You are on page 1of 30

Kaima Likitane Party 1

KAIMA
LIKITANE
Daga Taskar Muawiya Muzzy Yola
08149299509

Muawiya Muzzy 08149299509


Kaima Likitane Party 1

GABATARWA
Alhamdulillah, Dukkan godiya ta tabbata ga
Allah tabbataccen sarki, mabuwayi mai iko,
cikin yardar sa da ikon sa yauma Ya sake bani
dama na wallafa muku wani sabon littafi wanda
nai masa laƙabi da TASKAR AJA'IBU ZALLAH,
wannan littafin zai taimaka sosai musamman
ga Almajirai masu aikin makaranta wanda cikin
ikon Allah zasu mallaki asararu na aja'ibu kala
kala wanda kuma insha Allahu zasuji daɗinsu,
ina roƙon Allah daya sanya wannan littafin ya
zamo silar farin cikin Al'umman manzan Allah
(S.A.W) Kuma ina fatan ya zama silar taimako
ga kowa, Allah ina roƙonka da kai salati marar
adadi ga shugaban mu ja gaba annabi
Muhammadu (S.A.W) da alayen gidan sa da
kuma sahabbansa, ina tawassali dan soyayyar
Shehu ga annabi da wulayar abu abas dan
ijabar Shehu gibirima dan darajar Shehu aliyu
harazimi dan hasken mai barewa dan ƙaunar da
manzan Allah ke yiwa nana Fatima Allah yasa
littafin nan ya amfane mu duniya da lahira.

Muawiya Muzzy 08149299509


Kaima Likitane Party 1

Da farko wannan hukuncin yanada matuƙar


amfani sosai ga duk wani ɗalibin hisabi yadda
zai gane dukkanin abinda ke damun mutum a
jikin sa, kamar abinda ya shafi cuta ko wani
ciwo da aka rasa gane kanshi misali mutum in
yazo gunka yanaso yasan meyake damunsa

Da farko zaka haɗa sunan mutumin dana


iyayensa ma'ana mahifiyarsa da mahaifinsa sai
kuma ka haɗa adadin sunan ranar da yazo da
kuma lissafin shekarar da ake na larabci

Misali
sunan ta zainab = 69
Sunan mamanta Amina 96
Sunan babanta Muhammad 92
Ranar Lahadi tazo kunga ‫ اﻻﺣﺪ‬zai kama 44
Shekarun Arabic 1444

Muawiya Muzzy 08149299509


Kaima Likitane Party 1

Inka haɗa jumullar zai baka =1745


Sai ka cire 28-28 zai rage 9

Sai ka duba a huruf na ‫اﺑﺠﺪ‬


Wanne ne yake ɗaukar namba 9

To ga jerin cututtukan nan da kuma maganinsu

IDAN DAYA NE YA RAGE WATO HARAFIN ALIF


KENAN (‫)ا‬
Kace masa jinnune masu yawo ranar asabar
kuma ranar suka kama shi sannan basa
barinshi ya ambaci sunan Allah

ALAMOMIN CIWON
1 - Tsananin ciwon kai
Muawiya Muzzy 08149299509
Kaima Likitane Party 1

2 - ciwon ƙafa
3 - ciwon zuciya
haka idanuwanshi zasuke mishi ciwo

MAGANI:
Ana rubuta Qulhuwa, da falaki da nasi, farkon
suratul nahal, farkon suratul Ali-Imran, farkon
suratul A'a-raf, da Ayatul Kursiyu a bashi yasha
ya shafe jiki
Amma da Ma'ul wardi za'a Wanke Rubutun
Sai kuma ai akara rubuta shi a fefa a rataya
masa sannan da ma'ul wardi da za'afaran da
miski za'a haɗa tawadar ayi layar sai a turare
layar da jawi da lubban zakar Zai warke insha
Allahu

Muawiya Muzzy 08149299509


Kaima Likitane Party 1

IDAN KUMA BIYU NE YA RAGE WATO HARFIN


(‫)ب‬

To sihiri ne akai masa wanda aka haɗa da


sassan jikin ƙare, sannan aka je ruwa (kogi) aka
jefa har aka haɗasa da jinnu kuma macece tayi
wannan sihirin

Alamomin ciwon:
Murɗan ciki, idan yayi bacci zakaga ya tashi
yana ta yawo kamar bugagge, saboda yana
bacci mai nauyi sosai

MAGANI:
Ana rubuta Ayatul-Shifa, Ayatul-Kursiyu, da
hatimin Suratul-Baƙara, da Huruful Nuwraniyat
da Musallasin Gazaliy, yayi laya
Sannan a rubuta masa Qulhuwa da Falaki da
Muawiya Muzzy 08149299509
Kaima Likitane Party 1

Nasi da kuma Fatiha da Ayatul-Kursiyu acikin


ƙwarya a wanke a bashi yasha

IDAN KUMA UKU NE YA RAGE WATO HARFIN


(‫)ج‬
Wasu daga cikin ƙungiyar Mayu ko yan shan jini
ko masihirta su suka kama shi, kuma ranar
juma'a ne lokacin yana ƙailula

ALAMOMIN CIWON
Mai wannan cutar Yakan yi korafin jin kasala a
gabobinsa, Ga yawan jin bugun zuciya, kansa na
jijjiga, wani lokacin kuma ya kan yi korafin
dukkan jikinsa nai masa ciwo.
MAGANI:
Ana rubuta Harz Abi Dajanah sannan a rubuta
masa Fatiha da ayatul Kursiyu, da kuma Huruful
nuraniyat da kuma Qulhuwa da nasi da falaƙi
Muawiya Muzzy 08149299509
Kaima Likitane Party 1

wannan shine harz abu Dajanah

Muawiya Muzzy 08149299509


Kaima Likitane Party 1

Muawiya Muzzy 08149299509


Kaima Likitane Party 1

Muawiya Muzzy 08149299509


Kaima Likitane Party 1

IDAN KUMA HUDU NE YA RAGE WATO HARFIN


(‫)د‬
Lallai Wannan Cutar Daga Allah ne, Sannan
sanyi ne da kuma danshi
ALAMOMIN CIWON
Zaike fama da ciwo a jikin sa nau'i uku: (Na
farko) shi ne jikinsa, wanda kodayaushe zai
kasance babu ƙarfi; (Na biyu) kuma zai kasance
mai rauni, ma'ana shi mai rauni ne a kowane
lokaci. (Na uku) shi ne rashin barci, damuwa, da
ciwon zuciya)
MAGANI:
Dole ayiwa mai wannan ciwon (hijama) wato
ƙaho Sai a Rubuta masa suratu Al-Duwr, a
takarda sai a turara wannan takardar da miƙlul
azraq an gama ƙahon sai a liƙa wannan
takardar a gun ƙahon har ya daina zubar da jinin,
sannan sai ake bashi Ma'ul wardi yake sha na
tsawon kwana uku
Muawiya Muzzy 08149299509
Kaima Likitane Party 1

IDAN KUMA BIYAR NE YA RAGE WATO


HARFIN (‫)ﻫﺎ‬
Wato wannan ciwon yasameshine lokacin daYa
fado daga bayan watq dabba, ko daga wani wuri,
ko accident lokacin kuma sai ya firgita, ya yi
sauri ya sha ruwa to wannan shan ruwan da
yayi a wannan lokacin shiya jawo matsalar.

ALAMOMIN CIWON
Ciwon kai da ciwon zuciya da ciwon ƙashi
MAGANI:
Maganin fyaucewa da kuma buguwa yakesha
kamun yaci komai sannan ayi masa hirzi wato a
rubuta suratul jinn sai ayi wa wannan takardar
hayaƙi da ud da kuma kusbara da jawi sai a
naɗe ayi laya

Muawiya Muzzy 08149299509


Kaima Likitane Party 1

IDAN KUMA SHIDA NE YA RAGE WATO


HARFIN (‫)و‬
Ya shiga cikin ruwan domin yayi wanka, amma
lokacin da ya shiga ruwan bai ambaci sunan
Allah ba, kuma hakan ya faru ne a ranar Lahadi,
sai igiyar ruwan da yake ciki ta buge shi.
ALAMOMIN CIWON
Hakan ya jawo masa ciwo a bayansa da
kashinsa, wani lokaci yana kama shi sosai, wani
lokacin kuma yana jin sanyi sosai
MAGANI:
Ake rubuta masa wannan acikin takardu guda
bakwai sai ake kona su hayaƙin takardun suke
bugan jikinsa kullum, ga abinda za'a rubuta
٨٥٤٧٢ ١١٨٤٣٤٥ ٢٤١٢٢٢٢٤ ١١٢٢٦٣
Sannan sai a rubuta masa ayatul shifa'u da
ayatul Kursiyu da wa'yannan harfofin
١٠٤٩٨٣١٤٩٧٥١١ ٥٩٥٣٥١
Muawiya Muzzy 08149299509
Kaima Likitane Party 1

Sannan sai arubuta wannan hatimin tare ayi


laya
‫ى‬ ‫ر‬ ‫ا‬ ‫ب‬
‫ب‬ ‫ى‬ ‫ر‬ ‫ا‬
‫ا‬ ‫ب‬ ‫ى‬ ‫ر‬
‫ر‬ ‫ا‬ ‫ب‬ ‫ى‬

IDAN KUMA 7 NE YA RAGE WATO HARFIN (‫)ز‬


Ranar Juma'a yana tafiya a wani wuri da babu
mutane wurin sai wani shaidani (aljanu) ya bi
shi ya watsa masa turbaya, ko kuma ciwonshi
sihirine daga matarsa.
ALAMOMIN CIWON
Ciwon kai, raunin jiki, da rudani a wurin aiki
MAGANI:
A rubuta masa ayoyi guda 7 na farkon suratul
kahfi, sannan sai a rubuta masa ‫ﻗﻞ ﻣﻮﺳﻰ ﻣﺎ ﺟﺌﺘﻢ‬

Muawiya Muzzy 08149299509


Kaima Likitane Party 1

‫ﺑﻪ اﻟﺴﺤﺮ ان ﷲ ﺳﻴﺒﻄﻠﻪ ان ﷲ ﻻ ﻳﺼﻠﺢ ﻋﻤﻞ اﻟﻤﻔﺴﺪﻳﻦ‬


Abashi yasha kullum har ya samu sauƙi
IDAN KUMA 8 NE YA RAGE WATO HARFIN (‫)ح‬
Watarana ya shiga wani wurin da ya lalace
kuma babu kowa, ko kuma ya shiga kogi da
rana bai ambaci Allah ba, kuma bai nemitsari
daga Shaidan la’ananne ba.
ALAMOMIN CIWON

MAGANI:
IDAN KUMA 9 YA RAGE WATO HARFIN (‫)ط‬
Wannan wata mata ce fajira ta bashi abun ci ko
sha kuma acikin wannan abun akwai asiri
ALAMOMIN CIWON:
Mutum zaike jin ba daɗi ga bacin rain
MAGANI:
A haɗa ibɗali
Muawiya Muzzy 08149299509
Kaima Likitane Party 1

IDAN KUMA 10 NE YA RAGE WATO HARFIN (‫)ي‬


Asiri ne daga Yahudawa ko Banasare ko kuma
asiri irin na yahudawa da banasare
ALAMOMIN CIWON
Ciwon ƙashi, sannan zakaji cikin kanka na
sarawa, sai kuma ciwon haƙori da kasala, wani
kuma har faralais ne ke kamashi
MAGANI:
Ana rubuta suratul sharhi, wato alamnashrah,
sannan sai farkon suratul yasin har zuwa ayar
SALAMUN ƘAULAN MIN RABBI RAHIM, sai
kuma sunan Mala'iku guda huɗun nan
‫ ﻋﺰراﺋﻴﻞ‬،‫ اﺳﺮاﻓﻴﻞ‬،‫ ﻣﻴﻜﺎﺋﻴﻞ‬،‫ﺟﺒﺮﻳﻞ‬
Ayi masa layarsa a rataya masashi insha Allahu
za'a ga biyan buƙata
IDAN KUMA 11 NE YA RAGE WATO HARFIN (‫)ك‬
Wanna kwanciya yayi a bakin ƙofa a wurin da da
ba mutane har iblis da tawagar sa suka shafe
Muawiya Muzzy 08149299509
Kaima Likitane Party 1

shi ma'ana ALJANU kenan, hakan shi ya jawo


masa wannan cutar
MAGANI:
Wannan maganin su, shine a rubuta masa
suratul hashar da farkon suratul Hadid da
farkon walfajri, da kuma ayatul shifa, da suratul
ikhlass، ajikin roba irinta ALMAJIRAI, amma
kalar robar ta kasance green, bayan an rubuta
sai a bashi yasha kwana uku amma fa a saka
sukari a ciki kaɗan
ALAMOMIN CIWON
Mutum zaiji jikinsa yayi masa nauyi, zaike jin
kamar wani abu yana giftawa ta gefenshi,
sannan kuma bazaike samun lokacin bacci ba
IDAN KUMA SHA BIYU NE YA RAGE WATO
HARFIN (‫)ل‬
Wannan ido ne yai masa yawa ko kuma adawa
ALAMOMIN CIWON:

Muawiya Muzzy 08149299509


Kaima Likitane Party 1

Mutum zaike jin ciwon kai, ciwon ciki, da kuma


jiri, sannan duka jikinsa zaike masa ciwo,
wanda zakaga tafin ƙafan mutum da hannunsa
yayi yellow
MAGANI:
Wannan a rubuta masa ayatul Kursiyu da kuma
suratul JINNU zuwa ayar da Allah yace rashawa
ayi masa laya a rataya masa ko kuma a rubuta
masa duk wani hirzi mai kyau.

IDAN KUMA 13 NE YA RAGE WATO HARFIN (‫)م‬


Wannan akwai sa'ido da kuma kamun aljanu
ALAMOMIN CIWON:
Mutum zai rasa ƙarfin jikinsa, zai zamo bashida
ƙarfi ko himma ko kuzari, a jikinsa shi bai iya
tashi, kuma bai iya kwanciya sai an taimaka
masa.
MAGANI:
Muawiya Muzzy 08149299509
Kaima Likitane Party 1

A rubuta masa suratul nun, da Fatiha, da kuma


‫وان ﻳﻜﺎد اﻟﺬﻳﻦ ﻛﻔﺮوا ﻟﻴﺰﻟﻘﻮﻧﻚ ﺑﺎﺑﺼﺮﻫﻢ ﻟﻤﺎ ﺳﻤﻌﻮا اﻟﺬﻛﺮ‬
‫وﻳﻘﻮﻟﻮن اﻧﻪ ﻟﻤﺠﻨﻮن‬
Da suratul ikhlass da falaƙi da nasi abashi
yasha sannan kuma a sake rubutasu a farin
takarda ayi layarshi.

IDAN KUMA 14 NE YA RAGE WATO HARFIN (‫)ن‬:


Wanda wannan adadin ya rage mishi, yana nuna
akwai ciwon ƙwaƙwalwa
ALAMOMIN CIWON:
Yawan ciwon zuciya, sau dayawa zai ke jin
komai baya masa daɗi
MAGANI:
A samu takarda a rubuta masa ayatul Kursiyu,
falaki da nasi da kuma ƙulhuwa, a rataya masa
ko kuma a nema masa maganin ciwon
ƙwaƙwalwa.
Muawiya Muzzy 08149299509
Kaima Likitane Party 1

IDAN KUMA 15 NE YA RAGE WATO HARFIN (‫)س‬


Wannan asiri akai kasa, ko kuma wani ne ya yi
masa baki, wani mai ƙaton ido, ko kuma akwai
wanda yake tsoro
ALAMOMIN CIWON:
Bugun zuciya, yawan mantuwa, rashin bacci,
rashin sha'awa
MAGANI:
A samu takarda a rubuta masa Ayatul Kursiyu,
da kuma suratul lamyaku, da suratul ƙadri, da
suratul ƙuraish, yayi laya dashi insha Allahu zai
warke
IDAN KUMA 16 NE YA RAGE WATO HARFIN (‫)ع‬:
Wannan sihiri akai masa dan a haukatashi
ALAMOMIN CIWON:
Mutum zai kasance yana yawan yin wasu

Muawiya Muzzy 08149299509


Kaima Likitane Party 1

abubuwa kamar Wauta, ko yajishi yana wani


abun kamar bashi ba wasu lokutan
MAGANI:
A rubuta masa suratul bara'atu da wannan
abubuwan
‫ﻧﻬﻄﻬﻄﻴﻞ ﺟﻬﻄﻬﻄﻴﻞ‬ ‫ﻗﻬﻄﻬﻄﻴﻞ‬ ‫ﻣﻬﻄﻬﻄﻴﻞ‬ ‫ﻟﻬﻄﻬﻄﻴﻞ‬
‫ﺧﻬﻄﻬﻄﻴﻞ ﺿﻬﻄﻬﻄﻴﻞ‬
Sai kuma hijabul nuwr, a bashi yasha sannan
kuma ayi laya a rataya masa shi
IDAN KUMA 17 NE YA RAGE WATO HARFIN
(‫)ف‬:
Wannan adadin yana nuna, akwai lokacin da
mutum yake tafiya shi kaɗai, JINNU suka
kamashi
ALAMOMIN CIWON:
Mutum zaike jin jikinshi ba ƙarfi, sannan zaike
razana idan yana bacci, ga ciwon zuciya, da
yawan wasu wasi
Muawiya Muzzy 08149299509
Kaima Likitane Party 1

MAGANI:
Wannan a rubuta masa suratul WAQI'AT da
QULHUWA da falaƙi da nasi da kuma FATIHA a
bashi yasha sannan ayi masa layarshi insha
Allahu zai ji daɗi
IDAN KUMA 18 NE YA RAGE WATO HARFIN
(‫)ص‬:
Akwai sihiri a jikinsa ko kuma kamun Jinnu,
ranar Alhamis, ko kuma yayi bacci a wani gun
da ba mutane aljanun gun sun kamashi
ALAMOMIN CIWON:
Ciwon zuciya, ciwon baya da kuma ciwon cinya
MAGANI:
A rubuta masa suratul Rahman
‫وﻟﻮ اﻧﺰﻟﻨﺎ ﻫﺬا اﻟﻘﺮان ﻋﻠﻰ ﺟﺒﻞ‬
Zuwa ƙarshen sura
Sai kuma wannan

Muawiya Muzzy 08149299509


Kaima Likitane Party 1

‫ﻧﻬﻄﻬﻄﻴﻞ ﺟﻬﻄﻬﻄﻴﻞ‬ ‫ﻗﻬﻄﻬﻄﻴﻞ‬ ‫ﻣﻬﻄﻬﻄﻴﻞ‬ ‫ﻟﻬﻄﻬﻄﻴﻞ‬


‫ﺧﻬﻄﻬﻄﻴﻞ ﺿﻬﻄﻬﻄﻴﻞ‬
Sai kuma wannan
‫ ﺷﻠﺸﺎﺋﻴﻞ‬،‫ ﻋﻮراﺋﻴﻞ‬،‫ ﺛﻮرﺋﻴﻞ‬،‫ وﻗﻼﺋﻴﻞ‬،‫ روﻗﻴﺎﺋﻴﻞ‬،‫ﻣﺨﺎﺋﻴﻞ‬
Sai kuma wannan
‫ﻧﻬﻄﻬﻄﻴﻞ ﺟﻬﻄﻬﻄﻴﻞ‬ ‫ﻗﻬﻄﻬﻄﻴﻞ‬ ‫ﻣﻬﻄﻬﻄﻴﻞ‬ ‫ﻟﻬﻄﻬﻄﻴﻞ‬
‫ﺧﻬﻄﻬﻄﻴﻞ ﺿﻬﻄﻬﻄﻴﻞ‬
Sai wannan
‫وﻗﺪﻣﻨﺎ اﻟﻰ ﻣﺎ ﻋﻤﻠﻮا ﻣﻦ ﻋﻤﻞ ﻓﺠﻌﻠﻨﻪ ﻫﺒﺎء ﻣﻨﺜﻮر‬
‫ﻗﺎل ﻣﻮﺳﻲ ﻣﺎ ﺟﺌﺘﻢ ﺑﻪ اﻟﺴﺤﺮ ان ﷲ ﺳﻴﺒﻄﻠﻪ ان ﷲ ﻻ ﻳﺼﻠﺢ‬
‫ﻋﻤﻞ اﻟﻤﻔﺴﺪﻳﻦ‬
Ake rubuta masa yanasha sannan kuma sai ayi
masa layanshi
IDAN KUMA 19 NE YA RAGE WATO HARFIN (‫)ق‬:
Idan wannan adadin ne ya rage to mayune suka
kamashi ranar talata, kokuma aljanun ruwane
suka kamashi saboda ya shiga ruwa (kogi ko
tafki) bai ambaci sunan Allah ba.
Muawiya Muzzy 08149299509
Kaima Likitane Party 1

ALAMOMIN CIWON:
Matuƙar ciwon kai, sannan zaiji kamar wani abu
ya tokare masa zuciyarshi, ciwon ƙafa, jikin sa
sauti nauyi
MAGANI:
A rubuta masa suratul kahfi, zuwa ‫رﺷﺪا‬
Sai kuma suratul mulk, sannan sai
‫وان ﻳﻜﺎد اﻟﺬﻳﻦ ﻛﻔﺮوا ﻟﻴﺰﻟﻘﻮﻧﻚ ﺑﺎﺑﺼﺮﻫﻢ ﻟﻤﺎ ﺳﻤﻌﻮا اﻟﺬﻛﺮ‬
‫وﻳﻘﻮﻟﻮن اﻧﻪ ﻟﻤﺠﻨﻮن‬
Sai kuma bashi yasha sannan a rubuta masa a
takarda yayi laya dashi
IDAN KUMA 20 NE YA RAGE WATO HARFIN (‫)ر‬:
Wannan matsalar ta samu ne ranar Lahadi ko
ranar Laraba, yana rubutu a wani gun da akwai
aljanu, shine suka kamashi, ma'ana ko rubutu a
jikin katanga ko a ƙasa ko a wani abun.

Muawiya Muzzy 08149299509


Kaima Likitane Party 1

ALAMOMIN CIWON:
Mura, sannan zaike jin kamar ana taɓa masa
fatar jikinsa, ciwon kai da kuma zuciya
MAGANI:
Wannan a rubuta masa maganin aljanun iska
(ma'ana jajayen ALJANU)
Za'a iya rubuta masa farkon suratul saffat zuwa
‫ﺛﺎﻗﺐ‬
Sai kuma farkon suratul kahfi sai a turara layar
da tufaful Jinnu

IDAN KUMA 21 NE YA RAGE WATO HARFIN


(‫)ش‬:
Wannan ya shiga wani tsohon gu, wanda anjima
baa cika shiga gun ba, misali kamar wani
tsohon gida da aka jima baa shigaba, shine
jinnun gun suka riƙeshi, sannan sun taɓa kanshi,
Muawiya Muzzy 08149299509
Kaima Likitane Party 1

da zuciyarshi.
ALAMOMIN CIWON:
Ciwon kai, zaike jin jikinshi kamar ana hura
wuta
MAGANI:
Wannan a rubuta mishi maganin jinnu
IDAN KUMA 22 NE YA RAGE WATO HARFIN
(‫)ت‬:
Wannan jinnune ke sonshi, ko kuma sa'ido na
mutane, ko kuma wata mata tai masa asiri
saboda tana son shi tanason hankali shi ya
dawo kanta
ALAMOMIN CIWON:
Ciwon kai, da kuma zafin jiki
MAGANI:
Wannan shima a haɗa masa maganin jinnu ko
kuma maganar karya sammu

Muawiya Muzzy 08149299509


Kaima Likitane Party 1

IDAN KUMA 23 NE YA RAGE WATO HARFIN


(‫)ث‬:
Jinnu ne, wani ƙaulin akace ɗan Sarkin aljanu
ALAMOMIN CIWON:
Ciwon baya, ciwon kai, da zafin ido
MAGANI:
Wannan maganin jinnu za'a haɗa masa
IDAN KUMA 24 NE YA RAGE WATO HARFIN
(‫)ض‬:
Wannan sihiri akai masa, a wani ƙaulin kuma
ɗan aljani ne ya kamashi ranar Lahadi
ALAMOMIN CIWON:
Ciwon baya, gushewar hankali, kamar mantuwa,
rashin samun cikakken bacci
MAGANI:
A rubuta masa wayan nan surorin
Muawiya Muzzy 08149299509
Kaima Likitane Party 1

‫ﺳﻮرة اﻻﻧﻔﻄﺎر‬
‫ﺳﻮرة اﻻﻧﺸﻘﺎق‬
‫ﺳﻮرة اﻟﻄﺎرق‬
‫ﺳﻮرة اﻟﺬارﻳﺔ‬
‫ﺳﻮرة اﻟﻌﺎدﻳﺎت‬
Ayi masa laya sannan arubuta masa yasha.

IDAN KUMA 25 NE YA RAGE WATO HARFIN(‫)ظ‬:


Iskane suka kamashi a ƙarƙashin wata bishiya
ko kusa da wani kududdufi
ALAMOMIN CIWON:
Jikinsa duka zaiyi rauni, ga kuma matuƙar
ciwon zuciya
MAGANI:
A rubuta masa suratul yasin da ayatul shifa
kullum a bashi yanasha sannan ayi masa laya
Muawiya Muzzy 08149299509
Kaima Likitane Party 1

dasu

IDAN KUMA 26 NE YA RAGE WATO HARFIN (‫)غ‬:


Wannan aljanune suka kamashi ranar juma'a ko
kuma dai wani babban mutum ne ya rufe masa
harkokinsa ko kuma akwai wa'yanda yake tsoro
ALAMOMIN CIWON:
Ciwon baya da zuciya da kuma ciwon kai,
sannan za'a ga mutum yana rama
MAGANI:
A rubuta masa laqad ja'akum
Sai kuma a rubuta masa suratul nuwr, a bashi
yasha kuma ai masa laya

Muawiya Muzzy 08149299509


Kaima Likitane Party 1
Alhamdulillah anan maka zo ƙarshen wannan
littafin mai albarka, mu haɗu a kashi na biyu
mai suna KAIMA LIKITANE 2, duk wanda Allah
yasa ya mallaki wannan littafin to ya saka iyaye
na acikin addu'a da dukkan musulman duniya
baki ɗaya

Ina muku tallan littafina mai suna


1 Ɗalasimai zallah
2 Kaima likita ne 2
3 Kumfayakun
4 Aja'ibu Zallah
5 Jalabi Zallah
6 Dafa'i Zallah
Da sauran litattafan mu, ku tumtuɓe mu ta
wannan layin WhatsApp ko kira 08149299509

Sannan zaku iya binmu ta Facebook ta wannan

account ɗinmu MUAWIYA MUZZY

Muawiya Muzzy 08149299509

You might also like