You are on page 1of 3

1.

Kocin Super Eagles ta Najeriya Gernot Rohr ya ce babu wani sabon dan wasa da zai gayyata don
wasan neman tikitin shiga gasar cin Kofin Afirka na 2021 da tawagar za ta kara da jamhuriyar Benin da
kuma Lesotho. Da yake hira da manema labararai kuma a ka watsa a shafin YouTube na kungiyar, bayan
dawowarsa Najeriya ranar Litinin, Rohr ya karyata rahotannin kafofin yada labarai na cewa FIFA ta baiwa
wasu sabbin ‘yan wasa izinin buga wa Najeriya kwallo. Kocin dan kasar Fransa da Jamus ya dage kan
cewa yana da kwararrun 'yan wasa a hannun sa kuma ba zai yi tunanin kawo wani sabon dan wasa ba a
yanzu, yayin da' yan wasan ke shirin wasan karshe na wasan neman cancantar shiga gasar cin kofin
kasashen Afirka ta 2021. Super Eagles, wadanda ke saman teburin rukunin L da maki takwas a wasanni
hudu, za ta kara da Benin a waje ranar 22 ga watan Maris, kafin ta karbi bakuncin Lesotho 30 ga watan
Maris.

2. A Jamhuriyar Nijar,kotun fasalta kudin tsarin mulkin kasar ta fitar da sakamakon zaben farko na
watan Disemba shekarar da ta shude, inda ta bayyana cewa yan takara Bazoum Mohammed daga
jam’iyya mai mulki PNDS da Mahamane Ousmane daga jam’iyyar RDR Canji. Kotun fasalta kudin tsarin
mulkin kasar ta Nijar ta yi watsi da akasarin karar da jam’iyyun siyasar kasar suka shiga na cewa an tafka
magudi yayin zaben shugaban kasa zagayen farko. A cewar jami’an kotun dan takara Bazoum Mohamed
daga PNDS ya samu kashi 39,67% na kuri’u da aka kada,yayinda Mahamane Ousmane ya tashi da kusan
kashi 16,99% kuri’u da aka kada.

3. Shugaban Amurka Joe Biden ya ce, ba zai janye takunkuman da ke kan Iran ba muddin ta ci gaba da
karya ka’idojin yarjejeniyar nukiliyar da ta cimma da manyan kasashen duniya. A lokacin da aka
tambayi Biden a yayin wata hira da kafar CBS kan ko zai dakatar da takunkuman da aka kakaba wa Iran
domin shawo kan kasar don ganin ta dawo teburin tattaunawa, sai ya kada baki ya ce, A ‘a. Sai dai
shugaban na Amurka ya nuna cewa, za su samu jituwa da Iran da zarar kasar ta daina habbaka
makamashin Uraniun dinta. Sai dai a jiya Lahadi, shugaban juyin juya halin Musuluncin Iran, Ayatollah Ali
Khamenei ya ce, dole Amurka ta fara janye daukacin takunkuman kafin ita kasar ta koma mutunta
ka’idojin da aka shimfida mata. Yarjejeniyar ta nukiliyar Iran ta fara tangal-tangal ne tun dai lokacin da
tsohon shuagaba Donald Trump ya janye Amurka daga cikinta a 2018, yayin da kuma. Amurkar ta sake
laftawa Tehran takunkumi. Shekara guda bayan matakin na Trump, Iran ta jingine mutunta ka’idojin
yarjejeniyar ta nukiliyar da aka cimma a shekarar 2015. Tuni gwamnatin Biden ta bayyana aniyarta ta
sake shigar da Amurka cikin yarjejeniyar , amma ta hakikance cewa, sai fa Tehran ta ci gaba da mutunta
ka’idojin.

4. Jami’an agaji a China sun samu nasarar ceto mutane 11 daga cikin masu hakar ma’adanai 22 da
suka shafe akalla makwanni 2 makale a ramin da suke aiki, dake gabashin kasar. Gidan talabijin dan
kasar China ta nuno yadda aka ceto mutun na farko cikin ramin sanya da bakin Kellen baiwa ido kariya
da sanyin safiyar yau. Bayanai sun ce an gano mutum na farko da aka ceto ne shi kadai a wani bangaren
ramin hakar ma’adanan. Tun ranar 10 ga watan Janairun da muke ciki, mahakan ke makale a ramin
hakar ma’adanai na Hushan mai zurfin daruruwan mitoci dake lardin Shandong.

5. Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince da murabus din daukacin manyan hafsoshin
sojin kasar inda ya maye gurbin su da wasu sabbi. Sanarwar da mai ba shi shawara a fannin yada labarai
Femi Adeshina ya raba wa manema labarai ta ce, Buhari ya amince da nadin Manjo Janar Leo Irabor a
matsayin Hafsan Hafsoshin tsaro, yayın da Manjo Janar Ibrahim Attahiru ya zama shugaban sojin kasa,
sai kuma Rear Admiral A.Z. Gambo a matsayin shugaban sojin ruwa tare da Air Marshall I.O Amao a
matsayin shugaban sojin sama.Wadannan hafsoshin za su maye gurbin Janar Abayomi Olonisakin da
Janar Yusuf Tukur Buratai da Air Marshal Abubakar Sadiq da kuma Vice Admirał Ibok Ekwe Ibas.
Shugaban kasar ya taya sabbin hafsoshin murna, yayın da ya gode wa wadanda suka yi ritaya.

6. Burnley ta kawo karshen wasanni 68 da Liverpool da buga Anfield ba ayi nasara a kanta ba. Wasanni
68 da Liverpool tayi na Premier ba a doke ta ba a Anfield ya zo karshe ne, bayan da Burnley ta doke ta da
ci 1-0 a wasansu na daren Alhamis. Wannan na nufin cewa, tawagan Jurgen Klopp sun gaza yin nasara a
wasanni biyar da suka buga a jere, lamarin da ke neman ruguza damar kare kabbinsu, ganin cewa ratar
maki shida ke tsakanin su da Manchester United dake jan ragamar teburin, a matsayi na hudu. Rabon
Liverpool ta dandana shan kashi a Anfield tun a watan Afrelun shekarar 2017.

7. Hukumomin kasashe sun soma sake daukar matakan rufe iyakokinsu don dakile barazanar annobar
coronavirus da taki yiwa duniya sassauci wajen lakume rayuka gami da bazuwa tamkar wutar daji. Yau
Litinin Amurka ta tabi sawun Faransa, Isra’ila da kuma Sweden da suka rufe iyakokinsu ga matafiya daga
Birtaniya, Brazil, Ireland da kuma wasu karin kasashen Turai da dama, saboda dakile yaduwar sabon
nau’in cutar Korona da ya soma bayyana a Afrika ta Kudu da kuma Birtaniya. Tsaurara matakan yaki da
Koronar dai na zuwa ne bayan da shugaban kasar Mexico Andres Manuel Obrador ya zama fitaccen
mutum da a baya bayan nan, ya kamu da cutar. A birnin Washington, shugaban Amurka Joe Biden ya
sake rufe iyaka ga matafiyan da ba ‘yan asalin kasar ba, daga kasashen Brazil, Birtaniya, Ireland da kuma
Afrika ta Kudu, bayan da a makon jiya ya kafa dokar tilasatawa Amurkawa sanya takunkumin rufe baki
da hanci. Kawo yanzu annobar Korona ta halaka mutane sama da miliyan 2 da dubu 100, daga cikin
kusan miliyan 99 da suka kamu da cutar a fadin duniya, annobar kuma tafi ta’adi a Amurka bayan halaka
sama da mutane dubu 400 a kasar kadai, daga cikin sama da miliyan 25 da suka kamu.

8. Birtaniya ta dakatar da zirga zirga tsakaninta da wasu kasashen Afrika 11, haramcin da tace zai
wanzu tsawon makwanni 2. Cikin sanarwar da ta wallafa a shafinta, gwamnatin Birtaniyar tace ta dauki
matakin ne don dakile cigaba da yaduwar sabon nau’in cutar coronavirus da ya samo asali daga Afrika ta
Kudu. Kasashen da Birtaniya ta haramtawa ‘yan kasar shiga cikinta dai dukkaninsu na kudancin nahiyar
Afrika ne, da suka hada da Nambia, Zimbabwe, Zambia, Malawi, Angola, Lesotho, Eswatini, Bostwana,
Maurituis, Seychelles da kuma Mozambique, ba ya ga Afrika ta Kudu da tuni ta dakatar da zirga-zirga
tsakaninsu. Akaluman ma’aikatar lafiyar Birtaniya a ranar Juma’a sun nuna cewar akalla mutane dubu 1
da 325 annobar coronavirus ta halaka a kasar cikin sa’o’I 24, adadi mafi muni da kasar ta gani tun bayan
bullar cutar cikin kasar sama da shekara guda.

9. Hukumomin kasa da kasa sun kara azama wajen aiwatar da shirin yiwa jama’a allurar rigakafin
cutar coronavirus a sassan duniya, a yayin da kamfanin magunguna na BioNTech ya shirya samar da
karin miliyoyin sunkin maganin annobar ta Korona. Ranar Litinin kamfanin na BioNTech yayi bazata
wajen bayyana shirinsa na samar da alluran rigakafin cutar coronavirus akalla biliyan 2 a cikin wannan
shekara ta 2021, a maimakon alluran rigakafin biliyan 1 da miliyan 300 da yayi alkawarin samarwa a
karashen shekarar bara. Birtaniya ce kasa ta farko data soma amincewa da alluran na hadin gwiwar
kamfanonin BioNTech da Pfizer, kafin daga bisani ta amince da karin magungunan kamfanin Moderna da
kuma na hadin gwiwar AstraZaneca da jami’ar Oxford. Kawo yanzu dai kusan mutane miliyan 2 cutar
Coronavirus ta halaka a sassan duniya, shekara guda bayan bullarta.

10. Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana cewar har yanzu maganin rigakafin AstraZeneca na da tasiri
wajen yaki da cutar Korona a duniya, bayan da Afirka ta kudu ta jinkirta fara amfani da shi sakamakon
rahotan binciken masana kan sahihancinsa. Ministan lafiya kasar ta Afrika ta Kudu Zwelli Mkhize, yace
dakatar da fara amfani da allurar na wucin gadi ne, domin bada damar tattauna wasu batutuwa, bayan
da kasar ta karbi allura miliyan guda da rabi daga kamfanin. Kamfanin Astrazeneca yace har yanzu yana
kan bakansa dangane da tasirin maganin, wanda yace zai kare lafiyar masu dauke da wannan cuta. A jiya
Litinin kwararrun hukumar lafiya ta duniya suka gudanar ta taron tantance ingancin allurar rigakafin
cutar Korona da hadin gwiwar kamfanin AstraZeneca da jami’ar Oxford ya samar, sakamakon shakkun da
ke karuwa kan ingancinsa a tsakanin wasu kasashe.

You might also like