You are on page 1of 25

AMFANI DA SASSAN KALMOMIN TSOHUWAR HAUSA A LITTAFIN

QARSHEN ALEWA QASA NA BATURE GAGARE


Hudu Salihu
Sashen Hausa
Kwalejin Ilimi ta Jihar Kaduna, Gidan Waya
08062096837
hudsale1@gmail.com
Tsakure
Tsohuwar Hausa ta shafi amfani da kalmomi na harshen dauri waxanda suka shuxe.
Amfani da waxannan kalmomi na taimakawa wajen xorewar al’ada da taskace tarihi.
Wannan maqala ta dubi yadda Bature Gagare ya yi amfani da sassan kalmomin
tsohuwar Hausa don taskace tarihi da ci gaban al’ada. Haka kuma, maqalar ta
gudana ne a qarqashi ra’in nahawun xoriya, kasancewar ra’in ya tafi a kan ta firkin
tasirin walwalar harshe, musamman yadda yake gani ana iya fahimtar ma’anar
harshe gwargwadon yadda marubuci ya sarrafa shi. An gudanar da wannan maqala
ce ta hanyar tarken sassan tsofaffun kalmomin Hausa hamsin da biyar (55), waxanda
suka danganci tsohuwar Hausa da aka tsamo daga cikin littafin ‘Qarshen Alewa
Qasa’ na Bature Gagare. Game da tantance bayanansu musammam ta’arifinsu, an
tsamo ma’anoninsu ne daga qamusun Bargery (1993) da na CNHN (2006). Sannan
kuma maqalar ta gano cewa marubucin ya qware wajen sarrafa sassan kalmomin
tsohuwar Hausa, haka kuma ta fito da yadda ya yi amfani da dabarun sarrafa
gundarin kalmomi da suka shafi vangarorin walwalar harshe guda takwas, waxanda
suka haxa da; Kalmomin Tufafi da Kalmomin Sunan Laqabi da Kalmomin Kayan
Kixa da Kalmomin Makaman Yaqi da Kalmomin Maguzanci da Kalmomin Motsa Jiki
da na Magani da Kalmomin Abinci da na Kayan Aikin Gida da kuma na Kalmomin
Tsarin Sarautar Gargajiya. Wannan maqalar za ta amfani al’ummar Hausa ta hayar
taskace wasu daga cikin kalmominsu da al’adunsu na dauri, musamman a halin da
ake ciki na gurvacewar harshe da al’adun da aka gada kaka da kakani.

1.0 Gabatarwa

Kasancewar Bature Gagare marubuci ne da yake alfahari da harshensa, sannan kuma

ya qware wajen sarrafa shi. Ganin haka ne ya sa wannan maqalar kudurtar zaqulo da

nuna irin gwanintar sarrafa sassan kalmomin tsohuwar Hausa, musamman yadda yake

amfani da su a muhallan da suka dace a cikin matani. Masana da dama waxanda suka

1
haxa da Furniss (1996) da Abu Sabe (2010) sun yi tsokaci a kan wannan littafi, sai dai

duk sun mai da hankali ne a kan warwarar jigon littafin. Wannan givin da aka samu

na rashin nazartar yadda marubucin ya yi amfani da sassan kalmomin tsohuwar Hausa

wannan ya ba da qarfin guiwan gudanar da aikin. Mukhtar (2010) ya faxa cewa

littafin Qarshen Alewa Qasa na xaya daga cikin littattafan gasar da aka gabatar a

shekarar 1982, a cikin wannan shekara Hukumar Al’adu ta Tarayya (Federal

Department of Culture) ta yi hovvasa inda ta shirya gasa ta qagaggun littattafaina

Hausa inda ta buga wasu littattafai na waxanda suka yi nasara kamar haka Turmin

Danya na Sulaiman Ibrahim Katsina da Tsumagiyar Kan Hanya na Musa Muhammad

Bello da Qarshen Alewa Qasa na Bature Gagare da kuma Zavi Naka na Munir

Mamman Katsina. Bugu da qari, wannan bincike ya yi qoqarin nazarin sassan

tsohuwar Hausa da Garba Gagare ya tsarma su a cikin littafin ne.

An haifi Bature Gagare marubucin Qarshen Alewa da Qasa, a birnin Katsina cikin

watan Yuni na shekarar 1959. Ya yi karatu na firamare a makarantar firamare ta

Gobarau da ke katsina a 1965, sannan ya zarce kai tsaye zuwa kwalejin Barewa da ke

Zariya a tsakanin 1972 zuwa 1978. A shekarar 1979 kuma ya samu shiga makarantar

koyon aikin jinya da unguwar zoma ta Katsina, ya taka rawa wajen tarzomar xalibai

aka kore shi daga makarantar, a lokacin sai ya watsar da karatun ya koma Kano inda

ya samu aiki a masaqar Bagauda a shekarar 1980.

Wata uku da fara aikinsa nan ma aka kore shi daga aikin saboda aikin qwadago da ya

yi kai-da-fata, daga nan kuma ya samu wani aiki shi ma a masaqa ta Universal Textile

da ke Bompai duk dai a Kano, a nan ma aka kore shi daga aikin cikin watansa na

huxu. Bature Gagare ya koma aikin koyarwa a Kano aka tura shi Ringim daga 1980

zuwa 1981 inda ya yi aikin koyarwa na tsawon shekara xaya a wani qauye mai suna

Kyarana. Abu Sabe (2010), qara da cewa a shekarar 1981 zuwa 1983 ya koma

2
makarantar Kwalejin Ilmi ta Kafanchan domin zurfafa karatu, amma yana cikin

shekararsa ta biyu nan ma aka kore shi saboda jagorantar zanga-zangar xaliban

makarantar da ya yi, wannan shi ya sanya ya watsar da duk wani karatu.

2.0 Bita a kan Sassan Kalmomi a Tsohuwar Hausa

Sautuka ne ake haxawa wuri guda a cikin qayyadajjen tsari, a gina zantuka masu

ma’ana, yawancin waxannan sautuka suna matsayin kalmomi ne. Kenan sanin sautuka

da tsarinsu yana nufin sanin kalmomin harshe. Bayan sanin kalmomi da ma’anarsu,

dole kuma a san wasu bayanai game da kalmomin. Ana buqatar mutum ya san

rukunin da kalma ta fito daga ciki. Wato daga cikin nahawun harshe, kowane rukunin

nahawu yana da rabe-rabensa (Yakasai, 2012).

Masana irin su Leech (1968) da Mathew (1997:24) da BalSdick (2004) da Zarruk

(2001) kamar yadda Garba (2011) ya ruwaito, sun tofa albarkacin bakinsu a kan kan

tsofaffin kalmomi, a inda suka tafi a kan cewa tsohuwar Hausa shi ne salon sarrafa

kalmomi da sigogin harshen dauri, waxanda yayinsu ya shuxe ko kuma waxanda aka

yi amfani da su tun kafin samuwar fasahar karatu da rubutu. Haka kuma sun qara da

cewa tsofaffin kalmomi, su ne waxanda suka shafi sana’o’in gargajiya, da yanayin

qasa wanda suka shafi tsirai da halittu da kuma abubuwan da suka zama tarihi.

Sannan kuma ya qara da cewa kayan yaqi musamman na gargajiya suna xaya daga

cikin abubuwan da suka zama tarihi a qasar Hausa. Domin haka kalmomin da ke

bayaninsu, kusan a iya cewa sun vace ko kuma ba a jinsu sosai. Wannan dalili yasa

idan marubuta suka yi amfani da su, sun yi haka ne domin taskace tarihi. Ko domin

taskace kalmomi don gudun vacewa ko bayar da kariya ga tarihi da ke qunshe a cikin

ma’anar kalma, ko kuma ci gaban al’ada.

3
Kasancewar wannan fage fage ne mai muhimmanci ga harshe da al’ada, wannan ya sa

ake samun manazarta suke zurfafa bincike a fagen. Wannan ya sa Abdul (2018) ya

daddale sassan tsofaffin kalmomin tsohuwar Hausa a cikin waqoqin makaxa mata

bakwai a inda, ya fito da yadda suke sarrafa su da kuma irin rawar da suke takawa

wajen isar da saqo yadda ya kamata. Sai dai ya yi amfani da zavi ido rufe wajen fito

da tsofaffin kalmomin da mawaqan suka yi amfani da shi, wato ya kawo kalmmomin

ne kara zube. A wannan maqalar an yi qoqarin zaqulo ire-iren dabarun da Garba

Gagare ya yi amfani da shi wajen sarrafa sassan kalmomin tsohuwar Hausa,

musamman ta fuskar ma’anoninsu da hikimomin dake tattare da sarrafa ma’anonin

nasu. Haka kuma da yadda ya yi amfani da dabarun sarrafa gundarin kalmomi da suka

shafi vangarorin walwalar harshe guda takwas. an yi qoqarin tantance su ta fuskar

nahawun xoriya.

3.0 Hanyoyin Gudanar da Bincike

Wannan maqalar an gudanar da ita ce a qarqashin ra’in nahawun xoriya. Kasancewar

ra’in ya tafi a kan tasirin walwalar harshe ga marubuta, musamman yadda yake ganin

ana iya fahimtar ma’anar harshe ne kawai gwargwadon yadda marubuci ya sarrafa

shi. Wannan ne kuma ya bai wa kowani marubuci damar zavin abin da ya dace da

fahimtarsa da al’adunsa. Haka kuma ra’in yana bayar da kulawa ga gogewar marubuci

da yadda hakan yake tasiri a cikin rubutunsa, da la’akari da irin ma’anonin da ya ke

bai wa harshe dangane da fahimtarsa ga rayuwa da gogewarsa da kuma laqantarsa ga

harshe. Game da bayanan sassan kalmomin da aka yi amfani da su a wannan maqala

musammam ta’arifansu a Hausa an tsamo su ne daga qamusun Bargery (1993) da na

CNHN (2006).

4
4.1Kalmomin Tufafi

Tufafi abu ne wanda al’umma ta samar da shi, wanda ke xauke da ma’anar da ke

daidaita yanayin mu’amala. Wato, abu ne da ake sawa a jiki don rufe tsiraici kamar

riga da wando da zani da sauransu (CNHN, 2006). Daga cikin tsofaffun kalmomin da

suka shafi tufafi da marubucin ya yi amfani da su sun haxa da walki/warki wanda ke

nufin fata jemammi yawanci baqa wadda ake xaurawa a gindi ko a yafa. A shafi na 5

marubucin ya yi amfani da wannan kalmar kamar haka:

(1). Duk su duka sun ciwo adon farauta, watau da walkinsu


na gashin akuya

A misalin da ya gabata Garba Gagare ya yi amfani da wannan kalma ta walki sai da

ya yi wa kalmar xafa qeyar gajerar mallaka –nsu (walki-nsu). Haka kuma, a shafi na

95 ya yi amfani da kalamr xan kamfai wadda ke nufin gajeren wando mai shan

bante.. Misali:

(2). …saboda Dubiri yana shiga wajen cin abincin mutane daga
shi sai xan kamfai.

Sannan kuma a shafi na 5 Garba Gagare ya qara amfani da irin wannan kalma, a inda

ya kawo kalmar Gwado wando ke nufin abin rufa mai kauri da nauyi wanda mata

suka saqa ta yin amfani da masaqar gargajiya. Misali:

(3). Wannan kuwa shi ne, lagen gwado na farar saqa da


kuma gajeren wandoqwanjo

A shafi na 22 marubucin ya yi amfani da kalmar Bante wanda ke nufin wani qyalle

mai qusurwa uku da jela da maxaurai wanda ake xaurawa a gindi. sai dai ya yi wa

kalmar xafa qeyar gajerar mallakar –nka (bante-nka). Ga misalin inda marubucin ya

yi amfani da kalmar a littafin:

(4). Wannan za ka koma fadar sarkin Dodanni, ka tuve gwadon

5
ka da banten ka ka yi tsirara.

Bugu da qari, marubucin ya yi amfani da kalmar Xan tofi/fatari, a shafi na 56,

wanda ke nufin xan gyauto da mata ke xaurawa, sannan su xaura zani. A nan ma ya yi

wa kalmar xafa qeyar nasabar mallakar –na (bante-n) Misali:

(5). Xan tohin Malka kuwa, bai tava ganin sabulu ba, sai dai
jar kanwa.

Garba Gagare ya qara amfani da irin wanxannan kalmomin kamar yadda a shafi na 38

ya kawo kalmar havarkada wadda ke nufin wata irin hula mai lavva biyu wadda ake

sawa don rufe kunnuwa, musamman lokacin xari. Kamar haka:

(6). sai suka gwammace su riqa sanya ‘yar shara ta


namuzu da kuma hular havar kada.

Dangane da bayan da suka gabata na misalan tsofaffun kalmomin da suke da alaqa da

tufafi, za a fahimci cewa waxannan kalmomi kusan sun ba a jin xuriyarsu sosai.

Hakan ya faru ne sakamakon zuwan baqi abin da ya haifar fantsamar tufafinsu (baqi)

da watsi da tufafin da aka gada kaka da kakanni. Haka kuma wasu kalmomi an daina

kiransu da sunansu na asali ne aka koma ada baddalasu da harshen Ingilishi.

4.2 Kalmomin Sunan Laqabi

Suna wani linzami ne mai nuna taqaitaccen bayani game da amfaninisa ko dai don

rarrabewa tsakanin wannan mutum da wannan, ko kuma don danganta mutum da

al’ummar da ya fito cikinta. Daga jin Emeka an san Ibgo ne, haka ma Taiwo an san

Yaruba ne, amma da an ji Tanko an san Bahaushe ne (Aliyu, 2010). Sunayen

gargajiya, sunaye ne a bisa al’ada, da can asali in an sami haihuwa abubuwa da dama

kan ba da hasken sa wa yaron ko yarinyar da aka haifa suna. A kan yi la’akari yanayi

ko lokaci ko ranaku wajen laqabawa abin da aka haifa suna. Waxannan sunaye suna

6
da tasiri a al’adance ga wanda aka laqabawa. Garba Gagare ya yi amfani da wani da

irin waxannan suna ne a cikin wannan littafi.

Hausawa suna da sunayen da ake laqabi wa mutum dangane da halayyar da aka haife

shi a cikinta. Idan aka dubi shafi na 230, za a ga yadda marubucin ya yi amfani da

sunayen da ake sa wa yaron da aka haifa ta la’akari da yanayin haihuwa kamar haka:

(7). sunan wannan saurayin Abashe kuma ga shi sai da ya yi


alqawari a nan wurin Maguzi..

idan aka dubi misalin da ya gabata, za a ga cewa marubucin ya yi amfani da sunan

Abashe wanda ke nufin laqabin da ake wa xan da aka yi ta haihuwa kafinsa suna

rasuwa, watau xan-wabi.

Bugu da qari, a shafi na 231 Garba Gagare ya qara amfani da irin wannan sunan dake

da alaqa da halayyar haihuwa wato, mati laqabin yaron da aka haifa bayan haihuwar

mata:

(8). Leftana Mati ya ce “ni ne limamin rantsuwa…


za mu yi rantsuwar mu ce ta magus.

Haka kumaa shafi na 47 ya kawo sunan Nakande wanda ke nufin laqabi ne da ake

kiran wani da yake wurin Kande: Kande na nufin laqabin yarinyar da aka haifa

bayan haihuwar maza.

(9). waxannan biyun kuwa sunan xaya Nakande, xaya kuma


Adaka sunansa.

Idan aka dubi sunan da ke cikin kakkaurar rubutu wato, kande za a ga cewa ya faxa

cikin rukunin sunayen halayyar haihuwa. Bugu da qari, Hausawa kan yi amfani da

sunayen ranaku wajen laqaba wa abin da aka haifa suna. Ga misali inda marubucin ya

yi amfani da irin waxannan sunayen:

(10). Gafara dai masu gida,” Larai ta shigo gida da akushin

7
zogala a bisa kanta.

Idan aka dubi sunan da ke cikin kakkaurar rubutu wato, Larai wadda ke nufin laqabi

da ake wa yarinyar da aka haifa ranar laraba, da ke cikin misalin da ya gabata wanda

ke shafi na 57, za a fahimci cewa wannan suna ya faxa ajin tsofaffin kalmomi

kasancewar ana samun qamfar amfani da shi. Sannan kuma a shafi na 37 Garba

Gagare ya yi amfani da suanan Lami wadda ke nufin laqabi da ake wa yarinyar da

aka haifa ranar alhamis. Misali:

(11). Da aka uwarsu Mailoma lami a wajen kwanciyarta


na gaskiya…

Bugu da qari a shafi na 237 ya yi amfani da sunan Xanasabe wanda ke nufin laqabi

ne da ake wa yaron da aka haifa ranar asabar. Misali:

(12). Masu kalangun nan suka fara buga ma wannan yaron


mai suna Xanasabe

Misalan sunayen gargajiya ko tsofaffun sunayen da aka kawo bayanansu a misalan da

suka gabata, ana samun qanfar amfani da su yanzu. Hakan ya faru ne sakamon tasirin

addinin Musulunci. Wannan ya sa mutane a yanzu suka fi sa sunan da yake da

dangantaka da addinin musulunci, don kwaxayin samun albarkar sunan. Har ila yau,

Hausawa sukan laqaba wa ‘ya’yansu suna ta la’akari da lokaci, ko rana ko wata,

kaxan daga cikinsu akwai. A shafi na 1 marubucin ya yi amfani da tsofaffun sunayen

da suke da dangantaka da yanayin lokaci kamar haka:

(13). Hantsi ya ajiye qoqon da ya gama shan


burkutu da shi, ya yi wata doguwar miqa...

Idan aka dubi misalin da ya gabata, an ga yadda Garba Gagare ya yi amfani da sunan

Hantsi; wanda ke nufin lokacin da rana ta fito sosai zuwa kafin ta kai tsaka, kamar

tsakanin qarfe takwas zuwa sha xaya na safe, wanda aka haifa a daidai wannan

lokacin shi a ke kira da Hantsi. Haka kuma, a shafi na 57 ya yi amfani da sunan

8
Malka/Marka, wadda Laqabi ne da ake wa yarinyar da aka haifa a tsakiyar marka

(tsakiyar damina lokacin da aka fi lafta ruwa). Misali

(14). Domin Malka ta san halin mutumiyarta,


daga xanxano sai ta kai xanxanniya

Bugu da qari marubucin ya qara amfani da irin waxannan sunayen da suke da

dangantaka da yanayin lokaci a shafi na 2 kamar haka:

(15). Shi wannan xan tsohon sunansa Ciwake. Duk garin


Tsaunin Gwano da kewaye an san shi da yin jima

Idan aka dubi misalin da ya gabata, za a ga cewa sunan da ke cikin kakkaurar rubutu

wato, Ci-wake wanda ke nufin wanda aka haifa lokacin da ake roron wake, wato a

daidai lokacin da ake ciron wake a da kaka, na xaya daga cikin tsofaffun Hausa

waxanda suka yi qanfa wajen amfani da su a cikin al’ummar Hausawa.

4.3 Kalmomin Kayan Kixa

Kixa na da muhimmanci a rayuwar Hausawa, ban da lokacin cin abinci da ibada da

karatu, da wuya a sami wani aiki da Bahaushe yake yi wanda babu kixa a cikinsa.

Domin haka, akwai kayan kaxe-kaxe da yawa waxanda Hausawa suke yi a yau da

goben rayuwansu waxanda suka haxa da:

a. Ganguna/ganga Wani babban abin ba da ake kaxawa mai babban sauti. A kan yi

ta da rarakakken itace ko garwa a rufa fatu a bakunansu ana kaxawa da gula. Idan aka

dubi littafin nan marubucin ya yi amfani da tsofaffun kalmomin da suka shafi

ganguna. A shafi na 237 ya yi amfani da kalmar kalangu wanda ke nufi abin kixa mai

baki biyu da aka rufe da fata ake ratayawa a kafaxa ana kaxa shi da gula a wajen

wasan mahauta ko na ‘yan mata. Kalangu ya fi shahara ta fannin kixan farauta ko

kixan maza na ma’abuta jarunta ko kixan samartaka ko na jama’a da na fawa da na

9
dambe da na tauri (Gusau, 2008). Sai da marubucin ya yi wa kalmar xafa qeyar

madangacin –n (kalangu -n), ga misalin yadda ya yi amfani a kalmar kamar haka:

(16). Masu kalangun nan suka fara buga ma wannan


yaron mai suna Xansabe takensa.

Har ila yau, ya yi amfani da kalmar Tambari wanda ke nufin babban ganga mai baki

xaya da ake kaxa wa sarakunan yanka. Kixan tambari ya samo asali ne tun daga kixan

yaqi. Da shi ake tafiya wurin yaqi ana kaxa wa sarki. Ban da sarki ba wanda ake kaxa

wa tambari, don haka, Hausawa suke yi masa kirari “Tambari kixan mutum xaya”, ko

kuma, “Tambari a ji ka sama’u”. Haka kuma saboda babbar murya da amo na

tambari, da kuma girmansa, don wani tambari ya kai girman turmin daka, wannan ya

sa Hausawa suke ce wa, “Tambari wan ganga. A shafi na 229 za aga yadda ya yi

amfani da kalmar kamar haka:

(17). Bam! Bam! Bam! Tambari ya kaxa. Daga nan


kowa sai ya zauna…

Haka abin yake, wato Garba Gagare ya qara amfani da kalmar Kotso wanda Hausawa

ke wa kirari da cewa, “Kotso mai murya goma” Dalilin wannan kirari kuwa shi ne

makaxin kotso yana iya sarrafa shi, ya yi muryoyi iri-iri lokacin da yake buqata.

Kotso abin kixa ne mai baki biyu, xaya da rufi da kuma narkakken kakin zuma a

manne a jikin rufin, sannan da tsirkiya a gicciye da rufin; ana kaxa shi da hannu ga

sarakuna har ma da masu sukuni haxe da waqa. Sai dai an nan ya yi wa kalmar xafa

qeyar madangacin –n (kotso -n), Idan aka dubi shafi shafina 93 za a ga misalin kalmar

haka:

(18). Mucachos ya yi wuf ya fizge xan kotson wannanxan


kama xin mai bula a fuska…

10
b. Kayan izga ko Tsarkiya
Zare na qirgi ko izga wanda a kan xaura a baka ko a molo ko garaya da

makamantansu. Marubucin ya yi amfani da tsofaffun kalmomin kayan kaxe-kaxe da

suke da dangantaka tsarkiya. A shafi na 31 ya yi amfani da kalmar gurmi wanda ke

nufin abin kixa mai tsirkiya xaya. Ga yadda ya kawo kalmar a misalin da ke tafe:

(19). Hi-hi-hi-hi! Sai wata irin dariya mai kamar


ana kaxa tsohon gurumi ta cika.

Haka kuma, ya yi amfani da kalmar kukuma wadda ke nufin qaramin goge wato,

wani abin kixa da a kan rufa qoqo da tantani a giciya icen da aka xaura wa izgar doki,

kuma a tanka wata izgar ga wani icen kamar baka, sai a riqa goga ta a xaya izgar, sai

su ba da sautin da ake so. Idan aka dubi shafina 12-13 za a ga yadda yakawokalmar:

(20). Ga Manje mai kukuma a gefe xaya bisa turmi yana


goga taken waxanda suka riga mu gidan gaskiya.

c. Sauran kayan kixa Banda misalan tsofaffun kalmomin kayan kaxe-kaxen da

marubucin ya yi amfani da su, akwai sauran kayan kaxe-kaxen da ya kawo a labarin

nasa. Misali a shafi na 1 ya kawo kalmar kuge wanda ke nufin wani guntun qarfe

mai kama da allon kafaxa da ake kaxawa don sanarwa. Maqera suke qera kuge da

baqin qarfe. Ana yi masa baki xaya ko bakuna biyu, mai xan faxin ciki da matse

gindinsa. Kowane baki yakan fito da amon sauti daban. Ana buga kuge da wani qarfe

mulmulalle mai xan tsawo. A nan ya yi wa kalmar xafa qeyar gajerar mallaka –nsu

(kuge-nsu). Ga misali:

(21). Mai yin shela ya bar kaxa kugensa domin ya yi jawabi a


wani xan lungu da ya shiga.

Bugu da qari, ya qara amfani da kalmar Dutsen niqa wadda ku nufin abin da ake niqa

hatsi ko wani abu a kansa. Mata ne suke amfani da amon da yake bayar wa a lokacin

da suke suke niqan tsaba a dutsen niqa na gargajiya. Daga nan a samar da gari har a yi

11
abinci da shi. Wannan ya faru ne kafin a sami injunan niqa na zamani. Waqoqin sun

qunshi begen miji ko wani masoyi ko habaici ga kishiyoyi ko uwar miji ta hanyar

shaguve ko faxar wata damuwa da sauransu (Gusau, 2008). A shafi na 55 an ga yadda

Garba Gagare aya yi amfani da wannan kalmar kamar haka:

(22). Malka: Arauye iye nanaye Aye nanaye:


Labule…
Dutsen niqa: Kakir-Kakir…
Malka: Xan Bature na gindin xinya.
Dutsen niqa: Kakir-Kakir…
Malka: Ba ruwan ka da yaran kowa
To, zagaya ka chi gutsu,
A hankali- ba da garaje ba”
Dutsen niqa: Kakir-Kakir”

Shigowar kaya kaxe-kaxen zamani, irin su Fiyano da Jita da sauran kayan kixan

zamani, su ne suka kawo qanfar kayan kaxe-kaxen gargajiya da aka gada kaka da

kakanni.

4.4 Kalmomin Makaman Yaqi

Makaman yaqi na nufin abin da ake amfani da shi wajen far wa wasu mutane da faxa

domin a mulke su. Idan aka dubi shafi na 5 za a ga yadda marubucin ya yi amfani da

kalmar kwari da Baka wanda ke nufin gidan kibiyoyi da tanqwararran ice wadda ake

xaura wa tsirkiya don a harba kibiya da shi. Misali:

(23). wasu da wuqa a xaure ga qugu…wasu har da


su kwari da baka.

Haka kuma a shafi na 23 ya kawo kalmar kibiya abin da ke nufin tsinke ko sillan kara

da ake xosa wa wani qarfe mai qarfi da tsini don yin amfani da shi wajen harbi tare da

taimakon baka. Misali:

(24). A cikin kwarin nan akwai tsinkunan kibiyoyi


goma sha biyu,

12
Har lia yau, a shafi na 30 marubucin ya kawo kalmar kyauro abin da ke nufin sandar

da ake sa wa ruwan kibiya. Misali:

(25). Sai Mailoma ya sake cewa, “faxa mani, yanzu in


kin qiya ki sha kyauro!”

Sannan kuma, haka abin yake a shafi na 20, wato inda ya yi amfani da kalmar takobi

abin da ke nufin qarfe mai tsawonmai siffar wuqa wanda ake amfani da shi wajen

yaqi ko kare kai. A nan ya yi wa kalmar xafa qeyar gajerar mallaka, -nsa (takob-insa).

Misali:

(26). kafin mutum ya shiga duniyarmu ta matsafa sai


ya wasa takobinsa.

Har ila yau, a shafi na 47 ya yi amfani da kalmar kwalkwali wanda ke nufin hular da

mayaqa suke sawa wadda ake yi wa ado da qarfe mai qyalli-qyalli. Ko qarfen da mata

suke amfani da shi mai qyalli. Idan aka dubi misalin da ke tafe za a ga muhallin da

Garba Gagare ya yi amfani da kalmar:

(27). sai wani thohon bature mai dogon gemu


da kwalkwali ya nufo wajen sarki.

A zamanin da muke ciki yanzu, na ci gaban zamani da qere-qeren makamai na

zamani, wannan ya sa kalmomin makamai da aka yi tarkensu a baya, suka shiga cikin

sahun tsofaffun kalmomi.

4.5 Kalmomin Maguzanci

Maguzanci na nufin al’adu da tsafe-tsafen da maguzawa (mutanen da ba sa bautar

Allah, wato waxanda ba sa bin saukakken addini) suke yi. Daga cikin tsofaffun

kalmomin da Garba Gagare ya kawo waxanda suke da alaqa da maguzanci sun haxa

da: Bamaguje (mutumin da ba ya bautar Allah), idan aka dubi shafi na 208 za a ga

13
wannan kalmar wadda take nufin Bahaushen da ba ya bin wani saukakken addini.

Misali:

(28). Yanzu idan bamaguje ya shiga cikin birni, ya kuskura


hausawa suka san shi ne, ya zama kare…

Dangane da misalin da ya gabata, za a fahimci cewa shi kansa marubucin a labarin ya

nuna yadda ake qyamar wanda aka ce Bamaguje ne. tasirin shigowar addini ya kawo

qanfar kalmar. Haka kuma, a shafi na 21 Garba Gagare ya amfani da kalmar Sarkin

Arna wanda ke nufin mutumin da aka naxa ta hanyar gargajiya don ya shugabanci

mutane ta hanyar mulki da tsafi. Ga misalin yadda ya yi amfani da kalmar a littafin:

(29). Sarkin Arna…ya ba da Tayani sadaka. Amma a


wannan karon sarkin Dodanni bai amshi gaisuwar
ba saboda haka sai aka sake wani.

Haka kuma ya yi amfani da kalmar tsafi, wanda ke nufin hanyar ba da gaskiya ga

wani abu daban ba Allah ba. A shafi na 25 marubucin ya yi amfani da kalmar kamar

haka:

(30). Tsafi gaskiyar mai shi. Kafin qiftawa da bismilla


sai gida ya dawo yadda yake.

Har ila yau, ya qara amfani da kalmar Dodo wadda ke nufin

Wani nau’in tsafi da Maguzawa ke amfani da shi domin kwaxayin tara abin duniya.

Sukan keve wani ko wata iska da yi masa hidima da nufin samun danqon duniya ko

amfanin gona mai yawa (Guga, 2019). Idan aka dubi shafi na 12 za a ga yadda ya yi

amfani da Kalmar kamar haka:

(31). Wani babban abin da Mailoma ba ya son shiga harkansa,


shi ne dodon banza. Tun yana qarami yake jin labarin
wurin, da kuma mutanen da ake cewa yana ci.

14
Haka kuma, kalamr maiya wadda ke nufin mutumiyar da aka ce wai tana kama

kurwan xan’adam har ta kashe shi. (maita: halayya ta mayu wadda kan ba su damar

wai su kama kurwar wani su ci ya mutu). A shafi na 50 marubucin ya yi amfani da

wannan kalamr kamar haka:

(32). An kamo maiya; eho! Dattijan gari suna biye a


baya, wasu suna dariya…

Dangane da misalin da ya gabata, za a ga cewa wannan kalmar ta maiya za a

fahimci cewa marubucin ya yi amfani da wannan kalma a muhallin da ya dace. Bugu

da qari a shafi na 27 ya yi amfani da kalmar Qanqara wadda ke nufin wasu

qananun duwatsu da mayu kan fitar a jikin wanda suka kama idan an ba su wuya. Ya

yi wa kalmar xafa qeyar madangacin –r (qanqara-r) Ga yadda ya kawo kalmar a

cikin labarin:

(33). Ya xauki qanqarar nan yana luliya ta a hannu


yana mamakin yadda za’a ce wai har wannan
` ran wani mutum ne.

Dangane da misalan da suka gabata, an sami qanfar amfani da waxannan kalmomi ne

sakamakon tasirin addini. Kasancewar addinin Musulunci a koda yaushe, ana so

mutum ya yadda da qaddara mai kyau ko mara kyau, sannan kuma ya dogara da

Allah wajen neman mafita a kan duk matsalar da ya shiga ciki.

4.6 Kalmomin Motsa Jiki da na Magani

Motsa jiki na nufin abubuwan da akan yi ta hanyar aiki da jiki, amfani da gavovi don

nishaxi da kuma qara samun lafiya a jiki. Daga cikin wasannin kwaikwayon Hausa

akwai waxanda aka gina su a tafarkin motsa jiki, waxanda suka haxa da Langa da

Kokuwa da kuma Ature/Atule. Kamar yadda masana suna raba wasan kwaikwayo

wato, akwai na gargajiya wanda Hausawa suka gada kaka da kakanni da kuma na

15
zamani ko rubutaccen wasan kwaikwayo. Waxannan wasannin da suka gabata sun

faxa cikin rukunin wasannin kwaikwayo na gargajiya ne. Garba Gagare ya yi amfani

da sassan kalmomin waxannan tsohuwar Hausa a cikin matanin labarinsa. Idan aka

dubi shafi na 328 za a ga yadda yay i amfani da kalmar Langa wanda ke nufin wasan

yara da suke yi na riqe qafa xaya da hannu suna tsalle da qafa xayar da ta rage.

Misali:

(34). Muchachos…sai ya miqe tsaye yana hawan matakalu


da langa…

Bugu da qari,marubucin ya qara amfani da kalmar kokuwa wadda ke nufin wasan da

samari kan yi na kayar da juna. Wannan kalmar ita na xaya daga cikin kalmomin da

suka danganci wasannin gargajiya. A nan ma, ya yi wa kalmar xafa qeyar mahaxin

nasabar –r (kokawa-r gargajiya). Ga yadda ya yi amfani da kalmar a shafi na 224

kamar haka:

(35). Hantsi kuwa… aka tilasta ma wa ya riqa koya ma


xaliban Maguz kokawar gargajiya.

Haka kuma, marubucin ya qara kawo wata kalma ta ature/atile wadda ke nufin

wasan tila wa juna qasa da yara suke yi. Za a ga misalin yadda yay i amfani da

wannan Kalmar a shafi na 44 kamar haka:

(36). ….umurnin da aka ba shi ya yi alqawari da ya

je zai aikata. Na xaya shi ne ya sanya a yi ma


turawan ature,

Kalmomin da aka yi tarkensu a misalan da suka gabata, an sami qanfarsu ne

sakamaon wasannin da yaran Hausawa suke yi ya sami koma baya. Hakan ya faru ne

kasancewar kutsen da wasanninn kwaikwayo na fina-finai ya yi, wannan ya taimaka

wajen janye hankalin yara waje wasa. Haka kuma iyaye yanzu na sa ‘ya’yansu karatu

ko wasu abubuwan a daidai lokacin da yara suka saba wasa, to a nan za a iya cewa

16
qarancin lokaci da yara suke da shi, musamman a birane ya taimaka wajen shigar da

kalmomin nan cikin sahun tsofaffun kalmomi. Amma a kan sami xoriyar wasunsu a

qauyuku.

Magani wata hanya ce ta warkar da ko kwantar da ko rage wata cuta ta ciki ko ta

waje ko wadda aka samu ta haxari. Ko kuma neman kariya ga cuta ko abokan

hamanya ko neman xaukaka ta daraja ko ta buwaya ta hanyar siddabaru da sihirce-

sihirce na ban al’ajabi (Bunza, 1990). Marubucin bai yi qasa a guiwa ba wajen wajen

tsarma tsofaffun kalmomin da suka danganci magunguna a cikin labarin, kamar yadda

ya kawo a shafi na 20 inda ya yi amfani da kalmar sassaqe abin da ke nufin vawon

itace, musammam wanda ake yin magani da shi. Misali:

(37). Xakin nan ba ya warin komai sai na jini da sassaqe


sassaqe.

Har ila yau, a shafi na 22 Garba Gagare ya yi amfani a kalmar Turare, wadda ke

nufin itace ko ciyawa da ake zubawa a garwashin wuta ana shaqar hayaqin don wani

magani. Misali:

(38). ka tuve gwadon ka da bantenka ka yi tsirara. A lokacin


nan sai ka yi turare da wannan maganin.

Sannan kuma, idan aka dubi shafi na 20, za a ga yadda Garba Gagare ya qara amfani

da kalmar jiqo wadda ke nufin tsumammen magani. Haka muma ya yi wa kalmar

xafa qeyar mahaxin nasabar –n (jiqo-n magani). Misali:

(39). Sai ta xauko wani jiqon magani ta ce amshi shi.


Mailoma ya kafa kai ya shanye ruwan magani.

Bugu da qari, Garba Gagare ya kawo kalmar qaho wanda ke nufin tsattsaga jiki don

fid da jini ta zuqo shi da qaho, wanda wanzami (mai sana’ar yin aski kokaciya da

sauransu) kan yi wa mara lafiya. Za a ga misalin haka a shafi na 304, misali:

17
(40). Wannan faxuwar da aka yi ai ya kamata ka
nemi Xan wanzan ya yi maka qaho.

Bugu da qari, a shafi na 23 ya yi amfani da kalmar kambu wadda ke nufin maganin

sammu ko kariya da ake tufkawa a rufe da fata ko qyalle a xaura a dantse. Har ila yau,

a wannan shafin ya kawo kalmar tauri wanda ke nufin maganin da ake ci don kashe

kaifin wuqa ko wani makami don ya kasa huda jikin mutum. Misali:

(41). Ya xauko kambu nan da mahaifinsa ya yi masa


na tauri ya xaura.

Dangane da misalin da ya gabata, za a fahimci cewa waxannan kalmomi sun shiga

cikin sahun tsofaffun kalmomi, sakamakon shigowar tsarin kiwon lafiya na zamani

(asibiti). Kamar yadda aka sani, asibiti ba sa amfani da jiqo ko sassaqe da

makamantansu, wannan ya sa a yanzu idan mutum ma’abucin amfani da irin

waxannan magunguna ne, sai a riqa masa kallon xan gargajiya. Dangane da kalmar

kambu da tauri kuwa, tasirin addini ya sa mutane suka soma kauce wa jingina da

wani abu da ba Allah (swt) ba wajen neman kariya da tsari.

4.7 Kalmomin Abinci da na Kayan Aikin Gida

Abinci na nufin duk abin da ake ci don maganin yunwa. Daga cikin tsofaffun

kalmomin abincin da Garba Gagare ya yi amfani da su, sun haxa da kaskamai abin

da ke nufin wani irin abinci dunqule-dunqule da ake yi da garin xaurawa. Za a ga

wannan kalmar a shafi na 10 kamar haka:

(42). Bayan haka kuma ana amfani da garin ta wajen yi


gaskami.

Haka kuma, ya kawo kalmar daddawa a shafi na 10 wadda ke nufin wata baqar abu

da ake yi da kalwa ana sawa a miya don qarin zaqi, amma tana da wari. Sai dai ya yi

18
wa kalmar xafa qeyar mahaxin nasabar –r (daudawa-r). Ga misalin yadda yay i

amfani da wannan tsohuwar kalmar haka:

(43). Akwai itacen xorawa a gonar wanda ake xiban


‘ya’yan ana yin daudawar miya.

Dangane da misalin da ya gabata, za a fahimci cewa wannan kalma ta soma bacewa,

kasancewar jama’a da dama sun bar amfani da ita sun koma amfani da magi wajen sa

miyarsu ta yi zaqi. Har ila yau, ya qara amfani da kalmar burkutu wanda ke nufin

wata irin giya ta gargajiya da ake yi da hatsi. Idan aka dubi misalin da ya za a ga a

inda ya kawo kalmar burkutu a shafi na 1 a cikin littafin kamar haka:

(44). Hantsi ya ajiye qoqon da ya gama shan


burkutu
da shi, ya yi wata doguwar miqa…

Kalmaomin da aka kaurara a misalan da suka gabata, an sami qanfar amfani da su

sakamakon samuwar kayan haxa abinci na zamani.

Wani hanzari ba gudu ba shi ne, shigowar kamfanoni giya na zamani, ya sa ba a

amfani da burkutu in ba a qauye ba.

Har ila yau, daga cikin tsofaffun kalmomin da marubucin ya yi amfani da su,

waxanda suke da alaqa da qananun abubuwan da ake amfani da su a gida sun haxa

da: qoqo abin da ke nufin qaramar qwarya wato, mazubi da ake samu bayan an fafa

duma. Idan aka dubi shafi na 1 za a ga yadda yay i amfani da wannan kalmar kamar

haka:

(45). ya miqa masa giya cikin qoqo, Mailoma ya


karva…

19
Haka abin yake, a shafi na 56/7 Garba Gagare ya amfani da kalmar akushi abin da

ke nufin abin zuba abinci. Ga yadda marubucin ya yi amfani da kalmar a cikin

labarin:

(46). Dubu za ta yi musu, domin tana jin ko shara


ta yi sai ta tuna lokacin da ta ga Larai matar
Hantsi da akushi,…

Bugu da qari, ya yi amfani da kalmar dutsen niqa wadda ke nufin abin da ake niqa

hatsi ko wani abu a kansa. Wannan kalmar ya shiga sahun tsofaffun kalmomi,

kasancewar ci gaban zamani ya kawo injin niqa da na lantarki da wanda ake amfani

da hannu a niqa. Bature Gagare ya yi wa kalmar xafa qeyar mahaxin nasabar –n

(dutse-n niqa). Idan aka dubi shafi na 55 marubucin ya yi amfani da kalmar kamar

haka:

(47). Kakir-Kakir, dutsen niqa yana gugar dutse.


Malka sai rausaya take yi, wai ita waqa ta
sharo ta.

Har ila yau, a shafi na 62 ya yi amfani da kalmar tufaniya/asabari wanda ke nufin

gadon kara na gero ko na dawar da ba a vare wa ganye ba ko kuma wanda aka yi da

ciyawar qyara/gamba wadda ake rufe qofa da ita. Haka kuma ya y iwa kalmar xafa

qeyar madangacin –r (tufaniya-r). Idan aka dubi misalin da ke tafe za a ga yadda ya

yi amfani da kalmar kamar haka:

(48). Baqo ya zo qofar xaki ya sa qafa ya shure


tufaniyar da aka yi qyaure da ita.

Bugu da qari, Garba Gagare a shafi na 20 ya yi amfani da wata tsohuwar kalma ta

aci bal-bal wadda ke nufin abar da ake haskaka wuri ko xaki da ita. Idan aka dubi

misalin da ke tafe, za a ga yadda ya yi amfani da kalmar kamar haka:

(49). Mailoma yana tsugune a wani xaki mai


aci bal-bal a gaban Akkati.

20
Wani hanzari ba gudu ba shi ne, duk da cewa ana samun inda ake amfani da wasu

daga cikin kalmomin da aka yi bayaninsu a baya, musamman a qauyaku. Amma

akwai qanfarsu a birane, sakamakon cigaban zamani da ya haifar da samuwar qere-

qeren kayayyakin ayyukan gida na zamani. Wannan ya sa aka daina jin xoriyarsu

yadda ya kamata.

4.8 Kalmomin Tsarin Sarautar Gargajiya

Kamar yadda aka sani rayuwa tafe take da abin da ke yi mata jagoranci domin samun

nasarar gudanar da al’amura na yau na kullum. Wannan shugabanci ya fara tun daga

muqamin sarauta ta gargajiya har ya kai ga shugabannin qananan hukumomi da

kuma qasa baki xaya. Bisa ga tsarin rayuwa, waxannan matakai duk suna bisa kan

shugabancin al’umma da aka naxa ko aka zava ta hanyar siyasa ko ta qarfin soja ko

kuma ta hanyar gargajiya. Shugabanci na nufin mulki ko iko. Watau, xaukar nauyin

jagorancin al’umma ta hanyar tsara hanyoyin kiyaye lafiyarsu da shirya masu

qa’idojin zaman tare ta fuskar shari’a da gudanar da hulxa a tsakaninsu da qasashe

maqwabta (Yakasai, 2012).

A shafi na 20 Garba Gagare ya yi amfani da kalmar sarauta wadda ke nufin

shugabanci musamman irin na gargajiya. Wannan kalmar ta shiga sahun tsofaffun

kalmomi kasancewar a tsarin shugabancin siyasa na zamanin da muke ciki. Duk da

cewa ana samun naxe-naxen sarauta na gargajiya. Amma a hukumance ba wani

tanadi da kundin tsarin mulki ya ba su wajen gudanar da shugabancin al’ummarsu.

Ga yadda marubucin ya yi amfani da wannan kalmar:

(50). Kowa ya san cewa wannan tsohuwa ta kashe


mutane wajen xari duk don saboda xanta ya
sami sarauta.

21
Bugu da qari, a shafi na 47 ya kawo kalmar Sarki wanda ke nufin mutumin da aka

naxa ta hanyar gargajiya don ya shugabanci mutane ta hanyar mulki ko sana’a ko

wani abu. Ga misalin a cikin littafin:

(51). Sarki ya bada alama da yatsu don a kawo


Burkutu.
Haka kuma, a shafi na 108 ya yi amfani da kalmar fadawa wadda ke nufin mutanen

da rayuwarsu ta dogara da fada. Sun kasance masu wa Sarki da fada hidima a

kowane lokaci. Ga misalin kalmar a littafin:

(52). Sarkin Arna yana da yawan fadawa da ‘yan lukumunsa,


amma yanzu kowa ya kama hanyar gabansa.

Har lia yau, a shafi na 40 marubucin ya qara amfani da kalmar da ke alaqa da

shugabanci wato, ‘Yan doka wadda ke nufin ma’aikatan hukuma waxanda ke kula

da tsare dokokin qasa. A nan Bature Gagare ya yi wa kalmar xafa qeyar madangacin

–n (‘Yan doka-n) don fayyace kalmar. Misali:

(53). Azaluman ‘Yan dokan nan suka jawo Ciwake har


sabon gidan Sarkin Arna kamar tinkiya.

Kamar yadda aka sani duk sarki ya kan naxa Hakimai don su taya shi gudanar da

mulkinsa. A shafi na 39 Marubucin ya yi amfani da kalmar Hakimi wanda ke nufin

mai riqe da wani muqami na sarauta ko mai mulkin wata gunduma a qasar sarauta.

Ya yi wa kalmar xafa qeyar mahaxin nasaba –n (Hakimi-n). Ga yadda marubucin ya

yi amfani da kalmar a labarin:

(54). Idan kuwa suka kama wani wanda hakimin


qauye ya ce ya aikata aikin ashsha, …kashinsa
ya bushe.

Bugu da qari, a shafi na 47 marubucin ya yi amfani da kalmar bayi wanda ke nufin

mutanen da aka kama wajen yaqi ko aka saya don bauta.

22
(55). Waxanda suka tsaya har ya zo kuwa dole ne
Sai sun faxi qasa ko su yi nadama. Bayi suka
kama masa ya sauka daga goxiya.

Dangane da misalan kalmomin da suka gabata, za a fahimci cewa, duk da cewa ana

samun xoriyar wasunsu, amma ba su da tasirin a zo a gani. Misali Sarki ko Hakimi

ba su da wani wurumi a kundin tsarin mulkin qasa wajen gudanar da harkokin mulki,

sai da kawai a ce da su iyayen qasa. Game da kalmar bayi kuwa, a iya cewa sai dai a

yi amfani da kalmar ta wani fuskar, amma ba a kan waxanda aka kamo ko sayo don

bauta ba, kasancewar ba a bauta a yanzu.

5.0 Kammalawa

Kamar yadda wannan maqalar ta yi qudirin zaqulo da nuna gwanintar da wannan

marubuci ya yi amfani da shi. Sakamakon haka ne, maqalar ta gano cewa Bature

Gagare ya yi amfani da sassan kalmomin tsohuwar Hausa a littafin da suka shafi

vangarorin walwalar harshe guda takwas, waxanda suka haxa da amfani da sassan

kalmomin tufafi da sunan laqabi da kayan kixa da makaman yaqi da maguzanci da

motsa jiki da na magani da abinci da na kayan aikin gida da tsarin sarautar gargajiya.

Wannan ya tabbatar da cewa marubucin bai jahilci jiya ba, sannan kuma bai yarda

yau, wato baqin harsuna su rusa jiya wato tsohuwar Hausa ba. Wannan ya sa Bature

Gagare, kasancewa wata taska a harshen Hausa. Haka kuma akwai buqatar a zurfafa

wani nazari makamancin wannan a wannan littafin, musamman ta fuskar ginin juma

da adon harshe da fito da dabarun ishara da musanya. Wannan maqala za ta amfani

al’umar Hausawa ta hanyar taskace wasu daga cikin sassan kalmomin tsohuwar

Hausa, waxanda suke xamfare da falsafar Bahaushe ta fuskoki da daban-daban.

Musamman a halin da ake cikin na gurvacewar harshe da al’adun Hausawa, waxanda

matani ke kasancewa rumbu a garesu.

23
Manazarta

Abdul, I. F (2018). Nazarin Tsofaffin Kalmomi a Cikin Waqoqin Makaxa


Mata, Xunxaye Journal of Hausa Studies, Vol 2. No.1. June, 2018, Sokoto:
Department of Nigerian Languages, Usmanu Xanfodiyo University.
Abu Sabe, B (2010). Nazarin Danniya Da Babakere A Littafin Qarshen Alewa Qasa,
Himma: Journal of Contemporary Hausa Studies, Vol \. 2, October, 2010,
Katsina: Department of NigerianLanguages, Umaru Musa ‘Yaraduwa
University.
Aliyu, I. S. (2010). Laccar Aji ta Kwas Mai Lambar “Hau 213: Major Hausa
Traditional Personal Naming”. Kaduna: Department of Nigerian
Languages and Linguistics, Kaduna State University.
Bargery, G.P. (1993). A Hausa-English Dictionary and English-Hausa Vocabulary
(2nd ed). Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.
Bunza, A.M. (1990). Magungunan Hausa a Rubuce (Nazarin Ayyukan Malaman
Tsibbu) Kundin Digiri Na Uku. Kano: Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar
Bayero.
CNHN. (200). Qamusun Hausa na Jami’ar Bayaro. Kano: CNHN
Furniss, G (1996). Poetry, Prose and Popular Culture in Hausa, Edinburg: University
Press.
Gagare, B. (1980). Qarshen Alewa Qasa, Zaria: NNPC.
Garba, S. (2011). Salon Sarrafa Harshe a Waqoqin Aqilu Aliyu, Kundin Digiri Na
Uku, Zariya: Sashen Harsuna da Al’adun Afirka, Jami’ar Ahmadu Bello.
Guga, U.M. (2019). Kwatancin Bautar Iskoki a Qasar Katsina: Tsokaci a Kan Tsafin
Bagiro da na Uwar Gona, Kundin Digiri Na Biyu, Zaria: Sashen Harsuna da
Al’adun Afirika, Jami’ar Ahmadu Bello.
Gusau, M.A (2008). Waqoqin Hausa a Qasar Hausa, Yanaye-yanayensu da
Sigoginsu, Kano: Bnchmark Publishers Limited.
Muktar, I. (2010) Introduction To Stylistic Theories, Practice and Criticism,
(RevisedEdition), Kano: Usman Al-Min Publishers.

24
Salihu, H (2015), Tasirin Zamananci a Wasannin Zaman Duniya Iyawa Ne,
Yjollac:Yobe Journal of Language, Literature and Culture, Journal 3, 2015.
Damaturu: Department of Hausa, Yobe State University.
Yakasai, A. S. (2012). Jagoran Ilmin Walwalar Harshe. Sakkwato: Garkuwa Media
Servies.
‘Yar’aduwa da J (2007), Harshe da Adabin Hausa a Kammale. Ibadan: Spectrum
Books Ltd.

25

You might also like