You are on page 1of 6

HADISI NA UKU

29
HADISI NA UKU:

Daga Abu Huraira ‫رضیﷲعنه‬. ya ce: Manzon Allah (‫ﷺ‬.) ya ce:


((Imani kashi sittin da wani abu ne, ko kuma ya ce kashi saba'in
da wani abu, mafi girmansu shi ne: shaidawa babu abin bautawa
da cancanta sai Allah, mafi ƙarancinsu kuma shi ne kau da cuta
daga kan hanya, kuma kunya wani yanki ne na imani)) Bukhari
da Muslimu ne ya rawaito shi.

MARAWAICIN HADISIN:
Abu Huraira: Shi ne Abdurrahmanu Bn Sakhrin Addausiyyu,
Babban Marawaici a Musulunci. Ya lazimci Manzon Allah (‫ﷺ‬.)
ya kuma rawaito hadisai sama da dubu biyar daga gare shi. Amirul
Muminina Umar ( ‫رضیﷲعنه‬.) ya ba shi shugabancin Bahrain,
sannan sai ya cire shi. Kuma aka ba shi shugabancin Madina na
wasu shekaru a lokacin shugabacin Bani Umayyah. Ya rasu
shekara ta 57H.

SHARHIN KALMOMI:

(Da wani abu): Daga uku zuwa tara.

(Yanki): Ɗabi'a, kuma (YANKUNA) jam`i ne na (YANKI),


wanda a Larabci shi ne: Rassan bishiya wanda aka kamanta Imani
da shi. Sannan kuma ɗabi'unsa (Imanin) aka kamanta su da

30
bishiya ma'abociyar rassa, wacce 'ya'yan bishiyar ba za su cika ba
sai da cikar cikakkun rassanta.

(Kau da cuta): Kawar da shi da nesantar da shi. A abincda ake nufi


da cuta shi ne duk abin da zai cutar na daga dutse ko ƙazanta ko
ƙaya ko waninsa.

(Kunya): Sifface ta zuciya, tana sanya aikata abin da za a yaba, da


barin abin da za a kushe.

A Wannan hadisin Manzon Allah (‫ )ﷺ‬ya bayyana cewa imani ba


yanki ɗaya ba ne, sai dai yankuna ne da yawa.

Amma mafi falalar waxannan yankunan na imani kalma ɗaya ce.


Kuma ita ce"La'ilaha illallahu" wannan kalmar da za a auna ta da
sama da ƙasa to da zata rinjaye su, domin kalma ce ta tsarkake
zuciya, duk wanda ya kasance ita ce qarshen kalma sa a duniya
to zai shiga Aljannah, ita ce mafi falalar yankin imani.

Kuma kunya yanki ne na imani, kuma siffa ce mai kyau, ta


kasance ɗabi'ar Manzon Allah (‫ﷺ‬.), har ya kasance yafi budurwa
kunya.

31
FA'IDOJIN HADISI:

1- Tabbatuwar fifiko acikin imani da sassaɓawar muminai a cikin


mata kansa, kuma mafi girman dalili a kan cewa imani yana
raguwa kuma yana ƙaruwa.

2- Faɗinsa (( Imani kashi saba'in da wani abu ko kashi sittin da


wani abu)) wannan shakka ne daga wanda ya rawaito hadisin,
shin Manzon Allah (‫ﷺ‬.) ya ce ((Saba'in da wani abu ne ko kuwa
ya ce sittin da wani abu ne?))

3- Faɗin "La'ilaha illallahu" kalma ce ta tauhidi, wadda idan


mutum ya faɗe ta ya zama musulmi, idan kuwa ya yi girman kai
a kanta to ya zama kafiri, ita ce iyakar da ta raba tsa kanin imani
da kafirci, don haka ne ta zama mafi girma da falalar rassan imani.

4- Imani a wajen Ahlussunnah wal Jama'a ya ƙunshi furuci da


baki, da aikin gaɓɓai da kuma ƙudurtawa da aikin zuciya.

5- Kau da cuta daga kan hanya na daga yanki na imani, kuma


yana daga cikin mafi kyawun ayyuka.

6- Cewa kunya na daga cikin imani, jin kunyar Allah yana tilasta
wa bawa ya tsayu wajen yi wa Allah ɗa'a, kuma ya hanu daga abin
da Allah ya hana. jin kunyar mutane yana tilasta wa bawa
kamewa, ya aikata abin da zai ƙawata shi a wajen mutane, ya
nisanci abin da zai muzanta shi ya munana shi, kunya dukkanta
na daga cikin imani.

32
7- Manzon Allah (‫ﷺ‬.) bai bayyana dukkan yankunan imani ba,
wannan kuma daga hikimar Annabi (‫ﷺ‬.) ne da Allah ya ba shi,
domin musulmi ya dage da kansa, ya bi nassoshni Alƙur'ani da
Sunnah, har ya tattara waɗannan yankunan na imani ya yi aiki da
su, don kuma a gane mai kwaɗayi da mara kwaɗayin samun lada.

Kuma ma’anar (La’ilaha illal lahu):Babu abin bautawa bias


cancata face Allah Mai buwaya da xaukaka, don haka duk wasu
ababan halitta da ba Allah ba qarya ne, face Allah shi kaxai ba Shi
da abokin tarayya, domin Shi Shi ne gaskiya. Kamar yadda Allah
Wanda Ya yi albarka kuma Ya xaukaka Ya ce: (Saboda cewa
Allah Shi ne gaskiya, kuma cewa abin da suke bautawa koma
bayanSa shi ne qarya, kuma haqiqa Allah Shi ne Maxaukaki Mai
Girma) [Al-Hajji:62].

33
AUNA FAHIMTA

TAMBAYOYI:

Rubuta bahasi dake bayyana haƙiƙanin imani

..........................................................................................
..............................

..........................................................................................
..............................

..........................................................................................
..............................

2- Menene ma'anar "La'ilaha illallahu"

..........................................................................................
..............................

3-Ya za ka kafa hujja da cewa imani shine furuci da harshe, da


aiki da zuciya da gaɓɓai.?

..........................................................................................
..............................

..........................................................................................
..............................

34

You might also like