You are on page 1of 3

1.

Hukumomin agaji a Mozambique sun ce dubban mutane sun rasa muhallansu sakamakon
guguwar Eloise da ta ratsa kasar a karshen mako. Rahotanni sun ce guguwar dake gudun kilomita
150 kowacce sa’a, dauke kuma da ruwan sama, ta afkawa birnin Beira dake gabar ruwa, abinda yayi
sanadin raba mutane akalla dubu 7 da gidajensu, yayin da gidaje sama da dubu 5 suka
rushe.Hukumar agajin gaggawa tace mutane 6 sun mutu a hadarin, kana wasu 12 sun jikkata.
Shekaru biyu da suka gabata dai guguwar Idai ta tafka mummunar barna a garin na Beira dake gabar
ruwa, inda ta salwantar da rayukan mutane da dama da kuma janyo hasarar dimbin dukiya.

2. Jami'an agaji a Mozambique sun dukufa wajen aikin ceto, bayan da kakkarfar guguwa dauke da
ruwan sama ta afkawa birnin Beira dake gabar teku. Kawo yanzu babu rahoton hasarar rai, sai dai
rusa gine-gine da dama da guguwar tayi wadda masana suka wa lakabi da Eloise.Masana yanayi sun
ce guguwar na tsala gudun kilomita 160 a sa’a 1. Shekaru biyu da suka gabata dai guguwar Idai ta
tafka mummunar barna a garin na Beira dake gabar ruwa, inda ta salwantar da rayukan mutane da
dama da kuma janyo hasarar dimbin dukiya.

3. A Najeriya,Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle ya zargin wasu shugabanin al’umat da suka


hada da sarakuna da yiwa shirin samar da zaman lafiya da tsaro a yankin kafar ungulu. Gwamna
Matawalle ya fadi haka ne yayin wani taro da shugabanin rundunonin tsaro na yankin ranar alhamis
da ta gabata. Gwamnan Zamfara a fusace ya kalubalanci sanarwar shugaban majalisar sarakunan
galgajiya, daga cikin hukumomin galgajiyar yankin, sarkin Anka da ya bukaci hukumomi sun baiwa
jama’a damar mallakar bindigogi don kare kan su, ganin gwamnati ta kasa shawo kan wannan
matsalla. A karshe gwamna Matawalle ya ce lamarin tsaro ya tabarbare a yankin ga baki daya da ma
wasu yankunan Najeriya, to aman nauyi ya rataya wuyan kowane daga cikin mazauna kauyuka da
birni da kuma ya dace sun dafawa jami’in tsaro da bayyanai a duk kowane lokaci.

4. Gwamnatin Faransa tace ya zuwa yanzu ta yiwa mutanen kasar sama da miliyan guda rigakafin
cutar korona, kusan wata guda da fara aikin bada allurar. Fira ministan kasar Jean Castex ya sanar
da adadin, a yayin da yake godewa daukacin wadanda suka bada gudummawa wajen samun nasarar
aikin, da suka hada da ma’aikatan aikin lafiya da zababbun wakilai da cibiyoyin kula da lafiyar. Castex
yace gwamnati ta sanya sharadin yiwa jama’a miliyan guda rigakafin kafin karshen wannan wata,
miliyan 15 kuma nań da karshen watan Yuni. Hukumar lafiyar kasar tace za’a bada tazarar yiwa
jama’a allurar ta farko da ta biyu da makwanni 6 maimakon makwanni biyu zuwa uku da aka shirya a
farko.

5. A jiya lahadi ne aka yi jana’izar mutane 100 wadanda ‘yan bindiga suka kashe a kauyuka biyu
dake jihar Tilaberi dake Janhuriyar Nijar, bisa jagorancin Firaministan kasar Birji Rafini. Salissou
Issa ya tuntubi Gwamnan jihar Tilaberi Ibrahim Tijjani Kachalla don jin yadda suka ji da wannan rashi.
Jamhuriyar Nijar na daya daga cikin kasashen Sahel da mayakan jihadi ke cin karnen su ba
babaka,wadanan hare-hare na zuwa ne a wani lokaci da aka kamala zaben shugaban kasa da na yan
Majalisu, ta bangaren zaben shugaban kasa,hukumar zaben kasar ta fitar da sakamako da ke
tabbatar da cewa dan takara Bazoum Mohammed na jam’iyya mai mulkin kasar PNDS zai haduwa da
Mahamanne Ousmane daga bangaren RDR Canji a zagaye na biyu a cikin watan fabrairu . Tsaro na
daga cikin manyan kalubalen da sabon Shugaban kasar ta Nijar mutumen da zai maye gurbi Issifou
Mahamadou a wannan kujera zai yi kokari dawo da shi a kasar.

6. Gwamnatin Ondo ta soma yiwa Fulani makiyaya rijista da nufin kawo karshen zaman da
batagarin cikinsu ke yi a gandayen dajin jihar. Matakin ya zo ne a yayin da gwamnatin ta Ondo ta
gana da tawarorinta na jihohin Yammacin Najeriya, Jigawa da Kebbi, shugabannin Fulani, da kuma
manyan jami’an tsaro a garin Akure. Dukkanin bangarorin sun tattauna ne kan matsalolin da suka
biyo bayan matakin gwamnan jihar ta Ondo Rotimi Akeredolu na baiwa Fulani umurnin ficewa daga
Jihar cikin kwanaki 7.Daga karshe taron ya cimma matsayar kai zuciya nesa da daukar matakin yin
rijista ga duk wani makiyayi dake son kiwo a gandayen dajin jihar ta Ondo, tare da goyon bayan
umarnin ficewar makiyayn dake zaune a dazukan ba bisa ka’ida ba.Cikin wata sanarwa a jiya litinin,
gwamna Akeredolu ya musanta korar Fulani daga jiharsa, inda yace umarnin su fice daga gandayen
gwamnati da suke zaune ba bisa ka’ida ba yayi kawai amma aka yi masa mummunar fahimta.
Gwamnan yace ya dauki matakin ne domin kawo karshen matsalolin tsaron da ake zargin Fulanin
makiyaya da haddasawa a yankin.

7. Yau gwamnonin yammacin Najeriya ke gudanar da wani taro da shugabannin kungiyar Fulani
makiyaya sakamakon tankiyar da ta biyo bayan umurnin ficewar su daga Jihar Ondo kamar yadda
Gwamnatin Jihar ta basu umurni cikin mako guda. Rahotanni sun ce yanzu haka shugabannin
kungiyar Miyetti Allah sun isa Akure domin halartar taron wanda zai samu halartar Gwamnonin
Jigawa da Kebbi da kumą kwamishinonin Yan Sandan dake Yammacin Najeriya. Sakatare Janar na
kungiyar Meyetti Allah Baba Usman Ngelzerma ya tabbatarwa RFI Hausa isar su Akure yammacin
jiya, domin halartar taron.Umurnin da aka Aiwa Fulanin na ficewa daga Jihar Ondo da kuma harin da
aka Aiwa Sarkin Fulani a Jihar Oyo sun tada hankalin jama’a inda aka dinga samun musayar zafafan
kalaman dake iya raba kań jama'a’r Najeriya.

8. Kungiyoyin Falasdinawa biyu da suka hada da Fatah mai iko da Gabar Yamma da Kogin Jordan,
da Hamas dake iko da Gaza, sun bayyana shirin gudanar da wani taro a birnin Alkahira wannan
makon domin tattauna matsalolin dake yiwa shirin zaben su barazana. Shugaban Falasdinawa
Mahmud Abbas ya sanya ranar 22 ga watan Mayu mai zuwa a matsayin ranar zaben 'Yan Majalisu,
yayin da za’a gudanar da zaben shugaban kasa ranar 31 ga watan Yuli, kuma shine irin sa na farko
tun wanda akayi a shekarar 2006. Zaben baya da akayi ya nuna yadda kungiyar Hamas ta samu
gagarumar rinjaye a zaben 'Yan Majalisu, sakamakon da Fatah taki amincewa da shi. Masana na
cewa rashin hadin kan bangarorin biyu na daga cikin matsalolin dake dakushe kimar fafutukar da
suke yin a kafa kasar Falasdinu.

9. Asusun Bunkasa noma na Majalisar Dinkin Duniya, IFAD da Gwamnatin Najeriya na wani aikin
hadin gwuiwa da zummar ganin sun taimakawa kananan manoma da masu aikin samar da abinci a
Yankin Arewacin Najeriya domin farfadowa daga illar cutar korona. IFAD ta bada kashi na farko na
tallafin Dala 900,000 ta hannun shirin ta na taimakawa mazauna karkara domin rarrabawa irin
wadannan manoma domin sake farfadowa daga matsalolin da suka samu kan su a ciki. Yarjejeniyar
bada wannan taimako ya samu sanya hannu ministar kudin Najeriya Zainab Shamsuna Ahmed da
Daraktan IFAD dake kula da Afirka ta Yamma da Afirka ta Tsakiya Nadine Gbossa domin ganin
mazauna Jihohin Borno da Yobe da Jigawa da Katsina da Kebbi da Sokoto da Yobe da kuma Zamfara
sun amfana. A karkashin jagorancin ma’aikatar kula da ayyukan noma ta Najeriya kananan manoma
sama da 8,000 ake saran suci gajiyar wannan shirin wanda zai rage radadin matsalolin da suke
fuskanta sakamakon sauyin yanayi da annobar korona. Ministan kula da ayyukan noma Alh
Mohammed Sabo Nanono ya bayyana farin cikin gwamnatin Najeriya dangane da wannan taimako
da IFAD ya gabatar wanda yace zai taimaka gaya wajen rage radadin da wadannan manoma ke
fuskanta. Nanono yace gwamnati zata sayi tan 80 na irin masara da shinkafa da kayan marmari da
tan 722 na takin zamani domin rabawa kananan manoman. Ministan ya bayyana cewar kashi 50 na
manoman da zasu amfana da wannan tallafi mata ne, kashi 25 maza sai kuma matasa da zasu kai
kashi 25. Daraktan Hukumar IFAD Nadine Gbossa yace a shirye suke wajen ganin mata da matasa sun
amfana da shirin da ya kaddamar na basu tallafi. Daga shekarar 1985 zuwa yanzu, IFAD ta dauki
nauyin ayyuka daban daban har kasha 11 a Najeriya da kudin su ya kai kusan Dala miliyan 115, cikin
su harda Dala miliyan 510 na tsabar kudin da aka rabawa mazauna karkara miliyan 3 da dubu 900 a
Najeriya.

10. Gwamnatin India ta kaddamar da soma yiwa al’ummar kasar allurar rigakafin cutar Korona,
inda ta fara daga kan ma’aikatan lafiya. Hukumomin kasar ta India dai na fatan yiwa mutane miliyan
300 allurar rigakafin cutar ta Korona, kusan adadin daukacin al’ummar Amurka, abinda ya sa shirin
zama mafi girma a duniya. Daga cikin ‘yan Indian miliyan 300 da hukumomin lafiyar kasar ke fatan
yiwa allurar rigakafin, akwai kananan yara miliyan 26, likitoci da sauran ma’aikatan lafiya miliyan 30,
sai kuma sauran mutane miliyan 270 da shekarunsu suka fara 50 zuwa sama, ko kuma wadanda ke
fama da wasu cutukan da ka iya baiwa annobar ta Korona damar tagayyara su.Yawan al’ummar kasar
India ya kai biliyan 1 da kusan miliyan 400, kawo yanzu kuma akalla ‘yan kasar dubu 152 annobar
korona ta halaka daga cikin sama da miliyan 10 da suka kamu. Ranar 4 ga watan Janairu ma’aikatar
lafiyar India ta amince da inganci alluran rigakafin da hadin gwiwar jami’ar Oxford da kamfanin
AstraZaneca, sai kuma allurar da kamfanin kasar na Bharat Biotech ya samar.

You might also like