You are on page 1of 19

A. B. Dogarawa Fitar mata da’awah a masallaci ko wani waje 12.10.1443 (13.05.

2022)

HALASCIN FITAR MATA MUSULMAI GIDAJENSU DON YIN


DA'AWAH A MASALLACI KO WASU WURARE DABAN

✍ Ahmad Bello Dogarawa


Sashen koyar da aikin Akanta, Jami’ar Ahmadu Bello Zaria, Nigeria
abellodogarawa@gmail.com

Jumu’ah, 12 ga Shawwāl, 1443 (13.05.2022)

MUƘADDIMA
Bismillahir Rahmānir Rahīm. Alhamdu lil Lah. Was Salātu was Salāmu alā Rasūlil
Lah.

Bayan haka:

A Ranar Laraba, 10 ga Shawwāl, 1443 (11.05.2022) na fitar da wani tsokaci da


ta’aliƙi mai ɗan tsawo a kan wani video clip da ya ƙunshi fatawar ɗan'uwanmu
Sheikh Bashir Nuhu As-Salafiy Kaduna (Hafizhahul Lah wa ra'āh) game da
hukuncin fitar mata musulmai gidajensu zuwa wajen gudanar da da'awah.

A clip ɗin, Sheikh Bashir ya karkata ga rashin halascin fitar mace Musulma don yin
da’awah ko karantar da mata ko yin tafsiri a cikin masallaci ko a wani waje daban
in banda cikin gidajensu ko gidan wata daga cikin mata. Bai tsaya nan ba; ya ma
siffanta fitar tasu don gudanar da ayyukan da’awah a ƙarƙashin ƙungiyoyi irin su
FOMWAN, da Women in Da'awah, da Nisā'us Sunnah a matsayin "bidi'a
ikhwāniyyah" wacce ‘yan ikhwān suka ɗauko daga Turawa waɗanda ke ganin duk
abinda namiji yayi, mace ma za ta yi; sai kuma wasu daga Ahlus Sunnah suka
shigo da wannan “bidi’a” cikin tsarin da’awar Sunnah.

A fatawar da ya bada, Sheikh Bashir ya dogara da hujjojin da Sheikh Muhammad


Nasiruddīn Al-Albānī (rahimahul Lah) da wasu malamai suka bayyana a
fatawoyinsu da rubuce-rubucensu don nuna rashin halascin fitar mace gida don
yin da'awah, kamar yanda Ash-Sheikhah Sukainah bint al-Sheikh Nasiruddīn Al-
Albānī ta tattaro a littafinta ‫حكم خروج المرأة للدعوة (من فتاوى الشيخ اإلمام دمحم نارص الدين‬
‫ين‬
‫)االلاا‬.

A tsokaci da ta’aliƙi da na fitar, na yi taƙaitaccen sharhi da tsokaci a kan hujjojin


da Sheikh Bashir ya dogara da su cikin fatawarsa. Haka kuma, na kawo fatawoyi
1
A. B. Dogarawa Fitar mata da’awah a masallaci ko wani waje 12.10.1443 (13.05.2022)

guda bakwai daga Sheikh Abdul-Azīz ibn Bāz (rahimahul Lah), da fatawoyi guda
biyu daga Sheikh Muhammad bin Sālih Al-‘Uthaymīn, da fatawa guda ɗaya wacce
Sheikh Abdullah bin Jibrīn (rahimahul Lah) ya bada, da fatawar Sheikh Sālih Al-
Fawzān (hafizhahul Lah), da fatawoyin Sheikh Muƙbil Al-Wādi’iy (rahimahul Lah)
waɗanda suka tabbatar da halascin fitar mace don yin da’awah da karantarwa da
wa’azi a masallaci ko wani waje daban, matuƙar ta kiyaye ƙa’idodin Shari’ah
dangane da fita waje, da mu’amala da maza waɗanda ba mahram ɗinta ba, da
ƙa’idodin Shari’ah game da tafiyar da za a bar gari.

Dangane da fatawoyin Sheikh Al-Albānī waɗanda Sheikh Bashir ya dogara da su,


na bayyana wa mai karatu cewa Sheikh Al-Albānī ya bada fatawoyi mabanbanta
dangane da wannan mas’alar, wataƙila saboda dalilai na musamman ko bisa
la’akari da mabanbantan yanayi. Sheikh Nasiruddīn Al-Albānī bai garƙame ƙofar
fitar mata don yin da’awah ba irin yanda ɗan’uwanmu Sheikh Bashir ya yi. Don
tabbatar da haka, na kawo wata fatawa da Sheikh Nasiruddīn Al-Albānī ɗin ya
bada dangane da fitar mace ta yi da’awah ko ta karantar da ‘yan uwanta mata a
masallaci ko wani waje daban.

Kasancewa wancan tsokaci da ta’aliƙi da na rubuta ya yi tsawo sosai, musamman


da yake na kawo nassosin fatawoyi da malaman da na yi maganar su a sama suka
bada cikin larabci. Duk da na bada uzurin rashin iya fassara fatawoyin cikin
harshen Hausa ko Turanci saboda wasu zarafofi da ke gabana a lokacin, da kuma
gudun kada tsawon rubutun ya wuce misali, mutane da dama da suka karanta
tsokaci da ta’aliƙin sun nuna rubutun ya yi tsawo, kuma sun bada shawarar a
taƙaita shi, sannan a sake fitar da shi.

Bisa abinda ya gabata, na yanke shawarar sake fitar da bayanan da ke cikin


wancan rubutu a taƙaice. Wannan rubutu na yanzu, ya ƙunshi: (1) tsokaci da
taƙaitaccen bayani a kan hujjojin da Sheikh Bashir ya dogara da su; da (2)
waiwaye ga fatawoyin Sheikh Nasiruddīn Al-Albānī game da mas’alar da kuma
fahimtar da wasu daga manyan ɗalibansa suka yi wa fatawoyin nasa; da (3)
isharori zuwa ga fatawoyin wasu daga manyan malamai na duniya da nuna
halascin fitar mace don yin da’awah da karantarwa a masallaci ko wani waje; da
(4) kammalawa da kuma shawarwari ga mata masu da’awah.

Ina roƙon Allah Yasa rubutun ya amfanar da ni da sauran ‘yan uwa maza da mata,
musamman waɗanda suke cikin harkokin da’awah da karantarwa.

2
A. B. Dogarawa Fitar mata da’awah a masallaci ko wani waje 12.10.1443 (13.05.2022)

HUJJOJIN WAƊANDA KE GANIN FITAR MATA DA’AWAH HARAMUN NE KO


“BIDI’A CE IKHWĀNIYYAH.”

Sheikh Bashir ya dogara da hujjojin da Sheikh Al-Albānī da su Sheikh Yahya bin 'Ali
Al-Hajūriy suka kawo don nuna rashin shar'ancin fitar mata gida don yin da'awah.
Malaman sun ce:

(1) ba a samu haka cikin Sahabbai mata (Allah Ya yarda da su) da sauran
magabata ba duk da ɗinbin ilimin wasu daga cikinsu kamar Nana ‘Ā’isha da
Ummu Salamah;

(2) fitar mace don yin da’awah fita ce wacce babu buƙatar ta don haka ta yi karo
‫ين‬
da manufar ayar suratul Ahzāb, "‫ "وقرن ف بيوتكن‬wacce ta umarce su da zama a gida
ta yanda za su fita ne kawai idan akwai buƙata;

(3) fitar mata zuwa harkokin da’awah za ta iya jawo aukuwar fitina ga maza
kasancewa ita mace al’aura ce; fitarta wajen gudanar da ayyukan da’awah za ta
jawo gogayya da maza cikin aikin da ya keɓanci maza, kuma zuwan mata
masallaci don gudanar da da’awah ko karatuttuka kan jawo takura ga maza,
kamar yanda yake faruwa a wasu ƙasashe;

(4) tunda Hadisai sahihai sun nuna fifikon su yi salla a cikin gida fiye da zuwa
masallaci, me yasa za su fita gidajensu da sunan yin da'awah?

TSOKACI DA TA’ALIƘI A KAN HUJJOJIN WAƊANDA KE GANIN FITAR MATA


HARAMUN NE KO “BIDI’A CE IKHWĀNIYYAH.”

Kowa ya yarda mace za ta iya fita gida idan akwai buƙata ko kuma saboda wata
maslaha tabbatacciya. A zamanin Manzon Allah tsira da aminci su tabbata a gare
shi, mata sun fita zuwa ziyara, da gaishe da mara lafiya, da jajantawa wanda ya
shiga wata jarabawa, da gona, da bikin aure, da makamantansu, kamar yanda
suka fita don yin musharaka da maza wajen sallar jam'i da īdi da jihadi da
‫ين‬
sauransu. Wannan ya nuna yin hujja da ayar " ‫ "وقرن ف بيوتكن‬ba zai zamanto bisa
_iɗlāƙ_ (sake-ba-ƙaidi) ba. Matuƙar akwai buƙatar a fita, toh mace za ta fita.
Abinda a ke buƙata shi ne ta kiyaye ƙa'idodin Shari'ah game da fitar ta.

Maganar ba a samu mata sun gudanar da harkokin da’awah a zamanin Manzon


Allah (tsira da aminci su tabbata a gare shi) da Sahabbai (Allah Ya yarda da su),
haka ne. Amma shin akwai buƙatar su Nana A'ishah da sauran matan Manzon
Allah (tsira da aminci su tabbata a gare shi) su fita don yin da'awah a zamanin
Manzon tsira, irin yanda 'yan FOMWAN da Women in Da'awah da Nisā'us Sunnah

3
A. B. Dogarawa Fitar mata da’awah a masallaci ko wani waje 12.10.1443 (13.05.2022)

da sauransu suke yi a yau? Tabbas babu buƙata domin Manzon Allah (tsira da
aminci su tabbata a gare shi) yana cikinsu, kuma kowa wajensa yake zuwa don
sauraren da'awah da karatu. Hatta ma Sahabbai maza, ba sa shiga lunguna da
kwararo-kwararo na Madina don yin da'awah irin wacce muke yi a yau ballantana
su fita garin Madina da sunan da'awah idan ba Manzon Allah (tsira da aminci su
tabbata a gare shi) ne ya tura mutum/mutane wani waje ba.

Bayan wafatin Manzon Allah (tsira da aminci su tabbata a gare shi), matansa da
matan sahabbansa (Allah Ya yarda da su) ba su yi haka ba, a fahimta ta saboda
babu buƙata. Ga dalilai:

Na farko; mafi yawan musulmai suna zaune a garuruwa 'yan kaɗan, kuma maza
masu karantarwa da yin da'awah suna da yawa, sannan wuraren da a ke taruwa
don da'awah an san su kuma masu yin da'awar da masu saurare duk suna bada
lokacinsa. Don haka, babu buƙatar mata su fita gida don shiga harkokin da’awah
duk da suna fita don biyan wasu buƙatu nasu.

Na biyu; a wancan lokaci, su ma kansu maza ba a samu cewa suna shiga lungu da
saƙo don yin da'awah ba ko kuma a gayyace su wasu garuruwa don yin da'awah,
kamar yanda a ke yi yanzu. Me yasa? Saboda babu buƙata. Toh, idan akwai
buƙatar yin haka a yanzu saboda maslaha 'āmmah, me zai hana a yi?

Na uku; wataƙila wani zai ce a babin " ‫خيا ما سلقون إليه‬


‫"لو كان ر‬, tunda dai magabata
ba su yi ba, bai halasta a yi shi ba yanzu bisa ƙa'idar "sunnar bari", wato ‫السنة‬
‫ ر‬Idan aka ce haka, ni kuma zan ce ai kusan duk malaman da suka yi rubutu
‫اليكية‬.
‫ سنة ر‬sun kawo sharuɗɗa da dhawābiɗ.
game da hujjar ‫اليك‬

Daga ciki, akwai (1): ya zamanto rashin aikata wannan abu a zamanin Manzon
Allah (tsira da aminci su tabbata a gare shi) ko Sahabbai (Allah Ya yarda da su)
saboda babu buƙatar yin haka ɗin ne a lokacin. Idan haka ne, aikata wannan abu
daga baya saboda buƙata ta taso, ba zai zamanto bidi'a ba. Misali, tattara
Alƙur’ani waje ɗaya a matsayin mushafi da Sahabbai (Allah Ya yarda da su) suka yi
bayan wafatin Manzon Allah (tsira da aminci su tabbata a gare shi), da tattara
Hadisai da aka yi daga baya a matsayin littafai duk sun shiga ƙarƙashin wannan
dhābiɗ. Ba za a ce an yi bidi’a ba saboda babu buƙatar yin haka a lokacin da
Manzon Allah (tsira da aminci su tabbata a gare shi) yake raye. Bayan rasuwarsa,
an yi haka saboda buƙata ta taso. Hatta ma tafsiri da a ke gudanarwa a masallatai
da sauran wurare a watan Ramadan zai shiga cikin wannan ƙa’idar. A zamanin
Manzon Allah (tsira da aminci su tabbata a gare shi) da Sahabbai (Allah Ya yarda
da su) da Tābi’ai da almajiransu (Allah Ya jiƙansu) mayar da hankali ga karatun
Alƙur’ani (da tadabburinsa) a ke yi a watan Ramadan; ba a yin tafsiri ballantana

4
A. B. Dogarawa Fitar mata da’awah a masallaci ko wani waje 12.10.1443 (13.05.2022)

jerangiyar wa’azozi. Yanzu fa? A wancan lokaci babu buƙata, amma yanzu akwai
buƙata.

Daga cikin dhawābiɗ na ‫اليك‬ ‫ سنة ر‬akwai (2): ya zamanto babu wannan abin a
zamanin Manzon Allah (tsira da aminci su tabbata a gare shi). Idan abin ya
bayyana bayan wafatinsa kuma ya zama zai taimaka wajen ingantawa da
kyautata wani abu da yake da asali a Shari'ah, babu laifi a yi shi. Wannan yana
daga hujjojin mafi yawancin sababbin hanyoyin isar da saƙo na zamani waɗanda a
ke amfani da su wajen yin da’awah.

Daga cikin dhawābiɗ na ‫اليك‬ ‫ سنة ر‬akwai (3): ya zamanto akwai abin a zamanin
Manzon Allah (tsira da aminci su tabbata a gare shi) ko akwai buƙatar a aikata
abin a zamaninsa, amma ba a yi ba saboda wani māni'i, ko kuma an fara aikata
amma aka bari don gudun kada wahayi ya sauka game da wajabcinsa ko gudun
kada a samu cakuɗuwar abubuwa a waje ɗaya. Idan wannan tsoro ya gushe ko
wannan māni'i ya kauce, shikenan sai a cigaba da yinsa. Ba za a ce an yi bidi’a ba.
Misali, sallar tarāwih ko tahajjud wacce a ke yi cikin jam’i a watan Ramadān ta
shiga wannan dābiɗ. Ya zo cikin Hadisi cewa Manzon Allah (tsira da aminci su
tabbata a gare shi) ya yi sallar sau uku, daga nan ya daina fitowa. Ya shaida wa
Sahabbai (Allah Ya yarda da su) cewa bai fito ba saboda tsoron kada a wajabta
sallar dare cikin watan Ramadān a kansu kuma su kāsa. Daga baya, Sayyiduna
‘Umar bin al-Khaɗɗāb (Allah Ya yarda da shi) ya rayar da wannan Sunnah ta yin
tarāwih ko tahajjud cikin jam’i a watan Ramadān saboda tsoron da a ke yi cewa
kada wahayi a sauko da wajabcinta ya gushe tunda wahayi ya gama sauka kuma
Manzon Allah (tsira da aminci su tabbata a gare shi) ya bar duniya.

Dangane da tsoron fitina idan mata sun fita yin da’awah a masallaci ko wasu
wurare; wannan ya danganta ne da yanda mutum ya kalle shi. Misali, Nana
‘Ā’isha (Allah Ya yarda da ita) ta nuna damuwarta game da yanda ta ga mata suna
fita zuwa masallaci (wasu su sanya turare, wasu su caɓa ado) tun a zamanin
Sahabbai (Allah Ya yarda da su). Hakan yasa ta yi fatawa game da haramcin su je
masallaci, duk da ta san su yi salla a gidajensu ya fi su je masallaci? Akwai wani
Sahabi da ya haramta? Bayan wannan, tunda Sheikh Bashir ya ce mata za su iya
zuwa masallaci don sauraren karatu/wa’azi, shin fitowar da za su yi daga gida, su
je masallaci wajen wa’azi/tafsiri/karatu ba zai iya jawo fitina ba, sai dai idan su ne
za su gabatar wa junansu?

Bisa bayanan da suka gabata, za mu fahimci cewa idan babu buƙatar mata su fita
gida don yin da'awah a zamanin su Nana ‘Ā’isha (Allah Ya yarda da ita) da sauran
magabata kuma babu buƙatar samar da ƙungiyoyin da'awah na mata, hakan ba
zai hana yanzu a yi ba tunda akwai buƙata da maslaha.

5
A. B. Dogarawa Fitar mata da’awah a masallaci ko wani waje 12.10.1443 (13.05.2022)

Bayan wannan, na lura cewa mafi yawan malaman da suka mara wa fatawar
Sheikh Al-Albānī baya bisa la'akari da mahangar ƙa'idar "hanyoyin da'awah ba a
yin ijtihadi cikinsu (‫)وسائل الدعوة توقيفية‬, wasu daga cikinsu sun samu kansu a tsaka-
mai-wuya saboda amfani da ake yi da na'urorin ɗaukaka murya kamar
microphone da loudspeakers, da kuma amfani da kafafen rediyo da talabijin
wajen isar da da'awah, sannan kuma wasu daga cikinsu sun yarda a yi tafsirin
Alƙur’ani ko a buɗe majalisin ilimi ko a tsara jerangiyar muhadorori cikin watan
Ramadān, haka kuma wasu daga cikin malaman sun bada fatawar halascin yin
wa’azi wajen walimar aure duk da magabata ba su yi ba, tare da cewa akwai
damar a yi a wancan lokaci.

Mafi yawan malaman sun yi amfani da dhābiɗ na biyu da na ambata a sama


wajen halasta amfani da sabbin hanyoyin isar da saƙo cikin harkokin da’awah
cewa kasancewa babu su a zamanin Manzon Allah (tsira da aminci su tabbata a
gare shi) da Sahabbai (Allah Ya yarda da su), kuma amfani da su a yanzu zai
taimaka wajen isar da saƙo (‫ )إبالغ‬fiye da rashin amfani da su, za su shiga cikin
ƙa'idar "hanyoyi na da hukuncin abinda za a kai gare shi (‫)الوسائل لها حكم الغاية‬. Haka
kuma sun yi amfani da dābiɗ na farko wajen tabbatar da halascin yin tafsirin
Alƙur’ani cikin watan Ramadān bisa hujjar cewa a wancan lokaci, babu buƙatar a
yi, amma yanzu akwai buƙata. Tunda suna da asali na Shari’ah, aikata su a yanzu
ba bidi’a ba ce.

A ganina, babu abinda ya bambanta tsakanin wancan da suka haramta da


wannan da suka halasta. Fitar mace don yin da'awah babu buƙatarsa a zamanin
Manzon Allah (tsira da aminci su tabbata a gare shi) da Sahabbai (Allah Ya yarda
da su). Yanzu akwai buƙatar su fita a fafata da su don bada ta su gudummawar. A
zamanin Manzon Allah (tsira da aminci su tabbata a gare shi) da Sahabbai (Allah
Ya yarda da su) babu buƙatar a samar da majalisi na tafsiri a watan Ramadān; don
haka, tilawar Alƙur’ani a ke yi. Yanzu akwai buƙatar a yi haka. Wannan yasa a ke
yi. Haka kuma a zamanin Manzon Allah (tsira da aminci su tabbata a gare shi) da
Sahabbai (Allah Ya yarda da su) babu na'urorin ɗaukaka murya irin su public
address system, haka kuma babu kafafen yaɗa da'awah irin su rediyo da talabijin.
Yanzu akwai su, kuma suna da matuƙar amfani wajen harkokin da'awah. Duk da
an ƙa’idar ‫وسائل الدعوة توقيفية‬, an yarda a yi amfani da su. Kenan kowanensu ya
samu goyon baya da tagomashin dhabiɗ guda ɗaya daga dhawābiɗ na ‫اليك‬ ‫سنة ر‬.

6
A. B. Dogarawa Fitar mata da’awah a masallaci ko wani waje 12.10.1443 (13.05.2022)

WAIWAYE GA FATAWOYIN SHEIKH NASIRUDDĪN AL-ALBĀNĪ GAME FITAR MATA


DA’AWAH DA FAHIMTAR DA WASU DAGA MANYAN ƊALIBANSA SUKA YI WA
FATAWOYIN NASA

Akwai manyan fatawoyi guda biyu na Sheikh Al-Albānī da a ke yin hujja da su


wajen bidi’antar da fitar mata don yin da’awah a masallaci ko wani waje daban.

A fatawar farko, an masa tambaya game da hukuncin ziyarar da wasu mata suke
kaiwa gidajen ‘yan uwa mata don gabatar da darussa. Sheikh Al-Albānī ya amsa
da cewa wannan bidi’a ce. Ya ƙara da cewa idan mace tana da ilimi kuma ta cika
sharuɗɗan koyarwa, toh ta zauna a gidanta don mata su je su koyi karatu
wajenta.

Saurari kaset na 189 daga ‫سلسلة الهدى والنور‬. Haka kuma za a iya karanta nassin
fatawar a https://al-maktaba.org/book/31888/1096#p7

A fatawa ta biyu, an tambaye shi hukuncin mace ta fita gida don gudanar da
harkokin da’awa. Sheikh Al-Albānī ya amsa da cewa wannan yana daga masifun
da ke faruwa yanzu a duniya. Ya tsawatar a kan haka. Ya nuna idan mace ta yi wa
Musulunci hidima, toh ta yi a cikin gidanta. Ya nuna fitar mace gida da sunan
da’awah ta ƙunshi yin katsalandan cikin fannin da ba nata ba.

Za a samu fatawar a: https://al-maktaba.org/book/7682/423#p11 kamar yanda


‫ين‬
yake shafi na huɗu a ‫ المكتلة‬- ‫ حكم خروج المرأة لممارسة نشاط إسالم‬- ‫االلاا‬ ‫دروس للشيخ‬
‫الشاملة الحديثة‬.

Banda waɗannan fatawoyi, akwai fatawar da ke cikin fatawar Sheikh Al-Albānī


game da fitar mata da'awah a kaset na 25 a ‫فتاوي حدة‬. Haka kuma za a iya
sauraren fatawarsa a wannan link ɗin:
http://www.youtube.com/watch?v=S_NcJSibYHM

Abin mamaki shi ne, waɗanda ke ƙoƙarin kafa hujja da fatawoyin Sheikh Al-Albānī
don haramta fitar mata da’awah ko karantarwa a masallaci ba sa yin ishara ga
wasu fatawoyin nasa waɗanda suka saɓa wa fatawoyin da suka zaɓa don kafa
hujja da su. Haka kuma ba sa gaya wa mutane cewa wasu daga manyan ɗaliban
Sheikh Al-Albānī sun bayyana cewa fatawoyin malaminsu game da hana mata fita
yin da’awah ba bisa iɗlāƙi suke ba. Shi da kansa Sheikh Al-Albānī ya bada wasu
fatawoyin da ke nuna halascin fitar mata da’awah a masallaci ko wani waje
daban, matuƙar sun kiyaye ƙa’idodin Musulunci game da fitarsu.

7
A. B. Dogarawa Fitar mata da’awah a masallaci ko wani waje 12.10.1443 (13.05.2022)

Misali, Nāsir Abdul-‘Azīz Al-‘Abdaliy ya tattaro maganganun Sheikh Al-Albānī


game da haɗuwar mata a masallaci don yin da’awah ko gabatar da karatu, a
littafin:
‫ين‬
‫التوضيح والبيان لمسألة تحليق المرأة ف المسجد فهما واستنلاطا من كالم محدث العرص الشيخ دمحم‬
‫ين‬
‫االلاا رحمه هللا تعاىل‬ ‫نارص الدين‬

Sheikh Mashhūr Hasan Salmān ne ya yi murāja’ar littafin kuma ya amince a buga


shi a matsayin haƙiƙanin abinda Sheikh Al-Albānī yake nufi da fatawoyinsa. Sheikh
Muhammad Sālih Al-Munajjid ya yi ishara zuwa ga littafin kuma ya kafa hujja da
shi a wata fatawa da ya bada wacce za a samu a wannan link ɗin:
‫ين‬
https://islamqa.info/ar/answers/309709/‫المسجد‬-‫ف‬-‫النساء‬-‫و‬-‫للبنات‬-‫المراة‬-‫تدريس‬-‫حكم‬

Don Allah, ina son Sheikh Bashir ko waninsa ya yi ta’aliƙi a kan wannan littafi.

Sannan, ni fa gani nake da yawa daga ‘yan uwanmu da ke bidi’antar da fitar mata
da’awah bisa fatawoyin Sheikh Al-Albānī sun taƙaita kansu ne ga wasu daga
fatawoyinsa ba tare da sun bibiyi wasu ba, ko kuma wataƙila mu ƙaddara ba su ga
wasu fatawoyin ba.

An fa yi wa Sheikh Al-Albānī tambaya game da fitar mace ta je gidajen mata ‘yan


uwanta don yin da’awah. Ya bada amsar cewa ya halasta matuƙar za ta fita cikin
hijabi kuma ba za ta yi magana ba sai bisa ilimi. A saurari kaset mai lamba 81 a
‫سلسلة الهدى والنور‬.

Kai har ma a cikin masallaci, Sheikh Al-Albānī bai garƙame ƙofa ga mata masu fita
da'awah ba irin garƙamewar da ɗan'uwanmu Sheikh Bashir ya yi har kuma ma ya
ce wai bidi'a ce ikhwāniyyah.

Lokacin da wata mata ‘yan ƙasar Aljeriya ta tambaye shi game da hukuncin shigar
su masallaci don yin da’awah duk da tsangwamar da wasu ‘yan ƙungiya ke musu.
Sheikh Al-Albānī ya halasta musu ci gaba da yin da’awah a masallaci kuma ya yi
musu nasihar su yi haƙuri bisa tsangwamar da a ke musu a masallacin matuƙar
‘yan ƙungiyar ba masu ta’assubanci ne sosai ba. A duba wannan link ɗin don
samun fatawar: https://al-maktaba.org/book/31621/38042#p1

Bisa wannan dalili ne yasa Sheikh Al-Munajjid da wasu malamai suka nuna
fatawoyin Sheikh Al-Albānī game da rashin halascin fitar mace don yin da’awah a
masallaci ko wani waje daban, fatawoyi ne masu dalili na musamman. Idan
mutum ya saurari bayanan Sheikh Al-Albānī a kaset na 24 a ‫سلسلة الهدى والنور‬, zai
ƙara fahimtar haka.

8
A. B. Dogarawa Fitar mata da’awah a masallaci ko wani waje 12.10.1443 (13.05.2022)

ISHARORI ZUWA GA FATAWOYIN MANYAN MALAMAI DA KE NUNA HALASCIN


FITAR MATA DA’AWAH

Kafin in gabatar da fatawoyin wasu daga manyan malamai na wannan zamani


game da halacin fitar mata da’awah da karantarwa a masallaci ko a wani waje
daban, bisa ƙa’idodi na Shari’a zan yi tsokaci akan abubuwa biyu.

NA FARKO; a fatawar da ya bada, Sheikh Bashir ya ambaci cewa Sheikhah


Sukainah ta tattaro fatawoyin manyan malamai kamar Sheikh Ibn Bāz da Sheikh
Al-‘Uthaymīn da Sheikh Fawzān game da bidi’ancin fitar mata da’awah. Tunda ni
dai a wannan rubutu na kawo fatawoyin da ke nuna akasin bayanan Sheikh Bashir
daga waɗannan malamai tare da nuna inda za a ga/ji fatawoyin kai tsaye, zai yi
kyau shi ma ya naƙalo wani sashe na fatawoyinsu da ke goyon bayan fatawarsa.

Haka kuma, tunda ba a san Sheikh Ibn Bäz (rahimahul Lah) da Sheikh Muhammad
Sālih Al-Uthaymīn (rahimahul Lah) da Sheikh Fawān da ikhwāniyanci ba kuma ba
mu taɓa jin wani malami salafī a ƙasar Yemen ko wata ƙasa ya siffanta ɗayansu da
ikhwāniyyah ko ikhwananci ba, idan ya tabbata sun yi fatawar halascin fitar mata
da’awah, me Sheikh Bashir zai ce?

NA BIYU; ina cikin wannan rubutu, sai na ga wani martani da ɗan’uwa Ustaz
Muhammad Auwal Nuhu ya rubuta a kan tsokaci da ta’aliƙi da na fitar ranar
Laraba. A martanin, ya nuna na yi ƙoƙarin kare ƙungiyoyin mata musulmai na
FOMWAN, da Women in Da'awah, da Nisā'us Sunnah wai bisa son zuciya tsantsa
saboda wai fatwoyin su Sheikh Ibn Bāz da Sheikh Al-‘Uthaymīn da Sheikh Ibn
Jibrīn sun sha banban da abinda na yi ƙoƙarin karewa. Ya bada misali da fatawa ta
farko wacce na kawo daga Sheikh Ibn Bāz. A martaninsa, ɗan’uwa Muhammad
Auwal Nuhu ya ce Sheikh Ibn Bāz ya yi togaciyar halasta fitar mata da’awah da
sharaɗin a kiyaye abinda Allah Ya yi umarni da shi na sanya hijabi da suturta jiki
da rashin bayyana ado da rashin faɗa wag a abubuwan da ke kawo fitina.

Wanda bai karanta wancan rubutu da na yi ba, sai ya ɗauka abinda wannan
ɗan’uwa ya zarge ni da shi gaskiya ne, alhali babu ƙamshin gaskiya ko kaɗan a
cikin maganarsa. Abinda na rubuta a ƙarƙashin fatawar farko ta Sheikh Ibn Bāz
bayan na yi ishara ga tambayar da aka yi masa, shi ne:

“Sheikh Ibn Bāz ya bayyana cewa fitar mata bisa ƙa’idodin Shari’ah don yin
da’awah abu ne mai kyau. Ya ƙara da cewa babu laifi idan ma a cikin da’awar sun
yi wa maza nasiha”.

9
A. B. Dogarawa Fitar mata da’awah a masallaci ko wani waje 12.10.1443 (13.05.2022)

Ban san abinda ɗan’uwa Muhammad Auwal Nuhu ya fahimta da ƙa’idodin


Shari’ah da na ambata wajen amsar tambaya ta farko ba! Ko kuwa dai wani salo
ne na ƙin bayyanar da abu yanda yake don cin amanar ilimi?

Ga abinda na rubuta a matsayin shimfiɗa tun kafin in jero fatawoyin Sheikh Ibn
Bāz:

“A wajen Sheikh Ibn Bāz, ba kawai ya halasta ga mace ta fita gida don yin
da’awah ba, a’a, abu ne ma mai kyau da ya kamata mata masu ilimi su yi, bisa
ƙa’idodin Shari’ah da suka shafi fitarsu gida.

Dangane da misali na biyu da ya kawo a martaninsa, Ustaz Muhammad Auwal


Nuhu ya yi da’awar cewa tambaya ta biyu ta tabbatar a gidan matan suke zama!
A tasa fahimtar tunda a gida suke zama kamar yanda tambayar ta nuna, babu
alaƙa tsakanin fatawar Sheikh Ibn Bāz da mas’alar fitar mata da’awah. Abin
dariya! Muhammad Auwal bai karanta tambayar ba ce ko kuwa bai fahimci
tambayar ba? A tambayar, an bayyana suna barin ƙasarsu, su tafi Pakistan na
tsawon kwana arba’in don yin da’awah da karantarwa. Duk da a tambayar an
bayyana idan sun je can, mata suna zama ne a gidan ɗaya daga cikin ‘yan uwa
mata, amma kuma sai a ka tambayi Sheikh Ibn Bāz, “ ‫فهل يستحب خروج النساء للدعوة؟‬
‫”مع العلم أنهن رييكن أطفالهن عند أحد ااقارب؟‬. Mai karatu ya yarda da da’awar Ustaz
Muhammad Auwal Nuhu cewa babu alaƙa tsakanin fatawar Ibn Bāz da mas’alar
da na tattauna a wancan rubutu? Kowa ya yi hukunci da kansa.

Sannan, a gaskiya na yi mamakin ɗan’uwa Ustaz Muhammad Auwal Nuhu. Na yi


wa kaina tambayoyi kamar haka:

(1) Ya saurari fatawar da Sheikh Bashir Nuhu ya bada game da fitar mace da’awah
ko kuwa bai saurara ba?

(2) Ya tantance mahallin nizā’ (abinda aka yi saɓani kansa) kuwa? Domin ina
‫ محل ين ين‬a mas’alar, ba zai kawo maganar kurakurai ko
ganin idan har ya tantance ‫الياع‬
matsalar aƙida da wasu mata masu da’awah ke da ita ba a matsayin martani ga
rubutuna tunda fatawar Sheikh Bashir ba a kan kurakuransu ko matsalolin aƙida
da ‘yan Tabligh ke fama da ita ta ginu ba. Fatawarsa a kan asalin hukuncin fitar
mata gida ne don yin da’awah a masallaci ko su tafi wani gari su yi da’awah, ba a
kan kurakuran da suke yi ba. Idan da a kan kurakuransu ne ko kwamacalar aƙidar
‘yan Tabligh, wataƙila ba zai kafa hujja da su Nana ‘Ā’isha da Ummu Salamah
(Allah Ya yarda da su) don tabbatar da bidi’ancin fitar ta su ba.

10
A. B. Dogarawa Fitar mata da’awah a masallaci ko wani waje 12.10.1443 (13.05.2022)

(3) Ustaz Muhammad Auwal Nuhu ya karanta duk fatawoyin da na danganta wa


Sheikh Ibn Bāz a cikin rubutuna ko kuwa ya taƙaitu ne ga guda biyu kacal, sannan
ya yi azarɓaɓin yin martani bisa son rai, da ƙāge, ba tare da ilimi ba? Domin a
fatawa ta farko na yi maganar wajabcin kiyaye ƙa’idodin Shari’ah kamar yanda
Sheikh Ibn Bāz ya ambata. A fatawa ta biyu, babban jigon tambayar shi ne barin
gida zuwa wata ƙasa don yin da’awah. Wataƙila da ya karanta rubutuna cikin
nutsuwa da niyyar ya fahimci abinda a ke saɓani kansa, kuma ya gwama bayanan
da na yi da fatawar Sheikh Bashir wacce shi yake son karewa ta kowace hanya, ba
na jin zai ce waɗannan fatawoyi na Sheikh Ibn Bāz ba sa ƙarfafar mas’alar. Banda
wannan, me zai ce game da fatawar Sheikh Al-‘Uthaymīn da Sheikh Ibn Jibrīn da
Sheikh Muƙbil? Su ma ba su da alaƙa da mas’alar?

(4) Shin karanbani ne Ustaz Muhammad Auwal ya yi wajen yin tsokaci a mas’alar
fitar mata gida don su yi da’awah, ba tare da ya yi nazari cikin maganganun
malamai ba?

(5) Ina da’awar da ya yi cewa ya karanta rubutun da na fitar ranar Laraba tare da
insāf? Ƙin bayyana abinda na ɓalo-ɓalo da jingina mani abinda ban ce ba, shi ne
insāf a wajensa? Tun daga farkon rubutun har zuwa ƙarshensa, na yi ta nanata
wajabcin kiyaye ƙa’idodin Shari’ah ga wacce za ta fita da’awah. Me yasa ya nuna
ban ce hakan ba? Me yake so ya cinma?

Ina roƙon Allah Ya mana muwafaƙa kuma Ya karemu daga makauniyar biyayya da
ta’assubanci.

Ga fatawoyin wasu daga manyan malamai da ke tabbatar da halascin fitar mata


da’awah bisa ƙa’idodin Shari’ah. Zan kawo su fatawoyin ta hanyar ishara zuwa ga
abinda suka ƙunsa, tare da nuna wuraren da za a same su cikin sauƙi, in sha Allah.
Fatawoyin su ne kamar haka:

Fatawoyin Sheikh Ibn Bāz game da halascin fitar mata da’awah

(1) An tambayi Sheikh Ibn Bāz game da hukuncin mata su yawaita fita gida don
yin da’awah. Sai Sheikh ya bayyana cewa fitar mata bisa ƙa’idodin Shari’ah don
yin da’awah abu ne mai kyau. Ya ƙara da cewa babu laifi idan ma a cikin da’awar
sun yi wa maza nasiha.

Ga link ɗin da za a samu wannan fatawa: https://binbaz.org.sa/fatwas/4243/-‫حكم‬


‫تعاىل‬-‫هللا‬-‫اىل‬-‫للدعوة‬-‫المراة‬-‫خروج‬

11
A. B. Dogarawa Fitar mata da’awah a masallaci ko wani waje 12.10.1443 (13.05.2022)

Ga kuma link ɗin da za a samu audio da ke ɗauke da muryar wannan fatawa ta


Sheikh Ibn Bāz:
https://files.zadapps.info/binbaz.org.sa/fatawa/fatawa_dross/fatawa_dross0294.
mp3

(2) An tambayi Sheikh Ibn Bāz game da hukuncin fitar mace ta bar ƙasarta don yin
da’awah a wata ƙasa kamar Pakistan har na tsawon kwana arba’in (irin yanda
‘yan Tabligh suke yi). Sheikh Ibn Bāz ya yi fatawar cewa fitar mata don yin
da’awah bisa ilimin da Alƙur’ani da Sunnah ya tabbatar game da aƙida da
hukunce-hukuncen Shari’ah abu ne mai kyau, kuma idan sun yi haka, sun
kyautata.

A duba ‫مجموع فتاوى ومقاالت الشيخ ابن باز‬, 9/295-296. Kuma za a samu nassin fatawar
cikin sauƙi a wannan link ɗin: https://binbaz.org.sa/fatwas/2511/-‫النسـاء‬-‫خروج‬
‫للدعـوة‬

(3) An tambayi Sheikh Ibn Bāz ra’ayinsa game da fitar mata don yin da’awah.
Sheikh ya bayyana cewa mace tana da nata wajibin na yin da’awah, kamar yanda
maza suke da shi. Ya jaddada wajabcin mace ta lazimci ƙa’idodi da ladubban
Shari’ah wajen fita don yin da’awah.

A duba: ‫مجموع فتاوى ومقاالت الشيخ ابن باز‬, 7/328. Haka kuma za a samu bayanin a
wannan link ɗin: https://binbaz.org.sa/fatwas/2057/‫وجل‬-‫عز‬-‫هللا‬-‫اىل‬-‫والدعوة‬-‫المراة‬

(4) Wani ya tambaye shi game da hukuncin mace ta yi da'awah. Sai Sheikh Ibn Bāz
ya bayyana cewa mace za ta iya yin da'awah ga mata da maza tare da wajabcin
kiyaye ladubban Shari'ah.

Za a samu muryar fatawar a:


https://files.zadapps.info/binbaz.org.sa/fatawa/nour_3la_aldarb/nour_158/1580
3.mp3

Haka kuma za a samu nassin fatawar a: http://www.binbaz.org.sa/mat/18320

(5) An tambayi Sheikh Ibn Bāz hukuncin fitar mace don yin da’awah a matsayin
hanyar samun dama da kuma ci gaba ga al’umma. Sheikh Ibn Bāz ya bayyana
cewa shi dai bai san wani abu da yana a ɗauki mace ta ƙwarai aiki ba ko ta yi
da'awah ga 'yan uwansa mata.

Za a samu fatawar a kaset na 437 a jerin ‫الشيخ ابن باز من فتاوى نور عىل الدرب‬. Haka
kuma nassinta yana 18/338-339 na littafin da aka tattaro fatawoyin ‫فتاوى نور عىل‬

12
A. B. Dogarawa Fitar mata da’awah a masallaci ko wani waje 12.10.1443 (13.05.2022)

‫الدرب‬. Za a iya duba wannan link ɗin: http://fatawapedia.com/-‫المرأة‬-‫خروج‬-‫حكم‬


53830-‫هللا‬-‫إىل‬-‫للدعوة‬

(6) An tambayi Sheikh Ibn Bāz game da hukuncin mace ta fita gida don yin
da’awah da kuma hukuncin idan tafiyar da za ta yi zuwa wajen da'awar ta kai
nisan tafiyar da a ke yi wa ƙasaru. Sheikh Ibn Bāz ya bayyana cewa mace ba ta fita
gida sai idan akwai maslaha da buƙata. Idan matar aure ce, sai da izinin mijinta.
Ya ƙara da cewa fitar mace don yin da'awah da karantarwa, buƙata ce mai girma
wacce a ke nema. Aiki ne mai kyau wanda aka umarce ta da yi, kuma abu ne da za
a gode mata a kansa kuma ta samu lada.

A duba a littafin: ‫الشيخ ابن باز من فتاوى نور عىل الدرب‬, 18/394-396.

(7) An yi masa tambaya game da yanda mace za ta iya haɗa aikinta na cikin gida
da harkokin da'awah kuma a nemi ya yi ƙarin bayani game da zaman mata a gida
‫ين‬
da Alƙur’ani ya ambata, “ ‫”وقرن ف بيوتكن‬. Sai Sheikh Ibn Bāz ya ce idan mace tana
da ilimi, toh ta yi da’awah ko da a cikin gidanta ne tare da iyalinta da mijinta da
waɗanda ke kawo musu ziyara har zuwa lokacin da za ta samu damar fita zuwa
wuraren da mata ke taruwa a makarantu da sauran wurare don yin musu
da’awah.

A saurari kaset na 128 a jerangiyar: ‫فتاوي نور عىل الدرب‬. Haka kuma a duba wannan
‫ين‬
link ɗin: https://binbaz.org.sa/fatwas/8705/-‫مجامع‬-‫ف‬-‫هللا‬-‫اىل‬-‫الدعوة‬-‫من‬-‫المراة‬-‫منع‬-‫حكم‬
‫النساء‬

Ga kuma audio da za a saurari fatawar daga bakin Sheikh Ibn Bāz:


https://files.zadapps.info/binbaz.org.sa/fatawa/nour_3la_aldarb/nour_284/2840
2.mp3

(8) An tambaye shi game da hukuncin karantarwar mace a masallaci bisa la’akari
da cewa akwai malamin da yake ganin bai halasta ba (wataƙila an yi ishara ce ga
matsayin Sheikh Al-Albāni game da mas’alar). Sai Sheikh Ibn Bāz ya ce idan zai
yiwu mace ta karantar da ‘yan uwanta mata a cikin masallaci cikin hijabi ta yanda
ba za a samu fitina ba, ko kuma a keɓantaccen waje da maza ba sa zuwa (a
masallacin), babu laifi. Sheikh Ibn Bāz ya ƙara da cewa abinda yake da
muhimmanci shi ne mace ta isar da ilimi ga ‘yan uwanta mata musulmai ko
ɗalibai mata a masallaci ko a makaranta ko a gidanta ko gidan wata daga cikin
mata.

A duba: https://binbaz.org.sa/fatwas/10974/‫وتعليمهن‬-‫جنسها‬-‫لبنات‬-‫المراة‬-‫دعوة‬

13
A. B. Dogarawa Fitar mata da’awah a masallaci ko wani waje 12.10.1443 (13.05.2022)

A na iya sauraron muryar Sheikh Ibn Bāz a wannan link ɗin:


https://files.zadapps.info/binbaz.org.sa/fatawa/nour_3la_aldarb/nour_419/4190
9.mp3

(9) Wata mace ta tambaye shi game da abinda ya fi ga mace mai da'awah: ta fita
da'awah shi ne ya fi ko ta zauna a gida don yin hidima ga 'ya'yanta da mijinta? Sai
Sheikh Ibn Bāz ya ce “idan mace tana da ilimin Shari’ah da za ta iya yin da’awah
da shi bisa usulubi mai kyau, toh wajibi ne ta yi iyakar ƙoƙarinta wajen kiran ‘yan
uwanta mata. Sheikh Ibn Bāz ya ƙara da cewa abinda ya fi gareta shi ne ta samu
amintacciyar mace wacce za ta rinƙa barin ‘ya’yanta wajenta duk lokacin da za ta
fita da’awah.
‫ين‬
A duba shafi na 80 a littafin Hamūd bin Abdillah Al-Muɗar: ‫مواقف مضيئة ف حياة اإلمام‬
‫علد العزيز بن باز رحمهاهلل‬

Fatawoyin Sheikh Ibn Al-‘Uthaymīn game da halascin fitar mata da’awah

Bayan fatawoyin Sheikh Ibn Bāz, akwai fatawoyin Sheikh Ibn Al-'Uthaymīn game
da mas’alar.

(1) An tambayi Sheikh Ibn Al-'Uthaymīn (rahimahul Lah) game da yanda mace za
ta yi da'awah da kuma ɓangarori/wurare da za ta yi da'awah. Sheikh Al-Uthaymīn
ya tabbatar mace za ta iya yin da'awah a wajen da 'yan uwanta mata suke
taruwa, a makarantu ne ko masallaci.

Za a samu fatawar a wannan link: http://fatawapedia.com/-‫الدعوة‬-‫المرأة‬-‫تحقق‬-‫كيف‬


53434-‫هللا‬-‫إىل‬

(2) An tambaye shi shin da’awah wajibi ne a kan mace kuma a ina za ta yi
da’awah? Sai Sheikh Ibn Al-'Uthaymīn ya bayyana cewa duk abinda ya tabbata a
haƙƙin maza, toh ya tabbata a haƙƙin idan ba akwai dalili sahihi da ya keɓance su
ba. Ya tabbatar da cewa mace za ta yi da’awah a wuraren da mata suke taruwa, a
makaranta ko masallaci.

Wannan fatawa tana cikin shafi na 255 a littafin Khaulah Bashīr ‘Ābidiy: ‫عالم المرأة‬
‫المسلمة‬. Ana kuma iya duba wannan link ɗin: https://al-
maktaba.org/book/31621/38043#p1

(3) An tambayi Sheikh Ibn Al-'Uthaymīn game da wajen da ya fi dacewa mace ta


je don yin da'awah. Aka ce, su haɗu a gidan ɗaya daga cikinsu ne ko su yi a
masallaci? Sheikh Ibn Al-'Uthaymīn ya bayyana cewa tunda mace ba za ta samu

14
A. B. Dogarawa Fitar mata da’awah a masallaci ko wani waje 12.10.1443 (13.05.2022)

damar fita ba kamar namiji, yana ganin zai fi mata idan ta je makarantu da mata
masu yawa suke taruwa don ta yi musu da’awah. A cikin fatawar Sheikh Ibn Al-
'Uthaymīn ya nuna rashin gamsuwarsa da mata su taru a gidan wata mace, haka
kuma ya bayyana tawaƙƙufinsa (rashin samun matsaya) game da tafiyar mata
wasu wurare don yin da’awah.

A duba shafi na 124 cikin littafinsa: ‫ ضوابط وتوجيهات‬:‫الصحوة االسالمية‬. Haka kuma
za a samu nassin fatawar a: https://www.ajurry.com/vb/forum/-‫اإلسالمية‬-‫المنابر‬
‫ين‬
‫للدعوة‬-‫المرأة‬-‫خروج‬-‫بحث‬-25704/‫السلل‬ -‫البيت‬-‫مني‬
‫ رب‬/‫العامة‬

15
A. B. Dogarawa Fitar mata da’awah a masallaci ko wani waje 12.10.1443 (13.05.2022)

Fatawar Sheikh Abdullah bin Jibrīn game da halascin fitar mata da’awah

(1) An yi wa Sheikh Ibn Jibrīn tambaya game da fitar mata cikin hijabi don yin
da'awah ga 'yan uwansu mata wani lokaci ma har su bar ƙasashensu zuwa wata
ƙasa. Sai ya amsa cewa babu laifi su fita cikin hijabi tare da mahramansu don yin
da'awah ga 'yan uwansu mata kuma su rinƙa haɗuwa da ɗalibai da malamai mata
don yin musu wa'azi.

Za a samu fatawar Sheikh Ibn Jibrīn a: https://ar.islamway.net/fatwa/70633/-‫جواز‬


‫هللا‬-‫إىل‬-‫للدعوة‬-‫النساء‬-‫خروج‬

Fatawar Sheikh Sālih Al-Fawzān game da halascin fitar mata da’awah

Sheikh Sālih Al-Fawzān bai garƙame ƙofa ga mata masu barin gidajensu don su je
da’awah ba irin garƙamewar da Sheikh Bashir ya yi musu, matuƙar dai sun kiyaye
ƙa’idodin Shari’ah.

(1) An tambayi Sheikh Al-Fawzān hukuncin macen da ta tafi da’awah ba tare da


mahram ba. Sai Sheikh Al-Fawzān ya ce “ta fara yi wa kanta da’awah” don nuna
inkari ga tafiyar da mace za ta yi da sunan yin da’awah ba tare da mahram ba
(matuƙar tafiyar ta kai yini ɗaya ko yini biyu)?

A duba wannan link ɗin don samun fatawar:


https://www.alfawzan.af.org.sa/ar/node/4439

Fatawar Sheikh Muƙbil Al-Wādi’iy game da halascin fitar mata da’awah

Abin mamaki, daga ɗan binciken da na yi, hatta fatawar babban malamin
salafiyya a Yemen, Sheikh Muƙbil Al-Wādi'iy game da wannan mas'ala ba ta kulle
wa mata musulmai ƙofar fita da'awah ba, a masallaci ko wani waje daban.

(1) An tambaye shi game da zuwan mace masallaci don ta karantar da 'yan
uwanta mata. Sai Sheikh Muƙbil ya ce babu laifi ta je masallaci don yin da’awah
idan ta amintar da kanta daga fitina kuma ta amintar da mazan da ba mahram
ɗinta ba daga fitina, amma idan ta mata suka biyo ta gidanta, wannan shi ya fi.

A saurari sautin Sheikh Muƙbil game da fatawar a:


https://www.muqbel.net/files/fatwa/muqbel-fatwa4110.mp3

16
A. B. Dogarawa Fitar mata da’awah a masallaci ko wani waje 12.10.1443 (13.05.2022)

Za a samu nassin fatawar a wannan link ɗin:


https://www.muqbel.net/fatwa.php?fatwa_id=4110

(2) Bayan wannan, an tambaye shi game da hukuncin fitar mace don yin da'awah.
Sai Sheikh Muƙbil ya ce, “wannan abu ne da ya kamata a yi mata godiya a kansa,
da sharaɗin za ta yi da’awar ce ga mata kuma ba za ta yi tafiya ba sai da
mahram.” A ƙarshen fatawar, ya yi kyakkyawar addu'a ga matan da suke
jajircewa wajen yin da'awah ga mata ‘yan uwansu kuma ya nuna wajabcin a
taimaka musu wajen ayyukansu na da'awah.

A duba littafinsa: ‫قمع المعاند‬, 2/580. Haka kuma za a samu nassin fatawar a
wannan link: https://www.muqbel.net/fatwa.php?fatwa_id=2914

Za a samu audio na fatawar a: https://www.muqbel.net/files/fatwa/muqbel-


fatwa2914.mp3

KAMMALAWA DA KUMA SHAWARWARI GA MATA MASU DA’AWAH

Daga bayanan da suka gabata, ina ganin mai karatu zai gamsu cewa ba zai yiwu a
ce fitar mata don yin da'awah ko karantarwa ko gabatar da tafsirin Alƙur'ani ga
'yan uwansu mata a gidan wata daga cikinsu ko a makaranta ko masallaci ko wani
ɗakin taro bidi'a ce ba. Haka kuma ba zai yiwu a mahanga ta Shari’ah a ce
ayyukan da'awah da ƙungiyoyin mata musulmai irin su FOMWAN, da Women in
Da'awah, da Nisā'us Sunnah, da MSO ko ɓangaren 'yan uwa mata a MSSN ko IIITN
wai bidi'a ce ikhwāniyyah ba, ballantana har a ce wai ya kamata a hana su damar
amfani da masallaci don yin da'awah ba.

A ɓangaren hukunci, sanannen abu ne cewa ba za a haramta wani abu ba ko a


bidi’antar da shi saboda kurakuren da wasu ɗaiɗaikun mutane ke yi. Don haka,
wajibi ne a banbance tsakanin hukuncin fitar mata da’awah a asali da kuma
kurakuran da wasu ɗaiɗaikun mata masu da’awah suke yi. Ba daidai ba ne a yi
kuɗin goro garesu ta hanyar yin gamagarin hukunci a kansu.

Ƙololuwar abinda za a ce shi ne wannan mas'ala ce ta ijtihadi kasancewa babu


wani nassi tabbatacce kuma iyakantacce ( ‫ )قطع الثبوت‬wanda yake nuni ga wani
hukunci tabbatacce kuma iyakantacce ( ‫ )قطع الداللة‬dangane da fitar mata gida
don yin da'awah. Fatawar Sheikh Al-Albānī da waɗanda suka goyi bayansa ba za
ta taɓa rushe fatawar su Sheikh Bin Bāz da Sheikh Ibn Al-'Uthaymīn da Sheikh Ibn
Jibrīn da Sheikh Muƙbil ba. Mun ma ga cewa shi kansa Sheikh Al-Albānī yana da
fatawar da ta saɓa wa fatawar da ɗan'uwanmu Sheikh Bashir ya dogara da ita.
Don haka, a wajena, fatawar Sheikh Al-Albānī ba ta da ƙarfi. Idan ma mun

17
A. B. Dogarawa Fitar mata da’awah a masallaci ko wani waje 12.10.1443 (13.05.2022)

ƙaddara tana da ƙarfin da za a iya yin amfani da ita, toh, ba ta dace da halin da
muke ciki ba. Kamar yanda aka sani, fatawa za ta iya canjawa saboda canjin lokaci
ko waje ko mutane.

Tabbas, akwai kurakurai waɗanda ɗaiɗaikun mata masu da’awah ke yi dangane


da tsarin fitar su gida, da shigar da suke yi, da yanda suke mu’amala da mazan da
ba mahramansu ba, da abinda ya shafi tafiye-tafiye wajen ayyukan da’awah, da
sauransu. Wajibi ne kowace mace ta bi ƙa’idodin Shari’ah cikin dukan waɗannan
al’amura kuma su ji tsoron Allah.

A ƙarshe, ina kira ga ƙungiyoyin FOMWAN da Women in Da'awah da Nisā'us


Sunnah da sauransu da su ƙara dagewa wajen ayyukan da'awah kuma su ji tsoron
Allah su kiyaye dokokin Shari'ah game da (1) fitar mace da tufafinta, da mu'amala
da mazan da ba mahramanta ba, da tafiyar da za ta kai ga barin gari. Haka kuma
wajibi ne wacce za ta da’awah ta tabbatar fitar da za ta yi ba ta sanya ta tozartar
da wajibinta ba game da tarbiyyar ‘ya‘ya da kula da gida.

a) Ƙa’idodin fita gida da abinda ya shafi tufafin mace musulma


َ‫النب ُقل أ َا ْجز َواج َك َو َب َنات َك َون َساء ْلال ُم ْجؤمن ين‬
َ‫ي ُي ْجدن ين‬ ‫َ ىَل َ َّي‬ ‫ىَل‬ ‫ْل‬ َ َ
‫ي‬ ‫ِ ِر َ ِر‬ ُِ ِ ‫ِ َ ْل‬ ِ ‫ىَل‬ ‫[ يا أيها ْج ِرب‬Ahzāb, 33] ‫اا ِل َّيي ِة ااوىل‬ِ ‫َوال ت ربَ َّيي ْجج َن ت ربَي َج ال َج‬
َ ‫[ َو ُقل ِّل ْلل ُم ْجؤم َنات َيغ ُض ْجض َن م ْجن أ ْجب َصارا َّين َو َي ْجحفظ َن ف ُر‬Ahzāb, 59] ‫َع ىَلل ْجيه َّين من َج َ بيبه َّين‬
َ ‫وج ُه َّين َوَل ُي ْجلد‬
‫ين‬ ِ ِِ ِ ِ ِ ِ
َ ‫َ َ ُِ َّي َّي َ ىَل ِ َ َ ِ ِ ْج‬
[Nūr, 31]‫ِزينتهن ِإَل ما ظهر ِمنها‬
َ َ ‫ْل ْج‬ ‫إ َذا َشه َد ْجت إ ْجح َد ُاك َّين ْلال َم ْجسجد َف َ َت َم َّي‬
[Bukhāri] ‫[ َول َيخ ُر ْجج َن ت ِف ٍت‬Muslim] ...‫س ِط ًيلا‬ ِ ِ ِ ِ
ٌ ٌ ‫ىَل‬ ‫ْل َ َ َ ينْج ُ َ َ َّي‬ َ ‫َّي ىَل ْج ىَل َ ُ َ َ ْج ٌ َ َ ُ ْج َ ٌ ىَل ىَل ْج‬ ‫ْج ىَل ْج‬ َ ‫ْج‬
‫اس َيات َع ِارَيات‬ ِ ‫اس َو ِن َس ٌاء ك‬
َ ‫الن‬ ‫رصبون ِبها‬
ِ ‫ي‬ ‫ر‬ ِ ‫ق‬ ‫ل‬ ‫ال‬ ‫اب‬
ِ ‫ن‬ ‫ذ‬ ‫أ‬ ‫ك‬ ‫اط‬ ‫ي‬ ‫س‬ِ ‫م‬ ‫ه‬‫ع‬ ‫م‬ ‫م‬ ‫و‬‫ق‬ ‫ا‬‫م‬‫ا‬‫ىَل‬ ‫ر‬ ‫أ‬ ‫م‬ ‫ل‬ ‫ار‬
ِ ‫الن‬ ‫ل‬ِ ‫ا‬ ‫ِصنف ِان ِمن أ‬
ُ َ ُ ‫ْل َ ىَل َ َ ْج ُ ْل َ ْل َ َّي َ َ َ َ ْج َ َ َ َ َّي َ َ ىَل‬ ‫ْل ْج‬ ‫ىَل‬ ُ ‫ال ٌت ُر ُء‬ َ َ ٌ َ ُ
‫وجد ِم ْجن‬ ‫وس ُه َّين كأ ْجس ِن َم ِة ال ُلخ ِت الم ِائل ِة ال يدخلن الجنة وال ي ِجدن ِريحها و ِإن ِريحها لي‬ ‫مميالت مائ‬
َ ‫َ ِ َ ىَل َ ِ َ ىَل‬
[Muslim] ‫م ِس ري ِة كذا وكذا‬

b) Tsarin mu’amala da waɗanda ba mahramai ba


ً َ ‫ين َ ْل َ َ ٌ ُ ْل‬ َّ ‫َ ْج‬ َ ‫ْل‬ َ ‫َ َ ْج‬
[Ahzāb, 32] ‫ض َوقل َن ق ْجوال َم ْجع ُروفا‬‫فال تخض ْجع َن ِبالق ْجو ِل ف َيط َم َع ال ِذي ِف قل ِل ِه مر‬
‫َ ْج ُ َّي‬ ُ ‫ىَل‬ َ َ ‫ىَل ًة‬ ‫يد َخ رْج ٌي ىَلل ُه ِم ْجن ىَلأ ْجن َي َم َّي‬ َ ‫َ َا ْجن ُي ْجط َع َن ينف َ ْلرأس ىَلأ َحد ُك ْجم بم ْجخ َيط م ْجن‬
‫[ َل َيخل َون‬Ɗabarāniy] ‫س ْجام َرأة َل ت ِحل له‬ ٍ ِ‫د‬ ‫ح‬ ِ ٍ ِ ِ ُِ ِ ‫ىَل ِ َّي‬
[Bukhāri da Muslim] ...‫َر ُج ٌل ِب ِا ْجم َرأ ٍة ِإَل َو َم َع َها ذو َم ْجح َ ٍرم‬

c) Tafiye-tafiye don yin da’awah


‫ْل ىَل ُ َّي‬ ُ َ
[Bukhāri da Muslim] ‫َل ت َس ِاف ْجر ال َم ْجرأة ِإَل َم َع ِذي َم ْجح َ ٍرم‬

18
‫‪A. B. Dogarawa‬‬ ‫‪Fitar mata da’awah a masallaci ko wani waje‬‬ ‫)‪12.10.1443 (13.05.2022‬‬

‫ين‬ ‫ين‬
‫قال الحافظ ابن حجر رحمه هللا ف فتح اللاري‪" :4/76 ،‬قال اللغوي‪" :‬لم يختلفوا ف أنه ليس للمرأة‬
‫ين‬ ‫ين‬
‫غيه‪ :‬أو‬
‫أسية تخلصت‪ .‬وزاد ر‬ ‫غي الفرض إال مع زوج أو محرم إال كافرة أسلمت ف دار الحرب أو ر‬
‫السفر ف ر‬
‫امرأة انقطعت من الرفقة فوجداا رجل مأمون فإنه يجوز له أن يصحبها ر‬
‫حب يللغها الرفقة"‬

‫‪d) Rashin tozartar da kulawa da gida da kuma tarbiyyar ‘ya‘ya‬‬


‫َّي َ َّي َ َّ ُ ىَل ْل َّي َ‬ ‫َّ ُ َ َّي ًة َ ُ ُ َ ْج َ َ ُ ُ‬
‫وت َو ُا َو َغ ٌّش‬ ‫َ‬
‫اا َعل ْجي ِه ال َجنة ]‪َ [Bukhāri‬ما‬ ‫اا ِل َر ِع َّيي ِت ِه ِإال حرم‬ ‫يه اا ر ِعية يموت يوم يم‬ ‫ِ‬ ‫َما ِم ْجن َع ْجل ٍد َي ْجس ر ْجي ِع‬
‫َ َ َ َّي‬ ‫ْج‬ ‫َّي ىَل‬ ‫اا َرع َّيي ًةة‪َ ،‬ف ىَلل ْجم َي ُح ْجطها َبنص َ‬
‫عاه َّ ُ‬‫من َع ْجلد ْجاس رَ ْجي ُ‬
‫الجن ِة ]‪[Bukhāri da Muslim‬‬ ‫يح ٍة‪ ،‬إَل ل ْجم َي ِجد ر ِائحة‬ ‫ِ‬ ‫ِ‬ ‫ٍ‬ ‫ِ‬

‫‪Wallahu A’alamu.‬‬

‫‪Allah Yasa mu dace. Alhamdu lil Lah. Was Salātu was Salāmu alā Rasūlil Lah.‬‬

‫‪19‬‬

You might also like