You are on page 1of 36

1

Labarin Hajja ‘Yar Fulani

Da sunan allah mai rahma mai


jinkai, tsira da aminci su kara
tabbata ga manzon tsira manzon
rahma (SAW), cikin farin ciki nake
gabatarwa al’umma wannan littafin
wanda zai kara wayarda kan
iyayenmu mata kan matsalolin
aure fatan sanyawar albarka daga
gareku.
2

zaune nake da mijina lafiya daga ni


saishi wato dai irin zaman da mata
keso, babu maganar kara aure kullum
burinsa ya faranta mun wannan shine
yake bani damar kyautata masa
kowanne abu zanyi domin farin
cikinsa, banyarda wata tazo tayi aiki
ko dafa abinci ba, komai nine nakeyi,
haka nake wuni ina aiki kamar baiwa
domin nasamu lada kuma na samu
kusanci a zuciyar mijina, idan
yayimun laifi addu'a nake masa bana
iya fushi dashi, idan kuma nine nayi
masa bana bari yayi fushi dani, koda
yake matarsa ta farko ta rasu amma
yayi fatan da ace nine wacce ya fara
aura koba komai da wanda ya aura
afarko tana raye,
3

Domin a tunanin mijna idan tana raye


bazata bari ya aureni ba, kuma allah
ya hukunta saiya aureni, to amma a
koda yaushe nakan fada masa
kabarinsa haka allah ya
hukunta.

domin inganta zaman aurenmu na


kanyi amfani da magunguna da suka
dace domin kuwa banida wajen ajiyar
kudi adakina amma wajen ajiyar
magani zaka hada shago guda, bana
amfanida abu daya,
4

Koda yaushe domin sanin


muhimmancinsu nakan canja wani
kalan, kuma ban damu da saiya yabeni
ba, kasancewa ta amatsayin matarsa
ya isheni.

kada kuyi mamakin wannan abunda


nakeyi dukda muna zaune lafiya kowa
hankalinsa kwance zancen gaskiya
nasha wahala kafin na sameshi
amatsayin mijina shiyasa nake
ganinsa tamkar zinare, Labarine mai
tsawo amma a takaice bari mu koma
baya na baku asalin labarin.
5

A dai sanin kowane namiji baya taba


auren matar wani wanda ba matarsa
ba duk Wanda kaga yakai ga auren
mace tofa dama matarshi ce, itama
mace haka komai dadewa a gidansu
mijinta zaiyi dakon haduwar su
shiyasa hausawa ke fadin
kabarinsa.

Wannan kam wani abune da kowa ya


sanshi saidai yafi armashi afadeshi
abaka madadin yarda da hakan,
6

Saboda Wanda ta samu jinkiri wajen


samun Miji ana daukanta Wanda
batada farin jini ko kuma marar
kamun kai bincike akanta daban
daban akarshe saidai ta toshe
kunnuwanta amma zancen mutane
bazai taba kyale taba,

Kamar dai yanda kowacce mace keda


burin auren wanda takeso nima nayi
wannan burin koda yake ni banida
tsanani akan saina auri me kudi saidai
amma dai naso nasamu wanda
nakeso, domin zan iya auren wanda
bayasona amma bazan taba auren
wanda banaso ba, sannan inason miji
wanda yasan darajar mace wanda zai
iya jure rauninta,
7

Sannan yanada ilimi kuma yakeda


mu'amala me kyau wannan mijin
shine naso nazaba amma saidai
kaddara ta batamun wannan tanadin a
lokacinda nakeso ba, kowanne namiji
nahadu dashi sai naga be cika
wadannan ba, haka dai nake zaune a
gidanmu,

Ana cewa akwai wani mataki da mace


ke kaiwa idan ta kasa aure da wuri
shine kowanne namiji zai iya nemanta
ba tareda tayi bincike akansaba don
gudun kada ya fasa,
To nima naje wannan matakin saidai
ni ra'ayina ya banbanta dana sauran
mata dalili kuwa na yarda na zauna
babu miji har abada amma ban yarda
na rasa kimata ta mace..
8

Ko kuma auren wanda banasoba,


Fulani sunada akida kala biyu, na
farko kunya na biyu kuma gudun abun
kunya, tayaya ‘yar wannan kabila zata
iya furtawa na miji tana sonsa? Haka
nan dai naketa addu’a na samun miji
nagari,

Tofa saidai hakan bai hana naji inason


wani ba saboda tunda nake aduniya
shikadai naji inaso nayi rayuwa dashi
amatsayin mijina to amma na kasa
furta masa haka shima ko alama baya
bukatar muyi dogon zance don yana
matukar jin kunyata, haka muka shafe
shekara takwas muna tare dukda yayi
aure ban rabu dashi ba,
9

Haka zalika babu wani wanda nakeso


sama dashi,
Tabbas komai yayi farko zaiyi karshe
domin saida matarsa ta rasu yana
kokarin sake wani auren anan ya
fahimci soyayyata kuma dukda cewar
nine na fara nuna masa soyayyata
amma yafini farinciki,
Bazan taba mantawa da abu biyu ban
a farko Anyi aurena inada shekaru
talatin a duniya, na biyu kuma mijin
dana aura shine saurayina na farko a
duniya,
10

Tofa ta haka ne nake ganin babu


wacce tafini sanin muhimmanci miji,
kamar yanda be kamata asamu wanda
zata shiga zuciyarsa sama dani ba.
Wannan shine takaitaccen labarin
aurena sai kuma magugunan da suka
kara temakona wajen samun
zuciyarsa.
11

Kamar yanda mukayi bayani abaya Ba


sai lalle matan aureba budurwa ma
tana iya fitar da iska a gabanta wanda
yake kama da tusa lokacinda take
tafiya ko tsuguno ko kuma taji iska
tana shigarta,
wannan yana faruwane sakamakon
rashin kyakkyawan kula daya kamata
budurwa tayi a gabanta,
12

Kamar mace tarinka zama ba wando


ko barin iska na shigarta da yawan
amfanida abu me sanyi kamar tsarki
ko wanka, yawan bude kafafu da tsalle
wadannan suna daga cikin abubuwa
da suke saka budurwa tana fuskanta
irin haka, koda yake ba shine yake
saka mace ta rasa budurciba amma
dai zai bude gabanta.

Matan aure da dama suna fama da


hakan musamman wajen saduwar
aure wanda wasu budewa kesa iska
fita domin idan mace ta haifu tana
bukatar gyaran gaba sosai bawai
kawai tana shiga ruwan zafi ba,
13

Anaso tayi gyara yanda ciki zai hade


jikinta yayi dumi, kuma kowacce
haifuwa hakan yanada muhimmanci a
zaman aure.

sannan ki kiyaye shan Abu me sanyi,


ki daina bari iska tana shigarki
Sannan anaso ki yawaita shan shayi
mai citta idan kinada hali ki yawaita
cin farfesu mai dauke da kayan yaji,

ki yawaita cin citta tafarnuwa zuma


tare da dabino suna da matukar
amfani wajen sanya jikin mace yayi
dumi ya hade sannan ki kiyaye wanka
da ruwan sanyi a koda yaushe.
14

Ba shiga cikin ruwan ake ba haka


zalika ba dundume ake da ruwanba,
wannan tsarkine kadai zakiyi da
ruwan itatuwan domin farfado da yan
matancin mace tamkar daren farko, ba
matsi yakeba amma koda yaushe miji
zai kasance me zumudin saduwa da
mace saboda jin dadin saduwa da ita,
shine tsarkin jaraba wanda a
shekarun baya na kawo makamcinsa
15

Saidai dukda cewar shima wannan


yana cikin magungunan sirri wanda
ba kowa ke saniba amma a wannan
karon mun bayyanashi a ko ina
musamman duniyar maganin mata.

itatuwa biyar da zaki wankesu tas


sannan kisamu tukunya ki tafasa saiki
tace ruwan ki zuba a buta kiyi tsarki
sau uku arana idan mijinki yana nan,
idan ya kare ki sake dafa itatuwan
domin kina iya dafasu sau biyu.
16

jijiyar taba
itacen dan madina
itacen dan kadafi
itacen idon zakara
ki samu icen farar biya rana danye ki
bare saiki dauresu haka ake musu
kafin a dafa.
17

Bayan kamala bayanin daya gabata


wanda su itatuwane zallah masu gyara
zaman aure wanda sirrine babba
amma awannan karon kuma itacene
da kuma ganyensa wanda ake kira

mata suna amfanida lalle wajen tafasa


jijiyarsa da ganyen magarya suna
zama aciki don kawarda ciwon sanyi
da kuma gamsuwa wajen saduwa,
18

Amma hakan yakan bawa wasu matan


matsala domin bincike na zahiri ya
nuna lalle agaban mace na daya daga
cikin abunda ke kawowa mijinta
saurin inzali, hakan yasa besamu
karbuwa ba a wannan fannin, harlau
yakan mayarda gaban mace wani kala
wanda akarshe zaiyi baki musamman
farar mace.

Akwai hadin da ake masa wanda


bashida wahala sai aiki wajen bawa
miji nishadi haka zalika yana gamsar
da miji sosai,
19

amma shi garin lallen ake bukata ki


tabbatar yayi laushi sosai saiki
kwabashi da zuma fara da man zaitun
kiyi matsi dashi bayan kamar sa'o,i
uku saiki wanke sannan ki shafa man
zaitun kafin kwanciya da miji.
20

Ba wannan shine karon farko danayi


rubutu akan maganin mallaka ba,
saidai wannan shine na farko dana
duba wasu dabbobi guda hudu da ake
rububin samunsu don samun biyan
bukata musamman akan abunda ya
shafi kwanciyar aure wanda mace
zatayi ko namiji yayi.

Magani ajikin dabba wanda shari'a ta


yarda dashi shine wanda ya zama
halak aci, amma wanda cinsa
haramunne aiki dashi ma haramunne,
kamar dai kare ko jaki da kuma duk
abun daya zama mushe da dai
sauransu.
21

Akwai kuma salon amfani dashi ko


kuma yanda ake yankashi duk wata
dabba daya zama akwai sharuda aciki
kafin akaiga amfani dashi ya zama
tsubbu ko sihiri, wannan bayanine me
tsayi don haka zamuje ga wasu daga
cikin dabbobi da ake aiki dasu kai
tsaye wajen jin dadin rayuwar aure.
saidai bayanin zaizo a takaice ne,
22

maganin cututtuka na muslinci wanda


yakeda tsohon tarihi daga nononsa
zuwa fitsarinsa, rakumi yanada suffa
babba wanda yakeda kwarjini a ido
saidai idan aka saka masa akala komai
kankantar yaro zai jashi inda yakeso,
yanada biyayya ga duk wanda ke rike
da akalarsa wannan shine sirrin da
aka fara samu akansa, kuma wannan
yasa mata ke aiki da akalar wajen
samun zuciyar miji, sannan anayin
gumbar kwakwal warsa,
23

Bayan haka ana dafa naman tozonsa,


namiji yana shan fitsarinsa ko kuma
ya dafa gabansa yaci, wadannan duka
suna saka namiji dadewa yana saduwa
da mace.

Daya daga cikin sirrin gyaran aure


kenan, koda yake wasu da dama sun
kallah a rumbum video dake youtube
dina, wanda ake hada albasa da zuma
da nonon rakumi ana bawa namiji
yanasha. kamar ita kuma mace idan ya
zama bata iya dadewa ana mu'amalar
aure da ita to zata sha zai bata
sha'awa yasa tana dadewa bata gaji ba
kamar yanda namiji zai dade yana
saduwa da matarsa matukar yanasha,
24

Ayanyanka jar albasa suyi kanana sai


azuba nonon rakumin aciki abarshi ya
dade kamar rabin sa'a ko sa'a daya sai
atace nonon sannan azuba farar zuma
kadan agauraya asamu waje me kyau
a ajiye idan yadan dade asha sau daya
a mako daya
25

Akwai zunzurutun muhimmanci


kusan abu biyu akan damo, na farko
yana jin kunyar kowa harma da wanda
ke shirin yankashi, na biyu kuma
yanada hakuri da saukin kai wajen
matarsa domin idan yana saduwa da
matarsa koda za'a a kasheshi bazai
dainaba, wani abu kuma dayake dashi
wanda shima ya temaka wajen samun
sirrinsa shine baya saduwa da kowa
saida matarsa
26

idan kuma ya rasa matarsa tofa saidai


ya kashe kansa, yanason matarsa
fiyeda ransa wannan itace babbar
dabi'arsa, babban sirrin maganin
mata ajikinsa shine kitsensa da
zuciyarsa tabbas muhimmancinsu
yakai makura wajen gamsuwa
tsakanin ma'aurata, mace me aiki
dashi tana samun kulawa wajen miji
haka zalika hakuri da saukin kai.
Ana iya hada man damo da man
ayu da miski ayi matsi amma
duka anaso asamu original
wannan keda kanki zakisan kin
gamsar da miji, ko kuma ki shafa
shi kadai wannan ma yana aiki
sosai wajen bawa miji nishadi
sannan miji ya kasance dake
akoda yaushe,
27

Wani Abu me muhimmanci shine kafin


amfani dashi ki hadashi da gadalin mata
lokacin narkashi shine zaiyi yanda akeso
wato ki taka wannan gadalin idan ya
bushe ki zuba acikin kitsen lokacinda
kike narkawa,
Sannan yana tasiri akan namiji idan
yanaso yana gamsarda matarsa ya rinka
shafawa amma shi namiji yana hadashi
da man zaitun kuma idan ya dade zai
wanke kamar dai ya samu sa’o,I biyu,
koda mace batacijn dadinsa zayaji.
28

wannan shima abu biyu sunada


muhimmanci asani akanshi, na farko
soyayya na biyu kuma kishi, sau daya
yake soyayya da zaran an rabasu to an
raba rayuwarsu, sunada alkawari
yanda kowanne daga ciki bazai taba
rabuwa da dan uwansa ba, idan anaso
ayi magani dasu hadasu akeyi ayanka,
29

Galibi mata ke aiki dashi wajen samun


soyayyar miji ko kuma amare dake
shirin aure sune ke dafawa a kowanne
mako kuma anayi sau uku kafin auren,
hadin kai wajen amarya da ango ga
soyayya a koda yaushe idan baki iya
dafawa ba.

kisamu sauyar yadiya da sauyar


malmo da sassaken baure sai kukuki
da ganyen zogale sai ganyen raihan
wadannan zaki dafasu ki tace ruwan
30

Sannan ki dauko tantabaru aure


wanda dama kin gyarasu ki saka
acikin wannan ruwan saikiyi garin
dan kumasa da 'ya'yam zogale ki zuba
aciki sannan ki saka kayan miya yanda
zaki iyaci shikenan yana dafuwa zaki
iyacin kayanki, wannan sirrin dafashi.

ko abu daya ka sani akan ayu ya


isheka samun sirrinsa wato
31

Yanada sha'awa fiyeda kowacce dabba


aduniya shi kadai yana iya sa'o,i goma
shabiyar yana saduwa da matarsa,
saduwa yafi masa abinci muhimmanci
domin yunwa bata gabansu idan suna
saduwa, saboda mafi yawan masu
kamasu sai lokacin suna saduwa ake
zuwa kansu, ayu yanada masifar fada
amma idan suna saduwa yana zama
mai saukin kai sai yanda akayi dashi,

dabbace wanda kullum cikin shauki


take da bukatar saduwa shiyasa
babban sirrinsa a maganin mata shine
nishadi wajen kwanciya, shine yake sa
namiji yaji dadin mace, haka itama
mace taji dadin namiji,
32

Abu biyu kuma da sukeda


muhimmanci shine kitsensa da
gabansa
wadannan
amfani dasu a
bayyane yake
kamar
wajen samun
namiji shima yakanyi
nishadi, koda
amfani da mansa kafin
yaushe miji
saduwa yana shafawa a
yakan zama
gabansa, itama mace
cikin shaukin
tana iya tsarki da gaban
mace, kamar
ayu bayan ya jika haka
yanda itama
zalika tana iya dakashi
ke mararinsa.
yayi laushi ta kwaba da
zuma tayi matsi kafin
saduwa.
33

A karshe wannan shine Dakakken


yajin maza da mata musamman
wadanda ke bukatar wanke dattin
mara ko kuma kariya daga ciwon
sanyi, wadanda sukafi aiki da wannan
yaji sune wadanda ke shirin yin aure
namiji wanda yakeso kullum yana
gamsarda iyalinsa, domin koda mace
tanada ciwon sanyi kuma ya shiga ciki
ahankali ahankali zai fitar dashi
musamman masu yawan ciwon mara,
34

Shidai wannan garin yajine da ake iya


zubashi kamar cokali daya acikin
ruwan zafi abarshi ya huce sai a
gauraya a tace sannan asaka zuma
asha, sau daya a rana akeshansa.

Domin hada wannan yajin ana


bukatar kayan hadi guda bakwai
(1) garin habba
(2) garin tafarnuwa
(3) al banunaj
(4) kirfat
(5) kanunfari
(6) citta
(7) garin ma'ukhal
idan an hadasu ana dakawa sosai
yanda garin zaiyi laushi.
35

karshen wannan
littafin kenan kuna iya cigaba da
karanta wasu amma sai anyi register
damu a whatsapp ko telegram a
wadannan lambobin

idan kuma kayanmu ake bukata shima


sai a tuntubemu
36

suna Auwal Muhammad


Inkiya Auwal Azare
Jaha Bauchi
Sana’a Kasuwanci

You might also like