You are on page 1of 15

DARUSAN TAFIYA ZUWA ISTANBUL, TURKEY

DAGA
DR. SAIDU AHMAD DUKAWA
BUK
Na san watakila masu bibiyata suna bina bashin guzurin tafiyar da na yi zuwa
Kasar Iraqi a watan bakwai na wannan shekarar (daga 23/7/23 zuwa
30/7/23), amman ban samu rubuta komai ba. Sai gashi kuma na yi wata
tafiyar zuwa Turkiyya (Türkiye, TURKEY), ita kuma daga 17/11/23 zuwa
28/11/23. Duka tafiyar akan al’amuran da suka shafi ilimi ne.
Tafiya zuwa Iraqi na halarci taron Kasa da Kasa ne akan baje kolin Jami’o’in
Duniya. Wannan shine karo na farko da na san cewa ana baje koli akan
harkar ilimi, ba kawai akan kayan alatu da na kwalam da makulashe ba! Na
kasance a cikin tawagar da ta wakilci Jami’ar Al-Istiqama da ke Sumaila. Don
haka a aljihun Distinguished Senator, Dr. Abdulrahman Kawu Sumaila,
OFR, naje. Tunda labarin wannan tafiyar ya yi kwantai, zan maida hankali ne
akan tafiya zuwa Istanbul, Türkiye. Kuma tunda labarin ya yi kama da juna,
wajen darusan da suke ciki, ina fatan masu karatu ba za su yi rashi mai yawa
ba.

Ita kuwa tafiya zuwa Türkiye, Jami’ar Bayero Kano ce tare da hadin gwuiwar
Asibitin Malam Aminu Kano da kuma Bankin Duniya (World Bank) suka dauki
nauyinta. Babban burina na bada labarin wannan tafiyar shine na zaburar da
matasa (harma da wandanda suka manyanta) wajen zage dantse game da
neman ilimi. Marigayi Akilu Aliyu yana cewa: “an lura ba da tangarda ba, mai
ilimi shike morewa; kwalkwoliyar daraja shi hau shi dare dam! Kasgi, maras
ilimi kuwa ko hangawa!” Baya ga wannan babban burin, sai kuma duk wata
fa’ida da take tattare da labarin tafiya; wadda fa’idar da take cikin tafiya ba za
ta gididigu ba, tunda Al-Qur’ani mai girma ya kwadaita yin tafiya a bayan
kasa.

Watau wani tsari ne da Bankin Duniya ya shirya shi tare da hadin gwuiwar
Jami’ar Bayero wanda ake dauko ma’aikatan kiwon lafiya daga kasashe
daban-daban na Africa, ana tattarasu a Asibitin Malam Aminu Kano domin yin
karatun digiri mai zurfi (Masters degree) a fannoni daban-daban, tare da hada
su wuri guda domin koya mu su fannonin da suka ratsa kowanne fanni. Cibiya
aka samar sukutum da guda domin gudanar da wannan tsarin. Sunan Cibiyar
a Turance “Africa Centre for Excellence in Population Health and Policy
(ACEPHAP)” wadda za a iya fassarawa da “Cibiyar Kwararru ta Africa mai kula
da lafiyar al’umma da tsaretsaren gwamnati na kula da harkar lafiya”. Cibiyar
tana karkashin shugabancin kwararriyar Likita, Farfesa Hadiza Shehu
Galadanci. Fannin Cibiyar na koyarwa game da kudurori da tsaretsaren
gwamnati na kula da harkar lafiya shi ya shigo da ni cikin masu
koyarwa. Tsarin inganta ilimi da kwarewar Malamai ya na da karfi a wannan
Cibiyar, saboda haka na samu wannan tallafin na halarci horon karawa juna
ilimi/bita (workshop) a kasar Türkiye, guda daga kasashen da nake da
kishirwar zuwa.
Wannan dan gajeran rubutun takaitattecn bayani ne game da tafiyar tawa
zuwa Turkey, wanda ya hada da yadda tafiyar ta kasance a jirgin sama, da
muhimman wurare da na ziyarta, da abubuwan al’ajabi da na gani, da al’adun
mutanan kasar da na lura da su, da makamantansu. Amman labarin bai hada
da na ita kanta bitar ba, domin wannan sai wadanda aka yi dominsu, watau
dalibaina da za mu tattauna da su a aji.
Rubutun yana da gaba 23, zan rika jero gabobin gwargwadon yadda nake
fatan ba zai kosar da mai karantawa ba.
Ina fatan Allah Ta’ala ya sa a fa’idantu da rubutun.

1. Bayan dawainiyar neman bita ta gajeran zango (short course/workshop),


wanda na fara tun a Erbil, Kasar Iraqi, yayin da na je can a watan bakwai,
kamar yadda na ambata a shimfida, a karshe wanda na hadu da shi dan
Kasar Turkiyya, Mr Ammar, ya samo min abinda nake nema a London Elite
Center. Sun sama min bitar kwana biyar.
2. Daga nan sai dawainiyar neman visa, wacce ta dauki kusan wata guda, tare
da zuwa Abuja sau biyu.

Alhamdu lillahi, visa ta samu, Jami'a ta amince min ta biya duk kudin
dawainiyar da na sha. Haka kuma an biya min kudin bitar, an saya min tikitin
jirgi, Qatar airways, ba a da bayan kudin guzuri. Duk wannan ina so ne
matasa su san idan an yi hakuri, an yi aiki kamar yadda ya kamata, Allah
ya kan aiko da sakamako ta wasu hanyoyin daban daban, don haka ba sai sun
ci da zuci wajen bin wasu hanyoyi da ba su kamata ba.

3. A Ranar Juma'a 17/11/23 da misalin karfe 4.30 na yamma jirgi ya tashi


daga Kano zuwa Abuja, da ‘yan mutane kalilan, ya je Abuja inda aka cika shi
da fasinja. Wannan yana nuni da cewar akwai karancin matafiya daga Kano a
dalilin raunin tattalin arziki; a yayin da mafi yawan fasinjoijn Abuja suka
kasance ‘yan kudancin kasar; alamun cewar sun fi ‘yan Arewa karfin tattalin
arziki da yawan masu zirgazirga don kasuwanci ko neman ilimi. Muka bar
Abuja da misalin karfe 7.15 na yamma muka doshi Doha, babban birnin
Qatar.

4. Na yi sallar juma'a a gida kafin na kama hanyar Malam Aminu Kano


International Airport (MAKIA). Na yi sallar la'asar a MAKIA kafin mu shiga
jirgi. Na sallaci Magriba da Isha' a cikin jirgi, da yake tafiyar ta kai awa bakwai
da doriya daga Abuja zuwa Doha.

5. An raba kayan taba ka lashe a cikin jirgi, kafin daga bisani a ka raba
cikakken abincin dare. Shi ma dai mai kama da taba ka lashe din. Saboda
nau'ukan abincin sun kai hudu, banda ruwa da lemo da shayi.

6. Daya daga cikin abin sha'awa a tafiya a jirgin Qatar airways, da kuma na
sauran kasashen Musulmi, shine yadda kafin jirgi ya motsa za a saka kaset
(cassette) na adduar abin hawa: "Subihanalladhi sakkhara lana haza, wa ma
kunna lahu mukrineen, wa inna ila Rabbina la munqalibuun" (tsarki ya tabbata
ga wanda ya hore mana wannan abin hawan[shine Allah], wanda ba don Shi
ba da ba zamu samu ikon sarrafa shi ba, kuma ga Ubangijinmu [Allah] muke
komawa).
Sannan akwai na'ura mai kama da talabijun (television) a gabanka wadda
kake da zabin abin yi da ita. Ko ka kalli finafinan Turawa, masu nuna tashe-
tashen hankali, da ta'adi, da harbe-harben bindiga, da ire-iren rayuwar su ko
ka kalli kwallon kafa, ko ka rika kallon tafiyar jirgin, ana nuna maka wurare da
garuruwan da ake wucewa, da lokacin da ya rage muku isa garin da kuka
dosa, da yanayin sararin samaniya, da irin saurin da jirgin ya ke yi, da
makamantan bayanai da suke da alaqa da tafiyar jirgin. Ko kuma ka kunna
karatun al-Qur'ani, ka zabi Qari din da kake da bukatar karatunsa (akwai
Abdul-basid Abulsamad, da Khusari,Manshawi, da Aliyu Jabir, da sauransu,
kimanin makaranta 24), ga kuma shafin Qur'anin an bude maka, kana sauraro
(ta hanyar earpiece, na kusa da kai bai san me kake ji ba) kuma kana bin
bakin kana karantawa, ka zabi surar da kake bukata, daga Bakara har Nasi.
Don haka babu kai babu kosawa ko jin cewa ka bata lokaci, sai idan kai ka
zabi hakan. Allah ya nuna mana ranar da yan kasuwarmu masu harkar jirgin
sama za su sa a rika saka musu irin wannan addu'ar a jiragensu, da ma
talabijin din ta yadda za su baiwa fasinjoinsu damar sauraren karatun al-
Qur'ani, ko su ma sa rika samun kamasho.

7. Na koma kallon yadda tafiyar jirgi take yayin da aka sanar da cewar kowa
ya fara shiri za a sauka a kasa da minti arba'in (ya rage kimanin kilomita 458
a isa Qatar) a tafiyar 1030klm/hour. Kimanim karfe 1.00 na safe a Nigeria,
karfe 4.00 na safe a Qatar.

8. Jirginmu ya taba kasa da misalin karfe 4.30 na safe, a Doha. Na yi sallar


asuba, na nufi wurin shiga jirgi zuwa Istanbul.

9. Jirginmu na zuwa Istanbul ya tashi daga Hamad International Airport da


misalin karfe 8.00 na safe (daidai da karfe 5.00 na asuba a Nigeria). Mun
sauka a Istanbul da misalin karfe 12.00 na rana, tafiyar kimanin awa hudu.
Duk da tururuwar mutane a airport din, amman cikin kankanin lokaci aka
sallami kowa, saboda wadatar Ma’aikata da kayan aiki da kwarewar
ma’aikatan. Allah ya nuna mana ranar da za mu samu haka a kasarmu,
Najeriya!
10. Na sauka a masauki mai suna The Craton Hotel, wanda yake a tsakiyar
gari, guda daga cikin wuraren da suke da Otel Otel da kantinan zamani masu
yawa. Kuma anan ne wurin da aka yi bitar da ta kaini. Ana kiran sunan wajen
Şişli (Shishli).

11. Ranar Lahadi, 19/11/23, muka fita zuwa wani gari da ake kiransa Pendik (za
a iya kamanta shi da karamar hukuma, saboda a wurin yankasar kauye ne
wanda ake yin tattaki domin sayo kaya a sassaukan farashi. Amman dai a idona,
garin yafi Abuja kyau, da tsari, da tsafta, da yawan ginegine. Sai dai kada a
manta cewa Turkiyya sharkwatar Musulunci ce kimanin shekaru 600 zuwa 800 da
suka shude. Ma’ana kamar ka ce America ce ta wancan zamanin). Abin hawa uku
muka yi amfani da shi zuwa Pendik, da Bus mai tafiya a tsakiyar titi (metro bus),
da jirgin karkashin kasa (metro rail) da kuma Taxi. Tafiyar kuma ba ta wuce ta
minti 40 ba. Garin sai an tsallake ruwa mai suna Bosporous, wanda ya raba
Türkiye biyu, rabi a tsallaken Turai (Europe) inda Istanbul take, rabi kuma a
tsallaken Asia inda Pendik din take.

12. Ranar Litinin, 20/11/23, muka fara bitar da naje yi. Wanda ya jagoranci bitar
ana kiransa da suna Dr. Fadi Iboor, dan asalin kasar Syria amman ya kara da
karbar shaidar zama dan Kasa a Turkiyya. Yana da digirin digirgir guda biyu a
fannin Tsarin tattalin arziki a Musulunci da gudanar da mulki. Ya yi karance
karancensa a Syria, da Ingila da Turkey da America. Yana da kwarewa daidai
gwargwado, amman shima ya jinjinawa kwarin ilimin ‘yan Najeriya. Alhamdu
lillahi Rabbil alameen!

13. Bayan an tashi daga tattaunawa a rana ta farko, na dan yawata gari a inda
na shiga babban kantin zamani mai sunanTrump Towers. Tagwayen bene ne,
guda mai hawa 37, dayan kuma hawa 39. Gini guda yana dauke da ofisoshi,
guda kuma yana dauke da kantinan zamani (shopping malls) da dakunan
kwanan baki (hotels da gidajen haya). Na kara fahimtar dalilin da ya sa ‘yan jari
hujja suka yiwa Duniyar rikon kazar kuku!

14. Istanbul gari ne da ake gwagwarmaya tsakanin Muslunci da Turanci. Kimanin


kaso 95 a cikin 100 (95%) na al’umar suna cewa su Musulmi ne. Akwai
masallatai fiye da 3333, amman masu shiga masallacin su yi sallah kalilan ne.
Shigar mafi yawan mutanen irin ta Turawa ce. Ana dauka cewar duk matar da
aka gani da hijabi ko dai daga kauye take, ko bakuwa ce, ko kuma ‘yar zafin
addini ce. Masu shan taba suna da yawa. Wasu kuma har ma giya suna sha.
Shugaban Kasar, Recep Erdogan, yana matukar kokari wajen dawo da kimar
Musulunci. Alal misali, idan ya ga sharholiya ta yi yawa a wuri sai ya gina
katafaren Masallaci a wurin, sai masu sharholiyar su yi kaura. Idan wani ya nemi
lasisin bude gidan giya da gidan rawa, sai ya bashi lasisin (an fita hakkinsa na
dan Kasa), amman wasu al’umar za su kaiwa gwamnati kokensu na ba sa son
makwabtaka da gidajen giya; sai a janye lasisin; suma an fita hakkinsu na ‘Yan
Kasa. A yanzu haka yana nan yana kokarin yadda zai soke dokar da Ataturk ya yi
wacce ta haramta auren fiye da mace daya amman ta halatta ajiye dadiro komai
yawansu. Amman mafiya yawan ‘Yan Majalisar Kasar da mafi yawan mutanen
Kasar ba sa so. Don haka yana nan yana nazarin yadda zai kaucewa cin karo da
su, kuma ya dora su akan turbar da ta fiye musu alheri Duniya da Lahira. Ire-iren
wadannan dabarun da yake musu, na rage sharholiya, ya janyo masa bakin jini
ta yadda a zaben da ya gabata da kyar ya sha (51%). Haka kuma Turawa suna
nan sun saka shi a gaba, jifa jifa ana ta yunkurin hallaka shi ta hanyar bata-
garin ‘yan kasa.

15. Ranar Talata, 21/11/23, bayan tashi daga zaman bita na dan zagaya wasu
daga cikin manyan kantinan zamani (shopping malls) na kashe kwarkatar idona,
na dada ganin yadda rayuwar al-ummar take. Lallai Birnin Istambul a wannan
zamanin yana cike da al’umma masu al’adu mabanbanta. A waje guda ga masu
radin ‘yancin dan Adam na zabin yadda ya ke so ya zama. Don haka masu
kokarin chanza halitta gasunan a sarari; kaga namiji ya rikede, shi bai yarda ba
mace ne, wasu ma mazaje biyu su rika rungumar junansu, wai su mata da miji
ne. Wasu kuma mata ne biyu su rika sunbatar juna a bainar jama’a; wai nan
masoya ne wadanda watakila za su auri junansu, ko ma sun riga sun yi auren. A
waje guda kuma ga masu shiga ta kamala, yadda Musulunci ya bada umarni,
wani lokacin suna ganinka Musulmi su rangada maka sallama irin ta addinin
Musulunci. Lalai Imam Shafi’I ya fadi gaskiya da yace a cikin tafiya akwai faidoji
guda biyar; guda daga ciki shine sanin al’aldun mutane daban daban.

16. Ranar Laraba, 22/11/23, na shiga jirgin karkashin kasa zuwa muhimman
Masallatan nan guda biyu. Da Sultan Ahmet Mosque wanda aka fi ambata da
Blue Mosque (Shudin Masallaci, saboda shuwadan kayan gini harma da rufi da
aka yi amfani da su wajen gina Masallacin), a inda na yi raka’atanil masjid, da
kuma Aya-Sofya ( Hagyia Sophia) a inda na samu jam’in magriba na tashi na
sallaci isha’. Daman Masallatan a daura da juna suke,dan tattaki da bai wuce na
minti bakwai zuwa goma ba. Masallacin Ayasofya asalinsa Chochi ne, Daular
Usmaniya ta mayar da shi Masallaci, Kamal Attaturk ya hana salla a ciki,
ya mayar da shi gidan tarihi (Museum), Erdogan ya sake dawo da shi Masallaci.
Kusan gaba dayan unguwar tsohuwar fadar Sarakunan Daular Usmaniyya ne.
Amman yanzu akwai kantina masu yawa a wurin. Ga wanda ya taba zuwa aikin
hajji, wurin ya yi kama da wurare masu yawa wadanda Alhazan Najeriya suke
zuwa yin sayayya a Makka ko a Madina. Jirgi biyu na hau zuwa wajen, da na
karkashin kasa da na doron kasa. Haka kuma na yi amfani da damar na je gindin
ruwan Bosporous, har ma na dauki hoto a wajen. A gaskiya idan mutum ya dubi
yadda aka gina kasa, aka saita yadda ababan sufuri suka wadata, suke aiki babu
dare ba rana, da yadda wutar lantarki ta tsaya da kafarta, mutum zai san
shugabanci yana aiki a irin wadannan wurare. Lallai Bahaushe yayi gaskiya da
ya ce tafiya mabudin ilimi! Kuma shi ya sa Imam Shafi’i ya ambaci samun sabon
ilimi a matsayin daya daga cikin fa’idojin tafiya.

17. Ranar Juma’a, 24/11/23, mun tafi yawan bude ido a cikin tawagar wasu yan
yawan bude ido (Tourists), muka kama hanyar Bursa (Garin da Musulmi suka
fara mayarwa sharkwatar Daular Usmaniyya, kafin daga baya a mayar da ita
Istanbul). An zo har Hotel da nake an dauki wasunmu, aka je kamfanin motar da
ta dauke mu aka dauki sauran matafiya. Bursa a tsagin Asia take. Don haka an
wuce da mu ta kogin Bosporous, wanda na yi bayaninsa a baya. An isa wata
gaba ta kogin a inda muka shiga cikin jirgin ruwa har bus din tamu, aka tsallakar
da mu, muka dora da tafiya.

Ko da yake na taba shiga jirgin ruwa a Kasar Tanzania, daga Darussalam zuwa
Zanzibar, amman wannan karon abubuwa biyu sun kayatar da ni. Na daya shiga
cikin jirgin da motocin masu yawan bude ido, duk da cewa jirgin ba shirgege ne
irin wanda ya ke yin dogon zango a Teku ba. Sai kuma wasu tsuntsaye da suke
bin jirgin mutane suna jefa musu biredi da biscuits suna cafewa su yi kalaci.
Allah Mai iko!

Mun cigaba da tafiya a mota, jifa jifa ana shiga ta cikin duwatsun da aka rarake
aka yi hanyar mota (wadanda suka taba zuwa aikin Hajji za su iya tuna irin
wadannan, ana kiransu kuburi), guda daga ciki an yi tafiya a cikinsa mai tsawon
gaske. Na dada ganin muhimmancin wutar lantarki, domin da ita ne ake samar
da haske a cikin ramin, da ma iskar shaka.

Garin Bursa, shima babba ne, mai yawan bishiyar zaitun, da kamfanoni,
musamman na harhada mota (manufacture/assembly), ga yawan Masallatai, ga
tsabta. Wuraren ban sha’awa a Bursa sun hada da tsauni mai tsawon gaske, mai
tsananin sanyi irin wanda dussar kankara (snow) take sauka. An yi wuraren
hawa da sauka na mota mai tafiya a igiyar lantarki (cable cars).

Shima garin Bursa akwai Masallaci mai tsohon tarihi, ana kiransa da koren
masallaci (Green Mosque) saboda yadda aka yi masa kwalliya da koren fenti da
shimfudin salla masu koriyar kala. Na sallaci Magriba da Isha’ a Masallacin. Sai
dai abin takaici, Masallatan kalilan ne. Kuma tun da aka shigo da sallar bada
tazara da juna lokacin Korona har yanzu a haka suke yin sahun sallarsu. “Allah
Daya Gari banban!”

Gabadayan tafiyar mun shafe kimanin awa goma sha biyu (tun daga karfe 8.00
na safe sai kusan karfe 8.00 na dare muka dawo).

Wuraren cin abinci suna da yawa kuma ko’ina abincin halal ne. Haka kuma
al’ummu daban daban za suiya samun wurin da ake yin irin abincinsu. Amman
dai duk wanda ya taba zuwa aikin Hajji to zai ji kamar a Makka ko Madina yake;
ga wuraren abincin zamani (junk foods), ga kuma wuraren sayar da abincin
gargajiya. Don haka duk tsawon tafiyar babu wata damuwa game da abincin da
mutum zai ci.

Wani abin sha’awar kuma shine yadda ake da karfin network a Turkey. Duk
tsawon tafiyar nan, babu a inda service ya dauke. Idan mutum ya neme ni daga
Najeriya bai same ni ba sai dai idan daga Najeriya ya rasa service din. Sannan na
lura a kyauta na rika amsa kira daga Najeriya, har tsawon wasu kwanaki kafin a
fara caza ta. Amman duk yayin da na je Ghana ko Liberia da zarar an kirani daga
Najeriya nan da nan sai kudin wayata ya kare. Wannan yana nufin an saukaka
sadarwa tsakanin Africa da Kasashen Turai, amman an tsawwala a tsakanin
kasashen Africa. Wannan wani nau’in ne na mulkin mallaka. Wallahul musta’an!

Amman akwai babban abinda ya fi komai rashin dadi game da tafiyar a tare da
ni. Shine yadda a kullun nake bude tashar talabijin (Televsion) ta Al-Jazira ina
ganin yadda Kasar Yahudu ta Isra’ila take tafka ta’asa a Gaza. Tun ranar
7/10/2023, har izuwa makon da nake hado inawa-inawa zan baro Turkey
(kimanin wata guda da mako biyu) a kulla-yawmin sai Isra’ila ta rusa gidaje, da
makarantu, da asibitoci, da kasuwanni da sauran wuraren amfani na al’umar
Gaza. Ko a kwanakin da aka ware na tsagaita yakin, kasar Isra’ila ba ta tsagaita
gaba daya ba. Shugabannin Duniya kuma a kullun sai ‘yan jarida suke tarawa
suna bayani akan ya kamata Isra’ila ta tsagaita bude wuta haka. Kasashen Qatar
da Misra sun yi kokari sosai wajen tabbatar da yarjejeniyar tsagaita wuta na ‘yan
kwanaki domin taimakon Al’Umma. Shugaban Isra’ila, Natenyahu, sai tara ‘yan
jarida yake yi yana gurnanin cewa tsagaita bude wutar na iya kwanaki ne, yaki
zai cigaba sai ranar da sojojin Isra’ila suka kakkabe ‘yan Hamas daga doron kasa!
Abin akwai takaici ainun, kaga wanda za su iya tabuka wani abu sun ki yin
komai, kamar kace “ko a jikinsu”; wadanda kuma suke fama da jin takaici su
kuma ba za su iya yin komai ba! Allah ka zama gatan masu rauni.

Duk da cewar a tsakani an dan samu labarin faranta rai na ‘yanto Falasdinawa da
suke garkame a kurkukun Israel akan laifuka kamar kama mutum yana tuka
mota kusa da sojojin Isra’ila, shikenan sai a gurfanar da shi a yanke masa
hukuncin shekara takwas ko goma. Kuma fa kusan a kullun sai an sami wani da
irin wannan laifin an yanke masa makamancin wannan hukuncin. Idan al’umma
ta rasa kungiya irin ta Hamas wacce jifa jifa za ta yi kukan kura ta gwada
kubutar da wannan al’umar daga makamanci kaskanci irin wanda Falasdinawa
suke ciki, ko yaya sauran al’umar Duniya za ta kalli wannan al’ummar, ni ban
sani ba! Allah ya taimaki ‘yan Falasdinu a wannan al’amari.

18. Ranar Asabar, 25/11/23, ban yi yawo sosai ba na baiwa kaina hutu, na kintsa
‘yan komatsaina, na daure su, domin shirin komowa gida washegari. Sai kuma
wayoyi da WhatsApp calls dana sha yi.
19. Ranar Lahadi, 26/11/23, na yi sallama da mutanan gari na isa tashar jirgin
sama (airport) da wuri. Na je wajen karbar tikitin hawa jirgi (boarding pass) sai
akace min jakunkunana guda biyu daya tafi daya nauyi. Aka ce na je na rage
kayan cikin guda na mayar cikin dayar. Ko da na tafi yin hakan na dawo sai na
taras sun rufe kanta, ma’ana nayi “missing flight” kenan. Don dole na nemi wani
jirgin, wannan karon na Saudia, na biya na kara kwana guda. Wannan kwanan
ya hada harda sake komawa cikin gari da neman otel da sake dawowa filin jirgi
washegari. Yana da kyau matafiyi ya tabbatar ya tanadi isasshen guzuri har
dawowarsa gida ko da makamancin hali irin wannan yaka same shi. Ni kam,
Allah ya kiyaye ni, saura kuma ni da Qatar Airways. Na tattara hujjojina zan
tinkaresu naga yadda zata kaya tsakanina da su!

20. Ranar Litinin, 27/11/23, na sake dawowa filin jirgin sama an Istanbul. Jirgin
Saudi ya daga da mu da misalin karfe shadaya na dare. Da misalin karfe 2.10 na
dare aka bada sanarwar karshe ta kowa ya daura damararsa (belt) za a sauka a
Jidda, kuma tun sannan na fara gano hasken garin, shima iya ganin mutum, duk
da cewar kasar a shimfide take babu hawa da sauka kamar na Istanbul. Abin
gwanin sha’awa, kamar na dauko hoton garin na saka a labarina. Zuciyata ta ce
“yanzu fa da yawa daga cikin shugabannin Najeriya suna ta zuwa wuraren nan
suna ganin yadda wutar lantarki ta wadata, amman sun gaza samar mana da ita
a kasarmu; Allah ka shirya!!!” mun taba kasa da karfe 2.20 na safe. Zuciya ta ce
“ina ma lokaci zai bayu na karasa na yi umrah; Allah ka kawo dama.” Alhamdu
lillahi na yi aikin hajji biyu, na yi umrah biyu. Allah ya baiwa duk mai niyya ikon
zuwa yin wannan ibada.

21. Na nemi wurin yin sallah a aiport na kishingidar da ba ta wuce awa biyu ba,
aka yi kiran sallar asuba. Bayan idar da sallah na nemi wurin jiran shiga jirgin
(gate 22a&b). Anan muka hadu da masu dawowa daga umrah da wasu da suka
dawo daga wasu kasahen kamar su India da sauran inda ake zuwa asibiti. Da
misalin karfe 7.05 na safe aka duro mu cikin jirgi mai tahowa Kano. Wani abin
sha’awar da ban taba gani ba a kowane jirgin sama, a dan yawatawar da na yi,
shine a jirgin Saudia an tanadi wani dan sarari domin yin sallah idan ta kama ana
tafe. Watau a can bayan jirgin aka cire kujeru kamar layi uku, aka kewaye wurin
da labule, aka saka kafet din yin sallah. A yadda na lura, kimanin mutum shida
za su iya yin sahu biyu na bakwai dinsu ya jagorancesu sallah. Ina ma dai duk
kasashen Musulmi za su yiwa fasinjoijnsu irin wannan gatan. Su kuma fasinjojin
Musulmi surika fifita hawa jirgin da yake da wurin sallah! Da kuwa da sannu duk
jiragen da suka san suna yawan daukar fasinja Musulmi sai sun samar da irin
wannan tsarin. Da kuwa an hutar da fasinja yin sallah a zaune idan lokacinta
yayi.

22. Allah ya saukemu a Kano lafiya, da misalin karfe 11.00 na safe. Tun lokacin
da na yi tafiya zuwa Iraqi na lura sashen tashi da saukar jiragen kasa-da-kasa
(international wing) na filin jirgi na Malam Aminu Kano ya yi kyau, kamar na
sauran kasashen duniya. Kwas kwas da shi. Ma’aikata sun wadata kuma suna
mu’amala mai kyau. Sai dai fa wata sanarwa da take yiwa mutane maraba da
shigowa Najeriya kuma ana baiwa mutane hakuri cewa akwai ‘yan matsaloli na
rashin wutar lantarki, har yanzu tana nan, fiye da wata hudu. Da har na fara
tunanin neman wani ma’akacin na ce me ya sa ba za a cire sanarwar nan ba, har
yanzu matsalar ba ta kau ba ne? Kwatsam sai aka dauke wuta! Nace shikenan ga
amsar tambayar da zan yi nan ta samu. Wannan wani ala’amari ne idan mutum
ya bar gida har mantawa yake yi cewa wai wutar lantarki ta kan yi rawa. Muna
jaddada kira ga shugabanni da su yiwa Allah su mayar da hankali wajen samar
da wutar nan.

23. A takaice, ziyarata zuwa Turkey ta nuna min yadda shugabanci yake aiki. A
shekara ta 2000 jam’iyyar Erdogan (the Justice Party) ta samu mulki, shekara
guda kenan bayan dawowar mulkin farar hula a Najeriya. Amman a tsawon
shekaru ashirin da doriya sun magance manya-manyan matsalolin da suke
damun kasar: ilimi ya inganta (daga kasancewa mafi koma baya a nahiyar Turai
zuwa guda daga cikin inda ya fi inganci a nahiyar); sufuri ya inganta (daga
matsayin koma-baya a nahiyar Turai zuwa guda daga cikin wadanda suka fi
inganci); haka labarin ya ke a tsabtar mahalli, daga komabaya zuwa abinda yafi
kyau. An yaki yunwa; an samarwa da matasa aikin yi; ana ta faman yaki da
tabarbarewar tarbiyya a cikin nasara. Tsabtataccen ruwa wadatacce ya samu;
wutar lantarki ta tsaya tsai! Da sauran nasarori masu tarin yawa. Duk a dalilin
shugabanci nagari da aka dace da shi.

Misali daya tal daga cikin nagartar shugabancin Erdogan shine yadda ya ki kulle
kasar gaba daya a lokacin annobar Korona. Abinda ya yi shine ya nemi kowace
ma’aikata ta zauna da ma’aikatanta su shawarta yadda za su rika yin aiki a
lokacin Korona. Sai wasu suka ce za su rage kwanakin aiki; wasu suka ce za su
rage awannin aiki; wasu kuma suka ce za su rika aiki daga gida; wasu ma cewa
suka yi za su yi aiki kamar koda yaushe abinda kawai suke bukata a wadatasu da
kayan kariya, kuma aka wadatasu din. Lokaci kalilan sai sauran kasashen Turai
suka matsu da wasu abubuwan larura da sai a Turkey kadai za su iya samu, don
haka sai Turkey ta yi ta chaba ciniki baki alaikum! Allah ka azurta Najeriya da irin
wannan shugabancin.

KAMMALAWA: Bahaushe yana cewa “na zaune bai ga gari ba!” kuma yace
“tafiya mabudin ilimi!” A koda yaushe mutum ya yi tafiya sai ya dace da daya ko
biyu daga cikin fa’idojin da Imam shafi’I ya ambata a baitinsa. Yake cewa, “ka yi
tafiya, domin a cikin tafiya akwai fa’idoji biyar: (1) zaka huta da kwaramniyar yau
da kullun, (2) zaka samu wani abin duniya, (3) zaka samu wani sabon ilimi (4)
zaka san al’adun mutane daban-daban, da (5) zaka iya dacewa da wani abokin
da zai amfaneka a rayuwa. A tafiyata zuwa Istanbul ta kasar Turkey na dace da
samun duka biyar din.
Alhamdu lillahi Rabbil Alameen!

A karshe ina fatan mai karatu ya sani cewar tafiya irin wannan tana da dadi ne
idan an yita ta halastacciyar hanya. Amman idan mutum ya yita ta hanyar da
muke jin labari game da bakin-haure, to ya sani zai sha wulakanci. Wasu daga
cikin ‘yan Kasar akwaisu da kyamar baki, ga kuma jami’an tsaro masu kama da
zabaniyawa! Don haka mafi alheri shine mutum ya je inda zai je ta halastacciyar
hanya, yayi abinda zai yi na halaliya, da zarar ya kammala ya dawo gida; ciki-
lafiya, baka-lafiya. Ya yi hakuri da halin da muke ciki a kasarmu (Nigeria) har
zuwa lokacin da Allah zai yaye mana abubuwan da muke kuka da su. Bahaushe
yace “guntun gatarinka ya fi sari-ka-bani”!

Allah Ta’ala ya agaza mana.

Ina godiya da addu’o’in da wadanda suke bibiyata suka yi min. Na amsa wasu
daga cikin tambayoyin da suke neman Karin bayani. Kuma na yi liking comments
da yawa. Amman dai ina godiya ga kowa da kowa.

Wadansu kuma sun nemi karin bayani akan wasu abubuwan da na riga na san
suna cikin rubutun. Ina fatan sun gamsu da iya abinda ya sawwaka.

Ina rokon Allah (SWT) ya amfanemu gaba daya game da wannan rubutun.

Wassalamu alaikum wa rahmatullah.

You might also like