You are on page 1of 7

COCMOSA 2021 25th December, 2021.

Rawar Da Tsaffin Dalibai Zasu Ta Wajen Magance Wasu Daga Cikin Matsalolin Da Suka Addabi
Al’ummar Nijeriya Muhammad Abbas Usman CNSS

RAWAR DA TSAFFIN DALIBAI ZASU TAKA WAJEN MAGANCE WASU DAGA


CIKIN MATSALOLIN DA SUKA ADDABI AL’UMMAR NIJERIYA

- Muhammad Abbas Usman CNSS


usmanmabbas90@gmail.com

GABATARWA

Nijeriya qasa ce da Ubangiji Ya yiwa albarka mai tarin yawa, ya kuma sanya mutane
masu bambamcin al’adu da addinai kala daban-daban ke rayuwa acikin ta. Qasar
takasance daya daga cikin manyan qasashe masu fada aji a nahiyar Afrika. Hakan ya
samo asali ne saboda karfin tattalin arziki da ta ke dashi, amma duk da haka tana fama da
wasu giggan matsaloli da suke mata dabaibayi wajen gogayya da saura qasashen duniya
da suka cigaba.

Kadan daga cikin manyan matsalolin da qasar ke fuskanta sun haxa da:

1. Matsalar tsaro
2. Tavarvarewar ilimi
3. Tattalin arziki
4. Kimiyya da fasaha
5. Rashin daidaito, DSS

Saboda qarancin lokaci zanyi magana akan abubawa guda biyu kaxai acikin wannan
qasida tawa; na farko matsalar tsaro da kuma ta biyu Tavarvarewar ilimi.

MATSALAR TSARO

A kwanankin baya Gwamnatin Nijeriya ta fitar da wasu jerin matsaloli a cikin kundin
manufofin tsaron qasar wanda shugaban ya qaddamar a ranar Laraba, 4 ga watan
Disambar 2019.

Manyan matsalolin rashin tsaro da shugaban ya ayyana sun haxa da:


 Ta'addanci.
 Tsattsauran ra'ayin addini.
 Garkuwa da mutane.
 Fashi da makami.
 Rikicin makiyaya da manoma; da kuma

1
COCMOSA 2021 25th December, 2021.
Rawar Da Tsaffin Dalibai Zasu Ta Wajen Magance Wasu Daga Cikin Matsalolin Da Suka Addabi
Al’ummar Nijeriya Muhammad Abbas Usman CNSS

 Rikicin ‘yan aware masu son cin gashin kansu

Matsalar tsaro a Najeriya ta daxe tana ci wa qasar tuwo a qwarya. Tana kuma daga cikin
manyan matsalolin da suke yi wa kasar tarnaki ta fannin ci gaba.

Xaya daga cikin manyan matsalolin tsaro a Najeriya akwai matsalar Qungiyar Boko
Haram. Sai dai ko a kwanakin baya Shugaban kasa gwamnati na ikirarin cewa an samu
sauqi dangane da ayyukan kungiyar ta Boko Haram, inda ya ce an karya lagon 'yan
kungiyar. Duk da cewa cikin satin da ya gabata sai da qungiyar ta kai harin rokokin kusa
da filin sauka da tashin jiragen sama na Maiduguri aranar da Shugaba Buhari ke ziyarar
buxe wasu ayyuka a Jihar a ranar 23 ga watan Disamabar shekarar nan ta 2021.

Amma jerin wasu manyan matsalolin tsaro da kasar ta fitar na nuna alama har yanzu
akwai sauran rina a kaba.

Me ya sa suka zama barazana?

Kungiyar Boko haram ita ce kungiyar da ta yi kaurin suna wadda gwamnatin Najeriya da
sauran kasashe suka ayyana a matsayin kungiyar 'yan ta'adda.

Kungiyar ta fara kai manyan hare-hare ne a Najeriya a 2009 bayan kashe shugabanta
wato Muhammad Yusuf. Har yanzu gwamnatin kasar na nan tana fafatawa da kungiyar ta
Boko Haram.

Matsalar Garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa na daga cikin manyan matsalolin
tsaro a Najeriya, ta yadda a kwanakin baya wasu ke kwatanta girmar matsalar da ta Boko
Haram.

Masu Garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa sun kwana biyu suna cin karensu
babu babbaka a jihohin Kaduna, Naija, Sokoto, Zamfara da Katsina da wasu jihohin da
ba a rasa ba a musamman na yankin arewa maso yammacin qasar nan.

Wannan matsala ta haramta wa mutane da dama bin hanyar Kaduna zuwa Abuja, inda
yawancin mutane suka koma bin jirgin qasa domin kauce wa fadawa hannun masu
garkuwa da mutane.

A bangaren rikicin manoma da makiyaya, gwamnatin kasar ta dade tana fama da wannan
matsalar, duk da cewa masu sharhi kan al'amuran tsaro na ganin an samu sauki ta wannan
bangaren.

2
COCMOSA 2021 25th December, 2021.
Rawar Da Tsaffin Dalibai Zasu Ta Wajen Magance Wasu Daga Cikin Matsalolin Da Suka Addabi
Al’ummar Nijeriya Muhammad Abbas Usman CNSS

A shekarun baya an samu rikice-rikice tsakanin manoma da makiyaya a jihohi irinsu


Benue da Nasarawa da Zamfara. Hakan ya yi sanadiyar mutuwar jama'a da dama, baya ga
asarar dukiyoyi.

A wani bangaren kuma, masana tsaro da dama a Najeriya sun sha kokawa a kan yadda
iyakokin kasar na kan tudu suka zama sakaka. Ana zargin hakan ya ba da dama ga
batagarin da ke fasakwaurin makamai da da miyagun kwayoyi zuwa cikin kasar.

Sai dai a kwanakin baya gwamnatin Najeriya ta kaddamar da wani atisayen mai suna
'SWIFT RESPONSE' a matsayin daya daga cikin matakan da ta xauka na tsaftace
iyakokin kasar.

Atisayen dai na hadin gwiwa ne tsakanin hukumar kwastam da ta shige da fice da


rundunar sojoji da 'yan sanda da kuma sauran hukumomi masu kayan sarki.

TAVARVAREWAR HARKAR ILIMI

Wata gagrumar matsalar da qasar nan ke fama da ita itace matsalar tavarvarewar ilimi,
wadda masana da yawa na ganin kusan manhajar da ake amfani da ita a qasar ma ta zama
tsohuwar yayi, don ba ita zamanin da ake ciki yake bukata ba.

Tabbas idan za’a yi lissafi, to kusan 15 daga cikin jihohin qasar na Arewa su ke duk suna
fama da wannan matsala. Sai dai kawai da wuya a ce ga qarshe a wani matakin, dalili
kuwa shi ne, ba da ma’auni daya ake suna nagarta, qwazo, kulawa da kuma samar da
ingantaccen ilimi ba.

Yayin da Hukumar Daukar Malaman Makaranta ta Najeriya ke auna nagartar ilmi ta


hanyar qwararrun malamai, ita kuwa WAEC ta na auna wa ne da yawan daliban da su ka
ci jarabawar kammala sakandare.

Yayin da UBEC da SUBEC ke auna nagartar ilimi a jiha ta ma’aunin samarwa da wadata
makarantun firamare da kayan koyon karatu da suka hada har da samar da azuzuwa, ita
kuma JAMB ta na auna nauyin nagartar ilmi a jihohi ta yawan daliban da su ka ci
jarabawar shiga Jami’o’in qasar nan.

SABUBBA 10 DA SU KA DURKUSAR DA ILMI A AREWA:

1. BOKO HARAM: A kwanakin baya shugaban Hukumar Daukar Malamai ta Kasa,


Josia Ajiboye, ya ce Boko Haram sun kashe malamai har 611 a Arewa maso Gabas, daga
2009 zuwa yau, sannan malamai 19,000 sun rasa muhallin su duk sanadiyyar harin Boko
Haram.

3
COCMOSA 2021 25th December, 2021.
Rawar Da Tsaffin Dalibai Zasu Ta Wajen Magance Wasu Daga Cikin Matsalolin Da Suka Addabi
Al’ummar Nijeriya Muhammad Abbas Usman CNSS

Dubban yara sun zama marayu ta yadda karatun ya gagare su. Dubban iyaye matan da
aka kashe mazan su, ba su da qarfin daukar nauyin yaran da su ka kasa ci gaba da zuwa
makaranta.

2. SIYASA: Siyasa na daya daga cikin musabbabin lalacewar ilimi a Arewa. A nan ana
maganar yadda gwamnoni da ‘yan siyasa ke shigar-kutse a harkar ilmi ana daukar
malaman da akasarin su daqiqai ne, su na koyarwa a makarantu, don kuwa yanzu har ta
kai ko jarrabawa ba’ayi idan za’a dauki malamai. Kawai ana yin haka ne don a saka musu
ladar wahalar yaqin neman zave.

3. DAQIQAN MALAMAI: Wannan matsala ce mai zaman kan ta. Kuma laifin
hukumomin ilimi na jiha da kananan hukumoni ne. A a kwanakin baya an bayyana cewa
akwai dakikan malamai har 300,000 a Najeriya. Jihar Kano ce a sahun gaba wajen yawan
dakikan malamai har 25,000. A kididdigar 2010, jihar Adamawa na da dakikan malamai
6,231.

Hakan ya fito qarara a lokacin da gwamnan jihar Kaduna yayi wa malaman jihar
jarrabawa wadda kusa malamai 22,000 fadi kuma ya sallame su daga aiki ya dauki
qwararri 25,000 a shakarar 2017.

4. RASHAWA DA CIN HANCI: Su ma sabubba ne na lalacewar ilmi, ta yadda mayan


jami’an gwamnati ke karkatar da maqudan kuxaxen da ya kamata a inganta harkar ilmi
da su. Ko kuma a aiwatar da ayyuka marasa inganci bayan an ware maqudan kuxaxen da
ya kamata a yi nagartaccen aiki.

5. RASHIN MALAMAI MASU KISHI: Malamai da yawa babu kishin bayar da ilmi a
kan su har ma a zuciyar su. Yawancin malamai basu zuwa makaranta kan lokaci. Wasu
ma sai ranar biyan albashi ake ganin su.

Malamai da yawa su na sakin aikin koyarwa su tafi kabu-kabu da babur din achaba ko
Keke NAPEP. Da yawa na tafiya kwadago a lokacin da ake darasi a azuzuwan su.
Saboda abinda ake basu bai taka kara ya karya ba, baya wadatar dasu kansu ballantana
iyalinsu.

6. RASHIN KULA DA MALAMAI: Jihohi da yawa ba su biyan albashi sai an nemi a ba


hammata iska. Jihohi da yawa kuma ba su damu da sauran hakkokin malaman makaranta
ba. Ana samun matsala wajen karin girma ko karin mataki ga malamai.

7. MALAMAN BOGI: Jihohi da yawa na fama da matsalar malaman bogi. Ga dai sunan
malami a takardar sunayen masu karbar albashi, amma babu malaman, kuma ba’a san
mai karbar albashin nasa ba.

4
COCMOSA 2021 25th December, 2021.
Rawar Da Tsaffin Dalibai Zasu Ta Wajen Magance Wasu Daga Cikin Matsalolin Da Suka Addabi
Al’ummar Nijeriya Muhammad Abbas Usman CNSS

A wasu qananan hukumomi sau da yawa shugaban qaramar hukuma na da nasa sunayen
na bogi, haka mataimakin sa. Shi ma shugaban Jam’iyya har ma da hakimai duk su na
karbar albashin sunayen bogin da su ka dafkara ana karbe albashin.

8. MAKARANTU MASU ZAMAN KAN SU: Su ma babbar matsala ce ga makarantu na


gwamnati. Yadda ake bayar da karatu a makarantu masu zaman kan su, ya sha babban da
makarantu na gwamnati.Dalili kenan ba a ganin kokarin dalibin da ya gama firamare ko
sakandare ta gwamnati.

Sai dai kawai za’a iya cewa makarantu masu zaman kan su akwai tsada. Amma kuma
dama Bahaushe ya ce: ‘daidai kudin ka, daidai shagalin ka.’ Duk masu hikimar zance
sunce ‚Arha ba ta ado‛. Kuma haka zalika babu wani abu mai inganci da amfani a
rayuwa da ake samu kayuta.

9. WATSI DA MAKARANTUN GWAMNATI: A yau tun daga kansilan karamar


hukuma har shugaban kasa babu wanda dan sa ke makarantar gwamnati.

Babu ‘ya’yan ministan ilmi, babu ‘yar gidan kwamishinan ilmi ko wani darakta ko
Sakataren ilmi. Kowa ya tura ‘ya’yan sa makarantu masu zaman kan su, inda ilmi ya fi
nagarta da inganci.

10. RASHIN DORA DALIBAI KAN HANYA: Akasarin daliban makarantun gwamnati
duk ‘ya’yan talakawa ne. Da yawa iyayen su na tura su makarantar ne kawai don kada su
zauna cikin unguwa su sangarce, amma ba don su zama wani abu a gaba ta dalilin cin
moriyar ilimi ba.

RAWAR DA TSAFFIN DALIBAI ZASU TAKA DON MAGANCE WADANNAN


GIGGAN MATSALOLI

‘Ilimi shine gishirin zaman duniya’ kamar yadda masu iya magana ke cewa, bisa nazarin
masana kuma masu nazarin yau da gobe, bincike ya nuna cewa rashin ilimi (na addini da
na boko), talauci, rashin daidaito da adalci, da kuma rashin samar da ingantacciyar
rayuwa ga al’umma kusan sune manyan matsalolin da suka haifar da dimbin matsalolin
kasar nan.

Ko shakka babu tsaffin dalibai nada irin da zasu rawar taka don yiwa wadannan matsaloli
tifkar hanci:

1. Shiryar tarukan sada zumunta makamantan irin wannan da muke ciki yanzu haka.

5
COCMOSA 2021 25th December, 2021.
Rawar Da Tsaffin Dalibai Zasu Ta Wajen Magance Wasu Daga Cikin Matsalolin Da Suka Addabi
Al’ummar Nijeriya Muhammad Abbas Usman CNSS

2. Ziyartar tsaffin makarantu don bibiyar halin da suke ciki tare da kokarin
magancesu a matakin da zasu iya.
3. A inda matsalar ta fi karfinsu yana da kyau su tura bukatarsu zuwa ga hukumar da
dace su kuma rika bibiya don tabbatar da biyan bukatar su.
4. Shirya laccoci na musamman ga dalibai masu karatu akan yadda zasu zabi fannin
karatun gaba da sakandare (Guidance and counseling).
5. Horas da dalibai masu karatu da kuma waxanda suka gama basu samu gurbin
karatu na gaba da sakandare ba, akan sana’o’in dogaro da kai.
6. Taimakawa wajen koyar da darussa a fannonin da ake fama da qarancin malamai.
7. Samar da gidauniyar nemowa makatun hanyoyin biyan bukatunsu.
8. Samar da ayuukan yi ga abokanai wadanda suka gama karatu kuma suke cikin
bukatar taimako.
9. Wayar da kan dalibai akan illar cin hanci da rashawa, nuna masu muninta da kuma
koyar da su hanyoyin guje mata.
10. Yawaita kira ga gwamnati tare da janyo hankalin ta wajen havvaka makarantun
dake karkashin kulawar ta.
11. Yana da kyau matuka qungiyoyin tsaffin dalibai su shiga harkokin siyasa ka’in da
na’in don tabbatar da cewa ana tafiya da ra’ayinsu a gwamnatance.

DON NEMAN KARIN BAYANI

Hanson, B. T. (2010). Leadership and social development of people. Journal of


Elementary School, 1(2). Holy Bible – Revised Standard Version.

https://hausa.premiumtimesng.com/2017/10/nazari-tsakanin-tabarbarewar-ilimi-
da-dakikan-malamai-a-arewa/

https://pdfs.semanticscholar.org/e30a/05bed626c587f292f57749dbe134a69b521
e.pdf

https://www.bbc.com/hausa/labarai-50687765

https://www.channelstv.com/2021/12/07/kaduna-govt-conducts-fresh-
competency-test-for-35000-teachers/

Ibia, E. I. (1999). Sociological foundation of Nigerian education. Calabar: Cats


Publishers.

Lambora, V. E. (2009). Leadership behaviour of militant youths in the Niger Delta


region. Educational Development Journal, 1(2).

6
COCMOSA 2021 25th December, 2021.
Rawar Da Tsaffin Dalibai Zasu Ta Wajen Magance Wasu Daga Cikin Matsalolin Da Suka Addabi
Al’ummar Nijeriya Muhammad Abbas Usman CNSS

Thompson, E. F. (2008). Basic income and poverty alleviation in rural areas of west
Africa. Ibadan: Evans Publishers Ltd.

Ukpong, D. E. (2003). Essentials of sociology of education. Uyo: Afahaide and


Brothers & Co.

You might also like