You are on page 1of 7

MAKO NA DAYA

Batu: Zan Buga, Kar Ka Buga

Wannan wasan tashe akan sami yara maza guda biyar ko shida. Yaron na guda cikin su, shi ake
daura wa igiya a kunguru sa’annan a sami wani ya rike igiyar, daga nan sai yaro mai rike da igiya
a kunguru ya dauki babbar sanda ya shige gaba in sun je wajen wani mai kayan sayarwa a tebur
ko shago sai ya daga sandar say a ce, “zan buga” sai sauran su ja shi su ce “kar ka buga” a wani
lokaci, yaron mai igiyar a daure yakan yi kamar zai shiga cikin shago ya bugi kayan shago amma
yaron da ke rike da igiyar zai jawo shi baya.

Haka za su dinga yi har abasu sadaka, sa’annan su je wani shago.

Abun da wasan ke darasi akai

1. Hakuri: Hausawa gaba daya mutane ne masu hakuri da natsuwa da cikakkiyar da’a, mu lura
cewa yaron da igiya ke kungurun sa, ba za ya buga kayan mutane ba domin sauran yaran ba
su bas hi izinin ba.

2. Umurni: Yaro mai rike da igiyan nan a kungurun sa, ya bi umurni da aka ba shi cewa kar ya
buga.

3. Shugabanci: Yaron da ke rike da igiyar a kungurun sa ne da duka iko.

MAKO NA BIYU

Batu: “Ga Mairama, ga Dauda”

Wannan wasan “Ga Mairama, ga Dauda” yan mata biyu ne ke yin shigar amarya ta yi lullubi
yadda ya kamata. Sai dayan kuma ta yi shigar ango. Idan sun je gidan da za su yi tashen sai
“amarya” wato Mairama ta shimfida tabarma ta koma gefedaya ta zauna. Shi kuma “ango” sai
ya sami wuri daga gefe daya ya kakire.

A gefe guda kuma sauran ‘yan mata sun yi danki da ‘yan kwanonin ci da na sha. Sannan
su koma gefe guda su tsaya. Sai daya daga cikinsu ta fara waka saura kuma sub a da amsa.

Jagora Ga mairama, ga Daudu

Amshi Ga Mairama, ga Daudu

Jagora Ga mairamu Sharifiya

Amshi Ga Mairama, ga Daudu

Jagora Don Allah dauko Mairama

Amshi Ga Mairama, ga Daudu

Jagora Don Alllah ki ba shi tuwo ya ci

Amshi Ga Mairama, ga Daudu


Jagora Don Allah ki bas hi ruwa ya sha

Amshi Ga Mairama, ga Daudu

Jagora Sai kin yi rausaya da ki ba shi

Amshi Ga Mairama, ga Daudu

Jagora Don Allah ki ba shi fura ya sha

Amshi Ga Mairama, ga Daudu

Jagora Sai kin yi rangwada da ki ba shi

Amshi Ga Mairama, ga Daudu

Darasuna su ne

1. Tsarin auren saurayi da budurwa bayan an yi aure ana koya yadda ya kamata amarya ta yi
wa mijinta.

2. Wasan ya kuma ire abincin hausawa guda biyu, tuwo da hura.

3. Wasan “Ga Mairama, ga Daudu” yana ba da tarbiyya ta musamman ga ’yan mata dangane da
hakkokin miji a kan mara tasa.

4. Da kum yanna bayyana muhimmancin aure ga jama’a.

MAKO NA UKU

Batu: Bukukuwan Gargajiya

Ma’anar biki shi ne nuna farin ciki ga wani abin muhimma da ya faru.

Ire-iren bukukuwan gargajiya

1. Bukukuwan addini

2. Bukkukuwan taya murna

3. Bukkukuwan shekara-shekara

- Bikin sallan Idi: Bikin Sallan Idi guda biyu ne. Akwai Babbar Sallah, wato Sallan layya, wato
wadda ake yi don murnar aikin Hajji, da kuma karaman sallah wadda ake yi bayyan an gama
azumi.

- Sallar Cika-ciki: wannan biki ne da ake yi ranan tara da goma ga watan muharram
wato watan farko na addinin musulunci.

- Sallar Mauludi: wannan biki ne da ake yi domin tunawa da ranar da aka haifi
shugabansu, annabi Muhammadu tsira da aminci su tab’bata a gare shi.

- Sauran bukukuwan da addini ya haifar sun haifar da sallar sane, da sallar takufaha.

- Bikin aure: Bikin taya murna. Bikin aure, bikin suna, bikin nadin sarauta, wannan
bukukuwan ba she lalle shekara-shekara ba.

Bikin shekara-shekara

- Bikin budar dawa: wannan biki a na yin sa shekara-shekara ne don neman tsari daga
bala’oin shekara.

4. Bikin shan kabewa: shi ma wannan biki an yi sa shekara-shekara ne yan bori su ne suke
taruwa suna yin sa da kaka, sarkin bori shi yakan tanadi kabewa da za a dafa a sha.

MAKO NA HUDU

Batu: Tsarin Sassaukar jimla

Me ake nufi da jimla, jerin kalmomi ne masu ma’ana. Jimla it ace jera kalmoni a cikin magana
mai ma’ana.

Sassaukar Jimal: limla ce mai sauki wadda ta kunshi aikau da aikatau.

Misalign jimla sassauka

1. Bala ya zo

2. Yara sun gama

3. Rakiya ta yi aure.

Duk wadannan saukakan jimloli ne wadanda ke dauke da aikau da kuma aikatau.

Hadaddiyar jimla: It ace jimla wadda ta hada saukakan jumloli guda biyu. Misalin su

Kuma

Da, sai, sa’annan, amma da sauransu.

Misali

1. Musa ya rubuta jarabawa kuma ya yi nasara.

2. Rakiya ta yi aure ammabata haihu ba har yanzu.


3. Bala ya je Kano sa’annan ya wuce Katsina.

4. Ba a yi kasafin kudin ba sai badi mai zuwa za a yi.

Sarkakkiyar jimla: Ita sarkakkiya jimla, jimla ce da ta kunshi jimla fiye da biyu su ma ana amfani
da wadannan harulfa na “kuma” da “sai” da “sannan” da kuma dai sauransu.

Misali;

1. Manomi ya shuka gero da dawa, sa’annan ya gitta wake, kwana biyu kuma ya sa taki isasshe.

2. Lokacin da yan majalisar kasa suka nemi tsige shubaban kasa, sai ‘yan barandar siyasa
suka yi rica suna soke-soke da zage-zage irin na ‘yan baranda.

MAKO NA SHIDA

BATU: AURE

Aure shine daidaitawa tsakanin saurayi da budurwa.

Idan saurayi ya ga budurwa da ya so ta da aure, sai ya yi mata Magana. In ta yarda zai rika zuwa
wurinta, idan suka gane wa juna sai a sanar da iyaye daga wannan lokaci sai a yi baiko a kuma
sa ranar daurin aure. Kafin a daura auren, akan kawo kayan zance da kuma lefe da kayan sa
ranan.

A ranar daurin aure, akan gayaci mutane, ko jama’a don su zo zama shaidu. Daga nan sai
waliyyan amarya ya sanya saddaka, waliyyan ango kuma ya biya. Sai a raba goro, a yi adu’a a
tashi. Aure ya dauru.

Bikin Aure

Idan ranar biki ta zo, za’a kawo amarya daga nan za’a kai amarya gidan uban wanka. Bayan an
gama wanka, sai a kai amarya gidan mijin ta. Za’a yi budar-kai. A wurin budar-kai ne ake yi wa
amarya kwaliya da kayayyaki. Daga nan sai sayen baki. Ango ya shiga dakin sa.

Ire-iren Aure

1. Auren budurwa

2. Auren bazaura

Kayan Dakin Amarya

- Gado
- Katifa

- Tabarma

- Jere

- Kwanuka

- Daro

- Kumbo

- Madubi

- Kabet

- Kujeru

- Labule

- Tasoshi

- Kwati

- Kwalla

MAKU NA BAKWAI

Batu: Aure

Alaka ce ta zaman tare tsakanin na miji da mace, ana yin sa ne saboda abin da ake Haifa ya
sami assaili da mutunci da kiwon iyaye, kuma shine maganin zina da yay a marasa iyaye.

Ire-iren Aure

1. Auren soyayya

2. Auren Tillas

3. Auren zumunta

4. Auren sadaka

5. Auren diba wuta

6. Auren dauki sandar ka

7. Auren gayya

8. Auren daukar buta


1. Auren soyayya:

Aure da ake yi masoyan suna so da kawnar juna. Ma’ana, aure da mutum ken ga matar da
yake so, ya zamana son aminci da juna har auren yay u.

2. Auren Tillas:

Aure ne da ma’aurata basu so, da kaunar juna, ma’ana an yi aure ne a bias tillas ta
ma’auratan mafi akasari an fi yi ma budurwa auren tillas. Shine dai ake cewa auren dole.

3. Auren zumunta:

Shine wanda ake kira auren hadin gida. Aure ne da ake nema wa yaro yarinya daga cikin
dangin uwa ko uba, ba tare da an shawarci yaron ko yariyar ba. Irin wannan aure ana yin sa
ne don kara dakon zumunta tsakanin yan uwa.

4. Auren sadaka:

Shi kuma aure ne da ake bayar da yarinya sadaka ga wani don neman tabarraki kamar
sadakar da ake ba wani mallami ko almajiri, mussaman in yarinyan ta yi girma bata sami
manemi da wuri ba.

5. Auren diba wuta:

Aure ne wanda bayan an sake mace saki uku, kokuma tana son komawa gidan mijin da ya yi
mata saki ukun, toh dolle sai ta aure wani miji ta fito, sa’anan koma gidan na bayan.

6. Auren dauki sandar ka:

Aure ne wanda mutum kan auri matar da ke saune da gidan kan ta.

7. Auremn Gayya:

Idan matar mutum ta fita alhali, kuma yana son ta, ya dai sake ta ne don ta addabe shi, toh
maza zai yi sauri ya yi wani aure kafin ta gama da sauransu.

Mako na takwas

Batu: Al’adun Hausawa

Al’ada na nufin duk wani abu wanda alumma ta yarda da shi. Kuma jama’ar take amfani da shi
wajen harakokin yau da kullum. Wanan kuwa ya shafi abubuwa da yawa, waton daga haihuwa
zuwa mutuwa. Al’ada kan iya zama kadai ta argajiya wadda aka gada daga kaka da kakanni, ko
kuma ta zamani wata wadda ake samu saboda zuwan baki, waton irin na larabawa ko turawa.

Don haka, in muka yi nazarin al’adun hausawa, zamu ga cewa daga haihuwa zuwa
mutuwa, akwai abubuwa kamar haka;

1. Suna:

Lakabi ne da ake sa ma mutum don a san bambancin wannan da wance. Hausawa kan
ba da suna dangane da ranar hauhuwa ko lokacin hauhuwa. Misali;

- Tanko: yaro da aka Haifa bayan mata.

- Gambo: Na miji ko mace da aka haifa bayan tagwaye.

- Talle: Yarinya/yaron da aka haifa bayan rasuwar daya daga cikin iyayensa.

- Dan Jummai: Wanda aka haifa ranar juma’a.

- Dan Asabe: Wand aka haifa ranar asabar.

- Dela/delu: Mace wadda aka haifa bayan haihuwa maza.

- Yelwa/yelwah: mace aka haifa iyayenta na cikin wadata.

- Altine/Alti: Mace da aka haifa ranar litini.

- Kande: Mace da aka hiafa bayan maza dayawa

You might also like