You are on page 1of 8

ILLAR AUREN MACCE GUDA

Gabatarwa
Da sunan Allah mai Rahama mai jinkai. Godiya ta tabbata ga Allah SWT
wanda ya halicce mu daga rai guda. Mun shaida cewa babu abin
bautawa da gaskiya sai Allah Shi kadai, ba shi da ko mata ko kama ko
wani abokin tarayya ko mataimaki. Mun kuma shaida cewa Annabi
Muhammad (SAW), Bawan Sa ne kuma Manzon Sa ne wanda ake koyi
da Shi akowane hali, tsira da amincin Allah su tabbata gare Shi da
Alayen sa da Sahaban sa da wanda su ka bi tafarkin Su har ranar tashin
kiyama.
Bayan haka, wannan Takarda mai taken “Illar Auren Macce Guda” na
rubuta tane a matsayin goron Sallah karama ga Yan Uwa Musulmi.

Sanin Kowa ne cewar al’adu da kuma dabi’un Malam Bahaushe na


samun Tabar-Barewa a bisa sauye-sauyen da zamani ya kawo. Daga
cikin su akwai rike Macce guda a matsayin abokiyar rayuwar aure. Duk
da dibon yanda yawan Mata da Yan Mata marasa aure keta karuwa yau
da kullum. Haka nan kuma Mutane suna kaucewa Sunnar Annabi
Muhammad (S.A.W) ta auren macce fiye da daya.
Mutane na Koyi da yahudawa ta hanyar auren Macce guda wanda yana
daga cikin abinda ya janyo yawan aikata barna (zina) a bisa doron kasa.
Haka kuma Mazajen yanzu na tsufa da kurciyar su saboda tashin
hankali, bala’i da Masifar dake tattare da zama da macce guda.
Wasu Mazajen kuma sun zama mazan Hajiyoyi sai yanda akayi dasu a
gida saboda tsawon lokacin da matar ta dauka babu abokiyar zama.
Wadannan dama wasu na daga cikin dalilan da yasa na rubuta wannan
takarda. Ina rokon Allah Yasa Takardar ta cimma Manufar da yasa aka
yita, Amin.

MI AKE NUFI DA AUREN MACCE GUDA?


Auren Macce Guda a cikin wannan takarda na nufin namiji ya auri Macce
kwaya daya tilo ba tare da ya karo mata abokiyar zama ba. Sannan shi
namijin yana da lafiya, da wadata ta muhalli da kuma wadatar dukiya.
ILLOLIN AUREN MACCE GUDA:
Wadannan Illolin na kasa su gida Ukku :
1. Illar auren Macce guda a kan Mijin
2. Illar auren Macce guda akan ita karan-kanta Matar
3. Illar auren Macce guda ga al’umma

ILLAR AUREN MACCE GUDA A KAN MIJIN


I. KADAICI DA KUNCI: Mai mata guda sai yayi hankuri matuka
domin rashin samun karancin kyautatawa da kulawa daga
matarsa, don tasan komi tayi ita kadai ce ba abokiyar hamayya.
Idan ka dawo aiki ko kasuwa kana iya isko ta rufe gida sai kayo
cigiyarta makwabta. Randa tayi tafiya ko ta fara jinin al’ada ko ta
haihu bakada hus, idan Matsananciyar sha’awa gareka to sai kaita
azumi.

Haka nan kuma idan wata jarabawa ta fada mata kamar ta rashin
haihuwa ko hauka ko shafar aljannu, to mutum na iya tsintar
kansa cikin kuncin Rayuwa.

II. RASHIN SAMUN TANTAGARYAR SOYAYYA: Ganin cewa ita


kadaice tilo, Mijin iya fuskantar rashin samun rashin samun kular
da ya kamata, kama daga furta masa kalaman soyayya, kira nai da
sunayen soyayya, yimasa kwalliya da gyaran jiki, yin kwalliyar
shiga kwana, gama abinci kan kari, kawo mashi abinsha, tanadar
ruwan zafi na wanka, wanki da guga da sauransu. Duk wadannan
sai randa ta ga dama zatayi.

Masu mata da yawa na fadin cewar, mutum bazai san dadin


soyayyar aure ba sai ya aure mace sama da guda. Domin gasa
matan ka kullawa tsakanin su, kamar an aza masu cin kofin
duniya. Kowace fatan ta taga ta faranta maka rai.
III. TSUFA DA WURI: Bincike ya nuna cewa mai auren macce guda
tilo yafi saurin tsufa bisa ga mai auren mata da yawa. Mazajen
yanzu na tsufa da kurciyar su saboda tashin hankali, bala’i da
Masifar dake tattare da zama da mata daya. Koda yaushe Mijin na
cikin hargitsi yabi ya yamutse saboda babu kwanciyar hankali.
Rigimar safe daban ta dare daban. Gashi yana ci yana sha amma
ba samun cikakkaen kwanciyar hankali.

Shi Jima’I sai randa taga dama, ko randa ya rarasheta wata ma


har sai an biyata (saboda jahilci) sannan zai samun biyan bukata.
ita maganar samun soyayya da kalaman soyayya basu ko taso ba.
To Irrin wadan nan mazaje zaka gansu ba shekaru, amma duk sun
buge, sun yamutse, kansu cike da furfura, tsufan ya taso masu
saboda wahala. Da zaka isko matar ita ko zaka ganta bul-bul
kamar giwa.

IV. KOYI DA YAHUDAWA: Mun sani Yahudu da Nasara na wannan


lokacin suna yaki da duk wasu halaye na musulmi wadanda suka
sabawa ra’ayinsu, kamar yawan Yaya da Mata da sauransu. Su sun
yarda da mutum ya auri Macce guda sannan yayi budurwa ko
nawa yake so wadda zai rinka fasikanci da ita. Amma kuma basu
yarda da yin mata sama da guda ba

Mutun mai Arziki, mai cikar kamala da wadata da kuma addini, bai
kamata yayi koyi da karatun su ba. Idan muka dubi Magabatan
mu, Iyayen mu, Maluman mu da kuma shuwagabannin mu duka
mata fiye da guda ke garesu. Kai su suna ganin ma idan mutum
nada mata guda to bai cika kamala ba, kuma ko alkalanci da
shugabanci ba’a bashi.

V. MUTUWAR MATAR: Wannan itace mafi girman matsalar zama


da Macce guda. Za’a dau shekaru masu yawa ana tare, kwatsam
sai mutuwa ta dauke Matar. Ta bar mijin da tarin diya a gabansa.
Mene ne makomar yaran, wazai rika mashi su. Daga nan sai a fara
tunanin raba yaran ga danginai. Daga nan kuma aci gaaban da
zaman teburin shawarar Wa zai auro (budurwa ko Bazawara).
Daga karshe in bai samo matar kirki ba da tsufan nashi ta rushe
gidan ko ta kori diyan kokuma ta rinka gallaza masu kai koma ta
kashe shi ta gade dukiyar ta kara gaba.

Amma idan mutum nada mace fiye da guda, koda irin haka ta
faru, sai sauran matar ko matan su rike gidan da diyan mamaciyar.

ILLAR AUREN MACCE GUDA AKAN ITA KARAN-KANTA MATAR


A. YAWAN AIKIN GIDA DA RASHIN HUTAWA: Yana daga cikin
Illar zaman Macce ita kadai a gida yawan aikace-aikacen. Kullum
itace da girki, tsabtar gida da ta yara, kaima Maigida abinci, ruwan
sha, ruwan wanka da sauran su. Ta gama duk garambubuwar ta a
tsakar gida, daren farko maigida yai ta wahalsheta. In ta gamu da
dan kullum-kullum mai hadawa da kwayoyi ta shiga ukku, Haka
zata yi ta fama.

Maccen da take ita kadai bata da hutu a gidan mijinta. Bata yin
tafiya zuwa wani gari wajen biki ta kwashe kwanaki masu yawa.
Ko tayi sammako wurin ziyarar dangi ba tare da ta dafa masa
abinci ba ko kuma tayo dare. Babu ranar da ba ta girkin ta ba,
balle a dafa a kawo mata tana mike da kafafu.

B. Rashin lafia: Randa Macce bata da lafiya, idan ita dai take wazai
rika mata aiki? Da yawa zasu iya cewa diyanta ko yar aiki, to idan
bata lafiya wa zai rike mata shimfidar Mijinta a cikinsu?

Ba ko wane irin aiki diya da yar aiki ke iya yi ba cikin gidan,


abunda ya danganci Tarbiyar shima yana daga ciki. Ta iya yuwuwa
a kwantar da matar assibi ta bar yaran a gida hakan na iya zama
sanadiyar lallacewar tarbiyar diyanta mata.

Haka nan kuma kula da addinin diyanta shima sai da lafiyarta.


Dukkanin wadan nan abubuwan in bata lafiya kuma tana da
abokiyar zama, to zata iya jinyarta, ta rike mata diyanta da ta
kuma kula da mai gida ran kwananta in bata lapia.
C. RASHIN KWANCIYAR HANKALI DA KUMA DOREWAR
ZAMAN TA ITA KADAI: Akwai fargabar zaman mace ita kadai a
wajen Mijinta na karo mata abokiyar zama. Ba abunda ke tada ma
mata hankali irin maganar karo kishiya. Shi Yassa wadanda suke
su kadai a wajen mijin su sune zaka gani da ciwon hawan jini da
suka da kuma infection. Kuma irin wadan nan matan sunfi saurin
mutuwa saboda yawan damuwar lamurran miji. Bata da mai taya
ta kuka.

Matan da suke su biyu ko fiye a wajen Mijin su sunfi kwanciyar


sannan sunfi lafiya kuma sunfi tsawon rai.

Haka nan akwai rashin kwanciyar hankali idan tayi tafiya, wa zai
kula mata da diyanta musamman mata. Wata kuma tayi zargin
mijin na iya kawo wata a cikin gidan. Babban rashin kwanciyar
hankali ga mai tunani shine idan ta mutu, wa zai ci gaba da
tarbiyantar mata da diyanta, yaya makomar diyan zata kasance
tunda basu saba da kowa bas ai ita. Shin wadda mijin zai auro
zata ci gaba da zama dasu koko yaya?

D. RASHIN DOGARO DA KAI: Mafiya yawan mata wannan zamani


na sakin Karatun su ko aikin da sukeyi ko kasuwanci don
barazanar da miji ke masu na karo masu abokiyar zama. Sai su
dawo su zauna hannu rabbana wanda kuma daga karshe bai hana
shi ya aikata abunda yayi niya.

Mata da yawa nayin nadamar irrin wannan hasarar kuma daga


karshe suce miji yaci amanar su. Akwai kuma wadanda keda
hankali, suna kyale maigidan yaje ya karo aure nai, su kuma suci
gaba da gudanar da karatu ko aiki ko kasuwancin su, da karshe
kila ma matar da mijin da gidan duk su dawo karkashin ta (amma
yan kadan keda wannan tunani).

E. FADA MA SHIRKA: Akwai yuwuwar maccen da take ita kadai ta


fada ma shirkar zaman dorewar ta ita kadai hardai in babu
cikakken addini. Mata da yawa suna sihirce-sihirce don kada a karo
masu kishiya. Sun yarda da su Sabawa Allah Mahalicci bisa ga a
raya Sunnar Manzon Tsira (S. A. W.).

Mifiya yawan irin wadannan matan suna kaskanta a rayuwar su,


kuma diyan su basu albarka, kuma daga karshe ayo kishiyar tazo
ta koreta daga gidan tanaji tana gani.

F. RASHIN ARZIKI DA KUMA SONKAI: samar da abokiyar zama


a gidan macce da take ita kadai na nuni da cewar ita cikakkiyar
mai arziki ce domin bata da hassada ko kyashi balle kishi. Rashin
hakan shi ke nuni da cewar ba mutumiyar arziki bace, saboda bata
son alkhairi ga kowa sai kanta.

Haka kuma akwai illar sonkai ga duk matar dake zaune ita kadai a
wajen mijinta domin zaa wayi gari taji bata son ko wace diya
macce ta shigo gidan aurenta. Sauran matan dake waje duk yanda
zasuyi ohonmata. Bata kula da ana iya wayewar gari wani mai
mata yazo auren diyarta shin idan shima matarsa ta hana shi ya
zataji.

Akwai kuma wasu iyaye mata da sunyo zaman su sukadai ba tare


da kishiya ba. Yanzu kuma sunga dansu da arziki sai suyi ta matsa
mai ya karo aure wai don kada matar ta mallake shi. Shin in babu
dadi irin haka, ke me yasa kika so kanki kika hana mahaifinshi ya
karo aure?

ILLAR AUREN MACCE GUDA GA AL’UMMA


1. Hana Wasu Mata Samun Miji: Yana daga cikin Babbar illar
auren mace guda ga al’umma shine tarin yawan ’’yan Matan da
basuda aure. Idan muka dubi Makarantu Islamiyya dana Boko
haka kuma muka hada da Manayan Makarantun gaba da
sakandare zamuga cewar Mata sunfi Maza yawa. To idan mutane
suka ci gaba da auren Mata guda-guda, su sauran ya za’ayi dasu?
Ya kuma ake son suyi?
2. Yawan Zinace-Zinace: Auren macce guda da mazaje keyi na
haifar da yaduwar zina a cikin al’umma. Yawancin Maza nason
karo aure, amma kalubalen matansu na cikin gida nasa su jingine
Maganar auren sai suci gaba da barikancin su a waje wanda shike
haifar da kwaso cututtuka masu illa su yaba ma matansu da kuma
rugujewar arziki. Haka suma ta mangaren matan, idan aka gamu
da wacce bata da Hankuri, kuma ta dauki tsawon lokaci bata yi
auren ba, sai aga ta fada ma barikanci in ba Allah ya tsare ta ba.

3. Rashin Ganin Kima A Idon Al’umma: An fi gani kimar mai


mata biyu, ukku ko hudu a cikin al’umma sama da mai mata guda.
Saboda irin namijin kokarin da suke wajen sauke Nauyin Iyalan su
da kuma Hankuri da zamantakewa da su wajen gudanar da
rayuwar yau da kullum. Wanda shi zai bashi dama ko shugabanci
aka bashi, zai kasance mai hankuri da talakawa nai.

4. Yankewar Zuri’a: Mutumin da ka kokarin takaita Iyali da Matan


aure ba bisa wani kwakkwaran dalili ba na iya ruguje yaduwar
zuri’a tai. Koba komi dai akwai mutuwa, wadda ba’a kayyade mata
yanda zata zuwa. Hakan yasha faruwa a cikin al’umma, kaga
magidanci yayi tafiya tare da dukkan iyalin sa a mota guda, da
zaran an samu mummunar Hadari, bakin nan zuri’a tai ta yanke,
ba mai tuna shi balle ayi mai addu’a.

RUFEWA:
Wannan matsala ta auren mace guda ta mutanen Birni ce. Ba’a cika
samun ta ga mutanen kar-kara ba. Ko cikin mutanen Birnin kuma anfi
samunta ga ‘Yan Boko akida da dai-daikun yan kasuwa, kosu badon
basu so ba, amma sai don tsoron fitinar iyalan su na gida.

Haka kuma wasu na kyamar auren Macce fiye da daya don tsoron
Talauci, sun manta da cewar arzikin ciyarwa gabadai ga Allah yake.

A karshe ina kira ga Al’umma su dubi girman Allah (Mai Arzutawa) su


duba matsalolin Al’ummar mu da yawan Matan da ke garemu. Duk
wanda yasan yana da halin kari na Lafiya da arziki to ya Kara. Wannan
shi zai sa a rage yawan Matan da ke garemu kara zube ta hanyar auren
macce fiye da daya. Kuma shi zai rage zinace-zinace a cikin al’umma.
Hakan zai kara yawan al’ummar musulmi duba da hadaroran da muka
shiga na yawan kashe-kashen mutanen da akeyi babu lissafi.
Allah Ubangiji ya ganar da Al’umma cewar kara aure ba abunda yake
kawowa sai zaman lafiya, kwanciyar hankali, wadata, arziki da kuma
yawancin rai.

Nagode, Dan Uwanku a Musulunci

Abba Ja’afar Makau


Shawal,1444
May, 2023
Domin Karin Bayani ana iya tuntubar mu ta wadan nan hanyoyin
Address:
Masallacin Malam Dahiru Usman,
Gundumi, Kaura-Namoda,
Zamfara State.
Phone Number
Malam Dahiru Usman: 07018580922 ko 08131204774
Jamilu Bello Dan-Ayya: 07030904624
Abba Ja’afar Makau: 08035130157 ko 09077036769

You might also like