Professional Documents
Culture Documents
Hasken Musulumci.
Hasken Musulumci.
FARILLAN ALWALA
Farillan alwala sune, Nafarko shine Niyyah, wanke dukkan fuska, Da wanke
hannaye biyu 2, Da shafar kai, Da wanke kafafuwa biyu 2, Sannan ka gaggautawa
da cucudawa.
SUNNONIN ALWALA
Nafarko wanke hannaye biyu 2 (ku,i), Kurkure baki, Shaqar ruwa a hanci ka face
ruwar, Da woda shafar kai, Shafar kunne guda biyu 2.
MUSTAHABBAN ALWALA
Nafarko shine wuri mai tsarki, Da yin bismillah, Da Qaranta ruwa, Farawa da dama
kafin hagu, (Wanke hannye da Qafafuwa) Da jera sunnoni, Da yin Aswaki.
FARILLAN TAIMAMA
Na farko shine yin Niyyah, Da shafe fuska da hannaye biyu na ku’I, Da waje mai
tsarki, Da jerantawa.
FARILLAN SALLAH
Da farko shigan lokacin sallah, tsarkin jiki, tufafi, wajenda za ayi sallar, Da suturta
Al’aura, tsayuwa, fuskantar al’qibla, Halarto da niyyah yayin gabatarda sallah, Da
kabbarar Harama, Da karatun Fatiha, Da ruku’I Da dagowa daga ruku’I, Da sujjada,
Da dagowa daga sujjada, Da zaman tahiya.
SUNNONIN SALLAH
Karatun sura, Da fadin Amin, sirinta karatu a inda ake sirrintawa, Da bayyana
karatu a inda ake bayyanawa, Da Nutsuwa da daidaituwa, Da kabbarori, fadin sami
Allahu liman hamidahu, Da karanta tahiya, Da yin tasbihi a ruku da sujjada.
ABUBUWANDA SUKE LALATA SALLAH
Akwai Hadasi, Da yawan Magana a halin mantuwa, Hakanan qaranta Magana da
gangan, Da yin Dariya da gangan, Hakanan tareda mantuwa, Da barin wani abu
daga rukunin sallah, Da tuna wata sallah, Da barin rabi daga karatun fatiha, Da
yayewar al’aura ba tareda lalura da mantuwa ba, Da yanke niyyah.
Sujjada Qabli: Ana yinta idan a sallar farillah mutum ya manta ya rage wani abu
daga salla, Za kayi sujjada biyu tareda tahiya da sallama.
Ko idan kana shakku shin ragewa kayi, ko ka rawa kayi? Sai kayi Qabli.
SALLAR JUMMA’A
Sallar jumma’a tanada sharuda, Da rukuni, Da ladabi, Da alkairai masu yawa, ku
yawaita salatin Annabi Muhammad s.a.w.
FARILLAN ZAKKA
Yin niyyah, Da yanci, Da nisabi, Da hauli.
FARILLAN AZUMI
Da farko kasan watan ramadan ya kama, Sannan yin niyyah, Da barin ci da sha, Da
jima’i.
SUNNONIN AZUMI
Gaggauta bude baki, kafara da cin Dabino ko Ruwa, Da jinkirta yin sahur, Da
tsayuwar sallah.
FARILLAN HAJJI
Yin niyyah, da Sanya harami, Da tsayuwar Arfa a dare a lokacin alfijir a wani dutse
wanda da Asubahi a ranar sallar layya, Sannan da dawafi (Amma lazimi ne yin
dawafin).
SUNNONIN HAJJI
Kada ayi aski, da yanke farce, An hana Sanya haraminda yakeda aljihu, An hana a
shafa turare.
NA KAWO KARSHEN WANNAN LITTAFI MAI ALBARKA, IN KA RISKI WANNAN
LITTAFI KADAURE KAYI SHARING DINSA ZUWA GA SAURAN MUSULMAI MU
AMFANA GABA DAYAMMU.
NA YI IZINI ABUGA WANNAN LITTAFI, A RABAWA DUKKAN WANDA YAKE BUQATA.
NUMBER WAYAN MARUBUCI IN KANADA TAMBAYA: 08130581754