You are on page 1of 159

🌈🌈🌈

🌈🌈
🌈
*𝗕𝗔𝗕𝗕𝗔𝗡 𝗬𝗔𝗬𝗔*
𝚁𝚎𝚗𝚎𝚠

Story & written by


*FATIMA AMINU*
*Ummu Saddi'q*

1️⃣
chapter

"Wayyo Aunty Mamana! wayyo Aunty Mamana!! wayyo Aunty Mamana!!! za a kashe miki ni
dan Allah Babban Yaya kayi haƙuri",belt ɗin hannun shi yaƙara naɗawa yana ɗagawa
sama aka riƙe,ƙanƙame ido nayi amma naji shiru a hankali na buɗe ɗaya a kanne naga
Aunty Mama,sutalewa nayi na miƙe ta bayanta na ƙanƙameta na saki kukan ƙarya"kai
yanzu Habib miye abin duka jikin Nana kalli yanda ka naɗa belt kamar zaka daki
Saddiq ko Ashiru",ajiyar zuciya ya yi yana lumshe kyawawan idanuwan sa akaina ya
buɗesu dan yana ganina ina kallonsa duk da na ɓoye kaina"Aunty Mama kinsan me
yarinyar nan takeyi alayi,sun fa taso islamiya wai ta tsayawa koyawa wasu yara rawa
a kan hanya","kaii Babban Yaya"na faɗa ina tsaida kukan iskancin dana ke"ƙarya nayi
kenan","a a ni bance ka gilla ba kawai dai ka gyara zancenka kace Dj ake na tsaya
koya musu dan basu iya ba",dariya ce ta kama Aunty Mama"amma dai kasan Nana
yarinyace ko ai ba dukanta zakayi ba faɗa zaka mata","haba Aunty Mama shekara sha
ɗaya ne yarinya kullum ana taɓata kice yarinta sai yaushe zata girma","zata girma
mana nan gaba kaɗan",maida belt ɗinsa jikinsa yake yace"ma gani ai girman wannan ai
akwai matsala ciki","ba wata matsala kai dai jeka",yana fita na fito a bayanta
kunne na ta kama ta murɗe"kinga Nana kiyi a hankali da Yayanku wataran zai yanka
miki dukan da zaki kasa bacci",ƙanƙance ido nayi"to Aunty Mamana","muje ki cire
wannan uniform ɗin kuma in ki ka bari Maman ku tasamu labarin abinda kikai to in
shi bai dake ki ba ita ta zaneki",ɗage nayi na rufe ma ta baki"wai kiyi shiru dan
Allah karma taji kinsan kamar dangin macizai take gun ji",kama bakin tayi"Nana ina
rabaki da kiwon kyalla kina akuya ta haihu",dariya maganar ta bani na shiga
ƙyalƙyalata"in tambayeki Aunty Mama ance ita ta haifeni amma meyasa bata sona yanda
ki ke yi",dariya tayi"ba sonki ne batayi ba wannan rawar kan naki ne bata so",taɓe
baki nayi na ɗaga kafaɗa"barta kawai muje kimin wankan","Allah ya shiryeki
Nana","ameen Aunty Mamana".

Rashin jina bai tsaya a iya haka ba kullum sai na jawo magana an kawo ƙarata amma
da zarar za'amin hukunci sai Alhaji Baffa ko Aunty Mama wani ya tare, wannan yasa
bama shiri da Maman mu daga harara sai ranƙwashi ke shiga tsakani na da ita nida
Babban Yaya kuwa bana yadda ma mu haɗa hanya bare sahu.

Ƴan gidanmu muna da yawa amma ba wai iya ƴaƴan Babanmu ba,family ne mu Baban su
Babban Yaya shine Babba a gidan su sunanshi Alhaji Aminu amma Allah ya masa rasuwa
yaransa goma sha uku kuma kowa na nan amma Babban yaya ne Babba a maza kaf familyn
mu sai yayunsa mata akwai Aunty Hasiya da Aunty Mabaruka sai Aunty Aisha ƙanensa
mata da yawa akwai Aziza, Maryam, Khadija,Nabila da dai sauran su sannan maza
Hashim,Isma'il,Ibrahim,suma dai akwai wasu,sai Abban mu Alhaji Haruna amma anfi
saninsa da Baffa,mu goma ne yaransa nice ta takwas duk sun girmeni sai ƙanina,
yayuna biyar mata biyu maza ɗayan shine ƙanina matan,Fatima
Asma'u,Usaina,Lubabatu,Amina,Saddiq sai ni sauran ƴan ɗakin Aunty
Mamane,Ashiru,Ruma da Abdulkarem muna kiransa ƙarami,kuma suma su Baffa da mahaifi
da mahaifiyar su,Baban su sunan sa Alhaji Abdulkarem amma anfi saninsa da Alhaji
Baffa mahaifiyarsa kuma Hajiya Aisha amma muna kiranta Iyyo saboda masifarta son
ungo shi yasa take masifar ƙaunar Babban Yaya amma tace kaf sauran ƴan mata suke
kaiwa kuɗinsu dan bataga suna bawa iyayen su ba,mijinta ya fita sauƙi saidai magana
ɗaya yake baya ta biyu, sai ƙannen Baffanmu huɗu Kawu Rabilu,Yaransa huɗu biyu
maza Kamis da Sadis biyu mata Sumayya da Ruƙayya,Kawu Ibrahim yaransa nada yawa ga
ƙananu sosai harda na goye amma acikinsu akwai Kamal Abduk aziz muna kiransa da
Abdul sai Aisha da yake masu sunan muna da yawa Humaira muke kiranta da dai saura
da yawa,Kawu Nuhu ɗansa ɗaya Haruna kuma mahaifiyarsa ta rasu ta gidan ba ita ta
haifeshi ba kuma bata haihu ba itama sai dai tana da kirki amma sauran matan to
akwai masu mutuci a ido,sai gwaggo Asama'u Yaranta huɗu,Aisha Zainab,Fatsima da
Khadija duk mata ne amma fa bata da kirki ko kaɗan duk wannan abin zaman lafiyar
gidan mu ke basu haushi dansu sun kasa zama lafiya saboda kishin juna da suke,amma
Mama da Aunty Mama bama ka banbance ƴaƴan su dan dukkansu akwai kyau kuma farare
Baffa ma fari shi yasa halittun gidan mu sai kallo,duk da sauran ma haka
suke,musamman gidan su Babban Yaya dan Umma buzuwar chadi ce kuma iyayenta can
yankin larabawa suke,Alhaji Baffa mutumin Nigar ne cikin tsantsar sahara amma
sauran akwai sirki saboda aure aure da mazansu suke.

Mama sunan ta Halima shuwa'arab ce ƴar chadi macece ita mai zafi shi yasa kaf gidan
ba mai wasa da ita saima yanzu da jikoki suka fara tasowa dolenta tasau fuska,nice
dama mai janta kuma cin ubana take,kamar dama hali yasan wuri Abba da Mama halinsu
guda wallahi komai kamar haɗin baki suke yi dashi duk da ba zama yake ba, haka
Aunty Mama sunan ta Halima,bafulatana ce sosai dan in tana yarensu saika ɗauka a
ruga take,macece ita mai haƙuri da kirki haka ƴaƴan ta dan ta iya tafiyar da
kowanne marajin magana bama ya ni nunamin soyayya da take yasa aɗakinta ma nake
kuma ita kaɗai ke cewa na bari na bari nan take amma ko Babban Yaya sai mun kwafsa
nake bari,zaman Mama da Aunty Mama abin ba'a cewa komai,ance harshe da haƙori ma
ana samun saɓani to su suna sarrafa nasu bana ce na taɓa jinsu suna faɗa ba ko da
hararar juna ne.

Baffa mutum ne shi mai aƙida ɗan ahalussunna dan haka baya wasa inaga kamar dama
ansan hali aka haɗa shi aure da Mama sai dai fa akwai kirki ya banbanta da sauran
ƴan uwansa sukam sai a hankali wallahi kodan dama ba'a fara rayuwar birnin ba da
wuri ba oho musu daga su har ƴaƴansu suna da matsalolin gaske,kaf ɗin mu alayi ɗaya
muke saboda filayen Alhaji Baffa ne ya mallakawa kowa shine suka gina,mu ba masu
kuɗi bane amma muna da rufin asiri gashi Baffa na aiki staff ne shi a companyn
Fanta haka su Ya Saddiq duka suna aiki shi yana ma lagos,a tsarin kaf familyn du
wata kowa da abinda zai aje tunda suka fara aiki kuma ba'a taɓa samun matsala da
gidanmu ba sai dai sauran shi yasa suke shan zagi wajen Iyyo bata ragawa ɗa bare
iyayen su dama sunfi shiri da Umman su Babban Yaya dan goya Iyyo ne kawai batayi
amma har yanzu ita ke ma ta wanki ta mata kitso,shi yasa duk su Ya Ruma, Ya Aziza
da Ya Mero kenan suke shan zagi tace basu iya komaiba sangartattu basu iya komai ba
sai ɗinki da ɗaurin zoɓo,iyakarsu suce ma ta ai shima sana'a ce.

vote
share
comments
Sisters

Û̬m̬̂ m̬̂ û̬ ŝ̬â̬d̬̂ d̬̂ î̬q̬̂

🌈🌈🌈
🌈🌈
🌈
*𝗕𝗔𝗕𝗕𝗔𝗡 𝗬𝗔𝗬𝗔*
𝚁𝚎𝚗𝚎𝚠

Story & written by


*FATIMA AMINU*
*Ummu Saddi'q*

2️⃣
chapter

Bayan shekara biyu na ƙara girma akan na da muna tsakar gida Ya Ruma namin kalba
dan kaina baya kitsuwa,Babban Yaya ne ya shigo"My Life"fincike kan nayi na tashi da
gudu tunkan ya ƙarasa shigowa na bisa bakin ƙofa,rungumeshi nayi"gani nan My
Life",riƙoni ya yi muka shigo ciki kaina ya shafa kitso ake miki",girgizawa nayi"ok
jeki a gama kizo ki rakani wani wuri"da sauri na cikashi naje na zauna kamo
hannunta nayi na ɗora akaina"cigaba kinji yace unguwa zamu",kallonsa tayi Ya Ruma
tayi tana dariya"Babban Yayan mu sai ina kuma kaida Life ɗin taka yau an shirya
kenan","Eh to munshirya yau zance zata rakani","kai amma ina murna an samo mana
Yaya kenan",murmushi nan da yake yi da ƙyar yasakar ma ta"an samo muku amma ba
yanzu ba auren sai nan da shekara biyu dai dai da naku nima zanyi","shike nan
Babbabn Yaya Allah ya sanya alkhairi ya kaimu lafiya",galla mata tsunkuli
nayi"nidai kimin kitsona sai zuba ki ke kamar famfo ya lalace",ba shiri sukai
dariya,nan ya wuce "ku gama bari naga Mama"gashin taja"wallahi ki kiyaye ni Nana ko
na miki mara kyau kalli yadda ki ka tsunkule min fata","to yi haƙiri","au haƙiri ma
zanyi",dariya nayi ma ta"to yi haƙuri",ƙwafa tayi ta cigaba.

Ƙofar ɗakin ya ƙarasa"Assalamu alaikum Mama","amin wa'alaikumul salamu Habibu shigo


mana",shigowa ya yi yana durƙusawa"ina wuni Mama","lafiya lau Habibullahi ya Umman
naku","tana lafiya tace a gaisheki","ina amsawa zauna mana",cikin sadda kai ya
zauna"baiyi magana ba saida ta kalleshi"Habibu yadai ka ke ta murmushi,ƙeyarsa ya
shafa"dama fita zamuyi da Nana ne zata raka wurin yarinyar da nake ɗan neman
aurenta","to shine saikazo ka tambayeni ai kaima ƙanwarka ce gatacan ta tasa Ruma
wai saita ma ta kalba ƙananu irin wanda ake yowa asabon gari",ɗan murmushi ya yi
kumatunsa ya lotsa","ai Nana akwai daru Mama",baki ta kama tana jijjaga kai"na
fitar hankali ma dan ma uwar ta ta yau bata nan ai da yanzu gidannan yana nan kamar
an kunna radio","ohh Aunty Mama bata nan","eh taje Dutse ana bikin ɗan ƙanin
babansu shi can yake zaune da iyalansa","ok Allah ya dawo dasu
lafiya","amin"...ɓurun na ban kaɗo labulen"Darling Yaya an gama","ok muje
to",dakatar shi Mama tayi"kai Habibu tsaya kalleta fa ahaka zaka fita da ita,kee
wuce ki watsa ruwa kisa wasu kayan",kafim Mama takai aya nakai uwar ɗakanta dama
akwai bayi ciki wanka nayi da sabulu ba zancen fita danma fatar ba nunwa take
ba,mai kawai na goga na zaƙulo rigar da aka ɗinka min kwanaki ta atamfa na zura na
rasa mayafi na buɗe wajen kayan Mama na ɗakko ɗan kwalin abayarta na fito sai sauri
nake","Kaiii Darling sis kinyi kyau",goshi Umma ta dafe"amma da alama makaho ne kai
ko kalli yadda take ƙyalli kamar ta shafa mangyaɗa amma kace wai tayi kyau kee
ƙyallari wuce muje a goge wannan man",tusani tayi agaba zuwa ɗakin wani towel
ƙarami tasa ta goge min man tas sannan ta shafa min powder ta naɗa min gyalen duk
saukar da ya yi saida kitsona ya zarta shi haka ta barin na fito,baki ya kama"ba
magana yanzu Darling sis"Allah ko Darling Yaya muje to",miƙewa ya yi dai dai Mama
na fitowa kansa ya duƙar"muntafi Mama","a dawo lafiya agaishe da ƴar tamu,kuma kayi
a hankali da wannan karta bada kai a wurin mutane",ƙafa na fara bugawa aƙasa"niɗin
niɗin","ke ɗin nasan ba'a abin arziƙi dake ne"tarar maganar ya yi"yau zatayi
Mama",zama tayi" to gaka gata ai"fitowa mukai nasa takalmina halfcover baƙi yama
ƙafar ɗas,fita mukai tacan ɓangaran Iyyo mukabi zai ɗauki mashin ɗinsa,tun daga
nesa take kallonmu muna ƙarasowa tace"su kayya da kulla ina aka nufa kuma",hararar
ta nayi"wallahi Iyyo kin fiya sa ido","in bansa ido ba hanci ki ke so nasa kaji min
yarinya",dariya nayi Babban Yaya ya yi murmushi danshi dariyarsa ta siyarwa ce baya
wa kowa ita,"kisa idonki Iyyo zance zan raka Sweety Yaya"haɓa ta riƙe tana taunar
goro,"Kai Habibullahi yanzu da wannan zabayar zaka wurin budurwa salon ta
razanata",zabura nayi"kambala'i Iyyo nice zabaya ko dayake bana ji haushi ba ai
kalar mu guda daga suna har fata da jiki",haɓa ta tare da bayan hannu"Allah ya
rufan asiri nayi kala da shawara kalleki fa muddin kaje da wannan sai kowa ya
gudu","saboda ga dodo ko to budurwar ma in batai min ba canjata za'ayi ko Darling
Yaya",numfashi yaja"zancenki haƙƙun Baby","kinji ko dan haka kisa saɓa
tsohuwa","fata zansa dan uwaki Halima ƙarama ayi dai mugani in tusa zata hura wuya
ku wuce kuban wuri ni kin dameni","mun tafi tsaffuwa ta tsaffo ni innai tusa bawuta
zata hura ba gobara zata haddasa","to kaji dai kai Deli sai kai hankali karta soya
ka",murmushi ya yi ya matso kusa da ita ya rage murya"ai Iyyo indai ita zata soyani
ba matsala",hangame baki tayi tana ɗora hannuwanta aka"kai yau ina ganin rayuwa ku
tafi ku bani wuri",dariya mukai ya kama hannuna muka wuce ina ma ta gwalo,kai ta
girgiza"kai Allah ya shiryeki Nana kaima ƙato da kai Allah ya shiryaka",mashin
ɗinsa lifan tsuntsun soyayya muka hau tun daga gareji muka fito tare dama yasa
baƙin glass ɗin nan mai tsorata yara bai tsaya kula kowa ba muka wuce ina kallon
yaran gidan Kawu Iro na hararata damasu akwai gulma.

Munyi tafiya mai nisa sannan mukazo wata unguwa,unguwar sabuwace gidan da muka
tsaya mai mugun kyau babba dashi a bakin gate ɗin yay parking sannan ya ƙwanƙwasa
megadin ya fito,yashe baki ya yi"a a Alhaji ne ka shigo mana ya zaka tsaya
anan",kama hannuna ya yi muka shiga sai kallona mutumin yake kamar zai faɗi,fakar
idon Yaya nayi na galla mai harara ina zaro mai ido,saurin ɗauke kai ya yi yana
musmus da baki bangane dai me yake cewa ba,har wajen wasu kujeru ya kaimu"Alhaji
bismillah bari na kira Hajiyar",ya juya da sauri zuwa cikin gidan,zama Babban Yaya
ya yi na zagaya bayansa na ratayo wuyansa na kwantar da kaina akan wuyansa,hannu ya
miƙo ya shafa fuskata"lafiya dai ko","lau Yaya barni a haka","dama nace ki sake ni
ne",ɗan murmushi nayi,dai dai wata murya na sallama,ɗagowa ya yi yana amsawa,kujera
taja tazauna yana yanga"Habibina sannu da hanya","yauwa ya ki ke","lafiya a a da
baƙuwa kazo min ne",sai a sannan na juyowa da kaina gareta"ina wuni","subahanallahi
Habibina ina ka samo wannan"kasaƙe mukayi muna kallonta dan bamu gane ina zancenta
yasa gaba ba,lura tayi bamu ganeba sai ta kamo hannuna dake wuyansa"naganta
kyakykyawa ne",murmushi ya yi"ƙanwata ce",gabanta ta tsaidani kamar me neman wani
abu a jikina take ƙare min kallo janye hannuna nayi na koma gabansa na rike mai
hannu,gefensa ya maida ni na kwantar da kaina a kafaɗarsa"ya makaranta Hajara",fari
tayi ta ido tana gyara wuyan riga cikin iyayi","lafiya lau Habibi amma wannan
ƙanwar taka bata da yarda ko","ba wani rashin yadda tsabar salo ne wannan
botsararriyar kece dai kikai sa'a abin bezo takanki ba",ƴar dariya tayi"a kabar min
ita mana zuwa anjima kazo ka ɗauketa",kafin takai ayar maganarta na ɗago har
gyalena na faɗuwa,gashina ta kallah"kai Habibi ƴar ƙanƙanuwa da ita kuke ma ta
ƙarin gashi",murmushi ya yi yana kama kitson,cikin idona yake kalla"Hajara wannan
gashin real ne haka ƴan gidan mu suke musamman ma ƴan gidan su",wani dam ƙirjinta
ya buga nan da nana taji tashin hankali na shigarta inta fahimta yana nufin ba ƴar
gidansu bace waro ido tayi"badai itace Nana ba","yauwa kin fahimta kenan itace Nana
RUHIN YAYAN TA",wani kallo ta masa shi baima san tanayi ba maganar daga zuciyarsa
take fitowa zuwa sarari ganin baima san me yake faɗaba,yasata barin zancen tai
murmushi kawai ta bara abin a haɗuwar jinine dan yarinyar bata yarwa bace"amma
Habibi maganarmu fa",ido cikin ido na kalleta amma hararar ta nake da kula da
kyau,kansa na koma da shagwaɓa"ni bazan zaunaba gida zan tafi zanje islamiyya fa in
na makara yasayyadi ba tausaya min zai ba cuwaɗa ni zaiyi","ok ƙanwarmu na fahimta
sai ku tafi tare"shiru nayi ina kallon wani wurin,hirar da bansan kanta ba sukeyi
shammatarsa nayi na galla masa mintsini,saurin gyara zama ya yi "kai kai kika
tsunkuleni","to ka tashi mu tafi bakaji ana kiran la'asar ba in naje makaranta a
latti dukana za'ayi",na ƙarashe kamar zanyi kuka saurin tashi ya yi yana gyaramin
mayafin kaina,kallonta ya yi"zamu wuce Hajara banaso a daketa",ƙugu na kama kai
kace wata sa'ar su ce"kamar gaske Darling Yaya kaimafa lakaɗata ka ke kamar
jaka","eh mana in ban lakaɗeki ba so kike ki girma asangarce in kasa tanƙwara
ki",kamar wadda ta gane me yace nace"naji dai muje",saƙare tayi tana mamaki kamar
ma ya manta tana wurin,wannan sunan kumafa wai Darling Yaya,shine kawai ya tsaya ma
ta arai",kama hannuna ya yi yana juyawa gareta"munwuce Hajara ki gaida ƴan
gidan",numfashi taja"ku ɗan tsaya ina zuwa",ta wuce ciki ba jimawa ta dawo ɗauke da
leda"ga wannan ƙanwata ki gaida mutanen gidan",karɓa nayi"nagode",nan ta rako mu
har waje muka hau mashin ɗin muka wuce gida.
vote
share &
comments

Û̬m̬̂ m̬̂ û̬ ŝ̬â̬d̬̂ d̬̂ î̬q̬̂

🌈🌈🌈
🌈🌈
🌈
*𝗕𝗔𝗕𝗕𝗔𝗡 𝗬𝗔𝗬𝗔*
𝚁𝚎𝚗𝚎𝚠

Story & written by


*FATIMA AMINU*
*Ummu Saddi'q*

3️⃣
chapter

Ciki ta koma amma ta rasa ma wane tunani zata yi har yayarta ta lura da ita gyara
zamanta tayi ta janye littafan gabanta ta kira sunan ya"lafiyanki kuwa
Hajara",ajiyar zuciya taja tana gyara zamanta"wallahi sis ko wani abu ne ke damuna
nama rasa wane mataki zan ɗora abin","tohh wane abu ne wannan kuwa","ba nace miki
Habib yazo da wata ƙanwarsa ba","eh hakane","to gaskiya da ƙyar in ɗakinsu ɗaya a
yanda yake nunawa,dan yarinyar nan kamar tana da wani babban matsayi a cikin
rayuwarsa","to shine me ko ɗaki ɗaya ko ba ɗaki ɗaya ba saime,naji kince yarinya
nasan dai bata kaiki ba ko?","kaini kuma sis bafa tafi shekara sha biyu ba ko sha
uku","mitss shine kika bi duk kika ɗaga hankalinki dama yara ai sun gaji haka dole
akwai wanda yafi wani haɗuwar jini a ƴan uwansu komu anan gidan ai hakane kinsan
dai mu ba'a mana kishiya dan haka ki nutsu kawai ammanko aurenshi ki kai saikina ja
baya da ita sannan a gabanshi kina nuna ma ta mugun so zakiga ta rage shiga jikinsa
da kanta hikimar hakan saikin shiga gidansa zaki sa ni",wani ɗan ihu tayi"kaii amma
nagode wallahi da narasa ina zan saka kaina",wani irin juya kai tayi na ƴan
duniya"ai in kika shiga duhu ki nemo mu zamu feto dake cikin haske",tafawa sukai"to
shike nan ai na ɗau haske,bari naje zamu fita da Mommy","ku dawo lafiya"ta tashi ta
fita.
***
Muna shigowa layin a ƙofar gidansu ya tsaya da gudu na sakko na shige Umma na wanki
na ɗane bayanta"oyoyo Ummana"dariya tayi tana ɗauraye hannunta ɗagowa tayi tana
riƙoni"yanzu na aika akira min ke akace kun fita da yayanku","Eh Umma zance
mukaje","lallai to sannunku ina yake shi","Assalamu alaikum gani nan Umma me zaki
bani","uwaka zan baka dama Yusuf ne yazo nemanka"kan ya yi magana nayi"Umma ga
tsarabar nan ki cinye na tafi insa uniform lokacin islamiyya ya yi","a a tsaya
kaiwa ƴan gidanku ai naku ne ni banacin waɗannan abubuwan kin sani kai maidata inda
ka ɗakkota",kansa ya dafa,na dubeshi"baka da lafiya Babban Yaya",hararata ya
yi ,nayi nace wa Umma"to Umma na tafi in kinyi murjin taliya zanzo na karɓa","to
shikenan ki gaida maman taku",hannunsa na kama muka fito a ƙafa muka ƙarasa,da Ya
Ashiru muka haɗu saboda jan magana na kalleshi"kai Yaya wallahi wannan wuyan rigar
ya yi girma telan baima iyaba",kama baki ya yi ya tsaya yana kallona,hannu ya miƙo
zai kamani"saina daka ki wallahi"hararar sa Babban Yaya ya yi"kai barnan","Allah
Babban Yaya","to agaban nawa zaka duketa",wucewa ya yi yana ƙwafa"ai zan kamaki ne
zai tafi ai",gwalo na faki idon Yaya na masa"wato gwalo kike masa ko ke kin raina
uban kowa ko","Allah Babban Yaya ban raina kowa ba kawai wasa nake","saiki dage
wataran wani yasaki jinya ai ko",dai dai muna shiga gidan da sallama,Mama ce ta
amsa suna zaune a baranda da baƙuwa,"sannu da gida Mama","kun dawo Habibu","eh Mama
gata nan zata tafi islamiya","to taje tasa kayanta dan yaran duk sun wuce ita kaɗai
ta rage"suna magana na fito,ko takan ledar dana aje agaban Mama banbi ba"Darling
Yaya ban biyar","biyar saikace wata ƴar tsana","goma to","gadai ashirin kiyi maza
karki tsokani kowa","na maka alƙawari kuwa Babban Yaya","to aje","na tafi
Mama","adawo lafiya",nayi waje da sauri"Mama na wuce sai anjima","to shike nan
Habibu Allah ya kaimu",ya fita wannan matar kamar idonta zai faɗo sai kallonsa take
da gani munafurci na cinta ne dama dillaliya ce an ƙware awannan fannin.

Bata cewa Mama ƙala ba dan tasanta bata yadda da irin waɗannan maganganun na
gulmar wasu, kayan da zata siya kawai ta ɗauka sannan ta bata kuɗinta dan su Mama
basu yadda da bashi ba.

Daga nan gidan bata wuce ko ina ba sai gidan Gwaggo Asama'u tana ganin ta fara
washe baki dan basu da maraba dama gun gulma,wurin zama ta kawo ma ta sannan ta
kawo ma ta ruwa,kujera ƴar zuƙunne ta jawo ta zauna"Hajiya Tasalla dama ana ganin
ku",ruwan da take ƙyanƙyama ta aje tai gyatsa"gamu kuwa Hajiya Asama'u ya gida ya
yaran da me gidan",wani taɓe baki "yara na nan shima yana nan" ya kasuwar
fa","kasuwa gata da kyau ga kayan sabon ɗauka ki kwasa na kaiwacan gidan ƴan uwanki
duk sun kwasa","oho saida ki ka kai musu suka ɗiba sannan zaki kawo min
sauran","kwantar da hankalinki mana ba saura na kawo miki ba naki daban dama na
kwasa harda ƴan matan ma na kawo musu humra ta musamman","ato shike nan miƙomin su
na zaɓa",tana kwasa ne Tasalla ta kalleta gulma na sakatar ta"bakiji ba Ma'u","ina
jinki Tasalla da tsegumine","Babba ma kuwa nace ba me yasa acikin yaranku ba zaku
haɗa wata aure da wannan zankaɗeɗen matashin ba","wani matashi kenan
Tasalla","Habibun nan mana",gyara zama tayi"ki bari kedai Tasalla wannan maganar
har Alhaji Baffa nayiwa ita amma ya takan burki kuma yace kadan na kuma wannan
maganar saiya saɓa min","tabɗi amma kuwa ya kwafsa muku agaskiya ina hango babban
al'amari dan gane da wannan yaron da ganinsa ƙashin arziƙi gareshi kuma naga yafi
shigewa su Halima akan ku","hakane Tasalla aisu waɗannan kyan yaransu ke ruɗar
mutane ake sonsu musamman wannan me kama da zabayar Nana, amma ai in bamu same shi
ta wani fannin ba to ta wani fanin zamu samesa","Allah ko saiku dage dan naga
wannan ƴar jariryar yarinyar ta iya salo ga iyayi tsiya kamar babbar mace","kai
Tasalla ai Nana ta wuce tunanin ki bata da kunya kuma ƴan gidansu kawai take so
agabana take faɗawa yaran nan ita bata ganin kowa da gashi amma barni da ƴar banza
za'a sha mamaki akanta", suka tafa nan dai sukaita maganganun mutane daga wancan
sai wancan,Tasalla na famfata har abinma da ba'aiba sai labarun ƙarya take girba ma
ta ita kuma tana yadda,kafin su rabu saida ta ƙara dasa ma ta tsanar su Mama
aranta,haka ko bayan fitar Tasalla zama tayi tana cin burika tamanta Allah ke komai
ko muguntar zakai sai yabaka dama sannan zakayi.
*****
Shida saura aka tashemu naƙi biyo kowa naja gefe ina tafiyata,fancam naji an
watsamin wani abu me ɗoyi,da sauri na waiga naga Humaira na dariya"yi haƙuri Nana
bansani bane nataka kwata ta fantsamar miki",ganin tana dariya nasan ƙarya take
tana sane tamin haka,nan na zuciya wata yarinya na bawa riƙon jakata na kwasa da
gudu na shaƙeta na hau dukanta duk da ta fini girma amma na fita ƙarfi,duka na mata
ga yakushi da cizo,da ƙyar Ya Ruma ta rabamu taja hannuna zuwa gida bamu faɗama
kowaba mukai shiru,Mama ke tambayar meya sameni nace kwata na faɗa tace" kije kiyi
wanka mana" wankan nayi nasa riga da wando masu laushi sosai,ina ɗaki raina sai
ƙara ɓaci yake in na tuna abinda Humaira ta min naji Mama na kirana"Nana
Nana","na'am Mama gani nan zuwa",fitowa nati inasa hijabi nasan aikena zata yi"ki
ɗauki wancan kwanon ki kaiwa Ummanku karki zauna kinga an kusa sallar magariba","to
Mama",na ɗauka ina fita naje kusa da ƙofar gidan Kawo Iro naji an hankaɗe ni Allah
yaso kwanon kula ce bai buɗeba,kafin na tashi Humaira ta danneni ta hau jibga ta
kamar jaka saida tamin duka sannan naji Babansu na magana"barta haka ai kin
rama",ɗagani tayi duk jikina ƙasa na miƙe ina hawaye ga ƙafata na zafi musamman
babban yatsana,ranƙwashina naji anyi na ɗago na kalleshi"daina kallona mayya in
kika kuma dukanta sai naga wa ya tsaya miki",ƙuri na masa da ido banyi magana ba
dan in nace zanyi zatayi zafi kuwa,a kusa damu taxi ya tsaya saiga Aunty Mama ta
fito ganina a haka ta nufoni da sauri,da gudu na tafi na rungumeta ina rushewa da
mugun kuka kamar raina zai fita,ruɗewa tayi"lafiya wa ya dakeki faɗamin"cikin
shassheƙar kuka nace"Kawu Iroro ne suka min duka shida Humaira akan ta watsamin
kwata muna dawowa a makaranta kuma tahaumin dariya shine mukai faɗa a wurin wai
yanzu shine suke tareni suna duka da zagin ubana da uwayena",kaf maganar da nake
abin dariya ce amma amma Aunty Mama sai ta shaƙa tafara faɗa"wallahi kaji kunya Iro
faɗan yara ka ke shiga kalli yadda ku ka daki ƙaramar yarinya saboda zalinci
wallahi anji kunya ke kuma ki ke zare ido kamar baƙuwar mujiya zan kamaki
ne",hannuna taja nace"aikena akai Aunty Mama ga yatsana yana zafi","kai Ƙarami
ɗakko wancan flas ɗin ina zaki kai","Umma zan kaiwa","wuce ka kai ma za, ke muje
gida naga ƙafar taki",su kuwa saƙare sukai jin yanda na gindaya musu sheri na faɗi
magana kamar duka haka akai,yanzu baya raba layan biyu sai wannan abin ya zama
babba.

Vote
Share &
Comments

Û̬m̬̂ m̬̂ û̬ ŝ̬â̬d̬̂ d̬̂ î̬q̬̂

🌈🌈🌈
🌈🌈
🌈

*𝗕𝗔𝗕𝗕𝗔𝗡 𝗬𝗔𝗬𝗔*
𝚁𝚎𝚗𝚎𝚠

Story & written by


*FATIMA AMINU*
*Ummu Saddi'q*

4️⃣
chapter

Shigowar mu ina ɗingishi yasa Mama kallon mu taganni da Aunty Mama dariya tayi tana
faɗin"kice da rabon faɗa kika fara daga dawowarki",kallon Mama tayi rai ɓace"haba
Yaya taya za'ace kina gidan nan amma anawa yarinyar nan haka kalli fa saboda aikin
banza wai Iro ne ya biyewa ƴarsa sukai ma ta duka haka",dariya Mama tayi"kibar
batun nan kawai ƴar uwata bana son tashin hankali kinga mijinmu baya gari ace in ya
dawo yana samun irin waɗannan labaran bazaiji daɗiba ko",sanyi jikin Aunty Mama ya
yi ko nima haka"shike nan Yaya","yauwa sannu da zuwa,to ko na ɗumama muku ruwa ne
ki gasata","barshi bama so ai zamu iya dafawa",dariyar Mama ta kuma tayi dama
tsokana ce"Allah raka taki gona daga taimako","bama son taimakon naki",sukayi
dariya,ɗakin muka shiga wanka ta min ta shafa min mai da maganin zugi a ƙafar,
anan Ya Ruma take faɗa ma ta abinda ya faru,"nasani zasu aikata Ruma Nana fa kawai
dan bata barin kota kwana ne shine ake ma ta kallon maraji amma yaran gidan Iro ga
fitsara da rashin kunya da baƙar mugunta ba komai",kaɗa kai Ya Ruma tayi"shi kenan
Aunty Mama na tafi zanyi karatu ne","to Ruma jibi Fatu da Usaina sun ce suna tafe
na haɗu dasu can tasha zasu unguwa suma ","Yauwa sai sunzo da wuri zan dawo a
makaranta","ai shikenan",suna magana ni kuwa har nayi bacci nan kan kujera.

Ana sallar isha Umma ta shigo gidan nan tsakar gida suka zauna suke maida zancen
nan Umma ke cewa"ni dai abin mutanen nan na bani mamaki wallahi yanzu wannan ƴar
yarinyar miye na Iro ya taya ƴarsa su duketa","hakane kam amma abar zancen kar yaje
kunen Alhaji Baffa da Iyyo dan akan Nana zasu iya ciwa kowa mutunci",kuka sukaji a
bayansu nan suka waiga da sauri Iyyo ke kuka nan suka tashi da hanzari suka nufi
wurinta hankali tashe"Iyyo lafiya"suke tambayarta atare"wallahi kin cuceni Halima
yanzu ƴar amata kallar wannan dukan amma kice abar zancen da ba ke ki ka haifi
Aisha ba sai nace mugun tace ko ƴar fari kina nuna ma ta so amma banda autar ki
wallahi sai Iro yasan ya taɓa min Nana",tana kaiwa nan ta fita da sauri,dafe kai
Mama tayi"ki bar wannan abin kawai Halima kinsan Iyyo sai ta ɗauki mataki
dole","wallahi bana son tashin hankali",Aunty Mama ta kalla da take
dariya"hankalinki ya kwanta ba","wallahi kuwa dama ke ke tsoron fitina ni kuwa bana
tsoronta tunda zalinci akai dama biyayya na miki matsayinki na wadda ke da iko da
gidan sannan kuma wadda ta girmeni ke kuma yanzu saiki yi biyayya ga wadda ta
girmeki kuma uwa agareki kinga ƴata ma tayi bacci ni kuwa na tafi kallo dan da
abaka labari gara ka bayar"tana kaiwa nan ta fice dama da hijabi kanta da tayi
sallah,kallon Mama Umma tayi"narasa me yasa waɗannan mutanen huɗu kewa Nana mugun
so haka Habib duk da suna faɗa kuma yana dukanta amma mugun so yake ma ta in kika
shiga ɗakinsa ko zaki sha mamaki kaf ɗakin zanen Nana ne da hotunan ta tun tana
zanin goyo,Iyyo duk faɗanta da masifarta kina taɓa Nana kun gama duk shirin da ku
ke sannan Alhaji Baffa shima haka baya ganin laifinta sai uwa uba abokiyar zamanki
ba mai cewa ba ita ta haifeta ba","eh mana bakiga ma da ita take kama ba har zubin
jiki na Halima ne kinga Ruma ko ita bata kama da ita yanda Nana keyi Allah dai ya
barsu tare nikam naja kaina gefe",dariya Umma tayi"ai da yafi kam muzauna tsaiwar
ta isa haka sukam gidan sunga banu yau ai sai abinda suka gani","hakane Allah ya
yayyafawa abin ruwan sanyi","amen dai".

Kwasar tuwo Umman su Humaira ke yi fuuu taga wucewar Iyyo kafin matan
gidan suyi wani motsi Iyyo ta janyo Humaira ta fara jibgarta,kansu matan gidan
sukayo amma Iyyo ta dakatar dasu"duk wadda tazo nan saina haɗa da ita wallahi tunda
ta daki Nana ita da ubanta saina rama ma ta mugwaye kawai",ta cigaba da dukanta
saida tayi san ranta sannan ta barta sai ihu take tana kuka"kuma dan ubanki ko
kallon banza ki ka ƙara ma ta saina karya ki bar gani na tsohuwa sai in ɓalla mutum
da wannan jikin nawa",sannan ta kalli matan"kuma in Iron ya dawo yazo ina nemansa
yau basai gobe ba",tai wucewarta Aunty Mama tagani tana dariya"muje Halima ko uwar
Nana kadan ta daketa ba akan tayi komai ba saina rama ma ta bare waɗanda dama basu
san mutuncin kowa ba",haka suka fito Iyyo nata masifa Aunty Mama na zugata can
gidan Iyyon ta bita sukai tayi suna jiran Alhaji Baffa.

Umma ce ta kalli Mama"Halima dama inaso muyi magana","inajinki Sa'adatu","dama


cewa nayi muyiwa Alhaji Baffa magana akan Habibu yace ya samo mata kuma sunce ya
turo to kinga ba maza atsakani tunda Baffansu bayanan sauran kuma ba abokan shawara
bane mune ɗin dai","haba Sa'adatu ai wannan mai sauƙi ne tunda naji ana sauran
yaran ma su Ruma duk suna gama makaranta za'a aurar su ai sai a haɗa kawai zamuje
da safe saimu faɗa masa","to shike nan dama yace min wai zata ƙarasa kartunta ma
sai nan da shekara wajen biyu","hakan ya yi Sa'adatu Allah yasa alkhairi","ameen
ameen Halima yaran da za'aiwa auran ai yawa ne dasu in hakane nan ne ma kawai Ruma
amma ni ai mutum wajen shida ne harshi sauran gidanjan ma za'a samu uku
uku","hakane fa to Allah ya hore mana dan biki ba wasa ba","wallahi hakane amma
Allah zai dafa mana ai dashi muka dogara","lallaikam dan Ruma nice uwarta dan
Marƙofa ita ta koma tana magana ita ɗaya duk dai akan Aunty Mama.

Ƙarfe tara Alhaji Baffa ya dawo dama yaje zaria ne ɗaurin aure kasantuwar yau
asabar yana da kayan barkono su ya siyar,a tsakar gida ya samu su Iyyo suna maida
zancen,da sauri Aunty Mama ta ɗakko mai shimfiɗa nan suka fara mai sannu da zuwa
ruwa da abinci aka fito mai dashi"sannunki Halima lafiya dai naganku atsaye
A'i","ƙwafa tayi sannan ta fara magana"kai dai bari Alhaji wai dan abin kunya yara
sunyi faɗa shine dan zubda girma Iro zai kama ya daki Nana wai ya ramawa
ƴarsa",hannun da yake wankewa ya daina ya ɗago yana kallonta"wane Iro ɗin
kuma","kaji ka ma Alhaji Iro nawa muke dashi babban Iron dai","me ya haɗa yaran da
ya kama ya shiga har ya daki jaririyar yarinya",bayani Iyyo ta shiga kwance mai
kamar gabanta akai"amma wai Halima tace a bar maganar sai wannan Halimar ce ranta
ya ɓaci amma ta nuna",kansa ya girgiza"kwantar da hankalinki A'i kema Halima koma
gida zanwa tufkar hanci",sunkuyawa tayi "to Baffa,Iyyo saida safe","to ƴar nan
Allah ya miki albarka saida safen","ameen Iyyo",ta wuce tana jin daɗin yanda tun
zuwanta gidan mutanen basu taɓa daina nuna ma ta so ba har yanzu da girma ya sawo
kai".

Alhaji Baffa abincin shi yaci ya ƙoshi sannan yasa aka kira masa Ya Ashiru da
sallama ya shigo"kai Ashiru jeka tasomin kawunka Iro ku taho tare injini","to
Alhaji Baffa",ya tashi ya fita yana dariya yasan yau akwai drama.

Vote
Share &
Comments

Û̬m̬̂ m̬̂ û̬ ŝ̬â̬d̬̂ d̬̂ î̬q̬̂

🌈🌈🌈
🌈🌈
🌈

*𝗕𝗔𝗕𝗕𝗔𝗡 𝗬𝗔𝗬𝗔*
𝚁𝚎𝚗𝚎𝚠

Story & written by


*FATIMA AMINU*
*Ummu Saddi'q*

5️⃣
chapter

Baffa kallon Iyyo ya yi"narasa me yasa kwata kwata Iro yake irin haka baya da
ɗabi'a irinta Rabilu gwarashi ba komai yake shigaba amma shi sai kace mace komai
shiga yake","bari kai dai Alhaji kuma matansa ne ke ɗaurewa yaran gindi suke abinda
sukaga dama suna tsefe kama kamar majinyatan birarrika",ƙwafa ya yi"ai zasu haɗu
dani kaf har yaran nasu","Assalamu alaikum",sallamar su ta dakatar da Alhaji Baffa
daga maganar da yake"ameen wa'alaikumul salamu Ashiru yauwa ka samo shi,sannu Iro
yanzu fisabilillahi ƴar ɗan uwanka ba ƴarka bace shine gotai gotai da kai zaka kama
ka duki Nana ƴarka ta wajen ashirin dan girman banza,kuma ku riburbuɗi yarinya
kaida ƴarka",dafe kai Kawu Iro ya yi dan sharrin Nana baisan zaiyi tasiri haka
ba"wallahi Baffa ban duketa ba kawai dai na ranƙwasheta nace karta kuma","shi
ranƙwashin ba duka bane kuma sa'arka ce ma wai ka kiyayeni fa akan Nana zamu raba
hanya dakai",ƙara kallon Baffa ya yi yana ƙifta ido saboda ɓacin rai"yanzu Baffa
ace wai wannan ƴar yarinyar tana kitsa abu amma kuna ɗauka kuma kaf yarannan
jikokin ka ne amma kana nu na kafi san ta duk yawansu","an nuna ɗin kaji nace an
nuna ɗin",Iyyo ce ta dakatar dashi"kai har kana da abin cewa anan yarannan naku
inba tasu ta kawo su ba ko ƙeyarsu da niyar gaisuwa muna gani har matanku basa
shigowa nan sai su Halima da yaran su sai Sa'adatu in aka tashi kullum safiya sai
sun shigo sungaida mu inda aiki suyi haka masu auran ma suna da iyaye amman in
sukazo nan suke sauka daga baya suje ga iyayensu amma naku fa,to bari kaji ko
hararar Nana ƴaƴanka suka kuma yi basu zan daka ba kai zan daka agaban ƴaƴanka sai
dai ciwon zuciya ya kashe ka,tashi ka bamu wuri anan",baice ƙala ba a matsayin su
na mahaifansa ya ɓata musu rai sai ya wuce yana wulla hannu kamar wani yaro
ƙarami,Ya Ashiru ne ya zauna inda Baffa ke zaune yana ta dariya tun ɗazu",Alhaji
Baffa ne ya kalleshi"kai kanka ɗaya ka ke ta dariya,da ƙyar ya dakatar da
dariyar"yanzu Alhaji Baffa kan Nana ku ke wannan ɗaga muryar",Iyyo ce ta
harareshi"kanta ne fa ubanmu ya akai","wallahi ku daina biyewa Nana batajin magana
itama..."bai kai ayaba Iyyo ta ɗakko taɓarya da gudu ya miƙe ya fice yana
dariya"lallai ma tsaffin nan sunyi nisa bari na kama kaina dan tsaf wannan tsohuwar
zata gicciyeni"ya wuce wurinsu Ibrahim daya hanga can rumfar me shayi ana zabga
hira kamar yaƙi.

Kamar wata ƙaramar yarinya haka Aunty Mama ta shigo tana sanɗa amma kash kamar a
sama taji muryar Mamar da take sanɗar dan karta ganta"sannu uwar Nana kun gama
ɗaukar fansar",dakatawa Aunty Mama tayi tana juyowa"sannu da gida Dada wallahi mun
gama kuma agaban iyayenta Iyyon ta lakaɗeta itama kai ai yau naji daɗi","ai kun
kyauta taho muci abinci ke nake jira",da sauri ta ɗago ta kalle Mama wadda ta shige
cikin falonta,jiki sanyaye tabi bayanta a falon ta cire hijabinta suka
zauna,abincin ta janyo fulas ta tura ma ta"zuba mana Mamar Nana",ƴar dariya
tayi"kai Dada","to me kike so nace na lura nan gaba kaɗan filin dambe zaki buɗe
saboda Nana",tana zuba abincin tayi ƴar dariya"sakko Dada, nifa baki sa ni ba wani
irin so nakewa Nana kawai ki barni Allah wallahi kinji na rantse bana son su Ruma
yanda nake son Nana shi yasa bana daure abu in aka ma ta",cikin sanyin murya Mama
ta e"na yarda dake Halima amma kinayi a hankali wataran kar dai ta kaiki ta
baro",dariya tayi"karki damu akan wannan nasan Nana nada tsokana amma tanada faɗar
gaskiya wani sa'in ne in tsiyarta ta motsa abinda ma ba'aiba sai tace anyi","to dai
ku kuyi a hankali kar wataran ta jawo azo har gida a muku dukan tsiya"kwashewa tayi
da dariya"haba dai Yaya bamai dukanmu kafin takai wannan matsayin ta girma kika sa
ni ko tashiga ɗakinta da wuri","uhmm magana kanta ta isheni kinga ɗazu Ruma kece
min waɗannan yaran zasu zo gobe","eh kuma sunce kwana biyu zasuyi","to Allah ya
kaimu goben","ameen Dada gashi ma ƴata tayi bacci bata ci komaiba wallahi","saiki
tafi dashi dan kinsan tabbas zata tashi ta nema komai dare","haka za ayi kuwa"bayan
sun gama cin abincin sun jima suna hira sannan Aunty Mama ta ma ta saida safe ta
fita.

****
Kamar an kunto shanu haka ya shiga gidan ball yake da duk abinda ya tare masa gaba
Umman su Humairan suna tsaye dama suna ta zage zage kan abinda ya faru,ihu bayan
hari kenan sai gashi kuwa ya shigo Saude ɗaya daga matansa kenan ita ta fara magana
"haba Malam miye hakan kalla yadda ka ke ball da kaya inka fasa mana fa siya mana
zaka yi",cikin masifa ya hayayyaƙo kanta"bazan siya ba kinji nace bazan siya ba
kuma saina ma fasa",yasa ƙafa ya take buta ƴar lamba biyar"gashi na fasa yi uwar da
zakiyi ingani ɗauki mataki nace ni sai inci uban mutum wallahi",Umman Humaira ce ta
tare"wai Malam maye hakan kalla abinda akazo har gida aka mana amma kazo kana ta
mana hayaniya maimakon ɗaukar mataki","rufe min baki Rabi ai nagani kuma nasani ko
an faɗa miki ban sani ba bane,ni kinsan mai akai min to ki barni ai itama Aishan
dan uwarta tasan halin waccan sheɗaniyar yarinyar da baƙin sheri amma ta shiga
sabgarta ita ta sa ni nidai abinda na sani saina kassara rayuwar yarinyar wallahi
dalla malamai ku wuce ni ku bani abinci"ya wani bugo wata kujera ya zauna akai,taɓe
baki sukai suna jan tsaki nan mai girkin ta kawo mai abincin tuwone na masara miyar
kuɓewa bashasshiwa amma in ka ganta saika ce kai aka wanke,wani ashar ya lailayo ya
ƙunduma"wannan wane irin tuwone Rabi kalli tuwo kamar talge kalli miya kamar a
bursun ina kuɗin cefanen da na bayar,kinyi zubin dashi wallahi baki isaba mutum
yaci wannan ai sai ya yi zawo zoki kwashe shi kan naci miki mutunci wallahi",sumi
sumi ta zagayo ta kwashe ji yake kamar ya rufeta da dukan tsiya amma ya barta,tashi
ya yi ya fice bin bayansa tayi da tsaki tana hararar sa anan Saude ma ta harareta
ta kyaɓe baki tace"dama an auro jinin zazzagawa ai dole aci tuwo mai ruwa kamar ba
garin ɗaure shi miya kuwa ana burin kere sa'a ran auren ƴa ai dole asha garara
Allah dai ya kyauta","ke Saude ki kiyayeni wallahi saina zubar da waɗannan haƙoran
kamar ɓarin tsaba ai gwara wannan tuwon kan nagidan tsoho da ace nacan yafi na nan
ai da tuni an ware amma an nane saboda hakan samune","wallahi kinsha ƙarya Rabi ina
zaman gidannan ne dan ƴaƴana ba dan ina gudun karna fita a dafa su a cinye dan
nasan kurayen gidan nada yawa"cak Jummai da tazo wucewa ta dakata kanta ta ɗago ta
ƙare ma Saude kallo"ke Saudala ki iya bakinki kuma ki tsaya iya inda aka ja ki
karki sa wanda zai soya ki dan haka ki iya bakinki ko yanzu kinsan nasa a aunaki
gidanku mu dafa mu suye ƴaƴan tunda dangin mu ɗaya dake duk mayu ne mu",tana kaiwa
nan ta antaya musu harara tai gaba tana juya ƙugu kamar na kura",Saude ma hararar
Rabi tayi ta buga tsuka tai gaba nan ita Rabi tai ball da kayan gabanta ta shige
ciki tana zage zage.
Yana fitowa ya haɗu da Kawu Rabilu ganin sa fakan fakan yasa shi tsaida
shi"Rabilu ina zuwa haka kamar zaka tashi sama",tsayawa ya yi yana tsaki"bari Iro
ace wai mutum ya haɗa mata amma kaf ba tagari kalli ace wai megida a gidansa amma
abinci mai ɗanɗano ba za'a iya yi masa ba kullum rana ta Allah ina jiyo ƙamshin
abincin gidan margayi kona gidan Nuhu amma ni matana sai son zuciya da burin tara
abin aljihu",tsakin shima ya yi"muna ɗaya dakai ai muje muci abinci mai kyau da
kuɗin mu kowacce shegiya taci wanda ta girka tunda haka sukace",wucewa sukai zuwa
ga wajen me shayin da su Ashiru ke hira, kallon su Ashirun ya yi yana son yin
dariya yana tsoro amma shida Ibarahim da Haruna sai dariyar ciki suke suna gani
suka zauna kowa yace abashi indomie guda uku manya da ƙwai huɗu sai shayi da
biredi,ba a ɗau wani lokaci ba aka miƙo musu nan sukaita zaƙal ƙala tashin duk
yawan abincin sukai tas sannan suka biya kuɗin kamar wasu samari suka koma gefe
suna hira amma kaf ta baje sirrin gidajen su ce sai bawa juna muguwar shawara suke
a haka suka rabu,Ashiru ne ya kalli Haruna da Ibrahim ya kwashe da dariya sunsan
halinsa sarai akwai jan magana"gaskiya ƴan uwa mun mori iyaye bari kuga zuwa goma
ƴan matan gidan ma zasu fara zuwa siyan tasu haka ma su Sumayya wallahi gwarama su
musu aure har tausayi suke bani ace agidanku ba za a girka mai daɗi ai dole suyi
son kuɗi","zancenka haƙƙun yanzu su Maryam duk randa suke son abu bamu da kuɗi ko
to su suke haɗawa ko su faɗawa Babban Yaya a kawo musu kaza kuma wallahi ko taya ne
sai ya kawo musu in ba ranar ba washegari",cewar Ibrahim"hakane nima ni ɗaya amma
matar nan da kuɗinta take mana abu ni da Baba kasan ƴar kasuwa ce",Haruna ya faɗa
kwashewa sukai da dariya suka tafa,Ashiru yace"wallahi Ibrahim Nabilan gidan ku
nake so to amma nasan ita bata sona dan nasan tana da saurayi ko na ma ta magana
bazata saurare ni ba","kai haba amma nayi farin ciki sosai da kaina zan ma ta
magana shi wanin na yafi nagida ne ai ka kwantar da hankali kawai kamar ka samu ƴar
farar yarinyar nan suka saka dariya","sannunku sarakan gulma",juyawa sukai sukaga
Babban Yaya"a a Babban Yaya yau kuma yawon dare kaje","kuji min yara yawon dare
saikace wata mace karuwa,ban sani ba ku biyoni gida akwai maganar da zamuyi ko
kuma ku bari ma haɗu a masallaci da asuba naso harda sauran amma nasan ba zasu
fahimce ni ba kawai iya ku kuɗin ma haɗu",tom suka amsa sannan ya wuce gida garejin
gidan Iyyo ya shiga ya aje mashin ɗin sannin sunyi bacci yasa bai shiga ciki ya
fito ya shige gida,tsakar gidan shiru sai ya wuce ya buɗe ɗakinsa ya shiga ko ina
ashare tas har turaren wuta aka saka kuma yasan aikin su Maryam ne sun san shi baya
shiri da datti.

Vote
Share &
Comments
Ƴan uwa

Û̬m̬̂ m̬̂ û̬ ŝ̬â̬d̬̂ d̬̂ î̬q̬̂


🌈🌈🌈
🌈🌈
🌈

*𝗕𝗔𝗕𝗕𝗔𝗡 𝗬𝗔𝗬𝗔*
𝚁𝚎𝚗𝚎𝚠

Story & written by


*FATIMA AMINU*
*Ummu Saddi'q*

6️⃣
chapter

shirt ɗin dake jikinsa ya cire ya zauna bakin katifa yana sauke numfashi maganganun
mutumin da suka haɗu ɗazu na faɗo mai aransa wane irin aiki zai bashi da yace dama
mutum irinsa yake nema ya yi iya tunaninsa amma bai hango komai ba da sanyin jiki
ya miƙe ya ɗau riga mara nauyi yasa ya fito tsakar gidan zuwa ɗakin Umma tana zaune
dasu Maryam ana shaƙiyanci ita kuma tana musu dariya,ya yi sallama ya shigo"Babban
Yayan mu ba irin nakowa ba sannu da zuwa"suke faɗa,kaɗa kai ya yi"Allah ya shirya
minku kuna nan kuna zuba ba kuyi bacci ba",dariya sukai sukace"kai muke jira ka
kawo mana tashi watstsake",hararar su ya yi"a a tashi aguje zan kawo muku yau bani
da kuɗi kunga wata yaje ashirin kuma na biya bashi da kaf kuɗin ko account ɗina
wayam yake sai dai in Umma ce zata zuge wannan babbar lalitar tata ta bamu mu siyo
ƙwai da hantun"ya faɗa yana kallonta","mai ƙwan zan baku ku siyo ba ƙwai kai wuce
ka bani wuri","to kunji ku bari gobe zan samu wasu kuɗi jibi duk Katsina zamu sada
zumunta tunda kunga juma'a ce ranar lahadi saimu dawo",ihu sukai aka kashe
hannu"Allah ya biya Babban Yaya"saiku faɗawa Ruma",suka ƙarasa "da ƴar rigimarka ba
kasan ko a ƙasa zamu saitaje",ɗan murmushi ya yi"na sa ni ai harda ita","tom Babban
Yaya",Ummace ta kallesu"in kun gama zubar saiku ɗakko masa abincinsa",Aziza ce ta
miƙe ta ɗakko masa nan ya zauna yaci sannan ya fice yana musu saida safe,Umma ta
kallesu"kuma ku koma ɗakinku gasu Nabila can duk sunyi bacci ammanku kuna nan aje
magana",tashi sukai suna dariya"Hajiya Umma mai komai dozin mun tashi saida
safe","zan kamaki Aziza badan karatun bama da acan wurin Mubaruka za'abarki
wallahi na rage wannan hayaniyar",baki ta turo"ni bazan zauna ba inda ba ke"tashi
Umma tayi ta kama haɓa da mamaki "me kika ce Aziza ke da zakiyi aure ki ke maganar
bazaki zauna in da bani ba",baki ta zumɓuro"to basai mu tafi tare ba",daƙuwa ta ma
ta"tunda agarin mahaukata muke ko "Ibrahim dake shigowa ya katseta","yauwa Babana
faɗa ma ta dai ai ni bansan bata da hankali ba sai yau","bama sai na faɗa ma ta ba
in ranar tazo saita ɗauke ki ma ta tafi dake malamai ku wuce sai soki burutsun fara
jin bacci kuke",dariya sukai"Umma saida safe"da Allah ya kaimu ta bisu nan shima ya
ma ta saida safen ya fita shima,Umman zama tayi jikinta a sanyaye Allah dai yaba
yaranta miji nagari,sai bayan Babban Yaya ya fita ta tuna bata faɗa masa mutuniyar
ba lafiya ba,amma ta bari da safe ta faɗi masa sai dai bata son tada rigima tasan
tabbas yaji abin bazai taɓa mutuwa ba sai dai ikon Allah dan tasan shi akwai haƙuri
amma zuciyar dake jikinsa tafi ƙarfinsa in ya yi fushi musamman akan Nana to
tanƙwarashi baya yuyuwa ta daɗi,tana nan zaune saida kowa gama shigowa sannan ta
rufe gidan ta kwanta,a falo ita dama anan take kwana tace me ƴaƴa mata baiga ta
bacci ba a ƙuryar ɗaki duk da tasan gidan da maza kuma da kariyar ubangiji wadda
take roƙa kullum.

Yana ji kowa ya kwanta sannan ya fito ya ɗebi ruwa a rijiya ya shiga wanka
dan shi ya saba da wanka kafin ya kwanta kodan ya yi boading ne oho wankan ma acan
har gasar sa ake dan kar ace maka ƙazami gasu maza kaji wani ɗakin ɗum da ƙauri
kamar riƙaƙƙun bunsuraye,bai shafa mai ba ya dai goge jikinsa tsaf ya ɗakko
kayansa farare tas yasa sannan ya janyo ƙaramar laptop da Alhaji Baffa ya siya masa
ya kunna kallo,anan gefen katifar ya jingina ya ajeta aƙasan carfet ɗin,kallon yake
amma gaba ɗaya fuskar Nana ke a idonsa kashewa ya yi ya kwantar da kansa a jikin
katifar ya lumshe idanuwansa ya fara magana shi ɗaya"ina ƙaunarki Aisha amma baki
isa aure ba naso nayi rayuwata dake ɗaya saboda ba wata mace da zata samu gurbin da
ki ka samu a rayuwata baki ɗayan ta,amma ke tawace na tabbata ko zanyi mata uku
kece ta huɗu saina mallake ki ko bakya sona ni zan koya miki yadda zaki so ni",haka
yay ta soki burutsunsa ranar rabi bacci rabi mafarkin Nana ta girma suna zuba
soyayya ya yi.

Asubar fari na tashi da yunwa ƙafar ma da sauƙi tashi nayi na zauna Aunty Mama na
bacci nan kusa dani,fulas na hanga can wajen inda take sallah saukkowa nayi na buɗe
shi abincin ciki da sauran ɗumi bakina na wanko nazo na fara ci kaɗan na rage
asannan akai assalatu kamar a kunnen Aunty Mama ta sai gashi ta buɗe ido tana
addu'a akaina ta dire"ya ilahi Nana tashi ki kai da yunwa ko",kyaɓe baki
nayi"wallahi kuwa Aunty Mama kamar naci bashi haka naji shine naga wannan kwanon na
sauke kansa","ai dama naki ne saiki tashi muyi sallah ya ƙafar fa","da gudu kuwa
Aunty Mama da sauƙi ai ba sosai take yi ba shima hakan saina matsa","to sannu tashi
muje",kaf ƴan gidan kowa ya fito sallar asuba a bakin famfo duk anan mukai alwalar
sannan aka tafi bada farali.

Bayan idar da sallah a masallacin nan suka zauna dan suna tine da maganar Babban
Yaya,gaisawa sukai ajuna sannan ya kalle su"dama abinda yasa nace inason magana
daku shine so nake a junan ku kuna neman auren ƴan uwanku in babu acan akwai acan
karku duba alaƙa kuyi domin Allah saboda ko ba komai in akai wannan aure riba biyu
ce gata alaƙar iyaye ga kwanciyar hankalin kowa saboda duk wanda ya cutar da wani
kansa ya cutar ni dai wannan wata shawara na kawo karku sa dani aciki kunfi kowa
sanin halina waɗanda sukai dai dai na aura aciki babu su in ma akwai to ba a inda
nake muradi ba kuma koba yanzu ba zanyi",kai suka jinjina anan suke sanar masa sun
amince kuma zasu bi umarnin sa kodan ƙara zunmunci,ƙara tattaunawa sukai waɗanda
keda muradi dama suka sanar masa duk ya aminta dasu sannan suka ƙara
tattaunawa,atare suke fitowa a masallacin kowa ya wuce gidansu.

Vote
Share &
Comments

Û̬m̬̂ m̬̂ û̬ ŝ̬â̬d̬̂ d̬̂ î̬q̬̂

🌈🌈🌈
🌈🌈
🌈

*𝗕𝗔𝗕𝗕𝗔𝗡 𝗬𝗔𝗬𝗔*
𝚁𝚎𝚗𝚎𝚠

Story & written by


*FATIMA AMINU*
*Ummu Saddi'q*
7️⃣
chapter

Ɗakinsa ya wuce direct ya hau azkar saida ya gama tsaf sannan ya fito a ɗakin ya
shiga ɗakin Umma tana zaune su Maryam na haɗa koko da wainar gero suna rabawa a
ƙasa ya zauna yana gaisheta da fara'arta ta amsa,sannan suka kawo masa nasa kan
kujera ya koma ya dubesu"yau waye ya yi wannan wainar",Nabila ce tai saurin cafe
maganar tana dariya "ba anan akaiba Iyyo ce tayi wai tana sadaka saboda kar bakin
mutane ya kama Nana tsiwa","sadaka kuma akan Nana me akai ma ta kuma take sadaka
saboda ita","wai faɗa sukai da Humairan gidan Kawu Iro shine bayan sun dawo gida a
hanyarta ta zuwa gidan nan suka tare ta shi kawun da Humairan suka ma ta duka harda
targaɗe",tun kafin ya gama ji ƙwarewa ya yi ya hau tari baji ba gani amma kaf
maganar sannun da ruwan da ake basa bai bi takansu ba ya fice a fusace,Umma ce ta
ɗirka ma Nabila dundu"agidan ubanwa aka ma ta targaɗen kawai ƙarawa abin fetur
Nabila kinfa san halinsa irinsu guda da Iyyo amma shine ki tsaya iya gaskiyar abin
ma bazaiyu ba shine harda sheri"sosa wurin tayi"wallahi Umma ina sane yaran basu da
kunya shekaran jiya fa cemin tayi shegiya na barta ne kawai saboda Ya Ashiru yace
na barta kinsan ina ganin mutuncinsa","zaki ga ma kafi mutunsa ke dai kika sa ni,
yanzu Allah kaɗai yasan me wannan safiyar zata haifar","ai gara ya yi musu kaca
kaca kinsan dai kawu Iro mugun tsoron Yaya yake wai ƙirar samudawa gareshi ya
danƙeka zakaci ubanka kinsan tunda yawa Garba dukan tsiya yake shakkarsa saboda
sunfi su goma amma sun kasa ƙwatar Garba kuma kinsan me ya yi to Aunty Maman ce
tace yazo ta aikeshi yace ai itama ta haihu ta aiki nata","kai Nabila bansan
sharri","shike nan Umma ki tambaya Ya Ruma a gabanta akai Iyyo harda kaɗa
jarka",dariya Umma tayi"kai Iyyo Allah dai yaja kwana su kuma Allah ya
shiryesu","ameen Umma harda mu",Maryam ce ta galla ma ta harara"kai Nabila akwai
magana ana hutu wannan karon gidan Honorable zan fece dama Adda Usanina ba surutu
gareta ba kuma kullum yara makaranta suke wuni ko ba komai bawa ya shawo ac","tare
zamu ko"Aziza ta tare zancen","kutt kibi wa wallahi nemi wurin zuwa ko kuma ki tafi
can Kaduna ku cancare keda Ya Hasiya dama kinga Ya Hashim nacan","ai shike nan
canma ai akwai ac manya ma",Umma dai najinsu suna tayi kamar walƙiya Nabila taja
hijabi"na tafi wurin Iyyo muyi hira","kin tafi gulma dai",Khadija da ta shigo ta
amshe zancen"kai Ya Dijama","ba wata Ya Dijama shige kya bamu labari",tana dariya
ta fita.

Kamar daga sama Mama taganshi ya shigo a fusace tasan halinsa sarai in ranshi ya
ɓaci bai iya control ɗin fushinsa ba"Habibu ƙalau ka ke kuwa","Mama ina Nana","tana
nan ɗakinsu mana",ina jin muryarsa nasan cewa a kunne yake dan haka da sauri na
tashi tsaye ina ɗingishi na nufi Aunty Mama,kallon mamaki ta shiga bina dashi ganin
na sauya tafiya lokaci guda zatai magana na rigata cikin shagwaɓa da hawaye
nace"wallahi Aunty Mama ƙafar nan kamar na cire na yar haka nake ji zafi take",haɓa
ta kama zatai magana aka ɗaga labulen ana sallama,kaɗa kai Aunty Mama tayi sai
yanzu ta gane kan abin mamaki ne ya kasheta wai ina nufin wannan makirci
nayi,amsawa tayi"shigo mana Habibu",shigowa ya yi ganin ina kuka yasa ya duƙusa
kusa dani"sannu kinji Darling saina rama miki kema",a gwiwarsa na kwantar kaina
shafa kan ya yi yana haɗiyar zuciya,kallon rashin fahimta Aunty Mama ta shiga yi
masa badai akan wannan abin yake wannan uwar haɗiyar zuciyar ba,da idanuwasa da
sukai ja ya ɗago ya kalleni"zaki iya tafiya",kaɗa kai nayi na taɓe baki ina
kallonsa hawaye na zuba,share min ya shiga yi"am sorry kinji sweety tashi muje zan
riƙeki ",miƙewa na yi hannuwana a nasa muka fita,ajiyar zuciya Aunty Mama tayi
tafara magana a fili"kan uba akwai babbar cakwakiya nan gaba kaɗan a wannan
ahalin",fitowa tayi taga Mama tsaye da ludayi tayi foster,dariya tayi ta
taɓata"Dada ƙalau kuwa kuwa","inafa ƙalau kalli yarinyar nan bata warke ba amma
yana zuwa ta zama kamar wata jaririya kalli yadda ya wani tarota kya rantse wata
uwar mata ce ke naƙuda",kwashewa da dariya tayi"au danma ba'a gabanki akai film ɗin
ba kenan yi aikin ki fansa ta biyu za'a ɗauka","to Allah ya kyauta duk akan wannan
uwar tsiwar ake wannan jelen",ta shige kitchen Ƙarami da Ya Ruma suna kwasar
dariya suma.

A ƙofar gidan sukai karo da Humaira kan tayi wani abu ya ɗauketa da mari saida ta
faɗi,nan ta buɗe baki zatai ihu ya ɗora hannunsa akan leɓensa"shiiii kina tari
saina murjeki anan wurin wawuyar banza kawai"gum tayi tana jan numfashi,tsawa ya
daka ma ta"muje ciki inga kawun a gabanshi zan farfasa miki jiki harda nasa duka
duk zan haɗa na miki tunda ina da tarbiya bazan iya dukansa ba",sumi sumi ta wuce
gaba,ko sallama basu samu arziƙinta ba sai ganin Humaira sukai dafe da kunci muna
shigowa kawu ya zabura"kaima rama matan kazo yi saboda an taɓa ƴar gwal ko","eh
kawu shi me gaskiya masoya gareshi fili da ɓoye",ƙara hayayyoƙo wa ya yi"wannan
fitsararriyar yarinyar itace mai gaskiya",katseshi ya yi"ga fitsararru nan ka tara
a gidanka duk sun fitsare ƙafarsu yasa basa ganin girman kowa ciki harda
kai,wallahi kashedi nazo nayi koda wasa wani daga gidan ya kuma dukanta saina nasa
shi jinya ke kuma fuska kamar jiƙaƙƙen abinci in ki ka kuma jan wani faɗa bama ita
ba zakiga yanda zanyi dake",cikin ɗaga murya kawu yace"kace harda ni a kashedin
mana kaga yanda zanyi daku",shima muryar ya ɗaga masa"ai gida nace kaga kuwa igiyar
gugar gidan ma harda ita bama kai ba,muje kinji Darling sis","tom Darling
Bros",muka fito kowa ya kasa cewa komai sai Jammai da ta sheƙe da dariya"amma anji
kunya Iro ɗanka yazo har gida ya yanka maka kashedi kuma ka karɓa",zaburowa ya yi
kamar zai duketa"ki iya bakinki Jummai zan karya ki fa",wani gantsarewa tayi"haba
saikace Saude kai kasan ko mota zata karya ni ne saboda ƙarfin gudu amma ba wai dan
girman jiki bare kai kamar ana ɗibanka ana miya",ta buga cinya ta
wucewarta,fuffuka da zage zage ya shiga yi amman a banza tunda wanda yake dansu
basu san yana yi ba.

Bamu shiga gidan ba muka shige gidan Iyyo tana zaune kan tabarma a baranda ta gama
sadakar"a a kune haka da sassafe ya yadai langwai ƙafarce har yanzu",kyaɓe baki
nayi"eh Iyyo","sannu kinji ai har gida naje naci musu mutunci babu mai ƙara
taɓaki","nagode Iyyota","kai kuma ina kakaita haka","nima kashedin naje
nayi","yauwa ɗan albarka shi yasa nake sonka to kuzo ku zauna"hira mukai tayi har
wajen tara da rabi sannan ya maida ni gida ya wuce.

Wajen goma da wani abu Umma tazo suka shiga wajen su Iyyo suna tsakar gida
suka shigo,tabarma Iyyo ta shimfiɗa musu sannan suka gaisa Alhaji Baffa ne ya
dubesu da gani yasan akwai abinda ya kawo su"Sa'ada lafiya dai ko","dama Baffa akan
yaran nan ne Habibu akwai wata yarinya da yake nema to iyayenta sunce ya turo in da
gaske yake asan da maganar kafin yarinyar ta gama makaranta a tsaida
lokaci",numfashi yaja"hakan ya yi kyau dama anan ma inaso su gama karatun yaran nan
mata a tsaida musu da lokaci suma amma tunda hakan yazo ki turo min shi ya kaini
gidan su yarinyar tunda wanda ya kamata yaje bayanan","to shike nan za a turo maka
shi insha Allahu mungode Allah ya ƙara girma zamu koma Hajiya iyyo kakar Nana","ku
faɗa da ihu wato harda ke ko Sa'a",dariya sukai nan suka fito Iyyo na musu a
gaida,bayan fitarsu Iyyo ta kalli Alhaji Baffa tace"Alhaji infa Habibu zai auri
mata uku sai an cika min alƙawarina kan na mutu kai ko bayan na mutun ma ayi",Insha
Allahu kuwa A'i zaki farin ciki ke dai Allah ya bamu lafiya da tsawon kwana","to
amin Alhaji amma nikam yarannan mata masu auren suna da yawa fa",eh mazan su sai
gaba gara kowa ya yi ƙwari tukun bana son yawan haya A'i kowa ya gina gidansa duk
ƙanƙantar sa haya masifa ce musamman su yara ace kullum kana kwasar kaya kana sauya
wuri wataran ma tashinka za'ayi baka shirya ba kuma balallai ka samu inda zaka
zauna adaidai lokacin ba ko kana da kuɗin kamawar,amma kinga ni yanzu inada inda
kowa zai gina in bayason wurin sai ya saida yaje inda yake so ya saya ya gina ni
duk maiso ma aginin zansa hannu miye amfanin kuɗin dana ke tarawa tun ina
jeji","Allah sarki Alhaji Allah ya biyaka ina alfahari dakai a kullum baka duba
yadda sauran ƴaƴanka suke maka duk da bani na haifesu ba wallahi Alhaji bana son
abinda Rabilu da Iro keyi kalla Nuhu baya yi amma su sai suna nuna ba'a sonsu
kullum,amma shawara guda yaran nan kawai duk maison auran ya yi ","to shike nan
Allah ya zaɓa mana abinda yafi zama alkhairi,su kuma ki barsu ai Hamisu da Sadisu
saida naci musu ƙaniya sannan suke shiga cikin su Ashiru dama shi Haruna bashi da
matsala","hakane kam to Allah ya shirya","amin A'i bari naje nan wajen Malam Bala
akwai maganar mu dashi","adawo lafiya a gaida shi".
Umma gida ta wuce wai ta tafi dambu dan yau akwai manyan baƙi Ya Fatu da Ya Ushe na
tafe shi yasa bata shiga ba Maman kawai ta shige itama.
Umma na shiga yana fitowa a ɗaki"a a sai ina kuma Habibu","Umma zani wajen
wani bawan Allah ne daga ganina akan titi yace wai nayi masa dama yana neman mutane
irina","ikon Allah to me kayi da ka birgeshi haka","wallahi Umma daga rabon faɗa
kuma ɗaya ne keneman cutar ɗaya kuma mai cutar yafi wancan baki duk ya zaƙalƙake ni
kuma na fahimci me ke faruwa shine nashiga fa ashe mutumin kuma akan idonsa akai
komai shine yasa aka masa magana dani yaban adress wai nazo yau dama yana da
matsala yana neman mai masa maganin ta,shine zanje","to kayi addu'a Allah ya baka
nasara mai ɗorewa a dawo lafiya yauwa inka dawo Alhaji Baffa na neman ka","ameen
Umma nagode in na dawo zanje",ya fito su Maryam na masa Allah ya bada nasara.
Bayan Rabuwar mu da Babban Yaya na ware ƙafar na miƙe Ya Ruma ta kalle
ni"ubangiji ya shiryeki Nana waike nan makirci ki ka ƙulla wallahi ki kiyayi kanki
ko kuma ki jajubowa kanki masifa Allah ya haɗaki zaman aure da kishiya",wani juyi
nayi agabanta na haɗa hannu na buga"he he he Ya Ruma ai ni dama bazan auri saurayi
ba me mata zan aura shi yasa ki barni na goge tun daga yanzu",ranƙwashina naji anyi
na dafe wurin na harba can bayan Ya Ruma ashe Mama ce,daƙuwa ta min"wallahi Nana ki
kiyayeni ƴar ƙarama dake sai zancen manya mijin ma ashe kin ware wanda zaki
aura"baki na buntsuro ina buga ƙafa a ƙasa muhucin hanunta ta jefa min"ja'ira zoki
wuce ki bar wurin nan ko in kamaki in miki dukan tsiya",ihu na ƙwala"Aunty
Mamataaa",da gudu ta fito daga ɗakin zaninta a hannu"Nanata! Nanata!!waye ya
taɓaki,zagayowa nayi na koma bayanta na rungumeta,haɓa Mama ta kama"yau naga
takaina ni Halima bari dai na fita shirginku keda uwar taki",ta wuce kitchen,kama
hannuna Aunty Mama tayi muka shige ɗaki Ya Ruma sai dariya take dan gidan mu ba'a
faɗa sai dai dariya,muna shiga ɗakin Aunty Mama ta kalleni tace"buduruwar Yayanku
wacce irice",kwashewa nayi da dariya"wallahi Aunty Mama banufiya ce","banufiya
kuma","eh wallahi Aunty Mama har yaren suke kinsan nasan Mama Mari to kallar yaren
komai da komai",dariya Aunty Mama tayi"kice tafi ki komai koda nan gaba kin
girman",wata zubura nayi na miƙe daga kan kujerar"kaiii da wannan bajajjen hancin
Babban Yaya fa yace ba macen da zata kaini haɗuwa idan na girma","au haka yace
shima","eh mana","to shike nan saiki dage kina cin abinci kina kumari karki girma
ki zama kamar sanda kinga yace baya sonki ko",kuka na saka"wallahi kina bani abin
sa kumarin dan wallahi Babban Yaya nake so","ai nasan da hakan dan haka duk abinda
na baki kina cinyewa banda wasa","na yarda Aunty Mama","to goge hawayen naki kinga
ma Ummansa da ƴan gidan su kowa nasonki kirki na musu tsiyar taki","ai banayi kuma
nima ina sonsu ai","to shike nan kwanta ki huta kiyi baccin ki abinki","to Aunty
Mama"na kwanta kuwa dan tasan halina da bacci muna shiri,kai ta girgiza kawai ta
fito suka kama aiki da Mama nan da nan sukai dukkan abinda zasuyi kafin azahar
saboda baƙin.

Vote
Share &
Comments
Ƴan uwa

Û̬m̬̂ m̬̂ û̬ ŝ̬â̬d̬̂ d̬̂ î̬q̬̂

🌈🌈🌈
🌈🌈
🌈

*𝗕𝗔𝗕𝗕𝗔𝗡 𝗬𝗔𝗬𝗔*
𝚁𝚎𝚗𝚎𝚠
Story & written by
*FATIMA AMINU*
*Ummu Saddi'q*

8️⃣
chapter

******
Babban Yaya gidan Iyyo ya shigo yana sallama,kamar zubar ruwan sama ta
tareshi da magana"malam Habibullahi sai ina haka aka sha shadda","Iyyo kenan tamu
ta mutunci albarka nazo asamin zani wani waje duk da bansan dalilin kiran nawa
ba",yashe baki tayi "to Habibullahi nawa ni kaɗai Allah ya haska fuskarka akan tasu
ya baka nasara ha haska maka alkhairin dake cikin lamarin",kusa da ota ya duƙusa
dan yaji daɗin batun ta"ameen Iyyo ta nagode sosai da wannan addu'a Allah yaja
kwana ya ƙara lafiya,Alhaji baya nan","eh amma baiyi nisa ba kabi ta hanyar babban
titi zaka samesa anan wajen wannan abokin nasa",tashi ya yi"tom Iyyo saina dawo","a
dawo lafiya Allah ya kiyaye","ameen ameen Iyyo ya fita,ta can inda ta faɗa ya biyo
yana nan kuwa,tun daga nesa suka hangoshi nan malam Bala ya kalli Alhaji Baffa
yace"Alhaji a gaskiya kayi dace da zuria kalli jikanka namijin gaske yana birgeni
yaron yasa mu tarbiya sosai",ɗan murmushi ya yi"ni kaina ina son Habibu ya ɗauke ni
mahaifi ne ba kaka ba yanzu haka ka zuba ido kayi kallo abinda zaiwa mahaifinsa shi
yazo yamin","kamar ya fa Alhaji"bai bashi amsa ba ya ƙaraso wurin yana
sallama"Assalamu alaikum manyan tsofifin wannan ƙasa",ƴar dariya sukai"amin wa
alaikumul salamu Habibu manyan yaran wannan ƙasa",ɗan murmushi ya yi ya durƙusa"ina
wuninku",cikin fara'a suka amsa sannan yacewa Alhaji Baffa"Alhaji zamu wani wuri
asa mana albarka",murmushi ya yi"to Habibu Allah ya bada nasara ya bada sa'a a kula
da kalar mutanen da za'a shiga cikin su, kasan mutane adole duk inda zaka shiga sai
kaga masoya da maƙiya dan haka ayi a hankali da mutane","nagode Alhaji kuma zanyi
sai na dawo kiran da ka ke min ma in na dawo zanzo","to adawo lafiya Allah ya bada
nasara","amin amin",daga haka ya wuce zuwa bakin babban titi dan ba da mashin zashi
ba,yana bada baya abokin Alhaji Baffa ya ɗora"gaskiya ka faɗa Alhaji Allah ya musu
albarka ya haska rayuwarsu","amin nagode sosai Malam".

******

GIDAN GWAGGO MA'U:


Ƴar wayar nokia ta Gwaggo Ma'u keta tsuwwa,kware murya tayi tana magana"ke Hadiza
miƙomin wayar nan mana kinaji tana ta ƙara",Hadizan ma cikin ihu ta maido ma ta da
maganar"nifa aiki nake kizo ki ɗauka mana","inye dani kike Hadiza",kumbura baki
tayi"to a zaune fa ki ke kuma nasan wannan ƴar takurar ce Ya Aisha tun ɗazu take
kira kuna magana amma kunƙi gamawa itama dama ga gulmar tsiya",a fusace Gwaggo Ma'u
ta taso zuwa ɗakin kanta ta hayayyaƙo"zanci ubanki ƴar iska mara kunya kin min
shiru ko kuwa",baki ta muguɗa ta kauda kai tana ƙunƙuni,wayar ta ɗauka tabar wajen
tana ɗagawa,
"Halo wake magana ne",daga can ɓangaran aka amsa cikin laushin murya"kai Umma kinƙi
ki waye kullum na kiraki saikin ce waye","ai Zainaba ce","nice Umma ya
gidan","lahiya lau ya megidan da yaran","kowa lafiya Umma zamu shigo ai wani
satin","to Allah ya kaimu ya maganar mu dake",ɗan jim tayi"gaskiya nifa Umma bazan
iya waɗannan abubuwan ba mijina namin komai bana neman abu a wajensa in rasa to
Umma miye na mallake shin",tsawa ta daka ma ta kamar tana gabanta ne"ke dalla
wawuya rufen baki ai abinda za'a masa ba wai saikin tambayesa abu ya kamata ya miki
ba da kanshi zaina dunƙula ya baki ba kya kallon waɗannan yaran su Fatu harfa mota
ce dasu ga filaye suna siya","to Umma ca aka miki malamai suke bi, su ɗinma dukkan
su tsantsan biyayya ce tasa suke samun cigaba a gidajansu da rayuwarsu",katseta
tayi"rufen baki shashar banza ana nuna miki gabas kina ga yamma","ni dai Umma kibar
maganar nan gaskiya",ta kashe wayarta tana fashewa da kuka a fili ta fara
sambatu"wannan wacce irin uwace haka ace dakanta take nu na miku inda zaku halaka
wallahi bazan bi ba saidai tamin ko me zata min amma ni mijina da zuciya ɗaya nake
sonsa kuma da ita zan zauna dashi",ta goge hawayenta ta gyara fuskarta sannan ta
fito a ɗakin,da sauri ya shige ƴar kwanar wajen ɗakin dan kar ta ganshi komai take
faɗa ya gama jinta tsaf wani so da ƙaunarta yaji yana daɗa yi kuma zai ƙara
jajircewa wajen ganin ya kyautata ma ta shima.

A kan tabarmar da take ta wullar da wayar tana tsaki"wannan ƴa ko shegiya dama


nasan bazata amince ba yanzu ƴan kuɗin da malam yace in na kawo mutum zaina bani
tamin buƙulu wawuyar yarinya kawai amma tunda Aisha ta amsa tasan zata samu wani
abu mai tsoka ta wajenta",sallamar da ake tasa tai shiru tana amsawa,haɓa ta
kama"au Fatsima ke ce ke doka sallama haka kamar kin shigo gidan mutane dubu",ƴar
dariya tayi"to Umma in banyi sallama ba kai tsaye ki ke so na shigo",dakatar ta
tayi kamar kashi na ma ta magana"naji ni yimin shiru ni miye wannan a
hannunki","cefane ne Baba yace na taho dashi","mitsss nazata ma saurayi kikai
kukaje ɗan yawo aka kawo min ƴar kaza",da mamaki take bin Ummar tasu da
kallo"saurayi kuma Umma sannan da bakinki ki ke ambatar yawo Allah ya tsareni koda
kuwa ke kinason hakan,kuma dan uwar saurayin koda wasa yace muje yawo saina jefar
mai baki da dutse wallahi",ta aje ledar ta shige ɗaki,da harar tabi bayanta"banza
wawuya wallahi keda Zainaba banyi dacen ƴaƴa ba gara ma ita ni na haifa amma
kam"sai tayi shiru ta janyo ledar tana buɗawa,wani koren tattasai da attaruhu ne
sai wani tumatur ƴan ficifici kamar tumaturin tsohuwa"na shiga uku ni Asama'u yanzu
shi Ya'u wannan kayan miyan ne saikace na wasan yara wallahi bazan girka komai ba
sai dai kowa ya zauna da yunwa",Hadiza dake fitowa a ɗaki ta kalle ta kamar wata
sa'ar ta"wallahi ke zaki zauna da yunwa Umma shi dai kinsan kullum yana tuburin mai
shayi kuma ai ba zaman banza yake a wurin ba zaici ya ƙoshi abinsa,mu kuwa kinsan
ba mai zama da yunwa gwarama waccan ustazar dama nasan Baba dan ya mana mugunta
yasa yace bazamu zauna a can layin su Alhaji Baffa ba,dan yasan ko ba komai zamuna
shiga muci tsamiya girkin tsaffi da nama amma na gidan yara kamar a gidan
yari","gaskiya ki ka faɗa kuma Hadiza ai kuwa wannan gidan saimun komashi zani na
lallaɓa Alhaji ya bani mukulin mukoma shi sai ya zauna anan shi ɗaya",wani tafa
cinya tayi"gwara dai Umma dan kuwa kinsan zaice bazai bimu ba","hakane fa Hadiza
komawa kamar da ƙasa",
Ana kiran isha wani yaro ya shigo gidan yana susar kai"wai ana sallama da
Khadija a waje","kace ina zuwa",yaron ya fita yakai saƙo ga wanda ya aiko shi
sannan ya wuce,ɗaki ta shige aka shafa turare mai mugun ƙamshi wanda ko mai aure ta
shafa ba lallai ta wanye ƙalau ba wajen maigida bare budurwa wadda manemi take jira
wasu riga da siket da suka matseta tasaka sannan ta yafa mayafi bashi da maraba
dana after dress ta ƙara fesa wani turaren sannan ta sako takalmi mai tsini ta fito
sama da ƙasa Fatsima ta kalleta tana gyaɗa kai tai gum dan tasan tana ma ta magana
bazasu wanye ƙalau ba,ta gaban Umma ta wuce ta fita amma batai ma ta magana ba,tun
da ta fito yake kallonta ta mudubin motar shafa kansa ya yi yana cizon
yatsa"gaskiya yarinyar nan ta haɗu akwai kaya shi yasa su Mannir suka maƙale ma ta
kenan"katse masa maganarsa tayi da ta ƙwanƙwasa glass ɗin motar,zugeshi ya yi yana
murmushinsu na manyan mayaudara"ahhh Baby shigo mana tsaiwa anan ai ba girmanki
bane",murmushi ta saki sannan ta buɗe ta shiga","Hii"tace tana tsuke leɓe tana juya
ido,wani shork ne ya kamashi ya fara murza hannu"Hello Baby ya ki ke","normal ya
garin",kafaɗa ya ɗaga"gashi nan sai a slow amma danai arba dake sai nake ji normal
nima",wata ƴar dariya tayi tana kallonsa"Allah ko amma ban ganeka ba","ohhh am
sorry Baby daga zuwa na kama miki surutu ban gabatar miki da kaina ba ko sunana
Sultan anan ƙasan ku nake ƙofar ruwa karki damu da sanin waye ni a hankali zaki
sanni muddin ki ka saki jiki dani dan gani ɗaya na miki na fara sonki amma sai yau
na gano gidanku",wani murza ido tayi"karka damu indai a wannan ɓangaren ne nima na
karɓeka hannu biyu","ok ina godiya ya
🌈🌈🌈
🌈🌈
🌈

*𝗕𝗔𝗕𝗕𝗔𝗡 𝗬𝗔𝗬𝗔*
𝚁𝚎𝚗𝚎𝚠

Story & written by


*FATIMA AMINU*
*Ummu Saddi'q*

Babban Yaya Free ne amma me so ya biyo ni Pc in sa a group don shagalin Nana na


buƙatar comments
08146711395

9️⃣
chapter

*****
Yana fita bakin titi ya tare ɗan keke napep ganinsa ɗan zamani ya miƙa masa
katin hannunsa''abokina wannan address ɗin zaka kaini fatan ka gane",ɗagowa ya yi
ya ƙare mai kallo"kace wannan address ɗin zan kaika kasan kuwa ina zaka shigo muje
fatan nima alkhairin ke kirana","au abokina wurin na musamanne kenan","kaidai shigo
a kyauta ma zan kaika fatan zaka haɗani nima da wanda zaka wurinsa","bazan maka
alƙawariba dan nima zuwan farko zanyi wajensa",burga babur ɗin ya yi suka ɗauki
hanya suna tafe sai hira auke har Rijiyar zaki shi kanshi layinda suka shiga sunan
dake cikin katin shine a jikin symboard ɗin mamaki ne ya rufe shi ganin kaf layin
gida ɗaya ne amma fanni fanni kuma kowanne da get ɗinsa da number sa,get dake
kallonsu anan ya faka sojoji sai zare musu ido suke,"ɗan uwa na kawoka fa",sakkowa
ya yi yana kallon get ɗin"wannan ne gidan da gaske","kalli katin hannunka mana
abinda yasa kagan munzo harnan ma saboda adaidaita sahu ne wai ko mata aka ɗakko
shiyasa muke iya shigowa har anan","tabɗi nawane kuɗinka","kawai kawo ɗan
uwa",hannu yasa a aljihu ya ɗakko kuɗi ya ƙirga ɗaribiyar ya bashi","nagode sosai
aboki",ya juya kenan ya dakatar dashi ɗan uwa ga number wayata in wata dama ta samu
digiri ne dani",dariya yayi ya ciro tasa ya miƙa masa ya karɓa yasa number ya
bashi"me zansa to","kasa Abubakar mai mashin",dariya ya yi"ni kuma kasa Babban
Yaya","yauwa zanma fi ganewa ba","to shike nan sai mun kuma haɗuwa",ya buga mashin
ɗinsa ya bar wurin,ƙofar gidan ya ƙarasa ya tsaya kawai buɗewa akai akace shigo
cikin mamaki da faɗuwar gaba ya shiga,gida ne ƙerarre na faɗa a jarida wani ne da
uniform yazo"bismilla ance na shiga da kai ciki"sadda kansa ƙasa ya yi yabi bayan
mutumin zuwa inda yaga ya dosa bin gidan da kallo yay tayi yara nata wasa wani
babban wuri suka nufa wani ginine a gefe kamar rumfa amma wurin ya ƙayatu ga
shimfiɗu na alfarma,mai masa jagorar wurin mutumin ya ƙarasa ya sunkuya daga baya
"rakai daɗe ga shi ya ƙaraso",ɗagowa ya yi yana murmushi"tom sannu Musa","ba komai
Alhaji",ya tashi ya bar wurin"bismillah mana Habibullahi","barka da warhaka
Alhaji"ya hayo wajen nan gefe ya zauna ",Alhaji ya dubesa "zauna da kyau mana kaida
kazo gida",gyara zama ya yi Alhaji yace"yauwa ko kaifa",wata ce da uniform itama ta
ƙaraso wurin ɗauke da tire babba a gabansa ta aje sannan ta juya"Habibullahi
bismillah","Alhamdulillahi Alhaji ina godiya","ba komai yarona"coffe kawai ya zuba
sannan ya dubi Alhajin"Alhaji gani nazo me yasa kace kana nemana",numfashi yaja ya
gyara zama sosai"Habibullahi nidai sunana Alhaji Aminu Tijjani inada yara bakwai
duk mata kuma basu yi girma ba kai yaran ma duka bamai sha huɗu,ina da mata huɗu
duka suna gidajan nan daka gani a lungun nan,ɗan kasuwa ne ni inada company guda
uku fitattu a duniya sannan inada hannun jarika masu yawa a duniya, a gaskiya tun
ganina dakai na wancan ranar naji kamin nai maka kallon ɗa kai tsaye shi yasa nace
kazo inada matsaloli dayawa wanda da ace inada ɗa namiji nasan zai shige min gaba
saboda na kawo inda ƙarfina ya yi ƙasa kuma duk na tare dani suna son suci riba
dani ne ko amin wayo kuma harda na tare dani masu min aiki manyan wato manajojin da
na ƙasa dasu,a yanzu wani lamarine ya taso kuma nayi iya bincikena naga kamar ba
riba aciki sannan abin ya zama kamar gasa ne inaso na zame kuma bana so suce tsoro
naji kasan dai masu kuɗi da ƴan kasuwa yanda suke","hakane Alhaji kukam akwai
abubuwa dayawa na ƙalubale a gabanku kuma kuna ƙoƙari sosai","Habib wannan abu ba
komai bane wani company ne a America na ƙera motoci kaf companyn shine na ɗaya
aduniya gun sarrafa mota kowacce irice hannun jari zamu saka a wannan ma'aikata na
zunzurutun kuɗi dala ba naira ba dala million dubu biyu a ayanda tsarin yake zai
zama a komai da za'ayi ba mutum ɗaya zaina fitarwa ba rabawa za ayi kai ɗaya kowa
ya fitar nasa inda yake so to wannan abu yasani a ruɗani sosai ina son shiga amma
bana so kai me kace",tagumin da ya yi ya cire yana duban Alhajin "tabbas dole kayi
tunanin wannan abu Alhaji kasan kuwa waye bature kasan wayonsa bazai taɓa haɗa abu
dakaiba muddin ba zaici riba sama da uwar kuɗinsa ba,a yanzu ku nawa ne ƴan wannan
ƙasar a cikin abin","to dai a yanzu waɗanda zamu sa hannu a Abuja zuwa dare mu
talatin da ɗaya ne amma ɗayan ba indiye ne","talatin Alhaji kana nufin ku talatin
da ɗaya kowa million dubu biyu tabɗijan amma baku da wayo wallahi gaskiya,a nigeria
akwai irinku dama to wallahi karma ku fara wannan ta'asar",murmushi Alhaji ya yi
yana jin daɗi aransa ganin yanda ƙaramin yaro har ta gano da illa a abin"ban ganeba
Habibullahi ko kuma ba dani zakai wannan ba dakai zamu tafi Abujan kawai ayi acan
ko",shafa kansa ya yi"dani Alhaji","eh mana kai ba ɗana bane suma suna zuwa da
ƴaƴansu kuma zaka gani in munje yanzu kasanar da gidanku zuwa la'asar za'a azo a
ɗaukeka kawo wayarka nasama number ta zuwa lokacin mai laukanka zai kiraka",bashi
ya yi yasa masa shima ya ɗauki tasa sannan ya miƙe"au tafiya zakai ",sosa ƙeya ya
yi"Alhaji ƙanwata ce Nana ba lafiya shine zanyi na koma na ganta"tashi ya yi shima
"lallai wannan Nana da alama itace ƴar tawa",ɗan sos ƙeya ya yi"eh to Alhaji amma
ai yarinya ce ba yanzu ba","ai wannan ba matsala bace yarona muje nasa akaika saima
kawai ya gano wurin basai ma ana masa kwatance ba","hakane rankai daɗe",nan ya
shiga gaba ya bisa a baya,wajensu Murtala ya nufa suna ganinsa suka miƙe"sannu da
fitowa Alhaji","yauwanku Murtala kai wannan gida ka gano hanyar zuwa la'asar zaka
koma ka ɗaukko shi","to Alhaji,rankai daɗe bismillah","ok Alhaji sai anjima","Allah
ya nuna mana Habib ka gaida min da Nana ka ma ta sannu kafin nazo dubiya",ƴar
dariya ya yi ya wuce dan har ya fito da motar nan ya shiga aka buɗe musu get suka
fita.
Sarakan gulmar unguwar majasar Iliya ne shayi na nan anyi do do sukaga babbar
mota ƙirar zamani latest ta parker a ƙofar gidan su Babban Yaya acikin ƴan wajen
wani ya kalli Ibrahim"IB kunyi manyan baƙi fa","wane irin manyan baƙi bansan gulma
fa","inafa gulma ka taɓa ganin kalar wancan motar a layin nan idan ba wucewa tazo
yi ba amma kalla yau a ƙofar gidan ku ta tsaya"..shiru ya yi sakamakon ganin wanda
ya fito a motar,kuma driver ya fito suka ɗanyi magana sannan ya shiga ya juya ya
bar layin,"kutumar kai IB ai Babban Yaya ne ya fito a motar can",wani ya faɗa yana
ɗakabmai duka acinya mgana daɗi kenan"wallahi ka isheni Rabi'u kaga nabar maka
wajen",yana wucewa suka dasa gulma daga ina yake kodawa ya haɗu haka dai sukaita yi
baji ba gani,Ibrahim ma bai shiga gidan ba ya wucewarsa ya shige gidan kawu Rabilu
an tafi musu dasu Sumayya da ya shiga ma basa nan suna gidan mu su Ya Fatu sunzo
ana faɗa masa shima ya shiga.
A tsakar gida yasamu su Umma suna tsigar zogale da sallama ya shiga suka
amsa"a a harka dawo",a kan wata kujera yaja ya zauna yana dubanta"eh Umma dawowa
nayi na shirya zamu Abuja da mutumin anjima da la'asar amma da alama sai gobe zamu
dawo","to Habibu Allah ya tsare ya bada nasara a kula dai da shiga cikin
manya","insha Allahu Umma","yauwa ga ƴan uwanka can sun iso gidan Baffan ku Fatima
da Usaina","kai kice akwai baƙi a gidan bari naje ma mu gaisa","to ni naje suma
yaran wasu nacan waɗannan dan su tayani aiki na hanasu zuwa","ai kuwa dai naje to".

Tun daga sallamarsa Ya Usaina ta fito da gudu"bi a hankali karki faɗi da yara
huɗu baki daina wawta ba",dariya tayi"ina Babban Yaya ai wannan halin bai ɓata
shima maigidan haka yake shi yasa abin yaci gaba","kun haɗu da aiki da to,sannunku
da zuwa ina yaran","sunacan sunbi Nana siyan wai alawar tsamiya","ita da ba lafiyar
ƙafa ba amma ta fita yawo","to kai Babban Yaya manta Nana kayi ne kai dai mu
shiga,Ya Fatu tace fushi ta ke da kai","nasani wannan Fatimar ƴar rigima
ce","wallahi dai kam",tai sauri ta dafe bakinta ganin tana harararta ashe tana
bakin ƙofar,shima murmushi ya yi yana faɗin"sakuwa waya taɓamin ke ne",da sauri ta
juyo"kutt wace sakuwar taka wallahi ka girmeni innakai shekarunka ai na banu sai
kishiyoyi","kai Fatu bansan me yasa bakyason kishiya ba","banaso kuwa amma shigo
dai mu gaisa hirar tafi daɗi a zaune",ɗakin fal ya ganshi ya shiga shima"kai aku
dalla kuyiwa mutane shiru","da sauri suka ɗago jin muryar Babban Yaya,Sumayya ce
tayi gyaran murya"ansutu ko mutum yaci naman me kilago yanzu",dole dariya ta
kamashi ya yi yana Sumayya daƙuwa"wallahi kun fiya surutu","kai Babban Yaya kaf
dangin yawa saika same su akwai magana","ai kuwa kune sample ina makaranta fa duk
naganku anan da ina cewa zamu KT gobe kuma wani uzuri ya taso min bazamu samu zuwa
ba sai dai kadan wani satin",kai Aziza ta dafe"kash an ɓata min shiri tabbas","ya
kuwa ɓatu tunda uzuri na yafi naki muhimmaci"nan ya zauna sukaita yi,hirarsu ba
ƙarewa take ba sai kiran sallah ne ya fito dasu nan duk suka tsaya a tsakar
gida"sannunku da zuba,dariya sukai suna faɗin"Aunty Mama zamuyi sallah muzo muci
alala da kunun aya","saikun zo Habibullahi ga naka can akula ka tafi dashi ","na
gode Aunty Mama",ya ɗauka ya fita,yana fita na fito a ɓuyar da nayi duk abinda nake
Mama na kallona"Allah ya shiryeki Nana",Ya Fatu na dariya ta amsa da "ameen Mama ai
da anyi hutu da ita zan tafi",tunkan ta gama magana nace"ban zuwa wallahi tabb ba
Aunty Maman acan ban iya zama","to ai sai kuyi zamanku","yauwa Ya Fatu unmm ina ma
wannan me aikin naki me bajajjen hancin nana",kai ta dafe"na shina ni Fatima ƴar
yayar Hajiya ce fa wannan da ki ka gani ba me aiki bace","yo Ya Fatu nan ƴar gidace
amma takeyi kamar ƴar wanke wanke",dariya sukai"Nana matsalu ita wannan haka take
ko agidansu har dukanta ake","to Ya Fatu ai ma ta aure ƙauye mana","Innanillahi
tayi auren ma ai Nana amma tana Abuja",zabura nayi kamar wadda aka faɗawa
mutuwa"Abuja dai Abuja tamu ta state and capital amma wannan miji ko ɗan iska shi
ya rasa wazai aura sai mai zubin ƴan ƙauye","ƙaniyanki Nana ke har kinsan matar da
ta dace a aura","lallaima ya Fatun nan kullum muna yawo maƙota muna ganin ya ake
rayuwar ai yaci muyi hadda","hakane kam amma dan ubanki inkina ƙarewa mutane kallon
gidan su kema naki haka za'a ana masa kallon tsaf kuma duk kyansa sai an
kushe",taɓe baki nayi"sun haɗu da wahala kuwa ni kinga na tafi gidan Gwaggo Asama'u
jan magana kinsan kullum naje saita min tass tace min mai kama da aljanu ita kaf
danginta ba mai kama dani anya kuwa uwata da tana da cikina batai gamo ba",dariya
sukaita yi ni kuwa ko ajikina kuma nasa hijabina na fita inaji Mama na kirana nai
burus da ita.

Huɗu saura ni asannan nake cin nawa abincin a tsakar gida sai masifa nake an
shanye kunun aya ba'a rage min ba naji muryar Babban Yaya na sallama,tashi nayi da
gudu na ɗane masa jiki cak ya ɗagani sama "Darling sis ashe kin warke",kai na
sunne"eh mana dama can na warke ai sonake kawai ka rama min shi yasa nayi wannan
lamfar",sauke ni ya yi"kin kyauta ai ina su Mama","suna ciki kazo muci abinci","ni
naci abinci kije kici naki",buga ƙafa nayi na fara wulla hannu zanyi kuka,da sauri
ya riƙoni"sorry zanci muje",a tabarmar ya zauna munaci tare kallona ya yi"Sweet sis
zan tafi Abuja fa yanzu",baki na hangame "Babban Yaya Abuja tamu ta Nigeria
zaka","eh mana kimin addu'a","Allah ya kaika lafiya ya tsare yasa kayi nasara a
abinda kaje yi",lumshe ido ya yi ya haɗa hannunsa da nawa"naji daɗin addu'arki bari
nayiwa su Mama sallama","to kayi na rakaka waje"ciki ya shiga ya musu sallama suka
masa addu'a sannan ya fito na bishi har gidan Umma da zai tafi harda kukana,shima
da kansa da saida jikinsa ya yi sanyi yasan bana son kotafiyar wuni ya yi bare yau
ta kwana ka rantse aurena yake.
Saida naga motar ta ƙule sannan na koma cikin gidan"Umma ina kunun","to Nana
ya fushi kuma yanzu yanzu",kukan daya maƙale min na saki"ni Umma kice ya
dawo"bokitin hannunta ta aje tazo ta kama hannuna"kiyi shiru mana bakyason yayanki
yazama wani a duniya","inaso mana","to kiyi masa addu'a Allah yasa yasamu nasarar
abinda yaje yi","to Umma","yauwa ƴar albarka jeki ga kunun can ki ɗauka in bai
isheki ba kizo ki ƙara","zaima isa Umma na tafi gida","au bazaki tsaya ni ba","to
Ummata gama ina jiranki","yauwa Nanan Iyyo Nanan Alhaji Baffa Nanan Yayanta",ƙafa
na buga aƙasa nai juyi"wayyoUmma kamar na goyaki",ranƙwashi naji na dafe kan"kai
kai"na juya da sauri"Ya Maryam daga tafiyar Babban Yaya har an fara
cinzalina",dariya tayi ta janyo hannuna"bana son sharri Nana yi haƙuri kar yana
dawowa ki ƙala min kisa ya mazgeni dan ba kunyar dukanɓ na zaiji ba","to kinyi sa'a
Umma ta ceceki sabida ta razgan kirari mai daɗin gaske","Allah ya shiryeki
Nana","amen inda gaske ki ke","ohh ni Maryama","bakiga komaiba muddin kina tare
dani",tafiya tayi tana dariya nima haka,Umma na jira ta gama sannan muka tafi gidan
mu tare tana ɗauke da bokitin kunu,tsabar gulma nacin Saude har ta kusa faɗawa
kwata tana waigen Umma ni na lura da ita nai saurin ma ta magana"zaki faɗa kwata
fa",da ta sauri dai daita kanta tana hararata,hannuna Umma ta kama muka shige gida
sai sheƙa dariya nake kamar taɓaɓɓa"ku kuma fa haka Umman yara",Mama da ke gab da
soro ta fara tambaya"bari Halima wannan yarinyar sai fatan shiriya","ai Nana sai
addu'a wallahi"duk ina jinsu amma nai burus,yaran su Ya Fatu ma naja muka shige
gidan Iyyo.

🤚🏻😂🤚🏻
Shagali Nana

Vote
Share &
Comments
Ƴan uwa

Û̬m̬̂ m̬̂ û̬ ŝ̬â̬d̬̂ d̬̂ î̬q̬̂


🌈🌈🌈
🌈🌈
🌈

*𝗕𝗔𝗕𝗕𝗔𝗡 𝗬𝗔𝗬𝗔*
𝚁𝚎𝚗𝚎𝚠

Story & written by


*FATIMA AMINU*
*Ummu Saddi'q*

Babban Yaya Free ne amma me so ya biyo ni Pc in sa a group don shagalin Nana


na buƙatar comments.
08146711395

1️⃣ 0️⃣ chapter 1️⃣0️⃣

A filin sauka da tashi na Malam Aminu Kano suka sauka garin luf luf ba rana
mai zafi sosai motoci na musamman ne suka zo ɗaukarsu har hotel ɗin da zasuyi zaman
dan abin na kusa ne ba a buƙatar kowa ya yi nesa shi yasa aka bawa kowa masauki
anan,shima ɗaki daban aka kaishi nana Abba ya yace ya huta sosai kamin lokacin
yayi da to ya bishiya zauna shi kuma Alhaji ya fita zuwa nasa masaukin ransa
fes,bai jima da fita ba wani ma'aikaci ya shigo janye da keken da ake sagale kaya
tashi ya yi ya aje masa kayan a wurin yana risinar da kai cikin harshen turanci ya
fara magana"Alhaji yace ka shirya bayan sallar isha zanzo na raka ka inda
yake",shima amsa masa ya yi sannan ya fita,kallon set set na suit ɗin ya shiga yi
gasu nan har bakwai kuma kana gani kasan ba ƙana na bane,kuma zama ya yi ya janyo
wayarsa ya kira ƴar nokiar Umma ya faɗa ma ta sun sauka lafiya addu'a tamai sannan
ya kashe yana ajiyar zuciya,bai kuma magana da wani ba har ya fita ya yo sallar
magaruba yana shigowa wayarsa tayi ƙara ɗaukkowa ya yi yaga Hajara kan kujerar
wurin ya zuna yana ɗagawa"barka da sauka shine baka kira kasanar min ba","mun sauka
lafiya ban kira ki bane ko kin manta kin faɗan bakya gida zaki kai amarya","eh
hakane am sorry amma komai normal","sosai ma","to sai anjima",kan ya yi magana ta
kashe,bin wayar ya yi da kallo shi baisan meyasa bata iya magana ba saita suyi aure
ayi kaza ayi kaza Babban Yaya sarkin wanka yanzumma shi ya shiga ya jima sannan ya
fito,saida ya shafa mai da yake ajiyeye a kowanne ɗaki na hotel ɗin dan dama Alhaji
yace daga shi sai kayan jikinsa zai taho,sanda ya gama shirin ana sallar isha tasa
ya yi sannan ya zauna jiran lokacin,ba daɗewa saiga Alhajin da kansa ma yazo
kallonshi ya shiga yi kamar maisonntuna wani abu amma ya kasa gano komai game dashi
saima murmushi da ya yi"lallai ɗana ashe babban mutum ne kai haka",kansa yaɗan
shafa yana risinar da kai"haba Alhaji waye babban wannan ai sai ku","Habib"ya
kirasa cikin muhimmanci"na'am Alhaji",kaɗarsa ya dafa"karna ƙara jin ka kira ni da
Alhajin nan ni Abbanka ne ka ɗauke a haka har ƙarshen rayuwar mu dama ni a ɗa na
ɗaukeka tun ganin farko","shike nan Abba bazan kuma ba insha Allahu","madallah muje
bana son shiga wuri ana ƙarshe","hakane"nan ya shige gaba yabi bayansa amatsayinsu
na maza to duk inda suka bi kallonsu ake sama da ƙasa,har ɗakin taro hakanne kuwa
ba a gma taruwa ba,bin Alhajin suka shigayi da kallo suna mamaki dama yana ɗa babba
haka amma ya ɓoyeshi,gaggaisawa akai sannan sauran suma suka gama shigowa tunkafin
fara kowacce magana ya gabatar musu dashi amatsayin ɗansa,sannan aka fara abinda ya
tarasu a wurin wakilin kowa na wurin Alhaji Abubakar jega shine ya fara gabatar da
asalin abinda ya haɗa su wurin cikin harshen turanci saboda akwai yare waɗanda
hausar su batayi nisa ba sosai sannan gama Dr Kumar wanda ya zaɓi zaman ƙasarmu
saboda yaga amanar mu ta masa,kamar yadda ku ka sa ni zamu saka hannayen jari ga
babban company na motoci dake ƙasar america kuma ayau muka yanke zamu sa hannu a
takardu na yarjejeniya sai dai tun awancan lokacin Alhaji Aminu bai gama yadda da
wanna magana ba yace abari dai zuwa yau aƙara tattaunawa akai kuma kowa nada damar
ya amince ko akasin haka ko kuma ku kawo shawarwari waɗanda suka danganci wannan
batu sannin kanku ne zamusa kuɗi a wannan harka saboda cigaba ne ba wai faɗuwa
ba"hannu ya ɗaga masa nan take ya yi shiru ɗago kai ya yi yakallesu kowa ya shaida
ransa aɓace yake ga wani kallo yana musu tsit sukai kamar suna gaban ubansu ƴaƴan
saura dake wurin mamakin irin wannan nuna ɓacin rai sukai,jayo ƴar loudspeaker ta
gabansa ya yi ya miƙe tsaye dan abin yafi gaban zama kamar zai rufesu da duka ya
fara magana"bazaku sa hannun ba kuma bazakuyi haɗin gwiwa dasu ba"kallon kallo aka
shiga yi ya yinda wani sanyi ke ratsa zuciyar Abba yasan tabbas dama za ayi
haka,katsewa kowa tunani ya yi"ku yanzu banda abinku dama kuna da irin waɗannan
dukiya haka amma bazaku taimaki ƙasarku ba ku kalla yadda muke fama masu digiri ba
aiki amma kuna son ƙarawa masu ƙarfi me ku ke tunani ne waɗannan turawan zasuti
harka daku ne batare da sun gano zasu sami riba mai gwaɓi ba,to bari kuji wallahi
tallahi bature bature bazai taɓa aminta da baƙar fata tafishi ɗauka ka ba wayo
kawai zasu muku su kaiki ƙas kai bawai Allah ana ganin ka ba indiye ne dan Allah
faɗa musu suwaye turawa dan ina tsammanin kunfi kowa shan wahala ahannun su sannan
ku ka sami ƴanci,wannan ƙasa ta Nigeria a kaso ɗari na India ko ɗaya bamu ɗauka
gaba ɗayan ƙasar Nigeria mu million ɗari da sittin ne ko kana zaɓe ko baka yi ƙasar
india su million dubu ne da ɗari biyu ko ɗari uku kunga ko yawan ƴan sandan su bamu
kaiba amma anan ƙasar bamu iya komai ba sai zaman banza da gulmar duk wanda ya
gilma,to wallahi bazaku yi wannan harkar ba kun ma ji ai ni ɗanku ne ko to
saurareni da kyau",kamin ya gama maganar Dr Kumar ya miƙe ya fara tafawa sannan
kowa ya shiga tafawa suna murmushi dan ya birge kowa sai sukaji inama ɗan su ne
wannan yazo da wannan babbar fasaha murmushi ya yi ya gyara tsaiwa dan ya kasa
zaman ma ji yake kamar ya yi bindiga dan haushi"abinda nake so kowa yasa nutsuwarsa
akan maganar da zanyi,a madadin shiga harkar mota wadda tazama gama gari bakanike
ma sai ya haɗa mota,mai zai hana mu zama masu ƴan kasuwa ta fannin daban
daban,ma'ana zamu yi company da za'ana sarrafa copmuter ta ma'aikata da laptop,ipad
wayoyi na zamani manya da ƙanana waɗannan kaya dana lissafa akullum kasuwarsu sama
takeyi bata ƙasa kuma kullum kasuwa ake shiga dan yin harkarsu,wannan company zaiyi
mazauni ne aƙasar Dr Kumar sabida sun fimu igiyar sadarwa mai ƙarfi,za 'ayi wannan
aiki kamar yadda ku ka ambata akan kuɗaɗen da ku ka yanke,ba ƙarin ko ƙwandala da
kuɗin za'ayi aikin a zuba kayan aikin sannan aɗebi ma'aikata,wannan company kayan
da za'a sarrafa cikinsa ba dun ƙuleshi za'ana yi ba rabashi za ayi kowa ya fitar
dukkan abinda kasuwa tayi anan za a haɗa a cire albashin ma'aikata acire na kayan
aiki sannan ku raba sauran wannan da zaku raba shine zaina zama asalin dukiyar ku
na kayan aiki kuma sune na company za anayin hakan har sai kowa ya maida kuɗinsa
kunga company ya zama ria kenan in an gamashi kuma baza'a karɓi hannun jarin
kowaba sai wannan magana ta farko ta gama haɗuwa sannan za a bawa kowa damar shiga
ayi dashi kama daga nan ƙasar da sauaran asashe,wannan aiki za haɗu ne ta hanyar
ɗan kwangila Ni kenan babu wanda zamu ɗora mu zamuyi komai da kanmu kuma sauran
masu ƴaƴa irina kowa ya nasa ya fito sai kowa ya hau kan abinda yafi ƙwarewa akai
da Dr Kumar haƙƙin nemo wajen siya wato fili da ma'aikata da gamsar da tsaretsare
na ƙasar su yana wuyansa,wannan ne zaisa bazamu matsala ba amma tabbas idan aka
nemo bare to za ayi mana ƙisa kuwa,ni da zan jagoranci aikin zan zana wurin zannan
kowa yana office a cikin ku kuma zai baza komar neman ma'aikata masu ƙwarewa akan
hakan nan da can ƙasar,nayi alƙwarin wannan aiki bazan karɓi ƙwandalar kowa ba har
agama shi muji dai da waɗanda zamu iba aikin,ku duba maganata",zama ya yi yana
binsu da kallo kowa ya shiga hankalin sa sunji bayani zallar basira kaifin tunani
da hangen nesa samun riba da haɓɓaka cigaban ƙasa samar da aiki ga mutane bila
adadin kenan an rage ɓata gari an taimakawa masu buƙatar taimako,kowa ya gama
nutsuwa da ƙyar Alhaji Abubakar jega ya buɗe ya yi kabbara"ALLAH YA MAKA ALBARKA
YARO",sai asannan kowa yasamu bakin magana ana ta amen kuma ana gaisawa da juna
alamar sun karɓa kenan,magannun amincewa ke tashi anan ɗaya daga cikinsu ya fara
magana"to Alhamdulillahi dama haka Allah yake ikonsa duk mu ba muyi wannan tunanin
ba gaskiya mungode da sako ɗanka da kayi a cikin wannan al'amari da tuni mune da
danasani","haka zancenka yake Alhaji wannan yaro Allah ya masa albarka Alhaji Aminu
mun yadda da duk abinda ɗanka ya faɗa kuma da zai tsara nan gaba kawai bayaninka
zamuna saurara kuma ƴaƴan mu kaf zasu zo gareshi can garin kanon sai suna shirya
dukkan abinda ya kamata tare saboda suna ƙara samun hasken kai irin nasa",shima
tashi ya yi"ina godiya a gareku amma kusani wallahi bai faɗamin komai dangane da
wannan ba anan ya tsara komai nasa nima bani da masaniya kan me zaice to nima nabi
sahunku mungode Habib",dariya sukai nan sukaita bashi goyan baya Dr Kumar na sanar
musu sati mai zuwa za'a fidda wakilai su tafi tare dan a samu wuri mai fasali asaya
kamin nan kuma zaisa afara duba masa wurare masu kyau da fuska,asannan ya miƙe yace
inada magana"kuyi takardar kunjanye bada hannun jarinku a wancan company ku aikawa
musu dan nasan suna can suma suna shirya yadda zasu cucemu","hakane"kowa ke
faɗa,sunfi awa huɗu tun 8 sai shabiyu da rabi sannan taron ya tashi ko gajiya ma
basu yiba,Abdallah ɗan Alhaji Salihu ɓaɓura da Is'haq ɗan Alhaji Balarabe kano sai
Sulaiman ɗan Alhaji Abubakar jega sune suka matso inda yake"aboki sannu da
ƙoƙarifa",hannu ya basu suka gaisa"karku damu nan da lokaci kaɗan komai zai dai
daita mu zama abu guda","hakane to zamu wuce saida safe mu anan muke kaga mayi
sallama ko kafin ku wuce","ba matsala Allah ya kaimu",suka wuce sannan kowa ma ya
kama gabansa ransu fess.
Har ɗakinsa Alhaji ya rakosa yana tafe yana kallonsa mamakin yaron yake ashe
ganin da ya masa a titi baiga komaiba yaron baiwa garesa a ɓoye,kallonsa ya yi
yace"Habib lamarinka ya ɗaure min kai sosai wallahi amma bari da safe mayi magana
ka faɗamin da yaushe kayi wannan hasashen kai daka san maganar jiya ni da najima da
sanin maganar ma banyi wannan tunanin ba kwata kwata ko ince mu",ya faɗa yana
dariya,shima dariyar yabyi"karka damu Abba wannan mai sauƙi ne nayi wannan tunanin
ne tun sanda ka faɗa min naga ba hannun jari ya kamata ku sa ba kamata ya yi asa
muku kuma wallahi kaji na rantse waɗannan turanwan wayo sukai niyar muku dan sunsan
kaf ɗinku baku da kotun da za'a iya gurfanar dasu nasan irin waɗannan matsalolin na
karanci halayensu sosai alittafan tarihi da dama da kuma maganganun manya na ƙasar
hausa dake a ƙunshe a waƙoƙi da kuma takardu,muddin kaga bature ya maƙalewa abota
da kai to tabbata kanada mamora mai gwaɓi danshi baisan faɗuwa ba sai riba shi yasa
baya jure baƙinci sai ya kashe kansa in daɗi ma ya masa yawa sai kashe
kansa",ajiyar zuciya Alhaji yayi"lallai kai mai ƙwazone kuma ina jinjinawa iyayenka
fatan zasu bani aron ka",dariya ya yi kawai yana shafa kansa"Nana ko bazaka iya
tahowa wurina ba mu zauna saboda ita",da sauri ya ɗago kai ya kalleshi"ba haka bane
Alhaji","hakane mana amma dole ta haƙura wannan karon kaima haka da hakane zata
gane cewa waye kai sannan kaima zaka gane wacece ita bayan mun koma zanzo naga
iyayen naka","to shikenan Abba Allah ya kaimu lafiya"sannan ya fito zuwa nasa ɗakin
dake can sama,shi kuma ya cire kayan ya watsa ruwa abinci yaci ya ƙoshi sannan ya
janyo wayarsa 1:45 am kwanciya ya yi yana tunanin yanda zai fara rayuwa ba Nana.

Vote
Share &
Comments
Û̬m̬̂ m̬̂ û̬ ŝ̬â̬d̬̂ d̬̂ î̬q̬̂ 🌈🌈🌈
🌈🌈
🌈

Babban Yaya Free ne amma me so ya biyo ni Pc in sa a group don shagalin Nana


na buƙatar comments.
08146711395

1️⃣ 1️⃣ chapter 1️⃣1️⃣

*****
Ana sallar magariba kaf ɗinmu muka shige gidan Iyyo rawa tai tayi ita dai Allah ya
ma ta gata jikoki ta ko ina dariya mukaita ma ta anan muka raba dare sannan muka
shigo gida Ya Usaina ce ta kwanta a gadon Aunty Mama da yaranta na shigo kenan na
hangesu har sun yi bacci"kam bala'i wallahi kowa bai isaba a ƙasa ake nufin zan
kwanta lallaima"fuuu na fito daga ɗajin Aunty Mama na falo naje na tasheta hannuna
ta kama zuwa ɗakin saboda masifa na cina na manta tana jingine katifa janyo min ita
tayi na kwanta kai sannan ta fita ta koma ta kwanta,ina kwanciya bacci ya sace ni.

Da safe kafin mu tashi su Mama har sun gama abin kari,dama al'adar gidanmu kana
tashi da wanka zaka fara shi yasa kullum bama rabo da ruwan ɗumi,yanzun ma wankan
mukai sannan kowa yaja abin karin sa mukai da'ira kamar a tsangayar ƙauye.

Yaran Ya Fatu shida babbar itace sa'ata sai yaran Ya Usaina guda huɗu muka shirya
zaga gidajen iyaye nice a gaba ba kwalliya ba komai sai doguwar riga da ɗan hijab
dana saka,gidan Kawu Nuhu muka fara zuwa har kayan daɗi ta bamu dan tana gullisuwa
da alawar madara,sai gidan Kawu Rabilu Umman su Ya Sumayya ce ta kula mu amma Haule
ko kallo bamu isheta ba shi yasa muma da zamu fito ko kallonta bamuyi ba munaji
tana mana habaici,sai gidan Kawu Iro shi kuwa aƙofar gida muka haɗu da gudu ya koro
mu wai bazamu shigar masa gida ba harda zagi wai shegu masu kama da fara,haƙura
mukai muka tafi gidan Gwaggo Asama'u jan magana dan munsan koro mu zatai amma sai
mukai sa'a batanan ta shiga unguwa tsurku shi yasa mukai zaman mu da Ya Fatsima har
ɗanmalele ta mana mungama muna wanke hannu ta shigo katsam sai idona cikin
nata"lalala a gidan wa ku kai wannan abincin har ku ke tanɗe baki kamar baku taba
cin abinci ba",ɗagowa nayi na kalleta"a gidan Gwaggon wadda har lahira uwarmu ce
mukaci in wata zuciyar ta isa ta kore mu tace mu jininta bane",saƙare Gwaggo Ma'u
tayi tana dubana tama kasa magana,Baba dake a bayanta ya yi dariya"to sannunku
yaran Gwaggon su",juyawa tayi ta harare shi sannan ta wuce ciki fakan fakan,cikin
raɗa nace"ku ɗakko hijabanku mu gudu kan ta fito kunsan ta sarauniyar mazga ce su
Ya Fatsiman ma mazgar su take bare mu ƴan tsaki",ai kuwa da sanɗa muka janyo
hijaban mu duk manja muka silale muka gudu Ya Fatsima sai dariya take,muna fitowa
saiga Ya Hadiza wani ya ajeta a mota hararata tayi,na kuwa cije baki araina nace
'zaki gane baki da wayo'sai nayi sauri na ƙarasa ina yafito su Hameda da hannu ina
zuwa saina duƙu har ƙasa suma sukayi yarda nayi "ina wuni Yayan mu",yashe baki ya
yi"lafiya ƙanne na ya ku ke","lafiya lau Ya Hadiza ina wuni",wata harara ta zuba
min a fakaice amma saita washe baki"lafiya lau Nana Hameda kunzo lafiya","au ƙannen
ki ne da sauri na rigata magana"ni ƙanwarta ce su kuma waɗannan ƴaƴanta ne","kina
nufin yaran Yayarta","yauwa ka gane ashe"tare mukai dariya hannu yasa aljihu ya
fiddo kuɗi ƴan ɗari ɗari ya bamu kowa biyar biyar gamu da yawa mu shaɗaya ne dan
har ta goye muka ɗakko,godiya mukai muka ƙara gaba muna karya kwana muka fara
dariya dan muna kallonta kamar ta warce kuɗin,muna shiga gida aka fara lafiyanku Ya
Fatu muka bawa kuɗin muna bata labari"ai kuwa ku shirya cin ubanku dan saita daki
kuɗin saurayinta da ku ka karɓo",kar kace ƙugu nayi"wallahi bata isaba tunda ba
danneshi mukai muka ƙwata ba kuma ba roƙarsa mukai ba ko ya kika ce Hameda","hakane
ƙawata uwata",taban hannu muka tafa muna shigewa ɗaki ana wata dawarar,kai kawai
Mama ta girgiza tana kallon Aunty Mama"wallahi uwar Nana rayuwar ƴarki na faɗar min
da gaba ta iya kissa ta fitar hankali ga wayon masifa anya kuwa za'a wanye lafiya
inta girma","kina ma ta addu'a Dada kamar yanda nake ma ta ni kaina Nana tsoro take
bani kinganta fa amma inta kitsa abu ni kaina tunanin taya tayi hakan nake","addu'a
kam zamu ƙara dagewa amma akwai babbar matsala agaba dan ina hangota kuma koda
ubanwa muke yawo kinsan alƙawarin Iyyo baya tashi","hakane kam to Allah ya fisshemu
alkhairi akansu baki ɗaya","ameen Halima mijinki yau banji ya kira waya ba","eh
kinsan abi sai a hankali ƙila ya kira zuwa anjima","to Allah yasa lafiya",suna
aikinsu suna hirarsu Ya Usaina nata musu vedio da wayarta tana dariya wai wallahi
saita nunawa maƙwaftanta ga iyayenta su sun zauna kishi kullum gidajansu kamar
filin yaƙi duk akan namiji wanda yake fita batare da sunsan ina zashi ba kai mata
sun haɗu da wahala ki gama haukarki ya auro miki yarinyar da kika fi yadda da ita
alayinku wadda take shigowa gidanki tayi yadda taga dama kai wallahi Allah ya
sauwaƙawa maza,wayar Aunty Mama ke ƙara ta ɗauka ta duba Babban Yaya ne ɗagawa tayi
tana amsa sallamar da yake ma ta"sai yaushe kuma Habib","ban sa ni ba dai Aunty
Mama amma da wuya mu shige gobe","to Allah ya bada sa'a nasan dai mutuniyar ka ke
nema ko",kamar tana ganinsa ya shafa kansa yana murmushi,kira naji Aunty Mama na
feso min da gudu saura kaɗan na bi takan ƙwaurin Ya Usaina ta janye ƙafarta,wayar
ta miƙo min tana faɗin "Yayanku ke magana",karɓa nayi naja gefe na durƙusa"hello
Darling Yaya",tacan lumshe ido ya yi yana cizon lips ɗinsa"hello Darling Nana","ni
Babban Yaya fushi nake da kai","akan mi",ya faɗa muryarsa can ƙasa"sai fa yanzu ka
neme ni tun jiya daka tafi","am sorry Darling Sis jiyan bansamu kaina da wuri ba
sanda na nutsu kuma dare ya yi bazan iya kira ba","um um bayan da ƙyar nayi
bacci",na faɗa ina kwaɓe fuska,numfashi ya furzar"sorry fa nace","tom Darling Yaya
ammanka dawo yau","an gama tawan me zaki tanadar min","um zanma wainar fulawa mai
ƙwai da yawa aciki","ok ni kuma zanyo miki tsaraba wadda zata dace da wannan
kyakykyawar surar taki",ƙyalƙyalewa nayi da dariya"Sweet bro dama ina da kyau
haka","kaiii karki kuma wannan tambayar a fuskokin mata kaf waɗanda ke gilmawa a
idona ko farcenki basu kama ba","Allah Sweet bro ka fini kyau ai","mari bakinki
maza kan nazo kinyi saɓo",dariya nayi"hunm ai dama bazaka yadda ba amma wataran
za'a baje wannan musun","ina fatan Allah ya nuna min wannan rana dana fi kowa farin
ciki",nocking ƙofar akai"Nana kashe zan kira ki anjima anzo wajena ne","ok Darling
Yaya karka kula mata fa","an gama Sweet sis"cire wayar nayi na kashe na miƙe arba
nayi dasu Ya Fatu sun min duru duru,"zo nan dan ubanki abin naki har yakai haka ina
ki ka koyi wannan lanƙwasa muryar da waɗannan sunayen","kai Ya Fatu harkin tsorata
ni na zata bakya duniyar ai danaga kiyi foster,ni me nayi wai","zonan Usaina kinga
makirar yarinya tun tana ƴar ƙarama","bari Maman Hameda wallahi na kasa magana
ma",zuruu na musu danni banga me nayi ba suke wannan abin,"jeki Nana ta"Aunty Mama
ta faɗa,wayarta na miƙa ma ta na shige ɗaki raina fess amma da duk cunkus nake
jina,Aunty Mama ce ta kallesu Ya Fatu"ku basai ku zaunaba ƙaramar yarinya ta sace
zuciyar ƙaton saurayi irin Habib bari na faɗa muku Habib ya gama mutuwa kan Nana ko
wannan zancen auren da ake kamar dole ya zame masa dan baya ta kowacce sai Nana
kunganta dai in Nana na kusa da Habib wallahi baya gane mutane sosai sai ita,mu
kanmu abin mamaki yake bamu yadda yarinya ta iya sarrafa murya haka ta iya salo
daban daban agaban Habib shi kuma duk sai ya rikice waccan goɗimar Ruma Hashim take
so shima haka amma kowa ya kasa faɗa saidai ku duba yanzu haka kaf unguwar nan
indai kana da hankali kasan me yake tsakanin Nana da Habib",ajiyar zuciya sukai
suna jinjina kai"wallahi nima dai zan sauya caɓ kalli yadda jaririyar yarinya ta
mallake namiji kamar wata uwar mata js 2 take duk da hakama a karatun dan tana da
kwanya ne tai nasarar yin gaba haka","hakane kam Usaina lallai akwai kallo a gidan
Babban Yaya Nana da kishiya","ni ai Maman Hameda har matar ta fara bani
tausayi",Mama dake gefe kawai ta kaɗa kai tace musu "ai ni akan Nana tuni nake
tausayawa duk wadda zata raɓi Habib tana kusa kuma wai a haka Alhaji Baffa ke cewa
Iyyo ma haka take sai dai tanada kawaici da shanye al'amari kuma Nana ma haka
take","ai Mama ba tambaya bakiga mugun son da take ma ta ba ido rufe kamar wasan
drama","ai saiku tayata da addu'a Allah ya sassauta lamarin dan Nana a sha'anin ta
za'a sha famar gaske ba wai na rigima ba zatasa shi ƙin aikata dai daito acinkin
gidansa muddin tana da rabon shiga","lallaikam Mama to Allah ya shirya wannan kissa
ta Nana",Umma ce ta shigo nan labari ya ɗora har ita akan Nana dai.
wayyo ni jama'a
Hhhhhhhhh

******
Tashi ya yi ya buɗe ƙofar yaga Abdallah da Is'haq ne,matsawa ya yi suka shigo
yana musu sannu da zuwa,dawowa ya yi suka gaisa"badai shirin tafiya kayi ba",kansa
ya shafa yana murmushi"na dai shirya ne amma sai anjima zamu tafi","gaskiya aboki
ka haɗu sosai dama akwai mutane masu kishin ƴan uwansu a ƙasar hausa har yanzu
kasan anwa bahaushe shaida kan beson cigaban ɗan uwansa"gyara zamansa ya yi yana
murmushi"wannan ra'ayin wasu ne da kuma camfawa da akayi amma miye dan wani yasamu
cigaba ta hanyarka ai abin farin ciki ne,kuma kowa zai iya taimakon kowa da izinin
Allah in mutum ya ƙudurta","hakane",cewar Abdallah"amma a wannan zamanin masu
zuciyar hakan kaɗanne sai dai fatan dacewa a wannan rayuwar dan asamu tsira ranar
gobe","tabbas to Allah yasa mu dace",Babban Yaya ya faɗa,hira sukai kamar sun jima
da sanin juna har saida Alhaji ya shigo sannan suka kuma fita tare mutane daban
daban yay ta haɗuwa dasu dan Alhaji da gaske yake ya maida shi ɗa na halal,basu
samu hutuba sai bayan la'asar sannan suka wuce airport.

******
GIDAN GWAGGO ASAMA'U
"Ke Fatsima ubanwa zai miki wannan wanke wanken kin tara yara sun ɓata min gida
dan sakarci har kina dafa musu abinci tunda ke ki ka aje min",da sauri ta fito ta
ɗauki omo kan windo ta nufi bakin rijiya amma ƙala bata ce ba"au ina miki magana
kin maidani banza","kiyi haƙuri Umma bazan kuma ba","kaiii kima kuma mana ai saikin
je gidajan su kin anso min abuna"juyawa tayi kawai ta fara wanke wanken tana sauri
gudun wata fitinar,Baba ne ya shigo yana dariya ya kalli Fatsima"ƴata Fatsima
albishirinki",tana dariya ta juyo"goro Babana","gobe zaki makarantar da zaki zana
jarabawa a miki tambayoyi kawai saiki koma can ki ƙarasa",wani miƙewa tayi tana
tsalle"wayyo Baba amma naji daɗi sosai Allah ya kaimu goben","ameen gama aikinki
kizo kiji","to Baba gani nan",ta saurin duƙawa tana ƙarasawa zuciyarta kamar ta
fashe dan murna ko a ina Baba yasamu kuɗin canza ma ta makaranta,tsaki Ummansu
tayi"aikin banza kawai kalli yadda ku ke wani abu kamar ƙananun yara",ko kula ta
ba wanda ya yi Baban da ciki zai shiga amma yay fitarsa yana kallon Hadiza amma ko
kallo basu ishesa ba ya kuma wuce su ita kuwa banzar ko tacema saurayin ga Babana
saima ta ɗauke kai,Fatsima na gamawa ta kwashe kayan ta wanke wajen ta zari
hijabinta"Umma na tafi na samu Baba a waje",bata jira me zatace ma ta ba tai wuf ta
fito tasan tsaf zata hanata,ilai kuwa Umman niyar dakatar ta take amma kafin tayi
magana harta kai soro,tsaki tayi"kuyi tayi keda shi amma agidan nan sai anmin aikin
komai sannan za'a wata makaranta ta ƙaƙale"ta miƙe tana buga cinya Hadiza ce ta
shigo kaya niƙi niƙi da sauri Umma ta tareta"ƴar albarka har kin dawo lale maraba
ƴata", *('kuji saikace wata wadda tazo daga wata uwa duniya kuma wai tana tambatar
harkin dawo')* ,tsaki ta ma ta"Umma wannan yarinyar mai zubin aljanu sainaci ubanta
wallahi",kayan ta aje ta riƙe ƙugu,cikin fushi Umman tace"waye ya miki wani abun
badai waccan shegiyar yarinyar ba Fatsima","inafa Umma Nana mana wai wannan
yarinyar ta jawo yaran nan duka hartana wa saurayina bayanin su suwaye kuɗin dazai
bani ya kwashe ya raba musu","lahhhh amma wannan yarinya ko ƴar buƙulu yanzu haka
ta miki zan kamata kuwa saina ma ta kashedin ko a hanya ta ganki karta kuma nuna
tasanki","yauwa Umma dama kinsan in ni na ma ta magana saita ma ga dama zata
fuskanci me nake faɗa","barni da ita kinji taho",suka shige ƙuryar ɗaka.
"Assalamu alaikum Baba gani","zoki zauna ƴata",kan bencin da yake ta
zauna"Fatsima ɗazu nayi wani baƙo nima bansan sa ba yazo min da maganar yasan inada
ƴaƴa amma sun daina makaranta to akan maganar yazo duk maison karatun shi zai ɗauki
nauyi take na gaya masa akwai ke ɗaya kina aji biyar yanzu dan nasan ko nace da
Hadiza bazata yi ba","amma Baba ai daka gwada","ki barshi kawai yanzu nifa Hadiza
ko gaisuwa ba ta haɗa ta dani koma ko a ina zata ganni bata kulani","nasani Baba
kana ma ta addu'a kawai Allah ya shiryeta","ina ma ta ƴata amma zan ƙara kije gida
ki gama aikin kafin lokacin islamiya ko","to Baba nagode sosai",ta tashi ta tafi
Baban nabinta da kallo"Allah ya yiwa rayuwarki albarka fatan karna mutu sai kinga
tushenki Fatsima badan Yayanku yace karna faɗa miki gaskiyar sanadin karatunki ba
dana faɗa miki Allah ya miki jagora.

******
Suna sauka a filin jirgi sun nufo motocin da zasu ɗauke su Alhaji ya kalle shi
yaga yanata murmushi,dafa shi ya yi"na Nana duk ka ƙagu ko kaje kaganta",shafa
ƙeyarsa ya shiga yi yana murmushi"kanaji ko karɓi waccan motar kai tsaye ka wuce
gida motar takace dama Abdallah da Is'haq ne suka baka tun jiya",da sauri ya kalle
shi"kar kai mamaki kaje da abarka ta halal ce ikonka ce dama haka Allah ke
lamarinsa ita ɗaukaka lokaci guda take zuwa muddin ka kasance mutum nagari",kasa
magana ya yi yana jinjina abin mota shiɗin da gaske,da ƙyar ya lalubo kalmar godiya
ya yiwa Alhajin"daina gode min ni ai Babanka ne",murmushi ya yi suka zo bakin motar
tare sannan na ciki ya fito ya miƙa masa mukullin addu'a ya yi sannan ya shiga,ko
anan saida yaƙara birge Alhaji akan idon Alhaji ya fita a wurin sannan ya shiga
motocinsa suka wuce gida,koda suka isa matansa da yaransa sunsan yana cikin farin
ciki sosai,Hajiya Fulera uwargidansa mai yara Mata uku itace tama tambayeshi amma
yace ma ta ba komai irin abinda take baƙinci kenan da yake ma ta baya taɓa faɗamata
sirrinsa kamar yasan cewa ba zuciya ɗaya take zaune dashi ba.

Tunda yashigo layin da motar ake binsa da kallo a ƙofar gidan Iyyo ya gyara parking
ya jima aciki sannan ya fito,baki ƴansa ido suka shiga hangamewa ciki harda Sadis
da Khamis ƙannensa"kai Khamis wancan ba Babban Yaya bane kalli fa kayan jikinsa
harda mota",kallonshi Khamis ya yi ka sa ni ko arowa ya yi tunda yana neman auren
ƴar masu kuɗi","haba yauwa sai dai hakan amma fa komai ya shiga da shi ina ma nasa
ne wayyo ai wallahi saina ari motar naje nayi burga sosai a gari","wallahi bansan
me yake damunka ba Khamis yanzu a ina zai samo wannan motar saikace ɗan mafiya
kaidai a bari a arotan ya yi",mukkullin ya danna ta kulle sannan ya shiga soron
gidan,muna cikin alwalar sallar magaruba naji sallamar muryar Babban Yaya watsar da
butar nayi na yanko a guje na daka tsalle sai ajikinsa"oyoyo Darling Yaya",saurin
riƙeni ya yi yana dariya ya rungumeni"oyoyo Darling Sis amma saikin faɗi kinji ciwo
kinja min masifa kin manta banaso ko ƙurji ya fito akan wannan fatar dan kar ta
sauya launi",a kunnensa na raɗa masa"na daina Babban Yaya",dire ni ya yi yana kama
hannuna muka ƙarasa ciki,Ya Fatu da Aunty Mama da akai komai akan idonsu kallon
juna sukai Ya Fatu tace"zahiri Aunty Mama akwai babbar drama nan gaba kaɗan dan
bana tunanin Nana Babban Yaya zai bari tayi girma ba a hannunsa ba kalli yadda kaf
idanunsa suka rufe ƴar yarinya ƙarama ta taɓashi ina kuma ga ta cika tayi fam dama
gata ɗiyar fulɓe gaba da baya gata shuwa'arab tabbas a kula da jikin Nana wannan
ƙashin ya kama gabansa","kin fahimta kenan Fatu nima na fara wannan shirin da ta
shiga aji uku a makaranta","kin kyauta saura ni",Yaran ne suka taho duk suka
yanyame shi suna hayewa jikinsa amma yana riƙe tam da hannuna yaƙi saki sai amsa
gaisuwar yake,sunkuyowa ya yi dai dai kunnena ya raɗa min"nayi mota tana
waje",gwalo ido nayi na wani fasa ihu saida suka baje yaran nayi waje da
gudu,dariya ya yi ya juya yana gaisar dasu Mama,Ya Usaina dake riƙe da haɓa dan
mamaki tace"Babban Yaya meka faɗawar jaririyar taka ta baza yara haka",murmushi ya
yi"ƴarsa ido kina nan da halinki ashe to bazaki ji ba ki bita kiga me taje yi
wajen",ba musu kuwa suka biyo bayana,ina fito nao arba da mota me shegen kyau a
ƙofar gida,ihu na fasa"MOTAR BABBAN YAYA",cak masu wucewa masallaci suka tsaya suna
juyowa hakama ƴan gidanmu masu biyoni,su Sadis da maganar ta sauka a kunnen su ai
kamar sa kifa suka ƙaraso"ke Nana wannan motar ƙatuwa mai tsada itace ta Babban
Yayan a ina ya samota",juyowa nayi cike da masifa"kai Ya Sadis ka daina gulma amma
muje na rakaka ka tambayoshi a ina ya samota",waigawa bayansa ya yi"ke yarinyar nan
munafuka ce wallahi daga tambaya","munafukai dai dani damai dattin hula",ya ɗaga
hannu kenan zai kaimin duka ya tsinci waɗannan fusatattun idanun na Babban Yaya
yana kallon sa da sauri ya sauke hannunsa ya matsa a wurin gudun karshi yasha marin
dayay niyar min,wurin ya ƙaraso yana faɗa musu tashi ce dan mu a dangin mu ba mai
tsoron maganar wani banda haka aida Babban Yaya zaiyi shakkar cewa wannan motarsa
ce kai tsaye,a magarubar nan ba wanda bai fito ganin mota ba Iyyo rawa ta shiga yi
wai jinin ta akwai albarka ga farinjini da kwarjini aiki ɗaya na magana ya kawo
sauyi a rayuwar jikanta,farin ciki ya cika zuciyar wasu yayinda baƙinci da hassada
suka turniƙe wasu dan wani da yanda zaiyi ya ɓatar da motar adaina kallon ta ma da
ya yi sai dai kash lamarin Allah ba mai ja dashi,a ranar ya haɗa Alhaji Baffa Iyyo
Umma Mama da Aunty Mama ya musu bayanin komai tun daga farko har ƙarshe,sunsha
mamaki gaskiya sannan sukai masa addu'ar fatan nasara a lamarin sannan Allah ya
kaimu goben suna jiran zuwansa,bai nemi Hajara ba sai washegari yaje amma bai faɗa
ma ta komaiba dan ba yanzu ya kamata tana sanin irin wannan ba sannan ya faɗa ma ta
Kakansa na nan zuwa asatin ayi maganar aurensu ba kunya tashiga murna a gabansa wai
ta matsu ma ta gama karatun ayi aurensu susha soyayya shi dai da ido ya shiga bin
ta yana mamakin ita ƴar kunyar nan ma ta ƴan mata bata da ita kodan suna gidan masu
kuɗi ne.

Vote
Share &
Comments

Û̬m̬̂ m̬̂ û̬ ŝ̬â̬d̬̂ d̬̂ î̬q̬̂


🌈🌈🌈
🌈🌈
🌈

Babban Yaya Free ne amma me so ya biyo ni Pc in sa a group don shagalin Nana


na buƙatar comments.
08146711395

1️⃣ 2️⃣ chapter 1️⃣2️⃣

A ranar da yamma misalin biyar drivern da ya kawo Babban Yaya waccan ranar yawa
Alahji jagora har ƙofar gidan mamaki da ganin motocin shi ya shiga yawo a zukatan
ƴan layin babu jimawa da tsaiwar su ya fito a gidan zuwa wajen motocin Alhajin ne
ya fito a motar yana kallon layin sannan ya kallesa"Habib na ɗauka Nana zaka turo
min ta tareni","afuwa Abba bansan kafi son haka ba dana turo ta amma bismillah" nan
ya masa jagora zuwa cikin gidan Alhaji Baffa cikin karramawa da mutuntawa Alhaji
Baffa ya fito yana masa sannu da zuwa cak maganar tasa ta maƙale"HABIBU KAINE DA
GASKE"kallon kallo aka shiga yi wai da wane Habibun yake ne,ganin basu fahimcesa ba
yasa ya fara kiran Iyyo"A'i Ai fito ga Habibunki abokin Aminun ki",kamar zata kifa
ta fito a ɗaki"yana ina Alhaji"turus tayi a wurin "Habibu Allah mai iko kai Habibu
a ina kasamo wannan mutumin",ta faɗa tana nuna Babban yaya,saƙare ya yi yana binsu
da kallo"Iyyo nifa ban gane ba shima sunansa Habibu ne a ina kuka sanshi?",dubansa
Alhaji Baffa ya yi"jeka zo da Ummanku da Halima babba",juyawa ya yi ya fita ya rasa
ma wane tunani zaiyi saida ya taho da Umma sannan suka shigo suka tasa Mama a gaba
ta ƙofar da aka tsaga wa su Iyyo ta gidan suka shiga,Alhaji da ya yi saƙare kansa
na bugawa kallonsu yake yi yana ganin tamkar yasan fuskokin nan amma ya manta inda
yasan su,Alhaji Baffa ganin bai gane su ba yasa yace"mu shiga daga ciki mana,ko
kuma A'i sa shimfiɗa nan baranda cikin zafi su sun saba da ac",dariya tayi ta ɗakko
tabarma da ƙatuwar darduma ta shimfiɗa a barandar suka zauna,tunda suka doso wajen
Umma da Mama suka cika da mamaki ganin fuskar da bazasu taɓa mancewa da ita ba a
rayuwar su,Mama harda Saurinta gun ƙarasowa wajen"YAYA HABIBU"ɗagowa ya yi ya
kalleta"wallahi Yayana ne wannan Sa'adatu kalleshi da kyau",Umma kuwa kasa magana
tayi da ƙyar tace"dama kana nan bawan Allah",saƙare Alhaji da Habib sukai suna
binsu da kallo,Alhaji Baffa ne ya kalli Habib"jeka zo min da Nuhu da Liman ma za
yanzu ana ƙara lokaci za'a samu matsala sauri",da saurin ya fita sukai kiciɓis da
Kawun a waje"yauwa kawu kazo inji Alhaji bari na kira liman",baiji me zaice masa ba
ya wuce a masallaci ya samesa ya isar da saƙon Alhaji Baffa atare suka taho cikin
gidan,Alhaji Baffa ne ya kalli Liman yace"Liman ga mutumin da nake ta baka labarin
nan yau sanadi ya kawo shi gida amma da alama abin yana nan bai baje ba dan bai
gane mu ba",gyara tsaiwa Liman ya yi"Allahu akbar Alhaji yanzu shine wannan haka
cikakken babban mutum amma gaskiya an ƙwareshi an cutar da rayuwarsa ace mutum irin
wanan baisan kowa nasa ba bakomai zamu warware koma miye kai Nuhu fara karatu
Habib a ina za'a samu zuma","akwai wurina"Iyyo ta faɗa,tana tashi taje ta kawo
masa,karɓa ya yi yace abashi faranti nan ya juyeta ya fara karatu a fili haka ma
Kawu Nuhu cikin ƙanƙanin lokaci kamar mazari jikin Alhaji ya fara rawa kar kar
hannunsa Alhaji Baffa ya riƙe ana cigaba da karatun wani sautin ihu ne ya fita daga
jikinsa kamar turiri sannan ya yi baya ya kwanta,zumar Liman ya ɗiba ya cire hular
kansa ya shafa masa akan take ya fara wani ihu yana magana"zan fita zan fita
malam","waye kai me ka ke ajikinsa shekara da shekaru saboda tsabar rashin imani ko
da yake nasan ƙaton kafiri ne kai shi yasa ka aikata hakan","wallahi malam zan faɗa
wancan ya daina ƙonani","kai Nuhu cigaba","wallahi zan faɗa zan faɗa","muna jinka
Alhaji Baffa ya faɗa"wani ɗan ƙara ya yi sannan ya fara magana bama da kalar muryar
Alhajin ba"ni sunana Oju kafiri ne ni wannan aikin wani bokan kan dutse ne
yasani,kuma shima wata mata ce tasa shi an haɗani dashi ne dan na shiga jikinsa da
sunan kurciya shine na ɓatar dashi amma na kasa hanashi ya yi kasuwanci duk garin
dana kaishi farin jini yake hannun ƴan kasuwa yanzunma bansan ya akai ya haɗu da
ɗansa ba kuma dama makarin abin shine ya yi magana ko a rashin sa ni ne da ɗansa
tofa asiri zai tuno sai gashi lokacin ya yi ashe",liman ne ya katse shi"ka kyauta
ai ka cutar da mutum na shekara talatin da biyu zakaiwa Allah bayani yanzu ka faɗi
mana waye yasa amai aikin kurciyar",tunkan ya gama maganar ya fara bashi
amsa"kishiyar Babar abokinsa Aminu"salati Iyyo tasa tana juya kai,liman ne ya ƙara
magana"to mun jika yanzu zaka fita ko mu babbake ka","zan fita mana aiko baku
cireni ba ruhin ɗansa bazai barni na zauna lafiya ba","to fita yanzu kuma karka
cutar dashi kar ka ƙara dawowa wannan ahalin kuma wancan ahalin nasa karya manta
su","bazan ƙaraba suma bazai manta ba",wani baƙin hayaƙi ne ta baki ta hanci ya
fara fita na ƴan mintuna yana gama fita Alhaji ya fara tari ruwa aka kawo aka bashi
sannan Habib da yay saƙare ya taso yana goge mai zumar kansa,yana cikin shan ruwan
kamar wanda ya tuna wani abu ya janye kofin bakinsa yana kallon su Alhaji
Baffa"Baffa kaine anan"kallon mutanen wajen ya shiga yi"Halima Sa'adatu Nuhu",duk
amsawa sukai,ai sai ya zabura"Baffa ina Aminu da Haruna",Iyyo ce ta fashe da
kuka"Habibu !Aminu ya rasu shekara goma sha uku kenan yanzu kasan ka dawo
hayyacinka",fashewa ya yi da kuka sosai ya koma ya zauna sai juya kai yake"nasani
Iyyo nasan na dawo hayyacina yanzu abokina ɗan uwana ya tafi ya barni ashe ba rabon
mu gana"kallon Habib ya yi"dama kai ɗan wannan a halin ne ashe shi yasa naji a
jikina duk duniya kai ɗana ne ashe banyi kuskure ba",Alhaji Baffa ne yace"wannan ba
ɗan Aminu bane ɗanka ne shima sunan sa Habibu",ba Babban Yaya ba Alhajin ma ya
fishi ruɗewa,da ƙyar Babban Yaya ya haɗa kalaman bakinsa yace"bangane ba Alhaji
Baffa shine kuma Babana to margayi fa","wannan batu ne mai tsawo Habibu ya kamata
ayi shi agaban iyalansa wato matansa",cikin sanyin jiki ya dube su"Baffa za'a zo
dasu yanzu",wayarsa ya ɗauka ya kira Hajiya Fulera jin muryarsa cikin sanyi yasa ta
faɗin"lafiya Alhaji","ki faɗawa sauran ƴan uwanki da yara kaf ku fito yanzu za'a zo
ɗaukarku akawo ku inda nake","kamar ya Alhaji meke faruwa ne","ina gidanmu ne nima
naga iyayena da ƴan uwana dana faɗa miki ina nema","ka warke ne Alhaji","sosai ma
kuwa na koma kamar da sanda baku sanni ba kawai ku fito","to Alhaji",yana kashewa
ya kira waɗanda ya bari a waje ya basu Umarnin suje su ɗakko su hajiya acan gida su
kawo su nan suma,kowa jigum ya yi abin kamar almara.
Baƙaramin tashin hankali Hajiya Fulera ta shiga ƴan uwa kuma da dangi ita da take
ƙara assasa abin dan kar ya gane kowa nasa hatr ya bar duniya'kunji kamar tasan shi
zai fara mutuwa ko tasan gawar fari tsakaninsu dan hauka',wata number ta kira da
wayarta tayi magana cikin wani yare na ƴan mintuna sannan ta kasheda ƙyar ta
lallami kanta ta tura yaranta suka kai saƙon ga sauran matan sannan suka fito aka
kwaso sunsha mamaki ganin unguwar da aka kawo su har ƙofar gidan aka buɗe musu mota
suka firfito yaran sai tsalle suke nan aka nuna musu gidan suka shiga da
sallama,wato kana ganin su kaga matan mai kuɗi saboda kalar fatarsu ma ta musamman
ce,sannu da zuwa su Mama ke musu fuska sake suke amsawa dama an ƙara shimfiɗu a
waurin nan duk suka zauna aka shiga gaisawa cikin girmamawa da mutunci dan Hajiya
Fulera ganin Alhaji Baffa yasata ta shiga hankalinta dan ya ma ta kwarjini bana
wasa ba,gyaran murya Alhaji Baffa ya yi ya dubesu dukkansu,sannan ya kalli Babban
Yaya"Habibullahi Rayuwar da akai anan gidan a gaskiya da wuya ayi irinta a wani
wuri a zauna lafiya Babanka Habibu shine mahaifinka na ai nahi wato wannan,shi
Babanka Aminu abokaine na haƙiƙa masu sadaukarwa junansu farinciki,nasan kana
mamakin wannan ce mamanka ko kana da yayu ƴaƴanta na wajan Aminu sannan ace ta
haifeka kuma ace Babanka daban? sannan ga ƙanne ƴaƴan Aminu ko to abin inba bayani
aka maka ba bazaka taɓa ganewa ba,amma zan warware muku abin yanzu",gyara zama ya
yi haka kowa ya nutsu ana saurarensa"Asalin lamarin da ni da Baban Habibu abokai ne
sosai acan garinmu kuma maƙotane iyayen mu tare muke komai na rayuwa dashi bamai
rabanmu kuma, sanda na fito kusuwanci wannan garin tare muka zo dashi amma da muka
koma sai Allah ya masa rasuwa alokacin yanada yara biyu Sadiya da Habibu nima ina
da yara biyu Aminu,Haruna sai cikin Nuhu dana tashi dawowa inda nake kasuwanci
saina ɗebo gaba ɗayansu ƴaƴana da matata da yaran da abokin nawa ya bari na taho
dasu saboda asamu mahaifiyarsu tayi aure dan ƙauye ba ruwansu da yaranki aure zaki
muddin mijinki ya mutu,sanda mukazo nan saina sa su a makaranta amma iya mazan dan
Sadiya tayi ƙanƙanta kuma a sannan ba'a sa yara mata karatun boko,sanda nazo nan
ƙasar gidan dana sauka da fari shi mai gidan shine yamin hanya nasai wani gidan
babu jimawa da zuwa na haɗu da Haulatu ban taɓa jin ina sonta ba amma nace saina
aureta,babu daɗewa da maganar na aureta kwananta arba'in A'i ta haihu ɗanta namiji
Nuhu kenan tun sanda Haulatu taga A'i ta ƙara haihuwar namiji sai tasa wani hali
aranta kullum tanawa A'i habaici itama ai mazan zata haifa,ni shaida neA'i bata
taɓa tankawa Haulatu ba duk kuwa abinda take ma ta,har Allah ya bawa Haulatu ciki
ta haifi namiji Rabilu,bayan ya ye shi tare suke da wani cikin nan Hankalin Haulatu
ya tashi ta rasa ina zata sa kanta cikin A'i nada wata biyar ya ɓare murna sosai
Haulatu tayi agaban kowa,amma ba wanda ya kulata,bayan ƴan watanni Haulatu ta haihu
ɗa namiji Ibrahim murna tayi sosai in na mutu tanada kaso mai tsoka a
dukiyata,bayan yaye Ibrahim Haulatu ta ƙara haihuwa amma mace to tayi murna amma
burinta ta haifi maza da yawa sannan macen ta biyo baya,a gidan nan Haulatu ta
takurawa Habibu da Aminu komai aka rasa agidan nan saitace sune ni kuma da yake
nasan halinta bana kula maganarta har suka girma tsakanin Aminu da Habibu akwai
abota ɓoyayya ta musamman,watarana na tura Habibu ɓaɓura bayan ya dawo sai yake
faɗamin yaga wata yana so kuma zai koma,nayi murna sosai kwana kaɗan sai ni da
Aminu mukaje Gaya anan Aminu ya gano Sa'adatu yace yanaso ashe wani ya ragashi bamu
sa ni ba ni kuma danawa Babanta magana da yake abokina ne sai ya bani auranta,mun
dawo gida akai shirin biki mukaje can ƙasarsu aka ɗaura auran dan ba ƴan nan haka
ba ne,sanda aka kawo yarinyar ashe itace Habibu ya gani a ɓaɓura gidan yar babanta
maganar da ya ma ta shine ta faɗawa mahaifinta tace yace zaizo,amma waɗannan yaran
tunda ta shigo gida bai taɓa nuna yasanta ba itama haka,haihuwarta biyu Hasiya da
Mabaruka,a sannan na haɗa auran Sadiya da Haruna,tare suka sake haihuwar mata,duk
wannan abu da ake Haule na kallo amma bata magana tayi zuru ashe ta ciki na ciki
ita taje tayo bincike miye tsakanin Sa'adatu da Haruna a ranar sunan haihuwar yaran
da sukai Haule tai niyar yiwa Sa'adatu sharri da Habibu amma Allah ya yi musu
taimako suna tare ne danta ɗauka shi kaɗai ya shiga ɗakin mejegon da asirinta ya
tonu anan ta shiga fallasawa kuma aka tabbatar hakanne,kwanan Sa'adatu sittin da
haihuwa batare da shawara da kowaba Aminu ya saki Sa'adatu saki uku,na shiga tashin
hankali sosai da sosai amma ba yanda na iya,amma me sai Aminu yazo da wani wai
saita gama ma idda sannan zata koma ma garinsu a haka na amince masa babu jimawa
Aminu yazo ya tasa ni agaba saida na ɗaura auren Habibu da Sa'adatu abin saikace
almara koda akai auran suna nan aɗinke suna kasuwanci gashi hannunsu akwai albarka
komai suka taɓa sai ya hau,wannan aure ya baƙantawa Haule amma A'i murna tayi
saboda halinsu ɗaya da Aminu suna son farantawa wani koda su zasu cutu,Haule tayi
ta buge buge kan a raba auran nan amma Allah yace eh dole ta haƙura da abin yaƙi,
bayan auran da shekara biyu sai kwatsam aka nemi Habibu aka rasa tashin hankali iya
tashin hankali mun shige shi kullum Aminu a hanya yake wuni yana kwana neman abokin
shi da haka har akai wata huɗu saiga cikin Sa'adatu ya bayyana wannan ciki Aminu ya
ɗauki son duniya ya ɗora masa har Allah yasa aka haihu ɗa namiji ranar suna Aminu
ya saka masa Habibu tana arba'in bana nan a gidan haka A'i taje ƙauye sai kawai
Sadiya da Haruna sukaga Haule na watso kayan Sa'adatu wai tabar gidan tunda bata da
gado a cikinsa,tana kuka tafito anan Sadiya ta fito ta shiga da ita ɗakinta jifansu
taita yi harna dawo na tarar kaca kaca na ma ta kuma na saketa saboda yau abin nata
ya ishe ni na gaji da halinta,muna cikin haka Aminu ya dawo ya tarar tsaki ya yi
jin me take ya fita ma agidan,itama kayanta ta ɗiba ta tafi babu jimawa aka kawo
min gawarta tifar yashi ta bige ta bakin ti,anan gidana aka mata sutura aka
binneta,tunda ta rasu A'i ta riƙe yaranta ba tsana ba tsangwama sai dai kash sun
riga sun ɗauki halayenta kuma har yau kai a unguwar nan da muka dawo ba wanda yasa
ba ƴaƴanta bane,bayan shekara biyu Aminu yasake maida auransa da Sa'adatu shike
nan,amma kullum bai daina neman abokinsa ba,har Allah ya masa rasuwa da sunan
Habibu a bakinsa ya tafi,Habibullahi ya tashi da wayo ga farin jini ga hikima dan
in ya yi abu saika ɗauka ya shekara sittin wannan halin nasa yasa ƙannensa ke
mutuƙar tsoronsa kuma suna girmamashi gashi nan ku yara wannan yayanku ne
fa",iyayen share fuskarsu sukai saboda saida kowa ya yi kuka,yaran kuma na kallon
Babansu na kuka su shine yasa su nasu kukan,jikin Babban Yaya suka haye suna kuka
ganin babansu nayi saboda wasu dai basu san me ake cewa ba,ɗaga kai Babban ya yi
nai sauri komawa soron ina Hawaye"zo nan Nana",cak kukan Alhaji ya tsaya ya ɗago
kansa,Nusaiba ce tashiga goge mai fuskar"Abba na kayi shiru to",take tambayar sa"so
ki ke sirikata ta ganni ina kuka",juyowa kowa ya yi yana dubansa shima kallonsu ya
yi"Halima ai kina ganin Habib kinga Nana dan baya magana biyu bai ambaci Nana ba
duk inda ya zauna sunan ta yake rubutawa,ƴar waye ne?",murmushi Iyyo tayi "ƴarka ce
ai","ƴata Iyyo","eh mana Autar Halima ce",bakinsa ya dafe"lallai Allah mai iko",da
sanɗa na shigo wuff naje na shige ƙarƙashin hannun Babban Yaya,ƴar dariya Alhaji
Yayi"fito mana Nana na ganki ƙara ɓoyewa nayi naƙi fitowa,kama haɓa Umma
tayi"Halima dama Nana nada kunya haka","nima yau dai nagani"duka dariya akai nan
Hajiya Harira tace"a a kubarta ai wurinmu zata koma"da sauri na ɗago"ba inda zani
na bar Aunty Mama"dariya suka saka,suna tambayar wace Aunty Mama",Iyyo ce tasa a
kira ta nan sukaga kamar ita ta haifi Nana dan suma sunga ta fi kama da ita,gaisawa
sukai da baƙin sannan Umma take faɗa musu abokiyar zaman Halima ce itama sunan ta
Halimar,mamaki sukai tayi nan Alhaji Baffa yace ayi sallar isha sannan akira masa
kowa yazo kafin su tafi sugan na gani sauran a haɗu daga baya,da wayo Babban Yaya
ya ɓoyeni muka shiga gida sannan na fece aguje ciki.

Bayan sallar isha kowa yazo dan antafi kiran matan Kawu Rabilu saiga Gwaggo
Asama'u a hanya itama amma abinda ya kawota daban,samun abubuwa biyu a rayuwa
farilla ne wato farin ciki ko baƙin ciki,to hakan ne ya faru yau muraran wasu suka
nuna farin ciki wasu kuma suka shiga yaƙe saboda abin bai musu daɗi ba,amma duk
wannan abin ƙiri ƙiri naƙi zuwa,ina nan laɓe ina leƙensu na sakankance naji caraf
an kama min hannu ihu na buɗe baki zanyi naji Abba na magana"to gashi yanzu na
kamaki kuma ƙafata ƙafarki","wayyo Abbanmu kayi haƙuri","to shiga ciki",saɗaf saɗaf
na wuce dama falon Mama ake na zauna can gefe ranƙashina Ya Sumayya tayi"munafukar
ƙarya waike mai wayo ko","wayyo Babban Yaya",kafin na rufe baki ya zuba ma ta
rankwashi aka ita batasan ma sanda yazo kusa da ita ba,Allah yasota ma kanta ba
kitso da taji ajikinta,dafewa tayi tana tashi da gudu"Allah shi ƙara waya ce ki
daki waccan tsuwwar kinsan yana nan",Ya Dijama ta faɗa tana dariya,hararar ta
tayi"wallahi zan kama ki","ba komai in kama ni nasan ba iya dukana zakiyi ba",ƙwafa
tayi tana shafa wurin,dariya su Hajiya Fulera suka yi nan ta dubi Iyyo"Hajiya muna
neman alfarma guda ɗaya","tame Fulera","a bamu Habib mu tafi dashi saboda gidan nan
na buƙatarsa ni nasan matsalolin Alhaji lamarinsa yanzu sai ɗansa",dariya sukai,nan
Iyyo tace"ai wannan Sa'adatu zaki tambaya",da sauri Umma tace"a a Iyyo gashi nan su
ɗauka ai dama namiji shi ɗan zaga duniya ne ba mai zama wuri ɗaya ba ne","mungode
sosai da wannan alfarma da ki ka mana kuma Habib har abada naki ne ki ƙaddara ko ya
yi nesa dake tofa yana nan a zuciya da ruhinki kina binsa da addu'o in nema tsari
da kariya kina sawa rayuwarsa albarka sai komai nasa yana haske","insha Allahu
Hajiya",wannan maganganu yasa zukatan matan Kawu Iro da Gwaggo Asama'u baƙi
sosai,kishin bata haifi ɗa namiji ba ya kamata inama sanda Habibu ya nuna yana
sonta ta amince da yanzu tasan itama tana ɗa dashi amma wai kaf dangin ace Habib ne
magajin wannan dukiya wallahi tayi alƙawarin saita lalata mai rayuwa,ido da ido
sukai da Hajiya Fulera kamar tasan me Gwaggo Asama'u ke saƙawa aranta ai kuwa ta
kwaɗa ma ta harara da kashedin kar ki soma yin me ki ke tunani da ido dan san Habib
take ita da gaske ta tabbar da zata tara abin duniya a hannun Alhaji muddin yaga
tana sonsa da gaske,sai wajen goma sannan duk suka fito aka musu rakiya bakin
mota,amma Babban Yaya bai bisu ba yace sai gobe zai shigo,koda ya shirya kayansa
tare da Umma da Aunty Mama sukaje sun yaba da yadda suka tsara masa inda zai zauna
sannan an tarbesu da mutunci sosai.

Vote
Share &
Comments

Û̬m̬̂ m̬̂ û̬ ŝ̬â̬d̬̂ d̬̂ î̬q̬̂ 🌈🌈🌈


🌈🌈
🌈

Babban Yaya Free ne amma me so ya biyo ni Pc in sa a group don shagalin Nana


na buƙatar comments.
08146711395

1️⃣ 3️⃣ chapter 1️⃣3️⃣

Bayan wata ɗaya yau Babban Yaya yake shirin barin ƙasar gaba ɗaya ina ɗakin
Aunty Mama ya shigo"zo nan Darling sis",da sauri na taho wajensa"gani Sweety Babban
Yayan mu","yauwa zauna"ina zama ya juyo ya kama hannayena,cikin murya mai sanyi ya
fara magana"kinga zan tafi ko kimin alƙawarin zaki dage kina karatu kinji banda
wasa so nake naga kinyi har digri",murmushi nayi"insha Allahu zan dage","Yauwa
Sweety ƙanwa"ya kamo hannuna muka fito a lokacin da ƙyar muka rabu,ina ta kuka baji
ba gani ranar da fushi na wuni sai masifa nake da haka aka ɗebi kwana uku da
tafiyarsa ganin ba sarki sai Allah na haƙura tunda dai banga zai dawo ba bare yace
ya fasa ne.

Da tafiyarsa abubuwa da yawa sun faru saboda sun masa albashi yana turo mana
kaf abinda yake samu ga Abban ya dawo gida kullum yana nan wajen Iyyo wai ƙara'i
yake sai ya rama zaman da baiba na da a gidan haka zai tasa mu yay ta kallon
ƙuruciya,makaranta kowa yana zuwa haka su Ya Ruma can gidan Umma Ya Fatsima dasu
Sumayya su dama basa biyewa yayyensu da iyayen su muna kula juna kuma ko zamuje
gidan akoro mu sai mun koma,Umma hankalinta ya kwanta dama akullum tana rayawa
aranta Abban Babban Yaya na raye ashe hakanne tana farin ciki yanzu ƴaƴanta kaf
suna da abinyi kuma sunaji da ita tunda Isma'il ma na aiki haka Hashim ga Ibrahim
shida baima gama karatun ba ga su Khalid da Umar duk suna karatu abin dai ya yi dai
dai.

******
Acan ma bayan sun sauka su goma ne wakilai suka tafi Kumar ya yi bajinta an
samu fili mai fuska kuwa a nan garin GOA sannan aka siya komai dai na buƙata sun
nemesa hakanan sun samu ma'aikata bila adadin,sati da fara ginin labarin ya fita
nan da nan masu buking aikin suka fara wasu ma cos aka ƙara turasu kamin lokaci ya
yi ana haka ya saka takardun Saddi'q da Haruna saina Isma'il, babbar magana sanda
kira yasame su Abba dakanshi yaje gidan kuɗin jirgi ya tura ma saddi'q da Isma'il
nan da nan suka dawo abinka da manya asati visa ta haɗu nan Abba ya sako su a gaba
suka taho tare suma cos aka tura su,koda Abba ya gama bincikar gini abin gwanin
sha'awa sunyi ƙoƙari sosai su kansu sauran da sukazo daga baya sukaga ƴaƴansu a
wannan halin saida abin ya burgesu wato girman kai ba abinda yake ƙarawa face
ƙasƙanci yau ga yaransu suna aiki tuƙuru dan ba zaman kallo suke ba kowa inda
basirar sa take anan yake aikinsa sunata tsare tsare batare da kowane ɗan ƙaƙale ya
taya su ba bare asamu mana ƙisa,koda Parker yasamu labarin abinda sukayi bayan sun
sanar musu sun fasa saida baƙin ciki ya kamasa ashe wayo sukai bai sa ni ba,a
wayance yazo har india yaga me suke yi takaici na sashi ya yi ya koma aranar dan
bazai iya kallaba ya tabbata suka buɗe wannan company sai sun doke shi ashekara
guda,haka dai abin yake tafiya kullum yana waya da gida ga Hajiya Fulera da Hajiya
Harira dake janshi a jiki abin da yasa Alhaji ke warware musu account kenan yana
basu kulli waisu ƙaru,Hajiya Salma da Amaryar Alhaji Safiyya su basa nuna komai ba
yabo ba fallasa da yaje akwai wani babban sirri agidan Alhaji wanda yake ɓoye
tsakanin Hajiya Salma da Safiyya akwai ɓoyayyar alaƙa wadda ba wanda yasan da ita
sai iya su kaɗai ko iyayensu basu san da hakan ba alhalin ansansu a inda suke
ƙawaye ne amma sunyi faɗa harda zubda jini tun daga nan akai baran baran ba ne kula
wani sanadin iyayen ma suka raba wajen zama,amma su ashe manyan munafukai ne zamuji
me ne alaƙar su ta auren miji ɗaya kuma suka ɓoye hakan ba wanda ya sa ni.
Wannan abu na ɗaukar su Saddi'q ya haddasa rigima agidan dan ƙiri ƙiri su
kawu Rabilu suka yima Baffa magana ba'a haɗa da ƴaƴansu ba saboda ana musu baƙin
cikin kar ƴaƴansu ci gaba kaf abinda suke Abba najinsu basu sa ni ba,ƙarasa shigowa
ya yi ya kalli su kawun yace"duk suje su kawo masa takardun karatun yaran ko na
secondry ne shi zai basu aiki amma har bayan sati shida Abba ya dawo ba'a ƙara
tayar da maganar ba saboda ba takardu kuma sun san sauran dai takardu aka kai amma
su nasu yaran bama su tsaya karatun ba kullum akoro su ake saboda rashin ji da jan
magana.

Yau gidan mu a farin ciki muke Baffa zai dawo,ko ina na gidan yasha gyara ga
abincin tarba iri iri dan yanzu bama layin tsakure duk da ada ɗinma ba tsakuren
mukeba saidai wadatar yanzu tafi ta da Abba da Babban Yaya sun tsaya mana,mun taso
a islamiya ina ta gaban ƙofar Iyyo ina masifa naji anja min hijabi a masifance na
juyo naga wani wanda ya isa ne ya yi min haka"Baffffaaaaa"na ƙwala ihu ina
ƙwaƙumeshi kunnensa ya toshe"wayyo autar mata zata fasawa Baffanta kunne,da gudu
Ƙarami ya fito daga gidan Kawu Nuhu ya doso Baffa shima su Ya Ibrahim dake can gefe
duk suka taso suma,nan da nan wajen ya cika ana masa sannu da zuwa Alhaji Baffa da
Abba ne suka fito a gidan foster Baffa ya yi dan duk abinda ake bai san komai ba,da
ƙyar yasamu ya janyo ƙafarsa ya matso kusa dasu,hannunsa har rawa yake ya taɓa Abba
yaji mutum ne ko kuwa,tabbatar da shine yasashi yin ajiyar zuciya"Yaya Habibu dama
kana raye",ya faɗa maganar na kasuwa,musabiha sukai nan suka koma ciki dama ƴan
sannun sun watse anan wajen Iyyo auka zauna kamin suka shiga maida zance ya daɗe
sannan na jashi muka shiga ciki,sannu da zuwa gun su Mama kamar bakisu zai yage
haka muma kaf mun hanashi motsin kirki.
A ranar da Baffa ya dawo Gwaggo Asama'u tazo wajen Alhaji Baffa harda kukan
munafircinta wai abata mukullin wannan gidan can hayarsu ya ƙare kuma basu da kuɗin
biya,tausayi su ɗaya Baffa yaji ya bata mukullin saboda mijinta ne yana son mijinta
danshi kamilin mutum ne kuma baya taɓa roƙo ko yazo ƙofar gidan dan abashi wani
abu,ana bata ta tashi ta tafi ya dakatar da ita kora ma ta ya yi muddin dai dai
darana ɗaya ta ɗagawa mijinta harshe ko kallon banza akan wannan gidan saiya tsine
ma ta kuma ya ƙwace gidansa tunda ba nata bane bare ace mutuwa ya yi taci gadon
gidan, washegari da daddare suka hau kwashe kaya gobarar titi inji Baba dama baya
da kuɗin biyan wannan shekara a tunaninta tayi haka dan ta baƙanta masa amma
batasan sauƙi ne ta nema masa ba,dama Fatsima duk ta wanke masa kayansa ta masa
guga saida Ummansu tazo da niyar kwasar kayansa a wulaƙance sai tagansu a natse a
sif dolenta tasa jaka ta kwashe batare da ta ɓata ba,duk fa bala'in Umma tana
mutuƙar tsoron Baba saboda bai iya fushiba gashi masifar sonsa take,Hhhhhhhhhhh
saboda Baba ma fa ba baya ba wajen kyau kawai dai yana da duhun fata bai kai ƴan
uwanta haske ba fari sai Abba Habibu ga hutu ga jindaɗi da jikin yasamu shi yasa
baya tsufa ma.

Tunda su Mama suka samu labarin dawowar Gwaggo Asama'u layin suka san da wata
ƙasa inba hakaba ba yanda za'ayi ace ta dawo layin lokaci,Aunty Mama ce ta farawa
Mama maganar nan tace ma ta"karki damu Halima yanzu fa ba da bace duk matar da ta
taka mu mutaka muma ai ba ragowa yazu kingan mufa ciki rufin asiri bamu rasa
komaiba wallahi kima cire komai a ranki in ta tako gidan nan munada basawa fa ko
kin manta ne"da haka Aunty Mama ta ɗauri aniyar ba ragawa ma ta wannan karon kome
zai faru ya faru.

Bayan wata shida:

Gini ya yi nisa an ɗau haramar gamawa shi yasa wannan satin sukayo gida iyasu
banda masu cos su shekara zasuyi a ƙasar da suke.

Misalin taran dare ya shigo unguwar yana sanye da suit blue gashin kansa yasha
gyara ya ƙara zama murjajjan mutum kana ganin kasan waye ya cika akirashi namijin
gaske,Umma suna falo ana kallo ya ɗaga labulen da sallama,ihu suka fasa ga Babban
Yaya ga Babban Yaya tun daga soro na shigo kenan naji ana ga Babban Yaya bokatin da
aka aikoni dashi nasaki nan ya fashe fass ban lura ba ma na faɗa ɗakin da mugun
gudu a bakin ƙofa yake duk da ban tabbatar ba a haka na daka tsalle na haye
bayansa,ajiyar zuciya ya saki yana murmushi sai yanzu yasan ya shigo ƙasar sa dan
Nana ce duniyarsa,"sannu da zuwa Babban Yaya","yauwa sannunku Maryam,Umma sannun ku
da gida","am Habib ai na kasa magana ne dama kana hanya ?","wallahi kuwa Umma",duk
wannan maganganun da yake fa yana tsaye ina bayansa yake yinsu,"saiki sakko ai
tunda dai ya dawo adaina bacci da surutai saikace mai ƙwanƙwamai",Ya Aziza ke
faɗa,ɗagowa nayi na murguɗe ma ta baki,sakko ya faɗa yana jawo ni na dire a gabansa
murmushi ya yi"a lallai su Umma sun iya kiwo kalli yadda ki kai kumatu","kai Babban
Yaya kwakwar manja fa nake ci shine nai kumari",dariya suka kwashe da ita,"Darling
Yaya zo muje na nunawa su Mama kai harma Baffa kasan ya dawo",hanun nawa ya riƙe
muka fito nan akaita shigowa da kayan da yazo dashi,koda mukaje canma sunsha mamaki
sai wajen sha ɗaya mukarabu da ƙyar.

Washegarin zuwansa nan Alhaji Baffa yasa asanarwa na kusa dana nesa yana neman
kowa nan da kwana uku,aikuwa saƙon ya iske kowa tun ana i gobe taro wasu suka fara
sauka kai masha Allah aranar inka shigo unguwar saika ɗauka biki ake kowa ya taru
har iyalan Abba gidan ya yi danƙam da mutane bayan sallar la'asar a tsakar gidan
akayi shimfiɗu dama gidan Iyyo akwai girma da rushe shi za ayi da an gina Babban
gida kowa zama ya yi aka nutsu nan Alhaji Baffa ya fito ya zauna kan farar Kujera
iyayen maza ya kalla yana mumushi"Alhamdulillahi ina godiya ga Allah da yasa kaf
ɗinku ku ka amsa kirana baƙi daga cikin mu ina fatan yanzu duk ansan juna
madalla,na taraku anan ne dan inaɓ sanar muku zan tsayar da ranakun aure na
waɗannan ƴaƴa dama nayi magana da manemin kowacce amma wasu ni na haɗa abuna da
ƙwarin gwiwar bazasu bani kunya ba,Babban Yayanku duk kun sa ni yana neman aure can
gefe wata ɗiya Hajara masha Allahu naje munyi magana dasu sunce kome muka yanke
asanar musu tunda mu namu da yawa,kuma anyi sa a babba mahaifin yarinyar yayane ga
Fulera to naji daɗin hakanma,bayan shi akwai Maryam babba tanada manemi dama tuni
wato Saddi'q ɗin Baffanku Haruna sannan Ruma duk tuwona maina ne ita kuma Isma'il
shi ya nema da bakinsa sannan Sumayya kowa yasani akwai ɓoyayyar alaƙa tsakanin ta
da Hashim sai yanzu ya faɗa shima bawai cusa masa akai ba sai Dijama itama Haruna
ya yi magana sai Aziza ƙanin mijin yayarta Amina shi yace yana so haka Ruƙayya
itama tanada manemi tuni kuma an tsaida magana sai Kamal yace yana son ƴar
maƙotanmu nan Maryam shima nayi magana sai Aminan Iro Sadisu yace yana so kuma na
amsa itama ta amsa sai Abdul'aziz shima yanada wadda yake so shi,sauran Hadiza da
Fatsima ku nake jira koba wannan taron ya kamata ku kawo min naku,ina sauraren ku
me ku ka ce",Fatsima kallon Baba tayi nan ya ɗaga ma ta kai,da ƙyar ta zaƙulo
kalmar "Baffa ina da shi yace ma da daddare zaizo kuyi magana","to shike nan ƴar
albarka ina jiransa Hadiza fa" Umman su ce tayi magana"Baffa a barta ita sai nan
gaba",da yake Baffa ba ɗan zafi bane sai yace"Allah ya kaimu da alkhairi,maganganu
da tsare tsare sukai tayi har magaruba ta taho sannan akai addu'a aka tashi,matan
kawu Iro na komawa gida bala'i ya tashi Umman su Amina tace ƴarta bazata auri
faƙiri ba ana haɗa kowa da inda zai huta amma su sai ahaɗasu wanda kasuwar ma basan
zuwa yake ba,Alhaji Baffa tazo ta gayawa yace tayi banza dasu danshi Baban nasu
harda duka wai baisan suna soyayya ba da tuni ya raba su,kuji fa kamar wadda aka
cikin maƙiya ɗanfa nashi ne tunda na ɗan uwasa ne uwa ɗaya uba ɗaya amma suke
wannan abin sun manta aure haɗi ne na Allah ba ruwansa da gidan kuɗi kona talauci
matar mutum kabarinsa.
Duk abinki a wurin Abba sai kin tafi da jari mai tsoka kwana uku bayan taron
kowa ya watse saimu yamu kwana huɗu bayan tafiyar kowa Babban Yaya ya sauya min
makaranta masha Allahu ina karatu sosai har Babban Yaya ya koma,lamuran gidan mu
dai dai suke tafiya cike da farin ciki in kaga matsa sai a sauran gidajan dan gidan
Kawu Iro dama kamar filin yaƙi yake.

Vote
Share &
Comments

Û̬m̬̂ m̬̂ û̬ ŝ̬â̬d̬̂ d̬̂ î̬q̬̂


🌈🌈🌈
🌈🌈
🌈

Babban Yaya Free ne amma me so ya biyo ni Pc in sa a group don shagalin Nana


na buƙatar comments.
08146711395

1️⃣ 4️⃣ chapter 1️⃣4️⃣

Bayan wata takwas:

Cikin taku nan na Babban Yaya kamar wani ɗan sarki yake fitowa acikin jirgi yasha
baƙin yadi ɗinkin zamani hafjamfa sai baƙin cover shoe gashin nan sai ƙyalli yake
yasha baƙin glass bayansa Ibrahim da Saddi'q ne sai Haruna sun murje duk sunyi kyau
bakace su bane,Abba da kansa yazo ɗaukar su ya yi farin ciki ganin yanda ɗansa
yazama, waɗanda suka rayu cikin kuɗi da hutu da gata ma basu kaishi ba kai ko
rabinsa basu kai ba,cikin layinmu suka shigo dama layin yasha gyara hakama gidajan
sun koma kalar na zamani ga tiles yasha, soron gidan ya shigo ban lura dashi ba
naji muryarsa a kunnena,"ina zaki ki ke dube dube"kamar saukar ruwan sama naji
muryar sa karma na juyo naga bashi bane yasa na juyo idona arufe,wani dam ƙirjinsa
ya bashi ganin yanda wani kyau ya futa a fuskata gashi fuskar a murje ba
rama,hannunsa ya ɗaga ya ɗora a fuskata shafa fuskar ya yi cikin nutsuwa a hankali
na buɗe suka sauka ciki nasa da hanzari na faɗa jikinsa na fashe da kuka,bugun da
zuciyarsa keyi ne ya sauya jin yadda jikina ya taɓa nashi cikin muryar mai sanyi ya
fara magana"ya akai ne ki ke kuka",cikin shassheƙa nace"bakaine kaita cewa zaka
dawo ba tun wancan watan amma kaƙi","am sorry Sweet Sis gani na dawo uzuri ne ya
tare ni",ɗagowa nayi ina murmushi wanda ya kusa tarwatsa masa zuciya ya kira sunana
bai sa ni ba amsawa nayi"kina yawo ko kina kula maza kiyi faɗa ahanya ko","wallahi
Babban Yaya bana yi kuma ka tambaya kowa sai dai in anmin in tama mutum yana
shigowa gidan Iyyo yofa zai gane bashi da wayo",murmushi ya yi yasan bana ƙarya shi
yasa yake yadda da maganata,hannuna ya kama muka shiga ciki, ihu da murna ne ya
fara tashi saima da sauran suka shigo farin ciki ya kama Umma ta rasa ina zata saka
kanta ganin sun zama mutane,saida suka huta sukaci Abinci sannan aka fara gaishe
gaishe.

Watansu guda da zuwa aka haɗa kayan lefe salo salo a gidan Iyyo amma na Babban
Yaya hidimar na gidan Abba Hajiya Fulera ke komai amma fa tana tatsar kuɗi wurin
Abba shi kuwa tilawa kawai yake wai lefe ake haɗawa nan,ranar daya haɗu aka kawo
gidan Iyyo su Mama ne suka kai gidan an karrama su sosai kuma sunyi murna da
wannan kaya dan abin fa ya ɗau hankali da yawa,dama duk kayan da za'a kai to da
ranar auren suke tafiya wata uku masu zuwa,tunda ake maganar bikin Babban Yaya ban
taɓa sa baki ba dan haushinme faɗa ma nake ji kuma shima baya firar dani sai dai fa
a lefen can da aka kai kaɗan ne basu kaiba kayan da Abba yamin dan kaf kayana na
sif Mama takwashe ta bayar wai sun min yawa hakama Babban Yaya kamar zai goyani
yake min amma hakan bai hanashi ba jiya ya zane min jiki wai nayiwa Gwaggo Asama'u
rashin kunya shike nan na daina masa magana in ma naganshi sauya hanya nake in yaga
nayi hakan sai dai ya yi murmushi ya wuce shima.

Kawo kayan lefen Ya Fatsima ya ɗagawa Umma hankali sosai saboda kaya ne harda na
hauka komai kamar za'a buɗe shago a gaskiya kayan sunyi amma ƴan gidan basu san
angon ba itama sau ɗaya yake zuwa asati ba lallaima in taganshi a hanya ta gane shi
ba.

Bacci nake hajaran majaran naji ƙamshin turaren Babban Yaya a hancina juyawa nayi
naji na dunguri mutum buɗa ido nayi nagansa zaune kusa da ƙafafuwana,tashi nayi zan
bar wurin ya riƙo hannuna ya jawo ni gabansa na tsaya,juyar da kaina nayi wai bazan
kallesa ba lanƙwasa murya ya yi sosai"haba Darling Sis wannan horon ya isa haka
mana kalli yanda na rame fa bana iya bacci bana iya cin abinci sabida kina fushi da
ni,ki sassauta min haka mana tawan",murmushi nayi masa sannan na zauna kusa
dashi,yana ganin hakan yasan na haƙura kenan,tun daga ranar muka shirya nan akaita
mana dariya,ban damu ba amma fa ta ko ina Shirin biki ake har yazo yau mutanen
gidan suka fara sauka washegari ƴan nesa suka fara sauka musamman dangin Umma ita
mai aurar da mutum shida gaskiya amaren sunsha kyau sun ɗau gyara fa ba ƙarya haka
Aunty Hajara Babban Yaya yasakar mata kuɗi sosai shi yasa take fantamawa ga kuma
gatan da ake nuna ma ta a gidan su.

Yau kamu gidan ya cika da mutane ansha ankon atamfa da akayi ni ina nan duk na
burkita kayana ina neman ɗankwali ban ganta ba Aunty Mama na kalla"Aunty Mama ina
ɗankwalin atamfar ankona",kanta ta dafe tana tsaye jikin sif"ki duba cikin ledar
kayan mana kinsan dai babu daidaike agidan nan bare aɗaukar miki ɗankwali ba",tana
rufe baki na hangeshi can kan kaya ɗakkowa nayi na fito da sauri da Ya Amina na
haɗu"ke me hankali zoki rufe wannan gashin in ba haka ba mutane su cinye shi",ɗan
kwalin na ware na yafa sannan na fita,gidan Iyyo na shiga ta bayan Ya Hasiya na
zagaya na fasa ma ta ihu a kunne,salati tayi tana kawo min wafta"wallahi Nana ciwan
kai ce ke",wata mata ce a gefenta tace ma ta"ai Nana zama da ita sai mai hankali
bama mai haƙuri ba","wallahi hakane ai mutanen nan dake tare da ita suna ƙoƙari",ni
dai tunda na gudu ban kuma bi takansu ba inda za'ayi kamun na tafi ni kowa ma
haushi yake bani,Ya Amina ce ta ganni ta ƙwala min kira zuwa nayi ina tura baki"ta
Babban Yaya ya akai ne",kwaɓe fuska na ƙara yi "bashi nake ta nema ba tun jiya ban
gansa ba",dariya ta ɓoye"kiyi haƙuri mana wurin baƙi yake tun jiya zai dawo ai ina
ganinsa zan faɗa masa jininsa na nemasa",kai na kaɗa na fita a gidan,ina shiga
gidanmu naga kowa na fara'a yana washe baki magana in an min saidai na harari mutum
kawai,mamaki abin yake bawa kowa Mama ce kwwai ta girgiza kai takalli Aunty Mama"ga
ƴarki can kishi zai kasheta",tana ɗago kai ta ganni na shige ɗakinta"bari kedai
Dada kullum da zazzaɓin dare take kwana abin har mamaki yake bani","ya daina baki
mace haka take indai tanason mutum taga wani zai raɓeshi","to ai shike nan bari
naje na lallashi a bata","saiki ɗaura niyya kar ciwan zuciya ya kamata"dariya tayi
"kai Dada"ina rizgar kuka ta shigo"ƴar Mama wa ya taɓaki ne",cikin kuka nace"ba
Babban Yaya ba ne ya share ni dan zai yi aure","kai kai bai kyauta ba kam ungo waya
ta ki kirashi"da sauri na ansa ita kuma ta fita,number sa na kira bugu ɗaya ya
ɗaga"Assalamu alaikum Aunty",shiru nayi ina jan numfashi"Nana",rushewa nayi da
kuka,muryarsa ya sanyaya"am so sorry Darling zaisha nasan lafina baƙi ne dani kinji
amma gani nan zuwa",kashewa nayi ina goge hawayen fuskata.

*****

Daga can dama yana gidan da Abba ya bashi ya sauki baƙi shida su Abdallah da sauran
da suka haɗu daga baya sai asalin abokan sa amma kamar ansan juna tuni yana wayar
suna kallonsa yana saukewa suka fara masa dariya suna tsokanarsa wai amaryar ta
matsu ne haka,kai ya girgiza''ba ita bace","kamar ya"har suna haɗa baki wajen
faɗa"Ƙanwata ce","ƙanwa dai kuma ka ke wannan abin kamar wata matarka",tashi ya yi
yana gyara agogon hannunsa"ai ba wai insha Allahu",Yusuf asalin abokinsa ne ya
kallesu"ai shi wannan yana da wani buking ɗin bayan wannan amaryar to akwai
wata",tafawa sukai cikin shaƙiyanci wani daga cikinsu yace"kaga kogin wayo wato
bayan wannan tayi sanyi akwai wata me ɗumi kenan to wallahi ku tashi muje
muganta",tashi sukai ya kallesu yana dariya"ku yanzu Nanar zaku gani yarinya ce
fa","ko yau aka haifeta sai munga me kakewa wannan zumuɗin",murmushi ya yi ya wuce
duk suka fito motocin suka shiga nan suka wuce unguwa su,idona a kulle naji ƙamshin
turaren sa a kusa dani buɗe ido nayi mukai ido huɗu,baki na buntsura na juya mai
baya,dawowa ya yi inda nake kallo ya durƙusa yana kama kunensa"afuwa Ruhina ba
laifina bane",ƙara rushewa nayi da kuka na kifa kaina akan kafaɗarsa,wani abu me
ɗaci ne yaji yana tsirga mai har cikinsa,da ƙyar ya haɗiye shi hannunsa yasa ya
shiga shafar gashin kaina daya wargatse duk gyaran daya sha da haka nayi
shiru,ɗago ni ya yi"tashi ki shirya ina kayanki ki saka mu fita",ajiyar zuciya nake
na girgiza kaina"ban zuwa ko ina ka tafi wajen amaryarka bayan saboda hidimarta ka
manta da ni",da sauri ya riƙo hannayena"kalle ni nan Nana",ɗaga kai nayi na
kalleshi"bana jin ko mutuwa nayi tunda gawa najin komai tana ganin komai ace zan
manta dake kuma kinsan dikkan mai hidima dole amasa uzuri ko,to ki daina wannan
tunanin tashi kiyi abinda nace",tashi nayi na shiga cikin ɗakin Aunty Mama fuskata
na wanko sannan na shafa mai da hoda kamar gaske les doguwar riga na ɗakko na saka
sannan farin hijabi ƙarami nasa takalmi na fito,ajiyar zuciya ya yi ya miƙe yana
kama hannuna muka fito mutane na kallon mu amma ba mai magana danshi ba fara'a ce
dashi ba bare amai wasa dama dai acikin ƴan gidan ne,muna fitowa naga mutane a
tsaitsaye da mamaki nake kallonsu nasan wasu abokan Babban Yaya ne amma bansan
sauran ba,har wajen muka ƙarasa"to ƴan ganin ƙwaƙwaf gata",baki suka hangame
Abdallah yace"wallahi kana da gaskiya nima yau nabi bayanka kuwa"dariya sukai nan
na gaishesu,da fara'a sosai suka amsa min,jinjina ya musu"ya zaku koma ne ko kuma
nan zaku zauna ni unguwa zamu",''ku dawo lafiya komawa ai munsan hanya malam","ok
saikun ganni",motarsa muka shiga ban san ina zai kani ba sai gani nayi a wani ƙaton
super market shiga mukai yace na ɗauki kome nake son ɗauka ba wata tantama naita
jidar kayan banza har saida na fara dariya sannan ya saki nasa ran sai magaruba
muka dawo gida sai mamaki suke wannan wane irin abu ne saidai kawai ayi dariya ni
kuwa ko ajikina ,washegari ɗumbin jama'a suka shaida ɗaurin auran mutane daban
daban anfi awa biyu sanan aka gama aka tashi kowanne ɓangare a unguwar kadan ka
duba sha'ani ake angwaye keta shiga gidaje ana gaisawa dasu na Ya Fatsima ne suka
shigo gidan anata musu maraba,gaishe she aka shiga anan aka nuna musu angon kamar
akan idon Ya Hadiza wa zata gani saurayinta mai kuɗinnan wanda suka kai wajen
malamai dan ya aureta shine ya auri Fatsima Bashir lallai akwai tashin hankali
babba,wani luuu taji badan tayi ta maza ba da tuni ta faɗi a wurin ganin zasu tashi
yasata fitowa sosai dan yaganta,ai kuwa dama ita yake raba idon gani sai gashi kuwa
yana ɗago kai sunzo fita suka haɗa ido murmushin nan nasa mai kasheta ya ma ta
sannan ya ƙarasa fita inta fahimci wannan murmushin yana sane kenan yazo ya auri
ƴar uwarta dan bata tunanin Fatsima tasan Bashir sai daishi lin da biyu ya yi
hakan,wani tunani tayi kawai tayi murmushi tana gyara zamanta a bakin gadon ɗakin
da take kome ta ƙitsa kuma oho,gidan Kawu Rabilu suma taro ya yi taro haka gidan
Umma ai nan ne cambar bikin sai gidanmu a gaskiya Ya Ruma ta wanku kamar yanda Ya
Isma'il ya faɗa to yaga kala malam ga gyara ta ɗauka abinka da farar fata kalar
fulɓen usul ba jaja amare ba ko jikin bliching,a wannan biki Alhaji Baffa da Baffa
fa Abba sun hana bidi'a saidai da yamma aka shirya gagarumar walima wadda ta
ƙawatar ko fatin baza suyi abinda akayi a wurin ba,sai bayan sallar isha sannan aka
fara fitowa da amare ana sawa amota har aka fice dasu,ƙarfe tara saura sannan aka
kawo matar Babban Yaya nan bayan mu dama Abba ya gina babban gida tunda yasan da
zaman auren sa gidan nan ya yi kyau sosai suma sun cikashi da kaya na gani na
faɗa,sun daɗe da kawota sannan suka baje sunata santin gidan ƴan uwanta marasa
hankali sunata ma ta famfo karta ragawa duk wanda bai raga ma ta ba,abin mamaki
anata hira bayan goma sai ƙafar Babban Yaya suka gani a cikin gidan,Ya Usainace da
mamaki ta kalleshi"ango me kuma ka ke anan bayan kamata ya yi ace kana gidan
amarya",hannun sa ya ciro a aljihu ya yafito ta "zo na faɗa miki dalili",ya ɗaga
labulen ɗakin Aunty Mama ya shiga",saboda tsautsayi yasa ta biyo shin kuwa,zaune ta
sameshi saman kujera itama ta zauna","inajinka Babban Yaya",in serios ya kalleta ya
fara magana"Usaina har acikin zuciyata nai baƙin cikin da za'ace ɗakin matar da zan
shiga yau ba Nana Aisha bace a yanzu nazo naganta ko zan sami sauƙin abinda nake ji
acikin zuciyata,kuma koda naje inda take itama zata bar tarihin angon da daya
tsallake amarya kamarta ya yi asarar daren farkonsa",yana kaiwa nan ya tashi fice a
ɗakin yabar ma gidan gaba ɗaya,kasa motsi Ya Usaina tayi gumin goshinta ta share
kenan abinda suka ɗauka wasa ashe gasken gaske ne yanzu Babban Yaya yafi son Nana
da kowacce mace lallai abin ya shige wasa",dafata akai da sauri ta ɗago kanta taga
Ya Hasiya ce,ajiyar zuciya tayi murmushi tayi"ki daina damun kanki wannan al'amarin
yafi gaban tunanin mu dan gwarama ki cirewa kanki shakku ki kalli gabanki Nana ta
Habib ce",dariya tayi "to Allah ya nunamin randa zanga ƴaƴansu","insha Allahu kuwa
muje",nan suka wuce ɗakin da suka sauka dan kwanciya,ni kuwa ɓuya nayi a bayan gado
dan kar ma naga shigowar shi wai shi mai mata har nayi bacci ban ma san ya shigo
ba.

Vote
Share &
Comments

Û̬m̬̂ m̬̂ û̬ ŝ̬â̬d̬̂ d̬̂ î̬q̬̂


🌈🌈🌈
🌈🌈
🌈
Babban Yaya Free ne amma me so ya biyo ni Pc in sa a group don shagalin Nana
na buƙatar comments.
08146711395

1️⃣ 5️⃣ chapter 1️⃣5️⃣

A cikin wannan daren bayan ɗaukar Ya Fatsima Ya Hadiza take faɗama Umman su kaf
abinda ya faru,ba ƙaramin tashin hankali ta shiga ba kuma tayi dana sanin ko sau
ɗaya batacewa Baban saurayin bazaizo ya gaisar da ita ba,rasa sukuni tayi tace taje
ta kwanta ta barta da wannan abin ita tasan me zata shirya sai wannan aure ya mutu
kuwa,duk abinda suke ƙullawa Baba na jinsu kawai ya yi murmushi sannan ya wuce
ɗakinsa saboda yau yana jinsa sakayau kamar an ɗauke masa wani kaya akansa,gidan
kowa ya yi kyau dan Abba ya yi ƙoƙari ya hana Alhaji Baffa ya yi komai wai miye
amfanin kuɗin nasa in baiwa Alhaji Baffa amfani dasu ba,albarka sosai yay tasa
masa.

******
Wurin Umma ya shiga nan ta haɗasu ta musu nasiha mai ratsa jiki sannan kowa ya
fito ya kama hanyar gidansa,
Gidan Babban Yaya da maigadi shi yasa ya buɗe masa ya shiga,da addu'a ya buɗe
ƙofar falon ya shiga ko ina fes amarya na zaune kujerar falo,sallama ya ma ta
sannan ya ƙarasa inda take dai daita kansa ya yi ya saita muryarsa da ta cunkushe
masa,"amarya amarya barka da warhaka",ɗan murmushi ya yi ganin yanda ta motsa
alamar taji me yace,a kusa da ita ya zauna yana ɗaga mayafin"masha Allah kiyi kyau
sosai",murmushi ta saki tana fari da ido"ai kafi ni kyau masoyina",baki ya kama"wuu
wane ni Habibu nai dai dai da kyan ki","abar dai maganar nan","ok to mushiga
ciki",da yanga da yauƙi ta miƙe tabi bayanshi kowa da ɗakinsa dama nata ya rakata
sannan ya fito ya wuce nashi,kamar yadda ya saba haka ya yi wanka yay nafilarsa
sannan ya kwanta awajen ba jimawa ya yi bacci,itama wanka tayo ta sauya kaya jin
shiru bai zo ba yasata lallaɓowa ta leƙa ɗakin da take tunanin shine nasa ganin
yana bacci sai tayi mirmushi sannan ta koma ɗakinta ta kulle wayar yayarta
takira,tana ganin kiranta tai saurin ɗauka itama"gaskiya Yaya ke dabance wallahi
baishigo ba ya yi baccin kuma","ai dama na faɗa miki malam ya iya aiki wannan
baccin haka zaina yinsa har kwana bakwai sannan angama miki aiki saiki bashi dama
akwashi amarci da hujja yana kwanciya dake to kin gama mallakarsa kowa sai abinda
kika aminta sannan zaiyi kinga kema saiki sami rabonki tunda shi yanzu ɗan gata ne
gun mahaifinsa komai bashi zaina yi","ai fa na aminta dake dan haka duk rabon dana
samu tare zamu raba",kamar ba amarya ba haka sukaita hira sai can dare sannan suka
kashe wayar Yayar nata ma ta dariya aranta dan ita kaɗai tasan burinta kan Hajara.

Bayan kwana goma ban ƙara tsayawa Babban yaya ya ganni ba kuma saiya shigo
gidan su kansu basu san ina nake ɓoyewa ba yauma sallama ya shigo zasu wuce india
tare amma inaji naƙi fitowa har suka fita gidan itama ranta ƙal farraƙunta ya yi
aiki kenan,yana fita na fito a bayan gadon ɗakin Aunty Mama na zauna nasha kukana
sannan na fito ban kula kowa ba na wuce wajen Iyyo ta,itama ɗin bacci ma take sai
kawi na haye kujera na kwanta nima.
Tunda suga shiga jirgi baya umm baya ko motsin kirki gaba ɗaya ransa aɓace yake
wato dai da gaske ƴar yarinyar nan daya raina kishi take,har suka sauka baya magana
sai in ita ta masa gidan da suka sauka ma ya ruɗa Hajara ashe nan ma agatan daya fi
nacan yake,Soyayya sosai take nuna masa ko maganar Nana baya ma ta hakan ya
tabbatar ma ta ya manta ma da ita har suka ɗebi watanni acan.
*****
Dukkan bin malamai da zuwan gidan Ya Fatsima da Ya Hadiza keyi sai a sanar ma
ta bama asan wa take nema ba haka duk wanda ta tambaya baya cewa yasan shi kuma
bayan da duk tare suke ita tasani,tashin hankali ta shiga sosai har Umman amma ba
yanda zasuyi dan suna magana za'ace da wata a ƙasa shi yasa sukai shiru malamin
kuma ya musu alƙawarin wanda ya fishi zaizo,shi yasa suka sakankance ita kuma tana
ƙara botsarewa da buɗe ido cikin ƴan bariki.
*****
Basu jima da tafiya ba na shiga SS ONE,amma karatun yana tafiya ne da tunanin
Babban Yaya,saidai ba wanda ya gane kai saika ɗauka mantawa nayi dashi.
Yauma ina saka kayana asif Aunty Mama ta shigo"wato ke Nana kishi ko to kiyi
sake fadar taki da take hannun Yayanki duk waccan ta haɗa ta ƙwace bakisan wannan
burus ɗin da kikayi bashi da alfanun komai sai nesanta kanki da kikayi dashi kalla
fa kin fara girma amma kin nesanta kanki da wanda zaki je hanunsa watarana ki dai
yi karatun ta nutsu kina wayo ai",tana kaiwa nan ta fita ta fita tabarni,to tun
daga ranar kullum saina masa text a wayar Aunty Mama amman in ya kira bazan ɗauka
ba,hakan daya gani ne yagane magana dashi ne bazan ba kawai ya bari muyi ta magana
ta haka nan dan nan farin cikina ya dawo shima haka nan nacigaba da ƙulla tsiyata
dan saima abinda ya ƙaru tsakanina da duk wanda yace bazan iya ba kullum faɗa amma
naƙi dainawa gashi Iyyo tayi Allah ya isa ga duk wanda ya dake ni ko bayan ranta
waifa ita nan Babban Yaya ta wakilta shi yasa wai takeji dani wannan jin to na
mutum biyu take yi.

Tunda suka zo sai a wannan lokacin ta lura yana cikin farin ciki sosai kuma
yana bata dukkan kulawar da ta dace,shi yasa kaf ta allaƙa hakan da aikin malamin
su,yauma yana dawowa yake sanar ma ta tashirya sati mai zuwa sazu koma tunda komai
ya gamu sannan kowa ya kama aiki cikin kulawa da cikakken tsaro da ƙasar ta
basu,bataji daɗin hakan ba amma dolenta tashirya dan tana gudun yin wani da zai
ɓata nasa rai yanzu zai birkice kamar wani mai iskokai.
*****
1:30 muka tashi a makaranta dan haka a ƴan mituna na shigo gidan takalma na gani
a ƙofar ɗakin Mama sai na shige ɗakin Aunty Mama a kujera na jefa jakar haka
hijabin nima na bisu ina faɗin wash"sannu Darling sis"naji maganar sa bagatatan da
fari tunani na zaunayi wake tsokanata ko Ya Ashiru ne sai dai na daure na kalli
gefe"Babban Yaya" na zuba uban ihu na juya na haye kansa ina ihu"zaki karya ni fa
ƴar afiruwar Aunty","wayyo Allah yaushe ka dawo","kina makaranta shine nai zamana
nan sai naganki zan fita","wayyo tsaya ni mu fita tare dan Allah","to ina
jiranki"ɗaki na shige da gudu na faɗa banɗaki ruwa kawai na watsa na fito na saka
doguwar riga da ƙaramin hijabi na fito"kai harkin gama","ƙwarai makuwa har wanka
nayi fa",haɓa ya riƙe "ainasan ki sarai da tsaka tsaka mi",ƙafa na fara dirawa
aƙasa"amma kasan ina wanka ai",hannuna ya riƙo"farin sa ni ma kuwa to muje",tare
muka fito"Mama mum tafi gidan Yaya"da sauri ta kalleni shi kuma yana musu sai
anjima suna amsawa,Mama dai banda kunyarsa da tace bazani ba dan tasan sarai
sainayi wani abin kuma ta lura da matarsan ma basan wani ya raɓeshi take ba amma
adole tai shiru tana fatan a wanye ƙalau.
Tunda aka buɗe masa get ta leƙo ta ganshi amma bata ganni ba dan yamin tsawon
da ba lallai ta ganni ba,turare akaje aka ƙara shafawa saboda salon birge maigida
Babban Yaya Hhhhh,sai dai wannan karon tana fitowa aɗaki muna shigowa nice agaba
shi kuma abaya daurewa tayi ta washe baki"My Love ƙanwata ka kawo min"murmushi ya
yi"eh naje na ɗaukota ne tazo muyi hira dan na daɗe banjita akusa dani ba kuma
hakan cutuwa ne agareni",wani malolon baƙin ciki ne tokare ma ta maƙoshi saboda
kalamansa sunfi saukar ruwan zafi a jikinta,itama murmushin ta ƙaƙalo amma dana
kalleta wani mugun kallo take watsamin,tun daga nan nagane dama maganarta bata kai
zuci ba,zama ya yi yana ajiyayar zuciya ganin ban zaunaba yasa ya kamo hannnuna na
zauna kusa dashi hannun tabi da kallo kamar ta guntuleshi,amma ta daure itama ta
zauna tana ƙaƙalo hirar dole"ajinki nawa yanzu a makaranta",Babban Yaya na kala
naga shima ni yake kallo"ajina huɗu ss 1",kama baki tayi tana kaɗa kai"ashema
yarinya ce ke to saiki dage da karatu kiyi nisa sosai kema kiyi ƴar digiri ɗin da
akeyi sannan ki asamu zankaɗeɗen saurayi a aura miki ko",wani kallo muka shiga bin
ta dashi amma na shanye maganganun ta nayi murmushi"ai Aunty Hajara ni mijin da zan
aura ma ba'a auri uwarsa ba dan haka ki daina tunanin zanyi aure nan kusa","Allah
ko amma kiyi a hankali karki tsufa baki aure ba danmu asannan mun aurar da ƴaƴan
mu","Aunty ai saiki aurar damu tare ko","to shike nan Nana da nayi murna kuwa",wani
irin takaici ne ya kama min wuya na haɗiye abinda nake ji na juya na kalli Yaya
naga ya rufe ido ya jingina kansa da kujerar,tashi nayi "Yaya na tafi",kafin suyi
magana nakai bakin ƙofa,ina fitowa nasa takalmana na bar gidan,ban shiga gida ba na
shige gidan Umma tana zaune kan tabarma tana yankan alaiyahu,kan ƙafarta na faɗa na
rushe da kuka"subahanallahi Nana lafiya wa ya taɓaki haka",kasa magana nayi sai
kuka,kaina ta shiga shafawa har kukan ya lafa"me aka miki ne",da ƙyar na saita
kaina"ba komai Umma makaranta ne wata ta zageni na rama shine aka duke ni","wayyo
yi shiru kiyi haƙuri ki daina faɗa a makaranta bakiga kin girma ba","ai ba ni na
jata ba Umma itace ta fara","to kiyi shiru kinji ƴar Umma"kai na ɗaga taita
lallashina har zuciyata tai sanyi sannan na tashi na tafi gida,suma suna ganina
suka tabbatar da matsala amma ba wanda ya tanka min.

Ina fita ya kalleta kana gani kasan ransa ya yi masifar ɓaci"yanzu abinda ki kai
kin kyauta kenan wannan ƴar yarinyar kika tasa da waɗannan maganganun",fari tayi da
ido ta taso ta dawo kusa dashi ta zauna kamar zata shige mai ciki,cikin salo tana
shafa jikinsa tace"haba My Love yanzu me nayi baka gani itama ta iya magana ai Nana
ba yarinya bace tafi Babba iya magana ko baka gani ba",ture hannunta ya tashi ya
wuce ciki bai kulata ba,itama ko ajikinta ta miƙe sosai ta ƙure speaker tana shan
kiɗa,a ɗakin kasa zama ya yi baima san tunanin me zaiyi basai safa da marwa yake
agabansa akaiwa Nanan sa haka amma baiyi magana ba kuma tabbas yasan ranta ya ɓaci
shi yasa ta tafi tabar gidan, yana nan yana zagaya ɗakin har akai la'asar sannan ya
yo alwala ya wuceta tana ta shaƙar bacci,bayan sunyi sallar a masallaci da Alhaji
Baffa sukai hira saiga Abba ma yazo sun jima sunayi sannan ya tashi ya fita ya
barsu,gidan Umma ya shiga da sallama bayan ya gaisheta ya samu wuri ya zauna
kallonsa Umma tayi"me kukaiwa Nana ɗazu tazo nan tana kuka kuma kune sanadi sai dai
yarinyar saboda tana da sirri duk haukanta da ke gani bata faɗamin me aka ma ta ba
kuma an sanar min daga gidanka ta fito tunda na aika kiranta akace kun fita
tare",kallon Umma ya shiga yi"Umma ita da Hajara ne ni banma san me zance miki
ba","to tunda bakasan me zaka ce ba kar ka ƙara zuwa da Nana gidanka muddin ba ita
taje da kanta ba,kun ɓata ma ta rai nan tazo tana kuka amma dana tambayeta saitace
wai amakaranta ne aka taɓata",shiru ya yi abin na basa mamaki kenan Nana zata iya
rufa masa asiri aduk halin da yake"kiyi haƙuri Umma hakan bazai kuma faruwa ba","ai
ni bance komaiba kawai dai ka ankarar da matarka Nana ba kanwar lasa bace tun tana
ma ta tana kuka wallahi randa tajuyo kanta ita zatai kukan kuma ta rasa mai
lallashinta","to Umma",Dijama ta kira ta fito a ɗaki sanye da hijabi"ki ɗauki
wannan kwanon ki kaiwa su Iyyo abincinsu ne kuma ki dudduba gidan inda aiki
kiyi","to Umma"ta ɗauka ta fita ƴar hira sukai kamin ya tashi ya wuce,abin mamaki
tana nan a kwance tana bacci abinta ta manta ma a inda take wataƙila,tashinta ya
shiga yi tai sallah da ƙyar ta motsa duk da haka haushin tashin da aka ma ta take
ji da ta shiga ɗakin ma saita ƙara kwanciya batai sallar ba.

Kashe komai ya yi ya jingina kansa da kujerar ya lumshe ido yana son Nana amma
baya son Hajara ta gane yanzu dan tabbas yasan in ta gane zatai mugun tsanarta shi
kuma bazai lamunci hakan ba dan yasan komai nata a yanzu haka kullun saita bincike
masa waya in taga number mace saiya ma ta baya nin wace ita agareshi sannan zai
samu lafiya,kwata kwata ya kasa nutsuwa barin ma da Umma ta faɗa masa yarinyar ta
rufa maganar sai yaji wani mugun ƙaunarta ya ƙara shigarsa,a nan ya zauna saida ya
gaji sannan ya shirun ya yi yawa ya bita ɗakin a gado ya ganta tanata bacci da
alama ma batai sallar ba dama haka take masa da rana taita shirgar bacci da daddare
ta hanashi nasa gata kamar mai shan ƙwaya abu kaɗan baya isarta saidai aitayi kamar
wasu injina,da ƙyar yasamu ta tashi tai shiga toilet saida tayi wanka ta
watstsake,koda ta fito cikin wasu kaya masu kama tsirara ta shirya sannan tasa
hijabi tai sallar da ake binta sannan tayi magaruba dan har an shiga ma,tana idarwa
ba addu'a ta miƙe ta shiga kitchen taliya da miya tayi dan tana da markaɗaɗɗen
kayan miya suna dawowa aka kawo ma ta daga gidansu,tana cikinyi ya shigo bai nemata
ba ya shige ya fesa wanka kamar wanda zashi babban taro ya shirya cikinn ƙanun kaya
ya gyara kansa walet ɗinsa kawai ya ɗauka ya baro ɗakin kichen ɗin ya bita tana
ganin sa ta zagayo tana faɗin"wow Habibe ni kawa wannan kwalliyar",kai ya kaɗa da
bana kwalliya ne sai yau,to fita zanyi",haɗe rai tayi tashi guda dan kishin sa taji
wata ta gansa a haka tasan dole ko azuciya ne sai an yaba ma ta miji"fita fa kace
zuwa ina awannan lokacin",juyawa ya yi yana faɗin"zuwa saita rayuwata mana inba
hakaba kema zata shafe ki",yana gamafaɗar hakan ya ƙarasa fita a kitchen
ɗin,ludayin hannunta ta buga a ƙasa ta kama kwankwaso yanzu duk wannan shigar bata
gigita shi ba yake nufi taga alama ma ko kallo bata ishesa ba amma zai dawo ya
sameta ai,da ƙyar ta kammala girkin ta kai falo kwanciya tayi ta jawo wayarta ta
shiga chatin da ƙawaye da abokai da groups na wayarta amma ta ciki na ciki.

Da mota ya fito a ƙofar gidan mu yay parking saida ya yi salkar isha sannan ya
shigo muna tsakar gida nida ƙarami ina koya masa home work bai gama shigowa ba na
miƙe da gudu na shige ɗaki,baki Mama ta kama ta kalleshi"da alama dai kunyi halin
ko",ƴar dariya ya yi yana shafa kansa"barta Mama mutuniyar akwai zuciya","ai dama
sai dai gaka gata nan",tashi ya yi yashigo ɗaki Aunty Mama da sallama ina bayan
labule kuma kusa da wurin ya zauna yana kallon labulen dan yasan ina wurin"fito
kiji mana tawan"ya faɗa cikin karya murya,a hankali na fito na raɓashi zan wuce ya
riƙo hannuna"haba Zaisha ban sanki da hakaba ni ne fa"fashewa nayi da kuka ina buga
ƙafa aƙasa,sakina ya yi"shike nan bari na tafi to tunda bakya son nazo inda ki
ke",kumbura baki nayi"inka tafi na daina kulaka kuma",dawowa ya yi ya zauna"to zoki
ji",zama nayi kusa da ƙafarsa,"yauwa ƙanwata shi yasa nake ƙara sonki kiyi haƙuri
kinji da abinda ya faru ɗazu",katsae shi nayi"dan Allah kabar maganar nan Babban
Yaya ta wuce","yauwa tawan",murmushi nayi araina nace'ai bakai kamin ba kuma ita
wadda tamin taci bashi ne a wurin ma darajarka taci shi yasa ban faɗan ma ta wadda
zata tasa ma ta hawan jini ba sai dai muje zuwa',girgiza kaina ya yi"ana haɗawa
wani kitirmurmura ne",saurin jallonshinnayi"kai haba Yaya bani da matsala da
kowa",amma araina nace'saida matarka',"tunda ba matsala tsakaninmu da kowa to bari
naje na sayo miki abin daɗi ko","yauwa Darling Yaya saika dawo",har waje na rakoshi
ya shiga mota ya wuce,na dawo ciki ina dariya harda buga ƙafa"Allah ya shiryeki
Nana","amen Mama inama Aunty Mama ta tana nan yau da munsha caskale a gidan
nan",bata kulani ba muka tafa da ƙarami.

Vote
Share &
Comments

Û̬m̬̂ m̬̂ û̬ ŝ̬â̬d̬̂ d̬̂ î̬q̬̂


🌈🌈🌈
🌈🌈
🌈

Babban Yaya Free ne amma me so ya biyo ni Pc in sa a group don shagalin Nana


na buƙatar comments.
08146711395
1️⃣ 6️⃣ chapter 1️⃣6️⃣

Koda ya fita bai zame ko ina ba sai babban mall kaya ya siyo min dogwayen
riguna da takalmi da hijab sai kayan ciye ciye fal ledoji sai wajen goma ya shigo
ina tsakar gida nasa doguwar riga ta material nasha red jambaki da kwalli baɗau ita
kanta Mama saida tayi dariyar wai nan me nake nufi amma dai tayi shiru taga ikon
Allah,ina ganin ya shigo na tashi da sauri na karɓi kayan hannunsa,ajiyar zuciya ya
yi yanata kallon fuskata kai kace kyau nayi amma shi a wurinsa sai yau ya taɓa
ganin zahirin kyan fuskata kunsan kwalli fa babban sirri ne dashi,ganin yanata
kallona yasa na ce"Darling Yaya ya akayi ne",goshinsa ya sosa" jeki kai kayan ɗaki
kizo",ɗakin Mama na shiga dashi dan Aunty Maman bata dawo ba sai gobe,tana kallona
na ajiye na kuma fitowa inda yake,nida bansan kan maza ba sai nazo gabansa nai
tsaye inajin numfashinsa a fuskata"tawan kinyi kyau sosai yau amma in zaki fita
karkina yin irin wannan kwalliyar,sannan dan Allah ki maida hankali kiyi karatu in
kika bari wannan lokacin ya wuce ki baki karatu ba tofa bazakiyi ba dan ƙwaƙwalwa
bata ɗaukar karatu inta fi taki girma,ni kuma so nake kiyi ilimi mai zurfi ki zama
babbar mace kafin kiyi aure",dariya nayi daɗi zai kasheni"shikenan Sweet bro bazan
nayi ba kuma sannan zannan karatu sosai zanma ƙara dagewa over yadda zakai alfahari
da ni fiye da kowacce mace","yauwa ta wajena haka nake son ji shi yasa nake
sonki"muka tafa"bari na wuce ko kinga dare ya fara yi ko","hakane Darling Yaya
saida safe",yana tafe yana juyowa ina ɗaga masa hannu har ya fita,ɗakin na faɗa na
tarar Mama nata dariya"Mama me aka miki kike dariya","zonan Nana",kusa da ita na
zauna ina jin tsoro"waike me kika ɗauki kanki ne kina nufin nan mace ce ke",rasa me
zance ma ta nayi kawai nasa ma ta kuka"a a ni me na miki wannan fuskar taki kamar
aljana wai ita Habibu yaga kinyi mugun kyau",dariya na shiga yi nima"eh mana Umma
baki ji yace kar in nayi ba in zan fita waje kuma nasan baya so ne wani ya
kalleni",dariyace ta ƙara kamata"Allah ya kyauta muku to",tashi nayi na baje kayan
ita kanta Mama saida ta jinjinawa kayan"gobe ki bishi har gida ki masa godiya","to
Mama"na faɗa ina tuna tsiyar dana shiryawa wannan goɗamar matar ta Babban
Yaya,ranar saida nasha kayan ƙwalam ɗin daya kawo min sannan na kwanta bacci.

Goma da ƴan mintuna yashiga gidan bayan ya gyara parking ya fito ya shiga ciki
tana nan hakimce ranta in ya yi dubu a ɓace yake amma da yake namijin duniya ne sai
ya washe baki"uwargidan Habibu ta gaban goshin Habibu",ya faɗa yana zama kusa da
ita,ba shiri tayi dariya"yanzu ka kyauta kenan kalla lokacin da ka ke dawowa gida
wannan adalci ne",murmushi ya yi"babban adalci ma kuwa shi namiji da kike gani wani
sirrine shi da Allah ya aje a ban ƙasa mata su aka halattawa tuhumar me suke daga
ina suke ko ina zasu amma ba namiji kamata mai hankali ba,dan haka ki kula tunkan
na fita na sauke haƙƙinki na gaya miki cewa na fita dan haka ba ruwanki da ina
naje,shigowar namiji gida ba tuhumarsa akeyi daga ina yake face sannu da zuwa dan
wataƙila fitar ma ke zata amfana ba shi ba",kauda kai tayi dan duk abinda yake faɗa
bazata ce ga ɗaya da ta gane me yake nufi"naji to amma ka daina kaiwa warhaka a
waje",ɗan murmushi"naji to amma banda uzuri in yakamani zan fita,bani abinci
tukun",gabanta ne ya faɗi dan tasan ba kasafai yake ƙaunar talliya ba daurewa tayi
tace yana dining",tashi ya yi ya isa biyo shi tayi ta fara buɗewa tana murmushin
yaudara,saboda yasan shima ya ɓata ma ta sai ya basar yaci taliyar haka,amma yana
mamakin yanda akai kamarta bata iya sarrafa abinci daban daban ba,gashi yana gani
agidansu duk yara ne amma in suka zuba girki kamar a babban hotel akayi,tunani ya
yi ita agidan hutu ta tashi sannan kuma ita bama a takura ma ta kamar sauran saboda
an fi sonta wanda nu na hakan annabi ya hanemu fifita wasu ƴaƴan mu akan sauran ƴan
uwansu ƴaƴa,tun kan ya gama ci ta fara shafa mai jiki tana shinshina shi bai
kulata ba ya barta harya gama,yauma kamar kullum ya gaji amma ta hanashi sakat daga
ƙarshema kunna hasken ɗakin ya yi yana ƙare ma ta kallo sai wani miƙa take alamar
bata gajiba ko kuma harkar bata isheta ba"please ka taho mana"ta taso ta ƙara
faɗawa jikinsa tana neman haɗa bakinsu,kauda kansa ya yi ya riƙe ma ta fuska"kinsan
Allah kodawa kike yawo bacci zanyi yanzu kalli agogo biyu da rabi ma ta wuce to ko
Annabi kasa darensa yake dan haka baki isa ki ƙarar min da nawa daren anan ba dan
haka kwanta ko na bar miki ɗakin",batare da taji daɗin abinda ya ma ta ba ta kwanta
dan tasan ya gaji ita kuma ƙwayar da Auntyn ta bata ce take ma ta haka yanzu ko
bata shaba ma sai hakan ta faru gashi tanajin shi iya namiji ya kai a wurinta da
ƙyar tayi bacci shi kuwa ai ya daɗe a birnin lantsandan baima san tayi bacci ba ko
batayi ba,asubar fari ya tashi duk da idanuwan sa na cike da bacci amma ya gabatar
da nifilfilu sannan ya tasheta da akai assalatu shi kuma ya wuce massalaci dan
gabatar da farali mai girma wato sallar asuba dan tun baifi shekara shida ba sallar
asuba ta shiga jikinsa kuma hakan abu ne mai kyau ga duk ɗa namiji dan ita salkar
asuba tana ya ye dukkan damuwa da baƙin ciki.

Bai shigo ba saida rana ta ɗaga kuma ya tarar bata ko motsaba,mamakin ta


kullum ƙara kamashi yake da ƙyar ya samu ya tasheta tayi wanka sannan tayi sallar
azkar ɗinsa ya gama sannan ya tashi ya koma ɗakinsa ya yi wanka ya shirya cikin
ƙananun kaya masu kyau ya gyara sumarsa kamar yadda ya saba,tara da rabi ya shiga
ɗakinta amma tana bacci bai tasheta ba ya wuce ya fita ko taɓa get wai duk bata ji
ba,sanin Abba na jiransa yasa ya wuce bai nemi kowa ba,koda ya isa gidan ma ba kowa
a falon dan haka sai shima ya miƙe ya kwanta kan doguwar kujera dama shi yafi kowa
buƙatar bacci,bai jima da kwanciya ba Abba ya fito ya gansa yana bacci,murmushi ya
yi ya duƙa kusa dashi ya shafa kansa"sannu Habib wannan matar bata dace dakai ba
tabbas huta mun fasa fitar ma",miƙewa ya yi ya kulle ƙofar falon dan kar aturo a
shigo daman inka ƙwanƙwansa ma baji za'ayi ba,ɗaki ya koma yaja glass ya saka ya
cigab da karatun alƙur'ani dan yanzu aikinsa kenan saboda wannan matsala ta baya da
aka magance kuma alƙur'ani shine maganin farko na kowanne ciwo kuma ya yaye ƙunci
da damuwa ko wacce iri dukkan wanda yazo ya taɓa ƙofar yajita a garƙame saiya koma.
******
Wajajen goma da rabi nai wanka na tsaf na shirya zuwa gidan Babban Yaya amma
har falon na shiga wayam ba kowa tabbas ajikina nake ji baya gidan nan shi yasa na
haye kujera na kunna tv nasa chasu abuna tsabar neman rigima.
Bata farkaba sai bayan shaɗaya wanka tayo sannan tayi sallah tasa wasu kaya
kamar ƴan can garin kai bakace ta iya hausa ba,alamar ƙiɗan nan ne yasata fitowa
tana rangwaɗa ta zata shine sai kawai tai arba dani na kishingiɗa kamar wata
yayarta ko matar gidan ga ina cikin doguwar riga wadda sai wance da wance masu
mallakarta ina kallon duk kallon da take min amma na basar da ita jira nake ta
tanka min,ilai kuwa kamar zata rufeni da duka ta ƙaraso kaina"dan ubanki wayace ki
shigo min gida har ki kunna min kiɗa",duk da naji zafin zagin da tamin kuma zan iya
ramawa amma bazan rama ba sai gaba kaɗan dan haka saina miƙe"gidan ki gatsau ko
kunya baki jiba gidana dai koda yake in baki sa ni yau ki sani wannan gidan ma na
fi ƙarfinsa inzan kwanta da mijinki wannan gidan da ɗakunansa sun min kaɗan saidai
ke ɗin....",ban gama magana ba ta kawo min yaga kamar karya da gudu na nemi ƙofar
fita amma ta tare"wallahi saina kashe ki yau agidannan da mijin nawa zaki kwanta
kalla ƙirjinki ƙirgen dangin ma bai nuna ba",katseta nayi"daina tantama malama da
wannan ƙirgen dangin saina gigitar da mijinki na sumar da shi kalla nan jiya kin
ɓata min ya tafi wurina tun magarubar fari wannan rigar ta jikina ma ta ban
haƙurice dan bashi da bakin magana akaina inyaga raina ya ɓaci","rufe min baki
shegiya mai zubin zabaya dama ni tun ganin farko da miki ban yarda dake ba nasan
cewa watarana saikin bani matsala a rayuwata to baki isaba yarinya kafin wannan
lokacin da kike hasashe na gama dake ke yau ma basai watarana ba","anan ne kikai
kaɗan mijinki nawane ni tasa ce tun inazanin goyo inbaki sa ni ba Babban Yaya nice
rayuwarsa ko baki taɓa jiba ya kirani da MY LIFE"katseni tayi ta hanyar jifana da
wani rose vase da sauri na kauce ta samu Tv dariya nayi"kin ɓata kayanki ɓuleliya
baki sa ni ba ma angona ya tsani mace tiƙeƙiya Hhhhhhhh",tayo wani tsalke ta kawo
min danƙa nai sufa ta bayanta na fice a ɗari"sai anjima uwargidana"kan ta fito ma
na fita agidan gaba ɗaya ina sheƙa gudu.
Da gudun itama ta biyo ni amma batai nasarar ko ganin ƙurata ba komawa tayi
tana kai komo"lallaima yarinyar nan yanzu ni take kallon tsabar idona tace zata
kwanta da mijina ni dama na gaya Aunty wannan yarinyar shaƙuwarsu bata ƴan uwan
taka bace daganin kallon da yake ma ta tun bata kai mace ba,to wallahi kin taɓo
masifa da bala'i kozanyi yawo tsirara baki shigowa gidana",a haukace ta shige ɗaki
ta janyo wayarta ta dannawa yayarta kira tasa a handsfree ta aje kan mudubi tana
ɗagawa ta fara magana"dama na faɗa miki wannan yarinyar mijina take so yau gashi ta
faɗan baki da baki shi dama basai ya faɗa ba dan nasa ni amma wallahi basu
isaba","waime ya faru ne kike wannan masifar","au tambaya ma kike to bari kiji"nan
ta zayyane ma ta komai"wai da gaske kike Hajara wannan ƴar yarinyar ta miki haka
anya kuwa mutum zallace","ai bari kedai da alama tanada ƴan rakiya","kina jina ko
Hajara ki kwantar da hankalinki ina nan zuwa","to shike nan saikin zo ina jiranki
fa karki shakkar komai dan inada kuɗi masu yawa kuma komai zan iya yi akan
mijina",ta kashe ta yar tana zama jaɓar bakin gadon,"lallai yarinya kin ɗebo ruwan
dafa kanki.
Ban zame ko ina ba daga nan sai gidan Gwaggo Ma'u na tafi jan magana dan nasan
dai wadda nake zuwa wurinta bata nan.

*******.
Bacci ya yi sosai bai farkaba,saida ya jima yana baccin sannan ya tashi agogo ya
kallah shabiyu saura salati ya yi yana kallon inda yake tashi yay zaune saiga Abban
ya fito a ɗaki"a a ka tashi sannu ga abinci can adining dan da kallon wannan fuskar
yunwa kake ji jeka wanke fuskar ka aɗakina kazo kaci nayi baƙi zance can muyi
magana kan ka gama zan turo Yasmin ta kaika can inda nake",kansa ya sunkuyar "to
Abba",fita ya yi yana murmushi har wani faɗi yake ji in ya kalli Habib ace wannan
ya kasance ɗansa ne guda,tashi Babban yaya yai ya shiga ɗakin bai kalli komai ba ya
shiga toilet ya wanke fuskarsa da bakinsa ya fito a dining ya karya sosai dan baya
son ya koma ya tadda taliyar nan ko shinkafa shi mamaki ma yake kamar ba ƴar zamani
ba ko ƴan kayan ƙwalam ɗinnan na zamani ita bata iya ba ko ganda ce ohoo bai sa ni
ba,bai jima da gamawa ba Yasmin ta shigo da gudu "Big Broo in ka gama kazo na kaika
inda Abban yake",tashi ya yi yakama hannunta suka fito zuwa inda Abban yake bin
Abban da kallo ya shiga yi ganin yanda gefen idonsa ya yi kore kuma idanuwansa
kamar mai cutar asma,ɗauke kansa ya yai ya mai da kan mutanen dake zaune harda
turawa da baƙaƙe ƴan uwa,da sallama ya ƙarasa nan suka bashi hannun suka gaisa yana
mamaki manya mutane haka na bashi hannu a ƙasa ya zauna nan Abba yace ya dawo sama
amma yaƙi,mutanen jinjinawa tarbiyarsa sukai nan Abba ya kallesu yace"gashifa MR
Josep",kai ya kaɗa ya shiga miƙo masa takardu yana sa musu hannu har aka gama
sannan suka faɗa masa angama sauran yaran naka a kira kowa yasa hannu, amma ko
iyayensu basu sa ni ba saida aka gama sannan da kansa ya karɓi wasu yasa hannu ya
miƙa musu bayanin"kayan suna a store a lagos komai yana akimtse a kawo min su zuwa
dare bana so sukai safiya","ok"suka amsa sannan suka kwashi takardun suka
tafi,"tashi ka zauna sosai Habib"zaman ya yi kamar yarda yace sannan ya dubeshi"ka
saurare ni da kyau bani da wasu ƴan uwa sama da Halima bani da iyaye sama da Baffa
da Iyyo Habib ka nutsu sosai ka sauarareni kuma kome zan gaya maka karka ɗaga
hankalinka dan babu wanda ya isa ya hana Allah ikonsa,a yanzu haka akwai guba
ajikina wadda watanta bakwai amma bata gama cika ba zuwa gobe ko jibi zata cika kai
ko yau ma kuma hakan shine ƙa'idarta dan haka dole tana cika zan mutu"nan tarin da
yake ya ƙara taso masa da sauri ya miƙe jikinsa na rawa ya tallabeshi"haba Abba
taya zaka ɓoye wannan abu baka nemi magani ba kuma baka faɗamin ba"hawayen dake
zuba afuskarsa ya share masa,"haka Allah ya nufa saboda da likitocin aka haɗa baki
naje a dubani aka min abinda bashi naje nema ba kayi haƙuri Habib naso na faɗa maka
suwaye amma sai nayi tunanin irin rigimar dazan haddasa a acikin al"saidai inaso ka
kula da kyau da mutanen da zaka shiga cikinsu nan gaba dan abinda ka mallaka zaija
maka ɗaukaka waɗannan gidajan kaf naka ne ba bu wanda na mallakawa ko ɗaya har
matana duka na mallaka musu wasu dan bana son kowa ya zauna akusa da kai koda na
mutu ka tattaro danginka duka ka zuba su amma wancan na kudun ba kowa ciki sabone
kasa iyalanka ciki nawa Nana komai na ƴa nan da shekara goma kawai buɗe ma ta za ai
ta shiga ka riƙe wannan yarinyar ina hango alkhairi masu yawa atare da ita kuma
zata saka ka farin ciki karka damu da rigimarta duk Aisha ta duniya haka take Habib
ga ƙannenka nan na bar maka amana duk nasan bayan babu ni suka tsinci wasiyyata
bazasu baka riƙonsu ba amma ka zama idonsu aduka ƙasar da suke zaune nasan wannan
zaman nawa da kai shine na ƙarshe sai dai ka riƙe wannan sirrin karka faɗama kowa
amma kasan wani abu ɗana"kai ya girgiza hawaye kamar famfo na zuba a idonsa"ka zama
namiji mana da wannan basirar taka nasan zaka gano masu hannu a wannan abin wataran
Allah ya muku albarka da zarar babu ni mutane zasuyi ta zuwa wajenka saboda ina bin
mutane da yawa bashi sai dai komai na bashin mallakinka ne na riga na zartar da
hakan ba wani batun gado bayan na mutu dan bani da ƴan uwa bare ace na musu baƙinci
kuma koda dasu kai ka kore komai kasan tuwarka ɗa namiji na halal",ya ƙarashe yana
tari"kayi shiru da wannan bayanin Abba"hannunsa ya ƙara riƙewa sosai"ai na faɗa
maka zafinta ya haɓaka fa abinda nake ji ba zai fasaltuba Habib ka kawo min Alhaji
Baffa amma karka faɗa masa komai"kansa ya girgiza "bazan iya tafiya na barka
ba",kafin ya gama magana tarin ya ƙara turniƙeshi,miƙewa ya yi kamar zai tashi sama
ya fito a ɗakin da kansa ya fito da mota sai kallonsa ma'aikatan suke amma sunyi
shiru masu abu da abunsu,ɗakin ya koma yatarar Abba ya faɗi jini ta ko ina a
fuskarsa har ido,jajircewa ya yi ya danne zuciyarsa ya fito da Abba shi ɗaya suna
ganin haka hankali ya tashi nan danan gidan ya hargitse amman kafin kowa yazo ya
fita dashi daga gidan security's suka mara masa baya,da gudu Yasmin ta shiga ɗakin
Hajiya tana ihu"Mommy Abba bashi da lafiya gashi can Yaya ya fita dashi ko ina
ajikinsa jini",lumshe ido tayi"naji jeki ganin zan fito"da mamaki take bin ta da
kallo ganin bata nuna razana ba sai dai ta fito,tana fita Hajiya ta janyo wayarta
ta kira wata number"Hello Alhaji lokaci fa ya yi gashi can antafi asibiti
dashi",magana akai can ɓangaran ta amsa da "yanzu ma kuwa",ta kashe ta ɗau mayafi
tana ƙaƙaro kuka ta fito fuskarta sharkaf da hawaye,kallon mamaki Yasmin ta bita
dashi ita dama tasan ta faɗawa Mommy hakan ai dole tayi kuka sai yanzu ta aminta da
Mommyn,atare suka fito nan sukaga matan ma duk sun fito ko wacce da kuka a fuskarta
amma kana gani in kana da hankali kasan abin baikai zuci ba,motoci suka shiga aka
fita dasu zuwa asibitin.

Vote
Share &
Comments

Û̬m̬̂ m̬̂ û̬ ŝ̬â̬d̬̂ d̬̂ î̬q̬̂


🌈🌈🌈
🌈🌈
🌈

Babban Yaya Free ne amma me so ya biyo ni Pc in sa a group don shagalin Nana


na buƙatar comments.
08146711395

1️⃣ 7️⃣ chapter 1️⃣7️⃣

P17

Yana shiga asibitin motar kawai aka kalla nan danan likitoci sukaiwa motar
dafifi da kansu suka fito dashi zuwa ciki shi kuma yabi bayansu emagency sukai
dashi nan aka shiga dubashi aman fin lokaci mai tsayi ba labari yana nan a wurin
sai safa da marwa yake bai sallah ba har suka fito kowa ya jigata kallonsu sukai
dan sun cika wajen,nunashi sukai "biyo mu",abin mamaki kafin su gama magana Hajiya
ta katse su gun faɗar"Doctor damu zakai magana ba dashi ba saboda basu jima da
haɗuwa ba duk da yana ɗansa baisan komai nasa ba",gyara tsaiwa Dr ya yi"to waya
gaya miki wani abu na Alhaji muke son sa ni kuma ina ruwan mu da basu daɗe da
haɗuwaba ko jiya suka haɗu ya fiku matsayi a wurinsa duk da kuna matansa kuma hakan
da kikai ya nuna bakece ki ka haifi ɗan ba kenan dan haka maida harshenki taho
rankai daɗe"ya juya zuwa wani lungu,wani kallo Babban Yaya ya watsa musu wanda yay
bala'in kaɗa musu hanji amma suka shanye suna ƙara kalar tausayi,bin bayan Dr ya yi
zuwa inda yaga sun shiga shima ya shiga wani falo ne kamar wurin meeting duk zama
sukai shima ya zauna,mai yanayi da shugaba acikinsu shine ya fara magana"am sorry
yallaɓai mahaifinka babu abinda za'a iya masa sai dai a zubawa sarautar Allah ido
kafin lokacinsa ya yi saboda komai na jikinsa ya lalace har ƙwayar idanunsa kuwa
saidai bamu gano komai dan gane da abinda ya haifar da hakan ba",numfashi ya yi
kansa na bugawa ya miƙe tsaye yana sa hannu a aljihu"ba komai Doctor Allah ya kawo
sauƙi ya yin tafiyarsa inaso karka bari kowa yaga Abbana koda kuwa matansa ne har
Allah ya amshi abinsa","karka damu game da wannan zamu kaisa inda ma ba wanda zai
ya shiga sai dai munso kafaɗa mana meke faruwa dan munsan abinda ke iya zama haka
amma munaso muji nasa dan da alama kasani","ba ƙarya a wannan abin Doctor gubace
aka masa allurarta amma ba a ƙasar nan ba nasan kunsan ta sai dai samunta anan yana
da wuya dan haka nasan komai ina godiya agareku"ya fito aɗakin ya bar asibitin duka
batare da kowa yasa ni ba.
Alhaji Baffa ne yaganshi ya shigo kamar zai faɗi da sauri ya tareshi ya zauna
akan ɗan bulon barandar ginin dafashi ya yi"Habibu lafiya kuwa",shiru ya yi ya kasa
magana Iyyo ce ta fito"kai kuma miye hakan ina iyalin taka",nan ma shiru ya yi
saida Baffa ya gaji da magana sannan ya buɗe baki daƙyar yace"Abba ne",ya yi shiru
kuma"faɗi mana Habibu ko sokake ka ƙarasa mu dama zuciyar ta tsufa",Iyyo ta
faɗa"Abba ne Iyyo zai mutu sun kashe shi",yana kaiwa nan ya fashe da kuka mai taɓa
zuciya, saurin ja baya Iyyo tayi tana salati"ban gane sun kashe shi ba Habibu yimin
baya ni sosai",dakatar da kukan ya yi,tsaf bayanin Abba yawa Alhaji Baffa,wannan
batu ya kaɗa Baffa dayawa dan saura ƙiris ya fita ahayyacinsa da ƙayar ya dawo dai
dai,jin motsi yasa su juyawa Mama ce tsaye fuskarta sharkaf hawaye alama taji komai
kenan ƙarasowa tayi"kaini nagansa Habib ko kallon ƙarshe na masa",tashi ya yi ba
wani bayani har Iyyo da Alhaji Baffan suka shiga motarsa zuwa asibitin da isarsu
suka tarar su Hajiya Fullera nata hauka sai ankaisu inda yake amma likitocin nan
sunyi mirsisi kamar ba dasu suke magana ba,yana shigowa suka nutsu abin har mamaki
ya ba mutane kuma kana kallonsu shi suke kalla shi kuwa ko kallo basu ishesa ba
bare yasan me suke,ta wani ɗaki suka kaisu inda yake idonsa biyu amma baya
hayyacinsa kana gani,duk ƙarfin zuciya irin na Alhaji Baffa saida ya fashe da
kuka"Habibu kaine ka zama haka kalli yadda ka koma dama rashin zuwanka duk wannan
ne kace ba komai da nace maka zanzo Allah yasaka maka ɗannan yasa can tafi maka
nan",Mama dake akansa ta toshe bakinta hawaye kawai ke zuba a idanuwanta baya ta
matsa dan bazata iya kallonsa ba saidai addu'a da take masa can ƙasan
zuciyarta,kusa dashi Habib ya matsa yaga hawaye yana zuba a idonsa da sauri ya
ƙarasa ya kama hannunsa mara ƙarin ruwa ajiki,muryarsa na rawa ya fara magana
ahankali "Abba kayi min magana please waye da wannan abin suna kawai ba bayani ba
dan Allah Abbana",tari ya yi sannan ya mai alama ya durƙuso numfashi yaja na ƴan
mintuna sai kuma ya yi shiru yana salati,bai ɗago kansa ba yanaji yagama salatin a
kunensa saida ya gama ya ɗago idanuwansa na hawaye,baya Iyyo taja ta fashe da kuka
hakama Alhaji Baffa,cikin dauriya ya rufe masa idanuwansa yaja masa mayafin ƙarin
ruwan ya cire da duka na'urorin yaja baya ya jingina da bango yana jin tashin
hankali na shigarsa da gudu likitocin suka shigo ganin yanda aka masa suma da kansu
suka matsa dan sunga manya ne awurin sunsan komai ya kammala Allah ya jiƙansa,atake
suka basu shi nan suka turo shi waje ai su Hajiya da yaran na ganin haka sai suka
hau hauka suna faɗuwa awurin sai burburwa suke a wurin kota kansu ba wanda yabi aka
fito dashi zuwa motar jinya mallakin asibitin ba a wani ɓata lokaciba zuwa gidansa
dan masa sutura hakama daga asibitin duk nacan suka dawo gidan kowa ka kalla kuka
yake sosai kan kace me can unguwar ma kowa yazo dan har Hajara Umma ta turawa tazo
itama ta shiga tashin hankali dan mijin ƙanwar ubanta ne,shaƙiƙansa ne su Kawu Nuhu
sukai mai wanka aka shiryasa tsaf zuwa gidansa na gaskiya ana ta mai addu'ar dacewa
halinsa nagari ya bishi,inka kalleni agidannan ka ɗauka Baffana ne ya mutu saidai
kowa yasan Abban Babban Yaya ai Abbana ne nima kuma gaban kowa yake nuna min so.
Bayan andawo abinneshi nan duk aka zauna anata jimantawa juna,cikin sati baƙi
kala kala sun zo gaisuwa masu zaman gulma kuma a washegari kowa ya kama gabansa sai
masu takaba da yaransu.

Bayan sati huɗu:


Hajiya Fulera ke sanye da wani uban material mai ƙyalli sai shining take su Hajiya
Harira da haɗa a falon,tana zaune a kan kujera ta naɗe ƙafa ta kalle su tana wani
yatsina,abin haushi kaf ka kallesu baka cewa masu takaba ne dan sunsha ado iya
ado"nasan baku san me yasa na taraku ba ko to inaso ne muyiwa wancan taka hayen
dukiyar ya bamu dukiyarmu dan nasan shida wancan tsohon suna ƙulla yazasuyi damu
ne",Hajiya Salma ce ta kyaɓe baki tanawa Safiyya signa nan kuwa ta gyara zama"ai
dama Hajiya ke muke jira kiyi magana tunda kece babbar gidannan duk a ƙarƙashin
muke",wani fasuwa kanta ya ƙarayi"to ku kwantar da hankalinku ranar arba'in gaban
kowa da kowa zamu dizga shi mu wullaƙantashi sannan mu koreshi agidannan dan abinda
bai sa ni ba nice kawai nasan sirrin Alhaji kuma duka abinda yake dashi nasa ya yi
singhning da sunayen yaranmu bai sani ba",heeee sukai shewa,murmushi Babban yaya ya
yi yakoma sama dama yana ɗakin Yasmin ne suna karatu ya fito yajisu suna wannan
maganar saida suka tashi sannan ya sakko ya fita.
*****
Da sallama ya shigo gidan Iyyo ina kwance baccin iskanci ya zama na gaske a
kusa dani ya zauna yana gaida Iyyo,tana cikin amsawa naji sautin ta tunkamin na
buɗe ido nasan dawa take magana,ido na ƙyallarawa na ganshi yana sanye da yadi mai
laushi ɗinkin ya amshi jikinsa gashin kansa kamar kan mace ƴar gayu sai shining
yake kai gaskiya Babban Yaya ya haɗu,bai jimaba ya tambayeta Alhaji Baffa ta faɗa
masa ya fita amma zuwa anjima zai dawo,kishingiɗa ya yi nan kusa dani bai daɗe ba
Bacci ya kwasheshi Iyyo ba ruwanta ita ta tashi tai fitarta zuwa tsakar gida.
Umma ke sallama da Hajara dama tana gidanta tun ɗazu an zo shigar da kai kamar
yarda Yayarta ta koya ma ta harda dafo farfesun kifi dan gulma tana fitowa ta shigo
gidan Iyyo tana ta sallama shiru,inajin muryarta na tashi da sauri na cire ɗan
kwalin kaina na baza gashin na raɓo jikinsa na kwanta fuskata na kallon tashi na
kulle idanuwa na adole mai bacci,Iyyo da ta shiga ɗaki bataji sallamar ta ba dan
haka ta ɗago labulen ta shigo kyakkyawan gani tayi mijinta kwance da wadda ta tsana
kuma da alama wani abu sukai danta gama lura ƴan gidan ma sun mutu akan wannan
shashashar soyayyar,wani irin bugu ƙirjinta keyi dan haka batai maganaba a hankali
ta juya ta fita daga gidan da yake ba nisa da ƙafar da tazo ta koma tun a falo ta
fara jefar da kayan jikinta dan wani masifaffen zafi take ji,tuƙuƙi zuciyarta ke ma
ta tama rasa me zatayi kome zata tuna,da ƙyar ta ƙwaƙulo ashar taita ƙundumawa ita
ɗaya kamar mahaukaciya.
Tana fita na miƙe na maida kaina yanda yake ba jimawa ya farka yana
kallona,shafa fuskata ya yi"uwar rigima har yanzu yi ake kenan"ɗan motsawa nayi
madadin ya barni a a"ke tashi bakiga time ɗin islamiyya ya kusa ba",buɗe ido nayi
ina hammar masu bacci cikin idanuwana ya kalla ya girgiza kai"ba bacci ki ke ba
kuma baki da gaskiya faɗa min me ki ka aikata",wuri wuri nayi kamar zanyi
kuka,muryar shagwaɓa nayi"Darling Yaya ni banyi komaiba",kaina ya dafa tashi muje
gidana na baki wani abu",watsal nayi na miƙe naja hijabina"Iyyo nabi Babban
Yaya",na faɗa da ƙarfi"ku gaida nagaba ja'irai",dariya nayi na kama hannunshi muka
fito ni kaɗai nasan me nake girbawa a araina yau matar nan zataga wata masifar dan
nasan tana can ta hau kamar an ma ta ɗurar yist.
Yana gaba ina bayansa ya yi sallama yana tura ƙofar falon,zumbur tayi ta miƙe
tayo kansa ta shaƙeshi zatai magana kenan ta ganni a bayansa sakin sa tayi tana
nufoni"au biyoshi kikai nan dan ki ƙara tabbaɓe min shi wato kin nuna min kin
kwanta dashi ɗin da gaske ko",zaro ido nayi kamar zanyi kuka"ni ɗin Aunty Hajara
miye kwanciya dashi kuma"ya yinda Babban Yaya ya kira sunan ta da ƙarfi" Hajara
kina da hankali kuwa Nana ki ke faɗawa ta kwanta dani dan hauka me wannan tasani da
ki ke ma ta irin wannan zancen",da hanzari ta juya gareshi"me kace wannan ƴar
barikince yarinya bata san komai ba to bari kaji daga kai har ita baku isaba
wallahi saina yi maganin ku ke kuma",ta kawo hannu ta danƙeni mari ta kifa min
saida naga taurari saurin riƙeta ya yi yajanyeta gefe"dama baki da hankali Hajara a
gabana zaki daki RAYUWAR TAWA",wani dam ƙirjinta ya bayar ta fincike kanta cikin
tsantsar masifa take dubansa kamar zata rufeshi da duka"Habib a gabana kake kiran
wata da rayuwarka to kasani yau rayuwar taka zata ƙare dan saina kasheta a
gabanka",gyara tsaiwa ya yi yasa hannu a aljihu ya matsa ma ta yanda tana fuskanta
ta"kasheta Hajara gata kashe wallahi tallahi dasai kaf na ƙarar da danginki sannan
nazo kanki",batai gigin taɓa ni ba sai dai kumbura da take,ni kuwa kamar na sheƙe
saboda dariya amma na basar sai matsar ƙwalla nake,matsowa ya yi ya kama hannuna
yaja ni zamu fita,kamar walƙiya naganta zata daki baya na nai saurin juyo ma ta
ƙirjina ta sameni baya nayi zan faɗi darajar hannuna dake anasa ban kai ƙas ba ya
janyo ni jikinsa nai saurin ɗauke numfashina kifani ya yi a ƙirjinsa yana kiran
sunana amma ina na suma dan sheri,silalewa nayi ƙasa ya bini yana riƙeni da
kyau,''Nana!Nana!!"amma ina nayi shiru bayan ina jinsa hannunsa ya ɗora akan
ƙirjina ya danna amma shiru,kwantar dani ya yi flat sannan ya haɗa hannayensa duka
biyun ya ɗora aƙirjina ya danna nan ma shiru,lumshe idanuwansa ya yi ya buɗe da
sauri sunkuyowa ya yi ya buɗe bakina yasa nasa yana hura min iska,buɗe idanuwana
nayi sai cikin nata,damabtun tunda taga na faɗi ta ɗora hannu aka yau tana ganin
rashin mutunci ruwansa, ido ɗaya na kashe ma ta sannan na ɗaga ma ta babban yatsa
na,jin zai ɗago na koma yanda nake saida ya yi sau huɗu sannan na kawo numfashi da
sauri ya tareni yana dafa ƙirjina ɗagani yay ya jingina da jingina da jikinsa"My
Life sannu please kar ki kuma yimin haka badan ni ba wallahi bazan iya rayuwa ba
babu ke",maganar da yake saki ce tasa Hajara ƙara danna hannu aka dan wanda tayi da
bai ma ta ba,dan kana ganinsa bai san me yake cewa ba,murmushi na masa ina ɗaga
kai alamar amsa abinda yace,cikin wani irin yanayi ya ɗago kai yana ma ta wani
razanannan kallo zai yi magana na tareshi"indai ni ce your life karka kulata na
yafe ma ta ai matarka matsayinku guda agareni Babban Yaya",kaina ya dafa Allah ya
miki albarka zo muje nakaiki shan ice cream",ya ɗagani zuwa inda ya yi parking
agidan,ita kuwa kallo bata ishesa ba tana gani muka fita a gidan ina ma ta
gwalo,muna fita ta zube awurin ta rasa ma me zatayi kawai ta miƙe ta koma ciki ta
fara maida kayanta itama ta fice agidan,muna tafiya amota yana bani haƙuri har
mukaje wani babban mall fama yay tayi na fita naƙi dama ya matsan saina afashe da
kukan iskanci,rufe ido ya yi ya jingina kansa da kujerar motar cikin sanyin murya
yace"me kike so a miki",ɗan dakatawa nayi ina taɓe baki"ni bana son ice cream",yana
a yadda yake bai gyaraba yace"saime ki ke so"ni ni muje danja kasai min kaya in
nagani zan nuna maka","nagane me ki ke nufi ba danja zamuba bari kiga inda zamu",ya
kunna yaja baya muka bar wurin,tabbas kamar yasan me nake nufi wajan kayan
makaranta ya kaini naita jidar kaya mun gama ya biya muka fito muna shiga motar ya
dubeni"ashe dai zakiyi karatun danake so",kai na rangwaɗa"sosaima ai saikace ya isa
haka Nana" ƴar dariya ya yi yana kunna motar hargida ya kaini nida kayana,sannan ya
wuce bansan ina zashi ba dai,Aunty Mama ce taganni da kaya niƙi niƙi tashi tayi ta
karɓeni"Nana waɗannan kayan fa kamar wadda za a kai makarantar kwana" "aje na
hannuna nayi"ba wata makarantar kwana Aunty kawai shirin karatu nake","a lallai
nafi kowa murna to a dage kinji ƴar albarka","insha Allahu Aunty Mama na".

Koda ya koma gidan bata nan wanka ya yi kawai ya fito yana dawowa gidan Iyyo
ya tarar Alhaji Baffa ya dawo anan ya zauna ya faɗa masa kaf abinda ake ciki"karka
damu Habib masu haƙƙin wannan zaka wa magana aranar kowa ya hallara amma su tozarta
ka basu isa ba jinin Habibu ya wuce wulaƙanci a wurinsu","insha Allahu Alhaji nawa
Kawu Haruna waya yace zaizo kafin ranar","to shike nan anan ya zauna sukaita
tattaunawa har akai magaruba sannan ya bar gidan,sanda ya koma ta dawo amma sai
kumbura take ƙala baice ma ta ba ya shige ciki ya barta nan,ƙwafa tayi"zaka shiga
hannuna Malam kome ka ke ji dashi saina zubar da shege Nana kuma ko a hanya ka
ganta ta zama babbar maƙiyiyar ka" ta tafa cinya tana shigewa ɗaki,saida suka kwana
biyar a haka sannan taga abin bana ƙare bane taje ta faɗawa Umma nan ta kirasa ta
masa faɗa sannan komai ya wuce .

*****
Yau Abba ya yi arba'in duk su Mama suna gidan baƙi da abokansa duk sunzo haka
ma sauran matan su kawu Iro kai kace biki ake,a Babban falon da yake zaune da baƙi
su Hajiya Fulera suka shigo kamar yadda suka tsara nan mutane sukaita gaida su suna
wani yatsina suke amsawa duk abinda suke Alhaji Baffa na kallonsu saida suka gama
gaisawa da mutane sannan ba kunya suka zauna wurin suna duban Habib sukai su kuma
mutane na dubansu da mamaki dan tabbas sunyi abin mamakin cikin maza ba kunya ba
ɗar matsayinsu na mata matan ma masu takaba.

Vote
Share &
Comments
Ƴan uwa

Û̬m̬̂ m̬̂ û̬ ŝ̬â̬d̬̂ d̬̂ î̬q̬̂ 🌈🌈🌈


🌈🌈
🌈

Babban Yaya Free ne amma me so ya biyo ni Pc in sa a group don shagalin Nana


na buƙatar comments.
08146711395

1️⃣ 8️⃣ chapter 1️⃣8️⃣

Alhaji Baffa tun zaman su yake binsu da kallo shi yasan waɗannan dama ba matan
arziƙi bane suna son mijin ne dan dukiyarsa yana tsaka da tunani yaji sunawa Habib
magana"to Habib a musulinci ma yaune ya tabbata ka bawa masu gado haƙƙinsu tunda ba
naka bane",runtse idanuwansa ya yi dama tun zamansu ransa ke masa zafi kawai yana
danne kansa ne,ɗan murmushi ya yi ya nuna musu mutanen dake gefe gasunan harda
turawa da alƙali Babba sananne kunga ba ja kenan tsit akayi aɗakin ana sauraransu
wannan bature shiya fara magana kamar haka"Alhaji ya bar mana dukiyarsa mu kasafta
masa ita yadda yace tunda baya da ƴan uwa na jini sai ɗa namiji da Ƙanwarsa sai
tsohuwar matarsa sannan Baffansa da Ummansa,a bisa tsari yadda ya bayar matansa
huɗu kowacce da yaranta Hajiya Fulera ga naki,Hajiya Harira ga naki,Hajiya Salma ga
naki Hajiya Safiyya naki,Alhaji Baffan sa yana ina",nuna shi akai nan ya miƙa masa
takardu daban daban ka duba da naka dana Ummansa kamar yadda yace sannan na
ƙanwarsa da tsohuwar matarsa,sannan wannan bayanin da takardun na ɗansa ne amma
gashi alƙalin abin zaiyi magana da kansa",duk maganar da yake da turanci yake wanda
baya ji na kusa dashi yana gaya masa,gyaran murya alƙalin ya yi ya fara
bayani"kafin mutuwar Alhaji ya mallakawa ɗansa dukiya mai tari yawa dan yana da
yaƙinin zai taimaki al'umma bila adadin wannan dukiya bawai ya bashi bane dan ya
nunawa sauran iyalansa yafisu a wurinsa ba,dan haka wannan muhalli ma da ku ke
ciki ya mallaka muku wasu ya barwa danginsa wannan gaba ɗaya dan haka aduk sanda
suka buƙata zaku matsa naku ku basu wuri saiku duba dukkan takardun wuraren ku zaku
ga inda ya mallaka muku,sannan margayi yabar ragamar ƴaƴansa a hannun yayansu koda
kuwa suna wurinku ne kenan bazasuyi komaiba saida izininsa wannan kenan ga wasu
takardu daya bar wasiyya wacece Nana ina mahaifinta",Alhaji Baffa ne ya nuna Baffa
dake can gefe a zaune"miƙa masa takardun hannunsa ya yi"ga wannan nata ne a kula
kuma ya roƙi da'a kula da ita dan akwai wani babban sirri dangane da ita sannan
Habib ɗansa ya kasance ya cika alƙawari na maida Nana matarsa komin daɗewa wannan
ne wasiyyar sa gata arubuce" ya mimmiƙawa na kusa dashi takardun su gani dan sunfi
copy ɗaya,duk wanda ya duba zaice hakane,dukkan mutanen dake wurin sun kance akwai
makusanta matan Alhaji kamar Baban Hajara Alhaji Bello yayan Hajiya Fulera tofa
sunfi kowa shaƙa dan abin bai musu ba ba haka suka so ba,yana gama bayanan sa kamar
wasu fari haka suka miƙe"wallahi ba'a isaba muyi wahala dashi shekaru masu yawa
sannan su daga baya aka samesu sai ace an mallaka musu komai wallahi ba wanda ya
isa a haɗe komai a rabashi kuma gida ba wanda ya isa mubarshi sai kaf suzo mu zauna
tare",wannan suɓul da baka da Hajiya tayi bata sa ni ba shi yasa alƙalin
murmushi"ai hajiya gado ya rabu kuma zamanku dole sai sun amince sannan zaku zauna
tare in basu aminta ba kuwa saidai kubar musu muhallinsu,sannan ki shiga hankalinki
bamai ƙwace wannan abu da Allah ya basu dan da basu samu ba shine yanzu ya turo mai
basu maija da wannan to zashi kotu ayi acan inda raban wannan ma asake kasawa
shinkenan bisimillah ina jinki"yayanta ta kallah ya kaɗa ma ta kai alamar karta
yadda da hakan shiru tayi suna ta muzurai,Hajiya Salma ce tai ta maza"mun yarda da
rabon gado amma bamu yarda da barin gidaba"Alhaji Baffa ne ya riga kowa magana"mun
yarda zamu zauna dasu rankai daɗe",wani murmushin kun tafka kuskure matan suka saki
duka Alhaji Baffa na kallansu"masha Allahu to sun amince muku dan haka ku zaku
tattara awaje ɗaya saiku basu sauran wuraren tunda ba'a buƙatar komai a wuraren
zaman,Alhaji tsoho wannan karramawa taka Allah ya biya Allah yaja kwana,ke
uwargidan Alhaji gaba ɗaya ƴan uwan zamanki zaku tattaru a ɓangarenki dan karki
manta nasan wurin mata shida zasu iya rayuwa batare da wani ya matsantawa wani ba
ga takarda zansa hannu nan da kwana bakwai zaku haɗe su kuma zasu dawo Allah ya
jiƙan Alhaji ku dage masa addu'a da sadaka shine gatan kawai da zaku masa da
dukiyar da yabar muku kai Habib kabi lawyer zai baka address inason ganin ka",yasa
hannu ya miƙawa lawyer shi kuma ya miƙawa Alhaji Baffa,ba yanda su Hajiya suka iya
haka suka fice gwiwa sage amma sunyi alƙawarin duk wanda zai zauna dasu da ƙafarsa
zai bar gidan,basu san akwai uwayensu hauka ba a dangin nan Gwaggo Asama'u kaɗai ta
ishesu riga da wando bama azo kan matan Kawu Iro ba,a wurin Hajiya Fulera suka haɗu
nan sukai jigum suna kallonta,ajiyar zuciya ta saki ta kallesu,"nasan zakuce taya
na amince muka karɓi wannan dukiya ko to inaso ku sa ni wannan alƙalin ba kanwar
lasa bane kuma in bamu karɓa ba zamuyi biyu babu saboda wannan da ku ka ga anbamu
ba ƙaramar dukiya bace bare ga maƙudan kuɗi na fitar hankali dan haka inaso ku
nutsu kuji ba sanya awannan zaman da za'ayi ba ragawa wani ba mutunci har sai sun
gaji sunbar mana gidan sannan wannan ɗan banzan magajin sai naga bayansa ku wuce
kar ace wani abu muke kuma ku adana takardun ku ko ku kawo su nan na haɗa na aje
mana kunsan yanzu zasuna harin abinda aka bamu baran kunsan akwai ƙarti adanginsu
kuma banyarda da wannan tshon ba",da yake watan ɓatan basira da rashin rabo ne ya
kama musu sai suka miƙa ma ta tai wani mugun murmushi ta karɓa ta buɗe locker duka
ta saka,tashi sukai suka fita kowacce farin ciki fal ranta dukiya tasamu,rashin
sani yafi dare duhu su Hajiya Harira sun faɗa tarkon Hajiya Fulera basu sa ni ba da
sun san wace ita da basu bata dukiyar su ba,kuma basu isa su amsheta ba dan damata
gama dasu daga maganar farko ta kubani kuma suka amince,suna fita ta fice acan wani
saƙale suka haɗu da yayanta kaf abinda tayi ta faɗa masa jinjina ma ta yay kuma
yasanar ma ta akwai wani boka can enugu yake zaije akan wannan abin yakamata kuma
suje tare tace ta amince tama manta takaba take.
Ana gamawa Alhaji Baffa ya musu godiya nan suka wuce kuma alƙalin ya tafi da
takardun wurin Baffa sannan yace Babban Yaya yazo da nashi kaf anjima,hakan kuwa
aka yi kaf ya ɗiba yaje dasu ya jima acan sannan ya dawo direct gida ya wuce yay
wanka a gaba ya taso matarsa yazo ya tarar Alhaji Baffa ya tara su Mama yace kowa
ya shirya rana ita yau zasu koma can gidan wohoho zoka murna ciki da bai na wannan
gidanjan bama ya Gwaggo Ma'u haka itama Hajara sai dai ita tafi kowa murna da hakan
dan su kaɗai suka san cikinsu ita da iyayenta wannan dangin tsiyar.
A satin kuwa rankatakaf muka koma can Alhaji Baffa da kansa ya nunawa kowa
inda zai zauna kuma hakan ya dace da kowa suma kuma yanda yace haka kowa ya yi
ɓangaren gidan Babban Yaya kuwa ai burin danginta yanzu ya cika gata ga Innar ta
sun tabbatar komai zaizo musu da sauƙi yadda basuyi zato ba da ita zasuyi amfani
komai nashi ya dawo hannunsu.
cikakkun wata uku ana zaman kadaran kadahan sai dai Alhaji Baffa yasa ido sosai
akan kowa kuma duk masu miji yajawa mazajansu kunne kan suyiwa matansu kashedin duk
wadda taja rigima to zata koma inda ta fito ta zauna ita ɗaya ko ƴaƴa basu bin
ta,makaranta kowa nazuwa haka masifarmu ni da Aunty Hajara tana nan saima abinda ya
yi gaba zagi dai ina shansa ko agaban waye dan yanzu kowa yasan tasan meke
tsakanina da Babban Yaya itama,kuma duk wanda take tuntuɓa yasanar ma ta wannan
al"amari fa kawai tayi haƙuri kuma abinda bama yanzu ba duk wannan bayanai basu
gamsheta ba ita kawai na bar ma ta mijinta.
Yauma na dawo daga makaranta du arikice dan inacan Babban yaya ya bini wai zai
koma India na ɗauka wasa yake sai ya nuna min harda kayansa a mota,ina tuɓe kayana
na sheƙa gidan Iyyo ita ta tabbatar min ya tafin kuka nasaka ma ta da mamaki take
dubana"ke miye hakan ki ke kuka dan ya tafi",baki na buntsuro"to meyasa zai tafi da
waccan ƙatuwar matar salon ana masa dariya acan su da suke da matansu ƴan
caras","waya ce miki da ita ya tafi tana nan gida yace ba yanzu zai ƙara komawa da
itaba"wani uban ihu na buga na miƙe ina rawa da cashiya,dariya Iyyo tai tayi"Allah
ya shiryeki Nana","ameen Iyyota",na gantsare ma ta ƙugu na fito da gudu mukai karo
da wani baya nayi zan faɗi ya taroni na faɗa jikinsa ƙamshin turarensa yasa na
saurin ɗagowa ina kallonsa ihu na buga"wayyo Babban Yaya bai tafi ba Iyyo",saki na
ya yi ya toshe kunensa"Nana zaki fasa min dodon kunne"hannunsa na riƙo Babban Yaya
ka sayi ticet kuma kayi asararsa sabodani dan Allah ka tafi ai kuɗin ba aƙasa ake
ɗebowa ba",kaina ya ɗago yana murmushi da ban taɓa ganin ya yi irinsa ba"Iyyo fito
kiji Nanata ta zama babbar mace tasan zafin nema da nakeyi",fitowa tayi tana
dariya"bana faɗa maka ba ai Nana gaba kaɗan saita kere kowa hankali da hangen nesa
a yaran nan","na aminta dake Iyyo tamu ta mutunci",wayarsa ke ƙara ya fito da ita
daga aljihu ya ɗaga"ok"kawai yace yana dubana"zan wuce yanzu jirgi ya samu dama
wancan matsala ya samu ashe rabon zan dawo na ganewa idona ne Nanata ta
girma",fuskata na rufe"zan bika to","da ace hakan zata yiwu basai kinfaɗa ba amma
wataran ƙafata ƙafarki duk inda zani","kayi alƙawari","nayi",ya faɗa yana dafa
kaina,hannunsa na riƙe muka fito agidan kowa na kallon mu ƙawata abokiyar faɗana ce
muka haɗa ido na ma ta gwalo,ba kunya ta ɗaga hannu biyu tamin daƙuwa ni kuma na
kwantar da kaina a hannun mijinta tana kallo kuma,muna jikin motarsa ta ƙaraso ana
kwarkwasa ta gefensa ta tsaya jikinta na taɓa nasa,baki na taɓe na faki idonsu na
ƙwala ƙara da sauri ya juyo har yana tureta bai lura ba kamin na dire a tsallen ya
ɗaukeni cak a wurin ya yi gefe dani yana tambayar lafiya,taɓe baki nayi nai rau rau
da ido"ba ji nayi ba kamar wani zare zare nabimin ƙafa",na rushe da kuka sunkuyawa
ya yi yaja rigar jikina sama har gwiwata sannan ya juyo da ita zare da yagani a
jiki ya fizge sannan ya sau rigar ya miƙe yakama hannayena ya janyo ni jikinsa
kamar zai rungumeni "ya isa haka mana kukan kina sosamin raina",goge fuskata na
shiga yi"na daina Darling Yaya kaga ma Aunty duk ta damu",juyawa ya yi yana
kallonta shi wallahi yama manta da ita awurin basarwa ya yi amma mamaki yake yadda
ta aza hannu aka alamar ta shiga uku"ke kuma miye na aza hannu aka",saukewa tayi
tana harararsa"mai zaisa bazan aza hannu aka ba kalleka gotai gotai da kai amma in
kana agaban wannan jaririryar saika rasa nutsuwarka",dake Babban Yaya babban ɗan
rainin hankali ne sai ya yi murmushi"au Nana jariryace awurinki amma naji daɗin
hakan kinga saina ɗakko abata tun yanzu tafi miki daɗin raino",yana kaiwa nan ya
shige mota,da sauri tace "wallahi karma ka fara kawo min wannan ƙadangaruwar gidana
zan soyeta kuwa","da nafi murna saina tama ki ci "ya kalleni nai kamar banji me
suke cewa ba,hannu na ɗaga masa na juya dan in na bari muka kalli juna da Aunty
Hajara tabbas dariyar mugunta zan ma ta amma na tausaya ma ta tunda mijin ma fecewa
zaiyi ya barta da ni ɗin dai.

Vote
Share &
Commentss
Û̬m̬̂ m̬̂ û̬ ŝ̬â̬d̬̂ d̬̂ î̬q̬̂
🌈🌈🌈
🌈🌈
🌈

Babban Yaya Free ne amma me so ya biyo ni Pc in sa a group don shagalin Nana


na buƙatar comments.
08146711395

1️⃣ 9️⃣ chapter 1️⃣9️⃣

Bayan tafiyar Babban Yaya da kwana biyu lamarin gidan ya fara canjawa su Hajiya
Fulera suna barin maza gaba gaɗi suna shigowa gidan kuma Alhaji Baffa nagani ya
barsu dan ya riga ya gane wato Babban Yaya suke tsoro sai ya barsu ai insun san
wata basu san wata ba.

****
Daga ɓangaren Iyyo na fito ina tafiya mukai karo da Hajiya Fulera baya
naja"yi haƙuri Mommy banganki bane",ban gama magana ba naji saukar mari mai zafin
gaske,dafe kuncina nayi na ɗago ina kallonta a mamakance"dan na baki haƙuri shine
kika mareni",hararata tayi"ko zaki rama ne",kai na girgiza"bazan rama ba dan inada
tarbiyya amma zakiga abinda zai biyo baya","ina jira dan dama an faɗamin ƴar sharri
ce ke","iya nan aka faɗa miki aini ƴar masifa ce ma bari kiga sample" bataga
abinda nagani bane Gwaggo Asama'u ce tazo zata wuce nai gwaraf aƙasa na rushe da
kukan masifa,da sauri tai burki ta juyo"ke Nana wannan tsiyar taki baki dainawa ko
agaban matar Baban naki kike wannan borin"ƙara kware murya nayi"wallahi Gwaggo
dukana tayi wai danna gaisheta bata amsa ba nace inatamiki magana baki kulani ba
shine tace ai kaf danginmu ba wanda ya isa ta kulashi kuma ko Ma'u da kuke taƙama
da ita bata isa na kulataba ke saima na dakata tunda ba gado gareku ba gidan kawai
taka haye aka musu aka bamu",kafin in gama magana Gwaggo Ma'u ta hayayyoƙo kanta da
masifa zagi ta uwa ta uwaba tana kai ma ta duka kan kace kwabo antaru a wurin,
wallahi Hajiya Fulera takasa magana saidai in mun haɗa ido na ma ta gwalo Gwaggo
Ma'u nakai ƙarshen maganarta ta kamo hannuna"zonan ƴar albarka muje kuma karki ƙara
gaida ta "kai na kaɗa ina taɓe baki muka bar gun,tsbar dariya Aunty Mama
saida ta zauna a ƙasa,Iyyo dake dariya ce tace"wallahi Halima ƴarki sai a hankali
kalli yadda ta shirya da uwarta wadda tun haihuwarta basa shiri sai yau",tashi
Aunty Mama tayi tana bin Hajiya Fulera da kallo"kisan me Iyyo gatsefa ta ma ta ita
kuma Nana ba hankali shine ta haɗasu faɗa da ita kuma fa kawai wucewa Ma"un tazoyi
dake kusan halisu guda fannin sharri shine ta saƙale ta haɗawa Fulera kitimurmura
da ita","Allah dai ya gyara amma Nana tabb",wucewa sukai dama Mama kome ake bata
fitowa kalla ita haka halinta yake,muna wucewa nace"Gwaggo zanje intafi islamiyya",
sakin hannun nawa tayi"ma za karki makara to".
Hajiya Fulera kasa zaune tayi ta kasa tsaye ita wannan yarinyar zataiwa haka
dama Hajara na faɗa ashema yarinyar tafi haka masifa da sharri to ta taɓo inda
bazata ƙara kwana lafiya ba da ƙyar ta saita kanta sannan tazo ga baƙin da tayi
dama su zataje tara bakin get tsautsayi ya haɗa mu.

Yau watan Abba huɗu da kwana shida Alhaji Baffa yaga yadda ake shirya biki
agidan amma bai kula ba baƙi tako ina ake wato matan wai zasu fita takaba saura
kwana biyu da daddare ina kwance ɗakin Iyyo Alhaji Baffa ya dubeni" karɓi wayar nan
kira min Habibu",karɓa nayi na kira masa shi dayake su acan rana ce yanama office
yaga kiran ɗagawa ya yi yana magana na miƙa masa ya karɓa ya yi sallama"Alhaji
tsoho","na'am Alhaji yaro ya aikin","Alhamdulillahi lafiya dai naji muryarka kamar
baka jin daɗi","lau nake Aisha ce dai ba lafiya kaganta nan sai amai take duk ta
fita ahayyacinta sai kiran sunanka take kowa yakasa gane kanta",a razane ya miƙe
muryarsa na rawa"meya sameta dan Allah",kafin Alhaji Baffa ya yi magana ya katse
wayar,saukewa ya yi daga kunensa ya ajeta yana kallon mu ni da Iyyo ganin yanda
mukai duru duru kamar kaji,ɗan murmushi ya yi"hakan dana masa shi zaisa yazo batare
da tambayar kowa ba'asi ba inda cemasa nayi ga abinda ake shiryawa agidan cewa
zaiyi abarsu suyi ni kuma bazan bari awa Habibu bikin iskanci ba da
dukiyarsa",ajiyar zuciya nayi ina dariya"kace su barikin ma su basu iya ba yau ga
tsoho zai gwada musu duniya",da carbin hannunsa ya kawo min duka na goce ina
dariya.
Acan ba yanda bayyi yasamu tiket aranar bai samu ba saina washegari adole ya
karɓa amma kwana da wuni bai runtsaba kuma bai kira kowaba har tsawon wannan
lokacin.
Tunda muka tashi da safe ranar gidan ya kacame da ƴan soye soye da dafe
dafe,tunda kowacce danginta ta tara masu yawa inka shigo gidan saika ɗauka bikin
mutum goma ƴan gata ake,ana sallar azahar manyan ƴan Dj da aka ɗakko suka gama jera
komai nasu nan da nan sauti ya fara tashi ƙawayensu da ƴaƴan ƴan uwa mata da maza
sai cashiya suke,yana sauka a airport ya hau taxi zuwa gidan batare da yasanar da
kowaba tunda suka doso layin yaga mutane nata shige da fice ga kiɗa har titi kafin
yaƙarasa get anan yasa aka sauke shi ya shigo gidan tun daga bakin get yasa hannu
a aljihu ya lumshe idonsa ya tabbatar Nana ƙalau take wannan al'amarin yasa Baffa
yace masa Nana ba lafiya dan yazo bawai dan bata da lafiyarba yama tabbatar in
rashin lafiyarce baza a faɗa masa ba sai yanzu ma hakan ta faɗo masa,buɗe idonsa ya
yi ya yana ƙarema ƙarti zunduma zunduma kallo ganin yanda suke yawo agidan su na
matan aure matan sunna,nan danan idanuwansa suka sauya cikin ɓacin rai ya taka zuwa
cikin gidan kotakan su Murtala masu sannu da zuwa baibi ba,daga ɓangaren mu na fito
zan tafi islamiyya adole saina biyo ta wurin da ake kiɗan dan haka ba ruwana na
ratso ta tsakiyarsu Aunty Hajara sai cashiya ake a tsayar maza wai ƴan uwa ne nan
kallonta nayi ina dariya ta harareni tana cije baki,zan giftata wani ya kawo zai
taɓani na maza na matsa"dalla malam miye hakan an faɗa ma jikina na irin wannan
waɗannan jakan ne"na faɗa ina nuna su Aunty Hajara da ƙanenta,wani tun zurowa tayi
tasha gabana",yau zanci ubanki abinda ki ke taƙama dashi dan mijina saina sa wasu
sun latse su yanzunnan",hannu na ɗaga ma ta"da kuwa kin tarowa kanki ruwa ko
aurenki bai mutu ba zaiyi muguwar girgiza",da hannu tawa mazan alama suka matso
mari ta kawo min na kauce tasa hannu ta tunkuɗa kan ƴan uwansu mazan
nan,ƙarasowasa kenan wajen idanuwansa sukai kai abinda ke shirin faruwa ganin
yanda ta hankaɗani yasan shirinta ne hakan da hanzari ya shiga tsakiya na faɗa
jikinsa runtse ido nayi mai makon jikin wasu sai naji ƙamshinda ko bacci nake idan
najiyoshi zan faɗi waye,hannuwana na buɗe na rungumeshi na rushe da kukan tashin
hankali kuji fa dan Allah da banyi kukan ba sai yanzu,cikin tsananin ɓacin rai ya
ɗago yana dubanta ta razana sosai amma ta dake,su kuwa mazan da basu gane waye ba
tsautsayi ya ɗebesu suka kawo hannu gareshi yana dafe dani a jikinsa ya ɗaga ɗayan
hannun ya kama hannun wancan sai ji kake ƙarasss,cikin ƙiftawar ido ya ɓalla mai
hannu ba ita ba ba mai karayarba harta ƴan Dj saida ƙarar ta isa garesu kan kace me
mata da mazan sun dare sai gudu shi kuwa mai karaya ya zube a wurin yana shure
shure da ihu,masu gudu na gudu amma shi yana nan riƙe da ni a wurin har su Hajiya
Fulera labari yaje musu nan akai dafifi awurin ana kallon mu ni kuwa naji sauyi na
lafe ajikinsa ina shan ƙamshi,duk wanda yake awurin nan salati yake mahaifiyar
yaron Yayar Hajiya Fulera ita tai kansa tana ihu tana tsine ma wanda ya yima ɗanta
haka ko kallon inda take baiba,tattaro shi sukai zasu wuce ya janyeni ajikinsa ya
tare su yana kallonsa"ka buɗe kunne da kyau kasaurareni koda wasa ka ƙara niyar
taɓa abinda yake mallakina ko kuɗine ba mace ba indai nawa ne to ka kiyayi haɗuwa
ta dakai",yana kuka yace"wallahi bansan taka bace Yaya Hajara ce tasa ni amma ko
inuwar gidanka bazan ƙara kalla ba bare abu mallakinka",cikin faɗa uwar ke
kallonsa"au harma magana kake da wannan azzalumin",katseta ya yi"kinga Umma wayace
miki azzalumine ADALI dai ni kinsan me nayi ne to? kuma sakeni nakai kaina aɗorani
maganina ma yanzu ke da kika gayyatomu ace namu uban ne ya mutu haka zakiyi kuma mu
kalleki wallahi bamu kyauta ba Allah ya baka haƙuri",yana kaiwa nan yaja hannunsa
ya bar wurin,wasu jikinsu ya yi sanyi yayinda iyayaen suka ƙara ɗaukar zafi,hanuna
yaja mukai ciki yayinda tunkan yama ƴan Dj magana suka kwashe yana su yanasu suka
fece ba shiri tunda Alhaji Baffa yaji shiru sai ya yi murmushi ya aje carbin
hannunsa adai dai lokacin mukai sallama falon"Habibullahi ɗan Habibullahi Allah ya
maka albarka ɗa ɗaya tamkar da dubu","kai Alhaji tsoho ai saika fasa min kai
dayawa",Iyyo ce tayi magana"ai yabon gwani ya zama dole maraba sannu da hanya",saki
na yayi ya zauna yana amsawa ƙafa na doka aƙasa"ni ka taso ka rakani makaranta inba
hakaba dukana za ayi kamanta wannan basu Ya Sayyadi bane da NAke ci musu kashi
aka",fasa zaman ya yi ya miƙe"Iyyo bari nayi rakiya kar ataɓamin jikin ƴar
Baby","kai Babban Yaya ɗimemiya dani shine ka ke ce min Baby",ƴar dariya ya ɓoye
"to Big Girl",dariya nayi muka fita tare har makarantar ya rakani sannan ya juyo
gida,da sallama ya tura ƙofar falon ya shiga ba kowa hakan yasa ya wuce ɗakinsa yay
wanka sannan ya fito kaya marasa nauyi yasa sannan ya fito falo a zaune ya ganta ko
bi takanta baiba ya ɗau wayarsa yana dannawa daurewa tayi tace"wai kai yanzu akan
Nana saika karya mutum",wani kallo ya ɗago yana wurga ma ta"da bake nakarya ba
shine ki ke tambayata to bari kiji na fiki hauka da rashin ta ido in kika bari na
juya miki baya baki da abinda zaki da zai sa na juyo gareki dan haka tashi ki bani
abinci ko na sauke kaf fushina akanki wato ku ne masu mana budiri akan ankai
mahaifinmu rami ko to daku da naku iyayen kaf kowa sai yaje inda yaje kunyi da ɗan
halak zakuga rashin mutunci mara wando wallahi tashi anan kiban abinda nace ko nayi
awangaba dake",jikinta har rawa yake ta wuce kitchen tana mamakin shi sai taga
kamar abinda take masa baya aiki kalli yanda yake ma ta tsawa kamar bata masa
maganin ko kallon banza bazai iya ma ta amma ya rufe ido yanka ma ta masifa baki ta
cje tana kaɗa kai, dama an kawo ma ta kaf abubuwan da aka dafa su ta jero ta kawo
masa da lemon kwali buɗewa ya yi ya gama kallon abincin"wannan na fatin ne da akai
kwasheshi kan nasa ki cinyeshi du"da sauri ta kwashe dan yau wani mugun shakkar shi
taji tana yi lemon kawai yasha ya kwanta a wurin ya jima ita kuma tana zaune can
aka buga ƙofar tashi tayi ta buɗe ashe Hajiya Fulera ce tunkan Hajara tayi magana
ta tureta gefe ta shigo falon"kai ɗan marasa mutunci tashi ka aikata ta'sa sannan
kazo nan ka kwanta a Ac, ai ni tun ganin farko dana maka nasan cewa shigowarka
gidannan ba alheri zai haifar ba sai dai masifa gashinan kuwa alokacin in nafaɗa
ba wanda zai yarda kalleka kamar nagari amma mugun nufi aranka ya yi yawa to bari
kaji wallahi tunda kajiwa ɗan ƴar uwata rauni to kaima sai waɗanda ka ke so sun
raunata ka zuba ido ka gani koba yau ba amma wannan alƙawari nayi",tunda ta fara ko
motsi bai ba duk da yana jinta amma ya shareta dan maganganunta basu bashi tsoro ba
kwata kwata,ganin bazai kulata ba saita fice tana zage zage,bayan ta fita ne ya
tashi yana murmushi ko kallon Hajara baiba ya fice,bayansa tabi da kallo anya kuwa
wannan mutumin yana da saiti batasan ta ina zata faraba shi yasa itama tabi bayan
Hajiya Fulera .
Mama na zaune falo ya shigo da sallama"Habibu kaine ya hanya tafiya haka ba
sanarwa kodan Umman ka bata nan ne",zama ya yi yana faɗin"ki daina faɗar haka mana
Mama banma san bata nan ba,wallahi tafiyarce ba shiri nayota wancan tsohon ne ya
dama min lissafi wai Nana bata lafiya shine fa na ɗebo hanya ashe waɗannan
shashashan matan ne kewa mutane hauka agida",kai ta kaɗa"kai dai bari ai waɗannan
mutane bansan irinsu ba gashi dai agidan ma kowa ya sauya hali dan inkaji ana
hayaniya dama to sababbu ne keyi sai mazajansu amma mudai dama kasan ba yi ake ba
Alhaji ya maka hakane dan yasa ka dawo shi inzaiyi musu magana yasan baji zasuyi ba
amma daga zuwanka naji ana kajiwa wani ciwo Habib ka daina shiga shirgin mutanen
nan","bari Mama ai mai ciwan ma yagane bashi da gaskiya sudai keta haukar su","to
nidai ka kula dan Allah kaga yanzu babu Yaya kaine komai nasa kaine madadinsa
awurina ka taimaka kadaina biye musu","shike nan Mama insha Allahu","amma Habib
yunwa ka ke ji ko?",da sauri ya ɗago ya kalleta zaiyi magana ta dakatar dashi ta
miƙe zuwa kitchen abinci mai lafiya ta kawo masa"taso kaci inba hakaba anjima kaɗan
ka fara daina gane mutane",murmushi ya yi yana tashi zuwa kan capet ɗin ya
zauna"Mama taya akai ki ka gane inajin yunwa","saboda kai da Nana in kuna jin yunwa
idonku ciki yake komawa",ƴar dariya ya yi"lallai Mama kin gama sanin mu abincin
yaci sosai",saida ya gamaci sannan ya zauna suna hira wayarta ce tai ƙara ta duba
Aunty Mama ce dama tare suka tafi Gaya suna da Umma can dangin Umman ɗagawa tayi
tana sallama kukanta taji da sauri tayi magana zuciyarta na tsistsinkewa"lafiya
kuwa Halima",jin batai maganaba tana kuka saita ƙara ma ta magana"Halima kinsa ni
atashin hankali fa meya faru ne",da ƙyar tayi magana"Dada Yaya Sa'a ce ba lafiya
tunjiya da muka iso ciwan ciki sai gashi yanzu ta tafi ta barmu ta
rasu","innanillahi wa inna ilaihi raju'un"wayar faɗuwa tayi ta miƙe da gudu zata
fita Babban Yaya ya bita ya riƙeta"Mama lafiya meya faru"tsabar ta ruɗe ta manta
waye Habib bakinta na rawa tace"Sa'a! Sa'a!! ce"wani dam ƙirjinsa ya bada ko bata
gama faɗaba ya gane metake nufi saura ƙaɗan ya faɗi ya daure ya riƙe Mama"ki yi
haƙuri Mama haka Allah ya nufa",hannunsa ta kama tana kuka sosai,dawowata kenan
daga islamiyya na tarda su abakin ƙofar falo ganin halinda suke ciki saina ƙarasa
da sauri ina tambayar"Babban Yaya lafiya","jeki kira Alhaji Baffa da Iyyo",da sauri
na wuce naje na tattagosu mukazo tare,suma tashi hankalinsu ya yi nan suka fara
tambayar lafiya,runtse ido ya yi"Ummace ta rasu

Vote
Share &
Comments
Ƴan uwa

Û̬m̬̂ m̬̂ û̬ ŝ̬â̬d̬̂ d̬̂ î̬q̬̂


🌈🌈🌈
🌈🌈
🌈

Babban Yaya Free ne amma me so ya biyo ni Pc in sa a group don shagalin Nana


na buƙatar comments.
08146711395

2️⃣ 0️⃣ chapter 2️⃣0️⃣

"Innanillahi wa inna ilaihi raju'un",gigita da tashin hankali ne ya ziyarci


kowa ya yinda wani irin yanayi mai kama da suma naji ya ziyarce ni lokaci ɗaya ya
yinda sauran ma hakan take sai a hankali naji su Alhaji Baffa suna salati amma daga
nan ban ƙara gane komai ba,zuwa jimawa na tashi a firgice ɗakin ba kowa da gudu na
fito ina kuka na tarar da ƴan gidan duk a waje kowa da shiri gasu Murtala atsaye
bangaje su nayi na isa ga Babban dukansa na shiga yi ina kuka"wallahi ba haka bane
Umma tana nan"janye ni Ya Dijama tazo zatayi ya hanata da ƙyar na daina dukansa na
faɗa kansa ina kuka kai kace uwata mahaifiya ce ta rasu tunda kowa ke kuka shi sai
yanzu yaji hawaye ya zubar masa da sauri ya share ya kamani na miƙe da uniform ɗina
yasa ni amotar sannan shima ya shiga ranar kowa dashi aka tafi ba abar kowa ba sai
ƴan mulkin gidan saboda wulaƙanci ko mace ɗaya bata biyo mu ba Hajara ma motar su
Iyyo ta shiga dan ko kusanshi ma bata zoba,a motar ma kan ƙafarsa na kwanta har
Allah ya kaimu sannan tara ma na dare ta kusa Sallar magaruba da isha suka ja burki
sukai sannan suka shigo ciki har an haɗata fuskarta aka buɗe mana Allah sarki
tamkar tana murmushi,kuka sosai Mama tayi anan ta kwana a gabanta tana kallonta
washegari tun bakwai akai ma ta sallah aka kaita makwancinta gidanta na gaskiya
duniya kenan.

Kwanan Umma bakwai muka dawo,gidan duk ba daɗi haka kowa yasauya dan rashin
Umma ba ƙaramin giɓi bane a ahalinmu mun daɗe bamu saba da rashinta ba sai da ma
aka dawo dasu Ya Dijama gidan mu sannan muka ɗan sake bayan Umma tayi arba'in haka
Babban Yaya ya koma saidai gidan ba me gane inasu Hajiya Fulera suka saka gaba
amman yaransu muna tare koda za a musu faɗa,bayan Umma tayi wata bakwai Alhaji
Baffa ya saka ranar su Ya Dijama su biyar ciki harda Ya Hadiza ta kawo bazawari dan
ba'ace masa saurayi ba Alhaji Bukar gashi ɗikeke abin bankyan gani amma tace taji
ta gani shima Alhaji Baffa ya amince ma ta aka sa ranar da ita murna kamar ta
kasheta dan yanaji da ita ga gata yana nuna ma ta kuma yana kashe kuɗi ita da
Babarta shi yasa idonsu ya kulle akan shi,sai dai Ya Fatsima shiru har yanza amma
Baba kullum yace tana lafiya shi yasa hankalinmu ke kwance.
Baffan mu ya dawo zaman gida ya yi retire amma ba ruwansa da kowa bashi da
abokan hira sai mu sai Alhaji Baffa da Kawu Nuhu dama su Kawu Iro suna nan da
halinsu sai fatan Allah ya gyara.
Sirrin dake ƙadan dane da Hajiya Fulera ba wanda yasanshi sai ita.
Yau biki saura sati biyu gashi anyi hutun makaranta jiya sai murna muke,ɗinki
muka tafi karɓa har magaruba tamana can zoo road bamu dawoba Ya Ashiru ne naga ya
tsaya da mota a bakin shagon dariya na kwashe da ita na kalli Ya Nabila nace"Ya
Nabi kinga can me ke ne ya biyoki dan kar amasa kasassaɓa ya riga ya ƙulle
kunkuminsa",zaro ido sukai kamar na watsa musu yaji"miye hakan kuma ku ke min
kallon baƙunta","mun shiga uku Nana dama haka kike waye ya ɗaure kunkumin
nasa",baki na murguɗa musu"wancan mana"na nuna Ya Ashiru,kunne ne na Ya Dijama ta
kama"Nana dama haka kike kina magana kamar wata yayarmu",ƙwacewa nayi"malamai ƙyar
fa nake kallon kowa bari ma kuji Nana ba kalar ku bace da kwanyar ta",ina kaiwa nan
na fito ashagon ina dariya"Ya Ashiru ka biyo kayanka ne kar mu maka wasa
dashi",baki ya riƙe yana muzurai"ubanki dama baki da kunya to ba kayana na biyo ba
Babban Yaya ya dawo ya tarar bakya nan shine ya kaɗo ƙeyata ina masallaci ina
addu'a yace nazo na ɗaukar masa ke kinga bani na biyo kayana ba shine da yake
tattala nashi wanda sai nan gaba zai samu shime yace nazo kinji yanda akai",dariya
nayi ina sara masa na shige motar suma sukazo suka shiga muka ɗauko hanyar gida,dai
dai wani restuarant da Babban Yaya ke saya min ice cream mukazo ihu na sheƙa da
sauri ya taka burki ya yi gefen titi,duka ya kawo min na matsa jiki murfin
motar"keee baki da hankali zaki kashe mu da shegiyar muryarki kamar ta gyare"dariya
nayi"ba mai mutuwa sai kwanan sa ya ƙare Ya Ashiru ice cream zaka siya min anan
Babban Yaya ke saya min",hararata ya yi"bazan saya ba ko ni Babban Yaya ne ",ya
kunna motar muka tafi ana buɗe masa get dama gidan kamar rana dan hasken fitulun na
daban ne, Babban Yaya na hango a jikin wata mota shida amaryar tasa yana sanye da
jeans da Tshirt sun masa kyau ita kuma tana sanye a rigar atamfa da mayafi kamar
wata ƴar budurwa,tun kamin ya gama parking na zunduma ihu ina rushewa da kuka kan
ya tsaya fuskata har tayi ja kamar wadda akama bugun tsiya ko aka mammara yana
tsayawa na fito da gudu na nufe shi shima da hanzari ya ƙaraso na faɗa jikinsa
rungumeni ya yi jikinsa har rawa yake"Nana waye ya taɓa min ke faɗamin",ɗagowa nayi
na taɓe baki kamar zan faɗi abin arziƙi nace"ba Ya Ashiru bane mukazo wucewa ta
wannan wurin masu ice cream ɗin shine nace ya saya min sai ya dungure min kai wai
bazai saya ba inma cikin Babban Yayan gareni sai dai ya zube ko yazo ya saya min da
kansa,danace ya taimaka sai yace na sauka nabar masa mota duk abinda zai sameni
yasameni in yaso ka mutu",da yake suna bayana suma sun fito kowa aka ya ɗora hannu
suna mamakin maganata baranma ta gefe wato Aunty Hajara wadda ta zama kamar
sumammiya"fuskata ya tallafa hannu biyu"yi shiru kinji zan saya miki ko ma menene
kai kuma ɗan buƙulu sai dai kaga zubewar ciki akan matarka amma ba akan ta ba kuma
ba abinda zai meta bare ta na mutu"ya zuba masa ranƙwashi yaja hannuna muka wuce
mota da kansa ya buɗe min na shiga sannan shima ya shiga muka fice a gidan,jifff
sukaji an faɗi da sauri suka juya sai sukaga ashe Aunty Hajara ce sai zare ido take
kamar an kama ɓarawo dama ba shiri take da kowa ba hakan yasa basu kulata ba suka
wuce sai a hanya sannan suka fara dariya koda suka bawa su Mama labari suma dariyar
sukai dan abin baka cewa nice na faɗa ko Baffa da ba komai yakewa dariya ba saida
saida ya dara yana kaɗa kai.
Kayan ice cream yamin da alawa kala kala sannan muka dawo,gida ya wuce ya
tarar da masifa na jiransa da ƙyar ya ƙwace kansa ya shige ɗaki ganin haka ta gama
masifarta ita ɗaya sannan ta wuce ɗakinta ta shiga wanka dake bata da zuciya saita
shirya da rigar baccinta ta biyoshi ya kwanta kenan ta shigo yana jinta ta kwanta a
jikinsa murmushi ya yi daman yasan haukar ta banza ce ba inda abin zashi musamman
da abin yake dare ita kuma yafi komai daɗi awurinta yau ba bacci ya faɗa
aransa,ilai kuwa sai wajen biyu da rabi ya ƙwaci kansa ya kwanta yana jinta tana ta
mita wai yafiya ragwanta banza ya ma ta danshi bai taɓa gamsuwa da ita ba yana dai
biya ma ta tata buƙatar ne.
Ni da ita kuwa ban ƙara yarda mun haɗu ba dan inta gano ni tun daga nesa take
yanko min daƙuwa dan haka da gudu nake canja hanya ina ma ta gwalo.
Ana gobe kamu aka shirya tafiya lalle amma kowa yaƙi biya min dama gidan ya
cika da kowa da kowa an hallara,Babban Yaya na hau nema can ɗakin Iyyo nasamoshi
suna magana ganina rai ɓace ya riƙo hannuna"Rayuwar Yayanta waya taɓata ne",baki na
tura masa"ba lalle duk suka tafi ba amma an rasa me biyamin har amaren sunma yi
tafiyarsu",kumatuna ya riƙe"muje na kaiki zasu gane basu da wayo in muka haɗu",da
murnata muka fito sai gidan lalle can Fagge dama can muke zuwa tun muna tsohuwar
unguwa shi yasa sun sanmu mun saba kuma,a ƙofar gidan ya tsaya muka fito samarin
layin sun masa zuru suna kallon haɗuwa ta musamman,"jeki kira min mai lallen nayi
magana da ita da kaina"ina juyawa saiga Yayarsu ta fito"a a Nana tsiwa yanzu nake
tambayar ina tawajena ne aka ce min banda ke za awa shine nace to ba wanda zanyiwa
kuwa gidana ma zan koma","yauwa Ya Aisha ga Yayana yace na kira mai lallen tunda
gaki shike nan",fuskarta washe tace"Babban Yaya ne da kansa ai naganeka sunanka ya
iso ni tuni",ɗan murmushi ya yi"hakan ya yi gatanan amata nata yafi na kowa
kyau"yasa hannu a aljihu ya zaro kuɗi ya miƙa ma ta,karɓa tayi tana"baka da matsala
da hakan amma ba ciki zamu shiga ba nayi aure ga gidana can acan zamuyi namu batare
da kowa yagan mu ba kawai dai ka kawo ma ta abinci dan nasan ita ƴar gayu ce ba
komai take ciba","baki da matsala a dai fito min da ita",ya shiga mota ya koma mu
kuma muka wuce gidan nata,kurkur da dilka tamin sannan lallen iya ja sai wani
sample shiba purple ba ba pink ba dashi akai madadin baƙin bayan la'asar na fito
kamar amaryar nima fatata tayi wani mugun kyau sai laushi da ta ƙara har wanka tasa
ni nayi sannan yazo ɗaukata,ai Babban Yaya kasa gane ni ya yi da kyau shi kansa ya
yaba da yadda nayi bama da mukazo gida ai amaren harda dungure min kai saida Babban
Yaya ya shigar min sannan suka barni a ranar da daddare mukaje gyaran kai wannan ai
muna da yawa sai kasuwa ma mukai amma anga kala kalar gashi.
Washegari akasha kamu munsha ankon less a gidan akayi komai dan Alhaji Baffa
ya hana wani shagali yadai ce ayi komai agida amma banda waje hakan yasa sai dare
aka watse,da safe tun wajen tara ƴan ɗaurin aure sun fara cika gidan abokan kowa da
ƙawaye da manyan mutane iyaye da ƴan ƙauye duk sunzo,su Hajiya Fulera ma suna nasu
taron daban kaji gulma.
Ina saka kaya Ƙarami ya shigo"Babban Yaya na kiranki",to nace amma matsalar
ban tambaya yana ina ba sai na wuce part ɗinsa saida na shiga sannan naga basu bane
aciki ashe ƙawayen Aunty Hajara ne sun cik ɗakin sai shisha suke sha mamaki ne ya
kamani amma saina daina nasan zata iya ma'amala da kowa saboda ƴar masu kuɗi ce
itama kuma suma da gani babu tambaya,ido suka zubamin kamar sa cinye ni hakan yasa
na juyawa zan fita mukai karo da ita baya nai zan raɓata na wuce saita tare
hanyar,wani kallon ƴan iska ta shiga bina dashi"ƙaramar karuwa ya dai ko an biyo
shi nan ne aƙara lallatsa masa jikin dan nasan a jikinki dai babu abin latsawa
tunda dai ɗan breast ɗin bai wuce ƙuli ɗan tara sisi ba,amma ahaka kike taɓa maza
har wani rawar jiki suke in sun taɓaki konace in ya taɓaki dan na lura ke naki
karuwancin iya kansa ya tsaya dan kinga yafi kowa haɗuwa ko,to bari kiji bazaki
taɓa haɗa makwanci da mijina ba dan iya nawa ne ni ɗaya kuma na masa farraƙu da
mata musamman ma ke alƙawarin na kakanni sai dai ya kashe kowa ciki harda ku,ni
banga ta inda kika isa awa namiji kamunki ba koda yake tsammani ake jikin naki zai
haɓaka nan gaba ba'asan na kasheshi ba a haka zaki ta zama inda kike masa kamu kuma
ko pencil bai shiga bare ingarman namiji irin mijina",wani irin duka maganganun ta
suke min dama wannan mara hankalin haka take kalla yadda take zayyane ya mijinta
yake agaban ƙawaye da alama to halinta kenan,tureta nayi zan wuce ta dawo dani
baya"malama sake ni kona kula ki ne",hannu ta ɗaga zata mareni na riƙe"kula kuma
dan in kina cin ƙasa ki kiyayi ta shuri wannan fuskar saidai hannun mijinki ya taɓa
badai naki ba kuma ki rubuta ki aje yau saina kwana da mijinki koda kuwa a bola
ne"na yarfar da hannun nata na fita,wai amma nan jinjina suke ma ta tamin rashin
mutunci.
Tsabar yadda zuciyata ke tafasa ban nemi kowaba na wuce wajen Iyyo batama
ɗakin na kwanta kan kujera Alhaji Baffa ne ya shigo"Nana ta meke damunki haka kowa
na waje ke kina ɗaki","Baffa kamin wani abu mana","ME NE SHI ƳAR LELE",tashi nayi
na
zauna ina kallonsa nace.......................👉👉👉👉👉👉👉👉👉

Vote
Share &
Comments

Û̬m̬̂ m̬̂ û̬ ŝ̬â̬d̬̂ d̬̂ î̬q̬̂


🌈🌈🌈
🌈🌈
🌈

Babban Yaya Free ne amma me so ya biyo ni Pc in sa a group don shagalin Nana


na buƙatar comments.
08146711395

PAGE 21

"Kome nace kamin zakamin","zan miki mana faɗi kawai Aishatu",Iyyo na kalla na
maida kallon gareshi"NIMA KA ƊAURAN AUREN DA BABBAN YAYA","an gama ƴar lele amma
karatunki fa kinsan dai muddin aka ɗaura miki aure dashi bazai bari ki fita zuwa
wata makaranta ba","na aminta Baffa ai nayi karatu wanda Allah ya bani nagode inda
rabo da hannunsa zaikai ni makaranta","shike nan Aishatu",ya tashi ya fita,kwanciya
na koma nayi gabana na mugun faɗuwa ƙirjina har wani ɗagawa yake dafa ni akai na
ɗago naga Iyyo ce,zama tayi tana cewa"Aisha kefa kika nema dan haka karki damu nima
ina bayanki amma ki kula kinsa kanki a uku",tashi nayi"wallahi ko a ɗari nasa kaina
nasa ni kawai ku cika min burina",kaina ta dafa Allah ya miki Albarka tashi maza ki
koma cikin mutane",dariya nayi na miƙe na fito Ya Amina na hanga tana bawa su
Walida wani abu a leda da gudu na ƙarasa ta bayanta na warce ledar na zura
aguje,kanta ta dafe tana dubansu"saiku haƙura uwarku ta ƙwace",dariya sukai"zamu
bita ta bamu",suka watse aguje,dariya tayi ta wuce suka bini bansan sunzo ba naji
an kama min riga tsayawa nayi ina dariya"ku tsaya mu raba to da alawar madarar za'a
shanye ba ni".
Babban Yaya dasu Abdallah ne suka zo wucewa yana sanye da manyan kaya shadda
gizzinace harda babbar riga amma ta gayu da akeyi yanzu bai ganni ba saboda jan
magana na ɗaga murya sosai"Angon yau",tsayawa sukai suna waiwaye na ɓuya ciki yara
dariya sukai shi kuma ya girgiza kai suka wuce amma yasan waye,a wajen ɗauri auren
an gama na kowa sai Alhaji Baffa ya kalli Baffanmu ya miƙa masa kuɗi rafa biyar ƴan
dubu dubu ya karɓa sannan ya kalli Kawu Nuhu ku ɗaurawa NANA AISHA da HABIBULLAHI
aure"kallon kallo aka shiga yi"ku ɗaura mana lasifiƙar tamkar an ƙara ma ta zaƙi
sanda suka fara,Babban Yaya ji ya yi kamar an ɗura masa ruwa akunne anya kuwa dai
dai yakeji ba ɓata akaiba a waɗanda za'a ɗaurawa auren ai bashi",amma ina yana
tsaka da wasi wasi yaji fatiha sai fuskokin abokansa dake kallonsa suna dariya
tashi ɗaya yaji wani farinciki ya lilliɓeshi nan yaga mutane sun gayeshi kamar shi
kaɗai aka ɗaura aure a wurin hannu kala kala ya shiga gaisawa dasu ana masa Allah
yasanya alkhairi kan kace kwabo labari ya watsagidan nan al'ajabi ya cika
gidan,inacan cikin yara muna rabon alawar madara naji an shaƙeni ta baya watsar da
ledar nayi na riƙe hannun koma waye nan yaran suka watse suna kiran iyayen su,da
sauri Ya Hasiya ta watsar da kayan hannunta ta ƙaraso iya ƙarfinta tasa ta ƙwace ni
da hanzari ina nishi na koma bayanta na ƙanƙame ta ina numfashi da ƙyar sai sannan
naga ashe Aunty Hajara ce wani sanyi ne ya tsirga min har ƙafata wato aikin gama ya
gama shine taji tazo kasheni ita kuma,Ya Hasiya ce ta daka ma ta tsawa cikin ɓacin
rai tace"dalla malama kina hauka ne da zaki ma ta wannan shaƙar ko kuma ita ta
ɗaurawa kanta aure da mijin naki to bari kiji wannan haukar taki ba inda zata kaiki
anan gidan kuma ki gwada ma ta haka a gabanshi kiga ya zaku kwashe",kasa magana
tayi dan ta shaƙa kawai saita fara ɗura ɗuren ashar tana hauka,da sauri Aunty Mama
ta ƙaraso ta janye ni zuwa jikinta wani kallon warning ta watsa ma ta nan ta tasani
gaba zuwa cikin gida ita kuma aka barta dasu Ya Hasiya da ƙyar ƙawayenta da Hajiya
Fulera suka janye ta zuwa ɓangaren Hajiya Fulerar dan tabbas suma abin ya ɓata musu
rai.
Can ƙuryar ɗaka Aunty Mama tasani"karki kuskura ki fito na faɗa miki kiyi
zamanki anan","to Aunty Mama"na faɗa ina fashewa da kuka","kiyi shiru ina zuwa"ta
fita,kuka sosai na shiga yi amma wallahi bansan dalilin yinsa ba,tana fita ta tarar
ƴan uwan Hajara da sukazo sai zage zage suke amma ƙirmisisi Mama ta hana kowa
tankawa kuma hakan akai bamai kulasu daga baya ma sai suka tattara yanasu suka tafi
can ɓangaren Hajiya Fulera suka ɗora daga inda suka tsaya anata zugata ita kuma
tana daɗa hawa,bai biyo sahun angwayen ba zuwa ciki ya zame ya kira Ya Usaina da Ya
Hasiya sukazo can inda ya gaya musu tun daga nesa suka tabbatar yana cikin farin
ciki wasu mukulai ya basu ya nuna inda zasu buɗe da kansu zasu san me zasuyi sunyi
mamaki amma auka karɓa sukaje can gidansan suka buɗe inda ya gaya musu suka shiga
shashin tsan tsar mamaki ne ya kamasu ganin komai na kayan ɗaki aciki duddubawa
sukai sannan suka fito"Usaina wannan kayan kuwa ba Abba ne ya tanedusu ba","gaskiya
Ya Hasiya nima nayi tunanin hakan amma meyasa to ya nuna mana tun yanzu dan ayanda
akai auaran yasan ba yau zata tare ba","hakane Usaina inaga ya nuna mana ne ko in
munji za'a siya muce akwai",tafawa sukai"hakane kuma" suna shiga suka tarar Iyyo
nata rawa wai burinta ya cika ɗan baƙin ciki sai dai ya mutu,mutane da yawa dariya
suke amma banda matan Kawu Iro su sunso ace ƴarsu ɗaya ta aureshi itama ta gaji
wannan dukiya,Ya Saddi'q da da Ya Isma'el keta liƙi saiga Ya Ashiru shima ya shiga
tayata rawar yana baza babbar riga ciki kwalliya ta gani ta faɗa amaren suka fito
nan da nan auka ɗau hankalin mutane aka zagayesu anata hotuna daɗi ya ishi Iyyo
Alhaji Baffa ne ya shi har cikin gidan yagansu ƙarewa kallo ya yi yace"ina
Nana","tana ɗaki"Ya Ruma ta faɗa"kamarya taya za'a ɓoyeta kamar abin abin munafurci
ina uwar tata ne ko da yake tana aiki ke Hasiya, Mabaruka, Fatima Amina ku shirya
min ita itama ta fito yanzu ta shiga cikin ƴan uwanta ai kayanta su waɗannan ma
amaren shirin basu da irinshi",guɗa Ya Mabaruka tayi"angama tsoho mai ran ƙarfe
kuma ka faɗi gaskiya ja ka zauna yanzu zaka ganta.
Ina nan inda Aunty Mama tabarni suka shigo da sauri na tashi ina zare ido
ƙarasowa sukai fuskarsu ba rahama na zata Alhaji Baffa ya faɗa musu abinda nayi ne
ganin zan fashe muau da kuka sai suka kwashe da dariya Ya Fatima tace"su Nana matan
aure an shiga sahun mu shekara mai zuwa war haka mu ɗau ɗan mu",wani razanan nan
kallo na musu kamar mara wayo sai kuwa na rushe da mugun kuma nai baya na faɗa
gadon dariya suka shigayi Ya Mabaruka ta zagayo ta zauna kusa da ni ta dafa ni"ke
daina kuka mana ai burinmu yau ya cika dan haka ba kuka zakiyi ba tashi maza kiyi
wanka kinga amaren can atsakar gida amma babu ke Alhaji Baffa harya far faɗa",share
fuskata na shigayi sannan suka tasa ni nayi wanka kayana suka tattaro suka zaɓo
wani shegen material da aka min doguwar riga sky blue ne da ratsin dark blue sai
walwali yake da kansu suka shiryani kwalliyar ma da kansu sukai min dan sun iya
dama musamman ma Ya Hasiya har shago gareta,a gaban mudubi suka tsaida ni"kalli
kanki Nana",Ya Usaina ta faɗa,a hankali kamar mai tsoro na ɗaga kan na kalli
mudubin ni kaina banda nasan kaina da nace bani bace wannan zankaɗeɗiyar baiwar
Allahr, gaba suka taso ni zuwa tsakar gidan ya Allah raiiii haka mutane sukai min
amma saida muka wuce can inda su Ya Dijama suke nan suka kaini Alhaji Baffa farin
ciki ya kamashi yay murmushi sannan ya bar wurin su Ya Ashiru ne sukazo nan fa
flasher waya ta fara aiki dukkan abinda ake ƙirjina tara tara yake duka ina tunanin
haɗuwa da Babban Yaya nasan wallahi saiyaci ubana dan zaisan ni nace amin auren,har
yamma can sai gashi ya shigo gidan wuf na tashi zan gudu Ya Dijama ta riƙeni a dole
na zauna amma tamkar zanyi fitsari a wando nakji,su Walida ne suka janyo shi"Big
Uncle zokaga Aunty Nana ta zama queen",biyosu ya yi har wurin da muke fuskar nan
kamar haɗuwar kaka amma daya ƙaraso saiya saki ransa ya zauna kisa dani wayoyinsu
suka ɗakko suna ɗaukar mu hoto gaba ɗaya zamansa yasa na ƙara tsurewa shi kuwa sai
ya sau fuska kamar ba shiba,tun zamansa baimin maganaba harya gama yabar wurin ya
shiga cikin gidan ganin yanda ƴan uwan Umma suka taru sosai hankalinsa ya tashi
baiwa kowa magana ba sai Ya Hasiya da ta hangoshi ganin ya koma ta tashi da sauri
da bishi dan tasan kwanan zancen,"Habib Habib"take kiransa amma bai juyoba bare ya
tsaya tana gani ya wuce can ɓangaren Abba inda ya rufe bai bar kowa ya shiga ba
dama,ciki ta juya jikinta a sannan ya ye tabbas tasan sai yafi kowa jin rashin
Ummansu dan yafi kowa kusanci da ita ana cewa mace ce ƙawarki in kika haifa amma
bandashi,kasa nutsuwa tayi koda ta zauna ta rasa taya zataje inda yake gashi waccan
matar tashi tana hauka an ma ta kishiya ita kuma uwar sanaben taga duk afirgice
take amma duk da haka saita tura ta ƙila ya nutsu,muna nan zaune sai ga Ya Hasiya
kusa dani ta zauna"amarya kinsha ƙamshi ɗan biyoni mana",tashi nayi na bita duk
inda muka bi kallona ake kamar mutane zasu sauyan halitta,a can ta ƙofar shiga ɓan
Abba ta tsaya"shiga ciki maza akwai saƙo dana aje ki ɗakko min",batare da tunanin
komai ba na shige,ita kuma ina juya tabar wurin tana dariya,ƙofar falon na tura na
shiga ko ina fes amma bakowa aciki shiga na gama yi ina dube dube amma banga komai
juyowa nayi zan fita naji kamar nishin mutum juyawa nayi can ƙaramin falon dake
hannun damana na hango Babban Yaya ya kifa kansa da kujera amma bansan meyake ba
saidai numfashinsa har inda nake inaji,kamar zan fita dan tsoronsa nake amma na
daure na shiga inda yake kamar kaza mai ƙwai a ciki haka nake tafiya harna ƙarasa
inda yake kamar ace ƙyat na gudu haka nace"Babban Yaya"ajiyar zuciyar da yake ya
tsayar yana ɗago kansa"innanillahi"na faɗa ina juyawa da gudu dan idanuwansa kamar
sunyi taruwan jini kuma ba kuka yake hakan dana ganine ya tsoratani na gudu,wani
abu dake akusa dashi mai kama da remort ya dannan sai ƙofar tai garam ta rufe,burki
naja ina riƙe da rigata,takusa naji na ƙanƙame jiki wuri ɗaya ina durƙusa
awurin,inajin tsaiwarsa akaina naji rugugugu a cikina ƙanƙame jikina nayi na ɗaga
hannu ina kare kaina kamar wadda za'a duka"wallahi Babban Yaya bansan kana nan Ya
Hasiya ce tace nazo na ɗaukar ma ta saƙo kuma banga komai to ai nama manta banda
hamaganci na wake aiken amarya ma kuma fa ba shiga nan ɗin ake bare nace da dagaske
ta ajiye abu a wurin",yanda nake zaro zance kuma ina kaina shine ya bashi dariya da
bazaiyi dariya sai ya yi murmishi"ni ne saƙon da zaki kaimata ai",sauke hannun nayi
ina miƙewa da ƙyar dan nagaji da zuƙunnon"haba Babban Yaya goɗoɗo dakai zatace
nakai ma ta kai","to tunda baki yadda ba kama hannuna ki kai ma ta ni kiji me zata
ce",kunsan ni da wawta saina kamo hannun nasa kuwa muka fito riiiii duk inda mukai
ana kallon mu ni kuwa ko ajikina tanacan tana rabawa yara lemo na hangota har qurin
muka kai ta bayanta ba ta ganmu ba saida nayi magana"Ya Hasiya ga saƙon",jiyowa
tayi na miƙa ma ta hannun Babban Yaya saida ta kama sannan na sakeshi,haɓa ta riƙe
da hannu ɗaya"na daina fargabar zaki iya zaman aure dama kina hankali haka Nana
nagode kuwa jeki abinki",da ɗi ne ya kamani yamin ram kamar nayi rawa ma kalli
Babban Yaya na ɗaga mai babban yatsana alamar jinjina shi kuma ya kaɗa min
kai,juyawa nayi ina dariya na tafi bayana yabi da kallo duk damuwar da yake ciki ya
nemeta ya rasa Ya Hasiya ya kalla"to sake ni mana ai kin turamin maganin damuwar
tawa ba komai yanzu Allah ya jiƙanta",hannunsa ta ƙanƙame"ameen ɗan uwana dan Allah
ka riƙe yarinyar amana karka bari tayi kuka kaga yanda duk ƙanƙantarta amma take
murna an ɗaura ma ta aure sai kaima da take tsoro karka ɗauka ita ta saka ayi
hakan",ɗan tsaiwarsa ya gyara"ita tace ai hakan mana kuma akayin kinsan kamar uwa
haka Alhaji Baffa yake jin maganarta",baki ta kama"kai Nana amma wannan yarinyar
akwai taɓargaza tasan aure kuwa ta manta karatunta ajinta fa huɗu kwata
kwata","tasan aure mana faɗa sukai da hajara akaina wai bata ta kwanta ma ta da
miji ba shine ta nuna ma ta itace bata isa ba tunda gashi ta aure ni kuma ta ma ta
alƙawarin saita kwana da ni yau yanda hakan kasance ne bansani ba kuma makaranta
doke zatai karatu ai bazan barta hakaba makomar ƴaƴana fa",kansa ta dungura"kuma
saura ka watsa ma ta ƙasa ido ƴaƴa sakoya a makaratarsu",bakinsa ya dafe"wane
Habib ai dole nayi biyayya amma ƴaƴana wallahi da uwa me ilimi zasu zauna",ya faɗa
yana dariya "bari naje wajensu Abdallah nasan suna jirana duk da babu matsalar
komai da zasu buƙata"sakinsa tayi"to shikenan ɗan uwa sai anjima",ya wuce yana
jinsa sayau kan ya kai inda ya musu masauki ya haɗu da Yasmin anan take zayyane
masa duk abinda su Aunty Hajara da ƙan uwansu sukai,kanta ya dafa"karki damu Sis
jeki aikin gabanki","ai Big Bro wajen Aunty Nana na fito zan gudu tun ɗazu an
hanani fitowa","to jeki tanacan gidan mu bata gidansu","to Big Bro thanks",ya wuce
yabi ta da kallo ko bata faɗa masa ba yasan za'ayi haka amma basu da hankali su ai
dama anan ya musu mazauni tuni nan ya wuce ko ajikinsa.
Ana sallar la'asar wadda zatai lucture ta ƙaraso dama an shirya wajen
ankonmu na atamfa duk muka saka sannan aka haɗa mu waje ɗaya akan dadduma sai kowa
kuma ya zauna,wa'azi mai shiga jiki tayi da nasiha amma duk tsoratawa da take akan
zaman aure baiko razana ni ba saima ƙwarin gwiwa da naji su kansu mamaki suke suna
hawaye amma sukaganni ƙiyau miyau sai suka alaƙanta hakan da bani da hankali ne,ana
kiran magaruba aka tashi a taron bayan raba kayan walima gaskiya hakan ma yafi
party daɗi kuma duk duk taurin kai na Ya Hadiza saida Ya Aisha da Ya Zainab suka
tasota agaba tazo ta shiga cikin mu.
Bayan antashi Ya Umme da Ya Sakina suka wuce gidansu ni kuma da Ya Dijama da
Ya Nabila muka shige gida Ya Hadiza ma suka wuce,da yake ba duka ne auten cikin
gidan ba su Ya Umme na komawa su Ya Sumayya suka shiga shirin miƙasu ɗakunan su
yayinda Ya Ashiru aka fara shirin kaimasa Ya Nabila sai Ya Haruna aka fara ƙoƙarin
miƙa masa Ya Dijama nasa gidan.
Duka hanani zuwa akai naita uban bori amma aka hana naje can kan gado na
kwanta ina fushi har naji gidan tsit tasowa nayi na tafi wurin Iyyo tana ganina ta
fara min waƙa ina dariya nan na kwanta,bayan awa biyu gidan ya ƙara kacamewa da
hayaniya alamar sun dawo kenan ban fitaba saida Aunty Mama ta biyoni ita da Ya
Hasiya dama Ya Usaina ta rigasu yo gaba,a nan Alhaji Baffa ya taresu da maganata
dariya Ya Hasiya tayi badan sai an zauna ba a ayau za'a miƙa Nana ɗakinta dan tana
komai a gidanta Abba ya siya ma ta komai kan Allah ya karɓi abinsa,mamaki kowa ya
shiga yi anan Ya Usaina ta shiga nuna musu komai a wayarta da ta ɗakko,Alhaji Baffa
ne yace"Allah yawa yaron nan rahama yasa albarka a abinda ya bari","ameen Alhaji
Baffa suka faɗa",yace"to yanzu abinda za'ayi gobe in Allah ya kaimu kuje ku gyara
ma ta komai dan zaman ɗakinta zatayi itama",da to suka bishi nan sukai cikin gida
Aunty Mama kuma ta ɗakko ni muka shiga tare can ƙuryar ɗaka tasani sannan ta
fita,tsaye na miƙe ina tunanin me zanyi Babban yazo yanzu kaina na ɗaga sama ina
tunani.
Tunda ya sallami abokansa bayan sallar isha ya shiga gidan dan ya wtsa ruwa
koya kori gajiyar da ta masa yawa,yana shiga ya fara karo da kaya kai ya ɗaga yaga
falon kaca kaca dukkan katan ɗakinsa ne ta farfasa na fasawa sannan suturarsa kaf
ta yanka masa ita gata nan a ƙasa,wani irin yanayi ne ya ziyarce shi na ɓacin rai
da danasanin aurenta da ya yi ayau duk abinda take baijin ya yi danasanin aurenta
sai yau,kan kujera ya ganta ta harɗe ƙafa tana riƙe da almakashi tana yanka masa
zanin gadon sa da niyar ya ma ta kaca kaca ya ɗaga ƙafarsa amma photon Abba dake
saitinsa ya taka masa burki ganin kamar yana masa murmushi,a wurin da yake ya tsaya
ya ɗakko wayarsa ya yi kira ba jimawa ya kashe ita kuwa tanajinsa yana magana amma
bataji me yace ba dan yau antuna asali da fitanci yay maganar,Aunty Mama ce ta
shigo"sako hijabinki ki biyoni",da hanzari na saka nabi bayanta Mama dake tsaye
tace"ku muje"nidai binsu nayi sai naga sunyi fannin Babban Yaya ban tankaba har
suka tura ƙofar suka shiga nima nabi bayansu.
Turus Mama dake gaba tayi ta fara salati"naga takaina ni Sadiya miye hakan
Hajara kalli yadda kika ɓatawa mijinki kaya dan rashin hankali kishi haukane",tana
inda take batai motsiba ni kuma ina ganin haka sai na matsa kusa dashi na saƙala
hannuna a nasa na kalleshi shima ni yake kallo murmushi nayi"ba komai Mama ai tayi
da mai arziƙi da ace matsiyaci kamar saura da sai ransa ya ɓaci amma wannan kayan
da tawa haka ai kanta ta ɓatawa lokaci shi kuma ta rage mai aiki dama in sutura ta
taru da yawa bakasata tsinema take kinga saita kwashi wannan takai bola sai muyi
sabon zubi ko Babban Yaya",murmushi ya yi yana danƙe hannuna sosai"hakane ta
wajena,tunda na fara magana tamin zuru tanaji aranta kamar ta daɓa min wuƙa kamar
walƙiya sai gata agaban mu Babban Yaya na tura baya na shiga gaba na kame ƙugu
turus tayi tana bina da kallo ɗan baya taja yau sai taji wannan yarinyar in bata
kasheta ba sai ita ta mutu wato ma nan shigar masa tayi kenan,juye juye ta shigayi
a wurin ta ɗakko wani yankakken glass tayo kaina shi kuwa Babban Yaya yau yaga abin
na manya ne sai yasa hannu a aljihu yana kallon ikon Allah,da sauri Aunty Mama ta
yunƙura zata tare na ɗaga ma ta hannu tana ƙarasowa ta kawo min yanka dashi na goce
ina tura Babban Yaya a ƙasa ta faɗi na kama hannun Babban Yaya muka shige ɗakinshi
ina ma ta gwalo,su Mama dariya ma abin ya basu suma suka fita ba wandda tace ma ta
cikanki,muna shiga ɗakin na kulle na zauna a ƙasa ina dariya ganin yanda tasa
jambaki ta ɓata bangon ɗakin da rubutu wai SAINA KASHE NANA shi kansa dariya abin
yabasa ya zauna gefen gado da shima akasa reza aka zazzanawa katifar,ƙofar ka shiga
bugu amma da yake ta gaske ce sai takeyi kamar ana bugawa da key,da hannu ya yafito
ni na miƙe naje na tsaya agabansa kusa dashi ya nuna min na maƙale kafaɗa
hannuwansa na kama na buɗa na juya na zauna a ciyarsa ina dariya,fari nayi da ido
cuna baki kamar gidan tsutsa"ai Babban Yaya ka rage min matsayi ka manta ada ma
anan nake zama bare yanzu da nasamu lasisi".

Baki ya kama yana karkato kai yana min kallon mamaki,kunyace ta kamani na
sunne kaina akafaɗarsa murmushi ya yi ya bubbugi kafaɗata"ɗago ki faɗamin lasisin
me ki ka samu",tashi nayi da gudu na koma bayansa na haye gadon ina dariya gyara
zamansa ya yi yana fuskantata"a ina zaki kwanta da ki ka kawo mu nan kallafa ko ina
glass ne",sakkowa nayi ina cire hijabin jikina"anan zamu kwana mana saidai ɗan
baƙin ciki ya mutu bari kaga"dama nasan inda ake aje tsintsiya a ɗakin dan haka ita
na ɗakko na dawo inda yake"Babban Yaya tayani mu ɗaga wannan katifar dan nasan
nauyi zatai",tashi ya shima ya zare rigar jikinsa dama ya cire babbar rigar tun
aɗakin Abba acan ma ya barta dan da ya barta anan data kassarashi inta yanka mai
rigar tarihinsa,a gefe ya ajeta ya zagaya ya ɗaga katifar shi ɗaya kifata ya yi
saman ya koma ƙasan sannan na fara tattaro komai ina sharewa duk da ransa yana ɓaci
in ya kalli abinda ta masa dan har funitures ɗin tasa zarto ne ko wuƙa ta kakkarce
su, amma duk da haka ganin yanda nake sharewa sai shima ya basar kawai ya shiga
ɗauke abinda tsintsiya bazata iya kawar wa ba da haka na share ko ina sannan naje
toilet na ɗakko towel ɗinsa na jiƙa nazo na goge duk inda ƙafa zata taka gudun
tsakin glass ɗin dire towel ɗin nayi"wash Babban Yaya wannan matar taka wallahi
gobe ka kaita Dawanau a buɗe ma ta file ƙato"na faɗa ina wara hannuwana,mumushi ya
yi ya gigiza kai,ya fito ni ya yi da hannu alamar zo da sauri naje"gani","baki
gajiba ne"ƙugu na dafe"tsabar gajiya ma bacci nakeji a tsaye","to jekiyi wanka kizo
ki kwanta"ido na fiddo na matsa baya"wanka a ina kenan anan ɗakin wallahi a
a","meyasa bazakiyi ba anan ɗakin",kaina na sunkuyar"kunyarka nakeji mana kawai ka
gane min jiki bayan matarka tace ba komai ajikin nawa tafini komai inka kalleni ma
amai zkaji",kiji sharri,,,matsowa ya yi"to bari na miki da kaina tunda nima na samu
lasisi ai kuma duk maganarta ki share yanzu fa kikace akaita Dawanau"aguje na juya
na shige toilet ɗin na rufo ƙofar lin yace zai min tsaf nasan halin Babban Yaya
wallahi saiya tuɓeni yamin ba kunyar da zaiji shi an faɗa masa duk haukar da nake
zan tuɓe rigane agabansa,anan ma ina cirewa amma gani nake kamar yana kallona ne da
ƙyar nayi wankan nasa under wares ɗina na ɗaura towel na yafa wani,na jima abakin
ƙofar sannan na buɗe na fito da sanɗa yana jikin gado a tsaye bansan tunanin me
yake ba nagadai yanata juya tafin hannunsa sannan ya juya bayan ta bayansa na tsaya
nace"Babban yaya na fito gashi ba ko ƙyalle aɗakin nan bare mutum yasa ga waccan
matar taka har yanzu bugun ƙofa take nace tayi bacci ko riga mai yagace na lallaɓa
na ɗakko nasa",murmushi ya yi ya durƙusa jikin locker da yake mukullin jiki ya
murɗa saigata ta zaro wata leda mai ƙyalli ya ɗakko ya miƙe tsaye yana fuskanta ta
ɓareta ya yi ya zazzago koma miye aciki saiga wata jar riga mai mugun kyau miƙo
min ya yi"zaki iya sawa dan ki faranta min",da sauri na saki towel ɗin kaina
gashina ya zubo janyewa nayi na karɓi rigar na koma toilet ɗin na saka innanillahi
dana kalli kaina a mudubi nima ban gane kaina ba bare wani ya gane ni ba wata
fargaba na fito daga toilet ɗin baki ya buɗe yana kallo na"tsaya anan"yace yana
ɗaga min hannu tsorata nayi amma sai naga ya ya ɗakko ipad ɗinsa ya shiga min photo
kamar ƴar fation ɗin nan na kayan bacci da ake liƙawa a jikin kwalin da ake sawa
aledar rigar sai ya gaji dayi sannan ya aje"zo nan"zuwa nayi ina sunkuyar dakai sai
murɗe yatsu nake hannauwan nawa ya kama ya ɗagosu bansan me zaiyi ba naji ya ɗauke
ni sama dariya nayi"kai Babban Yaya kamar ka ɗau kara","to ke kin zata nauyi
zaki",murmushi nayi ina kwantar da kaina akafaɗarsa"to ai Babban Yaya ance mace duk
sirantarta nauyi gareta","banda ke "ya faɗa yana murmushi ,a gadon ya ajiye ni
yajawo min filo ya ɗora kaina"ma za yi bacci tawan"shagwaɓe fuska nayi"kaifa ina
zaka","wanka zanyi mana yanzu zanzo na kwanta dake tawan",tashi nayi zaraf da gaske
Babban Yaya","sa wasa yarinya kawai ki shirya badai bazaki musu ba",babban yatsana
na ɗaga ina jinjina masa"ai kasanni ba musu a tsakanin mu","to kwanta ina zuwa"ya
juya ya sauka ya shige toilet yana mirmushi, ni kuma nai girif ta baya na kwanta
ina wulla ƙafa sama"woni woni Nana na zan kwana da Babban Yaya na"ya jima sannan ya
fito yana ɗaure da towel gadon ya kalla ya ganni nayi bunga tuni,murmushi ya yi ya
ƙarasa jikin locker ya buɗe ya ɗakko nasa kayan farare tas marasa nauyi yasaka ya
maida towel ɗin kusa dani ya zauna yana kallona"waida wannan yarinyar mai ta ɗauki
kwanciyar ne nafa fuskaci batasan komaiba kawai fitinace ita adole saita nuna tasan
komai"ya faɗa yana dariya ƙasa ƙasa dan wani nishaɗi yakeji yau ji yake kamar an
masa gafara wani irin yanayi yakeji a ransa da jikinsa kai gaba ɗaya duniyarsa ta
canja yau,addu'a ya tofa min sannan ya kwantar da kansa akan filon da nake hannu
biyu yasa ya ɗakko ni cak ya ɗora akansa gyara kwanciya nayi na tura kaina a
wuyansa dafe bayana ya yi yashafa kaina ya sumbaci goshina ya lumshe idonsa ba wani
tantama ko fargaba tuni bacci ya kwashe shi.
Aunty Hajara kuwa tafi awa uku tana bugawa amma ba'a buɗebe gashi duk windows
na ɗakin sunƙi buɗuwa safa da warwa ta shigayi tana hauka da zage zage amma ba
abokin yi da yake bacci ba ƙanin uwar kowa bane kuma shi duk duniya ba wanda
yakaishi ƙarfi in yazo ɗaukarka koda babanka kake yawo saiya sureka to itama hakan
tana shiga ɗakinta ta zauna bakin gadonta tana ɗure ɗuren ashar anan bacci ya
kwashe ta bata sa ni ba.
Mama suna komawa mamaki ya kashesu nan suka faɗama Baffa,shima yace abarta
zatayi ta gama ai dama wasu matan haka kishinsu yake.
Kiran sallar farko ya tashi Babban yaya yana salati sai ya jishi wasai
kamar ya kwana ya wuni yana baccin a hankali ya gyara min kwanciya shi kuma ya
shiga toilet saida ya watsa ruwa sannan ya fito kayansa na jiya ya mayar akan tiles
ya tayar da sallar nafila ni kuwa ina shan bacci na manta ma inda nake saida za'a
shiga sallah sannan ya tasheni ina ganinsa na fara zare ido ina masa kallon tuhuna
dan na manta meya faru jiya jijjigani ya yi dan ya fuskanci ina wannan kallon ya
nufa "tashi kiyo al'wala muyi sallah saiki cigaba da tunanin",banyi musu ba
sakkowa nayi na shiga nayo al'wala sannan na fito siket ɗina da hijabin nasaka nima
nabishi mukai sallar a wurin ya daɗe yana addu'a ya shafa ya juyo kenan ya ganni
nayi nisa a bacci ɗaukata ya yi ya ɗora agado sannan ya kishingiɗa a gefen juyowa
na zata filo ne na ɗaga kaina na ɗora acinyarsa murmushi ya yi ya gyarani sosai shi
kuma ya cigaba da tunaninsa a haka har rana ta fito kumatuna naji ana bubbugawa a
hankali na buɗe ido na sauke a kansa murmushi nayi"ina kwana Babban Yaya"wani daɗi
ne ya kamashi"lafiya lau tawan ya rigima da neman tsokana",dariya nayi ina tashi
zaune"ai Babban Yaya jiya naga drama saura ta yau kuma","to kafin afara tashi na
maidaki gida"sakkowa nayi na kama hannunsa muka fito yana taɓa murfin ƙofar na
ƙanƙame hannunsa,juyowa ya yi"matsoraciya ai in kina wurina haka to ko mutuwa
zatayi karar ta tunkaro ki danta ɗauke ki a gabana bare wata Hajara",dariya
nayi"wallahi Babban Yaya jiya da taga fuska a nan zaka kwana agabanta kamar
ɗanta",ɗan murmushi ya yi yana buɗewa muka fita abinda bamu sa ni ba tanacan tanata
bacci kamar mushe har muka isa gida shiru a bakin ƙofa ya sake ni ya juya"bazan iya
shiga naga Baffa ba yanzu inajin kunya na kwanta masa da ƴan sai anjima ke
jeki"hannu na ɗaga masa na shige inajin kunyar maganar da ya yi, sallama nayi suna
ganina suka fara dariya Ya Amina ce tace"a a amaryar rabon faɗa daga rabiya sai
mujiki shiru",baki na turo"ina ruwanku to naga mijina ne kome mukayi ba ruwanku"na
shige ɗaki su kuma suka shiga dariya ina zama Aunty Mama ta shigo"sannu matar
Habib",dariya nayi ina jin kunya"kai Aunty Mama","to mezance Nana"ta faɗa tana
ɗaukar jug akan frig ta fita a kujera na kwanta nan bacci ya ɗaukeni ban sani
ba,hayaniyace tayi yawa yasa na tashi ashe su Ya Usaina ke break fast dire ƙafata
nayi ina ƙare musu kallo"to ina nawa kuke ci ku kaɗai","karki mana masifa uwarmu
gashi"Ya Ruma ta faɗa tana miƙo min hijabin na miƙe na cire na juyo zan zauna naga
sunmin zuru nima binsu da kallo na shiga yi abinda suke kalla na kalla ashe rigar
jikina suke kallo,baki na taɓe"wai Ya Amina me ku ke kallo ne?","rigar jikiki mana
matar aure",Ya Fatima ta faɗa"au wannan rigar bari ma kuga kyau gareta" na sunkuya
na cire siket ɗin lahhhhhh suka saki salati"Nana miye hakan a haka kika tsaya
agaban Babban Yayan",ido na juya"sosaima duk wannan yanka kayan da matarsa ta yi to
nawa daren na gidanta ina da riga wadda bata san inda take ba bare ta haɗa da
ita",mamaki na ne ya kamasu na zuƙunna na ɗau abincina na wuce ɗaki a haka ina juya
musu ƙugu kallon juna suka shiga yi can Ya Asma'u ta kallesu tace"kishiyar Nana
zata Dawanau tabbas kowa ya shirya jin wannan labarin wataran",dariya suka kwashe
da ita nan sukaita hira akaina ina jinsu sufa basu san kar nake kallon kowaba.
A ranar suka kuma yawon gidan amare amma saida na bisu dan Ya Aziza ce ma ta
tambayomin amma nasan dan suna tare dasu Baffane ya amsa naje,duk inda mukaje saina
goga musu shaƙiyanci muke tafiya munje ko ina amma banda gidan Ya Hadiza wai a
daren bayan kaita suka hau jirgi zuwa Abuja mudai da Allah ya kiyaye muka bisu ana
azahar muka dawo nan suka wuce wai gidana suka fara jere dan kayan su suke jira
dama sosai suka haɗa ko ina ɗaki uku kowanne da kayansa kuma kala daban haka falon
akwai ƙarami amma kayansa sunfi na babban kyau komai na nan yellow ne ba sirki
hatta cafet da center cafet ga kayan kallo tv ƴar dai dai ta babban falonce kanta
me miya kamar mutum ke atsaye sai bayan sallar isha suka gama nan suka baɗeshi da
turaren wuta kaminsu kulle su fito.
Tun safen nan bai koma ba Alhaji Baffa ne ya hanashi yace wai ya batta tasha
iska dan in tana ganinsa abin ruruwa zaina yi da wannan yasa ya tare ɓangaren Abba
dama akwai kayansa nan tunda Abba ya nuna masa su bai saba sai yau,ana gama sallar
Isha ya shiga amma ko ina arufe mai gida da gidansa wani key ɗin ya ɗakko ya buɗe
ya shiga bata nan bai damu ba yasan wallahi da kanta zata dawo tarkacen wurin ya
kira akazo aka kwashe har na ɗakinsa sannan ya fice dan baiga zaman me zaiyi
ba,ganin ba kowa cikinsu Hajiya Fulera yasan itace jaban wannan tafiyar su Hajiya
Salma kawai yagani dama ko cikanku baya haɗasu dashi baya musu magana basa masa
inba rashin mutuncin ne ya motsaba su taresa ayi kacakaca dama baya ragawa uban
kowa a cikinsu.
Suna dawowa Alhaji Baffa ya kirasu nan suka shaida masa sun gama yace to su
kira masa shi a waya suka kiran shi yazo har Baffa saida ya kira dasu Ya Ashiru kai
dukkansu mamakin kiran kowa yake nan ya kallesu ya kalli Babban Yaya sannan
yace"Nuhu ku faɗawa ɗanku an gyarawa yarinyata inda zata zauna dashi amma bazan
bashi ba sai ya yo ma ta lefe na ƴar gata nan da shekara guda sannan sai na bashi
ita amma ko gobe ya kawo sain bashi ita hakanan ",ba wanda ya tsammaci maganarsa
alokacin amma sai ji sukai yace"habadai Alhaji shekara saikace bana buƙatar
ta",salati kowa saka ana juyawa ana kallonsa mirsisi ya yi ya ɗauke kansa,Alhaji
Baffa ne yace"to tunda kana buƙatar ta naga komai kafin jibi gatanan saika ɗau
abarka",tashi ya yi yace"ba matsala Ya Hasiya ina wurin Aunty Mama duk ku taho kai
Ashiru iyayen gulma kowa yasan nayi kona kira matanku nace musu kun tafi zance",da
sauri suka miƙe suna saida safenku da dariya aka bisu nan suka ɗunguma ciki dan
amsa kiran Babban Yaya.
A ɗakin Aunty Mama ya zauna yace ko wacce ta ɗakko wayarta ta rubuta masa
abinda zai saya da wanda zai sayawa Hajara kamar wani game haka kowacce ta ɗakko
wayarta ta shiga rubutu saida ko wacce ta gama bama ya Yaya Hasiya da Ya Mabaruka
su dama ƴan kasuwane suna saida atamfofi lesika da dadai nau'in kaya duk na mata
har lefe suke haɗawa in kana buƙata cewa ya yi ko wacce ta tura zai duba da safe
zai musu magana,haka sukai washegari tun tara ya shigo nan ya basu uban kuɗi yace
suje kasuwa shi zaije wani wuri yasiyo akwatin abin nasu kamar wasa sai gashi zuwa
yamma sun haɗa kaya kamar hauka dan komai ba na wasa aka siyowa kuma bai sayi kaya
masu arha ba masu tsada ya saya kuma gasu da yawa,su suna wannan Aunty Mama kuma
tana haɗamin kayan gyaran jiki ba shaba sunce bankai wannan matsayin ba jikina dai
ake gyarawa nan danan akwana biyun na ƙara canjawa sosai kuma tun daga ranar bai
kuma ganina koda kuwa ya shigo gidanne haka zai ƙaraci mitarsa ya fita har fushi ya
yi wai an hanashi ganina,kayan da ya warewa Hajara ya ɗauka yakai ɗakinta ya ajema
ma ta suma inka gani yakai lefe uku na wasu.
Alhaji Baffa da Baffan mu basu faɗawa kowa ba suka nufi gidan su Hajara da
yake uban shima uwar ta shanye akan yaran ita ya kira musu amma matar nan ta rufe
ido taci musu mutunci ba ƙaramin ɓaci ran Alhaji Baffa ya yi ba suka dawo goda suna
cikin faɗawa Iyyo abinda aka musu ya shigo a ƙofar ya tsaya gama jinsu sannan ya
shiga shiru sukai nan ya dubesu"ku cigaba da maganarku mana ai bani nace kuje ba
yanzu Baffa saika biyewa wannan tsohon kuje wancan gidan da kunbarsu ai wallahi
Hajara da kanta zata dawo","to maganin mu Habib sai dai mutanen basu da kirki
gaskiya","ba komai Baffa karku damu kuyi haƙuri",Alhaji Baffa dai ya yi shiru abin
bai masa daɗi ba.
Aunty Mama batare da tayi shawara da kowa ba dukkan kayan da ta jima tana
siya da wanda ta fita yau itama tasiyo ta kira Ya Mabaruka da Ya Ruma sukaita jidar
kayan suka kaiwa nan suka ɓare na ɓarewa suka saka a inda ya dace sannan kaf kayan
ma ta na adon gida dana buƙatar yau da gobe saida ta siyo sai abin ya zama su suna
ta lefe ita tana gyara gidan ƴarta,labulaye kamar zata buɗe kanti haka taje tayo
wasu waɗanda zasu dace da kayan gidan Aunty Mama dai kamar ba kuɗi take kashewa
ba,ƙaton showglass Mama tamin fal da turaren wuta dama Ya Aisha a washegari ta koma
gidanta dan haɗo kan turare dan haka da sassafe ta iso dukkan wanda ya kawo turare
dama akwai wani showglass ɗin nan ake zubawa,kafin yamma gidan ya haɗu zam na
amarya par gata abin ba magana Iyto da aka kaita ta gani saita fashe da kuka wai
itace yau aɗakin Allah mai baiwa.

Washegari kamar sabon biki haka gidan ya cika da mutane harda amaren maau
kwana biyu ana sallar magaruba Aunty Mama tazo ta tasa ni agaba nayo wanka da kanta
ta shirya ni ganin tana farin ciki sai nima na dake atamfa mai kyau da hijabi ta
bani na saka bayan underwears komai sabo da yake Alhaji Baffa ya yi kashedin yimin
faɗa ba wanda yamin faɗa ƴan uwana da iyayena ne suka tattarani zuwa gidana kamar
yanda naji suna faɗa masha Allah kowa ke faɗa saida duk suka ƙara gyara ko ina
sannan auka fita suna min dariya wai saga ayadda za'ayi wannan zaman ina cikin
gida,biyosu nayi ina cewa sai nayi wata ban shiga gidan ba ma,su dai dare suke ni
kuwa ko ajina wallahi basu jima da fita ba saiga su Ya Ruma da Ya Fatima sun kawo
kayan akwatinan naga kayan da yawa naita murna a ɗayan ɗakin suka aje sannan Ya
Ruma ta kalleni"gobe da safe ki fidda duk wanda kike so a ɗinka miki saiki kirani
da wayar Babban Yaya zansa azo aɗauka amiki ɗinkuma saka maigida tsalle",tsallen
kuwa nima nayi nace" to",sannan suma suka tafi,ɗakunan na fara shiga ina kalla daɗi
kamar ya kasheni wai nan duk nawa wayyo dana kitchen kamar nayi ihu dan daɗi ɗayan
ɗakin danaga yasha ado ga kayan kantama kantama komai ma ɗakin special ne ka toilet
ƙato mai kyau saina fito na kullo shi"wannan ɗakin Babban Yaya ne tunda yafi
kowanne kyau da haɗuwa juyawa nayi na kama ƙugu"wannan ɗakin ana zamuna raƙashewa
kallo da wasa mu biyu abinmu"nayi wani tsalle ina harba ƙafa falon na dawo na zauna
ina kallon ƙofa kozanga shigowarsa.
😀😀😀😀

UMMU SADDI'Q🌹🌹🌹🌹
🌈🌈🌈
🌈🌈
🌈

Babban Yaya Free ne amma me so ya biyo ni Pc in sa a group don shagalin Nana


na buƙatar comments.
08146711395

BABAN YAYA

22

Na jima banji motsinsa ba na miƙe a kujerar na kwanta ba jimawa nayi


bacci,'kunjifa wata amarya to siyan bakin fa da naketa buri',a hankali ya turo
ƙofar ya shigo da sallama tura ƙofar ya yi ta rufe ya gama shigowa kan kujera ya
hangeni ina bacci dariya ya yi"tofa ita wannan amaryar haka akeyi tun angon baizoba
kinyi bacci",ladar hannunsa ya ajiye ya zauna abakin kujerar,yana zama na buɗe ido
kamar wadda aka tasa haɗa ido mukai na turo baki ina kauda kai,murmushi ya yi"me
nayi kuma madam Babban Yaya",agogo na nuna masa ya kalla gyaɗa kai"sorry amaryas
naje siya miki kayan tarbar amarya ne ko hannu siƙau ki ke so nazo",kai na kaɗa"ai
da bazan kulaka ba ma","to kingani taso ki sakko ƙasa kici abinci in baki tsarabar
shigowa gidana saboda kin faranta min raina kinyi abinsa na jima ina buƙata",da
sauri na sakko gabansa na zauna shima ya sakko ledojin ya buɗe,wayyo ana kawo wa
amarya kaza ni kilishi da ice cream aka kawo min ci nayi inata dariyar abin bayan
mun gama nature kayan can gefe na matsa na haye ciyarsa nai daram hannuwana ya riƙe
duka biyun yana kallon fuskata"kina sona",kai na girgiza alamar a a,murmushi ya
yi"meyasa?"baki na turo"ai na raian wannan tambayar ne Babban Yaya kaifa ajinina ka
ke mezaisa kuma saina soka ko na ƙaunaceka bayan kaine ni",hannayesa ya buɗe ya
rungumeni"to dan Allah komai faru karki bar gidan ko kice zaki yaji gwara kikai
ƙarata amin faɗa",dariya nayi na ɗago"ai bazankai ƙararka ba ma sai dai mu
daku","da kyau manyan mata to zan gani kuwa amma yanzu rufe idonki",rufewa nayi ina
dariya hannuwana ya zirawa awarwaro sannan zobe sarƙar wuyana ya cire yasa min wata
sannan ya da ɗankunne"buɗe to"buɗewa nayi zaraf na miƙe na fara juyi ina murna
sannan nai sufa na faɗa kansa"nagode Babban Yaya na rasa ma me zance",fuskata ya
shafa na rufe ido ina kwantar da kaina a ƙirjinsa mayar da hannayensa ya yi ya
rungume ni sosai da wannan na kuma bacci shi wallahi da yaji shiru ma bai zata nayi
bacci ba dani ya miƙe tsayen zuwa ɗaki akai sa'a wancan na ƙarshen ya buɗe yanda
akaiwa ɗakin ya masa kwantar dani ya yi yaja ya tsaya yana kallona shi mamaki ma
abin ke basa shekararsa talatin da shida shine yake auren ƴar shekara sha shida dan
batakai sha bakwai,toilet ya wuce ya yo wanka sannan yazo ya shirya tsaf yasha
turaransa mai sanyin ƙamshi,saida ya hau gadon sannan ya kalleni kayan sunmin
nauyi tashi ya yi ya fara cire min sarƙara sannan hijabin dogon wuyana ya shiga bi
da kallo yana murmushi Allah ya gani yana son Nana,ɗankwalin ya cire gashin ya zubo
mai a hannu murzashi ya yi ya kai fuskarsa kai yana shaƙar ƙamshin da yake ɗagowa
ya yi ya kifo ni ƙirjinsa ya zage zif ɗin farar half best ce kawai a jikina ba
ruwansa haka ya zare rigar yana ɗagoni wani irin bugawa ƙirjinsa ya yi ganin yanda
breast ɗina sukai dam ko a mafarki bai ɗauka zan zama hakaba ganin abin zai ɗaga
mai hankali yasa ya kwantar dani ya zare siket ɗin sai sai ƙarami fari tas mara
kauri cinyoyina ya shiga bi da kallo suna ta ƙyalli hannu yakai ya ɗora akai ya
lumshe ido zuciyarsa na bugu da ƙarfi,janye hannunsa ya yi ya kwashe kayan yasa
agefe sannan ya kwanta a kusa dani sanadin ya yake hukuncin ni zan zama aminyar
jikinsa yasa ya janyoni ya ɗorani akansa na ƙara bajewa kuwa kamar ina akatifa
tunda muka fara bacci ranar saida ana shiga sallah sannan ya buɗe ido a sannu ya
sauke su akaina dagani sai pant ya Allahu komai ya kama gabansa yana ahaka ya saki
murmushi yana ƙara rungume ni shi bai taɓasu ba gashi su sun taɓashi ganin zai
makara ya kwantar dani yana mayar min da best ɗita amma banda siket ɗin sannan ya
ahiga toilet ya yo alwala ya fito kayansa na jiya ya mayar ya fita agidan zuwa
masallaci,bai daɗe da fitaba na tashi ina miƙa da hamma ɗakin na shiga bi da kallo
sai kuma nayi dariya"ashefa ɗakina ne wai kai Allah yawa Albarka ya jiƙansa wai
wannan ɗakin duk nawa",ina sakkowa a gadon naji ni empty kallon jikina nayi na
kwashe da dariya"kai Babban Yaya kalli yanda yamin ya gama ganemin jiki ko da yake
ai ahine mai ni kullum ma ahaka zan na kwana ko nasa riga saina cire ai Aunty Mama
tace na lura da abibda yafiso ajikina infi bawa wannan wurin kulawa zanfi
burgeshi",baki na cije nayi shiru kawai na kaɗa kai ni nasan me nake saƙawa kawai,
hunnmmmn na shige toilet nima nai abinda zan fito na hau sallah,ban jima da idarwa
ba naji ya shigo a wurin nai saurin kwanciya ina munsharin ƙarya koda ya shigo
kallona kawai ya yi ya taɓe baki"in zaki tashi ki tashi yarinya wannan minsharin ma
bai miki kyauba",buɗe idona nayi ina dariya"Darling Yaya ina kwana",ƙarasaowa ya yi
inda nake ya duka"haka ake gaida miji",da sauri na tashi zaune ina dafa ƙafarsa"ya
akeyi to koya min",tashi ya yi tsaye yaja da baya ya zauna sannan ya miƙo min
hannu,kamawa nayi na tashi zuwa inda yake a ciyarsa ya ɗora ni yamin kiss a kumatu
ya rungumeni"haka kawai nake so ko baki magana ba ya wadatar",tashi nayi nace to
bari ayi sample kwatantawa nayi amma ni nawa kiss ɗin harda baki saida
nawa,murmuahi ya yi"naji daɗi da yadda ki ka saki da jiki da ni",shagwaɓe fuska
nayi"to me ka ke tunani da nifa ko Babban Yaya wallahi zan iya rayuwa dakai ɗaya ba
kowa kuma bazanje gun kowa ba",nai fari da ido,wani da ɗi ne ya kamashi baisan
sanda na rungumeni ba yana min kiss a fuska,"tashi ki kwanta naga bacci ki ke
ji",saurin tashi nayi daga jikinsa"bacci kuma wanka zanyi wallahi nasha kwalliya so
ka ke sai su Yayus ɗin can sunzo sun tarar dani kamar kurar wasa,dariya yasaka"to
afuwa tashi kiyi wankan ki ni kwanciya zanyi",tashi nayi daga jikinsa naja hannunsa
ya miƙe muka zagaya ɗayan ɓarin in kika ganni saiki ɗauka ɗana zan kwanta a hankali
na turashi ya zauna sannan na kama kafaɗarsa na kwantar dashi komai nake samin ido
yay yana bina da kallo bargon naja masa na fara jijjiga masa kafaɗa"yi baccin ka
Babban Yaya na Nana",hannuwana ya kama yamin kiss yana murmushi harga Allah yaji
daɗin abinda na masa,shafa fuskarsa nayi idanuwansa suka rufe cikin gashin kansa na
tura ya tsuna ina murzawa mirmushi kawai ya yi saida naga ya saki fuskarsa sannan
na tashi da sanɗa na shige toilet.
kamar wata uwar mata haka na fesa wanka na ɗauro towel ban bari na jiƙa
gashina ba dan ya ɗau gyrar sosai a hankali na fito na fice a ɗakin zuwa ɗayan inda
aka saka min kayana kwalliya nayi sosai nasa riga doguwa ta atamfa tamin ɗas sannan
na karkata ɗaurin ɗankwali na baje gashin ya sauka har fin tsakiyar bayana sannan
fesa turare gyara kayan nayi na fito da towel ɗin na mayar wancan toilet ɗin
sarƙata ta jiya na kwaso na saka na dawo falo ina zama naji ana ƙwanƙwasawa tashi
nayi na buɗe su Ya Hasiya ne dariya nayi" ku da sassafen nan",kallon juna sukai
suka kwashe da dariya"sannu amarya to mu tafiya zamuyi shine mukazo mugan idon
amaryar tamu",dariya nayi"idona kuma to gashi nan ral ku shigo",shigowa sukai nan
suka aje kwanukan hannunsu suna bina da kallo Ya Fatima ce ta janyo hannuna na
zauna akusa da ita"ke wannan sarƙar fa",dariya nayi"Babban Yaya ne yace na faranta
masa shine ya bani wai kyauta",baki suka kama suna zaro ido dan su sun fahimci me
wannan maganar take nufi amma ni ban fahimta shiya na faɗa musu,Ya Mabaruka ce
tace"to adage da faranta masa ba dare ba rana mu ai haka muke so yana ina
ne","bacci fa yake",ƙara ƙunshe dariya sukai nan suka tasani da magana waccan tace
kaza waccan tace kaza kuma duk na kwashe wallahi sun ɗan daɗe sannan suka tafi sai
kuma an kwana biyu,wayyo ni ƙuruciya ko irin ɗan jin badaɗin mana inji a a garau
nake jina ba wata damuwa,bayan na rufe ƙofar naje na buɗe abincin na gani banci ba
na rufe na koma zauna ba jimawa na koma ɗakin ina shiga yana buɗe ido da gudu naje
na haye kansa"Babban Yaya taso kaji wata magana amma kayi wanka tukun","kai ya ɗaga
min ya miƙe ya shiga toilet mamaki ne ya kamashi ganin ruwan wanka kuma daya taɓa
ruwan ya dace da dai dai da lokacin,yana shigewa na gyara inda ya bari sannan na
fita zuwa falo koda ya fito babu kayansa a ɗakin wayarsa ya ɗauka ya kira ba jimawa
ya je ya fito falon,ina ganinsa na gwalo ido sannan na rufe"wayyo Babban Yaya kasa
riga kalli jikinka",ɗan murmushi ya yi ya ƙaraso inda nake ban sa ni ba saiji nayi
ya zauna a kusa dani kan nayi wani motsi ya ɗauke cac ya ɗora akan cinyarsa,ƙara
damƙe idon nayi"buɗe idon nan ki kalleni ni ba mijinki bane me ki ke tsoro
ajikina",a hankali na buɗe ina kallonsa sai kuma na kwashe da dariya"wallahi Babban
Yaya jikinka yana kyau kalli gshi kwance ga laushi fatarka",hannuwana ya kama ya
ɗora ajikinsa "taɓani kanki tsaye ai kin samu lasisi konkin manta ne tawajena",ba
ɗar ko ɗaya na kwanta a jikinsa lumshe ido ya yi yana rungumeni sosai Allah ne
kaɗai yasan yanda yake ji in na taɓa jikinsa shi ko ahaka za'a basshi da matarsa
zai iya zama da ita batare da komai ya shiga ya tsakaninsu ba hakan ma ya masa to"
{Kuji sharri in ta cika tayi fam kuma fa ka lallaɓo fa}Hhhhhhh.
ƙwanƙwasa ƙofar akai nabtashi shima ya tashi"karɓo min kaya ne",buɗewa naje
nayi ashe Ya Aziza ce ta ƙara dawowa bata shigoba ta bani ta juya,har ɗakin na kai
masa ina nishi a gado na dire su na"wash Babban Yaya wannan kayan fa kamar abasu
tuwo",ɗaya ya za ra kayan"gasu nan mana tambayesu",fita nayi da gudu ina dariya
ganin zaisa kaya agabana,ina nan ina wukka ƙafa ya fito ya yi kyau cikin ƙanun
kayan da yasa,ta sowa nayi da gudu na ɗaneshi"kayi kyau sosai Babban Yaya",riƙeni
ya yi da kyau"aikin fini kyau Sweet wife",kiss na masa a kumatu "ga abinci can an
kawo muje muci",dani ahannunsa ya ƙarasa wurin ya ɗorani akan kujerar dinin ɗin
sannan ya zauna shima,caraf na tashi na haye table ɗin na zauna"ai kaine zaka zauna
anan ni anan zan zauna a baki zan baka abincin yau",murmushi ya yi yana nuna min
kwanukan nan na buɗe su"lahhh bari na ɗakko flat da cups",tareni ya yi"yi zamanki
ina zuwa ,da kansa yaje ya kawo sannan na zuba da kaian nake bashi abaki shima yana
bani har muka gama sannan ya ɗaukeni zuwa kitchen muka wanke hannu a falo yazo ya
zauna ƙasa ya kunna tv kan cinyarsa na zuna amma hakan baimin ba tashi nayi na
kwaye rigar na cireta na haye kansa nai daram bina ya shiga yi da kallo ganin ko
ajikina ma abinda nayi bayan daga ni sai half best da ɗan gajeren wando shima ita
rigar tazo dashi,a bayana ya ɗora hannunsa ya kwanto dani kan hannunsa yana kallon
fuskata"kina zama da ni a haka kullum zanfi jindali in ina kallon zahirin mata
ta",alamar kiss na masa"an gama Darling Yaya suma inkace na cire saina cire",dariya
ya yi"ki rufamin asiri ba yanzuba in kina nuna minsu a haka ai za'a sami matsala
kisani sharia da Alhaji Baffa",duk da ban gane me yake nufi saina yi
dariya,"bazakuyi sharia ba ai ni takace yanzu zakaga komai duk sanda kaso",dariya
sosai yake yasan wannan maganar tawa ƙuruciya ce zalla"yi bacci ƴan matan Babban
Yaya"ya faɗa yana ƙara rungumeni biye sa nayi kuwa ba jimawa nayi baccin,shi kuma
ya jingina kansa da kujerar yana murmushi ko damuwa da Hajara ya hana zuciyarsa
tayi ɓaci ransa ma yake in ya tuna ɓarnan da ta masa da tabar kayannan dako sadaka
ya yi dasu ai yasan ladansa mai tarin yawa ne kan capet ɗin kwanta duk da haka ina
maƙale dashi.

😄😄😄😄

UMMU SADDI'Q CE 🌹🌹🌹🌹🌈🌈🌈


🌈🌈
🌈

Babban Yaya Free ne amma me so ya biyo ni Pc in sa a group don shagalin Nana


na buƙatar comments.
08146711395
PAGE 23

*GIDAN SU HAJARA*
Duk suna falon gidan kamar yadda Abbansu yace suzo magana dai ɗayace anwa ƴarsa
kishiya suna tsaka da magana saiga Aunty ta shigo ko kallo basu isheta ba ta wuce
sama ba jimawa ta fito a kansu tazo ta tsaya"wallahi Hajara ke kidahuma ce ta
ƙarshe ita innar mu kishiyoyi uku gareta a gidanta na farko ana biyu ma haka shine
ke take zugaki ko to wallahi ki zauna ƴar ƙaramar yarinya ta nuna miki bariki,kaiii
ni wallahi ma haushi kuke dukkanku wai Abba harda kai nan kishi ka ke tayata wai to
wallahi kiji ni da kyau mu nan da kike gani duk bamu da aure kuma harda shawarar
Inna Fulera da nuke ɗauka shine duk auren mu ya mutu to kema ki baje da kyau kinga
in ya gano ɗanɗanon ƴar shila sai yazo ya sallameki kinga mun zama mu biyar kenan
ke Umma ko kunya bakyaji ace ƴaƴanki kaf zawarawa amma me auren kin tsaya kina
kallonta zatawa kanta sagegeduwa da taimakon wannan ƙanwar uban namu",tana kaiwa
nan ta juya sam kowa yasanta wurin faɗar gaskiya amma bata da mutunci ko ɗaya shi
yasa Hajiya Fulera tayi gum dan tasan tanada lefi kuma ita dama haka take mugunta
ce aikinta kuma ita tafi iyawa,kallon kallo aka shigayi nan Umman ta miƙe"nima ina
bayan Ummita inkinga zaki koma bisimilla mutanen nan har nan sukazo amma muka
wulaƙanta su wallahi nayi nadama"ta wuce tana ƙwafa nan ka barsu masu hali ɗaya
kenan dama,Abban ne yace"karki wani koma Hajara me wannan tatsitsiyar yarinyar zata
masa dole kiga yazo neman ki da ƙafarshi",duk sauran ma haka suka goyi baya kuma da
yake doɗaɗɗiyar kwanya gareta saita aminta da batunsu ta biye musu ta zauna
kuwa,saboda tsabar bata wayo tana kallo Hajiya Fulera tabar gidan ta nufi nata amma
batai tunanin komai ba tabi maganarsu.
Tunda Hajiya Fulera ta shigo gidan da motar ta take bin gidan da kallo ba
wanda ya kulata ta wuce ɓangarenta zuciyarta fal da tunanin yanda zata jawo Nana
jikinta dan ta lura Hajara ba abinda zata ma ta'ni kuwa nace ganganci',a ranar kasa
sukuni tayi tana ta tunani dan tsoron terere take tasan tsaf inta tareta da wata
magana zata ma ta kwakwazo amma intasan wata batasan wata ba tasan dawa zata haɗata
da kanta zata shigo jikinta yanda ba wanda zai zargi wani abu.
Bayan kwana biyu
Kowa fa mamaki ya kamashi gani na shiru banzoba kuma shima da yahe ba suga alamar
akwai matsalaba hakan yawa kowa daɗi bama ya su Mama Aunty Mama kuwa ai kullum ita
ke kawo mana abinci ko gajiya basa yi yau dai nace a faɗa musu kar aƙara kawowa zan
dafa dariya sosai Babban Yaya dake zaune a bayana ya shiga yi ganin yanda na fiƙe
ina magana kamar wata uwar mata,a gabansa na tsaya ina dira ƙafa"ni kadaina min
dariya fa",bai daina ba ya kamo hannuna na zauna akan ƙafarsa fuskata ya tallabo
yana kallon cikin idona"tsaya madam Babban Yaya wane abinci kika iya da zakice
adaina kawowa",zumbur na miƙe"me ka ɗaukeni ne Babban Yaya amma na fasa magana zaka
gani a aikace nida ake turani kitchen tun inada shekara shida",ƙara riƙoni ya
yi"nasan hakan ai ba wannan ne iya abinci ba","naji ai muje asiyo komai na
buƙata","an gama ta wajena ai ko tuwan ɓula zakina min zanci har ki koyi
wani",dariya na kwashe da ita ina nuna shi,bin fuskata kawai yake da kallo yana
murmushi jana ya yi na kwanta ajikinsa shima ya kwanta a kujera a hankali ya fara
magana yana murza gashin kaina "tawa tafi ta kowa gata ƴar ƙarama ina sonki
Nana",kaina na ɗago ina murmushi naja kumatunsa"nima nawa yafi nakowa duk da ya
girmeni nesa ba kusa ba nima ina sonka Babban Yaya ka tashi ka goyani",murmushi ya
yi yana tashi tsaye dani a jikinsa"ba goyaki zanyi ba zo muje ɗaki kiga wani
abu",kai na ɗaga muka shiga ɗakin akan sofa ya ajeni ya sunkuya ya janyo wata locer
leda ya ciro aciki ya miƙomin "saka wannan rigar naga",da sauri na karɓa na buɗe
ledar tsalle nayi na diro na juya mai bayana ya zuge min zif ɗin rigarna juyo
gabansa ba ruwana na cire rigar bina da kallo ya shiga yi rigar na zura da kansa ya
ɗaure min igiyoyin sannan na juyo na wara mai hannunwana"nayi kyau"baiyi maganaba
ya kamo hannuna muka fito falo ya zauna yana jana na faɗa jikinsa hannuwansa yasa
awuyana yana murza kunnena"kinyi jyau sosai kiban tukwaici na",murmushi nayi na
wulƙita ido sukai harr"me ka ke so na maka faɗi zan maka shi ba shakka",bakinsa ya
muna"yimin kiss na gaske bana wasaba",ɗan murmushi nayi"na ƙara sama namai kiss
abaki",riƙo fuskata ya yi"ba hakaba kinga haka",ya ɗora bakinsa anawa yana min kiss
nasan dai sunan sa amma bansan haka akeyi ba wani irin salon kiss yakema bakina sai
naji abin ba dama daɗi wallahi ƙara shigewa jikinsa nayi janyr bakinsa ya yi a nawa
yana kallona"ya dai matar Babban Yaya",yatsana na zagaya akunne"daɗi wallahi a
ƙara"dariyace ta kamashi ganin yanda nake da ido kana gani kasan a auren bansan
komai kawai iyayi ne,ƙara ɗora bakinshi ya yi anawa bazato mukaji tsawa akanmu ni
kaɗaice na saurin ɗagowa nai duba naga waye Aunty Hajara dariya ce ta kamani dana
kalleta sama da ƙasa gadaita fess amma afirgice take kana ganinta,Babban Yaya kuwa
ko motsi baiba,kaina tayo zata danƙeni nai ma za na bar wurin na koma bayan Babban
Yaya ina murmushi hannuwan na saƙale a wuyansa"wayyo Honey ka ganta ko"duka ta
kawomin"shegiya mai kama da aljanu ƴar mitsitsiya dake wai kisan a shafa miki jiki
harma faɗi kike da daɗi aƙara miki wallahi nayi kuskure dana bar miki mijina wai
Honey ko ko ubanme kika sani da kike ce masa Honey",ta ƙara she bakinta na kumfa,in
kujerar nan tayi motsi to wallahi Babban Yaya yasan da ita a wurin ganin ya yi
burus saina nace"Honey mu koma ɗaki kamin kaga anan akwai mutane kuma kar aga
sirrin mu ana yama ɗiɗi damu",baice uffan ba ya miƙe ya juyo ya ɗaukeni cak ya nufi
ƙofar ɗaki,wani irin harzuƙa tayi tasha gabansa"kai yanzu bakaji kunya ba kalli ƴar
wannan abin ka ke lalubewa miye abin taɓawa ajikinta da bani da shi miye tafini ka
faɗamin",ta faɗa tana kama ƙugu sai jijjiga jiki take,"ban hanya"kawai ya faɗa
cikin wani kalar yanayi yana zuba ma ta wani kallo da idanuwansa da suka sauya
launi,kwarjini ya ma ta sosai sai matsa masa ya tura ƙofar ya shiga,da gudu ta fita
aɗakin tana kuka,dira nayi daga jikinsa na rungumeshi kaina ya shafa"ya dai
Baby",ɗagowa nayi nace"kai sama dani please in maka kiss kaga bazan kaiba a
haka",caraf ya ɗagoni na masa kiss a baki na langwaɓe kai"kasan me Babban Yaya
Aunty Hajara na sonka sosai nice bata so kawai kaje tunda ta dawo da
kanta",murmushi ya yi kawai ya hale bakin mu yashiga nin ta ɗazu kamar kar adaina
naji dan har tafin ƙafata nakejin kamar ana sosamin ban ƙi ba saida ya zare bakinsa
dan kansa sannan ya direni"bari nayi wanka ko tawan",tsalle nayi"ƙwarraima kuwa
Babban Yaya",ya shige toilet yana ɗago min hannu,falo na fito ba ruwana da wani wai
ta dawo na cigaba da sabgata.
Tana shiga ɓangarenta taga an kwashe duk ɓarnar da tayi ɗakinta ta shiga
sannan ta fito ta shiga nasa nan kuma ba komai ko furniture duk yasa an fita dasu
tsaki tayi ta fito"badai yarinyar nan dani tace zatai kishi ba to saina salwantar
ma ta da rayuwa dan ubanta ai nasan dame na dawo".
Ina kunna tv ya fito yasha wanka ya hale cikin suit blue da jar Tshirt a
ciki agogo mai jar fata da baƙin rufaffen takalmi baki na dafe sai kuma na yarfe
hannu na ƙanƙame jiki"Babban Yaya ka haɗu over wayyo ni Nana",abinda nayi ne yasa
shi dariya ya matso kusa dani"kice ni ɗin na musamman ne","sosai ma kuwa kamar na
haɗiyeka tabbas"kai kawai ya girgaza ya sunkuyo da kansa saitin kunnena"nine nakeji
kamar na haɗiyeki Sweet heart",kunya ce takamani na faɗa jikinsa ya rungumeni,agogo
ya kalla "bari naje na dawo",ɗagowa nayi"byee a dawo lafiya",na faɗa ina ɗaga mai
hannu,rakoshi nayi har bakin ƙofar ya fito ina ɗaga mai hannu a bazata na buɗe
murya nace"kai Babban Yaya zaka faɗi wannan saurin duk na zuwa wurin uwargida ne
dama nasan ka gaji sao ka ke ta dawo",wani irin burki yaja amma kamin ya juyo na
maisa ƙofar na rufe na jingina da ita ina dariya,dawowa ya yi ya buga naƙi buɗewa
ya daɗe tsaye ya rasa ma abinyi maganatace kawai ke mai yawo rai wannan yana nufin
kishine fa tsabarsa da ƙyar ya wuce amma ko kallon ɓangaren Hajara bai kalla ba ya
fito yabar gidan.
Jikin ƙofar na bari na shige ɗaki na ƙara ɗame gado dama na ƙware awannan
fannin daga nan da awo falo na kunna kallo daga waccan tasha sai waccan nifa waya
bata dameni ba ƴan ajinmu har dariya suke min aka rashin waya amma wallahi ban damu
ba ina nan haka nai bacci.

A kan idon Hajara yabar gidan jikin window ta bari tana murmushi kanta ta
nuna"ni Hajara wai namiji yakewa wulaƙanci dun ina basirata ne da duk masifata wai
ya akai na canja ne amma bakomai zan gwada masa bariki yau kuwa",Hijabi tasa ta
lakaci rob ta fito ta nufi gidanmu Baffa da Alhaji Baffa na zaune ta shigo kanta
ƙasa duk ta goga rob a fuska tananzuwa ta zube awajen su tana sakin kuka
rarrashinta suka fara nan ta shiga basu haƙuri wallahi ba laifinta bane,suma da
ɗaurewa ƙarya wani wuri sai sukace ba komai ta shiga ciki su sun zatafa zuwanta
kenan,tana shiga ma haka tawa su Mama suma na suka shiga tausaya ma ta,amma kallo
ɗaya Aunty Mama ta ma ta ta gane wallahi ƙarya take amma sai tai murmushi,Alhaji
Baffa ne yasa aka kira masa shi a waya yace yazo da ni yana neman mu,yana kashe
wayar sai ya yi murmushi afili yace" Hajara kenan duk son da waɗannan mutanen zasu
miki baran Nana ne amma bari muga da wacce kika zo kuma",takardun da yaje sa hannu
su ya gama yaba PA ɗin Abba da ya zama nasa sannan ya shigo mota ya dawo gida
danshi ɗaya yake yawo inka guard to zai bar garin ne yace kana garin haihuwar miye
na yawo da matakan tsaro madadin kaima kaima kabada ranka akan ɗan ƙasar ka.

Ummu Saddiq ce🌹🌹🌹


🌈🌈🌈
🌈🌈
🌈

Babban Yaya Free ne amma me so ya biyo ni Pc in sa a group don shagalin Nana


na buƙatar comments.
08146711395

24

Ina ganin anyi azahar na shiga kitchen na duba me nake dashi murna yi ashema
akwai abin dafawa harada kayan yama fara lallcewa dan ma mai kyau ne sosai kuma
akan ƙasa aka zuba doya na dafa na daketa na fara haɗa miya komai tsarin gidanmu da
naga anayi shi nake bi alaiyahu ne kawai ba bu Aunty Mama ta tanadar min komai na
girki sarrafata nayi tayi wani irin kyau ta duddunƙule ba sai ma ansa ma ta
alaiyahu bakifin da nasa ya yi ɓaro ɓaro a manya kula masu na zuba sannan na yanka
kankana na markaɗa ta na samu madara Nana anga banza ruwan ɗumi nasa ma ta sannan
na juye a kankanar na ƙara markaɗawa na juye a kan rariya na tace sannan nasa ƙaton
jug na tsafashi a frig na gyara wajen agurguje na baro kitchen ɗin kai girki
wuya,wajejan huɗu nayo wanka na shiraya da doguwar riga fara tas mara nauyi amma
har asa take saboda iskanci ko half best ɗin ban saba yau sai sukai tsaye dama dame
auka wuce na ƙirgen dangi,'bafa in jini ba inji Aunty Hajara"ɗan boom short nasaka
na shafa humra kala kala sallah nayi na dawo falo na naɗe ƙafa ko hijabin ban cire
ba.
Ƙwanƙwasawa akai na taso da sauri ina dariya na buɗe tare da komawa bayan
ƙofar shigowa ya yi kamar zai wuce wuf ya juyo inda nake"na kamaki"dariya na
ƙyalƙyale da ita na faɗa jikinsa ba ƙaramin da ɗi yajiba sai yanzu ya gane wato
ɗazu iskance yasa na masa ba wani kishi,sama ya ɗagani"ƙamshin mata ta yafi nakowa
daɗi",wani farin ciki ne ya kamani na ƙanƙame kansa a cikina,dire ni ya yi"kakan ki
rigimammen cen yace muje da sauri yana neman mu",hannunsa na kama"muje to tare muka
fito na kulle sannan muaka nufo gida ina riƙe da Hannun a bazata saiga Hajiya Salma
da Safiyya wani kallo suka mana amma dukkansu shi suke kallo kamar wasu ƙananan
yara da yake aduniya shima ƙwallo ne ko kallonsu baiba yaja hannuna muka wuce
su,wani kallon juna sukai suka tafa a kacigaba da tafiya ana yanga.
Tun daga baki ƙofar na ƙwace hannuna na shiga da gudu akan ƙafar Mama na dira
na rungumeta wallahi ban lura da kowa afalon ba,rungumeni Mama tayi taji daɗin
yanda ta ganni ga ƙamshi mai daɗi inayi,tashi nayi na nufi stef ɗin Aunty Mama sai
gata ta fito a ɗakin ƙasa tsalle nayi na ɗaneta"Aunty Mama ta","oyoyo ƴata tafi ta
kowa",dariya nayi na ɗago daga jikinta"ina Baffana","baki ganshi nan waje ba suna
tare da Alhaji Baffa","bangansu Aunty Mama",sallama sukai nan suka shigo har
Alhajin suna zama na zagaya ta bayansa namai ihu a kunne,dafe kansa ya yi"Nana
ta",zagaowa nayi na zauna kusa dashi ina gaisheshi bina da kallo ya shiga yi yana
mamakin zaman da nayi na ƙara kyau a ƴan kwanaki,maganar da Alhaji Baffa ya fara ce
anan naga Aunty Hajara mamaki ne ya kamani amma na shanye nasiha sosai ya mana
sannan yace mai magana ya yi Aunty Hajara ce cikin muryar tausayi tace"a haɗamu a
part ɗaya Kaka bawai tanacan ina can kunga yarinya ce gara muna kusa akwai ma ɗaki
a inda bake ba kowa kuma shi matafiyi ne gara ace muna haɗe ma na jin motsin juna
zaman yafi mana daɗi",kowa maganar ta bashi mamaki wani irin tashin hankaki naji
yana shigata nan kuja ya tasomin a fusace na miƙe amma Baffa ya riƙoni"indai ƴatace
wannan to ta zauna tayi duk abinda akace",da hanzari na zauna nayi shiru amma kana
kallona kasan haɗiye koma miye araina nake dan ƙirjina har ɗagawa yake,Alhaji Baffa
ne yace"ba komai Hajara za'a haɗaku ai kayanta na dayawa a ɗakko seti ɗaya a
kaimata can saiku zauna taren",kowa na wurin abin bai masa daɗi ba amma haka aka
amince ina nan zaune ya kira wayar Ya Dijama nan sai gata Ya Rumana ma tana nan sai
gata nan ya haɗasu da Aunty Mama yace suje suyi abinda ya dace ba yanda suka iya
haka har Hajaran suka wuce tashi nayi na haye saman can ɗakin Mama Hijabin na
wullar na ahiga kuka baji bagani a haka Maman ta shigo ta sameni bata kalke ni ba
ta ɗau abinda zata ɗauka tabar ɗakin a ƙasa na dire na fara shure shure dama nasan
Mama ba sona take ba tunda tana kallona ina kuka tasan ɓatamin akai amma bata
kulani ba,ba zato naji an rungumeni koban duba ba nasan waye da hanzari na
rungumeta"Mama",kaiana ta shiga shafawa"yi shiru Nana nima banji daɗin abinda ka
miki ba amma kinga Abbanki yace kiyi biyayya kuma Abbanki Habib zaiyi alfahari dake
kinganshi can a mudubi yana kallonki",da sauri na ɗago kaina sai naganshi yana min
murmushi nima yi nayi ina goge hawayen fuskata na kalli Mama"nima naganshi Mama"na
juya ina nuna ma ta sai naga wayam sadda kaina nayi"bakomai Mama na haƙura zan
zauna amma ki kirasu kayan Babban ɗakin nake so akai min amma sai an kira companyn
kayan sun turo masu cirewa bazasu iya cirewa ba","shike nan ƴar albarka jirani bari
nawa Babbanki magana",ta tashi ta fita bin ta nayi da kallo"kodan kiyi farin ciki
zan zauna da ita amma zan rashin kunya sai haƙuri kawai na miƙe na haye gado na
kwata.
Tunkan Mama tazo har Babban Yaya ya kirasu sun turo mutane dan sun san ina
ne,da Mama tazo ta faɗa musu ya sanar ma ta ya kira tana kallonsa tasan ransa bai
masa daɗi ba shima tabbas akwai takura irin wannan amma tana musu fatan
alkhairi,ian kwancen ta shigo ta zauna kusa dani kaina na ɗaga na ɗora acinyarta
gashina ta shiga shafawa"in baki wani sirri Nana","ina jinki Mama","wannan zaman ne
ya kamata ki lura da mijinki ki maidashi tamkar jariri ya zama kamin yace yimin
kaza inkinsan yanason amasa to ki masa kunya tana da matakai sannan tana da inganci
ga mace amma awani wurin saikin kaudar da ita duk da yarinya ce ke baki gama kaiwa
matakin da jikinki zai cika ba to dawanan ƙuruciyar zaki jawo shi jikinki
kinji,karki kuskura kuma kina kai ƙarar abokiyar zamanki kome zata miki kuwa ki
daure nasan baki iya wasu abubuwan ba amma zan siya miki waya duk abinda baki gane
ba ki kirani ko Mamanki kinji ko",kaina na ɗaga ma ta"Mama ɗinkina fa","gasu can
ɗazu ta kawo in zaki tafi ki tafi da abinki ki kasance kullum cikin ado dan baki
dai da wata damuwa ta aiki ko wani abu dazai hanaki yin yanda nace","to
Mama","yauwa Nana bari naje zan shiga kitchen kinji",ɗagata nayi ta fita zama nayi
ina murmushi ni ɗaya"kin ɗebo wutar gasa ki Aunty Hajara badai dani zaki zaunaba to
da kanki zaki maida ni ɗakina kuwa",gashina na haɗe na tubke kawai na zauna ina
karanta tsiya salo salo da zan aiwatar ma ta zataga tsiya muda muka gaji rashin
mutunci gun su Gwaggo Asama'u waɗanda masifa tsoronsu take.
Ba jimawa da gama maganar sai gasu sunzo har ɗakin ya kaisu dama su Aunty
Mama sun gama kwashe kayan buƙata un hala agefe,nan suka shiga kwance kayam suna
fita dasu a haka har suka gama a wancan ɗakin suka fara kafawa Hajara tayi kane
kane tana tsaye ko kallo bata ishi Aunty Mama ba dan a hasale take komai daurewa
kawai take,suna gamawa suka shigar da kayana da duk abin buƙata dama ɗakin yafi
kowanne girma a haka ma space ɗin a kuma saka kayan set biyu ɗakin ya yi kyau sosai
abuncina ma anan suka aje dan har frig ɗin suka ɗakko aka saka min aɗakin wani
lungu Aunty Mama ta samu ta kwaso min kayan girkina ta aje min suna gamawa ko
sallama basu ma ta ba suka dawo gida a sannan takwas da rabi tayi su Baffan na
ganinsu amma Aunty Mama bata kula kowa ba ta wuce,Alhaji Baffane yace"anfa taɓa
manya yau akwai daru",girgiza kai Babban Yaya ya yi"wallahi kuwa Baffa","tashi kaje
ka tafi da matarka",Baffanmu ya faɗa yana kallon sa kai kawai ya kaɗa ya ƙara
jingina kujerar ɗakin Iyyo dan tun sallar isha ɗakinta kuma kome ake tana ji amma
tayi shiru bata tankawa kowa ba.
Ina zaune kan darduma ta shigo da gudu na tashi na tashi na faɗa jikinta na
rushe da kuka itama kamar tai kukan haka taji amma ta shiga lallashina"haba jarumar
mata kar kuma kiban kunya mana a cikin zamani yaushe rabon da kiji matar aure mai
shekarunki sai yanzu akanki me kuma zaki damu dashi bayan mijin yana sonki ki daina
kuka ba abinda zai faru da kanta zata bar miki mijinki ta zama ƴar kallo zo muje
kiyi wanka ku tafi ko in kika nuna ma ta kin damiɓu sai tana miki dariya ai",ɗagowa
nayi ina goge hawayen"ai dama na daina kuka kuma bazatai nasara akaina ba insha
Allahu","haka nake sonji",Mama na kallonmu muka fito zuwa nata ɗakin wanka nayi
taban kaya daga cikin sabbin nawa nasaka humra kala kala na shafa sannan na fito
kamar mara lafiya na gansa falo shi ɗaya,zagayowa nayi ta bayansa na rungume kansa
a jikina,ajiyar zuciya ya yi ya lumshe ido da sauri ya riƙoni ya rungumeni
tsamtsam"wayyo Babban Yaya zaka ɓallani",sassauta min riƙon ya yi"tashi mu tafi ko
matar",miƙewa nayi ba ko sallama muka fito,tun a hanya nake mintsininsa in
yace"wayyo",nace "da saura ma",sai ya yi dariya ina kallon ƙofata amma na bi
bayansa muka shiga ciki da sallama tana zaune a falon ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya
tana taunar cingam sai ƙas ƙas take ta matse cikin riga da wando ita adole shigar
rashin mutunci bata amsa mana sallamar ba saima ta ɗago ta watsa mana wani kallo
sannan ta kwashe da dariya"laila majunun ashe an gama fushin an taho dama na faɗa
maka indai ina raye kaida wannan akun bazaku taɓa jin daɗi ba a rayuwar ku",wani
murmushi daya bayyana asalin kyansa ya saki yana kama hannuna muka matsa kysa da
ita wallahi na zata magana zai ma ta sai kawai yaja hannuna muka wuceta zuwa ɗakin
daya zama nawa,"wow"na faɗa ina daka tsalle ɗakin ya yi kyau fin can ma gyale na
yar na juya na ɗane shi"Babban Yaya kaga kamar ɗakin ƴan film amma ya yi kyau kai
Aunty Hajara nagode miki",dariya kawai yake yana bina da kallo dira nayi na kwasa
aguje"na tafi ma ta godiya ai ni gaba ta kaini dama irin wannan ɗakin ne
burina,kamin yamin magana har nakai bakin ƙofa tana nan tana jijjiga jiki dan
abinda ya ma ta ya bata haushi ita so take ya kulata suyi amma yaƙi yadda shi yasa
abin ke ara ƙular da ita,bata ankara ba ta ganni da gudun masifa nai burki a
gabanta hannayena na haɗa alamar godiya"Aunty Hajara ina sonki wallahi wannan haɗi
naki ya bada citta ɗakin yamin burina kenan dama anan ne zaki kalli asalin film
ɗin"ina kaiwa nan na koma na barta da sakakken baki gyara tsaiwa tayi"wai me
yarinyar nan ke nufi da ni ne",bata da sa ne yasata juyowa kawai ta ganshi a
bayanta hannayensa a aljihu,turus tayi tana hararar sa matsowa ya yi gaf da
ita"madam shiryo ina son ganin ku keda abokiyar zamanki",bai tsayaba ya wuce ina
cire siket ya shigo ban daina ba na zare haka ma rigar dagani sai half best itama
Aunty Mama ce ta bani amma boom short ɗin na nan tura ƙofar ya yi ya ƙaraso inda
nake juyawa nayi ya tsaya abayana ya janyoni jikinsa hannunsa ya ratayo ta cikina
yana shafawa"kai wannan cikin yunwa yakeji da alama",da saurin na janye ina dube
dube a ɗakin can kan mudubi naga coler ajiyar zuciya nayi na juyo ina
kallonsa"Babban Yaya ai tunawa nayi da abincina ashe gashi can bari nasa riga nazo
na baka abaki kaci girkin nawa kaji",kai ya kaɗa ya kamo hannuna"zauna a haka nake
son ganinki",dariya nayi"an gama na wajena taho ka cire wannan kot ɗin muje
muci"matsowa ya yi kawai ya tsaya bakin gado na jashi na haye na fara ɓallemasa
yana bin duk motsina da kallo cire masa ita zanyi najaja baya na sunkuyo ƙirjina
ya sauka a fuskarsa,lumshe ido ya yi ya rungumo bayana na kifa akansa sakin rigar
nayi jinyanda ya shiga sumbatar wurin dariya na farayi dan kunsan ni abin dariya ba
wuya yake min ba shi kuwa wani hali yasa kansa ɗagowa ya yi ya kalleni take naga
idanuwansa sunyi ja gum naja bakina nayi ian shirin tambayarsa miye ya lora bakinsa
anawa shiru nayi dan wannan fanin yamin daga yi ɗaya ƙara ƙanƙameshi nayi rigar da
ta maƙale masa a ɗayan hannun ya saki ya kwanta dani a gadon ban hanashi ba ko na
masa musu amma me hannunsa ya ɗora kan ƴan breast ɗina ya fara murzawa ban hanashi
ba dan ni banga abin taɓawa anan ba,da abin ya yi nisa basai ya zare rigar ba ya
shiga murzar su ni kuwa mezanji daɗi ne yamin karo shi yana nishi ni kuwa ina ihu
abin nawa dariya ya shiga bashi ammabya shanye saida ya mujesu tas sannan ya barni
bule ido nayi naga yanata kallonsu,jikinsa na faɗa ina shura ƙafa"ni ka mayar min
rigata ka gama ganinsu ka taɓa shikenan ai amma kullum saika musu haka inba haka
suyi fushi",wata muguwar dariya ce ta kamashi bai taɓa yin irinta ba ba shiri ya
saketa yana ƙara ƙanƙameni"na yadda da wannan batun amma nima kar a hanani fa
kowanne lokaci muna haɗuwa zan musu haka abin ya yi musu kenan",juyowa nayi ko
kunya ban jiba na ɗauki hannunsa na ɗora akai"jifa yadda sukai ɗumi ai ana musu
haka kullum nima shirya",kallon tsabar yarinta yake afuskata ta maganata sai ya
rungumeni yana sumbatar kaina"ina son matata","nima haka mijina","yauwa tashi maza
sa kayanki muje falo Hajara na jiran mu",saboda tsabar iskanci bansa kayanba saina
binciko hijabi ƙato har ƙasa yake ja nasa shi kuma a hakansa muka fito tana nan
harɗe da ƙafa muka fito,inda ya zauna nan na zauna ian ɓuya tunkan ya yi magana ta
rigashi"kar kace min raba kwana kazoyi tsakanina da wannan jaririyar to inkuwa
hakane kaji kunya kana kwana da ƴar da in auren wuri kayi ka haifeta",cikin wani
salon rainin hankali Babban Yaya ya ɗago yana kallonta yace"amma dai ba ƴar tawa
bace ko to ai kwana da ita ba matsala bane dan haka na rabashi kwana biyu biyu kuma
yau kwanan ta huɗu tana ragowar kwana uku dan haka saida safe",yana kaiwa nan ya
miƙe ya kama hannuna zamu wuce,ai da yake na ƙunso tsiya kuma banba sai na tsaya ya
juyo"ya akai Babyn Yayanta",shagwaɓe fuska nayi"ruwa zan ɗakko acan"na nuna frig
sakina ya yi"ɗakko to",ina zuwa na ɗakko na taho ina sane na saƙala ƙafata da capet
nai gaba zan faɗi ya ƙaraso da sauri ya tareni na faɗa jikinsa hijabin ya ɗaga,kuma
akan idonta sannun ya shiga min ya yinda ta gwalo ido tana bina da kallo ruwan ya
ɗauka muka wuce na juyo na ma ta gwalo,daƙuwa hannu biyu tamin na ƙara ma ta gwalo
ina juya ma ta bombom ɗina dai dai da muna shiga ɗakin.

😀😀😀😀😀

UMMU SADDI'Q CE 🌹🌹🌹🌹🌈🌈🌈


🌈🌈
🌈

Babban Yaya Free ne amma me so ya biyo ni Pc in sa a group don shagalin Nana


na buƙatar comments.
08146711395

25
******
Har bakin gadon ya kaini ya ajiye ni sannan ya zare hijabin half best ɗin ya
ɗakko yasamin,yana zuwa da kansa ɗakko abincin ya aje kan capet ɗin nan mai laushin
tsiya kwanukan da yaga an aje dan ujila yaje ya ɗakko na amfanin kamarbyasan me
nayi ya kawo sannan ya koma jiki sif ya fara zare kayansa kauda kai nayi harya gama
sannan ya shige toilet bai jimaba ya fito kansa jiƙe da ruwa amma a haka yazo ya
zauna a kusa dani jikinsa mai sanyin ruwa yana taɓani dalilin da yasa na farka
kenan tashi zaune nayi nasa hannuna na zagaya na maƙale shi na kwantar da kaina
akafaɗarsa,gashin ya shafa"taso kici abinci nasan baki ci wani abu mai yawa
ba","muci dai"na faɗa ina riƙe hannunsa,aƙasan ya zauna nima haka buɗewa ya yi yaga
miye zaro ido ya yi"ke ki kai wannan abincin Nana",kaɗa kai nayi ina juya
ido,jinjina yamin ya zuba mana yafaraci tunkan na basa gyaɗa kai kawai yake ganin
ba jirana zaiba saina sa hannu nima na fara ci,saida muka gama sannan ya
kalleni"ina jinjina miki tawan ashe ke ɗin ma gwanace tun yanzu na yadda wannan
renon nasu Mama ne gadon Iyyo",dariya nayi "kai Babban Yaya","gaskiya ne ai",hannun
muka wanko da bakin mu sannan yazo yasa kaya amma ni naƙi sawa yana kwanciya
nabishi na haye kansa murmushi kawai ya yi ya rungumeni.
A ranar Hajara kasa rintsawa tayi ga jaraba na cinta amma ba yanda ta iya
washegari tun asuba ta fito falo ko zataga fitarsa amma shiru aman bacci ya
ɗauketa,mukuwa makara ya yi hakan yasa bai samu sallah ba saidai mukayi ta anan
tare muna idarwa na matsa kusa dashi na kwanta akan ƙafarsa na koma bacci shi kuma
ya cigaba da azakar ɗinsa,rana ta fara fitowa kenan ta farka a firgice taga dai bai
fitoba saita tashi ta fara dukan ƙofar kamar mahaukaciya,yana jinta amma ya shareta
saida ya gama sannan ya miƙe da ni ya kwantar a gado ya shiga toilet wanka ya yi ya
fito ya shirya cikin suit baƙa ya fito a ma'aikacinsa ɗan gayu bai tasheni ba ya
fito yana jan ƙofar wuf ta miƙe ta nufeshi bai ankara ba taci mai kwala"inka isa
Allah ya tsinemin mai wannan jaririyar yarinyar keda shi da har zaka na zaman
wurinta haka mai zakaji ajikinta",hannayen nata ya kama ya cire a wuyansa"indai
bazaki daina mamakin me Nana keda shiba da nake zaman wurin ta indaɗe to kuwa zaki
ta zama ke ɗaya ba bu ni saboda ba komai nata nakeso ba face itaɗin gabaɗayanta ni
komai nata yamin amma in haɓaka kike so tayi ta zama kamar ke to kiban sati biyu
kacal zata samu abinda kike so ta samu saiku jera",ya saki hannun nata ya fita ko
ɗar baya ji na ya barni da ita,bayansa tabi da kallo bakin ta yaƙi rufuwa anan ta
zauna jaɓar to wai me zatayi ne ma wannan yarinyar ya daina kulata tayi abubuwa da
dama amma shiru amma bariki zata nuna masa ta yadda bai bazai iya tsallakewa ba
zata nemi zaman lafiya na gangan da wannan zata gasani,wani mirmushi tayi ta miƙe
wayarta ta ɗauka ta kira mai aikinta tasanar ma ta ta dawo tai ma za tazo ta gyara
ma ta gida,kafin wani lokaci ta iso nan ta shiga gyaran sannan ta ma ta wanki harad
pant sa bra dan abin kunya.
Saida nasha baccina sannan na tashi ɗakin ba kowa dama tun jiya ya faɗa min
zai ɗan fita da sassafe hakan yasa ban damu na tashi na fara gyara ɗakin sannan na
biɗeshi da turaren wuta na shiga wanka ina fitowa mai nashafa da kwalliya kaɗan
sannan nasa riga mai hannun best ko half best ɗin bansa ba na kwaso kwanukan na
fito a sannan su kuma suna tsaye tana aiken mai aikin ta ta,wucewa nayi ina
faɗin"Aunty Hajara barka da tashi",harara ta tayi"kyacemin barka da tashi mana
tunda da fukafiki kika ganni","Allah baki haƙuri Aunty na ta kaina ina kwana to",na
wuce kitchen ban aje kwanikan ba na wanke abuna na goge ina ganin inda ta warewa
kayana wuri nai murmushi na aje nan sannan na ɗebo ruwan ɗumi a mug na fito,suna
nan tsaye na wuce dining madara da ovaltine na gambaɗa aciki ko sugar bata samu
wurin zama ba nazo na wuce su bina da kallo tayi sannan ta kalli ƴar aikin itama ni
take kallo harara ta zuba ma ta"miye ki ke ma ta wannan kallon haka","Aunty wallahi
yarinyar tana da kyau ta haɗu dayawa wannan namiji ya sameta ai zai huta dan hannu
na fara taɓa jikinta zata haɓaka",wani kalar kallo ta ma ta"ita wannan jariyar abin
a tsaye a bushe ita maza ke so dan sakarci","ba sakarci bane Aunty wannan a tsayen
da ki ke gani maza shi suke so kuma wannan ƙanwar take ko da wuri zata mallake
namiji da alama batasan komaiba kome ze ma ta yadda zatai in taji daɗi kuma gobe da
kanta zata kawo kanta",wani gumi ne ya karyo ma ta ta zauna ba shiri da mamaki ta
zauna a ƙasa"Aunty lafiya kuwa",kallonta tayi"wannan ba ƙanwata bace matar megidan
ce",me aikin zabura tayi ta wara hannu"a kin gama Aunty wannan ƴar shilar kina me
ki ka bari aka aurota kumanaka kawota nan cikin ɓangarenki duk girman gidan
nan","ni nasa akawota nan dan na nuna ma ta manya bakalar yara bane",gudun karta ma
ta rashin mutunci saita zuƙe maganarta ta koma"ai ku irinku daban ne Aunty musamman
ma ke ki kalleki fa ai wannan zaki mallake mijinki ki korata ta fita ai dama in
suka samu gidadawa shine zasu iya ƴwace musu mijin","hakane kuwa yanzu jeki kasuwar
ki dawo",to tace sannan ta tashi ta fita amma maganar da tayi harga Allah ba ita
tayi niyar faɗaba sai dai tayi kallo.
A ɗakin ma zamana nayi na shanye abinda na haɗo sannan na fito na maida cup
ɗin nazo zan wuce tasha gabana"matan aure masu miji nasan dai abin duk burga ne
ƙofar bazata biyu ba dan da an bita da ba za'a yi wannan kaɗiri feren ba",gyara
tsaiwata nayi"shi ya faɗa miki bai bita ba Hajiya to bari kiji wannan ta gaban naki
wato ni kenan matar aure nake cikakka irinki ni da nake ma mai tsukakken jiki amma
nasan kekam",banngama maganar ba ta kawo min danƙa na goce nai ɗaki da gudu ta
biyoni kan tazo na rufe ina dariya bubbugawa ta shigayi"saina fasa wannan bakin na
marasa kunya shegiya karuwar yarinya kawai",duk ina jinta amma nayi shiru ta gama
masifarta tabar wurin,me aikin na kawo ma ta saƙon tace suyi girki haka ta zage
sukai girkin amma shinkafa ce da miya sai coslow sai lemukan kwali ta kama ta cika
dining,ban fitoba saida yunwa ta isheni tana ɗakinta na fito ban kula dining ɗin ba
na wuce kichen ƙwai na soya mai yawa dan ba bread a gidan na kuma haɗa shayi shaf
shaf na gudu ɗaki na cinye ƙwan du sannan na kwanta ba jimawa nayi bacci.
1pm ya shigo gidan da kaya niƙi niƙi a falon ya aje ya kuma fita ya shigo
da sauran zama ya yi akujera yana furzar da iska mai ɗumi dan ya gaji sosai,Hajara
ce ta fito ta ganshi cikin fara'a ta ƙaraso inda yake ta zauna"sannu da zuwa
Habibe",wata sabuwa ya faɗa aransa wannan salon fa bai gwaleta ba sai ya amsa tana
jujjuya kai tace"da alama ka shawo gajiya ga abinci can",ɗan murmushi ya yi"nagode
kuwa amma bari nayi wanka",yana falar haka ya miƙe ya bar wurin zuwa ɗajina murɗawa
ya yi ya shigo inata bacci murmushi ya yi ya wuce toilet wanka ya yi sannan ya fito
kwanukan dana ci abinci ya kalla da sauri ya dafe kanshi ya manta ƴan sinadaran
breakfast bai siyo ba,sanyin ruwa naji na bule ido idona a hankali na ganshi yana
murmushi amma kansa ajiƙe da alama wanka ya yi,tashi nayi zaune na shige
jikinsa"oyoyo Babban Yaya nayi kewarka",rungumeni ya yi"nima nayi kewarki ma za
tashi ki watsa ruwa muje kici abinci",sakkowa nayi a gadon ian faɗin"to Babban
Yaya",na shige toilet bin bayana ya yi da kallo ya girgiza kansa kawai.
wankan ma ban tsaya nayi mai kyau ba na fito a gurguje na wuce ga mirrow na
fara shafa mai duk yana kallona wallahi na manta yana ɗakin na cire towel ɗin harda
yarwa na shafe jikina da mai na juyo zan je sif naganshi ƙurii yana kallona baki na
hangame sannan na kalli kaina a wurin durƙusa ina dariya"Babban Yaya ka kallar min
asirin jikina",tasowa ya yi yana dariya"to nawa zan biya amma sai na ƙara
gani",ɗagowa nayi na kalleshi"zaka biya da gaske na miƙe ka kuma ganin bonus","eh
mana million guda zan biya",wuf nayi na miƙe"iya wannan kallon a miliyan Babban
Yaya to kullum zakana kalla sau goma sha",tsabar dariya saida ya zauna dan tabbas
yaga zallar yarinta anan ma",wucewa nayi na ɗaura towel ɗin nima ina dariya sai
yanzu na gane wayo yamin ya kalleni sadaka,anan na barshi na wuce sif wata blue
body hog mai ƙaton wuya nasa da baƙin trequater na ɗaure gashina da ribom blue na
juyo ina murmushi,tasowa ya yi"wow tawan ta haɗufa",yaban hannu muka tafa"ka shirya
kaima to","saikin tayani",ni na ɗakko mai kayan yasa sun masa kyau sosai jeans da
riga mara nauyi,najuya ya riƙoni yana nuna ƙirjina"waɗannan yara baza'a samusu tasu
rigar ba",dariyace ta kamani amma na ƙwace jikina na matsa"ni a haka zan zauna",na
faɗa ina maƙale kafaɗa"baki isaba kuwa"ya kawo min danƙa na fito da gudu ya biyo ni
Aunty Hajara na zaune na wuceta na tsaya a kwiɓinta"Aunty Hajara ki masa magana
yana barinsu su huta wai dole sai ya jasu sunyi girma kamar naki wai naki yake so
ba nawa ba",da mamaki tana hararata tace"me kenan?",ba kunya na nuna ma ta
ƙirjina,da sauri ta miƙe tsaye"zance ubanki in ki ka min karuwanci anan shegiyar
yarinya kamar aljana kinƙi ki barni ko tunani nayi kin kanainaye mijin shine yanzu
zaki biyo takaina kimin iskanci wato dai saikin faɗa min yana taɓawa ko",kai na
kaɗa ina taɓe baki"jiya har ma cewa ya yi suna birgeshi musamman in yana
kallonsu","innanillahi"ta faɗa tana zama jaɓar yayinda Babban Yaya ke bayanta yana
dariya harda riƙe ciki,ni kuwa nayi mirsisi sai taɓa baki nake wai ni shagwaɓa.

Ɗago kaina nayi zan ma ta magana tai saurin ɗaga min hannu"kina magana saina
mareki",maida ta bakina nayi na sumkuyar da kai kamar wata tagari,tasowa ya yi
yakama hannuna"zo muje kici abinci kin tsaya fitina",kamar wata ƴar ya ye haka na
bishi zugwi zugwi yaja kujera ya zaunar dani sannan ya koma itama ya kamo hannunta
yazo ya zaunar da ita dana ɗago kai saimu haɗa ido harara take watsamin ni kuma
nayi iya dauriya na riƙe dariyar da ke cina,da kansa ya buɗe abincin ya fara zubawa
kowa yana murmushi ina hangar naman kaza da coslow na ture abincin na janyo kwanon
naman da coslow ɗin na fara ci ina zare ido tana kallona taƙi min magana danta lura
danja ce ni kowacce magana ina da amsarta,saida naci na cinye sannan na harari
kwanukan su naman kwanonsa na janye na faraci yamin banza saida na cinye sannan na
miƙe na kwashe nata na zura da gudu ɗaki kamar zata ƙware tace"zoki ajemin ko mijin
naki ya biyani gomanshi ke kuma na kamaki saina miki dakan sakwara",hannu kawai na
ɗaga ma ta na shige ɗaki a ƙasa na zauna na faraci nafa ƙoshi tsabar neman magana
ne yasa na ɗakko ma ta,kallonsa tayi"ka sa ni saika biyani namana ko in na kamata
na daki abuna",wani hamagon kallo ya ma ta"wai Hajara bake ki ka ce zaki iya da
Nana ba Nana kuna mutunci ma ya aka cika bari bakwayi nama kuma ai gashi nan a
gidan ko ɗanye ki ke buƙata gashi nan inshi zaki ci",hararar sa ta yi"saboda ka
maida ni mayya ko",ƙala baice ma ta ba ya gama ya tashi ya barta a wurin dan dama
ita haka take akwai ci,ina nan zaune na wanko hannuna ya shigo fuskarsa na kalla
nagansa a Babban Yaya na farko dana sa ni saina shiga hankalina,wucewa ya yi ya
zauna abakin gado"zo nan Nana"jiki sanyaye na tashi naje a ƙasa na zauna na
sunkuyar dakaina"gani"na faɗa murya ta na rawa"me yasa ki ke raina Hajara ko na
taɓa gaya miki bana sonta ne",kai na kaɗa ina ƙaƙalo hawaye"to karki kuma bari naga
kin ma ta rashin kunya dan ina son matata"kai na kuma kaɗawa ina rushewa da
kuka,cikin mamaki ya shiga bina da kallo"me aka miki kuma ki ke kuka haka",ƙara
sauti nayi kamar ana cizona,da sauri ya ɗagoni ya ɗora a kan ciyarsa yana tallabo
fuskata"me aka miki ki ke kuka",taɓe baki nayi cikin shagwaɓa nace"bakai kaine kace
baka sona ba matarka ka ke so",kansa nu na"niɗin nace bana sonki Nana"kaina kaɗa"eh
mana gashi nan kana min kashedi akanta ni shike nan baka sona",na ƙara rushewa da
ihu saurin rungumeni ya yi"shiiiii ni bance bana sonki ba kece mace ta farko da
naso kuma ta ƙarshe ko wacce mace da zata shigo rayuwata sai dai ta zauna a wajen
zuciya ta badai a ciki ba",ƙara rungumeshi nayi ƙamƙam na ɗago namai kiss a
baki,ƙara rungumeni ya yi ya ɗora bakinsa kan nawa ya shiga tsosarsa kamar sweet ni
kuwa ƙara rungumeshi nayi muka kwanta ina kallon ya tabar jikin window nayi
murmushi kawai'badai kince da Nana zaki ja ba',irin ta jiya aka maimaita murje ni
ya yi tas ƴan breast ɗina sunci ubansu maganina ma kenan,buguzum ta shige ɗaki ta
tuge ɗankwalin kanta ta faɗa gado a haukace ta miƙe ta koma gaban mudubi"me kenan
Hajara kina nufin zaki barwa ƴar wannan yarinyar mijinki,inaaaa"ta faɗa da ƙarfi
tana watsar da kayan kan mudubin wayarta ta wartako ta danna kira wanda ta kira ko
magana baiba ta fara aje masa bayani,ashe yayarta ta kira katseta tayi"kinga Hajara
ki nutsu zaki iya komai amma ki bari sai kwananta ya fita anan ne zaki gasa tunda
dai dole ranar ɗakin ki zai kwana ba saina koya miki komaiba yaushe ne zai koma
ɗakinki","jibi ne","yauwa to kibari gobe kin magana bayan sallar magariba",to shike
nan tace ta aje wayar ta nemi wuri ta zauna sai asannan zuciyarta ta lafa.
Daga ya mutsani nayi bacci shima haka sai la'asar muka tashi,tsiya da taɓara
na tashi da ita na hanashi sakat rasa ina zaisa ni ya yi kawai ya ɗaukeni zuwa
toilet ya aje ni ya kunnamin ruwa ina gani ya min tas yasa soso yamin wanka ya naɗo
ni a towel ya dawo dani ɗaki mai ya shafa min yasa min komai na ciko sannan doguwar
riga ta les ya ɗakko min Hijab yasamin"taso muje"ya kamo hannuna nasa takalmi muka
fita tana ɗaki batama sa ni ba,bai zame dani ko ina ba sai gidan Ya Ruma,murna da
tsalle na shiga yi anan ya barni ya fita,a falonta na kwanta ta shigo da kofi a
hannunta na karɓa ƙaremin kallo ta shiga yi"ke Nana me kike ci haka kalli
ƙirjinki",a tsorace na tashi ina kallon ƙirjin nawa"me ya sami ƙirjin nawa Ya
Ruma",zama tayi tana ƴar dariya"gani nai ba haka ki ke ba amma yanzu naga sun
cika"a jiyar zuciya nayi"to Aunty Ruma ba dolensu su fito ba tunda maisu yana
buƙatarsu da wuri",baki ta kama tana dariya"au ashe abin na manya ne to bari zan
baki wani sirri zaki jure ai ko","sosaima kuwa amma da zaƙi ko","sosaima kuwa Nana
ta",yanzu zo muje na koya miki wani abin daɗi,shanye abinda ta bani nayi sannan
nabi bayanta naji daɗin kuwa abinda ta koya min sannan ta nuna min abinda tace sai
ayan sallar magariba sannan yazo zamu tafi a bayansa na laɓe a bakin get"me ne ne
Nana",kasa magana nayi na shiga yarfe hannu kamar wadda aza'a doka"hannun ya
riƙe"faɗamin me ki ke so"um um dama"janyo ni ya yi jikinsa"ki nutsu faɗamin me ki
ke so","dama dama kuɗi zaka bani zan baya Ya Ruma ta siyo min wani abu",ƴar dariya
ya yi ya janyeni a jikinsa ya ciro kuɗi a aljihu ya ciri dubu goma ya bani tsalle
nayi na rungumeshi"nagode Darling Yaya",hancina yaja"kai ma ta kizo mu tafi",da
gudu na koma nakai manta na dawo muka tafi,matar gidan na zaune a falo ta saki kiɗa
sai rawa take muna shiga na fizge hannuna na yadda Hijabin na mara ma ta baya
tsayawa tayi tana kallona shima haka da hanzari ya ƙaraso yamin ɗaukar yara ya nufi
ɗaki dani na wantsala ƙafa bai aje ni a ko ina ba sai toilet"yi alwala kizo kiyi
sallah",daga haka ya fito,ni kuma nayi abinda yace,yana fitowa falon ya kashe kayan
kalkon duka ya nunata"bana nason ki ƙara kunna min kiɗa a gidannan na faɗa miki",ya
dangwarar da remort ɗin ya juya ya fita hararar bayansa tayi"ƙaryar banza ihu bayan
hari wallahi saina kunna ta shige ɗaki,bayan ya idar da sallar isha yaje ya
siyamana abinda zamuci iya daren dan ya shigo baiga alamar abinci ba gashi yasan
daga sallar isha nake bacci muddin a zaune nake waje ɗaya.
wucewa ya yi ya zauna abakin gado"zo nan Nana"jiki sanyaye na tashi naje a
ƙasa na zauna na sunkuyar dakaina"gani"na faɗa murya ta na rawa"me yasa ki ke raina
Hajara ko na taɓa gaya miki bana sonta ne",kai na kaɗa ina ƙaƙalo hawaye"to karki
kuma bari naga kin ma ta rashin kunya dan ina son matata"kai na kuma kaɗawa ina
rushewa da kuka,cikin mamaki ya shiga bina da kallo"me aka miki kuma ki ke kuka
haka",ƙara sauti nayi kamar ana cizona,da sauri ya ɗagoni ya ɗora a kan ciyarsa
yana tallabo fuskata"me aka miki ki ke kuka",taɓe baki nayi cikin shagwaɓa
nace"bakai kaine kace baka sona ba matarka ka ke so",kansa nu na"niɗin nace bana
sonki Nana"kaina kaɗa"eh mana gashi nan kana min kashedi akanta ni shike nan baka
sona",na ƙara rushewa da ihu saurin rungumeni ya yi"shiiiii ni bance bana sonki ba
kece mace ta farko da naso kuma ta ƙarshe ko wacce mace da zata shigo rayuwata sai
dai ta zauna a wajen zuciya ta badai a ciki ba",ƙara rungumeshi nayi ƙamƙam na ɗago
namai kiss a baki,ƙara rungumeni ya yi ya ɗora bakinsa kan nawa ya shiga tsosarsa
kamar sweet ni kuwa ƙara rungumeshi nayi muka kwanta ina kallon ya tabar jikin
window nayi murmushi kawai'badai kince da Nana zaki ja ba',irin ta jiya aka
maimaita murje ni ya yi tas ƴan breast ɗina sunci ubansu maganina ma kenan,buguzum
ta shige ɗaki ta tuge ɗankwalin kanta ta faɗa gado a haukace ta miƙe ta koma gaban
mudubi"me kenan Hajara kina nufin zaki barwa ƴar wannan yarinyar mijinki,inaaaa"ta
faɗa da ƙarfi tana watsar da kayan kan mudubin wayarta ta wartako ta danna kira
wanda ta kira ko magana baiba ta fara aje masa bayani,ashe yayarta ta kira katseta
tayi"kinga Hajara ki nutsu zaki iya komai amma ki bari sai kwananta ya fita anan ne
zaki gasa tunda dai dole ranar ɗakin ki zai kwana ba saina koya miki komaiba yaushe
ne zai koma ɗakinki","jibi ne","yauwa to kibari gobe kin magana bayan sallar
magariba",to shike nan tace ta aje wayar ta nemi wuri ta zauna sai asannan
zuciyarta ta lafa.
Daga ya mutsani nayi bacci shima haka sai la'asar muka tashi,tsiya da taɓara
na tashi da ita na hanashi sakat rasa ina zaisa ni ya yi kawai ya ɗaukeni zuwa
toilet ya aje ni ya kunnamin ruwa ina gani ya min tas yasa soso yamin wanka ya naɗo
ni a towel ya dawo dani ɗaki mai ya shafa min yasa min komai na ciko sannan doguwar
riga ta les ya ɗakko min Hijab yasamin"taso muje"ya kamo hannuna nasa takalmi muka
fita tana ɗaki batama sa ni ba,bai zame dani ko ina ba sai gidan Ya Ruma,murna da
tsalle na shiga yi anan ya barni ya fita,a falonta na kwanta ta shigo da kofi a
hannunta na karɓa ƙaremin kallo ta shiga yi"ke Nana me kike ci haka kalli
ƙirjinki",a tsorace na tashi ina kallon ƙirjin nawa"me ya sami ƙirjin nawa Ya
Ruma",zama tayi tana ƴar dariya"gani nai ba haka ki ke ba amma yanzu naga sun
cika"a jiyar zuciya nayi"to Aunty Ruma ba dolensu su fito ba tunda maisu yana
buƙatarsu da wuri",baki ta kama tana dariya"au ashe abin na manya ne to bari zan
baki wani sirri zaki jure ai ko","sosaima kuwa amma da zaƙi ko","sosaima kuwa Nana
ta",yanzu zo muje na koya miki wani abin daɗi,shanye abinda ta bani nayi sannan
nabi bayanta naji daɗin kuwa abinda ta koya min sannan ta nuna min abinda tace sai
ayan sallar magariba sannan yazo zamu tafi a bayansa na laɓe a bakin get"me ne ne
Nana",kasa magana nayi na shiga yarfe hannu kamar wadda aza'a doka"hannun ya
riƙe"faɗamin me ki ke so"um um dama"janyo ni ya yi jikinsa"ki nutsu faɗamin me ki
ke so","dama dama kuɗi zaka bani zan baya Ya Ruma ta siyo min wani abu",ƴar dariya
ya yi ya janyeni a jikinsa ya ciro kuɗi a aljihu ya ciri dubu goma ya bani tsalle
nayi na rungumeshi"nagode Darling Yaya",hancina yaja"kai ma ta kizo mu tafi",da
gudu na koma nakai manta na dawo muka tafi,matar gidan na zaune a falo ta saki kiɗa
sai rawa take muna shiga na fizge hannuna na yadda Hijabin na mara ma ta baya
tsayawa tayi tana kallona shima haka da hanzari ya ƙaraso yamin ɗaukar yara ya nufi
ɗaki dani na wantsala ƙafa bai aje ni a ko ina ba sai toilet"yi alwala kizo kiyi
sallah",daga haka ya fito,ni kuma nayi abinda yace,yana fitowa falon ya kashe kayan
kalkon duka ya nunata"bana nason ki ƙara kunna min kiɗa a gidannan na faɗa miki",ya
dangwarar da remort ɗin ya juya ya fita hararar bayansa tayi"ƙaryar banza ihu bayan
hari wallahi saina kunna ta shige ɗaki,bayan ya idar da sallar isha yaje ya
siyamana abinda zamuci iya daren dan ya shigo baiga alamar abinci ba gashi yasan
daga sallar isha nake bacci muddin a zaune nake waje ɗaya.
Washegari da sanyin safiya aka tashi Hajiya Fulera da yaranta ba bu kowa
kuma ko tsnke basu ɗauka sai takarda da ta bari Alhaji Baffa ne yace a kira masa
shi,wayarsa aka kira ina shafa mai a jikin mirrowa na gani na ɗaga saboda Baffa
nagani"Nana kice mijinki yazo ana kiransa","to Baffana",na kashe dai dai yana buɗe
ido miƙa ya yi"waye Nana","Baffa ne yace wai kaje yanzu",da hanzari ya sakko ya
saka jallabiya na wuf na zira riga da hijabi na bisa dan mu ba'a bamu labari gara
mu bayar yana fita yaji ina tsayani mana,hannuna ya kuma muka nufi gidan,duk
mutanen jihar suna gidan saboda gulma su Hajiya Harira anyi wuƙi wuƙi ga Hajiya
Salma da Safiyya,yana shigowa aka mai caaaa da magana baima gane me kowa ke faɗa ba
saida ka bashi takarda sannan Alhaji Baffa yace"karanta kowa yaji",a fili ya fara
karantawa.
"Barkanku kishiyoyina marasa wayo na tabbatar sanda zakuga saƙona na yi nisa
daku nayi tunanin na zauna na ƙwaƙule duk abinda yake hannun ɗan mijina kamar yadda
na ƙwaƙule na hannun abokan zamana ko basu faɗa muku ba ni na faɗa muku na ƙwace
komai nasu yanzu ziro suke kaima Habib naga wannan yarinyar bazata barka ka
tsinanawa kowa komaiba shi yasa ma na barka amma ina nan dawowa kar kayi tunanin
har abada na barka su kuma sai kuna tallafa musu da shinkafa da mai amma su da
dukiyarsu sunyi bankwana".
Ɗagowa ya yi ya kallesu kawai ya yi murmushi ƙala baice musu ba ya juyo ya
kama hannuna muka fito a gidan ya yinda suka shiga ihu suna kuka amma bai iya mai
iya taimaka musu dan sanda zasu bata ba suyi shawara da kowa ba.

UMMU SADDIQ🌹🌹🌹
🌈🌈🌈
🌈🌈
🌈

Babban Yaya Free ne amma me so ya biyo ni Pc in sa a group don shagalin Nana


na buƙatar comments.
08146711395

26

Tun a hanya nake ce masa"Babban Yaya wannan matar amma cikakkiyar ƴar duniya
ce","wa ya faɗa miki ta gwada musu cikakkun mahaukata ne su"dariya na kwashe da
ita"amma wallahi basu da wayo ai ko ni baza'a min wannan wayon ba na yarda","ai ke
ki ka ce su kinga ai an musu yanzu sai inga ƙaryar a raba a basu kar na cinye","au
haka sukace ma to Allah shi ƙara Allah yasa yanzu tana china",ba shiri ya yi
dariya"nifa matsalata dake addu'ar mugunta in tana china yanzu ai su da kuɗinsu sai
a ƙiyama","eh hakan nake musu fata mana ni aƙiyamar ma kar abasu suyi ta zama a
matsiyata",matse min hannu ya yi"ai yanzun ma suna da kuɗi musamman Salma da
Safiyya ɗayar ce dai abin tausayi","kai ka ke tausaya ma ta amma goɗogoɗo da ita
ace kawo na aje miki kamar ƴar yaye ta ɗauka ta bada"sakina ya yi yana dariya"Nana
anya kuwa ba babbar ƙarama ce ke ba"dariya nayi"ai in hakane kafi kowa sa ni yauwa
Babban Yaya please zo muje gida kaga wani abu","to Nana ta muje",Aunty Hajara na ta
bacci muka shigo mai aikinta harta gama tana niyar tafiya muka shigo da sauri ta
durƙusa" Alhaji ina kwana","lafiya lau zonan uwata",zuwa tayi ta durƙusa"gani","in
tambayeki mana","Allah yasa na sa ni Alhaji","ba tun farkon zuwanki gidan nan ba
naji kince ansa miki rana amma har yanzu shiru ko lokacin baiba ne",kanta ta
sunkuyar"harma ya wuce da wata tara","subahanallahi"nai saurin faɗa"me yasa ke
kuwa","Aunty wallahi lokacin da yazo ba bu kuɗin kaya kuma dama ɗan unguwar ne
shine aka zigeshi wai ko ya aureni shi zaina ci da gidan mu kuma ya yarda shine
yace ya fasa",wani haushi ne ya kamani"kai amma mutane basu da kirki wallahi kiyi
haƙuri Allah ya zaɓa miki abinda yafi zama alkhairi","ameen ameen nagode",ɗagowa ya
yi ya kalleta"sanda abin ya faru baki faɗawa uwarɗakin naki ba","na faɗa ma ta tace
Allah ya kyauta maza ƴan iska ne",runtse idonsa ya yi"kiyi haƙuri kina irin wannan
gidan kina aiki amma a kasa taimaka miki lokacin da ki ke cikin matsala ki yafe
mana","dan Allah Alhaji ka daina roƙona","dole mu roƙeki muddin baki yafe mana ba
sai Allah ya miki sakayya babba akanmu",da sauri tace"na yafe muku duniya da
lahira","to mungode yanzu kina da mane mi","a a Alhaji kowa guduna yake","ba komai
amma zaki auri duk wanda na kawo miki",sadda kai tayi cikin kunya ta kaɗa kai"shike
nan waye yasan gidan ku anan gidan","daga Aunty Babba sai Murtala","shikenan jeki
amma tsaya ta kawo miki saƙo ki kai gidan naku",tana ta godiya yaja hannuna muka
wuce tana binmu da kallo,muna shiga ya wuce wajen locker ya jawo ta saiga uban kuɗi
a ciki ya za ra sannan ya miƙo min"kai ma ta"banyi mamaki ba ko na tsaya tambaya na
karɓa na kawo ma ta hannunta na rawa ta karɓa sai zuba godiya take ta tashi ta fita
kamar zata kifa,kaɗa kaina kawai nayi na wuce da gudu na ƙarasa na faɗa kansa"kai
Babban Yaya kai ɗin na daban ne"rungumeni ya yi yana sumbatar bakina"to miye
amfanin kuɗin sabida irinsu Abba yabar min kuɗin",hancina na shiga goga masa a
fuska"Allah to ya haɓaka ta ta ninka haka sau malala gashin tinkiya",zaro ido ya
yi"sai muyi ya ya da ita kuma","muyi ta rabawa mutane mana","haka ne to yanzu ya za
ayi kenan wa ki ke ganin za'a haɗata dashi aure agidan nan",zugum nayi ina kallon
fuskarsa"kaga dai mu a yanzu a gidajan mu ba bu wanda ya isa aure kuma ba za'a yiwa
ƴan uwana kishiya ba sai a ma'aikatan gidannan ka nemi wani,yauwa ga Muryala ko
Sabitu",murmushi ya yi yaban hannu muka tafa"Sabitu bai daɗe da aure ba amma
Murtalan zamu tuntuɓa ko tare ma zamuje amma sai da yamma zamu bakin get neman aure
ko",dariya na shigayi yana bina da kallo hannauwana ya haɗa ya riƙe"komai ki kai
kyau yake miki tawan",kumatunsa na riƙe ina jijjigashi"kaima haka Sweet
Yaya",kwanto da kaina ya yi jikinsa yana shafa bayana da haka na koma bacci shima
haka.
Babu jimawa da kwanciyar mu sai ta tashi ita kuma wanka tayi tai sallah ƙarfe
goma dan iskanci,wasu ƴan iskan kaya ta saka rabi sutura rabi tsirara ta dawo falo
ta zauna dama yau ba ai break ba tun jiya tacewa Sadiya kar tayi dan haka tea kawai
ta hala dama ya kawo kayan snacks su ta ɗauka taci ta ƙoshi ta ware kiɗa tana sha.
Munfi awa biyu muna baccin sannan muka farka a tare banyi sanyar komaiba na
sauya riga zuwa iya gwiwa silki ce dan haka komai nawa ya fito ba ko ɗan kwali zan
wuce kitchen na ganta kwance tana kaɗa kai"Hiii" na faɗa ma ta na wuceta tashi
tayi,kutumar wannan yarinyar ita zata gaisar a haka wato jiya ganin idon mijinta ne
yasa ta nuna ma ta ladabi hunnm zata riƙeta ne,ta maida kanta ta kwantar,sai gashi
yafito cikin suit ash colour sun masifar karɓarsa ido ta zuba masa kamar zata
cinyeshi dan ya tafi da ita,a kusa da ita ya zauna ya ɗau remort ya kashe kiɗan da
yake shiri take nema sai batai magana ba ma ta shiga gaisheshi ya amsa yana kallon
ƙofar kitchen ɗin sannan ya kalleta ya kalli flat da cup har biyu sai ya kalli
dining baiga komai ba kaɗa kai kawai ya yi wato tana sane tai hakan kamar zai ma
ta magana sai ya barta ya manna ma ta hauka dan ita kanta ta zata zai yi magana da
baiga break fast ba a dining.
Ni kam arish na fere na soya sanna na soya ƙwai mai albasa na gasa snacks
ɗin daya kawo na haɗo tea mai kayan ƙamshi cup biyu na ɗakko a babban tire na fito
da sauri ya taso ya karɓa yana kallon me nayi daɗi ne ya kamashi ya aje a nan ƙasa
ya jawo hannuna ya zauna dani ba wani sanya ya shiga bani abaki"ci da hannuna na
jinjina miki"dariya kawai nayi na ɗaga ma ta hannu ta gabzan harara na janye idona
akanta har muka gama tana binmu da kallo da kansa yakai kwanukan kitchen ya
dawo"zan fita ni bayin Allah",da sauri na miƙe"adawo lafiya Babban Yaya Allah ya
tsareka ya kare min kai a duk inda ka ke","ameen ameen Nana",ya juya ya fita nazo
wuceta ta makan harara na shareta na wuce,ɗakin na gyara tsaf sannan na dawo na
zauna ba jimawa na fito falon na wuce kitchen na fara haɗa me zan dafa rasa me
zanyi nayi kawai na hau dambun kuskus dana akwai komai a gidan hayaniya naji ban
kula ba dan nasan da alama baƙi tayi nafi awa biyu ina abu ɗaya sannan na gama na
jiye a babbar coler sannan na fito zan wuce zuuuuu suka min da ido ta tafasa bance
musu ba na wuce wata ce daga ciki tace"Hajar ashe a shema kishiyar taki ƙwaila
ce",shewa sukai suka tafa tace"gata nan dai abin basu nuna ba amma a haka ake nuna
min ansan komai kuma anyi komai",wallahi harzan kulata sai nafasa nayi niyar wucewa
ɗaki naji sallamar Ya Rumana da gudu nabtaho na rungumeta"oyoyo Yayata",itama
oyoyon take min na karɓi kayan hannunta ta ƙarasa shigowa"baƙi kukaita faɗa tana
kallonsu cikin murmushi mugunta na dubesu nima nace"eh Ya Ruma ƙawayen Aunty Hajara
ne gasu nan komai ya nuna amma basu kai inda za'a mora ba",wani irin juyowa sukai
suna bina da kallo dai dai da ita ƙawar tasu ta kasa magana har muka wuce Ya Ruma
na ƙunshe dariya dan ta lura kamar ramuwar gayyace tafi ta gayya zafi,muna shigewa
ɗaki auka juya suna dubanta"ke dama wannan yarinyar haka take bata da
mutunci",dakatar da ita ɗayar tayi"wallahi kome ta muku ku ku ka tanka dama wannan
a fitsarun da ganint bazata bar kota kwanaba",su samu suyi maganar amma ɗayar ta
hanasu dole sukai shiru,akan sofa Ya Ruma ta sauka tana faɗin "wash","sannu Ya Ruma
ɗan nan namu na gaskiya yana gasa ki","soya ni dai Nana ni kaɗai nasan me nake
jikina buɗe ga kayanki nan blander ku dai na niƙa komai ko","eh kusan kai bakwai
ne da ita","to shikenan yanzu kwaso ta da kayan aikin ki muyi abinmu anan"to,nace
na wuce ta gabansu basu tanka min ba na ɗakko abinda tace na dawo a nan ɗakin ta
haɗa komai ta juye min a babban bokiti nasa a frig sannan na kawo ma ta kayan motsa
baki muka hau hira dan tace bazataci abinci ba,har akai la'asar muna tare sai bayan
ta ta tafi amma baƙin Aunty Hajara na nan,ban kulasu ba na wuce ciki na shiga wanka
na fito na shirya cikin riga da siket na atamfa kamar ajikina aka ɗinka su nayi
kwalliya na baje gashina a bayana na sha humra mai tada hankali na fito bina sukai
da kallo suna dariya"maga me za'a shiryawa mijin bayan mun cinye abincin"ta tafasa
bance musu ba na wuce abina cabinet na taka na ɗakko coler dana ɓoye dan tabbas
saida na aiyana za ai min haka fitowa nayi da ita da kifin dana soya shi dama a
locer nasa ban bari inda za'a gani ba,baki suka saki ganin ina shirya abincin
kallon juna sukai ni kuwa sai waƙa nake "anzo gidan ƙawa an wuni",harare harare
suka shiga yu,ba jimawa sai gashi ya shigo sallamarsa naji na fito da gudu daga
kitchen na ɗaneshi da sauri ya riƙeni yana dariya"saiki faɗi Nana",murmushi nayi na
ɗora goshina akan nasa"muddin kana kusa nasan bazan taɓa kaiwa ƙasa ba",dariya ya
yi abinda basu taɓa gani ba ƙawayen mamaki ne ya kamasu sauka nayi na kama
hannunsa"zo muje kaci abinci nasan yunwa ka ke ji kayi wanka daga baya","yanda ki
ka ce tawaje na",har dining na kaishi ta tafasa baice ma ta ba ita da ƙawayenta
fitowa nayi zan ɗakko ruwa naji sunce"anya kuwa wannan kishiyar taki yarinyace ni
ban yarda yarinya bace bata shekare a ciki ba kuwa sannan aka haifeta",a fusace na
juyo ina ma ta kallon baza ita mai maganar nace"shakaruna arba'in a ciki sannan aka
haifoni kinga yanzu shekarun mu ɗaya dake kenan harma da Aunty Hajaran",a hautsine
ta miƙe tayo kaina"nice shekara arba'in ɗin a gidan uabanwa nayi kama da me
shekarun nan","haba Aunty Hajara kinyi mana komai naki fa na ƴan da ne ko baki
luraba kishin na ƴan 1939 ki ke"wani irin dunƙule hannu tayi nai ma za na ture
ƙawarta na gudu wajen Babban Yaya na ɓuya,kallon ƙawayen nata tayi"ku fitar min nan
jakai kawai",haushi ne ya kamasu suka ɗauki jakunkunan su suka fita,ɗaki ta wuce
kamar zatai hauka,fitowa nayi a bayansa ina dariya kai kawai ya kaɗa"Allah ya
shiryeki Nana","ameen Babban Yaya"abincin ma ɗaki nakai naja shi muka gudu.

******
UK

Dama Hajiya Fulera tasan mutane masu yawa a UK hakan yasa ta tura kuli maƙudai aka
sama ma ta muhalli acan kosa ta isa bata sami matsalar komai ba.

*****
Hajiya Harira kuwa ai sun zama kamar mahauakata sai kuka da dana sa ni take amma
su Hajiya Salma damuwar su bata kai haka ba dan su suna da kuɗi kuma ƴan harƙalla
ne amma ai wadda ta kwasa ta wajensi ko kaso ɗaya bisa ɗari batakai waccan ba,amma
ba yanda suka iya sai dai su sukasan me suke ji a zukatansu.
Da magariba da Babban Yaya mukaje bakin get muka sami Murtala yana ganin mu
ya taso"rankai daɗe sai ina","wurinka mukazo","to rankai daɗe Allah yasa ba laifi
nayi ba","bakai komai ba kana da aure kuwa",baki ya kama"ina dashi yallaɓai","to
zaka iya ƙarawa in na maka matar","da gudu ma kuwa rankai daɗe","madalla ɗan ina ne
kai","Gezawa yallaɓai","ok to kasan yarinyar nan mai Hajara aiki Sadiya","eh
yallaɓai","to gobe zamuje ka nemi auranta kafin muje garinku mu faɗawa ƴan
uwanka",zubewa Murtala ya yi a wurin"nagode nagode yallaɓai","tashi mana sai
goben"mukaar wurin sai godiya yake.

UMMU SADDIQ 🌹🌹🌹🌹


😀😀😀😀
🌈🌈🌈
🌈🌈
🌈

Babban Yaya Free ne amma me so ya biyo ni Pc in sa a group don shagalin Nana


na buƙatar comments.
08146711395

27

Daddare Alhaji Baffa yasa aka kira masa su Hajiya Harira sai kuka take har
zazzaɓi ya kamata,da yara huɗu an mata haka ta shiga uku ina ta kama ba uwa ba
uba,kwantar musu da hankali ya shiga yi amma ina saima abin ya yi kamar turasu ake
ba yadda ya iya haka ya barsu suka koma.
Iyyo kuwa ko a jikin ta dariya ma take musu,ta dubi Alhaji Baffa tace"wai
riɗa riɗa dasu amma an musu wayo,ranar da za'ayi rabon abun kuwa nunawa kowa sukai
kamar a kansu aka halicci wayo Hhhhhhhh",ta kwashe da dariya kaɗa kai kawai ya
yi"har yau kina nan da halinki A'i","wallahi Alhaji abin ne abin dariya","to ai
maganinsu kinga sun lura da duniya ko","hakane kam to Allah ya kyauta".
Daddare ko sau ɗaya bamu ganta ba saida ma na fito na haɗa tea ne naganta
nuna ni tayi tamin alamar duka ni kuma na taɓe baki na shige ɗaki"ke kuma ke dawa
ki ke taɓe baki",shagwaɓe fuska nayi na aje kofin na faɗa jikinsa,riƙe ni ya
yi"kinga ki daina min wannan dirar girma fa ki ke",dariya ce takamani"Babban Yaya
wallahi in kana magana kamar ba daga bakinka take fitowa ba",hancina yaja"ai za'a
faɗawa haka wannan ɗan bakin naki bansan a ina ki ka koyi magana ba in ki ka sako
zance sai na rasa me zance","ai bari kaji Babban Yaya niko in ina magana kawai ji
nake tana zuwa tare da wani nannaɗaɗɗen rashin mutunci",dariya ya yi"ai naga alama
kuwa ta wajena","Babban tea ɗin",ɗakkowa ya yi ya fara sha ina kallonsa"ya kai zaki
sha ne",kai na ɗaga ya miƙo min,kafaɗa na kaƙale na nuna bakinsa,murmushi ya yi
yazuba shayin a bakinsa ya kwanto da kaian ya ɗora bakinsa kan nawa ya juye min na
shanye da haka yasha ya bani har ya ƙara zan tashi ya janyoni na faɗa gado ya
kwanta kusa da ni zanyi magana ya ɗara bakinsa kan nawa ya shiga kiss na daban ƴar
rigar ma jefar da ita ya yi ya hau murza ƙirjina cikin wannan lokacin ya kansa a
wani yanayi da ranar ya jefa shi a wani hali da ƙyar ya samo kansa ni kuwa nayi
bacci tuni,saida ya yo wanka sannan yazo ya sa ni ajikinsa ya kwanta shima bacci ya
kwasheshi".
Washegari da farar safiya Mama ta aiko mana da kunu da waina naji daɗi sosai
dan haka muna gama baccin safiya muka karya sannan na shirya muka fita ita hajiyar
ma ko tashi batayi ba da Murtala mukaje har gidansu Sadiya ni na shiga sannan akai
musu iso cikin gidan yasha mamakin gidan ginin har ya sauka kamar zai faɗo amma
suna rayuwar farin ciki ba ruwansu,tunkan ya fara magana suka fara godiyar kuɗin
jiya,ba komai ya faɗa musu sannan ya fara maganar da ta kawo sa,sunyi murna sosai
kuma basu wani ja ba sukace ya turo sannan ya faɗa musu a gidan sa zata zauna ba'a
ko ina ba,murna sosai da tsalle suka shiga yi sannan yace Baban su ya samo masu
aikin gini a lissafa nawa za'a kashe a sauya ginin tunda gidansu ne in an gama
lissafawa a faɗama Sadiya ta faɗa masa,kuka Baban yasa yana godiya da wannan muka
fito sai shi mana albarka suke.
Nima a hanya kan kafaɗar sa na kwantar da kaina"Allah ya biya ka Babban
Yaya","karki damu yiwa wani yiwa kaine bari mu biya ta wani wuri ki siyo kayan
break fast saboda kinsan zan koma aiki kuma da wuri nake fita kinga kuma baa ɗkin
ki nake ba kullum ko","hakane nawan muje",kaya sosai na ɗebo na girki sai mamaki
yake a ina na sa ni wani glass na saida waya mukazo na turje ina kallon su sai
yarfe hannu nake,kafaɗa ta ya riƙo"kina so ne",da sauri na ɗaga kai,zugeshi ya
yi"ɗakko wadda ki ke so",da sauri na ɗakko wata kwankwaɗeɗiya mai cameras reras
karɓa ya yi"tayi kyau muje",tsaywa nayi"Aunty Hajara fa","wa ya ce miki tana
buƙatar waya wancan satin na siya ma ta wayar dubu ɗari uku taho nan",baki na
kama"kai kuɗi har haka","eh mana Nana ai ba bu itace ɓarna","hakane kam to Allah ya
rabamu da ita ya nesanta mu da ita","ameen ameen",kuɗi masu yawa ya biya a wurin
sannan muka dawo gida sabon kitchen ware naje can ɓangarena na ɗakko nazo wani ɗan
kwana na aje shi na jere komai akai,wayar ya haɗa yasa sim dama yana dasu sannan
ya kunna ya miƙo min,ihu nayi na rungumeshi tare da kiss na godiya juyo da fuskata
ya yi ya shigar da bakinsa nawa ya jima yana yanda yaso da dani ban hanasa ba,da
kaina na rakasa toilet na haɗa masa ruwan wanka na fito na barsa duk bana jin daɗin
barina da zai amma na share,yana fitowa ya shirya yaƙara fita,misalin huɗu na yamma
ya shigo gidan Aunty Hajara ansha wanka cikin material ga kwalliyar aljanun nan da
take tasha kuma nan har gida aka zo aka ma ta wai zata karɓi girki magunguna kuwa
tasha bila adadin wai yaji ta sama dani,da sauri ta tashi ta rungumeshi bai
gwasaleta shima ya rungumeta duk da yana kallona ban wani damuba ita da mijinta
hannu na ɗaga masa"sannu da zuwa Babban Yaya",murmushi ya yi ya gane bazan taso
bane,hannunsa ta kama zuwa ɗakinta sai dai ba'a saba ba da kansa ya yo wankan ba
kayansa a ɗakin hakan yasa dolenta tabarshi ya fito,ina kwance kan sofa naji
danshin ruwa a wuyana,ɗagowa nayi naga shine"lahh Babban Yaya ya ka shigo nan","ba
kayana acan shine nazo wajenki ki saka min",zaro ido nayi"ka koma zan raba kayan na
kawo ma ta nan ta aje amma yanzu kaje karta zargi wani abin",mamaki ya tsaya yana
yi ta ya akai nasan waɗannan matsalolin amma baiyi mamaki ba ta wani wurin dan
yasan aɓni akwai farin shige shige,baiƙi ta tawa ba ya fita ni kuma na tashi na
fara kwasar kayan ina ajewa agefe sai naga bazan iya ɗauka ba sannan na danƙo su na
fito ko gabana bana gani da ƙafa na doka ƙofar,suna ciki itafa yau mai miji sai
shafa masa jiki take bugun yasashi yazo ya buɗe dan yasan nice,ba riga a jikinsa
ta wani zo bayansa ta maƙalesa tsayawa ya yi yana kallon kayan kamar duka na ɗebo
haushi ne ya kamani"Aunty Hajara ki karɓa mana ko ki matsa ya karɓa dan in suka
zube ban ƙara ninkewa tabbas",harara ta tayi ta matsa konkunya bataji wai ita nan
zata nuna min duniyanci ne tana taɓa shi na gani naji haushi,dariya ya ɓoye bayan
ta matsa ya karɓa ni kuma na juya.

Da kansa ya shirya kayansa a sif tana kallonshi bata taya shi ba,bayan ya gama yasa
kaya ta taso shi a gaba zuwa dining flat taja zata zuba mai abincin ya riƙe
hannunta"bari na kira Nana tazo taci",a yanda ya yi maganar fuska ba walwala yasa
ta bar zubawar ya tashi shi kuma,ina zauna da waya na rasa ma ina zan danna dan iya
ba sama dariya da nake ta ma ta sai kace wani mutum,a bakin ƙofar ya tsaya yana
kallona"sannu mai waya",ɗagowa nayi ina dariya"bari Babban Yaya na rasa ina zan
danna",miƙo min ita nan na saita miki na baki wayata kuma ki kwashi numbers kamar
hauka dan kowa ina number sa",da sauri na taso na kawo masa"to taho muje kici
abinci",kafaɗa na noƙe"na ƙoshi ni sai dare zanci abinci","kin tabbata",kai na kaɗa
ina komawa ciki shi kuma ya fita da wayar,wallahi yunwa nake ji sosai bana so naje
saboda karna kashe ma ta karsashin da take dashi akan mijinta dan nasan tana ganina
komai zai lalace ma ta ni kuma bana son na ɓata ma ta tunda a gidan ta nake duk da
ita jawoni amma ba komai dai yana fitowa taga ba bu ni sai tayi murmushi yana
kallonta amma ya share madadin ta tambaye shi sai ta yi shiru shima haka,saida yaci
abincin sannan ya saita wayar ya shiga saka numbers yana savinga yanda zan
gane,ganin hankalin shi ba ya kanta saita ƙwace wayar"zan fasa wannan wayar in baka
maida hankalinka kaina ba","bani nan Hajara"tasan halinsa sarai saita miƙa masa ya
aje yana kallon ta"ina jinki","ka taso muje ɗaki to" tashi ya yi ya bita yabar
wayar a nan,basu jima da wucewa ba na fito ina sanɗa abincin na ɗiba na kwashe
naman na ɗau lemo a hankali na koma ɗaki ahi kuma dawowa ya yi ya ɗau wayar ya
ganni ina sanɗa kansa kawai ya girgiza a fili yace"Nana ba'a gane ina ki ka dosa
lokaci ɗaya" ya ɗau wayar ya koma ɗakin dan ya lura yau a wurin Hajara ya shiga
takwas ma ba uku ba.
Cinye abincin nayi na mayar da kwanon na dawo ina jiran waya amma shiru
gajiya nayi babu shi babu wayar na taso na fito ƙofar na ƙwanƙwasa amma shiru na
daɗe a wurin sannan ta buɗe ko kayan kirki babu a jikinta ni kuwa ba abinda ya
daman na kalleta tsaf"me miji aban waya ta ko",tana wani goge goshi ta koma ta
ɗakkomin shi kuwa gwanin ban gansa ba ma na karɓi waya ta nabar wurin,ƙwafa tayi
taso ace naji haushin abin da tayi batasan indai nice ba tayi da dutsen dala
Hhhhhh.
Ina zuwa na fara dubawa naga numbobi da yawa kira na shiga yi ina faɗar nayi
waya sai murna ake tayani na ɗebo lokaci mai yawa ban gama ba ana kiran sallar
magariba na tashi nayi anan na zauna da ƙur'ani na ina karatu har akai sallar isha
ba jimawa da idarwa nayi bacci a wurin.
Hajara kuwa ta hana shi sakat bayan sallar isha yaje ya siyo abinda za'a ci
amma tace ita zata kawo min bai hanata ba ya bata koda ta shigo ta gan ni ina bacci
saita aje tayi fitar ta tace masa ta kawo ranar kam an sha amarci ni ina can ina
bacci kamar matacciya baiyi tuanin banyi sallah ba saida ya dawo a masallaci rana
ta fara fitowa sannan ya shigo"innanillahi"ya faɗa yana yowa kaina da sauri ɗagoni
ya yi zuwa jikinsa"Nana kece a kwance a ƙasa kaicona wallahi",a hankali na buɗe
idona da sauri na yunƙura"wayyo wuyana",na koma yadda nake ba shiri,wuyan ya
dafe"sannu me yasa zaki kwanta a ƙasa"hankalin sa ne yakai kan ledar jiya"baki ci
abinci ba ma",shagwaɓe fuska nayi"bayan daga sallar isha nayi bacci daka kawo
abincin basai ka tashe ni ba",shiru ya yi cikin tsan tsar ɓacin raia yace"Hajara ta
kawo miki kuma tace ta baki kin ma fara ci","ƙila a baccin ta bani",kaɗa kai ya
yi"taso muje kiyi wanka ki gasa wuyan",da ƙyar na miƙe zuwa toilet ai shigo na
hanasa kuwa na rufe ƙofar saida na gasa kamar yadda yace sannan nayi wanka da
alwala na fito ɗaure da towel yama zaune gefen gadon nayi murmushi"au kana nan
bakaje ka kwanta ba","kwanciya kuma zoki sallah ni muje ki ɗumama abincin ki
kici",a gaban sa na shirya nai sallar ya taso ni gaba da ledar har kichen Sadiya na
ta aikin ta tana ganin mu ta matsa tana gaishe mu"nifa Sadiya ki daina gaishe ni
kinfa girmeni",dariya tayi"dole kuwa na gaishe ki ko yallaɓai","hakane mamana barta
kina gaishe ta amma kaɗan",duk dariya mukai na yake tambayar ta masu aikin sunzo
kuwa"eh sunzo ga takardar da suka ce a baka a kwai number wayarsu ma a jiki",karɓa
ya yi"to ya yi saura ke me ake yi in za'ai aure koda yake kema ki lissafa ki kawo
min takardar tunda ni ne Baban amarya in sai komai nawa da wuri ko Nanas",babban
yatsana na ɗaga masa"haka yake Babban Yayan na mutunci",ba shiri sukai dariya ya
yin da mamaki ya kashe Sadiya dama haka yake da sauƙin kai kodan yana gaban amarya
ne,wani baƙauyen ashar mukaji bagatatan da sauri na ɗago kaina na kalli Aunty
Hajara dan nasan sai ita shi kuwa ko motsi bai ba ya yinda jikin Sadiya ya kama
rawa,ƙarasowa tayi tana wani kama ƙugu"mai aikina ce take hira da mijina saboda
samun sake dan kutumar...",da hanzari nace"kai wallahi kar ki sa amana girgizar
ƙasa salon a kifemu duka dan tayi hira da mijin ki miye gani dai ba taɓawa a sarar
hannu",hannuwan ta ware tamin daƙuwa kamar wata ƴarta"ba komai Aunty Hajara kinyi
sa'a da Yaya Hasiya miye dan kin zagen ai ni ƴarki ce",da gudu tayo kaina kamin
kowa ya lura na shige ƙarƙashin dining ina dariya,shi ko kallon ta bai ba ma ya
cigaba da maganar sa da Sadiya tana bashi amsa a tsorace maganar taso ta fahimta
amma bata gane ta juyo garesu"me nake ji ne haka Habib",ina ƙarƙashin bencin na
rigashi magana"aure zaiwa mai aikin kuma ku zauna gida ɗaya kinga gaba takaita ke
kuma baya kuna aure gida ɗaya da mai aikin ki","zan kama ki Nana","in kin kamani ki
soya ni",shiru tayi danta lura saina haukata ta inta biyemin,"Habib kaine zaka ma
ta auren ina iyayen ta",bai saurare ta ba ya sakko a kan frig ɗin da yake"ina
jiranki Sadiya","to yallaɓai nagode",dungure ma ta kai tayi"shi yasa ake cewa kar
na ɗau ƴar aiki amma naƙiji",da sauri na katse ta"dama ki kai sa'a ke ba mijinki ta
aura ba drivern sa ne","NANA"ta faɗa da ƙarfi,dariya na kwashe da ita ya yin da
Sadiya ke ɓoye ta ta dan in ta yi ta taga banu,bazar bazar tabi bayansa zuwa ɗaki
amma yana toilet taɓa ƙofar tayi tajita a kulle dole ta zauna zaman jiran sa,tana
tafiya na fito na ɗauke abincin dana sa a oven da na ƙarasa haɗa tea ɗin sannan
naba Sadiya cup"haɗa ki fece wallahi waccan matar in ta kama ki saita daka
ki",dariya tayi"nagode ƙaramar Aunty","ki tsaya salo harta fito ɗauki ledar can ma
za ki kawo na ɗiba miki wannan snacks ɗin ki tafi dashi",da sauri ta kawo na kwashe
ma ta du na zuba ma ta madara da sugar da ovaltine nace"fece yasin dan na ma ta
ɓarna"tana fita nima na gudu inata dariya"naga me zaki ci yau".
Yana fitowa ta tare shi da masifa bai kulata ba ya cigaba da shirinsa maganar
ce ta ishesa ya aje cumb ɗin hannun sa ya juyo gareta"kuɗin ki ne?",shiru tayi"to
tunda ba kuɗin ki bane in ki ka ƙara min magana saina sauya miki kamanni dan ni ko
da asiri ba wanda ya isa ya hanani inyi alkhairi ina fatan kin gane dama kince Nana
taci abinci ashe bacci ma take sanda ki ka kai ma ta hakan ya ɓata min rai
sosai",yana kaiwa nan ya ɗauki ƴar saman rigar sa ya fito,wani irin tsaki tayi tai
wurgi da towel ɗin da ya aje ta zauna jaɓar tana dafe kanta",na gama kenan ya
shigo"uwar rigimammu me kuma ake ƙullawa naji ki shiru haka",tasowa nayi na faɗa
jikinsa"ina kewar ka Babban Yaya",rungumeni ya yi tsam"nima haka matata",ɗago kaina
nayi ina kallon sa na mai alamar kiss sunkuyo da kansa ya yi ya ɗora bakinsa kan
nawa biye masa nayi dan ina kallon ta ta labulen ƙofa wato matar nan laɓe ne aikin
ta ko bari na ma ta tsiya janye bakina nayi a nasa ina buga ƙafa da sauri ya saki
rigar ya riƙoni"me ne kuma",ƙirjina na nuna masa"ba tunjiya da ka barsu ba aukw
ƙaiƙayi",wani kallo yamin yana murmushi"cire ma za na kauda wannan ƙaiƙayi bayana
na juya shi kuma yana facing labulen hannun rigar na sauke ko kunya banaji na matsa
jikinsa hannun sa biyu yasa ya shiga murzar su yanda yaga dama,ba shiri ta matsa a
wurin tana mamakin yanda gaba ɗaya ya ruɗe ya rasa ma ina zaisa kansa daga taɓa ƴan
waɗannan a bubuwan a wurinta kuwa sai dai ita ta ruɗe shi kuwa ko gezau ba ya
yi,mun share mintuna a haka sannan nace sun daina ya barni yana lumshe ido ta
bayansa na kwanta na zagaye cinkinsa da hannuwa na bule idon ya yi"zaki bacci
ne",kai na ɗaga janye ni ya yi ya tashi"zoki kulle ƙofar ki ni zan wuce office",bin
bayansa nayi na kulle na dawo ina tsalle da rawa na maida rigata na janyo waya ta
na shiga kiran Ya Nabila.

😀😀😀😀😀

UMMU SADDI'Q CE 🌹🌹🌹🌹


🌈🌈🌈
🌈🌈
🌈

Babban Yaya Free ne amma me so ya biyo ni Pc in sa a group don shagalin Nana


na buƙatar comments.
08146711395

28

Jama'a kwana biyu fa Aunty Hajara na neman yanda zata ɓata min ta rasa komi tayi
saina maida ta mahaukaciya kona maida ma ta da ɓacin ran kanta gaba ɗaya ya rasa ya
zata yi dan haka yau saita kira yayarta ta faɗa ma ta meke faruwa shawara ta ba ta
kuma ta ɗauka,gashi kuma yau girkina ne.
Tun da safe ya faɗamin zaiyi baƙi hakan yasa na tashi tsaye kamar wata uwar
mata na haɗa masa abinci mai kyau bayan sallar magariba ya shigo na zata ma zan
gansa da baƙin sai naganshi shi kaɗai wanka na rakasa ya yi"Babban Yaya ina abokan
naka fa","suna gidan da na sauke su yanzu zan kai musu abincin amma fara ba ni nawa
naci dan yaunwa nake ji",dariya nayi na kama hannunsa zuwa daning sannan na kira
Aunty Hajara ta fito tana yanga da yauƙi"Habibe welcome"ɗago kai ya yi ya
kalleta"baki iya hausa ba",hararar sa ta yi kaɗan shifa wannan gayen ɗan latsin
rainin wayo ne"sannu da zuwa to","yauwa ya gida",wani taɓe baki ta yi"gashi nan dai
ba daɗi in baka nan kasan kaine sinadarin gidan","madalla to"daga haka yay shiru ba
haka taso ba sotai ya biye ma ta suyi ta maganganu,ni kuwa ko a jikina abinda ta
yi,tavriga kowa zuba abincin sannan na zuba masa naja gefe na zauna,kallona ya
yi"ke baki ci ne",kai na kaɗa"naci dana gama ai",maida kansa ya yi kan abincin ya
ɗiba yakai bakinsa ba zato ba tsammani wani azababban gishiri da mugun yaji ya
kaiwa kwanyar sa ziyara a take ya fesar da abincin bakinsa nan da nan idanuwan sa
sukai ja ya ahiga tari baji ba gani da sauri nayi kansa"Babban Yaya lafiya"kafin
kace me hawaye ya wanke min fuska ruwa na bashi yasha sannan tarin ya lafa,amma duk
ya yi wujiga wujiga,sannu nake ta jero masa sai dai ko ɗaya bai amsa ba,wani kallo
ya ɗago yamin wanda yasa cikina ƙugi sarai nasan Babban Yaya bai iya fushi ba
sunkuyar da kaina nayi kawai gabana na faɗuwa,itama ci tayi ta furzar da sauri"Nana
wane irin abinci ne wannan yaji da gishiri kamar zasu fasa ƙwaƙwalwa"ɗagowa nayi a
fusace na ce"ke ce ki ka zuba yaji da gishirin ko amma ni dai nasan ƙalau na gama
abinci na s...."tass naji saukar mari a fuskata ɗagowa nayi da sauri naga Babban
Yaya a tsaye kamar zai rufe ni da duka dafe kuncina nayi na fashe da kuka,tsawa ya
daka min saida na tsorata"rufe min baki mara kunya ta faɗa miki gaskiya ne zaki ma
ta rashin kunya",cikin kuka na ɗago kaina nace"wallahi banyi abincin nan da yaji ba
bansan ya akai yaji da gishiri suka je ba",tass ya ƙara min wani"to ƙafa garesu da
zasu kenan"tashi nayi da gudu ina dafe fuska ta na wuce ɗakina gado na faɗa na
shiga kuka dan abin yamin ciwo ba marin ke damuna ta ya akai gishiri da yaji yaje
cikin abincin da naci ɗazu amma banji ba a sannan sai yanzu ga abincin da yawa
kenan sai dai ayi a sara kuka sosai nake har kaina ya shiga ciwo ba ƙaƙƙautawa amma
naƙi shiru,Hajara ce ta tashi tazo inda yake ta shige jikinsa"kayi haƙuri Habibe
kasan yara a hankali zasu gyara kaga abinci can nayi su Yaya sunce zasu amma sun
fasa sai jibi ka kai musu kawai shima da yawa",godiya ya ma ta sannan ta rakashi da
kwanukan mota ya fita,banji sanda ta shigo ba sai dai naji maganar ta a kaina"ya
dai manyan mata ta ya a kai haka ta kasance ne,ko da yake na faɗa miki karki
kuskura ki haɗa sabga da ni amma kinƙi ji to kisa ni da irin waɗannan salon sai kin
gudu da ƙafar ki kinbar gidan nan",ina daga kwancen na go ge fuskata sannan na ɗago
fuskata duk shatin yatsun hannun sa,wani kafirin murmushi na ma ta na shafa
fuska"kece baƙuwar kiga Babban Yaya ya dake ni to bari na baki wani labari Babban
Yaya harda belt ɗin injin markaɗe ya dake ni ya zane ni da bulalar dorina a
makaranta gaban kowa ke a titi Babban Yaya ya mazge ni amma bari kiji wata sabuwa a
gaban Mama Babban Yaya ya durƙusa ya ba ni haƙuri dan nayi fushi dashi,wannan marin
kuma da yamin gyara ne in baki sa ni ba kinga ya nu na in nayi abu in na lura
saboda miyagu,sannan kisa ido ki baje kunne zakiga ya zata kaya a gidan nan
tsakanin ni dake na miki alƙawarin saikin daka yajin da yafi na farkon aure ne da
kikai kin ƙara nufar gidan ku kuka kuma wallahi sai kinyi goman nawa ai ni nan da
ki ke gani sau ɗaya ake nasara akaina ba na barin ayi ta biyu saboda ni ɗin ta
musamman ce kinyi da ƴar halak uwargidan Babban Yaya ko ba komai kin nuna min insan
zaman da zanyi dake ni da na zauan Gwaggo Asama'u birnin masifa duk duniya nita
tsana kamar ance ma ta nice ajalinta amma Allah bari kiji da ƙanwar gyatuminki na
ma ta tarko saida ta kirani da ƴar albarka kinga ƙanwar ubana ce amma da daga mayya
sai shegiya take kirana kinga kuwa ke ba komai bace,fitar min a ɗaki tunda ba
kiranki nayi ba ko billahi in miki sharrin da har ki mutu bazaki manta da ni
ba",tun da na fara magana tayi zuru tana kallona kunsan ni mutum ya faɗi ɗaya na
faɗa masa tamanin ne,ƙala ba ta ce ba ta fita dai tana dariya batasan na ganota ba
yaƙe ne take.
Ina idar sallar isha na samu nayi wanka da towel ɗin na kwanta hawaye nabin
gefen ldanuwa na ga yunwa inaji amma na kasa cin komai,sai wajen goma kuwa ya shigo
sanda ya shigo gidan tasha wanka ta matse cikin kayan bacci fan ɗarin ka tsirara
kome take tunani oho da hanzari ta shi ta rungumeshi jansa kujera ta yi ya zauna
tana ta shafa shi sai niyar kiss take masa,gajiya nayi da kwanciyar gudun kar yunwa
ta lahanta ni yasa na tasho a haka na fito dan zuwa kitchen in samo ruwan ɗumi ko
tea nasha,fitowa ke da wuya na gansu amma sai na ɗauke kaina na wuce ita ta ganni
shi kuwa saida na shiga kitchen ya ganni ruwan ɗumi da kullum yana buta shi na ɗiba
a bakin ƙofar na tsaya na goge hawayen fuskata sannan na fito na koma,tashi ya yi
yana ma ta saida safe kan tayi magana ya wuce,tsaye nake ina zuba madara a ruwan
ɗumin dana ɗebo ya shigo da sallama da sauri na aje kofin na go ge hawayen fuskata
na juyo da murmushi a fuskata"sannu da zuwa Babban Yaya",wani irin sanyi jikin sa
ya yi rigar ya jefar a ƙasa ya nufoni,da hanzari na juya wani irin hawaye na sauka
a kumatuna duka hannuwan sa yasa ya rungumo ni jikinsa wani irin zafi yaji a jikin
nawa ya lumshe ido,kuka mai ƙarfi ne ya ƙwace min na rufe idona na shiga reroshi
kamar raina zai fita,juyo da ni ya yi ya rungumeni sosai"am sorry Nana nayi kuskure
ki yafe min"kwantar da kaina nayi a ƙirjinsa jikina har rawa yake wani haushin
kansa ma yaji yana ji ta ya akai kawai ya mareta daga ɗan kuskure kuma ma ai tayi
ƙoƙari da ta iya yunƙurin girki mai yawan haka,ɗaukata ya yi cak ya aje akan sofa
share fuskata ya yi da hannunsa sannan ya ɗakko kofin yazo gabana ya durƙusa da
kansa ya shiga ba ni tea ɗin ina sha ina kuka kaɗan nasha na kauda kaina na janye
hannunsa daga gabana"ina baki ƙoshi ba kinga fa jikinki na rawa kuma yunwa ce","ni
na ƙoshi"na faɗa cikin kuka aje kofin ya yi ya tashi tsayi ya ɗau key zai
fita"Babban Yaya ina zaka je","zan samo miki abinda zakice ne bazan iya jurar ganin
kina haka ba saboda yunwa",tasowa nayi nazo na kwanta a bayansa na zagaye cikinsa
da hannuwana"karka fita miye amfanin abincin gidan zan dafa naci ka raka ni
kitchen",aje mukullin ya yi ya kama hannuna muka fito da sauri ta koma ɗakin ta
tana haki"kaga shegiyar yarinya na zata zatai fushi tamai rashin kunya ya koreta ko
kuma ya dawo ɗakina mistttt wannan ƴa ko mayya wallahi" .
Muna shiga na fara haɗawa indomie kayan ƙwalam sannan na ɗorata kome nake
yana ta bina da kallo amma ni ban kalle shi ba ko sau ɗaya,jingina nayi da sink nai
shiru kafaata ya dafa ya juyo dani zanyi magana ya sunkuyo ya ɗora bakinsa kan nawa
wani irin sumbata ya shiga masa yana tura hannunsa kicin gashin kaina saida ya gaji
dan kansa sannan ya zare bakinsa a nawa nai saurin juya masa baya ina goge hawayen
dake zuba,lumshe idon sa ya yi ya dawo gabana ya kama hannuwa na ya durkusa
gwiwarsa a ƙasa"ki yi haƙuri please mana *RAYUWA TA* nima durƙusawa nayi na faɗa
jikinsa ina sakin kuka"kayi haƙuri bazan ƙaraba wallahi bansan ya akai haka ba amma
zan kula a gaba",ƙanƙameni ya yi yana shafa kaina"baki min komai ba kuma nayi
kuskure dana mareki amma zaki rama ai ko?",dukansa na shiga yi"ni bazan rama in
mari mijina ko naci masa kwala sai ka ce jaka".
Da sauri Aunty Hajara tabar ƙofar kitchen ɗin tana kama baki ranta in ya yi
dubu ya ɓaci kenan ita yarinyar ke nufi da jaka.
Tashi nayi ma za nayi ina sauke indomie sannan na soya ƙwai mai yawa suk
yana kallona a tire na ɗora ya ɗakko da kansa muka fito zuwa ɗaki tare muka ci yana
ta lallaɓa ni kamar ƙwai shi ne kawai ya yo wanka sannan yazo ya ɗaukeni cak ya
kashe glope ya kwanta yana janye towel ɗin jikina zallana na kwanta a
jikinshi,ganin ba haske yasa a dole tabar window ta koma ɗakin ta,amma ta kasa
bacci ta rasa ina zata kanta dan baƙin ciki.

Washegari kan ta tashi ma ya fita dan yana da aiki tunani ma yake zaije india
ne dan akwai taron da yake so suyi na nasarar da suke samu.

Wanka na ɗauka na tsuke cikin jeans pencil da wani ja mai kyau da baƙar riga ko ƴar
cikin ma ban sa ba ɗaure gashina nayi na fito da kwanukan da nama Babban Yaya break
tun da farar safiya,fitowa ta ke da wuya muka haɗa ido da ita na aika ma ta wani
musulmin murmushi na wuce ina ce ma ta"kin tashi lafiya",jefo Ni t yi da filon
kujerar hannun ta"ta ina zan zauna lafiya ina tare dake shegiya ƴar bariki",ban
kulata ba saida na kai kwanukan ma dawo na tsaya a gabanta cak na kama ƙugu"wai me
ki ke tunani Aunty Hajara inji haushi dan ya daki halalin sa in ya dawo na masa
hauka lala mu namu salon fushin shine wanda ki ka gani jiya bama hauka amma sai an
kai gwiwa ƙasa a kan mu kinga kenan salona daban ne dan haka ki bi ni a hankali
madam Habib"nai wucewa ta na barta,tsaki ta yi"zanyi maganin ki ne salon naki sai
ya gudu ya barki ƴar ƙarama dake sai kaɗiri fere",kome take faɗa ina jinta amma nai
shigewa ta ɗaki na gyara shi tas sannan na kwanta kan sofa ina dan na wayata kira
ne ya shigo naga Babban Yaya na da sauri na ɗauka"Babban Yaya namu na
mutunci",dariya ya yi"ya ki ke","lau nake kaifa","lau ba lau ba","meya same ka na
faɗa cikin shagwaɓa"kewar kyakkyawar matata nake","to ka dawo gida mana","sai
anjima akwai abubuwan da nake settling ne","to Allah ya yi jagora ya bada
sa'a",kiss ya min ta wayar nima na masa mai ƙara yana dariya ya kashe.

Bayan kwana huɗu ya fara shirin tafiya india dama bansa rai ba da dai matarsa
ne saida sukai kaca kaca sannan ta haƙura,sosai Ya Rumana ta shiga tayya ni masa
shiri kayan ciye ciye kala daban daban na masa shi kansa da ya gansu yaji daɗi
sosai ana gobe zai tafi ya shigo gidan da kaya a hannunsa kuma abin takaicin wurin
ta shine kwana na ne ba yanda zatai dole ta bar min shi,tun magariba na saka abuna
a ɗaki ina kuka yana tsaye riƙe towel a hannunsa ya juyo ya kalleni"wannan kukan
naki fa na iskanci ne na sa ni",tasowa nayi na faɗa jikinsa"to in tafi ba waɗannan
zasuyi tamin ƙaiƙayi ba",hannunsa ya ɗora a ƙirjina"daga yau in muddin ba ana gobe
zan dawo ba kar ku kuma ma ta ƙaiƙayi zan saɓa muku",yanda yake yi ne yasa ni
dariya ba shiri sura ta ya yi muka faɗa gado yana ina samansa bakina ya laluba ya
ɗora nasa wani zazzafan kiss na shiga karɓa mai haukata kwanya,a ranar kuwa sunci
ubansu bakina har wani zugi yake kuma duk leƙen da take bata gano komai ba dan
dinɗin yawa ɗakin yau.
Tun safiya na haɗa masa break ya karya ina ta binsa sau da ƙafa kamar tare zamu
tafi daman kayansa sunyi ready a mota tuni yana gamawa nace"to ka yo ma ta sallama
mana a bata kulawa sosai yadda bazata damu ba in baka nan ai kana da sauran wajen
awa biyu tunda sai tara zaku tashi ni bari na jiraka a gida",nasa hijabina yana ta
bina kallo"ka taso mana"tare muka fito na wuce ƙofa ina ɗaga masa hannu"kayi komai
fa ni na yarje maka"na fita ina dariya,kai kawai ya kaɗa yana jin wani irin sanyi
a ransa,tana kwance tana kuka ya shiga tana ganin sa ta tashi ta rungumeshi tana
sumbatarsa biye ma ta ya yi ta yi mamaki sosai ganin yanda ya biya ma ta buƙarta ba
tare da damuwa ba,bata biyo shi ba shi kaɗai ya ƙaraso ban nu na komai ba na fito
zamu rakashi motar da ya shiga na shiga tun da banyi kukan ba sai yanzu shi kansa
dariya ya shiga yi sannan yace"ki nuysu mana kiji zan ɗora miki wani nauyi zaki
iya"shiru nayi ina kaɗa kai,wani chek ya ɗakko ya yagi uku yasa hannu sannan ya
bani"ga waɗannan ki riƙe da kyau ki ɓoye karki bari fa wani ya gani nayi magana da
masu aikin gidan su Sadiya zasu zo gidan nemana duk kuɗin da suka ce za'a kashi ki
rubuta kina cirowa da wannan chek ɗin ki basu,duk abinda Sadiya ke nema kuma kuɗin
ɗakin ki ai kinga nake ɗakkowa kina ɗauka anan ki ma ta amfani dashi shima Murtalan
na sallameshi kema in zaki amfani da kuɗi ko zaki bawa wani kina ɗauka kanki tsaye
Hajara ma na sallameta dan haka ki kula da kanki banda tsokana kinji na yarda dake
ne shi yasa na barki a gidan tare da ita,sannan akwai leda a ɗakin ki ƙasan mudubi
ki duba miye a ciki duk a binda ki ka gani ki kirani kawai",a kafaɗar sa na kwantar
da kaina"duk zanyi abinda kace Babban Yaya Allah ya tsare ya bada sa'a",kaina ya
ɗago"ameen Nana ta kina min addu'a kinji",kai na ɗaga masa ya sunkuyo da kansa ya
min kiss a baki,dai dai motocin na tsayawa tare muka fito saida ya shige ciki
sannan muka koma mota sai gida ban tsaya ko ina ba na shige cikin ɗakina na ɓoye
chek ɗin da ya bani sannan na ɗakko ledar da ya faɗa ina buɗewa na buga tsalle na
kwaɗa ihu uniform ne a ciki kala uku da sandals uku da jaka sai littafaina da text
books wani kati ne aciki na ɗakko na duba anan naga makarantar mu ce ai rawa na
shiga yi nai ma za na kira shi dama bai shiga jirgi ba ya ɗaga"yadai ƴar
makaranta","wayyo Babban yaya nagode nagode Allah ya maka a binda kamin","ameen
Nana kikula sosai banda wasa banda ƙawaye barkatai ki faɗa musu ke kina da aure ba
kowa ki ke kulawa ba","shike nan Babban Yaya Allah ya kare ka","ameen Nana zan kira
ki"tom, nace na kashe na aje ina faɗawa kan kayan,tashi nayi da aauri na ɗakko
dutaen guga na tuɓe kamar zanyi dambe na go ge su tas sannan na fito"Aunty Hajara
sai ina kuma",juyowa tayi tana hararata"inda ki ka aiken can zanje ƴar rainin
wayo",taɓe baki nayi"ni na fasa aiken koma to",filon kujera ta ɗauka ta jefo ni
dashi"shegiyar yarinya mai kama da mutanen farko",cafe filon nayi"a dawo lafiya a
yo min tsaraba ko na ada tsiya","uwar tsiya zaki tada"tasa kai ta fita,nayi dariya
kawai na wuce kitchen doya mai yawa na fere na dafa sannan na soya ta da wai na
cika kula wanka naje nayi nasa doguwar riga da gyalen ta na ɗau kulata na rufe
gidan na kamo hanyar gida.
Hayaniya na jiyo a falon Mama na nufi can da sallama na shiga,da sauri na aje
flas ɗin na an taya kansu ina ihu dariya suka fashe da ita"Allah ya shirye ki
Nana","Aunty Fatima amma yanzu ku ka zo naga ban daɗe da tafiya ba","yanzu muka zo
yau zamu koma kuma hanya ce ta biyo damu kaya muka zo saya nan da wata huɗu za'ai
bikin ƴan mata huɗu a gidan mu amma duk zaku zo ko","sosai ma kuwa"na juya ga Aunty
Mamaa tashi nayi na faɗa kanta"Aunty Mama zan koma makaranta",da sauri ta
rungumeni"da gaske ƴata","eh wallahi ya siya min komai ran monday zan fara zuwa
kinga ai gobe friday basai naje ba","hakane Allah ya bada sa'a to","ameen Aunty
Mama ta",anan gidan na wuni sai yamma na koma bata dawo ba banji tsoro ba nai
zamana ni ɗaya har dare ya yi shiru bata dawo ba kulle ko ina nayi na koma ɗaki nai
addu'a na kwanta a buna dan na kirashi ba ta shiga ba.
Washegari da safiya ya kira ni da sauri na ɗauka na rushe da kuka,daga can
lumshe ido ya yi"yadai sweet Nana","nayi kewar ka fa sosai","nima haka matata amma
da fari ki daina kukan nan tukunna kashe na kira ki vedio call",da sauri na kashe
na tashi na tashi na sauya riga zuwa halb best na kunce hashina na gyara kwanciyata
a kan gado saiga kiran ya shigo da sauri na ɗauka"Hii Husband",lumshe ido ya
yi"Hello wife kinyi kyau sosai"murmushi nayi namai kiss",ba shiri ya yi dariya"Nana
ta takaina","Babban Yayana na kaina ji nake kamar na biyo ka","in kin biyo ni me
zaki min madam Habib",tashi na yi zaune na janye gashin dake ƙirjina"sosa min su
zakai kaga ba suji maganar ka ba jiya hana ni bacci sukai",dariya ya saka ba
shiri,turo baki nayi na maida kaina na kwanta saiga hawaye sharr"shiiiii yi shiru
mana matar ai da wuri zan dawo bazan daɗe ba kamar da kiyi ta tar ƙaiƙayin
ki",dariya nayi"au dama ana tara ƙaiƙayi","eh mana in ma ba'a ayi za'a fara daga
daga kanki","to shike nan yimin waƙa sai nayi shiru ko kuma nayi ta kuka","karki
kuka My Madam buɗe kunan ki da kyau",kamar wasa Babban Yaya ya shiga rera waƙar
Aisha ina ta dariya mun dale muna vedio call sannan ya kashe sai naga kamar tare
muke tashi nayi na gama aikina na fito falo Sadiya na shara,kallon ta nayi"uwar
mutane dayawa ashe kin shigo wa ya buɗe miki ƙofar","Hajiyar ki mana"ta faɗa tana
ɓoye dariya,kama baki nayi"Hajiyar su dai"yauwa in kin gama kizo muyi magana","to
Aunty",duka nakai ma ta"wallahi ni ba Aunty ki bace ɗimemiya dake kina ce min wata
Aunty",dariya ta yi"to matar oga",da gudu na biyota"matar oga sai kace wasu
arna",dariya take tana"yi haƙuri na daina Nanar Babban Yaya"tsayawa nayi"a she ma
kinsan wace ni ƴar rainin hankali","yauwa zo kiji Madam",ta faɗa tana matsowa,a
kunne tami raɗa na ɗago ina zaro ido"wallahi ba ruwana in ta kama mu zance
kece","karki damu inta fara bacci sai rana tsaka take tashi",tafawa mukai muka
shige kitchen.

UMMU SADDIQ🌹🌹🌹🌹
🌈🌈🌈
🌈🌈
🌈

Babban Yaya Free ne amma me so ya biyo ni Pc in sa a group don shagalin Nana


na buƙatar comments.
08146711395

BABAN YAYA

08146711395

Tsaida bikin Sadiya yasa muka zama ƙawaye muje siyayya tare dake itama ƴar yi ce
tace muyi wancan mu ci miyi wancan musha sannan ina zuwa makaranta ga abubuwan da
Aunty Mama ke ɗora ni akai cikin wata biyu na canja jikina ma haka daga ranar in
kuma in ya kirani vedio call bana ɗauka sai nace ba ya yi,bamu sami matsala da
Aunty Hajara ba dan bata zama ma a gidan tun safe in ta fita sai dare sannan ma
nayi bacci.
Wata biyu da tafiyar sa a kai bikin Sadiya komai da Babban yaya yace na ma
ta,na mata shi harma da ƙari kuma dani akai bikin nan gidan namu kuma da kaina na
shige gaba aka gyara Boys quaters aka ma ta jere abin ta Sadiya ba ta da matsala
tun da tayi aure ni nake gyaran gidan kullum amma ban taɓa nu na na gaji ba madam
ce wai bazata iya zama ƴar aiki ba sai ƙara ɗakko wata me wankakken ido dan randa
ta fara zuwa naga zata min isa gaban Aunty Hajaran naci ma ta ƙaniya sannan na buga
ma wadda ta ɗakkota kashedi akan ta shiga tsakanin mu in ba haka ba zan tarwatsa ma
ta tunani.
Bayan wata uku
Kwance nake ina bacci naji wayata na ƙara ɗauka nayi inji waye naji muryar Mama
tana Ruma ta haihu,ihu na daka na sakko a gadon na fara tiƙar rawa,gadon kawai na
gyara na faɗa toilet nayi wanka ƙaramar kit ɗita na ɗakko na ɗebi kayana da sauri
sauri na fito ina kulle ɗakina ɓam saboda tsaro Hajiyar gidan na bacci na fita.
Ba wata sanya na isa gida da murna ta na shige ɗakin Mama mai jegon na zaune
tana cin abinci nai tsalle na hayeta"wayyo Nana zaki ƙarasa ni"ɗagata nayi ina
dariya"sannu Ya Ruma ke ki ka haife wannan ɓulelen ɗan haka","bari Nana ai kuwa
naci ubana ba",dariya na saka"ai dole Allah ya raya shi saura sauran tunda kin buɗe
musu ƙofa","to suma Allah ya rabasu dashi lafiya","ameen ameen",a wannan ranar
gidan yini mukai acike anan nayi zamana ban koma ba kowa uazo mamakin yadda na zama
nake wata huɗu amma na zama ɓuleliya komai ya cika,a kwana uku da haihuwa neman ayi
ya kaini gidan Gwaggo Asama'u Ya Hadiza na gani kwance fuskarta a kumbure har ido
da mamaki na isa kanta"Ya Hadiza kece haka",tashi tayi tana kuka da sauri na zauna
kusa da ita"me ya sameki haka ina mijin naki kuma","kiyi shiru Nana ni dai banyi
sa'ar miji ba ashe ɗan mafia na aura ban sani ba yanzu nan da kika ganni daga Abuja
har kaduna nazo a ƙafa ta jeji ban ma bi titi ba bare wasu su ganni dan sawa ya yi
a kamo masa ni ya yanda kinga yanda na koma kullum dukana yake kan naƙi yadda da
buƙatar sa","ɗan mafiya kuma ki gane min shege ɗan bagidajiya buƙatar me zaki biya
masa",cikin kuka tace"ba dai kin san kwanciyar aure ba","kai na ɗaga alhalin bansan
komai ba"to wai shi sai dai ya yi amfani dani ta baya ki faɗan wannan wace kalar
ƙazanta ce",dafe baki nayi ina ɗora hannu a ka"ta baya kina nufin ta wajen kashi",a
yanda nayi maganar ne yasata sakin dariya ta kaimin duka"ke dai bazaki sauya hali
ba ko","Allah Aunty Hadiza abin ne kamar almara wallahi gara da ki ka gudu yaje can
ya ƙarata amma dai ya sakeki ko","tun washegarin kai ni",salati na buga"kice kin
gama idda ma",Gwaggo Ma'u dake gefe tana jinmu ta saki dariya ta ce"Nana ko ƴar
banzar yarinya",juyowa nayi ina kallon ta Allah Gwaggo ai kinga ta huta wallahi ma
ta tashi muje gida ai kowa yazo baki faɗa ma ta ba ne Gwaggo","na faɗa ma ta wai
kunyar shiga cikinsu take tunda da ba ta shiga ba sai yanzu",kama hannunta
nayi"taso muje kiga ya za'a buga wasan",ba taso ba ta biyo ni Baba na kallon mu
yana girgiza kai.
Duk suna falo ana kallo da sharhi muka shigo Allah sarki suna ganin ta suka
taso kanta"Hadiza lafiya Hadiza lafiya"kawai saita zube a wurin ta saki kuka mai
ratsa zuciya,binsu da kallo nayi"ku baje kunnen ku da kyau kuji mijin da ta aura ne
ya shiga ƙungiyar asiri shine saboda ɗan taure ne shi wai an bashi abinda zaiyi
irin abinnan ko ka bada jinin ka ko dai wani abu saɓon Allah to shine shi da aka
bashi nashi mai makon yaje waje sai yazo wajenta wai zai yi amfani da ita ta
magudanar kashi shine ita kuma taci mai uwa kawai ta fece ta dawo garemu da kuka
ganta nan daga Abuja saida ta kusa kano a ƙafa sannan ta samu taimako shi yasa tai
wannan firgicewa kamar wadda tai dambe da zakuna itama maganin ta da bata aiki sai
kaɗiri fere da kula samari ƴan gayu kunga yanzu ta ga duniya ta nutsu",basu da nake
faɗawa ba ita kanta mai kukan dariya ta saka,Ya Hasiya ce tace"ubanki Nana haka ake
faɗin abin alhini",dakatar da ita nayi"to me zance ai wallahi dama ni so nake nagan
mu a haɗe kamar kashin awakai kudai da ku kai nisa kuje amma a kanta murna nayi
dama ya saketa dan da bai saketa ba saina sa an kamo min ja'iri na masa tunɓur na
kora shi titi in yaso tatan tai mai biji biji",dariya sosai suka shiga yi nan
sukaita ma ta sannu da kuma Allah ya kiyaye kuma basu nu na ma ta komai ba suka
jata jikin su aka cigaba da hira,silalewa nayi naje na janyo Gwaggo tazo ta gani
hannuna ta kama"nagode Nana ta",'kuji gulma wai Nanar ta',yaƙe ma ta baki nayi"ba
komai Gwaggo ai dukkan su nan da ki ke gani har ita Ya Hadizan ƙaramar ƙwaƙwalwa ce
dasu kalli daga magana ɗaya duk sun shiga jimami",ba shiri Gwaggo ta kwashe da
dariya Iyyo dake bayan mu zata shigo tace"gaskiyar margayi Habibu ke alheri ce
Allah ya miki albarka Nana kin ga ni ko Asama'u ada ita ki ka fi tsana amma yau
kinga me ta miki","haka ne Iyyo ai na ma ta godiya ma kuma daga yau baza'a ƙara
samuna da wani abu ba saura ta gyara sauran iyayen ta ma",dariya nayi"kai Kawu iro
da da yake kamar kacar mashin ta lalace wallahi bai gyaruwa da wuri gara ma kawu
Rabilu shi yana jin Allah yake sanyi amma zanyi maganin su",dariya suka saki Iyyo
ta ce"iyayen naki ki ke wa haka","ai Iyyo nafi kowa sanin su fa amma komai lokaci
ne muje ciki Gwaggo".
Da yamma Ya Surayya suka zo nan ma dai akaita zama ana hira bayan sallar isha
na kwashi jiki sai wajen Hajiya Harira duk ta rame tai muzu muzu kammar kura ta
shekara ba abinci dama na kwashi rafa biyu na kai ma ta nace inji Babban Yaya kuka
ta saka ta ansa tana ta godiya,da sauran dake a ƙuguna na wuce wajen Hajiya Salma
duk na kai musu suma ba kunya suka karɓe saura bandir ɗaya na taho gida dan munce
anko zamuyi yanda kowa ya shigo gidan zai gane mu,a hanya naga Kawu Iro sai sauri
yake kamar zai kifa da sauri nabi bayansa zuwa gidan ɓuya nayi yadda ba wanda zai
ganni,Saude ce ta kwaso kayan shi ta watso ƙasa tanabta bala'i,da hanzari ya yi kan
kayan"ke Saude bashi hauka ne dan kina bina kuɗi sai kina min tijira kalli abinda
ki ke min",kamar zata cinye shi tayo kansa ita kan ya yi wani abu taci mai kwala"eh
ka biya ni kuɗina nace dubu hamsin ɗita da kasan baka da kulin aurar da ƴar taka ka
amincewa wanccan uban...","keee Saude dakata",na fito ina saurin ɗaga ma ta
hannu"sakar min uba tunda ba ɗanki ba ne ko ɗanki ne ma in yay wannan girman ai ya
wuce ki ci mai kwala bare shi mijinki",ƙin sakin sa tayi nazo na ɓanɓare hannunta a
a jikin rigar sa na turata baya,rigata na kwaye na ciro kuɗin wandona na miƙa
masa"ungo Baba dan na dena ce maka Kawu ma ka ƙirgi iya kuɗinta ka bata taje can ta
ƙarata kuma karka ƙara ma ta ko sisi",sannan na juya gareta"to baƙuwar kuɗi andai
ji kunya shekara da shekaru yana ci dake goɗoɗo amma wai yau kan kuɗi ki ke tozar
shi gaban kishiyoyin ki dan abin kunya an dai yi asarar hali ga kuɗi nan za'a baki
ki sai duniya ma kiga in zata amfana miki wani abu ni nan da ki ke gani iyayena
sunfi ƙarfin a wulaƙanta su kan kuɗi dan mu jinin arziƙi ne duba kiga kalleshi
shima banda kawu da gane gane a ina ma ki ka dace dashi ai ahi sai ɗiyar sarakai
kin ganki fa baƙa ga ido kamar tasa kalli ƙafafunki kowa ya ganki a yasan saman ki
akwai girma amma shi kalleshi ɗan sawal wali...",ban gama ba ya taho da sauri
kaina"hakan yake ƴata takaina ni wallahi banma san a ina naganta ba nace ina
so",zare ido ta fara tana susar kai ƙare ma ta kallo na shigayi da alama ba ta da
gaskiya kai na kaɗa"Kawu kai kace kana sonta ko ita tace tana sonka",ɗan jima ya
yi"na manta Nana amma tambayar mana ita",juyawa nayi ina kallon matan gidan Haule
na nuna"yauwa Baba Haule kece aminyar ta a gun talla ta ya akai yace yana
sonta",zaro ido sukai suna kallon juna taya akai nasan ƙawaye ne su amma anan basa
nuna wa,kanta ta shiga sosawa"wajen wani malami taje",salati muka saka kamar munga
mutuwa ya yinda Kawu ya miƙa ma ta kuɗin ta"dama na sa ni sai in rasa ma sonki nake
ko ƙaƙa",dariya na riƙe tamau nace"kefa Baba Haule amma ke shi yace yana sonki
ko",wuri wuri ta shiga yi ya yinda Saude saurin cewa"itama wajen malamin
taje",dariya na saki ina nu na shi"to kai kawu farin jini gareka haka amma baka
samo mai kuɗi ba sai talakawa",shima dariyar ya yi"sai yanzu nima nayi tunanin
haka","to wallahi tun wuri ka nemo wadda ka ke so ka aura kasan daɗin soyayya nasan
ta ukun ma dai tohhh"da sauri ta shige falon su kamar zata faɗi,Kawu ne ya kalle
ni"ga sauran kuɗinki Nana Alkah ya miki albarka yasa ki fi haka a rayuwa yasa a
lahira ki zama ta musamman nagode da taimako na da ki kai",hannun sa na kama na
juya mai da kuɗin da kuɗin"ka riƙe Kawu wannan ya wuce in Babban Yaya ya dawo zamu
zo muji ya za'ayi da shagon ka na kasuwa shi kuma Yaya Kamal karka ƙara
kulashi","Allah ya miki albarka Nana","ameen Kawu na saida safe","Allah ya tashemu
lafiya ƴata",da sauri Ya Amina ta ɓuya tana sauke wayarta hawayen fuskarta ta goge
dama na dariya ne ya zama na tausayi,saida na wuce sannan ta fito ɗakin au ta wuce
ta ɗakko akwatin ta ta buɗe wata leda ta ciro ta buɗeta kuɗi ne a ciki masu yawa ko
ƙirgawa batai ba ta fito yana kwashe kayansa a ƙasa tazo ta durƙusa"Baba ga wannan
kuɗin ni na kawo maka",ɗagowa ya yi yana dubanta karɓa ya yi"nagode Amina","babu
godiya tsakanin mu Baba kawo kayan na kwashe zan kai ma ɗakinka","to Allah ya miki
albarka",ya bata ya tashi ya fita daga gidan duk jikinsa ya yi sanyi.
Gida na koma na wuce ɗakin Aunty Mama nayi wanka nasa kaya na dawo falo akaita
hira kuɗin mukai za'a haɗa gobe a siyo atamafar teloli bakwai na dama a cikinsu
hakan yasa sukace zasu ɗinka,duk wannan abin da ake ko barka Aunty Hajara ba ta zo
ba kuma ban ma ta magana ba duk da kullum sai naje bama samun ta nake ba in ba da
sassafe naje Sadiya ce ta dai zama ƙawata kullum muna tare itama sai in dare ya yi
ne take komawa gidan ta su Hajiya Salma anga idi suma kullum suna tare da su Maman.
Washegari da sassafe naje ɗauko kaya na maida waɗancan dama na wanke na goge
na fito kenan saiga Aunty Hajara zaro ido nayi ban kulata ba sai da naje bakin ƙofa
sannan nace"Aunty Hajara ba zaki ki mana barka ba kullum bakya nan ai ko hajji da
umara ki ke yaci ace kin gama wata uku harda kwana ki",jim tayi tanajin zuciyarta
kamar zata fashe haushina take ji kamar ta kasheni sunyi yawan malamai kamar hauka
amma an faɗa musu in ta matsa zata kashe wannan auran zata mutu murus,ɗagowa tayi
ta kalle ni"bazan je ba zoki ja ni",watsa hannu nayi kamar kunama ta harben na ɗora
yatsu a haɓa"wuhuhu wane ni da kai ki ai da ƙafarki zaki harma ki kai kayan barka
bari dai in gama ɗaukan zafi dake",zuru ta yi tana kallona ina magana kamar
uwarta",abin duka tai wuri wuri tana nema kan ta juyo nakai inda zankai,ƙwafa tayi
tai fitar ta,a tamfa mai kyau aka siyo kuma aka fara ɗinkawa har Aunty Hadiza kowa
na gidan murna yake yadda muka zama to miye amfanin faɗan,da yamma waanda basu zoba
suka gama zuwa da sassafe muka tashi da gagarumin sunan YUSUF da misalin goman safe
kowa ya shigo anata hoto Ya Amina ce ta tattaro su kaf har mazan tasa a ɗaki ta
kulle laptop ɗin ta ta ɗakko ta jona wayar ta"kuzo ku kalli abinda ƴar shabakwai da
watanni tayi",kunna musu tayi a bin da ya faru a gidan su tayi,dariya sukai tayi
harda hawaye Aunty Mama ce ta ƙwanƙwasa aka buɗe ma ta"ku lafiyanku kun kama kun
shige ɗaki kun kulle",ba magana Ya Zainab ta kamo hannun ta zuwa wurin ta dawo ma
ta dashi ba ya ita kanta da ta kalla saida tai hawaye abu sai kace film amma hakan
ya musu da ɗi sosai.
Bayan azahar muka saka anko munyi kyau over gashi yasha gyara ɗan kwali an
ɗaura shi iri iri Ya Usaina ce tazo ta tasani da wayarta hoto kala kala tamin
sannan tamin a waya ta ta tafi,wayarsa ta tura hotunan.
Dama yana zaune a gida yau basu fita ba harsu Ya Saddi'q yana fara buɗe
hotunan ya miƙe tsaye magana ya fara shi da waya"tabbas itace"ƙara buɗe sauran ya
yi yana mamakin yanda na zama ji ya yi kaf zaman garin ya ishe shi tashi ya yi ya
wuce sama ko kallon su baiba duk da sun zuba ma sa ido,yana wucewa suka tafa Haruna
yace"Saddi'q ƙanwar ka na kawo wuta fa baka ga ta ruɗa mutumin ba yau mun shiga uku
da faɗa wallahi office zanzo na tafi",riƙo shi ya yi ai nima haka ko mota ma bazan
ɗauka ba dan kar yaji fita ta",tafawa sukai suka fita ba tare da ya sa ni ba a
ranar kuwa da ƙyar ya yi bacci gashi aiki ne dashi wallahi da dawowa zaiyi.

Suna ya gudana lafiya dan haka bayan kwana biyu kowa ya watse ƴan nesa suka
koma ya yin da ƴan kusa muka ƙara jonewa,a waɗannan watannin mutum huɗu ne suka
haihu mun sha yawon suna bamu can bamu can sai daga baya sannan muka nutsu.

Bayan wata uku:

Bayan wata uku na ƙara girma jikina ya murje kullum ni da Aunty Hajara kamar
kaji zagina take kamar me wai na zama karuwa ga jikina nan sai haɓaka yake miji
bayanan bare ace shine ni dai bana kulata amma abin nata ya fara tirani na dai
faɗawa su Mama Aunty Mama ta ce na dawo gida Mama ta ce sam sai na zauna ba yanda
muka iya haka na zauna amma nayi alƙawarin seta ma ta zama dan bazan yadda da zagin
cin mutunci ba ana haka tafiya ta samu zuwa Niger Alhaji Baffa da kansa ya faɗa
masa kumanya aminci gashi zamu kwana biyu dan ma munyi hutu kwana ki da maganar
muka ɗau hanya kuma mun sauka lafiya.

Biki ne akai har sau uku sannan muka fara shirin dawowa kiran mu ya yi yace
su tafi su barni zai biyo tanan mu dawo tahowa washegari da daddare ya sauka dama
ɗakin Yayar Mama nake kwana ita ke da girki bama ta ɗakin ɗanta ne yaje ya ɗakko
shi kuma ya kawo shi har inda nake sannan ya fita,bina da kallo ya shiga yi yana
mamakin yadda na zama ƙatuwa gashin fuskata ya janye ya sumbaci kumatuna kan
kujerar ɗakin ya zauna ya cire takalmi da safar ƙafar sa ya cire ƴar saman rigar ya
aje ya sassauta botir ɗin wuyan ƴar cikin ya jimgina kansa da kujerar yana furzar
da iskar bakinsa ya lumshe ido,bai jima da jingina ba bacci ya ɗauke shi dama ya
gaji sosai,cikin dare na tashi zanyi fitsari kawai naga mutum a zaune yana barci
baki na dafe na zura mai ido ya yi mugun kyau ya ƙara fari rasa me zanyi nayi ni ba
gidan mu ba ga dare bare nayi ihu kusa da shi na zauna nama daina jin fitsarin
kwantar da kaina nayi a kafaɗar sa,a haka na koma baccin nima kiran sallah ne ya
tashe shi jin nauyi kusa da shi ya duba ya ganni ɗauka ta ya yi yakai kan gado yaja
min bargo ya wuce ya fita dan zuwa masallaci,bayan rana ta fara ɗagawa suka shigo
da ƴan gidan a falon suka zauna anata gaishe gaishe ga abin kari ana haɗawa harda
ni a masu aikin tunda ya shigo sai raba ido nake na kasa magana shima in ya kalleni
sai dai ya yi murmushi a haka aka karya sannan aka shiga rakashi yana gaida mutanen
garin har dare ya yi,
wani gari akace zamu dama yasan garin megidan ne ya bashi mota sabuwa dal dama mai
kuɗi ne nan na shirya cikin atamfa nayi kyau sosai tunda yazo dama ba muyi magana
ba muna shiga motar ya fita a gidan ɗan gefe ya parker da sauri na tashi na faɗa
jikinsa ya rungumeni tsam yana a jiyar zuciya ɗagowa nayi ina shafa fuskarsa"Babban
Yaya kayi kyau sosai","Allah Nana ta ai ke ce ki kai kyau fiye da tunani",kiss
namai a baki "ka fini ai",lumshe ido ya yi ya kwanto da kaina fuskar sa ya ɗora
bakinsa kan nawa an daɗe ba'a haɗuba ni kaina sai naji daban haɗin kai soaai na
bada mun daɗe a haka sannan ya zare bakinsa a nawa"munje ko dare nayi hanyar akwai
sahara sosai,gyara zamana nayi sannan ya kunnan motar muka tafi garin da nisa ace
munyi kwana kenan mukaga ana haska mu da fitila lumshe ido ya yi yana ambatar
innanillahi wa'inna ilaihi raju'un",faɗuwa gabana ya yi "Babban Yaya lafiya
waɗannan mutanen fa",hannuna ya kama ya damƙe"kwantar da hankalinki ɓarayi ne karki
nu na kina jin tsoro",ƙwace hannuna nayi"to da tsoron su nake kan ya buɗe motar na
buɗe shima ya fito ganin bamu ɗaga hannu sama ba yasa ɗayan ya yi dariya"oga manya
fa muka samu ko baka ga motar bane","na gani kawo min su nan",hankaɗo ni sukai yay
saurin tare ni a fusace ya haska ma wanda ya turoni mari ba shiri ya sau bindigar
ya dafe kuncinsa ogan ne ya miƙe"kai riƙaƙƙe shine ka mare shi",nuna shi ya yi da
yatsa"kaima idan kace zaka taɓa saina mareka",baya mutumin yaja"yeehooooo mun samu
kalarmu mara tsoro amma zamu sa kaji tsoro yanzu kai ku ladabtar min dashi kusan su
takwas suka zagaye shi suna duka amma ya yi ƙyam,da gudu na taho ina kuka zan ture
su suka riƙeni runtse ido ya yi saida ya ce su bari sannan suka dakata suna
gurfanar dashi a gaban ogan nasu kallon sa nayi bakinsa nata zubar jini haka gefen
idon sa ma,ogansu ne ya daka mana tsawa"da ganin ku ansa daga gidan danshi ku ke
wannan wa ce ce ɗinka",shiru ya yi ƙara daka mai tsawa ya yi"wa ce ce wannan
ɗinka"nan ma shiru ya yi tasowa ya yi yana dariya to bari na baƙanta maka rai yanda
zakaji daɗin mutuwa dan baƙin ciki hannu ya kawo zai taɓa ni,da sauri ya yunƙura
zaiyi magana na rigashi"ni ƴar megidan sa ce",dakatawa yay yana kwashewa da dariyar
mugunta yana ɗaga hannun sa sama"ashe ma ba da kaina zan baƙan ta maka ba,da kanka
zaka baƙantawa kanka kai ku tuɓe mai ita ya ma ta fyaɗe da kansa in ta mutu ya
kaiwa megidan sa gawa inta rayu ya kai masa mushe",wani iri faɗuwa gabansa ya
yi"dan Allah kuyi haƙuri yarinya ce fa ku bari",ɗago haɓar sa ya yi da bakin
bindiga"ok so ka ke mu kasheta sai kayiwa gawarta harma mu taya ka",ɗago kansa ya
yi kalle shi"please kuyi haƙuri ku barta kumin koma me zakumin amma banda
ita",dariya ya ƙara saki"mu ce maka a kai kuɗi muke buƙata wannan motar kawai zamu
ɗauka sannan kayi me mukace ko kuma bari na fara sai ka biyo ba ya",a gudu na tashi
na faɗa kansa ina kuka"dan Allah kayi me sukace akan waɗannan jakunan su kashe ni
gara na mutu a hannun ka",girgiza kansa ya yi wani baƙin ciki yana ƙara tsirga masa
ji yake kamar ya yi bindiga,jana sukai a wurin suka yar ina kuka sannan suka saita
bindiga a cikina da sauri ya tashi"ku bari zanyi zanyi nace",dariya sukai suna
matsawa ba ya ba yanda ya haka yana gani suka ɗaure min hannu suka tura wani ƙyalle
bakina,hawaye ne kawai ke fita a idona bansan komai ba duk iskanci na bansan mene
kwanciyar aure ba nasan me ake yi amma ai bansan ya abin yake ba tsanin azaba da na
fara shiga shi yasa na fara motsi amma ba halin ƙwatar kai su kuwa sai dariya suke
suna rawa da bindiga sama sanda wani irin zaba yaja min suma ban sa ni ba su barshi
a haka amma in saida suka saka shi ya ɗebi fin awa biyu a kaina sannan suka barshi
ya tashi wani irin jini ke ambaliya a jikina fashewa ya yi da kuka ya ɗagoni ya
rungume su kuwa sai ihu suna dariya ƙarar harbi suka ji kan kace kwabo sun watse
mutane yaji a kansa ya ɗago yana kai dubansa kansu sojojine suka zo wucewa
fahimtar meke faruwa sukai nan ɗaya a cikinsu yace"ku shiga jejin nan duk inda
mutanen nan suke ku kawo min su nan da kwana uku"sarawa sukai suna yin cikin
jejin,durƙusawa ya yi a gabansa yana dafashi"Aboki kayi haƙuri",a razane ya ɗago
jin na kawo numfashi shima mutumin kallonsa ya yi ya ce"bata mutu ba",kan Babban
Yaya ya yunƙura shi ya rigashi ɗaukata zuwa motar su su kuma sauran suka ɗago shi
shima zuwa motar ganin jinin dake zuba ajikin yasa sojan nan zaro ido da hanzari ya
cire rigar sa ya ɗaurata a ƙuguna sannan suka shiga sai asibitin da ya faɗa musu
dan su ne ƴan gari,likitocin na gani sojoji suka fito dukkan mu suka kwantar amma
kafin kace me shi ya dawo hayyacinsa ruwan ma da aka saka masa ya fincike shi ya
fito zuwa ɗakin da nake wannan sojan ya gani hankalinsa ya fi na kowa tashi sai
zarya yake yana amsa waya akai akai ganin ya fito yasa ya tare shi"ya ka taso
kuma",hannu ya ɗaga masa"ka barni kawai likita ce ya fito ya fiskan ce su"gaskiya
tana cikin ma wuyacin hali ta rasa jini mai yawa dan haka shi zamu fara ƙara ma ta
kafin kowanne bin cike ya biyo baya sannan dole za'a ma ta aiki a mafitsarar
gaskiya an cutar da ita Allah ya saka ma ta",juyawa ya yi ya faɗi a wurin baisan
sanda kuka ya ƙwace masa ba haka shima wannan jarumin soja soboda itama likitar
kukan take kana gani kasan lallai abin yakai maƙura,sojan ne ya riƙeshi ganin yana
buga kansa da kujerar wurin"haba Aboki ka bari mana karka lahanta kanka",ɗagowa ya
yi yana kuka sosai"kabarni in mutu ya za'a ce da kaina nawa matata haka yarinya ce
batasan komai ba me yasa ban bari sun kashe mu ba",bakinsa ya rufe masa"ba a bin da
za sameta na maka wannan alƙawarin ka zama jarumi mana kalleka sai ma ace kaine
sojan ba ni ba taso muje a gwada jinin mu in ya yi basai an sa ma ta jinin kowa
ba",da kuzari ya miƙe suka je aka gwada su da mamaki likitar ta dubesu"Major wannan
ɗan wanka ne dama kana da ƴan uwa",kallon ta ya yi"a a likita ban sanshi ba ma"da
mamaki ta kalle shi"ban yarda ba amma mu gama da mara lafiyar tukunna akwai alamar
tambaya akan ku",kallon juna sukai suka kalleta jinin da ta ɗiba ta kwasa ta fita
sannan tace su huta ko kula maganar ta ba suyi ba tana fita suka fito suma.
Har safe ana a kaina amma ban farfaɗo ba jinin har ya ƙare koda likitar ta
oto ta nuna musu sai an ƴara jira nan ransa ya ƙara dugun zuma ya shiga kaiwa da
komowa suna nan tsaye a wurin yaji wayarsa na vivrating sai yanzu ma ya tuna da ita
da sauri ya ɗakko yaga ɗan wancan gidan ke kiran sa bai ɗaga ba saima ya kashe ya
nemi wata number yay kira ba jimawa aka ɗaga"Hello friend",ajiyar zuciya ya
yi"na'am friend kana gida na sa ni","eh lafiya kuwa naji ka haka","a kwai matsala
ina ƙasar ku mata ta na asibiti a bani jet zan wuce india",cikin tashin hankali da
salati ya ce"wane asibitin"faɗa masa ya yi","gani nan zuwa a shirya ta
tukunna",kashe wayar ya yi ya kalli sojan nan dake murmushin ƙarfin hali,jinjina ya
masa sannan sukaje sukaima likitar bayani itama nan take ta amince dan abin ya fara
bata tsoro nan da nan ta fito ta shiga shiryani ba jimawa jiniya ta karaɗe asibitin
nan wanda sukai waya ya shigo da sauri kayan bacci ne ma a jikin sa yana ganin ya
taho ya rungumeshi"me ya faru ne Habib"lumshe ido ya yi ya shiga masa bayani wani
irin tashin hankali ya shiga nan likitar ta fito wanda ta gani ne a asibitin yasa
ya sauri ƙarasowa"rankai daɗe da kanka","dole ki ganni anan wannan abokina ne na
musamman an gama haɗata",kai ta ɗaga yace a fito da ita dukkan su har sojan suka
ɗunguma inda jirgin yake musayar number sukai da sojan ya bashi tacan sannan suka
rabu yana faɗa masa zaije ya ɗau motar sa yi waya ya faɗa masa wa zai zo ya karɓa,
sojanan yana ji kamar zai rabu da ɗan uwansa ne,saida jirgin ya bar wurin sannan
abokin nasa ya koma mota.

India

Kamin saukar mu ya kira su Saddi'q hankali tashe suka je madakatar da zamu


sauka da motar asibiti suna jiran mu.
UMMU SADDIQ Ce 🌹🌹🌹🌹🌹
🌈🌈🌈
🌈🌈
🌈

BABAN YAYA

Babban Yaya Free ne amma me so ya biyo ni Pc in sa a group don shagalin Nana


na buƙatar comments.
08146711395

30

A bin da suka gani suma ya ɗaga masu hankali sosai amma da yake ƙwararru ne a
kwanaki suka gama komai harma na fara motsi sai dai ban tashi ba,da inda muka baro
da gida kawai yace musu ya koma da ni ne saboda wani aiki su Saddi'q ma basu faɗa
ba kowa ma sai uziri mai ƙarfi yake kunna wayarsa abokan aikinsa kuwa ransu ya
ɓaci so sukai susa a bincike musu jejin ya faɗa musu akwai mai wannan aikin ya
baro,kwana na goma sha huɗu sannan ya samu cikakken result a kaina shi yasa ya
shibo da sassafe har office yaje ya sameta gurin zama ta bashi sannan ta cire glass
ɗun fuskarta ta fuskance da kyau"Sir matar ka ta samu matsala mai wuyar warkewa duk
kuwa inda zaka a duniya nan kat inda za ace kuzo to muma mun bincika da wuya
mahaifarta ta iya haihuwa duk kuwa sanda kuka gantaa da ciki to ku kawo mana ita
nan",lumshe ido ya yi yana jin wani hawaye na taruwar masa girgiza kai ya yi sannan
ya buɗe idon ya sauke kan likitar"ba komai Allah ya bata lafiya","kuma kota warke
ka bata saman wata huɗu saboda wajen a kwai duk sanda aka taɓa shi jini zaina fita
kuma hakan yana iya kai barazana ƙwaƙwalwar ta amma a wannan wata huɗu komai nata
ya zama normal","ba matsala Dr","zaka iya shiga ka ganta",tashi ya yi jikinsa a
sanyaye ya wuce ɗakin da nake,ƙofar ya turo ya ahigo Ya Saddi'q ya gani a tsaye ya
nale hannu a ƙirji yana kallona komawa ya yi da sauri,Ya Saddi'q da yaga fitar ya
fito shima"Babban Yaya ya ka fito ai ni ba haushin ka nake ji ba bafa laifinka
bane",joyowa ya yi"nasan da haka Saddi'q in naga Nana a kwance a wannan hali bana
iya yafewa kaina","ka bara wannan maganar ka shiga ka ganta ai tana samun sauƙi",ba
yanda ya iya haka ya shiga ɗakin amma ba ya iya tsayawa ya kalleni da kyau,da haka
na ɗebi wata biyu sannan na buɗe ido ganin su Ya Saddi'q sai na fara kuka dan ban
manta komai da gudu na tashi Ya Saddi'q ya riƙe ni"ina zaki kuma",duka hannunsa
nayi"ni ka sake sun kashe shi ko dama basu da imani ai wallahi saina rama",wani
irin abu ne ya taso ya tsaya masa a wuya yana kallon ko me nake ta wayar gaban
aljihun Ya Saddi'q dan shi bazai iya zuwa inda nake ba,kokawa sosai nayi dashi
saida ya nemi cin ubana sannan na haƙura na zauna"wa yace miki ya mutu yana nan
bazai iya zuwa inda ki ke ba ne ya kasa yafewa kansa akan shi ya miki haka madadin
ya fanshi ke da ransa to bazai iya tsayawa wani ya miki haka ba yana raye"ara
volume wa kukana nayi "to ai ni nace ya yi me yasa zaice haka ni na yafe masa dan
Allah kuce yazo",ina duk wannan abu da ake har na koma gidan su da zama bana
ganinsa kuma kome zanyi inje wajen aikin ma bana samun ganin sa kuma kowa yace yana
nan ko ace yanzu ya fita a haka na ƙara wata biyu.
Tsaye nake ina saka kayana a akwati ga tiket ɗina a gefe zan koma gida sai kuka
nake dan har yanzu ban samu haɗuwa dashi ba,bayan na gama haɗa kayan na ɗau
fayafina na saka na janyo akwatin a ƙasan bene naga Ya Saddi'q yana jirana sakkowa
nayi muka fita agidan ƙala baice min ba bare yace nayi shiru,a haka har airport
tare zamu taho da Ya Saddi'q shi yasa muke tare a jirgin ma kujerar mu ɗaya,muna
zama ya ɗago kansa daga sadda shi da ya yi ashe shine a kujerar bayan mu bamu sa ni
dukkanmu,duk wannan tafiyar muna tare har Allah yasa muka sauka lafiya Ya Ashiru ne
yazo ɗaukar mu a yadda ya ganni jikinsa ya masa sanyi da muka zo gidan ma da kukan
na tasa su na yashi hankalin kowa na gidan,dalilin wannan kukan tashin hankali suke
nema na kuwa bayyane musu kome kowa ya ahiga tashin hankali sukaita kuka suna min
sannu ni ina au nemo min mijina haƙuri suka shiga bani da na dangana zai dawo komai
daɗewa nafa san halin sa in ya yi zuciya kwana na uku a gidan na kwashe kayana na
koma ɗakina.
Wata sabuwa...🙄🙄
tunda na koma gidan bana kula kowa iyakata makaranta sai in dafa iya abinda zanci
ganin haka ya sa matar gidan fara shiga shirgina kamar dai yau riga ta siket ne a
jikina sun min in ka ganni baka cewa nice na ƙara dau komai ma na daina sha amma
jikina kamar ma ƙara tura shi na ke ta gabanta na zo na wuce kitchen na dafa abin
da zanci na dawo zan wuce naji saukar muryar ta"keee ƴar bariki kalli yadda ki ka
bige min ƙafa",ɗan dakatawa na yi nai dam sai kuma na wuce bance ma ta uffan ba dan
nasan neman magana ta ke ba bu abin da na ma ta,saura kaɗan na shiga ɗaki naji ta
tankaɗa ni gaba da hanzari na dage ban faɗi ba na ƙarasa shiga ɗakin na turo ƙofa
ta na kulle na zauna naci abinci na na ƙashi sannan na fito maida kwanon tana gani
na saita miƙe"ke wallahi zanci...","kutumar uban mu ni da ke Hajara"na juyo da
zafina na faɗa ina ɗaga ma ta hannu,wani tashi ta yi tana nu na kanta"ni ki ka zaga
Nana",gyara tsaiwa na yi"eh na zaga rama dan Allah",kaina tayo da dukkan ƙarfinta
na ɗiba da gudu na shige ɗaki ina kulle ƙofar,dukan ƙofar ta shiga yi ba ji ba ga
ni amma na shareta na shiga hidima ta,daga haka saida nai kwana huɗu bana bari mu
haɗu.

Bayan sati uku


Abin ya ishe ni haka nan ba bu Babban Yaya ba bu labarin sa amma ita naga ba
ruwanta nice dai nakai maƙura a damuwa har na fara zazzaɓi wanda saida ya kai ni ga
kwanciya a asibiti kowa abin na basa mamaki saboda Babban Yaya na zama haka kwana
na biyu aka sallameni.
Washegarin sallamata ban tsaya gun kowa ba na koma ɗakina da sassafe nayi
shirin makaranta na wuce,an fito break na samu can kusurwa staff room nan ne ba
hayaniya nayi zamana,monitor ɗin mu ve tazo"Aisha kije inji pc","ok Fatima",na
tashi na nufi office ɗin da sallama na shiga wani irin dam naji a ƙirjina,Babban
Yaya zaune kan kujera yana murmushi,murza ido na na yi na buɗe na ƙara ganin sa
mintsinin kaina nayi na ƙara ganin sa,wani irin kuka na saki na nufe shi da gudu na
faɗa kansa na cukwikuye shi gaba ɗaya a hijabina ina kuka kamar ana min duka,ƙara
rungumeni ya yi sosai"am sorry Nana",a fusace na ɗago na rufeshi da duka"ni ban
haƙura saika faɗamin me yasa ka guje ni",bai riƙe hannuna ba ya barni nayi na gaji
na ƙara rungumeshi,wani irin hawaye ne ya zubo masa yasa hannu ya share akan idon
pc hakan ya faru,zaro ido tayi"rankai daɗe wannan karatun yaufa bazai yiwu ba ɗauki
matarka ku tafi gida kayi lallasshin acan",kansa ya ɗan shafa"to Madam nagode
sosai,kama ni ya yi na tashi tsaye fuska duk hawaye na kalleta nace"Mommy sai wani
satin",daga shi har ita dariya suka saka tace"to Aisha kin ɗau hutu kenen ko"sunne
kaina nayi a bayan hannun sa ina kaɗa ma ta kai"to Allah ya kaimu",hannuna cikin
nasa muka fito kowa kallon mu yake amma ni ko ajikina.
Sanda muka isa gida su ashe sun san ya dawo direct muka wuce gidan mu Aunty
Hajara an tafi yawan barbaɗar ba a dawo ba tunda muka shiga na dasa kuka ina bori
ya rasa ma ya zaiyi da ni tashi ya yi ya maida ƴar saman rigar sa"to bari na koma
tunda bakya son ganina dama na sani",ina kallon sa yaje bakin ƙofar da gaske dai
naga fita zaiyi da gudu na tashi nabi bayan sa kan yakai ƙofar na faɗa bayan sa na
rungumeshi sosai na ƙara fashewa da kukan"dan Allah karka tafi mana",dakatawa ya
yi"to daina wannan kukan ko na koma sai na shekara ban dawo ba",kan ya rufe bakinsa
nayi ɗif sai a jiyar zuciya nake",jiyowa ya yi cak ya ɗauke ni"ƴar lukuta ta haka
ki ka ƙara zama",kwantar da kaina nayi a ƙirjinsa"Babban Yaya me ya sa zaka min
haka ka tafi ka barni bayan kasan bazan iya rayuwa ba ba bu kai",bakin gado ya
ƙarasa ya zaunar dani yana zare hijabin jikina bina da kallo ya shiga yi a hankali
ya shiga zaren kayan makarantar"inyee ta Babban Yayan ta ba kice mun girmi half
best"binsa da kallo na shiga yi nima Babban Yaya yabrame sosai sai tsawon sa daya
ƙara bayyana sosai lura da kamar baya son maganar da nake sai na barta na shiga
biyewa maganar da ya ke"eh mana baka yanda suka zama ba sai bashin susar ƙaiƙayi da
suke bin ka",rigar jikin sa ya fara cirewa"su sha kurumin su duk abin da suke ji
dashi nima ina ji da shi",da sauri na miƙe ina ja baya rigata dake kusa na ɗauka na
kare ƙirjina girgiza kai nayi"ina wannan susar banda yau shugaba ka manta ba
girkina ba ne",daina abin da yake yi ya yi ya min zuru,murmushi ya yi"zo nan
Nana","to tsaya nasa riga kar Aunty Hajara tazo ta ganni a haka ta zargi wani
abu",ina tsaka da saka rigar naji bam an banko ƙofa banyi zato ba naji saukar
muryar ta"to ƙaramar kilaki ya dawo ɗin kenen shine ki ka saka shi a ɗaki saboda
tsabar ƙwarewa a satar kwana har kin fara tuɓe riga wallahi kina ba ni mamaki ƴar
yarinya dake amma kin daɗe da sanin daɗin namiji",wani baƙin ciki ne ya kama ni
kamar zanyi kuka amma na shanye ya yinda shugaba yana tsaye ya zura ma ta ido kan
nayi magana ya riga ni",kin gama zubda girman?",juyowa ta yi kansa"kamarya zubda
girma?"ta faa tana wani girgiza,cire hannun sa ya yi a aljihun ya nu na ta zai yi
magana na saurin shan gaban sa na riƙe hannun lumshe ido nayi na ɗora hannun kan
breast ɗina"kayi haƙuri ko dan waɗannan sunyi kewar ka ne sosai kasan sun saba kai
tun kan nazo nan yanzu ma suna son su gaisa dakai ne shi yasa da ganin ka suka fara
ƙaiƙayi amma sun haƙura suma sai ranar su sa samu biyan buƙatar su yanzu dai"na
cire hannun na kamo nata na haɗa da nasa"kuje can ka ƙaiƙaya ma ta kasan na manya
basa jure rashi kamar namu na yara su nasu yanzu sai ya fara zuba",ina kaiwa nan
kamar yara na jasu zuwa ƙofa na tura su waje na saki hannun su na kulle ƙofa ta.

Tsaye ya yi a wurin ya ma rasa me zaiyi dariya zaiyi ko haushin abin da


Hajara tayi zaiji,sharewa ya yi ya cire hannun sa anata ya bar wajen zuwa ɗakin ta.
Ina rufe ƙofar na jingina a jiki sai maida ɓacin ran nake da ƙyar na samu na
dawo hayyacina na wuce ciki na watsa ruwa na dawo nayi zamana ji ma nake me yasa na
dawo a makarantar ko da yake ido na ya rufe a lokacin na manta ma da ita a gidan,a
ɗakin nai ta zama har sallar magaruba dama ina da abinci a ɗakin sai sallar isha
sannnan nayi wanka banyi kwalliya ba sai riga mara hannu da na sa roba ce kuma da
kaɗan ta wuce gwiwa duk rabin ƙirjina a waje yake humra mai sanyin ƙamshi na shafa
gashina na ware ya zuba a bayana,a gaban mudubi na tsaya na gama ƙarewa kaina kallo
murmushi nayi na ɗau pink jambaki mai ƙyalli na rambaɗa sannan na fito da zummar ko
da suna falon inyi ba wurin su nazo ba,ilai kuwa suna zaune kan dining a raina
nace,'wato abincin ma ba zaki kira ni naci ba ko to wallahi saina ci koda uban ki
ke yawo',tun da na fito ya zuba min ido kamar zai haɗiye ni,ita ma ganin ya raja a
a kallon wani wuri ta ɗago taga me ne sai ta ganni wani dam taji har ranta nan
baƙin ciki ya kamata wai yarinyar nan me take sha ne take zama haka kalli ƙirjinta
ai dole namiji ya kalleta,hannunta ta miƙa ta juyo da fuskar shi gareta ƴar dariya
ya yi kawai dan abin nata dole ya ba da dariya nan kishi ne kenan,bankula su ba nai
shigewata kitchen bayana ya zubawa ido mamaki duk ya kashe shi wai yaushe na zama
haka bai sa ni ba,saboda neman fitina da sanin me na taka ban sawa tukunya komai ba
na ɗora ta na kunna gas ba jimawa kaɗan na kai hannu na taɓata tukunyar ihu na
kwaɗa na janyeta,dama kamar akan gwiwa ya ke da hanzari ya miƙe zuwa kitchen ɗin
ina ta yarfe hannu da tsalle"mijina ka taimaka min hannuna"a gigice ya shigo kaina
ya nufo duk ya gigice"Nana me ne ne?"da sauri na ƙaraso na faɗa jikinsa na ƙanƙame
shi ina kuka"hannuna! hannuna!! Mijina",kai kanajin wannan ihun kasan iskanci ne
tunda taimakon ma akwai wanda na zaɓa ya kawo min shi,ƙara ruɗewa ya yi ya ƙanƙame
ni sosai"me yasa mi hannun naga"ƙi nayi ya gani sai kuka nake ina burbuwa a jikinsa
ɗagoni ya yi daga jikinsa ya zubawa fuskata ido bakina sai walwali ya ke haka ga
hawaye sai zuba ya ke rasa ya zaiyi da ni ya yi kawai ya sunkuyo kansa ya ɗora
bakin sa kan nawa ware hannuna nayi na rungumeshi,shigowar ta kenan ta yi turus
ganin meke faruwa wani irin hawa ta shiga yi ina kallon ta amma nayi kamar bana
ganin ta saida ya jima yana ssarrafa bakina sannan ya ɗago kansa yana bin fuskata
da kallo,murmushi nayi shima haka"yadaina ko",dariya nayi"ba dolensa ba tunda ga
ingataccen maganin sama yawa ƙasa aiki ai dama abinci nazo zan ɗora",kamo hannuna
ya yi"ga abinci can zo muje kici",ya kamo hannuna zai ja ni na turje"ban zuwa ko
ina da ba kunsan dani ɗin ba ku ke zaƙalƙalal abin ku baku kira ni ba",saki na ya
yi ya kama kunnen sa"sorry Aunty"kama kunnen na yi"da fatan bazai kuma mantawa da
ni ba",haɓa ya kama"shi ya isa wane shi amma a mai a fuwa yau ɗaya",dariya na
kwashe da ita"kai Babban Yaya kana da abin dariya wallahi",tashi ya yi daga ƴar
risnawar da ya yi"tunda kin haƙura muje",muna juyowa muka ganta kame da ƙugu ko tun
yaushe take oho saida ma mukazo dai dai ita sannan yace"muje mana"wani a jiyar
zuciya ta saki sannan ta wuce,a dining ma tsokana ta hana naci abincin sai da ƙyar
yamin jan ido naci anan na barsu dan kar ma ya biyo ni sai nace"saida safe iyayen
gidana"ganin na faɗi haka saita saurin cewa"Allah ya kaimu"shi kuwa ya bi ni da
kallo dan yasan me nake nufi sallamar.

Bayan kwana biyu ras na rayu da su duk salon Aunty Hajara na ta ɓata min wai
tanawa Babban Yaya abu a gabana dan naji haushi saina wanke mata kai ta hanyar nu
na ma ta ita da mijinta miye nawa da zanji haushi abin da ke ƙara ƙular da ita da
ni kenan,a kwana biyun nima na shiryawa mijina ras dan ina karɓar shawar wari daga
mutane daban daban shi yasa nayi nawa shirin na musamman nima yanzu ai ba yarinya
bace nasan komai,dan haka tun sha biyu na shiga kitchen na haa abinci mai lafiya
har biyar saura sannan na gama dama yau yaje office sauri sauri na shiga nayi
wanka na haɗe cikin material dack brown nayi kyau dama na wanko kaina dan haka
saina sauke gashin na ɗaura ɗankwalin akai humra kala daban daban na shafa nan da
nan na ɗau ƙamshi gama gyara wurin dana ɓata nayi sannan na haɗa ruwan wanka na
fito kenan a toilet nagan mutum tsaye yana tuɓe riga murmushi nayi"oyoyo Babban
Yaya",naje na faɗa bayan sa,lumshe ido ya yi dan tabbas wannan ƙamshin ya shige shi
sosai,kamoni ya yi na dawo gaban sa ya rungumeni sosai kaina na ɗago zan masa
magana yay saurin ɗora bakin sa kan nawa lumshe ido nayi jin yanda yake sarrafa
harshena tsaiwar gagarar shibtayi saida ya sada mu sofa sosai ya samu nutsuwa da
hakan sannan ya zare bakin sa a nawa ya sumbaci goshina banyi magana ba na jashi
yaaɓ shige toilet dan ya watsa ruwa,bayan ya fito yana ɗaure towel da kaina na ta
mashi ya shirya sannan na jawo shi falo har dining ganin bata falon yasa nace
masa"zan kira Aunty Hajara",kai kawai ya kaɗa min dan yau na lura a zumin magana
yake,tana baje a gado na shiga daga bakin ƙofar na tsaya"ki zo kici abinci"wani
kallo ta ɗago ta watsa min"bana ci bar nan mayyar maza",maganar ta ɓata min amma
sai nayi murmushi"ba laifina bane mijinki ne ya saba latse ni tun bansan wace ni ba
kinga dan na manne masa ai ba aibu"ina kaiwa nan na fito na barta mamaki amsar dana
bata take ina zama sai gata ta fito ko kunya ba taji ba ta sauya riga zuwa wata ƴar
ƙarama mai hannun best murmushi nayi kawai a raina nace'wannan matar sai na ma ta
bariki da farar rana sannan zata kiyaye ni inaga'cije baki nayi na fara zubawa kowa
abincin saida na gama na zuba nawa kaɗan sai naman dana kusa juyewa yana kallona
kawai yana murmushi yasan halina ina ƙaunar nama,a bazata naji muryar ta"ke me yasa
bakya da aiki saicin nama kamar kura",da sauri ya ɗaga kai ya kalleta zaiyi magana
na girgiza masa kai sannan na kalleta ina murmushi"ke bakyason nama to wallahi ki
canja tunani dan nama abinci ne na haƙika musamman ki samu ƙashi wanda yay laushi
ma ana yaron nama wayyo kina cinshi yana danƙo danƙo sai ki gama ci bai bushe ba
haka ƙashin ma in kina buƙata ki taune ƙashin ki ma haɗiye shi amma in nama ya
tsufa ko ragone ga wuyar dahuwa ga ta ci gashi ya bushe ƙayau saima kayi ƙoƙarin
ɗanyata shi da yawun bakin ka sannan yake ciwuwa kan ka gama kayi tilis kaji
haƙoranka kamar ka bada a jiya",banyi shiru ba naji ya fashe da dariya ni kaina
nayi mamaki bare ita datai dagalo tana kallona a magana goma bata fahimci rabin
ɗaya ba sai dai tasan duk yanda akai baƙa na yaɓa ma ta,mutmushi kawai nayi"Aunty
Hajara in baki gane ba kiyi bayani bawai kiyi shiru ba",da sauri ya katse
dariyar"ci abincin ki zan sa ma akawo miki frig na je nama",miƙewa nayi na daka
tsalle na juya na ƙara juyawa ko ina nawa saida motsa kansa nayo na zauna a cinyar
sa"yau kana da babban tukwici fatan kana da wurin ɓuya"kai ya ɗaga yana murmushi
sannan na tashi na koma mazaunina na fara yagar tsoka,yana ta kallona ganin ya raja
a akallon wani wuei itama ta kalla rabin ƙirjina ne ya fito waje saboda motsin da
nayi ɗazu,wani irin haushin shi ne ya kamata ƙiri ƙiri taga alamar zalamar wannan
ƴar jariyar a tare dashi murmushin ƙeta tayi a ranta ita kaɗai tasan me take
kitsawa'zan lalata wannan daren yau sai dai wataran amma ba yau ba',ba hamagiya a
tunanin ta yau ne farko batasan Niger aka barwa wannan tarihin ba,muna tsaka da cin
abincin aka ƙwanƙwasa ƙofa da kansa yaje ya buɗe aka shigo labulen dining na
ɗaga"Ya Hadiza"na faɗa da ƙarfin masifa saida ta toshe kunne,da gudu na taso na
ɗane ta tana dariya"kau Nana karki karya ni"dariya nayi"wane ni na karya matar
Alhajin Abuja masu ci ta bayan hannu",dariya tayi tana dafe kanta,dungure min kai
tayi"wallahi Nana kisan abu ma matsala ne",kwashewa nayi da dariya na kama hannun
ta muka zauna a falon,Babban Yaya ya yi saƙare wannan amintar da yaushe aka fara ne
bai sa ni amma sai ya bincika akwai lauje cikin naɗi,"Dije ba magana ne"juyowa
tayi"afuwan Babban Yaya wannan tsiwar ce ta ɗauke min hankali ina kwana au ina
wuni","kwanan dai Hadiza","a a Babban Yaya wunin dai",gaisawa sukai ya koma
dining,tashi nayi na kawo ma ta abincin da lemo da ruwa sannan na ɗauko nawa,kalla
ta yi"na shiga uku Nana halin na nan",juya ido nayi"saima abinda ya yi gaba Ya
Hadiza ke dainci naki ki ka biye ta ni baki ƙoshi wallahi",dariya ta yi ta fara
ci,tsagal na aje nawa kwanon na kama hannunta"Ya Hadiza ina da tambaya",tsorata ma
ta yi"kai Nana kin ba ni tsoro wallahi tambayar me",dining na kalla gama muje
ɗaki",kai ta kala sannan muka cigaba da cin abincin shegen zance na ƙwaƙulata,bamu
gama ba Aunty Hajara ta taso ta wuce ɗakin ta da kallo Ya Hadiza ta cike da mamaki
goɗoɗo haka da irin wannan shigar ko girkin ta ne ai bai dace ba amma sai dai ta yi
shiru dama aranta take kitsa haka tana gamawa na kwashe kwanukan nakai kitchen shi
Babban Yaya ma fita ya yi mukuwa muka shige ɗaki harda kulle ƙofa.
Kan sofa ta zauna tana ƙarewa ɗakin kallo"kai Nanata kin samu ɗaki amma fa ya
yi kyau",kusa da ita nazo na zauna"wa ya ga ya miki ɗakina ne nan to kinga part
ɗina can wannan ƙallagaggiyar matar ita tasa aka dawo da ni nan","ban gane ba da
wajen ki kuma adawo dake cikin part ɗin kishiya","eh mana to ai ita ta nema ni kuma
nace na amince darajar su Alhaji Baffa","eh haka ne kam nima jiya mun dai daita
dashi da Iyyo","kai amma naji daɗi sauranki miji gangariya kiyi auren ki tunda
bazawara ai bata wuyar auruwa","haka ne kam Allah ya kawo nagari to","ameen ameen
yauwa tambayata fa",juyowa ta yi muna fuskantar juna"ina jinki Nana","yauwa nace ba
kinga wannan matar ko kullum sai tana zaƙewa ita miji nata ne kalleta fa yau
girkina ne amma tayo wannan shigar",ƴar dariya ta yi"eh mana ai haka kishiya take
kullum sobtake tana nuna miki ta fiki a wurin me gida","to ya zanyi ne in yiwa
Babban Yaya abin da ko gilmawa ta ya gani sai yaji ni kawai yake da buƙata",zaro
ido ta yi"Nana ai wannan lamarin da wuya zaki iya kuwa","wallahi zan iya faɗa min
kawai","to shike nan kinga wannan al amarin na kwanciyar aure sai kin daure karki
na zama raguwa da yawan ƙorafin kin gaji ya kasan duk sanda yazo wajenki kina
maraba da shi",fannin rikita oga fa","eh shima abu ne musamman dole saikin cire
kunya ya zama duk abinda ya miki kina masa kuma ki kasance kullum jikinsa nan ne
wajen zaman ki hira mai daɗi da nu na masa salo salo na tarairaya kar kina la akari
da wai ya girmeki in kina nuna masa kece babba to wallahi sai ya zame mikintamkar
jarijari kar kuma kina jin kunyar wannan goɗamar tunda itama ba kunyar take ji
ba","to shikenan ya Hadiza yau darasin ki zai fara aiki dama tunda na dawo Sadiya
ke koya min abubuwa da yawa na tsuma jiki yau ysumi zaici ubansa",dariya sosai ta
shiga yi"a a fa Nana duk da dai kin haye siraɗin farko amma maimaici na da wuya dan
jikin namu da alama na gado amma dai tom","nafa gano ina ki ka dosa dan naji su Ya
Fatima na faɗar wai da tayi kwana biyu ba a taɓa ta ba sai ta koma kamar budurwa
ada ban gane ina maganar su ta dosa ba amma kwanaki na fahimta da Ya Amina da Ya
Dijama suna ta yi da sunam Ya Ruma","gaskiya suka faɗa","to shike nan Allah yasa
haka wallahi da anyi tsiya",ɗaka min duka tayi"shegiya aku ni bari na tafi kinga
magaru ba ta yi a tashi asha tsumi",miƙewa nayi nima"ai tsumi ya tsumu tun kwanaki
ke dai kawai bari muga ina ɓulle yau",dariya ta yinna rakota har bakin ƙofar gidan
sannan na koma ciki wanke wanke nayi na gyra dining dan ba buatar abincin dare sai
mutum yaga dama ko tea yasha dan ni haka nake mudin naci abinci da yamma bana cin
na dare.
Jin shiru bai shigoba har bayan sallar isha yasa na faɗa wanka na ƙalƙale
jikina da sabulu mai ƙamshi sannan na fito humra da lotion na shafa kaf jikina
sannan na ɗauke wata riga duka da kaɗan ta wuce ƙirjina sai siket shima ɗan ƙarami
bayan na gama na shafa turaruka masu tada hankali dan duk Aunty Mama taban dawowa
ta daga india banda wanda siyo acan nan da nan na haukata ɗakin da ƙamshi,takalmin
zanin gado na saka na fito dan naje na dafa ruwan tea tana ƙame a falo nazo na wuce
cije da mamaki ta bini da kallo sannan ƙamshin da ke bina ya makar ma ta fuska
kishi ne ya kama ta tasan wannan ƙamshin mace sai taji ya tafi da hankalin ta bare
namiji,ban gama shiga kitchen ɗin ba naji shigowar sa anan na coge har ya gama
shigowa ita dake zaune bai ganta ba sai ni da nake can ƙofar shiga kitchen wajena
ya yo na taho da gudu na faɗa jikinsa na ƙanƙame shi"oyoyo mijina","oyoyo mata
ta",ya rungume ni sosai,ɗagowa nayi ka shiga ciki zan dafa maka ruwan ɗumi
ne",gashi na ya saka hancinsa akai ya lumshe sannan ya buɗe ɗaukata ya yi cak"bar
wannan ruwan zafin zo muje ki faɗan sirrin wannan ƙamshin da nake jin kamar na
dauwama dake a haka ina shaƙar sa",zagaye hannuwana nayi a wuyansa"ka fasa shan tea
ɗin kenan",kai ya girgiza bana buƙatar komai yau sai ke",rufe idona nayi"gani ai
mijina sai yadda kayi da ni",murmushi ya yi ya wuce dani ɗaki nan ƙamshin yaje
wanda yafi na falo kamawa,muna shiga ta biyo bayan mu ya tura ƙofar da ƙafarsa amma
baisan bata rufu ba a kan gado ya ajeni na ɗago ina murmushi"muje kayi wanka ko
kaga dare ya fara","hakane kam taso ki rakani",ba musu na bishi amma ina gama haɗa
mai ruwan na fito na barshi,
Bai daɗe ba yau ya fito yana tsane ruwan jikin sa tashi nayi na ɓuya a cikin
labule ƙyale ni ya yi ashe yaga ƙafata a ƙasan labulen saida ya gama abin da yake
sannan yazo ya tsaya a gefen labulen shima ya ɓuya ƙamshinsa naji na ɗaga kai shima
na gansa a wurin ƙyalƙyalewa nayi da dariya zan gudu ya kamoni yana min cakulkuli
ina zillewa a wurin na kwanta ina harba ƙafa bina ya yi ya kwabta akaina ina gwama
numfashi na ce"wayyo zakai kisan kai",tashi ya yi"in na kashe ki na zauna da wa
kenan",tashi na yi na haye jikin sa a fuskar sa na ɗora tawa ƙirjina akan nasa na
busa masa iskar bakina na yi ya lumshe ido bakina na ɗora akan nashi cikin wani
irin salo na fara tsotsar laɓɓansa kamin na tura harshena cikin bakin sa na fara
juyawa,wani irin yanayi ne ya ziyarshe ya ƙara matseni a jikinsa ya tura hannunsa
cikin rigata yana shafo ƙirjina cikin lokaci ƙalilan na zage na fidda shi a
hankalin sa jikinsa har rawa yake yana niyar janye rigar jikina muka ji wani wani
uban ihu mai tada hankali lumshe ido ya yi ya miƙe da ni a jikinsa hijabina dake a
ƙasa ya janyo yasa min ya kama hannuna muka fita daga ɗakin Aunty Hajara ne ashe
muna shiga muka sameta tana ta juyi a ƙasa ga jini a wurin da sauri ya yi kanta ya
ɗaga tayi sharkaf da gumi sai taune baki take kallon inda jinin yake nayi kawai
naga yana ƙyalli nan na gane ba jini ba ne abin ƴan film ne,kenan ciwon ƙarya take
ni zata lalatawa nawa daren kinyi kaɗan wallahi na faɗa a raina a gigice nima nayi
kanta"Babban ka kira Doctor","wayar na ɗaki",cikin wahalalliyar murya tace"a a ba
sai an kira kowa ba ka kaini nayi wanka"rigashi magana nayi"me yasa zamu barki a
haka sai kace marasa hankali kalli halin da ki ke ciki",ban bari tayi magana ba na
wuce na ɗaki na ɗauki wayarsa na kira Doctor mukai magana dama nasanta nan tace
gata nan zuwa ba jimawa sai gata allurai ta ma ta sannan aka gyara ma ta
jikinta,kallon mu ta yi"na ma ta allurai na releaf da na bacci ku barta ta huta in
tai bacci sai gobe da rana da zata tashi",godiya mukai ma ta sannan ta tafi tana
mamakin yadda ƙaramar yarinya ta iya shiryawa mace kamar kitimurmura,tana tafiya
nace Babban Yaya kaje ka wanke jikinka kamin tai bacci zan taho",na faɗa ina goge
hawayen fuskata ni a dole tausayi,kaina ya dafa"kiyi haƙuri zata samu lafiya"kai na
ɗaga ya fita yana jan ƙofar dariya na sheƙe da ita ina dubanta ta fara lumshe ido
kanta na ƙarasa"sannu mara lafiya ni zaki gogewa hadda to shugaban da ya kowa miki
wannan makircin a wurina yake darasi kullum wai kina tunanin kiyi shekara da
shekaru kina morar mijin sai ni yau mai ranar farko zaki ɓata min rana ta wallahi
kinyi kaɗan yanzu kinga yadda nasa aka maida ke ko saima gobe da rana zaki tashi ba
da safe ba ki kiyaye ni fa Aunty Hajara karki bari wataran na nuna miki asalin
kalata wannan duk kaɗan nake miki Allah ki fita hanyata ko nasa a fatattake ki daga
gidan ko nasa ya daka miki yaji shan shekara guda",kanta na shafa"ma za bacci sai
da rana dan ko magana bazaki iya ba saida ranar",na miƙe ina ma ta byee jinin
ƙaryar ta ta na duka na shafo na goga a jikina sannan na miƙe ina ma ta dariya
gyara wurin nayi na fito ina kulle ma ta ƙofar na wuce ɗaki ina go ge
hawaye,fitowarsa daga wanka kenan na shigo kallona ya yi jikina duk ya ɓaci kama
hannuna ya yi muka koma toilet ɗin da kansa yamin wanka duk ya ruɗa kansa da shafa
jikina yake a towel ya naɗoni zuwa ɗaki bai barni na shafa ko mai ba ya kashe wutar
ya dawo inda nake,kai nifa ko faɗuwar gaba bana ji sai ace wai ana tsoron maza to
banda ƴar Haruna,zuwansa kaina towel ɗin kawai ya janye yasa ni a jikinsa bai tsaya
sararawa komai ba da kuzarin sa ya shiga jijjiga min kwanya ina taya shi wayyo
Allah naga banu ranar amma naƙi kuka sai baƙar wuya da nasha dan bai ɗagan ƙafa ba
sai kace wanda aka jona da inji amma tsiya irin tawa taƙi bari na nuna na gaji
saida amarya taci ƙaniyanta tukunna shi ya tausayan sannan ya barni,baccin azaba na
shiga gabatarwa kamar ba gobe ina ga ni da Aunty Hajaran aga mai tashi da rana.😂😂😂
😂😂😂😂

UMMU SADDI'Q CE 🌹🌹🌹

(Wallahi kar Amin ruwan sharhi aga tsiya🙄🙄🙄🙄)


🌈🌈🌈
🌈🌈
🌈

BABAN YAYA

Babban Yaya Free ne amma me so ya biyo ni Pc in sa a group don shagalin Nana


na buƙatar comments.
08146711395

31

Tunda na fara baccin azaba bansan inda kaina yake ba saida naji sanyin ruwa a
fuskata a hankali na fara buɗe ido na sauke su akansa yana zaune kusa da ni kansa a
jiƙe da ruwa murmushi ya saki"barka da safiya amaryar Babban Yaya",wani murmushin
azaba na saki ina hararar sa"ina Babban Yayan"na faɗa ina kallon gefe da gefe ƴar
dariya ya yi dan ya gane nufi na"ba gani anan ba ki ke kallon wani wurin",maida
kallona nayi garesa"ai daga yau ka canja suna a wurina wallahi dama haka yayun suke
su zage su ware ƙwanji ba tausayi su suburbuɗa ma ka azaba to wallahibda yau sunan
ka ILA",dariya ya shiga yi ni kuwa na ƙara zaƙalƙalewa,ganin na dage ina magana
yasa ya sunkuce ni duka na anan ya yar da zanin gadon tik da ni ya nufi towel,tab
ashe zuƙunno bata ƙare ba wata azabar na sha ta ruwan zafi sannan ya min wanka da
kansa ya hanani nayi komai,har ɗakin ya kawo ni yamin shirin sallah duk ina binsa
da kallo har wurin sallar ya kaini"oya yi tukunna saiki kiyi zancen"leɓe na cije na
tada sallah ya zauna a bayana yana ƙaremin kallo,miƙewa ya yi ya kwanta akan gadon
yana murmushi shi kaɗai yasan me yake ji me yake mai yawo a jiki wani irin filing
yake ji yana ƙara tasar masa in ya tuna me yaji jiya rufe idon sa ya yi yana
murmushi,bayan na idar na tashi tsaye da ƙyar na tsaya ina kallon sa sai murmushi
yake idon sa a rufe,wani kuka ne ya taso min na faɗa kansa ina duka,da sauri ya
buɗe ido yana sa hannuwan sa duka biyu ya rungumeni tsam daina dukan nayi na shiga
rera masa kuka kamar karatu,nutsuwa ya yi yana saurarena ganin bazan daina ba sai
ya ɗago kaina ya hale bakin mu ban farga ba ya fara sarrafa jikina wani tsit nayi
nace"nayi shiru wallahi dan Allah ka tausaya min haba Babban Yayana"ɗago kansa ya
yi ya zauna yana jawoni jikinsa"ina alfahari dake Aishatu kin zama ni na zama ke
kome nawa mallakin ki kiyi yadda ki ke so Allah ya miki albarka",a ƙirjinsa na
kwantar da kaina ina murmushi ɗago ni ya yi"ba kwanciya zaki ba Madam tashi kici
wani abu sannan kisha magani ko tawan",da sauri na ɗago na kalle shi"maganin me
zansha","dole kisha magani dan jikinki ya dai dai ta dan fa ba haƙura zanyi dake
ba",shagwaɓe fuska nayi"kabarni na huta mana dan Allah","ai sunan mu kenan ango
baka bari dan Allah",dariya na saka sosai ina nuna shi"Allah Babban Yaya kana bani
kunya",haɓa ya kama"ahhh to bani abata amma a tasheta daga gidan nan dan ni Nana
nake son gani kawai Nana ta ta da",ya faɗa yana ban hannu muka tafa,a haka dai ina
ƙi amma yaban magani sannan na kwanta bacci,shi ya gyara min komai sannan ya fita
sabuwar me aikin Hajara ya samu itama tana nata aikin gaishe shi tayi ya amsa yana
tura ƙofar ɗakin tana kwance tana ta bacci nan ya ƙara tausaya ma ta fitowa ya yi
yace me aikin tayi abinci cikin girmamawa ta amsa da to sannan ya koma ɗakin cire
kayan sa ya yi ya kwanta a bayana nan na ƙara shigewa jikinsa ya rungumeni.
Wajen 11 am ta tashi daga baccin allurar wanka tayo sannan tazo ta zauna tana
tuna jiya wani irin baƙinciki ne ke ƙara shigarta ji take kamar ta fashe
tashibtayi ta fara safa da marwa ko kaya bata sa ba magana ta shiga yi afili"wai ya
zan yi da yarinyar nan ne asiri ya ƙi cinta kissa taƙi tasiri a kanta wai me zanwa
yarinyar nan na rabata da gidannan...","baki da shi Hajara",na katseta"nice dai zan
raba ki da gidannan ko kinƙi ko kinso amma ba yanzu ba zan ɗaga miki ƙafa dan
wannan dramar ta ki tana min daɗi",nu na ni tayi da yatsa"wane ke yarinya ni ɗinnan
daki ke gani nafi gaban tunanin ki...","a daƙiƙanta ba Hajara kalle ni da kyau ki
gani a shekarun ne kawai nake yarinya amma a kwanya dake da malaman ki da bokayen
ki duk na shanye ku dan haka karki sarara min zuwa gaba kiga ya abin zai kaya
saboda dai Nana TSAMIYAR KAN KABARI ce baƙin cikin masu kunu ke kifa baini a
hankali dan nasan sirrinki na ƴan uwanki da ƙanwar gyatimin ki dana shi gyatumin
naki dan haka don't stop my hanya"ina kaiwa nan na juya ma ta hips ɗina dana ɗame
cikin skintight na fita a ɗakin zuwa kitchen ba ruwana da me aikin na shiga nawa
aikin dan be san na taso ba.
Jaɓar Hajara ta zauna tana dafe kanta kwata kwata ma ta rasa tunanin me zatai
tasan sirrin su kuma kamarya rasa ma me zatai tayi kawai ta janyo wayarta ta shiga
rubuta wata number ba jimawa ta kira aka ɗaga"ƙawata kizo ina son ganin ki",daga
haka ta kashe ta miƙe tana murmushi.
Tashi ya yi a baccin yana salati ganin bana nan ya yi murmushi ya sakko ya
shige toilet yasha wanka kamar zashi wani wuri mai muhimmanci daga kitchen naga
fitowar ta daga ɗakin ta ta zauna a falo tana kiran me aikin,ba jimawa da zaman ta
ya fito ƙare ma ta kallo ya shigayi ganin ta ras ƙarasowa ya yi inda take"ya jikin
Hajara",bata kalle shi ba tace"na warke ai","to Allah ya baki lafiya"yana maganar
na fito a da cup a hannu da gangan na sutale zan faɗi da azama ya ƙaraso ya riƙe ni
yana min faɗa"me yasa kin san baki iya tafiya ki ka fito maimakon ki tashe ni na
kawo ki",shagwaɓe fuska nayi kamar zanyi kuka"to ai so nake na warke saboda anjima
kar naji zafi shi yasa na fito ina ɗan taka ƙafar",ɗaukata ya yi cak"ban yarda da
wannan wayon naki ba muje na maida ki ɗakin in baki warke ba ai akwai gaba ko",ya
faɗa yana wucewa da ni ɗaki dan ya manta da ita a wurin,ɗan zamo kaina nayi baya na
kashe ma ta ido ɗaya,da ƙuwa tamin na ma ta gwalo a ɗakin ma ya hanan ni motsi
saidai na gaji da magiya na barshi,a haka muka wuni baije ko ina ba duk habaicin da
tai ta sakar masa bai kulata ba amma ya gane kaf dashi take.
Washegari naji garau sai tsiya ban fasa ba bama a gidan na wuni ba wurin
Iyyo na tafi na wuni can sai dare yaje muka taho ina sako ƙafa falon naji an buga
min abu a ka baya nayi na faɗi kafin ta yi wani yunƙuri ya sheƙa ma ta mari mai
hankali nan ta saki farantin hannun ta ta dafe fuskarta kamani ya yi na tashi tashi
tsayi sai nayi luuu na faɗa jikinsa,riƙe ni ya yi ya ɗago ni yaga bana numfashi
ɗaki ya wuce da ni ya ɗebo ruwa ya yayyafa min nan naja numfashi ɗago ni yay zuwa
jikinsa"am sorry Baby","don't wary Babban Yaya ya wuce ai"kaina ya shafa ya
rungumeni"ina son wannan haƙurin naki",cije leɓe nayi kawai,ya daɗe tare da ni har
wajen shabiyu sannan ya fita ranar kwana ya yi bala'i kai Babban Yaya masifaffe ne
ashe duk yana yi irin na ginin da ƙofofin ina jinsa da haka gari ya waye mana koda
muka haɗu ban nuna ma ta komai ba sai bayan kwana shida ranar girkin ta ne mai
aikinta ta je ruwan gogar tiles na zuba shampoo a ciki taje ƙofar ɗakin ta tana
goge ma ta ta fito da sauri ai kuwa ji ka ke tikkk tai zaman ƴan bori a wurin ina
tsaye a ƙofar ɗaki na taho da gudu"sannu matar gidan nan bari na ɗaga ki" wani
haushi ne ya kamata"in kika zo nan sai naji miki rauni"dakatawa nayi ina dariya
ƙasa ƙasa da dabara ta miƙe ƙugunta yace ƙass ƙass,ido na zaro"wayyo matar gidan
nan yau ba aiki sai dai ya tara na kwana biyu ya juyewa ɗaya matar gidan"da sauri
ta juyo tana kallona dan maganata ta bata mamaki amma batai mamaki ba in tai la
akari da yadda na zama kwanan nan faɗar magana nake gaba gaɗi kuma yana ji amma
baya tankawa,kamar na ma ta baki kuwa waishi tausayi kwata kwata yaƙi taɓata duk
nacin ta,bayan kwana biyu ranar girkina bayan sallar isha na fito dining da wata
shegiyar riga har nippile ɗina ana gani kuma sai naƙi zama kusa dashi nai zauna
pacing ɗinsa nan ya shiga bina da kallo ba wani cin abincin nake ba sai wasa
harshena nake ina shafa wuyana kallon da yake min ne yaja itama take kallon sa
sannan tana kallona daga baya ma ture kwanon nayi na miƙe ba magana na wuce ɗaki da
sanina na sauya tafiya ta har na shige ɗaki,zaraf ya yi ya miƙe tana masa magana
amma bai san tana yi ba yana shigowa ya danƙen sai majalisar tattaunawa tsakanin
Babban Yaya da ƙaramar ƙanwar sa,washegari da safe tana kitchen na ahigo na buɗe
frig taga na ɗau abu a roba na shanye na yar sannan nazo fita naji muryarta" ke
ƙaramar ƴar duniya"tsayawa nayi na juyo"na am waɗanda suka yankewa ƙasa
cibi",hararata tayi" wai nan kina nufin maganin mata ki ka sha","of couse da
matsala ne",dariya ta yi",kenen har kin san wani daɗin namiji da ki ke shan magani
domin sa",taɓe baki nayi"ni dai ban sa ni ba amma dai nasan shi in ya fara ya dinga
ihu kenen yana Nana da ɗi ki ke shi yasa nake sha dan na tsatstsafowa kan dare
kinga jiya harda naki aikin na karɓa"ban bari ta yi magana ba na fito ina ɓoye
dariya,bina da kallo kawai ta yi batasan me zatai ba kawai saita shiga marin kanta
Hhhhhhhhhh.

ALGERIA

Wata farar mata ke zaune a falo ya yinda surukar ta ke yanka ma ta fruit tana
miƙa ma ta ƴar dariya ta yi"Zahra kifa daina shagwaɓani haka ko kina so in zaki
koma gidan ki na biki ne"murmushi ta yi nan asalin kyanta ya bayyana"Allah kuwa
Mamana da na ji daɗin gaske ki bimu kawai kinga kawai saiki na zuwa ganin
gida...","ba inda zata lallai ma matar Uncle ɗin nan,nan nan fa Niger nace ta bini
sai tace wai ita bata iya barin ƙasar ta","kai Habib bana son sharri",Maman ta
faɗa","to shikenan Mamma ki bisu kawai nima dama zanje Nigeria kai wa ni saƙo sai
mu tafi duka","to shike nan amma dan Zahra ta zani",ihu sukai suna murna dai dai
wani matashin mutum yana shigowa"ku lafiyanku ku ke ihu kamar anci ƙwallo",da murna
Habib yace"Mamma zata biku ƙasar ku nima kan na koma aiki zan biku na kai wani
saƙo",murna sosai ya yi da hakan dama ya daɗe yanason ya ɗaukar yayar tasa ɗaya
tilo tazo ta zauna dashi a inda yake dan bai rasa komai ba bayan kwana huɗu suka
tattaro 9ja su duka Zahra da ƙaramin ɗanta sannan Mamma da Habib sai uban gayyar
Alhaji Mustapha.

Koda suka sauka part guda aka ware ma Mamma sannan Habib kwanan su bakwai da
sauka amma Habib ya rasa ta ina ma zai nemi wanda yazo dan shi washegarin ranar tun
safe Mamma tasa Zahra da Mustapha a gaba kan sai tazo gidan su tare suka shirya
tsaf mota sabuwa ta ga ni ta faɗa suka shiga driver ya jasu sai gidan su Zahra ita
kuwa gaba ɗaya ta shiga damuwa dan batasan me zata tarar ba shekara biyu harda
rabi.

******
Yau tun safe gidan yake a hautsine Hajiya Harira ba lafiya nan ɓangaren Iyyo
aka kawota sai yayyafa ma ta ruwa ake shigowa nayi ina hamma dan bacci nake ji naga
abin da ake mata ga wasiyya tana ta bayarwa kwashewa nayi da dariya ina nuna ta nan
kowa ya shiga bina da kallo cikin ɓacin rai Baffan mu yace"ubanki Nana dama baki da
hankali ban sa ni ba",tsit nayi na nutsu"ya haƙuri Baffa ai ciwan nata ne abin
dariya ku kun ɗauka mutuwa zatai",Hajiya Salma ce tace"haba Nana kalleta fa ai
wannan sai yadda hali ya yi","Allah Aunty Salma ciwan kuɗin ta fa take","hakane
Nana muma ai hakan ce zata kasance damu gaba kaɗan ni duk jikina ma ya yi
sanyi",cewar Safiyya,dariya na ƙarayi "Babban Yaya matsa kaga yanzu zata
warke"baiyi musu ba ya matsa naje kanta na tsaya"Mama Harira sannu Allah sa can ta
fi miki nan"mirgina kai kawai take tana salati,rigata na tattare na fiddo wani
damin takarda"tashi ga takardunki karki mutu wa zai rainar miki ƴaƴan ki"cikin
ƙiftawa da Bismillah ta ware ta tashi zaune ta warci takardun hannuna salati
mutanen wurin suka saka kafin kace me Hajiya Salma da Safiyya suna cafke min
hannu"mufa Nana mufa","suna haɗe kowacce ta duba nata",kan Hajiya Harira sukai
cikin ƴan sakanni kowa ya karɓi nashi,mutuwar tsaye duk mutane sukai da masu su
suka tabbatar musu na gaskiya ne,Babban Yaya ne ya matso kusa dani yana kama
hannuna"Nanata ta kaina a ina kika samo waɗannan takardun?",ɗago kai nayi na kalli
Aunty Hajara sannan na kalli mutanen wurin nace"kasan a mutane ma akwai masu cin
abinci amma a zahiri dusa suke ci to haka waɗannan matan na Abba suke shi yana basu
shinkafa su suna cin ɓuntu wai ginɗima ginɗima dasu amma wannan ramarmiyar matar ta
musu wayo kuma su waɗannan musamman ma biyun nan sai suna nuna a dole su wayayyu
ne,ko uban wa ya faɗa musu ana yadda da kishiya muddin ba irin Aunty Mama ta
bace"kwashewa akai da dariya har mai shirin barin duniyar mu,"ranar da aka raba
gadon naje wajen Yasmin sai naje ta wajen garden ɗin shanu anan na tsinkayi Hajiya
Fulera da yayanta suna tsara yadda zasuyi a sannan na ma ta karɓi takardun tunda
naji haka ni kuma nasan wannan matar wataran zata shuka tsiya shine na zama ƙawarta
a dole kullum ina zuwa wajenta naita shirga mata ƙarya da bata kulani saboda abinda
na taɓa ma ta amma dana nace sai take kulani har muke zuwa ɗakin ta muyi ta hira da
dabara naita neman takardun amma ban samu ba sai watarana naje sai aka kirata a
waya da yake ta maida ni tinkiya inta zuwa makaranta tun ina ƙarama ubana yay ta
kashe kuɗi shine ta zata ɗan jaki primary nayi ina ɗan dolo secondry sai tai waya
agabana da wani har yana tambayarta ita ɗaya ce tace masa a a amma ta tare da ita
bata jin turanci ni kuma nai kwance na nuna banaji ɗin anan to naji guduwa take
sonyi,tunda naji haka sai na ƙara sa ma ta ido watarana da sassafe naje sai na
tarar mai aikinta na shara sai nace ta kawo na taya ta sai tace to na sharo ɗakin
Hajiya amma na karkaɗe ko ina to dama kullum da takardun da nabi Alƙalin nan ya
bani a ƙuguna dan shima ce masa nayi Abba ya sani abu amma yaban takardu na shaida
zanyi amfani dashi bai duba ƙanƙanta ta ba ya bani shine nazo na cike tsaf dan naga
wata takarda wurin Babban Yaya to ita na kwafa,dana shiga sharar nan naita zaro
loka banga komaiba sai naga wata jakar makaranta nasan dai ɗakin yara daban to me
jakar makarantar su zatai anan sai kawai na ɗakko na bule ashe takardun ne a ciki
ba wasa na share na ciki na zuba ma ta na bogi to dasu ta ɗane London tana can tana
shan kodimo abin ta",dukkansu ukun zuwa sukai suka rungumeni harda kukansu da ƙyar
suka saken kowa na wurin yana shimin albarka ya yinda kishiyata keta yankan
harara"ku dakata"na faɗa ina duban su Hajiya Harira,tsayawa sukai nan na matsa kusa
dasu"ko wacce ta lissafa sau nawa ina kai ma ta kuɗi",da mamaki suka duban nace"ku
lissafa mana",lissafawa sukai nakai musu wajen dubu ɗari takwas takwas"to bari kuji
yasin kuɗin ku ku ka ci"cikin mamaki suka buɗe baki dariya nayi na kama ƙugu"dame
ku ke tunani inta kwaso kuɗin mijina ina baku kuna ci bayan shi kullum yana zarya
tsakanin tashar mota da ta jirgi dan tara nasa kuɗin to takardar shaida da Abba ya
rubuta ma kowaccen ku da ita nake karɓo kuɗi in naje makaranta sai na kawo muku
kunga ko badan Allah ba ai yasha addu a wurinku"dariya sosai ake yi a wajen nan
Alhaji Baffa yace"ku masu kuɗi to kuyiwa Nana godiya da kyau sannan Nana ita kuma
Fuleran fa?","barta kawai tsoho zaku ganta ta dawo ba shiri dan nata takardun ma
suna wurina zan rabama almajirai ko Kawu Iro?","hakane kuwa ƴata ni zan ma kaiki
wata babbar tsangaya","kaji ko Alhaji"dariya sosai akai a wurin nan Alhaji Baffa ya
yiwa kowa nisiha aka watse sai yaba min ake ni kuwa daɗi kamar ya kashe ni.

Tunkafin mu kai gida Hajara ta kira Abbanta a waya ya bata number Hajiya Fulera
nan yake faɗa ma ta ai tunda ta tafi bata kira shi ba kashewa ta yi ta shiga zagaye
a ɗakin taya zata raba ni da takardun da nace yana wurina rasa ya zata yi ta yi dan
haka saita barwa ranta duk randa bana nan zata bincike ɗakin ta ɗauke.
da yake ranar girkina ne dan haka muna komawa na shiga haɗa break yana bina
a baya wai so yake yaga a ina wayo na ya maƙale,in yana maganar sai dai nayi dariya
kawai amma nima ina mamakin abin da nake,bayan na gama ya karya ya fita sannan na
gyara ɗakin inda na aje waɗancan takardun naje na sauya dan hakanan nake jin ajiyar
bataiba,fitowa nayi falo na kame ina kallo sai kwasa dariya nake naji an turo ƙofar
kaina na juya naga mata ne su huɗu riɗa riɗa ban kulasu ba ganin ta fito tana musu
sannu da zuwa wurin zama ta basu na tashi naje na kawo musu ruwa da lemo sannan na
duƙa nace"ina wunin ku"washe baki sukai suna dariya suna amsawa tashi nayi ina
kallon ta"bari na koma ciki kuji daɗin gaisawa ko" na wuce a ladab ce a ɗanlokon da
daya ɗaga na coridon na laɓe jin ɗayar na cewa"kai Hajara amma akwai ki da sharri
dama kishiyar taki haka take da ladabi ga girmama mutane gaskiya tama fiki
kirkin","hakane kam ni da take cewa yarinyar bata da kunya bata da mutunci su Zina
na tayata na ɗauka gaske ne"cewa ɗayar,kasaƙe tayi tana dubansu dan tabbas ba ta da
abin cewa kota faɗa ma bazasu yarda ba dan kowa nawa haka ƙaryar sa ace zanyi wa ta
tijira ya amince,dariya nasha na shige ɗaki ina magana ni ɗaya"kina wasa da ni
Hajara ni sai na rabaki da mutanen ki ma wallahi duk su dawo wurina suma waɗannan
naga ƙaramar ƙwaƙwalwa garesu irinki",anan na zauna"gaskiya bari Babban Yaya yazo
ya siya min tv ko mai doro ce"waya naji na ringing na shiga dubawa ashe shine ya
manta da ita My number na gani tana kiran saina ɗaga dan na gane da ɗayar wayar
kenan ya kira"Hiiii My Sweet Miji"dariya ya yi"kina birgeni My Sweet Mata"ƴar
dariya nayi"ya aikin fa","normal ma za jeki get akwai baƙi Murtala yace baisan su
ba kuma tace masa ƴar gidan ce yace ko yasanta ya manta ta kinsan na hana abar kowa
ya shiga gaba gaɗi","ok yanzu zanje"na kashe nasa Hijab na fito"Aunty Hajara zanje
get na dawo"ba yadda ta iya tace"saikin dawo"fitowa nayi ina dariya na ɗan daɗe ina
tafiya sannan na isa suna ganina suka miƙe suna"Hajiyar manya"dariya nayi dan haka
suke faɗa tun daga auran Murtala buɗe min get sukai na fita nima ban gane su ba
saida ta gefen wani saurayi ta juyo ihuu na buga nai kanta da gudu"Oyoyo Ya
Fatsima"da sauri itama ta taho muka rungume juna wannan saurayin sakin baki ya yi
yana mamakin gani na,da ƙyar muka saki juna sannan na shiga musu sannu da zuwa,bina
da kallo wannan saurayi ke yi na juya muka haɗa ido"kai malam daina kallo na ni
matar aure ce"dariya suka kwashe da ita ya yinda yace"ai nafi kowa sani ranar da
ki ka zama matar auren ma da gaske ina wurin",da hanzari na kalleshi na kauda kai
Ya Fatsima ta dafa ni"da gaske ki ke kinyi aure ke Nana bana son sharri","Allah Ya
Fatsima ni da Babban Yaya mun jone tuni"dariya sukai har matar da suke tare sannan
nace mu shiga mana,tunda muka doshi gidan naga yadda take a tsorace batasan Gwaggon
yanzu bata da bace,ƙofar falon na tura da hanzari na"Ya Hadiza fito kiga"na faɗa da
ƙarfi daga kitchen da ta fito"Nana nan kuma ki ka taho..."shiru ta yi tana kallon
wadda ke bayana ido ta zaro ta taho da gudu"Fatsima"kan tazo itama ta tafi suka
ƙanƙame juna sai suka fashe da kuka,wannan matar mumushi ta yi tana jin daɗin ganin
akasin abinda suke faɗa ma ta kullum,jin kuka yasa Gwaggo fitowa tana faɗin"ke dawa
kuma Hadiza"turus tayi ganin wata matar me kuɗi rungume da ƴarta ɗago kai Ya
Fatsima ta yi"Umma",tahowa Gwaggo ta yi da mamaki"Fatsima ce da gaske",sakin Ya
Hadiza ta yi tana nufar ta"nice Ummana"da sauri Gwaggo ta taho"ƴata jama a ƴata"sai
ta fashe da kuka nan ta rungumeta ƙamƙam"ki yafe ƴata ki yafemin dan Allah",cikin
kukan itama take cewa"kiyi shiru Umma kiyi shiru"sai sannan Umman taga matar da
suke tare sakinta tayi tana ƙarasawa ga matar"Hajiya Bismillah yi haƙuri an barki a
tsaye"ƴar dariya ta yi"ai ba komai naji daɗin ganin hakan a tare daku",nan tashigo
ta zauna Umman nata hidima da ita sai sannan nace"Gwaggo ai kin bar ɗan naki a
waje","lahh Nana ce su shigo",fita nayi nace su shigo sai sannan suka shigo wannan
saurayin sai kallo na yake hararar sa nayi,nu na ni nayi"kin daina hararata ko
saina maida ki Niger",kallon mamaki na masa au ashe acan ya ganni shi yasa yake
kallona,baki na kama na maka masa harara"ai ni da Niger ko ta aljannace na
yafe",dariya sukai nan nace Gwaggo na tafi kai rohoto saina dawo"da sauri wannan
saurayin yace"ki kira min mijinki kice ya yi baƙo daga bariki ta Niger","naƙi in
faɗa ɗin kaita jiran sa sai biyar zai dawo","jeki ai naga bake kaɗai bace a
gidan",fita nayi ina dariya nan naje na faɗawa su Mama sannan na kira Babban Yaya
na faɗa masa saƙon wancan kan na gama faɗa ya kashe da mamaki na zare wayar ina bin
ta da kallo.

Su Mama kaf sunje sauran matan ma saiga Babban Yaya cikin hanzari har falon
ya shigo da sallama wannan saurayin ne ya tashi yana dariya"kaga angon garin
wasu"hannu ya bada suka tafa ya yinda ya juya ga matar nan da sauri matar ta miƙe
ta dafe ƙirji baya ta ja tana nuna Habib tana son yin magana amma ta kasa.
UMMU SADDIQ CE🌹🌹🌹🌈🌈🌈
🌈🌈
🌈

BABAN YAYA

Babban Yaya Free ne amma me so ya biyo ni Pc in sa a group don shagalin Nana


na buƙatar comments.
08146711395

32

Da ƙyar ta samu baki tace"amma kai ɗan Habibu ne ko?",cikin mamaki kowa ya
bita da kallo a hankali ya kaɗa kaɗai"eh nima sunan Babana Habibu amma ba ka lallai
asance wanda ki ke sa ni ba ne",kai ta kaɗa jinin Habibu ko a mafarki na gashi zan
gane dan Allah ka nuna min ko hoton sa ne in tabbatar"kunsan ni da shishshigin
masifa a wayar hannuna na kamo hoton na matsa gaban ta na nuna ma ta,danƙar wayar
tayi"wallahi shi ne wannan mijina Habib ga ɗan uwanka nan kama ka daina min tijarar
na haifeka ba ta hanyar aure ba",cikin tsantsar mamaki kowa ya buɗe baki,amma fa ta
dage sai da aka kira Alhaji Baffa shima ya yi mamaki nan nace kowa ya dakata ina
zuwa,shiru akai ana kallona nan na tafi can gida na bin ciko wani hoto ƙarami
fuskar ma ba sosai ake gani ba na dawo bata nayi nace"wannan hoton waye"karɓa ta yi
ta duba"ni ce wannan ai a ina ki ka samu?",murmushi nayi na dubi Babban
Yaya"gaskiya ta faɗa"cikin mamakin mamaki aka saka salati"ke Nana taya akai ki ka
san da zamanta?"ɗan murmushi nayi"kun ɗauke ni yarinya amma shi Abba baiga yarinta
a gare ni ba har yake sawa a ɗakko masa ni yaban labarai nayi dariya sannan yaban
wasu sirrika nashi wanda bai taɓa faɗawa kowa ba a irin wannan labaran ne yake
faɗamin ya auri wata mata a Niger amma ƴar Algeria ce ya barta da ciki sanadin wani
abu da Babanta yace, dai dai da sakin da ya ma ta Babanta ne yace in bai sake ba
zai tsine ma ta to ganin shi baƙo ba shi da kowa sai ya sauwaƙe ma ta to ya tafin
ne kawai sai yaji ya ƙara mantawa da komai akuma sanda ya tuna lokaci ya ƙuri dan
wannan allurar da mugayen can suka masa ta fara tasiri...",saurin shiru nayi ina
wai gawa naga Babban Yaya da wannan ɗayan Habib ɗin sun zura min ido ganin basu min
magana ba sai na gane basu fahimci me nake nufi ba dan haka saina cigaba"to shine
ya zayya ne min komai yaban wannan hoton yace ita kaɗaice mai hoton in ta gani zata
san itace a jiki ɗan kuma ko baya kama da kowa zai yi kama da Mama dan Babban Yaya
ma da ita yake kama",cike da mamaki Alhaji Baffa yace"tabbas shi yasa Habibu yace a
kula dake to kai Habib saika ƙara kulawa da matar ka kallon juna sukai wato Habib
da Habib da ne,Mamace tace baiwar Allah taya akai kika yarda ki ka auri mutumin da
bakisan a salin sa ba?",a jiyar zuciya tayi"gaskiya na aminta dashi ne dan yaron
Babana ne sunkai wata biyar da haɗuwa amma bansan a ina ska haɗu ba sai yazo dashi
gidan mu dama asannan za a min aure bana son mijin kawai sai nagansa nace shi nake
so kowa ya yi mamaki shi kuma Babana ya amince saboda ni kaɗai ya haifa mace sauran
duk maza ne,bayan auren mu da wata biyu sai Habibu ya ɗaukaka kasuwanci kamar ƙasa
har yafi Babbana mutane to sai Babana ya fara jin haushi watarana aka zo aka ce
yaje inji mahaifina sai yamin sallama ya tafi sa ilin ina da ciki wata huɗu to
tunda ya tafi kuma ban kuma ganinsa ba har yau dan Allah yana ina",sunkuyar da kai
kowa ya yi da salama Hajiya Salma tace"ya rasu muma matan sa ne"fashewa ta yi da
kuka ya yinda Habib ya sunkuyar dakai yanajin kaɗaici ina ya taɓa haɗuwa da shi ko
sau ɗaya ne ai da ƙarar da koda kamar sa ce,hwnnunsa Babban Yaya ya kama sannan ya
ɗago ya kalle shi"kayi haƙuri dan kaine yanzu take sabuwa a wurinka"kaɗa kai ya yi
yana ɗan murmushi saida kowa ya nutsu sannan aka maida zancen ya Fatsima godiya
kowa ya musu da yadda suka bata kulywa ga ɗanta ƙato, A gidan aka ƙarasa wunin yau
sai da magariba sannan Alhaji Baffa yasa aka kira masa Habib da mamarsa sannan
kawun sa sai ni da Babban Yaya da Mama da Baffan mu dubansu ya yi yace"Hajiya gashi
Allah ya kawo wani ɗan na Habibu sai dai an raba ga do tuni amma ni..."da sauri na
katse shi"Alhaji Baffa shima fa da nasa zan ɗakko masa yana can ɓangaren Abba ni
nasan inda ya aje",da mamaki suka dube ni sai dai ni dariya nake shima Baffa
dariyar ya yi"Hajiya Nana kice shima wannan sirrin kin iya ɓoye shi to kunji kai
Habibu matar yayanka tace zata baka naka kason",ƴar dariya ya yi"ai zan ɗauke su
ita da mijin nata mu koma barikin Niger da zama"da sauri na galla mai harara"kai
kuwa anya kana son yayan naka ka ke haɗashi waccan jahannamar"dariya sukai gaba
ɗaya yana cewa"Niger ɗin ce jahannama","eh mana ai ni duk kuɗin goro na musu malam
kaga bacci na ke ji ka lallaɓani gobe na ɗakko maka dumus yaro",kwashewa ya yi
dariya"to matar Babban Yaya zan kuwa lallaɓa ki yanzu ma tashi kije ki kwanciyar
ki",miƙewa nayi na musu sallama Mamma da Mama suna Allah ya tashe mu lafiya ban bi
takan Babban yaya ba na shige gida frig ɗin Aunty Mama naje nai sibare dan tun
yamma naga ta haɗa wani ta juye a robar faro shine yanzu naje na ɗauke kunga koma
na waye na jaza ma ta ko? direct gida na wuce dan akwai haske bana tsoro kuma bana
son takurawa Babban Yaya shima ya zauna da ɗan uwansa suji ɗumin juna.
Baya sun fito Mamma ɗaki guda Gwaggo ta ba ta ita kuma Ya Fatsima suna
manne da Ya Hadiza suna ta hira da bawa juna haƙuri dama Baba baya nan yaje garin
su ɗaurin aure ai da bire ɗen yafi haka,daga wajen Alhaji Baffa mota suka raka
Alhaji Mustaphan ya wuce sannan su kuma ya wuce da Habib ɓangaren Abba Habib yasha
mamaki yanayin wurin kamar ana rayuwa a ciki har ɗakin ya kaisa yace"ka kwana anan
sai kafi jin daɗi zakaji kamar Abba na nan ne",godiya ya masa sannan ya fito zuwa
nasa makwancin.
Ɗakin Hajara ya shiga ya ganta sai kwasar bacci take tana warti fitowa ya yi
yana ja ma ta ƙofar harna fara bacci naji motsi buɗe ido nayi na gansa yana sa riga
da alama wanka ya yo tasowa nayi na kwanta a bayan sa ina zagaye hannuwana a cikin
sa,murmushi ya yi ya ɗora hannunsa kan nawa"Madam Habib sarkin basira
yadai",zagayowa nayi ta gabansa ina langwaɓar dakai"wallahi yau nayi magana da yawa
kaina ciwo yake",ɗora hannunsa ya yi a goshina"ayya sorry bari na samo miki
magani"yana ambatar magani na sau shi"ai ma na warke Babban Yaya dama,kaci abinci
taho mu kwanta bacci nake ji",ɗan murmushi ya yi ganin na masa wayo akan maganin na
waske,hannuna ya kama zuwa bakin gado ya zaunar dani sannan ya kawo pracitamol ya
bani ba yanda na iya haka nasha ina ɓata rai fushi nayi na kwanta na juya mai baya
maida ruwan da maganin ya yi sannan ya kashe ya hayo inda nake,banyi motsiba nai
shiru wani bacci a cikina naji hannun shi yana shafa nan ma shiru na masa kome zai
min na masa shiru saida ya birkitoni dukkana ya ɗora kansa sannan ya kamo fuskata
ya ɗora bakin sa kan nawa wannan juyayin ne na kasa juyawa baya a dole na miƙa wuya
dama naje na sato tsumin Aunty Mama ai kuwa na gurzu.

Kwana uku da zuwan Ya Fatsima mukai taron family har su Ya Saddi'q sun wanko
ƙafa sun dawo anyi dasu wannan abu ya dasa farin ciki a zuƙatan mutane kuma anyi
yafiyar juna bama ya Kawu Iro da matansa sun nemi ya fiyar Iyyo sosai dan haka
wanzar da yadda za'a cigaba a gidan akai kuma gashi an ƙaru dan Habib shima ya zama
ɗan family sai yamma na ɗakko masa wasiyarsa kowa yasha mamakin abinda ya bar masa
kuma acan Niger da Ageria ne suke zan wuce ya zaro wata takarda ya miƙo min"ga
ladan ajiye sirri matar Babbar Yaya"tsayawa nayi ina kallon sa sai kuma na kwashe
da dariya"kaga bana son salo nima ina da nawa yamanfi naka yawa",dariya ya yi"ai
nasan da haka da nawa yafi naki da haɗa miki zanyi duka dan kin cancanta a miki
komai","nifa bana son salo kaga ɗan Niger",dariya ya riƙe"kuma dama acan abinda na
baki yake"da sauri na ƙara gaba"bana so bana so kaba matar da zaka aura"a bazata ya
juya ya miƙawa Ya Hadiya"cak na tsaya ina kallon sa washe baki nayi"da gaske ka ke
ita zaka aura",ƴar dariya ya yi"indai kin amince nasan zata amince dan na ma ta
magana tace ana tambayeki",kallon ta nayi"ni matsala dake Ya Hadiza ƴar Sakkwato ce
ke madadinbtun alokacin ki amsa",tasowa tayi ta kama hanuna"ban amsa bane saboda a
yanzu kece mudubina dake nake so nayi koyi ko kaɗan ne dan haka saikin amince
sannan zan amince",rufe ido nayi ina jin tausayin ta ita babba amma ta maida kanta
ƙarama saboda kuskuren da ta yi tun farko,buɗe idona nayi"na amince Ya Hadiza Allah
ya sanya alkhairi"ƴar dariya tayi ta juya ta karɓi takardar,tafi su Ya Hasiya suka
shiga yi ya yinda wani sanyin daɗi ya kama zuciyar Mamma yau burinta ya cika ɗanta
a danginsa sannan zaiyi aure a danginsa,shagalin mu ƙaruwa ya yi har kwana biyu ana
taron sannan aka gama.

BAYAN WATA UKU

A gidan mu a ka sha bikin Ya Hadiza kamar kar a daina kwana uku da gama biki suka
ɗaga Niger Mamma da Ya Fatsima dama gida ɗaya zasu zauna.
Daga kitchen na fito naji Aunty Hajara na magana a ɗakin ta dama yayarta
tazo har zan wuce naje ƙofar ɗakin na tsaya ni ba laɓe nai ba amma in baka da
hankali da cikakkiyar nutsuwa to bazaka ganni ba ita kuwa ta dage sai zuba take"ai
ni Yaya na rasa ya zanyi da wannan ƴar masifar yanzu fa kiga ƙanin sa da nake faɗa
miki ƴar gidannan fa ya aura su sai dai suyi ta cin dukiyar a tsakanin su kin sanfa
Abba yana shirya wani abu amma yaƙi faɗama kowa..."katse ta nayi"zai raba Babban
Yaya da Babban company ko to kima faɗa masa karya soma in ji ni in ba haka zai
tsinci kanun labaran badaƙalar da ya aikata wani satin a jaridar daily trust sannan
da kafar ƴaɗa labarai ta BBC ke kuma tsohuwar kilaki ko zuwa ki kai kashe ma ta
nata auran kijata barikin? ko ki fita ko kuma na tona miki asirin sanadin ɗanki na
fari",kamar ƙiftawar ido ta suri jakar ta ta fita da gudu tun da take wani bai taɓa
bata tsoro ba irin na yau,itama Aunty Hajarar tsuru tsuru tayi kamar kaza a ruwan
zafi,fita nayi a ɗakin dan in ina kallon ta ji nake kamar na kasheta.

Rayuwa tayi nisa, tsaka ni na da mijina yana ba ni kulawa yadda ta dace a tsakanin
mu da Hajara ma baya banbanta mu sai in faɗan namu ya motsa muyi kaca kaca amma
agaban wasu sai in nuna ƙalau muke wannan abu kuwa na damunta,sannan tayi tayi ta
shiga tsakanin mu da Babban Yaya amma abin ya gagara sai dai fa tayi alƙawarin sai
ta shiga koda kuwa zatai sanadin nata auran.

******
Yau tun safe ta tafi gida ta samu Abbanta ta falo ta zauna ta faɗa masa kome ke
faruwa murmushi ya yi yana duban ta"ki kwantar da hankalin ki ba bu abinda zata iya
yarinya ce fa ƙuruciya ke damunta amma kafin takai matakin hankali zan rabata da
hankalin nata",girgiza kai ta yi"Abba in kuna cewa wannan sheɗaniyar yarinya abin
da ta ke wai ƙuruciya abin na bani haushi Abba wannan ƴar abar da ka ke gani zata
haɗa wutar da baka tunani",duk naji ƴata ki kwantar da hankalinki kedai ki samu
ɗakko waɗannan takardun sannan ki ɗakko min na mijinki ma iya wanda ki ka gani","to
shike nan Abba","yauwa yaushe ne tafiyar tasa",saura kwana huɗu","ok ki kula kisan
yadda zaki ki bishi kome yana can","to Abba",ranar wuni ta yi bata nan sai dare ta
dawo dama girkinta ne shi yasa ba ruwana da su nifa ranar da yake girkina bana taɓa
tunanin akwai wata shi kaɗai nake gani kuma nake ji araina ni kalai ce ba wata.

Ranar da zai tafi girki na ne kuma tunda na tashi gabana ke muguwar faɗuwa
sai dai nayi ta addu a sannan na kira Mama na faɗa ma ta tace nayi addu a ba abin
da zai faru,wajajen ƙar fe shabiyu zai tafi ya fita yakai ma Alhaji Baffa saƙo sai
gata ta shigo har ɗakina tana dariya hannun ta ɗauke da kofin ruwa ban kulata ba
saida ta dubeni tace"matan aure yau zanyi wasa da auren naki",dariya nayi"Allah ya
baki sa a dama shi ai rai ne dashi in ya mutu ba komai bane sai dai ki tuna shi
ramin mugunta gajere ne in zaka gina shi gina shi gajere",dariya ta kwashe da
ita"to wannan ramin naki ne yarinya"shiru ta yi jin ya taho sai ta fara yayyafa
ruwan hannun ta wurin harda jikina da saurin na miƙe"ke miyi ruwanki da ni ne ki ke
shiga rayuwata",sanyaya murya ta yi"haba Nana daga nace ki daina shan maganin hana
ɗaukar ciki ya kamata tunda ni banyi ba ke kiyi shine zaki zageni","what"na faɗa
cike da mamaki cikin fusata Babban Yaya ya ƙaraso ya warce maganin a hannunta yana
dubawa da idanuwan sa da sukai ja lokaci ɗaya ya ɗago yana dubana"miye wannan
Nana?"nima kallonsa nayi"ita da ka gani a wurinta ita zaka tambaya"tass ya kwaɗan
mari wanda saida naga taurari dafe wurin nayi na faɗi a ƙasa daɓas na fashe da
kuka,tsawa ya daka min mai razanar wa"ina sauran maganin yake"ɗago kai nayi"ita da
ta baka wannan saita ɗakko maka sauran ai ita ta bani tace maganin infection ne
shine nake banka kuma kullum huɗu nake sha",cikin tsanin faɗuwa gaba ta gwalo ido
tana dubana shima ɗaga kai ya yi yana kallon ta"Hajara"magana zatai ya fesa ma ta
mari ya ƙara ma ta wani saida ya ma ta huɗu sannan ya danƙi wuyanta ya haɗa bango
nan take idanuwan ta suka fito waje cikin tsananin fushi ya fara buga ma ta
kashedi"wato kinga batasan magani ba shine zaki cutar da ryuwarta bakisan matsalar
da ta ke ciki ba dama to bari kiji wallahi wani abu ya samu matata saina kashe
ki",kuka na rushe da shi ya sake ta ya taho takaina da sauri ya rungumeni"shiiii
Nana Allah ya kare min ke"saki na ya yi ya buɗe sif ya ɗakko trolly ta dana zo da
ita wancan karon ya shiga loda kayana komai ma ɗauka yake ni dai ina tsaye ina kuka
ya yinda itama take baje a ƙasa dafe wuya tana tarin wahala,yana gama zuba kayan
yaja hijabina ya ɗakko jakata duka trollyn ya jawo waje sannan ya kamo hannuna muka
fito a ƙofar ya dakata yana juyawa ya nu na ta"fito aɗakin nan kan nazo na ƙarasa
ki",da sauri ta rarrafo ta fito ya rufe ɗakin ya jawo hannuna muka fito banwa kowa
sallama ba yasa ni a mota muka bar gidan,a airport ba tare da ɓata lokaci ba aka
bashi tiket ɗina sannan ya dawo inda ya barni wayam ya gani mutanen dake zaune a
wurin ya kalla "Malam ina yarinyar dana bari anan yanzu",tashi ya yi tsaye"yanzu
wasu mata su huɗu suka zo suka tafi da ita mun zata gudowa tayi daga gida shi yasa
muka barsu suka tafi da ita",wani dam yaji a cikin kansa in ya fahimta mutumin na
nufin ta ƙarfi aka tafi da ita kenan.

*TUR ƘASHI*
*WA YA ƘWAMUSHE NANA MASIFA YA ƊAUKAR WA KANSA MASIFA?*

Ummu Saddiq ce🌹🌹🌹


🌈🌈🌈
🌈🌈
🌈

BABAN YAYA

Babban Yaya Free ne amma me so ya biyo ni Pc in sa a group don shagalin Nana


na buƙatar comments.
08146711395

33

Cikin lokaci ƙan ƙani Babban Yaya ya hautsina airport ɗin nan amma ba amo ba
labari kuma cameras nasu basu ɗauki komai ba kafin biyar na yamma tashin hankali ya
baza ko ina haka ma ƴan sanda suna ta bincike shiru wayarsa ce tayi ƙara ya ɗakko
ya duba BRO ya gani da sauri ya ɗauka"Bros ina kiran wayar yallaɓiya amma bata
shiga",runtse idon sa ya yi yana jin kamar zuciyarsa zata fashe da ƙyar yace
masa"tun safe nima nake nemanta ban ganta ba",wani irin ihu ya masa a wayar saida
ya janye ta daga kunnen sa jin ya lafa ya mayar sannan yana cewa"kamar ya ba a
ganta ba kuma ba a faɗa min ba why Bros","munzo airport na barta naje karɓa ma ta
tiket shine na dawo aka ce min wasu sun tafi da ita",daga can dafe kansa ya yi yama
kasa magana sai kawai ya kashe wayar,a dai ranar ba wanda ya kwanta daga addu a sai
kuka hankalin kowa ya tashi Aunty Hajara kuwa duk tsamar da muke saida hankalinta
ya tashi dan kana kallon kowa na gidan saika tausaya masa gida tashi guda ya zama
kamar na makoki tashin hankali ba babba ba yaro jaruman kaɗan ne dan Baffa ma ba a
barsa a baya ba ya nuna mutuƙar damuwarsa kan ɓatan ƴarsa shugaban kuwa ai har
yakai ga baya gane gabansa sai dai ya yi komai a hautsine mutanen nesa dana kusa
kowa ya sa ni dan wasu ma suna gida.

*KENYA*

Wani irin sanyin a zaba ne ya ke shiga sassan jikina hakan yasa na buɗe ido a
hankali cikin jin kan yamin nauyi bin inda nake da kallo nayi sai naga ɗaki ne
tafkeke bakomai ciki sai katifar da nake kai da wata tabarma a gefe banda shi ba
wani abu na ruwa,da dabara na tashi na zauna na dafe kaina,kamar amsawar flash naji
komai yana dawo min kaina da sauri na diro a katifar ina waige waige can gefe naga
ƙofa naje zan buɗe amma taƙi buɗuwa hasalima ko motsi batai ba duka na shiga yi
amma shiru hannu na ɗora aka ina salati da ƙarfi"ya Allah waye ya kawo ni
nan"juyawa kaina ya shiga yi na koma da baya na zauna jaɓar na rasa ma ina na kama
ni na kasa kuka kuma ba wanda ya shigo,ban jima da zama a wurin ba sai gashi an
buɗe ƙofar an shigo da sauri na kalli ƙofar wasu gandaƙa gandaƙan ma ta ne suka
shigo su wajen shida sai daga bayansu wata mata ce baƙa mummuna sai dai da ganin
tafiyar da take kasan wace ita wata kujera suka shigo da suka sa ma ta ta zauna
tana wani harɗe wai saika rasa me yasa idan mutum yana jin wata isa bazai zauna
normal ba sai an nuna maka ƙafa sannan za a zauna sosai,kallona tayi tana wani
kafirin murmushi"ƴan mata sannun ki ko",sheƙeƙe na kalleta"yauwa uwar ƴan mata amma
kan ki fara magana ya kamata kisan mutum ce ni ba dutse ko sai abani ruwa da
abinci",jinjina tamin"weldon Baby haka nake son mutum tsayayye Sara a bata
abinci"wadda aka wa maganar ce ta juya zata fita na dakatar da ita"bana cin abinci
ba nama ba lemo",wannan matar ce tace a kawo mata nama flat uku da abinci",kai
waccan ɗin ta ɗaga sannan ta fita ba jimawa ta dawo da ƙaton tire a gabana ta aje
ta matsa buɗewa na shiga yi dariya iskanci bayi na ɗago kallesu"amma a kidnppers
ɗin ma manyan masu hankali ne ku sannun ku da ƙoƙari Madam",ɗan murmushi tayi"ci
muyi magana"kai na ɗaga na shiga bawa cikina haƙinsa har saida na gama sannan na
ture"ohhhh Babban yayana ko yana ina yanzu ko wane tashin hankali yake ciki",na
faɗa a fili kallona matar tayi tace"kenan aure gareki?"kallon sama da ƙasa na ma
ta nace"au da baki sanni ba kinka ƙwamuso ni to kuma duk Allah ya turo a sace
ku"zabura tayi zata mare ni amma ta fasa"tana cewa"au ashe fa nace ba duka a
tsakani na dake amma zan aje ki anan harki mutu"dariya nayi"haba dai na mutu sai
kace wata kaza","kina tan tama kenan?","eh Wallahi ni ki maida ni wurin mijina ko
nawa ne zan baku ina da kuɗi"ƴar dariya sukai matar nan tace"da gaske kina da kuɗi
har nawa","billion goma"wani kallo tai maza ta ɗago tana min dan batai tunanin jin
haka daga gare ni ba taɗauka zan mata lisaafin yara na bankin kuɗin makaranta"da
gaske ki ke?","to ku da mai ku ka ɗauken kawai ku faɗan wa ya ce ku kawo ni nan"ƴar
dariya ta yi"wato kinga ina wasa da ke shine ki ke tambayata wa yace na kawo ki nan
to ki daina wannan fatan mu zauna da ni dake a haka kan tazo"kai na ɗaga",ashe kema
ƴar aiki ce ai na ɗauka kece shegiyar"zaro ido sukai suna mamakin yanda nake magana
ba tsoro,tashi ta yi tsaye tana gewaye ɗakin"to kuwa ki ku ka da kanki dan wancan
saita saita miki tunani","ba komai indai banda haƙƙi ai Allah zai saka min",kai
kawai ta kaɗa ta sa kai ta fita waɗannan matan suka take ma ta baya a ka barni ni
ɗaya.

Kwana na goma sha huɗu a wannan gidan ba mai dukana ko zagi wannan matar kuwa na
maida ta kamar kakata itama har zuwa take wai na bata labari randa na bata labarin
gidan mu saida tai ƙwalla ta dubeni tace"anya kuwa mutum ce ke yanzu nan har
kishiya kin hana ta miki makirci","tabbas ma kuwa to kanwa na kasa da zan bari
tamin hauka","haka ne kam ki shirya mai fushi dake gobe zata zo",ɗan jim nayi
sannan nace"to wai ita uwar me ma na ma ta"kafaɗa matar ta ɗaga"nima ban sa ni
ba","to shike nan saita zo",da yammar ranar ina zaune kewar gida duk ta dame ni
naji an turo ƙofar an shigo waɗannan shirga shirgan matan ne sai kuma wata mata
fara ƙal kyakykyawa tasa ado cikin wani arnen material an mai ɗin ƴan tasha kanta
ba kitso ta saki gashin kuma kana ganin sa na gaske ne ba ƙari ba sauke idona nayi
a kanta ina kallon wani wurin dan da alama wannan ba mutunci zatai ba kamar waccan
dana raina,kujera aka sa ma ta ta zauna tana nunan ƙafa amma ko kallo bata ishe ni
ba"sannu uwar son dangi",kallon mamaki na ma ta dan bangane nufinta ba"baki gane me
magana ta ke nufi ba ko? to ni budurwar Habib ƙanin mijinki ce"dariya na kwashe ta
ita ina nuna ta"to miye haɗina dake da ki ka sato ni kamar ƴarki?",kwaɗa min mari
tayi saida naga taurari,da sauri na dafe fuskata"kin mari wuta muguwa"cike da
mamaki take bina da kallo dan bata ga alamar zanji tsoron ta ba ita da take razana
mutane"ƙara min wani marin tayi saida bakina ya fashe wannan matar da nake wasa da
ita runtse ido ta yi kamar ita ake duka ƙafa tasa ta tankaɗa ni nai adungure a
ƙasan tasa aka janyo ma ta ni gabanta haɓata ta kama ta jijjiga kaina"kin san kuwa
dawa ki ke ja?",tofa ma ta yawu nayi"dawa zanja banda jahila jaka mai son
maza",sakin haɓata tayi ta goge fuskarta sannan kwaɗa min mari a karo na uku matan
nan ta kalla"ku zane min ita,da azamar kamar zasu ɗau buhu suka rufu a kaina da
hanzari wannan matar ta tare su"ku bari",dakatawa sukai sannan ta kalli matar
tace"Madam wannan fa yarinya ce bai kamata a ma ta wannan dukan ba",tashi tsaye
matar tayi tana bin ta da kallo"da kyau Baira ashe harkin fara sanyi haka","ba haka
bane wannan ɗince dai kar a daketa",hasala matar tayi ta kifa ma ta mari sannan ta
dubesu tace"ku ja min ita zuwa mota zan ɗauketa daga nan dan naga ba zaki min abin
da nake so kuma kin san sakamakon hakan ko,ta na gani aka jawoni ina kuka suna duka
na da ƙafa har suka fito daga ginin gashi da tsawo ta saman ta leƙo taga sun sa ni
a boot sannan ta shiga suma suka shiga tasu motar suka bar lungun,jungina da bango
tayi tana jin wani ɗaci a zuciyarta kai ta kaɗa" muja dake Aisha".

*MAROCO*

Cikin wani katafaran gida tasa aka aje ma ta ni kwana goma suna min allurai sannan
ba a bani abinci na zama kamar mahaukaciya,yau da wuri tazo inda nake ina zaune
nayi jigum bana iya tunanin komai dan alluran amfanin su kenan a gaba ta tasa ni
tana duka saida taga bana motsi sannan ta barni ruwan zafi tasa aka kwara min
saboda tsabar azaba ko motsin zafin ma ban ba gashina ta danƙo ta ɗago kaina sama
cikin idanuwa na ta kalla ta yi wata shegiyar dariya"haka nake so dama na maida ke
mahaukaciya"murmushi na ma ta na kaɗa kai"cikin mamaki take kallona"kina nufin
allurar da ake miki bata hanaki waɗannan mugayen tunanin naki ba",kai na kaɗa ban
ma ta magana ba ta kuwa yankan mari a baki take bakina ya fashe jini ya shiga zuba
ta watsar da ni gefe"ki tabbata a nan gidan zaki mutu waye ya gaya miki ana gasa
dani waike me amana shine kika ba Habib dukiyar da ko ubana sai ya masa ladabi ko
kin san kuwa yadda suke da Babana kamar wuta da ruwa suke naso Habib iya so amma
ban san miye a tsakaninsu ba da Babana ba ya tsane shi ada shima yaso ni amma tunda
ki ka shiga rayuwarsa a lokaci ɗaya ya juyan baya saboda munafurci harda shiga gaba
ya auri yayarki ko ni banga abinda ki ke da shi ba da har mutane suke miki
biyayya",katseta nayi"kinga ki kashe ni da wannan maganganun da ki ke dan ba ganewa
nake ba",juyowa ta yi"au harma magana ki ke","to ke ki ka haliccen da za ki hanani
magana",kaina ta ƙaraso zata daken"kina duka na yau zaki mutu"turus ta yi gabanta
na mugun faɗuwa da ƙyar na tashi tsaye na tsaya a gaban ta inajin azaba a cikina ga
yunwa ga ciwo amma na cije nace"Aisha ki ke kowa kina nufin ke ki ka sato ni ko to
bari na faɗa miki wani abu ubanki ne yasa ki ki ka sato ni baki sa ni ba dan ya
fiki matsala da ni kinga wannan gidan da yasa ki ka kawo ni to gida na ne shi yasan
hakan kina tunanin ya baki bayanai ne akan nasa Habib ya auri ƴar uwata ina ba haka
bane ya baki bayanai ne dan ki kawo masa ni cikin sauƙi dan shi sace ni zai masa
wuya dan kamar ƙarfe nake bana lanƙwasuwa ni da kika ganni bana laushi sai dai na
lausasa wasu,ke kima yi a hankali fa kamin masoyin naki yazo nema na tabbas ki ka
bari yasan ke ki ka ɗauke masa matar wa saiya ya rabaki da numfashin ki",shiru ta
yi kaf maganar tawa bata gane ba"ki daina dogon tunani ƙawata zaki mutu a banza a
kaina,kije ga mahaifinki dan shirin kashe ki yake saboda ya dawo da dukiyar daya
mallaka miki gunsa dan yanzu yasan ke ba ƴarsa bace uwarki siyo ki tayi kuma itama
ɗin shi ya kashe ta hunmm baki san waye wannan mugun mutumin ba ko to yana daga
cikin tarko na nan da ki ka ga ya dawo da zama kin ɗauka kamar da ne kasuwanci ya
kawo shi ha ha ha yarinya gudowa ya yi dan yana gudun haɗuwa da ni saboda nasan
sirrin sa dukkan rayuwar sa atafin hannuna take"shiru nayi na kama kaina da hannu
biyu na jijjiga dan ina jin kamar zan suma ƙara dubanta nayi"kije ki samawa kanki
mafita kan ya sheƙe ki",a fusace ta danƙi wuyana ta jijjiga ni ta watsar jakarta ta
fin ciko zaro wata kwalba ta matse ni ta ɗuran abin ciki sannan ta fita da gudu
masu ma ta gadi na ne sukayo kaina zasu danƙeni ba zato sukaji saukar duka aka,jin
sun faɗi yasa na jiyo wannan matar ce da gudu tazo ta kamani ta rungume ni"sannu
sannu zo mu gudu"ganin bazan iya tafiya ba ma saita goya ni muka fito a gidan duk
masu gadin gasu nan a kwance kashir ɓan.

Ko da ta isa gidan bata kula kowa ba ta wuce ciki Daddyn ta na zaune da wasu
mutane ta shigo kusa da shi ta zauna tana shagwaɓa"yadai ƴata","Daddy nagaji
ne","ok jeki huta zuwa anjima zamu unguwa","tom Daddy",ta tashi ta haye sama bata
shiga ba ɗakin saita wayance ta sakko zuwa kitchen anan ta laɓe dai dai yana cewa
mutanen"ita ce wannan zan kawo muku ita anjiman yanzu ku tafi ita akwaita da
bincike yarinyar da nace muku nasa ta sato tana wajenta so nake na gama da ita
wannan sannan waccan dan nasa tai ma ta allurori na fitar da mutum a tunanin
sa",dafe kanta ta yi saida mutanen suka fita sannan ta fito ta haɗo abincin yara
dan ita bata cin abinci kowane lokaci,a ɗakinta ta zauna duk a tsorace tana jin
Daddyn shima ya fita aje abin hannun ta tayi ta jawo manyan jakun kuna ta kwashe
kayanta da duk kayan amfanin ta ta jidi kayan takai mota da masu gadi suka
tambayeta saita ce na ƙawarta ne zatai aure yau shine zata kai ma ta yanzu ma zata
ta shirya,komawa ta yi ciki ta sauya kaya zuwa na party tayi kwalliya sannan ta
fito zuwa ɗakin Daddyn dama tasan taya ake buɗe passwod ɗin ƙofar ta buɗe ta shiga
safe ɗin ma tasan ya ake buɗewa dan haka ta buɗe duk takardun kadarar sa dana kuɗin
banki da kuɗi billions tasa wata trolly ƙarama kamar ta ta ce ta amfanin wajen biki
ta yashe kuɗin tas sannan ta rubuta masa gajeriyar wasiƙa kan ɗan table da yake
ajiyar jaridu ta fito tana tafiya ƙwas ƙwas nan da nan kuwa taja hankalin mutanen
sukaita kallonta taja mota ta fita agidan tana hawa titi ta fara yanka gudu gidan
da ta aje ni tazo taga wayam dama saki na tazo tayi kuji muguwa ko in ta saken
gidan uwarta zani,tana ganin bana nan ta fito ta gudu itama ba tayi tunanin komai
ba ta auna kayanta a jirgi sannan itama ta auna kanta China wurin ƙwayenta.

*******

Koda ta ɗakko ni dama da pravet jet tazo dan haka daga nan sai 9ja tasa aka
wuce ita direct,mota tasa wata abokiyar sirrin ta ta kawo ma ta airport ɗin bata
san ina zata kaini ba kawai ta shiga wata unguwa dare ya yi sosai ƙofar wani gida
ta shinfiɗa gyalenta ta kwantar da ni a wurin ta tafi tana waige na sha biyu da
mintuna ɗan gidan ya dawo daga gantali da yake a mota yake horn ya yi aka buɗe masa
ya danno haske zai murza taya ya murje ni maigadi ya lura da ni da hanzari ya shiga
gabansa taka burki ya yi shi kuma maigadin ya yi kaina,buɗewa ya yi ya fito yana
masifa amma sai ya yi shiru"kai Baba megadi miye wannan ka ke ɗauka","mutum ce aka
yar yallaɓai","mutum to shine zaka ɗauka shin kasan illar hakan","ba wa ta illa
saita mutu in aka barta a haka yallaɓai ka kaita asibiti",baya yaja yana dafe
ƙirji"ni ɗin wallahi ban kaita",ya matsa gefe,mai adaidaisahun gidan ne ya dawo
ganin mota a hanyar ya fito yana tambayar lafiya,Baba maigadi ne yace"yauwa Habu
taimaka min wannan yarinyar a cikin mawuyacin hali take yarda ita akai anan kai da
ganin yanda take a wurin kasan kwantar ta akai"da sauri ya ƙaraso ya taimaka masa
aka sa ni a mashin ɗin megadin ya shiga suka bar ɗan masu kuɗi anan,asbitin wani
ƙaramin pravet yaje maigadin yace"na gwamnati zaka kaimu nan wazai biya",kashe
mashin ɗin ya yi ya fito"karka damu Baba yanzu muna zuwa na gwammati sai an ce mu
kawo ƴan sanda anan kuwa muna cewa ƙanwata ce shikenan","to ɗan nan ai bamu da
kuɗi","ka daina damuwa Baba akwai cinikin yau a hannuna muje",ɗakko ni ya yi ya
shiga illai kuwa da saurin su suka karɓe ni suka shiga ciki bayan mintuna suka fito
likitan yace"akwai babbar matsala ku ƴan uwanta ne"kai mai mashin ɗin ya kaɗa
likitan yace"kuna ina ƙaramar yarinya take allurar cocain anya kuwa anan ƙasar take
ga yunwa ta taɓa ma ta hanji gaskiya a aikinta ana buƙatar kuɗi masu yawa dan haka
yanzu kaje ka kawo dubu ɗari takwas a fara da cikinta kafin ƙwaƙwalwarta kayi
hanzari nan da zuwa shaɗayan rana"kai ya kaɗa yana jin kamar zai faɗi a ina zai
samo waɗannan kuɗaɗe haka masu yawan gaske,bayan wucewar likitan ya kalli matashin
ya ce"Habu kaga irinta ko dama nasan hakan ce zata kasance su waɗannan kuɗi kawai
suka sa ni",dafa shi ya yi"karka damu Baba muje waje",suna fitowa ya ce masa zai
maida gida kamin goben sanda ya kawo shi Alhaji harya faɗa nan suka bashi haƙuri ya
aje mashin ɗin da sassafe ya dawo ya ɗauka yaje asibitin likitan na ganin sa ya ce
yafa dage ya kawo kuɗin tom ya ce ya fito ya fara aikin sa yana zaga gari wajen
tara Habu yaje ya saida sabon mashin ɗin mutane da yake ba a daɗe da siyan shi ba
kuma ga takardu har ƙari ma ya samu kan ɗari takwas ɗin da saurin sa ya kawo ya
biya akace ya zauna anan ya wuni sannan likitan ya fito sukaje office nan ya bashi
takar dar allura yace"duk ɗaya dubu goma ta kwana goma sannan a duba ƙwaƙwalwar ta
ta",tom ya ce ya karɓa ya biya rabi sannan kuɗin gado ya tashi bako ƙwandala dan
komai ya ƙare bai koma gida ba tun daga wannan ranar har bayan kwana biyar Alhajin
nan kan kuɗi ko kayansa bashi da mutunci dan haka yaje har gida yacima iyayen Habu
mutunci basu damu ba dan suna san waye ɗansu kuma dai suma ai basu ga dawowarsa duk
da yadda duniya ta zama sunsan duk inda yake yana lafiya kuma suna masa addu
a,ranar kwana na shida ya fita wurin abokinsa ya ranto dubu ashirin yana hanyar
dawowa Alhaji ya gansa nan ya fito yasa aka kama masa yana ihu wai ɓarawo ne anan
wasu ma suka kwashe kuɗin sannan yasa aka mai duka ya kira ƴan sanda suka kamashi
ba imani suma sukaita dukan shi wai ina yakai mashin ɗin shiru ya yi musu ai kuwa
sukaita laftarsa bisa ga umarnin Alhajin.

*NIGER*

A yanda ya shigo gidan ne ya bata tsoro kuma bai ma ta magana ba ya wuce ciki bin
bayansa ta yi"lafiya kuwa Habib naga kana haɗa kaya","kema haɗa naki in ba haka ba
na tafi na barki",da sauri ta shiga itama taja jaka ta fara zuba nata kayan batare
da ta tambaye shi ina zasu ba tasan halinsa in ya tutse ba daɗin sha'ani gareshi
ba,a tare suka zuge jaka ya jayo hijabin da take sallah ya ba ta sannan ya ɗauki
jakunkunan ita kuma ta biyo bayan shi falon ya tsaya ya kashe komai sannan suka
fito driver ne ya kaisu airport sai anan tasan ina zasu suna samun zama a kujera
tace"me ya ke faruwa ne a gidan",batare da ya kalleta ba yace"Nana aka ɗauke",wani
dam taji sai kuma abin ya ma ta ban barakwai"sata kamar ya saika ce wata
jaka","yanda dai na faɗa mikin ne hakan tun safe kumankowa na inda take ya tabbatar
sace ta akai",bai gama magana ba ta fashe da dariya,da mamaki yake kallon ta"kanki
ɗaya mutum fa nace miki an sace kuma ma ƴar uwar ki amma shi ne ki ke
dariya","wallahi ba dariyar murna nake ba kawai wanda ya jajibeta ne yake bani
tausayi Nana bala i ce kuma bata da tsoro amma zasu ci ubansu dan zata wahalar
dasu","ɗan murmushi ya yi"wato dai kema kinyi irin tunanina dan tabbas ba masu
satar mutane ne suka sace ta ba","haka ne kam akwai dai wa ta a ƙasa","to Khadija
sai muyi ma ta addu a","to shike nan amma harna tausaya musu wallahi"ta ƙara
fashewa da dariya shi dai sai kai ya girgiza.
Ba bu wanda yasan zasu zo shi yasa a dole suka hau taxi ta kawo gida anyi
mamakin ganin su dan dare ya yi a wannan yanayi dai suka kwana amma Hajara ko inda
yaje bataje ba dan tabbas ta tsorata da shi a kan Nana,duk ake bincike sun zaga
amma ba labari sai dare Alhaji Baffa yace su dawo kawai ayi addu a duk inda take
zata fito a dole suka dawo amma Babban Yaya yama rasa ina ya kama gani yake abin
kamar almara,kwata kwata baya bacci kullum yana gaban ubangiji yana kai kukansa
gare sa,Hajara ta yi iya binciken ta akan ta gano ko Abban ta ne amma bashi ba ne
shi yasa take a tsorace gashi baya ma ta magana an yace duk ita ta jawo,da wannan
abin ya fara nisa amma shiru ga bincike dai ana yi kuma Habib bai koma ba.

****
Da iyayen Habu suka zo suka ga halin da ya ke ciki hankalin su ya yi masifar
tashi Baban sa dai yasan ɗansa mutumin kirki ne nan ya lallaɓashi ya faɗa masa me
ya yi da kuɗin daya siyar da mashin ɗin mutane faɗa masa komai ya yi nan Baban ya
tausaya masa kuma yace insha Allahu zai biya masu mashin ɗinsu yanzu zaije ƙauye ya
saida gona kin sa yazo biyasu,saida zasu tafi sannan mamar tace"a ina aka kwantar
da yarinyar",kwatan ta ma ta ya yi sannan suka tafi suna gida Baban ya tafi ƙauyen
su ita kuma ta tafi asibitin bata sha wuyar nema aka nuna ma ta faɗa likitan ya
shiga yi nan taita bashi haƙuri har ɗakin nake ta shigo ina kwance ido na biyu amma
bana gane kowa bin ta da kallo nayi kawai likitan ne yace ma ta bata gane kowa amma
ina saran in an aka gama ma ta allurorin zata iya dawowa hayyacinta,ta tausaya min
sosai nan ta falwa likitan da zarar mijinta ya dawo za a ƙarasa biyan komai kwanan
Baban biyu ya dawo amma kuɗin mashin basu kai ba saboda zalinci kuma wai kuɗin
aikin da ya yi da yake basu sunce ladan amanar su da ya ci duk kuɗin da Baban Habu
ya basu,basu sa an sake shi ba saboda wulaƙanci ce masa ma sukai in bai ciko ba
zaisa a saida gidansa ya ɗauki kuɗin sa Baban baice komai ba ya fita ya basu
wuri,asibitin shima yazo sauran abin da ya ɓoye ya biya a asibitin,bayan kwana goma
ta cika binciken su ya nuna musu sai dai akai ni waje amma in basu da hali to su
cigaba da zama da ni a haka har Allah yasa na warke,hakan kuwa akai likitan ya
sallame ni suka zo da ni gidan su ya yinda Habu yana can ana bashi wahala a haka
har nai sati uku hannun su na shaƙu da Baba da Umma suna sona sosai.

******

Yau Babban Yaya ya karɓi baƙo Abdallah ya janjanta masa sosai sannan ya jashi shida
Habib zuwa wurin ƴan sanda daya sa ni bayan sun fito suka sami Baba da wani ɗan
sanda sai faɗa baban yake ya zasuna dukar masa ɗa haka ɗan sandan sai nuna shi yake
da hannu anan Acp Zubair ya daka masa tsawa"ya zaka na yiwa babba haka baka da
hankali ne",ƙamewa ya yi ya sara"sorry sir",juyawa ya yi ga Baban ya ce"kayi haƙuri
Baba me ya faru ne","rankai daɗe ɗana aka kama wajen sati shida kenan wata matsala
ce ta faru da ƙanwarsa ban sa ni ba ma yaje ya saida adaidaita sahun mutane ya biya
kuɗin asibiti yaron nan shekara wajen huɗu yanawa mutanen nan aiki suna ƙarar masa
da ƙarfinsa ya yi karatu sosai suna da yadda zasu nema masa aiki amma sunƙi shine
yau daga wannan kiskuren suka tozar ta shi haka kullum duka kamar wanda ya yi
kisa",kai Asp ya kaɗa"kayi haƙuri Baba muje na ganshi abokaina muje tare mana kuga
ciki",tare suka shiga sunsha mamakin yadda masu lefi suke a sake ba ruwan su kaɗan
ne a damuwa,inda yaron yake aka kaisu yasha wuya duk ya yi baƙi fito masa dashi
akai nan ya kalle shi ya kalli ƴan sandan"wa yace kuna dukan shi haka",ɗaya ne yace
sorry sir ya yi gardama ne shine mai abin uace a hukun ta shi ta yanda zai faɗi
gaskiya",dafe goshin sa ya murza kamar wasa ya fesa ma ɗan sandan nan mari da sauri
sauran suka ja baya cikin masifa ya ce"saboda shi zai koya muku yadda ake bincike
ko shi zai nuna muku ga yadda zakuyi aikin ku ko to ku kissafim waɗanda suka
dakeshi kaf albashinku shi zan ba a ƙasa suka sunkuya suna bashi haƙuri kafaɗar
Habu ya dafa"kayi haƙuri abokina kuɗin nawa ne ya rage",ɗago kansa ya yi zaiyi
magana suka haɗa ido da Babban Yaya"lahhh Babban Yaya"da mamaki ya kalle shi"na am
kasan ni ne",matsowa ya yi ya kama hannun sa"ni ne fa mai mashin ɗinnan dana kaika
gidan Alhaji Aminu kace kaima ranar ka fara zuwa",zaro ido ya yi yana dafa shi"ayya
abokina kayi haƙuri waccan wayar ta faɗi ne","ba komai wallahi","waye ka sayarwa
mashin","Wallahi Babban Yaya ƙanwata ce Babu lafiya na rasa yadda zanyi naje sayar
kuma fa Babana ya basu fin rabi ya ce zai cika amma duk da haka basu yadda ba","ba
komai Baba ka kaimu wurin mutumin",duka suka fito da motar su data hilux ta ta ƴan
sanda suka shiga unguwa da ke gidan su na farko kan na Alhajin mutane suka ga ni a
wurin sannan ga kaya ana watsi dasu wata ma ta na gefe rungume da ƴarta suna kuka
ga Alhaji sai baza riga riga yake shida wasu mutane kana ganin su kaga dillalai,da
sauri Baba ya fito"yallaɓai ka gani ko yadda suke mana tozarci akan kuɗi",duk kansu
ran kowa ya ɓaci tsawa Acp ya daka ƴan sandan sa"ku kamamin kowa masu watsi da
kayan nan",matsowa Alhajin ya yi"kaga yallaɓai sun ci min kuɗi shine zan koresu a
gidan in sun biyani sa dawo",bai gama magana ba Habib daya gama shaƙa ya sheƙa mari
hagu da dama da gudu dillalan nan suka baje suna guduwa,wayansa ya danƙa duk girman
sa"in ka koresu a bola ka ke so su zauna kenan anan zasu samo kuɗin su baka
ko",wuri wuri Alhaji ya yi nan Habib ya kalli matasan"ku mayar musu da kayan su ko
mutum yasha ruwan zafi yanzu"daga wandon jikinsa suka gane waye dan haka da rige
rige suka fara kwasar kayan suna mayarwa,sakin Alhajin ya yi ya matsa ga matar dake
kukan yace"kiyi haƙuri za a biya shi kuɗin sa ga ɗanki nan ya dawo"godiya ya ta
ahiga musu ya yinda Abdallah ya ƙirgi kuɗinsa ya miƙa masa ba kunya ya karɓa yana
ƙirgawa cif dubu ɗari da hamsin babbar riga ya baza ya sa a ciki ya wuce,kati
Babban Yaya ya basa yazo ya same shi kuɗi masu yawa dukkansu suka ba Baban sannan
suka shiga motocin su suka juya a motar Habib kallonsa ya yi"yadai kayi shiru
haka",kansa ya girgiza"ba komai Habib ji nake kamar naje inda Nana take",dafa
kafaɗar sa ya yi"ka kwantar da hankalin ka cikin ruwan sanyi zamu sa meta",haka dai
sukaita bashi baki har yaji sanyi a ransa.

*MAROCO*

Dai dai sanda Daddyn Aisha yace zai bawa mutanen nan ita lokacin nayi yazo tafiya
da ita amma me yana shiga ɗakin ta yaga wayam da sauri ya sakko yana tambayar masu
aikin gidan tana ina suka ce ta fita da kaya tace musu taje bikin ƙawarta,ɗakinsa
ya wuce abin mamaki ya gansa a buɗe yana shiga yaga babu komai a safe sannan ga
takarda a ajiye ɗauka ya yi cikin sharar zufa ya fara karantawa, *"Daddy nasan kaso
ni ada kenan sanda ka ke ɗaukata ƴa amma yanzu daka gano ni ba ƴarka bace shine
kamin zagon ƙasa kasa na cutar da wata akan wani buri naka to kasa ni ta gudu daga
hannuna kuma sirrin naka dai tana nan ta tasa ni kuma ita take faɗamin nayi ta
kaina sabosa zaka kashe ni ka maida dukiyar ka daka mallaka min wajen ka abin ka to
ka sa ni da wadda ka ba ni dama wadda baka bani ba na kwashe duka na gudu kuma ko a
lahira bazaka ƙara gani na ba"* anan rubutun ya datse ihuu ya kurma ya faɗi a wurin
da gudu masu aikin suka shigo anan suka sami Alhaji baje a ƙasa ya samu shanyewar
ɓarin jiki me mu ni.

UMMU SADDIQ CE🌹🌹🌹🌹


🌈🌈🌈
🌈🌈
🌈

BABAN YAYA

Babban Yaya Free ne amma me so ya biyo ni Pc in sa a group don shagalin Nana


na buƙatar comments.
08146711395

34

Koda suka koma gida yau dai Hajara ta bashi abinci yaci harma ya ma ta magana da ɗi
kuwa kamar ya kasheta da kuwa shashin Abba ya koma da zama ko kuma ya buɗe asalim
part ɗina ya shiga ya kwanta bacci kowa sai ɓarawo amma ba kullum yake yi ba dan ta
yi iya kwarkwasarta amma ta kasa jawo hankalin shi gareta ya manta da ni,bincike
kuwa ta bin cike ɗakina kaf amma bata samu takardun Hajiya Fulera kai na Babban
Yayan ma ko gilmawar ta bogi bata ga ni ba bate ta gasken a haka dai ta gaji ta
haƙura tsinuwa kullum saita min tana addu'ar Allah yasa kar a gan ni.

Bayan kwana ki kaɗan Babban Yaya ya samawa Habu aiki a wajensa yaji daɗi
sosai dan albashin wata uku aka basa nan da nan ya ciro mu acin wara abin da ya
basu mamaki da ni bana gane komai a binci amma ina gane nama shi yasa kullum sai
Baba yasa sa ni a gaba da nama ina ci yana dariya in ya ƙare nace"Umma a zuba
nama",sai suyi ta dariya,duk wannan abin kuma yana kaini asibiti dan likitannan
yace ana kawo ni.

Yau da wuri Habu ya dawo ina zaune akan tabarma inawa ƴar tsana kitso ya
zauna kan kujera"ƙanwata zaki unguwa?",kai na ɗaga ina dariya,"Umma fito
kiji",fitowa ta yi"ubana ƙalau dai ko yau naganka da rana haka","eh Umma suna ake
gidan su Oga shine nazo ku shirya na kai ku kinga ma ai kyawa iyayen sa godiya
ko","a lallaikam to bari na shirya taso ƴata",da sauri na watsar da kayan wasan na
bi ta ɗaki a tamfar da ta ɗinka min sabuwa dal ta saka min da hijabi sai wani
ƙaramin niƙaf bamai takura ba dan bata fita da ni haka fuska buɗe,koda muka fito
saida ya yi dariya"wai Umma tsoron me ki ke ne ki ke ɓoyeta haka","kai Habu wannan
yarinyar lamarin ta tsorata ni kullum na kwanta sai nayi mafarkin wasu gungun
mutane suna bin ta tana gudu wai sun kamata sun raba naman ta sunci","subahanallah
Unma to Allah ya ki ya ye ta","ameen Habu Malam ɗin yana waje","a a amma ai shi na
fara biyawa kasuwa na faɗama kamin nazo nan dan mota Oga ya bani nazo na kai ku
motar ma tasa",kai ta kaɗa"to dai a riƙe amana Habu irin waɗannan mutanen ka riƙe
musu amana shine zaka zauna dasu lafiya dan in wayo zakai sunfika wayo saboda su a
ankate suke da kowa","hakane Umma kuma zanyi iya ƙoƙarina wurin ganin bai samu
matsala da ni ba","to Allah yasa Habu",muna fitowa na kalli motar na nuna shi nayi
tsalle,kai ya kaɗa"daina murna ba tawa bace amma zan siya saboda kai ƙanwata unguwa
da yawo",dariya nayi dan ban fiya magana ba saita kurame,muna shiga naji kaina ya
yi dum da sauri na kalli Umma na kalli bayana,hannuna ta riƙe"me ya faru ne
ƴata",kai na kaɗa na cigaba da shafa kujerar motar ina jin kamar zanyi tunani amma
na kasa,koda ya tsaya a ƙofar gidan ana ganin motar aka buɗe masa get ya shiga
gidan danƙam da mutane mamaki ne ya kama Umma"kai Habu wannan gida ne ko
unguwa",dariya ya yi"gida ne Umma amma mutanen ciki na unguwa guda ne",kai ta
kaɗa"lallaikam",hannuna ta kamo nan ƙafata ta shiga rawa dafe ƙafar ta yi"sannu
ciwo take ?",girgiza kai nayi sannan na fito muka fara tafiya zuwa cikin gidan wani
fili da aka sawa rumfa yace"Umma ku zauna anan zanje naga Mamar su Oga sai na shiga
daku ciki",tom tace tana zaunar da ni kusa da mutanen dake zazzaune,ciki ya shiga
bai daɗe da shiga ba wani yaro yama mamar sa amai dama akwai famfo wurin nan Umma
ta tashi dan ta taya ta gyara yaron da jikin ta,tana matsawa naga gilmawar hannu
ana kira na tashi nayi na tafi wata ƙofa mai kyau na gani a buɗe na turata na shiga
takalma ne birjik a wurin ba wata sallama na shiga duk suna cin abinci ko ga ni na
ma basu yi ba na shige cikin wani ɗaki ƙofar dama a wangale take,ƙarewa ɗakin kallo
na shiga yi kamar nasan shi niƙaf ɗin fuskata na ɗaga na fara janyo kome na ga ni
ina yarwa ƙarar fashewa abubuwa tasa Hajara da suke hirar kar Allah ya dawo ni ta
taso zuwa ɗakin dan tasan yanzu ya fita kuma baici ace ya dawo ba,leƙowa ta yi tana
faɗin"ka dawo ne dama",shiru ta yi ganin yanda aka wargatsa ɗakin ƙarasa shigowa ta
yi"ke ke ƴar uban waye ke da ki ka shigo mana gida har ɗaki",ganin ban kulata ba
saita ƙarasa shigowa tana kai hannu zata taɓani na juyo,a razane tai baya ta kwaɗa
ihu nan da nan mutanen falon suka ƙaraso suma duk tsorata sukai kowa yay baya a
guje dan ba wanda zaice ga sanda na shigo da gudu itama ta fita tana ihu bin
bayansu nayi ina kallon su ina dariya turus mutane sukai ganina nan da nan aka buga
kwakwazo ga Nana ga Nana su Mama na tsakiyar mutane maganar kowa dai da hirar ta
Nana sai sukaji ana ga Nana kamar saukar aradu haka suka ji takai takai kowa ya
fito kamin suzo Umma tazo ta kama hannuna"kuyi haƙuri dan Allah wani abu ta yi ƴata
ce bata da lafiya ne",tana cikin magana ƴan gidan sukai da ira a wurin duk kaina
suka yo amma na yi ma za na ɓuya a bayan Umma jikina na rawa su idon su Mama idona
suka fashe da kuka sunawa Allah godiya mamakin abu guda dana basu shine na ƙi zuwa
wurin su sai wurin wa ta da basu santa ba ma,ƙara duban su Umma ta yi"kuyi haƙuri
dan Allah",Gwaggo ce ta matso tana cewa"baiwar Allah bakuyi komai ba ita wannan
yarinyar ta bayanki ƴarmu ce wannan gidan kaf nata ne haka mutanen ciki danginta
ne",mamaki da murna ne ya kama Umma ta fara faɗin"Allah na gode maka dama ƴar nan
gidan ce ai ɗana ne yaron mai gidan nan Habibu shine wai ya kawo ni suna nan ya
barmu ne ya yo magana da Mamar Ogan nasa shine tayo nan",matsowa Gwaggo ta yi zata
kama hannuna na janye kai kowa ma so yake ya taɓa ni amma naƙi yadda Iyyo kuwa kuka
kawai take tana azo a kira ma ta Alhaji Baffa,zamewa Ya Usaina ta yi ta ɗakko wayar
ta tai kira ba jinawa tana ringing aka ɗaga"Hello Usaina",fashewa ta yi da kuka nan
da nan hankalin sa ya tashi"lafiya Usaina","kazo"kawai tace ta kashe,Habib ne ya
kalle shi"lafiya dai",ya faɗa yana gyara parking a cikin gidan dama sun shigo a
tare suka fito bin gidan sukai da kallo ganin yanda aka taru waje ɗaya,Ya Mabaruka
ce ta gansu tazo ta kama hannun su ta jawo su har gaba inda nake,kukan nake ban
daina ba Ya Ruma ta zagayo ta ɗaga masa kaina fuskata ta yi jage jage da
hawaye,wani irin dam yaji nan da nan wani irin farin ciki ya lulluɓe shi haka ma
Habib da kansa ya ƙaraso inda nake zai kama hannuna na maƙale kafaɗa na matsa baya
duk binsu da kallo nake amma ban san su gashi sun ruɗa ni sai miƙo min hannu
suke,Habu ne ya ƙaraso"yallaɓai ƙanwata ce bata da lafiya ne",lumshe ido ya yi dama
ya fahimci hakan tuni,Habib ne ya ce'?"Abubakar wannan ƙanwar ka ce da gaske","a a
yallaɓai tsintar ta nayi itace wadda na saida mashin ɗin nan na biya ma ta kuɗin
magani",gaba ɗaya zuba masa ido akai bama ya Babban Yaya kamar yana neman wani abu
a fuskar sa,Habib ne ya matso ya kama hannun sa"dama akan wannan kasha wannan
wahalar kuma ka jure",kai ya ɗaga"eh ai sanda na ganta naji tausayin ta ne inka
ganta a sannan bazaka ɗauka mutum bace dan har purple jikinta yake",rungumesa Habib
ya yi"mungode Abubakar",ɗagowa ya yi"ban gane ba yallaɓai",nu na ni ya yi"wannan ai
matar Ogan ka ce ƴar nan gidan ce sace ta akai",salati Abubakar ya yi yana kallon
Umman sa kai ta ɗaga masa,murmushin farin ciki ya yi ya matso yana kama hannuna
Babban Yaya"kayi haƙuri yallaɓai dama itace wacce ka ke nema ai ban sa ni ba ta
daɗe a wurin mu ba tun wancan lokacin ina police station tama yi sati shida a gidan
mu,sai dai bata da lafiya karka yafewa wanda ya ma ta haka cocain akaita shaƙa ma
ta ana ma ta allurar sa shine ya birkita ma ta ƙwaƙwalwa ance na kaita ƙasar waje
tun sanda aka sallame ta a asibiti amma bana da hali shi yasa ban kaita ba",kafaɗar
sa ya dafa"ban san ma me zance muku ba Abubakar na rasa da wane baki zan maka
magana ko na ma godiya ko na jajanta ma ka wahalar daka sha akanta amma i promise u
sai ka yi dariya a rayuwar ka kuma ƙasar waje za a kaita ka tabbata ƙafarta ƙafarka
tabbas kaine ɗan uwan Nana na gaskiya ba taron mu nan ba",murmushi ya yi sanda
taron ƴan gidan sukai caa da godiya haka ma Umma nan aka jata ciki amma na ƙi
sakinta acan ma da ta zauna ina manne da ita kowa kalla farin ciki yake haka ana ji
da ni kamar a haɗiye ni,inda aka barsu nan Habu yace"ka bi a sannu Oga zata zo inda
ka ke",wani musulmin murmushi ya yi wanda saida Habib ya sara masa yana
dariya,duban su ya yi a gayance yace"zata zo wurina ma kuwa yanzu ku shiga mota
muje wani wuri",a take suka wuce Habu ke jan motar.
Hajara kuwa ai ina kamar mahukaciya ita da ƴan uwanta suka koma ciki a gaba
suka sata wancan yace ka za wancan yace ka za ita dai sai kuka take shikenan annoba
ta dawo yayarta ce tace"yanzu waɗannan mutanen zasu zama masu kuɗi wanda ya shekara
talatin ma ba zai kaisu tarawa ba",ƙaramar ƙanwar su ce tace"wallahi kuwa ina ma
nice na samota wayyo",ɗaka ma ta duka Hajara ta yi"dake ki ka samota da kashe ki
zanyi",baki ta tura gaba"akan me zaki kashe ni ai ko ban kawotan ba gashi nan masu
ƙashin arziƙi sun kawota",ta miƙe ɗauki ƴar swagger ta tayi tafiyar ta,haƙuri suka
cigaba da bata suna faɗar ba sanya bakiga mahaukaciya bace,sauri shiru ta yi"au ku
dama can kallon me hankali kuke ma ta to wallahi wannan aljanar yarinyar ba haukaba
kome take kina ma ta makarci zata ƙulla miki kitimurmura ni fa har yanzu ban manta
sharrin da ta ƙullamin ba nasha shaƙar mutuwa",dariya sukai amma dai duk haka anata
kiyi ka za ki ma ta ka za da kanta zata ƙara guduwa,ta yarda da magan ganun su dan
haka taɗau ɗamara dafa ni cikin ruwan sanyi.

UMMU SADDIQ CE🌹🌹🌹


🌈🌈🌈
🌈🌈
🌈

BABAN YAYA

Babban Yaya Free ne amma me so ya biyo ni Pc in sa a group don shagalin Nana


na buƙatar comments.
08146711395

35

Su Mama sun rasa ina zasu sa kansu dan daɗi hakama da Alhaji Baffa yazo ya
yi murna daga haka gidan suna ya ƙara ɗaukar mutane bila adadin kan kace me jikina
ya ɗume da zafi sai kar kar wa nake su Mama Umma ta faɗama nan Aunty Mama ta
ce"haka take in aka takura ma ta bari a bata magani,da dabara aka ban nasha amma a
ankare nake da kowa kome zasuyi ina kallon su wai kar a taɓani.

Basu jima da fita ba sai yace sukai shi inda ake saida nama ai kuwa Habu me
zaiyi inba dariya ba"Oga kace dama halinta ne cin nama","au tana muku ne","sosaima
kuwa ai yanzu har mu ta koya mana in bamu ci nama ba hankalin mu baya kwanciya ita
kuwa batawa ahinkafa loma uku ta ƙoshi sai nama dan a sanda ta fara na tashi daga
Habu mai adaidaita na koma Abubakar ma aikaci ai inaga wataran sai dai na karɓo
bashi cifa take bawai lasa ba",dariya sukai wacce rabon su da ita sun manta nama
kuwa aka siyo mai yawa dan saida suka siye shi aka musu take a way abin dariya yau
aga wata jaraba take away ɗin nama a gidan suna,sanda suka shigo unguwar ana
magariba dan haka sallah sukai sannan suka shigo gidan bakin shi ɗauke da addu a
Allah yasa na yarda da shi.

Sanda akai kiran sallah ɗakin Aunty Mama aka kai mu Umma sai mamakin girman ko
ina na gidan take da ƙyar tasa ni nai alwala ana koya min sallar ina yi abinda yasa
Aunty Mama fashewa da kuka kenan da ƙyar Umma tasa ta ta yi shiru amma ba abin da
take sai kallona,duk kansu suka shigo gidan har ɗakin Aunty Mama ina ganin su na
taho wajen Habu ina miƙa hannu kafaɗa ya ɗaga yana taɓe baki sannan yamin alamar ba
bu,Umma na kalla na nu na ma ta shi,haƙuri ta ba ni da hannu da mamaki Babban Yaya
yace"bata magana ne",Umma ce tace"tana yi amma saita san abu sosai take ke magana
akansa",kai ya ɗaga yana ƙara zuba ido yadda na rame sosai hannun sa yakai ya kama
nawa kamar an tsira min allura nai ma za na janye ina nu na wa Habu shi"ki bishi
zai baki nama da yawa ya siyo miki"saurin kai duba nayi bayan sa naga wayam sannan
na kalli fuskar sa,murmushi ya yi"kin sanni ne",idona na so sa sannan na kalle shi
na ɗaga kai"a ina ki ka sanni",cikin bazata sukaji nace"kana zuwa in ina bacci kace
zaka tafi dani india sannan ɗazu ma muna zuwa gidannan kaita kirana da hannu har
naje wani ɗaki anan wa ta jarababbiyar mata tai min ihu",saurin ta shi Umma ta yi
saboda mamaki shi ma Habu mamakin yake su kuwa Aunty Mama da Habib ba suyi mamaki
ba dan sun ko ada bana wa kowa magana shi in yazo zan masa,kai ya kaɗa yace"kina
son wannan ɗakin",da sauri na ɗaga kai"to zo muje na kai ki"juyawa na yi na kalli
Umma ta ɗagan kai haka ma Habu sai nabi shi,mun juya Habu yace"kar wanda ya ma ta
magana Oga ana tanka ma ta zata fasa binka wallahi",dariya sukai nan ya kamo
hannuna muka fita duk wanda mana magana sai ya kaɗa masa kai sai mutum ya fasa ni
kuwa tsoron su ma nake ji,har ƙofar falon muka je ya tura ya shiga yana riƙe da
hannuna matar ɗazu mai ihu na gani da sauri na ƙwace hannuna nayi kanta da azama ta
miƙe ina zuwa na tureta ta faɗa kujerar"muguwa mai ihu",saurin riƙo ni ya yi yana
mamaki wato faɗan mu a jini yake kenan sai yau ya shaida,ita kuwa mamaki ne ya
kamata ganin ba tsoro ko ɗaya a idona na ma ta haka,hannu ya ɗaga ma ta ya ja ni
zuwa ɗakin ƙara kallon ɗakin nayi nai dariya har haƙora na suka bayyana a gabana ya
tsaya na kalle shi sosai kamar nasan shi sai kuma na tuna mafarkina sai na barshi a
anan na sanshi,kama hannuna ya yi zuwa bakin gadon ya zaunar da ni sai binsa da
kallo nake ɗan india ne shima nake faɗa araina,kayan dana watsar ya kwashe ya share
wurin sannan yazo gabana ya duƙa gwiwarsa a ƙasa"zaki kwana anan ɗakin"ɗakin na
kalla sannan na kalle shi kai na girgiza alamar a a"me yasa","bana son mai ihu","ai
bazata ƙara miki ihu ba",murmushi nayi"zaka rama min inta min ihun","sosaima kuwa
Nana ta",bakin sa na kalla nai dariya"dama kasan suna na","au sunan ki Nana"kai na
ɗaga masa yay murmushi yana ɗaga hannuna ya ɗora akan ƙirjin sa"Nana rayuwata
ce",zaro ido nayi na nuna kaina da sauri ya ɗaga kansa ya fahimci na gane me
yace,murmushi nayi na ɗora kaina akan hannun sa shafa kaina ya yi na ɗago"muje ki
faɗawa Umman ki zaki zauna da ni",tashi na yi da sauri shima ya miƙe yana riƙeni
muka fito tare wajen da na ga me ihu na kalla ba ta nan sai na yi murmushi su Umma
harsun fito nai ma za na tafi wurinta ina ma ta magana da hannu,dariya ta yi"wato
kinga mijinki shine zaki gujeni ko",kai na ɗaga ma ta alamar eh,kawai sukai dariya
nan ta juya tana masa magana yana amsawa sannan suka shiga mota saida aka janye ni
sannan suka tafi wannan matar da nai sallah a ɗakin ta ne naga ta zo ta kama hanuna
da kanta tamin wanka sannan tasa min kaya masu kyau a gaban mudubi ta tsaida
ni"kallar min kanki anan dan Allah ki tuna ni",murmushi na ma ta na koma bayan ta
na kwanta,ajiyar zuciya ta yi"Allah ya isa wanda ya cutar dake ɗiyata,wani Babban
mutum ne ya shigo da sauri na nufi wurin sa ina dariya yasha mamaki dan an faɗa
masa komai amma hakan da nayi sai na burgeshi hannunsa na kama ina nuna masa jikina
kaina ya dafa"kinyi kyau Nana ta",murmushi na yi dan murna shima yasan suna na,ba
jimawa saiga wannan ɗazun ya dawo da azama na tafi wurinsa ina miƙa masa hannu
girgiza kai ya yi"zo muje ɗakin ɗazu na baki",da sauri na shiga gaba mayafin ma da
ƙyar ya sa min sannan muka fita.

Muna shiga na fara raba ido banga me ihu ba har ɗakin ɗazu ya kaini gyalen na
cire na yar na haye gadon girmansa da yadda yake da kyau shine yake burgeni shafa
shi na shiga yi ina dariya table ya janyo ya aje min take away masu yawa matsowa na
yi ya ɗauka ya buɗe ya miƙo min da saurin karɓa ina kallon shi kaian na nu na ya
ɗaga min kai da sauri na fara ci shi kuma naga ya shiga wata ƙofa yana ciki na
cinye na fara raba ido sai hawaye sharr fitowa ya yi daga wajen yana kai idon sa
kaina da sauri ya ƙaraso yana kama hannuna"me ne ne ki ke kuka",kwanon na nuna
masa,murmushi ya yi"kin cinye baki ƙoshi ba ko ai ba kuka zaki ba wannan duk naki
ne da saiki ɗauka ki ci",kafaɗa na maƙale sai ya ɗauka wani ya buɗe ya bani ƙin
karɓa na yi sai baki dana buɗe masa wato ya ba ni,zaunar da ni ya yi ya shiga ba ni
ina ci saida na kuma cinyewa sannan ya ɗakko wani ya buɗe karɓa na yi na leɓo na
kai bakin sa kai na kaɗa masa ya buɗe na bashi yaci murmushi nayi na ƙara ɗebowa na
bashi da haka da haka saida ya cinye nima na ƙara ɗakkowa na bashi ya cinye waige
waige na fara ya shiga bina da kallo sakkowa nayi zan fita ya taso ya riƙe ni"ina
zaki","ruwa",dawowa ya yi da ni sannan ya ɗakko ruwa da da lemo buɗe murfin ya yi
ya miƙo min karɓa nayi maimakon na sha saina nufi bakinsa da shi"au ashe ni ne zan
sha"kai na ɗaga sha ya yi har lemon sannan yaban nasha,hannuna ya kama"zo muje ki
wanke bakin ki",bin shi na yi da kansa yamin sannan muka fito a bakin gadon ya
zaunar da ni yana kama gashina ya ɗaure"kwanta to"kallon wurin nayi na kwanta a
hankali kamar me tsoron wani abu,daga yanayin kwanciyar zaka san a tsorace nake
wani irin ɓacin rai da tausayi ne ya taso masa bargo yaja ya lulluɓe ni ya zauna
yana shafa kaina lumshe ido na yi amma me kamar saukar aradu naji muryar wata tana
ihu"sannu bawan mace to ina jiranka kazo ka wani tare anan",ɗago kai ya yi yana ma
ta wani bahagon kallo"nazo na miki me ai ke da ni sai in Nana warkewa ta yi",cikin
magana da ƙarfi tace"inka isa shegiya nake Habib ada da batanan ma baka kula ni ba
shine yanzu ma bazaka kula ni ba",a fusace na watsar da bargon na tashi tsaye akan
gadon idanuwa na na watsa ma ta"muguwa muguwa me ihu kawai"saurin shiru ta yi
aranta tana cewa'wai wannan yarinyar me take nufi ne kar dai ta manta kowa banda
ni',dirowa nayi nayo kanta ya taso ya riƙe ni a jikinsa na kwanta"muguwa
muguwa"kaina ya shiga shafawa yana"shiiiiii"hanya ya nuna ma ta jiki a saluɓe ta
fita amma ranta kamar ana zuba wuta,da dabara ya jani ya kwantar yana min addu
a,rufe ido na yi ba jimawa na yi bacci bai bi takan ta ba kawai ya kwanta a bayana
amma bai kai ko hannun sa jikina ba,asubar fari dama yake tashi yanzunma hakan ne
amma bai tashe ni ba sai bayan sallar asuba shi ya koya min na yi,sannan na kwanta
a wurin can na miƙe ina waige waige na dafe cikina,tasowa ya yi inda nake"me ne ne
abinci ko",kai na kaɗa toilet ya kaini"kin iya wanka"kaina na ɗaga masa fita ya yi
wai ya barni inyi wanka wani abu na ga ni yana lilo na janyo shi na matsa saiga
ruwa dariya na shiga yi na fara fesawa jikina ina tsalle ji ya yi shirun ya yi yawa
ya buɗe ya shigo baki ya dafe ganin yanda nawa banɗakin wanka nawa kaina jalaf har
kayan jikina,ƙarasowa ya yi ya karɓa abin Allah yaso ba ruwan sanyi ba ne kuma ba
na zafi ba ne,tsayawa ya yi a gabana yana kallo na kayan sun manne min a jiki kauda
kansa ya yi sannan ya fara zare min kayan saida ya tuɓe ni tass sannan ya kunnata
ya fara zuba min ruwan da harna ɓata rai dan ya ƙwace ina wasa na da kansa yamin
wanka sannan ya naɗo ni a babban towel mai ya shafa min sannan yasa min doguwar
riga mai kyau da gyalenta hannuna ya kama muka fito me ihu da wata na gani ban ko
kalleta ba shima haka saida ya kaini ɗayan gidan sannan ya taho ya barni can da
yake ina son matar ban ma ta kuka ba sai dai duk inda ta gilma ina bin ta tun tana
in zauna har ta barni kome nayi kuma ta yi dariya da mutane da yawa a gidan kuma
suna ta jana jikin su wasu na kula su wasu ba na kula su ba amma sunji daɗin yadda
na yarda dasu bana musu iskancin nawa.

Koda ya koma faɗa sukai ya mata tas sannan ya shirya ya fita Habu ne yazo yana
tambayarsa ƙanwarsa yace tana ina Umma dariya ya yi"ai Umma da Baba jiya kamar
marayu haka suka zama","Allah sarki badan Nana nada aure ba ai da bar muku ita
zanyi","ba komai Oga zamu je wajen likitan ko dan na masa magana jiya","ok to muje
ina Habib dan ya riga ni shigowa","ban ganshi ba ina ga yana hanyar fita"," muje in
mun ganshi saimu wuce kawai",tare duk suka je anan likitan ya basu file ɗin shi
kuma ya kira wanda zai india sannan aka tura masa detail ɗin yace in ya duba zai
kira shi sallama sukai da likitan sannan su wuce company.

A hannun mutanen gidan na wuni suna kula da ni komai su ba ni suce naci baya
la asar ya dawo nan ya shigo kai tsaye ina kwance a falo kaina ba ɗan kwali wata da
naji suna Ruma ita tamin sai wa ta Amina naji ana ce mata mai jego da ita muka fi
shiri dan nama take ta bani ina ci ita kuma wata tsohuwa bini bini ta kawo wani abu
mai duhu a leda tace wai na shanye ina sha ne kawai saboda ina ƙaunar ta bansan
dalili ba,yana shigowa na ta shi da gudu na faɗa jikin shi,cikin wani irin farin
ciki ya rungume ni"Nana ta",ɗago kaina na yi na kama hannun sa na kai shi wurin me
jaririn nan nu na ta nayi"ina son wannan"da sauri ta miƙe ta rungumeni"ai da haka
duk zaki so mu ƴar uwa dukkan nu dangin ki ne",sauran da ta nu na nakalla sannan na
Habib,ƙura masa ido nayi sosai sai naji juwa da sauri ya riƙe ni"ki daina zafafa
tunani zaki shiga wata matsalar"zaunar da ni ya yi aka kawo ruwa ya ba ni nasha
sannan ya kalli Habib"ɗan uwa tafiya fa bata ganka ba da alama kai take son tunawa
anya kuwa zaka tafi",matsowa ya yi ya dafa shi"ba inda zani ɗan uwa nayi magana an
ban wata shida ne dama kuma yanzu wata na uku"tashi ya yi ya rungume shi ni kuma na
zuba musu ido,janyewa na yi ina kallon me jaririn nan sannan na nu na ma ta su"su
waye waɗannan?",matsowa ta yi ta kama hannuna"waɗannan ƴan uwa ne na jini wannan
shi yayan wannan kuma shine mijinki","miji"na mai maita"kai ta kaɗa taja baya ta
ɗakko yaron ta ta ɗora min a jiki"shi wannan yaron kina so?",da sauri na kaɗa
kai"to nima ina da miji shi yasa na same shi",riƙe ɗan nayi sannan na yi dariya na
tashi na kai masa yaron"kana so kaima",cikin murmushi ya kaɗa kai"ina so sosai",a
bazata suka ji na ce"kace ta bamu tunda kai ne miji",ba shiri suka kwashe da dariya
dan sun gane me zan faɗa,wa ta ƴar babba ta taso ta karɓi jaririn tana dariya"ci
kwalar mijinki yau ɗin nan ya nemo miki naki",da sauri na kalle ta ina girgiza
kai,itama kai da girgiza sai kawai na kwashe da dariya naje na kama hannun shi zuwa
hanyar fita,juyowa ya yi ya kalle su suka kwashe da dariya kai ya kaɗa"kun san fa
halinta ba tun yau ba bata iya naci ba kuma kun san matsalar da take ciki",wadda
tai maganar ɗazu ce ta ƙaraso"karka damu Bross ai wannan ba matsala bace a ko da
yaushe tana iya kaucewa kuma wannan halin da take ciki in kana nuna ma ta soyayya
shine zata maƙale ma ka bazata yarda da kowa ba sai kai",haka ne suka haɗa baki
suna faɗa,baice ƙala ba yaja hannuna yana samin hijabin da suka bashi muka fito ban
kula kowa ba ya ɗauki hanyar da muka zo ɗazu.

Tun daga wajen part ɗin ka ke jin tashin kiɗa ina ga ka shiga ciki kunne na
nake dafewa sai ya tsaya yana canja hanyar daga shiga nan ya nufi wata hanyar wani
ƙaton gini ya isa an gewaye shi da shuke shuke wurin a gyare yake tsaf sai ƙamshin
flowers ke tashi ƙofar shiga ya buɗe yana riƙe da ni muka shiga har tsakiyar falon
bin ko ina kallo na shiga yi jiri nake ji sai na daure a kan kujera ya zaunar da ni
yana sunkuyawa a gabana hannuwana ya riƙe"ki zauna anan kar kije ko ina bari na
kunna miki kallo amma ba a tv ba kar su baki tsoro zanje na ɗakko miki kayan ki mu
kwanan mu anan ko abar mai ihu ita kaɗai",da sauri na girgiza kai ina dariya ya
tashi ya ɗakko laptop ya kunan kallo ya ajen sannan ya fita bai jima da fita ba
abin da ya kunna ya mutu dama na ita dannan wa agidan Umma Habu yana da ita yana
bani na danna sake kunna wani nayi bai min ba na canja haka naita kunne kunne wata
ƙofa na gani a buɗe tashi na yi na shiga ɗakin bugawa kaina ya yi wani hoto na gani
ana min murmushi ga hoton na isa ina kai hannu sai ya ɓace ya ƙara komawa wani
bangon bin sa na yi haka yay tamin ni kuma sai na maida abin wasa wata laptop ɗin
na gani tayi datti ɗakkowa na yi"bari na kunna wannan waccan ba kallo a ciki",da
kaina na kunna sai wani vedio ya fara ni ce da wa ni mutum na sunkuyar da kaina shi
kuma yana murmushi sai ya fara magana"Nana",da sauri naji cikin kaina ya amsa nan
da nan naji wani irin zafi ya rufe min jiki"kalle ni mana Nana haba uwa ta",da
sauri na kalli laptop ɗin"Abba" naji bakina ya faɗa miƙewa nayi da hanzari kaina
yana juyawa ina kallon inda nake cike da mamaki na kalli kaina ba kayan da nasan ni
dasu ba ne zama na yi na jawo laptop"Abba Abba"na faɗa ina fashewa da kuka na tuna
komai yanzu cigaba da kallon na yi ina gyaɗa kai kamar a sannan yake magana da
ni"Abba maganar ka ta zama gaskiya gashi har losing memory na yi"sai kuma na yi
murmushi Allah sarki Umma da Habu duk na tuna komai tashi na yi na maida laptop ɗin
zan fito a ɗakin cikin ɗoki sai naji a cikin an ce"ke saiki nunawa mutane kin warke
ai wannan wa ta dama da hanya Allah ya baki danki cikawa Abba alƙawarin sa"cak na
tsaya ina faɗin haka ne fa amma za a sha iskan ci"sai na kwashe da dariya na koma
inda nake na kunna abin da ya kunnan na cigaba da kallo sai nishaɗi nake ji a cikin
kaina ko ina mutanen Maroco Allah dai yasa jakin can bai kashe Aisha ba dan bashi
da imani motsi na jiyo za a shigo nai ma za na tuɓe rigata daga ni sai bra na
kwanta ina kulle ido nai kamar na ga ji na yi bacci ne dan yafi awa biyu da fita
yanzu ma kiran sallah ake,da kaya da yawa ya shigo teddy ɗima ɗima kamar mutum ga
ƴar tsana ƙatuwa mai baho wata ƙatuwar dariya ce tazo min nai saurin haɗiyewa wai
ɗimemiya da ni aka kawo wa wannan abubuwan wato dai na zama yarinyar da gaske ake
nufi ai kuwa zaku ga aikin yarinta kaca kaca musamman mai ihu,aje kayan ya yi ya
juyo gareni da mamaki ya kalleni ya ganni a tuɓe amma ban zare rigar ba da dabara
ya mayar min ya miƙe ya shiga ciki ya yo alwala ya kuma fita ina kallon sa ƙofar ya
kulle da key sannan ya wuce,buɗe ido na yi ina tashi zune alwala nayo nai sallah
saina kwanta a wurin har akai isha ina ta tunane tunanen abubuwan da suka faru da
iri wuyar da nasha tashi na yi nai sallah sai na tume kayana duka bra da bomshort
kawai na bari na kwanta a ƙasan na ɗago ƙirjina sama dama brar ta ƴan gayu ce mai
kyau bawai ɓoye su take ba rabi a ciki rabi a waje suke ɗai ɗai nayi ina ta nishi
ina riƙe mara,"wohoho duniya"na kwashe da dariya.

🌈🌈🌈
🌈🌈
🌈

BABAN YAYA

Babban Yaya Free ne amma me so ya biyo ni Pc in sa a group don shagalin Nana


na buƙatar comments.
08146711395
36

Tun daga bakin ƙofa ya hango ni da azama ya ƙaraso kaina tattaro ni ya yi


zuwa jikinsa nan yaji wani irin ɗumi ya ratsa shi lumshe ido ya yi ni kuma namai
gwalo ina ganin zai buɗe na ƙara mannewa a jikin sa ina mutsu mutsu riƙe ni ya yi
yana magana da ƙyar"me ne ne Nana saurin tashi na yi zaune na haɗa hannuna namai
alamar jijjigar yaro,murmushi ya yi"shifa yaron nan da ki ke so ba haka ake samun
shi ba"da sauri na ɗaga kai"wato kin sa ni kenan"ƙara ɗaga kai na yi na ƙara komawa
jikin sa,kasa jure abin da nake masa ya yi ya juyo da kaina ya ɗora bakin sa kan
nawa lumshe ido na yi ina jin wani irin da ɗi har cikin raina yau na ƙara dawowa
hannun mijina hannun sa ne ya fara yawo a jikina yana shafa duk inda yaci karo
dashi,sakin jikina na yi sosai ba wani fulako muka darji amarcin da bamu taɓa yin
irin sa ba,da gasken gaske na basa mamaki ya zata zan masa raki ganin yanda na koma
komai kuka amma sai yaga aksasin haka da kansa ya min wanka yazo ya kwantar da ni
yana ta lallaɓa ta ni kuma ina narke masa a jiki ga bamai riga a cikin tudun
ƙirjina da yake ji duk sai ya ruɗe jikin sa har rawa yake kaina ya shiga shafawa
yana control kansa dan kar ya cutar da ni tunda ba lafiyar kai gare ni ba,ban damu
ba nai bacci na bar shi da aikin jijjiga ta yana sumbatar gashi na a hankali ya
fara magana shi ɗaya"Allah ka yafe min amma a kan ki kawai Nana nake jin daɗin
rayuwar aure nake cikakkiyar gamsuwa"shi kaɗai ya yi murmishi ya tuna a yadda ya
tsinci kansa yau,shima ba wani jamawa ya yi bacci,rana ta fara ɗagawa sannan na
buɗe ido cikin farin ciki wai na baro waccan uƙubar ba tare da sa ni na ba Allah
na gode ma,juyawa na yi ina kallon kyakkyawar fuskar sa da ta yi shar gashin da ya
ta ra ya yi masa sai ya zama kamar ɗan Pakistan a hankali na ɗora hannuna akan
gashin kansa na shafa a hankali ina murmushi,ban sa ni ba ya buɗe ido yana bina da
kallo idanuwan sa ne sauka zuwa wuyana ya bi jikina da kallo da sauri na kalli
kaina nai ma za na kifa a kansa ina dariya ƙasa ƙasa bayana ya shafa"yadai kina
kallo na ko kin san ni ne"dariya ce ta kamani amma na maza na kaɗa kai alamar ban
san shi ba,"zaki san ni a hankali ko Maman Baby",kai na ɗaga ina dariya a
sakaye,kaina ya ɗago"zo muje muyi wanka zan fita da wuri ina da shigar kaya yau"kai
na ɗaga ya fito a bargon ya sunkuyo ya ɗauke ni cak a wankan ma sai lallaɓani ake
kamar wanda yake taɓa ƙwai,Allah sarki wato baka gane me son ka sai wata sakayayyar
ƙaddara ta sameka musamman ma ta baƙin ciki dan baka gane maƙiyan ka dan abib farin
ciki ya sameka,shirin ma da kansa yake min yana yi yana nasa Allah sarki sai abin
kuma ya koma ban tausayi dan kana gani kasan sauri yakr ga wayar sa na ta ringing
kaya na ya rage min shi kuma yana ɗaura agogo tashi na yi naje ta bayan sa na
tsaya,juyowa ya yi yana hannayena"sorry zo na ƙarasa miki shirin ki kinji",kau na
kaɗa na nu a masa kayan sannan na nu na kai na sai na nuna hanya,murmushi ya
yi"kina nufin zaki sa kayan sannan kibtafi wurin su Mama",kai na ɗaga ina mai
jinjina rungume ni ya yi yana sumbatar kaina sannan ya sake ni yana tallabo
fuskata"please kar ki kuka in kinga ba dawo ba da wuri aikina nada yawa"kai nabɗaga
ina mai bye shima haka har ya buɗe ƙofar ya fita juyawa nayi na zauna ina shafa
cikina hakanan nake jin shauƙin shafa cikin da nake na jima a haka sannan nasa
kayan na gyare ko ina na ɓangaren sannan nasa hijabi na fito ban nufi wurin su Mama
ba sai na shige wajen Hajara tana falo tana break na shiga,tana gani na ta miƙe
tana bina da kallo wajen ta na nufa ina nuna ma ta kwanon abincin cikin mamaki take
dubana"zaki ci ne?",kai na ɗaga saita kama hannuna ta zaunar da ni ta miƙo min abin
cin karɓa nayi na nuna ma ta cup na tea"Nafi miƙomin wani cup ɗin"da sauri da ta
kawo ma ta shaga haɗan tea yadda nake yi sannan ta miƴomin karɓa na yi zansha naji
zafi sosai ajewa nayi na kamo hannun ta yatsun ta na kama na tsoma a ciki wani ihu
ta zun duma da sauri na toshe kenne na cikin masifa kamar zata dake ni tace"dan
ubanki wa yace miki haka ake abu na zafi shegiya kina ma da juyayyar kwanyar ba
zaki daina mugunta ba",tashi na yi na je ma ta abincin na ma ta gwalo"mai ihu mai
ihu kawai"hanya ta nu nan"fita anan shegiya gadon mugunta"gwalo na ƙara ma ta tai
min banza ta cigaba da kara hannunta jikin fankar ƙasa ga ruwan sanyi an kawo ma ta
tana tsoma hannun,fita na yi na tsaya a wajen naita dariya"da wannan damar zanta
gasa ki wallahi kuma kece shegiya",jin motsi nai ma za nabar wurin ina tafe a hanya
duk wanda ya min magana bana kula shi har na isa gida Aunty Mama na hango a falo
ita da Mama da gudu na shiga na faɗa kanta da sauri da saki ajiyar zuciya"Nana wa
ya biyo ki?",kai na kaɗa ina kwantar da kaina a kafaɗar ta dafa ni naji anyi na
ɗago Mama ce idon ta fal da hawaye ya yin da na Aunty Mama ke zuba nima haka muryar
ta na rawa tace"zaki ci abinci?",kai na ɗaga ina kama hannunta a raina nace"ku
daina kuka ina jin ba daɗi da da hali dana nuna muku na warke,kwanon kusa da ita ta
miƙo min na karɓa a hankali nake cin chips ɗin sannan aka ban tea na sha muna haka
a Baffa ya shigo tashi na yi na tafi wurin sa dariya ya yi ya kama hannuna"Nana
zaki bi ni ne gidan Iyyo zani"kai na ɗaga murmushi ya yi ya ja ni muka fita su kuma
suka bimu da kallo,fashewa da kuka Aunty Mama ta yi"duk mai hannu a cutar da
yarinyar nan Allah ka watsa rayuwar sa mugwaye kawai ace mutum iyayen sa ma bai sa
ni ba",dafa ta Mama ta yi"wannan ita ce ƙaddarar ta Halima insha Allahu zata koma
kamar da"kai ta ɗaga ma ta tana go ge hawayen fuskar ta.
Muna shiga falon Iyyo ta miƙe tana kama hannuna"ƴar nan sannu kinji an cuci
rayuwar ki"wani irin kuka ne yazo min ganin kaf dangina suna sona har haka ashe
anan wurin ta nai ta zama , ta shiga ɗaki na silale na fita,Gwaggo suna zaune da Ya
Hadiza na shiga itama da sauri ta miƙe tana kallon bayana"waye ya rako ki Nana kar
ki wani wajen fa",kai na kaɗa alamar ba kowa,zaunar da ni ta yi dai dai Ya Hadiza
na goge hawayen fuskar ta ta ɗago da murmushi ta kalle ni"Nana kin tashi lafiya"kai
na ɗaga ina ɗaga ma ta hannu kasa jurewa ta yi ta tashi ta shige ɗaki tana fashewa
da kuka Gwaggon ma haka gefe da gefe na kalla na kalli Gwaggo"ki daina kuka Gwaggo
nafa warke"saurin kallona ta yi sai kuma ta dawo in da nake tana riƙe ni"kin warke
fa ki ka ce","eh mana ke ba Gwaggo Asama'u bace ƙanwar Babana",cikin murna zati
magana na toshe ma ta baki"amma ai ke kaɗai na nunawa na warke a kwai aiki a gabana
shi yasa ban nuna na warke ba kiyi shiru na baki wani labari amma karki faɗawa kowa
sai dai zaki ta ya ni kin san ƙwaƙwalwar yaro tunanin ta ba kamar ta manya bace
kuma kome nake na bansan kowa ba kina taya ni a ban sa ni ɗin ba","to shike nan
Nana zo mu koma ɗaki kar wani yaji mu",a ɗakin ma saida ta kulle ƙofa sannan ta zo
in da nake ta zauna"ina jinki Nana me ya faru"...munfi awa biyu ina bata labarin
komai tsabar tausayin Abba saida ta fashe da kuka"amma mutane ƴan iska ne ina ganin
ina da san zuciya da son abin duniya ashe akwai kakanni na ki kwantar da hankalin
ki ƴata insha Allahu burin ki zai cika Habib ƙarami za ki samu sai ki a sannu yanda
zai gane kin warke shi kaɗai ne zai iya ta ya ki kiyi komai ba sanin kowa kin san
Yayan ku shi yana sa ni tawatsima za ai kuma wasu zasu iya wanke kansu gwara ai mai
dumu dumu","yauwa Gwaggota nagode ki maida ni wurin su Mama",tashi ta yi muka fito
da kanta ta maida ni sai sannan hankalin su ya kwanta an sun dudduba basu ganni
ba,bacci na wuni yi ranar sai yamma sannan Aunty Mama tasa ni na yi wanka tai min
kwalliya na yi kyau ina zaune a kujerar mirrow ta kalle ni ta mudubin ta go ge idon
ta kaina ta dafa"dan Allah ki tunani ƴata na kasa jurewa zuciya ta ciwo take"cikin
razana na kalleta da gaske take dan ta rame har duhu ta yi,hannun ta na kama na
ƙora saitin zuciyata saurin kallo na ta yi"kin san wace ni ne",kai na ɗaga tai ma
za ta rungumeni"Allah yasa ki tuna baya duka",cikin ƙaramar murya nace"to kice
zuciyar ki ta daina ciwo",ɗago ni ta yi ta tallabi fuskata"taji saƙon ki kuma zata
daina ta jirayi ranar da za a ce kin zama Nana ta da",murmushi na yi a raina na
ce'wannan Nanar ta ci uwar ta da ma iskancin da zatai duk sai kun gudu',kaya ta
kawo min tasa min da kanta ta ɗaura min ɗankwali gyalen na ɗauka na nuna ma ta
hanya"zaki gane kona raka ki dai",kai na ɗaga ina murmushi na nuna ma ta zan
gane,tare muka fito saida taga na ƙule sannan ta koma ciki ɓangaren Abba na koma na
kwaso duk kayan wasan jiya Hajiyar gidan na zaune da ƙwayen ta na shiga ban kulata
ba na wuce su.
Ɗaki na na shiga ina bin sa kallo sai naga ya yi ƙura cire hijabin nayi na fara
tattara shi lokaci bamai yawa ba na shigar dashi hankalin shi na kwashe kayan
shimfiɗar nayi na ɗakko sabon zanin gado nai shimfiɗu da shi in ka gani saika ɗauka
gadon hotel ne ƴan fation kiran sallar magaruba akai ɓnaje nayi wanka da alwala
nazo nai sallah har nai isha bai shigo ba dama yace zai daɗe riga mai kyau da
ɗaukan hankali na saka na kwanta a ƙasa kamar marainiya,ji na yi an tsaya akaina na
ɗago naga waye naganta cikin wasu kaya rabin ta tsirara wani kallo ta bi ni dashi
kamar mai neman wani abu a jikina sannan ta durƙusa ganin na tashi zauna kunnena ta
kama"dan ubanki yau kwana na ne kuma ki sa ni ba kina cutar mantuwa ba ko hauka ke
tuburana bazan bar miki kwana na ba wai ma ke ɗin ba lafiyar ki lau ba anya ba
iskancin ki ba ne kalli yadda ki ka gyara ɗaki saboda a haukar ma kinsan daɗin
namiji",kafin ta gama rufe baki na shaƙeta da ƙarfin zuciya zaro ido ta yi ta fara
ƙoƙari ƙwace kanta amma ta kasa idanuwana na zaro ma ta"dan ubanki ɗan iskan nan
mai neman ƙanwar sa dan tsafi munafiki ya miki ƙarya ke kin yarda saina kashe ki
muguwa kawai mai zuwa wurin boka ya ma ta wanka"da azama ta ture ni tana dafe wuyan
ta cikin gigita da kiɗima take kallo na sai huci nake kamar zanci ba bu tashi ta yi
tana nu na ni cikin magana da ƙyar ta ce"ni na sani ba losing memory ki kai ba
hauka kawai ki ke"kanta nayi da gurna ni naji an riƙe ni ta baya saurin shiga
hankalina na yi dan nasan waye juyowa na yi na faɗa jikinsa jikina na rawa rungume
ni ya yi sosai ya yinda yake watsa ma ta wani kallo na razanar wa"me ki ke anan
Hajara?",ya watso ma ta tambaya a firgice ta kalle shi saita mazr tana ɗan murza
wuyanta"shigowa nace tazo taci abinci shine ta shaƙe ni",hararar ta ya yi"ita da
jikinta yake kamar na jarirai ta ya taga ƙarfin shaƙe ki",miƙewa ta yi cike
mamaki"wannan mai ƙashi ɗayan ce mai jikin jarirai to walllahi ina ga da baka zo ba
kota kashe ni kota illata ni",ɗan murmushi ya yi"dan Alllah baki ji kunya ba kice
wai Nana zata kashe ki kalle ki fa","na kalle ni tunkan ma ka kalleni sai dai ni
nasan wace a kusa da kai","fita"ya nuna mata hanya,soƙo soƙo ta fita tan juyowa ta
kalleni nan taga sai ruwan hawaye nake,kai ta kaɗa a ranta tana zan kama ki ne ta
fita a ɗakin.
: Zaro ni ya yi a jikinsa ya tallabi fuskata tasa fuskar yasa yana gogawa kan
tawa lumshe ido nayi dan salon na sa yamin wato wani sirrin ne wannan na goge
hawayen masoyi ba murmushi na yi acan ƙasan raina ya jima yana min haka sannan ya
ɗago"ki daina kuka kinji ki daina tsoron mutane kowa ya miki abu ki rama ni nan na
tsaya miki,wa ya ce ki taho ma salon wani abu ya same ki"kwantar da kaina na yi a
ƙirjinsa ina ajiyar zuciya kace ƙarti goma ne suka zane ni,hannuwa na ya kama ya
zaunar da ni leda ya janyo ya zaunar da ni baki gadon ya janyo ledar da ya shigo da
ita take a way na nama yamin ba sanya ba jira na hau zaƙalƙalar abuna ina lumshe
sai da na gama yasa ni a gaba nayi brush sannan muka fito a toilet ɗin da kansa
yasa ni ajikinsa yana lallaɓa ta har nayi bacci ban sa ni ba da dabara ya kwantar
dani sannani ya tashi ya fita tana rashe akan gado ya shiga ko kallon sa batai ba
haka shima ya wuce toilet ya gama abinda yake sannan ya fito,shirin sa ya yi cikin
kayan baccin sa masu kyau sai ƙamshi yake a bakin gadon ya zauna yana addu a ido
yakai gareta yaga wuyanta ya yi ja ɗan matsowa ya yi ya duba yaga shatin yatsu ido
ya zaro yana dafe bakin sa saboda dariya da ta ƙwace masa a ransa yake cewa'ashe da
gaske take shaƙa tasha to amma Nana wane irin ƙarfi gareta da zata shaƙi babba
haka"bashi da amsa hakan yasa yay kwanciyar sa a hankali gudun karta tashi dan tana
tashi sunan baccin sa ƙarantacce Allah ya taimake shi kuwa har ya yi baccin ba ta
iya motsawa ba,kiran Assalatu ne ya tashe shi da azama ya wuce masallaci sanda ya
dawo garin ya yi haske ina zaune akan sallaya sai gashi ya shigo a bakin ƙofar ya
coge yana murmushi"ina sonki Nana harkin tashi kinyi sallah"murmushi na masa ina
ɗaga masa hannu,ƙarasowa ya yi ya zauna kusa da ni yana jawo ni jikin sa ɗagowa na
yi na kalle sa ina murmushi shima haka fuskata ya shafa"ranar talata zamu wuce
india ko nakai ki asibiti a duba min ke"kai na ƙara ɗaga masa sannan na kifa kaina
a ƙirjin shi ina shaƙo ƙamshin sa mai ratsa zuciya da wannan na yi bacci shi kuma
ya jingina kansa da jikin mirrow ya shiga tunanin rayuwar baya.

Yana jinginen sai maganar ta yaji akansa"sannu maci amana mugu kawai dan ba ta
da lafiya sai kana ba ta kwana na wallahi bazan yafe ba"ɗago kai ya yi ya kalleta
ya kaɗa kai kawai ya maida kansa yanda yake,abin da ya mata ne yay mugun ba ta hau
shi sai taci gaba"kanrufe ido mana akan wanna ƙwailar batun yau ba ka ke min haka
to ka sa ni kayi da ƴar halak saina lahanta ma ta rayuwa"ha ila yau shiru ya ma ta
dan yanzu ba ya da lokacin kowa bare asa ma sa damuwa wadda yake ciki ma ta ishe
shi,ina tsaka da barci naji masifa sama ta ka a razane na tashi ina dibi dibi yay
saurin riƙoni ido da ido mukai da ita ja baya ta yi dan na bata tsoro cikin zafin
nama na miƙe nai kanta kan tai wani yunƙuri na kai ma ta duka"muguwa muguwa mai ihu
kawai"tasowa ya yi ya janye ni na kuma komawa ya ƙara riƙoni na ƙwace na koma kan
nakai wurinta ta gudu,riƙo ni ya yi ya rungume yana jin yanda ƙirjina ke mugun duka
ɗago kaina ya yi ya ɗora bakin sa kan nawa a jiyar zuciya na shiga saukewa shi kuwa
sarrafa harshena ya shiga yi jikinsa sai tsuma ya ke leƙowa ta yi nan abin da ta
gani ya ƙara ƙona ma ta rai tai tsaki ta koma"zaka zo ka samen ne malam in ka bari
ka shigo ɗakina da yamma wallahi ba zaka fita ba",ya jima yana juya ni yadda yaso
kamin ya zare bakin sa a nawa yana buɗe lumsassun idanuwan sa
kwantar da kaina nayi a ƙirjin sa ina ɓoye dariya ba shi ya barni ba saida yamin
wanka ya shirya ni tsaf sannan ya kai ni wurin su Mama sai sannan ya dawo in da
take shi wallahi in ma ya kalleta dariya take ba shi,saida ya gama shirin aikin sa
sannan ta tare shi ya bata kuɗi zatai amfani da shi bai nemi ba asin komai ba ya
ɗauka ya bata sannan ya fita to darajar wannan kuɗi da ya ba ta saita sassauto a
fushin da take da shi,yana fita ba tare da ta faɗa mai ba itama ta fice dama bikin
ƙanwar su za ai shine aketa feleƙe tun saura sati shida.

Yau ne tafiyar mu tun sassafe Habu da Umma da Baba suka zo zuwa nayi na
rungumeta sannan na ɓuya a bayan ta har filin jirgin tare muka je da ita da ƙyar
muka rabu,saukar mu ba jimawa su Ya Saddi'q suka zo ɗaukar mu Wallahi suna jin daɗi
sun yi ƙiba sun ƙara zama farare,tunda suka ganni suke tausaya min ba ma da yana
musu bayanin yadda nake ubana Ya Saddiq harda hawaye,sanda mukaje asibitin sun duba
komai akan magani suka ɗora ni tunda sunce ai ba accident ba ne dama haka cocain
take wasu ma inta haukata su basa warkewa sai dai mutuwa,bai damu ba tunda dai gani
a gaban sa ai rashin nawa shine ɓarna,anan ma canja min gida ya yi ya shiga nuna
min kulawa taban mamaki kafin wani ɗan lokaci na canja nayi fresh kuma yanzu ina
ɗan ma sa magana ko na faɗi abin da nake so Habu nan su Ya Saddiq suka riƙeshi suna
tafiya company tare gaskiya yasha mamakin yadda kayan kuɗi ke fita kullum ba
almundahana ba cutar kowa haka ma aikata bakin ransu suke aikin dan ana bauta musu
ana ji dasu komai na company da ban yake ƴan ƙasar dake aiki ma sunfi girmama
baƙin.

Ba yanda ya iya magani baya aiki watan mu uku muka dawo tunda muka shigo
gidan Aunty Mama ke bina da kallo"Nana me ke damun ki ne naga kin zama ƙatuwa kalli
ƙirjin ki"murmushi kawai na yi"ke zonan"zuwa na yi na tsaya ta ɗaga rigata tana
kallon cikina ɗagowa ta yi tana dariya"kice da Babyn ki ka dawo"saurin kallon ta na
yi ta ɗaga kai da gudu na fita sai ɗakin Mama tana sallar nafila nai tsalle a gaban
ta na ɗaga ma ta rigata ina nu na ma ta cikina sallamewa ta yi"ke kanki ɗaya kuwa
miye hakan?"ƙafa na fara bugawa tai saurin riƙe ni"me ne ne kuma",a hankali na
ce"waccan da nake a wurinta ce ta ce nazo da Baby"saurin zama ta yi a bakin gado
tana kamo ni na zauna"da gaske ki ke","eh mana Mama"da hanzari ta kalle
ni"Nana"gefe na kalla da sauri"juyo da kafaɗata ta yi"Nana nasan kin warke tuntuni
miye na wannan abin kalla yanda ki ka sa kowa a damuwa haba Nana"fashewa na yi da
kuka na faɗa jikinta"rungumeni ta yi tana shafa kaina"me yasa zaki na zama a
haka"cikin kuka nace"Mama Abba in banyi haka ba za ana ɗaukar rai ɗaya bayan ɗaya a
cikin ƴaƴan sa ","me yasa Nana","Mama kibar maganar nan dan Allah zan faɗa miki
komai nan gaba kaɗan komai zaizo ƙarshe ne ranar da wannan ɗan na cikin yazo duniya
don shine maganajin ba Babban Yaya da Habib ba suma basu gaji komai ba an san hakan
shi yasa masu buƙatar abin zasu kawo kansu har inda muke","to shike nan ki tashi
kije ki tafi ɗakin ki ko shara kya yi"tashi na yi ta biyo ni har wurin Aunty Mama
tana dariya ta ce"ashe kaka zaki koma kwanan nan",tashi ta yi itama tana
dariyar"sosai ma kuwa Dada gobe gobe nan zan tafi siyan kwalli saima na gayyaci Ma
u dan nasan saita fi kowa murna dan ɗab Nana zai zamo laya tamkar da dubu ne","to
Allah ya albarka ce shi","amin Dada godiya muke da wannan addu a",da kaina na tafi
dan sun fita shida Habib saboda shigar safe mukai gyara ko ina na yi kafin shigar
magariba dan Hajiyar gidan ba ta nan sai da na gama abin da nake sannan sai gata
ta kamar tare suke tana shigowa shima yana shigowa wa ta fitar burgu na yi na
bankaɗe ta na isa gare shi na rungume shi,taga taga ta yi zata faɗi ta samu ta
zauna akan kujera da sauri ta kalle ni"keee mahaukaciya miye hakan ki ke yi kalla
yadda ki ke nema kai ni ƙas me ke damun ki"a zafafe na yi kanta na ɗaga rigata na
nuna ma ta cikina"Baby ne da ni kina so",wani wuuuu taji a cikin kanta saura kaɗan
ta suma wani irin hayaƙi hayaƙi taji yana fitowa daga cikin idon ta,sama naji anyi
da ni na kware baki zanyi ya juya da ni sannan ya dire"fuskata ya tallaba"ban taɓa
jin labari mai daɗin wannan ba zo muje kiga wa ni abu",yaja hannuna muka fita,ta
shi tayi tana wani kallon bayan mu,kwasar jakarta ta yi zuwa ɗaki a haukace ta
lalubi wayarta ta dannawa yayar ta kira bugu ɗaya ta ɗauka"na kaɗe Yaya na shiga
uku ance bazata haihu ba to wallahi ciki ne da ita kuma yarinyar ba ta
ƙarya","kwantar da hankalin ki Hajar ciki a jikin mahaukaciya i bazai wahalar
cirewa ba..."fauce wayar na yi"bada wannan cikin mahaukaciyar kina jina tsohuwar
kilaki ƴan barikin zuwa lahira da ƙafa ke dai ina ganin da ƙafarki zaki lahira bata
ƙarshin ƙasa ba anya kuwa ke mutum ce ace ke dai baki da aiki sai raka mutane
halaka to wallahi baki isa Aunty Hajara ba zata taɓa zama bazawara ba in kin kashe
ma ta aure in ya ya da mijin ƴar ƙanƙanuwa dani kuma cikina a hannun ta zata
ɗauke shi tunkan a mai wanka kashe wayar nan kan na faɗa ma ta kin fita marmarin
miji..."wuff ta kashe wayar ,juyawa na yi gareta na miƙa ma ta wayar"an faɗa miki a
haka zan ta zama ne ban warke ba kin san tamsil inji balarabe to wannan shine kuma
kin faɗa na warke ba mai yarda dan uwara tasan na warke Gwaggo na ta sa ni kune dai
baku sa ni ba kuma bazaku taɓa sa ni saina haihu na kama ɓeraye a tarko"ina kaiwa
nan na juya na fita,bina ta yi da kallo tana mamakin yanda nake abu jikin ta ne ya
yi mugun sanyi nan taji wani mugun kuka yazo ma ta nan ta fashe da shi" wannan wace
irin rayuwa ce Abba duk kai ka sa ni waɗannan abubuwan nasan ina kishin ta amma
bana son mijinta ya rabu da ita dan in ya sake ta ni me zan sa mu da ita na ganshi
da ita na same shi sai ace saina rabasu gashi ita tana da cikin ni kasa ni na
lalata mahaifata ban san dalilinka na yi hakan ba Inna Fulera ta taya ka na lalata
rayuwata ƴar mitsitsiyar yarinya zata haihu ni ina nan"kuka ne ya ci ƙarfinta ta yo
hanyar fitowa nai ma za nabar wajen wani irin tausayin ta ne ya kama ni tabbas ita
mace ce mai kishi amma abubuwan da take nasan sa ta ake da ace iya kishin ne nasan
ya zanyi da ita amma matsalar an sata a hanyar banza da wannan hanyar ya kamata na
fara rabata kafin tonuwar asirin iyayen ta bana son komai ya shafeta sai dai ya
tsaya iya su dan mijinta na aura duk da ba ta yara amma ai mijinta ne ni ce nai ma
ta kutse,na da ɗe ina wannan tunanin sannan naje nayi wanka na kwanta koda ya shigo
ya gan ni ina bacci fita ya yi yaja min ƙofar juyowa na yi ina tausayawa rayuwar su
shida ɗan uwansa amma Allah ya kawo mana ɗauki.

UMMU SADDIQ CE

🌈🌈🌈
🌈🌈
🌈

BABAN YAYA

Babban Yaya Free ne amma me so ya biyo ni Pc in sa a group don shagalin Nana


na buƙatar comments.
08146711395

37

Tana tsaye jikin mirrow ya shigo da sauri ta nufo shi"ya Nanan ta ke?"da
mamaki ya kalle ta sai kuma ta basar tana ɗan in ina ta ce"am am ya Nana?"zama ya
yi a bakin gado yana kamo hannun ta"kinga Hajara Nana ba ta da matsala da, ke ki
ke janta da rigima bari na faɗa miki kina wa Nana kallon yarinya amma tunda ta tazo
gidan nan take wahalar da ke ina sa ne da komai kuma ina lura da ke bata taɓa janki
da faɗaba ita sai dai tsokana zan roƙeki dan Allah badan ni ba kinga ni namiji ne
dole zan fita kinga dai halin da take ciki ki taimaka ki taya ni kulawa da ita"zama
ta yi tana ɗora hannun ta akan nasa"namaka alƙawarin bakin raina zan kula da Nana
komai na da ya wuce Wallahi zan kula da Nana ka yarda da ni",murmushi ya yi"na
yarda da ke saboda dama can ina yarda da ke kece kawai ki ka canja komai tashi ɗaya
daga sanda ki ka fahimci tsakanina da ita Hajara Nana ta shiga rayuwata tun tana
zanin goyo shi yasa ban bari kowa ya shiga rayuwar ta ba sai ni ɗaya na dasa ma ta
yadda zata so ni ne tun ba ta da wayo shi hakan da na ma ta shi yasa kwata kwata
Nana akaina ba ta da kunya koma kome girman ki ki ka nu na kina so na tabbas zata
tsaneki kome zaki ba ta kuma bazata soki ba ke Nana tana da ƴan family in wata tace
ina burgeta to ta daina kulata in ma zata kulatan to kullum faɗa ne aikin
nasu,halayen Nana ba zasu fasaltu ba amma ke tana raga miki harma tasan cewa in ta
saɓa miki ba ta kyauta ba tunda mijin ki ta aura amma fa da ita ce farko to da
bazata taɓa ɗaga miki ƙafa ba Hajara kin san me na sakawa Nana da shi a duk wannan
soyayyar da ta ke min da waɗannan hannauen nawa da wannan gangar jikin nawa wasu
shashashai suka saka ni na gana ma ta azabar da ko maƙiyinta ba zai ma ta haka ba
nasan baki fahimta ba naso na raini Nana ba tare da tasan me ne aure ba duk wannan
feleƙen da ki ka ga tana yi batasan me ne auren ba amma hakan bai samu wai ni ne na
maida matar aure a gaban ƴan fashi dalilin da ya kawo wa Nana jinya da fita hayyaci
na tsawon watanni hakan yasa na gujeta saboda ina tunanin ban kyauta ba sai dai
yarinyar ita nema na tavke ido rufe ta yi ciwo ta yi kuka duka akaina haba Hajara
yanzu wannan yarinyar ba ita ce ya kamata a aura ba ya kamata ta zama kishiya
ba,kin san wa zan kwaso in ban zauna da Nana ba"fashewa ta yi da kuka
sosai"innanillahi wa inna ilaihi raju un dama abin da ka aikatawa yarinyar da ta ke
matuƙar ƙaunar ka amma yarinyar kullum nu na wa take a sauƙi komai yazo ma ta wayyo
baiwar Allah dama tafiyar da kukai ta dawo ita ɗaya kana bin ta a baya baka magana
da ita wallahi ka nemi yafiyar yarinyar tun kafin Allah ya yi fushi da kai",tashi
ya yana zagaya ɗakin"Hajara tun kafin na nemi yafiyar ta yafe min sai dai ni yanzu
ya wajaba akaina na kare lafiyar ta da taimakon ubangiji da taimakon ki saboda Nana
na dawo da Habib nan da aiki amma zai koma ƙasar sa bayan wasu shekaru",ta shi ta
yi"to shike nan Allah ya mana jagora amma zaka fahimci matsaloli daga gareni dan
Allah kar kai min muguwar fahimta","na fahimce kinkice halayen dai baza su sauya ba
agaban mutane amma a baɗine ke ɗin kin canja",murmushi ta yi kawai ranar cikin
farin ciki suka kwana.
Tun farar safiya na tashi yana zaune bakin gado yana kallo na da mamki nake bin sa
da kallo sannan kuma na lura da ita tana tsaye jikin window kallon rashin fahimta
na musu dariya ta matso tana yi"kin ganmu cirko cirko ko gadin ɗan Babban Yaya da
Nana masifa muke"shi kansa sunan da ta faɗa saida ya yi dariya ta shi nayi ina musu
alamar ina kwana wani kallo tamin a ranta tana cewa"wannan sheɗaniyar yarinyar
wallahi tai tsawon rai za ai kallo Allah yasa ɗan ya yo halinta shike nan mun samu
gidan kallo a gidan mu",abin mamaki kwana goma sha shida amma banga wani mugun hali
ba tare da ita sai dai ni kota ƙyaleni saina tsoka ne ta sai naga ba ta fushi tun
daga nan na fara sakin jiki da ita sai na ga taji daɗi,matsalar farko da ta fara
fuskan na lura hakan kuma shine ƴan gidan su kusan kullum sai sunzo ko Abban ta ya
turo ta je sautari takan ɓoye ɓacin ranta inta ganni amma batasan na riga na ɗago
ba.
Bayan wata biyu cikina ya tonu kowa ya sa ni a sannan yana da wata biyar dai
dai amma fa iskanci sai abin da ya yi gaba yanzu Babban Yaya hankalin sa kwance ya
ke yama yi tafiya kaf dangin suna ba ni kulawa da sunan mara lafiyar tunani Umma
bata barni ba nima haka kuma a ɓoye ina kula da su sosai suna rayuwar sa ada.

Yau da azahar ina ɗaki baccin ƙailula naji hayaniya fitowa na yi da ciki
ina turo shi Aunty Hajara ce da yayar ta ta yi kicin da rai tana gani na taɗan
harare ni ina ganin haka na gane mugun nufi aka ƙullo kenan yayar ta ta ce kalle
ni"sannu masu ciki"ban kalle ta ba na kalli Hajara"Umma zanci abin ci",cikin sauri
ta ɗago ta kalle ni a ran ta ce"wannan tashar kuma aka kama Nana"tasowa ta yi kama
hannuna"zo ki koma ɗaki zan kawo miki kinga nan na yi baƙuwa",haɗa ido mukai da
yayarta ta na ɓalla ma ta harara"kar ki yarda da wannan zubin ƴan wuta ne da
ita",zaro ido sukai atare suna kallon juna cikin zafin nama ta taso"ke mahaukaciya
nice mai zubin ƴan wutar"kai na ɗaga"eh mana yanzu ba munafirci Babanku ya turo ki
yi ba in ki ka kuma zuwa gidannan saina tona masa asiri a duniya harda ke karuwar
gida",da sauri Aunty Hajara ta rufen baki"muje muje karki tonawa kowa asiri dan
Allah wannan fitinar ta ki bazata haifar da ɗa mai ido ba",ɗaki ta shigo da ni ta
sake ni dariya ta saki sai kuma ta kama bakin ta ta fito tana zare ido tare ta ta
yi"kin gani ko Hajara ki zuba ma ta wannan maganin kawai ta ƙara sa haukacewa
duka"karɓa ta yi"an gama Yaya amma yanzu ki tafi dan tana kuma ganin ki zata kawo
duka kuma gata kamar doki shekaran jiya da ƙyar na sha a wurin ta","ai shine ki ma
ta amfani da wannan maganin ta fice ma a gidan dama cikin tana sha sai wa ni",da di
hakan ta rako ta ta tafi ɗakin ta ta wuce ta zuba maganin a masai"Allah ya tsare ni
haukata wa ni da ɗin ma da na yi niyya na tuba kuma dama ku ku ka zagani","nagode
Aunty Hajara",ta ji an faɗa daga bayan ta jiyowa ta yi"ba komai Nana gwara ma da
nasan halin su kinga a yanzu na samu damar gane sirrin su",murmushi na yi"zo muje
kiji wa ta kitirmurmura dana ƙullawa Innar ki"biyo ni ta yi tana dariya har ɗakina
zama ta yi kan sofa na je can ƙuryar gado na ɗaga capet na ɗakko wani file na dawo
inda ta ke zama na yi na ɗora ma ta akan cinyarta"buɗe ki ga ni",zazzago su ta yi
ta fara dubawa ta shi tsaye ta yi"Nana mi ye wannan?","abin da ki ka ga ni haka ya
ke takardun da ki ke nema ki kaiwa Abban ku bana Hajiya Fulera ba ne na ki ne",zaro
ido ta yi ta zauna jaɓar duk ac dake a ɗakin amma fifita take da hannu"ban ga ne ba
Nana","yanzu zaki ga ne Abba bai bawa Hajiya Fulera komai ba suanyen da ta ga ni
liƙawa akai amma ba na ta ba ne kuma an ba ta tasa hannu a matsayin wakiliya ni
nasa hannu a wajen da zaki sa saboda nasan sa hannun ki ke ma baki san na sa ni to
wannan sirri ne kar ki ga no ni","wallahi saikin faɗan"dariya na yi"zan faɗa miki
amma akwai wata a ƙasa zan faɗa miki kamin kowa ya faɗa miki kimin alƙawarin riƙe
wanna har sanda abin zai tonu","na miki alƙawari Nana",ɗan sunkuyar da kai na yi
sannan na kalle ta"ba Abban ku ne Baban ki ba kuma Hajiya Fulera ita ta kashe Mamar
ki shi yasa ba sa son ki suke saka ki akan hanyar halaka..."
Miƙewa ta yi tare da watsar da takardun hannun ta cikin lokaci ƙalilan hawaye ya
wanke ma ta fuska kafaɗata ta kama jijjaga"ke Nana kalle ni nifa ba sa ar ki ba ce
kar kiga na fara kulaki ki tarwatsa min tunani",kama hannun ta na yi ta zauna"ki
nutsu Aunty Hajara wallahi tunda na ke ban taɓa ƙin ki ba na dai tsani ƴan uwanki
tabbas shi yasa na ke miki waɗannan rashin kunyar kuma da kin lura da faɗa da ki ke
da zagi kwata kwata basa miki kyau kawai zuga ki da ake shi yasa ki ke min haka
Aunty Hajara Mamar ki kishiyar Hajiya Fulera ce watarana Yayan ta wato Abban su dan
ba Abban ki ba ne shi Abban ki mutum ne nagari shi kuma wancan saƙagon ɗan iskan ba
Abban ki ba ne ko Abinci da ya ba ki da kuɗin mamar ki ya ba ki kuma ki ka yi
karatu,Yayan ta yazo sai mamar ki tazo wajen ta da niyar magana sai ta shiga ba
tare da ta nemi izni ba dan ta ɗauka ma ba ta nan al'amarin da ta gani ne ya sata
naƙudar dole Hajiya Fulera da ɗan uwanta na fasiƙanci,tasowa sukai ba kunya suka
kaita asibiti dan Abban ki sannan bashi nan yana wurin aiki can Lagos,bayan kaita
ta haihu lafiya sai suka samo Allurar guba suka ma ta nan cikin lokaci kaɗan Allah
ya ɗauki ranta ana mutuwar suka turama Abban ki da saƙon mutuwar bawan Allah garin
ya taho cikin tashin hankali a motar sa zuwa tasha yay hatsari ya mutu shine saboda
baƙin muna firci Yayan na ta ya ɗauke ki wai ita Hajiya Fulera aure zata yi Umman
ku mutuniyar kirki ita tai miki reno na tsaka ni da Allah dan nonon ta ta ba ki
sannan ita ta haihu amma ɗan babu rai",fashewa na yi da kuka itama ta shiga rera na
ta kamar ranta zai fita tana riƙe da hannuna"Nana kina ƴar ƙarama kanki ya iya
ɗaukar wannan babban al'amari haka dan Allah yafe min duk abin da na miki wallahi
ba a son raina ba be",sakkowa na yi na zauna inda ta ke"ai wannan masu saki keda
haƙi ko kin manta ni ba abin da ya same nifa asiri ba ya kamani dan bama asan a
watan da aka haife ba kansu sukai wa kuɗin ki da ki ka ɓa ta in sun aje nasu kin
gani ki sace kawai",dariya ta yi na shiri"kefa bakya faɗar abin arziƙi kullum saina
tsiya sata kuma zaki saka ni",nima dariya na yi"to ai Aunty Hajara ni ba na ya fiya
shi yasa kinsan sunan ki sunan Umman ki kenan Abban ki kuma sunan Babban Yaya zan
ɗakko miki hoton su amma fa yana ɓangaren Hajiya Fulera",kaina ta da fa"nagode
Ƙawan ta ban ma san me zan ce miki ba ni",janye hannun ta na yi na miƙe da ƙyar dan
cikina nauyi gare shi"ba wata Ƙanwar ki mu shirya cikin kutumar uban mu idan Hajiya
Fulera ta ga ne na sace ma ta takardu na baki shi kum Abban Babban Yaya fansar
iyayen ki ya miki da dukiyar da zai ba ta dan Abban ki abokin sa ne sosai",da
mamaki ta riƙe haɓa"Allah wadai na da banwa Abba biyayya ba","ba komai Aunty Hajara
shi kuma bai taɓa jin haushin ki ba dan yasan ba daga ke ba ne","to shike nan muje
ayi tuwan kar ɗana ko ƴata suji haushi na",dariya na yi ai nan gaba kaɗan cikin nan
jikin ki zai koma ni tsoron haihuwa nake karna mutu",baki na ta rufe"kar ki kuma
wannan batun ƙalau zaki haihu taho muje ki daina wannan soki burutsun yauwa Aunty
Hajara in kin je gida ko kiyi irin abin nan idan ana magana kice Abba wai sunan wa
naci ne sannan me yasa nake ƙaunar sunan Habib zaki ga yana gumi wallahi",dariya ta
yi"to Mama Nana",nima dariya na yi ranar cikin farin ciki muka wuni sannan muka
tafi gidan su Mama dama kowa ya daina mamkin tsakanin mu dan muna futa na koma mara
lafiyar kwanya.

INDIA

Ɗakin da suke taro cike yake kowa ka kalla farin ciki ya ke saida aka nutsu sannan
shugaban shige da fice da lura da kuɗi wato Babban Yaya ya fara
magana"Alhamdulilkahi muna godiya ga Allahda yasa mana albarka acikin wannan
company tun a watan baya kowa ya maida abinda ya kashe a wannan company a wata guda
komai da aka ƙara samu ya zama riba sannan company ya zama riba shima",murna ce ta
ƙara ƙaruwa sai gaisawa ake dakatar da su ya yi"iya mu masu iko a wannan company
muna nan amma a masaukin baƙi namu dana cikin garuruwa da ƴan gari ma ga baƙi can
sama da mutum dubu shida suna son saka hannun jari kuma dama kun san da haka tun
wancan lokacin na faɗa muku yadda komai zai kasan ce dan haka zan gara amsar su
daga ɗaya har mutum million guda",haka ne suke faɗa nan ya fiddo musu takar dar
tsari da sharuɗɗa da ya fitar kowa ya gani sai jinjina masa ake za ayi abun a tsari
yadda bamai cutar wani haka ba za a ƙwari company ba sanna za a daɗawa ma aikata
albashi,wannan abu fa ya yi daɗi fiye da tinani,sun daɗe suma tattaunawa sannan
suka tashi kowa so yake ya gaisa da shi,yanda ya aɗa haka ce ta kasance sati uku
yana karɓar baƙi kullum sama da mutum ɗari da wani abu sai a kwankin sannan mutane
suka sauƙi,cikin wata guda kaya suka nin ka da sau ɗari ɗaukakar company ya ƙara
zaga duniya sannan aka ƙara ma aikata.

Sai a kwanakin bayan an gama sannan ya samu kansa kullum suna vedio call yana
mamakin yanda gidan sa ya zama a laptop ake maganar yana ganin yanda kowa ya ke
gilmawa sai hankalin sa yake ƙara kwanciya,amma kullum Aunty Hajara na masa masifar
kayan jarirai zaina siya mana in ba haka ta biyo shi ai tasan inda ake sayarwa,da
ƙyar yake lallaɓata ta haƙura yana siyan kaya yana turo ma ta a ɗakin ta ma take
tarawa ni ban san tana yi ba,da haka cikin yake ƙara girma ni kuma iskanci na sama
sai dai ba a gane na warke.

Dawowar Habib kenan daga wurin aiki da kayan ma a jikin sa ya shigo ɓangaren
mu muna ta musu da Aunty Hajara ya shigo dariya ya yi muna masa sannu da zuwa
kallona ya yi"Yaya ta ni dama fa nasan ƙalau ki ke shine ki ke samu tausayin ki
kullum muna jajanta abu ɗaya",dariya mukai sannan Aunty Hajara ta ce"kasan
mutuniyar akwai tsare tsare yanzu ma tsarin ne ya biyo da haka shi ba ta nu na ba
daga ni sai Mama da Gwaggo Ma u sai kai kuma dama kai ta ce tana so ta faɗa ma sai
dia batasan ya zatai ba",ɗan murmushi ya yi"to ai yanzu na sa ni sai a faan
sirrin"tashi na yi na je ɗakko laptop ɗin ta wajen Abba na fito,zama na yi na
kallesu sannan na haɗe rai"amanatun amana a lahira ta ciku ta balbale ku sama da
ƙasa",kwashewa sukai da dariya Habib ya ce"ya zaki na kaimu jahannama kai
tsaye",dariya na yi baje na kulle ƙofa na saki labule sai bina suke da kallo,dawowa
na yi na zauna sannan na kunna juya musu ita suka fara gani na nida Abba muna hira
har abin ya dawo na bubuwan da ya faɗa min sannan da sirrin mutane masu mugun yawa
ga hoton su nan yana nunan ɗaya bayan ɗaya,fashewa Aunty Hajara ta yi da kuka da
buga kanta da bangon da yake kusa da ita innanillahi wa inna ilaihi raju un wai
mutane akan kule sai a aikata komai wannan wacce irin masifa ce haka,Habib kuwa
kamar zai fashe dunƙule hannu ya yi zai da ki laptop ɗin na janye ya tashi center
table ɗin"in ka fasa ta kuma mu kama ina malam gashi nan hannun ka na jini",tashi
ya yi ya fita a fusace Aunty Hajara kuma ta miƙe tana kwashe glass ɗin"Nana dama na
ce ba mutum ba ce ke kince mutum ce ke ta ya akai Abba da ke kaɗai ya yarda har ya
baki wannan sirrin",tashi na yi ina ta ya ta kawai ina murmushi sai bayan kusan
sati biyu sannan yazo ya sa me ni mukai magana mun daɗe sannan ya ta fi a kwanakin
Babban Yaya ya dawo munsha murna kuma ya tabbar gidan sa ya gyaru duk da ni bamai
lafiya ba ce a ganin sa,cikakken kwana ashirin ba a yi da dawowar sa ba ya tafi
Abuja,wajen sha ɗaya na dare ina bacci naji kamar ana ta shi na ashe ciwo ne tun
ina daurewa har na kasa kamar daga sama sai ga ta ta shigo ganin ina dafe ciki ta
fita da sauri ba ta nemi kowa ba ta juya mota tazo ta ɗauken ta ɗauki kayan da ta
shirya tuni sai asibiti Murtala ne kawai ya sa ni kuma tace kar ya faɗawa kowa a
sanda muka je ciwon baiyi yawa ba muna shiga kamar an kira shi nan da nan abin ya
yi yawa kusan an raba dare suka ce ma ta bari suyi min aiki nan tace ta amince amma
kafin aikin sai gashi na haihu fitowa sukai suna faɗa ma ta da gudu ta shiga ta
ɗauki ɗan amma ɗan baizo da rai ba kuka ta shiga yi kamar ranta zai fita cikin
hayyacina na dawo naganta tana kukan murmushin ƙarfin hali na yi"kiyi shiru Aunty
Hajara baizo da rai ba ko"kanta ta kaɗa tana ƙara ƙanƙame yaron gashi nan ƙato
kamar a kira shi ya amsa da ƙyar suka sa ta fita amma ta hana yaron haka dole suka
bar ma ta ta ɗau shawel ta nan naɗe shi ta ƙara rungume shi da ƙyar ta ɗaga wayarta
ta kira Gwaggo ta faɗa ma ta asubar fari suka cika asibitin wai jarda ni a bawa
Aunty Hajara haƙuri amma taƙi yin shiru saida Babban Yaya yazo da Baffa da Alhaji
Baffa da su kawu sannan ta bada ɗan aka sallameni muka koma gida wanka aka masa
suka mai sallah suka binne shi.
Zuwan wannan yaro babu rai ya taɓa kowa amma ba ya Aunty Hajara ko falo ba ta
fotowa kullum tana maƙale da wayar ta tana shafa wayar dan ta mai hoto yafi goma
kowa gida da dangi anzo sai mamakin yadda ni ragal amma kishiya ta damu da rashin
yaron a haka akai sati biyu duk mun haƙura da yaron.

UMMU SADDIQ CE🌹🌹🌹🌈🌈🌈


🌈🌈
🌈

BABAN YAYA

Babban Yaya Free ne amma me so ya biyo ni Pc in sa a group don shagalin Nana


na buƙatar comments.
08146711395

38

GIDAN SU HAJARA

Abba ne zaune kusan su shida sai Aunty Hajara da ke gefe tana hawaye kallon ta Abba
ya yi yace"wai akan kishiya ki ke wannan kukan kishiyar ma maƙiyar mu",kai ta
girgiza"haba Abba jariri fa na kashe",yayar ta ce ta harare ta"to bakin ce gwara
abar uwar da rai ba kina sonta yanzu"a fusace ta miƙe"eh nace ina sontan duk abin
da na ke ma ta bata taɓa jin haushina ko ta zageni kuma tana faɗa min gaskiya amma
ku fa me ku ke faɗan da zan ƙaru bayan halaka da kuke kai ni kuma na ce ku faɗamin
me ne manufar hakan kun ce sai nan gaba sai ku riƙe gaban ni ku barni da zunubin da
yake kaina"ya ɗau jakar ta ta fita tana kuka,dariya sukai Abba ya dubi ƴar ta shi
da abokan sa"da wannan hujar ita zamu kama ta mijin ya saketa dan tabbas bazai
zauna da ita ba in yasan ta mai haka kin ɗau vedion iya maganar ta ta kisan ko","eh
na ɗauka amma Abba ba yanzu ba sai zaman ya iƙa abin ya ma ta daɗi tana ganin kamar
tasha sai kawai mu tona ma ta asiri in ya korota muma nan sai mu koreta shike nan
ta koma titi"jinjina ya ma ta sannan suka cigaba tattaunawar su.
kuka Umman su ta shiga ɗaki tana yi da tasan haka ce zata kasan ce da bata
bar Hajara ta aikata wannan kuskuren ba wayarta ta janyo zata kira ta saita fasa
kawai ta shiga ma ta addu a itama tana neman yafiyar Allah akan abin da tasa baki
aka aikata da ita.

Abin ban mamaki Aunty Hajara ta zame min kamar Yaya ba ta son ɓacin raina
abin da ke damuna kullum sai munyi faɗa saita na zuwa har ɗakina tana kuka wai na
yafe ma ta wannan abu na ɗagan hankali,yau daibtana cikin faɗa na tare ta"nifa
wannan neman ya fiyar ya ishe ni ko rai li ka kashe min ai yaci ace na yafe
miki"saurin kallo na ta yi sai ta shi da gudu ta fita ni dai ban gane kanta ba sai
na barta kawai.

A wata uku na ware na kwashi jiki na bi miji india ba tare sanin kowa ba Aunty
Hajara takar da na rubuta ma ta dan wani ɗaukar fansa duk ba shi ba ne ta bakin
Abban in wani zai cutu karna ta da komai ya bar su ga Allah.

BAYAN SHEKARA BIYAR

*BABBAR CAKWAKIYA ZA TA ƁALLE*

Na gama makaranta na zama ƙatuwa mijin mu ya ƙara zama hanshaƙi haka ma Habib sai
dai shi yana gari biyu kowa yana cikin farin ciki ya yinda waɗanda bamu san ma da
zaman su ba sun samu a ƙahon zuci bama ya idon sauran wato Abban su Aunty Hajara
dan shine idon su.

Rayuwa ta fara yiwa wasu tsanani dan wasu daga cikin su sun fara tuhumar juna
ko suna cin dunduniyar junan su dan komai na su ya tsaya ta ko ina wannan dalili
yasa Abban su kiran Hajiya Fulera ta ce zata turo masa da kuɗi ya jira dan shima
abubuwan hannun sa da kadarorin sa bai san ina suke zuwa ba dan sun fara
ƙarewa,yana tsaka da jiran ta ta kira shi bata ga komai ba fa har waɗancan da ta
ƙwace na kishiyoyin ta wannan abu ya kusa sata ta yi hauka nan tace ma sa tana
hanya nan da kwana biyu ta dawo gida ta duba a kwana biyun kuwa ta dawo kwatsam
muna taron suna Ya Ruma ta haihu da sanyin safiya sai ganin ta mukai muna ta re da
Aunty Hajara munsa kaya iri ɗaya wa ta uwar atamfa mai golden sai sheƙi muke kana
ganin mu kasan muna hutawa,ba tare da kowa ya lura ba sai ga ni akai ta shaƙeni
dama ƙarfi gareta nan da nan aka taso kanta amma an kasa ƙwata ta ni kuwa sai zaro
ido nake ina jina a sama wani kukan kura Aunty Hajara ta yi ta haska ma ta mari
wanda saida ya razana kowa bare ita da ta sake ni ba shiri da sauri ta janye ni
zuwa bayan ta sai huci ta ke kowa yasha mamakin abin da ta yi ta mari ƙanwar uban
ta akan kishiya,cikin tsanin mamaki Hajiya Fulera ke duban ta" ni ki ka mara Hajar
akan na shaƙi kishiyar ki?",itama duban tsabar idanuwan ta ta yi"to me ta miki da
zaki shaƙe ta ko baƙar muguntar ce ta motsa wallahi bari kiji Fulera duk wanda yace
zai taɓa Nana ko mijin ta ne sai inda ƙarfina ya ƙare dan haka baki da gurbi a
gidan nan fita wato kinje ɓangaren ki kinga wasu a ciki shine zaki zo ki huce
akanta dan ita ta miki kashi a gado",wani irin duba Hajiya Fulera ke wa mutanen
gidan sai nan ta nu na ta"Hajara naja da uwar ki ma bare ke zaki ga abin da zai
same ki a yau ba sai gobe ba"tana kaiwa nan ta juya ta fita,juyowa ta yi tana shafa
wuyana"sannu Nana yi haƙuri",hawayen fuskata na share na rungume ta nan aka shiga
mana dariya amma baiwar Allah ita kaɗai tasan me ta ke ji a cikin zuciyar ta
faɗuwar gaba kamar ƙirijin ta zai ɓurma.
Tana shiga falon gidan yayan na ta dama Umma ba ta nan kallon sa ta yi"me ka
shirya kan Hajara so nake naja rayuwar ta kan titi na tarwatsa ta",ba kunya ya taso
ya kama hannun ta ya zaunar da ita wayar sa ya janyo ya nu na ma vedion shekara
biyar ba ya take tasa shi a aka turawa Babban Yaya.

Yana tsaka da magana da Ya Hasiya saƙo ya shigo ma sa nan ya ɗakko ya duba tun
kamin ya gama ga ni ya fara gumi karɓa Ya Hasiya ta yi ta shiga ga ni ta ɗago zatai
ma sa magana taga yay ya fita kanta ta dafe ba ta so ayi abin kunya a gaban mutane
duk ba baƙo a gidan ina ɗaura manta ɗankwali ba tare ta sa ni ba naji an ture ni an
fizgo ta ya kwaɗa ma ta mari nan take hakan ya janyo hankulan mutane aka taso kansa
ana tambayar miye hakan kanta ta sunkuyar amma ta dake zuciyar ta ba tai
kuka,tasowa na yi daga hankaɗar dana sha na ture shi shima"Babban Yaya miye hakan
zaka dake ta akan idon mutane in wani abu ta maka basai ka bari sai mun koma gida
ba..."ban gama magana ba ya haskan nawa marin da sauri ta janye ni ta tsaya agaban
sa"in laifi na maka ka hukunta ni ni ɗaya amma karka kuma dukanta",ƙara marinta ya
yi ya rufe ta da duka da gudu Habib ya ƙaraso ya janye shi"miye hakan Yaya ka ke
dukan matarka kamar kana dukan ƙato",cikin hasala ya ɗago kansa"ka barni na kashe
ta wannan muguwar dama ban yarda da ita ba tun farkon nu na son Nana da ta nu na
ashe kuwa zargi na ya tabbata ita ta kashe yaron da kanta",wannan magana ta doki
kowa amma banda ni vedio aka kawo aka shiga ga ni kowa ya shiga tashin hankali ana
ma ta tofin Allah tsine,wayar na fizga na kalla kai da gani kasan an yanke ne
tamfatsa wayar na yi da ƙasa"wallahi wannan vedion ba haka yake ba yanke shi akai
kuma ka duba waye ya turo manka kana gani kasan munafirci"kaina ya yo ta tari
gabansa"duk abinda ka ga ni haka yake amma na fi son Nana akan yaron shi yasa na
aikata hakan"tsawa ya daka ma ta"fitar min a gida munafuka mai fuska biyu"cikin
sanyin jiki ta wuce na bita da sauri"wallahi sai dai mu fita tare amma bazaki fita
a gidannan ba"tsayawa ta yi"Nana ni ce fa kashe gudan jinin ki ba ki da maƙiyiyya
sama da ni","nifa ki daina faɗar haka dan ban yarda in ma kin kashe ai ɗanki
ne"yanda haƙiƙan ce yasa aka fuskaci ashe dama lau na ke na warke daga wannan ciwon
sanadin hautsinin da ake yasa ba wanda ya kula hakan har shi kuwa,duk yadda na yi
ita sai da ta wuce ba jimawa ta fito da ƙaramar jaka da jakar ta ta hannu ta wuce
tana ɗaga min hannu,wani irin mahaukacin kuka na saki na faɗi a wurin da gudu na
tashi nai ɓangaren na mu na ɗakko hijabi da jaka ta na fito ina kuka tare ni sukai
duk yanda muje da kowa na gidan naƙi amma naƙi jin maganar Baffa da yanzu ya
tsinkayi abin ya fara min magana na zaro wuƙa nakai kan wuyana"duk wanda ya matso
saina kashe kaina har Habib mai magana ban kula ba na fita a gidan kan a kawo inda
na ke na hau ɗan sahu mota Babban Yaya ya shiga ya biyo mu ina kallon sa amma
saida nasa muka ɓace ma sa gidan Umma na nufa dama Habu ba ya ƙasar bare yasan ina
gidan faɗa ma ta komai na yi nan ta fara min faɗa shiru na yi iba kallon ta"in baki
shiru ba nima zan shiga duniya"shirun ta yi ita da Baban suka shiga bina da nasiha
amma na ƙi ji,duk inda zasu duba ina nake sun duba amma ba nan cikin ƙanƙanin
lokaci gidan suka shiga tashin hankali ni kuma ina gidan Umma ko ruwa na kasa sha.
Gida Aunty Hajara ta wuce ilai kuwa anan ma kaca kaca suka ma ta suka faɗa
ma ta asalin ta ba ta damu ba ta fito ta ɗau wayarta ta kira wata ƙawar ta sukai
magana sannan ta wuce gidan ƙawar ta ta anan ta kwana washegari ta hau jirgi tabar
ƙasar.

*EGYPT*

Tun a washegarin ranar ta sauka taxi ta shiga zuwa wata babbar unguwa a ƙofar wani
gida ta sauka ta danna ƙararrawa sallama wani ƙaramin yaro kyakkyawa shi ya buɗe da
sauri ya faɗa jikinta"Maama"rungume shi ta yi itama"oyoyo My Blood"ta ɗaga shi sama
wata farar mata ce ta ƙaraso wajen tana dariya"tun jiya dama yake kiran ki har zafi
jikin shi ya yi"shigowa ta yi ganin ta ba jaka ta ce"Ƙawata ina kuma kaya ababen
tafiya",murmushi ta yi tana shafa kansa"ba zama nazo yi ba zan ɗauki AL'AMEEN na
mayarwa iyayen sa dama na faɗa miki watarana zai koma",murmushi ta yi"gaskiya ne
ƙawata kin cika jaruma wadda za a yaba miki amma sai gobe zaki wuce ko","a a
jirgin dare zan bi na riga na shigar tun kan na taho","to shike nan muje ki huta"a
ranar matar ta haɗa ma ta komai na yaron zuwa dare ta kaisu airport harda hawayen
ta ta rabu yaron da take matuƙar so.
Washegari da safe ta sauka a gidan ta waɗanda suke cikin takardun nan saida
ta huta yaron ya yi bacci sannan ta shirya shi shigar magaruba ta nufo gida.

Tunda nabar gidan komai ya dame aka rasa kan Babban Yaya, mamakin yanayin abin
kamar wasan kwaikwayo ake,a gidan Umma ma ta gaji da faɗan ta yi shiru amma da
daddare kasa runtsawa na yi kar kuyi zaton tunanin miji nake ko halin da yake
ciki,ina ba wannnan ni tunanin kishiya na ke da fargabar ko a wane hali take.
HHHHHHhhh

Su Hajiya Fulera kuwa komai ya musu dai dai amma me ta biyo dare asalin ɗakin
ta ba kowa saboda kayan ta bincike ko ina tayi ba waɗannan takardu babbar
mahaukaciya ta zama haka ta koma ga ɗan uwanta shima haukar ta kusa saka shi dan
abin ya girgiza shi haka ma ƴaƴan sa da suka sha alƙawura ba yanda suka iya haka
suka zauna suna jimami ita kuwa uwar gayyar sai surutai take.

A ƙofar gida ta tsaya ta sauke mai kayan sa shi dai sai bin ta da kallo yake
dan baya gane me take niyar yi sunkuyawa ta yi a gaban sa"ka t ya cije leɓen
ƙasa"sunana Al'ameen ɗan Habeb da Nana Kawuna sunan sa Habeb Aunty na sunan ta
Khadija Kaka ta sunan Halima Kaka na sunan sa Haruna",jinjina ta masa a ranta tana
cewa"in baka iya magana ba ai ba ace Nana ce ta haifeka ba,gefe ta laɓe"ƙwanƙwasa
ka cewa megadi wajen Habeb kazo in ku ka haɗu saika basa wannan takardar",hakan
kuwa ya yi megadin yana ganin sa jikin sa ya fara rawa kayan ya fito ya kwasa ya sa
yaron a gaba har cikin gida duk suna falo kowa ya yi tagumi Babban Yaya yana kan
kujera a kwance me gadin ya yi sallama yaron na bayan sa kayan ya shigo dasu yana
faɗin Alhaji Habeb ga baƙo ka yi"kowa juyowa ya yi Baffa yana cewa"ina baƙon"dan
yanayin akwatinan kana gani kasan na yaro ne,juyawa ya yi yaga bai shigo ba labulen
ya ɗaga ya kamo hannun sa ya shigo da shi,wani irin tashi tsaye kowa ya yi yana
dafe ƙirji dan kana ganin yaron basai ka tambaya ba,shima kallon su ya shiga yi
yana murmushi kai kace Nana ce tana ƙarama Baffa ne ya matso inda ya ke"yaro waye
kai?",ɗan murmushi ya yi ya sosa wuya kawai Aunty Mama ta kwashe da dariya"ka daina
tambaya fa Baffa wannan ɗan Nana ne kenan dama bai mutu ba to ya akai haka",ƴar
dariya Baffa ya yi"na sa ni Halima bari na ƙara yarda tukunna,ina jinka yaro",nu na
shi yaron ya yi"Ni sunana HABEB amma ana ce min AL'AMEEN kai ne Haruna?",ya faɗa
yana ɗora hannu a jikin sa,dariyar da Baffa bai taɓa yi ba ya sa ki"eh ni ne kasan
ni ne?",kai ya kaɗa"nasan sunan ka dai kuma nasan sunan Baba na da Mama na amma
Babbar Mama ma sunan ta HAJARA"wani irin lumshe ido Babban Yaya yana juya kai da
sauri ya tashi ko takan yaron bai ba ya fita da gudu amma ina tabar ƙofar gidan
tambaya ya yi aka faɗa ma sa lallai ta shigo da mota amma ta fita daga layin,a
wajen ya zauna ya rasa ina zaisa ransa ina ma ya saurari Nana da baiyi wannan
ɗanyen aikin ba yanzu ina zai kai wannan abin kunyar,cikin lokaci ƙalilan ɓangaren
su Mama ya cika da ƴan gidan ansa yaron agaba amma fa duk wanda ya tambaye shi yana
da amsa sai dai baiga Baban nasa ba amma ya yi shiru bai sa ni ba ko baya nan ne
kamar daga sama Habeb ya shigo layin hasko mota da ya yi ne yagan sa zaune a waje
parking ya yi ya fito zuwa inda yake"Yaya lafiya me ka ke anan?",juya kai ya
yi"Habeb yaron nan bai mutu ba ashe yana nan Hajara ta ɓoye shi ban san dalilin ta
nayin hakan ba nayi kuskure Babba yau gashi ba bu ita ba bu Nanan",lumshe ido ya
yi"naji taso mu koma ciki kamin musan ya zamuyi"da ƙyar ya shawo kan sa suka loma
ciki.
A falon ma zama ya yi kawai yana kallon yaron wanda da ga ni kasan yaji gata da
hutu wato kenan duk wata tafiyar da Hajara ke yi sarin turare ba wani sari da take
in ma tana yi to akwai me ma ta duk yadda akai tana zuwa inda ta ɓoye wannan yaron
ne a gaskiya ya cika wawa a shekara biyar ace be taɓa bincikar ina take zuwa
ba,shima yaron ƙare mai kallo ya shiga yi yana kuma kallon Habeb can ya yi murmushi
ya dubi Baffa"Dada wancan da wancan wa da ƙani ne?",shima murmushin ya yi wancan na
zaunen shine Baban ka shi kama na tsayen shine kawun ka dukkan ku sunan ku ɗaya
abin da yasa ba su kula ka ba duka iyayen ka mata biyu sun gudu",da irin mamakin
nan yace"Nana da Maama",kwashewa akai da dariya saboda hausar ma taahi abin dariya
ce da alama dai ya yi gadon zaro zance,tashi ya yi tsaye ya nufe su Habeb ya da fa
ya juyo hannu ya miƙa masa suka gaisa sannan ya juya ga Baban sa ya miƙa masa
hannu,ganin bai bashi ba yasa ya gyaɗa kai ya juya baya"shike nan in ba ka gaisa da
ni ba bazan faɗa ma ka inda suke ba"da sauri Babban Yaya ya taso ya miƙa masa hannu
shima ya basa harda irin jijjigawa nan shi ga babba"to faɗamim ina suke",kai ya
juya ya sosa ƙeya"ta ya jan faɗa ma bayan ban sa ni ba",dariya aka kwashe da ita
ana nu na su shima murmushin ya yi ya janyo yaron ya rungume shi wata ƙaunar na
shiga jikinsa shima yaron rufe ido ya yi yana dariya,sai a sannan Iyyo da Alhaji
Baffa suka shigo dama ankai su dubiya ne asibiti duk abinda ake basa nan da mamaki
suke bin yaron da kallo Iyyo ce ta ce"kai amma wannan ɗan Nana ne ba?",dariya akai
nan Alhaji Baffa ya ce"tw ya akai haka ta kasance?","Hajara ce kawai ta sa ni
Baffa",cewa Baffan mu"to ina ta ke?",Iyyo ta faɗa,"bamu sa ni ba yaron kaɗai ta aje
megadi ya kawo shi a yanzu ba wandw yasan inda take",Aunty Mama ta faɗa kaɗa kai
Iyyo ta yi"Allah sarki Nana shi yasa ta ce ai bincike a bi a hankali ita ba ta
yarda da vedion ba kunji fa ita mara kai ma tasan haka",Gwaggo ce ta miƙe"wa ya ce
muku Nana bata kai garau ta ke tun kwana biyu da dawowarta"cik da mamaki ake kallon
ta bama ya Babban Yaya wanda ya yi kamar zai shige fuskarta"haka batun yake Habib
ya faɗa,salati aka saka Alhaji Baffa ya ce"da alama sai ta ce karku faɗawa kowa"a
tare suka ɗaga Alhaji Baffa ya yi salati yana ce wa"da alama dai Nana ta haifeku
bawai ku ka haifeta ba"dariya aka saka har Baffa nan Baffa ya ce"ya kamata gobe a
nemo Hajara Nana kuwa da kanta za ta dawo in ta samu labarin ƴan biyun tata ta
dawo",kowa ya gamsu da hakan nan yaron ya ciro takardar aljihun sa ya miƙawa Baban
sa"Abbu ga shi inji Maama",karɓa ya yi ya buɗe a fili ya shiga karantawa kamar
haka.

"(Habib gaskiya ne da farko bana son Nana saboda kishin ka da na ke da fari


nabi duk wa ta hanya wadda zan rabaka da ita amma na kasa nasha bin malamai da
bokaye duk akan na rabaku amma ban sami nasara ba sai dai ban san me yasa ba ban
jin shauƙin abinda nake aikatawa ba sai dai nasan zugar ƴan uwana ce ke tasiri
akaina watarana na taɓa zama nayi tunani ta ya za ayi ace ƴan uwa suna ɗora ƴar
uwarsu akan hanyar ɓata dimun da imun sai na ba raina hakan soyayya ce,ranar da
Nana tazo ta nu na tana da ciki sai naji tashin hankali da fa ri harna faɗawa ƴar
uwata nan ta shiga min famfo akan saimun ga bayan cikin,muna cikin magana sai ga
Nana ta warce wayar nan ta fara ma ta maganganu sai naga yayar tawa ta fara tsorata
da ita anan na gane Nana ƙalau take ashe,tana cikin yi wa yayata barazana sai ta
kashe wayar anan Nana yarinya ƙarama ta shiga zayyane min wa ce ce ni ashe ni ba
ƴarsu ba ce shi yasa suke kai ni halaka Nana tana sona ashe tun daga ranar na
yakice komai na riƙi Nana da zuciya ɗaya,har Allah yasa cikin ta ya yi girma
kwatsam saina tsinci kaina da samun barazana akan in ban kashe ɗan da zata haifa ba
su zasu kashe ta,jin haka yasa na zaɓi kashe yaron amma saina kasa saboda ɗan NANA
da BABBAN YAYA ɗana ne,amma dai ga ɗanka nan fatan komin daran daɗewa zaka
sauwaƙemin kar in na yawo da auren ka akaina saboda kwasar zunubi ni marainiya ce
bana da kowa sai dai Abba kan ya rasu ya haɗa ni da abubuwan da zanyi ingantacciyar
rayuwa ta hannun Nana nasan sanda zaka sami saƙo na nayi daɗe da yin nisa dakai,a
ɓangarena na yiwa Al'ameen ɗaki guda ka duba.
Fatan alkhairi a gareku duka fatan zaku kulamin da My Son Habib don ina
ƙaunar sa fiye da kowa a duniya sai anjima
HAJARA
Maama AL'AMEEN")

UMMU SADDIQ CE🌹🌹🌹


🌈🌈🌈
🌈🌈
🌈

BABAN YAYA

Babban Yaya Free ne amma me so ya biyo ni Pc in sa a group don shagalin Nana


na buƙatar comments.
08146711395

39

Jin wannan saƙo na ta ya karyawa kowa zuciya Al'ameen kuwa ya lafe a jikin Baban sa
duk ba gane me ake cewa ya yi ba shiru ne ya biyo baya kowa ya kasa magana dama su
ya Hasiya basu ta fi ba itace ta ɗau yaron zuwa ɗakin Aunty Mama dama shi ba shi da
damuwa tana kai shi ya kwanta sai bacci,sannan ta dawo"maganar gaskiya munyi babban
kuskure a al amarin Nana da Hajara akwai alamar tambaya Nana akwai abinda yasa ta
ɓoye ta warke sannan Hajara ba ta faɗi waye yasa ta ta yi kisan kai ba sannan ta ya
ta shirya wannan dabara har shekara biyar ba tare kowa ya ga ne ba akwai sarƙaƙiya
tabbas","hakane Ya Hasiya ya kamata dai a nemo su"cewar Ya Mabaruka"anan dai Alhaji
Baffa yace"kowa yaje ya kwanta abarwa gobe a dudduba a ga ni a ina za a sa mo su".

Ranar Babban Yaya kasa runtsawa ya yi sai zagaye ɗaki yake yana kallon gidan sa da
ya zama kango sakamakon kuskuren sa ta ya akai ya yi haka yana zaune da Hajara
shekara takwas ya kamata ace ko ɗan ta kashe ya nemi dalilin ta nayin hakan,haka
dai ya kwana sai asuba sannan ya kwanta.
*****
Ina tsaka da shan tea da safe nagan number Aunty Hajara tana kira na da saurin na
ɗauka na shige ɗaki"Aunty Hajara dan Allah kina ina zan zo wajen ki nima bana
gidan","me ki ka ce Nana ba kya nan kuma ina ki ka je?"turo baki na yi"bayan ke ce
ki ka fara fita shine nima na fita na bar musu gidan su ci kayan su",ƴar dariya ta
yi"ba ki da dama Nana kina ina nazo na ɗauke ki",da sauri na faɗa ma ta,tace na
fito sanɗa na yi Umma na ɗaki na fita ba ta sa ni ba can kan kwana na tsaya sai
gata da mota sabuwa mai ɗan karan kyau shiga na yi na kalle ta naga tanabfarin ciki
ƴar dariya na yi"wallahi Aunty Hajara kin talauta Hajiya Fulera kinzo kina facaka
da kuɗin ta",dariya ta yi ta tuƙa motar muka bar layin gidan na ta ma ya yi kyau
sosai anan muka wuni cir da yamma tace na koma na ce bana zuwa konina a nan zan ta
zama"to wai Nana haka zamu zauna da aure akan mu","eh mana ba ahaka suke so ba","to
ɗanki kuma wazai kula da shi",da mamaki na dube ta"wane ɗan kuma?",murmushi ta
yi"ai jaririn mu bai mutuba yanzu haka yana gida na kaishi tun jiya da
magaruba",wani kallon ta maida ni mahaukaciya na ma ta,ƴar dariya ta yi ta ɗakko
wayarta ta kunna wani vedio saida ta nu nan detail sannan ta kunna min tsaye na
miƙe cike da tashin hankali hannuna na rawa na ɗauki wayar wani irin ruwan hawaye
ne ke zuba a idona jikin ta na faɗa na fashe kuka rungume ni ta yi itama tana
hawaye"ki yi haƙuri Nana ban barki kin shayar da ɗanki ba na cuceki",wata irin
zuciya ce tazo min wuya ta shi na yi ina go ge hawayen"waye ya miki wancan
sharrin?","ba sharri ba ne haka abin yake kawai dai an canja abin ne amma kinga na
asalin",kunna min ta yi na kalla duban ta na yi ya akai haka ta kasance ba ki faɗa
min ba suwaye suka saka ki?",kama hannuna ta yi na zauna sannan ta ce"cikin ki na
wata takwas watarana na je gida sai na tarar da Abba da baƙi duk baƙuwar fuska amma
abin mamakin kin a ganin su masu kuɗi ne sai dai suna cikin shiga kamar marasa
ƙarfi ban daɗe da zama ba aka ce nazo inji Abba wallahi Nana saida gaba na ya faɗi
da zan gudu ne saina yi wani tunani in ma ban je ba koma miye za a sa wani ya yi
sannan ya cutar da ke kawai sai naje tasa ni sukai da barazana zasu kashe Abba zasu
kashe Umma haka dai sannan suka ce in ban kashe ɗan da zaki haifa ba to su zasu
kashe ki ba zasu kuma fasa ba sanin halin Abba da abinda ki ka nu na min yasa nasan
zasu yi abinda suka ce shi yasa sanda ki ka fara naƙuda ban faɗawa kowa ba sai na
kai ki asibiti ni ɗaya da farko haihuwar ta gagara sai daga baya sanda aka ba ni
jaririn da ki ka haifa take naji kamar ni na haife shi rasa ya zanyi nabyi ga wasu
mutane kamar likitoci da nurses suna ta kallo na duk sai na gigice,wani ɗaki na
faɗa ban sa ni ba ashe wata mata ce a ciki matar me kuɗi ce shi yasa aka ware ma ta
ɗaki daban,ga ni na da tai a gigice saita daina kukan da take tace min"ƙawata ya
haka zaki faɗi fa",kasa magana na yi kawai na fashe da kuka"da ƙyar ta samu ta taso
da nata ɗan a hannun ta tazo kusa da ni hawaye ta ke itama tana leƙa ɗan hannuna
sai taga yana motsi sannan ta kalli na ta"kinga fa nawa ɗan baya da rai ma ke naki
yana da rai amma ki ke kuka haka",dakatar da ita na yi"ba ɗana ba ne ɗan kishiyata
ne ance in ban kashe shi ba za a kashe ta kuma naga masu aikata hakan a asibitin
nan",dakatar da kukan ta yi cikin zaro ido gefe da gefe ta kalla sannan tai ma za
ta karɓi ɗan hannun nawa ta ban na ta,akan hannuna ta ɗora na ta"kimin alƙawari
zakiwa ɗana sutura ni kuma zan reni naki cikin aminci amma a yanzu ina da ƴar
matsala mijina ya rasu ga number waya ta ki kira ni sai muyi magana",kallon ta na
shiga yi ba wai na ƙin yarda da ita ba ne a a na mamakin abinda take niyar yi
ne,kai ta ɗaga min tana murmushi"kije da ɗan a haka ana cewa ya mutu za a ce a
wannan ɗakin da ki ka shigo ne ki ka kashe shin tunda kinga ba wanda yasan da mutum
a ciki"kai na ɗaga na fito,ta wata ƙofa na shiga inda ki ke na aje jaririn sannan
na fito na kira gida sanda suka zo nurse suka duba sai suka ga yaron mutu shine aka
ba mu gawar Nana akan wannan yaron na koyi wankan gawa in zaki lura ni na masa
komai,sanda akai kwana uku sai na kira wannan matar tana ɗagawa ta fara dariya
ajiyar zuciya na sauke sannan na koma can ƙuryar ɗaki ina ce wa"ƙawata ina
ɗana","gashi nan ƙawata sai lan karan kuka",murmushi na yi"ai dole ya yi kuka uwar
sa fitinanniya ce"ƴar dariya ta yi tana cewa"to kuwa gashi nan yana yi,dama nace
miki ina da matsala ɗaya ko ni a ƙasar Egypt nake mijina ba bahaushe ba ne ɗan can
ne daga karatu na aure shi muna cikin rufin asiri mai kuɗi ne sosai bayan ya mutu
sai dangin sa suka zo suka ƙwace komai a hannuna bayan haka da wani ɗan lokaci sai
ga ciki ya bayyanar min saina dawo nan gida harna na haihu a yanzu ina da gida acan
sai dai ki ɗau nauyi na na ƙara komawa can na reni ɗanki",ajiyar zuciya na yi cikin
farin ciki nacean gama kiban address nazo"ba ni ta yi a ranar da yamma na fita naje
inda ta ke nayi murna da naga yaron cikin ƙoshin lafiya kuɗi na tura ma ta account
sannan na ba ta wasu wallahi ban ma san nawa ba ne,sannan ta ce na sawa yaron suna
shine nasa masa HABIB amma tanance ma sa Al'ameen haka ta yarda da abinda nace
sannan taban kwatancen inda ta ke a can,na daɗe a wajenta sannan na dawo gida in
kin lura ko sati biyu baki yi da haihuwa ba nace zan fara kasuwancin turare Habib
ya amince zan na zuwa Misra da Sudan sarin turaren shine nake zuwa duk wata ko wata
biyu a haka muka re ni Al'ameen har Allah ya kawo ranar da Hajiya Fulera tazo zata
miki wannan abin na shiga shine sukai min haka dan ɗaukar fansa kin san maganar ki
ta tabbata da naje gidan korata sukai kuwa",hawayen fuskata na share ina dariya"an
gaishe da uwar Al'ameen ni Habib ba ɗana ba ne ɗanki ne na bar miki duniya da
lahira"saurin kallo na ta yi"da gaske kimke dan Allah",hannun ta na kama"da gaske
nake wallahi na bar miki",shiru ta yi"to Nana har ina murna ni da zama a sake
ni...","WA ZAI SAKE KIN?",muka ji maganar sa akan mu.

: Da sauri muka miƙe muna hangame ba ki ƙarasowa ya yi ciki hannun sa sanye a


aljihu ya yi kyau sosai cikin ƙana nan kaya zama ya yi ya harɗe ƙafar sa yana
kallon mu yana murmushi"me kuka ɗauke ke ni ne wai?ko in ce kallon me ku ke min
ne?"kallon juna mukai sannan muka haɗe rai a tare muka nufi ɗaki murmushi ya yi
yana gyara zaman sa ya ciro wayar sa ya yi kira ba jimawa aka ɗaga"in baku ganni ba
karku da mu abokina nakai asibiti ba shi da lafiya",yana faɗar haka ya kashe ya
ajiye shiru shiru ba mu fito ba har dare ya yi.
Kallon ta na yi"Aunty Hajara kije mana kin gan shi can fa anya kuwa ma yana
cin abinci",hararata ta yi kije kai ni dai ba zanje ba tunda ya mare ni har wani
riƙe shi ake wai zai da ke ni kamar yana faɗa da ƙato ɗan uwan sa"kwashewa na yi da
dariya sannan na miƙe to bari nidai na kwanta da safe ma haɗu"tasowa ta yi daga
gadon please mana Nana kije dan Allah ko kiss ki masa ya rage zafi",ɓoye dariya na
yi"ai wannan kin fi ni iyawa kefa tsogon hannu ce"saurin sakkowa ta yi na shige
toilet ina dariya tsayawa ta yi" kuma akwai riga a ciki ki saka ta ki fito kije
sama ma masa me zaici"komawa ta yi ta kwanta dama maganin mura ta sha nan da nan
tai bacci koda na fito ina ta magana naji shiru na zata da wasa ta ke ashe da gaske
ne rigar dana sa na kalla ai wannan tsirara ce tabɗi na gyaɗa kai turare mai ƙamshi
na jaka ta na saka sannan nasa hijabi na fito,yana kwance kan kujerar nazo na tsaya
akan sa kun san ni ba hankali ɗaka masa duka na yi hannun kan fuskar sa ya janye
yana bi na da kallo a hijabi na ke amma ya ƙurawa ƙirjina da na turo ido,ƙara gan
tsarewa na yi"wai dan Allah Babban Yaya ba ka ce baka son mu ba"murmushi ya yi a
cikin ransa sannan ya tashi ya zauna yana taune leɓe,juyawa na yi zanyi tafiya ta
ya fizgo ni na faɗo jikin sa matseni ya yi ya ɗago fuskata yana gewayeta da
idanuwan sa,cikin sanyin murya ya fara magana"dama zaki iya tafiya ba bisa kuskure
ba ki barni Nana kinsan dai bazan iya rayuwa ba ba bu ke me yasa zaki min
haka",hawaye ne ya zubo min na kwantar da kaina a ƙirjin sa"ba kai ne ina cewa
karka koreta ba saida ka koreta ni kuma nasan ƙarya ake ma ta dama","to kiyi haƙuri
itama haƙurin nazo ba ta ku yafe min","ni na yafe maka saura ita ta yafe maka",ƙara
rungume ni ya yi yana ajiyar zuciya"rabona da abinci tun randa ku ka daka min
barkono"ɗagowa na yi ina dariya"to basai kana shan sa ba harka ƙoshi",baki ya
kama"au kashe ni zakuyi kenan",ɗaga sgi nayi ina murmushi na zare hijabin"mun insa
mu kar Babban Yaya bari na sama ma ka abinda zaka ci",na wuce shi ina sauya tafiya
bayana yabi da kallo ina kallon sa,ina shiga kitchen ɗin ya biyo ni,ji nayi kawai
an jawo ni ba ya an haɗa ni bango runtse ido na yi dan nasan yau bakina zaici uban
sa kafin na gama tunani naji saukar bakin sa a nawa haka hannayen sa na zarya a
ciki rigata abincin da ba a nema ba kenan daga ƙarshe sai tea ya sha dama ta aje
boga sai ita ya ci anan falo muka kwana asubar fari ya tashi ina nan naɗe a jikin
sa kwantar da ni ya yi ya nufi ƙofar ɗakin da ya ga mun shiga gadon ya kalla ya
kaɗa kai yana wucewa toilet da ya fito sallah ya yi sannan akai assalatu tashi na
ya yi na wuce sannan shi ya fita dan jikin gidan akwai masallaci.
Umma koda ba ta gan ni ba ba ta damu ba tasan halina sarai bazanyi wani abu da
bai da ce ba.

Saida gari ya yi haske sannan ya dawo muna falo da sallama ya shigo muka
bishi da kallo zama ya yi a kujera saboda neman tsokana sai na dube shi na
ce"Babban Yaya ina kwana ta shi lafiya"kallona ya yi na tashi lafiya mana ko kinga
wani abu dabai kwana lafiya ba ajikina",ɓoye dariya Aunty Hajara ta yi tana kaɗa
kai"a a Babban Yaya daga tambaya","na kwana lafiya amma in hakan ki ke son sa ni
bari na nuna miki" tasowa ya yi da gudu na ɓuya a bayan ta shima yazo gaban ta ya
tsaya mamaki yake yanda ko kallon sa batai ba,ya maida hankali kanta na zame na
fece kitchen a raina ina Allah yasa ta haƙura mu koma gidan mu inga Al'ameen naga
da wa yake kama,hannu yasa ya ɗago fuskarta"haba Hajara ki kalle ni mana",ɗagowa ta
yi tana hararar sa,murmushi ya yi"kiyi haƙuri ki yafe min please",kai kawai ta
ɗaga"na haƙura ai tuni kodan ɗanmu me zaisa in na fushi dakai bayan kayi abu ne a
rashin sa ni ba bu sauran ɓacin rai tattare da ni da ace nayi abin da aka ce ne
shine zan dauwama a ɓacin rai",hannun ta ya kama"to mu koma gida kinga kowa na
cikin damuwa","ai dama zamu koma karyawa kawai zamuyi"fitowa na yi ina ta fi da
rawa,bina sukai da kallo kawai waya ta na ɗakko na saita camera basu sa ni kiɗa na
kunna na fara tiƙa rawa da sauri ta fito a kichen ta shiga ta ya ni shi kuma yana
zaune yana dariya saida na gaji sannan na zauna ina dariya"kai Babban Yaya ina
farin ciki wallahi ɗan mu bai mutu ba ga Aunty Hajara ta nutsu ta ga ne masu
cutarta shike nan sai muyi rayuwar farin ciki",da sauri ta tari numfashi na"ban
baki wani labari ba Nana Yaya ce ta raka ni wajen wa ni Boka dan nace yaban maganin
da zan koreki daga gida na shine yace wai sai na kawo masa gashin hammatar ki dana
kanki sannan da gashin gwaiwar jaki",kwashewa mukai da dariya"jaki jaki dai namu
ƙasar Hausa to ke me ki ka ce ma sa"ai ni a sannan na fara dawowa hayyacina kuma a
gidan uban wa ya taɓa ganin jaki da gashi a gwiwa banda rainin hankali,kawai sai
nace ai ke hammatar ki ba ta gashi kan ki kuma kamar gwaiwar amale ya ke shi jaki
me gashi a gwiwa ai ba a hallice shi ba tukunna"shi kanshi Bokan dariya ya saka dan
dama wani abun suna faɗa ne kawai dan su miki wayo in ki ka ce baki sanshi ba sai
ace ki ba da kuɗi a sa aljani ya samo miki",dariya muka shiga yi kai ta
girgiza"Allah ya yafe mana dai Nana amma Yaya ta cuce ni",tasowa na yi zuwa inda ta
ke"karki damu fa itace da wahala ita kinsan sirrin ta ki bari zan faɗa miki"kallona
Babban Yaya ya yi"nima zoki faɗamin sirrin me ki ke ta ɓoyewa ne amma kafin nan
Hajara ta ya kai ki ka ɓoye Al'ameen?",kafin ta yi magana na fara zayyano ma sa
yadda akai kamar a gaba na akai ba labari aka ba ni ba jiya jiyannan,ya sha mamaki
sosai kuma ya jinjina ma ta ganin yana bina da kallo yasa na ce"sai mun koma gida
yanzu inna fara faɗa maka sai mu wani anan",kai ya ɗaga sannan muaka karya muka
kulle gida muka shiga motar da ya zo da yazo da ita"Aunty Hajara kinga kin mana
guest house",dariya ta yi"lallai kam zamu sauya ma sa fasali da kayan ciki muna
zuwa kawai mu huta",tafawa mukai shi dai yana tuƙin sa,koda muka isa an sha mamakin
ganin mu tare kowa kan mu ya yo ana ba ta haƙuri da gudu ya fito daga ɗaki yana
sanye da jeans blue da jar riga ƴar ƙarama gashin kan sa yasha gyara kurɗowa ya yi
zuwa inda take ya rungume ta "Maama"lumshe ido tayi ta ɗauke shi suna dariya hancin
ta ya ja"Maama na",goshin ta ta ɗora akan nasa"Al'ameenn ɗina"suka kwashe da
dariya,da mamaki nake kallon yaron kamar mu ɗaya wayata na ciro na shiga musu hoto
idon sa ne ya sauka a kaina murmushi ya yi"Nana"ya faɗa a bazata saida kowa ya juyo
dan mamaki,ƙarasowa na yi"kasan ni ne?",kai ya ɗaga"kina zuwa in ina bacci kina ba
ni madara kince kuma sunan ki Nana",cikin tausayi Hajara ta rungume shi"am sorry My
Love duk laifina ne ni na rabaka da maman ka ka yi min afuwa"hawayen fuskar ta ya
shiga sharewa sai ga nashi sharr,rungumeshi ta yi sosai ta fashe da kuka,zuciyar
kowa saida ta karye nan Alhaji Baffa ya fara tambayar ya akai haka ta kasance,da
kanta ta shiga faɗa musu sun sha mamaki sosai nan akaita ma ta godiya sannan muka
shige ciki sai yamma sannan muka koma ɓangaren mu an gyara ko ina ɗakin kusa da ita
ta buɗe saiga kayan yara na wasa da na sawa kallon ta na yi"Maama Al'ameen wannan
fa duk muna ina akai haka?",dariya ta yi"ai ba zaki kura ba ke da ba komai ki ke
kalla ba ke kawai ta mijnki ki ke",fuska na rufe dan naji kunya wayata na kunna
muka shiga ciki naita ɗaukar su ina turawa ƴan gidan su saida aka kira sallah
sannan mukanfito muka barshi yana ta wasa"Nana kin san me?","yazan san me ni ba ƴar
akuya ba",kwashewa ta yi da dariya"kefa baki da kirki wallahi",nima dariyar na
yi"to ai lefin ki ne Aunty Hajara me fa ki ka ce","to na ji yanzu mace zaki haifo
min sannan ki haifi na ki",kai na ɗaga"tabb ai in na haifo mace tawace ke namiji
zan ƙara haifo miki kuyi ta dambe suna aure matan su suna hararar ki",tsabar dariya
saida ta zauna a wurin"gaskiya Nana yarinya ce ke","to da na mana kawai dan kin
tunzura ni ne nasa akai min auren wuri ni da aka ce sai na digire zanyi aure",tashi
ta yi"ke bana son iskanci a ina na tunzura kin"dariya na sheƙe da ita"kin manta
ranar da ƙawayen ki suka zo ana gobe bikin naje ɓangaren ki ke zagina kina cewa ko
ƙirgen dangin bai nuna ba nake son maza wurin ma kinsan ko pencil bazai wuce
ba",baki ta rufe tana dariya"ke Nana kin shiga uku kalli yadda ki ke faɗin abin
kaman shekara shida akai ba kamar yau a kai","to ai ni matsalata kenan bana manta
abin arziƙi ma bare na tsiya","to Allah ya shiryeki amma kina mantuwa
wallahi",wucewa na yi saida na je ƙofar ɗaki sannan na juyo"na fa haɗa miki
kitimurmura zaki sha kira daga gidan ku",zaro ido ta yi"me ki ka min kuma",hannu na
kaɗa ma ta agefen kunne na shige ɗaki na kulle,tunani ta shiga yi amma ba ta
fahimci komai ba gaka ta wuce ɗaki dan tai sallah itama.
: Bayan Sallar isha duk munyi wanka mun sha kwalliya munabfalo har Al'ameen sai
gashi ya shigo da sauri yaron ya sauka ya rungumo shi"oyoyo Abbu"aje kayan hannun
sa ya yi ya ɗauke shi sama yana juya shi dariya yaron ya yi ciki ya ƙaraso yana
sallama sannu da zuwa muka masa kallon mu ya tsaya yi dan mun birge shi sosai,zama
ya yi yana ɗaukar sa"kansa ya shafa ubana beyi bacci ba",kai ya ɗaga kawai yana
kallona,"daina kallo na kar ace ni na hanaka bacci"dariya ta yi"kai Nana ya da
tsarguwa haka ba ke ki ke ta shafa mai kai ba",baki na taɓe"nima dai zan haifi ƴata
na huta",dariya ya yi"to shike nan muna jiranki"ta faɗa tana dariya tare muka ci
abinci sannan ta ɗauki ɗanta takai shi ya kwanta kayan ciye ciye da ya kawo muka
haɗa a ƙasa kan capet muka zauna ti tsiye ni ya yi saina faɗa ma sa me ke faruwa
gyara zama na yi"kuma duk wanda ya gyangyaɗa saina watsa mai ruwa",dariya sukai
yana dungure min kai.
"A yanda Abba ya faɗamin bayan ya bar gida yana iya tuna komai amma ya kasa
komawa da fari ya yi wani uban gida mai arziƙi a Niger mutumin har masa na antu
gare shi da jiragen sama sanda suka haɗu a basu san juna ba amma daga haɗuwar su ta
kwanaki sai ya zama tamkar ƙanin sa wannan mutumi na ƙaunar Abba tamkar ransa dan
daga baya in an tambayeshi waye wannan sai yace ƙanin sa ne uwar su ɗaya uban su
ɗaya,shi Alhajin yana da ƴan uwa mazauna Marocco,Chadi da Gabia sanda Alhajin ke
yaɗa cewa Ƙanin sa labari yaje musu ashe abin da bai sa ni ba dama sun saka ido ne
a akan dukiyar tuntuni,su waɗannan ƴan uwa nasa ba mahaifiyarsu ɗaya ba ashe shi
Alhajin dukiyar tasa ta mamar sa ce dan ita ƴar sarki ce kuma bayan ta haife shi da
shekaru harma ya girma yasan komai sannan ta rasu to dama Baban sa ya rigata rasuwa
kunga bamai gadon ta sai ɗanta,su kuma waɗannan ƴan uwa nasa da ganin irin dukiyar
daya mallaja sai hankalin su ya tashi suka haa metting akan zasu kashe shi sai ɗaya
ya ce a a in suka kashe shi za ace su ne su bari sai an kwana biyu tukunna,sun
gamsu da shawarar sa dan haka sai suka kauda kai daga kansa sukai kamarbasu san
yanabda dukiya ba suka cigaba da zama lafiya,da yake Alhaji mai tsawon rai ne duk
sanda suka shirya kashe shi sai ya tsallake har Allah yasa ya kawo girma bai taɓa
aure ba shi kuma tasa ƙaddarar kenan sai dai shi mutum ne mai ibada ga kyautatawa
na ƙasa da shi ana haka sai Abba ya fara rashin lafiya sai ya fitar da shi ƙasar
waje aka duba shi sai aka ce ƙaba ce,nan Alhaji yasa aka mai aiki ya zauna da shi
har ya warke sannan suka dawo gida ba bu jimawa dawowar su Alhaji ya fara rashin
lafiya saidai kullum ana kawo ma sa takardu yasa hannu yana sawa n amma baisan na
miye ba,kwana kusa sai Alhaji ya rasu hankalin Abba ya yi mugun tashi bayan kwana
biyu da mutuwar sa sai ga hukuma wai ana zargin shi ya kashe shi dama ya yi
tsammanin haka bai damu ba ya bisu sai dai basu kai shi police station ba sai suka
kaishi wani wuri suka ɓoye shi ya daɗe sosai dan yace zai kai shekara sai kwatsam
mai bashi abinci yazo yake ce ma sa bafa ƴan sanda ba ne waɗanda suka kamoshi anzo
an ɓoyeshi ne dan su tattara dukiyar da Alhajin ya bari sannan su sake shi tofa
dukiya an duba ba bu komai Alhaji ya kyautar da ita kuma kai ya ba wa to yau sunce
zasu kashe ka ai dole a basu,sai dai shi mai basa abinci yace kuncesa yazo yi ya
gudu kar ya damu da dukiya ya tsira da ransa tukunna watarana Allah ya ba shi wa
ta,ya gamsu da maganar sa kuɗi mutumin ya bashi sannan ya sake shi ya gudu ta
jirgin ruwa Abba bai samu kanshi a ko ina ba sai Algeria da farko a bakin kasuwa
yake zama sai ya yi ubangida shine kakan Habib Mama ta bamu labarin sanadin rabuwar
aubti haka Abba ya faɗa min amma sanadin kuɗin Abban ba wancan kuɗin ba ne shi
Baban Mama in yaro ya shekara yana mai aiki sai ya ware shi ya bashi shago da
jari,to Abban ma haka ya masa sai dai shi Abba yana bashi jari sai wani bawan Alkah
da suke tare yazo ya same shi da maganar ya bashi bashin kuɗin da aka basa zaisa
wani jari amma nasa kuɗin bai kai ba kuma abin da riba,ba tare da shakku ba Abba ya
ɗau kuɗi duka ya ba mutumin shi kuma si ya fara kasa dankali anan sukai faɗa da
Baban Mama har yace sai ya dawo masa da abin da ya bashi mutane saida suka shiga
maganar akace ina ruwan sa ai ya bashi in ma zubarwa ya yi bashi da haƙƙin magana
akai da wannan batu ya rabu Abba bayan ɗab lokaci shagon Abba ya zama na kayan gona
ana ciniki sosai da sosai ana ƙara wani lokaci ba sai Abba ya ƙara shago ba har
guda biyu kuma siya bawai haya ba,kwatsam saiga kuma wannan mutumin ya dawo masa da
kuɗin sa da riba ninki biyar na kuɗin daya ba shi anan fa Abba ya gawurta a kasuwa
ya zama na ɗaya to wannan shine sanadin faɗan su da Baban Mama har ya
rabasu,watarana kawai sai yaji yana son barin wajen sai kawai ya kwashe kayan sa
yabar garin ya koma Ghana,sanda Abba ya koma Ghana sai ya haɗu da abokan kasuwancin
Alhajin nan take kuwa suka nu na masa karamci aka nema ma sa shaguna har guda shida
nan ya fara kasuwanci abin mamaki nan da nan sai ya haɓaka ya yi ƙaurin suna.
Waɗannan mutane da suka zo dan kashe shi suka ga bayanan sai mai bashi abinci
a kwance cikin jini asibiti aka kaishi bayan ya farfaɗo sai yake faɗa musu ai
wannan mutumin ya gudu sunyi farin ciki da fari saida suka koma akan mahukunta su
basu dukiyar shi wancan ya gudu sai suka ƙi akace ko bayan shekara ɗari ne in ya
dawo zasu bashi abin sa,ba yanda suka iya haka suka tafi nan suka shiga neman sa
gari gari gashi basu san ma ɗan asalin ina ba ne da suka rasa shi sai suka haƙura a
dole suna jiran ranar ganin sa ai in ya shahara dole za a nuna shi a duniya.
Zaman Abba a Ghana ya zama me kuɗi na gaske shekarar sa biyar ya dawo
Nigeria da zama sai ya sauka a garin Katsina kan kace me ai ya ƙara shahara fiye da
baya,anan ne Abba ya yi aure har mata huɗu zaku ji su ukun ta ya akai ya aure
su,amma Hajiya Fulera ya aure ta ne sanadiyar yayanta wanda suka haɗu a Ghana sanda
Abba ya fara kasuwanci a Ghana a duniyar kasuwar yayanta shine babba amma da Abba
yazo saibya doke shi ya yi niyar kassara Abba ko ya kashe shi amma sai ya gasa ya
haɗa metting da sauran ƴan kasuwar dake jin haushin sa,akwai wani babban ɗan kasuwa
shi baya zama sai yaran sa dan shi a Marocco yake,to shine yake faa musu kar suyi
komai sai ya shigo to sai kuma Abba ma yabar kasuwar sai suka ɗauka aikin su da
suka wani boka ya musu shine ya ci,auran Hajiya Fulera sai Abba yake nu na ma ta
bashi da wayo shibyasa ta shige jikin sa har ya gane alaƙatar da wannan ɗan kasuwan
da ya yi niyyar sakin ta sai kuma kawai ya barta dan yaransu biyu,kasuwan ci ne ya
kai Abba Niger nan wani babban lawyer na Alhajin nan ya ganshi bibiyar sa sukai ta
yi har suka gano inda yake kwatsam ya dawo Nigeria sai gasu sunzo wannan dukiyar
suka kawo baiyi niyyar karɓa amma da ya karanta wasiyyar Alhajin nan sai ya
karɓa,tashin hankali kenan dan labari yajewa ƴan uwan Alhaji anga wannan yaron an
bashi dukiyar kuma,nan suka shiga nemansa lungu da saƙo ana suka samu mutanen da
suka zauna dashi kuma wannan mutumin na Maracco yana da ga cikin ƴan uwan Alhaji
amma baisan wancan case ɗin ma da Abban ba ne,shine yayan Hajiya Fulera ya haɗe kai
dasu nan suka shiga narka masa dukiya akan ya kula musu da duk motsin sa.
Sanda Abba ya ganmu ya yi murna sosai amma matarsa Hajiya Fulera ji tayi kamar
tabyi bindiga dan haushi ,Allah sarki Abba rashin lafiya ce ta kama shi aka koma
wancan asibitin da aka taɓa masa wannan aikin anan sukai masa allurar nan ba ta
fara tasiri ba sai da ya dawo da wata guda Abba yasha wahala jikin sa na ciwo fatar
sa Abba yana jinsa kamar me sikila baya bacci baya iya cin abinci amma duk da haka
yana ɓoyewa yana nuna ba komai a wannan rintsi ne Abba yaje metting na ƴan kasuwa
ta duniya ransa ya yi masifar ɓaci da jin wasu tsare tsare da suke zayyana masa
kawai yana buɗar baki sai ya ce ai shi dukiyar ya barwa jikin sa wanda bama a auri
uwarsa ba bare a haife shi,abin ya ƙona musu rai tunda manyan alƙalai ne na duniya
a wajen takardar shaidar mallaka ya karɓa ya rattaba hannu ɗaukacin dukiyar wajen
Alhaji ya barwa jikin sa,sannan ya dawo gida ya kasa mana iya wadda ta rage a wajen
sa sannan Hajiya Fulera ko allura bai ba ta ba dan da bakin ta a masa allurar gubar
nan kuma ita tasan wa yake burin a aura a haifi wannan ɗa dan tasan ta lalatawa
Aunty Hajara mahaifarta,sauran matan Abba duk ya aure su ne ta hanyar hanya su
Hajiya Salma kuwa ƙawar sirri ce ta ƙawarta shi yasa suka auri miji ɗaya da sun ɗau
duniya da zafi amma sai Allah yasa sukai laushi ta ruwan sanyi,Habeb yasan wannan
bayanin kamin kai amma baisan fuskokin mutanen ba,saceni da akai anyi wani abu a
murɗe,ƴar ɗan uwan Alhaji mai gidan Abba itace ta sace ni akan tana son Habeb shi
kuma baya sonta shine zuwan sa nan da auren Ya Hadiza da ya koma sai ta ga ni anan
yake kora ta ma ta harda nu na ma ta hoto na ita kuma saita fara bincike akaina
bayan kwanaki sai take faɗawa Abban ta anan ya gano wace ni zugata ya shiga yi ya
haɗata da wasu criminal mata nan aka sato ma ta ni a ganin ta ita ta sato ni shi
kuma baban ta yana ganin shi ya sato ni,ni kuma ina ganin ni na sato su dan ni na
tura musu address ɗin inda nake sanda suka kai ni na shiga ran matar da ta sato ni
sai waccan ta fuskanci haka saita raba mu shine ta gana min wannan azabar da
cocaine ni kuma na haɗata faɗa da uban ta yanda ko zai haɗiye ƙur ani bazata yarda
dashi dan nace mata ba shi ya haifeta ba kuma zai kashe ta ne shine taje ta kwashe
dukiyar sa kaf ta gudu shi kuma ya yi mutuwar ɓarin jiki na gama da wannan kenan
ɗaya a cikin mutane sha huɗu Hajiya Fulera itace ta biyu na talauta yayanta shine
target ɗina na gaba zan tona masa asiri sannan dukiyar sa sadaka ce a gidan marayu
dan yasa hannu a takardar da nasa aka kai masa office da sunan ta ƴarin tsaro ce wa
dukiyar sa manyan ƴan iskan kuma sanin Al'ameen zaisa sunkawo kansu ba wanda zamu
haɗa da hukuma face su ɗanɗani azabar da Abba ya ɗan ɗana,kayi haƙuri Babban Yaya
ba a baya ba har yanzu zan ba da raina akan Abba da kuma Al'ameen dan Aunty Hajara
a makance aka saka ta a cikin lamarin batare da sun faɗa ma ta tushen
komai,ƙazantar dake Abban su da ƴaƴan sa mata da ƙanwarsa ta ɓaci shi ba ya zina a
waje sai a cikin gida ashsha yaso ya yi wa Aunty Hajara dan yasan ba shi ya haifeta
ba amma Allah ya kareta gata nan ta faɗa ma ka wace ita ni dai kaji iya ba tuna"ina
kaiwa nan na miƙe na shige ɗaki a ƙasa na faɗi na rushe da kuka mai tada
hankali,haka suma ina jiyo su Aunty Hajara na yi shi kuma ya yi shiru zuciyar sa
kamar ana hura wuta.
: Kasa ta shi ya yi da ƙyar ta lallaɓa shi suka shiga ɗaki amma ita tafi shi ɓacin
rai dan ta daɗe da sa ni amma ta yi alƙawarin gobe saita je gida ta tona ma Abban
asiri a gaban Umma koma me zai faru ya faru.

UMMU SADDIQ CE🌹🌹🌹🌈🌈🌈


🌈🌈
🌈

BABAN YAYA
Babban Yaya Free ne amma me so ya biyo ni Pc in sa a group don shagalin Nana
na buƙatar comments.
08146711395

40

Ranar kwana ya yi kai kukan sa ga Allah,washegari bai fita ba ni kuma ban fito
ba ina gado,motsi naji na ɗago kaina ina kwance a gado Al'ameen ke tsaye a bakin
ƙofa yana leƙowa"taho mana Babana",shigowa ya yi kamar mai jin tsoro har bakin
gadon ya tsaya yana murza"morning Nana",dariya ce ta kama ni kamar ahi ya raɗa min
sunan"morning Al'ameen ina Maama na ka?","ta fita da fushi tana sauri",da hanzari
na hantsilo daga gadon"da fushi kuma Abbu fa?","yana ɗaki a kwance",agogo na kalla
goma saura hannun sa na kama na ɗora shi a kan gado game na kunna masa a waya ta
nan ya fara dariya"yauwa My Boy yi game ina zuwa"kai ya kaɗa"thanks Nana"murmushi
na yi da sauri na fito sanin ba ta nan na tura ƙofar ɗakin da sallama na shiga yana
kwance yana kallon sama idanuwan sa sunyi jajir,"Babban Yaya lafiya?ina Aunty
Hajaran fa?Al'ameen ya ce ta fita me ya faru ne",kai ya kaɗa"kai Nana waɗannan
tambayoyin fa sunyi min yawa ai",ɗan murmushi na yi naje kusa da shi na zauna"yi
haƙuri wallahi duk na ruɗe ne","ta fita na ce ina zata ta ce ba ruwana",da sauri na
miƙe"bari na bi ta ni nasan ina zata",baki ya taɓe"kudai ku ka sa ni inda rabon
kunsha matsiyacin duka ai kwa dawo",kai kawai na girgiza na fita Al'ameen na kawo
ma sa na fito da sauri yau mota ta ga Nana.

Tana fita bata zame ko ina ba sai gidan su kuma kowa yana nan a tsakiyar
falon ta tsaya tana riƙe da ƙugu cikin ɗaga murya ta sheƙa musu kira"KUUU A HALIN
TSIYA",kamar kuwa sun san sunan daya dace dasu sai gasu riii kamar kaji,Umma ce ta
ƙaraso wajen ta"Hajara ke ce shigo mana","ina kwana Umma ni ba zama nazo yi ba ina
tsohon ɗan tashan ya ke",Abba da ke sakkowa ne ya kalle ta"Hajara dan uban ki ni ne
ɗan tasha in baki abinci a gidana kina cemin ɗan tasha",kallon sama da ƙasa
tamai"kaban abinci kuma kodai kaci abinci da dukiyar ubana azzalumi macuci",Umma ce
ta rufe min baki" a a Hajara babba ne fa",janye hannunta tayi"waye babban Umma?
babban macuci ba yana nan tun shekaru masu yawa yana cutarki shi da waccan tsohuwar
kilakin",kallon su ta yi ta kalle ni"ban ga ne ba Hajara","Umma Abba da Fulera
manyan fasiƙai ne na ajin ƙarshe tun basu san kowa ba kansu suka fara sa ni sun
kashe Mama na dan ta gansu suna masha a sun faɗawa Babana hakan ya yi sanadiyar
mutuwar sa dama nasan kin san asalina amma ai baki san asalin me ya faru ba Umma
Abba shi yake hana ƴaƴan sa zaman aure dan yana fasiƙanci da su yana tula musu
dukiya a gabana Umma kinsha faɗar abinda yake musu yana yawa ashe abin da yake
aikatawa dasu kenan suma manyan a wakai",wani irin jiri ne ya ɗauke ta sai gata a
ƙasa"Umma"suka yo kanta,suna kawo hannu jikin ta ta dakatar dasu"karku taɓa ni
Allah ya isa tsakani na daku kaima Alhaji kaje ga duniya nan Fulera kuwa zaki ga
sakamakon abinda ki ka min Allah ya saka min",kama ta tayi ta tashi tana kallon
Abba"albishirin ka ɗan kwangilar kisa ɗan da ka sa ni na kashe ban kashe ba yana
nan yana ta ka ƙasa",wani irin razana yay yi saura kaɗan ya faɗi a inda yake yana
bazo ma ta ido kanta ya yo ya shaƙeta sosai saida ya kaita bango Umma ce ta biyo
shi tana janshi"saketa wallahi Alhaji mugu"tana kuka tana janshi",cikin kakkausar
murya yake ma ta magana"dan ubanki ni zaki tozarta",cikin kakari itama ta ce"eh zan
tona ma ka asiri ma a duniya kowa yasan me ka ke su waɗancan ƴan iskan na ka basu
nu na maka hoton yaron ba ai Nana ta tura musu kaga suma munafukai ne kenen kuma
dakai muƙarraban na ka duk sai kun ɗebi abinda ku ka shuka kuma nasan dakai ka ashe
Abban Habib",cikin rawar jiki ya sake ta yana ja ba ya,dan ya razana jin abin da ta
faɗa duk da su basu ji ba dan muryar ba fita take ba sosai saboda shaƙar da ya ma
ta,wuyanta ta shiga murzawa tana mai Allah ya isa a cikin ranta wayarta ta ɗakko
kalli nan Abba"wannan shine jikan Alhaji Habib magajin dukiya mai tarin yawa
jiragen sama da kamfanoni ya ku ka iya Al'ameen kenan wannan ɗana ɗana kainuwa
kenan",ba bu wanda ya lura ya ɗakko wani ƙarfe fau ya kawo ma ta duka dashi da
sauri na hankaɗe ta ya sami kujera sai kowa ya tsorata dan tabbas da ya sameta
saiya kashe ta,ƙarfe na riƙe"haba tsohon najadu waɗan da ka kashe a baya basu isa
ba ne saika kashe ta itama",ƴaƴan gidan ne sukayo kaina da sauri na fizge ƙarfen
hannun sa na ɗaga sama nai kansa,ai da gidu suka watse har shi bin shi na shiga
yi"saina kashe ka nima kamar yadda ka kashe min Abba matsiya ci",kamar irin mai
haukar nan sai kuma na yi turus wuƙil na juya sai idona ciki na Hajiya
Fulera"tsohuwar ƴar bariki ya aka yi ana nan ana jimamin ba bu dukiya ne to ni na
kwasheta nai sadaka da ita ko baki sa ni ba ne na kwashe komai na ki naba Aunty
Hajara diyyar uwarta da ta ubanta sannan da ta mahaifarta da ki ka sa ta ta lalata
ya da magana ne",da yake ita dama ba tsoro gareta ba saita ma tso inda na ke","dan
kin ɗauki waccan ƴan tsirarun kuɗin shine ki ke wannan ɗaga kan to kina zaune da
dangwalen yatsa ɗaya na lanki komai na shi zai dawo gare mu",dariya mukai har Aunty
Hajara"dan gwalen wa kenan Al'ameen wai"kecewa na ƙara yi da dariya"baki san har an
ba ni file ɗin ba tun ranar da na haihu"zaro ido ta yi tana ja baya sai tik ta faɗi
a wajen,da gudu ni da Aunty Hajara muka fito a gidan motar da ta zo da ita muka
shiga fiii muka fe ce".
Kanta sukai dan duba me ya sameta nan suka ganta jirkice baki ya goce fuska
ta gicciye ido ya ɗaya ya janye ihuu suka saka nan aka cicciɓeta Umma kuwa na zaune
a inda ta ke ko kallon su batai ba sai kuka ta ke dana an cuceceta,asibitin da aka
kaita kuwa suna zuwa aka tabbar musu ta yi paralyze me mu ni hankalin kowa ya tashi
nan aka shiga da fice amma an sanar musu ko ina zasu bazata tashi ba sai dai ta
mutu a haka Abba ya fi kowa shiga tashin hankali nan ya shiga kiran ɗan yan shegen
da ke Maracco aɓma aka sanar masa gashi a gadon asibiti ya yi paralyze ai Abba
faɗuwa ya yi a wurin yana sambatu"kai wannan yarinya Allah yabtsine ma ta wato bama
zata kai abin kotu ba shine take kashe mu a tsaye to wallahi itama zan kashe ta
kamin tazo kaina",tashi ya yi fuuuu ya fita a asibitin bai tunkari gida ba dan
tsoron haɗuwa da Umma ya ke sai ya wuce gidan iskancin sa da ya keɓe.

Saida muka hau titi sannan na kalli Aunty Hajara ina dariya"waii ba dan
nazo ba da yanzu kin mutu ko kina doguwar suma",dariya itama ta yi"wallahi Nana
muguwa ce ke","wane irin mugun ta ko gaskiya wannan sambaɗeɗen ƙarfen da ya sambaɗa
miki shi a ka wallahi da tuni kina barzahu in shiga takaba",ɗaka min duka ta
yi"sai kace wani namiji zaki min takaba",kai na juya"abar zancen nan haka in ki ka
mutu wallahi binki zan dan zuciyata tsayawa tai",haɓa ta kama"kai na ciri tuta ashe
Nana masifa na so na",kai na jijjiga"sosaima kuwa kawai ke kin da ce",kwashewa ta
yi da dariya"wato ma na da ce ko",horn ta yi aka buɗe ma ta get tana shiga na
ce"ina zamu ce munje ne?",kai ta ɗaga sama"ke dai muje kinsan mijin namu muna ƙarya
ma zai ga ne kawai a faɗi gaskiya","shike nan",ai kuwa muna shiga suna tsaye a falo
sun kama ƙugu waisu sun yi fushi,carkewa mukai muna kallon su suma haka"daga ina ku
ke?",sosa ƙeya na shiga yi ina kallon gefe,tunda yaga ina haka yasan bazan faɗi
gaskiya ba sai ya koma kallon ta itama saita ce"gida na je mana shine ta
bini",girgiza ya yi"ai kun kyauta shine kuka je kukaiwa Abba duka shi da Hajiya
Fulera ba ku barsu ba har saida ku ka ga ta daina motsi yanzu gashi nan ɓarin jikin
ta ya shanye",saurin kallon sa mukai"duka"har muna haɗa baki wajen faɗa"shi Abban
ganɗameme da shi shine ya zabga mana alkazzibu haka shi ko kunya baiji ba ya ce ma
ka mun dake shi duk yawan su nasan dai na kai musu raraka dan sun kusa taɓa min
Aunty na",dariya ya fashe da ita yana matsowa inda muke"kun mun dai dai ƴan daba na
koda dukan nasu kukai amma a yanzu ma kun rage min raɗaɗin abinda dake cikin raina
koda hukuma muka je ba abinda zasu mana gwara kowa ya gane kuren sa a ƙarshe kuma
sa haɗu da Allah"a tare muka rungume shi Al'ameen ma yazo ya rungume mu,tun daga
ranar kullum muna saƙa ya zamu yi har Habib Gwaggo kuma na bamu hasken kai na
manyan ƴan duniya dan nasan baku manta Gwaggo Ma'u ba.

Bayan wata biyu Hajiya Fulera daga asibiti an turota gida komai sai an ma ta
Umma kuwa ta daina kula kowa kayan ta ma ta kwashe ta koma can bayan gidan da zama
kowa tsoronta ya ke shi yasa ba a ma ta magana ita kuwa rayuwar nan tafi ma ta daɗi
kan tana cikin su dan in tana ganinsu ciwo zai iya kama ta ta mutu lokacin ta bai
ba kai zaman nan ma dan ba inda za ta ne to baka da kowa aure shekara talatin da
takwas,masu kula da Hajiya Fulera ma Abba ne ya ɗakko su wasu ƴaƴan arna kuɗi yake
tila musu shi yasa suke kula da ita amma a bayan idon mutane dukan ta suke suna
ranƙwashinta dama arna akwai mugun tar masifa to da haka aka samu sauƙi akanta su
kuma ƴaƴan gidan kowa barikin sa ya ke basu ma saduda ba.

Yau nice da girki Aunty Hajara da Mama sunje Niger tare ma da ɗanta ta tafi,ana
sallar magaruba ya shigo gidan na fito daga kitchen kenan kallona ya shiga
yi"Hajiya Nana ya naga kina ƙiba ne kwana biyu kodai kodai",wurin sa na ƙaraso a
gaban sa na tsaya na juya masa jikina na cika dam ko ina ya yi sambarka dai"kai sai
yanzu ka fahimta tabb nan da wata shida zan santalo ƴata in namiji ne kuma ɗanta",a
ƙuguna ya ɗora hannayen sa yaja ni jikinsa sunkuyo da kansa ya yi yana shin shinar
wuyana hannaye na ya shiga shafowa zuwa kafaɗata fuskata ya tallabo ya ɗago kaina
sama kallo ya shiga ƙare min yana murmushi bakin sa ya ɗora kan nawa ya shiga
tsotsar sa kamar ba gobe yana ƙara maƙaleni a jikin sa ya fara shafo wuya na zuwa
ciki rigata na ƙwace jikina ina dariya"basu fara ƙaiƙayin ba adana susar ka sai na
da ƴan mintuna yanzu abinci na zai ƙone in biye ma ka",ɗan lumshe ido ya yi"ba
matsala bari na watsa ruwa kan lokacin isha dan na gaji yau su Saddi'q sun turo
kaya mai tarin yawa gaskiya company masha Allah","to Alhamdulillahi Allah ya ƙara
dafawa dama na haɗa maka ruwa tafaddal",wuce wa ya yi yana murmushi wai yau Nanan
sa rigimammiya ce ta zama haka yau Nana ke son wadda take sonsa lallai duniya mai
juyi,nima kitchen na shige ina murmushi Ba abu mai nauyi na haɗa ba dan haka da
wuri na kammala na wuce ɗakin Al'ameen dama na kai kayana can wanka na fesa na
shafa lotion mai laushi da ƙamshi sannan kwalkca mai tada hankalin maigida,rigar ma
ba ba ta mutunci ba ce dan bata da maraba da net sai dai ta haɗu gata mai
laushi,ina fitowa a ɗakin shi kuma yana ƙoƙarin zama fasawa ya yi ya tsaya kawai
yana bina da kallo,murmushi na masa na sauya tafiya ina tunkarar sa ta bayan sa na
zagaya ya yinda ƙamshi na ya zagaya shi ma wani irin yana yi ya shiga mai kama da
wanda yake jin shi a sama kwanciya na yi a bayan sa na zagaye hannuwa na a cikin sa
lumshe ido ya yi ya ɗara hannun sa kan nawa ya jawo ni gaban sa wani irin kallo ya
shiga yiwa jikina kamar bai sanni ba kaina na lanƙwasa"abinci Baby na jin
yunwa",saurin jana ya yi muka zauna da kansa ya zuba min abincin yana lallaɓata sai
iskanci nake shi kuwa duk ya susu ɓca dan ko abincin kaɗan yaci ya sure ni sai ɗaki
yanda yakewa jikina saika ɗauka ya daɗe ne rabon da yaganshi ko yakai hannu inda
yake,bakina kamar ranar ya fara ɗora na shi akai na ga soyayya wadda ba a iya
mantawa da ita a gaskiya mace ta daure ko ya yane ta koyi abinda zaisa mijin ta
yana ɗokin ta da zarar ya ganta ko yaje inda take yana nu na miki kamar ranar ya
fara ganin ki, sorry gayu na gama da Babban Yaya tun ina zanin goyo kun sa ni.

Kwana bakwai muna raƙashewa a gidan nan sannan yau na tashi da aiki ɗakin
Al'ameen da Maman sa duk na gyara sannan na ɗora musu abinci kala kala biyar da
rabi sai jin motsin su na yi da gudu na fito tun a bakin ƙofa na rungumesu suma
haka dama shi bai dawo ba,yanda na sauke ta da gyaran da na ma ta tasha mamaki
taita min godiya kamar zamuyi faɗa sannan ta daina gode min,sanda ya dawo ya same
su haka Al'ameen yay ta murna yana hawa jikin sa ba jimawa saiga Habib da Ya Hadiza
Al'ameen na ganin sa ya miƙe ya ɗane shi ɗaukar sa ya yi ya ɗaga sama"takwara na an
baiwa gobe zamu fara hawa jirgin ka",zaro ido ya yi"ai ban da jilgi ni","kana da
shi mana har biyu da pravet jet ɗaya",saurin dirowa ya yi"Nana wannan babban
gackiya yake fata",dariya na riƙe"gackiya ne mana kai bajaka shiga ba","jan shiga
amma Maama jaki bi ni ko kal cu caida ni",kwashewa da dariya akai na dungure mai
kai"wato maman ka kaɗai ka yarda da ita ko mu caida kai zamuyi ko",kamo hannun shi
ta yi"zonan ubana na kaina wazai saida kai a ƙasar nan aga in ban tashi gari
ba",sara ma ta ya yi"Allah ya biya Maama",dariya mukai harshi kan Ya Hadiza ya
nufa"Mommy yauce jaki haihu",kai ta laga sama kamar mai tunani"kana so na haihu
ne"kai ya ɗaga"eh ki haifi me kama da Nana"kwashewa da dariya ta yi"Allah ya biye
bakin ka wallahi dana koya ma ta wulaƙanci da rashin mutunci irin na Nana kuwa dan
kawai ana tsoron ta",dariya na yi"kai Ya Hadiza anya kuwa in ɗa ya yo halina a
dangi ai an shiga uku dan Allah ku daina wannan fatan ina tuna yanda Babban Yaya ke
saka ni a kwana ya tafke ni kamar jarkar da ake kalan mai",dariya sosai suka yi mun
jima muna hira har bayan tara sannan suka tafi ya bisu dan dan ya raka su,da kaina
nakai Al'ameen ya kwanta sannan na fito wajen Aunty Hajara na je na zauna ina
dariya ƙasa ƙasa,kallona ta yi"wallahi baki da gaskiya Nana"ɗan murmushi na yi na
ƙara gyara zama"ki tashi kiban waje fa",dariya na yi"ke ki tashi kije ki shirin
bacci kafin mijin ya dawo",saurin kallo na ta yi"ai na sa ni dama to tashi wallahi
miji na bar miki ni na gaji wannan tafiyar ya ta yada shege jikina banda ciwo ba
abin da yake wato ke nan har murna ki ke na dawo zansha wuya ko to koro zanyi tunda
kin koya masa shegiyar jaraba tun baki san komai ba"baki na dafe na miƙe
tsaye"wallahi ke ki ka ɓata abin ki nima nangajin ai shi yasa nake muran da dawowar
ki dan haka ga abinki nan kwana biyu na yi bacci da juyi na bararraje na
ɓararraje"kwashewa ta yi da dariya ni kuwa na gudu,danƙareriyar sakata na garƙama
na haye gado sai bacci ba kama hannun yaro ban san ya suka ƙare ba.
Sanda ya shigo yay shirin bacci duk tana jiran sa kallon ta ya yi"ya dai
matafiya yi magana mana dan na ganta a bakin ki",ɗan murmushi ta yi"dama ba wani
abu ba ne so nake a sare katangar kusa ɗakin Nana in wajen ya buɗe sai a fidda
corridor mai kama da falo Nana ta koma ɓangaren ta wannan ɗakin ta barshi in baka
nan saita dawo muna zama tare na zalinci yarinyar nan duk wannan tsawon lokacin ina
so ta koma amma nasan bazata yarda ba dan ta faɗamin sai sanda nake so ta koma ita
kuma ta ƙi dan Allah ka lallaɓata",zama ya yi a bakin gadon yana kamo hannun
ta"insha Allahu gobe goben nan zan cika miki burinki Nana kuma ki barta nima in na
ma ta maganar totsewa zatai dan ba shakkata take ba in tai fushi","nagode sosai sai
ana aikin batare da ta sa ni ba","to ya za a ma ta ne?"ɗan tunani ya yi"yauwa gobe
in zaku ɗana jirgi kawai ku wuce Abuja Ya Hasiya zatai murna sai kuyi zamanku saina
ce ku dawo kin san uwar ƴna yawo ce bazata damu ba barin ma ga ki","to shike nan
Allah ya kaimu amma kaya fa","karku damu zan aiko dasu","to shikenan ina godiya zo
mu kwanta kar bakin Nana ya kamani dan na gaji",ƴar dariya ya yi"ai nasan kin gaji
sai dai kinsan bana yafiya ko",ƴar dariya ta yi"na sa ni ai ni da zan ƙara gaba ma
gobe","eh duk da haka dai kina tarawa kanki bashi ne","naji dai taho".

Washegari na ta tashi na rigata tashi break na haɗa sannan naje na ɗauki wanka
na matsi cikin riga da zani na atamfa,Hhhhh.

Saida na fito ma sai gata ta fito tana zare ido dariya na kalleta na
yi"bashi bashi",kaina ta yo na tashi da gudu"dan Allah kiyi haƙuri je kici abinci
ki ƙara kuzari kan anjima",tsayawa ta yi"zan kama ki Nana","na yarda amma far bawa
hashimu ki dawo hayyacin ki",nu na ni ta yi ta nu na kanta"wato bana cikin
hayyacina yanzu",baki na dafe"ai ga alamar hakan na ga ni shi yasa nace ma kici
abinci kalli fa yadda ki ke masifa daga fitowar ki",kafin tai magana ya fito sai
sheƙa ƙyalli yake cikin wata muguwar suit da alama ma sawar ranar ce farko,nu na ma
ta shi na yi"kalli yadda yake shining ango ango",saurin kallona ya yi"ki raba kanki
da ni Nana","muddin ba ta Niger zaka kuma min ai bazan raba kaina dakai ba",ba
shiri ya kwashe da dariya"Allah ya shirye ki Nana kalli kamar baki ɗa",kallon sa
nayi"wallahi ba ni ɗa sai yanzu zan haifa,Aunty kice masa ya daina cewa ina da
ɗa","Abbu ka daina cewa tana da ɗa wannan nawa ne ita kuma yanzu zata haihu ko
ƙanwata",kai na ɗaga ina taɓe baki,ƴar dariya ya yi saiga Al'ameen ya fito da
gudu"Morning Nana","Morning ubana",ya ban hannu muka tafa dama ya gaisa da iyayen
sa tare mukai break sannan ya fita kallona tayi"zamu Abuja anjima",ihu na buga na
miƙe"dan Allah da gaske wayyo daɗi bari na haɗa kayana wallahi bazan dawo ba kwana
kusa saina huce",dariya ta yi"wallahi Nana kina da matsala.

Haka kuwa akayi da yamma jirage guda uku biyu na mutane da yawa ɗaya pravet
jet kai kowa yasha mamaki gashi arziƙin Al'ameen ya fara bayyana mintuna kaɗan
kamar almara sai gamu a abuja tasha mamakai dan ba mamaki kaɗai ba sauran ana isha
suka wuce mu kuwa mukai zaman mu ganin mu da kaya hakan yasa ta murna sosai nan ta
shiga hidima damu baji ba gani har tsawon sati guda sannan aka dawo ɗaukar mu muna
disar sashin mu na fara ganin chaji wurin ya zama ɗaya yasha uban screeding ginin
ya zama na daban a sati ɗaya cogewa na yi na juyo ina kallon ta ina ƙanƙace
ido"afuwa afuwa wallahi nabrasa da wacce fuska zan roƙeki ki koma ɓangaren ki amma
yau kaina ƙasa dan Allah ki koma ɗakin ki na wajena yana nan in ya yi tafiya sai ki
dawo nan mu zauna dan Allah",murmushi na yi"mu shiga to amma akwai sharaɗi in kin
yarda saina koma",da sauri ta ce"na yarda ma muje to"a falona muka sauka kai kai ko
mai sabo haka itama ɗakunan dai kayan ne zama mukai sannan na dubeta nace"Aunty
Hajara wallahi bamu da hankali ko na sisi",dafe ƙirjin ta tayi"me kuma muka yi
Nana?","Aunty Hajara wallahi mu chanja tsari a gidan nan ko Babban Yaya ya kwaso
mana ba indiya alhalin ba abin da suka fimu saima mun fisu diri sosai","nifa Nana
ban fahimta ba","to abinda na ke nufi daga yanzu Babban Yaya da ɗayar mu zaina
tafiya saboda bama da kai sai ya tafi yay watanni shi ɗaya mu muna muna dafa
shinkafa muna ci shi yana hotels yana cin nasa",ɗan jim ta yi cikin jin kunya ta
ce"wannan haka ne kuma laifi na ne nice Babba amma ban taɓa wannan tunanin ba yanzu
ya za ayi","ke zaki faɗa wallahi yana tashi tafiya sai dai yaga mai zuwa da kayan
ta","hakane Nana amma sai dai ke fara bin sa yanda sanda zaku dawo cikin ki ya yi
dai dai ba wai da tshon ciki kibi miji wani waje ba","to shike nan tunda haka ki ka
ce zan zauna anan amma wancan corridon mu dawo da dining nan sai a ɗebo sauran
kujerun a kara kwance noting ya ƙara girma","yanda ki ka ce Aunty Nana",ta faɗa
tana sunkuyar da kai,dariya na yi na dafa kan nata"zaki albarka",kwashewa ta yi da
dariya harda Al'ameen,ɗagowa tayi ta kalle shi"Babana kaga shaƙiyyar uwarka ko ta
raina ni dan taga gadon bacci na",ƙara dariya ya yi duk da bai gane me ta ke cewa
ba,sanda ya dawo ya same mu munƙara gyara wajen sai ya kaɗa kai kawai mamaki ma ya
yi da yaga abinci har an gama,muna zaune duka a dinnig ya kalle mu"wallahi baku da
kirki dama haka ku ka haɗa Hajiya Fulera da jinya",saurin dire cokalin mukai atare
muka ce"zuwa ka yi",zaro ido ya yi ganin yanda muka ɓata rai hannun sa ya ɗaga
sama"sorry officer's ba zuwa na yi ba labari ake ba ni",ƙwafa mukai nace"na zata
zuwa da sai ka biya ta ra"mamaki ne ya kama shi wannan wane irin so suke wa Abba
ne.

Kwana biyu da dawowar mu Ya Hadiza ta haihu wohoho jama a zo kuga murna wurin
Gwaggo Ma u Ya Fatsima da angon ƙarni,kai murna kowa ma yinta yake mudai kam ai
ba zama tun ana gobe suna gidan ya cika baƙi ƴan uwan Mamma dana su Mama kowa yazo
haka gayyar gidan nan kowa ya sauka harsu Ya Saddiq kai abin ba a magana washegari
muka tashi da gagarimin sunan Haruna na yi murna da wannan suna da kaina nasa mishi
inkiya da ASLAM kowa kuma hakan ya masa hidima sosai akai kamar ba a taɓa haihuwa
ba agidannan ƴan uwan Mamma sunsha mamaki akwati uku na yi na kayan barka sannan
ƙatuwar jaka ta Al'ameen ya siyawa ƙanin sa kaya da dukiyar sa wannan abu ya ba
kowa mamaki sosai Gwaggo harda kuka naita ma ta iskanci kuwa nan ta ce"in ki ka
haihu ni layya ma zanyi"munsha dariyar maganar ta kuwa,bayan sallar la asar mai
kiɗa ya kafa mana agidannan kai jama a gidan mu basa girma masu kiɗan ma nishaɗi
abin ya basu ga kuɗi suna kwasa rawa harda Iyyo abin kunya,kunsan in ana taro masu
abin siyar wa na shiga wuri bari gida ma irin namu duniya guda ranar get a hangame
mai saida alawar yara kala kala ita ta ba Al'ameen ɗaya gefe ɗaya taja shi can
wajen wanke wanke tana waige waige ta ce yasha,ina daga nesa na Aunty Hajara ta
taho da gudu ta janyo ni tunkan muzo ta ke faɗamin meke faruwa gabana ya faɗi sosai
amma na ake nai dariya"Aunty Hajara waye ya haifi Al'ameen?","ke ce mana","jinin
waye a jikin sa?","naki mana","to ki daina damuwa indai ni na haife shi bazai sha
ba",cak ta tsaya"haba Nana","shiiiii",na dakatar da ita dai dai Al'ameen na yake
jiki ya faɗi kan matar tai wani yunƙuri kumfa ta fara fita a bakin sa da sauri ta
gudu ta ɓuya cikin mutane Ya Hasiya ce ta fara yowa kansa tana ihu nam hankalin
kowa ya dawo gareta sungumar shi ta yi tana jijjiga shi"mun shiga uku jama
a",dafifi akai akansa har uba nan sa sun iso gamu sai salati muke wasu suna abashi
madara wasu suna abashi manja shi kuwa karkarwa yake cikin zafin rai Aunty Hajara
ta ɗaga hannu ta wankan mari ban kalle ta ba sai mutane da suka shiga faɗin"yi
haƙuri Hajara ai ba laifin ta ba ne",tana ku ka ta fara magana"laifinta ne mana
saida na nu na ma ta shi sanda zaisha abin tace wai bazai sha ai ga irinta nan",ta
ƙarasa tana ture ni,murmushi ta na yi kawai"Al'ameen tashi wannan ɓarin jin ya isa
haka",cak ya tsaya yana buɗe ido da ya ƙara zama fari ƙal,sakin baki akai ana
kallon shi"zubar da abin bakin ka ka falama maman ka ta daina jibgata kamar tana
karkaɗar kujera",dariya aka kwashe da ita,tofar da abin bakin sa ya yi ya nufeta ya
rungumeta"Maama OMO ne fa",wani irin ajiyar zuciya ta yi hawaye mai sanyi ya zubo
ma ta ƙanƙame shi ta yi,wuƙil na yi nabar wurin,kallon juna aka shiga yi omo kuma
Ya Mabaruka ce ta miƙe tana karkaɗe jikin ta"kar kuyi mamaki jinin Nana da Babban
Yaya ne fa a jikin sa in baiyi wayo ba tsaf sai walakiri yamai bugun tsiya",dariya
aka shiga yi nan akai ta yabawa yaron to taya ma akai yasan mugun abu aka bashi har
ya yi wayon ceton kan sa to wai a ina ma yaga Omo ne?Gwaggo ke tamabaya,Aunty
Hajara ce ta miƙe"Nana za a tambayi wannan"juyowa sukai amma suka ga wayam tambayar
ina nake suka shiga yi kawai Habib ya yi dariya"kufa daina neman ta dan wallahi
Aunty Nana ta zama ƴar daba",ba shiri aka kwashe da dariya har Babban Yaya da yake
kaɗa kai,saƙo ne ya shigo wayar Habib yana ganin number ta ya buɗe"Na tafi
operation ka kulan da Aunty Hajara",wani irin murmushi ya yi ya maida wayar aljihun
sa an kuwa bazai rubutu akan waɗannan kishiyoyin ba.

Ruwa mai sanyin masifa na ɗiba na kwara ma ta sai hodar fuskar ta na fita zaro ido
na yi"Ya Rakiya ke ce?",murmushi ta yi"ni ce ya ki ka ga ni mun gama da abin da ki
ke taƙama dashi ya ki ka ga wasan to",wata shegiyar dariya na yi"wai da ni zaki yi
wasa Rakiya lallai kinɗebo ruwan dafa kanki amma bari kiga nawa wasan yanzu ƙila ke
asibiti zaki ba kabari zaki naga alama",waya ta na ciro na kira number Aunty Hajara
vedio call,gaf da zata ɗaga na kalle ta na ce"kalli nan ƙaramar ƙwaruwa"kallo ni ta
yi da saurin na ɗebi ruwa kaɗan na watsawa fuskata nan na murjeta sai kuwa gashi ta
ɗaga"Nana kina ina dan Allah ki fito ki yafe min dukan dana miki...Nana waye ya
dake ki miye wannan a fuskar ki"kuka na fashe da shi"ki yi haƙuri Auntu Hajara
wadda ta ba Al'ameen wannan abin Rakiya ce yayar ki",wani zabura ta yi"to hakan bai
isheta ba saida ta dake ki faɗamin kina ina su suka sace ki ko?",kai na ɗaga nan na
ma ta kwatance a sifa ban gane wajen ba nima,kashe wa ta na miƙe a inda nake ya
yinda ta shiga bina da kallo"amma dai Nana ƴar wuta ce ke da alama ki sato ni
sannan dan baƙin sharri kice ni ce na sato ki bakisan Hajara ba ta da hankali ba in
ta tsane ka",murmushi na yi ina goge jinin bakina dana fasa da kaina"wuta ke zaki
kai ni ko tunda ta gyatumin ki ce ba,bari kiji ina sa ne na miki haka so nake ta
kashe ki da hannun ta bake ki ke raka ta wajen Boka ba dan ta kashe ni yau zata
huce a kanki dama tananjin haushin ki bare kun taɓa abu mafi soyuwa a gareta
AL'AMEEN",yunƙurinntasowa tayi amma igiyar dana ɗaureta ta hana ɓuruntu naji ana
kirana da sauri na sunkuya na kwance ta na watsar da igiyar na kwanta ina numfashi
sana sama,da hanzari ta nemi guduwa sukai gaba da gaba da ita,kamar namiji haka
Aunty Hajara ta tsaya a gaban yayar tata sai muzurai ta ke kallon zanci ubanki yau
ta ma ta,nu na ni ta yi"me ki ka ma ta?",dakewa ta yi itama"ban sa ni ba ko zaki
rama ma ta ne",kafin ta rufe baki ta lafta mari ta ƙara ma ta wani Yayar ba haƙuri
itama nan damben masifa ya kaure da sauri na ciro wayata na fara ɗaukar su juyata
Aunty Hajara ta yi ta haye kanta ta fara kirɓar ta ta ko ina kan kace me ta haɗa ma
ta jini da majina fuskar ta ta yi luhu luhu tasowa na yi irin da ƙyar ɗinnan na
janye ta sai haki ta ke,wani kakkausan warning ta shiga ma ta"kalle ni nan Rakiya
ko inuwar Al'ameen da Nana ki ka kuma kalla sai tsiyayar miki ruwar ido shegiya
karuwar gida",hannu na ta kama taja ni muka fita daga wajen dariya fal cikina muna
shiga mota na fashe da dariya"Aunty Hajara dama ƴar restling ce ke bamu sa ni
ba",kallona ta yi"lahhh dama ƙarya ki ke Nana","eh mana ba gashi kin huce takaicin
yawon banza ta saka ki ba","Allah ya shirye ki Nana muje gidan can mana
dubiya",dariya na yi"muje to"a waje mukai parking muna shiga muka ganta ana gasa ma
ta fuska dariya mukai Abban na nan yana ganin mu ya miƙe"daga ina ahalin tsiya da
masifa",saurin tarar sa na yi"a halinka kenan ko dan kowa ya ganmu yasan daga gidan
tarbiya da arziƙi muka fito ba wai daga gidan a kashe mutane a gaji dukiyar su
ba",saƙare ya yi yana kallon bakina ina idar wa ya cigaba"anya kuwa ke mutum ce ba
rhin sheɗanu a jikin ki ku fita daga gidan nan",ƙwafa Aunty Hajara ta yi"ni ba
wajen ka muka zo ba ina Umma","ban sa ni ba tunda ba uwar ki ba ce","ai kai ta ka
ce ko tsohon banza",na katse shi,bai kulamu ba yay gaba fuuu dan yana jin kamar ya
shaƙeni ya huta,gidan mukaita leƙe leƙe ba Umma,wani ɗaki na tura naga wata ƴar
aiki tana ranƙwashin wa ta wadda ke a kwance zaro ido na yi na shiga hankali"ƙara
ma ta shegiya muguwa azzaluma wannan azabar ma kaɗan ki ka gani insha Allahu sai
kin ɗan ɗani azaba dubun wadda Abba ya ɗanɗana kafin kije lahira a soya ki",bakin
da ke a waskace take motsawa amma ta kasa magana murmushi nayi"a haka zaki ƙare ba
zaki magana ba kinga kenan tun a duniya Allah ya nuna miki baya sonki dan ya ɗauke
miki baki karma ki nemi yafiyar wani,ke me aiki cigaba kullum kina ma ta raƙwashi
sittin muguwa",girgiza kai ta yi"wannan mutumin ko ajiya kana ganin shi shegene na
tsane shi ni a edo in kai mugu ne ina ganin ka nake ganewa","haka yake ke dai ki
cigaba da mazgar muguwa",Aunty Hajara ke kirana na fita da sauri tana ma can baya
zagayawa na yi nima Allah sarki Umma ke zaune kan tabarma tana cin garin kwaki a
gaban ta muka tsugunna"Umma lafiya kuwa kalli halin da ki ke ciki",hawayen fuskar
ta ta share"gwara min wannan rayuwar da ta baya ƙwandalar wannan gidan bana so
Alhaji ashe shi ya kashe min ɗana na fari wai na haifi namiji wanda in ya girma zai
ji ƙaina ash dama ba sona yake ba azzalumar dukiyar da ya ci da ni da ita ma ban
yafe masa ba",kauda kai Aunty Hajara ta yi tana hawaye,kama hannun Umma na yi"Umma
zo mu koma gidan mu",saurin kallona sukai"eh mana Aunty Hajara me zata yi a
gidannan kullum in tana ganin su ɓacin rai zaina kama ta gara tana gefe guda,ba
tare da kowa yasa ni ba muka fita,a gidan ma ƙin binmu ta yi tace ita wajen Iyyo za
ta zauna ai kuwa ba wanda yaƙi saima murna da kayi nan akaita ba ta haƙuri kowa da
kalar ƙaddarar sa ita muka ta ta kalar kenan,muna shiga gida ya tare mu"sannun ku
ƴan daba",dariya mukai kawai ko wacce ta wuce ta shige wanka.
Bayan kwana biyu da daddare Abban ya tashi dan ba ganin Umma yake ba dama
baima san tabar gidan ba fetur ya ɗauka ya zazzage inda ta ke ya cinna wuta yana
ɓaɓɓaka dariya ya bar wajen ya koma ciki masu gadi ne suka lura da sauri sukai ihu
amma ashe wutar nan ta nacan ta baya ta haure zuwa cikin gidan ta kama ɗakuna kashe
ta ka fara yi amma kamar ana tunzura ta fammm tai ƙara da gudu Abba ya fito amma ta
tare hanya ga ɗakuna naci da wuta mutanen unguwa ne suka fito dan kawo ɗauki amma
ina cin na ta ya yi yawa sai ƴan kwana kwana aka kira kan su zo wuta ta lafta ɓanna
Hajiya Fulera ta ƙone ƙurmus mai aikin nata dai a ƙafa ta ƙone sauran kuwa kowa ta
lahanta shi an yakewa Rakiya ƙafa ɗaya da hannu ɗaya ga rabin fuska yaci wuta
sauran ma an yanke wa wata ƙafa wata hannu haka dai ƙarshen su ya zama Abban kuwa
bayan sa ne ya ƙone duk suna zube a asibiti abin gwanin wasu su tausaya musu amma
banda mu.

UMMU SADDIQ CE🌹🌹🌹


🌈🌈🌈
🌈🌈
🌈

BABAN YAYA

Babban Yaya Free ne amma me so ya biyo ni Pc in sa a group don shagalin Nana


na buƙatar comments.
08146711395

41

MAROCCO
Asibitin da aka kwantar da Baban Aisha yau ƴan uwan sa ne suka cika shi kai kace
dubiya suka zo amma su sanin ƙasar da Al'ameen ya ke suka zo jin ba asi kuma ba
dalewa ba suka samu dan masu zuwa wurin sa duk sun san kan abin shidai na um ba um
um.

Mamaki ya isa mutane yadda Abba ke kwaɗa ihu a asibiti saboda rakin masifa
Hajiya Fulera kuwa sai wata makarantar almajirai aka kaiwa kuɗi suka binne ta,saura
kuma suka cigaba da karɓar atakin wurin azabar ƙuna.

Umma baiwarbAllah kullum kuka ta ke da addu'a da godiya ga Allah bisa ga


soyayyar daya nu na ma ta dan tsallake wannan bala'in ba ƙaramar nasara ba ce,sai
Iyyo ta yi ta yi da ita kan taje ta duba yaran ta amma taƙi zuwa kuma tace bazata
taɓa yafe musu cutar da suka ma ta ba Ibrahim ma dake makaranta har yanzu baisan me
ke faruwa ba to ɗan secondry me za a faɗa masa,haka aka barta tunda taƙi zuwa.

Abin da yay mutuƙar bawa Abba mamaki yanda ba bu wani ƴan ƙungiyar su ta
kasuwa ko aboki da ya zo inda yake har yanzu gashi ya yi asarar komai nashi ba
takardun wata kadara bare wayar sa,yau da wata masifar ma ya tashi banki sun sun
biyoshi jar asibiti kan kuɗin su da ya ci ganin basu sami komai ba suka fito zuwa
gidan sa aka saka shi a kasuwa nan aka siye shi kuwa aka basu kulin su canjin da ya
ragu sukamkai masa har asibitin ya yi takaici kuka ya shiga yi yana tsine musu har
suka bar asibitin.

****

Lamari fa ya yi musu tsanani dan ciwukan su Abban su Hajara sai lalacewa


suke,ya yinda Umma ba ruwanta rayuwa take free abin ta a gidan mu.

Kwana ki na tafiya haka rayuwar na juyawa waɗan da dama basu shuka khairan ba
bare su sami sassaucin ta,tun dare nake jina bani da lafiya amma na basar ga Aunty
Hajara da Al'ameen sai tambayata suke nace musu ba komai,misakin biyu muna shirya
dining ciwon yamin yawa dakatawa nayi a wurin da nake ina cije baki Al'ameen ne ya
ƙaraso da gudu"Nana sannu kawo inkai"ni mamakin maganar yaron nake Nana kamar wata
sa ar sa shi Auntyn ma bazai iya ce min ba,karɓar kwanon ya yi ya aje a dinnig yazo
ya wuce ni da gudu,tana ɗaura ɗankwali ya shigo da gudu"Maama Nana zatai
kuka"daina ɗaura ɗankwalin ta yi tayo waje da gudu"ni nasan dama bata lafiya tace
ƙalau take wannan taurin kan dai bazata daina shi ba"duk tana faɗar hakan ne kamin
ta ƙaraso inda nake,bata kulani ba ta wuce ɗaki ta ɗakko akwatin da ta haɗa ta fito
falon"Babana jeka ce Murtala ya juya min mota yanzu"da gudu ya fito baiji nisa ba
yaje bakin get yakai saƙon sako shi ya yi a motar ya dawo shi inda ake aje mana
namu motocin tallafoni ta yi zuwa motar batare da ta faɗawa kowa ba muka wuce
asibiti harda Al'ameen,bamu jima da zuwa ba na haihu ɗa namiji Aunty Hajara tsabar
murna kuka ta fashe dashi ji take kamar ita ce ta haihun,ana bata jaririn ta
rungume ta ɗau wayar ta takira number sa vedio call ba jimawa ya ɗaga ganin tana
kuka ya tashi zaune daga kan kujerar daya kishingiɗa"lafiya ki ke kuka","ka kalli
kafaɗata mana na ƙara samun Baby boy"da sauri ya miƙe tsaye"Alhamdulillah ya
Nana?","nutsu na Nana tana lafiya yanzu ma zan shiga wurin ta please ka taho muyi
murna tare",yanzu ma kuwa kwantar da hankakinki zan biya ko nawa ne na taho a
yau","yauwa Habibie saika zo",ta kashe wayar tana goge hawayen fuskar ta"wata nurse
ce tazo wajen ta da gudu"Madam bamu ga mai haihuwar ba"wani irin juu ta ji acikin
kanta tana wa nurse kallon ban fahimta ba"itama ta gane ta maimaita"mun gyara wadda
ta haifi wannan ɗan har wani little boy ya shiga amma yanzu bamu gan su ba ita da
ɗan saurayin yaron"wani damm taji a ƙirjin ta"na shiga uku ni Hajara anan ɗinma
binmu ake"cikin tashin hankali ta kira Baffa ta faɗa masa tsabar ya ruɗe bai faɗama
kowa ba ya taho asibitin shi ɗaya ganin yanda ta ruɗe tana zufa yasa shi tausaya ma
ta,itama saida ta ganshi sannan ta fashe da kuka"wai Abba waɗannan mutanen me suke
nema ne a wajen mu",ajiyar zuciya ya yi"ki yi shiru Hajaratu haka kuli suka gada ke
zamu su sa ayi abinda yafi haka","to Abba ba a tausayin ta da ɗanyen jiki ko wanka
ba bu a ɗauke ta ga Al'ameen ma tare aka kwashe su","ki kwantar da hankalin ki ba
bu abin da zasu iya ma Nana sai dai in taga za a cutar da Habibu ne zatai
komai","wayyo Baffa ni wai a basu kuɗin mana su bar yaron nan ya huta","to Hajara
ya zamuyi wannan ce ƙaddarar su ita da ɗan taso muje gida da wannan a masa
wanka",kallon yaron ta yi"Allah ya baka haƙuri ɗana bata shayar da kai ba bata
shayar dana farkon ba Allah ka taimake mu"kukan ta ne ya karyawa Baffa gwiwa da
ƙyar ya lallaɓata suka tafi ya yinda hukumar asibiti suna fita ƴan sanda suka ma ta
tsinke dan Habib kan su ƙarasa gida ta kira shi yana bariki amma ya tura musu
hukuma dan sunyi saka ci suma Likitar da ta karɓi haihuwar ita ka damƙa amma iya
bin cike bata san komai ba saida abin yakai Habib yazo da kansa nan ya gane an
shirya komai ne sanda take zuwa awo dan a asibitin take awon dama,da bincike yay
bincike ne aka gane ma aikatan da aka ɗiba sabbi acikin su ne aka turo masu musu
aiki kuma a yanzu a sabbin ba bu mutum uku kenan dama haɗin baki ne,sosai asibiti
ya shiga cikin tashin hankali dan ko address ɗin ma aikatan ƙarya ne abin ya ɗagawa
masu asibitin hankali,nan Habib ya gama binciken sa bai bar asibitin ba sai dare.

Suna isa guda aka ganta da jariri mamaki aka shiga yi a falo ta zauna ɗauke da
ɗan ana magana ta rushe da kuka basu shigo tare da Baffa ba ya wuce wajen Alhaji
Baffa ne,ganin yanda take kuka yasa Aunty Mama ta zauna kusa da ita ta miƙa hannu
ta karɓi jaririn"Hajara nasan Nana ce ta haihu me yake faruwa to naganki ke ɗaya
tana ina ita ɗin?",ƙara sautin kukan ta yi"Aunty Mama masu faƙon ta sun ɗauke min
ita tare da Al'ameen","inna nillahi wa inna ilaihi raju un Hajara dama wannan abin
bai ƙare ba ya ilahil alamena ka kawowa wannan yarinya ɗauki"tana ƙarashewa muryar
ta na rawa itama,Mama kam ƙala bata ce ba tasan wannan al amari ran yarinyar yake
nema,Baffa da Alhaji Baffa ne suka shigi da Iyyo tana kuka kan kace me zancen ya
karaɗe gidan nan aka yo ɗuuu wajen su Mama dan jin ba asi,suna nan Habib ya shigo
ya zayyana musu abinda ya faru amma ya samu hoton ɗaya daga cikin su wata ce ta
bashi amma ba wanda yasa ni suma nu na musu ya yi nan aka shiga turawa ko Allah
zaisa wa ni yagan ta bama ya mazan da suka shaƙa sukai abin ya fara kaisu
bango,Umman su Hajara ce take kuka"wallahi karku yarda kuje har asibiti ku ciwa
wancan mutumin mutunci zai faɗa muku inda take nasan ya sa ni"kallon ta Hajara ta
yi"Umma yanzu sun zare shi a cikin su bai san komai ba kawai dai muna musu addu a
Allah ya kuɓutar dasu"ameen kowa ya amsa nan akai jugum,shigar dare Babban Yaya ya
yi yazo ya iske tashin hankali ya jijjiga iya jijjiga amma ya daure ganin yansa
Aunty Hajara ta fishi jigata da tashin hankali dole ya koma lallashin ta ga jariri
ta hana kowa ɗauka madara kawai take bashi shima yaron mai haƙuri bai taɓa kuka ba.

Washegari tun farar safiya Habib ya fice dan bama su haɗu ba duk inda yasan
zai sami wannan yarinyar yaje amma ance masa basu daɗe da zama ba a garin dama kuma
sun tashi,yamma lis ya kira number sa yana ɗagawa ya ce"Yaya ina son ganin ka"nan
ya bashi kwatance ba jimawa sai gashi a wurin,abinci yasa aka kawo masa ya tura
masa"ci muyi magana Yaya"kallon ban fahimta ba ya masa","please Yaya"ya faɗa yana
haɗe hannayen sa,ba musu ya ci wajen rabin abincin sannan ya sha ruwa lemo kuwa ko
arziƙin kallo bai samu ba,kallon sa ya yi yana go ge bakin sa"ina jinka any
information",kafaɗa ya ɗaga"no information kawai dama dan kazo kaci abinci ne yasa
na kira ka dan nasan Aunty Hajara ba ta da nutsuwar lallaɓaka kaci abinci",wata
uwar harara ya zuba masa ya miƙe ko ƙala baice masa ba ya fita a wajen a bakin mota
ya tsaya yana murmushi sannan ya buɗe ya shiga ya figeta yabar wurin,bin bayan sa
da kallo ya yi"am sorry Yaya bazan iya bari yunwa ta kassara ka ba kamar ɓatanta na
waccan lokacin"yana gamar faɗar haka ya miƙe ya fita shima wani ƙaramin gida nan
kan hanya ya parker ya shiga gidam sabo ne ba kowa kuma wani ɗaki ya buɗe ya shiga
na urorine da abuwan buƙata sai ac da fanka,wata ce zaune kan kujera an ɗaureta tam
kamar goro ga baki a liƙe,hararar ta ya yi sannan ya yi murmushi"kin ɗauka zaki
ɓoyemin ne da ki ke saka wannan abin kulle fuskar ai bari kiji da ahaka ma ki ke
yawon ki ƙila ba lallai ma na gane ki ba amma kin rufe fuska kuma kina kallona in
ɗago kuma ki maza ki wayance tunda naga haka a unguwar da ki ka fara zama na ganeki
na ƙyaleki ne kawai dan na tabbatar ke ce shi yasa na cigaba da nemanki a duk inda
aka sanar da ni kina zama",kanta take kaɗawa saboda wahala da wannan ɗaurin yake ba
ta har fitsari saida ta yi a wurin ga kujerar bamai laushi bace ƙarfe ne ma,shima
kaɗa ma ta kan ya yi"kin yarda zaki faɗa min ina take na kunce ki?",da hanzari tana
gumi ta fara kaɗa kai"good girl"ya faɗa yana matsowa inda take,yana ɗaye gam ɗin
bakin ta ta ce"tana Algeria! Algeria!!"da mamaki ya ke kallon ta"Algeria kuma?","eh
can suka kaita sunyi hakane dan sun san baza ai tunanin can ba","kin tabbata?","na
tabbata wallahi har ƙaramin yaron yana can tare da ita",,"good"ya faɗa yana
miƙewa","ka kunce ni mana dan Allah ina da Mama bata da lafiya nasan tana can tana
jira na",juyowa ya yi ya watsa ma ta mari har sau biyu cikin fushi ya fara
magana"au dama kina da imani ki ka yarda ka haɗa kai dake aka raba uwar da ta haihu
take da ɗanta ita kin san ya zata ji",kuka ta fashe dashi"wallahi dole aka min anan
ƙasar bansan kowa ba daga can Ghana aka bawa ƙanin mahaifiya ta dake riƙe dau kuɗi
nan ya basu ni aka kawo nan aka nema min aiki tare da wasu biyu da fari ba a faɗa
min me zanyi ba sai daga baya da farko naƙi shine suka je suka zo da Mama na da
bata da lafiya suka ce in banyi abin da suka ce ba zasu kashe ta,ni ban ma ta komai
ba na mugunta nadai bule musu ƙofar Emagency wadda ba kowa ke shigowa ba sumka fita
da ita tanan ban ma san ina zasu kaita ba a wajen ɗayar naji tana waya
nima",girgiza kanshi ya yi"wow amma kunyi ƙoƙari sai dai sun ɗebo ruwan dafa kan su
zan sake ki amma da sharaɗin zamuyi aiki tare zaki cigaba da magana dasu har kisan
wane waje ta ke","na yarda tai saurin faɗa dan burin ta kawai ya kwance ta Ba musu
kuwa ya kwancetan da sauri ta miƙe tana murza hannauen ta da ƙafafunta"amma kai
soja ne ko?",saurin kallon ta ya yi"taya akai ki ka sa ni?","saboda sune farkon
marasa imani za suyi abu sun san da azaba amma zasu murje suyi kamar normal abu
sukai",ƴar dariya ya yi"madalla to ta ina zamu fara?",ɗan jim ta yi"ban waya ta
daka ƙwace mana",jakar ta ya janyo ya miƙa ma ta"karɓa ta yi ta ɗakko wayarta da
hanzari ta fara kiran wa ta number ana ɗagawa ta ce"Mama ya ki ke","lafiya lau Ummi
baki dawo ba yau","zan dawo Mama aiki ne yamin yawa kinsha maganin ki?","eh
nasha","to saina dawo duk wanda ya ƙwanƙwasa ƙofa karki buɗe kiyi kamar bacci ki
ke","to Ummi amma dai lafiya ki ke ko?","lafiya na ke Mama saina dawo ɗin",ashe
wayar ta yi tana ajiyar zuciya sannan ta kalle shi Allah ya taimake ka da naji Mama
ba lafiya ko zaka kashe ni bazan taimaka maka ba",hannu ya ɗaga ma ta"ai kinjita
lau ko maganin ma ni naje na bata wawuya kawai kina ba ta magani daban ciwo daban
Maman lau take damuwa ce ta ma ta yawa ki faɗa min me ke damunta"saurin kallon sa
ta yi"kaje gidan namu yaushe a ina ma kasan gidan namu?",hararar ta ya yi"kiban
amsar tambaya ta malama","to ai haka binciken lafiyar ta ya nu na ciwon zuciya ke
damun ta","eh naji gwajin lafiya ya nu na tana da ciwon zuciya amma ai bana shan
magani ba ne na samun kwanciyar hankali ne na ta me ya faru da ita da ta kasa
mantawa?",ɗan jim ta yi tana zama akujerar daya ɗaure ta"ni kaina bansan me ke
damun ta ba kawai dai nasan cewa Abba na ya mutu ta hanyar cin guba",kallon ta ya
yi"to ya zaki ce bakisan me damun ta ba bayan ga gaskiyar abin da ke damun ta nan
kin faɗa yanzu,da yaushe ne ya mutun?","wata tara kenan ko takaba ba ta gama ba
aka kawo mu nan",wani ɗan murmushi ya yi"a haƙiƙa kenan shima babanki su suka kashe
shi dan sunce suna buƙatar ki shi kuma yace bai yarda ba dan ke mace ce ba namiji
ba ko?",tashi ta yi tana masa kallon tsoro"ta ya akai kasa ni",hular hannun sa aje
yana murza yatsu"duk maganar da ki ke me amsa ki ke yi ai koma ya ya ne dai Allah
ya jiƙansa ya kuma bi masa haƙƙin sa ita kuma kin ƙoƙarin kwantar ma ta da hankali
bawai kina danna ma ta ƙwaya ba",ɗan murmushi ta yi"all right bari na kira naji
halin da suke ciki"ta ɗaga wayar ta ta kara a kunne".

UMMU SADDIQ CE🌹🌹🌹🌹


🌈🌈🌈
🌈🌈
🌈
BABAN YAYA

Babban Yaya Free ne amma me so ya biyo ni Pc in sa a group don shagalin Nana


na buƙatar comments.
08146711395

END

42

Tunda na buɗe ido ina kallon sama na tabbatar ba a asibiti nake ba cikin tsamin
jiki na samu na yunƙura na tashi zaune idanuwa na ne sukai arba da Al'ameen dake
yashe a ƙasa yana bacci sakkowa na yi daga kan gadon da nake cikin cije leɓe na
taka nazo inda yake da sauri na ɗago shi dan na zata baya numfashi fuskar sa na ga
ni ta yi ja jir ga jini gefen bakin sa tun kamin aje ko ina na hasasho a hannun su
wa muke kenan su suka dake shi dan rashin imani,ɗan murmushi na yi ina shafa
kansa"wato kayi gadon taurin rai da turin kai kenan shi yasa aka duke ka",maganar
da nayi a fili ita tasa ya buɗe ido,saurin rungumeni ya yi"Nana ina jalilin nace cu
maida ni wajen blos cine cuka duke ni","shafa kansa na shiga yi"ka kwantar da
hankalin ka muddin ina numfashi zaka rayu da ɗan uwanka koda ni bazan rayu da shi
ba",kaɗa kai ya yi ya ƙara lafewa a jikina,muna haka aka turo ƙofar aka shigo wasu
mutane ne sunkai su goma kowa kana gani kaga babban mutum amma a riga a zuci kam ba
girman an sheƙe shi gun son abin duniya,guard ne a bayan su suka shigo da kujeru
nan aka buɗe musu kowa ya zauna suna kallon mu,nima a tsaitsaye nake bin su da
kalkon dan na lura ba mutunci ne dasu ba ko daga yanayin kallon da suke mana,ɗaya
daga cikin su ne yay wa wani guard alama nan ya nufo kanmu gadan gadan ya kawo
hannu zai taɓa ni na daka masa tsawa cikin juya ido murya kamar gardi na ce"ka na
taɓa ɗayan mu zaka mutu"da sauri ya janye hannun sa yana matsawa baya,kallon ogan
nasa ya yi ya ce"sir kaji me take cewa","naji mana sai a kai ya ƙarya ta ke aljana
ce ita dalla ƙwato mana ɗan shine burin mu ba ita ba",zazzare ido ya fara gaban sa
ina faɗuwa amma ba yanda ya iya haka ya kuma kawo hannu,kallon sa na yi kawai"ashe
ƴaƴa biyar mata biyu da uwa da uwa ba zasu mutu lokaci ɗaya"wani rugugu yaji a
zuciyar sa yay ma za yaja baya"Allah ya baki haƙuri ai dangina ki ka lissafo duka
sune rayuwata dan Allah kar su mutu","to kacewa oganin ka su faɗi me suke so da mu
kamin tabar kanka ta shafi kowa"a tsorace ya kalle su"dan Allah sir ku faɗi me ku
ke so a wurin ta ko ma tsira da ranmu dama an faɗa muku ƙaya ce ita",ɗan murmushi
sukai suna tunanin komai zaizo musu da sauƙi,wata takarda suka wullo ta faɗo a
gabana,ɗauka nai na fara dubawa sannan na wulla musu nima"baza a sa hannun ba kuyi
abinda zakuyi"daga cikin su akwai wanda tunda suka zauna ƙala baice shine yafi
hasala"ku harbe min ita ku ɗakko min yaran ya dangwala mana da yatsan sa"wancan dai
baizo ba dan ya tsorata da gaske kusan makashi akwai tsoron mutuwa,ina a wurin wasu
uku suka ƙaraso suka danƙeshi amma abin mamaki sun kasa ɓamɓare hannayen sa a
jikina gashi kuma kamar me bacci tofa nima ɗin ai sai abin ya bani tsoro kuma ganin
yanda ake ƙoƙarin janshi yaƙi jawuwa sai suka miƙe tsaye dan abin daban mamaki,wani
irin ihu ya yi ya watsar da ƙartin ya miƙe tsaye yana zare ido nima baya naja ya
yinda suma suke ja bayan dan basu san me zeje yazo ba,cikin murya wadda kana ji
kasan ba Al'ameen ba ne ya fara magana"ba za a sa hannun ba kiyi yadda zakuyi"ya
buga ihu yay kansu nan kowa ya watse an tunkari ƙofa ta kulle kanta nan fa aka
watse a ɗakin ga window da ƙarfe ba za a iya ratsa shi ba,ni kaina gefe naja na
maƙure yau naga abin da yafi ƙarfina a ina Al'ameen ya kwaso Aljanu kuma,a cikin
ɗakin ya ruɗa kowa sai ihu suke inka yarda ya riƙe ma hannu ko ya shafa ka saika ji
kamar wutace take ƙona ka cikin ƴan sakanni ya ruɗa manyan Alhazai sai kwakwazo
suke suna ihu duk ga alamun ƙuna nan a jikinsu ihu suak cigaba da yi suna zagaye
ɗakin kuyi haƙuri bazamu kuma"to ina dukiyar ku da ku ke neman ta haram ko ku ku ka
tara mai ita ne",suna iface iface sana faɗin munyi kuskure kuyi haƙuri"ba wani
kuskure kuna sa ne kuma iya tsawon lokacin nan ni nake gadin dukiyar yau kun kaini
bango ne na sa ɗaya mutuwar ɓarin jiki nasa ƙona ɗaya shi kama ɗayan daya sa wutar
ya ƙone shida tawagar sa saura ku kuma zaku ƙone fiye da su",fashewa sukai da kuka
ninkuma na fashe dariya ban sa ni ba dan wallahi dole ka dara muddin kaga yadda
manyan mutane ke ɓarin hawaye,nufar su ya yi gadan gadan nan suka ƙara tsagewa da
kuka"mun tuba mun tuba rankai daɗe aljani bazamu kuma saka ido ko baki a wannan al
amarin ba wallahi zamu maida su gida a yau ba sai gobe ba bamu ƴara bi takan su
tamu dukiyar mungode Allah ma daya ba mu ita",dakatawa ya yi a inda yake"to maza
inga alama kunbar zancen nan",da rarrafe mai maganar ya matsaya ya jawo takardar ya
shiga yaga ta yana turawa a bakin sa ganin tamai yawa ya turawa na kusa da shi a
baki"ka gani ko yallaɓai aljani mun cinye ma dan Allah kuyi haƙuri","bazan haƙura
ba saina kun saka su a jirgi sannan zan bar ku ko kuma yanzu na bayyana a suffata
ta gaskiya"riiii suaka fara rigegen ɗaukar waya suna danna kira ba jimawa suka
kashe"mun faɗa za a kaisu yanzu dan Allah a mana afuwa",sharaf Al'ameen ya zube a
wurin da sauri na matsa ina jawo shi jikina,mutumin ɗazu ne ya cire hular kansa
yana fifita hannun sa da wuyan sa sannan yacewa yaran nasu"ku fitar mana da
waɗannan gayyar tsiyar anan wallahi da na san haka ce zata kasance da tuni na
haƙura da kuɗin nan kalli yanzu yanda muka ƙoƙƙone ko me zamu cewa matan mu gaskiya
dai munji kunya"tsawa aka daka ɗakin nan ƙofa ta nemi yin kaɗan mu kuma aka kwaso
mu kamar kayan wanki aka watsa mu a wani jirgi da dai mutane amma ba yawa sai
kallon mu ake dan ana ganin mu anga baƙi,anan suka barmu suka tafi suma ɗin dai sun
ƙone ɗin sun samu ladan gadi.
Suna hanyar komawa gida jansu wayar guard ɗin nan ɗaya tai ƙara ganin me
kiran yasa ya ɗaga yana ɓoye dariya ya ce"Hello Nurse",itama da sauri tace"ya kuwa
sun muku abin da ku ke so"da yake shi ɗaya ne sai ya kwashe da dariya"ina fa suka
mana munci ubanmu dai ashe aljanu ne waɗannan mutanen wallahi kiyi hankali kema dan
duk mun ƙone jiki yanzu haka mun kaisu cikin jirgin zuwa nan ƙasar Allah ya rufa
asiri amma mun sha wuya a hannun su",ƴar dariya ta yi"ban gane wuya ba",a harzuƙe
ya ba ta amsa dan yana jin dariyar da take"ban sa ni ba ki dai yi takan ki"ya kashe
wayarsa,da hans free ta sa kallon juna sukai ita da Habib dan shima yaji komai"to
yanzu ya za ayi ba a san wane jirgi ba ne kawai ka faɗawa yayan ka tunda shi yasan
ma aikata da yawa sai ya tambaya wane jirgi ne zai sauka da daren nan daga
Algeria","haka ne bari na kira sa to"wayar sa ya ɗauka ya kira shi.
Yana zaune riƙe da jaririn a hannu saiga kiran Habib da bazai ɗauka Aunty
Hajara ta ce"haba kai kuwa dan yasa ka kaci abinci shine bazaka ƙara ɗaukar kiran
sa ba ka sa ni ko ya samu wani baya ni ne akan su",ɗauka ya yi yasa maganar a
fili"Hello Bro please am sorry da abin da na maka dan Allah ka any airport wane
jirgi ne zai suka a daren nan daga Algeria",a daƙile ya ce"ok"ya kashe ya kira
wajen mutum goma sannan ya samu aka ce masa akwai mai sauka a Abuja zuwa 2am,kiran
sa ya yi ya faɗa masa,da shi da wannan Nurse suka fito nan kuma aka tsaya jimamin
ta ya za a tafi Abuja yanzu,ƙara kallon Habib ta yi"ka kira shi kace ma sa ya sama
maka jirgin Abuja Emagency ko nawa zaka biya",kallon rainin hankali ya ma ta"ko
nawa zan biya to shima ɗan sa jirage uku gare shi",zaro ido ta yi"am sorry ashe
abin yana da yawa shi yasa waɗancan mutanen suka ruɗe da yawa suma",kiran sa ya
kuma yi"Bro za ni Abujan ka nema min kujera mana",kai ya dafe"Habib!!!","please
Bro","ok ten mint",kashewa ya yi ya kira Abdallah dan ƙanin sa na aiki a air port
ne an samu ya kira sa ya faɗa masa amma ya yi sauri minti arba in da biyar ne ya
rage,anan suka rabu da nurse ta nufi gida shi kuma ya wuce air port.

A inda aka watsar damu nama kasa tashi bare yaro ƙarami da ya sha wahalar ga
jijjigar aljani ma aikatan jirgin ne suka ƙaraso kanmu da mamaki suke kallon nan da
nan suka yo kanmu suka kama muka miƙe ɗayar ce ta ce"sannu Hajiya ba kece
Mahaifiyar Al'ameen air ways ba",kai na ɗaga musu ina nuna musu shi da sauri suka
ɗauke shi suka kaimu wuri na musamman nan da nan suka cika mu da abinci har wanka
suka masa sun bamu kulawa sosai har Allah ya sauke mu lafiya sannan dare ne sosai
ga sanyi mayafin cikin jirgin muka lulluɓa na rungume shi a gefena dan bazan iya
ɗaukar sa ba gashi da ƙyar nake iya ɗaga ƙafata jikina ya gama tsami muna gama
sakkowa nai arba da Habib tsaye shi har ciki ma aka barsa ya shigo saboda sanin
manya da sukai,shima mu yake kallo tsayawa na yi a wurin kawai na fashe da kuka ban
taɓa jin karaya ba a rayuwa ta sai yau,da gudu ya ƙara so gare mu ya ɗauki
Al'ameen"sannu"kawai yace min ya nu na min inda zamu dan zamu koma ne a wani jirgin
amma sai asuba,ban iya koda motsin komai ba a inda muka zauna har asuba saida kai
sallah sannan muka hau jirgin.
Gari ya fara haske muka sauka motar da yazo da ita jiya ya bada ajiya ita muka
hayo zuwa gida.

Aunty Hajara na zaune a bakin gado tana sawa Baby kaya ta masa wanka dan ba
mai taɓa shi gidan ma madadin barka ja je ake zuwa dan haka gidan kullum cike
yake,kamar an ce kalli mudubi sai ta ganni tsaye lulluɓe ina kuka,saurin kallon
bayan ta ta yi ta gan ni da gaske ne a guje ta taso"Nana ke ce"tana kai hannu
jikina ta ji ni ɗin ce saita rungume ni ta fashe da kuka mai ƙarfi"Nana ke ce wayyo
Allah na jama a ƴar uwata ta dawo ina Al'ameen",ƙofa na nu na ma ta da sauri ta
fito ta ganshi a kafaɗar Habib,tun daga kallon da ta ke ma sa ta ga ne shine ya
samo mu da gudu taje ta karɓe shi ta rungume shi a ƙasa ta durƙusa"mungode mungode
Habib ba bu ɗan uwa irin ka a wannan zamanin Allah ya faranta ma ka yadda ka faran
ta mana"shima duƙawar ya yi"haba Aunty Hajara miye na durƙusa min kuma",bai gama
magana ba yaji saukar muryar sa a bayan sa"riƙe Nana Habib zata faɗi",ai kuwa kan
nakai ƙasa kaina ya taɓa center table ya riƙe ni"Aunty Nana"ina na daɗe da barin
wannan nahiyar da hanzari ya ƙaraso ya ɗauke ni cak ya fito daga ɗakin zuwa motar
da aje yanzu dana bai kwana agidan ba dama yana office dare ya masa ya kwana acan
yanzun shigowar sa kenan,ƴan gidan mu rakaɗi ne ya kaure anga Nana anga Nana Aunty
Hajara da ta fito ɗauke da Al'ameen Aunty Mama ta miƙama shi shi ita da Gwaggo da
Baba Saude suka shiga mota Habib ya jasu suka biyo bayan mu dan har ya fita daga
gidan,a asibitin ma abin ya basu mamaki dan jini ya ɓalle sosai yake zuba da ƙyar
da siɗin goshi jinin ya tsaya sannan likitar ta fito mamaki ne ya kama ta ganin
yanda wurin ya cika da mutane mutmushi ta yi a ranta tace ƴar gata aka kawo da
alama Alhaji Baffa tafi kalla ganin shi tsoho amma a tsaye kyam sai ƴar sanda ne
kyau,ƙarasowa ta yi nan akai ma ta duru duru da ido dama kowa na dashi dan Iyyo
muka kwaso,Babban Yaya ta kalla"yallaɓai a gaskiya tana buƙatar jini cikin
gaggawa..."kan ta gama maganar an yo ma ta caa kowa yana a gwada na sa da ƙyar ta
shawo kansu sannan aka fara gwadawa maaki ne ya kashe su ganin wani jini duk iri
laya masu ɗan kumarin tace a ɗebi nasu su Ya Ashiru kenan da Habib da Kawu iro sai
Ya Haruna sai Ya Khamis amma Babban Yaya da aka gwada shi sai tace muddin aka taɓa
sa to sai an ƙara masa wani dan jinin sa yafi nawa sama shi nashi har yaje ɗari
biyu da biyar tayi mamaki ma da ta ganshi a tsaye,a taƙaice Ya Ashiru ya bata
labarin abin da ke faruwa,sosai tai mamaki haka bayan saka min jinin tasa shi a
gaba saida yaje akai masa allura aka bashi magani ya sha anan cikin asibitin ya yi
bacci da dabara aka ɗakko shi zuwa gida ya kwanta dan samun hutun sa shine mafi
alkhairi kan ya rikice shima.

Kwana uku ana kula dani sannan na dawo dai dai harma yau Aunty Hajara tazo da Baby
na shayar da shi sosai tai murna da dawowata abin har mamaki yake ba mutane,yau aka
sallameni kwana na biyar a asibitin kwana shida kuma da haihuwata kenen gidan fal
da ƴan uwa na jaje dana suna a ɗakina na sauka dan haka yau ba masaka tsinke a part
ɗin mu Aunty Hajara ko gajiya ba ta yi sai hidima take da mutane washegari yaro
suna Ibrahim kawu Iro harda rawa wai shi Nana ta wa takwara to bama shi ba kowa ya
yi mamakin haka kuma ni da Aunty Hajara muka yanke hakan Babban Yaya kuma ya
yarda,a ranar sunan yaro ya kwashi kayan barka kamar za a buɗe shagon kayan yara
duk fa wajen kawu Iro haka aka sha suna abin gwanin sha awa.

Washegari tun farar safiya ƴan nesa sua fara komawa saboda makaranta su Ya Saddi'q
ma wannan karon da kaina nasa Babban Yaya kowa ya tasa matar sa su tafi wannan jeka
ka dawo ɗin ya yi yawa sunyi mamakin yadda na hangi nesa su ba wanda ya hangi hakan
koda su Baffa ne,haka kuwa akai bayan sati guda ina zune sai ga su Ya Maryam wai
sunzo min godiya kallon su nayi na kwashe da dariya"ku yanzu bakuji kunya ba kuna
mata amma tun waɗannan shekarun ba wadda ta taɓa tada boren zata bi mijin ta kuna
gani ni har guduwa ma nayi",kwshewa sukai da dariya"aike ɗin ta dabance mufa bamu
kai ki ƙwarin kwanya ba","to a gaskiya bari na baku shawara zaman inda mazajan ku
suke sai kun fidda kunya kun kula dasu ada an matan basu kai musu hari ba saboda
sungan ba fuska amma yanzu ganin ku wallahi zakuga suna kula su,zan shaidi ƴan
uwana bilhaƙƙi na zauna inda suke amma Allah basa kula mata dan haka kuma saiku nu
na musu gatan ta bazasu marmarin nacan ɗin ba",da mamakin maganganun da nake amma
haka suka yarda dan sunsan wace ni ayi watsi da maganata mutum ya shiga cakwakiya
dan ina hango nesa nima,tare muka wuni har suka gyara min ɗakuna na sai dare na
cika su da abin arziƙi sannan suka tafi suna ta godiya,,,,, ohhh ni Nana wai ni
akewa godiya.

Yau kwana na Hamsin da biyar da haihuwa kuma yau Aunty zata Hajara zata
tafi Ibadan dangin mahaifiyar ta kayan da nasa a kawo mun aka shigo dasu Babban
Yaya na shirin fita yaga Murtala na shige da kaya a ƙunshe da alama atamfofi ya ga
ni murmushi kawai ya yi ya wuce abin sa dan yasan ba a shiga tsakanin mu,da kaina
na kwashi kayan zuwa ɗakin ta tana saka hijabi har ta gama shirin ma ta ganni da
kaya niƙi niƙi"a a Nana wannan kayanfa"ajewa nayi ina nishi"kai kayan nan nauyi
aradu tsaraba ce na kawo ki haɗa da naki yadda dangi dayawa zasu san kinje kinsan
ɗan ƙauye in ka kai tsaraba ko bazai samu yana daraja ka so nake kije a taru
akanki",dariya ta yi"Allah ya shirye ki Nana kedai ba zaki canja hali ba ko",zama
na yi a bakin gadon ina zuge akwatin Al'ameen"dan Allah Aunty Hajara ki kimin wani
alƙawari mana",itama zaman tayi"ki kwantar da hankalin ki Nana indai kan kula da
Al'ameen baki da matsala da ni",kallon ta na shiga yi seƙe seƙe"wallahi Aunty
Hajara kina bada ni amma ina dawowa kula da Al'ameen ko Mama ce ƙarewarta zata ja
dake ne bare ni dan Allah kibar wannan zancen ni in kinje don Allah karki nu na
musu bake ki ka haife shi ba saboda zasu so ace a shekarun ki kina da ɗa
kema",sanyi jikin ta tayi"taya haka zaiyuwu Nana","me ya sa bazai yiwu ba baya kama
dake ne ko kuma da wata matsala ko ƴan uwana sunsan ɗanki ne please Aunty
Hajara","shike nan Nana naji daɗi yadda ki ke min akan yaron nan","daina jin daɗe
wallahi Mu azzam ma ina ya ye shi zan an tayo miki shi ko kin manta ƴaƴa maza naki
mata nawa",tafawa mukai"ban manta ba kice ni daia abayarwa zan ƙare ke kuma a karɓa
ko",dariya na yi"eh ai gwara hakan kinga ai baza muyi ƙasa ba ko","to hakane bari
mu tashi jirgi ba jiran mu zaiyi ba",miƙewa na yi ian turo ɗankwali gaban goshi"ai
kuwa dole a jira uwar me shi muje ni zan kaiku airport ai dan nasan kun gama da
Babban Yaya tunda naga ya fita","mun gama kuwa muje to uwar ƴan mata",ƙugu na
girgiza ma ta"wannan suna yamin uwar ƴan maza",duka ta kawo min na goce na fita da
gudu,Mu azzam tazo ta ɗauka sannan aka sa kayan a mota na wuce kai su air port.

Daga can gantali daɗi gidan Umma na wuce na tarar da ƙanwar ta tazo ita na
tasa a gaba tamin kitso tana yi tana mita wai warewa yake ni kuma nace sai anyi
tana gamawa tamin dilka cikin lokaci kaɗan na sauya na ƙara haske fiye da da ban
bar dai bar gidan ba sai la asar sakaliya nan ma wajen Auntyn Mama na wuce dan Mama
ma bata nan tana nasu garin tama fi sati a can,tana gani na ta shiga mamaki"wannan
yarinya Allah ya shirye ki gyaran jiki ki ka je",matsawa na yi daga kusa da ita"eh
mana Aunty Mama to an daɗe ba a haɗu ba ai gara yaji sauyi",salati ta saka tana
dafe kanta"ohh ni Halema to dan gidan ku tashi ki tafi ɓangarenki","yanzu ma kuwa
dama tsummin nan nazo ki ba ni kona sata",tashi ta yi tsaye"gashi jeki ɗauka karki
min fitsara anan",tashi na yi na lauk Mu azzam na ɗau galan ɗin tsumi amma da wasu
na tafi tana ta min dariya ina shiga na kwantar da shi na shige kitchen kazar tarar
ango na gasa sannan ƴan abubuwan da bazasu hana ciki sukuni ba ana magaruba na gama
na shige wanka na jima ina saɓe jikina da sabulun haɗi na asali na kashe kuɗi akan
sa shi yasa ko gifta ka nayi ba tare da nasa turare ba saika ji ƙamshi kwana arba
in da biyar kenan ina wanka dashi kunga kuwa ai yabi jiki ko,mai na ma daban yake
kudai wannan jiki nashan haɗi ko kun manta burin Nana ne kan Babban Yaya saian fi
masa ko wacce mace a duniya amma banda Aunty Hajara ta, saida nayi sallar isha
sannan na shirya cikin riga mara rufin asiri fam ɗarinka tsirara inji Mama shirya
Mu azzam nayi na sashi a gadon sa dan yau bai kwanta min a gado ya takura min,ina
falo a kwance kwanciyar ma ta iskanci ba bacci nake ba amma nayi kamar me bacci
sanda ya shigo bai ganni ba saida yazo zai wuce kawai ya ganni kwance duk ƙirjina a
waje aka ma cinyoyi na kai kace na shekara ne ina baccin da kayana zasu tattare
haka,fasa wucewa ya yi ya dawo baya inda nake saurin ƙara rufe idona nayi dan dama
kannewa na yi so nake naga zai wuce ne murmushi na yi a raina na ce ka kamu Babban
Yaya,zama ya yi a ƙasan kujerar yana ƙare min kallo saukar hannun sa naji a jikina
yana sha cinyoyina ban motsaba ganin haka ya ɗauka bacci nake saman wuyana ya shiga
shafawa zuwa ƙirjina inda ya fito lumshe ido ya yi"ina ƙaunar ki da komai naki Nana
ke ɗin a jinina ki ke bazan iya moruwa ba muddin bakya kusa da ni..."wuƙil na buɗe
ido na wuntsulo na faɗa kansa"da gaske ne Babban Yaya",murmushi ya yi yana lumshe
ido saboda jikin sa da kaya amma saida ɗumin jikina ya ratsa shi,rungume ni ya yi
sosai yana shinshinar wuya"fin ma haka Nana ke iya hakan baki na ya furta miki amma
yafi a haka a raina",kaina ɗago a bazata yaji na ɗora bakina akan nasa dama kaɗan
yake jira sai dai me yau abin yasha banban da ko yaushe hadda na shiga goge masa
dan dana sakesa ya miƙe kasa tsaiwa ya yi,hannun sa na kama ina dariya"taho muje
amarya dan yau nice angon ka kaza can babban gashi kaci kai ƙyat",ƴar dariya ya yi
ya bini ni na tayashi wanka yasa kayan bacci sannan muka zauna akan kafet a ɗakin
dan bamu je ko ina ba anan na aje komai saida yaci ya ƙoshi sannan ya huta yabi
jikin sa jimshi ya fara yi ba dai dai sai ya kalleni idanuwan sa na kalla nai
dariya"ka fara tsumuwa kenan to taho Babban Yaya ka gama tsumuwa a gado",shi dai
yana jina amma baya fahimta ta,tun anan na jefar da rigar na bishi gado tare da
aton bargona baƙi saboda ƴan sa ido kalar su o o dan bana so aje min wannan tarihin
suna tsokana ta.

Washegari saida nakai tara ina bacci shi kuma yana zaune yana kallo na yana
kallon Mu azzam dan shima bai tashi ba,buɗe ido na yi ina miƙa da salati kawai nai
arba dashi yana ƙaremin kallo,murmushi na masa shi kuma ya kaɗa kai"faɗa min me ki
ka ba ni naci nace shi kuma wancan me tashi tare da me kiran sallar me ki ka masa
yake bacci har yanzu"dariya na kwashe da ita ina cire bargon jikina"Babban Yaya
kenan sannu jiya ka darzu yajin angwaye na baka mana shi kuma na banka masa maganin
bacci dan karya hana amaryar samun nutsuwa bari kaga yanzu zai tashi",kan na gama
rufe baki ya tsala ihu"kaji ba yanzu kaima kwanta ni kuma bari na kula da
wancan"kai ya girgiza"Allah ya shirya min ke Nana","amma dai ba a wannan fannin ba
ko in na shiryu kuma ya za ayi kenan ana kwasar amarcin",cikin bargo ya shige yana
kaɗa kai ni kuma sauka a gadon ina dariya.

43

BAYAN WATA BIYAR

Nayi shar kamar ba ni ba a yanzu aka samawa Al'ameen makaranta nagartacciya kuma
hankali kwance dan mun daina tunanin komai kuma.

Rayuwar kowa a Familyn mu ta saitu Babban Yaya ya cika burin Abba kowa ya gane ɗan
uwan sa ba maƙiyin sa ba ne,yayyen mu da iyayen mu kai ya ƙara haɗuwa su Hajiya
Harira ko wacce ta yi aure amma Hajiya Salma da Safiyya miji guda suka kuma aura
abin ma abin dariya.

Su Abba ana nan ana wahalalliyar rayuwa rai kwa kwai mutu kwa kwai ko sau ɗaya
kuma basu taɓa ba mu tausai ba Umma ce kawai abin tausai ƴaƴa uku tayi asarar
haihuwa amma da yake mace ce ita mai kai zuciya nesa ko tunanin su bare maganar su
ma ba ta yi kullum tana tare da Iyyo ko tana wajen su Mama iya nan take rayuwar ta.

Habib ya koma Niger dama akwai yarjejeniyar duk sanda yake son dawowa zai koma dan
haka ya koma shida matar sa da ɗansa dukiyar sa kuma yana juyata yadda yake so.

Umma da Baba da Habu sai sam barka dan Habu ya tsaya da ƙafar sa shima da
taimakon ni da Babban Yaya a yanzu ma baka cewa ba ƴan uwa muke ba saboda yadda
muke zumunci shima anan gidan namu ya samu wadda yake so ƴar Kawu Iro an ma tsaida
magana an bashi ita aure ne ya rage kawai .

********

Yau tun safe na tashi dan Babban Yaya gobe zai tafi kuma tare da Aunty Hajara
zasu wuce shine wai kwanan ta ne tabar min na riga shi tashi dan yanzu bama shirin
wa ni abu dama dan ba mace a tare dashi ne dalilin da muke masa shiri,to yanzu
akwai dan haka kayan sa kawai na haɗa masa saboda da daddare zasu bi jirgi Abuja
gobe su wuce kuma.

Ina saka kayan sa a jaka naji an mintsinar min ciki,da sauri na goce dan nasan
shi ne"bashi kaci kasa ni bana yafiya","ni kuwa nasan bakya yafiya yarinya dan
gashi na ga ni kin rama abin da na taɓa miki",ƙara juyowa na yi"me ka min Babban
Yaya da har ban manta ba na rama ban san na rama ba?",ƴar dariya ya yi yana jawo ni
jikinsa"kawo kunnen ki kiji",kunnen na miƙa masa,a bazata ya cije ni ya miƙe yana
dariya"dama tsokanar ki na ke malamma Nana ustaziyyyya Nana",dafe kunnen na
yi"saboda kasan duk bana ɗaya daga ciki shine kasa musu alamar ja haka",kai ya
dafe"ihuu ai kuwa ke ce Babbar Malama kalli fa yadda ki ka janyo ra ayin Hajara duk
tsaurin ta da masifar ta take mugun son ki kamar ba kishiya ba"ƴar dariya na yi"to
ai duk macen da ke tsoron kishiya ma ni ta bani kunya kuma mazan in aka nu na muku
ana tsoron ta kunfi yin na ta","inye ke nan har me zaki cewa mata kuwa","kasan
Allah a yanzu a taron mata na duniya a tsaida ni a gaban su wallahi ina da abin
faɗa musu","in tambayeki mana Nana","ina jinka Babban Yaya Sahibin Hajara da
Nana",ɗan murmushi ya yi"me yasa bakya tsoron kishiya? kuma ki ke jin haushin wadda
tace baza a ma ta kishiya ba?",ɗan numfashi na ja na jawo shi ya zauna kusa da
ni"maganar me tsawo ce zauna kaji in da gyara saika min,kasan ita wannan rayuwar
yanzu kowa kanshi yake so,a zamanin da mata da kansu suke gano wa ta macen suce
mijin su ya aura badan sun gaza komai ba sai dan kawai a zauna tare kuma matan kan
layi sun ragu,mu matan yanzu wallahi hassada ce ta mana yawa mijinki na da kuɗi ko
rufin asiri saiki ce ke a dole ba za a miki kishiya ba kuma wata shegiyar ƙwandala
ma bazata bari wani ya ƙaru da shi a adukiyar mijin,wata ma kamar kuɗin ubanta
malamai da bokaye zata shiga ta hanashi alheri kai wallahi ko zakka za ai sai dai
ita ya ba ta,kuma masu wannan ka ɗiri feren da yawan su mata huɗu suka taso suka ga
ni a gidan su kai wata ma auran uban nata yakai sau goma sha,wai kuma itace ke cewa
ba za a ma ta kishiya kai bazama ta zauna da kishiyar ba kamar dan ita aka halicci
she,to indai kina da tunani da hangen nesa dole ki bari a miki kishiya kai
kishiyoyi ma kuwa muddin kina so ƴar ki ta auru kuma ƴar uwar ki ko ƙanwar ki su
auru to dole ki bari a miki ita to,ko dan kinje a ta farko a gidan ki saiki ce
lallai naki ma ana farko zasu waya faɗa miki haka, kar shakkar komai ki tuna kamai
ya yi zafi maganin sa Allah duk bin bokaye da ƴan tsubbun ta ki gama ta da Allah
kisha kallo komai daren daɗewa sai ta faɗo ƙasa warwas,sau tari mata ba kishiya
muke tsoro ba dame zata zo muke tsoro,to wallahi ni koda uwarta zata zo indai miji
na sona an wuce wajen tabbas zan saita ma ta zama ko na saita ma hanya ta koma inda
ta fito,dan wata shegiyar a gidan tazo ta same ki ke da ƴaƴanki sai tace sai kin
fita kin bar ma ta gidan da mijin kamar wani ƙanin uban ta, to wallahi bana tsoro
saina kwana dadduma ina miki muguwar addu'a ni da ke aga wazai nasara,wata kuma
zata zo da lumana ita uwargidan ce za a samu matsala daga ɓangaren ta kowa dai
akwai nasa amma tabbas dole ama mata kishiya ko kisamu kishiyar bariki dan basa
wuya",ƴar dariya ya yi zai magana Aunty Hajara da ke tsaye da Mu'azzam tun ɗazu ta
riga shi"zan buɗe miki makarantar faɗakar da mata Nana dan ko ni bazan iya zayya no
wannan bayanin naki ba amma zan na bada labarin farkon zaman mu kin wahalar da ni
nima",dariya na yi na miƙe tsaye"ai Aunty Hajara ina sassauta miki ma dan ina
ƙaunarki tun farko wallahi da ƙin gaske nake miki da yanzu kina da tabbai na bama
tabo ba dan bana da tausayi indai na siƙe",jinjina tamin"ni zan faɗi haka mana
tunda haka nan ki ka liƙamin suna wai muguwa muguwa me ihu kawai",kashewa mukai da
dariya ta miƙo min Mu'azzam tana faɗin"wallahi tsoron ki nake Nana tun da can,dan
ko a fuska aka kalle ki ansan makira ce ke shi yasa nake fatan kar yaran ki suyo
halinki dan in suka yo ki to zamu ɗinka gajerun wanduna ne dan ko basa fita ayi a
waje ai za a je makaranta, Allah dai ya ƙara haɗa kanmu ","to ameen"ya faɗa,dariya
muka ƙara sawa na ce"Allah ka shirye ni gaskiya na haɗa *GWARAMA*"

Alhamdulillah ƴan uwa anan kawo ƙarshen wannan littafi ina godiya ga Allah da
ya ara mana dama ni na rubuta ku kuma ku ka karanta fatana Allah yasa mu dace da
alkairin da ke ciki kuskurena kuma Allah yafe min kuma ku yafe min taku a kullum
*FATIMA AMINU*
*(UMMU SADDI'Q)*

*FATAN NANA TA FAƊAKAR DA KU BA SHIRME KAWAI TA MUKU BA*

*Mu sake haɗuwa a GWARAMA ɗin danjin wace badaƙalar ce kuma a ciki,shima fa masa
salon daban ne ku dai ku kasance da UMMU SADDIQ*

*Ina godiya ga Iyayen Jariri*


Mrs Abdullahi Writer
Mamie Yusuf Dabo
Maman Afrah Writer
Ameera Adam Writer
Leemart pinky Writer
Zee frety Writer
Meenerh Writer
Shamsiyya manga Writer
Hauwa Aliyu Sani(Maman Sajad)
N.Yarema
Muhammad MK
Abbas MK

*Ina gaishe da ƴan ƙungiyar First class kafatanin su*

UMMU SADDIQ TAKU ♥️


08146711395

You might also like