You are on page 1of 17

LITTAFI : UWA MAKARANTAR AL'UMMAH.

WALLAFAR: MALAMA BASMA SHEIKH ISMA'ILA IDRIS.

GABATARWA: FARIDAH BINTU SALIS (Bintus-sunnah)

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

MAHAIFIYA !!!
An karbo daga Abu Hurayrah (RA) yace: wani mutum yazo wajen Manzon
ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallam) sai yace: "Ya Manzon ALLAH waye yafi
cancantar kyakykyawar mu'amalata cikin mutane? Yace: Mahaifiyarka;
sannan wa? Yace : Mahaifiyarka; sannan wa? Yace: Mahaifiyarka; yace
sannan wa? yace mahaifinka."

Haka watarana wani mutum yazo wajen Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam)
ya nemi ya bashi izinin fita Jihadi, sai Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya
tambaye shi shin mahaifiyarka tana da rai? Sai yace tana da rai sai Annabi
(Sallallahu Alaihi Wasallam) yace ka lizimceta."

Wannan Baiwar ALLAH me ta aikata ne haka, har Annabi (Sallallahu Alaihi


Wasallam) ya hada ladar Lizimtarta dana jihadi? Abunda muke son mu
binciko kenan idan ALLAH ya yadda.

Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) yace ana auran mace don abubuwa guda
hudu; don kyawunta, dukiyarta, dangantakarta ko don Addininta. Amma Sai
Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya umurci al'ummarsa da su auri
ma'abociyar addini. Tun lokacin da mutum (Namiji) ya fara tunanin ya kamata
yayi aure ya kamata kuma ya tuna irin uwar da ya kamata 'ya'yansa su samu.

Idan mutum yayi tunanin auren Kyakykyawar mace, ya fifita kyau akan siffofi
ukun to ya tabbata ko mai kyan abu kamar karfe yake, wata rana zai yi tsatsa
kyan ya gushe, in kuma ALLAH ya baku 'ya'ya, kyau ya tafi, dama don shi ka
aurota, yaya Tarbiyar 'ya'yanka zai kasance?
Tunda mahaifiyarsu dai ba ma'abociyar addini bace. Kai kuma yaya
matsayinta zai kasance a zuciyarka tunda abinda ka aurota don shi ya gushe.

Idan ka auri mace don dukiyarta to shima ka tabbata ba mai dauwama bane.
Hakanan idan mutum ya auri matar data fishi dukiya to bai isa yayi iko a
kanta yadda ko wane Miji zai yi da matarsa ba, wani sa'imma sai ka samu
matar tana juya shi fiye da yadda shi zai juyata. In kuma ALLAH ya basu 'ya'ya
musamman 'Ya'ya mata suka ga yadda mahaifiyarsu take wa mahaifinsu,
kaga an samu shigar tsatsa zukatansu, yadda zai shafi rayuwarsu nan gaba,
suda mazajensu.

Hakanan in ka auri mace don Nasabarta, to kana son badda taka nasabar
kenan, don har in kuna da 'ya'ya zaka ga suna ta kokarin danganta kansu da
'yan uwan mahaifiyarsu bada na mahaifinsu ba, da zaka ce mishi "Kai dan
waye" cema zai yi "Ai ni jikan wanene" maimakon da yayi kokarin fadan
mahaifinsa, a'a sai ya kama kokarin fadan sunan kakansa na wajen uwa tunda
shi sananne ne, Mahaifinsa kuwa ba hakan bane.

Namijin da ya dorawa kansa auran kyakykyawa ko mai dukiya ko don


dangantaka badon addini ba yana tare da nakasu ga rayuwarsa dana
'Ya'yansa. Don haka Ma'aiki yayi horo da a auri ma'abociyar addini, wacce
kusan akanta nake son gina wannan dan littafi.

Kamata yayi in namiji zai yi aure, ya fara duba gidan da ya kamata ya nemi 'Ya
gare su, ba ina nufin gidan masu dukiya ko mulki ko wanin haka ba, ina nufin
gidan da aka riki addini sosai, don hakan zai fi bashi tabbacin samawa
'Ya'yansa uwa mai addini tagari. Wani lokaci akan samu albasa bata yi halin
ruwa ba, kaga iyaye kamammu masu addini amma 'Ya'yansu watsatstsu, ko
kuma su iyayen basu riqi addinin ba, su 'YaYan kuma ALLAH Ya kintsadda su.

Idan har ALLAH (SWT) Yasa ka dace da samun mace mai addini, kaga kana
da kyakykyawan zaton 'ya'yanka zasu zama masu addini, kaga kana da
kyakykyawan zaton 'ya'yanka zasu samu tarbiyya tagari. Wasu sukan auri
mace kyakykyawa don neman samun 'ya'ya kyawawa.

Akwai wata Hikaya ta wani mutum wanda ALLAH yaba ilimi sosai, yayi suna
ana jin labarinsa a durare da dama saboda wannan baiwa ta Ilimi da ALLAH
Ya bashi.

Wani lokaci sai kaga ALLAH (SWT) Ya daukaka mutum da wani abu, sannan
kuma bai bashi wani abun ba. To shima wannan Masanin ALLAH Ya bashi
Ilimi amma kuma bai bashi kyau ba, masu siffantashi da baki ne shi gajere
kamar an kife da kwando idanuwansa sun firfito zuru-zuru gashi kuma da
faffadan kai. Da ya tashi yin aure sai yaje ya sayo KUYANGA Kyakykyawar
gaske, ya sata a Daki, wai dabarar shi idan ALLAH Ya basu Da' zai gaje shi
wajen ilimi da hazaqa, Ya gaji Uwarshi ta wajen Kyau. Wannan Kuyangar da ya
sata a Daki, wato baiwar Kyau ALLAH Ya bata amma duk inda balidi ya kai da
rashin ilimi ta kai. To ALLAH (SWT) ba a masa wayo, da ya tashi basu Da' sai
ya basu sunkuyen abunda Uban D'an yake so, Ma'ana sai D'an ya gaji Uban
wajen Muninsa, Ya kuma gaji Mahaifiyarsa wajen Balidancinta.

Mai karatu kaga da ya aureta don Kyawawan dabi'unta da addininta da duk


haka bata faru ba.

UWA MAKARANTAR AL-UMMAH

To, da mutum ya auro mace ya kawota gidanshi, kamar ya bude Makaranta ce


ya kawo Malami ya saka ya Nemi Daliban da za'a dauka a koyar dasu. Da
zarar mace ta samu shigar ciki, to tun wannan lokacin zata fara Dawainiyar
wannan dalibi da za'a dauka a Makaranta. Idan an kai Yaro makaranta da
Niyar saka shi to ba ranar da aka kai shi za'a sashi a Aji ba, za'a dai dauki
sunansa ne, a gayawa wanda ya kawo shi ranar da za'a dawo dashi, da
abubuwan da ake buqatar yi masa kafin ya fara zuwa, kamar Uniform, Littafai
da sauransu.

Haka itama Makarantar Mahaifiya da zarar ta samu ciki to ta san Dalibi na


hanyar zuwa wannan makaranta, amma wannan kafin ya iso yakan jigatar ya
wahalar, ba kamar daya dalibin ba.

Wannan Dalibi da yake jigatar da Malamarsa wani lokaci, haka kurum zai
hanata cin wani abu abunda yake samunta, amma yanxu kar taci inda zata yi
kunnen uwar shegu taci, ba zata ga da kyau ba, Qilama sai ya kaita ga
kwanciya a asibiti. Yadda yake hanata cin abu, haka ya kan sata cin wasu
abubuwan da bata saba ciba, kamar su: kasa, Gawayi, Alli, bawon itatuwa
masu dacin gaske da sauransu. Yadda in taci abunda baya so zatayi fama,
haka idan taki cin abunda ransa yake so tofa nan ma ba zaman lafiya.

Bayan wadannan abubuwan da ya gindaya mata na tsirface-tsirface, ga kuma


ciwuwwuka da zata yi ta fama da shi da yawan kasala, kuma ance
Makarantar Uwa kafin ya fara zuwa daukan karatu sai an gindaya masa sayan
wasu abubuwan to haka suma Daliban makaranta kamar Uwace ita zata fara
saya masa kayan shiga makarantar.

SHIGAR DALIBI MAKARANTAR UWA !!!

Idan Mutum yayi sartse ko tuntube, duk jikinsa gaba daya zaiji ciwon tuntuben ko
sartsen, idan sartsen bai fita bama ya hana mutum sukuni, duk gaba daya jiki ya dau
ciwo, watakila ma har yasa Zazzabi.

To, ina ga ciwon da duk jikin mutum zai dau ciwo ko ina a jikinsa har faratun yatsu da
kasusuwa ciwo suke masa, abu kankani kamar sartse ya kidimashi to ina ga irin wannan
cutar ta komai da komai a jikin mutum? Kuma wace irin cuta ce?

Wannan cuta ita ce cutar Nakuda wacce kowace Uwa sai ta dan dana shi kafin ta samu
dalibi a makarantar. Wannan cuta da takan dandanata a duk lokacin da zata dau dalibi a
makarantar ance an tsakurotane daga cutar Ajali, ajaban wannan cuta da take gigita
masu fama da ita 'Yar kadance daga ciwon Ajali. Mai Karatu ya zaka kwatanta ciwon
Ajali kenan, ko kuma nace Mahaifiya ya zaki kwatanta mana ciwon Ajali tunda kin
dandana na Nakuda kinji.

ABINDA YA KAMATA AYI YAYIN HAIHUWA DA BAYAN HAIHUWA.

An ruwaito cewa Nana Fadima (RA) yayin da haihuwarta ta kusa wato tana
nakuda, Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) Ya umurci Ummusalma da
Zainab Yar Jahshi (RA) su ja mata ayatul Kursiyyu da "INNA RABBA
KUMULLAHUL LAZI KHALAKAS SAMAWATI WAL ARDI" zuwa karshen ayoyi
biyu. kuma su nema mata tsari da Kul'auzai biyu (Muta'awwizatan)

An karbo daga Al-Hassan Dan Aliyu (RA) yace: Annabi (Sallallahu Alaihi
Wasallam) yace "wanda aka masa haihuwa yayi kiran sallah a kunnensa na
dama da ikamah a kunnensa na hagu Ummussibyan ba zata cutar dashi ba"
wato (INNA) da muke kiransa a Hausance ba zata cutar da yaron ba."

Anan kunga amfanin auren mace mai Addini ya fito domin koda mijin ya
manta bai yiwa abunda aka samu kiran sallah da ikamar ba zata tunatar dashi.
Wadannan abubuwa ana bukatar yin sune kafin kwana bakwai za'a rada suna
idan yaro ya cika kwana bakwai ranar za'a ambace shi da sunansa.

Abdullahi Dan Umar (RA) yace: Lallai Annabi (Sallallahu Alaihi) ya umurci
kiran (Sunan) abinda aka haifa ranar bakwansa.

Kuma ya kamata mutum ya sanyawa danshi suna mai kyau, musamman


sunayen wadanda suka gabatar da ayyuka masu kyau don fatan wanda aka
sawa sunan yayi halin mai sunan na ainihi.

Ankarbo daga Abu Darda'u (RA) yace: Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi
Wasallam) Yace: "Lallai ku za'a kira ku da sunayenku ranar alqiyama don haka
ku kyautata sunayenku."

Ankarbo daga wahabul Hashmy (RA) yace: Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi
Wasallam) Yace: "Ku kira da sunan Annabawa kuma lallai mafi soyuwan
sunaye a wajen ALLAH Madaukaki sune: Abdullahi da Abdurrahman mafi
gaskatuwarta kuma Harisu da Hammam, mafi muninta kuma Harbu da
Murrah."

Wadannan Hadisai suna nuna mana Muhimmancin sanyawa yara sunaye


masu kyau, suna mai kyautatawa kamar addu'a take fa mai sunan. Ana kuma
iya chanja maras kyau zuwa ga mai kyau, don an ruwaito cewa Annabi
(Sallallahu Alaihi Wasallam) ya chanja sunaye maras kyau zuwa ga masu
kyau, kamar (Barratu zuwa Zainab, Huznu zuwa Sahl, Ambaki zuwa Jamila,
Sha'abul dalalatu zuwa Sha'abul Huda) hakanan ya chanja wa Banu Zinariyya
zuwa Banu Rushud)

Sau da yawa akan dauka in mace ta haihu ta gama wahala kenan, wadanda
suka zaci haka to ba haka bane.

Da zarar dai mace ta haihu, zata ji da ta dau wani kayane mai nauyin gaske
aka sauke mata, zata jita sakayau, in ta tashi tsaye ma za a iya daukarta
saboda rashin nauyi, sannan yawancin mata Suna haihuwa sai ciwon ciki yayi
musu sallama, wannan ciwon cikin yakansa wasu Suma, wasu kuma basa
suma amma yana iya fitar da mace daga hayyacinta, suyita sambatu saboda
wahala suna shure-shure, Mata da yawa Dana tambayesu game da wannan
ciwon cikin, cemin suka yi su sun gwammace ciwon nakuda da wannan
ciwon cikin domin yafi ciwon nakuda gigitarwa. Sannan kuma sau da yawa ba
abunda zasu sha yayi musu sauki, sai dai yayi iya yinsa ya daina don Kansa,
kuma ba dakikoki ko mintoci ko awowi yake yi ya daina ba kuma kwanaki
yake kafin ya daina.

Hakanan bayan ta haihu wata cuta ce kuma sabuwa da zata Shiga jinyarta,
wannan jinyar da zata yi shi ake qira JEGO.

Wannan cuta da jinyace-jinyace da mahaifiya take ta faman yi, sau da yawa ya


kan kasance don daukar dalibi daya daga cikin daliban makarantarta.

Wata za'a sameta tana da dalibai sama da goma a cikin makarantarta kuma
ko wani dalibi sai da tayi fama kamar yadda muka yi bayani a baya, wani
dalibin ma in ya tashi zuwa yazo da gardama har sai an yiwa malamar tashi
aiki da wuqaqe kafin a Ciro shi.

AJI NA FARKO DARASIN DA DALIBI ZAI FARA DAUKA A MAKARANTAR UWA !!!

Ranar da dalibin makarantar uwa ya iso makaranta in ba dai bata cikin


hayyacinta ba to a ranar zata fara lankwanta mishi darasi na farko.
Akwai darasi daya da kowane dalibin makarantar uwa yake isowa makarantar
dashi, Wannan darasin kuma shine: Dazarar dalibin nan ya iso makarantar
zaka ga yasa 'Yan yatsunsa a baki yana tsotsa. Kaga ya nuna mana cewa
yasan da abinci kuma yasan ta baki ake ci.

Idan mahaifiya ta dauke shi ta Bashi mama sau 1 kuma ta Bashi sau 2 to na 3
idan yaji yunwa kafin ta Bashi nonon da zarar yaji an dauke shi zai fara
karkata baki, yasan in an dauke shi za'a bashi nonon karkatar da bakinsa ake
yi. Kunga da fara shigarsa aji har ya dau darasi.

A koda yaushe yaro yake shan nono zaku ga ya kurawa mahaifiyarsa ido yana
kallonta, da haka har zai ganeta, kuma zai gane idan yana kuka ita ce take
sauri tazo ta dauke shi ta rarrashe shi, daga nan sai ya zama idan yana kuka
ko waye ya dauke shi bazai yi shiru da garaje ba idan ita ta dauke shi ba.

Lokacin da yaro zai iso makarantar uwa, zai iso bai San komai ba, idan yaji
bayan gida ko fitsari zai yi ne kawai. Baya damuwa da ina yake a hannun
Mutum yake ko a kwance yake akan gado yi kawai zai yi, da zarar yayi
mahaifiyarsa zata yi sauri ta cire masa kayan da ya bata ta wanke masa ta
sanya masa wasu don yaji dadin jikinsa, sannan kuma ta wanke wadanda ya
bata.

Bayan 'Yan kwanaki da yayi bayan gari idan mahaifiyarsa bata kusa, zaiji
jikinsa ba dadi daga nan sai ya kama kuka, don an saba wanke masa da wuri,
kunga ya kara daukan darasi sabanin da farko idan yayi bayan gari ko fitsari
sai dai aji wari ko zarnin fitsarin sai a wanke masa, amma yanzu yana yi zai
sanar ta hanyar kuka a wanke masa, ya gane zama da kazantar ba dadi.

Wani lokaci kana zaune zaka ji muryar mahaifiyarsa tana hira tana kecewa da
dariya, da zaka leqa Inda take, sai kaga da Dan wannan dalibin nata take hira
tana kecewa da dariyar kamar yana amsa mata.

Wani lokaci kuma waqa zata yi ta masa tana masa rawa, in kuma a bayanta
yake zata yi shiru musamman in kuka yakeyi zata Dan ringa jijjiga shi don yayi
bacci.

Wani lokacin inda zaka dauke shi ka tsayar dashi akan cinyarka sai kaga ya
fara rawa ko ba waqa, ko kuma idan yadanyi wayo ya juyo waqar da ake masa
rawar da ita sai kaga ya kama rawar shi kadai.

Kamar yadda muka ce a baya yaro ya kan iso makarantar uwa bai iya komai
ba sai abu daya da muka yi bayani a baya, idan ya kai wata 4 zata fara koya
masa zama ta hanyar sashi a kwali ko baho ko kuma makamancin hakan.
Wani lokaci kuma zama zata yi ta ware qafafuwanta ta sashi a tsakankaninsu
da haka Har ALLAH ya sashi ya iya zama.

Sannan kuma idan ya kai wata 6 zata fara koya masa cin wadansu abubuwan
kuma bayan nono.

HIKIMAR ALLAH A HALITTAR NONO !!!

Wata rana ina zaune a asibiti sai ga wani mutum ya shigo yana sabe da
'yarshi mai kimanin shekaru biyar a kafadarsa, bata da lfy sosai don cutar ta
ramar da ita kwarai sai kanta ne kawai yake da girma ainun a jikinta, ya karbi
kati yabi layin ganin likita ya zauna, yana zaune sai wani ma' aikacin jinya yazo
Yace me ke damun 'yar tashi, ya amsawa ma'aikacin Jinyar akan shi bai San
takamammen abunda yake damunta ba, haka kawai yaga ta fara ramewa,
wani lokaci kuma sai kafafunta da fuskarta su kumbura, sai ma'aikacin jinyar
nan Yace: "Ba wani abu ne yake damunta ba sai karancin abinci" mutumin sai
Yace ya za'ayi ace 'yarsa tana ciwon yunwa bayan bata rasa abinci a kullum
ba watakila ma sau uku a rana.

Watakila ma'aikacin jinyar ya karanci abunda na karanta a fuskar mahaifin


yarinyar don naji ya bashi amsa da: "Ba ina nufin cewa rashin cin abinci
samsam ne ya janyo mata cutar ba a'a ina nufin rashin cin abinci masu Gina
jiki, watakila abu daya take samun ci kullum, kamar tuwon masara miyar kuka
kuma miyar ba a hada mata kayan gina jiki dana kare jiki daga cututtuka ba,
kamar manja, tumatir, nama ko kifi, idan ba halin nama ko kifi ana iya watsa
wake duk amfanin su daya, kuma a dinga Dan canja miyar, yau in ansha
taushe gobe asha kubewa da sauransu, kuma idan an dama mata kunu ba
halin madara ayi mata na waken suya ana zuba mata, ba a rinqa cin abu daya
kullum ba, musamman ma ga yara wadanda aka yaye"

Fadinsa wannan bayanin na musamman ga yara, sai na fada kogin tunani,


naga yaro yana fadowa duniya a matsayin Dan jinjiri, za'a fara bashi nono ba
canji har yayi wayo, wani in yayi wayon ma aka bashi wani abincin bazai taba
yarda yaci ba sai dai nono har sai ya isa yaye, kuma ba zaka taba ganin chanji
a jikinsa ba na don yana shan abu daya ba.

Kuma abubuwan da Malamin jinyar nan ya lissafawa mahaifin yarinyar nan,


ba wanda zaka ci daga samun shi ba tare da ka gyara shi ta hanyar dafa shi
ko wanke shi ba.

Amma Nono koda yaushe yaro ya bukata ba sai ansha wuyar daura tukunya a
dafawa ba ko kuma tsayawa wankewa da gyarawa, haka kuma ba sai ance
bari aje a dumama ba, koda yaushe yaro zai sha da duminsa ba sanyi ba, ba
kuma zafi can ba.

Hikima da Rahamar da ALLAH (SWT) ya Sanya a halittar nono ta isa ga


kowani Dan Adam ya ringa godewa Ubangiji a koda yaushe saboda ni'imarsa
da ya lullube mu dashi

SHIGAR YARO AJI BIYU A MAKARANTAR UWA:

Sau da yawa za kaga yaro in yakai wata 6 zuwa 7 ya fara gane mahaifiyarsa
sosai, wani lokacin zai fara karya gwuiwa yana neman fara rarrafe, wani idan
ALLAH ya daga shi da wuri yana da wata 7 sai kaga ya fara tafiya.

Yawanci kuma a wannan lokacin zaka ga sun fara fitar da harrufa wajen yin
magana, malamarsa kuwa zata yita kokarin lakonta masa maganganu,
musamman sunayen mutanen gida kamar (Mama da Baba) kusan ko wani
yaro da sunayen mutum biyun nan yake fara magana musamman ma da yake
kowane daya daga cikin sunayen kalma daya ce ake maimaita ta, shi kuma
yaro sabon fara magana in yaji suna kalma daya yakan dauka yana maimaita
ta, musamman kalmar karshe kota tsakiya misali da zai ji ana yawan kiran
(Jamila) to idan yaga mai sunan zaka ji yana kiranta da (La) ko (Mi) har sai ya
kara wayo sai ya qara kalma daya yaringa kiranta (Jami) ko (Mila) har yazo ya
iya gaba daya.

Yara yawanci tun daga wata 3 ko 4 sukan fara cutar fitowar hakori, wasu
zazzabi sukanyi da ciwon ido, wasu kuma gudawa, a duk lokacin da yaro yake
fama da wannan cutar, zaka ga Malamarsa ta damu ainun, idan yana ramewa
sai kaga itama tana ramewa, kusan tare suke cutar, da zai kasa bacci da dare
to haka itama zata zauna bazata iya yin baccin ba, haka zasu yita fama har
ALLAH ya sauwaka masa cutar har hakoran su fiffito.

Lokacin da yaro ya fara tsayuwa zaka ga malamarsa ta rike ko wanne


hannyensa tana koya masa tafiya tana ce masa (Taa, Taa, Taa) ko yaushe in
tana koya masa tafiya sai ta dinga maimaita masa wannan kalmar don haka
ko ba a rike hannunsa ba idan yana tsaye yaji ance "Taa, Taa, Taa" sai kaga ya
fara kokarin tafiya da haka har ya iya.

Lokacin da Yaro yazo duniya zai dauka iya fadin dakin mahaifiyarsa iya fadin
duniyar kenan, ranar da aka fito dashi tsakar gida sai yaga ashe dai duniyar
tana da fadi, bare ranar da ALLAH yasa ya leka kofar gida yaga unguwarsu,
don haka yana samun kafa da ya faki idon mutanen gidan wuf sai yayi waje,
idan ya fita kuma tafiya zai kama yi ba tare da ya san inda zaije ba, don haka
da ya kai wannan lokacin malamarsa zata ringa kulle kofa.

Ta wajen Tarbiyyar magana kuma zata ringa koya masa idan an bashi abu
yace ya gode, idan yaji bayan gida yayi magana, idan yaji yunwa ya fada da dai
sauran kananan abubuwa kuma a wannan lokacin ne yaro yake kasancewa
gwanin kwaikwayo don haka malamarsa bata barin wani makami ko wani
abun cutarwa a kusa, kuma ko yaushe takan leka kicin dinta don gudun kar
dalibinta ya cutu.

AJI UKU NA MAKARANTAR UWA:

Idan ALLAH Yabawa yaro lafiya da wayo yana da shekara 4 zuwa 5 ko 6


maganarsa zata kasance ana ganeta sosai, adai dai wannan lokacin
malamarsa zata fara koya masa muhimman abubuwa kamar: sallama idan
zai shiga gida ko daki, gaida mutane, tsarki, alwala, karatun alqur'an mai
girma da dai sauransu.

Sallah kuma adaidai wannan lokacin zata na umurtarsa yana kwaikwayonta,


idan ya kai shekara 7 sai ta koya masa abunda ake fada a iqamah da kabbara
da tsayuwa da ruku'i da sujjada da tahiya da sauransu.

Yazo a Hadith cewa: A umurci yara suyi sallah tun daga shekara 7, a dake su
idan sunki yin sallah suna da shekara 10.

Ka ga mai karatu wannan shine amfanin auren mace mai ilimi mai addini
kenan, idan kaje ka auro kyakykyawa ba addini ko mai dukiya ba addini ko mai
nasaba ba addini, jahila kuma addini bai dameta ba, to ba zata damu data
matsawa yaranka suyi addini kota koya musu addini ba.

AJI HUDU NA MAKARANTAR UWA :

Idan yaro ya isa aji 4 na makarantar uwa a wannan lokacin zata matsanta
nuna masa amfanin addini da tsafta, ta kuma rinqa yi masa 'yan labarurruka
da zasu nuna masa aibin mai mummunan hali da wanda ya sabawa Ubangiji
da kuma kazami, da kuma wadanda zasu nuna kyakykyawan sakamako ga
wanda yayi biyayya ga ubangiji da mai kyakykyawan hali da kuma mai tsafta
da sauransu.

A wannan lokacin ne zata koya masa yin wanka da kansa sa sanya tufafi da
'yan qananan aikace aikace kamar dauko min kwano ko dan share min nan ko
sayo min abu kaza a kofar gida da dai sauransu.

Wasu sukan kai 'Ya'yansu makaranta tun suna qimanin shekara 3 ko 4, a


lokacin yana aji 2 ko farkon aji 3 a makarantar uwa.
Wasu kuma sai yaro ya kai shekara 7 yayi nisa kusan ya kai karshen aji 3 a
makarantar uwa.

Abun bukata dai ko yaushe nema dai ake saka yaro a malaranta shine idan ya
dawo, Malamarsa ta gida ta ware masa wani lokaci a rana da zaiyi bitar
karatunsa inda ya kasa ta rinqa tayar dashi. Ba idan yaje ya dawo ya ajiye
kayan karatun ba za'a sashi yayi bita ba sai washegari idan zai tafi a karkade
kayan a bashi ya tafi.

Anan ma amfanin samarwa yara mahaifiya ma'abociyar addini ya fito.

AJI MAFI HATSARI:


Malaman sanin halin dan Adam sun kiyasta aji mafi hatsari ga rayuwar yaro a
makarantar yana farawa ne yawanci daga shekara 11 zuwa 18.

A wannan ajin malamarsa takan wahala qwarai wajen karantar dashi, daidai
shigar yaron ajine mukan qira shi a Hausance da "TASHEN BALAGA" a
wannan lokacin yaro zaiji shima fa yanzu wani abu ne, zai kuma fara karkata
zuwa ga daya jinsinsa. Wato Yan'maza su fara karkata ga Yan'mata haka
suma Yan'matan.

Rayuwar wadannan jinsuna biyun a wannan lokacin zai koma ne kacokan


dinshi zuwa ga sha'awar abubuwan duniya, kuma a wannan lokacin ne yaro
idan zai lalace zai kama hanya idan kuma kintsuwa zai yi zai kama hanya.

Wannan mataki nada hatsari ga rayuwar yaro baya buqatan yawan duka ko
fada, abunda ya kamata mahaifa suyi shine: su cikawa yaran lokutansu da
aikace- aikace. Idan namiji ne bayan ya taso daga makaranta uban ya tafi
dashi wajen sana'arsa ko kuma ya nema masa wata sana'ar, kar dai a bar
masa lokaci ya zaina baya komai balle har ya tuna wani mummunan abu,
haka itama mace za'a cika mata lokutanta da ayyukan gida da koyon sana'o'i
kamar Saqa, dinki da sauran su, amma ayyukan fa sai sun dawo daga
makaranta.

Kuma kar amanta da yawaita yi musu addu'a. Annabi (Sallallahu Alaihi


Wasallam) yana cewa: "Ba abinda yake maida qaddara yakan kareta sai
addu'a"

Don haka kar muyi wasa da addu'a domin wata garkuwa ce da zata kare mu.

Yaro na fita daga wannan aji zai zama nitsatstse idan ya samu kyakykyawar
kula a ajinsa na baya, a lokacin ne kuma zai shiga ajin karshe a makarantar
uwa, ajin da idan ya shiga ba fita, domin ita makarantar uwa ba a taba
gamata, sai dai idan dalibin ya rasu ko kuma ita malamar.

Wannan aji na qarshe da dalibo yakan shiga baya shigarsa face ya mallaki
hankalinsa ya kuma san ciwon kansa. Darrusan kuma da zai rinqa dauka a
wajen malamarsa sune shawarwari. Hausawa sunce: "Abunda babba ya
hango yaro ko ya hau turmi bazai Ganshi ba."

UWAYE SUNA SUKA TARA !!!


Masu iya magana sukance: "Mata suna suka tara" ko kuma wanin haka, to
uwayenmu suna suka tara, akwai uwa mai ilimi akwai kuma uwa jahila.

UWA MAI ILIMI: Wani mai hikima yana cewa: idan mai ilimi zai yi tsiya zaka
ga tsiyarsa ta banbanta data jahili, yana da amfani matuka ga mutane gaba 1
idan ka shiga gidan mace kuma uwa mai ilimi zaka samu gidan an tsabtace
komai da komai, kuma ta gyara shi ta tsara shi daki-daki, tasan kazanta tana
cutarwa kuma tasan abunda take aikatawa 'Ya'yansu na kula suna lura kuma
qwaqwalwarsu tana dauka, suma zasu ringa aikatawa idan mai kyaune haka
zasu aikata don sunga mahaifyarsu nayi.

Don haka uwa mai ilimi zata yita kokarin aikata abubuwa masu kyau don
amfanin kanta da Maigidanta da yaranta.

UWA JAHILA: Subhanallah ALLAH shi yake halitta yana sanya kowa yadda
yaso, Uwa jahila kana shiga gidanta zaka gane banbancinta da mai ilimi zaka
ga komai bashi da takamammen waje. Idan kazo kitcen dinta yau ka debi
suga, gobe idan ka dawo ka tarar ka diba ka zuba a kunu sai ka dandana zaka
fahimci ai gishiri aka mayar a wannan gurbin. Da "NEPA" zasu dauke wuta da
dare sai kajiyota gwararam tana hada shirgi bata san takamammen inda ta
ajiye ashana ba.

Maigida a kullum ya shirya zai fita sai ranshi ya baci akan neman takalminsa
1 ko matashin kai ko wani abun daban, haka yara idan zasu makaranta sai
sun jikkata wajen neman uniform, takalmi, safa harma da littafan su, uwar
bata ajiye kayayyakin da tsari, don haka suma idan sun dawo kowane abu
wajen da aka jefa shi daban daban, littafai kuwa da yake ba mai yi musu bita
shima idan sun wurgar sai gobe idan zasu koma za'a nemo.

Kaga ranar Uwa mai ilimi kenan sai a dage wajen sanya 'ya'ya mata a
makaranta kamar yadda ake dagewa wajen sanya 'ya'ya maza.
FALALAR MAHAIFIYA:
ALLAH (SWT) Yana cewa: "kuma munyi wasiyya ga mutum game da
mahaifansa, magaifiyarsa ta dauke shi a cikin raini akan wani rauni ta kuma
yaye shi cikin shekaru biyu muka ce masa ka gode mini da kuma mahaifanka
makomarku gare ni take" [suratul luqman aya ta 14]

ALLAH (SWT) Yace:" kuma munyi wasiyya ga mutum game da mahaifansa


biyu da kyautatawa, mahaifiyarsa tayi cikinsa a wahala kuma ta haife shi a
wahala cikinsa da yaye shi wata talatin ne" [Suratul Ahqaaf aya ta 15]

Munyi bayani a taqaice a baya akan fadinsa Madaikaki; mahaifiyarsa ta daike


shi rauni akan rauni da mahaifiyarsa tayi cikinsa tilas kuna ta haife shi tilas.

Munga halin da takan kasance da zarar ta samu ciki har zuwa girman d'a, in
muka ce zamu yi bayani gamsashshe zamu rubuta mujalladai da yawa akai.

Amma duk da haka wannan gajeren bayani da muka yi ya isa kowane mai
karatu mace ce ko namiji ya gane muhimmancin mahaifiya.

Bana nufin a karkata ga mahaifiya kadai, domin shima mahaifi abun


girmamawa ne kwarai da gaske, don mahaifi abin alfahari ne ga kowane dan
Adam fiye da uwa.

In mutum zai kasance mahaifiyarsa 'yar manyan gida ce kuma ita kanta
shahararriya ce, amma kuma ba a san waye mahaifinsa ba, to fita cikin
mutane ma sai ya gagare shi.

ALLAH (SWT) Yace: "Ubangijinka ya hukunta da kada ka bautawa kowa sai shi
kuma ka zama mai kyautatawa ga iyayenka. Koda dayansu ya kai ga tsufa a
wajenka ko kuma dukansu to kada kayi musu tsawa kar kace "tir" ka fada
musu magana ta girma kuma ka sassauta musu fika fikan tausasawa ta
rahama kuma kace Ya ALLAH kayi musu rahama kamar yadda suka reneni ina
qarami. Ubangijinku shine mafi sani da abunda ke cikin zukatan ku, in kun
zamo na kirki to ALLAH ya kasance ga masu komawa gare shi mai gafara ne"
[Suratul Isra'i aya ta 23-25]

ALLAHU AKBAR wadannan ayoyi masu albarka, da 'ya'ya zasu lura dasu kuma
suyi tunani su tabbatar da cewa lallai ALLAH (SWT) Yayi horo da girmama
iyaye.

Iyaye mata suna yawan saurin yiwa 'ya'yansu baki wanda kuwa bakin uwa
bashi da wuyan kama yaro.
Muna iya gane hakan acikin wadannan kissoshi masu zuwa:

1• KISSA TA FARKO: wani mashahurin masanine yayi suna aka sanshi a


wurare da dama yana da iyali kuna mahaifiyarsa na nan da ranta, wata rana
yaje sanar da mahaifiyarsa yana da niyyar tafiya aikin hajji. Mahaifiyar tasa
tace bata yadda ba, kuma badai a wannan shekarar ba.

Ya koma gida yana tunani to ai aikin hajji zai bautawa ubangijinsa ne don
haka ko bata yadda ya tafi ba yana ganin ba abunda zai same shi kuma bashi
da laifi don haka yayi shiri ya sallami iyalinsa ya tafi.

Mahaifiyarsa tazo gidansa neman shi sai iyalinsa suka fada mata ya tafi aikin
hajji, jin haka sai ranta ya baci, sai tayi addu'a tunda yaqi jin maganarta
ALLAH ya dawo mata dashi a wani mummunan hali.

A lokacin a kafa ko akan dabba ake tafiya don haka shima wannan masanin
akan dabbarsa ya tafi ya yada zango a wani gari.

Ya shiga masallaci domin yin sallar magriba, bayan idarwarsa yana zaune sai
yaji ihu an yiwo masallacin ana cewa barawo !!! Masu ihun suna shigowa
masallacin sai suka farmasa da duka akan shine 6arawon, yana tace musu ni
ba barawo bane amma ina! Al'adar mutanen garin idan sun kama 6arawo
sukan yanke masa hannu 1 da kafa 1 don haka shima wannan masanin suka
masa haka, da yake sananne ne yayi suna yana tace musu nine wane! Har
ALLAH Ya taimake shi wanda ya sanshi ya gane shi bayan sun yanke masa
hukunci, Aka dauke shi aka mai dashi gida garinsu.

Mahaifiyarsa tana ganinsa hankalinta ya tashi ta rungume shi tana kuka. A


take ta roki ALLAH (SWT) da ya dau ranta ita da danta.

2• KISSA TA BIYU: itama akan wani bawan ALLAH ne mai yawan ibada
mai suna juraij yana yawan bauta acikin bukkarsa, aqasan bukkar kuma akwai
mai kiwon shanu, sannan akwai wata mata da take yawan zuwa wajen mai
kiwon shanun nan.

Sai mahaifiyar Juraij tazo wajensa wata rana yana cikin sallah, sai tace Yaa
Juraij! Yana cikin sallah, sai ya fada a ransa cewa ga babata tana kirana kuma
gashi sallah nake, sai yaga gwara ya cigaba da sallarsa, sai ta kara kwala
masa kira karo na biyu hakama dai karo na uku. Yayin da yaqi amsa kiranta
sai tace: Kada Allah ya kasheka har sai ka hadu da fuskar karuwa. Sai tayi
tafiyarta.

Sai aka zo wa da sarki wannan mata da take zuwa wajen mai kiwon nan ta
haihu, Sai sarkin ya ce mata dan wane ne? Tace na Juraij ne. Sarkin ya ce mai
bukkar nan? Tace eh!

Sarki yace kuje ku rushe bukkar kuma ku kawo mun shi, sai suka rusa
bukkarsa da wani abu na qarfe kamar guduma, har sai da ta hade da qasa,
suka kamashi suka daureshi suka sa hannunsa a wuya suka daure da igiya,
sannan suka tafi dashi wajen sarki. Sai Juraij yaga karuwai da yawa, sai yayi
murmushi, Su kuma sunata kallonsa. Sai sarki ya ce: Me wannan mata take
zato? Sai Juraij yace me take zato? Sarki yace tana zaton d'anda ke hannunta
naka ne. Sai Juraij yace mata haka kike zato? Tace eh! Sai Juraij yace ina
yaron? Sai suka ce gashi can cikin zanin goyo, sai Juraij yaje inda yaron yake
yace: Wanene babanka? Sai jaririn yace mai kiwon shanu.

ALLAH (SWT) Ya rufawa wannan bawan nasa asiri ta hanyar sanya jariri
magana domin ya fadi waye mahaifinsa.

Ya 'yan uwana uwaye ya kamata musan irin addu'ar da zamu dinga yiwa
yaranmu domun idan muka yi dubi da kussoshin nan 2 zamu ga duk
wadannan bayin ALLAHn babu wanda ya sa6awa mahaifiyarsa ta hanyar son
ransa, amma duk da haka sai kowanne addu'ar mahaifiyarsa ta kama shi.

Don ALLAH a guji kundumawa yara ashar da mummunan addu'a, domin ke


uwa malama ce gare su duk abunda kikeyi shi suke kokarin koya.

HALIN UWAYE A YANZU:


A cikin Arba'una hadith na Imamun nawawiy, a hadith na 2, Umar (R.A) ya
ruwaito hadithin, A ciki ya bamu labarin zuwan Mala'ika Jibrilu (A.S) wajen
Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yayi masa tambayoyi akan
musulunci da imani da ihsani. Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) kuma tana
bashi amsa sannan kuma ya tambayi Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam)
akan tashin qiyama, Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya amsa masa da
wanda ake tambayar bai fi wanda yake tambayar sanin amsar ba. Sai Mala'ika
Jibrilu (A.S) ya nemi Annabi da ya bashi labarin alamominta ita ranar tashin
alqiyamar, sai Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya bashi labari daga cikin
alamomin da Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya fada masa akwai:
"BAIWA ZATA HAIFI UWAR GIJIYARTA"

Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yayi gaskia, yanzu ko ina ka duba
zaka samu iyaye mata sun koma gurbin 'ya'yansu.
Sau da yawa na kanyi mamakin kasancewar haka, kuma nake tambayar me
ya kawo hakan?

Sai kaga 'Ya tana dakawa uwarta tsawa uwar kuma sai abunda 'Yar tace mata
zata yi. Uwa na tafiya da tsummokara a jikinta, 'Yarta kuwa sai kace diyar
wani sarki, ganin wasu iyayen sai ka samu abunda zasu ci da kyar amma duk
hanyar da za'abi a yiwa yarinyar zani mai tsada za'abi ayi mata koda zata
kaisu ga cin bashine don kawai gudun kada a batawa Yarinyar rai.

Da can yanda aka sani Yarinya har ta girma ta zama budurwa, to uwarta ta
samu hutun aiki, Yarinyar ce zata dinga yin ayyukan gida, to yanzu an samu
akasin hakan, sai kaga uwa nata faman kiciniyar aikin gida, yarinyar na
kwance a daki.

Wata ma idan uwar ta gama abinci sai ta kai mata, ta hau gunagunin cewa
abinci bai yi dadi ba, ta bar abincin ta fita ta sayo abunda ranta yake so a
waje, ta bar uwar da abincinta.

Sannan kuma yanzu ga wata babbar annoba ko kuma ince masifa dake
faruwa na zuwan 'YAN MATA DAKUNAN SAMARINSU, har ya kai ga wasu sun
daukewa samarin zuwa gidansu, su suke zuwa wajensu.

Wasu kam nasan 'ya'yan kanje ne ba tare da sanin iyayen su ba amma wasu
da sanin iyayen nasu, domin sai kaga uwa da sallah ko kuma idan bashi da
lafiya ta zauna ta shirya girki ta kuma yi saye saye tabawa 'yarta ta kaiwa
saurayin.

Kai jama'a ina zamu kai kanmu ne Yanzu, don tsananin ta6ar6arewar tarbiyya
wasu iyayen ma suna ganin Yan mata sina ta sintiri a d'akin d'ansu amma
basa cewa komai, wai an cigaba. Qarewa tsoron 'ya'yan ake ji wai kar a bata
musu rai.

Ni kam dan ALLAH mai karatu, wa zaka daurawa laifin lalacewar tarbiyyar
yara, iyaye maza ne ko iyaye mata ???

A nawa ganin laifin yana kanmu mu iyaye mata don maza basa zama bare su
san me ke faruwa.

Annabi (Sallallahu Alaihi wa sallam) Yace: "imanin dayanku baya cika har sai
ya sowa dan'uwansa abunda yake sowa kansa"

Yanzu akasarin Maza in sun tashi neman aure 'ya'yan masu kudi suke nema.
Saboda kwadayin abunda za'a kawo ta dashi, wani idan an bashi aure a hada
masa da gida da jari, don haka 'ya'yanmu talakawa suke rasa mazan aure don
bamu da abunda zamu bawa mazan idan sun aure su.

Mutum idan ya zamo baya tunanin aure sai 'ya'yan masu arziki to ya kamata
yayi tunanin cewa a danginsa akwai talakawa, wataqila ma yana da qanne
mata, yaya zaiyi dasu kenan idan kowa ya raja'a da irin wannan hali nashi ???

ALLAH dai Ya shirya mana. (Ameen)

KARSHEN LITTAFIN KENAN.

Bayanin Maigabatarwa Faridah Bintu Salis (Bintus-sunah):

Ina matukar farin ciki ga mika Godiyata ga ALLAH TA'ALA da Ya bani ikon
gabatar da wannan littafi, wanda muka ringa kawo shi kadan kadan har sau
24 wanda a yanzu na samu damar hada shi a PDF.

Littafin UWA MAKARANTAR AL'UMMAH Ya tattara abubuwa da yawa


acikinsa musamman bangaren rayuwa tsakanin iyaye da 'ya'yansu. Hakan ne
yasa nayi kwadayin dukkan 'yan uwana musulmai su fa'idantu da wannan
littafi mai albarka musamman 'Yan uwana Mata.

Ina rokon ALLAH ya jiqan mawallafiyar wannan littafi wato MALAMA


BASMAH SHEIKH ISMA'ILA IDRIS BIN ZAKARIYYAH JOS tare da Mahaifinta da
dukkan 'Yan uwa musulmai da suka riga mu gidan gaskia (Ameen)

Wasu daga cikin 'Yan uwa suna korafin cewa sun nemi littafin a kasuwa basu
samu ba, lallai hakan zai iya kasancewa domin nima tunda na same shi ban
sake jin wanda yace ya samu ba kuma ban sake ganinsa a wani waje ba.
Ga Address na wajen da aka buga littafin kamar yadda na gani a rubuce a
jikin littafin kamar haka:

"Printed @ Ishak Danjos Printing & Publishing, Dogon Agogo, Bauchi Road,
Jos 08037335593, 08097377272"

Ga wanda yake da bukatar wannan rubutun Littafin UWA MAKARANTAR


AL'UMMAH, Bayani kamar haka:

Akwai wani group a Facebook mai suna MALAMA BASMAH SHEIKH ISMA'ILA
IDRIS ZAKARIYYAH, Wanda wani dan'uwa ya bude, bai jima da budewa ba
asali ma bai saka mutane da yawa ba, ALLAH Yayi masa Rasuwa ALLAH Ya
jikansa ALLAH Ya gafarta masa (Ameen) to kusan dai postings din rubutun
wannan Littafin ne aciki, saboda haka idan aka yi searching za'a samu
rubutun wannan littafi tun daga farko har zuwa karshe.

Daga karshe ina yiwa Yan'uwa da abokan arziki fatan alkhayri tare da addu'ar
ALLAH Yasa mu amfana da abunda muka karanta (Ameen)

Ina rokan ALLAH Ya gafarta mana bisa abunda muka rubuta ko muka fada
bisa kuskure.

ALLAH Ya isar da ladan ga mawallafiyar wannan littafi tare da dukkan


al'ummar musulmai wadanda suka riga mu gidan gaskia (Ameen)

ALLAH YA KARA DAUKAKA MUSULUNCI DA MUSULMAI (AMEEN)

ALHAMDULILLAH.

'YAR-UWARKU A MUSULUNCI:
Faridah Bintu Salis
bintussunah1@gmail.com

You might also like