fito yace mu koma gida, fusk'ar sa dauke da murmushi kana da sauran
mamakina kan kwarewa ta, domin zanen yayi kƴau mai ban mamaƙi

Bayan munyi sallah, mun ci abinci a part di'n alhajin, ya mike ya shige bedroom d'in shi, babu jimawa ya
d'awo dauke da wata madaidaicin jaka ya mika min....

Fuska ta da alamun tambaya nace "menene wanna alhaji"

Murmushi yayi yace "hakika kai gifted ne, kana da talent na zane sosai, kayi matuk'ar iya zane, wanna jakar
mai dauke da million hamsin naka ne, ma'ana shine hakkin ka na zanen"
Sosai na shiga rudu, domin ban taba tunanin samun koda million ɗaya ba, cikin rudewa nace "Alhaji nawa
ne million hamsin? dan Allah ka fadamin, zai Kai na iya mallakan Fadeelah ta? kudin zai isa da har Daddy
zai bani auren Fadeelah?" Na fada hawaye na ciko idanuna, domin a lokacin burina na mallake ki.....

Sosai alhajin yayi mamakin ganin ban yi murna samun makudan kudaden nan ba, sai ma sunan ki daya ji
na kira, hakama matar sa.

Hannuna ya riko yace "hakika akwai abubuwa da dama cikin tarihin rayuwar ka, wacece wanna fadeelah'n
sannan waye zai ki baka auren ta?, ka fadamana labarin ka nayi alkawarin taimaka maka da dukiyata da ma
duk wani abu da zaka bukata"...

Ban musa ba, na basu tarin rayuwata, dama labarin soyaayyar mu, kin san menene? Ya tambayi Fadeelah,
girgiza kai tayi Yayinda taƙe k'irjin shi har yanzu.

Gani nayi alhaji yana zub da kwalla, matar sa kuwa rushewa tayi da kuka, wanda na zallan tausayi ne...

ɓaƴan wasu mintuna yayi gyaran murya yace "idan kace zaka yi aure da duk kudinan daka samu, Tayaya
zaka yi arziki? Tabbas mallakan Fadeelah a matsayin mata shine cikar farinciki ka, amma ba yanzu zaka je
gareta ba, business zaka yi da kudin nan, sannan zan maka hanya ta yanda duniƴa zata san cewa kai
babban architecture ne! hakan zai sa cikin lokaci kankani sunan ka ya daukaka, har ka dinga samun kudaɗe
masu yawan gaske, idan arzikin ka ya sake bunkasa sai ka fara gina gida, Bayan nan ka zuba motoci, Bayan
ka gama hada dukkanin abinda kasan cewa mahaifin ta zai baka auren ta, sai muje kwatsam"...

*******************************

Sosai suna na ya ɗauƙaƙa a duniya, a matsayin *Architecture FFM* duk yanda yan jaridah da yan gidan TV
suka so hira dani ban bari ba, kana ban bari sun dauki hoto na ba, ina mamakin wai nine yau yan jaridah ke
rububi akai, hakika idan baka da shi a duniya ka zama dan kalllo.....
Sosai na yarda da shawaran alhajin, cikin lokaci kankani na fara bushiness, ga manyan zane na masu kudi
da nake ta samu abin har yawa yake min...

In tak'aice miki, cikin watanin kalilan nayi arzikin da ni kaina ban san yawan su ba, abu na farko dana fara yi
shine gini na, wanda na zane ne da hannuna, na kuma yi shi a garin lagos domin nan nake sha'awan zama,
sannan na zubo motoci da duk wani abun more rayuwa, na zuba ma'aikata, hadi da bodyguard's masu bani
tsaro kamar yadda alhaji yace lallai sai na samu bodyguards domin tsaro......

a lok'acin dana shiga katafaran gidana sai dana yi kuka tuno Mahmah nah.
A dalilin rashin babu(kudi) cuta ya cita har ta koma ga Allah, sai bayan ranta nayi arziki da ban taba
mafarki ba, sai kuma ma tuna haka Allah ya kaddara mana....

Daga wanna lokacin alhajin ya dauke ni tamkar Ɗan sa, daga baya yake fadamin duk tarin dukiyar sa, Allah
bai basu haihuwa ba, amma mutum bazai gane hakan ba, domin suna zaune cikin farinciki, sun ƙuma
fawwalawa Allah lamarin su.

A lok'acin dana ji cewa anyi baikon ki da Jameel na kusan zaucewa, domin ina sa ayi min bincike akan
abinda ya shafeki..... Babu bata lokaci na samu Alhajina nace dan Allah ya taimaka su je tambayan min
auren ki domin bazan jure rasaki ba a karo na biyu...

Sosai alhajina ya kwantar min da hank'ali, yace akwai shiri na musamman da yake yi, yana so komai yazo a
bazata, yace na yarda dashi, na bar komai a hannun sa, ban sake cewa komai ba, amma kullum tunanin ki
nake, ina fargaban rasaki, ga kuma tarin sonki dake nukurkusata, sau da dama ina son zuwa gareki alhajina
ya hana yace na bari komai ya tafi kamar yadda ya tsara....

Makudan kudade da ban san hadadin su ba na bawa matar Alhajina domin ta hada min lefe, cikin kankani
lok'aci ta fita kasar waje ita da wata kawarta da kanwarta suka hado....
A ranar da loƙacin dasu Jameel za su kawo lefe duk muna sane, hakan yasa alhajina yace a kawo nawa
kafin su jameel su kawo nasu, hakan zai kawo rikitarwa.....

Nan matar Alhajina dama yan'uwan ta da wasu kawayenta suka k'awo lefen, Bayan kwana biyu muka zo
estate dinku Alhajina yayiwa Daddy bayanin cewa yayi haku'ri, mun yi nema cikin nema amma ba laifin sa
bane, Dan sa ya na matuk'ar son fadeelah da dai sauran su....

Abu biyu ne ya bani mamaki, Daddy bai ki amincewa ba, ban saniba ko dan alhajina yafi mahaifin Jameel
dukiya ne, Allah masani.
Sannan abu na biyu Daddy bai gane ni ba, bai gane cewa nine wanna bakin talaka fakirin bane...

Naso zuwa gareki a ranar da muka zo wajen Daddy, still alhajina ya hana yace na bari sai ranar daurin aure
domin inyi miki bazata....

Ajiyar zuciya Fadeel ya sauke kana ya cigaba...

har yau da aka d'aura mana aure, daddy bai san cewa nine Fadeel ba, ina matsayin dan Alhaji Sufyan Rufa'i
ne a wajensa.....

BACK TO STORY

Kara rungumeta da kyau yayi, yana jin farincikin mallakar ta a matsayin mata, yace

"wanna shine tarihin Bayan rabuwar mu a tak'aice...."

Muje zuwa da sauran chakwakiyya😎😎😎

A tayani share dan Allah👏🏻

Share fisabilillah
Comment

Vote

NoorEemaan
07082281566

I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*

💝ƘƳAUTAR ƘOƊA💝
(It's all about love, scracife, hatred and destiny)

*WATTPAD*
@NoorEemaan

ELEGANT ONLINE WRITER'S📚🖊

EDITING IS NOT ALLOWED❌

https://facebook.com/groups/943534712916776/
Masu amfani da facebook su yi join ta wanna link din.
Page 55-56

Kukan zallan farinciƙi Fadeelah ta sanya, a ranta tana mai godiya ga Allah. Ita ba arzikin ɗa yayi ya sanya ta
farinciki ba, dawowar sa gareta a matsayin miji yafi komai yi mata sugar. Duk da ta san cewa akwai
kalubale a gaba, amma bata wani damu ba, tunda sun zama ma'aurata ƴanzu burin su ya cika.

Duk da arzikin da yayi a kankanin lokaci abin mamaki ne, taɓɓas bata manta lokacin da ake yawan labarai a
gidan TV kan *The young billionaire architecture FFM* bata mantawa a falon Mommah suna zaune aka
hasƙo labarin, shi Kanshi Daddy sai daya jinjina arzikin wanna matashin, ashe Fadeel dinta ne bata sani ba,
duk da yayi fiye da arzikin da Daddy zai so, amma shin zai amince suyi zaman su cikin kwanciyar hankali
kuwa? Ta aiyana a ranta, sanin cewa bata da amsa ya sanya ta share, kana a fili tace "Am so happy my one,
Allah na gode maka, da gaske kai ka aureni? Wayyo dadi!" Raba jikinsu tayi ta nufi zanen hotunan dake
manne a bango.

Daidai kan na mahmah ta tsaya, ta goge kwalla sakamakon tuno Sadaukarwa mahmah a gareta wanda
kullum da shi take kwana take tashi, tabbas Mahmah ta zama sashen jikinta, Yayinda Fadeel ya zama jinin
jikinta.

Shafa fuskar zanen Mahmah'n take yi tana kokarin controlling hawayen dake zuba a idanun ta.

Cikin murya dake bayyana tarin kauna hadi da kewar mahmah tace "Allah ya jikan ki Mahmah, Allah yasa
kin huta, Mahmah ƙiƴi farinciƙi... a yau Fadeel din ki ya cika miki burin ki, mun zama ma'aurata, nasan kina
farinciki a inda kike yanzu, ina kaunar ki mahmah nah, muna kaunar ki duka" ta kara sa tana share wasu
hawaye masu dumin gaske.

A ɓazata ta ji Fadeel ya rungumeta ta baya, hannunwansa duka biyun ya d'aura saman shafaffan cikin ta.
Cikin wata murya da amon sa ke fidda tashin wani miki a zuciyar sa yace "Ameen ya tawwabul raheeem,
amma kin manta baki fada mata cewa zamu Haifa mata jikoki ba, sannan zamu kasance tare har abada, har
mu koma inda take a yanzu, duk runtsi duk wuya muna tare" ƴa ƙarasa cikin wani cool voice ƴayinda
idanunsa suka kara yin jaa...

Murmushi mai tafe da hawaye ya taho wa fadeelah a lokaci daya, cikin muryan kuka tace "eh mahmah!
Zamu haifa miki jikoki, sannan kullum sai na basu labarin ki, na sani cewa baza su taba ganin ki ba sai ɗai a
hoto, amma zasu rayu da son ki a jinin jikin su, sannan ni da Fadeel zamu kasancewa the best couple ever,
we love you Mahmah" ta karasa tana juyowa hadi da rungume Fadeel.

Shi ma rungumeta yayi ya shiga bubbuga bayanta har tayi Shiru tana sauke ajiyar zuciya. A hankali tace
"My one menene ma'anar FFM?"
Murmushi mai sauti ya saki, lumshe idanun sa yayi yace "it means *FADEEL, FADEELAH, MAHMAH*" ya
amsa a tak'aice...

"Wow!" Tace tana jin farinciki samun masoyi kuma miji kamar Fadeel.

Slowly cikin zazzakar muryar ta tace "Am so happy for you, I love you so much"

Wani shaukin sonta ne ya shiga ratsa jijjiya da jinin jikin sa, martani ya mayar mata kamar haka "I love you
too, fiye da tunanin mai tunani, ina matukar kaunar ki my Darling wifffy"

Murmushi ta saki, komai na Fadeel dinta ya sanja, magana, tafiya, kallo, murya, komai nasa ya dawo cikin
wani aji da salo mai tafiya da hankalin duk wata lafiyayyen mace.....

Hannun sa ta kamo suka zauna kan hada'dd'e kuma katon gadon ta, kallon ta yake yana jin wani farinciki a
ransa, ta yi masa kyau fi da tunanin mai tunani, still hakan bai hana shi ganin ramar da ta yi ba.

"I love your hennah Darling" Fadeel ya fada yana sumbatar had'add'en jan kunshin hannun ta.

Murmushin zallan farinciki tayi, ta kai idanun ta kan kunshin, tunda aka yi mata kushin bata ga kyaun sa ɓa,
haslima haushin sa take ji, sai a yanzu ta fara ganin kyawun K'unshin, wanda baya rasa nasaba da bayyanar
gwarzon masoyinta kuma mijinta fadeel.

Kallon shi tayi tace "my one amma ka kai ziyara wa yan'uwan mahmah da na baba ko?"

Take yaji ranshi ya baci a dan kausashe yace "ban je ba, ba kuma zan je ba, Tayaya kike tunanin zan iya
zuwa? Sun manta damu, sun manta cewa ina raye ma, sun ma san mahmah ta rasu? Basu sani ba, saboda
rashin zumunci, ƙo ɗan sun ga a cikin dangin talakawa ne mu shiyasa basa ziyartarmu, tell me tayaya zan je
wajen su, sam bazan je ba, idan ina dake, ina da komai Fadeelah, idan kika Haifa min 'ya'ya sune zasu
kasance duniya ta ɗa dangin na, hakan ya ishe ni rayuwa Alhamdulillah! Ki bar zancen su please" ya karasa
yana sauke numfashi....

Ganin yadda yake magana ya sanya fadeelah sanin cewa ranshi ya baci matuka, domin bata taba ganin
fushi ko bacin ran shi ba sai yau, Hakika dangin sa basu da zumunci, amma a hankali zata dinga yi masa
magana domin ya je garesu, saɓoɗa hannun ka baya taba rubewa ka yanke ka yar.
Hannun sa ta riko a fili tace "na bari toh, saki fuskar ka please" ta karasa a shagwa'be.

Murmushi ya saki yace "na saki toh, are you Happy now?"

"Yes! My one" ta amsa cikin wata had'add'iyar murya daya sanya shi jin wani yanayi na musamman a tare
da shi, a hankali ya matso daf da ita, baya tayi kadan, sai ya bi ta ya kwanta a kanta, hakan yasa ta zube kan
gadon...

Dan waro ido fadeelah tayi ganin bai taba kwantanta irin haka da ita ba, ko da su biyu ne ƙadai a wajen.
Amma tuna matsayin sa a gareta yanzu ya sanya ta sauke boyayyen ajiyar zuciya, amma sosai ta ji wani
kunyar sa ƴa shige ta.

Ganin ya nufo labb'anta ya sanya ta runtse idanun ta, dakatawa yayi yana murmushi mai sauti ganin yadda
tayi, hannunsa ya kai ya shiga shafo tattausan labb'anta yace "bana son gulma faaa, na san kin ji ma kina
son Fadeel ya sumbace ki ai, dan haka ki bud'e idanun ki" ya karasa cikin wani romantic voice.

"Ya Allah! Fadeel zai kashe ni da salon sa, hadi da kunyar sa, komai nashi ya Sanja ya dawo gwanin
burgewa fiye da baya" ta fada a ranta.

A fili kuwa tace "yaushe ka koyi sharri my one? ni ban taba wanna tunanin ba, Allah faaaaa" ta karasa
tamk'ar yarinya yar 13years...

Ɓata zata ba, unexpected ta ji ya kamo lallausan lips di'nta mai fidda k'amshin Mouth Wash na Lavender ya
fara kissing di'nta in a passionate and romantic way...

Sarkin kunyar kuwa bata san lokacin data shiga bashi hadin kai ba, gaba daya sun shiga wani yanayi mai
wuyar fassaruwa, ji suke dama sun dauwama a duniyar da suke ciƙi ƴanzu, ɗomin yanayi ne mai dadi da
bazai fadu ba. Sosai ƙuma suka birkita gadon dama kansu....

Bayan mintuna goma sha biyar... har ƴanzu suna abu daya, ganin ya fara zurmewa da yawa ya sanya
Fadeelah zare labb'anta da suka yi mugun jaaa, domin fadeel bai mata da wasa ba, tamkar lollipop yake
sha...

Ganin ta cire labb'anta ya sanya shi lumshe fitinanun idanun sa masu dauke da zallan sonta hadi da
kwadayin kasancewa da ita, kansa daya gama hargitsewa ya dora kan k'irjin ta yana sauke numfashi domin
babu k'arfi ko daya a jikinsa....
Hannunta na kan gashin sa tana murzawa a hankali Yayinda idanun ta ke a lumshe, sosai suke jin shauki
hadi da jin dadin kasancewa a haka.
"Wiffy" Fadeel ya kira ta slowly

"Uhm" ta amsa cikin murya kasala

"Kinyi enjoying kiss din ko?" Ya fada cikin tsokana...

"Ya salam! My one dama baka da kunya, please kabari kana bani kunya faaaa"

Bayan lokuta masu yawa daya k'asance cikin kunci da damuwa sai yau ya yi dariya mai sauti, domin ba
kadan ba ta bashi dariya. "Toh mena yi na rashin kunya yanzu?"

"Ni dai ka bari bana so" ta fada tana turo cute lips d'inta

Dagowa yayi ya bata light kiss a lips d'inta, hakika fadeelah'n sa daban take cikin mata, duk da kasancewar
ta wayayya domin daidaikun kasa ne bata je ba, kana duk wata wayewa tana da shi, haƙa ma ilimi, amma
hakan bai hana ta zama mara ƙunƴa ba, sosai kuma hakan ke burge shi domin kunya ado ne ga mace....

A fili cikin tsokana yace "ba wani bakya so, Bayan kamar zaki cinye min ba....."

Da gudu ta sauka ɗaga kan gadon ta ruga toilet.... Kwanciya yayi a gadon ya shiga dariya, domin sosai
Fadeelah'n ke bashi nishadi yau.

Fadeelah kuwa ajiyar zuciya mai dauke da murmushi take ta saki a bathroom.... Ta kai mintuna biyar a
wanna yanayi kana ta tube kayan jikinta tayi wanka da hada'dd'en *shower bath* dinta, kayan jik'in ta ta
mayar, domin bata son fita da bathrobe ya ganta haka, sosai kima, girma, haɗi da kunyar sa ta karu a
Idanunta musamman yau din daya zama miji a gareta...

A hankali ta rike handle din kofa ta fito, waro ido Fadeel yayi yace " me zan gani ni fadeeel, amarya ba
makeup a fusk'ar ta, tukunna ma wanka kika yi? ko dai ko dai" ƴa karasa ciƙin zolaya

Turo baki tayi kana tayi murmurshi domin ta dauka wani abu ne ya sa shi waro ido, a ranta tana mamakin
dama Fadeel dinta ya iya tsokana haka, bata bashi amsa ba, domin ta san kawai so ƴaƙe ya sata ƙunƴa.

Zuwa tayi gefen sa ta zauna, wani nishadi na shigar ta, ganin sa kusa da ita yafi komai yi mata dadi a
yanzu...

"Wait a minute! Anya kinyi breakfast kuwa? Domin dana shigo part dinnan naga kamar an shirya breakfast
a dining area da alama kuma babu wanda ya taba" Fadeel ya fada idanun sa kan fadeelah

"A'a ban ci ba, farincikin ganin ka ya sani na manta" ta fada cikin iyakar gaskiyar ta, domin wallahi ta manta
wani abu wai shi abinci...
Murmushi ya saki kana yace "duk da haka bai kamata kina min wasa da nan ba" ya fada yana shafa cikinta,
kana ya mike

"Ina zaka? Karka tafi dan Allah!" Ta fada a dame.

Murmushi mai sauti ya saki yace "ba tafiya zan yi ba, yanzu zan dawo kinji" ƴa fice zuwa dining area ya
bud'e duka warmers din, karshe dai porridge din Irish potatoes da zallan naman kaza ya zuba mata, kana
ya hada mata tea mai kauri, kan wani tray karami ya jera su kana ya nufi dakin...

Daidai ya bud'e kofa kenan zai shiga, hakan yayi daidai da sanyo kan Fadeelah waje domin zuwa dubo shi
ganin ya dade...

Kansu ne ya gware ɗa na juna "auchhhhh!" FADEELAH ta fada tana dafa kan.

Cikin sauri ya ajiye tray din, Allah yasa ma bai bare ba... "Sorry! Sorry!! my bride, ban san kin taho ba" ya
fada a dame yana Murza mata goshin daya dan yi jaaa abunka da farar fata jiki bai saba da wahala ba...

Ganin yadda ya damu ya sanya tace "ni faaa bana jin zafi, ka bar murzawa"

"Kina ji mana, gashi wajen yayi jaa" ya fada kamar zai yi mata kuka

Dariyar ta mai birgewa tayi tace "da gaske ba zafi"

"Are you sure?" Ya tambayeta

"Yes I am" ta amsa tana jifan shi ɗa ƙallon kauna

Ajiyar zuciya ya sauke kana ya mika hannu ya dauko tray din ya dora kan cinyar sa, cokali mai yatsu ya
dauka ya raba dankalin hudu kana ya cake yanka daya da fork din, hadi da kaza ya nufi bakin ta....

Ta bude baki ya sanya mata, haka ya shiga ciyar da ita har ta koshi, ƙuma taci sosai, kana ta shanye tea din
tana sauke numfashi tun bayan rabuwar su da Fadeel bata kara cin abinci cikin kwanciyar hankali ba, sai
yau.... Domin a lokacin damuwa baya barinta taci...

Bayan awa d'aya ya mike domin tafiya, fadeelah ta fara matso hawaye ita kada ya tafi ya barta, domin a
ganinta idan ya tafi baza ta kara ganin shi ɓa....

"Kwantar da hankalin ki, gida kawai zan je fa zan d'awo, nasan kina tunanin zan bar ki ne, ina zan iya barin
matata in tafi? So chill, zan d'awo domin mu ga yadda abubuwa zasu kasance, tun da burinmu ya cika ya
kamata zuwa yanzu Daddy yasan waye mijin 'yarsa na ainahi..."
Jinjina kai tayi cikin gamsuwa kana ta raka shi har bakin down stairs, nan ma basu rabu ba sai da ya kashe
mata jiki da salon sa sannan ya tafi cike da kewar ta da sonta.....

Yana fita yaga body guards d'insa tsaye jikin motocin sa, dan dafa Kai yayi shaf ya manta ma suna jiran sa,
har yanzu gidan a cike yake, sai dai ba kamar dazu ba, daya daga cikin motar ya fada kana suka fice a jere
reras....

Bangaren Fadeelah kuwa tana tsaye jikin window har motocin sa suka fice, ajiyar zuciya ta sauke tana fatan
kada wata matsala ta sake kunno musu, ta kofar baya ta bi ta nufi part din Mommah, domin duka kayan ta
na fitar biki yana wajen Mommah'n...

Ta kuma yi mamaki rashin kiran ɗa Mommah bata mata ba, har wani sauri take domin taje ta sanar da
Mommah dawowar gwarzon masoyinta Fadeel a matsayin miji a gareta........

Muje zuwa my beautiful people😍

Share fisabilillah

Comment

Vote

Noor Eemaan loves you all Habibtie's💋


07082281566

Tuesday September 28
1:41am

I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*

💝ƘƳAUTAR ƘOƊA💝
(It's all about love, scracifes hatred and destiny)

*WATTPAD*
@NoorEemaan

ELEGANT ONLINE WRITER'S📚🖊

https://facebook.com/groups/943534712916776/
Masu amfani da facebook su yi join ta wanna link din.

EDITING IS NOT ALLOWED❌

No editing🤒

Page 57-58

Tana shiga part din Mommah, nan kowa ya shiga bin ta da kallo cikin mamaki, ganin yadda walwala ya
kawata fusk'ar ta, sabanin dazu da kallo d'aya mutum zai mata ya fahimci tana ɗa ɗamuwa.

Murmushi fadeelah take saki ba tare da tasan tana hakan ba. Direct bedroom d'in Mommah ta shige, ta
kuwa same ta tana kokarin sanja kaya zuwa wani dan ubansu lace wanda kudinsa zai kai million daya da
doriya, dago kai Mommah tayi ta sakar mata murmushi, martani Fadeelah ta mayar mata kana ta bata rai
cikin shagwa'ba tace

"Mommah ko ki neme ni ko?"


Murmurshi ta ƙara saki tace "tayaya zan nemi ki bayan kina can tare da mijin ki abin sonki Fadeel... Ina
sane na barku ku gana sosai ai"

ihun murna Fadeelah ta saki ta rungume Mommah, ciƙin maɗauƙaƙin mamaƙi tace " yaya aka yi kika san
Fadeel ne ya aureni? Mommah please ki gayamin kinjii" fadeelah ta karasa cikin zumudi.

Raba jikinsu Mommah tayi suka zauna kan hada'dd'en gadon daƴa ƙawata daƙin yayinda fadeelah ta
kurawa Mommah ido cikin mamakin ta yanda aka yi ta sani...

Fuskar Mommah dauke da murmushi na zallan farinciki tace " a lok'acin da ake rikicin waye ya kawo lefen
farko, nima hankalina ya tashi sosai, nan na sake kiran wanna matar wacce ta kasance matar Alhajin
sufyan. Cikin dare na roke ta da Allah ta gayamin waye ya kawo lefen...
Matar bata boye min ba, ta gayamin komai, sannan tace kada na fada wa kowa domin shi Fadeel tare da
alhajin sa sun shirya yi miki suprise, sosai nayi farinciki mara mitsaltuwa ganin zaku mallaki juna, kuma
gashi finally burin fadeelah ɗa Fadeel ya cika"

"Wayyo! Mommah dama kina da labari baki gayamin ba, Mommah am so happy, bazan yadda zan yi
expressing farincikin ɗa naƙe ciƙi ba"

Sai kuma fusƙar ta ƴa baƴƴana ɗamuwa tace "amma Mommah yaya kike ganin daddy zai d'auki maganar
nan, zai aminci kuwa? Ina fargaban hakan Mommah"

"Kada ki damu kanki sweetheart, ina mai tabbatar miki Fadeel zai samu karbuwa wajen professor wanna
karon, ba dai arziki bane kuma gashi Allah ya bashi fiye da zaton mutum, dan haka ki kwantar da hankalin
ki kinji ko?"

Jinjina kai Fadeelah tayi fusk'arta dauke da murmushi, nan suka cigaɓa ɗa tattauna maganar.......

***** ***** *****

Bangaren minister Sa'id kuwa sosai hankalin shi ya sake mugun tashi, musamman daya samu labarin
daurin auren Fadeelah ɗa wani, ba da Jameel ɗan shi bane.
Ga jameel ya tada hankalin su, ya hargitsa ko ina na gidan irin na sangartattun wasu y'ay'an da basa samu
kwaba tun suna kanana.

Babu abinda minister Sa'id da matar sa suke sai kokarin lallashin sa, amma ina K'amar kara zuga shi suke.

Nan fa minister ya kara jin zafin abinda professor Imran mai naira yayi masa, bai taba tunanin amintakan
dake tsakanin su bai kai aminta ba sai ƴanzu, tunda gashi ya tsalle shi ya bawa wani auran Fadeelah'n....

Nan ya d'auki alwashin sai ya bincika, ya kuma bibiyi rayuwar yaron da aka aura wa fadeelah'n. Ɗomin yaji
shi dan uban waye ne, saɓoɗa sai yanzu tunanin sanin cewa Alhaji Sufyan Rufa'i bashi da 'ya ko ɗa a duniya
ya zo masa....

zuwa ƴamma estate din ya rage yan'uwan na jiki wandanda suke nesa, wanda su ma gobe zasu tafi...

Ɗa misalin ƙarfe tara na dare fadeelah ta fito ɗaga toilet sanye da bathrobe, lotion mai saukin zafi ta shafa
a lafiyayyan farar fatar ta, kana ta fesa tsad'add'en body spray mai suna *lalique* bayan nan ta shafa oil
perfume mai suna *fogg abnat* wani mugun k'amshi mai sa nutsuwa ke tashi a jikinta, wasu riga da
wando masu kauri na company'n *Dior Burberry* red color ta sanya, kana ta saka wani hula mai kyau baki,
sai irin gajeren Safan nan shima baki ta sanya domin garin da sanyi sosai...

Gado ta haye tana mai lumshe idanun ta masu cike da kewar Fadee din ta...

Ɓabu jimawa ta fara jin motsi daga window(taga) alamu mutum na haurowa, bud'e idanunta tayi, yayin da
taji gabanta ya tsanan ta fadu'wa, domin tana ƙara jin motsin mutum na kara ƙunsanto dakin...

Shiru tayi ta ma kasa motsi Saboda tsananin tsoro ɗaya lullube ta, gashi window a bud'e yake bata rufe
ba...

Bata gama firgicewa ba, sai ɗurowar mutum ɗa ta ji, ta kuma gani a dakin, sanye yake da irin shigar ta sai
dai nasa ɓaƙaƙe ne. Yayinda ya rufe kansa zuwa fusk'ar sa da hulan rigan, kafar sa sanye da fararen canvass
na company'n *dolce and gabbana* wanda kudin sa ya kai 451,507.
Tsananin tsoro, jikinta har wani mugun rawa ƴake, domin a tunanin ta aljani ne, saboda tsayin ginin ɗa
mamaƙi ace mutum ya hauro har saman inda take kuma ta taga.

Mikewa tayi tsaye ta ɗuro ɗaga ƙan gadon, idanunta sun kawo ruwan hawaye... Ganin yana kusanto inda
take yasa ta fara karanto d'uk add'uar data zo bakin ta, kana ta bud'e murya zata ƙwala ihu domin bai
daina zuwa kusa da ita ba.

cak! Mutumin ya tsaya kana a hankali ya zame hular rigar baya, take K'yak'yyawar fusk'ar sa ta bayyana,
yana sakar mata murmushi hadi da ware mata karfaffan hannayen sa alamun ta zo gare shi.

Haɗiye ihun tayi, tana ware idanun ta, ganin shi a lokacin da bata zata ba, domin bata kashe fitilun dakin
ba, hakan yasa kallo daya ta yi masa ta shaida shi...

Take farinciki ya maye gurbin tsoron, da mugun gudu ta isa gare shi, rungume ta yayi yana jin nutsuwa na
saukar masa. ƴayinda yake jin bugun zuciyar ta bai dawo dai² ba, alamun ta tsorata sosai kenan...

Ɓakin sa ya d'aura a daidai kunnenta dake tashin k'amshi yace "Am so sorry! Na baki tsoro ko? Fadeel ne
relax ok" ya karasa cikin sanyayyar murya mai cike da kulawa hadi da tsantsar soyaaya.

Jinjina masa kai kawai take, kana tace "ba komai, ya aka yi kasan ina kewar ka? Kazo a lokacin da nake
matuk'ar bukatar kasancewa da Kai"

Murmushi mai sauti ya saki, kana yace "you have no idea of how i miss you! hakan ya hana ni bacci har na
zo gareki matata, but am so sorry I scared you"

Wani mugun son sa ne ya karu a zuciyar ta, sosai take son yanɗa komai nasa ya sanja gwanin burgewa
tamkar an sauya sa ne, a fili kuwa tace "it's fine karka damu my one, amma meyasa ka bi ta window ka
shigo?"

"Ɗaga gida na ma ta wata hanyar na biyo, domin bana son masu tsaro na su ce zasu biyo ni. Saɓoɗa yanzu
lokacin hutun su ne bai kamata na shiga hakkin su ba, dana zo estate din ku ma Shiru, babu kowa daga
waje, har na juya zan tafi, domin bana son tashin kowa, kawai na hango wanna hanyar, na gwada shigowa
kuma Alhamdulillah naga ta kawo ni part din ki"

Murmushin alfahari da mijin ta ta saki kana tace "amma meyasa baka biyo ta kofa ba, zan bud'e maka ai,
shine ka wahalar min da kanka ka bi bango, amma bada kafa ka taho bako?" ta karasa a dame kana cikin
gaskiyar ta
Fusk'ar ta ya kamo duka cikin tafin hannayen sa yace " I thought kin yi bacci ne shiyasa ban biyo ta kofa ba,
da keke na zo" ya amsa mata a tak'aice.

Jinjina kai tayi cikin gamsuwa tana sauke ajiyar zuciya, hakika ba iya k'yau, haduwa, aji, Fadeel dinta ya
karo ba, har da jarumta....

Tana cikin wanna tunanin taji ya sunkuceta ya nufi kan gado da ita, idanun su kafe dana juna.

Zama yayi, ƴayinda take kan cinyar sa, tamkar baby doll. ganin ta ƙafa masa ido bata ko kiftawa ya Sanƴa
shi hura mata iskan bakin sa mai k'amshin mouth spray na vanilla.

Lumshe ƙyawawan idanun ta yi cikin kunya, murmushi ya saki kana a hankali ya nufi tattausan labb'anta ya
bata light kiss, a tare suka saki ajiyar zuciya....

Sun dauki mintuna a haka ba tare da yayi magana ba.


Can ya zaunar da ita kan gadon kana ya dora kansa a cinyar ta, gashin sa mai tauri irin na Africa take
shafawa a hanƙali hadi da yi masa tafiyar tsutsa, lumshe ido Fadeel yayi wani maganadisun dadi na ratsa
shi, sun dauki awa d'aya a haka kana ya ji Shiru, can ƙuma yaji Fadeelah ta fado k'ansa...

Murmushi ya saki domin ya fahimci bacci tayi, a hankali cikin dabara ya dawo da ita jikinsa ya rungumeta,
yana ji dama a gidan sa ne suka kasance a haka ƴanzu, amma yasan hakan bazai yu ba, dole sai Daddy ya
san waye shi sannan zai tafi da matar sa...

Idanun sa ne ya kai kan wayar ta, hannu ya mika ya dauki wayar, ya sanya lambar sa ya kira, take number ta
ya bayyana a screen din wayar sa.

Nan ya yi saving da *my Darling* kana ya ajiye mata wayar, agogo ya duba yaga karfe goma sha biyu har
ɗa mintuna hamsi...

Dan waro ido yayi, domin bai yi tunanin lokaci ya ja har haka ba, kokarin kwantar da ita yayi amma ta
k'amk'ame shi..., fusk'ar sa ta dan nuna mamakin hakan, domin bacci take sosai...

Ƙara gwaɗa ƙwantar da ita yayi, nan ma ta kara rungume shi tana bata fusk'a.
Ƙomawa yayi ya zauna kan gadon still dai tana manne a faffadar k'irjinsa, yana dan ɓuɓɓuga bayanta...

Mintuna goma suka sake shudewa a tunanin sa zuwa yanzu zata amince, a hankali ya shimfud'a ta a
gadon....
Ihu ta saki cikin shagwa'ba hadi da magagin bacci tace "stay with me, karka tafi please Fadeeeeeel"

"Nima ba a son raina zan tafi ba, kalli kiga karfe dayan dare ƴa wuce fa"

Zaro ido tayi domin bata dauka lokaci ya kure har haka ba, mikewa tayi tace "Toh ina tsoron ka tafi cikin
daren nan fa, ka kwana gobe da safe sai ka tafi"

Girgiza kai yayi yace "Hakan bazai yu ba Fadeelah. I have to go, babu abinda zai faru in sha Allah, Kiyi min
add'ua kinji, I love you!" Ya karasa yana kusanto ta kana ya kama lips di'n ta ya shiga bata kisses na
mintuna uku kacal, kana ya sake bin ta window yana sauka a hankali har ya dira kasa...

Bayan ya gama sauka ya dago kansa ya ƙuwa hango ta tsaye bakin window tana daga masa hannu, fusk'ar
ta dauke da murmushi...

kiss ya hura mata, kana ya hau keken sa ya bi ta hanyar daya shigo ya fita...

**** ***** *****

Bayan kwana d'aya da safe professor Imran mai naira na zaune a part din shi yana duba wasu takardu
wayar sa ta shiga ringing...

Sunan minister Sa'id ya gani baro baro a jikin screen din tsad'add'iyar wayar sa...

Sosai yayi mamaki domin rabon da ƴa yi waya tun ranar da suka yi bataciyya dashi, ba tare da ya kawo
komai a ransa ba ya daga kiran...

Ɗariyar minister Sa'id ya fara ji kana yace "pro kenan! dama na kira domin na Sanar da kai cewa *wanna
FFM the young architecture billionaire* daya yi mugun arziki cikin shekara daya da watanin nan, ba
kowa bane face wanna talakan da ka ki bawa auran 'yar ka FADEELAH toh shine dai yanzu ya aure ta, ba
tare da ka sani ba, hhhhhh, Saboda son aurawa 'yarka mai arziki har ya sa ka manta cewa Alhaji Sufyan
Rufa'i bai tana haihuwa a duniya ba, na barka lafiya, ka bincika sauran da kanka"

Kit minister Sa'id ya katse kiran, yayinda ya bar Daddy zaune ya hada uɓan gumi tamƙar
mutum_mutumi......

MU HAƊU RANAR ALHAMIS

Share✅

Comment✅

Noor iman💖

I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*

💝ƘƳAUTAR ƘOƊA💝
(It's all about love, scracifes, hatred and destiny)

*WATTPAD*
@NoorEemaan
ELEGANT ONLINE WRITER'S📚🖊

https://facebook.com/groups/943534712916776/masu amfani da facebook su yi join ta wanna link din.

EDITING IS NOT ALLOWED❌

Page 59-60

........Daddy ƴa ɗauƙi mintuna talatin zaune ya kasa motsi cikin madaukakin mamakin.

Sosai ƙalaman minister Sa'id suka shiga dawowa kwanyar sa, ya kasa yarda cewa wanna bakin talaka fakirin
ne ƴa dawo *the famous billionaire Architecture FFM* da labarin uban arziƙin yaron ya zaga duniya dama
Fadeel ne? wanna talakan ne? cikin wata murya ɗake fiɗɗa tsantsar ruɗani yace "impossible, tayaya hakan
zai faru?"

Tamkar wani zararre, domin har yanzu mamakin bai sake sa ba, haka ya nufi part din Mommah, har wani
rawa bakin sa ke yi, ya kuwa ci sa'a ya ganta zaune a falon ta, tana kallon tashar Zee world.

Cikin rawar baki yace "kin...kin...ji...wai talakan ƴaron nan da Fadeelah ta k'awo shine yayi uban arziki, ya
kuma auri Fadeelah? na kasa yarda da hakan, dan Allah ku warware min, tayaya hakan zai faru, ace yayi
arziki cikin kankanin lokaci haka?". Daddy ya fada cikin rudewa

Wani ƙasaitaccen dariya Mommah ta saki, ido cikin ido tace " professor! a da nace babu abinda ya shafeni
game da maganar auran Fadeelah! amma yanzu dole zanyi magana tunda RANAR dana jima ina jira ta zo.
Ka sani cewa komai lalacewar abu, matuk'ar yaji gyara ba shakka zai gyaru, yayi kyau fiye da tunanin mai
tunani"

Kallon ta Daddy yayi irin ban gane ba? fahimtar hakan yasa Mommah cewa "ina nufin a da kana yiwa
Fadeel kallon mutum talaka makaskanci, amma yanzu abun mamaki yazo har gabanka ka kasa gane cewa
shine wanna bakin talaka fakirin.
Kasan miyesa ka kasa gane cewa shine wanna bakin talakan faƙirin?" Mommah ta tambaye shi ido cikin
ido.

Tamkar wani karamin yaro haka Daddy ya girgiza kansa.


"Kudi! Kudi sune silan wanna sanjawar nasa daka gani, har ka kasa shaida shi, ina so ka sani cewa arziki riga
ce, duk wanda Allah ya so sanyawa, ba shakka zai sanya masa.

Saɓoɗa Allah ya jarrabe shi da rashin babu, ba hakan na nufin yafi son ka bane, kaddarar sa ce haka, gashi
ƴanzu Allah yayi masa dauƙaƙa fiye da tunanin mai tunani.
Ƙuma alkawarin Allah ya cika, fadeelah da fadeel sun mallaki juna. Ƙa kuma aura mata wanna bakin talaka
fakirin da baka so, ba tare da ka sani ba, kaga ikon Allah ko? Ina mai baka shawara professor ka bi duniya a
sannu, wanna arzikin da kake takama dashi za ka iya wayar gari kaga babu shi a tare da kai, ɓa fata naƙe
maka ba.
shin idan mai kudi da talaka basa tarayya tayaya zamu cigaba? Wanna duniyar yanzu mai yace kudi yace
lallai sai mai kudi dan'uwan sa ne zai rabe shi? Tayaya zamu cigaba, gabadayan ɗaga mai kudi har talaka
duk daya muke a wurin Allah, babu wanda yafi wani, sai wanda yafi tsoron sa, dan haka think wiser and
change professor, rayuwar nan babu komai cikin ta, in yau kaine gobe wanin ka ne" tana gama fadin haka
ta wuce shi zuwa bedroom dinta.

Tamkar status haka professor ya tsaya, ya kasa motsi har Mommah ta shige, yama rasa tunanin daya
kamata yayi, brain d'insa ya toshe.

A hankali ya sulale kan kujera ya zauna, gabadaya daya ya ma rasa a wani yanayi yake ciki, sosai mamakin
arzikin Fadeel cikin kankanin lok'aci ya dake shi.

Ta bangaren Mommah kuwa tana shiga dakin ta, ta saki ajiyar zuciya, sosai tayi mamakin ganin tunda ta
fara magana professor bai katse ta ba, bai kuma ce mata komai ba, ta kuma ji dadin amayar masa da
magananun daya jima makale a ranta...

*WASHEGARI*

Da misalin karfe goma sha daya na safe Alhaji Sufyan Rufa'i tare da aminin sa hadi da kaninsa suka yiwa
estate din Daddy tsinke kamar wancan karon.

Cikin mutuntawa da girmamawa Daddy ya karbe su...., ba tare da alhaji Sufyan ya boye masa komai ba, ya
fadama sa komai dangane da Fadeel din.

Sannan cikin hikima tamkar gugan zana ko nace indirectly alhaji Sufyan ya ke bawa Daddy shawara mai
hade da nasiha kan bin duniya a sannu da kuma illar wulakanta talaka, tamkar yadda Mommah tayi masa
dai, sai dai cikin hikima Alhajin yake masa magana.

Maganganun sun shiga Daddy matuk'a, dama tun jiya da Mommah tayi masa magana jikinsa ya fara sanyi.
Abin mamaki Daddy'n bai ce komai ba, da kuma dukkanin alamu ya amince Fadeelah ta zama mata ga
fadeel din.
Nan suka kara fahimtar juna, inda alhaji Sufyan yace jibi fadeelah zata tare a gidan mijin nata, kamar yadda
fadeel ɗin ya bukaci hakan.

Babu jimawa kuwa suka yi sallama dasu alhaji Sufyan din, domin a yau din zasu koma abuja...

Hajiya Mommah ta dukufa da kara gyara yarta da ingantatun magunguna natural, ƴanzu fiye da rabin
abincin da Fadeelah take ci a rana ya d'awo fruit masu Gina jiki, da kuma gyara mace hadi da bata ni'ima.

*************

A yau Da misalin karfe 4:00pm Fadeelah ce sanye da wani tsad'add'en atamfa, dinkin riga da skirt, kana aka
lullube ta da alkyabba golden yellow daya dace da atamfar jikinta.

Sosai Mommah ta gyara Fadeelah babu abinda ke tashi a jikinta sai k'amshi mai sa nutsuwa.

Daddy, Mommah, da kuma Grandma sune zasu kai ta gidan fadeel K'amar yadda suka tsara. Fadeelah
ƙuwa ta manne wa Mommah da Daddy sai kuka take, duk zumudi da son kasancewa tareda Fadeel amma
yau tana ji tamk'ar ta fas, ganin da gaske zata bar gidan iyayenta.

Mota d'aya duk suka shiga, wanda sabo ne dal Daddy yace a fito dashi domin kai Fadeelah'n sa gidan
mijinta. Sai sauran motocin goma wanda babu kowa a ciki sai bodyguards dinsu, haƙa suka fita a jere ....

Basu wani jima ba, suka isa hada'dden kuma katafaran gidan Fadeel, ko nace unguwar Fadeel kamar yadda
alhajin Sufyan yace (😜)

Sosai daddy yayi mamaki ganin ƙƴaun gidan ɗa haɗuwar sa, ƙuma ace mallakin Fadeel ne? aɓin ɗa
mamaƙi wani abu mai kama da kunya hadi da nadama ke kokarin ratsa shi.

Haka zalika Grandma kasa haku'ri tayi duk izzar ta sai data yabi tsarin gidan. Mommah kuwa murmushi
farinciki take yi, ta ji ɗaɗi ta Allah ya nuna mata wanna ranar da take iya hango wanna yanayi musamman
mai kama da nadama a idanun Daddy.
Ɗuƙ ɗa girman kansa bai bari ya fito fili ya nuna komai ba, amma wanda ya san Daddy farin sani tofah zai
hango wanna yanayin a tare dashi.
Fadeelah amarya kuwa tana lullube da alkyabba bata ga ƴa ƴa tsarin gidan ƴaƙe ba.

Sunyi tafiya mai nisa a mota kana suka isa part din Fadeelah daya gaji da haduwa, wanda fadin kyaun sa
bata lokaci ne. Nan ma Daddy ya kara shan mamaki uban arzikin Fadeel din.

Akwatunan ta hamsin bodyguards suka shigar wani room tare da taimakon ma'aikatan gidan...

Sosai Mommah ta yi wa yarta nasiha, da shawarwari, da ƙuma dabarun zama da miji...

Sai da suka zo tafiya Fadeelah ta fara kuka sosai, nan fa ta tada hankalin su, daddy fadi yake "I will miss you
my princess, ki kula da kan ki kinji? Allah ya baku zaman lafiya a raƴuwar Auranku" ya ƙarasa yana
rungumar ta.

Haka ma Grandma har da kwallar ta, Daddy kadai ne yayi k'arfi hali bai yi kuka ba, Mommah ta sai data sha
kuka sosai...

Haka Fadeelah ta zauna a inda suka barta, ma'aikatan duk suka kawo gaisuwa hadi da tambayar ta me
take so a kawo mata.

"Ba komai karku damu" shine amsar data basu ta mayar da Idanunta ta rufe, ɗomin wani ɓa ɗaɗi taƙe jin
jikin ta.

Sai bayan isha Fadeel ya d'awo sanye da shadda blue color dan uban su dinkin babbar riga, har kofar part
din Fadeelah escort d'insa suka rako shi, ƙana suka koma...

Ajiyar zuciya ya sauke a lokacin daya yi tozali da ita zaune a kasa ta dora kanta kan daya daga cikin
had'add'un kujerun falon da alama sallar tayi.

"My Darling!" Ya kira ta cikin wani unique voice, a ƙuma lokacin daya iso tsakiyar falon ta.

A hankali ta dago kumburarrun idanun ta da suka sanja launi ta sauke su kan shi.

Tattausan murmushi ya sakar mata, kana ya ware labb'ansa yace "come to your husband fadeelah"
Da gudu ta isa gare shi tana fashewa da kuka sosai.

"Ya salam! Kukan me kike yi? I thought yau ranar farinciki ne a garemu? so why are you shedding tears
uhm?" Ya tambaya a ɗame kana cikin kulawa..

"Ka barni inyi my one! Kukan farinciki nake, Alhamdulillahi tatimun salihat, Alhamdulillah ala kulla halin" ta
karasa tana kara kamkame Shi.

Murmushi ya saki, Yayinda fusk'ar sa ke fidda zallan annuri, wanda farincikin ganin fadeelah'n sa a cikin
gidan sa ya sanya shi hakan...

Ya jima yana rarrashin ta, har tayi shiru amma yaji jikinta da alamun zafi.

Fusk'ar ta ya kamo yace "wiffy kin jima kina kuka ko? Ga jikin ki yayi zafi"

Shagwa'be fuska tayi kana ta turo cute lips d'inta tace "Toh basu Mommah da Daddy bane suka tafi suka
barni"

Dariya ta bashi, amma ɓai ƴi ba, sai murmushi ɗaƴa saki, lokuta da dama yana matuk'ar son shagwa'bar
ta, domin tamkar yarinya yar shekara 10 haƙa take dawowa a idanun sa.

Kasa hakuri yayi har ya kamo lallausan labb'anta data turo ya tsotsa na sakan 10 kacal.

Zare labb'ansa yayi... cikin wani sexy voice yace "dole yanzu zan kira likita domin ya duba min ke, kada
wanna zafin jikin ya dawo fever"

"Kaiiii my one! I Will fine basai ka kira doctor ba"

"A'a ban yarda ba" yace yana dialing number'n likita...

Bata kara cewa komai ba, sai lafewa a jikinsa ɗata ƴi tana sauraran dad'add'an k'amshi dake fita a jikinsa...
Babu jimawa likita ya zo, nan Fadeel yace ya duba masa matar sa, yayi mata blood test ta yanda za a san
abinda ke damunta, baya son a bata magungunan ko yi mata allura kai tsaye ɓaɓu gwaji...

Nan fa likitan ya dibi jinin da sauran gwaje² kana yace gobe zai kawo result, sai yan magungunan daya bata
domin taimaka mata kafin goben.

Abincin da chef's din suka jera a dining suka ci, kana ya bata magungunan ta sha, babu jimawa kuwa bacci
ya dauke ta..

Tashi da ita yayi a jikinsa ya haura upstairs...

Wanka yayi ya sanja kaya zuwa pyjamas ƴayinda ya shiga zare kayan Fadeelah a hankali gudun kar ta tashi,
alkyaban da atamfar ya cire mata, sai inners wears daya barta ɗa shi...

Wutar dakin ya kashe, sai dim light daya bar musu, Add'uar ƙwanciƴa bacci ya tofa musu, kana a hankali
ya dora ta a k'irjinsa, yana sauke numfashi irin na farincikin nan, abinda ya jima yana jira ya zo, finally gashi
da Fadeelah'n sa manne da juna a gado daya, kana a daki daya.

Sanin cewa bata jin dadi ya sanya shi barin ta ba tare da yayi mata komai ba, burinsa yanzu ta samu sauki,
domin sam ko ciwon kai baya son ganin ta tana yi.

WASHEGARI
10:00am

Tun bayan sallar asuba Fadeelah ta koma bacci, bata farka ɓa har yanzu...

Goma da mintuna ashirin doctor ya kawo result din Fadeelah, nan yayi wa FADEEL bayanin cewa rashin
bacci da damuwa da ta yi fama dashi a ɓaƴa ne suka tarar mata, wanda sai yanzu yake nuna kan sa, sannan
zafin jikinta ma zai sauka kukan da ta sha ne ya kawo shi.

Nan tausayi da kaunar Fadeelah'n sa suka saƙe ratsa shi, godiya yayi wa likita, ya karbi result din.

Bayan ya sallame likita ya tafi kana ya zauna a falon ya bud'e result din, abinda ya gani a rubuce ya sanya
k'irjinsa wata mahauk'aciyar bugawa....
Share

Comment

_Har yanzu Sadaukarwa bai kare ba_

Ku biyo ni, jan yanda zata kaya😎

My readers
Noor loves you all💋

I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*

💝ƘƳAUTAR ƘOƊA💝
(It's all about love, scracifes, hatred and destiny)

*WATTPAD*
@NoorEemaan
ELEGANT ONLINE WRITER'S📚🖊

https://facebook.com/groups/943534712916776/masu
Masu amfani da facebook su yi join ta wanna link din.

EDITING IS NOT ALLOWED❌

Page 61-62

........kara Murza idanun sa ƴayi, domin ya taɓɓatar da abinda ya gani, take ya saƙe sauƙe idanun sa kan
result ɗin.

Sosai idanun sa sukayi jajur, jiyoyin saman ƙansa sun fito sunyi rudu-rudu hannunsa yasa ƴa rufe fusk'ar sa
dashi, yana mai jin bugun zuciyar sa na karuwa.

Ta ɓangaren Fadeelah kuwa, a hankali ta bud'e idanun ta masu cike da bacci.


ta ji dadin jikinta yanzu, sai kasala da take ji ƙawai, kallon gefen ta tayi ta ga ba kowa, mikewa tayi a hankali
tana yamutsa fuska...

Sai a lokacin ta lura an cire kayan da ta kwanta dashi, murmushi ta saki, domin tasan wanna aikin Fadeel
ne

Ƙyawawan kafafun ta, ta sauke kasa ta shige toilet, brush tayi, kana ta wanke fusk'ar ta da bar soap.

Towel tasa ta goge fuskar ta dashi, kana ta fito, zuge wardrobe d'insa tayi, ɗaƴa k'asance na glass,
gabadaya kayan sa ta gani a ciki, a hankali ta zaro wani T-shirt dinsa, fari, sanyawa tayi taga ya sauko mata
har saman cinya, kara zuge glass din tayi ta rufe kana ta fita daga dakin, domin ta ji Shiru babu motsin
shi...

Tun daga nesa ta ganshi, haka kawai taji gabanta ya fadi, cikin sauri ta karasa gare shi, hannun sa daya rufe
fuska ta cire, a hank'ali ya dago k'ansa idanun su ya sarƙe dana juna...
Take wani ɓugun zuciya ya ƙara riskan ta, ganin yadda idanun sa sukayi jajur tamkar an watsa masa
barkono

Hankali tashe tace "ya Allah! Fadeel lafiya? Talk to me what happened?" Ta fada tana kamo fusk'ar sa cikin
tafin hannayen ta.

Cikin sauri ya rungumeta yana matse ta sosai a faffadan k'irjinsa, ya shiga sauke ajiyar zuciya a kai kai...

Taji zafi yadda ya rungumeta, domin ba runguman wasa yayi mata ba, amma bata hana shi ba, saɓoɗa
halin ɗa ta gan shi a ciki, ga bugun zuciyar sa da take ji, ya fi komai daga mata hankali.

Bayansa take shafawa a hankali, tana busa masa iskan bakin ta, kara kamkame ta yayi tamkar zai balla ta.
(yi a hankali dai, kasan fadeelah siririya ce, ko ya kuka ce fans?😁)

Sun dauki mintuna ashirin a haka kana tayi kokarin raba jikinsu, amma tamkar jaririn goye ya kara matse ta
yana sauke tagwayen ajiyar zuciya.

Cikin damuwa tace


"ka sake ni muyi magana, please my one"

Shiru taji ɓabu amsa, sai saukar abu mai dumi da ta ji a bayanta, da k'arfi ta kwace jikinta tana kallonsa,
sosai hankalin ta ya kara tashi ganin yadda hawaye ke zuba a idanun sa, ɗuƙ ɗa idanun sa a lumshe suƙe.

Hannu tasa ta shafa hawayen fuskar sa, take itama hawaye suka zubo mata, sai ta fara sheshek'ar kuka,
tace "Hawaye? ɗa gaske Hawaye nake gani a idanun gwarzon mijina? Miya yi zafi haka? Please tell me
meke damun ka, wani abu ne ya faru?"
A hauƙace tamkar mayuwancin zaki ya motsa ta jikin sa, lallausan labb'anta ya kamo ya fara kissing din ta
hurrily.....

Gaba daya sun birkita juna, good 30minutes suka dauka a haka, har ya dauki wata hanyar, ya tuno abinda
ya gani a result din ta, hakan ya sashi mirginawa gefe yana sauke numfashi...

Fadeelah kuwa duk da ta tsorata da yanayin sa, amma haka ta mike zaune ta dauki rigar ta dake yashe a
kasa, ta sanya kana ta mike ta zauna kan cinyar sa, duk da tana jin kunya da tsoro tace "miye sa ka fasa?
hakkin kane fa" domin ita ta dauka damuwar ta sa kenan.

Rikitattun idanunsa ya lumshe yana sauke numfashi, kana a hankali tamkar mai tsoro Magana yace "No!"

Cikin daurewar kai tace "why no? Why are you behaving strange? I thought damuwar kenan. Toh ka
gayamin damuwar ka, ka sani a rudawa sosai" ta karasa muryar ta na rawa, alamun tana daf da sakin kuka.

Fahimtar hakan ya sashi dora kanta kan k'irjin sa yace "am sorry! Karki kiyi kuka kinji? Zamu cikawa
Mahmah burinta, in sha Allah..., ina bazan iya ba, bazan jure ba, hakan bazai faru ba...." Ya karasa yana
rungumeta da kyau cikin fitar hayyaci...

Cikin sauri ta dago kanta jin kalaman sa na karshe, gabadaya yau ta kasa gane kan shi, cikin rashin fahimta
tace" menene ba zai yu ba?"

Bai yi magana ba, ya mike rike da takardan a hannunsa ya shiga taka step biyu² har uku³ ma.

Da kallo ta bishi cikin mamakin wanna sabon sanjin nasa na damun ta, a hankali ta mike cikin mutuwar jiki
ta bi bayan sa, sai dai a rufe kofar yake, wanda sai da hannun sa ne zai bud'e kasancewar sa mai
thumbprint ne.

Tana iya hango shi kwance yayi ruf da ciki ta kofar glass din, tayi² ya bud'e yaki.

A sanyaye ta koma part din ta, wanda tamkar gini guda ne saboda girman sa, komai na buk'atar rayuwa
akwai aciki, daya daga cikin bedroom din part din ta shiga nan ta tarar da akwatunan ta a jere, bathroom
ta shiga tayi wanka, kana ta fito, ta sanya wani simple tsad'add'en material onion color, ta d'aura dankwali ,
ko mai bata shafa ba, Saboda bata da kuzarin hakan, still kyaun ta ya fito.

Zama tayi ta zurfafa tunanin ta, amma ta kasa fahimtar inda kalaman sa suka dosa, haƙa zaliƙa ɗamuwar
sa..

Har dare bai fito ba, tayi kukan har ta koshi, ɗomin ko bud'e idanunta ta kasa yi, bangaren Fadeel kuwa
sallah kadai ke tayar dashi, sosai ya shiga matsanancin damuwa, wanda har ya rasatunanin yi, , burinsa
yanzu ya samu mafita ɗamuwar ɗaƴa afƙo masa.

Sai karfe 9 na dare ya farga da Fadeelah'n shi, a zabure ya mike, ko ina na part din ɗa yake ya duba bata
nan, cikin sauri ya nufi part din ta, ya tarar da ita kwance hannunta dafe da cikinta.

Cikin sauri, kana da damuwa a fusk'ar sa yace "wiffy?"

A hankali ta yi kokarin bud'e idanun ta, saurin mayar wa tayi ta rufe sakamakon yajin ɗata ji yana mata,
tamkar yar baby ya daga ta cak! kana ya zauna a kujeran da take tana k'irjin sa, cikin muryan galabaita tace
"sauke ni! Ka sauke ni!! Ni wajen Mommah zan koma, me ye amfanin tarrayan mu matuk'ar zaka dinga
boye min damuwar ka? Na dauka damuwar ka tawa ce, ashe ba haka bane?" Ta fada tana kokarin sauka,
amma ta kasa domin babu k'arfi a jikinta, haka zalika shima, kawai dai jarumta ce irin tasa, Saboda
dukkanin su babu wanɗa yasha koda ruwa ne tun safe.

Cikin damuwa yace "yanzu fadeelah zaki iya rabuwa da ni? zaki iya tafiya ki barni? Bayan kin san banda
kowa sai ke? Ke ce hasken idaniyata, kece mai bani farinciki, please kar min haka" ya karasa yana sauke
numfashi.

Sosai ƙalaman sa suƙa karƴa mata zuciƴa Amma ta maze, cikin dakiya da barazana tace "eh! Idan baka
fadamin silar wanna damuwar taka ba, zan tafi na barka, tafiƴa mai nisa ƙuwa"

Kamkame ta yayi yace "No please karki yi haka, zan gaya miki kinji?, amma first sai kin ci abinci. Am so
sorry! hakika ban cika miji na gari ba, na yi wa matata horan yunwa, nasan baki ci komai ba tun safe"
Bai jira amsar ta ba, ya fita, babu jimawa ya dawo dauke da tray mai dauke da abinci marasa nauyi wanda
ya dace mutum yace da d'aɗɗare.

Ɓa musu ta buɗe baki ya fara bata chips da egg sauce, dama sosai yunwa ya ci ta, Idanunta sai yawa suƙe a
fusk'ar sa tana ɓin shi ɗa kallon asalin ƙauna, shi kam labb'anta dake tauna ships din ya kurawa ido.

Sosai taci, ƙana ta riƙe hannƴensa tana girgiza masa kai alamun ta ƙoshi.

"Are you sure you ok?" Fadeel ƴa tamɓaƴeta.

"Yeah!" Ta amsa cikin siririyar murya, kana ta karbi tray din, ta ɗora ƙan cinƴar sa, ta fara ciyar dashi itama..

Bayan sun gama ya dauke ta cak! zuwa saman stairs domin yau a nan part din yake son su kwana...

Ɓayan sun yi wanƙa, suka shirya cikin pyjamas kala daya farare, kwanciya tayi cikin matuwar jiƙi domin har
yanzu jikinta ba kwari. Fadeel ƙuwa ɗanna lock_code yayi a ƙofa ƴaƴi addu'a kana yazo ƙan gadon ya
kwanta a ɓayanta, ta ji kwanciyar tasa amma tayi luf, mirginawa yayi ya dawo da ita saman sa.

Ajiyar zuciƴa suka saƙi a tare, bayanta ya shiga shafawa a hankali.

Cikin wata murya dake bayyana tsantsar damuwa ɗa ƴaƙe ciƙi yace "wiffy kin san nace doctor yayi miki
check up, har da blood test ko"

"Eh" ta fada gabanta na fadu'wa da k'arfi, wanɗa ɓata san ɗalili ɓa.

Wani wahalallan numfashi ya sauke kana yace "na shiga tashin hankali sosai my Darling, ban taba tunanin
hakan ba, a safiyar yau lokacin kina bacci doctor ya kawo result din, blood group dinki ya nuna SS ne" ya
fada muryar sa na rawa.
Murmushi ta saƙi ta ce "yes nau! na san blood group dina kenan, amma ba kowa ya sani ba, domin baya
sani wanna rashin lafiyar irin na masu blood group din" ta karasa thinking is nothing...

Da mamaki yace "Wiffy! Wanna ba abin rashin damuwa bane, kin san mu dauki alkawarin haifawa
Mahmah jikoki, har kin ce zaki basu labarin ta, Fadeelah tell me, ta yaya zamu haifi yaya masu lafiya bayan
dukkanin mu *SIKILA NE! Nima blood group dina SS ne. Dole na damu, ya karasa wasu hawaye masu dumi
na zubo masa......

*follow and vote me on wattpad @NoorEemaan*🙏

Share fisabilillah habibtie's

Noor
07082281566

I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*

💝ƘƳAUTAR ƘOƊA💝
(It's all about love, scracifes, hatred and destiny)

*WATTPAD*
@NoorEemaan

ELEGANT ONLINE WRITER'S📚🖊

https://facebook.com/groups/943534712916776/masu
Masu amfani da facebook su yi join ta wanna link din.

EDITING IS NOT ALLOWED❌

Page 63-64

A zaɓure fadeelah ta miƙe zaune saɓoɗa wani mugun tsalle da k'irjin ta yayi, sakamakon aɓinɗa taji Fadeel
din ya fada.

Tamƙar statue haƙa ta tsaya kallon sa, rawa bakin ta yake, ƴayinda hawaye ke bin kuncin ta tamkar an balle
famfo, so take ta furta wata kalma amma ta kasa, ganin hakan ya sanya Fadeel mikewa zaune ya
rungumeta, sai a loƙacin wani kuka mai ciwo ya kufce mata, su kam suna ganin rayuwa, daga wanna
kaddaran sai wannan, amma yaya zasu yi, ko wani bawa da tasa kalar zanen kaddaran...

Ta jima tana kukan har zafin jikin ta ya d'awo, fadeeel ma hawayen yake ya kasa koda rarrashin ta ne.

Sun dauki lokaci mai tsayi haka suna kukan, daga karshe baccin wahala yayi nasaran daukar Fadeelah, still
cikin baccin tana sakin sheshekan kukan.

Fadeel kuwa yadda ya ga rana haka yaga dare, sosai ya zurfafa tunanin wurin nemo musu mafita, a haka
har aka kira sallar asuba...
Fadeelah ya fara hurawa iskan bakin sa, tabe baki tayi tamkar zata yi kuka, domin da alama ta fara jin dadin
baccin.

"Wiffy!" Ya fada cikin kunnen ta.

"Uhmm" she replied trying to open her sleepy eyes.

"It's time for salat, wake up mu fara nafila kafin a tayar.

A hankali ta mike, sai a lokacin duk abinda ya faru jiya ya shiga ɗawo mata k'wak'walwarta.

Take kwalla suka ciko idanun ta, amma bata bari sun zubo ba, toilet suka shiga, suka d'aura alwala, praying
mat (sallaya) ya shimfud'a musu kana suka tayar.

Sai ɗaya ji za a tayar da sallah a masallacin dake cikin gidan, sannan ya mike a dan gaggauce ya fita, Yayinda
fadeelah ta mike ta bi jam'i.

Ɓai dawo ciki ba, sai 6:30am, karan ruwa yaji a toilet hakan ya sashi fahimtar wanka take, ɗuƙ yanda yake
so yaga suna wanka da matar sa a ɓaƴi daƴa, amma yanzu bazai iya ba, saboda yasan dole mood dinsa zai
sanja har ya kasa controlling din kansa, ƙomai ƴa waƙana, idan Allah ya bashi nasarar jefa kwan sa a
mahaifar ta, baby'n yazo yana shan wuya a duniya ya zai yi? Ya sani fadeelah ce dukkanin farincikin sa,
sannan zai iya rayuwar farinciki da ita ko da babu 'ya'ya.

Amma ya zai yi da alkawarin cikawa Mahmah burinta? domin mahmah ta cancanci fiye da haka, numfashi
ya sauke kana ya fita zuwa wani bathroom, domin duk wani sashe na gidan akwai kaya da d'ukkanin
abubuwan bukatar ɗan Adam.

Wanƙa ƴayi ya shirya cikin wani 3quarter ash color da rigar jersey armless, sliver color, na company'n
*Nike*

Oiling Kanshi yayi ya taje, kana ya fesa turaren LOVE IN OUD FOR MEN.

Wajen fadeelah ƴa ƙoma, ya ƙuwa tarar da ita zaune tayi shiru, binta da kallo yake, ƙallon so da zallan
ƙauna, sanye take da tsad'add'en palazzo trouser ja, da farar top, sai fashion hula jaa ƴayinda gashinta ya
bazu a gadon bayanta, ƙasancewar ɓata ƴi parking ɗin shi ɓa.
Ɓabu ko digon makeup a fusk'ar ta, sosai jikinta ƙe tashin k'amshin *body mist na raspberry*

Kansa ya dora a cinyar ta yana kallon ta, sai a lokacin ta lura dashi, ajiyar zuciya ta sauke, ta kira shi ba tare
da ta kalla shi ba "zaujee"

Lumshe kyawawan idanun sa yayi domin ba kadan ba yaji dadin sunan, kallonta yayi ya samu nasaran jefa
Idanunsa masu cike da zallan sonta cikin nata.

Kallon ido cikin ido suke wa juna, ko kiftawa basa yi, daga karshe dai Fadeelah ce ta janye Idanunta, domin
ta kasa jure ƙallon, sak'amak'on wasu abubuwa da take hangowa a idanun sa, wanda baki bazai iya furta
ba, sai dai a bar wa zuciya.

Hannunsa ya miko mata, ta kama suka miki a tare, ta wata doguwar corridor ya bi sai gasu a wani
hada'dden waje wanna dinning da sauraran abubuwan abinci ne a wajen, sosai waje ya tsaru fiye da
tunanin mai karatu, tamkar dai wani tsad'add'en restaurant cikin VIP.

Ja mata kujera yayi ta zauna, kana shima ya zauna,, take wasu ma'aikata masu sanye da fararen kaya suka
bayyana ɗa alama sune chef's.
Cikin girmamawa suka gaishe ɗa su fadeel, amsawa suka yi, kana suka fara kokarin serving dinsu.

Fadeelah tace "sorry! I will do the serving my self, don't worry" sosai suka yi mamakin saukin kanta, da
murmushi a fuskar su suka ce "yes ma!" Kana suka fice cikin sanin makamin aikin su.

A nutse ta mike ta dauki serving spoon ƙana ta ɓude warmer domin serving dinsu, rike tsintsiyar hannunta
yayi, da mamaki ta kalleshi alamun "what?"

"Baki cancanci ki wahala ba, domin baki Saba ba, bayan nan ma kin manta ke amarya ce da babu kamar ta"
ya karasa cikin rada, so yake ya ɗawo da walwalwlar su, baya son wanna yanayin na su, zai yi kokarin ganin
yana bata farinciki, duk da kaddaran daya shigo musu yanzu.

Murmushi ne ya subuce mata, tace "my one saɓoda ni na taso a gidan gata, hakan baya nufin bana yan
kananun aikace² duk da Daddy na hana ni, domin a cewar sa muna da tarin ma'aikata, amma Mommah
bata barina, ta kan sa mu shiga kitchen wani zubin, amma ba kullum ba, mun fi yi musamman idan daddy
baya kasar " ta karasa tana ƙallon sa.
Murmushi ya subuce masa, tabbas yana ganin darajan Mommah domin ta rike masa fadeelah'n sa tamkar
ita ta haife ta, ya kuma ƴi mamakin jin cewa fadeelah ta iya shiga kitchen, sosai fadeelah ke burge shi,
domin bata da wulakanci ƙo dagawa irin na wasu yaran masu hannu da shuni.

Kamar yadda ya fada shi yayi serving dinsu da abincin, suka fara ci... Turo baki fadeelah tayi, "menene
wiffy?" ƴa tambayeta with care.

"Kaga su Mommah da Daddy basu kira ni ba ko? ni ban ma san a wani sashe na giɗan nan na ajiye waƴar
ba.

Murmushi yayi yace "kila saboɗa kada kiyi musu kuka shiyasa basu kira ba, crying-crying baby" ya karasa a
zolaye.

Dariya tayi suka ci abincin, banyan sun gama suka bi wata hanya, take suka bayyana a wani hada'dd'en
lambu mai cike da kayan itatuwa iri daban² ga wani ruwa fari kal dake bulbulawo daga gefen, ƴayinda wasu
duwatsu masu kyalli suke zagaye da inda ruwan ke bulbulowan sosai haƙan ƴa ƙara kawata wajen...

Wano hada'dden kujeran zama tamƙar 3sitter, irin na gargajiya amma an kawato shi da zamani wanda ya
hadu fiye da tunanin mai karatu suka zauna akai, sai lelo yake dasu, garden din nada sanyi sosai, babu
abinda ke tashi sai k'amshin furanin dana kayan itatuwa, dora kansa yayi a cinyar Fadeelah suna jin yanayin
mai dadi na ratsa su, sun kuma samu saukin damuwar su..

************************

BAYAN SATI DAYA

Ta bangaren Daddy kuwa, yana cikin matsanancin damuwa da hankalin sa ya kasa dauka, gabadaya ƴa
ɗawo zararre, Saboda a daran jiya yana zaune aka kira shi ana sanar dashi cewa kayan da yayi odar su
gabadaya sun nitse a babban ƙogi.

Taƙe tsad'add'en wayar sa ya fadi kasa, gabadaya jikinsa ya fara rawa, domin bai taba sanin cewa akwai
wata kalma mai suna DAMUWA KO RASHI ba.

Domin duk abinda yake bukata yana ganin cewa yana da dukiyar da zai mallakesu, amma yau gashi dukiyar
da yake takama da ita ya rasa kaso mai yawan gaske daga ciki...

Tamkar dan jariri ya dinga kuka wiwi, domin ya rasa kudi masu zunzurutun ƴawa, fiye da tunanin mai
tunani masu yawan gaske kuwa
domin BILLIONS DUBU SABA'IN ya fitar ya siyi kayan, domin yasan zai samu ninkin ribar abinda ya fitar,
amma ace tashi daga yayi asarar su, da zallan damuwa tabbas!

Gabaɗaƴa estate din ya dauka, yan'uwa sun cika part din ana jaje, sosai gidan ya dawo tamkar gidan
mutuwa, kowa fuskar sa babu walwala hatta da masu aikin gidan, Grandma har taso ta fi daddy zarewa
ma, Mommah ce mai k'arfin hali rarrashin su, ya kuma hana a sanar da Fadeelah, yace bayason hankalin ta
ya tashi...

★★★

10:00pm

Mommah ɗa Daddy na zaune a part din shi, aƙa hasko abinɗa ƴa faru da professor a TV. Gabadaya gari ya
dauka, sai hirar abinda ya faru aƙe daga masu Allah ya kiyaye sai masu jaje...

Haƙa zalika sakonin sun fi dubu biyar suna ta shigowa wayar Daddy daga abokan kasuwancin sa dama
aboƙan arziki, ko daya ya kasa bada reply, sai dai idan sun ƙira Mommah ko suyi mata text, message shima
ba kowa ta bawa amsa ba, domin abin da yawa...

A hankali ta dago Idanunta ta kalli Daddy, gabadaya cikin awanin 48 ya sanja har wata rama yayi, take taji
tausayin sa, an ce tsakanin miji da mata sai Allah amma hakan bazai hana ta gaya masa gaskiya ba.

Zuwa SunnahTv ta sanja channel din, domin rage masa damuwa, ta kuwa yi sa'a ana wa'azi ne kan yarda
da kaddara da kuma kasancewa mai haku'ri da duk yanda rayuwa ta zo maka...

Gyaran murya tayi tace "professor, ka yi haku'ri wanna abun yana daga cikin zanen kaddarar ka, Wanda
bawa bai isa ya tsalla ke ba.

Kaga irin abinda nake yawan gaya maka, wanna dukiya Allah ne ya baka shi, zai kuma iya amsa a duk
lokacin daya so.

RAYUWAR nan babu komai a cikinta, cikin seconds kalilan Allah zai iya sanja K'yak'yyawa zuwa mummuna,
ya kuma sanja mummuna zuwa kyakyyawa...

A akan me toh zaka ce baka ga inuwa da talaka, Allah ɗa kan shi ya ƙarrama dan Adam, wane mutum dazai
wulaƙanta hallitar Allah?
A yau ga misali ka gani a kanka, ina dagawa da dukiyar da ƙaƙe iko da taƙama dashi? Shiyasa nace kabi
duniya a sannu!

Da yawa daga cikin masu dukiya irin ku basa fidda ZAKKAH bayan hakkin Allah ne, dole a fitar. Wasu kudin
su ya kai yin zakkah amma basa yi, basa taimako mabukata, basa taimakon marayu ɗa sauran su.
Ɗa kuƴi haka, ƙu gwanmace kuyi wani abu wanda darajar ku zai karu a idon abokan ku masu hannu da
shuni.
Tayaya masifa baza su yi yawa a Al'ummar mu ba, I tell you akwai gidajen da basa d'aura tukunyar tuwo a
gidan su saboda rashin babu, I tell you akwai ahalin da rana zai fito ya faɗi amma basu saƙa koɗa loma
daya na abinci a baki ɓa tabbas akwai da yawa, wallahi aƙwai, kuma na san ka sani, amma da ku taimaka
marasa shi ku gwanmace kuyi facaƙa da kudin da ƴin abinda bashi da wani amfani, dan haka think
Professor! ka sanja, ka daina wulakanta talaka, kai taimaki marasa shi, ina mai tabbatar maka zaka ga sanji
da haske a rayuwar ka ta duniya dama lahira. Idan kalamai na sun bata maka rai kayi hakuri, amma gaskiya
ce dole na fada domin na fita hakkin ka.
Sai da safe na barka lafiya" Mommah ta karasa tana barin falon...

A kafatanin rayuwar Daddy babu kalaman da suka shiga kwanyar sa, kana suka samu muhallin zama a
zuciyar sa kamar wanna ba.

Sosai wani mugun nadama ya shige shi, abin ba a cewa komai, ya jima a zaune cikin zurfin tunani,
wulakanci da yayi wa fadeel da Sadaukar ɗa ƙodar ɗa Mahmah taƴi ga tilon 'yar sa yafi komai tsaya masa
arai, sai yanzu yake nadama mai tarin yawa.

Sai karfe biyun dare ƴa ɓar falon, ya shige bedroom din shi, toilet ya shiga ya yi alwala yazo ya shimfud'a
sallaya ya shiga jera nafilfili abinda ya dauki shekaru rabon shi da yi wato SALLAH'N DARE, daga karshe ya
dora da karatun Qur'an.

**********

Zaune take kan cinyar sa, Yayinda ya zagaye hannayen sa, kan shafaffan cikin ta.

So yake ya sanar da ita abinda ya faru, amma baya son damuwar ta, bayan wanda suke ciki, domin yau
kwana uku kenan daya samu labari abinda ya samu Daddy.

"Kallon shi tayi tace " my one anya su Daddy na lafiya kuwa? naga baɓu wanɗa ƴa ƙira ni"

"Cikin sauri yace "eh suna lafiya, so suke ki saba da gidana sannan ku fara kira, domin karki ce kin fasa
zama a nan, ki ɓarni " ya fada domin kwantar mata da hank'ali.
Murmushi ta saki tana jin nutsuwa a ranta, sak'amak'on abinda yace, hannu ya mika ya dauko wani
kyakyyawan jaka mai kyalli ɗaƙe gefen su ya dora kan cinyar ta.

Karba tayi tana bin shi da kallon mamaki, budewa tayi taga wayoyi ne masu tsadar gaske guda goma,
bakwai android sai uku keypad amma mai tsadar gaske, sai kuma kalolin rigar waya(pouch) masu k'yau da
kyalli zubin mata, ya siya mata diffrent colors ɗomin ta dinga sanjawa.

Cikin su akwai *Stuart Hughes iPhone 4s Elite gold wanna tsadar sa yakai $9.million, sai falcon supernova
wanna kudinsa yakai $6.2million sai iPhone 8pink diamond $48.5 million, sai Gresso las Vegas jackpot
wanda kudinsa yakai $1million, sai supernova iphone 6 wanda kudin sa $3millon, sai million goldish de
million wanda kudinsa ya kai $1.5 million, sai black diamond iphone wanda 10 kudinsa yakai $18.6million*
Da dai sauran su...

Sosai fadeelah tayi shiga zallan mamakin, she can't even say a word. Ganin wanna uban wayoyin haka,
wasu ma sun fi nata tsada ma.

"My one duka wayoyin nan nawa ne?" Jinina mata kai yayi cikin tabbaci.

"Amma sunyi yawa, baya ma ina da wayoyin amma ka siyi wadan nan" ta fada domin ganin ya kashe kudi
masu yawan gaske.

"Na san kina da wayoyi ai hajiya Fadeelah! amma bana son kiyi amfani da wandan can, so nake kiyi
amfanin da wanda na siya miki da kudina. Ban saniba ko tsadar wadannan ne basu miki ba, amma ina so
komai na wad'ata ki dashi, koda bazai kai tsad'ar wadanda kika saba amfani dasu ba, amma ina son kiyi
amfani da abinda ya fito daga hannuna domin hakkin nane hakan, duk namijin kwarai baya damuwa da
dukiyar da matar sa take dashi, matuƙar yana shi toh ya zama hakkin sa ya sauke, sai dai idan bukatar
taimakon juna ya tashi bashi da halin komai tofah wanna ba laifi su taimakawa juna" ya karasa yana dora
habansa kan kafadar ta.

Cikin jin dadi tace "lah! zaujee sam baƙa fahimce ni ba, a ganina tunda aƙwai waɗancan nawa toh, bai
kamata ka ɓata kudi ƙa siyi wasu ba, a ganina gwara ayi wani abun da kudin, ba wai ina nufin sun min
kaɗan ɓane, ko kuma ina nufin tsadar su bai yi min ba, amma kayi hakuri kajiiiii" ta ƙarasa cikin iyakar
gaskiyar ta.

Sai yanzu ya fahimce ta, tabbas shi shaida ne fadeelah ba mai rainuwa bace, shima ya fada ne kawai domin
jin abinda zata fada, jinjina mata kai yayi kana ya bata light kiss a kumatu yace "na mayar miki da dukkanin
sim dinki ciki, da sauran abubuwan amfanin ki, sannan na goge su daga wadancan wayar na kyautar dasu,
zaki iya amfani da wadannan domin duk na caja su, na so baki tun washegarin auran mu, na sha'afa
saboda abubuwan da suka sha min kai, in sha Allah da mun sake samun nutsuwa zan siya miki wasu..."

Kallon shi take with more admiration tace " a'a wallahi wadannan ma sun isa haka my one, Allah ya saka
maka da alkhairi fil duniya wal Akirah, Allah ya...."

Labb'anta ya kamo ya shiga kissing din ta, domin bai ga abin godiya ba, matuk'ar Allah ya hore mishi, zai
cigaba da wadata ta da dukkanin wani jin dadin rayuwa, domin ta cancanci fiye da hakan...

Ɗa yamma ya shirya zuwa estate wajen Daddy, amma sam bai sanar da Fadeelah'n inda za shi ba, har
bakin kofa ta kara shi suka yi sallama cike da son juna, nan ya shiga daya daga cikin motocin sa kirar
*Lamborghini zonda sian FKP* baki, sannan sauran motocin escort d'in sa suka faɗa sauran motocin, a
jera reras gwanin burgewa suka nufi *IKOYI*, unguwar su Fadeelah.....

Share fisabilillah habibtie's

Noor🔥
07082281566

I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*

💝ƘƳAUTAR ƘOƊA💝
(It's all about love, scracifes, hatred and destiny)
*WATTPAD*
@NoorEemaan

ELEGANT ONLINE WRITER'S📚🖊

https://facebook.com/groups/943534712916776/masu amfani da facebook su yi join ta wanna link din.

EDITING IS NOT ALLOWED❌

*A gaskiya ina godiya a gare ku habibtie's da kaunar da kuke nunawa kyautar koda har da papi ne! ina
godiya sosai ga readers din wanna tagwayen littafan nawa ɗa wanda na sani da wanda ban sani ba, ina
muku son so fisabilillah, Nooreemaan taku ce, Fadeelah da Fadeel ma naku ne😁*

Page 65-66

Tsakiyar yalwataccen farfajiyar cikin estate din motocin Fadeel suka tsaya, kana daya daga cikin escort d'in
sa suka yiwa security din estate din magana kan ya nemawa fadeel iso wajen Daddy surukin sa ne ya kawo
masa ziyara, ai fa babu bata lokaci security ya nufi falon professor ciƙin sauri domin ya sanar da shi...

Zaune Daddy yake a falo, ƴayi Shiru tamkar mara lafiya, har wata rama yayi gwanin tausayi, tare da shi
akwai Mommah, Grandma, da wasu yan uwa sa dake cikin estate d'in.

Cikin girmamawa security'n, yace "boss! mijin ma'am ne yazo"

Cikin zallan mamaki Daddy ke kallonsa, bayan tarin wulakancin da ƴa yiwa yaron nan har yazo gaishe shi,
kallon security yayi, a sanyaye yace "let him in"

Cikin girmamawa security ya juya ya koma, kana ya sanar da su Fadeel cewa Daddy yace ya shigo.
Cikin takun nutsuwa da birgewa ya nufi falon Daddy, bud'e masa kofa escort d'in sa sukayi, kana suka
gaishe da Daddy cikin girmamawa suka fita, sosai Daddy yayi dadin hakan, gaban Daddy Fadeel ya durƙusa,
gabansa na faduwa ya gaishe shi, wani yanayi ne ke shiga jikinsa, har wani tashi tsigar jikinsa yake, sosai
wani tarin nadama ya rufe Shi, hannu ya mika wa fadeel alamun suyi musabaha...

Sosai zallan mamaki ya rufe Fadeel, amma bai nuna ba, hannun ya mika wa daddy'n sukayi musabaha cikin
girmamawa, still dai kansa na kasa.

Mommah dake kallonsu tayi murmushi daya taho da zubar hawayen ta, wanda na zallan tausayi ne, ta ma
rasa wa take tausayawa a cikin su.

Gaishe da su Mommah yayi cikin girmamawa, amsawa suka yi, fusk'ar su dauke da murmushi, domin sun
san FADEELAH ta more miji...

Hannun shi Daddy ya kama ya zaunar shi kan hada'dd'en kujeran kusa da shi, yana jin farinciki na ratsa
zuciyar sa, hakika ba kudi kadai bane dajarar mutum, mutunci da sanin darajar dan Adam ma wani abu ne,
wanda bai fahimci hakan ba sai yanzu, sosai yaji dadin girmamawan da Fadeel ya bashi bayan duk tarin
wulakancin da ƙasƙancin daya masa...

Nan Fadeel yayi masa jaje sosai, ya kuma yi masa add'uar Allah Ya tsare gaba. Amsawa Daddy yayi har
cikin ransa ya ji dadi, hakan ma su Mommah...

Mintunan sa goma da zama ya daga tsadaddiyar wayar sa ya kira daya daga cikin escort d'in sa, magana
biyu zuwa uku yayi ya katse wayar...

Babu jimawa escort biyar suka shigo da manya_manyan jaka guda biyar, da kyar suke dagawa saboɗa
nauƴi, gaban Daddy suka dire, kana suka fice cikin girmamawa....

Kallon karin bayani da mamaki Daddy yayiwa Fadeel, ba tare da ya iya furta ko da harafi daya ba...

Ba bata lokaci Fadeel yace "hakika Daddy asarar daka yi, babu mai iya biyan ka, ko ya maye maka ɗa mafi
alkhairin sa sai Allah'n daya baka, wandannan kudaden billion dubu sitti ne, ka yi amfani da shi domin kara
farfado da business dinka"
Shiru wajen ya dauka tamkar ruwa ya cinye su, sosai mamaki da kyawun zuciya irin na Fadeel ya kama shi,
cikin wani mamakin Daddy ya fisgo maganar kamar haka "A'a ka bar shi, ka barshi please nagode kwarai,
akwai yan kudade a hannuna zan yi amfani dasu"

Tabbas Daddy is a changed person now, domin managar sa cikin sanin mutunci da darajar dan Adam yake
yinsa yanzu, Fadeel ya aiyana a ransa kana a fili yace "please Daddy ka karba, ba dan ni ba, idan baka karba
ɓa, hakan na nufin baka dauke ni d'a ko nace suruki a gareka ba"

Sosai kunya da nadama suka sake rufe Daddy, tabbas ya ji kunya ba kadan ba, wanda yake cewa baƙin
talaka fakiri shine yau ya bashi taimakon zunzurutun kudi har billion dubu sitti...

Cikin sanyi jiki yace "sam ba haka bane, amma duk tarin wulakancina a gareka har sai da ka taimaka min da
kudi har haka kai...."

Katse shi fadeel yayi da cewa "na manta komai Daddy, ban taba rike ka a raina ba, fadeelah ita ce jinin
jikina, dole na so komai nata, bare kai da kake ɗa ɓabban matsayi a gareta, sannan kudin nan ba taimakon
ka nayi ba, ka dauka cewa tamkar fadeelah ce ta baka a matsayin ta na 'yarka, nima d'a nake a gareka, ka
karba please Daddy hakan zai sa naji dadi"

Kasa magana Daddy yayi, sai rungume Fadeel daya yi zuwa jikinsa, ba tare da ya sani ba, yaji hawaye na
zuba a idanun sa, sosai yaji Fadeel ya burge shi kana ya samu muhallin a zuciyar sa, ji yake dama hannun
agogo ya dawo baya, ya goge tsana, cin fuska, hadi da wulakancin daya yi masa a baya...

Cikin hikima ya goge hawayen sa Saboda kada a gane, amma ina ya makaro domin fadeel ya ji digowan
hawayen a jikin sa...

Cikin sanyin murya Daddy yace "Allah ya yi maka albarka, ya baka dukkanin farincikin rayuwar ka, ka
yafemin, abubuwan dana aikata agareka, na san...."

Katse shi Fadeel yayi da cewa "babu komai Daddy baka min komai ba, ni zan tafi na bar fadeelah ita kadai"
ya fada feeling free domin baya iya 6oye tsananin son da yake wa Fadeelah'n shi ko a gaban waye...
Murmushin farinciki Daddy yayi, yana jin farinciki sosai, domin 'yar sa daya tilo ta samu miji mai tsananin
nuna kulawa da so a gareta, tabbas wanna abin farinciki ne.

Kallon Fadeel yayi yace "alright! my regard to my princess please, amma bata da masaniya kan abinda ya
faru dani ko? domin bana son hankalin ta ya tashi"

Jinjina kai fadeel yayi alamun "eh" domin shima bazai so tashin hankalin wiffy din shi ba.

Ɗukawa yayi, kana ya yiwa su Mommah sallama, albarka suka sanya masa, kana ya fita, yayinda suka bi shi
da kallon alfahari, har wajen mota Daddy ya raka shi,... fadawa mota yayi bayan sun sake sallama da
Daddy, a jere motocin sa suka bar gidan.

A hanya magriba tayi musu, hakan yasa suka faka motocin su a gefen hanya kamar yadda Fadeel ya bada
umarni, babban masjid din dake gefen hanyan suka nufa bayan sunyi alwala, yayinda wasu da ba muslimai
ba cikin escort din suka tsaye jikin motocin, suna jiran su Fadeel su idar da sallar, bayan mintuna goma sha
biyar suka fito, bude masa motar aka yi, kana escort's suka fada sauran motocin, wuta suka bawa motar
kana suka nufi BANANA ISLAND gidan Fadeel....

Zaune ya tarar da Fadeelah ta kurawa babban cinema ido, amma sam ba Kallo take ba, domin hankalin ta
baya wajen....

waya na makale a kunnen sa ya shigo, da alama da alhaji Sufyan yake, jin muryar sa ya sanya Fadeelah
dawowa daga duniyar tunanin da ta afka, ajiyar zuciya ta sauke kana ta nufi shi, ba tare da yayi magana ba
ya ware mata hannun sa daya, kasancewar dayan na makale da waya, da gudu ta shige jikinsa ya rufe
hannun sa, sun dauki mintuna goma suna waya da alhajin, har yace a bawa fadeelah su gaisa, babu musu
ya kara mata wayar a kunne, bayan sun gama gaisawa ya katse wayar, cillar da wayar yayi kan hada'dd'en
kujerar falon...

Hannunsa zagaye da waist din ta yace "wiffy ya gida?"

Turo baki tayi cikin shagwa'ba tace "Bayan ka tafi ka barni da kewar ka, wai ina ma ka je?"

"Am so sorry my Darling, naje wata yar unguwa ce, amma ki sani duk inda nake kina makale a nan dina" ya
fada yana nuna saitin k'irjin sa, rungume Shi tayi tana sauke ajiyar zuciya, ƴayinda dad'add'an k'amshin
turaren sa ke ratsa kofofin hancin ta, sun jima a haka suna jin dumin juna, kana Fadeel ya rike hannun ta
suka nufi wani sashe na gidan, wanna fadeelah bata san da shi, a kuma nan yake son su kwana yau....
_11:00pm_

A wahalce ya mirgina gefe yana sauke numfashi, babu abinda yake sai dafa marar sa, fadeelah ce ta
kwantar da kanta kan k'irjin sa cikin sanyin jiki, domin romance din da suka yi having ya saka jikinta
mutuwa ainun, numfashi ita ma ta sauke tana jin hawaye ya ciko Idanunta, lumshe idanun ta tayi
sak'amak'on shafa bayanta da yake, hakan ya bawa hawayen damar zubowa, cikin sheshek'ar kuka tace
"My one zuwa yaushe zaka cigaba da azabtar da kanka, Allah ya gani ni ban hana ka hakkin ka ba, sai ma
kai da kake ta ki, bana son ganin ka cikin wanna mayuwancin hali irin haka, na...."

"Shhhhh!" Yace yana dora soft hand dinsa saman tattausan labb'anta alamun tayi Shiru.

"Bazan iya ba fadeelah, bana son mu haifi ɗa da cuta, ina tsoro matuka, amma ina da mafita daya, zan
sama mana mafita ok, stop crying"

Cikin kuka tace "ta yaya zan daina kuka bayan kana wahala, toh ka dawo da numfashin ka daidai" ta fada
tana kallon yanda yake fitar da numfashi hurrily...

Dariya ta bashi, "banda abin ki my Darling ba fa ni nake yi ba, amma na daina kinji" ya fada shafa
yalwataccen gashin kanta da bai fiye cika ba, haka ya dinga kwantar mata da hankali, har bacci ya dauke ta,
shima baccin yayi da kyar, da niyyar dole ya samo musu mafita, duk da abinda yake shirin yi yasan akwai
hadari sosai, inma ya rasa ransa ko ya rayu, amma tabbas bai da mafita sai na yin hakan...

*WASHEGARI*

Da misalin karfe goma ta farka sak'amak'on hasken rana daya shigo ta window, sosai tayi mamakin nauyin
baccin da ta yi, dadin ta ma tayi sallar asuba, ta kuma san kan sallaya wani baccin ya sake daukar ta, amma
gashi ta ga kanta a gado, ta kuma san Fadeel ne ya dawo da ita kan gadon....

Kallon dakin tayi ta ga ba kowa, toilet ta fada tayi brush kana tayi wanka, fitowa tayi hannunta kan
kugunta, tana tunanin ta ina zata fara dubo shi cikin uban gidan nan mai girma, fadi, hadi da tsaho...
Saboda part da dakunan da yawa, bata san wani wajen zata fara bi ta neme shi ba, take kuma tunanin
kiran sa yazo kwanyar sa hakan yasa ta nufi daya daga cikin wayar ta dake kan gado, wata farar takardan ta
ga an dora kan wayar, haka kawai taji gabanta ya fadi, ta fara koƙarin kiran wayar sa, sai taji zuciyar ta na
azalzalar ta kan ta duba takardan, duk da gabanta na fadu'wa haka ta ware paper'n kyakyyawan rubutun
Fadeel mai k'yau da tsari ne ya bayyana, cikin sauri ta fara karantawa kamar haka...
_my wiffy_

_I knew zaki ga wanna takardan, domin ke na rubuta shi, ban sanar dake ba, saboda nasan zaki hanani kice
kece zaki yi, ina mai baki hakuri ban yi dan na bata miki rai ba, nayi ne domin shine kadai mafitan da muke
dashi, bayan sallar asuba, a yau na bar kasar nan zuwa America, na tafi domin a canja min jinina kaf zuwa
wani, ta hakan ne zamu haifi lafiyayyun yara, idan Allah ya nufa, add'uar ki nake nema, domin ban san
tsawon lokacin da zan dauka ba, ban kuma san zan rayu ko zan mutu ba, bayan an chanja min jinin. Domin
gabadaya jinina za a kwashe, a musanya min da wani jinin, domin blood group dimu ya yi match, ta hakan
ne za mu rayu cikin farinciki, kada kiyi kuka please, I will miss you so much fadeelah, kaunar ki kadai ce da
cikar burin mahmah ta sani yin hakan, kiyi min add'ua sannan ki kular min da kanki, FFM loves you_.....

*(Billahi banga ruwan comment ba, Baku ganin update ranar lahadi)*

Mu je zuwa Guys😎🔥

_Sai ranar lahadi idan mai kowa mai komai ya ara mana rai_.

Share fisabilillah

Comment din ku is needed

Noor Eemaan😍🔥

I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*

💝ƘƳAUTAR ƘOƊA💝
(It's all about love, scracifes, hatred and destiny)

*WATTPAD*
@NoorEemaan

ELEGANT ONLINE WRITER'S📚🖊

https://facebook.com/groups/943534712916776/masu amfani da facebook su yi join ta wanna link din.

EDITING IS NOT ALLOWED❌

*A gaskiya ina godiya a gare ku habibtie's da kaunar da kuke nunawa kyautar koda har da papi ne! ina
godiya sosai ga readers din wanna tagwayen littafan nawa ɗa wanda na sani da wanda ban sani ba, ina
muku son so fisabilillah, Nooreemaan taku ce, Fadeelah da Fadeel ma naku ne😁*

Page 65-66

Tsakiyar yalwataccen farfajiyar cikin estate din motocin Fadeel suka tsaya, kana daya daga cikin escort d'in
sa suka yiwa security din estate din magana kan ya nemawa fadeel iso wajen Daddy surukin sa ne ya kawo
masa ziyara, ai fa babu bata lokaci security ya nufi falon professor ciƙin sauri domin ya sanar da shi...

Zaune Daddy yake a falo, ƴayi Shiru tamkar mara lafiya, har wata rama yayi gwanin tausayi, tare da shi
akwai Mommah, Grandma, da wasu yan uwa sa dake cikin estate d'in.

Cikin girmamawa security'n, yace "boss! mijin ma'am ne yazo"

Cikin zallan mamaki Daddy ke kallonsa, bayan tarin wulakancin da ƴa yiwa yaron nan har yazo gaishe shi,
kallon security yayi, a sanyaye yace "let him in"
Cikin girmamawa security ya juya ya koma, kana ya sanar da su Fadeel cewa Daddy yace ya shigo.

Cikin takun nutsuwa da birgewa ya nufi falon Daddy, bud'e masa kofa escort d'in sa sukayi, kana suka
gaishe da Daddy cikin girmamawa suka fita, sosai Daddy yayi dadin hakan, gaban Daddy Fadeel ya durƙusa,
gabansa na faduwa ya gaishe shi, wani yanayi ne ke shiga jikinsa, har wani tashi tsigar jikinsa yake, sosai
wani tarin nadama ya rufe Shi, hannu ya mika wa fadeel alamun suyi musabaha...

Sosai zallan mamaki ya rufe Fadeel, amma bai nuna ba, hannun ya mika wa daddy'n sukayi musabaha cikin
girmamawa, still dai kansa na kasa.

Mommah dake kallonsu tayi murmushi daya taho da zubar hawayen ta, wanda na zallan tausayi ne, ta ma
rasa wa take tausayawa a cikin su.

Gaishe da su Mommah yayi cikin girmamawa, amsawa suka yi, fusk'ar su dauke da murmushi, domin sun
san FADEELAH ta more miji...

Hannun shi Daddy ya kama ya zaunar shi kan hada'dd'en kujeran kusa da shi, yana jin farinciki na ratsa
zuciyar sa, hakika ba kudi kadai bane dajarar mutum, mutunci da sanin darajar dan Adam ma wani abu ne,
wanda bai fahimci hakan ba sai yanzu, sosai yaji dadin girmamawan da Fadeel ya bashi bayan duk tarin
wulakancin da ƙasƙancin daya masa...

Nan Fadeel yayi masa jaje sosai, ya kuma yi masa add'uar Allah Ya tsare gaba. Amsawa Daddy yayi har
cikin ransa ya ji dadi, hakan ma su Mommah...

Mintunan sa goma da zama ya daga tsadaddiyar wayar sa ya kira daya daga cikin escort d'in sa, magana
biyu zuwa uku yayi ya katse wayar...

Babu jimawa escort biyar suka shigo da manya_manyan jaka guda biyar, da kyar suke dagawa saboɗa
nauƴi, gaban Daddy suka dire, kana suka fice cikin girmamawa....
Kallon karin bayani da mamaki Daddy yayiwa Fadeel, ba tare da ya iya furta ko da harafi daya ba...

Ba bata lokaci Fadeel yace "hakika Daddy asarar daka yi, babu mai iya biyan ka, ko ya maye maka ɗa mafi
alkhairin sa sai Allah'n daya baka, wandannan kudaden billion dubu sitti ne, ka yi amfani da shi domin kara
farfado da business dinka"

Shiru wajen ya dauka tamkar ruwa ya cinye su, sosai mamaki da kyawun zuciya irin na Fadeel ya kama shi,
cikin wani mamakin Daddy ya fisgo maganar kamar haka "A'a ka bar shi, ka barshi please nagode kwarai,
akwai yan kudade a hannuna zan yi amfani dasu"

Tabbas Daddy is a changed person now, domin managar sa cikin sanin mutunci da darajar dan Adam yake
yinsa yanzu, Fadeel ya aiyana a ransa kana a fili yace "please Daddy ka karba, ba dan ni ba, idan baka karba
ɓa, hakan na nufin baka dauke ni d'a ko nace suruki a gareka ba"

Sosai kunya da nadama suka sake rufe Daddy, tabbas ya ji kunya ba kadan ba, wanda yake cewa baƙin
talaka fakiri shine yau ya bashi taimakon zunzurutun kudi har billion dubu sitti...

Cikin sanyi jiki yace "sam ba haka bane, amma duk tarin wulakancina a gareka har sai da ka taimaka min da
kudi har haka kai...."

Katse shi fadeel yayi da cewa "na manta komai Daddy, ban taba rike ka a raina ba, fadeelah ita ce jinin
jikina, dole na so komai nata, bare kai da kake ɗa ɓabban matsayi a gareta, sannan kudin nan ba taimakon
ka nayi ba, ka dauka cewa tamkar fadeelah ce ta baka a matsayin ta na 'yarka, nima d'a nake a gareka, ka
karba please Daddy hakan zai sa naji dadi"

Kasa magana Daddy yayi, sai rungume Fadeel daya yi zuwa jikinsa, ba tare da ya sani ba, yaji hawaye na
zuba a idanun sa, sosai yaji Fadeel ya burge shi kana ya samu muhallin a zuciyar sa, ji yake dama hannun
agogo ya dawo baya, ya goge tsana, cin fuska, hadi da wulakancin daya yi masa a baya...

Cikin hikima ya goge hawayen sa Saboda kada a gane, amma ina ya makaro domin fadeel ya ji digowan
hawayen a jikin sa...

Cikin sanyin murya Daddy yace "Allah ya yi maka albarka, ya baka dukkanin farincikin rayuwar ka, ka
yafemin, abubuwan dana aikata agareka, na san...."
Katse shi Fadeel yayi da cewa "babu komai Daddy baka min komai ba, ni zan tafi na bar fadeelah ita kadai"
ya fada feeling free domin baya iya 6oye tsananin son da yake wa Fadeelah'n shi ko a gaban waye...

Murmushin farinciki Daddy yayi, yana jin farinciki sosai, domin 'yar sa daya tilo ta samu miji mai tsananin
nuna kulawa da so a gareta, tabbas wanna abin farinciki ne.

Kallon Fadeel yayi yace "alright! my regard to my princess please, amma bata da masaniya kan abinda ya
faru dani ko? domin bana son hankalin ta ya tashi"

Jinjina kai fadeel yayi alamun "eh" domin shima bazai so tashin hankalin wiffy din shi ba.

Ɗukawa yayi, kana ya yiwa su Mommah sallama, albarka suka sanya masa, kana ya fita, yayinda suka bi shi
da kallon alfahari, har wajen mota Daddy ya raka shi,... fadawa mota yayi bayan sun sake sallama da
Daddy, a jere motocin sa suka bar gidan.

A hanya magriba tayi musu, hakan yasa suka faka motocin su a gefen hanya kamar yadda Fadeel ya bada
umarni, babban masjid din dake gefen hanyan suka nufa bayan sunyi alwala, yayinda wasu da ba muslimai
ba cikin escort din suka tsaye jikin motocin, suna jiran su Fadeel su idar da sallar, bayan mintuna goma sha
biyar suka fito, bude masa motar aka yi, kana escort's suka fada sauran motocin, wuta suka bawa motar
kana suka nufi BANANA ISLAND gidan Fadeel....

Zaune ya tarar da Fadeelah ta kurawa babban cinema ido, amma sam ba Kallo take ba, domin hankalin ta
baya wajen....

waya na makale a kunnen sa ya shigo, da alama da alhaji Sufyan yake, jin muryar sa ya sanya Fadeelah
dawowa daga duniyar tunanin da ta afka, ajiyar zuciya ta sauke kana ta nufi shi, ba tare da yayi magana ba
ya ware mata hannun sa daya, kasancewar dayan na makale da waya, da gudu ta shige jikinsa ya rufe
hannun sa, sun dauki mintuna goma suna waya da alhajin, har yace a bawa fadeelah su gaisa, babu musu
ya kara mata wayar a kunne, bayan sun gama gaisawa ya katse wayar, cillar da wayar yayi kan hada'dd'en
kujerar falon...

Hannunsa zagaye da waist din ta yace "wiffy ya gida?"

Turo baki tayi cikin shagwa'ba tace "Bayan ka tafi ka barni da kewar ka, wai ina ma ka je?"
"Am so sorry my Darling, naje wata yar unguwa ce, amma ki sani duk inda nake kina makale a nan dina" ya
fada yana nuna saitin k'irjin sa, rungume Shi tayi tana sauke ajiyar zuciya, ƴayinda dad'add'an k'amshin
turaren sa ke ratsa kofofin hancin ta, sun jima a haka suna jin dumin juna, kana Fadeel ya rike hannun ta
suka nufi wani sashe na gidan, wanna fadeelah bata san da shi, a kuma nan yake son su kwana yau....

_11:00pm_

A wahalce ya mirgina gefe yana sauke numfashi, babu abinda yake sai dafa marar sa, fadeelah ce ta
kwantar da kanta kan k'irjin sa cikin sanyin jiki, domin romance din da suka yi having ya saka jikinta
mutuwa ainun, numfashi ita ma ta sauke tana jin hawaye ya ciko Idanunta, lumshe idanun ta tayi
sak'amak'on shafa bayanta da yake, hakan ya bawa hawayen damar zubowa, cikin sheshek'ar kuka tace
"My one zuwa yaushe zaka cigaba da azabtar da kanka, Allah ya gani ni ban hana ka hakkin ka ba, sai ma
kai da kake ta ki, bana son ganin ka cikin wanna mayuwancin hali irin haka, na...."

"Shhhhh!" Yace yana dora soft hand dinsa saman tattausan labb'anta alamun tayi Shiru.

"Bazan iya ba fadeelah, bana son mu haifi ɗa da cuta, ina tsoro matuka, amma ina da mafita daya, zan
sama mana mafita ok, stop crying"

Cikin kuka tace "ta yaya zan daina kuka bayan kana wahala, toh ka dawo da numfashin ka daidai" ta fada
tana kallon yanda yake fitar da numfashi hurrily...

Dariya ta bashi, "banda abin ki my Darling ba fa ni nake yi ba, amma na daina kinji" ya fada shafa
yalwataccen gashin kanta da bai fiye cika ba, haka ya dinga kwantar mata da hankali, har bacci ya dauke ta,
shima baccin yayi da kyar, da niyyar dole ya samo musu mafita, duk da abinda yake shirin yi yasan akwai
hadari sosai, inma ya rasa ransa ko ya rayu, amma tabbas bai da mafita sai na yin hakan...

*WASHEGARI*

Da misalin karfe goma ta farka sak'amak'on hasken rana daya shigo ta window, sosai tayi mamakin nauyin
baccin da ta yi, dadin ta ma tayi sallar asuba, ta kuma san kan sallaya wani baccin ya sake daukar ta, amma
gashi ta ga kanta a gado, ta kuma san Fadeel ne ya dawo da ita kan gadon....

Kallon dakin tayi ta ga ba kowa, toilet ta fada tayi brush kana tayi wanka, fitowa tayi hannunta kan
kugunta, tana tunanin ta ina zata fara dubo shi cikin uban gidan nan mai girma, fadi, hadi da tsaho...
Saboda part da dakunan da yawa, bata san wani wajen zata fara bi ta neme shi ba, take kuma tunanin
kiran sa yazo kwanyar sa hakan yasa ta nufi daya daga cikin wayar ta dake kan gado, wata farar takardan ta
ga an dora kan wayar, haka kawai taji gabanta ya fadi, ta fara koƙarin kiran wayar sa, sai taji zuciyar ta na
azalzalar ta kan ta duba takardan, duk da gabanta na fadu'wa haka ta ware paper'n kyakyyawan rubutun
Fadeel mai k'yau da tsari ne ya bayyana, cikin sauri ta fara karantawa kamar haka...

_my wiffy_

_I knew zaki ga wanna takardan, domin ke na rubuta shi, ban sanar dake ba, saboda nasan zaki hanani kice
kece zaki yi, ina mai baki hakuri ban yi dan na bata miki rai ba, nayi ne domin shine kadai mafitan da muke
dashi, bayan sallar asuba, a yau na bar kasar nan zuwa America, na tafi domin a canja min jinina kaf zuwa
wani, ta hakan ne zamu haifi lafiyayyun yara, idan Allah ya nufa, add'uar ki nake nema, domin ban san
tsawon lokacin da zan dauka ba, ban kuma san zan rayu ko zan mutu ba, bayan an chanja min jinin. Domin
gabadaya jinina za a kwashe, a musanya min da wani jinin, domin blood group dimu ya yi match, ta hakan
ne za mu rayu cikin farinciki, kada kiyi kuka please, I will miss you so much fadeelah, kaunar ki kadai ce da
cikar burin mahmah ta sani yin hakan, kiyi min add'ua sannan ki kular min da kanki, FFM loves you_.....

*(Billahi banga ruwan comment ba, Baku ganin update ranar lahadi)*

Mu je zuwa Guys😎🔥

_Sai ranar lahadi idan mai kowa mai komai ya ara mana rai_.

Share fisabilillah

Comment din ku is needed

Noor Eemaan😍🔥

I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*

💝ƘƳAUTAR ƘOƊA💝
(It's all about love, scracifes, hatred and destiny)

*WATTPAD*
@NoorEemaan

ELEGANT ONLINE WRITER'S📚🖊

https://facebook.com/groups/943534712916776/masu amfani da facebook su yi join ta wanna link din.

EDITING IS NOT ALLOWED❌

No editing🤒

Page 67-68

........Wani mugun ƙara mai hade da Salati fadeelah ta saki, kana ta shiga kuka mai sautin gaske gwanin
tausayi, fadi take "fadeelah don't do this to me, Ka dawo, ka dawo please kada ka min haka, ka dawo mu
rayu tare ko da baza mu haihu ba, bazan iya juran rasa ka ba, wanna aikin na da matuƙar hadari, ka dawo
please Fadeeeeeeeeeeel" ta kara sa tana zubewa kan gadon ta shiga rera kuka gwanin tausayi, ta jima
sosai tana kukan domin ta fi awa d'aya, har idanun ta ya fara yaji sosai ko bud'e su bata iya wa, sosai
zazzabi mai zafin gaske ya rufe ta.
Haka ta kasance har karfe hudun yamma, sallar azahar da la'asar ma a zaune tayi ta, domin ko k'arfin
tsayuwa bata da shi, tun safe bata sa komai a cikinta ba, minti d'aya biyu sai kaga hawaye ya balle mata
gwanin tausayi...

bayan sallar ishaq ta ga yunwa na kokarin yi mata illa sannan ta rarrafa bakin hada'dd'en medium size
fridge ta dauko yogurt mai mixed fruit, bakin ta na rawa haka ta kafa baki ta sha sosai fiye da rabi, kana ta
dire robar a gefe tana sauke numfashi tamkar wacce tayi tseren gudu....

Ta kai mintuna goma a zaune cikin mayuwancin hali kana ta Mike da kyar ta koma kan gado...

Sosai wani mugun sanyi ke shiga jikin ta, gashi dama bata saka kaya ba, domin tun towel din safe shine har
yanzu a jikinta, haka ta yi ta zumbula yalwataccen hijab take sallar da shi...

Da kyar ta ja duvet bedsheet ta rufe jikinta da shi tana sauke huci da numfashi irin na masu zazzabi....

Ta bangaren masu aiki kuwa sosai sukayi mamakin ganin su Fadeelah basu taba abinci safe, rana, bare na
dare ba, domin basu da matsaniƴa kan Fadeel baya kasar, gashi Fadeel bai bawa ma'aikatan sa damar shiga
part part din gidan a akodayaushe ba, musamman bedrooms din.

rashin taɓa abincin ya dan basu tsoro amma sai suka dauka ko basa gidan ne, domin sun san waye Fadeel
ya kan fita wani zubin bai sanar da su ba, musamman idan ba lokacin aikin su bane, domin a Cewar sa baya
son shiga hakkin ma'aikatan sa ...

*WASHEGARI*

Har yanzu fadeelah bata bar kukan ba, sai ma abinda ya karu, domin fadeel ya sabar mata kwanciya a jikin
sa musamman d'addare, hakan yasa ta ga daren jiya yayi mata nisan gaske...

Wanka tayi da kyar, tayi brush kana ta sanya wani palazzo trouser da wata riga daya zo mata guiwa, wanda
bai kamata ba, sai tayi rolling da black Veil, wani flat palm sandals ta sanya a kafarta, komai a sanyaye take
yin sa, amma hakan bai boye kyan ta ba, wani babban sunscreen (glass or tabarao) ta saka a fuskar ta
domin ya boye kumburin fusk'ar ta....
Waje ta fita, sosai tayi kokarin danne hawayen ta, nan ta tarar da tarin ma'aikata, security, hadi da escort
din sa, wasu a tsaye wasu a zaune, wasu na zaga gidan domin tabbatar da tsaro....

Cikin girmamawa suka shiga gaisheta, amsawa tayi tana kokarin k'ak'aro murmurshi, tun kafin ta isa wajen
har sun bud'e mata kofar wata had'add'iyar *Mercedes Benz* ash color domin ta shiga...

Kallon wanda ya bud'e motar tayi, tace "ku barshi zan fita ni kadai karku damu"

Kansa a kasa cikin girmamawa yace "sorry madam, bazai yu ki yi tuki ke kadai ba babu tsaro, domin
yallabai ya ja mana kunnen kan hakan tun washegarin ranar da kika tare, please ki yi hakuri ki barmu muyi
aikin mu kamar yadda boss din mu ya bamu umarni" Ya karasa cikin tsantsar ladabi.

"ok fine" fadeelah tace tana zama cikin motar a sanyaye, yayinda sauran suka fada sauran motocin domin
bata tsaro, a jere reras suka bar gidan, "estate dinmu muka nufa" abinda tace wa driver kenan ta lumshe
idanun ta Yayinda hawaye masu zafi suka ciko Idanunta ta, tsananin kewa da tsoron rasa shi ne suka yiwa
zuciyar ta kawanya....

Jin tsayuwar motocin ya tabbatar mata da sun iso estate dinsu, cikin hikima ta share hawayen ta, kana ta
daidaici muryarta tace wa driver'n daya tuko ta su tafi idan zata dawo bodyguards din estate dinsu zasu
dawo da ita, cikin girmamawa ya amsa, already an riga an bud'e mata kofa, hakan yasa ta sanya kai ta
fita....

Sosai ma'aikatan gidan suka gaishe ta, kowa fusk'ar sa dauke da murmushi da farincikin ganin ma'am dinsu
da ta san darajan mutane, sosai ta dinga sakar musu murmushin yake domin bata son kowa ya fahimci
halin damuwar da take ciki...

Part din Mommah ta nufa, tana daf da shiga Parlon mommah ta ga kukun Grandma to zo fita, hakan yasa
ta tsaya suka gaisa kana matar ta dora da fadin "ya muka ji da asaran da mai gida yayi, toh Allah ya tsare
gaba ya kiyaye"
Sosai zallan mamaki ya kama fadeelah, wani asara kenan Daddy yayi? Ta aiyana a ranta, amma sai bata
nuna ba tace "Alhamdulillah"

Cikin sauri ta nufi part din Mommah, cikin wani sabon tashin hankali, ta kuwa tarar da Mommah zaune,
tare da Daddy...

Cikin sauri ta fada jikin Daddy tana saukin wani kuka mai dauke da abubuwa da dama... Cikin tashin hankali
mommah da Daddy suka hada baki wurin fadin

"Subhanallahi! Sweetheart, princess, meya faru?"

Wani kuka mai sautin gaske ta kara saki tace "Mommah! Daddy! Fadeel ya...ta...fi...ya barni"

"Innalillahi! ya tafi ya bar ki, zuwa ina?" Mommah ta fada hankali a tashe, gabanta na fadu'wa,
sak'amak'on bata san amsar da Fadeelah zata basu ba...

Sai da Fadeelah ta saki wata sheshek'ar kuka kana tace "y...ya...ta..fi....a Sanja masa jinin sa zuwa wani
blood group din, domin shima blood group din sa SS ne"

"Innalillahi wa innah ilaihi raju'un" suka fada hankali a tashe, domin sun san had'arin dake cikin aikin, duk
da sun san cewa fadeelah SS ce, amma basu taba tunanin shima Fadeel din SIKILA bane sak'amak'on yana
da ginanan jiki, ga kuma yanda bikin yazo, hakan yasa babu wanda hankalin shi ya kawo kan suyi blood
group test irin wanda ma'aurata masu son mallakar junansu ke yi yanzu...

Daddy kasa magana ma yayi, domin sabon nadama, da kaunar Fadeel din ne ya rufe shi, tabbas Fadeel na
matuk'ar son gudan jinin sa, tunda har zai iya zuwa a cire masa jinin sa kaf a sanya masa wani, duk da
yasan hadarin dake cikin aikin, ya kuma godewa Allah da Fadeel ya kasance cikin ahalin sa, domin samun
kamar sa a wanna al'ummar tamu da wuya, haka kuma rasa shi a Al'ummah babban rashi ne.

Mommah kuwa sosai ta dinga taya fadeelah kuka, domin wanna maganar da Fadeelah ta zo musu da shi
ya shige ta matuk'a.

Duk jikin su a sanyaye yake, ga kukan fadeelah yaki karewa sannan suka hau lallashin ta hadi da kalamai
masu kwantar da hank'ali, Shiru tayi lamo jikin Daddy tana sauke numfashi, sosai suka tausaya mata,
Daddy ya kuma ji dadi da Fadeelah ta samu muradin ranta (fadeel) da bai san halin da zata shiga ba, domin
rashin ganin sa kadai ya sa ta shiga wanna halin, ina ga bata mallaki shi ba?...

"Daddy wani asara kayi naji kukun Grandma na mun jaje?" fadeelah ta katse masa tunani da muryar kukan
ta...

Daddy bai so ta sani ba, domin kada hankalin ta ya tashi, amma yanzu dole zai sanar da ita, saboda zancen
duniya bata 6uya...

Nan Daddy ya shiga sanar da ita dalla² daga asarar da yayi, wa'azajin mommah a gare shi, da zuwan Fadeel
gidan, hadi da uban kudin da Fadeel ya bashi, komai dai ya sanar mata.

Ai fadin zallan mamakin fadeelah da farincikin ta bata lokaci ne, taji dadi da Daddy ya gane gaskiya, ta
kuma yi mamaki kwarai da Fadeel ya bawa Daddy zunzurutun kudi amma ko sanar mata bai yi ba, in fact
batama san cewa yazo estate din su ba...

Sosai ta nuna mamakin ta, wanna hakan ma ya bawa su Daddy mamaki ganin bai sanar wa fadeelah uban
kudin daya bayar ba, sosai hakan yasa Fadeel kara samun waje a zuciyar su, tabbas da za a samu masu
kyawun zuciya irin na Fadeel a al'ummah da an samu cigaba sosai..
Haka dai suka Shiga lallashin fadeelah har aka samu bacci ya dauke ta kan cinyar Mommah, domin duk
maganar nan da suke hawaye ke zuba a Idanunta....

*****************

*AMERICA*

Hada'dd'en asibiti ne mai girman gaske, gabadaya ma'aikatan su farare ne, ma'ana masu jajayen kunnuwa
ne, ko wannesu sanye da uniform farare kal, yayinda majinyacin su ke saka light blue...

Kwance Fadeel yake babu riga ko daya a jikinsa, sai wani kyalle fari da aka rufe al'auran sa da shi, yayinda
wasu wayoyi masu yawa ke manne a duk wata gaɓa ta jikinsa inda jini ke yawo, an ɓula duk wani
maguɗanar jini dake jikinsa an saka wayoyi a a ciki, ta nan jinin ke shiga jikinsa.

ga jini masu yawa leda-leda rataye kan wasu karfuna a tsaye irin na karin ruwa nan, luckily cikin kudirar
Allah aka samu blood group O+

A yanda yake kwance zaka dauka matacce ne, domin baya motsi, banda zuciyar sa dake bugawa babu
abinda ya bambam ce shi da matacce...

******************************

NIGERIA (LAGOS)

*Bayan watanin goma sha daya*

Fadin tashin hankali da damuwar fadeelah bata lokaci ne, kuka kuwa shine abokin hirar ta, sannan hoton
zanen Fadeel dake part dinta shine abinda yake debe mata kewa.

Bata taba tunanin fadeel zai dauki wata uku bai dawo gareta ba, amma gashi yanzu 11month babu amo
babu labarin sa, tun su Mommah na lallashin ta har suka zuba mata ido, domin suma abin ya fara damun
su jin Fadeel din shiru, gashi sun sa anyi bincike har yanzu ba a gano asibitin da yake ba.
Ta bangaren ma'aikatan gidan da escort din sa kuwa, suna ganin alert duk wata hakan yasa basu damu ba,
domin a tunanin su wata tafiya mai muhimmanci sukayi domin fadeelah bata koma ba, a cewar ta bata
amfanin zaman gidan ba babu gwarzon ta a gare da ita, dama kuma fadeel ya kai albashin ma'aikatan sa na
tsahon lokaci banki, duk da bai san tsahon lokacin da zai dauka ba, amma sai da ya kai kudi masu yawa
wanda kowa zai samu albashi har na shekara daya da watanin, kana ya bada account number din kowa
yace duk wata ana biyan su, zai bar kasar zuwa wani lokaci, kasancewar da bank din yake amfani hakan
yasa ma'aikatan na samun salary dinsu duk wata....

*************

Sosai Fadeelah ta dawo so silent babu hayaniya, domin idan ba hirar Fadeel Mommah ko Daddy zasu mata
ba, bata magana da kowa, sosai suke tausaya mata, domin ita ba jiki ba dama, gashi kuma damuwa ya kara
zuketa.....

******************

AMERICA

1 MONTH LATER

A yau Fadeel yayi shekara daya da zuwan sa America, hakan kuma yayi daidai da shekaran sa daya a
kwance ba tare da yasan a wace duniya yake ciki ba, likitoci sun fara damuwa ganin har yayi shekara daya
bai motsa ba, sosai suka damu...

tun kafin a fara aikin sunan fadeelah'n sa ne a bakin sa, sosai suka tausaya masa, domin basa son wahalar
sa ta tafi a banza, musamman babban likitan mai suna KELVIN SMART domin sai da Fadeel ya bashi labarin
soyaayyar sa da Fadeelah ya amince za a yi masa aikin Saboda hadarin dake ciki, kasancewar sa bature,
dama an san turawa da sanin darajar soyaaya hakan yasa ya amince domin ya yarda da reasons din fadeel
din, taɓɓas samun irin wanna soƴaaƴar da wuya, koda cikin su turawa ne, ace uwa da ɗa duk sunyi
sadaukarwa mai girman gaske...

Zuwan KELVIN SMART na hudu kenan a safiyar yau domin duba fadeel ko ya farka, saboda ya fara jin
tsoro... a hankali ya tura kofar zallan glass din ya shiga, kamar a mafarki ya ga Fadeel ya fara motsa kafafun
sa......

Share fisabilillah
Comment

✨Noor larab ce✨

I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*

💝ƘƳAUTAR ƘOƊA💝
(It's all about love, scracifes, hatred and destiny)

*First edition*

ELEGANT ONLINE WRITER'S📚🖊

https://facebook.com/groups/943534712916776/masu amfani da facebook su yi join ta wanna link din.

EDITING IS NOT ALLOWED❌

Page 69-70
(Not Edited)

Sai kuma hannun sa, cikin sauri kelvin smart ya karasa wajen sa, farinciki fall fusk'ar sa, cikin sauri da sanin
makamin aiki ya shiga zare na'urorin dake manne a dukkanin jikinsa inda aka manna.

A hankali ya fara ware idanun sa, saurin mayar wa yayi ya rufe ruf, sak'amak'on hasken daya cika idanun
sa...

"Easy, take it easy" KELVIN SMART ya fada yana shafa kansa.

Ya dauki mintuna goma, kana a hankali ya shiga bud'e idanunsa sa, tar ya sauke su kan fuskar Kelvin Smart

"Welcome back to the world the lover boy" Kelvin smart ya fada cikin farinciki..

Jinjina kan sa Fadeel yayi yana murmushi irin na masu jinya, ji yayi jikinsa na masa wani iri, wani zafi da
bazai iya mitsaltawa ba, tamkar ciwo a jikin mutum ana fama masa...

A hankali ya mike zaune yana sauke numfashi, wani bowl da toothpaste hadi da brush Kelvin smart ya
kawo mishi, sosai yayi brush din bakinsa, toilet kelvin smart ya zubar da ruwan daya wanke baki dashi kana
ya dawo...

Wani kujera mai kyau dake gefen gadon ya zauna a kai, kana ya kalli fadeel yace "how are you feeling
now? (Ya kake ji yanzu? )"

Lumshe ido fadeel yayi, kana ya bud'e su, karon farko bayan shekara daya ya furta "yeah! not to bad, I
have to go home urgently, cos I know my wife is worried already, but for how long have i been here?(eh
babu laifi, ina son zuwa gida da gaggawa, domin nasan matata na cikin damuwa tuni, amma tsayin wani
lokaci nake wajen nan?)"

Murmushi Kelvin yayi, yana jinjina son da Fadeel ke wa fadeelah'n sa, kana yace " you have been here for
one year now(kana nan tsawon shekara daya yanzu)"
"What? Innalillahi wa innah ilaihi raju'un" ya fada cikin tashin hankali, ganin wai har yayi shekara daya a
wajen nan babu Fadeelah'n sa, mikewa Yayi a zabure duk da uban zafi daya ji amma bai damu ba, burin shi
ya bud'e ido ya ganshi a Nigeria, kusa ɗa fadeelahn'sa...

"Wait! Take it easy, where are you rushing to? (Tsaya! Yi a hankali, ina kake saurin zuwa haka)" Kelvin smart
ke wanna maganar...

A rikice Fadeel yace "I have to go doctor, my wife is worried, I want to see my fadeelah (zan tafi likita,
matata a dame take, ina son ganin Fadeelah ta"

Sosai doctor ya tausaya masa hakan yasa yace "I understand your condition, but take it easy, you can see
you are not wearing cloth, lemme get you some cloth and then book a flight for you)(na fahimci yanayin
ka, amma ka bi a sannu, kaga dai baka da kaya a jikin ka, bari na samo maka kayan sawa, Sannan na yi
maka booking jirgi)"

Jinjina kai Fadeel yayi, takalmar sa da wayoyin sa, da kuma wasu abubuwan sa masu muhimmanci ya gani
saman wani wardrobe, a hankali ya mika hannun sa ya dauki check book, kana ya rubuta kudi daƴa san zai
isa a yi booking jirgi da siya masa kayan, mikewa Kelvin smart yayi, ya fice cikin sauri...

Wajen booking flight kelvin smart ya fara zuwa, yayi sa'ar samun wanda zai daga zuwa Nigeria a daran yau,
komai d'aya kamata yayi, ya biya, kana ya nufi wani hada'dden boutique ya siya masa wando, riga, jacket,
p.cap, boxer, singlet, perfume man shafawa, sabulu da soso, a wani kyakyyawan jaka aka yi masa packing
komai kana ya fada motar sa ya nufi asibiti...

Kwance ya tarar da Fadeel, kayan ya ajiye a gefe yana yiwa Fadeel sannu, Kana ya mika masa ticket din
yana fada masa cewa karfe takwas na dare jirgin zai tashi zuwa Nigeria...

Da taimakon Kelvin smart ya yi wanka, domin ko taka kafar baya iyawa sosai, domin har yanzu jinin bai
zauna a jikin sa yadda ake so ba, ba kamar nashi na halitta ba...

Bayan ya gama shirya wa cikin kayan, Kelvin smart ya fesa masa turare,kana ya shiga bashi shawarwari ta
yanda zai dinga kula da jikinsa, da cin abinci mai kawo jini sosai da dai sauran su...
Sosai Fadeel yayi godiya ga doctor kelvin, domin yayi masa taimako sosai, wayar sa, hoton aikin da aka
masa wanda aka dinga dauka da bayanai yanda aka yi komai na ciki, wanda ka'idar asɓitin ce haka, ana
daukar hoto da bayanai, da dai duk wani abu mai amfani sa cikin wanna K'yak'yyawan jakan da aka saka
masa kaya a boutique, ya sanyawa Fadeel kayan a ciki, number'n Fadeel din Kelvin smart ya karba, domin
yace lallai sai ya gaisa da Fadeelah a waya, domin soyayyar su na burge sa matuka, ba musu Fadeel ya
sanya masa domin ya cancanta, haka ya dinga deɓewa Fadeel kewa yana jan shi da hira har agogon
America ta buga 7:00pm

Da kyar Fadeel ke jan kafarsa har wajen mota, domin tamkar mai koyon tafiya haka ya dawo, dan ma yana
ɗa jarumta da ko iya taka kafar ba zai iya ba, Kelvin smart ne ya kai shi har airport, rungume sa fadeel yayi
suka yi K'yak'yyawar sallama har sai da kelvin smart ya ga tashin jirgin su kana ya koma hospital din su....

***************

*NIGERIA*
A hankali yake saukowa daga matataƙalar bene.... Bayan ya gama saukowa ya bud'e jakar nan da kelvin
smart ya bashi, ajiyar zuciya ya sauke ganin wayoyin sa, domin da bai san ta yanda zai isa gida ba, in dai ba
taxi zai hau ba...

Gashi da yawan mutanen wajen basu san cewa shine the famous billionaire Architecture FFM ba,
sakamakon p.cap d'aya rufe rabin fuskar sa..

Hannu yasa ya dauki wayar ya kunna, hoping to see charge, luckily ya kuwa samu 98percent, Sosai yaji
dadin hakan, ya kuma san wanna aikin doctor kelvin ne, domin yasan cewa chajin d'aya zo dashi ya kare,
saɓoɗa shekara d'aya ba wasa ba, babu jimawa network suka hau kan wayar, dama bai cire layukan ba...

Number'n babban escort d'in sa ya kira, ya kuwa ci sa'a ya samu...

'Am at murtala international airport now" abinda ya iya fada kenan ya katse kiran.

Ɗaga bangaren escort ɗin kuwa sosai yayi farinciki, duk da bai san ina fadeel din ya tafi ba, amma yaji dadi
ainun daya ji ya dawo, nan fa ya shiga sanar da sauran, cikin kankanin lokaci gidan ya dauka cewa boss din
su ya dawo, kara gyara gidan suka yi, duk da kullum sai sun yi gyaran, amma wanna na musamman ne,
Yayinda chef's suka shiga yin aikin su na girki, escort din sa kuma suka nufi airport cikin sauri.
Tun daga nesa Fadeel ya hango su sun shigo, hakan yasa shi mikewa a hankali, domin ya kasa jure tsayuwar
har sai da ya zauna, cikin girmamawa da murna duk suka gaishe shi, da murmushi a fusk'ar sa ya amsa,
motar suka bud'e masa ya shige, kana suka bar airport din...

Bayan isar su gidan, sosai dukkanin ma'aikatan sa suka kawo gaisuwa, a mutunce ya amsa musu, kana ya
nufi bedroom d'in sa da kyar, ya duba ko ina bata nan, part dinta ya nufa nan ma bata nan, wasa wasa ya
shiga zagaye dakunan gidan amma babu Fadeelah'n sa, sosai tashin hankali, damuwa, hadi da mamaki ya
kama shi ya shiga tunanim ina taje? zama yayi a bakin matataƙalar bene yana sauke numfashi domin ba
k'aramin kokari yayi wajen neman ta ba, tunanin tambayar ma'aikatan gidan yayi, sai kuma ya fasa domin
baya son su san cewa baƴa da masaniya inda Matar sa take, tunanin kiran ta ya sake fado masa, amma sai
ƴa fasa, ya kuma yi tunanin zuwa estate din su ya duba ko tana can, da kyar ya mike ya koma part din shi ya
yi wanka yayi brush, kana ya Sanja wasu kananun kaya marasa nauyi.....

*******

Zaune suke a parlour'n Daddy gabadayan su. Mommah, Daddy da Fadeelah, fada Mommah take mata
sak'amak'on damuwar da take yawan saka kanta, domin abin ya fara affecting dinta, gashi kullum cikin
rashin lafiya take, cinyar Mommah ta fada ta shiga rusa kuka, ita kam hakurin ta ya fara karewa, ace
shekara daya da kwana d'aya babu mijinta babu labarin sa, ga gaban ta da ta ji yana fadu'wa sosai a yau
din..
tausayin ta ne ya kama Mommah sai ta shiga rarrashin ta, Daddy na zaune yana kallon su ya ma kasa
magana Sak'amak'on shima rashin dawowar Fadeel din ya fara damun shi sosai...

Suna cikin wanna halin, a bazata, ba tare da sun yi tsamanin ba, suka ga ya turo kofar ya shigo bakin sa
dauke da sallama...

A razane dukan su ukun suka maida kansu ga entrance din shigowa, Fadeel suka gani tsaye jikin kofa yana
bin su da murmushi Yayinda idanunsa suka ciko da kwalla ganin Fadeelah'n sa, cikin mayuwancin hali.

yes! shine a tsaye, duk da ya dan rame, ga kuma tabo a jikinsa a duk inda aka manne masa na'urori da ya
bashi jini, but he still remain the handsome Fadeel with a good heart. Daddy ya aiyana a ransa...

Fadeeelah kuwa Murza idanun ta tayi taga tabbas shine tsaye a gabanta ko kuwa? hakan yasa cikin sauri ta
mike ta nufi shi, da gudu ta dane shi yar jakar hannun shi ya wullar, ya rungume ta tsam, sosai ta fasa
kukan farincikin ganin mijin ta abin sonta a lokacin data fidda rai da samun sa, shima sosai ya k'amk'ame
ta, duk da rashin kwarin jikinsa sai d'aya rungumeta so tight domin ganin ta yasa har wani k'arfi yaji yana
shigar sa, fadi yake...

"Am so sorry Fadeelah, ki yafe min kinjiiiiiiii, I know you have pass through a lot, am so sorry for that" ya
karasa yana rungume ta da k'yau, Yayinda yake jin nutsuwa na saukar masa....
Da alama sun manta Mommah da Daddy na zaune.
fadeelah kuwa cewa tayi "meyasa kayi wanna abun mai hadari my one? ka tafi a shekara d'aya ban gan ka
ba, ni na dace nayi wa wanna sanjin jinin, ka sha wahala sosai a tarayyar mu, da ni ka bari nayi wanna
Sadaukarwa a soyayyar mu"

Murmushi mai sauti ya saki kana yace "Am so sorry Fadeelah, i swear ban san nayi shekara d'aya a kwance
ba, a lokacin da Doctor ya sanar dani nayi shekara d'aya ba karamin tashin hankali na shiga ba, domin
nasan kina cikin damuwa, kuma ni bazan iya juran ganin ki a wanna halin ba, ni ya dace nayi, domin kin
cancanci hakan, kin manta Mahmah ta ce mu haifa mata jikoki, idan ban yi hakan ba Tayaya zamu rayu da
zuri'ar mu cikin farinciki? Idan kuma so kike na auri wata sai mu haifi yara kin ga bazasu kasance SIKILA
ba...." Ya fada domin tsokanar ta..
.

Duka tayi masa a baya, sai kuma ta shiga shafa wajen da ta dake shi, tamkar yar baby tace "toh ai da ni
Mahmah tace ka haihu" ta karasa cikin salo na kishi, sosai hakan ya bashi nishadi, kara rungume ta yayi
yace "I love you so Much my Darling wiffy, I can't live without you Fadeelah"

"I so much love you too my one, you re my everything" sosai yaji dadin kalaman ta hakan yasa ya fara dan
juyi da ita a jikin cikin shaukin sonta...

raf raf raf... Mommah da Daddy suka Shiga yi musu tafi Yayinda hawaye ya cika idanun su na zallan
tausayin su, sosai kuma soyaayyar su Fadeelah da Fadeel ta birge su Mommah...

Sosai Daddy yaji dadi ya kuma yaba da wanna pure soyayyar da fadeel ke wa gudan jinin sa.

Sai a lokacin suka tuna ashe basu kadai bane a falon, kunya ne ya kama su biyu, a hankali ya tsunkuya ya
dauki jakar d'aya watsar, kana ya nufi wajen su, hannun fadeelah cikin nasa, yana kokarin dukawa domin
ya gaishe su, Daddy yayi saurin rungume Shi cikin alfahari da son sa, tabbas Fadeel shine masoyi na hakika,
ya kuma kara godewa Allah da bai rasa fadeel cikin zuri'ar sa ba....

Sosai suka yi masa barka, hadi da nuna farincikin da dawowar sa lafiya, fadeelah ba kunya ta manne a
gefen sa, domin ji take idan ta matsa daga wajen sa, zata neme shi ta rasa...
Jakar hannun sa fadeelah ta karba, ta bud'e, kuka ta saka ganin yanda Fadeel yake kwance kamar gawa a
hoto na'urori manne a jikin sa, bata kara kallon hoton ba Saboda tausayi...

Daddy da mommah ma sai da suka kalla duka, sun tausaya masa matuka, da kyar aka samu fadeelah tayi
shiru, nan ya shiga gaya musu komai daga zuwan sa ƙasar, bai kara sanin komai ba, sai Jiyan d'aya farfado,
sun yi mamaki ainun, Sannan sunyi farinciki ganin an samu nasarar aikin, ya jima sosai a gidan suna hira,
domin har kitchen Mommah ta shiga da kanta ta dafa masa wake da allaiyahu d'aya ji naman rago, kana ta
hada masa smoothie na kankana, ya kuwa ci sosai, domin a America abu mai ruwa ake bashi, shima ta
cikin wanna abin da ake durawa wa majinyaci abinci ya ci (na manta sunan abun, fatan kun gane)

Sun kai awa uku suna hira cikin farinciki kana Fadeel ya bukaci su tafi gida, Yayinda Mommah ta hada wa
fadeelah wani hadi na musamman na gyaran jiki, ta kuwa shanye duka, dama kullum haka take mata, cikin
tea, fruit salad, da smoothie take sanya mata maganin gyaran jikin, amma sam fadeelah bata sani ba,
domin maganin da zaki, duk da ta jima kuwa tana jin wasu sauye² a jikin ta amma, sam bata san cewa
maganin Mommah ne yake aiki ba....

Har haraban estate din, mommah da Daddy suka raka su, cikin girmamawa escort din sa duka suka gaishe
da Daddy da Mommah, a sake suka amsa, nan aka bud'e musu motar, fadeelah ce ta fara shiga kana Fadeel
ya shiga shima, a jere reras motocin sa suka bar gidan, ƴayinda su fadeel suka shiga dagawa su Mommah
hannu..., kwalta suka hau, kana suka dauki hanyar banana island inda tamfatsetsen gidan Fadeel yake....

Share fisabilillah habibti'es

Comment

*(Follow and vote me on wattpad @NoorEemaan)*

I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*

💝ƘƳAUTAR ƘOƊA💝
(It's all about love, scracifes, hatred and destiny)

*WATTPAD*
@NoorEemaan

ELEGANT ONLINE WRITER'S 📚🖊

EDITING IS NOT ALLOWED❌

🔥FITACCE🔥 FITACCE🔥

IDAN KAJI SAREWA🎺🎺🎺🎺 NA TASHI TO TABBAS AKWAI SARAKAI A WAJAN, *SARAUTA* HAYAƘI KIKE BA KYA
ƁOYA, FARAR ANIYYA MAI FARAR ZUCIYA, KADA NA CIKAKU DA SURUTU, DAGA FARKON MGN TA KUN SAN
INDA NA DUSA, FITACCIYAR MARUBUCIYAR NAN WACCE TAYI FICE A RUBUTUN LITTAFAN HAUSA, A CIKIN
JERIN MARUBUTAN ONLINE WTITERS, TANA FARIN CIKIN SANAR DAKU SABON LITTAFIN TA MAI SUNA *🌈
ABU_MALEEK🌈*

*🌈ABU_MALEEK🌈* LITTAFI NE NA TSANTSAR SARAUTA DA KUMA ZAZZAFAR SOYAYYA MAI NARKAR DA


ZCYR MASOYA, ZA KUJI YADDA *FOOTBALLER⚽* KUMA DA GA *SARKIN YARUBA (OBA OF YARUBA)* WATO
*YAREEMA* YAKE ƁUGEWA DA SOYAYYA DA MAKAUNIYA KUMA ALMAJIRAR KAN TITI, WACCE TA KASANCE
ABAR ƘYAMA GA KOWA😭.

*ABU_MALEEK* YA TUƁE YA SHIGA JERIN MA NEMA AURAN MAKAUNIYA KUMA ALMAJIRAR KAN TITI
INDA YA SHIGA JERIN MUTANAN DA ZA'AIWA *SHAƊI* 🤺, ANA DARA GA DARE YAYI A YAYINDA YAKE
NEMAWA MAI MARTABA MAGANI A WATAN ƘASAR YAY KATARI DA *ARNAN DAJI* KAFIN WANI ABU SUN
CIZAR MASA ƳAR MAKAUNIYAR SA, NAN TAKE TA KAMO DA LALURAR MAITAR SHAN JINI A DUK SANDA
ABUN YA TASHI JININ JIKINSA SHIKE MAYE MATA GURBIN ABINCI.

MAZA KU HANZARTA NEMAN NAKU, MARUBUCIYAR TA SHIRYA TSAF DOMIN BAKU FARIN CIKI,
ILIMANTARWA, NISHAƊANTARWA, SOYAYYA ZANBO CIKIN AMINCI.

ZATA FARA POSTING BAYAN AN KAMMALA BIYAN KUƊIN WANNAN LITTAFIN, WANDA YA KASANCE BOOK 1
2 3, ZA'A KAMMALA PAYMENT ZUWA END OF NOVEMBER BA ZATA FARA POSTING SAI TA KAMMALA BOOK
1✍🏾🔥, MASOYA *NA'IMA SULAIMAN NIMCYLUV* KU SHIRYA DOMIN DA SOYAYYAR KU TAKE TAƘAMA A
KODA YAUSHE.

BOOK 1 2 3
AMOUNT: #500
ACCT NO: 0116886423
ACCT NAME: SULAIMAN NA'IMA S
BANK NAME: UNION BANK
EVEDANCE OF PAYMENT
08119237616, GA ƳAN NIGER KUMA SUYI MGN TA NAN 84506476

MARUBUCIYAR SIRRIN MU🔥 UNCLE NE🔥MOON🔥AURAN FANSA🔥 THE NEW EMIR🔥JUYAYI, JIDDA, LAMRAT
DA DAI SAURAN SU.

DAN ALLAH DAN ANNABI SHARE FISABILILLAHI🤲🏼🤲🏼🤲🏼

https://facebook.com/groups/943534712916776/masu amfani da facebook su yi join ta wanna link din.

Page 71-72

Tafiyar mintuna talatin ya kawo su banana island gidan, tsayuwar motocin ya sanya su Fadeelah sanin
cewa sun zo cikin giɗan.

A hankali ta dago kanta daga kan kafadar Fadeel tana kallon shi ganin bai da niyyar fita.

A shagwa'be tamkar yaro dan shekara biyar yace "wiffy ki goya ni please"

Dariya ta fashe da shi, shagala yayi da kallon ta, Saboda dariyar tayi mata kyau ainun.

Gimtse dariyar ta tayi tace "my one ta ya ya zan iya goya ka" ta fada tana kara jin wata dariya na taho
Mata.

"Wato dariya kike min ko? Kisan Allah sai yanzu na fara jin rashin kwarin kafar nan, domin a lokacin da
Doctor Kelvin ya fada min shekara ta d'aya a gidan nan, hankalina ya tashi sosai,burina kawai nazo gareki,
sai yanzu na fara jin rashin kwarin kafar, ko taka ta bana son yi" Fadeel ya fada yana kallon beautiful face
din ta.
"Toh naji zan goya ka, hau toh" ta fada tana juya bayan ta, dariya sosai ta bashi wanda rabon sa dashi tun
kafin ya tafi america, fusk'ar ta ya riko, a tausashe yace "wasa nake wiffy, banaso karamar siririyar matata
ta balle"

Turo baki tayi jin yace karama, mannawa labb'anta kiss yayi kana yace "muje"

"To tsaya" tace tana fita da sauri, dayan bangaren ta zagaya, da taimakon ta ya fito, hannunsa ta dauka ta
zagaya ta cikin ta, yayinda ta dora daya a kan kafadunta, suka shiga takawa, Yayinda ma'aikatan gidan suka
Shiga kawo gaisuwa, duk inda suka wuce sai an gaishe su, a mutunci kamar yadda dabi'unsu yake suke
amsa gaisuwar.

Bangaren Fadeel suka nufa, a hada'dden falon sa suka yada zango, zaunar dashi tayi tana sauke numfashi
gajiya, hakika fadeel karfaffa ne....

"Allah my man dana goyaka dana balle wallahi kamar yadda kace"

Dariyar da bai yi niyya ba, ya saki...

Cikinsa ya shafa yace "Fadeelah yunwa nake ji, kuma girkin matata nake son ci, amma bana so ki wahala"

Murmushi ta yi tace "ba wani wahala my man, zan dafa maka kaji" ta fada tana nufar kitchen, duk da tayi
mamakin jin cewa yana jin yunwa, amma ba abin mamaki bane idan akayi duba da chajin jinin da akayi
masa, ga kuma maganin Karin jini wanda yake sa shi cin bacci sosai...

Sai da ta bacewa ganin sa kana ya dauke kansa. Bangaren fadeelah kuwa private kitchen din ta ta nufa,
tsaye tayi tana tunanin abinda zata girka masa da bazai dauki lokaci ba, Saboda kada fadeel din ta yaji
yunwa....

Tuwon semovita da water leaf soup daya sha naman kaza, stock fish, cat fish hadi da crayfish ta shiga
hadawa, bayan awa d'aya da mintuna goma sha biyar ta gama komai, har da lemon kankana da saka ice
block hadi da watermelon flavor tayi blending dinsu kana ta saka cikin wani jug mai k'yau hadi da kananun
cups din sa, gabadaya part din ya dauki kamshi sosai...

Kimtsa kitchen din tayi, ta wanke abubuwan data bata, kana ta dauki tray din ta fito, zaune ta tarar da shi
kamar yadda ta barshi, sai dai wanna karon hannun sa dafe saman fusk'ar sa, jin takun tafiyar ta ya sanyi
shi bud'e idanunsa yana sakar mata murmushi, martani ta mayar masa, kan center table ta dora tray din....

"Sorry na barka kai kadai ko?" Tace tana zama a gefen sa.
" dont worry, Sannu kinji wiffy na sa ki aiki, kamshin girkin ki yasaka saliva dina diga, saura kadan ki ganni a
kitchen din ki "

Murmushi kawai tayi tace "ka cancanci fiye da haka my one, yanzu da abinci zaka fara ko wanka?"

"Hmmmmmmm... wanka zan fara yi" ya fada yana kallon Hada'dd'en POP din saman dakin.

dawo da kallon sa gare ta yayi "kema kina bukatar wanka wiffy" ya fada yana mika mata hannunwan sa,
taimaka masa tayi suka nufi bedroom d'in sa, ruwa ta hada masa a jaku'zzie bayan ta saka bath soak, fita
tayi ta hango shi tsaye jikin kofar bathroom, kallon shi tayi tace "me yasa baka zauna ba, kafar ka fa"

"Rashin ganin ki yasa na taso domin zuciyata ta samu kusanci da taki zuciyar"

Murmushi ta saki mai sauti, ta hade hannayenta a k'irjin ta, sun jima suna jifan juna da kallon kauna, kana
ta riko hannun sa suka shige toilet din, sai da ta tabbatar ya shiga cikin jaku'zzie kana ta ruga a guje ta nufi
dayan bathroom, duk da kiran da yake mata kuwa, domin ta fahimci so yake su yi wanka tare...

Dariyar ta ta gimtse sanda suka yi tozali da juna, gashi ya riga ya ganta da towel babu halin gudawa, amma
taji kunya kam, domin towel din karamin ne sosai....

Gaban shi tazo ta zaunar da shi, duk yanda take jin kunya haka ta daure ta fara shirya shi, domin idan bata
taimaka masa ba, hakika bata kyauta ba, kananun kayan shan iska ta sanya masa, bayan ta shafa masa mai,
body spray mai dadi ta fesa masa, kana tayi oiling gashin sa ta taje masa, sosai kuwa yayi k'yau tamkar
black America.

Itama lotion ta shafa, body spray data fesa masa itama ta fesa a jikinta, kayanta ta saka wani straight fitted
gown mai spaghetti hand, hadi da saka head band golden color, kamar yadda gown dinta ya kasance
golden.

Light makeup tayi, daga hoda data shafa, sai kajol(kwalli) hadi da lipstick maroon color daya sata yin wani
sihirtaccen kyawu d'aya zai narka zuciyar Fadeel...

Bayan ta mayar da make up kit din mazaunin sa, take ta juyo gare shi...
Baki Fadeel ya bud'e yana kallon ta, sosai tayi masa k'yau tamkar an sanja masa ita, kasa hakuri yayi har sai
da ya ware mata karfaffan hannayen sa, da murmushi a fuskar ta shige jikinsa ya mayar da hannu sa ya
rufe.

Ajiyar zuciya ya sauke yace "my Darling kin yi kyau sosai, fiye da yanda bakina ba zai iya fadi ba, I love you
the mother of my unborn children"

"I love you too Fadeel" tace tana lumshe ido Saboda k'amshin turaren jikinsu dake ratsa kofofin hancin ta.

Sun jima suna hirar soyaayar su, kana suka nufi parlo domin ya ji abinci, kasan centre carpet ta suka zauna
bayan ta shimfud'a ledar cin abinci, a baki ta dinga bashi har ya koshi, sai ta siyaya masa lemon kankana ya
sha sosai kuwa yana santi, ta dinga shan dariya kuwa, shima kuwa ya ciyar da ita har ta koshi...

Har dare haka ta dinga dawainiyya da shi hadi da bashi kyakyyawar kulawa...

***********

Ta bangaren Jameel kuwa, sosai damuwar sa tayi yawa, ya rame sosai, har hakan ya daga hankalin su
minister... Baki jameel da minister suka hada kan kawar da mutum daya daga duniya, tsakanin Fadeel da
Fadeelah ta hakan ne zuciyar jameel zai kwanta, wanda ya san ya rasa ta ko bata duniyar akan wani ya rayu
da ita yana raye, tunda kidnapping dinsu ba abu bane mai sauki tunda kullum suna cikin tsaro...

A ranar sa suka gama hada plan dinsu, da yamma haulat ta kawo musu ziyara kamar kullum suka aikata
zinar su son ransu babu tsoron Allah...

Da bayan magariba sunyi wanka, haulat ta fada mota, suka yi sallama... Haulat ta yi nisa da tafiya, ta yi
karo da wata akori_kura, take motar tayi raga_raga, take haulat ta amsa kiran ubangiji, nan fa go slow ya
hadu sosai, wani mutum ne yaga tsadaddiyar wayar ta yashe a kasa screen din ta fashe sai dai ba sosai ba,
dauka yayi, luckily babu security kan wayar, number jameel ne Karshen kira hakan ya shi kira number'n...

Zaune jameel yake da wasu tantiran samari yana fada musu yanda aikin zai kasance kamar yadda shi da
minister suka tsara... Ringing din wayar sa ne ya katse masa maganar sa...

Ganin number haulat ya sashi dagawa, abinda yaji mutumin ya fada ne ya sanya gaban shi wata
mahauk'aciyar bugawa ba tare da ya shirya wa hakan ba.

Wani nauyi yaji kansa yayi masa, ba tare da bata lokaci ba ya figi mota sai inda aka yi masa kwantance. Ai
ganin gawar haulat ya so juye k'wak'walwar sa, hakika bai taba jin mutuwa data shige shi kamar na haulat
ba, ya kasa yarda haulat da suka gama zina mintuna da suka wuce ce ta mutu, kuka yake da idanun sa
sosai, take kuwa ya kira lambar iyayen haulat din kasa da mintuna ashirin suka zo hankali su a tashe, ganin
gawa 'yar tasu ya sanya hankalin iyayen ta tashi sosai, ubanta ne yayi k'arfin hali, amma uwar har da
birgima a kasa, jameel kuwa tamkar ruwa ya cinye shi, babu abinda ke fita a idanunsa kamar hawaye, cikin
dumbin al'ajabi, asibiti aka kaita, aka sake gwada ta, nan aka tabbatar rai yayi halinsa, a asibiti duk suka
kwana, jameel ya manta wani abu mai suna bacci, daya rufe idanunsa haulat yake gani, cikn dare d'aya
gabadaya ya burkice...

Da misalin karfe takwas na safe aka sadata da gidan ta na gaskiya, ganin an rufe haulat da kasa ya sake
daga masa hankali, take ya zube a Kasa yana kuka, duk gayu da kwalisar haulat yau babu shi, gata kwance
cikin kabarin ta daga ita sai halin ta...

Wani imani da tsoron Allah ya shiga ratsa Jameel, nadamar munanan aiyukan sa ya fara yi sosai, ko bacci
baya iyawa cikin dare, ji yayi duk wata k'yalek'yalar rayuwa ta daina burge shi, take ya soke contract din
kisan daya so a yi wa su fadeel....

Ganin jameel ya yada makaman yakin sa ya hakura ya sanya shi ma minister ya zubar da komai cikin
nadama, tabbas mutuwar Haulat ta daki jameel, minister da mummy'n sa kasancewar duk sunyi mata sani
na sosai...

Jameel kuwa sai yanzu ya fara jin son haulat a ranshi, ya kuma yi nadama da bai karbi soyaayar ta da hannu
biyu-biyu ba, sosai lokutan da sukayi having ya shiga dawo masa, nan ya hakura da Fadeelah ya kuma
fadawa minister cewa ya hakura har abada...

***********************

THREE MONTHS LATER

Zuwa yanzu fadeel yasamu sauki sosai, yana iya taka kafar sa yanda yake so, da taimakon Allah da kulawar
da Fadeelah take bashi, domin sosai tayi kokarin wurin bashi kulawa da kuma girka masa abinci masu Karin
jini hadi da kara lafiya, tabon jiknsa kuwa saura kadan² domin akwai cream mai goge tabo da duk dare
kafin su kwanta fadeelah take shafa masa....

Kamar yau sune zaune a falo, kallon ta yayi yace "wiffy Kin san ina nakeso muyi honey moon?"

Girgiza kai fadeelah tayi tana murmushi kasancewar yanzu ta saba da shi sosai duk da babu wani tarayya
aure da ya shiga tsakanin su har yanzu, amma ta rage kunyar sa ba kamar da ba....

Kusa da kunnen ta yazo ya rada mata "suprise!"

Dariya tayi bayan ta saka masa dafaffen kwai cikin bakin sa tace "I like surprises"

"Really?" Yace yana dage girar sa.


"Yeah" ta amsa masa itama.

"Then tashi muje" ba musu ta mike... yace "ki zura hijab kawai kan kayan jikin ki, duk sauran abubuwan da
zaki bukata akwai a can" dan karamin jaka kuwa ta saka musu wayoyi, charges, Bluetooth ta rufe zip din
jakar suka fito, mota suka fada kamar kullum tare da rakiyar escort suka fita...

Abinda ya bawa Fadeelah mamaki shine ɗa ta ga sun nufi unguwar su Fadeel na ɗa, so take tayi magana
domin ta tabbatar da unguwar ne, amma tayi Shiru... Tsayuwar motocin su a wani hada'dden gida Duplex
daya tsaru sosai tamkar a turai ya katse mata tunanin ta...

Juyowa yayi gare ta, yace "Fadeelah kin tuna wanna gidan?"

Cikin sauri ta girgiza kai domin har ga Allah bata fahimta ba...

Kallon gidan yayi, ya hadiyi wani abu mara dadi yace "gidan da muka rayu da mahmah ne a ciki, na sanja
ginin gidan ne, domin har abada bazan manta da gidan nan ba, haka kuma idan Allah ya azurta mu da
'/y'ay'a zamu dinga zuwa nan muna kwana biyu, haka zai sa mu dinga tunawa da mahmah" ya karasa yana
dora kan shi a kafadar ta...

Sosai tayi mamaki ganin mugun chanjin da gidan yayi, hakika duk abinda ya samu gyara komai lalacewar sa
zai gyaru, a yau ta sake tabbatar da hakan, shafa kansa take itama tana jin kewar mahmah na ratsa zuciyar
ta sosai, iya motar da suke ciki yayi horn, take mai gadi ya wangale musu gate ya Shigar da hancin motar
ciki, bud'e musu mota akayi suka fito, kana driver ya juya ya fita, su kuma suka nufi cikin gidan hannunsu
sarke dana juna....

Share fisabilillah

Comment

I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*

💝ƘƳAUTAR ƘOƊA💝

(It's all about love, scracifes, hatred and destiny)

Wattpad
@NoorEemaan

ELEGANT ONLINE WRITER'S📚🖊

https://facebook.com/groups/943534712916776/masu amfani da facebook su yi join ta wanna link din.

EDITING IS NOT ALLOWED❌

Page 73-74

Sosai cikin gidan ya burge fadeelah, madaidaicine, haka zalika ba tarkace cikin gidan da yawa, komai tsaf
gwanin burgewa.

Babban bedroom din cikin dakin ya jata, nan ma taga komai ya hadu sosai gwanin sha'awa, jakar data
rataya ta ajiye akan dressing mirror.

Bathroom ya ja ta suka yi wanka, kasancewar yanzu ta saba wanka tare dashi.


Bayan sun fito sun kimtsa sun saka kananun kaya, dama fadeelah ba Shiri take da manyan kaya ba. Farare
kaya kal suka saka, Riga da wando, fadeelah ta saka head band shima white, tamkar turawa haka suka
dawo gwanin kyau.

Da misalin karfe 6:40pm bayan sunyi sallar magriba ya ja ta zuwa kitchen... "Zauna ki tayani hira" ya fada
yana ja mata kujera ta zauna.

Ba musu ta zauna kana tace "menene zaka yi" murmushi yayi yace "kazar amarci zan hada miki da kaina,
kamar yadda kike na musamman, haka ya dace ki ci kaza na musamman, sam baki dace dana titi ko
restaurant ba" ya fada yana kunna gas din.

Murmushin karfin hali fadeelah ta saki, amma tsoro ne fal zuciyar ta, musamman daya ambaci amarci.

Cikin karfin hali tace "ok bari na tayaka"

"No! bana son ki yi komai wiffy, ki zauna kawai ina kallon ki" ya fada yana bud'e madaidaicin fridge ya
dauko mata lemo exotic da glass cup, zuba mata yayi ya mika mata, kana ya ja wani dogon stool ya dora
exotic din a kai.

"Ko yanka albasa ka bari in maka" tace tana sipping juice din.

"A'a my Darling babu fa abinda zaki yi" ya fada yana cigaba da yankan albasar sa.

Murmushi tayi kawai, tana kallon yadda yake komai cikin kwarewa, kasa hakuri tayi tace "my one dama
kana girki ne sosai? naga you re so perfect"

Murmushi yayi ya dan waiwayo yace "yeah! Ina taya Mahmah girki sosai, amma ba komai na iya dafawa
ba, bari na baki labarin yadda nayi girkina na farko a duniya, lokacin Mahmah ta tafi unguwa" nan ya shiga
bata labari...
Fadeelah har da kwalla Saboda dariya, sosai labarin ya bata nishadi, shima yaji dadi sosai ganin Fadeelah'n
shi cikin farinciki wanda burinsa a kullum kenan.

Bayan awa biyu ya gama hada had'add'iyar kazar sa har biyu, sosai kamshi ya cika ko ina, a cikin wani
babban tray ya jere su, har da garnishing yayi....

Wani wankan suka sake, suka yi sallar isha, kana ya sake jan su sallar raka'a biyu wanda ma'aurata kan yi a
daren su na farko, dorawa yayi da yi mata masu tambayoyi daya shafi addini, sosai fadeelah ta bashi
mamaki, Bai taba tunanin tayi zurfi a ilimin addini har haka ba, tunda kowa ya sani professor Imran mai
naira dan boko ne! a yau ya sake tabbatar wa ita din daban take cikin y'ay'an wasu masu kudin.

Kanta ya dafa ya shiga karanto add'uar, a sanyaye kana a hankali take amsawa da AMEEN.

Bayan nan, ya mike ya dauko mata wata had'add'iyar white silky night gown da iyakacin sa bai karasa
guiwa ba, da kan shi ya mikar da ita ya sanya Mata, tamkar mara laƙa haka ta tsaya ta kasa motsi, bayan ya
saka mata da Kanshi ya kama mata dogon gashin kanta, kana ya riko hannunta suka fice batare da ya saka
kaya ba, illa farin towel daya d'aura a kugun shi....

Ta cikin kitchen ya bi da ita, sai gasu a wani corridor, wanna fadeelah ma bata san da hanya a wajen ba, sun
danyi tafiya kadan, ya tsaya a wani kofa, tura kofar yayi sai gasu a wani hada'dden falon daya hadu matuka.

Kan wani lallausan center carpet ya zauna, kana ya ja ta tana daga tsaye ta fada kan cinyar sa, tray din
dazu daya zuba kaza ya janyo gaban su, Fadeelah tayi mamakin yadda akayi tray din yazo har nan dakin
bata sani ba, amma data tuna waye Fadeel dinta sai taga kadan daga aikin sa ne, dan karamin knife(wuka)
ya dauka ya yanki kazar, "ahha" yace yana kai yankar kazar bakin ta, a sanyaye ta bud'e cute lips d'inta ya
sanya mata.

Murmushi yasaki ganin yadda gabadaya ta tsorata, a fili ya ce "my Darling why the sudden change? Kina
tsoro ne? You know your Fadeel is gentle, so trust me bazan yi hurting dinki ba, kinji" a hankali ta daga
kanta alamun gamsuwa tana murmushi, Kumatun ta ya ja yace "fear fear girl kawai" dariyar da bata yi
niyya ba ta saki ya cigaba da bata kazar, sai daya tabbatar ta koshi ya bata juice ta sha kadan, ta bukaci
ruwa, wajen dispenser ya nufa ya siyaya mata ruwa ta sha, kana ya dawo ya ji kazar shima sosai ya kora da
juice, gani tayi ta ya mike da tray din ya fita, da kallon kauna ta bishi tana sauke ajiyar zuciya.
Jim kadan ya dawo, in a romantic way ya dauke ta cak! Ya nufi wata kofar, ya ture da kafar sa suka shiga.

"close your eyes " yace yana dire ta kasa.

Rufe Idanunta tayi, bayan seconds goma yace "open your eyes" ba musu ta bud'e.

"Wow!" Ta furta ba tare da ta sani ba, oh Fadeel kullum cikin suprising dinta yake, sosai bedroom d'in ya
hadu sosai wutar dakin sai sanja yake daga blue, red, zuwa yellow, hakan yasa dakin yin duhu ya kuma kara
masa kyau, babban gadon kuwa da aka lailaye da bedsheet fari kal sai jajayen rose flower shimfud'e a
gadon, anyi designing heartda shi, daga kasan kuma aka rubuta I LOVE YOU FADEELAH .

Da wani india romantic music dake tashi a hankali cikin dakin, sosai dakin ya hadu wanda fasaltashi
wasting of time ne.

Sosai taji dadin abinda ya mata, hakan yasa ta rungume shi ta ce "I love you too Fadeel, I love you zaujee"

Wani yanayi mai dadi ya shiga ratsa su, goshin su ya hade waje d'aya, follow by tip din dogon hancin su, sai
labb'ansu daya hade da juna, wani a ajiyar zuciya Fadeel ya sauke, Yayinda ya kama tattausan labb'anta ya
fara sha a hankali cikin nutsuwa, tun yana yi a hankali har ya dawo a zafaffe, sosai tsayuwa ta gagare su,
hakan yasa suka zube a bakin gado, wani remote dake gefe yayi nasarar dauka ya kashe music din dake
tashi, take wajen ya dauki Shiru sai fitar numfashin su dake tashi cikin sexual sounds.

Sosai fadeel yayi nisa sosai, ya shiga duniyar gajimare, baya ji baya gani, abinda ya saka a gaba yake yi,
uwar tsoro kuwa ta sakar masa jiki, sai daya dauki wata hanyar ta dawo nutsuwar ta, Fadeel daya ce he will
be extra gentle kuwa kasawa yayi, sosai ya fita a hayyacinsa.

_*4:40am*_

Manne yake da ita yana baccin sa cikin nutsuwa wanda bai taba jin dadin bacci irin na yau ba. A hankali ya
fara jin kukan ta na tashi cikin dakin, kasancewar suna da kusunci sosai, a hankali ya bud'e idanunsa ya
sauke kan fusk'ar ta dayayi jajur haka zalika labb'anta, Idanunta a rufe suke, Yayinda hawaye ke zuba a
fuskar ta, sosai ta kara yi masa kyau, sai dai kukan ta da baya so, a hankali ya fito da harshen sa ya shiga
lashe hawayen fuskar ta, kana ya shiga fada mata kalamai masu saka nutsuwa....
Luf tayi a jikin sa, amma still taki bud'e idanunta, jin ana kiran sallah ya sanya shi mike zaune da ita a jikin
sa, ganin sai a lokacin ya ga yanda bedsheet din ya baci ya kara tabbatar da barnan da yayi, sosai tausayin
ta ya kama shi, amma tabbas yasan bai yi mata da sauki ba...

Daidai kunnenta yace "Am so sorry wiffy for hurting you! But I didn't do it intertionally, na kasa controlling
kaina ne, I love you so much, Allah ya yi miki albarka, Allah ya bamu zuri'a masu albarka, mu haifa wa
Mahmah jikoki, ya Allah kasa nayi nasarar jefa kwai na a mahaifar fadeelah" ya karasa yana bata Peck a
dogon wuyanta.

Kara Lumshe kyawawan idanun ta tayi tana jin yanda kalaman sa ke ratsa ko wani sassa na jikin ta, sosai
soyayyar sa ke kara huruwa a zuciyar ta.

Matse shi tayi a jikin ta, ba tare da tace komai ba, kuma har yanzu Idanunta a lumshe suke.

Dago kansa yayi ya kura mata ido yace


"Fadeeeeeeeelerh please open your eyes"

"A'a" tace a shagwa'be tamkar yar baby girl.

Dariya ta bashi, haka kawai yaji yana son tsokanar ta yace "my Darling kin san me?"

Girgiza kai kawai tayi ba tare da tace komai ba.

"I really enjoy every bit of it, I mean our first night" ya fada cikin husky voice, kana a hankali.

Dukan wasa ta fara kai masa a kirji, dariya yake yana kaucewa, ita ala dole tayi fushi, hakan yasa ta sauko
da sauri zata dira a gado, ba shiri ta tsaya ta saki kara sak'amak'on wani radaddi daya ratsa ta.
Cikin sauri ya tashi ya rike ta yana mata sannu.
Ganin yadda ya rude yasa ta sarka masa murmushi domin hankalin sa ya kwanta, tace "Am fine fadeel, ka
daina yawan damuwa"

"Dole na damu fadeelah, muje in miki wanka domin ki ji dadin jikin ki, gashi har an tayar da sallah" ya fada
yana daga ta cak!

SHARE

COMMENT

NoorEemaan🥰

I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*

💝ƘƳAUTAR KOƊA💝
(Its all about love, scarifes, hatred, and destiny)

*Wattpad*
@NoorEemaan
ELEGANT ONLINE WRITER'S

EDITING IS NOT ALLOWED❌

https://facebook.com/groups/943534712916776/
Masu amfani da facebook su yi join ta wanna link din.

Page 75-76

Ya fada yana daga ta cak izuwa bandaki domin su yi wanka...

Bayan sun yi wanka, ya gasa ta sosai, suka yi sallar asuba a makare, pain reliever ya bata ta sha, kana ya
kwantar da ita, shima kwanciya yayi domin dukkanin su basu yi bacci mai yawa ba a daren jiya.

Karfe takwas Fadeel ya farka, kallon fadeelah yayi yaga tana baccin ta cikin nutsuwa, murmushi yayi ya
sumbaceta a labe kana ya sauka daga kan gadon a hankali gudun kada ta farka.

Toilet ya shige yayi wanka, hadi da yin brush, drying gashin sa yayi a toilet domin bayason karan hand dryer
ya tashe ta.

*FOGG MEN* body lotion ya shafa a black skin din shi mai kyalli kana ya fesa body spray, Riga armless baki
na Adidas ya sanya kana ya saka 3quarter ash color, sosai yayi kyau...

Kara kallon Fadeelah yayi ya ga tana baccin ta cikin nutsuwa, murmushi ya saki har fararen hakoran sa suka
bayyana kana ya fice yana jin shi sakayau kana cikin nishadi.

Porridge din Irish potatoes(faten dankalin turawa) daya ji zallar kaza, green beans, carrot, red bell, da dai
sauran spices masu saka dandono da kamshi ga abinci ya saka a faten...
Bacci take tana kara bud'e kofofin hancin ta sak'amak'on k'amshin girkin Fadeel dake ratsa kofofin hancin
ta.

A hankali ta bude lumsasun kana gajiyayun Idanunta ta sauke su tarrrr a dakin, a hankali ta yunkura ta
mike tsaye tana yamutsa fuska, domin har yanzu akwai sauran radadi, amma ba kamar dazu ba...

Toilet ta fada ta sake gasa kanta sosai, domin tabbas taji dadin jikin ta dazu da Fadeel ya gasa ta, brush tayi
ta fito, wani rigar sa fari mai layi_layin ja ta janyo, dogon hannu gare shi kana akwai botira jere a gaban
rigar.

Sakawa tayi ta makala botiran, ya sauko mata zuwa saman cinya, head band ja ta dauka ta saka a kanta,
tamkar yar baby haka ta d'awo dan kyau. *FOGG INTENSE AROMATIC ta fesa sama-sama kana ta fito, tana
taku a hankali.

Jin motsi a kitchen ya sanya ta nufar wajen, ta kuwa hango shi a tsaye yana kokarin kashe gas din.

Sai data bari ya kashe kana tayi saurin rungume shi ta baya tace "Good morning Fadeel"

A hankali ya juyo da ta, ya zamana suna kallon juna. "Meyasa baki bari na zo nayi miki wanka da shirya ki
ba?"

Murmushi tayi tace "naji sauki, gwanda na dinga yin wasu abubuwan da kaina domin jikina ya ware da
wuri...

Jinjina kai yayi yace " yeah it's true, amma bakya jin zafi ko, ya daina?"

"Yeah" ta ce masa tana murmushi domin taga gabadaya ya damu kansa.


Ajiyar zuciya ya sauke yace "alhamdulillah naji dadin haka" kana ya kama lallausan labb'anta ya fara kissing
di'n ta, tamkar zai cinye mata lebe, sosai fadeelah ta bashi hadin kai hakan yasa suka dauki tsahon lok'aci
suna abu daya.

Kanta ta kwantar a jikinsa, tana sauke numfashi, haka zalika shima, sun dauki mintuna biyar a haka, kana
ya bud'e fitinanun idanun sa...

"You look beautiful fadeelah" ya fada yana kallon yanda rigar yayi mata das a jiki, duk da bai kamata ba.

"Thank you my handsome Fadeel" ta fada kana ta dora da cewa "tun cikin bacci nake jin k'amshin girki,
hakan yasa ni tashi ba shiri"

Siririyar dariya yayi yace "girki nake wa 'yar albarkar matata taci idan ta tashi, domin nasan jiya na gama
jigata ta"

Murmushi ta saki, ta sani cewa Fadeel dinta romantic guy ne, amma bata san ya wuce tunanin ta ba, tuno
first night din su ya sanya ta sakin murmushi, duk da ta wahala iya wahala, amma hakan bai hanata
fahimtar salon sa ba.

Iska ya hura mata yace "tunanin me kike?"


"Ba komai" tace tana kallon shi da murmurshi.

Plate mai dan girma ya dauka ya hada musu abincin a kwano d'aya, ya sanya spoon guda d'aya.

Lemo da ruwa ya daukar musu duka ya jera a tray, fadeelah zata dauka ya hana ta...

Falon suka zauna kasan carpet, tana jikin sa ya shiga ciyar da ita, ta ci sosai fiye da rabi, kana ta sha ruwa
kadan domin ta koshi sosai, ragowar ya cinye ya sha lemon da ruwa, take yaji cikinsa ya cika shi ma.
Kitchen suka koma, yana wanke-wanke tana dauraye kwanon, yayinda suke hirar soyaayar su gwanin
burgewa...

***********

Satin su daya a gidan, suka koma gidan sa, kamar kullum komai a gyare tsaf-tsaf duk da basa nan amma
ma'aikatan suna aikin su yanda ya kamata.

_WASHEGARI_

Da misalin karfe 4 na yamma dawowar Fadeel kenan daga aikin zanen hoton wani babban hotel da za a
gina, bayan motocin sun faka, suka yi saurin bud'e masa kofar mota, daya daga cikin tsad'add'en wayar sa
ya shiga latsa wa, karawa yayi a kunne yace "my Darling am back! Kina wani sashe ne?"

"Alhamdulillah! welcome back mijina, ina part B" ta bashi amsa kamar yadda suka saka wa ko wani part
suna a gidan Saboda girma da yawan su.

"Alright" yace yana katse Kiran, sauka yayi, ya nufi part din, ya kuwa sameta zaune...

Da gudu ta tashi ta dane Shi, dariya yayi yana bubbuga bayanta yace "easy easy fadeelah! Da alama kin
warke ko? Irin wanna gudu haka" ya karasa a zolaye.

Dariya kawai tayi, domin ta fahimci abinda yake nufi, zai sake magana aka kira wayar sa, ganin number
babban security dinsa ya sanya shi dagawa...

"Hello boss! Ga wasu mutane suna ta zuwa neman ka, yau kwana hudu kenan muke sanar musu baku nan,
gashi kuma sun dawo yau"..
Mamaki ne ya kama Fadeel, domin bai yi da wasu zasu zo ba, katse Kiran yayi yana kallon Fadeelah dake
kallon sa itama.

"Kace su barsu su shigo, kila akwai abu mai muhimmanci da ya kawo su" domin taji abinda security'n ya
fada.

"Kina ganin haka fadeelah?" yace yana kallon ta.

"Yeah! Ka basu dama ka ga ko su waye, am sure alkhairi ne in sha Allah"

"Allah yasa" yace yana sake dialing number security

"Let them in" yace yana katse Kiran.

Kallon Fadeelah yayi ya ga doguwar Riga yar kanti ce a jikinta company'n *Valentino* Yayinda tayi rolling
da karamin mayafin sa.

"Kinyi kyau sosai, fiye da yanda bakina zai furta" yace yana manna mata kiss a lebe.

Itama kissing dinshi tayi tace "thank you!" Ta karasa tana zagaye hannun ta a kugin shi, idanunsu sarke
dana juna, yana dan juyi da ita.

Alarm da aka danna ya sanya su dauke idanun su daga kan na juna, hannun fadeelah ya ja suka zauna ya
bada umarnin shigowa.

Gabadaya suka shigo jiki a sanyaye, mata biyar, maza shida. Bayan sun gama shigowa security daya musu
jagora ya fita, Fadeel bai dago ba hankalin sa na kan wayar sa, yana duba massage din daya shigo masa ta
e-mail, Wanda wani shahararren attajiri ya bukaci yayi masa Zane na wani industry, mutumin mazaunin
jahar kwara Ilorin ne.
Fadeelah ce ta Mike tace "bismillah ku zauna, sannu ku da zuwa"

Zama suka yi a sanyaye, ta gefe ta dan mintsile shi alamun ya dago ya kalli bakin na sa.

"Zan rama" ya fada a hankali ba tare da ya kalle ta ba, yana ajiye wayar a gefe.

"Fadeel danmu" daya daga cikin mazan ya kira shi, wanda ya kasance wan mahaifin sa ne.

A hankali ya dago jin wata murya mai kama data mahaifin sa, ya sauke su tarrrr kan yayan mahaifin nasa.

Kankance ido yayi yana kallon su cikin zallan mamaki! Dama suna raye? ya aiyana a ransa.

"Me ku ka zo yi a gidana? Wallahi Dana san kune babu abinda zai sa na bari ku shigo min gida, And yanzu
zaku bar min gidana" ya karasa yana kokarin danna wa security kira.

Kwace wayar fadeelah tayi, domin ta fara fahimtar ko su waye. "Give me the phone" ya fada muryar sa na
rawa alamun baccin rai...

"Bazan baka ba, what are you trying to do huh? they are your family" ta fada ita ma a dame.

"Family! Did you just said family?" Dariyar takaici yayi kana yace "Fadeelah bani da wani family, my family
are dead! Suna ina a lokacin da mahmah na take bukatar taimako? Ina suke? Gabadaya sun yi watsi damu,
idan ma Mahmah ta kai ziyara wulakanci suke mata, Saboda suna da arziki?"

Numfashin bacin rai ya sauke yace " look you guys should live my house kafin raina ya baci"
"A enough please Fadeel! A enough! Nasani cewa hakan ba dadi, kayi hakuri kaji, just forget and forgive"
FADEELAH ta fada tana dan jijjiga shi domin taga ranshi ya baci matuƙa kana ya fara fita a hayyacin sa.

Daya daga cikin matan data kasance kanwar mahmah tayi saurin cewa "eh dan nan kayi haku'ri dan Allah!
Mun san cewa bamu da zumunci bamu kuma kyauta ba, amma hannun ka baya ribewa ka yanka ka yar"

"Sai dai idan hannun bai ishe ka da radaddi ba" ya katse ta, a zafaffe.

Nan fa gabadaya suka hada baki wurin bada hakuri, amma ina Kamar kara tunzura fadeel suke.

Daga Karshe ma ya bar falon a fusace zuwa sama, sosai fadeelah ta tausaya masa, amma hakan bazai hana
ta fada masa ya yafe musu ba, tunda sun gane laifin su.

"Ina zuwa" tace tana bin shi a baya da sauri, kwance ta tarar da shi yayi rub da ciki, hannunta kan k'irjinta
ta karaso gaban gadon, kwanciya tayi a jikin shi tace

"fadeeeeeeel".....

_tnx my readers for the love and support_😘

SHARE

COMMENT

NOOR✍️
I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*

💝ƘƳAUTAR ƘOƊA💝
(It's all about love, scracifes, Hatred and destiny)

*wattpad*
@NoorEemaan

ELEGANT ONLINE WRITER'S📚🖊

https://facebook.com/groups/943534712916776/masu amfani da facebook su yi join ta wanna link din.

EDITING IS NOT ALLOWED❌

Page 77-78

"Go away! Ba ki na goyan bayan su ba" ya fada kamar ƴaro dan shekara shida.
Dariya tayi, kana ta juyo da fuskar shi ta dan birkita shi da kisses, Sannan tace "sam ba haka bane, na sani
cewa basu kyauta ba, amma yaya zaka yi, sai hakuri, tabbas shine abinda ya dace kayi tunda sun yi
nadama, ina da tabbacin cewa da mahmah na raye, nasan zata yafe musu, kayi hakuri ka manta komai kaji,
rayuwar nan nawa take, kuma karka manta Allah yana tare da masu hakuri, dan haka kayi hakuri kaji my
handsome husband"

Shiru yayi yana jin yanda kalaman ta suke ratsa shi, musamman da ta ambaci Mahmah, ji yayi zuciyar sa
tayi sanyi. Kallon ta yayi yace "na hakura"

Rungume shi tayi, kana ta ja shi suka sauko kasa.


"Allah ya yafe mana gabadaya" shine abinda yace bayan sun zauna.

"Mun gode Fadeel dan albarka, Allah ya saka maka da alkhairi, dama mun san kyawawan halin mahaifan
ka a jinin ka yake, bacin rai ne ya janyo hakan, Allah yasaka maka da alkhairi" haka dai kowa ke fadin
albarkacin bakinsa, Sannan suka ɗora da yiwa Fadeelah godiya domin tabbas ta cika mata ta gari.

"Ina yaya take ne bamu ganta ba?" kanwar mahmah ta tambaya.

"Ta rasu" yace wani abu mai daci na ratsa ta cikin maƙwogaron sa.

Ai fa nan matan suka fasa kuka, yayinda suma mazan suka ji mutuwar domin sanin kowa ne cewa Mahmah
mutuniyar kirki ci, kuma har ga Allah basu san cewa Mahmah ta koma ga Allah ba, wanda babu abinda ya
janyo hakan sai rashin zumunci.

Fadeelah ma sai data yi kuka, sai da mazan suka tsawatar musu kan suyi Shiru add'ua kawai take bukata,
nan dai kowa yayi mata add'uo'i...
Sosai fadeelah da wasu Chef suka Shiga hidiman kawo musu abinci iri daban-daban bayan sun ci sun koshi,
aka bawa kowa daki da duk abinda zai bukata, domin fadeel yace su kwana tunda da nisa kada su koma a
yau dare yayi...

Washegari bayan sun shirya sunyi breakfast, kana ya saka aka kawo wa ko wannen su wasu sababbin kaya
suka sanja, already dama tun jiya yasa akayi musu booking jirgi, motocin escort din fadeel ne suka kai su
har airport, bayan ya gama cika musu jaka da kudade, sosai suka yi godiya hadi da shi masa albarka,
Sannan suka roke shi yana kawo musu ziyara da wanna suka yi sallama, suka tafi cike da mamakin arzikin
da Fadeel yayi, tabbas abin da mamaki, nadama ce ta kara rufe su, suna dana sanin dama sun taimaki su
Fadeel a lokacin da suke bukatar hakan.

**************

Watan su dangin Fadeel biyu ɗa komawa, su ma su Fadeel suka kai musu ziyara, wanda Sosai suka ji dadin
hakan, kwanansu biyu suka dawo bayan ya gama cika su da kudi, ya kuma siya musu babban gida sabon
gini, yace su saka haya a tsohon gidan suna raba kudin, haka zalika dangin Mahmah yayi musu the same
thing.

sosai suka gode masa, tun yana amsa godiyar har yayi shiru, domin godiya taki karewa, fadeelah ce ma ta
cigaba ɗa amsawa da ameen.

Daga nan suka wuce abuja wajen Alhaji Sufyan Rufa'i suka masa kwana biyu shima wanda yaji dadin hakan
sosai, domin basa kasar suma basu dade da dawowa ba, daga nan suka koma Lagos.

*****************

Kwance suke cikin jacuzzi suna wanka, gabadaya kumfa ya rufe jikinsu banda fuskokin su, ra bi wanka, ra bi
soyaaya suka yi, bayan sun gama wankan wanda suka dauki awa biyu suka yi kana suka dauraye jikinsu,
bathrobe jajaye suka sanya, kana suka fito...
Mai suka shafa suna hirar su gwanin burgewa, bomshort blue, da half vest pink ta sanya, sai ta raba gashin
ta biyu ta kama da siraran ribbon ta makale abin adon gashi gefe-gefe, kwalli da man labe ta sanya, ta
shafa oil perfume kana ta juyo ga fadeel dake shirya wa cikin kananun kaya ta dora hannu a kugu irin ka
kalle ni dinan, ya kuwa lalace a kallon ta domin sosai tayi kyau, kamar yarinya under 16 ta dawo.

Kasa hakuri yayi ya tsotse man leben kana ya riko hannun ta zuwa dining area, kujera ya ja mata suka
zauna kana yace "yanzu me zaki ci, nayi serving dinki"

Kallon abincin tayi ta murfin warmers din daya kasance na glass tace "Ni babu abinda ya min anan" tace
tana yamutsa fuska kamar taga abin kyama.

Ajiye serving spoon din yayi yace


"toh gayamin, me zaki ci?" Yana mamakin zaban abincin data fara yau kwana hudu kenan.

Turo baki tayi tace "wanna kazar daka taba hadamin a daran farkon mu ka tuna?" tace tana tande lebe.

Shafa kansa yayi, shi ina zai iya tuna yanda ya hada kazar "anya wiffy zan iya tunawa kuwa?"

"Toh ni wallahi shi nake so" tace tana bata fuska.

"Ok ok bari na hada miki"

Murmushi tayi tace "toh ka gama cin abinci tukunna"

"Are you sure zaki iya jirana in kammala cin abincin?" jinjina masa kai tayi, ta zuba masa abincin, ta bashi a
baki ya shiga ci ya kuwa ci sosai ya kora da fresh milk hadi da ruwa kana suka nufi private kitchen dinsu.

Sosai yayi kokari wurin hada kazar gudun kada tace ba irin shi bane, bayan ya gama ya zuba mata a tray
kana ya daukar mata lemo mara gas domin tace bata son mai gas yanzu....
Falo suka dawo nan ya ajiye mata a gaban ta, hannu baka hannu kwarya haka ta dinga yagar naman ta ma
ki bari ya bata, wai baya bata da sauri, bai gama mamaki ba sai daya ga ta tashi da katuwar kazar nan kaf,
har da tauna kasusuwan, lemo ya mika mata ta shanye tas tana sauke ajiyar zuciya.

"Ya ishe ki?" ya tambayeta

Jinjina masa kai tayi tace "thank you so much my one" ta fada tana dora kanta kan kafadar shi, bayan
mintuna goma yaji tana kokarin zamowa, sauri taro ta yayi, domin yasan bacci tayi...

Kwantar da ita yayi kan doguwar kujera, kitchen ya kai tray din, ya kuma debo ruwa a bowl ya wanke mata
hannu, bayan ya zubar da ruwan yazo ya zauna yana kallon ta, yana kuma lura da sauyen-sauyen ta.

Kasa hakuri yayi ya kira doctor yazo ya duba ta. Babu jimawa doctor yazo ya yi gwaje_gwajen sa yace zai
kawo result da yamma, Fadeel yace baya iya jira, ya daure ya kawo masa yanzu daya duba, likitan bai musa
ba ya tafi, Fadeelah kuwa bata san abinda ake ba, domin bacci take Sosai.
Awa daya da rabi doctor ya kawo result, jikin fadeel na rawa ya bud'e result, ai fadin zallan farinciki d'aya
kawata fuskar sa bata lokaci ne, sosai Fadeel ya shiga murna ganin Fadeelah'n shi da shigar ciki,
sujaddul_shukur yayi, kana ya mike ya shiga tsallen murna, wanda hakan ya tashi fadeelah...

Cikin muryar bacci tace "Fadeel what's it, Lafiya?"

Jin muryar ta ya sanya shi zuwa gaban ta ya ce "you are pregnant fadeelah, you re carrying my baby in your
womb" yafada yana nuna mata result din, cikin farincikin mara misaltuwa.

Abin dariya Ita ma mikewa tayi ta rike hannunsa suka shiga tsallen murna, sai da suka gaji suka zube kan
kujera suna mayar ɗa numfashi, kallon juna suke murmushi shimfud'e a fusk'ar su, a hankali suka matso da
fusk'ar su dab da juna, suka hade bakin su waje d'aya.

Kafin dare kuwa kowa ya sani, domin fadeel ya gama Kiran kowa ya fada musu, har da Daddy da Mommah
kuwa, a daran kuwa dady da Mommah suka zo duba ta, Daddy ya shiga tsokanar ta wai princess din shi ta
girma ta kusan zama uwa. Dariya tayi tana shigewa jikin Mommah cikin kunƴa.

**********

Ta bangaren Jameel kuwa ya sake nutsuwa sak'amak'on mutuwar haulat, wata yarinya data dade tana
son shi ya amince zai aure ta, duk da ba wani sonta yake ba, amma yasan With time zai so ta, shi kam
yanzu tsoron zina yake hakan yasa shi zaban yin auren..
A daran su na farko ya fahimci ita din ba budurwa bace, amma bai da ta cewa domin abinda ya aikata ne
yake dawowa kansa, sosai ya kara kyamar zina, yana kuma fatan idan Allah ya basu zuri'a kada y'ay'an su
su kasance masu aikata wanna mummunan zunubin...

Ta bangaren minister Sa'id kuwa har gida yazo ya roki Daddy kan ya yafe masa, domin shine ya saka aka
nutsar da Kayan shi cikin ruwa, ya biya matukan jirgin ruwa kudi masu yawa, ya kuma sake gaya masa
muguntar da suka sake shirya masa na kashe Fadeelah ko Fadeel, sosai dadi yayi mamakin hakan, lallai
duniya abin tsoro ne, tabbas minister Sa'id bai cancanci zama aminin sa ba, hakan yasa shi cewa kada ya
kara zuwa kusa dashi, cutar da shi da yayi kuwa ya yafe masa.
Jiki ba kwari minister Sa'id ya tafi cikin nadama, Yayinda ya kara godewa Allah daya bashi Fadeel a
matsayin suruki, yana kuma godewa Allah da ba Jameel bane mijin princess din shi (fadeelah). Wasu
lokutan abinda muke ki shine alkhari a garemu....

Share fisabilillah

Comment
I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*

💝KYAUTAR KODA💝
(It's all about love, scracifes, hatred and destiny)

*First edition*

ELEGANT ONLINE WRITER'S📚🖊

EDITING IS NOT ALLOWED❌

https://facebook.com/groups/943534712916776/
Masu amfani da facebook su yi join ta wanna link din.

#Ending

Page 79-80
*Bayan Wata Takwas*

A yau Fadeelah ta fara nakuda, babu bata lokaci suka nufi asibiti, Fadeel ya gama tayar da hankalin shi.

★★★

K'a'idar asibitin idan mace zata haihu sai mijin ta na dakin haihuwar shi ma sanye da kayan asibitin kamar
yadda fadeelah ta saka.

Add'ua yake tofa mata hannunsu sarke dana juna ta ki sakin sa, sai faman cije lebe take sakamakon
azaban daya ishe ta.

Chan tayi nishi, sai ga kan 'ya ya taho, kasa kalla Fadeel yayi Saboda tausayi, dama haka uwa ke shan azaba
idan zata haihu, a hakan wasu y'ay'an ke kasa yin ladabi biyayya ga mahaifiyar su? Wani imani ke kara
shigar sa.

Kan yar na fadowa ta canyara kuka, wani nishin ta fara yi, kan wata 'yar ya fara tahowa, wani nishin ta kara
yi kan da ya taho wanna karon namiji ne, mamaki ne ya kama Fadeel da jinjina iko da k'arfi buwayi gagara
misali, babu Wanda ya taba tunanin fadeelah zata haifi yaya uku a lokaci d'aya, domin cikinta bai da uban
girman nan, hawayen farinciki ne ya Zubo masa, at last, yes at last, a karshe sun cikawa Mahmah burinta,
sumbatar fadeelah data gama jigata ko hannunta bata iya dagawa yayi, ita kam bin shi take da kallo tana
murmushi Yayinda itama hawayen farinciki ke bin gefe da gefen fusk'ar ta.

Duk da jinin dake jikin yaran hakan bai hana shi daukar su daya bayan daya ba. Kafin dare asibiti ya cika,
kowa sai son barka, Daddy kasa boye farincikin sa yayi, ya kara tabbatar wa, fadeelah da Fadeel tarayya su
alkhairi ce.

Alhaji Sufyan Rufa'i da Daddy Kyautar ban girma suka bawa triplet (yan uku) din fadeel, su Mommah da
sauran yan'uwan na dangin Fadeel dana fadeelah sun cika asibiti, yan uku fa sun sha kyauta masu tsada
kuwa, wasu gidajen, wasu kudade, wasu motoci haka kowa ya dinga bada tashi Kyautar, kowa ka gani cikin
farinciki yake, kwanan Fadeelah hudu aka sallamesu.
Cikin masu kyauta har da Jameel ya aiko da nasa, fadeelah taki karba, amma Fadeel ya hana ta yace yin
hakan ba kyau, komai ya wuce, ko da baza su yi amfani dashi ba, sai ta kyautar, akan taki amsa.

Hakan kuwa akayi, ta karba, suka ce wa dan aiken yace "An gode"

*RANAR SUNA*

A wani babban hall mai cin mutane dubu dari biyar suka yi sunan, ko ina jama'a ne an cika kowa ka gani
fuskar sa shimfud'e da farinciki, yan uku da suka ci sunan Mahmah, sunan Mommah da kuma sunan baban
Fadeel, shirye cikin wasu had'add'un kuma tsadaddun kaya, ta farkon kamanin Mahmah sak ta dauko
tamkar an tsaga kara, ta biyun ta dauki kamanin fadeelah, yayinda ta uku ta dauki kamanin fadeel ana
musu lakabi da *ta farko little mah, ta biyu Amnah, na uku kuma amjad*

Daga baya na hango fans din ƘƳAUTAR ƘOƊA sun sha kyau cikin shigar tsadaddun material blue and sliver,
sai faman cin fried Rice da kaza suke, wasu kuma na cin tuwon sakwara da miyar egusi yaji nama, kowa dai
abinda ya zaba yake zubawa yaci da kansa.

Nan na hango su Darma, oum Abdul-rahman, sis suwaiba, Nafessah Aleeyu (feenah) Fatima Ali Adam,
biejarh, sis nabeela, hajency, hajiya Rukayya, sis laylerh sis hassana, maman sudais, narnah, sis Aisha, sis
Fatima, sis sadeeyerh, sis Mariam jumare, wai gaskiya kuna da yawa. Kyautar koda fans sun yi kara sosai a
sunan yan uku, har wajen fadeelah da Fadeel suka je aka dauke su hoto da yan uku....😂lolz

Bayan suna fadeel yayi wa Alhaji Sufyan Rufa'i albishir da cewa ya bashi Amnah kyauta halak malak da
zaran Fadeelah'n sa ta gama shayar da ita, sannan su little mah zasu dinga zuwa yi masa hutu, sosai
fadeelah ta ji dadi, domin Alhaji sufyan ya cancanci hakan.

A lokacin da Alhaji sufyan da matar sa suka ji wanna sadaukarwa da fadeel yayi musu kukan farinciki suka
saka, domin tabbas sun ji dadi ko ba komai zasu rage kewa, tabbas duk wanda Allah ya jarabta da rashin
haihuwa zai ji ba dadi taɓɓas, amma hakuri shine ya dace mutum yayi, ga shi kuma sun ci ribar hakurin,
tun kafin Amnah ta koma gidan suka ware mata daki babba suka saka mata kayan wasa iri,-iri na yara....

*One Year later*

*SAUDI ARABIA*
A hankali suke saukowa daga jirgi, fusk'ar su ɗauke da murmushi, Yayinda hannun su ke sarke dana juna,
suna kallon yadda little mah, Amnah, da Amjad suke sauka daga jirgi da sauri-sauri.

Sanye Fadeel da Fadeelah suke cikin shigar kananun kaya, yan uku sanye cikin riga da wando iri daya sun yi
kyau sosai, ga wayo kamar ba yan shekara d'aya ba.

Fadeelah tana nan yanda take bata yi kiba ba, sai ma Fadeel daya dan yi kadan, amma kallon daya zaka
musu kasan cewa suna cikin kwanciyar hankali.

Kamar yadda ko wani shekara akwai kasar da suke tafiya hutu, wasu lokutan da Alhaji sufyan da matar sa
wanda suke rike da Amnah kana suna nuna mata kauna iya kauna.

wanna karon saudiya suka taho domin sauke farali, amma banda su Alhaji Sufyan Rufa'i.

daga nan suyi yawan bude ido, wasu had'add'un motoci biyu ne suka zo daukar su, a wani hada'dden
hotel suka sauka.

A washegari suka fara gabatar da ibada, sosai suka yi ibada, da dare yayi su tafi masauki, a haka suka gama
tsaftataciyar ibadar su, sai dai fatan Allah ya amsa.

Wuraren tarihi kala-kala suka je, sunyi videos da hotuna kala-kala , Amnah kuwa ta dauki babban tablet
dinta tana video call da su Alhaji Sufyan rufa'i hadi da nuna masu wurare, domin sosai take son su Alhaji
Sufyan rufa'i ta ma fi sabawa dasu fiye da iyayen ta...

duk inda suka je sai yan uku sun ce "mummy, Daddy, ina ne nan?" iyayen su shiga basu labari, sosai suka yi
having fun.

Daga nan suka je wuraren siyar da abaya, da gwala-gwalai da azurfofi ya siya musu.
daga nan suka dawo masaukin su a gajiye bayan ta yiwa yaran wanka, Fadeel ya shirya su cikin kayan
bacci, suka kwantar da su a dakin da suka kama kasancewar mai two bedroom ne, kamar kullum haka
suka dinga taya y'ay'an nasu hira har bacci ya sauke su, add'ua suka tofa musu, suka lullube su hadi da
kashe wuta suka bar musu dim light.

Fadeel ya kamo hannun matar sa suka nufi nasu bedroon din, bayan sunyi wanka a tare suka fito, kayan
bacci suka saka, tana manne a kirjin sa yace

" i love you wiffy, you re my everthing"

" i love you too my one, you re the best husband ever"

Murmushi yayi ya kara rungume ta yace " my Darling ya kamata a yau na Samar wa su little mah kani ko
kanwa, nasan kin gaji amma please ki bani....."

Bata bari ya kai karshe ba ta kama lallausan lips dinsa ta fara birkita shi
da salon ta, nan da nan suka Lula duniyar ma'aurata..

#hamdan lillahi

Share fisabilillah to others

Comment dinku is needed

Special thanks to all kyautar koda fans, son so fisabilillah habibtie's💞

_na so zayyano duka groups din da kyautar koda yaje domin na nuna special thanks dina a gareku, buh
Lokaci bai bani dama ba, amma ina so ku sani duk inda kyautar koda yaje, da makarantar kyautar koda ina
son ku fisabilillah_💖😘
A nan na kawo karshen novel dina mai Suna kyautar koda, kurakuran ciki Allah ya yafe min da ni da
makaranta, fadakarwan ciki Allah ya bamu ladan.

sannan zan so cin ra'ayoyinku a kan littafin ƙƴautar ƙoɗa da darasin dake ciki.

caution

Littafin kyautar koda hakkin mallakan NoorEemaan ne! Ban yarda a juya min shi ta ko wace siga ba, idan
kunne yaji.....

NoorEemaan ce🔥😍
07082281566

Sat, October 2O21

I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*

You might also like