You are on page 1of 26

GISHIRIN AURE

NA

ALQAMAH HASSAN MAYALO


GABATARWA
Da sunan Allah mai rahamah mai jinkai, godiya ta tabbata ga Allah madaukakin sarki,
tsira da aminci su tabbata ga shugaban halittu {S.A.W} da iyalan gidansa da matansa
tsarkakku. Bayan haka, wannan littafi GISHIRIN AURE ya kunshi abubuwan da suka
faru gidan Manzon Allah {S.A.W} kamar:
 Hankurinsa da matansa
 Iya zamantakewarsa da su
 Nuna soyyayarsa garesu don muyi koyi da fiyayyen halitta
 Dakuma wasu hadisan da suka shafi zaman aure
Don haka GARGADI ga mai karatu kada ya kuskura ya soki daya daga cikin
UWAYENMU wato matan Manzon Allah {S.A.W} domin Qur’ani yafada mana cewa su
uwayen muminai ne duk wanda ya sokesu baida imani {Suratul Ahzab Ayah:6}. Zanyi
kokarin fadin inda nasamo kowace magana da na fada Insha Allah.
Allah yabamu ladar da ke ciki.

Alqamah Hassan Mayalo

2
DALILIN RUBUTA WANNAN LITTAFI
Daga lokacin da na fahimci cewa ‘yan uwa mata suna yawan karatun littafan soyayyar da
bata da asali, wadda masu rubuce- rubuce akan hakan suke tsarawa, wata karya ce ko
kuma abinda yafaru amma babu karantarwa musulunci aciki, nafara tunanin ya zanzo da
wani litttafi wanda ya kunshi soyayyar gidan Annabi{S.A.W} don karantarwa,
nishadantarwa, da kuma koyi da Manzon Allah{S.A.W} sai Allah ya hadani da wata
matashiya don yin hakan, itace wata muhadarah da Ash-shekh Aliyu al-qarni na saudiya
yayi akan hakan mai suna Ummul-Afaf wato Aisha{R.A}.
Bayan na saurareta sai na samu matashiya akan wannan aikin ina rokon Allah ya sakama
Shekh da mafificin alkhairi dani dakuma duk wanda yataimaka wurin yada wannan littafi
da kuma wanda ya karanta ko saurara yayi aiki dashi. Amin.

Alqamah Hassan Mayalo

3
AURE NAKE SO
Wannan shine taken duk wani lafiyayye da yakai lokacin yin aure, yanada karfin hakan ko
baida, amma zai fadi wannan, to ga shawara:
Daga lokacin dakaji kana son aure, to kafara addu’a dare da rana, Allah ya baka mata ta
gari. Idan kaga wadda kake so, to sai kaba Allah zabi (Istikharah) kamar yarda Annabi
(S.A.W) ya koyar, ga ma’narta:
“Ya Allah inaneman zabin ka da iliminka, ina neman ikon ka da ikon ka, ina rokon
ka daga cikin falalarka mai girma, domin kai kasani, ni ban sani ba, kai ke bada iko
ni ban badawa, kuma kaine masani boyayyin abubuwa (gaibi). Ya Allah idan kasan
wanan al’amarin (aurena da wance/wane) alkhairi ne gareni da addinina da rayuwa
ta, da kuma karshen al’amarina, to ka bani ikon yin shi, idan kuma kasan sharri ne
(aurena da wance/wane) agareni da addinina da rayuwata da kuma karshen
al’amarina, to kajuyar da shi daga gareni, kuma ka kaudani daga gareshi, Kuma ka
kaddara mani alkhairi duk in da yake, sannan kasanya mani albarka a cikinsa” {Bukhari
7/162n.1166} Kuma akiyaye wannan addua’ar (Istikharah),wani baiyima wani, kuma ba
gaskiya bane cewa wai mafarki akeyi na sakamako ba. Sai dai kajira Allah ya zabarmaka
mafi alkhairi ba tareda kasa gaugawa ba.

AURO MAI ASALI `


Idan zaka aura ka zabi gidan kwarai mai asali mai kyau, saboda Annabi (S.A.W) yace “kuyi
zabi don iyalanku (gidan kwarai) domin jijiya ‘yar yaudara ce”. Wannan Hadisin da
masu kama da shi, suna umurtar wanda ke da niyyar aure da yayi bincike akan asalin
wadda zai aura, domin jini ko jijiya na iya bin salsala, ya ki bayyanarda halin gida ko
dabi’ar gida sai akan jika ko da.shiyasa ake samun uba nagari uwa tagari amma diya sai su
zama akasin dabi’ar iyayensu, kila kakan su suka biyo.
Dubi yadda Annabi (S.A.W) yazabi Khadija:
Menene asalinta ? Itace Khadija diyar Khuwailid dan Abdul Uzza dangantakarta ta hadu
da ta Manzon (S.A.W) a kakan ta na hudu (Qusaiyu) kakan Annabi (S.A.W) babanta kuma
Khuwailid ya Kasance shugaban Kabilarsa (Bani-Asad) ya kasance mawadaci, mutumin
kirki, mai yawan kyauta, rikon amana da kuma cika alkawari. Haka kuma dan baffanta
(Warakatu Bin Naufal) ya kasance babban Malamin Injila, kuma mai hikima ne da iya raba

4
gardama ko rikici. Ashe tafito gidan Ilimi da wadata da kuma dabi’ar kwarai {Dabaqaat Ibn

sa’ad:8/14-Al-isabah:4/281}.

Haka kai ma dan uwa, ka duba kafin soyayya ta shiga tsakaninka da wata kada so ya rufe
maka ido. Haka kema ‘yar uwa ana yawan rudar mata da kudi ko wani abu mai kama da su,
kada ki kada kanki cikin wahala kece mai zaman auren da dadi ko babu dadi.

GAUGAWA BATA KUNU


Akwai daga cikin matasa masu karancin tunani akan harkar aure, basu shawara da kowa
akan wadda zasu aura su kawai sun ga tayi masu, kuma basu yarda da kowa ba, bale ma
suyi shawara da shi, suna ganin kowa bai ganewa, su kadai ke ganewa, bayan aure sai suga
abinda basuso, matar ta hallakasu ko dai ta yanke zumuntarsu da danginsu, ko iyayensu ko
abokansu. Wannan duka dalilin rashin shawara ne kafin aure, domin aure ibada ne akwai
mataki da shari’a ta tsara wurin yinshi, daga ciki akwai: shawara.

ABOKAN SHAWARA
Abokan shawara iri biyu ne:
a) Mai goyon bayan ka akowane lokaci
b) Mai fadamaka gaskiya koda batayi ma dadi ba. wannan shine abokin shawara, cikin
‘yan uwanka yake ko ba ciki ba, mahaifin ka shine na farko akan hakan in babu
damar hakan mahaifiyarka itace ta biyu,
domin yana da wuya su kada ka cikin wahala. Idan kuma babu iyayen sai kasami
magabatan ka a shekaru da ilimi da kuma magabatanka a harkokin rayuwa.

YADDA AKE KAI SHAWARA


Idan ka kawo shawara ga wani to kada kayi matsaya cikin bayanin ka, domin dayawa
mutum zai kawo shawara amma kafin yagama magana yayi matsaya, ya nuna cewa
yarinyar diyar kwarai ce, tana da kirki gidan kwarai take, babanta ance shine wane wuri
kaza, kuma dalibar wane ce sannan yace takwarai ce batada matsala. To wannan labarine,
ba neman shawara ba, domin ko anfada masa gaskiya bazai yarda ba yariga ya zabarma
kansa, son yarinyar koda zata zama matsala gareshi, domin so ya rufe idanunsa, ko ka
nuna masa sharrin ko matsalar aurenshi da ita bazai yarda ba.

5
Haka kema kada ki yarda ki amince da auren wani matukar bakiyi shawara ba, karanta
hadisin Fadimatu diyar Qaisi (R.A) lokacinda tazo wurin Manzon Allah (S.A.W) tana
neman shawara cikin mutune uku dasuke neman ta, Mu’awiya bin Abi sufyan da Abu
Jahm da kuma Usamah bin Zaid sai Manzon Allah ( S.A.W) yace “Abu jahm baya sauke
bulalarsa (wato yana yawan bugun mata) mu’awiya kuma yanada karancin tattalin
arziki ina ganin ki auri Usamatu bin Zaid” (sai ta bugi kirjin tat ace Usamah bin Zaid?
yakara cewa “ki auri Usamah” har sau uku sai na aureshi kuma Allah yasa albarka cikin
auren. {Muslim: 1480}

wannan yana nuna cewa ashe mace itama bata auren wani face sai tayi shawara da
magabatanta, domin tana yiyuwa ita soyayya ta rufe mata ido, bata iya hangen matsalolin
masoyinta, kalli wannan fadimah bint Qaisi (R.A) data kawo shawara tsakanin mutune
uku, sai Manzon Allah(S.A.W) yace ta auri Usamah saboda abinda ya hango mata cikin
matsalolin wadancan, da ace ta auri daya daga cikinsu, da taga abinda zai bata mata rai,
kodai tasha duka ga Abu jahm ko kuma matsalar tattalin arziki gidan mu’awiya, amma da
tayi shawara sai aka bata shawara ga wanda hankalinta bai bata ba, taci amfanin shawara.
‘yar uwa kidaure kiyi shawara kafin ki kada kanki cikin ciwon soyayya don kisamu rigakafi
kafin ciwo. Sannan kada ki dauki shawara abin wasa, kije ki kaima tsaran ki abokiyarki
wadda batasan matsalar aure ba,ko ki kaima wadda bata fadamaki gaskiya.

INA GANIN KUN DACE


Yana da kyau asami wasu daga cikin abokan arziki ko ‘yan uwa, a wurin zaben mata ko
miji, wadanda zasu duba dacewa tsakanin wane da wance,su auri junansu,saboda kila wane
mutumin kirki ne ko wance diyar kwarai ce, kamar yarda auren Aisha da Manzon Allah
(S.A.W) ya kasance:
Wata mata da ake kira Khaulatu bint Hakim, tazo wurin Manzon Allah (S.A.W) tace
mashi “ya Manzon Allah (S.A.W) bazaka nemi wadda zata debe maka kewar Khadija
(Matarsa ta farko) cikin budare ko zaurawa ba, sai Manzon Allah (S.A.W) yace “A
cikinbudare wa kike gani ta dace”? tace babu wadda ta dace da kai inba diyar Abubakar
(R.A) ba, yace “To, tafi ki neman mani ita gareshi” Khaulatu ta tashi ta tafi zuwa gidan
Abubakar (R.A) tace: ya Ummu ruman (Mahaifiyar Aisha) Allah Ya saukar maku albarka

6
cikin gidan ku, Manzon Allah (S.A.W) ya aiko ni in nema mashi Aisha”, sai Ummuruman
(mahaifiyar Aisha R.A) tace: zauna har babanta ya dawo.
Koda Abubakar (R.A) ya dawo sai Khaulatu ta fada mashi, yace: tana yi mashi ?diyar dan
uwarsa ce fa? Khaulatu tafi tafada ma Manzon Allah (S.A.W), sai yace: kwarai shi dan
uwana ne kuma diyar sa tanayimani. Sai ta koma wurin Abubakar (R.A) tafada mashi,
sai yace: jirani inzo. Khaulatu (R.A) tace aba Annabi (S.A.W) aure sai an tsaya jira?
Mahaifiyar Aisha (R.A) tace: yayima wani alkawarin ta, kuma Abubakar (R.A) bai taba
alkawari ya saba ba” Sai gashi yadawo yace: ya yarda, bayan yaje ya tambayi wancan
mutumin da yayi ma alkawarin ta, ya nuna ba shi ke son auren ta ba, danshi ya nema ma
ita koda zai musulunta idan ya auri Aisha (R.A), sai Abubakar (R.A) yace to ni zan aurar
da ita ga Manzon Allah (S.A.W){Aghmad:6/210-211}
Kalli yadda Khaulatu (R.A) tayi kokarin hada auren Manzon Allah (S.A.W) da Aisha (R.A)
Allah yasaka mata da Aljannah Amin. Ke ma kiyi kokari ki hada auren mutanen kirki ki
sami alkhairin da ke ciki.

BIREDI A BOLA
Wannan kalma tana nufin kyakkyawar mace amma babu tarbiya,da yawa ake samun maza
marasa zurfin tunani, da zaran sun ga fuskar mace, sai su rude cewa suna son ta komai
illar ta. Sai bayan aure illar ta tabayyana gareshi sai yadawo cizon yatsa. Dan uwa kada
acuce ka da hoda, kada arudeka da kyallin ido, tsaya kazabi matar kwarai. Manzon Allah
(S.A.W) yace “ana auren mace domin abubuwa guda hudu:
i-Domin dukiyarta
ii-Domin dangantarka
iii- Domin kyawonta
iv-Domin addininta, to karibanta da mai addinin hannunka zai ribanta” (Bukhari:
n.5090 da muslim).

Wannan hadisin na nuna mana cewa: ashe akwai dalilan da kesa a auri mace, sai dai
gudane mai kyau. Akan hakan dan uwa katsaya ka natsu kafin neman mata,kazabo mai
addini, wadda zata ji tsoron Allah akan lamuran ka, Imani bai bari ta cutamaka. Amma
duk ka biye ma kyawon mata to zaka tabbata cikin bakin ciki, domin kullun sai an haifi
mace wadda tafi matan zamaninka kyau sai yaya? kullun zaka sake budurwa ko mata?

7
Wannan kesa wasu yin auri-saki su tara yara sama da goma babu mahaifiyar ko daya daga
cikinsu tareda dashi, sai tarbiyarsu ta mashi wuya.

BAN SON SHI


Wannan shine korafin duk wata diya wadda iyayen ta suka shiga gaba wurin auren ta,
kuma suka zabar mata miji da kansu kuma bataji yayi mata ba. Sai dai, karki manta cewa fa
su (iyayenki) suka haife ki, suna sonki fiye da yarda kike son kanki, don haka baza su kaiki
wurin da zaki wulakanta ko wahala ba.
Duk da akwai gure-gurbin iyaye, masu biyema dukiyar da aka basu, idan kika fahimci
hakan, to, ki cigaba da rokon Allah akan yayi maki mafita. Idan babu alkhairi ciki gareki da
yarda Allah ba za’ayishi ba.
Kuma idan kika yi hankuri dazabin su Allah zai kawo maki mafita, karanta wanan Tarihi:-
Akwai wata baiwar Allah zamanin Manzon Allah (S.A.W) mai suna:Zainab bint Jahash
watarana Manzon Allah (S.A.W) yazo yace mata “Ki auri Zaidu bin Haritha, Annabi
(S.A.W) yana matsayin waliyinta ko mai ba da aurenta,tace bazata auri bawaba,saboda
Zaidu bawane sai dai akawo mata wani kuma yakasance da ne, ana cikin hakan sai ga
Ayah ta sauka cewa “bai yi yuwa ga masu Imani (maza) komasu Imani (mata) idan
Allah da Manzonsa suka yanke hukunci yazama suna da wani zabi (wato masu
Imani) acikin al’amarinsu”. {Suratul Ahzab Ayah:36}.
(Wato bai yiwuwa ga mumini namji ko mumina mace ace Allah da Mazonsa sunce kaza, ya
tsaya zabi cikin wannan al-amari, yace ni nafison abu kaza, ko inda dai Allah yace kaza).
Zainab tana jin hakan sai tace “Na yarda da zabin Allah”. A karshe akayi auren kuma Allah
yakaddara mutuwar auren. Sai Allah ya aurar da Zainab ga Manzon Allah (S.A.W) ba wai
nan kasa aka daura auren ba, Allah da kanshi ya aurar da ita gareshi {Ibn Kathir:Suratul-Ahzab Ayah
36}.

mai karatu, ba sai na tambayeka ba wayafi tsakanin Manzon Allah (S.A.W) da kuma Zaidu
bin Haritha? kowa yasan cewa Annabi (S.A.W) yafi, amma da ace Zainab batayi biyayya
ga Allah da Manzonsa ba, da ta halaka Duniya da Lahira, kuma bazata sami abinda takeso
ba. Ashe idan iyayenki suka zabarmaki miji kar kice bakiso kai tsaye, ke dai yi hankuri ki
tashi cikin dare kiyi Sallah’ Raka’a Biyu ko fiye da hakan, ki daga hannunki kice: ya Allah
kasani wane bani son shi, amma zabin ka shine zabina, na kawo kukana gare ka,Allah ka

8
share mani hawaye na idan kuwa alheri ne Allah ka tabbatar mani da shi kuma ka sanya
mani son shi” sai ki cigaba da fadama Allah kukanki kullun kina haka dare da rana har sai
kega abinda kike so, kuma ki cigaba da yin Istikhara kullun, kamar yadda yazo farkon
littafi, in Allah ya yarda zaki ga sakamakon alheri.
Kuma karanta tarihin Julaibibu da Amaryar sa kisha mamaki.

AUREN DOLE
Shin hakane ana iya yima mace auren dole a musulunci? A’A wannan ba gaskiya bane
musulunci ko kadan bai yarda da haka ba. Mu karanta hadisan Manzon Allah (S.A.W)
akan hakan don debe shakka cikin zukatanmu. Abdullahi ibn Abbas (R.A) yace Manzon
Allah (S.A.W) yace “bazaura tafi cancanta akan waliyyinta (wurin aure) budurwa
kuma ana neman izninta kuma shirunta shine yardarta” {muslim da Bukhari:n.5136}
Haka kuma akwai hadisin khansa’u Al-ansariya wadda babanta ya aurar da ita ga wanda
bata so lokacin ma tana bazaura takawo karar hakan wurin Manzon Allah (S.A.W) sai
Annabi (S.A.W) ya raba auren. {Bukhari: 4845}
Wadanan hadisan da masu kama dasu suna hana aurar da mace kowace iri ce bazaura ko
budurwa kafin neman yardarta, kuma koda anyi auren ana iya rabashi. Haramun ne yin
auren dole domin yana cutarda mace cuta ta har abada.

ILLOLIN AUREN DOLE


Idan aka aurar da mace ga wanda bata so yana kawo matsaloli kamar haka:
a) Zaluntar matar
b) Saka rayuwar mijin cikin hadari
c) Saka zuri’ar da suka samu cikin kiyayyar uwarsu
d) Kiyayya ta har abada tsakanin ma’aurata
e) Lalata zumunta tsakanin zuri’ar gidan ma’aurata
f) Keta hakkin dan adam wanda musulunci bai yarda dashi
g) Yana kawo yawan mutuwar aure
Da sauran matsalolin da ban ambata ba, wadanda kaima ka sansu, saboda haka duk auren
da zai iya jawo wadanan matsaloli musulunci bai taba yarda da shi, ba kuma bazai taba
yarda shi ba. Mun gani kuma munji da yawa da suka haukace cikin mata saboda hakan,

9
rayuwa nawa aka rasa saboda wannan bakin aure? Karuwai nawa aka samu saboda auren
dole? Ina kira ga iyaye da su ji tsoron Allah su tuna cewa lallai diyansu amana Allah yaba
su kuma akwai mumunar azaba ga wanda yaci amanar da akabashi.

SON MASOYIN WANI


Son masoyin wani akace koshin wahala, mai karatu wani lokaci ana
tausaya ma wandanda Allah yajarraba da wannan yanayin na son wanda bai son su. Ya
kasance cikin gidan Manzon Allah (S.A.W) akwai wata mata da ake kira da Barirah
takasance farkon lamari baiwa sai A’isha (R.A) ta sayeta takuma ‘yantarda ita to mijinta
wanda ake kira Mugithu anjarrabe shi da son ta kwarai da gaske, ita kuma anjarrabe ta
kinsa kwarai da gaske. tace shi bawa ne ita kuma yanzu diyace baiyiyuwa ta auri bawa,
takai har yana bin lungu-lungu yana kuka,idan yaji ance ta biyo hanyar, karshe da
kiyayyar tayi yawa sai ya zo wurin Manzon Allah (S.A.W) yace Manzon Allah kashiga
cikin maganata da Barirah (R.A) Manzon Allah (S.A.W) ya kira Barirah (R.A) yace
“Barirah mijinki ki koma mashi” tace Manzon Allah umurni ne kake bani dole in koma ?
“Yace a’a ina neman ceto ne kawai” (ga mugithu mijinki) tace to ban ra’ayinshi.
{Bukhari: 4979}

Mai karatu kaji yadda ta kasance gidan Manzon (S.A.W) akan son masoyin wan, don
wannan hadisin ya haramta auren dole idan diya bata so ba’a tilasta auren wani. Domin
duk tausayin Manzon Allah (S.A.W) bai tilasta Barirah (R.A) ba auren Mugith (R.A).

‘YAN MATAN AMARYA


Akwai wasu al’adu da musulunci bai hana ba matukar basu keta haddin Shari’a ba, daga
cikin su akwai wannan: yan matan amarya, dalili shine lokacin da Manzon Allah (S.A.W)
ya auri Aisha (R.A) akwai wata mata mai suna Asma’u bint Yazid (R.A) tace “bayan mun
kai Aisha (R.A) dakinta Manzon (S.A.W) ya shigo ya samemu cikin dakin amarya (Aisha)
sai aka kawo mana madara, Manzon Allah (S.A.W) ya sha yaba Aisha (R.A) yace tasha sai
ta kama jin kunya, sai nayi mata tsawa nace ta karba, sannan ta karba tasha, sai yace “ba
‘yan uwanki” mukace bamu sha, Annabi (S.A.W) yace “karku hada yunwa da karya” sai
muka karba muka sha.{Adabuz-zifaf: Albani}

10
Mai karatu: lura da wannan hadisin: Ango (Manzon Allah) ya shigo dakin amarya (Aishah
R.A) ya taradda wasu ciki kuma bai hana ba, to kenan ba laifi bane hakan idan an tsaya a
haka.Amma abinda ‘yan matan Amarya sukeyi yanzu, kaga kowace yarinya tareda
saurayin ta, wanda nan wurin ake kulla wannan soyayyar, bai halatta ba, abin yakai har
ana yin alfasha a lokacin kai amarya dakin ta. Allah ya tsaremu Amin.

HALAN BAIWA KA AURO


Haka wasu matan zamanin mu suke cewa idan mijinsu ya umurce da wasu ayukka
wadanda ga al-adar mu maza aka sani da su, kamar wankin mota ko kula da wasu dabbobi
da mijin yake dasu. ‘yar uwa tayani karatun wannan hadisin mai zuwa na Asma’u diyar
Abubakar Assidik (R.A) matar Zubair dan Awwam (R.A) tace Zubairu ya aure ni lokacin
da baida ko sisi kuma baida bawa (ko dan aiki) in banda doki guda daya wanda ni nike
zuwa in debo mai ruwa (in bashi ya sha) kuma in tafi in nemo mashi haki, kuma lokacin
ban iya kwaba dussa ba, wasu cikin makwabtanmu na madinah suke kwaba mani dussa
don sun kasance matane masu gaskiya, kuma na kasance ina zuwa gonan Zubair (mijinta)
in samo haki ko harawa (don in ba dokin) wata rana sai na hadu da Manzon Allah (S.A.W)
harawa na saman kai na, shi kuma ya jawo rakumi sai ya dukar da rakumin sa yace in hau,
sai naji kunyar hawa nawuce ban hau ba, saboda ina jin kunyar in bi bayan maza kan
hanya, kuma natuno kishin mijina Zubair, koda na iso gida sai na iske Zubair (R.A) na
fadama shi abunda ya faru kan sai yace “wallahi ni dauko harawar da kikayi (gaban Manzo
Allah (S.A.W) yafi tsanani gareni akan hawan rakumin da zakiyi” Asma’u (R.A) tace haka
na kasance har sai da Abubakar (R.A) ya aiko mani bawa wanda yadauke mani nauyin kula
da doki, tace naji kamar ya ‘yantadda ni. {Bukhari: 4926}
Allahu akbar matar sahabin Annabi (S.A.W) ace ta kasance tana kula da dokin mijinta har
tayo mashi haki ko harawa, anya matan mu na iya yin hakan? ke taba wanke motar mai
gidan ki ko sau dayane ? wai ma shin yaya zaman ki yake da ke dashi ? shin kesan cewa
karkashin kyautatamashi aljanarki take ?
Sai gareka Alhaji, kasan ko ka fahimci cewa lallai gaskiya ne maza sun fi mata kishi ?
domin duk da wahalar da Asama’u takeyi ba kunya kadai ta hanata hawan rakumin
Manzon Allah (S.A.W) akwai tsoron kishin mijinta inda zai ganta kafin su isa gida tareda

11
Manzon Allah (S.A.W) ya dauko ta, dole in Zubair (R.A) yagansu sai ya ji wani abu
azuciyarsa. Ashe kubar lakama mata kishi su kadai har ku maza kuna da naku.

WASAR KANEN MIJI


Daga cikin miyagun al’adun kasar nan akwai wannan al’ada wasar kanen miji, wanda
dayawa ana hallatadda wannan wasar alhali Allah ya hana ta, ya zo acikin hadisin Manzon
tsira (S.A.W) hadisin Uqbatu bin Amir yace Manzon Allah(S.A.W) yace “na haneku daga
shiga cikin mata” sai wani mutum daga cikin mutanen madinah yace “ya Manzon Allah
wasar kanen miji fa? Sai Annabi yace “wasar kanen miji mutuwa ce” {Bukhari:n.5232 da

Muslim:n.1341}

Mai hankali, kalli halin da muke ciki yanzu dangane da wannan matsala, daga cikin iyaye
akwai masu ganin idan mace bata wasa da kanen mijinta to yakamata asake ta, don bata
son dangin mijinta, shi mijin ace matarshi ta raba shi da danginsa ko ace sihiri tayimasa.
Allah ya kyauta, to jama’a musan cewa lallai haramun ne kanen miji ya shiga gidan matar
yayansa idan babu muharraminta, balle har takai asamu wasa tsakaninsu. Ba’ayima Allah
wayo, sau nawa aka samu akasin wasa tsakanin kanen miji da matar yayansa? Diya nawa
aka haifa tareda kanin miji?

KAR KA MANTA
Kasance mai tuna alkhairan matarka ko bayan ranta, Saboda Manzon Allah (S.A.W) yana
yawan tuna alkhairan matar sa Khadija.Daga ciki akwai watarana da wata bakuwa ta shigo
gidan Aisha sai Annabi (S.A.W) yayi mata tarbo mai kyau, yana cewa “yaya su wane?
Yaya su wance? Kowa na lafiya?”
Aisha kuma (cikin fushi da kishi) sai ta tambayi Manzon Allah (S.A.W), wannan kuma
wacece kake girmama ta haka? Sai Manzon Allah (S.A.W) yace “ta kasance tana kawo
mana ziyara lokacin Khadija” Aisha {R.A} tace wai kai haryanzu bakaga wata mace
wadda tafi Khadija ba? tsohowar da ta mutu tun da dadewa? Annabi (S.A.W) yace “Allah
bai bani kamar Khadija ba” {Ahmad:6/117-118}
Fa’idah:

12
Dan uwana kula da wannan Hadisin, harbayan ran Khadija Annabi (S.A.W) yana tuna
alkhairanta yana kyautatawa abokanta, wannan yana nuna soyayyar Annabi (S.A.W) da
Khadija babba ce, kuma ya nuna cewa sunyi zama mai kyau tare.
‘Yar uwa ki rika kyautatawa mijinki kamar yarda Khadija ta kasance tanayiwa mijinta
Annabi (S.A.W) Wanda bai mance da ita ba har bayan mutuwarta. Kamar yarda zakiji
zuwa gaba, amma tambaya inda ke ce matsayin Aisha yazakiyi? Wannan abokiyar
Khadijah ce kawai, amma Annabi{S.A.W} yayimata tarbo mai kyau kuma gaban matarsa
Aishah{R.A} tana gani, to kenan inda Khadijah{R.A} ce fa, me zai faru? Yaya kishin Aisha
zai kasance?

BAKA FAHIMCE TA BA NE
Da yawa ake samun rashin fahimta tsakanin ma’aurata, mata tayi wani abu domin
kyautatawa mijinta amma sai tayi kuskure, sai kaga miji ya fusata, maimakon yayi
tambayar dalilin yin hakan. Sai ya zartar da hukunci cikin fushi kuma yadawo yana
nadama. Karanta Hadisinan mai zuwa:
Imamul Bukhari ya ruwaito cewa wata rana Manzon (S.A.W) yayi wata tafiya koda ya
dawo sai ya taradda Aisha (R.A) ta sawo wasu kayan gyaran daki don Annabi (S.A.W) ya
ga kyawon su, daga cikinsu akwai Labule mai hoto, koda Manzon Allah (S.A.W) yaga
labulen da hoto sai yaki shiga dakin Aisha (R.A) sai ranta yabaci, sai Annabi (S.A.W) yace
“menene wannan ya Aisha? Tace “Labule ne nasawo” (don inyima kawa dashi ya Manzon
Allah (S.A.W) sai yace “Ai Mala’ikun Rahama basu shiga gidan da keda kare ko hoto”
{Bukhari:n.5957}

Lura da wannan Hadisin, zaka ga cewa Aisha{R.A} tayi kokarinta don taga cewa ta burge
Manzon Allah (S.A.W) amma kuma sai tayi kuskure, da yake Manzon Allah (S.A.W)
mutum ne mai sanyi hali, bai yimata fada ba, ko ya zargeta, sai dai ya koyarda ita abinda
bata sani ba. Irin hakan tana faruwa tsakanin ma’aurata dayan su ya aikata wani abu don
burge dayan, amma sai yayi kuskure, masamman mata, zata aikata wani abu don burge
mijinta, shi kuma idan bai fahimce ta ba sai yayita fada, karshe sai ta rude tarasa
yazatayi.Allah ya tsaremu daga hukunci babu bincike

13
TAYA TA JINYA
Da yawa ake samun wani kuskure daga ma’aurata, idan daya na rashin lafiya daya bai kula
shi yadda yakamata.
Karanta wannan daga gidan Annabi (S.A.W) wata rana Manzon Allah (S.A.W) ya dawo ya
sami Aisha (R.A) tana jin mura da ciwon kai, sai tace “wayyo kai na!” sai Manzon Allah
(S.A.W) yace “a’a wayyo kaina dai” {Bukhari: 5666}
Darasi:
Ashe idan mata tana ciwo to ya shafi mijinta, tare zasu yi jinya, ko haka mijin ki yake?
Kema haka kike?
Wani wai shi kunya yake ji, ko kuma baison matarsa tarenashi, amma ya manta cewa da
ace gidansu take, da iyayenta ne za suyi jinyar ta tareda cikakkar kulawa. Amma yacirota
daga gidansu yakawota gidansa ya aje babu cikakken tausayi. Allah ya tsaremu da
bushewar zuciya.

BAI IYA SAKIN KI, KYALE SHI KAWAI


Kwarai duk mai wannan aikin mijinta bai iya sakinta, koda kuwa tana mashi laifi. An
ruwaito daga Manzon Allah (S.A.W.) cewa watarana ya saki Hafsah (R.A) diyar Umar dan
Khaddab {R.A} sai ga Mala’ika Jibril (A.S) yazo yace “mashi Allah yana umartar ka
kamaida Hafsah {R.A}domin ta kasance mai yawan azumin nafilah kuma mai yawan
tsayuwar dare” {Sallar nafilah}
Wato matukar mace tana yawan Azumin nafilah da kuma Sallar dare (Nafilah) to Mijinta
ko yaya suke samun rashin jittuwa, bai iya sakinta domin Allah yana tareda ita kuma zata
daina cuta mashi da yarda Allah. Dama karancin ibada kesa shedan ya samu shiga tsakanin
ma’aurata. {Assahihah:Albani:5/17}

JIRATA MANA
Watarana Manzon Allah (S.A.W) yadawo daga wata tafiya sai ya tsaya yayi zango kan
hanya, matarshi Aisha tana tare da shi a wannan tafiyar, sai tafita daga cikin rumfarta don
ta biya bukatar ta, sai Sarkar ta tafadi ta nemeta bata gani ba, sai ta dawo tafada ma

14
Manzon Allah (S.A.W) yace ma Sahabansa (R.A) ku tafi kunemo sarkar Aisha (R.A) suka
tafi sukata neman ta basu ganeta ba, har aka dauki lokaci mai tsawo, kuma gashi basu
tareda ruwa don alwala ga lokacin sallah yayi.sai ran Sahabai (R.A) ya baci akan dadewa
da akayi wurin suka tafi suka fada ma babanta Abubakar (R.A) don yayi mata magana sai
Abubakar {R.A} ya tafi wurin ta ya sameta Manzon Allah (S.A.W) ya kwanta akan
kafafunta yana kwana, Abubakar (R.A) yazo yanata yi mata fada, cewa yaya zaki tsare
Manzon (S.A.W) da mutane akan sarka?
Aisha (R.A) tace Abubakar (R.A) ya kasance yana ta dangwarata da sanda, kuma ina jin
ciwo sosai, amma ban motsaba saboda kada in ta da Manzon Allah (S.A.W) daga barcin
sa… {Bukhari:7/106 n.3773= Muslim:9/228 n.5164}
Abbubwan fahimta:
Nafarko:
Jirata (wato matarka) dayawa wasu idan zasu fita da iyalansu, sai anyi ta samun matsala da
juna, shi (Mijin) baida hankuri, ita kuma macece sai tayi halinsu nagado (wato jinkiri) ta
dauko wannan ta dauko wancan, to kai namiji kayi hankuri kajira ta matukar jiran ba zai
kawo matsalar da tafi shi ba, hujja ga hadisi ka karanta akwai hikima cikin halittar mata da
rauni domin da kamar maza suke da aure bai dadi kowa kamar dutse ko gatari.
Na Biyu:
Kada karena kayan matarka, kaga wannan sarka ce wadda ana iya sayenta, amma Manzon
Allah (S.A.W) ya bata muhimmanci kamar yadda Aisha (R.A) ta bata muhimmanci, kai
kake ganin wannan ba wani abu ne ba, amma ita wurinta babba ne.
Na Uku:
Ki yi kokari kiba mijinki kyakkyawar natsuwa musamman idan yana barci, don ke ji Aisha
(R.A) babanta yana dukar ta amma bata motsaba don kar mijin ta ya farka daga barcin sa.
Saboda haka hana kowa magana ko motsi idan mai gida yana na barci, ibadace wurin ki
bashi damar barci ko hutu, kuma kinada lada akan haka.
Na hudu
Ashe matar babba itama babba ce don kunji Aisha (R.A) tasa an tsaida mutane saboda ita.
Sai dai matar babba kijin tsoron Allah ki tausayama yan aikin gidanki kada Allah yajuya
lamarin kidawo kasa sukoma sama, don Allah na da karfin yin hakan. Domin da yawa ake
samun matan manya suna wulakanta ‘yan aikinsu, suna zama dasu tamkar dabbobi ko bayi,

15
kusani Allah yana iya juya zamanku sama ta dawo kasa, kamar yadda Manzon Allah
{S.A.W} ya fadama Abu Mas’ud (R.A) lokacinda ya mari bawansa. Bawani abu kikaba
Allah ba yahalicceki hajiya ba, su kuma ba laifi suka yiwa Allah ba ya halicce su ‘yan aiki
ba, Allah yasa mugane amin.

CE KA YARDA
Na’am ce ka yarda, idan matar ka tace ga yadda takeso duba idan babu laifi, to ka yarda
koda kai baiyi ma ba, yi hankuri don kaine babba akanta kalli wannan:
Lokacinda Aisha (R.A) tayi aikin hajji tareda Manzon Allah (S.A.W) da kuma sauran
matansa, Haila ta kama Aisha {R.A} bayan aikin Hajji sai dai kawai batayi dawafiba (na
umurah) sai tace ma Manzon (S.A.W) tana son taje ta sake dauko niyar aikin (umurah)
don tayi Dawafi sai Annabi (S.A.W) yace “To ai ke kare aikin umurarki” tace: ina jin
wani abu (azuciya ta) cewa banyi dawafi ba” Sai Manzon Allah (S.A.W) yace: ma Abdul-
Rahman (kanenta) ya tafi da ita (Tan’im) ta sake dauko niyar aikin, kuma Annabi (S.A.W)
yasa aka jirata har sai da takare. {Bukhari: 1692}
Darasin hadisi:
Wato Aisha kishi take da sauran matan Manzon Allah (S.A.W) cewa kowa daga cikin su
tayi dawafi (nakarshe) sai dai ita kawai, kuma Manzon Allah (S.A.W) yanada saukin hali
kuma yayi hankurin jiranta har sai da takare.Dan uwa matar ka, riketa kwarai,ka yarda da
zabinta koda bai yima ba matukar bai saba ma Allah ba, sunnah ce domin kai ne kawai
gareta tausaya mata.

KISHI NA BAI SANI YIN KARYA


Kadan daga cikin mata ne suke da wannan juriyar, cewa basu yi wa kishiyoyinsu karya,
daga cikin su akwai Aisha (R.A) lokacin da take yabon sauran matan Annabi (S.A.W) ga
abinda tace ga sauran matan
Ban taba ganin mace mai riko da addini,tsoron Allah, gaskiyar labari, (duk abinda tafadi
gaskiyane) sada zumunta, girman sadaka, da tsananin bada rayuwa ga duk aikinda zai
kusantadda mutum ga Allah irin zainab ba. {muslim}
Tace ga Swafiyyah {R.A} Ban taba ganin macen da ta iya abinci mai dadi irinta ba.
{mu’minat:Bakar ismail}

16
Tace ga Juwariya {R.A} Bantaba ganin matar da dake da girman albarka ga ‘yan uwanta
ba irinta. {Al-rijalu wan nisa’u}
Tace ga Maimunah {R.A} Duk ta fimu tsoron Allah (mu matan Annabi S.A.W) kuma tafi
mu sada zumunta. {Imamul-Hakim}
Tace ga Saudah Ban taba ganin matarda naso inzama cikin dangintaba irin
Saudah.{muslim}
‘Yar uwa ba karamin aiki bane fadin alkharin kishiya, sai karfin Imani, roki Allah yasa ki
cikinsu. Domin mafi yawan matan mu na yanzu bas u fadin alkhairin kishiyar su karshe
ma karin maganar su yana karewa ne akan sukar kishiyar su misali daga cikin fadarsu:
a. Abu dunkule ba’a san me yakunsa ba= cikin kishiya
b. Bakin ciki= ganin kishiya kullum
c. To! hankuri dole= tunda an auroni da kudin kishiya.
Dadai sauran maganganu marasa dadi akan kishiya, amma mace mai Imani ba’a samunta
cikin wannan, kisani fadin alkhairan abokiyar zamanki zai taimaka wurin zama mai kyau
tsakaninku, kuma matar da take fadin alkhairan abokiyar zamanta miji yafi sonta, saboda
gaskiya tana taimakon mai fadinta.

TANA DA DALILI
Kwarai tana da dalili tayi kishi matukar bai taba Shariah ba Imamu Muslim ya ruwaito
cewa wani dare Manzon Allah (S.A.W) ya fita daga cikin dakin Aisha (R.A) sai kishi
yakamata koda Annabi (S.A.W) yadawo ya ga tana kishi (fushi) sai yace “Aisha kishi ya
kamaki? Sai tace “Don me mata Irina bazata yi kishin mijinta ba irinka? {Muslim: 2815}
Wato dolene matar babban mutum tayi kishin mijinta wannan shi kesa anfi samun kishi a
wurin matan malamai da masu mulki, domin malamai su ke karanta ‘yan cin mace a
musulunci kuma wasunsu suna kokarin baiwa matansu wannan'yancin sai ita kuma matar
ta dauka ta mallake mijinta bai iya sakinta ko ladabtadda ita. Su ko masu mulki saboda
suna yawan karin aure, wani lokacin don samun kuri’a ko wani dalili na daban.
Manufa:- wato matar fiyayyen halitta dole ne tayi kishinsa kar wata ta amshe shi, wannan
darasin matan malamai shuwagabanni, da masu dukiya ne, idan kaga matar ka bata kishin
ka, to akwai matsala, kai ba kowa bane ko kuma bata sonka.

17
INDA KAI NE, YA ZAKAYI ?
Wani abu ya faru gidan Manzon Allah (S.A.W) wata rana kwanan A’isha (R.A) yayi baki,
ita kuma A’isha (R.A) tayi daren tuwo sai Manzon Allah (S.A.W) ya aika gidan daya daga
cikin matansa (R.A) ta aiko da abinci, sai A’isha (R.A) ta kasa hankuri ta labe kan hanya sai
da yaro ya biyo sai ta kife abincin yazube, kuma kwanon ya fashe. Sai Manzon Allah
(S.A.W) ya zo ya kwashe abincin kuma ya kai shi wurin baki yace “kuci mamar ku tayi
kishi” bayan ancanye sai A’isha (R.A) ta aiko da nata kuma aka canye, sannan ya dauki
fasasshen kwano ya aika ma A’isha (R.A) nata kwanon kuma ya aika ma dayan matar (R.A)
kuma Annabi bai nuna ma A’isha (R.A) komai ba da yadawo gida, ba fada ba zagi.{ fathul bari:
9/324}

Zaka iya hankurin wannan? ace kayi baki mai girki ta makara kuma kasamo abinci wani
wuri amma kuma tazubar wai don kishi?
To, kema inda kece me zaki ji? ke zubarda abinci don kar aci amma kuma akwasheshi
hakanan da kasar aci me yafi wannan haushi? Amma tace Annabi (S.A.W) bayan hukuncin
da yayi mata daukar kwanonta akaba swafiyyah (R.A) mai abincin farkon bai kara yi mata
maganar ba har yabar duniya.
in da nine ko kai,farko dai sai tasha duka da zagi,in har ba’a saketa ba,kuma da sai anyi
shekaru ana maimaita wannan magana. Kai dadin zaman aure sai Annabi (S.A.W)
Tambihi: Jama’a ana yima mata uzuri wani lokaci, idan kishi ya kwashe su zuwa ga laifi,
domin idan kace komai zaka yi fada akanshi sai kazama mahaukaci don kullun sai ka ga
irin hakan. Domin itama A’isha (R.A) bayan ta huce tayi nadama kan wannan kuskuren,to
don Allah kabarta taji da haushi guda.

TABDI JAM, MAGANA TA GIRMA


Tabbas magana tagirma Imamu Muslim ya ruwaito cewa Aisha (R.A) watarana tacema
wadanda ke tareda ita (dalibanta) kuna son inbaku labarina da Manzon Allah (S.A.W).
Suka ce muna so.
Tace wani dare ne Manzon Allah (S.A.W) yana daki na sai da ya bari na kwanta ya zaci
nayi kwana, sai ya dauki takalminsa ahankali, ya dauki mayafinsa ahankali ya bude daki
ahankali, ya fita ahankali, ni kuma na dauki mayafina na bishi bai sani ba, yana tafiya ina
binshi haryakai makabarta, ya daga hannunsa yana addu’a, sai ya juyo, ni kuma ina gaban

18
shi, sai ya kara sauri, nima na kara sauri, sai yakama gudu nima na kama gudu na rigashi
shiga daki, ko da ya shigo sai yajini ina numfashi yace:Aisha me ya same ki kinata nishi
haka? Na ce babu komai ya Manzon Allah (S.A.W) sai Annabi (S.A.W) yace ko dai ki
gayamin ko kuma Allah ya gayamin.Sai nace nagaka fita sai naji tsoron ka shiga wurin
matan ka shiyasa na bika.Sai Manzon Allah (S.A.W) yace“Jibirilu ne yazo min
yace:Ubangijinka ya Umurce ka kaje ka yima mutane makabartar baki’a Addu’a, sai
naji tsoron kar in tadake kuma kar kiji tsoro” {muslim:2/669 n.974}
Faidar hadisi:
a. Son Aisha {R.A} ga Manzon Allah (S.A.W) wanda har bata iya barci sai inyayi
barci.
b. Kulawa mai kyau tsakanin mata da miji ta yadda Aisha (R.A) tana kula Manzon
Allah (S.A.W) dare da rana.
c. Hankuri Manzon Allah (S.A.W) ta yadda baiyima Aisha {R.A}fada ba bayan ta
fada mashi cewa tabishine har makabarta kuma tana tunanin ko ya shiga wurin
matansa, inda kai ne yaya?...kana iya cewa bata yarda da kai ba don haka sai fada ko
duka.
d. Kishin mata wanda ya halatta matukar bai wuce haddin shari’ah ba yakai ga
hasada, domin wasu matan suna labewa da sunan kishi amma suna hasadar sauran
mata.
e. Kulawar Manzon Allah (S.A.W) ga Aisha {R.A} ta yadda ya ji tana numfashi ya
tambaye ta lafiya?
f. Tsananin son Aisha (R.A) ga Manzon Allah (S.A.W) ta yadda ta bi dare duk inda
ya shiga suje tare, har yagama abinda ya ke yi sudawo tare, don kada wani abu ya
sameshi.
g. Mata tana iya bin mijinta ba wai don bata yarda da shi ba, sai dai don kiyaye lafiyar
shi, kada ya fada wani hali cikin duhun dare ko rana, karshe ita zata fada cikin
wahala.

19
KISHI YA GIRMA
Haka ne wannan kishin babba ne bayan Manzon (S.A.W) yace ma Aisha (R.A) a cikin
Hadisin da ya gabata (na jinyarta) cewa “ni dai ne zance wayyo kaina” sai yace: baki son
kirigani mutuwa, inyimaki wanka da sallah insamaki turare da kaina? Tace don
kadawo ka auro wata mata kasata dakina ko? Kaidai karigani mutuwa nafi son haka {Bukhari:
5666}.

Darasi:
Wato Aisha (R.A.) bata yarda ace ayi mata kishiya ko bayan bata da rai ba, sai dai tun da
Allah ya halatta hakan ba yadda zatayi Radiyallahu Anha. Wannan ya nuna girman kishin
Aisha (R.A) domin bata yarda ace Manzon Allah (S.A.W) kanshi yayi mata wanka ba,
kuma musani duk matar da bata kishin mijinta bata shiga Aljannah.

BASU GANE BA (KISHIYOYINTA)


Dayawa idan miji ya karkata ga amarya ko uwar gida, sai ace ai sihiri tayi mashi alhali
karya ce, kula dashi tafi sauran mata. karanta kiji:
Gidan Manzon Allah (S.A.W) irin hakan ta taba faruwa tsakanin Zainab bint Jahash(R.A)
da kuma Aisha da Hafsah (R.A) duk lokacin da Manzon Allah (S.A.W) ya shiga dakin
Zainab (R.A) sai yadade bai fito ba, saisu Aisha da Hafsah {R.A} suka shiga kishin hakan,
suka rasa ya zasu yi, sai suka ce idan Manzon Allah (S.A.W) yazo muce yana (wari kuma
bai son ace yana wari), kawai sai gashi ya shigo gidan daya daga cikinsu sai kawai ta rufe
hancinta, Annabi (S.A.W) yace lafiya? Tace:
Manzon Allah (S.A.W) me kaci ne? yace me kika ji? Tace wani wari nake ji. Yace ni banci
komai ba, in ba zuma da na sha dakin Zainab {R.A} ba, tace kila shine, sai yace matukar
baku son shi, zan daina shan shi, sai yafita kafin Ya isa zuwa gidan dayar, sai Allah
yabashi labarin kulle-kullensu, da ya shiga cikin gidan dayar sai tafada mashi kamar
maganar ta farkon, sai yace: “kudai makirci ne kuka kulla don in daina shiga gidan
Zainab bint Jahash” (kuma Zainab tana kyautata mani) {Ibn Kathir: Suratut Tahrim}
Dan uwa lura da wannan hadisin ashe matan Annabi (S.A.W) suma mutune ne irin mu,
mata ne irin matan mu, suna kure suna yin dai-dai. Kuma wanda duk ya soke su to Allah
zai azabtar dashi tun nan duniya kafin lahira, dubi masu zagin su, Allah ya sanya azaba
cikin ibadarsu da suke kira ibada, kamar saran junansu da takobi, ko tafiya akan wuta

20
dadai sauransu Allah ya tsareni ya tsreka daga wannan.Amin.Matukar suna bacin matan
Manzon Allah (S.A.W) to Allah zai cigaba da azabtar da su duniya da lahira.
Zaka fahimci cewa:
1. Ashe yazama dole ga mace farkon abin da zatayi shine ta gano abinda mijinta ya
fiso, na abinci, kwalliya, ko magana don tarika yin hakan kullum.
2. Ashe sihiri bata lokacine kawai, kyautatama miji shine mafita mafi lada da sauki da
matunci, don kina iya shiga harkar sihiri karshe yadawo akanki ko ki haukace, koki
lalace, ko diyan ki susaki hawan jinni, na har abada, kegani ga zunubi ga kafirci, ga
wahalar duniya, karshe ga shiga Jahannama, Allah ya tsareni, ya tsareki. Amin.

HADIN KAN KISHIYOYI ALHERI NE GA DUKKANSU ?


Hakane da yawa ake samun gidanda keda mata biyu wadanda basu shiri da juna, amma
idan mai gidan yakaro ta uku, sai su hade ma ta uku kai bata samun goyon bayan su ga
komai. To idan hakan tafaru ya zaka shirya gidanka? Karanta wannan gidan Manzon
Allah (S.A.W) yakasance Manzon Allah (S.A.W) yanada mata tara ko kace sha daya, to
irin matan mu ne tafuskar halitta da dabi’a, wato suna kishin junansu,kamar matan mu.
Hakan tasa sun raba kansu kashi biyu, kashi nafarko ya kunshi A’ishah (R.A) da Hafsah da
Swafiyyah da kuma saudah (R.A) kashi na biyu kuma yana bayan Ummu salamah (R.A) da
sauran matan, kuma sahabai sun fahimci yadda Manzon Allah (S.A.W) yake son A’ishah
(R.A) sai yazama idan suna da kyauta da zasu kawo wurin Manzon Allah (S.A.W) sai su
bari sai yana dakin A’ishah (R.A) sai suzo da ita. Sai ‘yan bangaren Ummu salamah (R.A)
suka shiga kishin hakan sukace ita Ummu salamah tayi ma Manzon Allah (S.A.W) magana
yayi ma sahabai magana duk mai kyauta to kawota duk inda Manzon Allah (S.A.W) yake
basai dakin A’isha (R.A) ba. Lokacinda yake kewaya gidajensu da yazo wurinta sai tafada
mashi hakan bai ce mata komai ba.sai suka tambayeta me yace? Tace bai ce komai ba,
sukace ki sake yi mashi magana har sai yayi mata magana,da yadawo wurinta tasake fada
mashi maganar sai yace “kada ki cuta mani akan (lamarin) A’ishah domin wahayi bai
taba saukar mani ina cikin tufafin daya daga cikin ku ba sai A’isha” sai tace ina tuba
zuwa ga Allah daga in cuta maka ya Manzon Allah (S.A.W) . sai dai sauran matan basu
hankura ba, sai su kira fadimatu (R.A) diyar Manzon Allah (S.A.W) suka aika ta zuwa ga
Manzon (S.A.W) cewa tafada mashi yarika yin adalci tsakanin su da A’ishah (R.A) sai

21
fadimatu ta tafi zuwa wurin babanta tafamashi abinda suka ce, sai Annabi (S.A.W) yace “
yake diyata shin ashe baki son abinda nake so? Tace ina so, “yace to ki so wannan”
(yanuna A’isha). Sai Fadimatu ta dawo da sakon babanta zuwa garesu, suka ce ki koma ki
sake yi mashi magana,tace wallahi ban sake yimashi akan wannan. Sai suka aika Zainab
bint Jahash (matarsa) da tazo sai ta tsananta magana ga Manzon Allah (S.A.W) sai A’ishah
(R.A) ta maida ma Zainab da magana mai zafi har sai da Zainab tayi nadamar zuwanta, sai
Manzon Allah (S.A.W) ya dubi A’ishah (R.A) yace “kwarai sai diyar Abubakar” {fathul

bari:5/207}

Hikimomin hadisin:
Tafarko mun fahimci cewa ashe matan Annabi (S.A.W) irin matan mu ne tafuskar halitta
ko dabi’a.
Ta biyu tsananin son Manzon Allah (S.A.W) ga A’isha (R.A)
Ta uku mai mata biyu zuwa sama alkali ne
Ta hudu hikimar Manzon Allah (S.A.W) wurin hukunci tsakanin matan shi, domin a iske
ka tareda matar ka kuma ace bakada adalci akwai ciwo, amma Annabi (S.A.W) yayi
hankuri bai yi fushi ba.
Ta biyar ashe ana yima mace uzuri idan kishinta ya motsa, domin lokacin bata iya rike
zuciyarta tana fadin abubuwa marasa kyau, kalli wadanan da suka ce Annabi bai yi masu
adalci. Idan Annabi (S.A.W) ance mashi hakanan nifa? Kaifa?

ALLAH AIKO MINI KUNAMA KO MACIJI YASARE NI


Mai karatu nasan zakayi mamakin wannan Addu’ar, amma biyoni ahankali zaka fahimci
addu’ar. Al’adar Annabi Muhammad (S.A.W) idan zai yi tafiya yana yin kuri’a tsakanin
matanshi duk wadda takuri’arta tafito da ita za’ayi tafiyar. {Bukhari:2594 - Muslim:2443}
Wata rana Manzon Allah (S.A.W) zai yi tafiya sai yayi kuri’a tsakanin matansa, A’isha
(S.A.W) da Hafsah (R.A) suka ci kuri’ar. bayan ana kan hanyar dawowa anyi zango kan
hanyar, sai A’ishah (R.A) tace ma Hafsah kidawo saman rakumi na niko in hau naki
rakumin kina kallona ina kallon ki, Hafsah tace babu komai na yarda akayi hakan, kuma
dama Manzon Allah (S.A.W) yana da al’adar duk lokacinda yake kan tafiya idan dare yayi
yana komawa saman rakumin A’ishah (R.A) don yadebe mata kewa saboda zamanta
karamar yarinya. koda ya hau rakumin sai ya taradda Hafsah (R.A) sai kawai yayi zaman

22
shi tunda dai duk matanshi ne, lokacinda A’ishah taga hakan sai kishi yakamata tace “yace
Allah ka aiko mini kunama ko maciji ya sare ni (in yi kuwa) don Manzon ka ban iya ce
mashi komai” {Bukhari:9/310 n.5211 – Muslim:3/1894}
Dan uwa wannan itace mace, kishi bai bari ta hango matsalar harbin kunama ko cizon
maciji, kuma ashe Hafsah da A’ishah (R.A) ba hadin kansu guda ba? kamar yadda gabata?
Saboda mata don sun ce wai kansu gudane, ba ko ina bane ka kiyaye kada bata ma dayar su
rai baka sani ba.
Sa’annan wannan tsarin na A’isha (R.A) anyi shi ne wai don a nuna ma sauran matan
hadin kai tsakanin A’isha da Hafsah (R.A) amma kash, kishi ya hana. Saboda haka gareka
mai mata dayawa.

ME YASAME KI, KE HAUKACE NE ?


Wannan abin dariyar ya faru ne gidan Manzon Allah (S.A.W) wata rana Manzon
Allah(S.A.W) ya zo da wani bawa gidan Aisha (R.A) maimakon ta kula dashi kar ya gudu
sai taci gaba da wasarta har bawa ya gudu, sai ga Annabi (S.A.W) ya dawo yace: Aishah
me yafaru ga bawa ? sai tace ni kam nan nabarshi ina wasa ban sani ba ashe ya gudu, sai
Manzon Allah (S.A.W) yace mata “me ya sameki haka? Allah ya katse ya hannayen ki”
{wato irin tsawarda akeyima yara don su maida hankali ga abinda ake magana akai} sai
Manzon Allah (S.A.W) ya fita ya sanarda sahabai cewa bawa yagudu atafi akamo shi, suka
je suka kamo shi, sai Annabi (S.A.W) yadawo ya iske Aisha tana jujjuya hannayen ta
{tunaninta hannayen zasu katse} sai yace me yasameki ke haukace ne ? tace a’a addu’arda
kayi mani ce nake jira inga wani hannu za a fara katsewa. {Imamu Ahmad: 6/52}
Mai karatu wannan kadan daga cikin mutane suke iya jure shi kalli abinda A’isha(R.A)
saboda yaranci ko kuriciya ta aikata, saboda Annabi(S.A.W) ya aure ta tana karamar
yarinya ‘yar shekara shida, saboda haka zai ga kurciya daban-daban dole yayi hankuri
domin yaranci dake tareda ita, amma wai inda kai ne zaka iya hankurin hakan ? matsayin
bawa wancan lokacin kamar matsayin babbar mota ne mai tsada, kasawo sai ka bada
mabudin motar ga amarya sai tabari wani yadauke mabudin ya wuce da motar, kana iya
hankuri ? to kasani matarka mace ce tunanin ku ba guda ba ne, wasa tafi yawa cikin
rayuwarta, kuma kodai kayi hankurin wasar ko ka sanyata cikin wahala da rudani da kuma
tashin hankali na har abada.

23
WATA SABUWA
Mata kowane lokaci kokarinsu dai shine kada mijinsu yakara aure amma idan suka gano
cewa lallai basu iya hanawa, sai su kawo wadda suka san cewa bata iya yin kishi da su sai
suce mijin ya aure ta don kada yakawo wata can wadda basu iya juyata yadda su keso.irin
wannan tafaru gidan Manzon Allah (S.A.W) matar shi Ummu habibah(Ramlah diyar
Abusufyan) tace ya Manzon Allah (S.A.W) ka auri ‘yar uwata Azzah, sai Annabi (S.A.W)
yace kinason hakan?tace na’am ni banyi ma rowa kuma inason in har zanyi tarayya da
wata cikin alkhairi tazama ‘yar uwata, sai Annabi yace “wannan bai halatta gareni” sai
tace munji ance wai zaka auri Durrah diyar baban Salamah sai yace “diyar baban
salamah” nace na’am sai yace “koda ace ba agolar gidana ce ba, bata halatta gareni
domin diyar dan uwana ce ga shayarwa. Suwaiba ta shayar dani da kuma babanta
Abu-salamah, kubar turo min diyanku da kuma ‘yan uwanku” {Bukhari: 5101 }
Darussan hadisin:
 Agola bata halatta ga mai gidan da take ciki matukar yayi jima’i da mahaifiyarta,
amma kafin jima’I bakomai yana iya sakin uwar ya auri diyar idan diyar ta yarda.
 Ashe wasu mata basu baka shawarar karin aure sai in sunji labarin zaka kara da
wadda zata iya fin karfin su.
 Kishine yasa Ummu-habibah tabada shawarar karin aure kada Annabi(S.A.W) ya
auro wadda bata zama karkashinta.
 Ashe kuma mace na iya ba mijinta shawarar karin aure idan taga wadda zasu fi
dacewa ga mijin su zauna tare.
 Ki yi kokarin ba mijin ki shawara kafin ya auro miki wadda baku shiri.

MAKIRCI NE KYALE AMARYAR KA


Uwar gida idan bata son ayimata kishiya tasan duk hanyar zata bi don ta hana hakan, wani
mutum daga cikin mutanen Amir dan Sa’a-sa’ah yace Manzon (S.A.W) na kasance inada
mata sai nakaro mata amarya sai uwar gida tace wai ta taba shayar da amaryar nono sau

24
daya ko sau biyu{don ta haramtar da amaryar ga mijinta}. Sai Manzon (S.A.W) yace
“konkoda daya ko biyu bata haramtarwa”{muslim: 1450 nisa’I n.3308}
Abin lura daga hadisin
 Konkoda daya ko biyu bata haramtadda komai
 Wata uwar gida kishi ya na sa ta bi kowace hanya don hana kawo amarya ku
kiyaye ma’aurata.

GIDAN BUKI
Akwai wasu kura-kurai da suke faruwa a gidan buki wanda matan mu basu kula dasu ba ko
basu san hukuncin su ba, daga ciki akwai:
a. Tube tufafi yadda aka ga dama lokacin da aka so koda ba gidan muharramansu
bane, tareda cewa Manzon Allah (S.A.W) yace kamar A’ishah da Ummu ad-
Darda’u (R.A) suka ruwaito daga Annabi (S.A.W) yace “Na rantse da wanda
rayuwa ta take ga hannun sa babu wata mata da zata cire tufafin ta ba gidan
iyayenta ba (ko gidanta ba) face ta kece dukkanin sitirar da tsakanin tad a
Allah mai rahamah” {Ahmad:6/361-362 da Hakim:4/288 Abu-dawud:4/39 n.4010}
b. Gulma ko cin naman ‘yan uwa musulmai, tareda da cewa Allah yace “kada sashen
ku su ci naman ‘yan uwansu. Shin dayanku yana son ya ci naman dan uwanshi
matacce?” {suratul-Hujirat. aya ta:12}
Yar uwa ko kesan wace dabbace take cin naman moshe? Wannan sai kare kas-
kantacce wanda kowa bai son akira shi da suna kare, amma saboda kawai son hirar
wani ko wata ba’a gaban idanunsu ba kin koma mai dabi’ar karya. Kuma Allah bai
yafe wannan zunubin sai mai anroki wanda akaci naman shi yafiya.
c. Taba mutuncin ‘yan uwa musulmai ta hanyar fadin wasu abubuwanda suka faru
akansu boye amma sai atona asirinsu cikin miutane duk da akwai hadisin da
Manzon Allah (S.A.W) yace “Riba tana kofofi guda sittin ko saba’in da wani
abu, karamin zunubin riba shine misalign mutum yayi zina da mahaifyar sa,
mafi munin zunubin riba shine (taba) mutuncin mutum musulmi”
{Almustadrak:2/37}

‘yar uwa keji munin yin hirar wani da abinda bayason ji wato (giba) ace hukuncin
ta yafi na mai zina da mahaifiyar sa Allah ya tsare mu Amin.

25
UWAR GIDA SARAUTAR MATA
Wani lokaci babbar mata masamman mai son zumunci tana tabka kuskuren da mijinta
bayaso, amma bai iya yi mata magana saboda kada dangi su hau shi da fada, haka zai
cigaba da zama da bakin cikin wannan abin a rayuwarsa. Laifin dai shine uwar gida tana
barin kofa bude ga duk wanda ya ga dama ya shiga gidanta batareda izinin mijinta ba,
wanda hakan yana iya haifar da fitina ga ma’aurata, karanta hadisin nan:
Wata rana wani daga cikin kannen baban A’ishah (R.A) ta gefen shayarwa yazo gidan ta
ya nemi izinin shiga gida, A’ishah (R.A) ta hana shi sai da ta fadama Manzon Allah
(S.A.W) yace “babu komai ai baffanki ne ya shiga dai” … {ummuhat-almuminin fis-sunnatin-
nabawiyya:Dr.muhammad sulaiman}

Faidah
Yau da matanmu na yanzu zasu kiyaye hakan da soyyayarsu da mazajensu ta karu domin
yanada natsuwa akan gidansa babu mai shiga sai wanda ya yarda da shi.
Uwar gida kada kibari ana shiga gidan ki babu izinin mijinki.

Anan muka kawo karshen wannan littafin sai mun hadu kashi na biyu insha Allah.
Godiya ta musamman ga duk wanda ya taimaka har wannan aiki yakawo haka Allah ya
saka ma kowa da alkhairi. Amin

26

You might also like