You are on page 1of 314

[10/2, 12:27 PM] Zeenaran🫶🏻: *_Typing📲_*

*_BABU SO....!!_*
_(Miya kawo kishi?)_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_01_*

*_MALAYSIA (SABAH)_*

..........A hankali sautin kukan ke tashi tamkar mai rairashi da gayya. Sai dai
daga jin yanda salonsa ke fita kasan tsabar daɗewar da maiyin nasa ya ɗauka yana
yine ya kaisa ga galabaita. Kasa jurewa nai na kutsa kaina cikin gidan madai-daici
da ke ɗauke da dukkan kayan more rayuwa najin daɗi. Falo ne babba masha ALLAH, sai
dai duk girmansa banci karo da kowa a cikinsa ba. Shiru nai alamar tunani, (to ta
ina kenan sautin kukan da yaja hankalina ke fita?) rashin mai bani amsa ya sani
fara waige-waige a falon. Tabbas ba'a nan ɗin bane, hakan ya sani kutsa kaina dan
zuciyata ta banni tabbacin a window da naji kukan ɗakine.
Takun sakkowa da stairs ɗin da'aka kawata adon falon da shi ya sani
maida hankali can. Hamshaƙiyar mace kamila mai yanayi da fulanin ƙasar Nigeria ce
ke taku cike da nutsuwa da kamala tamkar yanda shigarta ta kamala ta ƙawata
mutuncinta ga mai kallo. Sam banyi zaton ko (zo na kasheki) ta sani da yaren hausa
ba, amma a mamakina saina tsinkayi kamilar muryarta na ƙwala kiran sunan *_Anam!_*
a ɗan kausashe. Ƙara kausasa muryarta tayi ganin babu alamar wadda take buƙatar
ganin data kira da suna Anam ɗin ta fito.
“Anam! Idan har kika bari na shigo inda kike ki tabbatar sai jikinki yayi
tsami kafin kibar ƙasar nan. Shashasha kawai wadda bata kishin kanta. To banda mara
kishin kai wake ƙin tushensa? Ba kukan hawayeba kiyi na jini ma babu fashi zuwa
Nigeria ki zauna agareki, k idan ma kika ƙuleni ALLAH kin koma can da zama kenan
keda ƙasar nan sai yawo”
Sautin kukan da aka sake fashewa da shi ya sani waigawa da sauri, ƙyaƙyƙyawar
budurwa black beauty mai ɗaukar hankali da sam bata kama da matar a yanayin jiki
sai na kamannin jini kaɗan. A ƙiyasi na yanayin jiki kai tsaye zance bata wuce
shekaru sha bakwai ba. Sai dai a mizanin hankali da sanin masu irin yanayin jikinsu
wajen ɓoye shekaru zan iya karyata zuciyata. Amma kai tsaye ban san shekara nawa
zan bata ba. Dan sam bata da wani tsaho, tana nan dai ƴar cif-cif ga karamin jiki
ga rashin tsayi kamar wata ƴar kanwata can (😂🤣ban dai faɗi suna ba ato😜). Tabbas
kyaƙyawa ce, dan duk da kukan da idanunta suka nuna alamun taci hakan bai hana
bayyanarsu dara-dara ba duk da suna a cikin farin siririn gilashi. Ga gashin gira
da dogon hancinta (kamar na bilyn Abdull🙄 saura wani yace ba haka ba, bansan
jealous😒😜). Kai atakaice dai yarinyar masha ALLAH. Sosai hawaye ke cigaba da bin
kumatun ta tamkar an bude fanfo. Matar daketa masifar ta sake zuba mata harara a
kausashe tace,
“Haɗiye min kukan nan kafin nazo na sassafa ki a wajen sakarar banza”.
Da ƙyar ta shiga ƙoƙarin haɗiye kukan nata. Sai dai hawayen sunƙi riƙuwa.
Cikin rawar murya ta dubi kamilar matar da take kamani da ita a ɗan fisge, “Mamie
na tuba ALLAH na daina duk abinda baƙwaso ke da Abie ”.
“Dainawar taki ko cigaba bazai miki amfanin komaiba ai, dan zuwa Nigeria dai
babu fashi tunda kin san abu mai muhimmanci ne zai kaiki. Dolene kije kiyi saves
ɗinki a ƙasar haihuwarki kodan gaba zai miki amfani, dan nan ɗin da kika ɗauka
ƙasar uwa da uba ta aro ce lokaci kaɗan ya rage mu barta muma ta ishemu”.
Kuka ta sake fashewa da shi tana daddaga ƙafa. “Ni wlhy bana son Nigeria,
zafi, sauro ga shegen hayaniya. Ni basai nayi saves ɗin ba dan bazan taɓa rayuwar
Nigeria ba balle har na damu dayin aiki saves yaymin amfani. Please Mamie....”
Cikin katseta Mamie taja wani tsaki. Kota kanta batabi ba ta nufi wata ƙofa a
fusace tana faɗin, “Ki wuce driver ya kaiki wajen gyaran jiki dan Abie ɗinki yace
da wuri zaku wuce, kin san kuma baya son wasa da lokaci”.
Kuka ta sake barkewa da shi kai kace Abie ko Mamie ɗinne aka aiko mata sun
mutu. Harga ALLAH bata son zuwa Nigeria dan tana matuƙar wahala da yanayin zafinsu.
Ga shegen sauro ɗinnan na kano tamakar kasuwancinsa sukeyi. Uwa uba zaman gidan
Uncles ɗinta data tsana saboda mugun halin matar Daddy, na matar ma bai cika
damunta ba dan sai ka shiga sabgarta take takuraka. Tafi tsanar babban ɗansa mai
shegen baƙin hali da mugunta da har ya zarta uwar tasa. Sam bata ko ƙaunar ganinsa
dan basa haɗa ko hanya bare shan inuwa guda, shiyyasa a mafi yawan lokaci idan taji
zai zo malaysia take guduwa wajen Aunti Mimi. Da ance kuma zai je wajen aunty Mimi
ɗin itama dake aure anan ƙasar malaysia ɗin sai ta gudo ta dawo sabah. Har ya gama
zamansa bata yarda su haɗu. Kai itafa a kaf rayuwarta ma bai fi sau uku ta taba
ganinsa ba. Tun kuma a ganin farko taji ta tsanesa saboda tsawa da yay mata dan ta
fasa glass cup a mistake a gidansu, ita kuma ta murguɗa masa baki yako kama lips
ɗin ya murje har sai da sukai kumburi duk da shekarunta basu wuci goma ba a lokacin
ta kasa mantawa ta kuma kasa daina jin haushinsa. Hakama haɗuwarsu ta biyu sai da
yay mata mugunta, kai idan bata mantaba ma dukansu yay ita da Aysha ƙanwarsa saboda
sunje wajen bikin birthday na ƙawar Ayshan ba'a sani ba. Aiko dukan nan ya shigeta
dan harda zazzaɓi kasancewar tunda ta tashi da wayonta da hankalinta ba'a taɓa
dukanta ba sai shi mugu.........
Ta jima a wajen tana saƙa mai fishsheta kafin ta haura saman stairs.
Cikin mintunan da basufi sha biyar ba ta fito sanye cikin wando da riga ta ɗaura
jibgegiyar rigar sanyi data kai mata har gwiwa kasancewar lokacinsa ne, duk da veil
data naɗo a kanta kamar yanda larabawa keyi hakan bai hanata jan hular rigar da
bakinta keda gashi mai laushi har saman kanta ba. side bag dake hanunta ta saƙala
cikin wuyanta sai faman tura baki take. Duk da Mamie na zaune a falon tana yanka
tufa ko kallonta batai ba....
“Mamie na shirya kuɗin to”.
Batare da Mamien ta tanka mata ba ta tura mata card ɗinta na ciran kuɗi. “Na gode
ALLAH ya ƙara buɗi mai albarka”. Ta faɗa tana kama hanun Mamie ta sumbata tare da
ɗagowa ta sumbaci kumatunta kamar yanda dai larabawa sukanyi. Mamie bata kulata ba,
hakan yasa taƙi tafiya idanunta har sun cika da kwalla, dan tunda taga Mamien bata
maida mata murtanin sunbar datai mata ba tasan har yanzun tana fushi da ita.
Haka kawai murmushi ya suɓucema Mamie, ta girgiza kanta da kamo hanun tilon
ƴar tata da a kullum cikin jimamin ranar da aure zai rabasu take, dan ta tabbatar
hakan na gab da faruwa. A ido zaka ɗauka Anam bata da wani shekaru saboda ƙaramin
jiki da ALLAH ya bata. Sai dai kuma a zahiri shekarunta ashirin da uku kenan a
duniya. Itama sumbatarta tai da ɗanjan kumatunta, hakan yasa Anam yin ƴar dariyar
jin daɗi ta rungume Mamien. Mamie tai murmushi.
“To sarkin taɓara tashi kije ko ƙya dawo da wuri”.
“Okay Mamie bye”.

Batafi awa uku da fita ba sai gata ta dawo, ta kara wani irin ƙyau da
kwarjini tabbacin taci gyara tako ina. Dan babu abinda fuskarta keyi sai shining da
glowing, ga wani uban ƙamshi mai saka nutsuwar mai shaƙa. Fuskarta ƙawace da
murmushi ta nufi ƙyaƙyƙyawan dattijon dake tsananin kama da ita dan shima black
beauty ɗinne, amma kasancewar akwai jin daɗin rayuwa baka ganin komai tare da shi
sai ƙwarjini da ƙyawun haiba. Ga baƙin sajen fuskarsa daya ƙara ƙawata ƙyawun nasa.
Shima dai bashi da wani jiki, dan komai na Anam bashi da maraba da nashi, hakan na
nufin dai kamaninta ɗaya da mahaifinta.
Zuwa tai ta rungumesa ta gefe tana dariyar farin cikin ganinsa. Shima fuskar
tasa da murmushi ya riƙo hanunta cikin nasa. “Uhhm Mamana irin wannan ƙamshi haka
kamar amarya”. Fuskarta ta ɓoye a kafaɗarsa tana dariya. “Nidai Abie ba wani
amarya”. Dariya kawai yayi baice komai ba. A haka Mamie ta fito daga kitchen ta
samesu. Fuskarta ɗauke da murmushi take kallon mijin nata abin sonta da ƴar tasu
tilo ɗaya a duniya. Anam ta zame veil ɗin kanta tana nunama iyayen nata kanta daya
sha gyara masha ALLAH, sai sheƙi yake da ƙamshi gashi da tsaho sosai. Gaba ɗaya
kamaninta irin na Abie, gashin kai da gira zuwa gashi ido ne kawai irin na Mamie,
sai ko maganarsu dake kama itama.
Sosai suka shiga yaba ƙyawun da gyaran nata yayi, cikin tsokana Abie ke faɗin,
“Mamana kin zama kamar wata amarya da gaske, kodai kawai idan munje na aurar dake
ma?”.
Idanu tai mugun zarowa, sai kuma ta kwaɓe fuska har hawaye na cikon mata ido.
Lips ɗinta sai rawa suke tama rasa mizatace. Dariya Mamie da Abie suka shiga
yimata, hakan yasata tashi da gudu ta haura sama. “Kin gani kin kunnata”.
“Na kunnata ko ka kunna abarka”.
Cewar Mamie tana murmushi. “To aini abin na damuna, idan na tuna wataran aure zatai
ta barmu hankalina na matuƙar tashi, gashi shekaru sunyi nisa, kamata yay ma data
gama saves ɗin nan kawai a wuce wajen Humairah”.
Ajiyar zuciya mai nauyi Mamie ta sauke. Murya a raunane tace, “Hakane ya dace,
sai dai kuma a kullum cikin korar samarin take ai taƙi bama kowa dama anan ɗin
balle Nigeria. A kullum kallon kanta take a yarinya”.
“To ai yarinyarce, duka yaushe kika haifamin ita. Ni badan auren ya zama
doleba dana bar abuta naita kallo kawai”.
Sosai Mamie ke dariya, cikin riƙe baki tace, “Lallai ashe mu iyayenmu basa
sammu kenan da aka ɗakko aka baku. Lallai ashe lokacin auren munada kallo kenan dan
za'a sha show rabuwar ƴa da uba”.
“A zakusha kam. Dan mijin nan zai sha gargaɗi, shiyyasa nafi son ma ta auri
ɗan Nigeria dan ƙasar nan ta isheni haka”.
“To ALLAH ya zaɓa abinda yafi alkairi. Ya kawo nagari”.
Da amin Abie ya amsa cikin jimami da damuwar rabuwa da tilon ƴarsa.

*_Washe gari_* kamar yanda Mamie ta faɗa hakance ta kasance. Dan kuwa dai Abie da
Anam sun wuce ƙasar haihuwarsu Nigeria. Tasha kukan rabuwa da Mamie duk da tasan
bazatai shekaran Mamie bataje ba tunda ita sunce bazata zo ba har saita kammala. A
jirgi barci ta dinga ramuwa wanda ta gagara yi a daren jiya saboda alhinin yin nisa
da iyayenta datai matuƙar shaƙuwa da su take mu'amula da su tamkar ƙawayenta. Sune
abokan shawararta, sune abokan kukanta, sune abokan dariyarta, sune abokan
rayuwarta. Bata da kamarsu dan su tafi sani fiye da kowa a duniya.

*_04: 25pm_* jirginsu ya sauka ƙasar Nigeria Aminu kano international airport, a
gajiye Anam take matuƙa duk da barcin da tasha, sai faman langarema Abie take,
shiko lallaɓa abarsa yake dan yasan yanayinta bata son wahala sam. Abu ƙalilan ke
galabaitar da ita tai laushi tiɓis. Ajiyar zuciya ya sauke a hankali lokacin da
suke fitowa idonsa ya sauka akan ƴan uwansa abin ƙaunarsa. Suma da alama idonsa na
kansa, dan tuni suka nufosa fuskarsu ɗauke da murmushi. Abie yay azamar nufarsu
shima suka rungume juna suna maijin farin cikin haɗuwa.
Sosai Anam take dubansu da murmushi, tana ƙaunar uncles ɗin ta kam, dan suma
suna ƙaunarta. Matar big Uncle ɗin nata da ɗansa babba ne dai sai a slow, amma
sauran matan small Uncle da yaransu duk bata da matsala da su musamman Aysha
aminiya.
“Oh my Mah-mah welcome”. Uncle ɗin da suke kira da Daddy ya faɗa lokacin da
suke sakin juna da Abie ya buɗe mata hannayensa alamar tazo garesa. Hanun trolley
ɗinta ta sake da nufarsa a kasalance fuskarta ɗauke da murmushi ta matsa ya ɗan
rungumeta ta gefe.
Small Uncle ɗinta da suke kira da Abbah yay murmushi tare da shafa kanta
yana faɗin, “Ayya Mamana kina nan dai a ƴar ficikar ki ba tsaho ba girman jiki ga
ragwantaka”. Fuskarta ta ɓoye jikin Daddy tana dariya da faɗin, “Lah Abbah na ƙara
girma fa, kuma yanzu bana ragwanci”.
Daga Daddy har Abba da Abie dariya sukeyi, Daddy yace, “Nima dai ban gani ba,
jibeki a galabaice a ƴar wannan tafiyar ta awoyi, shekara huɗu kenan ban ganki ba
amma kina nan yanda kike fa”.
Sosai ta shagwabe masa ƙyaƙyƙyawar black beauty face ɗinta tana ƙyafta
idanunta manya ta cikin glass ɗin da alamu suka nuna na ƙarin gani ne.
Ko amota ma Abie da Daddy da abbah dake a baya zaune tuni sun balle hira,
itako kallon hanya kawai take dan tana gaba a gefen driver. Jikinta liƙis yake da
gajiya, ga wani irin zafi dake shigar ƙofofin gashinta kamar ta fasa kuka dan bata
ƙaunar zafi, shiyyasa duk sanda zasu zo Nigeria sai tai kuka bana wasa ba, idan
sunzo kuma sam zaka sameta babu sakewa inhar lokacin zafi ne. Shiyyasa mafi yawan
lokuta Abie yafi son shirya musu zuwa Nigeria a lokacin sanyi ko damuna saboda ita.
Sun sami tarba ta mutuntawa daga matan gidan guda biyu, wato aunty amarya
da mom. Amma babu Big mom balle alamarta. Hakan ba sabon abu bane, shiyyasa daga
Abie har Daddy da Abbah basu nuna sun damu ba. Yaran gidan dai duk sun wuce
islamiyya, sai ma'aikatan ne keta shigowa suna mika gaisuwarsu domin duk wanda ya
kwana ya tashi a gidan yasan muhimmancin Abie ga Daddy da abbah dama jama'ar gidan
gaba ɗaya. Sai da suka kwashe kusan mintuna arba'in sannan Mommy ta shigo tana wani
ciccin magani. Babu wanda yabi takanta harta samu waje ta zauna tana gaida Abie.
Cikin sakin fuska ya amsa mata tamkar sauran ƴan uwanta, ya kuma tambayeta yara.
Duk wannan bidiri Anam na kwance a kujera lamo tana kallon kowa a galabaice,
dan ma ta samu sauƙin zafin tunda suka shigo sanyin ac'n falon Daddy na ratsata.
Gaishe da Mommy tayi itama a ɗan shagwaɓe, bata wani amsa mata da ƙyau ba. Sai taji
duk babu daɗi har fuskarta ta nuna hakan dan ita yarinyace mai son kulawa. Hakan
yasa Mom tai murmushi da shafa kanta cike da kulawa take faɗin, “Mamanmu har yanzu
dai ke raguwa ce”.
A langabe Anam take dubanta har idanunta na nuna alamar tara kwalla. Murya a
raunane tace, “Mom na gajine ga zafi”.
Dariya duk aka sanya a falon, aunty amarya cikin dariya tace, “Babbar magana.
A haka za'ai saves ɗin kuma.....?”.
“Kema dai ƙya faɗa Hafsatu. Dan wannan ƴar taku ragwantarta harta wuce
tunani, ina tausayama mijin da zaku mannawa”.
Mom da aunty Amarya suka shiga kare Anam da faɗin koma waye zasu iya
dashi ai. Mommy kam sai faman taɓe baki take da yatsine fuska tamkar bata a falon
ma....

A duk sanda suke a ƙasar gidansu dake jikin nasu Daddy ne masaukinsu,
wannan karon kuma babu Mamie sai Daddy yace bai yarda su sauka anan ba duk da Abie
ya nuna shi dai zai shiga can ɗin dan bazai so takura iyalan ƴan uwan nasa ba duk
da kanine shi a garessu. Babu yanda su Daddy suka iya suka haƙura kawai suka barsa
akan zuwa anjima sai ya shiga can ɗin yanzu masu aiki zasuje su gyara. Hakan kuwa
akayi, masu aiki sukaje suka tsaftace ko'ina da taimakon aunty Amarya, ita kuma ta
koma sashen Mom ɗin kodan kawarta Aysha da basu san da zuwanta ba dan su Daddy sun
ɓoyema kowa. Duk da jin zafinta bata wanka da ruwan sanyi, dan haka ta haɗa mai
zafi sosai tai wankan a bedroom ɗin Mom kafin su Aysha su dawo islamiyya, tana
fitowa kobi takan abincin da Mom ta ajiye mata bataiba ta ƙure ac ta kwanta sai
barci. Yin barcin nata babu jimawa sai ga yaran gidan an dawo dasu daga islamiyya
cikin katuwar bus ɗinsu ta zuwa makaranta. Kowannensu sashen uwarsa ya nufa, mazan
kuma suka nufi sashensu na samari duk da kuwa babu wanda ya haura ashirin a
cikinsu.
Basu san da zuwan Anam gidan ba sai bayan sallar magrib, samarin suka fara cin
karo da Abie a massallaci, ana idar da sallar isha'i sai gasu da gudu sashen Mom.
Sune suka fargar da ƴammtan gidan, aiko cikin ƙanƙanin lokaci suka hargitse ɗakin
Mom da hayaniyarsu wadda ta tashi Anam ɗin dake tsaka da jin daɗin barci dan bata
salla tana fashi. Tsawa Mom ta musu dan tana salla amma suke ihun nan, tsitt
bedroom ɗin yayi suna sauraren faɗan da take musu na wannan shirmen nasu. Sai da ta
gama suka bata haƙuri tare da janye ra'ayin ƴar uwarsu suka bar ɗakin.
Kai kawai ta ɗan girgiza fuskarta da murmushi, dolene yanda suke murna da
ganin ƴar uwar tasu ya birgeka. Ita kaɗaice ware a cikinsu amma suna nuna mata
tsananin so kamar yanda suma kawunansu yake haɗe duk da dai wataran Mommy kan
birkita kan yaran idan tanajin fitinarta, musamman idan ta takalesu basu kulataba
sai tabi duk hanyar son zuciya ta cusama yaranta ƙananun magana a zuciya da zakaga
sun janye jikinsu da ƴan uwansu har wataran ma kaga an taɓah faɗa, a wasu lokutan
faɗan nasu nayin nauyi, amma wani sa'in sukan fahimci juna da wuri musamman idan
wanda suke shakka a gidan yana ƙasar dan shi babu ruwansa ubansu yakeci gwargwadon
iko. Duk da mutum ne shi mai haƙuri da rashin son yawan magana, sam baya son raini
da damuwa. Sannan duk da halin uwarsa bazaka taɓa ganinsa ya nuna banbanci akan
yaran gidan ba, matan kuma yana girmama kowa yanda ya kamata duk ɗa nagari
yayi........✍

KU DAI KU GARZAYO A DAMA DAKU A CIKIN WANNAN ZAZZAFAR TAFIYAR CIKIN SALON NA ZAFAFA
BIYAR MASU ZAFIN GASKE.

DUKKA LITTAFAN AKAN NAIRA DUBU DAYA (1k) KACHAL

IDAN KUMA DAYA KIKE SO (300)


BIYU (400)
UKU (500)
HUDU (700)

KARKU BARI A BAKU LABARI, DAN WANNAN SALON NA DABAN NE KUMA TAFIYAR MA TA DABAN CE!

ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN

HAFSAT UMAR KABIR


ZENITH BANK
2270637070

SAI A TURA SHAIDAR BIYAN

07040727902

IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA

09134848107

KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN
MASU MATUKAR SANYA NISHADI.

MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.

SAI MUN JIKU MUTANEN AMANA!💃🏼💃🏼💃🏼

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*


[10/2, 12:27 PM] Zeenaran🫶🏻: *_Typing📲_*

*_BABU SO....!!_*
_(Miya kawo kishi?)_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_02_*
.........Alhaji Mustapha Ɗaher wanda akafi sani da (MD Shareff) shine asalin mai
gidan. Tsohon soja ne dan kuwa suna sahun farko na sojojin da sukaima ƙasar Nigeria
hidima tun a farkon ƙarni. Matansa uku. Uwargida Hannatu bata taɓa haihuwa ba har
yanzu da tsufa ya risketa, sai dai ta riƙe ɗan matarsa ta biyu tamkar itace ta
haifesa saboda zaman lafiya da sukai baka taɓa cewa kishiyoyine ba. Matarsa ta biyu
itace Hajarah haihuwarta huɗu da shi. Muhammad shine babba wanda tun bayan yayensa
ya koma hanun Hannatu da suke kira da (Gwaggo). Sai Halimatu itace ta biyu, sai
Abubakar, sai auta Umar. Sai kuma amarya Juwairiyya nada biyu. Usman da Maryam.
Rayuwar gidan MD Shareff rayuwace bahaguwa, dan kuwa dai Uwargidansa da matarsa ta
tsakkiya kansu a haɗe yake, bazaka taɓa ganinsu ka ɗauka kishiyoyi bane. Amma
Amaryarsa Juwairiyya a ware take a cikinsu, dan kuwa sam batajin daɗin zama da su
sai ma ɗan karen azaba da ta dinga fuskanta daga garesu kasancewarta kurmiya.
Juwairiyya nada matuƙar haƙuri da kawaici, duk da wahalar da take sha a hanun
kishiyiyinta bata taɓa ko nunawaba a fuska balle ga wani sai dai idanunka ya gane
maka. MD Shareff yayi iya bakin ƙoƙarinsa na ganin matansa biyu sun daina gallaza
rayuwar amaryarsa amma hakan bai faruba har yabar duniya ya barta da sabuwar
gwagwarmayar rayuwa a cikinsu.
Duk da tsana da tsangwama da su Gwaggo kema Juwairiyya da ware ƴaƴanta hakan
bai hana yaran gidan tashi da ƙaunar juna ba, sai dai kuma Halimatu ta fita zakka a
cikinsu, dan akwai shegen baƙin hali, sam bata yarda Maryam ta raɓeta duk da itace
kanwarta mace tilo. Ahaka dai aka gungura har yara suka tasa Juwairiyya bata huta
ba, ga shi babu miji, ƴan uwanta kuma sunƙi janta a jiki balle ta koma garesu taji
sanyi, wanda ke ɗan tausaya matan yana ƙasar Malaysia yana karatun daya samu tafiya
ta hanyar scholarship. Shima yayantane dan shi take bimawa. Haka tacigaba da haƙuri
har ALLAH ya kawo Yayanta ƙasar Nigeria ganin gida tare da matar da yake aure wadda
ya aura acan ƙasar Malaysia ɗin, amma ƴar Nigeria ce karatu take a hanun yayanta
acan. Kowa ya nuna ƙin matar tasa itako ta nuna soyayyarta gareta dan bataga
aibunta ba tunda musulma ce. Daɗin abinda tayi yasa Yayan nata da matarsa shiga
suka fita wajen ɗauke mata Usman dake gab da kammala secondary school. Ita kuma ya
saya mata gida tabar cikin su Gwaggo.
Wannan abu ya musu matuƙar ciwo, dan ƙiri-ƙiri suka nuna ƙiyayyarsu da
kishinsu akan hakan, tare da dagewa wajen cusa tsanar Usman da Maryam a zuciyar
sauran ƴaƴansu, ita dai tai musu sallama harda kukan sabon zama ta ɗauka diyarta
Maryam da Usman ke kira Mimi suka koma sabon gidansu.

Rayuwa ta shuɗa, komai ya canja yara duk sun girma. Tafiya da Usman yasa
Gwaggo da Mama jajircewa wajen ganin su Muhammad sunyi karatu mai zurfi dan kar
Usman yafi ƴaƴansu. Sai dai shi UBANGIJI ba'ai masa dole, dan kuwa shike bama wanda
yaso a kuma lokacin da yaso. Sun sami nasara sosai ta rayuwa saboda zukatansu cike
suke da son ganin ɗan uwansu bai zartasu ba kamar yanda iyayensu kullum ke kwaɗaita
musu, dan zuwa yanzu da gaske ƙiyayyar Usaman da nuna masa ƴan ubanci tai tasiri a
zukatansu saboda huɗubar mahaifiyarsu da abokiyar zamanta. Sun buge gidansu na gado
kasancewar babba ne sosai tare da siyen na maƙwafta dake son tashi suka ware ma
Usman da Maryam nasu gefe su suka gina nasu a tare su huɗu tare da kason ƴar uwarsu
Halima da tuni tayi aure, koda Usman yazo Nigeria yaga ɗan abinda aka rage musu
baice komaiba, saima ƙoƙarin ganin ya samu kusanci da shaƙuwa da ƴan uwansa yake
kamar da. Hakan bata samu ba, dan babu abinda suke masa sai ɗagawa da fariyyar
sunada kuɗi yanzu, koda aka kaisa turai bai fisu da komai ba. Murmushi kawai yayi,
dan al-amarin nasu yanzu dariya kawai yake bashi. Watansa kusan uku a Nigeria ya
tattara mahaifiyarsa da ƙanwarsa Mimi suka wuce Malaysia, wannan ma ya sake ɗaga
hankalin su Gwaggo, suka cigaba da tunzura su Muhammad.
Tsahon shekara huɗu bai sake waiwayarsu ba sai da aurensa da ɗiyar kawunsa
tilo da suka haifa ya tashi, dan kawun nasa da matarsa mai suna Asiya haihuwarsu
ɗaya mace Aysha Humaira, shaƙuwar dake tsakanin Usman da Humaira ta ɓaci dan kusan
shine yay rainonta, Hakan yasa soyayya mai tsanani shiga tsakaninsu. A Nigeria
sukazo akai bikin duk da ƴan uwansa nata masa wulaƙanci, shidai baibi takansu ba
sai fatan shiriya yake musu.
Haka rayuwa ta cigaba da shuɗawa shi da Humaira ALLAH bai basu haihuwa da
wuriba har ALLAH yayma mahaifiyarsu Juwairiyya da Asiya rasuwa a ƙasar saudia sunje
aikin hajji, mutuwar tasu ta samu asaline dalilin accident daya wanzu a cikin
harami a wannan shekarar. Sun shiga tashin hankali sosai, wanda har yay sanadin
kawunsa ya samu ciwo shima yabar duniya. Girma ya dawo hanun Usman, dan kuwa
ragamar rayuwar ƙannensa biyu ta dawo garesa, wato dai Humaira data zama matarsa da
Mimi. A wannan gaɓar ƴan uwansa sun kirashi sun masa gaisuwa, yaji daɗi har cikin
ransa.
Bayan ya aurar da Mimi ga wani abokinsa dake anan Malaysia shima dai ɗan
Nigeria ne babu jimawa ALLAH yayma Hajara (Mama) mahaifiyar su Muhammad ƴan uwansa
rasuwa itama. Har Nigeria yazo tare da matarsa da ƙanwarsa Mimi dake fama da
ƙaramin ciki, hakan da yayi sai ya sanyaya jikin ƴan uwan nasa dan kuwa su ko auran
Mimi duk da ya basu hakkinsu ƙin zuwa sukai, hakama rasuwar mahaifiyarsa da kawunsa
da uwar matarsa a waya kawai sukai masa ta'aziyya. Ya nuna musu hakan ba komai bane
su manta kawai.
Ɗan shirin da suka samu a tsakaninsu a wannan karon ya samu damar sanin duk
iyalansu, dan kuwa a baya basu taɓa yarda yasan fuskokin matansu ba ma balle adadin
ƴaƴansu ba. Muhammad matansa biyu. uwargidansa Wasila ɗiyar ƙanwar gwaggo nada yara
huɗu a lokacin, babban shine Al-Mustapha da yaci sunan MD Shareff mahaifinsu suna
kiransa da *_Shareff_*. Sai Maheer, Binta, Ishaq da ƙaramin ciki da take kan
laulayinsa. Wasila da yara ke kira Mommy a gidan ba wani sanin Usman taiba amma ta
mugun tsanarsa saboda huɗubar Gwaggo, ƙinsa take tamkar itace ƴan uban nasa ba
mijinta ba. a gefe tana matuƙar jin kishin yana rayuwa a ƙasar waje a ganinta kodai
yaya ya fisu nasibin rayuwa. Ta shiga matuƙar takaicin ganin su Muhammad sun fara
sakkowa akan ƙin ɗan uwansu da sukeyi, dan haka ta shirya sake haddasa sabuwar
ƙiyayya a tsakaninsu kamar yanda Gwaggo ke ɗaurata akan hanya. Sai amaryarsa Ubaida
da suke kira (Aunty Amarya) nada ciki tsoho itama haihuwa yau ko gobe, mace ce mai
son jama'a da haƙuri, duk da ƙiyayyar iyayen miji da take fuskanta da iskancin
kishiya ta zama mai haƙuri da kawaici a gidan. Sai matar Abubakar Mariya da suke
kira Mom. Itama mace ce mai dattako da mutunci. Ba wani daɗin iyayen mijin nata
takejiba saboda Gwaggo itace ke juya Mama, bata son kowa yay farin ciki a gidan sai
ɗiyar ƴar uwarta. Amma haka taita kawaici da shanye haɗata fitinar da aka dingayi
da uwar mijin tasu har ALLAH ya rabasu lafiya da ita. Itama dai yaranta biyu duk
maza. sai dai tana da ciki ɗan watanni biyar. Umar dai yaƙi aure, hasalima ya zama
fanɗararre a cikinsu sai addu'a. Tuni yana kudancin ƙasar sai ya gadama yake
waiwayen kano tun daga karatu, su kansu ƴan uwan ba'a komai suke sakashi a
lissafinsu ba. Rasuwar ma baizo ba sai bayan kwana bakwai duk da mahaifiyarsu ce.
Kamar yanda ƴan uwansa suka gabatar masa iyalansu shima haka ya gabatar da tasa
matar a garesu. Ƙyaƙyƙyawar bafulatana mai tarin ilimin zamani dana addini. Ga
tarbiyya da mutunta mutane.
Babu laifin zaune babu na tsaye Mommy ta tsinci kanta da tsanar Humairah wanda
babu makawa kishine kawai da hassada ke cin ranta, dan kuwa ko ba'a faɗaba Humairah
ta fisu komai na rayuwa. Kasa biye ƙiyayyarta tai ta dinga nunata ga Humairah datai
kamarma bata fahimta ba, dan mace ce data iya zama da mutane matuƙa, sai dai koda
wasa taƙi bada fuskar da Mommy ɗin zata kawo mata raini.
Rasuwar Mama yasaka baƙin halin Gwaggo fitowa muraran gasu Muhammad. Dan kuwa
sun fahimci Gwaggo itace ke tunzura mahaifiyarsu aikata wasu abubuwan ashe. Duk da
tana nuna itace uwa a garesu kamar da can, a yanzu hakan baya hana ta nuna musu
bata haifesu ba ko wani abu makamancin haka. Sannan a kullum burinta taga babu
zaman lafiya tsakaninsu da ƴan uwansu biyu kacal da ALLAH ya basu, kai hatta
lalacewar Umar sun fahimci Gwaggo nada kamasho dan kuwa dai shi da Muhammad sune
ƴan ɗakinta, a yanzu kuma Shareff ma a hanunta yake yaron gaba ɗaya ya tashi a
taɓare ga rashin kunya da rashin mutunci. A kullum cikin jibgar ƴaƴan anguwa yake
da musu ƙwacen abu idan ya gani gashi baya son karatu sam.
Abubakar da yaran gidan suke kira da Abbah ne ya fara nusar da Yayan nasa
Muhammad da suke kira Daddy abinda ke shirin faruwa, yana tsoron su sake samun bara
gurbi bayan Umar a zuri'arsu. Sannan koba komai Shareff shine babba a ƴaƴansu
lalacewarsa na nufin rugujewar sauran ƙanensa. Sosai Daddy ya fahimci Abbah, suka
zauna shawarar matakin da zasu ɗauka akan yaronsu duk da gida ɗaya suke da Gwaggon
sashenta daban itama inda suke zaune da Mama kafin rasuwarta. Suna a wannan halin
Usman yazo Nigeria domin fara ginin wani fili daya saya, a ganinsa ya ƙyautu ya
mallaki muhalli a ƙasar haihuwarsa. Zuwansa ya musu daɗi, dan basu ɓoye masa komai
game da halin da Shareff ke neman shiga ba a hanun Gwaggo. Ya jimanta al'amarin
tare da sanar musu subar komai a hanunsa shi zai ɗauke Shareff ɗin ya koma hanunsa
insha ALLAH. Ba karamin farin ciki sukai ba, tare da ƙara ɗinkewa kamar komai bai
faruba a baya. Ginin da yazo da niyyaryi a nesa da su sai suka hana hakan, suka
tilastashi zuwa ya gina filin da suka rage masa tare da ƙara masa dana cikin
gidansu kasancewar gidan nasu ƙatone sosai kowace mace ma da part ɗinta, ga kuma na
Umar ma da babu kowa a ciki tunda yaki zama. Dan da farko ma na Umar ɗin sukace ya
ɗauka yaƙi.
Cikin ƙanƙanin lokaci aka fara ginin daya tada hankalin Gwaggo da Mommy, babu
kunya suka tada rigimar basu yarda ba. Su su Daddy ma abin har mamaki ya dinga
basu, dan sun rasa dalilin Gwaggo na son nisantasu da ƴan uwansu. Basubi takanta
ba, dan a lokacinma ne suka nuna mata bore, a wajen Halima kawai ta samu goyon baya
dan ita dama sai a hankalice. Wannan rigima bata kwantaba kuma maganar komawar
Shareff hanun Usman ta sake tasowa. Nanma dai ansha ƙaramin yaƙi dan Mommy haukane
kawai bataiba ɗanta zai koma hanun maƙiyanta. Tsiya ta dinga zazzagama Usman harda
masa gorin haihuwa. Shi dai bai kulata ba kamar yanda bai kula Gwaggo da Halima ba.
Iyakaci ma idan suna abun nasu sai dai yayi murmushi. A gefe kuma bai fasa shiryama
Shareff tafiya ba.
A lokacin da zasu wuce dole sai sace Shareff akai daga gidan batare da
sanin Mommy da Gwaggo ba, dama ita Halima tana gidan aurentane zuwa takeyi, itama
dai yaranta uku ne a yanzu tana auren ɗan wan gwaggon dan ita ta haɗa....

Humairah da Mimi sunyi farin cikin ganin Shareff, sai dai kuma sam babu
cikkakkiyar tarbiyya ga yaron. Dan ba ƙaramin wahala da azabarsa suka sha ba duk da
kwata-kwata shekararsa tara ne a duniya lokacin. Haka Ruƙayya taita juriyar ganin
ta sauya tarbiyyarsa ita da Usman. Basubi takan zagi da walakancin da Mommy ke kira
a waya ta musu ba akan su dawo mata da ɗanta idan sunji haushi su haifa nasu.
Gorinta na musu ciwo, amma sukaita dannewa tunda sun san domin ALLAH zasuyi ai da
ɗan uwansu. Tunda dai sun san bazatazo ta ƙwacesa ba.
A hankali komai ya fara daidaita, Shareff ya fara nutsuwa da son karatu, ga
kulawa yana samu da soyayya ga iyayen ruƙonsa. Shaƙuwa kuma mai nagarta ta gama
shiga tsakaninsu. Bashi da kamar Abie da Mamie yanzu a duniya sai aunty Mimi da
akoda yaushe yakanje gidanta kodan yaronta data haifa Su'ad. Shareff nada shekara
biyar a wajensu ALLAH ya bama Mamie ciki. Zokaga murna da farin ciki wajensu,
yayinda Mommy ta shiga baƙin ciki dan taso ace sun ƙare rayuwarsu ne babu haihuwa.
Kuma har yanzu tana kan caccakarsu akan su maido mata ɗanta. Sudai basa kulata, dan
ko ƙasar zasuzo basa zuwa da shi ma.
Mamie tasha rainon ciki har ALLAH ya sauketa lafiya ta haifo ƴarta mace.
Mommy da Gwaggo sun ɗanji sassauci dan a ganinsu darajar mace bata kai ta namiji
ba. Dan haka suka shiga shigi da fici gidan malamai kai harma da bokaye akan wai a
tsaida haihuwar Humairah. Humm abin dariya, dama basu wahal da kansu ba dan iya
abinda ALLAH ya rubuto a ƙaddarar bawa shi kaɗaine rabon dazai samu ai dama. Ita
dai batama san sunai ba, dan kuwa da ALLAH ta dogara. Su Daddy ne kawai sukaje
Malaysia ganin gudan jinin ɗan uwansu, duk da Gwaggo taso binsu ganin ƙwaf sukaƙi.
Yarinya taci sunan *_Juwairiyya_*, mahaifiyar su Abie kenan amma suna mata alkunya
da *_Anam (Blessings of GOD)._*

Rainon Anam ya dawo kamar a hanun Shareff ne. Bashi da damuwa a yanzu sai
ta Anam, daya dawo makaranta tana hanunsa, bacci ne kawai ke rabasu shima sai Mamie
tayi jan ido. A haka aka yayeta ta buɗa ido da sanin Shareff matsayin Yayanta
kawai. Dan kuwa duk wani gata da kulawarta tamkar ta koma hanunsa ne. Dan hatta
wanka da abubuwan da uwa zatayi duk shike mata. A koda yaushe tana maƙale da shi
kamar cingam. Hatta da Abie wani lokacin ƙiwa take masa sai shareef. Lokacin da
take cika shekara shidda a duniya a lokacin Shareff ya kammala secondary school
ɗinsa. Abie yay masa shirin wucewa jami'a a ƙasar Indonesia. Ya shiga damuwar
rabuwa da ƴar ƙanwarsa, dan kuka sosai ya dingayi duk da lokacin yanada shekaru sha
takwas a duniya dan ya zama ɗan saurayi abinsa. Haka dai babu yanda ya iya ya
tattara ya tafi badan yaso ba. Yasha matuƙar wahalar kewar Anam a ƙasar Indonesia,
dan da ƙyar ya haƙura ya maida hankali ga karatunsa kodan faranta ran Mamie da Abie
ɗinsa. Fara karatun Shareff a ƙasar Indonesia ya ƙara bama Gwaggo da Mommy ƙwarin
gwiwar cigaba da shiga da fita domin ganin hankalinsa ya dawo garesu, su kuma
nisantashi dasu Mamie. Zuwa lokacin gidan nasu ya ƙara haɓaka da ƴaƴa. ALLAH kuwa
ya amsa musu, dan kuwa dai a hankali rayuwar Shareff da hankalinsa suka fara dawowa
Nigeria, ko hutu ya samu da yaje Malaysia dake kusa da shi gara ya wuto Nigeria.
Takai yakan ma jima bai je inda su Abie suke ba. Sai dai abinka ga ikon UBANGIJI
har lokacin soyayyar bayin ALLAHn nan na'a ransa babu abinda ya canja. Kawai dai
baya son zuwa inda suke ne batare da yasan dalili ba, sai kuma Anam da sam a yanzu
bayama ko san tunata dan babu dalili ya tsani yarinyar. ko Malaysia yaje babu
abinda ya damesa da ita, wani lokacin ma kafin ya taho sai ya bugeta. Itako dama
tama manta da shi tuni, rashin sakewar da yake da ita yasa basa shan inuwa ɗaya, ko
inda yake bata kusanta balle ta nuna tama sanshi, idan kuma tsautsayi ya haɗasu ko
hararta yay sai ta rama saboda tsiwarta.
A haka rayuwa ta cigaba da shuɗawa Shareff ya kammala karatunsa ya zama
cikakken *_Architect Al-Mustapha Muhammad Shareff_*. Maimakon ya nufi Malaysia
kodan nuna godiyarsa ga ALLAH ga waɗanda suke tsaye kan ɗawainiyar karatun nasa sai
kawai ya nufo Nigeria. Hakan ya matuƙar bata ran su Daddynsa, yayinda Gwaggo da
mahaifiyarsa Mommy suka bashi goyon baya da kariya. Sosai ran Daddy ya ɓaci har
suka sami saɓani tsakaninsa da Mommy irin wanda basu taɓa samu ba. Ya kuma fito
fili ya nunama Gwaggo kuskurenta. Aiko saita zauna ta dinga kuka wai su Daddy sun
nuna mata ba itace ta haifesu ba. Shareta sukai, harta haɗa kayanta tabar gidan,
ganin abin zaiyi tsamari Mom ta sanarma Mamie, itako ta sanarma Abie. Daga ƙarshe
dai Abie ne yazo Nigeria ya kwantar da tarzomar tare da nuna shi bai ɗauka abinda
Shareff ɗin yayi da wani ɓacin rai ba, abin birgewama sai yay zaman bashi shawarar
mizai hana ya buɗe company kawai basai ya zauna neman aiki ba.
Sosai Shareff yaji kunya, ya dinga bama Abie haƙuri akan shima wani lokacin
yana rasa gane kansane akan nisantarsu. Murmushi kawai Abie yay dan ya jima da
fahimtar komai akan farraƙa yaron akai da su, bai kuma taɓa yunƙurin nuna ya sani
ba tunda yasan dai Mommy akan abinda yake nata take hanƙoro mizaisa ya damu tunda
shima ALLAH ya bashi tashi. Shareff bashi da kuɗin buɗe company, amma sai Abie ya
bashi shawarar su haɗa gwiwa kawai.....
A haɗin gwaiwar ma Shareff baida ko kwatar kuɗin da zata gina company ɗin,
amma sai Abie bai damuba shi ya bada duk kuɗin da ake buƙata aka kammala aikin
cikin ƙanƙanin lokaci, ya kuma gargaɗi Shareff akan baya son Gwaggo da Mommy su
sani, kawai suci gaba da tafiya akan shine ya gina abunsa. Sai dai sun zauna da
lauyoyinsu an ajiye komai a rubuce tare da su Daddy matsayin shaida.
Ginin wannan company yasa Mommy fara hura hanci, a ganinta karan ɗanta yakai
tsaiko shima. Har habaici takema su Mom da su Mamie ko kunya babu. Mamie ce kawai
tasan gaskiyar lamarin, su Mom kam da aunty amarya suma duk tasu ɗaukar Shareff
ɗinne ya gina da kuɗinsa. Gwaggo ma ta ɗau abun da zafi, dan ita taita tunzura
Mommy akan su ƙara tashi tsaye su nisanta Shareff da su Abie wai kar wataran Abie
yay tunanin haɗa Shareff da Anam aure tunda sunga ya kuɗance har yama fisa arziƙi.
Wannan fanfi kuwa yay tasiri ga Mommy, dan tuni suka bazama shige-shige saboda ko'a
mafarki bata fatar haɗa zuri'arta dasu Abie a duniya.....

Abubuwa da yawa sun faru bayan wannan, ciki harda karatun Anam da ko Nigeria
ɗin ma sai jefi-jefi ake kawota, dan idan har suka zo ta dinga kuka kenan zafi-
zafi. Anam yarinyace ƙyaƙyƙyawa black beauty, tana tsananin kama da mahaifinta a
komai, sai dai akwai kamannin Mamie tattare da ita ta wasu wajajen. Yarinyace mai
ƙiriniya da rashin ji, ga tsiwa. Sam ƴar babu ragice, dan ko cikin yaran da suka
girmeta bata bari a cuceta balle sa'aninta, tanada baki sosai. A ɓangaren karatu
kuwa sam bata da wani ƙoƙari saboda kasancewar ta yarinya mai son wasa, sai da su
Abie suka miƙe kanta sosai sannan ta fara fahimtar karatu. Shekaru na karuwa gareta
rauni daga idanunta na sake bayyana, dan takai idan abuna'a nesa da ita bata
ganinsa, hakama da daddare idan waje babu haske mai ƙarfi bata ganin abu har saida
lalube. Lokacin da su abie suka fahimci wannan matsala hankalinsu ya tashi, sai dai
babu ɓata lokaci suka dangana ga likita, ya tabbatar musu idanunta nada raunin
gani, amma zai ɗaurata akan magani da gilashi dazai taimaka mata. Wannan shine
dalilin kasancewar eyeglasess a idon Anam koda yaushe. Abin mamaki kuma sam basa
shan inuwa guda da Yaya Shareff. Hasalima haduwarsu tayi matukar wahala, idan ya
fisge yaje Malaysia ma bata barin su haɗu sam, hakama idan tazo Nigeria baifi su
haɗu sau biyu uku ba shikenan, a kuma duk haɗuwar tasu sai ya mata muguntar datake
jin ƙarin tsanarsa a ranta kamar yanda shima haka kawai bai son yarinyar saboda
tsiwarta da rashin kunya ido fiƙi-fiki injisa. Idan ma tana waje ya dinga ɗaure-
ɗauren fuska kenan kamar an aiko masa da mutuwa, ko gaishesa tai sai ya gadama ya
amsa shiyyasa tama daina gaidashi take nuna bama tasan ƙurar data kwasosa a duniya
ba. Tuni company ya fara aiki cikin lumana da nuna ƙwazon shugaba kwata-kwatansa
wato Architect Al-Mustapha Muhammad Shareff. Da mafi yawan mutane sukafi sani da
*_MM Shareff_* a taƙaice. Company ne da aka haɗa masu ƙwazo kuma ƙuraye, dan Ya
Shareff bai yarda ya ɗauka ma'aikatan banza ba sannan sam baya wasa da aikinsa bai
bama ma'aikatansa damar yin wasan kuma.
Jajircewar tasa tai matuƙar birge Abie, ya kuma ƙara tsayawa tsayin daka ta
bayan fage yana bama Shareff ɗin gudunmawa dan yana matuƙar kaunar yaron har cikin
ransa tamkar Anam ɗinsa ƴa ɗaya tilo.
To ayanzu dai ga Anam ta dawo Nigeria da shirin zaman shekara guda domin
yin saves da su Mamie suka takura mata. Ga kuma ɓeranta da tuni yayi nauyi a
Nigeria kodan hidimar kamfanin da mahaifinta keda kamasho mai ƙarfi a cikinsa da
shares batare da Mommy da Gwaggo dake hura hanci sun sani ba.........✍

_Ko yaya wasan zai kasance🤔? Kudai kawai ku zamto tare da littafin *_BABU SO...!
MIYA KAWO KISHI? dan jin yaya cakwakiyar zata kasance. Littafine da yazo da wani
irin sabon salo na musamman da nake tabbacin ni Bilyn Abdull ban taɓa zuwa muku da
kalarsa ba sai yanzu. Domin kuwa ya taɓo zahirin rayuwa ne da zamanin da muke ciki
a yanzu da rawar da tarbiyyar ƴaƴanmu ke takawa a social media batare da saninmu ba
ko da sanin namu. Kar dai na cikaku da magana my guys, kumuje zuwa kawai dan duk
wanda akai babu shi lallai ruwa tasha da shi kawai, saboda Zafafa biyar da gaske da
zafinsu suke😉🥰🥰😘🚶🏻._

KU DAI KU GARZAYO A DAMA DAKU A CIKIN WANNAN ZAZZAFAR TAFIYAR CIKIN SALON NA ZAFAFA
BIYAR MASU ZAFIN GASKE.

DUKKA LITTAFAN AKAN NAIRA DUBU DAYA (1k) KACHAL

IDAN KUMA DAYA KIKE SO (300)


BIYU (400)
UKU (500)
HUDU (700)

KARKU BARI A BAKU LABARI, DAN WANNAN SALON NA DABAN NE KUMA TAFIYAR MA TA DABAN CE!

ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN

HAFSAT UMAR KABIR


ZENITH BANK
2270637070

SAI A TURA SHAIDAR BIYAN

07040727902

IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA

09134848107

KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN
MASU MATUKAR SANYA NISHADI.

MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.

SAI MUN JIKU MUTANEN AMANA!💃🏼💃🏼💃🏼

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏽


[10/3, 10:44 AM] Zeenaran🫶🏻: *_Typing📲_*

*_BABU SO....!!_*
_(Miya kawo kishi?)_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_03_*

..........Tuni sun tattare kansu a sashen aunty amarya idan ka cire ƴan manya-
manyan yaran gidan samari da basu gama dawowa da ga wajen aiki ba da kuma masu
shiga school lectures ɗin yamma. Zagaye suke da Anam suna kwasar dariyar hausarta
da bata nuna da ƙyau ba. Dan cike take gwamutse da yaren malay da turanci, wai a
hakanma Abie na matuƙar ƙoƙarin mata hausar ne shi da aunty Mimi dan Mamie ma ba
wani iyawa tai sosai ba harma gara Anam ɗin, tunda dama acan itama ta tashi, ko
Nigeria tazo tafi yin turanci da jama'ar gidan. Aysha dake naniƙe da Anam ɗin da
suke sa'annin juna dan dama idan tazo bata da ƙawar data wuceta a Nigeria, cike da
kulawa take tambayarta dalilin matsar ciki da take famanyi.
A yatsine Anam ta sanar mata tana jin yunwa ne, dan ta kasa cin duk abincin
da aka shirya musu a gidan. Dama can idan sunzo Mamie ce ke musu girki shiyyasa
Anam bata da matsala tunda abinda ta saba ci ne, a yanzu ko babu Mamie dole sai
abincin Nigeria da har yanzu ta kasa iya ci, ƴan abubuwan da take iya cin ƙalilanne
kuma babu su.
Idanu Aysha ta ɗan waro, cikin harshen turanci take cemata miyasa zata zauna
da yunwa bayan abinci da akai domin su tunda sun iske tarin kwanika a sashen Daddy
lokacin da sukaje gaida Abie. Sunada tabbacin kuma an shiryasune dan zuwan su Anam
ɗin. Fuska a marairaice ta sanarma Ayshan ita bata iyacin duk abincin ba ai. Ba
Aysha kaɗaiba duk yaran sai da suka dara, dan sosai ragwantakar Anam ke basu
dariya, kodan tana ganinta da ƙaramin jiki ƴar ficika da ita yasa a kullum bata
sanin ta girma? Sosai Aysha ta fita girman jiki, sai ma ta saɓeta ta goya dan ita
ta kwaso tsayi da garin jikin Mommy mahaifiyarsu.
Sake ɓata fuska Anam tai kamarzatai kuka, sai faman matse ciki take da cizar
lips dan da gaske yunwar takeji, shi kansa Abie yana canne amma hankalinsa na kanta
dan yasan bazata iyacin kowanne abinciba da ya gani an tara masa.
“Am so sorry sweetheart. Kar kiyi kuka faɗi abinda kike so sai a samo miki,
ko a kira Yaya ya sayo miki tunda shi yasan inda yake samo abincin naku, dan shima
dai ya jima yana wahala kafin ya saba da abincin Nigeria, ko yanzu ma ba komai yake
iya ci ba”.
Fahintar wa Aysha ke nufin za'ama magana ya samo mata abinci ya sakata
girgiza kanta, a langwaɓe ta kamo hanun Ayshan cikin nata. “No don't worry rakani
wajen Abie na nidai kawai”.
Batama bari Aysha tace wani abuba ta miƙe har lokacin hanunsu cikin na juna,
ɗayan hanunta kuma nakan cikinta. Wando da rigane a jikinta marasa nauyi, wandon
irin mai faɗin nan sosai da ƴan Nigeria ke kira a fantama😂, sai fingilar top da
tabi jikinta ɗas kamar dan ita aka halicceta, sai siririn veil data sakaya gashinta
a ciki sai dai hakan bai hanashi bayyana ta gaba ba saboda veil ɗin daya zama baya.

Itace ta farayin sallama a hankali cikin sassanyar muryarta, ta dora da


faɗin, “Daddy mu shigo?”.
Murmushi Daddy da Abbah keyi idonsu akan ƙofar. Abba ne ya amsa da “Shigo mana
Mamanmu”. Hanun Aysha taja zuwa ciki, sai dai taku uku kacal tai ta tsaya turus
fararen idanunta da sukai laushi saboda yunwa tsaye ƙyam akan wanda ke zaune bisa
lallausan carpet ɗin falon gab da ƙafafun Abie ɗinta, yayinda hankalin Abie kacokan
ke akansa da alama ma bai san da shigowarta ba.
Sosai ƙirjinta ya harba dan ko kusa batai zaton ganinsa anan ɗin ba, tunma
data duro gidan addu'arta shine karma su haɗu kwata-kwata. Zancen Aysha na ɗazun ya
tabbatar mata yana ƙasar, hakan kuma na nufin dole su haɗu koda ba yau ba. Amma
batai tsammanin yanzu ba. Kamar yanda tai masa kallo ɗaya ta ɓata fuska da gyara
yanayinta haka shima yay mata kallo guda duk murmushin fuskarsa ya ɓace, har wani
yamutse fuska yay tamkar yaci karo da tutun safiya na cikin sanyi......
“Mamanmu ƙaraso mana”.
Daddy ya katsesu a tare dan duk yaga irin kallon tsanar da sukaima juna. Shikam ya
rasa wannan ƙiyayya ta Anam da Shareff bayan kowa yasan irin dunbin son daya nuna
mata tana jinjira har zuwa sanda ya wuce Indonesia, amma a yanzu baka ganin komai
sai ƙin juna a tsakaninsu tamkar basu taɓa sanin juna ba. Yitai kamar bata gansa ba
taje ta zauna kusa da ƙafafun Daddy, cikin marairaice fuska tace, “Daddy ina jin
yunwa sosai”.
“Ya salam mamana garin yaya haka? duk abincin dake gidan nan ga wasuma ko
taɓawa ba'ai ba kuma dan k kawai aka shirya su”.
Kanta ta girgiza kamar zatai kuka. “Daddy bana son su ban iya ci ba ai”.
“Sai ki fara koya yanzu ai”.
Abie ya faɗa kafinma su Abba suce wani abu yana hararar Anam duk da kuwa bai kai
zuci ba, dan ransa cike yake da damuwar zamanta da yunwar tunda yasan da gasken ba
iya cin tai ba.
Daddy yace, “A'a ba'ayi hakaba ai. Tunda tace bata iyaba da gaske bata iya
ɗinba kuma bataso. A bita a sannu zata koya ci insha ALLAH tunda tana nan. Shareff
ka ɗauketa kuje a sama mata abinci dan kaine kafi kowa sanin inda kake ciyo abinda
ta iya ci”.
Tamkar saukar aradu haka Shareff yaji saukar zancen Daddy a kansa. Ya ɗago
da sauri yana duban mahaifin nasa tamkar a razane. Harara Daddy ya zuba masa.
“Lafiya ka tsareni da idanu halan?”.
Ƙasa ya risinar da idanunsa batare da yace komai ba. Sai dai fuskar ta sake
rinewa tamkar an aiko masa da saƙon mutuwa.
“Daddy ni dai nama ƙoshi kawai zansha ko tea to”. Anam da itama ta haɗe
fuska tana hararsa ƙasa-ƙasa ta faɗa baki a tunzure”.
Maimakon Daddy ya amsa mata sai ya kira sunansa a tsawace. “Shareff Are you
daft?”. Kansa ya girgiza kawai yana miƙewa, idonsa a ƙasa yace, “Zanje na sayo
kawai.....”
“Da ita zakaje ta zaɓa abinda take so”.
Dady yay saurin faɗa cikin katse masa hanzari. Wani irin rumtse ido yay da
ƙarfi da cije lip ɗinsa na ƙasa uwa zai huda shi. Sai dai baice komai ba ya kama
hanyar fita. “Basai kaje ɗakko key ɗin mota ba zo ka dauka wannan”. Abbah ya
katsesa dan ya tabbatar Mommy ta gansa zata hana itama. Nanma baice komai ba ya
dawo ya amshi key ɗin hanun Abban.
“Maza bishi mamana kuje, ki kuma zaɓo duk abinda kike so kinji”.
Kanta ta ɗagama Daddy tana murmushi, dan ganin yanda Shareff ɗin keyi yasata
jin zama ta bisa kodan ta baƙanta ransa...
Kasancewar ya fita zafin nama sanda ta iso harabar gidan harya tada motar
yana reverse, maimakon ya faka saitin inda take ya ɗauketa sai ya harba motar har
bakin gate. Anam tai ƙwafa da taɓe baki, cikin kunƙuni da gurɓatacciyar hausarta
tace, “Duk baƙin halin da kake sai naje saika mace idan kasha zuciyanka mugu mai
baƙin rai”.
Oho baima san tanai ba. Cike da wani takun isa tazo ta buɗe murfin ta shiga
kanta a gefe. Bawani duban kirki yay mataba a ciki, dan haka bai gama tantance
kayan jikinta ba. Tana shiga ya fisga motar da ƙarfi har yanayi kamar zai taka mai-
gadi ma, sai da yay tsalle gefe ya bashi hanya cike da mamakin mike damunsa. Dan
shi shaidane Shareff mutum ne daya san mutuncin mutane, ko yaya kake a ƙasansa bai
yarda ya ƙasƙantaka ba balle wulaƙantaka. Yayi imani da ALLAH ransa a ɓace yake
bada son rai yay masa haka ba.

★ Sosai gidan abincin ya haɗu, ya samu waje yay parking batare da yace da ita
komai ba ya fice a motar. Baki taɗan taɓe kaɗan da yima ƙeyyarsa gwalo, sai kuma ta
zabura ta buɗe motar tamkar wadda ta tuna wani abu. Yana gab da shiga ta cimmasa
saboda da ɗan gudu-gudu take tafiya. Cak ya tsaya, dan haka itama ta tsaya kanta a
ƙasa dan duk fitsararta a bayan idone kawai dama.
“Idan kika bari ƙafarki ta shiga wajen nan sai na ɓallata”. Da yaren malay
yay maganar, dan haka komai ya shiga kunnenta tsaf. Baki ta tura fuska a kumbure
idonta na tara ƙwalla harya shige tana kallon bayansa ta ƙasan ido. Maimakon ta
koma mota sai ta nema waje a gefe tai tsaye tana kallon mutanen dake. a ciki ta
cikin glass da aka ƙawata wajen.....
“Hallo....”
Aka faɗa a bayanta cikin wani irin sallon daya tilastata ɗago idanunta masu
haske, matashin saurayine ƙyaƙyƙyawa fari tas. Sanye yake cikin ƙananun kaya da
sukai matuƙar karɓarsa ga wani ƙamshi na musamman a tare da shi. A hankali ta janye
idanun nata ganin yanda ya tsareta da idanunsa birkitattu. Gefen data maida fuskar
ya sake dawowa yana gyaran murya, ta sake ɗauke kanta gefe....
“Dan ALLAH ki kulani ƙyaƙyƙyawa ”. Ya faɗa cikin marairaicewa da haɗe
hannayensa waje guda alamar roƙo. Baki taɗan taɓe gefe tana yamutsa fuska da kai
hannu ta gyara glass ɗin idonta dake ƙara fiddo ƙyawunta duk da tana sakawane badan
gayu ba, kamar bazatace komaiba sai kuma dai ta tanka masa saboda ALLAH daya haɗata
da shi. “Ka fara koyan sallama tukunna kamar zaifi bature”. Kansa ya dafe, cike da
jimami yace, “Am sorry Assalamu alaiki ƙyaƙyƙyawa”. Nan ɗin ma bata amsaba sai da
tasha masa ƙamshi tana wani ɗauke kai. “Wa'alaikassalam. kuma ni ba sunana
ƙyaƙyƙyawa ba”. “Tabbas sunan shine ya dace dake, sai dai dazanji na yankan zanfi
yin farin ciki”. Banza ta masa har kusan minti ɗaya, ganin yana neman matsowa
jikinta tai saurin ɗagowa a masife......
A dai-dai nan Shareff ya fito daga wajen hanunsa ɗaukeda ledoji masu
tambarin wajen abincin. Duk da idonsa a kansu ya fara sauka sanda yake buɗe ƙofar
sai ya ɗauke tamkar bai gansunba. Sai dai ya sake tsuke fuska. Yazo zai giftasu a
fisge yace, “Second ɗaya kika ƙara a wajen nan jikinki sai ya faɗa miki”. Daga ita
har saurayin da sauri suka maida dubansu garesa dan ita bama ta lura da shi ba da
farko. Ko kaɗan bazaka taɓa cewa shine yay maganar ba. Tuno dukan da sukaci ita da
Aysha randa sukaje birthday party ya sata zabura da sauri tabi bayansa bakinta a
tunzure tana hararar bayansa, da sauri shima saurayin ya take mata baya. Tana
ƙoƙarin rufe murfin motar ya riƙe da hanzari..........✍

KU DAI KU GARZAYO A DAMA DAKU A CIKIN WANNAN ZAZZAFAR TAFIYAR CIKIN SALON NA ZAFAFA
BIYAR MASU ZAFIN GASKE.

DUKKA LITTAFAN AKAN NAIRA DUBU DAYA (1k) KACHAL

IDAN KUMA DAYA KIKE SO (300)


BIYU (400)
UKU (500)
HUDU (700)

KARKU BARI A BAKU LABARI, DAN WANNAN SALON NA DABAN NE KUMA TAFIYAR MA TA DABAN CE!
ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN

HAFSAT UMAR KABIR


ZENITH BANK
2270637070

SAI A TURA SHAIDAR BIYAN

07040727902

IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA

09134848107

KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN
MASU MATUKAR SANYA NISHADI.

MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.

SAI MUN JIKU MUTANEN AMANA!💃🏼💃🏼💃🏼

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏽


[10/3, 10:47 AM] Zeenaran🫶🏻: *_Typing📲_*

*_BABU SO....!!_*
_(Miya kawo kishi?)_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_04_*

..........Kallon juna sukai cikin ido, tai saurin janye nata saboda wani irin
harbawa da ƙirjinta yayi......
“Please Beauty ko details ɗinki ki bani mana”. Saurayin ya faɗa a marairaice.
Ai kafimma ta bashi amsa mai gayya mai aiki ya fisgi motar da ƙarfi. Da sauri
saurayin ya saki murfin yana mai yin tsalle gefe dan saura kaɗan ya takashi. Sosai
yanzu kam Anam ta firgita, dan har hannunsa ta riƙo batare data sani ba. Tureta yay
a jikinsa tare da mika hannu ya rufo ƙofar gefen da take ɗin. Sai kawai ta fashe
masa da kuka tana kiran sunan Mamie da Abie. Bai nuna yama san tanaiba, saima
hankalinsa daya maida ga motar dake bin bayansu, sai da suka hau titi sosai hasken
solar ya bashi damar ganin fuskar guy ɗin da suka baro ne. Lip ɗinsa ya ciza da
ƙarfi yana wani fici-fici da idanunsa, sai ya koma tafiya a slow-slow harya zam
saurayin ya ɗan gota su. Gefen titi ya gangara, sai da yaga saurayin na ƙoƙarin
dai-daita nasa gudun danya sauka gefe titi shima saboda ganin sun tsaya sai kawai
yay warming motar da wani irin karsashi ya sake harbata saman titi tamkar
shikaɗaine a kansa. Tabbas da ace akwai ƙasa babu abinda zai hanashi bulama
saurayin ita.
Wani irin duka saurayin ya kaima steering ɗin a ƙulle da kufcewar damar daya
samu. Ya kife kansa yana furzar da huci mai zafin gaske, dan harga ALLAH yarinyar
ta matuƙar tafiya da dukkan imaninsa.

Kamar yanda ya fita a fusace haka ya dawo a fusace, ko parking bai gama
daidaitawaba da ƙyau ta ɓalle murfin motar ta fice da sauri. Wani irin mugun kallo
yabi bayanta da shi, sai kuma ya janye yanayin ƙwafa ya kashe motar ya fito. Zaune
ya sameta kusa da Abbah tana zuba surutu, dan har yanzu suna a falon suna hira.
Sosai takaici ya riƙe masa maƙoshi, ya harareta yana ɗauke kai da zube ledojin
hanunsa gabanta. Fuskarta ɗauke da murmushi kamar ba itace ta gama kuka a hanyaba
yanzu tace, “Jazakallahu khairan Yaya Shareff”. Ta ƙare maganar da masa gwalo yanda
su Abba basu luraba sai shi.
Yi yay tamkar baima gantaba duk da tsaurin idonta na bashi mamaki, sosai
ƙanensa ke shakkarsa a gidan, amma sam babu irin wannan tsoron da yake gani a idon
ƙanensa tattare da ita. Kai tsaye take abunta garesa, abunda ya fuskanta dukane
kawai bata so, dan tun dukan da ya taɓa mata ita da Aysha ta shiga hankalinta a
lokacin har tana wasan ɓuya da shi. Sallama yayma su Abie dake saka masa albarka ya
fita fuskarsa ɗauke da murmushin daya saka Anam sakin baki tana kallonsa da mamaki.
Dan inba Abie ɗin ba da wahala kaga murmushi a fuskarsa, kullum fuska a ɗaure kamar
ɗan raka gawa....

Washe gari da ƙyar Aysha ta iya tashinta danta shirya. Haka tai wanka
tanata mitar ita barci bai ishetaba. Shiri tai cikin wando da riga, sai dai anan
babu maganar fita a haka duk da zafi da ranar da akeyi a Nigeria, dole ta ɗaura
abaya, Sosai tayi ƙyau kamar ka saceta ka gudu. ɓata fuska taketa faman yi dan bada
son ranta tasa abayar ba, sai dai yanda Mamie ta gargaɗeta ta dingayi tunda tasan
kayan nata duk ba irin na sawar Nigeria ba ne. Shiyyasa ta zubo mata abayoyi kusan
goma tanata mita bata kulata ba. Kasancewar akwai sanyin safiya sai bata damu da
saka abayar ba sosai.
Sashen Mommy suka nufa ita da Aysha, sai dai daka kalleta kasan ba'a san
ranta bane. To amma kodan Aysha da kunya tace bazataje ba. Mai aiki kawai suka samu
a falon tanata aikin gyarawa, suka gaisa Anam na amsasu cike da fara'a, dan haka
kawai ita dai Ladi ke birgeta. Bedroom ɗin Mommy suka nufa daga nan, bayan sallama
aka basu iznin shiga. Zaune suka sameta a kujerar mirror tana murza ɗauri, ganin
aysha ta rissina tana gaisheta itama saita ɗan rissina batare data yarda sun haɗa
ido ba. Bata amsa na Anam ɗin ba, sai Aysha data watsama harara... “A ina kika
kwana?”.
“A sashen Mom ne”.
Aysha ta bata amsa cikin ɗari-ɗari dan tasan faɗa zata sha. Aiko kamar jira Mom ta
rufeta da faɗa, ta inda take shiga batanan take fitaba. Itadai Aysha haƙuri kawai
take bata. A tsawace tace. “Ɓacemin da gani shashasha da bata san ciwon kanta ba”..
Kafinma aysha tai yunƙurin fitowa tuni Anam tai waje ranta fal ƙarin mamakin
masifar Mommy ɗin...
Da sauri tai baya jin suna neman yin karo da mutum. Ta tura baki gaba tare da
ɗan matsawa gefe saboda hararar da yake watsa mata. Yana ƙoƙarin raɓata da nufin
wucewarsa tai tunanin bugeta zaiyi, kamar ƙiftawar ido yaga ta zura da gudu ta
fice. Idanunsa ya ɗan lumshe tare da girgiza kansa kawai. Anan ɗin ma yana ƙoƙarin
shiga ɗakin Mommy Aysha ta fito tana sharar hawaye, rissinawa tai ta gaishesa,
maimakon amsa mata sai ya jeho mata tambaya idonsa kafe a kanta, “Mike damunki?”.
Kanta ta girgiza masa. “Ba komai Yaya Mom ce, dan naje sashen Mom na kwana
shine taketa faman faɗa, ni kuma saboda naga Anam ne tunda nasan idan mukazo nan
bazata barta ta kwana ba”. Shiru yay yana cigaba da kallonta kawai, batare da yace
komaiba kuma sai ya raɓata ya wuce ɗakin Mommy ɗin.
Anam kam sai da ta tabbatar tabar sashen sannan ta ƙara kumbura baki,
sashen Gwaggo ma da tun jiya batako kallaba sai da Abie ya korata sannan ta tafi
fuska a haɗe kamar zatai kuka. Bata son kakar tasu dan itama tasan ba sonta take
ba. Koda ta shigo sashen tsohuwar a ciccije take. Tamkar bama tasan Anam ɗin ba
take kallonta, hakan yasa itama Anam ɗin tsumewa tai kamar bama wajenta tazo ba.
Cikin ƙunar rai Gwaggo ta ture ƙaton kofin shayin da take sha gefe tana kallon Anam
cike da tsana,
“Fitsararriya cokalin banza. K ko kunyar kanki bakijiba sai yau kike zuwa
gaisheni? Da yake baki da mutunci. to in bakizoba k ai ubanki shi yazo dan uwarki”.
Shiru tai taƙi cewa komai, hakan sai ya sake tunzura Gwaggo ta fara bala'i ta
inda take shiga bata nan take fita ba. Ko motsi Anam bataiba ballema tai mata
gaisuwar da akace tazo tayi, sai da ta tabbatar mintunan da Abie bazai zargi komai
ba sun cika sannan ta gaida Gwaggo dake yayyafa ruwan bala'i da zage mata iyaye tai
ficewarta batare da ta jira amsa ba. Biyota Gwaggo tayi tana ƙwala mata kira.
“Zuwairah!! Zuwairah!! yanzu nan ni kikema wannan ɗibar albarkan? To ko
ubanki ai bai isaba, ke ko kakarki ma data haifi uban naki balle ke yarin....”
“Ki cinye kanki fitinanniyar tsohuwa”. Anam ta faɗa a hankali tana ƙara sauri
dan ko muryarta bata buƙatar ji. Taji daɗin samun Abie harya shiga mota, dan haka
ta buɗe wuf ta shige duk da bataji daɗin yin tafiyar da wanda ta gani zai jasu ba.
Sai da suka fita a gidan gaba ɗaya Abie daya lura bata gaida Shareff ɗin ba ya
dubeta ta mirror.....
“Anam!”.
“Na'am Abie ”.
“Kin gaida Yayanki kuwa?”.
Ido suka haɗa da shi ta mirror, ita ta fara ɗauke nata idon ganin kallon banzar
daya jefa mata. “Abie na gaishesa tun ɗazun ma ai da muka haɗu a sashen Mommy”.
Idanunsa da basu gama bajewar kumburin barci ba ya sake ɗagowa ya dubeta. Itako ta
ɗauke kanta cike da basarwa. Abie kam daya yarda sai kawai yay murmushi da maida
hankalinsa ga lap-top ɗin dake a cinyarsa yana dubawa, ta Shareff ɗince yake nuna
masa ayyukan company duk da dama can komai za'ayi yana sanar masa. Sai dai a kullum
cikin ƙara bashi wuƙa da nama yake da nuna masa duk yanda yayi dai-dai ne kawai.
Koda suka iso inda zatai daidaita komai daya shafi hidimar ƙasar nata bata yarda
tako kalla Ya Shareff ba, shima bai shiga sabgartaba dan koba komai yana jin nauyin
Abie sannan shi sam baya wasa da yara dama can, itacema kawai za'ace ta ciri tuta a
wajensa tana ƙarama.
Komai da taimakonsa shi da Abie ya kammalu, basu sami nutsuwa ba sai kusan
azhar. Maimakon gida sai suka wuce company. Tunda akai
Companyn Anam batazo Nigeria ba, dan haka ta ɗan nutsu a kallon tsarin wajen da
yanda ma'aikata keta kaikawo na daidaita kansu tun shigowar motar tasa. Koda suka
fitoma sai gaisuwa ake miƙa musu cike da girmamawa da mutuntawa har suka isa
katafare kuma haɗaɗɗen office da yaji komai na more rayuwa da saka nutsuwa ga
mazaunin cikinta. Abayar jikinta ta shiga ƙoƙarin cirewa. “Wayyo Abie zafi”.
Yanda tai maganar ya sashi ɗan juyowa ya dubeta, ai da sauri ya ɗauke kansa
ganin kayan dake a jikinta. Wando ne dayay matuƙar fidda surar jikinta da ƴar riga
da itama bata ɓoye komai ba. Sun mata ƙyau sosai kuma dai-dai da halittarta ta masu
ƙaramin jiki. Har veil ɗin data naɗa bata bari ba sai da ta yaye, ɗaurarren
gashinta da yasha gyara ya bayyana, sai dai tuna gargaɗin Mamie yasata warware veil
ɗin duk da ba wani girmane da shiba sosai taɗan yafa tana duban sashen da yake....
“Yaya Shareff Please kasa ac zafi”. Tayi maganar ne tamkar zata fasa kuka,
dan da gaske zafine ya taso mata lokaci guda, har wani dimm kanta ke mata. Ta ƙasan
ido ya harareta, sai dai baice komaiba ya ɗauka remote ɗin ac dake a desk ɗin
office ɗin nasa ya kunna ɗin. Ajiyar zuciya ta sauke cike da jin daɗin jin yanda
sanyin ya wani buso mata da faɗin, “Alhmdllhi, Abie ALLAH da kamar ana dafamin
fatar jikina fa”.
Ƴar dariya Abie yay yana mai girgiza kansa da kallon Shareff dake ƙoƙarin buɗe
wajen da yake gudanar da duk ayyukansa na zane. Babu mai shiga wajen sai shi kaɗai,
sai ko Fharhan da Khaleel da yakan bama dama a wasu lokutan su kuma Engineers ne,
dan company ɗin nasu aikinsa kenan, mai buƙatar zane amasa, idan da gini duk a
haɗa, kai dai kawai ka ajiye kuɗi ne kaga biyan buƙata.
“Babana kaji fa wani shirme, dama zafi na dafa fata ne?”.
Murmushi ya ɗanyi cikin sanyin muryarsa da shafa kansa yace, “Abie akwai
zafinne ai”.
“Oh ka goya bayanta kenan dai kawai”.
Murmushi ya sake saki mai faɗi fiye dana ɗazun. Sai dai baice komaiba,
saima ɗan hararan Anam data saki baki tana kallonsa ganin murmushi a fuskarsa yayi.
Itako ko gezau kallonsa take kamar ta samu hoton bango. Fuska ya ɗan tsuke da ɗauke
kansa daga saitinta. Itama sai ta janye tana taɓe baki.
Tare da Abie suka shiga, yayinda gaba ɗaya hankalin Anam ke ga littafin data
ɗauka mai tambarin company ɗin nasu da alama samples ɗin ayyukan sune a wajen. Koda
taji shigewar tasu bata maida hankali kansu ba, ta jima tana kalle-kalle, wasu su
birgeta wasu ta taɓe baki harta fara hamma. Sai kawai ta zame ta kwanta a
kujerar.........✍

KU DAI KU GARZAYO A DAMA DAKU A CIKIN WANNAN ZAZZAFAR TAFIYAR CIKIN SALON NA ZAFAFA
BIYAR MASU ZAFIN GASKE.

DUKKA LITTAFAN AKAN NAIRA DUBU DAYA (1k) KACHAL

IDAN KUMA DAYA KIKE SO (300)


BIYU (400)
UKU (500)
HUDU (700)

KARKU BARI A BAKU LABARI, DAN WANNAN SALON NA DABAN NE KUMA TAFIYAR MA TA DABAN CE!

ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN

HAFSAT UMAR KABIR


ZENITH BANK
2270637070

SAI A TURA SHAIDAR BIYAN

07040727902

IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA

09134848107

KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN
MASU MATUKAR SANYA NISHADI.

MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.

SAI MUN JIKU MUTANEN AMANA!💃🏼💃🏼💃🏼

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏽


[10/4, 1:29 AM] Zeenaran🫶🏻: *_Typing📲_*

*_BABU SO....!!_*
_(Miya kawo kishi?)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_Ƙarshen free page_*

*_05_*

...........Sun jima a ciki yana nunama Abie abubuwa, yanda yaketa faman bayani da
murmushi saika rantse bashi baneba. Dan har dariya sukeyi tare da Abie. Kiran
sallar la'asar ne ya fiddosu, hakan yayi dai-dai da shigowar ɗaya daga cikin
ma'aikata office ɗin, sannan kuma dai-dai da farkawar Anam data sha barci hankali
kwance sanyin ac ya gama ratsata.
Shigowar ma'aikacin mai suna Abeed tazo masa a bazata, dan hankalinsa gaba
ɗaya nakan system ɗin gabansa, sai sallamarsa da buɗe ƙofa ne a lokaci guda suka
shiga kunnensa. Da sauri ya ɗago idanunsa batare daya amsa sallamar Abeed ɗin ba ya
kai dubansa gareta. Anam da bata san mike faruwaba duk da itama taji sallamar tai
yunƙurin miƙewa tana laluben veil ɗinta da nufin ɗan lulluɓama jikinta. Abie ya
riga ya shige toilet ɗin cikin office ɗin ɗaura alwala tunkan sallamar Abeed....
“You are vary stupid!! Zaka shigo min kai tsaye”.
A yanda yayma Abeed tsawar da jefa mata rigar suit ɗinsa dake a jikin hanger ba shi
Abeed ɗin ba hatta ita sai da ta zabura. Da sauri ta ɗane kujerar baki ɗaya ta
ƙudindune kanta dan sam bata ƙaunar tsawa a rayuwarta. Cikin rufewar ido da manta
Abie na'a office ɗin ya sake dakama Abeed tsawa da cigaba da masa masifa. Shi dai
yay ƙasa da kansa dan bai san laifinsa ba anan har yanzu, tunda ya san ya yi
sallama ya kuma yi knocking....
“Get out!!”.
Ya sake faɗa a tsawace. Da sauri Abeed yay baya da rufe ƙofar. A fusace ya maida
dubansa ga Anam da ke leƙosu ta cikin rigarsa. Ya watsa mata wata uwar harara,
cikin gargaɗi mai kaushi,
“Idan kika ƙara fitowa da wannan ƴan iskan kayan saina kashe fuskarki da
marukan da bazata ganuba. Stupid girl! An faɗa miki nan muna buƙatar sune”.
Baki ta tura gaba duk da ta mugun tsorata da yanayinsa. “To ni Yaya MM wannan
duk sune kayana ai, kuma ni su na iya saw.......”
Ganin ya yunƙuro zai tashi ta miƙe da sauri ta koma bayan kujera fuska a kwaɓe.
Ƙwafa yay da sake watsa mata harara. Abie dake tsaye da ga bakin ƙofa yana kallonsu
tun ɗazun basu lura da shi ba yay murmushi, domin kuwa wasu abubuwa masu ban mamaki
ya hango a cikin ƙwayar idon ɗan nasa, ya girgiza kai kawai da ƙarasowa ciki. Sai
lokacin Shareff ya lura da shi. Ƙasa yay da kansa dan shi gaba ɗaya yama manta Abie
na'a office ɗin. Miƙewa yay sum-sum ya nufi toilet batare da ya yarda sun haɗa ido
da Abie ba. Shima baice masa komai ba sai binsa da yay da kallo kawai. Anam dake a
laɓe sai da taga ya shige sannan ta fito, cikin taɓe fuska ta ƙaraso inda Abie yake
tana faɗin,
“Uhhm Abie ALLAH Yaya Shareff baida kirki, yanama staff ɗinsa ihu bai masa
komaiba kuma”.
Nanma murmushi kawai Abie yay baice komai ba. Zata ƙara magana Ya Shareff ɗin
ya fito tai saurin komawa bayan Abie ta ɓuya. Sai dai hakan bai hanata ganin
hararar daya watso mata ba.

★★★★★

Washe gari su Abie suka wayi gari da shirin kai kuɗin auren Ya Shareff,
wanda dama yana ɗaya daga cikin dalilinsa na zuwa Nigeria, dan data Anam ne kawai
turota zaiyi tunda yasan akwai mai iya mata komai ai. Ita dai Anam bata san mike
faruwaba ma, dan ta jima bata tashi a barcin safe ba kasancewar daren jiya tunda
aka ɗauke wuta ta kasa komawa barci saboda zafi, duk da kuwa Mom ta kawo mata fan
ta kunna mata saboda tsaki data dinga zubama su Husna kamar wata dangin tsaka, sai
dai kuma fahimtar iya gaskiyarta ne yasa Ikram zuwa ta faɗowa Mom ɗin. Ganin
akwatuna har set uku a falon Mom masu shegen ƙyau da tarin kayan sa rana ya sata
tambayar Ya Khaleel first born ɗin Mom. Shima dai saurayine zangarere da shi dan
yana shekara ta 26 a duniya. Khaleel ƙyaƙyƙyawa ne shima kuma nutsatstse. Sai dai
akwai tsare gida da rashin son raini harma yafi Shareff zafi, dan shi Shareff inhar
baka shiga gonarsa ba babu ruwansa da kai, sannan yana da sakewa da jama'a fiye da
Khaleel. Shine na uku a haihuwa a gidan. Dan sanda Mom ta auri Abba haihuwar Mommy
biyu ne. Daga Shareff sai Maheer da take goyo. Duk da Shareff ya bama Khaleel
shekaru sosai hakan bai hana ƙaunar juna shiga tsakaninsu ba, dan tunda ya dawo
daga Indonesia bashi da wani aboki a gidan kamar Khaleel. Da taimakonsa ya san
wajaje da yawa daya manta, sannan tun a baya idan yazo hutu dama shine abokin
yawonsa saboda nutsuwar yaron na birgesa. Yafi Maheer hankali sosai da sanin ciwon
kansa, dan yanada himma da ƙwazon nema duk da ko maganar aure bayayi ma.
Duk ɗaurewar Khaleel suna ɗan shiri da Anam, sai dai itama ba wani sake mata
yake ba dan miskilanci a jininsa yake. Kamar bazai tanka mataba yanata aikin danna
wayarsa sai kuma ya kalleta. “Kayan auren Yaya Shareff ne”.
“Ya mi?! Dama aure zaiyi!?”.
A yanda tai maganar ya tilastashi sake dubanta da ƙyau, haka kawai yaji dariya ta
taho masa. Amma sai ya gimtse.
“Kinada matsala da auren nasa ne Granny”. (Dan haka yake kiranta mafi yawan
lokaci).
“Kuji Ya Khalel ɗin nan da wani magana. Ni ina ruwana da wani aurensa da har
zai zamar min wani damuwa. Ai sai dai nai murna zai tafi can ya barmu mu huta matan
ta kwashi baƙin hal......”
Jin ta gagara ƙarasawa yasa Khaleel fashewa da dariya, dan dama dai tun ɗazun
ya lura da Shareff daya fito daga bedroom ɗin Mom. Ita kuma sam ALLAH baisa ta lura
ba sai yanzun da yaƙe ƙoƙarin baro corridor ɗin baki ɗaya dan dama kamar ya ɗan
tsayane yana sauraren su, amma a zahiri waya yake dannawa. Duk da ba inda take yayo
ba da gudu ta afka ɗakin barcin su harda murza key.
Shiko dama daba inda take yayo ba harara kawai yawatsama Khaleel da faɗin,
“Dalla tashi muje ka zauna kana abu kamar wani yaro”.
Har yanzu dai dariya ƙunshe a bakin Khaleel ya miƙe. Idonsa na duban ƙofar
da Anam ta shige. Suna ƙoƙarin fitowa yace, “ALLAH my best yariyar nan sam bata da
wayo har yanzu. A hakan wai kuma ta kammala karatu. Bayan rashin wayon ƴan fari a
jikinta harda taɓarama na ganin ita kaɗai ce a gaban su Mamie. Jiya fa harda kuka
ta dinga yima su Mon wai zafi saida aka kawo fan aka kunna mata”.
“Mom ɗince ta biye mata mtsoww ”.
Ya faɗa cikin halin ko in kula. Shi dai Khaleel yace, “Gara dai da aka kunna mata
dan bata saba da zafin nan bane namu. Su da suke fama da dusan ƙanƙara ma wasu
lokutan dan tsabar sanyi. Kaga ko tazo nan dole ta shiga wani yanayi dan kano ogace
ta zafi..”
Komai bai ƙara cewaba yay gaba Khaleel ya bisa.

Kasancewar da Mom da Aunty Amarya sai wata ƙanwar Momy da yayarta za'aje yasa
Anam maƙalema Mom sai taje. Mom bata hanata ba, dan ita tanada sauƙin kai sosai
shiyyasa suke zaune lafiya da Mommy tsahon shekaru, duk da dai itama Mommy ɗin
bawai tanada faɗa bane ko rikici, kawai dai ta tsani Mamie ne saboda tun farko akan
hakan Gwaggo ta ginata, ta riga ta nuna mata shi Abie ɗan uba ne a cikin su Daddy
duk da kuwa ba itace ta haifesu ba. Sai kuma ta kasance mace mai son komai ace
itace sama da kowa, sannan a wajenta ake neman komai, a ganinta bazai yiyu ita
matar farko a gidan ba, sannan mijinta shine babba ace wata a matan ta fita. Fin da
Mamie ta mata kuma ya ƙara ƙiyayyar, itako Mom Abbah bai kai Daddy ba gaskiya, sai
dai na waje bazai taɓa fahimtaba kasancewar ana ganinsu kansu a haɗe a koda yaushe
kuma suna gida ɗaya ne.
Kasancewar matar da Shareff ɗin zai aura ɗiyace ga gwaggo halima (ƙanwar
daddy), kuma mahaifinta yaya a wajen mommy gawurtaccen ɗan siyasa mai muƙamin babba
a jihar ta kano gidane katafare suka iso. Komai yaji na more rayuwa. Fadwa shine
sunanta, ɗiya ga Alhaji Sadiq Dakata. Mahaifinta kamar Yayane ga Mommy. Dan da
mahaifiyarsa, da Mahaifiyar Mommy da gwaggo duk uwarsu ɗaya ubansu ɗaya. Zumincine
mai ƙarfi a tsakaninsu, dan haka ita da Gwaggo suka zaɓama Shareff Fadwa matsayin
mata tunkan ya dawo gida Nigeria. Sunyi hakane a cewarsu dan kar Abie yay tunanin
basa auren Anam. Da farko dai Shareff bai maida hankali ba duk da baice baya sonta
ba. Sai da Mommy ta masa jan ido sannan ya ɗan ke kula Fadwa ɗin. Fadwa ƙyaƙyƙyawar
yarinya ce gwargwado kuma ƴar gata, sannan kuma sele (celebritie) a social media,
musamman tictok da istagram harma da twitter. Idan zan zauna fayyace muku wacece
Fadwa zamu cinye labarinne a kanta. Kuje zuwa dai lokaci zai nuna muku ainahin
Fadwa Sadiq Dakata.
Sun sami tarba ta girma da girmamawa. Inda babu kunya Fadwa ta fito tare da
tarin ƙawayenta da suka cika gidan kallon kaya tun a gaban su Mom. Yayinda su Abie
ke can suna tattaunawa da su Alhaji Sadiq domin tsaida rana. Dama dai shine yace
baya son aita jeka ka dawo, su haɗo komai rana ɗaya su kawo har sadaki sai kawai a
tsaida ranar ɗaurin aure.
Su dai su Mom wannan abu ya sakasu jin lallai akwai gyara a lamarin wannan
amarya, duk da kuwa ƴar gida ce dan sun san wasu a cikin halayenta saboda kowa
yasan ƴaƴan gwaggo Halima basu da ƙwaɓa. har cikin rai suna jin tausayin Shareff
ɗin kasancewarsa bai wani cika zafi da yawan magana ba a mafi yawan lokuta. Amma
sauran ƴan uwan Mommy da yake ƴan uwansune suma sai basuji komaiba a lamari, dan
kuwa dai basu nuna a fuska ba sai dai in sun barma ransune suna nuna normal ne a
zahiri.
Fadwa tasan labarin Anam a wajen Mommy da Gwaggo da mahaifiyarta. Sai dai
bata santa a zahiri ba sosai saboda gwaggo halima ba shiga duk abinda ya shafi su
Abie take ba, tasha jin sunzo ƙasar tabi duk hanyar datai mata ta toshe haɗuwarsu
sai idan wata fitinar suka shirya da su gwaggo shima ita kaɗai take zuwa babu
ƴaƴanta. Hakan yasa yaranta basu wani san Abie ɗin bama balle ƴarsa, shima kuma
bawani gama sanin ƴaƴanta yay ba tunda bata bari su raɓesa. Hakan yasa Fadwa bata
nuna damuwarta da ganin Anam tare da su Mom ba. Amma dai yanda Anam ɗin ta zama
miskila a wajen tana kallon komai ya ɗan ja hankalin su Fadwa da ƙawayenta gareta.
Har takai babu kunya Fadwa na tambayar su Mom ina suka samo Anam ɗin?. Murmushi
kawai Mom tai da faɗin “Itama ƙanwarki ce”. Daga haka ta tsuke bakinta duk da
tambayar bin ƙoƙwanto da ƙawayen Fadwa ke cigaba da jefamasu Mom ɗin. Aunty Amarya
dama bata tanka ba dan ita bata da farin jini a garesu kasancewarta kishiyar Mommy.
Har dai suka baro gidan Fadwa da ƙawayenta basu san matsayin Anam ba. Ita kuma
ta miskile ko ruwa bata sha ba a gidan har suka taho. Gwaggo halima ma duk da taga
kamanin Abie a jikin ta kuma tasan sun zo bata tanka ba bata nuna komaiba.
Anam ma sai da suka ɗakko hanyar gida ta fara yima su Mom mitar Fadwa da
ƙawayenta masu shegen rawar kan tsiya da nuna wayewa. Murmushi kawai Mom da Aunty
sukeyi dan mota ɗaya suke su uku, ƴan uwan Mom ma na nasu su biyu.
Bayan sun iso gida kowa yaji ainahin watan bikin a bakin su Abie. Nan da
watanni biyu. Sauran yaran gidan nata murna duk da wannan ba shine karon farko da
za'ai biki ba. Anyi bikin Rahma dake bima Khaleel, da Binta ƙanwar su Shareff dake
bima Maheer. Yanzu Aysha ce a layi kuma sa'ar Anam ce dan watanni ta bama Anam ɗin
kawai, itace ɗiyar Mommy ta biyar daga ita sai autoci su twins. Ga Anam kam babu
dalili ta wani tsume sai kallonsu take da taɓe baki, har bayan magrib babu fara'a a
tare da ita. Rashin walwalar tata yasa koda Aysha ta tambayeta. Sai tace ba komai.
Sai bayan magrib suna hira duk kusan yaran gidan a falon aunty Amarya, gaba
ɗaya hirar tasu ta ta'allaƙa ne akan shirin biki. Sai dai Anam taƙi tako tanka sai
faman game take bugawa a waya. Sai dai kuma kunenta duk yana a garesu ne. Jin sun
cigaba da damunta ta tashi zaune tana wani taɓe baki da harar Nusaiba mai gwada
rehearsal na rawan da zasuyi wai a wajen dinner....
“Kun wani dage sai tsara events kuke bayan amaryar ma ko aji bata da shi
mtsoww!!”.
Lokaci ɗaya falon yay tsit duk suka juyo suna kallonta. Hussaina ta ɗan waro ido
da ƴar tsiwa tace, “Aiko dai aunty Fadwa nada aji gata ƙyaƙyƙyawa ƴar babban gida
bama son jealous”.
“Jealous!!. K! Hussaina dani kikeyi wai! kowa ma? Ni Juwairiyya ce zanyi
jealous ɗin wancan farin ƙasan mai kama da ƴar tallan kasuwa. Baki da hankali”.
A yanda take maganar a fusace yasa Hussaina tsorata, dan in tsiwa takeji Anam
kakartace a iyawa. Amma shirun nata badan tsoron bane kawai, harda wanda idonta ya
hango ya shigo falon ne yasa tai shiru. Anam kam da sam bataji ko sallamarsa ba sai
faman faɗa take da sule Fadwa iya gaskiyarta. Tsaki ta doka da fisgar tab ɗinta
dake hanun Hashim da nufin barin wajen, karaf idonta ya sauka a kansa. Yana tsaye
tamkar an dasashi ya kafeta da manyan idanunsa masu razana wanda ya shiga gonarsa.
Sosai gabanta ya faɗi, amma da yake ƴar gagiyar bata yarda aga gazawarta a fuska ba
sai ta ɗaukesu cike da wani irin sallo da kaɗasu kamar mai harara ta nufi hanyar
kitchen domin bi ta baya, dan tana shakkar bi ta gabansa tunda a ƙofar falo yake
tsaye. Duk da bai nuna yama ji abinda tace ɗin ba hakan bai hana su Aysha ƙara
nutsuwa ba.

Washe gari Abie yay shirin komawa. Anam ta zauna taita kuka itafa sai dai
su koma tare. Yasan halinta akan kafiya, baiyi da wasa ba yay mata fata-fata, sai
su Abba ne da aunty Amarya keta lallashinta da Ya Khalel. Shareff kam duk da yana
wajen ko tari baiyiba. Yamaƙi nuna yasan abinda akeyi. Sai da zai buɗema Abie baya
zai shiga ne ya harareta. Ƙasa tai da kanta ta sake fashewa da kuka.
Daddy da yaga hararar Shareff na ƙoƙarin shiga mazaunin driver ya dakatar
da shi. “Kaga ku wuce da Mamana tai rakkiyar itama”. Kansa ya duƙar ƙasa fuskarsa
na sake tsukewa da satar kallon Mommy. Murya a rissine yace, “Daddy zanje wani
wajene fa bayan airport ɗin”.
“Sai ku tafi tare da ita tama huce kafin ku dawo gida”.
Sosai takaici ya sake lulluɓesa. Sai dai baice komaiba. Daddy da kansa ya buɗe
gefensa ya sakata dan Abie baya ya shiga. Koda suka bar gidan shi da Abie ne kawai
keta hirarsu. Itako tai tsit kamar bata a motar, sai ajiyar zuciya take faman
saukewa idanunta a lumshe sanyin ac na ratsata. A airport ɗin ma Abie shareta yay
har sai da aka fara shelar masu tafiya a jirgin da zaibi sannan yaɗan fara
lallashinta da ƙara mata nasiha. Daurewa kawai takeyi, amma ita dai bata ƙaunar
zama a ƙasar batare da iyayenta ba. Da ƙyar ya ɓanɓareta a jikinsa domin amsa kira,
tana ganin ya shige ta dirƙushe a wajen. Takaici ya saka Shareff buɗe motarsa yay
shigewarsa. Jin ya mata key ya sata miƙewa da sauri dan ta tabbatar kaɗan daga
aikinsa ya wuce ya barta a wajen.

Sunbar airport ɗin kaɗan kiran Momy ya shigo masa. Idonsa ya ɗan rumtse kafin
ya kai hannu ya ɗaga. “Kana ina?”. Ta faɗa tunkan yay sallama. “Mommy can gidan
mana”. Ya faɗa a tausashe. “What! Al-Mustapha kana da hankali kuwa? Da wannan
yarinyar kake nufin kaje?! To ina mai tabbatar maka maza ka sakota a napep ta dawo
gidan ko ranka ya ɓaci bansan iskanci”. Ɗan jimm yay na sakanni biyu. Sai kuma ya
ɗan saki murmushi. “Okay Mommy ba damuwa”. Numfashi ta sauke a hankali da faɗin,
“Yauwa ko kaifa. Bana son wannan karon naji abinda bai minba kaga dai yanzu akwai
banbanci da da. Ka kula ka bita a yanda take so dan ALLAH”. Nanma murmushin kawai
yayi batare da yace komai ba, sai dai har cikin kunnenta tajisa dan haka tai masa
sallama ta katse kiran. Wayar ya ajiye shima ya cigaba da tuƙinsa a nutse har suka
iso.
Da sauri ta waro idanu waje ganin inda suka zo, ta dubesa idanunta nayin
ƙwal-ƙwal na tahowar kuka. “Yaya! nidai ka kaini gida bazanje wannan gidan ba”.
Harara ya zuba mata, batare da yace komai ba yay parking a ƙofar gate ɗin.
Sanin abinda zatai nan gaba shine roƙonsa ko guduwa ya sashi dubanta, “Haɗiyemin
wannan silly hawayen banzan kafin nai miki dukan mutuwa a wajen nan”.
Babu wasa a zancen nashi, dan haka ta haɗiye sautin kukan sai dai hawayen kam
sun kasa tsayawa. Wayarsa data fara tsuwwa ya ɗauka, ganin mai kiran ya sashi
ɗagawa da kaita kunne. “Ina waje”. Kawai ya faɗa tare da yanke wayar. Ko mintuna
biyar basu gama cikaba Fadwa ta fito cikin yauƙi da yanga. Wando da riga ne a
jikinta parkistan ƙirar Egypt. Sosai kalar kayan ya fidda mata ƙyawunta. Musamman
yanda ƙaton gilashin data saka ya kusan mamaye rabin fuskar tata da haska farar
fatarta. A hankali Anam taja guntun tsoki da ɗan laɓe baki. Sarai Shareff ya jita,
sai dai komai baice mataba har Fadwa takusa ƙarasowa garesu.
“Fita ki koma baya”.
Yanda yay maganar a dake batare da ya kalleta ba ya sata juyowa ta kallesa. “Are
you daft?!”.
Maganar tasa tayi dai-dai da isowar Fadwa jikin motar tana ƙoƙarin buɗe gaban
ta shiga dan batai zaton ganinsa da wani ba ma balle wata. Da sauri Fadwa taja
baya saboda yanda Anam ta buɗe murfin a fusace. Saura kaɗan ta bugeta ma ALLAH dai
ya taƙaita abun. Ko kallon inda take Anam bataiba tai ƙoƙarin barin wajen maimakon
baya daya bata umarnin komawa. Sai dai kuma Fadwa tasha gabanta da sauri....
“K! K! Dakata k! Ƴar uban wacece a motar mijina?”.
Ba kowacce hausa Anam ke ganewa ba, dan haka a yanzun ma bata fahimci furucin
farko ba hakan yasata kasa haɗa ma'anarsa dana ƙarshe da ƙyau. Amma a yanda Fadwa
tai maganar ta tabbata ba'abune mai ƙyau ta faɗa ba. Wani banzan kallo ta watsa
mata kawai dajan tsaki ta ratseta zata sake barin wajen. Hannu Fadwa tasa ta
fisgota ta maidota baya a wani irin fusace, kasancewarta mutum mai saurin zuciya da
son yanke hukunci sai kawai ta ɗaga hannu da nufin zabgama Anam ɗin mari.........✍

*_Tofa babbar magana, wai ɗan sanda yaga gawar soja. Hajiya Fadwa daga ganin sarkin
fawa sai miya tai zaƙi. To ku garzayo cikin tafiyar zafafa biyar domin ganin yaya
wannan wasan zai kasance😂. Dan tabbas akwai cakwakiya, idan nace cakwakiya ina
nufin cakwakiya ƴar gaske. Yanda Fadwa take a tsaye Anam ɗin ma ba kanwar lasa
bace. Littafine daya ƙunshi abubuwa da yawa. Rikicin zumunci, makirci, son zuciya,
kishi, cin amana, kai harma da SARAN ƁOYE. Wasa ne kashi-kashi, dake da players
daban-daban. Karku bari ayi babu ku, zafafa dabanne masoya, musamman na wannan
ƙarnin da zasu zo muku a cikin zafi na musamman. Karna cikaku ku dai ku garzayo
kawai._*

_Dan girman ALLAH, dan girman ALLAH, dan girman ALLAH kizo ki mallaki halak
ɗinki, idan baki da kuɗin saye ko baki da ra'ayin saye basai kin damu da karantawa
ba dan baya cikin wajib. Mai tunanin siya ko mana mugunta ki fitar kiji tsoran
ALLAH karki cutar damu bamu cutar dake ba, idan kinyi shirin haka da gayya ko
izgilanci a garemu muna roƙon UBANGIJIN al'arshi mai rahama mai jin ƙai, mai sanya
alkairi a zukatan dake ƙudurta sharri ya shiryeki ya ganar dake gaskiya ya kuma
bamu kariya daga abinda zuciyarki ke ƙulla miki😊🙏🏻._

KU DAI KU GARZAYO A DAMA DAKU A CIKIN WANNAN ZAZZAFAR TAFIYAR CIKIN SALON NA ZAFAFA
BIYAR MASU ZAFIN GASKE.

DUKKA LITTAFAN AKAN NAIRA DUBU DAYA (1k) KACHAL

IDAN KUMA DAYA KIKE SO (300)


BIYU (400)
UKU (500)
HUDU (700)

KARKU BARI A BAKU LABARI, DAN WANNAN SALON NA DABAN NE KUMA TAFIYAR MA TA DABAN CE!

ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN

HAFSAT UMAR KABIR


ZENITH BANK
2270637070

SAI A TURA SHAIDAR BIYAN

07040727902

IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA

09134848107
KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN
MASU MATUKAR SANYA NISHADI.

MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.

SAI MUN JIKU MUTANEN AMANA!💃🏼💃🏼💃🏼

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏽

[10/26, 7:15 PM] My Zafafa: *_Typing📲_*

*_BABU SO....!!_*
_(Miya kawo kishi?)_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_07_*

.........Tunda suka tafi tsakanin shi da ita babu wanda yayma ɗan uwansa magana.
Yanata tuƙinsa da amsa wayoyi itako tana buga game a wayarta cike da nishaɗi har
suka iso. Motar ta buɗe tai ficewarta tana taɓe baki, sai da ta rufe masa ƙofar
batare data kallesaba tace, “Jazakallahu khairan” tai gaba abinta. Fusgar motar yay
da ƙarfi yay gaba har yana tada ƙura. Hakan yasata faɗin, “Kaji dashi in kayane
dai”.

Koda ya tashi a aiki baibi takanta ba yay wucewarsa gida. Tun Anam na jira
da marmari har ranta ya fara ƙuna gashi bata sayi layin Nigeria ba har yanzun.
Sosai ranta yake a ɓace ga yunwa dake bala'in cin hanjinta dan bawani abun kirki
taci da safeba ta fito, da rana ko inibi data taho dashi a bag kawai tasha da
strawberry. Ganin yamma na ƙara mata, gashi bata san yanda zata kira wani a gidan
ba tunda babu waya ta fito domin samun abun hawa ko zata iya ganewa. Ga wani irin
zafi dake ratsata duk da rana ta risina kasancewar anyi la'asar, sai dai ita zafi
takeji matuƙa kodan inda ta fito akwai ac ne.
Ta tare abin hawa yafi sau huɗu amma ta rasa yanda zata musu misalin
anguwar, wasuma basa gane jagulalliyar hausarta da yaren malay ya cinye, turancin
ma idan tayi wasu suce basaji wasu suce basu fahimci kwatancenta ba. Kanta ta dafe
ƙwalla na cika mata ido dajin wani irin tsanarsa a cikin ranta, tabbas bata ƙaunar
wulaƙanci shiyyasa bata wulaƙanta kowa, kai bama ta tashi taga iyayenta na
wulaƙanta wani ba kowa abin girmamawarsu ne koda bai kaisu wani matsayi na duniya
ba. Hannu takai a hankali ta share ƙwallar idanunta tana maijin kewar iyayenta da
ƙaunarsu, waɗannan matsalolin na ɗaya daga cikin abinda ta guda a zuwanta hidimar
ƙasa Nigeria, amma su Mamie suka kasa fahimtarta.......
Harya gota ta ya dawo baya da mamakin kodai gizo idonsa ke masa. Dai-dai
saitin da take yay parking da sauke gilashin motar. Tabbas itace inhar bai ruɗeba,
dan yanda yarinyar ta shiga ransa bayajin zai manta fuskarta koda a barci ya tashi.
“Beauty!”.
Ya faɗa cikin tsantseni da taraddadin wasiwasi.
Duk da tajisa tunma tsayuwarsa hakan baisa ta ɗago ba. Sai ma sake haɗe
fuska da tai ta ɗauke kai gefe fiye da yanda ya sameta. Murmushi ya saki dan yanda
tai ɗin ya tabbatar masa ita ɗince. Buɗe motar yay cike da farin ciki ya fito. “A
gafarce ni. Assalamu alaiki ƙyaƙyƙyawa”. Duk da bata saki fuska ba ta amsa masa. Ya
koma ta gabanta cikin sake raunana murya. “Inaji a jikina ke rabonace Beauty. Ranar
Yayanki ko saurayinki ne ban saniba ya gudumin dake gashi yau ALLAH ya haɗamu daga
ni sai k”. Karon farko ta ɗan ɗago ta dubesa, ya sakar mata murmushi. “Dan ALLAH
kar kice baki ganeni ba”.
“Bamma taɓa ganinka ba”.
Ta faɗa da ƙoƙarin barin wajen. Sauri bin bayanta yay. “Please dan ALLAH karkimin
haka. Ni ne wanda muka taɓa haɗuwa a GJ restaurant da daddare”. Sarai ta ganesa tun
kiranta Beauty da yay dan muryarsa bata bace mata ba. Amma sai ta sake ɓata fuska
aɗan fusace tace, “Bani bace Please kabar bina”.
“Kiyi haƙuri bazan iya daina binki ba wlhy dan kullum cikin addu'a da sadaka
nake akan ALLAH ya sake nunamin ke. Ya kuma amsamin sai nayi sakaci da damata”.
Sosai ya bata dariya a wannan gaɓar, wai sadaka. Dan kawai ya ganta zaiyi
sadaka. Hararsa tai zata sake wucesa ya babbake ko'ina. “Dan ALLAH ki saurareni”.
Kanta ta dafe dan yanata faman haɗata da abinda bazata iya jayayya ba. Hakan yasa
dole ta nutsu ta sauraresa. Bawata magana sukaiba damar kaita gida kawai ya nema.
Bata da mafitar data wuce binsa, amma maimakon gida da yace zai kaita sai kawai ta
buƙaci ya kaita inda zata sai layin waya. Bai musa mataba, dan a ganinsa hakanma
wata damace.
Kai tsaye office ɗin mtn dake cikin wata plaza yakaita duk da yasan sun
tashi aiki yanzu. Sai dai yanada alfarmar da za'a iya biya mata buƙatarta a wajen.
Ilai kuwa tarba ta mutuntawa taga ana masa a wajen, yanda kuma suke gaisuwa da ogan
wajen taji a ranta ɗan uwansane ko aboki.
“Mutumina wannan ƴar shilar fa haka?”.
Abokin ya tambaya cike da shaƙiyanci cikin zaurancen hausa da Anam ta kasa gane
komai dan shima ya fahimci bata iya hausan ba, saboda yanda yay mata tambaya da
hausa ta gagara bashi amsa mai ƙyau. Dole suka koma magana da turanci. Murmushi
kawai yay batare daya bashi amsaba, sai ma danna waya da yake faman yi abinsa.
“Wai ka zama kurma ne?”.
Abokin ya sake tambaya yana harararsa.
“Sarai ina jinka. Kai dai yi aikinka kawai ba buƙatar tambayar ne”.
Dariya kawai abokin yay ya cigaba da ƙoƙarin ɗaukar Anam hoto. Tun a gurin ta
ɗora layin akan wayarta, ta kuma tambayesu ko zata iya amfani da shi. Kasancewar
abokin nasa babban ma'aikaci sai ya amshi wayar yay ƴan danne-danne ya miƙa mata.
“Indai kiran gaggawa kike sonyi da shi bashi nan da mintuna talatin sai kiyi”.
Godiya ta masa tare da duban saurayin da har yanzu ko sunansa bata sani ba.
“Zamu iya tafiya?”.
“Why note Beauty”.
Ɗan murmushi kawai tai da mikewa. Shima ya bama abokin nasa hannu suka cafke.
“Friend ina zuwa ka jirani Please ”.
“Ba damuwa”.
Cewar abokin nasa yana dariya.

Ganin sun ɗan gota plaza ɗin tace su ɗan tsaya mintuna talatin ɗin su cika. Bai
musaba sai dai ya kalla agogonsa duk gudun kar lokacin salla ya shiga. “Beauty
inaga muɗan matsa gaba akwai massallaci sai na shiga nai magrib ko”.
“Babu damuwa”.
Ta faɗa hankalinta akan wayarta. Tun fitarsa a motar babu abinda take sai irga
mintuna har ALLAH yasa suka cika. Kai tsaye number ɗin Abie tahau gwadawa dan ta
loda kati daga kuɗinta na bank a ciki. Taƙi samunsa saboda network. Komawa tai kan
Mamie itama dai yaƙi tafiya kiran. A take idanunta suka sake cika da ƙwalla, ta
kife kanta a gwiwarta tana karanto duk addu'ar da tazo mata a baki. A haka ya dawo
ya sameta. Sai dai tanajinsa tai azamar goge hawayen nata ta haɗiye kukan.
“Beauty ina muka dosa yanzu kenan?”.
“Abinda nake tunani kenan, dan kona maka kwatance ba lallai ka gane ba.
Amma in ban takurakaba ka kaini restaurant ɗin nan kawai ka ajiye zan samu mafita”.
Kallonta kawai yake cike da nazari. “Na miki wani tambaya mana in bazaki
damu ba?”.
Shiru kamar bazata amsashi ba. Sai kuma taja numfashi da jinjina masa kanta.
Gyara zamansa yay sosai yana fuskantarta. “Harshenki ya tabbatar min idan ma ke ƴar
Nigeria ce ba'anan kike rayuwa ba? Hakan na nufin ke baƙuwace shiyyasa bazaki iya
gane inda zakije ba?”.
Nanma kamar bazata amsashi ba sai kuma ta ɗan kallesa ta duƙar dakai. “Karka
damu ka kaini inda nace kawai Please”.
“Baki son na sani ko?”.
“No, kawai”.
Ta faɗa a taƙaice. Bai sake magana ba ya ɗan rausayar da kansa da yima motar key
yana murmushi.

Koda suka iso kamar yanda ta buƙaci ya tafi ya barta a wajen bai yarda
yayi haka ba. Cikin lallashi ya sata suka shiga wajen. Yabi ya takura mata akan ta
faɗi mi take son ci amma taƙi, dan Anam nada wani hali inhar bata saba da kai ba
bata taɓa yarda ta sake da kai. Shi kansa badan tana neman mafitaba bazata bisaba
tun farko ko wane irin naci zai mata kuwa. Haƙura yay ya amsar musu drinks kawai da
snacks amma ko kallon natan bataiba balle yasan zataci.
Tunanin kiran Aysha ne yazo mata a rai. Ta sake zaro wayarta dake cikin bag ta
hau lalubenta. Cikin sa'a kuwa kiran ya shiga, sai dai harya katse ba'a ɗaga ba.
Bata gajiba ta cigaba da kira har wajen 8missed call amma babu amsa. Da ƙyar ta iya
ƙoƙarin danne kukan dake son taho mata......

_______________________

Ko kaɗan baiyi tunanin bazata iya maido kanta gida ba. Hasalima zuciyarsa
raya masa take tuni ta dawo ɗin saboda yayi over time a office yau yana aiki, ga
kansa na masa ciwo. Daya shigo gidan ma a ɗan gurguje ya shiga suka gaisa da Mommy
ya fito. Wanka yayi a gaggauce shima saboda magrib dake kusantowa. Koda ya kammala
shiri ya fito a compound ya haɗu da Abbah da Khaleel suma zasu massallaci. Tare
suka fice, bayan an idar da magrib basu dawo gidaba sukai zaman jiran isha'i....

Tun kafin su ƙaraso suka hango Mom da Aunty Amarya tsaye cirko-cirko a ƙofar
sashen aunty Amaryar. Dukansu sai suka nufi can dan da alama babu lafiya. Shidai
kusan shine ƙarshe dama. Daddy da suka haɗu a massallacin ne ya fara jefama su
aunty amarya tambayar “Lafiya kuke tsaye anan haka?”. Aunty amarya ta bashi amsa
cikin damuwa da ruɗani. “Daddyn Shareff lafiya ba lafiya ba. Anam ce bata dawo
gidaba har yanzun. Mubarak yaje har wajen aikin nata kuma maigadi ya tabbatar masa
babu kowa a ciki ita ɗincema kusan ƙarshen fita, ta kuma jima a titi kafin yaga
wani ya ɗauketa a mota”.
“Innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un”. Daddy da Abba suka faɗa kusan a tare.
Shareff ma dake daga bayansu gabansa ne ya faɗi, suka haɗa ido da Daddy daya juyo
yana masa kallon tuhuma. cikin son danne abinda keson taso masa yace, “Shareff
nasan dai kaji mi mamarku ta faɗa ina ka baromin yarinya?”.
Sosai ƙirjinsa ke luguden duka. Ya girgiza kansa da risinar da idanunsa da
sukai sirkin ja kaɗan saboda gajiya da ciwon kai.
“Ba girgizamin kai zakaiba ka buɗe baki kai magana!!”. Daddy ya sake faɗa a
tsawace.
Kansa a ƙasa yace, “Ban baro office ba sai kusan 6, shiyyasa nai
tunanin ta dawo gida”.
“Shareff are you out of your senses?!! Har kake gayamin kazata tama dawo gida.
Kana da hankali kuwa? Innalillahi wa-inna'ilaihirraji'un”.
“Wai lafiya mike faruwa ne?”.
Mommy da Hassan yaje ya sanarma gidan babu lafiya ta faɗa tana ƙarasowa wajen. Babu
wanda ya iya bata amsa saboda maganar da Daddy ya cigaba dayi a kausashe cikin kuma
tsananin ɓacin rai....
“Wlhy na baka nan da zuwa ƙarfe sha biyun dare ka kawomin yarinyata gida,
inba hakaba sai ranka yayi mummunan ɓaci Al-Mustapha!!”.
Cikin sauri Mommy ta dakatar da shi itama a fusace. “A'a Alhaji kamarya
da wannan hukunci haka. Shine ya ɓatar da koma wacece ake neman da za'ace ya fita a
wannan daren nemanta bay......”
“Babu ruwanki a wannan maganar, idan kuma kikace zaki shiga wlhy zan sakaki
nadama ne!!”.
Gaba ɗayansu binsa sukai da kallo ganin yanda yabar wajen a matuƙar fusace.
Banda Shareff da kansa ke ƙasa. Abba ne ya dubesa da damuwa shima, sai dai cikin
sauƙaƙa murya dan bai kai Daddy zafi ba yace, “Son kayi kuskure. Ka manta Anam babu
inda ta sani, ko anguwarnan bana zaton ta san sunanta ma, kag........”
A harzuƙe Mommy ta katse Abba “Anam!!. dama akan wannan tsifatar yarinyar ake
wannan tada jijiyar wuyar? Shareff bance ka fita harkar yarinyarnan ba a gidan
nan?”.
Bai iya ya ɗago ya kalleta ba, dan baisan wace amsa zai bataba. Tana ƙoƙarin
nufosa isowar Gwaggo ya dakatar da ita. “Wai hayaniyar mi nakeji a gidanne haka
kai?”. Duk juyawa sukai gareta. Ganin kowa ya kasa cewa komai Khaleel yace, “Anam
ce bata dawo gida ba”.
“Shine miya faru kuma? Ita ɗin yarinyace?”.
“Haba Gwaggo ya zakice haka? Nawa Anam ɗin take? Sannan ina ta sani bayan
kinsan kamar baƙuwa take a ƙasarnan bama garin kano ba”.
Harara Gwaggo ta zubawa Abba mai maganar. “Oh to kana faɗaminne ko kana
tunamin Abubakar? Gallaƙeƙiyar budurwa da yanzu idan aka sakata ɗaki da namiji zata
samo ciki kake sanarmin nawa take? Toni abindama ban ganeba mi'akema hayaniyar
anan?”....
“Titsiye Shareff sukai yaje nemanta kamar shine yace ta tafi yawon tazubar
ɗin, dan nasan bai wuci can ɗin ta tafi ba tunda an saba a inda aka fito..”
“A lallai kuna bukatar Addu'a Abubakar. Shi Mustapha ɗinne ya kaita ya ɓatar
da zakuce yatafi nemanta a wannan daren bayan wahalar da yaje ya gama shawowa a
wajen aiki ya dawo. Kai Mustapha muje naga ubanda zai saka fita ko nan da gate a
daren nan dan.......”
Sauran maganar ta maƙale ganin kaf wajen babu alamar Shareff ɗin. Su dukansu
babu wanda yasan yama sulale yabar wajen. Horn da ƙarar buɗe gate ya sakasu juyawa
can gaba ɗayansu. Sai dai kafinma wani yay wani yunƙuri har motarsa ta fice.....

Wajen aikin nata ya fara zuwa, sai dai kamar yanda maigadin wajen ya
faɗama Mubarak shima haka ya sanar masa. Lokacin da yake tafiya a hankali ya dinga
tafiya kozai ganta a hanya. Amma ko alamarta babu duk da titin wajen tako'ina akwai
hasken fitulun solar. Duk da hakan bai fasa sake bi a hankali yanzun ma yana
dubawaba har ƙarshen titin. Ganin har tara ta gota na dare yay fakin gefen titi ya
kifa kansa kan sitiyari dan ciwo yake masa matuƙa kamar zai faɗo ƙasa. Dama tuƙin
yinsa kawai yake cikin dauriya.

A gida kowa ka kalla a cikin damuwa yake, idan ka cire Gwaggo da Mommy
da suketa bala'i da kowa ya kasa fahimtar dalilin yinsa. Aysha harda kukanta. Dan
ansan ko wayarta aka nema baza'a samuba tunda bata da layin Nigeria. Abba da Daddy
da Khaleel ma sun fice police station.
“Aunty wayarki sai haske yake tun ɗazun”. Hassan ya faɗa yana duban Aysha
data zuba uban tagumi tana sauraren masifar Mommy kawai daketa faman kai kawo
tsakanin bedroom ɗinta zuwa falo. Kamar Aysha bazatabi takan wayarba sai kuma
tacema Hassan “Ciromin daga cajin”. Ciro mata yay, ganin bata san no ɗinba tai
tsaki ta ajiye. Duk kiran da aka cigaba dayi har kusan sau biyar bata kulaba. Sai
ma ɗaukar wayar datai rai a ɓace zata kashe sai saƙo ya shigo da no din da aketa
kiran nata. Guntun tsaki tai ta buɗe dan taga wai waye ma ya addabeta ya barta taji
da damuwarta ma itakam. Zumbur ta miƙe da waro idanu, har zata fasa ihu sai kuma
tai saurin gumtse bakinta da satar kallon inda Mommy take. Tai saurin haɗiye farin
cikinta ta nufi bedroom ɗinsu da sassarfa. Jikinta har rawa yake ta maida ƙofar ta
rufe harda saka key tana dailing number ɗin...
“Blood da gaske kece?”.
Kamar jira Anam keyi ta fashe mata Aysha da kuka. “Ya ALLAH Blood Please kibar
kuka, kina ina ne yanzu? Ga gida duk hankalin kowa a tashe da rashin dawowarki su
Yaya dasu Abba duk sun fito”. Ta ɗanji sanyi, amma hakan bai hanata jin zafin
Shareff ba. Da ƙyar tace, “Zan tura miki address ɗin yanzu bansan inaneba”.....
Aysha na katse kiran tai kiransa.

Har yanzu kwance yake kawai akan sitiyari, yama rasa wane kalar tunani zaiyi
shi kam. Ring na wayarsa ne ya katse masa tunani. Yay banza da wayar harta tsinke
aka sake kira. Nanma bai ɗaukaba sai ana uku ya ɗago a fusace da nufin cin uwar mai
damun nasa yaci karo da sunan Aysha. “Lafiya kika isheni da kira ke kuma?”.
“Kayi haƙuri Yayah. Anam ce ta kiranifa yanzu da wani number sai kuka take.”
Idanu ya rumtse da ƙarfi yana sauke wata irin bahaguwar ajiyar zuciya da har
Aysha na jinsa. “Turomin number”. Ya faɗa a takaice kawai da katse kiran. Mintuna
biyu kacal number ɗin da address ɗin data turo mata duk ta turo masa. Wayar ya
cilla gefensa yayma motar key da fisgarta a guje yabar wajen. Tafiyar mintuna
ƙalilance ta kawosa wajen saboda uban gudun daya zabga..........✍

_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_


*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:


07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇


09134848107

*_ALLAH yasa yau a rama mana marinmu😹😹😜🚶🏻_*


[10/26, 7:15 PM] My Zafafa: *_Typing📲_*
*_BABU SO....!!_*
_(Miya kawo kishi?)_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_Da sunan ALLAH mai rahama mai jin kai. Ya rabbi ka bani ikon rubuta abinda zai
amfani al'ummarka. Ka tsareni rubuta abinda zai cutar da ni da su. ALLAH ka
gafartama mahaifina da dukkan sauran musulmai. Ka ƙara mana lafiya da zaman lafiya
a wannan ƙasa. Ka azurtamu da shugaba na gari mafi alkairi a garemu da ƙasarmu_*

*_06_*

...........Kafin ta sauke nata data ɗaga Anam ta sauke mata lafiyayyen mari daya
saka Shareff ɗago idanu a karon farko ya kallesu. Fadwa tai saurin dafe kuncinta
tana kallon Anam dake jifanta da wani shegen kallo na gargaɗi tana huci. Mamaki,
al'ajab da tsantsar ruɗanin daya haɗu da azabar zafin mari take kallonta ƴar ficit
a gabanta. Ba ita kaɗai ba, hatta Shareff wutar kansa ta ɗauke dan mamakinta da
ƙarfin hali dama tsaurin idanu.
A fusace Fadwa ta kai hannu da nufin shaƙota. Wani shegen kallo ta sake watsa
mata da riƙe ƙugu, babu alamar tsoro kona sisi a idanunta cikin zafin rai da
harshen nasara ta nunata da yatsa.
“Niba takalmi bace, ballantana ƙafafunki suyi tunanin takawa a duk sanda
sukaga dama. Respect your self ok? Shashasha”. Ta ƙare faɗa tana barin wajen cikin
takun izza...
Tamkar gunkin da aka dasa haka Fadwa ta kasance tsaye tana binta da kallo, dan
da gaske wutar kanta ce ta ɗauke baki ɗaya har tama rasa hukuncin da zatai mata.
Kusan taku biyar da barin Anam wajen Fadwa ta dawo hankalinta, zabura tayi zata
bita Shareff da mamaki ya hanashi motsin shima ya buɗe motar ya fito, cikin bada
umarni yace, “Ƙyaleta”. Juyowa tai tana kallonsa idonta jajur, hakama fuskarta tayi
ɗan ja abinka da fara. Tana bala'in jin shakkarsa, amma sai ta kasa daurewa cikin
ɗaci tace, “Soulmate! Na ƙyaletafa kace?”.
Kansa ya jinjina mata cikin ɗan lumshe idanu da jingina da motar, sosai take
masa kallon tunzura, amma tai ƙoƙarin haɗiye dukkan abinda ke bakinta. Batare da
tace komai ba ta juya da nufin komawa gida. Hanunta yay saurin riƙowa, tai ƙoƙarin
fisgewa amma ya hanata damar hakan. A jikin mota ya jinginata idanunsa akan
ƙyaƙyƙyawar fuskarta da hawaye ke sauka. Ba abinda Anam tai mata bane ya sata kuka,
hanata ɗaukar matakin da yayi ne yafi ƙona mata rai.
Handkerchief ya mika mata, idanunsa na mata kallo cikin lallashi “Nace miki
bazan ɗauka mataki bane?”. Idanunta dake ƙara cikowa da hawaye ta ɗago ta kallesa.
Ya jinjina mata kai alamar tabbatarwa. “Bana son ɗaukar mataki cikin fushi akan
kowanne irin abu ki kiyaye wannan. Shiga muje”.
Ƙara ƙuna zuciyarta tayi da kalamansa, kamar tace bazataje ba ta fasa sai
kuma ta danne saboda shawaran su Mamanta akan ta danne komai dazai mata a yanzu har
ta shiga gidansa. Sannan koba komai tana son sanin wacece yarinyar nan, amma cikin
fushi tasan bazai sanar mata ba ɗin. Umarninsa tabi ta buɗe motar ta shiga,
idanunsa da suka kaɗa sukai jaa ya ɗan bita da su, sai kuma ya janye dayima motar
key yay reverse.
Kasancewar anguwace da kakan daɗe bakaga abin hawaba yasa har suka
cimmata. Tafiya take tana sharar hawaye. Duk da horn da aketa faman mata baisa ta
juya ba. Ransa ya ƙara ɓaci, a fusace yay parking tare da fitowa yasha gabanta,
kanta ta ɗauke gefe kamar bata gansa ba zata raɓashi ta wuce.
Hannayensa ya tura cikin aljihun wandon Jeans ɗinsa. “Idan kika ƙara step
ɗaya a wajen nan sai jikinki ya faɗa miki!”. Cak ta tsaya iya taku biyun da tai,
wasu irin hawaye masu zafi suka ƙara ciko mata idanu. Motar ya nufa idanunsa tamkar
zasuyi aman wuta. Duka kawai take tsoro, dan haka ta share hawayenta dan bata
bukatar da ga shi har budurwar tasa su gani, motar ta buɗe ta shiga. Yay ƙaramar
ƙwafa da buɗewa shima ya shiga, ya fisgeta da gudu zuwa kan titi batare daya ƙara
kallon kowaccensu ba. Sunyi tafiya kusan na minti biyar dai-dai gidan wani abinci
Fadwa ta dubesa, “Please Soulmate banyi breakfast ba”. Shiru yay kamar bazai tanka
ba, bai kuma da alamar tsayawa, itama kasa ƙara cemasa komai tayi saboda yanda ya
haɗe fuska matuka. Harma ta haƙura sai taga ya gangara gefen titi dai-dai wani
restaurant da bama tasan da shi ba. Buɗe motar yay ya fita batare da yace musu
komaiba, itama Fadwa sai ta fita tana harar Anam data maida hankali ga latsa waya
kamar bata a motar.
Suna ƙoƙarin barin wajen yakai dubansa gareta, dai-dai ta ɗago itama suka
haɗa ido. Fuska ta sake ɗaurewa tamkar yanda shima ya sake tsuke tasa. A yanayin
fusata ta janye nata da ɗan kallar gefen Fadwa. Har suna gab da shiga wajen bata da
niyyar fitowa ita, sai da suka shige da kusan minti biyu sannan ta fito dan haka
kawai zuciyarta ta raya mata ta bisu koba komai zata ragema Fadwa jin daɗi ai.
Cikin taku a hankali ta shigo wajen, dai-dai yana magana waiter idonsa ya sauka
a kanta harta ƙaraso inda suke, kujera taja ta zauna. Idanun nasa ya ɗauke gefe,
tare da yin kamar bai ganta ba ya ɗauka wayarsa ya hau dannawa. Kallonsa ta ɗanyi
tana tura baki, batare data kalli inda Fadwa take ba itama ta hau latsa tata wayar
cikin kwaikwayon salon da yayi.
Ta gefen ido ya dubeta, numfashi ya ɗan ja a fisge tare da maida hankalinsa
ga wayarsa a zuciyarsa yace (azababbiyar yarinya).
Kamar tasan mi yake ayyanawar ta ƙara ɗaure fuska tana hararsa shi da Fadwa
da hankalinta itama gaba ɗaya ke kan wayarta da alama akwai abinda takeyi mai
muhimmanci. Isowar waiter ɗauke da tray ya sakasu ɗagowa su duka. Har waiter ɗin
ta gama shirya musu abincin tabar wajen idon Anam nakan nasa. Ya ɗau cokali zai
fara ci tace, “ALLAH Yaya abincinka yafi nawa nama”.
Duk yanda yaso basar da ita ya kasa. Ya kafeta da idanu kamar mai harara
“Kuɗinki ko kuɗina?”.
Fuska ta taɓe “Naka ne. Amma kuma ai ina cikin masu cin gadonka idan ka mutu,
kaga banda laifi idan nayi magana”.
Wani wawan tsaki Fadwa ta saki tsanar Anam na ƙara faɗi a ranta.
“Shiga shanu ba sharo”Anam ta fada cikin sakin siririyar dariyar data sake kular
da Fadwa (*Sharo ba shanu* bahaushiyar malaysia😹😆)
Tattausan murmushi kawai ya saki a karo na farko da cigaba da cin abincinsa.
(Batun yanzuba ya fahimci bata da riƙo. Sai dai ya tabbatar wannan sauyawar tata
lokaci guda ba'a banzaba akwai abinda ke ranta).
Fadwa ta kafesa da kallon mamaki, sai dai shi yaƙi yarda ya kalla inda take.
Saurayin dake kusa da su da drama ɗin tasu taja hankalinsa tun ɗazun yay ƴar dariya
idonsa akan Anam shi kuma. Juyawa tai taɗan kallesa. Ganin shima ita yake kallo ta
ɗauke kanta tana harararsa, abincin Shareff ta ƙara kallo, burinta kawai ta yanda
naman kan plate ɗin nasa zai dawo nata, ganin hankalinsa nakan wayarsa tace.
“Yaya!”.
“Uhhyim!”.
Ya amsata batare da ya daina abinda yake ba. “Na faɗa maka wani abu?”.
“Uhhm”
Nanma ya sake faɗa batare daya ɗago ɗinba. Ɗan shiru tai tana nazari. Bayan kusan
sakan talatin ta dubesa sai kuma ta ɗan harari Fadwa ta maida dubanta ga ƙofar
shigowa. “Lah Yaya wannan ba Aunty bace?”.
Kamar bazai ɗagoba sai kuma ya ɗago ɗin jin kamar tayi maganar a serious.
Kallonsa ya kai ga ƙofar duk da bai san wace aunty take magana ba akai kamar yanda
itama Fadwa da gaba ɗaya takaici ya turniƙe takai kallonta wajen. Wuff ta kwashi
kusan rabin naman daya tsole mata ido ta maida a plate ɗinta. Lokacin da yake
juyowa fuska a tsuke harta miƙe a table ɗin ta koma na kusa da su da guy ɗin da duk
hankalinsa ke kansu yake.
Plate ɗin abincin nasa ya kalla sai kuma ya kalleta. Kauda kansa yay gefe
saboda murmushin dake neman suɓuce masa. Ya ɗan jinjina kansa dayin ƙwafa. Fadwa
dai kallonsa kawai take mamakin tsaurin idon yarinyar nan na nema shaƙureta.
Saurayin da gaba ɗaya komai na Anam ya gama tafiya da imaninsa shima
fuskarsa ɗauke da mayataccen murmushi yake kallonta. Ya sake sakin murmushi ganin
duk laumar abincin da zata kai sai da yankan nama. Cikin murya ƙasa-ƙasa yanda ita
kaɗai zataji yace, “In ƙara siya miki wani gimbiya?”.
Kai ta ɗago ta kallesa, sai kuma ta saci kallon Shareff. Ido suka haɗa, ya
zuba mata hararar da hanjin cikinta suka kaɗa, amma saita fuske cikin dakewa. Ƙasa
tai da idanunta Tana ƙoƙarin sake kai abincin bakinta kamar bata gansa ba, saurayin
ya sake ɗan matsota cikin ranƙwafowa har tana jin hucin numfashinsa yace, “Queen
Please”.
Wani irin cije baki Shareff yayi da ƙarfi, sai kuma ya miƙe gaba ɗayansa.
Gabansu ya iso ya ɗauka wayarta da saurayin ke ƙoƙarin ɗauka. A kausashe yace,
“Tashi muje”.
Kamar bazata ɗago ba sai kuma dai ta ɗago tana kallonsa. “Ni banfa gama ba, ba
yanzu muka fara ba, ga budurwarka ma bataci nata ba”.
“I will slap you in baki tashi ba”.
Miƙewar tayi fuska a kumbure. Ya nuna mata hanyar waje, ko kallon saurayin baiyi ba
yayma waiter nuni tazo. Kuɗinsu ya bata, tareda wasu yace ta masa takeaway na naman
rago. Fadwa da ko lauma ɗaya bataiba dama ta miƙe tsam da wayarta a hannu ta fice,
bayansu yabi, sai dai kafin ya fito Fadwa ta tsaida napep ta shige abunta, Anam ko
jikin mota ya sameta ta haɗe fuska tamau. komai baice mata ba ya buɗe ya shiga, a
dai-dai nan aka kawo masa takeaway ɗin da ya saka akayo. Jin ya kunna motar tai
saurin buɗewa itama ta shiga. Sai lokacin ya lura babu Fadwa, motar ya sake buɗewa
ya fito yana dube-dube.
Wata shaƙiyyar dariya Anam ta ƙyalƙyale da ita harda kwanciya, tana ganin
zai dawo ta haɗiye kayarta da gyara zama ta fuske...
A dake yace, “Malama dawo nan”.
Ido ta ɗan waro tamkar bata san mike faruwa ba. “Yaya Auntyn kuma fa, ba fitsari
taje bane?”.
Kallon banzar daya watso mata ya sata buɗe murfin ta fita tana danne dariya da
ƙyar, ƙasa-ƙasa take faɗin, “Ai daga yau daga kai har ita kun shiga uku da ni. Sai
tasan ita ƙaramar ƴar iska ce”......

★★★★

A kallo ɗaya zaka fahimci tsananin ɓacin ran dake tattare da ita. Tunda
Gwaggo Halima ta kirata ta sanar mata abinda ya faru take kiran wayarsa amma yaƙi
shiga. Kasa daurewa tai ta dawo falo tare da tura Hussaina gate zaman jiran
shigowarsa. Mintuna goma kuwa ba'aiba cikakku da zaman Hussaina a gate sai ga
motarsa ta shigo. Anam ce ta fara fitowa, Hussaina ta bita da kallo harta shige
sashen Mom. Shima dake binta da kallon fitowa yay hanunsa ɗauke da ledar takeaway.
Hussaina ta taso da sauri tana washe baki dai-dai yana sama motar lock da key ta
waje.
“Yaya sannu da zuwa”.
Batare daya kalleta ba ya amsa mata. Idonta akan ledar hannunsa ta kuma faɗin,
“Yaya Dama Mommy ce tace kaje tana nemanka”. A yanzu kam idanunsa ya ɗago yana
kallonta. Sai dai baice komaiba tsahon sakkani ya janye. Ganin zai bar wajen takai
hannu ga ledar. “Bara na ɗauka maka to”. Harararta yay, babu shiri taja baya tana
tura baki gaba. Baibi takantaba ya nufi sashen Mom. Fawwaz kawai ya samu a falon
zaune yana kallon cartoon. Yaron ya taso da gudu ya nufosa. Ledar ya ajiye gefe
fuskarsa ɗauke da murmushi ya ɗagashi sama. “Oh my Friend ya kake?”.
“Lafiya lau Yayanmu. Good morning”.
Kumatunsa ya ɗan ja yana murmushi. Kafin ya ɗan kalla falon. “Gentlemen ina
Mom ne?”.
“Tana ɗaki da aunty Rahma tazo”.
“Okay! To kace ina gaisheta.”
Kai ya jinjina masa. Sai kuma ya kai bakinsa kusa da kunnen Shareef ɗin, cikin
raɗa yace, “Aunty Anam kuma yanzu ta dawo sai fushi takeyi”.
Idanu ya ɗan waro waje kamar yanda yaron yayi, “Haba dai?”.
“ALLAH kuwa. Ko kulani ma batayiba ina gaisheta da nuna mata Cartoon ɗina”.
“Ayya am sorry my dear, maybe bata da lafiyane. Amsa wannan ka kai mata sai kuci
tare”. Duk da ledar ta masa nauyi da ɗan gudunsa ya nufa ɗakin cike da murna yana
ƙwala kiran “Aunty Anam! Aunty Anam!!”.
Idanu yaɗan lumshe a hankali da harɗe hannayensa duk biyu a ƙirji yana
murmushi har yaron ya shige ciki. Haka yake shi mutum ne mai tsananin son yara. Bai
shirya aure yanzu ba, amma saboda son da yakema yara ya sashi amsar tayin su Mommy
dan ta matsu taga yay aure ya rasa dalili?.

Shigowarsa falon yasa Hussaina saurin yin shiru ta haɗiye sauran gulmar da
take faɗama Mommy. Sai dai kuma yama riga yajita, kallon daya watsa mata yasa tai
saurin barin falon tana tura baki gaba.
“Shareff kai dawa kaje gidan Halima!!”. Mommy ta faɗa a fusace tunkan yace
mata komai. Ɗan jimm yayi na wasu sakanni, sai kuma ya ɗago yaɗan dubeta. “Mommy ni
ban shiga gidanba ma balle naje da wani”. Harara ta watsa masa. “Wlhy Al-Mustapha
ka kiyayeni a gidannan. Idan kace zamu saka ƙafar wando ɗaya da kai bazakajita da
daɗi ba! Yanzu na kiraka nace kasata a napep ta dawo shine danka rainani ka ɗauketa
kukaje wajen wadda ke shirin zama matarka har kana mata walaƙanci a gabanta ko?!
Ita kuma shegiyan yarinyar mai kama da ifiritin aljanu haihuwar bakwaini tana mata
rashin kunya, to idanma wani abune a ranta tun wuri ta fiddashi dan har abada bazan
haɗa zuri'a da Usman ba, sunga ta rasa miji a can shine zasu kwasota su kawo nan
talla......”. Murmushin yay da tasowa ya dawo kusa da ita, sai dai a ƙasan carpet
ya zauna ya ɗora kansa jikin ƙafarta, hanunta ya riƙo cikin nasa murya a sanyaye,
“First-luv Please cool down, yaronki bashi da wata mata bayan zaɓinki, idan ma
hakane a ransu ai bani kaɗai bane ɗa a gidan ko?!.....”
“Ko kai kaɗaine bazaka aureta ba, kuma ko yanzu dan kayi aure idanma hakane
a ransu Maheer ma yafi ƙarfin nan sai dai suje can su nema mata miji dan ko Khaleel
saina hana uwarsa yarda”.
Murmushi ya saki mai faɗi da lumshe idanunsa. Yayinda kunensa ke cigaba da
sauraren banbamin masifar Mommy. A haka su Aysha suka shigo suka samesu. Gaisuwar
da suke masa ce ta sashi buɗe ido da tashi daga jikin Mommy yana kallonsu. Kafinma
yace wani abu Hassan yay saurin faɗin, “Yaya daga aikan Gwaggo muke fa”. Komai
baiceba ya miƙe ya fita a falon.

___________________

A yau da Anam ke cika kwanaki biyar a gidan ya kamata ta fara shirin fita
aiki, amma mutuniyarku barcinta take sharɓa saboda jin daɗin ɗan sanyi-sanyin
safiyar dan bata isashen barcin dare daboda zafi. Da zarar an ɗauke wuta bazata
sake rintsawaba. Dan ƴar fan ɗin da Mom ta bata Fawwaz ya joganeta jiya taƙi ɗaukar
caji. Gaba ɗaya Mom ta shafa'a da batun fara fitar Anam ɗin yau itama, shiyyasa
batai tunanin tadata ba tanata ƙoƙarin shirya su Fawwaz karsu makara tafiya
makaranta suma. Sai daga baya ta tuna taje ta kakkaɓeta da ƙyar..

Kamar kullum cikin shirin fita office ya fito. Shareff mutum ne mai himma,
bashi da wasa akan aikinsa shiyyasa a kullum cikin haɓaka kamfani yake. Zamansa
tsayayyen mutum yasa ma'aikatan ke tsananin shakkarsa da kiyaye dokokin kamfani,
dan shi babu ruwansa yana ganin baka serious zai sallameka ne acewarsa a kwai dubu
masu buƙatar gurbinka zaune a gida. Sashen Mommy ya fara shiga, ƙanensa nata
ƙoƙarin karyawa suma. Cikin girmamawa duk suka gaidashi. Amsawa yay yana ƙoƙarin
kaiwa zaune a ɗaya daga kujerun falon dan bazaka taɓa ganinsa cikinsu yana cin
abinciba. Mommy dake tsaye itama a dining ɗin tana haɗa masa tea ta ƙaraso garesa.
Tunkan ta ƙaraso ya miƙe fuskarsa ɗauke da murmushi ya amsa mug ɗin. “Good morning
First-luv”.
“Morning dear, how are you?”.
“Alhamdulillahi”.
“Haka ake so ai. A saka maka Irish ɗin?”.
“No Mommy wannan ɗin ma is ok for me. Yau na makara gashi inada meeting eight
thirty”.
“To aiko gara ka hanzarta tunda gashi eight ɗin gab yake dayi”.

Koda ya fito sashen Mommy wajen aunty Amarya ya shiga suka gaisa kamar yanda
ya saba duk safiyar duniya zai shiga ya gaida kowa na gidan. Daga nan kuma babu mai
sake ganinsa sai wata safiyar, sai dai duk ranakun juma'a da laraba zai sayo fruit
bayan ya tashi aiki ya shiga kowane sashe yakai musu, hakama duk ƙarshen wata zai
sayi kayan tea dasu sabulai omo MacLean kayan dai buƙata kananu yakai kowane sashe.
Tun Mommy najin haushi da masa faɗa har dai ta tattara ta zuba masa ido amma hakan
na damunta da ɓata ranta saboda zugar Gwaggo. Sashen Gwaggo ya nufa itama ya
gaisheta dan itace a tsakiyar Mom da aunty amarya. Yasanta da son su zauna hira dan
haka ya maƙale daga ƙofa suka gaisa duk da tayin kunun gyaɗa da take masa kuma
ransa naso.
“Gwaggo na makara, amma zubamin zanje da shi office nasha. Bara na gaida Mom
a kaimin mota”.
Kafinma tace wani abu ya fice da sauri zuwa sashen Mom idonsa akan agogon dake
a tsintsiyar hanunsa. Gaisuwar su Fawwaz ya fara amsawa dake fita da gudu zuwa
school bus ɗinsu. Kafin ya ƙarasa cikin falon su gaisa da Mom. Itama nan koda tai
masa tayin abinci cayay Alhmdllhi ya fito da hanzari. A jikin motarsa ya samu Ladi
mai aikin Gwaggo ɗauke da ƙaramin basket. Tunkafin ya ƙaraso ya buɗe motar da key
tai ƴar ƙara. “Ranka ya daɗe gashi inji Gwaggo”. Baice komaiba ya amsa basket ya
ajiye a gefen mai zaman banza, fitowar Daddy ta dakatar da shi daga yunƙurin shiga
motar da yay niyya ya nufi Daddyn ɗin duk da sun gaisa bayan fitowarsu massalaci da
asuba, tare kuma suka fita motsa jiki....
“Babana har an fito?”.
“Eh Daddy nama so makara dan inada meeting”.
“To ai yau da gobe sai ALLAH ko”. Daddy ya faɗa dai-dai da fitowar Anam daga
sashen Mom. Tsaf take shirya cikin kayan NYSE da sukaima jikinta cif kamar ka
saceta ka gudu. Ta naɗa yololon veil ɗinta tare da ɗora p-cap ɗin samansa, saita
goya bag ɗinta mai suffar teddy data zuba komai a ciki. Tayi ƙyau sosai sai zuba
ƙamshi take mai daɗi. Fuskarta ƙawace da murmushi ta nufo inda suke, sai da ta
sauke hular daga kanta tace, “Good Morning Daddy”.
“Good Morning Maman Daddy. how are you?”.
“I'm fine Daddy, sai dai zafi da dare barci babu daɗi”.
“Ayya mamana ba'akwai fan a ɗakin naku ba?”.
“Akwai Daddy, idan suka ɗauke nepa ɗinne fa, fan ɗin da Mom ta bani yaƙi ɗaukan
cagi jiya”.
Kanta ya ɗan shafa da faɗin, “Am sorry insha ALLAH za'a saya miki wata to koda
an ɗauke wutan, koma ac za'a sayo dai?”.
Ƴar dariya tayi da satar kallon Shareff da tun zuwanta wajen ya haɗe fuska
yana danna waya kamar bai san da zuwan nata ba. Shima Daddyn dariya yay da duban
Shareff ɗin, “Kun gaisa da Yayan naki ko?”.
Baki taɗan tura gaba da ɓata fuska, sannan tace, “Good morning”.
Duk da sarai yajita bai amsaba, sai duban Daddy yay yana tura wayarsa a
aljihu da faɗin, “Daddy bara na wuce ina ƙara makara”.
Daddy yace, “Ato shikenan sai kije ya saukeki tunda hanyarsa ce”.
Idanu ta waro da ƙyau tana ƙyaƙyƙyafta su. “Daddy Abie yace driver zai dinga
kaini”.
“No na dakatar da shi ai. Duk motocin gidan nan ace sai an ɗauka miki wani
driver. Idan Shareff zai fita sai ya dinga tafiya dake, idan ya tashi aiki kuma ya
ɗakkoki ba shike nan ba”.
Zatai magana ya girgiza mata kai alamar kartace komai. Shirun kuwa tai,
sai dai kamar zatai kuka takeji. Sam bata buƙatar haɗa sabgarta da shi. Duk
miskilancin Khaleel tafi jin daɗin zama da shi, shiko Maheer dama mutum ne mai
sauƙin kai da faran-faran, shiyyasa da akace mata bayanan taji duk babu daɗi.
Ganin shima baice komai ba Daddy ya dubesa “To ALLAH ya bada sa'a. Sai ka
wuce da Mamana ko”. Kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa. Ya ɗan rissinar da kansa
ƙasa da fadin. “Mu yini lafiya”. Jinjina masa kai shima Daddyn yayi. “ALLAH yasa.
Mamana bishi ALLAH ya bada sa'a”. “Amin Daddy” ta faɗa dabin bayan Shareff da tuni
yay gaba abinsa kamar ta make masa ƙeya..........✍

_🤭🤗maza ki make to dan ALLAH_.

_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_


*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:


07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇


09134848107

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*

[10/26, 7:15 PM] My Zafafa: *_Typing📲_*

*_BABU SO....!!_*
_(Miya kawo kishi?)_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


*_08_*

..........Tunda ya amsa wayar ya turama wadda ta kira da sister ɗinta address ɗin
inda suke yaketa lallashinta ko ruwa tasha amma taƙi sai faman sharɓan hawayema
takeyi. Hakan yasa yay tagumi kawai yana kallonta. Komai tai birgesa takeyi, Duk da
ƙaramin jiki da take da shi kai kasan ba yarinya bace, sai dai a kallo ɗaya zaka
fahimci lallai ƴar gatace a gidansu dan saurin karayanta yayi yawa. Hoto ya fara
mata yana murmushi batare data sani ba.....
Tunda ya shigo idonsa ya sauka a kansu. Wani irin baƙin ciki da ɓacin
ransa sai suka ƙara ninkuwa. Nufarsu yay rai a ɓace sai dai bazaka taɓa fahimtar
hakan akan fuskarsa ba duk da ya ciskulleta sam babu fara'a. Kamar ance ta ɗago
idonta ya sauka a kansa. Babu shiri ta miƙe zumbur dan yanayinsa ya tsorarata, bata
manta dukan da yay musu ita da Aysha ba. Wani irin mugun kallo yay mata ya ɗauke
kansa ya maida ga saurayin da shima ya miƙe dan ya gansa. Kallon banza da tsana
yake masa yayinda shi saurayin yay ƙoƙarin mika masa hannu suyi musabaha yana
murmushi duk da yaga kallon banzar amma ya shanye.
Kallon hannun yay ya wani ɗauke ido da maidawa kan fuskarsa yana mici-mici da
idanunsa dan sarai ya gane shine ranar yayta binsu daga wannan restaurant ɗin.....
“Kana buƙatar ka zauna lafiya?!!”.
Duk da a yanda yay maganar cike da isar gadara hakan bai hana saurayin sakin
murmushi ba da jinjina kansa. Cikin sauƙaƙa tasa muryar yace, “Sosai kuwa babban
Yaya. Ai magabatanmu kance zaman lafiya yafi zama ɗan sarki”.
Kansa ya ɗauke duk da shine ya buƙaci amsar kuma aka bashi. Wani ɗan juya
harshensa yay cikin bakinsa cike da basarwa yana sakin murmushi mai harshen damo.
Sai kuma ya jinjina kansa da sake maido dubansa ga saurayin fuska a haɗe. “To daga
yau, daga yanzu, karka bari na sake ganin wannan fuskar taka a inuwa ɗaya da ita.
Inba hakaba......”
Ya ƙarasa da wani shegen murmushi dimple ɗinsa na loɓawa, yaɗan bubbuga kafaɗar
saurayin. Bai saurari amsar da saurayin zai bashiba ya fisgi hanun Anam dake maƙure
waje guda zuciyarta kamar zata kifo ƙasa. Da tasan shine zaizo ɗaukar tata data
aminta da shawarar saurayin daya buƙaci Aysha ta tura address ɗin gidan shi ya
kaita amma taƙi. Jakkarta dake kan desk ɗin ya fusga itama tare da wayarta yay gaba
da sake yima saurayin warning da idanunsa dake rine matuƙa fiye da yanda ya shigo
wajen.....
Turata yay a motar ya rufe har saida ta zabura dan kaɗan ya hana ya datse
mata yatsun hannu. Ya zagayo mazauninsa tare da figar motar a guje yabar wajen.
Yanda yay ɗin yay masifar sake firgitata har sai da ta faɗa gefen hanunsa ta
ƙudundune fuskarta tana kiran sunan ALLAH, dan ta zata gabzama motocin gabansu karo
zaiyi ma. Ƙuwwww!!! Ya taka birki da daka mata wata razananniyar tsawa. Saurin
sakinsa tai tai baya a firgice, sai kuma ta fashe da kuka dan gaba ɗaya ya sake
firgitata ta tsani tsawa...
“Stupid! shut up!!. Idan baki rufemin shegen bakinki ɗin nan ba na fara
kashe fuskarki da maruka sai kin suma. Wawuya kawai. K har idonki yay tsurin bin
motar saurayi kuje restaurant?! Dama abinda kikazo yi kenan a Nigeriar?!!!”.
Yanda ya ƙare maganar a matuƙar tsawace ya sake birkitata. Amma sai ta danne
cikin ƙarfin hali tace, “ALLAH ya kiyaye danni ba mayyar maza bace”.
Ya sake watsa mata harara kai kace cinyeta zai da jajayen idanun nasa. Sai
kuma yay ƙwafa da ɗauke kansa yana sake tada motar. Ko motsin kirki bata sakeyi
tunda ta samu bai maketa ba. Kukan ma ta daina na zahiri na zucici takeyi. Gaba
ɗaya jitake tama gama tsanar Nigeria, ita dai gaskiya bazata iya wannan masifar ba,
tun farko abinda ta guda kenan amma su Mamie sukaƙi fahimtarta. Itakan duk ma yanda
za'ai a satin nan sai tabar Nigeria hidimar ƙasar nan bazata yuwuba.....

Ko gama dai-daita parking baiyiba ta fita dan mutanen gidan duk suna
tsakargida tsaitsaye Gwaggo da Mommy ne kawai babu sai irin su Fawwaz da sunyi
barci tuni basu san abinda akeyiba. Aysha ce ta taho da gudu suka rungume juna, sai
kuma ta saketa taje ta rungume aunty amarya da Mom. Su Daddy da tuni Aysha ta
kirasu suka dawo gida zaman jiran isowarsu suma ajiyar zuciya kawai suke saukewa..
Mom dake shafa kanta da murmushi tace, “Kukan ya isa haka mana mamana. Tunda
kuma an dawo gida sai muce Alhmdllhi. Jeki gaida iyayenki”.
Babu musu ta saki Mom tana share hawaye ta nufi su Abba. Gaishesu tai hawaye na
sake silalo mata, abinka ga ƴan boko kasa daurewa Daddy yay sai da ya ringumeta.
“Haba Mamana ina kika shige haka duk kin tada mana hankali”. Ya faɗa yana mai
ɗagota a jikinsa. Murmushi tai tana share hawayen da suka ƙi tsayawa. “Daddy na
kasa ganewane, idan na tsaida masu keke ɗinnan sai suce basu gane yanda nake faɗa
musu gidan ba”. Tausayinta sosai ya ƙara kamashi, kanta Abba ya shafa yana
murmushi. “Dole ki dage ki koya hausa a zaman nan Mamana, dan rashin iyawan ya taka
rawar gani cikin accident ɗin nan”.
“A'a Abba dan ALLAH ni zan koma Malaysia”.
“Tsit gurin yay babu wanda ya iya cemata komai. Sai Shareff ne ya wani taɓe
baki da barin wajen ko uffan baicema kowaba balle bayanin yanda ya samota dan a
matuƙar gajiye yake ga ciwon kan nasama zazzaɓi yake neman komawa. Daddy ya kashe
shirun wajen da faɗin, “Kuje ciki tai wanka taci abinci dan tana buƙatar kwanciya
da wuri. Mamana mayi magana da safe”.
Badan tasoba tabi Mom dan bata iya musu ba kuma. Duk da yanda Aysha ke tsoron
faɗan Mom haka tabi Anam sashen Mom da ƙudirin su kwana tare, dan jitake kamar
kafin safiya za'a ƙara cemusu ba'a gantaba ta sake ɓata.

Washe gari tunkan ma Anam ta kira Abie ɗinta ta sanar masa Daddy ya kirasa sukai
magana. Yayma Shareff kuma faɗa sosai kamar zai ari baki. Daga ƙarshe ya kafa masa
dokar hukuncinsa shine kai Anam wajen aiki kullum ya kuma ɗakkota. Idan ko wata
matsala ta sake shigowa akan Anam to lallai ya kuka da kansa dan sai ya matuƙar
ɓata masa rai a gidan.
Shi dai Shareff ɗin baice komai ba akan hukuncin. Sai Mommy ce tace sam bata
yardaba ɗanta ba driver bane ba. Ko kallonta Daddy baiba, ya dai tabbatar mata idan
Shareff ya isa yaƙi bin umarninsa.
Ai wannan magana ta dagula ran Mommy a safiyarnan. Dan tata masifa ita da
Gwaggo data fito tana goya mata baya. Daga Daddy har Abba babu wanda ya sake tofa
tasa dan sukam dai yanzu sai dai su kalla Gwaggo kawai tunda sun fahimci bata
ƙaunar zaman lafiyarsu da ɗan uwansu, Halima ce kawai ta kasa fahimta sun kuma
barta wataran zata gane da kanta musamman da suka san idan akai auren nan na Fadwa
da Shareff.

★★★★

Duk yanda Mommy taso hana Shareff ɗaukar Anam hakan bai yuwuba. Dan shi dai
haƙuri kawai ya bata da nuna mata illar fushin mahaifinsa a garesa. Ya roƙeta ta
kwantar da hankalinta a hankali zai janye jikinsa ya samama Anam ɗin driver kowa ma
ya huta. Wannan magana tashi ce taɗan kwantar mata da hankali ta maida kanta ga
hidimar shirye-shiryen bikinsa.
Daga ɓangaren Anam ma taci uban borinta akan malaysia zata koma ta fasa
hidimar ƙasar su Mamie suka lallasheta da tabbatar mata cewar idan sukazo bikin
Shareff zasu san abinyi. Hakanne yaɗan kwantar mata da hankali ta zauna zaman jiran
lissafin kwanakin bikin. Yayinda ta cigaba dabin Shareff ɗin a takure. Shike kaita
shike ɗakkota, daga gaisuwa babu abinda ke haɗasu sai harara. Ita kuma tata tura
baki kenan da ɗaure fuska ita a dole haushinsa takeji duk da bata da riƙo sam
wannan karon dai ta riƙe.

Yau a gurguje yay shirin tun 7 ma batai ba ya fito saboda wani babban
uzirin dake gabansa a office ɗin. Ga baƙi zaiyi akan wani babban project da suke
saran samu insha ALLAH. A tsaitsaye ya shiga sashen Mommy suka gaisa koma shayin
bai zaman shaba yau dan yaran kansu duk suna ɗaki basu gama shiri ba. Baije sashen
Gwaggo ba dan ya gaji da mitarta akan ɗaukar Anam da yake yasan zata ɓata masa
lokaci. Aunty Amarya ma a tsaitsaye suka gaisa ya nufi sashen Mom. Bayan sun gaisa
da Mom ɗin cikin raba ido da kallon ko'ina na falon yace, “Mom tana ina zan
makara?”.
Da mamaki Mom ɗin ke kallonsa. “Wai kana nufin Anam?”.
Kansa ya jinjina mata. “Eh Mom, yau zan fita da wuri inada uziri shiyyasa na
sanar mata tun ɗazun ta shirya da wuri”.
“Tab ɗi, to aiko banama zaton ta tashi a barci Babana. Ni kuma ban saniba ai
da na tadata ta shirya”.
Cikin ɓacin rai ya ɗan sake duban agogonsa da rumtse idanunsa. Ganin Mom ta
nufi ɗakin yaja ɗan siririn tsoki. “Mom bara naje idan Khalel zai fita su taho tare
inada meeting ne mai muhimmanci”.
“To bara na tasheta dan nasan shima ɗin gab yake da fitowa kuwa”.
Komai baice ba ya juya ya fita.
Ba ƙaramin jan ido Mom taima Anam ba kafin ta tashi. A gurguje tai shiri
saboda Khalel daya leƙo ya mata gargaɗi. Tasan halinsa shima ba mutunci ya cikaba
shiyyasa tai ƙoƙarin shiryawa aɗan gurguje tanata kunƙuni dan barcin bai ishetaba.
Tsaf ta shirya cikin kayan NYSE kamar koyaushe, sun mata cif kamar ka saceta ka
gudu, ƙaramin baby hijjab tasa yau. Tayi ƙyau sosai sai zuba ƙamshi take mai daɗi.
Khalel da gaba ɗaya yake ƙage da fitowar tata hanata zaman shan tea ɗin da Mom ta
haɗa mata yayi.
“Mom Please ki barta tasha a hanya ko a office ɗin, ALLAH idan na makara Yaya
zaimin faɗa duk da shine yace na ɗauketa, gashi meeting ɗin nan inada alaƙa dashi
nima.”
“Amma Khalel ta fita bata karyaba? Bayan kasan bako wane abinci take iyaci
ba. Kai da Shareff ɗin duk wutar ciki tamuku yawane kawai, amma duka ƙarfe nawane
yanzu ɗin? An faɗa muku kowane zai dinga iya uban sakkonku da aiki kamar
matching?”.
“Mom bazaki ganeba wlhy. Please ki barta nidai”.
Kafinma Mom ta sake magana Anam tace, “Kibari zansha a can ɗin Mom kinsan
masifar wancan mutumin tafi ta Yah Khaleel”. Murmushi kawai Mom din tayi yayinda
Khaleel ke hararta.

Sosai Khalel ya zumbuɗa gudu a hanya, lokacin da suka isa wajen aikin nata
har bakwai da rabi ta kusa gotawa. Sai dai sauƙinsa ma babu nisa mai yawa da
company ɗinsu dan duk titi ɗaya ne. Baki ta taɓe ganin yanda duk Khalel yabi ya
damu kansa tunda suka taho yake mata masifa a mota wai idan tace lalaci zatai to
zata dinga hawo motar kasuwa kuwa shi dai baza'a dinga sashi ya jirata ba. Ita dai
komai batace ba sai faman ɓata fuska dai takeyi tana cin inibi ɗinta data taho da
shi daga gida da buga game a waya har suka iso.
“Kije idan an fita break zan kawo miki abinci”.
Sosai ta waro idanu waje. “Har ƙarfe nawa kenan Yah Khaleel?”.
Harararta yay yana ƙoƙarin jan murfin data riƙe zai rufe. “Lokacin zuhur
mana”.
“Haba Yah Khaleel one fa kenan? Kaga ƙilama yunwa ya halakani kawai”.
Dariya ta bashi amma sai baiyiba. “Naji zan roƙa Ya Shareff idan an tashi
meeting zanyi squeezing time na kawo miki”. Kafia tace komai yaja motarsa yay gaba.
Tabi motar da kallo tana tura baki gaba.

Kamarko yanda yay alƙawarin ya cika. Dan wajen sha ɗaya aka kawo mata
saƙo. Koda ta buɗe sai taci karo da takeaway na abincin da take tsananin so. Daɗin
da taji ya sata tura masa text message na godiya, dan hakan tamkar tarbiyyar su
Mamie ne a gareta, indai an mata alkairi komin ƙanƙantarsa sai tayi godiya harma da
addu'a.
Saƙonta ya shigo wayar Khaleel ne a dai-dai sanda wayar ke a hanun Shareff.
Yazo nuna masa hoton wani zane da aka turo masa daga lagos sai kira ya shigo masa a
ɗaya wayarsa, bazai iya ɗaukar wayar a gaban Shareff ba shine ya fita. Baiyi niyyar
buɗe saƙonba, amma ganin sunan daya turo saƙon ya sashi buɗewa. Shiru yay na wasu
sakkani yana kallon saƙon tamkar mai bitar karatunsa, sai faman cizar lip yake,
sallamar Khaleel ta sashi danne saƙon ya aunashi a delete gaba ɗaya. Wayar ya
miƙama Khaleel batare daya kallesa ba. “Kaje da shi zamuyi magana daga baya kawai”.
Ɗan jimm Khaleel yay yana kallonsa, dan sanin maganar tasu muhimmiyace,
hasalima shine ya damesa da kira tun ɗazun akan yazo duk da yasan suna meeting ne.
Amma kuma sai bai kawo komai a ransaba yace, “Okay Yaya. To koma dai na tura maka
shi kawai saika sake nazari kafin?”.
“Okay yayi”.
Ya faɗa a taƙaice kawai. Kasancewar shima Khaleel ɗin miskilin kansa ne sai bai
sake tofa komaiba ya miƙe ya fita abinsa. Haka kawai ya samu kansa da binsa da
harara harya fice. Tsaki yaja da rumtse ido kamar irin mai takaicin kansa ɗin nan.
Ya sake jan tsaki ya miƙe gaba ɗaya yabar table ɗin. Can jikin ƙaton window da aka
ƙawata office ɗin da shi wanda ake hango har titi da cikin compound ɗin company ɗin
kasancewar a saman upstairs office ɗinsa yake yaje ya tsaya. Ya jima wajen a tsaye
hannayensa duka a aljihu yana kallon kaikawon mutane daga titi zuwa cikin company
ɗin...

Da lokacin tashi yay addu'a tai tayi ALLAH yasa Khaleel zai dawo ɗaukarta,
har kiransa tayi dan taji sai dai bata samesaba network ya hana. Tun shigowar
motarsa wajen tasan addu'arta bataci ba. Ɗan duban Yaseer abokin aikinta kuma shima
ɗan hidimar ƙasa ne dake gefenta tai a sanyaye. Ya sakar mata murmushi dabinta da
ƙyaƙyawan kallon da yake hanata sakewa da shi. “Ga Yayana yazo bye”.
Manyan idanunsa ya lumshe da sake buɗewa a kanta. Shima ya miƙe har lokacin
idonsa a kanta. “Haba dai Friend haka ake Friendship ɗin anama juna rowan dangi?
Kamata yay kice muje na gaida Yayanmu ai ko? Kullum sai dai naga yazo ɗaukarki baki
taɓa gayyata ta na gaisar da shi ba”.
Murmushi kawai tai batare da tace komaiba. Ganin tayi gaba yay saurin bin
bayanta har sai da tafiyarsu ta dai-daita. Kasancewar tinted glass ne yasa Yaseer
knocking duk da sarai yasan wanda yake ciki ya gansu. Shiru babu alamar za'a sauke
ya ƙara knocking fuskarsa faɗaɗe da murmushi. Zai ƙara na uku Anam ta girgiza masa
kai a hankali, dama abinda ta gudar masa kenan shiyyasa taso hanashi tun farko.
Tana ƙoƙarin buɗe baki ta bashi haƙuri aka sauke glass ɗin a hankali.
Kallon daya watsa mata ya sata kauda kanta tana taɓe baki, Ƙara ɗaure
fuska yay da duban Yaseer daketa faman shafar ƙeya yana murmushi.... Kafinma yace
wani abu Yaseer ɗin yay saurin faɗin, “Good afternoon Yayanmu”.
Kamar bazai amsaba sai kuma ya miƙa masa hannu alamar suyi musabaha, babu
musu shima Yaseer ɗin ya basa suka gaisa, a mamakin Anam harda cema Yaseer ɗin,
“Yaya aiki?”. Yaseer ya amsa fuskarsa na sake washewa ga sinne kai yana famanyi
kamar wanda ke agaban surukai. Anam ta ɗan taɓe baki tana jinjina kanta, a ranta
kuwa gulmarsa take. Tana son ɗagama Yaseer dake ɗago mata hannu nata hanun tanajin
shakka, sai da taɗan faki idonsa ta ɗaga sau ɗaya ta fuske. Sai dai batasan yama
rigada ya gantaba. Bai daiyi maganaba ya tada motar suka wuce.
Shiru babu wanda ke magana tsakanin shi da ita sai redion motar daketa
karaɗi, ganin inda suka shiga saɓanin gida daya kamata su nufa ya sata kallonsa a
sace tana muy-muy da baki alamar akwai magana a bakinta sai dai babu damar faɗa.
Sai da ta karanta symbol ɗin wajen ta gane Saloon sukazo, mamaki ya sata dubansa
dan batasan mi sukazo yi wajen ba. Ido suka haɗa yana ƙoƙarin kai waya kunensa tai
saurin ɗauke nata. Shima janye nasa yay da cire wayar daga kunensa hango Fadwa na
fitowa a wajen tamkar tarwaɗa. Tayi ƙyau sosai cikin doguwar rigar atamfa, sai veil
siriri data yafa iya kanta ta naɗesa a kafaɗa, ga wani uban glasess daya cinye
rabin fuskarta sai dai ya mata matuƙar ƙyau kasancewarta fara ƙyaƙyƙyawa. Gefe da
gefenta ƴammata biyune suma ƙyawawa kamarta farare tas da su. Yanda suke dariya zai
tabbatar maka wata maganar sukeyi dan har ita Fadwan fuskarta cike take da
murmushi. A hankali Anam taja siririn tsaki daya sashi ɗan waigowa ya dubeta, sai
dai ta wani kauda kai gefe kamar wadda taga kashi. Sarai ya fahimci dasu Fadwa
take, amma sai baice komaiba ya buɗe murfin motar ya fita fuskarsa sam babu walwala
dan ya tsani taron ƙawayen Fadwa da suka zame mata kamar jela. Idan ka ganta da
wannan yau gobe da waccan zaka ganta, na jibima daban ne...........✍

*_Haɗuwar iliya da wargaji😂 kunsan dai ba sauƙi😹😹, ku faɗama yarinyar nan taku yau
sai mun rama marinmu ko shi Yayan nata bai isa dakatar damu ba ehe😜🤭._*

_ZAFAFA BIYAR_
*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_


*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:


07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇


09134848107

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻


[10/26, 7:15 PM] My Zafafa: *_Typing📲_*

*_BABU SO....!!_*
_(Miya kawo kishi?)_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*. *_Typing📲_*

*_BABU SO....!!_*
_(Miya kawo kishi?)_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


*_09_*

.........Murmushi Fadwa ta sakar masa, cikin narke murya taima hannunta kiss da
hura masa .
“I miss you my Soulmate”.
Kansa kawai ya jinjina da wani ɗan guntun murmushinsa iya laɓɓa. Cikin iyayi da
feleƙe ƙawayen nata ke gaishesa idanunsu kamar zasu faɗo a kallonsa. Ɗan tsuke
fuska yay yana amsa musu sama-sama.
“Baby am sorry na saka wahala”.
Fadwa ta sake faɗa tana sake narke masa har tana saka tsigar jikinsa tashi. Nanma
murmushi kawai yay mata da kauda kansa daga gareta dan shi kaɗai yasan halin da
dama yake ciki ita kuma tana son sake kunnashi da wani. Cikin motar yay ƙoƙarin
komawa da nufin ɗakko mata saƙonta, ita kuma batare da tunanin tare yake da kowaba
ta nufi ɗayan side ɗin a zatonta anan ya ajiye saƙon nata ne, tana kuma son ƙara
birge ƙawayenta da akaikaice tasa ake musu hoto acan gefe batare daya sani ba....
Sosai Anam ta cika tayi fam da takaici, tayi yunƙurin buɗe motar ta fita
taji ya sakata a lock dan yasan dama abinda zata iyayi kenan tace zata fita kamar
wancan ranar. Ya ɗakko ledar dake a back sit ɗin Fadwa ta buɗe ita kuma. Ido huɗu
sukai da Anam, ta watsa mata wani kallon banza ta ɗauke kai dajan siririn tsaki da
faɗin “Ballagaza” a hankali....
A yau kam tayi laƙawarin bazata ƙyale ƴar iskar yarinyar nan ba. Cikin jin
ɗacin (ballagaza) data kirata dashi tace, “Kin yima ubanki dan uwarki.”
Duk da Anam bajin hausa take da ƙyau ba tasan zagi, amma sai tayi kamarma
bataji Fadwa ɗin ba, taciro Bluetooth daga bag ɗinta ta fara ƙoƙarin maƙalawa a
kunne Fadwa ta buge hanun Bluetooth ɗin ya faɗi ƙasa. Ƙafa tasa ta takesa da shegen
takalminta mai tsananin tsini......
“Fadwa!”.
Shareff ya faɗa a ɗan kausashe.....
“......Amma dai Soulmate kanajin tsakin da taimin ai, ranar na ƙyaleta daboda
darajarka, amma yau gaskiya bazan iyaba, ban son raini..!”
Itama ta faɗa da sauri cikin tarar numfashinsa.
Anam data sake cika tai fam tai yunƙurin hanɓarata baya ta futa. (Yo dama
a gayama kura gayyar cin nama bayan bidirin nasu ne🤣. Ba'a takali Anam ba ma yaya
aka ƙare balle anzo har gida da goron gayyata😂).
“Idan kika fita a motarnan sai ranki ya ɓaci!!”. Yay maganar a tsawace da
fisgota ya maida ya zaunar. Kuka ta fashe masa da shi dan zuciyarta tazo wuya.
Baibi takantaba yay yunƙurin fita a motar sai ya hango Fadwa can ta nufi motarta a
fusace ƙawayenta na take mata baya. Idonsa ya rimtse da taune hakwaransa, sai kuma
ya furzar da huci mai zafi yaja murfin a fusace ya rufe, na side ɗinta ma shine ya
rufosa ya tada motar suka bar wajen dan tuni su Fadwa ma sun fice a wajen har tana
bulama mutane ƙura.

Cikin sake tunzurasa da kukanta keyi yaja birki da ƙarfi, firgita tai ta
ɗago da sauri tana kallonsa. Harara ya watsa mata tare da gangarawa gefen titi ya
kashe motar. “Nidai ka kaini gida, kuma saina sanarma Daddy mata na maka kiss a
titi da rungumek....”
Bamm ya bige bakin nata, kukan ƙarya ta sake fashe masa da shi dan ko hawaye
babu yanzu sai dai taji zafi sosai. “Har Abba ma saina faɗawa da Abie da Mamie da
Mom da aunty Amarya”. Ta sake faɗa da ɓalle murfin motar zata fice. Riƙota yay ya
maida murfin ya rufe yasa lock. Takaicinsa da haushin abinda Fadwa ta masa yasa
takejin zafinsa batare data san dalili ba, cizo tai ƙoƙarin kaima hanunsa dake riƙe
da nata....
“What!! Ni zaki ciza?”.
Bata kulashi ba ta sake kaima hanun cizo. Babu shiri tilas ya saketa, yana mai
girgiza kansa. A hankali yakai kwance jikin kujera bayan ya kwantar da ita,
hannayensa duka harɗe a ƙirjinsa ya lumshe idanu yana mata kallon ƙasan ido. Tunba
yanzuba yasan Anam fitinanniya ce dama, sai dai yayi zaton tabar tsiwa zuwa yanzu,
amma tun tana ƴar ƙaramarta boss ce daman. Yasha zuwa hutu ya samu an kawo ƙarar
Anam daga school ta naɗi ƴaƴan mutane babu dalili, idan kuma gidansu akazo nanma ta
jibga, idan gidansu taje yaran ba tsira sukeba. Ƴaƴan aunty Mimi ba ƙaranar wahalar
Anam sukaci ba duk da wasu sun girmeta bata ɗaga musu ƙafa........
“Nidai ka buɗemin, bazan sake shiga wannan motar ba da akeyin wannan
abun....”
Duk yanda yaso danne murmushin dake son fita ya gaza hakan, gefe ya maida
kansa yay murmushin kafin ya tashi zaune sosai fuska a haɗe ya riƙo hanunta dake
jikin handle ɗin ƙofar, baki ta buɗe zata saƙi ƙara dan matse hanun yayi yasa
yatsunsa biyu ya riƙe lips ɗin nata fuskarsa a tsananin haɗe. Sosai idanunta suka
sake firfitowa, ga tsoro ga tsiwa......
“Haɗiyemin wannan kukan, ki kuma faɗi miye abunda akeyin kona tattakaki”.
Tsaf ta haɗiye kukan zuciyarta na bugawa da sauri dan kusancinsu yayi matuƙar
yawa, kanta ta fara jujjuya masa a hankali. Idanu ya zare mata da sakin lips ɗin
nata, “Ai saikin faɗa mara kunya”. A tsorace take amma bakin yaƙi mutuwa. Taja
jikinta baya da maƙurewa a jikin ƙofa, “To ka bari muje gaban su Daddy ɗin basai na
faɗa ɗin ba....”
Bakin ya sake kaima ɗalli tai saurin duƙewa da cusa kanta a tsakanin
cinyoyinta. Ƙwafa yay da komawa jikin kujerar ya lafe yana kallon waje, kusan
mintuna huɗu suna a haka ring ɗin wayarsa ya katse shirun nasu. Iska ya ɗan furzar
da kallon wayar, ganin Daddy ya sashi ɗagawa yakai kunne a ladabce yay sallama.
“Shareff kuna ina?”.
Ɗan jimm yay saboda jin muryar Daddyn, sai kuma ya gyara zama da ƙoƙarin yima
motar key yana bashi amsa. “Daddy gamu a hanyar tahowa gida”. “To inna jiranku”.
Kafin ya sake cewa wani abu ƙitt an yanke wayar. Shiru yay yana kallon wayar sai
kuma ya sake furzar da numfashi. Ruwa ya ɗauka a baya ya miƙama Anam da itama ta
ɗago tun ɗaga wayarsa. “Malama anshi ki wanke wannan banzan hawayen”. Baki taɗan
tura gaba kafin ta amsa, ta buɗe murfin motar batare data fita gaba ɗaya ba ta
wanke fuskar. Bag ɗinta dake kan cinyarta ya ɗauka ya buɗe, zatai magana ya
harareta. Komai babu na kayan kwalliya da ƴammata kan ɗan fita da shi a bag sai
lipsgloss kawai. Baice komai ba ya maida jakar ya rufe, tissue ya ɗiba guda uku ya
miƙa mata sannan ya harba motar saman titi.
Tafiyar mintuna ƙalilan ta kawosu gida, tunda aka buɗe musu gate ya sake
tabbatar da babu lafiya, dan ganin masu baƙaƙen kayan nan yasan Aunty Halima ce a
gidan. A karon farko yaji zafin hakan matuƙa, shikenan da abu ya faru tsakaninsa da
Fadwa sai iyaye sun shiga ciki, to shikam idan anyi auren yaya kenan kuma?. Ita dai
Anam ba fahimtar komai tai ba, dan tun kan ma ya gama kashe motar tai ficewarta
sashen Mom a zatonta ma ko baƙi Abba ko Daddy wani yayi. Binta yay da kallo harta
shige, ya sauke numfashi a hankali shima yana fitowa. Sashen Daddy ya nufa duk da
yasan bai wuce ɓacin rai zai tarar ba.
Tun kafin ya ƙaraso yake jin hargowar Gwaggo Halima daketa masifa, ya girgiza
kansa kawai ya shiga falon da sallama. Da Fadwa dake faman rusar kuka suka haɗa
ido, ya ɗauke idanunsa fuskarsa na sake tsukewa. Sosai Mommy ke antaya masa uwar
harara, hakama Gwaggo. Daddy dai kallonsa kawai yakeyi cike da nazari. Shiko Abba
murmushine ma akan fuskarsa yana sauraren ƴar uwar tasu kuma yayarsa. Ƙasa ya zauna
ya shiga gaishesu. Abba ne kawai ya amsa da daɗin rai, sai Daddy daya sauke ajiyar
zuciya. Mommy kam da Gwaggo hayayyaƙo masa sukai da masifa kamar yanda Gwaggo
Halimar ta rufesa da tata. Shi dai babu wanda yacema uffan a cikinsu, kansa a ƙasa
ma yake. Sai da sukai mai isarsu sukai shiru duk da Abbah nata son dakatar da su
sunƙi saurarensa.
“Ina ita mara kunyar dan ubanta? Kai yanzu Shareff ko kishinmu ma bakayi
duk yawan ƴan uwanka da muka haifa karasa wadda zakai yawo da ita a motarka sai
bare.....”
Haka kawai maganar ta bashi dariya, amma sai baiyiba yay murmushi kawai da
ɗagowa ya ɗan dubi Gwaggon tasa datai maganar.
“Eh kalleni da ƙyau mara mutunci, ko kanada wata alaƙa da ita bayan ubanta dake
matsayin ɗan uba a cikinmu da har kake wulaƙantamin yarinya akanta?”.
“Dan ALLAH ya isa haka Halima, maganar yarinya ko matsayinta duk bashi
bane ya taramu anan. Kai Shareff miya haɗaka da ƴar uwarka?”.
Numfashi ya sauke a hankali da ɗagowa ya dubi Abbah da yay maganar ya sake
sunkuyar da kansa. “Abbah ni bansan wani abu ya faruba. Ina office ta kirani tana
buƙatar abu, duk da ina buƙatar zuwa na huta kuma tana ƙasa dani na ɗauka nakai
mata har inda take badan ina jin tsoronta ba.......”
“Amma daka tashi zuwa ai da wancan bakwainin yarinyar kazo. Dama ranar da ita
kaje gidanmu taimin rashin kunya da marina ka hana na ɗauki mataki kace zaka ɗauka
da kanka, yau kuma harda zagina tayi tanamun kallon banza irin like akwai wani abu
tsakaninku. Ni gara idan sonta kake ka faɗamin na barmata kai kawai dan bazan iya
shearing ɗinka da wancan jakar ba....”
Idanunsa yay bala'in rumtsewa tare da dunƙule hanunsa da masifar ƙarfi.
Daddy dake kallon hanun nasa ya ɗauke kai yana ɗan murmushi, sai dai kamar yanda
tun ɗazun baice komaiba yanzunma baice ba. Fadwa ta cigaba da sakin zance tana kuka
har sai da Abbah ya ƙwaɓeta dan sai zagin Abie take da Anam....
“You're vary stupid. Baki san shi ɗin wanene ba a gareki? Ashe muma zaki iya
zaginmu mara kunyar banza......”
A zabure gwaggo ta tare numfashinsa da faɗin, “Yo Abubakar wane matsayi Usman
kedashi a wajenku bayan ɗan uba da zaka balbaleta danta zagesa?”.
“Haba Gwaggo wane irin magana ne wannan?”. Abba ya katseta ransa a ɓace.
Gwaggo Halima zatai magana ya dakatar da ita ta hanyar ɗaga mata hannu. “Bana
sonji, daga yau kuma idan na sakeji a cikin ƴaƴanki wani ya zagi Usman to lallai ke
kanki sai ranki ya ɓaci tunda akoda yaushe ke hankali baya isa miki cikin jiki.
Wannan magana kuma na kasheta anan, sannan Mamana nine nace kullum Al-Mustapha ya
sauketa a wajeb aikinta ya kuma ɗakkota tunda shine babba wataran sunan uba zai
amsa a garesu. Bana son sake jin ƙananun maganganun nan daga yau, nakuma dawo da
bikinsu baya zanje na samu Alhaji Sadiq ɗin, magana ya ƙare ok”.
Babu wanda ya iya sake cewa komai, sai dai har cikin rai maganarsa ta farko
ta zafi wasu a cikinsu, ta ƙarshe kuma ta musu daɗi kusan su duka idan ka cire uban
gayya daya shaƙa yay fam. A wannan gaɓar yaji mugun haushin Gwaggo a ransa fiye da
koyaushe, dan ya gama gane itace ke assasa tsanar juna a tsakanin iyayensu da ƴan
uwansu guda biyu kacal dan kawai suna matsayin ba uwarsu ɗaya ba. Shi ya fara
ficewa a falon batare da ko kallon wani ya sakeyi ba.
Da sauri Fadwa ta mike tabi bayansa har tanayin tuntuɓe zata faɗi. Tana
kiransa ko waugota baiyiba duk da sarai yajita. Duk da taji zafi haka ta cigaba da
binsa har part ɗinsu, yana ƙoƙarin shiga ɗakinsa tai azamar shan gabansa ta tare
ƙofar. Mugun kallo ya watsa mata, sosai hanjin cikinta suka kaɗa amma saita daure
ta marairaice masa fuska.
“Haba My Soulmate yanzu ɗinma wulaƙancin zakamin?”.
“Bani hanya!!”.
Yanda yay maganar a tsawace idanunsa har suna firfitowa yasata saurin matsawa.
Hannu yasa ya ƙarasa ingijeta ya buɗe ɗakinsa ya shige tare da bugo ƙofar da ƙarfi
har sai da ta sake zabura....

Acan falo kuwa Daddy ne yay amfani da damar fitar su Shareff ya shiga yimusu
nasiha musamman Gwaggo da Gwaggo Halima da Mommy da duk matsalar take daga garesu.
Duk da a cikin lalama da son bada shawara yay maganar sai Gwaggo ta fashe da kuka
tana matsar ido da fyatar majina wai ta fahimci laifinta suke gani dan bata
haifesuba. “Shikenan Muhammadu nadai fahimci laifina kake gani, nidai ALLAH na gani
ba inayi bane dan na rabaku da su kamar yanda kuke kallo sai dan kare martabarku da
takaicin da uwarsu ta shaƙa mana a gidannan wajen mahaifinku. Babu annamimanci da
kutungula da Zuwairah bataiba agaremu, akwai randa har sakinmu tasa mahaifinku yay
a daren duk da ana ruwa yace mubar masa gidansa. Akwai randa ta ɗau hanun Halima ta
turɓuɗa cikin murhu wuta naci wai dan ta zungurar mata icce. Kai har kusan jefa
mahaifiyarku tai a rijiya lokacin tana goye da Umaru. Taya azzalumar mace irin
wannan zanso ƴaƴanta kuma na baku goyon bayan kusota duk da abinda taima ƴar uwata.
Ai shara'armu da Zuwairah sai dai a lahira, gashinan makirar jikarta ta gadota a
komai na makirci. Dan haka bazaku taɓa samun nutsuwaba a gidannan tunda annamimiya
tazo jinin munafukai.....” Fyaaaatttt. Ta face majina da ƙarfi da nufar hanyar ƙofa
ta fita.
Mommy ma tashi tai a fusace tabi bayan Gwaggon tata. Cikin ɓacin Rai Gwaggo
Halima ta dubi su Daddy. “Yaya kaji ko, duk da abinda uwarsa taima tamu uwar amma
kuke nuna sonsa kamar.....”
“Halima!!”.
Daddy yay saurin dakatar da ita shima ransa a bace. “Amma Yaya itafa gaskiya ɗayace
daga ƙinta sai ɓata. Wlhy wlhy kaji na rantse bazan taɓa son su Usman ba a
gidannan. Har duniya ta tashi sunansu ƴan ubane a gareni, bawai ƴan uwa ba”. Fuuu
ta figi jakarta ta fice. Duk da kallo suka bita. Abbah ya fara sauke ajiyar zuciya
da maido kallonsa ga Daddy da ransa ke matuƙar ƙuna. Ya rasa mizai fassara Gwaggo
da shi. Tun basu san kansu ba take ƙulla raba kansu, ALLAH gafurun kuma rahimun ya
ganar dasu gaskiya hakan taƙi yuwuwa, amma bata barsun ba har saida haƙanta ya
cimma ruwa. Sukazo babu dalili suka tsani ƴan uwansu da basu taɓa masu komaiba su
da mahaifiyarsu sai alkairi, ALLAH ya ƙara taimakonsu suka gane suka canja. Gashi
yanzu tana son saka ƙiyayya kuma a tsakanin ƴaƴansu, wace irin fitinace wannan,
kenan itama data haihu a gidan basu isa su jitu da nata ƴaƴanba......”
Taɓashin da Abba yayne ya maidosa hankalinsa. Ya sauke numfashi a
hankali da ɗago idanunsa irin na Shareff da sukai jajur yana kallon ɗan uwan nasa.
Cikin ɗacin murya yace, “Abubakar itace silar komai. Duk wata ƙiyayya tsakanin Umma
da Mama itace taita haɗata. Bata barsu sun zauna lafiya ba muma ta hanamu gashi
zata hana ƴaƴanmu ma. Yanzu ƴar ɗaya tilo da ALLAH ya bama Usman ma bazata barta
tasha iskar farin ciki a cikin namu ƴaƴan ba. Kana ganin Maryamu ta daina zuwa da
ƴaƴanta ƙasar nan saboda Gwaggo. Haka kuma zamu cigaba da zuba idanu kenan
Abubakar?!”.
“Bazai yuwu ba yaya. Dolene a wannan karon mu ɗauki mataki. Yaya Halima tafi
kowa bani haushi. Sam ta kasa fahimtar halin Gwaggo tamkar ita ɗin ba mace bace ba.
A zatona da ake cewa mata sunfi kowa zuminci ita ya kamata ta fara farga da son
ganin mun dunƙule abu ɗaya amma da ita ake makamin rusamu. Bazan ɓoye makaba ina
tausayin Shareff akan wannan auren. Bazasu barsa ya zauna lafiyaba dan itama
yarinyar nan da kake gani shaiɗaniyar kantace Yaya”.
Sosai zuciyar Daddy ke ƙara tafasa dan yasan duk gaskiya ɗan uwan nasa ya
faɗa. Shi kansa yana tausayama Shareff dan yana cikin kwatankwacin irin halin da
suke neman jefasane akan mommy. Tunda ya aureta Gwaggo ta hanasu su zauna lafiya
saboda kawai tana taƙama ɗiyar ƴar uwartace......

★★

Tunda ya shiga ɗakin bai sake fitowaba. Kwance kawai yake a gado ko takalmi bai
cireba balle maganar wanka har aka kira magrib. Tashi yay ya nufi bayi yayo wankan
a gurguje da alwala. Tsabar bai buƙatar haɗuwa da kowa ta baya yabi ya fita
massallaci. Bai kuma dawo ba dan koda akai sallar isha'i can ya koma kan wani
dakalin maƙwaftansu ya zauna.....

Tunda suka dawo gidan batabi takan kowaba. Tadai shiga ta gaida Mom sannan ta
wuce ɗakinsu. Wanka tayi batare data ko shafa mai ba balle saka kaya ta kwanta da
towel ɗin jikinta dan wani irin barci ke rinjayar idanunta kasancewar sanyin ruwan
wankan dana jiƙar towel ɗin na ratsata. Barci sosai mai nauyi ya kwasheta, acikin
barcin taji kamar abu na binta. A ɗan zabure ta farka ta hau dube-dube. Ganin jini
ya sakata zaro idanu da dafe goshi. Shaf ta manta da batun zuwansa duk da sai jibi
ya kamata ta gansa ma. Gadon ta ɗan dudduba, ganin bai ɓaciba ta nufi toilet da
sauri, towel ɗin dai ya ɓaci kasancewarsa sky blue ya nuna sosai. Tasan yana mata
zuba sosai shiyyasa bata wasa, gashi tanata son siyen audiga dama amma shiririta
tasata mantawa dan ta saba sai da taga Mamie ta ajiye mata da lokacin yinsa yayi
gareta. A gurguje ta gyara jikinta ta fito, baƙar abaya kawai tasa ta ɗauka atm
ɗinta tayo waje. Ɗakin Mom ta leƙa ta samu tana salla, bazata iya jiraba dan akwai
matsala zai iya sake ɓatata. Yanzunma handkerchief ɗinta sabo tai amfani da shi
kafin. A falo ma duk sauran yaran sun fita massalaci kasancewar duk yaran Mom
mazane aunty Rahma ce kawai mace, Husna ɗiyar ƙanwartace take riƙo bayan auren
Rahama.
Su Daddy sun riga har sun shigo ciki, hakan yasa bata samu matsalar isa
gate ɗin ba duk da batasan a ina zata samo audiga ɗin ba, kawai zatai dai tambaya
ko gurin mai shagon layinne da sukan siyo ƙananan abubuwa wajensa koza'a samu
kokuma ya faɗa mata inda zata samo....
Cak ta tsaya tare da saurin ja da baya saboda karo da sukaci, sosai gabanta
ya faɗi, ta zabura da zummar komawa da baya tana kauda kai dan har yanzu haushinsa
takeji akan abinda ya faru, Juyawa tai da sauri.....
“Idan kika ƙara stap ɗaya saina karya ƙafafunki”.
“Wayyo Anam kin mutu kawai”.
Ta faɗa tana rumtse ido da cije lip ɗinta kamar zata fasa ihu. Sai kuma ta juyo
tana wani tamke fuska batare data yarda ta sake kallonsa ba, ita ala dole bata son
yaga lagonta..........✍

_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_


*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:


07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇


09134848107

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*🙏🏻😭


[10/26, 7:15 PM] My Zafafa: *_Typing📲_*

*_BABU SO....!!_*
_(Miya kawo kishi?)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_10_*

*_BABU SO....!! AREWABOOKS_*

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718

Shin ko kunada labarin Yar Zuru mamar ZEE ZEE Mai maida tsohuwa yarinya wadda ta
shahara wurin hada kaya kamar haka kamar su
Kaza
Zabo
Zakara
Ciccibi
Zuciya
Tsimin kankana d rake
Tsimin tabaje
Zumar dabino d kwakwa
Zumar gorun tula syrup
Garuka masu kama jiki kamar su
Bita zai zai
Dan wata bakwai
Madarar mata
Bata🤐🤐🤐
Ba kishiya ba Ko mugun mutan d mugun aljani sai sun barki
Matsin kinfi budurwa
Kalolin gumba dsauransu
Address maberar jariri bayan FGC sokoto
Phone 08068526455
Instergram Yar Zuru mamar ZEE ZEE kayan mata
_________________

.........Ido ya ɗan tsura ma atm ɗin hanunta cike da nazari, kusan mintuna biyu
harta ƙosa da tsaiwar sannan yay magana.
“Ina zakije?”.
Yanda yay maganar babu alamar wasa yasata ɗan ɗagowa a marairaice ta dubesa. “Abu
zan siyo”.
“Shi abun bashi da suna?”.
Ƙasa tai da kanta tana tura baki batare datace komai ba.
“Kin kurumuce ne?”.
Kamar zatai kuka tace, “Sirrine fa Yaya MM, kuma acan shagonne bada nisa
bane”.
“Koma ciki”.
“Yaya zanfayi amfani da shine yanzu”.
Ƙoƙarin zagayeta yay zai wuce da faɗin, “Idan kin matsu da koma miye sai ki
faɗa kafin ki fitan”.
Ƙafarta ta ɗan buga a ƙasa kamar zatai kuka sai kuma ta nufesa da sauri tasha
gabansa. “Yaya Shareff dan ALLAH. Wlhy important ne”.
“Inda important ɗinne da baki tsaya raimin wayo ba. Tashimin a hanya ko nabi
ta kanki”.
Matsawa ta ɗanyi ya raɓata zai wuce. Ganin da gaske tafiyar zaiyi tace “Audiga
zan sayo”. Cak ya tsaya daga yunƙurin barin wajen, kamar wanda akaima tilas ya juyo
yana kallonta. Sai dai ita nata kan a ƙasa sai faman ɓata fuska take dayin muy-muy
da baki alamar akwai abinda take son faɗa koma take faɗar a zuciyarta. Harga ALLAH
abinda ya fahimta zatai da audigan da ban. Dan haka ya dalla mata harara.
“Duk audigan dake cikin First aid box's ɗin gidannan kirasa audigan amfani
sai kin fita saya? Bar nan kona mareki, mu nan ba'a mana fitan dare”. Kukane kawai
ya rage bata saki ba. Har tayi niyyar yin zuciya sai kuma ta tuna halin da take
ciki da wanda zata iya tsintar kanta kafin anjima kaɗan. “Yaya Please zanyi amfani
da shine ALLAH”. Ransane ya ɓaci, ya ƙaraso inda take a fusace kamar zai kai mata
mari ta zabura gefe. “Ina miki magana kina faɗamin zakiyi amfani da shine”. Ganin
ya ƙaraso kanta ta zabura da gudu sai sashen Mom. Baiyi niyyar binta ba, sai dai
kawai zuciyarsa ta kitsa masa ya amshe atm ɗin hanunta shiyyasa yabi bayanta. A
falo ya sameta tana kumbure-kumbure Mom da su Salim zagaye da ita ana tanbayarta
lafiya? Dan babu wanda yasan tama fita.
“Wai bazakiyi magana bane Anam ana tambayarki kinyi shiru?”.
Shigowarsa ta hanata bama Mom amsa, duk suka maida hankalinsu garesa yaran na
gaishesa. Amsawa yay idonsa a kanta. Batare da yayi magana ba ya miƙa mata hanun
fuska a tsuke. Ta fahimci mi yake nufi ta bashi dan haka ta zabura zata gudu.
“Kika tashi a wajen nan sai kinyi kukan da baki taɓa yin irinsa ba bani”.
Mom ta kalla idanunta cike da ƙwalla. Mom data kasa fahimtar inda suka dosa
tace, “Babana miya faru ne?”.
A taƙaice ya faɗama Mom abinda ya faru. Cikin mamaki Mom ɗin ta kalleta dan
tasan dai Anam da tsoron dare, itada da dare yayi ko'a cikin gidan akace taje wani
sashin aika saita nema ƴan rakiyya. “Anam”. Mom tai kiran sunanta. Ɗagowa tai ta
dubeta sai kuma ta maida kanta ƙasa.
“Ina zakije?”.
A hankali tace, “Audiga zan siyo”.
Ɗan jim Mom ɗin tayi na nazari. Sai kuma ta girgiza kanta “Yanzu Anam har sai kin
tafi siyen audiga basai ki tambayeni ba, idan ma babu ai za'a bada a sayo miki.
Amma ko fitama bansan kinyi ba”.
“Kiyi haƙuri Mom naje naga kina salla”.
Girgiza kai kawai mom tayi, ta maida kallonta ga Shareff, “Ƙyale shashancin
wannan Babana, nasan yanda zatai maka bayanin ne yay mata nauyi”.
Janye idanunsa yay daga harar Anam ɗin, komai bai sake cewa ba ya fice. Binsa
tai da kallo tana taɓe baki, sai dai shi baima san tanai ba.

★★★★★★

Kamar yanda Daddy ya faɗa game da matso da auren Shareff ɗin hakane ta kasance.
Dan shirye-shirye aka cigaba da yi babu kama hannun yaro. Dama ankai komai gidan su
Fadwa, sai gidansa daya rage a ƙarasama ayyuka wanda dama kamfaninsa keyin ginin
shi kuma ya zana kayansa da kansa. Sosai yay busy a tsakanin, Anam ma wataran sai
Ya Khaleel take bi ya sauketa ya kuma ɗakkota. Tana dai shan masifa idan ta makara.
Ita dai yitake kamarma batasan hidimar da akeba a gidan, ko anko da aka fitar nata
cewa tai bataso ita batason kayan zafin nan sai da Mom ta mata faɗa sosai randa
zasuje wajen tela sannan ta yarda tabi su Aysha tanata kumbure-kumbure.

★Yau data kasance alhamis daya rage 1week bikin Shareff ƙarfe sha biyu ta
baro wajen aiki sakamakon mura da take fama da shi. Dama cikin dauriya ta fita
aikin har Khaleel na mata faɗa. Zazzaɓi daya rufeta ya hanata sukuni ga ciwon kai,
Yaseer ne ya samu shugabansu yay complain aka bata damar zuwa gida. Karan farko
data yarda ta shiga motarsa, dan tayi ƙoƙarin zame masa amma ya ɓata rai. Maimakon
ma gida sai ya fara nufar asibiti da ita, taso masa magana ciwon da kanta keyi
yasata hakura ta zuba masa ido kawai.
Basu wani samun tangarɗar ganin doctor ɗin ba, kasancewar akwai sanayya
tsakaninsa da Yaseer ɗin. Da ɗan mamaki Dr Jamal ke duban Anam ɗin, daga ƙarshe dai
ya kasa daurewa ya jeho mata tambaya. “Anam baki ganeniba ko?.”
Ɗagowa tai daga kwanciyar datai akan desk nasa ta ɗan dubesa, sai kuma ta
maida kanta ta kwantar tana ɗan girgiza masa kai. Shiru yay yana kallonta na wasu
daƙiƙu kafin ya cigaba da rubuta musu maganain ya bama Yaseer da tun tambayar da
yayma Anam ɗin ya shiga tunani. “Babu wani damuwa Yaseer murane kawai kuje a sai
waɗannan drugs ɗin tasha insha ALLAH fiver da headache ɗin zai sauka”.
Godiya Yaseer yay masa da basa hannu sukai musabaha. Ya bisu da kallo lokacin da
suke fita kansa a matuƙar ɗaure. Jiyay bazai iya haƙuriba ya ɗauka wayarsa domin
lalubo abokinsa dan tabbatarwa. A kiran farko dai ba'a ɗaga ba, duk da yasan
daliline ya hana hakan sai ya kasa daurewa ya sake kira....
“Ai harna fara tunanin bazaka ɗaukaba nai tracing naka ninazo inda kake”.
Daga can aka amsa da “Saikace wani ɓarawo”.
Dariya Dr Jamal yay dakai hannu ya shafi gemunsa. “My Man ai baka da maraba da
ɓarawon da ake nema ruwa a jallo yau a wajena. Dan nasan bazan iya haƙuriba”.
“Ai dama koda yaushe kai ba haƙurinne da kai ba. Miya faru?”.
“Muje a hakan bani da haƙurin. Wai dama mutuniyar ta shigo Nigeria amma ko
labari?”.
“Malam jeka kai tsaye kan maganarka waye mituniyar? Dan na kula kai
baka gajiya da kwashe-kwashe”.
“Oh ALLAH shaidar da kai min kenan? To Anam nake nufi. Dan yanzu suka bar
wajena ita da wani yaro Yaseer ya kawota a dubata”.
Ɗiff yayi kamar wanda ruwa ya cinye har Dr Jamal na tunanin kota yankene,
wayar ya cire a kunnensa ya kalla, ganin yana online ɗin dai ya shiga faɗin “Hello!
hello! Bakajina ne?”.
Ɗin! Ɗinn! kiran ya yanke, bai wani kawo komai a ransa ba ya ajiye wayar da
tabbacin bayaji ɗinne, shawarar daya yanke a zuciyarsa na anjima zaije har gida
kawai ya sashi ƙin sake kira.

★★

“To Alhmdllhi, indai banyi kuskure ba nan shine gidan”. Yaseer ya faɗa yana
duban Anam da tunda suka baro asibiti ta kwantar da kanta jikin sit ta lumshe ido.
Shiru bata motsa ba, yaɗan leƙa fuskarta yana murmushi da ɗan bubbuga gefen
kujerar. Idanun ta buɗe a hankali ta kallesa. Kamar yanda yake mata murmushi itama
saita ɗan sakar masa mai kama da yaƙe....
“Nan ne ko?”.
Ya faɗa a hankali kamar mai raɗa da narke mata idanusa. Janye nata tai daga garesa
a ɗan daburce ta kalli gate ɗin. “Nan ne, na gode sosai ALLAH ya bada ladan
zuminci”. Murmushi ya mata kawai ya buɗe ya fita. Side ɗinta ya zagayo itama ya
buɗe mata. “Thanks”. Ta faɗa a hankali da ziro ƙafarta ƙasa zata fito idonta ya
sauka akan Shareff da shima fitowarsa kenan daga gida hanunsa riƙe da key ɗin
motarsa dake anan waje fake, ita sam bama ta lura da motar ba sai yanzu daya danna
key tai ƙara. Ganin yanda ya kafeta da idanunsa ya sata yin ƙasa da nata ta ƙarasa
fitowa gabanta na faɗuwa. Ɗan baya tai kamar zata faɗi saboda jiri Yaseer yay
azamar kai hannu zai riƙota, dafe motar tai da sauri ta tsaya da ƙafafunta. “Ayya
sorry Friend”. Yaseer ya faɗa a hankali yana janye hanunsa da bai kai ga taɓata ba.
Ɗan satar kallon inda Shareff yake tai, yanzun kam zaune yake cikin motar sai
dai ƙafafunsa a waje yana danna waya tamkar bai san da wanzuwarsu a wajen ba.....
“Wancan ba Yaya bane?”.
Yaseer ya katseta yana fuskantar inda Shareff yake. Kanta kawai ta jinjina masa. “A
to bara naje mu gaisa ko?”. Nanma batace komai ba, ganin ya nufi inda Shareff ɗin
yake ita kuma gashi kwanciya kawai take buƙata, ga hararar daya mata sai kawai tai
shigewarta gida...
Shiru gidan babu gittawar kowa. Ta nufi sashen Mom da tunanin ko barci
suke. Nan ɗinma shiru har ɗakin Mom ta leƙa bata samu kowaba, kitchen ta nufa inda
take ɗan jin motsi. Iyami kawai ce tana ƙoƙarin ɗaura girkin rana. Gaisawa sukai
kafin ta tambayi su Mom da hausarta da Iyami bawani fahimta take da ƙyau ba. Iyami
ta bata amsa da cewar dukansu sun fita harsu Gwaggo amma batasan ina suka tafi ba.
Fitowa tai ta shige ɗaki ta kwanta, ko mintuna biyu bata cika ba aka buɗe ƙofar, a
tunaninta Iyami ce, sai dai kuma ƙamshin turaren da taji ya sata buɗe idanunta da
sauri...
Ido suka haɗa tai saurin janye nata ta maida ta rufe.
“Tashi”.
Sake buɗe idanun tai kamar zatai kuka, sai dai yanda yay kicin-kicin da fuska
yasata kasa musa masa ta tashi zaunen. Hanyar ƙofa ya nuna mata. Saita waro
idanunta da suka canja launi na mura ga ƙwalla a cikinsu.
“Banda lafiya fa Yaya. Ina zanje?”.
Ganin ya nufota ta miƙe da sauri hawaye na sakko mata saman kumatu. A falo ta
kusa faɗuwa saboda jirin dake ɗibarta, a bazata taji tattausan hanunsa cikin nata.
Gaba ɗayansu sai da tsigar jikinsu ta tashi, sai dai babu wanda yay yunƙurin cirewa
musamman ita dake buƙatar taimako dama. A haka suka fito har waje, ya taimaka mata
da kansa ta shiga mota sannan ya zagaya nasa mazaunin, tana sonyin magana tana jin
shakka dan haka tai shiru, saima ta kwanta abinta jikin sit ta lumshe idanu..
Wani clinic ya kaita dan a dubata. Data sanar masa sunfaje asibiti wata
muguwar harara daya wulla mata bata sake magana ba. Doctor ya rubuta musu magani
fuskarsa ɗauke da murmushi yake kallonsu da faɗin, “To amarya ALLAH ya ƙara afuwa
kafin biki”.
Idanu taɗan waro da kallon Shareff da shima kallonta yake, zatai magana ya
harareta yana miƙama doctor hannu. “Thanks you doctor”.
“No babu damuwa ango ALLAH ya ƙara lafiya sai ranar ɗaurin aure kuma”.
Shareff ya saki murmushi yana jinjina masa kai. Yanzu kam bama ta jira sun
jera ba tai gaba da sauri, koda ya fito harta buɗe mota ta shiga abinta. Sai da
suka baro anguwar gaba ɗaya ya tsaya a wani babban pharmacy ya sayi magungunan da
aka rubuta, ya kuma shiga gidan abincin dake gefen pharmacy ɗin yay mata takeaway.
Duk batasan hidimar da yake ba saboda tunda suka baro asibitin barci ya ɗauketa,
dan haka batasan inda suka dosa ba har sai da suka iso. Gefen kujerar yaɗan
bubbuga, a hankali ta buɗe idanunta, ganin har ya fita ta yunƙura ta tashi, fitowa
tai tana dube-duben inda suke “Yaya MM ina ne kuma nan?”. Bai tanka mataba, ya rufe
inda ta fita yay gaba abinsa. Ƙara bin gidan tai da kallo, dagani dai sabone dan
duk ma ga botikan fenti nan a tsakar gidan da kayan aiki, gabanta ya shiga faɗuwa,
cikin zuciyarta take tambayar kanta (ina kuma ya kawota nan?).....
“Idan kika bari na dawo nan ALLAH sai kinyi kuka”.
Da ƙyar ta iya ɗaga ƙafa ta nufi inda yake, koda ya buɗe ƙofar da key matsa
mata yay ta fara shiga, ƙamshin sabon fenti dana sabbin furnitures ya daki
hancinta. Sosai falon yay mata matuƙar ƙyau, danma ciwon kai ya hanata damar kallon
komai da ƙyau. Ganin tana neman kaiwa kwance ya dakatar da ita. “No tashi kici
abinci kisha magani first”.
“Yaya banajin yunwa kadai ban maganin kawai”.
“Dole kici abinci, kin taɓa ganin ansha magani ba'aci abinci ba”.
Yanda yay maganar babu wasa yasata yin shiru. Ya buɗe mata abincin tare da tura
mata gabanta, “Kafin na fito ki tabbatar kinci”. Da kallo kawai ta bisa harya shige
ƙofar daya buɗe..... Kusan mintuna goma sai gashi ya fito, ganin ya canja kaya yasa
ta kasa haƙuri. “Yaya Shareff ina ne nan?”.
Batare daya kalleta ba yakai zaune cikin kujera da faɗin, “Gidan ƴan shan
jini”. Shiru tai, dan tasan baƙar magana ya mata. Ɗagowa yay yaɗan kalli abincin,
ganin taci sai baice komaiba yaja ledan magungunan. Da kansa ya ɓalla ya bata, duk
ta amsa tasha dan sam bata tsoron allura bare ƙin magani. Ganin zata kwanta a
kujerar ya sashi faɗin, “Tashi kije ciki ki kwanta”. Kallonsa tai kamar zatai
magana sai kuma ta haɗiye abunta ganin yanda kicin-kicin da fuska. Ya bita da kallo
ta ƙasan ido harta shige, ɓoyayyar ajiyar zuciya ya sauke tare da lumshe ido ya
buɗe yana furzar da ɗan huci. Sai kuma ya miƙe ya fita.
Gidan ya shiga zagayawa, dan jiya masu fenti suka ƙarasa na katanga. Bai kuma
samu shigowaba sai yanzu. Komai yayi masa yanda yake buƙata, shi kansa ya yaba da
gidan duk da shine ya zana abinsa companynsa kuma ya fidda kayan aikin ginashi.
Yanzu amarya kawai gida yake buƙata nanda kwanaki bakwai insha ALLAH. Motarsa ya
nufa ya ɗauka lap-top ya koma ciki. Haka kawai yake jin nishaɗin zama a cikin gidan
yau, saɓanin ƴan kwanakin nan da duk yake jin ransa a dagule, dan kayan sashen nasa
ma sai da Mommy ta masa jan ido ya bada damar shirya masa su dan ita da kanta tai
order ɗin komai tamkar itace mai aurar da macen ba namiji ba. Komai saida ta haɗa
masa. Tunda kuma aka shirya kayan baizo ya zauna kamar haka ba......
Ring da wayarsa tai ya sashi katse aikin da yake famanyi a laptop ɗin ya ɗaga.
A tausashe yace, “Mommy barka da rana”. Daga can Mommy ta amsa masa da “Barka dai
son kana ina ne?”. Ɗan jimm yayi kafin yace “Mommy kina son ganina ne?”.
“Eh to kusan haka, amma idan zaka iya aika wani gidanka ya kai mana keys ma
basai kazo ba. Dan gamu a hanya zamuje dasu gwaggo gidan, sannan Halima tai kirana
ma danginmu na wajen baban Fadwa zasuzo da masu Company da zasu shirya kayanta su
auna komai, shiyyasa muka yanke shawarar muzo muma ɗin kawai dan babu daɗi dangin
uba kawai ko?”.
Tun fara maganar tata zuciyarsa ke faman bugu da sauri, ya ture laptop ɗin
cinyar tasa gefe, cikin dauriya da danne halin daya shiga yace, “Okay Mommy! kuna
inane yanzu haka?”.
“Ai gamu ma mun shigo street ɗin gidan naka kamar dai in ban mantaba”.
Goshinsa ya dafe yana ambaton “Ya ALLAH a hankali”.
“Mi kace?”.
“No Mommy, canai ALLAH ya kawoku lafiya ai inama gidan nima na shigo ganin aiki
daga nan na ɗan huta”.
“Kaji ja'iri, bama ka bari iyayen naka su kaika ganɗoki muje biki”.
Ƴar dariyar yaƙe kawai ya mata da faɗin, “Sai kun iso”.

Da sassarfa ya nufi hanyar bedroom ɗinsa. Ya duba Anam dake barci


hankalinta kwance harda naɗewa cikin lallausan duvet nashi dako shi bai taɓa
lulluɓa da shi ba. Nufarta yay yakai hannu kamar zai tadata sai kuma ya fasa, ya
ɗan furzar da huci tare da dafe goshinsa yana ambaton sunan ALLAH. Ya tabbatar su
Mommy suka ganta ya shiga uku, dan baima san kalar ƙurar da zata iya tashi a family
ɗin MD Shareff ba yau. Jin horn ya sashi sake ambaton “Ya ALLAH”. Tare da fita a
ɗakin domin buɗe musu tunda babu maigadi har yanzu sai zuwa gobe idan ALLAH ya
kaimu yake saran Fharhan zai kawo shi.....

Tunda ya buɗe musu gate bakin Mommy da Gwaggo ya sake washewa. Suma dai su
Mom fuskarsu da murmushin jin daɗin ganin yanda ɗansu ya gina wannan gida dako
maƙiyi ya gani zai yaba ko'a zuciyane.
“Kai-kai! Anya kuwa Alhaji ƙarami bazan dawo nan ba irin wannan gida haka?”.
Gwaggo ta faɗa tana riƙe haɓa dabin ko'ina da kallo. Murmushi yay mata da shafa
kansa. “Indai bazaki dinga damuna da kwakwazonki ba sai na dawo dake”. Dariya su
Mom sukasa, yayinda Gwaggo tai masa daƙuwa. Nanma murmushi yayi kawai. Da kansa yay
musu jagora suka shiga ko'ina suna mai yabawa da masa addu'a, bakin Gwaggo da baya
iya yin shiru tace, “Toni abinda ban ganeba anan, Alhaji ƙarami yanaga sashe biyu,
gidan kamar na zaman mace fiye da ɗaya! Kar dai kacemin kaima halin Kakanka da
ubanka zakai tara mata?”.
Ganin duk su Mom sun juyo suna kallonsa, har fuskar Mommy ta sauya ya sashi
ɗan hararar Gwaggo ta ƙasan ido. “Kai tsohuwarnan kedai bakinki bai iya shiru,
kawai dan mutum yayi wadataccen waje a gidansa sai yazam na aure? Nayine saboda ke
in kinzo kwaɗayin jar miya”.
Dariya su Aunty Amarya suka sanya. Mommy ma ta ɗan saki fuska tana murmushi
dan tun farkon fara ginin gidan da tazo ta gani ta masa irin wannan maganar ganin
sashe biyu da nasa na uku, amma sai yace yayine kawai saboda baƙi. Haka kawai
zuciyarta taƙi aminta da shi taita masa bin.....
“To shikenan muje ka kaimu naka sashen muga namai gida”.
Gwaggo ta katse mata tunani. Gabansane ya faɗi, zaiyi magana Gwaggo ta nufi
ƙofar sashen da basu shiganba wanda tabbacin nasan ne, itama Mommy saita take mata
baya. Hakan yasa dole su Mom ma binsu. Da ƙarfi ya rumtse hanunsa da cije lip
ɗinsa. Ganin har Gwaggo ta shige yay saurin bin bayansu shima dan ya tabbata target
ɗinta na biyu shine bedroom ɗinsa. Kamar yanda yay hasashen kuwa hakane. Dan ko
falo bama tagama nutsuwa ta ganiba ta nufi ƙofar bedroom acewarta da nan zata fara
a sashen. Shigowarsa tayi dai-dai da ɗaura hanunta a handle ɗin ƙofar.............

*_🙆🏻Yau munga idi wagga tsohuwa babu man kai zata ɓaro aiki. Dangin Anam kuna
ruwa, maganin masu bin mazan mutane kenan🚶🏻😂🤭_*

_ZAFAFA BIYAR_
*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_


*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:


07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇


09134848107

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻


[10/26, 7:15 PM] My Zafafa: *_Typing📲_*

*_BABU SO....!!_*
_(Miya kawo kishi?)_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_12_*

..........A karon farko ta ɗago ta kallesa da mamaki ganin inda yay parking. Magana
take so tayi, sai dai ta kasa. Shi kuma yaƙi cemata komai, sai ma wayarsa daya
ɗauka yay ƴan danne-danne yakai kunensa. “Fito”. Kawai ya faɗa ya yanke wayar. Ba'a
rufe minti uku ba wata budurwa mai tsananin iyayi ta fito daga shagon saloon ɗin
tana tafiya kamar tarwaɗa. Haka kawai abin nata ya bama Anam haushi, taja siririn
tsaki da taɓe fuska ta janye idonta. Duk da tayine a hankali sai da yaji, sai dai
bai nuna yajinba balle ya tanka, sai ma faman daƙilar waya yake, amma ya buɗe
murfin kafarsa ɗaya a waje take.
“Assalamu alaikum Yah Musty barka da zuwa”. Budurwar ta faɗa murya a
lanƙwashe lokacin da take isowa wajen. Kansa kawai ya jinjina mata yana janye kunne
ɗaya na earpiece dake a kunnensa. Kamarma bata damu da abinda yay matan ba. Murya
ta ƙara tausasawa cike da iyayi tace, “To Bismillah muje ko”.
Nan ɗinma bai tankaba, sai da yaja wasu sakanni ma sannan yay yunƙurin fita
a motar.
Baƙin ciki, haushi da takaicin ballagazanci na wasu mata ya tokare maƙoshin
Anam. Lokaci ɗaya taji tama tsani budurwar.
“Sai an fito da ke ne?”.
Ya faɗa cike da gatse idonsa akan Anam. Jitai kamar karta fita ɗin, amma sai yaci
darajar Yaya da yake gareta tabi umarninsa. Yanda budurwar batai mata magana ba
itama bata nuna tama san da zamanta a wajen ba. Gaba sukai tana binsu a baya,
budurwar sai ƙoƙarin dai-daita tafiyarta take da shi tamkar dole, ga baki ta saki
sai surutu kai kace hanyar kasuwar wanbai aka buɗe da safe. Sosai wajen Saloon ɗin
ya haɗu dan yaɗan birge Anam kaɗan, sai dai bata nuna a fuskaba saima kicin-kicin
data sakeyi da fuska duk da gaisuwa da ma'aikatan wajen ke musu na girmamawa daya
bata mamaki matuƙa. Wajen zama aka basu, harda ajiye musu abinsha kafin budurwar da
taji ma'aikatan sun kira da aunty Deena ta dubesa cike da yauƙi da shauƙi.
“Sir za'a mata kitso ne?”.
Bai jita ba, saboda earpiece dake manne a kunnensa. Hannu takai ta cire kunne
ɗaya, ya ɗago ya dubeta yana sake tsuke fuska. “Am sorry, nayi magana ne bakaji ba,
nace za'a mata kitsone?”. Idonsa ya ɗauke daga gareta ya maida ga Anam datai kicin-
kicin da fuska fiye da yanda suka shigo dan ta fahimci ita ya kawo kenan. “Komai ma
daya dace kumata”. Ya faɗa a taƙaice da maida earpiece ɗinsa.
“Ni wlhy bance inaso ba. Kuma kaina a wanke yake, hakama......” Hararta yay
yana mai zare kunne ɗaya na earpiece ɗin, tai saurin sake haɗiye maganar tana matso
hawaye. Ɗauke idonsa yay kamar baima ganta ba. Tanaji tana gani aka kwance mata
kalbar kanta aka saka mata relaxer aka wanke fes. Bayan an rage ruwan da towel akai
steaming ɗinsa. Wadda take mata gyaran tambayarta tai tana son kitso ne? Amma tai
mata banza. Ganin haka ta juya ga Shareff dake zaune komai anayi gaban idonsa.
“Sir za'a mata kitson ne ko a barta?”.
“Barta kawai a mata lalli”.
Yay maganar batare da ya kalleta ba yana maida earpiece ɗin kunensa.
Ana fara wanke mata ƙafa da gyaran farcen hanunta ya miƙe ya fita, Anam ta
bisa da harara ƙasa-ƙasa tana tura baki. Cikin ƙunƙunai tace, “Gwarama da zakai
aure mu huta da baƙin halinka”.
Murmushi mai mata wankin ƙafa tai saboda jin abinda tace. Lokacin da aka fara
zana mata lalle harda ɗaukar video, dan tana son lalli sosai kitsone dai kam saida
dambe da Mamie tsaye kanta, dan ko Mamie ce tace zata mata ba yarda take ba da
arziƙi. Abie kam lallaɓata yake ko yace a barta sai wani lokaci tunda bata so.
Sosai ta fito ras tai ƙyau tamkar wata sabuwar amarya. Sai faman kallon
kanta take a manyan mirrors na wajen tana murmushi da ɗaukar hoto kamar ba'itace ta
gama rikiciba yanzun. Sai da tai mai isarta sannan ta fito waje kamar yanda Deena
ta tabbatar mata Yaya Shareff na nan na jiranta a waje. “Okay”. kawai tace mata tai
ficewarta. Deena da yaranta suka bita da kallo baki taɓe. Fuska ta haɗe tamau tana
cika baki da iska lokacin da take fitowa, ta buɗe motar ta shiga tana wani kauda
kai taƙi kallon inda yake.
A jiyar zuciya ya sauke a hankali yana ɗagowa daga kwanciyar da yay jikin
kujerar, murmushin daya tsaya iya laɓɓansa ya ɗan saki ganin yanda taketa faman
kauda kai gefe wai ita a dole haushi take da shi. Hanunsa ya kai ya zame veil ɗin,
tai saurin riƙewa tana tura baki. Kallon daya wulla mata ya sata sakin masa babu
shiri, sai da ya gama ƙarema gashin kallo cikin ɗan lumshe ido da buɗewa ya maida
mata ya rufe. Sosai gashin nata yasha gyara sai ƙamshi mai daɗi da ƙyalli yake.

Koda suka iso a gate yay parking, tana fita yaja motar yay gaba abinsa. Da
harara ta raka motar, sai kuma ta kalli hanunta da ƙafa da sukasha lalli tai
murmushi. Gidansu tai shigewarta. Dan cikin gida tun daga waje kana iya jiyo
hayaniyar daya sake ɗauka alamar baƙi sun ƙaru kenan. Gidan nasu ma cike ta sameshi
da baƙin da suka iso bayan fitarta. Sai su Aysha dake shirin komawa gidansu amarya
bayan magrib Arabian night. Tambayarta wanda yay mata ƙunshi suka shigayi kowa na
yaba ƙyan da yayi. A takaice tace musu Yayane ya kaita wani waje kawai. Koda suka
buƙaci jin wane Yaya a ciki bata amsa musu ba tama shige toilet dan son watsa ruwa
kasancewar gab ake da kiran sallar magrib saboda sun jima a wajen ƙunshin nan ba
laifi, gashi ko sallar la'asar batayi ba.
Ana idar da sallar magrib ƴammatan gidan suka sake ficewa wajen event na
arabian da aka shirya amma banda Anam yanzu ma. Dan kwanciyarta taima tana kallo a
lap-top hankali kwance kamar bata san bikin da akeyi ba. Har magana Amrah tai mata
amma tace karta dameta. Yanda tai maganar cikin masifa yasa kowa bai sake magana ba
sukai shirinsu suka fice.

★★★★★

Washe gari kam gida ya sake cika danƙam da ƴan uwa da abokan arziƙi na nesa dana
kusa. Abokan Yah Shareff na Nigeria da wajenta duk wanda ya iso anan ake saukarsa
gidansu Anam a sashen Shareff ɗin da tuni Abie ya ware dominsa duk da ba zama yake
ba a hanunsu yanzun. Duk hidimar da ake Anam na ɗaki batako fitowa sai yunwa ta
isheta. Bamai ganin ko fara'arta. Mamie tayi faɗan harta watsar da lamarinta,
hakama Aysha fushi take da ita dan ita bataga mi Anam ɗin kema fushe-fushen ba
tunda babu wanda ya mata wani abu ai. Aima gaba ɗaya ta tsame kanta daga shagalin
bikin tamkar Shareff ba ɗan uwanta ba. Da yamma kusan rabin jama'ar gidan suka wuce
gidansu Fadwa amarya kamu amma nanma Anam bataje ba. Kai barci ma suka wuce suka
barta tana sha hankali kwance. Koda suka dawo kuma su Aysha nata labarin yanda kamu
ya kasance da ƙayatarwa Anam sai tai tsaki tama fice a ɗakin gaba ɗaya. Da kallon
mamaki duk suka bita, sai dai babu wanda ya kawo komai a ransa game da al'amarin
nata tunda ansanta da miskilanci da kuma tsanar da sukaima juna ita da ƴan gidan su
Fadwa batun yanzu ba.

*_WASHE GARI* ta kama ranar ɗaurin aure, har sha biyu Anam na ɗakin Abie
tana shaƙar barci. Dan tun bayan sallar asuba ta gudo daga ɗakinsu saboda hayaniya
tafi ƙarfi acan downstairs. Duk tashin da Mamie ta mata taƙi, sai kawai ta shareta
ta cigaba da hidimar baƙinta, dan nan ɗinma dai ya cika taf da dangin Mamie da ƴan
uwa da abokan arziƙi kasancewar wannan shine karo na farko da zata fara aurarwa,
duk da ba'ita ta haifi Shareff ba an mata karar riƙesa da tai tamkar ɗanta auren ya
koma tamkar a hanunsu ne.
Mutane sai tambayar ina Anam akeyi, sa'ointa ma na family ɗin sunata zuwa
nemanta. Bata tashi ba sai kusan ƙarfe ɗaya, batare da tayi ko brush ba ta fito
sanye cikin kayan barci fuska a kwaɓe dan yunwa takeji. Fitowar tata yayi dai-dai
da shigowar ango da tawagar abokansa, yayi ƙyau har ya gaji cikin ɗanyer shadda
fara tas sai baza ƙamshi yake yi. Ga wani kwarjini na musamman da kwalliyar ta basa
tabbacin yau ɗin ta daban ce a garesa. Hakama abokansa kowa ya sha ƙyau.
Anam ta kafesa da manyan idanunta da barci ya sa su yin wani luf-luf da sake
girma, shima tunda ya shigo nasa idon a kanta suke, sai dai lokacin ɗaya ɗan
murmushi dake a saman fuskarsa ya bace ɓat, ya ɗan harareta ya ɗauke kansa
kasantuwar caa da ƴan uwan Mamie sukai masa kowa na faɗin albarkacin bakinsa cikin
yabawa.
Murmushi ya ƙaƙaro yana kaiwa rissine domin gaishe su kamar yanda abokansa
sukayi suma, kafin ya miƙe zuwa gaban Mamie da tun shigowarsu idonta ke kansa tana
murmushi. Gabanta ya durƙusa ciki sanyin murya mai nuna rauni yace, “Mamie zamu
tafi masallaci”.
Hannu ta ɗora saman hularsa, itama muryarta a raunane da sanyi tace, “ALLAH
yay maka albarka Al-Mustapha. ALLAH yasa a ɗaura a sa'a, kuma yasa abokiyar
arziƙinka ce har a aljannah”.
Gaba ɗaya falon aka amsa da amin. Shareff da kansa ke ƙasa ya kasa ɗagowa,
hakan yasa Mamie kamo haɓarsa da yatsunta biyu ta ɗago fuskarsa. A hankali hawayen
dake maƙale a idanunsa suka gangaro, murmushi ƙarfin hali tayi da ƙoƙarin son danne
nata hawayen dake son zubowa amma hakan ya gagara. Itama sai kawai ta saki kuka
mara sauti tana goge masa nasa hawayen da hanunta duka biyu. Sun birge kowa, sun
kuma bama kowa tausayi, duk da wasu basu san dalilin kukan nasu ba kai tsaye.
Mamie dake murmushi ga hawaye tace, “Tashi kuje karku makara su Abie ɗinku sun
wuce tun ɗazun. Kai Shareff ya gyaɗa a hankali, sai kuma ya kai hannu shima ya
share mata nata hawayen, ta saki murmushi da shafa kansa. “ALLAH yay maka albarka”.
Da amin aka sake amsawa. Ya miƙe idonsa na kallon ɗan lungun da zai sadaka da
hanyar upstairs inda Anam take. Har yanzu tana gurin, hasalima leƙensu take baki a
taɓe dan ita bataga miye na kuka ba inba gulma ba. Harda faɗin, “Su Mamie an iya
kalan dangi, Mommyn sa batako kallona da arziki amma ke kinama ɗanta wannan kulan”.
Ganin ya miƙene yasata komawa ta maƙale, jin kamar sun nufi hanyar fita ta sake
leƙowa. Ido suka haɗa dashi yana tsaye shi da Aunty Mimi suna magana. Fuska ta taɓe
da murguɗa baki tabar wajen. Numfashi ya saki a ɗan fisge da lumshe idanunsa ya
ɗauke kansa shima. Aunty Mimi da duk taga komai tai murmushi kawai tana kallonsa.
Fuska ya ɗan kwaɓe. “Miye kuma small Mom?”.
Dariya tayi da faɗin, “A'a babu komai My son. Kuje karku makara ALLAH yasa a
ɗaura a sa'a.”
“Humm”
kawai yace mata yay gaba abinsa. Ta sake ƙyalƙyalewa da dariya. “Ita dai wannan
Humm ɗin bata magani Yarona”.
Murmushi kawai yay batare daya juyo ba ya fice abinsa. Dr Jamal da Fharhan
da suka rage na take masa baya..

Bayan ficewarsu Aunty Mimi bin bayan Anam tai. Ganinta zaune tana kallon su
Aysha daketa faman shiryawa ta korata itama tai wanka. Ta kuma tabbatar mata idan
har ta sake shigowa ta ganta bakamar kowaba saita ɓata mata rai matuƙa. Babu yanda
ta iya dole tabi umarninta, su dai su Aysha sai faman dariya suke. Bata kulasuba ta
shiga tai wanka, ta fito ta shiryawa a ɗaya daga cikin kayan fitar biki da su Daddy
sukai musu. Sai dai kalar nata daban tasa saɓanin ƴan uwanta da duk suka saka
atamfa. Sosai lass ɗin yamata ƙyau kasancewarsa skirt da riga kuma bata saba sakawa
ba. Tai ɗas abinta kamar itama amaryar ce (Anam team😜).

_________________________________

Alhamdulillahi bayan idar da sallar juma'a dake massallacin juma'a na


anguwarsu ɗunbin al'ummar musulmi daga sassan daban-daban na Nigeria da wajenta
suka shaida ɗaurin auren *_Al-Mustapha Muhammad Shareff_* da amaryarsa *_Fadwa
Sadiq Dakata_* akan sadaki naira dubu ɗari biyu. Ɗaurin aurene daya tara manyan
mutane masu alaƙa da ango da iyayensa harma da ɓangaren amarya.
Kamar yanda nan gidan su Shareff ke cike da ƴan uwa da abokan arziƙi acan
gidansu amarya Fadwa ma hakane. Taci ado na faɗa aji daya amsa suna ado irin na
amare ƴan ƙwalisa masu ji da lokaci (😘😍Sai dake tawan😂😉). Tana tsakkiyar ƙawayenta
daketa aikin zuba hotuna da videon ɗorawa a tiktok. Tun kafin yau amarya Fadwa ta
roƙi angonta da zarar an ɗaura aure ya taimaka ya kirata ya fara sanar mata da
kansa. Da farko bai amsaba, sai dai yanda ta dinga nacin damunsa da maganar tsahon
lokaci yace zaiyi. Shi mutum ne dabai ɗaukar alƙawari bai cikaba, sai dai hakan ta
kasance bisa akasi. A yanzun ma harya shafa'a alƙawarin ya faɗo masa a rai. Yana
tsaka da gaisuwa da abokansa yay excusing kansa ya koma gefe yana mai ƙoƙarin
cikawa. Ga amarya Fadwa kam harta fidda rai zuciyarta sai faman kaikawo take kamar
ta fasa kuka. Ta riga ta gama shiryawa da ƙawayenta domin jiran wannan lokaci, sai
dai shiru kakeji sun fara jin kishin-kishin na cewar an ɗaura auran. Dama tasan
itama gangancine kawai, Shareff ba irin mazan da ke ɗaukar kowane kalar shirme
bane, hasalima ita har yanzu bai san tana harkar yanar gizo ba, da tana da tabbacin
sai sun kwashi ƴan kallo da shi.......
Ring ɗin wayarta ya katse mata tunani, tamkar maijin tsoro ta ɗauka wayar
tana dubawa badan ta saka ran ganin shi ɗin bane. Kasa ɗagawa tai har sai da babbar
aminiyarta Sima ta ɗaga mata tasa a hansfree dan sunada tabbacin abinda suke zaman
jiran ji ne daga angon dama. Sassanyar muryarsa data ratsa cikin wayar ta saka
ɗakin ƙarayin tsitt, masu video recording na faman ɗauka. Cikin rawar murya ta
amsa, dan haka kawai taji kuka ya taho mata batare data san dalili ba. Daga can yay
murmushi saboda jin yanayinta, ashe da gaske aure yaƙin mata ne, dan yasan abinda
zai saka Fadwa karaya ba ƙarami bane. Yay ɗan gyaran murya da sake kwantar da
murya. *_“Habibtie kin zama Matar Al-Mustapha, ina roƙon UBANGIJIN daya nufemu da
ganin wannan rana ya bamu lafiya da zuri'a masu albarka, tare da haƙurin zama da
juna, mai cike da kulawa da soyayya na har abadan. Finally Al-Mustapha ya zama
naki”._* Kalamansa sun ratsata daga ita har ƙawayenta da abun yay matuƙar burgesu,
sai kawai ta sakar masa kukan da taketa faman haɗiyewa. Murmushi yayi, da sake
faɗin, “Congratulations once again dear, i love you”.
“I love you too”.
Ta amsa masa da sake fashewa da kuka. Gaba ɗaya ɗakin ya ɗauki wani irin ihu da
sowa harda masu guɗa. Jama'a dake waje kuwa har ture juna ake wajen son shigowa aga
mike faruwa.

Cikin ƙanƙanin lokaci video ɗin da ƙawayenta suka ɗauka suka ɗaura a tiktok,
istagram ya fara yawo fiyema da yanda sukai zato ko tsammani a kowane shafi na sada
zumunta kamar yanda sauran hotunan da suketa ɗaurawa na sauran kwanakin ke yawo
dama . Wanda ma followers ɗinsu basu kaiba tuni ƙaruwa suke. Comments da like kam
ai bama a magana. Ƴammata sai alwashi ake ɗauka da zuwan tasu makamanciyar wannan
rana. Wanda ko bikinsu ke shirin zuwa next week dama cikin satin tuni sun fara
neman angunan nasu da ƙawaye yanda zasu tsara nasu suma. (Hummm media-media gidan
kashe ahu😣).

★★★

Daga wajen ɗaurin aure gayyar abokan ango da abokan su Daddy dama sauran jama'a
suka ɗunguma hall ɗin da aka shirya walimar cin abinci domin su. Anci ansha anyi
hotuna kafin ango da tawagarsa su nufo gida. Yanzun kam sai da suka fara shiga
gidansu yakai kansa ga Mommyn sa. Rungumesa tai cike da farin cikin yaronta ya zama
babban mutum yau burinta ya cika. Ƴan uwa da abokan arziƙi nata tayasa murna da
masa fatan alkairi. Anyi hotuna shida dangin Mommy dama sauran jama'a har da wanda
ke a tsakar gida na kusa. Daga nan gidan su Anam suka nufa da gayyar abokansa tunda
dama nan ne masaukin nasu, Mamie kuma tama sake shirya musu wasu abincin anan dama.
Nan ɗin ma gidan cike yake da ƴan uwa da abokan arziki. Shigowarsu ta saka
wasu fara sakin guɗoɗi, yayinda maroƙa keta aikin kirari na al'adar biki. Su Aysha
da duk suke zaune a harabar gidan suma kan kujerun roba da aka zube miƙewa sukai
cike da farin ciki suka nufi Yayan nasu dan tayasa murna suma. Anam dake faman
latsa waya duk hayaniyar da ake gidan batako ɗaga kanta ba taja siririn tsaki, tare
da gyara zamanta dan babu alamar zata bisu.
Har aka fara ɗaukar hotuna bata ko kalli sashen da suke ba. Sai ma mikewa
tai da nufin barin wajen taji an riƙo hanunta. Juyowa tai a fusace da tunanin cikin
su Amrah ne, sai tai arba da aunty Mimi. Baki ta tura idonta na tara hawaye, aunty
Mimi ta girgiza kanta da faɗin, “ALLAH ya shiryeki Mamana”. Hanunta taja har cikin
taron, ta kaita har gaban Shareff ta tsayar.
Ƙoƙarin haɗiye hawayen dake son zubo mata ya hanata iya ɗagowa ta kalli kowa
take, ga idanu tanaji a kanta da maganar da aunty Mimi ke mata akan ta ɗago mai
hoto zai ɗauka. Aunty Mimi zata ƙara magana Shareff ya girgiza mata kai, tare da
yima camara man ɗin nuni daya dauka kawai. Aiko ɗaukar ya farayi abinsa, bayan an
musu su kaɗai kusan kala uku mutane suka fara shiga, daga haka aka cigaba da ɗauka
batare da ko sau ɗaya Anam ta kalli camara ba. Daga ƙarshe ma ƙoƙarin zame jikinta
a wajen ta shiga yi dan kukan da take dannewa ƙoƙarin fin ƙarfinta yakeyi. Taku
ɗaya tai taji an riƙo hanunta, cak ta tsaya, tare da juyowa da sauri zuciyarta na
ƙara zuwa wuya. Ɗaukewa numfashinta ya nemayi a dalilin shigar idanunta cikin nasa,
ya kuma sarketa da su da iyakar ƙarfin ikonsa. Ga hanunta har yanzu yana riƙe a
cikin nasa. Tuni camara man ya maida hankalinsa a ɗaukarsu hoto. Ƙoƙarin janye
hanunta tayi ya hana hakan, ga idanunta ma sun gagara fita a cikin nashi. Hawayen
da take maƙalewa ne suka silalo a fuskarta a hankali, ta fisge hanunta da sauri
tabar wajen harda ɗan haɗawa da gudu. Waɗanda hankalinsu ke kansu duk suka bita da
kallo kamar yanda shima ya bita har sai da ta ɓace. Ido suka haɗa da aunty Mimi yay
saurin ɗaukewa shima yana barin wajen..........✍
*_Ko anƙi ko anso, aure dai ya ɗauru, murna muke daga zuciya har zuwa ranmu💃🏻😍😜.
(Anam team ya take ne🤣😂😉😜?)_*

_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_


*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:


07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇


0913484810_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_


*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:


07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇


09134848107 ko

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏽


[10/26, 7:15 PM] My Zafafa: *_Typing📲_*

*_BABU SO....!!_*
_(Miya kawo kishi?)_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_11_*

.......Ɗin! Ɗinn!! Horn dake nuna alamar isowar dangin amarya Fadwa ya saka Gwaggo
juyowa baki a washe tana faɗin, “A to ga masu ganin gidan nan ma sun iso ai? Kai
Alhaji ƙarami muje ka buɗe musu ƙofa ɗin saina tarbesu ai ko”.
A hankali ya lumshe idanunsa da sauke ɓoyayyar ajiyar zuciya. Mommy ma bin
bayan Gwaggo tayi, suma su Mom sai suka bisu kawai dan abu kaɗan zai iya jawo
Gwaggo taita surutu. Har zai bisu ya dawo da baya, zuciyarsace ta bashi shawaran ya
sakama ƙofar key, dan haka ya kulle da sauri ya fidda key ɗin ɗakin a cikin keys ya
saka aljihu sannan yabi bayansu...

Mota uku ce a jere kai kace jeren kayan sukazo. Motar farko Fadwa ce ta fara
fitowa a ciki, sai ƙawayenta uku. Ta biyu kuma ƙannen babanta ne su biyu da cousin
ɗinta biyu suma dai duk masu aure ne. Sai aminiyar Gwaggo Haliman. Motar ƙarshe
babban yayan Fadwa sauran kuma ƴan kamfanin da zasuyi aikinne dan motarma akwai
tambarin kamfanin. Cikin mutunta juna aka gaisa tunda dama akwai alaƙa, kafin su
ɗunguma gaba ɗaya zuwa can. Fadwa sai satar kallon Shareff take amma yayi kicin-
kicin kamar ma bai ganta ba. Dama tun waccan ranar ko kiransa tai baya ɗagawa, idan
tai masa magana koda yana a online kuwa ko buɗewama bayayi. Tabi duk hanyar daya
dace su sasanta amma yaƙi kulata dan yayi alwashin koya mata hankali a wannan
karon.
Ko'ina sai da suka shiga kowa na yabawa dan gida kam yayi sai dai maƙiyi.
Ma'aikatan kamfanin da zasu saka kayan kuwa nata faman gwaje-gwajensu tunda dama
amarya ta gama zaɓar wanda take buƙata tun a gida. Zare jikinsa yay ya koma
sashensa batare daya amsa tambaya ko ɗaya ba akan ɗayan sashen dasu Gwaggo sukai
magana suma. Shi dariya ma suke bashi da mamaki, ina ruwansu da sashen to tunda
basu suka basa kuɗin ginin ba, sashen dama ko ƙarasa masa ayyuka ƙananu ba'aiba ya
tsolema kowa ido.
Baifi mintuna biyar da shigowa ba Fadwa ta biyo bayansa. Bai nuna alamar yasan
da shigowar tata ba. Duk da shariyar tasa ta sosa ranta sai ta shanye ta shiga yaba
yanda sashen nasa yay matuƙar ƙyau shima. Yanda tsarin ya kasance na black and milk
da ratsin ash ya matuƙar ƙayatarwa.
“Soulmate!”.
Ta kira sunansa a hankali tana kaiwa zaune kusa da shi. Bai amsa ba, bai kuma ɗago
ya dubeta ba yanata aikinsa kamar yanda ta samesa. Murmushin takaici ta ɗanyi tana
kallonsa, ta lumshe ido ta buɗe akansa zuciyarta na raya mata abubuwa masu yawa dan
ba ƙaramin haɗin kayan mata tasha ba. Sake matsawa tai jikinsa a kasalance ta ɗaura
kanta a shoulder ɗinsa ta saki kuka.
Cak ya tsaya da aikin da yakeyi, yaja numfashi ya fesar yana mai rufe idonsa
da buɗewa a lokaci guda.....
“Dan ALLAH kayi haƙuri ka daina fushi dani haka nan Yaya Al-Mustapha.
Karka manta kwanaki takwas kacal ya rage mu zama abu guda, ina buƙatar ganin
murmushi a fuskokinmu yayinda jama'a zasu fara taruwa dominmu daga gobe. Naji nayi
laifi kuma na amsa na kuma bada haƙuri bazan sake ba mijina”.
Kalamanta sun ɗan saka masa sassauci, sai dai baida alamar cewa wani abu a
zahiri. Kanta ta ɗago daga kafaɗarsa tana kallonsa idanunta na rige-rigen matso
hawaye, ta riƙo hanunsa dake dafe da lap-top har yanzu sai dai ba aikin yake ba.
“Baka haƙuraba ko My Soulmate? Shike nan na baka damar kaimin kowane irin hukunci
amma dan ALLAH banda naƙin kulani na tuba”.
Karon farko ya ɗago idanu ya dubeta, kafin ya maida ga hanunsu dake cikin na
juna. Nasa ya janye tare da ɗan bada tazara daga kusancinsu. “Naji ya wuce, sai dai
ki tabbata kika sake hukuncin dazan ɗauka bazakiji da daɗi ba. Ni da ke zamu zauna
bada iyayenmu ba, dan haka matsalarmu mune ya kamata mu fuskanceta basai wasu sunyi
alƙalanci a ciki ba”.
“Insha ALLAHU zan kiyaye mijina”. Tai maganar tana faɗawa jikinsa ta
rungumesa. Hannu yasa ya janyeta. “Nasha faɗa miki bana son ɗabi'ar nan sam. Domin
babu wani hallaci daya halatta hakan garemu”.
“To kayi haƙuri, amma karka manta kwana takwas ya rage kacal mu zama
ma'auratan ai ko, kaga kenan akwai banbanci da da yanzun”.
“Sai ki bari sai mun zama ɗin, a yanzu dai haramunne”.
“Hummm” kawai ta faɗa dan bata bukatar su sake wani rikicin kuma saboda kar
yay amfani da damar yaƙi halartar duk events da suka shirya gara ta lallaɓasa ayi a
tashi lafiya karya kunyatata ga ƙawayenta. “My Soulmate bara na ɗanyi using toilet
Please”.
Ɗagowa yay ya ɗan dubeta dan harya sake maida kansa ga aikin gabansa. “Yanzu a
barowanki gida har sai kinzo wani waje kin shiga toilet?”.
Murmushi tayi daya sake ƙawata ƙyawun fuskarta. “Oh My Soulmate nan ɗin
aiba wani waje bane na daban, shine fa gidana nanda kwanaki kaɗan zan dawo rayuwar
cikinsa. Bawani abu zanyiba part zan canja dan bana iya wuce awa ɗaya da shi a
jikina”.
Idanunsa ya ɗauke daga kallonta, haka kawai yaji wani iri a ransa ganin babu
ko ƴar kunya tattare da ita take faɗin part zata canja. Da hannu ya nuna mata
toilet na falon.
“Ah-ah my Soulmate bara dai na shiga bedroom mana. Nan kuma idan cikin
su Mommy wani ya shigo fa”. Komai baice mata ba, harta nufi hanyar bedroom ɗin Anam
dake barci a ciki ta faɗo masa. Dakatar da ita yayi. “No ki shiga wannan ɗin can
ƙofan nada matsala ne, sai angyarasa a rufe yake”.
“Okay! To bara naje naga bedroom ɗin namu ko?”. A ɗan kausashe yace, “Shi nake
nufi”. Ɗan jimm tai tana kallonsa. Sai kuma tayi murmushi cikin rausaya kai ta nufi
na falon kawai. Shima aikinsa ya cigaba dayi, a zuciyarsa yana ALLAH-ALLAH su
kammala su tattara subar gidan.
Addu'arsa kam ta karbu, dan koda ta fito bata zauna ba kasancewar ƙanwar
abbanta nata faman kiranta a waya akan ta fito zasu wuce.. Tare da shi suka fita,
yaji daɗi sosai da su Mommy sukace suma zasu wuce ne magrib na gabatowa.

Bayan duk wucewarsu ya dawo ciki, kai tsaye bedroom ɗinsa ya nufa, key ɗin
daya cire yasa ya buɗe babu zato ko tunanin ta tashi a ransa.... Kusan a tare
ƙofofin guda biyu suka buɗe. Shi yana shigowa ita tana fitowa daga bathroom. Wata
irin ƙara ta fasa da ƙanƙame guntun towel ɗin data ɗauro a jikinta dake ɗigar ruwa
tareda faɗawa saman gado ta cukuykuye zanin gado da duvet ɗin gaba ɗaya a
jikinta....
“you are vary stupid!!”.
Ya daka mata tsawa jin tana barazanar fasa masa dodon kunne.
“Na shiga uku ni dai ka fita, dan ALLAH ka fita, Yaya wlhy babu ƙyau ganin
tsiraicin wani. Wayyo ALLAH Mamie banji maganarkiba nashiga halaka.......
“Shut up! Stupid!”.
Ya sake faɗa da matuƙar takaicinta. Bedsheet ɗin ta tusa cikin baki tana gyaɗa masa
kai ga hawaye na faman mata gudu a fuska kai kace wani abu yace zai mata. Shiko
gaba ɗaya idanunsa sun birkice dan takaici, ya ƙarasa takowa gaban gadon yana watsa
mata mugun kallo. “Ubanwa ya saki yin wanka anan ɗin? Ko an faɗa miki nan gidan
wanka ne?”. Kanta take girgiza masa tana ƙara maƙurewa waje guda, dan ita a yanzu
ba faɗan nasa take tsoro ba a yanda ya ganta da a yanda take. “Dan ALLAH kayi
haƙuri Yaya. ALLAH zafine ya dameni kamar fatana zai ɗaye zufa ya jiƙani ina
ƙyanƙyami shiyyasa nayi”. Rasama mizai ce mata yay, ga jikinta sai rawa yake
matuƙa. Tsaki yaja ya juya ya fita kawai. “Mintuna biyar na baki”. Ya faɗa dai-dai
yana jan ƙofar har saida ta zabura saboda bugata da yay.
Kanta ta cusa tsakanin ƙafafunta ta ta sake sakin wani kukan na baƙin cikin
ya ganar mata jiki abinda wani mahaluki bai taɓayiba bayan Aunty Mimi da Mamie. Duk
da bawai tsirara ya ganta ba a ganinta ƙanƙantar towel ɗin baida maraba da hakan
ita kam. Tuna abinda ya faɗa na karshe da yay yasata zabura. Durowa tai a gadon ta
nufi ƙofar ta saka sakata, da sauri ta kwashi kayanta duk da ɗunbin ƙyanƙyamin da
take musu ta shiga maidawa a jikinta da sauri-sauri. Bata kammala ɗaure igiyar
abayar jikinta ba ta fito. A falo ta samesa tsaye sai faman kai da kawo yake tamkar
mai safa da marwa. Tai ƙasa da kai dan a yanzu kam babu abinda take gudu kamar su
haɗa ido, wani irin matsanancin kunyarsa takeji har ƙarƙashin zuciyarta. Shima bai
dubi inda takenba ya nufi bedroom ɗin nasa, bai koyi mintuna biyu ba ya fito da
kayansa da sukazo gidan suna jikinsa. Magungunanta da lap-top ɗinsa ya ɗauka yay
waje. Da sauri tabi bayansa dan dama kamar jira take ace ar ta kwasa ana kare.
A motar ma hankalinta ta maida gaba ɗaya waje badan tana fahimtar abinda
take kallo ba, sai dan bata buƙatar koda kallonsa. Shima ɗin dai aikin tuƙinsa yake
kawai lokaci-lokaci yakan amsa waya har suka iso gida. Yana gama parking ta fice.
“Waye zai biki da wannan?!”. Baya ta dawo kanta a ƙasa ta ɗauka ledar magungunanta
daya ɗaura saman mota ta wuce har tana harɗewa saboda yanda take tafiya da
sassarfa.

★★★★

Shirye-shiryen biki ya ƙara kankama, yayinda Anam ke faman wasan ɓuya da


Shareff. Sam ta daina yarda su fita aiki tare, kafin ya fito ta shirya tabi bus ɗin
su Fawwaz da ake kaisu school. Data tashi aiki kuma zata saka wani abokan aikinta
ya tare mata Napep ta dawo gida. Bata yarda dai ta faɗama kowa abinda ya faru ba,
sai dai tun ranar har yanzu bata sake ganin Yaseer ba. Ya daina shigowa aiki ta
daina samun number ɗinsa kuma. Ta tambaya iya wanda suke mu'amula a wajen aikin
nasu duk sun sanar mata suma basu san miya hanashi zuwa aiki ba. Amma dai ance ya
kawo reason nashi wajen oga. Haƙura tai tabar bin kowa, sai ma haushinsa ya kamata.
A yanda suke tana ganin ya dace ace ya sanar mata idan zaiyi tafiyane kokuma wani
abu ya samesa ai.
Ranar laraba gidan aka tashi da shirin isowar su Abie. Wannan ne ya ɗauke
mata dukkan hankali ta manta da batun Yaseer. Taso ace da ita za'aje tarbo iyayenta
airport sai dai batasan waye zaije ɗakkosu ba, dan haka ta haƙura kawai tai zaman
jiransu a gida. Aiko ƙarfe huɗu da rabi na yammaci sai ga Shareff da Dr Jamal
abokinsa ɗauke dasu a motocinsu ashe sune sukaje tarbosu. Cikin ƙanƙanin lokaci
gida ya hautsine da murna dan harda aunty Mimi da yaranta itama. Duk da an share
musu nasu gida an gyara komai tsaf anan suka fara sauka. Anam ta rungume iyayenta
harda kukan daɗi su Mubarak na mata dariyar ta girma batasan ta girma ba. Duk
wannan kaikawo da ihun yara da hayaniya Mommy da Gwaggo ko leƙe basu leƙo ba duk da
kuwa sun san su Mamie sunzo ne domin bikin ɗansu. Hasalima duk wani ɗawainiyar biki
Abie da Mami suka ɗauka. Acewarsu Shareff ɗansu ne, sune suka cancanci yimasa aure
ba kowa ba. Hatta lefe da duk abinda aka kai gidansu Fadwa sai da Abie ya dawowa
Daddy da Abba abunsu. Mommy taita masifa amma Daddy ya taka mata burki tun wancan
lokacin dan a sanda Abie ya rako Anam ne. Sai da sukaci suka sha sannan suka shiga
suka gaida Gwaggo. Mommy kuwa basu nuna sun san da zamanta a gidan ba Gwaggon ma
dan uwa ce shiyyasa suka bata girmanta. Ai tuni Anam tabi su Mamie can gidan, dan
taci alwashin bazatai zaman gidan nan ba dan bata ra'ayin ayi bikin nan da ita, duk
da kuwa katanga ɗayace tasan wasuma zasu shigo gidansu a ƴan bikin, amma dai ko
yayane bazai kai nan gidan ba ai. Sai dai kuma batasan tayi gudun gara bane ta faɗa
gidan zago😚.

★★★

Acan gidan su amarya Fadwa kam wannan rana itace ranar ƙunshi, suna can ita da
taren ƙawayenta wayayyu da gayyar media an ware musu part guda sunata shagalinsu
harda su shisha. Ga hotunan amarya sun baje media musamman tiktok da istagram da
amaryar ta tara ɗunbin followers da suka sakata yin ƙaurin suna cikin jerin
celebrities da akeji dasu. Amarya tasha ƙyau da gyara harta gaji, sai dai ba'ai
mata nata ƙunshin bama sai gobe idan ALLAH ya kaimu alhamis.

★★★

Bayan sallar isha'i Mom ta aiko kiran Anam data maƙale taƙi bin su Aysha can
gidan yin ƙunshi. Amma hatta da Amrah ɗiyar Aunty Mimi dake kusan sa'anni dasu Anam
ɗin tana can itama za'ai mata. Cewa tai bataso itakam, dan ko wankin kai da sukaje
yau ita ƙin zuwa tayi. Sai da Mamie tamata jan ido ta biyo ƴar aikin Mom. Amma da
ta langaɓe wai kanta ke ciwo. Koda tazo anan ɗin ma faɗa Mom tai mata akan batun
ƙunshin. Amma saita hau hawaye wai ita bata da lafiya. Kowa kallonta kawai yake da
mamaki a falon, dan kuwa dai ko awanni huɗu bata cikaba da gama murnar isowar su
Mamie ai. Ganin yanda take kuka Mom tace mata taje ta kwanta ayi mata gobe idan
ALLAH ya kaimu. Ai kafinma ta rufe baki tayo waje. Maimakon taje ta kwanta ɗin can
ta samu inda babu wadataccen haske ta zauna taci kukanta da batasan daliliba itama
sannan ta koma gidansu tai kwanciyarta.
Washe gari wajen sha biyu yaran gidan kowa da ƙunshi abin sha'awa amma banda
Anam dako wanke kai bataiba balle maganar kitso. Tana gani suka shirya suka fita
hausa day itako tace bazataje ba. Sai faman baƙin rai takeyi na babu gaira babu
sabar. Mamie dai tunda taimata tambaya ɗaya tace bakomai bata sakebi takanta ba.
Sai aunty Mimi ce ke faman lallaɓata da lallashinta. Sai tace kawai ita bata da
lafiya ne.
A wannan lokacin Shareff dake gidan batare da Anam ta sani ba ya shigo.
Gabantane yay masifar faɗuwa. Ta miƙe zaram da nufin guduwa aunty Mimi ta dakatar
da ita cewar ta kawo masa breakfast ɗinsa dake kitchen wanda Mamie dakanta da girka
abinta kuma irin abincin ƙasar Malaysia ne. Jitai kamar ta fashe da kuka dan
takaici, koda ta kawo ta ajiye masa ƙoƙarin juya tai zata bar wajen ya watsa mata
mugun kallo saboda ido da suka haɗa by mistake. Baki ta murguɗa masa itama ta haura
sama da gudu.
“Kai kaji shasha lafiyarki kuwa Mamana?”. Aunty Mimi da bata lura da abinda
ya faru ba ta faɗa da mamaki tana kallon hanyar da Anam ɗin tabi. “Babana wai kaga
mi yarinyarnan tayi kuwa? Sai kace mai tsoron wani anan?”. Murmushi kawai yay baice
komaiba. Ta hararesa. “Kaifa tsiyarka kenan ai magana ka bama mutum amsa da
murmushi”.
“Oh ALLAH small Mom rigima. Ni yanzu mikike so nace anan kuma? Ina ruwana da
shirmenta”.
Hararsa ta ƙarayi ta ɗauke kai. Yay dariya da shafa kansa yana buɗe
kwanikan. Ƙamshin ya sashi lumshe ido murmushinsa na ƙara faɗaɗa. “Lallai na shaida
Mamie na kusa dani”.
Dariya aunty Mimi ta sanya masa da faɗin, “Makwaɗaicin banza”. Dariyar yayi
shima da faɗin “Naji ɗin”. Haka ya fara cin abincin cike da nishaɗi suna hirarsu
har Mamie ma ta fito daga sashen Abie ta samesu. Zama tai itama suka ɗora, daka
gansu kasan akwai shaƙuwa mai faɗi a tsakaninsa tun ba yanzu ba. Anam na jiyo
dariyarsu daga sama taƙi sakkowa har saida ya wuce massalaci sallar azhur. Aunty
Mimi kuma ta fita zuwa can cikin gida ita da Mamie.
Ta idar da salla tana shirin sakkowa ƙasa ta samu abinda zataci suka kusa cin
karo da Fawwaz.
“A'a autan Mom daga ina haka da gudu?”.
“Yaya ne yace na kiraki”.
Kafin tace da shi wane yaya ya kwasa da gudu ya fice. Ta girgiza kai tana murmushi.
Ɗaki ta koma ta ɗauka abaya kasancewar kayan jikinta wando da rigane marasa nauyi.
Duk zatonta Khaleel yake nufi, shiyyasa ta fito hankalinta kwance. Harta nufi gate
ɗin shiga cikin gida motar dake fake a tsakanin gidansu da cikin gida tai mata
horn. Kamar bazata juyaba sai kuma ta dubi motar ganin an sakeyi alamar da ita ake,
tunanin ko Yah Khaleel ɗin ne a ciki ya sata nufar can duk da tasan ba motarsa
bace, bama tasan motar ba dan kamar ma sabuwa.
“Tofa, wai su Yah Khaleel sabuwar mota akayine halan?”. Tai maganar fuskarta
ɗauke da murmushi tana shafa motar har side ɗin mazaunin driver. Kanta tsaye ta
buɗe murfin. Duk abinda take dama idonsa a kanta, kuma yana jinta dan ya ɗanyi ƙasa
da glass kaɗan. Da sauri ta saki murfin tana ambaton ALLAH tamkar wadda taga wani
shaiɗan ko aljani. Ɗaga kafa tai da nufin juyawa ya dakatar da ita.
“Idan kika bar wajen nan sai na mareki”.
Tsayawar tayi, sai dai taƙi ta juyo. Hasali ma auna yanda zata arta da gudu
takeyi.....
“Zagaya ki shiga”
Ta tsinkayi muryarsa a dake. Shiɗin ba abun wasanta bane, musamman a yanda yay
maganar babu alamar wasa a cikinta. Ta haɗiye ƙwallar da suka taru mata a ido cikin
cije lip tabi umarninsa. Sanyin ac da kamshi na musamman suka ratsata a cikin
sabuwar motar da ko leda ba'a cirema kujerunta ba. Ɓoyayyar ajiyar zuciya ta sauke
da lafewa cikin kujerar ranta fal tunanin ina zai kaita? Bata da mai bata amsa dan
haka taja bakinta ta tsuke ta zubama sarautar UBANGIJI idanu..........✍

_🤣Tofa, su Shareffudden ango ko'an fara kidnapping ne bamu sani ba😣, to magana ta
gaskiya ƴan team ɗinsa ku faɗa mana gaskiya mu fara rigakafin killace kammu kar'a
sakamu a ruɗani😂😆?._

_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_


*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:


07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇


0913484810_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_


*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:


07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇


09134848107 ko

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*


[10/26, 7:15 PM] My Zafafa: *_Typing📲_*
*_BABU SO....!!_*
_(Miya kawo kishi?)_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_13_*

..........Gab da magrib aka kawo amarya Fadwa, kamar yanda Daddy ya bada umarni nan
gidan aka kawota wajen Mamie. Hakan ba ƙaramin zafar Mommy da su Gwaggo Halima da
aka kira aka sanarwa abun yayi ba. Gwaggo kuwa kasa shiru tai sai da ta tanka,
Daddyn yace ya gama yanke hukunci, miye ma abin magana bayan gobe idan ALLAH ya
kaimu za'a maidata gidanta. Badan rigimar ta kwantaba akai daiyi shiru kowa yaje ya
fara shirin tafiya dinner.
Bayan sallar isha'i aka fara kwasar mutane inda za'a gudanar da dinner, sai
dai har aka gama kwashe kowa babu Anam babu alamarta. Hasalima tuni taje tai
kwanciyarta a falon Abie batare da kowa ya sani ba. Wajen dinner ya ƙayatar matuƙa.
Amarya da ango sunyi ƙyau har sun gaji. Anci ansha ƙawayen amarya sun sami yanda
sukeso suda amarya wajen daukar hotuna da videos wasu har live suke ɗauka ana kaiwa
tiktok. Nera tayi kuka kamar yanda aka zubar da mutunci galan-galan dan anci rawa
casss da warrr ƙawayen amarya ta rashin mutunci, amaryar kanta ta cashe kamar babu
gobe, sai dai rashin yin rawar ango ta jawo cece kuce sosai dan wasu na ganin
amarya Fadwa ta zaƙe da yawa. (Komadai miye ni ina ganin ranar farin cikin tace a
barta ta shana😜). Ƙarfe sha biyu taro ya tashi lafiya aka kwaso jama'a aka dawo
gida.

WASHE GARI aka gudanar da walima tare da yinin biki anan gidan, yini guda babu
wanda zaice yaga Anam sai Mamie kawai da aunty Mimi, dan tana falon Abie kwance
babu lafiya zazzaɓi ta kwana da shi har sai da doctor yazo ya dubata da safe ma,
dan haka yau ko kwalliyar bikin ma batai ba abinta. Lokacin da taji sallamar
Shareff zai shigo falon wajen Abie tashi tai ta gudu bedroom ɗin Abie ɗin, tanaji
yana faɗama Abie baida kafiya shima da ciwon kai ya kwana kuma har yinin yau ɗin
bai sakesa ba yana ganin hayaniyar nan ce. Baki ta taɓe cikin rashin damuwa tai
kwanciyarta har sai da taji ya fita. Har dare bata sauka ƙasa ba dan bata buƙatar
ganin Fadwa har tabar gidan. Hakan kuwa akayi, dan washeri lahadi akai buɗan kai
bayan sallar azhar. Anayin la'asar aka ɗunguma raka amarya Fadwa gidanta, yayinda a
bangaren ango yaketa ƙoƙarin sallamar abokansa na nesa da zasu wuce gida yau.
Hakama baƙin nan gidan wasu daga rakkiyar amarya bazasu dawo nan ɗin ba...
Gidan amarya kam sai sambarka. Komai yaji zam masha ALLAH. Har kusan bayan
magrib sannan mutane suka gama watsewa aka barta ita da ƙawayenta kawai dake jiran
abokan ango.....

★★

“Wai nikam wane irin ango ne kai Al-Mustapha? A irin wannan ranar irinka ɗoki da
zumuɗi baya barinsu amma kai tun ɗazun sai fama ake da kai ka shirya a rakaka
kanata jamana aji”.
Duk da sarai abinda Dr Jamil ɗin ke faɗa yana shiga kunnensa tunda a kusa
da shi yake amma babu alamar zai motsa. Sai cigaba da danne-dannen tab ɗinsa yake
hankali kwance. Fharhan dake faman musu dariya ya miƙe ya fige tab ɗin. Ɗagowa yay
yana harararsa da miƙa hannu, Isma'il ya amshe tab ɗin daga hanun Fharhan shima
yana dariya. “ALLAH baza'a baka ba. Garama ka tashi kaje ka shirya mu miƙaka muma
muje musa haƙarƙarinmu a katifa matanmu na jiranmu.”
Isma'il ɗin ya kafe da idanu kamar zaiyi magana sai kuma ya girgiza kai
kawai. Dr jamil ya dafa shi, “Wai nikam Musty ko tsoron amaryar kake ne? Idan akwai
matsala inada kayan gyara masu inganci wlhy da zaka baje kolinka babu ragi babu
ragowa”.
Naushi ya kaima Dr Jamil, da sauri ya duƙe yana dariya su Fharhan na tayasu.
Hararsu yay da miƙewa ya shige bedroom.

Jin gidan ya rage hayaniya sosai ta sakko downstairs. Su Mamie ne kawai


zaune da ƙannenta, gaishesu tai kowa na tambayarta ya ƙarfin jikinta. Tace da sauƙi
tana zama gefen Mamie ta kwantar da kanta a kafaɗarta. Ko mintuna uku batai da zama
ba suka shigo da sallama. Shine a gaba cikin ɗanyar shadda milk color sai ƙyalli
take harda hula a kansa. Sai su Fharhan biye da shi. Jitai kusan su dukansu
idanunsu akanta suke kamar ta tashi ta arta da gudu, sai dai ta dake dan bata fatan
sake tafka abin kunyar datai a ranar ɗaurin aure😝.
Sai da suka gama gaisawa da su Mamie Dr Jamil dake jin kamar ya haɗiyeta
fuska ɗauke da murmushi yace, “A'a Anam banda ke a kai amaryar kenan?”.
Kanta ta jinjina masa tana ɗan murmushi batare data kallesu ba. “Banda lafiya
ne shiyyasa”. Ta faɗa a hankaki tana ƙara sinne kanta jikin Mamie.
“Ayya ai ban sani ba dana kawo ɗauki. Yaya jikin yanzun?”.
“Na samu sauƙi”. Ta faɗa a taƙaice tana ɗan ɗagowa. Cikin idonsa natan suka
shige, tai saurin janyewa ƙirjinta na bugawa da ƙarfi....
“My son kuje kar dare yayi an bar ɗiyata ita kaɗai, ALLAH yay muku albarka,
ya bada zaman lafiya na har abada. Ayi haƙuri ayi haƙuri ayi haƙuri. Mu mata a duk
inda muke haƙuri ake damu akan komai dan halittane masu wahalar sha'ani. Banda
yanke hukunci cikin fushi, duk abinda aka gani ba dai-dai ba abu asannu a ruwan
sanyi a kawo maslaha a cikinsa. Ayi ƙokurin sauke duk hakkin da ALLAH yace duk da
bani da damuwa a kanka game da wannan. ALLAH ya azurtaku da zuri'a masu albarka”.
Gaba ɗaya suka amsa da Amin. Anam dai ma ta maida hankalinta ga wayarta kamar
bata jinsu. Ƴan uwan Mamie ma sun masa tasu nasihar suka sallamesu dan dare na
ƙarayi. Dai-dai yana mikewa suka ƙara haɗa ido da Anam data ɗago itama. Wani
kasalallen kallo suka sakarma juna. Ta kauda kanta tana taɓe baki zuciyarta na mata
zafi. Shima iska ya ɗan furzar yana janye nasa a wani yanayi. Bata sake yarda ta
ɗago ba har suka fice Dr Jamal na faɗa mata sai yazo dubiya ta musamman. Bata
tankasa ba, sai Aunty Nasara dake kamar ƙanwar Mamie ta bashi amsa cikin dariya.
Tsam ta mike tabar falon dan ji take wani ɗan zazzaɓi ma na neman rufeta, ta
nufi ɗakinta da fatan su Aysha su kwana a cikin gida yau bata bukatar su anan......

*_MONDAY MORNING_*

Tana tsaka da barcinta na safe mai daɗi kasancewar bata samu yin na dare
ba sosai saboda zazzaɓi mai zafi data sake kwana da shi aunty Mimi ta tasheta akan
ta tashi ta shirya za'a aiketa.
“Wayyo aunty ina su Aysha ki aika a kira miki su suna cikin gida fa ALLAH
bana jin daɗi”.
Hararta Aunty Mimi tayi. “Ai nasan dasu Ayshan na tasheki. Maza tashi kina
ɓatamin lokaci. Da ƙyar ta miƙe ta shiga bayi kamar zatai kuka. Wanka tai da ruwa
mai ɗumi dan duk son sanyinta kuma bata wanka da ruwan sanyi. Gudun masifar aunty
Mimi ya sata shiryawa a ɗan gurguje cikin shigar da tafi so a ko yaushe wando da
riga ta ɗaura abaya pink a sama ta naɗa veil ɗin abayar. Tayi ƙyau sosai sai zuba
kamshi take duk da bawani kwalliya tai mai yawa ba. A falon ƙasa ta sameta har su
Mamie wanda suka makara nata breakfast. Gaishe dasu tai tana karasawa inda Aunty
Mimi take.
“Yauwa ɗiyar albarka. Ai jeki kawai waje ga Ikram can na jiranki a mota da
driver ”.
“To aunty saƙon fa?”.
“Yana wajensu a motar”.
Kai kawai ta jinjina taima su Mamie sallama ta fita. Baya ta buɗe ta shiga yayinda
Ikram ke gaba tanata zubama driver surutu da hausanta da bata iyaba wai ita a dole
koyan hausa takeyi. Itace autar aunty Mimi shekararta goma sha uku, kasancewarta
girman turai sai take abu kamar wata yarinya ƙarama ga tabara ta autoci.
“Good morning aunty Anam”.
Ta faɗa lokacin da Anam ke ƙoƙarin rufe murfi. “Morning dear how are you?”.
“Am fine, sai ƙafana dake ciwo saboda rawan da mukai a wajen dinner ranar”.
“Good for you”.
“Kai aunty maimakon kimin sorry”.
“Tunda ni na aike ki”.
Dariya Ikram tayi. Sai kuma ta shiga bata labarin yanda shagalin dinner ya kasance.
Shiru Anam tai mata, da taga zata isheta sai ta buɗe bag ta ɗakko bluetooth ta saka
waƙa har suka iso gidan da bazata taɓa iya mantawa ba. Kasa motsi tai balle magana
har driver yay horn maigadi ya buɗe masa gate suka shige. Jitai kanta na juyawa, ta
dafesa tana ambaton sunan ALLAH. Da tasan nan aunty Mimi zata aikosu da duk ma
yanda zatai taƙi zuwa ALLAH da sai tayi. Yanzu kuma tana ƙin shiga wannan akku
sarkin zancen zataje ta bazata a fassarata a mai baƙin ciki. Siririn tsaki taja da
buɗe motar a fusace ta fita dan Ikram tuni ta fice har driver ya buɗe mata booth
suna fidda kayan breakfast da sukazo da shi. Ƙin daukar komai tai sai driver da
ikram ɗinne suka kwasa.
Daga can baya ta tsaya Ikram ta shiga yin knocking tana kiran sunan Yaya
Shareff. Sun kai kusan mintuna goma sha sannan aka buɗe har ta gama yanke shawarar
juyawa ta koma. Shine ya buɗe ƙofar Ikram ta riƙo hanunsa cike da shagwaɓa. (Wayyo
Yaya ƙafafuna har zafi suke da hannuna”.
Kanta ya dafa da rufe idonsa daya nuna alamar a barci ya tashi yana buɗewa.
Ya matsa mata alamar ta shigo yana maida dubansa ga Anam datai tsaye tana kallon
wani waje daban. Kusan minti ɗaya yana kallonta ko ƙyaftawa babu sannan yay magana.
“Tsaiwar ta miye?”.
Baki ta taɓe tana ƙara tsuke fuska. Batare da tace komai ba ta nufosa. Harta
ƙaraso idonsa na kanta yanzu ma. Ya ɗan matsa mata alamar ta shiga itama. Ɗagowa
tai suka haɗa ido, tai saurin janyewa da raɓashi ta shige tana murguɗa baki. Shine
ya shiga da kayan cikin falon da kansa, Ikram sai faman yaba falon take dan babu
ƙarya naira tayi kuka. Itako tana tsaye tamaƙi zama, ta dai jingina da bango tana
daƙilar wayarta.
“Ina kwana”.
Ta faɗa batare data yarda ta kallesa ba. Bai amsata ba, sai hankalinsa daya maida
ga Ikram da bakinta yaƙi shiru. Haushi ya ƙara kume zuciyarta, gashi ta fara gajiya
da tsaiwar, amma sai ta cigaba da daurewa. Kusan mintuna biyar yana biyema shirmen
Ikram tamkar ma ya manta da ita a falon. Ƙaton agogon dake bangon falon ya duba,
tare da dawo da kallonsa gareta.
“Bani plate a kitchen”.
Kallonsa tai da mamaki, sai kuma ta sake ɓata fuska. “Ni ban san kitchen ɗin
ba”. Da hannu ya nuna mata ya ɗauke kansa. Kitchen ɗin ta nufa wani haushi na ƙara
turniketa, cikin taɓe baki take bin ko'ina na kitchen ɗin da kallo. Tabbas yayi
ƙyau, sai dai hakan ba yana nufin wani abu na cikinsa ya burgeta ba. Abinda ya
aikota ta nufa ta ɗauka, sai dai ta nufi sink dan ta ɗauraye, sai ƙunƙuni takeyi da
bazaka iya sanin mitake faɗa ba. Juyowa tai tana jan tsaki, da sauri taja baya har
plate ɗin na neman suɓuce mata. Duk ta daburce dan sam bata san ya biyo bayanta ba,
ga idanunsa masu kaifi daya kafeta da su. A hankali ya tako gabanta duk hannayensa
cikin aljihun jallabiyar jikinsa, ya tsaya dab da ita har tana iya jin hucin
numfashinsa. Sai taji gaba ɗaya kwarjininsa ya cika wajen har bata shaƙar numfashi
a wadace...
“Ya jikin ki?”.
Yay maganar cikin taushin muryar da bata taɓa ji daga garesa ba. Kasa jurewa tai
sai da ta ɗago ta kallesa. Har yanzu idanunsa a kanta suke, tai saurin janye nata
tana girgiza kanta. Muryarta da ɗan rawa tace, “Alhamdulillahi”.
“Kin tabbatar?”.
“Nifa zazzaɓi ne dama kawai Yaya MM”.
Jin baice komaiba ta ɗago ta dubesa, still dai har yanzu idonsa a kanta. (Ya
ALLAH! lafiyarsa kuwa?) ta ayyana a ranta tana ƙoƙarin son barin wajen. Amma sai
furucinsa ya sakata dakatawa babu shiri.
“I'm sorry”.
Kasa yarda tayi daga bakinsa furucin ya fito, musamman da babu alamar shi ɗin
ya faɗa a yanayinsa. Sannan bata san dalilinsa na faɗarba. Kamar ya fahimci ƙarin
bayani take buƙata sai ya bar wajen cike da basarwa. “Zoki dafamin lipton”. Shiru
bata motsa ba, da alama bata tare da tunaninta ma. Ya juyo ya dubeta fuska a tsuke.
“Badake nake magana ba!”. Itama fuska ta haɗe, sai dai cikin sanyin murya tace,
“Yaya matarka fa?”. Ido ya tsura mata na wasu sakanni, sai kuma ya janye. “Nasan
da ita ai na sakaki. Sannan ganin amarya a kicin irin wannan ranar kema kin san
bamai yuwuwa bane”.
Da hausa yay maganar, dan haka ba komai ta fahimta da ƙyau ba. Amma sunan
amarya kawai daya shigo ciki ya saka yanayinta ƙara canjawa. Sai dai bata sake cewa
komai ba, ta ɗauka tunkuyar daya fiddo mata domin dafa shayin ta ɗauraye, ruwa ta
zuba dai-dai shan mutum ɗaya, tana ƙoƙarin rufewa taji tsaiwarsa a bayanta, kafin
tayi wani yunƙuri ya janye hanunta da sake buɗe murfin ya buɗe fanfo ya ƙara ruwan.
“Nadai bazan dafama wata ƙatuwa shayi tana kwance tana barci ba”.
Karon farko ya saki murmushi, sai dai komai baice ba ya rufe mata tukunyar. Zata
sake magana ya dakatar da ita. “Zakimin abinda na saki ko tsiwa? Trouble maker!”.
“Ga babbar Trouble maker can ka bari a ɗaki”. Tai maganar ƙasa-ƙasa yanda
bazaiji ba. Da kansa ya kunna mata gas ɗin, ta ɗaura tukunyar sannan ta ɗiba kayan
ƙamshi da lipton da duk ya fiddo da kansa ta zuba. Flask daya fiddo a kwali shima
ta ɗauka ta ɗauraye tare da kofi duk yana tsaye yana kallonta. Baiyi mamakin yanda
take komai a tsaftace da kuma tsari ba, dan sai dai ya bama wani labarin Mamie
badai a bashi ba, yasan kuma hakan duk tarbiyyar data samune daga gareta. Yana
kitchen ɗin harta kammala komai, ya sake ɗaukar kofuna uku ya ɗauraye da kansa ya
haɗa da wanda ta wanke. Bata tanka masa ba, ta ɗauka flask ɗin kawai ta fita. Shine
ya ɗauka sauran kayan ya fito da su, samunta yay tanama Ikram masifa akan ta tashi
su wuce gida, ashe da wayarsa ya haɗata shi ya tafi neman magana kitchen..
“Sai kun karya, tunda tace bakuyi breakfast ba kuka fito”.
Ranƙwashi takaima Ikram ɗin, amma sai ta kauce tana dariya da faɗin, “Wlhy Yaya
ita a barci ma aka tasota gara ni nasha tea”. Wani ranƙwashin zata sake kaimata ya
zuba mata hararar data sata dakatawa, sai dai tayi gefe da kanta tana ƙunƙuni.
“Oya zauna ki haɗamin yunwa nakeji”. Ya faɗa yana ajiye ledar dake ɗauke da
kayan tea da abokansa suka rako shi da su a daren jiya tare da kaza. Batai magana
ba, shima kuma bai sake maganar ba ya nufi ƙofar fita yasa key sannan ya wuce
kitchen. Harara ta dinga zubama Ikram tana haɗa tea ɗin, tsabar mugunta ta zabga
masa sugar. Ikram ta mikama nata tana faɗin, “Makwaɗaiciya kawai, daga zuwa gidan
mutane”.
Ikram tace, “Ni banyi kwaɗayiba tunda gidan Yaya ne”. Fitowarsa ta hanata bama
Ikram ɗin amsa, ya dire babban plate dake ɗauke da kaza sai turiri take alamar
ɗumamata yay. Zata miƙe yace, “Koma ki zauna.” babu wasa a lamarinsa dole tabi
umarni, sai dai idonta harya fara tara ƙwallar takaici. Hanyar corridor ɗin da take
ƙyautata zaton bedrooms ne ya nufa, cikin jin haushin da babu dalili ta raka
bayansa da harara. Wayarta ta ɗauka ta cigaba da daƙila, kusan mintuna uku sai
gashi ya fito, zama yay a ƙasan carpet ɗin shima kamar yanda take zaune. Yace,
“Bani tea”.
Batai magana ba, ta ɗauka flask ta zuba masa ruwan zafin akan kayan tea ɗin
data haɗa a kofin. Sai da ta juya ta tabbatar sugar ɗin ya haɗe sannan ta miƙa
masa. Duk da yaga bata haɗa nata ba sai baice komai ba yaja nasan gabansa da ƙyau,
kaɗan ya ɗiba a cokali yakai baki dan yaji yaya test ɗin. “Ya ALLAH!”. Ya ambata da
sauri. Tasan tsiyar da tai dan haka taƙi ɗagowa. “Kina hankalinki ƙuwa zaki saka
min wannan sugarn?”.
“Toni Yaya nasan yanda kake so ne?”.
Idanu ya zuba mata kawai tsahon wasu sakanni. “Idan ma mugunta ce harda kanki
zaki mawa, ba wadda take cikin gidan kawai ba, dan duk dodo ɗaya zaku yima tsafi”.
Komai bata fahimta a zancensa ba. Wani kofin ya ɗauka ya raba shayin biyu, ya ƙara
kayan tea ɗin banda sugar ya sake zuba ruwan zafi. Ikram dake ta faman latsa waya
tana shan nata tea ɗin yace ta sakko.
Duk yanda Anam ta so nuna ta ƙoshi bai saurareta ba. Haka ya tilasta mata
karyawa tare da shi da breakfast ɗin da suka kawo da kazar daya ɗumama. Sai dai ita
taƙi cin kazar ko sau ɗaya. Ikram kam komai sai da taji yakai mata sannan tai
hamdala. Tayi niyyar suna gamawa su wuce, amma sai taga babu dacewar barin
kwanikan, ita ta kwashe komai zuwa kitchen, ta ɗauraye kwanikan da suka ɓata. Koda
ta fito bata samesa a falon ba, tacema Ikram ta tashi su wuce gida.
“Lah aunty Anam Yaya yace mu jirashi zai fito muje tare”.
Harara ta zuba mata, “Shi kuma driver daya kawomu fa yake zaman jiranmu?”.
Fitowarsa ta hana Ikram bada amsa. babu abinda ya canja a jikinsa sai key ɗin
mota daya ɗakko, ta ɗauke kanta gefe harya ƙaraso ya amsa wayarsa a hanun Ikram.
Suna gaba tana binsu a baya har wajen mota, bataga driver ba, ba kuma ta tambaya
ba. Ganin Ikram ta shige baya itama tai yunƙurin shiga....
“Waye driver ɗinku?”.
Fuska ta tsuke tana hararar Ikram kamar itace tai maganar. “Malama koma gaba”.
“Ni dai aunty ki barni anan nafi son baya cikina ya cika da yawa zan kwanta”.
A fusace ta ƙara yunƙirin yin magana ya dakatar da ita. “Bana son shirme fa kina
ɓatamin lokaci nabar matata tana barci kowane lokaci zata iya tashi, ganina kusa da
itane kuma abinda tafi buƙata a yanzun”.
Tamkar saukar aradu haka furucinsa ya daki ƙirjin Anam saboda da yaren malay
yay maganar yanda zata jisa ta fahimta da ƙyau. Idanunta ta rumtse ta buɗe motar ta
shiga batare datace masa komai ba. Shima bai sake cewarba ya harbar motar zuwa waje
dan maigadi dama ya wangale masa gate tuni........✍

*_🚶🏻🤕😣askiya kuyima ƴar mitsilarnan taku kashedi ta fita sabargar angonmu.😚_*

_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_


*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:


07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇


0913484810_ZAFAFA BIYAR_
*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_


*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:


07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇


09134848107 ko

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*


[10/26, 7:15 PM] My Zafafa: *_Typing📲_*

*_BABU SO....!!_*
_(Miya kawo kishi?)_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_14_*

..........Ko parking bai gamayi ba da ƙyau a ƙofar gida ta buɗe motar ta fice. Ya
bita da kallo harta shige gida. Ƴar ƙaramar ajiyar zuciya ya saki tare da murmushi.
Ikram ta fito tana masa bye-bye. Hanun shima ya ɗaga mata har lokacin da murmushin
a fuskarsa. Motarsa ya tada tare dayin reverse yabar anguwar dan baizo da niyyar
shiga ko'ina ba tunda ko wanka baiyiba. Ga Fadwa dake buƙatar taimakonsa ya baro
tana barcin gajiyar daya tara mata a daren jiya wadda shi kansa barcin bawai ya
ishesa bane ba, kawai dai sawun giwa ne ya take na raƙumi.

Anam batai magana da kowa ba ta haye sama, tasan ɗakinta zai yuwu su Amrah
na ciki yanzu, na Mamie ma tana jiyo maganar mutane a ciki. Dan haka tai wucewarta
falon Abie. Nan kam kowa bata samuba, hakan ya bata damar kwanciyarta ta saki kuka
mara sauti. Kuka tayi sosai bana wasa ba har barci ɓarawo yay awan gaba da ita
batare data sani ba. Wajen sha biyu Abie daya shigo ya ganta ya shiga taɓa goshinta
da tunanin ko zazzaɓin nata ne ya dawo. Amma sai yaji babu zafi jikinta. Idanu ta
buɗe da suka maita nauyi dan kukan data sha. Ta dubi Abie ɗin dake mata murmushi.
“Sleeping beauty na ta tashi”.
Murmushi tai da tashi zaune. “My Abie good morning”. Ta faɗa a marairaice.
“Morning Darling duk gajiyar bikince ta saki zuwa nan ɓuyan barci?”. Fuska ta ɗan
ɓata. “Abie su Amrah basa barina nai barci mai ƙyau dan surutunsu. Gashi ƙasa nake
kwana dan bana son kwana da kowa ɗakin ma ya mana kaɗan”.
Murmushi kawai yay da shafa kanta. Sai kuma ya dubi idanunta da suka sake
fitowa da ƙyau. “Mamana idanun nan kamar anyi kuka da su?”. Da sauri ta girgiza
masa kanta. “Abie rashin barcine fa”. Bai gamsu ba. Sai dai baice komai ba. Itama
mikewa tai da faɗin, “Bara naje nayi wanka”. Tai maganar da zuwa ta kama hanunsa ta
sumbata. Da kallo kawai ya bita, dan yasan tayi hakane dan karya cigaba da
tuhumarta akan kumburin idonta daya tabbatar kukane ya sakasu komawa hakan tunda ba
yau ya santa ba.

Ta fito wanka tana shafa mai Amrah ta shigo ta sanar mata tayi baƙo. Da
mamaki take kallonta sai dai batace komai ba. Amrah ma ta juya ta fita abinta. A
nutse ta ƙarasa shirinta ranta fal tunanin wanene?. Ba ta da mai bata amsa dan haka
ta fesa turare da ɗaukar wayarta ta fito. Tayi ƙyau sosai cikin wando da rigar
jikinta, sai siririn mayafi data yana a kanta. A wajenta wannan shigace normal
saboda a inda ta tashi, sannan rigar bata kama jikinta ba ta kuma sakko har kan
mazaunanta. A falo ta samu su aunty Mimi, har zata zauna Mamie ta harareta. “Bake
naji ance anzo nema ba?”. Cikin ɓata fuska tace, “Ni banyi da kowaba fa zai zo
Mamie”.
Aunty Hamida tai dariya. “To ɗiyata kika sani ko a ƴan biki ne wani yay sau da
baya?. Tashi kije dan da alama mun kusa dawowa wani shagalin insha ALLAHU”.
“Hu'um aunty ALLAH ya kiyaye ni karatu ma zan koma”.
Daƙuwa aunty Hamida tai mata. “Karatun gidan ku, a wannan shekarun naki ai aure
ne ya dace ko dan kina ganinki ƴar ficika da ƙaramin jiki? Maza tashi kije ana ɓata
masa lokaci”.
Badan taso ba ta fito, Mamie na kiranta tazo tasa hijjab bama taji ba dan a
fusace take da taikaicin koma wanene.

Dr Jamal dake daƙilar waya ya ɗago fuskarsa ɗauke da murmushi yana kallonta.
Itako kallo guda tai masa ta kauda idonta. Kujerar dake gefensa ya gyara mata, ta
ƙaraso fuska babu walwala tana masa sallama. Amsawa yay murmushinsa na sake faɗaɗa.
“Barka da fitowa gimbiyar mata”.
“Ina yini”.
Ta faɗa a takaice.
“Lafiya lau. Bismillah ki zauna mana”.
Kamar zatace a'a sai kuma ta zauna.
“Kiyi haƙuri nazo babu izini. Sai dai karki manta dama nace zan zo dubiya”.
Ɗan murmushin yaƙe tayi, a taƙaice tace, “Babu damuwa”.
Idanu ya ɗan kafeta da shi, a ƙasan ransa yana tattaro abinda ya dace ya faɗa.
Ɗagowa tai ta dubesa itama fuska a murtike. Ya kauda nasa idon. Cikin zolaya yace,
“ALLAH ni sai ma naji ina jin tsoronki kamar”.
Haka kawai yanda yay maganar ya bata dariya, ta shiga ƙyalƙyalawa shiko ya
kafeta da idanu yana murmushi. A dai-dai nan aka buɗe gate ɗin gidan mota ta shigo.
Su duka sukabi motar da kallo har lokacin kowanne da dariyar kan fuskarsa. Dr Jamal
ya faɗaɗa tasa ganin Shareff, itako haka kawai sai da gabanta ya ɗan faɗi.
Ya kai kusan mintuna huɗu bai fitoba idonsa kafe a kansu, sai dai shi basa
ganinsa kasancewar tinted glass ne da motar. Murfin motar ya buɗe ya fito da nufin
shigewarsa ya nuna bai gansu ba kawai. Sai dai Dr Jamal daya taso fuska ɗauke da
murmushi ya hana hakan. Fara'ar dole ya ƙaƙaro yana mika masa hannu kamar yanda
shima ya miƙamasa. “Ango! Ango!! Ƙyallinka dabanne”.
“Haka dai kace”.
Shareff ya bashi amsa hankalinsa nakan Anam data ɗauke kai kamar bata gansa ba.
“Haka ɗinne ma abokina. Dan ko kamshinka yau ya sake bunƙasa fiye da kullum.
Muma dai gamu nan fara kafa foundation mukai matsayin nan naku haka nan”.
Gabansa ne ya fadi, amma sai ya dake ya saki gajeren murmushi. “ALLAH yasa
haka to.”
“Insha ALLAH wannan karon da gaske nake abokina”.
Nan ɗin ma murmushin yayi kawai da faɗin, “Bara na shiga na gaida su Mamie”.
“Okay to a fito lafiya”.
Ido suka haɗa da Anam ya wulla mata wani mugun kallo data jima bata gani daga
garesa ba ya wuce. Dr Jamal daba lura yay ba ya dawo ya zauna yana dariya. “Kinga
Yayan nan naki da gaske angwancin nan fa ya amshesa. Kwana daya kacal harya canja
kamar bashi ba”.
Ƙin cewa komai tayi, sai dai tayi ƙaramin murmushi. Shima murmushin yayi
yanaji kamar ya haɗiyeta. Sallamar Amrah ta katsesa daga kallon da yake mata. Duk
suka dubeta. Gaishe da Dr Jamal tai, ya amsa cike da fara'a da tambayarta gajiyar
biki. Tace masa Alhmdllhi tana maida kallonta ga Anam. “Anam Yaya Shareff yace yana
jiranki zai amshi ajiyar daya baki”.
Kallon Amrah take cike da mamaki da rashin fahimta, sai dai ta rasa abin
cewa. Sai Dr jamal dake kallonsu ne ya katse shirun da faɗin, “Inaga jeki kawai ki
basa saƙon sai na jiraki. Dan da muhimmiyar magana nazo”.
Kamar zatace ita babu wani saƙonsa a wajenta sai tai shiru kawai. Ta mike
zuciyarta na mata kaikawo da mamakin Yah Shareff ɗin. Yaushe ma har suka fara shiri
dazai bata wani ajiyar abu..? Ita kaɗai ta nufi hanyar falon, dan Amrah fita tai
dama cikin gida zata ya bata saƙon. Ta shigo ɗan lungun dazai sadata da ƙofar
falonsu ya kuma zama hanyar dake tare data garden taji an fusgota. Ihu tai niyyar
yi yay azamar rufe mata baki. Sai da ya maida ƙofar ya rufe sannan ya saki mata
baki yana binta da wani shegen kallo data kasa fahimtar na minene.
Baki ta tura tana gyara mayafinta. Ya sake harararta da binta da kallon sama
da ƙasa fuskarsa a tsananin ɗaure. “Daga yau na ƙara ganinki da wannan banzar
shigar gaban kowane ɗan iska ki tabbatar saina ɓaɓɓalaki na zubar. Ki kuma koma
ciki, kona haɗa k da shi na zafafa. Tashi min anan kona kashe fuskarki da mari
stupid”.
Da gudu tabar wajen hawaye na silalo mata. Yaja tsaki mai kauri yana furzar
da zazzafan huci daga bakinsa. Fitowa yay daga garden ɗin ya nufi falon shima dan
dama ko shiga baiyi ba. Zama yay suna gaisawa da su aunty Mimi da ƴan uwan Mamie
dama Abie ɗin. Kasa haƙuri sukai sai da suka tambayesa ko lafiya? Dan yanayinsa ya
nuna ransa a ɓace yake. Ya kaƙaro murmushi yaƙe yana shafa kansa. “Bakomai fa
auntys karku damu. Gajiya ce kawai da bata gama sakinmmu ba”.
Mamie dake fitowa a kitchen tai yar dariya. “To banda abun babana aida basai
mun gankaba yau, sai kai zamanka ka huta sosai a gida ko”. Kansa ya shafa yana ƙara
risinarwa. “A'a Mamie gara dai nazo na dubaku kuma hankalina zaifi kwanciya ai”.
“To shikenan ALLAH yay maka albarka yaya ɗiyar tawa itama?”.
“Lafiya lau tana gaisheku da muku bangajiya.”
“Duk muna amsawa”.
Bai wani jima sosai ba ya fito, a waje ya sake samun Dr Jamal. Ya nufesa fuskarsa
kadaran kadahan. Shiko Dr Jamal tasa kawace da murmushi. “A'a ango mijin amarya
Fadwa har ka fito kenan?”.
“Eh, ina so na ɗanje na sake hutawa kasan gajiyar biki. Kaima nayi mamakin
ganinka anan kai da ya kamata ace kana can kana kwasar barci”.
“Tab barci ai sai ku angwaye. Muko kwanciya mutum yayta rungumar fillos ai
da gajiya. Gara mu fito farautar namu kayan kamar zaifi”.
“Hakane, amma sai naga baka tafi farautar ba ai”.
“Kajimun ɗan iska mi kazo kaga inayi? Inama take? Tunda kai akace kana
kiranta”.
Fuska ya ƙara tsukewa da ƙyau yana kallon Dr Jamal ɗin. “Yaka kafeni
da idanu kamar naci bashinka?. Tunda kace babu ruwanka ni nazo da kaina na kafa
gwamnatina”. Kansa ya kauda yana jan karamin tsaki. Kafin ya dawo da kallonsa
garesa. “Jamal amma kasan bana son jan raini ko? Duk manyan mata dake garin nan da
suka amsa sunansu mata karasa wa zaka so sai wannan ƴar abar haihuwar jiya”.
Dariya sosai Dr Jamal keyi, “Oh badai an haifeta jiyan ba? To ni wlhy ko
yanzu aka haifota ina son kayata a haka. Yarinyarnan ta haɗa duk abinda nake so ga
matar da nake fata ta zama abokiyar rayuwata. Ni bana ganin waɗancan manyan matan
sam a idona. Kai dai tunda ka ɗauka taka barni nima lokacina ne”.
Tsaki yaja mai karfi da barin wajen. Dr Jamal ya bisa da kallo yana murmushi.
“A gaishe da amarya sai munzo cin cin-cin”.
Bai tanka masa ba, bai kuma juyoba ya shige motarsa ya fice. Agogo shima Dr
Jamal ɗin ya kalla. Ganin lokacin da Anam taci babu alamar zata fito yay tunanin
bara kawai ya wuce ya dawo anjima da dare. Yaran Aunty Hindu dake can gefe suna
wasa ya kira babban. Leda dake dauke da kayan ciye-ciye na kwaɗayi ya bashi yakaima
Anam ɗin shi kuma ya nufi motarsa.....

______________________________

Washe gari monday Anam ta koma aiki, Abie da kansa ya kaita. Hakan ya
mata daɗi, ya kuma sakata a farin ciki har fuskarta ta kasa ɓoyewa. Da Yaseer ta
fara cin karo, wanda rabonsa da zuwa aiki tun randa ya kaita gida. Kallon kallo
suka tsaya yima juna, farin cikin da take ciki ya sata fara sakin murmushi. Cikin
harshen turanci da mutsukka idanunta take faɗin, “Ko aljani ne kemin gizo”.
Duk yanda ya so daurewa sai ya kasa. Ya saki murmushi yana gyara tsaiwarsa.
“Ba aljani bane ifiriti ne”. Dariya maganar tasa ta bata. Ta ko ƙyalƙyalawa cike da
nutsuwa tana kare bakinta da handkerchief. Jiyay gaba ɗaya ya narke a kallonta,
harma zuciyarsa na jin anya kuwa zai iya kiyaye dalilin da ya sashi jin zai
nisanceta kuwa?... Matsowarta kusa da shi ta katse masa tunani. Har yanzu fuskarta
ɗauke da murmushi mai bayyana haƙwara. “ALLAH da gaske naji kewarka Friend. Wane
laifi mukai haka ake fushi damu harda tafiya babu sallama?”.
Hannayensa ya haɗe alamar ban haƙuri🙏🏻, fuskarsa a marairaice sai dai baice
komaiba. Cikin ƴar dariyar data ƙara zuwa mata tace, “Shikenan ya wuce muje ciki”.
Tare suka shiga, suka cigaba da hidimomin gabansu. Koda aka tashi aiki
Maheer ne yazo ɗaukarta. Ta nuna farin ciki anan ma dan tunda yazo hidimar biki ta
hana su zauna su gaisa da ƙyau. Maheer baida damuwa, yanada sauƙin kai sosai ga
barkwanci, sai dai Shareff ya fisa haƙuri nesa ba kusa ba, kawai dai yafisa sakewa
da mutanene shiyyasa ake ganin kirkin Maheer fiye da Shareff ɗin.
Bai wuce da ita gida kai tsaye ba. Sai da suka biya wani joint sukaci kayan
kwaɗayi sukai hira sosai sannan. A hanya yake cemata yaushe zata rakasa gidan
amarya yaga gida. Cikin taɓe baki ta bashi amsa da “Yah Maheer kaje abinka kai
kaɗai kawai”.
“Miyasa bazakije ba ke?”.
“Ba komai, kuma ni nama riga naje ai”.
“Idan kin koma ma ai duk cikin zuminci ne”.
Maimakon ta amsa masa sai ta canja da wata hirar. Shima sai bai sake maganarba
har suka isa gida.

A kwana a tashi ango da amarya sukaci kwanaki shidda da angwancewa. Soyayya


ce ake zubawa tamkar babu gobe. Basu da matsalar abinci, dan kullum sai Mamie ta
aika musu na safe na rana harda na dare ma, sai da Yah Shareff ɗin da kansa yace a
daina kai na daren sannan Mamie ta hutar da kanta. A komai nane suke da juna tamkar
su haɗiye kansu. Basu da wata damuwa sai suci suyi ƴar soyayyarsu. Babu inda yake
zuwa dan ya ɗauka hutu na sati biyu dama, duk da sati ɗaya yay niyya Fharhan ya
takura masa akan biyu dai sannan gajiyar biki ta sakeshi. Ya dauka sati biyun dai
kawai badan yana tunanin zama har su cika baije office ba, dan yasan sunada ayyuka
danƙam harma da wasu sabbin projects da yake fatan samu wanda zasu fito ne daga
gwamnati.
Yakan je gidansu a kullum da yamma ya gaida iyayensa, sai dai koya shigo
wajen su Mamie basa haɗuwa da Anam. Dan a mafi yawan lokuta yakan zone bata dawo
aiki ba. Bakuma dan lokacin dawowar tata baiyiba. Kawai dai yanzu Maheer na matukar
ɗauke mata hankaline, yama hana Abie kaita da safe shi ke kaita ya kuma je ya
ɗakkota, bakuma su dawowa gida sai sun ɗan zaga gari wani lokacin ma sai bayan
magrib. Wannan dalilin yasa duk sanda Yah Shareff yazo baya samunta a gidan. Bai
dai taɓa magana ba, hasalima bai nuna ya san da wanzuwarta ko saɓanin haka ba.
Itako dama ko'a jikinta harma mantawa take da shi yanzun, dan koba komai ta huta da
harara da kallon dake matuƙar ƙona mata rai daga garesa.

Yau ta kasance juma'a. Da wuri Maheer ya ɗakkota a wajen aiki da jaddada mata
ta shirya da wuri zatai masa rakkiya wani waje. Batare data tambayesa ba tace to.
Ciki ta shige, bayan ta gaida Mamie da Abie ta wuce ɗakinta. Dan aunty Mimi da
yaranta sunje Abuja gidan yayan mijinta, amma yau suke saran dawowarsu. Wanka tai
ta shirya tsaf cikin kwalliyar doguwar rigar material dan Yah Maheer yace mata tasa
kayan hausawa. A lokacin har tana ɓata fuskar cewar ita suna damunta bata son zafi,
lallaɓata yay, dan yafi son ganinta a kayan saboda ƙyawun da suke mata. A bikin nan
ba ƙaramin son ganin kwalliyarta ya dingayi ba. Koda Mamie tace ta zauna taci
abinci catai a'a zasuci a wajen cin abinci Yah Maheer zata raka wani waje. Mamie ta
ɗanyi jimm sai kuma ta sauke numfashi, gargaɗi tamata nata kama kanta tare da jin
tsoron ALLAH.
“Insha ALLAHU Mamie bazaki taɓa yin kaico akaina ba, yanda nake a gaban
idonki haka zan cigaba da kasancewa a bayan idonki. Domin UBANGIJIN dake azaba ga
wanda ya saɓa masa, yake rahama ga wanda ya bisa yana kallona koda ke baƙya
ganina”.
Murmushi Mamie tayi, cike da jin daɗi da alfaharin tarbiyyar da suka bama
gudan jininsu tilo duk da suna rayuwa a inda kowa ke ganin dole ne yaro ya lalace,
sai dai ba hakan baneba, kowane tsuntsu kukan gidansu yake yi. “ALLAH yay miki
albarka, ya kuma baki ikon tabbatarmin da hakan”.
“Amin Mamie na uwa ɗaya tilo”.
Ta faɗa tana sumbatar hanun Mamie sannan tai mata sallama ta fice.

Tun tafiyar tasu batai nisa ba sosai ta fara fahimtar inda suka dosa. Taso
ta share amma saita kasa. ta dubesa a shagwaɓe “Yaya nifa....” Da sauri ya dakatar
da ita ta hanyar fadin, “Ban son kice komai. Ai ni zaki raka ko”. Shiru tayi badan
taso ba. Dan tana ganin girmansa da kima sosai a zuciya da ayyuka. Hira ya cigaba
dayi mata, wani ta amsa wani tai murmushi har suka iso. Har ciki ya shiga da motar,
kamar yanda ya saba mata a tsakanin nan shine ya fara fita sannan ya zagaya ya buɗe
mata fuskarsa dauke da murmushi kamar yanda tata ma ke ɗauke da murmushin mai
bayyana haƙora. Tace, “Kai Yaya Maheer shine har da wani ɗan respect?”.
Dariya ya sanya, idanunsa akan fuskarta yana ji kamar ya haɗiyeta dan murmushi
na mata masifar ƙyau. Ƙara risinawa yay irin na respect ɗin yana nuna mata hanya
alamar suje. Dariyar ta sake sanyawa da salute nashi itama....

A hankali ya lumshe idanunsa da ɗaukesu daga garesu yana sakin siririn tsaki
dan komai yana faruwa ne akan idanunsa kasancewar yana daga barandar sashensa tare
da Fharhan da Khaleel suna magana akan office. Tsakin nasa yasa Khaleel da Fharhan
da suma ke kallon su Anam ɗin maido dubansu garesa. Sai dai kasancewar ya riga ya
maida ga lap-top ɗin dake cinyarsa yasa basu fahimci da ainahin wa yake ba. Khaleel
ya mike yana miƙama Maheer daya iso wajen hannu yana faɗin, “A'a Brother dama nan
kawo ashe?”.
“Eh wlhy, ai ban san kaima nan din kayo ba damun haɗa tafiyar ma ai”.
“Ai babu damuwa tunda ga ƴar rakiya ka samo”.
Murmushi kawai Maheer ɗin yayi da maida hankalinsa ga Fharhan suka gaisa cikin
mutunci dan duk abokan Shareff suna ɗaukarsu yayu suma.
“Babban Yaya barka da yammaci”.
Maheer ya faɗa idonsa akan Shareff. Sai lokacin ya ɗago, ya ɗan dubi Maheer ɗin
fuska babu yabo babu fallasa. “Daga ina haka?”.
“Daga gida muke. Yau dai nace bara nazo na gaida amarya na huta da gorinta”.
“Hakan nada ƙyau”.
Ya faɗa a taƙaice hankalinsa nakan abinda yakeyi dan dama tuni ya maida kansa ga
lap-top ɗin. Shima Maheer maida dubansa yay ga Anam data coge can taki karasowa.
“Hajjaju ƙaraso mana ku gaisa da su Yaya”.
Baki ta tunzura, badan taso hakan ba ta nufesu tana ƙunƙuni. A jimlace ta
gaishesu, batare data damu dawa ya amsa ba waye bai amsa mata ba tabar wajen. Shima
Maheer bayanta yabi sai dai ganin ta sake cogewa alamar bazata shiga falon ba yaja
hanunta. Ƙoƙarin amshewa take amma ya hana hakan sai da suka shige ya saketa. Kowa
babu a falon sai uban ƙaurin abinci daya gaurayesa, ga falon a ɗan hargitse alamar
dai yau bai samu gyara ba koma ba yau ɗin kawai ba. Anam ta yamutse fuska kamar mai
tsantsami tana bi ko'ina da kallo a karo na farko dan waccan ranar batai ba.
“Ni kamar ƙaurin abinci nakeji fa?”.
Ya Maheer ya faɗa yana dubanta. Baki ta taɓe da kauda kanta batare data
amsashi ba. Shima sai bai sake magana ba ya shiga ƙwala kiran sunan Fadwa a
tunaninsa ko ta shiga wani uzirinne a ciki batasan abincin na ƙunewa ba. Kusan sau
uku sannan ta fito daga hanyar bedroom hanunta rike da waya tana murmushi, da alama
abu take dubawa da yake sakata nishaɗi...........✍

_😣😣Wayyo Fady baby ya zaki bamu kunya haba selen mu so kike ƴan uba su sami na faɗa
yau🤕. Koda yake munada bakin ramawa🚶_

_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_


*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:


07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇


0913484810_ZAFAFA BIYAR_
*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_


*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:


07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇


09134848107 ko

*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*😭🙏🏽


[10/26, 7:15 PM] My Zafafa: *_Typing📲_*

*_BABU SO....!!_*
_(Miya kawo kishi?)_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BABU SO.👉🏻AREWABOOKS🫶🏻_*

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718

*_15_*

..........Da kaurin abincin ta fara cin karo, dan haka ta kwasa da ɗan gudu zuwa
kitchen tana faɗin, “Wayyo ni Fadwa yau ma yayi ƙauri”.
Daga Maheer har Anam da kallo kawai suka bita, Anam ta taɓe baki da neman
kujera ta zauna. Ganin haka shima Maheer ɗin sai ya zauna yana ƴar dariya. “Tofa
bama yau aka fara ƙonawaba kenan. Lallai Yaya an shigo abba tuwa ashe. Nikam
gaskiya bazan iya haƙuri da mace bata kulamin da cikina ba”. Ya ƙare maganar yana
tsare Anam da idanu.
Idanu ta ɗan waro da ɗage kafaɗarta baki a tabe alamar I don't care, sai kuma
ta ƙyalƙyale da dariya. Ihun da Fadwa ta saki ya hanashi cewa komai ya mike da
sauri ya nufi kitchen ɗin. Anam kam maimakon ta tashi sai ta ɗauka waya tana cigaba
da dariyarta. A dai-dai nan shima ya shigo falon kasancewar Fharhan da Khaleel sun
wuce office saboda sunada uziri. Buɗe ƙofar ta sakata rage dariyar da ɗan kallon
ƙofar, sukaima juna kallon ido cikin ido. Nata ta fara janyewa saboda hango wani
irin yanayi mai kama dajin zafinta a cikin nasa idanun, itakan ta rasa mitaima Yaya
Shareff ya tsaneta a duniyar nan, idan dan tazo gidansa ne ya kwantar da hankalinsa
wannan shine zai zame mata na ƙarshe insha ALLAH. Bata sake yarda ta kalla inda
yake ba, sai dai har yanzu tanajin nasa idanun a kanta. Hakan ya sakata a matuƙar
takura, sai dai kuma ta kasa motsawa balle ko yinƙurin barin wajen tayi....
Dariyar Maheer ta sakashi janye idanunsa a kanta ya juya garesa, sai yay karo
da idanun Fadwa dake tsaye ƙyam a kansa tana masa kallo mai cike da tuhuma. Fuska
ya sake tsukewa cikin basarwa ya maida hankalinsa wajen bin falon da kallo. Sosai
ransa ya ƙara ɓaci fiye da wanda yake ciki tun ɗazun, duk gargaɗin da yay mata akan
karya shigo ya sake ganin falon nan haka da datti batajiba kenan. Ya ɗan cije lip
ɗinsa kawai batare da yace komaiba ya juya ya fita. Hakanne yasa Maheer bin bayansa
shima. Anam ma mikewa tai, ta zabgama Fadwa dake binta da kallon wulaƙanci harara
sannan ta fice tana jan ƙaramin tsaki.
Duk da kiran da Maheer yay mata batai niyyar binsu sashen Shareff ɗin ba. Sai
dai ganin Fadwa na leƙenta ta window rai ɓace ya sata nufar can tana wani murmushi
daya ƙawata fuskarta. A bakin ƙofa ta coge, Maheer ya juyo yana kallonta, cikin
tsokana ya wulla mata ƙaramar harara. “Malama wa kikema aikin gadi zaki mana tsaye
anan? Zoki zauna jareh”.
Murmushi kawai tayi itama, batare da tace komai ba ta zauna a kujerar kusa da
shi tana satar kallon Shareff dake latsa waya kamar ma bai san da shigowar tata ba.
Baki ta taɓe itama ta ɗauka tata wayar ta shiga latsawa. Ba'a rufa mintuna huɗu ba
Fadwa ta shigo ɗauke da babban basket dake ɗauke da kuloli da duk abinda maicin
abinci zai iya buƙata. Maheer ya miƙe ya karbeta yana dariya, cikin ƙasa da murya
yace, “Badai mai ƙaurin zaki bamu ba?”. Harara ta ɗan sakar masa da kai masa
ranƙwashi ya kauce, dining ya nufa domin ajiyewa, ita kuma ta nufi inda Shareff ke
zaune har yanzu idonsa akan wayarsa. Zama tai kusa da shi tana mai rungumesa tare
da manna masa kiss a kuncinsa. “I miss you my Soulmate”.
Maimakon amsa mata sai ya ɗago ya ɗan saci kallon Anam. A zahiri idonta akan
waya yake, sai dai kunenta da hankalinta na tare da su..... “Wai har yanzu fushin
kake?”. Fadwa ta faɗa cikin kunnensa hanunta ɗaya na cikin nasa ɗaya na shafo
wuyansa zuwa gefen kunne. Hanunta dake kan wuyansa ya janye, a hankali yace, “Miye
haka wai, muje ki bani abinci”. Bataso haka ba, sai taji inama ya biye mata kodan
ta turama wannan yarinyar haushi. Amma ko yanzu ma bata ɓaci ba, tayi alwashin sai
Anam ta daina zuwa mata gida har abada daga yau dalilin abinda ta shiryama ranta
zatai mata. Cike da isa da yauƙi tabi bayan Shareff zuwa dining, dama shi Maheer
tunda ya dire abinci yaja kujera ya zauna acan abinsa.
Cikin bada umarni Maheer yacema Anam ta taso suci abinci, ta ɗago tana
girgiza masa kai alamar a'a. Hararta yayi, “Kinsan ALLAH idan na taso ɗaukarki
zanyi kamar bab.....”
“You're vary stupid!!”.
Ya faɗa cikin suɓutar baki idanunsa na wani irin ƙanƙancewa. Furucin da fusatar
tasa ya saka Maheer haɗiye sauran abinda ke bakinsa. Anam da Fadwa kam gaba ɗayansu
suka zuba masa ido dan yanda yay maganar a fusace duk sai da suka zabura. Waya
yakeyi, wayar da kafin zancen Maheer yinta yake da murya can ƙasa dako Fadwa dake
kusa da shi tana ƙoƙarin fara zuba masa abinci bajinsa take ba. Hannu takai da
nufin taɓashi ya maka mata harara dole ta janye, sosai abun ya bama Anam dariya,
tako yi gefe da kanta tanayi sai dai ƙasa-ƙasa. Maheer ya kalleta yana murmushi
shima. Cokali ta ɗauka ta saka a cikin abincinsa babu ko ɗar ta kai baki, da sauri
ta ɗiba tissue ta tufosa a ciki tana ambaton ya ALLAH. Shima dai Maheer yay cak ya
kasa cigaba da tauna na bakinsa. Yayinda shima oga kwata-kwatan ya tufo nasa cikin
tissue ɗin daya fisga yana kallon Fadwa rai a ɓace.
“Kinada hankali kuwa? Wannan gishirin fa!”.
Ɗan zabura Fadwa tai baya jikinta na tsuma. Ya sake jan tsaki da miƙewa zai
bar wajen tai saurin riƙosa. A fusace ya juyo gareta sai dai saurin rungumesan da
tayi ya sashi haɗiye kakkausan furucin da yay niyyar jifanta da shi. Jin bai tureta
ba ta ɗago da sauri dan a gareta wannan damace da zata aiwatar da shirinta, babu
zato kuwa babu tsammani ta haɗe bakinsa da nata. Da sauri Maheer yasa handkerchief
ya rufe fuskarsa yana dariya...
Faɗuwar abu da tarwatsewarsa kan tiles tare da sakin siririyar ƙarar Anam ya
sakashi saurin ture Fadwa yana jan numfashi da ƙarfi. Maheer ma da sauri ya janye
handkerchief ɗin dake fuskarsa tare da haɗiye dariyarsa. Kusan a tare suka zabura
kanta, sai dai Maheer ya rigashi kai hannu zai riƙo Anam, a ɗan fusace ya fisgo
hanun Anam ɗin da Maheer ya kama ta dawo jikinsa, cak ya ɗagata daga dirƙuson da
tai ya maida saman kujera, ƙafarta dake fidda jini ya ruƙo yana kaiwa tsugunne
gaban kujerar, sai da ya rumtse ido sannan ya tsige yankin kwalbar cup data
shigeta. Tako sake sakin ƙara jikinta na rawa dan har cikin ƙwaƙwalwarta taji cire
glass ɗin. Handkerchief ɗin hanun Maheer ya fisga ya ɗaure mata ƙafar, sannan ya
sake ɗaukarta cak yay waje da ita. Maheer da shima ke a rikice bin bayansu yay da
sauri.....
Sosai zuciyar Fadwa ta kumburo cikin ƙirjinta tamkar zata fashe, itace ta
tura kofin da hanunta ya faɗi lokacin da taga Anam zata miƙe a yanda ba kowa ya
gani ba musamman ma Shareff data rungume. Tsabar yanayin da take ciki ko
kwakwkwaran motsi ta gagarayi har tajiyo fitar motar mijinta. Hajijiyar da taji
tana kwasartace ta sata saurin dafe kujerar dining...

Basu san ba ƙaramin ciwo Anam taji ba sai da suka isa wani clinic dake anan
cikin anguwar. Sun fara mata allurar rage raɗaɗi kafin su tabbatar musu ciwo taji
sosai kuma sai an ciro sauran kwalbar daya karye a wajen sannan a mata ɗinki. Basu
wani ja zancen ba akai mata duk abinda ya dace tana faman kuka da raki. Sai da
komai ya nutsa ta samu nutsuwa da daina kuka har sun fita sunyo sallar la'asar sun
dawo sannan suka sami damar ganinta. Tausayinta dukansu ya sake kamasu, dan cikin
ƙanƙanin lokaci har ƙafartata ta kumbura. Ƙin yarda tai ta kalli ko sashin da
Shareff yake. Cike da shagwaɓa tace, “Yaya Maheer ni ka kiramin Mamie da Abie su
zo”.
“A haba dai sarkin rigima. Ni babu wanda zan kira dan maybe ma su sallamemu
yanzu mu wuce gida. Wai ni garin yaya ma hakan ta faru ne? Keda ke zaune a
kujera?”.
Fuska ta sake tsukewa matuƙa, taƙi kuma cewa komai sai harar gefen ido
data ballama Shareff daya tsareta da idanu shima alamar bukatar son ji.
“Ina saurarenki ya akai hakan ta faru?”.
Nan ma ƙin cewa komai tai, sai dai ta ɗago yanzu sosai ta kalli Yaya
Shareff har suka haɗa ido. Saurin kauda nata tayi da zamewa ta kwanta tana son
maida hawayen dake ƙoƙarin zubo mata. Maheer da bai hakura da son jiba yay ƙoƙarin
zagayawa inda ta juya fuska Shareff ya dakatar da shi. “Malam ya isa”.
Kamar Maheer zaiyi magana sai kuma ya fasa saboda shigowar Nurse. Sannu tai musu
tare da mikama Shareff dake kusa da ƙofa takardar hanunta. “Yallaɓai zaku iya
tafiya da ita gida yanzu, ga wannan magungunan sai a saya mata tai amfani da su,
ALLAH ya kiyaye gaba”.
Amsar takardar yay da gyaɗa mata kansa kawai. Sai da Nurse ɗin ta fita sannan
ya dubi Maheer dake tambayarsa ko can gida zasu wuce kawai?. Bai ce masa komai ba
ya fita a ɗakin, shi kuma Maheer ya koma inda ta juyar da fuskarta.
Kallonsa tai da faɗin, “Yaya nidai mu tafi gida kawai, bazan koma gidansa ba,
kuma wlhy ta kwana da sanin yanda ta zubarmin da jini sai na rama koba yanzu ba”.
Ɗan zaro ido Maheer yayi da zama a kujerar dake gaban gadon. Kafin ya samu
damar cewa wani abu Shareff da wasu Nurse suka shigo ɗakin. Kallonta yake cikin ido
saboda yaji abinda take faɗa. Maheer ma kallonta yake sai dai ya kasa cewa komai
dan bai fahimceta ba. Da taimakon Nurses ɗin aka kawota wajen mota, tanata mitar
ita dai a kaita wajen Mamie. Bai kulata ba, sai Maheer dake lallashinta. Sun tsaya
wani pharmacy ya bama Maheer takardar da atm ɗinsa tare da faɗa masa pin......

★★

Tun bayan fitarsu take auna son kiran Mamah (Gwaggo Halima) sai dai gargaɗinsa
akan kai ƙararsa ga iyayenta ko nashi na taka mata birki. Sosai ta kasa zaune ta
kasa tsaye balle tsaida shawara. Har cikin ranta tsoro ne da shakku ke cizon
zuciyarta dake ayyana mata abubuwa masu dama. Ta rasa miyasa yarinyar nan ke yawan
shiga mata hanci ne? Kodai akwai alaƙar da suka jima suna jin tsoron ta kasance ne
ta ƙullu tsakanin mijin nata da baƙar yarinyar nan? “Kai ina, wlhy zuciyata bazata
iya ɗauka ba”. Ta faɗa a zahiri da ƙoƙarin kauda mummunan zaton dake kawoma
zuciyarta farmaki. Ba yau ta fara irin wannan tunanin ba, shiyyasa a koda yaushe
take ƙara jin tsanar yarinyar bayan wadda mahaifiyarsu ta cusa musu akan iyayenta
da ita kanta, bata son ganin wata alaƙa tsakanin Mijinta da Anam, amma abin tsoron
a kullum kusanci take gani a tsakaninsun, kusanci irin wanda tafi shiga tashin
hankali da shi a yanzu fiye dana baya.. Tabbas lokaci yayi da zata ɗauki mataki,
idan tace mataki tana nufin koma wane irine in har zai nisanta tsakanin mijin nata
da wadda takema kallon maƙiyya tun a zamanin tsatson kakanni da suka haɗa
kishi.....
Harta danna kiran Mahmah ta yanke, dan tasan rashin haƙuri da haɗiye abu
irin nata, maida akalar kiran nata tayi ga Mommy, bugu ɗaya kuwa ta daga. Ta
gaidata cikin ladabi da kwantar da murya. Itama Mommy sai ta amsa da kulawa sosai.
Shiru ya biyo baya, Fadwa na tunanin ta inda zata fara...
Mommy ta katse shirun da faɗin, “Fadwa babu dai wata matsala ko?”. Nan ma shiru
kamar bazatace komai ba, sai kuma taja ajiyar zuciya da fara kukan da bata san yana
makale a makoshinta ba. “Lafiya Mommy”. “A'a Fadwa, ya zakice lafiya kuma kina
kuka. Kinga kar kiji komai faɗamin matsalarki kinji, Shareff ne ko?”.
“Bashi bane Mommy yarinyar nan ce Anam”.
“Anam!!”.
“Eh Mommy”.
Shiru Mommy tayi zuciyarta na tafasa, taja nannauyar ajiyar zuciya tana mikewa.
Falon ta fara zagayawa har lokacin wayar na a kunnenta sai dai ta kasa cigaba da
cewa komai kamar yanda itama Fadwa tai shiru. Kusan mintuna biyu sannan Fadwa ta
katse shirun da faɗin, “Mommy wlhy ni bazan iyaba. Zuciyata bazata iya ɗaukar
cigaba da ganin wannan yarinyar mai ƙirar karuwai na shigomin gida ba. Inba hakaba
zan iya kasheta na halaka banza.....”
Rai ɓace Mommy ta katseta da faɗin, “Shi Shareff ɗinne ya kawota gidan?”.
“A'a tare da Yaya Maheer sukazo. Yanzu haka daga ta ɗanji ciwon da tana
akan sani tayisa dukansu sun kwasheta zuwa asibiti a ruɗe. Kusan awa huɗu kenan har
yanzu basu dawo ba. Wlhy Mommy na tsaneta, dan ALLAH nidai ta daina zuwa min gida”.
Katse wayar Mommy tayi, ranta a matuƙar jagule ta fara laluben number
Maheer, harta katse ba'a ɗauka ba, ta sake kira nan ma ba'a ɗagaba. Ranta ya sake
ɓaci ta maida akalar kiran ga Shareff. Tana gab da tsinkewa ya ɗaga, cikin
girmamawa a gareta da tausasa harshe na ɗa nagari ga iyaye yay mata sallama da
faɗin, “Mommy barka da yamma”.
“Kuna ina?”
Ta jeho masa tambaya batare data amsa gaisuwar tasa ba. Ɗan jimm yay alamar tunani,
sai kuma ya kalli Anam dake kwance cikin kujera idanunta a lumshe. Kamar mai raɗa
ko tsoron tada jariri a barci yace, “Pharmacy”.
“Kai da wa?”.
Kallon Anam ɗin ya sakeyi suka haɗa idanu, a marairaice ta janye tana kauda kanta
gefe. Numfashi ya ƙara saukewa, cikin sake tausasa harshe yace, “Ni da Maheer
ne....”
“Dawa kuma?”.
Ta tare numfashinsa tun kan ya ƙarasa. Bai iya karya ba, shi mutumne kai tsaye koda
ace gaskiyarsa zata ja masa laifi ko matsala zai faɗa ya amsa hukuncin daga baya.
Dan haka yace, “Mommy da Juwairiyya ne da taji ciwo”.
A fusace tace, “Waye Juwairiyya kuma?”.
A hankali yace, “Anam”.
“Kusameni kai da Maheer”.
Ta faɗa tana yanke wayar. Tsirawa wayar ido yayi kamar mai son ganin Mommyn a ciki,
sai kuma ya ɗan girgiza kansa ya ƙara kallonta ya ɗauke kansa yanama motar key
saboda hango Maheer na fitowa. Baicema Maheer ɗin komaiba ya canja hanyar zuwa
gidansa zuwa amsa kiran Mommy. Shima Maheer ɗin baiyi magana ba a tunaninsa mitar
Anam ce ta sashi canja shawara.
Gidan su Anam ɗin ya fara tsayawa, sai dai bai shiga da motar ba yay parking
a ƙofar gate. Kusan atare suka fito shi da Maheer. Maheer ɗinne ya buɗe mata murfin
yana faɗin, “Kefa yau kin zama gimbiya sai dai a ɗaukeki ko?”.
Kanta ta jinjina masa tana murmushi duk da hango mugun kallon da Shareff ya
watso mata. Tana ƙoƙarin miƙa masa hannu duk da tsokanarsa dama tai niyyar yi su
Abie suka fito shi da baƙon abokinsa da suka jima basu haɗu ba. Hannun Maheer ya
janye ya nufi su Abie ɗin kamar yanda Shareff yayi. Abie dake kallonsu fuska ɗauke
da murmushi ya riƙo hanunsu su duka yana kallon abokin nasa. “Waɗan nan yarana ne,
Babana Al-Mustapha muna kiransa Shareff. Architect kuma Shugaba mai mallakin
companyn da nake maka bayani, sai Barrister Maheer”.
“Masha ALLAH yaran albarka”.
Murmushi duk sukayi suna mai rissinawa da gaishesa. Ya amsa cike da kulawa yana
riƙo hannayensu shima. Albarka ya dinga saka musu kafin ya juya ga motarsa dake
fake a gefe yana faɗin, “Ato ga ɗan uwanku ma ai tare muke da shi sai ku gaisa ko”.
A tare duk suka kalli motar, dai-dai da fitowar Anam daga mota itama cikin
matuƙar son nuna dauriya sai dai ta kasa taka ƙafar ta nema zubewa. Da sauri
Shareff ya nufeta saboda ratsa kunuwansu da siririyar ƙararta tayi, ya riƙota dai-
dai ta kusa kaiwa ƙasa.
“Ance ki fitone?”.
“Nifa na gajine ga zafi a motar”.
Kamar zaiyi magana sai ya fasa saboda idanun su Abie dake kansu, yayinda kunnuwansu
ke jiye musu bayanin da Maheer ke musu na cewar ciwo taji a ƙafa.
Ƙoƙarin ɗaukarta Shareff ɗin yake yi tai saurin ja da baya cikin zare
idanu da bugawar ƙirji sakamakon ganin wanda batai zaton gani ba.
“W...waya kawoka gidanmu?”.
Ta faɗa idonta kar a kansa kamar yanda shima ita ɗin yake kallo. Su kuma su Abie su
dukan suke kallo. Tattausan murmushi ya saki yana mai janye idanunsa cikin na
Shareff da yay wani irin mugun kicin-kicin da fuska, akan fuskarta ya maida cikin
ɗaga kafaɗa yace, “Ina tare da Daddyna ne. Amma badan nasan nanne gidanku ba Beauty
”.
Sau ɗaya ta kalli abokin Abie ɗin ta maida kanta ta duƙar. Cikin sake
faɗaɗa murmushi Alhaji Abu kalla ya dubi ɗan nasa da ƙyau. Kansa ya shafa yana mai
kauda kai da sakin ƙaramar dariya. Alhaji Abu Kalla yay ƙaramar dariyar shima da
ɗauke idonsa ga ɗan nasa ya maida ga Abie da shima dai murmushin yake da sonjin
ƙarin bayani..........✍

_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_
_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:


07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇


0913484810_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_


*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:


07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇


09134848107 ko

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏽

[10/28, 11:42 AM] My Zafafa: *_Typing📲_*


*_BABU SO....!!_*
_(Miya kawo kishi?)_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BABU SO.. 👉🏻AREWABOOKS🫶🏻_*

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718

*_17_*

........Kasancewar Abie a wajen ya sashi ƙin cewa komai ya ɗauketa gaba ɗayanta ya
haura sama aunty Mimi biye da shi. Ɗakin Mamie suka nufa kamar yanda Aunty mimi
tace.
Wata wawuyar ajiyar zuciya ta saki mai ƙarfin gaske lokacin da yake ajiyeta
akan gado, dan tunda ya ɗakkota ta ɗauke numfashinta da rumtse idanu zuciyarta na
bugawa da sauri-sauri. Shi ɗimma dake ƙoƙarin dannewar tashi zuciyar bugu take da
gudu a ƙirjinsa har numfashinsa na seizing. Ajiyar zuciyar ya sauke tamkar ita, sai
dai tasa ta fitane a ɓoye. Sallamar Mamie ta sashi haɗiye abinda ke masa kaikawo,
tray ɗin hanunta ya amsa yana ɗan murmushi da faɗin, “Mamie da kanki”.
Murmushin itama tayi batare da tace komai ba, ta harari Anam dake kwance lamo
tana sauke ajiyar zuciya. “Mai rakin tsiya yanzu waye yaji daɗin? Nikam zanga yanda
zaki ƙare lokacin rainon ciki balle ranar haihuwa, mijinki dai yaga takansa ai”.
Dariya aunty Mimi ta sanya, yayinda Anam ke tura baki gaba, taɗan saci kallon
Shareff sai ko idonta cikin nashi. Sosai ya sarƙeta da su, sai da ƙyar ta samu
damar fisgewa tari mai alamar sarƙewar yawu na kufce mata. Wani irin yanayi data
kasa bama fassara ta karanto a cikin ƙwayoyin idanunsa, hatta da tsigar jikinta
yamutsawa ta shigayi, ga tarin yaƙi tsayawa har sai da Aunty Mimi ta tadata zaune
tana bubbuga bayanta. Kamar ba shine sanadin komaiba cike da basarwa ya miƙama
Aunty Mimi ruwan, a baki ta saka mata, sai da tasha sosai kafin tarin ya lafa
idanunta har sunyi jajir. Sannu Mamie tai mata tana ƙoƙarin ficewa domin nuna kara
garesu tunda dai duk suna ƙoƙarin nuna kulawa gareta bai kamata ita saita tsaya ba.
Yana daga tsaye har Aunty Mimi ta bata umarnin fara cin abinci bayan ta ɗaura
mata tray ɗin akan cinyarta. A hankali ta fara cin abinci, sai ƙunƙuni take a
zuciyarta na zamansa ɗakin. Oho bai san tanayi ba, dan babu alamar zai fita ɗin.
Aunty Mimi ta miƙe ta fita saboda kiran mijinta daya shigo mata a waya.
Shiru ɗakin bakajin motsin komai sai na ƙarar spoon da take juyawa a plate,
dan gaba ɗaya tama kasa cin abincin yanda ya kamata, tarasa mike damunta, kunyarsa
ko haushinsa, dan abinda ya faru a gidanta ɗazun ya gagara barin zuciyarta. Jin
shiru kamar baya ɗakin ya sata ɗan ɗagowa da nufin satar kallonsa sai suka sake
haɗa ido. Kanta ta maida ga abincinta tana sake tsuke fuska.
(Sai kallon tsiya) ta faɗa a ranta. Kamar yaji mitake faɗa ya zura wayarsa a
aljihu yana ɗan jan siririn tsaki. “Baki iya komai ba sai kallon mutane laziness”.
Kasa daurewa tai sai da ta ɗago ta kallesa idanunta cike da tsiwa. “Toni da
baka kalleniba zaka san ina kallonka ne.....”
“What!”.
Ya faɗa cikin ɗan kausasa murya da waro idanunsa kanta sosai. “K! Wai yaushe na
zama abokin wasanki ne a gidan nan?”.
Ƙin cewa komai tai, sai dai bakinta a sama kamar zai taɓo silin. A ranta ko
addu'a take aunty Mimi ta dawo kafin ya fara zazzabga mata maruka. Ganin yana
matsota tai saurin faɗin, “Amma matarka ɗazun datai iskanci agaban mutane baka
hukuntata ba sai ni, kuma jinina da aka zubar sai na rama”. Ta ƙare maganar wasu
zafafan hawaye dake nuna tabbacin abun na ranta kamar zanen dutse har yanzu suka
shiga rige-rigen sakkowa. Cak ya tsaya yana kallonta, kuka take sosai kamar wadda
aka doka, kusan tsahon minti guda da wasu sakanni ta gagara tsaidasu. A hankali ya
rumtse idanunsa, tare da furzar da ƙaramin huci daga bakinsa. Shiru bashi da alamar
cewa komai balle lallashinta, itako sai ƙara matso hawayen take wani baƙin ciki da
takaicinsa na sake hasalata, tabbas da ace lafiyar ƙafarta ƙalau ɗakin zata bar
masa....
“K sau nawa ina hanaki tarayya da wannan yaron amma kika maidani sauna?
Bayan shi ba muharraminki ba itako *Matata ce!*”.
Karan farko da tunda ta fara kukan ta ɗago jajayen idanunta tana kallonsa
cikin tsakkiyar ido. Shima kallon nata yake a tsakkiyar idon......
Ita ta fara janyewa cikin ƙunƙuni tana faɗin, “Ni dai baza'a rabani da
masoyina ba”.
Sosai kalaman nata suka daki ƙirjinsa. Sai dai kafin yay wani yunƙuri aka
dakatar da shi.
“Mike faruwa anan?”.
Aunty Mimi dake shigowa ta faɗa cikin dariya. Ita ta fara janye nata idanun,
batare da tace komai ba ta zame ta kwanta. Shima numfashi ya ɗan fisga, cikin
yanayi kamar mai borin kunya ya ɗaga kafaɗarsa. “Nothing Aunty. Zan wuce gidane
goodnight”. Kafin ta samu damar cewa wani abu yayi ficewarsa. Da kallo ta bisa har
ya fice, kafin ta juyo ga Anam dake faman sauke ajiyar zuciya.
Komai batace mataba, sai da ta tadata zaune ta bata abincin da kanta tare da
magungunanta sannan ta fiskanceta da ƙyau. Kai tsaye tace, “Mamana kina son Shareff
ko??!...”
“God for bid Ummie”.
Ta faɗa cikin tarar numfashin Aunty Mimi da saurai.
“Sure?”.
“Yes Ummie”.
Yanda ta bada amsar da ƙwarin gwiwa yasa Aunty Mimin haɗe fuska tana mata kallon
sama da ƙasa. Cikin rashin wasa tace, “To *_BABU SO MIYA KAWO KISHI?!”*.
“Kishi kuma Aunty? A dalilin mi zanyi kishinsa?”.
Ko amsa ɗaya Aunty mimi bata amsa mata ba, sai dai ta kafeta da ido ganin
hawaye na ciko mata ido. cikin ɗan ɗage kafaɗa tace, “Okay fine kwanta kiyi barci”.
Kwanciyar tayi, tana ta faman ALLAH ya kiyaye ta so wannan mutumin a zuciyarta,
a fili dai bakinne kawai ke motsawa babu sautin fitar magana......

★★

A hankali yake driving ɗin tamkar baya so ko kuma shi kaɗaine a titin, motoci da
yawa sai sun masa horn yake ɗan kaucewa ya basu hanya su wuce, ga kiran Fadwa dake
faman shigo masa waya babu ƙaƙƙautawa. Sai da tai wajen bakwai baida alamar ɗauka,
ana takwas ɗinne ya fisgi wayar a fusace daga change daya sata yakai kunne. Sai dai
baiyi magana ba dan inhar ransa ya ɓaci baya son ya ringa cewa komai....
“My son!”.
Muryar aunty Mimi tazo masa a bazata. Da sauri ya cire wayar a kunensa ya kalla.
Tabbas Aunty Mimi ɗince ba Fadwa ba. Yawu ya haɗiye da ƙoƙarin saisaita kansa. “Yes
small Mom ko nayi mantuwa ne?”.
“Da alama tunda ka tambaya ƙila kayo ɗin”.
Ƴar dariya yayi yana shafa kansa da lanƙwasa kan motar ya shiga layin gidansa.
“Aunty kenan, da alama magana kike nema dai kawai”.
“Kusan hakan, sai dai kai tsaye zan yita, kamar yanda nayi a ɗayan
ɓangaren”.
A hankali ya tsaida motar a ƙofar gate, sai dai baiyi horn ba. “To ina
saurarenki mamana!”.
“Babana kana son Anam ko?!”.
Da ace ruwa yake sha ko cin abinci babu shakka sai ya ƙware dan abinda Small
mom ɗin nasa ta faɗa yazo masa a baza. Ya haɗiyi yawu da sauri jin maƙoshinsa na
ƙafewar danshi. Yay ƙoƙarin saisaita kansa kai tsaye yace ni da nai aure sati guda
kuma”.
“Ba labarin aurenka nake tambaya ba, dan nima ban manta lissafin ba. Ka bani
amsata kawai”.
Steering ya ɗan daka yana cije lips, cikin son kauda mata dukkan wani
tunani babu ko gargadar murya ya bata amsa.
“Aunty ni matata kawai nake so, bayan ita babu wata a raina”.
Shiru Aunty Mimi tai, sai kuma ta saki murmushi mai sautin da har yaji,
cikin dakewa tace “Sure?”.
“Babu kokwanto a maganata Mom”.
“Okay fine. To amma *_BABU SO MIYA KAWO KISHI?!*”.
“Kishi kuma?! Sai dai na zuminci”.
Ƴar dariya aunty Mimi tai da faɗin, “Lallai kam”. Tana yanke wayar.
Tamkar wanda aka zarema lakar jiki haka yay baya luuu jikin sit ya kwanta,
idanunsa da suka canja launi ya lumshe, tsahon mintuna ya kasa horn balle yunƙurin
shiga gidan. Ga kiran dake shigo masa waya da baya raba ɗayan biyu Fadwa ce amma ya
kasa yin komai. Sai da ya sake shafe kusan mintuna goma sha biyu har mai gadi ya
gaji da leƙowa ransa fal mamakin lafiya sannan yay masa horn.
Da ɗan gudunta ta fito, duk da ranta a ɓace yake saboda kiran da take jera
masa yaƙi dagawa sai ta danne saboda shawarar su Sima da take hange mafita a gareta
basai ta cigaba da tada jijiyar wuya a wajensa ba. Ta ɗanesa tare da maƙalƙalesa,
ko kulada yanayinsa batai ba ta haɗe bakinsu. Ƙoƙarin janyeta yay yana kauda kansa
kodan maigadi da yake da tabbacin zai iya hangosu amma ta hanashi damar hakan. Dole
yay ta maza ya tura murfin motar da kafarsa ya ɗauketa gaba ɗayanta yay sasheta
bayan ya raba bakinsu da ƙyar. A kujera ya zube da ita jikinsa, babu wani ɗaga kafa
ta sake maida bakinta kan nasa. Baya buƙatar komai a halin yanzun, sai dai bazai
iya ƙin bata hakkintaba koda ace faɗan doke-doke sukai indai ta nema zai biya mata,
balle ma baya buƙatar haɗa wata matsala tasa ta waje da cisgunawa iyalinsa wannan
alƙawarine ya daukama kansa insha ALLAH, laifinta kuma zai mata hukunci a lokacin
daya shirya. Duk da babu wani karsashi tare da shi ita ke kiɗanta tana rawarta bata
damuba, sai da ta tabbatar ta isar da saƙon da take bukata sannan ta barsa tana mai
kallonsa cikin ido cike da so da kaunarsa.
“I love you my Soulmate”.
Idanunsa ya ɗan lumshe ya buɗe akanta. Batare da yace komai ba ya lakaci hancinta
da yatsansa. Sai kuma ya ɗanbi falon da kallo. Ganin komai tsaf yaji haushinta ya
ragu a ransa. Ya ɗan rungumota jikinsa da sumbatar hancinta. “Haka nake so na dinga
ganinki k da gidan nan a koda yaushe”.
Kai ta jinjina masa tana murmushi da faɗin, “Zaka sameni mai aikatawa”.
“ALLAH yay miki albarka bari naje na ɗan watsa ruwa”.
“Kodai ka fara cin abinci”.
Ɗan kallonta yayi na wasu ƴan mintuna, “Sure baiyi ƙauri ba na yau?”.
“ALLAH bai yiba”.
“Okay muje”.
Duk da ba son cin abinci yake ba haka ya dinga turawa, dan babu makusa a girkin sai
abinda ba'a rasa ba. Dan kawai ya bata ƙwarin gwiwar cigaba dayi kamar hakan ya
yaba tare da saka mata albarka..

★★★★★

Kwanaki sun cigaba da shurawa Anam na samun lafiyar ƙafarta. Tun daga ranar dai
bata sake ganin Shareff a ƴan dubiya ba. Sai dai takanji maganarsa yazo gidan ko su
Amrah suce mata yazo. Dan kamar da gayya sai ya daidaici lokacin da bata falon yake
zuwa. Bata damu ba, dan a wannan gaɓar bama ta buƙatar ganin nasa sam. Tana son
ƙara zama nesa da shi dan tunanin da aunty Mimi keyi a kanta ya gushe har abada.
Kwanakinta biyar ta take ƙafarta sarai ta koma zuwa aiki. Kullum takan shiga gaida
matan gidan cikin gida kamar yanda Mamie ke jaddada mata. Sai dai kuma iyakar Mom
da Aunty Amarya kawai take zuwa ta gaida bata shiga sashen Mommy dana Gwaggo. Wajen
aiki kam tare suke fita da Khaleel, wataran ya dawo da ita wataran Yaseer ya
maidota dan yanzu ta ɗan fara sakin jiki da shi ganin bai nuna mata wata alama data
danganci soyayya sai abota kawai. Muzzaffar ma yasha gwada zuwa ɗaukarta a office
ɗin amma taƙi bashi fuska sam, hakan yasa ya fara zuwa gida kai tsaye dan shikam
dai yaga matar aure. Tun tana noƙewa harta ɗan fara sakewa saboda huɗubar Aysha.
Sai dai duk da hakan taƙi yarda ta amsa tayin son sa. Tana dai saurarensa darajar
Abbansa abokin Abie ne kuma abota mai ƙarfi tun ƙuruciya dan tare sukai secondary
school, a yanzu haka kuma suna ɗan huɗɗar kasuwanci tare.
A haka kwanakin hutun Shareff suka cika, Maheer ma ya koma katsina wajen
nasa aikin tun satin daya shige. Da farko Shareff baya zuwa gidan da safe sai ya
taso aiki yake shigowa ya gaidasu. Sai randa yazo sallama da su aunty Mimi da zasu
koma Malaysia saboda yara makaranta ya samu Yaseer ya kawo Anam gida. Kuma har
cikin gida Yaseer ɗin ya shigo gaishe da su Mamie, a yanda suka amshesa da alama ba
wannan ne ma farko ba kamarma ya zama ɗan gida. Komai baice ba, sai dai koda Yaseer
ya gaida shi hannu kawai ya ɗaga masa, daga karshe ma ya miƙe ya fice batare da an
kammala sallamar ba. Da kallo kawai aunty Mimi ta bisa tana ƴar dariya, Anam kam ta
taɓe baki da sake maida hankalinta ga Yaseer tana dariyar maganar Amrah kamar ma
bata san da Shareff ɗin ba. Dan koda ta shigo ta gansa a taƙaice tace “Yaya good
evening” tai wucewarta. Shi kuma bai amsa mata ba sai hararar da yabi ƙafafunta da
su dan kansa a duƙe yake yana daƙilar waya.
Washe gari da shi akaima su aunty Mimi rakkiya airport, daga can kuma yay
wucewarsa office. Anam kuma suka wuce tare da Khaleel daya buga mata warning ɗin
kar ta sake tabi wata mota zai zo ya maidata gida da kansa koda bai tashi aiki ba.
Badai tace masa komai ba, amma ta bisa da kallon mamaki. Hakan kuwa akai, tun kan
ma a tashi aiki yazo yana zaman jiranta, washe gari ma haka sukai haka har kusan
sati biyu da su Mamie suka fara shirin komawa suma. Nan fa hankalin Anam ya tashi,
ta dinga kuka da magiyar zata bisu Mamie tace bata isa ba. Daga ƙarshe tai mata
kaca-kaca sannan ta dawo lallashi da nasiha. Haka tanaji tana gani suka tafi suka
sake barinta a Nigeria ita kaɗai. Cikin gida ta sake komawar dai sashen Mom dan
nasu gidan an rufe kuma, ranar haka ta yini sukuku kamar mara lafiya, da ga ƙarshe
ma har zazzaɓin sai da tayi. Sai da Khaleel ya samo mata magani.
Su Mamie juma'a suka wuce, dan haka bata fita ko'ina ba sai monday tai shirin
zuwa wajen aiki. A cikin ɗaya a dogayen abaya da Mamie tazo mata da su tai shirin,
bayan ta saka kayan hidimar ƙasa a ciki dan sanyi takeji yau. A hankali ƙamshinta
ke fita, ga black skin nata na shining exactly cikakkiyar ƴar Africa. Bisa matsawar
Mom ta zaman yin breakfast da abinda take iya ci da Mom ta jura girka mata batare
da gajiyawa ba. Kaɗan ma taci ta miƙe tana faɗin, “Alhmdllhi”.
“Badai ƙoshi ba?”.
Mom ta faɗa tana kallonta. Murmushi tayi mai sanyi tana jinjina kanta, dan gaba
ɗaya ta zama wata sukuku. “ALLAH Mom na ƙoshi, yau kwata-kwata banajin cin komai
ne”.
“Anjima fa zaki iya jin yunwa”.
“To Mom bara naje da shi office ɗin”.
Babu musu Mom ta juye mata a kula mai ƙyau. Sai da ta jira Khaleel yasha shayi
shima sannan, fita yay akan ta samesa waje zai shiga ya gaida jama'ar gidan. Saboda
kar yasata binsa zuwa gaida su Mommy da tun kan su Mamie su wuce bata zuwa gaida
su, shiyyasa ta noke akan zata samesa a mota. Sai da ya fita da kusan mintuna huɗu
sannan ta fito. Waige-waige ta shigayi a harabar gidan babu alamar motarsa, tasan
yakan kaita waje wani lokacin, dan haka ta nufi gate idan ya fito kawai sai su
wuce.
A wajen gate ɗin kuwa ta samu motar Khaleel tare da makanike, ta ɗanyi tsai
tana kallon motar da tai fakin a kusa da motar Khaleel ɗin. Kamar tasan motar, sai
dai ta manta mai ita dama yaushe ta taɓa ganinta.... Horn ɗin da akai ya sata
haɗiye sauran tunaninta. Makaniken dake duba motar Khaleel ya ɗago yana kallonta
“Hajiya kamar dake ake fa”.
Ba laifi yanzu kanta ya ƙara buɗewa da jin hausa fiye da yanda tazo, ta jinjina
masa kanta kawai batare da tace komai ba. Da farko bataji zataje ba, sai kuma ta
canja shawara da tunanin ko Yaseer ne ya ɓadda kama. Murmushi ta saki akan wannan
tunanin tana nufar motar.
Yanayin sanyinta a tafiyar ya sashi kafeta da ido cike da nazari, gashi bayan
murmushin dake fuskarta babu wani alamun nishaɗi ko farin ciki a tattare da ita.
Zuciyarta ta gama yanke mata shawarar Yaseer ne, hakan yasata nufar ɗayan gefen
batare da neman sanin waye ba ta buɗe ta shiga cikin ƴar dariya tana faɗin “Lallai
ma Yaseer, kana tunanin ɓadda kama zata sa na gaza gane k.....” Sauran kalmomin
suka kasa ƙarasa fita a bakinta saboda ƙamshin turaren da sai a yanzu ta samu
nutsuwar banbancewa. Da sauri ta juyo batare data ƙarasa rufe motar datai yunƙurin
yi ba. Har cikin rai ta tsorata da katoɓararta, amma sai ta dake cikin son kame
kanta tace, “Oh Yaya yi haƙuri, ALLAH nama zata Yaseer ne ina kwana!”.
Shiru kamar bazai amsaba, dan tunda ta shigo bai kalleta ba ko sau ɗaya.
Idanunsa da suka surku da ɗan ja ya ɗago ya zuba mata. Ƙoƙarin dannewa da ɓoye
tsoranta take a fili, ta kai hannu kan ƙofar da nufin buɗewa ta fice ko zata samu
damar shaƙar iska yasa lock.
(Ya ALLAH, wannan mutumin zai iya cinyeni fa a motar nan wlhy gara na lallaɓa)
ta ayyana a zuciyarta. Idanu ta marairaice kamar gaske ta ɗago tana kallonsa, “Yaya
kayi haƙuri ALLAH ban san kai bane”. Motar yayma key batare da yace mata komai ba
ya fisgeta har yana bulama bakaniken dake duba motar Khaleel ƙasa.
Sunayen ALLAH kawai take ambata a ranta dan tasan itakan yau sai romanta za'a
samu a hanun mugun nan......
“Mina faɗa miki akan yaron nan kwanaki?!”. Ya faɗa a kausashe dai-dai yana
hawa kan babban titi. Kallonsa tai fuska a dake, ta kuma ɗauke da sauri saboda tasa
fuskar ma tafi tata dakewar. Cikin ɓata fuska da tura baki tace, “Toni Yaya bamfa
san wa kake nufi ba ai”.
Komai baice mata ba, ya cigaba da driving nasa, sai da suka iso dai-dai wajen
nata aikin yay fakin daga ɗan nesa. Da mamaki ta kallesa, “Yaya yanaga ka tsaya
na.....?”
Rinannun idanunsa daya dasa a kanta ya sata haɗiye sauran maganar muƙut,
tai ƙoƙarin ɗauke idonta ya hana hakan cikin tsareta da nasa da duk suka firgitata.
“Ni kike faɗama bakisan wa nake magana akai ba.”
Da ƙyar ta fisgi idanunta tai ƙasa da su zuciyarta na bugawa da sauri saboda
yanayinsa ya masifar tsoratata. Da sauri ta rumtse idanunta saboda jin yatsun
hanunsa a kan haɓarta, ya ɗago fuskarta sosai tare da matsota garesa har suna iya
shaƙar numfashin juna. “Buɗesu kona mareki!!”.
Buɗewar tai da sauri saboda kusancinsu ba ƙaramar rikitata yay ba, hatta shi
kansa yana iya jin sautin bugun zuciyarta ta hanyar ɗagawa da ƙirjinta ke ɗanyi da
sauri-sauri..........✍

_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_


*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:


07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇


0913484810_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_


*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:


07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇


09134848107 ko
[10/28, 11:42 AM] My Zafafa: *_Typing📲_*

*_BABU SO....!!_*
_(Miya kawo kishi?)_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


*_16_*

.........“Ita kuma f...”


Bai karasaba Abie ya bashi amsa da faɗin, “Mamana Juwairiyya (Anam)”.
“Woow masha ALLAH! Masha ALLAH. kace ɗiyar tawa ma ta girma ashe. Damma ƙaramin
jiki ya ɓoye shekarun”.
Gaidashi Anam tayi batare data sake yarda ta kallesu ba, ya sanya mata
albarka itama da mata sannu akan ciwonta tare da addu'ar samun sauki. Su Maheer
suka amsa da amin, banda Shareff dake ƙoƙarin ciro wayarsa a aljihun wandon jeans
ɗin jikinsa da kira ke shigowa. Saurayin ya karaso gabanta idonsa ƙyam a kanta ko
ƙyafatawa bayayi. Ɗagowa tai itama ta kallesa. Ya kashe mata ido ɗaya yana sake
faɗaɗa murmushinsa. Cikin ɗan rankwafowa da murya can ƙasa yace “Kona ɗaukeki da
kaina”.
Kanta ta girgiza masa tana satar kallon su Abie da Shareff dake waya duk da
idonsa baya kansu, amma abinda bata sani ba kunnensa sarai yaji masa abinda
saurayin ya faɗa. Shima ɗan janyewa yay daga kusa da ita ya mikama Shareff daya
gama wayar hannu. Fuska ɗauke da murmushi yace, “I'm Muzzaffar Abu Kalla”.
Cikin ido ya kallesa da ƙyau. Ganin su Abie a wajen ya sashi yarda ya mika
masa nasa hanun kamar mai ciwon baki yace, “Al-Mustapha Muhammad Shareff”.
“Nice name and nice to meet you”.
“Same”.
Shareff ya faɗa a takaice yana janye hanunsa. Muzzaffar ya mikama Maheer shima
suka gaisa. Hakan yayi daidai da fitowar Aysha. Itama gaidasu tai su duka cikin
girmamawa. Shareff yace ta kama Anam su shiga ciki. Sai da yaga shigewarsu sannan
shima yayma abokin Abie sallama ya shige batare daya sake kallon sashen da
Muzzaffar yake ba. Ganin haka shima Maheer yay musu sallam yabi bayansa.
Kai tsaye sashen Mommy suka nufa saboda kiranta dake ta faman shigo masa a
waya, duk da kuwa ya ɗaga na farko ya tabbatar mata suna ƙofar gida zasu shigo
yanzun. Amma ta kasa haƙuri da tunanin suna raina mata wayone kawai. Da sallama
suka shigo falon, har yanzu tana tsaye sai faman kai kawo take kamar an bata gadin
kayan falon. Babu zato babu tsammani ƙarar lafiyayyen mari ya shiga bada ƙarar amsa
kuwwa a illahirin falon. Maheer ya dafe kuncinsa wata azaba na ratsashi, wani ta
sake kifa masa a ɗayan kuncin nasa. Cikin huci mai nuna tsananin ɓacin rai take
nunasa da yatsa. “Wannan kaɗanne namaka daga cikin abubuwan dana tanada maka inhar
rayuwarka bata nisanta da jinin Usman da Maryam ba anan gidan wlhy wlhy
Maheer.....”
“A wane dalili rayuwarsa zata nisanta da jininsa data kasance dolensa
kenan Nafisa?”.
Muryar Daddy da basuyi zato ko sanin yana biye da su ba ta karaɗe kunnunwansu,
ya dakatar da Mommy dake ƙoƙarin juyawa ga Shareff da mutuwar tsaye ta samesa
sakamakon marin da Mahaifiyarsu ta sakarma ɗan uwansa na bazata
“Nafisa! Wai miyasa akoda yaushe kike son nuna ƙarfin iko akan ƴaƴanki wajen
wargazamin zuri'ata? To bara kiji, na rantse da ALLAH, daga ranar da tunanin
ƴaƴanki ya fara sauyawa zuwa shiga hurumin zumincina da ɗan uwana ko iyalinsa kamar
yanda kike ƙoƙarin yi, zan tabbatar da shigarki nadama irin wadda bakiyi tsammani
ba daga gareni. Idan kuma kinaga bazan iyaba saboda ɗaga miki kafa danai na tsahon
shekaru ku ku gwada aikatawa ku gani”. Ya ƙare maganar da nuna su Shareff cikin
tsananin ɓacin rai tare da juyawa ya fice batare da ya jira cewar waninsu ba.
Daga ita har su da kallo suka bishi. Wani irin ɓacin rai na nuna kansa a
fuskar Mommy. Ta watsama su Maheer wani mugun kallo batare data sake cewa komaiba
itama tabar falon. Da kallon dai itama suka bita harta shige, Yaya Shareff ya sauke
nannauyan numfashi da maida kallonsa ga Maheer, kafaɗarsa ya ɗan bubbuga alamar
lallashi, dan fuskarsa duk tayi sayin yatsun Mummy.
Cikin ɗacin murya Maheer dake kallon yayan nasa ya ce, “Amma Yaya
Mommy......”
Kai ya jinjina masa alamar baya son jin komai, ya ɗan ƙara bubbuga kafaɗarsa
tare da ɗan hugging nashi ta gefe sannan ya fice. Maheer ya bisa da kallo....
Mommy da duk ke tsaye a bakin ƙofarta tana kallonsu tai ƙwafa. A ranta
kuwa babu abinda take ƙullawa sai tabbatarma Daddy bataji maganarsa ba. Dan kuwa ko
ana ha maza ha mata sai ta tabbatar da ƙiyayyar maƙiyanta a zuciyar ƴaƴanta ya jima
baiyi abibda ya ɗauka alwashin ba. Iyaka dai yace ya saketa ko! To sai me, ko
rabuwa tai da shi ta san yanzu Shareff da Maheer sun taka matsayin da zasu iya riƙe
rayuwarta fiye da shi. Hussaina dake daga ɗakinsu tana sauraren komai itama ta
ƙwalama kira, da sauri ta iso tana faɗin, “Gani Mommy”.
“Ki bimun Yayanku kiga ya tafine ko ya koma can gidan”.
“Okay Mommy”.
Ta faɗa tana ƙoƙarin ficewa. Maheer ma yabar falon, dan haka ta fita da saurinta
sai dai kuma dole tayo baya ta ɓuya dan hango yayun nata a tare. Yaya Shareff na
waya ne, sai Maheer tsaye a gefensa alamar jira yake ya kammala.
Wayar ya sauke bayan yayi sallama da Dr Jamal. “Miya faru kuma?”. Ya faɗa
cikin kafe Maheer da idanunsa da launinsu ya canja gaba ɗaya. Shima Maheer ɗin
kallonsa yake rai ɓace. “Ni zanje na ƙara duba Anam yanzu, dan bazan iya ƙinyin
hakanba gaskiya”.
Wani irin murmushi da Maheer ya kasa bama fassara Shareff ya saki, sai kuma
ya ɗago yana dubansa cikin ido “Brother be careful!”. Ya faɗa murmushin fuskar tasa
na ɓacewa.
Da kallo mai ƙara harzuƙa zuciya Maheer ya bi Yayan nasa, dan tuni harya
bar wajen ya nufi gate. Cikin dakewa itama Hussaina tazo ta wuce sa kamar aikenta
akai, a mota ta samu Shareff, yana kwance cikin kujera idanunsa a lumshe, a can
gefe ta ɓuya tana kallonsa, ya kai kusan mintuna goma a wajen kafin yayma motar key
yabar anguwar. Juyawa tai ta koma gida, bata samu Maheer a inda ta barsa ba, dan
haka takaima Mommy bayanan data aiketa. Jin Shareff bai shiga gidan su Anam ba yasa
Mommy sauke nannauyar ajiyar zuciya, sai dai acan ƙasan ranta ta gama shirya
makaman yaƙar su Mamie ta yanda inhar suka tashi tafiya sai sun wuce da ƴarsu
wucewar da har abada bazata sake leƙo Nigeria ba balle ta raɓu mata ƴaƴa.

★★★

Duk da ta faɗama Mommy damuwarta hankalinta bai kwanta ba. Sai faman kaikawo
take na neman mafita. Zuciyarta ce ta bata shawarar kiran biyu daga cikin ƙawayenta
da tafi aminta da su. Cikin sa'a kuwa dukta samesu, umarnin suzo gareta ta bada kai
tsaye kai kace itaɗin haihuwarsu tai. Babu ko wanda ya musa mata saima tabbatarwa
kafin mintuna shafiyar data basu zasu iso.
Hakan kuwa akai, dan mintuna goma sha biyu bai gama cika cif ba Sima da Amal
suka iso. Amal da Sima ƴaƴan talakawane fitik, sun haɗune da Fadwa a media. Komai
tayi a shafinta na istagram cikin yabonta da mata Comments suke, idan wani ya
zageta zasu haƙiƙice wajen kareta koda kuwa akan gaskiya aka zagetan. Waɗan nan
garkuwa da suka dinga bata yasa ta fara kulasu har takai da sun haɗu a zahirin
rayuwa. Da farko ganin su ba ƴaƴan kowa bane yaso sakata ja baya da su, sai kuma
hakan ya gagara dan suna taka rawar gani a duniyarta ta yanar gizo sosai. Dole ta
buɗe bakin aljihu wajen gyara su Sima ɗin ta hanyar siya musu kayayyakin sawa da
kaisu wajejen gyaran jiki na manyan yara. Maimakon ƙananun man bleaching da suke
shafawa saita ɗaurasu akan manyan harka masu tsada, dan ita Amal ma allura akai
mata. Cikin ƙanƙanin lokaci ta canja musu rayuwa suka fara karo da manyan yara.
Fadwa nada wasu ƙawayen bayan su Sima dan ita macece mai yawan kwashe-kwashen
ƙawaye, ita da mafi yawan ƙawayenta sunyi matuƙar suna a media musamman tiktok a
yanzu dake taka rawar gani a rayuwar yaranmu. Komai na rayuwar Fadwa da ƙawayenta a
bayyane yake, duk inda zasu samo location ko baground ayi vedio bai musu wahalar
zuwa koda a wajen kano ne. A ɓangaren lalacewa bazamuce dukansu a lalace suke ba,
dan kuwa akwai wanda a cikinsu da yawa babu ruwansu da mazan inba a ɗan ɗauka vedio
ba ko abota shikenan. Fadwa na ɗaya daga cikinsu, dan tunda ta tashi Shareff kawai
take gani a idanunta da soyayya. Hakan yasa duk haɗuwar namiji ko kuɗinsa bai cika
zama a gabantaba inba wani abun hanunsa take buƙata ba, tana samu kuma zata watsar
da shi a wuce wajen. Duk kuma tanayi cikin taka tsantsan da Shareff baisan hakan
ba. Hatta harkar media ɗinta Shareff bai sani ba kasancewarsa mutum da yafi damuwa
da aikinsa fiye da komai, idan ka gansa a yanar gizo akan abinda ya shafi cigaban
rayuwarsane ba kalle-kallen banza ba, sai ko ganin labarai masu muhimmanci da yafi
ziyartar irinsu bbc koya zauna ya kalla a talabijin ma yafi masa sauƙi. Amma a wani
lokaci Fharhan ya taɓa masa shaguɓe da tsiyar da Fadwa ke tsulawa a yanar gizon
harya nuna masa wani vedio. Ransa ya ɓaci matuƙa duk da iyayensune suka matsa ya
auri Fadwa tun baya kulawa haryaji ya fara sonta saboda son da take masa bana wasa
bane. Sosai ya mata faɗa da gargaɗi harda barazanar barin rayuwarta inhar ya sake
ganin wannan shirmen banzar daga gareta. Tayi kuka da alƙawarin dainawa a lokacin
har sai ta baka tausayi. Daga haka bai sake bin diddiginta ba dan baida wannan
halin sam ga waninsa, ya daiyi imanin yanda yay mata insha ALLAH bazata sakeyi ɗin
ba. Sai dai kuma ba hakan bane, dan kuwa ko sati biyu kasa cikawa Fadwa tai saboda
ta riga ta saba, amma tabi shawarar ƙawayenta ta samu Fharhan har gida tai masa cin
mutunci da gargaɗi bayan ta gano shine ya nunama Shareff vedion. Daga haka ta
cigaba da harkokinta sai dai cikin taka tsantsan. A ɓangaren shaye-shaye kam basa
shan komai sai shisha da yaranmu suka maida fashion a yanzun, wanda ta koyane shima
wajen wata ƙawar tata har su Sima suma suka koya a wajenta...
“Baby Fady mike faruwa duk kin tada mana hankali?”.
Amal ta faɗa cikin nuna tsananin damuwa da tashin hankali.
“Miyema bai faruba Amal. Na tsaneta, na tsani yarinyarnan fiye da mutuwata amma
Soulmate ya kasa fahimtar hakan. A yanda nakeji ALLAH zanfa iya kasheta ma....”
Idanu duk suka zaro na tsorata da kalamanta. Cikin girgiza kai da tarar
numfashinta Sima tace, “Kinga nutsu kimana bayani yanda zamu gane Please. Wacece?
Miye haɗinta da mijinki kuma da har ya kasa fahimtarki?”.
Maimakon amsa saita fashe musu da kuka. Hankalinsu sake tashi yayi, suka
zagayeta suna lallashi. Sai da tayi mai isarta sannan ta fara basu labari. Da farko
sun yabama salonta na kissing mijinta gaban Anam. Daga ƙarshe suka nuna tsantsar
takaicinsu da biyema yarinyar da su Shareff sukai na yarda da wai taji ciwo.
Sima tai murmushi tana kaɗa kai da taune lips. “Karku damu inada shawara, wadda
nasan inhar kika bita Fady har abada yarinyarnan sai ta fita rayuwarki, nifa tun
randa muka haɗu da itan nan a Saloon tare da shi nasan yarinyarnan ba ƙaramar ƴar
bariki bace, sai da kika sake sanarmin haihuwar turai ce tashin can na ƙara
tabbatar da e lallai hasashena nakan hanya ashe. To a wannan karon aurensa kike,
dolene kiyi komai domin ki rabata da mijinki dama hanyar gidanki gaba ɗaya......”
“Nifa wannan dogon bayanin naki ya isheni Sima. Dan ALLAH ki faɗa kawai ina
saurarenki”.
“Hhhh daɗina dake wutar ciki Baby Fady. Kwantar da hankalinki, indai dan wannan
yarinyar ce mai kama da ƴar tsanar roba kisa a ranki zamaninta ya shafe a duniyarki
zo muje daga ciki”.
Bedroom ɗinta suka shige, suka shiga famfata tako ina. Sun ɗauka kusan mintuna
arba'in kafin su fito fuskarta washar da murmushi kamar ba'itace a birkice ɗazun
ba. Ganin har lokacin Shareff bai dawoba ta sakasu su gyara mata gidan. Duk da
yanda ta sakasu aikin cikin bada umarni ya sosa musu rai haka suka zage suka hau
mata gyaran lungu da saƙo, itako tana zaune a falo tana duba Comments na sabon
posting da tai ɗazun a tiktok kafin su Anam suzo. Dan danan ko ina ya ɗau ƙamshi.
Ta nuna musu jin daɗinta, amma duk da haka sai ta sakasu su mata girkin dare kuma
tare da gyaro sashen Shareff. Kowacce da hanzari ta amsa ita zata gyara sashen
Shareff ɗin. Hararsu ta shiga yi, sai dai kuma batare komaiba.
Da sauri Amal ta waske da faɗin, “Na fahimci kowa girkinne bayaso, to muyi
girkin tare aje a gyara can ɗin tare”. Sima tace, “To hakan yafi kam”. Sai a
lokacin Fadwa tai dariya da faɗin, “Duk zame-zamenkun dai sai kunyi, inba hakaba na
fasa sayen ashoben Meerah ɗin”.
Suma dariyar suka shigayi da faɗin ai ba'ayi hakaba duk zasuyi. Hakan kuwace ta
kasance. Sukai mata girki tare da gyaro sashen mijinta batare da hakan ya dameta
ba. Dan hatta bedroom da toilet saida suka gyaro masa. Tsakar gida kuwa dama
maigadi ke sharesa fes shiyyasa da wahala kaga datti. Ganin magrib ta kusa ta basu
kuɗin ankon datai alƙawari da cewa su tafi mijinta ya kusa dawowa bata bukatar ya
dawo ya gansu. Basuce mata komai ba akan hakan sai dariya da sukayi kawai, tai musu
rakkiya har gate suka wuce.

Shawarar da suka bata ce ta sata goge duk wani ɓacin ranta har na rashin
dawowar Shareff gidan har yanzu. Wanka tayi tare da tsara kwalliya mai ma'ana. Ta
tsuke cikin wandon jeans da top da sukai matuƙar fidda ainahin ƙyawunta da ƙyawun
sura. Kamar yanda gidan ke kamshi itama kamshin take bulalawa. Ganin yanda tai ƙyau
saida tai ɗan shot video tare da bin waƙar da akafi yawan challenge akanta a yanzu
ta ɗaura a shafinta na tiktok da istagram. Ita ɗin mai followers ce, cikin ƙanƙanin
lokaci likes ɗinta suka fara hauhawa, video ɗin ya fara trending ko'ina kamar ita
kaɗaice ke lokaci. Sosai farin ciki ya mamayeta damuwarta ta ƙara gogewa baki daya
musamman da ƴan koranta na kusa suna koɗata da zafafan Comments. Yayinda masu kishi
da ita da ganin ta fisu suka fara jefa Comments na baƙar magana harda masu zagi, a
gefe masu gaya mata gaskiya na jeho nasu akan ya kamata ta rage yin video da
ƙananun kaya da gashi a buɗe kodan igiyoyin aure dake a kanta a halin yanzun. Su
Sima ne suka taƙarƙare wajen maida murtani ga masu irin wannan Comments da masu
zaginta, itako sai ma ta kashe datar acewarta sai Comments ɗin sun taru zatazo ta
duba....

★★★

Ɓacin ran jin asalin abinda ya faru daga bakin Anam duk da bashi take faɗawa ba
da tabbacin Fadwa ce ta kira Mommy ta sanar mata wannan Accident ɗin ya hanashi
komawa gida. Dan ya tabbatar in har ya koma a yanayin da yake zai iya yanke mata
kowanne irin hukunci da yazo masa a rai. A yanzu kuma baya buƙatar haka a garesu,
dan bazai so ace daga yin aure sati ɗaya kwana biyar da tarewa hakan ya fara faruwa
ba. Office ya wuce kai tsaye, inda Fharhan da Khaleel sukai mamakin ganinsa tunda
sun san duk wani abinda zai iya kawosa office ɗin sun kai masa shi har gida ya
duba.
Ko gaisuwar da sakatariyarsa ke masa bai amsa ba, hannu kawai ya ɗan ɗaga
mata duk da washe baki da take faman yi da tayasa murnar aurensa. Har ya kama
handle ɗin ƙofar office ɗinsa zai shige ya juyo. “Bana bukatar kowa yasan ina nan
ok”.
“Yes sir”.
Ta faɗa cike da girmamawa a garesa. Shigewarsa yay harda murzama ƙofar key, bai
zauna a cikin office ɗin ba ya shige ainahin ɗakin da yake gudanar da zane-zanensa.
Har mafi yawan ma'aikata suka tashi babu ɗuriyarsa, Khaleel yaso shiga ya dubasa
sai kuma ya fasa saboda tun bayan shigiwarsa ya biyo bayansa amma sakatariya ta
sanar masa yace baya bukatar kowa.
Kiran sallar magrib ya sashi fitowa, shiru companyn alamar kowa ya tafi gida,
sai masu gadi su biyu kawai dake gate. Nan ya tsaya yay salla tare da su a
massallacin dake cikin company ɗin sannan ya fito. Harya ɗauka hanyar gidansa ya
canja, gidansu ya nufa, sai dai kai tsaye a gate ɗin gidan su Anam yay horn, mai
gadi ya buɗe masa ya shige.

Duk suna falo gaba ɗaya zagaye da Anam dake faman rakin za'a gasa mata ƙafa
da ruwan zafi. Taƙi yarda Mamie tai mata hakama aunty Mimi da suka dawo ɗazun.
Amrah ce ta kira Abie, isowar Abie ɗin kusan dai-dai da shigowarsa, kusan su duka
suka juya suna kallonsa da amsa masa sallamar da yayi. Cikin girmamawa ya rissina
ya gaida Abie da Mamie, aunty Mimi ma suka gaisa.
Tun shigowarsa ta ƙara ƙarfin kukanta, takuma ƙi yarda tako kalli sashin da
yake. Haushinsa takeji sosai batare da tasan dalili ba. Takaici ya saka Mamie daka
mata tsawa..
“Wai wane kalar iskanci ne hakan Anam? Shin ke ɗin ƙaramar yarinyace da kowa
zaita fama dake akan abinda zai amfaneki.....”
Da ido Abie yay mata alamar tayi haƙuri, ta ɗauke kai da ƙoƙarin barin wajen
cikin takaicin ƴar tata. Abie yay murmushi da maida kallonsa ga Shareff da ke faman
daƙilar waya kamar bai san abinda ake a falon ba, sake kallon Anam ɗin yayi cikin
sigar lallashi “Mamana to Yayanki yay miki ko?”.
Da sauri ta ɗago tana girgiza kanta, “Garama kowa yamin akan shi yamin
Abie”. Ta faɗa cikin zafi-zafi da share hawayenta. Amrah ta taɓe baki da barin
wajen, yayinda aunty Mimi da Abie ke dariya.
“To saboda mi baki son nashi? Bayan tun ɗazu muke nan ana fama dake ga ruwan
har sun huce”.
“Aunty Mimi nidai bana so ke kimun”.
Aunty Mimi zata kai zaune Shareff da har yanzu bai nuna yasan mi suke ba ya
dakatar da ita. “Aunty barta, a canja ruwan dai”. Babu musu Aunty Mimi ta bashi
waje ya zauna, ruwan zafin ta ɗauka ta nufi kitchen. Anam kuwa ƙafarta ta shiga ja
baya, sai dai ta kasa jan jikinta saboda table daya tokare ta. Shi dai bai kulata
ba har aunty Mimi ta dawo da ruwan, Abie kuma dama yayi ficewarsa saboda wayarsa da
aka kira. Ganin yanda ruwan ke turirin zafin ya ƙara ɗaga hankalin Anam, cikin
marairaicewa take duban Aunty Mimi amma tai kamar bata gantaba itama.
“Ni wlhy bana son naka!!”.
Ta faɗa da ɗan ƙarfi da son sake jan jikinta baya ganin ya amshi towel babba da
ƙarami a hanun aunty Mimi. Babban ya ɗaura akan cinyarsa batare da ko kallonta yayi
ba, ƙafin kuma ya saka ƙaramin a ruwan zafin, ƙafar tata ya kamo takai hannu zata
rike, wani mugun kallon daya sata janye hanunta babu shiri ya watsa mata,
“Idan hanunki ya sake kawowa nan saina ɓallashi shima kiyi jiyyarbaki ɗaya”.
Kamar ta rushe da kuka takeji, sai dai tayi alwashin bazata bar hakan ta faruba
insha ALLAH. Yana ɗaura towel ɗin daya naɗoma ruwan akan kafarta dake kan cinyarsa
alwashin nata ya zama tarihi, dan da gaske kukan ta sanya musu mai ƙarfi tana
ƙanƙame ƙafar aunty mimi dake kusa da ita tana matso masa towel ɗin daga ruwan
zafi.
Sosai yanda takeyi ɗin ke neman sakashi dariya, amma ya danne da ƙyar ya
cigaba da daddana mata ƙafar a nutse. Ta haɗa uwar zufa kafin a gama, hatta da
aunty mimi da tasha riƙo ta haɗa tata zufar dan ba riƙon wasa Anam tai mata ba. Su
Amrah da kukan Anam ɗin ya sasu sake fitowa dole sun kasa daurewa sai dariya suke
kwasa, aiko ta wawushi throw pillows ta shiga jifansu da shi. Duk yanda yaso
daurewa kasawa yay sai da ya shiga layin ƴan dariya da Abie ma ya dawo yana yin
tasa a gefe, Mamie ma dake a kitchen dariyar take kwasa dan borin Anam dabanne
dana kowa.
Ba ƙaramin ƙuleta dariyarsa tayiba fiye data kowa, shi dai da baisan laifinsa
ba bai bartaba sai da ruwan ya huce ya shafa mata man da aka bata a asibiti sannan
ya saki ƙafar da kumburin har ya fara saɓewa, sai ga mutuniyar gyangyaɗi na ɗibar
idonta. Da ɗan sauran murmushin da bai bar fuskarsa ba yake tambayar aunty Mimi ko
taci abinci dan yana son tasha maganinta.
“Inafa taci, tunda Aysha ta kawota fa takema mutane bore a gidan nan har sai
da Mamie ta mata tas. Anam ɗin ya kalla cikin ido, babu zato hararar data wullo
masa ta iso garesa. Da sauri ta kauda fuskarta dan batai tunanin zai juyo ba. Abie
dake kallosu a gefe yace, “Bara na maidata ɗaki sai taci abincin acan kawai ta
kwanta”.
Dakatar da Abie ɗin yayi cike da girmamawa, dan bai kamata shi yana wajen ba
yabarsa yay jigilar ɗaukar Anam ɗin. Cikin matuƙar zaro idanu da suɓutar baki Anam
tace, “Wai Yayan ne zai ɗauke ni?”.
Harara ya wurga mata, ta kauda kai gefe cikin ƙunƙuni take faɗin, “Ni dai
ALLAH bana so, garama a nemomin wheelchair........”
Ranƙwafowarsa kanta na shirin ɗaukar nata ya sata haɗiye abinda take faɗar da
sauri tana ƙoƙarin zabura gefe...........✍

_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_


*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:


07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇


0913484810_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_


*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:


07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇


09134848107 ko

*_ALLAH ka gafartama iyayrnmu_*😭🙏🏽


[10/28, 11:42 AM] My Zafafa: *_Typing📲_*

*_BABU SO....!!_*
_(Miya kawo kishi?)_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718

*_18_*

..........Sosai idanunta ke faman marmari ga ƙwalla na ƙoƙarin taruwa a cikinsu.


“Juwairiyya!! Wlhy! wlhy! daga yau na sake ganin yaron nan ko wani ya ɗaukeki
a motarsa koya kaiki gida sai na miki mugun dukan da zaki kasa tashi, kuma ki koma
gidana da zama stupid kawai”. Ya ƙare maganar da ture fuskar tata gefe.
So take ta fashe da kuka amma tana ƙoƙarin son dannewa, sai dai hakan bai hana
rawar jikinta bayyana ba. A tsawace ya sake faɗin, “Get out of my car! Kafin na
marmashe ƙashinki anan stupid”.
Da sauri ta ɓalle murfin ta fice tamkar mai jiran umarnin nasa dama. Yaja
dogon tsaki da figar motar yay gaba, badan titi bane da sai ya bula mata ƙura,
murfin ma sai da yay gaba kaɗan yaja abinsa ya rufe.
Duk yanda taso ƙoƙarin danne komai hakan ya gagara. Dole ta samu wani dutse a
gefen titin ta zauna ta fashe da kuka. Duk abinda kaga Anam ta zauna yima kuka
lallai ya taɓata sosai, dan tsiwarta da giringiɗishi bai cika barinta maida abu
serious ba, ga kuma yanayin rayuwar data tashi a ciki, ita kaɗai a gidansu sannan a
ƙasar da kowa kansa ya sani kawai.
Ring da wayarta ta farane ya sata share hawayenta ta daga dan tasan su Mamie
ne, a kullum tana waya dasu a irin wannan lokaci da kuma in zata kwanta. Video call
ne, dan haka ta shiga son ɓoye damuwarta da murmushin farin cikin ganinsu. “Good
morning my sweetheart”.
Dukansu babu wanda ya amsa mata, dan duk da ƙoƙarin da take na ɓoyewa
idanunta sun tabbatar musu tayi kuka. Abie yaja numfashi a hankali yana sake kafeta
da ido. “Mamana mi yake faruwa da ke? Waya saki kuka? Ko baki da lafiyar ne har
yanzu? A ina kike nan?”.
A karan farko ta saki murmushi dan jin tambayoyin mahaifin nata a jajjere.
Samun kanta tai da kasa faɗar gaskiya duk da ƙarya ko ɓoye-ɓoye ba halinta bane, ta
sake share hawayen da suka ciko mata ido tana murmushi, “Abie ba komai fa, kawai
kewarkuce har yanzu ALLAH. Kuma a wajen aiki nake ban dai shigaba ka gani”. Ta juya
masa wayar yanda zai iya hango gate ɗin wajen.
A jiyar zuciya suka saki shida Mamie, kafin su shiga lallashinta duk da ita
Mamie a ranta bata gama yarda da cewar har yanzu kewar tasu bace. Amma sai ta barta
a hakan dan tasan Anam da rashin ɓoye-ɓoye koma miye wataran da kanta zata sanar
musu. Sai da suka tabbatar sun sakata farin ciki tana ƙyalƙyala dariya kamar ba ita
ba sannan sukai mata sallama Mamie na faɗin ta gaida mata Yaseer. Farin cikin waya
da iyayenta ya taushe abinda Shareff yay mata ta shiga wajen aikinta da walwala
kamar yanda ta saba ko yaushe.
*_MALAYSIA_*

“Humairah waye naji kina faɗin Mamana ta gaida miki?”.


Cikin rashin damuwa Mamie tace sirikinka ne duk da dai naga ɗiyar taka bata
son a gane hakan.....”
Cikin sauri ya ɗago yana kallonta, har ya kasa dannewa sai da ya ambaci
“Suruki kuma?”.
Ƴar dariya Mamie tai, “Eh bashi kake fatan ganiba daman?, bayan shi ma ai
akwai wasu. Yaron nan Muzzaffar da kuma wani abokin Shareff Jamal. Amma naga
hankalinsu yafi zuwa ɗaya da Yaseer ɗin nan kamar”.
Jin shiru baice komaiba ta ɗago ta kallesa, kallonta yake kamar mai nazari
ko tunani, ta ɗan taɓashi, ajiyar zuciya ya sauke. “Abien Anam akwai matsala ne?”.
Kai ya ɗan jinjina mata yana gyara zamansa, “Babbama kuwa Humairah, miyasa
tun muna Nigeria baki sanar min hakan ba.”
Sosai maganar tasa ta sakata kafesa da ido dan mamaki, amma ta kasa cewa
komai. Fahimtar hakan ya sashi jinjina mata kai, “Basai kin tambayeni komai ba
Humairah, amma idan lokaci yayi ko baki tambayeni ba zan baki amsa da kaina”.
Gaba ɗaya kanta ya ƙara ɗaurewa ita kam, sai dai rashin sabo dayi masa dagiya
yasa ta kasa cewa komai ta bisa da kallo kawai ganin ya miƙe yana kai waya kunensa.
Yana gab da shigewa ɗakinsa taji ya ambaci sunan Yaya (tasan Daddyn Shareff yake
kira da hakan). Jitai kamar ta tashi ta bisa amma sai ta dake kawai, zata bisa a
sannu dan tasan dalilinsa na son hana Anaam ɗin tsayawa da samari bayan kuma duk
fatansu kenan ita da shi tunkan ta wuce Nigeria.....

★★★★

Sauraren sakatariyarsa kawai yake batare da yana fahintar abinda take faɗa
masa ba, idanunsa ma gaba ɗaya nakan kula ɗin daya shigo dashi, wadda baya raba
ɗayan biyu Anam ce ta manta ta...
“Kinga jeki zan nemeki”.
Ya faɗa cikin katse sakatariyar da ke faman zuba bayani cike da yanga da kwarkwasa.
Bataso hakan ba, sai dai sanin shi sam baya wasa yasata bin umarninsa. Sai da ta
fice da kusan minti ɗaya ya sauke kakkauran numfashi tare da furzar da shi, yakai
bayansa kwance jikin kujerarsa yana mai lumshe idanu. kusan mintuna uku ya ɗauka a
hakan kafin ya bude idanun, kular ya ɗauka ya buɗe. Ya tsirama abinda ke ciki idanu
tamkar mai irgawa ko lissafa abinda aka sarrafashi da shi. Abincine irin na ƴan
ƙasar malaysia, shima yana bala'in son sa a lokacin da ya rayu acan, ko yanzu kuma
da yake a Nigeria yakan je takanas ya siya a inda yasan zai samu. Hannu yakai ya
ɗauka spoon ɗin dake ciki ya ɗiba dan tabbas wannan ɗin da gani an masa haɗi da
girki na musamman ne. Sosai ya lumshe ido lokacin da yake taunawa, koda ya haɗiye
sai ya sake ɗiba yakai baki, kamar da wasa sai gashi ya cinyesa tas dan dama bai
karyaba ya fito gidan, shayi kawai ya sha, shima sai da Fadwa ta ɓata rai dayin
korafin ganin saurin da yake faman yi duk da ta fahimci shi mai fitar wuri ne
office sannan ya sha a tsaitsaye ya barota tana tura baki gaba.......
Shigowar Fharhan ta sashi ture kular gefe yana goge bakinsa da tissue.
Fharhan dake kallon kular da murmushi ya kai zaune yana faɗin, “Ɗan gatan madam,
abincin ma sai an baka kazo office kuma ba gayyatar masu tayaka ci ka kulle office
kai kaɗai”.
Murmushi kawai yay yana miƙa masa hannu sukai musabaha. “Kai ka cika sa ido
wlhy, ka hucema kanka takaici kai auren kaima sai a ringa baka kana zuwa da shi
kana hanamu”.
“A'a karka damu alhaji, ai abun bana gori bane muna hanya da iznin ALLAH”.
“Haka muke so ai muma. dan kun ishemu a tituna”.
Dariya sosai Fharhan yake da maganar ta Shareff, yace, “Kaima yaushe kabar
titin. Ba komai zan rama”.
Shima ƴar dariyar yayi. Cikin komawa serious yace, “Yanzu nake duba
saƙonka ta email ai. Mutanen nan ya zasu mana haka kuma?”.
“Wlhy nima abin ya ɗauren kai, jiya badan karna takurakaba da a daren zanzo na
sameka gida tun shigowar saƙonsu, na kira wayoyinka kuma duka switch up”.
“Mtsoww! Kabari kawai, wlhy ban san madam ta kashesu ba sai da asuba na
gani. Amma gaskiya abun nan nasu yayi tsauri, anya kuwa bazamuce mun janye ba”.
“Amma janyewar sai nake gani kamar akwai matsala Musty. Sakamakon company na
buƙatar babban aiki irin wannan a halin yanzun, na biyu mun riga munyi zama da su
har munyi signing akan agreement ɗin, kasan kuma turawan nan dai musamman chines
ɗin nan da basa wasa da damarsu”.
Huci ya ɗan furzar yana mai komawa jikin kujera ya kwanta. Har ga ALLAH
abubuwa masu yawa ne ke masa kaikawo a cikin rai. Amma duk sai ya haɗiye abunsa
yana sake fuskantar Fharhan dake kallonsa. “Ni gaskiya da tafiyar ta zama nine dole
zanyi shine matsalata Fharhan”.
“Oh saboda amarya?”.
Hararsa Shareff yayi, “Ko saboda ita ma ɗin ai inada hujja”.
“hhhh hakane ango kafa ɗan ɗana. To mizai hana kaje da ita kawai”.
“Zan so hakan nima, sai dai bazai yuwu ba”.
“Mi yasa?”.
Shiru kamar bazai amsa ba, sai kuma ya girgiza kansa da furzar da iska ya sake
komawa jikin kukera ya kwanta yana ɗan juyata. “Ina hasashen Fadwa nada shigar
ciki, sai dai ko ita kanta bana jin ta sani. Yin tafiya da ita a irin wannan gaɓar
zai iya zama haɗari”.
“Masha ALLAH! Alhmdllhi. Lallai wannan angon da gaske sharp shooter ne.
ALLAH ya inganta mana”.
Shareff ya ɗan murmusa da faɗin “Amin” akan laɓɓa. Cigaba da tattaunawa
sukai, daga ƙarshe dai shawara ta zauna akan shi zaiyi tafiyar tunda dai wata uku
ne kawai insha ALLAH.
Bayan fitar Fharhan ya buƙaci shigowar sakatariyarsa, daga haka ya cigaba da
ayyukansa har zuwa lokacin break....

★★★★

Duk da bata ɗauki gargaɗinsa da muhimmanci ba sai ta kasa sakewa da Yaseer gaba
ɗaya yau. Kullum shike fita da ita su ciyo abinci a inda yasan za'a samu abinda
take iya ci. Amma yau saita ɓoyema ganinsa. Daga salla ta maƙale a massallaci taƙi
fita. Sai ma ta ɗauka alkur'ani tahau karantawa.
Sai da ta daidaici lokaci yaja sosai sannan ta fito. Kamar jira tana fitowar
wani abokin aikinta yazo ya sanar mata tana da baƙo. Da mamaki take kallonsa dan
bata tunanin wani zai iya zuwa wajenta a yanzu. Daga Muzzaffar har Dr Jamal bata
tunanin ganin wani anan, garama Muzzaffar yakan zo idan ya daidaici sun tashi yace
zai ɗauketa sai dai bata taɓa yarda ba. Kamar bazata je ba sai kuma taga gara taje
dai taga wanene.
Turus tayi lokacin data iso taga mai kiran nata, zaune yake a cikin mota
✍🏻
sai dai ƙafarsa ɗaya na waje dan ƙofar a buɗe yake..........

_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_


*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:


07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇


0913484810_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_


*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:


07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇


09134848107 ko

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏽


[10/28, 11:42 AM] My Zafafa: *_Typing📲_*
*_BABU SO....!!_*
_(Miya kawo kishi?)_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718

*_19_*

.......... Ɗagowa yay daga latsa wayar da yake yana kallonta, dan ƙamshin turarenta
da takunta ya sanar masa da zuwanta duk da ta kasa magana. Idanunta ta ɗauke daga
kallonsa tana faɗin “Good Afternoon”.
“Ni kike ma gaisuwa kina juyar da fuska?!”.
Juyowa tai Idanu cike da ƙwalla tana kallonsa. “Ni wlhy Yaya ban san mina maka
ba duk kabi ka tsaneni ka takura ni. Komai nayi a duniyar nan a wajenka ban iyaba”.
Ta ƙare maganar da sakin siraran hawaye.
Kallonta kawai yakeyi ko ƙyaftawa babu. Ji tai kallon ya sake saka mata
jin haushinsa, juyawa tai da nufin barin wajen.....
“Kika bar wajen nan sai ranki ya ɓaci”.
Idanunta ta rumtse tana jin wasu zafafan hawaye da sukafi na farƙo na neman
kufce mata. Ita kam ta rasa mita tsarema bawan ALLAHn nan a duniya, tana fatan
watanin nan bakwai da suka rage mata su maza suzo ta kammala abinda ya kawota tabar
ƙasar nan, dama tun farko abinda ta gujemawa kenan amma su Mamie suka kasa
fahimtarta. Haɗiye hawayen tai batare data barsu sun zubo ba sannan ta juyo garesa,
yana a yanda yake har yanzu, sai dai idanunsa masu kwarjini da kaifin dake hana
ƙarfin halinta tasiri na nan tsaye kanta ƙyam har yanzu. Kasa jurar kallonsa tai,
tai ƙasa da nata, shima sai ya janye nasan, juyawa yay kujerar gefensa ya ɗakko
ledar dake ajiye. Miƙa mata yay kansa tsaye.
Ledar ta fara kalla tare da hanunsa dake ɗaure da agogo da zoben azurfarsa da
ya jima yana birgeta, har addu'ar damar sace zoben ta taɓa yi a zuwa na karshe da
tai kafin wannan.... Saurin ɗagowa tai tana kallonsa jin ya kamo hanunta cikin
nasa, ya wani sake ƙanƙance idanu cike da salon kallon da a duk sanda ya jefeta da
shi yake firgitata, ta fara son zame hanun a hankali dan gaba ɗaya lakar jikinta
neman daina aiki takeyi, kanta ta fara juya masa tamkar mai ciwon wuya, tana son
zare idanunta daga cikin nasa amma yaƙi bata damar hakan nan ma, sai kawai ta sakar
masa kukan karya.
Hanun nata ya saki a hankali bayan ya saka mata ledar, kamar wadda ake control
da remote fitt ta ɓace a wajen. Tsabar sauri har tintiɓe tayi ALLAH dai ya
taimaketa bata faɗi ba ta dafe gate.
Murmushi ya saki mai ɗan sauti daga ƙirjinsa yana kauda kansa. Ya maida
ƙafafunsa cikin motar tare da rufeta yabar wajen.

Itama koda ta shiga sai da ta samu jikin wata mota ta huta tare da share
hawayen ƙaryarta sannan ta buɗe ledar. Shawarma ce da ice-creem sai yogurt da robar
ruwa. Haka kawai sai kuma ta samu kanta da sakin murmushi. A fili tace, “Ga rashin
mutunci ga kirki idan yaso”. Dariya ta sake ƙyalƙyalewa da shi dan haka kawai drama
ɗin tasu ta yanzu take maimaita kanta a zuciyarta tana saka mata nishaɗi.
Yau kam tayi aniyar kozai daketa bazata yarda tabi motarsa ba, dan haka
kawai ragwantakar data nuna ɗazun a gabansa ke hanata sukuni, sai dai murmushi ya
kasa barin fuskarta har Yaseer sai da ya kasa haƙuri ya tambaya. Ƴar dariya kawai
ta masa batace komai ba. Ana tashi itace farkon fitowa, bata son bin Yaseer ɗin
badan tana jin tsoron tabbatar hukuncin Yaya Shareff ba, ba kuma ta buƙatar shiga
tasa motar shima gara ta hau napep. Sai dai kuma cikin rashin sa'a tana fitowa taci
karo da motar tasa a wajen gate, kuka kawai ya rage ta fasa ta huta, tai tsaye ta
kasa matsawa ga motar har tsahon wasu sakani. Sauke glass ɗin da dariyar Khaleel ta
sata sakin ajiyar zuciya, dan tunda ta fito idonsa a kanta. “Ai ba mai motar bane
sai ki taho mu tafi farar kura kawai”.
“Humm ALLAH Yaya bazaka ganeba. Shi Yaya Shareff ɗinne ya cika takura da hana
mutane sukuni suji daɗin rayuwa”.
“Maybe yana tsare mutuncin kayansa ne kar kiga laifinsa”.
Bata wani gane mi Khaleel ɗin ke nufi ba, saboda da hausa yay maganar ta buɗe ta
shiga tana dariya kawai. Shima yasan bata gane ɗin ba dan haka ya dara.

____________________________

Tun daga waccan ranar Anam ta sake kafa wasan ɓuya da Yaya Shareff, motar
Khaleel ta samu matsala, sai kawai ta koma bin school bus na yaran gidan.
Kasancewar suna fitar sassafe kafin Shareff daya tsiri zuwa gidan da safe ya iso
har sun wuce. Ana tashi kuma zatai wuff ta fito ta tari napep. Motar Yaseer ma dai
ta daina shiga duk da yata bibiyarta da son jin ba'asi tana tabbatar masa babu
komai.
Samarinta biyu da sukafi takurama rayuwarta taga sun rage manne mata. Dr Jamal
da Muzzaffar. Kowannesu kuma yanada gurbi na musamman data ajiyesa dan koba komai
suna sakata nishaɗi a wasu ɓangatorin na rayuwa. Sai dai ta gagara neman jin
dalilin kowannensu akan ɗan janye mata da yayi, garama Muzzaffar sukan ɗanyi waya
jefi-jefi ko chart wasu ranakun.
A gidan nasu kuwa bata da wata damuwa sai su Hussaina wataran, dan idan
rashin kunyarsu ya tashi sukan mata sai dai bakinsu nashan bugu dan bata ɗaga musu
ƙafa. Ta daina zuwa gaida Mommy da Gwaggo sai in ta ritsa sun haɗu a hanya taita
sinne kai wajen gaishesu. Ko kallonta basayi, dan a ganinsu ma ƙin zuwa gaishesun
ta taimakesu koba komai sukan manta da wanzuwarta a gidan. Hakan baya damunta,
takan wataya tsakanin sashen aunty amarya da Mom abinta. Ita da Aysha da sauran
yaran gidan kuwa sai sambarka. Hakama Daddy da Abbah a koda yaushe cikin bama
rayuwarta kulawa suke fiyema da yaransu, dan kullum da tsarabar da waninsu zai kawo
mata gidan da kuma mata nasihar tsare mutuncinta suke.
Kusan kwanaki goma kenan basu haɗu da Shareff ba, sai a yau da akai sa
ranar auran Maheer da sam bata san da zancen auren ba sai da taga akwatina a sashen
Mom akace na auren Maheer ne yau za'a saka rana da kai akwatinan. Tayi mamaki sai
dai batace komai ba, sai daga baya Aysha ke bata labarin ai Maheer ɗin baya son
auren Mommy ce ta takura kamar yanda ta takurama Shareff shima. Auren zumincine da
ɗiyar ƙanwarta. Sosai Anam taita mamakin hali irin na Mommy, a ganinta ta cika
takurama ƴaƴanta a gidan, musamman Yaya Shareff da Yaya Maheer ɗin. Gashi suna mata
matuƙar biyayya fiye da duk sauran yaranta, dan tasha ganin Mommy nama Aysha da su
Hussaina faɗa suna ƙunƙuni. Itace ma kema Aysha faɗa da nuna mata illar hakan ga
iyaye. Sai kuma gashi masu mata biyayyar sunfi shan wahala a hanunta fiye da su
Ayshan da sai abinda suke so sukeyi.
Batabi takan duk hayaniyar da ake a gidan ba, kasancewar ma a sashen Mom
baƙin da zasuje kai kayan suke isowa, saita fito domin wucewarta sashen aunty
amarya ta huta dan asabar ne. Kamar ta juya taji, lokacin dataga motarsa na ƙoƙarin
yin fakin gab da sashen Mom ɗin, amma sai ta dake ta fuske zata wuce abinta.
Siririn tsakin da taji anyi dai-dai zata gitta ya tilasta ta juyowa, dan sam
baiyi kama da tsakin Yaya Shareff ba. Fadwa ce a tsaye cikin shigar madam getzner
shadda da taci uban aiki sai walwali take, tabbas tayi ƙyau sosai. Anam ta sakar
mata wani murmushin ƙularwa da kashe mata ido ɗaya ta cigaba da tafiyarta. Kusan
ɗan cin karo sukai da Shareff daya zagayo waya manne a kunensa yana magana. Shima
dai sanye yake cikin shaddar fara tas datai masa ƙyau da fiddosa a asalin
bahaushensa ɗan arewa dan harda hula. Ta ɗan ja baya yayinda shi kuma ya tsaya cak
dan gaba ɗaya hankalinsa akan waya yake baima san wainar da suke toyawa da Fadwa
ba. Kallonsa tai tana wani ƙyaƙyƙyafta idanu, sai kuma ta tunzura baki gaba ganin
kallon nata da yakeyi shima tamkar idanunsa zasu cinyeta. “Good morning”. Ta faɗa
tana gittasa da ƴar sassarfa.
Cikin basarwa ya cigaba da wayarsa, hakan sai yayma Fadwa data tsaresu da
idanu daɗi harda matsowa zata rungumesa ya kauce mata yana nuna mata sashen Mom.
Cikin shagwaɓa tace, “Ni dai ka gama mu shiga tare ALLAH kunya nake ji”.
Sarai yasan ƙarya takeyi, amma sai baice mata komai ba har ya kammala. Gaba yay
ta bisa a baya....

Bata buƙatar zaman tunanin abinda ya shafi waninsu, dan haka tai connecting
bluetooth ɗinta ta manna a kunne. A hankali takai kwance bisa grass carpet dake a
ɗan ƙaramin garden ɗin dake bayan ɗakin aunty amarya tana lumshe idanunta cike da
nishaɗi, dan waƙar da take saurare tana matuƙar sonta, mawaƙin ɗan ƙasar malaysia
ne, waƙar ma anyitane da yaren malay sai dai an cakuɗa da turanci. Tayi nisa sosai
wajen sauraren waƙar fuskarta shimfiɗe da murmushi, ga idanunta a lumshe sanyin
inuwar wajen na ƙara girmama nishaɗinta, bakinta sai motsawa yake a hankali alamar
bin waƙar takeyi....
Jin ƙamshinsa ya ƙara ƙarfi cikin hancinta ya sata kasa cigaba da jurewa ta
buɗe ido a hankali batare da tabbacin mai ƙamshin bane a wajen. Sai dai kuma cin
karo da shi ɗin tsaye ya sakata ɗauke numfashi na wucin gadi. Da sauri ta tashi
zaune duk tana jinta a daburce, hijjab ɗinta dake gefe ajiye ta ɗauka ta rufama
jikinta dake sanye da wando three quarter da top ƙarama, zafine ya isheta ta sakasu
kasancewar a ɗaki take, sai da taji hayaniyar mutane zasu dameta ta sako hijjab
kawai ta fito, ganin babu kowa anan ya sata cirewa ta ajiye dan ta samu iska mai
ƙyau ta shigeta.
Rigarsa ya ɗan tattare sama ya zauna shima bisa grass carpet ɗin dake a
share tas dan aunty amarya kullum cikin kulawa take da wajen saboda tsananin son
garden da takeyi. Mace ce ƴar gaye mai son hutu da gudun yawan hayaniya. Duk da
Anam taji wani irin da zaman nasa wajen amma sai ta dake abinta. Sai dai ta kasa
cigaba da bin waƙar daketa maimaita kanta. Shima da tun zuwansa wajen baice komai
ba kallonta kawai yayi na wasu ƴan sakanni, sai kuma ya kai hanunsa kunnenta ya
zare bluetooth ɗin ya saka a nasa kunnen. Juyowa tai tana kallonsa da mamaki, ya
lumshe idanu ya buɗe tare da kauda su a kanta yana sauraren waƙar.........✍

_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_


*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾


ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:


07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇


0913484810_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_


*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:


07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇


09134848107 ko
[10/28, 11:42 AM] My Zafafa: *_Typing📲_*

*_BABU SO....!!_*
_(Miya kawo kishi?)_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718
*_20_*

.........“Waye mawaƙin nan?”.


Cikin shakku da mamakin ta kallesa. Ganin zai kallota tai saurin janye
idanunta a kansa, ta bashi amsa cike da basarwa.
Ɗan Murmushi yayi dan ya riga ya ganta. “Ya iya waƙa gsky, kuma cikin
nutsuwa da ma'ana”.
Itama Murmushi tai a karon farko tana dubansa. “Shiyyasa nake son waƙoƙinsa
sosai nima ai. Bashi da hayaniya, sannan duk abinda zai faɗa yakan dace da furicin
zuciyoyi”.
Tsareta ya ɗanyi da idanunsa, hakan yasa ta kauda nata. “Wane furucine ke
dacewa da ma'anar zuciyoyi?”.
A yanda yay tambayar tamkar mai raɗa ya sata juyowa ta sake kallonsa, sai kuma
ta janyesu har yanzu murmushinta bai ɓace ba. “Yaya bai zama lallai tunanina dana
kowa yazam iri ɗaya ba ai, zata iya yuwuwa nice kaɗai ke fassara haka ko fahimta a
lokacin da nakejin waƙoƙin nasa”.
“Uhhm nice. Kinga nima sai ki turamin maybe na fahimci irin taki fahimtar ko!
Ki samun duka waƙoƙin sa ta WhatsApp”.
“To ai bani da number ka”.
Cikin ido yake kallonta, ta risinar da nata dan bazata iya jurewa ba. Shima
sai ya ɗauke nasa ya maida ga tsuntsaye biyu dake shan ruwa a ɗan kaskon da aunty
amarya kan zuba dan su. “Baki so hakan bane shiyyasa baki da ita”.
Murmushi kawai tayi, amma batace komai ba, ta dai cigaba da kallon tsuntsayen
kamar yanda shima har yanzu idonsa na kansu. Shiru kusan mintuna uku, tashin
tsuntsayen ya sashi katse shirun nasu da faɗin, “Zanyi tafiya zuwa China, kuma zan
jima dan zan samu a ƙalla kwanaki ɗari acan ko ƙasa da hakan insha ALLAH”.
Mamakinsa ya sata ɗagowa ta dubesa, kasancewar nasa idon na kanta ya sashi
ɗan lumshewa alamar tabbatarwa... Bata da zaɓin daya wuce kaɗa masa nata kan itama.
“ALLAH ya tsare hanya, ya kuma bada abinda za'aje nema mai albarka. Ya tsareka daga
haramun, ya haɗaka da halal”.
Ajiyar zuciya yaja mai ƙarfi, har takai ta sake ɗagowa ta kallesa, murmushi ya
sakar mata, irin wanda zata iya rantsewa bata taɓa cin karo da shi a gareta ba. Ta
ɗanyi tsammm tana kallonsa, gaba ɗaya ganin al'amarin nasa take na yau kamar
almara. Lakace mata hanci da yay ya sata saurin ɗauke kai cike da kunyar kanta. Ya
ɗan murmusa yana gyara zamansa. “Zaki koma gidana k da Aysha ku zauna har na dawo”.
“What! Yaya ni ɗin?”.
A yanda tai maganar ya sashi kafeta da idanunsa sosai. “Bazakije ba kenan?”.
Fuska ta ɓata da tura baki gaba, “To ai ni dai kasan bama shiri da matarka”.
“Idan kikaje zama yanzu ai sai ku fara shirin kafin na har abada”.
Ba wani fahimtarsa tai sosai ba saboda da hausa yay maganar, amma sai ta girgiza
kanta. “No bazamu taɓa shiri da matar can taka ba. Dan nama kusa fara kai mata
naushi idan tana cigaba da min kallon banza. Karta ɗauka tsahonta da girman jiki
zai razana ni”.
Yanda take maganar cike da masifa da tsiwa ya bashi dariya sosai. Ya kauda
kai gefe yana murmushi. Kafin ya sake juyowa fuska a haɗe yana kallonta. “Matar
tawa zaki nausa?”.
Batace komai ba, sai dai ta sake tura baki gaba. Zaiyi magana ring ɗin wayarsa
ya dakatar da shi, Mommy ce, dan haka yakai kunne cike da ladab yay sallama.
“Kana ina ne wai Shareff? Ga matarka sai amai take anan duk ta galabaita kazo
kuje asibiti”.
“Ya ALLAH!”.
Ya faɗa a hankali yana lumshe ido. “Okay Mommy ina zuwa. Amma bara na kira
Jamal kin san yau weekend ne ba lallai mu samu yanda muke so a asibitin ba”.
“To ya hanzarta dan ALLAH”.
“Okay bara na kirasa ɗin”.
Koda ya yanke wayar kasa haƙuri Anam tayi, dan bata san wa akace baida lafiyar
ba. “Yaya waye za'a kai asibiti?”.
Yana ƙoƙarin kiran Dr Jamal ya bata amsa kai tsaye. “Fadwa ce keta amai
wai, duk ta galabaita”.
Sosai ta nuna jimaminta kasancewarta mutum mai tausayi. “Ayya ALLAH ya bata
lafiya, dama bata da lafiya kuma ka yarda ta fito Yaya?, ai da ka barta a gida
tunda kowa yasan ciwo”.
Numfashi ya ɗan furzar, rashin ɗaukar wayar Dr Jamal ɗin ta bashi damar
bata amsa. “Bawai kwance take ba, yanzu ma inaga taji ƙamshin abinda bata so ne
shine aman yazo”.
Kallonsa tai cikin mamakin amsar tasa, sai dai kafin tace wani abu kiran
Mommy ya katseta. Ɗagawa yay yana mikewa. “Mommy na kira bai ɗaga ba maybe baya
kus... Yauwa gashi ma yana kira ina zuwa”. Yankewa Mommy tai, shi kuma ya samu
damar ɗaga kiran Dr Jamal ɗin. Ya ɗan matsa da ga wajen Anam ɗin suna magana. Da
kallo ta bisa, sai kuma ta ɗan ɗage kafaɗa da ɗauke kanta cikin ɗan taɓe baki.
Hijjab ɗin da taketa faman ƙudundune jikinta ta warware ta sanya da ƙyau itama ta
miƙe da nufin komawa sashen aunty Amarya tai kwanciyarta kawai ko ɗan chart tayi da
ƙawayenta na Malaysia.
Ya gama magana da Dr Jamal ya juyo kawai ya hangota har takai ƙofar baya ta
kitchen ɗin aunty amarya. Idanu ya tsira mata harta ɓacema ganinsa. Ya ɗan ja
numfashi tare da barin wajen shima.

★★★

A sashen Mommy Fadwa sai sake langaɓewa take ganin yanda Mommy da Mamah suka
rikice. Dan itama Mamah (Gwaggo Haliman) tazo wajen saka ranar ta Maheer. A haka ya
shigo ya samesu zagaye da ita. Sai kawai ta fashe masa da kuka tana miƙa masa hannu
wai itafa yazo zata mutu. Cijewa yay yayi kamar baiga hanun da take miƙo masa ba,
koba komai ai sa raga dan iyayensu. Sannu yay mata tare da zama yana gaida Mahmah.
Cikin kulawa ta amsa masa itama. “Dama bata da lafiya ne haka Babana?”.
Ɗan duban Fadwan yayi ya janye idanunsa. “No Mamah bawai tana kwance bane,
kawai dai idan taji ƙamshin abinda bata so ne take amai, amma baima taɓa kaiwa
kamar na yau ba”.
Kallon juna Mamah da Mommy sukai, kowanne zuciya cike da son ƙarin bayani, sai
dai sun san ba lallai su samu daga Shareff ɗin ba bara kawai su jira zuwan Jamal.
Babu ko wani jimawa Jamal ya iso, Shareff ɗinne ya fita ya shigo da shi. Bayan ya
gaishesu ya ɗan yima Fadwa tambayoyi tana amsa masa da ƙyar. Da ga ƙarshe ya bata
tsinken gwaji.
“Inaga yi amfani da wannan mugani ko abinda nake zargi ne. In ba shi din bane
sai na ɗeba jininki”.
Mommy ce ta amsa, ta kamata suka shiga toilet ɗin nan cikin falo. Bayan wasu
mintuna suka kawo masa tsinken kamar yanda ya bukata. Murmushi ya saki yana mai
kallon Shareff cikin ido, ya ɗauke kansa da maidawa gasu Mommy. “To inaga ma basai
ta kaimu da gwajin jininba a yanzu-yanzun, dan abinda nake zarginne dai. Ko zuwa
monday zata iya zuwa asibiti ta sameni ALLAH ya inganta ya ƙara lafiya. Bara na
bata wannan maganin zai sa ta ɗan samu nutsuwa daga galabaitar da tai nayin aman”.
Sosai bakunan su Mommy yake a washe, yayinda su Hassan suka cika falon da
ihun murna suna faman rungume Fadwa. Shi dai uban gayyar tuni sun fice shi da Dr
Jamal, sai dai har cikin ransa yaji daɗi duk da ya jima da zargin hakan a ransa. Dr
Jamal ya sake masa Congrat, cikin tsokana yana faɗin, “Lallai abokina ka zama
namijin duniya, irin wannan bugu na daga kai sai mai tsaron gida haka. ALLAH ya
inganta mana”.
“Ɗan iska kaji da shi dai. Yanzu ina ka nufa?”.
“Gida ya kamata na koma, amma tunda ka kawoni nan nima bara naima tawa flower
ɗin barruwa”. Ya ƙare maganar yana laluben number Anam. Sarai Shareff ya fahimcesa,
dan haka baice komaiba sai ma basar da zance yay kamar baiji ba. Kusan sau uku yana
kira ba response, ya ɗan ɗage kafaɗa yana duban Shareff. “Musty inaga yarinyar nan
bata kusa da wayar. Bara kawai na wuce na dawo taɗin dare. Yaushe ne tafiyar taka
jibin?”.
“Zan wuce da safe ne dan zan fara shiga Abuja, da ga can zan wuce”.
“Okay to da yamma zan shigo gida insha ALLAH”.
Sallama sukai ya wuce, shi kuma ya koma wajen su Mommy da suka dasa sabuwar
tarairaya ga Fadwa.

Dawowar ƴan kai kaya da saka rana ta sake baje labarin cikin Fadwa a gidan.
Kowa sai sambarka da fatan saukarta lafiya yake. Gwaggo harda ƴar rawarta. Shi dai
Shareff tuni yama bar musu gidan, sai yamma ya dawo suka fita salla da su Daddy.
Bayan sun dawo ma tare da su yaci abinci. Ya ƙara tattauna batun tafiyarsa da su,
daga karshe suka sakko masa zancen matarsa fa? Nan zata dawo da zama ko gidansu
tunda dama ba daɗin jikinta take ji ba dan suma labarin ciki har yazo musu.
Ajiyar zuciya ya ɗan sauke. Kansa a rissine yace, “Da dai tayi zamanta kawai
acan ɗin, nayi magana da Khaleel zai koma kwana acan, Aysha da Anam sai suje suma
su tayata zama tunda bawani abu suke anan ɗin ba”.
Abba dake murmushi yace, “Hakan ma yayi to. ALLAH ya baka sa'ar abinda
zakaje dominsa. Ya kuma dawo mana da kai lafiya”.
Da amin suka amsa shi da Daddy. Daga haka suka cigaba da tattauna wasu
batutuwan daya shafesu da kuma tafiyar tasa.

★★★
Anam bata san mike faruwa akan komawarsu gidan Yaya Shariff ba sai washe gari,
dan bata wani bama maganarsa ta jiya muhimmanci ba. Koda taji batun cikin Fadwa
kuma batace komai ba. Tadai saka albarka a sa ranar Maheer da akace wata huɗu.
Da yamma ta dawo aiki Mom ke sanar mata ta haɗa kayanta ita da Aysha zasu je
su taya matar Shareff zama kafin ya dawo. Cikin waro idanu da mamaki take duban
Mom. “Mom ni kuma? Kin san fa yanda matar nan tabi ta tsaneni ga Gwaggo da Mommy da
Mamah a gefe...”
“Anam duk na kawoma Abbanku irin wannan misalin, amma ya nuna min sun riga
sun gama yanke hukunci. Kinga sai kibi umarninsu kawai ALLAH ya kaɗe
fitina”..iyayenmu😭🙏🏻_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_


*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:


07040727902
IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇
09134848107

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*


[10/28, 11:42 AM] My Zafafa: *_Typing📲_*

*_BABU SO....!!_*
_(Miya kawo kishi?)_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718

*_21_*

......Sosai Anam taji kamar ta fashe da kuka. Sai dai bata iya jayayya ba. Dan haka
tabi umarnin Mom bayan tayi wanka taci abinta ta haɗa kayan da basu wuci kala
bakwai ba, sai abinda ba'a rasa ba. Dan tanajin da wahala zamanta yay nisa a gidan
basu kwashi ƴan kallo da Fadwa ba. Aysha ce ta shogo, ganin ƴan kayan data haɗa
tace bata isaba. Canja jakkan kayan tai zuwa babban akwatinta, ta dinga ɗibo kaya a
wadrobe tana zubawa, duk da dakatar da ita da Anam keyi taƙi saurarenta, dan harda
kayan da aka ɗinka mata da ko sakasu ta kasa farayi har yanzun. Aysha da taƙi
saurarenta taja a kwatin tana faɗin, “Yaya har yazo, kiyi maza ki kammala kin san
sa da azalzala”.
Harara ta wulla mata batare data amsaba. Aysha ta fice tana dariya. Dole
itama ta miƙe ta karasa kimtsa abinda ya rage mata. Sannan ta fito yima Mom
sallama.

A can ɓangaren Mommy sai yanzu tasan harda Anam za'a zauna gidan Shareff. Ranta ya
ɓaci, dan haka kai tsaye tace bata aminceba in har itace ta haifi Shareff. Shi dai
baice komai ba, sai Daddy ne yace bata isaba, idan kuma tai wasa zai matuƙar ɓata
mata rai ne. Ganin sunata cacar baki Aysha taje ta sanarma Gwaggo duk da tasan
itama ɗin dai sai a hankali ce. Dandanan ko sai gata tazo, da yake Aysha ta faɗa
mata abinda ke faruwa koda tazo sai ta goyi bayan Daddy akan tabar Shareff ɗin ya
wuce dasu Aysha dare nayi, ai zaman Anam ɗin acan ba komai bane. Rai ɓace kuma
cikin mamaki Mommy take duban Gwaggo. Gwaggo ta kyafta mata ido alamar kartaji
komai ta sallama. Shiru tayi kawai amma har sannan ranta na mata suya, sai dai tama
ƙagara su tafin taji dalilin Gwaggon nayin haka.
“Kai tashi ka ɗaukesu ku wuce dare nayi”. Daddy ya faɗa yana duban Yaya
Shareff da kamar bashi a falon. Mikewa yay kuwa yay musu sallama. Aysha tabi
bayansa suka fice. Bai shiga kowane sashe ba, dan zai dawo da safe musu sallama
kafin ya fice tunda bada sassafe zai wuce ba Khaleel ne ma zai kaishi airport. Suma
su Ayshan dan yana son suje tun a yau ne ya haɗasu da Fadwa yay musu gargaɗi tunda
yasan da gaske za'a dinga samun saɓani ne tsakanin Anam da Fadwa. Aysha ce ta shiga
ta kirawota.
Doguwar riga ce jikinta mara nauyi, sai ƙaramin veil data yana a kanta.
Tana riƙe da ƙaramar jakar data haɗa kayanta na ciki da Aysha bata kwaso ba saboda
sauri. Ta gaida sa batare data kallesa ba. Ɗauke kansa yay yana amsa mata, tare da
buɗe motar ya shiga. Aysha tai wuff ta shige baya, zata shiga itama ya hararesu.
“Dalla malamai ni drivern ku ne?!”.
Aysha ta tura Anam dake ƙoƙarin shigowa. “Blood kefa na barma can ki shiga”.
Baki ta buɗe zatai magana ya juyo a fusace. “Bana son shashanci fa, kuna ɓatamin
lokaci”. Hararar Aysha dake mata gwalo tayi, batare da tace komai ba ta zagaya ta
shiga gaban ta zauna. Motar yayma key ya fice bayan sunyi sallama da maigadi.
A hankali yake driving ɗin kamar baya so, motar shiru babu mai ko motsin
kirki. Dan ita Anam ma har ta fara gyangyaɗi kasancewarta mai barcin wuri musamman
idan waje da sanyi. Yanzu kam sanyin acn ke ɗibarta dama ga gajiyar aiki. Karatun
alkur'ani ya kunna har suka iso, gidan shiru kamar babu kowa, sai maigadi dake
sauraren taskar labarai a redio. Yayma uban gidansa sannu da zuwa bayan ya buɗe
masa gate.
Shi da kansa ya fiddo musu akwatinsansu a booth, Aysha taja ɗaya tana turama
Anam ɗaya. Hamma tayi cikin ɗan layin barci ta jingina da motar tana dafe akwatin.
Ita da akwatin yayma kallo ɗaya ya ɗauke kai, batare da yace komai ba ya sama motar
lock da key ya ja akwatin yay gaba. Baki taɗan tunzura sannan tabi bayansu cikin
ɗan layin barcinta.
Basu sami kowa a falon ba, hatta da tv a kashe take, Aysha ta kallesa cikin
zumuɗi tana faɗin, “Yaya Aunty Fadwa fa?”.
Gitta ta yay kamar bazai amsa ba, sai da ya kai akwatin ƙofar ɗakin da
zasu zauna ya juyo. “Maybe ta kwanta, na barta kanta na ciwo”.
“Ayya ALLAH ya bata lafiya”.
Amin ya faɗa kan laɓɓa idanunsa akan Anam data zauna a hannun kujera ta kwantar da
kanta dan da gaske barcin takeji. “Ki tadata kuje ku kwanta kuma kawai”.
“Okay Yaya sai da safe”.

Kasancewar tayi wankanta tayi salla tun a gida suna shiga ɗakin ta faɗa kan gado
tai kwanciyarta, addu'a ma sai Aysha ce ta mata tana mintsininta cikin tsokana da
kiranta kasa anji sanyin ac. Hannunta ta buge, ta juya taci gaba da barcinta.

________________★

“Gwaggo nifa wlhy duk kin sani a duhu. Ko kin mance wai yarinyar nan ce dana
tsana ita da iyayenta fiye da komai a rayuwata”.
Murmushi Gwaggo tai irin na makircinsu na tsoffin hannu. Ta dafa kafaɗar
Mommy. “Daɗina dake gaggawa. Kema kin san bazan amince da zamanta can ba in babu
wani abu a ƙasa. Dan haka kwantar min da hankalinki da safe zakiji komai...”
“Miyasa ba yanzuba Gwaggo?”.
“Saboda idon mijinki yanzu akanmmu yake.” Kai kawai ta jinjina badan taji sauƙi a
ranta ba. Gwaggo tai mata sai da safe ta fice tana murmushin da sam Mommy ta kasa
fassarashi a kowane mizani....

*_WASHE GARI_*

Shine ya musu knocking ƙofa da zai wuce massallaci da asuba, sai da ya tabbatar
sun tashi sannan ya fice. Ana idarwa gida ya dawo, azkar ma sai da ya zo yayita a
gida bayan ya sake tada Fadwa dake barci duk da ya tadata kafin ya fita amma bayan
fitarsa ta koma ta kwanta. Tana mitar ita har yanzu kanta ke ciwo ta nufi bayi tayo
alwala. Bai tanka mata ba harta zo ta kabbara salla. Bayan ta idar ta tashi ta koma
gadon, a jikinsa ta lafe tare da sumbatar laɓɓansa. “Good Morning my Soulmate”.
“Good morning wife ykk ya baby?”.
Murmushi tai da kamo hanunsa ta ɗaura kan cikinta, murya cike da shagwaɓa
tace, “Gashi har ya fara kewar Daddynsa”. Murmushi ya saki a karon farko, ya
sumbaci laɓɓanta shima. Cikin ɗage mata gira ɗaya yace, “Nima cike nake da kewarsa
shi da mamansa. Amma karya damu bazan jima ba zan dawo garesa insha ALLAH”.
Rungumesa tai sosai, tare da fara bashi wasu zafafan salon da ya sashi biye mata.
Bayan komai ya lafa tana kwance a jikinsa idanunsa a lumshe ya kirayi sunanta.
“Uhhyim”.
Ta amsa tana ƙara ƙanƙamesa. Cigaba yay da shafa kanta har yanzu idanunsa a rufe.
“Jiya nazo da su Aysha da zasu tayaki zama. Koda wasa bana son jin wata fitina. Ki
riƙe girmanki da mutuncinki. Idan naji wata fitina kezan fara hukuntawa matsayinki
na babba”.
“Insha ALLAH babu abinda zai faru, Ayshan ita da Hussaina ne?”.
Kansa tsaye yace, “Da Anam”.
Baima gama rufe baki ba ta miƙe zumbur zaune. Shima sai ya buɗe idanu yana
kallonta. Kai take girgiza masa hawaye na ciko mata ido... “Ni gaskiya bazata
zaunamin gidaba, taje kawai Aysha ta isa”. Idanunsa ya kauda yana tashi zaune ya
jingina da fuskar gadon. “Karki ɓatama kanki rai a banza. Juwairiyya da Aysha zasu
zauna tare dake, shima Khaleel anan zai dinga kwana....”
“Bazai yuwu ba”.
“Sai ki hanasa yuwuwar mu gani tunda gidanki ne”. Ya faɗa a fusace yana sauka a
gadon. Da sauri ta yayibi bedsheet ta sakko tana ƙudindine jikinta a ciki tasha
gabansa. “Dan ALLAH ka tsaya muyi magana. Wlhy iya gaskiyata nake gayama na tsani
yarinyar nan bazan iya zama inuwa ɗaya da ita ba har abadan dan zan iya halaka ta”.
Sosai yake kallonta cikin tsakkiyar ido. Ya riƙe ƙugu da dukkan hannayensa yana
ƙoƙarin danne fushinsa. “Zaki iya halaka ta? To sai dai in ki halakata ɗin, dan
babu fashi zata zauna anan tunda ba dake na haɗa kuɗin na gina gidana ba. Ki bari
mu rabu lafiya Fadwa!!..” Ya ƙare maganar cikin tsananin zafin rai ya ɗan banjajeta
ya ficewarsa.
Zubewa tai a wajen ta fashe da kuka. Itakam ta shiga uku wannan shegiyar
yarinya ta zamewa rayuwarta jaraba. Wayarta ta ɗauka tai kiran Mahmah, sai dai kuma
a kashe, Mommy ta kira, bugu ɗaya ta ɗauka. Ko sallama babu balle gaisuwa ta fashe
mata da kuka tana faɗa mata ita dai inhar da Anam zata zauna to sai dai ta koma
gidan su. Sai da ta gama surutanta sannan Mommy tai magana..
“Fadwa na fiki shiga ɓacin rai da zaman wannan yarinyar anan gidan, dan a
daren jiya banyi barcin kirki ba saboda baƙin ciki. Amma ina son ki kwantar da
hankalinki Gwaggo tace tanada plan akan zaman nata....”
“Mommy Shi plan ɗin baza'a iya aiwatar da shi tana nan ba dole sai ta raɓu da
gidana?”.
“Nima na faɗa miki ba son hakan nake ba. Amma mu saurari mi Gwaggon zatace zuwa
anjima. Yanzu dai ki daure ranki ku rabu lafiya da mijinki bayan ya tafi anjima
kaɗan zan zo gidan ai”.
“Mommy....!”
“Kiyi yanda nace”.
Mommy ta tari numfashinta a fusace tana yanke wayar, dan ƙara hasalata Fadwan take
ma..........✍

_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_


*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:


07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇


09134848107
[10/28, 11:42 AM] My Zafafa: *_Typing📲_*

*_BABU SO....!!_*
_(Miya kawo kishi?)_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718

*_22_*

.........Kiran Gwaggo ne ya shigo tamkar tasan mike faruwa. Kamar bazata ɗagaba sai
kuma ta ɗaga. Tai shiru taƙi magana. Ban san mi Gwaggon tace daga canba ta tunzura
baki da faɗin, “Naji ina kwana”. Amsawa Gwaggo tai daga can sannan ta shiga gaya
mata abinda yasa ta kirata. Ajiyar zuciya Fadwa ta saukea hankali da fara share
hawayenta. Kamar tana a gaban Gwaggo ta jinjina kanta da yin ɗan murmushi tana
mikewa bayan ta yanke wayar. A gurguje ta faɗa banɗaki tayo wanka, ko busar da kan
batai zaman yi ba ta saka hula da doguwar riga ta fice. Kitchen ta shiga, ta dafa
shayi da soya kwai ta haɗa kayan a tray. Sashesa ta nufa, dan dama jiya ya kwana a
sashenta ne saboda ta ya buƙaci hakan. Babu kowa a falon, ta ajiye tray ɗin a
centre table ta nufi bedroom ɗinsa. Shigowarta dai-dai da fitowarsa wanka. Yay mata
kallo ɗaya ya ɗauke kansa. Zuwa tai ta rungumesa tana kwantar da kanta a gadon
bayansa. “Kayi haƙuri mijina na tuba, na fahimci nayi kuskure bazan sake ba”.
Shiru kamar bazaice komai ba, dan yasan wannan ba kalaman Fadwa bane wanine
ya bata su akan harshe. Sai dai kuma shi ba mutum bane mai son zurfafa zargi, dan
haka ya kamo hanunta ya zagayo da ita gabansa. Idanu suka ƙurama juna, sai faman
sakar masa murmushi take, shiko tasa fuskar kadaran kadahan. “Nace fa kayi haƙuri".
Ta faɗa cike da shagwaɓa tana girgiza masa hannu. Cikin ɗan turo numfashi waje
yace, “Okay fine ya wuce”. Rungumesa tai, kafin taja hanunsa zuwa gaban mirror. Da
kanta ta shafa masa man a jiki tana masa duk wani salon kwarkwasa dazai sashi cire
komai a rai kamar yanda Gwaggo tai mata huɗuba. Ta ɗan samu ya biye mata badan
komai ba sai dan yana son su rabu lafiya. Yayi ƙyau cikin kananun kaya ga ƙamshi
data feshesa da shi na tashi suka fito falo. Zama yay idonsa akan breakfast ɗin
data ajiye....
“Inaga ki kirasu mu karya gaba ɗaya, dan ina son nayi magana da ku”. Kamar
zatai gardama sai kuma ta haɗiye, cikin taushin murya tace, “Amma ƙwan iya naka na
soya anan fa”.
Yanda ta amsa ɗin shima ya sashi tausasa nasa harshen dan yana son su rabu
lafiya. “Kiyi haƙuri ki soya musu suma, dan yau tamkar baƙi suke anan”. Maganar
Gwaggo tasata amsawa, sai kuma sanin halinsa. Juyawa tai ta fita a sashen gaba
ɗaya, ya bita da kallo harta fice. Mintunan da basu gaza goma sha biyar ba ta
kammala soya ƙwan ta leƙa ta kirasu batare data yarda tako dubi sashen da Anam take
ba. Itama dai Anam ɗin bata ko kalleta ba sai Aysha ce ta gaidata da tasowa ta
rungumeta. Anam ta taɓe baki da sake juyar da kai tamkar bata gansu ba.
Su suka fara shiga falon ita kuma tana biye da su a baya. Yana zaune a
inda ta barsa, sai dai yanzu waya ce a hanunsa. Koda ya amsa musu sallama kuma bai
ɗago ba.
“A haɗa a dining ne?”. Ta faɗa tana kallonsa. Ɗan ɗagowa yay ya kalleta ya
maida kansa, “No barsa mu zauna nan zaifi balance”. Kai ta jinjina masa. Aysha da
Anam suka shiga gaishesa. Ya amsa musu da ɗan sauƙaƙa murya batare daya dubi
kowacce a cikinsu ba. Saboda kar Anam ta zauna a kusa da shi Fadwa tai saurin jan
hanun Aysha ta zaunar, sai ya zam sun sakashi a tsakkiya, ita kuma inda Anam take
zaune sai yazam sunyi facing juna ita da shi. Haka kawai taji abun ya bata dariya,
dan tana lura da sanda Fadwa taja hanun Ayshan. A zuciyarta tai dariya, a zahiri
kam babu ɗigon fara'a a fuskar tata.
Aysha ta haɗa mata shayin da ajiye mata gabanta dan taƙi taɓa komai, a
hankali tace mata ‘thanks’. Ba wani iya cin komai tai sosai ba har yanzun, dan haka
koda Aysha tace a saka mata ƙwai kanta ta girgiza mata da nuna mata bread ya isa.
Ɗagowa yay suka haɗa ido, lokaci ɗaya tsigar jikinta ta tashi. A hankali ta janye
idanunta daga cikin nasa, shima nasan ya janye batare da yace komai ba. Fadwa kam
bama ta nuna tajisu ba, sai Aysha ce tace “K kullum a baki iya cin abu ba bazaki
koyama kanki ba?”. cikin yin ƙasa da murya tace, “Ni bana sonsa ne fa”.
“To k dama indai abinci ne ai komai bakya so”.
Hararar Ayshan tayi, batare da ta sake cewa komai ba ta cigaba da juya cokali a
shayin tana tsakurar bread ɗin. Ɗagowa kam bata sake yarda tayi ba balle ta haɗa
ido da shi har suka kammala. Ita da Aysha suka tattare wajen, suka kwashi kwanikan
zuwa sashinta. Kasancewar yace su aje su dawo basu ɓata lokaci ba suka koma. Fadwa
suka samu zaune a jikinsa, shigowarsu kuma bai sa ta jaye ba, sai shine yay mata
nunin ta zauna da ƙyau da ido. Ganin yanda fuskarsa take babu wasa yasa ta matsawa
sai dai ranta bai so haka ba. Oho wadda take dan itan ma bata san tanai ba, dan
koda suka shigo Anam bata yarda ta kalli ko sashen da suke ba. A ƙasa suka zauna,
ya fara addu'ar da MANZON ALLAH yace muyi a duk sanda muka samu kammu a irin
makamancin zama haka kafin ya ɗaura da nasiha a garesu, da ga ƙarshe ya ƙare da
gargaɗi mai cike da kurarin tabbatar musu in har yaji wani abun ɓacin rai daga
garesu su duka ransu sai ya ɓaci, kowacce ta kama kanta, su su girmama matarsa a
matsayinta na Yaya a garesu kuma matarsa, itama ta riƙesu a matsayinsu na ƙannenta
kuma ƴan uwansa. Daga ƙarshe ya rufe da jawabin zaman Khaleel a gidan, sai dai shi
kwana kawai zai ringa zuwa yayi sai kuma cefane da duk wasu buƙatun gidan su
nemesa. Daga haka ya sake rufe taron da addu'a yana miƙama Anam kuɗi, kamar tace
a'a amma sai ta amsa tayi godiya, itama Aysha kamar na Anam ɗin ya bata. Cike da
zumuɗi ta amshe abinta tai godiya, daga nan ya sallamesu.

Koda suka koma ɗaki Anam kwanciyarta tai tunda yau babu fita aiki, Aysha
kam tai zaman lissafa kuɗinta dayin budget ɗinsu cike da farin ciki duk da dubu
goma ne kawai. Barcinta da yay nisa ya saka har Yaya Shareff yabar gidan bata sani
ba, koda Aysha ta fito masa rakkiya wajen mota dan da Fadwa zaije har airport cike
da makirci Fadwan ke tambayar ina Anam. Aysha tace, “Barci take aunty ko'a taso
ta?”. “A'a ki barta kawai kar'a tadata kanta yazo yana ciwo ko”. Duk yana jinsu,
sai dai baice komai ba. Sai da Aysha taga fitar motar tasu sannan ta dawo itama ta
kwanta dan barcinne a idonta.
A gidan su yaja kusan awa biyu, yay sallama da kowa sannan Khaleel ya
ɗaukesa shi da Fadwa zuwa airport, basu wani jima suna jiraba jirgin da zai kaisa
abuja ya keta hazo. Khaleel ya ɗakko Fadwa dake hawaye yana mata ƴar dariyar tsonar
shagwaɓar tata. Ganin ya nufi hanyar maidata gidanta tace ita dai ya kaita can
gidan zata ɗauka abu wajen Mommy, idan ma yanada wani uzirinne ya barta zata maida
kanta gida kawai. Bai ƙiba ya canja hanaya.

Duk yanda Mommy da Fadwa suka so ayi maganar zaman Anam ɗin Gwaggo tace ba
yau ba, ransu yaso fara ɓaci, sai dai Gwaggo ta nusar da su gaggawa ba tasu bace.
Ita dai ta koma gidanta koda wasa karta nuna rashin son zaman Anam ɗin a gidan daga
nan har zuwa sanda zata sanar musu abinda ta ƙulla. Fadwa bawani ta gamsu bane, dan
haka batama gama sauraren Gwaggon ba ta figi handbag nata tai ficewarta. Duk da
kallo suka bita, Gwaggo ta taɓe baki tana duban Mommy.
“Idan baki tashi tsaye akan wannan surukar taki ba to lallai ina tabbatar
miki nan gaba kaɗan sai tasha kanki. Dan hatsabibiyar yarinyace da kanta kawai ta
sani, halinta dana uwarta bashi da banbanci”.
Wani bahagon numfashi Mommy taja da ƙarfi tana duban Gwaggo tamkar mai son
samo ƙarin bayani akan fuskarta, Gwaggo ta taɓe baki tana miƙewa. “Kinga ni jeki
kafin mijinki da shi bai rabo da zargi yasan kina nan, nima kwanciya zan ɗanyi
barci bai isheni ba jiya da dare”. Da kallo kawai Mommy ke binta hartai shigewarta
bedroom. Itama tashin tai cike da rashin zaɓi ta fito dan tasan Gwaggon tayi hakane
dan gujema kowace irin tambaya daga gareta.
Gwaggo dake laɓe jikin ƙofa tana leƙen Mommy ta taɓe baki, cikin ƙara yamutse
fuskarta da tsufa ya gama nuna kansa tai murmushi mai cike da ma'anoni masu yawa da
fahimtarta sai dai ALLAH.

(Mi tsohuwar ga ke ƙullawa ne🙀🙀?)

★ A ɓangaren Fadwa kam maimakon gidanta sai ta nufi gidansu, dan ranta gaba
ɗaya a mugun ɓace yake, ta tabbatar idan ta koma gidanta a haka tofa tanayin
sallama jibgar Anam ce zata biyo bayanta. Mamah (Gwaggo Halima) batai mamakin
ganinta ba, saboda babu jimawa suka gama magana da Gwaggo a waya, sai dai su
dukansu babu wanda yay tunanin nan Fadwa ɗin ta taho. Hasalima kiranta take son yi
sai gata. Kuka ta fashema Mamah da shi, dan haka ta tsaya tana kallonta kawai.
“Wlhy Mamah sai dai na dawo nan da zama inhar akace sai ta zauna min gida.
Ai dama tun farko haka mukai da shi zan zo nan na zauna har sai ya dawo, amma yana
zuwa can gidan aka canja masa tunani, ni na gane Mommy da Gwaggo duk bakinsu
ɗay.....”
“K bana son shashanci, ke ko Fadwa wai sai yaushe ne zakiyi hankali ne? Idan
an faɗa miki ki dinga saurara..”
“Mamah dan baki san abinda ke faruwa bane fa, baƙar yarinyar can ɗiyar wancan
mutumin na Malaysia fa aka kawo wai su tayani zama gida ita da Aysha. Na nuna masa
ban yarda ba yana neman min azaba da masifarsa. Na faɗama Mommy amma Gwaggo ta nuna
wai tanada shiri. Wane shiri gareta? Na fahimci tsohuwar nan bata sona kawai
yanzun...”
“Fadwa!!”
✍🏻
Mamah ta katseta a tsawace. .......

_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_
*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_


*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:


07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇


09134848107
[10/28, 11:42 AM] My Zafafa: *_Typing📲_*

*_BABU SO....!!_*
_(Miya kawo kishi?)_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718

*_23_*

.........“Anya ƙwaƙwalwarki na aiki da ƙyau kuwa? Kin san wacece Gwaggo a wajen mu?
To muna mata kallone tamkar mahaifiya, domin tana bamu dukkan gata irin na uwa tun
mahaifiyarmu na raye. Su kansu su Yaya da suke mata wani abun a yanzu babu abinda
ke ɗawainiya da su sai asiri da ƴan uba sukai musu saboda su basa samun koda sakin
fuska daga gareta, sai dai Alhmdllhi na gagara a garesu, ƴan uwana ma zan dawo da
su hanyar da aka kautar dasu. Bari na tuna miki idan kin manta, shi wannan auren da
kike takama da shi Gwaggo ce tai ruwa tai tsaki akan kowa har shi Shareff ɗin da
uwarsa, dan haka kisa hankalinki waje guda, na tabbata tunda tace mu bata lokaci
akwai abinda take shiryawa. Kema ina so ki kwantar da hankalinki Fadwa, kinga bake
kaɗai bace ba, ba'a bukatar duk wani tashin hankali daga gareki yanzun, indai
matsalar ƴar Usman ce dake gidanki, ki bamu ƙankanin lokaci, ba gidanki kawai ba,
Nigeria gaba ɗaya zata bari, barin da har abada bazata sake waiwayowa ba ita da
iyayenta. Sai dai hakan bazai faru ba har sai kin haɗiye komai yazama ba komaiba,
inba hakaba tashin hankalinki na nufin samun cikar burin Usman na ganin ya nanama
Shareff ita ya aura.....”
Wani mugun tari ne ya sarke Fadwa, sai da Mamah ta bata ruwa tasha, hawayena
sharara a fuskarta. “Mamah dan ALLAH kar kimin baki”. “Ba baki nake miki ba Fadwa,
mun jima da fahimtar ƙudirin Usman na son haɗa auren ƴarsa da Shareff, a yanda su
Yaya suka canja kuma komai zai iya faruwa idan har ya fiddo buƙatarsa a zahiri.
Shiyyasa muke son amfani da zamanta a gidan naki tunda mijinki bayanan mu mata
abinda zatama bar ƙasar gaba ɗaya har uban nata bazai sake sha'awar zuwa ba balle
tunanin ƙulla wata alaƙa damu”.
A hankali Fadwa ta sauke ajiyar zuciya. “To amma Mamah bana ƙaunar ganin
yarinyar nan wlhy”. “Haka zaki daure na ɗan lokaci ne, kiyi kamar ma baki san da
zamanta a gidan ba, dan so muke ta saki jiki sosai saboda shirinmu yay tasiri”. Har
cikin rai bawai ta gamsu bane, dan ba ƙiyayyar wasa takeji a zuciyarta akan Anam
ba. Dan kamar an raini zuciyarta da tsanar iyayen Anam ne tun tana ƴar karamarta,
hakanne yay tasiri matuƙa tare da cakuɗuwa da kishi ya nunku akan Anam ɗin, dan ko
yaya Amrah kan samu sassauci a wajenta duk da itama ba sonta take ba kamar yanda
bata son mahaifiyarsu. Sosai Mamah ta zauna ta kara lallashinta da maganganu masu
daɗi har ta ɗan huce, kwanciyarta tayi anan sai washe gari ta koma gidanta da
yamma.

Aysha kawai ta samu, Anam bata dawo aiki ba. Itama Ayshan ƙin sake mata tayi, sai
daga baya kuma mitagani oho mata saita fara janta da hira da tambayar jiya basuji
tsoroba dai ko su kaɗai. Aysha bata da saurin fushi, duk da tsumewar da Fadwa ta
shigo tana mata sai bata ɗaukesa komai ba. Kanta tsaye fuska da murmushi ta shiga
bata amsar basuji ba saboda Yaya Khaleel yazo da wuri, shine ma yake sanar musu
bazata dawio ba sai gobe. Murmushi kawai tai, daga haka ta canja hirar.
Sai kusan ƙarfe bakwai Anam da Khaleel suka shigo, da alama bayan sun tashi
aiki can gidan ya wuce da ita, sai da ya gama kimtsowa suka taho tare. Yanda Fadwa
bata kulata ba. itama sai batabi takanta ba tai shigewarta ɗaki ta barsu suna
gaisawa da Khaleel, tanaji suka zarce da hira bata fitoba sai ma tai kwanciyarta
dan dama taci abinci wajen Mom abinta. Har tai barci Aysha bata shigo ba, sai da ta
farka ta ganta kwance, dama Aysha a ƙasa takeyin kwanciyarta dan Anam bata iya
barci ita da wani a gado, shiyyasa a ranar farko tai kwanciyarta a sofa, ganin
hakan yasa Aysha jiya tace ta hau gadon ita zata kwanta a ƙasan dan Anam ɗin kasa
barci tai. Alwala tayo tai nafilfilinta sannan ta dawo ta sake kwanciya.
Koda sukai sallar asuba bata koma ba, shirin fita aiki tai har Aysha na mitar
sammakon nata bata dai kulata ba. Lokacin da suka fice ita da Khaleel Fadwa bata
fito ba ma. Sai mai aikinta da jiya tazo da ita daga gidansu ce keta faman aikin
gyaran falon.....

________________________★

Yau kwanakin Shareff biyar kenan da wucewa ƙasar China. A zahiri


tsakanin Anam da Fadwa babu mai shiga harkar wani. A baɗini Fadwa ta kasa jin zata
haƙura da jiran shirin su Gwaggo. Dan kuwa kullum jin ƙarin tsanar Anam ɗin take a
ranta musamman idan tana waya da Shareff ya tambayeta lafiyarsu. A yanzun ma har
faɗa sukai dan yace taba su wayar su gaisa tace Aysha kawai zata bama wayarta banda
Anam. Ya tambayi dalili tace saboda Anam ɗin bata isa ba.
“Nasihar dana muku kafin na taho bata shigaba kenan? Fadwa miyasa kike son
kawo min raini ne akan duk abinda na sharɗanta miki?”.
“Ni laifina kawai kake gani ita bazaka bincika mitaiba. Yarinyar nan tunda tazo
gidan nan sai dai taci ta kwanta tai wanka ta fita. Ko gaidani batayi, kai kallo ma
ban isheta ba ina matsayin matar gidan. Ya kake so nayine Soulmate? Sai naita binta
tana jana a ƙasa duk da ina sama da ita? Ai Aysha ba haka takeba, zata zauna muyi
hira ta taya mai aiki aiki, kai kullum ma itace mai mana abinci, finta tai a gidan
da ita bazata zauna ayi da ita ba. Shiyyasa tun farko nace ban yarda ta zaunamin
gida ba amma kaƙi saurarata....”
Ƙittt ya kashe wayar, hakan ya sake harzuƙa zuciyarta sai kawai ta fashe da
kuka. Kuka taci har ta gode ALLAH. Tana cikin kukan sai gasu Sima tamkar an jehosu
gidan har su huɗu. Anam na baranda zaune tana karatu suka wutota. Yanda basu mata
sallama ba itama ko kallonsu batai ba dan ta gane Sima. Turus sukai suna kallon
Fadwa da duk ta koɗe ta fita hayyacinta a kwana kaɗan, dama sun bar ganin posting
ɗinta ne gaba ɗaya shiyyasa sukazo suga ko lafiya, dan bata cika zama gwanar kiran
waya ba ita dama, ko kiranta kai sai ta gadama take ɗagawa.
“Baby Fady kina lafiya kuwa?”.
Cewar Siyyah da tun randa suka kawo Fadwa ɗin bata sake tako gidan ba sai yau.
Komai batace ba, sai wasu hawaye da suka sake gangaro mata. Da sauri Amal takai
zaune kusa da ita ta rungumota jikinta tana shafa bayanta cike da lallashi, kusan
mintuna uku Fadwa ta fara sauke ajiyar zuciya, hakan yasa Amal ɗagota. Tissue Sima
ta ɗibo ta miƙa mata, babu musu ta amsa ta share hawayenta. Bibah da tunda suka
shigo batace komaiba sai yanzu ta kalla Fadwa. “Baby Fady kinsa duk jikinmu sanyi,
badai namijine ya fara nuna miki butulcinsu na cin moriyar ganga a yada kaurenta
ba, kin ganki kuwa duk kin wani yamutse kin fita a kamaninki kamar wata mai ƴaƴa
huɗu”.
Baki ta buɗe zatai magana turaren ɗaya daga cikinsu dake ta faman hawa mata
kai ya sata tashi da gudu tai toilet. Da kallo duk suka bita, sai da ta fara
kakarin amai ne suka mike a zabure suka rufa mata baya. Da taimakonsu ta wanke
bakinta, Sima na yatsine-yatsine ta gyara wajen.
“Tabɗi babbar magana. Da alama dai Baby Fady cikine da ke”. Siyyah ta faɗa cikin
riƙe baki. Sima ta ƙarɓe zancen da “Wane irin ciki kuma ana zaune ƙalau
Shamsiyyah?”.
Fadwa da ta fahimci turaren Bibah ne ke hawa mata kai hanunta toshe da
hancinta tace, “Bibah turarenki ne matsalata wlhy, buɗe Wadrobe ki ɗau wasu kayan
ki canja a fidda waɗan nan karki kashen.....” bata karasa ba aman ya sake tahowa
dole da sake mikewa da gudu tai bayi. Yanzu kam yi sukai kamar bazasu bitaba, sai
daga baya cikin ƙunkuni Sima tabi bayanta ta taimaka mata. Kodan karsu cigaba da
bautar kwashe amai dole suka takurama Bibah ta tashi tai wanka ta canja kaya. Daga
haka aka samu sauƙi hankalin Fadwa ya samu nutsuwa harta kira mai aikinta ta kawo
musu abinci da kayan ciye-ciye. Ta tambayi Aysha fa? Tace barci take. “Bakar
yarinyar nan fa?”. “Ranki ya daɗe tana waje tun ɗazu kamar karatu dai take”. Baki
Fadwa ta tabe, cikin bada umarni tace rufemin ƙofar falo bana bukatar shigowarta
har sai ƙawayena sun wuce”. “Okay ranki ya daɗe an gama”.
Bayan fitar mai aiki su Sima suka shiga tambayarta tana da damuwane ko kuwa
cikinne ya maidata haka har yazam ba'a ganinta a online gaba ɗaya. Ranta a ɓace
yake sosai da abinda ya faru tsakaninta da Shareff yanzu, ga damuwar hanata ɗaukar
mataki akan Anam da su Mamah suketa famanyi har yanzun. Ita kuma tanajin cewa bafa
zata iya juriyar zaman jiransu ba a halin yanzu tunda har takai mijinta na kashe
mata waya dan ta faɗi laifin Anam. Su Sima ƴan amanarta ne da take kallo fiye da
kowa a cikin ƙawaye. Bibah da Shamsiyya ƙawayentane tun na ƙuruciya sannan ƴan
uwanta ta ɓangaren mahaifi. Dan haka kanta tsaye ta shiga zayyane musu dukkan
damuwarta akan zaman Anam a gidan dama abinda take tsoro wanda dukan sunsha cemata
dama suna zargin Shareff da Anam na soyayya ne tana gwalisesu.
Dukan su kowa da abinda yake ayyanawa a zuciyarsa. Dan kowannensu akwai
manufarsa a kanta tun ba yanzu ba. Fadwa nada ƙyau gwargwadon iko sun sani,
mahaifinta nada arziƙi gwargwado shima sun sani. Sai dai Bibah ta fita ƙyau nesa ba
kusa ba, hakama mahaifin Siyyah yafi na Fadwa arziƙi nesa ba kusa ba. Amma ta fisu
abubuwa da yawa da suke ganin ya kamata ace sune ke da shi ba ita ba. Hatta su Sima
data raini wayewarsu da ɗaukakarsu da kanta kowanne da nasa manufar....
Ta bisu da kallo ɗaya bayan ɗaya idonta cike da ƙwalla. “Ina son kowannen ku
ya bani shawara guda ɗaya akan matsalata domin kaina ya kulle ina neman mafita.
Mafita ta gaggawa kafin matsalarmu da mijina tafi haka faɗi dalilin ta”..........✍

_😹😹😹Keda ke a gidan aure, amma kina neman hanyar warware matsalar rayuwar aure
a hanun wanda basu taɓayi ba. Bayan kin fisu sanin abubuwa da yawan daya kamata ace
a wajenki zasu nema shawara idan sunyi nasu auren. Mata a kula, nasan akwai masu
hankali acikin wanda basuyi auren ba da yawa da zasu iya baki ƙyaƙyƙyawar shawara
mai ɓullewa. Sai dai ki sani, ba kowacce ƙawa bace zakiyi aure ki barta a titi taso
ta ganki cikin nutsuwa da farin ciki a gidan aurenki kema. Hakama wanda suke gidan
auren ba kowacce bace zata so ta ganki a samnta. Amma kumuje zuwa muji ko shawarar
da Fadwa zata samu ga ƙawayenta ita zata ɓulle da ita🤕🤕🤧._
_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_


*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:


07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇


09134848107

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*


[10/28, 11:42 AM] My Zafafa: *_Typing📲_*

*_BABU SO....!!_*
_(Miya kawo kishi?)_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718

*_24_*
..........Shiru ɗakin ya ɗauka na wasu mintuna kamar kowa bazaice komai ba, kusan
mintuna uku Amal ta nisa. Cikin ɗan ɗari-ɗari ta fara magana. “Ni dai a nawa
nazarin da hange sai naga kamar cikin nan shine matsalarki. Kin san fa wasu mazan
basu son da anyi aure ace ciki ɗin nan. Kigafa yanda Shareff ke sonki amma ace haka
na faruwa tsakaninku wata baifi uku ba da aure, amma dai bamu san zuciyarsa ba
kuma”.
Ta ƙare maganar da ɗan shafo gefen wuyanta ganin yanda suka tsura mata idanu
su duka. Yanzu ma kamar bazasu ce komai ba, harta fara tsarguwa sai Siyyah ta katse
fargabarta.
“Kuma fa maganar Amal kamar tana a kan hanya. Musamman idan mukai dubi da
yanayin mijinki. Anya kuwa cikin nan bashine matsalar ba...”
Nufashi Fadwa taja da ƙarfi, zuciyarta babu abinda take hasaso mata sai yanayin
Shareff a randa Dr Jamal ya tabbatar musu tana da ciki, ƙanensa da iyayensu kowa na
murna amma shi bataga ko murmushinsa ba, da suka dawo gida ma baice mata komai game
da cikin ba amma yana bata kulawa da duk take buƙata. Kenan in dai maganar
ƙawayenta gaskiya ne kulawar yana bata ne kawai domin kar ace baya farin ciki? Ya
ALLAH itako yaya akai ta kasa ganewa sai yanz.........
Sima ce ta katse tunaninta da faɗin, “Fady nima dai ina ganin maganar su Amal
nakan hanya gaskiya, dan na tabbatar badan cikin nan ba maybe ma tare da ke zai
wuce ku ɗanyi honeymoon ɗinku. Amma gashi ciki ya muku cikas dole yayta maida
allura galma a tsakaninku, ta hakanne kuma wannan yarinyar zata samu damar cika
burinta akansa. A yanzu ma ɗaukar ciki duk ta wajigaki miji na gudunki inaga kin
haihu, wlhy yara haukataki zasuyi ki fita hayyacinki. Baki ga miji hatta da
followers naki sai sun gudu, dama kece mai kankaro mana mutunci saboda a yanzu kina
cikin manyan tiktokers dake lokaci da kuma tarin followers a arewacin Nigeria,
sunanki ya riga yayi zarra, da kin saki video tamkar wuta jaje haka yake danne duk
wani posting, kiyi tunani”.
Da ƙyar ta iya haɗiye hawayen da suka ciko mata ido saboda maganganunsu sun
matuƙar shigarta. Ta sake nisawa cikin ɗacin zuciya batare data kallesu ba. “Naji
duk bayanan ku, sai dai ban san yaya kuke so nayi da cikin ba tunda ya riga ya
shiga jikina, tun kafin faruwar haka ya kamata na ɗau mataki, amma a yanzu na riga
nayi latti..”
“Bakiyi latti ba Fady, har yanzu kina da sauran dama”.
Ido ta tsirawa Bibah da tai maganar. Bibah ta jin jina mata kai da cigaba da
faɗin, “Da gaske bakiyi latti ba, kwata-kwata cikin ana maganar ko wata biyu bai
cika ba, ki zubar da shi kawai, hakan zai baki damar sasantawa da mijinki tare da
fatattakar shegiyar yarinyar can a rayuwarsa. Idan ya fara nuna son ƴaƴan da kansa
sai ki bama cikin damar shiga hankalinki kwance”.
Sosai maganar ta doki ƙirjin Anam dake saurarensu ta jikin window, dan a
inda take zaune windown ɗakin Fadwa ne, tun kuma shigarsu ɗakin tana iya jiyo
tattaunawarsu, sai dai da farko bata maida hankali ba sai da Amal ta fara danganta
ciki da matsalar Fadwa. Duk da bata son Fadwa addu'a take a ranta kada ta ɗauki
shawarar su Sima........ Ring ɗin wayarta ne ya katse mata tunani, Mamie ce, hakan
ya sata mikewa a wajen tilas tana amsa kiran dan video call ne.....

Wayarta da Mamie ta hanata jin ƙarshen hirar su Fadwa, dan dai-dai tana
kammala wayar suke fitowa kowannensu fuskarsa ɗauke da dariya. Su dukansu kallon
banza suka shiga watsa mata suna jan tsaki, wasun su ma har da jeho mata kalmar
zagi. Batako kalli inda suke ba, tamayi kamar bata gansu ba. Koda Fadwa ma ta dawo
daga rakkiyarsu bata nuna ta ganta ba itama.
Itama ciki ta koma zuciyarta na kaikawo na neman mafita duk da bata san yaya
ake ciki ba a yanzu. Fadwa ta karɓi gurguwar shawararsu kokuwa?Ba komai ta fahimta
a hirar tasu ba dan ma suna haɗawa da turanci ne shiyyasa na zubda cikin yafi tsaya
mata a rai. Ganinta shiru yasa Aysha data fito a wanka tambayarta ko lafiya. “Babu
komai” ta bata amsa tana mikewa itama ta faɗa bayi.

Kusan sati ɗaya dayin wannan magana har Anam ta sakankance Fadwa bata amshi
shawarar ƙawayenta ba sai kawai ga Khaleel da yazo ɗaykarta an tashi aiki yake
sanar mata Fadwa na asibiti ta samu miscarriage. Tsabar yanda zancen ya daketa
batama san sanda ta maimaita kalmar miscarriage ɗin ba cikin waro iro. Da damuwa a
fuskar Khaleel ya gyaɗa mata kai. “To ya za'ayi, haka ALLAH ya ƙaddara, wajen 3 na
yamma Aysha ta kirani wai Fadwa tace cikinta na ciwo ta rakata asibiti. Suna zuwa
likita yace cikintane ke son fita yay mata allura don hana faruwar hakan amma ba'a
dace ba. Yanzu haka su Mom ma duk suna can nima dan ɗaukarki na fito dan ta zubar
da jini sosai gaskiya”.
Har cikin rai Anam kejin zafin abin dan ta tabbatar Fadwa da kanta ta zubar
da cikin nan, kuma tabbas da likitan suka haɗa baki dan a ɓadda kama wa Ayshan. Jin
batace komai ba Khaleel ya dubeta. “Ya naji kinyi shiru?”. Numfashi ta fesar da
zuƙa, cikin kauda kai tace, “Ba komai ALLAH ya kiyaye gaba”. “To amin ya rabbi.
Amma dai kowa baiji daɗin fitar cikin nan ba. Yaya Shareff ma koda na kirasa kasa
magana yayi ya yanke wayar. Sai daga baya na sake kiransa wlhy bakiji muryarsa ba
kamar yayi kuka. Hakan yasa na fahimci ba ƙaramin so da ƙwallafa rai yayi akan
cikin nan ba fiye da kowa”.
“Huhmm!”.
Kawai Anam ta iya cewa saboda sun iso asibitin. Duk ƴan gidansu suna a wajen har
Mommy da Gwaggo Halima. Ta gaida kowa da tambayar mai jiki ta koma kusa da Aysha.
Babu jimawa da zuwansu su Abbah ma suka iso, daga gani daga wajen aiki suka wuto
nan suma. Har sannan ba'a bar kowa yaga Fadwa ba. Amma dai doctor yace da sauƙi sun
mata allurar barci ne dan ta jigata matuƙa.
Kasancewar kusan duk daga wajen aiki ko makaranta sukayi nan Daddy yace suje
gida haka nan abar wanda zai zauna da ita. Gwaggo da ƙanwar Fadwa ɗin aka bari, sai
Gwaggo Halima da tace sai zuwa anjima zata tafi ita. Su dai sallama sukaui musu
suka wuce kowa na cigaba da jajanta abun a ransa.

Washe gari kafin su wuce office nan suka fara zuwa ita da Khaleel, sai Aysha
data biyosu dan kawo breakfast. Sun samu Fadwa zaune tana waya da alama ita da
mijinta ne, dan sai faman marairaice murya take hatta da Gwaggo dake kusa da ita
bawani jinta take ba. Ganin tana waya Khaleel ya fita dan ganin doctor, Aysha tabi
bayansa da sauri dan tana son amsar kuɗi a wajensa nayo cefane daya manta bai bada
ba. Gwaggo da tun shigowarsu tai kamar bataga Anam ba ta miƙe tana ɓantarar goro.
Hanyar fita ta nufa dan so take ta tare Khaleel a waje ta amshi kuɗi itama. Ɗakin
ya rage daga Anam sai Fadwa dake waya tana ɗan ɗaga murya yanzu wai dan Anam taji.
Anam ɗin kuwa tana ji, sai dai tayi kamar bataji ɗin sai faman buga game take a
waya. Lokaci-lokaci takan kai yatsa ta gyara zaman gilashinta.... Tsakin da Fadwa
taja lokacin da ta kammala wayar yasa Anam ɗan dubanta. Kallon juna sukai cikin
ido, Anam ta janye nata cikin halin ko in kula.....
Yanda tayi sai ya batama Fadwa rai, duk da halin da take ciki muryarta ko
fita bayayi da ƙyau ta watsama Anam harara da jan tsuka a karo na biyu. “Ban cika
son ganin wanda ban gayyata cikin lamurana ba, ko kuma ban sani ba ko zargin namu
ya zama gaskiya ne lashemin jariri akayi..”
Da turanci tai maganar, hakan yasa komai ya shiga kunnen Anam. Batai niyyar
harta bar asibitin ba tai magana amma sai ta kasa hakan, dan a wannan gaɓar taga ya
dace ta bama Fadwa amsa dai-dai da ita. A hankali ta taka gaban gadon tana zira
wayarta a aljihun wandon uniform ɗinta na hidimar ƙasa. Babu alamar tsoro ko shakka
a cikin idanunta ta tsaya gaban Fadwa dake mata kallon mamaki. Idanunta dake cikin
farin gilashi ta lumshe ta sake buɗewa akan Fadwa. “Tabbas jaririnki kam cinyesa
akai amma da allurar zubda ciki. Dan haka masu zargin zan basu amsar da suke bukata
har shi mai cikin dan yasan ɗansa ko ƴarsa sun salwantane ta hanyar abortion bisa
shawarar ƙawayenki masu ɗauraki a hanyar da bazata taɓa ɓullewa da ke ba. Ai ban
san ke ɗin cikon bench bace ba sai yanzu. Ki fita a sabgata, idan kuma kikace zaki
iya dani wasan biri zanyi da ke a tsakkiyar kasuwa na rantse da ALLAH! Be careful”.
Ta ƙare maganar da ɗalla yatsunta biyu a saitin fuskar Fadwa tana wani irin
murmushi da kashe mata ido ɗaya.
Numfashi Fadwa taja da ƙarfi, dan tun fara maganar Anam tai sumar wucin
✍🏻
gadi........

_Wannan yarinya tsaurin idonta yayi yawa kudinga mata fada ta kiyaye Fady babynmu
inba hakaba za'ai yakin duniya na 79 a kanta_

_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_


*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:


07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇


09134848107

*_
[10/28, 11:42 AM] My Zafafa: *_Typing📲_*

*_BABU SO....!!_*
_(Miya kawo kishi?)_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718

*_25_*
........“A'a lafiya?”.
Khaleel dake shigowa ya faɗa idonsa a kansu. Baya Anam ta ɗan ja tana murmushi, ta
girgiza masa kanta. “Ba komai Yaya ina dubata ne kawai”.
“Okay tom ai haka yana da ƙyau. Bara nima mu gaisa sai mu wuce kar ki
makara”.
Kai kawai ta jinjina masa. Ta watsama Fadwa harara ta juya ta fice a ɗakin. Da ƙyar
Fadwa take iya amsa tambayoyin Khaleel, gaba ɗaya a birkuce take da kalaman Anam.
Domin kuwa zancen Anam ɗin na nuna mata tabbas taji duk shirunsu da su Sima kenan.
Cikin ƙanƙanin lokaci zufa ta gama jiƙe mata jiki. Har Khaleel ya fahimci haka ya
tambayeta ko jikin ne?. Kanta ta jinjina masa cikin kaƙaro murmushi. “Kawai inaga
allurar da sukai mince bata gama sakina ba barci nake ji”.
“Ayya ALLAH ya ƙara lafiya. Doctor ɗin ma yace zuwa anjima zai sallameki,
inaga bara na ajiye Anam a wajen aiki karta makara zan dawo yanzun”.
Kanta kawai ta iya jinjina masa nan ma. Yana fita ta jawo wayarta cikin rawar
jiki. WhatsApp ta shiga, ta haɗa group da sauri tare da adding su Siyyah a ciki.
Cikin sa'a ta samu Bibah da Sima a online. Cikin bada umarni tace suyi kiran Amal
da Siyyah su hau online tanada magana da su. Duk sun san tana asibiti tun jiya, sai
dai basu zo ba kamar yanda suka shirya har sai ta koma gida dan karma wani ya zargi
wani abu. Tsoron yin voice note wani yajita ko kiransu ya sata tafa musu duk yanda
tai da Anam yanzu. Suma hankalinsu ya tashi amma duk sai suka danne kowa ya shiga
faɗin albarkacin bakinsa.
Maganar Sima ta sakasu duk maida hankalinsu gareta, dan zancen ya dauki
hankalinsu. *Sima* _Inaga ba hankalinmu ya kamata mu tayar ba, idan ita tace kwalba
ce uwar sheri sai mu nuna mata muɗin gilasai ne mun fita haɗari. Kafin ta faɗama
wani zancen nan dolene mu juya komai kanta, hakan ma zai zama hanya mai sauƙi da
zata bar miki gida dan koshi mijinki daba son cikin yake ba na tabbatar sai ya
tsaneta._
Cikin ɗan tsumar jiki ta tafa saƙo tana tagging maganar Sima. _Kinga Sima
bar zagaye-zagaye faɗi minene shirin naki kai tsaye kawai dan ALLAH_.
*Sima* _Kafin ta faɗi kin zubar da cikin mu zamu fara sanarwa itace ta zuba
miki maganin zubda ciki._
*Bibah* _Ta yaya hakan zata faru tunda bamu da wata hujja Sima?!”._
*Sima* _Muko keda hujja. Doctor zamu samu ya faɗama su cikin ya zube ne ta
hanyar magani da aka sha, bayan kowa ya gama ji da ɗaukar ɗumi akan maganar mai-
aikinki ta tabbatar musu taga shegiyar sanda take zuba maganin. kinga sai mu samu
ƙwaya asa a abinda kika sha na karshe dan ya zama shaidarmu ta biyu, yanda kowa
yasan ita da iyyenta ba ƙaunarku suke ba tuni za'a yarda wlhy”_.
*Siyyah* _Woow gaskiya wannan shawaran yayi Sima. Shiyyasa kike
birgeni, dan kuwa na tabbatar wannan maganar bazata zama ta wasaba. Maybe ma a
kanta har sai iyayen Shareff sun maidata inda ta fito”._
A hankali Fadwa ta sauke ajiyar zuciya tana murmushi, jin motsin kamar za'a
shigo ya sata ajiye wayar da sauri ta zame ta kwanta tana fidda numfashi ɗaɗɗaya.

★Kamar yanda suka shirya ɗin hakance ta kasance. Dan kuwa bayan dawowar
Khaleel Doctor yake sanar masa bayanan bincikensu akan zubewar ciki. Hankalin
Khaleel ya tashi a take ya kira Daddy a waya ya sanar masa. Cikin ƙanƙanin lokaci
magana taje kunen kowa daya dace, dan haka daga asibiti gidan su Shareff aka wuce
da Fadwa. Anan su Gwaggo suka tirketa da tambayoyi. Faɗa musu tai ita wlhy bata sha
komai ba dan cikin ya zube. Daga dai gama shan lemo cikinta ya kama ciwo shine tace
Aysha ta rakata asibiti, suna kuma zuwa Doctor yace cikin na barazanar zubewa. Yay
mata allurar kariya daga hakan amma sai ba'a dace ba. Kan kowa ya kulle da zancen,
daga ƙarshe Abbah ya tambayi su nawane a gidan.
Cikin kukan da take faman sharɓa ta sanar masa su huɗu da mai aiki sai
maigadi a waje da Khaleel da sai dare yake zuwa, da safe kuma ya fice. Babu ɓata
lokaci aka tattaro kowa har maigadi sai kulle gidan yayi. Su Anam dama daga wajen
aiki nan suka yo. Kafin kowa yace komai Gwaggo Halima ta fara zazzaga masifa akan
bazata yarda ba, duk wanda ya salwantar mata da jika sai inda ƙarfinta ya kare,
Hakama Mommy sai kumfar baki take. Itako Gwaggo sai ta saka kuka tana kafe Anam da
kallo...
Hakan yasa kowa maida hankali kan Anam ɗin. Ta nuna Anam da yatsa tana sake
fashewa da kuka. “Kar ku raba ɗayan biyu yarinyar nan ce ta aikata. Lallai ilallah
itace da wannan aika-aikar, tunda tana ganin Mustapha ya mata nisa shiyyasa ta
ƙulla wannan sharrin na salwantar masa da ɗan tayi. Kai wannan yarinya anyi
azzaluma makira, dama yaya ɗan ɗan uba zai taɓa son abokin burminsa da alkairi,
dama ni dai dan kar ace an hanata zuwa ne amma naji ajikina wani abu mai muni zai
faru, sai dai banyi zaton mai girma irin wannan ba........”
Abbah ya katseta da sauri cikin ɓacin rai, “Haba Gwaggo wannan wace irin
magana ce haka. Yaya Anam zatai wannan babban al'amarin nawa take?”.
“Eh kace haka fa, Abubakar kasan miye mace kuwa? To mace ko ƴar kwana ɗaya
ce ta wuce da saninka a fanin makirci da shaiɗanci. Idan kana ganinta karama wlhy
sai ta aikata maka abinda mai ɗari bazaiyiba. Kuma idan kitsa mata hakan akayi
fa...”
“Wannan dai maganar bashi da amfani gaskiya a bari dai ayi bincike.
Ƙilama ita Fadwan da kanta tasha abint.....”
“A'a gaskiya Yaya kar kai irin wannan yanke hukuncin. Taya za'ai ciki na
jikinta ta zubar”. Gwaggo Halima ce ta katse Daddy a matuƙar harziƙe mai maganar..
Ran Daddy ya ƙara ɓaci amma sai baice komai ba yay shiru. Abba ne ya ƙara dakatar
da hargowar Mommy da Gwaggo. Dole sukai shiru aka fara yima Aysha tambayoyi. Bayan
ta gama bada amsa aka juya kan Anam da zuciya tazoma wuya da kalaman su Gwaggo
Halima duk da ba komai take fahimta ba saboda hausa sukeyi. Tambayarta itama Abbah
ya shigayi sai dai ta kasa bada amsa ko guda ta saki kuka....
“You see! Kun gani ko. Shi mara gaskiya ai ko'a ruwa jiɓi yake. Munafuka
dangin tsiya wlhy ko za'a tada yaƙi bazan yarda ba”.
Mommy ce mai maganar, dan haka Daddy ya katseta a tsawace har sai da Anam ta
zabura ita da su Aysha. Fadwa ta watsama mai-aikinta harara cike da gargaɗi saboda
hango tsoro da firgici cikin idanunta. Ƙyale Anam Abbah yayi ya maida hankalinsa
gamai aikin dan ya fahimci zuciya ce ta tokare Anam ɗin. Tiryan-tiryan yanda suka
tsara mata ta faɗa. Ko haɗiyar yawu bata gama ba su Mommy suka hargitse falon da
hargowa har suna kaima Anam duka da ranƙwashi sai dai Khaleel ya fara kareta. Duk
yanda su Daddy suka so suyi shiru hakan ya gagara. Dole Khaleel yaja hanun Anam
suka fice da sauri. Mota ya turata ya tayar yabar gidan a guje duk da kiran da
Gwaggo Halima ke masa akan ya dawo da Anam ɗin bai saurareta ba..

★Kuka take sosai har numfashinta na fisga. Yayinda Khaleel ke waya da


Shareff cikin bacin rai da ƙunar zuciya. Shima daga can yana jiyo shashshekar kukan
Anam ɗin. Sun jima suna wayar kafin ya miƙo mata. Ƙin amsa tai sai da Khaleel ya
ɗaura mata akan kunne yana faɗin, “Yaya Shareff ne fa”.
“Malama amsa wayar ban son shashanci”. Ya faɗa da alamun ɓacin rai a
muryarsa daga can. Amsar tayi, sai dai ta fashe masa da sabon kuka. Shiru bai sake
cewa komai ba da alama dai yana saurarenta. Tsawon minti ɗaya taƙi tai shiru ya
yanke wayar yana jan tsaki. Kanta ta cusa cikin ƙafafunta tare da sakin wayar ta
saki wani sabon kukan. Ba sharrin su Fadwa ya sata wannan kukan ba. Zagin iyayenta
da su gwaggo Halima keyi da aibanta su ne ke mata zafi. A hakan ma dan ba komai
take iya ganewa ba musamman manya-manyan hausa. Tana matuƙar son iyayenta, bata
ƙaunar a aibanta mata su. Amma tunda ta fara wayo ta fahimci waɗanda Abie ɗinta ke
kira family nasa basu da wani buri daya wuce cin zarafinsa shi da Mamie da ita
kanta dake matsayin ƴar su. Ta rasa mi iyayenta sukaima Mommy da Gwaggo da Gwaggo
Halima haka da zafi a duniyar nan?...
Khaleel da kukanta ke ƙara ƙona zuciyarsa da takaicin su Mommy ne ya shiga
lallashinta, da ƙyar ta ɗago idanunta da sukai jajir tana kallonsa. Zatai magana ya
girgiza mata kai alamar tai shiru. Shirun kuwa tayi sai dai hawayenta sun kasa
tsayawa. Khaleel ya miƙa mata goran ruwa dai-dai kira na shigowa wayarsa. Ganin mai
kiran ya sashi ɗagawa babu ɓata lokaci ya kai kunne sa.
“Bata wayar”. Daga can aka faɗa cikin bada umarni. wayar ya sake miƙa mata.
Bata musa ba ta amsa tana cire goran data sha kusan rabin ruwan cikinsa. A jajjare
ta dinga sauke ajiyar zuciyar dake shiga har cikin kunensa daga can.........✍

_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_


*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:


07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇


09134848107
[10/28, 11:42 AM] My Zafafa: *_Typing📲_*

*_BABU SO....!!_*
_(Miya kawo kishi?)_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718

*_27_*

..........A hankali ta ajiye wuƙar tana murmushi, ta miƙe cike da isa da izza tana
magana da shan gaban Anam, “To ƴar wasa da biri, ya akai ke kika zama birin kuma a
hannun ƴan wasa?”.
Idanunta dake cikin gilashi ta ɗago tana kallonta, ta saki ɗan murmushi da
kauda idanun kamar bazatace komai ba. Sai kuma ta hurar da numfashi da sake maida
kallonta gareta. “Mi kikeci na baka na zuba Madam. Da Juwairiyya kike tare fa,
_Juwairiyya Anam Usman MD Shareff_ bana gaggawa akan al'amarina, sai dai ina bama
maƙiyi damar da zai sharemin hanyar fagen isar da saƙona. Su kin faɗa musu ni na
zubar miki da ciki right? Tom ki jira shi kuma mai cikin yazo ya ɗaura bincikensa
akan yanda akai na zubar ɗin, daga haka game ɗin zai fara ok!”. Ta ƙare maganar da
kashe ido ɗaya ta rabata ta wuce tana dariyar rainin hankankali.
Wani irin bugawa ƙirjin Fadwa ya shigayi da sauri-sauri, tabita da kallo
harta shige. Juyawa tai ta kalli mai aikinta, ganin aikinta take hankalinta baya
kansu tai saurin barin wajen ta nufi bedroom ɗinta. Kai kawo ta shigayi cikin
tashin hankali, dan da gaske kalaman Anam sun mugun dukanta, kanta ya kulle harma
ta rasa kalar tunanin da zatayi. Tayi waya da Shareff a daren jiya amma bai nuna
mata komai ba akan maganar rigimar zubda cikin balle tace ko Anam ɗin ta sanar masa
ne. (To mi yariyarnan take nufi?) ta tambayi zuciyarta batare da tasan ta inda amsa
zata fito ba. Ganin ta rasa ina zata kama ta yanke shawarar kiran Sima, dan tana da
basira sosai, tasha warware mata ƙulluka da ita ta gaza kuncesu musamman da abokan
hamayyarta irin su Anam ɗin......

Sima tazo, sai dai Fadwa ta jata sun fita can garden ɗin gidan dake bayan
sashen maigidan saboda kar a ƙara maimaita irin na ranar. Acan suka tattauna. Har
Sima ta wuce Aysha da Anam basu ma san da zuwanta ba dan suna can suna kwasar
barci. sai yamma sosai suka tashi saboda saurayin Aysha daya kira ta zai zo.....

*******************

Tun daga waccan ranar Fadwa bata sake shiga sabgar Anam ba. Itama Anam
ɗin bata shiga tata ba aikinta ma ya ɗauke kaso mafi yawa na hankalinta. Babban
burinta tayi ta kammala tabar Nigeria ta huta. Bata sake waya da Shareff ba tun
waccan ranar shima. Sai dai taga sunayi da matarsa wadda in ta gama Aysha kawai
take cewa Shareff ɗin na gaidawa. Takanyi murmushi a duk sanda hakan ta faru, duk
da kuwa a ranta tanajin zafi da haushinsa. Sai dai takan ce inma baice yana gaida
tan ba sai me.

★A ranar wata alhamis da tai dai-dai da zubewar cikin Fadwa Daddy yay
kiran Aysha da Anam akan su samesa a gida. Daga wajen aiki Anam ta wuce, inda ta
samu Aysha tuni tana can. Basu sami zama dasu Daddy ɗin ba sai bayan sallar isha'i.
Cikin kulawa su Abban ke tambayar su babu wata matsala dai ko?. Murmushi Anam tayi,
dan kai tsaye tambayar tafi ƙarfi a kanta ne. Tace, “Babu wani damuwa sai na zafi”.
Dariya Daddy da Abbah sukai mata.
Bayan sun sarara Daddy ya dubesu a tsanake, “Yauwa kun san miyasa muka
kiraku nan?”. A tare sukace a'a. Daddy ya jinjina kansa da cigaba da faɗin “Magana
ce mai muhimmanci akan aure, yanzu dai kunga kun kammala karatunku, babu abinda ya
kamaceku sai aure inba so kuke mu zuba muku ido ku tsufa a gabanmu ba, dan haka
muna mai baku umarni ba shawara ba, kowaccenku ta bama wanda yake zuwa wajenta dama
yazo mu gana da shi”.
A ɗan tsorace Anam ta ɗago tana kallon daddy, ganin shima kallonta yake ya
sata maida kanta ƙasa. Aysha kam murmushi ne ya suɓuce mata, dan kuwa dama Junaid
nata damunta akan hakan, itace taƙi bashi dama saboda ganin yanxu ta Yaya Maheer
akeyi ba suba.
“Mamana yaya dai?”.
Abba ya katsema Anam dogon tunanin data tafi. Kanta ta girgiza idonta na cikowa da
ƙwalla. “Abba babu komai, kawai dai....” sai kuma tai shiru.
“Kawai dai mi? Faɗi kanki tsaye kinji Mamana. Maganar aure ba maganace ta
wasa ba, shiyyasa muka zaɓi baku damarku duk da hakkinmu ne zaɓa muku mazan aure
matsayinku na ƴammata”.
“Tabbas babu wanda zuciyarta ta aminta zata iya tsaidawa, sai dai kuma bata
iya jayayyaba, koda wasa bazata iya ƙin bin umarninsu ba dan batun yanzu ba Abie
yasha sanar mata su ɗin kamar shi suke a gareta, idan har taja da su akan koma
minene na rayuwa dabai zama saɓama UBANGIJI ba tamkar tayi jayayya da shine. Sannan
wani ɓangaren ta sani babu abinda iyayenta ke buri a yanzu tamkar ganin tayi aure,
kuma itama a karan kanta tana son taga wannan rana kamar kowace ɗiya mace duk da
zatai matuƙar kewar iyayenta a kusa da ita. Abu na gaba kuma burin Abie ɗinta ta
fidda miji a ƙasarsu ta haihuwa Nigeria, ta tabbata kuma hakan zaisa su dawo kusa
da ita suma duk da can yafi musu kwanciya hankali fiye da nan... A hankali taja
numfashi, batare data yarda ta kallesu ba ta gyaɗa kanta alamar amsa umarninsu.
Daga Abba har Daddy sunji daɗin hakan, dan haka suka sallamesu akan suna jiransu.

Gaba ɗaya Anam rasa sukuninta tayi a kwanakin da suka gabata, musamman
akan wanda ya kamata ta tsayar matsayin miji a tsakanin samarin dake faman mata
kaikawo su biyu. Wato Muzzaffar da Dr Jamal. Daga ƙarshe da ta fahimci zata saka
kanta cikin wani hali sai kawai ta kira Mamie domin neman shawararta. Mamie uwace,
sai dai ta raini tilon ƴarta da matsayi kala daban-daban bana uwa kawai ba.
Shiyyasa Anam bata da wata ƙawa ko aminiya a duniya sama da Mamie, dan ko shawara
zatai da Aysha ko Amrah sai ta gama da Mamie, koda abun mai nauyine a gareta
tanajin kunya zata rubuta ta bama Mamien a rubuce. Yanzun ma hakan tayi, dan haka
koda Mamie ta gama karantawa sai tai murmushi, Abie dake zaune a kusa da ita ta
nunawa, shima dai murmushin yayi harda ƴar dariya. Ya amsa wayar yana faɗin, “Nine
zan bata amsar daya dace da ita”.
Mamie tai dariya da fadin, “Uhhm nidai naga yanda zaku ƙare a wannan rana”.
Dariya kawai Abie yayi, ya tafa saƙon ya turama Anam da dama zaman jira take. Shiru
tai tana kallon saƙon, zuciyarta cike da wasiwasi. Sai dai kuma a ganinta tunda
Mamie tace mata yayi to itama koda son sa bai kai mata har can cikin zuciya ba zata
aminta da shi kuwa watarana zata so sa da izinin ALLAH. Sai dai kuma kamar yanda
Mamie tace kartai masa magana da kanta bazatayi ba, tunda dama ya jima bai zo
wajenta ba bai kuma kira wayarta ba sai lokaci-lokaci sukan ɗan gaisa a chart,
shima kullum cikin cemata uzirine ya riƙesa yake.

★Kwana takwas dayin wannan magana abin al'ajabi ya sauka a MD Shareff


family, ba komai bane kuwa sai baiko da saka ranar Anam da Muzzaffar, Aysha da
saurayinta Junaid, za'a haɗe biki tare dana Maheer.
Su Mommy kasa magana sukai dan mamaki, duk da wani sashe na zukatansu sunji
tamkar an musu rahama ne, amma kuma sunajin ɗaci da zafin ganin Anam ɗin zata auri
wanda shima ba baya ba, dan mahaifinsa akwai kuɗi, shima kuma Muzzaffar ɗin a karan
kansa akwai kuɗin dan wani babban gwaska ne a kamfanib MTN. Duk yanda suka so kuma
danne abin a rayukansu kuma kasawa sukai har saida suka haɗu suka tattauna, sai dai
a ɓangaren Fadwa ranar har ruwa ta zuba ƙasa tasha. Jitai kaso talatin cikin ɗari
na tsanar Anam ya sauka a zuciyarta harta kasa ɓoye hakan. Ita Anam ma data lura da
ita sai abun yay matuƙar bata dariya........✍

_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_
*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_


*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:


07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇


09134848107

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*


[10/28, 11:42 AM] My Zafafa: *_Typing📲_*

*_BABU SO....!!_*
_(Miya kawo kishi?)_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718

*_26_*

..........Gyaran murya ya ɗanyi bayan yaja wasu seconds yana sauraren yanda take
sauke ajiyar zuciya a jajjere. “Bazaki daina wannan kukan ba wai?”. Ya faɗa a
hankali tamkar ba shi ba...
“Na daina”.
Ta bashi amsa wani kukan na sake kufce mata. A karon farko taji yayi murmushi har
tana iya jiyo sautinsa a cikin kunnenta, ya ɗanja numfashi da sake sauƙaƙa muryarsa
“Ya isa nace ko. Ki ɗauka ruwa ki wanke fuskarki zan ƙara kira”.
Cikin jan numfashi tace, “Nace fa na daina Yaya”. Dan haka kawai take jin
daɗin yanda yake mata magana da lallashi.
“Ni banji kin dainaba ai, tunda ga hawayenki ina gani na sauka a z....”
cikin sauri ya haɗiye sauran maganar da dafe goshinsa yana cije lips ɗinsa jin zai
saki layi. Itama da ba wani gama fahimtar maganar tasa tai ba cikin rawar murya
tace, “Yaya dan ALLAH ka faɗama Abie zan dawo Malaysia, idan nice nace zaimin faɗa
shi da Mamie”.
Furzar da numfashi yayi, cikin ɗan kaurara muryarsa yace, “Bazan sanar musu
ba, kuma kema karna sake naji kin sanar dasu wani abu ok”.
“Amma Yaya kag.....”
“Umarni ne ba shawara ba”. Yay saurin katseta. Baki ta tura da hararar wayar kamar
yana gabanta, “To nidai bazan koma gidanka ba, sai dai na koma gidan uncle Jafar da
zama (Ɗan uwan Mamie da abie ne).
“Ashe kuwa zan zane miki jiki da bulalai”.
“To ni Yaya ya kake so nayi? Sai na dinga zama inda ba'a son ganina kamar wata
mara gata”.
“Waye baya son naki?”.
“Matarka mana. Kuma ALLAH idan bata fitamin a ido ba zan fito mata da ainahin
kalata, dan zan koya mata hankali...”
Dariya ce ke son kufce masa, sai dai ya riƙeta ya dai saki murmushi.
“Uhuyim! Ke har wata kala ce da ke ashe? To faɗamun yaya kalar taki take dan mu
kiyaye ni da matata”.
“To ni ai bance kai ba”.
“A idan zaki koyama matata hankali ai dole ina ciki. Kinga gara mu kama kammu kar
truth color ɗinki ta samu barin Nigeria auntynmu”.
A yanda yay maganar ya saka Anam fashewa da dariya. “Oh oh ya kaga Anam
Auntyn su Yaya, gaskiya kowa zaiji a jikinsa ne, yanda kake mana mazurai nawa sai
yafi ALLAH Yaya”. Sai ta ƙara ƙyalƙyalewa da dariya.
Kansa ya ɗan girgiza da shafawa yana sakin murmushi, yasan ta iya surutu,
sai dai bata taɓa sakewa da shi ba irin haka. Sai dai yaji surutunta da wani. Ya
ƙara sakin murmushi da fesar da numfashi a hankali yana lumshe idanunsa da sake
lafewa cikin kujerar falon daya kasance masaukinsa. Haka kawai ya tsinci kansa
cikin nishaɗi dayin wayar tasu......

Yayin da Anam da Shareff ke waya anan acan gidan Mommy ce ke neman wayarsa a
fusace saboda hukuncin da Daddy ya yanke cewar Anam bazata bar gidan Shareff ɗin ba
kamar yanda suka buƙata har sai ya dawo kamar yanda shima ya buƙata. Amma sai taƙi
samunsa anata nuna mata waya yakeyi. Ranta ne ya ƙara ɓaci ganin mintunan dake ta
ƙara tafiya amma ana sake jadadada mata ana amfani da layin. Ta tura massege babu
reply. Ga Fadwa nata musu kuka ita indai Anam zata koma mata gida to ita bazata
koma ba..
“Wai ni yaron nan da ubanwa ma yake waya hakane? K Hussaina jeki ki gano min
Daddynku waya yakeyi”.
Miƙewa Hussaina tayi tana amsawa da to ta fice. Mintuna kaɗan ta dawo ta sanar
mata ba waya yake ba, hira yakeyi ma shi da Abba.
“Kai! To da ubanwa yaron nan ke waya?”.
Kuka Fadwa ta sake fashewa da shi. “Wlhy yanzu haka shegiyar yarinyar can ce ta
kirashi tana ƙulla mana sharri a wajensa. Na tsaneta, bana sonta. Idan ta koma min
gida saina kasheta”.
Shigowar Gwaggo falon ya hana Gwaggo Halima da Mommy bama Fadwa amsa. Takai
zaune tana murmushi idonta akan Fadwa. “In dai bazaki kiyayi gaggawa akan
al'amuranki ba kuka yanzu kika fara shi. Da kinyi haƙuri kin cigaba da jiran nawa
shirin da ba'akai ga haka ba. Ku kuma kun biye mata. Duk yanda kuke tunanin
yarinyarnan tabar gidan Mustapha da ƙarfin tuwo bazai yuwuba, wannan kuma zancen
ita ta zubda ciki da kuka ƙulla ƙara kusantata ma da gidan kukayi tunda gashi su
Muhammadu sun tabbatar muku yanzuma ta fara zama. Duk wanda ya baku shawarar juya
zancen zubewar ciki da ita ta zubar ya baku gurguwar shawara ne ga tabbaci kun
gani”.
Mommy da takai zaune cikin sanyin jiki da maganganun Gwaggo ta dubi Gwaggo
Halima. “Maganar Gwaggo haka take Halima. Munyi kuskure nima na fahimta. Da Fadwa
ta sanar mana zatai hakan ya kamata mu dakatar da ita mu fara yin nazari, tare da
bincikarta wanda ya bata shawarar yin hakan tunda mun san zubewar cikinta bashi da
alaƙa da yarinyar da gaske”.
Itama Gwaggo Halimar ajiyar zuciyar ta sauke. Sai kuma ta jinjina kanta,
“Hakane Gwaggo anyi kuskure, ba kuma kowa ya jawo hakan ba sai Fadwa da shegen
gaggawarta. Na faɗa mata ta kwantar da hankalinta mu jira naki shirin amma rashin
haƙuri yasata yanke wannan hukuncin. Gashi yanzu bai haifar da ɗa mai ido ba tunda
abinda take son yay nesa da ita da mijin nata damu baki ɗaya bai tabbata ba. Kuma
tabbas zaman yarinyar nan cikinmu ba alkairi bane, na tabbatar yanda bamu ƙaunar
ubanta shima bazai taɓa son mu ba, amma ya kawota cikinmu saboda sharri irin na ɗan
uba da baka ganesa sai ALLAH kawai. Gwaggo kiyi haƙuri, yanzu minene mafita?”.
Baki Gwaggo ta taɓe. “Toni mizance yanzu kuma. Nawa shirin ma ai kun ruguza
da shirmen ƴarku. Sai kubar yarinyar ta koma gidan kamar yanda Muhammadun ya faɗa.
Zanje na sake sabon shiri a kanta dan wannan karon dole ne muyi shirin da zata koma
inda ta fito kuma har abada bazata sake dawowa ba. Kai bama ita da suka haifa ba,
har Usman da Maryam (Aunty mimi) bazasu sake waiwayo ƙasarnan ba har abada balle
ita karan kaɗa miya”.
A take fuskokinsu suka washe da murmushin jin daɗi. Fadwa tace, “Amma ni dai
gaskiya ayi da sauri. Dan wlhy idan ina ganinta a gidana ji nake kamar na shaƙeta
ta mutu. Bana son Soulmate ya dawo ƙasar nan tana gida na”.
“Batun kafin ya dawo ƙasar nan bazai yuwuba. Domin kin ɓata komai ga shirin
yin hakan kuma ai. Dolene muyi ɓadda kamar da zasu cire ɓaranɓaramar da kikai a
ransu gaba ɗaya daga nan har zuwa lokacin bikin Maheer, so nake da bikin idan sun
zo su tattara ƴarsu su wuce yanda bazasu sake dawowa cikinmu ba har abada. Idan
kuma kika ƙara yin wanu shirme to kiyi kuka da kanki bani Hannatu ba kuma”.
Baki Fadwa ta tura gaba sai dai batace komai ba. Nan su Mommy suka shiga
jadadada mata ta kiyaye kar kuma a sake samun wata matsalar kamar yanda Gwaggo ta
faɗa. Idan tai haƙuri komai zai zama labari dan suma basu da burin daya wuce Anam
ta bar gidan ai. Miƙewa Gwaggo tayi, “To bara nayi nan karma wani ya shigo ya
ganni. Shima kuma Mustapha kar wanda ya kirasa akan maganar mu jira muga ko wani
zai sanar masa a cikinsu”.
Duk sun gamsu da hakan. Daddy dake bakin ƙofar yaja da baya a hankali yana
ƙoƙarin danne ɓacin ransa. Dama yazo ne dan ya sake kwantar ma da Fadwa hankali da
nuna mata tabar zargin kowa akan zubar cikin ta ɗaukesa matsayin ƙaddara. Amma sai
gashi yaji ainahin abinda ma ke faruwa. Bai bari Gwaggo data fito tana murmushi ta
gansa ba, sai ma ya juya yabar wajen ya fasa shigar...

Washe gari Daddy ya sakasu komawa can gidan Fadwa na ɗacin ran kasancewa da
Anam. Khaleel ne ya ɗauke su su huɗu har mai aikinta dan maigadi shi tun jiya ya
koma. Anam tai murmushi tana kauda kanta gefe ganin uwar hararar da Fadwa ke zuba
mata kamar idanunta zasu zubo ƙasa. Sosai murmushin ya ƙular da Fadwa, sai dai
batai magana ba har suka iso.
Kiran da Abie yay ma Anam a waya ne ya sata dakatawa su suka shige su uku.
Itako ta tsaya anan jikin motar Shareff dake lulluɓe tana amsawa. Ta jima tana
wayar kafi. ta nufi ciki itama fuskarta ƙawace da murmushi. Matar gidan kawai ta
samu a falo zaune ƙafa ɗaya kan ɗaya tana jijjigawa da yanka apple. Sai mai aikinta
✍🏻
dake gyaran falon. Yi tai kamar bata ganta ba tai ƙoƙarin wucewa........

_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_
*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_


*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:


07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇


09134848107

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*


[10/28, 11:42 AM] My Zafafa: *_Typing📲_*

*_BABU SO....!!_*
_(Miya kawo kishi?)_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718

*_28_*

...........A haka aka shiga shirye-shiryen bikin Maheer, Anam da Aysha. Yayinda
kwanakin dawowar Shareff da ba'a sanar da shi komaiba ke kusantowa. Asabar ɗin daya
rage saura sati uku biki Anam da Aysha acan gidan suka yini ana shirye-shirye da
tsare-tsare. Anam dai ba shiga sabgar duk wani shirye-shirye take ba, su Fadwa ne
dai ƙirjin biki keta kaiwa da kawowa duk da ango Maheer bawai yana ko leƙowa yaji
yanda abubuwan ke tafiya ba ne, dan shi ƙiri-ƙiri nunawa yake baya son auren nan.
Haka itama Anam Muzzaffar yayi tafiya dan tunda aka fara maganar auren ma
bata gansa ba, a wayama sai jefi-jefi dan baya ƙasar yaje wani aiki mai muhimmanci
a yankin larabawa.
Washe gari lahadi Khaleel ya dauketa ita da Aysha kamar yanda yay mata
alƙawari zuwa wajen tela. Kayanta takai na ɗinki, Mom ce ta bata su takai ɗinki
kusan kala goma sha biyar. Kayane masu ƙyau da tsada har tana mamakin miyasa aka
banbantata da Aysha, dan telan nata ma na musamman ne saboda Mommy taƙi yarda Aysha
ta kawo nata nan. Bayan sun zaɓi ɗinkunan da take so ya gwadata ya faɗa misu bill
ɗin kuɗin. Accaunt number ɗinsa Khaleel ya amsa, ya saka masa rabin kuɗin rabi yace
sai ya kammala aikinsa. Daga nan gidan wata ƙawar Mom suka nufa ƴar sudan. Har
Khaleel ɗin suka shiga ciki, yanda aka tarbesu ya bada tabbacin Khaleel ɗan gida
ne. Sun ƙara tabbatar da hakanne lokacin da wata ƴar budurwa ta kawo musu abinsha
tana ta faman sinne kai na kunya, yayinda Khaleel ke faman jifanta da wani kallo.
Cikin yanayin tuhuma Anam ke kallonsa tana murmushi, yay murmushi kawai da ɗauke
kansa gefe.
“Uhm to lallai ALLAH ya sanya albarka Yaya Khaleel, amma auntyn tamu fa tayi
dan kun dace”.
Salute ɗinta yayi, hakan ya sakata kwashewa da dariya Aysha na tayata, dan ita
ta kasa cewa komai tunda ba wasa yake da su ba. Fitowar matar hamshaƙiya ƴar gayu
ya saka Anam haɗiye dariyarta. Suka gaidata cike da girmamawa itama tana amsa musu
da kulawa cikin hausarta da bai gama nuna ba. Khaleel dake faman sinne kai ta
kalla, “My son wacece a cikinsu?”.
Anam ya nuna, kansa a risine yace, “Itace wannan Mama”.
“Masha ALLAHU, ALLAH ya sanya albarka. Kace mata insha ALLAH bazai gagara ba,
nima zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu zan shigo dan maybe zuwa laraba mu fara, kaga
zamu samu kwana goma sha bakwai kenan”.
“To shikenan insha ALLAHU zan sanar mata”.
Daga Anam har Aysha babu wanda ya fahimci inda zancen ya dosa. Sai dai ganin akan
Anam ɗin ake magana ya tsaya musu a zukata. Ƙagara sukai su fita suyi tambaya. Amma
sai matar ta tsaresu akan sai sunci wani abu. Su kaɗai suka ɗanci snacks. Shi dai
Khaleel ruwa kawai yasha dan kunya. Ganin haka tasa budurwar nan mai suna Suhaima
tai musu packaging ɗinsu dan harda gasashshen nama.
“Yaya Khaleel mufa kun samu a duhu.” Anam ta faɗa dai-dai suna shiga mota.
Murmushi yayi yanama motar key, cikin basarwa yace, “Akan mi?”.
“Komai ma”.
“To kuyi addu'a ALLAH ya haskaka muku”. Daga haka yaja bakinsa yay shiru. Duk yanda
sukaso jin ƙarin bayani bai basu fuska ba har suka iso gida. Kasa haƙuri Anam tayi
sai da ta tambayi Mom. Kai tsaye Mom tace mata gyaran jiki na bikin amare za'ai
mata dan taga duk tayi duhu. Murmushi kawai tai dan da gaske itama ta fahimci tayi
duhun ko dan fitar da take kullum ne oho. Daga haka bata sake bin ta gyaran jiki
ba.

*_Yau litinin_* da tai dai-dai da saura kwanaki goma sha ɗaya biki. A yau ake
saka ran saukar su Mamie Nigeria sai dai Anam bata san da hakan ba. Hasalima ta
tashi ne da ɗan zazzaɓi. Wajen ƙarfe sha biyu Muzzaffar yay kiranta a waya. Yanda
yaji muryartane ya sashi ruɗewa yace zai zo ya kaita asibiti. Amma sai taki
acewarta tasha magani. yata lallaɓata amma taƙi yarda dole ya barta dan yasan
mutuniyar tasa ƴar tutsu ce. Koda sukai sallama ma sai ta kashe wayar gaba ɗaya ta
gyara kwanciya. Wani barcin ne ya sake awon gaba da ita saboda maganin da Aysha ta
bata tasha. Bata farka ba sai kusan uku. Alhmdllhi zazzaɓin ya sauka dan hakata
samu tai wanka ta ɗanci abinci. Bayan sallar la'asar tana waje zaune ita da Aysha
sai ga kiran Muzzaffar, kai tsaye ya sanar mata gashi a ƙofar gida. Murmushi kawai
tai ta yanke wayar, dan zuwa yanzu kam Muzzaffar ya samu wani gurbi na musamman a
zuciyarta duk da sun jima nesa da juna dan baifi kwana uku da dawowa ƙasar ba. Yau
ne ya fara zuwa gidan suyi hira, dan haka sai da Aysha ta fita tayo masa iso, anan
inda suke zaune da Aysha saman kujerun roba ya zauna. Aysha ta shige ciki ta kawo
musa ruwa ta koma domin basu dama...
“Da alama zazzaɓin nan yaci amanar ango da yawa harfa kin rame dama gaki ba
auki ba”.
Veil ɗinta taja ta ƙara rufe fuskarta tana murmushi. Shima ya murmusa cikin
ƙara sanyaya murya yace, “ALLAH da gaske nake madam. Kodai aje asibiti?”.
“A'a ni naji sauƙi fa”.
“Kin tabbata?”.
Kanta ta jinjina masa. Murmushi ya sakeyi mai faɗi da shafa sajen fuskarsa.
“Alhmdllhi ALLAH ya ƙara lafiya to”
“Amin ya rabbi.”
Shiru sukai na wani ɗan lokaci kafin ta saci kallonsa. Ganin ba ita yake kallo ba
ta maida idanunta ƙasa ranta fal mamakinsa, dan babu rawar kan nan tasa, kuma bai
kirata Beauty ba ko sau ɗaya. Murmushi yayi da gyara zamansa. “Madam nifa da magana
nazo a bakina yau”.
Fuskarta ta ɗan buɗe sai dai bata kallesa ba. Ya cigaba da faɗin, “Juwairiyya
gaskiya nima aure nake so”. A karan farko ta ɗago kai ta zuba masa dukan idanunta
dake cikin gilashi. A hankali ya lumshe nasa ya sake buɗewa. “Wannan kallo ai sai
kisa na gagara faɗar abinda ke raina”.
A yanda yay maganar ya sata sakin siririyar dariya. Hakan yayi dai-dai da buɗe
gate da maigadi yayi motar Khaleel ta shigo. Su duka basu maida hankali ba, sai ma
dariyar da yake tayata shima yana ɗan duban fuskarta da take kaudawa gefe, yanda
yaketa ƙara ƙoƙarin son ganin fuskar tata sai yake ƙara bata dariya harta kasa
dainawa....

“Alhamdulillahi lallai yau jama'ar gidan nan zasusha surprise na ganinka


Yaya fiye da yanda ƴan can gidan suka sha”. Khaleel ya faɗa yana kashe motar. Bai
saurari amsaba ya buɗe gefensa ya fito, zagayawa yay ya buɗe masa fuskarsa ɗauke da
murmushi.
Badan glass dake rufe da idanunsa ba babu abinda zai hana aga tsantsar ɓacin
ran dake cikinsu. Tuni sun kaɗa sunyi jajur, duk wani annurin dake saman fuskarsa
na farin cikin dawowarsa cikin zuri'arsa ya ɓace ɓat. Cike da izzar da fushi ya
haddasa ya zuro ƙafafunsa ƙasa ya fito, hakan yayi dai-dai da juyowar Anam dake
shirin ɗagama Khaleel hannu.. Hannun nata da numfashinta a tare suka maƙale,
ƙirjinta yay wata irin bugawa da batasan dalili ba. A hankali laɓɓanta suka motsa
ta ambaci sunansa...
“Yaya Shareff”.
Duk da akan laɓɓa tai maganar hakan bai hana Muzzaffar gane sunan wa ta kira ba,
juyawa yay shima a hankali. Cikin dariya Khaleel ya ɗago musu hannu da faɗin,
“Surprise”.
Murmushin yaƙe ta saki, mamakinta na sake bayyana akan fuskarta, ta miƙe
a hankali kamar wadda ƙwai ya fashema a ciki ta nufesu, hakan yasa shina Muzzaffar
miƙewa fuskarsa da murmushi yabi bayanta..........✍

_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_


*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾


ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:


07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇


09134848107

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*


[10/28, 11:42 AM] My Zafafa: *_Typing📲_*

*_BABU SO....!!_*
_(Miya kawo kishi?)_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718

*_29_*

........“Sannu da zuwa Yaya”. Ta faɗa har yanzu mamaki shimfiɗe akan fuskarta.
Idanunsa ya ɗauke daga kanta batare daya amsa ba duk da ba gane hakan ake ba saboda
idanun nasa na sakeye a cikin gilashi. Taji haushin yanda yay mata ɗin, sai dai
yanayin tsukewar fuskarsa ya sata jin shakka da ƙara ganin kwarjini da fresh daya
ƙaro. Muzzaffar ya ƙaraso wajen fuskarsa da murmushi shima yana masa sannu da zuwa.
Shima ɗin akan laɓɓa ya amsa masa, koda ya miƙo masa hannu dan suyi musabaha kuma
kamar bazai karɓa masa ba, sai kuma ya miƙa nasa shima da ƙyar. Anam ta taɓe baki
cikin takaicin shan ƙamshin nasa tana kallon Khaleel da shima yanayin Yayan nasu ya
sashi kama kansa, sai dai a ƙasan ransa yana mamakin komawarsa haka dan cikin
nishaɗi da farin ciki suka baro gidansu daya fara sauka, kuma da farin cikin ya
ɗakkosa a airport.
Dai-dai suna shigewa ya zare gilashin fuskarsa ya watsa mata wani shegen
kallo mai cike da gargaɗi ya wuce. Tai tsamm a waje ɗaya zuciyarta na bugawa da
dauri-sauri, amma dan ƙarfin hali sai ta murguɗa masa baki. Muzzaffar kam da kallo
ya bisa yana sakin murmushi zuciyarsa na cuɗa masa abubuwa daban-daban duk da ba
yaune karon farko daya fahimci wasu abubuwa a idanun Shareff ɗin ba. Numfashi ya
sauke a hankali yana nuna mata suje. Itama ajiyar zuciya ta sauke a hankali, jiki a
sanyaye ta bisa suka koma wajen zamansu.

A ciki Aysha da ke kitchen tana girkin dare ita da mai-aiki ce ta fara


leƙowa saboda jin sallamar Khaleel, ta wani zaro ido waje da sakin ihun murnar daya
saka Fadwa fitowa zumut daga bedroom. Itama idanu ta zaro na mamaki, dan sam bata
san da batun dawowar mijin nata ba. Ya ALLAH, ai tama manta da kowa na falon ta
fasa ihun murna da kwasowa da gudunta garesa. Baiƙi bata dama ba, dan shima yayi
missing ɗinta, ya ware mata hannaye tako shige jikinsa tare da ɗanesa.
Dariya Khaleel ya saki yana kauda kansa gefe, hakama Aysha da gudu ta koma
kitchen tana dariya ita da mai aiki. Acan waje kuwa Muzzaffar ƙoƙarin yima Anam
hira yake yi cike da kulawa amma sam sai ya fahimci hankalinta baya tare da shi,
yay murmushi da miƙewa yana faɗin, “Bara na barki madam gobe idan ALLAH ya kaimu da
dare maybe zan shigo sai mu ƙarasa, ya kamata kije kema ayi murnar dawowar Yayan
dake”.
Murmushin yaƙe ta ɗan masa, dan duk suna jiyo ihun Fadwa. Ya miƙa mata ledar
da yazo da shi tare da mata bye-bye. Ajiyar zuciya ta sauke a hankali lokacin daya
fice a gate ɗin baki ɗaya, ta ɗan kalla ledar daya bata sannan ta nufi ciki. Har
shigowarta Fadwa na ɗane jikinsa, ya wani rungumesa tsam tana hawaye da faɗin wai
tayi missing ɗinsa. Sosai ƙirjinta ya ƙara ƙarfin bugun da yakeyi, tai azamar dafe
kujera dan jitai kanta ya fara juya mata kamar maijin hajijiya, amma sai tai
matuƙar dakewa fuskarta ƙawace da murmushi. Shi kaɗai da idanunsa ke a ƙofar dama
ya ganta, ya sauke sassanyar ajiyar zuciya da har sai da Fadwa taji, cikin jin daɗi
ta ƙara maƙalƙalesa tana raɗa masa yanda tai tsananin kewarsa a cikin kunensa.
Karon farko tun shigowarsa falon ya saki siririyar dariya, a hankali ya ɗan kaima
wiyanta sumbata idanunsa na kallon Anam ƙasa-ƙasa. Sai akai sa'a itama dai-dai ta
ɗago nata idanun da hasken cikinsu gaba ɗaya ya kore duk da a cikin gilashi suke.
Ɗauke idanunta tai tana taɓe baki da juyasu cikin salon ko'a jikina. Numfashi mai
ɗaci ya saki da ƙoƙarin dakatar da Fadwa dake ɗan jan hanunsa.
“Shiiii!!”
Ya faɗa cikin wani salo yana ɗaura yatsansa akan bakinta da kashe mata ido ɗaya
wanda komai ya ƙara faruwa akan idon Anam data ɗago. Wayarta dake ring ta ɗaga da
kaiwa kunenta ta sakin murmushi da ajiye ledar hanunta ta nufi hanyar bedroom ɗinsu
cikin ƴar sassarfa.
Khaleel da sai yanzu ya lura da ita ya ƙara sakin ƴar dariya dan duk zatonsa
shi kunyace itama ta sakata yin hakan. Ledar data ajiye a wajen ya ɗauka yana
faɗin, “Ƴar ficikar nan mi kika samo mana haka ne?”. Maganar tasa ce ta saka Fadwa
saurin juyowa dan itama bataga Anam ɗin ba, a yanzu kuma har ta shige abunta. Ta
buɗe baki zatai magana Aysha ta fito daga kitchen ɗauke da tray. Kai tsaye gaban
Shareff da yakai zaune cikin kujera ta dire.
“Yayanmu sannu da zuwa kazo lafiya? Ya hanya?”.
Kanta ya shafa kawai batare da yace komai ba. Hakan ya sakata sakin murmushin
jin daɗi, ruwan data tsiyaya a kofi ta miƙa masa. Ya karɓa idonsa akan Fadwa da ita
sam bata da niyyar hakan ma a garesa... Khaleel daya fahimci kallon da Shareff ɗin
yay mata ya dubeta shima. “Madam kina tsaye Aysha ta kwashe ladan daya kamata ki
samu, anya kuwa bazamu ƙaro amarya ba a gidan nan dan ba'ai mana tarbar data dace
ba”.
Har ƙasan zuciya maganar Khaleel ta soki Fadwa, ta kalli Shareff dake shan
ruwansa tamkar baya jinsu dan hankalinsa na kan tv ne, kallonta ta maida ga Khaleel
cikin haɗe fuska. “Yaya Khaleel wane fatan tsiyane wannan dan ALLAH da yammacin
nan?”.
Zama yay yana faɗin, “Naga kamar haka ya kamata muyi ne ai hajjaju, idan
kuma baki son amarya sai ki gyara kurenki da wuri”. Da gaske magana ya faɗa mata a
kaikaice, amma kuma cikin wasa da murmushi Aysha na tayasa da dariya. Hararar
Khaleel ɗin tayi, a karo na farko taji tsanarsa, sai dai batace komai ba taje kusa
da mijinta ta zauna fuska a ɗaure. Kofin hanunsa ya ajiye yana miƙewa, bedroom
ɗinta ya nufa yana faɗin, “Haɗamin ruwan wanka, ke kuma Aysha kuje ku gyaramin side
ɗina”.
“To Yaya”.
Aysha ta amsa cike da girmamawa. Matar gidan kam takaicin Khaleel ya hanata
amsawar, sai dai ta miƙe cike da isa tana gallama Khaleel ɗin harara tabi bayansa.
Daga Aysha har Khaleel sunga harar, tana shigewa Aysha tai dariya. “Yaya Khaleel ka
sakama Aunty Fadwa jin haushin maganarka fa”. Cikin halin ko'in kula ya ɗage kafaɗa
da taɓe bakinsa irin I don't care ɗin nan. Ƴar dariya Aysha ta ƙara saki da mikewa
zata nufi waje dan kiran Anam ya sanar mata tana ciki ta shigo...
“Tabbas na kusa fara shukama Khaleel rashin mutunci a gidan nan in har yana
min wannan maganar banzar”. Ta faɗa a fusace tana shigowa ɗakin, dai-dai Shareff na
ajiye agogonsa daya cire saman mirror ɗinta idonsa akan wayarta dake maƙale a ɗan
sama. Video take ɗauka zatai posting a tiktok ihun Aysha ya sakata fita, ALLAH
yasota wayar ta gaji ta rufe kanta. Jin bai tanka mata ba ta ƙara maimaita abinda
ta faɗa tana kallonsa. Yanzu dai ya juyo ya kalleta sai dai baice komai ba ya ɗauke
kansa yana ƙoƙarin jan necktie ɗin wuyansa.
“Soulmate kanaji fa ina magana”. Ta faɗa a shagwaɓe da rungumesa ta baya.
Kamar bazai tanka mata ba, sai kuma a taƙaice yace, “Miye nawa, maganarku ce”.
“Hakama zakace?”.
Ta faɗa tana juyowa gabansa. Idanunsa ya ɗan lumshe ya buɗe akan lips ɗinta, sai
kuma yay ƙoƙarin kaudawa amma ta riƙo fuskar tasa, bai samu damar cewa wani abuba
ya haɗe bakinsu.....

Aysha ko koda ta shiga ɗaki sai ta samu Anam duƙunƙune cikin bargo, tana
taɓata taji zafi sosai a jikin nata zazzaɓinta ya dawo. Sannu tai mata, ta maida
mata bargon ta lulluɓa mata. Ita kaɗai taje tai gyaran, hakan ya sata jan lokaci
bata gama ba duk da babu datti sosai saboda sukan gyara lokaci-lokaci. Tana cikin
saka turare Shareff ya shigo sanye cikin jallabiya fara tas. Sannu ta masa, ya amsa
mata da kai yana bin falon da kallo. Baiyi magana ba dan komai ya masa yanda yake
so, ya wuce bedroom ɗinsa baifi mintuna uku ba ya fito ya sake ficewa. Itama
kammalawa tai a gurguje ta fito dan kiraye-kirayen salla aketayi.
Ita ta tada Anam sukai salla, suna idarwa ta koma gado ta kwanta. Kyaleta
Aysha tai sai da aka ƙara kiran sallar isha'i sannan ta sake tadata. Koda suka
kammala babu yanda batai da itaba akan suje falo taci abinci tasha magani amma
taƙi. Dole Ayshan ta barta ita ta fito. Fitowar tata kusan dai-dai ta fitowar
Fadwa daga kitchen tare da mai-aiki. Sannu tai musu dan suna faman shirya abincine
a dining, itama tayasu tayi, suna tsaka da shirya abincin ya shigo falon yana waya.
Kai tsaye dining ɗin ya nufo dan yana son ya ɗanci abincin yaje ya kwanta da wuri a
gajiye yake matuka. Mai-aiki tabar wajen da sauri saboda hararar da Fadwa ta zuba
mata. Aysha dai kujera taja masa baya. Zama yay idonsa akan matarsa dan sabuwar
kwalliyar tata ta masa ƙyau sosai. Ta ɗan duƙo ta sumbaci gefen fuskarsa. Hannu
yakai ya ɗan shafi tata fuskar ya cigaba da wayarsa. Aysha dai ta ɗauke idonta a
✍🏻
kansu tun sanda Fadwa takai masa kiss........

_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_


*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾


ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:


07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇


09134848107

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*


[10/28, 11:42 AM] My Zafafa: *_Typing📲_*

*_BABU SO....!!_*
_(Miya kawo kishi?)_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718

*_30_*

..........Ganin tanata bubbuɗe abincin tana nuna masa ta kurma yay mata nuni da
fruit salad kawai. Ta nuna masa abinci, yay mata alamar 1spoon kawai. Yanda ya
buƙata haka tai masa, sai dai tasa masa haɗin salad a gefen shinkafar da ɗan yawa
saboda tasan yafi buƙatar hakan. Da idanu yay mata alamar ‘thanks’ ta sakar masa
murmushi.
Sun fara cin abincin yay sallama da wanda suke wayar ya ajiye. Harya maida
hankali ga abincinsa ya ɗago ya kalla Aysha. “Ina Anam?”. Ya faɗa a taƙaice. “Yaya
tana ɗaki bata da lafiya, nayi-nayi ta taso taci abinci amma taƙi kuma ko magani
bata sha ba”. Idanu kawai ya zubama Ayshar, sai abincin dake bakinsa da yake
taunawa a hankali. Sai kuma ya janye kamar baiso yace, “Kiramin ita”. Mikewa Aysha
tai da faɗin to.
Da ƙyar ta taso Anam, amma da tace bazataje ba ita abarta. Sai da Ayshan
tace, “Kin san dai zai iya zuwa har ɗakin nan ya ɓata miki rai ko”. Kamar bazata
tashin ba sai kuma ta tashi tana ɓata fuska ga idanunta jazur. Ya ɗan juya musu
baya, dan haka har suka ƙaraso wajen bai ɗago kansa ba. Sai da Fadwa tai magana
idonta akan Anam datai gefe da fuska sannan ya ɗago. Kallonta yay da ƙyau ya janye
idanunsa. Hakan yasa Fadwa sake yin magana cike da kissa. “Baki da lafiya kuma sai
kije ki kwanta da ciwo a ɗaki Anam?”.
“Uhhm”.
Kawai Anam ɗin tace a taƙaice, amma ko kallonsu taƙi yi daga ita har mijin nata.
Murmushi Fadwa ta sake saki a zahiri, sai dai a ranta daɗin damar data samu takeyi,
cikin sake sakin fuskarta tace, “Kije ɗakina saman mirror cikin First aid box akwai
maganin zazzaɓi sai ki duba wanda zaki iya sha”.
Yanzu kam sosai ta juyo ta zuba mata idanu, mamakin kissa da sabon salon
Fadwan fes a kan fuskarta, sai dai kafin tace wani abu Shareff da yay kamar
bayajinsu ya katseta. “Ki wuce ki ɗakko kizo kici abinci kisha”. Baki ta buɗe zatai
magana sai kuma ta fasa, ta jefama Fadwa dake murmushi har yanzu wani kallon banza
ta wuce zuwa bedroom ɗin nata da yau ne karon farko da zata shigesa. Sai da ta gama
ƙarema ɗakin kallo tana taɓe baki sannan ta nufi mirror zuciyarta na ƙoƙarin danne
abinda ke taso mata saboda kayansu data gani a watse a ƙasa da saman gado alamar
ansha bidiri dai. Magunguna ta samu zube akan mirror ɗin wanda har ta ɗauke kanta
ta kasa sai da ta sake kallonsu.
Wani irin mummunar bugawa ƙirjinta yayi lokacin da idonta ya sauka akan
sticker ɗin ɗaya daga cikin magungunan. Batama san sanda tai wurgi da maganinba ta
fasa ƙara dayin tsalle gefe jikinta na maƙyarkyata. Aysha da Fadwa har rige-rigen
isowa ɗakin suke. Yayinda uban gayyar ya shigo a ƙarshe fuskarsa a haɗe. Aysha dai
dama kanta tayi, Fadwa kam dariya ta fara sai dai shigowarsa ya sata gimtsewa da
sauri itama ta nufi Anam ɗin. Da robar maganin data cillar yaci karo, ya ɗauke
kansa da maida dubansa gareta saboda abinda take faɗa tafukan hanunta rufe da
fuskarta taƙi yarda Aysha ta buɗe.
“ALLAH ya isa! ALLAH ya isa ƴar iska wayyo Mamie na ban yafe ba ban yafe
ba.....”
“Ikon ALLAH badai mu bane ƴan iskan ko Anam?!”. Fadwa ta faɗa cikin tafa
hannaye da nuna damuwa na makirci saboda ganin ya shigo. Shi kuma ɗakin yabi da
kallo har idonsa ya dawo kan robar data cillar ɗin, baima san sanda yakai hannu ya
ɗauka ba yawun bakinsa na ƙoƙarin kamewa. Idanunsa ya rumtse da ƙarfi ya buɗe akan
Fadwa ransa a ɓace. Sai da gabanta ya faɗi ganin yanda idonsa ya kaɗa yay jazur
cikin lokaci ƙanƙani.
“Kamata ku fita!”.
Ya faɗa cikin bada umarni ga Aysha. Hanun Anam daketa faman jera ALLAH ya isa har
yanzu ta kama suka fice. Sai da suka fice ya tako ya zauna a bakin gadon ya dafe
kansa bayan ya ajiye maganin gefensa. Ƙoƙarin danne tsoron dake faɗi a ranta tai ta
nufesa, cike da kissa takai hannu kan kafaɗarsa. “Soulmate wlhy na man....”
“You're vary stupid da zaki faɗamin kin manta. Kinsan suna shigo miki ɗaki
zaki ajiye waɗan nan abubuwan a inda idonsu zai gani. Koke da kika saka kanki
ajiyewar dole ne sai kin bar stickers nasu a jikinsu saboda baki da hankali!!”.
Yanda yake masifa ba ƙaramin bugu zuciyarta ke mata ba. Ta shiga girgiza
masa kai dan yana yine kamar zai mareta. Ta matso da nufin rungumesa ta basa haƙuri
ya tureta ya fice. A falo ya sami su Anam har yanzu tana faman kwarara ALLAH ya
isa, Aysha na tambayarta wai miya faru ta kasa bata amsa.
“Shut up!! stupid!”.
Ya faɗa a tsawacen daya tilasta Anam gimtse bakinta da janye hanunta dake akan
fuskarta har yanzun. Da sauri ta sake maidawa ta rufe ganinsa tsaye a gabansu.
“Idan kika ƙara wani magana anan saina mareki, dalla kuwuce kuci abinci”. Kusan a
tare duk suka miƙe zuwa dining ɗin, yabi bayansu yana jan tsaki mai ƙarfi. Aysha ta
zuba mata abincin, jin yanda yaketa faman jan tsaki a jajjere ya sata cin abincin
badan taso hakan ba. Laumarta baifi uku ba tai yunƙurin mikewa ya watsa mata
harara. Da sauri ta koma ta zauna kamar zatai kuka.
A daidai nan Fadwa ta fito jiki a saɓule, sai dai daka kalleta zaka san
tayi kuka. paracetamol ta ajiye gaban Anam tana satar kallonsa, fruit ɗinsa yake
sha sai dai fuskar tamkar zatai aman wuta. Kujera taja ta zauna. shiru wajen ya
ɗauka babu mai ko tari sai ƙarar cokula. Anam ce ta fara turo nata dan da gaske
zazzaɓin nata neman dawowa sabo yake. Aysha ta ɓalla mata magani ta bata. Amsa tai
tasha babu musu, tana kammalawa tabar wajen da ɗan gudu-gudu dan karma yace zai
dakatar da ita. Itama Aysha sauri-sauri tai ta gama ta gudu ta barsu a wajen......

★★★

Washe gari duk da ta sake tashi da zazzaɓi tana idar da sallar asuba tahau
haɗa kayanta da suka rage, dan tun dare ta tattare wasu. Tambayar duniya Aysha ta
mata akan miye take haɗa kaya bata tanka mata ba. Har Ayshan taji haushi tai shiru,
tamayi kwanciyarta ta juya mata baya. Koda taji ƙarar jan akwati da fitarta bata
motsaba tamayi kamar tai barci ne.
Taji daɗin ganin babu alamar wani ya tashi a gidan, ko mai gadi ma sai da ta
ƙwanƙwasa masa ƙofar ɗaki ya fito ya buɗe mata da mamakin ganinta da kaya. Sai dai
yanda tai kicin-kicin da fuska bai bashi damar mata tambayar dake a ransa ba. Duk
da nauyin akwatin nata ga wata jikkar data ratayo haka taita jansa har titi. Hijjab
din Aysha ne har ƙasa jikinta saboda da kayan barci ta fito. Sai da ta iso har
babban titi ta samu napep, ALLAH ya sota ma babu nisa zuwa titin. Kai tsaye ta faɗa
masa anguwar dazai kaita. Ya faɗa mata kuɗin tace suje kawai.
Sanda suka iso gidan ba kowama ya tashi ba musamman yara dake hutawa saboda
cikin hutu ake. Da mamaki Mom ke dubanta, ta tura baki gaba da faɗin, “Mom bani two
hundred zan bama maigadi a wajensa na amsa naba mai napep.” Komai Mom batace ba ta
mika mata five hundred. Fita tai ta kaima baba maigadi amma sai yamaƙi amsa. Dawowa
tai ta bama Mom kuɗin tare da faɗawa saman three sitters ta kwanta. Mom dai na
binta da kallo. “Lafiya da kaya da sassafen nan?”.
“Ni Mom na gaji dama da zaman gidan can ALLAH. Kawai na taho ne ni tunda
Yayan ya dawo ai”.
“Hummm”.
Kawai Mom ta faɗa ta ɗauke kanta. Anam kuwa barcine ma ya ɗauketa take a wajen dan
jiya kasa barcin kirki tayi, haka kawai ta dinga mafarkin abinda ta gani saboda ta
saka abin a ranta harda amai tai kusan sau uku a daren jiya dan ƙyanƙyami abin ya
dinga bata. Tunda take bata taɓa ganin halittar namiji ba a rayuwarta koda a hoton
ma saboda tsayin daka na tarbiyyar iyayyenta a kanta, duk da kuwa ta tashine a wani
yanki da yasha banban da nata. Hatta wayarta tanada matakan tsaro kashi-kashi da
idon iyayenta ke akai akoda yaushe saboda bata kariya daga faɗawa tarkon musibar
zamani na gane-gane dake zama silar watsa tarbiyyar yaranmu da yawa a wannan
zamanin ta hanyar waya..
Ganin barcin nata zaiyi nauyi Mom tace ta tashi ta koma ciki. Batai musu ba ta
mike ta shige ciki ta kwanta. Barcin daya gagareta a daren jiya shi ta samu damar
ramawa, dan bata farka ba sai kusan sha biyu da rabi. Wanka ta farayi da alwala tai
salla ganin one yayi sannan ta fito dan hayaniyar su Fawwaz dake ɗaukar
hankalinta..........✍

_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_


*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:


07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇


09134848107

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*

[10/26, 12:49 PM] My Zafafa: *_Typing📲_*

*_BABU SO....!!_*
_(Miya kawo kishi?)_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718

*_31_*

.........Sai ƙarfe goma da wani abu Fadwa ta baro sashen Shareff, dan tun a daren
jiya ta lallashi abunta ya sakko duk da dai yaƙi sakin fuska har yanzun. Amma da
yake maza su babu ta ido wani lokacin duk da tsuke-tsuken fuskar tasa hakan bai
hanashi ya biye mata ba ya sake murjeta san ransa a daren da safiya ma. Duk kewar
kwanakin da sukai ba tare da juna ba sai da ya fanshe kayansa da fatan ALLAH yasa
ya samar da madadin abinda ya rasa na tayin cikinsa. A gefe kuma magungunan mata da
tasha su Mamah suka ɗura mata sumane suka sake susutar da shi ya kasa kauda mata
ido.
Ta samu mai-aikinta harta kammaa gyara ko'ina, almajirin ma dake zuwa ya
share tsakar gidan har yayi ya gama abinsa ya tafi, dama da sassafe yake zuwa shi.
Ɗan motsin da taji a kitchen ya sakata leƙawa. Mai aiki ce keta gyaran kitchen ɗin.
Cikin girmamawa ta gaisheta, ta amsa mata sama-sama da tambayarta mita musu na
kalaci.
“Hajiya ai baki faɗi komi za'ayiba, shiyyasa sai na dafa shayi kawai na soya
ƙwai”.
Tsaki taja da buɗe kular da ƙwan ke ciki. Sai kuma ta juyo tana kallon mai aiki.
“Wannan ai shirme ne, Soulmate bazaici ƙwai kawai ba. Ita Ayshan yau wani saban
salo ne ya hanata fitowa kuyi breakfast ɗin tare?”.
“Wlhy hajiya ban saniba, badai ta fito ba har yanzu. Itama waccan ɗin yau
banga fitowarta ba”.
Ɗan tsaki taja ta wuce store. Ta ƙwala mata kira da sauri ta sameta, “Ki soya
Irish, kuma ban san shirme karki cika masa gishiri. Sai ki ɗumama farfesun jiya
dabai ciba zanje nayi wanka”.
“To hajiya”.
Fita tai batare data tanka mata ba. Itako ta bita da harara tana ƙunƙuni duk da
kuwa ta girmi Fadwa nesa ba kusa ba. Shigewarta babu jimawa Aysha ta fito, kitchen
ta nufa kanta tsaye mamakin da gaske Anam ta wuce gida na cinta, dan yanzu tai
kiran wayarta Husnah ta ɗaga tace barci takeyi. Suka gaisa da iya cikin girmama
juna.
“Maman Abu yau duk mun makara kenan ba'ai breakfast da wuri ba ko?”.
“A'a tun ɗazun na dafa shayi aka soya ƙwai, amma hajiya tace a sauyawa Alhaji
bazaici ba”. Cikin ɗan waro ido waje Aysha tace, “Kina nufin Yaya bai karyaba har
yanzu? Sha ɗaya saura fa”.
“Eh ai yanzu hajiyar ta dawo daga wajensa ma”.
“Lallai ma Aunty Fadwa, shine ita bazata zauna ta haɗa masaba kuma ta bar miki.
Na kula har yanzu bata gama sanin wanene Yaya ba.”
“Maman Abu dai batace komai ba, dan ita kanta yau ta jinjina wautar Fadwa
ɗin duk da tun jiya take mamaki akan duk abinda ya faru. A yanda ta santa da
soyayyar Shareff tun suna gida batai zaton zatazo gidan aure tai sakaci haka ba,
tunda dai komai na mace Fadwa ta iya nan kuma mahaifiyarsu (Gwaggo Halima) batai
sakaciba gaskiya musamman ma akan Fadwa data kasance mace babba. Fatan dai ba raye-
raye a wayar nan dake ɗauke mata hankali tazo ta cigaba dayi anan ɗin ba, dan tara
ƙawayen data saba tun acan taga har anan kullum cikin zarya suke.
Da taimakon Aysha aikin ya kammala yanda tasan Shareff zaici a kwanciyar
hankali. Suka ɗiba nasu ta shirya na Shareff ɗin da Fadwa. Tana ƙoƙarin fita Fadwa
ta fito cikin kwalliya sai zabga ƙamshi takeyi. Gaisheta Aysha tayi. Ta amsa cikin
raba hankalinta biyu tana buɗe abincin. Da murmushi ta kalli Aysha. Aysha ta mayar
mata batare da tace komai ba. “ALLAH ya kaini ran aurenki shatu. Dama inata zullumi
nakai abincin nan ya gane banice nayi ba”. Ita dai Aysha dariya tayi kawai. Fadwa
zata ɗauka tray ta amsa da cewa. “Bara na ɗauka sai na gaishesa daga nan”.
A tare suka nufi sashen nasa, sun samesa a falo zaune yana waya. Aysha da
tasan bai cika damuwa da zaman dining cin abinci ba sai ta dire tray ɗin saman
centre table. Fadwa kam gefensa takai zaune dan haka ya ɗan kalleta idanu ƙasa-ƙasa
dan kwalliya na ɗaukar hankalinsa matuƙa ga mace, Fadwa kuwa gwanace wajen iya
tsarawa nan ɓangaren ta ciri tuta dan batajin ganda kamar girki da sauran ayyuka da
latsa waya ke hanata nutsuwar yinsu yanda ya dace. Ya ajiye wayar daya kammala yana
kallonta da ƙyau, sai kuma ya ɗauke kansa ya maida ga Aysha dake gaishesa.
“Kin tashi lfy?”.
“Lafiya lau Yaya, ya gajiyar tafiya?”.
“Alhmdllhi”.
Ya faɗa a taƙaice. Harta yunƙura zata tashi ya dakatar da ita. “Ku har kun karya
ne?”.
“Yanzu zanje na karya Yaya”.
Ɗan jimm yay kamar bazaice komai ba. Dan har ya ɗauke idonsa a kanta sai kuma ya
sake juyowa.
“Har yanzu tana kwance ne?”.
Ta fahimci Anam yake nufi. Dan haka ta girgiza kanta. “Tun ɗazun ta tashi ta
wuce gida”.
Fadwa da sai yanzu ta saka musu baki, tace, “Gida kuma? Rijiyar zaki wai?”.
“Eh aunty, tana idar da sallar asuba kusan 6:30 nama zata da wasa take na
shareta sai dana tashi naga da gaske ta tafi shine na kirata Husna tace min tanama
barci”.
Daɗine ya sauka har cikin ƙasan zuciyar Fadwa, ko banza shirinta na jiya
yayi aiki tunda Anam ta bar mata gida a kan gaɓa. Amma saboda mazuran da yay jiya
sai ta nuna rashin jin daɗinta a yanzu har hakan ya bama Aysha mamaki dan tasan dai
ba shiri suke da Anam ba. Zaman nan da akai tare dan ya zama dolene kawai. Shiko
mai gayya komai bai ce ba. Sai ma umarni ya bata akan ta tashi ta bashi abinci.
Cikin shauƙin farin cikin tafiyar Anam ta miƙe ta fara haɗa masa tea. Aysha kuma ta
miƙe ta fice ta basu waje.
Kusan itace ma ta basa abincin a baki tana zuba masa hirar wahalar da taci
lokacin da ta samu miscarriage. A ransa yana jin rashin daɗin rasa ɗan tayinsa,
amma ya barma ALLAH tunda dama shine ya bashi bada wayonsa ba. A fuska kam
tausayintane sosai sai dai baice komaiba. Rashin maganar tasa yasa ta sake yarda da
maganar su Sima lallai da gaske baya buƙatar cikin a yanzu daman. Ta godema ALLAH
data farga da wuri ta ɗauka mataki gashi yanzu farin cikin dake neman kufce mata na
dawowa gareta.
Basufi awa ɗaya da yin breakfast ɗin ba ya miƙe ya shiga bedroom, babu
jimawa ya fito cikin shirin fita. Kallonsa take da mamaki. “Soulmate badai fita ba
ko?”. Yi yay kamar baijita ba, ya kai zaune da ɗaukar wayarsa ɗaya, danne-dannensa
yay yakai kunne alamar kira, hakan ya sata yin shiru tana kallonsa har ya kammala.
Sake dubansa tai a shagwaɓe. “Dan ALLAH Soulmate fita zakai wai?”. Wayar daya gama
ya ajiye gefensa, batare daya kalleta ba ya bata amsa. “Dama munyi dake bazan fita
ba?”. Baki ta tura da dawowa kusa da shi ta zauna ta narke masa a jiki. Zata fara
shagwaɓa sallamar Khaleel ta dakatar da ita. Kai tsaye ya bashi umarnin ya shigo,
maimakon ta tashi a jikin nasa saita sake narkewa har Khaleel ya shigo. Kallo ɗaya
yay musu ya ɗauke kansa tunda indai taɓarar Fadwa ce ba yau ya fara gani ba.
Shareff daya fahimta bata da alamar tashi ɗin, ya dubeta yana ɗan tsuke
fuska. “Gyara mana”.
Baki ta ƙara tura masa, sai kuma ta tashi fuska a murtuke tabar falon ko amsa
gaisuwar Khaleel batai ba dan har yanzu haushinsa na jiya na ranta ya mata addu'ar
kishiya. Baibi takanta ba shi dai ya gaida Yayansa. Suka mike a tare suka fice dan
motarsa Khaleel ɗin ya amso wajen wanki da yakai tun sassafe. Khaleel ne ke driving
ɗin, yana gefensa suna hira da gaba ɗaya ma akan company ne. Sai ɗai-ɗai data shafi
zamansa a gidansa wanda duk shine ke masa tambaya akan wasu abubuwan.
Sun fara shiga sashen Daddy inda suka sami iyayen nasu uku zaune suna shan
hira. Dan in har Abie na gari to bazaka taɓa rabasu ba sai dai in sun fita aiki,
yau kuma babu aikin shiyyasa har breakfast tare sukayi. Bayan ya gaisheasu su duka
suke masa fatan alkairi akan abinda yaje yayo cikin kulawa. Yaji daɗin addu'oin
iyayen nasa dan su duka yana matuƙar jinsu a ransa. Ya ɗan jima anan tare da su
suna hira har Khaleel ya fice ya barsu, sai da aka kira sallar zuhur suka fito suka
nufi massallaci. A lokacin Anam nacan cike da farin ciki. Dan bata jima da tashi a
barci ba Fawwaz ke sanar mata su Mamie sunzo. Da farko bata yarda ba su Husna harda
Mom nata mata dariya. Ganin haka yasa ta mike ta nufi gidansu, tun a gate maigadi
ya sanar mata, aiko da gudu ta shiga tana ƙwala kiran Mamie!! Abie!!. A lokacin
Abie na can tare da su Shareff zasuje massallaci.
Bayan an idar da salla koda ya shigo gidan sashin Mom ya fara shiga, suka
gaisa har da ƙannensa sannan ya shiga wajen aunty Amarya. Daga can sai sashen
Gwaggo data tsaresa yaci birabisko data dafa. Baici ba, amma yace ta saka masa a
kula zaije dashi gida yaci. Taji daɗin hakan har cikin ranta, ya fito yana
murmushin tsokanarsa da take. Sashen Mommynsa ya nufa inda anan ne ya zauna sukasha
hirarsu har take kawo masa ƙarar Maheer da yay biris kamar ba shirin aurensa ake
ba. Haƙuri ya bata da tabbatar mata zai kira Maheer ɗin a satin nan zai taho gida
insha ALLAH. Taji daɗin hakan har a ranta. Yay mata sallama akan zaije gida sai
zuwa dare zai sake leƙowa.
Daga nan gidan su Anam ya shiga. Inda ya sameta nanuƙe da Mamie da Abie tana
zuba surutu tana cin abinci. Suko sun biye mata sai dariya suke cike da farin cikin
kasancewa da abarsu. Shigowarsa baisa ta daina surutunta ba. Sai dai taƙi yarda ta
kallesa ko sau ɗaya dan tunda taji sallamarsa tai gefe da kanta. Shima kallo guda
yay mata ya ɗauke kansa, ya maida hankalinsa gasu Abie. Tayin abinci Mamie ta masa
babu musu yace zaici. Kasa haƙuri Anam tai sai da ta kallesa. Ya wulla mata harara
ta tura masa baki da ƙyaƙyƙyafta idanu. Fuska ya sake tsukewa cike da gargaɗi a
gareta ta taɓe baki. Duk abinda suke Abie na lure da su sai dai yayi kamar baya
gani har Mamie ta dawo da abincin. Mace ce da sam bata da son jiki, yau da safe
suka iso ƙasar amma bata zauna jiran wani ya basu abincin rana ba bayan na safe da
suka samu Mom ta shirya musu. Tayi girkinta kodan farin cikin Anam, dan abinda tafi
sone ta girka. Abincin ya faraci a nutse suna hirar China da su Mamie, itako ta
daina hirar tana cin abincinta a shiririce tana saurarensu, sai dai sai balla ma
Shareff harara take ta gefen ido.
Sai da aka kira la'asar suka fita da Abie massallaci. daga can ya wuce gida
dan tun ɗazun yake ganin kiran Fadwa na shigo masa yaƙi ya ɗaga, saima wayar da
yasa a silent.........✍
_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_


*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:


07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇


09134848107

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*


[10/26, 12:50 PM] My Zafafa: *_Typing📲_*

*_BABU SO....!!_*
_(Miya kawo kishi?)_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718

*_32_*
...........Itama Aysha a ranar ta dawo gida da dare, shine ma ya kawota tare da
Fadwa. Anam najin sanda suka shigo gaida Mamie ta maƙale a ɗaki har suka fita bata
leƙo ba. Washe gari Mom tazo da mai gyaran jiki. Ba hajiyan bace zatai mata da
kanta, ma'aikatan ta ne, amma saboda Mom tai alƙawarin shigowa kullum ayi a gabanta
insha ALLAH. Ita dai Anam bata damu da wannan zancen gyara ba tun amsar da Mom ta
bata a waccan ranar, dan haka koda suka korata a falo da zasuyi magana ko'a jikinta
tama nufi can cikin gida wajen Aysha dake fushi da ita ta barsu. Da wannan damar su
Mamie sukasha hirarsu dan Hajiyar Sudan tasan Mamie ɗin sukan haɗu idan ta shigo
Nigeria.

_________________

Tun daga wannan ranar aka farama Anam gyaran jikin mai inganci. Yayinda a
cikin gida aketa shirin biki gadan-gadan babu wasa. Ita da Shareff dai haɗuwa ta
gagara. Da zaran taji ya shigo gidan zata bar falo idan har tana zaune ne ma. To
yanzu ma gyaran da ake mata babu dare ba rana yasa bama zaman falon take sosai ba
saboda dokar Hajiyar sudan. Randa Maheer ango ne dai ya iso ta kasa haƙuri sai da
ta fito cike da farin ciki suka gaisa. Sai dai yanayinsa ya saka mata sanyin jiki
dan duk ya ɗan rame gashi babu fara'a tattare da shi.
Washe garin da Maheer ya dawo biki na saura kwanaki goma sha biyar da daddare
Shareff yazo gidan ya samu iyayensa a falon Daddy. Sune sukace yazo sunada magana
da shi. Bai wani damu ba dan duk zatonsa maganar dai bata wuce akan Maheer ba daya
kasa kwantar da hankalinsa akan auren nasa.
Bayan ya gaishesu Daddy ya fara bayani kai tsaye kamar haka. “Shareff mun
kiraka nanne matsayinka na Babba ga duk yaran gidan nan. Da farko dai akan maganar
auren ƴan uwanka ne, Maheer ya samemu jiya akan yanada wadda yake so ba wannan da
ake shirin masa aure da ita ba, sai dai mahaifiyarku tace bazai aureta ba, hasalima
ta haramta masa auren yarinyar. Munyi-munyi da shi yaƙi ya sanar mana wacece, sai
dai ya roƙemu mu roƙa masa ita ta amince masa dan ALLAH. To kai tsaye dai mun amsa
wannan roƙo nasa, sai dai munce yayi haƙuri a ɗaura wannan ɗin tunda an riga an
gama magana karmu kasance ƙananun mutane, munga rauni a tare da shi, duk da baiyi
jayayya damu ba. Dan haka munaso ka kasance da shi dan hankalinsa ya sake kwanciya.
Sai auren Aysha da shima aka ɗaga kamar yanda dangin ango suka buƙata, duk da dai
bakama san da zancen ba dama mun bari sai ka dawo a sanar maka”.
Numfashi Shareff ya sauke a hankaki, kansa a ƙasa cike da girmamawa yace,
“Insha ALLAH Daddy zanyi hakan, ita kuma ALLAH ya zaɓa abinda yafi alkairi, duk
yanda kukayi dai-dai ne ai”.
“Amin ya rabbi. Magana ta gaba kuma akan ƙanwarkane itama Mamana”.
Gabansa ne ya faɗi, amma sai ya cije bai nuna alama ba, sai ma ruwa daya ɗauka ya
ɓalle murfinsa ya kai baki.. Daddy ya cigaba da faɗin, “Wasu dalilai sun sa mun
yanke shawarar aurar da ita itama rana ɗaya da na Maheer ga wani bawan ALLAH da
muke da tabbacin zai riƙe mana amanarta da izinin ALLAH. Itama an gama tsaida
komai....”
Gaba ɗaya ya watso ruwan daya gumtsa har yana fesama Abbah dake a kusa da
shi. “Subahanalillahi” Abba ya faɗa yana yana riƙo ruwan dake neman subucewa a
hanun Shareff ɗin. Daddy da Abie kam sannu suka shiga masa dan bayan fesar da ruwan
tarine mai ƙarfe ya sarƙesa. Idanunsa da sukai masifar kaɗawa da ja cikin ƙanƙanin
lokaci ya ɗago yana kallon Daddy.
Sannu Daddyn ya ƙara masa hakan ya sashi maida idanun ya risinar. Daddy ya
cigaba da faɗin “Karka damu munyi bincike mai zurfi a kansa kafin yanke wannan
hukunci, sannan munada dalilai masu ƙarfi akan hakan. A matsayinka na babba saika
sanya albarka a lamarin duk da yazo a ƙurarren lokaci ko”.
Kansa ya ƙara ɗagowa da ɗan haɗiyar yawu yana murmushin yaƙe. “ALLAH ya
sanya alkairi”. Ya faɗa a takaice yana maida kansa ya dukar. Da amin suka amsa
masa, daga haka suka cigaba da bayanin abinda yasa suka kira san. Bai bar wajensu
ba sai kusan goma da rabi, ko'ina bai shigaba dan yasan duk sunyi barci ma yanzu ya
shiga mota jiri na kwasarsa ya bar gidan....
★Ranar laraba aka saka amaryar Maheer a lalle, ga Anam dai babu abinda ya
danganci hakan sai baƙi da suka fara cika gida. Sai a ranar alhamis ne da safe Abie
da Mamie da Aunty Mimi da Abba da Daddy suka zaunar da ita. Bayan gama mata nasiha
suka koma lallashinta, sai dai gaba ɗaya bata fahimtar wani fari ko baƙi a zantukan
nasu, dan da alama brain nata ta raba tafiya da ƙwaƙwalwarta wajen yin aiki. har
suka gama lallashinta taron ya tashi babu alamar numfashinta na fita daga gangar
jikinta, a da kamar bata damu da auren ba, sai a ƙwanakin nan kuma jikinta ke mata
matuƙar sanyi, rauninta na bayyana a zahiri. Bata samu damar fashewa da kuka ba sai
da Aunty Mimi ta kamota suka komo ciki dan da suna a falon Abie ne.
Mamie dai kasa tsayawa tai, sai aunty Mimi ce ke lallashinta amma kuka ya
gagara tsayawa. Gaba daya ta birkice cikin ƙanƙanin lokaci har takai idanunta sun
fara daina gani da ƙyau. Hankalin su Mamie ya tashi, amma basu yarda kowa ya sani
ba wani abokin Abie amintaccensa doctor ne na ido yazo ya dubata. Ya tabbatar musu
damuwace ta kawo hakan, dan haka ya basu shawarar ai mata allurar barci ta huta.
Wannan shine dalilin hana yin kamun amarya a yau da aka shirya sai dai anyi ɗan
shagali duk da ba kowa yasan minene ya hana ɗin ba. A take ƙananun magana suka baje
gida musamman ga su Mommy.
Duk da sun kasa gane kan zancen sunji farin ciki, har Gwaggo ta kasa haƙuri
sai da tabi diddigin jin ba'asi, jin amarya Anam ce babu lafiya sai gata itada
Mommy da Fadwa wai duba Anam ɗin lamarin zam-mamaki. Suna fita kuwa suka sanya
dariya. Dan dama tun jiya suke dariya da ƙananun maganar rashin kawo lefen Anam
gidan, acewarsu wane aurene haka kamar auren sadaka. Duk da zancen nasu ya koma
kunen su Mamie harda su Daddy ma babu wanda yace komai.
Suna tsaka da wannan farin ciki Dr Jamal ya kira Fadwa yace tazo gida. Sagale
tai tana kallon wayar dan ya yanke, kamar zata share sai kuma dai ganin da number
ɗin Shareff ya kirata ta yanke hukuncin zuwa duk da kuwa a cikin tashin hankali
suke da shi a kwanakin nan. Tadai danne ne kowa bai sani ba sai kawayenta su Sima
dake ƙara tunzurata da tabbatar mata itace mai gaskiya.
Tasan bama suba duk wanda zataima bayani dole zai bata gaskiya. Dan kuwa
ita dai babu abinda tai masa a kwanakin nan ya ɗorama kansa wani irin baƙin rai da
yafi halinsa data sani. A gaba ɗaya satin nan baya fita aiki kullum yana gida
kwance, da farko ta fara lallaɓashi da son jin minene matsalarsa? sai ya dinga daka
mata tsawa da faɗin karta damesa, ta shanye na farko dana biyu ana uku takaici da
ɓacin rai yasa tai fushi itama ta sharesa. Sai shekaranjiya da Dr Jamal yazo ya
dubasa wai bashi da lafiya, haka ta haɗiye taje ta masa sannu ta kula da shi kuma,
amma hakan baisa ya sake mata ba. Zuciyarta ta ƙara tunzura tun a jiya ta haɗo
kayan tahowa nan gidan biki, gudunma karya ƙara ɗaukar azaba ya ɗora mata ta
sanarma Mommy ta masa magana akan zata dawo nan gidan har sai an gama biki, bata
san yaya sukai Da mommy ba tadai kirata tace ta taho, koda taje masa sallama bai
tanka mataba sai hannu kawai ya ɗaga mata, itako tai fushi tai fitowarta ta barosa
duk da taga kamar baida lafiya, ga wata rama da yayi a ƙanƙanin lokaci. Amma murnar
Anam zatai aure yasa takejin dolene ta zam gaba-gaba a bikin nan ai, shiyyasa ta
tsallakesa tai tafiyarta........✍

*_Tofa, su kawu Sharuffudden mike hwaruwa ne haka da ciwo kuma?🤭🤪🚶🏻_*

_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_


*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:


07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇


09134848107

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*


[10/26, 12:51 PM] My Zafafa: *_Typing📲_*

*_BABU SO....!!_*
_(Miya kawo kishi?)_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718

*_33_*

.........Mommy ce ta shigo falon tare da aunty Iklima, batare data lura da halin da
Fadwa ke ciki ba tafara magana cikin raba hankalinta biyu. “Fadwa a fiddo gift ɗin
nan dan yanzu nake son ku wuce gidan wankin amarya ɗin nan ke da Bintu kafin sauran
su biyoku a baya”.
“Mommy inaga sai dai aunty Bintun tayi gaba. Dr Jamal ne yay kirana asibiti”.
“Asibiti kuma? Mi ake acan ɗin?”.
“Inagafa jikin Soulmate ne, dan nata kiransa dama ɗazun bai ɗagamin ba sai nai
tunanin baƙin ran nasa ne bai gama sauka ba”. Ganin tana tafiya tana magana Mommy
ta riƙota da sauri. Kafin tace komai Fadwa ta rigata magana da ƙoƙarin yin gaba.
“Mommy wlhy hankalina a tashe yake idan na dawo mayi magana”. Sakin nata Mommy
tayi, Fadwa ta ƙarasa fita da sauri. Cikin sa'a ta samu napep data ajiye wasu mata.

Azalzalar mai Napep data dingayi yay gudu ya sakasu isowa da wuri, ta miƙa
masa dubu, yana mata maganar ga canjinta bama ta sauraresa ba tai gaba dan a rikice
take. Tana tafiya tana kiran Dr Jamal, cikin sa'a ya ɗaga ya sanar mata inda zata
samesa, sai dai bata gane ba. Dan haka ya turo mata Nurse ta shiga da ita.
Yana kwance samɓal Dr Jamal na gyara masa ledar ƙarin ruwan da ake masa. Ta
ƙarasa cikin sassarfa gaban gadon, idanunsa a lumshe suke alamar barci, yayi wani
fayau da shi saboda ramar da yayi sosai, wadda ita sai ma yanzu ta sake ganinta a
bayyane garesa.... Dr Jamal da gaba ɗaya yake cike da haushinta ya juyo yana
kallonsa babu walwala tare da shi. “Fadwa yanzu kinyi dai-dai kenan? Mijinki na a
cikin irin wannan halin amma kika tsallake kika tafi gidan biki kika barsa?. Badan
ALLAH ya kai Khaleel gidan ba kin san kuwa komai zai iya faruwa?”.
Kukan da take rikewa ta saki, ta kai duƙe gaban gadon tana kamo hanunsa da
babu ƙarin ruwan. “Doctor ni ban san jikinsa yayi tsanani hakaba wlhy, duk ta inda
na ɓullo dan nasan damuwarsa ya kasa bani damar hakan..”
“Amma sai ki sanar a gida tunda ke yaƙi ya sanar miki....”
Shigowar su Abba ya hanata bashi amsa. Khaleel dake gaba ya watsa mata harara
ya ɗauke kansa. Taga harar tasa amma sai ta ɗauke kanta, tare da zare hanunta daga
cikin na Shareff. Abba da Abie dai sai maimaita sunayen ALLAH suke a bakunansu, dan
yanda Shareff ɗin yay fayau na rama a ƙanƙanin lokaci ya basu tsoto. Dr Jamal ya
gaidasu, tare da kwantar musu da hankali akan su masa addu'a dan jikin nasa da
sauƙi. Addu'ar fatan ƙara samun sauƙin sukai masa, tare da jajanta al'amarin. Abie
ya kalli Fadwa dake gefe tsaye, faɗa ya fara mata akan miyasa bata sanar da kowa
Shareff ɗin baida lafiya ba. Shiru tai taƙi tankawa, sai ma fuska data ɗaure tamau
dan kamanin Anam data gani tattare da dattijon ya bata tabbacin shine baban Anam
ɗin kuma ƙanin Mamansu da suke uba ɗaya. Duk da cikin taushin murya da sauƙaƙawa
yake mata faɗan sai ta murguɗa baki, babu wanda ya lura da abinda tayi sai Abie.
Maimakon yaji haushi amma sai yay Murmushi kawai.
Abbah da jin bata amsawa Abie ɗinba ya dubeta shima ransa a ɓace, baida faɗa
amma in aka kuresa shima ɗan babu sauki ne. Aiko ya balbaleta da masifa yana
zaginta akan shiru dataima Abie ɗin. Haƙuri Abie ya fara bashi amma yaƙi
saurarensa, sai da yayi mai isarsa har Fadwa ta fara share hawaye sannan ya ƙyaleta
dalilin dawowar Dr Jamal ɗakin.

Cikin ƙanƙanin lokaci rashin lafiyar Shareff ɗin ta shiga kunnen kowa. Waɗan
da basu riga sun wuce wajen kamu ba sai suka zarto asibitin dubasa. Babu wanda aka
bari ya shiga wajensa dan ba'ason masa hayaniya. Sai Mommy data matsa ita da Gwaggo
suka leƙasa. Har dare anata shigowa asibitin duba san, dan wandama sukaje gidan
kamu daga can nan suka dinga zartowa. Hakan sai ya tabbatarma da jama'a mara
lafiyan ɗan dangi ne. Har sha biyu bai farka ba, anata ma ƙara masa ruwa har
lokacin, dole kowa ya tattara ya tafi aka bar Khaleel da Maheer a wajensa duk da
Fadwa harda kukanta itace zata zauna da shi. A can gida ma Anam tana kwance rijif
da zazzaɓi duk da doctor yazo ya dubata bayan na ido. Haka dai aka kwana zukatan
mutane da yawa babu daɗi.

Washe gari aka tashi da shirin ɗaurin aure duk da rashin daɗin da ake ciki
akan ciwon Shareff dan na Anam ba kowa ya sani ba. Da sassafe Fadwa ta wuce asibiti
ita da Mommy data zillema mutane da ƙyar. Sun samu ya farka har Maheer ya taimaka
masa zuwa bayi yayo alwala. Yana cikin yin sallar daya makara ne suka shigo. Sun
ɗanji sanyi a ransu. Suna zaune harya idar, suka shiga jera masa sannu yana amsa
musu da kai dan sam baya son yin magana. A dai-dai lokacin suma su Abba suka shigo
harda Daddy, kamashi su Khaleel sukai ya koma saman gado, cikin magana ƙasa-ƙasa da
bata fita da ƙyau ya gaida su. Cikin kulawa duk suke amsa masa da tambayar ƙarfin
jikinsa. Ya amsa musu “Da sauƙi” akan laɓɓansa. Abba ya fara masa faɗa akan ya akai
ya zauna da ciwo haka babu wanda ya sani? Sai kace wanda baida kowa?.
Ɗan murmushin ƙarfin hali yayi na yaƙe, murya ƙasa-ƙasa yace, “Abba
zazzaɓine kawai shiyyasa. Kuma naji sauƙi Alhamdulillahi”.
Abie ya girgiza kansa yana mai dubansa da tausayawa. “Wannan yafi ƙarfin
zazzaɓi kawai my son. Kaga kuwa yanda ka rame? Sannan a kwanakin nan gaba ɗaya babu
mai ganinka, mu duk mun zata aikine ya maka yawa shiyyasa”.
Ɗan murmushin yake ya kumayi sai dai baice komaiba anan ma. Idanunsa da
sukai wani irin kaɗawa jazur ya lumshe da jingina a jikin filon da Khaleel ya saka
masa. Ya buɗesu a hankali ya saci kallon Mommy da Fadwa dake zaune kowa ya zuba
tagumi. A hankali ya furta “Mommy inajin yunwa”.
Kai Mommy ta jinjina masa, tare da taɓa Fadwa datai zurfi a duniyar tunani.
Numfashi ta kawo mai haɗe da ajiyar zuciya ta kalli Mommyn. “Kira su Bintu muji wai
ba'a kammala abincin bane gashi yace yunwa yake ji”. Da to ta amsa. Tana shirin
kiran waya sai ga sallamar Mom da Mamie. Su Abba ne kawai suka amsa da Khaleel.
Suka shigo Maheer biye da su ɗauke da basket, sai Mubarak da carton na ruwa. Daga
Mom har Mamie fuskokinsu sun kasa ɓoye damuwarsu akan yanayin Shareff ɗin, suka
shiga masa sannu da jera masa addu'a su Daddy na amsawa da amin. Mommy da Fadwa dai
sunyi kamarma basu san da zuwansu ba. Abba ne ya bada umarnin Maheer ya zuba masa
abincin dasu Mom ɗin suka kawo tunda yace yunwa yakeji daman...
Shigowar Doctor ta sakasu duk suka fito, Daddy ya dubi agogo, ganin lokaci
yaja gashi yau juma'a ga ɗaurin aure yace su ai gara su wuce gida ma Khaleel da
Fadwa sai su zauna a waje sa, dan dama acan gida sune suka hana kowa zuwa har
Gwaggo. Cema mutane akai kawai an ma sallamesa dan haka kowa ya dakata da yunƙurin
zuwa aka maida hankali ga shagalin biki. Fadwa da Khaleel aka bar masa, su kuma
gaba ɗayansu suka wuce gida, sai dai Maheer bai so hakaba, soyay shima a barsa anan
basai yaje ɗaurin auren ba. Amma babu yanda zaiyi su Abba suka korashi, ga Mommy
sai zabga masa harara takeyi.....

★★

Gidajen biyu duk sun gama cika da jama'a, bakajin komai sai hayaniya da al'ada
irin ta biki. Maza duk sun wuce massallaci domin halartar sallar juma'a da ɗaurin
aure. Yayinda amarya Anam ke ƙudundune har yanzu taci kuka harta godema ALLAH,
zazzaɓi ne mai tsananin zafi tattare da ita. Haushin kowa takeji a gidan, har shi
Muzzaffar ɗin da rabonta da shi a zahiri tun randa Shareff ya dawo, saita waya
jefi-jefi yake kiranta daga gaisuwa kuma sai yace mata yana da uzuri. badan bata
son sa ba take jin haushinsa, kauce-kaucen da yake mata ne yafi komai mata zafi,
musamman a kwanakin matsowar bikin. Su Abie sun isa da itane shiyyasa take danne
komai saboda farin cikinsu, ko sai bayan sun ɗaura mata aure suka gaya mata bazata
taɓa jayayya da su ba saboda matuƙar girma da darajar da suke da shi a gareta. Amma
shi mizaisa ya dinga mata kauce-kauce kamar dole akai masa ya aureta bashi yazo
yace yana sonta ba?, ya kuma ɗauke ƙafa da zuwa inda take ma sai kace zasuyi auren
ƙiyayya?. Hawaye ne suka cigaba da silalo mata a hankali dan bata da ƙarfin yin
kuka, a wannan yanayin barci ya saceta saboda allurar barci da doctor ya mata.

★Tun bayan barin su Daddy asibitin yaƙi ya sake magana da kowa, Fadwa da
Khaleel ma cayay su bashi waje yana buƙatar kaɗaici. Ran Fadwa ya ɓaci sosai har ta
kasa shanyewa ta dubesa zatai magana Dr Jamal ya ɗan girgiza mata kai da mata
alamar roƙo kar tace komai. Harara ta watsama Shareff tai fitowarta. Shiko Khaleel
biyota yay fuskarsa ɗauke da murmushi, yayi tunanin ma asibitin zata bari gaba
ɗaya, amma sai ya sameta a waje zaune tana danna waya alamar kira take ƙoƙarin yi.
Baice mata komai ba ya kai zaune a kujerar dake kallonta, waya ya ɗauka shima, yana
jinta tana faman jan tsaki da alama wanda take kiran bai ɗauka ba. Suna a wajen
zaune Dr Jamal ya fito, Fadwa ya kalla dake cika tana batsewa. Yay murmushi da
girgiza kansa. “Madam kiyi haƙuri kar kiji zafinsa da yawa, shi mai ciwo haƙuri ake
da shi dan bakomai ake masa yaga an masa daidai ba. Zaki iya komaa yanzun ya samu
barci, amma ba'a buƙatar motsi mai ƙarfi dan barcin nasa bazaiyi nauyi sosai ba”.
“Amma Doctor dan mutum na ciwo sai ya dinga dizga mutane kuma. Shi baya ganin
ƙoƙarin mu ne?”. “Bawai baya gani bane, yanayin da yake ciki ɗinne sai anyi haƙuri
da shi Please. Ki ƙara haƙuri ki koma ciki mu zamuje massallaci ne”. Bata sake cewa
komai ba ta tashi ta shiga, su kuma suka fice shi da Khaleel da yaƙi saka baki a
maganar tasu dan ƴan miskilancin na kusa..........✍
_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_


*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:


07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇


09134848107

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*


[10/26, 12:51 PM] My Zafafa: *_Typing📲_*

*_BABU SO....!!_*
_(Miya kawo kishi?)_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718

*_34_*
...........A wajen ƴan biki kuwa dawowar ƴan ɗaurin aure ya sake ruɗa gidajen biyu,
bakajin komai sai guɗa da kirarin maroƙa tako'ina. Bakin su Daddy ya kasa rufuwa
saboda tsananin farin cikin da suke ciki na sake samun damar aurar da yaransu a
karo na uku. Hakama Mommy tana a cikin tsananin farin cikin cikar burinta na sake
aurar da Maheer ɗinta a ganinta ta raba ƴaƴanta biyu da ƙaya. Shiko ango Maheer ko
walwala baka gani a fuskarsa, dauriya kawai yake na amsa gaisuwar jama'a da taya
murna a garesa saboda baya son su Daddy suga kamar bai ɗauka shawararsu ba......
A ɓangaren Mamie da Abie ma duk da wannan rana ta tilon ƴarsu tazo musu a
yanayin da basu gama shiryata yanda suke so ba hakan bai hanasu kasancewa cikin
ɗunbin farin ciki ba, dan albarkar auren suke nema mata ba wai tsarabe-tsaraben
cikinsa ba. Fatansu ALLAH ya bata zaman kafiya da zuri'a masu albarka ita da
mijinta. Suna zaune a ɗakin Abie da take barci suna kallonta fuskikinsu murmushi ya
kasa sauka, ga ɗunbin tausayinta da ƙaunarta na ratsasu. Abie ya kauda kai gefe
yana murmushi ganin Mamie na sharar hawaye, cikin son danne nasa dake ƙoƙarin
sakkowa ya miƙe yana kai waya kunnensa tamkar zaiyi kira ya gudu a ɗakin......
Ƙananun maganar da suka fara fitowa a bakunan mutane saboda jin yanda
ɗaurin aure ya kasance suka fara yawaita a gidan har wasu a dangin Mommy ya fara
isa kunnuwansu. Da yawansu mamaki suke nunawa jin yanda al'amari ya kasance dan su
dai basu san da wannan aure ba. A cikin ƙanen Mommy da abin ta jisa tamkar saukar
aradu ta kasa haƙurin shanyewa kamar kowa ta shiga neman Mommy. Da ƙyar ta samota a
sashen gwaggo wajen tsoffi na ƴan uwa da ƙawayen ta da suka taru acan.
“Ke ko lafiyarki kuwa Samira kika shigo mana kamar wadda take a rikice”.
Gwaggo ta faɗa ganin yanda aunty Samiran ta shigo har tana cin tuntuɓe. “Gwaggo
dole kike ganina a haka, wani mummunan labari nake jiyowa yana tashi a gidan nan
dana gaza gaskatawa, Aunty dama akwai auren wata bayan Fadwa akan Shareff?”.
“Samira ban son takale-takalen masifa ina cikin farin cikina wane aure
kuma?”.
“Humm aunty kenan, aure nawane aka ɗaura a gidan nan yau, kidai bincika dan yanzu
naji anata ƙus-ƙus wlhy wai dama matarsa ce sai dai yau aka sanar.” A rikice Mommy
ta kalli gwaggo, itama gwaggon kallonta takeyi baki buɗe. Cikin ƙarfin hali gwaggo
tace, “Nifa sam bamma gane wannan soki burutsun nakiba wlhy Samira”.
“Nima da nake faɗa mukun na kasa ganewar, inaga bincikawar dai kamar ya
kamata kuyi”.
Suɓucewa plates dake a hanun Mommy sukayi, ƙirjinta na matuƙar bugawa da sauri-
sauri. Fitt ta fito ɗakin Gwaggo na ƙwala mata kira amma bata juyo ba. A yanda ta
fito ɗin yaja hankalin mutane da yawa suka shiga binta da kallo. Kai tsaye sashen
Daddy ta nufa, sai dai koda ta shigo bata samu kowa ba sai kwanikan abinci dake
barbaje alamar anci. Har bedroom ta leƙa, nan ma babu kowa a ciki. Da sauri ta
shiga laluben wayarta dake cikin handbag ɗin hanunta da take tara kuɗin yinin
bikinta dan yau takeyi, hannunta ma rawa yake, tadai samu da ƙyar ta lalubo number
Daddy tai dailing. Sai da ta kusan tsinkewa ya ɗauka, babu ko sallama tace, “Daddyn
Shareff wani shirme nakeji yanzun, nazo sashenka kuma baka nan?”.
Kai tsaye ya gano abinda taji ɗin, dan haka a dake yace “Ina waje tare da
mutane, idan na shigo sai muyi magana...” ƙitt ya yanke wayarsa tana ƙoƙarin
dakatar da shi. Tsananin tsoro ne da firgici ya ƙara saukar mata. Tabi wayar da
kallo kamar zata gano Daddy ɗin a ciki. Kai ina bazata iya haƙuri ba sam, akalar
kiran nata ta maida ga wani yayansu data tabbatar Daddy baya ɓoye masa komai dan
abokinsa ne shaƙiƙi tun ƙuruciya. Bugu biyu ya ɗauka, tai ƙoƙarin shanye tashin
hankalinta dan tasan saita lalama Yaya Awwalu zai faɗa mata abinda take bukatar.
Bayan ta gaishesa yake cemata tayi haƙuri bai shigo ya mata an ɗaura aure ba wani
uzirine ya taso masa amma zuwa anjima zai dawo gidan.
“A'a babu komai Yaya ai kai mai yine, yanzuma na kiraka ne saboda inji ko
kana tare da abokin naka dan zuwa anjima ina son ka ɗan ƙarama Maheer faɗa kasan
yaran nan da taurin kai, Shareff ya fisa haƙuri da biyayya tunda kaga shi duk
aurarrakin nan zaɓinmu ne amma ko yau bai tada hankalinsa ba akai”.
Yaya Awwal yay ƴar garan murya irin ta manya da ɗan murmushi, “A'a karki
damu shima zai kwantar da hankalinsa ai, kuma hankalinsa aiba ɗaya dashi Mustapha
ba. Amma zan shigo ɗin insha ALLAH, yaya jikin shi Mustapha ɗin ma? Dan ina
tambayar bangansa ba akace yana asibiti babu lafiya”.
“Eh wlhy zazzaɓine ya kadashi amma da sauƙi, inagama yau za'a sallamosa tunda
ba'a kai amarya babu ango ba”.
A karon farko yay ƴar dariya mai sauti da faɗin, “Wannan gaskiya ne, ALLAH dai
ya basu zaman lafiya da haƙuri da juna tunda duk gidane, sai dai dan ALLAH kiyita
ƙara nusar dashi da tausarsa tunda su duka ƴan uwansa ne kar zuminci ya samu
matsala azo ana hai hai babu daɗi. Gaba ɗayansu ɗaya suke a wajensa babu wadda tafi
wata.......”
Tunda ya fara jawabin nasa na ƙarshe jikin Mommy ya hau rawa, bazata iya
jin ƙarshen zancem ba dan haka ta yanke wayar. Hajijiya taji tana neman ɗibarta, a
dai-dai nan Gwaggo da taga shiru bata dawoba ta biyota ta shigo. Salati ta saka da
riƙeta da sauri. “Ke ko kina lafiya zaki kashe kanki Nafisa?”.
Kuka Mommy ta fashe da shi, “Gwaggo sun kasheni, wlhy sunyi a banza, har
abada jinina dana Usman bazasu zauna a inuwa gudaba. Gwaggo na rantse yau duk
masifar da za'ai a gidan nan sai dai ayi sai Shareff ya saketa, ni Muhammad zai
cima amana, ni Muhammad zai yaudara ya zalunta.....”
“K wai miya farune kin sani a duhu?!”.
“Gwaggo aure fa suka ɗaurama Shareff da ɗiyar maƙiyana, wai ƴar gidan Usman. Kuma
tabbas batun yau ba ma.”
“Ƴar gidan Usman?!!”.
Gwaggo ta faɗa a razane, Mommy bata amsa mataba ta mike fuu ta fito hanunta dafe da
kanta dake juya mata. Gwaggo na ƙoƙarin tsaidata yanzu ma bata saurareta ba. kai
tsaye hanyar gate tayi, Samira ta biyita da sauri. “Yaya! Yaya miya faru ne? Da
gaske ne ko?”.
Bata iya bama Samira amsaba ta fisgi gyalenta tai waje, kasancewar anata ɗaukar
ƴan biki da kawosu ta samu a napep. Daddy daya hangota da yake suna zaune a ƙofar
gidan cikin runfa ya miƙe, sai dai kafin yazo har napep ɗin tabar wajen.......

★Tun ɗazun ya farka saboda zuwan gayyar abokansa da sukaje ɗaurin aure.
Shidai kallon mamaki yake musu, dan baiyi tsamanin ganinsu haka da yawa ba a waje
ɗaurin auren ƙanin nasa. Suko sai faman washe baki suke da tsokanarsa a sigar daya
kasa ganewa dan kowa ya kasa fitowa fili yace wani abu saboda ganin Fadwa tare da
shi. Ga kuma dama Dr Jamal ya rokesu kar suce komai anan Please. Basu wani jima
sosai ba suka fita acewarsu zasuje cin abinci zuwa anjima zasu dawo duk da Doctor
yace maybe ma zuwa dare su sallamesa. Bayan fitarsu Fadwa ta dawo kusa da shi.
Ganin yanda tai kicin-kicin da fuska sai yaji wani iri, hannu ya miƙa mata alamar
tazo, tai kamar zata noƙe sai kuma ta nufesa ganin yay mata alamar roƙo. Jikinsa ya
jawota ya rungume, ya sakar mata sumba a gefen wuyanta tare da ɗaura kansa a
kafaɗarta yay shiru. A hankali ta lumshe idanunta da haɗiye kukan dake neman ƙwace
mata.
“Shii!!”.
Ya faɗa a hankali cikin kunnenta yana kai hannu ya tallafo fuskarta ya juyo da
ita...... Burumm ta faɗo ɗakin kamar an jehota. Su dukansu sukai saurin kallon
ƙofar, ganin Mommy ya sashi janye jikinsa cikin jin tsananin kunya, Fadwa kam wani
irin takaici ne ya tsargi ranta kamar ta dannama Mommy zagi. Mommy kam da sam
hankalinta bama yakai kan yanda suke ɗin ba ta jefa masa takarda da biro saman
jiki......
“Rubuta mata saki uku yanzu-yanzun nan da manyan baƙi yanda iyayenta zasu
gani da ƙyau bama ƙanana ba...”
Cikin tsananin mamaki da rashin fahimta yake duban mahaifiyar tasa. Yayinda
ƙirjin Fadwa yay wani irin mahaukacin dokawa tamkar gagarumar aradu ta bada sautin
fashewa. Ita dai tasan ita kaɗaice matarsa ai........
Takarda da biron ya tattara ya ɗauka, a hankali cikin muryar mara lafiya
ya dubi Mommy. “First luv ban gane ba. Wazan saka?”.
“Shegiyar yarinyar da aka ɗaura maka aure da ita a ɓoye mana, inba hakaba zan
tsine maka Al-Mustapha, tsinuwa mai muni kuwa da a duniya ko kai bazaka ƙara morar
kanka ba balle waninka!!”.
A kusan tare zuciyarsa data Fadwa ta nema wantsalowa waje. Cikin rawar lips
shi yay ƙarfin halin faɗin, “A...Aure kuma? First luv n... Ni aka ɗaurama aure??”.
Sake fusata ta tambayar tayi, cikin tsananin kaushin murya ta sake bashi
umarni batare data amsa masa tambayarsa ba. “Bani da lokacin maka wani bayani anan,
dan wlhy zan iya tsine maka Al-Mustapha. Da manyan baƙi cikin sakanni ashirin kacal
ka rubuta Kai Al-Mustapha Muhammad Shareff, ka saki ƴarsu Anam Saki uku har abada
bakai babu ita. Inko ba hakaba shinuwa zata tabbata a kanka bayan cikar waɗan nan
sakannin”.........✍

*_🙆🏻Ni balki wannan jidali har ina. Wannan fa shine TA LEƘO TA KOMA!. Shareffuddeen
zaɓin Mommy ko zaɓin Daddy?🤐🚶🏻._*

_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_


*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:


07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇


09134848107

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*

[11/3, 7:19 PM] My Zafafa: *_Typing📲_*


*_BABU SO....!!_*
_(Miya kawo kishi?)_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718

*_35_*

_ASSALAM ALAIKUM DEARIES ... BARKAN KU DA KOKARI .. KAMAR KODA YAUSHE. WANNAN KARON
MA MUNA BARAR ROKON KU WAJEN TEMAKAWA CHANNEL DIN SUDEIS DAKE MANHAJAR YOUTUBE_

_YARO NE DAYA TASHI DA SON KARATUN ALQURANI ME GIRMA. YA KE KUMA KWADAYIN GADON ME
SUNAN SA SHEIKH SUDEIS. DAN ALLAH A TEMAKA A DANNA MASA SUBSCRIBE. A KUMA YI
VIEWING DA LIKING. A TEMAKA DA SHARING MA... JAZAKUM ALLAH KHAIRAN AS YOU DO...💕_

Assalamualaikum dear sisters and brothers.

Welcome to ummu sudais YouTube channel🥰


A channel where the Holy Quran is been recited from different Angles.
Click on this link and listen to the Beautiful recitation that will melt your heart
https://youtu.be/Lafgc749sK8

Your subscription to our channel is of Great important. Please help us grow our
channel by subscribing and liking our videos fisabilillah.
Thank you so much

--------------------

..........Cak numfashin Fadwa ya ɗauke daga ƙirjinta, idanunta suka fara ganin
duhu-duhu, tai baya luuu zata faɗi dan wani irin mugun hajijiyace ta lulluɓe
ganinta da jinta saboda maganar tazo mata ne tamkar saukar nokiliya.... Laɓɓanta
matuƙar rawa suke na alamar sonyin magana, amma bushewar yawun dake taimakawa
maƙoshinta ya hanata damar hakan. Sai faman raba idanu take a tsakanin Mommy dake
tsaye tamkar bajimar zakanya taga abin farautarta da Shareff da alamu suka nuna
shima yayi ƙamewar wucin gadi ne saboda wani dalili na mamakin furicin Mommy ɗin ko
wani abu daban da bata hasaso ba.....
Shigowar Daddy ɗakin tamkar an jehosa ta maido Shareff a tashi sumar tsaywar
jinin data riskesa tabbacin hasashen Fadwa, dan shima dai jinsa da ganinsa a take
suka rabu da gangar jikinsa baki ɗaya, sai idanunsa ne kawai tsaye ƙyam akan Mommy
na tabbacin bashi da maraba da sumamme.
“Bazan hanashi bin umarninki ba, sai dai nima a nawa umarnin, wlhy! Wlhy!
Wlhy!! Idan har Al-Mustapha ka saki Mamana! Nima zan saki uwarka dai dai da adadin
sakin da ta sakaka ka rubuta!!.......”
“Dana haɗa jini da Usman da Ai'sha gara na barka har abadan abidina
Muhammad!!”. Mommy ta tari numfashin Daddy a tsawace.
“Okay fine! Haka kikace ko?. Kai Al-Musta..........” Shigowar Abba da Dr
Jamal ta hana Daddy ƙarasa faɗar abinda ke bakinsa, sai dai wani irin mugun kallo
da yake bin Mommy da shi, har cikin ranta yake ratsata, sai dai zuciyarta tayi
bushewar da take jin zata iya ɗaukar koma minene daga garesa akan wannan auren da
rabashi shine kawai samun nutsuwar ruhi a gareta. Gwaggo ta riƙo hanunta tana
faɗin, “Altine kina lafiya kuwa? Kai Muhammadu karka sake cewa komai kumuje gida”.
Mommy ta fusge hanunta daga riƙon da Gwaggo taimata. “Wlhy Gwaggo babu inda
zanje sai Al-Mustapha ya saki yarinyar nan, dan bana buƙatar auren nan ya sake
minti guda a kansa!!”.
Dr Jamal da gaba ɗaya ya rikice cikin roƙo yace, “Dan ALLAH Mommy kiyi
haƙuri, bara na basa sallamar sai aje gida wannan maganar bata nan bace ba”. Kafin
tace wani abu Gwaggo taja hanunta suka fice, ganin shima Daddy ya fita ya sata
yarda ta bita. Abbah ya kama Shareff shi da Doctor Jamal. Wata Nurse kuma ta kama
Fadwa da har yanzu babu alamar ta dawo hayyacinta.......

Sun sami gida ya gama hargitsewa shima. Dan Gwaggo Halima da komai yaje
kunnenta gaba ɗaya ta haukace, sai zagin Abie take da tone-tone, dan waje ta fito
tana faɗar maganganu marasa daɗi, Abie ya miƙe ya shige cikin gidansa, amma sai ta
bisa har can. Jin zagi da tonan asirin yayi yawa Aunty Mimi ta kasa haƙuri duk da
kowa ya santa mutumce mara faɗa da son hayaniya. Amma zagin mahaifiyarsu da Gwaggo
Halima keyi bazata iya jurewa ba ta fara tayata. Cikin ƙanƙanin lokaci hayaniya mai
tsanani ta tashi dan dangin Mommy irinsu Samira tuni sun shigo gidan suna taya
Gwaggo Halima.
Ran Daddy ya ƙara ɓaci, yayinda hankalin Abbah dana Shareff sukai matuƙar
tashi su kuma. Da ƙyar Gwaggo ta hana Mommy shiga gidan, yayinda Dr Jamal ya
taimakawa Shareff zuwa ciki, wasu mata kuma suka kama Fadwa da zuwa yanzun ta fara
kuka sai dai babu uhhm babu uhhm-uhhm.
Daddy kam daya faɗa gidan Abie lafiyayyun maruka guda biyu ya sauke akan
fuskar Gwaggo Halima. Tamkar ƙiftawar idanu gidan yay tsittt, ya kuma sauke mata
wasu biyun da suka saka zukatan mafi yawan mutane girgiza. Gwaggo Halima maiji da
kanta, Gwaggo Halima babbar mace hamshaƙiya mai taƙama da tunƙaho da sunan mijinta
da muƙaminsa koda a tsakkiyar cikin dangine, yau itace ake saukema waɗan nan
marukan, dole ne gida yay tsit. Daddy ya ɗaga hannu zai sauke mata na huɗu Abie ya
riƙe masa hannu. Cikin tsananin damuwa yake girgiza masa kai alamar roƙo. Ɗagowa
Gwaggo Halima tai tare da ware hannu zata mari Abie taji an riƙe mata hannu tare da
murɗesa. Abbah ne da wannan aikin, ransa a matuƙar ɓace tamkar bashi ba.....
“Ko'a mafarki kikai tunanin wannan kuskuren sai mun tabbatar da nadama a
rayuwarki Halima!!”. Kalaman Abbah dake amsa sunan ƙani a gareta sukai matuƙar
ratsa kunnuwanta dama duk wanda ke a wajen.
Sosai fa gida ya ƙara harmutsewa da ruɗewa. Har hayaniyar ta saka Anaam dake
barcin wahala farkawa. Tun farko ma Mamie ce da hankalinta ya tashi ta rurrufe
windows yanda bazai kawo kunnen Anam ɗin ba, sai dai ƙurar data sake tashi a yanzu
tafi ƙarfin ta farko. Da ƙyar aka fidda Gwaggo Halima dake cigaba da ɗurama Abie da
Mamie da Aunty Mimi harma da su Daddy zagi daga gidan. Sai dai can cikin gidan ma
Mommy ce ke borin sai Shareff ya saki Anam. Shiko ya shige bedroom ɗin Daddy ya
kulle kansa sai faman dukan ƙofa take da tabbatar masa zata tsine masa.
Yana jinta, sai dai baya gane mi take faɗa saboda hajijiyar dake juyawa da
kansa. Yana zaune bakin gado hanunsa dafe da kansa hawaye na zirara akan fuskarsa.
Tunda yake a rayuwarsa bai taɓa ganin makamancin irin wannan tashin hankaliba.
Daddy da gaba ɗaya idanunsa sun rine da ɓacin rai ya fisgo Mommy dake faman jijjiga
ƙofarsa tana jaddama Shareff ya buɗe kota tsine masa. Babu zato ko tsammani ya
sakar mata nata lafiyayyun marin itama da iyakar ƙarfinsa. Dan tsabar azaba da
firgita sai da ta faɗa kan kujerar dake daura da ita hannunta duk biyu dafe da
wajen da ya maretan.
“Muhammad ni ka mara?!!”.
“Idan kika ƙara cewa tak ma, zan iya miki dukan mutuwa ba mari kawai ba!!”.
Kalamansa sunyi matuƙar razana duk wanda ke'a falon. Sai dai shi a garesa babu ko
gezau ya sake tabbatar mata ta hanyar faɗin “Idan kuma kinji ƙarya bismillah gwada
na tabbatar miki!!”.
Bakin kuwa tai shirin buɗewa zatai maganar dan zuciyarta ta rigada ta bushe
Gwaggo tai saurin toshe mata shi, dan ita kam taga tsantsar wutar bala'in dake ci a
cikin idanun Daddy irin wadda bata taɓa ganiba a rayuwarta. Duk yanda Mommy taso
Gwaggo ta sakar mata baki taƙi, nanfa suka hau kokawa, sai dai ALLAH ya taƙaita
abun a dalilin shigowar yayun Mommy maza da Abbah yay kiransu a waya harda wanda ta
kira ɗazun taji komai a bakinsa da ƙanin mahaifin Fadwa.
A tsakar gida dai ƴan biki masu gudun tashin hankali tuni sun fara zare
jikinsu suna guduwa dama Magrib tayi, wanda kuwa zasu kwana anan da ƴan son ganin
yaya za'a ƙare na zaune jugum-jugum, ƴan bani na iya kuma nata ƙus-ƙus. Fitowar su
Daddy zasu wuce massallaci ya saka gidan ɗaukar tsit dan ko'ina akwai hasken wutar
nefa, sai dai wasu basu daina magana ƙasa-ƙasa ba sosai musamman waɗanda ke'a ɗan
nesa da su.....

Bayan sallar isha'i duk wani mai faɗa aji a gidan ya hallara a sashen Daddy
ne. Dan hatta Anam da bayan farkawarta kunnenta ya jiye mata wasu maganganun da
harta ɗan fahimci abinda ke faruwa da akema jidalin tana wajen. Sai dai kuka take
har muryarta bata fita, dan kunnenta ya jiye mata wasu manya-manyan zagi da Gwaggo
Halima ta dinga jifan iyayenta da su. Gashi kuma Mamie na kuka ita da Aunty Mimi da
babban yaron Aunty Mimi ɗin da Amrah. Tsabar kukan da take har amai tayi dan ji
take kamarma ta mutu itakam ta huta, sai dai taci alwashin bazata taɓa zaman aure
da Shareff ba itama.....
Yayan Mommy da suke kira da Baba Ibrahim ne ya gama ƙarema kowa kallo,
ganin babu Shareff a wajen ya tambaya. Anan ne Abbah ya mike ya nufi ƙofar bedroom
ɗin Daddy. Zaune yake a kan sallaya hanunsa dafe da kansa dake matuƙar sara masa
kamar zai faɗi, sallarma da ƙyar ya iya tashi yayita ganin lokaci zai shige dan har
magtib ya haɗa. Jin muryar Abba ta sashi miƙewa da ƙyar ya nufi ƙofar ya buɗe, Abba
dake kallonsa cike da tausayawa ya ɗan riƙo kafaɗarsa.
“Yaya dai Babana kanne ke ciwo?”.
A hankali ya iya jinjin kan nasa da ɗago idanunsa da sukai jazur ya ɗan kalli
Abban. Murmushin ƙarfin hali yay ya maida kansa ƙasa ya risinar. Sannu Abban yay
masa cikin tausayawa da riƙosa suka fito, kusan kowa sai da ya zuba masa ido a
falon, shi kam bai yarda ya kalla kowa ba ya zauna kusa da ƙafafun Abba.
Baba Ibrahim ya buɗe taro da addu'a, kafin ya fara magana cikin nasiha dajan
hankalinsu akan muhimmancin zuminci a musulunci da zamantakewar rayuwa. Ya ɗora da
faɗin, “Wannan aure a ganina abin alfaharine a gareku dan koba komai ya dunƙuleku
ne waje ɗaya a matsayinku na jini guda. Fatan alkairi da ƙarfafa gwiwa kawai ya
rage kuyi ga shi Shareffuddeen da nauyin ya rataya a kansa, amma ba wannan shirmen
ba, gaba ɗaya yaran nan fa a ƙarƙashin ikonku suke, bazakuyi fatan bijirewar
waninsu gareku ba in har kunada hangen nesa. Amma ke Nafisa minene naki na tada
jijiyar wuya yaro ya saki matarsa??”.
Mommy dake cike fam da nasihar Yayan nata ta saki kuka, “Wlhy ni dai Yaya
bana buƙatar wannan haɗin, inhar nice na haifi Shareff to ina umartarsa ya saki
yarinyar nan hakan zaifi mana zaman lafiya a gidan nan bana buƙatar wannan
kwamacalar. Taya yana auren ƴar wajen Halima kuma ace ya auri wannan ai an haɗa
husumane dan kishi ba wasa bane, babu wani zama tsintsiya maɗaurinki ɗaya da hakan
zai kawo sai ma wata sabuwar musibar. Kuma wannan ai munafunci ne, inba munafunci
ba miyasa zasu ɗaura auren bada sanin kowa ba....”
“ALLAH ya rabamu da ita. Ban san hujjarki na kawo wannan misalan ba, ba kuma
na buƙatar sani, sai dai zan miki adalci ɗaya, shine jin ta bakin shi Shareff da
ayanzu ikon zartarwa ke hanunsa akan matarsa, dan nasan su dai su Muhammadu da
yardarsu da son su sukai wannan haɗin alkairi, kuma basu ɓoye dan munafuntarku ba
sai dan kawo masalaha saboda sanin halinku. Dani kuma aka ɗaura auren tun waccan
ranar kafin a ɗaura na ita ɗiyar halima da kike magana, domin kuwa da safe muka
ɗaura na ita Juwairiyya iya mu kaɗai batare da sanin ko shi kansa Shareffuddeen ba,
kafin a ɗaura na ita wannan yarinya Fadwa bayan sallar juma'a......”
Baki ta buɗe zatai magana ya ɗaga mata hannu, dole tai shiru dan tana bala'in
shakkarsa. Kallonsa ya maida ga Shareff da kansa ke ƙasa har yanzu bai ɗago ya
kalli kowa ba, sai dai komai na shiga cikin kunensa kamar kowa, yayinda jawabin na
Baba Ibrahim ke shigarsa tamkar almara, taya ya kasa gane an ɗaura masa aure da
Anaam? Miyasa kuma aka zaɓi ɓoye masa shima?...... “Shareffuddeen!”. Ya kirayi
sunansa cike da kulawa.
Bai ɗago ba, sai dai ya amsa da “Na'am Baba”. Cikin dasashshiyar muryarsa
dake tabbatar da baida lafiya. “Nasan kanajin komai basai na ƙara maimaici ba,
iyayenka sun baka mata domin ƙoƙarin ƙara ƙarfafa zuminci a tsakaninsu da ku da
suka haifa, shin kai ka amince da hakan a matsayinka na ɗa a garesu ko kuwa kanada
ja tamkar mahaifiyarka?”.
Tsitt falon yayi kowa ya zubama Shareff ido musamman Fadwa, Mommy da Gwaggo
da Gwaggo Halima.........✍

_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_


*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:


07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇


09134848107

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*


[11/3, 7:19 PM] My Zafafa: *_Typing📲_*

*_BABU SO....!!_*
_(Miya kawo kishi?)_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718
*_36_*

.........Burin Mommy kawai ya kalleta amma yaƙiyin hakan. Tsahon minti guda baice
komai ba yana satar kallon fuskokinsu ta gefen idanu. Tabbas ya hango tashin
hankali kala-kala musamman a fuskar Mommy da Gwaggo da Gwaggo Halima da Fadwa, ya
haɗiye busashen yawu da ƙyar tare da tattaro dukan ƙwarin gwiwarsa da jarumtarsa.
Cikin dakewa ya ce, “Baba bani da ja akan hukuncinku”.
“Kan ubanka Al-Mustapha!!”.
Mommy ta faɗa cikin suɓutar baki, Murmushi Abba da Abie suka saki kusan a tare,
hakama aunty Mimi da Mom da aunty Amarya sai da sukai kananun murmushi. Ɗayan
yayanta da suke cema Yaya Kamil ya harareta, a kausashe yace, “Nafisa! Dama kina
buƙatar ya bijirema iyayensa ne? A matsayinsu na mahaifa a garesa su zartar da
hukunci ki nunama duniya k baki bama ɗanki tarbiyya ba saboda wani banzan tunaninki
da hujjojinki? Karna sake jin bakinki a wajen nan, in ba hakaba ranki zaifi haka
ɓaci billahillazi!!”.
Dole tai shiru saboda a maganar Yaya Kamil ɗin babu wasa sam. Baba Ibrahim
ya sake maida hankalinsa ga Shareff. “Ka bamu amsa ne a dunƙule Shareff, kana nufin
ka amsa auren kenan?”.
Sai da ya ɗan saci kallon Mommy ta gefen ido, tako zuba masa ido cikin
matsanancin ɓacin rai, janye idanunsa yayi ya maida kan Daddy shima ya tsume kamar
fuskar tasa zatai aman wuta.
“Shareff kai muke saurare, in har a ranka kanajin auren nan cutuwane a gareku
ka saki yarinyar nan tun yanzu anan karka saka ku a wani halin da zai wargaza
zuminci”.
A hankali ya girgiza kansa dake rissine a ƙasa. “Baba ku gafarceni bazan iya
sakinta ba tunda an ɗaura....”
Kukan da Anaam ta fashe da shi ya hana Gwaggo data ɗauki sallami tana tafa
hannaye ƙarasawa, hakama Mommy da Gwaggo Halima da suka zaburo. Fadwa ma kuka ta
saki mai ƙarfi yayin da Aunty Mimi da Mom da Abba suka saki wata nannauyar ajiyar
zuciya, Abie ko murmushi ya saki, shi ko Daddy ya ɗan lumshe idanu. Mamie dai kanta
a ƙasa yake babu mai iya gane yanayinta. Albarka su Baba Ibrahim suka shiga sanya
masa da suma murmushin ya ziyarci fuskokin su, hakan ya ƙara tunzura kukan Anam da
Fadwa....
“Nidai bana Son sa baba, akwai wanda naima alƙawari zan aura nima, kuma shi
nake so!!”. Furucin Anam cikin matsanancin kuka ya daki kunnuwan kowa dake a falon.
Cikin sauri da zaburowa Mommy tace, “Shima ai ba son naki yake ba, shegiyar yarinya
mai kama da ifiratan aljanu. Yaya ai kaga abinda nake gudun masa tun farko, mizaiyi
da wannan mara tarbiyyar yarinyar har tana wani iƙirarin ba son sa take ba
fitsararriya.....”
Hayaniyace ta nema sake kaurewa a falon, yayinda Anam ke rusa uban kuka ita
akwai wanda take so. Tsawar da Abie ya daka mata ce ta saka gaba ɗaya hayaniyar
kukan Fadwa da Hargowar Mommy data Gwaggo yin tsitt. Anam ta maƙure jikin Aunty
Mimi tana sake fashewa da kuka. Baba Ibrahim ne ya kalla Abie cikin murmushi, kansa
ya girgiza masa cikin dattako. “Ayi haƙuri Usmanu abita a hankali sai a samu
masalaha sahihiya. Tsanani baya kai kowa ga hanyar nasara. Juwairiyya zonan kinji”.
Da taimakon aunty Mimi ta mike taje gabansa, kusa da ƙafafunsa ya nuna mata,
ta zauna tana shashshekar kuka da sharɓar hawaye da gyalen data rufe har fuskarta.
Cikin lallashi yace, “Kukan ya isa haka to, maza share hawayrnki”. Da ƙyar ta iya
danne kukan, sai dai hawayen basu bar zirara ba.
Cikin lallashi yace, “Faɗa min wa kike so?”.
Kai tsaye tace, “Muzaffar!”.
“Miyasa shi Shareffuddeen baƙya son shi?”.
Shiru tai ta kasa magana, ya ƙara maimaita mata tambayar.
“Kawai Baba”.
“Ai shi mutum ba'a ƙinsa kawai Juwairiyya. Amma zan baki wata dama da kuma alfarma
kin yarda?”.
Cikin share hawaye ta jinjina masa kanta. Yay murmushi irin nasu na manya
masu basira.
“Ina so kimin alfarmar yarda a kaiki gidan Shareffuddeen. Daga nan zuwa wata uku
in har baki samu wani farin cikin zama da shi ba, kizo ki sanar min, ni kuma na
miki alƙawarin da kaina zan saka shi ya sallama miki”.
Karon farko ta ɗago ta kallesa. Cike da tabbatarwa ya jinjina mata kansa
yana murmushi. Ta kai dubanta ga Shareff, cikin sa'a kuwa suka haɗa ido. Wani
shegen kallo da taima fassara dana tsana ta hango cikin idanun nasa, sai taji
ƙwarin gwiwar cin nasarar shawarar baba ibrahim, dan kuwa ta tabbatar babu wani
farin ciki da zata samu daga Shareff ɗin musamman idan ta auna irin tsanar da yay
mata a rayuwa. Idan haka ne gara ta amince kodan goge laifinta da su Abie zasu iya
gani, cikar wata uku kuma dai-dai da kammala Serves ɗinta kenan......
“Baki ce komai ba”.
Baba ibrahim ya katse mata tunani.
“Baba na amince”.
Murmushi ya saki mai ƙayatarwa, hakama abie da Abbah da Daddy duk sai da suka saki
ajiyar zuciya. Yayinda Mommy tai ƙwafa sai dai babu damar cewa wani abu.. Baba
Ibrahim ya sake ƙara musu nasiha baki ɗaya musamman Gwaggo dake a matsayin uwa
garesu su duka a wajen. Hakama Mommy data hau dokin zuciya da yasan bazata taɓa
tanƙwasuwa ta sauƙi ba. Itama dai Fadwa da Gwaggo Halima sun sami nasu rabon
musamman ma Fadwa da yaketa lallashi dan yasan an mata laifi. Suma dai su Daddyn ya
musu nasihar ya kuma ƙara bama kowa haƙuri da fatan komai ya wuce sannan yay addu'a
taron ya tashi dan dare ya farayi.....

★★Washe gari an tashi ne mafi yawan rayuwuka a ɓace, ga amaryar Maheer ta


iso tun daren jiya, tana a sashen Mom kamar yanda Daddy ya sharɗanta. Aunty Halima
dai tun daren jiya tabar gidan tare da Fadwa, acewarta dai su Daddy basa ƙaunarta
babu ita babu su, Fadwa ma tabar gidan Shareff kenan sai dai ya biyota da
takardarta. Komai babu wanda yace mata a cikinsu, sai Gwaggo dake faman matsar
ƙwalla tana faɗar maganganu. A haka dai babu daɗin rai akai walima washe gari dan
dama ango Maheer shi bai yarda da wani event ko ɗaya ba, butsutsunsa yasa Mommy
haƙura duk da taso a sha shagali tamkar bikin Shareff da Fadwa.
Shareff ma dai tun a daren ya koma can gidansa tare da Khaleel da Maheer ɗin
da suka kwana da shi a can saboda yanayin jikinsa daba gama daidaita yay ba. Itama
dai Anam bata kwana da lafiya ba dan tunda sassafe ma sai da Abie ya kaita asibiti
da kansa aka bata gado. Dan haka har yamma tana can tare da Aunty Mimi da Abie ɗin,
sai su Mom da su Daddy da sukaje daga baya dubata. Wannan ya kawo ƙaracin armashin
buɗar kai da akai na amaryar Maheer, bayan sallar la'asar danginta da wasu a dangin
Mom sukai mata rakkiya gidan mijinta. Gida yayi ƙyau dan Maheer ma yayi ƙoƙari sai
sambarka. Sannan iyayen amarya ma sunyi nasu ƙoƙarin dan kun san dai Mom dama duk
inda take na masu manda ne. (Tana bala'in son huɗɗa da masu kuɗi a gidan sanyi🤣).
Tun a ranar mafi yawan baƙi suka kauce dan uwar bikin a birkice take.
Tako'ina Mommy ɗin ta birkicema kowa. Gida yayi lafiya, baƙin da suka rage
kalilanne, Hakan yasa koda aka sallamo su Anam daga asibiti sanda suka shigo gidan
tsitt yake.

Washe garin data kasance lahadi sai ga mahaifin Fadwa har gida ya maido
Fadwa, babu ragi yay mata tatas a gaban su Daddy ita da Mommy. Fafir kuma yaƙi
sauraren zantukan Gwaggo duk da uwa take a garesa. Wannan dattako daya nuna ya
matuƙar faranta ran kowa a gidan ciki harda Shareff da aka sashi zuwa gidan. Daga
ƙarshe kuma ya bisu da nasihar zaman haƙuri dana riƙe junansu domin samun kwanciyar
hankali da nutsuwar zuciya. Bayan wucewarsa su Daddy suka sake zama da Shareff, sun
basa umarnin ƙarasa abinda ya rage masa dan nan da sati ɗaya amarya zata tare
ɗakinta. Yaso yace suɗan ƙara masa amma baiga wannan damar a fuskokinsu ba dan
umarni suka bashi ba shawara ba. Daddy kuma ya turkesa a wajen yace ya biyasa kuɗin
sadaki dan shine ya ranta aka biya a waccan ranar. Dole yayma Daddy transfer ɗin
kuɗinsa take a wajen sannan ya barsa ya tafi.
Ƙin shiga wajen Mommy yayi dan wasan ɓuya yake da ita tun ranar, ya aika
Aysha ta kira masa Fadwa tazo su wuce. Amma sai Mommy tace a faɗa masa Fadwan ta
ƙarfi ce idan yanada ƙarfin yazo ya ƙwata. Murmushi kawai yayi sanda Aysha ta zo
masa da amsa, batare da yace komaiba ya shiga motarsa ya fice a gidan dan gwara
wannan wasan ɓera da magen da yake da Mommy ɗin akan tunkararta face to face a
yanzun.

★ Kamar wasa ciwo ya kwantar da Anam sai da aka kwasheta aka koma da ita
asibiti a daren yau. Dawowar su Amrah cikin gida yasa su Mom suka sani, dan daga
Mamie har Abie da Aunty Mimi duk suna acan asibitin. Duk da dare ya farayi haka
Abbah da Daddy suka fita, Khaleel ne ya jasu a motar bayan sun kira Abie sunji
asibitin da suke.
Lokacin da suka iso har an bama Anam ɗin gado amma saka mata ruwa barci ya
ɗauketa. Ta rame sosai dayin wani irin fayau da ita, suna cikin jajantama juna
Shareff ya shigo, Khaleel ne ya tura masa sms ya sanar masa sanda zasu taho, dan
haka ganin nasa ya bama kowa mamaki har Abie ya kasa haƙuri yay magana.
“Babana waya saka fitowa a wannan daren haka? Ga anguwarku da nisa?”.
Ƙaramin Murmushi yay idonsa na satar kalllo Anaam dake barci duk ta koɗe tayi
fayau da ita abin tausayi..........✍

_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_


*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:


07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇


09134848107

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*


[11/3, 7:19 PM] My Zafafa: *_Typing📲_*
*_BABU SO....!!_*
_(Miya kawo kishi?)_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718

*_37_*

.........Kiran sallar farko ya farka, dama ba wani barcin kirki yayi ba, dan bai
baro asibiti ba a daren jiya sai kusan ƙarfe ɗaya, shima sai da Abie ya korashi dan
suma duk lokacin suka wuce aka bar aunty Mimi kawai da Anam dake barci. Sai da ya
watsa ruwa kozai samu ƙarfi sannan yay alwala ya fita massallaci, gari ya ɗanyi
shaa ya shigo gidan, ya ɗan ja tsaki dan gaba ɗaya gidan yay masa wani irin girma,
yayi niyyar sakama Fadwa ido yaga iya gudun ruwanta amma a yau yaji bazai iya hakan
ba, dan ya kula sai ya fito mata ta inda bata zato sannan zasu samu dai-daito.
Wayarsa ya ɗauka yana zama bakin gado dayin ƙaramar ƙwafa, aunty Mimi ya kira, bugu
biyu kuwa ta ɗauka suka gaisa, ya tambayi yamai jiki tace da sauƙi amma bata
tashiba har yanzun dai.
“Masha ALLAH, nima zan shirya yanzu zan shigo, ko kuna buƙatar wani abu ne
shiyyasa na kira?”.
Aunty Mimi ta amsa da “To ALLAH ya kawoka lafiya. Bama buƙatar komai tunda bata
tashiba balle aji ko ita tana son wani abu ɗin”.
“Okay to sai nazo”.
Ya faɗa yana yanke wayar. Bai wani jima ba ya kammala shiryawa ya fice, sai da ya
shiga mota ya fara kiran number Fadwa, harta tsinke ba'a ɗagaba, ya sake tsuke
fuska ransa na ƙara ƙuna dan ya tsani raini a rayuwarsa. Wayar ya jefa kujerar
gefansa yay ma motar key ya fice.

Gama wayar aunty Mimi babu jimawa ta farka, da taimakonta taje toilet dake
a cikin ɗakin, jikinta sam babu ƙarfi, hakan yasa Aunty Mimi taimaka mata ta ɗan
watsa ruwa mai ɗumi sosai sannan tai alwala suka fito. Murya a karye irin ta mara
lafiya tace, “Ummie bazan iya salla a tsaye ba ina ganin jiri”. Taimaka mata aunty
Mimi tai ta zauna kan sallaya, dai-dai nan masu gyara ɗakin suka shigo tare da wata
nurse. Su dukansu suka gaida Aunty Mimi da tambayar mai jiki, ta amsa musu da
fara'a.
Gyaran gado mai sharar ta fara, yayinda Nurse ɗin ke tsaye tana jiran Anam
ta idar. Sai da tai addu'a Nurse ɗin ta taimaka mata ta koma saman gado, kwancia ta
ƙarayi dan gaba ɗaya batajin ƙarfin jikinta. Harta lumshe ido sallamarsa ta sakata
buɗewa, kallo ɗaya tai masa ta maida ta rufe abunta fuskarta na sake tsukewa.
Gaisheshi Nurse ɗin tai hakama mai sharar, ya amsa sama-sama yana ƙarasawa gaban
aunty Mimi ya ajiye ledojin hanunsa. Aunty Mimi dake dubansa da murmushi tace,
“Babana mun hanaka barci ko?”.
Murmushi ya ɗanyi da kaiwa zaune a ɗayan gadon dake ɗakin, ya rissina yana
gaisheta kafin ya bata amsa da “Ko badan kuba dole na fito ai yau akwai office”.
“Tofa ango guda da zuwa office”.
Idanunsa ya sauke akan Anaam batare daya ce komai ba, cikin son basar da zancen
yace, “Har yanzu bata tashi ba?”. Kallon Anaam aunty Mimi tayi, ganin tayi luff
kamar bata jinsu tai ƴar dariya. “Yanzun nan tai salla ma, tana komawa saman gadon
kana shigowa. Sallamar Doctor ta hanashi cewa komai, tare yake da nurse ɗin ɗazun,
ya miƙa masa hannu suka gaisa yana tambayar yamai jiki. Da aunty Mimi ma suka gaisa
sannan ya ƙarasa gaban gadon.
Cikin tsokana yace, “My patient barcine ko likimo?”. Duk da ta jisa bata
motsa ba, sai dai taɗan buɗe idonta ta kallesa ta maida ta rufe. Murmushi yayi da
sake faɗin, “Alhmdllh ALLAH ya ƙara lafiya. Sister Rabi taimaka mata ta tashi”.
Da taimakon Nurse daya kira sister Rabi ta tashi, sai langaɓewa take kamar
zata saki kuka, cikin lallashi doctor yake mata ƴan tambayoyi akan yanayin jikinta
tana bashi amsa, ko sau ɗaya taƙi yarda ta kalli sashen da Shareff yake. Bayan
doctor ya kammala ya bada umarnin a bata abinci ko kaɗan taci zai aiko a sake saka
mata ruwa da allurai uku, dan suna buƙatar ta samu barci sosai da alamu suka nuna
kwana biyu bata samu. Koda ya fice shi da Nurse ɗin bata yarda ta kalli inda yaken
ba, saima ƙoƙarin kwanciya da taso yi aunty Mimi ta dakatar da ita. Idanunta ta
ɗago cikin marairaicewa ta kalli aunty Mimi, har ƙwalla sun taru dan ma gilashin
idonta ya ɗan ɓoyesu duk da fari ne tas, karaf suka haɗa ido, ta sake yin kicin-
kicin da ɗauke kanta tamkar bata gansa ba. Shiko ya kafeta da nasa idanun sai dai
shima tashi fuskar tsamm take babu wasa.
“Ummie jiri”.
Ta faɗa a hankali.
“Na sani mamana ki daure kici abinci kamar yanda doctor yace sai ki kwanta ɗin.
Bata iya musu ba, dan haka tai shiru. Aunty Mimi ta bubbuɗe ledojin da Shareff ya
shigo dasu, kayan tea ne a leda ɗaya, ɗayar kuma abincine dai-dai cin mara lafiya
kuma abinda Anam ɗin take matuƙar so. Amma da yake daru takeji sai tace ita bata
son shi, aunty Mimi sai lallashinta take amma ta kafe ita bata sonsa a kira Mamie
ta kawo mata wani.
Sarai yana jinsu amma bai tanka ba, sai danna wayarsa yake kai kace hankalinsa
baya kansu sam. Ana cikin badaƙalar Khaleel ya iso. Cikin shirin office yake, ya
gaida aunty Mimi da Shareff ɗin yana ajiye basket na abinci da Mom ta aikosa ya
kawo. Kafin ya karasa gaban gadon yana kallon Anaam da ƴar sakin fuska dan shi
murmushi ma kakan daɗe baka gani ba tare da shi. “A jiki yayi sauƙi granny tunda
gaki zaune, jiya har mun fara ƴar ƙwalla da murnar cin gummba”.
Murmushi ta saki tana kallon Khaleel ɗin kamar ba ita ke bori ba. “Kai Yaya
Khaleel, kai ashe soma kake na mutu?”.
Murmushi yayi shima a karon farko, “To Granny na sani ko lokaci yayi jikin
tsufa”.
Ta ɗan hararesa tana ɗauke kanta, dariya yayi nan ma. A ɗan shagwaɓe
tace, “Yaya mika kawo min?”.
“Breakfast ne Mom tace a kawo miki kafin su ƙaraso”.
“Na gode”.
Ta faɗa tana maida dubanta ga Aunty Mimi da ke kallon Shareff daya miƙe fuskarsa
kicin-kicin kamar zaiyi aman wuta. “Ummie zanci”. Da ga shi har Aunty mimi kallonta
sukai, yay mata wani mugun kallo ya ɗauke kansa. Itama harara ta balla masa ta
ɗauke nata idon. Sarai yaga harar dan haka ransa ya ƙara ɓaci, batare da yayima
kowa sallama ba ya fice abinsa.
Daga aunty Mimi har Khaleel da kallo suka bisa.....

★Yini guda ƴan dubiya nata leƙowa jefi-jefi, sai dai babu Gwaggo babu
Mummy, Aysha ma satar hanya tai ta biyo su Mom da zasu zo tazo ta duba Anam ɗin.
Dan Mommy ta hana yaran ɗakinta duka. Shareff dai bai sake leƙowa ba sai kusan
takwas na dare, da alama daya tashi aiki sai da yaje gida sannan ya dawo nan dan
jallabiya ce a jikinsa. Yanzu ma Anaam yitai kamar bata san ALLAH yayi ruwansa ba,
shima kuma daga gaisuwa da yay da Aunty Mimi da wata ƴar uwar Mamie data zo duba
Anaam ɗin yaja bakinsa ya tsuƙe. Aumty Mimi suka fita zataima baƙuwar rakkiya aka
barsu su biyu. Shiru ɗakin ya ɗauka kamar babu masu rai, sai ƙarar iskar fanka
kawai kakeji, taƙi yarda ko sau ɗaya ta kallesa sai faman cin apple ɗinta take da
aunty mimi ta yanka mata hankali kwance. Idanu ya ɗan tsura mata amma duk da haka
ta ƙi ta nuna tasan da zamansa....
“A tunaninki wannan rashin kunyar taki zaisa ki samu biyan buƙatar taki?”.
Shiru babu alamar tama jisa tanata dai cin apple ɗinta, ransa ya ƙara ɓaci,
cikin jin zafi da ɗacin da muryarsa ta kasa ɓoyewa yace, “Oh ga mahaukaci na magana
ko? K! Ki shiga hankalinki wlhy, inba hakaba zakisha baƙar wahala a banza stupid
kawai”.
Babu ko ɗar a cikin idanunta ta ɗago ta zuba masa su duk da suna cikin
gilashi, “Yaya Shareff ALLAH bazai baka damar bani wahalar ba kuwa, dan hanyar
jirgi daban ta mota daban. Aure ne dai nace bana so kuma komi za'amun bazan so ba
dan inada wanda nake s......”
Ji kake “bumm!” akan bakinta, sam batama lura da sanda har ya taso ya iso
gareta ba. Ya ture hanunta da take ƙoƙarin ɗaurawa saman lips ɗinta ya maye
gurbinsa da nasa yatsun biyu, cike da baƙar mugunta ya shiga murzasu. Duk da dukan
da take kaima hanun nasa bai janye ba sai da ya tabbatar ya murjesu san ransa
sannan ya saki. “Karki fasa rashin kunya, nima bazan fasa ɗaukar mataki akanki ba”.
Ya ƙare maganar gab da fuskarta har yana busa mata numfashinsa da iskar bakinsa
dake ƙamshin mouth freshener na banana.
Kuka ke son taho mata amma tanata ƙoƙarin dannesa dan taci alwashin bazata
sake barin hawaye akan fuskartaba game da wannan auren, zata ƙwaci kanta da
ƙarfinta kuma duk abinda za'ai mata sai dai ai mata bazata zauna zaman aure da shi
ba. Shima baibi takanta ba dan harya fice ma abinsa rai ɓace. Taja wani shegen
tsaki da ɗaga gilashinta ta share ƙwallar da suka taru a fatar idon dan ta danne
sauran ta hanasu tasiri. Koda aunty Mimi ta dawo bata tambayeta ina Shareff ɗin ba,
da alama dai sun haɗu a waje ne.
Daga ita har shi haka suka kwana rai a ɓace. Washe gari ma shine ya fara zuwa
asibitin, sai da yaje wajen doctor ya biya komai ya basu sallana sannan ya iso
ɗakin. Da aunty Mimi kawai yau ma ya gaisa, ƴar darun tasa na kwance ta juyama ƙofa
baya baima san idonta biyu ko barci take ba. Shine ya sanar ma aunty Mimi an
sallamesu, tai godiya ga ALLAH sannan ta miƙe ta fara haɗa kayansu. Ya ɗauki kayan
ya fita da su, ita kuma ta tada Anaam da dama idonta biyu ta taimaka mata ta shirya
sannan suka fito bayan doctor ya shigo sunyi sallama. Tsaye suka samesa a jikin
motarsa yana waya da alama a cikin su Daddy ne. Ƙin yarda tai ta kallesa duk da shi
tana jin nasa idon a kanta. Aunty mimi zata sakata gaba ta tirje akan ita dai baya
take so, kokuma subi napep.
Faɗa aunty Mimi ta fara mata dan ta kaita wuya kuma, shiko kamarma bai san
sunai ba ya shige motar abinsa bayan ya gama wayar tasa. Dole dai ta shiga gaban
✍🏻
bisa tursasawar aunty Mimi........

_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_


*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:


07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇


09134848107

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*


[11/4, 12:31 PM] My Zafafa: *_Typing📲_*

*_BABU SO....!!_*
_(Miya kawo kishi?)_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718

*_39_*

.........Alhmdllhi amarya ta iso gidanta lafiya, ta kuma samu tarba daga wajen
dangin mahaifiyar su Daddy da suma sukazo suka taru anan domin nuna gata gasu daddy
ɗin, duk da tun zuwan nasu ƙawayen aunty Halima dake gidan zagaye da Fadwa suka
kirata suka sanar mata. Babu ko kara na tuna cewa dangin mahaifiyarta ne ta kirasu
tai musu tas a waya da tabbatar musu zata iya da makircin kowa daya nuna goyon
bayansa akan aima ƴarta Fadwa kishiya, kishiyarma ɗiyar ƴar uba. Inna Suwaiba!
Wadda ta kasance ɗiyar wan maman su daddyn ce ta amshi waya tai mata tas itama dan
in masifa ce ta fita iyawa, ai ko babu shiri ta yanke wayar tana zage-zage.

Kowa ya yaba sashen amarya tare da jinjinama ƙoƙarin iyayenta, dan tabbas
kam sun nunama duniya ita ɗin ɗaya ce tilo a garesu kuma ƴar gata. Cikin raɗa Mom
da Hajiyar sudan suka sake yima Anam da keta sauke ajiyar zuciya nasiha. Rungume
Mom tayi, muryarta a ɗashe alamar taci kuka mai yawan gaske tace, “Mom ni bana son
sa dan ALLAH, Mom karku barni anan zan iya mutuwa”. Mom dake rungume da ita tana
shafa kanta tai murmushi. “To kiyi haƙuri, zan samu Abbanku nai masa bayani yanda
zai fahimceni, yanzu dai ki kwantarmin da hankalinki kinji”.
Da sauri ta fiddo fuskarta dake cikin mayafi tana kallon Mom da jajayen
idanunta da suka kumbura matuƙa saboda kuka. “Mom dan ALLAH da gaske?”. Hajiyar
Sudan Da Mom suka haɗa ido, murmushi sukayi, kafin Mom ta jinjina mata kanta “Da
gaske mana. ba Baba ibrahim ma yace nanda wata uku indai da wata matsala zai ɗauki
mataki ba”. Sake rungumeta tai tana jinjina kanta fuskarta na bayyanar da murmushin
da tunda aka fara badaƙalar auren nan ba'aga irinsaba a fuskarta. Cikin dabara
hajiyar Sudan ta fita a ɗakin, dan dama su kaɗaine suka rage mutane duk sun fice
kowa na tsoron ya rasa mota. Lallashinta Mom ta ƙarayi, kafin itama ta miƙe cikin
dabara da plan ɗin da suka haɗa da hajiyar sudan.
Hajiyar Sudan ɗin ce ta leƙo tai kiranta wai tazo taga wani abu, miƙewa Mom
ɗin tai tana gyarama Anam zama. “Kinga zauna ina zuwa”. Ji Anam tai kamar dabara
zasu mata, sai dai kafin tai wani yunƙuri Mom ɗin har ta fice a ɗakin, tun tana
irga seconds harta koma minutes, ganinfa alamar mintuna kusan goma sun cika babu
alamar motsi ma ya sakata miƙewa da sauri hawaye na ciko mata ido. Tabbas babu kowa
a falon, hakama sauran ɗakunan zuwa kitchen, wasu irin zafafan hawaye ne suka
silalo mata, ta dafe kujera saboda jiri dake neman ɗibarta, da ƙyar ta iya maida
kanta bedroom ɗin da suka barta, ta zube a kan gadon hawayen na cigaba da sauka a
guje dan bata da ƙarfin yin kuka mai sauti.....

Gida ya koma tsitt, duk da sashen Fadwa har yanzu akwai wasu ƴan uwan babanta
uku na hanun damar Gwaggo halima da su Mommy basu da alamar barin gidan, sun zagaye
Fadwa dake kuka suna ƙara mata fanfo dan ba'ace nasiha ba. A kallo ɗaya zaka
tabbatar da taci kuka itama har ta godema ALLAH, dan hatta da muryarta ma ta dishe.
Gaba ɗaya ji take Shareff ɗin ma ta gama tsanarsa, ko ganinsa bata sonyi shi da duk
wanda ya shafesa. Tsoron mahaifintane kawai ya taka mata birki akan ƙudirinta na
barin gidan, amma batajin zata iya cigaba da rayuwa da Shareff ƙarƙashin inuwa guda
da maƙiyarta, yarinyar datai matuƙar tsana a rayuwarta ace a yau itace kishiyarta,
kishiyarta da zata iya shearing da mijinta abin sonta. Kai ina wannan ma maganar
tatsuniyace, za kuma ta tabbatarma duniya cewar tatsuniyar ce...

Duk wannan hidima da akeyi ango Shareff na can gidansu gurfane gaban su Daddy
suna sake masa nasiha da jaddada amanar matan nasa a hanunsa domin a yanzu matsayi
guda suke amsawa a wajensa. Kuma su dukansu ƴan uwansa ne na jini da basa fatan
zuminci ya samu wani nakasu ko rauni a dalilin aurensu. Basu barsa ya baro gidan ba
sai da ƴan rakiyar amarya suka koma. Yay musu sallama ya fito. Babu sashen daya
shiga, dan shima yasan baida wannan damar a yanzu. Ga kuma kansa na masa matuƙar
ciwo ma na hayaniyar da aka sha ga kuma jikinsa da bawai ya gama dawowa dai-dai
bane shima dama. Dauriyace kawai da ƙarfin zuciya irin ta maza.
Duk yanda abokansa suka so masa rakkiya kamar auren Fadwa ƙi yay, dole suka
haƙura suka gudu sai Fharhan ne kawai dazai jasa a mota dan shi bama zai iya
driving ɗin ba. Da farko tsokanarsa ya dingayi, sai da yaga baya cikin good mood ne
ya koma nasiha a garesa, dan kuwa dai shi ɗin shaidane akan abinda Shareff yake
ɓoyewa a zuciyarsa tsahon shekaru, sai dai ko'a yanzun ma bai nuna masa yama
fahimcesa ba yadai bashi shawarwari kawai. Har suka iso bai dai ce komai ba, sai da
zai fita ne yace masa “Thanks” a taƙaice. Da kallo kawai Fharhan ya bisa, sai kuma
ya girgiza kansa yana murmushi.

Kai tsaye sashensa ya wuce duk da yanada tabbacin zuwa yanzu babu kowa a
gidan, ya zube cikin kujera yana furzar da huci mai zafi lokacin da yake kai
bayansa ga kujerar. Ya lumshe idanunsa da yake jin sun masa matuƙar nauyi. Kusan
mintuna goma ya ɗauka a wajen yana kokawa da abinda zuciyarsa ke saƙa masa, kafin
ya miƙe ya nufi bedroom ɗinsa. Wanka ne a ransa, dan haka bai zauna ba ya zame
kayan jikinsa ya shige bathroom. Koda ya fito jikinsa kawai ya tsane ya zura
jallabiya yasa turare kaɗan. Hakkinsa ne ya duba kowaccensu, duk da kuwa tunda
Fadwa ta dawo gidan taƙi yarda su haɗu. Sashenta ya fara zuwa batare da tunanin zai
samu kowa ba. Turus ya ɗanyi da mamaki, hatta fuskarsa sai da ta nuna dan bai zaton
samun kowa ba. Fadwa da ke kwance ta ɗora kanta saman cinyar aunty Malika tai masa
kallo ɗaya ta kauda kanta tana jan siririn tsaki ciki-ciki yanda bazaiji ba.
Kallonta yake amma taƙi yarda su haɗa ido, ya ɗan girgiza kansa kawai. Komai baice
ba ya fito a falon dan ko sallamarsa babu wanda ya amsa a cikinsu, sai kuma binsa
suke da kallon banza....
“Lallai wannan mijin naki ya cika ɗan iska Fadwa. Yanzu muna amtsayin ƴan
uwan uwarsa amma yay mana wannan kallon banzar babu ko gaisuwa ya fice”.
“Ke ko ya zai gaishemu kansa na hayaƙin asiri Safarah. Ai bayin kansa bane, dole
fa su Aunty Nafi (Mommy) sai sun tashi tsaye dan Shareff ya shiga kaidun waɗannan
mutanen wlhy”.
Kuka Fadwa ta sake rushewa da shi tana kiran ta shiga uku. Cikin zafin rai
wadda batace komaiba tun ɗazun ta daka mata tsawa. “A gidan ubanwa kika shiga ukun?
Idan taƙamarsu asiri da tsubbu gaban iyayen gidansu sukazo. Har miye su? Mi akai
akayi wannan ƴar yarinyar da bata wuce ki fetota a hancinki da makirci kawai ba.
Danni banga abin ɓata lokaci agareta ba balle kuɗi na neman asiri. Wannan yaƙin da
kanki zakiyisa in har kin cika ke ɗin jinin baba yalwa ce (Kakarsu data haifi
mahaigiyar Mommy, Gwaggo, mahaifin Fadwa, mahaifiyar Bibah).
“Aunty Lawusa dolene nai kuka, wlhy shima na tsanesa, bana son ganinsa
munafiki ne”.
Yanda take maganar tana kuka yasa Aunty Malika sake jawota jikinta ta rungumeta.
Kuka ta sake fashewa da shi. “Aunty yanzu fa zuwa zai ya kwana da ita, shike nan
sun rabani da mijina.....”
“Basu isa rabaki da mijinki ba, ki kuma kwantar da hankalinki shi bai isa
kusantarta ba, bama a yau ba har abada, yanda ta shigo haka zata bar miki gida sai
dai ta koma ta cigaba da rabama abokan shashancin nata a ƙasar data fito”.
Ɗagowa Fadwa tai tana girgiza kai, “Aunty baki san waye Shareff bane, wlhy sam
baida haƙuri akan mace, ko faɗa yay da ita zai iya neman biyan buƙatarsa shi babu
ruwansa”.
Dariya aunty Lawusa tayi sai kuma ta haɗe fuska. “Malama ki mana shiru haka,
idan shi hrj ne ƙarshen dai maitar mace kenan ko? To bai isa tarayya da yarinyar
can ba har abada tunda ya taka abun can da ƙafafunsa”.
Sosai Fadwa ta zaro idanu “Aunty wane abu wai?”. A tare suka sanya mata dariya,
aunty Malika ta fiddo ƴar kwalba a jikkarta har guda 2. Ba kinga nayi turaren
wannan ba ɗazun? Na kuma barbaɗe ƙofar falonki da wannan yanzun?”. Kanta ta jinjina
mata. Ta dafa kafaɗarta tana murmushi, to wannan da kike gani sunansu *ɗan kaɗafi
da ni kaɗai ce mace* mu dukanmu nan babu wacce bata aiki da shi a gidanta, kuma
munga biyan buƙata shiyyasa kema muka amso miki, dan haka ki kwantar da hankalinki
indai wannan yarinyar ce da ƙafafunta zata bar miki gidanki, ko zasu kwana manne da
juna wani abu bazai taɓa shiga tsakaninsu ba”.
“Ni wlhy ko gadon ma bana ƙaunar su haɗa aunty, kai ko hanunta bana son ya
taɓa riƙewa a gidan nan”.
“Wannan duk mai sauƙi ne, kedai kawai ki saki bakin aljihu, dan yanzu babu boka
babu malam maganin mata sune ke ƙwatar mace, shiyyasa mukayo miki haɗinsu gasu nan
na musamman yanzu haka ma Hajarah zata taho miki da wasu daga Niger, Fadwa sai kin
koma juya Al-Mustapha inda kike so, balle ke ma da kika gama morewa da samun
mabuƙaci, ta wannan hanyar zaki banbance masa tsakanin aya da tsakkuwa ki kuma
damƙe abunki dan dama naki ne shi kaɗai. Tun farko su Aunty (gwagg halima da Mommy)
sunyi sakaci ai da basu haɗaki da haɗi na musamman ba kafin aure da Shareff bai
taɓa kallon wata mace ba, kai auren nan ma da bai sai sun wahal da kansu ba da
kansa zai bijire wlhy. Amma ko yanzu bata ɓaci ba muna tsaye kanki”.
Fuskar Fadwa ta washe da murmushi, ta rungume auntys ɗin nata cike da farin
ciki, jitai gaba ɗaya duk wata damuwarta tama gushe, dan tayi imani da duk abinda
suka faɗa tunda ita ɗin shaidace akan yanda suke juya gidansu da mazajensu duk da
sunada kishiya, aunty Malika ma su uku ne amma idan kaga yanda mijinsu ke rawar kai
a kanta saika ɗauka ita ɗaya garesa ko kuma amarya, sai dai itace ta
✍🏻
tsakkiya........

_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_
*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_


*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:


07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇


09134848107

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*


[11/4, 12:31 PM] My Zafafa: *_Typing📲_*

*_BABU SO....!!_*
_(Miya kawo kishi?)_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718

*_40_*

...........Ya jima tsaye a ƙofar sashen tamkar mai nazari, kafin ya ɗaura hanunsa
akan handle ɗin ya murɗa a hankali. Ƙamshi dai da aka sani da sashen kowace amarya
ne ya fara tarbarsa, ya shiga da sallama kan lips ɗinsa idonsa na zagayawa kan
komai na falon. Ya turo numfashi mai ɗan ƙarfi ta hancinsa, cikin tafiya kamar mai
irga steps ya nufi bedroom ɗin da yake saka ran samunta, dama 3bedrooms ne a sashen
iri ɗaya dana Fadwa ne, sai kitchen, store, falo, bedrooms biyu suna facing juna a
corridor guda, ɗaya na a can gefe kusa da dining alamar dai na baƙine. Nan ɗin ma
dai sai da yay ɗan jimm sannan ya tura ƙofar, babu kowa, sai dai shima yasha kaya
tsaff. Maidawa yay ya rufe, ɗayan ya buɗe.
Kwance take ta dunƙule waje ɗaya, tare da lulluɓe duka jikinta da bargo. Hawaye
take sosai ga rawar sanyi alamar zazzaɓine a jikinta. Ya ɗau tsahon minti uku yana
kallonta duk da ba fuskarta ce a buɗe ba kafin ya cigaba da takawa cikin ɗakin
sosai fuskarsa a tsume har yanzu da takaicin su aunty Lawusa, dan ma baiji abinda
suke shiryama Fadwan ba kenan..
Isowarsa gab da gadon ya bashi damar jin yanda take sauke ajiyar zuciya a
jajjere har tanayi kamar zata shiɗe. Sai kuma rawar sanyin da takeyi har yana iya
ganin kaɗawar jikinta duk da a lulluɓe take. Hannu ya kai ya yaye bargon baki ɗaya,
hucin zafi sosai ya bugesa.....
“Shiii!! wayyo sanyi-sanyi....” ta faɗa tana ƙoƙarin riƙo bargon da ya janye
ɗin, bai bata damar yin hakan ba, ya kai hanunsa na dama saman goshinta. Sosai kan
nata ma ya ɗauki zafi. Zumbur ta miƙe, dan sai yanzune ƙamshin turarensa ya kai ga
hancinta, gaba ɗaya tama shafa'a da inda take. Tai saurin gyara glass ɗinta da ya
sirranta kumbiri da jaan da idonta sukai tana ja da baya...
“Kina tunanin hakan da kika zaɓama kanki shine maslaha? Duba yanda jikinki yay
zafi, idanunki suka kumbura saboda kukan da bazai miki amfani ba bayan kin san
hakan a gareki matsala ce babba. Garama ki nutsu domin kukanki da borinki bazai
canja komai ba”.
Wani irin kuka ne ya kufce mata na takaici da ƙara jin zafinsa. Yaja
siririn tsaki da juyawa ya fice a ɗakin. Fillo ta ɗauka ta wurgama bayansa duk da
ya riga ya fita sai ya samu ƙofa, ta ƙara ɗaukar wani ta jefa. Sai da ta jefa uku
sannan ta zame ta kwanta tana cigaba da kukanta da ita kanta ta gaji da yinsa.
Kusan mintuna bakwai ya dawo, akan fillos ɗin data wuwwulo ya fara sauke idanunsa,
ya ɗan girgiza kansa kawai ya tsallakesu. Cup ɗin da ɗauke da tea ya ajiye tare da
magani, batare da yace mata komai ba ya sake fita, bai jimaba ya dawo da goran
ruwa.
“Tashi zaune” ya faɗa cikin bada umarni, dan yasan idan yay mata laku-laku
bayin yanda yake so zatai ba. A yanzu ɗin ma duk da a yanda yay maganar sai da ya
sake maimaita mata a ɗan tsawace sannan ta tashi. Da kansa ya gyara mata filo jikin
fuskar gadon ya kuma taimaka mata ta jingina da ƙyau. Kusa da ita ya zauna yana mai
kallonta tamkar mai nazari. Ita dai taƙi yarda ko sau ɗaya ta kallesa. Numfashi ya
ɗan furzar da ɗakko kofin shayin ya miƙa mata. Cikin ɗashewar muryarta tace, “Ni na
ƙoshi”.
A karon farko ya saki guntun murmushi dan shi dariya ma take bashi, yana
dannewa ne kawai. Ya ɗan rufe idonsa ya sake buɗewa a kanta. “Shi borin naki ya
shafi har cikinki da lafiyarki kenan?”. Ya faɗa cikin sauƙaƙa muryarsa har yanzu da
murmushi akan fuskarsa. Baki ta tura gaba da ƙoƙarin zamewa zata sake kwanciya ya
riƙota. Son zame jikinta take amma ya hana hakan, sai ma jawota da yay gaba ɗaya ta
dawo jikinsa. Tsuma jikinta ya farayi, murya na rawa tace, “Nidai ka sakeni bana
so”.
“An gaya miki nima ina so ne?”.
Yay maganar a hankali cikin kunenta. Da sauri taso janye jikinta amma ya hana
hakan, murmushin dake son sake kufce masa ya danne, ya ɗakko cup ɗin shayin ya sake
miƙa mata, ɗago idanunta da suka cika da ƙwalla tai ta kallesa, ganin ganda yay
kicin-kicin da fuska ta maidasu ƙasa. “Bacci nake ji gashi kina ɓata min lokaci”.
So take ya fita ya barta dan haka ta amsa, ya ringa ya gama wucewa, dan haka
ta kafa kofin a baki tai masa shan ruwa. Shi da kallonta kawai yake, ta miƙa masa
kofin zata sake zamewa ta kwanta ya riƙota. Zatai magana ya harareta, baki ta
murguɗa masa a kaikaice sai dai sarai ya ganta, baibi takanta ba ya ɓalla magani da
ruwa ya bata. Tana gama sha bata yarda ta kallesa ba tai wuf ta kwanta tare da jan
bargo ta rufe har saman kanta. Shima baice mata komai ba ya ɗauka wayarsa yana
dubawa. Sai da ya tabbatar barcinta yayi nisa sannan ya ɗauka kofin data sha tea
ɗin ya fito bayan ya kashe mata wuta....
A hankali ta sauke ajiyar zuciya dan likimo dama tayi ba barcin take ba. Ta
ɗanji ƙarfin jikinta dama akwai yunwa tare da ita, sai dai duk da hakan jiri na ɗan
ɗibarta kaɗan-kaɗan. Ƙofar ta tashi ta sakama key sannan ta cire kayan jikinta ta
saka masu sauƙin nauyi, toilet ta shiga tayo alwalar kwanciya ta dawo ta haye gadon
dajan bargon ta ƙudundune dan har yanzu sanyin bai gama sakinta ba.

Daga shi har ita makara sallar asuba sukai, haka ya sashi yin salla a gida,
yana kuma idarwa ya koma ya kwanta kamar yanda itama a nata ɓangaren kwanciyar ta
sakeyi. Barcine cike da idonta, da alama maganin daya bata yana saka barci.
Ƙarfe kusan sha ɗaya ta farka. Alhmdllhi babu zazzaɓin hakama ciwon kan. Sai
dai jikinta babu ƙarfi kamar yanda zuciyarta babu daɗi. Ɗakin ta gama ƙarema kallo
da yaba ƙoƙarin iyayenta duk da batajin zatai tsahon zangon zama a wannan gidan. Ta
wuce toilet tana sake tabbatarma kanta taƙaitaccen zama zatai. Da ruwa mai ɗumi
sosai tai wanka, koda ta fito har ta gama shiryawa babu motsin kowa, taci alwashin
bazata ƙuntata kanta ba, ba kuma zata sake yarda tayi kuka ba zatai yaƙin barin
gidanne da ƙarfin zuciya dana ƙwanji, dan haka ta gyara gadonta sannan ta fito
falo. Anan ɗin ma komai ya mata ƙyau dan an saka kalar da tafi so ne a rayuwarta.
Tai ɗan murmushi tausayin iyayenta na ratsata, da sun sani basu wahal da kansu ba
ma. Kitchen ta shiga shima ta ƙare masa kallo har store dake cike da kayan abinci
na gara. Ta shiga ɗayan bedroom ɗin nan ma komai abin birgewa. Tunawa da wayarta
data baro bedroom ya sata komawa, ta ɗakko ta fito ta tuna bata shiga ɗayan ɗakin
dake facing nata ba. Kanta tsaye ta shiga kamar ko'ina, tai turus da ganin wanda
batai zaton gani ba a ciki. Zaune yake a bakin gadon da alama yanzu ma ya tashi a
barci, buɗe ƙofar ya sashi ɗago idanunsa. Ita ta fara janye nata cike da basarwa
taja baya da nufin maida ƙofar ta rufe tana ɗan tsuke fuska da faɗin “Good
morning”.
Bai amsa mata ba, bai kuma janye idanun nasa a kanta ba harta maida ƙofar ta
rufe. Cikin ɗan ƙunƙunini da murguɗa baki tabar wajen. Falo ta koma tai zamanta
ƙafa ɗaya kan ɗaya tana kunna wayarta.
Agogon dake ɗakin ya kalla, ganin har goma da rabi tayi ya sashi miƙewa ya
fito a ɗakin, harya nufi hanyar falo sai ya tsaya cak, da baya ya dawo ya buɗe
ɗakin data kwana ya shiga. Bai damu da rashin samunta a ciki ba ya shige toilet
ɗinta, wanka yayi tare da ɗaukar cikin sabbin brush ɗinta ya buɗe ɗaya yay amfani
da shi. Towel ɗinta ya ɗauro, ya riƙo wani a hannu yana goge jikinsa. Gaban mirror
ɗinta ya ƙarasa yana bin kayan kwaliyyar dake kansa da kallo ɗaya bayan ɗaya, iska
ya ɗan furzar daga bakinsa, sai kuma ya nufi ƙofa, kaɗan ya leƙa kansa duk da yasan
bawai zai iya hangota bane....
Har yanzu tana falon zaune abinta tana buga game hankali kwance, kai kace ba
ita bace ta gama bori da rusar kuka ba jiya da sauran kwanakin da suka gabata. Jin
kamar ana kiran sunanta ya sata ɗagowa takai dubanta ga hanyar corridor ɗin. Baki
ta murguɗa jin ya ƙara kiranta cikin ɗan daga murya, cikin magana ƙasa-ƙasa da
ba'ajin mi take faɗi ta miƙe. Harta nufi hanyar ɗakin data barsa ɗazun ta dakata
sakamakon jin gyaran muryarsa a nata ɗakin, idanu ta zaro da riƙe ƙugu tana duban
ƙofar, ta cije lip ɗinta na ƙasa cikin takun fusata da tsaurin ido ta nufi ɗakin
tana wani ɗaure fuska ita a dole bazata masa ta sauƙi ba........✍

_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_


*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*
YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:


07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇


09134848107

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*

[11/23, 10:16 PM] My Zafafa: *_Typing📲_*

*_BABU SO....!!_*
_(Miya kawo kishi?)_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718

*_41_*

..........Gaba ɗaya tsiwar dake bakin nata ta maƙale akan harshenta, ta juya baya
da sauri tana rumtse idanu ƙirjinta na bugawa da karfi. Duk abinda takeyi yana
kallonta ta cikin mirror, cigaba yay da goge sumarsa kamar bai ganta ɗin ba, keys
ɗin dake ajiye saman mirrorn ya ɗauka ya miƙa mata. “Je ɗakina ki samomin kaya....”
Kafinma ya rufe baki tai gaba har tana neman yin tuntuɓe. “Da haƙwaranki zaki
buɗe ƙofar?”. Ya faɗa cikin katse mata hanzari. Jitai kamar ta fasa ihu, amma sai
ta daure idanu a rufe ta juyo tare da miƙa masa hannunta. Kansa ya ɗan girgiza ya
ajiye keys ɗin ya cigaba da abinda yake yi. Kaɗan ta buɗe idanunta, tana tura baki
gaba ta ɗauka batare data yarda ta kalli inda yake ba ta fice da hanzari. Haka
kawai abin nata ya bashi dariya, amma sai ya haɗiye baiyi ba.
Baki ta shiga taɓewa tana bin ko'ina na sashen da kallo. Babu dai tarkace
babu kuma mugun datti, amma yana buƙatar gyara dan da alama shi yake aikin gyara da
kansa tunda taji ance Fadwa na gida sai jiya aka dawo da ita. Bakinta dai bai furta
komai ba ta buɗe wadrobe nashi. Anan kam komai a tsare yake, ga kuma ƙamshi kayan
nayi. Taja wasu mintuna tana bin kayan da kallo daki-daki kafin dai ta zaɓi wanda
suka kwanta mata a rai, cikin ɗan taɓe baki take faɗin, “Ko basu makaba dole ka
saka, ko kunyar zama da towel a gabana baiji ba tirr” sai kuma ta taɓe baki,
“Mutumin nan fa Sassaƙeƙen ƙato ne fa yasin” tai ƴar dariya da kai hannu ta buge
bakinta.
Tafiyarta take hankali kwance batare data lura da su ba, daga aunty Malika har
aunty Safarah, Fadwa aunty Suwaiba sun saki baki suna binta da kallo harta wucesu,
baya Fadwa tai kamar wadda jiri ke neman kwasa ALLAH ya sota akwai bango bayanta
“Aunty kenan wajenta ya kwana fa?”. Ta faɗa hawaye na rigegen sakkowa. Su duka
kallonta sukai, a ɗan hasale aunty Malika ke faɗin, “To ke kam dai lallai takaicin
kishiya zai karki idan baki nutsu ba, kuma in har kika bari ta gano lagonki wlhy
kin mutu. Mi kwanan nasa wajenta ya amfana masa tunda gata nan tsaye kan ƙafafunta
babu alamar tanada daraja na mace a wajensa. Ashema kina kokwanto akan maganin
nan?”.
“Aunty ki fa......”
Cikin katseta Aunty Safarah tace, “K washe garin da aka kawoki gidan nan a haka
kika kasance?”. Wata wawiyar ajiyar zuciya Fadwa ta sauke mai ƙarfi saboda tuno
wahalar data sha a hanunsa a daren da aka kawota, washe gari kam komai bata iya
hasalama kanta ba sai da taimakonsa, dan ko tafiya sai da taita cin azaba kafin ta
dai-daita bayan kwanaki biyu, ta share hawayenta tana murmushi, tabbas ta yarda
mijinta bai taɓa yarinyar nan ba, dan babu macen da zataje hanun mijinta a karon
farko a ganta a haka, shi ɗin namiji ne, idan tace namiji, tana nufin namijin
gaske... (🤕dama akwai mazan ƙarya? Ƴar uwa kisa a ranki kema mijinki namijin gaske
ne😚😉).

Anam da batasan sunai ba koda ta isa sashen nata bayan tayi sallama a
ƙofar ɗakin cogewa tai taƙi shiga, sai ƙofar data buɗe ɗan kaɗan ta zira hanunta da
kayan a kai. Yana zaune a bakin gadonta yana waya ya hango hanunta, ɗauke kansa yay
kamar bai gani ba ya cigaba da wayarsa. Jitai hanunta yana neman sandarewa, ta
harari ƙofar tamkar tana ganinsa, cikin tunzura baki ta shiga ɗakin, da baya-baya
ta dinga tafiya a hankali harta iso gaban mirror, ido suka haɗa da shi ta ciki daga
inda yake zaune dan ya gama wayar, da sauri ta kauda kanta ta ajiye kayan a kujerar
mirror ɗin tai gaba. “singlet da boxer kuma fa?”.
“Yayaaaa!”
Ta faɗa da sauri dajan sunan cikin salon kai bakajin kunya tana juyowa. Suna haɗa
ido tai saurin sake juya baya “Ni dai babu ruwana”. Jin motsin tashinsa tsaye ta
fice da sauri. Sai da ta gama yima ƙofar harara kala-kala sai kace wata ƴar yarinya
sannan ta wuce ɗakko masa. Shima daga can ƙaramin tsaki yaja da faɗin, “Girma ba
wayo”.
Yanzu kam bata kai ɗazu daɗewa ba ta dawo, cikin dakiya da ɗaure fuska ta
shigo ɗakin kanta tsaye, har gabansa taje ta ajiye ta juya ta fita batare data
yarda ta kallesa ba. Da kallo kawai ya bita a ransa yana raya (anya yarinyar nan
bata da aljanu ma kuwa?) rashin mai basa amsa ya sashi sake jan wani tsakin ya
ɗauka kayan ya saka. Tana zaune a falon ta wani tsume kamar sarauniya a kujerar
mulki ya fito, da farko tayi kamar bata gansa ba, sai da ya ƙara matsowa sosai taji
ƙamshin turarenta a jikinsa. “Yaya satar turare ka koma kuma?”. Ta faɗa tana
tsatstsaresa da idanu. Shi rasama mizaice mata yayi, zata ƙara magana akai
knocking. Ɗauke idonsa yay daga kallonta ya nufi ƙofar ya buɗe. Cikin girmamawa
Mubarak ya risina ya gaidashi. Kai ya jinjina masa yana amsawa.
“Yaya dama breakfast ne akace a kawo”.
“Okay ya mutanen gidan?”.
“Kowa lafiya yake”.
Komai bai sake cewa ba ya matsama Mubarak ɗin ya shiga, shi kuma ya nufi sashen
Fadwa. Taso sharesa amma kwarjininsa da cikar haibarsa ta kasancewar sa namijin
tsayayye da bazai ɗauka raini ba ya sata nutsuwa, idanunta a ƙasa tace masa ina
kwana. Falon yake ɗan bi da kallo batare daya amsa mata ba, sake gaisheshin tayi a
ɗarare, sai dai bai amsa ba yanzun ma, saima tambaya daya jeho mata...
“Masu zugakin sun tafi kenan?”.
Saurin ɗagowa tai ta kallesa, ganin ya tsatstsareta da idanunsa masu kaifi ga
fuskarsa a tsume matuƙa ya sata saurin maida idanun nata ƙasa sai dai ta kasa cewa
komai. Ya furzar da numfashi mai zafi da zurfi. “Daga yau na haramta musu zuwamin
gida, idan kuma sukai kuskuren sake zuwa ɗin zan ɗauka kowane irin mataki a kansu.
Kema bazance karki ɗauka huɗubarsu ba, amma ki sani idan naci karo da wani hali a
gareki saɓanin wanda na sanki da shi kamar jiya zakisha mamaki na”.
“Humm” kawai tace a ƙasan maƙoshi, dan ta ɗauka zantukan nasa da suna borin
kunya irin mazan da sukaci amanar matansu wajen ƙara aure. Sai dai kamar yanda su
aunty Malika sukai mata huɗuba bazatace da shi komai ba, zatabi komai a sannu harta
cimma nasara akansa daga shi har amaryar tasa. Humm ɗin tata ta matuƙar zafarsa da
ɗaukarta raini, sai dai a yanzu baya buƙatar wani tashin hankali dan haka baice
komaiba yay ficewarsa. Sashensa ya nufa, ya ɗauka key ɗin mota da lap-top bag ɗinsa
ya sake komawa sashen Anaam, har yanzu Mubarak na nan bai wuce ba, yana tsaye daga
bakin ƙofa yace, “Ni na wuce office”.
Ɗagowa tai ta ɗan dubesa, ganin fuskarsa babu alamar wasa ya sata shanye
abinda ke bakinta, a taƙaice tace, “ALLAH ya bada sa'a”. A kan laɓɓa ya amsa mata
ya juya ya fita. Miƙewa Mubarak yay shima, “Aunty Anam bara naje nima akwai aiken
aunty a wajena kar taita jira”. Fuska ta ɓata cikin damuwa, sai dai batace masa
komai ba ta gyaɗa kanta kawai. Tanaji tana gani ya fita ya barta ita ɗaya. Sai taji
gaba ɗaya sashen ya mata girma da faɗi na rashin sabo, haka kawai kukan da taketa
fatan kartayi ya kufce mata, sai da tayi mai isarta sannan tai zaman cin abincin da
Mubarak ya kawo, tana kammalawa barci ya kwasheta a falon batare data shirya hakan
ban.
Cikin barci sautin mahaukacin kiɗa dake tashi a gidan ya karaɗe mata kunne,
ta tashi a ɗan zabure tana dafe kanta daya sara mata, a dai-dai nan su Amrah suka
shigo falon. Su duka kanta sukai suka rungumeta, cikin dauriya da jin daɗin ganinsu
ta janye hanunta tana kallonsu fuskarta da murmushi. Aysha tace, “Uhhm su Blood
matar Yaya Shareff, wlhy har kin canja dare ɗaya”.
Kai kawai Anam ta girgiza tana hararta, Amrah ta kwashe da dariya ita da
Husnah. Cikin salon ƙara tsokana Aysha tace, “ALLAH karkiji wasa blood, sai sheƙi
kikeyi kamar hasken farin wata, ba kamar matar Yaya Maheer ba da muka tarar wujiga-
wujiga da ita tana faman kuka”.
Kafin Anam da zancen ya tsikara tace wani abu Husnah ta karɓe da faɗin,
“ALLAH nima taban tausayi, kamar ma wadda bata cikin hayyacinta, daga ganinta
zamuyi sa'anni da ita amma kamar bata da wayo sosai wlhy, ko ƴar 18years bazatai
wannan sakaka ɗin nata ba ai balle ita”.
Amrah da batace komaiba ta ɗan girgiza kanta, “Ni kam sai naga ba laifinta
bane wlhy, kamar matsalar daga Yaya Maheer ne, kugafa yanda yaketa mazurai kamar ba
shi ba. Anya kuwa auren soyayya sukayi sisters?”.
Tsitt sukai lokaci guda kowa na nazarin maganar Amrahn, Anam ta fara furzar
da numfashi tana faɗin, “Inaga kubar zancen nan haka dan ALLAH kamar zaifi. Wai shi
wannan kiɗan daga ina yake fitowa?”. Aysha ce ta taɓe baki da jan tsoki, “Daga ina
kuwa inba sashen aunty Fadwa ba, shaggun ƙawayen nan natane su Sima fa kamar a
gidan. Halan Yaya baya nan ne ko?”.
Kai kawai Anam ɗin ta jinjina batare da tace komai ba, ta kuma daƙile maganar
duk da ta fahimci tana cin bakunansu. Basket ɗin da suka kawo ta jawo gabanta tana
buɗe kulolin ciki, da haka ta ɗauke hankalinsu da zancen abincin babu wanda ya ƙara
sakko maganar kidɗan dana gidan Maheer.

Zuwansu ya matuƙar ɗauke mata hankali, da taimakonsu ta gyara ko'ina duk da


babu wani datti, zuwa la'asar wasu daga cikin ƴan uwa danginsu Abie ɓangaren
mahaifiya sukazo. kayan gara na fulawane da ƴan abubuwan daba'a rasaba suka kawo
mata saboda baƙi da zasu ɗan ringa shigowa ganin ɗakin amarya, harda drinks mai ɗan
yawa da ruwan roba. Sai lokacin sukaji sautin kiɗan dake tashi a sashen Fadwa ya
tsaya, babu wanda yay magana suka cigaba da harkokin gabansu.......✍

_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_


*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:


07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇


09134848107

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*


[11/23, 10:16 PM] My Zafafa: *_Typing📲_*

*_BABU SO....!!_*
_(Miya kawo kishi?)_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718

*_42_*

.........Tsitt gidan ya koma bayan wucewarsu, sai ta sake komawa sukuku da ita.
Cikin dauriya ta ƙarasa saka turaren wutar dasu Amrah suka fiffido mata da
fresheners masu ƙamshi ko'ina ya ɗauki ƙamshi dama sannan ta wuce bedroom yin
wanka. Koda ta fito shiri tai cikin doguwar riga mara nauyi ta ɗan gyara fuskarta
da sakama jikinta ƙamshi ta tada sallar magrib. Bayan ta idar ne wani tsoro ya
dinga tsikarar zuciyarta, dan shirun gidan yayi yawa matuƙa, sauƙin ma akwai wutar
nepa dan anguwar suna samun wuta sosai. Bata damu da rashin ganin Shareff balle
tunanin ya dawo gidan ko bai dawo ba. Tana nan zaune saman sallayar taji tsoronta
na ƙara girma, sai ta ɗauka wayarta ta fara karatun alkur'ani a ciki.....
A daidai nan motar Shareff ta shigo gidan, a gajiye yake matuƙa saboda yau
yayi yawo ne sosai cikin wani katafaren aikin babban estate da companyn su ke aikin
ginawa. Yana China aka fara aikin, tunda ya dawo kuma ciwo ya kwantar da shi bai
samu zuwa ya duba ba sai yau. Kai tsaye sashensa ya nufa, mamaki ya kamashi ganin
ko'ina tsaf an gyara, ga wani ƙamshin turaren wuta na musamman na tashi ba irin
wanda ya sani ba. Hatta da toilet ɗinsa tsaf yake sai ƙamshi ke tashi, ya ɗan saki
huci wani kaso na gajiyarsa na raguwa dan shi mutumne mai tsaftar tsiya da kuma son
tsafta. A gurguje ya zura jallabiya ya fesa turare ya fice massallacin anguwar tasu
da ake ƙoƙari tada salla....

Tun daga shigowarsa ta farko har fitarsa a idon Fadwa ne dake leƙe ta window,
taji matuƙar farin cikin ganin sashensa ya nufa ba sashen Anam ba. A ranta tace,
(anya wannan amaryar kuwa ta cika amarya?) sai kuma ta bushe da dariya ranta fes,
musamman data tuna sanda take cin nata amarcin yanda ya dinga nanan da ita kamar
ƙwai. Amma sai gashi yau harda fita aiki bai kuma tashi dawowa ba sai yanzu.
Gaskiyarfa su aunty Malika hayaƙi ba nata baneba, dole ta kwantar da kai taga da mi
shegiyar ta shigo, shima kuma ina ya dosa... Falonta ta sake kalla taga komai tsaf
ga ƙamshi na musamman irin wanda ta saka a sashensa na tashi, hakama jikinta babu
wata makusa wando da rigar sun matuƙar amsarta. Ta sake sakin murmushi da ɗaukar
sweet ɗinta mai ƙamshi ta jefa baki ta koma cikin kujera ta ɗaura ƙafa ɗaya kan
ɗaya tana daukar ɗan guntun bidiyo da zata poster a tiktok kodan maƙiya da suka
tasota gaba da izgilin an mata kishiya a watanni biyar kacal.. Tana tsaka da editin
ɗin bidiyon ya shigo falon da sallama. Da sauri ta fito daga tiktok ɗin tana ajiye
wayar fuskarta da ɗan murmushi tace, “Sannu da dawowa”.
Sosai mamaki ya ƙara neman kashesa, dan kuwa ya jima baiga Fadwa cikin irin
wannan tsaf ɗin ba ita da sashenta. Cikin ɗan salo ta tashi tsaye tana faɗin,
“Soulmate wai mi kake kallo ne haka kamar baƙo a sashen?”.
A karan farko ya ɗan ware idanunsa a kanta da sakin guntun murmushi, kansa
tsaye dan bai iya ɓoye-ɓoye ba yace, “Dama da gaske ne mata idan aka musu kishiya
sunfi yin hankali da tattalin miji?”.
Duk da maganar ta mata zafi sai ta dake, cikin murmushi ta matso kusa da shi ta
rungumesa. “Haba Soulmate kamarya? Da bana tattalinka?”. Hannayensa duka biyu yasa
ya ɗago fuskarta ya riƙe a tafin hanunsa, yayinda itama nata hannayen ke zagaye da
shi sun manne da juna. Kallonta yake cikin ido, kaifinsu na sake narkar da ita a
soyayyarsa da ƙaunarsa harma da kishinsa mai tsanani, dan tasan mijinta irin mazan
da mafi yawan mata basa kalla su kauda ido ne saboda abubuwa da yawa daya tara
musamman miskilanci dake saka mafi yawan mutane shakkarsa har ita a karan kanta...
A hankali ya hure idanunta, tai saurin rimtsewa ta sake buɗewa cikin nasa da har
yanzu suke a kanta. “Da gaske kin canja, haka nake so ki kasance mai yawan kula
akan komai my love. Indai kika riƙe zaki mallaki Al-Mustapha a tafin hanunki cikin
sauƙi”.
Wani irin shauƙin daɗi ne ya ratsata, ta sake rungumesa da jin kamar su
dawwama a haka. Lallai kwallin idonka idona ɗin nan yayi, cikin ƙanƙanin lokaci ga
aikinsa kai babu abinda zatace da su aunty Safarah sai ALLAH ya biyasu. A hankali
ya janyeta a jikinsa, da sumbatar goshinta. “Bara naje naga ƙanwarki itama, dan ina
son na zauna daku yanzun nan”.
Kanta ta gyaɗa masa tana murmushin yaƙe, bai sake cewa komaiba ya fice ransa
na ƙara sanyi da canjawar tata......

Bayan ta idar da sallar isha'i har shafa'i da wutirinta tayi, batajin wata
yunwa dan haka ta yanke shawarar shan yogurt kawai da Mamie ta sakko a cikin drinks
ɗin da aka kawo mata, fita tai da nufin ɗakkowa ta dawo bedroom ɗin, da tasha zatai
kwanciyarta dan ita dama akwai saurin barci. Koda ta ɗakko yogurt ɗin sai ta haɗo
da dubulan guda ɗaya dan tana matukar sonsa balle wannan da yasha riɗi da zuma mai
ƙyau. Daga wutar falon har ta kitchen duk kashwa tai, sai dai kuma rashin sabo yasa
ta manta da rufe ƙofar falon ta wuce bedroom, tamkar jira tana shiga ana ɗauke
wuta, dai-dai nan shima ya ɗaura hanunsa a handle ɗin ƙofar falon nata ya shigo.
Ƙarar data saki ce ta ratsa masa dodon kunne, karo sukaci a tsakkiyar corridor ɗin
bedrooms ɗin nata, sai kawai ta zabura ta sake fasa wata ƙarar.
Da ɗan lalube ya samu ya riƙota a cikin duhun ya manneta da jikinsa da
lalubo kunenta yana faɗin, “K! Calm down ni ne fa”. Yanda yay maganar cikin raɗa ya
saka tsigar jikinta tashi baki ɗaya, ta sake ƙanƙamesa da sakar masa wani
shagwaɓaɓɓen kuka.... Baice mata komai ba, sai dai yana shafa bayanta a hankali
hawayen na sauka a ƙirjinsa duk da bata kai har can sama ba saboda rashin tsahonta,
dan shi sai da ya ɗan ranƙwafo sosai ya samu rungumeta da ƙyau. Maido wuta da akai
ne ya sakata haɗiye sauran kukan ta shiga sakin ajiyar zuciya, sai kuma kamar wadda
aka cikara ta zabura ta janye jikinta... Bai hanata ba ya saketa, suna haɗa ido tai
saurin juya masa baya tana tura baki gaba. Bayanta ya ɗan tsurama ido, sai kuma ya
zagayeta ya wuce bedroom ɗin nata. Da mamaki ta wara idanunta da basu gani da ƙyau
tana binsa da kallo dan batama san inda glass ɗin nata ya faɗa ba, “Wannfa ai shine
ƙarfin rai mai sata da sallama” ta faɗa ƙasa-ƙasa tana harar ƙofar. (Ƙarfin hali
ɓarawo da sallama bahaushiyar malaysia😹😜).
Bin bayansa tai dan taga mi zaiyi mata a ɗakin. A bakin gado ta samesa zaune
da wayarta a hanunsa. (Ƙarfin hali....) ta raya a ranta da nufar glass ɗinta dake
yashe a ƙasa ta ɗauka ta saka. Dai-dainan ya ɗago ya dubeta ya kauda kai. “Babu
abinci a gidan ne?”.
Bata fahimci tambayar tasa ba, dan haka ta gagara cewa komai, sake ɗagowa yay
ya dubeta yana ajiye wayar tata. “Baki jini bane?”.
“Ni ban san zakaci ba shiyyasa naba maigadi, naga da safe da aka kawo baka
ci ba, na rana daya rage ne na bashi na kumace kar Mom ta aiko na dare”.
“Kin bani na safen ne da kikaga ban ciba” ya faɗa cikin kafeta da ido, kallo
ɗaya tai masa ta maida nata ta rissinar dan wani irin girma da kwarjini ya ƙara
mata. Sai taji gaba ɗaya tsiwar tata bazata yuwu ba. Shima ɗauke nasa idanun yay a
kanta batare da ya damu da rashin amsawar tata ba ya ƙara jeho mata wata tambayar.
“K mi kika ci?”.
Ƙasa-ƙasa tamkar mai tsoron a jita tace, “Zansha yogurt”.
Maida kallonsa yay ga yogurt ɗin da dubulan data ajiye a bedside drawer, dama
ruwa ta tuna bata ɗakkoba ta shirya komawa ɗakkowa aka ɗauke wuta. Jin baice
komaiba ta saci kallonsa, “Kaima na kawo maka?”. Ta faɗa ganin har yanzu idonsa
akan dubulan ɗin.
Miƙewa yay batare da yace komai ba, sai da ya ɗanzo gab da ita sannan.
Idanunsa a kanta kansa tsaye yace, “Ki kawo, ki kuma haɗo da ruwa”.
Raka bayan nasa tai da hararar gefen ido, cikin kwaikwayon maganarsa da
umarnin nasa ta maimaita abinda yace tana ciccijewa kamar dai yanda yayi. Sai kuma
ta taɓe baki ta matsa wajen hijjabin sallarta ta ɗauka ta saka sannan ta fito duk
tunaninta yana a falonta yana jira. Sai dai koda ta fito wayam, babu shi babu
alamarsa. Cikin mamaki tace, “Wai miye nufinsa? Nakai masa can sashensa ko mi?
Hu'umm”. Mi kuma ta tuna oho mata sai ta murgiɗa baki ta nufi kitchen ɗin nata.....

Tun shugarsa sashen Anam tana laɓe tana leƙe ta wimdonta da kallon agogo,
ganin ya wuce mintunan datai tsammani zuciyarta ta sosu, ƙwafa tayi cikin takaici
da son danne abinda ke ranta tana cusama kanta huɗubar su Aunty Malika, koda ya
fito jitai kamar taje ta kamasa da duka amma babu damar hakan, barin wajen window
ɗin tai ta shiga bedroom, ƙara gyagygyara jikinta tai da ƙara turare ta ƙara
kwallinta da jambaki sannan ta fito hanunta riƙe da wayarta ta yano siririn mayafi
batare da tunanin basu kaɗai bane ita da shi. Cikin yauƙi da yanga ta nufi sashen
nasa tana murmushin data aro ta yafa ma kanta.....
A dai-dai lokacin Anam da batasan akwai zama ba ta shiga falon nasa bayan tayi
sallama da knocking ya bata izinin shiga. Zaune yake a saman 1sitter ya miƙe
ƙafafunsa duka biyu saman centre table da lap-top akan cinyarsa yana aiki. Ɗan
ɗagowa yay ya dubeta da amsa sallamarta ya maida kansa ya cigaba da aikinsa. Ta
ɗanyi mamakin jin falon na kamshi yanzu kuma a gyare tsaf ba kamar ɗazun da safe
data shigo ba, sai dai ba huruminta bane hakan sai kawai ta ajiye a saman centre
table ɗin gefen ƙafarsa kaɗan. A niyyarta data ajiye ta juya ta fita, sai dai tana
ajiyewar kafin ta ɗago Fadwa ta shigo da sallama...........✍
_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_


*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:


07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇


09134848107

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*


[11/23, 10:16 PM] My Zafafa: *_Typing📲_*

*_BABU SO....!!_*
_(Miya kawo kishi?)_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718

*_43_*
........Shine ya amsa sallamar tata, da ɗan ɗagowa yana kallonta. Ta ƙaraso
zuciyarta na mata zogi irin wanda aka san kowacce mace da kishi ke saka mata. Amma
sai ta dake ta sakarmasa murmushi kamar yanda shima yake mata. Ɗan sumbatar gefen
fuskarsa tai da bashi side hug. Nanma murmushin ya ɗanyi da lumshe mata ido irin na
godiya...
Anam taji wani irin tsammm a jikinta, dan tunda aka kawota gidan sai yanzu ne
suka haɗu da Fadwa, wani irin ƙululu yazo ya tokare maƙoshinta akan abinda Fadwa
tai masa duk da bawai kallonsu take ba. Amma sai ta dake ta fasa ɗagowar datai
niyyar yi, goran ruwan ta ɗauka ta ɓalle bakinta, ta tsiyaya rabin glass cup data
haɗo da shi ta ɗago ta miƙa masa fuskarta a tsuke...
“Gashi”.
Idanunsa ya ɗago ya kalleta, tai saurin janye nata saboda haɗuwa da sukai cikin
na juna, sai ta ɗan tura baki gaba jin ya haɗa hanunta da kofin duka ya riƙo, kafin
ya zare kofin yana faɗin, “Thanks” a samman lips ɗinsa...
Ta gefen ido Anam ta dubi Fadwa datai wani zaman ƙasaita tamkar bata ganta ba,
lips ɗinta ta ɗan cija na kasa a ranta tana ayyana (Tabbas bana son mijinki bakuma
zan zauna da shi ba. Amma kafin nabar gidan nan saina tabbatar miki zama birin
wasana a tsakkiyar kasuwa kamar yanda nai alƙawari tunda naga haka kike buƙata) A
zahiri kam sai ta saki lallausan murmushi, dai-dai ya gama shan ruwan ya miƙa mata
kofin sai akan idonsa. Idanunsa ya ware da ƙyau yana mata kallon mamaki, amma saita
kauda kamar bata gansa ba. “A saka yogurt ɗin?”. Ta faɗa a hankali kamar mai raɗa.
Kallon Fadwa ya ɗanyi, ganin idonta a kansu itama fuskarta kamar da ɓacin rai
amma ta dannesa da murmushi ta ƙarfin tsiya ya sakashi dubar Anam da itama tata ke
bayyanar da murmushi har yanzun. “Bari na kammala aikin nan zan sha”. Ya faɗa yana
maida kansa ga lap-top ɗin...
“Okay” ta faɗa a taƙaice da komawa kujerar gefansa ta zauna, har ƙafarta ta
naɗe zuwa saman kujerar, hakan ya bama zaman nata damar facing ɗinsa, amma saita
maida hankali wajen buga game a waya kamar yanda itama Fadwa dake zaune ta ɗayan
gefensa ƙafa ɗaya kan ɗaya itama kujera daban, hankalinta ke kan waya tana duba
Comments na mutanenta.
Aikin yake sai dai lokaci-lokaci yakan ɗan kalla kowaccensu ta gefen ido,
dariya suke bashi, dan kowacce ta tsume ita a dole hankalinta nakan wayane bata
damu da ƴar uwarta ba, amma a zahiri babu ɗigon walwala akan fuskarsa. Kusan
mintuna 17 ya kammala abinda yakeyi, system ɗin ya ajiye da furzar da numfashi yana
ɗan lanƙwasa yatsun hannayensa daya haɗe waje ɗaya. Kallonsa Fadwa tai, ta saki ɗan
murmushi da faɗin, “Waldon sir!”.
“Thanks you dear”.
Ya amsa mata yana sauke ƙafafunsa dake kan centre table ɗin suma ya zauna da
ƙyau. Duk Anam najinsu, amma tai biris abinta. Yay ƴar gyaran murya da sake zama
serious, hakan yasa itama Anam ɗagowa ta dubesa. Bai yarda ya kalla kowaccensu ba,
cikin bada umarni ya fara karanto addu'ar da MANZON ALLAH ya horemu dayi a yayinda
wani zama ya haɗamu makamancin hakan, kafin ya ɗora da faɗin, “Ina son ku bani
dukkan hankalinku nan.”
Babu wasa a cikin umarninsa, dan haka duk suka sake nutsuwa kowacce ta ajiye
wayar hannunta, sai dai Anam bata canja daga yanda take zaune ba, dan taji daɗin
zaman. Itama Fadwa dai tana yanda take ɗin sai muskutawa datai yanda zatafi sakewa
da ƙyau.
“Da farko zan fara da godema UBANGIJIN daya haɗamu a ƙarƙashin wannan inuwa,
hikimarsace hakan kuma rubutaccene daga taskarsa tun kafin zuwanmu duniya. Gaba
ɗayanku ina horanku da bani haɗin kai na wanzar da zaman lafiya da kwanciyar
hankali a cikin gidan nan, ina kuma tuna muku tsoron ALLAH a cikin zaman da zamuyi.
Ku dukanku matsayi ɗaya gareku a gareni, fatana ku cicciɗani da bani goyon bayan
tsaida adalci a gareku. Ban yarda wata ta haɗa da shirka ko zalinci ba a wannan
zaman, duk wadda tai hakan bazan yafe mata ba. Fadwa dake zan fara dan kece babba,
duk da a shekaru na tabbatar zakuyi sa'anni koda tsiran zai-zama kaɗanne. Ki riƙe
girman da ALLAH ya baki waje zaunar da adalci a gidan nan garemu baki ɗaya, kin
fita sanin ilimin zaman gidan nan, kin fita sanin abubuwa akaina a yanzu zaki iya
nusar da ita idan kikaga bata fahimta ba cikin sauƙi. Duk wata fitina da zata taso
zan iya fara hukuntakine matsayin babba dan haka sai ki kiyaye”.
Cikin danne komai dake a ranta ta jinjina masa kai da sakin murmushi. “Insha
ALLAHU zaka sameni fiyema da yanda kake so a gidan nan Soulmate. ALLAH ya bamu
zaman lafiya”.
“Amin ya rabbi” ya faɗa yana maida dubansa ga Anam da duk take saurarensu.
“Juwairiyya!”. Ɗago idanunta tai ta ɗan kallesa batare data amsa ba. Shima bai damu
da amsawar tata ba ya cigaba da faɗin, “Ina fatan zaki bani haɗin kai wajen wanzar
da zaman lafiya a gidan nan kema, sannan ki ɗauka Fadwa matsayin babba a gidan nan
ku zauna lafiya, saɓanin hakan ba yana nufin zan hukuntata bane ita kaɗai, har dake
zan haɗa domin matsayinku duk ɗayane a gurina. Abinda baki fahimtaba daya shafi
gidan nan ko ni zaki iya zuwa gareta ta sanar miki”.
Kanta ta ɗan jinjina da faɗin, “Insh ALLAH”. A ƙasan maƙoshi.
“Bana son jin wani abu saɓanin abinda nake fata a gareku, dan yanzu ba da
bane, a cikin gidana kuke ƙarƙashin ikona ku duka, zan iya ɗaukar kowanne irin
mataki akan duk wadda ta shirya bani matsala ko raina ƴar uwarta. Mu dukammu jini
ɗaya ne ku dinga tunawa da hakan a duk sanda shaiɗan ya bijiro muku da wani abu a
zuciya ko wasu a cikin dangi. Dan na tabbatar a yanzu kowanne zai iya zama ashana
da fetur ɗin cinnama gidana wuta adalilinku, kuma bazan amince ba, zan ɗauka mataki
akan duk wacce ta bada wannan fuskar a cikinku da su wanda zasu iya kasancewa
zagaye daku wajen haddasa min fitina” Bai jira amsarsu ba ya cigaba da faɗin, “Akan
kwana, idan aka cire kwanaki bakwai miye tsarinku?”.
Anan dai Fadwa ce kawai ta amsa, Anam kam dai shiru tayi. Fadwa tayi matuƙar
danne raɗaɗin da takeji ta maye gurbinsa da murmushi, “Ni dai a nawa shawaran
Soulmate kwana bibbiyun is ok ai ko?”.
“Okayyy!”
Ya faɗa cikin ɗan jan y ɗin da maida dubansa da Anam, taƙi cewa komai, taƙi kuma
yarda ta kalla kowa. Sai dai tana jin idanunsa masu kaifi a kanta, kanta ta sake
duƙarwa da tura baki gaba dan ita kam kunya ma maganar ke bata, fahimtar hakan da
yayi ya sashi ɗauke idonsa da faɗin, “Hakan yayi kawai. Duk mai girki itace zata
ciyar da kowa na gidan nan abincin dare, zakuma muci tare anan. Na cire safiya da
rana ne saboda mafi yawan lokaci ina fita da wuri, na rana kuma bana gida kowa zata
iya ra'ayin kanta amma zata bama maigadina tilas. Sai dai a weekend zakuyi har na
safe kamar dai gobe”. Ya ƙare maganar yana kallon Fadwa..
Sam hakan baima Anam daɗi ba itama, amma batai magana ba. Fadwa dai ta amsa
masa da “ALLAH yasa haka shi yafi alkairi”. Ya amsa da amin batare daya damu da
rashin cewar Anam ɗin ba dan yasan a komai yanzu baƙuwace dole suyi mata uziri na
kunyar zaƙewa akan wasu abubuwan har zuwa sanda zata zama ƴar gida. Daga haka ya
rufe taron da addu'a. Anam ta fara miƙewa da nufin tafiyarta dan barcine cike da
idonta har goma saura...
“Bani yogurt ɗin”.
Ya faɗa cikin katseta da bada umarni yana ƙoƙarin canja chennal a tv. Bata da
zaɓin daya wuce dakatawar duk da idonta har lumshewa sukeyi. Amma hakan bai hanata
ɗan tura baki ba dajin kamar ta saki kuka. Miƙewa Fadwa tai tana faɗin, “To ni bari
naje na kwanta, sai da safenku”. Ta ƙare maganar da matsowa ta ɗan sumbaci gefen
fuskarsa kamar ɗazun sannan ta fice tanama Anam ɗin saida safe itama.
Sosai hakan ya soki zuciyar Anam, harta kasa amsa mata, ɗagowa yay ya ɗan
kalleta yaga fuskarta kicin-kicin. Glass cup ɗin data cika da yogurt ɗin ta miƙa
masa. Tsaii ya ɗanyi yana kallonta batare daya amsa ba, sai hakan ya ƙara
tunzurata, ta ɗago idanunta dake cikin gilashi ta kallesa. Saurin janyewa tai tana
ɗan yamutsa fuska. “Yaya dan ALLAH ka amsa zanje na kwanta barci nakeji”.
Bai amsa ɗin ba, bai kuma daina kallonta ba, saita sake dubansa a
marairaice kamar zatai kuka. Ɗan murmushin daya tsaya iya laɓɓa ya saki batare data
gani ba, amsa yay da sake maida hankalinsa ga television ɗin. Ƙara miƙewar tai
yunƙurinyi.
“Ki jira na gama ki tafi da kayan”.
Ya faɗa batare daya kalleta ba. Ai kamar ta ƙwala kuka taji, amma sai ta koma ta
zauna batare da tace dashi komai ba, jin sosai barcin na rinjayar idonta ta naɗe
har ƙafafunta a kujerar kamar ɗazun. Kallonsa ya cigaba dayi yana shan yogurt ɗin
da cin dubulan ɗin kaɗan-kaɗan har aka kammala hirar da yake kallo a tashar ta NTA
da wani babban ɗan siyasa na jihar ta kano. Ya juyo da tunanin itama kallon take
sai ya samu harma tayi barci. Kafe fuskar tata yay da kallo na wasu sakkanni kamar
mai nazari, sai kuma ya kai hannu ya zare gilashin nata a hankali. Tashi yay ya
fita, bai jima sosai ba ya dawo da keys ɗin sashenta a hanunsa ya ajiye...
Motsawa tai, taɗan buɗe ido kaɗan saita gansa dishi-dishi, da farko ta zata
yanar barcin data fara ɗaukarta ce, sai ta rumtse idon ta sake buɗewa amma still
taji raunin ganinta a bayyane. Cikin sauri ta kai hannu ta shafa fuskarta, jin babu
glass ɗinta ya sata kai hannu ta fara laluben cinyarta zuwa kujerar, dan falon babu
fitila mai haske ya kashe. Hanun ta janye da sauri saboda sauka da yay a gurbin da
bashi tai hasashen kaiwa ba. Shiko tamkar bai jitaba yay biris. Cike da borin kunya
ta sauka a kujerar tana ƙara duddubawa, saida ta tabbatar dai ba gani zatai ba
sannan ta dubesa fuska a tsume, sai dai shakkarsa bai hana bayyana cikin tsumewar
tata ba.
“Yaya MM gilashi na fa?”.
“Kin bani ajiya ne?”.
“Toni inma ban bakaba dai ai a falonka ya ɓata”..........✍

_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_


*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:


07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇


09134848107

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*


[11/23, 10:16 PM] My Zafafa: *_Typing📲_*
*_BABU SO....!!_*
_(Miya kawo kishi?)_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718

*_44_*

...........Banza yay mata kamar baiji ba, sai ma ƙoƙarin mikewa yake bayan ya latse
remote tv ya mutu. Ganin zai bar wajen tai saurin riƙo hanunsa dan in har ta bari
ya wuce bazata iya kai kanta ko nan da ƙofar fita ba saboda da gaske bata gani da
ƙyau a cikin duhu sai da taimakon glass ɗin.
“Yaya Please ka bani”.
Hanun nata ya kalla tare da ƙoƙarin juyowa, da sauri ta janye nata a yanayin jin
kunyar aikatawa. Kafeta yay da idanu yana ƙarema fuskarta kallo kai tsaye, yayinda
ita kuma ta kasa ɗagowa ta kallesan. A cikin ransa yake faɗin, (Fitsararriya ashe
kinada kunya?). A zahiri kam babu alamar wasa tare da shi yace, “Muje ki kwanta”.
“Ina ɗin?”.
Ta faɗa cikin waro makantattun idanunta da mai kallo a haka bazai taɓa tunanin
rauninsu ba saboda girma da hasken dake cikinsu tamkar wadda ke iya hango abinda ke
faruwa a kilomita huɗu na gabanta. Gab da ita ya matso har tana iya jin saukar
numfashinsa a fuskarta. Cikin magana tamkar mai raɗa “A inda kike?”.
Baya taso jan jikinta bugun ƙirjinta na daɗuwa amma sai ya hana hakan ta
hanyar tokare hanun kujerar da take jiki da hanunsa. Duk sai ta daburce. Ture
hanunsa tai da ƙarfi, tai gaba da nufin guduwa ƙafarsa ta nema taɗeta tai gaba zata
faɗi ya riƙota, ɗan fisgota yay ta faɗo jikinsa, baima jira tako maida numfashi ba
ya ɗauketa cakk ɗinta yay hanyar bedroom ɗinsa dan ya gaji shima kwanciya yake
buƙata. Inko ya biye mata sai dai su raba hali. Watsal-watsal take da son ƙwace
jikinta tana faɗin, “Ni wlhy ka saukeni bana so, bana son haka Yaya MM, ALLAH zan
cijekaaa!!”. Ta ƙare faɗa da ɗan ƙarfin sautin daya sakashi direta a saman gadonsa
da sauri.
“Kina da hankali kuwa? Fasan kunne zakiyi?”.
Mikewa tai cikin sauri da nufin barin masa ɗakin dan ita kam dai bazata taɓa
yarda ta kwana a ɗakinsa ba, gidan nasa ma domin yin biyayya da iyayenta ne da son
cimma burinta cikin sauƙi zaisa ta zauna har zuwa lokacin data ƙayyadewa shirinta.
Bai hanata ba dan tuni ya zare keys ɗin ɗakin, sai ma toilet daya nufa cikin halin
ko'in kula. Jin ƙofar a kulle ya sata juyowa da sauri duk da ba fes take iya ganin
komai ba amma kasancewar da fitila tana gani fiye da acikin duhu. Sosai hankalinta
fa ya tashi, dan abu ɗaya zuciyarta ta iya bijiro mata zaisa yay mata hakan, a
gareta kuma shine abu na ƙarshe da bazata iya mallaka masa ba koda a yau zaice zai
mata dukan da shine kawai abinda take shakka da tsoro tattare da shi. Haɗiye duk
wani fargabanta tai tai tsayuwar sojan badakkare a jikin ƙofar tana dakon
fitowarsa. Tsahon mintuna 6 sannan ya fito duk tana lissafa ta hanyar kallon agogon
dake bangon ɗakin. Yi yay tamkar bai ganta ba ya hau zame jallabiyar jikinsa.
Bayyanarsa a zahirinsa da ga shi sai boxer ya sata juya masa baya da sauri tana
ambaton sunan ALLAH. Kayan barci ya ɗakko a wadrobe ya saka harda fesa turare
kamarma bai ganta ba. Ya haye gadonsa yana faɗin, “Baƙya buƙatar kwanciyar ne?”.
Maimakon amsa sai ta fashe masa da kukan ƙarya. “Yaya dan ALLAH ka bani key
da glass ɗina na wuce barci nake ji, ALLAH haka babu ƙyau, kuma kaina zai iya yin
ciwo”.
“Idan kin so hakan kenan”.
Ya amsata yana jan bargo cikin halin ko'in kula. Kukan ƙaryar tata ta dakatar
zuciyarta na mata zafi, sai dai hango keys ɗin a bedside drawer ɗin inda yake ya
saka mata jin sauƙi, cigaba tai da tsaiwa a wajen har kusan minti ɗaya kafin ta
nufi wajen cikin sanɗa da tunanin yayi shammatarsa ta warto. Tana gab da isa ya
fiddo hanunsa dake cikin duvet ya ɗauke, rigarsa ya ɗaga ya ɗaura saman cikinsa ya
maida bargon ya rufe. Ganin ta dakata daga yunƙurin tahowar ya ɗan buɗe ido yana
kallonta a sigar da ita bata fahimci haka ba musamman saboda matsalar nata ido.
“Gashi anan ki ɗauka”
Kanta ta ɗauke idonta na ciko da ƙwalla na gaske a yanzun. Dan tsaf ta fahimci
tarko ne ya kafa mata. Hannu tasa ta share hawayenta, sai kuma ta taka da baya-baya
ta koma saman kujerar dake a bedroom ɗin ta zauna..........

★Tun barowarta sashen nasa ta kasa zaune ta kasa tsaye, sai faman kaikawo
take hawaye masu zafi na kishin mijinta na ragargazar zuciyarta tamka irin kowacce
macen da aka kawowa abokiyar zama, ba ita kaɗai ba, irinta da yawa sukan azaftu
matuƙa da rashin barci da ƙunci a irin waɗan nan kwanakin bakwai da amarya takan
samu matsayin na amarcinta. Kai wasu ma borinsu har yakan zarta natan, ga masu
ƙarancin imani ma kwana suke shiryama zukatansu munanan abubuwa harma da masu
aikatawa. To ita dai Fadwa saita kasance a jerin masu azaftuwar ƙuntatama kai da
ƙiyasta abubuwa da dama da bai dace zuciya ta ƙiyasta ɗin ba ta kasance duk da su
Aunty Wasila sun bata tabbacin hakan bamai faruwa bane ta kasa nutsuwa, sai dai
babu tunanin mugunta ko shirka a ciki, ita dai kawai mijinta take hangowa da wata a
yanayin da ita kaɗai ta sanshi.
Tsahon lokaci ta ɓata tsaye jikin window tana kuka da dakon kallon hanyar
tsumayen fitowar Anam da mijinta, amma sai saɓanin hakan ne ya biyo baya, domin
kuwa shi kaɗai taga ya fito zuwa sashen Anam ɗin, bai kuma ɗauki tsahon lokaci ba
ya fito ya sake komawa nasa sashen. Neman zubewa tai ƙasa kuka mai cin rai na kufce
mata dajin tsananin tsanar su Daddy da take ganin sun ƙulla wannan aurenne saboda
basa ƙaunarta ita da mahaifiyarta dalilin asiri da Abie da Mamie da aunty Mimi
sukai na raba kansu tamkar yanda a koda yaushe Gwaggo ke faɗa. (karku ga laifin
Fadwa, a haka aka raini zuciyarta, a haka ta girma da ƙiyayyar waɗanda bata da wani
tabbataccen laifinsu a zahirin rayuwarta, da yawa iyaye na kuskuren wajen ƙoƙarin
fidda matsalarsu da ƴan uwansu ga ƴaƴansu, sun kasa gane hakan yanada matuƙar
tasiri ga zukatan ƴaƴan, dan in har akai wasa su ƴaƴan zasu tashine da ƙiyayya mafi
muni da tsauri ta waɗan nan ƴan uwan nasu koda ace su daga baya sun haƙura sun
yafema juna ne. Shiyyasa mafi yawan zuminci ke ƙara lalacewa da taɓarɓarewa a
zukatan kowacce zuria fiye da ƙyamatar kafurci. Tasirinsa ne a tsakanin *_Anam da
Fadwa_* duk da suna amsa sunan jini ɗaya, amma tunda ba uwa ɗaya ta haifi iyayensu
ba, sun ɗauki hakan babbar tazara da bazata iya basu wata ƙyaƙyƙyawar jituwaba sai
ƙyara da hantarar juna kawai. Sai kuma ga *KISHI* ya ratsa, wanda yake zamtowa
linzami na rasa imanin *MATA* da yawa a dalilin zafafawa, ko da sunada tabbacin
bazasu iya canja ƙaddara ba).
A jiya kasancewar su Aunty Malika tattare da ita ya sama zuciyarta salama
da ɗauke kaso mafi yawa na hankalinta, musamman da zuciyarta ta dinga ayyana mata
Shareff a sashensa ya kwana. Amma yau ganin zahiri ya hanata nutsuwa balle fahimtar
kanta da kanta a matsayin abinda bazai iya canjawa ba ko samuwar ikon hanawa tamkar
kowacce mace irinta. Kuka taci bana wasa ba, wanda ya jata lokaci mai tsayi har
kusan ƙarshen dare sannan barci ɓarawo ya fara rinjayarta. A hankali ta sulale akan
gadon ƙirjinta cike da nauyi tamkar yanda idanunta ke tattare da nauyin barci.
(Koma dai miye ta bani tausayi, mu ƙiyasta kammu a matsayinta bisa adalci na
rayuwa. ALLAH ka bamu kishi mai sauƙi da bazai sakamu a nadama ba🙏🏻😣).

★A lokacin da Fadwa ke can tana kuka da tunanin kasancewarsu a tsakkiyar


lambun fure mafi girman daraja a garesu ba hakan baneba. Anam ta jima zaune akan
sofa barci na rinjayarta tsoro na fisgota, sai dai bata da wata mafita ko ƙwarin
gwiwa saboda babu ɓarawo mafi iya sata kamarsa. Kujerar 1sitter ce guda biyu, hakan
yasa bata samu gamsuwar kwanciyarba duk da ta naɗe dukan jikinta a kanta. Daga inda
yake kwance yaka hango yanda take mutsu-mutsu tamkar magen data sha matsa a hanun
mafarauta. Guntun murmushi kawai ya saki, akan laɓɓansa ya furta “Azababbiyar
yarinya”. Yana lumshe idanunsa dake cike da barci. Kusan mintuna goma ya bata domin
barcinta ya ƙara nauyi sannan ya miƙe a hankali ya taka gareta. Cikin dabara ya
ɗagata gaba ɗayanta yakai saman gadon ya kwantar yana danne dariya. Shi baima taɓa
tunanin tanada nauyin barci hakaba, hijjab ɗin ya zare mata sannan yaja mata bargo
shima ya koma ya kwanta yana sauke ajiyar zuciya. Tsakanin Anam da Fadwa bai san
wanene yafi wani daru ba. Itama yaso zuwa sashenta yay mata sai da safe amma tsoron
abinda zai tarar ya sakashi haƙura. Bai taɓa tunanin da gaske *MAZA* najin shakkar
matansu a irin wannan lokacin ba, dan duk yanda yake jin kansa da mazantakarsa da
ƙin ɗaukar shirme sai nauyi da kunyar Fadwa ke zagaye da jininsa duk da auren nasa
yazo a cikin wani kashine da yasha banban dana sauran maza mafi yawa irinsa.
Numfashi ya furzar a hankali da juyowa gaba ɗayansa yana facing ɗinta, kallon
fuskarta yake a cikin wani irin yanayi mai sanyi da zungurar zuciya, ya matsar da
fuskarsa gab da tata tare da saƙala hanunsa saman jikinta ya rungumota a nasa jikin
sosai, kamar wadda aka isarwa da saƙo ta buɗe ido, sai dai rashin ganinsa da ƙyau
ya sata jan numfashi ta haɗiye tare da nasa da yake busa mata saman fuska. Jan
jikinta tasoyi baya ya ƙara matseta.
“Yay......”
Kalmar ta kasa ƙarasuwa a zahiri tamkar yanda taso furtawa sai a cikin bakinsa, ba
ƙaramin bugawa zuciyar Anaam tayi ba, duk da abinda takema tsoro kenan tun farko
dama hakan bai hanata jin mamaki da shiga bazata ba. Bata da wani ƙarfin ƙwatar
kanta, sai ma ƙoƙarin zare mata duk wani kuzarinta da razani yake ta hanyar cigaba
da sarrafata a wani salo mai kashe jiki da ruguza dukkan alwashi na duk ɗiya mace
mai lafiya. Tun tana iya cijewa harta fara amsar salon nasa dan takai shekarun da
gangar jikinta ke a matuƙar buƙatar fiye da hakan ma. Sosai ya fitar da ita daga
hayyacinta tamkar yanda shima nashi hankalin ya barranta da gangar jikinsa da
zahirin rayuwarsa..........✍

_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_


*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇


09134848107

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*


[11/23, 10:16 PM] My Zafafa: *_Typing📲_*

*_BABU SO....!!_*
_(Miya kawo kishi?)_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718

*_46_*

.........Kaɗan ya rage ta hamɓarar da wayarta dake ajiye, Baki ta tura da sakin


numfashi mai kauri tana kai hannu saman ƙirjinta dake bugawa da sauri-sauri. Har
lokacin bai motsa daga tsaiwar da yay jingine da bango ba ƙafafunsa a harɗe cikin
na juna hakama hannayensa, sai dai cike da basarwa ya kauda idanunsa da tun ɗazun
suke ƙare mata kallo tamkar ya samu television.
“Gaskiya irin haka babu ƙyau, a tsorata mutum idan zuciyarsa ta buga fa?”.
Ƙasa-ƙasa take maganar da yaren Tamil (shima yana cikin yarukan ƙasar malaysia,
kuma Anam ta iya sosai, sai dai bata san shima Shareff yana jin yaren ba, duk da a
yanzu bazai iya magana mai tsaho da shi ba, sai dai komai ka faɗa zaiji zai kuma
baka ƙananun amsoshi). Ta ɗan saci kallonsa, sai kuma ta juya cike da basarwa tana
faɗin, “Good Morning”.
Maimakon amsawarsa tsaiwarsa taji a bayanta, taso ta dake, amma kusancinsu
yaƙi bata damar hakan. Sai ta kashe oven ɗin kawai ta juyo da nufin barin wajen,
komawa tai da sauri ta lafe jikin kitchen cabinet ɗin tana marmar da idanu, abubuwa
da yawa sai tsarga mata suke da ga tsakkiyar kai zuwa ƙafafu saboda tsaretan da yay
da idanunsa masu matuƙar kaifi da saka mata shakkarsa a lokuta da dama. Rashin
mafita ya sata sake cemasa “Good morning” a karo na biyu.
Kansa ya jinjina mata idonsa akan fuskarta da babu kwalliya. Yana matuƙar son
yaga mace da kwalliya, musamman jambaki, hakan yana ɗaya daga cikin abinda Fadwa ke
tasirantarwa a zuciyarsa. “Mi kikeyi anan?”.
Ya faɗa cikin dakewa idanunsa har yanzu na yawo a jikinta. Itama dakewar tai,
cikin ƙin nuna fargabar kusancin nasu da pretending ɗin daren jiya ta bashi amsa.
“Ina warming meat pie ne”.
Komai bai ceba, sai dai ya kai hannu zai cire meatpie ɗin daga cikin oven data
riga ta kashe, ƙwara uku ne kawai sai cinyar naman kaza ɗaya. Wani plate ɗin ya
ɗauka ya rufe sannan ya dubeta.
“Muje”.
Mamaki bayyane a kan fuskarta tace, “Yaya ina kuma?”.
“Inda ake saida mutane”.
Tasan baƙar magana ya gaya mata dan haka tai shiru. Har tayi gaba taji ya riƙota,
idanu ta rumtse wani abu na tsarga mata, ta juyo a hankali ta kallesa da idanunta
dake cikin glass, ganin ita yake kallo shima ɗin ya sata kauda kai bakinta a sama.
Jawota yay gaba ɗayanta ta faɗa jikinsa, tana yunƙurin ɗagawa ya saƙalo hanunsa a
ƙugunta ya maidata ya manne. Kusancin fuskarsu ya basu damar shaƙar numfashin juna.
Sosai ta ƙwaɓe fuska tana son janye jikinta amma yaƙi bata dama. Sai idanunsa dake
yawo a fuskarsa ne ke neman dagula mata lissafi.
“Yau ta zama ta ƙarshe da zaki sake tahowa bada izinina ba”.
Kallonsa tai, sai kuma ta janye idanun da sauri. Shima janyeta yay a jikin nasa ya
nuna mata hanya. Bata da zaɓin daya wuce bin umarninsa dan gaba ɗaya yaci dukkan
ƙudirinta da yaƙi a halin yanzun. Kwarjini da kamewarsa ta saka mata jin kasa masa
musu. Kusan a tare suke tafiya duk da yanda take takun a hankali duk dan ya
wuceta....

Sosai ta dinga ƙarema gadon kallo zuciyarta na bugawa da sauri-sauri. Ga wani


irin zafi da zogin da ƙirjinta yake mata. Jitai bazata iya ƙarasa abinda tai niyya
ba, tai saurin fita a ɗakin kanta na wani irin sara mata alamar ciwo. A falo ta
zube ta shiga ƙoƙarin saita kanta tun kafin waninsu ya shigo. Sai dai kuma har
tsahon mintunan data gaji da irgawa babu ko mai kamarsu, hakan ma ya ƙara sosa mata
rai, tana shirin miƙewa ta tafi sai gasu sun shigo kowane da sallama ciki-ciki. Da
ƙyar ta iya amsawa batare data kalli Anam ba.
Sai da duk suka zauna cikin son danne komai tacema Anam ɗin ina kwana. Anam da
tun shigowarta itama bata dubi sashin da take ba tai mata banza kamar bataji ba.
Haka dama Fadwa ke buƙata, dan haka tai murmushi tana satar kallon Shareff da yay
kamar hankalinsa baya kansu.
“Amarya nace an tashi lafiya?”.
Ɗago ido tai a karan farko ta kalleta ta watsar, sake maida hankalinta ga wayarta
dai-dai da ɗagowar Shareff ya dubi Anaam ɗin ransa a ɓace, sai dai kuma ya haɗiye
fushin nasa da kai hannu kan bluetooth ɗin dake manne a kunenta a zatonsa shine ya
hanata jin Fadwa ɗin kuma. Saurin dafe kunnen tayi da kallonsa dan tasan babu
abinda take saurare a ciki kawai dai bazata amsawa Fadwa ɗin bane. Ta zareshi gaba
ɗaya fuskarta da babu kwalliya na ƙara shagwaɓewa.
Hannunsa ya miƙa mata alamar ta bashi, amma sai ta maƙe kafaɗa, cikin muy-muy
da baki take faɗin, (Mazuran nan fa dai kowa ya iya ai, niba tsoro nake ba dan
kayi), A fili kam sai cewa tai, “Yaya miya faru?”.
Hararta ya ɗanyi da sake miƙa mata hanunsa. “Karna sake ganinki da wannan
abun a lokacin da muke tare baki ɗaya. Ana magana ko jin mutane baƙyayi. Bani
nace”.
A marairaice tace, “Nafa cire”.
Matsowar da yay idonsa tamkar zai faɗo saboda kallon da yake watsa mata mai kama da
harara ya sakata zabura tai ɗan baya kaɗan tare da tura bluetooth ɗin cikin rigarta
saboda hango murmushin da Fadwa tai na alamar cin nasara, sai kuma tunawa da yanda
yay mata da key jiya da dare ya sata ganin itama idan tai haka dole zai barta ai,
dan hanunsa dai tasan bazai shiga nan ya ɗauka ba.
Tsamm Fadwa ta miƙe ta nufi kicin ɗinsa ranta fes da ganin fushi a fuskarsa,
ta tabbatar Anaam ta cigaba da jaa akanta zai saukesa. Laɓewa tai tana leƙensu da
kasa kunne da ƙyau dan jin yaya za'a ƙare.
Cikin bada umarni da ƙara tsuke fuska ya sake miƙa mata hanu “Ciro ki bani da
arziƙi”.
“To ni Yaya dan ALLAH mi zakayi da shi? Badai na cireba shike nan, kuma ai
banji bane”.
“Dama ba lallai sai kinji ba ai, bani”.
Kanta tai niyyar ɗaukewa taji ya damƙo hannayenta, zabura tai tana waro idanunta
dake cikin gilashi gaba ɗaya waje saboda tsantsar firgicin jin ɗayan hanunsa cikin
rigarta yana laluben bluetooth ɗin data tura a bra....
Har taune harshe take wajen faɗin, “Yaya Please w...Wlhy zan baka, tsaya ka
tsay...”
Ko nuna alamar ya jita ma bai ba ya tura hanun nasa har cikin bra.. ɗin ya
ɗakko bluetooth ɗin. Zuwa sannan gaba ɗaya jinin Anam ya tsaya cak da daina
zagayawa tsabar firgita da abinda yay ɗin. Shiko ƙememe babu alamar kallon abinda
yay ɗin da girma tattare da shi. Saina hararta da yayi ya ɗauke kansa.
Fadwa dake yunƙurin fitowa tai mutuwar tsaye, dan jitai tamkar saukar aradu a
tsakkiyar kai, a zatonta yanda ya harzuƙa da farko mari zai saukewa Anaam akan
fuska. Jin hawaye na ciko mata ido tai yunƙurin komawa cikin kitchen ɗin
“K kuma ina zaki?”.
Ya faɗa dai-dai yana saka bluetooth ɗin cikin aljihun wandonsa idanunsa akanta.
Amsa ta bashi batare data yarda ta kallesa ba tana wucewa. “Ina zuwa nayi mantuwa
ne.
“Kin san dai yunwa nakeji”.
“Kayi haƙuri ina zuwa”.
Ta amsa masa hawaye na sakko mata. Da ƙyar ta iya kai kanta jikin kitchen cabinet
ɗin ta jingina saboda jin hajijiya na neman zubdata. Tasan shi din mutum ne kai
tsaye, amma batai zaton iya yin hakan a gabanta ba, koda yake ba'a gabanta bane
tunda ta tashi, maybe kuma baiga sanda ta fito ba shiyyasa. Da wannan ta bama kanta
ƙwarin gwiwar share hawayenta ta goge fuskarta ta sake fitowa.
Kofuna da plates data ɗakko ta ajiye tana magana cikin ɗan murmushin yake.
“Am sorry Soulmate, bismillah ku sakko”.
Harta kammala zuba Irish ɗin ma kowa Anaam da har yanzu mamakin Shareff ya
kasa barinta bata iya ta sakko ba. Sai da suka fara cin abincin ya ɗago ya harareta
sannan. Bataci dankalin ba, meatpie ɗinta ta ɗakko. Yi yay kamar bai ganta ba, sai
Fadwa ce tai magana cike da kulawa a gareta. Dan burinta bai wuce ta wanke zuciyar
Shareff akanta ba ya tabbatar ta amshi nasiharsa a gabansa, ta hakane kawai za'a
fara wasan da zataci nasara akan Anaam dake nuna ƙuru-ƙuru kishinta takeyi, ba kuma
zata iya ɓoye abu ba, tabbas hakan nasararta ce ta yaƙarta cikin sauƙi a wajen
mijinta. “A'a Amarya bara a haɗa miki tea ko, kamar zai fi ki haɗa da shi”.
Anaam data kalli kamar rainin wayon Fadwa ya fara yawa a kanta ta ɗago tana
mata kallon ido cikin ido. “Madam mind your business abeg. Shin dole ne sai kin
sakani a sabgarki ne wai?”.
Cikin sauƙaƙa murya da karyar da kai Fadwa tace, “Ayya I'm sorry dear
ban.....”
Ɗagowar Shareff dake hararar Anaam a fusace ta sakata haɗiye sauran maganar bata
ƙarasa ba. “Ashe zan fasa bakinki yay jini idan wata maganar banza ta sake fitowa a
cikinsa. Ya tana miki magana cikin lalama kina wani botsarewa dan walaƙanci!!”.
Tuni ta daina tauna meatpie ɗin, babu abinda zuciyarta keyi sai tafasa da
kumburowa cikin ƙirjinta, musamman da taga murmushin da Fadwa ta saki tana
kallonta. Hawayen takaici suka ciko mata idanu, tsam ta miƙe dai-dai Fadwa na
faɗin, “Lah babu damuwa wlhy Soulmate. Inaga bata fahimceni bane ba shiyyasa......”
Bata gama jin ƙarshen zancen ba tai ficewarta..........✍

*Tofa masu karatu da alama yanzu za'a fara wasan. Wadda ta iya allonta tsakanin
Amarya da Uwargida saita wanke.😉😆😝🚶🏻.*

_Ni dai anawa gaskiya daga Fadwa har Anaam kowanne salon nasa kishin akwai
*Dai-dai* akwai *Laifi*. kumuje zuwa domin fahimtar kuskurensu da dacewarsu gaba
ɗaya🤌🏻, dan a wannan gaɓar a zahirin rayuwarmu nake so muyi kallo da zamansu bawai
rayuwar littafi ba, kunga kenan wadda ta iya allonta itace star a wajenmu, duk da
dai a tsarin labarin muna yinsa ne akan *Anaam* gaskiya, domin itace kamar ke jan
zaren labarin, sai dai hakan bashi ke nufin ƙyawawan halayen Fadwa bazasu fito ba
ko kuskuren Anaam. Ina fatan zaku fahimceni dan naga wasu sun fara cewa a saki
Fadwa. 😌To bara kuji zama daram Fady babynmu ko yaji bazatayi ba garama ku shirya
kishi yanzu muka fara da ƴar mitsilarku😎🫣🥱🤪😂👌🏼._

_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_
*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_


*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:


07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇


09134848107

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*


[11/23, 10:16 PM] My Zafafa: *_Typing📲_*

*_BABU SO....!!_*
_(Miya kawo kishi?)_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718

*_45_*

.........Saukar hanunsa a wani sashe na jikinta ya sakata dawowa hayyacinta babu


shiri, ta damƙe hanunsa da fisgar kanta baya tana sauke numfashi da sauri-sauri
kamar yanda shima yake sauke nasan. Kunya tsoro da firgici suka zagaye zuciyarta a
lokaci guda. Jin abin take gin-girin-gin tamkar a mafarki, bargo taja da sauri ta
naɗe jikinta da juya masa baya amma sai ji tai ya riƙota, maidota yay jikinsa har
yanzu yana kokawa da numfashinsa da bai gama daidaita ba. So take tace wani abu
tsoro ya hanata, sai jujjuya masa kai take alamar ya barta.
“Ni ba'a juyamin baya yayin kwanciya”.
Ya faɗa cikin kunnenta da sake matseta a cikin jikinsa yanda bazata iya ko motsi
mai ƙyau ba. Bata da zaɓin daya wuce yin shiru, dan tasan babu wani yunƙurinta da
zaiyi tasiri tunda ruwa ba sa'an kwando bane. Sai dai kuma bata samu nutsuwar yin
barci ba har sai da taji shi yayi..

Rashin kwanciya da wuri baisa ta gagara tashi alokacin da sanyin asuba ya


busa cikin ƙofofin fatar jikinta ya kaima jininta saƙo ba. Ta buɗe idanu a hankali
tare da ƙoƙarin yin miƙa da tabbacin ta mance inda take. Rashin gani da ƙyau
sakamakon duhun ɗakin ya taimakawa zuciyarta harbawa da ƙarfi irin na razana. Da
sauri ta sauke hanunta kan abinda ƙwaƙwalwarta ta bata tabbacin mutum ne. Firgicin
lokaci guda ya hanata damar tunawa balle yin nazari tai zaburar data farkar da shi
daddaɗan barcin daya riskesa fiye dana farkon dare....
Cikin zafin nama ya maidata jikinsa ya matse tare da kai ɗayan hanunsa ga
makunnar fitila ya kunna. Tabbas badan hakan da yay ba babu abinda zai hanata
wantsalawa ƙasa sakamakon gab suke da gefen gado ashe.
“Relax!”
Ya faɗa cikin sarƙewar muryar wanda ya farka a barci, domin samar da nutsuwa daga
mutsu-mutsun data cigaba dayi har yana iya jin yanda zuciyarta ke harbawa da sauri-
sauri akan ƙirjinsa. Babu alamar zata nutsu ɗin, dan jin muryar tasa ma da alama
sake hargitsata yay a dalilin ganewa da tuna komai mai alaƙa da inda take. Sarai ya
fahimci yanzu ba tsoron bane, borin kunyane kawai tattare da ita, dan duk ƙoƙarin
da yake na son tama buɗe ido ta dubesa hakan ya gagara, sai faman san zame jikinta
take da nashi da kuma ƙoƙarin hana ƙirjinta sauka kan nasa ta hanyar tokare
tsakaninsu da hannayenta. Dariya sosai ta bashi, amma sai ya gimtse baiyiba ya
matsa kaɗan daga gareta. Damar data samu kenan ta wantsala gefe faɗuwar dai daya
gudar mata tun farko sai gata tayita, zafin daya ratsata ya sata sakin ƴar ƙara.
Yanzun kam bai iya daurewa ba sai da ya murmusa, batare da yace mata komai ba ya
tashi yay shigewarsa bayi har lokacin da murmushin akan fuskar tasa.
Sai da ta gama ƴan matse-matsen hawayenta sannan tai wuf ta miƙe jin kamar
alanar zai fito, key ɗin da idonta ya gani a gadon ta ɗauka ta nufi ƙofa da sauri
hijjab ɗinta a hannu da galashinta da shima ALLAH ya bata sa'ar gani. Fitowarsa
dai-dai da ficewarta a ɗakin.....

Bayan idar da salla tagumi ta zabga ranta fal takaicin abin kunyar daya faru
a ɗakin Yaya MM daren jiya, ta rintse idanunta dake cikin glass tana cije lips
kamar ta tariyo komai ta goge a rayuwa da zuciyarta ko zata samu sukuni. Tamkar
tana a gabansa ta murguɗa baki da miƙewa, tana naɗe sallayar tana mita cikin yaren
malay. “Idan kaga ma na sake kallon hanyar sashen can naka ba riƙeni na kwana ba
kace har abada bazan fitoba ma mana, ko kunya bayaji yana mazurai da zare ido amma
zuciyarsa saninta sai ALLAH. Toni an faɗa masa waccan shashashar matar tasa ce dake
hauka akansa, mtsoww! Tana wani fiffika ita mai miji kamar ance ana son mijin
natane balle ra'ayin zama da shi. Aikin ɓurr miye abin so jikin wannan mutumin mai
baƙin hali, sai dai ita ɗin dan dama duk jirgi ɗaya ya kwaso su mtsoww!!”. Haka ta
dinga mitar har takai kwance kan gado, kasancewar barci ne taf da idon nata cikin
ƙanƙanin lokaci yay awan gaba da ita tsiwa fal bakinta daya tashi sama kamar zai
taɓo p.o.p.

★★★

Kamar su, itama dai makarar tata bai hanata tashi yin salla akan lokaci ba,
koda ta idar kuma kasa komawa tai ta kwanta kamar yanda tai niyyar yi, sai ta ɓige
da kiran wayar aunty Malika dan a yanzu sune ke bata dukkan ƙwarin gwiwar da bata
samunta a gun kowa hatta mahaifiyarta data san suma suna a cikin tasu damuwarne
game da wannan auren *ƙaddara ko biyayyar* daya sami mijinta da rana tsaka. Cikin
muryar barci suka gaisa da aunty Malika...
“Fadwa badai kin saka shashanci a zuciyarki kin gagara barci ba? Yanzu saboda
abunda baida amfani kika zaɓi hana idanunki barci bayan mun gama miki da
matsalar?”.
“Aunty naso mantawa da komai tamkar yanda kuka faɗa sai dai na kasa. Wlhy na
tsaneta shima a yau naji na tsanesa. Tare fa suka kwana a sashensa da ita”. Ta ƙare
maganar da rushewa da kuka. Aunty Malika taja tsaki tana tashi zaune. “Lallai Fadwa
ke shashasha ce gaskiya, yo duk da nasan cewar baki girmi yarinyar nan ba sai dai
kuyi sa'anni kuma ita ɗin girman turaice ai banyi tunanin samunki haka muguwar
lusara ba. Har mi akai wai akai wannan tsefatar yarinyar da kaɗan tafi wada tsaho.
Fadwa kefa girman Nigeria ce, Nigeria ɗin ma Arewa, arewar ma kano kuma matsayin
ƙabilar hausawa. Tunda kika taso a gidanku bayan mahaifiyarki kin sameta tare da
wata matarne kafin ta fita tabar gidan, kinga kenan kinsan minene kishiya, kin san
ilimin zama da ita tunkan ki buɗe ido kiga wata da sunan kishiyarki. Idan har kika
cigaba da zubar da mutuncinki wajen zaman yin kuka ko bari Mijinki yaga lagonki to
lallai k baki cika jinin zuri'armu ba.....”
Cikin tarar numfashin aunty Malikan tace, “Aunty wlhy nayi dukkanin ƙoƙarina,
ban aikata wani abu saɓanin wanda kukace nayi ba”.
Ajiyar zuciya aunty Malika ta sauke. “Haka nake sonki ƴa tagari, ki zama
jaruma kuma jajirtacciya a gidanta bawai lusara ba. Kamar yanda na faɗa miki yanzu
ba'a bin boka ba'a bin malam akan kishi, kissa da kisisina da magungunan mata sune
takubban ƴaƙar kishiya musamman irin taki da babu abinda ta sani sai kauɗi da
buɗewar ido a cikin masu jajayen kunne. Kafin duniya ta goge mata idanu ta hango
abinda kikema sakaci ki jajirce ki ƙwaci mijinki da wannan damar inba hakaba dare
zaiyi miki, dare mai duhun tsiya da tafin hanunki ma sai kin gagara gani balle
hanyar ceton ranki. Dan haka yanzu ki tashi ki haɗa breakfast mai rai da lafiya
irin wanda baki taɓa masaba, kije ki shirya musu a sashen nasa kamar yanda ya
buƙata”.
Hawayenta ta share, duk da sam wannan shawarar batai mata daɗi ba amma zata
jure, dan ita shaidace taga alfanun danne zuciya a jiya, badan ta shanye komai ta
maidashi ba komai ba Shareff bazai ko dubeta ba akan abunda ta dinga masa tun daga
fara rikicin auren nan. Amma gaskiyar su aunty Malika namiji tamkar yaro yake, duk
kunnasan da kai da zarar ka lulluɓesa da kwalba sai kaifinsa ya zama mara tasiri ya
koma haska maka zuciya da hasken wutar daka kunna masan. Da layin barci da dauriya
ta shirya breakfast mai sauƙi kuma mai daɗi tamkar ba Fadwa mai babbake abinciba.
Maimakon ɗauka takai sai ta fara shiga wanka, tsaf ta shirya cikin doguwar rigar
lass ta caɓa ado tamkar ita ɗince amaryar, ta baje jikinta da kalolin turarren da
tasan yafi so da ƙauna sannan ta fice ɗauke da basket ɗin data haɗa komai cikin
yauƙinta da iya taku...
Fitowarsa da ga bedroom yayi dai-dai da shigowarta. Sanye yake shima cikin
ƙananun kaya masu taushi da rashin nauyi yanata bulbula ƙamshi. Ta sakar masa
murmushi da faɗin, “Good morning Soulmate”.
Idanunsa ya lumshe da jinjina mata kansa, laɓɓansa shima da ɗan murmushin.
“Morning dear! how are you?”.
“Alhmdullh” ta faɗa tana kauda kumburarrun idanunta da yakema kallon tuhuma,
tasan shi mutum ne mai saurin fahimta, amma zatai duk yanda zatai domin hanasa
hakan a wannan karon. Hanunsa ɗaya dake cikin aljihun wandonsa ya zare dai-dai yana
ƙarasowa gareta, ya amsa basket ɗin. Batai musun bashi ba. Cikin zolaya da cigaba
da kafeta da idanunsa dake tsumata ya kashe mata ido ɗaya.
“Ai da nasan haka zan dinga samun gatan nan a wajenki dana jima da ƙara aure
gaskiya”.
Har cikin ƙwaƙwalwar kai maganar nan ta soketa. Harta kasa ɓoyewa fuskarta ta
canja, amma sai tai ƙoƙarin saita kanta ta hanyar maida abun wasa ta hararesa da
juya baya kamar tayi fushin wasa. Basket ɗin ya ajiye ya rungumota ta baya yana
ɗaura habarsa akan kafaɗarta da murmushi bisa fuskarsa. “Juyawa Shareff ɗinki baya
yana nufin lalacewarsa matata. Amma da gaske wannan aure yamun ranar zama ɗan gatan
Fadwa”.
Ita shaidace bai iya ƙaryaba, ko tace baya ɓoye-ɓoye. Duk abinda ya fito a
bakinsa koda mai ɗaci ne shine iya gaskiyar dake zuciyarsa. Ta sani tayi kuskure a
baya na gazawar bashi kulawa, duk da taci matuƙar burin hakan a garesa kafin
aure......
Jan hanunta da yay ya katse mata tunani, ya zaunar da ita a kujera yana faɗin,
“Kinga jirani anan ina zuwa”. Kafin ta samu damar tuhumarsa harya fice. Ta bisa da
kallo zuciyarta na ƙuna har hawaye na ciko idanun nata. Duk da gargaɗinta da zuciya
keyi haka ta miƙe ta nufi bedroom ɗinsa wai ko zata samu sauƙin ranta idan bataga
alamar abinda take tsoro ba.....

★Da sallama ya shigo akan laɓɓansa idanunsa nabin ko'ina na falon da kallo,
yayinda ƙamshin dake tashi ke masa maraba da amsa sallamar tasa. Samun falon shiru
bai hanashi cigaba da kutsa kai ciki ba har zuwa bedroom ɗinta. Anan ɗin ma dai
tsaf, sai dai babu alamar tana a ciki. Ya ɗanyi jimm na tunani sannan ya fito,
falon ya dawo ya nufi hanyar kitchen...
Tsaye take ta juyama ƙofa baya tanata kici-kicin saita sabon oven da take son
ɗumama meat pie da take son yin breakfast da shi. Bluetooth ne a kunenta tana
sauraren sabuwar waƙar mawaƙin nata da wata ƙawarta ta tura mata daga can malaysia,
hargitsin bikin nan ya hanata zaman ji sai yau ta tuna da ita. Atamfa ce jikinta,
wadda akaima ɗinkin fitted gown da yabi jikinta ya kwanta luff da fidda surarta
matuƙa tamkar an zanata da pen, daga cinya zuwa ƙasa rigar ta buɗe matuƙa har tana
zan ƙasa daga can baya. Bata cika son irin kayan nan ba, amma gargaɗin Mamie da
nasiharta ana gobe za'a kawota ya sata daurewa ta tsara zata dinga sakawar insha
ALLAH koda ba kullum ba. Bata iya ɗaura ɗan kwali ba, dan haka a maimakonsa saita
kawo hula ta saka irin ta zamanin nan mai kama da ɗan kwalin. A jikinta taji tamkar
ana kallonta, gabanta ya faɗi ta juyo da sauri dan dama dauriya kawai take na
kasancewa ita kaɗai..........✍

_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_


*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:


07040727902
IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇
09134848107

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*


[11/23, 10:16 PM] My Zafafa: *_Typing📲_*

*_BABU SO....!!_*
_(Miya kawo kishi?)_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718

*_48_*

........Hannunsa daya ɗaga kamar zai mareta ya dunƙule, yanda ilahirin fuskarsa ta
canja kammani ya matuƙar girgiza zuciyar Anaam amma ta sake aro jarumatar dole ta
baibaye tata fuskar da zuciya da shi.
“Ita ƙaddarar data kawoki, ita zata dawwamar dake a cikin gidan sai dai ki
haɗiyi zuciya ki mutu! idan kuma k kin isa mara kunya ce ƙafarki ta taka ko gate
mugani stupid girl”.
Kafin ta samu damar cewa wani abu ya fice a ɗakin, hawaye ne suka cigaba da
rige-rigen sakkowa a kumatunta, zubewa tai a saman gadon ta rufe fuskarta da
tafukan hanunta. Taja tsahon mintuna tana kukan kafin kiran daya shigo wayarta ya
katse mata shi. Amrah ce, kamar bazata ɗauka ba sai kuma ta ɗaga takai kunne batare
da tayi magana ba. Daga can Amrah tamkar mai tsoron ajita ta fara faɗin, “Kina jina
Anaam?”. A taƙaice tace mata eh kawai.
“Ke kaɗai ce?”.
Cike da ƙosawa tace, “K dalla faɗi abinda zaki faɗa”.
“Mtsoww! K daɗina dake masifa. Ina yarinyar na ƙawar Fadwa da muka gansu ranar
da aka kai lefen Yaya Maheer?”.
“Amrah dan ALLAH ki barni wane shirmene wannan?”.
“K Please karki kashemin waya maganace mai muhimmanci wlhy. Ina dai kin ganeta”.
“Muje na gane, kamar Bibah suke kiranta”.
“Yes! Exactly ita fa. Kin san yanzu ana tsaka da rigima a gidan nan kin san
Mommyn su Yaya Shareff tana nan har yanzu tanata rikicin sai an raba aurenku, na
fito daga gida zanje zan shiga cikin gidan kawai naga Bibah ɗin tare da Gwaggo da
Maman Bibah a lungun mai shop ɗin nan, shine fa na lallaɓa naje kamar zan sayi abu
a shagon, ki duba WhatsApp ɗinki na turo miki voice recording ɗin dana musu dan
naga yanzu ma kin fini gane wani hausan”.
Kamar Anaam zata gwaleta sai kuma tace mata “Okay” a taƙaice ta yanke wayar.
Daga can Amrah bata damuba dan ta saba da halin Anaam tun suna yara, sai dai a
yanzu ma ta fahimci kamar a cikin damuwa take dan muryarta da alamar tayi kuka.
Taso share zancen Amrah ɗin amma sai yayta tsunkulin zuciyarta. Data ɗinta ta
buɗe tare da shiga in box ɗin Amrah ɗin. Maganar ya ɗanyi ƙasa sosai, da alama ba
gab take da su ba. Earpiece ta saka yanda zataji da ƙyau. Maman Bibah ce ta fara
magana cikin alamun ɓacin rai.
_“Amma ba haka kikai min alƙawari ba, kin tabbatar min idan shirinki na zubar
da cikin nan na Fadwa ya tabbata da Shareff ya dawo zakiyi duk yanda zaki ya aure
Bibah, sai kawai naji wai ga wadda ya aura, kin kuma ƙi saurareni tun ranar ɗaurin
auren nan, na kira ta waya Gwaggo da kinji muryata sai ki kashe”.
Da ɗan zafin rai Gwaggo ta amshe da faɗin, “Haba Luba, wace magana kikeyi
haka. Kina zaton zan faɗi abinda bazan cika bane, ai ni na fara miki tayin haɗa
Bibah da Mustapha saboda ganin dacewarsu, na kuma tabbatar miki kasancewar Fadwa a
gidan bazai hanata shiga ba duk da ƴar uwa take a gurinta itama. To amma su
Muhammadu sukai wannan sarƙa-sarƙar da kema kin san gwagwarmayar da aketayi na hana
faruwarta. Ba yin kammu bane, kuma bamu san sun ɗaura auren nan ba. Amma ki kwantar
da hankalinki, ni bana rama alkairi da sharri, Bibah kamar ta shiga gidan Mustapha
ne ta gama. Yanzu dai kuje gida zanyi duk yanda zan a satin nan na leƙi gidan naku
kinga wani zai iya ganinmu anan, kuma za'a iya zargin wani abu shiyyasa ma nace
kada ku ƙaraso gida mu haɗu anan”.
Mamaki, al'ajabi, ruɗani duk suka dirga a zuciyar Anaam lokaci guda, ba komai
ta fahinta a zancen ba, sai dai maganar zubar da cikin Fadwa da su Bibah suka bata
shawarar yi ta fahimci cewar Gwaggo ce ta sakasu su bama Fadwa shawaran kenan,
sannan Bibah ma son Shareff take kuma Gwaggo ta mata alƙawarin samunsa matsayin
miji duk da da wadda ta haifi mahaifin Fadwa, da maman Mommyn Shareff, da Kakar
Bibah wadda ta haifi Mamanta da Gwaggo uwarsu ɗaya ubansu ɗaya. Kai kai kai wannan
makirar tsohuwa da abin mamaki take, ta ƙyalƙyale da dariya dake tabbatar da ƙunar
zuciyarta a bayyane. Cikin bushewar zuciya da cin alwashi ta jinjina kanta.
“Yes bazan tafi ba, amma Yaya badan kurarinka ba, sai dan koyama matarka da
Mommy da aunty Halima hankali har da kai kanka a dalilin tsohuwar banza Gwaggo,
yanzu na ƙara fahimtar matar nan itace take ƙulla komai dake a family ɗin nan
tabbas. Zan tabbatar mata *Karen bana! Shike maganin zomon bana* kuwa..

Bayan sallar la'asar sai gasu Amrah, tayi farin ciki da zuwansu matuƙa,
musamman Ikram mai shegen surutu da bakinta baya shiru. Suka shiga buɗe kulolin
abinci dake a falon wanda ita bama tasan da su ba, sai dai kai tsaye ta gane Fadwa
ce ta kawosu tana ciki. Koda suka tambayeta ita ta dafa? Kai tsaye tace musu matar
gidan. Amrah dai kasa ɓoye mamakinta tai sai da tace, “Wai kina nufin Fadwa?”.
“Bayan ita akwai wata matar ne a gidan?”. Ta faɗa batare data kalli Amrah ɗin
ba. Harararta Amrah tai da faɗin, “Banza kefa idan kina kan dokin zuciya ba'a
maganar arziƙi dake”. Shiru Anaam ɗin tamata hankalinta na kan hotunan su Gwaggo da
Amrah ta dauka. Dukansu ta tura cikin wayarta, daga haka suka cigaba da hira.
An fara kiran sallar magrib Shareff ya shigo, fuskarsa murtik da alama har
yanzu ransa a ɓace yake. Ikram ta sheƙa da gudu garesa dama tun ɗazun take tambayar
yana ina Anaam ta mata shiru. Ɗaurewar fuskar ya ɗan sassauta yana shafa kan Amrah.
“Autah yaushe kuka zo?”.
Hanunsa cikin nata tana murmushi tace, “Yaya tun around Four. Inata tambayar aunty
Anaam kana ina? Taƙi amsani”.
Kallonsa ya kai ga Anaam ɗin, anyi sa'a itama ta ɗago nata idanun a lokacin.
Janyewa tai cikin salo tana ɗan taɓe baki, shima sai ya janye nasan yana ayyana
(Zanyi maganinki ne) a ransa. Gaishe sa su Amrah sukai, ya amsa musu yana ficewa da
basu umarnin tashi suyi salla. Bai dawo gidan ba sai da aka idar da sallar isha'i.
Kai tsaye nan ya zarto domin maida su Ikram gida. Anaam jitai kamar karsu tafi, tai
musu rakkiya har wajen motarsa, sai da taga ficewarsu sannan ta nufi komawa suka
kusa cin karo da Fadwa.
Kallon kallo sukema juna, Fadwa ta saki siririyar dariya tanama Anaam kallon
sama da ƙasa. “Amarya! Amarya! Ta ango baƙya laifi ko kin kashe ɗan masu gidaaa
hhhhh. Uhhm kamar haka ake kirarin ko?”. Tai maganar cikin sigar tambayar rainin
wayo ga Anaam dake kallonta ita dai. Dariya Fadwa ta sake kwashewa da shi “Oh sorry
amarya, ALLAH kina bani tausayi, dan ban taɓa gamo da amarya irinki ba ko'a
hikayoyin marubuta. Dama tsiyar auren cushe kenan fa”. Ta ƙarayin ƴar dariya da
matsowa gaban Anaam dake kallonta uwa ta samu tv ko bata fahimtar yaren da take
magana da shi. Cikin yin ƙasa- ƙasa da murya murmushi shimfiɗe a fiskarta ta cigaba
da faɗin, “Zan baki shawara ƙyauta dana tabbatar zatai miki amfani ƴar turawa,
karki bari ki zubar da ƙuruciyarki da lokutanki masu muhimmanci a inda ko kallonki
ba'a da bukatar yi, gara ki taimaki kanki, ki tattara komatsanki kibi tsoffinki ku
koma inda kuka fito koda baki gama serves ɗin ba, koda yake dama mun san bashi
akazo yiba neman miji akazo. Bokanku ya iya aiki tunda gashi kin samu ta hanyar
cushe, sai dai kuma akwai matsala mai yawa dan basu jehoki gurbin daya dace ba,
gara ki sani tun yanzu, wannan gidan sai ya zame miki tamkar kurkuku mafi muni da
ƙuntata a rayuwarki, kina da zaɓin taimakon kanki ko cigaba da zaman cin kwakwa,
AL-Mustapha Muhammad Shareff anyisa ne domin Fadwa Sadiq Dakata kawai”. Ta kare
maganar da ƙyafta mata ido.
A karon farko Anaam ta saki murmushi tana girgiza kai. “Hauka maganinka
ALLAH, ke kuma sanyin da wannan yanayin yazo miki. ALLAH ya ƙara afuwa”. Tai gaba
abinta.
“Ubanki ne mahaukaci ƴar iska”.
Anaam ta cigaba da tafiyarta tana dariya batare data waiwayita ba. A falo ta zube
maganganun Fadwa na dawo mata ɗai-ɗai cikin amsa kuwwa. Tabbas bata da burin yin
dogon zango a zaman gidan nan, sai dai ya zame mata dole zaman a yanzu kodan kawo
ƙarshen makircin Gwaggo, na biyu zata cika burin iyayenta akan zumincinsu da suketa
ƙoƙarin ganin sun toshe duk wata hanya da zata wargazashi. Na uku Fadwa, dolene ta
koyama Fadwa hankali ta kuma tabbatar mata sufa *Mata suna suka tara* lokaci shi
zai nuna *Zarah*. Na huɗu Mommy, na karshe Shareff, zata tabbatar masa da cewar ita
ɗin ba kanwar lasa bace, daga shi har matarsa sai ta goge musu hadda a cikin gidan
nan...
Ta saki murmushi a karon farko bayan ta kammala rubuta dukkan abinda ta gama
lissafawa a cikin wayarta sannan ta mike. A dai-dai nan ya shigo falon da sallama
ciki-ciki. Itama ciki-cikin ta amsa masa tana ƙara tsume fuska. Shima dai tasa
fuskar a tsuke take, ya ajiye ledar hanunsa yana kallonta tamkar mai harara. “Shi
wancan ɗakin da kika bari babu gyara waye zai gyara miki?”.
Shiru kamar bata jisa ba, ya sake dubanta a harzuƙe.
“Baki jini bane?!”.
Baki ta tura gaba, cikin magana ƙasa-ƙasa da tunanin bazaiji ba tace, “Matar
taka ta gyara maka mana”.
“Tunda ita ta kwanar miki a ɗakin ko”.
Kallonsa tai, dan batai zaton yaji ba, ta kauda idanunta da sauri ganin kallon da
yake mata. Ƙafa ta ɗaga da nufin barin masa falon cafka ɗaya ya fisgota ta dawo
gabansa. Marmar ta farayi da idanu da ƙyaƙyƙyaftasu, ta fara mutsu-mutsun ƙwacewa
ya murɗe hannun. Ƙaramar ƙara ta saki da ƙanƙame masa hannu ta fashe da kuka.
“ALLAH zai sakamin, kuma wlhy komi kamin sai na sanar da su Daddy...”
“Bakin ki bazai mutu ba kenan?”. Ya faɗa da ƙara matse hanun. Wata muguwar
wawura ta kaima hanunsa ta ƙallara masa cizo a ƙaramin yatsansa..........✍

_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_


*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:


07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇


09134848107

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*


[11/23, 10:16 PM] My Zafafa: *_Typing📲_*

*_BABU SO....!!_*
_(Miya kawo kishi?)_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718

*_47_*

..........“Wayyo kaga kasa tayi fushi da abincin fa Soulmate”.


“Ita ta sani”.
Ya faɗa cikin halin ko'in kula da cigaba da cin nasa. Fadwa zata cigaba da masa
magiyar ya bita itama ya balla mata hararar. “Malama idan zaki ci naki kici bana
son damuwa”. Shiru tai cikin kama baki kar kuma ƙaiƙayi ya koma kan masheƙiya. Har
suka kammala breakfast ɗin babu wanda ya sake magana a cikinsu, sai dai cikin
nishaɗi ta cigaba da cin nata a yanzu, amma a zahiri tayi kalar damuwa dan karya
ramfota.

★★★

Acan rijiyar zaki kam zaman lafiya yaƙi tabbata tsakanin Daddy da Mommy. Duk
yanda kowa ke tausarta cikin ƴan uwanta akan ta nutsu abi komai a hankali amma fir
ta nuna taƙi fahimta. Ita dai burinta kawai Shareff ya saki Anam. Babu kalar
tujarar da su Mamie basa gani daga gareta, sai dai babu mai nuna yama san tanayi su
dai fatansu zaman lafiya ga yarinyarsu. Babban abinda ke sake wutar tashin hankali
a zuciyar Mommy shine rashin zuwan Shareff gidan, dan kuwa Daddy ya haramta masa
sake zuwa gidan a yanzu har sai komai ya daidaita, kowa yasan yayi ne saboda Mommy
ɗin. Gwaggo kuwa tunda ta nunama Mommy cewar ta kwantar da hankalinta zata nemo
mafita, amma Mommyn ta murje idonta taima Gwaggo tas akan ita bata buƙatar wata
mafitarta sai Gwaggo ta koma gefe ta naɗe hannu tai shiru, tayi tamkar ma bata
gidan bata san borin da Mommy ɗin ke zubawa ba.
Ba bori da tujarar Mommy bace kawai ke wanzuwa a gidan, harda Gwaggo Halima
dake ganin ƴan uwan nata sunma ɗiyarta gudan jininta rashin adalcin raɓata kishi da
ɗiyar ɗan uba. Itama dai bata da burin daya wuce ta ɗakko Fadwa ta dawo gida har
sai Shareff ya saki Anaam sannan ta koma, sai dai baban Fadwa ɗin yay mata katanga
da hakan. Hasalima ya bata sharaɗin ko gate ɗin gidansa ta taɓa da nufin fita a
bakin aurenta da babu dawowa har abada. Dan shi mutum ne da dama baida wasa sam,
badan haka ba da ya jima da zama mijin hajiya a gidansa saboda azabar Gwaggo
Halima. Hatta da yaransa suna matuƙar shakkarsa, kuskuren da aka samu kawai shine
siyasa ta kwashe kaso mafi yawa na hankalinsa har takai a yanzu bai iya saka idanu
a kansu. Gwaggo Halima ta nutsu a gidanta cikin matuƙar tashin hankali da baƙin
ciki, tasan ko giyar wake tasha bazata taɓa gangancin rabuwa da uban ƴaƴanta ba,
domin yin hakan a gareta ba ƙaramin nakasu bane, shiyyasa ta nutsu a gida zuciyarta
na mata zafi da raɗaɗi musamman naƙin jin Fadwa har a waya dan Abbansu yayi seizing
wayar tata duk dan kar suyi waya, ya kuma hana har ƙanenta zuwa gidan Fadwan wannan
shine dalilin da yasa a ƴan gidan su babu kowa a kusa da ita sai su aunty Malika
dake matsayin ƙanne ga Abban nata.

Yau ma dai kamar kullum tun bayan kai Anaam gidan Shareff da tujarar Mommy
aka tashi gidan. Sai dai babu wanda ya kulata sai Gwaggo ce da tazo wuya ta fito
tai mata tatas a tsakar gidan saboda ita kam dai haukar Mommy ɗin ya fara kaita
maƙura. Tun Mommy na ƙoƙarin son nunama Gwaggo irin ɗaci da zafin da takeji a
zuciyarta har tayi shiru ta koma kuka...
“Gwaggo baki san irin zafin da nake ji bane a zuciyata wlhy, ji nake kamar na
tsinema Shareff na huta. Ni yaron nan zai wulaƙanta a idon duniya ya nuna ubansa ne
ya isa da shi bani ba!!”.
“Ai taimakonki yay, saboda yin biyayya ga mahaifin nasa ne ya janyowa
igiyoyin aurenki cigaba da wanzu har yanzu a gidan nan shi da Usman. Ban san mike
damun kankiba Nafisa, ina wayonki ina hankalinki ne? Kinbi kin ruɗa kanki akan ɗan
abu ƙanƙani da maganinsa ke'a hanunki cikin sauƙi.....”
“Gwaggo taya zakice cikin sauƙi? Da'a sauƙine Shareff zai kai iyanzu bai
saki yarinyar nan ba har zuciyata ta cigaba da ƙuna?”.
“Kinbi hanyar da bazai saketa ɗinneba ai. Idan kin shirya cin nasara akan ɗanki
sai ki nutsu ki dawo hayyacinki” ta ƙare maganar da miƙewa ta fice tabar Mommy da
binta da kallo cikin rashin fahimtar kalamanta........

_________________________________

Gaba ɗaya yau bashi da ra'ayin fita ko'ina, sai dai hakan bai hanashi yin
wasu ƴan ayyuka ba ta cikin system ɗinsa. Zuwa yanzu babu kowa a sashen nasa, itama
Fadwa tunda ta fita bata dawo ba. Shi kuma bai nema kowaccensu ba yanata harkokin
gabansa har akai kiran sallar zuhur. Shigarsa bedroom ɗinsa domin ɗauro alwala ya
sashi jan tsaki, dan yana nan a yanda suka tashi barci suka barshi. Har cikin rai
abin ya sosa masa zuciya, yana da mace har biyu a cikin gida amma sashensa ya
gagara samun shara. Ba yau ya saba ganin hakan ba, sai dai bazai yarda itama Anaam
ta zama haka ɗin ba tunda yaga Fadwa ta fara gyara nata halayen itakuma. Jiya itace
tai masa gyara, bazai yuwu kuma yau tayi ba bayan ba itace ta kwana a ɗakin ba.
Koda ya fito sai da ya leƙa sashin Fadwa dan tabbatar data tashi yin salla
kamar yanda musulinci ya koyar da duk magidanci na ƙwarai. Da mai-aikinta data dawo
ya fara cin karo a falo, ta zube har ƙasa tana gaidashi. Hannu kawai ya ɗaga mata
ya nufi bedroom ɗin Fadwa ɗin. Kwance ya sameta tana ramuwar barcin data hana kanta
yi daren jiya, ya ɗan kafeta da ido na wasu sakanni kafin ya tasheta. Ɗagowa tai da
ƙyar tana kallonsa cikin rufewar idon barci..
“Tashi kiyi salla sai ki koma ki kwanta”.
Da ƙyar ta iya amsa masa da to, yasan kaɗan daga aikinta yana fita ta koma, dan
haka ya cigaba da tsaiwa a kanta har sai da ta tashi ta shiga toilet sannan ya
fito. Sashen Anaam ya nufa, itama dai bai sameta a falo ba sai bedroom, saɓanin
Fadwa ita kwancen kawai take amma ba barci take ba. Taji shigowar tasa amma taƙi
ɗagowa ko sau ɗaya balle ta nuna tasan da wanzuwarsa. Tun a kallo ɗaya ya fahimci
ba barci take ba, sai dai idanunta sun nuna taci kuka duk da suna a rufe dan ta
cire glass ɗin.
“Ki tashi kiyi salla”.
Bata tanka masa ba, kuma bata motsaba ya juya yay ficewarsa. Idanunta ta buɗe ta
raka bayansa da harara tana laɓe baki. Sai da yaja kusan mintuna uku da fita sannan
ta tashi domin gabatar da sallar, a ranta tana addu'ar zuwan jininta a nan kusa.
Bayan ta idar da sallar saman sallayar ta cigaba da zama tana sharar
hawaye, buƙatar kasancewarta da iyayenta ce ke damunta. Abinda Shareff ɗin yay mata
ɗazun a dalilin makircin Fadwa har yanzu yana cizon mata rai. Ta san tun farko dama
ya tsaneta, taya bazai goya bayan matar son sa ba koda ace itace mai gaskiya. Itako
ta ɗauka alwashin baza'ai nisa ba balle har su sami galabar ƙuntata shi da matarsa,
a yau ɗin nan za'ayi mai yuwuwa ita ba shashasha bace...
Yawaitar ƙamshin turarensa a ɗakin ya tabbatar mata shigowarsa, amma sai tai
kamar bata jiba duk da taji sallamar da yayi ciki-ciki. Ta gabanta yazo ya gitta ya
zauna a bakin gado ta kusa da ita kaɗan, dan ƙafarsa ɗaya ma akan sallayar take.
Ido ya ɗan tsura mata na wasu sakanni, tayi kicin-kicin da fuska tamkar bata san da
shigowarsa ba...
“K kina ganin ba'a isa ace miki kinyi ba daidaiba kenan? To bari na faɗa miki
matata ba abin rainawarki bace, a baya kunyi abinda kuke so k da ita, amma a yanzu
bazan ɗauka raina juna daga kowaccenku ba. Dole ne duk mai buƙatar son zama lafiya
da ni ta zauna da ƴar uwarta lafiya a gidan nan kuma cikin girmamawa da daraja
juna!”.
Yanda yay maganar a kausashe ya sata jin zuciyarta a wuya, hawaye ne suka
shiga rige-rige sakko mata saman fuska, “Ni bance ina buƙatar zaman gidan ba ai,
balle naima wata ƴar iska biyayy.....”
Bummm ya buge mata baki da bayan hannu. Ba ƙaramin zafi ne ya ratsata ba, ta
dafe bakin tana kallonsa da idanunta da sukai jazur ta cikin glass, sai dai babu
hawaye yanzu a cikinsu sai tsantsar baƙin ciki da ƙunar zuciya. Ya miƙe tsaye yana
nunata da yatsa. “Idan kin isa mara kunya a gidan nan ki sake yima matata ko kallon
banza kiga yanda zanyi dake mara kunyar banza”
Hawayen da take riƙewa suka ɓalle mata, ganin zai fice bata amayar dana
cikintaba ta miƙe zumbur, “Idan na zauna kenan har za'ayi yadda za'ayin dani, inda
kun kwantar da hankalinku ni dama banzo wannan gidan naku da niyyar zama ba, matar
taka kuma wlhy tasa a ranta bashi taci, dan ni naci uwarta iya wasan data ɗau layin
muyi, dan bata kai matsayin mace ba a wajena. Itace jaka da har take tunanin mijin
nata wani abin a SO ne, ni baka cikin irin mazan dazan iya SO Yaya balle muradin
zama a shi gidan, ƙaddara ce ta kawoni nan badan rasa masoya ba. Zan kuma barsa a
yanzun nan bari na har abada, dan ALLAH kuyi kwaɗon juna ku cinye......”
A wani irin mugun fusace ya juyo gareta, dan har ya saka kafarsa ɗaya zai
fice a ɗakin batare daya kulata ba, sai dai kalamanta na ƙarshe-ƙarshe sun masa
saukar mashi ne a tsakkiyar ƙirji. Ko ɗar bataji da yanayin nasa ba dan itama
zuciyar tata irin tasance kuma a wuya take fiye da tasan. Kallonta yake da jajayen
idanunsa da suke neman wargaza duk wani ƙwarin gwiwar ta amma ta dake.........✍

_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_
*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_


*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:


07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇


09134848107

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*


[11/23, 10:16 PM] My Zafafa: *_Typing📲_*

*_BABU SO....!!_*
_(Miya kawo kishi?)_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718

*_49_*

.........Da sauri ya saketa yana yarfar da hanun, tako kwashe da dariya ga hawaye
sharɓan a fuskar. “Kaɗan ma ka gani indai nice Yaya”. Ta faɗa cikin riƙe ƙugu da
murguɗa baki.
Idanunsa da har sun kaɗa alamar cizon ya shigesa matuƙa ya ɗago yana kallonta
da kaiwa zaune cikin kujerar dake kusa da shi. Ƙoƙarin barin falon tai tana masa
gwalo, zamewa ƙafarta tai a dalilin turza carpet tai baya zata faɗi. Da ƙyar ta
samu nasarar dafe kujerar da yake zaune, samun rinjayen jikinta a nasa ya tilasta
mata zubewa kansa inba hakaba dole sai ta faɗin. Jikinta har rawa yake wajen son
yunkurawa ta tashi ya sake saka ƙafa ya taɗota ta koma. Ya saƙalo hanunsa ta saman
ƙugunta ta yanda bata isa sake ko yunƙurin tashin ba, fuskokin su gab suna shaƙar
numfashin juna. Idanunta dake cikin gilashi ta shiga ƙyafta masa zuciyarta na wani
irin bugu da sauri-sauri saboda bata taɓa tsintar kanta a cikin irin wannan halin
tare da namiji ba bayan shi, ta sake yunƙurin tashi gaba ɗaya dan kunya ta gama
dabaibaye rayuwarta bakinta cike da tsiwa tana motsashi sai dai bayajin abinda take
faɗa. Ƙafarsa yasa ya sake harɗeta da manneta da jikin nasa dai-dai lokacin da
Fadwa ke ƙoƙarin shigowa falon ɗauke da ƙaramin basket a hannu, cak numfashinta ya
tsaya, sallamar datai niyyar rangaɗawa ta maƙale a maƙoshi.
Idon Anaam yaga Fadwa sarai, dan haka ta dakata daga yunƙurin tashi da takeyi
duk da tsumar da jikinta ke mata, shiko da bai lura da Fadwan ba saboda baya ya
bata kaɗan sai ya kamo haɓar Anaam ɗin tare da sake matso da fuskar tasa gab da
tata. Ya ɗan ɗage girarsa ɗaya a sama yana kallonta cikin tsakkiyar ido.
“K bakin ki bazai taɓa mutuwa ba ko?”.
A salon da yay maganar ba ƙaramin tsargawar zuciya ya saka Anaam ba, sai dai
tai matuƙar daurewa wajen tura masa bakin nata sabida tunawa da Fadwa a wajen. Lips
ɗin ya ɗalla da ɗan yatsa, babu shiri taja kanta baya da ƙoƙarin dafe bakin ya hana
hakan ta hanyar buge hanun ya ɗaura nasa lips ɗin akan nata. A matuƙar bazata abin
ya zomata. Cikin tsumar jiki ta ƙanƙamesa zuciyarta na luguden daka a ƙirjinta
tamkar zata wantsalo dan wannan shine second kiss nata a tsayin rayuwarta duk da
kuwa ta kasance girman cikin jajayen fata. Ko saurayi irin na school ɗin nan Anaam
bata yarda tayi koda ance ana sonta, sai takai ma tsiwarta da rashin ragowa yasa
matasan samarin makarantar tasu na shakkar tararta da abinda ya shafi soyayya,
kaɗan daga aikinta ta maka tatas a gaban kowa ita ba ruwanta, hatta da ƙawa ɗaya
gareta itama dan hali yazo ɗayane shiyyasa suke shiri, dan itama fitinanniya ce ta
bugawa a bangon class. Hakama data shiga jami'a bata shiga sabgar kowanne namiji
duk nacinsa kuwa inba akan abinda ya shafi karatu bane ba.
Ta kowanne ƙofar jininta saƙonsa shiga yakeyi jikinta, ya kashe dukkan wani
sauran kuzarinta da yunƙurinta, sai da ya barta dan kansa ta samu damar kife kanta
a ƙirjinsa tsigar jikinta na tashi, shekara ashirin da uku ba shekara sha uku bace,
itama mutum ce tamkar kowa kuma lafiyayya dake samun ingantaccen abinci mai gina
jiki, ga kwanciyar hankali, giɓin rashin mahaɗinne kawai tattare da ita dama.
Samuwarsa gareta a halin yanzu kuwa tamkar motso mata dukkan abinda ke ɓoye a cikin
jininta ne ko tana so ko bata so.. Hannayensa duka biyu ya ɗaura a saman bayanta,
tare da kai bakinsa saitin kunenta murmushin dake ta ƙoƙarin son bayyana kansa a
fuskarsa na ƙoƙarin kufce masa.
“Daga yau da wannan zan dinga punishment ɗin bakin rashin kunyar tunda shi
idan aka faɗa sai ya maida”.
Janye kanta ta rinkayi dan yanda yake maganar a cikin kunenta da busa mata
numfashi sai yake neman sake hargitsa mata lissafinta. Nasarar janye jikinta ta
samu ta silale ƙasan kafafunta, shiko ko'a jikinsa, sai ma umarni daya bata cikin
kame murya.
“Malama tashi ki bani abinci, muje kuma ki gyara bedroom ɗin can yau
komin dare”.
A yanda take kai a kife cikin cinyoyinta ta gallaro masa harara da murguɗa
baki, sai da taja wasu sakanni sannan ta miƙe bisa shawarar zuciyarta, dakewar kuwa
tai itama, tai kicin-kicin da fuska ta kuma ƙi yarda tako kalla sashin da yake.
Bataga Fadwa ba yanzu, da alama tuni taba kafarta abinci. Haka kawai taji murmushi
ya suɓuce mata ta ɗan harari ƙofar tamkar har yanzu tana a wajen ne.
Fuskarta a gefe tace, “Nifa banda abinci anan”.
Ɗan dagowa yay daga latsa wayar da yake ya dubeta, sai kuma ya dubi ledar daya
shigo da shi ɗin wadda yasan sarai itama ta gani ɗin. Sake maida kansa yay ga wayar
batare da yace komai ba. Jitai kamar ta makesa dan duk tana kallonsa ta gefen ido,
batare da ta sake magana ba ta ɗauka ledar ta nufi kitchen tana kwaikwayon yanda
yay magana cikin bada umarni shi a dole mai kame girma bayan ya gama tsotse mata
baki.
Bayan wasu mintuna ta dawo da abinda ke cikin ledar cikin plate data juyo
sai ruwa da lemo da cup duk ta haɗo a saman tray. Ta ajiye a saman centre table
batare data yarda ko sau ɗaya ta kalla sashen da yake ba. ALLAH ya sota ma waya
yakeyi, takoyi wuff tabar wajen. Da kallo ya bita harta shige, ya ɗauke kansa da
ɗan furzar da numfashi yana cigaba da sauraren Fharhan....
★Gaba ɗaya brain ɗinta kusan daina neman yin aiki tayi, kukan da take sonyi
dan taji daɗi ma yaƙi fitowa ko ɗigo ɗaya. Tasa ƙafa ta hankaɗe basket ɗin abincin
data tafi da niyyar kaiwa Anaam ɗin saboda ganin Shareff ya shiga can, dan koda ya
dawo sashenta ya fara shiga ya kai mata ledarta, da tace masa ga abinci cewa yay ya
ƙoshi tunda bai daɗe da cin na rana ba. Taji haushi amma ta dake harya barota
fuskarta da murmushi, yana fita ta zabgama ƙofar harara da faɗin, “Munafuki” (Ƴan
uwana mata a kiyayi zagin miji koda a zuciya😕). Harta zauna zata buɗe ledar daya
kawo matan sai kuma ta mike, abincin data shirya domin shi ɗin ta tattara cikin
ƙaramin basket ta ɗauka da nufin zuwa ta kaima Anaam a gabansa, Cikin ranta har
tana saƙa abinda zai faru dan tayi shirin kunna Anaam ɗin ta yanda yau ko kwana a
ɗaki ɗayan ma sai ya gagaresu duk da tasan iya shi ɗinne zai faru a tsakaninsu
saboda ta yarda da su aunty Malika ɗari bisa ɗari. Amma maimakon hakan sai tai gamo
da abinda ya nema saka zuciyarta faɗowa ta baki, wai yau mijinta, abin sonta Al-
Mustapha ne rungume da yarinyar data tsana fiye da komai a rayuwarta yana kissing.
Ta rumtse ido da sauri komai na dawo mata tamkar a film, ƙara ta saki dayin cilli
da throw pillows ɗin dake a kujerar da take ƙasa, hawayen da take ta faman son zubo
mata na rige-rigen sakkowa a bala'in guje.....

★Rashin fitowarta har ya kammala wayar ya sashi kiran wayarta, tana zaune a
bakin gado abubuwa da yawa na mata kaikawo cikin zuciya da ƙwaƙwalwa. Batare da
sanin shi bane ta ɗaga kiran dan bata da wannan number tasa. Shiru batace komai ba,
jin anyi shiru daga can ma tai sallama muryarta a sanyaye dan da gaske ya rusa mata
dukkan ƙarfin jikinta da kuzari. Numfashi ya sauke a hankali, batare da amsa
sallamar tata ba.
“Idan kika bari na sameki a ɗakin nan komi ya faru kiyi kuka da kanki”.
Sarai ta gane shine, kafin ta samu damar cewa wani abu har ya yanke wayar, ta
dafe kanta dake sara mata kaɗan-kaɗan. Da gaske kunyarsa takeji, kunya irin wadda
bata taɓaji akan waninsa ba, abinda yake mata yakan zo a bazata gareta. Sanin
halinsa na cika magana idan ya faɗa ya sakata miƙewa ta fito. Kallo ɗaya tai masa
bata sake ba, shiko baima nuna yasan da fitowarta ba abincin sa yake ci hankali
kwance. Itama sai ta fice.
Da gaske bedroom ɗin yana a yanda suka tashi suka barsa, cikin taɓe baki da
hura hanci tace, “Uhhm kaima dai ƙazaminne ashe”. Haka ta fara gyarawa ranta fal
mita, bathroom dai koda ta shiga ta fahimci an wanke sa, amma hakan bai hanata sake
wankewa ba. Tana saka freshener ya shigo, ido suka haɗa tai saurin ɗauke kanta.
Shima baice komai ba ya nufi wadrob ɗinsa, ficewa tai dan Alhmdllhi ta gama.
Hankalinta kwance ta koma sashinta, da tunanin sun rabu kenan tunda ta masa aikin
sai yabi wani sarkin kuma. Ta tattare kayan da yaci abinci ta kai kitchen, ta fito
ta kashe komai na wuta ta nufi bedroom ɗinta. Duk da tanajin tsoron kwana ita ɗaya
hakan yafi mata sauƙi, insha ALLAH zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu zataima Mamie
magana a kawo mata mai tayata aiki ko motsinta takeji taji sauƙi. Ranta fal farin
cikin babu mai takura mata yau take saka kayan barci. Da sauri ta haɗe ƴar saman
kayan barcin nata da bata kai ga ɗaure igiyarba tana waro idanu na mamakin ganinsa,
shima janye idanunsa da suka riga suka gama kalle abinda take rufewar yay cike da
basarwa. Maƙoshinsa da yay bushewar wucin gadi ya kai hannu ya shafa yana kaiwa
zaune a bakin gadon..
“Bani ruwa mara sanyi”.
Ya faɗa murya a shaƙe.
A hankali ta saki numfashin data riƙe, tamkar jiran umarnin take dama tai wuf ta
fice. Jikin ƙofar ta jingina tana sauke nannuyan numfashi idonta a rufe, sai kuma
ta buɗe tana ƙarema kanta kallo, a cikin zuciyarta kam kanta take bama ƙwarin gwiwa
na baiga komaiba. Ta ɗan buɗe Jacket ɗin tana kallon ƙirjinta da kusan rabi ke
bayyane ta sama, dan ƴar rigar cikin ƙarama ce sosai, babu bra kuma a jikinta,
hakama wandon iyakarsa rabin cinyarta, sai ya zam saka iya su tamkar mutum baida
maraba da zigidir. Ta samance har kusan ƙasa mai santsi da kauri. fuska ta ɗan
marairaice da haɗa yatsun hanunta biyu tana jujjuyawa a saitin fuskarta dake a
ƙwaɓe kamar zata saki kuka. “Wayyo ni Mamie idan ya gani ya gama dani”. Sai kuma
ciki girgiza kan cikin bama kanta ƙwarin gwiwa tace, “Insha ALLAH bai gani ba. Yes
bai gani ba”. Ta kara maimaitawa cikin tabbatarma kanta. Sai dai kuma zuciyarta
taƙi gamsuwa.........✍

🤭Idan ma ya gani ba sadakinsa bane, kujimin ƴar iya😝🚶🏻.

_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_


*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:


07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇


09134848107

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*


[11/23, 10:16 PM] My Zafafa: *_Typing📲_*

*_BABU SO....!!_*
_(Miya kawo kishi?)_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*
https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718

*_50_*

..........Tasirin maganganun Gwaggo ya hanata sukuni, ta kasa zaune ta kasa tsaye


ta kuma gagara basu fassarar data dace. Gwaggo dai uwa ce a gareta, domin
mahaifiyarta haihuwarta kawai tai da shayar da ita. Dan tun daga yaye da Gwaggo ta
ɗakkota bata sake waiwayen gidan mahaifinta ba sai da yawo. Ita ɗin tarbiyyar
Gwaggo ce kuma rainonta. Ta samu gata irin wanda alƙalami bazai iya zanawa ba a
takkada da ga gareta, domin kuwa a zamanin ƙuruciyarta kosu Muhammad (Daddy) dake
ƴaƴan MB Shareff na cikinsa basu kaita jin daɗi ba a hanunsa. Gwaggo wata irin
mutum ce da gane zuciyarta sai ALLAH, hakan yasa har Umma Hajarah tabar duniya bata
taɓa hankaltuwa da wacece Gwaggo ba. Ba Umma Hajarah ba hatta su Daddy a yanzu basu
fahimci kaso talatin cikin ɗari ɗin halayen Gwaggo ba sam, duk wannan faɗi tashin
nasu akan zumincin da suke tada jijiyar wuyan ganin bai salwance ba. Tai gajeren
murmushi da sauke ajiyar numfashi mai nauyi, dan tabbas mafitar data kasa nutsuwa
ta samo akan wannan auren da bazata taɓa yarda da tabbatuwarsa ba tana wajen
Gwaggo. A ganinta miya rage? Kawai ta kwantar da hankalin nata bisa shawarar
tsohuwar ta kuma bita daki-daki domin cimma nasara. Sai dai a sanin datai mata kota
tunkareta a yanzu bazata samu abinda take buƙataba dan haka zata barta har zuwa
safiyar gobe idan ALLAH ya kaimu......

★Jin kamar motsinsa yasa ta bar wajen da sauri, ruwan ta ɗakko ranta duk a
dagule na rashin ƙwaƙwaran hujjar ya ganta ko bai ganta ba. Sai dai wani gefe na
zuciyarta na ƙarfafata akan ta dake ta fuske kawai, (haba sai kace ba Anaam ba!
karki bada mata mana). Da wannan kurarin ta dake ta koma bedroom ɗin, inda ta barsa
nan ta samesa, sai dai yanzu ya warware lap-top ɗinsa a saman stool ɗin mirror daya
jawo gabansa alamar aiki zaiyi. Ganin yana ɗan kusa da side drawer na gado saita
ɗaura anan, sai faman riƙe rigar take da hannu ɗaya duk da a yanzu ba'a ganin komai
jacket ɗin ta rufe ruf. Duk yanda taso zuciyarta nutsuwa ta gagara, ta ɗan saci
kallonsa, hankalinsa gaba ɗaya yana ga aikin da yakeyi, hasken screen ɗin laptop
ɗin ta haske fuskarsa. Gani tai ya ƙara mata wani ƙyau da kwarjini, ta haɗiyi yawu
da ƙyaƙyƙyafta idanu domin abinda take son faɗa mai nauyi ne, sai dai gaskiya
bazata iya jurewa ba gara dai ta tabbatar.
Murya a noƙe tace, “Yaya MM!”.
“Uhhyim”
Ya amsa mata batare da ya bar abinda yake ba. Sai da ta sake juya maganar a ranta
kafin ta furta kamar zatai kuka.
“Dan ALLAH in tambayeka zaka gayamin gaskiya?”.
Karon farko ya ɗago ido ya ɗan kalleta, tai saurin sauke nata idanun ƙasa. Idanun
nasa ya sake maidawa ga aikinsa. Harta fidda rai da amsawar tasa ma.
“Malama kiyi maganarki kai tsaye”.
Baki ta tura gaba da ɗan murguɗawa kaɗan harda masa ƙaramar harara, zuciyarta sai
ƙwaɓarta take amma wata na ingizata kuma. Cikin in ina da tsantseni ta cigaba da
magana. “Dan ALLAH ɗa..zun da ka shi...go k...a...ga..n..ni k..o?”. Ta ƙare maganar
kamar zatai kuka.
Cak ya tsaya da ga danna keyboard ɗin laptop da yake yi, ya ɗago idanunsa da
suka canja launinsu tun ɗazun ya kalleta. ɗan ƙara tsuke fuska yay tamkar abinda
take maganar a kai bashi ke neman hanasa sukuni ba, murya a dake ya bata amsa kai
tsaye...
“Kina min talla na ƙara gani ne?”.
Babu shiri ta ɗago da sauri, sai ko idanunta cikin nasa. Ta zabura baya tana zagaya
hanunta ta saman kanta “God forbid! Sai kace wata ƴar iska?. Kuma nidai ALLAH ya
gani ai tambayarka nayi, dan zuciyata ta kasa nutsuwa nasan ka iya fuskewa da
mazuranka bayan kuma k..k..k.....” ta kasa ƙarasawa saboda kallon da yake jifanta
da shi mai matuƙar yawan aji-aji na fassara.
“Ni dai naji, shike nan sai da safe. Dan ALLAH a dinga knocking idan za'a
shigo”. Ta ƙare maganar da zagayawa bayansa da hayewa gado tana murguɗa baki. Zaune
ta tashi da sauri, muryarta na rawa kamar zatai kuka, “Ni Juwairiyya, nifa kamarma
cakai ina maka talla ka ƙara gani!, kenan ka gani ɗin fa? Wayyo Mamie na, ki
roƙamin gafarar ALLAH Yaya ya fara komaw......”
Muƙut ta haɗiye zancen ganin ya hawo gadon, ta zabura zata wulƙita ƙasa ya
damƙota. Gaba ɗaya idanunta sukai wiƙi-wiƙi tamkar an kama tsohon kwarto a ɗakin
surukarsa. Duka hannayenta ya maida baya ya riƙe da hannu ɗaya, ta shiga girgiza
masa kai cikin magiya da roƙo muryarta na rawa tabbacin kuka na gab da zuwa.
Ƙafafunta da take turzawa ya sa ƙafarsa ya danne, ya kai ɗayan hanunsa kan igiyar
rigar tata, ja ɗaya yay mata ta warware dama ɗaurin zarge tai mata. Rigar ta buɗe,
ƙara ta fasa masa, babu shiri ya kai hannu ya rufe bakin. Muƙutt ta haɗiye abinda
ya rage bai fito a bakin nata ba, idanunsa da suka ƙara canja launi ya watsa mata,
“Ba haka kike so ba na buɗe na gani”.
“ALLAH ya kiyaye wlhy”. Ta faɗa da sauri tana son motsa jikinta ko yaya amma
yayi mata riƙo na gaske.
“Idan wannan bakin naki ya sake cewa (tak!) saina yage ɗayar ma silly girl”. Ya
ƙare maganar hannunsa na sauka saman wuyan rigar da gaba ɗaya ya bayyana ƙirjinta
saboda girmansa, rabin jikin nata ma duk a waje suke gashi ta kamata tsam
kasancewar roba ce sannan copy lass mara nauyi.
Fashewa tai da kuka na tsananin borin kunyar daya jefa rayuwarta a ciki, dan
ita harga ALLAH bada tunanin komai tai tambayar ba. Sai da ya tabbatar ya firgita
ta sannan ya saketa, wani irin kwakusa ta kaima duvet ta ƙudundune har kanta...
Ƙara danne abinda ke hargitso masa brain yay da ƙyar ya koma ya zauna.
Robar ruwan data kawo masa ya ɗauka, batare da yabi takan kofin ba ya ɓalle murfin
ya dasa a baki. Tass ya shanye ruwan yay wurgi da robar yana rumtse idonsa da
jijjiga kai tamkar mai girgije ruwan cikin suma. Ture stool ɗin da laptol ɗinsa ke
kai yayi yana jan wani bahagon tsaki, toilet ya nufa cikin sassarfa kai kace
ingizashi ake da remote.
Anaam da bata san yanai ba na maƙure cikin bargo tayi luff takaicin kanta da
kanta ya gama dabaibayeta. Ji take tamkar ta ciji kanta dan haushi. A gaba ɗaya
abinda ya faru sai yanzu take iya lissafa rashin wayonta, mima ya kaita masa
tambayar? Ta cije lip da ƙarfi tana kaiwa gado mugun mintsini tamkar shine ya mata
laifin.. Jin shirun ɗakin yayi yawa ta ɗan leƙo kanta kaɗan, wayam babu shi a
ɗakin, jitai wani farin ciki ya ratsata, ta miƙe da sauri ta dire a gadon, ƙofa
taje ta sakama key duk a tunaninta fita yay a ɗakin. Ranta fess ta juyo tana
karkaɗa keys ɗin da faɗin, “ALLAH na gode maka daya fita azababbe, sai iya fassara
mutum akan abinda ba haka yake ba, kuma ban yafe ba ganinmun jiki da akai da
way......”
Numfashinta ya tafi zuuu ta haɗiyeshi tare da yawu, da ƙyar ta iya ɗago ido
kaɗan ta kalla abinda taci karo da shi. Shine ɗin dai ba wani ba, zirr! Zirrr!
Zirrr!! Haka jininta ke gudu a cikin jijiyoyinta yana kaima zuciyarta da ƙwaƙwalwa
rikitattun saƙwanni masu tabbatar da firgicin mutum a cikin idanu. Miya rage? Kawai
ta kwasa da gudu tabar ɗakin nan. Zuciyarta ta ayyana mata cikin ƙarfafawa domin ta
tabbatar babu makawa yaji abinda take faɗa ɗin.
Hannu ya miƙa masa alamar ta bashi keys ɗin. Cikin langaɓe kai da girgiza shi,
hannunta ɗaya na tattare da rigarta da taketa faman kare ƙirji. “ALLAH bafa da kai
nake ba, kayi haƙuri zan maka bayani yanda zaka fahimta...”
“Nazo na amsa da kaina kenan?”.
“A'a wlhy, ni dai ba sai kazo ba, daga nan ma zan maka bayani”.
Yunƙurin matsota yay, da sauri ta jefa masa keys ɗin ya cafe. Cikin aljihun
wandonsa ya zurasu da nuna mata gado. “Wuce ki kwanta”.
Hankali tashe ta buɗe baki zatai magana....
“Idan kika furta (A) sai na miki fata-fata a ɗakin nan. Idan kuma kinji ƙarya
bismillah”.
Summ summ ta wuce hankalinta a matuƙar tashe. Ya raka bayanta da wani shegen
kallo tamkar idanun nasa zasu wantsalo waje........✍
_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_


*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:


07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇


09134848107

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*


[11/23, 10:16 PM] My Zafafa: *_Typing📲_*

*_BABU SO....!!_*
_(Miya kawo kishi?)_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718

*_52_*
..........Sake maido da ita yayi da riƙo fuskarta cikin hanunsa da ɗage gira sama.
“Faɗi abinda ke ranki mana yarinya. Koba angon bane?”.
“Kaima kasan bashi ɗin bane ba, dan auren wata uku ne, kamar yau ne zai
ƙare”.
“Oh really?”.
Cike da confidence ta bashi amsa. “Ka rubuta ka ajiye”.
Wani ƙayataccen murmushi daya nema sumar da ita ya saki, yaja hancinta da
kashe mata ido ɗaya har sannan murmushin bai bar fuskarsa ba. “Kin tabbatar zaki
iya?”.
Da ƙyar ta iya jawo yawu mai kauri ta jiƙa bushashshen maƙoshinta tana
ƙyaƙyƙyafta ido. “Babu tantama a alwashina Yaya MM”.
Juyata yay suka koma tsakkiyar gadon, ta koma ƙasa shi kuma ya dawo
samanta. ƙara ta saki da ƙoƙarin son turesa sai dai ko gezau, ta fara jan numfashi
da fesarwa da ƙyar dan gaba ɗaya ya sakar mata nauyinsa dan mugunta. Ɗan ɗagata yay
sai dai ba duka ba, ya kalla cikin tsakkiyar idanunta da har sun canja launin
farinsu zuwa ja harda tara ƴan ƙwalla. Murmushi ya kuma saki da shafa lips ɗinta
kaɗan da yatsun hanunsa. Ya ɗan kashe mata ido ɗaya da kai bakinsa saitin kunenta
ya fara magana kamar mai raɗan. “Wannan bakin naki ne zai kaiki ya baroki yarinya.
Idan kikace zaki buga game ɗin nan dani zubar hawaye bata shirya barin idaniyarkiba
kenan....”
Janye fuskarta tayi saboda wani zirrr da takeji a cikin jikinta. Cike da tsiwa
da son hana ganin lagonta ta sake maido fuskar “Never for ever, ka rubuta ka ajiye
Yaya nanda wata uku zamu koma gaban Baba Ibrahim da kai ka bani sakina, dan ni da
kai bazamu taɓa son juna ba, kaima kasan da haka ai”. Itama ta ƙare maganar da
salon kashe masa idanu daya nema ɗauke masa numfashi.
Jin zata zille yay azamar tareta da hannunsa, gaba ɗaya annurin fuskarsa ya
gushe, cikin ɗan kausasa harshe da zuba mata idanunsa da launinsu ya canja
tsakkiyar nata ya fara magana. “Kuma dole ki zauna da ni yarinya, zan kuma tabbatar
miki da hakan ki rubuta ki ajiye”.
Alwashin nasa ya matuƙar tsaya mata a rai, amma sai ta basar cike da
rainin wayo ta saki siririyar dariyar data saka tsigar jikinsa tashi. “Yaya MM kana
wasa da wannan Anaam ɗin, amma dai muje zuwa, hausawa kance ba'a san maci tuwo ba
sai miya ta ƙare, nanda cikar wata uku zan tuna maka wannan”.
“Ni kuma kafin cikar wata ukun zan maimaita miki”. Ya faɗa yana janye jikinsa
a nata ya sauka a gadon baki ɗaya. Harara ta dallama bayansa zuciyarta na bugawa da
sauri-sauri, harda sakin ɓoyayyar ajiyar zuciya. Ita kanta ta yabama kanta da
kanta, dan tasan ba ƙaramin dauriya taiba na riƙe tsoronta. Sai da taga ya fice a
ɗakin gaba ɗaya ta dafe ƙirji da rumtse ido. Sai kuma ta buɗe da ɗan mangarin
kanta. “Stupid girl! Anaam kina da hankali kuwa?. Wayyo ni ALLAH miya kaini yin
waɗan nan cika bakin yanzu idan yaƙi sakin fa?” (Sai ki kaisa kotu) zuciyarya ta
bata amsa kai tsaye. (Ya zakiyi da su Abie kuma?) wani gefen ya tambayeta. “Shike
nan na mutu” ta faɗa a fili tana sake dafe kanta. Ganin zata zarar da kanta sai ta
miƙe cikin murguɗa baki da faɗin, “Koma miye bazan yarda yaci galaba a kaina ba.
Kafinma wata uku nayi gaba abina”.

🤣To bara muga yaya wasan zai kaya ƴar mitsila😝.

★★★

Duk yanda taso danne zuciyarta yau ta musu breakfast kasawa tai, koda maman Abu
kuma tace zatayi saita hanata. Kallo ɗaya zakai mata ka fahimci taci kuka sosai dan
idanunta har sun nuna. Tun tana kallon agogo da tsumayen shigowar Shareff harta
daina zuciyarta na cigaba da mata zafi da raɗaɗi. Da alama ya fita ko sallama bai
mataba kenan dan yanzu dai lokacin zuwa office ya gota matuƙa, ta kuma tabbatar
bazai zauna har zuwa yanzun bai fitaba dan bai haɗa aikinsa da komai ba. Zuwa yanzu
ta yarda kuka rahama ne, dan jiya tayi kuma taji sauƙi da sassaucin zuciyarta. Amma
yanzu ya gagara fita ko kaɗanne balle taji sauƙi. Wani irin tsanarsa da haushinsa
takeji mara misaltuwa, zuciyarta kuma ta kasa tsayawa waje guda da tunanin abu
biyu. Shin maganin su Aunty Malika ne baiyi aiki a kansa ba? Kokuwa dai asirin dasu
Gwaggo suka jima suna faɗa iyayen yarinyar nan nayine yafi nasu ƙarfi. Kanta ya
kulle, ta rasa ina zata kama. Zafafan hawayen da taketa son fitarsu suka sami damar
silalowa saman kumatunta masu matuƙar zafi, daga haka kuka mai cin rai ya kufce
mata har ya shigo bata sani ba.. Ƙamshin turarensa dake ƙara yawaita a ɗakin da
hancintane ya sakata ɗagowa kaɗan ta dubi ƙofar. Tsaye yake cikin ƙananun kaya masu
taushi da sukai matuƙar fidda ƙuruciyarsa ta matashin namiji alamar yau bai fita
ko'ina ba kamar yanda tai hasashe. Wani irin damm zuciyarta ta bada sauti a cikin
ƙirjinta, abinda zai hana Shareff fita office kam lallai ba ƙarami bane, hawaye ne
suka sake ziraro mata, ta sake ɗago ido ta kallesa har yanzu yana a ƙofar tsaye
hannayensa duka a cikin aljihun wandonsa idanunsa a kanta tamkar ya samu
television. Sakkowa tai a gadon da gudu taje ta rungumesa. Murmushi ya saki mai
faɗi, tare da zare hannayensa daga cikin aljihu shima ya rungumeta. Ta saki ajiyar
zuciya da sake kanƙamesa. Kusan mintuna uku suna a haka tsaye kafin ya ɗagota,
fuskarta ya rike a tafukan hannayensa yana raba idanu akan hawayenta, ya girgiza
mata kansa yana binta da wani kallon ƙasa-ƙasa.
“Kukan bai isaba?”.
Ya faɗa idanunsa cikin nata.
Kasa jure kallon nasa tai dan tamkar yana zuba mata wasu maganaɗisune masu wahalar
ja'inja. Tai ƙoƙarin maida idanun nata ƙasa amma ya hana hakan ta hanyar ɗora lips
nashi kan nata. A tare suka lumshe ido. light kiss ya sakar mata. Taja numfashi da
ƙyar da ajiyar zuciya mai ƙarfi.
Murmushi ya saki da kai goshinsa saman nata ya haɗe, “Kin huce ko?”.
Baki ta tura masa zata kautar da kan nata ya hana hakan. Dole ta haƙura ta tsaya
tanata sauke ajiyar zuciya a jere. Sai da ya tabbatar ta nutsu sannan ya saketa
suka koma bakin gado. tissue ya miƙa mata, babu musu ta amsa ta share hawayenta.
“Kin tashi lafiya?”.
“Alhmdllh”.
Ta faɗa a taƙaice. Shiru ɗakin ya ɗauka kamar wasu baƙin juna. Taso ta danne komai
kamar yanda taga ya basar, sai dai bazata iyaba. Ta ɗan dubesa muryarta na rawa.
“Yau bazakaje office ba ne?”.
Bai iya ɓoye magana ba ko kwana-kwana, dan haka kai tsaye ya bata amsa da
“Haba dai Madam, ango a office ai a koro ni. Ko ke ɗin nan ai baƙya so ganina a can
ba ko. Ina hutu ne sai monday insha ALLAH”.
Ido ta tsura masa ko ƙyaftawa babu, “Sati ɗaya fa kenan?”.
“Kinga sun ragemin mudu ba kamar lokacin naki amarcinba ko? Nima dai inajin
kamar zanyi bore na ƙara wani satin akan wannan na more angwancina da kyau, amma
bani shawara kar ace na cika son bati”.
Da yasan yanda zancensa ke ƙona zuciyarta da bai cigaba da yinsa ba. Ta
janye idanunta dake cikowa da ƙwalla a kansa tana jan numfashi da haɗiye abinda ya
tokare maƙoshinta da ƙyar.
“Babie kinyi shiru?”.
Kanta ta girgiza masa hawaye na sakkowa a kumatunta. Ta miƙe batare data bari ya
gani ba, toilet ta nufa tana faɗin, “Wannan ai maganar amarya ce ba tawaba ita ya
kamata ka samu kaga ko wata guda saiku je a ƙara muku”.
Ƙofar toilet ɗin data bugo da ɗan ƙarfi ya tsurama ido, zuciyarsa na jujjuya
maganar tata da son bata fassara. Ganin zai takura kansa akan son fahinta sai kawai
ya ɗage kafaɗu da ɗan taɓe bakinsa. Shiru-shiru taƙi fitowa har kusan mintuna
biyar, ya kalla agogon dake ɗaure a hanunsa tare da kai dubansa ga ƙofar toilet ɗin
da mamaki. “Wai nikam mi kike a toilet ɗin nan haka kizo ki bamu breakfast”.
Shiru babu alamar zata amsa masa balle fitowar tata. Ya sake maimaita maganar
sai dai anan ɗin ma babu alamar motsinta. Miƙewa yay zuwa ga ƙofar cikin ɗan
tunzura ya bubbuga. “Wai kina jina inata magana kikai min banza?”.
Nan ma yitai kamar zata sharesa sai kuma ta buɗe, ganinta ɗaure da toilet
ya sashi faɗin, “Wai dan walaƙanci dama wanka kika shiga kika barni anan?”.
“Toni ai ban san zaka tsaya jirana bane kayi haƙuri”.
Ta faɗa cikin son yanƙwala shi tana nufar mirror. Da kallo ya bita kawai. Sai kuma
ta ɗan juyo ta kallesa. “Kana buƙatar wani abu ne?”.
Bai tanka mata ba, bai kuma janye idanunsa akanta ba, sai dai haka kawai
zuciyarsa ta sosu da yanda take masan. Idanunsa ya ɗauke kawai da nufar ƙofa ya
fice abinsa... Ta raka bayansa da harara cikin taɓe baki.

Shawarar fita neman abinci ya yanke a ransa, sai dai kuma wata zuciya ta
ƙwaɓesa dayin hakan dan ba mutuncinsa bane yana da mata har biyu ace yana fita
yawon gidajen abinci siyowa. Sai dai kuma ko yunwa zata hakalashi yayi alƙawarin a
yanzu dai bazaici abincin na Fadwa ba. Sashensa ya koma, ya zube a kujera hanunsa
dafe da kansa. Kusan mintuna uku ya samu zaune shiru, sai da ya tabbatar zuciyarsa
ta ɗan nutsu sannan ya ɗauka waya yay kiran Anaam.
Kammala wankin toilet ɗinta kenan kiran nasa ya shigo mata. Batai saving
number ɗin ba duk da ranar ya kirata da ita. Tai ɗan jimm kafin ta ɗaga da tunanin
wanene. Shiru babu wanda keda alamar magana a tsakanin ita da shi. Ganin haka a ɗan
harzuƙe tace, “Nikam idan mai kiran nan baida abinyi ni ina da”.
Guntun murmushi yayi. Har cikin rai yake jinjina tsiwar yarinyar nan, ita
kowa bata jin shakka na waya ma da batasan ko wanene ba bazata raga masa ba. Ya ɗan
girgiza kansa da furzar da numfashi. “Ki samo min tea da wani abu ki kawo min”.
Kafin ta samu damar tofa tata ya yanke wayar. Tai takwa-takwa na takaici sai
kuma ta tsuke baki da buge wayar.........✍

_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_


*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:


07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇


09134848107

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*


[11/23, 10:16 PM] My Zafafa: *_Typing📲_*

*_BABU SO....!!_*
_(Miya kawo kishi?)_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718

*_51_*

.........Kwance ta kai tana faman tuttura lips gaba, a zuciyarya kam babu abinda
take sai masifa, sai dai babu damar yi a fili. Tashi tai zaune zaram kamar wadda
aka tsikara tana kallonsa, ganin ya koma ya zauna gaban laptop ɗinsa.
“Yaya MM?”.
Shiru ya mata yaƙi ya amsawa, amma tsabar bazata iya haƙuri ba saita cigaba da
maganarta kamar sharetan da yay bai zafeta ba.
“Amma dai can ɗakin zaka koma ka kwana kamar ranar idan ka kammala aikin
ko?”.
Banza yay mata nanma, takaicinta ya bayyana har tana jin tuƙuƙimsa a maƙoshi,
harara ta dallama bayansa, cikin jin zafi ta fara ɗaukar pillows ɗin gadon ɗaya
bayan ɗaya ta jera a tsakkiyar gadon tun daga farko har ƙarshe tana muy-muy da baki
alamar magana take. Ƙarshen gadon ta koma da salon kwanciyar kai da ƙafa ta kwanta
badan zuciyarta ta bata nutsuwar haƙurin sake kwanciya ɗaki ɗaya, gado ɗaya da shi
ba. Dan tayi alƙawarin kafin cikar wata ukunnan bazata taɓa bari ya samu nasara a
kanta ba.
Duk abinda take yana jin motse-motsenta sai dai bai juyi ba, aikinsa kawai yake
badan yana fahimtar wasu abubuwan ba. Bayan shuɗewar kusan mintuna arba'in da biyar
yaji shiru ta daina sukur-sukur da motse-motsen da takeyi, kaɗan ya juyo ya
kalleta, a can ƙarshen gado take ƙudindine da bargo ta juya masa baya. Ya maida
kallonsa akan pillows ɗin data jera, kansa ya girgiza kaɗan wani ɗan guntun
murmushi na suɓuce masa. Hankalimsa ya maida ga aikinsa, wanda ya sake jansa kusan
awa guda, ganin two ta kusa ya ga hamma yanata jerawa ya sashi tattara komai ya
ajiye. Alwala yayo, ya shimfiɗa abin salla, sallar nafila ya gabatar raka'a biyu,
yay addu'oi dan barci sai faman rinjayar idonsa yakeyi. Bai cire shingen datai musu
ba yay kwanciyarsa bayan yayi addu'oi. Babu jimawa barci yay awan gaba da shi
shima.
Duk da ta rigashi kwanciya shine ya rigata farkawa, ya yunƙura da ƙyar ya
tashi bayan karanta addu'ar barci, shanyayyun idanunsa da har yanzu barci ke cike a
cikinsu ya zuba mata ta ɗan hasken lamp dake a ɗakin kaɗai. Yanzu kam ta juyo
fuskarta, sai dai tana a inda take kwance tun jiya. Sai da yayo alwala sannan ya
tasheta, a ranta ALLAH-ALLAH take ya fice ta sama ƙofarta key, sai da yaga ta shiga
toilet sannan ya fice zuwa sashen Fadwa itama ya tashesu. Koda ta fito kai tsaye
ƙofar ta nufa, amma wayam babu keys ɗin alamar ya zare. Ta dallama ƙofar harara da
murguɗa baki.
Sai da gari ya ɗanyi sha ya shigo, har sannan tana zaune tana azkar. Batare
da ta yarda ta kallesa ba tace masa ina kwana. A taƙaice ya amsa yana kaiwa kwance
dan barci ne fal idanunsa. Jin ya fara sauke numfashi ta ɗan juya ta kallesa, ya
juya mata baya, amma ta fahimci barci ne ya ɗauke sa. Itama dai ƙarasa azkar ɗin
tai ta koma ta kwanta tunda ba wani aikine da ita ba.....

★★★★

Tsabar yanda ta kwana da abubuwa masu yawan gaske a ranta tana idar da salla
sashen Gwaggo ta nufa. Burinta kafin su Daddy daga massallaci su shigo ta shige,
dan ita yanzu ko ɗakinsa bata zuwa, shi kuma yaƙi ce mata komai akan hakan. Gwaggo
na zaune tana lazimi Mommy ta shigo, kallonta kawai take baki a sage, sai dai kuma
batai mamaki ba musamman akan sanin halin rashin haƙuri irin nata. Mommy ta
gaisheta kamar yanda ta saba, damuwa ƙarara akan fuskarta.
“Wai Nafisa kuwa anya hankalinki na jikinki? Wace irin rayuwace wannan duk
kin firgita kanki akan abinda bai taka kara ya karya ba. Da alama yau ko barcin
kirki ma bakiyi ba ko?”.
“Humm Gwaggo ina naga ta barci nikam, kema kin san babu wani barci dazan iya a
wannan halin. Ki duba fa kiga Shareff ya ɗauke ƙafa gaba ɗaya a gidan nan tamkar ya
manta dani a raye, ko'a waya baya kirana tumma yanzu kenan za'a rabani da yarona.
Maheer ma yaƙi zuwa duk da shi nasa bai cika damuna ba nasan fushin banza da wofi
ya sakama ransa bayan ni gata naima rayuwarsa. Gwaggo taya zanyi barci a wannan
yanayin to? Na kasa gane kan Shareff sam. Son yarinyar nan yake da yake gudun
haɗuwarmu ko yaya ne?”.
Ƴar dariya Gwaggo tai. “Banda abin Nafisa halin namiji kuma kika manta! Shi
yanzu Mustapha a wannan gaɓar bake kaɗai ba kowama zai iya rasa gane kansa ai.....”
“Gwaggo to saboda mi? Ni wlhy kaina duk ya kulle”.
“Uhhm haka dai, tunda kin ruɗa kanki ba dole kanki ya kulle ba. Kina tunanin
duk ƙin da yakema yarinyar zai kawo ido ya saka mata ne a gidansa”.
Kaɗan ya rage Mommy ta haɗiye harshenta. Cikin in ina da shiga ruɗani take
magana. “Gwaggo wai kina nufin ya kwanta da yarinyar nan?”.
“Har kuwa ki ganta da ciki nan da watanni kaɗan”.
“Aiki dana tsine masa”.
“Ki tsine masa! Kinga Usman da Ai'sha sunci riba a kammu kenan. Ki kiyayi
harshenki da ambaton tsinuwa ya ƴaƴanki saboda kawai ranki ya ɓaci. Ki koyi nutsuwa
a duk lokacin da kikaci karo da abinda bai miki ba. Nafisa idan kikai sakaci k da
kanki zaki tabbatar da nasarar maƙiyanki akan ƴaƴanki. Yanzu dakin kwantar da
hankalinki tun bayan da akai rikicin farko akan auren nan da yanzu mun kai ga
mafita. Mustapha da kike gani hatsabibin yaro ne mai shegen zurfin cikin tsiya da
wayo. Gaggawa a al'amarinsa ba shi bane mafita, kuma tsananinki ba shi bane zaisa
muci nasarar rabashi da yarinyar cikin sauƙi, musamman da matarsa dama ta kasance
shashasha, dan nikam sai yanzu nake dana sanin yin wannan haɗin nasu”.
Da mamaki Mommy tace, “Wani abun ya faru ne Gwaggo?”.
“Nafisa ai shiyyasa nace ke ɗin ruɗaɗɗiyar mutum ce, yo banda haka halin Fadwa
har wani ɓoyayye ne da zaki kasa ganewa. Duk wani baƙin halin Halima shine tare da
ƴarta, kodan shi Mustaphan bamai yawan magana bane da kullum zai zauna faɗa miki
matsalarta shiyyasa kike kasa fahimtar halinta?”
“Gwaggo bawai ban fahimci wasu abubuwa bane, dan ni kaina yawan kirana
da takeyi kullum tana kawomin ƙararsa ya mata kaza ya mata kaza yana cimun rai,
sannan Aysha ta faɗa min ko abinci sai ta gadama takeyi a gidan sai dai mai-aiki,
Shareff da ko'a gidan nan baicin abincin masu aiki”.
“Humm zatayi abinda yafi haka ni na sani. Amma karki damu zamu fara gyara
mata zama. Yanzu abinda nake so da ke ki sassautama zuciyarki komai, ki nunama su
Muhammadu komai ya wuce kin ajiye makamanki, shima ɗin Mustapha ki kirashi a waya
ya sameki ki nuna masa komai ya wuce. Mu kuma daga nan zamu fara namu yaƙin, badai
wata uku shi Ibrahim ya bata ba, to duk yanda zamuyi sai munyi nanda wata ukun
tabar gidan, babban fata na dai ace bai taɓata ba. Kai koda ya taɓatan ma ba
komai”.
“Gara dai karya taɓatan Gwaggo, danni bana fatan haɗa kowace sabga da Usman
balle shegiyar matarsa”.
Ƴar dariya kawai Gwaggo tayi da faɗin, “To ALLAH yasa haka. Yanzu dai inaga
kima Sakina magana yau taje mana gidan taga yaya zaman nasu yake”.
“Wannan shawaran yayi gwaggo, bara na sanar mata yanzun nan kuwa”.
Daga haka suka cigaba da tattaunawa kuma har gari yay haske sannan Mommy ta
koma sashenta zuciyarta na ɗan sassauta nauyin da tai kwana biyu. Masu aikinta ta
bama umarnin haɗa abincin Daddy. Duk da sun ɗanji mamaki babu wanda yace komai
tunda ba huruminsu bane, itako ta shige domin shiryawa tunda dama girkin tane.....

★★

Kusan ƙarfe takwas ta farka. Ganin har yanzu shi barcinsa yake hankali kwance
sai ta koma ɗayan ɗakin tai wanka ta shirya a can. Ganin har lokacin baida alamar
tashi saita nufi falo ta gyara duk da ba wani datti bane ba. Yunwa takeji matuƙa,
dan haka ta haɗa tea ta dawo falon tai zaman sha tana buga game a waya. Koda ta
kammala a falon ta cigaba da zama tana game ɗin har kusan ƙarfe tara.
“Wai mutumin nan bazai tashi bane? Koya manta yau monday akwai office?”.
Ta faɗa tana kallon agogon dake falon, miƙewa tai kanta tsaye ta nufi bedroom
ɗin. Mamaki ya ƙara kamata ganin har yanzu dai a kwance yake, (Lallai babu lafiya)
ta ayyana a ranta tana ƙarasawa gaban gadon, dan ita dai a sanin datai masa na
rashin wasa da aiki inda ƙalau yake babu yanda za'ai yakai yanzun yana barci.
Fuskarsa ta ɗan tsurama ido dan kwance yake a rigingine. Lumshe idanu tai da sake
buɗewa a kansa, ita shaida ce Shareff ƙyaƙyƙyawa ne, ƙyawu irin na masu kwarjini da
cikar haiba bawai na fitar hankali ba. ALLAH ya bashi dukkan kamala ta cikakken
mutum tamkar wani babba. Baida yawan hayaniya, sannan bai da yawan fara'a. Mutane
da yawa kance mata yanada sauƙin kai da daɗin zama, sai dai ita har yanzu bata
ganinsu tattare da shi, dan zata iya bugar ƙirji tace babu wadda yatsana a
rayuwarsa ƙila sama da ita, ta rasa minene laifinta a gareshi. Ta taɓe baki da juya
idonta, a fili ta furta “Yo karya soni ɗin nima ai ba son sa nake ba humhh”. Ta
ƙare maganar da murguɗa baki ta juya zata bar wajen a bazata taji an riƙota. A
firgice ta juyo dan ta tsorata, sosai idanunta suka firfito waje dan batai zato ko
tsammanin shi ɗin bane tunda taga barci yake. Idanunsa ya ɗan rufe ya sake buɗewa a
kanta tare da fisgota ta faɗo kansa.....
“Wayyo Yaya zaka karyani ne?”.
Komai baice mata ba, sai dai kafeta da idanunsa dake a yanayin wanda ya tashi
barci. Ƙoƙarin son zame jikinta take a nasa amma ya hana hakan ta hanyar ɗora
hanunsa a bayanta ya tallafeta da ƙyar a saman jikinsa, fuskarta dake a gab da
tashi ta kautar gefe saboda yanda yake kallonta tsigar jikinta har tashi take.
Ɗayan hanunsa yasa ya maido fuskar tata a saitin tasa har yana jin saukar
numfashinta.
“Kina yin miye tsaye a kaina?”.
Idanunta ta waro sosai, sai kuma ta tura baki da ƙara ƙoƙarin janye fuskarta dan
bazata iya jurar kallonsa ba. “Ni to mizanyi? Kawai nazo tadaka ne dan naga lokacin
office yana wucewa”.
Agogon dake ɗakin ya ɗan kalla tare da maido idanunsa a kanta lokaci guda.
“Dama ango na zuwa office ne?”.
Sosai ta yatsine fuska tamkar wadda aka faɗama wani mugun abu. sai kuma ta taɓe
baki da sake yunƙurin barin jikin nasa........✍

_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_


*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:


07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇


09134848107

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*


[11/23, 10:16 PM] My Zafafa: *_Typing📲_*

*_BABU SO....!!_*
_(Miya kawo kishi?)_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718

*_53_*

.........Da sallama ta shigo ɗauke da madaidaicin tray mai ƙyau, a samansa


madaidaiciyar butar shayi ce da kofinta ɗaya, sai tea spoon da sugar a ƙaramin
bowl. Sai kuma plate dake rufe da robar ruwa ɗaya duk da tasan za'a iya samun ruwan
a sashensa. Kaɗan ya juyo daga kallon tvn da yake ya ɗan dubeta, sai kuma ya ɗauke
da amsa sallamarta akan lips. Gaba ɗayansu haushinsu yakeji dan kowacce da kalar
laifin datai masa, sai dai yafi ganin sassaucin na Fadwa akan wannan tsiwatacciyar
yarinyar da har yanzu maganganunta na ɗazun basu daina masa zafi a zuciya da ruhi
ba.
Ita dai da bata san yanayi ba ma koda ta gama zuba shayin ɗan ɗagowa tai ta
dubesa da zata saka sugar. A taƙaice yace, “biyu” ya cigaba da kallonsa. Baki ta
ɗan taɓe itama ta jefa masa biyun ta saka cokali. Plate ɗin datai warming sauran
naman jiya daya kawo da dare ta zubo a ciki ta buɗe masa, sai sauran meatpie ɗinta
da shima dai baiyi komaiba kasancewar a fridge yake shima dai tayi warming ɗin
nasa.
“Bani waya a bedroom”.
Ya faɗa dai-dai tana ɗagowa alamar ta kammala aikinta. Ganin yanda yake tsume-
tsumen fuska ta wuce salin-alin batare da tace komai ba. Babu jimawa ta fito da
wayar a hannu. Harya fara cin abincin hankalinsa rabi a tv. Nanma dai tana bashi
tai ficewarta tabarsa.
Motar da bata san kota wacece ba take shigowa gidan. Bata san wani a gidansu
da motar ba, dan haka tai wucewarta batare da maida hankali ba dan maybe baƙin
Fadwa ne kona mai gidan...

“Kinga kallon da yarinyar can taima motarmu ta watsar kuwa Sakina?”.


Hajiya Luba ƴar uwa ga Mommy kuma mahaifiya ga Bibah ta faɗa idonta akan Anaam
dake shigewa sashenta. Aunty Sakinar ma kallon nata take, tai ƙwafa da ɓalle murfin
motar ta fita. “Yaya Luba ba dole tai mana kallon banza ba tunda wanda ya kawota
gidan ya nuna mata tafimu, yo ta fimu mana tunda ya zaɓeta sama da umarnin uwarsa
ma”.
“To aikuwa zasu ci ubansu daga shi har ita, dan zamu sauke mata abinda ke kanta
yanda uwarta ta mallake ubanta mu anan AL-Mustapha yafi ƙarfin haka. Jiba yanda
take yawo da wata ƴar iskar shiga dan ALLAH”.
“Duk dama ta samu ai ke dai Yaya Luba, muje dai”.
Wanda ya kawosu babban ɗan Aunty Sakina ɗinne, ya girgiza kai duk zuciyarsa babu
daɗi, dan shi dai baiga abinda yarinyar tayi ba suke cusa mata wannan zagin, shikam
harma ya fara tausayin Yaya AL-Mustapha wlhy.

Suko sashen Fadwa suka fara nufa, a falo suka sameta zaune tana shan lemun
fata, mai-aikinta zaune daga ƙasa itama. Kallon sukeyi na wani horro film sai dai
sam hankalin Fadwa ba gaba ɗaya yake akan film ɗin ba. Maman Abu ta miƙe tana musu
sannu da zuwa. Da ƙyar suka amsa mata, bata damuba ta nufi kitchen ɗakko musu ruwa
dan ba yau ta saba da halinsu ba tunda sanda tana can gidan su Fadwa ɗin ma suna
zuwa babu kalar wulaƙancin da basa gani su masu aiki a wajensu su a dole ƙanen masu
gida (Karku manta suma ƙanen uba suke ga Fadwa, kuma ƙanen uwa ga Shareff).
“Baki da lafiya ne?”.
Aunty Sakina ta faɗa idonta fas akan Fadwa. Kanta ta girgiza mata kawai. Baki
aunty Sakinar ta taɓe. Hajiya Luba ta karɓe da faɗin, “Ciwo ya wuce baƙin cikin
miji da kishiya mai kama da karuwai, k yanzu nan Fadwa har waccan ƴar tsefatar
yarinyar ce zata razanaki ki koma haka firingau-firingau ido luhu-luhu. Kuka kenan
kika zauna kinayi kamar wata sakara?”.
Hawayen da taketa riƙewa ne suka silalo mata. Aunty Sakina da Hajiya Luba suka
ɗauki sallallami da tafi kamar waɗanda sukai gamo. Ita dai Fadwa kanta a ƙasa tana
hawayenta.
“A to wlhy aiki ya ganki kuwa, yima kishiya kuka. Kishiyarma wadda bata wuci a
sati ki kaɗa shegiya ba tabar gidan saboda ke ɗin shashashar ce kika zauna kinamata
kuka. To bara kiji, idan zaki dawo cikin hankalinki ki dawo, a duk zuri'armu babu
sakarai. Balle ke da mijin nan naki tako ina jininki ne, da ubansa da uwarki uwarsu
ɗaya ubansu ɗaya, da ubanki da uwarsa iyayensu uwarsu ɗaya ubansu ɗaya. Gaba da
baya aka tsaga jikinku jini iri ɗaya za'a gani, itako fa miye haɗinsa da ita banda
ɗiyar ɗan uban ubansa, dalla malama sharemin waɗan nan banzayen hawayen ki tashi ki
rakamu sashen shegiyar”.
Hawayen Fadwa ta share, sai dai kuma tuna yana gidan yasa ta kasa tashi.
“Aunty yana nan fa a gida”.
“Shi wa ɗin?”.
Cewar Hajiya Luba.
“Shareff! Yau bai fita aiki ba wai hutu ya ɗauka harna sati ɗaya”. Ta ƙare faɗa da
rushewa da kuka tabbacin abinda ke cin zuciyarta kenan tun ɗazun.
Cikin riƙe baki Aunty Sakina tace, “Iyee wato sati guda, amma uwarsa nacan ko
sau ɗaya baije ya gaisheta ba. Shiko dai Al-Mustapha yayi asara. Aini namaji daɗin
samun nasa a gidan zanfi jin daɗin cin uban shegiyar yarinyar a gaban nasa
sallamamme kawai. Tashi muje ki kaimu, kuma karna sake ganin waɗan nan hawayen
banzar kema shashasha”.

Anaam na kwance cikin kujera tana buga game suka faɗo mata ko sallama
babu. Da farko tayi kamar ta share dan Fadwa ce ta fara shigowa, sai dai ganin su
Aunty Sakina ya sa ta tashi zaune tana danne sosuwar da zuciyarta tayi akan shigo
mata kai tsaye da sukai. Ta san aunty Sakina dan sun taɓa zuwa gidanta ita da
Aysha. Daga Hajiya Luba har aunty Sakina bin falon suke da kallo baki a taɓe, sai
dai acan ƙasan ransu razani ne na gaske, dan ko makaho ya shigo ya laluba yasan
annunama duniya yariyar ƴar gata ce.....
Cigaba da game ɗinta tai domin basu dama su gama kalle-kallen, saiko da
sukai iya iyawa sannan suka juyo gareta.
“Oh lallai, ga ƴan iska sun shigo ko?”.
Aunty Sakina ta faɗa murya a sama. A karan farko Anaam ta saki murmushi, ta ɗago
idanunta dake cikin gilashi tana kallonsu, cikin hausarta dabai gama nuna ba ta
gaishesu kamarma bata fahimci harzuƙowar aunty Sakinar ba..
“Uhm lallai kam Shareff ka amshi ruwan dafa kanka. Wato k a dole ƴar
bariki”.
Sarai ta fahimci abinda Hajiya Luban ta faɗa, dan kuwa zuwa yanzu Alhmdllhi
hausa ta fara zauna mata a brain da harshe da ƙyau saɓanin farkon zuwanta. Amma sai
tai kamar bata fahimci komai ba, fuskarta da murmushi ta miƙe tana faɗin, “Aunty ku
zauna Please bara na kawo muku ruwa”. Bata jira cewarsu ba ta nufi kitchen.
“Babbar b*r* uba kai. Wai wannan yarinyar tana nufin bama tajin mi muke faɗa
ko mi?”.
Fadwa da batace komaiba tun shigowarsu tana kuma daga tsaye dan bata zauna ba
tace, “Hummm! Tana jin komai sarai iskanci ne kawai fa Aunty. Ni dama kun barta dan
ALLAH kawai....”
Harara Hajiya Luba ta zuba mata. Shigowar Shareff a bazata ta saka Fadwa
haɗiye abinda zata faɗa babu shiri da risinar da kanta ƙasa, wani yawu mai kauri ya
wuce muƙut a maƙoshinta ƙirjinta na bugawa.
Idanunsa ya janye a kanta da ƙarasowa cikin falon hannayensa duk biyu a
cikin aljihun wandonsa.
“Oh dama kana gidan?”.
Aunty Sakina ta faɗa tana hararsa.
Duk da sarai ya jita sai bai amsa ba, sai da yakai zaune cikin kujera da ɗora ƙafa
ɗaya kan ɗaya sannan ya dubesu. “Barkanku da safiya aunty kune a gidan namu?”.
Sosai ransu ya sosu da salon rainin wayonsa su duka. Sai dai kafin wani yace
wani abu a cikinsu Anaam ta fito ɗauke da tray shaƙe da kayan ciye-ciye da ruwa da
lemo. Itama dai ta ɗanji wani iri na ganin nasa, amma saita fiske abinta ta ajiye
tray ɗin a gabansu tana murmushi. “Aunty ga ruwa to....”
A matuƙar harziƙe Hajiya Luba ta tura tray ɗin da ƙafarta tana ballama
Anaam harara. “Tunda shine ya kawomu ba, k ki kama kanki wadda ta haifeki ma a
tafin hanunmu take balle ke kanki...”
“Juwairiyya bani lap-top dana bari a ɗakinki”. Shareff ya katse hargowar
Hajiya Luba tamkar bai ji mima take faɗa ba. Tsamm Anaam ta miƙe batare da tace
uffan ba, ba kuma ta kalli sashen da Shareff ɗin yake ba balle Fadwa ta ɗauka
wayarta ta wuce bedroom.
“Oh ke ko ga mahaukata suna magana dole ka sata aika. K! Fadwa shaƙomin
ƴar iskar yarinyar can na nuna mata wacece ni dan ubanta”.
Muƙutt Fadwa ta haɗiyi yawu da ƙyar a karo na biyu domin jin umarnin Aunty
Sakina tamkar saukar aradu bisa kai. Ta ɗan saci kallon inda Shareff ke zaune a
harɗe har yanzu kai kace baima san wainar da ake toyawa a falon ba. Kanta ta
girgiza a hankali, so take tayi magana amma ta kasa motsa lips ɗinta sai kawai ta
juya da sauri ta bar falon ma gaba ɗaya. (Tabbas Fadwa nada kurari da hayaƙi, amma
kuma tanada tsoro bata cika iya jure hatsaniyar faɗa ba. Idan mai karatu bai manta
ba kokuma ya lura da ƙyau zai fahimci Anaam ta fita tsiwa, saboda a lokuta da dama
takan takaleta faɗa amma a ƙarshe Anaam ɗin ke tsigeta itako sai tai laƙwas. Tabbas
a cikin raunanan halayanta wannan yana ciki rashin juriyar hatsaniya, a wani fannin
kuma zamu iya kiransa haƙuri😜).
Daga aunty Sakina har Hajiya Luba baki suka saki uwa sakatar sakarai dan
al'ajabin Fadwa. “Oh ni Sakina ato lallai Fadwa kema kin cika asararriyar yarinya,
to kodai ba Al-Mustapha ɗin kawai aka shanye ba harda ke ɗin kema?”.
Maimakon samun amsa daga Fadwa data fice sai Hajiya Luba ce ta amsawa Aunty
Sakinar. “A to ga halama kin gani kuwa Sakina. Ƙanƙanuwar yarinya ke juya gida miji
da kishiya duka a tafin hanunta.”
Ƙololuwar ɓacin rai kam Aunty Sakina takai, musamman biris da su da Shareff
yayi. Tsabar wulaƙanci ma sai latsa wayarsa yake yana ɗan girgiza ƙafarsa da yay
crossing. Anaam dake danne dariyarta da jinjina tsaurin idon mutumin nan ta ƙaraso
ɗauke da lap-top ɗin a hannu. Gabansa gab ta matsa, ta miƙa masa harda takardun
data haɗo da su. Idanunsa dake akan wayar ya ɗago yana kallonta, ta ɗan tura baki
gaba tana son dangwarar da kayan bisa cinyarsa ya riƙo hanunta. Fuska ta ɗan narke
da ƙyaƙyƙyafta idanu tai ƙoƙarin janye hanunta.........✍

_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_


*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:


07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇


09134848107

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*


[11/23, 10:16 PM] My Zafafa: *_Typing📲_*

*_BABU SO....!!_*
_(Miya kawo kishi?)_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718

*_54_*

.........Ƙara riƙo hanun yay da ƙyau idanunsa masu kaifi na saukar mata da kasalar
data mantar da ita wanzuwar su aunty Sakina a falon. Dama haka yake buƙata, ta
manta da wanzuwar tasu ya samu damar isar da gargaɗinsa garesu batare daya samu
wani tangarda daga gareta ba.
“Dama haka ake bama miji abu?”.
Ya faɗi maganar a salon daya nema ɗauke numfashin Anaam na wucin gadi, dan muryar
da yay mata magana da ita muryace da zata iya rantsuwa bata taɓa ji daga garesa ba.
Da ƙyar ta iya ƙwato kanta, tai ƙoƙarin ajiye masa kayan a hanun kujerar da janye
nata idanun daya sargafe a nasa dan ta gama yanke shawarar barin wajen kafin a samu
matsala yaga rauninta. Tana daga kafa ya riƙo hanunta tare da jawota sai gata ɗaram
a cinyarsa tamkar walƙiya. Kafin tunanin wani abu ya risketa har ya yimata zobe da
hanunsa ta hanyar ɗorawa a saman cikinta ya manne bayanta da ƙirjinsa kansa bisa
wuyanta yana shinshina da fara magana cikin kunenta da wani salon daya saka tsigar
jikinta tashi.. “A haka ake bama miji abu ba'a tsaye ba”.
Saukar wata mulmulalliyar ashariya cikin kunnuwansu ta tilastata ƙanƙamesa
babu shiri dan da gaske ta tsorata dama gata a tsakkiyar wani firgicin. Harga ALLAH
ta manta da su a falon, saɓanin shi da duk abinda yakeyi domin su ɗinne dama. A
firgice ta ɗaga ido zata kallesu ya hana hakan, dan kuwa hanunsa ya tura cikin
rigarta sai dai akan cikinta ya tsaya.. Ɗan matsawar da yay ta sata saki ƙarar
ruɗewa dan a bazata abin yazo mata kuma taji zafi......
Rige-rigen fita aka farayi tsakanin Hajiya Luba da Aunty Sakina, saboda ƙarar
Anaam ɗin fassara daban suka bata. Aunty Sakina ma harda gwara kai a jikin garu
lokacin da suke turereniyar ficewa.
Hanunsa da taketa faman kaima mintsini ya janye, ta mike zumbur daga
cinyar tasa idanunta taf kunya. Riƙota ya sake yi fuskarsa ɗauke da murmushin ƙeta.
“Malama nace na gama n....”
Hararar data wulla masa ce ta hanashi ƙarasa faɗa ya saki dariyar data ƙara
ƙular da ita tana jin zafinsa har cikin maƙoshinta. Sake fisgota yay ta dawo saman
cinyar tasa. Ya haɗe hannayenta duk biyu dake son turesa ya danne akan cikinta.
“Idan idanunki suka cigaba da harararta daga yau sai na miki haɗiyar ɗan sululu a
gidan nan fitsararriya”. Mutsu-mutsunta ta cigaba dayi na son ƙwacewa yaƙi bata
dama. Saima lanƙwansota yay ta kwano jikinsa ya kai goshinsa kan nata ya haɗe. Yawu
ta fara kokawar haɗiyewa da sauri-sauri ganin yana daidaita lips ɗinsu.
“Please Yaya dan ALLAH kar kayi bana so”.
Gira ya ɗaga mata da kashe ido ɗaya, “Fitinanniyar yarinya minace zanyi to?”.
Bakinta da take faman karewa da hannu tatura gaba da ƙoƙarin kauda fuskarta ya
tare da hannunsa, tare da janye nata hanun ya manne lips ɗinsu. So take ta turesa,
amma tasirin abinda yake matan a cikin jini yana barazanar hanata kowanne irin
yunƙuri, daɗin daɗawa ya riƙe hanunta ta yanda bazata iya ko motsashi ba. A karon
farko ta fara maida masa murtani a yau dan tasirin salon nasa jinin jikinta ya fara
amsarsa da ƙarfin gwiwa da wani sirrin ɓoye dake can ƙasan zuciyarta da ita kanta
har yanzu bata san da zamansa ba tattare da ita. Hakan tamkar ƙara zugane a garesa
da dukkan haƙurinsa, dan kai tsaye zuciyarsa ta fara ingizasa ga kaiwa inda bai
gama shirya kai kansa ba. Ring na wayarsa ne ya dawo dasu duniyar da suka jima da
yin nisan barin cikinta da lissafi irin na masu hankali. Sakinta yay, zaram ta miƙe
kamar wadda take a tsinin allura. Da sassarfa ta bar falon ko waiwayensa taƙi tayi.
Da kallo ya bita yana sakin kakkauran numfashi da murmushi, a hankali yakai bayansa
jikin makarin kujera ya kwantar yana mai lumshe idanunsa da sake sakin ajiyar
zuciya a jajjere yana kai hanunsa ya shapo lips ɗinsa....

Tun fitowarsu take faman kaikawo a harabar gidan, dan ko sashen Fadwar sun
gagara komawa tsabar mamaki da jinjina ƙwarewar iskancin Shareff ɗin a yau. Yaron
da ko ido bai cika ɗagawa ya kalla mutane ba shine yay musu wannan baƙin iskancin.
Ina bazata iya haƙuri har sai sunje gida ba, dole ne ta kira Mommy kam ai. Takai
wayar kunenta tana faman kaɗa ƙafafu da jijjiga jiki na tsantsar bala'i. Cikin sa'a
aka ɗaga mata gab da zata tsinke.
“Sakina har kun isa gidanne?”.
Mommy ta faɗa tunkan aunty Sakinar tace wani abu. Aiko cikin matuƙar ɗacin murya ta
tare numfashin Mommy din da faɗin, “A dole Mustapha kam yafi karfinki wlhy Yaya
Nafi! Dan tabbas babu makawa an wanke an basa ya sha.”
Ƙirjin Mommy ya buga da ƙarfi, sai dai kafin tace wani abu Aunty Sakina ta
cigaba da bata labarin abinda ya faru yanzu-yanzun nan. Ta ƙare da faɗin, “Zama dai
kam bai gammu ba dan wannan yarinyar tafi uwarta hatsabibanci. Nan gaba babu makawa
zaima iya cewa kwanciyar aure zaiyi da ita a gabanki saboda ya tabbatarma duniya
shi ɗin tantirine na gask......” Ƙitt!! Wayar ta yanke. Tai saurin cirota a kunenta
tana kallo a tunaninta ko kuɗine suka ƙare. Ƙoƙarin siya tai ta banki ta ƙara kiran
Mommy ɗin. Sai dai kuma number busy ake nuna mata alamar waya take ko kiran
wani.....

Ring ɗin wayarsa ne ya sake sashi buɗe idanunsa da har yanzu ke'a rufe. Ya
kafe fuskar wayar da kallo tamkar mai tsoron ɗauka ganin sunan First Luv ruƙu-ruƙu
na yawo. Rabon da suyi koda waya ne harya manta, ya kuma tabbatar gargaɗin da yayma
su Aunty Sakina ya risketa ne matsayin saƙo. Bazai iya ƙin ɗaga kiranta ba koda
yana jin tsoron dukkan wani furuci daga bakinta, kimarta da girmanta sun wuce a
musalta a cikin idanunsa da zuciyarsa. Hannu ya kai ya ɗaga tana gab da tsinkewa,
yakai kunen nasa cikin ƙarfafa kai....
“First luv barka da safiya”.
“First ubanka ba first luv ba. Al-Mustapha wlhy ina gab da jamaka kalmar ALLAH ya
i.....”
“Please First luv, abeg kar kice haka dan girman ALLAH.”
“Idan ka sake kirana da sunannan ALLAH sai naci ubanka. Kuma kazo ina nemanka idan
ba hakaba ka bari na tako ƙafata gidanka da kaina yarinyar nan na a ciki wlhy wlhy
wlhy kadaiji na rantse ko! Sai na jamaka ALLAH ya isa da manyan baƙi no-no na daka
sha dan bakai kaɗai na haifa ba balle ka ɗauramin hawan jini”.
Harshensa har sarƙewa yake wajen faɗin, “Shi... Shike nan naji zanyi, zan
zo, amma kimun alfarma Mommy dan ALLAH sai gob.......”
“Alfarma ubanka, Al-Mustapha ni kake son tozartawa a idon maƙiyana dai ko?
Kana nunama duniya mace ta fini daraja da kima a idonka?”. Ta faɗa tana fashe masa
da kuka. Idanunsa ya rumtse da ƙarfi, ya girgiza kai tamkar yana a gabanta. “Mommy
wlhy babu wata mace da darajarta zata ko kama ƙafarki a wajena. Dan ALLAH ki
fahimceni Mommy ina a tsaka mai wuya......”
A fusace ta yunƙuro zatai magana Gwaggo ta fisge wayar. “Nafisa wai kin rasa
hankalinki ne halan?! A tunaninki wannan butsutsun naki akan Mustapha shine mafita
ta ƙarshe da zakibi wajen raba auren?!!......”
Wata wawuyar ajiyar zuciya ya sauke da lumshe idanunsa ya saki wayar a
jikinsa batare daya ƙarasa jin abinda Gwaggon ke faɗa ba. Dan kuwa tabbas a wannan
gaɓar ta taimakesa taimako irin wanda bakinsa bazai iya maimaita faɗa ba, sosai
al'amarin Mommy ke daɗa tayar masa da hankali, ya rasa ta inda zai kama domin shawo
kanta akan wannan aure. Har yanzu yarasa gane minene takamaimai laifin su Abie a
gareta da take musu irin wannan ƙiyayyar (Niko nace Shareff a haka ta tashi, tun
tana ƙaramarta an riga an cusa mata ƙinsu. Haka ɗan adam yake, a duk lokacin daka
koyar da shi wani abu ƙyaƙyƙyawa ko mummuna yakanzo ya fika iyawa. Iyaye tabbas
muna kuskure, kuskuren da shike saka ƴan ubanci a zukatan ƴaƴanmu tsakaninsu da ƴan
uwansu. A kullum baki da aiki saina aibanta kishiyarki gaban ƴaƴanki, baki da aiki
sai na zaginta da nuna cutarki take zaluntarki take bata sonki, bata ƙaunarki,
maƙiyarki ce kuma a gaban ƴaƴanki. Tayaya kike tunanin bazasu tsaneta su tsani
ƴaƴanta fiye da yanda kike tsanarta ba, saboda ke ra'ayin ƙinta ya shigekine da
girmanki da hankalinki, idan kin so zaki iya yaƙarsa, suko kin raini zukatansu ne
akan wannan ƙiyayyar, dolene su dawwama da ƙinta da ƙin duk wani abinda ya shafeta
koda bata aikata musu komai ba na ƙi ɗin. ALLAH ka gafarta mana ka gana damu
gaskiya koda bazata mana daɗi ko zuwa dai-dai da son zukatanmu ba).
Anan falon yabar lap-top ɗin da takardun ya fice, koda ya fito su Aunty
Samira sun wuce dan baiga motarsu ba. Motar ya shiga shima ya fita a gidan, dan
yana buƙatar yin nesa da su har zuciyarsa ta huce. Haka yake baya son yanke hukunci
cikin fushi, ya gwammaci yin nesa da abu a duk lokacin da zuciyarsa ta harzuƙa.
Asibiti ya nufa wajen Dr Jamal, sai da ya shigo cikin asibitin sannan ya kira
wayarsa..
Daga can Dr Jamal yace, “Ka shigo mana, ni kaɗaine ma a office”.
Ƴar ƙaramar ajiyar zuciya ya ɗan sauke da yanke wayar, bai cika san buɗe cikinsa
ga kowa ba. Amma dai mutane biyunnan sun wuce abokai kawai a garesa aminaine na
gaskiya. Daga Dr Jamal har Fharhan abokansa ne tunna ƙuruciya, koda yabar ƙasar
kuma basu yarda juna ba. Basu da abokin shawara sama da shi, duk da shi yakan jima
basuji nasa cikin ba saboda yanada zurfin ciki matuƙa. Na ukunsu kuwa shine
Khaleel, duk da kasancewarsa ƙani a garesa hankalin yaron da nutsuwarsa kansa ya
kallesa tamkar aboki, sannan shima Khaleel ɗin bashi da wani amini sama da shi duk
da yana amsa sunan yayansa ne.
Sai da yay knocking aka bashi izinin shiga sannan ya shiga. Dr Jamal na zaune
a kujerarsa ya amsa masa sallamar da yay fuskarsa da murmushi. Cikin danne kishin
rashin Anaam yace, “Ango kasha ƙamshi”. Harararsa ya ɗanyi ya ɗauke kai, ya zube
cikin kukerar dake gaban desk ɗin Dr Jamal ɗin yana furzar da iska mai nauyi. Dr
Jamal dake binsa da kallo danya fahimci damuwa a fuskar abokin nasa ya miƙa masa
hannu sukai musabaha.
“Wai yana ganka haka kamar mara lafiya? Ko jikinne har yanzun?”.
Kai ya girgiza masa, sai dai baice komai ba. Dr Jamal ya tsura masa ido na wasu
sakanni, sai kuma ya miƙe ya ɗakko masa ruwa. Baiyi musu ba ya amsa, murfin ya
ɓalle ya kai bakinsa. Tass ya shanyesa yana dire robar da lumshe idanu ya sake
lafewa a kujerar yana sauke numfashi. Kusan mintuna uku suna zaune a haka shiru,
kafin ya buɗe idanunsa da gaba ɗaya launinsu ya canja ya kalla Dr Jamal daya tsura
masa ido...
“Kai kurwana da ɗaci irin wannan kallo haka”.
Dariya Dr Jamal ya kwashe da shi. “Ɗan wulakanci, inda ni maye ne ALLAH kamun kaɗan
a ci ɗan iska kawai”.
Murmushi yay a karon farko da gyara zamansa. “To zama mayen mana kaga idan zan
ciwu a wajenka mara mutunci”.
Dr Jamal yay dariya kawai. Sai kuma ya miƙe daga kujerar zamansa ya dawo
inda Shareff ɗin ke zauna shima ya zauna suna facing juna. “Mike faruwa? Damuwa ta
kasa ɓoyuwa a kan fuskarka my Dude”. Nannauyan numfashi ya sauke da ɗan ɗage
kafaɗa, “Bani da wata damuwa kawai dai nace bari in gaisheka”. Idanu Dr Jamal ya
tsura masa fuskarsa na canjawa zuwa jin haushi........✍

_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_
*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_


*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:


07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇


09134848107

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*

[11/11, 12:16 PM] My Zafafa: *_Typing📲_*

*_BABU SO....!!_*
_(Miya kawo kishi?)_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718

*_55_*

............“To na gode da gaisuwa”. Ya faɗa da miƙewa zai bar wajen. Riƙosa


Shareff yay ya maida ya zaunar.
“Wai haushi kaji?”.
“Mizaisa naji haushi?”.
Murmushi Shareff yayi da cike lips. Sai kuma yace, “Manta kawai”.
“Ka gwammace ka cigaba da riƙe damuwarka kenan. Look Musty! Idan kasan zaka iya
shanyewa miyasa zakazo min nan to?. ALLAH kana bani matuƙar mamaki. A yanda muka
riƙeka sam kai ba haka baneba, ban saniba ko baka yarda damu bane har yanzu oho.
Well koma dai minene matsalarkace, mudai har gobe da jibi bazamu daina kallonka
matsayi mai girmaba insha ALLAH....”
“Humm Jamal”.
“Miye wani Humm Jamal. Na jima da fahimtarka ai Shareff kai har yanzu matsayin
abokai gama gari muke a wajenka. Mune dai kawai ke ɗaukarka da muhimmanci dan bamu
san ciwon kammu ba”.
“Ya ALLAH ni kamun gurguwar fahimta ne kawai. Yanzu dai ajiye wannan harzuƙar
taka gefe muyi magana.”
Harararsa Dr Jamal yayi ya ɗauke kai. Shareff ya sake yin murmushi kawai.
“Idan ka gama nuƙu-nuƙun to ina jinka”.
Kafaɗa Shareff ya ɗan ɗage da taɓe baki, “Bafa wani abu bane babba. Akan auren
nan ne dai kawai. Jamal na rasa ina zan ajiye zuciyata naji sauƙi. Mommy bori,
Fadwa bori, itama kanta Juwairiyya bori. Duk sun kasa fahimtar komai da suke a
kaina yake komawa bawai junansu ba. Jamal ALLAH jinina bana tantama a yanzu haka ya
hau sama ƙololuwa”.
Sosai tausayinsa ya bayyana saman fuskar Jamal, ya furzar da iska shima.
Tabbas yaso Anaam, har yanzuma sonta baije ko'ina ba a zuciyarsa. Amma hakan baya
nufin baza iya yin sadaukarwa ba. Shareff ya fishi dacewa da ita, sannan ya ɗarashi
buƙatar zama da ita saboda wasu hujjoji daya riƙe. Yaɗan kallesa yana jinjina kai.
“Tabbas matsalace wannan babba. Musamman ma ta Mommy dan na Fadwa da Anaam duk mai
sauƙi ne a ƙarƙashin ikonka suke zaka iya ladabtar da su dole kuma su nutsu.”
“Dama nasun bawai ya cika damuna bane, kawai dai bana son a yanda suken suma.
Amma Mommy da Daddy humm, na rasa ina zan kama Jamal. Ko gidan na kasa zuwa
gaishesu kwana uku kenan”.
“Damuwa dole ce kam, domin Daddy Mommy duk sunada iko da muhimmancin
bijirewaka kuskurene, babbar matsalar kuma a ra'ayin da suke mabanbanta, inda ace
ra'ayinsu ɗaya ne nakane ya bambanta zaka iya sadaukar da naka ka faranta musu ta
hanyar bin nasu. To amma yanzu gaskiya al'amarin akwai ruɗani, inba dai ɗaukar
Anaam zakai kubar ƙasar nan ba kawai. Nan da wani gajeren lokaci sai ku dawo sannan
Mommy ta huce”.
“Ita kuma Fadwa fa? Sannan aikina fa? Ita kanta service takeyi miye
makomarsa?”.
Nannauyar iska Dr Jamal ya furzar da faɗin, “Ya ALLAH! ALLAH!”.
Shiru kowansu ya kasa cewa komai, tsahon wasu sakkani Dr Jamal ya katse shirun. “To
ko Anaam ɗin zaka ɗauke zuwa wani ɓoyayyen guri a garin nan, inaga hakan zaisa
Mommy ta ɗan sauka kafin asan mafita. Danni dai banga ta inda maslaha zata samu ba
a yanzu tunda buƙatar Mommy kawai shine ka saki Anaam. Sai dai kuma idan sakin nata
zakai.....”
“Baka da hankali”.
Ya faɗa cikin tare numfashin Dr Jamal. Murmushi Dr Jamal yayi da haɗe hannayensa
alamar ban haƙuri. “Understand me, nima nasan hakan abune mai wahala da bazaka
iyaba, sannan bama zan so hakan ba. Amma kaje dai kayi tunani nima zan ƙara ko zamu
sami wata mafitar datasha banban da waɗan nan na yanzu”.
Kansa ya ɗan jinjina alamar gamsuwa da hakan, a dai-dai nan kiran Gwaggo ya
shigo masa. Yay ɗan jimm kafin ya ɗaga wayar yakai kunnensa da sallama. Daga can ta
amsa masa tamkar ba ita ba. Gaisheta yayi, nan ɗin ma ta amsa masa murya a sake.
“Kana jina ko Mustapha! Ka kwantar da hankalinka nayi magana da ita. Sai dai wannan
wasar ɓuyan da kake damu ba shine mafitaba a gareka inhar kana neman albarka. Ya
rage naka kai tunani irin wanda ya dace, na barka lafiya”.
Wayar ya sauke daga kunnensa, ya girgiza kansa da furzar da huci mai faɗi.
“Jamal bara naje kawai”. Ya faɗa yana miƙewa da zura wayar a aljihu.
“Wata matsalar ce kuma?”.
Kansa ya girgiza masa. “Wadda ake cikin ce dai. Gwaggo ce”.
“Gwaggo kuma?”.
“Uhmm! Kasan dai bazataƙi goyon bayan ɗiyarta ba ai.
Ya gane Mommy yake nufi dan haka baice komaiba. Har inda ya ajiye motarsa ya
rakosa, ya buɗe ya shiga sannan ya bashi hannu sukai musabaha. Sai da ya fice Dr
Jamal ya iya sauke ajiyar zuciya, tausayinsa yakeji har tsakkiyar zuciyarsa. Al-
Mustapha mutum ne mai kyawun zuciya ga kowa dazai zauna da shi. Bashi da matsala
komai nasa a nutse yake kuma a tsare, yanada halin manyan mutane, dan a lokuta da
dama idan yay abu saika ɗauka tunanin wani babban mutum ne mai shekaru saba'in....

Maimakon ya nufi gida sai kawai ya zarce wajen aikin da companynsu keyi. A
can ya samu Khaleel. Ya danne dukkan damuwarsa da haɗiyesa yana mai kallon ƙanin
nasa jarumi da halinsu ke kamanceceniya tamkar uwa ɗaya ta haifesu. Murmushi yay da
miƙama Khaleel ɗin dake gaishesa hannu alamar yafi son suyi musabaha. Hannu Khaleel
ya bashi suka gaisa, ya mika masa irin hular dake a kan duk wanda ke'a wajen. Babu
musu ya amsa ya saka, daga haka suka fara zagaya ginin da ayanzu ya fara bayyana
kansa gamai kallo. Tabbas aka kammala estate ɗin ba ƙaramin ƙyau da ɗaukar hankali
zaiyi ba. Duk inda suka gitta ma'aikata gaishesa suke da girmamawa shiko yana amsa
musu da kulawa. Inda yaga gyara yay magana, inda ya kamata ya yaba ya yaba musu.
Hakan sai ya ɗauke kaso mafi yawa na damuwar da yake a ciki har lokacin sallar
azhar yayi suka nufi massallaci. Koda aka idar da salla wani gidan cin abinci suka
nufa anan kusa da ƙafa. A lokacinne kiran Fadwa ya shigo wayarsa. Ɗagawa yay yakai
kunne sai dai baiyi magana ba.
Muryarta a raunane cikin kuma ɗari-ɗari tai masa sallama. Amsa mata yay kadaran
kadahan, sai duk ta daburce, amma cikin dauriya da in ina tace, “Am sorry dan
ALLAH. Wlhy babu ruwana sai da nace karsu je. Ganin bazasuji maganata ba yasa na
bisu da tunanin ko kana can.”
“Is ok”.
Ya faɗa a taƙaice. Ita tasan is not ok a cikin muryarsa. Amma sanin baya son nacin
magana saita saki waccan ɗin kamar yanda ya buƙata. “To ga abinci na kammala amma
naga baka dawo gida ba har yanzun”.
“Karki damu gashi zanci a inda nake”.
Zatai magana ya dakatar da ita da faɗin, “Zanci na dare idan na dawo bye” Ya
yanke batare da ya jira amsarta ba. Kiran nata ya ɗan sakama masa jin sassauci, dan
garama ita, Anaam ko zai cika duniya da fushi ai bata taɓa nuna masa ta damuba a
kwanakin datai gidan nasa duk da yasan sarai tana sane da komai na halin da yake a
ciki dangane da aurenta. Yaja siririn tsaki a ƙasan zuciyarsa yana ayyana (Zanyi
maganinki vary soon).
Khaleel da tun shigowarsu yana wajen siya musu abinci ya dawo tare da waiter
dake biye da shi. kujera yaja ya zauna. “Am sorry babban Yaya na daɗe”.
“Don't worry”.
Ya faɗa a taƙaice hankalinsa akan wayarsa. Sai da suka fara cin abincin a nutse
Khaleel ya ƙara maida hankalinsa garesa. “Yaya nikam kuna waya da Yaya Maheer?”.
Idanu ya ɗago ya zubama Khaleel ɗin, kafin kuma ya girgiza kansa alamar a'a.
Khaleel yaja numfashi ya fesar. Ruwa ya ɗauka ya ɗan sha ya ajiye. “Naje gidansa
jiya da yamma. Saboda su Abbah suna maganar ya daina zuwa gida gaba ɗaya sannan
wayoyinsa duk a rufe. Yaya banji daɗin yanda na samesa ba shida matarsa. Gaba ɗaya
Yaya Maheer ya canja tamkar bashi ba. Sam babu wata ƙyaƙyƙyawar alaƙa tsakaninsa da
matarsa abin ya tsoratani wlhy”.
Kasa magana yay ya kuma kasa cigaba da cin abinci har Khaleel yakai aya, sai
dai idanunsa gaba ɗaya launinsu ya sake canjawa. “Mike faruwa?”.
“Yaya komai ma na faruwa, a yanzu haka so take tabar gidan amma mahaifiyarta
ta tabbatar mata zata tsine mata inhar ta bari Yaya Maheer ya saketa. Shi kuma yaƙi
bata kowacce irin dama wlhy bakaga yanda yake treating nata ba like dai wadda suke
rayuwa a.... Mtsoww oh my god babu dai daɗin faɗa kawai. Na fara masa nasiha amma
yaƙi saurarena, daga ƙarshe ma a gabana ya mareta wai tana haɗashi da ƴan uwansa,
so abin is to much wlhy”.
Numfashi ya sauke zazzafa ransa duk a jagule. Still dai ya kasa cewa komai
kallon Khaleel ɗin kawai yakeyi. A ƙasan zuciyarsa kam yana jin rauni matuƙa. Ya
rasa miyyasa Mommy ta kasa fahimtar rayuwa irin ta yanzu ta aure tasha banban data
zamanin baya, a da daga maza har mata kowa nada kawaicin iya karɓar aure a duk
yanda yazo masa. Amma a yanzu ba haka baneba, auren soyayyar ma yaya aka ƙare balle
na tilastawa. Shi kansa dabai jureba za'a samu irin wannan matsalar ne a lokacin
data tilastashi auren Fadwa. Amma daya jure yayta gayama ALLAH da tilastama kansa
tanada mahimmancin amsar ko minene daga umarninta sai gashi ALLAH ya saka masa son
Fadwa ɗin. Sai dai Mommy ta kasa fahimtar shida Maheer za'a iya samun banbancin
juriya akan wannan al'amarin. A ganinsa data barshi ya aura wadda yake so da an
samu maslaha. Dan gashi abinda takema gudun bai tsallaketa ba tunda ga Anaam dai
matsayin matar gudan jinin nata bisa ƙaddarar UBANGIJI da babu wani hannu daya isa
gogewata....
Numfashi ya sauke a hankali saboda taɓasan da Khaleel yayi. Abincin suka
cigaba da ci batare da wani ya sake magana ba, sai dai Shareff tsakura kawai
yakeyi. Baimaci na kirki ba ya ture gefe. Haka Khaleel ya biya kuɗin suka sake
komawa wajen masu aikin. Har yamma yana a wajen, bai tafi ba sai da masu aikin suka
tashi. Sai da ya sai kayan fruits ya bama Khaleel ya kai musu can gida shi kuma ya
zuba na nasa gidan a mota shima ya wuce. Ana kiraye-kirayen sallar magrib ya shigo,
dan haka bai nema kowaba a cikinsu ya wuce sashensa. Ruwa ya fara watsawa jikinsa
na ɗumi a gaggauce, ya fito ya saka kaya nanma a gaggauce ya fice massallaci dan
har an fara sallama..........✍

_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_


*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:


07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇


09134848107

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*


[11/11, 12:16 PM] My Zafafa: *_Typing📲_*
*_BABU SO....!!_*
_(Miya kawo kishi?)_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718

*_57_*

.........A hankali ya tura ƙofar ɗakin laɓɓansa na motsawa alamar sallama, kamar
mai irga steps ɗinsa ya cigaba da shigowa cikin ɗakin idonsa akanta duk da
ƙudundune take cikin bargo, zaune ya kai gefenta tare da kai hannu ya yaye bargon.
A yanda ta miƙe zumbur da alama bata san da shigowar tasa ba. Idanunsa sukai
ƙyaƙyƙyawan ganin daya sakashi jan numfashi a fisge, dan shaiɗaniyar rigar jikinta
bata bar komai a sirrance ba, a waccan ranar ya ganta, sai dai a yau rigar tafi
bayyana masa komai har idonsa na neman tsolewa. Ita kuma data manta a yanda take
komawa tai zata kwanta cikin taɓe fuskarta dan wani haushinsa da takaicinsa ne suka
sake kamata. Riƙota yay, ta shiga fisgewa da fashe masa da kukan ƙarya.
“Ni ka sake min hannu, kuma bana son ganinka ka koma can wajenta ita matar
son naka, ƙarewar kiss kace ta cinyeka mana...”
Sassanyar ajiyar zuciya ya saki, komai baice ba, bai kuma saki hanun nata ba sai
dai murmushi ya suɓuce masa akan fuska kaɗan, ta cigaba da turesa da ƙoƙarin kai
masa ƴan ƙananun duka a damtsen hanunsa. Bai hanata ba yana dai ta ƙoƙarin danne
dariyarsa. Ganin abun nata bana ƙare bane ya rungumeta gaba ɗaya ya tura a jikinsa.
Duk yanda taso cigaba da fisge-fisgen ya hana hakan, ya fara kai ma fuskarta da
wuyanta kiss har yanzu murmushi bai bar fuskarsa ba. Ƙarfin kukanta ta ƙara da ture
masa fuska amma yaƙi ya daina, sai da yay mai isarsa sannan ya barta da ƙara
matseta a jikin nasa.
“Shikenan sai bori ya ƙare an biyaki kiss ɗinki, ai ban san kina so bane
amarya mai aji, nazo da ƙoƙon bara yau a barni na samu tubarrakin wannan tsadar
tsada sarauniyar mata kona samo tukuycin nan da kikai alƙawarin badawa”
Zabura tayi da nufin turesa tana waro ido sosai waje jin wai ashe duk yaji mita
faɗa ɗazun, amma yanda ya naɗeta a jikin nasa yasa baiko motsa ba. A karan farko ya
sakar mata siririyar dariya cikin kunnenta da cizonsa da haƙori. Ƙara ta saki kaɗan
duk da bawani zafi na azo a gani taji a cizon ba.
“Ni dai wlhy ka tashi ka fita yaya, kaje ka ƙarata da matarka ni duk abinda na
faɗa iya laɓɓana ne kaima kuma ka san...”
Ruff ya rufe bakin nata da nashi tare da ƙara matseta gamm ya fara mata wani
salo daya nema zuƙe numfashinta gaba ɗaya taja ajiyar zuciya tankar mai shirin
shiɗewa. Salo ne da bai taɓa kwatantashi ga wata bama, tun tana da zarrar yin
yunƙuri harya ci galaba a kanta ta koma masa laƙwas sai dai ta kasa maida murtani
sai ma jikinta dake tsuma.
“Yaya Please ALLAH wasa nake mata”. Ta faɗa a wahale tana janye bakinta daya
sassauta riƙewa a nasa. Ganin yana neman sake cafkowa ta tura kanta cikin ƙirjinsa
ta kanannaɗesa.
Murmushi ya saki da mata zobe da hannayensa, furzar da ƙaramar iska yay da
ɗaura bakinsa kan kunenta. Cikin wata irin kasalalliyar murya mai ɗaukar amon sauti
daga bututun gudun jini zuwa ƙahon zuciya ya fara fidda aman sauti “Haba autar mata
kiji tausayin yayanki mana ki basa dama ya tabbatar miki ke wacece a aikace. Ko
kina buƙatar sai naje ƙasa ne bayan kin gama min ɗaurin da wata ƴa mace bata taɓa
yima namiji ba.”
Kasancewar da yaren malay yake maganar babu shiri ta ɗago ruɗaɗɗun idanunta a
dalilin jin furucinsa. Cikin tsakkiyar ido suke kallon juna na kusan mintuna biyu,
daga ita har shi tsuma jikinsu yake kowa da abinda ke masa kaikawo a zuciya, lips
ɗinta suka shiga motsawa kamar zatai magana amma sai ya hana hakan ta hanyar haɗe
goshinsu waje guda. Baya buƙatar bata wani space a wannan gaɓar, dan ya tabbatar
hakan zai iya zame masa kuskure wajen tsaiwar amsa ɗunbin tambayoyin daya hanga
cikin idonta da bakinta.
Duk da a zaune suke gangar jikinsu ta kasa ɗaukarsu, dole yakai kwance da ita
jikinsa na matuƙar rawa da tsuma irin na an daɗe ba'a haɗuba, daɗin daɗawa kuma
ango yake, a yau zai sake zuwa irin duniyar da bazai taɓa mantawa da ita ba duk da
a waccan gaɓar shima ɗin ya jigatu, ya kuma wahala kasancewar na farko a garesa, a
yanzu kam sai dai ya zama malamin wasu inda ana koyarwa a aji.
Ya matuƙar rikita hankalin Anaam da wani sabon salo. Ta shiga ruɗani irin
wanda baka iya banbance fari da baƙi sam. Ita yanzu ba Anaam ɗin Abie da Mamie
bace, wata sabuwar Anaam ce a wata duniya da hasashe bai taɓa kaitaba koda a
lissafin hange. Ita ba Anaam ɗin data ɗauka alwashin jiran cikar watanni uku bane
na barin gidan Yayanta. Ita ba Anaam bace dake tuna da Yaya MM take tare. Ita ba
Anaam ɗin dake tuna bayan ita akwai wata mata tare da shi ba ce, ita ba Anaam ɗin
dake buƙatar ɗunbin amsoshin tambayoyinta daga garesa bace, ita ba... Ita ba... Da
yawa da bazata iya tunawa ba a karan kanta balle wani tsarinta ko burinta..
Tuni ya jima da rabata da rigar kamar yanda ya raba kansa da tasa suturar
shima, ya naɗesu a cikin bargo tare da mirginawa da su tsakkiyar gadon. A daidai
gaɓar da Anaam ta dawo hayyacinta kenan dan a yanzu an ɗauki wani layine daya sata
zaburowa a razane ta ƙwalla ƙara da ƙanƙamesa jikinta na rawa ta fara son turesa
cikin magiya da roƙo.... Da gaske baya jinta, sai dai rufewar idon tasa bata
hanashi fara ambaton addu'ar da MANZON ALLAH ya horar damu karantawaba yayin
ziyartar juna........

Sosai jikinta ke ɓari, tana saki wani irin nishin kuka mai ban tausayi irin
na wanda yay matuƙar galabaita da jigatuwa. Muryarta tayi ɗashewar da ba'a iya jin
wani furuci daga bakinta. A hankali ya mirgino gareta, a jikinsa ya maidata ya
rungume. Lallashinta yake son yayi, hawayenta yake son tsaidawa amma ya kasa. Ƙara
tsuma jikinsa yakeyi da wani irin karsashi da zuciya ce kaɗai mai ajiye da wannan
kundun sirrin bawai gangar jiki ko kalaman kan harshe ba. Bashi da wani zaɓi face
sake matseta a cikin jikin nashi yana mai jujjuya mata kansa duk da a cikin ɗan
hasken da suke na lamp bazai wadatar da idaniyar da yake da yaƙinin a rufe take iya
ganinsa ba.
“ALLAH yayi miki albarka”.
Ya iya furtawa da ƙyar kuma a fisge yana sake matseta tamkar ya tsaga fatar jikinsa
kawai ya turata ya huta. Tsahon lokaci ya kasa yanke shawarar abinyi na gaba, itako
tana faman cigaba da juya kanta dake a ƙirjinsa laɓɓanta na motsawa a hankali
alamar akwai abinda take faɗa da ba'aji, hawayenta masu ɗumi da zafi na cigaba da
sauka a ƙirjinsa kai kace zata iya ƙarar da su ne a wannan dare baki ɗaya.
Jin kamar jikinta ya saki ya saka zuciyarsa harbawa da ƙarfi, babu shiri ya
miƙa hannu ya kunna fitilar ɗakin. Sosai firgici ya bayyana akan fuskarsa, yatsunsa
biyu ya ɗaura a kan hancinta. Da gaske bata numfashi. Zuciyarsa tai wani uban
tsalle tamkar zata fito waje. Kansa ya dafe da cije lips ɗinsa da ƙarfi yana
ambaton sunan ALLAH. Sai kuma ya shimfiɗeta saman filo ya fara laluben abinda zai
suturta jikinsa. Rigarsa ya samo da ƙyar acan ƙasa, baiko saka botiran dai-dai ba
ya sauka zuwa gefen gadon. Ruwan daya shigo da shi ya ɓallema murfi, ya zuba a
tafin hanunsa ya shafa mata a fuskarta dake jage-jage da hawaye. Babu alamar zata
kawo numfashi. Ruwan ya gumtsa ya fesa mata a fuska. Gaba ɗayanta ta zaburo tare da
jan numfashi mai ƙarfi. Da zafin nama ya tallaffota ta koma cikin tafin hanunsa,
“Juwairiyya!”.
Ya faɗa cikin sarƙewar harshe...
Jin bata amsa ba kamar ma ta ƙara koma masa lakaf ya sake girgiza mata kai ta
hanyar rike haɓarta da sake kiran sunanta cikin nutsuwa.
“K! Juwairiyya K!?”.
Siririn kuka ta sakar masa, murya a ɗashe tace, “Zafi, wayyo Mamie na”.
Ta furta da ƙyar da buɗe idanunta kaɗan sai kuma ta maida ta rufe kanta na juyawa
kaɗan-kaɗan.
“Ya ALLAH! ALLAH!!”.
Ya faɗa da sake girgizatan, sai kuma ya mannata da ƙirjinsa ya ƙanƙame ya kama
hanunta ya fara murza tafin cikin kulawa. Wani bahagon numfashi ta fusga azabar
zafi na ƙara ratsata. Sai dai bata da ƙarfin koda ƙanƙamesa balle gane a halin
rayuwa take ko mutuwa. Yasan Anaam nada raki, sannan akwai ƙarancin ƙwarin zuciya
na ɗaukar wahala a tattare da ita saboda yanayin rayuwar data tashi. Ita ɗin ƴar
gata ce, rainon madara da biscuits da chocolates😝, bata taɓa fuskantar makamanciyar
wahala irin wannan ba a rayuwarta. Abinda ta sani kawai taci ta sha ta tafi
makaranta, koda ya kama tayi wani aiki bamai yawa bane da zai tabbatar mata da ana
wahala a duniya. Gashi kuma yasan baizo mata da sauƙi ba sakamakon tunaninsa
shekarunta zasu iya ɗauka, bai san abun ba'a shekarun yake ba dan ƙarfin zuciya da
juriyar ɗaukar wahala babu ruwanta da shekaru...

Sabon ragwanci da raki ya ƙara ɓarkewa a toilet yayin yake taimaka mata
wajen samun nutsuwa dan ya fahimci wannan itace masalaha ta farko daya kamata ya
bata agaji da ita. Kuka take masa sosai irin wanda yafi na farko dan a ɗazun wahala
ta hanata yin kukan. Yanzu kam saita samu damar ɓarje guminta wajen yinsa fiye da
abinda takeji. Rashin ƙarfin jiki ya tilastata sallama masa dole yana jujjuyata a
yanda yake so cikin ruwan zafin. Koba komai ta ɗanji sassauci, sai dai hawayeta sun
gagara tsayawa dan su kaɗai ne abinda take iyayi wajen nuna irin raɗaɗin da takeji
da galabaitar da rayuwarta da yayi. A cikin ruwan ya barota ya fito, ya kintsa
gadon ta hanyar canja bedsheet sannan ya koma fito da ita. Har cikin rai tausayi
take bashi, duk da ya fahimci rakinta ne gaba-gaba wajen sake girmama narkewar
tata. Koma dai minene ai shi ya takaloma kansa tunda yasan hali. Tun yana hasashen
zatai haƙuri tai shiru sai saɓanin haka ya biyo baya, dan kuwa ƙiri-ƙiri ta hanasu
barci sai gabanin asuba da ɓarawon yaci galaba a kanta. Kansa ya girgiza kawai, dan
bai taɓa sanin darun yarinyar nan da rikicinta yakai faɗin haka ba sai a yau.
Rashin barcin da wuri ya jawo musu makara. Bai fara tashinta ba sai da ya idar da
tasa sallar, abinda yake gudunne kuwa ya faru, dan rikice masan ta farayi da kuku
wuwu. Haka kawai yake jin nauyi da kunyarta shi kansa, domin yasan dai magana ta
ƙare tunda a daren jiya ta gama ganin ƙarshen girmansa duk da matsayin ƙanwa da
take da shi a garesa. Da farko ya lallaɓata har tai salla, ganin fa bata san zuru
ba ya rumtse ido cike da borin kunya ya balbaleta da masifar da bata kai ciki ba,
dan da ƙarfin hali yake yinta kawai....
“Kin isheni fa da kuka. Idan baki rufamin bakinki da kukan banzar nan ba
ALLAH yagalgalaki zanyi da safen nan, dan na fahimci kukan naki harda na rashin
ƙoshin dalilin yinsa...”
Kukan ta sake fashe masa da shi tana duƙunƙune kanta cikin bargo, dan hatta
muryarsa razani take saka mata a zuciya. Tsoronsa takeji mai girma da tsananin
shakkarsa. Ta cigaba da hawayenta batare da barin sautin kukan na fita ba sai dai
yana jin yanda take jaa da shaƙar ajiyar zuciya tamkar zata shiɗe. Tashi yay ya
fita, mintuna kaɗan sai gashi da kofin shayi. Yasan halin butsutsunta, dan haka ya
ɗaure fuska cikin bada umarni yace ta tashi. Duk yanda taso zama da ƙyau domin
shakkarsa ta gagara hakan, dole sai jinginata yay da jikinsa zuciyarsa na raya masa
akwai matsala kenan. Da kansa ya bata tea ɗin tana sha da ƙyar, ko rabi bataiba
tace ta ƙoshi. Bai barta ba har sai da ta ƙara sha, ya bata paracetamol dan jikinta
akwai zazzaɓi. Kwanciya yay da sakata jikinsa yana shafa bayanta, sai kuma ya
sumbaci kanta dake a ƙirjinsa da ƙara rungumeta da ƙyau, cikin lallashi ya fara
magana a kunnenta...
“Kukan ya isa haka to mai tsadar tsada uhhmyim. Ko kina so a dinga kiranki
raguwa ne? Jarumar mace bata irin wannan rakin da kike yi ai. Bakinki taf da tsiwa
amma sai ragwantaka”.
Kukan ta sake fashe masa dashi da son turesa a jikinta amma bata da ƙarfi, yay
murmushi da sake sumbatar kanta. “Oh ashe kinada sauran ƙarfi ma na wani zauna
kallonki, bara na sake komawa kawai ko zan ƙara farauto baby na uku, dan insha
ALLAHU jiya dai na samar da biyu da zakiyi tukuyci da su.........✍
_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_


*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:


07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇


09134848107

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*


[11/11, 12:16 PM] My Zafafa: *_Typing📲_*

*_BABU SO....!!_*
_(Miya kawo kishi?)_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718

*_56_*
.........Bai shigo ba sai da aka idar da sallar isha'i. Ya kwashi ledojin daya bari
a mota. Na Fadwa ya fara ɗauka ya nufi sashenta. A falo ya sameta zaune cikin
kwalliya da waya a hannu. Ga tv a kunne tana faman aiki. Yana mamakin yanda a koda
yaushe waya bata barin hanunta, tun baya maida hankali akan hakan har ya fara sosa
ransa, sai dai bazaiyi maganaba a yanzu sai anzo gaɓar data dace.
Fuskarta ƙawace da murmushi ta taso garesa. Rungumesa tai da manna masa kiss
a kuncinsa na dama. Ya sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi dan babu abinda yafi buƙata
kamar ɗumin matarsa a yanzu. Ya sani ba ƙaramar jarumta yayi ba, dan rabonsa da
Fadwa kusan sati uku kenan cikin na huɗu. Hanunta saƙale a wuyansa fuskarsu gab da
juna. Bakinsu take son haɗewa amma ya kauda kai kaɗan dan ya tabbata ya biye mata
bazai iya ƙyaleta ba kuma hakan ba daidai bane ba tunda akwai haƙƙin wata a kansa
bayan ita ɗin.
Cikin son basar da ita ya janye hanunta dake saƙale a wuyansa yana faɗin, “Ki
shirya abincin”. Jiki a sanyaye ta gyaɗa masa kai, harya nufi ƙofa ta kasa haƙuri.
“Har yanzu baka huceba ko? Kana ganin laifi na!”.
Tsayawa yay, sai da takai aya ya waiwayo yana kallonta. Tai ƙasa da kanta
zuciyarta na sake raunana dan da gaske abin ya dameta. Shima ɗin ta bashi tausayi,
dan shi shaida ne Fadwa nada tsoro da tsananin gudun ɓacin ransa, wannan halin nata
na ɗaya daga cikin abinda ya saka masa sonta. “Zan iya miki uziri ana yau, amma ki
kiyaye dan anan gaba makamancin haka ta sake faruwa ni kaina ban san irin matakin
dazan iya ɗauka ba har asu kansu, dan bazan ɗauka wulaƙanta matata da hanani zaman
lafiya ba a gidana”.
Bai jira cewartaba ya fice. Ajiyar zuciya ta sauke mai nauyi, zuciyarta na
rage cinkushewar da tai......

Idar da sallarta kenan takai bakin gado, muryar Mamie take son ji duk da sun
gaisa ɗazun da safe. Maimakon normal kira saita ji sha'awar kiranta video call.
Tana ƙoƙarin yin hakan da ɓare lollipop sweet takai baki ya shigo ɗakin. Ɗagowa tai
suka haɗa ido, tai saurin janye nata dan wani irin matsanancin kunyarsa ta tsinci
kanta a ciki saboda abinda ya faru ɗazun da shi ta yini cikin rai. Inda taken ya
ƙaraso ya zauna kusa da ita gab. Batare data sake iya ɗagowa ta kallesa ba tace,
“Barka da dawowa”.
“Uhhumm”.
Ya faɗa a miskile idonsa nabin jikinta da kallo. Kaya ƙanana ne da sukai matuƙar
kama ɗan jikinta komai ya fita fili tamkar an zana. Ya janye a kasalance dan dama
acan ɗin ma kwalliyar Fadwa ba karamin tasiri tai a ransa ba. Ya yarda matan nasa
duk ƴan gayu ne, sai dai Fadwa tafi Anaam son ƙyale-ƙyale, dan da wuya kaga fuskar
Fadwa babu kwalliya hakan kuma na matuƙar burgesa. Saɓanin Anaam da zai iya cewa
bai taɓa ganin kwalliya ba a fuskar tata ba, sai dai idan ya manta. Idan son samune
itama zai so ta dingayi ɗin dan yana da tabbacin zata mata ƙyau.
“Da rana mi kika ci?”.
Ya jeho mata tamyar idonsa na kallon bakinta dake juya alawar a ciki batare data
riƙe tsinken ba. Yanzu ma bata iya ta kallesa ba, ta damƙe wayarta da take juya a
hanunta da ƙyau. Muryarta can ƙasa tace, “Noodles”.
Ɗan jimm yay da tunanin taya ta dafa. “Dami kika dafa to?”.
Ɗagowa tai ta dubesa da mamaki. “Kamar ya?”.
“Nasan baki da gas ai”.
“Nayi amfani da electric ne”.
Ajiyar zuciya ya sauke na samun nutsuwa, dan gaba ɗaya ya shafa'a ne ma, dama yau
yaso a siyo mata gas ɗin a kuma haɗa mata tvn ta.. Duk yanda yaso basar da abinda
ke tsikararsa ya kasa. Ƙara matso jikinsa yay a nata sosai da riƙo hannayenta duka
numfashinsa na sauka a gefen wuyanta. A take tsigar jikinta ta tashi, taja jikinta
baya zata matsa ya rungumota, kallonsa tai fuska a marairaice, sai dai bazata iya
jurewa ba tai ƙoƙarin rissinarwa amma sai ya hana hakan ta hanyar tallafo haɓarta..
“Yanzu tsabar rowa bazaki sammin sweet ɗin ba?”.
Wutar kan Anaam neman ɗaukewa tai, tsigar jikinta ta tashi har tana ƙoƙarin yadda
alawar babu shiri. Gaba ɗaya yanayin nasa da muryar dayay amfani wajen mata maganar
ya matuƙar rikitata, dan bata taɓa jin irin muryar tare da shi ba. Hannu takai jiki
a mace zata zare alawar a bakinta ya riƙe hanun tare da matsota suna kallon juna
cikin ido.
“A haka nake son sha”.
(Ya ALLAH) ta faɗa cikin zuciyarta, a zahiri kam tuni idanunta sun fara marmarin
firgici da tsantsar mamakinsa. Ya kashe mata ido ɗaya da sake kusanta fuskarsu,
baya ta ƙara jan jikinta ya bita, ta ƙara matsawa shima ya matsa, ta ƙara ya ƙara,
sai kawai ta zube a gadon da ƙokarin tufo alawar waje kawai a ganinta hakan shine
mafita gareta.
Murmushi ya saki a karo na farko, shanyayyun idanunsa da launinsu ya canja
gaba ɗaya na bin fuskarta da kallo, ya ɗauka alawar ya saka a bakinsa ya ɓalla
kaɗan. “Ni ban iya rowa ba zan sammiki” ya faɗa tare da ɗage mata gira ɗaya yana
matso da bakinsa gab da nata.
“Ba gashi nan na baka ba”. Ta faɗa a hankali kamar mai raɗa.
“A cikin bakinki nake son sha ni”. “Ban yarda ba”.
“Ba sai kin yarda ba dama tunda nawa ne”.
“Naka? Yaushe ya zam....” Ruff ya rufe bakin tare da tura mata sweet ɗin a
nata bakin, ya haɗa da harshenta ya fara tsotsa. Wani irin miƙewa illahirin gashin
jikinta sukai, takai hanunta saman ƙeyarsa da nufin janye masa kai hakan ya gagara.
Domin wani irin salo yake mata mai narkar da ita, dole ta lumshe idanunta a hankali
ta fara bashi gudunmawa. Sai da suka shanye alawar tas a cikin bakinta sannan ya
janye. Kanta ta kauda gefe wata irin kunyarsa mai girma na ratsata. Sassanyan
murmushi ya saki da leƙa fuskartata, tai saurin ɗaukar fillo ta ɗora tana murmushi
itama. Ƴar dariya yayi da ƙoƙarin tashi tsaye. “Ga tsoro ga tsiwa, kona dawo mu
shanye sauran?”.
Da ƙyar ta iya fisgar numfashi ta haɗiye, ta bude idanu hannunta dafe da
ƙirjinta. Dariyarsa ya danne da ƙyar yana gyara rigarsa da jifanta da wani kallo
daya sata janye nata idon akan sa, “Oya tashi muje cin abinci”. Ajiyar zuciyar ta
ƙara saki, batare data yarda ta kallesaba ta girgiza masa kanta. “Ni na ƙoshi fa”.
“Amma kin san zan iya ɗaukarki daga nan har can kuma akwai Matata”.
Har cikin rai maganarsa ta soketa, to ina ruwanta wayace ba matar tasa
bace. Ta murgiɗa baki a zahiri da ɗauke kai gefe tana ƙunƙuni. (Wani yace ba
matarka bace balle ka mana burga). Sarai ya jita, amma sai baice komai ba ya ɗan
matso kusa da ita. Zabura tai gefe tana tura baki. “To bana tashi ba dai”. Hanya ya
nuna mata. Hijjabin sallarta ta zara dayin gaba tana kumbura fuska, ya biyota a
baya yana murmushi dan ya gama yanke shawarar ayita ta ƙare kawai ya tabbata haka
shi zai kawo masalaha ta ƙarshe da zuciyarsa ke tabbatar masa..

Sun sami Fadwa harta kammala shirya abinci, a cikinsu babu wadda ta kalli ƴar
uwarta, kuma kowacce ta tsuke fuska babu sauƙi. Shi dai ya cigaba da shan alawarsa
yana ƙumshe dariya, a zahiri kam shima tashi fuskar a tsuken take. Fadwa dake zuba
masa abinci ta ɗago tana kallonsa, da ido yay mata alamar thanks. Ta ɗan saki
murmushi, sai dai ta tsurama sweet ɗin bakinsa ido. Fahimtar hakan da yayne ya
sashi zarota ya miƙa mata, ƴar kaɗan ta rage a jiki yama kusa shanyewa, hannu ta
kawo zata amsa fuskarta da murmushi itama Anaam dake ɗayan gefensa tai kamar zata
ɗauka kofi ta tanƙwaɓe hanunsa sweet ɗin ta faɗa cikin miya. Fiskewa tai kamar
bataga abinda tai ba, hasalima taƙi kallonsu. Wani irin takaici da baƙin ciki ya
turnuƙe zuciyar Fadwa, amma sai batace komaiba.
Kallonta yay ta gefe ido shikam dai, sai kuma ya maida ga abincinsa guntun
murmushi na suɓuce masa. Ganin har sun fara cin abincin bata da alamar zubawa ya
sake ɗagowa ya kalleta. “K bazaki ci abincin ba?”.
Fuska ta ɗan yatsina da taɓe baki, “Ni ban iya cinshi ba”. Karon farko Fadwa ta
kalleta, itama fuskar ta yamutse baki a taɓe. Cikin gatse da jin bazata iya shiru
ba tace,
“Sai ki fara koya ai”.
Itama a gatsen da taɓe baki tace, “Ba buƙatar hakan”.
Baki Fadwa ta sake laɓewa da ɗauke kai abinta. Itama sai ta harareta ta cigaba da
buga game ɗinta.
Duk yana jinsu amma yay shiru bai sake yin magana ba, sai ma hankalinsa daya
maida ga abincinsa hankali a kwance kamar bai san sunai ba. Har suka kammala dai
Anaam bata ci ba, shine ya fara barin dining ɗin ya koma falo ya zauna. Fadwa dake
shan lemo a hankali ta saki murmushi, dan da farko tayi zaton zai kama lallashi
Anaam ɗinne kamar yanda ta san itama Anaam ɗin tayi ne dan ya lallasheta. Amma sai
gashi yay biris. Mikewa tai tana tattare kayan da sakin ƴar karamar dariya. “To
mudai wannan amarya ta gidanmu uhumm babu alamar ta cika amarya, hausawa na cewa
amarya kota buzuzu ce ɗokinta ake, sai dai mu gata mutum a namu gidan bata da wani
fawa”.
Da gaske saƙon na Fadwa yana isa har tsakkiyar kan Anaam. Dan kuwa da turanci
take maganar hakan yasa komai ta jisa. Zuciyarta ta fara luguden dakan fusata da
sukar da kalaman ke mata amma sai ta saki murmushi a zahiri. Babu burin zamanta a
wannan gidan hakan yasa bata fatan Shareff ya nema wani abu a gareta, dan hatta
kissing ɗinta da yakeyi tayi alƙawarin baza'a sake na huɗu ba. Sai dai tabbas saita
shayar da Fadwa mamaki cikin sauƙi batare da ta rasa mutuncin nata da take tattali
ba... A yanzu dai batace komai ba har Fadwa na koƙarin barin wajen fuskarta ƙawace
da murmushi. cigaba da zama a dining ɗin tai kamar mai latsa waya, a zahiri kam
komai ta kasayi tsabar raɗaɗin da ƙirjinta ke mata.....
“Amarsu mu kuna lafiya”..
Fadwa ta faɗa tana ɗaga mata yatsu biyu da ɗan ranƙwafawa ta sumbaci gefen fuskar
Shareff. Fuskar tata ya shafo shima yana murmushi. Idanunta da suka ciko da ƙwalla
ta kauda daga kansu, dama ta gefen ido take kallonsu. Jitai bazata iya barmata ba,
dan haka ta miƙe tasha gaban Fadwa dake gab da fita...
Cike da salon ƙularwa fuskarta ƙawace da murmushi take kallon Fadwa da
mamakin yanda ta tareta ya sata diriricewa, to amma a gareta hakan zai zama riba
tunda tasan Shareff bazai ragawa Anaam ɗin ba.
Anaam data gama fahimtarta ta ƙara sakin murmushi da naɗe hannayenta a ƙirji
“Amaryar data kai mace ba'a samunta ta sauƙi ai, saboda tsadarta tafi tsada tsada
madam, ki rubuta ki aje a duk lokacin dana sallama wlhy sai kin zama ƴar kallo a
wajen mijin naki, idan kin isa mu ƙulla”. Ta ƙare maganar ƙasa-ƙasa tana kashema
Fadwa ido.
Yawu mai kauri Fadwa ta haɗiya saboda ganin alwashi cikin idanun Anaam, ta saci
kallon gefen Shareff sai taga su yake kallo. Murmushi ta saki cike da kirsa. “Ayya
Anaam miya faru da wannan magana haka?, ai shi ɗin mijinmu ne mu duka ba nawa
kawaiba, kinga kuwa basai mun ƙulla wata yarjejeniya a kansa ba, kuma indai nice
wlhy nama ƙara muku sati biyu akan ɗayan”.
Anaam dako kallon inda Shareff yake batayi ta saki wata siririyar dariya data
ƙona ran Fadwa da tafa hannayenta. “Woow! kai kai kai Uwargida abun birgewa. Muna
godiya da wannan ƙyauta mai tsada”. Sai kuma ta kashe mata ido da maida muryarta
can ƙasa kamar mai raɗa. “Karki damu kinada kaso, za'a samo miki tukuycin baby da
zaina tayaki hira tunda kin hana masa zuwan abokin wasansa yayansa duniya”.
Duk da a hankali sosai Anaam ta faɗi furucin ƙarshe kaɗan ya rage zuciyar
Fadwa ta wantsalo waje. “Sautin bai miki ba na ƙara n.....” Da sauri Fadwa ta
fice cikin sassarfa daga falon, wani irin zufa na tsatstsafowa ta illahirin ƙofofin
jikinta har tana kifawa kamar zata faɗi. Anaam ta danne dariyarta da ƙyar, da binta
da kallo harta fice. Sai da Fadwan ta fita da kusan mintuna biyu sannan tabi
bayanta zuciyarta fes tunda ta rama.
Da kallo ya bita ta gefen ido, ya jinjina kansa da sakin murmushi dan duk
abinda ya faru a tsakaninsu yaji. Hatta maganar farko da Fadwa tai a dining, yayi
shirune dama dan yaga wane mataki ita kuma Anaam ɗin zata ɗauka. Wato Fadwa a
gabansa ne take nuna ita ɗin mutuniyar kirkice, ita kuma Anaam bata iya ɓoye-ɓoye
ba sai take nuna nata babu wani munafurci a ciki. idan ya auna da kallonsa da Fadwa
takeyi tana magana cikin canja yanayi danta kunnasa ne ya hau kan Anaam kenan kamar
yanda taga yanayi a kwana biyun nan idan tai makirci. Lallai mata sai ka barsu,
idan kai wasa sai su kaika wuta da sheɗana, dolene ya nutsu wajen ƙara fahimtar
halayen kowacce kuwa.
Duk yanda yaso cigaba dayin kallon kasa hakan yay, dan kalaman Anaam babu
abinda suke sai tsikarar zuciyarsa, dole ya miƙe ya kashe komai ya shiga bedroom
ɗinsa. Sabon shirin barci ya sabunta da mulke jikinsa da turarurrukansa masu ƙamshi
har kusan kala biyar, haka kawai yake jin saka ɗaya bai gamsar da shi ba. Bakinsa
kansa yasha Mouth fresheners kusan kala uku, ya sake duban kansa a mirror ya saki
murmushi da kashema kansa ido ɗaya... _“Dole ne yau a tabbatar min da wannan
tsadar da tafi tsadar tsada my girl”_.

★Ransa fes ya fito hanunsa ɗauke da fresh milk. Kansa tsaye sashen Anaam ɗin
ya nufa, baiyi mamakin rashin ganinta a falo ba. Sai da ya fara shiga kitchen ya
ɗauka ruwa da glass cup sannan ya nufi bedroom ɗinta bayan ya kashe komai ya rufe
ko ina.
Tunda ta fito a sashensa da murmushi ta iso nata sashen, ya kuma gagara barin
fuskarta har tai shirin barci dan dama tayi wankanta, brush kawai tayi ta haye gado
batare data ɗaura jacket ɗin rigar barcin ba a kan ta cikin data kasance ƴar
fingila iyakar cinyoyinta, sannan hanunta siriri ne. Rufda ciki ta kwanta da jan
bargo ta lulluɓe har kanta tana cigaba da sakin murmushi.........✍

_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_


*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:


07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇


09134848107

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*


[11/14, 4:12 PM] My Zafafa: *_Typing📲_*
*_BABU SO....!!_*
_(Miya kawo kishi?)_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718

*_58_*

Assalamualaikum

NAFISAT K ABDULLAHI
Is an actress in the kannywood industry

She's a singer and can sing all types of songs

You can't afford to miss her newly released song named *KADDARATA* part 1-4 on her
YouTube channel *OFFICIAL FEENAT*

You can only click on this link and stand a chance to listen and watch her
amazing video

https://youtu.be/t__84EwU7Fo

Dont only enjoy the emotional video but also *SUBSCRIBE* to anable you to be
notified when ever she upload another video

Like and drop your comment under the video to encourage her do more of that .

The only way you can support and encourage her is by *SUBSCRIBING* to her YouTube
channel below

https://youtu.be/t__84EwU7Fo

She is used to noticing those following and commenting on her videos .

*GUESS WHAT*?

https://youtu.be/t__84EwU7Fo

Click and see for yourself


Thank you so much
_______________________

........Hanunta take ɗagawa daƙyar tana kai masa ƙananun duka, ya fara ƴar dariya
da ƙoƙarin riƙe hannayen nata. Duk yanda yaso su koma barci hakan ya gagara, dan
ƙorafinta na zafi da raki ya gagara tsayawa. Ga zazzaɓi mai zafi dake ƙara rufeta
bayan sauka ya kamata yayi tunda tasha magani. Dole ya tashi zaune da ita a jikinsa
yana ƙoƙarin son su haɗa ido amma taƙi yarda. Bai damu da hakan ba, dan yasan kunya
dole ce. Shi kansa wani nauyi yakeji amma yana ta ƙoƙarin ganin ya fuske abinsa..
“Faɗamin miye matsalarki kuma Noorii na?”.
Shiru ta kasa bashi amsa, sai ƙoƙarin son kauda kanta kuma take yaƙi bata dama.
Dole ta buɗe baki muryarta a ɗashe irin ta wanda yaci kuka ya more, dan ko fita
batayi da ƙyau. “Inajin zafi mai raɗaɗi, dan ALLAH ka kiramin Mamie ko ka kaini
wajenta”.
A ransa yace, (Ko ɗaya a ciki bazaki samu ba) a zahiri kam wayarsa ya ɗauka
zuciyarsa na masa kaikawo akan waya dace ya kira. Har yai dailing number Dr Jamal
sai kuma ya katse, text message ya tura masa. mintuna kaɗan kuwa sai ga kiransa.
Kamar bazai ɗauka ba sai kuma ya ɗaga da miƙewa ya fice a ɗakin.
“Malam ba kirana nace kayi ba, Nurse daka aminta da ita nace ka turamin”.
Dr Jamal yay murmushi da shafa kai daga can, “Oh to ai ko asibitin ban
fitaba shiyyasa nace bara na kiraka naji waye babu lafiya?”. Jimm yay na wasu ƴan
sakkani, sai kuma ya furzar da huci a hankali ya furta “Juwairiyya!”.
“Ayya ALLAH ya bata lafiya, mizai hana ka kaita asibiti kawai sai mu haɗu, dan
gaskiya a iya hasashena ban san wace Nurse zan tura maka ba indai irin wadda nasan
zaka buƙata ce. Amma Dr Bilkisu na tabbatar ta iso yanzu zatafi kulawa da ita da
sanin matsalarta kai tsaye inma mune baka son mu duba maka ita..”
“Kai ka sani”.
Ya bashi amsa a taƙaice da yanke wayar. Daga can Dr Jamal yay ƴar dariya da ajiye
wayar ƙasan zuciyarsa na masa kaikawo amma yana turewa dan yayi alƙawarin mantawa
da ita, zai cigaba da mata kallone kawai irin na ƙanwa kuma matar amininsa insha
ALLAHU.
Shawarar Jamal ta masa, dan haka ya taimakawa Anaam daketa hawaye har yanzu
ta shirya, shima dai a gurguje yay nasa shirin. Duk yanda yaso tai taku daga
bedroom zuwa waje ta kasa, ko bedroom ɗin ta kasa iya ƙarasa fitowa zafi kawai take
ambata tana hawaye, gashi duk ta langaɓe masa kamar mara ƙashi a jiki. Dole ya
ɗauketa gaba ɗayanta ya fito.....

★Ranta fes ta tashi yau kamar yanda ta kwanta sakamakon jin ƙwarin gwiwa daga
sirrin su aunty Safarah. Gaba ɗaya cikin yaƙini da imanin maganin da suka batan
yayi aiki take. Tana idar da salla cike da karsashi ta shiga kitchen da kanta haɗa
breakfast. Hakan ba ƙaramin mamaki ya bama maman Abu ba. Sai dai bata iya cewa
komai ba dan ta fahimci uwar ɗakin nata tana a farin ciki, tasan kuma yana da
nasaba ne da abinda taga tanayi jiya. Sai taji inama zata fahimceta kuma ta isa ta
bata shawara akan abinda take kallo ba komaiba. Taji sanda su aunty Safarah ke
tabbatar mata maganin matane suka bata, ita kuma ta aminta da hakan saboda bata da
ilimin banbancewa, ta sani Fadwa nada rawar kai da ɗagawa, dan duk wanda ya kwana
ya tashi a gidansu yasan ita ɗin boss ce musamman akan ƴan aiki, to amma kuma duk
da kasancewarta a haka ɗin bata taɓa tunanin ganinta da wani mugun hali da ya zarta
waɗannan ɗin ba, tanaji a ranta kuma da wani zai fahimtar da ita abinda su aunty
malika suka bata nada banbanci da maganin mata ƙila bazatai amfani dashi ba duk da
bata san zuciyarta ba dai.
Tana aikin gyaran sashen nata ita kuma tana haɗa breakfast mai rai da lafiya a
kuma nutse, dan dama dai shiriritarta da son jiki ke hanata yi ɗin a yanda ya
kamata bawai dan bata iya ba. Cikin ƙanƙanin lokaci ƙamshi ya gauraye ko'ina, cike
da nishaɗi ta kammala ta koma bedroom ta gyara jikinta. A yau zata kawo duk wani
iskanci da jiji da kan Anaam a gidan nan, dan babban burinta tai gaba ta barta da
mijinta salin alin.
Ƙarfe takwas da wasu ƴan mintuna ta nufi sashensa dan tasan ya tashi zuwa
yanzu, shi ba ma'abocin barcin safe baneba ma, amma a yanzu tunda yana gida ba aiki
zai fitaba tasan ko yaya zai ɗan kwanta.....

Fitowar Fadwa yayi dai-dai da fitowarsa ɗauke da Anaam daga sashenta. Babu
shiri taja birki ƙirjinta na dukan tara-tara bama uku ba, shi sam baimaganta ba dan
hankalinsa gaba ɗaya ya tafine ga kallon Anaam yana murmushi, saboda tsokanarta
yake akan raguwace ita tana tuttura masa baki da kauda fuskarta gefe. Anaam ɗin kam
sarai ta ganta, duk da halin da take ciki hakan bai hanata ganin wannan wata dama
bace, ada taƙi yarda ta riƙesa, a yanzu kam saita saƙalo hannayenta a wuyansa duk
biyu tana sake sakin kuka da cusa kanta a ƙirjinsa. Shiko da bai san dalilin yin
hakan ba sai ya ɗan manna mata kiss a goshi da sakin siririyar dariya. A hankaki
yake taku har zuwa wajen motar tasa, ya dureta ƙasa tare da jinginata da motar.
“Ina zuwa”.
Ya faɗa yana barin wajen, batace komai ba sai dai idanunta na satar kallon sashen
da Fadwa dake binsu da kallo har yanzu kamar a birkice take. Da sauri Fadwa tai
baya alamar bata buƙatar ya ganta, shima da yake ALLAH yasa hankalinsa ba wajen
yake ba sai bai lura da ita ba ya wuce yanzu ma. Mintuna da basu fi uku ba ya sake
fitowa hannunsa da key ɗin motarsa. Sake wucewa yay abinsa batare da yanzu ɗin ma
ya ganta ba dai...
A gaban idonta ya sake ɗaukar Anaam ya saka a mota, shima ya shiga suka fice
gidan. Tai baya kamar zata faɗi maman Abu da itama komai ya faru akan idonta ta
riƙota. “Hajiya dan ALLAH ki kwantar da hankalinki”. Maman Abu ta faɗa muryarta
cike da damuwa itama. Da taimakonta Fadwa ta koma ciki, ta ɗakko mata ruwa amma sai
ta hankaɗar da shi ya zube, wasu zafafan hawaye da sai yanzu suka sami damar fita a
idanunsata suka shiga rige-rigen sauka a fuskarta. Maman Abu dai batai fushiba,
takai zaune kusa da ƙafafunta a ɗarare ta sake faɗin, “Hajiya dan ALLAH karki ɗaga
hankalinki, wannan kaɗanne daga halin maza idan suka ƙara aure. Amma inaga ki
bincika kiji mike faruwa tukunna kamar zaifi. Koba komai kin jefa tsuntsu ɗaya da
dutse biyu. Na farko dai zaki san mike faruwa, na biyu kuma zaiji kunyarki idan
fitar bata da wata babban dalili da farar safiyar nan. Amma idan na shiga hurumin
daba nawa ba kiyi haƙuri..”
Idanu Fadwa ta sake rumtsewa da ƙarfi zuciyarta na wani irin zafi da raɗaɗi,
dan tabbas abinda Shareff yayi ya sake zuzuta zafin daya sauka mata lokaci guda,
kishi ya rufe idonta ta kasa ji a ranta wata matsalace ta sakasu fita gidan da
safen nan bawai lafiya ba.....
Waya ta ɗauka da sauri ta fara laluben layin aunty Safarah. Bata tsaya ko
gaisuwa ba ta sakar mata kuka.
“Subahanallahi Fadwa lafiya kuwa?”.
“Aunty Wlhy maganin beyiba, yanzu fa da safen nan ya fito ɗauke da ita suna
farin cikinsu da dariya suka bar gidan nan. Alhalin jiya babu wani kusanci
makamancin hakan tattare dasu. Aunty na shiga uku idan hankalinsa ya koma kan
yarinyar nan. Jiyafa taimin alwashin indai ya fara kasancewa da ita saina zama ƴar
kallo....”
“Kinga nutsu ki saurareni Fadwa. A yanzu haka gani tare da Aunty (Gwaggo
halima) kuma duk tana jinki, dama nazone zan amsa sako da zamuje wani waje saboda
ke”.
Sunan maman ta fara kira cikin kuka, Gwaggo Halima da tun fara bayanin Fadwa
wutar kanta ya ɗauke saboda shi babba duk inda yake babba sunansa, tuni zuciyarta
ta hasko mata wani abu ya shiga tsakanin Shareff da Anaam kenan, dukan kokarinsu na
hana faruwar hakan bai yuwuba kenan, taja numfashi. “Fadwa kinga nutsu kuka ba naki
baneba. Karki damu damun bayanin komai na riga na sani domin ni na aiko su Safarah
wajenki dama nace ne karsu faɗa miki. Yanzu ki jira zamu kiraki ina zuwa...”
Kafin tace wani abu aka yanke wayar, ta zube a bakin gado da sake fashewa da
kuka mai cin rai....

_______

Cikin ƙanƙanin lokaci suka iso asibitin, yanzu dai taso nuna jarumtar hanashi
taɓata amma ina hakan bai yuwu ba. Dan taku biyu kacal ta nema zubewa tamkar ta
fasa ihu dan zafi. Dole dai ya ƙaraso ya ɗauketa.
“Ni dai Yaya ka saukeni zan iya”.
Ta faɗa tana sharce hawayen dake ambaliya akan fuskarta saboda hango Dr Jamal dake
nufosu alamar yasan da zuwan nasu.
Murmushi yay da kashe mata ido ɗaya “Da wannan tafiyar tonamin asirin ne zaki
iya?”.
Idanunta ta rumtse kunyar duniya a kanta, dan gani take kowa zai iya sanin
miya faru da ita ne. Da taimakon Dr Jamal suka sami ganin Dr Bilkisu a sahun farko.
Ganin Anaam taƙi amsa tambaya ko guda ɗaya a gaban Shareff daya tsatstsareta da ido
yasa Dr Bilkisu kallonsa da ɗan murmushi. “Alhaji Al-Mustapha ko zaka ɗan bamu
wajene dan naga patient ɗin tawa kasancewarka tare damu ya hanata cewa komai”.
Ido suka sake haɗawa da Anaam. Tai azamar janye nata da tura masa baki.
Mikewa yay yana murmushi batare da yace komai ba ya fita. Ko'a bayan fitar tasa ma
sai da Dr Bilkisu ta sha fama sannan Anaam ta amsa mata wasu daga cikin tambayoyin
nata tana faman sinne kai, a yanda ta fahimci ta kasa zama da ƙyau tai hasashen
abinda Anaam ɗin ke faman ɓoyewa. Batace komai ba ta taimaka mata zuwa gadon da
suke duba marasa lafiya, ganin tana neman ɗage mata doguwar riga ta riƙe da sauri
tana girgiza kanta...........✍

_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_


*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:


07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇


09134848107

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*


[11/14, 4:13 PM] My Zafafa: *_Typing📲_*

*_BABU SO....!!_*
_(Miya kawo kishi?)_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718

*_59_*

.........Murmushi Dr Bilkisu tayi, cikin sigar lallashi tace, “Kiyi haƙuri dubawa
kawai zanyi, dan idan yazam yaji miki ciwo ne ba'a ɗauki mataki ba nan gaba zaki
iya fuskantar wata matsalar da ba'a fata. Gara tun yanzu yana a ɗanyensa a ɗauka
mataki kinji ƙanwata. Badan Anaam taso ba ta bar Dr Bilkisu ta duba, dan sosai ta
dinga lallaɓata da nuna mata illar rashin dubawar harta amince.
“Ya ALLAH”. Dr Bilkisu ta faɗa da sakin rigar Anaam ɗin takai hanunta saman
goshi tana murzawa. Sosai ranta ya sosu, sai dai kuma ta fahimci matsalar daga
jikin Anaam ɗinne. Amma duk da haka an nuna mata mazantaka da yawa da ƙawazuci.
A tsorace Anaam dake kallonta tace, “Doctor wajen ya daina aiki ko?”.
Murmushin da babu niyya Dr Bilkisu ta saki, ta girgiza kanta da kallonta. “A'a bai
daina aiki ba ƙanwata, kawai dai anyi ɓarna ne da alama angon naki tsohon tuzurune
halan shiyyasa ya gagara binki a sannu. Gaskiya yayi miki ɓarna da yawa da dole sai
anyi ɗinki”.
“Na shiga uku”.
Anaam ta faɗa tana fashewa da kuka. “A'a kinga kwantar da hankalinki baki shiga uku
ba. Mata da yawa sunci karo da matsala fiye da taki ma a dalilin first night, ban
san mike damun mazan ba da suke muku irin wannan zuwan haka, ko soyayyace ke
ingizasu oho, koda yake suma iyaye akwai laifinsu, zaka kai yarinya buduwa gidan
miji amma kaita tsumata da kayan mata. Sune suke saka gushewar hankalin mafi yawan
mazan har su aikata mummunar ɓarna ga yarinya, a yanzu haka inada irin cases ɗin
nan da yawa ga wata can ma kwana uku kenan da mata ɗinki har huɗu kaɗan ma ya rage
ita mijin ya kasheta dan a sume aka kawo mana ita tana bleeding kamar mai haihuwa”
(Iyaye wlhy da gaske matsalar nan tana cutar da yaranmu, maganar mai ɗinki da
bleeding ɗin nan da nake muku ya faru a gaske ALLAH har kuka naima yarinyar, amma
koda aka binciki mijin iya gaskiyarsa ya faɗa cewar ya fita hayyacinsa ta yanda ya
gagara jin tausayinta balle tuna ita din virgin ce, koda yarinyar ma akaji ta
bakinta daga baya akan ko tasha wani abu ne bata ɓoye ba ta sanar da irin kayan
matan da aka dinga ɗirka mata har ji ta dingayi kamar ta jawo auren koma ta bashi
kanta kafin a ɗaura. Ya ALLAH, iyaye mata a duba dan ALLAH a gyara, ƴarki budurwa
ce bata san komai ba, koda ɗan kayan fruit kika gyarata da su zuma da mazarƙwaila
sun wadatar ai, sai maganin sanyi da a kullum bana gajiya da tuna muku shine mafi
muhimmanci kafin kikai ƴarki gidan aure ki tabbatar bata tare da imfection yafi
maganin matar nan da za'a iya cutar miki da yarinya a dalilinsu. Dan mazan da yawa
sukan kasa controling kansu ne harsu fatattaka miki yarinya a banza taje yoyon
fitsari ya sameta. Dan waccan yarinyar da nake gaya muku sai da yakai ko fitsari
bata iyayi da kanta saida taimakon robon fitsari tsahon wasu wattani. Shin riba
akaci ko faɗuwa kenan🤦🏻?).
Kuka sosai Anaam ta dingayi har ba'ajin sautin muryarta a yayin da ake
mata ɗinkin, tabbas ita din ragguwace bata wasa ba. Ko yaya abu ya sameta ta dinga
raki ke nan balle wannan da ya zame mata makafin ajewa a tarihi dan bata taɓa
riskar azaba makamancin hakanba. Shareff yasha tarin ALLAH ya isa da inda tarasu
za'ai waje guda buhu-buhu zai ɗiba ya kaima Mommy ajiya saboda tarihi😝😆.
Sosai ya dinga kaikawo dan yana iya jiyo kukanta da kiran Abie da Mamie da
take famanyi, har da wasu a ALLAH ya saka matan da take ambata da ja masa ALLAH ya
isa. Sosai hankalinsa a tashe yake dajin ɗunbin tausayinta da takaicin kansa. Da
yanada damar dawo da ciwon jikinsa da yayi ko zai samu sassauci a zucyarsa, dan
itaɗin wata abace mai daraja a zuciyarsa da baki ko alƙalami ƙaryarsa zanawa. Ita
ke kukan amma tare suke raba raɗaɗin a zuciya. Koda aka kammala Dr Bilkisu tasa aka
kaita wani ɗaki danta huta yana shigowa ta fashe da kuka wai bata son ganinsa Dr
Bilkisu ta koresa. Duk da haushinsa da Dr Bilkisu keji kasa daurewa tai sai da tai
dariya. “Tunda patient ɗina bata bukatar ganinka jeka abunka mun sallamaka Alhaji
Al-Mustapha. Dan gaskiya kai mai laifine mai girma a wajenmu ɗin”.
“Gutun murmushi ya ɗanyi iya laɓɓa sai dai bai fitan ba. Ya jingina da bango
hannayensa zube cikin aljihun wandonsa ya zuba mata idanu. Bargo taja ta rufe har
fuskarta ita a dole bata buƙatar ganinsa ɗin dai. Dr Bilkisu ta janye daga kallonta
tana ƙara sakin ƴar dariya itama. Inaga ka bata dama ta huce sai muyi magana a
office”.
Kansa ya jinjina mata kawai. Ta juya ta fita. Cigaba yay da tsaiwa a wajen har
bayan minti biyu da fitarta sannan yabi bayanta, har sannan kuma Anaam bata buɗe
fuskar taba ɗin.

A office ɗin doctor batare data kallesa ba ta miƙa masa takardar data gama
rubutu a jiki. “Taji ciwo ne, amma mun mata ɗinki. Na fahimci cewa ƙaramin jiki
ALLAH ya bata, amma shekarunta sun kai ga hakan. Sai dai kuma yanayin halittarta
tana buƙatar bi a sannu, domin masu irin yanayinta zakaga ko'a wajen haihuwa ana
shan fama dasu matuƙa saboda jikinsu bashi da wani ƙwarin gaske, sauƙinta ma ita
tanada wannan ƙaramin jikinne, da irin raɓo-raɓo ɗin nan take akwai matsala, hakan
na nufin ko anan gaba za'a bita a hankali inba hakaba kullum zata dinga shan ɗinki
kenan. A yanzu dai zan riƙeta anan gaskiya har zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu ta
samu nutsuwa yanda ya kamata saina baka ita da sharuɗɗa masu tsauri. Muna buƙatar
waɗan nan drugs ɗin dana rubuta anan.”
“Uhhim”.
Kawai ya faɗa yana miƙewa. Dr Bilkisu ta bisa da kallon mamaki, irin miskilan
mutanen nan na bata tsoro, sai sun tafka tsiya ka rasa ta inda zaka auna yaya ma
sukai. Kiji fa ta gama masa bayani akan kuskurensa ya bita da ‘uhhim’ kawai tsabar
miskilanci. Bai san ta ɗaga masa ƙafa bane kawai saboda Dr Jamal. Amma da yaga
yanda ake ruwan masifa yau, duk da kwarjininsa shima ya taka rawar gani wajen cika
mata ido ko fushinta ta gagara nuna masa akan fuskarta.
Pharmacy ɗin asibitin ya nufa domin sayo magungunan, sai da aka gama haɗawa
zai ɗauka waya dan musu transfer yaji babu wayar a jikinsa, kansa ya dafe yana
ambaton sunan ALLAH. Dole ya bar musu maganin akan zaije ya dawo. Ɗakin da take ya
sake komawa, saboda yana son jin ko tana buƙatar wani abu. Samu yay tana barci a
yanda ya suka barta, ya kai hannu ya yaye bargon data lulluɓe har kanta tare da
kaiwa tsugunne gaban gadon. Duk da barci take kumburin idonta bai hana ya bayyana
ba, ya saki murmushi yatsansa na kaiwa a saman idanun ya shafa, a hankali ya
gangaro har saman fuskarta zuwa lips ɗinta. Yatsansa ya shiga zagayawa a kansu,
kafin ya sake matsar da fuskarsa gab da tata murya ƙasa-ƙasa ya furta “Tabbas kin
cika mai tsadar da tafi tsada tsada autar mata”. Ya ƙare maganar da manna mata lips
ɗinta kiss
Motsawa tai tamkar wadda ta jisa, ya sake sakin murmushi yana cigaba da
kallonta. Tsahon minti biyu sannan ya miƙe tsaye, ɗan ranƙwafawa yay a kanta ya
tsotsa lips din nata da sumbatar goshinta ya ƙara miƙewa. Kaɗan ya ɗalli lips ɗin
da yatsansa. “Bari muga idan bakin tsiwar zai mutu”. Ya faɗa akan lips ɗinsa har
yanzu murmushi bai bar fuskarsa ba....

Duk yanda mmn Abu ta lallaɓata akan ta koma ciki ta kasa motsawa, dan haka
harya dawo gidan tana a wajen zaune ita bamai rai ba ita ba sumammiya ba, har yanzu
kuma su Gwaggo halima basu kiratanba. Bai shigo ciki da mota ba, dan haka har ya
ƙaraso bata san da shi ba. Yay tsaye yana mata kallon mamaki ganin hawaye share-
share akan fuskarta dan ma wasu sun jima da bushewa...
“Baki da lafiya ne?”.
Ya faɗa yana kaiwa tsugunne gabanta da ɗago fuskarta daya riƙo haɓarta da hanunsa
na dama. Maimakon amsa sai kawai ta sakar masa sabon kuka. Sosai hankalinsa ya
tashi, dan zuciyarsa ta fara ayyana masa ko wanine ya mutu ma.
“Ya salam, wai mike faruwa? Wani ne ya mutu ina magana kin mun shiru?”.
Hanunsa tai ƙoƙarin turewa zata miƙe ya maidata ya zaunar. “Fadwa....!”
ya faɗa aɗan tsawace
“Ni ka ƙyale ni!!”.
Ta faɗa a matuƙar tsawace itama da fisge duka jikinta ta shige ciki a fusace.
Kallo ya bita da shi ransa na sosuwa da mamakinta, shi yarinyar nan takema tsawa
wai?. Kallonsa yakai ga Mmn Abu dake tsaye kanta a ƙasa idonsa cike da matuƙar
ɓacin rai. “Mi'aka mata?”.
“Nima Alhaji ban saniba, tun ɗazun dai na sameta tana kuka anan lokacin
da zaka fita da Hajiya Amarya”.
Ɗan jimm yay na tunani yana idonsa akan Mmn Abu ɗin har yanzu. Komai baice ba
yay wucewarsa sashensa yana jan tsaki. Akan kwanikan abinci da aka ajiye ya fara
sauke idonsa, kenan idan lissafinsa yayi dai-dai Fadwa taga fitarsa da Anaam shine
take wannan haukar. Ƙaramin tsaki yaja da girgiza kansa kawai ya shige bedroom. Bai
jimaba ya fito. Sashen Anaam yaje, ya ɗauka mata abinda za'a buƙata ya sake ficewa
a gidan batare da yabi takan Fadwan ba.

Tun a hanya ya sayo dukkan maganin, koda ya dawo asibitin har lokacin tana
barci, ya ajiye kayan ya nufi office ɗin Dr Jamal. Saida suka fito yin sallar azhar
ya ɗan leƙa Anaam, har lokacin barci take, dan haka Dr Jamal yasa wata Nurse shiga
ta zauna da ita saboda Shareff yace masa zaije wani waje daga nan tunda yaga ba
yanzu zata farka ba....
Barci tasha sosai, sai kusan biyu da rabi ta farka. Jinta take kamar ana
mammatsa mata ƙasusuwa, ga ɗinkin da akai matan nayi mata kamar a takure babu dai
daɗi. Nurse ɗin nan ta taimaka mata zuwa bayi kamar yanda ta buƙata. Harda kukanta
wajen yin fitsari, wani haushin Shareff na ƙara zuwa mata a maƙoshi. A daddafe ta
sake fitowa da taimakon Nurse ɗin, tai salla jiri na ɗibarta na yunwa da rashin jin
daɗin jiki. Ta idar da sallar tana addu'ar ya shigo da sallama Aysha biye da shi
ɗauke da basket, Aunty Mimi a bayansu. Batai niyyar ko kallonsa ba, sai dai jin
muryar Aunty Mimi da Aysha ya sakata ɗagowa da sauri.........✍

_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_


*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇


09134848107

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*


[11/14, 4:13 PM] My Zafafa: *_Typing📲_*

*_BABU SO....!!_*
_(Miya kawo kishi?)_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718

*_60_*

.......Cikin nasa idanun suka shiga, sakamakon kallonta yake shima. A karan farko
taji hakan babban abune a gareta kallon tsakkiyar idonsa tai masa koda harara ne.
Janyewa tai a kasalance ta maida ga Aysha dake kallonta fuska da damuwa duk da bata
san mike damu ƴar uwar tata ba. Dan ita dai tana gida ya kirata a waya wai ta ɗakko
kaya kala ɗata ta fito ta samesa an kwantar da Anaam asibiti. Ya kuma mata gargaɗin
karta sanarma kowa, Mommy ma tace mata zataje waje Fadwa ne. Hakaɗin tayi shine ta
sami damar fitowa dan itama Mommyn na buƙatar aje mata gidan Shareff ɗin duk da
tasan ba lallai ta sami abinda take so ga Ayshan ba. Amma tasan ta inda zata dinga
binta tana jin koma ai. Amma sai ta kasa kallon aunty Mimi da itama kallonta take
duk da bata san mike damunta ba, ya sanar mata dai kawai Anaam babu lafiya, sai dai
bai son su Mamie su sani.
Matsowa Aysha tai suka rungume juna, idon Anaam cike da ƙwalla.
“Blood mike damunki?”.
Ɗan satar kallonsa tai shi da aunty mimi, idanunsa ƙyam a kansu, Hawayenta ta share
da girgiza mata kai kawai alamar babu komai.
“Blood ba'a zuwa asibiti ai babu komai, dan ALLAH ki faɗamin”.
Katse Ayshan yay da faɗin, “Idan kinji maganin mi haka zai miki?, malama tashi
ki bata abinci ban son surutu mara amfani”.
Badan Aysha taso ba dole tai shiru. Aunty Mimi ta ƙaraso ta zauna saman
kujera, gaba ɗaya Anaam ta kasa kallonta, idanunta a rissine tace “Ummi good
afternoon”.
“How are you feeling?”.
Kasa amsawa tai sai hawaye data matso. Aunty mimi tai murmushi, “Mamana har
yanzu baki san kin girma ba, shagwaɓa dai shagwaɓa dai why?” nanma batace komai ba,
aunty mimi da zuciyarta ke ɗan hasko mata wani abu ta kalla Shareff, shima kansa
yay saurin kaudawa gefe yana shafo bayan ƙeyarsa da hannu. “Humm” tace kawai. Itace
ta taimaka mata ta koma saman gadon. Aysha kuma ta fara zuba mata abinci. Takowa
yay daga inda yake tsaye ya zauna kusa da ita a gefen gadon. Jitai kamar ta makesa
sai dai babu dama. Koda Aysha ta gama zuba abincin shine ya amsa, sake gyara
zamansa yay yana fuskantarta da ƙyau, sai dai taƙi yarda koda wasa su haɗa ido.
“Ko zaki sha tea ne kafin kici abincin?”. Ya faɗa idonsa a kanta. Girgiza masa
nata kan tayi, murya a shaƙe tace, “Bazanci komai ba na ƙoshi”.
Komai baice mata ba, ya ɗibo abincin zuwa bakinta yana faɗin, “Hahh!”.
Sosai ta ƙwaɓe fuska, ta ɗan ɗago cikin marairaicewa tana kallonsa, sai kuma ta
saci kallon gefen aunty mimi. Ganin basu take kallo ba ta ɗanji sassauci kaɗan.
Kanta ta girgiza masa “Banajin cin komai ALLAH”.
Ƙasa-ƙasa yace, “Gashi kuma dole sai kin ci! In ba haka ba kuma.....” ya ɗage
mata gira ɗaya batare daya ƙarasa faɗaba. Dole badan taso ba ta buɗe bakin ya fara
bata abincin da tun a ɗanɗanon farko ta gane girkin Mamienta ne. Kasa ɓoyewa tai.
“Yaya wajen Mamie ka amso min abinci?”.
Kansa ya jinjina mata da kai babban yatsansa ya goge mata mai daya taɓa gefen
bakinta. Sai taji kunya ta kamata kasancewar Aunty mimi da Aysha a ɗakin. Shiko
babu alamar hakan ya damesa ma ya sake miƙa mata wani daya ɗibo a spoon. A haka Dr
Bilkisu ta shigo ta samesu yana bata abincin, a ranta ta ayyana (Maza ga zaƙi ga
harbi kenan). A zahiri kam idonta akan Anaam tana murmushi. “Masha ALLAH my patient
jiki yayi daɗi”.
Cikowa idanun Anaam sukai da hawaye, ta girguzama Doctor kanta. “Har yanzu
inajin ciwo a wajen”.
Idanu ya waro da sauri jin zatai masa fallasa, ya daura yatsansa akan lips
ɗinsa alamar tai shiru, ta gefe kuma yana nuna mata aunty Mimi da ido. Sai dai kuma
bai san sarai aunty mimin na kallonsu ba ita da doctor. Ta ƙunshe dariya da kyar,
Dr Bilkisu dai kasa dannewa tai sai da tayi tata.
“Ayya karki damu insha ALLAHU zai daina, idan na sallameku zan baki dukkan dabarun
da zasu taimaka miki har ki dawo normal a cigaba da amarci ko”.
God forbid”.
Ta faɗa a hankali samman lips ɗinta. Da ɗan ɗagowa zata hararesa suka kuwa haɗa
ido. Babu shiri ta mayar ta risinar. Har doctor ta gama ƙara duddubata bata sake
yarda ta kalla sashen da yake ba dan tuni tace masa ta ƙoshi da abincin. Shima dai
kunya ta hanashi sake wani motsi, dan ya san dai aunty mimi ta gama fahimtar komai
kuma. Magungunnanta ya bata ta sha kamar yanda Doctor tace. Sai da ya tabbatar
komai yayi normal sannan ya mike yana kallon agogon hanunsa.
“Small Mom ni zanje gida nai wanka bara na maidaki, inaga sai zuwa anjima
zan dawo. Aysha ki kula da ita idan da buƙatar wani abu sai ki kirani a waya. Bana
buƙatar wani yasan da zamanku anan, idan hakan ta faru ranki sai yafi nawa ɓaci”.
Aysha ta amsa masa da to.
“Karka damu Babana jeka kawai harka dawo, bara naga likitar nan. Aunty Mimi ta faɗa
kai tsaye tana miƙewa ta fita. (Shike nan na mutu) ya ayyana a ransa da bin aunty
Mimin da kallo. Itako Anaam tuni tai kwanciyartama ta juya musu baya. Har tayi
zaton ya fice sai ga saukar numfashinsa a cikin kunnenta, da sauri ta juyo dan ta
tsorata, hakan ya bawa fuskarsu damar haɗuwa, ƙoƙarin jan tata tai baya ya hana
hakan ta hanyar riƙota.
_“Ina alfahari da ke a wannan rana, alfahari irin wanda zuciya bazata iya
ƙayyadewa ba, hannu bazai iya zanawa ba, ke ɗin zinariya ce, idan nace zinariya ina
tabbatarwa duniya zinariya a tsakkiyar duhuwar jeji, amsar itace, *Haskenki kaɗai
za'a iya gani*”._
Daburcewa tai, sakamakon saukar lips ɗinsa akan nata, ta shiga son ture masa
fuska, amma yaƙi yarda da hakan har sai da yay yanda yake so da ita. Yana sakinta
sashen da Aysha da aunty mimi suke ta fara kalla, sai dai wayam da alama ma duka
basa a ɗakin. Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke da saurin kauda kanta saboda ido da
suka haɗa da shi. Murmushi ya saki mai faɗi da yalwa dan ya fahimci catake su Aysha
na a ɗakin.
Sake ranƙwafowa yay kanta har lokacin murmushi shimfiɗe a fuskar tasa. “A
ƙara ko? Nima ban ƙoshiba”.
Ture fuskarsa tai da sauri tana jan bedsheet ɗin dake a matsayin bargo ta
ƙudundune kanta. Murmushinsa ne ya ƙara faɗaɗa, ya girgiza kansa kawai da juyawa ya
fice a ɗakin.

Sallamar Aysha ta sakata sakin ajiyar zuciya, sai da taji ta zauna a kusa da
ita sannan ta buɗe kanta. “Da alama dai kin samu sauƙi tunda naga Yaya ya fita yana
faman murmushi”.
(Ba dole ya fita yana murmushi ba tunda ya gama yayyagani) a fili kam sai ta
taɓe baki da yunƙurawa zata tashi zaune. Taimaka mata Ayshan tayi ta zauna cikin
dauriya dan ƙasanta sosai yake mata zafi zamanma dai tayisane irin na kishingiɗa
ɗin nan..
Aysha ta sauke ajiyar zuya tana kallonta, “Dan ALLAH ki kwantar da hakainki na
tabbatar zaki ji daɗin zama da Yaya Shareff insha ALLAHU Blood. Yanada ƙyawawan
halaye da lokaci ne zai tabbatar miki da hakan kamar yanda nasan kema kina da su.
Hatta Fadwa bana son ki biye mata dan ita kanta komai na ƙiyayyarki tanayine ba'a
kan tunaninta ba, tunanin su Mommy shike sarrafata tun farko, amma wlhy inhar kika
jajirce sai kin ƙwace komai kuma a hankali Mommy zata fahimceki halayen banzar da
Gwaggo ta ɗorata a kai duk zata ajiyesu kodan son da takema Yaya”.
A karan farko Anaam ta saki murmushi. “Blood wannan ba magana bace ta nan,
Please share kawai yanzu dai ya mutanen gidan? Ina kewarsu ALLAH kamar nai
tsuntsuwa na ganni ciki”.
“Aiko bazaki ganki ɗin nan ba, dan a gabana su Abba sukace kar Yaya ya kawoki
gida sai bikina”.
Sosai ta waro idanu waje, “Bikinki fa? Hum'um ALLAH bazan iya ba. Dana koma
aiki monday zaku ganni”.
“Hhhhh ashe Yaya zai ɓalla miki ƙafar baya kuwa”.
(Yanzu ma ai ya ɓalla min) Anaam ta faɗa a zuciyarta, a zahiri kam sai tayi
murmushi kawai....

★★★★

Yanzun ma daya dawo gidan bayan la'asar yaso shareta, sai dai zuciyarsa ta
gargaɗesa a kan hakan dan koba komai hakkintane a wuyansa. A falo ya sameta zaune
ta ƙurama tv ido. Mmn Abu na daga kitchen tana aiki dafa mata indomie dan duk yau
taƙi cin komai sai tea kawai. Sai yanzu da yunwar ta cita ne sosai bayan tayi wanka
ta fito falo tasa mmn Abu din ta dafa mata. Kallo ɗaya tai masa ta kauda kanta, sai
dai ta amsa masa sallamar da yay ciki-ciki itama akan lips. Motsin mmn Abu a
kitchen ya sashi wucewa bedroom.
“Ki sameni a ciki”.
Shiru kamar bazata bisaba, sai raka bayansa da tai da harara ƙasa-ƙasa. Sai da taja
kusan mintuna biyu sannan ta miƙe ta bisa. Tsaye ta samesa ya jingina da mirror.
Taima fuskarsa kallo ɗaya ta ɗauke kanta da kaiwa zaune bakin gado.
“Ɗazun ina tambayarki mike damunki kin tashi kin barni saboda raini. Ina
gargaɗinki da karki tsiro da wata sabuwar ɗabi'ar banza, hakan zai sa mu sami
matsala da kowaccenku idan tace zata dinga kawomin raini wlhy”.
Tasan halinsa, dan haka a hankali tace, “Kayi haƙuri”. Batare data ɗago
idanunta da suka cika da ƙwalla ba.
Duk girman laifin dakai masa idan ka bashi haƙuri yakan ɗanji sassauci ko yaya.
Dan haka ya furzar da huci kawai. Sai kuma ya sake kafeta da idanun nasa. “Kina
fushi da ni saboda na fita da ƴar uwarki, maimakon ki fara neman ba'asin mike
faruwa kodan jimawar da kikaga munyi a waje batare da mun dawo ba. Sannan yanayin
dana fita da ita a gidan nan yana nuna akwai matsala amma duk kika zaɓi ganin
baƙina akan bincikawar!”.
Hawayen da take maƙalewa ne suka silalo mata. Tasa hannu ta sharesu. “Ni
baca nai kayi laifi ba, amma ya kamata tunda ina a gidan na sani, a ƙalla dai an
nuna inada daraja ko yayane, amma ta gabana ka wucefa Soulmate tamkar baka ganni ba
saboda ka ɗauka mace a hanunka....”
“Macen dana ɗauka matata ce, kinga hakan yana nufin babu haramci a ciki
kenan, kema kuma nasha ɗaukar taki ai. Ki tsaya a laifin ba'a faɗa mikiba kawai
bawai ɗaukarta ba. Sannan wannan ya zama na farko ya zama na ƙarshe da zanzo ina
miki magana koda kuwa laifin na miki ki maimaita irin abinda kikaimin ɗazun, bazan
ɗauki wannan salon ba ga kowace”.
Duk da maganganunsa sun ƙona mata zuciya saita jinjina masa kai kawai. Shima
bai sake cewa komaiba yay ficewarsa zuwa sashensa. Har yanzu ba'a kwashe kayan
abincin safen ba. Dan haka yay kiranta a waya. Tana ɗagawa ya sanar mata tazo ta
kwashesu ya yanke wayar.
Wanka yay, koda ya fito sai ya ɗan kwanta duk da barci yake sonyiba yana
son hutawa dan shi ɗin kansa jikinsa duk ciwo yake masa. Ga yunwa na cinsa kaɗan-
kaɗan dan duk yau bai wani ci abincin kirki ba. Lokacin da sukaje salla da Dr Jamal
bayan sun fito massallaci gidan abinci sukaje. Amma sai ya kasa nutsuwar cin komai
sai doughnut kawai ya ɗanci da drink. Daga nan ya nufi gidansu sai dai bai shiga
wajen su Mommy ba ya shiga nasu Anaam da niyyar ɗakko Amrah ta zauna da ita a
asibiti sai ya iske bata nan. Mamie tayi masa tayin abinci amma sai yace ya ƙoshi
yana sauri ne, amma baiwar ALLAHr sai gata da shi ta haɗo a basket saboda tasan
abincin da yake matuƙar so ne. Harda plate da drink da alama tayi tunanin office
zai koma dan yace mata yazo ɗaukar wasu takardune zai koma wajen aiki. A sirrance
ya sanarma Aunty Mimi suka fito tare kamar zasu cikin gida, hakan yasa Mamie bata
sani ba. Abincinne ya kaima Anaam taci shiko baima cin ba duk da yana so..........

_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_


*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:


07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇


09134848107

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*


[11/14, 9:00 PM] My Zafafa: *_Typing📲_*
*_BABU SO....!!_*
_(Miya kawo kishi?)_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718

*_61_*

........Aunty mimi ta ɗan jima wajen doctor Bilkisu sannan ta dawo, sai faman
murmushi take, a ranta kuwa faɗi take (ƴan banza kukace da bakwa son juna. Yanzu
kuma ina ƙiyayyar taje harda ɗinki?). A zahiri kam zama tai tana kallon Anaam
daketa faman sinne kai taƙi yarda su haɗa ido sam. “Wai nikam na zama surukarki ne
halan Mamana? Tun ɗazu sai wani sissinemin kai kikeyi daga ke har mijin naki wani
abu ya faru ne?”.
Dariya Aysha ta sanya. “Ummie surukartace ke mana, ba ɗanki take aure ba”.
Dariya itama Aunty Mimi ta sanya da faɗin, “Bayan haka ma akwai dai wata a ƙasa
ma”. Anaam ta ballama Aysha dake ƙara kwashewa da dariya harara. Sai kuma ta koma
ta kwanta tare da lulluɓe har kanta tana murmushi.

★Da shirin tafiya massallaci daga can ya wuce asibiti ya fito. Har yayi
niyyar ficewarsa sai kuma ya shiga wajen Fadwa. Samunta yay tayi alwala. Yanzu kam
ya ɗanga sassauci a fuskarta, sai dai ba'a sake masaba yanda aka saba. (Idan ka
biye ta matan nan baka da maraba da ball ɗin ƙwallonsu) ya ayyana a ransa. A fili
kam sai ya juya kamar zai koma yana faɗi,
“Zanje masallaci, daga can zan wuce asibiti”.
Muryarta a dasashe batare data kallesaba tace, “Bara nai sallar sai na jiraka
nima zanje na dubata”.
Yanji daɗi har cikin ransa. Dan haka yace, “Okay”. yana ficewa. Da kallo ta bisa,
ta sauke ajiyar zuciya da taune lips ɗinta ta haɗiye abinda ya tokare mata maƙoshi.
Batai niyyar zuwa ba, Mamanta ce ta kirata tace taje, kuma ta saki ranta duk wani
fishi da takeyi ta dainashi hakan zai bama shirinsu damar tafiya yanda suke so.
Maimakon yin sallar magrib ya shigo sai da yay isha'i, ya iske ta cikin
shiri dan haka basu ɓata lokaci ba suka fito mmn Abu biye da su da abincin da Fadwa
ta sakata shiryawa wanda tayine saboda maigidan. Sai dai kuma Gwaggo halima tace
mata ta ɗaukesa ta kaima Anaam ɗin, itama kuma sai ta yarda da hakan tunda da wuya
yace zaici a yanda yake kan dokin zuciyarnan. Shiru motar babu mai magana har suka
fito daga layinsu. Ya harba motar saman babban titi.
Ɗan kallonsa tai ta gefen ido. Har yanzu fuskarsa ciɗin-ciɗin babu alamar
fara'a, sai tuƙinsa ma yake tamkar bai san da zamanta a motar ba. Idonta ya ciko da
ƙwalla ta maida kanta gefe tana ƙoƙarin haɗiyesu. A wajen masu saida fruits ya
tsaya ya sayi laida biyu yasa a baya, ya kuma tsayawa ya sayi gasashen kifi shima
ya saka a baya.
“Sorry na saki jira”.
Kanta ta girgiza masa.
“Babu komai”.
Bai sake cewa komai ba ya tada motar sukai gaba.

★Suna kallon film a wayar Aysha suka shigo, Aunty Mimi kuma nakan sallaya
tana addu'a dan ta idar da sallar isha'i ne. Sam Anaam bata kawo a ranta ganin
Fadwa ba. Sai da Aysha ta ambaci sunata sannan ta ɗago. Kallon juna sukai cikin
ido. Kowanne ya janye lokaci guda. Aysha ta sauka a gadon da sauri ganin Shareff na
kaiwa zaune kusa da Anaam ɗin yana nunama Fadwa kujera.
“Kun daiyi salla ko? Da kuka zauna kallon film?”.
“Eh Yaya munyi”
Cewar Aysha. Oganniyar kam tayi kicin-kicin da fuska sabida wani takaici taji na
ganin Fadwa. A tunaninta kawai ya kwashe sirrinta ya faɗama Fadwar ne....
Murmushi yayi da ɗan leƙa fuskar tata. “Har yanzu fushin ne autar mata?”.
Cin dauriya da son cusama Fadwa baƙin ciki ta saki ɗan murmushi. Cikin
disashiyar muryarta da tura baki tace, “Ni nace ina fushi ne dama?”.
“Uhm-uhm fa, bayan ɗazun har ana jeramin ALLAH ya isa da juyamin baya”.
Da sauri ta saci kallon Aunty mimi, sai taga sallama ta sake kabbarawa da
alama shafa'i da wutiri zatai, ganin idon Fadwa a kansu sai ta sakeyi murmushi da
ɗan kallonsa. Sai dai batace komai ba ta janye dan kallonta yake cikin wani yanayi
daya saka tsigar jikinta tashi lokaci guda. Shima murmushi yayi idonsa akanta ko
ƙyaftawa bayayi kamar ma ya manta Fadwa na tare da su fa a wajen, ga Aysha kuma da
aunty Mimi.
“Kar dai a sani yarda babu komi aje can ana kuka a bayan idona. Dan naga ke
kam baki raina abin kuka”.
Cikin ɗan tura baki tace, “Kuka ai rahama ne”.
“ALLAH?”.
Ya faɗa cikin sigar tambaya da ƙoƙarin ɗago fuskarta.
Murmushi tai da ture masa hannu tana kauda fuskarta gefe. Yay ƴar dariya kawai
da jinjina kansa.
Fadwa daketa ƙoƙarin danne hawayen da suka ciko mata idanu ta ɗan dubi Anaam.
“Ya jiki? ALLAH ya ƙara afuwa”.
Ciki-ciki ta amsa mata, batare data yarda ta kalleta ba. Dai-dai nan Aunty Mimi
ta idar da salla, Shareff ya juya yana gaisheta. Amsawa tai da kulawa tare da duban
Fadwa data ɗauke kai bata da alamar gaishetan ita. Murmushi kawai aunty Mimi tayi
“Fadwa kuna lafiya ko?”.
Yitai kamar bataji ba, Shareff ya kalleta cikin ɓacin rai a ɗan kausashe yace,
“Kina cikin hankalinki kuwa? Itace zatama gaisheki?”.
“Nagafa tana salla ne shiyyasa”. Sai ta juya tana gaisheta. Tsaki yaja mai
ƙarfi, yayinda Murmushi ya suɓucema aunty mimi ta girgiza kanta kawai tana amsawa.
Aysha kanta sai bataji daɗin yanda Fadwa ɗin tayiba. A ganinta koba komai yaci
Fadwa ɗin ta danne ta amsawa Aunty Mimi cikin daɗin rai tunda har ta karya ƴancinta
ta fara gaisheta, tunda ita ta kasa banbance dai-dai ta gaisheta matsayin babba
gareta kuma ƙanwar mahaifiyarta. Sai dai batace komai ba saboda Yayansu. Shiru
ɗakin yayi zuciyar Shareff a ɓace. Amma sai ya danne a bisa uzirin suna asibiti,
sai dai yaci alwashin taka mata birki dan bazai ɗauka wannan banzan halin ba.
Fadwan ce ta katse shirun ta hanyar tura musu basket ɗin da ta shigo da shi.
“Ga abinci nan ALLAH yasa zaki iya ci, bansan a asibiti kike ba sai yanzu da
Soulmate ya faɗa da an miki wanda zai fi dacewa da mara lafiyan ai”.
Banza Anaam tai mata, sai bayan wasu sakanni tace “Ayya” a taƙaice taja
bakinta tai shiru.
Matuƙa ran Shareff a ɓace yake dan har fuskarsa ta nuna hakan, amma tsarinsa na
ƙin yankema mutum hukunci cikin fushi ya sakashi yin shiru. Aysha ma kai kawai ta
girgiza. dan ta fahimci inhar a haka Fadwa tace zata rayu a zaman aure lallai zata
wahala. Domin fidda kishin mace ƙuru-ƙuru a ƙasar hausa tamkar gogama kanta baƙin
fenti ne ga mijin dama kowa, domin al'ummarmu kanyi hukunci da zahiri ne a kowanne
al'amari musamman akan kishin gidan malam bahaushe. Aunty mimi kam murmushi kawai
tai ta maida hankalinta ga Aysha.
Anaam dai kwanciyarta tai ta juya musu baya ma, a ranta tana ayyana saita
koyama fadwa hankali wlhy, dan abinda taima aunty mimi ya matuƙar sosa mata zuciya.
Aunty mimi suna hira ita da Aysha shi yana faman latsa waya fuskarsa a murtuke. Sai
ya kasance ita kaɗaice shiru, sai kuma hakan ya sosa mata zuciya har ƙwalla na cika
mata ido, kiran wayarta da akai ne ya kawo mata sassauci ta miƙe tabar ɗakin. Anaam
ta rakata da harara, amma sai gilashin idonta ya sirrantasu, juya kwanciyarta tai
itama zuciyarta na tauna da raɗaɗin abubuwa kala-kala, sai dai taji sassauci a
ranta a yanayin da Shareff ɗin ya nuna ɓacin ransa ga Fadwa kan abinda taima aunty
mimi, tasan kuma bawai ya barta hakanan ba zasuyi mai dalili idan sun bar asibitin.
Shigowar Dr Jamal ce ta saka fuskar Shareff sassautawa. Ya gaishe da Aunty
Mimi da juyawa kan Anaam da tambayarta ya jiki sannan suka gaisa da Fadwa da
shigowarta kenan. Aysha ma gaidashi tayi. Jan hanunsa yay suka fita, kusan mintuna
goma sha biyar sannan suka dawo. Batare daya zaunaba yacema Fadwa ta tashi su tafi
dare nayi.
Fakar idon aunty Mimi yayi ya ranƙwafa kan Anaam ya sakar mata kiss. Zai ƙara
na biyu dakai hanunsa saman ƙirjinta tai saurin buge hanun tana waro idanu waje
harda ƴar zaburarta. Tsaye ya miƙe yana dariya, sai ko suka haɗa ido da aunty Mimi.
Juyawa yay da sauri ya fice yana cigaba da dariyarsa.....

*_WASHE GARI_*.

Sai wajen takwas yabar gidan zuwa asibiti batare da yabi takan Fadwa ba,
tun da suka baro asibiti jiya suke tafka rigima da ita, dan kuwa ya mata tatas akan
abinda taima aunty mimi, ya kuma tabbatar mata inhar ta ƙara sai ya mata abinda
bata taɓa zato ko tsammani ba daga garesa.
Gargaɗinsa ya sakata kwana kuka, ta kira gwaggo halima kuma ta hanyar wayar
mmn Abu data kira wayar cikin masu aikinsu aka haɗata da maman, zayyane mata
komai tayi, suka haɗu sukaita zagin su aunty Mimi wai asiri ne ke cin Shareff ɗin.
Amma zata ɗauka mataki ta saurareta.

Ya iske Anaam ɗin na toilet tare da Dr Bilkisu tanayi sit bath. Yana iya jin
rakin da take zubawa daga nan, ya girgiza kansa kawai da kaiwa zaune a bakin gadon
yana murmushi. A haka Aysha ta shigo hanunta ɗauke da flask ɗin tea. Gaisheshi
tayi, ya amsa yana kallon flask ɗin.
“Daga ina?”.
“Yaya gidan Dr Bilkisu mukaje amso ruwan zafi anan cikin asibitin”.
Bai sake cewabkomai ba akan hakan. Itama saita ajiye flask ɗin.
“Kunyi barci dai babu wata matsala ko?”.
“Eh Yaya. Ai da yake a magungunan nata kamar akwai masu saka barci harma makara
tayi sallar asuba.”
Bai samu damar bata amsa ba suka fito Anaam na tafiya da ƙyar. Suna haɗa ido
ta dalla masa harara dan duk wannan dai bala'in shine yaja mata ai. Shi dai
kallonta kawai yake murshi na neman suɓuce masa, tana tafiya kamar wata ƴar kaciya.
Doctor ce ta katsesa daga kallon nata. Ya ɗauke kai suka gaisa. Baƴani ta ƙara masa
na cewar zatama sallamesu amma sai zuwa anjima kaɗan dai haka akwai abinda zata ɗan
jira a kawo mata da zata bama Anaam ɗin.
A taƙaice ya mata godiya yana maida hankalinsa ga Anaam daketa faman sauke
ajiyar zuciya daga kwancen da take ta juya masa baya. Tai musu sallama ta fice tana
faɗama Aysha taba Anaam ɗin abinci amma ta fara da tea mai zafi. Kamar jiya dai
koda Aysha ta haɗa abincin shine ya karɓa. Cikin bada umarni yace ta tashi zaune.
Taso sharesa, sai dai a yanda yay maganar ya tilastata tashi dole bakinta a sama.
Yi yay kamar bai ganta ba. Ya miƙa mata shayin ta amsa kamar zata fasa ihu. Sai da
ta gama shanye tea ɗin tas sannan ya miƙa mata abincin, amma sai tace ta ƙoshi. Bai
saurareta ba ya fara ɗiba yakai bakinta, ta kalesa kamar zatai kuka.
“Nifa Yaya nace na kos...”.
Ta kasa ƙarasawa saboda kallon daya wulla mata cikin tsakkiyar ido. Idanunta ta
lumshe tsigar jikinta na tashi, dole ta buɗe bakin ya zuba mata. A dai-dai nan Dr
Jamal ya shigo. Da alama ma shigowarsa asibintin kenan. Sun gaisa ya tambayi mai
jiki, bai jimaba ya fita yanama Shareff dariya da shaƙiyanci da ido. Bai dai
kulasaba shi dai.

Karfe kusan sha ɗaya aka basu sallama. Zuwa lokacin yaje office ɗin Dr Jamal
ya dawo. Aysha ta tattare kayansu shi kuma ya kama Anaam ɗin da taso botsare, sai
dai ya hana hakan ta hanyar tabbatar mata zai ɗauketa. Dole ta nutsu tana tura masa
baki. Yay murmushi kawai da sumbatar wuyanta. Mintsininsa tai ya dafe wajen yana
ɓata fuska shima. Sai ta saki dariya da masa gwalo.........✍
*😝😜Za'a koma filin wasa🚴🏼*

_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_


*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:


07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇


09134848107

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*


[11/14, 9:00 PM] My Zafafa: *_Typing📲_*

*_BABU SO....!!_*
_(Miya kawo kishi?)_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*
https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718

*_62_*

.........A waje suka sami aunty Mimi tare da Dr Bilkisu. Khaleel ne yazo ɗaukarta
ita gida zata wuce. Anaam ta shiga zazzame jikinta a nasa amma yaƙi sakinta har sai
da ya sakata a mota. Ya ranƙwafo zai sumbaceta ta kauce tana faɗin “Kai yaya wai
bakajin kunyar aunty mimi”.
Kai ya kaɗa mata da lumshe idanunsa “Ƴar kaɗan”.
“Kake jin kunyar tata?”. Ta tambaya cikin sigar waro masa idanu.
“Eh mana ba mamata bace. Ba buƙartar na ɓoye mata muhimmancin autar mata ai”.
Rufe fuskarta tai da tafukan hannayenta tana murmushi. “Ni dai babu ruwana”
Murmushi yay da sumbatar kunenta. Ƙarasowar Aunty Mimi wajen ya sakashi ɗagowa.
Sai lokacin takejin batare da Aunty mimi zasu tafi ba. Fuska ta kwabe da rokonsa
zatabi aunty mimi ama yaki. Sai kawai ta kama hawaye.

★Shiru babu mai magana a motar har suka iso gida. Har mai rake ta gani tana so
amma ta gwammace tai haƙuri da tace ya tsaya ya siya mata. Itace ta fara fita a
motar tun kafinma ya kashe, daga shi har Aysha suka bita da kallo. A ransa ya
ayyana (Ni nasan maganinki yarinya).
Aysha ce ta kwashi kayansu, a dai-dai lokacin Fadwa ta fito daga sashenta dama
tana laɓe duk tana kallonsu tun shigowar motar gidan. Tayi ƙyau cikin kwalliya sai
baza ƙamshi ake. Tai masa sannu da zuwa Aysha ta gaisheta. Itace ta taya Ayshan
kwashe kayan zuwa sashen Anaam ɗin. Sun sameta kwance cikin kujera ido a rufe kamar
mai barci, kuka take son tayi akan hanata bin aunty mimi amma yaƙi ya fito, shine
tai luff a wajen zuciyarta na suya. Sallamarsu baisa ta buɗe idanun nata ba, har
sai da Fadwa tace mata ya jiki. Ciki-ciki ta amsa mata, Fadwan ta nuna kamar bata
damuba ta sake mata addu'a sannan ta fice.
Aysha datai tagumi ta girgiza kai kawai. Tashi tai ta fara gyaran sashen duk
da bawani datti bane ba. Harta kammala da falo ta koma bedrooms Anaam na'a wajen
kwance, Shareff kuma bai shigo ba. Ayshar ce bayan kammala aikin nata ta fito tace
mata ta tashi taje tai wanka ga ruwa can ta haɗa mata. Batare data tanka mata ba ta
miƙe. “Ki fara shiga ruwan zafin kamar yanda doctor tace.”
Kanta kawai ta jinjina mata tai shigewarta. Aysha ta bita da kallo cikin
tausayi, dan ita tausayi take bata, saboda ta fahimci abinda Anaam ɗin ke gudu
danta jigata a matuƙa a hanun Yaya Shareff ɗin.
Shigowarsa ce ta katse mata tunani, yabi falon da take bazama turare da kallo,
sai dai baice komai ba yakai zaune.
Burner ɗin Aysha ta ajiye da nufar kitchen, babu jimawa ta dawo ɗauke da
ruwan. Zata zuba a kofi ya karɓa goran ruwan, murfin kawai ya buɗe ya kafa kai. Bai
ajiye ba sai da ya shanyesa tas, da alama ƙishin yakeji dama. Sai lokacin yace,
“Tana ina?”.
“Tana ciki yin wanka”.
Ƙofar ya kalla na wasu ƴan sakanni, sai kuma ya miƙe. “Ki shirya zuwa anjima saina
maidaki gida”.
Da to ta amsa masa. Shi kuma ya shige corridor ɗin bedrooms ɗin Anaam. Tana
faman ƙunƙunin ruwan da Aysha ta zuba mata na sit bath yayi zafi da yawa ya shigo,
cikin sauri ta juyo kuma a rikice dan babu komai a jikinta. Daburcewa tai gaba ɗaya
tama rasa ina zata saka hannu ta rufe, yi yay tamkar bai ganta ba, ya ƙaraso cikin
toilet ɗin. Ruwan da take sirkawa ya sakama hannu, ya ɗago yana kallonta. Juyar da
kanta tai gefe da ƙara tsuke fuska.
“Humm”
Kawai yace ya fara ƙara ruwan zafin.
“Yayi zafi fa da yawa”.
Ta faɗa da sauri kamar zatai kuka. Dai-dai nan ya ɗago dan ya masa yanda yake
buƙata, da sauri ta yunƙura zata fice ya damƙota, ƙoƙarin ture hanunsa ta shigayi
tana wani ciccijewa ita a dole bata wasa bace. A karon farko ya saki murmushi,
hannun nata ya saki ya damƙe towel ɗin, ta ɗago a matuƙar firgice tana kallonsa.
Ido ɗaya ya kashe mata da cije gefen lips ɗinsa shima, dole ta kauda kanta dan
salon nasa saida tsigar jikinsa ta tashi. Matsota yay tare da ranƙwafowa bakinsa
saitin kunnenta.
“Bakin ya mutu ne ƴammata?”.
Fuskarta ta sake kaudawa gefe da son ƙwace hanunta. Sai kawai jitai ya since towel
ɗin nata. Ruɗewa tai, tai ƙasa zata duƙe ya ɗagata cak ya dire a ruwan zafin.
Azabar data ratsata ta zafin ruwan ta sakata sakin ƙaramar ƙara mai kama da kukan
shagwaɓa. Matso da fuskarsa yay gab da tata, saukar numfashinsa akan tata fuskar ya
sata ɗan buɗe idanunta dake rufe, dai-dai lips ɗinsa na sauka kan nata, sai kawai
jikinta ya hau rawa. Ya cigaba da binta a wani salo daya saka jikinta saki lokaci
guda, sai dai bai samu haɗin kanta ba kamar yanda yake buƙata. Bai damu ba ya
cigaba da sarrafata a hakan tunda dai saƙonsa na isa kamar yanda yake buƙata. Nisan
tafiyar ya sakata tuna azabar da tasha a daren shekaranjiya, ga gargaɗin doctor na
ta kiyaye har sai ciwonta ya warke. Kota warke ɗin ba buƙata take ba balle yanzun.
Laushin da gaɓɓansa sukai ne ya bata damar janye jikinta, ta miƙe zumbur jikinta na
ɓari. Bashi da zaɓin daya wuce shima miƙewar, ta nane da bango tana girgiza masa
kai ganin ya ɗago idanunsa da sukai matuƙar canja launi yana zuba mata.
Hannayensa duk biyu ya dafe da bangon tana a tsakkiyarsa. Ƙasa tai da idanun
nata da sauri tana ƙara damƙe towel ɗin data fisga tun miƙewarta ta suturta
jikinta. Ƙasa ya farayi da hanun damarsa a hankali har zuwa kan makunnar shower,
sai saukar ruwa kawai taji a kansu a bazata harta ɗan tsorata babu shiri ta ɗago,
bazata iya jure kallon cikin idanunsa ba, dan wani irin al'amari daya girmi
ƙwanyarta take hangowa a cikinsu da har suke neman sare ƙarfin gwiwarta, faɗawa tai
jikinsa kawai ko hakan zai bata nutsuwa. Haka yake buƙata dama, ya saki ɗan
murmushi da naɗe hanunsa duk biyu a bayanta ya rungumeta ruwan na cigaba da sauka a
kansu. Kusan a tare suka saki nannauyan numfashi, cikin dabara ya janye towel ɗin
da taketa faman riƙo yay ƙasa da shi, tsam ta matsesa dan bata buƙatar ya ganar
mata jiki. Murmushi mai ƙayatarwa ya sake saki da ƙara matsetan shima yana saki
wasu zafafan ajiyar zuciya a jere....

Gaba ɗaya ya ƙulleta da kunya, tai wuff ta fara fitowa daga toilet ɗin da
alama bakin tsuwar dai ya mutu, sai dai ko gaban mirror bata kai ba shima ya fito.
Tana ƙoƙarin ɗaukar hijjab dan tasa ya riƙesa, saman gado ya wurgasa tareda ɗaura
mata towel ɗin hanunsa saman kai ya fara tsane mata jiƙaƙƙiyar sumarta.
“Har yanzu fushin ne dai baki huceba?”.
Tayi kamar bata jisa ba, sai dai taɗan saci kallonsa ta gefen ido fuskarta a
kwaɓe.
Ya ɗan ɗalle mata lips. “Nifa bana son shariya”.
Bakin ta dafe da janye hanunsa da towel dake saman kanta zata bar wajen. “Ni karka
sake kulani, kuma matarka ta daina shigomin sashe ban son gulma. Kuje can ku ƙarata
kuma cinye kanku tsabar son kai”.
Dariya sosai taso kufce masa, amma yay ƙoƙarin dakewa sai dai murmushinsa ya
ɗan bayyana. Shima ƙarasawa yay gaban mirror ɗin inda takai zaune saman stool tana
ƙoƙarin zuba mai a hanunta. Ta bayanta ya ranƙwafa tare da ɗaura kansa a wuyanta ya
dafe duk hannayensa akan katakon mirror ɗin.
“Mi matata kuma tayi? Ko zaki huce haushinnne a kanta. Faɗamin, wai *_BABU
SO! MIYA KAWO KISHI?_*”.
Dakatawa tai daga shafa man datai niyyar farawa, ta ɗago idanunta dake cikin
gilashi suka haɗa ido ta cikin mirror. Da sauri ta janye nata tana cuna baki gaba.
“Yaya kaima kasan SO ɗin da kishin. Da zaka rarrabe munma wlhy dana biyaka”.
Murmushi ne ya sake suɓuce masa, yasa hannu ya karɓe man hanunta ya ajiye,
sake ƙoƙarin ɗauka tai ya riƙe hannun. Dole ta ɗago tana kallonsa, hakan ya bashi
damar da yake buƙata, ya sarƙe idanunta a cikin nasa yanda ya tilasta mata tsaiwa
suka kurama juna ido, kallon juna suke irin na tsakkiyar idon nan mai ratsa jinin
jiki da bargo ya sunce duk wani ƙwarin laka da jijiyoyi. A hankali lips ɗinsa suka
fara motsawa...
“Kin tabbatar idan na rarrabe mikin zaki biya ni?”.
Da wani salon zamtowarta jiki a kasalance ta janye idanunta a slowly, shima
janye nasan yay da wani salon lumshewa da buɗewa tare da miƙewa da ƙyau ya juyota
suna fuskantar juna saboda kujerar na juyawa.
“Yayaaaa!”.
Ta faɗa a shagwaɓe.
“Yayoo”.
Ya bata amsa da sake ranƙwafowa akanta tamkar ɗazun, banbancin kawai yanzu
suna fuskantar junane. Turashi ta ɗan farayi amma ko gezau, sai ma hanun daya riƙe
ya ɗaura saman fuskarsa daga gefen kunne. “Idan kin isa kalla cikin idona ki
maimaita abinda kika faɗa”.
“Ba buƙatar haka ai Yaya tunda nasan kaji. Aysha fa na gidan nan, kaima kuma
matarka nacan na jiranka”.
“Uhmm Madam pretender ke kuma budurwa tace ko?”.
“Hu'um nayi me da kai? Kamun tsufa”.
“Yanda kikai dani daren shekaranjiya mana”.
Janye hanunta tai da ƙoƙarin juyawa tana faɗin, “Kai dai ka sani”.
Yanzu kam ƙaramar dariya ya saki mai faɗi da miƙewa sosai akan ƙafafunsa. Yitai
kamar bata jisa ba taci gaba da shafa manta yana kallonta kamar ya samu tv. Saukar
kiran salla a kunnensu ya sakasa kallon agogon ɗakin, ya ɗan furzar da numfashi dan
yasan sai ya sake sabuwar alwala.
Binsa tai da kallo ta gefen ido, yana shigewa ta taɓe baki da miƙewa tana
magana ƙasa-ƙasa. Kaya ta saka sauri-sauri kafin ya fito. Tayi ƙyau sosai dan ƙanan
kaya sun zame mata jiki matuƙa, har takai komi ta raɓama ɗan jikinta sai ka ganta
kamar ka sace. Kallo ɗaya ya mata ya ɗauke kansa, dan ya tabbata ya cigaba sunan
alwalarsa karyayya again. Ita bama tasan yanai ba, powder take ɗan shafama fuskarta
da ɗan lipsgloss, dan ko kwalli ba sakawa take ba sai Mamie ta tsaya a kanta. A
ransa yake raya da kwalliyar tafi haka daya so, sai dai yasan ita ƴar darun tasa a
wajenta hakan normal ne. A haka ɗinma tayi ƙyau sosai.
Ita ko sanin kaya yake canjawa yasa taƙi juyowa, harya gama shiryawa cikin
wandon jeans blue da pitch shirt mai dogon hannu. Jin tsaiwarsa a bayanta ya sata
ƙoƙarin barin gaban mirror ɗin, amma saiya riƙota ta hanyar saƙala hanunsa saman
cikinta ya manna bayanta da ƙirjinsa duk da bata kai har can sama ba. Ɗagowa tai
tana kallonsa kamar yanda shima yake kallonta. Ganin ya ɗago lipstick da dayan
hanunsa ta maida idonta akai. Saman lips dinta ya ɗaura, zatai magana yace mata
“shiii!”.
Shiru ta haɗiye abinda take son faɗar, shi kuma ya fara goga mata. Sai da ya
gama ya juyota suna fuskantar juna, bakin ta ɗan tunzura gaba ganin yanda yake
kallonta.
“Nifa shanyewa nakeyi shiyyasa bana sawa”.
“Oh really? To bara na shanye abuna kafimma ki shanye min”.
Idanunta ta waro waje da zaburowa zatai magana ya samu damar sauke lips ɗinsa akan
natan. Dole ta koma tai laƙwas dan bai musu kamun wasa ba........✍

_Shareff adai rage cin amanarmu😚🚶🏻🤕._

_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_
*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_


*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:


07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇


09134848107

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*


[11/15, 11:40 PM] My Zafafa: *_Typing📲_*

*_BABU SO....!!_*
_(Miya kawo kishi?)_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718

*_63_*

.........Tsaf ya shanye jambakin, zaune takai tana sauke numfashi, shima barin
wajen yay da ɗan hanzari, tanaji ya buɗe toilet amma bata iya ta ɗago ba. Babu
jimawa ya fito da alama wata sabuwar alwalar ya sakeyi. Ƙofa ya nufa batare daya
yarda ya sake kallonta ba yana faɗin, “Ki tashi kiyi salla”.
Iska ta furzar mai ƙarfi da dagowa tana kallon kanta ta cikin mirror, sai
kawai ta samu kanta da kai hannu ta shafi lips ɗin nata da sakin murmushi.
“Fitinanne”. Ta faɗa a hankali tana mikewa. Itama alwalar ta ɗauro, bayan ta
gabatar da salla samun kanta tai da komawa gaban mirror ta sake gyara fuskarta da
ƙyau cikin simple kwalliya. Kwalli, lipstick ɗin daya saka mata ta ɗan gyara
girarta siririya da ƙara powder. Ita a karan kanta sai da ta tsaya kallon kan nata
dan wani ƙyau taga ta kara, tai guntun murmushi da ɗaukar turare ta ƙarama
jikinta..
Ana idar da salla ya dawo gidan, saboda makara salla daya nema yi bai
shiga sashen Fadwa ba ya wuce, yanzu kam daya dawo sai ya fara nufar can, wannan
ƙa'idarsace, akowace salla in har yana gida sai ya tabbatar da mace tayi hankalinsa
ke kwanciya, ko yana office yakan ƙokarta ya kira domin tambayar kinyi salla, hakan
ya ƙara ƙarfafa Fadwa domin waya takan ɗauki hankalinta ta kasa tashi yin salla
akan lokaci kafin zuwanta gidansa matsayin mata. A bedroom ya sameta ta idar da
salla fuskarta duk babu walwala. Ya ɗan tsura mata ido na wasu sakanni kafin ya
ƙaraso ciki sosai. Sau ɗaya ta kallesa ta janye idonsa da masa sannu ciki-ciki.
“Wani abu ya faru ne?”.
Ya tambaya a maimakon amsa mata sannun da tai masa. Batai magana ba, sai dai ta
sake ɗan tsuke fuska.
“Nasan kin jini fa”.
Kamar bazatai magana ba sai kuma ta ɗago idanunta dake tara ƙwalla tana kallonsa,
“Soulmate karka juyamin baya dan kayi aure, maƙiya zasu iya yimin dariya”.
Mamaki shinfiɗe akan fuskarsa yake kallonta. “Juya baya kamar ya? Anyi wani
abu ne?”.
“In ma ba'aiba ga hanyar yi nan an ɗakko ai. Tunfa da matarka ta dawo gidan
nan yau baka sake leƙoni ba, kana ganin hakan adalci ne? Yaufa ko zuwa kacemin na
tashi nai salla bakayi ba, kuma tun ɗazun kana'a sashenta ita dan daga can ka wuce
massallaci, gaka nan harda canja kaya alamar yin wanka”.
“Dama kin saka a ringa miki gadina ne? Ko kuma shiga sashen nata ma akwai wata
ƙa'ida ta mintunan da zanyi na fito? Ni da matata kuma kina tuhumata dayin wanka
kamar wanda ya ajiye wata karuwa”.
“Niba haka nake nufi ba, amma dai koyaya ai sai kana adalci. Jiya yini guda
kuna tare a asibiti, hakama yau tun fitar safe da kai kuka dawo tare kana a
sashenta”.
Sosai ɓacin rai ya bayyana akan fuskarsa, idanunsa daya tsareta da su har suna
canja launi. “Okay ke da sokike na watsar da ita kenan a asibitin nazo na tare a
wajenki bayan nine sanadin zuwanta can. Ko kuma dan kar ranki ya ɓaci bazanyi wanka
a sashenta ba?. Look Fadwa idan kikace zaki ɗaukemu zuwa wannan layin bazaki taɓa
shan lalai a wajena ba. Idan kin manta bara na tuna miki, Juwairiyya matata ce,
idan yanzu na shiga inda take ta rayamin kasancewa da ita zan samar da wannan farin
cikin nai wanka na fito koda anjima hakan zai ƙara bijiromin idan ma wannan kikema
zagaye-zagaye zargin nayi. K da ita duk abu ɗaya kuke a wajena, ina fatan kuma
tsaida adalci akan kowaccenku. Duk wacce take da wani tuggu nason rinjayata gareta
ita kaɗai na cutar da ƴar uwarta ALLAH ya hanata wannan damar ko wacece a cikinku.
Abu na ƙarshe dazan gaya miki shine daga yau ki sani *_Ina son Juwairiyya!_* bawai
cushenta akai minba kamar yanda na fahimci ke tunaninki ke kaiki. Yanda na aureki
domin so bisa jagorancin iyaye haka itama na aureta, kuma koda ace iyayenmu basu
ɗaura mana aure ba ni da kaina *_Zan nema aurenta_*, dan hakan burina ne, hatta
wannan gidan da sunanta aka ginashi itama, kema shaidace tunda sashe biyu kika
tarar. Kinga sai ki sakama zuciyarki salama, ki nisanta kanki da zama mai fuska
biyu a gareni, dan bazan daina kasancewa da ita ba domin farin cikin. Sannan ita
bata taɓa nuna damuwa da kasancewata a wajenki ba abinda ke gabanta takeyi, mtsoww
stupid har kina faɗamin wai na dinga adalci”. Ya juya ya fice a fusace.
Da gaske Fadwa tayi mutuwar zaune tun fara maida mata raddi da yayi, ga wata
irin zufa dake jiƙa duk sassan jikinta sharkaf. Buga ƙofar da yay da ƙarfi ya sata
zabura ta dawo hayyacinta, rawa lips ɗinta suka fara alamar magana take sonyi amma
taƙi fita, sai kuma ta mike zumbur tana rarumar wayarta ta kunna fitila duk da kuwa
ɗakin akwai hasken wutar nefa. Tabbas maganin data zuba ɗin gashi nan, sannan ya
taka kuma ai kamar yanda Aunty Safarah da Mama suka tabbatar mata idan ya taka babu
wani magana da zatai ya musa mata. Hakama zoben da suka bata na mallaka har biyu
gashi a hanunta, sun kuma tabbatar mata mata da yawa suna rububin saya kuma yana
aiki akan mazajensu. Mi (hakan ke nufi?) ta tambayi zuciyarta ƙirjinta na bugawa da
sauri-sauri idonta ƙyam akan zoben mallakar dake a yatsanta tana murzashi da
tunanin ko batayi dai-dai bane ɗazun daya sshigo.
*_(Mata ku daina ruɗar da kanku da wannan zoben da kuke saya, wai miyasa
munada ilimi amma basirarmu ke toshewa akan kayan matane?. Kwanaki nai wata baƙuwa,
kamar wasa muna hira sai aka kai har kan illar shaye-shayen maganin mata da wasu
mata suka maida tamkar ibada a rayuwarsu har ana ribatarsu da su ana basu kayan
tsubbu a zuwan maganin mata kamar dai fadwa. Sai kawai take bani labarin ai wani
zobe ma ya shigo wai na mallaka. Ana saidawa dubu uku har sama da haka. Ban ɗauka
abin serious ba sai a wajen wani taron suna. Hhh abin dariya, mu anan yankin ma
tsabar dukan hancin da akema mata zoben ana saida musu ne a 5k 6k 7k har 10k idan
aka tabbatar ke hamshaƙiya ce, kunsan kuma su wannan manyan matan sunfi son ace abu
nada kuɗi mai yawa sunfi bashi daraja. Humm abin mamaki wai sai ga mata na mugun
rububin zobe kamar ƙiftawar ido ya ƙare, har wasu na shiga damuwa basu samu ba. 🤦🏻
haba mata mi muke son mu zama ne wai dan ALLAH? Shin wai mallakar nan mizata amfana
miki? Nasan kowace mace tana so mijinta ya sota ya kuma ƙaunaceta, amma sai nakega
akwai hanyoyi masu ƙyau da zakibi shi namiji ya soki domin ALLAH. Sannan ku fahimta
da ƙyau wlhy namijin bahaushe komin son da yake miki da wahala ya lalace a jikinki
koda yaushe kamar wasu a cikin ƙabilun nan. Ɗabi'ar da suke nuna mana kuma ba itace
rashin so ba, dan kinga mace na nanaye a media da miji bashike nufin ita ƴar gata
bace, dan kinji mijin novel ya lalace jikin mace karki ɗauka dole naki mijin sai ya
kasance a haka ki yarda yana sonki. Wani abun ana sakashine kawai dan nishaɗi. Mu
kiyayi zantuka ko labarai ga ƙawayenmu su gidajensu kaza kaza ta yanda hankalinki
zai tashi kiga gazawar mijinki, wlhy koyaya mijinki yake sunansa jan gwarzo, idan
kika nutsu yanada tasa baiwa da kalar soyayya da farin cikin da yake baki kema ba
sai lallai irin wancan da kike hange ba. Idan kina cikin wani ƙunci a gidan aurenki
ki ɗauka harabawace ke kuma bautar ALLAH kikeyi sakamakonki nagaresa, idan kikai
haƙuri sai ya sakaki a aljanna. Amma mu kiyayi zurmawa akan shaye-shayen magungunan
matan nan da bamusan kansu ba suzo suna mana illa a banza a wofi, su kansu wasu a
cikin masu saidawar basu da ilimi a kansu bamu kawai sukeyi. Ki samu mai inganci
wanda kika yarda da hadinsa da mai saidashi ki saya kisha gwargwado bata yanda zaki
saka kanki a dana saniba kizo kina jama kanki illa da kwasar imfection a banza a
wofi. Kuyi hakuri masu magani nasan akwai nagari acikinku dan kowane sana'a akwai
na kwarai akwai na banza. Masu na banzar suke bata na kwarai da disashesu akasa
ganinsu a idanun al'umma. amma dan ALLAH mata a kiyaye, zoben nan da sayensa gara
ki samu kazarki kici tai miki amfani babu abinda ke tattare da son zuciya dake zama
ɗorarre).

Sashensa ya nufa rai ɓace, ya zube a falo yana cigaba da jan tsaki, shi ya
rasa mike damun waɗannan yaran, musamman ma Fadwa, dan Anaam ita kai tsaye take
abunta bata iya ɓoye-ɓoye ba. Kuma tunda ya santa haka take, tunda ko'a shigowarta
gidan nan ya hukuntata sau da yawa akan yima Fadwa abu amma hakan bai hana ta ƙara
gobe a zahiri babu wani ƙumshe-ƙumshe. Itako Fadwa yau ta nuna ita mai kirki ce,
musamman idan da Anaam a waje, anjima ya sameta tana baƙin rai da ƙananun magana
akan Anaam kaza-kaza. Ya rasa mike damun tunaninta, shi kuma ya tsani wannan banzan
halin dan yana kamanceceniya dana munafukai. Ƙwafa yay mai ƙarfi, a ransa yana
ayyana zaima tufƙar hanci....

★★★

“Blood zan baki wata shawar dan ALLAH ki fahimceni”. Aysha ta faɗa tana direma
Anaam plate na abinci data dafa musu a gabanta.
Wayar da take latsawa ta ajiye, da maida hankali ga Ayshan. “Tofa shawarar mi
kuma blood?”.
“Ta zamanki a wannan gidan. Na fahimci gaba ɗaya a haguggunce kike, sai dai na
miki uziri domin rayuwace da baki saba da ita ba kuma baki santa ba. Kin tashi a
rayuwar da kowa yana komai akaran kansa kuma kai tsaye batare da wani munafunci ba
ko boye-boye, dolene a wannan gaɓar kisha wahala sai dai nai alƙawarin bazan bari
hakan ta faru ba. Blood daga yanzu dan ALLAH komi Fadwa zatai miki ki daina nuna
ƙinsa a gaban Yaya koda ace bai miki ɗin ba, domin na fahimci da wannan makamin
take amfani wajen kai miki duka a tsakaninki da Yaya. Ki duba ranar yanda ya nuna
jin haushinsa akan abinda kikayi, wlhy ina ganinta sanda take murmushi, hakama yau
da muka dawo, dan munafunci hardafa rakomu nan”
Murmushi tayi da ɗaukar spoon ta fara cin abincinta dan tafi son cinta da zafi.
“Amma blood ban katseki ba, miye amfanin kwaikwayon halin wani bayan hanyace mara
ƙyau, ɓoye ƙinta kamar yanda take ƙina bashine zaisa na birgeta ba ko shi na
birgesa. Tsakanina da ALLAH idan nace zan zauna shanye haukar wannan matar zan kamu
da ciwon hawan jini, nafi yarda da kamun na maka a wuce wajen dan nasan itama
munafunci kesata yimin wani abun”.
Sallamarsa ta tilasta Aysha haɗiye abinda tai yunƙurin faɗa, dole ta juya
tana amsa masa. Anaam kam kallo ɗaya tai masa ta ɗauke. Shiko kasa ɗauke nasa idon
yay a kanta, ko sannun da Aysha tai masa hannu kawai ya iya ɗaga mata. Kujerar dake
facing Anaam ya zauna. Hakan yasa Aysha miƙewa a ɗan ɗarare tace, “Yaya a kawo maka
abincin?”.
Abincin ya kalla na wasu sakanni, sai kuma ya miƙe daga inda yake ya koma
kujerar da Anaam ke zaune kasancewar 2sitter ce. “Bara naci kaɗan anan kawai”.
Cikin jin daɗi Aysha tai murmushi, Anaam kuwa ɗagowa tai idanu a ware tana
kallonsa, ya ɗaga mata gira da kashe mata ido ɗaya yanda Aysha bazata lura ba, da
sauri ta kalli sashen da Ayshar take, sai dai ita hankalinta ma ba kansu yake ba.
Spoon ɗin hanunta ya zare da sakin guntun murmushi, yana motsa lips ɗinsa
a hankali alamar akwai abinda ya faɗa. Batai tunanin da gaske yake ba, sai ganin ya
ɗiba yakai bakinsa tayi.
“Wai da gaske kakeyi?”.
Ta faɗa cikin magana ƙasa-ƙasa dan kar Aysha taji tana waro masa idanu da ƙyau.
Shima ƙasa yay da muryar tasa cikin kwaikwayonta da kashe mata ido yace,
“Bayan wannan zahirin kina buƙatar ganin wani ne?”.
Idanun ta ƙara warowa sosai “Are you ok?”.
“I'm not...”.
Ya bata amsa a taƙaice yana danne dariyarsa dan da gaske tayi bala'in diriricewa.
Tsabar son ƙureta abincin ya ɗibo yakai bakinta. Da sauri takai hannu zata kare.
“Idan kikaƙi amsa ALLAH cak zan maidoki jikina sannan na baki wanda na tauna a
bakina kuma a gabanta harda tsotse lipstick ɗina”.
Yanda ta saki baki da hanci tana kallonsa ya sashi dungure mata kai yana
murmushi, tana buɗe baki da nufin yin magana ya juye mata shi. Dole tai saurin rufe
lips ɗinta dakai hannu ta kare bakinta. Dai-dai nan Aysha da ta wuce kitchen batare
da sun sani ba ta dire babban tray data shirya abinci kamar yanda akema kowanne
magidanci a saman centre table ɗin gabansu. Lokaci guda suka sauke ajiyar zuciya,
Anaam ta kalleta shiko ya fiske fuskarsa na komawa normal kamar ba shine ke
murmushin ba.
Aysha na ƙoƙarin barin falon Anaam tai saurin faɗin, “Blood ina kuma zaki?
Kizo muci abincin mu”. Da sauri Aysha ta shige bedroom ɗin baƙi kamar ma bata jita
ba.
“Yaya ka gani fa ka koreta?”.
“So take ki samu ladan da mata ke samu kema, tunda garden ɗina kin haɗa baki da
doctor ɗin can kar naje barruwa.”
Maganarsa ta farko kawai ta fahimta. Dan haka cike da basarwa ta bashi amsa.
“Matarka ai tana dafa maka ta samu ladan, kaga ya wadatar da kai ai”.
Shima fahimtar hakan ya sashi juya harshe zuwa yaren Maley.
“Ke minene naki sunan?”.
“Kanwarka kaima da kowa an sani”.
“Really?”.
“Yap!”.
“Idan suka ganki da tsarabar furen garden sai su cireni a jerin Yayun naki ai ok”.
“Kai ka san wani garden Yaya”.
“Kema kin sanshi sai dai ƙari. Ni fa janbakin nan ya tsolemun ido a bani na shanye
kayana k......”
Abincin data ɗebo ta juye masa a baki kamar yanda yay mata shima ɗazun, dole ya
haɗiye sauran maganar itako ta shiga ƙyalƙyala dariya dan lauma babba ne........✍

_ZAFAFA BIYAR_
*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_


*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:


07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇


09134848107

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*


[11/15, 11:40 PM] My Zafafa: *_Typing📲_*

*_BABU SO....!!_*
_(Miya kawo kishi?)_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718

*_64_*

........Dariya take tana masa gwallo. Fuska ya ɓata, da harɗe hannayensa a ƙirji
irin yayi fushin nan. Yanda yay ɗin sai ya saka Anaam shiga ƙyalƙyala dariya da
faɗin.
“Kai Yaya shagwaɓa kuma?! ALLAH kamafi ƙyau a haka fuskanka so cute”. Ta ƙare
maganar da kashe masa ido dariyarta mai ƙaramin sauti na bayyana fararen haƙoranta.
Ta nuna lips ɗinta da kaɗa masa idanunta dake cikin gilashi.
“Indai lipstick ɗin nan ne Yaya ba shansa zakai ba garama ka haƙura”.
“Oh oh haba princess kiji tausayina mana”. Yaya maganar da matsar da
fuskarsa gab da tata.
Baya taja dasa hanunta ta kare bakinta, “Babu wani princess na daɗin baki fa
Yaya, barima kaga na shanye abuna, idan baka ganiba ai dole ka haƙura”.
Yana ƙoƙarin riƙota ta tura lips ɗinta cikin baki da sauri.. Idanunsa ya waro
sosai yana kallonta cikin langaɓe wuya. Ta fito da lips ɗin tana dariya da masa
gwalo.
“Sai kaci abinci yanzu babu”.
“Ni ko? Yarinya zan rama ne”.
Dariyarta ta cigaba dayi ƙasa-ƙasa, shiko ya ɗauka spoon ɗin ya cigaba da cin
aincinsa fuskarsa da ɗan murmushi.
“Nifa yaya karka cinye min abinci na”.
Idanunsa ya ɗago yana kallonta, sai kuma ya ɗibo abinci ya nufi bakinta, “Ba
marowaci bane irinki ai hahh”.
Bakin ta buɗe ba musu ya zuba mata, a hankali ta shiga taunawa da faɗin, “Nima
ai bana rowa”.
“Kika min yanzun?”.
“Baga abincina kana ci ba”.
Murmushi kawai yayi batare da yace komai ba. Itama bata sake magana ba, ya cigaba
da bata abincin shima yana ci. Suna gab da kammalawa wayarsa tai ring, ɗauka yay ya
duba, ganin Khaleel sai kawai ya ɗaga. Bata san mi'akace masa a wayarba, sai gani
tai ya miƙe da kama hanunta....
Da mamaki take kallonsa zatai magana ya girgiza mata kansa. Baki ta ɗan tura
dan ita dai bata ƙoshi da abincin ba, sai dai babu yanda zatai dole ta bisa. Hango
Khaleel jikin wata mota mai ƙyau fara tas jingine ya sata zare hanunta cikin nasa,
bai ce komai ba har suka ƙaraso. Ita ta fara gaida Khaleel ɗin, ya amsa mata fuska
da murmushi sannan ya maida hankalinsa ga Yayansa. Gaisheshi yay da girmamawa. Ya
amsa masa da kulawa.
“Daga ina haka mazan fama?”.
Murmushin Khaleel ya faɗaɗa dan yana son Yayan nasa ya kirasa da sunan nan. Wani
ɗan ƙaramin gift🎁 ya ɗakko a gaban motar, ya dubi Anaam dake kallon motar da ita
kanta an naɗeta da zaren gift. Sai kuma ya sake maida kallonsa ga Shareff ɗin da
shima dai motar yake kallo. “Saƙone daga Abie. Abawa Granny”.
Idanu ta waro matuƙa da kai hannunta duk biyu saman bakinta, sai kuma ta dubi
Shareff da shima murmushi ke shimfiɗe akan fuskarsa. Shine ya amsa ya buɗe key na
mota ya bayyana. Ai batama san sanda ta rungume Shareff da faɗin, “Wayyo Yaya daɗi
zai kasheni”.
Rungumeta yay shina da sakin dariya kamar yanda Khaleel shina ke dariyar.
Ɗagowa tai ta amsa key ɗin tana kallo, sai kuma ta ɗagasa a saitin fuskar Shareff
tana kaɗa masa. Murmushi ya sake saki mai faɗi da faɗin, “ALLAH ya sakama Abie da
alkairi Congratulations dear”.
Da amin ta amsa, Khaleel ma ya amsa da kallonta. “Congratulations Granny.
Saura kuma tukuyci na, k ko Yaya wazai bani?”.
“Karka damu Yaya Khaleel, saika zaɓa”. Ta bashi amsa da shigewa motar da
Shareff ya buɗe mata, daidai nan Fadwa ta fito hakama Aysha. A tare suka ƙaraso
wajen, Fadwa da gaba ɗaya ranta ke'a jagule tun maganganun da Shareff ya yaɓa mata
ta dubi Khaleel fuska a tsuke. Kafinma tai magana ya nuna musu motar ita da Aysha
yana murmushi. “Ƙyautace daga Abie aka kawoma Anaam”.
“Woow!!” Aysha ta faɗa cikin zaro ido da shafa motar tana kallo, Fadwa kam
mutuwar tsaye tai. Dai-dai nan Shareff da Anaam dake cikin motar suka fito kowanne
fuskarsa har yanzu da murmushi. Khaleel ya miƙa mata hannu, “Nifa a tafamin
tukuycina”.
Kafin tace komai Shareff dake danna wayarsa ya miƙa masa, saka details ɗinka”.
“Woow da kyau babban yaya da gudu kuwa”.
Yanda Yay ɗin ya saka Anaam da Aysha kwashewa da dariya. Shigar saƙo a wayarsa
yasa bai tankasu ba, ya buɗe da sauri, “What!”. Ya faɗa yana ɗago kai da sauri ya
kalli Shareff. “Yaya duk tukuyci?”.
Murmushi Shareff yay da kallon Anaam, “Idan tace a ƙara maka ma sai a ƙara
maka ai”. A salon da yay maganar da ɗage mata gira ya sakata rufe fuskarta da
dukkan tafin hanunta dan taji kunya. Matsota yay tare da ranƙwafawa saitin kunenta.
“Nima ina jiran nawa tukuycin yanzun nan, inba hakaba a gaban Khaleel zanyi.....”
Da sauri ta buɗe idanunta... “Kayi mi?”. Maimakon amsa sai ya nuna mata lips
ɗinsa cikin kashe ido. Sarai tasan zaiyi ɗin, amma sai ta kauda ido da nufin cewa
a'a. Akan Fadwa da sam bata san da wanzuwarta a wajen ba ta saukesu. Sukaima juna
kallon ido cikin ido, ita ta fara kauda idonta da sakin wani tattausan murmushi mai
ma'anoni da yawa ta maido dubanta ga Shareff. Murmushi ta sakar masa shima ta ɗan
saci kallon Aysha dake a mota hankalinta baya kansu, ta maida ga Khaleel, ganin shi
ɗin dai zaiga komai sai ta ɗanyi jimm na tunani. “Yaya Khaleel kalla can”. Ta faɗa
da sauri tana mai ɗane Shareff a bazata ta manne tausasan lips ɗinta kan nasa lips
ɗin.
Numfashinsa neman shiɗewa yay saboda rashin zaton hakan daga gareta. Baya ta
nema janyewa ya ƙara cafkesu da saka hannu biyu saman ƙugunta ta zuba masa mintsini
a gefen ciki da janye jikinta kunya kamar ta nutse..
Khaleel daya waiga baiga komai ba ya juyo da nufin hararar Anaam, ai babu
shiri ya sake maida kansa gefe da sauri yana dafe bakinsa da sakin siririyar
dariya. Aysha da bata san mike faruwa ba ta fito a motar tana rungume Anaam da
faɗin, “Wayyo blood motar nan ta haɗu wlhy ALLAH yasa a kashe da kai”. Wani bahagon
tari ya sarƙe Fadwa, cikin sassarfa kamar zata kife ƙasa dan sauri tabar wajen
hawaye masu azabar zafi na kufce mata.
Gaba ɗayansu kallonsu suka maida gareta, dan sai yanzu ma shi Shareff yasan
Fadwar na'a wajen. Cike da son basarwa itakam Anaam ta rungume Ayshar. “Thanks you
blood, thanks you”. Shima dai gogan ya basar a binsa kamar komai bai faru ba, ya
nunama Khaleel hanya alamar su shiga ciki idonsa akan Anaam. Anyi sa'a itama ta
ɗago suka haɗa ido. Baki ta ɗan murguɗa masa. Ya taune lips dinsa da sakin murmushi
alamar azakizo hannu. Kafaɗa ta ɗage masa da labe baki irin na i don't care taja
hanun Aysha suka koma motar...

Da ƙyar Fadwa ta iya kai kanta sashenta saboda jiri dake ɗibarta da lulluɓe
ganinta gaba ɗaya. “Subahanalillhi. Hajiya lafiya?”.
Mmn Abu ta faɗa da nufo Fadwa da sauri dake neman zubewa ta tareta. Kuka ta
sakar mata kamar wata karamar yarinya, maman Abu duk sai ta rikice. Kamata tai har
bedroom. Tana son tambayarta mike faruwa tana jin tsoro, dole ta fito ta barta
cikin damuwa. Tadai san labarin kitse baya wuce ƙoƙi dan ta jima da fahimtar Fadwa
na cikin jerin mata masu tsananin kishi. Gata da hali irin na ɓoye abu a rai da
idan bakai dogon nazari akanta ba saika ɗauka kishiya cutarta take musamman irin
Anaam da bata iya ɓoye abinda ke ranta. “ALLAH ya ƙyauta”. Ta faɗa da komawa
kitchen ta cigaba da aikinta.....

Anaam kam da tuni sun koma ciki tana can cikin farin ciki tana waya da Mamie
da Abie ta video call. Addu'a take zubama iyayen nata harda hawaye, yayinda suma
suke kallonta murmushi shimfiɗe a fuskokinsu da tsananin ƙaunarta da tausayinta
harma da alfahari da ita na kai mutuncinta gidan aurenta. Dan aunty mimi ta sanarma
Mamie komai, hakama Mamie ta sanarma Abie, shiyyasa ya danƙara mata mota najin
alfahari da ita akan riƙe tarbiyyar da sukai mata. Sai dai su kansu sun san sun
kaita wani filin gwagwarmayar rayuwane na yankin kaddararta, amma sukanji sassauci
da tunawa zumincin ALLAH suke son karfafawa insha ALLAHU sadaukarwarsu bazata taɓa
zama a banza da wofi ba..

______________________________

Tafiyar dai Aysha bata yuwu a yau ba, dan tuni Shareff ya fice gidan tare da
Khaleel yin godiya ga Abie, Anaam kuma sai ta ƙara samun sauƙin jikinta insha ALLAH
zai kaita. Sai da suka fara biyawa ta office yin wasu muhimman baƙi, ba wani dogon
zama sukai ba sai zuwa monday idan ya dawo aiki. Takardar da zai basu suje su duba
kafin zaman ya nema ya rasa, cikin ɗan dafe kai ya dubu Khaleel da Fharhan. “Inaga
fa nama bar file ɗin nan a gida wlhy, Khaleel saika koma kenan dan dole ne mu basu
suje su duba.”
“Okay bara naje ai bawani nisa bane”.
“Okay ba damuwa, kafin ka isa zan kira su ɗakko maka kawai”.
Kansa ya jinjina masa ya fice. Shi kuma ya shiga ƙoƙarin kiran layin Fadwa.
Harta tsinke ba'a ɗagaba, yay mata uzirin ko bata kusa ya sake kira, amma nan ma
dai hakan, ya ƙara kira har sau uku sai aka koma danna masa number busy. Ransa ya
sosu matuƙa, dan ya gane tana kan sani. Amma sai ya shanye kodan baƙin dake tare da
shi ya maida akalar kiran ga Anaam. Gama wayarta da su Abie kenan kiran nashi ya
shigo, bugu biyu ta ɗauka har yanzu muryarta cike da farin ciki tai masa sallama. A
hankali ya sauke ajiyar zuciya, ya amsa mata.
“Har yanzu murnar motar ce?”.
“Humm Yaya bazaka ganeba”.
Murmushi yayi, “Okay idan na dawo ai sai ki ganar dani, yanzu nidai nutsu na saki
aiki”.
“Okay” ta faɗa kanta tsaye.
“Ki duba a study table ɗina, akwai wani file green a wajen ki ɗaukama Khaleel zai
zo ya amsa yanzun”.
“Tom”.

Ta duba a kurkusa inda yace amma bataga file ɗin ba, sai dai kuma
hankalinta ne kawai bai kaiba saboda ya dannesa da wani book. Ta shiga bin komai
daki-daki da kallo tana ɗan ɗagawa harda buɗe drawers ɗin wajen. Saukar idonta akan
wani ɗan akwati ya sata nutsuwa tana kallonsa, harta maida drawer ɗin ta rufe sai
kuma ta sake buɗewa ta ciro akwatin. “Uhhm su Alhaji Yaya mm mi kuma ake ɓoyewa
anan? Koma dai miye zuciyata na son gani”.
Tana ƙoƙarin buɗewa kira ya shigo wayarta, shine dan haka ta ɗaga. Kafinma yay
magana tace “Yaya ban ganiba fa, inata nema kuma tun ɗazun”.
“Kamarya? Bayan nasan yana nan akusa-kusa. Ki ɗan ɗaga kayan wajen Khaleel
na waje yana jiranki amfani zanyi da shi”.
“Oh sorry kamarma gashi anan ka ɗaura littafi akai”.
“Ok ki kai masa yana jiranki”.

Koda ta kaima Khaleel littafin sashen ta sake dawowa. Dan zuciyarta naga
akwatin nan haka kawai batare data san dalili ba. Kiciniyar buɗewa ta shigayi, da
ƙyar ta dace ya buɗu bayan ta haɗa da ƴan dabaru. Da littafi ta fara cin karo, ta
ɗan jujjuyashi tana taɓe baki ta ajiye. Sai envelope brown babba. buɗeta tai ta
zaro albom na hotuna mai tudu sosai sai dai bai cika girma ba a tsaho. “Hotunan
sirri ne kenan su Yaya aka ɓoy....” ta kasa ƙarasa abinda ta faro. Ko'a magagin
barci aka tasheta babu gilashi a idonta aka nuna mata hoton babu gargada zata bada
amsar itace. Hotone da taga irinsa yafi guda ashirin a gidansu. Hoton ne da aka
ɗauketa a ranar haihuwarta tun a asibiti. Tana rungume a hanun Yaya Shareff Abie da
aunty Mimi sun sakashi tsakkiya suna leƙenta a hannunsa ya babbake ya hanasu gani.
Da sauri ta koma na ƙasa, shi kuma a ranar sunanta ne ita da shi, na gaba itace da
shi da Mamie da Abie da aunty Mimi. Ta cigaba da buɗe albom ɗin mamaki fal ranta
dan ta kasa fahimtar ma'anarsa. Hotuna na gaba sun kasance a gurare daban-daban.
Wani wajen ita kaɗai, wani ita da shi, wani har da su Abie. Ranar birthday ɗinta na
cika shekara ɗaya. “Ya ALLAH” ta faɗa tana cigaba da kallonsu daki-daki. Jikinta ya
ɗan fara rawa ganin hotunan da har tana a shekarar shiga primary, secondray, kai
har jami'a ma akwai, bayan zuwa lokacin Shareff baya tare da su. Duk wani hoton
birthday ɗinta akwaisa, hakama hotunan bikin salla kona wani taron makaranta kona
islamiyya duk akwai. Hoton ƙarshe da yay matuƙar bata mamaki shine na ranar ɗaurin
aurensa da Fadwa, itama kuma ranar nata ɗaurin auren da bata sani ba. Rubutun da
yay a jikin hoton ya matuƙar firgitata..........✍
_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_


*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:


07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇


09134848107

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*


[11/15, 11:40 PM] My Zafafa: *_Typing📲_*

*_BABU SO....!!_*
_(Miya kawo kishi?)_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718

*_65_*
........ *_Cikar burina shine ganin irin wannan ranar tare da ke gimbiyar mata,
kece sirrin ruhuna, nima inajin raɗaɗi fiye da wanda na gani a cikin ƙwayar
idanunki. I'm sorry! ranarki tana zuwa_*.
Ta haɗiye yawu da ƙyar, da sake maimata karatun kamar mai bita, dan yayisa ne
da yaren maley ta tabbatar batayi kuskuren karantawa ba. Zaune takai dan ƙafarta ta
kasa ɗaukarta. Ta cigaba da zaro sauran abinda ke cikin akwatin. Akwai kashi-kashi
na ribbons ɗinta, ta gane hakanne saboda matuƙar son da takema wasu, wasu kuwa ta
gansu a hotunanta dake cikin albom ɗin can tun tana yarinya. Sai wani ɗan abunta
mai kamar kwalba cikinsa da taurari da wata suna yawo, a tsakiyarsu da alkur'ani a
buɗe, idan bata manta ba Mamie ce ta bata shi as gift ɗin kammala haddar alkur'anin
ta, amma saita nemesa ta rasa a daga baya duk da kuwa a side drawer na gadonta
yake. Har kuka tayi na rashinsa, kai tsaye kuma ta zargi mai aikinsu ce ta fasa
amma ta ɓoye. Mamie ce ta kashe wutar a lokacin ta sake saya mata wani sai dai
yasha banban da wannan ɗin dan haka taita mitar batason sa har sai da Abie ya shiga
zancen ya lallasheta. Ashe Yaya MM ne ya sacesa. Ta cigaba da kallon abubuwa da
dama nata, kuma masu muhimmanci a gareta data nemesu ta rasa a lokuta mabanbanta,
wanda a iya tunaninta ta rasa mai ɗaukar mata su, duk da har su Amrah yaran aunty
mimi tasha zarga. Book ɗin ta ɗauka saboda ji a ranta shima ya shafeta. A shafin
farko sunanta ne da rubutu kamar haka.
*_Juwairiyya Anaam! kece matar aurena kuma uwar ƴaƴana da izinin
UBANGIJINA. Ni kaɗai aka haifawa ke, zan kuma rayune domin ke insha ALLAHU._*
Ta buɗe shafi na biyu zuciyarta na tsitstsinkewa. _Da ace wani bawa nada
damar tsara labarin rayuwarsa da wanzuwarsa, zan tsara nawane kawai domin ke kaɗai
a wannan duniyar. Ina roƙon UBANGIJI ke ɗin karki zama a cikin ƙaddarar abinda
ALLAH bazai mallakamin ba, zuciyata bazata iya ɗauka ba, ya rabbi ka zama gatana
akowane hali_.
Haka ta cigaba da karanta abubuwa daban-daban akan rayuwarta da tasa daya dinga
rubutawa tamkar labarin littafi. Mafi ƙololuwar ruɗa tunaninta da saukar da
hawayenta shine a gaɓar da Mommy ta takura masa auren watanta. Duk wani tashin
hankalinsa ya zanashi da fargabar karta suɓuce masa. Zuwanta Nigeria da sunan
hidimar ƙasa mafi girman sassauci dajin ƙwarin gwiwar yin biyayya da cusa son Fadwa
a ransa matsayin sadaukarwa ko UBANGIJI zai masa tukuyci da samun Anaam. Kukanta ya
ƙara ƙarfi jin cewar ya kwanta jiyyane akan jin za'a aurama waninsa ita ba shi ba,
harda barazanar kamuwa da ciwon hawan jini daya nema shafar lafiyarsa.
“Innalillahi...” ta shiga ambata da kifewa jikin desk ɗin nasa ta shiga raira kuka,
wani al'amari mai girma na ratsa dukkan magudana da jijiya ta jikinta. Sai da tai
kuka sosai harta gode ALLAH kafin ta ƙarasa ganin wasu zane-zane da yayi wanda duk
fuskartace ya zana, kai kace tana tsayene a gabansa yay zanen. Da kyar ta miƙe ta
tattare komai ta maida masa yanda yake ta maida a drawer ɗin sannan ta fice jikinta
a saɓule.

Aysha dake zaune a falo tana aikin nata na tiktok data koya gun Fadwa ta
bita da kallo. Ganin zata wuce bedroom batare data tanka mata ba ta riƙo hanunta da
sauri. Juyowa tai tana kallonta, hawaye masu ɗumi na sauka mata a kumatu, sai kuma
ta rungume Ayshan tana saki wani marayan kuka da ita kanta bata gama tantance na
minene ba.
Hankalin Aysha ya ƙara tashi, ta ɗagota da sauri. “Ya ALLAH blood wai miya
farune? Yaya ne ya miki wani abu?”.
Kanta ta girgiza mata.
“To minene? Ko dai maganar aurence dai har yanzu? Da zaman wannan gidan?. Dan ALLAH
ki kwantar da hankalinki Anaam. Ki saurareni a wannan gaɓar na buɗe miki kanki ta
yanda wlhy sai Yaya Shareff ya dawo tafin hanunki ta hanyar soyayya da bin dokokin
ALLAH. Na fahimci rashin sanin minene kishi da rayuwar gidan malam bahaushe ke
sakaki tafiya a haguggunce a wannan gidan har Fadwa ke jan akalarki da makirci. Ki
nutsu ki saurareni Please”.
Bataƙi ta Ayshan ba, suka koma suka zauna cikin hikima da basirar da ALLAH ya
bama Aysha. Da kasancewar ta tashi a rayuwane ta cikin gidan yawa dama salon kishin
Mommy da Aunty Amarya. Ga karance-karancen littatafan nan na hausa duk tana taɓawa
ta shiga warware mata abubuwa masu yawan gaske. Anaam irin mutanen nanne masu
saurin haddace abu idan an faɗa musu, musamman akan abinda ke wahalar da su, ko
wani abu da basa ƙaunar a kaisu ƙasa. Hakan ya bata matuƙar gudunmawa wajen
fahimtar Aysha daki-daki babu kuskure. Sosai taji daɗin bayanin dan haka ta rungume
Ayshan.
“Na gode blood, nagode, irin godiyar da babu alƙalamin dazai iya rubutawa. Sai
dai ki sani duk abinda kikaga inayi a gidan nan kamar mara wayo ba rashin wayo bane
sarai ina lure da komai da binsa daki-daki, sannan akan sani nake aikatawa saboda
wasu dalilai nawa. Idan banyi hakaba shi kansa bazan gama fahimtar halayyarsaba
balle ita. Tabbas nasan bazan taɓa iya kaiku wayon zama a irin rayuwar da kuka
tashi ba, sai dai koba komai ina shigowa cikinku nima ina ganin wasu abubuwan.
Daliline ya sakani zaɓar yin duk abinda nakeyi. Sai dai a yanzu kalar rubutun zai
sha banban da kalar takardar. A yanzu lokacina ne, kisa a ranki lokacin Juwairiyya
Usman MD Shareff zai fara a gidan Al-Mustapha Muhammad MD Shareff. Nayi alƙawarin
bazanyi abinda zai cutar da kowa ba, sai dai zan nunama kowa kowacce mace da ilimin
zaman gidan aure UBANGIJI ya halicceta, kuma ko wacece ita ko'a ina ta tashi zata
rayuwu, ta kuma riƙe kambunta na ɗiya mace. A kwanakin da nayi biyar a gidan nan,
na karanci abubuwa masu dama a cikinsu, zan kuma fara sharar fadata da su domin
samun damar shimfiɗa mulkina batare da wani datti ya sha gaban cikar burina ba”.
“Woow vary interesting my blood. Haka nake sonki dan ALLAH. Ki haukata mana
Yaya Shareff, ki kuma dawo mana da Fadwa hanya tabar bin karatun su Mommy, ta zama
mai ra'ayin kanta”.
Anaam ta ƙyalƙyale da dariya, zuciyarta fes tamkar an sauke mata dukkan wani
nauyi da ƙuncin da takeji a yau a yanzu yanzu. Basai amfaɗa ba, da ni da mai karatu
duk zamu fahimci hakan nada nasaba da abinda taci karo da shi wannda a baya bashi
take kallo a fuskar Shareff ba. Sun ƙara tattaunawa sosai akan wasu abubuwan da
dama da Aysha kafin ta miƙe ta koma sashen Shareff domin gyarawa bisa shawarar
Aysha.
Bata jin daɗin jikinta saboda ɗinkin da akai mata na sakata jinta tamkar a
takure, ga tafiyarta har yanzu bai zama normal ba kamar da. Amma haka ta jure a
daddafe na rashin sabon da wahala ta gyara ko'ina na sashen nasa, sauƙin ma babu
datti mai yawa. Sai da ta tabbatar ko'ina ya mata da kamshi sannan ta rufe ta fito.
Baki ta saki tana kallon yanda Aysha ta ƙara gyara sashenta itama. Ta saki murmushi
da harar Ayshan dake tsaye tana karanta mata taje tayi wanka ta ɗauki ado dan Yaya
Shareff na gab da dawowa. Akwai tsoro tattare da ita na abunda ya faru, amma
gargaɗin likita akan Shareff ya bata ƙwarin gwiwar tabbatarma kanta babu wani abu
tunda ko dai baya cikin hayyacinsa ai baya nema wani abu daga garetaba zaren ɗinki
na a jikinta. Da wannan tunanin ta faɗa wanka. Koda ta fito tsareta Aysha tai wai
sai ta mata kwalliya. Badan taso ba dole ta tsaya kuwa Aysha ta zaneta tsaf dasu
jaja leɓe da barbaɗa kumatu na zamani. Turare kuwa har ji take yana hawa mata kai
dan khumras nata sun sami haɗine na musamman daga hajiyar sudan, ga kuma *_YERWA
INCENSE AND MORE +234 809 521 5215 da miss xoxo tayo mata haɗi da sai ƴar gata ke
samunsa😋_*. Hakama na kanti duk masu tsadane da ƙamshi na musamman da aka zuba a
lefe. Ƙanan kayan nata taso sakawa, sai dai Aysha ta hanata hakan, acewarta kayanmu
na gida sunfi mata ƙyau. Dole badan taso ba ta haƙura ta shirya cikin skirt da riga
na lass daya zauna mata a jiki tamkar ka saceta ka gudu. Aysha tai mata ɗauri na
zamani daya saka ita kanta kasa rufe baki sai faman kallon kanta takeyi a mirror da
ƙyalla hotuna da wayarta.....

A gajiye ya iso gidan bayan idar da sallar isha'i. Ya fiddo ledojin daya shigo
da su na fruits kashi biyu. Sashen Fadwa ya nufa, ya sameta zaune a falo ƙafa ɗaya
kan ɗaya tanata cika da batsewa. Kallo ɗaya yay mata ya ɗauke kansa dan ko
sallamarsa bata amsa ba. Ledar ya ajiye batare daya ce ko a ba yay ficewarsa yana
ƙwafa. Dan a yanda ta masa ya bashi tabbacin tana kan sani taƙi ɗauka masa wayarsa.
Sashen Anaam ya nufa da ɗayar ledar yanata faman furzar da hucin ɓacin rai......✍

_🤪🤪Shike nan an shiga tsakaninmu da Soulmate 🙆🏻, dolene mu koma gidan.... Basai na
faɗa ba😭_.
_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_


*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:


07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇


09134848107

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*

[11/23, 10:16 PM] My Zafafa: *_Typing📲_*

*_BABU SO....!!_*
_(Miya kawo kishi?)_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718
*_66_*

.........Fitowarsu falon kenan suma babu jimawa, Anaam dafe da kanta dake mata ciwo
saboda kukan da tasha ɗazun, ga jikinta har yanzu sam baya mata daɗi irin na shiga
sabuwar rayuwar da ba'a saba ba. Aysha ce ta amsa masa sallamarsa, ya ƙaraso ciki
idonsa akan Anaam. Ya miƙama Aysha dake masa sannu ledar hanunsa.
“Ita wannan lafiya kuwa?”.
“Kanta ne ke mata ciwo, nayi-nayi tasha magani kuma taƙi”. Zaune yakai kusa da ita,
ya janye hanunta dake dafe da kanta. Kasa kallonsa tai, dan haka kawai take jin
wani irin matsanancin kunyarsa. Shiko ya matuƙar shagala ne a kallon kwalliyar dake
zane akan fuskarta, a kasalance yakai hannunsa kan haɓarta ya ɗago fuskar da ƙyau,
hakan sai ya tilasta mata ɗago nata idanun dake cike da ƙwalla ta kallesa. Ba
ƙaramin jarumta yay wajen jawo numfashinsa dake neman kufcema ƙirjinsa ba, ya
matsota jikinsa tare da ɗaura hanunsa saman goshin nata.
“Wannan idon naki kinyi kuka da shi, ko muje asibiti ne?”.
Ya faɗa a hankali cikin kunenta. Kanta ta girgiza masa da ƙara lafewa a jikin nasa
har hakan ya so bashi mamaki. Dan yasan dai koshi ya ringumeta turesa take kota
janye jikinta, amma yanzu ga saɓanin hakan yana gani, koda yake tunda abin nan ya
faru ya fahimci ta zama wata shiru-shiru, tsiwar taɗan ragu kaɗan ko likimo ne,
mata sunji maza kenan. Fitowar Aysha ta sakata janye jikinta, shima sai ya miƙe
yana faɗin, “Bara na watsa ruwa sai a samo miki magani”.
Baki ta ɗan tura masa da kaiwa kwance. “Ni basai nasha magani ba fa”.
Juyowa yay daga niyyar barin falon da yayi, “Oh tunda hakane tashi na fasa
barinki anan ɗin”.
Dole badan taso ba ta miƙe, dan ya tsuke fuska babu alamar wasa, duk da dama dai
tunda ya shigo babu fara'ar tattare da shi. Aysha da tuni ta koma kitchen yay kira.
Fitowa tai da sauri tana amsawa.
“Gyaramin fruits ɗin nan”.
“To Yaya. Ko'a haɗa salad?”.
“Duk yanda kikai is ok”.
Kanta ta gyaɗa masa, shi kuma ya kama hanun Anaam suka fice. Ta bisu da kallo
murmushi bayyane akan fuskarta. Tana fatan ALLAH ya hana su Mommy raba wannan auren
har abada. Dan sun kasance abin birgewa best couple ever matuƙa”.
Koda suka iso sashen nasa a falon ya zauna, ya riƙota saman cinyarsa ya
zaunar. Yanzun ma cikin mamaki yaga ta lafe a jikinsa. Ya ɗan murmusa da shafar
fuskarta idonunsa na bin fuskarta dake ƙwaɓe alamar rashin jin daɗi da kallo.
“Kodai har yanzu garden ɗin na zafinne? Noorie!?”.
Kanta ta sinne a ƙirjinsa da riƙo hanunsa dake kaiwa jikinta, dan zuwa yanzu ta
fahimci mi yake kira garden ɗin. “Yaya Please ka daina”.
“No Aunty babu wannan zancen”.
Ya faɗa cikin kwaikwayon muryarta. Murmushi ya kufce mata tare da ƙara cusa kan
nata cikin jikinsa. Dan yanda yay maganar ya matuƙar bata dariya. Shima murmushi
yay da kaima wuyanta kisses. Tsoro ne ya kamata, tai ƙoƙarin jan jikinta baya amma
ya hana hakan.
“Wayyo kaina zai fashe Yaya”.
Dakatawa yay daga ƙoƙarin cusa hanunsa cikin rigarta. Ya riƙo kannata. “Ayya.
Sorry, sorry”. Sake langaɓewa tai kamar gaske. A ƙasan ranta kuwa dariyace ke taso
mata tana dannewa. Da gaske kan nata na ciwo, amma yanda takeyi ɗin yanzu harda
pretending. Yin hakan kuma shine mafita a gareta saboda ganin yana neman sakin
layi, itako a yanzu in ba giyar wake tasha ba mizai kaita sallama masa ya kasheta.
Ai anyi kenan babu ƙari tunda abun azaba kawai akesha a ciki. Ita jiya tunaninta
gaba ɗaya akan tayaya wasu matan ke iskanci a cikin wannan wahalar? Ko kuwa su
basajin abinda taji da bazata taɓa mantawaba har duniya ta tashi.
Zaunar da ita yay a kujerar ya shiga bedroom ɗinsa. Dai-dai nan Fadwa tai
sallama. Anaam tai kamar bazata amsa ba sai kuma ta amsa ciki-ciki. Sam Fadwa
bataji an amsa ba, sai dai sanin halin mai sashen da kuma halin da suke ciki na
fushi da juna ya sata shigowa a ganinta kobai amsa ɗin ba zata shigo. Turuss ta
ɗanyi na ganin Anaam, sukaima juna kallon cikin ido kowacce ta janye da takaicin
ƴar uwarta da tsagwaron kishi.. Basuyima juna magana ba, Fadwa ta nema waje ta
zauna.
Fitowarsa ta saka Fadwa ɗaga kai tana kallonsa, shima ita ɗin yake kallo da
mamaki a ƙasan zuciya, sai dai a fuska babu ko ɗigon hakan sai ma janyewa da yay
cikin halin ko'in kula ya nufi Anaam dake kallonsu ta ƙasan ido. Ita dai bata san
sunada wata matsala ba a gidan. Dan haka bata kawo komai a ranta ba game da ɗaure-
ɗauren fuskar tasu. A hanun kujerar da take kwance ya zauna,
“Tashi kisha. Kimmaci abinci kuwa?”.
Sai da ta ɗan saci kallon gefen Fadwa sannan ta ɗan tura baki da narke fuska.
“Ni banajin ci”.
“Uhhm baƙya son ci, yarinyar nan ki rage taɓaran nan naki, yanzu abincin ma sai
kin nuna masa hali? Yanzu dai kinga ba'a shan magani sai da abinci, faɗamin mi zaki
ci?”.
Kallonsa ta ɗanyi da juya ƙwayoyin idanunta, sai kuma ta narke fuska da
girgiza kai. “Da gaske bana son ci, barci nakeji kawai”.
“Uhm-uhm fa, bana son zama da yunwa sam! Ki dai sha ko fruits ɗin can ne idan
Aysha ta kawo. Zakisha ko?”. Ya ƙare maganar da ranƙwafowa kanta yana sinsinar
wuyanta. Ta gefen ido ta saci kallon Fadwa, sai taga su take kallo fuskarta ciɗin-
ciɗin kamar zata fashe har wani jajaja takeyi na alamar ɓacin rai abunka da fari.
Murmushi tai mai sanyi dakai hannu ta shafi fuskar tasa a ranta tana faɗin (Ashe
kin san akwai ciwo ni kike yi masa kiss a gabana, zan koya miki iya zaman duniya).
Hanunta da take neman janyewa ya cafke da sauri yana maidashi akan tattausan gashin
kumatun nasa. “Kin yarda zaki sha?”.
“Ni dai ɗan kaɗan”.
Ta faɗa a shagwaɓe.
Da ƙyar ya iya jan numfashi, dan shagwaɓar tata ba ƙaramin susutashi take ba. “Good
girl”.
Murmushi tayi da janye hanun. Riƙeta yay, ta marairaice masa. “Nifa fitsari
zanyi”.
“Okayy to ana buƙatar abokin rakkiya?”.
“Naƙi wayon”.
Ta faɗa da zille masa tana ƴar dariya. Bedroom ɗinsa ta nufa batare da ko sashen
Fadwa ta kallaba. Tana shiga ta zube a gadonsa dan babu wani fitsari dama. Kawai
dai taba Fadwa space ne. Domin rama abinda tai mata bashike nufin bazata mata
adalci ba. Kuma koba komai yanzu kawai ta nuna mata cewar alwashinta tabbatacce ne
akan mantar da Yaya MM ita in har tana a tare da shi.

Shiko daga can da kallo ya bita har saida ta shige, a hankali ya haɗiye
murmushi kan fuskarsa. Miƙewa yay kamar zai bar falon. Tasan idan tai wasa da
wannan damar zatafi haka shan wahala. Kamar yanda Mama (Gwaggo halima) ta faɗa mata
ba haka ake buƙata ba, taje ta shirya dashi kodan kasancewar gobe ne zata amshi
girki, suna buƙatar tai aiki da wasu fitinannun maganin mata da aka kawo dominta
tun daga ƙasar sudan.
“Dan ALLAH kayi haƙuri” ta faɗa da sauri tana ƙoƙarin haɗiye hawayen da tun
ɗazun take son su zubo ko zata samu sassauci. Ratseta yay zai wuce tai azamar
riƙosa. Bai juyoba amma ya dakata. Ta share hawayenta hanunta riƙe da nasa. “Dan
ALLAH kayi haƙuri, nasan nayi kuskure. Amma wlhy sharrin shaiɗanne”.
Ransa a ɓace ya dubeta da wani mugun kallo daya matuƙar neman gigitata. Saurin
sakinsa tai da girgiza masa kai. “Nasan nayi kuskure amma dan ALLAH kayi haƙuri
haka bazata sake faruwa ba”.
“Tashi kibar min falo”.
“Please Soulmate dan ALLAH”.
Sallamar Aysha ce ta sakashi haɗiye maganar bakinsa, ya koma ya zauna da amsa mata.
Itama hawayenta ta shiga sharewa idonta na satar kallon ƙofar bedroom ɗinsa, dan
zuciyarta raya mata take Anaam na wajen laɓe tana saurarensu. Sosai takejin raɗaɗi
da ɗacin hakan, amma taci alwashi komi zai faru a yanzu ɗin bashi ne Anaam ɗin
zataci itama zata rama.
Aysha ta dire tray ɗin hanunta a gabansa, fuskarta da murmushi ta gaida Fadwa
da taƙi kallonta saboda kar Aysha ta fahimci tayi kuka. Kanta kawai ta jinjina
mata. Ayshan bata damu ba, dan tasan halin Fadwa wani lokacin itama akwai yarfi.
Hankalinta ta maida akan Shareff, “Yaya a zuba?”. Kai ya girgiza mata alamar a'a,
sai kawai tai musu sallama ta fice a ranta tana ayyana akwai matsala gaskiya, sai
dai rashin ganin Anaam yasa taji wani iri.
Kusa da shi ta taso ta dawo, “Soulmate......”
Hannu ya ɗaga mata a fusace. “Fadwa! leave me alone. Tashi ki fita”.
Idanu ta tsura masa zuciyarta na mata raɗaɗi, tasan a cikin fushi yake, kuma
shi baya son yanke ma mutum hukunci cikin fushi. Jiki a saɓule ta tashi ta fice
wasu hawaye masu zafi da jin matuƙar tsanar Anaam na ƙaruwa a ranta. Dan a ganin
duk an mata hakane saboda Anaam, ta kuma tabbatar ba haka iyayen Anaam suka bar
Shareff ɗin ba kamar yanda Mama ta sanar mata yanzun.
Ya jima zaune a wajen zuciyarsa na masa raɗaɗi da ƙuna, baya son ɓacin rai da
damuwa, yama rasa ina zai kama da halin matan nasa. Ya samu ita Anaam ɗin ta sakko
ya fara samun kwanciyar hankali ita kuma Fadwar na neman rikita masa lissafi. dole
ne ya musu sabon shiri na zama da kowacce da halinta. Yasan duk abinda Anaam zatai
tana yinsane a karan kanta sannan bata da ɓoye-ɓoye. Fadwa kam ya fahimci akwai
zugar mutane baibaye da ita, dan tun zuwan Anaam gidan ya fahimci ta ajiye wasu
halayenta na zahiri ta aro waɗansu daban, idan bai tashi tsaye a kanta ba zasu iya
laɓewa a bayanta su tarwatsa masa farin cikin gidansa, shi kuma harga ALLAH yana
sonta itama. Ya furzar da numfashi mai ɗaci, tunawa da Anaam dake cikin bedroom ya
sashi miƙewa ya nufi bedroom ɗin. Da mamaki yake kallonta kwance a gado har tayi
barci, ya tsugunna saitin fuskarta yana sakin murmushi da kai hannu ya shafa kanta.
“Dama fitsarin ƙarya ne kenan?”.
Idanu ta buɗe a hankali dan dama barcin baiyi nisa ba, sai kuma ta maida zata
lumshe da ture masa hannu. Hannun nata ya riƙo cikin nashi, fuskarsa gab da tata,
“Tunda kin tashi muje kisha fruit ɗin”.
“Ni na ƙoshi barci nakeji Yaya”.
“Ni kuma ban yarda ba idan kika sha sai kiyi barcin”.
“Uhhum-uhhum”. Ta faɗa tana noƙe kafaɗarta. Miƙewa yay yana murmushi, ya ɗagata
gaba ɗayanta. Watsal-watsal ta farayi da ƙafafunta. “Wayyo Yaya! Wayyo Yaya ni ka
saukeni na ƙoshi”.
“Wayyo Aunty! Wayyo aunty ni bazan saukeki ba sai kinsha”. Ya faɗa dai-
dai suna kaiwa falon.........✍

_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_


*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:


07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇


09134848107

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*


[11/23, 10:16 PM] My Zafafa: *_Typing📲_*

*_BABU SO....!!_*
_(Miya kawo kishi?)_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718

*_67_*

.........Da ƙyar ya iya lallaɓata tasha fruit salad ɗin, dan da gaske barcine a
idonta sosai. Ganin tanata faman lumshe idanu dole ya barta. Itama sai ta miƙe tana
ɗaga masa hannu. “Yaya good night”.
Kafin ya samu damar cemata komai tabar falon da hanzarinta dan bata buƙatar
yace zai dakatar da ita. Shima baiyi yunƙurin dakatar da itan ba. ya dai bita da
kallo.

Kamar yanda ya saba bayan gama duk wata al'adar rayuwarsa yay shirin barci.
Yaso yin kwanciyarsa anan amma zuciyarsa taƙi aminta da hakan. Ya fito a nutse yana
kulle ƙofar. Sashen Fadwa ya fara nufa dan bazaiƙi sauke nauyin da ALLAH ya ɗaura
masa ba komi sukai masa na laifi. Yayi mamakin samunta a falo bata kwanta ba. Sai
dai hankalinta gaba ɗaya yana akan waya ne. Ta mugun shagala a yin editing video da
zatai posting, wanda ɗauka ce mara daɗi, dan kuwa faɗa suke da wata mai suna Teema.
Faɗan kuma ya samo asaline akan ita Teema ɗin ta ɗaura hoton Shareff a shafinta
tana bin waƙar soyayya. Sai wasu a cikin followers ɗinta suka ɗakko videon suka
dinga tagging Fadwa da gaba ɗaya a yau bata buɗe data ba sai da yammar nan, dan
tashin hankalin Anaam ya saka a kwana biyun nan ta rage yin posting akai akai kamar
da da arana takan ɗora videos sama da uku. Sima itace ta fara kiran Fadwa ta sanar
mata lokacin fitowarta a sashen Shareff kenan. To shine fa tun ɗazu ɗin ake tafka
rigima tsakanin Fadwa da mabiya bayanta su Sima. Itama Teema da nata magoya bayan
sunama Fadwa izgilin Teema zata shigo itama ata uku kafin shekara ta ƙare. (😜gsky
naso ace kuje tiktok kuga rigimar nan guys🤣😆).
Tsaiwarta a kusa da ita ta sakata wani mugun zabura, daka ganta kasan ta
firgita. Ta kife wayar akan kujera a daburce take masa sannu. Idanu ya tsira mata
cike da mamaki matuƙa, dan baiga abin zabura ɗin ba anan. Ya maida dubansa ga wayar
da take faman ja tana turawa ƙasan throw pillow, zuciyarsa ta ɗarsu a karo na biyu
game da ganinta da ɗaukar hankalinta da waya keyi, sai dai na yau yafi ƙarfi dan
ƙarara alamun rashin gaskiya sun bayyana akan fuskarta. Komai baice mata ba ya juya
ya fice.
Ta bisa da kallo zuciyarta na luguden daka, dan ta tabbata shirunsa wani abu ne
mai zaman kansa. Gaba ɗaya sai hankalinta ya rabu biyu, matsawa tai jikin window,
sai ta hangosa zai shige sashen Anaam. Jikin windown ta bari, ta ɗauka wayarta da
sauri ta nufi bedroom harda murzama ƙofar key.

A falo ya samesu Anaam najan hanun Aysha akan sai taje su kwanta a ɗaki
ɗaya. Ita kuma Aysha ta dake cewar ita bazata ba a ɗakin baƙi dake kusa da dining
zata kwana. Shigowarsa ta sakasu dakatawa daga jayayyar tasu, Aysha kuma ta samu
damar zare hanunta ana Anaam tana mata gwalo.
Filon dake saman kujera tai saurin ɗauka ta jefama Ayshan, da gudu Aysha ta
ƙarasa shigewa ɗakin tana cigaba da dariyarta. “Zan kamaki ne ai yarinya”. Ta faɗa
tana kallon Shareff dake kallonta.
“Barcin kenan?”.
Kanta ta langaɓe masa gefe fuska a narke sai dai batace komai ba. Cigaba da
takowa yay har zuwa gabanta, ya kamo hanunta yana faɗin, “Muje”. Kafaɗa ta noƙe
masa. Dan haka ya tsaya yana kallonta. “Miyasa?”. Ƙara narke masa tai murya a
karye. “Sai dai ka goya ni”. Ya waro idanunsa sosai a kanta, fuskarsa na sassauta
tsukewar da take. “Da ɗinkin zan goyaki?”.
“To bakai kaja akayi ba”.
Karon farko ya saki murmushi har haƙoransa na bayyana. Jikinsa ya rungumota da
ɗaura kansa saman kafaɗarta. “Muka dai ja akayi”.
“Dawa?”.
Ta faɗa da sauri tana ƙoƙarin jan jikinta daga garesa. Ƙaramar dariya ya saki dan
yanda tai ɗin kamar wadda aka kirama mutuwa. “Da ke mana, harfa wani kanannaɗeni
kike. Ko muje a ƙara yanzu ma? Na san dai ya daina zafin ai”.
Kukan ƙarya ta sakar masa wai ya mata sharri sai sunje shari'a gaban su
Abba.
Cikin ɗage gira da ƙoƙarin damƙota ya ce, “Oh really? To kafin muje bara na
idasa abinda na fara shari'ar tafi armashi”.
Saurin goce masa tai tabar wajen da gudu. Binta yay da sassarfa, cikin saurin ya
riƙe ƙofar da take neman rufewa ya shige shima. Sosai ta marairaice fuska, dan da
gaske ta ɗauka yin zaiyi. “Please Yaya MM wlhy ni bana so, kawai kaje wajen matarka
ka kwanama na yafe”.
Damƙota yay tare da ɗagata cak ya dire saman gado, watsal-watsal ta
shigayi da turasa, hakan yasa suka shiga ƴar kokawa wadda ya ƙyaletane kawai. Ya
fara kai mata cakulkule tana dariya da turesa. Shima dariyar yakeyi da ƙoƙarin
kaima wuyanta zuwa kirjinta kiss. Da haka yaci nasarar haɗe lips ɗinsu waje guda.
Tun tana son kauda kanta har yaci galabar shagaltar da ita ta fara bashi haɗin kai.
Romancing juna sukeyi cike da sauka a layin manta matsayin junansu. Da sauri ta
damƙe masa hanunsa dake ƙoƙarin zame rigar barcinta da tuni ya sauketa akan ciki
dama. Jin yana ƙara ƙasa da ita ta dawo hayyacinta. Dakatawa yay tare da buɗe
shanyayyun idanunsa dake cike da fitina yana kallonta, dai dai itama ta buɗe natan
dake da raunin gani dan tuni ya zare gilashinta dama. Ƙoƙarin janyewa tai ya
sarƙesu cikin nasa.
“Why?”.
Ya faɗa da ƙyar muryarsa a matuƙar ɗashe tamkar mai mura.
“Akwai ciwo”.
Ta bashi amsa cikin raɗa itama dan muryar tata ko fita batayi rawa take ma
kamar mai shirin sakin kuka. Kansa ya girgiza mata alamar kar tayi, amma kamar ya
zugata sai gasu suna zirarowa da gudu. Rungumeta yay tsam a ƙirjinsa tamkar mai
tsoron a ƙwace masa ita.
_“Zubar hawayenki dai-dai suke da ƙuna mai raɗaɗi a zuciya. Ni mai raunine akan
ki Juwairiyya. Da ke kaɗai aka raini wannan zuciyar tun daga ƙuruciya har girma.
Nakanfi buƙatar nisantarki a zahiri, amma a baɗini ke ce sirrin ƙwarin gwiwar
dukkan wani nasarorina. Nakanji himma da ƙawa zucin jajircewa a karan kaina domin
ke kaɗai ƙwalli. Idan na danganta matsayinki a zuciyata da kalmar *SO* kawai
nakanji tayi ƙanƙanta da rage miki kimar zamowa ke wacece ɗin. Da ace so kwalba ne
da tuni ƙarfin ikonki ya tarwatsashi daga zuciya saboda *GIRMAN KI*. K ɗaya tilo, k
ɗaya ƙwalli a tarihin da UBANGIJI ne sarki mai ikon sarrafa zukata kawai ya lulluɓe
saboda hikimarsa. Ki rayu dani duk tsanani koda ace baƙya buƙatata a irin matsayin
da ke kike da shi a wajena. Na miki alƙawarin nawa ya wadatar damu da har ƴaƴan da
zamu haifa.”_
Maganar yake da harshe, amma ita zuciyarta ce ke neman ɓarkewa gida biyu domin
yana karantasune a gareta tamkar maimaici akan abinda ta gani a ɗazun. Taigar
jikinta gaba ɗaya ta gama miƙewa, da ace ba rungume take a jikinsa ba babu abinda
zai hana ya ga yanda take tsuma. Ya ɗago kanta a hankali tare da daidaita
fuskokinsu. Da sauri ta maida fuskarta ta sinne a ƙirjinsa, yay ƙoƙarin sake ɗagowa
amma ta hana hakan.
“Please Babie say something”.
Kuka kawai ta sakar masa dan zuciyarta mai rauni ce, a yanzu kuma ta ƙara
raunana ne fiye da raunin daya kasance halittarta, jiyay gaba ɗaya ma ya rikice, ya
tashi zaune da ita a jiki, buƙatarsa kawai ta kallesa, sai dai taƙi yarda tai hakan
sam. Dole ya barta, ta sake zamewa ta kwanta tare da jan bargo ta ƙudundune jikinta
har kanta. Shiru yay yana kallonta ƙirjinsa na harbawa da ƙarfi. Ya jima tsahon
lokaci a haka, kafin ya miƙe ya shiga toilet ya ɗauri alwala......

★A lokacin da Shareff ke a ɗakin Anaam yana raya wannan dare a gaban UBANGIJI
a ɓangaren Fadwa dare ta raba tana maida murtanin faɗa ga Teema ta hanyar video, da
farko sai tayi recording take posting, da abun ya rikice sai aka koma live. Faɗa ne
da tun anayinsa iya kan Shareff sai ya koma ƴar tone-tone musamman akan su Sima.
Tuni masu bibiyar faɗan wasu a followers nasu ke ƙara tunzura al'amarin ta hanyar
Comments.....

Sai kusan ƙarfe uku yay addu'a da rufe alkur'anin daya kammala karantawa
ya koma kan gadon, tuni Anaam tayi barci, ya tsura mata idanunsa tsahon lokaci.
Kafin ya sauke nannauyar ajiyar zuciya da kaiwa kwance. P.o.p ya tsurama idanu
abubuwa biyu na masa kaikawo. Yanayin Fadwa na ɗazun yaƙi barin ransa. Fargaban
samun tabbaci daga furucin Anaam na randa aka bayyana ɗaura aurensu na masa amsa
kuwwa tamkar a yanzune take faɗar bata sonshi waninsa take so har ma da alƙawarin
aure. Juyawa yay yana kallonta da idanunsa da suka kaɗa sukai jajur. Sosai yake jin
raɗaɗin kalmar. Ashe da gaske take har cikin ranta ne ba bore bane kamar yanda ya
ɗauka daga baya.........✍

_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_


*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:


07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇


09134848107

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*


[11/23, 10:16 PM] My Zafafa: *_Typing📲_*

*_BABU SO....!!_*
_(Miya kawo kishi?)_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718

*_68_*

........Yau ta kasance cikar kwana bakwai na kwanakin Anaam a gidan, miji zai koma
hanun Fadwa kenan. Sai dai kuma tunda garin ma ya waye bata ganshi ba. Tunda
sassafe ya fice sakamakon kiran daya samu daga Engineer ɗin dake kula da aikin
ginin wani ƙaton mall da sukeyi na wasu larabawa da suka buɗe branch anan kano.
Shine ya zana mall ɗin kamfaninsu kuma ke ginawa, to yanzu a dalilin wani mai musu
zagon ƙasa wata matsala ke neman shigowa.
Su dukansu ma babu wanda ya san baya gidan sai zuwan Khaleel tare da mai
haɗama Anaam tv. Anaam taji wani iri dan a tunaninta ko abinda ya faru a daren jiya
ne ya sakashi fitar tunda sassafe. Amma sai batace komai ba dama duk sukuku ta
tashi. Itama Fadwan ta jingina fitar tasa ne akan abinda ya faru jiya da dare, sai
dai saɓanin Anaam ita tsorone ya kamata da tunanin kodai ya gano tana tiktok ne? To
amma idan hakane ai ba fita zaiba wayarta zai fara bincike. Sosai ta shiga
taraddadi, cikin tsaida mafita ɗaya ta nema zuwan su Sima gareta. Cikin ƙanƙanin
lokaci kuwa sai gasu sun iso harda Bibah da Siyyah suka ƙulle a ɗaki suna
tattaunawa. Maman Abu ta girgiza kai da jinjina wautar Fadwa matuƙa, abinda duk ya
faru tsakaninta da Shareff jiya ta gani, ta kuma fahimci raye-rayen da Fadwan keyi
Shareff ɗin bai sani ba. Shiyyasa ta tsorata da tunanin ya ganta a jiya. Inama
Fadwan zata saurareta data bata shawarar dawowa kan hanya domin gujema zuwan ranar
dana sani, dan ta tabbata waɗan nan ƙawayen nata data bama amanar rayuwarta sune
waɗan da zasu fara kaita ƙasa kafin su Aunty Malika. Mata irin Fadwa da yawa rashin
alƙiblar kansu ke tarwatsa musu rayuwa da nasarori koda ace akwai wasu ƙyawawan
halaye abin dubi tattare da su, kafin su farga taurarinsu ya gama disashewa a idon
duk wanda zai kasance zagaye dasu, a lokacin kuma dukkan damanmakinsu sun kufcewa
yunƙurinsu da taɗesu ga zuwa nasarar da su suke kallo a cikin idanunsu duk da suna
ƙoƙarin cimmatane a cikin kuskure na son zuciya.

Anaam kam dai sukuku ta yini har yamma akan rashin ganinsa, zuwa la'asar sai
zuciyarta ta kasa dauriyar ɗauka dan koba komai shi ba abin yadawarta bane ba.
Wayarta ta ɗauka, ta gwada kiransa yafi sau goma kafin tai ƙuru ta danna number da
ko saving nata ta gagarayi amma ta gama haddaceta tun a kiran da yay mata jiya
bayan ta gama ganin kundin sirrinsa mai ɗauke da sirrikan da ita kaɗai suka shafa.
A lokacin yana zaune ne ya gama yin liƙis da gajiya da yunwa. Dan duk yau
ruwa kawai yake iya kaiwa bakinsa tsabar zafin da kansa ya ɗauka akan al'amarin
dake zagaye da su. Bashi ba hatta Fharhan da Khaleel da wasu a cikin staff ɗinsa a
jigace suke. Juma'a guda haka ta riskesa ko wanka baiba da kayan dake jikinsa
kanana sukaje sallar juma'a. Baiko duba waye mai kiran ba ya kai kunnensa. Can
ƙasan maƙoshi tai sallama kamar maijin tsoro. Curo wayar yay a kunensa da mamaki,
ganin tabbacin ita ɗince ya maida yana sauke wata nannauyar ajiyar zuciya da har
tana iya jiyowa. Ta ɗan murmusa daga can, tare da langaɓe kai kamar tana a gabansa.
“Yayaaa!”.
Yanda ta ambaci sunan cikin ƴar shagwaɓa ta saka tsigar jikinsa tashi, yaja
numfashi a slowly.
“Uhhum autar mata”.
Ta saki siririyar dariyar data ƙara tunzurashi. “Yaya ka rufamin asiri da sunan nan
kar mata sumin duka”.
Murmushi yayi a karon farko, da ɗan gyara zamansa. “Kice na faɗa da shela
ko hakan zaisa su tabbatar ke ɗin ta ƙarshe ce tabbacin Autarsu”.
“Nidai ba ruwana gaskiya. Wai kaje ina ne?”.
“Yawo mana”.
“Yawo fa Yaya? Ai nasan baka yawo, kai da kullum kana company ina zaka aiki, ina ka
dawo aiki”.
“Oho shaidar da kikamin kenan?”.
“ALLAH gaskiya na faɗa. Dan ALLAH ina kaje?”.
“Kina kewata ne?”.
Kamar tana a gabansa ta rufe fuskarta da filo. “Ɗan kaɗan”.
Dariya yayi kam yanzu har Fharhan na kallonsa.
“Wato ɗan kaɗan? Autar mata kiji tsoron ALLAH fa”.
“To ai nama daina ji yanzu gaba ɗaya”.
“Oh-oh, maimakon na samu ƙari sai a kwashemin ma duka? Aji tausayina mana
diamond girl”.
Sosai take dariya sai dai a nutse, (kece farin cikin duniyata) ya ayyana
a cikin zuciyarsa yana mai lumshe idanunsa. Ji yake tamkar yaga kansa a gabanta
kawai. Daga can Anaam data tsagaita dariyarta da iya gaskiyarta tace, “Am serious
gidan babu daɗi dan ALLAH ka dawo”.
Da ƙyar ya iya danne zuciyarsa dake tsalle-tsalle, murya can ƙasan maƙoshi
yace, “Mi kika tanada min ne?”.
“Duk abinda kace kana so”.
“Kin tabbata ko minene shi zan samu?”.
“Ga wani ma tun kafin kazo”. Ta faɗa dayin kissing wayar. Har tsakkiyar
kansa yaji saukarsa. Kafin ya samu damar cewa wani abu ta yanke wayar ƙit. Ƙoƙarin
dakatar da ita yake amma bataki jisa ba, yay ƙoƙarin sake kiranta taƙi ta ɗaga,
hanunsa ya kai yana murza goshinsa da cije lips.

Itako dariya takeyi daga can zuciyarta cike da farin ciki mai ban mamaki. A
haka Aysha ta shigo falon ta sameta. “Blood wai kin san wace kwamacala na gani
kuwa?”.
“A ina kenan?”.
Anaam ta faɗa tana tashi zaune da ƙyau. Cikin tsananin ɓacin rai Aysha takai zaune.
“Wai ƴan iskan ƙawayen can na Fadwa fa naga takai sashen Yaya suna masa gyara”.
“What!! gyara fa?”.
“Wlhy na rantse miki gasu can ma kuwa”.
Miƙewa Anaam zatai Aysha ta maidata. “Kinga kwantar da hankalinki ba so nake
kije ba. So nake kiyi duk yanda zakiyi Yaya ya dawo gidan nan yanzu shine kawai
maganinsu. Dan yanzu in bai gani ba su Mommy zasu iya ƙaryatawa tunda ba san laifin
Fadwan suke ba”.
Shiru Anaam tai tana kallon Aysha. Tabbas maganarta haka take, sai dai kuma ta
yaya zata saka Shareff ɗin zuwa bayan yanzu suka gama waya ma.......

A lokacin da su suke shawarar yanda zai dawo gida a garesa ma akwai himmar
hakance tattare da shi. Jiyay gaba ɗaya tattaunawar tasu ta gundiresa. Ya miƙe yana
tattare takardun gabansa. “Fharhan kubar abinda ya rage zuwa gobe idan ALLAH ya
kaimu a ƙarasa. Tunda namayi magana da Abie sai zuwa gobe zamu tattauna da shi yau
yana Abuja shi da su Daddy”.
Mamaki shimfiɗe a fuskar Fharhan yake kallonsa. “Dude amma kaine fa kace sai
an ƙarasa komai yau miye na canja shawara?”.
“Na gaji ne, ga yunwa na neman fara katsamin hanjin ciki”.
“Uhhmyimm!!. Kodai soyayya malam. Lokaci yayi da zaka bar wani ɓoye-ɓoye ka
buɗe mana mu kalla ko ma samu na kwaikwayo”.
“Banza ɗan sa ido”.
“Naji ba komai. In ka isa kace ƙarya na faɗa mana. Da an langare ana mana ciwo
tunda kaji ka samu sai mukaji tsitt”.
Spoon dake cikin kofin daya sha coffee ya dauka ya jefa masa. Fharhan yabar
wajen da gudu yana dariya. Gaba yay shima yana faɗin, “Munafuki mai barci da ido
ɗaya. Haka zaka ƙare rayuwarka a bibiyar tawa bakai aure ba tuzurun banza”.
“Aniyarka ta bika wlhy, insha ALLAH nanda 2months zaku kaini”. Fharhan ya faɗa
daga jikin motarsa yanama Shareff dakuwa.
Murmushi yay da buɗe mota ya shige batare daya sake tanka masa ba....

Tafiya yake amma ji yake kamar motar bata sauri, ya ƙara gudu tamakar mai
shirin barin garin na kano. Cikin ƙanƙanin lokaci ya iso gidan, horn yayi har sau
biyu amma maigadi bai buɗe masa ba. Yay dan tsaki da buɗe motar ya fita ya ƙarasa
shiga da ƙafa da niyyar yima maigadin faɗa sai ya samu ashe yana bayi ne. Kansa
kawai ya girgiza yay gaba, dan ya gwammace zuwa anjima ya shigo da motar kawai.
Harya nufi sashen Fadwa ya fasa, kai tsaye nasa sashen ya nufa dan yafi
buƙatar watsama jikinsa ruwa kafin komai. Tun a ƴar barandar gaban sashen nasa yaci
karo da takalman mata. Mamaki yay matuƙar kamashi wani gefen zuciyarsa kuma na
ayyana masa ko Mommy ce da muƙarraban ta, to amma takalman basuyi kama da wanda
Mommy zata iya sakawaba dan duk hills ne. Kamar mai tsoron shiga ya tura ƙofar a
ɗarare.
Dai-dai nan Amal dake goge-goge a falon ta ɗago da tunanin Fadwa ce da taje
ɗakko turaren mopping ta dawo. “Yauwa baby kin ɗakk....” sauran maganar ta maƙale a
harshenta. Ƙaf yawun bakinta ya ƙafe ta saki towel ɗin hanunta ƙarami da take goge-
gogen da shi.
Ana haka itama Bibah dake gyara bedroom ta kawo jiki zata fito, ai ba shiri ta
koma da sauri cikin harbawar ƙirji. Sima dake kitchen ce ta shiga ƙwalama Amal
kira, sai dai Amal ta kasa amsawa saboda tsabar firgita datai da ganin Shareff.
Cikin ƙanƙanin lokaci idanunsa dake cike da gajiya sun matuƙar kaɗawa zuwa launi
mai razani. Duk da baice da su komai ba kowacce a cikinsu jikinta rawa yakeyi, Amal
sarkin tsoro ta fara daga hannaye sama cikin rantsuwa da rawar murya..
“Wlhy tallahi ba laifinmu bane ba yallaɓai, Fadwa ce ta sakamu mu taimaketa da
aikin, amma ALLAH ba mune muka kawo kammu ba, kuma aikin kawai muke maka ba wani
abu ba...”
“Eh wlhy aikin kawai mukeyi Yaya Shareff”. Cewar Siyyah cikin son karfafa kai
dan ita bata ruɗe kamar Amal ba, amma daka ganta kasan a firgice take. Sima kam
tuni ta fice a kitchen ta ƙofar baya, itace taje a birkice ta sanarma Fadwa dake
kitchen tare da Mmn Abu ana haɗa abincin tarbar Shareff ɗin. Ita kaɗai ta nufo
sashin a rikice, sai dai tana ƙoƙarin hana ruɗewar tata a zahiri saboda shawarar
Sima.
Bibah dake bedroom kam taƙi fitowa, da sauri ta shiga kiran Gwaggo a waya.
Tana ɗagawa ta sanar mata komai. “Bibah k mahaukaciyar inace da zaki biyema wannan
sakarar yarinyar keda ke shirin shiga gidan matsayin matar gida. Duk yandama za'ai
karki sake ki yarda Mustapha ya ganki a cikinsu. Inba haka ba kini sai k da shi sai
dai kallo”.
“Gwaggo kar kimun haka dan ALLAH”.
“To laifinama zaki gani kenan? Yanzu banda ku shashshune taya zaku zauna ƙawa
na baku aiki”.
“Wlhy Gwaggo na biye musu ne kawai dan dan tace ɗakinsa ne, nidai ki taimakeni
yaya zanyi na fito gashi can a falo ya tsare su Amal.”
“Humm sai ki jira matar gidan ta shigo, kiyi amfani da wannan damar kiyi wuff ki
fita batare daya ganki ba”.
“To to...to Gwaggo nagode sosai, idan da wata matsala zan kiraki dan ALLAH”.
“Naji”.
Gwaggon ta amsa tana yanke wayar. Cikin laɓe baki.

Shigowar Fadwa tayi dai-dai da saukema Siyyah data matsoshi cikin kwarkasa
lafiyayyen mari da sai da taga taurari masu maƙata😆😜. Ba ita da aka maraba hatta
Amaal sai da ta dafe kuncinta da zabura baya kaɗan ya rage ta faɗa kan kujerar
dining.
“Ya salam! Soulmate mari kuma? Shamsiyya ce fa?”.
Wani matsiyacin kallo ya jefeta da shi fuskarsa na wani irin fusatar azabar
dake soya masa ƙirji. Ƙasa tai da idanunta, amma saita matso garesa cikin dauriya
ita a dole tana son fahimtar da shi.........✍

_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_


*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:


07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇


09134848107

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*


[11/23, 10:16 PM] My Zafafa: *_Typing📲_*

*_BABU SO....!!_*
_(Miya kawo kishi?)_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718

*_69_*

............“Soulmate! Please ka s......”


Da sauri ya ɗaga mata hannu, da karkaɗa mata yatsarsa manuniya lips ɗinsa na
rawa alamar gargaɗi. Sai dai ya kasa furta komai saboda takaici.
Dole ta dakata jikinta na wani irin tsumar tashin hankali, hawaye rige-rigen
sakko mata sukeyi.
Har zai shige ya sake juyowa “Ku kuma na baku minti ɗaya tak, ku kwashi
tarkacenku ku ficemin anan kafin na fara ɓallaku ƴan iska!!”.
Ai har turereniya ake na fita tsakanin Amaal da Siyyah, dai-dai nan Bibah ta
fito daga bedroom ɗinsa fuskarta a lulluɓe yanda bai ganta da ƙyau ba. Da gudu
itama ta fice. Kansa dake sara masa ya dafe da sauri, jin jiri na neman kwasarsa ya
dafe bango da sauri yana ambaton sunan ALLAH, da ƙyar ya iya ƙarasa kai kansa cikin
ɗakin ya zube a kujera yanajin raɗaɗi da ƙunar zuciya.....

Fitowar su Amal da gudu daga sashen Shareff ɗin ya saka Anaam da Aysha
kallon juna baki buɗe, Aysha ta zunguri Anaam “Blood jeki kiga mike faruwa? Naga
oganiyar tasu ita bata fito ba”.
“A'a blood babu buƙatar haka, wannan tsakaninta da mijinta ne ai. Dama su nafi
buƙatar yaci ubansu, amma ita matsalartace ita da shi”.
“ALLAH k banza ce, wlhy idan kece hakan ta faru a kanki ba ganowaba har
dariyama sai tayi zamanyi”.
Dariya Anaam ta saki da kaima Aysha duka. “Kefa wlhy muguwa ce”.
“Babu wani mugunta, dan ALLAH kije”.
“Okay ina zuwa”.
Ta faɗa da nufar sashen maigidan. Hango Anaam yasa da sauri Fadwa dake ƙoƙarin
fitowa komawa ciki, bedroom ɗinsa ta nufa da ƴar sassarfa. Zuwa yanzu ya miƙe yana
cire kayan jikinsa, shigowarta baisa ya juyo ya kalleta ba, hakan ya ƙara sanyaya
jikinta, amma sai ta danne ta ƙarasa gabansa. Tasanshi mai saurin karayane da ganin
hawaye, dan haka ta fara matsosu. “Soulmate dan ALLAH ka saurareni na maka bayani.
Wlhy ba.....”
“Get out of my room!! Idan ba hakaba duk abinda nai miki ke kika saya
stupid!!”. ya dakatar da ita a matuƙar tsawace.
“Please Soulmate n...”
Saukar lafiyayyen mari a saman fuskarta ya hanata ƙarasawa. .
Cak Anaam dake ƙoƙarin shigowa ta tsaya, ba ƙaramin harbawa ƙirjinta yay da jin
ƙarar marin ba. Wani irin ihun kuka mai ƙarfi da Fadwa ta saki, ya sata toshe
kunenta, da sauri ta juya ta fice zuciyarta na bugawa da sauri-sauri. Shiko baiko
nuna yasan Fadwa tanai ba ya shige bathroom abinsa. Hankali tashe Fadwa ta fita
zuwa sashenta dafe da fuskarta datai jazur abinka da fara. Mamanta ta fara kira
tana kuka, sai dai ba'a ɗaga wayarba, sai kawai ta koma kiran Mommy.
Mommy dake zaune ta kalla wayar taja tsaki, haka kawai takeji a ranta ƙofari
Fadwa ta kawo mata. Kamar karta ɗauka sai kuma dai ta ɗaga takai kunne batare da
tayi magana ba. Maimakin sallama da kuka ta fara cin karo, Fadwa dake kiran ta
shiga uku ta shiga zayyanoma Mommy cewar Shareff ya mareta, dan kawai ƙawayenta
sunzo Anaam ta tunzuroshi. Dama kwana biyun nan babu abinda yake mata sai wulaƙanci
akan Anaam ɗin....
“Mari!!?”.
Mommy ta faɗa a razane.
Kuka Fadwa ta sake mashe mata da shi, hakan yasa Mommy yanke wayar da sauri. Aysha
ta kira, cikin sa'a kuwa wayar na'a hanunta ta ɗaga.
“K faɗamin, mike faruwa Yayanku ya mari matarsa? Akan ƴar iskar yarinyarnan ne
ko?”.
Aysha da dama yanzu Anaam ke faɗa mata cikin tashin hakanli ta taɓe baki. “Wlhy
Mommy babu ruwan Anaam. Ƙawayenta ta kawo suna masa wai gyaren sashensa shine ya
shigo ya samesu, harda su Shamsiyya”.
“Shine dan bata da kunya ta kirani tana kawomin ƙararsa, to lallai ya kamata a
wannan gaɓar na takama yarinyarnan birki dan na kula neman maidani ƴar isaka
takeyi.”
Aysha tace, “To Mommy bakece ke biye mataba da su Gwaggo. Kamarma itace kika
haifa bashi Yayan ba. Ita Gwaggo Haliman ma ba tanayin komai bane dan ɗiyarta, ki
duba akan auren Anaam yanda kika biye mata kuka hau kansa kukaita zagi gashi kinaji
kina gani Abba ya hanashi zuwa ki gansa ma amma ita kullum tana waya da ƴarta. Kuma
wlhy yanzu kusan kullum su Aunty Malika suna gidan nan kawo mata magani anata
zubama Yaya a abinci....”
“Na shiga uku, magani kuma Aysha?”.
“Wlhy Mommy da gaske nakeyi, to duk kusancinki dasu Aunty Malika matsayinsu na
ƴan uwanki dasu ake haɗa kan cutar da Yaya, jiya bakiga abubuwan da suka kawo mata
ba harda zoben mallaka wai bazai sake kallon wata mace ba a duniya sai ita sai
abinda tace masa ko ke albarka, na rasa yaushe suka ɗinke da Gwaggo Halima haka har
suke abu batare da ke kin sani ba keda Gwaggo”.
“Na shiga uku, ni halima zataci amana ta haɗa kai dasu Malika a sabautamun
yaro saboda ƴarta tayi farin ciki?....”
Fitt Anaam ta ƙwace wayar daga hanun Aysha ta kashe. “Blood kinada hankali kuwa?
Ya zaki faɗama Mommy irin wannan maganar?”.
“Ya bazan faɗa mataba Anaam. Kin san ko suwaye su aunty Safarah? Wlhy rashin
faɗar shine mafi munin kuskure dan hatta ke da kanki sai sun sabauta rayuwarki, ɗan
sauran zuminci kuma da muke tattali su ɓarar mana da shi. Ita kanta Fadwa ɗin
taimakonta nayi, dan wata ƙungiya garesu ƴan baza'a zauna da kishiya ba, inma an
zauna da ita saita koma tamkar babu ita a wajen miji, kina tunanin a hankali bajan
ra'ayinta zasu cigaba dayi ba harta koma cikinsu. Koba komai ita ɗin jininmu ce,
yana da ƙyau muyi duk yanda ya dace domin ta dawo hayyacinta. Yaya baya son yanke
hukunci cikin fushi, amma tunda kikaga yau yakai da marinta to idan takaisa maƙura
komai zai iya lalacewa”.
(Aysha kenan, dan ma bakisan akan sani ta zubar da ciki ba akan makircin
kakarku) Anaam ta faɗa a zuciya, a fili kam saita kai zaune tana mai dafe
kanta.....
A ɓangaren Fadwa kam Mommy na yanke waya kiran Gwaggo Halima na shigo
mata. Sabon kuka ta ɓarke da shi tana zayyana mata abinda ya faru, harda kiran
Mommy datai amma ta yanke mata waya...
“Kan ubancan, mi Nafi ke nufi Shareff ya mareki ya mari banza?. A to lallai
idan tace wannan layin zamubi ni da ita bazatai mana ƙyau ba. Ai dama su Malika sun
tabbatar min abinda yafi hakama zai iya faruwa saboda Nafi maciji ce da fuskar
tana. Aiko zan tabbatar mata Shareff bai mareki a banzaba dan wlhy saina rama
miki”. Ta yanke wayar.

★Sai da Gwaggo ta gama sauraren Mommy data isa sashenta a rikice tsaf sannan
ta saki murmushi irin nasu na tsoffin makirai. Domin kuwa anzo gaɓar da ta jima
tana jira kenan. Kallon Mommy tai da dafa kafaɗarta. “Nafisa Halima zata iya fiye
da haka domin wannan ƴar tata. Jikina ya fara sanyi da al'amarinta tun lokacin
zubewar cikin Fadwa. Karki manta itace ta fara kawo shawarar a sami malamin dazai
aiki akan Mustapha da yarinyarnan ta wajen Usman. Abinda yasa naƙi yarda a lokacin
na tabbatar idan muka biye mata wataran zata haɗo wani abin a bama Shareff yaci a
zuwan dan ana son rabashi da Zuwaira ne. Ki tuna Halima ƙudace, domin samun biyan
bukatarta rai ba'a bakin komai yake ba. Tunda kuma ta haɗa kai dasu Malika to komai
zai iya faruwa da Mustapha ciki harda rabashi da ke kanki uwarsa, dan kuwa ke
shaidace, nice na haɗa auren Halima da Sadiqu, amma gashi nan babu mai cin
dukiyarsa daga ita sai ƴaƴanta sai wanda ta zaɓa a dangi. Gasu Muhammadu nan ƴan
uwanta tasan yanda zata samesu gefe ta kalallame ta dawo wajenmu tana nuna mana
tana tare damu. Kin dai san duk son da Halima zatamana bai kai ya na ƴan uwanta ba
tunda ba haihuwarsu nayi ba. Kuma kodan wannan dukiyar dake zagaye da Mustapha ai
Halima bataso zaunawa ba tunda tasan yanda ta mallake Sadiqu dolene itama ƴarta ta
mallaki Mustapha yanda koke kanki bai isa yaji maganarki ba, danni tawa mai sauƙice
kwana nawa ya rage ALLAH na tuba”.
Kalaman Gwaggo ba karamin hautsuna zuciyar Mommy sukai ba. Gaba ɗaya tama rasa
ina zata kama ta riƙe a wannan gaɓar. Shigowar kiran Gwaggo Halima ya saka
tunaninta katsewa. Ta dubi Gwaggo, “Itace fa take kirana”.
“Ɗaga muji mizata faɗa, nasan dai ƴar tata ta kirata itama ai”.
Dagawa Mommy tayi, ta saka hansfree yanda itama Gwaggo zata iya ji. Daga can
Gwaggo Halima dake a wuya muryarta a shaƙe ta fara magana batare da ko gaisuwa ba.
“Yanzu Fadwa ke kirana Shareff ya mareta, tace kuma ta kiraki ta sanar miki amma
bakice komaiba kin yanke waya. Kome hakan ke nufi kenan?”.
A harzuke Mommy ta maida mata murtani. “Abinda duk zuciyarki ta baki
Halima. Nifa bazan ɓoye miki ba na gaji da yawan kai ƙarar Fadwa. Ita kullum bazata
iya haƙuri da miji ba saita kawo kararsa. Ko haka taga wani a cikinmu nayi? Sannan
kin tambayetama mita masan ya mareta? Taya zata kai masa ƙawaye ɗakinsa na sirri su
gyara saboda rashin sanin ciwon kai. Ni yamun dai-dai, kinga gobe idan ta sake
saiya mata dukan tsiyama ba mari ba. Sannan Halima ki sani, dukkan ƙulle-ƙullen da
kukeyi ke da su Malika naji kuma na sani......”
“To idan kinji kin sani ɗin sai yaya Nafi? Kin goya bayan ɗanki akan marin da
yay yarinyata ma, to wlhy ki sani da hannuna zan rama mata marin da yay mata, idan
shi ɗin mahaukacine zan maidosa hankalinsa kuwa. Kuma karki manta duk wani ƙulli da
tuggunki a tafin hanunna suke, ko dama wanzami baya son jarfa ne, yanda kika
mallakemin ɗan uwa kike tunanin ke naki ɗan bazai mallaku ba. Hhhhh Nafi idan
kikace wannan layin zamubi ni da ke akan Shareff da Fadwa wlhy muje zuwa ɗan halak
ka fasa....”
“Halima idan kin isa ke tujararriyace mu zuba ɗin dan ALLAH, ni dake za'aga
mai iko akan wannan auren. Shiyyasa dama ni tun farko ban so wannan haɗin ba kika
katsatstsare ke da Gwaggo sai anyisa. Bayan nasa ƴarki bata da tarbiyya ko misƙala
zarratin..”
“Matsalarkuce kuma wannan, ni nagama dake kuma muje zuwa ɗan halak ka fasa”.
Gwaggo Halima ta faɗa da yanke wayar. Wani jijjiga Mommy tai zata maka wayar da
ƙasa Gwaggo ta riƙeta.
“Kefa daɗina dake baki da hankali idan ranki ya ɓaci, ki nutsu, har mi akai kai
Halima ne ma. Ai wannan yaƙin namune gaba ɗaya, shiyyasa naita nuna miki ki kwantar
da hankalinki akan haukan da kike na tsinema Mustapha a banza saboda farin cikin
Halima da ƴarta. To gashi nan tun ba'aje ko'inaba sun fara nuna miki halinsu”.
Kukan takaici da baƙin ciki Mommy ta fashe da shi...........✍

😆Ashe haka duniya take ƙafar kazace. Aminai biyu ya hakane🤪? Yanzune fa wasan na
ainahi zai fara, dan za'ai yunwa muga cikin kowa🤣🚴🏼👌🏼.

_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_


*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:


07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇


09134848107

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*


[11/23, 10:16 PM] My Zafafa: *_Typing📲_*

*_BABU SO....!!_*
_(Miya kawo kishi?)_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718

*_71_*

..........Gigitacciyar tsawa Daddy ya daka musu. “Wlhy duk wadda ta sake cewa tak
sai ranta yay mummunan ɓaci, idan kuma kunji ƙarya bismillah marasa mutunci kawai.
Ku har kun isa ku maidamu mutanen banza. Ku tashi kufita bama buƙatar zaman kowacce
a anan”.
Cikin ɓacin rai suka mike su biyun suka fice. Daddy ya cigaba da faɗa tamkar
zai ari baki, da ƙyar dai su Abie ɗin suma suka taushesa. Haɗuwa sukai akan Fadwa
da Shareff ɗin duka sukai musu tatas da faɗa musamman Fadwa a matsayinta na mace.
Sai kuma suka koma nasiha a garesu. Daga nan suna jiyo hayaniyar Mommy da Gwaggo
Halima, hakan yasa Gwaggo da har yanzu bata tofa nata ba ta miƙe ta fita wai zata
tsawata musu. Nasiha Abie ya sake musu ta fahimta data saka zukatansu samun
nutsuwa, musamman ma Fadwa da taga an nunama Shareff kuskuren marinta da yayi kuma
ya nuna nadamar yin hakan da alƙawarin bazai sake ba. Duk da dai itama tasha nata,
sun kuma nuna mata illar biyema su aunty Malika cikin hikima. Basu san babu abinda
ke cizon zuciyar Shareff ba kamar maganar su aunty Safara'h ɗin nan. Sai dai baice
komai ba dan a samu zaman lafiya, amma yay aniyar da kansa zaima tufƙar hanci insha
ALLAHU.

Da ƙyar wajen ƙarfe goma suka baro gidan, dan kuwa rikici ne na gaske ya
ɓarke tsakanin Gwaggo Halima da Mommy har sai da Baban Fadwa ya kira waya dan baya
ƙasar ne shiyyasa harta samu damar fitowa. Ya kuma janye mata wancan sharaɗin
lokacin da zaiyi tafiyar saboda haƙuri data bashi akan komai ya wuce. Ashe akwai
wani a gaba. Mommy dai taci alwashin sai ta nunama Gwaggo Halima itace ta haifi
Shareff ba wani shege ya haifa mata ba. Haka itama Gwaggo Halima ta tabbatar mata
cewa ita bata isa komai ba domin Shareff ɗin ba nata bane ita kaɗai..
Kuka Fadwa ke masa tunda suka taho, dan kuwa rikicin Mommy da Mamanta ya
matuƙar ɗaga mata hankali kuma, tana matuƙar tsoron abinda zai rabata da Shareff,
tana masa so ne mai tsanani, wanda takejin in har aka rabasu zata iya rasa har
ranta. Ya gaji dajin kukan, saboda shima zuciyarsa a wuya take kuma yanajin ƙuna da
raɗaɗin abubuwa masu yawa. Sai dai shi jarumin mutum ne mai maida komai ba komai ba
koda kuwa a ce ya zame masa komai. Dan haka har suka iso gida bai ce mata komai ba.
Shine ma ya fara fita ya barta a motar, saida ta kai kusan minti huɗu a ciki tana
cigaba da kukanta sannan ta fito ta rufe motar. Sashensa ta bisa kai tsaye, yana a
falo zaune cikin yanayi na wanda baka iya ganemawa. Cikin jan ƙafa ta ƙarasa
gabansa, ta tsugunna tare da dafa guyawunsa.
“Ina tsugunne ne gabanka a matsayin ƙanwa Yaya Shareff, nasan ni mai
laifukace a gareka tari-tari, na kuma yarda nayi kuskuren da kake son na fahimta
tun kafin akai ga wannan gaɓar. Wlhy bana son zumincin iyayenmu ya lalace saboda
aurenmu......”
“Garama ya lalace, dan ta hakane kawai dake da su zaku dawo rayuwar hankali
irin ta mutane. Ke kam rayuwarki naban mamaki matuƙa, mamaki irin wanda nake shiga
kokwanto. Ba haka nai miki zatoba sam-sam a rayuwata ba, amma bazance ki dainaba
kiyi tayi, shawara ɗaya zan baki kuma ta ƙarshe. Ya rage naki ki dawo akan
ƙyaƙyƙyawar hanya ɗaya tak ki gyara halayenki muyi zaman aure na gaskiya, idan ba
hakaba wlhy wlhy zan ɗauki mataki ne na ƙarshe dan bazaki maidani mahaukaci ba.
Shawara ta rage gareki, ki cigaba da biyema duk wani mai zuwa gidan nan yana
ɗauraki a hanyoyin da shi yake ado da su, koki zama mace tagari ki gina taki
rayuwar a karan kanki. Idan kuma kika sake amfani da wani abu na kauce hanya domin
mallakata, ko bani wani abu a cikin ruwan sha ko abinci ALLAH ya isa ban yafe ba!”.
Ya ture hanunta tare da miƙewa ya shige bedroom abinsa.
Hawayen da take son su zuba ma sam sunƙi zubar a yanzu, sai dai tasan gaskiya
ya faɗa mata, dan kuwa a yanzu tana rayuwa ne da rayuwar su aunty Safarah, a baya
komi za'a bata ta zubama Shareff a abinci bata taɓa yin hakan tunma tana gida, duk
ma yanda zatai ƙoƙarin hanawa sai tayi, sai dai in Mama ta aikata bada saninta ba.
Amma a wannan gaɓar ta rikice, idonta ya rufe saboda kishiya da kanta take aikata
komai dan taga haske. Sai dai saɓanin hakan duhu take gani, sannan mai makon
mallakarsa suɓuce mata yakeyi, kenan su magungunan na ƙarya sunfi yawa a cikinsu
kenan? Ƙalilanne ake dacewa suyi aikin kuma basa wani jimawa sai kaga abubuwa sun
ƙwaɓe. ‘Ya ALLAH’ ta faɗa tana mai fashewa da kukan zahiri.

_____________★

Harta fara jin barci a jiya bai dawo ba, dan ita bata san tare da Fadwa ya
fita ba. Koda ta shirya ɗakin da Aysha ke kwana taje ta kwanta abinta. Ayshan
batace da ita komai ba dan tasan yau Shareff ya koma wajen Fadwa. Ta ɗanyi murmushi
ganin Anaam ɗin sukuku, ko bata fito ta faɗa ba tasan kewar Yayansu ke
nuƙurƙusarta. Sai dai sanin itama Anaam nada halin I don't care wasu lokutan yasa
babu wannan alamar akan fuskarta sam. Sai dai kuma koda suka kwanta ta jima batai
barci tanata juye-juye. Sai da Ayshan ta ɗauke hankalinta da wasu labarai sannan
ɓarawon yay mata kamun kazar kuku. Ajiyar zuciya Aysha ta saki mai ƙarfi da kai
hannu ta riƙo na Anaam ɗin. Tausayinta da ƙaunar ƴar uwarta na ratsa mata zuciya
matuƙa....

★Kamar yanda ya saba da asuba sai da yazo ya tada su, Anaam ƙin yarda tai ta
kalla inda yake taima shigewarta toilet. Juyawa yay ya fita shima yana mai sakin
guntun murmushi. Itama Fadwa sai da yaje ya tadasu sannan ya wuce massallaci. Daya
dawo bai shiga sashen kowacce ba ya koma nasa sashen ya kwanta dan jiya ya jima bai
barci ba yanata faman ƙullawa da kwancewa akan yanda zai ɓulloma matan nasa. Barci
yasha sosai dan sai kusan goma da wasu mintuna ya iya tashi, baiyi mamakin ganin an
gyara ko'ina ba ga ƙamshi na tashi, sai dai yaji sassauci a ransa dan Fadwa ta nuna
masa ta yarda ta gyara abinda take shirin ɓararwa a idanunsa. Wanka ya farayi ya
shirya tare da baje jikinsa da ƙamshin turarurrukansa masu ƙamshin daɗi. Koda ya
fito a falo ya sami Fadwa zaune cikin kwalliya mai ɗaukar hankali. Tabbas ta ɗauka
hankalin nasa da gaske, sai dai ya basar abinsa. Gaisheshi tayi, ya amsa a daƙile,
bata gazaba wajen sake jero masa kalaman ban haƙuri da tabbatar masa zata canja
fiye da yanda yake buƙata. Har cikin rai ya ɗanjin tausayinta, dan yasan ya mata
hukunci dai-dai da laifinta da har idan ita ba ibilisiya bace ya kamata yaga
canjin. Huci ya ɗan furzar tare da ware mata hannayensa. Ai da gudu tazo ta shige
jikinsa. Ya saki ƙaramin murmushi tare da sauke hannayensa akan bayanta ya fara
shafawa alamar lallashi. Hawayene suka dinga silalo mata, ita kanta ta ƙara
shaidawa Soulmate ɗinta zuma ne, ga zaƙi ga harbi. Ya ɗagota yana kallon fuskarta
har yanzu dai babu fara'ar da take muradin gani a garesa.
“Kin san bana son kukan nan ko?”.
Kanta ta jinjina masa tana sharewa, ya raɓata ya wuce yana faɗin, “Ina zuwa bara na
duba waɗan can ya suka kwana”. Kanta ta jinjina masa, ta bisa da kallo tana ƙara
tsane hawayenta dake sakkowa. Ta san bawai ya gama hucewar bane, amma ko yanzu ta
samu sassauci. Zakuma tabi duk hanyar data dace domin ganin ya huce baki ɗaya sun
koma rayuwar farin cikinsu....

A falo ya samesu su duka. Anaam na tsaye riƙe da cup na shayi idonta a


tv tana murmushi. “Wato blood film ɗin nan fa zaiyi daɗi, sai dai guy ɗin film ɗin
sam baimun ba shegen kunensa uwa na zomaye ALLAH”. Dariya Aysha ta sanya harda
ƙyaƙyƙyawa tana leƙowa daga kitchen. “Amma wlhy kinci zarafin mutumin nan, ni banga
wani kunen da kike masa sheri da su ba.”
“ALLAH da gaske yanada kunnuwa gasu nan, ga shegen rawan kai a wajensa uwa
dangin makaɗan zamanin jahiliyya, ALLAH an cuceta da aka haɗata da shi”.
Alamar komawa yay ma Aysha data leƙo zatai magana, tai saurin komawa cikin
bin umarninsa harda turo ƙofar kitchen ɗin dan ta tabbatar wata taɓarar za'ai.
Rayuwar Yayansu na birgeta tun akan Fadwa, gashi dai mutum miskili da baya ɗaukar
raini amma matansa nashan sharafin soyayyarsa. Cigaba yay da tsayawa a bakin ƙofar
hannayensa harɗe da ƙirjinsa yana kallon Anaam ɗin kawai. Ita ko sam bata san da
zamansa ba amma tanajin ƙamshin turarensa a hancinta wanda take ganin hakan normal
ne tunda dama yana shigowa maybe tunna baya ne. Juyowa tai zata koma saman kujera
suka kusa cin karo da shi dan ya baro ƙofar. Da sauri ta ɗanyi baya a zabure dan
tsoroma ya bata. Cikin zafin nama ya riƙe cup ɗin shayin dake neman antayewa a
jikinta.
Baki ta tura gaba da ƙwaɓe fuskarta da tasha kwalliya. “Kai Yaya ALLAH ka
tsoratani”.
Idonsa akan lips ɗinta ya ɗage mata gira ɗaya, “Kin dai so ki tsorata madam”.
Bakin ta ƙara tura masa tana ƙoƙarin janye jikinta. Hanata hakan yay ta hanyar riƙo
ƙugunta, ya zuba mata mayun idanunsa cikin nata idon, tare da matso hanunta da nasa
dake rike da kofin shayin yakai bakinsa. “Wayyo Yaya ni ALLAH zaka shanyemun tea
ɗina”.
“K miyasa rowanki yayi yawa ne?”.
“To kai miyasa kwaɗayinka yay yawa ne”.
Murmushi yayi da kai yatsarsa ya ɗalle mata baki, “Magananniya da ba'a kadata.
Sammin lipstick ɗin shima Please”.
“Tab ni ban saka da kai ba ni kaɗai zan shanye abuna”.
Dariyarsa ya danne da ƙyar, ya ɗan ƙwaɓe fuska da langaɓe kai gefe, “Babie
Please mana”.
“Naƙi wayon”. Ta faɗa dayi masa gwalo tana tura lips ɗin cikin baki. “Ni kikama
rashin m ko? Zan rama ALLAH”. Dariya ta ƙyalƙyale da shi da masa gwalo. “Kafin ka
rama na ƙara wani rashin m ɗin ma”. Ta zille, riƙota yasoyi amma tai tsalle gefe
tana masa gwalo. “Zan rama ne yarinya ai zaki zo hannu. Oya muje breakfast”..
Idanu ta ɗan waro, “Gashifa Aysha na mana anan”.
“Kin manta tsarina kenan”.
Shiru tai cikin ɗan tauke fuska. Dan ta ƙwallafa rai a abinda Ayshan keyi. Amma sai
batai musu ba ta kaɗa masa kai. Tare suka fita, sun iske Fadwa na ƙara gyara dining
ɗin. A yau ma babu wacce ta kalla ƴar uwarta a cikinsu. Dan haka ya duba kowacce
fuskarsa a tsuke. “Kun gaisa da juna?”.
Shiru duk sukayi kowanne idonsa a ƙasa dan a serious yay maganar. Fadwa ce tai
ƙoƙarin dannewa a shaƙe tace “Kin tashi lafiya?”. Baki Anaam ɗin ta taɓe da amsawa
a shaƙen itama. “Alhmdllhi”. Komai bai sake ce musu ba, dan yasan a haka a haka
watarana zai ci nasara. Wayarsa da yake latsawa ya ajiye, Fadwa ta fara haɗa masa
abincin. A daidai nan Aysha ta shigo da ƙaramin tray. Wani irin ajiyar zuciya Anaam
ta saki a hankali. Ya ɗan saci kalonta ta gefen ido sai yaji tausayinta. Ya fahimci
tana son abinda Ayshan ke musu amma tabi umarninsa ta taho, shiyyasa yayma Aysha
text yace ta kawo mata. Kasa ɓoye farin cikinta tayi har sai da ta kalla Aysha da
murmushi. “Thanks you blood”. Murmushi Aysha ta mata. Itama sai ta sake murmusawa.
Har Aysha ta juya zata fita Fadwa tace, “Ki dawo mu karya mana Aysha”.
“No Aunty gashi can na baro kar a barsa ya lalace shima”. Tai maganar tana
nufar hanyar fita da ɗan hanzari dan karma Shareff ya tsaidata. Batama san shi
baida niyyar tanka musu ba. Abincinsa yake ƙoƙarin fara ci kawai............✍

_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_
*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_


*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:


07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇


09134848107

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*


[11/23, 10:16 PM] My Zafafa: *_Typing📲_*

*_BABU SO....!!_*
_(Miya kawo kishi?)_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718

*_70_*

........Wasa farin girki wai amarya da tuƙa tuwon tiya goma. Ashe rikici a waya
tsakanin Mommy da Gwaggo Halima somin taɓi ne. Dan kuwa ba'a rufa awa guda
cikakkiya ba sai ga Gwaggo Halima tazo gidan. Hakan yayi dai-dai da dawowar Daddy
daga wajen aiki gidan shima. Yay sagade yana kallon Gwaggo Halima data ƙaraso
garesa tana huci.
“Halima lafiya kuwa da magribar nan?”.
“Inafa lafiya Yaya, Shareff ya buɗe ƙwanji ya shashsheka ma Fadwa mari amma
saboda son zuciya irin na matarka ta goya bayansa saboda itace ta haifesa”.
Da mamaki sosai yace, “Mari fa dai? Ya ALLAH mike damun Shareff haka?
Wannan ba maganar nan bace shiga ciki nafara zuwa salla kafin su Abubakar su dawo”.
A maimakon sashen Mommy ko Gwaggo da da idan tazo gidan take shiga yau sai ta
nufi sashen Mom.....
________________★

Rashin fitowarsa har aka kira sallar magrib yasaka Anaam kasa zaune ta kasa
tsaye. Tana son zuwa dubashi tanajin tsoro. Gani take kamar itama ɗin marin nata
zaiyi. Harga ALLAH tana matuƙar tsoron duka a rayuwarta. Koda wani taga ana duka
firgicewa take. Ballema har abada bazata taɓa iya manta dukan dayay musu ba ita da
Aysha. Da sauri ta juyo jin motsin buɗe ƙofa. Sukaima juna kallon cikin ido ita da
shi, ita ta fara janye nata tana sauke ajiyar zuciya dajin shakkar kallon fuskarsa
dake a matuƙar tsuke.
“Ki tashi kiyi salla”.
Ya faɗa a taƙaice da juyawa zai fita. Harya kama handle ɗin ƙofar zai fita ya tsaya
cak, juyowa yay a hankali yana kallonta saboda ganin yanayinta. Sai dai baice
komaiba ya juya ya fita. Numfashi ta saki a hankali da miƙewa ta shiga toilet domin
ɗauro alwala.

Bai dawo gidan ba sai bayan sallar isha'i, kai tsaye kuma sashenta ya zarto.
Tunda ta idar da salla ta kasa tashi a wajen, babu abinda ke mata kaikawo, haka
kawai marin nan na ɗazun da yay ma Fadwa ya matuƙar tsaya mata a rai, duk da kuwa
ƙararsa kawai taji bawai yinsa akan idonta ba. Harya ƙaraso gabanta bata san da
shigowarsa ba, ya kai tsugunne gabanta, tare da ɗago haɓarta. Cikin idanunsa ta
zuba raunannun nata da babu gilashi, bata ganinsa fes yanda ya kamata, amma hakan
bai hanata tsaidasu a tsakkiyar nasan ba...
“Mike damunki?”.
Ƙoƙarin janye idanunta tai a cikin nasa ya hana hakan, taso kauda kanta gefe
nanma ya hana, saita ƙara tsuƙe fuska da tura baki. A karon farko ya saki murmushi,
tare da kai yatsansa ya ɗalli lips ɗin nata. “K wai baki san shekarunki sun girmi
wannan taɓaran ba Autar mata?”.
Hanunsa ta ture zata tashi, yay saurin damƙota yana dariya, jikinsa ta faɗa,
dan haka suka zube ƙasa gaba ɗayansu. Ƙafarsa ɗaya ya kwanta, tare da jawota ya
kwantar a cinyarsa ita kuma. Ya tokarar da ɗayar ta jingina kanta. “Nayi laifi ne
wai?”.
Hanunsa dake kan cikinta ta kamo, ta saka babban ɗan yatsan a bakinta ta
ciza. “Wai wai shiii! Wace mugunta ce muka wannan?”. Dariya ta ƙyalƙyale da shi.
“Noorie muguntafa babu ƙyau sam sam”. Ka ɗan ta murguɗa masa baki “Punishment ɗin
mai yawo ne ai”.
“Shi kuma punishment ɗin mai rashin kunya fa? yaya ya kamata ya kasance?”.
“Sai an binciko a littafin shara'a”.
Ta faɗa tana ƙoƙarin mikewa ta gudu. Riƙota yay yana ƙaramar dariya. “Sarkin wayo
ai ni tuni na binciko. Yanzu kuma zan ƙaddamar da shi”.
“Wayyo yaya! Wayyo ni yunwafa nakeji, tun safe banci komai ba.”
“Nima ita nakeji ai”. Ya ƙare maganar da manne lips ɗinsu waje guda. Ko sau ɗaya
batai ƙoƙarin hanashi ba, saima gudunmawa data fara bashi, burinta kawai taga ya
huce daga fushinsa. Cikin ƙanƙanin lokaci ta gama hautsina masa kwanyar kansa, tun
yana binta a salon jarumta harya fita a hayyacinsa ya ɗauka wata hanya da ban da
karatun da ya kasance mai girma ga Anaam. A yanzu kam ita ya nema gigitawa, yayinda
shi tuni ya fita hayyacinsa har baya gane ita ɗinfa ƙanwarsa ce. Sunyi matuƙar
shagala a farantama junansu ring ɗin wayarsa ya shammacesu. Da ƙyar Anaam ta iya
janye jikinta dake rawa gefe. Shima nashin rawar yake fiyema da tata, sai dai
jarumtar ƴan mazan ta ɓoye haka, ya rimtse ido da ƙarfi ya sake buɗewa saboda ganin
mai kiran. Ko'a turu a kwantosa bai isa ɗaga wayar nan ba, dan babu makawa sai
Daddy ya gane halin da yake a ciki. Haka ya barta harta tsinke wani kiran ya ƙara
shigowa. Yanzun ma kasa ɗagawar yay har saida ta yanke, da ƙyar ya samu iya ɗan
dai-daita kansa bayan wasu mintuna sannan yay kiran Daddyn Back.
Koda Daddy yaji muryarsa a shaƙe a zatonsa duk ɓacin rai ne, dan kuwa yasan
wanene Shareff idan yay fushi. “Ka sameni a gida yanzun nan kai da Fadwa”. Bai jira
cewarsaba ya yanke kiran. Shima ɗin baice komaiba ya koma kwance tare da mirginawa
jikin Anaam data juya masa baya ya rungumota da ɗaura kansa a gefen wuyanta yana
shinshina, ga sanyin tiles na ratsasu dan harya huda sallayar tana iya jinsa a
jikinta shima haka..
Jin saukar hanunsa a ƙirjinta tai saurin riƙewa. “Yaya kirankafa Daddy
yakeyi”. Iska ya ɗan hura mata cikin kunne da ture hanunta ya ɗaura a inda yay
niyya tun farko. “Koratama kikeyi kenan?”.
“Eh mana, Daddy ba abin wasa bane ai, umarninsa yana sama da muradanmu”.
Sassanyan murmushi ya saki da sake ƙanƙameta a jikinsa, a hankali ya furta
*_Ina ƙaunarki da yawa_*”. Sosai tsigar jikinta ta yamutsa saboda yanda yay furucin
a cikin wani irin wahalallen sauti. Taja numfashi mai kauri da cije gefen lips
ɗinta sakamakon saukar kiss ɗinsa saman wuyanta. Bata iya ta ɗago ta kallesa ba
harya fice daga ɗakin. Ta sauke sassanyar ajiyar zuciya da sake kananneɗe jikinta
waje guda wani abu mai girma na tsikarar ƙasan zuciyarta....

A sashen Fadwa kan duk da yaji a ransa itace takai ƙararsa wajen su Daddy
bai mata magana ba, umarnin kawai ta samesa a mota ya bata ya juya ya fita abinsa.
Taja wasu mintuna kafin ta fito dan har ya kunna mota ma.
Tafiya suke amma kowanne fuskarsa na gefe, ita tana kallon mutane shi kuma titi
har suka iso. baiyi mamakin samun Gwaggo Halima ba, Fadwa ta nufeta ta rungumeta
tana sakin kuka. Lallashinta ta shigayi tana shafa bayanta da fuskarta wai tana
neman tabon marin. Abin sai ya girmi kan kowa amma babu wanda yay magana sai Mommy
ce taja tsaki da taɓe baki. Shareff kam zama yay ƙasa a tsakkiyar ƙafafun Abie da
Abba. Kansa a ƙasa batare daya kalla kowa ba ya gaishesu. Haka kawai yakejin
tsananin kunyar Abie da Mommynsa fiye da kowa a wajen.
Abba da yaga mulmular da Gwaggo Halima kema Fadwa na neman yin yawa ya
magana a kausashe. “K Fadwa tashi ki zauna da ƙyau bama son shashanci”.
Tashin tai zaune, sai a sannan kuma take gaidasu. Iya su mazan kawai suka
amsa. mommy da Gwaggo babu wanda ya tanka. Gwaggo Halima tai ƙaramar ƙwafa da
ayyana (Zanyi maganinku) a zuciyarta.. Abie ne ya buɗe taron da addu'a, kafin ya
maida hankalinsa ga Shareff cikin serious matuƙa.
“Al-Mustapha miya haɗaka da matarka harda mari? Bayan wannan ba ɗabi'ar dakaga
wani a cikinmu nayi a gidan nan bane?”.
Ƙasa Shareff ya ƙarayi da kansa, cikin matuƙar girmamawa. “Kuyi haƙuri
Abie nayi kuskuren aikata hakan, sai dai saida na umarceta ta tashi tabar inda nake
dan bana son yanke hukunci cikin fushi, amma taƙi yin hakan har takai nayi marin”.
“Amma banda abinka Babana ai kai babbane, da taƙi tashi sai kai ka tashi ka
bata waje tunda kasan baka iya controling kanka a yanayin fushin. Su mata haƙuri
ake dasu a kowane hali, domin hangenka da nasu sam ba ɗaya bane ba, sai dai sunada
sauƙin sha'ani kuma ba koda yaushe ake cizawa a kansu ba”.
“Hakane Abie, insha ALLAHU hakan bazata sake faruwa ba......”
“Tama sake faruwar mana. Wlhy da kaina zan rama mata mara mutunci kawai. Kai
yanzu dan baka da kunya Shareff har kanada hanun ɗagawa ka daki Fadwa a gidanka?”.
“Yaya Halima! Ya kamata kiyi shiru abi komai a sannu”.
“Wane kuma sannu Abubakar, bayan kanaji yana lallaɓashi saboda ba ƴarsa aka mara
ba”.
Murmushi Abie yay da girgiza kansa. Cikin dattako da nutsuwar da kowa ya sansa
da ita ya fuskanci Gwaggo Halima. “Ba haka bane Yaya Halima. Da Shareff da Fadwa da
Anaam duka su ɗin ƴaƴanmu ne, bazamu taɓa sakaci da cutuwar ɗayansu ba ai. Da kinyi
haƙuri zan kai inda kike buƙata nima ai”.
Baki ta taɓe da juya kai gefe. Nanma Murmushin Abie ya saki kawai ya sake
maida hankali kan Shareff da ransa ya ɓaci. “Babana ina jinka miya haɗaku takai ga
mari?”.
“Ban taɓa fatan dan na samu matsala da wata a cikinsu sai munzo gabanku ba.
Amma tunda ita tafi zaɓar hakan a koda yaushe fine. Fita nai a gida tun safe ina
wajen matsalar can data taso a company, na dawo kawai na samu ta cikamin sashe da
ƙawayenta wai suna min gyara. A yanda suke komai kai tsaye ya tabbatar min ba yau
ce rana ta farkon hakan ba. Korarsu kawai nai na ƙyaleta domin ita tasan bana son
yanke hukunci cikin fushi, amma saita biyoni bayan nace ta ƙyaleni a yunƙurin farko
da tai. Taya zata kawomin wasu ƴan iska sashe, ta san adadin abubuwan dana ajiye
masu muhimmanci a ciki? Ko bamma ajiye komaiba ita bazatai tunani da hankalinta
rashin dacewar kai wani can ɗin”.
“Inafa zata san abinda ya dace tunda a nuna mata barbaɗa magani shine kawai
zaman aure”.
A harzuƙe Gwaggo Halima ta dubi Mommy mai maganar. “Nafi wlhy ki iya bakinki
domin zai kaiki ya baroki allura ta tono galma”.
“Yo ta tono mana dan ubanta, abu mai sauƙi bayan ta tono ita galmar ta
turbuɗata cikin ƙansa yanda ko mayen ƙarfe ƙaryarsa sake ganinta”.
Aifa nan take falon ya harmutse da hayaniya tsakanin Mommy da Gwaggo Halima.
Mamaki al'ajab sukabi suka sanya Shareff cikin madaukakin imani. Yau kuma aminai
biyune kema juna tujara haka akan abinda suke ganin shine mafi ƙololuwar alkairi a
garesu idan suka ƙulla. Kai duniya ina zaki kaimu ne haka?. Da ƙyar su Daddy suka
samu sukai shiru. Gwaggo kam tayi kamar bata a falon tai muƙutt da cuno baki gaba
ita a dole takai maƙurar ɓacin ran abinda su Mommyn ke aikatawa. Acan ƙasan ranta
kuwa dariya taketa kwasa. Yanzu kam Abba ne ya amshe da zancen yana mai fuskantar
Fadwa.
“K shashashar inace da zaki bama ƙawaye damar shiga ɗakin mijinki? Haka kikaga
iyayenki na mana? Wace irin mace ce ke da baki kishin mijinki? Ai wannan jama kanki
rainine ma wajen su ƙawayen naki da shi kansa mijinkin. To saurara ki jini, daga
rana mai kama irin tayau, hakan ta sake faruwa ni da kaina zan hukuntaki sannan
shima nasa ya hukuntaki tunda koba aure tsakaninku Yayanki ne.. Kinaji na da
ƙyau?”.
Hawaye ta ta share tana jinjina kanta. “Zan kiyaye Abba insha ALLAHU. Amma
Abba dama fa haushina yakeji, dan dama a kwanakin nan banda wulakantani babu abinda
yakeyi saboda ya ƙara aure. Baya ganin kowa a gidan sai ita ƴar gwal.....”
“Shiyyasa kuka dage boka da matsubbata ke da uwarki domin sabautamin ɗa. Su
Malika na kawo miki barbaɗe-barbaɗe kina faman zuba masa dare da rana. To wlhy babu
lallai babu dole tun kan ai nisa sai ya datse igiyar auren tunda bake kaɗaice mace
ba a duniya......”
“Dan ALLAH Nafisa idan baki sakashi ya datse igiyar aurensu ba baki cika uwarsa
ba, kuma shi din bai haifuba a cikinki...”
“Haka kikace?”.
“Eh na faɗa. bandama ƙaddara mi Fadwa zatai da wani Shareff can. Ko dama kun ƙulla
a haɗasu aure dan ku dinga maidamin yarinya baiwarku”.
“Hahaha yo baiwa kuma ta nawa Halima. Sai dai wata kuma dan ita kam ta
riga ta gama zama labari”.
Ƙara hargitsewa falon yay, da ƙyar yanzu kam Abie da Abba suka sakasu yin
shiru, dan Daddy dai ya mugun shaƙa zuciyarsa har wani zallo takeyi, gata tokare a
maƙoshinsa kamar yay amanta ya huta.............✍

_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_


*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:


07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇


09134848107

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*


[11/23, 10:16 PM] My Zafafa: *_Typing📲_*

*_BABU SO....!!_*
_(Miya kawo kishi?)_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718

*_72_*

.........Abincin yakeci cike da nazarin kowaccensu. Fadwa nayin komaine a taka


tsantsan na gudun yin kuskure fatanta komai ya wuce. Yayinda Anaam ke komanta kai
tsaye hankalinta kacokan naga abincin da takeci tamkar ta manta da zaman kowannensu
a wajen ma. A haka dai suka kammala Fadwa ta fara gyara wajen, dakatar da ita yay
dan haka ta koma ta zauna. Anaam data ɗauka waya yayma magana, itama ta ajiye suka
bashi hankalinsu. Nasiha ya fara musu a nutse tare da jan gargaɗi. Daga ƙarshe
cikin kaushin murya da tabbatarwa ya ɗan bubbuga table ɗin da yatsansa.
“Bazan lalace wajen zargi akan ku balle ƙin cin duk abinda kuka bani ba, sai
dai zan tabbatar muku, duk wadda ta zuba wani abu koda a ruwan sha ɗinane domin
samun wani cikar burinta ban yafe mata ba. Kuma idan na kamata bazan yafe mataba ko
iya cigaba da zama da ita duk da babu tsarin rabuwa da ɗayanku a zuciyata. Shawara
ya rage naku, kumu haɗu mu zauna don ALLAH cikin soyayya da mutunta juna, ko kuma
kowa ya ɗauka layin da yaga zai dace da shi a shirye nake wajen maganin duk wadda
take tunanin zata iya fin ƙarfi na. Na ƙarshe respecting juna da kuma iyayenmu.
Wlhy idan wata a cikinku ta sake kuskuren yin abinda bai dace ba akan wani ko wata
a cikin iyayrenmu sai na sakata nadama ta har abada, ya rage naku ku dawo
hankalinku kokuma ku ɗaura daga inda kuka tsaya”.
Har ƙasan zuciya kausasan gargaɗinsa sun shigesu, sai dai sunfi ratsa Fadwa
musamman akan zuba masa magani a abinci fiye da Anaam da wannan gaɓar bama komai ta
fahinta ba. Amma dangane da girmama iyayensu da juna ya shigeta matuƙa, dan
yanayinsa ya tabbatar musu zai iya komai. Bayan ya sallamesu kowacce ta nufi
ɓangarenta tana ƙullawa da kwancewa. Shima fita yay a gidan zuwa can gidansu gaida
su Mommy tunda yanzu Daddy ya janye masa sharaɗin hana zuwa gidan. Sai dai koda
yaje ya samu Mommy da Gwaggo basa nan. Bai so haka ba, dan yazone takanas ya
lallashi mommy ɗin da bata haƙuri akan komai ma daya faru, sannan ya yini da ita
yau. Gidan su Anaam ma ya iske Mamie da aunty Mimi sun fita, dole dai ya koma gida
dan gwara yaje ya huta kawai shima.

A ɓangaren Mommy da Gwaggo gidajen su aunty Malika sukaje sukai musu tatas,
inda akai hargitsi bana wasa ba har saida takai an gurfana a kotun baba Ibrahim.
Shima al'amarin ya ɓata masa rai, dan yajima dajin tsiyatakun da su Malikar keyi a
gidajen aurensu. Sai gashi yau suna neman saka Fadwa itama kuma abin takaicin harda
haɗin kan mahaifiyarta. Sosai yayima Gwaggo Halima dake matsayin matar ɗan uwansa
faɗa, ya nuna mata kuskurenta na son ɗaura ɗiyarta akan bigiren da zai rusa
rayuwarta a dunuya da lahira. Suma kuma su Mommy yay musu nasu faɗan, dan tun farko
da basu nunama Fadwa komai tayi a gidan aurenta dai-dai bane daba haka ba. Yanzu
gashi sun ɗanɗana mata tana niyyar zartasu kuma sun shiga damuwa, ta riga kuma ta
ɗanɗana ba lallai abin ya iya barinta ta sauƙi ba.
Nasihar Baba Ibrahim bata canja komai a jin haushin juna da Mommy da Gwaggo
Halima keyi ba. Sai ma ƙara jin zafin juna dan kowacce nada sirrin ƴar uwarta a
tafin hannu. Kuma kowacce taci alwashin nunama ƴar uwarta fawa ɗinta akan ƴaƴan
nasu da kuma mazajensu da suke amsa yayanninsu. Da haka aka sake rabuwa baran-
baran.....

____________________________

Ga Shareff kam tun yana shashshare Fadwa harya dai ya sakko, mata da miji
sai ALLAH. Sai gasu kamar komai bai faruba aka koma faranta ran juna, dan aranar ba
ƙaramin rikita Soulmate ɗin nata tai ba, har yaji a karan kasa ta cancanci yafiya.
Sai dai tsananin kishin mijinta na nan a zuciyarta. A duk sanda ta tuna akwai wata
a yanzu bayan ita tare da shi takanji raɗaɗi mai zafi a zuciyarta. Sai dai ta ɗauka
alƙawarin daina biyema su Aunty Safarah, bazata ƙara amfani da wani magani ba insha
ALLAHU. Zata tsaya da ƙafafunta wajen kishin mijinta da ƙyautata masa kowacce ta
ƙwaci kanta kawai. Dan tayi imani bazata taɓa son Anaam ba a zuciyarta, saboda
tunda ta tashi a rayuwa da tsanar iyayenta da ita kanta ta rayu.
A ɓangaren Anaam ɗin itama sosai take jin kishin mijin nata, dan akwana biyun
nan da yake tare da watanta ba itaba tana matuƙar jin raɗaɗi da zafi. Abinda ya
sauƙaƙa mata kawai zaman Aysha tare da ita. Amma ko shigowa yay wajensu sai tayi
matuƙar dauriya take iya kallonsa har ta sakar masa murmushi. Banbancinsu da Fadwa
kawai ita bata zafafa ba. Bata son Fadwa tun fil'azal saboda tunda ta mallaki
hankalinta tasan Gwaggo Halima da su Fadwa basa son iyayenta basa respecting nasu
kamar su Daddy. Amma batajin tsananin tsanarta dan ita bata zafafama kanta abu,
kawai idan ya ɓata mata rai ta nuna fushintane take anan da kwakwazo a wuce wajen.
Daga haka kuma ta watsar zata fuskanci nagaba mai wucewane. Tadai ɗauka alwashin
ƙyautatama mijinta da basa tarin tukuycin soyayyar daya jima yana mata tun bata san
kanta ba. Duk wuya bazata yarda ta bijirema umarninsa ba ko cutar da Fadwa. Amma
zata ƙwaci kanta akowane hali idan akai yunƙurin cutar da ita.

Lahadi da yamma mijinta ya dawo hanunta, ya gama kwanakinsa a wajen Fadwa. Da


taimakon Aysha suka haɗa abincin dare na gaba daya kamar yanda ya sharɗanta. Ta
nufi sashensa domin gyarawa Aysha kuma ta gyara mata nata duk da ma babu wani datti
mai yawa kasancewar babu yara ba kuma wasu jama'a ne da yawa ke shiga da fita ba.
Duk kaiwa da kawowar da Anaam keyi a sashen Shareff a idon Fadwa ne dake leƙe ta
window ɗin falonta. Kai tsaye tasan wannan rawar jikin na Anaam wai za'a tarba miji
ba basirarta bace Aysha ce. Tai ƙwafa da cije lips, a ranta tana ayyana yarinya ni
dake mu zuba a nan gidan. Oho bama tasan tanaiba, dan koda ta kammala rufo sashen
tai harda saka key saboda ya bama kowacce key. Batare data ko lura da Fadwa ba ta
nufi sashenta dan ta samu tai wanka tunda tasan a koda yaushe zai iya dawowa gidan
tunda ba aiki ya fitaba. Yaje can gidane Mommy ta kirashi duk da a cikinsu babu
wadda tasan da hakan. Yadai ce musu zai fita kawai.

★Ransa fes ya iso gidan domin jiya ma yazo ya gaishesu kuma shida Mommy
babu wata damuwa. dan koda ya bata haƙuri akan duk abinda ya faru tace masa komai
ya wuce a gareta kawai. Yaso yaji kamar ba haka bane a ransa, amma saita kore masa
dukkan tantama ta hanyar sakin jiki da shi sukai hira da suka jima basuyi irinta
ba. Kuma abin mamaki ko sau ɗaya bata kawo maganar Anaam ba ko abinda ya shafi
aurenta. Hakama Fadwa. Sun tattaunane kawai akan auren Aysha da kuma komawar Maheer
wajen aiki a yau.
Sai da ya shiga dukkan sashen mutanen gidan ya gaida kowa sannan ya nufi
sashen Mommy a ƙarshe. Tana falonta zaune Hussaina na haɗa mata ƙwaɗon zogale ya
shigo. Fuskarta da murmushi ta amsa masa sallamarsa. Ya kai zaune shima fuskar tasa
da murmushi.
“First love daɗi zakici haka?”.
Murmushi tayi mai nuna haƙora. “Ai gaka kaima kazo sai muci tare ko?”.
“Harma na fiki lauma”.
Dariya tayi daga ita har Hussaina dake yin tata a ƙumshe. Ya gaida Mommyn, Hussaina
ma ta gaishesa sannan tabar falon bayan ta kawo masa ruwa. A kwano ɗaya sukaci
zogalan da Mommy cike da nishaɗi. Suna tsaka da cinne Gwaggo ta shigo.
“Ja'iri kazo zaka cinye mata ɗan zogalan bayan acan na baka kaƙi ci”.
Murmushi yay da taɓe baki, “Naki kin saka ƙuli ne itako gyaɗa ta saka shiyyasa”.
“Oh, da gyaɗar da ƙulin duk ba abu ɗaya bane?”.
“A wajena ni dai da banbanci”.
Mommy dai dariya take musu kawai.

Sai da suka kammala Gwaggo da Mommy suka dubi Shareff ɗin cikin komawa
serious da ƙyau. Hakan daya ganine ya sashi nutsuwar shima ya maida hankalinsa
garesu.
Gwaggo ce ta fara magana. “Mustapha abubuwa da yawa sun faru waɗanda basai mun
zauna lissafi akansu ba ko sake maimaita batunsu anan gurin. Sai dai waɗanda suke
faruwa a yanzu sune abun dubawa. Kayi haƙuri munyi kuskuren tilasta maka auren
Fadwa ba'a san ranka ba, sai dai mu munyune domin ƙarfafa zumincin ALLAH. Amma ashe
zuciyar uwarta cike take da tsatsa. Tunda har a matsayinka na ɗan ɗan uwanta zata
iya neman asiri taba ƴarta ta zuba amaka a abinci ko abinsha ya tabbata zata iya
kasheka wataran domin farin cikin ƴar tata. Mudai bazamuce dole sai ka saki Fadwa
ba. Amma ka zauna kayi tunani mizai iya zuwa ya dawo nan gaba. Dan hatta cikin
datai ɓari kwanaki mun fara zargin yarinyar nan zubar da shi tai tana akan sani”.
A matuƙar razane Mommy da Shareff suka dubi Gwaggo. Har Mommy ta kasa
haƙuri....
“Gwaggo miyasa zakice haka a ina kikaji wannan maganar kuma?”.
Baki Gwaggon ta taɓe, “Yo Nafi abin duniya na ɓuya ne, kawai nayi shiru ne ban
faɗa mikiba. Amma a jiyyarta da nai asibiti na karanci abubuwa da yawa game da
yarinyar wlhy. Sai dai ban tabbatar ita ɗin ta zubarba. Amma Mustapha kaje kayi
bincike harka tabbatar da gaskiya. Sai dai kayi komai a sirrance basai ka faɗa
mataba a yanzu dan karta toshe duk wat hanyar gaskiyarka. Abu na gaba akan aurenka
na biyu ne, mudai ba son auren nan muke ba sam, amma munga kai kamar kana so. Dan
haka mun yanke shawarar barinka da matarka ku zauna. Sai dai da sharaɗin zaka ƙara
aure. Kuma munma zaɓa maka wadda zaka aura yarinyar kirki da tasan mutuncin kanta,
idan ƙyau ne kuma duka matan naka ta fisu. Mun tabbatar zakaji daɗin zama da ita
insha ALLAHU duk wani ƙuncinka zata ƙwaranye akan waɗan nan ƴan iskan yaran”.
Sosai ya tsurama Gwaggo ido ko ƙyaftawa bayayi, babu abinda zuciyarsa keyi
sai luguden daka. Ya haɗiye yawu da ƙyar. Harshensa na rawa yace, “Aure kuma
gwaggo?”.
Mommy ta amshe da “Eh aure Babana. Shine zai baka kwanciyar hankali muma kuma
ya bamu, dan nidai kasan matarka ta biyu ba zan taɓa sonta ba, amma na haƙura in
har kabi umarni na a yanzuma zan barka da ita. Idan kuma ka bijire su duka biyun
zaka sakesu ka ƙara auren kuma koda bada zaɓina ba. Dan wlhy itama Fadwa ta fitamin
arai. Ko kaunar jin sunan yarinyar nan banayi yanzu. Kuma ina nan saina tabbatar da
nunama uwarta kai ɗin jinane ni na haifi abuna kuma. Dan haka kaje kayi shawara
daga kwana daya har sati guda muna jiranka. Duk abinda ka yanke sai mu sani.”
“Amma First love......”
“Bana son jin komai Shareff. Kaje kawai kayi tunani kafin ka yanke hukunci,
yarinyar da muke so ka aura itace *_Bibah_* ɗiyar Luba na san dai ka
santa”............✍

_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_


*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:


07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇


09134848107

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*


[11/23, 10:16 PM] My Zafafa: *_Typing📲_*

*_BABU SO....!!_*
_(Miya kawo kishi?)_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*
https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718

*_73_*

.........Innalillahi.... Kawai yake jerawa a cikin zuciyarsa har ƙarshe. Ya kafe


Mommy da Gwaggo da idanu ko ƙyaftawa bayayi.
“Katashi kaje kar magriba tayi, gashi kace gobe zaka koma aiki kana da buƙatar
yin wasu kimtse-kimtse. Dan bana ma son Daddynku ya dawo ya ganka a gidan nan”.
Kansa kawai ya iya jinjinawa, ya miƙe jiki a saɓule ya fice idonsa har
wani yaji-yaji yakeyi. Da farko maganar Fadwa ta zubar da ciki ce ta dakesa. Sai
dai maganganunsu na gaba sun goge na farko dan a ganinsa Gwaggo ta kawo zancen
Fadwa ce ta zubda ciki domin baƙantata su sami damar shigo da zancen auren Bibah,
amma kuma zuciyarsa taƙi daina masa wasiwasi. Bashi da wani ra'ayin zama da mata ko
biyu tun ful'azal. Sai dai ƙadararsa ta zama haka. A yanzu kuma bayajin duk wuya
duk rintsi zai iya rabuwa da Fadwa da Anaam. Dan kowacce da irin kalar soyayyar da
yake mata a cikin zuciyarsa. Yama rasa ina zai kama ya riƙe ne a zancen nasu......
Koda ya shigo gidan tsabar yanda zantukan su Mommy suka rikita masa lissafi
baibi takan kowa ba tsakanin Anaam ɗin mai karbar girki, da Fadwa mai fita. Kai
tsaye sashensa ya nufa. Sai bayan sallar magriba mmn abu ke sanarma Fadwa kamar fa
taga motar Shareff. Da mamaki tace “Yaushe ya dawo gidan ban sani ba?”.
“Inaga lokacin kina ciki ne kina wayar nan”.
Ɗan jimm Fadwa tai na wasu mintuna, sai kuma ta shiga bedroom ta dan karo
turare ta fito. Kai tsaye sashen nasa ta nufa. Cikin taɓe baki take bin ko Ina na
falon da kallo tana mai shaƙar daɗaɗan fresheners da Anaam ta baza ko'ina tare da
turaren wuta. Bedroom ɗinsa ta nufa dan baya a falon. Fitowarsa a wanka kenan, ya
juyo yana kallonta. Taku take cikin gayu da yanga, sosai kwalliyar tata ta fita da
ƙyau dan ko makaho ya shafa yasan ita ɗin gwanace wajen zaman zanawa. Ji yay kaso
ashirin bisa ɗarin damuwarsa sun ragu. Ya sauke numfashi a hankali tare da buɗe
mata hannayensa alamar tazo gareshi. Da sasaarfa ta karasa ta shige. Suka sauke
ajiyar zuciya a tare. Sumbatar gefen wuyanta yayi, muryarsa a sanyaye ya raɗa mata
“Kinyi ƙyau Babie na”.
Ajiyar zuciya ta saki da murmushi, ta ɗago tana mai kallonsa, sai kuma ta
manna masa kiss a ƙirjinsa. “Nagode Soulmate barka da dawowa”.
Kansa ya jinjina mata, ya kai hannu ya ɗan shafi fuskarta. Murmushi ta sakar
masa da janye jikinta a nasa. Baice komai ba ya karasa gaban mirror domin shafa
mai. Itama sai takai zaune a bakin gado tana faɗin, “Kayi wani iri kamar mai
damuwa. Ko wani abu ya faru ne?”.
Ta cikin Mirrorn ya kallota. Ya ɗan fesar da numfashi a hankali. “Babu komai
na gajine kawai”.
“Ayya kona maka tausa?”.
“A'a karki damu nagode wannan aikin ƙanwarki ne ai ko”.
Har cikin rai taji zuciyarta ta sosu, amma saita danne tai ɗan murmushi da
mikewa. “Uhhm hakane na shafa'a ne kawai. Kasan idan ina a tare da kai mantawa nake
da komai da kowa kai kaɗai ɗin kawai nake iya gani”.
Murmushi yayi mai sanyi yana mai kallonta ta cikin mirror ɗin. “Ngd ƙwarai
da gaske Sweety na. ALLAH ya barmu tare har abada”.
“Cikin matuƙar jin daɗi tace amin”.
Itace ta taimaka masa ya shirya, ta rungumesa bayan ta feshesa da turare. Lips
dinsu ya haɗe waje guda yana mai mata wani irin fresh kiss da ya nema zautar da
ita. Sai da ya tabbatar ya samu wata nutsuwar sannan ya barta suka koma sauke
numfashi. agogo ta kalla zuciyarta na raunana ganin lokacin fitarta girki yayi. Dan
kuwa ya tabbatar musu daga 6 na yamma ne. Jitai inama ta jawo mintunan su koma
baya, dan wata irin matsananciyar buƙatarsa takeji saboda ya sakata a cakwakiya.
Sanin komai zai iya faruwa ta fita da sauri tana faɗin tana zuwa. Murmushi yayi har
hakwaransa na bayyana ya bita da kallo......
Anaam da bata san da dawowarsa ba ta fito a toilet daga yin alwalar sallar
magrib ya shigo. Sannu da zuwa ta masa. Idanunsa kafe a kanta ya amsa mata. Sosai
itama tata kwalliyar ta wuce da nasa imanin. Yaji daɗi har cikin ransa ganin yanzu
tana kwalliya. Shiyyasa ya hana Aysha wucewa dan yasan koba komai zata taimakama
Anaam ɗin da abubuwa masu yawa da bata gama sani ba a irin rayuwar Nigeria.
“Haka ake tarbar miji dama?”.
“Kai yaya alwalafa nayi”. Ta faɗa murya a karye. Murmushi ya saki yana matsota. Ta
matsa da sauri zata koma toilet. “Nidai ALLAH karka karya mun alwala”. Dariya yayi
da yin ƴar ƙwafa ya juya ya fita. Itama saita sauke ajiyar zuciya dan ta san kaɗan
daga aikinsa yace zai shanye jambakin dake a lips ɗinta.

Bai dawo gidan ba sai bayan sallar isha'i. Kai tsaye kuma sashinsa ya nufa,
inda ya iske har an shirya abinci a dining. A falon ya zauna yana sauke numfashi da
ƙoƙarin kunna television, so yake ya kauda duk wani damuwarsa domin more wannan
daren. Kusan mintuna sha biyar da zamansa babu Anaam babu labarinta. Dan haka ya
dauka waya yay kiranta. “An barni ni kaɗai kamar maraya”.
Murmushi tayi da har yaji sautinsa a kunensa. “Immhum ni ai bansan ka dawo bane
ba fa”.
“Okay, ai yanzu kin sani”.
Min tuna kusan bawai tsakani sai gata ta shigo, tun kan ta iso ƙamshinta ya
karaso. ya rasa a matan nasa wacce tafi wata iya gayune. Duk randa sukejin abin
arziƙi susutashi sukeyi gaba ɗaya. Ta bayan kujerar ta tsaya, tare da ranƙwafowa
kansa ta manna masa kiss a wuyansa. Numfashi yaja mai yalwa tare da fesarwa. Ya
kamo hanunta ya zagayo da ita ya zaunar a cinyarsa. “Irin wannan wanka ai sai ki
sakani manta kaina autar mata”.
Murmushi tai da ɗan tabe baki, “Ban san daɗin baki ni dai Yaya”.
“Kinfi ƙarfin daɗin baki ai a wajena. Duk abinda bakina ya furta a kanki shine ai
nahin gaskiyar zuciyata”.
Sosai taji daɗi har cikin ranta. Amma dai batace komai ba sai murmushi kawai
da taɗanyi. “Yau dai lipstick ɗin nan nawane ko?”.
“A'a”.
“Ashe zan miki kuka”.
Dariya ta sanya tana mai lafewa a jikinsa. “Oh oh ya kaga Yaya ana kuka”.
Murmushi yayi mai faɗi da lakace hancinta. “Wato harma hasasowa kikeyi ko”.
“Sosai ma”.
“Uhhyum mugunta.com”. Yay maganar da kaima lips nata kiss. Bai bari ta shaƙi
numfashi ba ya maida lips ɗin nasa kan nata again. Sai dai a yanzu salon dabanne
dana farko, dan sai da ya shanye lipstick ɗin tas hankalinsa ya ƙwanta. Lamo tai a
jikinsa tana sauke ajiyar zuciya a hankali. “Tsadar tsada ke ta musamman ce”.
Muryarta a dashe tace, “Ai kaima ɗin na musamman ne”.
Ido yake son su haɗa amma taƙi yarda. “Please ki kalla cikin idona ki faɗa
Noorie”.
Murmushi tai da juyowa kamar zata kallesan, sai ta mike zumbur daga jikinsa.
Kamota yay yunƙurin yi ta zille tana dariya. “Biyu kenan fa, idan kika bari na
kamaki zakiji jiki”. Gwalo ta masa da nufar dining. Ya murmusa cikin jinjina kai.
Waya ya ɗauka yay kiran Fadwa. Cikin murya ƙasa-kasa yace, “Babie kizo
muyi dinner”.
“Uhm-uhm”. Ta faɗa a shagwaɓe.
Ɗan kallon Anaam yay, ganin hankalinta ba kansa yake ba ya sake ƴin ƙasa da muryar
cikin lallashi. “Why”.
“Nifa bana jin cin komai”.
“Idan kika bari nazo da kaina akwai hukunci kenan”.
Dariya tayi da ga can. “Naji zanzo”. Shima sai yay murmushi da faɗin
“Matsoraciya”.
Juyowar Anaam dai-dai yana ajiye wayar. batare data fahimci mi yayi ba ta
ɗaga masa yatsu biyu. “Hy Yaya abinci na jiranka”.
Fuskarsa ya dan marairaice. “Kin yarda zaki bani da kanki?”.
Ɗan jimm tai na tunani, sai kuma ta kaɗa kanta alamar eh.
“This is for you my Noorie”.
Ya faɗa yana mai kissing hanunsa ya hura mata.
Dariyar da tafi kama data mugunta ta sakar masa. Ta tare kiss ɗin tana mai
lumshe idanu da mannawa saitin zuciyrta. Rungumeta yay sannan ya kai zaune a kujer
data ja masa baya. Dai-dai nan Fadwa ta shigo. Koda suka kalla juna ita da Anaam
sai kowa ya watsar da ɗan uwansa. Sai da ta karaso ta zaunane Anaam ɗin tace,
“Barka da yamma”. A takaice itama Fadwa ta amsa da “Barka”. Sai kuma ta ɗan saci
kallon Shareff ta sakar masa murmushi. Murtani ya mayar mata ya ɗauke kansa.
Anaam daba lura tai da su ba tana ta ƙoƙarin zubama kanta abinci, koda ta ɗago
sai suka haɗa ido itama da shi. Murmushi suka sakarma juna. Nanma ya kauda kansa
batare da Fadwa ta gani ba dan itama ta maida hankalinta ga zuba nata abincinne.
Yau ne kuma karon farko da Anaam ta fara girki a gidan, duk da dai tayisane da
taimakon Aysha dan bata iya girke-girken Nigeria ba sai ƙalilan a ciki. Saukinma
zuwa yanzu ta iya cin abubuwa da yawa ba kamar farkon zuwanta ba.

Gaba ɗayansu cin abincin suke cike da nishaɗi, dan kowacce ta samu irin
farin cikin da take buƙata daga mijinta. Wanda a nata wautan gani take itace ɗaya
ƙwalli ƙwal a zuciyarsa. Shiko cin abincin yake wani yanki na hankalinsa naga
umarnin su Mommy, sai dai wani yanki najin matuƙar farin cikin ganin farin cikin
matan nasa da har kowacce ta kasa ɓoyewa. Koda suka kammala Fadwa bata wani jimaba
tare da su tai musu sai da safe ta wuce zuciyarta cike da kishin mijinta. Anaam
kuwa ta shiga tattare kayan waje guda. Falo suka koma ita dashi, ya zauna a 3sitter
tare da jawota jikinsa....
Sai da ta bari sun shagala da kallo yana mai cakuɗata a yanda yaso sannan
taja numfashi. “Yaya gobe zan koma gun aiki ko?”.
Tamkar saukar aradu yaji maganar amma sai ya danne. Yay shiru kamar bai
jita ba sai da ta ƙara maimaita masa tana ɗagowa ta kallesa. Shanyayyun idanunsa ya
zuba mata na wasu sakanni. sai kuma ya dan lumashe da kaɗa mata kai kawai. Ta sauke
ajiyar zuciya tana mai hamdala ga UBANGIJI. “Nagode Yaya wlhy na zata zakace a'a”.
“Humm”.
Kawai yace mata.
Tasan ya shaƙa dan haka tai shiru, ita dai tunda ya yarda zata koma ai
Alhamdulillahi koma mi zaiyi mai sauƙine kuma. Saida ya kammala kallon labarai
sannan suka mike. Ta fita domin zuwa tai shirin barci shi kuma ya nufi bedroom
ɗinsa bayan ya bata umarnin idan zata dawo tazo masa lipton. Ya mata hakane dan
kartai tunanin ƙin dawowar. Kamarko ya sani batai niyyar dawowa ba. Amma babu yanda
ta iya kodan son komawarta aiki salin alin tabi umarnin nasa.
Sai da ta shafe kusan mintuna talatin sannan ta dawo cikin zumbulelen hijjab
har kasa da cup na lipton. Rashin ganinsa a falo ya sata nufar bedroom ɗinsa kai
tsaye. A bakin gado ta samesa yana haɗa wasu takardu da laptap ɗinsa alamar kayan
zuwa office yake tattarawa. Ta ajiye cup din a bedside drawer dake gefensa.
“Jazakallahu khairan”.
Cikin jin daɗi ta amsa da “Amin ngd”.
“Kin rufe falon ko?”.
Hakan ya bata tabbacin nan ɗin zata kwana dai, dan haka ta girgiza masa kanta.
“Okay ki rufe kawai”.
Nan din ma kanta kawai ta jinjina cike da tsoro. Sai dai babu yanda zatai dole taje
ta rufe ɗin ta dawo. Ta samesa ya fara shan shayinsa. Ya nuna mata gadon da fadin,
“Bisamillah ki kwanta gobe akwai fitar safe. In kuma kikace zaki mun irin lattin da
kike mun a gida zan tafi na barki ne”.
Baki ta ɗan tura masa batare da tace komai ba. Hijjab ɗinta ta cire ta hau
gadon ta kwanta tana mai addu'ar ALLAH yasa kar yace yana bukatar komai. Dan duk da
zaren ɗinkin da kansa ya fita saboda yawan shiga ruwan zafi da takeyi ba ƙaramin
tsoro da fargaba take shigaba a duk lokacin data tuna za'a iya sake ratsa wajen
again. Sauri-sauri tai addu'a ta gyara kwanciya da rokon ALLAH zuwan barci kafin ya
kammala shan shayin nasa...........✍

🤣Abun dariya abun tausai😜


_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_


*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:


07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇


09134848107

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*


[11/23, 10:16 PM] My Zafafa: *_Typing📲_*

*_BABU SO....!!_*
_(Miya kawo kishi?)_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718

*_75_*
........Rungume yake da ita yana sanya mata albarka bayan samun nutsuwarsu. “Noorie
na wai miye sirrinne?. Kwana biyun nan fa kin ƙara zama mai tsadar tsada ta gasken
gaske. ALLAH gigitani kike na manta da kaina gaba ɗaya. Ni'imomi sun ƙara cika
garden ɗina”.
Kunya ta sakata tura kanta a ƙirjinsa tana murmushi. “Kai Yaya ko kunya
bakaji?”.
“Kunyar mi zanji ina a gaban autar mata. Idan ban faɗa miki abinda ke raina
game da ƙyautarki da ALLAH ya bani ba mi zanyi tauraruwa a cikin taurari?”. Ya ƙare
maganar da manna mata kiss a gefen kunne. Tsam ta ƙara matsesa a cikin jikinta.
Ƙaunarsa ta musamman na sake ratsa zuciya da ɓargonta. A duk sanda take tare da shi
mantawa take da kowa da komai, bata tuna bayan ita akwai watanta. Farin ciki take
bashi fiye da hasashen zuciya. Kamar yanda shima yake riritata tamkar ƙwai a
cokali. Ya gama ɗorata da koya mata salo-salo na rayuwa dakan ƙara raunana rauninta
taji koda agaban wanene batajin shakkar nunasa matsayin *_Jan-gwarzonta_*....
Sumbatar goshinta yay cikin katse mata tunani, ya ɗagota suna mai kallon
juna a tsakiyar ido. “Anya bani da ajiyar baby a wajen nan Noorie?”.
Idanu ta waro sosai a kansa. Ya dage mata gira daya da ƙyafta idanun yana
murmushi. “Am serious kin canja Juwairiyya. Jiba nan ya ƙara girma. Baƙya raki
kamar da, saima so cikin zalama. Garden ya ƙara zama zakwai-zaƙwai”.
Doke masa hannu tai da ƙoƙarin juya baya ya riƙota. “Shike nan, shike nan na
daina magana. Yanzu dai na haƙura Ki shirya kije kawai, bazan hanaki zuwa bikin
ƙawarki ba”.
“Woow dan ALLAH da gaske My hero?”.
“Yes my Heartbeat”.
Wani irin ɗan ihun farin ciki tayi, tare manne lips ɗinsu waje guda. Cikin
ƙanƙanin lokaci ta susuta masa lisaafi.....

(🚶🏻🤕jaraba).

★Shi da kansa ya kaita, bayan yayima Fadwa magana ta shirya itama taje ɗin
har sai biki ya tashi tace a'a. Bai matsanta mataba ya ƙyaleta, dan shima dai yana
buƙatar ɗaya ta zauna tare da shi kar a maidashi gwauro.
Sosai Anaam ta tsinta kanta cikin farin cikin ganinta tare dasu Abie ɗinta.
Nan fa sabuwar shagwaɓa ta tashi. Suko suna biye mata dan farin cikine baibaye da
zukatansu. A ranar akai ƙunshi, sai dai tana nane da su Mamie bata shiga cikin gida
ba. Washe gari kamu ta tashi duk batajin daɗin jikinta tun safe. Amma sai ta
danganta hakan da kewar Shareff dake damunta. Tun wajen sha biyu ta shige cikin
gida, kasancewar sashen Mom dana Mommy duk cike yake da baƙi saita nufi sashen
aunty Amarya dan su Aysha nacan da gayyar ƙawayenta. Tuni ta shige cikinsu anata
shan shafta har akai mata ƙunshi da Aysha ta matsa. Tun ana lallin take complain
ayi maza a gama kanta ciwo yake, Aysha na hararar ta wai ƙunshinne bataso, in ma an
gama anjima kaɗan tare zasuje Saloon ko taƙi ko taso.
Kamar wasa tace musu jiri takeji, kuma tana ganin hayaniyar gidance, Aysha dai
taita lallaɓata ta shige bedroom ɗin aunty Amarya ta kwanta. Sai da ƙawayen amarya
suka gama shiri suka fita tsakar gida Aunty Rahma ta shigo ta gata ita da Aunty
Bintu. Sune suka sakata tashi dole tai wanka. Amrah ta kawo mata kayanta ta shirya
anan. Jin yanzu babu jirin saita fito tsakar gida inda kamu ke gudana. Dan ƙarfin
hali harda shiga fili taima amarya liki. Masu kiɗan kwarya suka shiga koɗata da
kirarin Amaryar babban yaya Shareff. Ana haka Khaleel ya shigo shi da Shareff da
Maheer. Anaam ta nufesu tana murmushi ta farama Khaleel ɗin liƙi. Hakan yasa aka
dawo aka baibayesu masu kiɗan ƙwarya na cigaba da kwarzantata. Shareff dake
kallonta yana murmushi baima san ya zaro nasa ƴan kudaɗen ba ya fara liƙeta, hakan
yasa shima Maheer zarowa yana musu liƙin su duka uku. Aifa sai waje ya ɗauka ihu,
dangi aka zagayesu su duka huɗun ana musu liƙi. Tun Anaam najin hayaniyar sama-sama
harta fara jinta nesa-nesa. Idanunta suka fara limshewa tai baya zata sulale
Shareff daya farga yay saurin tarota jikinsa. A take waje ya ɗau shiru. Da sauri
Aunty Bintu ta kawo ruwa aka shafama Anaam ɗin saita kawo nannauyan numfashi. Kanta
ta riƙe hawaye na ziraro mata. “Yaya kaina, kaina zai fashe Yaya”.
Hankali tashe ya sungumeta akai sashen aunty Amarya da ita, dan nan ɗinne
kawai keda karacin mutane, dama ƙawayen amaryane sai danginta tsiraru kasancewar ba
ƴar kano bace, kuma duk sun fito. Maheer ne yay kiran Dr Jamal. Cikin ƙanƙanin
lokaci sai gashi ya iso, har yanzu Anaam na'a jikin Shareff tana masa kukan kanta.
Yana riƙe da kan yana mata addu'a, su aunty Amarya zagaye da su. Dan hatta Mom da
Aunty Mimi duk suna a wajen. Tuni kuma an kaima Mommy da Gwaggo rahoto sai dai basu
fitoba. Mamie ma nacan cikin damuwa a tsakar gida amma dattakonta ya hanata shigowa
taga halin da Anaam ɗin ke'a ciki. Su Daddy dai suna can gidan su Anaam din tare da
Abie dan can ɗin babu mutane sosai duk anyo nan cikin gida.
A kallo ɗaya Dr Jamal ya fahimci matsalar Anaam ɗin, dan haka ya kalli
Shareff cikin ido. Hararsa yayi yana motsa laɓɓansa ahankali alamar magana yayi sai
dai bata fitoba kasancewar falon cike yake da su Mom. Jininta ya ɗiba ya kuma bata
maganin ciwon kan kawai. “Inaga zanje ai text first, amma dai tasha maganin sai
taje inda babu wannan hayaniyar ta kwanta ta huta. Inba hakaba ciwon kan zai cigaba
da damunta. Zuwa da safe insha ALLAHU zan kawo sakamakon ”.
“Kana nufin wannan maganin kawai zaka bata ka barmin mata cikin ciwo
kenan?”.
Shareff ya faɗa cikin suɓutar baki dan ya ma manta da su aunty Mimi dake wajen.
Babu wanda baiyi murmushi ba, ƙanensa na gulmarsa a zuciya ina miskilancin nasa
yaje. Sai dai babu mai damar cewa komai. Maheer kam jikinsa ne yay sanyi, ya dubi
matarsa da sam tama ƙi sakewa a gidan saboda a wajensa ma bata samu farin ciki ba.
Auren watanni huɗu ya kasa sakin ransa ko kusantarta yaƙi yi, ita kuma ta tura masa
aniyarsa duk abinda ya dace mace ta gari taiwa miji bata gazaba tana masa
gwargwadon iyawarta.
Yanzun ma ko kunya babu shine ya kaita can gidansu dan acanne kawai
akeda ƙarancin hayaniya. Kai tsaye sama ya kaita ɗakin Mamie ya kwantar a kan gado,
yana daga zaune kanta bisa cinyarsa yana tofa mata addu'a a kanta aunty Mimi ta
shigo ɗauke da ƙaramar roba da towel ƙarami a ciki. Shine ya amsa, tai murmushi a
ranta tana faɗin, (Ƴan banzan yara dakun cigaba da pretending da rabo ya kashe har
mu bama ku kaɗai ba. Dan wannan daga gani ciki ne). A zahiri kam juyawa tai tayi
ficewrta ta bar musu ɗakin. Towel ɗin ya dinga matsewa a cikin ruwan yana goga mata
a goshi zuwa fuska har wuyanta da hannayenta. Sai da kanta dake zafi ɗau ya huce
sosai sannan ya koma kafafunta. cikin ƙanƙanin lokaci sai ga barci ya ɗauketa. Ya
sauke ajiyar zuciya da komawa gefen gadon ya tsugunna saitin fuskarta. Kallonta
yake da murmushi, ƙaunarta na ƙara ratsashi. Ya kai lips ɗinsa kan nata ya sumbata,
hakama idanunta dake lumshe. Har cikin ransa yana fatan hasashensa ya zama gaskiya.
Addu'a daya jima yanayi ta samun rabo daga kowaccensu ta tabbata a wannan karon.
Dan ko kwana biyu ba'ai ba da gama yima Fadwa ƙorafi akan hakan.
Shigowar Mamie data kasa haƙuri ce ta sashi mikewa yana shafar ƙeya. Haka
kawai yanzu yake jin tsananin kunyarsu ita da Abie babu gaira babu sabar. Cikin
sanɗa da dabara ya zare jikinsa ya gudu a ɗakin.....

Su Daddy ma sun shigo dubata bayan sallar isha'i, har sannan kuma bata tashi
ba tanata barci. Sun mata addu'ar samun lafiya suka fice. Sai da Abie ya rakatane
ya dawo domin sake duba tilon ƴar tasa. Yana a ɗakin Shareff ya dawo, ji yay duk ya
daburce, dan haka yaki sakewa ya gudu, duk da Abie nace masa ya dawo shi fitama
zaiyi amma yaƙi tsayawa wai dama yazo ya sake dubatane zai wuce gida goma tayi.....

*_WASHE GARI_* al'ummar wannan family suka tashi da farin cikin bayyanar cikin
Anaam ɗan watanni biyu da wasu kwanaki da adadinsu baida yawa na cika watanni uku.
Zokaga murna wajen su Mamie da su Daddy. ALLAH mai alheri, su sunsha kuka da
damuwar rashin samun haihuwa da wuri ga Anaam da bata rufa watanni huɗu ciff ba da
ciki. Wannan rahama ce ta UBANGIJI mai yin yanda yaso a lokacin da yaso. Isar
wannan al'amari kunen Gwaggo da Mommy tamkar saukar aradune a tsakiyar dare mai
duhuwa. Dama dama ma Mommy bataji zuciyarta ta zafafa ba a wannan karon har hakan
ya bata mamaki. Amma Gwaggo gaba ɗaya birkicewa tayi har bakinta ya dinga subucewa
wajen sakin wasu maganganu. Koda ta kira Mommy gefe kan hakan sai Mommyn ta nuna
mata ita duk da bata son Anaam da su Abie taji son cikin dan koba komai gudan jinin
Shareff ne ai. Wannan furuci ya matuƙar ƙona zuciyar Gwaggo. Dan haka ta ɗau
alwashin sai ta ɓata taron bikin nan. Cikin halin ko'in kula Mommy tai komawarta
cikin danginta ta cigaba da hidimarta. Gwaggo ta bita da kallo zuciyarta na suya
matuƙa, ita Nafisa zataima wannan ɗibar albarkar, to ai idan tasan wata bata san
wataba wlhy. Barin wajen tai fuuu kamar zataci tun tuɓe zuwa sashenta tana ƙulla
wutar da zata kunno a gobe idan ALLAH ya kaimu.
Bayyanar cikin Anaam ta matuƙar tada hankalin Fadwa, musamman dataga kamar
dai nata Shareff bai wani zumuɗi ba ko rawan kai a zahiri. Amma kuma yanayinsa na
son nuna kulawa ga Anaam ya tabbatar mata nunawarsa a fili bashi ke nufin baya son
haihuwaba. Kawai dai hakan naturally ɗin halayyarsace ɓoye sirrin zuciya. Ba ita
kaɗaiba hatta Gwaggo Halima maganar cikin nan ya tada mata hankali. A karon farko
sai gata gidan Shareff ɗin dan bata taɓa zuwa ba. Cikin shirin tafiya gidan biki
take, dan acewarta zataje bikin Khaleel ne bana Aysha ba, dan ita da Mommy a yanzu
babu shiri kwata-kwata, saima yaƙar juna da akeyi.
Kuka sosai Fadwa ta dinga yimata akan ta shiga uku itakam, ga Anaam tazo a
bayanta ta samu ciki amma ita tun miscarriage data samu babu wani bayani (Karfa ku
manta ko Gwaggo Halima bata san Fadwa zubda ciki taiba. Ƙawayenta ne da Gwaggo
kawai suka san wannan sirrin, sai ko Anaam. Gwaggo ma ita da Bibah da hajiya Luba
maman Bibah kawai suka sani).
“Kinga kwantar da hankalinki a gama hayaniyar bikin nan sai mu tafi Germany
kiga likita, karma ki bari wani abu ya tada miki hankali kinji shalele”.
Lallashin Mamanta ya saka mata samun ƴar nutsuwa harta shirya ta bita sukaje
gidan bikin, inda da ace sun san mi Gwaggo ke ƙullawa da basuje ba, sai dai bawa
bai isa sanin gaibuba daga kadarar abinda zai faru a minti guda na gaibunsa
sam.........✍

Humm, yau fa akeyinta🚶🏻🤕🚴🏼😝.

_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_


*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾


ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:


07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇


09134848107

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*


[11/23, 10:16 PM] My Zafafa: *_Typing📲_*

*_BABU SO....!!_*
_(Miya kawo kishi?)_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718

*_74_*

.......Dariya kawai yake dannewa dan sarai duk ya gama fahimtar inda ta dosa. Sai
dai shi yasan a yau bawai zai iya haƙuri bane gara ya maidata ƴar hannu a wuce
wajen. Amma a zahiri ya basar tamkar bai san mitake ba. Dan koda ya kammala shan
shayin toilet ya shiga ya dauro alwala. Shafa'i da wutiri yayi sannan ya hawo gadon
bayan ya fita ya leƙa tsakar gidan ta windows ɗinsa na falo. Ganin babu wani damuwa
ya dawo bedroom ɗin shima ya hau gadon ya kwanta. A hankali ya kwanto bayanta yana
mai ɗaga duvet din da taja har saman kanta.
“Bana faɗa miki ni ba'a juyamin baya a gado ba?”.
Shiru tai ita ala dole tayi barci. Yaji a jikinsa pretending ne kawai, dan haka
ya fara mata cakulkule. Duk yanda taso fiskewa hakan ya gagara, dole ta fara dariya
da ture hanunsa. Bai bartaba har sai da yaga ta juyo yanda yake bukata. Ya haɗe
goshinsu waje guda yana murmushi. “Ni na rasa miyasa kika rainani”.
“Saboda kana mun mugunta mana”. Ta faɗa tana murmushi.
“Kin cika tsokana ne shiyyasa”.
Hanunsa da yake cusawa jikinta ta mintsina. “Ouch!!”. Ya faɗa batare daya janye ba.
Murmushi tayi zata kauda kanta ya riƙo fuskar. Duk yanda taso ƙwacewa babu damar
hakan. Dan wani salo ya ɗauka wanda yasha banban da karatun farko daya koya mata.
Cikin kankanin lokaci ya sakata sakin masa jiki ya fara yanda yake so. Tafiya tayi
tafiya sun gama cakuɗa juna yanda suke so ya ɗauka babban hanyar garden. Ai tuni
mutuniyar taku ta fara sakin magiya da roƙo amma ya nuna mata sam yau babu ɗaga
ƙafa garden zai sake komawa ziyara. Hankalinta bai kara tashi ba sai da taji yana
ambaton addu'a...
Wiya kam dai yau ma ta shata, duk da dai ba irin ta farko bace dan babu ma
haɗi, dan yau ya bita a hankali kamar yanda Dr Bilkisu ta gargaɗesa. Yau din ma dai
harda kukanta. Amma baiyi nisaba kamar na waccan ranar. Tasha albarka kala-kala
tare da daɗaɗan kalaman da suka sanyaya mata rai raɗaɗin taji ya raguma. ya taimaka
mata ta shiga ruwan zafi kafin su dawo gadon ya bita da tukuycin tausar data sakata
yin barci. Ajiyar zuciya ya sauke mai nauyi da sake sakar mata kiss a lips da
idanunta yana faɗin, “ALLAH yay miki albarka”. Daga haka shima ya rungumeta suka
lula duniyar barcin tare..

*_WASHE GARI_*

Rashin sabon ɗaukar gabaran gida kafin fita aiki yasa saida taimakonsa dana
Aysha suka shirya fita akan lokaci, gashi sai langaɓewa take wai jiya ya wahal da
ita. Shi dai nashi murmushi kawai, itako tana faman tura baki da tsuke fuska. Kamar
kullum tayi ƙyau cikin kayan hidimar ƙasa, sai dai ta ɗaura Abaya yau a sama sannan
ta naɗa veil ɗin abayar a kanta. Ƙin fitowa tai har saida ya shiga sashen Fadwa
sukai sallama ya fito sannan ta fito suka wuce. A hanya take tambayarsa yaushe zata
fara koyan tata motar. Shiru kamar bazaice komai ba. Sai da ya kaucema mai napep
ɗin dake neman shiga masa hannu sannan ya ɗan dubeta bayan yaja tsaki da yima mai
napep ɗin daƙuwa.
“Mu bari weekend, idan kuma Fadwa ta koya miki to?”.
Baki ta tura gaba sai dai batace komai ba. Hakan yasashi fahimtar zancen nasa
bai amsu ba. Ya girgiza kai kawai ransa fal mamakin kishin matan nasa. Ita kanta
Fadwan daru ya barta tanayi akan fitar tashi da Anaam. Wai sai dai idan ranar
girkintane kawai zasuke tafiya tare. Amma ranar nata bata yarda ba. Itama baice
mata komaiba yay fitowarsa, to ga Anaam ɗin ma yace Fadwa ta koya mata mota ta nuna
bata so.
Ita ya fara saukewa, da gargaɗi mai girma akan Yaseer sannan yay gaba. Ya
samu tarba ta musamman a wajen staffs nashi. Inda sukai ƴar gajeriyar walima
lokacin break acewarsu tunda ba'ai ta aure ba. Kasancewar ya samu aiki da yawa
Khaleel ne yaje ya maida Anaam gida, shiko sai bayan isha'i ma ya kona gidan. Sanda
ya iso ya iske komai yanda yake buƙata, dan dawowar Anaam ɗin tayi amfani sosai.
Yau ɗin ma dai yasha sharafinsa, inda mutuniyar tasa taita masa raki, baibi
takanta ba, amma yabita a sannu gudun ɓaro aiki. Washe gari har wani farin ciki
takeji zai koma wajen Fadwa ta huta, duk da dai kishinsa na zaune daram a ranta
babu sassauci. Safiyar talata sai dai yayma Fadwa ƙaramin hauka akan fitarsa da
Anaam sannan suka samu dai-daito, dan ta dage bazai ɗauka Anaam ba dan ranar
girkintane. Amma ganin ya juye mata yanda bata kauna dole tai shiru, ya fita ya
barta tana rusar kuka

Haka kwanaki suka cigaba da tafiya, tun Anaam na masa raki a duk ranar
girkinta harta fara zama ƴar hannu, duk salon da yazo mata da shi zata amsa kuma ta
bashi haɗin kai yanda zai samu farin ciki. Babu abinda ya dameta da sabgar Fadwa,
abinda ke gabanta kawai takeyi, sai dai kuma bata ragawa idan Fadwan ta shiga
shirginta. Dan kuwa saita tsefeta tas ake samun zaman lafiya a gidan. Shareff yayi
kurarin yayi masifar akan tsiwarta amma a banza, dan tace in ba'a shiga gonartaba
bazata shiga ta mutum ba. Ita kuma Fadwa tsokanar magana ne matsalarta. Komai ta
gani saita tanka. Duk kankantarsa sai tayi magana ga Shareff ɗin ko ga Anaam. Sauki
ɗaya aka samu ta rage kai ƙararsa wajen iyaye, koda yake yanzu fa itada Mommy babu
wani mutunci, dan kuwa ranar daya kaisu gidan su duka domin gaishesu Anaam tasha
kallo, Mommy ta dinga yamutse-yamutse, abibda ya bata dariya Fadwa zata fara iyayi
ita masu Mommy, mommy ta gwaleta. Aiko ta fita baki gumtse tana danne dariya. Tuni
ta gudu gidansu wajen Mamie, inda ta ruƙunƙumesu harda kukanta wai tayi missing
nasu. Suma sunyi missing nata matuƙa, amma sai suka dinga lallashinta. lokacin da
Fadwa da Shareff suka shigo gaida su Abie ɗin kowa yayi mamaki Fadwa, dan yau babu
rashin kunya ta gaishesu da girmamawa saboda tsoron butsutsun Shareff, dan kafin su
taho ya buga mata warning bana wasa ba akan su Abie ɗin. Sai kuma abinda Mommy tai
mata a gaban Anaam ya sake dagula mata lissafi.

Zuwansu gidan da kwana biyu maganar auren Bibah da Shareff ta fito, dan kuwa a
kwanakin nan dama sunata bugawa ne tsakaninsa da su Mommy, ta kuma tabbatar masa
idan yana fa son zama da matansa sai ya auri Bibah, a gefe kuwa burinta ita da
Gwaggo ya auri Bibahn su fidda Fadwa da Anaam kuma a gidan dan sun ɗau alwashin
bazasu barshi zama da su ba.

Wannan maganar aure itace ta tada gagarumar ƙurar data tada hankalin kowa a
family guda biyu, dan kuwa sarƙa-sarƙar tayi yawa ai. Saboda Shareff na ɗan gatan
duniya sai a dinga haɗa masa ƴaƴan dangi yana aure dai. Mamie da Abie dai basu ce
komai ba, sun kuma yima Anaam nasiha akan koda a fuska karta nunama Shareff komai.
Taji ciwo a ranta, sannan taci kuka amma sai tabi maganar iyayenta.
A ɓangaren Gwaggo Halima kuwa sabon yaƙi ne ya tashi tsakaninta da su Mommy,
nanfa aka shiga ƴar tone tonen asiri ta yanda har akaima Shareff asirin daya
nisantashi da su Abie. Abubuwa dai babu daɗi, dan tsabar takaicinsu Daddy har sai
da yaji ƙwalla sun cika masa ido. Gwaggo Halima tace sai Fadwa ta koma gida babanta
yace ƙarya haramun, idan Fadwa ta rrabuda Shareff ta nema wani uban bashi ba. To
itama dai tana son mijinta, duk da kuwa maganar zai ƙara aure yake, kuma da kawarta
data san sirrikanta.
Ruguntsumin masifa akeci na haƙiƙa a wannan gaɓa tsakanin Fadwa da Bibah,
Gwaggo Halima da su Mommy da maman bibah. A gefe kuma ga shirye-shiryen bikin
Aysha, sai kuma Khaleel da tasa budurwar shima. Sosai hankalin Shareff ya kasu. Ga
company, ga rikicin Mommy da Gwaggo data noƙe tabar Mommy na raba hali. Ga rikicin
Fadwa, Dan ita Anaam da sauƙi. Bata fasa komai da take masa ba amma yabar ganin
murmushinta gaba ɗaya itama. Dama zuwa yanzu da motarta take fita wajen aiki
kasancewar ta ƙware, dan bai kulla sati biyu yana koya mataba da yake ta saka kanta
sai gashi ta iya, idan zasu fita yana gaba tana biye da shi, komuma tana gaban yana
biye da ita duk dai dan ta ƙara sanin hanya.
An shiga shagalin bikin Aysha ne cikin ruguntsumin maganar Bibah, amma hakan
bai hana Shareff sharɗantama matan nasa zuwa taron bikin ba. To Anaam ma basai an
sharɗanta mata ba. Bikin Aminiya ya wuce tace bata zuwa, hakama Yaya Khaleel. Dan
haka tun ranar kamu tace masa zata koma can gidan gaba ɗaya har sai biki ya tashi.
Da farko yace bai amince ba, tako saka masa kuka. Da farko shareta yayi, sai dai
ganin kukan nata bana kare bane yace taje cikin fushi. Sai kuma jikinta yay sanyi.
Yayi zaton zai taso aiki ya tarar ta wuce, sai ya samu tana gida babu ma
niyyar tafiyar tare da ita. Ganin kallon da yake binta da shi ya sata tunzura baki
gaba ta ɗauke kanta gefe.
Baki ya ɗan taɓe, “Motar ce babu mai komi?”.
“Ni na fasa”.
Ta faɗa idonta na cikowa da ƙwalla.
“Dalili?”.
Kuka ta fashe masa dashi. “Toni ya kake so nayine dan ALLAH Yaya. Taya zanje wani
waje kana jin haushina. Salon kawai kasa ALLAH ya sakani a wuta”.
Ɗan murmushi yayi da girgiza kansa yana furzar da huci. “Ni bance ina
fushi dake ba kar kimun sharri, kune dai kuke fushi dani akan abinda na tabbatar
muku nima bana ra'ayinsa. Mi zanyi da wata Bibah can da har zamu zauna kuna dagula
min lissafi. Kun haɗe kai ku a dole bakwa son kishiya. Kun san tun yaushe ake
maganar nan ina ta yaƙin ganin bata fitaba? amma kuke ɗaukar laifi kuna ɗauramin.
Koda yake ke nagama kamar baki damu da zuwan amaryar tawa ba, dan kwanakin nan wata
ƙiba kikeyi da haske ƙyawu na musamman na fita a fuskarki, kamar wata black
American”.
Throw pillows ta ɗauka ta fara jefa masa. Ya shiga karewa yana dariya. Ganin
haka ya sata mikewa ta haye kansa tana cigaba da kai masa kananun duka da pillow.
Dariya yake mata da son kwace filon yana karewa, har dai ALLAH ya bashi sa'a ya
damƙe hanun ya mirgina ta koma ƙasa yana a sama. Turesa ta farayi shi kuma yana kai
mata kisses a wuyanta zuwa ƙirji. Kukan shagwaɓa ta fara masa ya koma mata
cakulkule dole ta fara ƙyarƙyala dariya. Daga haka labarin ya canja aka koma neman
lada. Dama a kame yake kwanakin nan ko nauyi bai iya saukewa saboda zafin da kansa
ya ɗauka matuƙa............✍

_ZAFAFA BIYAR_
*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_


*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:


07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇


09134848107

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*


[11/23, 10:16 PM] My Zafafa: *_Typing📲_*

*_BABU SO....!!_*
_(Miya kawo kishi?)_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718

*_76_*
..........Sun iso gidan biki inda yake tanƙam da jama'a. Dan maza nata shirin
wucewa massallaci saboda an haɗe ɗaurin auren waje guda har na Khaleel domin
sauƙaƙawa mutane. Cikin takama da isa Gwaggo Halima da Fadwa suka shigo cikin
gidan, anan fa kallo ya koma sama dan ko makaho ya shafa yasan naira ta zauna. Kai
tsaye sashen Mom suka nufa dan ko kallon sashen Mommy a yanzu Gwaggo Halima batayi
a gidan balle Gwaggo. Mom da babu ruwanta dama tai musu tarba ta mutuntawa duk da
kuwa tunda aka tsira bikin sai yau kowa yaga idon Gwaggo Halima a gidan. Tadai
aikoma Abba da Daddy Da mom gudun mawa. Shi kansa Khaleel mota ta danƙara masa duk
dan cusama Mommy haushi. Tuni ƴar rahoton Gwaggo taje ta sanar mata isowar su
Fadwan. Tai murmushi mai alamomi da yawa tana mai miƙewa, cikin toilet ɗinta ta
shiga, duk da kuwa ta hana kowa shiga mata bedroom dama. Amma duk da haka bata
yarda ta tsaya iya bedroom tai wayarba. Daga can aka ɗaga, fuskarta ƙawace da
murmushi cikin bada umarni kuma tace, “Ki tabbatar da an ɗaura aure ki tura masa,
dan ina son maimakon su iso gida da labarin farin cikin an gama ɗaurin aure lafiya,
labarin ya canja”. Batako jira amsa ba ta kashe wayar gaba ɗaya.

Cike da farin cikin sake aurar da yaransu lafiya su Daddy suka bar gida,
tare da tawagar sauran ƴaƴansu su Shareff da ango Khaleel da tarin abokansa da ƴan
uwa da abokan arziƙi. An fara yin sallar juma'a, sannan aka ɗaura auren Khaleel
matsayinsa na babba, sai na Aysha da nata angon. Nan fa bakin kowa ya washe anata
gaisuwa musamman su babban Yaya Shareff da Maheer. Anguna kam ai ba'a magana.
Bakunansu har kunne ko gonar audiga albarka. Daga massallaci aka kwashi tawaga zuwa
hall ɗin da aka shirya walimar cin abinci ta iya mazan kawai kamar yanda su Daddyn
kanyi a duk aurarrakin ƴaƴansu.
Ana tsaka da cin abinci saƙo ya shigo masa. Shi dama ba abincin yakema ci ba,
yana charting ne da Anaam ta WhatsApp. Baibi takan saƙon ba ya fita da nufin rufe
datan sai Anaam ta sake turo massege, ya koma da nufin buɗewa ya gani hanunsa ya
buɗe wancan a mistake. Ganin videos da yawa ya bashi mamaki, sai yay tunanin shiga
ɗaya a ciki yaga minene. Gabansa yay wani irin faɗuwa sakamakon cin karo da Fadwa,
best ce sanye jikinta fara da dogon wando, kanta babu ɗan kwali, da sauri ya fito,
mikewa yay zai bar hall ɗin dan bai kamata ya gani a gaban wani ba. Ya fito sai ya
samu wasu a abokan Khaleel tsaye su kusan huɗu tsaye, da alama suma sun fitone
susha iska. Suka gaisheshi ya amsa musu da fara'a, harya gota su sai ya tsinkayi
muryar wani a cikinsu na faɗin,
“Tabb bala'i, Mubeen da'alama yau zamusha kallo a tiktok. Gasu Sufi nan sun
taɓo mutuniyarka Fady Babie”.
Wanda aka kira Mubeen yaja tsaki, “Shegiyar yarinyar nan ai su Sufi ɗinne dai-
dai da ita. Ƙawartace jiya taima Ɗan soja wani Comment ɗin rainin wayo shine fa yay
mata tatas ya kuma ce yanada video ɗinta da taje ɗakin wani guy, idan bata kama
kantaba ana gab da cin kasuwarta a tiktok, shine ita mai bakin akku Fadwan ta maida
murtani jiya da dare, ai shagalin nan ne yasa bakama luraba, tun jiya aka fara
faɗan har suna zasu ɗakkoma su M soja ƴan sanda, shine shi Sufi ɗin ya shiga
faɗan”.
“Oh dama haka akai, taɓɗi jan. Ai dama ina fatan naga wanda zai kawo ƙarshen
ƴan iskan yaran nan, musamman Fadwa ɗin nan ta cika ɗaukar kanta wata tsiya. Ƴar
iska tayi auren ma kamar batai ba”.
“Ai bazaka ganeba yarinyarce ta haɗu, wlhy da farko ban yarda bahausa bace
ƴar arewa. Irin zuƙaƙan matan nan ai dole suyi girman kai dan ALLAH ya basu. Idan
fa tai shigar ƙanan kaya kamar wata balarabiya”.
Dariya mai maganar farkon yayi, “Shege ka ƙyasa kenan, to tana dai da aure,
akwai wani room mate ɗina, ya rantsemin idan yaga yarinyar nan har hankalinsa tashi
yake, har saida takai sai ya dinga wassafata a ransa ya buƙatarsa ta biya yake
samun nutsuwa”.
A tare suka kwashe da dariya. ”Kai wlhy bashi kaɗaiba. Akwai lokacin datai
wani shegen shiga tabi waƙar mara mutuncin nan ranar jinai inama-inama, bara kaga
video ɗin ALLAH yasa bata gogesa ba.”
Jiyay kamar jiri na ɗibarsa. Amma kun san halin ƴan mazan sai ya dake ya nufi
samarin domin tabbatar da Fadwa ɗinsa ko wata. A hankali ya iso ta bayansu batare
da sun fargaba. Wanda aka kira Mubeen na nuna musu video da yake faɗa. Ba ƙaramin
tsinkewa zuciyarsa ta shigayi ba, dan ko'a magagin barci aka nuna masa video ɗin
zai shaida wacece a cikinsa. Da baya-baya ya dinga tafiya har ALLAH ya bashi ikon
jingina da motar dake kusa da shi, dai-dai nan Khaleel ya fito da babban abokinsa.
Cikin salo irin na abokai yake ƙundumoma abokan nasa zagin mi sukeyi anan. Ganin
basuma ko jisa ba ya karaso inda suke.
A firgice yace, “What!!?”.
Yana mai fisge wayar. Shi kansa zuciyarsa ce ta shiga tsitstsinkewa, idanunsa sun
gaza cigaba da kallon videon dan koba komai matar Yayansa ce. Yayan nasa kuma mai
tsananin kima da mutunci a idonsa....
“Kai lafiya kuwa?”.
Mubeen ya faɗa yana fisge wayarsa. Dariya sauran suka kwashe dashi. Anas yace, “Ka
sani ko shima ya shiga tarko ne. To ka rufa mana asiri an jima zamu kaika ga taka
wannan dai kwalelenk....”
Ai Khaleel baima san ya kaima Anas ɗin mari ba. Su duka suka zabura da waro
idanu. Khaleel ya nunasa a zafafe. “Ka iya bakinka Anas, kasan ɗin ita wacece a
wajena? To matar yayana ce, idan ƙazamin bakinka ya sake faɗar wata magana mara
daɗi zan fasashi”.
Sun tsorata ƙwarai da gaske da rikicewar tasa. Mubeen ya dubi Khaleel ɗin a
karo na farko cin son yin tunani. “Khaleel dan ALLAH kwantar da hankalinka. Wlhy
sai yanzu dakai maganar matar yayanka wani abu ya ɗan dawo min a zuciya. Tabbas
sanda ta ɗaura wani hoto nata tunanin a ina nasan mutumin, hakama da take daurasa
matsayin mijinta na jima ina son hasasowa amma sai na kasa. Saboda sau ɗaya na taɓa
ganin Yayan naka shima ba wani mun jima bane. Da gaske wannan shashashar yarinyar
ce matar Yayanka? Kasan kuwa wacece Fadwa a tiktok? A ɓangaren shaiɗanun tiktok da
a kullum ake ALLAH wadai da su da ganin sakacin duk wani na kusa da su wlhy Fady na
sahun farko, dan ita a karan kanta mata uwar shaiɗanuce mai zaman kanta. Amma domin
tabbatarwa maza ka shiga shafin nata ka duba zakafi yarda dani dai”.
Gaba ɗaya Khaleel yayi mutuwar tsaye, dan kuwa tun fara maganar Mubeen
idanunsa suka hango masa Shareff dake tsaye alamar komai da suke yana jinsu. Shi a
karan kansa Khaleel ɗin baya tiktok, bawai dan yana kallon tiktok ɗin baida amfani
bane, a'a, a komai na rayuwa akwai mutanen banza a waje akwai na kirki. Shi bai
taɓa ƙalubalantar tiktok ba ko yima jama'ar dake mu'amulantarsa kuɗin goro. Ya
tabbata idan aka shiga tiktok za'aci karo da abubuwa masu amfani kamar yanda za'a
samu na banza marasa amfani. Kawai dai shima bamai ra'ayin yawan biye-biyen shafuka
bane kowanne iri. idan ma ya kama sai yabi abinda ya kaisa kawai yake zuwa yayi
saboda aikinsa na cimasa kaso mafi yawa na lokacinsa. Da sauri yabar inda su Mubeen
suke ya nufi Shareff daya shiga mota da alamar barin wajen zaiyi. Buɗewa yay ya
shiga gefensa.
“Please yaya k.....”
Hannu ya ɗaga masa alamar kar yace komai. “Ka gafarceni Yaya, ka bani to na
tuƙaka”. Bai sauraresa ba ya tada motar ya fice dasu da gudu. Duk magiyar da
Khaleel ke masa bai nuna yaji ko daya ba har suka iso gidansa cikin ƙanƙanin
lokaci. Tun a gate mai gadi ya sanar masa Fadwa ta fita ai tare da wata mata.
Reverse yayi, nanma Khaleel nata roƙonsa amma ya sharesa. Kai tsaye gidansu Fadwan
ya nufa, dan baiyi tunanin taje gidan bikin ba. Sai dai anan ɗin ma dai maigadi ya
sanar musu bataje ba, sai dai sunga hajiya ta fita zuwa gidan biki. Khaleel da
yasan ba saurarenaa zaiyiba yace, “Bara mu bincika ko tana can gidanmu din”. Bai
tankaba nan ma. Khaleel kuma bai fasa kiranba. Cikin sa'a ya samu Amrah, ita ya
tambaya ko Fadwa na gidan ta sanar masa eh tazo gashi ma ana rigima tsakanin Gwaggo
Halima da wasu dangin Mommy. Amma ga su Abba sun dawo gida yanzun nan....

Gudun da yay a yanzu yamafi na farko, dan cikin ƙanƙanin lokaci suka iso nan
gidansu, sai dai sun sami rigima ta ɓarke sosai tsakanin Mommy da danginta, da kuma
Gwaggo Halima. Har Fadwa ta mari aunty Sakina saboda itama tace zata mari Gwaggo
Halima. Gida ya cakuɗe harda dambe, Mommy na faɗin Shareff yazo sai ya saki Fadwa a
yau, Gwaggo Halima na iƙirarin itama sai Daddy ya saki Mommy a yau. Ran Daddy yakai
ƙololuwar ɓaci a yau shi da Mahaifin Fadwa daya biyosu gidan domin yima su Mommy
murnar an ɗaura aure. Hajiya Luba mahaifiyar Bibah itace ta fara ganin Shareff. Ta
nufesa tana kuka bayan ta gwargwaɗa ma Mommy cewar ga Shareff nan. Isowar Mommy
inda Shareff ɗin yake tana rantsuwar in bai saki Fadwa ba zata tsine masa Daddy ya
dakatar da ita, sai dai kafin ya faɗi abinda yay niyar faɗa Abie ya dakatar da shi.
“Please yaya karka ce komai dan ALLAH, inaga ya kamata a zauna dasu ko yaya
asan dalilin wannan tashin hankali. Ba'a gyara ɓarna da ɓarna na roƙeka”.
Da ƙyar Daddy ya saurari Abie a wannan gaɓar, Gwaggo da dama haka takeso tai
murmushi, sai kuma tai saurin nufosu tana matsar ƙwalla. “Ni wannan fitina ta
wannan yara ta isheni Muhammadu, gaskiya an shiga tsakanin Nafi da Halima dan da
dai ba haka sukeba. Yara kansu haɗe kamar uwa ɗaya uba ɗaya ta haifesu amma yanzu
komai ya canja.....”
“Kinga Gwaggo kiyi haƙuri komai zai daidaita insha ALLAHU, inaga ku mu shiga
can tunda nan da mutane.”

Gwaggo ce da kanta ta tattara su Gwaggo Halima zuwa gidan Abie, shi kuma
Abie ya saka su Shareff da gaba ɗaya yama rasa abinyi gaba. Sai da kowa ya hallara
har mahaifin Fadwa da su Baba Ibrahim dana duk wani mai faɗa aji a falon kasancewar
duk dangi na gidan, maza sun taso a wajen ɗaurin aure, matan kuma duk suna a cikin
gida. Ran baba Ibrahim a ɓace ya dinga zagin su Mommy a yau dan shikam halinsu ya
fara kaishi maƙoshi. Fitina daga wannan sai wannan kamar sune kaɗai mata a cikin
family ɗin.
Hayaniya na neman ɓarkewa ya daka musu tsawa, amma sukaƙi saurarensa.
Daddy da dama a wuya yake kai tsaye ya buga musu tsawar da tafi ta baba Ibrahim.
“Tabbas a wannan gaɓar na gaji da halinki Nafisa. Kije na sakeki saki ɗaya”. (biyu
kenan😲😱).
Lokaci ɗaya falon yay tsitt tamkar ruwa ya cinye kowa. Gwaggo da tafi kowa
firgita dan ita Gwaggo Halima take burin ganin an saka ta waro idanu, “A'a
Muhammadu bakai gaskiya ba, yo ai ba Nafi ta cancanci saki ba Halima ce, ko kuwa
dan ita ƴar uwarkace shiyyasa. To wlhy yanda ka saki Nafi kaima Sadiqu sai ka saki
Halima in har na isa da kai matsayin ƙanwar uwarka”.
Hajiya Luba ta fashe da kuka. “Gaskiyafa Gwaggo, Halima ita ta cancanci
saki kodan baƙin halinta ita da ƴarta.....”
Saukar mari Hajiya luba taji a kuncinta tauu, kafin ta dawo hayyacinta Gwaggo
Halima ta sake sauke mata wani. “Babbar magana kenan”. Cewar Gwaggo tana miƙewa.
“Halima shine zaki mareta dan ta faɗi gaskiya, to idan Mustapha da Sadiqu sun
sakeku ba dan an saki Nafi ai dole su sakeku dan zubarda ciki da Fadwa taima
Mustapha...........✍

😆😆Kai jama'a ALLAH ka rabamu dayin amai ka lashe kayanka dai.

_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_
_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:


07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇


09134848107

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*


[11/23, 10:17 PM] My Zafafa: *_Typing📲_*

*_BABU SO....!!_*
_(Miya kawo kishi?)_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718

*_77_*

........Kaɗan ya rage zuciyar Fadwa yin tsale ta fito, jikinta na rawa tace, “Wlhy
ƙaryane, munafukar tsohuwa da bazataga MANZON ALLAH ba”.
Saukar mari taji lafiyayye daga Mahaifinta. Gwaggo ta jinjina kanta cike da jin
daɗi, “Nagode Sadiqu. Ba laifinta bane uwace bata moraba. Yo dama yaushe Halima
taga wata tarbiyya balle ta bata. Ai bakai dace da mata ba wlhy”.
Cikin matuƙar mamaki su Daddy suke kallo da sauraran Gwaggo da alamu suka nuna
akwai suɓutar baki a kalamanta. Gwaggo Halima zatai magana Alhaji Sadiq ya dakatar
da ita. “Wlhy kikace tak sai kinyi nadama Halima...”
“Barta tace in ma tanada abin cewar mana. Dan kuwa inada ƙwaƙwaran hujjar ita
ta zubar da cikinta da kanta, saboda karya hanata waɗan nan raye-rayeda sukeyi na
zamani a wannan abubuwan da kuke kira yanar gizo-gizo ko uwar mima. K Luba kiramin
Bibah ta shigo da likitan da ta saka yaymata aikin. Amma kafin sannan fara latso
min ita a wayarki su gani”.
Cikin rawar ɓutiya Hajiya Luba ta latso Fadwa a tiktok ta miƙama Baba Ibrahim
dake a tsakkiyar Daddy da Abie, sai Baban Fadwa a gefen Daddy, Abba kuma na gefen
Abie. Wani video ne na rashin mutunci da aka ɗauka a ranar kamun Fadwa. Ana gobe
ɗaurin aurenta da Shareff kenan. Kayan barcine jikinta riga fingila iyakarta
cinyarta amma ta kusa gwiwa, sai gashinta dake a buɗe tama warwaresa akan kafada. A
yanda taketa komanta kai tsaye da farko na rawar wata wakar turanci zaka san bata
san ana dauka ba. Sai a kusan ƙarshe-karshe take kare jikinta da filo data ɗauka
tana masifar miyasa zatai mata video, sai dai anyi cutting sunan wadda ta ambata na
mata video ɗin. Bayan shi akwai wasu daban-daban na rashin mutunci, abindama zai
baka mamaki kamar an tsinto iya wanda tayi abin ALLAH wadai ɗinne kawai an ɗora a
shafin. Hatta wayarsu ta ranar daurin aure da Shareff duk akwai a wajen, duk wani
faɗa datai da wani a tiktok ko rawar banza cikin shigar wofi duk sune aka tato aka
ɗaura. Harda ma wanda bata kai tiktok ɗin ba
Komai ya ƙara tsayama Shareff cak, bama shi kaɗaiba hatta sauran jama'ar
falon gaba ɗaya. Kafin wani ya samu damar tofa tasa sai ga Bibah da likitan daya
zubdama Fadwa ciki. Harga ALLAH tayi matuƙar firgita. Zuciyarta ta dinga
tsitstsinkewa lokacin da Gwaggo ke faɗa masa ya faɗi miye alaƙarsa da Fadwa. Kansa
tsaye babu fargabar komai saboda an toshe bakinsa da kuɗi ya fara bayani tiryan-
tiryan tun zuwan su Fadwa da ƙawayenta Sima da Amal. Baice akwai Bibah da Siyyah
ba. Sai yanzu ne Fadwa ta samu damar fashewa da kuka.
“Wlhy wlhy ba haka akaiba. Bibah kiji tsoron ALLAH, dan kina son auren mijina
basai kin ƙullamin sharri ba.....”
“Sharri kuma. Idan sharri nake miki aiga wayarki a hanunki a amsa a duba
agani”.
Duk da Fadwa tasan duk waɗancan videos ɗin tayisu amma ta goge mafi yawa a ciki
saita bada wayar tata, saboda sanin masu dama-damar ne kawai a shafin nata na
yanzun. Baba Ibrahim ne ya amshi wayar, sai dai koda aka duba babu wani accaunt
akai sai irin wanda Bibah ta nuna.
“To'ai babu banbanci tsakanin wannan da wanda ke anan ciki”.
Ba karamin ruɗewa Fadwa tai ba. Harta fisgi wayar a hanun Baba Ibrahim batare da
tasan tayi ba. Koda ta duba itama sai taci karo da abinda suke maganarne kawai
babuma accaunt ɗinta data sani akan wayarta kwata-kwata. Mamaki da tsoro suka
risketa. Takai dubanta ga Bibah sai ta samu tana murmushi, hakan ya bata tabbacin
itace tai komai. Wata irin wawuyar mikewa tai ta shaƙi Bibah, nan take kokawa ta
kacame Bibah ta fara kakarin mutuwa. Da ƙyar Maheer ya rabasu shi da su Aunty
Bintu.
“Shareff idan baka saki Fadwa ba wlhy wlhy wlhy har abada babu ni babu kai.
Yanzu nan ka saketa, dan baka taɓa rayuwa da wadda ta zubar maka ciki ba dan son
zuciyarta, sannan ballagaza.”
Shareff da gaba ɗaya brain da Heartbeat ɗinsa sun tsaya cak daga aiki, ya dago
yana kallon Mommy.” “Ba kallona nace kayiba saketa nace, idan kuma bazaka saketaba
to wlhy zan......”
“Haba Nafisa kinada hankali kuwa, ki tsaya abi komai a sannu mana”.
“Yaya daina wani maganar a sannu, ai tunda Ubansa ya sakeni wlhy shima sai ya
saki Fadwa. Dan na tabbatar abinda na aikata bai kama kafar abinda taiba. Itafa
ciki ta zubar masa”. Kafin ma Baba Ibrahim yace wani Shareff da dake cikin
matsanancin fushi ya furta “Na saketa saki biyu”.
Tamkar saukar aradu Fadwa taji saukar wannan kalma. Tai baya ta zube ƙasa,
ihu take son yi amma ta kasa yi tsabar yanda falon ke juya mata tana ganib bibbiyu,
da sauri ta rarrafa gaban Shareff.
“Soulmate dan girman ALLAH ka saurareni, wlhy ba.....”
Wani irin hankaɗata yay tai baya ta zube har kanta na buguwa da kujera sai da
Abba ya tareta. “Wlhy idan kika sake koda matsoni zan iya shaƙeki ki mutu,
ballagaza. ALLAH ya isa ban yafe miki zubarmin da ciki ba, na tsaneki, na tsaneki,
bana buƙatar sake ganin mummunar fuskarki a rayuwata har abada. Idan har zaki iya
salwantar da ƙyautar da ALLAH ya bamu, abinda ke amsa suna gudan jininki to zaki
iya halakani nima, na tabbata zaki iya kasheni saboda cikar burinki. Kin wulaƙanta
aure na, kin nunama duniya ke ɗin baki da tarbiya, har wasu banzaye najin wani abu
akanki saboda kin nuna musu ke ballagaza ce. Anya Fadwa kinada ilimin addini kuwa?
Anya kin san darajar kanki kuwa? Anya kina tuna zaki mutu kuwa?, na godema ALLAH ma
da ban haihu da ke ba, dan bana fatan ƴaƴana su taso su kalleki matsayin mahaifiya
balle har halayenki su zama naso ga tasu rayuwar. ALLAH ya wadaran mace irinki mai
tara ƙawaye da bata da ra'ayin kanta sai nasu, kije ƙawayen naki su cigaba da baki
rayuwar da kike buƙata, kije, kije bana son ganinki wlhy”. Idanunsa har tara ƙwalla
suke na tsananin ɓacin rai, Shareff nada kishi matuƙa akan duk abinda yakeji ya
killace matsayin nashi. Yanzu haka yanajin kamar zuciyarsa zata tsage, babu abinda
ke masa amsa kuwwa sai zantukan samarin ɗazun a kanta. Wata muguwar shaƙa ya kai
mata jijiyoyin kansa na matuƙar tashi. “Fadwa na tsaneki, bazan yafe miki ba.....”
da ƙyar su Abie suka ƙwace Fadwa a hanunsa, sai numfashi take fiddawa da ƙyar na
wahala ga Gwaggo Halima na ihu da kururuwar kuka zai kashe mata yarinya. Kansa ya
kife a jikin Abie dake kusa da shi, yana mai ƙoƙarin danne hawayensa. Abie ya shiga
shafa kan nasa cikin lallashi tausayinsa na ratsashi. Ba Abie kaɗai ba kowama yaji
tausayin Shareff ɗin dan abune mai matuƙar ciwo ga duk namijin daya san ciwon kasa.
Su kansu sunajin raɗaɗi a zukatansu matsayin iyaye, mahaifinta kam ma ai ya kasa ko
motsi dan gaba ɗaya ya tattara laifin a kansa shima, zuciyarsa suka take matuƙa a
ƙirjinsa...........”
*_“Tabbs da ace kayi haƙuri saki bashi bane mafita Yaya MM”._*
Kusan gaba ɗaya suka waiwaya a inda sautin maganar ta fito. Anaam ce sanye da
hijjab har ƙasa. a kallo ɗaya zaka fahimci a barci ta tashi ma. Kuma yanayinta yana
nuni da batajin daɗi....
“Ke kuma a wa, kajimin ƴar iskar yarinya. To ko ubanki Usman da uwarku basu
isaba balle ke haihuwar yau”.
“Badan na isa bane na faɗa Mommy, ba kuma dan iyayena nada wani kusanci da
zama masu isa a wannan Family ɗin ba. Sai dan kusan gaskiya ku daina dukan jaki
kuna barin taiki (ALLAH yasa na faɗi hausar tawa dai-dai). Tabbas Fadwa bata taɓa
ƙaunataba. Kamar yanda Gwaggo Halima bata taɓa ƙaunar iyayena guda uku ba. Haka
kema baki taɓa ƙaunarsu ba. Kafin wata rana ina ganin laifinku matuƙa ina kuma jin
zafinku mai tsanani, sai dai lokaci ya saukaƙamun hakan sakamakon fahimtar kuma a
haka aka raini zukatanku. Zan faɗi gaskiyane a yanzu ma badan ku soni ni da
iyayena ba, sai dan ku sani wadda ta raineku ku kanku ba ƙaunarku take ba bawai
iyayena ne kawai take ƙi ɗinba. Lallai da sanin Fadwa aka zubar da cikin jikinta,
sai dai kuma Gwaggo itace ta tsara komai da taimakon momyn Bibah, su Bibah
ƙawayenta su huɗu suka ɗarata a hanya har komai ya faru.....”
Wani irin harziƙowa Hajiya Luba tayi, amma sai Baba Ibrahim ya dakata mata
wata irin razananniyar tsawa. Komawa tai ta zauna daɓar. Anaam tai murmushi mai
ciwo da dafe karfen benen takai zaune saboda jiri da take gani. Sai da ta ɗan dafe
kanta na wasu sakkani sannan ta ɗago tana ɗan murmushi. “Kuyi haƙuri.” Batare data
jira cewar wani ba ta cigaba da faɗin, “Ban faɗa muku wannan maganarba sai dana
riƙe hujja, kuma dama irin wannan ranar nake jira dan nasa duk yanda Maman Bibah da
Bibah zasuyi da Gwaggo sai sunyi domin Yaya MM ya auri Bibah, kuma Fadwa itace
kawai makaminsu da Mommy”. Ta ƙara maganar da miƙa wayarta dan bazata iya tasowa ba
saboda jiri. “Gashi komai na'a cikin nan. Ku kira Amrah ma kuji dan tasan abubuwa
da yawa itama”.
Aunty Bintu ce ta amso wayar, ta kaima Baba Ibrahim. Gwaggo ta miƙe a fusace
sai dai jikinta rawa yake. Amma sai Gwaggo Halima tasa ƙafa ta taɗota ta koma zaune
daɓar har tana sakin ƙarar azaba data ratsa ɗuwawunta. Sosai da mamaki mai cike da
ɗunbin razani suka bayyana a fuskokinsu Baba Ibrahim. Dan kuwa dai ga muryar Gwaggo
gata Hajiya Luba da Bibah. Su Mommy zasu fara hayaniya Baba Ibrahim ya hanasu,
cikin matuƙar razanarwa Baba Ibrahim yace Hajiya Luba ta faɗa kokuma ya ɗauka
mataki a kanta. Jikinta tsuma yakeyi, musamman da taga irin mugun kallon da Shareff
ke jifanta da dashi, wanda ba ita kaɗai ba, hatta Gwaggo haɗiyar yawu take da
ƙyar...
“Wlhy Yaya mu ba laifinmu bane, kawai dai Bibah ce ke tsananin son Shareff,
nayi-nayi Nafi ta fahimci abinda nake buƙata na mu haɗa aurensu taƙi, sai nunawa
takeyi da Fadwa za'a haɗa. Har nayi zuciya da hakan sai dai Bibah ta shiga damuwa,
shine nazoma Gwaggo da batun ko akwai yanda za'ayi, amma saita nunamin itama bata
san zancenba. Ban gajiba muka cigaba da binta har akai auren Fadwa da Shareff, sai
lokacinne ta fara saurarena, ta kuma tabbatar min idan har muka taimaka mata cikin
Fadwa ya zube zatai duk yanda zatai dan auren Shareff da Bibah ya yuwu”.
Salati falon ya ɗauka baki ɗaya, yayinda a lokaci guda Gwaggo Halima da Mommy
suka kaima Gwaggo shaƙa, da ƙyar aka ɓanɓareta a hanunsu idanunta har sun firfito
waje kamar na tsohon kwarto. Nan fa sabuwar hayaniya ta kaure har wani baijin
zancen wani, dan Fadwa kam tuni ta turmushe Bibah tana jibga, itama uwarta Hajiya
Luba ta turmushe Fadwan. Ƙurace sosai ta tashi a falon, wadda ta saka Anaam ji
kamar duniyar na juya mata. Cikin sa'a Shareff ya hangota tana jujjuya kanta. Da
sauri ya miƙe yay inda take, cak ya dauketa ya koma saman da ita tana faman jujjuya
masa kanta, Mamie da itama ta hangosu tai saurin bin bayansa dan ita kam ma ba
komai take fahimtaba a abinda ke faruwa a falon.
Faɗa sosai ya kaure, duk yanda su Abba sukaso kwantar da abun ya gagara, dan
tun anayi a falo har aka koma tsakar gida, kafin kice mi ƴan biki sun fara
tururuwar shigowa bama idonsu abinci tunda dama akwai ƙofar dake a tsakanin gidajen
wadda basai kaje gate ba. Cirko-cirko mutane sukai sunajin fallasa da tonon asirin
da su Mommy sukema juna, yayinda Gwaggo ke neman naɗe tabarmar kunya da hauka. Sai
dai fa ganin lamarin yafi ƙarfinta dan hatta Mommy yau la'antarta take ga ƴan biki
sai ta nema fita a gidan tana kuka wai su Daddy sun shirya wulaƙantata. Nanfa wasu
a munafukai masu son jin ba'asi suka take mata baya, sai dai taƙi sauraren kowa,
tana gab da barin layin nasu wani mai mota ya shawo kwana, duk da horn da yakeyi
sam Gwaggo daketa faman sambatu da surutai batajisa ba, shi kuma ALLAH ya hanashi
damar taka birki, ya kwasheta sama ya direma kasa, yana son riƙe kan motar ina
saida taya ɗaya ta dirza ƙafar Gwaggo har ana iya jin karar farfashewar ƙashi. Tun
ƙarar azaba ta farko data saki bata sake fahimtar ina take ba ta suma. Dan danan
aka rufu kanta, har su Daddy labari yazo musu sun fito, nan fa layin ya cika
dankam. Matasa zasu rufu kan mai mota da ƴan biki yazo dauka baba Ibrahim ya
dakatar da su. Kamalarsa da dattakon kasancewarsa tsohon arziƙi ya sakasu bin
umarni, sai dai an kama Gwaggo da babu alamar numfashi a jikinta an saka a motar
mutumin aka nufi asibiti.
Babu ko tausayi a fuskar Gwaggo Halima, sai ma faffaɗar magana take wai ai
ƙarshen Gwaggo kenan. ALLAH ma ya kara sakata a masifa fiye da hakan. Mafi yawan
mutane maganganun Gwaggo haliman basu ɓata ransu ba, sai dai duk da mugun halinta
baban Fadwa ya kasa haƙuri shima a wajen ya yanke igiyar auren Gwaggo halima biyu.
Ai sai lokacin Fadwa da Mommy suka sake tunawa da mutuwar nasu auren fa suma. Nan
guri ya kara daukar zafi faɗa ya dawo sabo fil da ƴar koke-koke abin zakkunya da
takaici...........✍

_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_


*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾


ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:


07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇


09134848107

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*


[11/24, 11:03 AM] My Zafafa: *_Typing📲_*

*_BABU SO....!!_*
_(Miya kawo kishi?)_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718

*_78_*

.........Wannan harmutsi da dangin mijin Aysha suka tarar yasa suka dakatar da
ɗaukar amarya, acewarsu ai basu san haka uwar amaryar da danginta suke ba.
Ƙololuwar tashin hankali Mommy ta sake shiga, har takai ta yanke jiki ta faɗi itama
dai sai da aka kaita asibitin. Gwaggo halima dake dariyar mugunta ta tafi gida
ranta fes Mommy da Gwaggo a bala'i, sai dai kuma mahaifin Fadwa ya hana mata koda
shiga gate, yace Fadwa kaɗai ce ƴarsa, itama zai bata mafakane har tai idda saboda
karya salwantar da rayuwarta a cigaba da samun bara gurbi a cikin al'ummar
musulmai. Amma ta sani bazata taɓa jin daɗi ko ɗigon farin ciki a gidansa ba.
Rikicewa Gwaggo Halima tayi, kamar yanda Fadwa dake kuka rirus dama dan da ƙyar
Gwaggo Halima ta jawota suka tahonan saboda ido rufe take neman Shareff amma taƙi
ganinsa. Masu aiki yasa suka shigo da ita, Gwaggo Halima kuma ya tabbatarma masu
gadi ko hanunta ya taɓa masa gate abakin aikinsu. A karan farko itama ta fara kuka,
dan a zatonta koda yay sakin guda biyu zai haƙura ya barta ta cigaba da zama cikin
ƴaƴanta har a sasanta. Sanin da yay mata zata iya ƙin nufar gida ya sakashi turata
a mota da kansa yaja motar ya maidata gidan su Daddy da tuni ƴan biki sun fara
watsewa, ba kowa na ɓangaren Mommy. Na ɓangaren Mom kuwa da dangin su Daddy zama
daram wasuma shirin tafiya dinner ɗin Khaleel da amaryarsa suke. Dan su Hajiyar
Sudan sun shiryama wannan biki kwarai da gaske....

Komai ya hargitse, komai ya rikice. Burin Gwaggo na watsa biki wani yankinsa
ya tabbata. Domin kuwa akan bigire na duk tsuntsun da yaja ruwa shi ruwa kan doka
ake. Ita dake amsa matsayin suna uwar daba tana can asibiti ƙafa a ragargaje batama
san inda kanta yake ba likitoci sun rufu akanta. Manyan dodannin fadarta su Mommy
sun masifar tsanarta fiye da rayukansu a yanzu. Dan kuwa Mommyn da kowa kema kallo
matsayin ƴarta da zata iya zama magajiya a gareta na kwance bisa gadon asibiti
jininta yay ƙololuwar hawa har yana son zarce abinda ba'a fata. Tana da saki guda
biyu a kanta, igiya daya ce kacal ta rage mata a yanzu, kuma Daddy ya tabbatar musu
daga asibiti su wuce da ita karta sake dawo masa gida. A daren daga gidan angon
Aysha takardar saki ta iso a cewar iyayen ango ɗansu bazai rayu da ƴar mace ba.
Wannan al'amari yayi matuƙar ƙona zuciyar su Daddy har Abie na tabbatarwa sai ya
kaisu kotu, da ƙyar su Abba suka lallashesa. Gwaggo halima data ɗauki Gwaggo tamkar
uwarta mahaifiya a yanzu babu wanda tafi tsana a duniya sama da Gwaggo, a sanadinta
ɗiyarta mafi soyuwa a gareta ta rasa ciki ta rasa aurenta, ita a karan kanta ta
rabu da ƴan uwanta shekara aru-aru a dalilin huɗuba ko muce tarbiyyar Gwaggo. Ta
rasa igiyoyin aurenta da ƴaƴanta a cikin abinda bai gaza awa shidda da barinta
gidan mijinta cike da fatin ciki ba.
Yayinda Aysha itama ke can tana rusar kuka tamkar ranta zai fita, dan kuwa ta
tabbatar alhakin mahaifiyarta da kakartane ke bibiyar ƙaddararta, a ranar da aka
ɗaura mata aure a ranar miji ya saketa ko gidansa ba'a kaita ba. mijin data ɓata
tsahon shekaru tana mutuwar so da ƙauna.
Haka zalika Fadwa celeb.... Wadda ke ganin ko ta tashi a rayuwar da ita a
karan kanta bata taɓa gundurartaba balle kallonta a juye. Shareff shine dukkanin
farin cikin duniyarta, da sonsa ta rayu da shi ta horu, a rana ɗaya dalilin
makircin ƙawayen data ɗauka babu yasu a duniyarta da cigabanta ta rasashi. Auren
mahaifiyarta da aka ƙulla tsahon shekara talatin yau ya girgiza shima a dalilin
wadda suke kallo gunkiyarsu da bayan horon tarbiyya ga uwarsu suma akan zaren
tarbiyyar tata suka horu.....
Shareff da komai ya ƙwace masa a wannan gaɓar tunaninsa yama rasa ina zai
kama ko samun mafaka, sai dai ya jure, ya danne wajen tattare hankalinsa kan
matarsa da jikinta yay ruɗewar da daren sai da Dr Jamal yazo ya sanya mata
ruwa...., ya kuma saka Fharhan a daren kaima su Sima, Siyyah, Amal, Bibah ƴan
sanda suka cafkesu, tare da doctor ɗin dayay aikin.
Abba, Daddy, Abie, aunty Mimi. Mamakin Gwaggo da ɗunbin al'ajabinta ya hana
zukatansu bugawar gaggawa a ƙirazansu. Sun rasa wane aji na duniya ya kamata sunan
Gwaggo ya fita, dan a iya hasashensu sun gagara kama minene dalilinta na duk aikata
waɗannan abubuwan?. Kenan akwai abubuwan da suka shuɗe da yawa a baya dake buƙatar
nazari mai faɗi da neman ba'asin dalilin aikatashi ko ganinsa a aikace. Sunyi ta
mazan bin su Baba Ibrahim asibiti, inda har dare ya raba suka dawo gida babu wani
bayani akan jikin Gwaggon likitoci dai sun rufu a kanta sunata faman kaikawo....

*_WASHE GARI_*.

Sai a yau asabar zuri'ar MD Shareff suka sami ganin Gwaggo, sun fara
shiga ɗakin da aka kwantar da Mommy itama bisa matsawar Abie suka dubata, inda acan
suka sami Shareff da Maheer tare da ita. Basu jimaba suka fito, Mommy da abubuwa da
yawa ke cin ranta musamman sakinta da Daddy yayi ta taso ta biyosu, duk yanda su
Shareff sukaso dakatar da ita taƙi yarda da hakan. Hankalinsu ya tashi da ganin
jikin Gwaggo, dan ƙafarta tayi wani irin mahaukacin kumbura daya ninka jikinta
biyu, gashi an yanketa daga gwiwa zuwa ƙasa dan can ɗin yayi ragargajewar da bazai
ƙara aiki ba. Sai kananun ciwuka da ba'a rasa ba. Da ƙyar take iya amsa musu, sai
dai abin mamaki idonta a soye babu ko alamar hawaye. Bayan sun jajanta da ɗaukar
kusan mintuna goma sha biyar a ɗakin sukai haramar tafiya. Muryarta a ɗashe, amma
hakan bai hanata fita da kaushi ba ta dakatar da su...
“Na rikeku na muku gata fiye da uwar data haifeku, amma a dalilin kanƙanin
abu kuke nuna alamun juyamin baya Muhammadu. Bazan hanaku ba, sai dai ku sani bazan
yafe muku wahalar dana sha a kanku ba”.
“Bakece zaki ƙi yafe mana ba, mune bazamu taɓa yafe miki ba Hindatu...”
Muryar Gwaggo Halima ta ratsa kunnuwansu a bazata. Su dukansu suka juya suna
kallonta da mamaki, dan kuwa babu lallashin da basu mata ba danta biyosu tace
bazata ba. Ta cigaba da takowa firingau-firingau dan a kwana ɗaya duk ta sususce ta
fita a hayyacinta tamkar ba halima ƴar gata ba. Ta ƙaraso gaban Gwaggo tana mai
share hawayenta. “Hindatu kamar yanda na faɗa mune bazamu yafe mikiba annamimiya
azzaluma. Musamman ni nan Halima. Hakama iyayenmu dake kwance a cikin kabari, da
sunada damar da zasuyi magana sautin yaje cikin kunnuwanki da sun nanata miki
kalmar ALLAH ya isa fiye da sau dubu. Kinga wannan ƙafar taki da aka yanke, ba
itace kaɗai ƙarshen azabar da zakisha a duniya ba. Yanzu kika fara gani, bayan
ɗanɗanar ɗacin rashin haihuwa na shekaru sama da sittin da kikai a duniya, yanzu
zaki cigaba da fuskantar raɗaɗin azaba ne mai muni tsinanniyar tsohuwa mai zubin
ƴan wuta.......”
“Ke ce dai mai zubin ƴan wuta...”
Cewar Mommy a hasale. Dariya Gwaggo Halima ta sanya. “Ke kumafa? Maza je kiji da
kanki shasha kawai. Hawan jini da zawarci ma sun ishi rayuwarki ƴar wahala, sannan
kema a gurinta baki tsira ba”.
“Hahaha garama ni, kuma koba komai zuwa yanzu na tabbatar miki Shareff jinina
ne tunda gaki a zawarci ƴarki a zawarci. Kuma yanda ya saki Fadwa itama Anaam sai
ya saketa dan bazai zauna da zuri'ar waɗanda basu san hallaciba. Ƴar dukiyar da
akaga ya tara akemawa to babu mai cinta har kai uban nasa”.
A karan farko Daddy ya ɗago yana kallon Mommy, amma sai kafin yace wani
abu Abba ya cafe murya a kausashe.
“Mu bamu kasance marasa halacciba Nafisa. Wannan tsohuwar dake da kika rayu a
gidanmu matsayin agola kune marasa halacci, kuma dukiya da kike takama Shareff ya
tara bara na buɗe muku zancen yau, kaso biyu bisa ukun abinda kuke ganin Shareff ya
tara na Usman ne.......”
“Please Yaya Abubakar ba wannan gaɓar mukeba...”
Abie yay niyyar katse Abba. Amma sai Abban ya fisge jikinsa. “Barni Usman, gara
wannan mahaukaciyar tasan ANNABI ya faku. Duk da ƙulle-ƙulle datai domin ganin ta
raba tsakaninku da Usman hakan bai hana ka cigaba da tallafa rayuwarsa ba, har take
iƙirari da fariyyar dukiyar ɗanta. ki shiga hankalinki kuma kisan mikikeyi, daga ke
har uwar taki, sakamako kuma yanzu kuka fara girba, dan wlhy Gwaggo alhakin
iyayenmu kaɗai bazai barki sake jin daɗi ko farin cikin rayuwa ba. Tur da masu irin
halinki na annamimanci da hana zaman lafiya a cikin zuri'a. ALLAH zai saka mana
matuƙar sakayya a ranar da gaɓoɓi zasuyi magana madadin bakuna”.
Tuni Mommy da kanta ke bada wani yuuuu na haurawar jininta sama ta dafe gadon
da Gwaggo ke kwance. Kallon Shareff take cike da son ƙarin bayani. Lips ɗinta na
rawa. Kansa ya jinjina mata tun kafin tace komai. “Mommy abinda Abba ya faɗa shine
gaskiyar magana. Dukiyar Abie ce ni nawa basu wice kudin siyan ruwa ba a cikin
taron biki”.
Wata irin ƙara Mommy ta saki da faduwa ƙasa daɓar, Gwaggo ma tuni gadon da
take a kai ya fara jijjigar shiga a tashin hankali. A halin da take ciki da dukkan
ƙarfin halin nata Shareff ɗin shine kawai gadararta a yanzu, dan ko maganar aikin
da ake faɗar za'ai mata na ƙafarta ta gama sawa a ranta ko kowa ya gujeta suna da
Shareff ai. Ashe-ashe abinda sukema gadarar ma ba nasu bane. Da tasan haka bazata
taɓa yarda taima su Abba hakaba. Da ta cigaba da musu fuskarta ta tun ƙuruciya.
Amma yanzu ta tabbatar bakin alƙalami ya rigada ya bushe kuma....
Cikin ƙanƙanin lokaci duk sukai waje, hatta Shareff da Maheer ji sukai bazasu
iya zama ba, dan dama tsananin kunyar su Daddy sukeji saboda abin kunyar da kakarsu
ta jima tana tafkawa da mahaifiyarsu duk da kuwa akwai Gwaggo Halima tare da
su......

_________★

Kwanaki sun cigaba da shuɗawa, ta tabbata dai Gwaggo Halima ta dawo gida da
zama, dole ta share sashen Baba Umar da babu wanda yasan a duniyar da yake yanzu ta
zauna. Mommy kuma ta koma gidan Baba Ibrahim kamar yanda ya shardanta mata, dan ya
hana su Shareff bata wajen zaman da sukai niyya. Yayinda Gwaggo ke cigaba da jiyya
mai wahalarwa a asibiti. Dan kuwa babu wani mai jiyyarta sai Nurse's dake kula da
ita. Mommy din ma data raina da kanta tace bazata iya jiyyarta ba dan ƙafar tata
duk da likitanci na kula da ita wari takeyi matuƙa. Su Daddy basuyi butulci ba tare
da su Baba Ibrahim da mahaifin Fadwa ke biyan kuɗin zamanta a asibitin. Hakama
Fadwa na gidansu, mahaifinta ya amshe wayarta, ya kuma kwashe dukan ƴan aikin gidan
yanzu itace ke komai ga ƙanenta, girki, gyaran gida, ya baza camaras tako ina, inma
bataiba ko baya gidan zai gani, hakama waya kota ƴan uwanta ta ɗauka da nufin kiran
wani itama tasan sauran. Duk ta fige ta fita a hayyacinta saboda kuka da tsananin
ƙulafucin mijinta da takeyi, ga Gwaggo Halima ta mata nisa yanzu, ƙanenta kuwa sai
zuba mata rashin kunya sukeyi tunda dama a haka suka taso na ƙasa baya girmama na
sama da shi. Satinsa uku a gidan maganar auren Babansu ya tashi da wata hamshaƙiyar
mace ƴar boko mai babban mukamin gwamnati a jihar ta kano...........✍

_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_


*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:


07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇


09134848107

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*


[11/24, 11:04 AM] My Zafafa: *_Typing📲_*

*_BABU SO....!!_*
_(Miya kawo kishi?)_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*
https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718

*_79_*

..........Yanda Fadwa ke jigatuwa a gidansu haka Mommy ke jigatuwa a gidan Baba


Ibrahim, dan kuwa matansa babu kanwar lasa a ciki. Basa raga mata koda da wasa.
Abinci kuwa iya abinda suka bata shine zataci, bata isa cewa tak ba Baba Ibrahim
zai silleta tass. Kaf ƴaƴanta an hanasu raɓarta har su Shareff kuwa. Itama duk ta
fige ta ruɗe da damuwa mai tsanani, ga rashin aure, ga rashin ƴaƴa, ga dukiyar ɗan
da take taƙama dashi ashe ta maƙiyintace. Kai ina itako zata saka kanta taji sanyi
wannan rayuwa haka.

Gwaggo Halima kam ai zamu iya cewa ta susuce a wannan gaɓar. Dan kuwa
maganar auren mijin nata ya risketa dan abune da aketa faman watsasa a gidajen
talabijin da rediyoyi. Bikine ake shiryawa na hamshaƙai biyu masu daidaiton ƙwarya
tabi ƙwarya. Ga rashin ƴayanta tare da ita, dan kuwa itama dai su Abba sun ƙwace
wayoyinta, sun kuma kafa mata sharadin inhar tana buƙatar zama da su sai ta nutsu,
inba hakaba zata bar musu gida, dan yanda sukayi haƙuri da ita a baya a yanzu kam
bazasuyi ba.

Kwanan su Sima takwas a police station aka shiga kotu, dan duk magiya da
roƙo da iyayensu ke ma Shareff ya rantse sai sunyi shari'a. Kasancewar laifinsu a
bayyane yake ba'awani wahalar da shari'a ba a zama biyu kacal aka yanke musu
hukuncin zama gidan yari na watanni goma shaɗa. Tare da tara mai tsoka. Kafin kace
mi media ta ɗauka, babu abinda ke trending kamar labarinsu. Manyan yaran da akeji
dasu a tiktok da istagram dama mafi yawan kafafen yanar ta gizo sunsha ɗauri a
dalilin shugabarsu. Ga labarin mutuwar auren Fadwa ya zama kamar wani abin izgili a
bakunan wanda suke jin haushinta. Sai dai wasu hakan ya sanyaya musu jiki matuka.
Dan inhar haka zata kasance ga Fadwa suma ɗin basu tsiraba kenan tunda duk iri aiki
guda sukeyi, wasu ma nasu yafi nata muni matuƙa. A take wasu suka fara goge wasu
videos na rashin tarbiyya dake a shafukansu, wanda kuwa ke kai musu ji suke yanzu
aka fara wasan ma. (Ya rabbi ka shirya mana zuriya damu baki ɗaya😭🙏🏻)

Kwanan Anaam goma sha biyar a gidan Shareff ya dauka matarsa suka koma gidansu,
dan ta ɗanji daɗin jikinta. Sai dai an sama mata mai aiki tare kuma da Aysha suka
koma can dan itama tana cikin kunci da damuwa abin tausayi, dan ma Anaam ɗin na
tsaye a kanta wajen ganin ta sakama ranta salama da daukar komai matsayin
jarabawa.. Komawarsu gidansu da sati guda su Abie suka koma, dan Abie yayi iya
koƙarinsa na ganin komai ya daidaita amma hakan yaci tura, ya zube kuɗi masu tsoka
na kula da Gwaggo a asibiti ya tattara iyalansa da su Aunty Mimi suka koma
Malaysia, inda suka bar Anaam na faman kuka sai da Shareff yayta lallashi...

★★★

Zuwa yanzu abubuwa da yawa sun ɗan lafa ba kamar da ba, Anaam da Shareff sun
buɗe sabon babin soyayya mai tsayawa a rai, mantawa suke da kowa da komai suna
kallon kansu tamkar su kaɗaine a faɗin duniyar kawai. Tun Aysha da mai aiki najin
kunya har da suka saba da gani. Dan kuwa dai tare da Shareff ake rainon cikin Anaam
ɗin. Tana da sauƙin laulayi, abinda kawai bata so hayaniya. Inhar waje ya cika
hayaniya yanzu zata jangwaɓe babu lafiya. Hakan yasa babu inda take zuwa sai bayan
sati uku zuwa huɗu ya kaita can gidansu ta yini. Gaba ɗaya ya tattara lamarin Fadwa
ya ajiye a gefe. Ko tunawa da ita ma baya sonyi balle jin sunanta. A dalilin ta yay
ma tiktok tsana mai tsanani, dan zuciyarsa na ayyana masa duk wanda ke a wajen
mutumin banza ne irinta. (Sai da Shareff da sauran ƴan uwa ba haka bane. A yanda
muke kallon tiktok ba hakan bane. Shima dai dandaline tamkar kowane dandali na
media. akwai na ƙwarai akwai bara gurbi. Kawai dai a komai bara gurbi sun fi saurin
yin shura a idon al'ummarmu ne da yaɗuwa. Kuma ita yanar gizo tamkar kasuwa take,
abinda kai niyyar shiga ka saya shine zaka nema kuma ka samu. Dan haka tiktok akwai
mutanen kirki a cikinsa masu yaɗa abubuwan alkairi saɓanin tunaninmu na musu kuɗin
goro. Fatanmu matan aure irinsu Fadwa da suka tsunduma rayuwarsu a waɗannan hanyoyu
ALLAH ya shiryesu. Hakama ƴammatanmu da basuyi aurenba ALLAH ya shiryesu ya basu
mazaje na gari, hakama zawarawa da samarinmu baki ɗaya).

Watanni kusan huɗu da faruwar komai aka sake ɗaura auren Aysha da Dr Jamal,
sai dai su Abie basu zoba sun dai saka albarka. Hakama Daddy ya haramtawa dangin
Mommy zuwa bikin har ita kanta Mommy din. Tako ci kuka mai zafafa zuciya, har
tanajin inama bata biyema Gwaggo ba da ayanzu haka tana nan an dawo da ita gida.
Sai dai kasancewar babu inda zata zauna a gidan baba Ibrahim aka haɗasu ɗaki ɗaya
da Mommy. Ko kallonta Mommy batayi, balle ta taimaketa koda da bada magani ne.
Kullum cikin mata ALLAH ya isa takeyi. Kaf dangi an rasa mai jinyarta, dan kuwa dai
ƙafarta da gaske ta ruɓe, a yanzu hakama ana shirin gundile har cinyar data ragene
saboda imfection ya shiga.

Zuwa yanzu cikin Anaam watanni bakwai ne ciff, hakama matar Maheer an gamu,
dan shima dai ya kwantar da hankalinsa zuwa yanzu ya rungumi matarsa. Matar Khaleel
ma dai nada cikinta ɗan wattani uku. Haka amaren suka cigaba da rainon ciki
musamman Anaam dake a gaɓar gangara. Shareff dai na shan shagwaɓa matuƙa. Dan kuwa
kun san mutuniyar taku da raki. Ga kuma cikin daya fara tsufa yana yawan sakata a
saurin fushi, hatta da mai aikinta taka tsantsan takeyi. kullum cikin rigimar ita a
Malaysia zata haihu take. Su Abie da Shareff nata lallashinta, acewarsu suma sun
kusa dawowa Nigeria. Haka dai akaita rarrafawa har ALLAH yasa aka shiga watan
haihuwa da ƙyar. Dole fa badan yaso ba Anaam ɗin ta koma gaban Mom ta cikagaba da
kula da ita ana jiran naƙuda. Shareff ma sai ya haɗa kayansa ya koma can gidan
shima. Dan kuwa dai nan ɗin ya masa daɗi shi kaɗai, yana matuƙar jin kewar ƴar
darun tasa.
A daren wani alhamis ta farka da naƙuda mai tsanani, babu shiri suka nufi
asibiti a daren. Sai dai fa tun ana jiran haihuwa har al'amarin yaci tura aka yanke
shawarar za'a mata cs kamar yanda Dr Bilkisu ta basu shawara, dan ta tabbatar musu
jikin Anaam baida ƙwari za'a iya zamun matsala gaskiya. Dole Daddy ne ya saka hannu
da Shareff kwata-kwata baya a hayyacinsa. Yana can maƙale da Anaam tana kuka yana
rungume da ita. Anyi-anyi ya bar ɗakin haihuwar amma yaƙi, dan shi gani yake daya
gusa zai iya rasata.
Alhamdulillahi zuwa ƙarfe ɗayan rana aka samu nasarar zaro mata ƴar babynta mai
kama da ita kamar tayi kaki ta ajiye. Kowa na murnar ɗaukar Baby shi baban baby
hankalinsa nakan uwar baby. Dan bai samu nutsuwar ganin ƴar tasa ba sai da aka miƙa
Anaam ɗakin hutawa, ya tabbatar ta ambaci sunansa cikin mayen barci sannan ya samu
nutsuwa. Cikin ƙanƙanin lokaci hoton babby ya zagaye dangi har ƴan malaysia, zo
kaga murna wajen Abie da Mamie tamkar zuyi tsuntsuwa su ganzu a 9ja kawai. Dangi
tako ina shigowa suke asibitin, harda dangin Mommy waɗanda ma ba'ai zaton gani ba.
Shareff dai na nane da natarsa harta farka, ya rungumeta yana mai sanya
mata albarka da tarin godiya. Bata da ƙarfin rungumarsa. Amma tana maijin daɗin
addu'oin da yaketa zuba mata da albarka. Ya sumbaci lips ɗinta suna mai kallon juna
da murmushi. Ƴar babyn ya ɗakko saitin fuskarta yana nuna mata, ta kai hanunta
saman kan yarinyar a hankali ta shafa, tare da sumbatar goshinta hawaye na silalo
mata. Ita Anaam itace da baby a hannu mallakinta, ita kaɗai iyayenta suka haifa
babu wa babu ƙani, yau sai gata da gudan jininta kuma. A hankali ta furta “I love
you Yaya MM”. Cak ya tsaya daga sumbatar babyn da yakeyi, ya tsura mata idanunsa da
ke nuna tsantsar rauni da jin kalmar a bazata. Tunda suke tare bata taɓa furta masa
ba. Kai duk soyayyar da yake ambata yana mata bata taɓa nuna ta damu ba balle ta
karɓa masa. Tana dai ƙyautata masa da kuma shagala a tare da shi a duk sanda shi
yake jadada tasa soyayyar a gareta harta bada gudunmawar maida murtani....
“Dan ALLAH ki maimaita Noorie, danna tabbatar ba mafarki nake ba”.
“Ba mafarki kake ba Yaya MM. kanwarka na tsananin ƙaunarka, kamar yanda ka rayu
da sonta haka itama ta girma da soyayyarka, sai dai wani nauyayan dalilai sun
matuƙar ɓoye hakan a zahiri. Kai kaɗai zuciyata ta taɓa so Yaya Al-Mustapha, bayan
kai kuma bazan taɓa son wani ba, ina fatan na zame maka mata har a gidan aljanna.
ALLAH yasa mu mutu tare...”
Ta ƙare maganar hawaye na ziraro mata. Hanunsa dana baby da batasan sunaiba
tanata baircinta ya haɗa waje guda ya share mata hawaye. sannan ya rungumeta yana
mai jera mata tari-tarin kwandunan godiya marasa adadi, tare da sake jadada mata
ɗunbin ƙaunarta dake ratsa jininsa da ɓarko a kowanne bugawar cikar sautin sakan na
agogo, “Na gode da waɗan nan kalami masu tsada tsadar tsada. Kece mace ɗaya tilo
dana fara so, bazan taɓa iya jera sonki dana wata ba har abada.”
A hankali Fadwa dake tsaye bakin ƙofa taja hanun ƙanwarta suka koma da baya.
Dama Daddynsu ne yazo da su suyi barka su kuma duba Anaam ɗin. Shi yana can tare da
su Daddy a waje akace su su shigo, shine tai gamo da wannan al'amari. Kuka take
rurus zuciyarta na mata raɗaɗi da zafi, tasan ko iya haka aka tsaya Anaam tayi
winning a kanta. Shareff kuma ya mata nisa, nisan irin wanda sama kema ƙasa. Duk
wanda ya ganta dole ya tausaya mata, dan tana a cikin tsananin ciwo na so da har ya
haifar mata da ciwo a zuciya. Tana tsananin son Shareff har bata san iyaka ba. A
ƙarshe wannan rana sai a asibiti ta kwana magashiyyan.

Washe gari su Mamie suka iso, nan fa sabuwar murna ta tashi, Baby taga ƙauna
a wannan ranar dan kamar za'a cinyeta. Har faɗa ake tsakanin Abie da Mamie wajen
ɗauka. Da wannan ya amsa sai ɗayan ya kwace, dole dai aka koma ƴar minti bayan
minti. Anaam da Shareff nata faman musu dariya. Kwananta biyar a asibitin aka
sallamesu suka koma gida. Kai tsaye wajen Mamienta aka wuce da ita. Inda suka samu
ana shirya gagarumin bikin suna da yafi na bikin aure. Dan kuwa su Abie sunce anan
zasu fanshe.........✍

_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_


*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:


07040727902
IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇
09134848107

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*


[11/24, 9:19 PM] My Zafafa: *_Typing📲_*

*_BABU SO....!!_*
_(Miya kawo kishi?)_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718

*_80_*

...........Ranar suna yarinya taci suna *_Ai'shatul-Humairah_* ataƙaice anma Mamie


takwara dai. Kowa yaji matuƙar daɗin karar da Shareff ya nuna. Shiko yace yayine
saboda Mamie uwace a garesa da bazai taɓa mantawaba. Mommy haihuwarsa kawai tayi,
amma badan ALLAH yasosa da rahamar komawa hanun Abie da Mamie ba da yanzu bama asan
yaya rayuwarsa take ba. Ga kawunsu nan Umar har kowama ya manta da shi a cikin
zuri'arau.
Tabbas burin su Abie ya cika wajen haɗa gagarumin taron suna daya sake
tabbatarma da duniya wanene Abie ɗin. Ashe duk wani waiwai da akeji a bayan kan
dukiyarsa abin ya zarce hakan. A ranar ya mallaka company ɗin dake hanun Shareff ga
Anaam ɗin da Shareff halak malak, sannan ya ajiye wata gagarumar ƙyauta ga jaririya
Aysha Humairah data girgiza kowa a wajen taron nan. Dan Mommy gaba ɗaya neman
susucewa tayi saboda ta halarta itama bisa jagorancin Baba Ibrahim. Gwaggo Halima
kanta a ranar jikinta ya ida yin sanyi da lamarin Abie. Dama gata a firgice da
ganin Amaryar Baban Su Fadwa da a yaune suka fara ganin juna. Da kuwa sai dai ta
ganta a television. Taci kuka matuƙa kamar yanda Mommy itama taci nata. Fadwa kam
dama dai batazo ba. Amma hakan bai hanata gani a wayoyin mutane dama television da
aka nunaba har a NTA. Itama dai ranar batai kwanan lafiya ba, dan kyarshe dai sai
dama aka bar ƙasar da ita a washe gari saboda ciwonta yay matuƙar tashi fiye da ko
yaushe. Hakanne ya sake birkita Gwaggo Halima ta koma kamar ƙaramar mahaukaciya.
Abin tausayi abin dariya.
Amaryar jego da angon jego kam sun sha ƙyau har sun gaji, dan kuwa kallo
guda zakai musu kasan naira tayi kuka. Sati biyu dayin suna su Abie suka ɗauke
Anaam sai malaysia. Shareff bai soba amma haka ya dake ya daurema ransa. Abinda ya
ɗan ƙara sauƙaƙa masa zuciya ganin Mommy ta matuƙar sakkowa a yanzu, sai dai
bayajin daɗin zagin da ake mata a dangi game da watsar da Gwaggo dake a cikin
mawuyacin hali. Dan anyi aikin ƙafar an guntule, yayinda likitoci suka gano kuma
tana ɗauke da kansar jini bayan ciwon zuciya mai tsanani. Kullum cikin kuka take na
rashin samun haihuwa, dan kuwa rashin kulawa daga Mommy na matuƙar caccakar
ruhinta. Ga ƴan uwa kuwa dama babu ta inda bata zama fitilar sharri data haska kowa
ba. dan haka kowa ɗin gudunta yakeyi, tunda ma wadda ta riƙa tamkar ƴarta ta gujeta
waye zai tsaya. Su dama ƴaƴan Baba Ibrahim da matansa basu zurfafaba. Iyaka su basu
abinci su koma gefe, dan hatta Mommy mai lafiyar ma ba daɗin zaman gidan takeji ba
sam. Sai dai babu yanda zatayi tunda nan dinnne kawai da ita ai. Idan tace zata
barsa ina zataje. Da kunya dai ta koma gidan ƴaƴa ta zauna. Ita da Gwaggo Halima
kam gaba sai abinda yay gaba. To take jerama Gwaggo ma ALLAH ya isa dake matsayin
uwa gareta balle bare.

Watannin Anaam biyu Shareff ya kasa haƙuri yay shiri yabi bayansu. Babu zato
ko sanin zuwansa kawai sai gashi, a lokacin Anaam na falo zaune tana shayar da
Muhseenah. Haka suke kiran babyn dashi. Mamie na gefenta tana gyara mata dan har
yanzu bata iya komai yanda ya kamata ba. Abie na daga tsaye a ƙafar upstairs yana
musu dariya dan Anaam ɗin na darune wai ita yarinyar ta cika ci ita kuma ta gaji.
Sallamar Shareff ta sakasu kallon ƙofar kusan lokaci ɗaya, sai dai kowanne
zuciyarsa taƙi gaskatawa sam. Abie ne yay ta maza yaje ya buɗe ƙofar. Ya waro
idanunsa sosai da faɗin, “Son! Kai ne ɗin dai da gaske?”.
Murmushi Shareff yayi idanunsa a ƙasa, zai rissina domin gaisheshi Abie ya
jawosa jikinsa ya rungume. “Ja'iri ka manta gaban Abie ɗinka kake?”.
Murmushi yayi dajin ƙaunar Abie ɗin matuƙa. Suka ƙarasa cikin falon inda
suka iske Mamie riƙe da Baby Muhseenah da Anaam ta manna mata ta gudu sama tun jin
Abie ya Ambaci sunan Shareff. Cike da jin nauyi da kunya ya ƙaraso gaban Mamie ya
durƙusa. Mamie dake murmushi tace, “Oh oh Babana miye haka. Tashi mana ni bana son
wannan sinne sinnen kan, ko baka iyayen damune yanzun ka ɗauka wani babi daban
kuma?”.
Da sauri ya girgiza kansa. Mamie tace, “Ato gara dai ka gyara kafin mu fara
fushi da hakan”. Ta kare maganar da miƙa masa Baby. Gani yay ta ƙara masa girma da
wayo, wataninta uku kenan a duniya, kamaninta da Anaam ya sake bayyana matuƙa.
Abubuwa ƙalilanne nasa ta kwaso. Ya rungumeta a ƙirjinsa yana maijin sonta da
ƙaunarta ta musamman, kafin ya kai lips dinsa ya sumbaci goshinta yana mai
ambaton , “ALLAH yay miki albarka NoorulAyn”.
“Amin ya rabbi”. Abie dake ta bayansa batare daya sani ba ya amsa masa. Ji yay
duk kunya ta lulluɓe sa. Amma tuni Abie ya kaudata ta hanyar zama kusa da shi. Dai-
dai nan Mamie ma ta dawo ɗauke da tray tana murmushi....

Duk yanda yaso ganin gimbiyar tasa taƙi bashi daman hakan. dan ƙiri-ƙiri taje
ɗaki ta ɓoye abinta, har yaci abinci ya gama bata fito ba. Mai aiki ta kammala
gyara masa ɗakinsa dake gidan ya shiga domin watsa ruwa ya ɗan huta. Sai dai kuma
hakan ya gagara. Wankan kawai ya iya yi ya fito cikin sanɗa. Sai da ya tabbatar su
Abie basa a falon yay wuff sama ɗakin Anaam..
Tana kwance rigingine ta kifa Muhseenah a saman cikinta waya manne a
kunnenta, yanda taketa faman murmushi zai baka tabbacin wayar na sakata nishaɗi.
Dan ko motsin shigowarsa ma bataji ba. Ɗakin yana a yanda ya sanshi, komai na
cikinsa kalar da tafi so da ƙauna. Tsaf cikin ƙamshi. Sai dai an samu ƙarin wasu
abubuwa na Muhseenah. A ɗan zabure ta buɗe idanunta dake lumshe jin an ɗaga
yarinyar daga jikinta, cikin ido suka kalla juna, ta lumshe nata tare da ƙoƙarin
kaudasu gefe tana sallama da Aysha da suke wayar, wadda itama take faman da
laulayin ciki a yanzun. Kwance ya kai kusa da ita shima tare da ɗaura Muhseenah a
saman cikinsa kamar yanda ya samesu. Tai ƙoƙarin tashi ya jawota jikinsa.
“Kai Yaya”.
“Shiiii!!. Ni kikema wulaƙanci ko?”.
Baki ta tura gaba, “Ni wulaƙancin mina maka?”.
“To fushi ne?”.
Tai ƙoƙarin janye jikinta ya hana hakan, sai ta fara masa kukan ƙarya. murmushi
yayi da sauke Muhseenah gefe ya rungumeta jikinsa da ƙyau har sai da ta saki ƴar
ƙara, kafin ta sami damar cewa wani abu ya manne lips ɗinsu waje guda ta yanda
abinda take son faɗa bai sami damar fita ba. Tun tana masa bori harta amsa ɗari
bisa ɗari. Sai da suka cakuɗa junansu matuƙa tafiya zatai nisa Baby Muhseenah ta
fara kuka. Da ƙyar ya iya raba jikinsu ya ɗauketa. Ya lakace mata hanci da sumbatar
goshinta cikin furzar da numfashi. “Mamana am sorry laifin mamanki ne fa”. Yay
maganar yana kallon Anaam. Hararsa ta ɗanyi da juya musu baya. Yay murmushi. Itama
dai koda ta juya ɗin murmushin takeyi, ƙaunarsa na sake ratsa mata dukkan jijiya da
ɓargon jiki. Sai da ya tabbatar Muhseenah ta koma barci sannan ya sake kwantar da
ita ya kwanto jikin Anaam da duk tana jinsu, a tare suka saki ajiyar zuciya.
“Kazo lafiya?”.
“Baki so sanin hakan ba ai”.
“To amma Yaya zakazo koka sanar min, sai kawai na ganka kamar daga sama?”.
“Dama idan mutum zaizo gidansu sai ya shelantama duniya zaizo?. Noorie na na
kasa haƙurine kewarku ta isheni ALLAH”.
“Ni ban yarda ba”.
“Sai na nuna a aikace kenan?”.
Da sauri ta zabura dan tasan ina ya dosa. Ya fara dariya yana maidata ya matse.
“Kefa na fahimci matsoraciya ce ALLAH”.
“Ai tsoro halak ne kuwa, ina zan iya da kai da wannan yankan a jikina. Nifa ba
ruwana yanzu an daina wannan dani kaje ka dawo da Fad....”
Ganin fuskarsa ta tsuke lokaci ɗaya ta haɗiye sauran maganar. Ƙoƙarin janye
jikinsa yay a nata ta sake lafe masa. “Miye kuma na tsuke fuskar? ALLAH ko ƙyau
bakayi”.
Muryarsa a ɗan tsaurare yana mai kallon tsakiyar ƙwayar idonta. “Idan ina tare
dake bana buƙatar maganar wata, inba hakaba zan hukuntaki”.
“Am sorry sir, baza'a sake ba ok”.
Ta faɗa tana mai sakar masa kiss a ƙirjinsa. Dole ya saki ajiyar zuciya da sake
ƙanƙameta tsam dan dauriya kawai yakeyi. Cikin kunnenta ya raɗa mata, “Zaki rakani
wani waje?”.
Itama a hankali tace, “Ina kenan?”.
“Ba'a faɗa ai”.
“Mu cema su Abie mi?”.
Cikin tsakkiyar ido yake kallonta yana murmushi. “Zaki raka mijinki mana”. Sosai ta
waro masa Raunanannun idanunta dake cikin gilashi. “Tab badani ba wannan ta'asar”.
Murmushi yayi mai bayyana haƙora sosai, “Shikenan sai muyi zamanmu anan
ɗakin kawai to”.
“Kamar ya?”.
“Kamar yanda kikaji mana. Kina nufin zan iya cigaba da haƙurin nesanta kaina da
zumata. Ina kewar garden matuƙa autar mata”.
Sosai maganar ta bata kunya, ta cusa kanta a ƙirjinsa. “Ni dai babu ruwana
ALLAH”.
“Shiyyasa naga kina maƙaleni”.
Turesa ta farayi yana riƙota suna dariya. “Wasa nake Sarauniya. Ai ke Ustazah ce na
sani babu ruwanki, Mamana ma fa a ruwan gidanmu kika shata”.
Dariya takeyi sosai da kai mata ƙananun duka yana ƙoƙarin riƙe hanun shima yana
dariya. Haka suka kasance a cikin ɗakin tare cikin farin ciki mara misaltuwa har
sai da akai kiran sallar magrib. Koda ya fito suka haɗu da Abie sai yayta sinne
kai. Shiko Abie yay tamkar baima fahimcesa ba. Atare sukai dinner cike da farin
cikin. Muhseenah na jikin Abie. Anaam da Shareff sai faman zinguran ƙafan juna
sukeyi ta ƙasan table. Daga Mamie har Abie na lure da su sai dai babu wanda ya nuna
ya gani ɗin har aka kammala. Falo suka dawo aka buɗe sabon babin hira cike da farin
ciki irin na kammaluwar family. Anaam ce ta fara guduwa dan ita bata iya doguwar
hira ba, Mamie ma ta ɗauka Muhseenah dan tai mata shirin barci tabar Abie da
Shareff. Sun ƙara ɗaukar lokaci suna hira kafin su tashi suma.
Duk yanda yaso yin barci sai ya kasa, haka yayta juye-juye cikin tausayama
kansa. Ya kira Anaam kuma bata ɗagaba, yasan tayi barci dan ita kasa ce bata
jimirin doguwar hira. Kasa jurewa yay ya miƙe ya fita, gidan shiru alamar kowa yayi
barci, ɗakin Anaam ya shige cikin sanɗa. Tuni kuwa tayi barci abinta, bayan ya
shafa kan Muhseenah dake barci cikin ɗan gadonta ya haye gadon tare da ɗage
lallausan duvet ɗin da take ciki ya shige abinsa. A jikinsa ya nutsata yana mai
sauke ajiyar zuciya, itako da bata san yanai ba tuni ta gyara kwanciya da sake
shigewa jikinsa. Sake ƙanƙameta yay yana maijin nutsuwa na saukar masa. A ransa kam
yana godiya ga UBANGIJI ne daya mallaka masa wannan halittar daya girma da sonta da
ƙaunarta mara misali a zuciya da ruhi, yana fatan su tabbata tare har ƙarshen
numfashi batare da wani gagarumin saɓani da zai taɓa zuciya ba.........✍

😝ALLAH yasa su Mamie suyi kamu🚴🏼🤣.


_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_


*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:


07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇


09134848107

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*

[11/25, 12:11 PM] My Zafafa: *_Typing📲_*

*_BABU SO....!!_*
_(Miya kawo kishi?)_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718
*_81_*

.........Da asuba yay wuf ya koma nasa ɗakin, lokacin da Abie ya sakko ƙasan har
yayi shirin massallaci suka fita tare. Koda suka dawo anan falo suka zauna shi da
Abie suna tattauna abinda ya shafi company har gari yay haske.
Mamie na Kitchen tare da mai aiki suna haɗa breakfast Anaam ta fito. Da ga
Shareff har Abie kallonta suke da murmushi, ta miƙama Abie Muhseenah da itama akai
mata gayu tanata zuba ƙamshi kamar uwar tata.
Abie dake murmushi ya lakace hancin Muhseenah. “To ni dai baza'a ɗauka
hankalina da wannan kwalliyar ba. Matata ma ƴar gaye ce”.
Dariya Anaam da Shareff dake satar kallon juna sukayi, kafin Anaam takai zaune
tana gaishesu. Ganin mayataccen kallon da Shareff ke binta da shi ƙasa-ƙasa ya sata
barin wajen tana ɗan masa hararar wasa. Kitchen ta nufa wajen su Mamie ta cigaba da
tayasu itama.

Yauma kamar jiya tare sukai breakfast gaba ɗaya, kamar yanda Shareff ya kasa
daina satar kallon Anaam haka itama ta kasa daina satar kallon nasa. Yauma dai
iyayen nasu na lure da su. Dan haka suna kammalawa sun koma falo Abie ya maida
hankalinsa ga Shareff. “Babana akwai aikin da zan turaka Indonesia kuwa, ni naso
wucewa a yau sai kuma wata ta tasomin anan ɗin, kaga zuwan naka yamun daɗi ai, dan
haka sai ku shirya zuwa dare insha ALLAH zaku wuce na kammala muku komai”.
Gaba ɗaya Shareff ya daburce, dan kuwa abinda zuciyarsa ke raya masa Abie ya
gama harbo jirginsa ne. Kafin ya samu damar yin wata magana Abie ya miƙa masa file
ɗin hanunsa. “Duk abinda zaka buƙaci sani yana anan. Sai ku fara shiri ni yanzu
zanje ana jirana....
Anaam dai kanta a ƙasa dan itama ta tsargu, daga ƙarshe ma tashi tai tabar
wajen kawai, tana mai jin cewa Shareff ya gama da ita kawai. (🙄kamar ba haka take
so ba dama😆)

★★Kamar yanda Abie ya faɗa a wannan dare suka wuce Indonesia, basai an tona
irin farin cikin da suka tsinta kansu ba a ciki game da wannan tafiya, domin kuwa
abin yazo musu ne tamkar wani gift da baka san mizaka gani a ciki ba. Ba wani kaya
suka ɗiba ba, dan bama su san adadin kwanakin da zasuyi ba. Shareff na ɗauke da
Muhseenah a kafaɗa Anaam na gefensa cikin abaya blue datai mata matuƙar ƙyau. Sai
ƙaramin trolley da kayan Muhseenah sukafi yawa a ciki a hanunta. Dolene su burgeka
domin kuwa sunyi matuƙar dacewa da juna.
Sun sami tarba ta mutuntawa ga wanda Abie ya tura musu, ya kwashesu zuwa
masauki na musamman. Gidane madaidaici da komai na more rayuwa akwai a cikinsa.
Komai tsaf fiye da yanda suke buƙata, hatta da abincin da zasuci an ajiye. Bayan
wanda ya ɗakkosun ya gama nuna musu tsarin gidan yay musu sallama ya wuce. Shareff
ya rungumo Anaam yana murmushi. “Yarinyar nan Abie ya riga ya harbo jirginki
shiyyasa ya turomu nan”.
“Ya dai harbo jirginka Yaya, zaka ƙala mun ni salihar nan dani”.
Ta faɗa tana mintsininsa da dariya. Dariyar shima yakeyi da kaiwa zaune ya ɗaurata
a cinyarsa. “Su saliha anji jiki fa, ALLAH har naji kunya kamar daga nan na gudu da
ku Nigeria kawai”.
“Kaga sai Mamie da Abie su ƙara yarda bakajin magana”.
Kai ya dungure mata da faɗin, “Bama ji dai”.
Ta ƙyalƙyale da dariya tana mai ɗanewa saman jikinsa. Shima dariyar yake tayata
da sake ƙanƙameta. Da ƙyar ya iya haƙurin sukaci abinci sukai wanka.
Tana zaune tana shayar da Muhseenah ya tasasu gaba yana kallo da murmushi.
Birgesa suke matuƙa, ji yake kamar ya haɗasu ya haɗiye kawai ko zaiji sassaucin
ɗunbin so da kaunar da yake musu. Ɗagowa Anaam tai cikin ɗan waro ido. “Oga karka
saka ta ƙware mana”. Idanun nasa ya kauda yana mai sakin wani tattausan murmushi.
Ta zunguresa da ƙafa kaɗan, ya sake ɗagowa yana kallonsu. “ALLAH murmushi namaka
masifar ƙyau Yaya MM. Amma baka sonyi”.
Wani murmushin ya sake saki yana mai girgiza kai, ya ɗan juya idanunsa dake
kallon tsakkiyar nata cikin wani salo mai nuna tsantsar ƙaunarta dake ransa. “Indai
ke kina gani ai ya wadatar basai kowama ya gani ba *_bugun zuciya_*”.
Murmushi ta saki itama da gyara Muhseenah datai barci. Fahimtar bazatace
komaiba ya sashi amsar Muhseenah ɗin daga hanunta, shine ya kwantar da ita tare da
mata addu'ar barci. Ya ɗago bayan tayi barci dai-dai Anaam na shirin barci, igiyar
rigar barcin da take shirin ɗaurewa ya riƙe. Ta kallesa kai a langaɓe tana marmar
da idanu. Matsota yake a hanakali yana mai narkar da nasa idanun cikin nata, harya
haɗe jikinsu waje guda. A tare suka sauke ajiyar zuciya, cikin salon shagaltar da
ita ya zame rigar saman tai ƙasa ta faɗi, zatai magana ya ɗagata cak zuwa kan gadon
yana mai manne lips ɗinsu waje guda. Dole ta haɗiye maganar ta amshe mijinta hannu
bibbiyu cike da kewa da tsoron abinda zai iya biyo baya ita dake da ƴar laɓuɓuwar
yarinya (😂😂kuji gulmammiyar yarinya fa).

Wannan dare ya kasance wani dare ne na musamman a cikin darare masu nisan
zango. Dan kuwa Anaam da Shareff sun tabbatar ma juna suna kewar junansu mara
iyaka. Muhseenah ce kawai ke taka musu birki idan sukai nisa. Washe gari ma tare
suka yini manne da juna sai ƴar ɗiyarsu sanyin idaniyarsu. Babu mai damunsu koda a
waya ne. Zuwa dare suka ɗan fita shan coffee.
Sai da suka kwana uku suna hutawarsu ana huɗu Shareff ya samu ganawa da wanda
Abie ya turosa wajensa. A ranar suka gama komai da shi, ya kira Abie ya sanar masa
an gama komai zasu taho gobe. Sai Abie yace suyi zamansu har sai garin ya ishesu
dan kansu. Tabb ba'ace suyiba ma sunyi inaga an basu dama. Lokacine da suka kirashi
na gwangwaje juna fiye da wanda suka riska a baya. Dan kuwa sabon babin Honeymoon
aka buɗe tsakanin waɗan nan ma'aurata dake jin tamkar su haɗiye juna su huta. Basu
da wata damuwa saita bama junansu farin ciki, sai Shareff dakan ɗan taɓa ayyuka ta
system ɗinsa a wasu lokutan. Watansu uku cirrr a ƙasar Indonesia kamar wasa, dan da
sunce zasu taho sai Abie yace su ƙara dai, sun zagaya wajaje da dama tare da yin
hotunan tarihi kala-kala. Zuwa yanzu baby Muhseenah ta ƙara ƙyau da girma. Dan har
zama anayi tayi ɓul-ɓul da ita abin sha'awa. Su Abie nata mamaki su kansu. Sati
biyu sukai anan Malaysia bayan sun je sunma Aunty Mimi sati guda itama suka nufo
Nigeria. Sun bar su Mamie da kewa mara misali, sai dai suma suna shirin zuwa
Nigeria ɗin bikin Amrah da Muzzaffar insha ALLAHU. Dan yanzu sun ƙulle abinsu suma
tunda Anaam ta kufce masa ya kama Amrah ya riƙe ram.
Tarba suka samu ta musamman ga zuri'arsu. Kowa sai nannan yake da su musamman
Muhseenah. Gwaggo Halima ce dai bata zafafa ba, tana daga gefe dan yanzu ta zama
sai a hankali, zaman gidan yay masifar isarta, badan bata samun komai ba, sai dan a
girman shekarunta ya wuce na zaman gida. Ga mijinta yana ƙoƙarin ɗarewa kujerar
mulki dan kowa na hasashen shine zai zama gwamna. A koda yaushe cikin nunasa akeyi
shi da amaryarsa ƴar ƙwalisa. Wannan kaɗai ya isa saka zuciyarta a ƙunci, balle ga
damuwar Fadwa da maimakon sauƙi kullum a cikin tashin hankali take, zuwa yanzu ita
da kanta ta yanke shawarar duƙawa gaban Shareff da Mommy da su Daddy akan su
tamaketa Fadwa ta koma ɗakinta koda ita bazata koma nata ba, Fadwa na cikin
mawuyacin hali na rashin Shareff, babanta kuma yayi alƙawarin bazai taɓa roƙa ko
tilasta Shareff maidataba sai in shine yay ra'ayin hakan a karan kansa. Kasancewar
saukar safe sukai zuwa dare suka nufi gidansu daya sha gyara, dama su kawai yake
jira da alama. Washe gari sukaje gaida Mommy aka kuma kai mata jikarta dan yanzu
Daddy ya basu damar zuwa suga mahaifiyarsu kamar yanda Baban su Fadwa ma ya barsu
zuwa ganin Gwaggo halima. Hakan duk ƙoƙarin Abie ne na ganin dai komai ya wuce.
Sosai tausayin Mommy ya kama Anaam, dan duk ta zube babu ƙibar nan tata, tayi duhu
sosai. A yanda ta tarbesu zai tabbatar maka ba Mommy ɗin da bace ba. Muhseenah kam
tasha gata a wajenta har da su goyo. Sun shiga sun duba Gwaggo dake kwance ana
faman jiyya. Tayi masifar tsotsewa a kwance, ɗakin da taken ko shiguwa bayayi
saboda warin fitsari da takeyi, masu kula da ita dasu Daddy sukasa aka samo suna
biyansu shi da su Abie sai sun gadama suke gyarata. Baba Ibrahim ba zama yakeba
shiyyasa, matansa kuma basayi basa faɗa masa abinda ke faruwa. Anaam har hawaye
tayi kasancewarta mutum mai tausayi, dan duk wanda yaga Gwaggo dolene ya tsarkake
sunan ALLAH mai rinjaye akan komai. Sai ya barka yay maka talala kaita aikata
tsiyatakun ka a ban ƙasa, randa ya shirya damƙarka kuwa hummm. Ga dai Gwaggo a
halin ha'ula na jiyya, da za'a bata zaɓin mutuwa ko rayuwa zata zaɓi mutuwar ko
zata huta akan wannan azabar da take a ciki. Sai dai mutuwarma ta zama mai tsada a
gareta dan taƙi zuwa kwata-kwata. Kullum cikin hawaye take idan ta tuna irin
rayuwar data taka a wannan duniyar, kishi ya rufe mata ido da raɗaɗin rashin samun
haihuwa ta cutar da matan mijinta, bata taɓa son su Daddy ba a ranta, kamar yanda
uwarsu ma ba sonta tai ba. Kawai dai lumbu-lumbu take mata, dan taso ace ta
tarwatsa rayuwar su Daddy ne kamar Umar, yanda itama bata haihu ba su Umma karsu
mora nasu ƴaƴan. Tsanar mahaifiyar su Abie kuwa ta ƙara ƙarfine a ranta saboda
tausayi da kullum mijinsu ke nunawa a kanta, sai take ganin ai yafi son bebiya ma a
kanta, dan bata damu yaso umman su Daddy ba ko karya sotan, ita dai kawai a sota
ita ɗaya. Sai dai kuma har yabar duniya da son bebiyan data tsana ɗin ya tafi,
shiyyasa tafi tsanar su Abie fiye da su Daddy. Babban burinta tarwatsa family din
MD Shareff gaba daya, su dinga tsanar juna da sukar juna ta yanda bazasu taɓa morar
kansu ba kamar yanda itama bata mora zama da shi ba tunda bata haihuba a wautarta,
sai dai hakan bata kasance ba da yake UBANGIJI shine mai zartar da hukunci akan
ƙaddarar kowa. Duk ƙoƙarin ka, duk walarka sai dai kayi a banza a wofi babu abinda
ka isa ka saka ko ka hana a karan kanka balle rayuwar waninka. Ba Gwaggo kaɗaiba,
duk wanda zai sakama ransa ganin bayan wani, ko taɗe rayuwar wani, ko ruguza
nasarar wani, ko baƙanta hasken fuskar wani, to ya tabbata shine zai dawwama cikin
rasa waɗan nan abubuwan a cikin nasa rayuwar, dan baka halicci wani ba baka isa
zartar da komai a kansa ba sai abinda ya kasance a ƙaddararsa. (ALLAH ka rabamu da
mummunar zuciya, ka nisantamu daga son kammu da son ruguza waninmu. Ka hanamu
nasarar cutar da kowa koda a lafazin bakine ko kallo da ido. Duk mai burin taɗemu a
rayuwa ALLAH ka zame mana garkuwa a tsakaninmu da shi. Ya rabbi ka wajabta tsoranka
a zukatanmu da soyayyar ANNABIN mu 🙏🏻😭).

Watansu guda da dawowa Anaam ta fara aiki a company, tana manne da mijinta a
ko'ina kenan gida da office. Da safe zasu miƙa Muhseenah wajan Mom, idan sun taso
su biya su ɗauketa. Aysha da matar Maheer sun haihu kusan lokaci guda, matar
Khaleel dama tun suna malaysia ita ta haihu. Ansha shagalin suna yanda ya kamata,
zuwa dare taro ya tashi lafiya kowa yana sanya albarka..........✍

_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_


*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾


ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:


07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇


09134848107

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*


[11/25, 12:11 PM] My Zafafa: *_Typing📲_*

*_BABU SO....!!_*
_(Miya kawo kishi?)_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718

*_82_*

.........Ranar wata alhamis dake dai-dai da saura kwana ɗaya cikar shekarar
Muhseenah ɗaya a duniya su Abie suka iso Nigeria domin halartar bikin Amrah da
angonta Muzzaffar. Anaam tayi farin ciki matuƙa, dan itace taje tarbarsu da Shareff
da Muhseenah. Anaam ce ke tuƙi Shareff na kusa da ita Muhseenah a cinyarsa. Sai
gwaranci take da tsalle-tsalle a jikinsa ita a dole zatai magana, sai dai kuma babu
abinda ta iya sai gunguni irin na alamar yaro mai son surutu. Babu baki amma tayi
ƙafa, dan kuwa tana tafiya sai dai bata gama nuna ba. Shareff dake dariyar son tura
masa biscuit da take a baki ya lakace mata hanci, “Mamana wai dole sai naci biscuit
ɗin nan ne?”.
Anaam dake ƙoƙarin ɗaukar titin airport tai dariya da ɗan juyowa ta kallesu ta
maida kanta. “Kunfi kusa ai, yanzu da nice da yanzu an fara ƙananun magana, da
zaka tsunkule hanun ai data barka ko”.
“Oh oh Noorie bana son zuga, Maman tawa zan tsunkula. To anƙi”.
Ya ƙare maganar da sumbatar Muhseenah a goshi, ita dai dariyarta take tana ƙara
mamuƙesa dan tsaye take a jikin nasa tsoronta karta faɗi. Anaam data cigaba da
tuƙinta batace komai ba ta taɓe baki. Shiko zaunar da Muhseenah yay. “Sweetheart
ɗina, idan kinga su Abie ki taka da ƙyau dan tun a airport ɗin nan nake son su san
kemafa kin faso munyi ƙafa”.
Anaam ta kwashe da dariya tana ɗan dukan steering. “Badai girin-girinba ALLAH,
kwaje wajen iyayi ku ci da ka”.
Shareff ya harareta, “Tufff bakinki ya sari kashi”.
Dariyarta ta cigaba dayi ita dai tana ƙoƙarin yin parking. Koda suka fito kai tsaye
wajen da zasu tarbesu suka nufa, kowa ya gansu sai sun baka sha'awa su da ƴar
ɗiyarsu.
Basufi zaman mintuna goma ba jirgin su Abie ya sauka, suka zuba idon dakon
fitowarsu. Shareff na hango su Abie ya sauke Muhseenah, mi Anaam zatai inba dariya
ba, ya dalla mata harara da kai mata mintsini ta kauce, su Mamie ɗinta ta nufa ta
rungumesu. Abie dake dariya yace, “Oh oh mamana bata girmaba har yanzu dai”. Fuska
ta ɓoye tana dariya, dai-dai nan Idon Abie yakai akan su Shareff. Mamie ya zungura
itama. A tare suka sanya dariya.
Mamie tace, “Ayya ana mana yanga da tafiya, to mungani duk da bata nuna ba”.
Shareff dake ƙarasowa yace, “Haba Mamie karki bamu kunya gaban ƴan
adawarmu”. Yay maganar da nuna Anaam. Dariya Abie da Mamie sukeyi, Anaam kuwa ta
taɓe baki da faɗin, “Waifa dole da tsiya-tsiya sai an nuna muku sun fara tafiya,
bayan basa iya taku goma zai sun faɗi”.
“Adai ringajin tsoron ALLAH hajjaju” Shareff ya faɗa yana harararta. Nanma
dai dariyar sukayi, Abie ya ɗauka Muhseenah yana ɗagata sama, saita sanya masa kuka
ita ƙiywa wajen Abbanta zata koma. Ya dungure mata kai, “Haba ƴar daru ni zakima
ƙiywa, to garama mu daidaita tun anan dan indai nine kinta ganina kenan daga yau”.
Mamie dake dariya tace, “Kaima kenan. Balleni kishiya”.
Cike da farin ciki suka bar airport ɗin, kamar koyaushe sun sami tarba ta
mutuntawa gasu Mom. Duk da dama dai Anaam ta shirya musu abinci na musamman a
wannan karon da kanta itama. Ranar duk yanda Shareff yaso lallaɓata su koma gida ƙi
tayi, dole ya barsu nan ya tafi shi kaɗai ya kwana cike da kewarsu. Dan yasan dai
ba sake ganinsu a gidan zaiyi ba sai kuma bayan biki. Hakan yasa shima ya tattaro
inasa-inasa washe gari ya dawo nan gida. Sam daga Anaam har Shareff basuyi waniyi
niyyar yima Muhseenah birthday ba, amma sai ga bazata gasu Mamie dan da alama da
shirinsu sukazo. Anko sha shagali mai ƙayartarwa, aka kuma sha hotuna masha ALLAHU.
Ranar sai da Gwaggo Halima tai hawaye, dan haka kawai taji tana taya Fadwa jaje
matuƙa. Mommy ma dai ba'a barta a baya ba sai da tazo, tunda tabar gidan wannan ne
karo na farko da tazo, duk da kuwa kullum cikin yima Daddy waya take da bashi
haƙuri kamar yanda Gwaggo Halima kema Daddyn su Fadwa. Da gaske sunyi laushi
kowacce burinta a yanzu ta koma gidan mijinta. Shareff kansa da su Maheer kullum
cikin bibiyar iyayen nasu suke, dan suna tausayawa Mommy sosai dake zaune a raɓe
duk da baba Ibrahim yaya yake a gareta uwa ɗaya uba ɗaya. itace kuma tace subi
umarnibsa na hanawa susai mata gida da yayi, tace zatai haƙuri ta zauna a gidan
nasa.
An shiga hidumar biki, dan dama dai aunty Mimi sun iso tuni suna Abuja ne
gidan yayan baban su Amrah ɗin. Suma sai juma'ar da akai birthday ɗin Muhseenah
suka ƙaraso kano, sai dai acan gidan mijinta daya siya shima suka yada zango. Sosai
biki ke bada citta, su Anaam ƙirjin biki babu zama ko ina sune. Bata da matsala da
Muhseenah tana wajen Mamie, dan haka ta sami damar yin komanta hankali kwance har
aka kammala biki amarya Amrah ta tare a gidanta da kowa keta sambarka.
Sai da Shareff yayma Anaam jan ido washe gari ta yarda suka koma gida. Sati
biyu da gama hidimar biki akai taron family. Duk wani da ake buƙata ya hallara. Tun
rabuwar Fadwa da Shareff sai yau ne suka haɗu da Anaam dama Shareff ɗin kansa, dan
ya toshe duk wata hanya da zata iya ganinsa kojin labarinsa. Duk ta rame tayi wani
irin sanyi. Anaam tayi kamar bata gantaba tanata ma Muhseenah data maƙale mata
wasa, dan kuwa dai yanzu a hanun su Momie take tama yaye kanta, dama Anaam ɗin ta
gaji sai hakan yay mata dai-dai. Fadwa ta tsira musu ido hawaye na silalo mata a
kumatu, ji take inama Muhseenah tata ce. Hankalinta bai sake tashi ba sai da
Shareff ya iso wajen. Yayi wani fresh da shi ga ƙiba da zama alhajin gaske da yayi,
sai ƙyalli yake cikin shadda irin ta jikin Anaam ɗin. ko kunya bai jiba ya ƙarasa
inda matarsa da ƴarsa suke. Duƙowa yay jikinta yana mai yima Muhseenah wasa tana
ɓangale masa baki da miƙa hannu ita a dole ta gane Abbanta.
Anaam ta kallesa da murmushi. “ALLAH Yaya kai ne ka koyama yarinyarnan ƙiywa
ba wani ba. Ita a dole duk inda ta ganka saita ganeka”.
“Toya son ranki? Jealousy woman”.
Ya faɗa yana mai kashe mata ido ɗaya. Murmushi tai baki a taɓe. “Fess mana, miye
abin jealous anan nima nawa na zuwa zan rama”. Shima murmushi yay idonsa akan
lipstick ɗin bakinta. Sarai ta ganosa, dan haka ta tura lips ɗin a baki ta shanye
tas. Kafin fitowar nan tasu ta saka yafi sau biyar yana tsotsesa, yanzu ma anan
gidan ta saka.
“Kije ke da ALLAH kuma zan rama”.
Ya faɗa cikin langaɓe mata kai. Dariya take gimtsewa ita dai, ya ɗauke Muhseenah
suka bar wajen. Da kallo ta bisu cike da so da ƙaunar ƴar da uban.

Bayan kammala halartar kowa aka buɗe taro da addu'a. Abbah ya fara da nasiha
mai ratsa jiki game da muhimmancin da zuminci keda shi a rayuwarmu, tare da son
zuciya akan abinda kai baka isa sakawa ko hanawa ba a ƙaddarar waninka ko kai a
karan kanka. Ya ɗora da roƙo da fatan su zama 1family, tsintaiya ɗaya maɗauri ɗaya.
Tare da illar nunama juna wani abu wai shi ƴan ubanci. Ƴan ubancin nan babu abinda
yake zama a family sai kassara rayuka da maidasu koma baya. Duk family ɗin da babu
haɗin kai bazasu taɓa zama masu cigaba ba, dan kuwa zasuyita gabane suna taɗo juna
akan ƙanƙanin abu. Sannan iyaye mata na Family ɗin su kiyayi kansu wajen tsaurara
ƙiyayya tsakaninsu da ƴan uwansu har ƴaƴansu su fahimta hakan kuskure ne. Kowa yay
haƙuri da ɗan uwansa yayin daya ɓata masa rai, dan mai haƙuri baya taɓa faɗuwa sai
cin nasara a rayuwa. Su Abie sun isa zama manuniya a garesu. Sosai nasihar ta shigi
kowa. Sai faman sauke ajiyar zuciyoyi akeyi musamman Gwaggo Halima. Bayan gama
jawabin Abba Abie shima ya amsa. Ya ƙara da musu tashi mai ratsa jiki, tare da
shawarar sakama yaranmu ido domin sanin abinda suke aikatawa a wayoyinsu. Dan
sakacin rashin bibiyar shike saka yaran ɗoruwa a hanya irin wadda Fadwa tabi a
baya. A yanzu tangal-tangal din tarbiyyar yaranmu ta riga ta koma ne a tsinin
ƙaddarar yanar gizo da wayoyin hanu suka kawo mana, kenan ya dace iyaye su sakama
wayoyin hannun ƴaƴansu ido, karkuma suce bazasu basuba dan in kin hanasu zasuje
suga ta ƙawaye ko aboki ko saurayi, baki san kuma minene a ciki ba. Sannan tarbiyya
babu ruwanta da inda ka taso, a duk duniyar da kake, a kuma kowacce ƙasa idan kaso
ɗanka ya zama na ƙwarai zai zama. Bawai dole sai ya shiryuba, a'a ALLAH ne kaɗai
mai shiryarwa, suma waɗanda nasu ƴaƴan suka kauce ba'a son ransu bane, karka ga
gazawarsu koka aibanta waɗan nan yaran, akwai ƙaddara amma wasu lokutan akwai
sakaci sosai na iyaye. Karka matsawa ɗanka, kar kuma ka sakesa da yawa. Dan matsi
na saka lalacewa tunda zai koma a tafin hanun neman sharar ƙawaye ko abokai ne,
sannan saki gaba ɗaya ma kuskurene, zai koma a tafin hanunun tarbiyyar ƙawaye ko
abokai. A wannan zamanin iyaye sun kashi kaso uku ne zuwa huɗu koma nace biyar ko
fiye da haka, masu raunin talauci da komai yaron yayi dan an sakar masa komai ne.
(Kamar dai su Sima da Amaal) kaso na biyu rashin wayewar kan sanin mi yaran ke
aikatawa ma ko ilimin sanin illar wayoyin ko yanar gizo. Kaso na uku ƴan boko
wayayyu da komai akai su a wajensu ba komai bane zamanine. Kaso na huɗu masu
tsananin tsaurarawa har ƴayan suna fakar ido suna aikata abinda sukema tsaurin.
Kaso na biyar ƴan fifita aiki ko kasuwanci fiye da saka ido akan al'amuran ƴaƴansu
komai na hanun ƴan aiki kosu yaran a karan kansu. Iyaye mata suna ƙoƙari matuƙa,
duk da a wani ɓangaren akwai sakacinsu, sai dai kuma laifin iyaye maza yafi
rinjaye. Da yawa ƴaƴa suna matuƙar shakkar iyayensu maza fiye da matan, sannan a
wani fanin iyaye mata nada rauni akan ƴaƴa, dan haka idan kana son ingantuwar
tarbiyyar ɗanka yanda ya kamata dolene a matsayinka na uba kaima ka tsaya tsayin
daka wajen taimakawa uwa mace ku gyara kuma ku tsawatar, sannan ku haɗa da addu'a.
A wani fanin Gwaggo halima tayi matuƙar ƙoƙari wajen tarbiyyar su Fadwa, domin kuwa
bata barsu kara zube ba akan wasu fanonin, hakan zaisa mai karatu ya fahimci itafa
uwa uwace koyaya take tana buƙatar ganin ɗanta a ƙyaƙyƙyawar nasara bawai faɗuwa
ba. Su Fadwa na tsoron mahaifinsu, amma maida hankalinsa a kan hidimarsa da
siyasarsa yasa bai maida hankali wajen sanin dukkan motsinsu ba, shi dai kawai idan
ya samo ya basu sunci sun sha sun samu komai basu da matsala ya gama nashi. Ba
mahaifin Fadwa kawai bane a irin wannan halin, mazanmu na yanzu musamman yarena
hausa dana sani wannan shine babban rauninsu akan ƴaƴansu gaskiya. Namiji ya fita
tun safe sai dare ko yamma zai dawo miki, komai ya sakar miki akan tarbiyyar yara,
masu ƙoƙarin ciki sune ke ɗan zama da yaran weekend, wanima da sun raɓesa zai
korasu shi an takura masa yana son ya huta, ko wani ya ɓato masa rai a waje ya
shigo gidan yayta tambotsai. Komai sai uwa dai, tayaya uwa zata iya da komai?
musamman akan yaran yanzu da sai dai addu'a. Abu mafi girma shine maida nauyin
gidajenmu a hanun ƴaƴanmu musamman ga iyayenmu talakawa. Taya zakice yarinya
budurwa baliga ko bazawara itace zata nema kuɗi ta ɗauka nauyin rayuwar gida? Ko
namijine a wannan zamanin dole ka kasance cikin taka tsantsan balle mace, anji
neman nakai nada daɗi, amma komi ƴarka zatai tayi a gaban idonka, bisa control naka
kona yayunta domin ceto rayuwarta daga faɗawa wata ƙazamar rayuwa. Tabbas wasu
iyayen basu san ƴaƴansu na abubuwan nan a media ba, saboda su basu da wayewar kan
sanin mima wayoyin suka ƙunsa ko yanar gizo, wasu kuma masu wayewar hakan basu cika
zama masu bin ƙwaƙwƙwafin yaran nasu ba. A ganina hakan duk kuskure ne, akwai
abinda baida ƙyau ka cika masa bin ƙwaƙwƙwafi kam, akwai kuma wanda saida bin
ƙwaƙwƙwafin komai zai tafi dai-dai. Karmu hana yaranmu wayoyi, kar kuma mu barsu da
su su zame musu komai. Idan baku da wayewar kai akan waya samu wasu da zasu dinga
bibiyar yarinyarki a kowane shafi nata/nashi suna kawo miki rahoto, idan kunada
ilimin bibiya a kowanne dare wayar yaranki musamman mata ko matasan samari masu
tasowa dan nasan na manyan gwasaken zaiyi wuya ta kwana a hanunki, dan dare shine
mafi girman fili dake basu damar aikata komai a yanar gizo. Sannan ki dage da
addu'a da yawaita nasiha mai tsoratarwa ga yaran akan irin waɗan nan abubuwan. Mu
kammu iyaye mata da muke shiga a irin waɗan nan abubuwan dan ALLAH muyima kammu
faɗa mana, kina tunanin zakiyi ƴaƴanki su kasa koyi dake? Shifa hali naso yakeyi,
Fadwa ta fara tiktok tun bata da aure, amma saboda ya zame mata jiki har taje gidan
aure tanayi a duk yanda taso. Wlhy wlhy maza da yawa na faɗawa a tarkon sha'awa a
kalle-kallen videos na yanar gizo da mata ke yaɗawa a duk shigar da suka gadama.
Karku manta wanifa abu kaɗan ke tada masa hankali, shiyyasa zinace-zinace sukai
yawa yanzu muka rasa gane daga inane, ada yarinya saita ɓalle daga gida ta shiga
duniya ake kiranta karuwa, wlhy yanzu a gabanki za'a maida miki yarinya karuwa ko
matarka ko ƙanwarka ko yayarka😭, dan wasu matan a dalilin abinda sukeyi wasu mazan
ke hillatarsu harsu bata musu rayuwa. Duk yanda mace take tana son a yaba mata,
shiyyasa maza mayaudara ke saurin samun galaba akan ɗiya mace saboda su duk hanyar
yabo da gwarzantawa sukebi, suna kuma samun abinda suke so su watsar dake su koma
gefe suna zagin iyayenki dake kanki matsayin mara tarbiyya. To hakane ke faruwa a
duniyar tiktok dama sauran kafafen sada zumunta, waɗan nan masu zugaki a Comments
kin haɗu, kin isa, kin kai, wlhy ba ƙaunarki suke ba, dan daza'ace ɗaya daga ciki
ya fito ya aureki sai kin nemesu kin rasa sun gudu. Maza dake kawo matansu ana
video su wai soyayya ban taɓa ganin waɗanda basu san ciwon kansuba irinsu wlhy,
matarka ta aure sirrinka itace kuma abin ado a shafin sada zumunta?, anya wannan
soyayya ce kuwa ta gaskiya? Muji tsoron ALLAH, mu dunga tunawa da mutuwa, mu dinga
tunawa akwai kwanciyar kabari, akwai hisabi, dubinki sunyi amma basuci ribaba,
tayaya ke kike tunanin zaki ribantu?, bazaku gane illar abinda kukeyiba sai kinje
gidan aure namiji na miki kallon zargi ko yana bin irin hanyar daya ganoki wajen
gani wasu matan duk da yana dake a gidansa. Ki dauka abu mai amfani ki yaɗa sai
kici riba, amma mummuna zakiyi bayani idan baki tubaba. Dan Fadwa a novel ta fito
shiyyasa wani a cikin hukuncunta yazo a bayyane, amma ke a zahiri kike ALLAH shine
zai hukuntaki idan baki tuba kin koma garesaba, ba kuma kisan ta hanyar dazai
hukuntakin ba ma. ALLAH ka shiryemu badan halinmu ba.😭🙏🏻

Shima Daddy koda ya amsa maganar dai ɗaya ce akan zuminci da tarbiyyar
ƴaƴanmu. Mu daina sakarma abokai ko ƙawaye ƴaƴayenmu hakan kuskurene. Dan zai zama
kina tufƙa wasu na warware miki, yanzu lalacewa basai a zahirin rayuwa ba. Daga
budurwa har bazawara da saurayi ko magidanci ko matar aure inhar suna biyema ƙawaye
ko abokai zama samu rayuwarsa tana tangal-tangal, dan zai koma ne baida ra'ayin
kansa sai nasu, hakan kuma babban kuskure ne.........✍

_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_
*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_


*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:


07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇


09134848107

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*


[11/25, 12:22 PM] My Zafafa: *_Typing📲_*

*_BABU SO....!!_*
_(Miya kawo kishi?)_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718

*_83 End_*

.........Matsalar ba'a raye-raye bane kawai ko abinda bai dace ba ko mara amfani.
Akwai canja abokai, dan dole ne yay abokai a wannan yanar gizon, tun ana ƴar nesa
da juna har a kai ga haɗuwa, bai san tarbiyyar waɗan can ba ko inda suka fito, sai
kiga an koya masa sabuwar ɗabi'ar da baki san yaronki ko yarinya da shi ba. Shaye-
shaye ne, maɗigo ne, luwaɗi ne, fashi ne, sata ne, yahoo ne, kai da ire-irensu
daban-daban. Wlhy ko a film naga yarinya na shan shisha inajin zafi a zuciyata, dan
wata daga wannan abinda ake ɗauka faɗakarwar zataji daɗi ta cigaba, saboda mu a
namu wautan ɗaukar shisha muke ba shaye-shaye ba ma. Daga faɗakarwa an koma feɗe
tarbiya, an gyara goma biyar bata gyaru ba. Kullum ƴarki abokai da ƙawaye na
janta/jansa bin joint-joint, inda anan zata haɗu da wasu masu buɗaɗɗen idon da yafi
nata kuma ko yafi nasa. Ya ALLAH, iyaye dan ALLAH mu dake da addu'a. Sannan muma a
karan kammu mu gyara halayen da muka san munayi marasa ƙyau. Dan ba media bace
bala'i kawai muma a karan kammu bala'in kammu da kammu ne. ALLAH yasa mu dace.

Ba Fadwa ba kowa ma a falon jikinsa yay sanyi matuƙa, hankalin iyaye da yawa
da ba ɗaukar komai suke matsayin komaiba ya tashi matuƙa, dan kamar an farkar da su
ne abinda suka kasa hangowa a tsayin hangensu. Fadwa kuka take matuƙa tana mai dana
sani da nadama mara misali. Dan kuwa yanar gizo bata bata komai bai sai komawa baya
da sakata a gurbin nadama saboda batabi hanyar da zata amfana da ita ba. Inama
sauran wanda suke hali irin nata suma zasu farga da wuri kafin su rasa abinda ta
rasa koma fiye da ita. Inama zata iya goge abinda ya wuce a zuciya da idanun
mutane?. Sai dai kaico, duk da ta daina a yanzu ko waya bata riƙewa haka bai hana
videos nata cigaba da yawo ba a media, saboda wasu sun adana a wayoyinsu, kuma suna
cigaba da zama illa a garesu tunda suna koyi da su matsayin abin birgewa. Duk wanda
ya koya daga gareta kuma ya lalace tanada kamasho na zunibi itama. Kenan ita baɗala
koda kayita ka daina sharrinta na biye dakai har bayan ranka, wani lokacin ma har
jikokin jikoki? Ya ALLAH ka ganar damu gaskiya tun kafin ta ƙuɓuce mana. Ka shiryar
damu tun kafin guri ya ƙure mana, ka ƙuɓutar damu tun kafin ajali ya riskemu. Ka
goge laifukamnu tun kafin ƴayanmu da jikoki su riskesu😭🙏🏻.

Abie ne ya katse tunanin kowa cikin gyaran murya. Hakan yasa kowa maida
hankali a garesa. “Babban abinda ya taramu anan shine sake bada haƙuri da roƙo ga
iyayenmu, yayunmu, ƴaƴanmu, kuma ƴan uwanmu. Yaya Muhammad, Alhaji Sadiq, Babana
Shareff. Musamman abinda ya faru ya rigada ya faru, kuma hukuncinku dai-dai ne dan
duk ɗan halak idan an zunguresa ya dace ya nuna yaji zafi kuma ya ɗau mataki.
Sannan wanda yay laifi idan anga nadama a cikin idanunsa da ayyukansa ya kamata ai
masa afuwa koda kuwa bazai samu girman daraja irin ta baya ba. Kamar yanda na roƙa
a tun sanda kukai sakin nan kuka maidasu bada sanin kowa ba har su a karan kansu
dan mu barsu su horu muga kuma idan zasu gane gaskiya, to Alhmdllh sun gane, a
tsahon kusan shekara guda. Ina roƙon alfarmar ku maidasu ɗakunansu, ya rage nasu su
riƙe igiya ɗaya data rage musu kosu barta itama ta katse a yanzu. Fatanmu zuminci
ya cigaba da gyaruwa ba ɓaci ba, sannan dama shi mai laifi ana masa gargaɗi idan
yaji to falillahil hamdu, idan ya nuna kunen ƙashi sai a barsa da halinsa ALLAH ya
hukuntashi da ikonsa. Halima da Nafisa kunada sauran igiya ɗaya na aure kuma mun
roƙa alfarma an maidaku tun kan ku kammala idda, amma bawai hakan na nufin ku
cigaba da abinda ranku ke so ba a wannan family, dan a wannan gaɓar mun shirya
ɗaukar mataki akan kowacce dazata zame mana iblis wlhy, babu kuma wani cikinmu
dazai sake mata alfarma.”
Sosai Mommy da Gwaggo Halima ke hawayen daɗi, har basu san sun fara zuba
godiya da addu'a akan Abie ba. Yay murmushi kawai dan kuwa bai taɓa tunanin ganin
irin wannan ranar ba. Hankalinsa ya maida ga Shareff dayay kicin-kicin da rai, sai
dai wani sashe na ransa ya masa daɗin maida Mommy, ya kuma sake jin kima da
mutuncin Abie a cikin idanunsa da ransa.....
“Babana”.
Abie ya katse masa tunani.
Ɗagowa yay ya dubesa, sai dai baice komai ba. Abie ya murmusa ganin yanda ya tsuke
fuska. “Nasan a gareka abune mai matuƙar wahala iya manta komai, shiyyasa ko a
wancan karon ban tunkareka ka maida Fadwa ba, na barka ka huce sosai da sosai kafin
muzo a wannan gaɓar. Babu mai tilasta maka a cikinmu, amma zamu roƙeka alfarma. Dan
ALLAH ka maida matarka tunda tayi nadama.....”
Kansa ya shiga girgizawa a hankali. “Abie batai nadama ba, tana muku lumbu-
lumbu ne kawai. Koda zan iya maidata domin darajarku bazan taɓa sake sonta ba,
bazan taɓa ganinta da mutunci ba, bazan taɓa iya sauke dukkan hakkinta ba. Har
yanzu ina ganinta a idona mai ɓakar zuciya, mai mummunan hali, mai karancin
tarbiyya, ballagaza da bata san kima da mutuncin kanta ba, Abie mazafa kallonta
sukeyi sunaji wani abu a ransu, shin yara matasa nawane da magidanta sukaji hakan?
Mutane nawane suka kalleta a hakan? Ta daina amma har yanzu abinda ta shuka na yawo
a wayoyin mutane? Bazan iyaba Abie, wlhy ko tunata bana sonyi, bana son ganinta
sam......”
“Karka tsaurara da ƙarfi babana. Nasan akwai ciwo, akwai ɗaci, akwai raɗaɗi.
Sai dai muɗin ba masu shiryarwa bane ba. Sannan samun miji na gari na ƙwarai a
gareta a yanzu abune mai wahala, duk da nasan wasu zasu iya amfani da nasibin da
ALLAH ya bama mahaifinta na suna da dukiya suce zasu aureta, tunda wasu a gurunsu
abinda ta aikata ba komai bane a wautarsu, sai dai bai zama lallai su zama na
ƙwarai ba......”
Fadwa dake kuka ta ƙatse Abie ta hanyar rarrafowa gabansa. “Wlhy Abie bazan
iya zama da wani namijiba inba shiba. Ina sonsa, kuma ni kaina ina kaico wa
rayuwata ta baya. Na ɗauka abinda nake ba komaiba sai nishaɗi kawai, na ɗaukesa
matsayin zamanine kawai, na ɗaukesa matsayin lokacina ne kawai. Wasu tsurarun
mutane da bazasu amfaneni da komai a duniya da lahiraba kwarzantawarsu a gareni na
ingizani inajin babu yani. A tunani na abinda nake ba komai bane tunda ba'a zahiri
baneba. Ashe mummunar rayuwace mai wargaza ƙyawawan ayyuka. Ashe ƙofofin matakin
zuwa ga zina ce, ashe raguwar darajace a gareni matsayin ɗiya mace, ashe tanadin
abin faɗa ne ga ƴaƴana ga ƴan uwana. Ashe makullun rusa dukkan farin cikina ne da
rayuwar aurena. Ashe ƙanƙantar da kaina nake tamkar dabbar da bata san inane rufe
ko buɗe ba. Kaico na da wannan rayuwa, kaicon duk wata mace mara kamun kai da
fahimtar rashin daidai matsayin nishaɗi ko birgewa. Kaicon mace irina dake nuna
rashin ingancin tarbiyya da mutuncin iyayenta wa duniya. Nima bazan matsa maka ka
maidaniba, amma bazan daina son ka ba, zan mutune da sonka Soulmate, zan amshi
wannan hukuncin domin nasan UBANGIJI ne yake horani ta hanyar aza sonka a raina
fiye da komai. Na godema ALLAH daya saka maka da mace tagari tun kan kasan niɗin
wacece. Na gode ALLAH daya fargar dani illar abinda nakeyi tunkan tsufa da mutuwa
su riskeni......”
Kuka ya sarƙeta, tausayinta ya saka Anaam fara kuka itama. Amma ga Shareff sai
ma faman taɓe baki yakeyi alamar ko'a jikinsa. Dan shikam dai har cikin ransa baya
fatan sake zama da Fadwan. Sai dai yana mata fatan shiriyar da tace tayi dan shima
yana fatan ALLAH ya shirya masa nasa ƴaƴan daya fara haifa da ƙanensa dama duk
ƴaƴan musulmi.

Duk fa yanda aka buga Shareff bai yarda da maida Fadwa ba. Dole aka ƙyalesa
dan har yanzu yana akan dokin fushi. Haka taro ya tashi su Mommy dai zasu koma
ɗakunansu.

..................

Rayuwa ta cigaba da shuɗawa har ALLAH ya sake bama Anaam ciki, a kuma lokacin
su Abie suka dawo Nigeria, dan haka Muhseenah ta koma hanunsu, wani lokacin kuma
tana wajen Mommy data dawo tuni, hakama Gwaggo Halima ta koma, sai dai kuma duk da
mijinta ya ɗare karagar mulki ta koma ƴar kallo, komai amaryace ke zartarwa itama
ake kira first lady. Haka Gwaggo Halima keshan kukanta, ta kuma ɗauka ɗammarar
haƙurin zaman ƴaƴanta. Anaam aka cigaba da rainon ciki har ALLAH ya sauketa lafiya.
Alhmdllhi wannan karon dai da kanta ta haihu ɗan ta namiji mai kama da Shareff,
anyi farin ciki matuƙa an kuma sha shagali. Yaro yaci sunan Daddy. Wato Muhammad
Ameen. Za'ake kiransa Muhammad ɗinsa. Anaam da Shareff suka cigaba da rainon ɗansu,
wani lokaci Muhseenah takanzo tai musu har sati suma duk da dai kullum sai sun
ganta idan sunje kai Muhammad gida idan zasu aiki ko sun taso. A haka shima ya
girma yakai yaye. A kuma lokacinne ALLAH yayma Gwaggo data koma abin kwatance
rasuwa, tanata kururuwa da ihun a kira mata su Daddy, sai dai kafimma suje rai yayi
halinsa. Dolene kaga gawar Gwaggo ta baka tsoro, ta mugun komawa ƴar tsurut kamar
ba gawar mutum ba. Ƙarshen Gwaggo ya sake sanyaya zukatan su Mommy matuƙa.

Muhammad nada shekara uku a duniya rabuwar Fadwa da Shareff kuma shekara
shida Abie ya sake roƙon Shareff maidata ɗakinta, dan har yanzu ta kasa aure,
mazanma da ake tunanin zasuzo kodan alfarmar mahaifinta tamkar ALLAH ya dakatar
dasu duk wanda yazo gareta sai da wata manufa amma ba aure ba. Takanci kuka matuƙa
idan suna mata izgilanci da abinda ta aikata baya. A wannan karon dai da ƙyar ya
amince, sai dai ya sake tabbatar mata bazai taɓa ƙara sonta ba, ba kuma zata samu
wani farin ciki daga garesa ba.
Tana sonsa dan haka ta yarda da hakan da tunanin zata iya haƙuri aka sake
ɗaura aure. Sai dai kuma a tarewarta gidan ta tabbatar da abinda ya faɗa ɗin, dan
ta kasa gane komai na Shareff, yana sauke mata dukan hakkin da ALLAH ya daura masa
na ci da sha da sauran buƙatun rayuwa, amma ko fara'arsa bata gani balle samunsa a
gado, kwata-kwata yaƙi kusantarta, babu wata soyayya a tsakaninsu yanzu, komai yana
mata alamar tilasne zama da ita ya zame masa dan iyaye. Takanci kuka ta gode ALLAH
musamman idan taga yanda suke soyewa da Anaam a gidan kamar suna mantawa da
zamanta. Dan ma Anaam ɗin kan noke wani lokacin a gaban idonta. Ga wata irin
soyayya da take gani yanama ƴayansa tamkar ya cinyesu. Dan cikin da Anaam ta samu
na uku a gidan sai da taji tamkar ta haƙura da auren ma. Gaba ɗaya ya gama lalacewa
a kan cikin, koda yaushe yana manne da Anaam ɗinsa da ƴan ƴaƴansa. Ita tsakaninta
dashi kawai abinda yake wajibi. Ya hanata riƙe waya kuma sai rakani kashi, itama ya
tabbatar mata zai barta da itane domin adalcin kiran iyayenta. Amma kuma kullum
cikin bin ƙwafɗin wayar yake. Hakan na damunta, dan a yanzu sam babu wata yarda a
tsakaninsu koda ta magana ce. Ko abu ta faɗa masa sai yace sai ya bincika. Tasan
alfarmar Abie kawai takeci na zaman gidan. Amma ta rasa Shareff har abada. Ga
haihuwa shiru kaleji babu labari har yanzu, koda yake ba'a kusanceka ba ina zaka
haihu. Hakan ma na sake tada mata hankali dayin nadama mara misali.
A yanzu ma kuka take tana kallon Shareff ɗin da su Muhseenah da tazo musu
weekend ta window. A tsakar gida suke suna buga ball harda Anaam dake fama da
tsohon ciki. A bisa tsautsayi Anaam ɗin ta gurɗe. Gaba ɗaya Shareff ya ruɗe shida
yaran duk sukai kanta, jikinsa ya jawota cikin tsananin tashin hankali, itako tana
faman riƙe ƙugu da kiran sunansa.
“Bayana Yaya, cikina, ƙafata ta riƙe, Yaya muje asibiti wayyo Mamie na”.
Ai babu shiri yay sama da ita yakai mota, dole Fadwan ta fita itama domin
taimaka musu. Amma sai yay kamar bai ganta ba har saida Muhseenah tai magana tana
kamo hanunta. “Mamah kizo kima Miminmu addu'a Please kinga tana kuka”.
Cikin ƙarfin hali ta saci kallon Shareff dake ƙoƙarin saka Muhammad a mota.
Amma yay kicin-kicin da rai. Muhseenah ta nufesa tana faɗin, “Abbu Please aje da
Mama mana ta riƙeta tunda kai zakai tuƙi”.
Har yayi niyyar ballama yarinyar harara sai kuma ya dake, ya ɗaga mata kai
kawai dan yasan fitinar Muhseena ba barinsa zatai ba. Balle gata da shegen wayo, ba
kuma ya son ko kaɗan tasan wani abu mara daɗi tsakaninsa da Fadwan. Dan ko Anaam
bayayi a gabanta tsakanin shi da itane kawai yake horata. A dalilin Muhseenah suka
tafi asibitin tare, suna zuwa babu jimawa ALLAH ya sauki Anaam ɗin lafiya namiji.
Cikin ƙanlanin lokaci zance ya zagaye dangi. Kowa sai murna da fatan alkairi,
dandanna asibiti ya cika da dangi. Sai da aka sallamesu ƙura ta koma can gidan aka
cigaba da shagali. Shima dai yaro yaci sunan Abbah ranar suna. Wato Abubakar Sadiq,
zasu kirashi da Saddiq ɗin. A wannan sunanma dai Anaam da jariri sunga gata, itako
da iyayenta babu abinda zasuce ma ALLAH sai godiya. Dan yanzu dai family ya zama
tsintsiya madaurinki ɗaya kowa na hakuri da ƙoƙarin kai zuciya nesa koda rai ya
ɓaci.
Bayan suna da wasu kwanaki Fadwa ta zaɓi neman saki ga Shareff bayan tayi
shawara da Gwaggo Halima, itama dai jikintane yay sanyi dan tasan dama an takurawa
Shareff bisa komawar Fadwa gidansa, yana jin kunyar su Abie ne kawai shiyyasa ya
amince. Amma a yanzu tunda ita Fadwan da kanta ta zaɓi haƙura da zaman ALLAH yasa
haka shine yafi alkairi a garesu, dan insha ALLAH a yanzu itakam bazata sake bari
wani abu ya shiga tsakaninta da ƴan uwanta ba, saboda komai Fadwa ta zama a baya
itama ta bada nata gudunmawar wajen karancin bibiyar al'amarinta da tsawatar mata.
A yanzu itama ta fahimci zamansu tamkar cutar da juna ne kawai, shi zuciyarsa a
ƙuntace da ganinta, ita kuma zuciyarta a ƙuntace da buƙatarsa ta kuma kasa samu.
Bai waniyi jayayyaba suka je gaban su Abie da kanta tai musu bayani, duk da sun
fahimci hakan shine sauƙi da farin ciki a garesu basuji daɗi ba. Amma sun musu
fatan alkairi, Shareff ya rubuta mata sakinta. Tana hawaye ta amsa dan harga ALLAH
tana matuƙar sonsa, bakuma zata daina son sa ba har ƙarshen numfashinta. Ta zaɓi
yin nesa da shine domin yazama cikin farin ciki, dan ta yarda da gaske baya son
ganinta, ya tsaneta a yanzu. Shi kansa dai yaji tausayinta a wannan gaɓar, amma dai
haka shine mafi sauƙi a garesu, dan yayi ƙoƙarin manta komai ya amsheta hakan ya
gagara, bayajin zai taɓa iya ƙara kusantar Fadwa, badan komai ba sai dan daya tuna
maganar samarin nan sai yaji tsananin tsanarta da zafinta, yanada kishi matuƙa akan
duk abinda yake nasa, dan haka koya cigaba da zama da ita sai dai yayta cutarta dan
yayi alƙawarin bazai sake kusantarta ba. Yana mata fatan alkairi, idan tuba tayi na
gaskiya ALLAH ya saka mata da abinda zai zame mata alkairi anan gaba.✍

*_To nima dai bari nace Alhmdllhi, ALLAH ka ƙaramana haƙuri da juriya a duk yanda
wasu zasu so ganin fushinmu ko ɓacin rai ko damuwarmu ALLAH ya hana. Ya ƙara mana
haƙuri da juriyar ɗaukar komai da zaizo a ƙaddarorinmu, ka hanamu yin kuka da dana
sani mara yankewa a rayuwa._*

*_ALHAMDULILLAHI_*
*_ALHAMDULILLAHI_*.
*_ALHAMDULILLAHI_*

Godiya ta tabbata ga UBANGIJIN talikai daya bani aron rai da lafiyar rubuta wannan
ɗan gajeren labari. Abinda na rubuta dai-dai ALLAH ka amfanar damu a ladar.
Kuskuren ciki ALLAH ka yafemin.

Wanda duk naima ba daidaiba a yayin rubutunsa ya yafemin, abinda yazo ba'a
haka kuka so ba kuyi haƙuri a haka labarin yazo. Ina fatan kuyi amfani da amfanin
ciki ku watsar da marasa amfani, dan wani abun ana sakashine dan kawai nishaɗi.
Yaranmu masu tasowa ba komai najin daɗin rayuwa dake zuwa a novels ake samunsa a
zahirin rayuwa ba. Kowanne bawa da ƙadarar da ALLAH ya tsaro a tasa rayuwarsa. Idan
kinga saɓanin rayuwarki dana littafi ki ɗauka wancan labarine dan fadakarwa da
nishaɗi bawai dan sai kin tabbata ko kin samu irin rayuwar ba.

ALLAHU ka gafarta mana ka gafartama iyayenmu. ALLAH ka yafe mana.😭🙏🏻

Kamar yanda na fada a tiktok akwai mutanen kirki, masu yada alkairi DA yawa, hakama
akwai na banza, mun tabo irinsu fadwa ne Dan su san illa na abinda suke aikatawa,
muna musu kuma fatan shiriya da gane gaskiya kafin komai ya kure musu fiye DA
Fadwa. Kazama mutumin kirki sai addininka DA al'adarka suyi alfahari DA kai. Ka
kuma zama cikakke a cikin al'ummar MANZON ALLAH (S.A.W) ba komai bane nishadi kamar
handa muke kallo a rayuwar wasu yan tiktok, wani abun zubda mutunci DA darajane
matsayinki na diya mace musulma.

Masoya muna godiya dan bazamu gaji da godiya a gareku ba akoda yaushe. Muna godiya
matuƙa da kasancewar ku da zafafa biyar cikin tafiya mai nisan zango. ALLAH yabar
zuminci ya kara mana zama lafiya da kaunar kauna. ALLAH ka bamu shugabanni na gari.
Wannan zabe dake tunkaromu ALLAH kasa ayi lafiya a gama lafiya. ALLAH ya zaunar
damu a gidajenmu lafiya bisa soyayya da kaunar juna tsakaninmu da mazajenmu. ALLAH
ka shirya mana yaranmu damu baki ɗaya. Waɗanan fitintunu da wayoyi suka kawo mana
da yanar gizo ALLAH ka bamu ikon tsallakesu. Wanda suka afka ciki ALLAHU ka
shiryesu ka ganar dasu gaskiya kafin lokaci ya kure musu. 🙏🏻

Fatan alkairi ga kowa da kowa a duk duniyar dankuke. Kaunar kauna irin trillions
ɗin nan masoya😍😍😍😍

Taku

Bilyn abdull ce😍🤗👌🏼.

_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_
*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_


*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:


07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇


09134848107

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*

You might also like