You are on page 1of 3

Wikipedia 

wani babban farfajiyar Manhaja ce dake tattare da Muƙalolin kundin bayanai akan ilimomi
daban-daban Dan samar da ilimi ga kowa da kowa, da ƙara haɓaka nazarce-nazarce, bincike-
bincike akan ilimomin dake duniya baki ɗaya a kyauta, saboda ganin kowani ɗan adam yasamu ilimi
batare da biyan wani abu ba.[1][1][2] [3]

tambarin shafin Wikipedia

Jimmy Wales babban shugaban Wikipedia kuma wanda yasamar da Manhajar


Larry Sanger mutum na biyu da suka ƙirƙiri Manhajar Wikipedia
Wikipedia Shafine dake yanar gizo wanda kowa na'iya shiga kuma ya amfana ko yataimaka dan
amfanar da wasu, ta hanyar taimako da ilimi ko gyare-gyare da sauransu, wikipedia tana tattare da
harsunan duniya masu yawa, a shafin kowa na iya ƙirƙira tare da gyara makala a kyauta domin
taimakawa asamu ilimi daga kowa da kowa, wannan ne yasa wikipedia yayi zarra a duk duniya
wurin Samar da ilimi daga asalin inda ilimin yafito Dan kuwa wadanda suka Samar da ilimin ko suke
da alaƙa da ilimin sune ke rubuta ilimin da Kansu, hakane yasa aka ba kowa damar yataimaka da
ilimi ta hanyar ƙirƙiran sabon makala ko gyara ta idan anriga an ƙirƙire ta amma bata cika ba ko mai
rubuta yayi kuskure. Harwayau babu wani shafi a duniya baki ɗaya, daya tattara ilimi da bayanai
a yanar gizo a yanzu, kuma miliyoyin ɗalibai ne da malamai, da sauran mutane suke amfana daga
manhajar a kullun.

Tarihi[gyara sashe | Gyara masomin]


An ƙaddamar da shafin Wikipedia ne a ranar 15 ga watan Janairun shekara ta 2001, Jimmy
Wales tare da Larry Sanger sune suka haɗa gwiwa wajen sammar da shafin. A farkon ƙirƙirar shafin
an kafa tane da Turanci kadai amma daga baya sanadiyar karɓuwa da shafin yayi ne yasa ake
samar da karin Harsuna akai akai har zuwa yanzu. A halin yanzu akwai makaloli sama da 5,652,162
a sashen Wikipedia na Turanci wanda kuma shine sashen da yafi kowanne shahara da tarin
makaloli. Ayanzu akwai sama da makaloli guda miliyan arba'in a mabanbantan yarurruka 301,
sannan shafin ya samu masu ziyara mabanbanta guda miliyan 500 da kuma masu ziyara adadin
duka masu ziyara biliyan 18 ko wanne wata tun daga watan Fabrairu na shekara ta 2014.

Hausa Wikipedia[gyara sashe | Gyara masomin]


A sashen Hausa na wikipedia kuma akwai makalolin da suka kai kusan 6,500, duk da yake sashen
yana da karancin masu bayar da gudunmuwa amma ahankali sashen yana kara bunkasa cikin
gaggawa.
Manazarta[gyara sashe | Gyara masomin]
1. ↑ Jump up to:1.0 1.1 "Wikipedia is 20, and its reputation has never been higher". The Economist. January 9,
2021. Retrieved  February 25,  2021.
2. ↑ Cite error: Invalid  <ref>  tag; no text was provided for refs named  Alexa
siteinfo
3. ↑ McGregor, Jena (March 17, 2020). "Wikimedia's approach to coronavirus: Staffers can work 20
hours a week, get paid for full time". The Washington Post. Retrieved  February 25,  2021.

You might also like