You are on page 1of 12

Illolin Shaye-Shaye ga Matasa a Rayuwansu ta Yau da Gobe (Dr Usman Bakari 2021)

Illolin Shaye-Shaye ga Matasa a Rayuwansu ta Yau da Gobe

Daga
Usman Bakari (PhD), Mcasson.
Department of Guidance and Counselling,
Faculty of Education,
Taraba State University Jalingo, Taraba State Nigeria.
bakariyawo@yahoo.com

“78th Islamic Vacation Course”( IVC Taraba Dec. 2021)


organized by
Muslim Students Society of Nigeria (MSSN)
22nd /Jumadal Awwal/ 1443AH
26th Dec, 2021.
1
Illolin Shaye-Shaye ga Matasa a Rayuwansu ta Yau da Gobe (Dr Usman Bakari 2021)

GABATARWA
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai. Dukkan Godiya ta tabbata ga Allah

Ubangijin halittu, madaukakin Sarki, tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi

Muhammadu (SAW). Muna farin cikin haduwa da ku a wannan taro mai

muhimmanci.

Wannan maqala ta kunshi bayanai kan Rayuwan mutane game da giya, ca-ca da

lodo kafin zuwan Musulunci, abubuwa biyar da musulunci yazo don tsaresu wa

dan-Adam, menene ma’anar giya a musulunci ko kwaya?, dalilen da yasa

mata/maza ke shaye-shaye, bayanin kan miyagun kwayoyi, matakan sharia game

da hana giya da kwayoyi a musulunci, hukuncin wanda ya sha giya ko kwaya a

musulunci, nauoin kwayoyi da tasirinsu ga dan Adam, illolin shaya-shaye ga mace

ko namiji a musulunci, Mafita game da shaye-shaye.

RAYUWAN MUTANE GAME DA GIYA KAFIN ZUWAN MUSULUNCI


Kafin zuwan musulunci mutane na shan giya kafin a hana gaba daya, larabawa kan
sha giya harma su yi wasiyya kan cewa in sun mutu a rinka zuba musu giya a
kabarinsu. Giya da lido da ca-ca na tare da dabiun larabawa kafin zuwan musulunci,
wassu daga cikin larabawa basu son giya, domin tana kawar musu da hankali, tana
zubar da mutunci su, tana lalata dabiu su masu kyau, giya da lido da ca-ca na haifar
musu da gaba a cikin mutane, suna tsirar da keta tsakanin mutane, kuma suna
tarwatsa al ummah. A jahiliyya wassu larabawa kan sha giya har suyi ta fada a
tsakanin su don rashin hankali ko buguwa, domin duk wanda ya bugu ba zai iya
aikata komai, don haka ake kiran giya uwar masifa. Ca-ca ko kuma yana sa la-la
cewar dukiya. Idan dukiya ta ragu sanadiyyan ca-ca yakan sa gaba a tsakanin
mutane.
2
Illolin Shaye-Shaye ga Matasa a Rayuwansu ta Yau da Gobe (Dr Usman Bakari 2021)

MAKASUDIN MUSULUNCI
Da Musulunci yazo ya sami mutane acikin wannan hali sai yasan ya musu lallurai
guda biyar, a ma’ana addini ne wadda yazo ya ceci mutane daga duhun jahilci. Yazo
ne ya tsare mutane daga abubuwa guda biyar. Kamar haka:-
1. Tsare wa mutane addininsu.
2. Tsare wa mutane hankalisu
3. Tsare wa mutane mutuncin su
4. Tsare wa mutane ransu
5. Tsare wa mutane dukiyansu.
Wadanan nan abubuwa biyar sune makasudin shariar musulunci ga mutanen
duniya. To idan dan-Adam ya tsare wannan kaidoji to fa ya tsira.
YAYA JIKIN MUTUM YAKE DAUKAN SAKO IDAN AN SHA GIYA KO
KWAYA? ZUWA JIKI HARYA FICE?12
SHIN GIYA DAYA TAKE DA KWAYA WURIN BUGARWA?
Akiyasan ce giya daya take da kwaya wurin bugarwa, wannan itace abin raayin mafi
rinjayen maluman Musulunci.
MECECE GIYA KO KWAYA ME BUGAR WA A MUSULUNCI?
kwaya me bugar wa dai yana nufin amfani da wani abu da zai gusar wa mutum da
hankali ko ya saka shi maye: ta hanyar sha, shinshinawa, ci, busawa ko kuma
allura3. Musulunci yace:-
.‫ َو ُك ُّل ُم ْس ِك ٍر َح َرا ٌم‬،‫ " ُك ُّل ُم ْس ِك ٍر خ َْم ٌر‬:َ‫َّللاِ صلى هللا عليه وسلم قَال‬ ُ ‫وقد جاء في صحيح اإلمام مسلم أ َ َّن َر‬
َّ ‫سو َل‬
‫ والخمر هو كل ما يخامر العقل أو ستره بغض النظر عن مظهر المسكر أو صورته وكل المخدرات‬، "
ُ ِ‫ وقال رسول هللا صلى هللا عليه وسلم " َما أ َ ْس َك َر َكث‬، ‫مسكرة ومفترة وهي حرام‬
‫يرهُ فَقَ ِليلُهُ َح َرا ٌم " وقوله صلى‬
‫هللا عليه وسلم"حرام على أمتي كل مفتر ومخدر‬

1
https://www.webmd.com/mental-health/what-is-dopamine
Dopamine:- is a type of neurotransmitter. Your body makes it, and your nervous system uses it to send messages between nerve cells. That's why it's sometimes called a chemical
messenger. Dopamine plays a role in how we feel pleasure. It's a big part of our unique human ability to think and plan.
1. Inhibitory neurotransmitters 2. Excitatory neurotransmitters
3
https://sirinrikemiji.blogspot.com/2021/10/illolin-shaye-shaye-da-hanyar-kawar-da.html
3
Illolin Shaye-Shaye ga Matasa a Rayuwansu ta Yau da Gobe (Dr Usman Bakari 2021)

Kamar yadda annabi ya bayyana a hadisin Muslim yace giya itace dukan abinda ya
bugar, kuma duk abinda ya bugar haramun ne anfani dashi. Giya itace duk abin da
ya bugar da kwakwalwa ko yatsare ta daga anfani.
‫ويمكن تعريفها على أنها كل مادة مسكرة أو مفترة طبيعية أو مستحضرة كيميائيا ً من شأنها أن تزيل العقل‬
‫ فتضرا لفرد والمجتمع‬،‫ بما ينتج عنه تسمم في الجهاز العصبي‬،‫ وتناولها يؤدي إلى اإلدمان‬،ً‫جزئياًأو كليا‬
Kwaya itace, duk wani abu mai bugarwa ko me yanke mutum daga dabiansa ta asali
ko abin da aka hada da sinadari (kemikal) me sa buguwa, me yawa ko dan kadan,
wadda shan sa zai jefa mutum cikin halin wuyan barinsa. Wadda zai iya kashe
gabobi.wadda zai iya shutar da mutum ko al’ummah. Karin bayani game da
ma’anan shaye-shayen kwayoyi:- shine
 Shan maganin da doka ta hana amfani dashi.
 Shan Magani berkete batare da izinin likita ba.
 Wuce umurnin likita wajen shan kwayoyi.
 Shan abubuwan da addinin Musulunci ya haramta4.
DALILAIN DA YASA MATA/MAZA KE SHAYE-SHAYE
Daga cikin dalilai da ke sa yara shaye-shaye sunanan kamar haka-
1. Shan magani bada izinin likita ba

2. Rashin amfani da magani a kan ka’idar da aka dora mutum

3. Matsalar bawa yara rashin kulawa5


4. Muamala da miyagun abokai
5. Don wata damuwa da ta samu dan-Adam
6. Ko don murnan abinda ya samu
7. Rashin iyaye
8. Rashin hankali da Hauka
9. Talauci

4
https://www.haiman.com.ng/2018/12/shaye-shayen-miyagun-wayoyi-tare-da.html?m=0
5
https://sirinrikemiji.blogspot.com/2021/10/illolin-shaye-shaye-da-hanyar-kawar-da.html

4
Illolin Shaye-Shaye ga Matasa a Rayuwansu ta Yau da Gobe (Dr Usman Bakari 2021)

10.Rashin ilimi
11.Kiriniya da kwakkwafi
12.Don cire tsoro da tausayi
13.Domin an gada daga iyaye
14.Mahallin da ake shan kwayoyi (environment).
MIYAGUN KWAYOYI (KAYAN MAYE)
1. Ana anfani da tabar wiwi ko tabar gida
2. Ana anfani da kashin kadan gare
3. Ana anfani da gawayi
4. Ana anfani da zakami
5. Ana anfani da bula
6. Ana anfani da kashin kaji
7. Ana anfani da tururin bayan gida
8. Ana anfani da petur
9. Ana anfani da sholusho
10.Ana anfani da correction fluid
11.Ana anfani da penti
12.Madarar suku day
13.Cin ashana
14.Babba jijji
15.Ana anfani da kwatami
16.Ana anfani da duk wani irin nauin kwayoyin chemist(kwayar diazepam,
paudar ibilis cocaine, tramadol, rohypnol,alabukun, aspirin, benelyn, tutolyn
ko balium)
17.Ana anfani da giya
18.Zakami
MENENE MATAKAN DA SHARIA TA DAUKA GAME DA GIYA KO
SHAYE-SHAYE A CIKIN ALKURANI?
5
Illolin Shaye-Shaye ga Matasa a Rayuwansu ta Yau da Gobe (Dr Usman Bakari 2021)
ࣰ ࣰ
( َ‫سنً ۚا إِ َّن فِی ذَ ⁠ ٰلِكَ لَـَٔايَة ِلقَ أو ࣲم يَعأ ِقلُون‬
َ ‫س َكرا َو ِر أزقًا َح‬ ِ ‫ت ٱلنَّ ِخي ِل َوٱ أۡل َ أعنَ ٰـ‬
َ ُ‫ب تَت َّ ِخذُونَ ِم أنه‬ ِ ٰ ⁠ ‫) َو ِمن ث َ َم َر‬
[Surah An-Nahl 67] Kuma daga 'ya'yan itãcen dabĩno da inabi. Kunã sãmudaga
gare shi, abin mãye* da abinci mai kyau. Lalle a cikin wannan, haƙĩƙa, akwai ãyã
ga mutãne waɗanda suke hankalta6

( ‫اِس َو ِإ أث ُم ُه َما أ َ أكبَ ُر ِمن نَّ أف ِع ِه َما َويَ أسـَٔلُونَكَ َماذَا‬ ِ َّ‫َكبِير َو َمنَ ٰـ ِف ُع ِللن‬ ‫ع ِن ٱ ألخَمأ ِر َوٱ أل َم أيس ِِر قُ أل فِي ِه َما إِ أث ࣱم‬
َ َ‫۞ يَ أسـَٔلُونَك‬
ِ ‫)يُن ِفقُونَ قُ ِل ٱ أل َع أف َو َكذَ ⁠ ٰلِكَ يُبَ ِي ُن ٱ َّّللُ لَ ُك ُم ٱ ألـَٔايَ ٰـ‬
َ‫ت لَ َعلَّ ُك أم تَتَفَ َّك ُرون‬
[Surah Al-Baqarah 219] Suna tambayar ka game da giya da cãcã. Ka ce: "A cikinsu
akwai zunubi mai girma da wasu amfãnõni ga mutãne, kuma zunubinsu ne mafi
girma daga amfaninsu." Kuma suna tambayar ka mẽne ne zã su ciyar; ka ce: "Abin
da ya rage."Kamar wancan ne Allah Yake bayyanawar ãyõyi a gare ku;
tsammãninku, kuna tunãni.
( ‫س ِبي ٍل َحت َّ ٰى‬ َ ‫عا ِب ِری‬ َ ‫وا َما تَقُولُونَ َو ََل ُجنُبًا ِإ ََّل‬ ۟ ‫س َك ٰـ َر ٰى َحت َّ ٰى ت َعأ لَ ُم‬
ُ ‫صلَ ٰوة َ َوأَنت ُ أم‬
َّ ‫ُوا ٱل‬ ۟ ‫وا ََل ت أَق َرب‬
۟ ُ‫َي ٰـأ َيُّ َها ٱلَّ ِذينَ َءا َمن‬
۟ ‫ُوا َما ࣰء فَت َ َي َّم ُم‬ ࣱ
‫وا‬ ۟ ‫سا َء فَلَ أم ت َِجد‬َ ِ‫سفَ ٍر أ َ أو َجا َء أ َ َحد ِمن ُكم ِمنَ ٱ ألغَا ِٕى ِط أ َ أو لَ ٰـ َم أست ُ ُم ٱلن‬ َ ‫علَ ٰى‬ َ ‫ض ٰى أ َ أو‬
َ ‫وا ۚۚ َوإِن ُكنتُم َّم أر‬ ۟ ُ‫ت أَغت َ ِسل‬
۟ ‫س ُح‬ ࣰ َ ࣰ
ً ُ‫غف‬
‫ورا‬ َ ‫عفُوا‬ َ َ‫وا بِ ُو ُجو ِه ُك أم َوأ َ أي ِدي ُك أم ِإ َّن ٱ َّّللَ َكان‬ َ ‫ط ِيبا فَٱمأ‬ ‫ص ِعيدا‬
َ )
[Surah An-Nisa' 43] Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku kusanci salla alhãli
kuwa kuna mãsu mãye, sai kun san abin da kuke faɗa kuma haka idan kuna mãsu
janaba, fãce mai ƙẽtare hanya, har ku yi wanka. Kuma idan kun kasance majinyata,
ko kuwa a kan tafiya ko kuwa wani daga cikinku, idan ya zo daga kãshi, kõ kuwa
kun shãfi mãtã ba ku sãmi ruwa ba, to ku nufi, fuskar ƙasa mai kyau, ku yi shãfa ga
fuskokinku da hannuwanku. Lalle ne Allah Yã kasance Mai yãfẽwa Mai gãfara.

( ‫ط ٰـ ِن فَٱ أجتَنِبُوهُ لَعَلَّ ُك أم‬
َ ‫ش أي‬ َ ‫اب َوٱ أۡل َ أزلَ ٰـ ُم ِر أجس ِم أن‬
َّ ‫ع َم ِل ٱل‬ ُ ‫ص‬َ ‫يَ ٰـأ َيُّ َها ٱلَّ ِذينَ َءا َمنُو ۟ا إِنَّ َما ٱ ألخَمأ ُر َوٱ أل َم أيس ُِر َوٱ أۡلَن‬
َ‫)ت ُ أف ِل ُحون‬

6
Tarjaman Quran zuwa Hausa Na Sheikh Mahmud Gumi

6
Illolin Shaye-Shaye ga Matasa a Rayuwansu ta Yau da Gobe (Dr Usman Bakari 2021)

[Surah Al-Ma'idah 90] Ya ku waɗanda suka yi ĩmãni! Abin sani kawai, giya da cãca
da refu da kiban ƙuri'a, ƙazanta ne daga aikin shaiɗan, sai ku nĩsance shi, wa la'alla
ku ci nasara7.
( ِ‫صلَ ٰوة‬ َ ‫عن ذ أِك ِر ٱ َّّللِ َو‬
َّ ‫ع ِن ٱل‬ َ ‫صدَّ ُك أم‬ َ ‫ط ٰـ ُن أَن يُوقِ َع بَ أينَ ُك ُم ٱ أل َعدَ ٰ َ⁠وة َ َوٱ ألبَ أغ‬
ُ َ‫ضا َء فِی ٱ ألخَمأ ِر َوٱ أل َم أيس ِِر َوي‬ َ ‫ش أي‬
َّ ‫ِإنَّ َما يُ ِريدُ ٱل‬
َ‫)فَ َه أل أَنتُم ُّمنت َ ُهون‬
[Surah Al-Ma'idah 91] Abin sani kawaĩ Shaiɗan yanã nufin ya aukar da adãwa da
ƙeta a tsakãninku, a cikin giya da cãca, kuma ya kange ku daga ambaton Allah,
kuma daga sallah. To, shin, ku mãsu hanuwa ne?
.‫ َو ُك ُّل ُم ْس ِك ٍر َح َرا ٌم‬،‫ " ُك ُّل ُم ْس ِك ٍر خ َْم ٌر‬:َ‫َّللاِ صلى هللا عليه وسلم قَال‬ ُ ‫وقد جاء في صحيح اإلمام مسلم أ َ َّن َر‬
َّ ‫سو َل‬
‫ والخمر هو كل ما يخامر العقل أو ستره بغض النظر عن مظهر المسكر أو صورته وكل المخدرات‬، "
ُ ِ‫ وقال رسول هللا صلى هللا عليه وسلم " َما أ َ ْس َك َر َكث‬، ‫مسكرة ومفترة وهي حرام‬
‫يرهُ فَقَ ِليلُهُ َح َرا ٌم " وقوله صلى‬
‫هللا عليه وسلم"حرام على أمتي كل مفتر ومخدر‬
Kamar yadda annabi yace acikin Sahihu Muslim “giya itace dukan abinda ya bugar
giya ne, kuma duk abinda ya bugar haramun ne anfani dashi. Giya itace duk abin
da ya bugar da kwakwalwa ko yatsare ta daga anfani.
HUKUCIN WANDA YA SHA GIYA KO KWAYA A DUNIYA
Azamanin manzon Allah ya sa an bugi mashaya da takalmi da duka da hanu.
Sahabbai sun hukunta cewa. Wanda ya sha giya hukuncin sa bulala arba’in ko
tamanin kamar yadda sahabbai sukayi ijma’I a sakaninsu.
َ ‫ " َم ْن ش َِر‬:َ‫َّللاِ ﷺ قَال‬
‫ب ا ْل َخ ْم َر فِي‬ ُ ‫ أَنَّ َر‬،‫ع َم َر‬
َّ ‫سو َل‬ ُ ‫ ع َِن ا ْب ِن‬،‫ ع َْن نَافِ ٍع‬، ٌ‫ أ َ ْنبَأَنَا َما ِلك‬:ُ‫َّللا‬
َّ ُ‫ َر ِح َمه‬،‫قَا َل الشَّافِ ِع ُّي‬
ِ ‫ ِم ْن َح ِدي‬،‫س ِل ٌم‬
‫ بِ ِه‬، ٍ‫ث َمالِك‬ ُّ ‫ ث ُ َّم لَ ْم يَت ُ ْب ِم ْن َها ُحرمها فِي ْاْل ِخ َر ِة َا ْخ َر َجهُ ا ْلبُ َخ ِار‬،‫ال ُّد ْنيَا‬
ْ ‫ي َو ُم‬
Imam Shafii Allah yajikansa da rahama yace Malik ya bani labara daga Nafiu
daga sahabi mai suna Abdullahi dan Umar yace lalle Annabi tsira da amincin
Allah su tabbata a gareshi yace” Duk wanda yasha giya a duniya saanan bai tuba
ba daga shanta ba za’a haramta masa ta lahira8’

8
Tafsirin Ibn Kathir
7
Illolin Shaye-Shaye ga Matasa a Rayuwansu ta Yau da Gobe (Dr Usman Bakari 2021)

:‫َّللاِ ﷺ‬ ُ ‫ قَا َل َر‬:َ‫ع َم َر قَال‬


َّ ‫سو ُل‬ َ ُّ‫ ع َْن أَي‬،ٍ‫ ع َْن َح َّما ِد ب ِْن َز ْيد‬،ِ‫الربِيع‬
ُ ‫ ع َْن نَافِ ٍع ع َِن اب ِْن‬،‫وب‬ َّ ‫س ِل ٌم ع َْن أَبِي‬
ْ ‫َو َر َوى ُم‬
‫ب ا ْل َخ ْم َر فَ َماتَ َو ُه َو يُدْمنها َولَ ْم يَت ُ ْب ِم ْن َها لَ ْم يَش َْر ْب َها فِي‬ ْ ‫ َو ُك ُّل ُم‬،‫" ُك ُّل ُمسكر َخ ْم ٌر‬
َ ‫ َو َم ْن ش َِر‬،‫س ِك ٍر َح َرا ٌم‬
ْ
‫"اْل ِخ َر ِة‬.
Muslim ya ruwaito daga abi Rabiy daga Hammad dan Zaid daga Ayyub daga
Nafiu dan Umar Yace; Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata agareshi
"yace Duk abu mai bugarwa giya ne, duk wanda ya sha giya yamutu yana mai sha
bai tuba ba zai sha giyan lahira ba"
:‫َّللاِ يَقُو ُل‬
َّ ‫ع ْب ِد‬
َ ‫َّللاِ ب ِْن يَسار؛ أنه سمع سالم بن‬ َّ ‫ع ْب ِد‬ ُ ‫ أ َ ْخبَ َرنِي‬:‫ قَا َل ا ْبنُ َو ْهب‬:‫ِيث آ َخ ُر‬
َ ‫ ع َْن‬،ٍ‫ع َم ُر ْبنُ ُم َح َّمد‬ ٌ ‫َحد‬
ُّ ‫َّللاُ ِإلَي ِْه ْم يَ ْو َم ا ْل ِقيَا َم ِة ا ْلعَا‬
‫ وال ُمد ِْمن‬،‫ق ِل َوا ِل َد ْي ِه‬ ُ ‫ "ث َ ََلثَةٌ ََل يَ ْن‬:‫َّللاِ ﷺ‬
َّ ‫ظ ُر‬ َّ ‫سو ُل‬ ُ ‫ قَا َل َر‬:‫ع َم َر‬
ُ ُ‫َّللاِ ْبن‬ َ ‫قَا َل‬
َّ ‫ع ْب ُد‬
‫ والمنَّان ِب َما أ َ ْع َطى‬،‫"ا ْل َخ ْم َر‬.
Wani hadisin daga dan wahab yace Umar dan Muhammad ya bashi labari daga
Abdullahi dan Yassar cewa shi ya ji Salim dan Abdullahi yana cewa Abdullahi dan
Umar yace Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi yace “Mutane uku
Allah bazai gansu ba ranan aliyama 1. Wadda ya guje wa Iyayen sa 2. Mai
dawwama kan shan Giya 3. Mai gori da abinda ya bayar”.
NAU’OIN KWAYOYIN MAYE DA TASIRIN SU GA MATASA
1. Akwai kwayoyi masu kara karfi(kuzari)(stimulants)
2. Akwai kwayoyi masu rage kuzari(sedatives)
3. Akwai kwayoyi masu sa nishadi(ecstasy)
4. Akwai kwayoyi masu sa bacci
5. Akwai kwayoyi masu rage kiba
6. Akwai kwayoyi masu kara kiba
7. Akwai kwayoyi masu cire hankali
8. Akwai kwayoyi masu sa dariya
9. Akwa kwayoyi masu cire zogi ko zafi
10.Akwa kwayoyi masu cire gajiya
11.Akwa kwayoyi masu cire takaici
12.Akwa kwayoyi masu sa nitsuwa
8
Illolin Shaye-Shaye ga Matasa a Rayuwansu ta Yau da Gobe (Dr Usman Bakari 2021)

13.Akwa kwayoyi masu cire nyinwa


14.Akwa kwayoyi masu kara gani da ji,
15.Akwa kwayoyi masu sa karfin jimai
16.Masu dauke hankali
ILLOLIN SHAYE SHAYE GA MUSULMI
1. Rashin ibadah
2. Rashin bin iyaye
3. Rashin tarbiyya
4. Yawan fada
5. Rashin nutsuwa a koda yaushe.
6. Talauci
7. Kora daga wurin aiki ko makaranta
8. Yana kawo hatsari ga wanda sukasha suna yin tukin mota ko babur.
9. Yana kawo ciwon huhu
10.Yana kawo ciwon hauka
11.Yawan tunani mai tsanani da muni.
12.Yana kawo lalacewan mazakuta.
13.Yana gadar da warin jiki
14.Yana kawo cutar kwakwalwa
15.Yana kawo cutan hawan jini ko matsala ta haila ko biki
16.Yana sa karya da yaudara
17.Yana sa sata
18.Yana kawo rashin jituwa tsakanin iyalai.
19.Yana sa zuban ciki ga mata
20.Yana gadar wa mata saki
21.Yana sa mutane su kyamashi mai shan taba ko giya
22.Yana hana sallah da azumi
23.Yana gadar da cutan hanta
9
Illolin Shaye-Shaye ga Matasa a Rayuwansu ta Yau da Gobe (Dr Usman Bakari 2021)

24.Yana sa cutar puka


25.Yana sa cutan mantuwa ko rikicewa
26.Yana gadar da rashin kunya
27.Yana sa fyade ko zina
28.Yana sa raunin fahimta
29.Yana hana garkuwan jiki aiki
30.Yana sa cutar zuciya
31.Yana sa tunani na karya
32.Yana hana kokari a jarrabawa
33.Yana hana tuna Allah
34.Yana gadar da cutan ajali
35.Yana gadar da rashin gani da ido kon hankali
36.Yana gadar da cutar nunfashi
37.Yana kara rashin tsaro a kasa
38.Yana hana alaka da abokai
39.Yana sa yawan fushi
40.Yakan sa mashayi yin kisa
41.Yana sa mutum kullum cikin datti
42.Yana sa rama, farin baki da zuban zufa mai yawa.
43.Yana hana mace mijin aure ko rabuwa da dangi
44.Yana sa mutum tunanin kashe kansa
45.Yana sa cutan rashin bacci
46.Yana hana muamala da maluma
47.Yana sa mutum gani, jin, fadan abinda ba haka ba.
48.Yana sa mace ta kashe mijinta
49.Yana sa mutum yayi fitsari ko kasha a jikin sa.
50.Yana hana mutum cimma burin rayuwa(makaranta ko aure).
51.Yana sa roko ko kwagayin abin mutane
10
Illolin Shaye-Shaye ga Matasa a Rayuwansu ta Yau da Gobe (Dr Usman Bakari 2021)

52.Yana sanya rashin haihuwa, zubar ciki da mutuwan yaro aciki


53.Yana hana yaro zama a mahaifa da kyau.
54.Masu shaye-shaye na sa jarirain cikin su rashin isashen sinadari,
55. Yana kawo cutan Tsida (HIV/AIDS) saboda idan hankali ya gushe ana jima'I
berkete
MECECE MAFITA?
Akwai mafita masu yawa wadda kwararru daga bangarori daban-daban ya kamata
su hada karfi da karfe don su taimaka a hana ko a rage. Akwai hanyoyi kamar haka:-
1. Iyaye su yawaita addua wa yaransu kuma su bibiyi ayyukan su a yau da gobe
don san abokan sun na kusa da nesa.
2. Iyaye dole ne su kula da bukatun yaran su, idan yaro na bukatan wani abu
yana kyau a hanzarta abiya masa in matukar ba matsala bace.
3. Yana da kyau in Iyaye sun gane yaro na shan kwaya su jashi kusa da su don
bashi shawara, kada su yadda su kore shi daga wurunsu.
4. Kada iyaye su zamanto masu kaushi kan yaransu su lallabesu kafin basu
shawara.
5. Iyaye su koya wa yaransu karatun alqurani da hadisin annabi Muhammad
SAW.
6. Iyaye su koya wa yara sanaoin daban-daban wanda zai bama yaran samun
abubuwan da zasu rike kansu.
7. Atura yara wurin masu bada shawarwura domin gamsashiyar samun daman
barin shaye-shaye.
8. Dole Iyaye su kula da lafiyan yaransu,insun gan chanji game da lafiyasu kada
su bari suyi tambaya domin dakile damuwan cikin lokaci.
9. Iyaye kada su kyamaci yaransu don sun kama su da shaye-shaye. Suyi kokari
su jasu ajiki don bada shawara.
10.Nasihantarwa da nisarwa sune mafita ta musamman ga masu shaye-shaye.
11.Hana fatauci da safaran kwayoyi da ta’ammuli da shi.
11
Illolin Shaye-Shaye ga Matasa a Rayuwansu ta Yau da Gobe (Dr Usman Bakari 2021)

12.Mu koma zuwa ga Alqurani da sunnan Annabi ta yadda zamu bibiyi rayuwan
sa da na sahabban sa muyi koyi da su. Wannan shine zaman lafiya ga
musulmi.
13.Masu sha su tuba zuwa ga Allah kafin mutuwan su.
14.Yana da kyau iyaye su kula da abokan yaransu, su san waenda ke yawo da
yaransu. Su zaba musu abokai na gari.
15. A ci abinci mai kyau don maye gurbin abin da aka rasa.
16. Dena taammuli da kwayoyin don jiki ya karbi sakon denawa(detoxification).
17.Masu sayar da wannan kwayoyi dole a hana su sayar wa sai da izinin likita.
In sun ki to a rufe shagunan su ko a kama su a rufe.
References
1. https://www.webmd.com/mental-health/what-is-dopamine
2. https://sirinrikemiji.blogspot.com/2021/10/illolin-shaye-shaye-da-hanyar-kawar-da.html
3. https://www.haiman.com.ng/2018/12/shaye-shayen-miyagun-wayoyi-tare-da.html?m=0
4. Tafsirin Ibn Kathir
5. Tarjaman Quran zuwa Hausa Na Sheikh Mahmud Gumi

12

You might also like