You are on page 1of 9

MARAWAICIN HADISI:

Umar Bn Alkhaɗɗab Bn Nufail, Abu Hafs Alfaruƙ, shugaban


Muminai, ya musulunta kafin Hijira da shekara biyar, ya lazimci
Annabi (‫)ﷺ‬, Musulmi sun masa mubaya'a ya zama shugaba bayan
Sayyidina Abubakar (R.A), a lokacin halifancinsa Allah ya ba shi
nasarar buɗe garuruwa da Musulunci, ya yaɗa addini, shi ya sanya
kwanan wata na Hijira, ya kafa kundin tsarin mulki, Abu Lu'u-
Lu'atal Majusiy ya kashe shi lokacin yana sallar asuba a shekara ta
23H.

SHARHIN KALMOMI:

(Ya ɗora tafukan hannayensa a kan cinyoyinsa): Ma'ana mai


tambayar ya ɗaura tafukan hannayensa a kan cinyoyinsa, yayi zama
irin na ɗan koyon karatu, wannan yana daga cikin tsananin ladabi
da girmamawa ga Manzon Allah (‫)ﷺ‬.

(Sai muka yi mamakinsa yana tambayarsa kuma yana gasgata shi):


Dalilin mamakinsu shi ne wannan ya saɓa ma al'adar mai tambaya
wanda bai sani ba, wannan maganar mai bada labari ne ga wanda
ake tambaya, ba wanda ya san haka sai Manzon Allah `.
(Kuyanga ta haifi uwargiyarta): Ta haifi shugabanta, wasu malamai
sun fassara shi da yaɗuwar Musulunci, kuma Musulunci zai
mamaye garuruwan shirka sai kuyangu su yawaita, sai yaron baiwa
da ta haifa wa shugaban ta ya zama shugabanta shi ma saboda
matsayin mahaifinsa.

(Masu kiwon awaki suna gina gidaje masu tsawo): Mutanen ƙauye
da makamantansu kamar mabuƙata da talakawa, an yalwata musu
arziƙi har suke alfahari da gine-gine.

(Lokaci mai tsawo): Shi ne faɗin Allah Ta'ala:


٤٦: ‫ﱡﭐ ﲢ ﲣ ﲤ ﱠ مريم‬

MA'ANA:

{Kuma ka ƙaurace min tun kana me mutunci}

SHARHIN HADISI:

Wannan hadisin ya tattara bayani a kan dukkan ayyukan ibada na bayyane da na ɓoye,
washen imani, da ayyukan gaɓɓai, da tsarkake zuciya, da kiyayewa daga dukkan
cututtukan dake samun ayyuka ɗka, har ta kai cewa ilimomin shari'a gaba ɗaya suna
komawa ne zuwa gare shi, kuma daga gare shi take rasabtuwa.
Musulmi ba zai gushe ba yana samun cigaba a cikin matakan addini har sai ya kasance
mafi kusantuwa zuwa ga Allah.

Kuma matakan addini guda uku ne: Na farkon su shi ne Musulunci, duk wanda ya
tsayar da gininsa da tabbatuwarsa, to haƙiƙa ya ɗaga zuwa mataki na biyu wanda yake
shi ne Imani wanda ya tabbatar da rukunin Imani to, ya ɗaga zuwa mataki na uku
wanda shi ne kyautatuwa wanda kuma shi ne mafi girman matakan addini.

FA'IDOJIN HADISI:

1- Ladabi a gaban malami kamar yadda Jibrilu (A. S) ya yi tare da


Manzon Allah (‫ )ﷺ‬lokacin da ya zauna gaban Manzon Allah `
zaman mai ladabi don ya ɗauki ilimi daga gare shi.

2. Falalar Musulunci, kuma ya kamata ya kasance shi ne farkon abin


da ya yi tambaya a kansa, saboda haka ne Manzon Allah (‫ `)ﷺ‬ya
kasance idan ya aika 'yan aike zuwa da'awa yake umurtar su da su
fara da shaidawa babu abin da ya fi cancantar da bauta sai Allah
kuma Annabi Muhammadu (‫ )ﷺ‬Manzon Allah ne, kafin a fara
komai.

3. Shaidawa Muhammadu `tana wajabta imani da cewa Allah ya


aiko shi zuwa ga dukkan halittu baki ɗaya, kuma mu yi imani da
cewa shi Manzon Allah (‫ )ﷺ‬shi ne cikamakin Annabawa, kuma
hakanan ya wajabta gasgata shi a kan abin da ya ba da labari, da koyi
da umurninsa da nisantar abin da ya yi hani a kansa.
Kuma kada a ƙirƙiri wani abu a cikin addini wanda Manzon Allah
bai zo da shi ba, a cikin aƙida ne ko a wajen magana ko aiki, kuma
ka ƙudurta cewa Manzon Allah (‫ )ﷺ‬ba shi da wani abu na
rububiyya (gudanarwa a cikin halittu), kada a kira wani wanda ba
Allah ba, kada a nemi agaji da shi sai lokacin da yake raye kuma shi
ma ɗin a kan abin da yake da ikon ya agaza.

4. Imani shi ne gasgatawa a zuciya, da faɗi da harshe, da aiki da


gaɓɓai.

5. Rukunan imani su ne imani da Allah da Mala’kunSa da littafanSa


da ManzanninSa da rana ta ƙarshe, da imani da ƙaddara mai kyau
da mara kyau, wannan ita ke haifar waa da mutum ƙwarin guiwar
yin ɗa'a da tsoron Allah.

Imani da Allah ya ƙunshi abubuwa guda huɗu:

a. Imani da samuwar Allah.

b. Imani da kaɗaituwar Allah da samar da halittu da jujjuya


al'amuransu, ma'ana mu yi imani da cewa shi kaɗai ne Ubangiji,
kuma Ubangiji Shi ne Mahalicci Mai mulki mai jujjuya al'amura.

c. Imani da kaɗaituwarSai, cewa Shi kaɗai ne ba Shi da abokin


tarayya.
d. Imani da sunayenSa da siffofinSa, da tabbatar da abin da ya tabbatar
wa kanSa a cikin littafin Sa ko cikin hadisin Manzon Allah (‫ )ﷺ‬na
daga sunaye da siffofi, ta yadda ya dace da girman Allah ba tare da
canzawa ko ɓatawa ko kamantawa ba.

6. Imani da dukkan Manzanni, da mutum zai yi imani da manzonsa


amma ya yi inkarin wanda ba shi ba, (wato duk sauran manzanni ya
ƙi Imani da su) to, bai yi imani da Manzonsa ba, ya kafirta, saboda
fadin Allah Ta`ala:

MA'ANA:

{Mutanen Annabi Nuhu sun ƙaryata manzanni}.

Tare da cewa Annabi Nuhu kaɗai suka ƙaryata, saboda ba wani


Manzo da yazo gabaninsa, amma ƙaryata ɗaya daga cikin Manzanni
ƙaryata ainihin dukkan Manzanni ne.

7. Imani da asalin littafan da Allah Ya saukar ga manzanninSa


waɗanda ba a canza su ba, da kuma imanin cewa waɗannan littafan
tabbas daga Allah ne, kuma dukkan littafan an shafe su da zuwan
Alƙur'ani, ba a aiki da sua shari'ance.

8. Imani da rana ta Ƙarshe, wato ranar Alƙiyama kuma imanin ya


ƙunshi imani da masaukin farko na lahira, wato ƙabari, da kuma
imani da ni'imar ƙabari da azabarsa.
9. Wajabcin imani da ƙaddara mai kyau da mara kyau, da kuma cewa
ita ƙaddara har abada babu sharri acikinta, domin ta zo ne daga
rahama da hikimar Allah, amma sharri yana daga yadda aka ƙaddara
maka, saboda faɗin Manzon Allah (‫(( )ﷺ‬Kuma sharri ba ya daga
gareka)). Muslimu ne ya fitar da shi.

10. Tabbatar da matakin Ihsani (kyautatawa), ka san cewa mafi falalar


imani shi ne matakin kyautatawa da kuma jin cewa Allah Yana ganin
ka yana tare da kai. Shi ne ka bauta wa Allah kamar kana ganin Sa,
idan kai baka ganin Shi, to Shi yana ganin ka, ka kuma sani cewa
Allah na tare da kai, duk lokacin da bawa yaji cewa Allah yana tare
da shi ya kuma ya halarto da haka a dukkan halin da yake ciki
musamman lokacin da yake ibada, to, samun ha kan shi ne mafi
girman abin da zai taimaka masa wajen jin cewa Allah Yana taimaka
masa kuma yana dakonsa, wanda hakan shi ne mafi girman matakan
imani, sai bawa ya haɗa tsakanin imani da sanin cewa Allah Yana
sama, da kuma halarto da cewa Allah Yana tare da shi.

11. Malami idan an tambaye shi abin da bai sani ba sai ya bayyana
cewa bai sanin ba, hakan ba zai rage shi da komai ba, sai dai ma ya
zama dalili na taka -tsan-tsan da jin tsoron Allah a gare shi.

Ingancin aiki gabaɗaya ana gina shi ne a kan kalmar shahada,


domin shaidawa babu abin bauta sai Allah yana wajabta tsarkakewar
zuciya, shaidawa Annabi Muhammad Manzo ne (‫ )ﷺ‬yana wajabta
bin Manzon, kuma dukkan aikin da ke kusantarwa zuwa ga Allah ba
a karɓar shi face da waɗannan sharuɗɗan guda biyu:
TSARKAKUWA ga Allah, da kuma BIN MANZON ALLAH `.

Shaidawa babu abin bauta bisa cancanta sai Allah yana wajabta
tsarkake zuciya ga Allah, kuma irin wannan nau'in tauhidin ana
kiransa da tauhidin Uluhiyya (Tauhidin kaɗaita Allah), kuma ana
kiransa da Tauhidin bauta, domin ma'anar la'ilaha illallahu shi ne;
babu abin bauta da cancanta sai Allah, kada ka bauta wa kowa sai
Allah, duk wanda ya ce la'ilaha illallahu kuma ya bauta ma wanin
Allah to shi maƙaryaci ne.

Kuma daga cikin surorin bauta ga Allah Ta'ala akwai: Addu'a, da


nema a wajen Allah, da niyya, da alwashi, da rantsuwa, da yanka, ba
ya halatta a yi wani abu (daga cikin waɗannan ibadun) ga wanin Allah.
AUNA FAHIMTA
TAMBAYOYI.

1. Kawo matakan Musulunci, tare da sharhin su, kuma wanne ne


mafi girman su kuma saboda me?

...................

..................

.................

2. Ka dogara da wannan hadisin ka tattauna da ɗan bidi'a, kana mai


dogaro da tushen abin da shi ne wajibi wajen gina aiki.

.................. ……………………………………………………….

.................. ……………………………………………………….

.................. ……………………………………………………….

3. Me yasa ƙaryata Annabi guda ɗaya yake zama ƙaryata dukkan


Annabawa?

.................. ……………………………………………………….

.................. ……………………………………………………….

.................. ……………………………………………………….

You might also like