You are on page 1of 1

ADDU'AR LARAB-GANA

Laraban Ƙarshen Safar Wacce Ake kira Larab-gana, itace a Alqur'ani Ake Cewa
"FI AYYAMIN NAHASATIN" wato "A Kwanakin Baƙinciki",
A Duk Laraba Irin Wannan Manzon Allah SAW Yace: Ana Saukar Da Bala'o'I
Guda Dubu Dari Uku Da Dubu Ashirin. Duk Bala'o'in Da Zasu Faru A Wannan
Shekarar To A Laraban Karshen Watan Safar Ake Sauko Da Su Zuwa Cikin
Duniya Kamar Yadda Duk Alkhairan Da Zasu Auku A Shekarar Ake Zubo Da Su
A Daren Nisfun Sha'aban.

Za ayi Sallah Raka'a huɗu (Sallama Ɗaya) a ranar larabar qarshe a

watan Safar. A kowani raka' sai a karanta wannan:

 Fatiha (1)

 Inna A'ataina (17)

 Qul huwallahu (5)

 Qul A'uzu bi rabbil falaq (1)

 Qul A'uzu bi rabbin Nas (1)

Bayan sallama, sai a karanta wannan ayar sau 360, ga ayar:

‫وهللا غالب على امره ولكن اكثر الناس ال يعلمون‬

WALLAHU GALIBUL ALA AMRIHI WALA KINNA AK'SARAN NASI


LAA YA'ALAMUN.
Sannan a karanta Jauharatul Kamali (3). Sai a ɗaga hannu a sigar Addu'a,

A ce "SUBHANA RABBIKA RABBIL IZZATI AMMA YASIFUN, WA

SALAMUN ALAL MURSALIN, WALHAMDU LILLAHI RABBIL

ALAMIN (1) A shafa!

Sai ayi sadaqa da kosai, ko waina (masa) ko duk wani abu da ake

soyawa.

BALARABE FARUK YUSUF

You might also like