Kimiyya A Sararin Samaniya
Kimiyya A Sararin Samaniya
_Daga: UsmannoorTheWriterBUK_
_Kashi na 1_
*_Duniyar wata tafiyace ta tsawon kwana 2 da kusan yini 1 a cikin rocket mai gudun
28,000km a cikin awa 1. Munada tazarar kilometers 400,000 tsakanin duniyarmu da
kuma kan wata (Alqamar)_*
*_Luna ko kuma mu kirashi da Moon, akwai abubuwan mamaki akansa, rashin bishiya
wanda hakan yana nufin babu iskar Oxygen, yana daga cikin abin al'ajabi ga wanda
yaje kan wata_*
*_A yanzu haka wata da muke gani a tsage yake kamar fashewar kwai, amman nisansa da
idanunmu yasa bama iya ganowa. Hujjar hakan tana cikin Suratul Qamar ayata 1 inda
Allah SWT yace: "Sa'a ta kusa, kuma wata ya tsage)_*
*_Hakan ya hade da mu'ujizar Annabi SAW a lokacinda kafiran Makka suka bukaci ya
sauko da wata da zummar idan hakan ta yiwu zasu karbi musulunci, ya roqi Allah,
hakan ta faru, watan ya tsage amman kadanne daga cikinsu suka musulunta_*
*_Shekaru kusan 3 zuwa 4 kenan ina bincike da nazari akan ilimin kimiyyar sararin
samaniya wato Astronomy_*
*_Burina naje duniyar wata, don na kara sanin ayoyin Allah SWT dake sararin Sama'ud
Dunya_*
_(Turawa yan uwa musulmai domin su amfana wajen sanin ayoyin Allah SWT dake sararin
samaniya)_
*_✍Usman Danliti Mato, A Public Writer, A Media Aide to Several Personnel (A Co-
founder Usmannoor Media BUK)_*
WhatsApp contact: 07035387476 Facebook: Usman D. Mato
_Daga: UsmannoorTheWriterBUK_
_Kashi na 2_
*_RANA (ASH-SHAMS)_*
_*Shin ko kasan zafin doron rana yakai 6,000℃ (degree celcius dubu shida), zafin
cikinta kuma ya zarce 16,000,000℃ (degree celcius million sha shida) ? Domin gane
matsanancin zafin, ka tafasa ruwa, idan yakai 100°C zai fara tafasa (saboda yakai
boiling point). Wani masanin kimiyya a sararin samaniya mai suna Johannes Kepler
yace: "Da'ace za'a matso da rana kwatankwacin kilometer 1 da kowa dake duniyarnan
ya qone saboda tsananin zafi haka kuma da'ace za'a nesantata damu misalin kilometer
1 da sai kowa ya zama qanqara saboda tsananin sanyi. Sai yayi tambaya menene
dalilin dayasa aka samu tazarar kilometer 150,000,000 tsakaninmu da rana ?*_
*_Wanda Dr Brian Greene yace tambayace rhetorical ma'ana wadda bata buqatar amsa
saboda kamata yayi yace mu mutane menene yasa muka tsinci kanmu a duniyarda takeda
tazarar 93 million miles tsakaninta da rana (Ash-shams) wadda again itama wannan
har yanzun sun gaza gano amsarta. Wanda mu kuma a matsayinmu na musulmai munsan
amsar tambayoyin gaba daya: amsar tambayar farkodai tanada nasaba da wani littafi
wanda Dr. Mario ya rubuta mai suna "Is God A Mathematician ?" Ma'ana shin Ubangiji
mai ilimin lissafine, wanda amsar hakan tana cikin sunayen Allah SWT tsarkaka 99
dinnan wato "ALHASIBU", ma'ana mai qayyadewa kokuma gwanin lissafi a ranar sakamako
(Ranar lahira)_*
_*Amsa ta 2 kuma tanada nasaba da wani maudu'i da Malamina Shaykh John Fontain
(Malami a Jami'ar Manchester dake kasar England) ya fitar mai taken "Is Life Just A
Game ?" Ma'ana "Shin Rayuwarmu Anyitane Don Wasa ?" wanda ya karade Clubs din
Celebrities yana jefa musu wannan tambayar, wasu sun sauraresa wasu kuma sunce
basuda lokacinsa. Abinda nakeson fada anan dai shine, rayuwa tanada purpose wato
manufa wadda tuni Allah SWT ya fadamana a cikin Suratu Dhaariyat ayata 56 "Wama
khalaqatul jinna wal insa illa li'ya'buduni" ma'ana "Kuma ban halitta Aljannu da
mutane ba sai domin su bauta mini". Sannan kuma munsan cewar Allah ya yalwata
wannan duniyar tamu da ma'adanai (natural resources) wadanda ya tanadar domin
amfani ga bayinsa kamar yanda ya fada a cikin Suratul Ankabu ayata 56 "Ya bayiNa,
wadanda sukayi imani ! Lallefa kasaTa mai yalwa ce, saboda haka ku bauta Mini"*_
_*Amsar Brian Greene ta fito anan wato abinda yasa muke rayuwa a duniyar Earth (Al-
ard) shine: Mu bautawa Ubangijinmu Allah SWT domin kuwa idan da ya halicci Annabi
Adam AS a duniyar Mercury (kamar yanda Astronomers sukace) rayuwa bazata yiwu
ananba saboda kusancin duniyar da rana domin kuwa doron kanta zabalbala yake kamar
talgen tuwo, kuma kamar yanda masana din suka gano cewar average temperature ta
bani Adam itace 37°C, haka kuma da ya haliccesa ya saukardashi a duniyar Neptune
shima rayuwar bazatayiwu ba saboda nisan duniyar Neptune din da rana, sanyin dake
kanta kadai azabane. Wancan a kimiyyance kenan ammanfa mu sani cewar babu abinda
yake gagarar Allah saboda fadarSa a cikin Suratul Mulk ayata 1 "...wahuwa ala kulli
shai'in qadir" ma'ana "...Kuma Shi mai ikone akan komai". Allah SWT shine
"ALHASIBU" mai qidaya komai da ajesa a muhallinsa, amsa ta fito, shakka ta fita*_
_*Kada mu manta cewar a ranar lahira, haka za'a sauko da ranar (Ash-shams) bisa
kawunan mutane (tazarar 1mile) alhalin a yanzun haka kilometer million 150 ne
tsakaninmu da inda take kuma nauyinta ya zarce tonne 200,000,000,000,000,000 (A
sauqaqaqqen harshe zaka iya cewa tonne septillion 200). Kasani cewar daga inda nake
(Rijiyar Lemo, titin jajira zuwa Zariya kilometer 157 ne kacal, zuwa Kaduna 230km,
zuwa Abuja kuma 415km ne kacal, zuwa doron kan wata kuma 400,000km ne. Tafiyace ta
nisan nisa, wadda saika fita daga hydrosphere, lithosphere, mesosphere, ionosphere,
exosphere, troposphere, thermosphere, stratosphere har zuwa atmosphere*_
_*Hasken rana ya ninka hasken wata sau 400,000 ko dayake daman shi wata bashida
hasken kansa, domin kuwa ranto haskensa yake daga ranar kamar yanda Allah SWT ya
fada a cikin littafinsa mai girma cewar shi wata (Al-qamar) Noor ne itakuma rana
(Ash-shams) Siraj ce. Akarshedai abu 1 ne cikin 2 zai faru, kodai muyi ayyukan da
zasu sa Allah ya sakamu a inuwar al'arshi kokuma la shakka sai munsha zafin ranar
nan wanda saboda gumi sai raquma 100 su iya sha basu koshi ba, kamar yanda hadisin
yazo a littafin Shaykh Abubakar Alhafiz ibn Khatheer mai suna "Albidaya wan
Nihaya". Wai kuma ahakanfa wasu suketa tara haram. Shin muna tunanin a banza
Mala'ila Jibrilu zai share shekaru 23 yana kawowa Ma'aiki wahayi akan hukuncin
Halak da Haram ? To Dabara dai ta rage ga mai shiga rijiya*_
*_Na dauki tsawon shekaru dayawa ina bincike da nazari akan ilimin kimiyyar sararin
samaniya wato Astronomy_*
*_Burina musulmai suje duniyar wata don su kara sanin ayoyin Allah SWT dake sararin
Sama'ud Dunya_*
_Muhadu a kashi na 3, insha Allah_
_(Turawa yan uwa musulmai domin su amfana wajen sanin ayoyin Allah SWT dake sararin
samaniya)_
*_✍Usman Danliti Mato, A Public Writer, A Media Aide to Several Personnel (A Co-
founder Usmannoor Media BUK)_*
WhatsApp contact: 07035387476 Facebook: Usman D. Mato
_Daga: UsmannoorTheWriterBUK_
_Kashi na 3_
*_RANAKU_*
*_Kafin mu gindayar da mai karatu yakamata muyi bayani dalla dalla akan batun
menene shekarun gudun haske (light years). A cikin 1 second (sekon 1) na agogo,
haske yana gudun 300,000km (kilometer dubu dari 300). Misali: ka qaddara kana aiki
a company NEPA, wutar lantarkin da ka kunna zata isa kasar Niger a kasada 1 second
(maana kafin ka qifta ido har yan Niger sunga ankawo wutar)_*
*_Kenan a cikin second 1 kacal haske zai iya zagaye duniya sau 7 (300,000km arabata
gida 22 zai zamo 13,636km, wanda fadin duniyarmu a diameter shine 13,500km). A
lissafin circumference kuma, duniyarmu takai 40,075km, wanda ahakan kana kunno
haske zai zagayata sau 7 a cikin second 1 kacal. A taqaicedai gudun haske ya zarce
na jirgin sama, rocket dakuma bindiga. Wannan lissafin second 1 muke, ita kuma rana
tanada tazarar shekaru 27,000 na gudun wancan hasken, bawai seconds, mintuna,
kwanaki ko watanni ake magana ba, shekaru 27,000 ake magana anan. Allahu Akbar !_*
*_A wannan matsanancin gudun da takeyi kuma bata cin karo da wata tauraruwar a
sararin samaniya (Alhamdulillah), kuma a hakan wasu taurarin suna daukeda
cincirindon duniyoyi wadanda suke daukeda watanni a tattaredasu. Kuma ko wannensu
dawafi (bautar Allah) suke a kewayen duniyarsu. Solar system dinmu tana jujjuyawane
a salon juyawar helix/spiral (helix motion) ma'ana katantanwa take tana juyawa a
duk awanni 24 (24 hours). Misali: ka samu ranwa, ka garata a kas, zakaga tana
juyawa, kamar hakane duniyarmu take juyawa_*
*_Wani zaice "Yanaji bana juyawa kuma alhalin ance duniyar tana katantanwa ?" Amsar
shine "Gravity kokuma kace maganadisu ne yasa baka jin juyawar" (Zamuyi bayanin
wannan aa wani Write Up din, insha Allahu) Astronomers sungano cewar Rana (Ash-
shams) tana ninqaya a sararin samaniya kamar yanda mai iyo yake ninqaya acikin
ruwa. Samada shekaru 1,400 da suka gabata lokacinda mutane suke tunanin Duniya da
Rana a tsaye suke qiqam, Allah SWT ya fada a cikin Qur'ani mai girma, cewar Rana
tana ninqayane a sararin samaniya. Allahu Akbar !_*
*_Anan mukazo karshen wannan zangon. Muna roqon Allah Ya tabbatardamu akan
musulunci bisa bin sunnar Ma'aiki SAW, ya rusa kafirci da kafirai_*
*_Burina musulmai su duqufa wajen binciken Astronomy domin su kara sanin ayoyin
Allah SWT dake sararin Sama'ud Dunya_*
_(Turawa yan uwa musulmai domin su amfana wajen sanin ayoyin Allah SWT dake sararin
samaniya)_
*_✍Usman Danliti Mato, A Public Writer, A Media Aide to Several Personnel (A Co-
founder Usmannoor Media BUK)_*
WhatsApp contact: 07035387476 Facebook: Usman D. Mato
_Daga: UsmannoorTheWriterBUK_
_Kashi na 4_
*_Allah SWT da ya halicci sama'ud dunya Shi kadaiNe yasan girmanta. Astronomers
sunce a iya Galaxy dinmu akwai taurari samada Trillion sau Billion sau 125. Sannan
kuma ahakandai akwai Galaxy samada Billion 100 zuwa 300 kuma dukkansu a sama'ud
dunya suke (Wallahu a'alam) Akwai wani littafi mai dadin karantawa mai taken
"KIMIYYA A SARARIN SAMANIYA" wallafar marigayi Dr. Bashir Usman Tofa (Astronomer),
na samu littafin ne a wajen abokina Abubakar Auwal Bala (A Chemist graduate from
BUK) yana daya daga cikin littattafai wadanda na qaru a cikin binciken da nake na
ilimin Astronomy, a cikin littafin Marigayi Dr. Bashir Usman Tofa yayi bayanai
dalla dalla akan yanda sararin sama take, ya kuma bada labarin ziyarar da sukai
zuwa duniyar wata (Moon), ga masu buqatar littafin sai su bincika a kasuwanni_*
*_Sararin sama tanada matuqar girma da fadi, domin kuwa dukkan wani nau'in ilimin
da yake a duniyarnan da ya shafi kimiyya da fasaha kamar irinsu Medicine,
Engineering, Agriculture, Microbiology da sauransu, inda za'a hadesu basukai 1%
bisa 100% na ilimin abinda yake a sararin sama'ud dunya ba. Allahu Akbar !_*
*_Bayani muke akan sama'ud dunya kadai (1st heaven) bawai sama ta 1 ba, ta
2,3,4,5,6 ko ta 7 ba ballantana kuma Aljannah wadda tana sama ta 7 kusada Sidratul
Muntaha wadda fadin Aljannar musulmi 1 tafi kassai 7 da sammai 7 idan za'a hadesu
waje guda, batun tsayin gidan kuma Allah kadai yasani tunda a al'adance munsan
tsayin abu yafi fadinsa kamar yanda Ya fada a cikin Suratu Al-Imran ayata 133 "Kuma
kuyi gaggawa zuwaga neman gafara daga Ubangijinku da wata Aljannah wadda fadinta
{dai dai da} sammai da kasa ne, anyi tattalinta domin masu tawawa" (ALBISHIR: Idan
mun kammala darasussukannan zamu shiga kai tsaye zuwa na gaba mai taken "NI'IMOMIN
ALJANNAH", insha Allahu)_*
*_Sammai da kassai guda bakwai daya bisa daya Allah ya dorasu, ma'ana kamar dai ka
samu qwarya ka wulla kobo a cikinta, dan karamin misali kenan. Idan muka koma cikin
hadisin Ma'aiki SAW ya bamu labarin girman sammai a cikin tafiyar da yayi ta Isra'i
da Mi'iraji inda yayi bayani akan da za'a dauki duniyarnan tamu ta Ard a wullata
cikin sama ta 1, to yanda kasan an wulla zobe ne a cikin sahara. Haka kuma da zaka
wulla sama ta 1 da abinda ke cikinta, ka sakata cikin sama ta 2 da bazata wuce
girman zobe ba a cikin wata saharar. Haka abin yake har zuwa sama ta 7. Allah SWT
yace a cikin Suratu Nuh ayata 15 "Bakuga yadda Allah ya halitta wasu sammai bakwai
dabaqoqi akan juna ba ?"_*
*_Yakai dan uwa/yar uwa mai karatu, da ace zaka daga kanka sama yanzun a matsayinka
na wanda yake a Africa, arewacin Nigeria maybe Kano sai kace sama ta 1 ta fara ne
daga can (inda idanunka suke iya gani) to wadanda suke a China, birnin Beijing daga
kudanci sukuma haka zasuce a'a sama tafara daga can ne (Kaga kenan anan anyi hannun
riga tsakanin wanda yake a Kano ta Nigeria dakuma wanda yake a Beijing ta China),
la'akarida duniyar kamar qwan jimina take (Spherical in shape) kamar yanda Allah
SWT yace "Wal'ardi ba'ada zalika duhaha" ma'ana "Kuma muka shimfida kasa bayan haka
muka maida ita kamar siffar qwai (Qwan jimina)" A cikin Suratu Nuh ayata 19 kuma
sai yace: "Kuma Allah ya sanya muku kasa shimfidaddiya", wannan ayar wasu mutane da
ake kirada yan flatter earth suke kafa hujja da cewar ai duniya a shimfide take
bawai a mulmule kamar qwai ba, wanda hakan kuskurene domin kuwa maybe iliminsu bai
kai cikin ayar can ta farko ba wadda har misalinta aka bamu (Kamar qwan jimina),
hakan yasa a karkace take a matakin degree 23.5°(Zaku iya duba office din wasu
Principals din idan akwai World map in Globe form zaku gane sosai) Ina tunanin
bayanin hadisin can na kamar an wulla zobe ya fito fili a misalinnan da na bayar_*
*_Sannan kuma a cikin Suratul Mulk ayata 3 Allah SWT yace "Allazi khalaqa sab'a
samawatin dibaqa..." ma'ana "Shine Ya halitta sammai bakwai, dabaqoqi akan
juna...". Wato wata kan wata. Sannan kuma a ranar lahira gaba daya duniya a tafin
hannunSa take SWT. A nannade a hannunSa na dama kuma daukacin sammai ne (Duba cikin
Suratu Zumar ayata 67)_*
*_Komai da komai da muke iya gani da wanda ma bama iya gani a duniyarnan kokuma a
sararin samaniya bauta suke ga Allah SWT ko mun gane ko bamu ganeba. Allahu Akbar !
_*
*_Wata bautar Allah yake, hakama rana {Duba Suratu Yasin ayata 38) da taurari, duk
suna dawafi ne a sararin samaniya kamar yanda Allah ya tsara musu, kuma basa
qetarewa basa gajiyawa, dan Adam ne kadai yake bijirewa saboda anbashi damar zabi,
sai yabi son zuciya ya bijire. Ahakan dan Adam ne yafi kowa iya bautawa Allah yanda
ya dace. Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah SWT, Ubangijin talikai_*
*_Anan mukazo karshen wannan zangon. Muna roqon Allah Ya tabbatardamu akan
musulunci bisa bin sunnar Ma'aiki SAW, ya rusa kafirci da kafirai_*
*_Burina musulmai su duqufa wajen binciken Astronomy domin su kara sanin ayoyin
Allah SWT dake sararin Sama'ud Dunya_*
_(Turawa yan uwa musulmai domin su amfana wajen sanin ayoyin Allah SWT dake sararin
samaniya)_
*_✍Usman Danliti Mato, A Public Writer, A Media Aide to Several Personnel (A Co-
founder Usmannoor Media BUK)_*
WhatsApp contact: 07035387476 Facebook: Usman D. Mato
_Daga: UsmannoorTheWriterBUK_
_Kashi na 5_
*_HALITTAR RANAKU_*
*_Idan yau Alhamis mune, wata Alhamis din ba mu bane, lokacin muna kabari. Musani
cewar tun sanda Allah ya halicci sammai da kassai 7 a cikin kwana 6 akai komai
kamar yanda Allah SWT ya fada a cikin Suratul A'araf, yau dinnan ranar Alhamis ne
(kwana na 6) a wajen Allah SWT yayinda kwana na 7 wato Juma'a zata zamo ranar
karshe (Alqiyama), shiyasa duk wanda ya rasu aka binneshi a kabari yana jiran
washegarine ma'ana Jumaa, ranar tsayuwa_*
*_Da can babu lokaci, hakan yana nufin Allah SWT ne ha halicci lokaci (Time).
Lokacinnan ya fara kirge daga O (sufuri) ta hanyar amfanida rana da wata (Wash
Shamsi Wal Qamar) hakan yasa aka samu dare da rana (Wallayli Wan Nahar) dukda cewar
wajaje irinsu Black hole basuda lokaci akasin Solar system dinmu mai daukeda rana
guda 1, watanni dayawa dakuma duniyoyi 8 (Pluto ba planet bace kamar yanda aka gano
a shekarar 2006) wanda malaman Astronomy sunce a qalla Universe zatayi shekaru
13.5bn (Biliyan goma sha uku da miliyan dari biyar), yayinda duniyarmu ta Al-ard
kuma tayi kusan shekaru 4.5bn_*
*_Halittar sammai 7 sun girmi halittar kassai 7 da tazarar kwana 3, maana idan ka
dauki kwanaki 6 na halittarsu gaba daya zakaga duniyarmu tanada kwanaki 2 na
kammaluwar halitta (Kamar yanda Allah SWT ya fada a cikin Suratul Fussilat) sannan
6 arabata gida 2 zai baka 3 (Ina fatan angane), idan ka dauki calculator ka lissafa
13.5 arabata gida 3 zai baka 4.5 (Adadin shekarun da duniyarmu tayi), haka kuma
idan ka dauki 4.5 ka ninkata sau 3 zai baka 13.5 adadin halittar sammai da kassai
din baki daya_*
*_Mutane suna yawan tambayata musamman dalibaina, wai shin Uncle tayaya ma akai
yasan wannan ilimin mai ban mamaki ? Amsar itace ta hanyar bincike a cikin kimiyya,
fasaha dakuma Qur'ani da Hadisin Ma'aiki SAW. A kimiyyance an gano wannan
lissafinne ta hanyar amfanida Hubble Telescope wanda sukace tabbas duniyarnan
tanada farko (wanda suna kiran abin Big Bang Theory), idan kuwa tanada farko to
dole tanada qarshe (shikuma sun kirashi da Big Crash Theory), big bang yana nufin
babbar qara wadda silartace aka samu komai da muke iya ganinsa da idanunmu domin
kuwa komai a hade yake, misali: wata daga duniya aka fitardashi. Tuni Allah SWT
yayi bayanin Big Bang Theory a cikin Suratul Anbiya ayata 30 "Shin wadanda suka
kafirta, ba su gani da cewa lallai sammai da kasa sun kasance dinke, sai Muka
budesu, kuma Muka sanya dukkan komai mai rai daga ruwa, shin bazasuyi Imani ba ?"
Ananma mu'ujizar Qur'ani ta fito fili. Allahu Akbar !_*
*_Shikuma Big Crash Theory shine tarwatsewar komai da yake a sararin samaniya (illa
wanda Allah yaso yabarshi), misali: angano cewar rana (Ash-shams) tana cinye zafin
kanta na hydrogen na nauyin ton tiriliyon samada 20 (20,000,000,000,000 tonne per
second) a duk second 1, wanda a karshe dai zai karene kamar yanda fitila mai
lagwani take mutuwa silar karewar kalanzir din dake cikinta. Allah SWT yace "Izash
Shamsu Kuwwirat" dakuma ayoyi irinsu "Izas Sama'un Fadarat". Wadannan ayoyin duk
bayani suke akan batun tarwatsewar rana da ita kanta sama. Babu wanda ya yasan
ilimin ranar Alqiyama ko a Annabawa, Manzanni ko a Mala'iku. Sahihin hadisi ya
tabbata wanda aka rawaito akan tambayar da mal'ika Jibrilu AS yayiwa Ma'aiki SAW
wanda yacemasa wannan ilimin na Allah SWT ne kadai_*
*_Wancan bayanine mai fadi wanda maybe nangaba mu bayyanashi amman yanzu mu dawo
kan gundarin batunmu na farko, akan batun Juma'a. Munsan cewar a ranar Jumaa aka
halicci Annabi Adam AS kamar yanda yazo a hadisi sahih, sannan kuma a wata ranar
daban ta Jumaa zaa tashi Alqiyama domin girbar abinda aka shuka. Lokaci ya kusa
wanda ba makawar zuwansa bisa laakarida kusan duk qananan alamomin sun bayyana
sauran manya, sai mu hankalta mu duqufa wajen aikata kyakkyawa da hani da mummuna
domin tsira daga wuta dakuma samun Aljannatil Firdous, Amin_*
*_Sabahul khaer yan uwa musulmi, barkanmu da safiyar ranar Asabar, ranarda Allah ya
halicci kasa kamar yanda Annabi SAW ya fada a cikin Hadisi sahih (Duba cikin
littafin RIYADUS SALIHEEN, hadisi na 1854)_*
*_Mu fito daga makwancinmu a hankalce, mu taka kasar da aka shimfida mana a
tsanake, mu yada sallama a sunnance, mu saki murmushi ga mutane a tausashe sannan
mutafi neman arziqin Allah a ilimance_*
*_A karshe inason mu yada iliminnan a hanzarce domin samun lada a wadace_*
*_Anan mukazo karshen wannan zangon. Muna roqon Allah Ya tabbatardamu akan
musulunci bisa bin sunnar Ma'aiki SAW, ya rusa kafirci da kafirai_*
*_Burina musulmai su duqufa wajen binciken Astronomy domin su kara sanin ayoyin
Allah SWT dake sararin Sama'ud Dunya_*
_(Turawa yan uwa musulmai domin su amfana wajen sanin ayoyin Allah SWT dake sararin
samaniya)_
*_✍Usman Danliti Mato, A Public Writer, A Media Aide to Several Personnel (A Co-
founder Usmannoor Media BUK)_*
WhatsApp contact: 07035387476 Facebook: Usman D. Mato
_Daga: UsmannoorTheWriterBUK_
_Kashi na 6_
_*Ba abune baqo ba idan akace maka musulmi suna zagaye dakin ka'abah a matsayin
dawafi, amman idan akace maka "Duniya, wata da rana duk dawafi suma suke" dole
mamaki zai baibaye mutum tareda tambayar to me sukeyiwa dawafin su kuma ?*_
*_Ilimin kimiyya a sararin samaniya ne kadai yakeda amsar wannan tambaya mai cikeda
sarqaqiya. Masana ilimin kasa sun gano cewar garin Makkah shine tsakiyar duniya,
tsakiyar Makka kuma dakin Ka'abah ne wanda aka fitarda Google map dinsa wanda
latitude na coordinate dinsa shine 21° degree, 25' minutes wanda idan ka dauki 2
din tafarko itace Sura ta 2 wato Suratul Baqara sauran numbobin kuma (125) na
Suratu Baqara din shine ayar farko a cikin Qur'ani wadda tayi magana akan dakin na
Ka'abah, inda Allah SWT yace "Wa'iz ja'alnal baita masabatallinasi..." Ma'ana "Kuma
a lokacinda Muka sanya dakin (Ka'abah) ya zama makoma ga mutane..." Tun shekaru
wajen 1,400 anfitarda location din Ka'aba a Qur'ani kafinma Geographers su gano
(Allahu Akbar !)_*
*_Kamar yanda marigayi Dr. Bashir Usman Tofa yace a cikin littafinsa mai suna
"Kimiyya a sararin samaniya": da awon matsawar launin shudin birnin Andromeda (Daya
daga cikin samada galaxy miliyon 100 dake maqotaka da tamu acan sama) ne aka
lissafa cewar yana dosomune da saurin kilometer 300 a kowanne second, amman kada
muji tsoro domin muma birninmu (Milkyway Galaxy dake jihar Virgo) ba a tsaye yake
ba, kuma da akwai dayawa masu nisantarmu da sauri fiyeda kilometer 1,000 a second
daya_*
*_Abin lura anan shine, komai a sararin samaniya tafiya yake yana zagaya wani abu
"tamkar dawafi" dukkansu daga dama zuwa hagu (anticlockwise direction) yadda
musulmi suke zagaya Ka'abah a doron wannan duniyar tamu ta Ard, haka wata (moon)
yake zagaye duniyarmu, ita kuma tana zagaye yar Shams (Rana), ita kuma ranar tana
zagaya badalar anguwarta (Suratu Yasin 36:38) da saurin kilometer 250 a kowanne
second, ita kuma anguwar tana zagaya tsakiyar birnin Milky way, shikuma yana zagaya
Jihar Virgo, ita kuma tana zagaya babbar jihar (Super Cluster ta hannun gefen
Orion) ita kuma tana zagaya wani, shikuma yana zagaya wani abu, shikuma yana zagaya
samaniya ta daya, ita kuma tana zagaya ta 2, har sai anje ta 7_*
*_Dakata da karatu, kadan duba babban dan yatsan hannunka (fingerprints) zakafi
gane bayanan dalla dalla, domin kuwa zakaga alamun kamar zagayen dawafi. Allahu
Akbar ! Nauyin Shams yakai kokuma ya zarce tonnes 200,000,000,000,000,000, amman
dukda haka tana tafiya zagayenta (dawafi) da saurin kilometer 2,150 a kowanne
second. Da wannan sauri takan dauki shekaru 250 kafin tayi zagaye daya, Ita kuma
duniyarmu (Ard) tana zagaye daya a cikin 23 hours 56 minutes (24hrs approximately)
dakuma kewaye (dawafi) daya a cikin kwanaki 365, wato shekara daya kenan. Allahu
Akbar !_*
*_Anan mukazo karshen wannan zangon. Muna roqon Allah Ya tabbatardamu akan
musulunci bisa bin sunnar Ma'aiki SAW, ya rusa kafirci da kafirai_*
*_Burina musulmai su duqufa wajen binciken Astronomy domin su kara sanin ayoyin
Allah SWT dake sararin Sama'ud Dunya_*
_(Turawa yan uwa musulmai domin su amfana wajen sanin ayoyin Allah SWT dake sararin
samaniya)_
*_✍Usman Danliti Mato, A Public Writer, A Media Aide to Several Personnel (A Co-
founder Usmannoor Media BUK)_*
WhatsApp contact: 07035387476 Facebook: Usman D. Mato
_Daga: UsmannoorTheWriterBUK_
_Kashi na 7_
*_Idan da ace zaka tsinci kanka a yanzu haka a birnin Andromeda galaxy (daya daga
cikin kungiyoyin taurari samada biliyon 100 dake sararin samaniya) to da bazaka ga
ci gaban gine-ginen da mutanen duniyarmu ta Ard (earth) suka samu ba, kamar irinsu
babban bangon China, manyan birane, dogayen benayen kasar Dubai kamar Burj Khalifa
wanda yafi kowanne gini tsayi a duniya, maimakon hakan wataqila saidai ka ga
mutanen farkon halitta (Na zamanin da) suna farautar abinda za su ci, dalilin
faruwar hakan kuwa shine: mutum yana kallon abinda ya wuce a can baya ne (past)
kusan kilometers biliyon 9 wanda yake kusan nisan gudun haske na shekara 2 da
kwata_*
*_Kamar yanda na fada a baya, a kalla da akwai biranen taurari wadanda Allah SWT ya
halitta samada biliyon 100 domin su zame mana ayoyinSa wanda kowannensu yana kunshe
da kusan taurari tiriliyon sau biliyon sau 125 kuma kowacce tauraruwa tana daukeda
a kalla duniya guda 1 kamardai yanda tauraruwarmu (rana) take daukeda duniyoyi guda
8 wanda Allah SWT ya halicci babanmu Annabi Adam AS da mahaifiyarmu Nana Hauwa'u AS
Ya sakasu a duniyar nan da muke takawa wadda itace ta 3 da take kewaye rana a kwana
365 wato shekara 1_*
*_Batu na gaskiya, idan ana magana akan adadin taurari, yawan taurari a galaxy
dinmu kacal yafi yawan qwayar yashin da yake a duniyarmu baki daya. Allahu Akbar_*
*_A bangaren lokaci kuma, munsan cewar lokaci kala-kala ne kamar yanda Einstein
Theory of Relativity ya fada, lokaci yana sauyawa a sararin sama. Masana kimiyya a
sararin samaniya sunce a da can kwana 1 daidai yake da second tiriliyon na yanzu.
Wanda kwana 6 na halitta daidai yakeda second tiriliyon 6 wanda idan aka raba da
adadin kwanakin shekara 1 ta yau wato 365.25 zai zamo shekaru biliyon 16 wanda
shine ake zaton asalin shekarun sammai da kassai na faruwar abinda masana suke
kirada Big Bang ma'ana Babbar Kara (Duba Suratul Anbiya ayata 30)_*
*_Abinda masana suka gano a kwanannan tuni Allah SWT yayi bayaninsu a cikin Qur'ani
mai girma. Allahu Akbar_*
*_A cikin ilimin probability, an dora Qur'ani a computer domin a gano wanene ya
rubutashi. Computer ta bada amsa kamar haka "Zaifi sauki ga mutum yace shine ya
halicci sammai da kassai, da ranaku da watanni da taurari, da ace mutum ne ya
saukarda Qur'ani" Ma'ana, wanda ya halicci sammai da kassai (Allah SWT) ne kadai
zai saukarda littafi mai cikeda hikima da ban al'ajabi wanda bashida kuskure ko
guda 1. A karshe dai baturen ya yarda da cewar Qur'ani zancen Allah SWT ne ammanfa
yace shidai kam addinin musulunci bazai iya karbarsaba. Wannan bature kam yayi
asara duniya da lahira !_*
*_Anan mukazo karshen wannan zangon. Muna roqon Allah Ya tabbatardamu akan
musulunci bisa bin sunnar Ma'aiki SAW, ya rusa kafirci da kafirai_*
*_Burina musulmai su duqufa wajen binciken Astronomy domin su kara sanin ayoyin
Allah SWT dake sararin Sama'ud Dunya_*
_(Turawa yan uwa musulmai domin su amfana wajen sanin ayoyin Allah SWT dake sararin
samaniya)_
*_✍Usman Danliti Mato, A Public Writer, A Media Aide to Several Personnel (A Co-
founder Usmannoor Media BUK)_*
WhatsApp contact: 07035387476 Facebook: Usman D. Mato
_Daga: UsmannoorTheWriterBUK_
_Kashi na 8_
*_Idan baku mantaba a cikin rubuce rubucen da na fitar a baya, na kawo muku bayanin
akan Babbar qara (Big bang theory) cewar da can tun asali komai a dinke (manne ko
hade) suke kamar yanda Allah SWT ya fada a cikin Suratul Anbiya ayata 30,_*
( ) َأ َو َل ْم َي َر ا َّل ِذي َن َك َف ُروا َأ َّن ال َّس َما َوا ِت َوا ْل َأ ْر َض َكا َن َتا َر ْت ًقا َف َف َت ْق َنا ُه َما ۖ َو َج َع ْل َنا ِم َن ا ْل َما ِء ُك َّل َش ْي ٍء َح ٍّي ۖ َأ َف َلا ُي ْؤ ِم ُنو َن
)30(*_ ال أنبياءAl-Anbiyaa*_
_*Shin kuma waɗanda suka kãfirta ba, su gani da cẽwa lalle sammai da ƙasa sun
kasance ɗinke, sai Muka bũɗe su, kuma Muka sanya dukan kome mai rai daga ruwa ?
Shin, bã zã su yi ĩmãni ba ?*_
*_Misali: da can wata (Al-Qamar) a manne a jikin duniyarmu (Al-Ard) yake kamardai
gutsuren dutse, ita kuma duniyar daga rana (Ash-shams) take, ranar kuma daga
taurari (An-Najm) su kuma daga hayaqi (Ad-Dukhan) wanda idan muka qara fadada
binciken zamu ci karo da asalin halittar Annabi Adam daga tabo (yunbu) ne wanda shi
kuma tabon nan akwai sinadarai guda 3 da suka fi yawa a jikin mutum, sune: carbon,
hydrogen dakuma oxygen wanda asalinsu daga wadannan abubuwan (rana da taurari
suke). Dukkan ilimi yana ga Al-Alimu (Allah SWT)_*
*_Kenan hakan yana nufin qashin (bones) kokuma muce endoskeleton wanda yake jikinmu
sinadaran calcium phosphate ne jibge, hade da sinadarin collagen wanda haqori ma ba
sai anyi maka dogon bayani ba zaka gane suma qasusuwa (bones) ne wadanda suke
daukeda miliyoyin qwayoyin halittu masu rai (cells) da suke fitarda mineral
substances domin amfanuwarmu. Allahu Akbar !_*
*_Kamar yanda aka gano asalin qarfe (Al-Hadid) ba daga solar system dinmu yake ba
la'akarida zafinsa a ma'aunin degree celcius ya zarce 7,000°C bi ma'ana ya fi ita
kanta ranar (Ash-Shams) wadda kwata kwata zafin bayanta baifi 6,000°C, dukda cewar
zafin tumbinta ya zarce miliyan goma sha shida, 16,000,000°C. Wane mutum. {Duba
Suratul Hadid ayata 26}. Ta irin wannan bincikenne aka aka gano cewar sinadarin
Calcium (Misali: dutse, qashi, bayan dodon kodi, haqori da sauransu) ma ba daga
anguwar ranar mu yake ba, daga tauraruwane. Allahu Akbar !_*
*_Akwai isassun sinadaran calcium da suke yawo a sararin sama silar fashewar
tauraruwa wanda hakan ke samarda trilliyoyin gallons din madara (milk). Masana
bincike sun tabbatarda cewar idan ka dauke sinadaran Hydrogen da Helium (wanda sune
suka hada gajimare) to duk sauran sinadaran da suka hada duniyarmu (Al-Ard) dakuma
gangar jikinmu an samesu ne daga fashewar manyan taurari (supernova)_*
*_Ya zama tilas a garemu (mata da maza) mu dinga tsaftace haqoranmu domin koyi da
sunnar ma'aiki SAW, wato amfani da asuwaki (As-Siwaq), domin kuwa rashin tsaftace
haqorin zaka budewa cututtuka kofar samun matsugunine a unguwar bakin ka, silar
lalacewar haqori dakuma warin baki, abin qi ga masu sauraronmu. An rawaito hadisi
sahihi daga Shuraih bin Hani RTA, yace "Na tambayi Nana Aisha (RTA) shin me ma'aiki
SAW yake fara yi kafin ya shiga gida ?", sai tace: "Ya kasance Manzon Allah SAW
yana yin asuwaki kafin ya shigo gida" (Muslim) Sannan a wani hadisin kuma idan ya
shigo yana sumbatar (kissing) matansa. (Muttafaqun alaihi)._*
*_Jama'a indai har ma'aiki SAW duk tsaftarsa zai yi asuwaki, to kai wanene da
bazaka dinga tsaftace bakinka ba. Ko kuma mun mantane da hadisin dake cikin Sahih
Muslim, littafina 2 hadisi mai lambata 0432 wanda Ma'aiki SAW yace "Annazafatu
minal iman" bi ma'ana "Tsafta tana daga cikin imani" ?. Ya Allah ka tsaftace
zuqatanmu sannan ka bamu ikon tsaftace haqoranmu da jikinmu baki daya_*
*_Anan mukazo karshen wannan zangon. Muna roqon Allah Ya tabbatardamu akan
musulunci bisa bin sunnar Ma'aiki SAW, ya rusa kafirci da kafirai_*
*_Burina musulmai su duqufa wajen binciken Astronomy domin su kara sanin ayoyin
Allah SWT dake sararin Sama'ud Dunya_*
_(Turawa yan uwa musulmai domin su amfana wajen sanin ayoyin Allah SWT dake sararin
samaniya)_
_{Subhanakallahumma wabihamdika ash hadu anlailaha illa anta astagfiruka waatubi
ilayk}_
*_✍Usman Danliti Mato, A Public Writer, A Media Aide to Several Personnel (A Co-
founder Usmannoor Media BUK)_*
WhatsApp contact: 07035387476 Facebook: Usman D. Mato
_Daga: UsmannoorTheWriterBUK_
_Kashi na 9_
*_Gobe Lahadi (26/02/23) idan Allah yakaimu da rai da lafiya, ka duba sararin
samaniya daga yamma kafin sallar Isha'i kamar 7:30pm, zakaga wasu fararen abubuwa a
qasan wata masu kama da taurari, to ba taurari bane ba, duniyar Jupiter da Venus ne
(2 daga cikin duniyoyi 8 da suke a solar system dinmu, masu dawafi ga rana kamar
yanda mukeyi ga ka'aba) Allahu Akbar ! Tsarki ya tabbata ga Allah SWT wanda ya
halicci sammai 7 da kassai 7 da abinda ke tsakaninsu
_*
*_Ana ganinsune a bayan kowanne shekaru 24 daga 20 ga watan February har zuwa ranar
Juma'a 10 ga watan March, 2023. Kenan rabon da aga wannan al'alamari tun a shekarar
1999_*
*_To kaga babu batun haduwarsu guda, la'akarida da akwai duniyoyi 2 a tsakaninsu
(Earth dakuma Mars) amman idan Allahn da ya haliccesu yaga dama sai ya hadesu din
wanda kuma hadesun zai janyo karshen rayuwar duk wasu haluttun da suke akan doron
duniyar ard din (earth)_*
*_MUHAMMAD BASHIR: Na fahimta ai ina tmby ne akan ilimin astronomy idan irin wannan
ya bayyana me yk nuni ze faru_*
*_USMANNOOR: Astronomically speaking, ba abinda zai faru sai abinda Allah SWT ya
qaddara wanda kuma mu makaluqai bamusan gaibu ba saidai Shi Alkaliqu ne kadai yasan
wannan ilimin (Saboda hujjar Laya'alamul Gaibu illallah)_*
*_Masu ilimin taurari da ake kirada Astrologists sune suke wannan duban wanda kuma
a shari'a babu kyau saboda hadisin da Abu Dawud ya rawaito: cewar Manzon Allah SAW
yace: "Duk wanda ya nemi ilimin sanin taurari yana neman daya daga cikin rassan
tsafi ne, tsafi kuma haramun ne a musulunci"_*
*_Saboda haka a zahiri kuma a kimiyyance babu abinda ke faruwa saboda taurari
basuda ikon gudanarda al'amura wannan iko na Allah SWT ne kadai kamar yanda a
kowacce shekara ake samun rashin lafiyar rana (solar eclipse) sau 2 zuwa 5 a
shekara (ganinsu ya danganta da kasar da kake a duniya), saikuma wanda yake game
duniya a kusan kowanne wata 18 shikuma rashin lafiyar wata (lunar eclipse) sau 2 a
calendar, wani lokacin kuma yakan kai 3,4 ko 5 kamar dai a shekarar 1935. To haka
shima ganin Venus da Jupiter a kowanne shekaru 24_*
*_Kuma kamar yanda nayi bayani daman can duk irin wannan lokacin ana samun aligning
(maqotakarsu: jupiter da venus din) in ka dauke Feb. 20 zuwa March 10 na kowanne
shekaru 24 to za kaga iya zara (venus) ce kadai kake iya hangowa a kusada watan
batareda kaga jupiter dinba alhalin ta koma muhallinta na 5 a cikin jerangiyar
sauran duniyoyi 8 din (Akula: ita duniyar venus itace wasu suke kirada tauraruwar
zara a rashin sanin cewar duniyace itama mai zaman kanta wadda kusan girmansu daya
da duniyarmu ta earth)_*
*_Burina musulmai su duqufa wajen binciken Astronomy domin su kara sanin ayoyin
Allah SWT dake sararin Sama'ud Dunya_*
_(Turawa yan uwa musulmai domin su amfana wajen sanin ayoyin Allah SWT dake sararin
samaniya)_
*_✍Usman Danliti Mato, A Public Writer, A Media Aide to Several Personnel (A Co-
founder Usmannoor Media BUK)_*
WhatsApp contact: 07035387476 Facebook: Usman D. Mato
_Daga: UsmannoorTheWriterBUK_
_Kashi na 10_
*_Usmannoor: Ba'a tsaye suke ba. Suna juyawa (kwana) sannan kuma suna zagayawa
(shekara) Bari mu dauki misali da wadancan duniyoyin guda 2, Jupiter da Venus:_*
*_Duniyar Venus tanada fadin kilometer 12,103 kuma tana zagayawa (shekara) a cikin
kwanaki 225 (kamar dai duniyarmu da take daukar kwanaki 365 a kowacce shekara)
sannan kuma Venus tana juyawa (kwana) a cikin kwanaki 243 (kamar yanda duniyarmu ta
earth take 24hrs a kullum)_*
*_A daya bangaren kuma Jupiter tana daukan shekaru 11 da wata 9 a cikin zagayen
shekara 1 kacal amman a bangaren juyawarta (kwana) tana daukar 9hrs da mintuna 55
ne, sabanin na earth 23.5hrs (approximately 24hrs) A taqaice dai dukkansu a waje
daya suke amman suna juyawa ne akan axis dinsu dakuma zagaya rana (Shams) a kowacce
shekara_*
*_Domin karin bayani saika duba rubutun da na fitar na can baya (a wannan dai babin
na kimiyyar) wanda yakeda alaqa da batun yanda sama take qara fadin kilometer
300,000 a kowanne sekwan 1_*
*_Abdurrahman Husain: Allahu Akbar, Allah Ya saka da alkhairi, Allah Ya ƙara mana
imani. Haƙiƙa wannan bayanin ya fito mini da ilimin cewa ba rana ce take juyawa ba,
duniyar damu ciki ce take juyawa..._*
*_Usmannoor: Tabbas. Kasan akwai turawan farko masu binciken sararin sama. Sunce
"The sun is at stationary" ma'ana rana a tsaye take qiqam. To amman shekaru 1400
can baya tuni Allah SWT ya fada mana a Qur'ani cewar rana ba a tsaye qiqam take ba,
kamar yanda wasu suke tunani hujjar haka tana cikin Suratu Yaseen (38)_*
( ) َوال َّش ْم ُس َت ْج ِري ِل ُم ْس َت َق ٍّر َّل َها ۚ َٰذ ِل َك َت ْق ِدي ُر ا ْل َع ِزي ِز ا ْل َع ِلي ِم
)38( يسYaseen
*_Kuma rãnã tanã gudãna zuwa ga wani matabbaci nãta. Wannan ƙaddarãwar Mabuwãyi ne,
Masani_*
*_To kaga anan gudu take sosai, saboda a duk sekwan 1 tana motsawa (juyawar)
720,000km/hr (kilometers dubu dari bakwai da ashirin a cikin awa daya tak) kenan
duk minti 1 tana gudun 12,000km (kusan girman duniyarmu a diameter) duk sekwan 1
kokuma duk kiftawar ido Rana tana yin tafiyar daga nan anguwarmu Rijiyar lemo zuwa
jihar Kaduna (Kamar yanda FRSC suka fitarda Signboard din anan kusada farko titin
jajira: Zariya 157km, Kaduna 230km, Abuja 425km)_*
*_To ammanfa dukda wannan gudu da Rana take saita shafe shekaru kusan 230 million
(miliyan dari biyu da talatin) kafin tayo kewaye daya a birnin taurarin anguwarta
da ake kirada Milkyway Galaxy, a sauqaqaqqen harshe ana nufin kamardai yanda
duniyarmu take kewaye Rana sau daya a shekara cikin kwanaki 365 haka itakuma Ranar
take kewaye Milkyway Galaxy a duk bayan shekaru miliyan 230, a matsayin dawafinsu
na bautar Allah, Allahu Akbar ! Wane mutum !_*
*_Abdurrahman Hassan: Allah Ya karɓi aikin Mal. Kada a gaji damu, tambaya ta itace:
shin rana tare da duniyar da muke ciki suke juyawa bai ɗaya? Kowannan su yana gudu
a lokaci guda kenan?_*
*_Usmannoor: Dukkansu juyawa suke saidai ba a speed iri guda ba laakarida girmansu
(tunda ita rana a jumhurin malaman Astronomy sunyi amfanida telescope sun auna
girmanta ya ninka girman duniya sau 1,300,000 a diameter. Bi maana sai an saka
wannan yar duniyar tamu sau 1.3 million a cikin rana, tunda gaba dayan fadin
duniyar tamu bai shige kilometer 13,500 ba (in diameter) Kenan kaga juyawarsu zata
banbanta. Kowanne dai da irin aikin da yake kamar yanda Allah SWT ya fada a cikin
Suratu Yaseen_*
*_Time is relative (ma'ana lokaci caccanzawa yake a space) Lokaci guda baya aiki a
space. Kowanne daban yake, gwargwadon nisan halitta gwargwadon sauyawar time
dinta_*
*_Mom Maryam: Ina tambaya malam. Toshin yadda muke kallon duniya guda biyun haka
muke a jere taredasu ? Kuma suna hango duniyarmu yanda muke hango tasu ?_*
*_Usmannoor: Ba'a jere muke da Jupiter ba la'akarida ita Venus itace ta 2 daga Rana
ita kuma Jupiter itace ta 5 kenan duniyarmu (earth) itace ta 3. Ga yanda suke a
jere: Mercury, Venus, Earth, Mars, Jupiter, Saturn, Uranus dakuma Neptune_*
*_Amsa ta 2: idan akace suna hango duniyarmu to ana nufin akwai wasu halittun acan
wannan kuma duk ilimin Astronauts basu gano halitta ko daya ba a sararin sama to
amman anan mu musulmai saidai muce Allah ya halicci halittu kala kala kuma ya
bazasu a cikin sammai 7 da kassai 7, misali: Mala'iku, Aljannu, Dabbobi dakuma
Kwaruka da abubuwan da bamusansuba a cikin sauran biliyoyin duniyoyin dake sama'ud
dunya, sauran bayani kuma saidai nace:_*
_(Turawa yan uwa musulmai domin su amfana wajen sanin ayoyin Allah SWT dake sararin
samaniya)_
*_✍Usman Danliti Mato, A Public Writer, A Media Aide to Several Personnel (A Co-
founder Usmannoor Media BUK)_*
WhatsApp contact: 07035387476 Facebook: Usman D. Mato
_Daga: UsmannoorTheWriterBUK_
_Kashi na 11_
*_MENENE HUJJAR DUNIYARMU TANA JUYAWA ALHALIN BAMA GANIN JUYAWARTA ?_*
*_Anas: Masha Allah anmafa ni haryanxu ban yarda duniya tana juyawaba. Saboda iya
binchikena da tambayar masana al-Qur'ani shin akwai aya wadda tayi magana akan
juyawar duniya kamar yadda 38 chikin surah yaseen tayi magana ni bansamu amsarba.
Idan akwai Wanda yasamu to inada bukata don indai na raba dayan biyu bissalam_*
*_Kuma nima kusan irin wannan tambayar nayiwa Shaikh Muhammad Sharu Rijiyar Lemo
wanda ya kasance masanin Qur'ani da Hadisi ne sannan ya shahara a wannan fanni na
kimiyyar sararin samaniya (Astronomy) Na qaru dashi a wannan fanni sosai (Ina roqon
Allah ya kara masa ilimi da tsoron Allah), wanda har SunnahTV suna dora programs
dinsa wanda silar hakan na ci gabada bibiyarsa harma nagano gidansa naje muka
gaisa_*
*_Nace masa "Mutane suna tambaya akan shin rana ce take fitowa daga gabas ta fadi a
yamma, kokuma duniyarmuce take juyawa ta yanda zata dinga nado safiya, da yammaci
kuma ta nado dare ?"_*
*_Saiyacemin "Duniyarmu juyawa take yi, bawai ranarce take fitowa daga gabas ta
fadi a yamma ba kamar yanda muke tunani ko kuma gani da idanuwanmu"_*
*_Shima har waccan ayar ya kawomin ta cikin Suratu Yaseen din, yayimin karin bayani
akanta yakuma qara yimin bayani akan bacewar rana a cikin ruwa (a zahiri bawai
ranarce take fada cikin ruwa yayinda tazo faduwa ba), a cikin Kissar Sarki
Zurqannain wadda take a cikin Suratul Kahfi ayata 86 inda Allah yace:_*
( ) َح َّت ٰى ِإ َذا َب َل َغ َم ْغ ِر َب ال َّش ْم ِس َو َج َد َها َت ْغ ُر ُب ِفي َع ْي ٍن َح ِم َئ ٍة َو َو َج َد ِعن َد َها َق ْو ًما ۗ ُق ْل َنا َيا َذا ا ْل َق ْر َن ْي ِن ِإ َّما َأن ُت َع ِّذ َب َو ِإ َّما َأن َت َّت ِخ َذ ِفي ِه ْم ُح ْس ًنا
)86( الكهفAl-Kahf
_Har a lõkacin da ya isa ga mafãɗar rãnã, kuma ya sãme ta tanã ɓacẽwa a cikin wani
ruwa mai baƙar lãkã, kuma ya sãmi waɗansu mutãne a wurinta. Muka ce: "Yã
Zulƙarnaini imma dai ka azabtar kuma imma ka riƙi kyautatãwa a cikinsu."_
*_A cikin tafsirin Suratul Kahfi ayata 86, malamai sun fassara: "...Kuma ya sameta
(ranar) tana bacewa (kamar) a cikin wani ruwa mai baqar laka", ijma'in malaman
tafsiri sun tabbatarda cewar rana ba a ruwa take faduwa ba, wannan ayar tana
maganane akan yanda Sarki Zurqannain yaga rana ta fadi a lokacinda yazo kusada
wannan ruwan tekun wanda hakan yana nufin yaje karshen kasa (inda babu al'umma
ballantana gidaje) kuma ko a yanzu duk mutumin da zaije gabar teku lokacin da rana
ta kusa faduwa to mutum zaiga kamar a cikin ruwan take faduwa_*
*_Malaman kimiyya sun gano cewar Rana ta ninka duniyarmu girma sau kusan miliyan
daya da dubu dari uku (1,300,000km in diameter) to ta yaya kuma wani zaice Rana
tana fadawa cikin Ruwan teku lokacin da yamma tayi ? Kaga kenan, Allah SWT misali
yake badawa na yanda Sarki Zurqannain yaga yanda Ranar take faduwa, shiyasa
mufassirun sukace "kamar a ruwan rana take faduwa" bawai "rana tana faduwane a
cikin ruwan ba" wasu malaman kuma sukace ta iya yiwuwa akwai wani kogi ne ya hade
da tekun silar gaurayewarsu kuma sai su samar da bakar kala shiyasa Allah SWT yace
"...cikin wani ruwa mai bakar laka". Wallahu ta'ala a'alam_*
*_Idan mun dawo batun wannan tambaya dakayi, to akwai hujjoji da suke tabbatarda
juyawar duniya kamar haka:_*
*_1) Idan ka ajiye camera akan titi ta kalli sama, sai ka fara video recording din
komai da yake a kusa da ita, kaita video recording tun da safe har zuwa dare. Idan
ka kammala kwana daya (24hrs) to ka zauna ka kunna video din a computer kayi masa
tariyar sauri (fast forward) zaka ga wucewar mutane da sauri, gudun motoci zai qara
sauri, idan jirgi ya wuce zaka ga yana sauri saboda wannan tariyar da akayi. Idan
dare yayi to zakaga taurari suna giftawa da sauri, anan take kuma zakaga video din
yana juyawa kamar dai yanda ake gara taya a kasa, rashin juyawar qallemun taya a
jikinta ba yana nufin tayar bata jiyawa yayinda yaro yake garata ba_*
*_To kamar hakane rashin jin mutum baya juyawa akan duniya ba yana nufin duniyar
bata juyawa da abubuwan da suke akanta ba, abinda yasa bama jin juyawar ta ta shine
abinda ake kirada karfin maganadisu (Gravitational force) karfin da Allah SWT ya
halitta ya sakashi a kasan duniya (Centre of gravity) wanda dukda gudun da take
na ...km a cikin second 1 amman bama jin gudun nata saidai muna iya ganeshine silar
juyawar da take a sarari wanda ganin yanda rana take nado yammaci shikuma yammacin
yake nado dare yana daya daga cikin misalan da zamu gane hakan_*
*_2) Yanayin yanda iska take kadawa tana kadawane kamar yanda ake wulla dutse
(catapult) ya dawo kasa kamardai ka lanqwasa hannunka ka kwatanta yanda maciji yake
fasa kai idan zaiyi sara (wanda a matsayinka na class mate dina, idan baka mantaba
a CAS Kano munyi darasi mai suna Projectile a cikin Physics)_*
*_3) Akwai kuma wani darasin da mukayi har ila yau a CAS Kano din mai suna Pendulum
swings wanda ake ajiye balabalan karfe wanda aka gano suna sauya muhallansu na
asali (direction), anyi bincike akan lilawar pendulum din a cikin awanni 8 angano
yana sauya mahalli har sau 4, kenan duk awa 1 yana canza muhallinsa na gabas da
yamma, hakan ya tabbatarda duniya tana juyawa, da ace bata juyawa da pendulum din
zaita jeka ka dawo ne har abada bazai sauya muhalli ba_*
*_4) Akwai wani abu da aka qirqira wanda yakeda wili (wheel) da yake juyawa ta ciki
ana kiransa da suna gyroscope, wanda aka ajiye irinsa guda 3 a muhallai guda 3,
suna kallon taurari guda 3 ta angles din dake tsakaninsu. Daya a tauraruwar kudu
mai suna Polaris, daya a tauraruwa mai tsananin haske mai suna Aldebaran na uku
kuma ya kalli rana (Ash-Shams), juyawar da gyroscopes din suke sabanin wajaje 3 da
aka saitasu ne ya tabbatarda cewar duniyar tamu juyawa takeyi (duba littafin "Proof
the earth rotates")_*
*_5) Yanayin yanda iska take kada teku (Ocean currents), tana kadawane kamar
juyawar agogo (daga clockwise zuwa anticlockwise) wato daga arewacin duniya
(northern hemisphere) zuwa kudancinta (southern hemisphere)_*
*_6) Idan akace duniya bata juyawa to zai zamana a tsaye take qiqam kamardai teburi
(flat table) idan kuma hakane to zai zamana bazamu dinga ganin yanayi 4 ba, rani,
damina, bazara da kaka (Summer, winter, autumn and spring), amman a maganar gaskiya
duniya a shimfide take sannan kuma a mulmule kamardai tamaula (ball), kamardai
yanda mahaliccinta ya fada a cikin Suratu Nazi'ati ayata 30_*
)30( النازعاتAn-Naazi'aat
*_Idan ka gara teburi bazai juyaba amman yayinda ka gara tamaula zata dinga
gangarawane har sai qarfinta (force) ya tsaya wanda hakan yana nufin duniyarmu zata
tsaya ta daina juyawa (zatayi reverse kenan) anticlockwise saikuma can ta koma
juyawa clockwise direction wanda silar hakanne za'aga rana ta fito ta yammaci ta
fadi gabas a maimakon yanzu da aka saba ganinta daga gabas ta fadi yamma (Tashin
Alqiyama kenan)_*
*_7) Munsan da cewar a kowacce rana munada awanni 24 ne, to amman a zahiri baikai
hakanba, awanni 23 ne da mintuna 56, menene kuma yaci mintuna 4 din ? Tambayar da
kusan takeda alaqa da irin taka kenan "Idan duniya tana juyawa to meyasa bama jin
juyawartata" ? Dalilin dayasa mukeda 23.5 hours yanada nasaba da karkacewar da
duniya tayi akan axis dinta wanda abin mamakin shine ta dan rankwafane da angle
23.5° (shiyasa ake cewa approximately 24hours per day) wanda wannan rankwafawar
tana nuni ne da yin ruku'u ga Ubangijin da ya halicceta, Allah buwayi gagara
misali_*
*_Sai ya zamana kusan duk abinda yake doron duniyar koyi yake da wannan
rankwafawar, misali: Idan Dan fulani yana kiwo sai ya gaji yana dan son ya huta,
zakaga ya tsayarda sandarsa yadan rankwafa, wanda kaga anan yasani ko baya sane
tabbas yana koyine da waccan rankwafawa da duniya tayi (23.5°) hakama idan Iya mai
saida tuwo zata kada miyar zogale zata kada miyarne muburginta a karkace (23.5°)
bawai a tsakiya zata saka mubirgin ba, burga miyar da take a karkace ko ta sani ko
bata sani ba tana koyine da yanda duniyarmu take a karkace (23.5°) Hakama idan
guguwa ta taso zakaga tana karkacewar 23.5° ne. Allahu Akbar ! Daman Allah SWT yace
duk wani abu da muke gani bauta maSa yake saidai wasu bazamu gane salon bautar nasu
ba_*
_*Silar karkacewar da kuma juyawar da duniyarmu (Al-ard) take ne ake samun dare
dakuma rana, kamar yanda Allah SWT ya fada:*_
( ) َو ُه َو ا َّل ِذي َج َع َل ال َّل ْي َل َوال َّن َها َر ِخ ْل َف ًة ِّل َم ْن َأ َرا َد َأن َي َّذ َّك َر َأ ْو َأ َرا َد ُش ُكو ًرا
)62( الفرقانAl-Furqaan
_"Kuma Shĩ ne wanda Ya sanya dare da yini a kan mayẽwa, ga wanda yake son ya yi
tunãni, kõ kuwa ya yi nufin ya gõde"_
( ) َو ُه َو ا َّل ِذي َخ َل َق ال َّل ْي َل َوال َّن َها َر َوال َّش ْم َس َوا ْل َق َم َر ۖ ُك ٌّل ِفي َف َل ٍك َي ْس َب ُحو َن
)33( ال أنبياءAl-Anbiyaa
_"Kuma shĩ ne wanda Ya halitta dare da yini da rãnã da watã dukansu a cikin wani
sarari suKe iyo"_
( ) ُي َق ِّل ُب ال َّل ُه ال َّل ْي َل َوال َّن َها َر ۚ ِإ َّن ِفي َٰذ ِل َك َل ِع ْب َر ًة ِّل ُأو ِلي ا ْل َأ ْب َصا ِر
)44( النورAn-Noor
_"Allah Yanã jũyar da dare da yini. Lalle ne a cikin wannan akwai abin kula ga
ma'abũta gannai"_
*_Kenan a taqaice dai da ace duniya bata juyawa kamar yanda kake tunani to da
saidai fa Rana ta haske iya bangare daya na duniya. Kodai Nigeria mu dawwama cikin
hasken Rana kokuma mu dawwama cikin duhun dare silar rashin haskenta_*
*_Akwai hujjoji dayawa amman ina fatan iya 7 dinnan ma zasu gamsar dakai_*
*_Burina musulmai su duqufa wajen binciken Astronomy domin su kara sanin ayoyin
Allah SWT dake sararin Sama'ud Dunya_*
_(Turawa yan uwa musulmai domin su amfana wajen sanin ayoyin Allah SWT dake sararin
samaniya)_
*_✍Usman Danliti Mato, A Public Writer, A Media Aide to Several Personnel (A Co-
founder Usmannoor Media BUK)_*
WhatsApp contact: 07035387476 Facebook: Usman D. Mato
_Daga: UsmannoorTheWriterBUK_
_Kashi na 12_
*_TAMBAYA:_*
*_Aslm. Iftar mubaraq. Inada tambaya su wadanda suke kamar a norway ya zasuyi
azumi, tunda kafin suga faduwar rana sai sunyi wata bakwai_*
*_AMSA:_*
*_Nasha cin karo da tambayoyi daga dalibaina na secondary school kamar: "To yan
kasar Norway din zasu share wata 6 suna bacci ne, su farka idan safiya tayi ?", yan
anguwarmu sukan tambayeni "To a cikin dare kenan suke gudanarda bukukuwan karamar
sallarsu idan watan 1 ga Shawwal ya kama ko kuma hakuri suke da bikin sallah tunda
yazo musu a cikin dare ?"_*
*_Bari na amsa tambayar "Musulman da suke a kasar Norway ta yaya zasuyi azumi tunda
kafin suga faduwar rana sai sunyi wata 6 ?"_*
*_A shekarar 1980 babu musulmai sosai a yankin Arctic Circle (doron duniya daga
saman kudanci, domin gane bayanin: ka kaddara a hannunka akwai kwai dafaffe to can
saman tudunsa shine kamar yankin kasashen Arctic kasar Norway tana cikinsu yayinda
kasansa kuma shine arewacin Antarctic), musulmai sun fara hijira ne daga kasashen
Somalia, Iraq, Pakistan zuwa kasashen Sweden, Norway dakuma Finland, wannan shine
silar yawaitar al'ummar musulmai a kasashen da ake share watanni a kalla 6 ba'aga
hasken rana ba, haka watanni a kalla 6 a cikin dare_*
*_Wani musulmi mai suna Hassan Ahmed, wanda aka yiwa irin wannan tambayar a garin
Tromsø, wanda gari ne a tsakiyar kasar Norway 350 kilometers daga Arctic Circle,
mutanen garin yawancinsu yan gudun hijirane daga kasar Somalia, da yawan musulmai
bai wuce 1,000 ba, wanda Hassan yayi bayanin cewar rana bata faduwa har watan
Ramadan ya wuce_*
*_Ya ci gaba da cewa "Munada fatawowi guda 2 da malamai suka bamu kodai mu dinga
azuminmu da kasar musulmai dake makotaka damu ko kuma mu dinga amfani da lokacin
Makka"_*
*_An tambayi Sandra Maryam Moe, wadda ta bata dade da amsar musulunci ba (revert)
wadda ta kasance manager ce a Tromsø community center tace "Tunda a cikin dare zamu
dinga rayuwa har watan Ramadan dinnan ya kare, sai muka zabi amfani da lokacin
Makka"_*
*_Hakan yana nufin idan rana ta fito karfe 5:00 am (na asuba) a Makka to mutanen
Tromsø sai su fara azuminsu daga karfe 5:00 am irin na kasar Norway (Norwegian
time)_*
*_"Dadin dadawa hakan yafi kwanciyar hankali da nutsuwa garemu saboda Makka suna da
kayyadadden lokacin (timetable) na fitowar rana da kuma faduwarta hakan yasa da
sallar da azumi suka daidaitu" inji Sandra Maryam Moe_*
*_A daren karfe 7:07 pm na Tromsø musulmai sukan tarune a masallachin Alnor suyi
iftar dinsu alhalin suna shan ruwa amman suna ci gabada ganin hasken rana ta cikin
windunan masallachin_*
*_Moe ta ci gaba da cewa "Kullum da daddare mukan cika anan musha ruwa tare muyi
sallah tare, lokaci ne na annashuwa a garemu a gaba daya watan Ramadan din"_*
*_Wani zaice to meyasa su wadannan kasashen suke samun irin wadannan lokatai, sai
muce ai saboda karkacewar da duniya tayi na 23.5° shine yasa ake samun yanayi guda
4: Summer: zafi, sai Winter: sanyi, da kuma Autumn: rani, sai kuma Spring: damina.
A shekara kusan gaba daya sassan duniya guda 4 (banda Arctic da Antarctic) suna
karban hasken rana kai tsaye ta yanda idan hasken rana ya hasko yankin arewa, su
kuma kudancin duniya zasu ji sanyi haka kuma idan ta haske kudu, su kuma yankin
arewa zasu ji zafi, wannan shine dalilin da yasa kasar Norway take share watanni 6
kafin rana ta haskota hakama watanni 6 kafin dare ya gushe. Allahu Akbar ! Dukkan
godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin mafadan rana 2 da mahudanta 2_*
*_To a takaice dai wannan shine amsar lokacin da yan kasar Norway suke shan ruwa
bayan sun kammala azumi alhalin basa ganin fitowar rana sai an share watanni 6 haka
kuma idan rana tayi basa kara ganin faduwarta sai wasu watanni 6 din sunyi_*
*_Burina musulmai su duqufa wajen binciken Astronomy domin su kara sanin ayoyin
Allah SWT dake sararin Sama'ud Dunya_*
_Muhadu a kashi na 13, insha Allah_
_(Turawa yan uwa musulmai domin su amfana wajen sanin ayoyin Allah SWT dake sararin
samaniya)_
*_✍Usman Danliti Mato, A Public Writer, A Media Aide to Several Personnel (A Co-
founder Usmannoor Media BUK)_*
WhatsApp contact: 07035387476 Facebook: Usman D. Mato
_Daga: UsmannoorTheWriterBUK_
_Kashi na 13_
*_Kamar dai yanda ake fasa kwai ya rabe gida 2 kuma a maidashi a manneshi to watan
da muke kallo da daddare shima kusan kamar haka yake_*
*_Dr. Thomas R. Watters, wanda ya kasance daya daga cikin Senior Scientist ne a
Smithsonian National Air And Space Museum dake Washington DC, jihar New York ta
kasar Amurka, yace a binciken da sukayi sun gano cewar wata ya taba tsagewa gida 2
sannan kuma ya hade (wanda har alamun tsagewar tasa sun gani da na'urorinsu na
LRO), wanda faruwar hakan shekaru ne ba wasu masu yawa ba dukda dai har yanzun sun
kasa gano dalilin da yasa watan ya taba tsagewar_*
*_Mu kuma a matsayinmu na musulmai sai muce musu ai wannan Mu'ujizar Annabinmu ce
SAW, saboda tuni hujjar hakan yazo a cikin sura kacokan wadda aka saukar mai suna
Suratul Qamar (Wata) sannan kuma akwai hadisai da dama da suka nuna faruwar hakan
lokacin da Manzon Allah SAW yana garin Makka_*
*_Surar wadda itace ta 54 tana karantar da musulmai tareda jan hankalinsu akan
cewar Alqiyama ta kusa kamar yanda Allah madaukakin Sarki ya fada:_*
)1( القمرAl-Qamar
*_Menene zai gagari Allah ? Amsar itace "BABU !" Nan take ya roki Allah, kuma aka
amsa masa, domin kuwa akan idanunsu sukaga watan ya tsage gida 2 ya sakko. Wanda
hadisai akan faruwar hakan sun kai matsayin mutawatirai, amman bari mu zayyano 3
domin hujja_*
*_Ya tabbata a cikin Sahihul Bukhari hadisi mai lambata 3869 cewar An karbo daga
Abdullahi Ibn Mas'ud RTA yace: "Wata ya tsage gida 2 a lokacin muna tare da Manzon
Allah SAW a garin Mina. Bangare daya na watan yahau kan dutse. Sai Annabi SAW yace
"Ku zama shaida" (Yana mai nuna yatsunsa zuwa ga watan) Allahu Akbar !_*
*_Hakanan kuma an karbo hadisi daga Anas Ibn Malik RTA yace: "Mutanen Makka sun
tambayi Annabi SAW ya nuna musu mu'ujiza, sai wata ya tsage gida 2, a tsakaninsa ma
suna iya hango Dutsen Hira"_*
*_Sannan kuma akwai hadisin da aka karbo daga Muhammad Ibn Jubair Ibn Mut'im, daga
mahaifinsa (Allah ya kara musu yarda baki daya) wanda yace: "Wata ya tsage a
lokacin Ma'aiki SAW har saida ya rabe gida 2, daya ya sauka a saman wannan dutsen,
dayan ma ya sauka a saman wancan dutsen. Sai (kafirai) sukace: "Muhammad yayi mana
tsafi. Sai wasu (daga cikinsu) sukace: "Idan har zai iya yi mana tsafi, ai bazai
iya yi ba ga kowa (sauran mutanen duniya)"_*
*_Kuma a lokacinda suka fadi hakan, sai aka samu wasu daga cikinsu suka tafi iyakar
Makka (boarder) domin su tambayi yan kasuwa wadanda zasu dawo garin Makka daga
kasar Sham (Yankin Syria, Jordan, Palestine), matafiya suna dawowa sai kafiran suka
tambayesu shin ko kunga wani babban al'amari da ya faru a kwanannan ?_*
*_Sai sukace eh tabbas munga wata ya tsage gida 2. Anan wasu dayawa suka musulunta
wasu kuma suka ci gaba da cewar ai wannan tsafi ne kawai daga Muhammad
(Wal'iyazubillah). Masu imani suka kara, kafirai kuma suka karyata mu'ujizar.
Shiyasa Allah SWT yace:_*
)2( القمرAl-Qamar
*_Kuma idan sun ga wata ãyã, sai su juya baya su ce: "Sihiri ne mai dõgẽwa!"_*
)3( القمرAl-Qamar
*_Kuma suka ƙaryata, kuma suka bi son zũciyarsu, alhãli kuwa kõwane al'amari (wanda
suke son su tũre daga Annabi) an tabbatar da shi_*
*_Turawa masana kimiyyar sararin samaniya (Astronomers) sunata qafafa sun binciko
sabon ilimi alhalin kuwa tun karni na 7 (14th century, samada shekaru 1440) Allah
SWT ya labarta mana abinda ya faru_*
*_Wannan yana daya daga cikin dalilan dayasa nakeson musulmai su dukufa wajen
binciken kimiyya a sararin samaniya (Astronomy), domin kara samun imani akan
ayoyinSa da suke a sama'ud dunya_*
*_Kuma wani abin mamakin shine, masu ilimin Qur'anic Science tuni suka gano cewar
Allah yayi ishara da daidai wacce shekarace mutane zasu saka kafarsu a doron
duniyar wata (wadda itace 20th July, 1969) wadda wannan shekarar tanada alaqa da
Suratul Qamar (mathematically), wanda In Sha Allahu a kashi na gaba zan yi bayani
akan hakan_*
_(Turawa yan uwa musulmai domin su amfana wajen sanin ayoyin Allah SWT dake sararin
samaniya)_
_{Subhanakallahumma wabihamdika ash hadu anlailaha illa anta astagfiruka waatubi
ilayk}_
*_✍Usman Danliti Mato, A Public Writer, A Media Aide to Several Personnel (A Co-
founder Usmannoor Media BUK)_*
WhatsApp contact: 07035387476 Facebook: Usman D. Mato
_Daga: UsmannoorTheWriterBUK_
_Kashi na 14_
*_KO KASAN DUTSEN DA IDAN KA HAU ZAKA IYA HANGO GOBE ?_*
*_Akwai wajaje masu matukar mamaki da ban al'ajabi a wannan duniya tamu ta Ard,
amman al'amarin garin da ake hango gobe mai suna Big Diomede da garin da ake hango
jiya Little Diomede yana daya daga cikin al'amarin da ya daurewa masana ilimin
kimiyya kai_*
*_Su wadannan wajajen sun karya ka'idar yanayin dokar lokaci gaba dayanta wadda ake
kirada law of time zones, wadannan wajaje sun kasance maqotan tsibiraine amman
sunada banbancin awanni 21 a tsakaninsu_*
*_Tsibiran 2 sun kasance a yankin Bering Strait wanda ya raba tsakanin Asia da
Amurka ta arewa (North America) a inda babban tsibirin Big Diomede yake a yankin
gabashin Russia da kuma Little Diomede da yake a bodar Amurka da tazarar 3.8
kilometers a tsakaninsu saidai akwai banbancin awanni 21 a tsakaninnasu_*
*_Tambayar da mutum zai fara yi kenan a yayinda yaji labarin wannan wajaje masu ban
al'ajabi, kokwanton hakikaninsu dakuma saukin bayaninsu a ilimance_*
*_Dalilin shine, saboda layin lokacin kasashen duniya (International Date Line)
wanda ya gifta a tsakanin wadannan wajaje masu suna Babban Diomede da Karamin
Diomede, wanda ya raba ta yankin daya daga cikin manya-manyan tekun duniya mai suna
Pacific Ocean wanda yake rage saurin juyawar duniya silar karfin kadawar tekun.
Allahu Akbar !_*
*_Da akwai tazarar awanni 21 kamar yanda nayi bayani acan baya wanda babban
tsibirin Diomede yake gaba da karamin tsibirin Diomed da tazarar awanni 21 silar da
yasa ake kiransu tsibirin Gobe dakuma Tsibirin Jiya, wanda aka gano a shekaru 295
da suka shude (16 ga watan August, 1728) wanda sunan tsibiran ya samo asaline silar
wani malamin Greek mai suna Diomede_*
*_An gano wannan al'amarinne a lokacinda wani video ya karade kafar sadarwar TikTok
wanda mutane sukaita tafka muhawara akan yanda lokaci ka iya sauya al'amura ta
hanyar da ba'a taba zato ba, yayinda wasu suke bukukuwan murnar shigar sabuwar
shekara (a yanayin A.M) wasu kuma can suna jiran washegari tayi domin fara murnar
tasu (a yanayin P.M)_*
*_A saukakakken zance zamu iya cewa da akwai awanni 24 a wannan duniyar tamu wanda
Allah SWT ya halicci dare da rana a cikinsu, idan mutum ya samu damar zuwa tsakiyar
tsibirancan wato awanni 12 (A.M da P.M) to tabbas ko shakka babu shi da kansa zaice
can safiya nake hangowa (gobe) can kuma a cikin dare suke (jiya) ni kuma a yanzu
nake (yau) shiyasa ake kiran tsibiran da Tsibirin Gobe dakuma Tsibirin Jiya bi
ma'ana mutum zai iya hango gobe dakuma jiya duk a waje daya ko kuma muce a lokaci
daya. Binciken da yafi wannan abin mamaki shine wani waje da aka gano inda zaka
taka gaba kadan (anjima) ka taka baya kadan (dazun) wanda ake kiran wajen da suna:
Magnetic North Pole dakuma Magnetic South Pole. Allahu Akbar ! (Zanyi rubutu akan
wannan wajen mai ban al'ajabi, In Sha Allah)_*
*_Ko kusa basada nasaba, kuma koda masu binciken sun ce sun san abinda zai faru
gobe na gaibu to karya suke domin kuwa sanin ilimin gaibu sai Allah SWT, kamar
yanda ya tabbatar a cikin LittafinSa mai tsarki kamar haka;_*
)9( الرعدAr-Ra'd
)6( السجدةAs-Sajda
)18( التغابنAt-Taghaabun
*_Da cikin Suratul Ma'idah ayata 109 da 116, Anam ayata 73, Tawbah ayata 78 da 105,
Saba ayata 48, Hashr ayata 22, da Al-Juma'ah 8 da dai wasu ayoyin duk a cikin Al-
Qur'ani mai Girma_*
*_Idan muka dauko karin maganar bahaushe da yake cewa "Sanin gobe sai Allah" wannan
tabbas haka yake domin kuwa da zahirin gobe da badinin ta duk Allah Ne masaninta,
kuma yana iya bayyana iliminta ga wanda ya so, misali: Allah SWT yana nunawa
bayinSa faruwar wani abu na bushara a mafarki kamardai mutum yayi mafarkin yana
dawafi a Ka'aba kuma mutum yaga abin ya faru a washegari a biya masa aikin hajji,
kaga kenan anan Allah Ne ya tsara abin da ya so a lokacin da ya so._*
*_Misali na 2, ya faru akaina, nayi mafarki matar wani abokina ta haihu ya mace,
anata murnar suna, bayan kwana 3 muka hadu dashi na labarta masa yayi matukar farin
ciki sannan yacemin yau kwana 3 kenan mukaje asibiti akayi mata awo aka gane tana
dauke da juna biya (Kuma nima kwana 3 kenan da yin mafarkin, ma'ana nayi mafarkinne
a ranar da akayi awon batareda nasani ba). A yanzu haka da nake rubutunnan, matar
tashi ta haihu ranar Lahadi (28 May, 2023 wanda yayi daidai da 8 ga watan Dhul
Qa'adah, 1444 A.H) kuma abin mamakin ya mace din dai ta haifa, nace masa ka tuna
fassarar mafarkinnan da nayi maka watannin baya da suka gabata, yace tabbas. Allahu
Akbar !_*
*_Kenan ko da mun samu damar ganin gobe (A.M) a zahiri/kimiyyance to bamu isa musan
badinin sirrin ilimin dake tattare da goben ba, sai ga wanda ya ga damar sanarwa
kuma dukkan wannan ilimin yana ga Mahaliccin Jiya, Yau da Gobe, Al-Hasibu
mahaliccin Kimiyya da Fasaha, mai iko da KUN wato kasance (Metaphysics) saikuma
abin da yafada din ya kasance wato FAYAKUN (Misali: Physics da sauran ilimummuka
duk muna ganin kasancewarsu silar KUN dincan), dukkan Isa da Godiya sun tabbata ga
Rabbus Samawati Wal-Ard, Allah SWT. Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga
fiyayyen halitta Annabi Muhammad SAW da ahlayensa da sahabbansa_*
_(Turawa yan uwa musulmai domin su amfana wajen sanin ayoyin Allah SWT dake sararin
samaniya)_
*_✍Usman Danliti Mato, A Public Writer, A Media Aide to Several Personnel (A Co-
founder Usmannoor Media BUK)_*
WhatsApp contact: 07035387476 Facebook: Usman D. Mato
_Daga: UsmannoorTheWriterBUK_
_Kashi na 15_
*_ARADU !_*
*_Bayan na dawo daga lecture da Shaykh Umar Sani Fagge ya gabatar a The Afficient,
kano, nakai dare a gida tareda yan uwana. Garin yayi lumi, iska mai dadi tana
kadawa, sama hadari sunata shawagi bisa umarnin mahaliccinSu, SWT_*
*_Kani na, Umarfarouk dan shekara 3, ya daga kansa sama yace "Yaya akwai qanqara a
cikin hadari ?". Nayi shiru na dan wani lokaci sannan nace "Eh, farouk, akwai kam".
Abinda yake qoqari fada shine: sautin tsawar da ya saba ji lokacin ruwan sama ne
yasa tunanin qanqara ya gifta a qwaqwalwarsa. A zahiri hakan yana faruwane
sakamakon haduwar qanqarori sama da guda 2 a cikin hadarin da ake kirada
cumulonimbus kamar yanda masana ilimin dabi'ar teku sukace_*
*_Kaninnawa ya tunamin da abinda Allah SWT yace a cikin Suratul Ra'ad ayata 13
"Kuma aradu tana tasbihi gameda gode maSa, da mala'iku domin tsoronSa. Kuma yana
aiko tsawawwaki, sa'an nan Ya sami wanda Yake so da su alhali kuwa su, suna jayayya
a cikin (al'amarin) Allah kuma ShiNe mai tsananin hila". Allahu Akbar !_*
*_Kuma ya tunamin da Hadisin addu'ar da ake lokacinda aka ji tsawa, an rawaito daga
Abdullahi Ibn Az-zubayr (RTA) duk lokacinda yaji tsawa yana yin shiru sannan yace
"Subhanallazi yusabbih ar-ra'du bi hamdihi wal-malaikatu min khifatihi" (Ma'ana:
Tsarki ya tabbata ga Allah wanda tsawa take tasbihi gareShi, hakama mala'iku saboda
jin tsoronSa) Surah Ar-ra'd ayata 13. Sannan kuma saiyace "Wannan gargadine ga
mutanen duniya. An karbo daga Al-Bukhari a cikin littafin Adabul Mufrad (723), Imam
Malik a cikin Muwatta (3641), Shaykh Albani Rahimahulla ya inganta isnadin Hadisin
a cikin Sahih Adabul Mufrad (556)_*
*_Nakan tuna lokacinda nake sanarda mahaifiyata, qannena maza da mata cewar duk
sanda sukaga hasken tsawa to su duba agogo, idan aka samu sakwanni 30 ko kasa da
haka ba'aji tsawa ba to akwai yiwuwar tsawa ta iya saukowa wadda ake kirada
qwaranqwatsa, sai a nemi mafaka, idan kuma ba aga haskenba to jin tsawar hanyace
mai sauke wajen gujewa hadarin tsawar, insha Allahu, anfi son mutum ya jira sakwan
30 bayan ganin hasken kafin mutum yabar inda yake lokacinda ake ruwa_*
*_Idan ka qirga sakwannin dake tsakanin hasken dakuma sautin tsawar sannan kuma ka
raba lissafin gida 5 to zaka samu tazarar zango (mile) zuwaga inda tsawar zata fado
ma'ana sakwan 5 daidai yakeda tafiyar zango 1 (1 mile), sakwan 15 kuma zango 3 (3
miles) sakwan sufuri (0 second) mutum yana kusada inda tsawar zata fado, saidai
idan Allah ya kiyaye_*
*_Meteorologists (Masu ilimin sanin yanayi, hasashen zubar ruwan sama dakuma
duwatsun da suke a sararin samaniya) sunada abinda suke kirada "dokar 30-30". Sunce
idan har aka samu tazarar sakwanni 30 tsakanin hasken da tsawar to aradu zata iya
fadowa mutum saboda haske yafi sauti gudu_*
*_Wannan ilimin yana daya daga cikin ilimimmikan da nake koyarda yan uwana a gida
musamman ma wannan watanni na mamakon ruwan sama. Ina fatan tareda addu'ar wataran
Umarfarouk zai zamo Islamic Astronomer (Masanin Kimiyya A Sararin Samaniya) idan
hakan zai zamo alkhairi musamman ga yan uwa musulmai, Amin_*
*_Anan mukazo karshen wannan zangon. Muna roqon Allah Ya tabbatardamu akan
musulunci bisa bin sunnar Ma'aiki SAW, ya rusa kafirci da kafirai_*
*_Burina musulmai su duqufa wajen binciken Astronomy domin su kara sanin ayoyin
Allah SWT dake sararin Sama'ud Dunya_*
_(Turawa yan uwa musulmai domin su amfana wajen sanin ayoyin Allah SWT dake sararin
samaniya)_
*_✍Usman Danliti Mato, A Public Writer, A Media Aide to Several Personnel (A Co-
founder Usmannoor Media BUK)_*
WhatsApp contact: 07035387476 Facebook: Usman D. Mato
_Daga: UsmannoorTheWriterBUK_
_Kashi na 16_
*_A yanzu haka bayan sallar asubah ina iya kallo ko kuma ince tozali da duniyar
Jupiter da idanuna a sararin samaniya daga gabas maso kudu_*
*_Duniyar Jupiter ta kasance katuwar duniyace da ta ninka tamu sau 11, ma'ana
tanada fadin kilometers 140,000 a diameter, sabanin duniyarmu da take da 13,500
kilometers a diameter, wadda Allah Azzawajallah ya halicci duniyar Jupiter da
sinadarin gas na Hydrogen da Helium, tana daukan shekaru 11 da watanni 9 kafin ta
kewaya rana sau 1, kamar dai yanda duniyarmu take daukan kwanaki 360 a shekara
kafin ta kammala dawafi ga rana, tanada siririyar atmosphere ta methane da
ammonia_*
*_Tanada qaqqarfan maganadisu da kuma radiation belts sannan kuma tanada manyan
watanni har guda 4 (Io, Europa, Ganymede da kuma Callisto) sabanin mu da muke da
wata guda daya tilo (Alqamar) da kuma qananan watanni guda 60_*
*_Tanada daruruwan zobuna wadanda sukai mata qawanya saidai basu kai yawan na
duniyar Saturn ba. Jupiter itace duniya ta 5 daga rana (ash-Shams) kuma ana kiran
Jupiter, Saturn, Uranus da Neptune da outer planets saboda sanyinsu silar yanda
suka nesanta da rana su kuma Mercury, Venus, Earth da Mars ana ce musu Inner
planets saboda zafi ko duminsi silar maqotakarsu da rana_*
*_Anan mukazo karshen wannan zangon. Muna roqon Allah Ya tabbatardamu akan
musulunci bisa bin sunnar Ma'aiki SAW, ya rusa kafirci da kafirai_*
*_Burina musulmai su duqufa wajen binciken Astronomy domin su kara sanin ayoyin
Allah SWT dake sararin Sama'ud Dunya_*
_(Turawa yan uwa musulmai domin su amfana wajen sanin ayoyin Allah SWT dake sararin
samaniya)_
*_✍Usman Danliti Mato, A Public Writer, A Media Aide to Several Personnel (A Co-
founder Usmannoor Media BUK)_*