You are on page 1of 569

Compiled By Umar Dalha Funtua.

An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na


www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na
yake yake dana soyayya

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu
kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama
sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana
magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490

A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci,
duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna
neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman
munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai
fi kyau ku riga dauko PDF da DOC

Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai
wayarku

This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng


You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to
download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography
including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490
its free we do not charge for our services

Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted
biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not
blame us

Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we
are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day,
any time you can visits our site and download it

Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF
or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
__

✍🏽 *~KUNDIN QADDARATA~*✍🏽
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*
*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*innama amruhu iza arada shai'an an yaqula lahu kun faya kun*

0⃣1⃣

          

Falo ne mai matsakaicin girma wanda ke dauke da set din kujeru labulaye carfet
wanda dukkansu kalolin ash ne turarre da kuma mai haske,daga bangare daya t.v
plasma ce 'yar matsakaiciya reciever da kuma D.V.D  wadanda aka qawata jeransu.

     Can daga kowacce kusurwa ta falon flower ce cikin plower vase dake a tsaye
masu matsakaicin kudi,sosai falon ya bada sha'awa duk da ba wani uban kudi aka
narka masa ba sakamakon yadda komai yake tsare a muhallinsa,bugu da qari kuma yadda
ya wadatu da tsafta yake bada qamshin turaren wuta mai sanyi

    Mamallakiyar falon ce zaune kan daya daga cikin kujerun falon,matashiya ce


wadda ba zata wuce shekara sha takwas ba,fara ce ba irin qal din nan ba,tana da
matsakaicin kyau wanda kwalliyar da tayi cikin shadda orange dinkin bubu ya sake
fidda kyanta,dan kwalin shaddar na ajjiye gefanta wanda ya zamo sanadiyyar bayyanar
kitson dake kanta qananu wadanda aqalla sun doshi guda dari da hamsin,yadda falonta
ke qamshi hakama jikinta yake yi.

    A hankali ta daga kanta karo na barkatai ta sake aza su kan agogon bangon dake
manne saman t.v plasma din dake gabanta maqale jikin bango.

     Sauke idanun nata tayi kana ta maida kan dan madaidaicin centre table din dake
gabanta,ta miqa hannunta ta dauki wayarta samfurin tecno w3 ta sake lalubo lambar
da tun dazun take ta nacin kira,duk da cewa amsa daya ake bata tun dazun cewa
lambar da take nema din a kashe take amma hakan bai sanyata ta daina kira ba.

   Yanzu ma amsar duka daya ce,bai saba kaiwa war haka bai dawo gida ba,yawancin
baya gota qarfe takwas indai ya dade da yawa bai dawo din ba,sau tari idan taga
hakan kuma ta tabbatar ba zaya wuce gidan babbar yayarsu ba hajiya yahanasu,saidai
yau duk sai taji gidan shiru babu dadi,saboda baki daya 'yan tayata zaman sun tafi
gida saura ita daya.

    Sauke ajiyar zuciya tayi tare da lumshe idanunta,ta dan zame kadan ta kwanta
saman kujerar tana jin kewa na ratsata,kewar yara take sosai,mutum ce ita mai
bala'in son yara,saidai Allah bai azurta ta da samun nata na kanta ba tsahon
shekara shida da aurenta,kasancewar tayi aure tun tana da shekara goma sha biyu
kacal a duniya.

     Tayi zurfi kadan cikin tunanin nata taji ana yunqurin bude qofar gidan da
muqulli,ta bude idanunta tana duban agogo,qarfe tara har da mintina arba'in da
biyar goma saura kenan,zumbur ta miqe ta janyo dankwalinta ta daura kana ta fito a
hankali ziwa tsakar gidan nasu wanda yake da yalwa babu laifi,bayan nata dakin ciki
da falo akwai dakuna biyu masu ciki dai dai wanda guda daya mallakin mai gidan
ne,dayan kuma 'yan karikicen da ba'a rasa ba take ajjiyewa ciki,sai kuma bandaki
daga bangare daya gefensa rijiya ce,sai kuma yalwataccen kitchen dake kallon dakuna
biyu masu ciki dai dai din wanda yayi girman dakunan nasu,fes tsakar gidan shima
yake kamar yadda ilahirin gidan yake,sumuntin tamkar ka zuba abinci a qasa kaci
saboda wadatar tsafta.

   
    Tana tsayen har ya kammala bude gidan ya turo babur dinsa(lifan)samfurin
companion,a tsakar gidan ya masa matsugunni gefe daya lokacin da take qarasowa
gareshi tana ambaton "sannu da zuwa" fuskarta qunshe da murmushi wanda lokaci guda
ya soma qoqarin gushewa daga fuskarsa sakamakon ganin fuskarsa sam babu annuri
lokacin da yake amsa mata da "yauwa sannu da gida,na barki ke daya na tsaya gidan
yaaya yahanasu"
"Eh nayi zaton hakan" ta fada tana sanya hannunta ta amshi jaka da ledar hannunsa
jikinta a sanyaye tana qara cika da mamakinsa saboda sam ba haka ya sabar mata ba
idan ya shigo gidan.

      Tana gaba yana biye da ita a baya tare da qare mata kallo,komai na sumayyarsa
na burgeshi,har yau baya manta lokacin da ya aureta da qananun shekarunta wanda
za'a iya kiranta qwaila,amma a ayanzun sai ka rantse ba sumayyar nan bace wadda ya
aureta shekara shida baya da suka wuce.

   A falon ta barshi ta dawo tsakar gida tana hada mishi ruwan wanka zuciyarta na
sake gaya mata akwai abinda yau ke damun mukhtar dinta,mutumin da ita ke tayashi
shigowa da babur dinsa ta hanyar bude masa qofa da rufewa,da ya shigo zai rungume
ta yana yaba kwalliyarta,a haka zasu qarasa falo,ko da ruwan wanka wani lokaci tare
suke hadawa,bai barin bakinta ya huta idan ya dawo,gwanin tsokana ne da son sanyata
dariya.

   Falon ta sake dawowa tana tsane ruwan hannunta,yadda ta barshi zaune haka tazo
ta tarad da shi,bata ce uffan ba ta qarasa gareshi ta rage masa kayan jikinsa,shima
bai tanka ba illa kallo da yake binta da shi har ta kammala ta miqa masa
towel,karba yayi ya rataya a wuyansa sannan ya fice.

   Kafin ya fito har ta kammala jera abinci zuwa ruwan wanke hannu,dakinsa ya wuce
kansa tsaye ya sanya jallabiya kana ya dawo cikin falon.

    Dukkaninsu jagula abincin kawai suke da cokulansu,damuwar data lura yana ciki
ita ta hana mata sakewa taci abincin,duk da yunwar da take ji saboda bata iya cin
abinci sai tare da shi,hakan ya sanya ko da rana ba don albarkacin yaran dake shigo
mata ba wanda ta maida tamkar qannenta da ba zata dinga cin abincin rana ba,tana
son tambayarsa amma bata son masa katsalandan,saboda shi da kansa yake sanar mata
damuwarsa ba tare da ta kai ga tambayarsa ba,kasancewar ya maidata tamkar abokiyar
shawara gareshi,sosai zuciyarta tayi ta kasa sukuni.

   A hankali ya daga idanunsa ya dora akanta sakamakon tuna a inda yake,sai yaji
tausayinta ya kamashi,baiji dadin sanyata a damuwa ba,ga uwa uba yana hasashen nan
gaba kadan zata iya shiga damuwar data linka wannan.

   Ajjiyr cokalin yayi yana qirqirar murmushi tare da kamo hannayenta ya riqe
"Lafiya qalau kuwa yau kike my sumy?" Cikin raunanniyar murya tana qoqarin maida
qwallar data taru a idonta kasancewarta mace marason damuwa,kanta ta langabe cike
da rauni
"Kai zan tambaya yaya mukhtar" ta qarashe fada muryarta na rawa,girarsa ya dage
"Me ya faru?" Qoqarin daidaita muryarta tayi
"Ban taba ganinka cikin damuwa yaa mukhtar irin haka ba,me ya faru da kai" kai ya
girgiza yana sake qirqirar murmushi yana qoqarin azawa fuskarsa,don baisan ta ina
zai fara sanar mata damuwarsa ba,ya tabbatar za tayi nauyi a qirjinta fiye da yadda
tayi nauyi a nasa qirjin,bai da buqatar fadawarta damuwa ko kusa,sai gashi yaya
yahanasu nason jefasu damuwa duka su biyun,sonta da tausayinta wani bangare ne mai
girma a rayuwarsa
"Sumayyaaaaah" ya dan ja sunan nata yana kallonta
"Babu wani abu da yake damu na,gajiya ce kawai,matso maza kici abinci don na
tabbata babu abinda kika ci" ya fada yana janyo plate din gabansa tare da zare nata
cokalin ya fara juya abincin da iya nasa cokalin da alamu yana nufin ciyar da ita
da kansa kamar yadda yake mata wasu lokuta.

   Kan ta ta girgiza idanunta cike da qwalla"ya mukhtar kayi haquri amma wlh ban
yarda cewa baka da damuwa ba,bazan ci abincin nan ba har sai ka gayamin meke
damunka"cokalin ya ajjiye kana ya sauke ajiyar zuciya,baya da nufin fada mata komai
amma ya fuskanci idan baiyi wani abu ba zata qi cin abincin ne kuma ta kwana cikin
damuwa saboda haka yace da ita
"Naji,zan gaya miki amma ba yanzu ba,kinga dare yayi sai gobe idan Allah ya
kaimu,yanzun ki matso kici abinci tukun"
"Kayi alqawari?" Dariya ta bashi saboda yadda quruciyarta ta fito muraran sanda
tayi maganar
"Eh nayi" ya fada shima.

    Ko da suka zo kwanciya haka ya dinga qoqarin boye damuwarsa,ya dinga qarfin


halin aiwatar da duk wani abu da ya saba yi mata su don cire zargi daga zuciyarta
da kuma son ganin ta sake,zamu iya cewa barcinsa kadan ne a daren ranar,cikin duhun
dakin ya dinga juyi yana sake bitar maganganun da sukayi da yaaya yahanasu a wannin
da suka shude dazu,yana cikin wannan tufka da warwarar bacci yayi awon gaba da shi.

    Washegarin ranar duk da maganar da sukayi daren jiya na maqale a zuciyarta tana
mata yawo wanda ya haddasa mata wata kasala hakanan da mutuwar jiki saboda har
wayewar garin damuwar dake fuskar sa bata bace ba,hakan bai mata tasiri ya hanata
yin duka wata hidima ta gidan ta ba,wanda ya kama da tsaftace gidan kafin tashin
mukhtar daga bacci,shirya abun kari da tanadar masa ruwan wanka.

     Yana tsaye bakin gado yana sanya links din hannun rigar shaddarsa,yayin da
take gaban madubi tana shirya masa ragowar kudadensa da ya taho da su daga kasuwa
da zai fita da su ya kaisu banki,hira suke jefi jefi duk da ba kamar yadda suka
saba bane.

     Bayan ya kammala ya tako gaban madubin yana gyara zaman hularsa a


kanshi,sumayya ta dubeshi cikin zuciyarta tana yaba kyawun da yayi,ya kula da ita
saboda haka cikin salon tsokana yace
"Ki fito kawai kice na fiki kyau yarinya,sai wani satar kallona kike" sau tari idan
ya fadi haka kunya da dariya yake bata,har ma wani lokacin musu ya dan kaure
tsakaninsu,yau din ma dariyar tayi,maimakon ta biye masa auyi musun su na ta fishi
kyau da iya kwalliya yadda suka saba sai tace
"Yaa mukhtar,yau ne fa sunan fiddausin" yanayin fuskarsa taga ya dan sauya,bai ce
komai ba yana daura agogon hannunsa,har ta fidda rai tayi zaton ba zaya ce komai
din ba sai taji yace
"Zaki je dinne?" Murmushi tayi saboda mamaki tambayar ta bata,fiddausi ai kamar
diyarsa ce saboda 'yar yaya yahanasu ce,kuma shi da kansa ya bada kudin ankon sunan
harda kudin dinkin ma
"Me zai hana yaa mukhtar,saidai idan kai ka hana" shiru ya sake yi har ya kammala
ya dauki jakarsa ya rataya sannan ya sanya hannu cikin aljihun rigarsa ya fiddo da
dari biyar ya miqa mata kudin cefane,sannan ya sake fitar da dubu daya daban yace
mata kudin mota,ya sake bata wata dubu biyun yace ta baiwa mai jego barka,hannu
biyu ta saka ta amsa tana jera godiya kamar yadda ya zame mata al'ada duk qanqantar
alkhairin da zaya yi mata,tako masa tayi ta rakoshi har ya fidda babur dinsa waje
tayi masa a dawo lafiya.
    Tana shirin mayar da qofar gidan ta rufe taga ya juyo
"Idan kika je kada ki dade,ki dawo gida da wuri,kuma bana son ki shiga cikinsu
kuyita faman surutu" dan jim tayi saboda bai taba cewa hakan ba idan zata shiga
cikinsu sai yau,amma sai ta share ta gyada kai kawai tace
"Insha Allahu".

    Qarfe sha biyu da arba'in ta kammala shirinta tsaf,tayi kyau cikin ankon sunan
duk da cewa qaramar atamfa ce 'yar leda wadda kudinta bai wuce dubu da dari biyar
ba,mayafinta takalmi da jakarta har sarqarta duka sun dace da atamfar,yau cikin
yaranta ba wanda ya leqo,hakan baya rasa nasaba da ce musu da tayi zata unguwa ne
gobe,yaran kusan tarbiyyarta ce,suna da hankali da nutsuwa,tsahon shekara shida
suna tare suke debe mata kewa,sanda aka kawota unguwar ita din ma tana
qwailarta,yaran basu wuce shekara biyu ba harda masu daya da rabi,ita ta dinga
rainonsu,don karbo su take su wuni gurinta,iyayensu sun riqeta tamkar 'yarsu,don
haka sabo da shaquwa ne tsakaninsu sosai.

   Gidan maman sadiya ta shiga saboda tahowa da nana yarinyar maman sadiya wadda
zata rakata,duk cikin yaran yarinyar tafi shiga ranta,a kitchen ta samu maman
sadiyan na dora girkin rana,nana anci kwalliya ana tsaye bakin qofar daki,hatta da
takalminta na qafarta,cikin barkwanci suka gaisa da maman sadiya kana tac" ga
mutuniyar nan,tun dazun ta addaba sai taje taga kin shirya,ni na hanata"dariya
sumayya tayi
"Ai na gama sai tafiya" fatan dawowa lafiya maman sadiyan tayi musu kana suka fice.

     Qarfe daya da wasu mintina ta isa gidan,tuni har ya fara cika da jama'a
kasancewar haihuwar fari fiddausin tayi,gaisawa ta dinga yi da duk wanda taci karo
har ta dangana da dakin mai jegon,'yan uwan mukhatar ne cike da falo zuwa uwar
dakan fiddausin,bata gajiya ba sai data bi ta gaida kowa,yayin da kowa ke amsa mata
cikin mabanbantan yanayi,wani ya amsa mata ba yabo ba fallasa,wani ya amsa mata
cikin shakulaton bangaro,yayin da wani bai amsawa ma sai an tabo shi ance ana
gaidaka,duk hakan bai dameta ba saboda shekaru biyu kenan da fara fuskantar irin
hakan daga garesu,mutum ce ita mai qaranta zargi qwarai a kan mutum,babu wani abu
da suka taba ce mata face sauyin fuska kawai da take gani daga garesu.

    Cikin uwar dakan ta cimma fiddausi tare da yaya bara'atu wadda ita ke bin
muktar sai mai bi mata fadima sai kubra 'yar yayan mukhtar,sai babbar 'yar yaaya
yahanasu mansura,jaririyar ta dauka fuskarta qunshe da murmushi tana fadin
"Kai masha Allah,jariri akwai abun sha'awa"
"Hmmm,ku kam ba ruwanku da ita ko?"cewar fadima kafin tace wani abu yaaya bara'atu
ta karbe zancen
"Nan da wata goma idan Allah yaso gidan mutari zamu suna,wannan karon kam shima
Allah ya kusa kawo masa"
"Allah yasa"inji fadiman.

    Hakanan ta samu kanta da fargaba hadi da faduwar gaba,bata fita daga wannan
yanayin ba maganar fiddausi ta katse mata zaren tunanin da ta fara qullawa
" au,ciki ne da sumayyan?"tabe baki yaya bara'atu tayi tana fadin
"Hmm,ina fa,yaaya yahanasu ke nema masa auren fa'iza" wata matsananciyar faduwar
gaba ta saukar mata,jikinta yayi sanyi qalau,ta dinga jin zuciyarta na bugawa da
sauri
"Alla ya sanya alkhairi" fiddausi ta fada tana kwashe rigunan barka na jaririyar
daga kan gadonta tana lodawa cikin sif,hakanan take,baka fiya gane alqiblarta kan
lamura ba.

    A hankali ta zame yarinyar daga cinyarta cikin kasala sakamakon shigowar 'yan
suna cikin dakin,ta budr jakarta ta fito da dubu biyun da mukhtar ya bata ta miqawa
fiddausin tana cewa
"Gashi,a siyawa baby turare" karba tayi tana fadin
"An gode".

     Duk yadda zancan ya daketa haka ta dinga dakewa tana yaqe,sam hankalinta ba'a
kwance yake ba,qarfe hudu da rabi ta musu sallama don komawa gidan,ba wanda ya damu
da tafiyar tata ballantana ya tambaya,sai data miqa nana gida sannan ta bude
gidanta ta shigr.

    Kan kujerar falonta ta zube tana kiran sunan Allab,tayi a qalla awa guda tana
saqa tana warwarewa,tabbas sauyin fuska da ta samu daga garesu yana da nasaba da
rashin haihuwarta?,aure kenan mukhtar zai qara?,eh mana,dole mukhtar ya qara
aure,'yana da buqatar ganin jininsa kamar yadda danginsa ke da irin wannan
buqatar',abinda zuciyarta ta tunasar da ita kenan,ambaton sunan Allah tayi ta
runtse idanunta,babu shakka don so tana son mukhtar,amma bata jin zata yarda ta
zama silar batawarsa da yayarsa wadda take tamkar mahaifiya a wajensu,tasan halin
yaaya yahanasu sarai,duk abinda ta quduri aniya sai ta aiwatar da shi,hana na nufin
bashi da amfani tace zatayi adawa da abinda ta umarceshi.

    Cikin mutuwar jiki ta miqe don yin sallar la'asar tana istigfari,saboda lokacin
ta da ya kusa qwace mata ba tare da ta yita ba,ko da ta idar ta jima zaune saman
abun sallar tana addu'o'i sannan ta samu ta miqe,kitchen ta shiga,ta riga da tasan
yau ta makara don haka bata da buqatar dora girki mai wuya saboda bata son mukhtar
din ya dawo ya buqaci abinci bata kammala ba.

    Tana girkin tana saqe saqe,tana ta faman hada daya da daya,sai yanzu ta
tabbatar cewa damuwar jiya da mukhtar ya shigo da ita bata rasa nasaba da wannan
zancan kenan?,da gaske ne kenan auren mukhtar zai qara?,sai tasa tafin hannunta ta
share qwallar da take zubo mata tana addu'ar neman agajin ubangiji,babu shakka
qauna ce ta sanya mukhtar ya kasa gaya mata komai.

    Jallope din shinkafa tayi da kayan lambu saboda haka ana kiraye kirayen sallar
magariba ta kammala,tuni dama tana da lemonta cikin dan qaramim fridge dinta wanda
zobo ne da lemon tsamiya saboda mukhtar na sonsu musamman lemon tsamiya saboda
maiqo.

    A gurguje tayi wanka ta hada da alwala,bayan ta kammala sallah ta shirya tsaf


cikin qananun kaya wanda take siya cikin gumama da ake budewa bayan layinsu,sosai
kayan suka yi mata kyau,sai ka rantse babu wani abu dake damun zuciyarta.

    Tana cikin yin turaren wuta taji bugun qofa,ta ajjiue kaskon ta zira hijabinta
kana taje ta bude,Amrah ce 'yar maqotansu daya daga cikin yaran gidanta kenan riqe
da kwanon samira a hannunta
"Anty yau duk bamu ganki ba,baki dawo daga unguwar da wuri bane?" Yarinyar ta
tambaya tana murmushi,murmushin itama sumayya tayi
"Da wuri na dawo amrah,banajin dadi ne sosai yau"
"Allah sarki anty sannu" yarinyar ta fada cikin nuna alhini,sumayyan ta amsa mata
tana karbar kwanon da amrahn ke miqo mata
"Gashi,dama mama ce tace na kawo miki dambu ne" murmushi ta sake yi tana cewa
"Ayyah ki cewa mama na gode,ashe bata manta da ni ba,jirani ina zuwa" ta fada tana
shiga da kwanon ciki,alewa ta ciro guda biyu cikin jakar alawar 'yar dari da hamsin
da take badawa ana siyo mata saboda yaran
"Ungo ki gaida mama da kyau" hannu biyu tasa ta amsa tana cewa an gode ta juya ta
tafi.

    Tana shirin maida qofar ta rufe horn din mashin din mukhtar ya dakatar da
ita,sai ta zare sakatar gami da bude masa qofar ta raabe daga can bakin qofar tana
jiran shigowarsa.
*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍🏽 *~KUNDIN QADDARATA~*✍🏽
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

_bismilla hir rahmanir rahim_

*_qul ya ibadiyal lazina asrafu ala anfusihim la taqnad'u minr rahmatillah_*

_____________________

0⃣2⃣

Shi din ma a yau kallo daya yayi mata ya tabbar akwai abinda ya mata kutse cikin
farinciki da walwalarta,sosai fuska da jikinta baki daya suka nuna gazawa da
kasawarta,gabansa ya fadi saboda wani tunani da ya darsu cikin zuciyarsa,a hankali
qirjinsa ya dinga bugawa.

Yarinya ce amma a dabi'unta sam ba zaka kirata haka ba,tana da halin manya da
dattako da sanin ya kamata,sai tayi qoqarin cilla duk wata damuwarta gefe guda ta
garbeshi yadda suka saba,a yau din ya sake sosai har ma yana tsokanarta,amma ta nan
fannin sai ta samu kanta da gaza amsa masa,duk da murmushin yaqen da take ta
qoqarin binsa da shi,wani abu ne cunkushe a qirjinta.

Tana ta kai kawon shirya masa abinci yana ta binta da kallo,babu shakka iya kula da
miji ba wai mace mai karatun boko kawai ta iya ba,shi ya yadda da wannan,komai na
sumayya a nutse yake,ba zaka taba tunanin bata taba shiga aji ba face ajinsa,shi ya
koya mata yadda zata yi karatu da rubutu,rainonsa ce shi ya raini abarsa,ko motsi
sumayya tayi yasan me yake nufi,hakan ya sanya a yanzu kallon da yake binta da shi
karantarta yake,duk wani motsi nata na gaya masa akwai damuwa mai yawa cikin
zuciyarta.

Hannunsa ya sanya ya ruqota lokacin da take duqe tana shirin zuba mishi abinci,sai
ta dago idonta take idanunsu suka gamu,ko baiyi magana ba tasan meke yawo cikin
idanunsa,sai ta narke qwalla ta cika idanunta,janyota yayi ta fada jikinsa ya
rungumeta da dukka hannayensa,kuka ne ya qwace mata ba tare data shiryawa hakan
ba,baice mata komai ba har sai da tayi mai isarta,ya fuskanci zuciyarta ta soma
sanyi sannan yace da ita cikin murya mai sanyi
"Me ya faru my sumy,me ya sameki?" Cikin muryar kuka maganar na kakkatse mata
saboda shishshiqar kukan dake kawo wa muryarta caffa
"Yaa mukhtar,yanzu saboda zakayi aure kake boyemin?,me yasa baka gayan ba ya
mukhtar saidai na tsincin zancan a waje?" Shiru yayi wuta ta dauke masa lokaci
guda,zancan da yake ta faman boye mata kenan,shi kansa cikin awanni kadan maganar
ta dagulamasa dukka wata nutsuwa tasa,ina ga sumayyar tasa,ajiyar zuciya ya saki
sannan yace
"Sumayya,bana son ki tada hankalinki kan wannan maganar,ni mukhtar a yanzu bana
sha'awar qara wani aure,ke daya sumayya kin isheni,kuma babu wanda ya isa ya sani
dole tunda ni zan zauna da ita".

Da sauri ta daga kanta daga qirjinsa tana dubansa tana kada kanta.

"Ko ba jima ko ba dade dole ya mukhtar sai ka qara aure,koda baka da muradi 'yan
uwanka zasu tursasa ka,tunda na kasa samar musu da abinda suke da buqata,na kasa
haihuwa....." Ta qarasa maganar kuka na sake qwace mata.

Da sauri ya sanya hannunshi ya rufe bakinta.

"Subhanallah,sumayya!,ina ilimin addininki ya tafi?,Allah kadai ke bada haihuwa kin


sani na sani kowa ma ya sani saidai klwa ya take saninsa,to saboda haka babu wani
sake auren da zanyi,mu barwa Allah lamuranshi har zuwa lokacin da yaga damar bamu".

Ta lura da gaske mukhtar yake ba zaya karbi auren da aka bashi ba,wanda hakan dai
dai yake ya debo baqin fenti ya yaba mata a idanun 'yan uwanshi,a yanzun ma tana
rakawa ne kawai da yanayin dangantaka da alaqarsu,ba zata iya tuna yaushe rabon da
ta ga wani da ya jibanceshi a gidansu da zummar ziyara ba,kawaici kara da yakanarta
ne kawai yasa bata dauki lamarin a bakin komai ba,ta riga ta sani ta kuma yi imani
da shi shine dukkan tsanani yana tare da sauqi.

Ji take a jikinta wannan ce kadai dama ta qarshe a gareta da zata dawo da


kyakkyawar alaqar da a da can baya take tsakaninsu

" ya mukhtar"ta kira sunansa,bata tsumayi jin amsarsa ba ta dora

"Don Allah da annabinsa kada ka yimin haka,kada kace ba zaka karbi auren nan ba"

"Sumayya,bana so kuma bazan karba ba,bana da buqatar qarin aure a yanzu haka,domin
babu abinda na nema na rasa ga mata ta" ya fadi yana dubanta kansa tsaye,rasa me
zata ce masa tayi saboda yadda taga ya tunzura kamar ta sokeshi da allura.

Qarar wayarsa ce ta sanyashi mai da idanunsa kan wayar,har ra qaraci ringing dinta
ta katse bai daga ba,tana katsewa wani kiran ya sake shigowa,sai da ta kusa katsewa
sannan ya daga
"Hello" aka fada daga can bangaren,ko bata ga sunan mai kiran ba tasan yaya
yahanasu ce,tana jiyo muryarta tar kasancewar tana jikinsa

"Assalamu alaikum"mukhtar ya fada

" sai yanzu kaga damar daga kiran nawa hamshaqi?"ta fada cikin fada

"A'ah ba haka bane...." Ta katseshi da sauri ta hanyar fadin

"Ba wannan nake so naji daga gareka,munyi maganar yarinyar nan fa'iza,naji shiru
baka ce komai ba" ransa ya sake baci fiye da dazu,har yanayin fuskarsa ya sake
munana fiye da dazun.

"Yaaya,kiyi haquri,inaga gaskiya gwara kawai abar maganar nan,kada in zama silar
bata zumuncinku ke da qawarki,domin a gaskiya bani da sha'awar qara aure a yanzu
haka,mata ta babu abinda na nema daga gareta na rasa".
" iyeeee,ni muntari kake gayawa haka,kai kuwa ka rasa komai daga matarka,shekararku
nawa tare,ko dan yatsa ta taba haifa maka?,hala ma haka sumayyan tace ka fadamin
kenan?".

"Babu ruwanta yaya,hasalima bata san da zancan ba banda yanzu,nine kawai bani da
ra'ayi".

" muntari ka bini a hankali,idan nayi maka baki fa sai ya kamaka wallahi kai ka
sani,aure kuma babu fashi wallahil azim,mu zuba ni da kai da ita kanta qaramar
alhakin sumayyar muga wanda zai kai qasa,banza shashasha kawai solobiyo,yarinyar da
a haihuwar tumaki ka haifeta zaka tsaya tana juyaka kana tsoronta"qit ta kashe
wayar daga fadin hakan.

Tuni sumayyan tayi nisa a duniyar kuka,so tayi ma ya saketa ta zauna qasa ko ta
kwanta ko zata fi jin dadin yin kukanta son ranta amma yaqi sakin nata.

Cikin jarumta ta hadiye kukan nata ta dubeshi


"Ya mukhtar,wallahi kaji nima na rantse qarin aure gareka babu fashi matuqar kana
qaunata da gaskiya kamar yadda ka fada,wannan kawai ya isheka ishara ka gane kashin
kaji kake shirin sake yabamin bayan wanda na goga a baya,saboda haka ya zama dole
ka yiwa yaayaa biyayya tunda mazaunin mahaifiya take a gareka" tana gama fadar haka
ta miqe daga jikinsa ta shige dakin gadonta.

Cikin kwanakin gaba daya ta daina yi da shi,ta tsame hannu daga sabgarsa ba wai don
haka ta so ba,tayi amanna auren da zaiyi ne kadai zai sama mata salama cikin
rayuwar aurenta,ta tabbata ba zasu barta ba ko ba dade ko ba jima tunda bata haihu
ba.

Kwanaki uku kenan zaman babu dadi,saidai ta tara yaranta suyita sabgarsu amma na
ruwanta da shi.

Ranar cikon ta hudun bayan ya dawo daga kasuwa,ya tadda kayan abincinsa ta jera
kamar yadda ta saba,tayi shigewarta uwar dakanta babu ita ba alamarta,toilet ya
shiga yayi wanka duka tana jinsa bata ko motsa ba balle ta fito,ya gama ya kintsa
cikin jallabiya,bai ko kalli abincin ba ya shiga uwar dakan tata,nan ya cimmata
saman gado zaune jingine da fuskar gadon,hannunta dauke da qaramin littafin
alma'asuraat,ba taka haue bace 'yar gado ce,domin gidansu gidan malamai ne akwai
ilimin addini tsantsa wanda hakan ya sanya yara matan gidan basa karatun boko sam
sam.

Bata dubeshi ba har ya hauro gadon ya sanya hannu ya karbe littafin ya ajjiye gefe
guda,ganin tana shirin yi masa bore ya sanyashi saka qarfinsa ya riqeta gam,cikin
salo ya soma rarrashinta da neman sulhu daga gareta,cike da tuburewa ta dubeshi
"Karbar auren nan ne kadai zaya samo maka kaina yaa mukhatar,idan ba haka ba zaka
iya tafiyarka muci gaba da zama a haka,ya fiye min akan danginka su dinga ganin na
mallakeka,kullum ban da kwanciyar hankali ko nutsuwa a cikinsu" ta qarashe maganar
zuciyarta na sake yin rauni,dama can a raunane take,dakiya da haquri yasa take iya
sabgoginta kamar bata da damuwa,tun asali mutumce mai zurfin ciki,bugu da qaari
zamanta da mukhtar babu wani abun tur da yake mata don haka bata iya fadar matsala
ko kai qara ba.

Ya kusan kwashe minti talatin cikin nazari da dogon tunani,har ta fara jan abun
rufa zata yi kwanciyarta tana tsammanin yana kan batunsa,ya waiwaya cikin sanyin
jiki ya dubeta
"Sumayya,ina sonki kin riga da kin sani,babu kuma abinda na nema na rasa daga
garekin,ban dauki rashin haibuwarki a wata matsala ba,saboda na riga da na sani
cewa bawa bai isa ya tasara kansa *KUNDIN QADDARARSA* ba,tunda kina gani shine
buqatarki kuma shine kwanciyar hakalinki na amince".
Duk da hakan take buqata saboda tasan shine samun salamarta daga hannunsu yaa
yahanasu amma sai da wata 'yar banzar faduwar gaba ta ziyarceta,ta hadiye wani abu
sannan tace

" shikenan,amma ya kamata gobe kafin ka dawo gida kaje ka sanar da yaayaa yahanasu
amincewarka,so nake ta daina zargi ko jin haushina"kallonta ya waiwaya yayi,saboda
a yadda tayi maganar shi zai nuna maka akwai ragiwar zallar quruciya a tattare da
ita,bai son zuwan saboda haka ya kada kai yace

"Bazan je ba saidai idan zaki shirya muje tare".

Ido ta dan zaro don har ga Allah batasan ya hafuwarsu zata kasance da ita ba,amma
sai dabara ta fado mata,kasancewar babu wani nisa sosai tsakanin gidansu da gidan
yaya yahanasun bazai wuce naira talatin ba kudin mota

" eh zani,amma saidai ka ajjiiyeni a gida,idan ka dawo kazo ka daukeni mu


tafi"baice komai ba ya tire bargon ya shige ciki tare da janyota jikinsa,da sauri
ta dubeshi
"Abinci fa kaci ne?" Kai ya girgiza mata
"Na qoshi"
"Amma yaa mukhtar bai......."
"Shshshshsh" yace da ita sai tayi shirun tare da komawa ta lafe ajikinsa,ta sani
tunda yace bzaici din ba bazai ci ba,ita kuma bata saba musu da shi ba saboda
girman da yake da shi a idanunta.

Cikin dare ta kasa barci,itadai bata san kishi ba tunda bata taba soyayya ba saboda
shekarunta sha biyu a sanda aka aurar da ita,tadai auri yaya mukhatar,kuma tanaji a
zuciyarta tana sonsa bata so wani abu ya rabeshi,amma tana jin babu dadi duk sanda
ta tuna zai kawo wata gidan ta zauna tare da su,ya dinga kulata kamar yadda yake
kulata,da tunanin yaqi qare mata sai ta sauko daga saman gadon,ta sadada ta fita ta
daura alwala ta kabbara sallah.

Kusan wannan tarbiyyar gidansu ce tun kafin tayi aure,mamarsu tasha gaya musu duk
sanda suka kasa barci da kwanciyar banza suyita zaman tunani gwara suyi salla,zasu
samu lada kuma daga bisani baccin yazo,a lokacin dariya sumayya take qyalqyalewa da
shi saboda tsantsar quruciya,takan ce
"Nikuwa mama mai zai hanani bacci?,bacci fa dadi ne da shi wallahi mama,baki ga da
qyar nake iya tashi nayi sallar asuba ba,wataran ma sai kin sanya tsumagiya kin
dakeni?" Murmushi kawai uwar takeyi kana tace
"Sumayya kenan quruciya mai dadi ko" sai ta sake yin dariya tace
"Hmmm,mama kenan,nikam babu abinda zai hanani bacci na,ga katifata mai laushi,ga
iskar fanka".

Washegari tare suka tashi,shi ya dinga taimakata da ayyukan gidan kamar yadda suka
saba yi wadansu lokuta,sunayi yana tsokanarta saboda ya fuskanci tamkar bata da
walwala,hatta sallar jiya a idanunsa tayi kasancewar shima bai samu isasshen bacci
ba,sai goma ya fita yana gaya mata ta shirya bayan sallar magariba idan ya dawo
zasu fita.

Qarfe shida ta kammala girkinta ta tsaftace gidan,ta hada kan yaranta ta zuba musu
abinci cikin kwano daya,sannan ta kwashe na mai gidan ta kai falo ta jera sannan ta
shiga wanka tana gaya musu saura ta jiyo su suna fada,duk wanda yayi fada ba
ruwanta da shi.

Tsaf ta shirya cikin wami swiss lace mai matsakaicin kudi cikin kayan sallarta
yake,sanyawarta daya wannan ne na biyu,mukhtar akwai qoqari da zuciyar yiwa
iyali,sosai yayi mata kyau,ya sake fidda zallar quruciyarta,tana cikin fesa turare
ta jiyo yaran na yi masa sannu da zuwa,bai shigo yau da babur din nashi ba saboda
zasu sake fita.
Ta fito sanda yake raba musu alewa suna karba suna godiya kana suka yi mata sallama
suka fice,haka ta koya musu,da ya dawo ko bata fada ba zasuyi mata sai gobe su tafi
saidai idan ita ta tsaidasu,idanunsa a kanta ya bude mata hannayensa ta tako a
hankali cikin kunya ta shige cike ya kulleta gam cikin qirjinsa yana fadin
" kinyi kyau my sumy ta"siririyar dariya ta saki cike da jin dadin yadda yake yaba
kwalliyarta.

Wanka ya shiga yayi a gurguje saboda qaratowar lokacin sallah magariba,y hada da
alwalarsa ya fice,bayan ya dawo ya shirya cikin shadda ruwan bula mai turuwa(dark
blue)wanda yayi shige da lace din jikinta,dariya ta dinga ganin yadda yake
waqar(munyi anko da anko)irin ta yara.

Gidan yaya yahanasu taga sun nufa,bugawa qirjinta ya dinga yi,bata so ta masa
magana yaga kamar tana qin 'yan uwansa,tunda duk tsiya naka naka ne,sai da ya faka
babur dinsa qofar gidan sannan yace da ita
"Idan mun gama da nan gidan mama zamuje ki gaidasu" hakan ne ya dan sake sa mata
nutsuwa,"to"kawai tace da shi.

Yana gaba tana biye da shi kamar wadda za'a kama,a tsakar gida suka ci karo da
yaron yaya yahanasu wanda bazai wuce shekara goma sha uku ba,ya gaida mukhtar ya
amsa yana ce masa
"Jeka qofar gida ka kulamin da machine dina kafin na fito"
"To kawu" ya fada yana ajjiye modar hannunsa saman randa ya fice.

Suna shirin shiga rumfarta tana daga labulen dakin


"Au sai yau kaga damar zuwa kenan......shashan yaro ana maka gata kana noqewa" ta
fada tana sakin labulen ta juya zuwa ciki.

Bata lura tare suke ba sai da suka shiga ciki suka zauna,sumayya ta gaisheta ta
amsa sama sama,ganin idonta sam bai hana yaya yahanasu yin duk maganganunta ba,ita
dai kam kanta ta sunkuyar,daga bisani ta miqe ta basu guri jin musu nason barkewa
tsakanin mukhtar da yaya yahanasu kan lissafin abinda suke da buqatar ya bada,kama
daga kudin aure kudin zance lefe har zuwa sadaki,yace zaya bada kudin aure da na
sadaki amma shikam bazaya iya yin wani lefe ba,kasuwa babu ciniki,nan ta barsu
batasan yanda suka kaya ba yadai fito yace ta tashi su tafi.

Ko sallamar da take wa yaya yahanasun bata tanka mata ba har suke wuce,suna kan
hanya babu wanda yace da dan uwansa komai har suka qarasa gidansu.

Ciki ya shiga suka gaisa da maman nata kasancewar abba malam mahaifinsu kamar yadda
suke ce masa baya nan,'yan qannanta duk suna tsakar gida mukhtar ya raba misu
biscuite kamar yadda ya saba,ya miqe zai fice yana cewa zai zaga bayansu gun wani
abokinsa idan ya dawo zai kirata su wuce tace tom.

Gaisawa sosai sukayi da mamanta ta tambayi lafiyarta da ta gidanta ta amsa mata da


komai lafiya.

Shiru ne ya biyo baya,tunanin abinda ya faru dazun gidan yaya yahanasu yayi nasarar
wafce tunaninta ba tare da ta shirya ba,haka maman ta tadda ta,ta ajjiye kwanon
dambun data je debo mata
"Lafiya dai ko sumayya" murmushin yaqe tayi ta janyo kwanon dambun tana budewa
sannan tace
"Mama aure yaya mukhtar zai qara" maganar ta dan taba maman,tsakanin da d'a da
mahaifi,tausayinta ta dinga ji yana ratsata,babu shakka abu ne mai wuya zama da
kishiya a wannan zamanin,abu ne da har yau yaqi dadi a cikin gidajen aurenmu,ga
yarinyar tata gwanar haquri da shegen zurfin ciki ce,amma duk da haka ta sani ba
duka aka taru aka zama daya ba,duk abinda zata gaya mata a yanzu shi zai zame mata
madubin dubawarta.
Murmushi maman tayi sannan tace
"Babu komai,ai namiji mijin mace hudu ne,Allah ne ya halasta masa,abinda nake son
gaya miki kawai shine kada ki soma cewa zaki tada hankalinki ko ki daga hankalin
mijinki,ki zauna da ita tsakani da Allah,ki sauke duk wani haqqi nata dake
wuyanki,sumayya kada ki sake kice zaki cuceta,idan kika cuceta sumayya ni
mahaifiyarki ban yafe miki ba".

Kai ta gyada" in sha Allahu mama zanyi duk abinda kika ce,da ikon Allah bazan zama
mai sabawa maganarki ba"a hankali maman ta dinga hilatarta tana kwantar mata da
hankali har ta kusa cinye dambun baki daya.

*mrs muhammad ce*

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍🏽 *~KUNDIN QADDARATA~*✍🏽
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

_bismilla hir rahmanir rahim_

*inna ma'al usri yusrah,fa inna ma'al usri yusrah*

______________________

0⃣3⃣

    Suna cikin hirar mukhatr ya turo qaninta mubarak yayi kiranta ta fito zasu
tafi,nan mama ta hada mata su kuka kubaiwa daddawa barkono har da tsakin masara
saboda dambu ko dan malele,tana hada mata kayan tana dada kwantar mata da hankali
tare da jaddada mata kada ta sake ta tashi hankalin mijinta ko ita kanta,ko tace
zata yi wani rashin kyautawa ga daya daga cikin 'yan uwan mukhtar,haihuwa kuwa
lokaci ne,idan Allah yaso ma sai taga sanadiyyar shigowar wata ita ma ta samu nata
rabon,ta dora da cewa
"Bare ma duka duka nawa kike sumayya,mu a da can Allah na tuba ba sai kiyi shekara
goma da aure baki haihu ba babu wanda ya damu da ke,haka kema baki damu kanki ba,ci
da zuci ne kawai yanzu irin na yaran zamani" maganar sai ta bama sumayya dariya da
kunya,har ta sanya tafin hannunta ta rufe fuskarta.

       Suna shirin kwanciya bacci lokacin yana zaune gefan gadonsu yana shan ruwan
baqin shayi,ita kuma tana taje kanta,ta cikin madubin yake qare mata kallo yadda
kullum take sake zama cikakkiyar mace,tamkar ba zata masa magana ba amma abun nata
cinta a zuciya,saboda daga shigowarsu gida zuwa shirin kwanciya da sukeyi yanzu
yaya yahanasu ta kira shi ya kusa sau biyar,duk da bata kusa amma ta fahimci
taqaddamar me suke,maganar lefe ne da yace ba zaya yi ba,ta dan cije lebanta sannan
tace
"Ya mukhtar"
"Ya akayi sumy?" Ya fadi yana saurarenta.

    Sai data jawo dressing chair gabansa ta zauna sannan ya dubeshi,cikin nutsuwar
nan tata hadi da kaifin hankali da zurfin tunani
"Ya mukhtar kayi haquri idan na maka shishshigi,sai nake ganin baka kyauta
ba",cikin rashin fahimta ya tambayeta
" da akayi me fa?"ta danyi jim kamar ba zata yi magana ba sannan tace
"A ganina bai kamata ka dinga sa'insa da yaya yahanasu ba,ko banza ta girmeka,bugu
da qari ita ta zame maka tamkar mahaifiyarka ka manta?,ita ta raineka har ka kawo
girmanka,ka san cewa dai ba zata taba yin abinda zai cutar da kai ba,a ganina auren
nan saboda qaruwarka ne take buqatar kayi,ko babu komai idan fa'iza ta haihu sai an
fara cewa danka kafin a ce dan yaya yahanasu ko?" Ta dan sarara da maganar tana
hadiye wani abu mai daci wanda bata san meue sanadiyyar tasowarsa ba daga qirjinta.

     Ko bata qarasa ba ya fahimci kan me take magana,saboda haka ya bata fuska


"Kinga sumayya,babu ruwanki da wannan maganar ki fita a cikinta,lefe ne nace
bazanyi ba suyi mata,ai bani nace ina son auren ba ko?,ina zaman zamana haka kawai
ina lallaba rayuwata sai su baro min aikin da bani na saka su ba?".

       Kai take gyadawa idonta cikin nasa wanda tuni ya tara qwalla shirin zubowa
kawai take
" na gode ya mukhatar,ina ka taba gani an auri budurwa ba'a yi mata lefe ba?bayan
haka kuma ka riga da ka san cewa matuqar bakayi lefe ba to sumayya ce ta hanaka,duk
wanda yaga laifina ko ya zageni ya mukhtar kai ka jawomin"sai ta tashi daga saman
kujerar ta haye gado ta lulluba har saman kanta kaana ta fashe da kuka.

     Har cikin ransa ya dinga jin shigar kukan nata,ya runtse ido yana jin bata can
can ci haka ba,da me zata ji cikin abu ukun,sai ya sanya hannayeshi ya dagota baki
daya zuwa jikinsa yana goge mata hawayen tare da fadin
"Ya isa sumayya,ya isa,me kike so ayi?,gaya min" sai da taja hanci kadan sannan
tace
"Kayi lefe kamar yadda yaya yahanasu ta buqata"
"Shikenan an gama,sunci darajarki" sai ta saki dan qaramin murmushi sannan tace
"Na gode".

       Washegari yana cikin karyawa kafin ya fita wayarsa ta soma ringing,sumayya


ta dauko ta miqa masa da yake tana kan t.v stand tana chargy,daga yanayin maganarsa
kawai ya tabbatar mata yaya yahanasu ce,kuma zancan jiya ne bai wuce ba,a gimtse ya
amsa cewa zaiyi laifen,amma fa sam shi ba kudi zai bada ba,zaiyi iyakacin abinda
zai iya ya kawo musu,daga haka ya kashe wayan ma baki daya,tana gefe tana
saurarensu kanta sunkuye tana wasa da yatsun hannunta,ya kammala ta masa rakiya
kamar yadda ta saba,dawowa yayi da baya ya rungumeta sannan ya sumbaci goshinta
" Allah yayi miki albarka"ya fada yana sakinta
"Amin ya mukhtar" ta fada cikin farinciki,saboda tuni maman ta ta gaya mata
albarkar miji na bin mace,hakanan fushinsa ko  yardarsa na tare da ta ubangiji.

     Cike da farinciki ta koma cikin gidan saboda albarkar da ya sa mata ta faranta


mata,taci gaba da kintsa ragowar ayyukan da suka rage mata,bata jima da kammalawa
ba ta zauna tana hutawa wayarta ta dauki qara,da sauri ta daga ganin sunan abbanta
na yawo bisa screen din wayar.

     Cikin girmamawa ta gaidashi ya amsa mata yana tambayarta gida da kuma mukhtar
tace ai yama fita.
"Mamanki ta gaya min mukhtar zai qara aure"
"Eh abba malam"
"To ina fata ba zaki watsa mana qasa a ido ba,ba za kiyi watsi da tarbiyyar da muka
baki ba"
"In sha Allahu malam"
"To Allah ubangiji ya albarkaceki ya albarkaci aurenki" daga haka ya dora mata da
nasiha cikin hikima da ilimi,cike da fadar Allah da ma'aikinsa,hakan ba qaramin
sake kwantar mata da hankali yayi ba,ya qare nasihar tasa da fadin
"Babu wani abu da kike buqata?"
"Eh babu malam" ta fadi hakan saboda babu abinda mukhtar ya gaza da shi,don hatta
kudin kashewa yakan qimanta ya bata,ya danganta da yanayin samun da yayi a kasuwa.

"To shikenan,haka ake so,inaga zan duba wajen sati na gaba ko wajejen satin
sama,zan aiko abubakar(yayanta ne shine na fari a gidansu,amma baiyi aure ba karatu
yake)zaizo. A fidda kayan gadonki da kujerunki a sauya miki wasu" farinciki ya
cikata,duk da cewa wadan nan natan ma babu abinda sukayi,don sanda sukayi shekara
hudu da aure mukhtar ya fitar da na aurenta na ainihi ya sauya mata su.

"Na gode,na gode qwarai malam Allah ya saka da alkhairi,ya qara lafiya da nisan
kwana mai amfani,Allah ya qara budi da rufin asiri"
"Amin ya Allah,amma abinda zaki biyani da shi kawai kici gaba da zaman aure cikin
gidanki"
"Da yardar Allah malam" ta amsa masa daga haka sukayi sallama.

     Sosai malam yake aon sumayya,don tun tana mitsitsiyarta halayyarta daban
take,tana da tarin haquri kawaici da zurfin ciki,shi yasa duk cikin yaransa yafi
sonta,duk da cewar dukan yaran nasa maman sumayyan ce ta haifesu,ko a lokacin da
suka aura mata mukhtar ma ce mata kawai yayi ga miji yayi mata kuma aure zaiyi
mata,bata ce komai ba don ba wayo gareta ba,duk da haka dama kunya gareta,gudu tayi
ma ta bar gurin sanda malam din ke gaya mata,ita ce yarinya mace ta farko a gurinsa
sai qannenta su hudu.

    Mukhtar zamu iya cewa rako wani abokinsa yayi gurin malam din kasancewar malam
din yana bada karatu tsakanin sallar magariba da isha'i wa matasa da dattijan
unguwa,gani daya ya yiwa sumayya yaji tayi masa kasancewarsa mutum wanda sam baya
da sha'awar auren macen da tayi zurfi a karatu,tunda yayi universty shima yaga irin
qazamar rayuwar da mafi yawancin 'yammatan keyi duk da ba duka aka taru aka zama
daya ba.

     To sara ne yazo kan gaba shima malam ba mai son yaransa suyi bokon bane,saboda
haka yana bincike kan mukhtar ya tabbatar da nagartar halayyarsa ya basu auren
sumayyan.

     Da fari 'yan uwansa sun so su turje kan mai zai sa ya auri yarinyar da
rainonta kawai zaiyi,musamman yaya yahanasu wadda ita ta riqe mukhtar din,saboda
bai wuce shekara biyar a duniya ba Allah ya yiwa mahaifiyarsu rasuwa wanda dama tun
mukhtar na da watanni a duniya mahaifinsu ya rasu,to amma daga bisani suka haqura
kasancewar sun lura mukhtar din bashi da niyyar fasa aurensa.

     Da fari sun karbi sumayyan a matsayin 'ya kuma qanwa,amma daga lokacin da suka
lura da gatan da mukhtar ke mata hassada ta soma aiki,duk da ba zaka kirashi mai
kudi ba amma mai arziqi ne,iyalansa sunfi qarfin yin kukan rashin wani abu cikin
gidansa,shekara uku tayi ta cika shekara sha shida,a lokacin ta zama mace saboda
Allah ya mata halitta da jiki mai kyau,sai suka juya akalar hassadarsu kuma zuwa sa
mata idon yaushe zata samu ciki?,yaushe zata haihu?,wanda har yau suna bisa wannan
bigire basu sauka daga kai ba

Wannan kenan.....
      Sati hudu suka sanya lokacin aurensu,sunata budirinsu suna shirye shiryensu
ango ko oho,kayan lefe ne yace zaiyi kuma bai fasa yi din ba.

     A falonta ta tadda shi yana amsa waya bayan ta gama soya masa wainar fulawa da
yace yana sha'awa har tana ta masa dariya qai qwalama ce kawai ta dameshi,mai ya
hadashi da abincin mata,ya sauke wayar daga kunnensa yana janyo plate din tare da
budewa yana fadin
"Yauwa amaryata kuma uwargida na" qeya ta juya masa tana turo baki
"Um_um,barni a uwar gidan dai,amaren na nan tafe" cikin sigar tsokana ya dan talle
mata qeyar data turo masa
"Ka jini da yarinyar nan wai itama ta iya kishi?" Duk da tasan wasa yake sai ta
juyo tana dubansa zuciyarta na raunana amma ta dake
"Don me bazanyi kishinka ba ya mukhtar?" Bai so maganar tayi tsayi don bata masa
rai maganar take balle ita saboda haka yace
"Haka ne" a taqaice sannan ya hau qirqiro santin waina duk da cewa a zahiri tayi
dadin,biye masa tayi tana masa dariya tare da kara masa filo a bayansa.

    Sai da yaci kusan rabi sannan tace da shi


"Nikam yaya mukhtar banga kana shiri ba" cikin son samun qarin bayani yace
"Wanne irin shiri?,name?"
"Banga wani sauyi ba agidan nan?"
"Kamar wanne iri fa" ya sake tambayarta
"Gani nayi kace na kwashe shirgin dake cikin dakin shirgin can nan amarya zata
zauna,nace maka ka hada mata da naka dakin itama ta samu falle biyu ka qiya,to a
barshi a hakan,amma ya kamata ace daga dakin nata zuwa tsakar gida ko shafen farar
qasa ka yi masa don ya haska ko,tunda nawa dakin ba'a jima da yi masa fenti mai
tsada ba fes yake kamar yau akayi".

    Banza yayi da ita kamar bai ji ba har sai da ta qosa tace masa
" kana jina kuwa ya mukhtar?"
"Ina jinki kuma bazan yi ba,ke wallahil azim kika sake yimin magana makamanciyar
haka sai ranki ya baci,idan zata zo ta zauna haka ta zauna,idan ba zata zauna ba ta
qara gaba dama ba ni na gayyatota ba,haba,dame kike so naji?".sai ya miqe a fusace
ya fice zuwa dakinsa ya barta da sauran wainarta.

     Jikinta ne yayi sanyi,tayi da na sanin yi masa maganar,sai data bashi kusan


awa guda sannan ta gyara gurin ta shirya zuwa shigar barci tabi bayansa don ta
lallashe shi.

     Bata sake masa maganar ba kuwa,sai ranar asabar ranar 'yan yaranta duka suna
gida saboda ba ranar karatu bace,ta aika nana tayi mata kiran wani dan saurayi dake
maqotansu,tace ya duba mata don Allah farar qasa kwano nawa zai isa dakin zuwa
tsakar gidansu ya gaya mata yadda yake zaton zata isa,cikin kudin da take adanawa
ta qirgo ta bashi har da kudin mota,cikin minti talatin ya dawo,tasa ya jiqa mata
sannan ya tafi ta masa godiya ta bashi dari tace yasha ruwa.

      Yaranta ta kalla wadanda sun kai su takwas,akwai


bilkisu,fatima,hauwa'u,khadija,aisha,ummi,asma'u sai nana ta gurinta
" maza kowa yaje gida ya cire kayan jikinsa ya saka marasa kyau zamuyi fenti"cikin
zumudi kuwa har suna rige rige suka fice suna murna.

     Kafin su dawo itama har ta sauya nata kayan,saiga yaran kuwa,nan suka zage
suka dinga shafen farar qasar,abinka da ba aikinsu bane tun safe har bayan
la'asar,nan ta musu girki suka ci,idan sun huta su dora.

    Cikin haka sai ga maman nana ta shigo,salati ta saka tare da kama habarta ganin
sumayya saman tsani,duk sunyi face face da farar qasa
"Ni salma,ai nayi zaton qarya nana take da tace fenti zakuyi ashe da gaske
take",dariya ta qyalqyale da ita tana saukowa daga kan tsanin
" to ya zanyi maman naana,ya mukhtar yaqi yarda yayi fenti,shi yasa na siyo da
kaina mukeyi ni da 'ya'ya na"(da yake ita kadai ta gayawa zancan,saboda yadda take
mata tamkar mamanta,tafi shaquwa da ita fiye da sauran iyayen yaran.

    kai maman naana ta dafe tana cewa


"Lallai sumayya quruciya na damunki,yanzu kishiya kike yiwa fenti da kudinki da
jikinki,Allah ya shiryeku" ta fada tana dariya
"To sauko hakanan na kira muku jamilu(babban danta) ya qarasa muku,tunda kun rantse
sai kunyi" murmushi tayi tana kakkabe jikinta tare da fadin
"Ai kuwa mun gode" da kanta maman naanan ta leqa ga nemo jamilun,cikin 'yan qananun
mintina ya qarasa musu inda basu qarasa din ba.

"Magana ba zata yiwu yau ba sumayya na dawo gobe,tunda yau kun zama 'yan qwadago
yinin fenti kukayi" ta fada tana miqa mata ledar data shigo da ita,tana dariya ta
amsa tana dubawa,ko bata ce mata komai ba ta fahimci meta kawo mata,magunguna ne
masu kyau ingantattu na 'ya'yan itatuwa data saba bata.

     Sanda mukhtar ya dawo yaga aikin da sukayi cak ya tsaya,sai kuma yayi gaba ba
tare da yace komai ba,qaunarta ke saka ratshi,uwa uba kuma tausayi don yasan har
yau da zallar quruciya tattare da ita,inda yasan zata yi da tun sanda yace ba zaiyi
ba da tuni ya hada da yimata hannunka mai sanda don kada ma tace zata yi din.

    Kamar yadda abba malam ya alqawarta mata,sati biyu da yin maganarsu kuwa saiga
motar kaya,irin kayan da sam sumayya bata zata ba,kaya ne 'yan italy masu kyau da
tsada har kujerun wanda ko a aurenta ba'a yi mata irinsu ba,har da qarin labulaye
masu kyau da door mat,mamam naana da maman ummi ne tare da uaran gidanta suka
tayata jerawa,saiga dakinta ya fito fes tamkar ma ita ce amaryar,mukhtar baiyi qasa
a gwiwa ba yace har gida yiwa abba godiya,hakanan shima ba'a barshi a baya ba,kayan
kitchen baki daya ya sauya mata,kasancewar yanzun an maida kitchen din bangare
biyu,hannun hagu da hannun dama,kowacce anyi mata kantarta da drowers dinta,hakanan
ya sauya maya plasma wadda tafi waccar girma harda qarin home thierther,sai ta
dinga mamaki da yace bashi da kudi da bazaiyi lefe da fenti ba,bata ce masa komai
ba tunda ta fuskanci dama ce bai gani ba,godiya ta dinga zuba masa sosai kamar
yadda yake al'adarta.

     Mamanta ita ta sauya mata showglass da kayan cikinta baki daya,farinciki duk
ya cika sumayyan,ta fuskanci ita 'yar gata ce sosai,batasan duk sunyi haka bane don
kwantar mata da hankali da sake sa mata nutsuwa,ba qaramin kyau dakinta ya sake yi
ba sai ka rantse amarya ce.

*mrs muhammad ce*

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍🏽 *~KUNDIN QADDARATA~*✍🏽
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*
*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

__________________________

_bismilla hir rahmanir rahim_

_iza qada amran fa innama yaqulu lahu kun fa yakun_


________________________

0⃣4⃣

      Sati guda da kammala gyara gidan ranar wata litinin mukhtar ke gaya mata ran
laraba masu kafin amarya zasu zo,sai da taji wata faduwar gaba da bata san ta mece
ba
"Allah ya kawo su" ta fada kawai kana tayi shiru tana dubansa yana rubuta lissafin
kasuwa cikin wani qaramin excercise book.

       Jin shirun yayi yawa ya sanyashi dago kansa ya dubeta,sai yaga littafin take
kallo,ya sanya tsinin biron ya dan mintsini cinyarta,sai ga dago tana dubansa
fuskarta dauke da murmushi tana sosa gurin
"Yadai 'yammata?" Kai ta girgiza tana murmushi
"Babu komai.....cewa nayi ai za'a yi musu girki ko,tunda naga ana yi",rai ya
bata,don yasan yanzu zata fara soko masa zantukan da baiso,ya tabbatar sumayya
danya ce shakaf,domin da wata macen ce aka yi mata zancan kishiya da tuni yanzu
gidan ya dade da zama dan qaramin sansanin yaqi,ya tabbatar ba qaramin dauki ba
dadi za'a yi ba,duk da quruciyarta ma ya tabbatar da gudun mawar qarin tarbiyya da
ta samo daga gida,tunda ko a gidansu bata taso taga mamanta da kishiya ba,da wata
ce wannan kadai ya isheta mafaka.

" ba da kayan abinci na ba,kuma kema ban lamunce kiyi ba,idan kunne yaji....."sai
ta ja bakinta ta tsuke,don bata son yayi fushi da ita irin na baya kan zancan fenti
da lefe.

     Washe gari ranar talata gefin magariba lokacin dawowarsa,ta gama komai kamar
yadda yake al'adarta,gidan nata qamshin turaren tsinke,tana tsakiyar yaranta ta
siyo madarar ruwa ta musu iloka ta rarraba musu suna sha,wani yaro dake bayan
gidansu yayi sallama dauke da akwati wasu yaran na bayansa.

"Wai gashi inji yaya mukhtar" ya fada kamar yadda yaji matar gidan na gaya masa,sai
mamaki ya kamata don bata ji alamar  shigowarsa ko qarar babur dinsa ba,tashi tayi
ta bude masa labulen falonta suka shiga da su,akwatunane guda shida masu kyau duka
iri daya uku set daya uku set daya.

    Suna fita ya shigo yana dauke da baqar leda,duka yaran suka masa sannu da zuwa
suna qoqarin tafiya gida,ya bibbisu da alawa kamar yadda al'adaraa take sannan suka
bi sumayya da
"Anty sai da safe.....anty sai gobe"
"To Allah ya bamu alheri" ta amsa musu suka fice ta rufe gidan sannan tabi bayan
mukhtar da tuni ya shige falon.

    Murmushi ta sakar masa kamar yadda ya sakar mata


"Kinyi kyau sumayya ta" kanta ta sunkuyar cikin kunya tana murmushi
"Na gode yaya na,sannu da zuwa" ta fada tana cire masa hular kansa da bai samu
cirewa ba
"Ya kasuwar" ta sake fadi tana qoqarin ajjiye masa ruwa mai sanyi
"Kasuwa alhamdulillah......kinga ai my sumy abinci zaki kawomin don yunwa nake
ji",ta dan zaro ido tana dubansa
" da wuri haka yau?,na zaci sai ka dawo daga sallar magariba",shafa cikinsa yayi
yana murmushi
"Salla bazata yiwu cikin nutsuwa ba ina fama da yunwa,taimakeni ki bani sumayya
magaribar da sauran lokaci,idan na kammala ko masallacin sun idar mayi jam'in da
ke"
"To" ta fada tana miqewa zuwa kitchen.

     Bayan ta gabatar masa da komai tuwon semo ne miyar kuka sai qamshin daddawa
take duk da babu nama amma tayi dadi qwarai,taasa bismillah sannan ta koma gefansa
ta zauna.

     Sai da ya kai loma biyu sannan yace


"Ga kayanku nan ki duba kiga" ya fada yana mata nuni da akwatunan dake jere gefe,da
to ta amsa masa sannan sannan ta sauka qasa ta janyo akwatunan ta soma dubawa.

    Tana dubawa yana zuba mata santin tuwo,yayin da itama ke santin kayan,komai
yayi kyau,sai data kammala tas,lokacin har ya gama cin twon ya jngina da kujera
yana kallonta tana ta daga kayan tana yabawa,ta rurrufesu yadda ta gansu sannan ta
dubeshi.
"Nayi zaton ma har an kai kayan ne naga lokaci ya qurato"

"Um um" ya fada a taqaice

"Sunyi kyau sosai ya mukhtar,Allah ya qara budi,saidai komai naga bibbiyu ka saka
kala daya,nufina kayan dake cikin akwatin kayan sawa sune a daya akwatin,under
wears da mayafai ma"

"Eh,akwatin uku naki ne uku nata", idanu ta zaro a firgice tana dubansa
" aini yaya ka manta ka yimin lefe na tun sanda zaka aure ni?"
"Na fiki sani,kayan fadar kishiya na miki".

    Tsoro ne sosai ya kamata,tsoron su yaya yahanasu,ina zata sa kanta idan suka ga


wadan nan kayan,komai iri daya ita da amaryarsu,hatta da man lebe iri daya
ne?,tabdi lallai ya mukhtar so yake ya janyo mata bayan lallabawa takeyi.

" gaskiya ya mukhtar ba'a haka,itafa amarya ce ya zaka hadamu kayi mana abu iri
daya?bayan kayan kitchen da kayimin,ka sauya min kayan kallo,kasan su yaya yahanasu
sai sunce wani abu idan ma basu ga laifina ba lo sun zargeni ba"

"Eh,saboda kin fiye min ita,ke din zabi na ce,kuma raino na ce,tun kan kisan ciwon
kanki kike zaune da ni,tun ana ciyar da mu bana daukar nauyinki,ita din ban santa
ba,bansan halinta ba bansan ko zata iya irin zaman da kika yi da ni ba,sannan idan
su yaya yaha da kike zance ai basu suka yimin ba,da kudina nayi balle a ce don
me?,kufi na ne kuma iyali na ne,saboda haka bana buqatar ki sake cewa komai".

    Tun asali ita ba mai musu bace da ya mukhtar din ba,girmansa take gani,kallon
yaya take masa saboda haka cikin sanyin jiki tsoro da sanyin murya tace
" hidimar ce naga kamar taso tayi yawa,na gode Allah ya saka da alheri,Allah ya
jiqan magabata ya basu aljanna madawwamiya"cike da jin dadin yadda ta yiwa
mahaifansa addu'a yace
"Amin,Allah yayi miki albarka"
"Amin ya mukhtar na gode sosai".

     Tun qarfe takwas washegari ta kammala komai saboda da wuri mukhtar yace zai
fita saboda masu jere,qarfe tara ta sallameshi,har ya fita ya dawo ya dubeta
" idan kinga babu dadi zaman gidan,na baki izini kina iya tafiya duk inda kike
so,idan yaso idan sai kimin waya ki gayan inda kike,idan na taso daga kasuwa sai na
biyo na daukeki"murmushin yaqe kawai tayi,don hakanan tunda ta tashi yau take jin
fargaba da bacin rai
"Babu komai ya mukhtar zan iya zaman ma,me zai hana"
"Kada dai ki takura kanki idan ba hali kiyi ficewarki"
"To,a dawo lafiya",ya amsa mata da " Allah yasa"ya saka kai ya fice.

      Tayi wanka ta shirya tsaf cikin atamfarta da abbanta ya dinka mata ita
kwanaki,dark brown ce da adon mint green ajiki,sosai ta mata kyau dinkin ya zauna
mata das a jikinta,falo ta koma ta zauna,jikinta a sanyaye bata san dalili ba,gidan
ya mata shiru kasancewar 'yan hirar tata duka ana makarantar boko sai sha biyu da
rabi suke tashi.

     Ganin akwai wuta ya sanyata jona kayan kallo,tashar arewa 24 ta kama,cikin


sa'a suna maimaicin shirin agent ragab,tana son film din sosai,kusan shi ya dauke
mata hankali har sha daya da rabi.

    Gamawarsu yayi dai dai da bugun qofa da ta soma ji,ta miqe ta fito tana
tambayar waye tare da nufat soron,tun kafin ta kai ga budewa taji cikin kakkausar
murya
"Malama ki bude bana son salo kin wani kama qofar gida kin rufe,bayan kinsan akwai
wadanda zasu zo,dadin abun saura 'yan kwanaki naga ta iyayi" da sauri ta qarasa
bude qofar domin tuni ta dauki muryar wace,yaya bara'atu ce sai fadima tsaye a
bayanta,dai sauran da bata san su waye ba,tasan dai ba zasu wuce dangin amaryar ba
tunda ita daga amaryar har 'yan uwanta babu wanda ta sani,iyaka dai tasan cewa
amaryar 'yar aminiyar yaya yahanasun ce.

      Saura kadan yaya bara'atun tayi gaba da ita badan tayi gaggawar matsawa gefe
ba ta wuceta saura suka biyo bayanta suka bar mazan da zasu shigo da kayan katakon
da kujerun.

     Bata qosa ba tabi bayansu zuwa dakin da aka bawa fa'izan wanda tuni yasha
fentin farar qasar data siya tayi da kudinta,babu komai a dakin a share yake fes
kasancewarta gwanar tsafta ce,tun kafin tace wani abun yaya bara'atun ta galla mata
harara yayin da sauran suka mata caa da ido
"Uban me kuma kika biyo mu ki mana?" Ta tambayeta tana huci,qasa tayi da kanta
saboda yaya bara'atun ta girme mata nesa ba kusa ba cikin ladabi tace
"Zuwa nayi mu gaisa ne"
"Riqe gaisuwarki bama so"
"Uhmm,wallahi kuwa" fatima tayi caraf ta karbi zancan
"Allah ya baku haquri" ta fada sannan ta juya ta fice kai tsaye falonta ta shige
taci gaba da kallonta.

       Miqewa tayi zata dauko wayarta dake uwar daki tana ringing ta hangosu suna
kici kicin budw kwadon dake rufe da dakin ya mukhtar wanda da kansa yasa ya rufe ya
tafi da abinsa,da taga a kulle yake sai ta saka tana fadin
"Lallai,kaddai yaya mukhtar daki daya ya bayar,tabdi lallai,yana nufin ita a falle
daya zata zauna waccar tana da ciki da falo....haka ne....mu shirya mata kayan idan
muka koma ma sanar da yaya yahan",bata ce uffan ba don ba mas'alarta bace,ko tata
din ce ma basu sako da ita ba.

      Ya mukhtar ne ya kira yana tambayarta komai lafiya ko tace eh sannan sukayi


sallama ya kashe wayar.

      Kafin wani lokaci gidan nasu ya cika da 'yan jeren,ko ina sai shewa ke tashi
da qananun magan ganu,take tsoro ya cika sumayya,ta dinga kiran lambar maman naana
kan ta shigo ta tayata zama amma wayar a kashe take,ta dinga leqe ta window dinta
taga ko akwai hanyar da zata ratsasu ta fice.
      Bata samu sararin gurin ba sai da suka fara daura alwalar sallar azuhur,tayi
hanzarin shiga uwar dakanta ta dauko hijabinta tare da padlock  ta sanyawa qofar
dakin nata ta fice.

     A qofar gida ta tarad da su naana suna tsaye,suna ganinta suka nufota da


sauri,ta dubesu tana cewa
" me kuma yau kuke tsaye a qofar gida?"bilkisu ce tace
"Hanamu shiga anty akayi?"
"Waye ya hana ku shiga?"
"Masu jeran amarya"inji nana,take taji ranta ya baci,sam bata son abinda zai taba
mata yaran,ba zata juri haka ba sam,bata ce misi komai ba sai
" kuzo muje,qila fitina zaku shiga kuyi musu shi yasa suka hanaku shiga don kada ku
bata masu kaya"
"Wallahi anty a'ah" inji aysha
"Shshshshah" sumayya tace da su,sun san me take nufi ko batayi magana ba,bata da
son su kawo mata hirar wani dama.

      Gidan mamam naana ta shiga,ta taras da ita tana kwashe abinci cikin kula
"Ina zaku haka ke da gayyar yaran naki,ina kika baro baqin naki,ai yanzu nake
shirin shiga kinga girki ya tsayar da ni ina so na kammala na turasu islamiya
sannan na shigo" murmushin yaqe tayi ta ja kujera 'yar tsuguno ta zauna daga bakin
qofar falon maman nanan,yaran nata suka zazzauna kusa da ita
"Eh wlh,na gaji da zama ni daya nace bari na leqo"
"Banda abinki sumayya aiko baki aiko na shigo miki ba kyayi waya a turo miki halima
da zainab ko su tayaki zama"
"Wallahi maman naana bansan haka akeyi ba ai" murmushi tayi tana tausayawa sumayya
da quruciyarta
"Ai shikenan,Allah ya bada zaman lafiya,ya kade fitina tsakaninku"
"Amin" sumayyan ta fada cikin faduwar gaba.

     Duka yaran ta zubawa abinci suka ci sannan ta tura kowa ya gida saboda ganin
lokacin tafiya islamiya yayi,ta shirya su naana ma suka tafi sannan suka daura
alwala sukayi sallar azahar ita da sumayyan.

     Shinkafa da miya har da salad da kifi abinda ta dafa ta zubo musi cikin plate
"Sauko sumayya maza muci" kai ta girgiza don a cunkushe take jin cikinta babu space
din abinci
"Na qoshi maman nana" tausayinta ya kamata amma ta dake tayi murmushi
"Sauko muci akwai abinda nakeson gaya miki" bata da jan doguwar magana saboda haka
ta sauko ta sanya hannu suka soma ci.

      Cikin hikima maman nanan ke kwatantawa sumayya dabarun zama da kishiya,qissa


dabara da wayo kala kala,ta dora da yi mata nuni da haquri,kau da kai kara da
alkunya,gaskiya da amana,zama na tsakani da Allah,sai gashi sun tashi da abincin
tas,har sai da hannayensu ya fara bushewa da miya saboda sun kasa tashi a gun
darussan maman naana sunqi su qare,saiga sumayya na kwasar dariya saboda wani abun
idan maman nanan na gaya mata kunya ce ke kamata ko mamaki.

     Hararta maman nana tayi dariya itama nason qwace mata itama amma ta dake
saboda yadda taga sumayya na dariya wani abu da ta gaya mata
"Au dariya ma nake baki ko?,zaki ci gidanku wallahi idan baki dauke duk abinda nake
gaya miki ba" cikin dariyar ta dafe baki
"Yi haquri maman nana,abunne wallahi" ta kuna saka dariya,kada kai maman nana tayi
itama dariyar ta qwace mata,ba shakka sumayya danyace har yau,ta miqe ta dauke
plate din da suka gama cin abincin ta fice da shi.

     Basu ankara ba sukaji ana qwala kiran sallar la'asar,nan suka tashi
sukayi,maman nana ta dubeta tace
"Ba zaki koma gida kiyi girki wa mukhtar bane"
"Ina som in koma maman nana amma ina zaton har yau basu tafi ba,bari na kira ya
mukhtar din naji mai zai ce".

     Koda ta kirashi cewa yayi tayi zamanta kawai idan ya dawo din ya kirata ta
dawo,a nan tayi zamanta suka ci gaba da hirarsu har su nana suka dawo daga
islamiya,sai qarfe shida kiran mukhtar ya shigo wayarta,ta yiwa maman nana sallama
ta wuce gida.

      Kaca-kaca ta tarad da gidan tun daga qofar gidan tamkar bata taba shara
ba,kwalaye da ledojin abubuwan da suka jera duja ko ina a gidan,ga kwanukan abinci
nan nata har da sabbi da bata taba amfani da su ba,da alama ma girki sukayi saboda
kitchen din na bude zasu jerawa amarya nata kayan a ciki,mukhtar na tsaye a tsakar
gidan riqe da qugu cikin bacin rai,da alama ransa ya baci da irin abinda sukayi,ga
abincin da suka dafa din ma basu iya cinyewa ba sun kuma lalata bare a bawa
wani,zai soma sababi ta shige jikinsa ta soma lallabashi,sai da ta sauke masa
temper dinsa sannan ya tayata suka fara kintsa gidan fes.

     Kafin su kammala anyi kiran sallar magariba,ruwan wanka ta dora musu sannan
sukayi alwala sukayi sallah,bayan sun idar ta juye musu ruwan sukayi wankan tare,ta
shirya tsaf tayi kwalliya cikin qananun kaya,zata dora musu girki yace ta barshi
kawai ya zura jallabiyyarsa ya fita.

    Cikin minti a shirin ya dawo da ledoji a hannunsa,ya ajjiye kan kujerar yana
cewa
"Dauko faranti ki juye mana wannan,ki hado da cups,hala ma yau duka bakici abinci
ba" murmushi tayi sanda take fita daga falon tana cewa
"Naci mana ya mukhtar a gidan maman naana" ,ta dawo dauke da plates din ta juye
abinda ke cikin ledar.

     Tsire ne da zafinsa sai zuba qamshi yake,sai rabin gasashshiyar kaza,ta bude
dayar ledar,lemon roba ne na fanta sai maltina wanda tasan ta mukhtar din ce tunda
ita bata dameta ba.

       A nutse suke ci suna hirarsu jifa jifa kamar babu wani abu dake damunsu.

      Suna tsaka da ci wayar sa ta dauki qara,sumayya ta miqe ta isa inda take


chargy ta ciro masa kana tazo ta miqa masa,baquwar lambace,yayi kamar bazai daga ba
amma yadda kiran keta nacin shigowa ya sanyashi dagawa ya kara a kunnensa.

*mrs muhammad ce*

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍🏽 *~KUNDIN QADDARATA~*✍🏽
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)
_________________________

_Bismillahir rahmanir rahim_

*_la yadillu rabbi wala yansa_*


_______________________

*_ina taya maman farida(dan maliki,baya tsami banza,hanyan ruwa)murna sauka lafiya
tare sa samun zan kadeden baby boy,Allah ya raya mana shi cikin musulunci,ya
albarkaceshi,ya qara musu lafiya ita da babyn,sannan kuma muna kamu tun yanzu,lol_*

0⃣5⃣

    Sallama yayi maimakon ya amsa hello da ake faman cewa,yayi jim yana jiran amsa
sallamar tukun,fahimtar abinda yake nufi da akayi ya sanya aka sa sallamar
"Da wa nake magana?",cikin karyar da murya akace
" mukhtar baka ganeni ba,fa'iza ce fa"
"Fa'iza?,wacce fa'iza" wani murmushi akayi mai fidda da sauti cikin siga ta nufin
jan hankali
"Fa'iza amaryarka mana".

       Hade rai yayi kana cikin dakiya yace"ok,ya akayi?",sake marairaice murya
tayi
"Haba mana mukhtar,ai ko gaisawa ka bari muyi tukunna ko?"
"Yayi kyau,ina gajiya?"
"Gata nan muna fama da ita mun fara shiga sabgogin biki,amma mukhtar ko marmarin
sake zuwa guna bakayi,haba"
"Wannan ne dalilin da yasa kika kira ni?" Kai ta girgiza kamar tana gabansa,cikin
ji haushin yadda yake amsa mata da qyar kamar wanda aka tilastawa
"A'ah ba shi bane"
"Fadi uzirinki kai tsaye".

      Gyara zama tayi sannan cikin salo da kisisina ta fara magana


"An ce daki falle daya ka bani,haba mukhtar,ya zaka bani daki falle daya sannan ka
bawa uwar gidanka ciki da falo alhalin nice amarya ni nafi cancantar ciki da
falo"tana direwa ya dora
"Ko?,a wanne hadisin?".

     Fara quluwa tayi amma ta dake"haka na ya dace ai"


"To ai babu damuwa,sai ki gayan nawa muka hada muka gina gidan sai na fidda miki
haqqinki" ya fada cikin jin haushi da sigar gatse,da sauri tayi saurin cewa don
kada kwabarta tayi ruwa
"Allah ya baka haquri ba nufina kenan ba" tayi saurin katse wayar,cilla wayar yayi
gefe yana jan tsaki kana ya tsame hannunshi daga tsiren ya wuce daki.

      Itama kasa ci gaba da cin tayi,saboda haka ta tsame nata hannun ta fada
wanka,ta gyara jikinta ta sanya kayan bacci sannan ta lullube farantin tsiren ta
bishi da shi,cikin kwantar da murya da tausasa harshe ta sanya shi suka cinye tare.

      Ranar alhamis ta siyi relexer,nan saloon din dake bayan layinsu ta shiga aka
wanke mata kanta aka busar mata cikin drayer,da yake tana da gashi babu laifi sai
ya sake kyau ya kwanta sosai,daga nan bata shiga gida ba,gidan maman nana ta shiga
wadda ta kwaba su madara ruwan kankana qwai su dilka da kurkur tana jiran
dawowarta,ita ta gyare mata jikinta fes,zuwa la'asar ta fito shar,fatarta ta sake
wani kyau da haske.

    Tsokanarta sosai mukhtar ya dinga yi,yana mata waqa


"Uwar gida na,amarya ta,amanata ki damqeta(waqar my habib(muhammad)" dariyar itama
ta dinga yi.

     Ranar juma'a aka zo aka mata lalle ja da baqi,ta aika halima da zainab suka
karbo mata dinkinta data bada kala takwas cikin kayanta,duka sai data gwada babu
wanda bai mata kyau ba,a nan su halima suka kwanar mata da anty dije qanwar mamanta
saboda washe gari asabar zata yi wuni saboda ranar sukace zasu kawo amarya.

       Wuni tayi babu laifi ta dan tara jama'a,sosai mutanen unguwar suka yi mata
kara sun shishshigo,maqotanta na kusa da gidan ne suka zauna mata suna jira a kawo
amarya su karbeta.

       Ana gab da sallar magariba ta shiga tayi wanka,ta sauya wasu kayan cikin
kayanta,shadda ce ja wadda aka yiwa baqin stone work,kwalliya tayi mai kyau da
tsari,sosai tayi kyau saidai komai da take yi cikin sanyin jiki take yinsa,haka nan
take ta fama da fargaba da faduwar gaba,anty dije nata azalzalarta kan ta shirya
kada 'yan kawo amarya su iso bata gama shiryawa ba,ta dauki turare ta feshe jikinta
sannan ta nemi baqin mayafinta mai kyau da kwalliyar duwatsu ta yafa ta dawo falo.

       Tun magariba suke zuba idon ganin amarya har qarfe takwas na darw babu ita
babu alamarta,hakan ya sanya maqotam suka fara tafiya da dai dai da dai dai saboda
dawowar mazajensu,wasunsu kuma sun bar yara a gida,har tara shiru hakan ne yasa
'yan uwanta suka fara mata sallama suma saboda tafiya nasu gidajen,babu wanda za'a
bar mata saboda anty dije tace hakan baiyi tsari ba,sai taji zuciyarta ta raurawa
qwalla ta cika mata ido,bata san me zata yi ba batasan ya zata yi ba hakanan bata
san yadda akeyi ba,anty dije da maman nana ne suka dinga kwantar mata da hankali
tare da bata shawarwari wadanda suka sake sanya mata nutsuwa,sukayi mata sallama
suka tafi,maman nana kawai ta rage.

       Qarfe goma na dare maman nanan na shirin tafiya itama ganin shirun yayi yawa
sai ga hayaniyarsu da ta motocinsu,hakan ya sanyata ta koma ta zauna tana tsumayin
isowarsu,saidai ga mamakinta yadda akeyi a al'adance a fara kai amarya ga uwargida
su ba hakan bane,dakinta suka bude kai tsaye suka shige da ita suna faman yada
kirari tamkar jinin maroqa
"Shiga da bismillah uwar 'ya'yan mukhtar".

       Da sauri maman nana ta soko ma sumayyan wata hirar don ta hana kunnuwanta
jin abinda suke fadin,saidai ko kadan bata cimma nasara ba saboda wani tashin
hankali da taji ya ziyarceta,gudun zuciyarta ya qaru,sai ta kalli maman nana
" maman naana,qirjina bugawa yake bansan me ya sameni ba"dan murmushin kwantar da
hankali tayi mata
"Kada ki damu,wannan shi ake kira kishin,kiyita ambaton hasbunallahu wa ni'imal
wakeel,ni'imal maula wa ni'iman nasir" kai ta kada hawaye na silalo mata,ta sanya
hannunta ta share tana mai bawa kanta qwarin gwiwa tare da hana kanta da kanta
kuka.

     Labule aka bankade aka shigo,fiddausi cs goye da 'yarta,ta dubi sumayyan


sannan tace
"Kije dakin amarya,yaya bara'atu na son ganinki",cikin mamaki maman nana ta dubeta
" a'ah,ai ba'a haka,amaryar ai ya kamata tazo ko?"duban maman nanan tayi sai ta
juya ta fice ba tare da tace komai ba.
     Ko minti daya ba'a qara ba saiga yaya bara'atun ta shigo
"Baiwar Allah ke a suwa kuma,wacece ke da har zaki hanata zuwa,to bari kiji,idan ma
irin masu shige da fice ne gidan kishiyoyi suna hurewa kishiya kunne wahalar da
sumayya kawai zakiyi,don zama fa'iza tazo yi ta kuma hayayyafa,ba mun kawota ne don
ta tafi ba,saboda haka ke sumayya ina jiranki", wani abu yazo ya tokare maman nana
a wuya,tamkar zata tanka sai taga hakan bashi da wani alfanu,tayi qoqarin kai
zuciyarta nesa,saboda koda ta tanka din qila qarshe abun ya juye kan sumayyan wanda
bazata so hakan ba,sai abun ya mata yawa ta rasa da wanne zata ji.

     Itama ta riqe hannun sumayyan cikin kalamai na qarfafa gwiwa ta mara mata baya
har zuwa dakin marya,babu laifi dakin ya cinye komai nata kasancewar yana da
yalwa,kuma ba wasu uban kaya suka mata ba,tunda gaba daya sun daga hankali ne anyi
bikin cikin matsatstsen lokaci ba tare da sun gama shiryawa ba su kansu.

   
       Gefe daya suka samu suka zauna,sumayyan ta gaidasu daidaikum cikinsu suka
amsa,maman nana kam babu wanda ta duba cikinsu don dama darajar sumayyan ya sanyata
shigowa dakin,wata 'yar tsohuwa ce dake zaune gefan amarya wadda ta lullube
fuskarta da mayafi tace
" to sumayyatu,ga 'yar uwa nan mun kawo miki,abokiyar zama,Allah ya baku zaman
lafiya,muna fata zaku hada kanku ku zauna lafiya"
"Kowa ya kwana lafiya ai shi yaso ato,fa'iza dai gata nan zama daram ila yaumut
takunu" yaya bara'atu ta karbe zancan daga gun tsohuwar,rai bace maman nana ta daga
kai ta dubi yaya bara'atu,mamaki take bata,wai 'yar yarinyar da duka duka take
cikin shekaru na sha takwas take zagewa babba da ita tana yadawa wadan nan habaice
habaicen da suka girmi kanta,babu lallai ma kan nata ya iya dauka,ina laifi ma ta
bar yaranta masu shekara sha hudu sha biyar su gayawa sumayyan?,wata qila ace wadan
nan sine dai dai da ita,amma ba ita ba wadda ta kusa linka shekarun sumayyar ba.

      Ta tabbatar idan taci gaba da zama cikin dakin tabbas za'ayi batacciya da
ita,bata so kuma wani abu na tsiya ya hadasu,tunda duk tsiya tafiya zasuyi ba zasu
shekara ba,kuma gidan dan uwansu ta shigo sunci albarkacinsa,tunda mukhtar kowa ya
shaidi halinsa,sai ta kama sumayyar ta miqar sannan ta ari bakinta ta ci mata
albasa,don ta fuskanci ba zata iya magana ba kuka take qasa qasa kanta duqe
"Insha Allahu baba babu wata matsala,don sumayya bata da damuwa mu mun shaideta tun
tana tatsitsiyarta muke tare da ita,zaman lpy an sameshi an gama da izinin Allah"
"To Allah ya yarda 'yar nan" cewar tsohuwar.

       Da sauri ta janye hannun sumayyan suka fice saboda ta soma ganin bakinsu
yana motsi suna shirin fara qananun maganganu,sai data tabbatar sumayyan ta samu
nutsuwa kana tayi mata sallama ta tafi,zuwa lokacin suma 'yan kawo amaryar suna
qofar gida suna shirin tafiya.

      Sha daya na dare agogon falon nata ya nuna mata,gidan yayi shiru kowacce na
dakinta,sauqinta daya akwai wutar nepa da ta haskake ko ina cikin gidan,ta sauke
ajiyar zuciya tana ci gaba da jan hasbunallahu wa ni'imal wakil,har zuwa lokacin da
taji an turo qofar gidan an shigo,sai ta miqe tsam a tsorace kasancewar basu taba
barin qofar gidan nasu haka ba.

      Tana ji aka rufe qofa ta biyu hakan ya alamta mata cewa mai gidan ne,ta aauke
ajiyar zuciya duk da cewa tana tsayen bata zauna ba.

      Da sallama ya daga labulen dakin idanunsa ya sauka a kanta,ta kowa yayi a


hankali ya shigo dakin yana dubanta yadda tayi carko a tsaye,cikin sanyin murya
yace
"me kikeyi a tsaye haka kamar wadda taga wani abun tsoro" ta saki ajiyar
zuciya,muryarta a sanyaye tace
"Ji nayi ana taba qofa ne",murmushi yayi yana ajjiye ledojin hannunsa
" ke kam farar kura ce sumy"sai tayi murmushin yaqe tana kawar da kai,ta qarasa
inda yake tana masa sannu da zuwa ya amsa yana zama kan daya daga cikin kujerun
falon
"Hada min ruwan wanka sumayya" ta danyi sororo kamar tace wani abu sai kuma ta fasa
tace to.

    Wanka yayi sannan ya sauya kayansa,falon ya dawo ya zauna yana maida numfashi
cike da gajiya,shiru ne ya ratsa tsakaninsu kowa ya rasa abinda zaya cewa dan
uwansa har kusan sha daya da rabi.

      Motsi suka dinga jiyowa a tsakar gida,kallo juna suke suna sauraron motsin ba
tare da kowa ya cewa kowa komai ba,sumayya ce ta fara fahimtar amarya ce,sai ta
dubi mukhtar
"Ya mukhtar bacci nakeji"
"Hala ma korata kike da dabara ko?"kai ta kada zuciyarta a cunkushe
" a'ah ya mukhtar ba haka bane"shiru yayi har kusan mintina goma wanda motsin da
suke ji na qara qarfi kadan kadan.

    Miqewa yayi ya dauki leda biyu cikin ledojin da ya shigo da su ya tura mata
daya sannan yace
"Tashi muje ki rakani" daga kai tayi kawai ta dubeshi,tamkar tace ba zata ba amma
sam bata iya rashin kunya da gardama ba,kuma ba zata fara a kan ya mukhtar din ba
da take ganin qimarsa.

      Mayafinta ta janyo ta yafa sannan ta miqe,tare suka jero har zuwa qofar
dakin.

      A tsaye suka sameta a bakin qofar dakin,tana ganinsu tayi hanzarin komawa kan
kujerar ta zauna,saidai kallo daya zaka mata ka fuskanci ko kadan babu walwala
saman fuskarta.

     Mazauni kowanne ya yiwa kansa,shiru ya dan ratsa,sumayya ta gyara zama tayi


qoqarin cewa
"Sannu amarya"
"Uhmmm" kawai ta fadi,shirun suka sakeyi,sai da ta mula don kanta wai ita an mata
laifi kana ta gaida mukhtar din,ya amsa sannan ya fara magana,daki daki daga bisani
ya gangaro ga rufewa
"Daga qarshe ban auroki don ki raina min mata ba,ban auroki saboda sumayya ta gaza
ta kowanni fanni ba,ina son mata ta matata tana sona,bana son tashin hankali cikin
gidana,na riga da nasan halin sumayya tun tana mitsitsiyarta,saboda haka ku hada
kanku ku zauna lafiya.....haka kema sumayya duk da nasan ki tun ba yau ba baki da
matsala,inaso ki dore kan halayenki kada kice zaki sauya,saboda bazan lamunci
rashin gaskiya ba......akwai wani sauran mai magana?".

      Jin shiru ya sanya duka suka gane ba zata yi magana ba,sai cika da take tana
batsewa,hakan ya sanya sumayya cewa
"In sha Allah ba zaka samemu da matsala ba,zamu zauna lafiya da junanmu,Allah ya
baka ikon yin adalci a tsakaninmu"
"Amin amin" miqewa sumayyan tayi sai shima ya miqe
"Muje na rakaki ko" duk da suyar da ranta yakeyi amma sai da yasa ta dan
murmusa,ina dakin fa'izan ina dakinta.

       A tsakiyar falon suka tsaitsaya suna kallon juna,hannayenta ya kama a


sanyaye yace
"Kiyi addu'a ki kulle qofar dakin,kiyi bacci sosai kada ki sa damuwa a
ranki,mukhtar naki ne kinji ko" kai ta gyada
"Sai da safe" ya fada yana juyawa a sanyaye.

       Duk yadda taso danne qwallar data cika mata ido abun ya faskara,duk yadda
taso jurewa ta kasa,ashe kishi gaskiya ne haka yake?,ada idan ana zancan shi
dariyarta take tuntsirawa abunta,sai ta cafko hannunsa ya waiwayo yana dubanta
"Ya mukhtar,ka zama mai adalci tsakaninmu,don Allah kada ka wofantar da ni" kai ya
gyada ya janyota jikinsa ya rungumeta yana share mata hawaye yana fadin
"In sha Allah" sai da ya tabbata ta hau gadonta ta kwanta sannan ya fice ya rufe
mata qofar.

      Ta rufe idanunta a hankali tana fata bacci ya dauketa,karo na farko kuma rana
ta farko a shekarun aurenta da zata fara kwana ita daya cikin dakinsu kan gadon su.

*mrs muhammad ce*

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍🏽 *~KUNDIN QADDARATA~*✍🏽
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*rabbana afrig alaina sabran watawaffana muslimin*

0⃣6⃣

       Idonta ta runtse tana jin qarar rufe maga qofar da yayi,ta gefe daya ta
kwanta ta sake mirginawa daya gefan,gaba daya take jin gadon yayi mata fadi.

        Ganin tana neman cinhe daren idanu biyu ya sanyata runtse idonta,ta damqe
filon da take kai tana fadin
"Ya rabb,afrig li sabra" tayi ta maimaitawa babu qaqqautawa,Allah maji roqon
bawansa,bata san lokacin da wani bacci ya sadado ya sace ta ba.

        Qarfe shida ta farka firgigit tana ambaton sunan Allah,tayi mamakin yadda
tayi bacci mai nauyi irin haka,cikin mutuwar jiki ta sauko daga kan gadon ta fito.

         A hankali ta murda qofar dakin nata kana ta tura ta ta bude,tashin farko


idanunta suka sauka kan qofar dakin fa'iza amarya,qofar dakin na kulle gam da alamu
ba'a bude ta ba tunda aka rufe,sai taji wani qunci na ziyartar zuciyarta,ta kau da
kai tana jan tsaki kana ta wuce bakin fanfo,ta taro ruwa ta shige bandaki ta kama
ruwa sannan ta fito ta daura alwala.

      Har qarfe takwas na safiya tana saman abun sallar,ta kalli agogo sannan ta
janyo rediyonta data kunna wadda ita ta tayata zama ta kashe,ta miqe ta zare
hijabin jikinta ta ajjiye ta fito zuwa tsakar gidan,ta saba tun tuni da kammala
ayyukanta da wuri saboda ya mukhtar bai wuce goma a gida.

         Idanunta suka sake sauka kan qofar dakin karo na biyu,sabanin dazu yanzu
an sassauta rufin qofar da alama an budeta ne,sake dauke kanta tayi sannan ta shiga
ayyukanta kamar yadda ta saba.

          Sai da ta tsabtace ko ina har zuwa dakinta sannan ta shiga tayi


wanka,tsab ta shirya cikim daya daga cikin ragowar sabbin dinkunanta,atamfa ce
dinkin riga da skert da ta fidda shape din qugunta yayi das,bata sake yarda da
kyawun dinkin ba sai da taga yadda yayi mata a jikinta,maman nana ce ta zabar mata
shi.

          Tsakar gidan ta dawo,kitchen ta shiga,sai yanzu taga jeran da aka ma


fa'iza,za'a iya cewa ta fita duk wani kayan aiki na kitchen nesa ba kusa
ba,bangaren ta ta nufa ta wanke tukunya ta tara ruwa ta dora ruwan tea wanda ya sha
hadin kayan qamshi sannan ta koma gefe ta fara fere dankalin turawa,babu abinda
mukhtar din bai siya ba na kayan abinci tun shekaran jiya.

       Aikin take amma zuciyarta a cunkushe take,fuskarta kawau zaka kalla ta gaya
maka hakan koda bata bude baki ta fada ba,ta gama firar ta wanke sannan ta juye
shayin cikin wani sabon tea flask wanda yake seat ne da farantansa da kofuna.

         Tana cikin suyar dankalin ta dinga juyo motsi a tsakar gidan,bata fasa
abinda take ba kamar yadda bata damu tasan waye cikin su biyun ba,aikinta taci gaba
da yi har lokacin da taji hancinta ya cika da qamshin turaren mukhtar,kamar ta
waiwaya sai ta fasa,wani haushinsa ta dinga ji tana ji hakanan.

     "Sannu da aiki uwar gida na" taji ya ambata yana takowa zuwa cikin kitchen
din,ta dan waiwayo hannunta riqe da abun tsame dankalin yana tsaye a bayanta gab da
ita,maimakon ta tarad da annuri da qyalli irin na ango sai ta tarad da sabanin
hakan,fuskarsa tana nan kamar kullum
"Ina kwana" ta fada a taqaice fuskarta a daure ba tare da ta damu da yanayin
fuskarsa ba,maimakon ya amsa sai taji ya sanya hannu ya karbe abun tsamewar ya
matsa gefanta ya shiga kwashe dankalin wanda shi yayi saura cikin man
"Sumy,me yake faruwa?" Ya tambayeta yayin da take jingine da kantocin fa'iza
hannunta harde a qirjinta
"Kamar me?" Ta tambayeshi tana debo qwan da zata soya tana zubawa cikin kwano,ya
bata amsa sanda yake qwace bowl din ya fara fasa qwayayen
"Babu fara'ar nan a fuskarki yau ko kadan" shiru tayi masa bata da niyyar
fankawa,ganin haka yasa shima ya ja bakinsa ya tsuke har ya kammala suyar.

       Nata kayan karin ta diba ta kammale musu nasu a kitchen ta wuce dakinta,tana
zaune kan kujera tana kallon mbc yayin da take zarar dankalin da dai dai da dai dai
tana ci tamkar bata so mukhtar ya shigo dakin,yayi kyau cikin dinkin shadda ruwan
qasa mai turuwa sai qamshi ke tashi
"A'aha,ya kike karyawa ke kadai ina namu break din"
"Yana kitchen" ta fadi tana ajjiye plate din hannunta,kai ya girgiza yana zama
gefanta
"Ba haka na tsara ba,ki shirya mana a nan falon naki,gaba daya zamu karya,daga nan
ki shiga ki kira fa'izan" bata ce komai ba ta miqe ta fita din ta dinga kwaso kayan
tana jerawa har ta kammala.

         A qofar dakin ta tsaya ta qwanqwasa mata,tunda tana ganin bai kyautu ta


fada mata kai tsaye ba tunda ba falo gareta ba,sai data qwanqwasa kusan sau biyar
sannan tace cikin alamun fusata
"Wai waye ne?"
"Sumayya ce", sai data bata kusan minti biyu sannan tace
" shigo"ciki ciki kamar wadda aka cusawa tsumma a baki.

        Kan gado ta tarad da ita kwance,ta samu gefan kujera tadan dosana tana
qoqarin dora murmushi saman fuskarta
"Sannu amarya" cikin shan qamshi da dauke kai tace
"Yauwa" ta danyi jim sannan tace
"Amm.....dama mukhtar ne yace ki fito mu karya" shiru tayi kamar bata ji ba sannan
ta bude baki da qyar tace
"Bazan samu fitowa ba,kuna iya karyawa", bata sake cewa komai ba ta miqe ta fice ta
isarwa da mukhtar saqon,kai ya kada sannan yace da ita
" zauna mu karya"gefan kujera ta zauna tana kada kai
"Nikam na qoshi"
"Ban son musu kinji ko,oya sauko" ya fada yana hada tea cup biyu,bata sake cewa
komai din ba ta sauko ta karbi cup din tea din daga hannunsa ta fara kurba.

       Duk yadda yaso janta da hira ta kasa sakin jikinta sama sama take amsa masa
shima bai tsawwala ba har suka kammala ya miqe ya ajjiye mata kudin cefane ya fita.

       Tattare kwanukan tayi da nufin fita da su ta dauraye,a bakin qofa taga


fa'izan a tsaye mukhtar na bakin qofar yana sanya takalminsa,fuskarta a quntace da
alama wani maganar take gaya masa
"Sai na dawo" ya fada bayan ya kammala sanya takalminsa,bata ce komai ba sai komawa
dakinta da tayi rai bace,sumayya ta miqe daga durquson da tayi ta bi bayansa ta
bude masa qofa kamar yadda ta saba
"A dawo lafiya Allah ya kiyaye ya bada sa'a"
"Amin my sumy" ya fada cikin jim dadi.

           Bakin famfon ta dawo taci gaba da wanke wankenta,tana iya jiyo qunquni
daga dakin fa'izan wanda batasan dawa take ko me take cewa ba.

         Tana gab da gama wanke wanken taji ta turo qofar ta fito,qerere tayi a kan
sumayyan
"Ke" ta fada cikin gadara,dago kanta tayi a hankali tana dubanta,sai yanzu ne zata
iya gane kamannin fa'izan,baqa ce sosai mai matsakaicin jiki,bata da qiba bata da
rama,tana da dogon hanci mai tsini sai qananun idanu,aqalla ta tasamma shekara a
shirin da uku zuwa da hudu zata bata shekaru biyar ko shida kenan
"Yana kitchen" ta fada tana ci gaba da wanke wankenta zuciyarta na bugawa,addu'a
take cikin zuciyarta kada Allah ya sanya fa'iza na daya daga cikin masifaffun
kishiyoyi,indai ko haka ne bata san ta inda zata sanya kanta ba,bata san inda ta
inda zata fara tarar wannan bala'in ba,mutum ce ita tun asali da bata son tashin
hankali saboda sam bata iya ba,wani tsaki ta ja sannan ta juya zuwa cikin kitchen
din.

         Sai gata ta fito hannunya dauke da flask din data zuba mata dankalin don
kada yayi sanyi,bude flaak din yayi ta sake tsayuwa a kanta cikin hayaniya tace
"Wai ke,kina nufin wannan abun zanci da ya sassanqame yayi sanyi?" Sai ta kuma
dagowa tana dubanta
"Ina zaton kamar baiyi sanyin da zaki kasa ci ba,tunda cikin flask yake ko" tayi
shiru tana jira taji ko zata tanka
"Shi yasa tun dazun ya mukhtar yace ko fito mu karya din gudun kada yayi sanyin"ta
fada tana dan murmushi

      Zaro ido tayi cikin masifa


"Iyeee,ashe abinda ake fada gaskiya ne lallai yarinya baki san wace fa'iza ba to
banyi niyyar karyawar ba alokacin,ko dole ne?,gidan miji na ne fa,saboda haka babu
wanda ya isa ya takurani sai abinda naga dama shi zanyi,saboda haka ki kiyayi shiga
hurumina" ta juya fuuu ta shige kitchen din.

        Ita dai binta kawai tayi da ido abun na bata mamaki,me tayi mata daga yin
maganar da bata kai ta kawo ba?,tana tattare kayan zata maida kitchen din sai gata
ta fito hannunta dauke sa dan matsakaicin kwandon tace taliya cike da dankali daya
hannun wuqa da kujera 'yar tsuguno ta dawo bakin kitchen din ta zauna.

        Bata ce mata komai ba ta rabe ta ta shiga kitchen din ta maida kayan wanke
wanken muhallinsu ta jera ta sake goge gurin sannan ta fito.

        Zamanta kenan taji muryar yaranta na sallama,murmushi tayi tana miqewa,ko


banza ta samu anokan debe kewa,don ta lura fa'izar akwai matsala tattare da
ita,haka take ko wani abun ke damunta oho Allah masani,miqewa tayi ta fito da
tabarma hannunta,da yake wani lokaci idan bata so su bata mata gu a tsakar gida
suke zamansu.

       Tana shimfida tabarmar yaran na gaida fa'iza da dai dai da dai dai,ta amsa
musu babu yabo babu fallasa,suka qaraso gun antyn tasu.

         Tana tsakiyarsu tana biyewa surutunsu,fa'iza na kitchen tana fama da suyar


uban dankali da qwai wanda a zahiri yafi qarfinta,so take tun daga yau ta fara
nunawa sumayya ikonta cikin gidan kafin ta haifo yaran da zasu zama ajalin zamanta
cikin gidan,kamar yadda yake cikin KUNDIN BURINSU ita da su yaya yahanasu.

        har zuciyarta sumayya take jin dadin hirarta da yaran,duk wani bacin ranta
ya gudu,ta miqe ta nufi kitchen don dauko dankalin da fa'izar taqi ci ta rarrabawa
yaran don kada ayi asararsa,a nan taga uban dankalin da fa'izar ke soyawa daidai
lokacin data kammala ta juye cikin babban bowl da tadauka ta fice,bata tanka ba
tunda dazun ta fara mata da jan kunnem fita daga sabgarta.

        'Yar carafke yaran keyi musu ya sarqe tsakaninsu kan rinton da aisha tayi
musu,sumayya nata qoqarin sulhuntawa,tsawa suka ji wadda ta sanya su yin shiru baki
dayansu suka waiwaya suna kallonta
"Dalla malamai kun cikawa mutane kunne,ina buqatar nayi ramuwar bacci kun hana
mutane aikin banza aikim wofi,to wallahi bazan lamunci takura cikin gida na ba ku
kintsa bakinku" ta banko qofar tata ta shige ciki.

        Tsuru tsuru yaran sukayi saboda basu taba ganin an musu haka cikin gidan
ba,sumayya ce tayi qarfin halin yin murmushi sannan ta miqe cikin son bagarar da
abinda tayi musun
"Ku zo kuyimin cefane maza" nan suka miqe da hanzarinsu kuwa ta rararba musu aiken
suka fice,yayin da ita kuma ta tattare tabarmar ta sake share gun kafin su
dawo,sannan ta moma kitchen ta gyara duk inda fa'iza taci ubansa har bangaren
fa'izar duka.

          Bayan sun dawo ta gyara kayan miyar ta bada suka kai mata markade,suna
dawowa ta rarraba musu alewa ta turasu gida ganin qarfe daya na rana tayi saboda
zuwa islamiyya.

        Shinkafa da miya da wake tayi niyyar dafawa a abincin rana,tunda mukhtar ya


aiko da nama daga kasuwa,tana tsakar gida tana yankan salad ta juyo sallama da
muryoyin mutane,ta daga kanta tana amsawa,baqi ne su kusan shida
"Sannunku da zuwa" ta fada fuskarta a sake,shigewarsu sukayi yayin da uku daga ciki
suka juyo suka mata kallon banza kana suka wuce,sanyi sosai jikinta yayi,wai dama
haka ake?,haka ake kishin ne wai?,ita kam sam bata sani ba ji take qwaqwalwarta ta
kasa jan zaren ko wanne tunani.

     Tana nan tana yanka salad din ta soma jiyo tashin maganganunsu gami da shewa
"Wai dama wannan ce kishiyar taki?
Cab di wannan ai ma'aikaciya kurum kika samu
Lallai ai wannan banga abun kishi ba
Ke irinsu fa sunfi iya tsiya wallahi,kada ki soma cewa zaki sakar mata fuska balle
ta rainaki,ki dasa mata tsoronki,bada umarni ne kawai tsakaninku
Wallahi ki bautar da shegiya,ki mori bati" take taji jikinta ya kama rawa gabanta
ya shiga faduwa,lallai ba shakka suna iya dukanta,haka zuciyarta ta dinga raya
mata,zuciyarta tsoro fal irin na yarinta,su kamsu suna sane suka dinga maganar don
ta jisu,saboda su dasa tsoro cikin zuciyarta.

        Kitchen din ta tattara ta koma tana ci gaba da ayyukanta,sai dai har yanzu
tsoron bai saketa ba,addu'a ta dinga yi cikin zuciyarta hakan ya sanya ta dan samu
nutsuwa.

       Tana gab da kammala girkin fa'iza ta shigo kitchen din ita da daya daga
cikin baqin nata tana fadin
"Ga bangare na nan,ki dafa duka abinda kuka ga ya muku yadda zai isheku" sumayya ta
waiwayo tana dubanta
"Amma amarya har da ku nayi abincin fa zaya ishemu duka,ina ga idan aka dafa wani
zaiyi yawa" juyowa itama tayi ta zabga mata wata harara sannan ta nunata da yatsa
"Ina cewa ko awa biyu ba'a yi ba da yi miki maganar ki guji shiga sabgata ba ko,ke
har kin isa kina sa'ar qanwata ki dinga dafawa kina bani iya limit din da kika ga
dama ina ci?,kin shirya cin na jaki kenan,don wallahi jibgarki zanyi a gidan nan
banza juya kawai" sai ta dauke kanta daga garesu ta maida kan girkinta,abun mamaki
sai kalmar juya yau tayi mata zafi,karo na farko kenan da ta taba jin hakan.

      Tana jinta ta gama gayawa baquwar tata abinda za'ayi ta fice,bakin fanfo ta
wuce ta tari ruwa ta shiga wanka don sai yanzu ta samu damar yin.

      Tana kammala girkin ta zubawa mukhtar nashi,ta zuba nasu fa'izan ta aza a
bangaren kantarta ta dibi wanda zata ci ta shige daki abinta,bata sake fitowa ba
har suka gama tsiyar da zasuyi suka tafi wajen qarfe biyar na yamma,a sannan ta
fito ta shiga kitchen don dora ruwan wanka.

      Tamkar ba'a taba guara kitchen din ba haka suka lalatashi,ga uban abinci nan
da suka dafa sun kasa cinyeshi cikin tukunya a bude,kwanukan duka vikin sink din
fa'iza gaje gaje,hatta wanda ta ajjiye musu sun cakalkala shi sun bar cooler rabi a
bude rabi a rufe.

         Ranta taji ya baci karo na farko,ta tsani almubazzaranci da abinci,saboda


tana da imamin abinda ka raina shi wani ke nema yasa a bakin salatinsa amma ya
gagareshi,to don me kai don Allah ya baka zaka wulaqanga,bayan ya baka ne ba don
kafi kowa ba.

        Bata gaji ba bayan ta dora ruwan ta soma tattara kitchen din,ta gyara ko
ina fes,saidai batasan ya zatayi da abincin ba tun kafin mukhtar ya gani yaji babu
dadi,ita ba leqe take ba kuma yaro gidan bare ta samu almajiri ta bashi,dole ta
jira dan aike yazo.

       Ruwanta na zafi ta juye ta shiga wanka,can ma sai da ta tsaya ta gyara,sam


bata qaunar taga guri ko yaya ya sauya yanayi.

        Taji qarar babur dinsa sanda take maida kaskon turaren wuta kitchen,sanin
cewar gidan a bude yake ba kamar sanda tana ita daya ba saboda haka ta toge a
tsakar gidan tana jiran shigowarsa.

          Cikin mintuna ya qaraso tsakar gidan,tana murmushi ta qarasa inda yake


tana niyyar karbar jakarsa,sai ya bude hannayensa ya kai mata runguma sai ta goce
tana murmushi tare da kallon qofar dakim fa'iza,qasa qasa da murya tace
"Bamu kadai bane fa a gidan" ta miqa hannu ta karbi kayan hannun nasa,sai ya
kalleta yana turbune fuska
"Haka kawai tun yau an fara shiga haqqina,ai shikenan" yayi maganar yana wucewa
dakinsa ta bishi a baya tana masa gwalo.

      Har ta kammala kintsa abinda ya shigo da shi babu fa'iza babu alamarta,sai da
ta gama zata fita daga dakin sukayi kacibus da fa'izan na shigowa,harara ta balla
mata,gefe ta matsa ta raba ta kawai ta wuce.

        Tunda ta gabatar musu da abinci tayi alwalar sallar magariba shigewarta


daki,bata sake fitowa ba sai da taji mukhtar na qwala mata kira,ta miqe a hankali
ta gyara daurin dankwalinta ta amsa tana fitowa.

         A kitchen ta tadda shi tsaye ransa bace yana qarewa himilin abincin
kallo,gefe guda kuma ga dankali da qwai da fa'izan ta soya a wulaqance cikin cooler
ba'a idasa cinye shi ba,ya dago idanunsa daga kallon coolers din ya maida su ga
sumayya,da hannu yayi mata nuni
"Me wannan?,meye haka sumayya?" A ladabce tace
"Nima ban sani ba ya mukhtar saidai ka tambayi amarya" baiyi musun hakan ba tunda a
gefanta yaga tarin coolers din,ya daga murya ya qwala mata kira,ta shigo kitchen
din sanye da hijab
"Gani" ta fada tana kallonshi.

      Ya kalli kayan ya kalleta sannan yace


"Wannan na waye?"
"Na baqin da nayi ne" ya hadiye wani takaici saboda yadda tayi maganar cikin halin
ko in kula da nuna rashin muhimmancin laifinta,wacce iriyar yarinya ce ita,yinin
farko kenan a gidan mijinta?,yayi qoqarin danne bacin ransa yace
"Na lura kamar harda dankali ya akayi aka dafa abinci yayi yawa haka?"

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍🏽 *~KUNDIN QADDARATA~*✍🏽
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

_______________________

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*hasbiyallahu la'ilaha illa huwa,alaihi tawakkaltu wa huwa rabbul arshil azim*


_________________________

0⃣7⃣

    Hannunta riqe kan qugunta tace


"Dankali ne ta barmin ya huce,ni kuma ban iya ci ba,abinci rana kuma gaskiya bazan
zauna qanwar qanwata tana dafa abinci tana bani ba,bayan ba cewa nayi bazan iya
ba", shiru yayi yana ci gaba da kallonta zuciyarsa na quna,da qyar ya samu ya
hadiye wani abu mai zafi a qirjinsa sannan ya gyada bayan wani tunani da yayi
" yayi kyau"kawai ya fada sannan ya ratsa ta tsakaninsu ya fice cikin bacin rai.

         Sa kai sumayya tayi itama tana shirin bin bayansa


"Banza munafuka,idan ma ke kika nuna masa an gaya miki wani abun zai min" bata
kulata ba tayi ficewarta ta koma dakinta,tana kammala sallar isha'i ta tura qofarta
tayi kwanciyarta.

         Washe gari shi ya shigo ya tada ta sallah,ta miqe tana mutstsuka idanunshi
a kanta,sam bata ma ji kiran sallahr ba yau
"Ki tashi haka kiyi sallar asuba" ya fada yana qare mata kallo ta cikin rigar
baccinta wadda tayi mata kyau
"Kinyi kyau sosai my sumy" ya fada sanda take qoqarin saukowa daga kan gadon,sai ta
waiwayo ta dubeshi,dan qaramin murmushi ta sakar masa wanda yaso rudashi,ya qarasa
inda take tsaye tana zura hijab dinta don fita waje tayi alwala,ya janyota da baya
ya rungumeta yana rada mata
"Nayi missing dinki sumy ta" sai ta zare daga jikinsa ta waiwayo tana dubanshi
idanunta a waje,ta maida su kana ta langabe kai
"Kai ya mukhtar,ni ban fafi haka ba sai kai dake da amarya?" Baice komai ba sai
wani guntun murmushi da ya saka ya sanya kai yana ficewa tare da ce mata ta fito
tayi salla.

         Yauma kamar jiya ta fito ta kammala aikinta,saidai sabanin jiyan yau a


bude taga dakinsa da alama yana ciki,saidai bata san ko me yake yi ciki ba,tana
fitowa daga wanka sukayi kacibus,ya zuba mata ido yana dubanta
"Yanzu sumayya ko ruwan wanka ma an daina bani?" Ya fada murya a karye
"Ba haka bane ya mukhtar,na dauka aikin amarya ne wannan ko,amma kayi haquri akwai
wani da na dora zan zuba a flask bari na juye maka" ta fada tana shigewa zuwa
kitchen din da sauri.

        Tare suka karya yauma,saidai bai aikata kiran fa'iza ba da kansa ya gaya
mata tazo zasu karya ya juya ya fito,saidai har suka gama karyawar bata fito din
ba,har ya fita daga gidan.

         Tana kwance kan doguwar kujerar falonta tana hutawa taji sallamar anty
dije,da sauri ta sauko daga kujerar tana amsawa don ko da wasa fa'iza wadda tafi
maqotaka da qofa bata yi kuskuren amsawa ba.

       Rungume anty dije qanwar maman nata tayi tana mata sannu da zuwa kana suka
wuce dakinta,bayan gaishe gaishe da tambayarta zaman gidan ta gaya mata komai
lafiya suka shiga hira,lokaci lokaci ta dinga tashi tana duba girkinta na rana da
ta dora.

         Kammalawarta yayi dai dai da lokacin sallah,saboda haka anty dije tace sai
tayi sallah kafin taci abincin,tare suka fito anty dije tayi bakin famfo ita kuma
ta nufi kitchen don gama kwashe abincin.

         A bakin qofar kitchen sukayi kacibus da fa'iza na shirin fitowa ita kuma
na qoqarin shiga,hannun fa'izar riqe da qatuwar kula da ta gama shaqewa da abincin
da ta girka wanda a zahiri ko yara gareta yafi qarfinsu su duka balle cikinta ita
daya,harara ta galla mata kana cikin daga murya tace
"Gafara malama na wuce,da wani idonta kamar jiqaqqiyar aya" rabe mata tayi tazo ta
wuce fuuu tamkar guguwa cike da tsoro sumayya ta bita da kallo.

         Duk a idanun anty dijen haka ya faru,ta kada kai cike da takaici ta wuce
bandakin ta daura alwalar.

          Tana saka hijabin sallarta sumayyan ta shigo dakin dauke da coolers din
abincin,tun kafin ta saukesu anty dije ta finciki hannunta tayi bedroom dinta da
ita,gefan gado ta zaunar da ita kana ta zauna kusa da ita suna fuskantar juna,cike
dabacin rai ta tsareta da ido sannan ta soma magana
"Kar dai kice min sumayya tsoron kishiya kike?,kada ki gayan cewa kin fara nuna
mata cewa kina tsoronta?" Da idanu sumayyan ke bin anty dijen cikin sanyi jiki.

        Cike da zafi tace da ita


"Me innarki ta gaya miki sanda za'a kawo miki abokiyar zama" duk sai ta rude saboda
tasan cewa anty dijen ba dai zafi ba,tsab ta mareka ba komai bane idan ka bata
mata,cikin tsawa ta sake maimaitawa
"Dake nake,nace me innarki ta gaya miki?" Cikin rawar murya da in ina wanda tuni
idanunta ya fara tara qwalla tace
"Tace min na zauna da kowa lafiya,kada na daga hankalin kowa,kada na zalunci kowa
kada na cuci kowa idan na cuci abokiyar zama na bata yafemin ba"
Kai ta jinjina ta kama hannunta tana matsawa da dan qarfi,cikin kakkausar murya ta
sake ce mata
"Tace ki zauna a cuce ki?" Kai ta kada,idanunta ta zaro mata
"Ki bude bakinki kiyi magana"
"A'ah" ta fada qwalla na gangaro mata.
"Tace ki zauna a zalunceki ko a rainaki?",nan ma ta amsa
"a'ah" kai ta jinjina.
"Da kyau......me yasa kika fara bawa fa'iza qofar da zata rainaki?,me yasa kika
fara nuna mata kina tsoronta" shiru tayi ta kasa bata amsa don itama bata san
dalili ba.

      Ganin haka ya sanya anty dije sasaauta fushin fuskarta ta sake matsowa ga
sumayya
"Bamu lamunci ki zalunci kowa bama balle abokiyar zamanki,amma......bazan lamunci
ki zauna ki zama bola ba,bazan lamunci ko zama raguwa matsoraciya ba,kishiyarki ba
mai son zaman lafiya bace,bamu ce ki biye mata ba,bamu ce ki zama mai son tashin
hankali ba,amma sam bazamu zuba ido ki zama banza ba.....kinsam wace
kishiya...kishiya ma irin taki sumayya" kai ta girgiza,anty dije ta soma warware
mata komai,dukkanin kunnayenta sumayya ta bata,sosai maganar ke ratsata,sai ta
dinga dauko ta maman naana tana hadawa da anty dije,tabbas dukkaninsu gaskiya suke
gaya mata.

        "Kada ki yarda naga ba haka ba kina jina ko?" Anty dije ta fada tana kama
kunnanta da kanta
"In sha Allahu" inji sumayya tana dan murmushi,dukansu suka fito any dije ta tada
sallarta ita kuma ta je ta daura tata alwalar tayi sallahr sannan suka ci
abinci,suna ci anty dijen na bata labaru kala kala na kishiyoyi,wani ya bata dariya
wani ya bata mamaki wani ya bata al'ajabi.

       Har soro ta rako anty dije sukayi sallama,tana shirin komawa ciki taki qarar
machine dinsa,hakan ya sanyata dakatawa ta bude mishi qofar ya shigo tana mamakin
dawowarsa yau da wuri haka bayan duka duka biyar da 'yan mintuna ne,saidai bata ce
komai ba kamar yadda anty dije ta gaya mata ta koyi yawan dauke kai da yin shiru
kam wasu al'amuran da ba cutarwa ne gareta ba,ko ba hiruminta bane,ko kuma bazai
cutar ko ya amfaneta ba yin magana akansa duk da cewar dama can ita din ba mai
shishshigi bace.

            Da murmushi saman fuskarta take masa sannu da zuwa,ya kashe mata ido
daya sanda suke shiga cikin gidan
"Ko ki tambayeni ma ta akai ka dawo gida da wuri ko?" Murmushi tayi tana rausayar
da kai
"Ai ba laifi kayi ba,kuma mai gida da gidansa ai yana da hurumin dawowa duk sanda
yaga dama"mintsinarta yayi a bayanta har sai da ta sanya dariya yace
" sarkin wayo da iya magana,ko yaushe duka kika koyi wannan wayon haka?"
"Ka manta rainonka ce?" Ta fada tana kashe masa ido daya
"Gaskiya ne" ya fada yana sanya hannunshi cikin alhjihunsa ya fiddo da kwado(key)
yana fadin
"Muje kitchen ki tayani wani aiki".....

*mrs muhammad ce*

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍🏽 *~KUNDIN QADDARATA~*✍🏽
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

______________________

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*wa iy yamsaskallahu bi durrin fala khaashifa lahu illahuw,wa iy yuridka bi khairin


fala raadda li fadhlih*
_____________________

0⃣9⃣

        Ya rantse sai ya hukunta ta,sai ta gane bata da wayo,'yar bariki ce ita ko


mai,zai nuna mata bata iya iskanci ba.

         Miqewa yayi ya dauki jakarsa zai fice sumayyan ta sha gabansa


"Ya mukhtar,bai kamata ka fita cikin wannan halin da kake ba" sai ya tsura mata ido
yana kallon yadda ta langabe kamar zata yi kuka,haka kawai ana son shiga tsakaninsu
da farincikinsu kam wani dalili can maras tushe,kan wani abu da basu isa su yiwa
kansu shi ba sai Allah ya ga dama,sai ya saki murmushi don ya kwantar mata da
hankali,ya sanya hannunshi ya shafi gefan fuskarta
"Kada ki damu sumayya,ina gane komai" yayi kissing goshinta yana fadin
"Sai na dawo" ya juya ya fita a gaggauce don bai son ma yaya yahanasu ta kuma
tsaidashi.

         Kai ta kada sannan ta fito daga dakin ta ja ta kulle masa ta tafi da key
din dakinta,cikin falonta tayi zamanta bayan ta kunna redio tana sauraran labaran
rana freedom.

          Tana kammala jin labaran ta shiga kitchen ta dora abincin rana,cikin


kitchen din ta zauna har ta kammala saboda jallop din shinkafa ta musu,ta zuba
cikin cooler ta ajjiye cikin kitchen din kana ta nufi dakin fa'izar,ita daya ta
taras da alama yaya yahanasun ta tafi wanda ita sam batasan ta tafin ba
"Ga abinci can cikin kitchen na gama" ta fada ta juya ta fice ba tare da ta jira
amsarta ba,bata zaci ta ci ba sai da ta shiga dora sanwar dare taga babu komai
cikin cooler din tas,mamaki ya kamata saboda batayi tsammamin zata iya cinyewa duka
ba,don har da yaya yahanasu ta dafa,ta kada kai ta shiga sabgar dora abincin dare.

          Sau biyu suna kacibus da fa'izan na fitowa a kitchen din sanda take tsaka
da girkin,tuwon semo tayi miyar kuka wadda ta wadata da man shanu da nama,ta
kammala ta jere komai cikin kitchen sannan ta nufi famfo ta tara ruwan wanka tana
jira botikin ya cika.

          Da sauri taga ta fito daga dakinta ta suri silifas ta fada bandakin ta


bame qofa,sai ta bita da ido kana ta dauke kai,tana tsammamin matsuwa fa'izan tayi
har haka?,ta kashe fanfon ta koma gefan rijiya ta zauna tana tsumayin fitowarta.

      Wasa wasa har ba fa'iza ba alamunta,abun har ya dan bawa sumayyan tsoro,sai
ta miqe ta isa ga bakin bandakin ta qwanqwasa qofar,gyaran muryar da taji tayi mata
ya tabbatar mata komai lafiya,sai ta koma bakin riniyar ta zauna tana ci gaba da
dakon fitowarta.

        Ba ita ta fito ba sai da taji shigowar mukhtar gidan,a qalla awa daya kenan
ta kwashe cikin makewayin,sumayyan ta miqe tana masa sannu da zhwa tare da jin
nauyin zuwa ya taddata babu kwalliya saboda ta riga da ta saba al'adarta ce daya
dawo ya sameta tsaf.

        Ta miqa hannu zata karbi ledar hannunta taji anyi wuf an karbe,da mamaki ta
waiwayo fa'iza ce wadda batasan sanda ta fito daga bayin ba ke tsaye tana ta faman
doka masa murmushi tare da yi masa sannu da zuwa,a dake yake sa mata,sai sumayyan
ta koma ta dauki botikinta zata shige wankan
"Ai wlh ni da ke ne cikin gidan nan,indai ina nan an daina wannan karuwar kwalliyar
daren" ta fada bayan da taga mukhtar ya shige dakinsa,waiwayowa tayi ta dubeta sai
ta saki murmushi sannan tace
"Ko?"cikin qufula da ganin yadda maganar bata da da ta da qasa yadda taso ba tace
" eh,ko kina musu ne?"kai ta gyada sannan a taqaice tace mata
"Zamu gani" ta shige bandakin abinta,yatsa ta ciza takaici ya kamata,wai dama can
yarinyar ba tsoronta take ba basaja take mata ko kuma zugata aka soma yi?,qwafa ta
ja domin bata da amsa ta shige dakin angon nata.

         Ga mamakinsu suna shirin soma cin abincin dare sai ga fa'izan,tana wani
murmushi ta raba gefan mukhtar din ta zauna
"Naga ya kamata nima adinga cin abincin da ni don qara donqon zumunci ko?" Ta fada
tana wani kashe masa ido,ha fuskanci yau sai wani rawar kai take,amma idan batasan
kan garin ba shi zai mata kyakkyawan kwatance,babu wanda ya tankata iyaka aka tura
mata kulolin ta debi yadda taga zata iya.

      Ita da sumayyan kusan tare kowannensu ya sanya lomar farko a bakinsa,idanu


sumayya ta zaro sakamakon wani dan banzan gishiri da ya cika harshenta har zhwa
kwanyarta,take qwaqwalwar tata ta tafi tunanin ta yadda akayi hakan ya faru?,a iya
saninta lafiyar Allah ta kammala komai ta gyatta shi,amma me ya kawo wannan
sauyin?,ko dai harshenta ke shirin samun matsala?,.

        "Qundun uban nan" abinda fa'iza ta fada kenan wanda shi ya tsinke zaren
tunanin sumayya,kallon mukhtar suke dukkansu kowanne da tasa manufar a
zuciya,zaquwar mukhtar yayi magana ta samu filin baje hajarta da kuma mamakin yadda
yaqi maida hankali ga kalamanta takeyi,cikinsu babu wadda ya kalla saici gaba da
sambada lomarsa yake,yayin da sumayya tayi qas da kanta ta daure duk wani abu da
take ji kan harshenta itama taci gaba da kai lomarta tamkar babu wata matsala dake
waka na.

       Idanu fa'iza ta dinga binsu da shi,to ko dai harshenta ne kadai ke gaya mata
tuggunta yayi dai dai?,ganin sunyi uwar watsi da ita ya sanya ta kasa shiru sai da
ta magantu
"Wai muntari bakaji uban gishirin dake cikin abincin nan ba ne?" Bai amsa maga ba
sai da ya sake wata lomar
"Wanne abinci fa?"
"Na gabanku mana" ta fada tana nuna kwanon da yatsa tare da qanqance idanu
"Hala kina da matsalar dan dano ko?" Kafeshi tayi da idanu tana tantama,sai kawai
ta miqa hannu ta kwaso miyar gabansa ta kai bakinta,tabbas iri daya ce haka ma
dandanon iri daya ne,to tsabar iya asiri ne na sumayya yasa bai fahimta ba ko sun
tasamma raina mata wayo ne,fa'iza macace da sam bata da siyasar zamantakewa,hakan
ne ya sa ta kasa boye fushinta ta tashi ta fice fuuuu ta bar dakin cike da
baqinciki,so tayi yau ya ciwa sumayya mutunci sannan ya janyeshi kuma ta kwana da
shi yau ta cusa mata baqinciki.

         Idanunta ta dora kan mukhtat fuskarta qunshe da tashin hankali,ta bude


baki zatayi magana ya dora yatsansa kan lebansa
"Shshshshsh!,kada kice komai,ita ta zuba gishirin kan ido na bayan shigarki
wanka,tana zaton bazanci ba,batasan ba maqaryacin so nake miki ba,zan iya cin wanda
yafi haka ma,bare ma shekararmu nawa da sumayyaty na santa qwarai wajen iya sarrafa
hatsi" yadda ya qare maganar ne ya bata dariya har sai da ta dara din,daga bisani
ya wanke mata duk wani damuwa tata suka bige da hira,yace idan ba zata iyaci ba
kada ta cuci kanta ta ajjiye ya sama mata wani abu shikam zai iya ci,tace sam tunda
har ya iya ci itama sai ta ci,qarshe dai ramun muguntar gun fa'izar ya koma tunda
ko banza ta tashi ciki babu komai.

         Yau din da kanshi ya mata sai da safe,kishi ya kamata sosai ta dinga


rayawa cikin ranta wato zashi yaje yayi abinda anty yahanasun ta umarceshi kenan
dazu da safe,ta dinga juyi saman gado ita daya da qyar bacci ya saceta.

         Bata jima da fara baccin ba ta dinga jin ihu sama sama cikin barcinta,a
sannu ta bude idanunta tarwai,tabbas ba mafarki bane,ihu ne daga dakin fa'izan kuma
muryarta ce cike da gunjin kuka,ta kasa kunne sosai ta dinga jin yadda take neman
agaji da dauki,runtse idanunta tayi sai kuka ya subuce mata ta sanya hannunta ta
toshe dukka kunnuwanta baccin da bata koma ba kenan.

         Kiran sallar farko na asuba taji an bude falonta,ta kasa kunne sai kuma
taji shuru har akayi kiran sallah na biyu,ta sauko daga san gadon da idanunta
wadanda sukayi luhu luhu saboda kuka,ta zira hijabinta ta fito daga dakin jiri da
dibarta.

        A falon nata taga kamar mutum kwance,gabanta ya fadi da sauri ta koma da


baya ta kunna makunni qwan lantarkin falon,haske ya qauraye ko ina,mukhtar ne
kwance saman doguwar kujerarta tafin hannunsa dafe da goshinsa.

         Dauke kanta tayi tamfar ma bata ganshi ba yayin da shi kuma ya bita da ido
har ta fice,sai da ta daura alwala ta dawo sannan ya tashi ya fice,tana kan abun
sallarta har gari ya soma haske,sallamarsa taji yana shigowa ta runtse idanunta har
ya qaraso gabanta,ya fuskanci me take nufi domin yana da tabbacin mawuyaci ne idan
baya jiyo qarajin fa'iza a jiya ba,saboda shi kadai yasan ta'asar da ga tafka mata
da gayya.

      Muryarsa a tausashe da irin salon dake kwantar da hankali da ratsa sassan


jikinta yace
"Sumayya,kiyi haquri don Allah,wlh ban shiga dakin fa'iza a jiya don naci fuskarki
ko na bata miki rai ba,kiyi haquri idan ranki ya baci,komai nayi nayi ne saboda
koya mata saboda ta fice daga rayuwarmu....kiyi haqur....."
"Ya isa ya mukhtar" ta fada da sauri tana katseshi
"Ka daina bani haquri,matarka ce kamar yadda nake matarka,kuma adalcin kenan" ta
fada duk da tana jin daci qasan zuciyarta amma hakan ba zaya hanata fadin gaskiya
ba.

     Hannunta ya sake kamawa sosai,kana ganin fuskarsa kasan cikin bacin rai
tsantsa yake
"Duk da haka nayi da na sanin kasancewa ta tare da ita,fa'iza......." Hannunta ta
dora saman bakinsa qwalla da digar mata
"Matarka ce bana son jin komai,don Allah ka tafi ya mukhtar kaji,ka tafi bacci
nakeji" da gaske take fadin maganar saboda haka ya saketa ya miqe a sanyaye ya
fice,tun tana kukan bilhaqqi har ta koma yi qasa qasa,da haka bacci ya sureta.

        A firgice ta farka sakamakon hasken rana da ya dalle ta wanda ke alamta


mata gari ya waye sarai,da sauri ta dubi agogo,har qarfe goma na safe,gabanta ya
fadi data tuna cewa babu abinda yau tayi a gidan,a hankali ta miqe ta isa falo ta
yaye labulen window dinta ta duba dakinsa,a kulle yake da muqulli tana jin mawuyaci
ne idan fita kasuwa ba kenan,dawowa tayi uwar dakin ta tsaya gaban madubi don duba
idanunta,bata so ta fita har fa'iza ga fuskanci tayi kuka ko ta fuskanci taji kishi
ko ta gane abinda ya faru daren jiya cikin gidan har ta raina ta,hudubar anty dije
ce boye duk wani abu da zai sa ta gane logonta,bare ta riqeshi ta dinga musguna
mata da shi,fuskarta fayau haka ma idanun sun koma babu kumburin,saima haske da
suka dada yi,hijabinta ta cire ta daura dankwali saman kanta ta fice tsakar gidan.

         Sai da ta kammala aikinta tas tana bakin rijiya tana diban ruwan wanka
sannan taga fitowar fa'izan,ta daga kai ta dubeta,da qyar take iya tafiya tamkar
yaron da aka yiwa shayi yanzu yanzu,idanun nan sun kumbura sunji jazur,hatta da
fuskarta a kumbure take,da alamu ba qaramar izaya mukhtar din ya ganawa rayuwarta
ba a jiyan,har qasan ranta sai da sumayyan taji ta tausaya mata,amma da baqar
zuciya irinta fa'izan sai data iya samun sararin wulla mata harara tare da fadin
"Baqar manufarki a kanki zata qare,anyi mai wuyar tunda yazo hannu ko,saiki saurari
zuwan 'yan dagwai dagwai" ita kanta tasan ta fada ne kawai amma ita daya tasan
halin da take ciki,dariya ta qyalqyale da shi sannan tace
"Wai.....a hakan,to bamusan gaibu ba" ta juya ta waiwayenta tare da sheqa dariya ta
shige daki abinta don bata ga dacewar tsayawa cacar baki da fa'izan ba,ai kuwa ba
qaramin qona mata rai dariyar tayi ba,sai ta dinga jin duk ta muzanta,ta dinga jin
tamkar mukhtar ya kwashe duka cin kashin da yayi mata daren jiya ya gayawa
sumayyar,ta dinga jin kamar ya gaya mata wace ce ita,jiki a sanyaye da jan qafa ta
lallaba ta dibi ruwa ta shiga bandakin.

        Bata fito ba balle ta biye mata suyi sai da ta kammala ta shiga daki sannan
tayi nata wankan,tana daki tana shiryawa taji kamaf motsi cikin falon ta,bata leqo
ba sai data kammala shiryawar,ta fito hannunta dauke da dan kwalinta tana
daurawa,fa'iza ce tsaye a falon karo na farko tunda tazo gidan,gaba daya ta shagala
da kallon yadda aka tsara falon,babu qarya babu fallasa amma yayi kyau matuqa,komai
a tsaftace a killace,sosai baqinciki ya rufe ta na yadda dakin sumayya yafi nata
kyau tsadar kaya tsafta da tsari bugu da qari ga yalwa dai dai gwargwado.

      "Lafiya dai ko?" Sumayya ta fada bayan ta gama kallon yadda take qarewa dakin
nata kallo,juyowa tayi cikin jin kunya da bori,ba tare da ta shirya ba abinda ke
zuciyarta ta fito
"Hmmmm,lallai kam,kaga masu daki,kin tatsi muntari kin gyara kanki shi yasa kikewa
kowa kallon banza ko?ayi mu gani naga ta yadda za'a mora" murmushi sumayyan tayi ba
tare da nuna damuwa kan batunta ba
"Fadi meke tafe da ke nasan dai ba wannan ne ya kawoki ba"cikin qanqance ido
fa'izan tace
" eh,ina abun karina?"ta tambaya cikin gadara,bata san cewa yau sumayyan jinta take
dai dai da yadda tazo mata ba,dariyar nan ta rainin hankali tayi mata sannan ta
zauna kan daya daga cikin kujerunta
"To idan banda abinki fa'iza amarya wanda yayi aika aikar ma ya tsallake ya tafi
don me zaki dinga haushin kaza huce kan dami a kaina,ki roqeni kawai na taimaka ma
baki abinda zaki sanyawa cikinki ko?".

        Sosai ta hasala har ta fara huci,ba shakka da acw da qwarinta babu abinda
zai hanata neman dambacewa da sumayyan,sanin cewa babu qarfin sai ta buge da nuna
ta da yatsa
" ke baki isa ba wallahi qaramar mara kunya,dududu nawa kike da zan nemi alfarma
gunki,na fuskanci kanki ya fara rawa ko bakisan wace fa'iza ba,wallahi sumayya ki
kuka da kanki don ke abar tausayi ce nan gaba sai kin zama abarkwatancen wa wasu"
"Bakinki ya sari danyan kashi jeki ki duba kitchen ki dauki da'amin tunda duka don
shi kike wannan dai ko?" Ta fada tana miqewa tayi komawarta uwar dakanta,nan ta
barta tana hauka sannan daga bisani ta fice,abu goma da ashirin ga wani baqinciki
da ta taras,dakin sumayyan ya kere nata da take taqama da shi,kuma tana da zaton
cewa daga jikin mukhtar din ta yaga,tana jin dole ta dau mataki kafin zuwan yaran
da zasu zama silar zamantowar gidan mallakinta.

*mrs muhammad ce*

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

______________________

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*wa ufawwidu amri ilallah,innal laha basirun bil'ibaad*


__________________________

1⃣0⃣
         Yau kam da ta dora girkinta zama tayi cikin kitchen din tana kallo cikin
wayarta har takammala girkinta,duk da cewa yau din akwai sauqim zirga zirgar
fa'izar tana daka tana jinya,yau daga ita har yaranta sun wataya abunsu.

         Yau ma tare sukaci abincin dare,saidai babu fa'izan,don tun sumayyan bata
jima da kammalawa ba ta fito ta kamfata ta fice,ita kam sumayyan mamakin shege cin
abinci irin na fa'izan take.

         Abin jiya akaso a maimaita ko kuma nace har ma ya wuce na jiyan,don kusan
har da dambe ne yaso kaurewa tsakanin fa'izan da mukhtar din,ba wai don tana
burgeshi ko abinta ya dada shi da qasa bane ya sanya shi dagewa kan sai yayi,ko
kadan,yana so ne ta bambance tsakanin aya da tsakuwa,yana so ne ya dasa mata qin
abun ta yadda ba zata sake marmari ko gigin nemansa ba.

       Iya wuya kam ta shata don har taso ta zarta ta jiya,don yau har mikin jiya
sai da ya dawo sabo fil baya ga sabon da ta yo guzirinsa,kamar jiya haka yayi
fitarsa da asuba,saidai wannan karon a masallaci yayi zamansa har gari ya ida
wayewa,shi kadai ya dinga murmushi saboda yasan ya gama koya mata lesson.

        Tun daga ranar ta shiga kulle qofarta,dariya ya dinga yi cikin zuciyarsa


yana fadin
"Ta dauka wani damuwa akayi da abinta,bata san ko giyar wake na sha bazan sake
rabarta ba" kewar sumayyansa ce kawai take damunsa sam fa'izan bata a cikin
lissafinsa.

        Har ta qarasa cinye kwanakinta bata sake yarda ya kwana dakinta ba,haka nan
sumayya ma qin yarda take ganin cewa ba kwanakinta bane,bugu da qari kuma maman
naana na tsumata,so take ta d'ai d'aita tunanin mukhtar din a duk lokacin da ya
dawo hannunta.

       Randa zai dawo dakinta tun safe take jin nishadi,ta shiga dakinsa ta masa
gyaran tsaf lungu da sak'o ta k'alk'ale ko ina,sai data kammala duk wani abu da ya
dace sannan ta zauna tana jiran zuwan yammaci.

         Tana kan kujerar falon ta kwance bayan sallar azahar tana hutawa taji
sallama qofar gida,saukowa tayi ta sanya hijabinta don ganin waye,don ta sani cewa
ko digewa mai yin sallamar zaiyi ba amsawa ko saurarensa fa'iza zata yi ba.

        Abdur rahman ne d'a ga qanin mahaifin mukhtar,gefansa qanwarsa ce bahijja


wadda zatayi shekaru sha biyar,fuskarta qunshe da fara'a tayi masa iso kan ya shigo
ta juya yabi bayanta,dai dai lokacin da fa'iza ke shimfida tabarmarta a tsakar gida
da alamu zama zata yi,abinda bata taba ganin fa'izar tayi ba tsawon kwanaki takwas
da zuwanta gidan,da kallo ta bisu suna gab da shigewa dakin sumayyan ta rabka
salati
"Meye haka zaki kama ki shigo mana da gardi cikin gida?" Waiwayowa sukayi
dukkaninsu suna dubanta
"Gyara maganarki qani yake ga mukhtar,muje bahijja" ta fada tana dage musu labulen
suka shige.

         Ruwa ta gabatar musu da lemo wanda ta tanada cikin cooler dinta saboda
mukhtar,kasancewar ya musu yawa yasa suma suka samu rabonsu
"Mutanen misra,kaga ko yadda ka koma abdur rahman,yaushe ka dawo ne?" Sumayya ta
tambaya tana murmushi,karatu ya tafiyi qasar misra saboda schoolership da ya samu
daga gwamnatin tarayya,kasancewarsa haziqin dalibi cikin daliban dake jahar wanda
ke karantar fannin da ya shafi addinin musulunci,shekararsa biyar da tafiya sai yau
ya dawo,a lokacin da ya tafi din shekararta daya da aure da mukhtar,da gidansu
jikin gidan mukhtar din yake kafin su tashi,wani lokaci idan mukhtar din nason fita
kuma baiso ta fita abdur rahman din yake kira ya tayata zama,hakanne yasa suka saba
har ya zama kamar wani abokin wasanta,a lokacin duka duka shekararsa sha bakwai
shima.

       Ruwan da yake sha ya ajjiye yana fadin


"Kwana na uku kenan,ashe yaya mukhtar bai gaya miki ba kenan?"kai take girgizawa
" bai gayamin ba kam ina ga ya sha'afa"
"Ya manta kam,irin wannan mace da ya ajjiye haka a gidansa babu kan gado" cewar
bahijja don ita ta qulu da abinda ta musun,murmushi sumayyan kawai tayi,abdur
rahman yace
"Itace matar da aka ce ya kuma aure?" Kai sumayya ta gyada masa sai yace
"Masha Allah,Allah to ya baku zaman lafiya,lokacin ina misra ai munyi waya da
alhaji yake gayamin don alokacin anata rikici ya mukhtar ya kai qarar umma
yahanasun" kai kawai ta kuma jinjinawa cikin mamaki din ita bata ma san ya kai
qarar ba,hira suka sha sosai,suka tuttuna baya sai wajen qarfe uku suka yi mata
sallama suka tafi bayan abdur rahman ya bata kyautar abaya har guda biyu masu kyau
ta rakosu har soro tana musu godiya tare da bawa bahijja dari biyar tace ta hau
mota.

         Ko da ta dawo fa'izan na zaune har yanzu a tsakar gidan,duka hirar da


sukayi da alama na cikin kunnenta,alwala ta daura tayi sallar la'asar sannan ta
shiga kitchen ta soma hidimar dora sanwar dare.

           Ta shiga ta fita ta shiga ta fita tayi hakan ya kusa sau biyar,ganin


haka ya sanya sumayya tayi zamanta a kitchen din taqi komawa daki saboda gujewa
sake afkuwar abinda ya faru ran nan,sai data gama komai ta kwashe nashi zuwa
dakinta sannan ta bar kitchen din.

          Sam bata nunawa fa'izan wanka zata shiga ba saboda ta gama gane ta
tsaf,bata tashi shigewa bayab gidan ta banke qofa sai taga tana shirye shiryen
shiga wanka,sai data fito taji fa'izan nata jan qwafa da tsaki,tayi dariya cikin
ranta ta shige dakinta ta hau shiryawa.

         Kan idanunta ta tarbi mukhtar wanda sai data gwammace tayi komawarta
daki,don kuwa yana gama ajjiye babur dinsa ya sungumi abarsa kamar yadda suka saba
a da can baya kafin qara aurensa ya dinga juyi da ita yana fadin
"Masha Allah my sumy,kyau kenan" duk da kunya ta dan kamata sai ta basar,ta gaban
fa'izan ya wuce da ita,bai direta ko ina ba sai kan gado ya bita ya turmushe yana
yamutsata tare da cakulkuli.

         Duk yadda taso qunshe dariyarta ko don fa'iza amma ina abun ya
faskara,haka ya sanyata ta dinga qyaqyatawa tana roqonsa ya bari,da qyar ta samu ta
tsaida shi tana goge qwallar da ta hada,kunnanta ya kai bakinsa ya rada mata wata
magana da ta sanyata jin kunya har ta rufe fuskarta da tafin hannunta.

        Ga mamakinsu sai ga fa'izan tazo cin abincin daren,duk da sumayyan bata so


hakan ba amma ta basar saboda kada taga kamar ta wulaqanta ta,shi kuwa yazo iua
wuya domin har wata shigar ya sanya sumayyan ta sake masa cikin qananun kaya.

            Suna kammala ci ta ja gefe ta sake sabon zama,da ido mukhtar ya bita


sannan ya dauke kansa yaci gaba da abinda yake,ba qaramin tsanar falon tayi ba
saboda yadda ya kere nata amma ta gwammace tayi ta zama ciki ko banza ta musguna
musu ta hanasu sakewa.

        Gefansa sumayyan ta dawo ta zauna tana kallon yadda yake shigar da wasu
bayanai cikin sabuwar laptop da ya siyo,tana da sha'awarta sosai hakan ya sanya ya
saki aikin da yake yana koya mata.

        Sosai ta qulu amma hakan baisa ta bar dakin ba,har suka kammala ya miqe ya
fita,cikin 'yan mintina ya dawo yana shigowa falon ya sunkuceta kamar dazu,har ya
kai bakin qofar dakin gadon ya waiwayo ya dubeta
"Ammm,idan kin gama abinda kike yi ki rufe mana qofar,sai da safe" ya fada yana
shigewa,da gayya ya dinga takalo sumayyan har sai da ya fuskanci ta fice musu daga
falon ta hanyar dukan kujera tare da banko qofar sannan ya saki murmushin mugunta
yana saukowa daga gadon don ya rufe dakin.

        Riqo hannunsa sumayya tayi tana masa kallo qasa qasa


"Kai ko.....ba'a haka ya mukhtar fa,nasan da gayya kake komai" murnushi ya saki har
yana fidda sauti sannan yace
"Koma me nayi ita ta jama kanta,ta yaya haka kurum zaka dage sai ka cusa kanka inda
baka da muhalli?,sai kayi zaman aure a inda ba'a da muradinka?" Ya fada yana sauka
daga gadon tare da cewa
"Jirani nazo sai muyi hirar sosai" ya fadi yana kashe mata ido daya,dariya ta saka.

**********************

      Wani irin zama ne yake wakana a tsakaninsu,cikin abinda bai wuce sati uku ba
gaba daya fa'iza babu layin da bata karade ba neman qawa,kasancewar duka maqotan
nasu mutanan sumayya ne,hakan ba qaramin qona mata rai yayi ba,bilhaqqi bata qaunar
sumayya ko wani abu da ya danganceta,hatta da yaran dake shigowa gun sumayyan
fa'iza qorafi take a kansu,idan taso tana iya korarsu,wani lokacin idan kan idon
sumayyan ne ta hanasu tafiya,tsoronta yaran keji hakan ya sanya wasu daga ciki suka
janye shigowa,mutum ce ita ta jama'a hakan ya sanya idan fa'izan nason yawonta
saidai tayi uwar tafiga zuwa can bayan layinsu.

         Tunda tazo gidan bata taba daukar tsintsiya da sunan shara ba baya ga ta
dakinta,koda ran girkinta ne da ta kammala zata bar wajen yadda yake tayi gaba
abinta,ko kadan sumayya bata lamunci qazanta ba ita zata killace komai ta gyara,ko
banza tasan tana da lada.

          Ko kadan mukhtar baya daga mata qafa wannan shi ya rage kaso casa'in
cikin dari na rashin mutuncinta,tun da can irin 'yammatan nan ne da basuqi su fito
da daurin qirji su dambatu da namiji ba,hakan ne ya bawa yaya yahanasu sha'awa a
gajeran tunani irin nata,tana ganin cewa ita daya ce zata iya zama cikin gidan
muntari ta take kowa ta kuma kawo musu abinda suke so,duk da cewa fa'izar ta taba
shege tuna gida aka zubar amma hakan ba aibu bane a gun yahanasu,tana ganin ma wata
dama ce dake nuna zata iya haifawa muntarin d'iyoyin da take tsammatar zasu iya
alfahari da su,tarbiyya cancanta kunya asali da cikakkiyar nasaba basu zame mata
mizanin ma'auni ba a gareta wajen hada qanin nata da ita.

        Ko daya sumayya bata taba shaidawa muntarin fitar barbadar da fa'izan keyi
ba,ta azawa ranta cewa idan kere na yawo zabo na yawo dole a hade,abu daya ne da ta
tsaya a kansa shine,bata yadda fa'izan ta shiga haqqinta kamar yadda ita bata shiga
nata haqqin har ma da hurumi da shirginta baki daya,sai yanzu take sake ganin
alfanun shawarar anty dije gareta,tabbas gaskiya ta gaya mata,kuma gata ta mata,ba
dan hakan ba da zuwa yanzu Allah ne kadai yasan yadda fa'izan zata maidata.

            Duk yadda ya dauki lamarin shigowa gidan muntarin da sauqi ya fice


haka,sai ta tadda soyayyar da muntarin kewa sumayyab bairin soyayyar nan bace da
tuggu ko makirci ke nasarar wargazata ba,soyayya ce mai azabar danqo da yauqi,amma
ta daukarma kanta alqawarin sai ta wargaza zaman lafiyar sumayyar ko ta halin
yaya,kafin ta waiwaya ta takawa su yaya yahanasu birki wadanda zuwa yanzu suka soma
yi mata lissafin zuwa yaushe zata dauki ciki,bata son takura ko sanya ido cikin
lamuranta,basu san wace ainihin fa'izan ba har zuwa yau
*A WANI DARE*

*_Masu karatu ku biyoni,yanzu aka fara littafin._*

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍✍✍✍
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)
________________________

*bismillahir rahmanir rahim*

*inna ma'al usr yusrah,fa'inna ma'al usr yusrah*


_______________________

1⃣1⃣

*A WANI DARE*

     Tun magariba ta shige dakinta kasancewar ba ranar girkinta bane,tun wajejan


yammaci take jin ciwon kai da fargaba kadan kadan,hakanne ya sanya tun tana saman
abun sallarta bayan ta kammala sallar isha'i bacci yayi awon gaba da ita,ko mukhtar
da yazo mata sai da safe haka ya sameta,daukarta yayi cak ya maidata saman gado
sannan ya ja mata qofar ya fice.

      Kamar cikin mafarki taji ana kiran sunanta,cikin wata iriyar murya ce wadda
sam bata ta dadin amo,a hankali ta dinga bude idanunta cikin duhun da ya gauraye
dakin nata,tabbas sunanta ake kira cikin wata murya mai kama da amon sautin kukan
kare.

      Idanunta ta ware sosai saboda wata siffa data dinga hangowa ta tokare bangon
dakinta daga inda take fuskanta,wata mummunar faduwar gaba ce ta ziyarce take gumi
ya rufeta baki daya,jikinta ya hau rawa
"Bismillahil lazi la yadurru ma'as mihi shai'un fil'ardi wala fissama'i wa huwas
sami'ul alim" haka ta dinga maimatawa,tun tana yi cikin zuciyarta har ya fito
fili,maimakon kiran sunan nata da ake a hankali sai aka koma da sauri sauri,sannu a
hankali siffar halittar da take gani jikin bangon ta bace bat.

         Cikin wani irin hanzari da kuzari ta diro daga saman gadon nata hannunta
dauke sa wayarta,falo tayo tana ci gaba da ambaton sunan Allah,ta kunna qwan dakin
tana mai qarewa falon nata kallo,babu abinda ta gani,cikin sanyin jiki ta zauna kan
daya daga cikin kujerunta dafe da kanta.

           Tsawon mintina ashirin ta dauka a haka sannan ta isa bakin t.v stand
dinta,ta dauki ruwan leda guda daya da ya rage wanda tash dazu,dankwalinta ta cira
ta ninka ta shimfida ta daura alwala a kai sannan ta fuskanci gabas.

          Sallah tayi raka'a hudu sannab daga bisani ta zauna,cikin surorin data
haddace ta dinga karantawa daya bayan daya,har zuwa sallar asuba bata samu ta
runtsa ba,a nan zaune mukhtar da ya shigo tayar da ita sallah ya sameta,yaso ya
danyi mamaki amma sanin cewa wani lokaci takan tashi da wuri ya sanya boye mamakin
nasa ya fita ya tafi masallaci.

           Sai kusan biyar da rabi ta koma saman kujerarta ta kwanta a nan bacci ya
sureta.

          Sallamar mukhtar ce ta tasheta,ta miqe tana mutstsike idanunta,a shirye


ya shigo da alama kasuwa zaya fita
"Lafiya kuwa kike sumayya,wani irin bacci yau kike haka sam ban ji motsinki ba?"
Murmushi tayi tana gaida shi ba tare data amsa masa tambayarsa ba
"Ni zan fita babu wata matsala ko?" Ya fafa kamar yadda ya saba fadi duk sanda zai
fita kasuwa,kai ta girgiza
"Babu komai,a dawo lafiya Allah ya bada sa'a"
"Amin" ya fada yana kashe mata idanunsa daya tare da cewa
"Yau ba rakiya my sumy?" Kai ta kada
"Kaima ka sani ba girki na bane,ka kuma san halin fa'iza sarai,ranar girkinta bata
son kowa ya rabeka ko?" Kai ya kada
"Ba ruwa na da ita,tunda kafin na san ta ke na sani ko,amma tunda kince haka
shikenan,sai na dawo" ya fada yana daga mata hannu kana ya fice.

            Sai da ya fita da wajen mintina biyar sannan ta miqe,daki ta nufa da


nufin shiga,gab da zata shiga din abinda ya faru jiya ya dawo mata tar a
kwanyarta,tsayawa tayi jim sannan ta karanto addu'o'i  ta shiga.

          Tsayawa tayi tana bin kowanne lungu da saqo da kallo bata ga komai ba
saboda haka ta dauki abinda zata dauka ta fito.

        Ga mamakinta tsakar gida ta taras da fa'iza zaune saitin window din dakinta
zaune,kallon juna sukayi sumayya ta dauke kanta ta nufi bandaki don yin wanka,yayin
da fa'izan ta bita da kallo,har ta kammala wankan ta koma daki ta shirya ta fito ta
shiga kitchen don samawa kanta abinda zata ci fa'izan na zaune,dim yawanci idan
ranar girkinta ne bata baiwa sumayya abin kari,to da yake ita din ma ba gwanar
abinci bace hakan baya dada ta da qasa saita hada duk abinda ya samu taci shikenan
an wuce gurin.

           Yauwa kamar jiya bacci ya dauketa da wuri,kamar jiyan dai cikin bacci
taji ana kiran nata,tarwai wannan karon bude idanunta nata cikin gigita,yau kam
siffar macizai take gani tsaye ya mamaye bangon
"A'uzu bi kalimatillahit taammati min sharri ma khalaq" ta dinga maimaitawa da
qarfinta har bata san tana daga murya ba ko kuma ta manta cewa dare ne,bat abun ya
bace sama ko qasa,a bakin qofar fita daga dakin sukaci karo,mukhtar ne yana tsaka
da bacci ya dinga jiyo muryarta,jikinsa ta fada gabanta na tsananin duka jikinta na
rawa,janyeta yayi zuwa falon suka zauna gefan kujerar yana tofa mata addu'a.
          Sai da ta samu nutsuwa sannan ya dubeta ba tare da ya tambayeta me ya
faru ba
"Muje dakina ki kwanta a can" kai ta kada tana zare jikinta daga nashi
"Kaje kawai babu komai zan iya kwanciya a nan,mafarki kawai nayi kuma yanzun nayi
addu'a" idanu ya zuba mata sai ta kada kanta tana son gamsar da shi kan abinda ta
fada din,kan doke saboda yadda ta kafe ya sanya shi barinta tare da sake mata
addu'a sannan ya fita.

           Qarfe tara na safw tuni tayi wankanta tana zaune a falon cikin rashin
kuzari da tunani barkatai,a haka mukhtar din ya taddata,bayan sun gaisa ya samu
gefanta ya zauna
"Sumayya,meke damunki,na tabbata akwai abinda ke damunki,yanayinki jiya ya tabbatar
min da haka,kada kuma ki soma cemin babu komai" qasa tayi da kanta don kada ya ga
tsoron dake cikin idonta,sai da ta saisaita kanta sannan ta dago
"Ya mukhtar,ina zaton akwai maciji cikin dakin nan"
"Maciji?" Ya tambaya cikin mamaki,kai ta gyada masa,sai yayi shiru na wasu daqiqu
kana daga bisani ya ajjiye jakar dake hannunsa yana mai miqewa
"Ina zuwa" ya fada yana ficewa.

          Minti kusan arba'in da biyar sai gashi ya dawo da wani matashin


saurayi,wanda aikinsa shine fidda maciji kowanne iri,dakinsa ya bude mata yace ta
shiga ciki ta zauna tare da kulle dakin,duk abin nan da ake fa'iza na cikin dakinta
tamkar bata cikin gidan,shi da matashin suka shiga cikin dakin nata.

              Duk wani salo da dabara irin tasa da ya gada ta fiddo da maciji ko


wani mugun qwaro daga bigirensa babu wanda bai gwada ba,saidai ko kusa ko alama
babu wani abu da yayi ka da maciji cikin uwar daka da rumfar tata,hayaqi yayi kusan
kala uku amma shuru babu maciji,hakan shi ya tabbatar masa babu wani maciji cikin
gidan ma baki daya ba dakin ba,yace amma ta sake kula sosai idan ta sake ganin
wulgawar wani abu nan da kwanaki uku ta sanar masa zaya dawo,mukhtar ya sallameshi
ya tafi.

         Shi ya taimaka mata suka maida suka kintsa dakin,suka maida komai
muhallinsa,bai samu fita kasuwa ba sai azahar ya fice,ita kuma ta nufi bakin fanfo
ta tara ruwa zata yi alwalar sallar azahar din.

           Sai lokacin fa'iza ta fito,wani kallo ta yiwa sumayyan kana ta sheqe da


dariya
"An tara haram an gyara daki dama ta yaya za'aji dadin zama a ciki?,kayan haram ne
fa?.......hhhhhh......hmmm kadan ma kenan" ta fada tana jan wani shegen tsaki tare
da juyawa ta koma dakinta.

           Cikin mamaki take binta da kallo tare da neman tsari cikim


zuciyarta,matar da duk artabun da ake cikin gidan tun safe bata fito ba sai
yanzu,watsar da tunanin tayi,me yasa dakinta ya tsone mata ido,koda yaushe bata da
magana sai nashi,da bata ce Allah ya sawwaqe ba ta ja bakinta tayi shiru
mana,itadai tunda ta riga da tasan cewa tayi addu'a koma meye zaizo ko da
QADDARARTA ne sai ya sameta din zaya zo mata da sauqi.

        Tana kammala sallarta kitchen ta wuce ta soma hidimar dora girki saboda yau
girkinta ne ita zata karbi mukhtar din,ita kuwa bata wasa da ranakun girkinta,tana
kitcehen taga ficewar fa'iza daga gidan.

_kuyi haquri da wannan ina cikin uzururruka_

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍✍✍✍
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)
________________________

*bismillahir rahmanir rahim*

*inna ma'al usr yusrah,fa'inna ma'al usr yusrah*


_______________________

1⃣1⃣

*A WANI DARE*

     Tun magariba ta shige dakinta kasancewar ba ranar girkinta bane,tun wajejan


yammaci take jin ciwon kai da fargaba kadan kadan,hakanne ya sanya tun tana saman
abun sallarta bayan ta kammala sallar isha'i bacci yayi awon gaba da ita,ko mukhtar
da yazo mata sai da safe haka ya sameta,daukarta yayi cak ya maidata saman gado
sannan ya ja mata qofar ya fice.

      Kamar cikin mafarki taji ana kiran sunanta,cikin wata iriyar murya ce wadda
sam bata ta dadin amo,a hankali ta dinga bude idanunta cikin duhun da ya gauraye
dakin nata,tabbas sunanta ake kira cikin wata murya mai kama da amon sautin kukan
kare.

      Idanunta ta ware sosai saboda wata siffa data dinga hangowa ta tokare bangon
dakinta daga inda take fuskanta,wata mummunar faduwar gaba ce ta ziyarce take gumi
ya rufeta baki daya,jikinta ya hau rawa
"Bismillahil lazi la yadurru ma'as mihi shai'un fil'ardi wala fissama'i wa huwas
sami'ul alim" haka ta dinga maimatawa,tun tana yi cikin zuciyarta har ya fito
fili,maimakon kiran sunan nata da ake a hankali sai aka koma da sauri sauri,sannu a
hankali siffar halittar da take gani jikin bangon ta bace bat.

         Cikin wani irin hanzari da kuzari ta diro daga saman gadon nata hannunta
dauke sa wayarta,falo tayo tana ci gaba da ambaton sunan Allah,ta kunna qwan dakin
tana mai qarewa falon nata kallo,babu abinda ta gani,cikin sanyin jiki ta zauna kan
daya daga cikin kujerunta dafe da kanta.

           Tsawon mintina ashirin ta dauka a haka sannan ta isa bakin t.v stand
dinta,ta dauki ruwan leda guda daya da ya rage wanda tash dazu,dankwalinta ta cira
ta ninka ta shimfida ta daura alwala a kai sannan ta fuskanci gabas.
          Sallah tayi raka'a hudu sannab daga bisani ta zauna,cikin surorin data
haddace ta dinga karantawa daya bayan daya,har zuwa sallar asuba bata samu ta
runtsa ba,a nan zaune mukhtar da ya shigo tayar da ita sallah ya sameta,yaso ya
danyi mamaki amma sanin cewa wani lokaci takan tashi da wuri ya sanya boye mamakin
nasa ya fita ya tafi masallaci.

           Sai kusan biyar da rabi ta koma saman kujerarta ta kwanta a nan bacci ya
sureta.

          Sallamar mukhtar ce ta tasheta,ta miqe tana mutstsike idanunta,a shirye


ya shigo da alama kasuwa zaya fita
"Lafiya kuwa kike sumayya,wani irin bacci yau kike haka sam ban ji motsinki ba?"
Murmushi tayi tana gaida shi ba tare data amsa masa tambayarsa ba
"Ni zan fita babu wata matsala ko?" Ya fafa kamar yadda ya saba fadi duk sanda zai
fita kasuwa,kai ta girgiza
"Babu komai,a dawo lafiya Allah ya bada sa'a"
"Amin" ya fada yana kashe mata idanunsa daya tare da cewa
"Yau ba rakiya my sumy?" Kai ta kada
"Kaima ka sani ba girki na bane,ka kuma san halin fa'iza sarai,ranar girkinta bata
son kowa ya rabeka ko?" Kai ya kada
"Ba ruwa na da ita,tunda kafin na san ta ke na sani ko,amma tunda kince haka
shikenan,sai na dawo" ya fada yana daga mata hannu kana ya fice.

            Sai da ya fita da wajen mintina biyar sannan ta miqe,daki ta nufa da


nufin shiga,gab da zata shiga din abinda ya faru jiya ya dawo mata tar a
kwanyarta,tsayawa tayi jim sannan ta karanto addu'o'i  ta shiga.

          Tsayawa tayi tana bin kowanne lungu da saqo da kallo bata ga komai ba
saboda haka ta dauki abinda zata dauka ta fito.

        Ga mamakinta tsakar gida ta taras da fa'iza zaune saitin window din dakinta
zaune,kallon juna sukayi sumayya ta dauke kanta ta nufi bandaki don yin wanka,yayin
da fa'izan ta bita da kallo,har ta kammala wankan ta koma daki ta shirya ta fito ta
shiga kitchen don samawa kanta abinda zata ci fa'izan na zaune,dim yawanci idan
ranar girkinta ne bata baiwa sumayya abin kari,to da yake ita din ma ba gwanar
abinci bace hakan baya dada ta da qasa saita hada duk abinda ya samu taci shikenan
an wuce gurin.

           Yauwa kamar jiya bacci ya dauketa da wuri,kamar jiyan dai cikin bacci
taji ana kiran nata,tarwai wannan karon bude idanunta nata cikin gigita,yau kam
siffar macizai take gani tsaye ya mamaye bangon
"A'uzu bi kalimatillahit taammati min sharri ma khalaq" ta dinga maimaitawa da
qarfinta har bata san tana daga murya ba ko kuma ta manta cewa dare ne,bat abun ya
bace sama ko qasa,a bakin qofar fita daga dakin sukaci karo,mukhtar ne yana tsaka
da bacci ya dinga jiyo muryarta,jikinsa ta fada gabanta na tsananin duka jikinta na
rawa,janyeta yayi zuwa falon suka zauna gefan kujerar yana tofa mata addu'a.

          Sai da ta samu nutsuwa sannan ya dubeta ba tare da ya tambayeta me ya


faru ba
"Muje dakina ki kwanta a can" kai ta kada tana zare jikinta daga nashi
"Kaje kawai babu komai zan iya kwanciya a nan,mafarki kawai nayi kuma yanzun nayi
addu'a" idanu ya zuba mata sai ta kada kanta tana son gamsar da shi kan abinda ta
fada din,kan doke saboda yadda ta kafe ya sanya shi barinta tare da sake mata
addu'a sannan ya fita.

           Qarfe tara na safw tuni tayi wankanta tana zaune a falon cikin rashin
kuzari da tunani barkatai,a haka mukhtar din ya taddata,bayan sun gaisa ya samu
gefanta ya zauna
"Sumayya,meke damunki,na tabbata akwai abinda ke damunki,yanayinki jiya ya tabbatar
min da haka,kada kuma ki soma cemin babu komai" qasa tayi da kanta don kada ya ga
tsoron dake cikin idonta,sai da ta saisaita kanta sannan ta dago
"Ya mukhtar,ina zaton akwai maciji cikin dakin nan"
"Maciji?" Ya tambaya cikin mamaki,kai ta gyada masa,sai yayi shiru na wasu daqiqu
kana daga bisani ya ajjiye jakar dake hannunsa yana mai miqewa
"Ina zuwa" ya fada yana ficewa.

          Minti kusan arba'in da biyar sai gashi ya dawo da wani matashin


saurayi,wanda aikinsa shine fidda maciji kowanne iri,dakinsa ya bude mata yace ta
shiga ciki ta zauna tare da kulle dakin,duk abin nan da ake fa'iza na cikin dakinta
tamkar bata cikin gidan,shi da matashin suka shiga cikin dakin nata.

              Duk wani salo da dabara irin tasa da ya gada ta fiddo da maciji ko


wani mugun qwaro daga bigirensa babu wanda bai gwada ba,saidai ko kusa ko alama
babu wani abu da yayi ka da maciji cikin uwar daka da rumfar tata,hayaqi yayi kusan
kala uku amma shuru babu maciji,hakan shi ya tabbatar masa babu wani maciji cikin
gidan ma baki daya ba dakin ba,yace amma ta sake kula sosai idan ta sake ganin
wulgawar wani abu nan da kwanaki uku ta sanar masa zaya dawo,mukhtar ya sallameshi
ya tafi.

         Shi ya taimaka mata suka maida suka kintsa dakin,suka maida komai
muhallinsa,bai samu fita kasuwa ba sai azahar ya fice,ita kuma ta nufi bakin fanfo
ta tara ruwa zata yi alwalar sallar azahar din.

           Sai lokacin fa'iza ta fito,wani kallo ta yiwa sumayyan kana ta sheqe da


dariya
"An tara haram an gyara daki dama ta yaya za'aji dadin zama a ciki?,kayan haram ne
fa?.......hhhhhh......hmmm kadan ma kenan" ta fada tana jan wani shegen tsaki tare
da juyawa ta koma dakinta.

           Cikin mamaki take binta da kallo tare da neman tsari cikim


zuciyarta,matar da duk artabun da ake cikin gidan tun safe bata fito ba sai
yanzu,watsar da tunanin tayi,me yasa dakinta ya tsone mata ido,koda yaushe bata da
magana sai nashi,da bata ce Allah ya sawwaqe ba ta ja bakinta tayi shiru
mana,itadai tunda ta riga da tasan cewa tayi addu'a koma meye zaizo ko da
QADDARARTA ne sai ya sameta din zaya zo mata da sauqi.

        Tana kammala sallarta kitchen ta wuce ta soma hidimar dora girki saboda yau
girkinta ne ita zata karbi mukhtar din,ita kuwa bata wasa da ranakun girkinta,tana
kitcehen taga ficewar fa'iza daga gidan.

_kuyi haquri da wannan ina cikin uzururruka_

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍✍✍✍
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)
1⃣2⃣

________________________

*Bismillahir rahmanir rahim*

*qul innal amra kullahu lillah*


_________________________

          Sallamar fadima ce ta ratsa dodon kunnenta,tana daga kitchen din ta amsa


mata,kai tsaye ta nufo kitchen din ta leqo,murmushi sumayya tayi qoqarin sannan
tace
"Au fadima ce?" Yatsina fuska tayi ta karkace baki tace
"Eh.....nice,ana ta kitchen ne anata fama?" Cikin jin dadin jin fitowar kyakkyawan
furuci yau daga bakin wanda ya jibanci mukhtar zuwa gareta tace
"Wallahi kuwa,kin ganmu muna ta fama da sanwa" bisa ga sabanin tunaninta sai taji
tace
"A'aha,anan dama aka fi kauri ai,aci a cika mana gida da kashi,sockaway nan da nan
ta tumbatsa" sosai maganar ta bata ranta,cin fuskar tana ganin kullum dada gaba
yake,me yayi zafi ne haka?,ba aure bane kuma ta bar dan uwansu yayi,tunda a yanzu
suna da wadda suke tunanin zata cika muradinsu ai yaci ace sun sakar mata mara tayu
fitsari yadda ya kamata,sai ta sake yin wani murmushin idanunta cikin na fatiman
"Ayyah,ai kayi auren ma kayi kashi cikin gidan mijinka ma rahama ce,wasu har yau an
rasa wanda zai daukesu ya kaisu gidansa ko kashin ne ma suyi" sarai ta fahimci
magana ta yaba mata,a fusace ta qarasa shigowa kitchen din tana tunkarar sumayya
kamar zata kai mata shaqa
"Da uban wa kike?"
"Da wanda ya tsargu" ta fada tana bude tukunyar miyarta tana juyawa,wuyanta ta ruqo
ta baya,a nutse ta juyo ta sanya hannunta ta zare shi daga wuyan nata tana nunata
da yatsa
"Kada ki kuskura fati" sumayyan ta fada kana ta ja tsaki ta juya taci gaba da
abinda takeyi.

        Baki ta saki galala tana dubanta,iya tsawon zamanta da su ko kallon banza


babu wanda sumayyar ta taba yiwa duk irin budurin da sukeyi tsakiyar kanta,kafin ta
kai ga cewa komai fa'iza ta sanyo kai cikin kitchen din tana cewa
"To malama,da kika zo nan kika tsaya kina kalen magana nan aka aikoki?" Ta bude
baki tayi da niyyar yin magana fa'izan ta tarbeta
"Kinga miqon saqona sai ki dawo kuyita yinta 'yar ayi jikar na saba" waiwayowa
fatiman tayi cikin mamakin kalaman fa'izar
"Wace 'yar ayi jikar na saba din?,babata da ta haifeni ta haifi mijinki muntari ko
innar babarmu?"
"Kinga duk wanda kika zaba cikinsu,zaki bani saqon ko kuwa?" Ba yadda ta iya saboda
yaya yaha ta jadda da mata saqon,amma ta sake yarda fa'iza ba mutunci gareta
ba,tsaf zata iya zagesu su dukan,haka tayi haushin kaza juye kan dami ta zabgawa
sumayya harara tare da jan doguwar qwafa
"Yar malamai ba'a haifa ba an shanye mana dan uwa" ta fadi tana shirin ficewa tabi
bayan fa'iza,dariya tayi
"Au ashe na isa ma" tana jin maganar kuma ta bata haushi tare da mamakin budewar
bakin sumayya amma haka ta haqura tabi bayan fa'izar.

          Qeme me fa'izan ta hanata kudin motar komawar bayan ta bata saqon,juyin


duniya tace bata da ai dan uwansu bai bada ba,haka nan ba don taso ba ta shiga
wajen sumayyan,a lokacin ta gama aikinta tana kan kujera tana gyaran
qumbarta(farce)
"Kudin mota nazo ki bani zan koma gida"a nutse ta daga kai ta dubeta
" da na aikeki ina?"fuska ta hade don kada ta rasa
"Ai na sancewa akwai kudi gurinki"
"Wadanda kika bani ajiya kenan dazu" sosai take shan mamakin yadda sumayyan ta
zama,amma babu komai komai ya kusa zuwa qarshe saboda haka ta dan sassauto
"Ba halinki bane sumayya ba fa,ko dari ce ki bani zata kaini gida" shiru ta danyi
sannan ta ajjiye rezar hannunta ta shiga uwar dakanta ta dauko dari biyu ta miqa
mata,babu godi bare na gode ta amsa ta juya ta fice,da kallo ta bita sannan ta
girgiza kai,ashe guri suka samu suketa shanya yadda suka so?,wato sam wani mutumin
baisan alkunya ba kenan,sai ka sauya launi kuke iya zama dai dai da shi?,idan banda
sun sayawa kai raini ina ita ina fadiman ina ita?wadda a qalla ta bata shekara
kusan shekara hudu ko biyar
"Allah ya kyauta ya rufa asiri" ta fada a fili tana ci gaba da abinda take.

          Lafiya lau yau tayi barcinta har ta kammala ranakun girkinta ta miqa
mukhtar din ga fa'iza.

         Kasancewar da safe suje miqa girki ga wadda zata karba ya sanya tana
kammala komai ta wanke kanta ta wuce gidan kitso nam qarshen layinsu,sai data fara
shiga gidan maman nana ta dauki saboda tana son zuwa gida sannan suka wuce.

           Zuwa sha daya na rana aka gama mata kitson ta wuce gidansu.

          A kitchen ta tadda innarta ta dora sanwar rana,gidan babu kowa saboda


qannen nata duk weekend na zuwa wata islamiya tun tara na safe sai biyar da rabi na
yamma suke dawowa.

         "Ina fatan lafiya kuke dai ko?" Innar ta tambayeta bayan sun gama
gaisawa,murmushi ta saki ta kada kai
"Lafiya qalau inna"
"To madalla haka akeson ji,aci gaba dai da haquri,zaman aure ko kai kadai ne sai
kayi haquri balle kuma da abokiyar zama,Allah yayi miki albarka"cikin jin dadin
addu'arta tace
" amin inna na gode"suka dan fada wata hirar kafin tace
"Wai ni kam inna ina ya abbakar?,ko leqoni fa inna baya yi" ta fada cikin shagwabe
fuska
"Hmmm,yayanku ai yanzu bai ga ta zama ba,ya dauko aure" cikim zumudi da murna
sumayya tace
"Allah innarmu?,wace a ina take"
"A'ah,sai ki jira shi yazo kuma wannan kyaji daga bakinsa" ta fada innar tana
miqewa saboda kasancewar abubakar dan fari a gunta.

          Tana nan har abubakar din ya dawo,nan suka sha hirarsu,sai kusan shida
saura ya dauketa kan babur dinsa ya kaita har qofar gida,tayi tayi ya shigo yaqi
haka ta haqura.

          Muqullinta ta sanya ta bude dakin nata ta sanya kai zata shiga,wani


dunqulallen abu ya tokareta,tashi daya taji wani azabbaben bacin rai ya
kamata,tsanar dakin ta mamayeta,sai ta koma da baya ta janyo kujera 'yar tsuguno
bakin qofar dakin ta zauna,duk da uban tarin gajiyar da ta debo amma sam bata
sha'awar shiga dakin.
           Har qarfe goma na dare tana tsakar gudan zaune,a nan tayi magariba tayi
isha'i kasancewar mukhtar baya gari yayi tafiya legos sarin kaya.

           Tsakar gidan yayi tsit sai ita daya,fa'iza ta gama kara kainarta ta qule
daka tana kyautata zaton ma tayi bacci,gashi babu hasken wutar lantarki don nepa
sunyi tsiyar,gidan taje ta rufe sannan ta dawo tsakar gidan,ta jima tsaye a bakin
qofar tana nanata addu'a sannan taji salama na saujarwa ruhinta,ta kwashi jakarta
ta shiga dakin gabanta na wani irin bugawa,kayanta kawai ta sauya ta haye gado a
takure wani tsoro da batasan na meye ba fal ranta.

            Cikin baccinta taji kamar ana tashinta,a firgice ta farka tana ambaton
Allah,tamkar ana korota daga dakin haka ta dinga ji,a gaggauce ta fito izuwa tsakar
gida jikinta na rawa,sulalewa tayi ta zauna dirshan jikin qofar dakin tana ci gaba
da kiran sunan Allah a haka asuba ta risketa,a nan ta daura alwala tayi sallar
asubar.

          Qarfe shida da rabi na safiya taji wani irin qwarin gwiwa na shigarta,ta
miqe cikin hanzari ta koma cikin dakin,tamkar ana tafasa zuciyarta da tsanar dakin
ta nufi uwar dakanta ta dangana da sif dinta,akwatinta ta jawo tamkar ana umartarta
ta shiga loda kayanta tsaf sannan ta sauya na jikinta ta rufe akwatin ta janyo shi
waje,sakatar gidan ta zare kana ta fice kai tsaye ta nufi bakin titi.

         Ta kusan a qalla awa guda tsaye bakin titin ba tare da ta samu abun hawa
ba kasancewar safiya ce babu yawaitar sawaye,sai da ta fara qosawa sa tsaiwar har
tana tunanin fara takawa da sawayenta wani mai adaidaita ya nufo inda take,da
hanzari ta tsaidashi gudun kada ya wuce ta rasashi,ta gaya masa inda zai kaita shi
kuma ya gaya mata abinda zata biya,ba tare da ta tsaya ciniki da shi ba ta hau tare
da tura akwatinta ciki shima.

*masu karatu muje zuwa,kada kuce komai kowanne dan adam da irin tasa QADDARAR*

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍✍✍✍
[9/25, 12:41 AM] +234 908 222 8222: ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

1⃣3⃣

______________________
*wa iyyamsaskallahu bi durrin fala khashifa lahu illa huw,wa iy yuridka bi khairin
fala raadda li fadhlih*
__________________________

           A qofar gidansu mai adidaita sahun ya ajjiyeta,ta biyashi sannan ta ja


akwatinta zuwq ciki.

         Ta jima a soron tsaye gabanta na faduwa,tana mtuqar shakkar


iyayenta,saidai hakanan taji ana ingizata zuwa barin gidan,wani irin qunci take ji
idan tana cikin gidan,numfashi ta ja sannan tayi shahada ta shige.

           Qannanta na tsakar gida suna karyawa jikinsu sanye da unifoarm din


islamiyya,innarta kuma na daga cikin rumfarsu,
"Lah sannu da zuwa yaya sumayya" suka fada halima na karbar mata akwatinta tare da
shiga da shi cikin rumfar tasu ita kuma tabi bayanta.

           "Lafiya sumayya da safiyarnan?" Innar ta tambayeta cikin fuskar


mamaki,gefan kujerar ta samu ta zauna sai kawai ta fashe da kuka ba tare da tace
komai ba,baki innan ta sake tana kallonta kafin daga bisani ta yiwa halima nuni da
hannu kan ta fita ta basu guri,daga qarshe itama da ta gaji da tambayarta sai ta
miqe ta fito tsakar guda ta hau ayyukanta ta barta cikin dakin.

           Wuni guda innan na tambayarta amma ta gaza cewa komai,to me zata ce mata
ya korota daga gidan,ba matsala bace tsakaninta da mijinta ba ballanta na tace,ba
wani abu sukayi ba,to meye dalilinta,sosai hankalin innan ya tashi ganin taqiyin
maganar,gashi kuma malam din baya gida sun tafi musabaqa ta jaha da ake gudanarwa
daga shi har yayan ta abubakar,amsa daya ta iya bata data tambayeta ina mukhtar din
ta sanar masa yayi tafiya,sai kan innar ya sake daurewa,har dare tana zuba ido ko
zata ga wani kan sumayyar amma shiru haka suka wayi gari.

            Mamaki innar ta kuma tashi da shi na ganin washegari sumayyan ta sake


sarai,walwalarta take kamar babu wani abu da ya shalleta,wannan damuwar da ta zo da
ita jiya duka yau babu ita.

           Tunda suka dauko hanya daren jiya yake Allah Allah ya iso gidan nashi
don yayi tozali da sumayyar tasa,qarfe uku da minti biyar dan adaidaita sahu ya
ajjiyeshu qofar gidan nasa ya sallameshi ya shige gidan bakinsa dauke da sallama
fuskarsa qunshe da murmushi don yana da yaqinin samun tarba mai kyau kasancewar ya
tafka sa'a cikin ranar girkinta zai dawo din.

           Mamaki ne ya maye gurbin doki murmushi da fara'ar da yakeyi ganin yadda


tsakar gidan yake a tarwatse babu cikakkiyar tsafta,sallama ya sakeyi karo na biyu
saidai shiru babu amsa,a hankali idanunsa suka sauka kan dakin sumayya,take yaci
karo da kwad'on da take kulle dakin duk sanda zata fita,mamakinsa ya sake
ninkuwa,ko da can sumayya sanda take da qananun shekaru ainun bata taba fita ba
tare da uzininsa ba koda kuwa maqota ne,ya maida kallonsa dakin fa'iza ana
sakaye,ya qarasa ya tura ya leqa kansa ciki bata nan,ya tura bandakin ya leqa nan
ma bata ciki,jikin bango ya koma ya jingina tare da ajjiye jakar bacco din
hannunsa,ba fa'iza ce damuwarsa ba sumayya ce,lambarta ya lalubo ya kira saidai an
sanar masa da cewa a kashe take,ya maida wayar cikin aljihunsa yana maida ajiyar
zuciya tare da shiga tunani.

          Maganar fa'iza ta katseshi wanda da alama da wasu dake daga waje take
maganar,ya zubawa qofar soron idon har ta qaraso,da fari tayi turus,sai kuma ta
qaraso tana dubansa
"Au......ashe kai ne.......ashe yanzu zaka dawo.....na dauka sai anjima gashi ban
tanada ma komai ba"
"Ina sumayya take?" Ya tambaya ba tare da ya kula da surutun da take zuba masa
ba,wani abu ya takore wuyanta,wato ta sumayya ma yake ko,zai gane kuransa ne
wlh,baki ta tabe sannan tace
"Ka bani ajiyarta ne?"idanunsa ya ware baki daya har sai da taji tsoro
" ke bana ciki da iskanci,ni kike gayawa haka,zan tattaki ne wallahi naga uban da
ya tsaya miki,banza sha sha sha,ina sumayya take nace miki"cikin gunguni tace
"Oho,nidai da asussuba naga ta hada kayanta ta fice bansan inda taje ba".

        Bai qara bi ta kanta ba ya shige dakinsa ya ajjiye kayan hannunsa,da sauri


ya sake zaro wayarsa saboda tunawa da yayi waccan satin sumayyan ta saka maaa
lambar wayar innar tata ta gaya masa ya abubakar ne ya siya mata waya.

         Bugu biyu zainab ta daga tana fadin


" ya mukhtar ga innar can bari a kai mata"da sauri ya katseta
"A'ah zainab,ina yayarku"
"Gata can a daki a kwance"
"Tun yaushe tazo gidan"
"Tun jiya"
"Ok" ya fada sannan cikin sauri ya ajjiye wayat,kayan jikinsa ya cire sannan ya
fito ya nufi tsakar gida,yana jin motsin fa'izan daga kitchen bai bi ta kanta ba ya
tara ruwan wanka ya fada bandaki.

           Sai da ya rama sallar azahar dake kansa sannan ya shirya cikin wani
yadin kufta ruwan toka(ash),ya feshe jikinsa da turare,yayi kyau matuqa,take
zatinsa da kwarjininsa suka fito,yana sanya takalminsa sau ciki irin na maza fa'iza
ta shigo dakin hannunta dauke da plate data ciko da jallope din taliya wadda keta
zuba qauri saboda uwar wutar da ta babbaka mata saboda saurin da take ta kawo masa
yaci tun kafin yaje ya maido da sumayya gidan plan dinta ya rushe.

       "A'ah,mutari ina zaka daga dawowarka,ga abinci na maka ai ko shi ka tsaya


kaci" kallo daya yayi mata ita da taliyar tata yaci gaba da sanya takalmansa yana
daga duqen ya jefeta da
"Bani da buqata" gabanta ya fadi ganin asara qiri qiri na shirin riskarta,kwana uku
tayi tana tattalin kayan tarkacen da ta dafa taliyar da shi sai gashi cikin
mintinan da basu gaza biyar yana son janyo mata asara.

        Matsowa tayi kusa da shi cikin marairaicewa da tausasa murya irin wadda bai
taba riska daga gareta ba ta soma hilatarsa,da sauri ya ja baya tare da jan
matsiyacin tsaki ganin tana gab da shafa masa maiqon abincin,maqullin babur dinsa
ha zara ya fice ya barta tsaye a nan dafe da kai.

            Tana kwance cikin falon yaro yayi sallama ya shigo


"Wai mukhtar ke magana a qofar gida" inji yaron,zumbur ta miqe zaune saboda wata
muvuwar faduwar gaba data tsinci kanta a ciki,da sauri ta qule uwar daka sanda taji
muryar inna na sanya hijabinta tare da cewa yaron ya shigo.

           Ta window ta dinga leqensa sanda yake tsugunne gaban innan kansa qasa
yana gaidata,sosai ya mata kyau,mukhtar akwai bala'in kwarjini da kyawun siga,sonsa
da qaunarsa ke dambarwa cikin zuciyarta,gefe guda kuma  wani mashahurin tsoro
fargaba da qin son komawa cikin gidansa ke kai kawo cikin wani irin qarfi cikin
qirjinta,sai ta koma gefan gado ta zauna jiki sanyaye tana fidda qwalla.

          Tana jin shigowarsu cikin falon shi da innar,ta sa baki tayi kiranta,sai
data kirata kusan sau hudu sannan ta samu ta fito,kanta a qasa tana digar
qwalla,gefe ta samu ta takure kanta a qasa ta gaidashi,ya amsa yana dubanta,har
yanzu mamakin da ya daureshi tun farko shi yaqi sakinsa,me ya samu sumayyar?,me
yayi mata ta baro gidansa ba tare da saninsa ba?.

"Ka ganta nan,nima hakanan na ganta da sassafe bansan me ya faru ba,kuma juyin
duniya meke faruwa taqi cewa komai,to gaka nan dai gata" inna ta fada tana dubansu
"Wlh nima inna dawowata ta ras bata nan,amma ki sake tambayarta inna ko wani abu
nayi mata"waiwayawa tayi cikin daurewar fuska dake nuna ba'a son wargi tace
" ke sumayya......dubeni da kyau banason rashin mutunci da iskancim banza,ki gaya
mana me mijnki yayi miki?"cikin muryar kuka tace
"Babu inna,babu abinda yayimin wallahi" cikin hargowa da bacin rai innar ta sake
cewa
"Babu abinda yayi miki don iskanci shine zaki debo qafa ki taho gida,to ki tashi
tun muna shaida juna tun kafin mahaifinki ya dawo sawunki a likkafa ki tattara
kayanki kibi mijinki" wani irin kuja ta fashe da shi tamkar ana cire ranta ba tare
da ta iya cewa komai ba,juyin duniya inna tayi mata ta tashi ta bishi taqi,har duka
ta kai mata amma a banza,ganin hakan ya sanya mukhtar tarar innar yace
"Inna,ki barta,barta kawai,idan malam din ya dawo ko zuwa gobe ne sai na dawo"
bacin rai tsantsa ne cikin ran innan haka mukhtar din ya fita.

          Sake qara sautin kukan nata tayi can qasan zuciyarta na mata zafi,ta rasa
dalilin da ya sanya ta yiwa mijin nata haka,can qarqashin zuciyarta itama son binsa
take,son kebancewa take da shi,tana da buqatarsa,tana buqatar jin duminsa amma
tsanar gidan ya taso ta danne komai.

        Tun innan na jin haushinta da jin haushin kukan nata har abun ya fara bata
tsoro,addu'a ta soma cikin zuciyarta tana fata ba abinda take tunani bane ya afkawa
sumayyan.

             Tunda ya koma gidan ya qulle kansa cikin dakinsa,fa'iza ta sake dawowa


da niyyar bashi taliyar,nacin duniya yaqi bude qofar,da taga haka kuma ta lura bai
dawo da sumayyan ba sai ta watsar da shi tayi komawarta daki tare da kwafar da
taliyar cikin kwandon shara tunda burinta dai ya cika,dama ba wai damuwa tayi da
yunwar cikinsa ba,aikinta dake cikin taliyar take yiwa kuma komai ya tafi dai dai.

          Tun a daren da malam din ya dawo ta zayyane masa komai,shiru yayi cikin
dogon nazari,innar tayi niyyar taso masa sumayyan ya dakatar da ita yace ta barta
zuwa safiya sa hadu.

           Qarfe bakwai da rabi na safe ta shigo dakin malam din sanye da hijabi,ga
mamakinta sai ta tadda su tare da mukhtar,gabansu kayan kari ne wanda malam din ya
gama karyawa kasancewar da wuri yake karyawa ya kuma takura mukhtar wanda shayi
kadai ya iya sha.

          "Sumayya,me ya hadaki da mai gidanki wanda har ya sanyaki fitowa daga


gidanki ba tare da izinin mai gidanki ba?bayan ba haka muka baki tarbiyya ba" Shiru
tayi qwalla na taruwa cikin idanunta ta daga kai ta dubi abba malam din,inna da
zuciya ta hasalota tace
"Tsabar rashin mutunci ne da sakarci kawai ba komai ba" da sauri malam din ya
dakatar da inna ta hanyar daga mata hannu sannan ya sake duban sumayyan
"Uhmmmm,ina jinki" ya fada yana zuba mata idanunsa,motsa bakinta ta shiga yi sai ya
fahimci tamkar bata son yin magana ne saboda haka ya bata qwarin gwiwa
"Kada ki ji tsoron komai kada ki kuma damu,ki gayamin ko ma mene,mu iyayenki ne
baki da kamar mu,baki da wanda zaki gayawa damuwarki sama da mu kinji ko?"kai ta
gyada sannan ta bude bakinta qwalla na ziraro mata
" Abba.......bana son gidan,haushin gidan da d'akina nake ji,tsoron dakin ma nake
ji,bana iya bacci,wani abu kullum sai ya fito ta bango yana kiran suna
na......"shiru ne ya ratsa dakin,kowa da tunaninsa,tausayinta ke yawo cikin ransu.

          Bayan dogon nazari da abba malam yayi sannan ya magantu


"Kin tabbata kina addu'o'inki kuwa?" Shiru ta danyi sannan cikin karyewar murya
tace
"Eh inayi amma wani lokaci ina mantawa bana yi" kai ya jinjina
"Shikenan babu komai,wani lokaci kuna sakaci da addu'a har shaidanu ke samun damar
rabarku su cutar da ku,ba komai ki shirya kibi mai gidanki zan baki qarin wasu
addu'o'in ki hada da na gunki,ki tabbata kin dage da yi babu fashi,insha Allah babu
abinda zai sameki".

           Ga mamakinsu sai ta fashe da kuka kamar wadda ake zarar ranta


" Allah abba malam bazan iya komawa ba,tsoro nake ji abba,don Allah ku
qyaleni"idanu suka zuba mata baki daya,bayan wani lokaci malam ya maida kansa ga
mukhtar ya dafashi
"Kayi haquri mukhtari,ka bar min sumayyah anan,bayan kwana uku kacal kazo ka
dauketa,kayi haquri kuma kada ka damu,ba zata wuce kwana ukun ba" kansa a qasa
cikim girmamawa yace
"To malam,na gode" ya miqe ya fice suka bishi da kallo.

     Inna ce ta soma cewa cikin laushin murya


"Meye hikimar yin hakan din malam?"
"Zaki gani habiba,ku shiga ciki ke da ita sai ki dawo ki dauko kin jakar fatar can
ta cikim uwar dakina"
"To" ta amsa sannan ta miqe ta kama hannun sumayya dake ci gaba da kuka suka koma
ciki.

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍✍✍✍
[9/25, 12:42 AM] +234 908 222 8222: ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

1⃣4⃣

________________________

*A hasiban nasi ay yaquluu amanna wa hum la yuftanun?*


_____________________

*Sadaukarwa ne ga*

*MAMAN HANIF NOVELS GROUP*👌🏽


      Qarfe goma na dare tana saman gadon innar tata,juyi kawai takeyi tare da
tuhuma da kuma bincikar kanta kan abinda ta aikata,batasan dalili ba batasan me
yasa ba amma ji ta dinga yi kamar ana ingizata barin gidan,wata qauna da kewar
mukhtar din suka kamata,halima ce ta shigo dauke da wayar innarsu
"Yaya sumayya,yaya mukhtar ne" ta fada tana miqa mata wayar,da sauri ta miqe ta
amsa wayar sannan ta kara a kunnenta halima ta juya ta fita,kasa cewa komai tayi
har sai da yace
"Sumayyah!" Muryarsa a tausashe
"Na'am" ta amsa muryarta na rawa
"Sumayya......me yasa kike son ki gujemin bayan kinsan zuciyata ba zata juri haka
ba?,sumayya ko cikin mafarki banson mu rabu bare a gaske,a zahiri kuma  idanu biyu"
tuni ta fara tara qwalla a idanunta,zuciyarta na sake karyewa
"Ya mukhtar ban sani ba,nima bansan dalili ba da ya sanya na tsani dakina ba,bansan
dalili ba na tsani dakina ma baki daya ba,kayi haquri ya mukhtar........kaji?"
Shiru yayi yana mamako,babu shakka gaskiya take gaya masa har cikin zuciyarta,ya
riga da yasan sumayyan sosai,koma mene yana jin ya haqura ya bada kwana ukun kamar
yadda malam yace yaci gaba da addu'a kamin zuwan kwanakin,ajiyar zuciya ya sauke
sannan yace
"Shikenan....babu komai kada ki damu kinji,muyi addu'a mu jira kwanakin ukun kamar
yadda malam yace"
"To" ta fada,sai ya kawar da zancan ya soko wani don son faranta mata rai da kawar
da zancan
"Yanzu me zan samu my sumy,nayi kewarki sosai,na dawo da kewar taki kuma tarar kin
min yaji" ya qarashe cikin sigar shagwaba,dariya sosai ya bata har ta dinga jiyo
sautinta ta cikin wayar wanda hakan ya masa dadi sosai,kewarsa taji ya kamata kamar
ta bude idanu ta ganta gabanshi,nan ya janyeta da hira har sai da ya qarar da dukka
kudin dake cikin wayarsa sannan ya haqura.

      Cikin kwanakin duk wani hadi da malam din ya sani na kariya daga shaidanu ya
hada ma sumayyan,suratul baqara itace ruwan shanta,ayatush shifa,da ayoyin karya
sihiri,hadin ganyan magarya,man habbatus sauda shi take shafawa saboda yana kore
duk wani shaidani da zai iya kusantarka,sai turaruka daban daban,azkar na safiya da
maraice da wasu qarin addu'o'in kan wanda takeyi

         Ita kanta cikin jiki da zuciyarta take jin salama da farinciki,dokin ganin
mukhtar da son komawarta dakinta take.

         Ranar kwana na biyun da maraice sai ga abdur rahman,sosai tayi mamakin


ganinsa yace mata yaje gidan bai tadda ta ba,wannan sabuwar abokiyar zaman nata ta
gaya masa bata nan,ta tafi kuma ba zata dawo ba,bata boyewa abdur rahman din komai
ba ta gaya mishi.

         Ya jima yana jinjina kansa sannan yace


"Idan zaki amince ina da buqatar muqullin dakin naki zan duba shi ko da taimakon da
zan iya miki,kinsan fannin magungunan musulunci na karanta,yanzun haka ma yaya
mukhtar din nazo kawowa katin gayyata zuwa bude asibiti da zamu dinga treating
cututtuka da magungunan musulunci" cike da gamsuwa ba tare da haufi ba ta shiga
daki ta miqa masa muqullin ya amsa ya mata sallama ya fice,a qofar gidan ha tsaya
ya fidda wayarsa ya kira mukhtar ya shaida masa,take ya bashi izinin shiga,sai da
yayi sallama sau biyar duka aka masa tare da dora
"Dalla a shigo an cikawa mutane kunne da wata sallama" a tunaninta yaya yahanasu ce
ta mata aike,kai tsaye ya doshi dakin sumayyan ya bude ya shiga.

          Cikin nutsuwa ya dinga nazarin dakin bayan wasu addu'o'i da ya dinga


karantawa a bayyane,fa'iza na tsakar gida kame da qugu tana leqen dakin gabanta na
faduwa,addu'arta daya kada ya zamto ya karya duk wani kafi da shiri da tasa aka
yiwa dakin.

         Tsawon mintina talatin ya kwashe cikin dakin yana karanta wasu ayoyi
sannan ya kulle dakin ya fice,da kallo ta bishi fa'izar kamar idanunta kamar zai
fado,sai da taga fitarsa sannan ta saki ajiyar zuciya tare da zama gefan rijiya.

             Saidai bai wuce wasu mintina talatin din ba sai gashi ya dawo,hannunsa
dauke da kaskon wuta mai garwashi sai qwarya,dakin ya sake budewa ya shiga bayan ya
tari ruwa cikin qwaryan,zama yayi sosai kan daya daga cikin kujerun yayi bismillah
ya fara karanta ayatur ruqya gabaki dayanta,sannan yabi kowanne lungu da saqo na
dakin ya yayyafeshi tas da ruwan,komawa yayi falon ya ajjiye qwaryar ya bude wata
farar leda mai dauke da 'ya'yan habbatus sauda ya watsa cikin dakin ya shiga turare
dakin ciki da falo.

           Kasa daurewa fa'iza tayi ganin sai da ta dangana da bakin qofar dakin
sumayyan ganin hayaqi mai qauri na fitowa daga dakin,gabanta ya fadi tana tunanin
wani qullin ake mata,cike da masifa tace
"Wai malam waye kai ne?,meye haka da zaka shigo gidan mutane kana wasu qananun
surkulle,bana ciki da rainin hankali da iskanci zo ka fice mim daga gida tun ban
tara maka mutane ba".

          Dago idanunsa yayi ya watsa mata,take wani kwarjininsa ya daureta,jikinta


yayi laqwas bakinta ya mutu,duk tijarar da taso yi ta koma ciki,kafeta yayi da
idanu har ta saki qofar labulen ta koma dakinta,zama tayi bakin gadonta tana
ta'ajjubin wanne irin mutum ne wannan yaron?,tana zaune nan har ya kammala ya kulle
dakin ya fice.

           Gidan ya koma ya riski sallar magariba tare da malam sannan daga bisani
ya nemi kebewa da shi,cikin falonsa dake zauren gidan suka shiga,bayan sun sake
gaisawa abdur rahman din ya gabatarwa da malam maganar sannan ya dora
" a abinda na fuskanta malam ba qaramin mugun nufi aka nufi sumayya da shi
ba,saidai koma mene Allah ya taqaita darajar addu'a ya rage kaifin QADDARAR
TATA,naje gidan kuma na aiwatar daga cikin abinda Allah ya horemin na sani kan irin
wadan nan mashaakilat din,kuma in sha Allahu komai yazo qarshe babu abinda zai sake
samunta da izinin Allah"gyara zamansa malam din yayi sannan yace
"Hakane,tunaninmu yazo daya abdur rahman,mun gide qwarai da gaske daka nuna
kulawarka kan lamarin,Allah yayi albarka,kuma in sha Allahu zamu ci gaba da
addu'ar,Allah ya tsare gaba"
"Amin amin malam" ya amsa a ladabce sannan daga bisani sukayi sallama ya bawa malam
muqullin dakin shi ya wuce.

           Qarfe takwas na dare suna tafe kan babur dinsa bayan ya daukota,wani
farinciki ke ratsa zukatansu,jinsa yake tamkar wani sabon aure.

            Murtala suya spot ya zarce ya siya musu kaza da damammiyar fura sannan
suka qarasa gida.

             A tsakar gida suka taddata tana ta faman safa da marwa,tunda ya sheqa


wanka ya fice da magariba ta kasa samun sukuni,far gabarta qara daduwa take duk
bayan wata daqiqa,qofar gida kuwa ta leqata yafi sau a qirga tana addu'ar ganinsa
ya dawo shi kadai,sallama sumayyan tayi hannunta dauke da leda kanta tsaye ta doshi
dakinta,sai da ta tsaya bakin qofar dakin tayi addu'a sosai sannan ta shiga,cikin
ikon Allah abinda ta zaci zata ji bata jishi ba,dakin gadonta ta wuce ranta qal
tamkar babu wani abu da ya taba faruwa da ita,tabbas babu shakka addu'a takobin
mumini ce.

            Sai da ya kulle gidan sannan ya tako zuwa tsakar gidan,ya ganta amma ya
dauke kai tamkar bai ganta ba yana shirim wucewa,sam har yau ya kasa sonta,ya kasa
jinta a jikinsa ko zuciyarsa ko da qanqani je,baisan dalili ba kwata kwata ya
tsaneta bata burgeshi.

           Ganin da gaske wucetan zaiyi ga wani dan banzan kishi na sakadarta ya


sanya ta saurin shan gabansa
"Wai me kake nufi ne?,wallahi babu inda zaka,daga dawowarta yau shine saboda
rashinvadalci zaka debi kwana ka kai maga,ai sai ka bari sai gobe ko" wani banzan
kallo ya jefeta da shi,yau din cikin farinciki yake kuma baya buqatar abinda zai
tarwatsa masa farincikin da yake sa ran samu a yau,cikin kakkausar murya yace
"Ki matsa daga gabana,umarni ne ba shawara ba" ya fada a tsawace,taji tsoro amma
taurin kai ya sanya ta shanye,ta bude baki zata sake magana ya sanya hannu ya
janyeta gefe daya ya wancakalar yayi wucewarsa.

             Wani kukan baqinciki da takaici ta saka,wankin hula na neman kaita


dare,duka magungunan da yaya yahanasu ta amshi kudadenta ta kawo mata tana zuzuta
mata aikinsu sam ba haka ta gani ba,haka kawai sun hadata da diyar malamai tana ta
faman wahala da ita,wahalar ma ya banza,eh ta banza mana tunda ko hankalin mukhtr
din ma da akeyi don shi har yau ta kasa janyoshi gareta,kullum kwanan duniya
kamarvsake sabunta qaunar sumayyan ake cikin ruhinsa ba qoqarin fidda ta cikin
zuciyarsa ba?,abu goma da ashirin kenan,sam wallahi ba zata sabu ba bindiga a ruwa.

           A fusace ta shiga dakinta ta lalubi wayarta,lambar yaya yahanasu ta kira


da niyyar yi mata wankin babban bargo saidai kash ta daki gurbi wayar tata a kashe
take,da sauri ta sauya akalar kiran nata zuwa ga fadima,cikin sa'a ta sameta,tun
kafin fadiman tace wani abu fa'iza ta soma sauke mata kwandon rashin mutunci,zagi
na tsamar nama ta dinga luluqa mata tare da laqaba musu sunan macuta,sai da ta
tabbatar ta rage farashin baqincikin da take ciki sannan ta datse layin tana huci
tare da cin alwashin gobe har gida zata yi tattaki taje ga yahanasun ayita ta
qare,don ba zata dauki asara ba sai ta biyata kudinta,tunda ai ba ita daya ke da
buri ba suma suna da buri don me zasu dinga cutarta suna wankarta ana amfani da
kudinta kadai?.

             Kwanan baqinciki tayi tare da kusan qarar da daren nata wajen zirga
zirga tsakanin dakinta da window din sumayya,su kam suna ca wata duniya basu san ma
me takeyi ba,kwanan farinciki qauna bege da faranta ran juna sukayi,yayin da tayi
kwanan gadi da safa da marwar da babu lada.

*tabbas duk wanda ya saki Allah yana tare da tarin wahala maras qarewa*

_wannan kenan muje zuwa masu karatu,har yanzu da sauran qaddarori wa sumayyan taku_

*zuku ji shiru gobe in sha Allah sakamakon uzirin dake gareni,idan kuma ya samu to
amma kada ku sanya rai,na gode.*

*mrs muhammad ce*

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍✍✍✍
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

1⃣5⃣
___________________________

*Bismillahir rahmanir rahim*

*wama tadri nafsun maza taksibu gada*


_____________________

           Kwanaki biyun da yayi a dakin sumayyan shi kansa ji yake ya zama tamkar
ango,zuciyoyin su fes,duk wani buduri da fa'izan keyi basu san da shi ba,soyayyarsu
kawai ta ishesu rayuwa.

            Cikin kwanakin da suka biyo baya damina ta shigo,wanda hakan shi yayi
sanadiyyar zubewar ginin maqotan yaya yahanasu ya fadowa gidansu har ya janyo
rushewar wani bangare na gidan,hakan ya sanya mukhtar yace su baro gidansh su dawo
gidansa don a samu sararin gyaran gidan nasu,ko bayan rasuwar mai gidan anty
yahanasu kusan shine jigo dake d'awainiya wa su yaya yahanasun.

           Qarfe biyu na azahar suka iso gidan tare da yaranta biyu jamila da
sayyada,sumayya na tsakar gida a lokacin tana wankin kayanta,da fara'arta ta taso
tana musu sannu da zuwa tare da qoqarin karbar jakar hannun yaya yahansun bayan
yara sun gama shigewa da sauran kayayyakin nasu d'akin fa'iza,kaucewa tayi gami da
jifanta sa wani kallo tana fadin
"Kada ki kuskura ki taba min jaka,matsa da Allah ki bawa mutane guri" ta fada tana
wuceta sauran yaran suka mara mata baya,a salube ta koma kan wankinta taci gaba da
yi har ta kammala tana jiyo shewarsu cikin dakin fa'izan kai kace yaya yahanasun
sa'arta ce,ya tabbatar cewa da ita ke shewa haka da yaya yahanasun sai ace bata da
mutunci bata da kunya,amma ga fa'iza na faman shewa da qyaqyatawa gabanta,matar da
ko sau daya sumayyan bata iya hada idanu da ita,biyayya take mata tamkar uwar
mijinta haka ta dauketa sakamakon ganin irin girman matsayin da take da shi gun
mukhtar.

          Tana kammala shanya kayan ta shige wanka saboda tana so taje kitso
sakamakon ita ke da girki gobe,har ta fito ta gama shiryawa ko alamun dora abinci
babu gun fa'iza,itama bata damu ba sai ta hada shayi kawai ta sha tayi ficewarta ta
barsu.

             Qarfe biyar ta dawo gidan saboda layi da ta taras a gidan kitson,tun


daga qofar gida ta soma jin muryar fa'iza cikin balbalin bala'i,ta kutsa kai cikin
gidan cikin mamakin ita da wa,dai dai lokacin da fa'izar ke fadin
"Yo da kika damen da zancan ciki laifin uban waye mayun 'ya'ya?,qanin naki yayi min
cikin mana ya gani idan ban dauka ba,wata uwar yake yimin idan kwana na ne banda
kwanciya da zaki uzzura min,to wallahi babu ma mai kwanarmin cikin daki balle ya
sanya min ido,dama daki ba daki ba ya zuciyar talaka,sai ku nemi gun kwana" ta fada
tana komawa cikin dakin tare da banko labulenta.

           Idanu sumayya tabi tsakar gidan nasu da shi,ko ina kaya ne na yaya
yahanasun a barbaje a qasa,gaban sumayyan ya fadi,jikinta yayi sanyi,ta qarasa
tsakar gidan,hannu ta sanya tana tattare kayan nasu waje daya,tsawa yaya yahanasun
ta daka mata
"Kada ki sake taba mana kaya shegiya munafuka 'yar gidan malamai,to wallahi bari na
gaya miki idan ma shiga tsakaninmu kikayi da fa'iza kinyi kadan,hakan da takeyi
bazai tunzura zuciyata tunda nasan ba cikin hayyacinta take ba,ke sayyada maza ku
hade mana kayan gefe guda mu jira shi muntarin ya dawo" sororo tayi tana dubanta
"Daina kallo na mayya,li'ilafi quraishi,ni baki isa ki cinyeni ba" sai ta kauda kai
ta wuce kai tsaye dakinta ta bude ta shige.

            Bata sake fitowa yayi zamanta cikin dakin,sai ta qirqiro wasu 'yan
qananun ayyaukan ma cikin dakin nata don kawar da duk wani tunani da zai
dameta,tana aikin tana ambatar hasbunallahu wa ni'imal wakil,allahumk finihim bima
shi'ita,hakan ba qaramin taimaka mata yayi ba,sai ya tafiyar da lokacinta cikin
sauqi har aka kira sallar magariba,ta miqe ta fito domin daura alwala,suna zaune
gefe daya na tsakar gidan da qullin kayansu,sosai har cikin zuciyarta taji babu
dadi,bai kamata mukhyar yazo ya taras da su haka ba,ko babu komai 'yan uwansa ne
jininsa ne,kuma tayi imami cewa idan wani nata ne shima mukhtar din ba zaya
wofantar da su haka ba,ta danne zuciyarta ta qarasa gurinsu,cikim sanyin murya tace
"Don Allah yaya ki shigi dakina,ko da ba zaki zauna din ba ki shigo idan yaso idan
ya mukhtar din ya dawo sai asan yadda za'ayi din" wani kallon banza ta bita da shi
"Ke wallahi ki fita a idona,wai ke wacce iriyar mayatacciya ce ne,nace bazan shiga
ba dole ne,to bari kiji,idan ma wani laqani aka baki na sai na shiga sannan zaki
samu galaba a kaina to wallahi ki gayawa malaminki kunyi qarya kun kwana da yunwa"
jikinta sai yayi sanyi ta kasa tafiya,zuciyarta na gaya mata basu zama masu
kyautawa mukhtar ba indai yazo ya tadda jininsa a wulaqance,duk da tarin izgilu cin
fuska da cin mutunci da ita yaya yahanasun ke jifanta da shi,ba ita take dubawa
karamcin mukhtar take dubawa.

          A haka mukhtar din ya shigo ya riskesu,tayi masa sannu da zuwa ta karbar


kayan hannunsa duk da ba ranar girkinta bane,ya amsa yana duban yaya
yahanasu."a'ah,yaya yanzu kuka zone na ganku a nan a zaune ku da kayanku"kai ta
girgiza
"Inaaa,ai tun azahar muna gidan nan" cikin mamaki ya dubeta tare da zaro ido sai ya
dubi sumayya yana jifanta da tuhuma,qas tayi da kanta don bata da ta cewa,ganin
haka yasa ya dubi yaya yahanasun
"Amma kuke zaune a nan?,kada kice min nan kuka wuni?" Waiwayawa tayi ta dubi
sumayya
"Sai ki bamu guri ko ko ban isa ba?" Bata ce uffan ba ta koma dakinta duk da alwala
ta fito da niyyar daurawa.

               Sai da taga shigarta dakin sannan ta maido dubanta ga fa'iza


"Mutuniyar tamu,wallhi lafiya lau ta karbemu,daga yi mata tambaya kan naji shiru
har yanzu mun samu qaruwa ko a'ah ta shiga masifa ta inda take shiga ba ta nan take
fita ba,qarshe tayo mana waje da kayanmu" sosai ransa ya baci,ya soma huci cikin
fushi yace
"Fa'izar?,to da tayi muku haka gidanta ne ko nawa?,bazan lamunci wannan iskanci ba"
ya fada yana juyawa zuwa ga dakinta wanda fa'izar na ciki tana jin kowa tayi lakur
abinta.

         Da sauri yaya yahanasun ta dakatar da shi


"Kaga muntari bana son hauka fa,laifi muka yi mata mu mika bata mata rai,nasan kuma
zata huce,don haka bance kaje ka sake bata mata rai ba,kadai lallabata har ta yarda
mu zauna taren" jagale yayi tare da juyiwa yana duban yayar tasa,take kuma ya tuna
sunfi kusa fa ita da fa'izan,ya ma kamata a yau din ya qyaleta taga halin fa'izan
taga wace ita ra'ayil ain wato ganin ido,saboda haka sai ya saki murmushi cikin
salon canza shawarar da yayi farat daya,gyada kai yayi
"Shikenan,muje to a lallabatan" da sauri suka miqe yaya yahanasun tana cewa
"To,to ai kaga hakan yafi" tabi bayansa.

          Tana miqe daga kan gadonta tana taunar chewing gum dai dai,zama sukayi
kan kujerarta dake fuskantar gadon,yayin da mukhtar ya qarasa gefan gadon ya
tsaya,duk da cewa ransa a matuqar bace yake,ji yake kamar ya janyo fa'izan ya yi
mata dan banzan duka ya watsar amma sai ya dake
"Fa'iza,me yasa ba zaki bar yaya ta zauna dakinki ba,ai ina ganin bai kamata ba"
hura hanci take tana tunanin ko yanzu mukhtar ya soma tsoronta,inko haka ne kowa
tasa ta qare,tabbas sai kowa ma yaci ubansa cikin gidan
"Mukhtar banga dama bane,bari kaji" ta fada tana miqewa zaune kan gadon
"Na farko bansan sa ido gaskiya kuma na fuskanci su sun fara koyar wannan
halayyar,na biyu na fuskanci ni aka rainawa wayo,ga mai daki ciki da falo can ba'a
dosheta ba saini mai daki daya kamar zuciyar talaka" ba qaramin dukansa maganar
tayi a zuciya ba amma ya hadiye don so yake ya jata aje gun ta dora da
"Saboda haka su nemi gurin kwana don ni bazan zauna da wadan nan qattan a daki na
ba" wani qullutun abu ne ya tokare masa wuya qanda ya hanashi sake magana,sai yaya
yahanasu da tace
"Haba ke kuwa fa'iza,kwana nawa ne duka duka mun koma gidanmu,ai ban zaci ko wani
na turo gidan nan ki masa sauki a dakinki ba zaki kasa,kada fa ki manta nice silar
zuwanki gidan nan" zabura tayi tana dakatar da ita
"Kinga kada ki sake kice zaki mun gori,don ke kika kawoni gidan ai bake kike aure
na ba,buqatar maje haji sallah kuma da taku buqatar ai ba haka siddan kika kawoni
ba,sabida haka kuje ni don Allah kada ku cikan kunne,tunda kun nace sai kun zauna a
dakin kuje zanyi tunani,ko kwana daya ne kuyi kafin ku koma inda kuka fito".

         Ba qaramin daurewa kan yaya yahanasun yayi ba da kalaman fa'iza,duk yadda


fadima ke gaya mata sai yau ta sake tabbatarwa da lamba daya ce ita wajen rashin
mutunci tsiya da tsiyataku
" fa'iza ni kike gayawa haka"kanga tsaye babu kunya tace
"Na fada din,ke kike aurena ne nace wai kawai da zaki takuran,wannan fa kamar kina
lissafin sau nawa nake kwanciya da mijina ne"tuni maganar ta sake dora yaya
yahanasun kan dokin zuciya
" ke qaramar mara kunya,ko bani nake aurenki ba kinsan ina da power din da zan sa
ungulu ta koma gidanta na tsamiya ko?"
"Bismillah,sai mu gani " ta fada tana murguda baki gami da turo daurinta gaban
goshinta ta dage kanta idanunta na kallon ceiling din daki.

          tabbas tana jin yau idan bata nunawa fa'iza isar da take da ita a wajen
mukhtar ba bata huce takaici ba,idanunta taf da bacin rai ta dubeshi
"Mukhtar,ina so a yau yau din nan ka sawwaqewa fa'iza,yanzun nan" ta qarashe cikin
daga murya.

        Duk da cewa ranshi ya kai qololuwa wajen baci kan abinda fa'izq ta yiwa
yaya yahanasun amma sai ya danne komai tamkar bai b'aci ba,ai dama duk wanda ya sai
rariya yasan zata zub da ruwa,to ya kamata yaya yahanasun taga yadda tata rariyar
ke zubar da nata ruwan,ruwan kuma da baiyi qasa a gwiwar malalowa ya jiqata sharkaf
ba,kai ya kada sannan yace
"Kan me zan saki fa'iza yaya,ni babu abinda ta yimin,hasalima fa'iza ai zabinki
ce,kinga bai kamaci na wofantar da ita ba,zan riqeta hannu bibbiyu kamar yadda kika
umarceni" tsawa ta daka masa
"Mukhtar,kai makaho ne?,ko kuwa kai kurma ne,baka ganin abinda ta yimin ne,ni na
umarceka nace ka saketa kamar yadda na umarceka ka aureta a baya" kai ya sake
kadawa tare da yin tattaki don barin dakin yana cewa
"Ki gafarceni yaya,amma yanzu na fara zama da fa'iza,don ni bata aikata min komai
ba" sai ya fice abinsa ya barsu ana kallon kallo.

             Kira ya qwalawa sajida ya sanyata suka dinga jidar kayayyakinsu yana


tayasu suna kaiwa dakin sumayya wadda ke zaune kurum tana ji da ganin sarautar
Allah,sai da suka kammala tsaf yaya yahansun na dakin fa'iza suna cecekuce,ganin
abun na sake qamari ya sanyashi shiga dakin ya janyeta yana fadin
"Kiyi haquri yaya yahanasu,kizo ku zauna dakin sumayya tunda itan da kuke so ta
qiya" sai ta waiwayo ta bishi da ido galala tana kallonsa,mukhtar din da baison
bacin ranta?,mukhtar din da baiso a tabata amma yau an mata cin kashin data jima
rabon ta da irinsa amma ya kasa cewa uffan,kardai mallaka fa'iza tayi masa wadda
baya iya qetare umarninta?,ranta ya shiga suya ta shiga fatar cewa Allah yasa ba
haka bane,bata da wani zabi a yanzun illa ta bishi,idan yaso daga bisani tayi
tunanin mafita a tsanake.

            Bayan sun shiga dakin ta zauna sannan ya kira sumayya ya fice zuwa
dakinsa.

           Zaune ta tadda shi dafe da kansa,a hankali cikin kasala ta zauna


gefansa,ta sanya tafin hannunta tana shafar bayansa a hankali,tasan fushin mukhtar
din,saboda haka ta tabbatar ransa na a bace ne,kusan minti goma baice komai ba
kafin daga bisani ya dago ya dubeta
"Sumayya" ya kira sunanta,a tausashe ta amsa sannan ya dora
"Gasu yaya yahanasu nan zasu zauna dakinki,kinsanta sarai ita da yaranta baki
daya,baki buqatar muraja'a kansu,na shaideki da haquri wannan halinki ne,to amma
don Allah ki nunka haqurinki,baqunta zasu mana na wani d'an lokaci,insha Allah
zanyi qoqari na kammala musu gyaransu cikin qanqanin lokaci,idan da na kammala ma
gini na sabon gida na can zan ara musu su zauna gudun fitina,kiyi haquri da su don
Allah ki sake ninka kawaicinki" kai ta girgiza
"Haba ya mukhtar,ai ba roqona zaka yi ba,umarni kadai zaka bada,da kai da kaya ai
duka mallakar wuya ne,nima yaya take agurina,insha Allahu babu wata matsala ko
damuwa"
"Na gode,Allah yayi miki albarka"
"Amin yaya" ta fada tana sakin qayataccen murmushinta wanda har sai da ya sanyashi
tsura mata idanu,hannu ta turo sautin idanunsa kamar zata tsone masa yaja baya suka
saki dariya baki dayansu.

             Cikin dakin ya barta ya fita sallah,kasancewar tana faashin sallah


sa'an nan kuma dakin nasa na hargitse don fa'iza ba kasafai take tsayawa ta gyara
ba ya sanyata tsayawa tana dan kakkabe dakin haka ya dawo ya cimmata,kafin ya kai
ga zama fa'iza ta fado dakin hannunta riqe a qugunta,shi ya fara cewa
"Me aka girka" ran nan nashi a hade tsaf wanda ita a nata zaton aikin da take kansa
ya fara tasiri,saboda haka kanga tsaye tace
"Yau duka ma banyi girki ba wlh a gajiye nake" ta fada tana yatsina,sam ya tsaneta
har yau ya kasa jinta dai dai da qwayar zarra cikin zuciyarsa,bata dameshi ba dama
bisa lalura kawai yaje rabarta,qoqarin adalci ne kawai irin nasa tunda ta riga da
ta rataya a wuyansa bisa alfarmar igiyoyinta uku dake hannunsa.

            Hannu ya miqa mata a daqile yace


"Bani muqullan locker din kayan abinci na" ba musu ta fice don dauko masa,ya juya
ya dubi sumayya
"Yau ba'ayi girki ba gida na,me kuka bawa yaya taci ita da iyalanta?" Kanta ta
duqar qasa sannan tace
"Ka mance na tambayeka zani kitso?,tunda na fita ban samu na dawo ba sai bayan
la'asar,dana shigo kuma nima yadda ka taddasu haka na taddasu" kai ya gyada ba tare
da yace komai ba,ta dawo da muqullin ta miqa masa,kai tsaye ya danqa su ga sumayya
"Jeki ka samar mana da abinda zamuci" hannu biyu tasa ta amsa kana ta danyi jim,da
kamar taqi abinda ya sata din,sai kuma taga hakan bai dace ba,idan bai isa da
fa'iza ba ita ai ya isa da ita,miqewa tayi zata fice fa'iza ta saki wani mugun
murmushi,ga zatonta sumayya ta shiga cakwakiya mukhtar zai soma azabtar da ita
kenan,fadawa tayi saman katifar kusa da shi tana fadin
"Ammmmm......idan kin gama kizo na gaya miki me mi kuma zaki dafamin" wannan karo
kasa hadiye takaicinsa yayi sai da juyo yace
"Da yake baiwar gidan ubanki ce ko,wato saboda kinga na miki shiru ne
ko......hmmmmm.....ki kiyayi ranar qin dillanci wallahi,wuce kije sumayya",sai ta
juya ta fice din,itakam ta ma rasa na cewa gaba daya,gaban fa'iza ya fadi,kaddai
jiya i yau ne dai mukhtar din,sai ta kasa hadiye qanin zagin da yayi mata ta miqe
tsaye
" wacce rana ce ranar qin dillanci,ba ranar da hajar mai gari ta bata ba?,idan ba'a
ganta a gun fa'iza sai me?"ta murguda baki tana niyyar ficewa,zuciya ce ta ciyoshi
ya miqe cikin zafin nama ya fincikota ya zabga mata wani lafiyayyen mari,a gigice
ta dafe kuncinta don bata zaci haka ba,karo na farko da mukhtar din ya soma taba
lafiyarta,ashar ta danna sannan tace
"Ni ka mara muntari,kayyasa kace yau da bala'i,wallahi baka daki bulus ba sai na
rama" .

           Daga hannunta tayi da niyyar kaiwa fuskarsa mari ya cafe hannun tare da
murdeshi har sai ta qashin hannun ya bada wani qasss da alamu ya targadata,tsananin
azaba ya sanyata sakin qara wadda ta sanya sumayya dake kitchen barin abinda take
ta taho dakin cikin hanzari,dadin da taji data lura su yaya yahanasun da suka qure
kallo cikin t.v dinta basu san me ake ciki ba,tun fara masa rashin kunyar duk cikin
kunnenta ne saboda muryar fa'izan na sama ne sosai.

             Sanda ta isa dakin ya daga hannu da niyyar sake bata wani marin,cikin
hanzari ta shiga tsakiyarsu taba riqe hannunsa,cikin taushi ta langabar da kanta
tana duban tsakiyar idonsa wanda hakan shi ya karya lagonsa,ya zare hannunaa daga
nata,bakinta bai mutu ba sai data wurga masa kalmar
"Wallahi wallahi sai kayi dana sanin dukan fa'iza,sai ka biya farashin duka na da
kayi,zaka gani,ke kuma ku zuba mu gani" sannan ta fice.

         Tabbas ba don har tanzu bai cimma qudirinsa ba akanta da yau babu abinda
zai hanata kwana cikin gidan ubanta,gefensa ta zauna ta sanya hannunta cikin nashi
sannnan tace
"Sam hakan ba girmanka bane ya mukhtar,tunda nake ban taba gani ka daki wani ba ma
bare matarka ta aure,yin hakan ba daidai bane,na roqeka don Allah kada ka sake sai
ka fara bani tsoro ai" ta qarasa fada a shagwabe,sai ya dago yana dubanta da
murmushi,take kaso saba'in cikin dari na bacin ransa ya zabge ga fadi sai ya dora
hannunsa shima saman nata
"Banaso ki fara jin tsoro na sumy ta,idan kika fara tsoro na na zauna da wa?,bazan
sake ba,kiyi haquri" kai ta girgiza tana murmushi
"Kai ya kamata nace kayi haquri yaya ka yafe mana,yau mun sanyaka cikin bacin rai"
kasa magana yayi sai ua rungumeta kawai cikin jikinsa yana jin duminya,yana ganin
girma da qimar wannan halitta mau tsananin hankali da biyayya a gareshi,shikam mai
zai hana shi faranta nata matuqar yana da iko?,me ya isa ya hanashi sonta a
duniya?,babu shi,babu shi ko mene,koda QADDARA ce baijin tana da wannan qarfin
ikon,baya fata ma QADDARAR tazo masa ta wannan sigar,gwara ta kowacce siga amma
banda wannan,wala'alla ya iya jurewa.

          Sai da suka fara jiyo qaurin girkinta sannan ya saketa ta miqe da hanzari
ta fice tana ce masa tana zuwa.

*mrs muhammad ce*


📚📚📚📚✍✍✍✍
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

1⃣7⃣

________________________
*Bismillahir rahmanir rahim*

*ma asaba min musibatun fil'ardi wala fi anfusikum illa fi kitabim min qabli an
nabra'aha*
_______________________

             Cikin mintuna qalilan ta kammala jallope din taliyar ta rarraba cikin


coolers,mukhtar din ta fara kaiwa,tana niyyar juyawa ta fita yace da ita
"Wannan cooler din fa na waye?" Ta dubi cooler din sannan ta dubeshi
"Na fa'ixa ne a ciki"
"Ajjiye a nan" ya fada yana gwada mata inda zata ajjiye din da idonsa,bata kawo
komai cikin ranta ba ta ajjiye din ta nufi dakinta.

            Can ta taddasu sun baje suna kallo,duk da cewa kallo daya zaka yiwa
yahanasun kasan tabbas har yau ranta a bace yake,ta dire cooler din tana cewa
"Ga abincinku yaya" wani banzan kallo ta watsa mata
"Eh zamu ci ai kuma zamu ambaci sunan Allah,in sha Allahu babu abinda zai
samemu,makira,idan ma shiga kika tsakaninmu da fa'iza har take wannan tashan rashin
kunyan to ni zanyi maganinku ke da iyan baki daya" kai ta kada ba tare da tace
komai ba ta shige uwar dakinta,ta tube kayanta ta sauya na bacci,sai tayi zamanta
gefan gado ta janyo RIYADUL JANNAH littafin addu'o'inta da malam ya bata wanda bata
rabi da shi ta soma duba wasu shafuka.

          Sumayyan na fita ya dauki cooler din baki daya ya fita da ita waje,wasu
almajirai da rabonsu ya rantse ya samu qofar gida zazzaune ya basu,take suka karba
suka rabe a tsakaninsu suna zabga godiya banza ta faadi garesu.

             Yana kammala rufe gidan sukayi karo da fa'iza wadda ta dawo daga dakin
sumayya ta bankade labulenta ko kallo su ya yahanasu basu isheta ba ta qwallawa
sumayya tambayar ina abincinta,tana daga cikin dakin ta gaya mata yana gun yaya
mukhtar.

          Dubansa tayi"ina abinci na?"banza ya bawa ajiyarta yayi wucewarsa,sai ta


bishi da kallo,bata haqura ba tabi bayansa tana sake tambayarsa,wani wawan birki
yaci wanda sai da ya sanyata ja da baya
"Baki daku ba kenan ko?,tare muka hada muka siyo abincin?,ko kinzo da bayi ne daga
gidanku?,uban wani ne ya hanaki dafawa kici,ki fice min daga nan tun kafin na
hasala na sake kikkifa miki mari" tana qunquni ta juya ta fice ranta qunci fal,ga
uwar yunwar dake sakadarta,abinka da mutum mai shegen ci ta riga da ta saba.

            A tsakar gida taci karo da jamila na wanke hannunta,da gayya ta


bangajeta tayi taga taga ta fadi,sai ta miqe kuwa ta lailayawa fa'izar ashar abinka
da itama tana ji da tata rashin kunyar,ai kuwa fa'izan tayo kanta zata huce bisa
kan nata,dai dai sanda yaya yahanasu ta qaraso tayi hanzarin riqeta ta gabza mata
mari dama tana ciki da ita ne,tana waiwayowa kuwa ta cakumi wuyan yaya yahanasun
take jamila ta shigarwa uwarta nan fada ya kaure tsakanin su ukun.

           Sumayya ce ta fara fitowa,cikin tashin hankali taje dubansu idanunta a


waje,dambe da yaya yahanasu?,tab,lallai fa'iza ta kai,dakin mukhtar ta nufa da
hanzari tana mamakin me ya hanashi fitowa,ga mamakinta yana tsaye bakin window yana
kallonsu,saidai idanun nan sun kada sunyi jazur,a hankali ya juyo ya zuba mata
su,itama sai jikinta yayi sanyi,tausayinta ya kamashi,babu shakka wata jarrabawa ce
ta fado rayuwarsu,idanunta suka cika taf da qwalla ta tausayin mijin nata,sai kawai
ya saki labulen ya taka a hankali ya fita tsakar gidan,wata gigitacciyar tsawa ya
sakarwa fa'iza dake tsakiyarsu tana cin na jaki wadda tsawar sai data sanya hanjin
sumayya hadewa ya cure guri guda,ta runtse idanunta tana jin ruguginta na ratsa
kunnanta.

         Nuni kawai ya yiwa fa'iza da hanyar dakinta yana mata wani irin kallo mai
cike da tsana,ba musu ta wuce jikinta na rawa,ya juya ya dubi yaya yahanasu sai
kawai ya kamata yayi dakin sumayya da ita.

          Bakin rijiya ta zauna,sai ta kasa daurewa idanunta ya shiga fidda


qwalla,wannan wacce iriyar masifa ce lokaci guda,duk wani farinciki da zaman lafiya
na gidansu yayi qaura lokaci daya?,tana share hawayen idanunta tana tausayin
mukhtar dinta.

           Tana zaune a nan mukhtar din ya fito ya shige dakin fa'iza,a nan ne ta
jiyo tashin muryarsa saidai nan din ma bata ji duka abinda yake fadi ba,daga bisani
ne ya fito,ta miqe tsaye ta isa gabansa tana kallonsa,tabbas taso ace yau ranar
girkinta ne,ta lallashi mukhtar din,saidai sam bata da wannan damar,karyar da kai
tayi murya a tausashe tace
"Kayi haquri don Allah yaya mukhtat,komai na duniya mai wucewa ne,jarrabawa ce daga
Allah" murmushin qarfin hali ya saki ya shafi gefan fuskarta
"Babu komai my sumy,kije ki kwanta,kuma ban lamunce ki sanya abun cikin ranki ba,ki
kwanta kiyi bacci sosai" ya sanya bakinsa yayi kissing  goshinta,sai ya bata kunya
har ta dan murmusa,yana tsaye har ta wuce dakinta sannan ya juya nashi.

           Ko da ta isa dakin tuni ta taras da su sun rarrashe kan gadonta,sai yaya


yahanasu dake zaune gefan gadon tana huci,abinda take da buqata ta dauka zata fice
taji sakin qwafar da yaya yahanasu tayi,ranar kan doguwar kujerar falo ta
kwana,saidai tayi qoqari kamar yadda mukhtar ya buqace ta tayi bacci ta qoqarta
tayi na 'yan awowi.

*******************

        Cikin kwanakin gaba daya mukhtar ya fita harkar fa'izan duk da cewa daman
can ba shiga yake yi ba,saidai duk wani abu da yake haqqinta ne kansa yana sauke
mata bakin gwargwado.

           Zaman yaya yahanasu a gidan ya dauki sabon salo,wani irin zama ake a
gidan,sosai yaya yahanasun kejin haushin fa'izan gami da ganin baikenta tun farko
data daure gindin dan uwanta ya zama miji gareta,sai dai kuma duk da wannan bai
hanata jin haushin sumayya ba,gani taje tamkar itace ta shiga tsakaninsu.

          Duk kwanan duniya gari na wayewa da zarar mukhtar din ya sanya qafa ya
fice itama fa'izan ke ficewa,ba zata dawo ba sai yaba gab da dawowa koda kuwa
ranakun girkinta ne,sai a sannan zata tsiri girkin dare shima tsoron hukuncin
mukhtar din ya hau kanta take,ba qaramin horata yayi ba lokacin da ya amshi
maqullin locker din abincinsa daga hannunta ba,da rana kuwa saidai kowa tashi ta
fishsheshi,shiga su jamila suke kitchen kansu tsaye su girka duk abinda suka ga
dama,su din ma ba baya bane wajen iya barnar abinci da ta'adi,sam ko sau daya
sumayyan bata taba daga kai ta dubesu ba bare ta gwadawa mukhtar abinda sukeyi
cikin gidan,dakinta kam tuni ta sallama musu shi,ta dauke kai baki daya da shi
saboda yadda suke abinda suka ga dama cikinsa,wani abun da gayya da gadara suke
mata,koda bata tankasu ba sukan bude baki suce "kayan dakin da kudin dan uwansu aka
sauya su" sau tari dariya abun yake bata,ta kuma godewa Allah da ya sanya iyayenta
masu rufin asiri da zuciyar yiwa iyalinsu ne,suma sun san da haka,babu shakka da
Allah kadai ne yasan halin da zata tsinci kanta ciki,hatta da kayan sawarta sai
suka fara dauka dai dai da dai dai suna sanyawa idan zasu fita wata unguwa ko
biki,ranar da mukhtar ya soma gani ransa ya baci matuqa,bai iya jurewa ba sai da ya
kirasu ya musu jan kunne.

            Ganin haka ya sanya mukhtar yace ta debe duk wani abu nata mai amfani
ta dawo da shi dakinsa,ya bude ma'ajiyarsa ya adana mata ciki.

            Fa'iza kuwa tsakaninsu da yaya yahanasun da yaran ma baki daya sai


harare harare da baqar magana,wanda yawanci ma sunfi yi da jamilan ko sayyada,bata
san me mukhtar ya gaya musu ba amma da alama shi ya kawo wannan dan qaramin sauyin
da aka samu.

          Cikin wata d'aya kacal mukhtar ya kammala musu gyaran suka tattara suka
koma nasu gidan,ko a ranar da zasu tafi din ma sai da ka kusa kwata ta ranar da
suka zo din,da zagi suka rabu,ba qaramin qona ran yaya yahanasun abun yayi ba ganin
mukhtar din ya gaza daukar kowanne irin mataki,abinda bata sani ba shine ya fita
jin takaicin abinda ke faruwar,saidai ya riga da ya tsarama ransa sai sun gama
d'aukar darasin rayuwa tukunna.

*********************

           Qarfe takwas na dare ya iso gida tun bayan fitar da yayi da safe
sakamakon aiki da suke a shagon sa na kasuwa,sosai yake a gajiye tiqis,saidai yasan
cewa abu mafi muhimmanci shine ya adana gajiyarsa,matuqar fa'iza ke da girki babu
wani abu da yake iya tsinta ko ya dorar a wunin ranar baki daya,qarin gajiyarsa
machine dinsa yau da ya masa tsiya ya baroshi gun bakinike ya tari adaidaita ya iso
gida.

         Babu wutar nepa a unguwar tasu hakan shi ya sabba ba duhun da gidan
yayi,sai hasken fitila daga dakin sumayya dakin fa'iza da kuma kitchen din gidan.

           Bashi da sha'awar yin tozali da fa'izar ko kadan,saboda haka ya bude


dakinsa ya shige da zummar zuwa ya rage kayan jikinsa ya koma bayi ya tanadi ruwan
wanka,hular kansa ya cire ya jefata saman gadonsa,ya balle maballan rigarsa ya
zareta ya ajjiye sannan ya nufi window dinsa ya yaye labulen don ya bawa iska damar
shigowa.

            Kamar wanda aka kira idanunsa suka sauka kan kitchen,fa'iza ya hango,da
farko yayi niyyar dauke kansa,saidai wani abu da ya hango shi ya ja
hankalinsa,idanu ya zuba sosai don yana son ya tabbatar da abinda idanunsa ke gane
masa,baiso yayi hukunci bisa kuskure zato ko tsammani.
            Sakin labulen yayi sannan a hankali ya fita izuwa kitchen din cikin
takun sanda,bakin window ya isa sannan ya lafe daga jikin bangon yana kallon komai
tar kamar yadda idanunsa suka soma nuna masa daga cikin dakinsa,yana tsaye harta
sheqe da dariya sannan tace..............

*mrs muhammad ce*

📚📚📚📚✍✍✍✍
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

1⃣8⃣

______________________
*Bismillahir rahmanir rahim*

*innal laha huwar razzaqu zul quwwatil matin*


______________________

"Mukhtar!,mukhtar!!,hmmmmm" haka ta fadi sannan ta maida murfin food


flask din ta rufe tana ci gaba da dariyarta cike da nishadi da jin dadi.

A hankali ya zare jikinsa,cikin tafiya ta sand'a kamar yadda yazo haka ya


koma,bakin gado ya zauna ya dafe kansa da dukkan hannayensa biyu,zuciyarsa na rawa
saidai baiso ya bata dama,oh Allah!,tun yaushe?,tun yaushe ya fara turawa kansa
wannan qazantar?,me ya samu yaya yahanasu ne har udanunta suka rufe ta kai ga
nannade hannu zata jefashi ramin halaka?,me ta gani ne wai gun fa'iza ya burgeta
har ta nemi suyi tarayya wajen hada zuriyya.

Sallamarta ta katse masa zaren tunaninsa,ya daga kansa wanda idanunsa


suka kada jazur ya dubeta,tayi ado yau cikin shadda koriya sgar,bakin nan ya sha
jan jambaki tamkar ya digo,zai iya rantsewa da Allah yau ne karo na farko da zai
iya cewa ya ganta tayi wata aba mai suna kwalliya tun bayan qare kwanakinta bakwai
na amarci.
Wani kwarkwasa na musamman yau din take masa,wanda dai dai da qwayar
zarra bata qara farashin qaunarta cikin zuciyarsa ba face rageta ma da tayi,haushi
takaici da baqinciki suka cika shi amma yayi namijin qoqarin dannewa
"Sannu da zuwa yaya mukhtar,yau kam ka jima baka shigo ba,Allah ya sanya lafiya" ta
fada tana zama dab da shi tare da kashe masa ido,tausar zuciyarsa yayi don yana son
ya ga gudun ruwanta,don idan baka iya kama b'arawo ba shi sai ya kamaka,tsawon
zamansu duk iya inda ya kai darensa indai ba a dakin sumayya bane to shi ta shafa
bata da damuwa,koda wasa bata taba tambayarsa ba
"Lafiya lau" ya fada yana miqewa tsaye,sai ta dubeshi gabanta na faduwa tana fatan
ba asarar aikinta zai mata ba yau ma dai
"Ina zuwa yaya mukhtar gashi na shirya maka abinci?"
"Wanka zan shiga nayi" ya fada bayan yayi kamar bazai amsa mata ba,ta miqe tana
fadin bari ta hada masa ruwan wanka sai ya dakatar da ita kan ta jirashi.

Kai tsaye dakin sumayya ya shiga,tana kwance saman doguwar kujera


hannunta riqe da wayarta tana kallon wani film 'DAN KUKA,dariyarta take mai sanyi a
hankali cikin nutsuwa,ya jima tsaye kanta yana dubanta cike da qauna da burgewa har
sai da ya sanya hannunsa ya zare wayar sannan ta miqe a firgice tana ambaton
"Bismillahi,hasbunallahu wa ni'imal wakil" sai suka hada idanu,ta shagwabe fuska
cikin muryar shagwaba tace
"Kai yaya mukhtar wallahi ka tsoratani" girarsa qwaya daya ya dage mata
"Eh amma naji dadi da kika ambaci sunan Allah yayin da kika tsorata din,haka akeso"
murmushi ta danyi,duban screen din wayar yayi ya tsayar da film din,cikin shagwaba
shima yace
"Wato yau ko ki nemeni ko my sumy?,hala ma kin daina damuwa da ni,kina nan kina
kallonki kina ta dariya abinki bayan bakiji shigowar sahibinki ba ko?"idanu ta zaro
tare da dafe baki sannan daga bisani ta hade hannayanta guri guda alamar roqo
" ka yimin afuwa don Allah,wallahi kewarka ce ta dameni shi yasa ma kaga ina rage
lokaci da kallon,ai kasan yaya kallo ba damuna yayi ba ko?"ta qarasa maganar da
sigar yarinta,idanu yasa yana kallonta sosai,babu shakka yana daya daga abinda ke
sake rura qaunarta cikin zuciyarsa wannan shagwaba da quruciya tata,murmushi ya
sakar mata
"Na miki sumayya ta,ai baki laifi a gurina" ya fada yana miqa mata wayar tate da
cewa
"Zan shiga wanka"
"A fito lafiya ranka ya dade"
"Allah yasa my sumayyata" ya fada sannan ya juya ya fice yana murmushi.

Kai tsaye sif dinsa ya wuce ya fidda jallabiya ya saka tana ta faman
zuba masa surutu,ko daya bai kula ta ba sai sabgarsa ma da yake,har ya kammala ya
zauna.

Cikin hanzari ta jawo abincin gabansa tana fadin bari ta zuba masa,idanu
ya zuba mata harta kammala ta dago ta dubeshi suka hada idanu,signa ta masa sannan
tace
"Gashi ya mukhtar sai ci ko"
"Qwarai kuwa" ya fada yana janyo abincin gabansa,fatanta daya kawai taga ya sanya
koda loma guda bakinsa ne,hakan ya sanya ta bata dukka lokacinta yau ko girkin rana
batayi ba cikin gidan ta tsara masa abincin da tasan yafi so.

Kamar ta sume don dadi sanda taga ya kai loma guda bakinsa sai kuma ya
dakata ya ajjiye cokalin ba tare da yaci din ba,ya dubeta ya sakar mata wani
murmushi
"Yau tare da ke nake sha'awar muci abincin,matso bismillah" tamkar an sanya guduma
an doki qirjinta haka taji amma tayi hanzarin mazewa ta girgiza kai
"Haba ai ba girmanka bane,baka ne kai kadai" idanu ya zaro
"Au bakison samun matsayi kenan irin na sumayya bayan naga shi kike ta fafutukar
samu maza matso,na saba tare muke cin abinci da ita duk ran girkinta" sai ta wani
kamme ido a dole sai ta ja ra'ayinsa
"Haba muntari wannan ai ba tarbiyya bace,miji na diba kema na diba,kaci kawai ni a
qoshe ma nake" kafada ya daga alamun rashin damwa daman ya san da kwanan hakan
"To shikenan,ba damuww,bari na kira sumayyan ta tayani ci" kamar ta tashi ta riqo
shi haja taji amma don kada ta bada kanta sai ta dake.

Daga bakin qofar dakinsa ya coge ya kirata don kada ma ta samu damar
sauya masa abincin,cikin mintuna qalilan sumayyan ta shigo dakin,kallonta yayi
cikin salo na burgewa
"Yayarki ta qi tayani cin abinci shi yasa na gayyatoki ki tayani" sai ta danyi jim
duk da murmushin da ta sanyawa fuskarta,ta sani cewa suna hada kwanon cin abinci ne
kadai idan ranar girkinta ce.

Matsowa yayi da kwanon da sauri gabanta don kada ma ta musanta masa


"Oya,matso mana" da sauri fa'iza tayi tsallen albarka ta dira gabansu,ta sanya
hannu ta rufe abincin,cikin daurw fuska tace
"Nifa gaskiya bana son haka,wannan ai bai kamata ba,ni ina shiga sha'aninku ranar
kwananta ne,to nima ban lamunta ba girki kai daya na yiwa shi kuma kai zakaci"
kallonta yake a nutse tsaf riqe da habarsa kamar yadda sumayyan ke
kallonta,murmushi ya aje cikin nutsuwa
"Ikon Allah,to aikam nima ban yarda ba cikin biyu dole ki zabi daya,ko ki tayani ci
ko my sumy ta tayani" ya fada yana sareta da idanunsa.

Take gumi ya yanko mata,ta fuskanci idan batayi da gaske ba wankin hula
zai iya kaita dare,kafin ta kai ga cewa komai nepa suka kawo wuta,haske ya wadaci
dakin,ba bata lokaci fuskar fa'iza ta bayyana,wadda tuni gumi ya yiwa jikinta
sharkaf,ganin yadda suke kallon gumin ya sanya ta fara nade tabarmar kunya da
hauka,wadda ta sake tonawa kanta asiri tsaf a gun mukhtar din ba tare da ta sani ba
"Lallai muntari,to me kake nufi?,kana nufin baka yarda da ni ba kenan?,ko kama
nufin wani abu na zuba maka a ciki?"
"Ni bance kin zuba wani abu ba,amma tunda kika fada din akwai qamshin gaskiya cikin
lamarin" miqewa tsaye tayi zata nade tabarmar kunya da hauka
"Lallai ma muntari,sharrin da zakamin kenan,sharrin d'a namijin da ake fada kenan
yau yazo kaina,eh lallai ba shakka" tsawa ya daka mata ganin zata masa hauka ya
miqe tsaye.

Kallon fuskarsa tayi ta tabbatar babu rahama a cikinta,take tsoro ya dirar


mata abu ya hadu kuma da rashin gaskiya,sai taja da baya ganin yadda yayi dab da
ita har tana jin hucin numfashinsa,tana niyyar guduwa ya damqi hannunta har da taji
azaba har tsakiyar kanta
"Fa'iza!" Ya kira sunanta a matuqar kausashe,hantar cikinta ta kada tamkar zata
saki fitsari a wandonta
"Basai na bata lokacina nayi doguwar magana da ke ba,wallahi wallahi duk ranar da
kika sake yunqurin zuba min wani abu mai kama da sihiri ko surkulle sai kin raina
kanki,ki kuma tabbatar daga ranar sunanki SAKAKKIYA!"

ba qaramin dukan qirjinta kalmar tayi ba,sam bata koda sha'awar jin wata
kalma makamanciyar haka daga bakin muntarin,don ko kusa bata marmarin komawa
gidansu wanda yake mata daidai da gidan kurkuku,gidan da talauci yunea babu masifa
da rashin tarbiyya ya yiwa katutu.

Sakar mata hannu yayi cikin rawar jiki ta juya zata fice don baya da
abun cewa,yanayinsa kadai ya tsoratata,balle ko shakka bata yi tasan cewa ya ganta
ne muntarin,tsawa ya kuma daka mata ya bata umarnin ta dawo ta kwashe abincinta
tasan yadda zatayi da shi baya da buqatar sa,haka ta kwashe kwanukan jiki na rawa
ta fice.

*kuyi haquri da wannan*

*mrs muhammad ce*

📚📚📚📚✍✍✍✍
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

1⃣9⃣

_________________________
*Bismillahir rahmamir rahim*

*ala bi zikrillahi tad'ma innul quluub*


______________________

Mamaki fal zuciyar sumayya,kanta ya daure tamau,ta kasa furta ma komai


sai kallon mukhtar da takeyi,ta tabbata ba qarya ya yiwa fa'iza ba domin ba halinsa
bane,amma halayyar fa'iza har ta kai haka?.

"Ina naki abincin?" Mukhtar ya tambayeta,ta katse tunaninta ta dago ta


dubeshi
"Ya d'aki"
"Ki dauko,ban amince kema. a yau kici ba,ki zuba a leda ki saka a shara a
zubar,shiga kitchen ki samar mana abinda zamu ci koda indomie ce sai ki hada mana
da qwai" ya fada yana kashingida gami da lumshe idanunsa,tsam ta miqe ta fice don
aiwatar da abinda ya umarceta.

************************

Cikin kwanakin ta dage sosai da addu'ar neman tsari,ta san tabbas


shartin mutum girma gareshi,zuwa yanzu ta kuma sallama kaidin fa'iza,ta fahimci
irinsu matan da suka dauki kishi ko a mutu ko ayi rai,irinsu wadanda zash iya
aikata komai saboda kishi,sosai take takatsantsan kan duk wani motsi da kai kawo
nata a gidan,ba ruwanta da sabgar fa'izan bare wani abu ya shiga tsakaninsu,koda
fa'izan zata shekara tana takalar tashin hankali bata bi ta kanta,don ta riga ta
tabbatar cewa akwai banbancin gida da kowaccensu ta fito,bai kyautu ta biye mata su
zamana kamar wadanda suka fito daga gurbi guda ba.

********************

Tun da asubahin ranar suka dinga jiyo kakarin amai a tsakar gidan
nasu,sumayya ta dubi mukhtar dake gefanta wanda basu jima da kammala sallar
asubahin ba kasancewar sun makara basu tashi da wuri ba
"Ya mukhtar,kamar kakarin amai nake ji fa a tsakar gida" shi din ma taji amma sam
bai da muradin fita,tamkar bazai tanka ba sai ya daure yace
"Eh nima naji" yaci gaba da jan carbinsa,ganin yayi shiru ya sanya ta sake cewa
"Ya mukhtar ka duba mana,inajin kamar fa'iza ce fa" shiru ya sake mata ganin hakan
ya sanya itama ta tsuke bakinta tayi shiru tana ci gaba da sauraran kakarin wanda
yake fita tamkar da kayan cikinta,ya kammala azkar dinsa ya haye gado abinsa ya
kashingida.

Zuciyar musulunci ya sanyata ta kasa daurewa,sai ta miqe ta fidda


hijabin jikinga ta nufi qofa,sanya baki yayi ya kirata tare da tambayarta ina zata
"Zanje na duba ne,bai kyautu da mutane cikin gidan ba kuma aqi fita a dubata
ba,bamu san meke damunta ba" kai ya girgiza
"Dawo tausa nake so kimin"
"Kayi haquri naje na dubata din minti biyu kawai zan dawo sai na maka tausar"
"Idan ban isa da ke ba shikenan kina iya hakan" ya fada yana maida kansa ya kwantar
kan pillow,sai jikinta yayi sanyi bata son saba masa ko kadan,saboda haka ta juyo a
sanyaye tahaye gadon.

A tausashe take masa tausar tana leqen fuskarsa ganin yaqi kulata,har
ta soma tara qwalla bata iya jure fushinsa,sai taji kawai ya birkitota ya danneta
da rabin jikinsa yana dariya qasa qasa
"Raguwa kawai sarkin kuka" ya fada yana lakuce mata hanci,dariya ta saki ya shiga
mata cakulkuli daga haka suja shige duniyar ma'aurata wanda hakan shi ya hanasu
fitowa da wuri.

Qarfe goma ya gama shirinsa zaya fita,a tsakar gida daga can bakin
qofar dakin fa'izan suka ganta zaune dirshan a qasa,ta wani wargaje can qafa can
qafa tana numfashi da qyar,da sauri sumayya ta qarasa inda take tana fadin
"Hasbunallahu lafiya fa'iza?"
"Bani da lafiya" ta fada qasa qasa da qyar,ta daga kai ta kalli mukhtar da bai
qaraso gun ba,yana tsaye abunsa bakin qofar dakin sumayyan yana daura agogo
"Yaya mukhtar,ko asibiti zamu?" Baice komai ba sai hannunsa da ya sanya cikin
aljihun wandonsa ya zaro naira dubu biyu ya miqa mata
"Gashi sai kun dawo Allah ya kiyaye hanya" ya sanya kansa soro ya tada machine
dinsa ya fice.

Tana jin rufe qofar gidan nashi ta miqe tamkar ba itace hajaran majaran
ba,duk da yanayin jikinta ya nuna bata da qwari sosai,ta sakarwa sumayya harara
sannan ta wafce kudin dake hannunta
"Babu inda zaki rakani munafuka" ta fada tana shigewa dakinta,kada kai sumayya tayi
cikin zuciyarta tana fadin
"Allah ka shirya,wato hali zanan dutse".

Tana daki tana shafa mai bayan ta kammala wanka ta jiyo fitar fa'izan.

Suna zaune zasu ci abincin dare bayan ya kammala komai,tana gabansa


tayi kyau cikin kwalliyar lace ja mai adon baqi tana zuba masa abincin data shirya
musamman saboda shi fa'iza tayi sallama ta shigo dakin fuskarta qunshe da murmushi
hannubta riqe da farar takarda,daya daga cikin kujerun dakin sumayyan ta samu ta
zauna,fuskarsa a hade ya dubeta
" daga ina kike takwas na dare?"sai ta rausayar da ido
"Haba mana muntari,ka tsaya kaji ji da nazo maka da daddadan labari"
"Ba wannan ba ki fara amsa min tambayar da na miki tukunna"
"Kash,labarin da zan baka yanzun duka yafi wannan muhimmanci,amma tunda ka nace sai
kaji to daga asibiti jikina ya rikice sai na wuce gida na kwanta acan,sai da
magariba na danji dama dama" shiru yayi ya soma cin abincinsa,ganin haka ya sanya
tace
"Ka godewa Allah muntari,Allah ya kusa cika maka burinka da ka dade kana fata,ka
kusa zama baba,an auna ni ina da juna biyu har na wata biyu".

Qwarewa yayi da lomar abincin da ya kai bakinsa,sai ya soma tari babu


qaqqautawa,cikin hanzari sumayya ta miqa masa ruwan tana jujjuya maganar cikin
ranta,indai hakan gaskiya ne to ya tabbata ITACE BATA HAIHUWA?.

Sai da ya sha ruwan sosai sannan ya ajjiye cup din,hannu kawai ya


miqawa fa'iza wadda keta doka murmushi tana tunanin farinciki ya sanya mukhtar
qwarewa,tabbas burinta ya kusa cika,zaman sumayya cikin gidan ya kusa zuwa
qarshe,ta kusa raba mukhtar da kowa sai ita.

Takardar ta miqa masa don ta fahimci ita yaje son gani,ya bude ta sosai
ya shiga nazarinta daga farko har qarshe,gashinan rubuce a jiki,cikine dan sati
takwas,amma sati takwas fa suka rubuta,har ya bude bakinsa zaiyi magana sai kuma ya
fasa,a yanzun ba muhallin yin maganar bane akwai muhallin yinta,saboda haka ya
nannade takardar ya cusa cikin aljihunsa ya janyo abincinsa yaci gaba da ci.

Dukkaninsu sumayyan da fa'iza sai suka zuba masa ido cikin mamakin
ganin bai ce komai ba,fa'izan ce cikin zaquwa da son jin abinda zaya fadi din tace
" ya baka ce komai ba muntari,Allah ya yi maka kyautar da ka dade kana jira amma
banga ka nuna komai ko kace min komai ba"kansa ya daga ya dubeta
"Naji ai kuma na gani,zan kuma magantun amma lokacin yin maganar ne baiyi ba,jeki
sai da safe Allah ya inganta ko?" Jiki a sanyaye ta miqe ranta cike fal da
mamaki,tayi zaton zai dauketa ne suyi rawa suyi juyin murna,ta yadawa sumayya
habaici yadda taga dama,amma duk da hakan ai lokaci na zuwa.

A sanyaye sumayya ta dubeshi bayan fitar fa'izan


"Amma yaya mukhtar kamar bai dace ba abinda kayin,sai nake ganin murna ya kamata ka
nuna irin wadda baka taba nunawa ba,d'a fa da kuje muradi shi Allah zai baka?"
Kansa ya daga yana dubanta fuskarsa qunshe da murmushi,sai kuma taga ya qyalqyale
da dariya
"Yanzu my sumy koda haka ne ya cancanci nayi murnar hada iri da waccar
matar?,fa'iza fa? Wadda ni da ke duka munsan halinta,bani da muradin samun zuriyya
da kowacce mace a duniya sai ke,kece nakeso ki zamo ta farko da kika samamin
zuria,ki bar maganar nan don Allah bana so in sake jin bakinki game da ita indai na
isa da ke"
"Insha Allahu" ta fada zuciyarta na karyewa,ina ma inama,ina ma tana da qarfin yaqi
da QADDARARTA?,ina ma tana da ikon baiwa kanta haihuwa?,ina ma ace zata iya samarwa
da mukhtar cikon farincikinsa,duk da bata da wannan ikon amma bata jin dai dai da
daqiqa daya bakinta zai rufu ko ya gajiya wajen roqon mai badawar da ya albarkaceta
ya azurta ta ya kuma bata haihuwa saboda karamci tausayi da kuma jin qansa,sai tayi
qas da kai hawaye na diga,da sauri ya daga kanta suka hada idani,da murmushi yake
dubanta gami da kada kai
"Bana so sumayya kin sani,ko ya kike sumayya haka nake sonki,sonki so ne na
fisabilillahi cikin zuciyata ba don wani abu da kike da shi ko kika rasa ba" bata
buqatar itama bata ransa saboda haka ta saki murmushi tasanya hannunta da kanta ta
goge hawayen.

Sosai fa'iza ta soma tsiro da tsurfa kala kala,gobe tace wannan jibi
tace wancan,da fari sumayya na qoqarim yo mata mukhtar na fuskantar haka yace bai
yarda ta sake hidimta mata kan komai ba,idan tana so ta tashi ta girka da kanta,nan
ma ya fuskanci an shiga babin barna da almubazzaranci shima ya soke yace taci duk
abinda ka dafa ko ta haqura,sosai abun ya qona ranta,duk yadda taso samu yaqi
samuwa.

Sai aka tsiro tsirfar zuwa dubiya kuma,daga bangare mukhtar zuwa na
fa'izan,saidai ko da wasa bata ga qafar yaya yahansu ko yaranta ba,saidai fadima da
ta zo,ita din ma sama sama fa'izan ta mata sannan ta tattarata ta watsar,sai data
gaji da zama ta ja qafafunta ta tafi,gidan sai ya zama kamar wani gidan biki,wuni
sumayya take tana karbar habaice habaice daga bakunan maziyartan gidan kala daban
daban,bata taba jin tsananin so da buqatuwar haihuwa ba irin na wannan karon,sai ta
zama wata mai raguwar zuciya,mikin data jima tana dannewa cikin zuciyarta na rashin
magaji ya zame mata sabo fil,duk sanda suka goranta mata sai ta kasa daurewa har
sai ta zub da qwalla ta rage radadin da take ji cikin zuciyarta.

Cikin hakan mukhtar ya fuskanci ta fara rama,juyin duniya yayi tambaya


tace masa lafiya babu abinda ke damunta,tilashinsa ya haqura saidai ya zuba ido
sosai bisa yadda lamuran gidan ke gudana.

A irin haka katsaham ya dawo gida ranar qarfe uku da minti talatin da
takwas ana shirye shiryen kiran sallar la'asar,wasu masallatan ma har sun fara
kiran,a lokacin tana qofar kitchen zaune tana hada girkin dare,yayin da dakin
fa'iza ke qunshe da baqin da qafarsu bata daukewa zuwa gidan da sunan dubiya,suci
na rana wani lokaci idan an kammala na dare ma suci sannan su tafi,musamman ranar
girkin fa'izan wanda taso qwarai a dauke mata girki mukhtar yace bata isa ba.

Yazo kuwa a gaba dai dai sanda suke jeranto gorin nasu,bai kula kowa
ba sai da suka kammala duk abinda suka zo da shi suka karkade qafafunsu,kowacce
tazo fita sai tayi turus ganin mai gidan zaune tsakar gida kusa da sumayyan yana
tayata aikin kitchen duk da babu wanda yacewa kowa komai cikinsu,sai su kama borin
kunya kana su fice sumi sumi.

Sai da suka gama ficewa tsaf sannan yayi kirab fa'izan ya kafa mata
sharudai,duk randa ya sake ganin qafar wani ya shigo har cikin gidansa ya ciwa
matarsa mutunci to sawunta a likkafa ta hada kayanta ta bisu tum gabanin ya dawo
gidan,wannan hargagi shi ya sake janyo tsana da jin zafin sumayya mai yawa a
zukatan mutane da yawa masu qinta musamman uwar tafiyar fa'izan,ta kuma sake cin
alwashi mai yawa akan sumayya,wannan kuma shi ya kawo taqaitar zirga zirgar 'yan
bani na iya din

*RANA DUBU TA BARAWO*

Tunda ta tashi yau kanta ke ciwo,don haka a daki ta kusa yini,koda


yaranta suka zo ma gida ta korasu don bata son hayaniya,naana ce kawai ta zauna
kasancewar duka ta fisu nutsuwa.

Har tayi baccin qailula ta farka yarinyar na gefanta zaune,ta miqe tana
salati duk da cewar kan nata ya rage ciwo amma bai sauka ba duka,ta cire hijabin
data kwanta da shi sabida zazzabin da ta fara ji ya fita tsakar gida ta dauro
alwala,cikin takaici taje duban tsakar gidan yadfa yayi kaca kaca,girkin fa'iza ne
amma bata damu ta gyara ba haka al'adarta take,matuqar sumayyan bata gyara ba to
saidai gidan yayi ta zama haka,to ita din ma bata da qyashi son jiki ko ganin ido
batq damuwa wai don bata gyara ba yin abinta take,hatta da wankin toilet zata iya
rantsewa bata taba ganin fa'izan tayi ba tunda ta shigo gidan.

Tana shiga d'aki ta sanya naana taje ta share mata tsakar gidan ita
kuma ta tayar da sallah.

Kafin ta kammala sallar nanan ta gama kasancewarta yarinya mai kazar


kazar da son aiki shi yasa sumayyan ke sonta,ta dawo gefanta ta zauna tana kallon
sumayyan har ta idar.

Tana shafa addu'a ga mamakinta fa'iza ta shigo d'akin dauke da cooler


dinta ta dire tayi ficewarta,tana nannade abun sallar sai ta lura naana nata
kallonta tana kuma satar kallon kwanon abincin,tasan akwai magana a bakinta ne ta
kasa fadi,kuma hakan yana da nasaba da hanasu dauko magana daga wani guri su gaya
mata.

Har ta koma saman kujera ta kwanta don bata da sha'awar cin komai
taga yari yar naci gaba da kallonta idan ta lura da kyau ma kamar qwalla ce a
idonta,a hankali ta miqe ta zauna tayi kiranta,yarinyar ta iso gabanta ta zauna
"Me ya faru?me ya sameki naga kamar zakiyi kuka,ko yunwa kike ji?" Sai ta girgiza
kai
"To mene ne gaya min" cikin raunin murya kamar kukan zai qwace mata tace
"Anty sumayya don Allah kada kici abincin nan" sai sumayyan ta hade rai tana
dubanta
"Me yasa?"
"Anty,naga amarya ta bude leda sanda kika sakami yin shara tana ta leqe sannan ta
koma kitchen ta bude flask din ta debo wani yalon abu ta barbada a ciki ta juya ta
rufe ta wanke hannunta" sosai taji gabanta ya fadi,saidai bata son ta bawa yaran
damar da zasu dinga labe ko qoqarin dauko gulmar fa'izan suna kawo mata,saboda haka
ta sake hade rai
"Ke me yasa kika labe kina kallonta?" Da sauri ta girgiza kai
"Allah ba labewa nayi ba,tsintsiyar ce ta kunce a bakin kitchen din sai na tsaya
daureta shine fa na gani" shiru tayi tana jinjina zancan cikin zuciyarta,sam bata
son ta baiwa kanta qofar da zata zargi fa'iza kan abinda idanunta basu gane mata
ba,saboda ko ubangiji ya fadi cewa HAQIQA WANI SASHI NA ZATO ZUNUBI NE,kai kawai ta
kada bayan ta koma ta kwanta
"Shikenan,bazan ci ba,amma kada ki gayawa kowa abinda kika gani kinji nana?"
"To anty" ta fada tana kada kai
"Zan tafi anty lokacin islamiyya yayi" ta amsa kana ta laluba gefanta ta dauko
alawa guda uku 'yan naura biyar biyar da takan ajjiye saboda su ta miqa mata,bata
fiya son basu kudi ba don kada su saba da su ta bata ma iyayensu tarbiyyar
yaransu,don ba kowa keson ka yiwa yaronsa kyautar kudi ba sabida gudun kada su saba
da su,randa kuma basu samu ba su nema kota halin qaqa,Allah ya kiyaye.

Sosai ta zurfafa cikin tunanin maganar da naanan ta gaya mata,sai ta


kauda tunanin daga ranta ta shiga addu'a cikin zuciyarta,ALLAHUMMAK FINIHIM BIMA
SHI'ITA ta dinga maimaitawa cikin zuciyarta,tana fata koma mene Allah ya mata
maganinsa ya sanya tsarinsa a gareta har wani baccin ya sake daukarta.

Koda ya dawo yau bai samu yin wanka ba sai bayan yayi sallar
magariba,yasan cewa ba samun ruwan wankan nasa zaiyi ba saidai ya debawa
kansa,hakan ne ya sanya yana shigowa ya tara ya shiga bandakin,har ya shiga ya
manta da towel dinsa hakan ya sanyashi fitowa.

Da hanzarinsa ya dawo zai shige,saidai wani abu da ya fisgi zuciyarsa


ya sanya shi dawowa da baya,abinda ya faru watannin baya yake ji a jikinsa tamkar
zai sake maimaita kansa ne a yau,a hankali ya zarw slippers dinsa ya taka zuwa
qofar kitchen din,idanunsa suka sauka kan cooler din sumayya dake bude gaban fa'iza
wadda ke dauke da dafa dukan shinkafa qarshen qurewar girkin fa'iza kenan.

Cike da hanzari fata da buri take barbada garin cikin abincin,don ta


fuskanci cewa sam sumayya ko bude kwanon abinci bata yi ba,amma wannan karo taci
alwashi kota halin qaqa sai ta sanya ta taci ko loma daya ce kai tama yankewa kanta
ko dura ce sai tayi mata.

Tana karkade hannunta cikin nishadi taji caraf an riqe hannunta,tun


kafin ta fahimci wake da alhakin riqe mata hannu gabanta yayi wata mummunar
faduwa,a hankali tamkar wadda ta warke daga cutar laka ta daga kai suka hada idanu
da mukhtar,wani matsanancin tsoro ya shigeta wanda kadan ya rage ta saki fitsari
cikin wandonta sakamakon yadda taga idanunsa sun sauya kala cikin sakannin da basu
wuce biyar ba.

Wani lafiyayyen mari ya yarfa mata wanda kafin ta ankare da a wanne


hali taje ciki ya sake bin fuskarta da wani,hakan ne ya tilasta mata sakin wata
gigitacciyar qara saboda ji taje tamkar fuskarta na shirin tsagewa ne,wannan shi
yayi silar zaburar sumayya ta miqe ta fito a razane tana tsammanin ko gobara ce ta
kama gidan nasu tunda ta bar fa'iza ne cikin kitchen.

Fitowarta yayi dai dai da wurgo fa'iza da mukhtar yayi zuwa filin
tsakar gidan
"Subhanallahi" sumayya ta fada da qarfi tana nufar inda fa'iza take don ta d'agata
"Kika tabata sai mun samu mummunan sabanin da bamu taba samun makamancinsa ba ni da
ke,sai nayi matuqar saba miki" taji mukhtar na ambata cikin wata kakkausar murya da
bata taba zata yana da ita ba.

Yadda ya sake nufo fa'iza gadan gadan ya tsoratasu baki daya,sumayya


ta janye gefe jikinta na rawa,bakinta na ambatar duk wata addu'a da tazo bakinta
tare da neman agajin Allah ya kawo sauqin kowacce iriyar masifa da zata faru yau a
gidan,yayin da tsoron da fa'iza taji ya sanyata sakin ihun neman agaji domin
tsantsar bala'in da zata fuskanta ya fito muraran cikin idanun mukhtar tun kafin ya
kai ga aiwatar da shi a kanta.

*mrs muhammad ce*

📚📚📚📚✍✍✍✍
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

2⃣0⃣

_____________________

*bismillahir rahmanir rahim*

*wa may yatawakkal alal lahi fahuwa hasbuh,innallaha baligu amrih*


_____________________
             Duban sumayya cikin shaqaqqiyar murya yace
"Jeki ki rufemin qofar gidan" tsayawa tayi tana dubansa jikinta na rawa,ta fuskanci
me yake nufi,wato don kada ma ihun fa'iza ya sanya ta samu masu kawo mata dauki
kenan
"Jeki ki rufemin qofar gida nace" ya maimaita cikin tsawa ganin bata da niyyar
tafiya,jikinta na rawa ta wuce taje ta rufo,bata kai ga dawowa tsakar gidan ba kuwa
taji ana bugun qofar gidan,daga inda yake ya bata umarnin kada ta bude ta dawo
ciki.

             Ga mamakinta fa'iza ke bawa mukhtar haquri hannu bibbiyu take


roqonsa,bai ko dubeta ba sai sumayya da ya kalla
"Shiga kitchen ki dauko min cooler dinki wadda take zuba miki abinci" babu musu
wannan karon ta shiga ta fito da ita,ya nuna maga gaban fa'iza da ido ta dire anan
din ta koma gefe ta tsaya jikinta na rawa.

              "Maza bude ki cinye abincin dake ciki yanzu yanzun nan" wani rugugin
aradun tashin hankali ya rufto mata,tirqashi,ai data ci abincin ciki gwara mukhtar
din ya kwana ya wuni yana jibgarta,domin cin abinci koda shinkafa qwaya tak dake
ciki ne dai dai yake da ban kwana da duniyarta,sai ta zube a qasa tana sake roqarsa
yayi haquri kuskure tayi kuma ba zata sake ba,wani murmushi mai tauri da d'aci ya
saki
"Ko baki fada ba ai dama har abada ba zaki sake aikata irn wannan mummunan aikin ba
cikin gidan mukhtar,afuwa daya da zan iya yi miki idan kina da buqatarta shine ki
dauki abincin nan ki cinye salun alun"
"Wallahi muntari bazan iya ci ba,zan iya rasa rayuwata,kayi haquri"sai yayi turus
ya zuba mata idanu cike da fargaba da kuma bacin rai
" kice ma niyyar kisan kai kika yi?,sumayyar tawa zaki kashemin?"ya fada cikin wani
irin zafin rai,da sauri ta girgiza kai tare da sake debo wata rantsuwa don gyara
baran baramar da take gab da sake tafkawa,ganin taqaddamar take qarewa har muntarin
na nade hannu zaiyiwa fa'iza dure ya sanya sumayya dake gefe kamar mutum mutumi
magantuwa,ta tabbata tunda har fa'izan ta toge kan bazata ci ba komai zaya yi mata
ya nuna akwai wani mummunan abu da ta qulla cikin abincin,wanda su kansu basu san
meye ba,ba kuma su san sakamakon da hakan zaya haifar ba idan taci din
"Ya mukhtar,ka qyaleta don Allah,koma meye tunda Allah ya kubutar da ni bayan muna
da masaniyar ba wayon mu bane sai mu gide masa ko?"
"Ok,haka ne fa" ya fada yana gyada kai tare da duban sumayyan,saidai kallo daya
tayi masa ta fuskanci bawai yana nufin ya haqura din bane
"Shikenan ki bar cin abincin" ya fada yana juyawa zuwa dakinsa.

           Murmushin nasara da farinciki fa'iza ta saki tana duban sumayya duba na


wulaqanci
"An gaya miki haihuwa kayan banza ce?,ni na sani ko darajar cikinsa dake jikina
kawai ta isheni,banza mara amfani ke zaki ci gaba da diban kayan takaici juya kawai
wad...........".

               Fitowar mukhtar dauke da belt ita ta maqale sauran zazzafar maganar


da take da burin ci gaba da yabawa sumayya,tsayawa yayi gabanta yana gyara belt din
tare da fadin
" babu batun cin abinci amma wallahi baki ci banza ba,sai na fanshe wahala da
baqinciki rashin zaman lafiya da rashin kwanciyar hankalin da kika shigo kika
haddasawa gidanmu,kinga gobe sai ki koyi darasin zaman duniya"kafin su ankara ya
fara jibgarta tako ina,tsoro da firgici ya hana sumayya tabuka komai,abinda
iyatsawon rayuwarsu bata taba gani mukhtar yayi ba,duka duka koda ga qaramin yaro
bare ga matarsa ta aure,lallai babu shakka fa'iza na shirin koyawa mijinsu mummunar
aqida idan bata tashi tayi da gaske ba,don daga haka miji ke farawa idan ba'ayi
wasa ba.
               Ta nufeshi da hanzari da niyyar dakatar da shi saidai tuni ya
hankadata gefe cikim zafin rai ba tare da ya san yayi ba,a rashin sa'a ta fadi kuwa
kan hannunta wanda sai da ya bada wani sauti ta saki kalmar wash! Cikin azaba,bata
sake yunqurin tashi ba ta zubawa sarautar Allah ido.

              Sai da ya tabbatar ta daku sannan ya dakata yana dubanta


"Ki tatattara duk wani tarkace naki da kika san kin shigo gidan nan da su ki koma
inda kika fito,na sakeki saki biyu" wani ihu ta kurma kamar zautacciya tana shirin
miqewa tsaye
"Wallahi baki isa ba muntari,zama daram wallahi sai na haife abinda ka qusa min ma
rainshi sannan" wata dariya ya saki sannan ya miqa hannunsa ya fincikota tare da
fusge zanin jikinta.

               Idanu sumayya dake zaune dirshan kan sumunti ta qwalalo ganin abinda
ya fado jikin fa'iza wanda da shi ake canza tafiya ake burga ake kira ciki ne,cikin
ma kuma wai na mukhtar dinta,tarin zannuwa ne aka hadasu aka qulle cikin zani daya
fa'izan ke daurawa
"Indai ciki ne gashi nan yau kin haifeshi ko,rainonsa kuma sai ki ajjiyemin kayana 
ko ni zan raini abu na" ya fada yana qyalqyalewa da dariya,gaba daya wani muzanci
ya kama fa'iza,me kenan?,meke shirin faruwa?,dama mukhtar yasan ba ciki bane shi
yasa ya qyaleta,shi yasa bai nuna farinciki ba da result din bogi data bashi,bata
kammala karanta wasiqar jakin ba maganar mukhtar din ta kuma katseta
"Kin maida mukhtar wawa shashasha jaki irinki ko?,don kinci sa'a na qyaleki tun
lokacin ban hukunta ki ba kan raina kin wayo da kikayi ba?,to wallahi kada ki yadda
na fito a wanka na taddaki cikin gidan nan,idan ba haka ba kowanne laifi da kika
aikata cikin gidan nan iya tsawon zaman da kikayi cikinsa sai na miki hisabinsa
tare da hukunci akansa daya bayan daya" ya fada yana yarda belt din ya dauki
sabulunsa da ya watse gefe ya shige wankansa.

             Cikin tsananin radadin ciwukan da taji ta miqe ta shige dakinta,bata


yi ko minti biyar ba ta fito dauke da jaka da hijabi,har ta gota ta dawo da baya ta
dubi sumayya
"Wallahi wallahi kada ki dauka kinci nasara a kaina,yanzu aka fara wasan" ta fada
tana mai ficewa da sauri jin motsin mukhtar na niyyar fitowa saga bandakin.

            Bin qofar data fice din yayi da kallo domin yaso ya taddata,sai a
lokacin ya maida dubansa ga sumayya
"Me take gaya miki?" Bata amsashi ba sai niyyar miqewa da take amma ta kasa,ganin
haka ya sanyashi qarasa gurinta da sauri yana nufin riqe mata hannu ta saki qara da
sauri sabida gun ciwon ya taba
"Subhanallahi,hannu kuma sumayya?" Ya tambayeta yana duban gun,banza tayi da shi
cikin son yunqurin tashi yayi niyyar taimaka mata da sauri tace
"Barni,bana so" ta tattara qarfinta ta miqe ta nufi dakinta.

            Binta yayi a baya da sauri,tana shirin shiga dakin ya cafkota,qara ta


saki saboda hannun ya riqe,sosai ya murde hannun har sai da ya bada qara alamun
inda ya gulle ya koma dai dai,kafin ya kammala ta gama hada gumi,jikinta yayi
laushi ya jata cikin jikinsa yana goge mata hawaye da gumin da ta hada.

         Cikin kujera ya ajjiyeta yana maida ajiyar zuciya ya fice zuwa dakinsa.

_busy!busy!!! Wlh_

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍✍✍✍
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖
*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

2⃣1⃣

*innal laha ma'assabirin*

            Cikin qanqanin lokaci yayi wankan ya shirya cikin shadda sea


grean,sosai tayi masa kyau,itama sabuwa ce cikin sabbin dinkunan da yayi shima,ya
kulle gidan suka fito.

           Sai daya bude mata gidan gaba ta shiga sannan ya zagaya shima ya shiga
daya bangaran yana duban ta,yadda fuskarta ta cika da farinciki tana masa
addh'a,sosai yaji dadi cikin zuciyarsa shima,yayi bismillah ya tada motar suka fice
daga layin a hankali.

               Suna tafe suna hirarsu cikin nishadi da walwala har suka iso qofar
gidansu sumayyan,cikin zumudi ta bude ta fice mukhtar ya bita da kallo yana
murmushi,tamkar yau ne ta fara zuwa gidan sai murna take.

               A tsakar gida ta tadda maman zaune saman tabarma sai fitilar qwai
dake kunne a gefanta kasancewar babu wutar nepa,ba kowa tsakar gidan sai ita kadai
"A'ah,sumayya da kece haka da daren nan?" Mama ta fada tana sake bude tabarmar da
take kai,gefanta ta qaraso ta zauna bakinta yaqi rufuwa
"Wallahi mama nice,ke kadai ce?"
"Eh duka sun tafi makarantar dare,amma gab suke da dawowa"
"Malam fa?"
"Sun tafi dubiya asibitin murtala shi da abubkar,maqwafcin mu malam sule ba lafiya"
"Ayyah baba sule,Allah ya sawwaqe......bari na yiwa yaya mukhtar din magana to ya
shigo ku gaisa"
"Au tare ashe kuke......maza shigo da shi" inji mama tana janyo hijabinta dake
gefanta ta zura.

             Cikin girmama juna suja gaisa sannan ya fada mata motarsa ya kawo su
sa mata albarka,tayi kuwa addu'a sosai don babu damar ta leqa malam din baya
nan,nan ya fice qofar gida ya barsu.

              Bai jima da fitar ba mama ta matsa mata ta shi su tafi tunda zasu
gidan yahanasu,ta miqe suka yi sallama da maman ta fito.

             Sai ta tadda mukhtar din da su zainab da halima ya bude musu motar


suna ciki,malam kuma yana gefe da alama isowarsa shi kenan don gaisawa ma suke,ta
qarasa cikin girmamawa itama tabi sahun mukhtar ta duqa ta gaidashi sannan ta gaida
ya abbakar,ya shiga tsokanarta ta hanyar cewa tayi qiba ta zama lukuta me mukhtar
ke dura mata ita kadai,ta kasa tanka masa sai dariya da takeyi kanta a qasa saboda
kunyar malam da takeyi.

          "Ai sai ku wuce ko kada dare ya muku" cewar malam yana shigewa gidan
bayan sunyi sallama,mukhtar ya fidda dubu biyu ya bawa su halima yace su sayi kayan
kwalliya,qin karba sukayi sai da sumayyan ta sanya baki sannan suka amsa auna
godiya suka shige gidan.

             Shiru ya biyo baya cikin motar,mukhtar ya sauke ajiyar zuciya sannan


yace
"Tarbiyyan gidanku na birgeni sumayya,naso a ce ina da wani dan uwa namiji da babu
shakka sai na aura masa halima ko zainab" murmushi kawai sumayyan tayi sabida tasan
koda yana da dan uwan babu ta yadfa su yaya yahanasu su yadda su sake hada zuri'a
da 'yan gidansu.

         Mintina qalilan suka isa gidan,ya kashe motar ya fice ta bishi a baya
bakinta cike da addu'a.

           Dukansu suna tsakar gida zaune kan tabarma suma saboda zafin dake dan
busawa a 'yan kwanakin,ga matsalar rashin isashshiyar wutar lantarki da muke fama
da ita ta kowanne bangare na qasar nan.

           Da fara'ar ta ta amsa sallamar amma jin muryar sumayya yasa ta gintse


'yar fara'ar data yo tsaraba,jamila dake gefen tabarmar ta matsa ma mukhtar,yayin
da sayyada taqi motsawa ko su samawa sumayya wani abun zaman,hakanne ya sanya
mukhtar din dubanta fuska a hade
"Ke,tashi ki bata guri" tuni ta miqe saboda tana shakkarsa kuma tasan halinsa
sarai,daki suka shige ita da jamilan baki daya.

             A girmame yake gaisheta ta amsa sannan sumayya ta gaidata,sama sama ta


amsa mata suka shiga hira da mukhtar din.

           Jamila ta fito da ruwan pure water mai sanyi guda biyu ta cup ta ajjiye
gaban mukhtar din sai ya turasu duja gaban sumayyan yana cewa
"Bude kisha,kince min kina jin qishirwa dazu" zuciyar yaya yahansu ta tunzura,ta
dinga jifansu da harara tana qwafe da su,ya maida dubansa gun yaya yahanasun
"Mota na kawo miki ki gani yaya,ta iso dazun da safe" sai ta harareshi
"Au shine sai yanzu kaga damar kawo min na gani kenan sai da ka gama nunawa duniya"
"Ba haka bane,data iso din ma a gareji na wuni ana mata service,ina dawowa gida
kuma nayi wanka naci abinci muka taho kawo miki"
"Sai kace makaho da baka iya tahowa kai kadai,kai Allah ya kyauta,ya warware mana
wannan masifar" ta fadi cike da haushi da tsana,don ya kauda zamcan don kada yayi
nisa sai ya miqe yana fadin suzo su ga motar,haka suka miqe suka fice suna
hayaniyar murna,tana zaune gun burinta kawai yace ta taso su tafi,Allah ya
taimaketa sayyada ta leqo tace ta fito su tafi.

         Tana zaune gaban motar shima haka amma sai zuba zance yayan taje wanda ya
hana musu tafiya
"To Allah ya tsare ya rabaka da sharrin masu sharri,Allah ya qara budi ya kawo masu
yi maka addu'a ya rabaka da wannan matsiyacin zaman kadaicin" bai amsa ba ya ciro
dubu uku ya miqa mata yana fadin
" ga wannan ku qara"hannu tasa ta karba zata sake barkewa da wani surutun ya samu
yaja motar suka wuce.

           Duk yadda taso boye damuwarta amma sai da ya fuskanta,kan dole yake zuwa
da ita gidan saboda yaya yahanasun dolensa ce,amma banda haka da tuni ta bar zuwan
gidan,da tuni ya yanke alaqar dake tsakaninsu,kan hanya ya tsaya ya siya musu
yoghourt manyan roba biyu masu sanyi da tsire mutumin sumayyan don duk ya faranta
mata,a hankali ya dinga janta da hira da labarukan ban dariya,sosai ta sake sake
masa jiki tana qyaqyata dariya wanda hakan shima ya masa dadi.

*~TSUGUNNE BATA QARE BA~*

              Shi da ita duka suna zaune cikin falon nata da ya sake gyara mata
shi,sanye suke da kayan barci saidai sai banbanta gun zama da ayyukan yi,shi yana
zaune kan qaramar kujera ta zaman mutum daya dauke da computer yana aiki,yayin da
ita ke kwance saman doguwar kujera tana kallo a tashar mbc inda suke hasko film din
ashqui,kusan bata taba zama ta kalli film din complete ba sai yau.

           Dakin ya dauki shiru kasancewar kowa ya bada muhimmanci kan abinda


yakeyi,wayar mukhtar dake saman jakar laptop dinsa ta dauki tsuwwa,ya dubi wayar
sai yaga baquwar lamba ce,kusan ya jima da daina daukar ire iren lambobin,to amma
sunyi da wani costumer dinsa zaya kirashi kan wasu kaya da zai siya a shagonsa,sai
yayi zaton shine saboda haka ya daga
"Assalamu alaikum" mukhtar din ya fada,kana yayi jim kusan daqiqa talatin sannan ya
sake cewa
"Wacce zainab?,daga ina?" Ya sake yin shiru na sakan biyar sannan ya ja tsaki ya
kife wayar yaci gaba da binda yakeyi.

            Ba'a cika minti biyar ba wani kiran ya kuma shigowa,ya dubi wayar ba
tare da yayi niyyar dagawa ba,lambar dazun ce dai sai ya sake dauke kansa yaci gaba
da abinda yakeyi din ransa na quna.

            Kiran da aketa maimaitawa a kai akai shi ya dami sumayya har ya ja


hankalinta,tana daga kwancen ta dubeshi
"Don Allah yaya mukhtar ka daga,wallahi ta dameni" ta fada a shagwabe,bai dubeta ba
yace
"Bazan daga ba,barta kawai" sai ta maida kallonta din batason ko gu daya ya wuceta.

           Bai haqura ba mai kiran yaci gaba da nacin kiran har sai da sumayyan ta
sake tankawa ya bata amsa irin ta dazun,sai ta tashi zaune tana gyara wuyan rigar
barcinta da ya salube tare da fadin
"Shikenan,bari ni na daga maka ko a bar kunnuwanmu su huta"
"Kema ba zaki daga ba" ya fada bayan ya dago idonsa wannan karon ya dubeta,dariya
ta saka tana tunanin wasa yake mata,dai dai lokacin da kiran ya sake shigowa ta
sanya hannunta da sauri ta suri wayar ta daga ta kara a kunnenta tana masa gwalon
taci nasara ta daga ba tare da wafce ba kamar yadda yayi niyyar yi da farko.

            A hankali ta cire wayar daga kunnenta qirjinta na bugawa jin muryar


macace tana gaya mata mukhtar take nema,miqa masa wayar tayi jiki a sanyaye.

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖
*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

2⃣2⃣

_______________________________
*Bismillahir rahmanir rahim*

*ma yaftahillahu lin nasi min rahmatin fala mumsika laha,wama yumsik fala
mursilalahu bin ba'a dihi*

_Allah ka sanya mu daga cikin wadanda zaka yita saukar da rahamarka garesu,alfarmar
sayyadina rasulullahi S A W_
_______________________________

         Hannu ya sanya ya amsa,sai ya latse wayar ya kasheta baki daya ya ajjiyeta


gefansa yaci gaba da aikinsa,wanda yana duba yanayin ginin gidansa wanda a yanzun
ake daf da kammalashi
"Sai da na gaya miki kada ki daga" ya fadi idanunsa na kan computer din,cikin wata
iriyar mutuwar jiki da kasala ta lallaba ta koma kan kujerar data tashi taci gaba
da kallonta,saidai sam ta daina fuskantar komai,wani abu mai kama da zazzafan kishi
ne ya shiga taso maga,ta dinga ambaton sunan Allah har zuwa sanda suka qare film
din ta koma dakin gadonta.

           Sam bacci yaqi zuwa mata face nazari da take tayi ita kadai har mukhtar
din ga gama abinda zaya yi ya cimmata akan gadon,jikinsa ya janyota sannan cikin
taushin murya yace
"Meke faruwa ne sumy uhmmm?"
"Babu komai" ta furta can qasan maqoshinta
"Ban santa ba nina sumayya,abinda kawai na sani customer dina ce,tazo shago na
siyayya ita da 'yan uwanta,ta buqaci number dita saboda koda zasu tashi zuwa wani
lokaci,tun daga ranar take matsanta min da kira ba yau ta fara ba,na gargadeta na
kuma ja mata kunne amma bata ji ba,wannan shine abinda na sani" shiru sumayyan tayi
taba nazarin maganar,sosai wani kishinsa ke taso mata
"Allah ya kyauta" ta iya cewa kawai,sai ya juyo da ita ta fuskanceshi
"Haka ma kadai zaki fada ko?,wato ma baki kishi na kenan sumayya" ya fada yana
matse mata yatsu har sai da taji zafi ta saki 'yar qaramar qaara,sai ya hade
bakinsa da nata cikin wani irin salo da ya mantar da su komai

         ***     ***       ***

            Ta maida kiransa ya zame mata tamkar ibada,idan ma bai daga ba zata


yita jelan tura masa saqonni iri iri wadanda dukkaninsu a akwatin share saqonni
yake zuba su.

           Sau tari wani abun dariya yake bawa sumayya,tana mamakin yadda mata suka
sauke farashinsu ya fadi qasa warwas,tana jin inda ita dince sam ba zata iya haka
ba,ko babu komai akwai kunya irin ta diya mace,duk da ta sani cewa koda matar
ma'aiki ta farko nana khadijatul kubra ta nemi ma'aiki da ya aureta,amma bata irin
wannan sigar bace,ta siga ce mai tsafta,mai ban sha'awa mai cike da hankali nutsuwa
da kuma KARAMCI,sa'an nan ta nemi a aureta a inda take da yaqinin samun qauna da
kulawa,a 'inda ko babu qauna akwai tausayi girmamawa da kuma MUTUNCI.

            Sau da dama idan saqonni da kiran ZAINAB ya ishi mukhtar yakan zauna
yayita sababi,sai ta sa baki da haqurqurtar da shi,wani lokaci kuma ta zolayeshi
shi kuma ya bita da harara,ko ya ranqwashi kanta,a haka lamarin yaci gaba da
wanzuwa har tsawon watanni uku cur babu sassauci haka na babu sauyi.

*Wace ce zainab?*

       Zainab haifaffiyar garin kano wadda ke zaune cikin unguwar sheshe,suna da


rufin asiri dai dai gwargwado,gida ne wanda ya kasance ya samu rarrabuwar kai da
sabanin mabanbantan ra'ayi ga jama'ar gidan,maman zainab itace amarya a cikin gidan
yayin da zainab ta kasance 'yarta ta uku baya ga maza biyu da ta biyo,mama amarya
mahaifiyar zainab ta zamewa mata biyu data tarar cikin gidan qarfen qafa,babu wanda
ke da fada a ji cikin gidan sai ita,ita ke juya kowa ciki harda mai gidan,taci
karenta babu babbaka har zuwa lokacin da Allah ya yiwa mai gidan rasuwa aka raba
musu gado kowa ya kama gabanshi,koda zainab tayi auren fari mama amarya ba irin
mijin da take so zainab din ta aura ba kenan,miji take so ta samu koda ba mai kudi
ba amma yana da abun hannunsa,wanda zasu maqale suyita tatsarsa suna tara abun
duniya,talaka ne bashir futuk,qarfin soyayyar da zainab din ke masa ya rufe mata
idanu har ta aureshi,tayi aurenta ne bayan data kammala kataratun ta na NCE a
federal college of education kano wato FCE,kusan zamu iya cewa bashir abokin
karatunta ne tare suke daukan lactures course dinsu daya,bayan kammala karatu kuma
aiki bai samu ba,sai shagon wani maqocinsu dake kasuwa yake zuwa yana masa jira ana
biyansa.

         Duk iya yadda mama amaryan taso ta fahimtar da zainab din taqi fahimta,duk
da kusan cewa babu abinda ta baro na daga halayen uwarta,bata cimma nasara ba sai
bayan da akayi auren,sukaci soyayyarsu suka cinye,a lokacin da gishiri ya fara fita
daga kan kaza ne zainab din ta fahimci bashir bai dace da ita ba,daya bayan daya ta
dinga bin sawun duk wata dabi'a da huduba da uwar ke azata kai.

        Cikin watanni biyar kacal suka balle auren,a lokacin tana dauke da ciki na
watanni uku,duk yadda suja zo zubar da cikin abin ya gagara,a cewar mama amaryan
baya da wani amfani tunda ubansa bai mallaki komai ba bare su saka ran samun wani
alfanu tattare da shi.

          Saidai kuma ina,maqaginsa ya riga ya QADDARA sai ya taka doron qasa,bayan


wata bakwai ta haife yaronta namiji,ko yayeshi bata yi ba ta soma balle zawarci mai
lasisi,a lokacin ta sake haduwa da qawaye kala kala idanunta suka bude,tasan duniya
sosai har fiye da yadda uwarta ta sani ta koma dorata akai,hakan ya so tsorata
maman har ta soma shirin hanata wasu abubuwan,amma ina.......maqeri ya riga mabada
hali,tuni zainab din tasa aka rufe bakin maman da yayyenta maza biyu,duk wani abu
da zata aiwatar bata laifi a idanunsu,musamman idan ta samo ta yaga musu.

           Tun randa taga mukhtar zuciyarta ta yaba da shi,bata bata lokaci ba


wajen bada sunanshi aka mata bincike a kansa,yadda takeso haka sakamakon yazo
mata,mukhtar din yayi dai dai da ra'ayinta,saidai bata qaunar kishiya ko misqala
zarratin,amma da ta samu labarin wace sumayya sai hankalinta ya kwanta,ta tabbatar
ba matsala bace a gunta,aiki guda daya tak zata mata rana guda ta koreta daga
gidan,duk da tana diyar malamai ai bata da maganin kirsa ko?.
        ***       ***      ****

    Hankalinta bai kwanta ba sai data gana da yaya yahanasu,wadda bata tunkareta ba
sai data yi shiri sosai akanta,qwarai yaya yahansun taji wata qauna da aminta wa
zainab,musamman data ji cewa ta taba haihuwar d'a namiji ma,nan zainab din ta zube
mata alkhairai masu tarin yawa tare da tsara yadda zasu cimma nukhtar din duk da
taimakon yaua yahansu wadda ke kiran kanta YAAYA kuma UWA a gunsa.

        ***       ***    ***

          Suna shirin cin abincin dare kiran yaya yahanasun ya baqunci wayarsa,dama
ya tsammaci hakan saboda tun yammacin jiya da ya ziyarci gidan yaga gilmawar wata
cikin layin nasu tamkar zainab din,zuciyarsa bata gasgata masa hakan ba tunda ya
riga da ya sani bata san muhallinsu ba,amma duk da haka zuciyarsa bata samu nutsuwa
ba har zuwa wannan lokaci.

"Kiyi haquri yaya,amma yanzu bazan samu damar fitowa ba" ya sanar da ita kai tsaye.

"La'ilaha illallahu,mukhtar yaushe kayi wannan riqar,akwai ranar dama da zata zo


zan buqaci ganinka kaqi mukhtar" sai ta sa kuka
"Lallai ba shakka sumayya ta gama da mu,taci galaba akanmu ta sake cutar min da
d'an uwa" sam baya son yaji kukan nata kamar yadda zuciyarsa ke quna idan yaji tana
zagi aibata ko zargin sunayyarsa,hakan ya sanya ya amsa mata kan cewa yaba zuwa.

          Wayar ya sauke yana duban sumayya


"Sumayya bana son fitar nan,ina zargin wani abu"ya fada idanunsa na sauya launi da
alamun ransa ya fara motsuwa,kai ta kada
"Ka zargi alkhairi ya mukhtar,tunda kasan koma mene yaya jininka ba zata taba
cutarka tana sane ba ko?" Shiru ya danyi sannan yace
"Na sani,amma matuqar abinda nake zaegi taje shirin aiwatarwa wannan karon wallahil
azim sunayya ba zata kwashe mana da dadi ba,bazan yarda a ringa walagigi da
rayuwarmu" duk da cewa a dunqule yayi maganar amma sai data haifar mata da
matsanancin faduwar gaba wanda ta sanya har ta kasa tankawa, ya miqe ya shiga
dakinsa ya dauki hularsa ya zura da muqullin babur dinsa don ya riga da ya ajjiye
motarsa a inda take kwana ya fice daga gidan.

        Kan kujera ta koma ta kwanta rigingine gabanta na ci gaba da lugude,a


hankali ta dinga ambaton
"Ya rabbi yassir wala ta'asir" sabida neman gudun mawa da daukin wajen ubangiji.

           Cikin falonta ya taddata wanda tun kafin ya kai ga shiga ya dinga jiyo
dariya da hirarsu ita da yaran da alama cikin nishadi suke da walwala,sallamarsa ya
katse hirar tasu,da daya da daya suka fice a dakin ya zama daga shi sai yaya
yahanasun.

        Suna kan gaisawa jamila ta shigo da jug guda biyu ruwa da lemo da kofuna ta
dire masa,ya dauke kai ya dubi yaya yahansun yace
"Gani" sai ta dan murmusa
"Haba muntari,sai kace wanda ake gutsura,ko ruwa ai ka sha ko?" Sai yaga rashin
dacewar yadda yazo matan,ko babu komai tsakaninsu ta bashi shekaru,saboda haka ya
rusuna ya tsiyayi ruwan yayi kurba daya ya ajjiye kofin.

          ***    ***    ***

         Tana jin qarar babur dinsa ta miqe da hanzarinta,har ya shigo da shi ya


kulle gidan ya qaraso falon tana tsaye,sam hankalinta ya gaza kwanciya a haka ya
sameta a tsayen.
         Saidai yanayin da taga fuskarsa ya zabge kaso mafi yawa na tashin hankalin
da ta shiga,har ta saki bayyananniyar ajiyar zuciya ba tare da ta sani ba,'yar
qaramar dariya ya saki yana fadin
"Me ya tsorataki haka?" Qwayar idanunta ta juya
"Kaine mana,hankalina ya qi kwanciya tunda ka fita"
"To ya kwanta,don babu komai sai alkhairi" duk da bata ji farinciki ko kadan ba
yadda ta tsammata sai tace
"To Allah ya lamunce ya shige mana gaba" tayi maganar tana zama.

           Ko kadan baiyi mata maganar komai ba,babu abinda yace mata kan hakan har
bayan kwana biyu,a tsarinta mutum ce da bata shishshigi cikin lamuran da suka shafi
rayuwar wani,hakanan ko da ga mukhtar din ne bata tambayarsa wasu lamura nashi na
daban saidai idan shi yaga dama don rad'in kansa ya sanar mata,hakan ya sanya itama
bata tambayeshi ba sai tayi zaton wani lamari ne da ya shafesu shi da 'yar uwar
tasa.

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

2⃣3⃣
________________________

*Bismillahir rahmanir rahim*

*wa'asa an takrahu shai'an wa huwa khairul lakum,wa'asa an tuhibbu shai'an wa huwa


sharrul lakum,wallahu ya'alamu wa'antum la ta'alamu*

*Allahumma farrij hammal mahmumin,Allahumm farrij karbal makrubin*


_______________________________

*Bayan kwanaki biyu*

*** *** *** ***

             a hankali ta shigo dakin ganin tunda ya kammala wanka ya shiga bai


fito ba bayan ta kammala shirya abincin dare sa zasu ci,turus ta tsaya tana
dubansa.
            Tsaye yake gaban mudubi sanye da sabuwar shaddarsa ruwan qwaiduwar qwai
dinkin boda,taje sumar kansa yake,sosai kayan suka masa kyau,sai ta jingina da
bango ta harde hannayenta tana dubansa,da alama ma baisan ta shigo ba.

        "Da kyau,irin wannan kwalliya haka da akemin?" Juyowa yayi ya dubeta yana
murmushi
"Girmanki ne ai,amma zan danje unguwa tukunna" sai ta danyi jim gabanta na
faduwa,take ranta ya darsa mata wani abu,batasan sanda bakinta ya subuce ba
"Zance zaka kenan" juyowa ya sakeyi yana ajjuye cumb din tare da takowa gabanta
"Ya akayi kika canka?,naso ace da kaina na gaya miki my sumy" wani irin abu taji
yana ratsata tun daga kanta har qafafunta,yanayin fuskarta ya sauya
"Wai don Allah da gaske kake ko wasa?"
"Da gaske nake mana sumayya,na taba miki irin wannan wasan" ya fada yana qoqarin
janyota jikinsa,sai ta zame jikin ta kana ta ja da baya,jikinta ya soma rawa hawaye
na shirin zubo mata,hakan ya sanya ta tallafi kanta ta hanyar zama gefan gado,baiyi
qasa a gwiwa ba ya bita ya zauna gefanta
"Yi a hankali mana sumayya,me na daga hankali kuma,koma wace zata zo ai kema kinsan
a bayanki take ko?" Idanunta ta dago wadanda suka cika da qwalla har sun fara
gangarowa ta dubeshi
"Meye na tada hankali kuma,shin ban cancanci nayi kishinka bane ya mukhtar?"
"Kin cancanci fiye da haka ma sumayya,amma kiyi haquri,in sha Allahu ina saka ran
wannan karon alkhairi ne auren da zanyi".

         Cike da mamaki ta watsa masa wani kallon


" wanne alkhairi ya mukhtar?,har ka manta wuyar da mukaci cikin shekara guda
kacal?....."
"No....ki kyautata zato sumayya ba haka na sanki ba....", qarar wayar sa ce ta
katse abinda yake shirin gaya mata,ya sanya hannu ya daga wayar bayan ya hade fuska
kamar yana gaban mai kiran
" nace miki gani nan ko?"daga haka ya datse kiran ya maida hankalinsa kanta.

          Hannu ya sanya ya share mata hawayen sannan ya miqe


"Ki bari na dawo zamuyi magana,ki kwantar da hankalinki sumayya kinji" bata iya
amsa masa ba har ya sanya hularsa ya fice.

          Wani kuka ta saki bayan da taji tashin motarsa,meke shirin


faruwa?,mukhtar ne yau ya tafi zance gun wata a gaban idonta bayan ya ganta tana
kuka,mukhtar din da baison bacin ranta balle har yaga hawayenta?
"Ya rabbi yassir amrih" ta dinga fada bayan ta zame ta kwanta saman gadon tana
digar hawaye.

          Kimanin awa biyu sai gashi ya dawo,lokacin qarfe goma har ta dan gota
ma,a dakin nasa ya sake taddata kwance,da sauri ya isa gareta ya dagata ya zaunar
yana duban idanunta da suka kumbura
"Subhanallahi.....sumayya meye haka?" Kamar jira take ta kuma fashewa da
kuka,tsawon mintina talatin ya ciyo kanta bayan ya tursasa mata sunci abinci,sai da
suka kammala sannan ya nemi magana da ita.

           "Ta hanyar yaya yahanasu zainab ta biyo sumayya,babu yadda za'ayi na iya
bijirewa maganar,ni kaina ina jin yadda da auren cikin zuciyata bansan dalili ba,ba
kamar auren fa'iza ba hakan ya sanya nake zaton QADDARATA ce zainab" yayi shiru
yana jin quna can qasan zuciyarsa da wata iriyar takura,saidai daga sama yana jin
kamar dole ake masa ya auri zainab.

         Jin shiru bata ce komai ba ya sanya shi cewa


"Yanzu haka cikin satin nan suke da buqatar na kai kudi a kuma saka rana baki
daya,idan da alkhairi sai kiga ta haifa mana yaro ta sanadin haka kema ki samu
naki" maganar sai tayi mata duka biyu,batasan sanda ta fashe da kuka ba
"Ta haifa maka dai yaya mukhtar,ni sumayya kam banda cikin haihuwa ai" tayi maganar
tana mai niyyar miqewa ta bar masa gun,yunqurin riqota yayi ta kauce tana fadin
"Ka qyaleni kawai ya mukhtar,ka qyaleni kaje kayi aurenka,ka auri wadda zata haifa
maka yara,na yarda nikam juya ce" ta qarashe maganar cikin gunjin kuka kamar zata
shide,da azama ya riqotan ya rungumeta yana lallashi,sam sai kalmominsa suka gaza
yin tasiri cikin zuciyarta,ta kasa bashi hadin kai wajen yin shiru da haquri
"Nace ma ka sakeni kaji ko?!" Ta fada cikin gunjin kuka.

         "Naqi na sakekin!" Ya fada a tsawace


"Yaushe kika koma haka sumayya?,yaushe kika koyi shegen kishi haka?" Ya fada yana
kwantar da murya,a hankali ta daga kai tana dubansa,ta karaya sosai wannan
karon,banbanci take hangowa qarara cikin idanun mukhtar din,sai ya janye idonsa
daga kanta yana tuhumar kansa akan tsawar da ya mata,a tausashe ya janyeta gefan
gado ya zaunar da ita sannan ya zauna daura da ita,cikin sanyin murya yace
"Kiyi haquri sumayya,baki na bazai gaji da baki haquri ba yau da gobe da kullum har
ABADAN ma sumayya,abu daya zan iya gaya miki shine inaji a jikina dole ne nayi
auren nan,bazan iya haqura da shi ba,ki yafemin sumayya,ki yafewa mukhtar dinki mai
qaunarki kinji sumayyata" ya fada cikin raunin murya tamkaf mai shirin yin
kuka,abinda bata taba ji daga gareshi ba kenan,idanunsa kadai zaka kalla ya
tabbatar maka da gaskiyarsa,take tausayi so da qauna sukayi tasiri a kanta,ta
rungumeshi tana fadin
"Babu komai ya mukhtar,Allah ne ya halatta maka,kaji tsoron Allah kawai ka kuma yi
adalci"
"In sha Allahu sumayyata,ki tayi ni da addu'a" ya fada yana kuma qanqameta.

        ***       ***     ***

       Cikin abinda bai wuce sati uku ba aka kai kudi bayan sati daya mukhtar din
ya hada kayan sa rana akwati biyu,bai shawarceta ba hakanan batasan zaya yi ba sai
ganinsa tayi da kayansa,yace ta duba tace basai ta duba ba Allah ya sanya
alkhairi,haka ya janyesu ya miqawa yaya yahansu,suna guda suna gwalli suka je suka
kai kafin lefe ya qaraso,fadi suke Allah ne ya karya alqadarinta,wannan karo kam ta
gamu da mai qarfin kurwa,kuma in sha Allahu zama daram tazo.

         Daga can bangaren zainab din ma haka suka gaya mata,sumayya bata barin
mace ta zauna da mukhtar ko anyi auren saita tarwatsa abun,dariya zainab din
tayi,don tasan komai game da sumayyan,tasan sarai akwai qarin gishiri cikin
maganarsu,ta lura mutane ne masu jarabar son kansu da nasu,tilas tayi maganinsu tun
da wjri,din ba zata lamunci abinda sumayyan ta lamunta ba,duk da hakan ba zama
zatayi ta zubawa sumayyan idanu ba,koba komai diyar malamai ce bata san nasu shirin
ba.

          Sosai sumayya ke ganin banbanci wannan karon,ashe da sam ba aure mukhtar


din yayi ba,wani rawar kai sosai take gani dangane da shi,sabbin dinkuna yake da
lissafe lissafe,tuni ya maida kai wajen ganin an kammala abinda bai kammalu ba na
ginin sabon gidansa,ita kanta yace ta kwashe duka kayan dakinta ta siyar ko ta
bayar zai sauya mata komai da sabo itama zata tare,saidai abinda ke daure mata kai
wani lokaci sai ya hau qunci shi kadai yana fadin baison auren nan,sgifa yana jin
tamkar ya fasa,bata san meye matsalar ba,data gaza gano haka sai taci gaba da
addu'a kan Allah ya sassauta lamarin ya kawoshi da sauqi,don zuwa yanzu ta tsinke
da lamarin kishiya,ashe a da tabbas quruciya ke cinta,batasan dadin mijinta ba sai
yanzu,bata san meye kishi ba sai yanzu.

          Kayan lefe ya mata itama yadda ya yiwa zainab kowa akwati hurhudu,bata yi
mamaki ba saboda budin da mukhtar din keta samu dai dai gwargwado.

          Biki ya rage saura sati biyu abdur rahman ya kawo mata ziyara,ta tarbeshi
yadda ta saba,suka gaisa cikin mutunci,saidai wannan karo babu walwala da zolayar
da suka saba,da ya tambayeta batayi qasa a gwiwa ba ta sanar masa,sosai ya mata
nasihar da ta sake kwantar mata da hankali,ya jaddada mata ta riqi
addu'o'inta,sosai taji dadi ta kuma gode masa,bai jima ba sukayi sallama ya tafi
dama mukhtar din yazo nema kuma bai taddashi ba ya tafi zance gun amarya zainab.

Saura sati daya bikin ta shirya ta je gidan anty dije,da biyu taje don ta
samu mai bata shawara,don sosai taji dadin shawarwarin da ta bata wancan karon,wuni
tayi mata sur ta kuma qaru matuqa da gaske,taji dadin maganganunta wadanda suka
sake kwantar mata da hankali.

Ranar da akema amarya jere ranar itama aka yi mata nata jeran cikin sabom
gidansu,sai ya zama na tamkar amare biyu ne zasu tare,sosai zainab tayi rawar ganin
hadawa kanta kayan daki,duk da haka babu abinda zata gayawa sumayyan,don itama
wannan karon dai komai sabo ne,babu abinda ta shiga da shi tsoho banda sutura su
dinma kusan rabinsu sababbi ne.

Ana ya gobe za'a kawo amarya ta tare,tare da 'yan rakiyarta suka je,sosai
gidan ya burge kowa,duk da ba wani kantameme bane amma da girmansa dai dai
gwargwado,da fari compound ne wanda ya dauke motar mukhtar din da wani space din
daban,sai qofar da zaka bude wadda me dauke da babban falo guda d'aya,daga hagu da
dama corridor ne guda biyu,daya na sumayyan daya na amarya,kowanne cirridor akwai
daki falle biyu da toilet,daga falon akwai qofa biyu,daya ta kitchen dinsu ne mai
yalwa wanda ka masa tsarin tsohon kitchen dinsu kowa da kantarsa,daya qofar kuma
idan ka bude baya ne inda aka yiwa 'yan shuke shuke,anan falon mukhtar yake da
bedroom dinsa shima,gida yayi dai dai gwargwado sai son barka.

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

2⃣4⃣

_____________________________
*Bismillahir rahmanir rahim*

*Man ja'a bil hasanati falahu ashru amsaaluha,wa man ja'a bis sayyi'ati fala yujza
illa misluha*
_________________________________
      Bata gayyaci kowa ba baya ga mutanen da suka mata rakiya suka ga gida suka
kama gabansu,hakan ga sanya randa za'a kawo amarya ita daya ce qwal,cikin dakinta
tayi zamanta saboda falon nasu cike yake da 'yan kawo amarya,wadanda tun daga
motsinsu ta karanci yanayinsu,su din ma dukkan alamau sun nuna babu arziqi,saboda
haka tayi musu aji guda ta sanya su.

       Bata fito ba sai da taji motsin 'yan uwan mukhtar wadanda da su aka dauko
amarya,fuska sake ta fito falon tana musu maraba,saidai kowanne wanu irin kallo
yake binta da shu,ganin babu dole ya sanya ta juya ta koma dakinta tun kafin su
yarfata cikin jama'a,yanzun kam ba da bace da quruciya ke dibarta balle ta nace sai
an kula ta ko ta faranta ran wanda bai damu da nata farincikin ba.

            Ganin tara na dare yayi hayaniyar ta sarara da alama sun watse sun bar
masu gidan da gidansu,sai ta miqe ta sanya turaran wuta cikin dakinta zuwa corridor
dinta a burner din da anty dije ta siya mata guda biyu kyauta,take qamshin ya
karade ko ina har zuwa falon nasu,wanka ta shiga ta tsala ado cikin wani marron
material wanda aka yiwa ado da golden din zare,sosai ya fidda salsalar farar
fatarta wanda jan lallen da tayi ya sake bada gudun mawa,baga wani cika kwalliya ba
ta dai yiwa kanta barin turare kama daga humra,body spray body mist zuwa perfume na
kaya.ta yane kanta da mayafi golden ba tare data buqaci daura dankwali ba ta kame
gefab gadonta tare da janyo wayarta ta soma 'yan danne danne don ta dauke mata
abinda take ji cikin zuciyarta.

          Qarfe goma taji sallamar mukhtar din cikin falonsu,burus tayi tamkar bata
jishi ba,wani kishi da matsananciyat faduwar gaba suka ziyarceta,sai ta dakata da
abinda takeyi din tayi shiru tana sauraron motsinsa da kuma bugun zuciyarta.

         A hankali ya yaye labulen yayi sallama,ta amsa ba tare da ta dubeshi


ba,idanu ya zuba mata,ta masa kyau sosai tamkar yau take amaryarsa,wanu qaunarta ke
taso masa ta wani lungu can dake saqon zuciyarsa wanda wani abu da baisan ko meye
ba ke qoqarin fatali da abinda yake ji din,ya rasa me yaje ji cikin zuciyarsa a yau
din,koda zaka ritsashi da bindiga ha zaya iya gaya maka ainihin me yake ji
ba,farinciki koko baqinciki,ya jima cikin wannan yanayin wanda baisan sanda ya
shige shi ba,da yayi yunqurin wani tunani kuma sai ya shagala,tunanin ya qwace
masa.

        Ganin bata da niyyar cewa komai ya sanyashi qarasowa gefanta ya zauna yana
zube ledojin hannunshi a qasa
"My sumy.....yau kan arziqin sannu da zuwan ma ban samu ba" ya fada cikin
marairaicewa,a hankali ta dago kai ta kafeshi da idanunta wanda suka sanya yaji
wata fargaba da kamashi,yayi kyau cikin shadda butter colour dinkin babbar
riga,yasha askin saisaye da gyarab fuska wanda ya sakw fidda shape sin kyakkyawar
fuskarsa.

       Tamkar an dorawa zuciyarta dutse haka taji saboda tsabar kishi,yau nukhtar
dinta zai sake zama na wata a karo na biyu,me yasa yaya yahanasu taqi barinsu su
huta,me yasa ba zata gane irin yadda take son mukhtar dinta ba,laifi ne dan baka
haihu ba?,shine lawai dalilin da yasa suke ta rabata da farincikinta  a lokuta
mabanbanta,ina ma ace ana siyar da haihuwa yau da ta sayeta koda zata rasa zanin
daurawa,koda zata rasa lomar abincin da zata sanyawa bakinta,don dai kawai su barta
da mukhtar suyi rayuwar farinciki.

          So take ta bude baki da gaya masa magana ko zata ji sauqin tuquqin da


zuciyarta ke maga amma sai ta kasa,girman mukhtar cikin idonta yafi gaban
haka,miqewa tayi gudu gudu sauri sauri idonta na saukar da qwalla kan
kuncinta,miqewa yayi biyita da sauri cike da muradin cimmata,saidai tuni ta afka
toilet dinta ta rufe qofa tare da sakin kuka.

         Bakin toilet din ya tsaya yana naci da magiyar ta fito,sai da suka kusa
kwashe minti ashirin a haka,ba zata iya kallonsa ya tafi dakin wata ba hakan ya
sanyata cikin muryar kuka tace
"Bana son ganinka yaya mukhtar ka tafi don Allah ka qyaleni"
"Yau nine sumayya baki son gani?.....yau......." Bai kamamala maganar ba wayarsa
dake aljihun gaban rigarsa ya hau ruri,hannunshi ya zira,ganin mai kiran ya
sanyashi dagawa
"Dear m,ina ka tsaya ne wai bayan na ji shigowarka",bazai iya tantance mai yaji
ba,so yake ya rufeta da masifa amma sai ya kasa,maimakon haka sai ya bige da cewa
" ina gun yayarki zance ko qanwarki ina lallashi"gabanta ha fadi haushi ta
turniqeta,kada fa ace duk abinda ake bata labari kan sumayyar gaskiya ne,amma babu
komai saura qiris tayi maganin abun
"Lallashin me kuma dear bayan ba wannan ne karo na farko ba da aka fara mata
kishiya,ka taho ko nazo da kaina na tafi da kai"
"Ok gani nan" ya fadi da sauri tare da katse kiran,maida idanunsa yayi ga qofar
toilet din,ya tabbatar taji duk abinda suka ce,kamar sumayyan ce ke gabansa ya
marairaice
"Shikenan sumayya zan tafi,ga ledarki can cikin daki Allah ya bamu alkhairi" ya
fada yana juyawa.

        Zamewa tayi tayi zaman dirshan saman tiles din bandakin sabon kuka na kubce
mata wanda ta sanya tafin hannunta ta toshe bakinta don kada su jiyota,duk da cewa
ita tace ya tafin bata yi tsammanin tafiyar tasa da gaggawa ba haka.

        Ta jima tana kuka a ciki kafin ta lallashi kanta bayan tayi tilawar
wasiyyoyin mahaifiyarta tun daga auren da aka qara mata na fari zuwa wannan da ya
kasance na biyu.

        Bata bar bayin ba sai da cikakkiyar alwala,ta koma daki ta sauya kayan
bacci,doguwar riga ce har qasa mai taushi da kauri,hijabi ta dora saman riga ta
shimfida abun sallaha ta tayar da sallah hawaye na layi kan kumatunta.

         Yana shiga ta miqe ta taroshi cikin karairaya da yauqi,ta amshi ledar


hannunsa ta ajjye kana ta rungumeshi,yaqe haqora kawai yake,ko daya bata burgeshi
ba,alamu sun nuna babu kunya ko qwaya daya cikin idanunta,ko daya baiji dadin
kasancewarta cikin jikinsa ba amma sai ya kasa cewa da ita komai,sai ya dinga dauko
daren farkon sumayya da na fa'iza da nata yana hadawa,tuni lissafin ya wargaje don
tako ina sun sha banban.

           Biye yake da ita kawai sai ido da yake binta da shi,ita ta hada musu
ruwa sukayi wanka sannan ta samo plate ta juye kazar a ciki,kusan ita ta dinga
ciyar da shi ta kuma ci da kanta har suka kammala ta janyeshi gado don tuni ta
dokanta,kusan ita ta gabatar da komai a maimakonshi,mamaki da haushi ke
tuqeshi,gefe guda wani irin takaici wanda idan ya yunqura zaiyi magana sai yaji ya
kasa cewa komai,data dubeshi kuma sai yaji komai ya wuce ya bar tasiri cikin ransa.

         Kwana tayi zaune bayan ta gaji da yin sallolin,abinda bata taba zata zata
iya ba,yaushe mukhtar ya sake zame mata wani na daban haka,ita kanta tana mamakin
yadda ta koyi kishinsa har haka,sai da ta gabatar da sallar asuba taji idanunta sun
soma nauyi da zugi,duk yadda taso ta yakice baccin amma bata samu nasara ba,haka
yazo ya saceta cikin gaggawa ya kuma mata nauyi wanda hakan ya sanya ta gaza sanin
meke wakana cikin gidan har misalin qarfe goma da rabi ma safe wanda ta farka a
firgice.

         Bandakin cikin dakinta ta shiga da yake bayan na corridor akwaai cikin


daki,wanka tayi bayan ta wanke bakinta ta dawo cikin dakin,jikinta babu qwari ta
shirya cikin atamfa doguwar riga wadda ta mata kyau,duk da bata jin qwarin jikinta
amma tayi lite make up wadda ta dace da yanayinta,babu dauda ko qura a rea dinta
sai dan kakkabe kakkabe kawai da tayi sannan ta fito don samawa kanta abinda zata
ci koda ruwan zafi ne,don jinta take iska na yawo da ita tsabar babu komai a
cikinta,ledar jiya mukhtar din ya bata ta dauka ta fice da ita.

         Bata kula da su ba sai data shigo cikin falon sosai,mukhyat sanye da yadi
mai taushi fari tas wanda ka yiwa aiki da zare ash,sai wandda idanunta suka sake
sauka kanta wanda bata tantama itace zainab din.

        Macace wadda kallo daya ta yi mata ta fuskanci ta girmesu ita da fa'iza


baki daya,A qalla tayi shekaru ashirin ta takwas wanda hakan ke nuna ta girmi
sumayyan da shekara goma tunda sai yanzu taje cikin shekararta ta goma sha
tara,baqa ce zainab din amma ba baqi can ba,tana da cika wadda za'a iya kiranta
qiba kai tsaye duk da wata mai yawa bace,bata daga cikin sahun kyawawa ko kadan
amma zaiyi wuya kai tsaye ka kirata da mummuna saboda yanayin iya gogayya da iya
salo,saidai tako ina sumayyan ta mata fintikau,abu daya zata iya nuna mata qwala
qwalan idanu da suke zagayayyu suka fi na sumayya girma,sakamakon natan lumsassu ne
ba kowanne lokaci kake iya gane girmansu ba,sanye take da material mai santsi wanda
aka yiwa dinkin riga da skert,breakfast sukeyi wanda ya qunshi tea da soyayyen qwai
da bread,sai kaji wanda ba tantama na jiya ne aka sake gasa su.

         Shi ya soma ganinta lokacin da zainab ke qoqarin bashi naman a baki,sai ya


goce wanda hakan ya janyo hankalin zainab din ta ankara da fitowar
sumayyan,murmushi ya sakar mata yayin da itama tayi qoqarin maida masa martani
"Kin tashi kenan,na leqaki na taras kina bacci"
"Eh,ban jima ai da tashi ba" ta fada tana takowa gabansu
"Kinyi kyau sumy ta" ya fada yana sake dubanta wanda kalmar ba qaramin dukan qirjin
zainab tayi ba,lokaci daya ranta yayi baqi,sumayyan ta yaga mata tako ina,kyau da
quruciya,akwai alamun nutsuwa tattare da ita sosai,hakan ta kwana da sanin lamba
daya ce ita cikin zuciyar mukhtar din,don ko darensu na jiya ya bata amsa,duk yadda
taso rikitashi ban manta sumayyan ba ita yake kira.

      "Na gode ango mijin amarya,da fatan kun tashi lafiya" ta fada wajen kaiwa
matuqa gurin boye kishi da damuwarta,sai ta dubi zainab
"Amarya ina kwana ya kwanan baqunta"
"Lafiya ya kike"ta fada tana yatsina tare da qoqarin baiwa mukhtar tea
"Qalau" itama sumayyan ta fada cikin yanayin data amsa mata tare da motsa kafada
kana ta nufi kitchen don kaucewa ci gaba da kallon abinda ke faruwa.

        Alamu sun nuna iyaka na cikinsu ne abincin,batasan waye yayi ba,amaryar ko


mijin amaryar,koma waye dama bata da buqata,sai ta dora tea kan gas da a yanzu shi
mukhtar ya siya mata take amfani da shi,ta bude kazar ta sake mata sabon hadi na
spices,ta duba dan madaidaicin ovean dinta ta soma kici kicin hadawa tare da duba
hanyoyin da ake hadawar.

       Cikin haka mukhtar din ya shigi kitchen din dauke da kwanukan da suka ci
abincin zainab din na biye da shi,bata bi takan sumayyan ba ta nufi side dinta ta
dire kayan,mukhtar ya dubu sumayyan
"Me za'a girka mana ne naga ana hada ovean"
"Ai baka da buqatar abinci na malam" ta fada cikin gatse,murmushi yayi yana
kallonta,lallai sumayyan ta fara zama babbar mace,tunda har tafara banbance
tsakanin aya da tsakuwa.

          Kafin ya furta komai muryar zainab ta ratsa kunnuwansu tana qwala masa
kira cikin wani irin salo,tamkar an soketa a qirji amma saita basar,ya juya yana
cewa da ita
"Ina zuwa"
"Banda buqatar dawowarka ma" ta fada kishi na cinta tana qoqarin danneshi.
        Har ta kammala babu shi babu alamarsa,ta juye ta koma daki da abincinta
zuciyarta na raunana,saboda wannan ne karo na farko data taba ganin sauyi daga
gareshi har irin haka.

        ****      *****    ****

     Cikin kwanakin wani amarci ta dinga gani cikin gidan wanda bata tsammata
ba,baki daya kamar daukar mukhtar din akayi aka sauya mata shi,hutu ya dauka na
fita kasuwa har na kwanaki bakwai,ko yaushe suna daki idan kaga fitowarsa salla ce
zaya yi,saita wuni sur bata sanyashi cikin idanunta ba,abun na taba ranta saidai
bata yarda ta fiya zurfafa lamarin cikin ranta,runda anty dije ta gaya mata dole
zata iya ganin wasu sauye sauye duk son da yake mata,amarya kota buzuz ce sai an
mata rawar qafa,to bare baya ga wannan babu wani sauyi da ta gani cikin ma'amalarsu
shi da ita.

*KUNDIN QADDARA TA*

          Kwanaki uku take zaton zaya yiwa zainab din tunda bazawara ce,sai gashi
ya shiga cikin kwana na hudu biyar shida har zuwa bakwai.

        Ranar kwana na bakwai din a ranar zaya soma fita kasuwa,tana kwance dakinta
bayan sha daya na safe taji sallamarsa,sai ta miqe ta zauna tana amsa masa,fuskarta
babu yabo babu fallasa,gefanta ya samu ya zauna yana fadin
"Ranki ya dade kinyi wuyar gani" ido ta daga ta dubeshi,lallai ne wai ita za'a yiwa
halin maza,magana yake gaya mata a fakaice koko yaya,duk da hakan sai ta dake ta
kuma basar ta kaufa zancan ta hanyar fadin
"Ina kwana"
"Lafiya sumy ta,kinga na qarawa zainab kwana ko,kinga baquwace tace kuma tan tsorom
zama ita daya" wani haushi ya taso ya turniqeta,budurwa ce zainab din ko yau ta
fara zaman gidan aure,ko ko tsabagen rainin wayo ne,wadan nan kalaman takeson
gayawa mukhtar din amma girmansa da take gani yasa ta gaza furtasu ta hadiye
kayanta sai ta bige da cewa
"Ko,Allah sarki" daga yanayin da tayi maganar kawai ya tabbatar masa cewa ta inda
zancansa ya shiga ta nan ya fice.

         Kafin su sake cewa wani abu zainab din ta daga labulen dakin ta danno tana
fadin
"Dear fito mana na rakaka,ina ta jira fa"
"Ai gani nan" ya fada yana fiddo kudin cefane daga aljihunsa,wani banzan kallo da
sumayyan batasan ta iyashi ba sai yau ta jefawa zainab sannan ta miqe zata fice ta
bar musu dakin,mukhtar yace
"Ina kuma zaki sumayya bamu gama magana ba"
"Baka shirya yin maganar da ni bane" ta fada tana shigewa toilet abinta ta soma
daura alwalar sallar walhar da dama ita take shirib tashi tayi.

        Tana jiyosu daga nan zainab din na gaya masa ya qyaleta yazo su tafi,yace
a'a taje falo ta jirashi zaya fito yanzu,a bandakin ya cimmata ta gama alwalar tana
gyara daurin kallabinta,fuska a hade cikin kakkaurar murya yace mata
"Wai wane irin hali kika koya sumayya wanda ban sanki da shi ba,wannan wannw irin
wulaqanci ne ina miki magana kina tafiya gaban zainab salon ki koya mata yadda zata
raina ni", tsayawa tayi tana kallon ikon Allah,lallai a daki mutum a kuma hanashi
kuka.

        " ai tare muka siyi foam din makarantar koyon sabbin halaye ni da kai muka
cike,muka kuma fara daukar darasi a ciki"sarai yaso ya fahimceta amma sai ya waske
"Wai duka sumayya don na qarawa zainab kwanaki kike wannan abun,yanzun ban isa da
gidana ba kenan?"
"Isa kai,tunda gashi ka nuna salon taka isar" ta fada tana kashe famfo tare da
qoqarin rabeshi ta wuce,sai ya janyota jikinsa ya matse gam,yasan kan abarsa take
ya fara sauke mata fushinta,yayi nasara kam don itama bata bijire masa ba,don babu
qarya tayi kewar mijinta sosai.

        Ita ta fara zame jikinta sannan tace


"Ka gayawa matarka kada ta sake shigo kin daki kanta tsaye,sabida hakan ya sabawa
dokar addinin musulunci idan ita din bata sani ba" sai ya lumshe ido ya dafe kai
"Oh sumayya harda mita ma sai da kika koya,to ayi haquri" daga nan sukayi sallama
ya ajjiye mata kudin cefane duk da suna da komai.

        Sosai zainab din ta qulu,ta fara lura sumayyan ta shalle zatonta,amma daga
yau zata fara dasa bamabamanta cikin gidan,shanye komai tayi ta masa rakiya kamar
ta hadeshu,duk yadda ya nuna jin dadinsa a fili amma zuciyarsa ta gaza karbar
hakan,a boye ma Allah Allah yake ta koma ya samu ya fice daga gidan.

        Da azahar ta shiga kitchen ta musu girkin rana,tana fitowa ta samu zainab


din a falon zaune tana kallo,qafarta daya kan daya tana amsa waya,har sumayyan ta
gifata ta taji ance
"Ke!" Da fari tayi zatan cikin wayarta ne sai taji ta sake cewa
"Ke dake nake magana sumayyata" waiwayowa tayi tana tsaye daga inda take
"Wai da ni kike?"
"Akwai wata mai sunan ne bayanke a gidan nan,koma ki dauko min abinci na".

         Baki ta sake tana kallonta cikin mamaki,ita kuma nata salon kenan,sai ta
kada kai kawai tace
" idan kin damu ki shiga da kanki ki dauko"
"Ni kike gayawa wannan maganar,lallai yau zaki gane niba irin sauran kishiyoyinki
bane,wallahi yau sai kin gane matsayina gun mukhtar" bata tsaya bi ta kanta ba tayi
komawarta daki don tana da abunyi.

        Lambar mukhtar ta soma laluba tana huci,yana tsaka da sallamar custumer


yaga kiran nata,sai da yaji wani dumm cikin kansa da yaga sunar,ko kadan baiyi
farinciki ba amma sai ya gaza share kiran
"Amarya bakya laifi,ya gidan"
"Gida ba lafiya ba,mukhtar na fuskanci ka auroni ne don matarka ta rainani"
"Ya salam,me ya faru me tayi miki?"
"Bazan hanaka sana'a ba kabari idan ka dawo kaji koma mene ne,amma wallahi idan
baka dauki mataki ba bazan ci gaba da zama cikin gidan nan ba" sai yaji wata
faduwar gaba da sauri yace
"Haba zainab ki daina fadar wannan maganar mana,mai rabu mu ai sai Allah,bari na
kira ita sumayyan naji" da sauri ta katseshi don bata son ya mata fadan tun yanzu
lamarin ya wuce ba tare data iza wutar tafi haka ba
"A'ah nidai ban saka ba,nace ka bari kawai ka dawo"
"To shikenan sai na dawo din" ya fadi yana sauke wayar,sam jikinsa bai bashi
sumayyan zata aikata wani abu na rashin mutunci ga zaina din ba,amma sai ya samu
kansa da yarda da duka magan ganun zainab din.

           Tun shuda saura ta gama fesa kwalliya tare da bade jikinta da turarenta
data tanada na musamman wanda ke hargitsa tunani da lissafin mukhtar ya dinga maida
su ba dai dai ba.

        Cikin izza da isa ta fito daga dakin nata hannunta dauke da jug na kwalba
wanda ta cikashi da lemin zobo da cups dinsa,tana tafe tana murmushin tarkon data
d'ana ta ratso ta falo don fita harabar gidan,so take mukhtar din ya fara karo da
ita kafin kowa saboda abinda ta tsara ya tafi dai dai ba tare da mishkila
ba,idanunta ne suka sauka kan sumayya tada tsume cikin tata kwalliyar,wani irin
material ne mai santsi kamar yanayin shufom saidai ya fishi kauri da aka matsawa
dinkin wata shegiyar gown wadda ta fidda duk wata qira tata,kalar pink(ruwan hoda)
ne mai turuwa,tayi amfani da dankunne da siririyar sarqa fashion baqaqe,hakanan
abun hannunta zuwa zobe,take farincikin dake ranta ya ja baya ta raina tata
kwalliyar data hasko farar fata ta hadu da pink da baqi,kishi ya sake taso mata,ya
zama lallai kota halin qaqa tayi rugu rugu da gwamnatin sumayyan cikin zuciyar
mukhtar ya zama tata ke wannan tashen,ta yadda zata yaga yarinyar yadda taga
dama,yarinyar na neman fin qarfin zatonta,don ba'a rufe awa ba taga yadda ta tashi
hankalin gidan da qamshin girkin abincin dare,ranta na suya ta fuce fuuu wanda
sumayya bata ma lura da ita ba sai ficewarta ta gani kamar guguwa.

_tofa,yanzu ake yinta,muje zuwa_

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

2⃣5⃣
____________________________

*wa tawakkal alal hayyul lazi la yamutu wasabbih bi hamdih*

_kayi tawakkali ka dogara da rayyayyen(Allah S W T)da baya mutuwa,kayi tasbihi/ka


tsarkakeshi ka kuma gode masa_
____________________________

        Guguwar dawowarta sumayya da taji ya sanyata daga kai ta bita da ido har ta
shige dakinta.

          Cikin mintinan da basu wuce biyu sumayyan ta fara jiyo qauri wanda yake
da alama da wani abu aka sanya cikin garwashin wuta,data lura sosai sai ta fuskanci
daga bangaren zainab ke fitowa,mai da kanta tayi taci gaba da kallonta,cikin
sakanni qaurin ya buwayeta,hakan ya sanya ta koma dakinta ta dauko burner da
turaren wuta ta fito falon wanda hakan yayi dai dai da sake ficewar fa'izan zuwa
harabar gidan,jikin socket din dake daura da kayan kallon ta jona ta cikata da
turaren wuta,mintina qalilan ya danne qaurin ya koma qamshi.

          Tana zaune taji bude get din gidan da qarar motar mukhtar din,wanda hakan
ke alamta dawowarsa,sai ta miqe ta koma daki ta sake feshe jikinta da turare sanna
ta nufo harabar gidan.

           Turus tayi ganin zainab gefan mukhtar tamkar zata shige jikinsa tana
dubansa,hannunsa riqe da cup wanda ta cika masa da zobo wanda tuni ya fara
kwankwada,yi tayi kamar ta juya saboda takaici sai kuna taga sam hakan baiyi tsari
ba,zai kuma faranta ran zainab har taci karenta babu babbaka tunda ta riga da taga
tsaiwarta.

         Fuskarta ta fadada da fara'a,sannu a hankai ta soma takowa gun wanda


takalmin qafarta duj da plate ne ya dinga bada sauti,hakan shi ya janye hankalin
mukhtar ya zuba mata ido,ta masa kyau sosai,ji yake kamar ya tafi ya sureta ya daga
sama yadfa suka saba,yau ta sauya masa sosai sumayyan,da wannan tunanin ta qaraso
inda suke ta tsaya gabansa tana jifansa da murmushi,so yake take sumayyata kinyi
kyau,so yake ya yaba mata,amma wani dunqulallen abun ya danne zuciyarsa,ya sake
duban qwayar idanunta sai yaji wani bacin rai ya kamashi,murmushin da yakeson maida
mata sai ya musanyashi da hade fusjarsa tsaf wanda hakan ya baiwa sumayyan
mamaki,saidai duk da haka bata karaya ba ta miqa hannu ta amshi jakarsa tana masa
sannu da zuwa.

          Bai amsa ba don ji yayi ya gaza amsawar


"Wash" zainab ta fada wanda shi ya sanya su duja suka dubeta,baikai ga tambaya ba
ta dora da nata jawabin
"Ka gani ko mukhtar,kaga abinda nake gaya maka ko?,yanzu fisabilillahi duk fadin
gurin nan bai isheta ba sai ta takani saboda tsabar raini?" Mamaki fal zuciyar
sumayya take dubanta,ya Allahu,nata salon kenan?matar da tazarar dake tsakaninsu ya
isa tiqa tiqan mata biyu su tsaya shibe zata ce har ta taka ta?,tamkar dama neman
abun fadan yake ya sake tunzura yana ji ana azqlzalar zuciyarsa,juyawa yayi yana
jifan sumayyan da wani irin kallo
"Halayyar banzan da kike son koya kenan ko sumayya?,halayyar da ban sanki da ita
ba?,to bari kiji ni bazan lamunta ba,bana son tashin hankali kin sani,har sau
yaushe zan huta daga dawowata ko iskar gidan ban gama shaqa ba daga shigowarki zaki
tada mana fitina?,to ki shiga hankalinki da ni idan ba haka ba zanyi mugun saba
miki", bata data cewa,to me zata fada ma tunda ya riga ya yarda ya hau kai kuma ya
zauna?,bata baki ne kawai tsayawa kare kai,saboda haka aladabce tace
" bansan na taka ta ba in sha Allah hakan bazai sake faruwa ba kayi haquri ya
mukhtar"sai da yaja fasali sannan yace
"Shikenan ta wuce"
"Au ni ba zaka ce ma ta ban haquri ba shikenan na gane matsayina wallahi" ta fada a
zafafe tana fashewa da kukan kirsa sannan ta kwasa tayi cikin gidan da sauri,don
sosai ta shaqa ba haka taso ya kasance ba,so tayi cikin biyu ayi daya,imma yace
sumayyan ta durqusa ta bata haquri,ko kuma tayi qoqarin kare kanta ko ta masa
turjiya ya jibgi banza a gabanta taci dariya ta more.

         Da idanu sumayyan tabi mukhtar din ganin yadda ya diba shima ya bita cikin
wani tashin hankali da yaji ya rikito masa sanda ya fara jiyo sautin kukanta,wanda
babu qwalla ko daya sai tsabar ihu da iya manaqisa,kai sumayya ta kada zuciyarta ta
karye,lallai babu shakka wani sabon SHAFIN QADDARAR TA NE YA SAKE BUDEWA CIKIN
KUNDIN QADDARARTA,sau ta lallashi kanta kawai ta shige ciki da jakar tasa ta ratsa
ta cikin falon nasu ta wuce sashen sa.

          A qalla ta dauki kusan minti talatin zaune kafin ya shigo bangaren


nasa,fuskarsa kadai zaka duba ta bayyana maka yanayin da yake ciki,kallonta yayi
tana zaune gu guda,tausayinta nason masa tasiri amma wani abu mai qarfi na maye
gurbin tausayin da jin haushi
"Na kai maka ruwan wankanka" tace da shi,bai amsa mata ba illa rage kayan jikinsa
da yayi ya shiga wankan kawai.

         Tana zaunw taga yana shiryawa cikin yadin kaftan ruwan zuma,ya kammala ya
zira hularsa tare sa daura agogom hannunsa,muqullin motarsa da taga ya dauka shi ya
tabbatar mata da cewa lallai fita zaya yi,da hanzarinta tace.
"Ya mukhtar baka ci abincinka ba fa,kuma naga kana shirin fita"
"Sai na dawo" ya fada yana ficewa ba tare da ko ya waiwayeta ba,sai ta zube agun ta
sanya kuka,da sauri ta sanya tafin hannunta ta qunshe kukan saboda fadan da
zuciyarta tayi mata na ba kuka zata yi ba,take ta kama ambaton 'Allahumma la sahla
illa ma ja'altahu sahla,wa anta taj'alal hazna iza shi'ita sahla'.

         Tana daga nan amma tana iya jiyo muryar zainab wanda hakan ya tabbatar
mata fita zasuyi kenan.

          Kusan awa guda da rabi ta share zaune tana ambaton sunayen Allah,ya zuwa
lokacin quncin dake cin ranta ya ragu qwarai,wayarta ta soma ruri,ganin sunan
mukhtar ya bata mamaki amma sai ta daga gabanta na faduwa jikinta na gaya mata ko
dai ba lafiya ba,a daqile ya amsa sallamarta sannan ha dora
"Ya zuwa yanzu nasan abinda kika girka tun yamma yayi sanyi,ina so ki tashi ki hada
min fried rice nan da awa guda ina bisa hanya" bata da hurumin da zata musanta masa
tunda iko yake da ita,biyayya a gareshi kuma tilas ne matuqar bai sabawa
mahaliccinta ba,tuni ya katse wayar don haka itama ta ajjiye ta nufi kitchen  kai
tsaye.

         Komai suna da shi alhamdulillah tunda yanzun kam arziqi ya zaunawa mukhtar
din gwargwado,da hanzarinta ta shiga hada komai,cikin abinda yai qasa da awa daya
da rabi ta gama tunda ba wata mai yawa bace can,bugu da qari kuna ta horu wajen
aiki.

         Dakinta ta wuce ta debo kayan baccinta ta koma sashen mukhtar din,cikin


toilet dinsa tayi wanka ta shirya tsaf,wannan duka cikin karatun anty dije
ne,falonsa ta koma ta kwanta saman doguwar kujerarsa,a hankali tunani yayi awin
gaba da ita tanayi taba sauke ajiyar zuciya.

         Tarayyarsu da mukhtar tun farkon aurensu kawi yanzu,bata taba sanin so ba


sai a kansa,da shi ta saba da shi ra qarasa mallakar hankalin kanta,dashi ta qarsa
cikasa kammaluwar hankali da rayuwarta,ta yaya zata iya jure wani baqin lamari daga
gunsa ta farad daya?,ya zata iya lamuntar juya baya daga gunsa,idan ma har laifi ta
masa a yau kam zata kawo qarshen horon da yake mata.

         Tana tsaka da tunanin ta jiyo muryarsu suna shirin turo qofa,hakan ya


sanya tayi hanzari foge qwallarta,tare suka ahigo manne da juna,sai ta kauda kanta
daga saitinsu din ragewa kanta kaifin kibiyar mashin da ta soketa,ba haka zainab
taso ba,wacce iriyar mayyace yarinyar mara zuciya,ita miji bai bata mata rai tayi
fushi da shi ne,sai ta zame jikinta daga na mukhtar tana masa sallana hannunta
dauke da leda mai dauke da tambarin SS store.

        Wuceta yayi kamar bai ganta ya ya shiga daki fuskarnan kamar ta mayunwacin
zaki,tamkar ba shine ya shigo yanzun yana dariya ba,jikinta sai ya mutu murus ta
kasa tashi har aka kusan cin minti talatin sannan ta yunqura ta tashi.

        Gefan gado ta sameshi yana waya wanda da alama da zainab din yakeyi,ya
ilahi ba yanzu suka rabu ba kuma?,sumayya ta fada a zuciyarta,kafin ta qaraso ciki
ya kashe wayar yana qoqarin kwanciya
"Yaya kace na maka fried rice kuma naga kana shirin kwanciya baka ci ba" a banzace
yace
"Bani zanci ba,don ni naci abinci gidansu zainab na cika cikina,ita zaki kaimawa
ita ke sha'awar ci" shiru tayi ta tsaya cak kamar an kafata,me kenan?,wannan zallar
wulaqanci ne,dama saboda cikin zainab din ya tasheta tara saura na dare ta hau
sanon girki?
"Ko ba zaki bane ni na taso da kaina na kai mata?" Ya fada yana daga kwancen,tabbas
da ta iya rashin kunya yau da zata yiwa mukhtar ko yaya take,saidai kowanne tsuntsu
ance kukan gidansu yakeyi, tunda ta taso gidansu dai dai da rana daya bata taba
katarin ganin innarta ta yiwa malam musu ba duk girma da wuyar umarnin da ya
bata,sai ta kada kai da dauki flask din ta nufi sashen zainab din.

        Har ta rufe qofar falonta amma ta qwanqwasa mata saboda cika umarnin
mukhtar din,minti biyu tsakani aka bude,tana sanye da kayan bacci,kallonta tayi
daga sama zuwa qasa sannan ta yatsina
"Ya akayi"
"Abincinki" ta bata amsa a qaice
"Mtsweeew,bazan iya ci ba gaskiya" bata jira sauran abinda zai biyo bakinta ba ta
juya,taku na shida cikin na bakwai taji tace
"Kawo dai na taimaka miki na dandana kada kiyi wahalar banza" idan kujerun dake gun
sun amaa to itama ta tanka,banza ta baiwa ajiyarta taci gaba da takunta,sai ta
tsinto muryarta
"A sannu dai yarinya,kishi da zainabu abu babu dadi,hattara wlh da ni,yanzu kika
fara gani sai kin fice sa qafafunki" ta fada tana qoqarin maida qofarta
"Ni nafi qarfinki,na kuma fi qarfin ire irenki,irinki dubu ma wallahi saidai suga
sumayya su qyale" cike da mamaki tace
"Au haka kikace?,bari Allah ya kaimu gobe zaki amshi sakamakon wannan diban
albarkar da kika yimin hannun mukhtar,sai nasa ya dakaki wlh cikin gidan nan" tsaki
sumayyan ta ja sannan tace
"Mukhtar ne taqamarki ni kuwa Allah na riqe,da ni dake maga wanda yayi riqo da
kakkaurar igiyar da bata tsinkewa" daga haka ta juya ta barta gun sake da baki tare
da saqa mugun zare sake tada qaimi a kan sumayyan,babu shakka sai tasa an mata
daurin butar malam yadda zata zamo qarqashin ikonta kamar yadda ta soma maida
mukhtar.

        Ta jima tsugunne gaban gadon tana zubda hawaye tare da roqon ya yafe mata
idan ta masa wani laifine da ya canza shi,yana jinta zuciyarsa na masa suya yana
tuhumar kansa na dalilinsa na quntatawa sumayyar,saidai wani sashe mai qarfi na
zuciyarsa na gaya masa yayi dai dai,da wannan ya shareta har ta gaji da tsugon nan
ta miqe.

         Bata bari tayi asarar daren ba,alwala ta daura,ta kuma duqufa qwarai wajen
roqon ubangiji ya kawo mata haske,ya tsaresu ita da mukhtar din,tana yi ta zubda
hawaye masu dumi,lallai sai yanzu tasan meye rayuwar aure,ashe a baya duk wasa
takeyi?kallon kitse take yiwa rogo?,ya jima cikin bargon yana kallonta,tausayinta
na son tasiri cikin zuciyarsa amma hakan ya gagara,a haka bacci yayi awon gaba da
shi.

        ****     ****    ****

*WATA RAYUWA..........*

       Wata bahuguwar rayuwa mai ban mamaki ta soma yi cikin gidan wadda ko cikin
nafarkai mafarkinta bai taba biyowa ta irin wannan bigiren ba.

        Zainab ta zama tauraruwa mai wutsiya cikin gidan,a zahiri idan kayi naxari
da tsinkaye ba zaka kawo ita ke sarrafa lamuran gidan ba,saidai ga duk wanda ya
taba katari da fadawa halin da sumayya ke ciki tashin farko zai fuskanci inda zaman
gidan ya sanya gaba.

          Ta bawa asiri amanna,kusan shi ya zame mata jagorar zamowarta mata ga


mukhtar din,baya ga haka,macace mai tsananin kissa wadda ta cakuda ta da asirin
take matuqar tasiri kan mukhtar din,cikin salo da sanabe zata bashi umarni kai
tsaye zaya aiwatar,wanda idan kai dake gefe ka kalla zakayi zaton tsabar iya
biyayya ce da iya zama da miji,saidai ina sam ba haka abun yake ba,asiri ke yawo
kan qirji da qwaqwalwarsa,dukkan wani lamari da ikon sarrafawa na hannunta,abu GUDA
DAYA TAK da yayi mata karen tsaye cikin tafiyar da aikinta shine SUMAYYA,ta kasa
maida ita qarqashin mulkin nallakarta,wanda hatta su yaya yahanasu yanzun na
qarqashin ikonta,,suna jin zafin yadda take mulkasun amma koda kudi basu isa suyi
qorafi ba,saidai a bayan idonta suyita zagi da qorafi iyakarsu kenan.

        Abu guda data fuskanta shine,sumayyan ta lazumci karanta qur'ani,alwala ta


zama abokiyarta,qur'ani ya zama abokin hirarta,koda wani abu ya tsorata ta abu na
farko dakw fitowa bakinta shine SUBHANALLAH KO BISMILLAH,bata mantawa akwai ranar
da aka kawo mata yaronta da ta haifa da bashir wato nafi'u,yaro ne maras ji sosai
suka batawa mahaifinsa tarbiyyar yaro tunda yanzun haka yana hannun mama amarya ne
mahaifiyat zainab,yana wasa da macijin roba,daidai fitowar sumayya ya wurga mata
shi wanda sam bata ma kula da yaron na gurinka ba,sosai ta tsorata amma abinda ya
fara fitowa daga bakinta shine BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM,daga haka ta shige zainab
din na taya dan nata dariyar yadda ya tsorata sumayyan kallo basu isheta ba.

          Kusan babu wanda yasan halin da take ciki banda anty dije itama don tana
ganin ita daya hankalinta bai kai mizanin sarrafa matsalolin irin wadan nan ba ita
daya,tana amfani da shawararta kuma ta qaruwa tare da ganin nasarori,duk da ayanzun
ta tattara lamarin mukhtar tana biyarshi da addu'a,sau tari wani lokacin ko ganinta
ta fuskanci baison yi,abinda tafi daga mata hankali kenan,wasu lokutan kuma sai ka
ganshi kamar ba shi ba ya koma mata yaya mukhtar dinta.

          Duk abinda ta gani tana dorashi ne kan mizanin nan da hausawa kance AURE
IBADA NE ta yadda kumma tayi imani da hakanne,don sau tari anty dije na maimaita
mata kalmar.

_muje zuwa babi na gaba_

*ina jin dadin comment dinku,ku karbi jinjina daga gareni*

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

2⃣6⃣

_______________________

*Bismillahir rahmanir rahim*

*wa may yattaqil laha yaj'al lahu min amrihi yusrah*

_duk wanda yaji tsoron Allah Allah zai sanya masa sauqi cikin lamuransa_
_______________________
        Su biyun ne zaune cikin falon kowa na sabgar gabanta,sumayya na guga saboda
socket dinta ya lalace ya tilasta mata fitowa falon don yin gugar,yayin da zainab
ke zaune saman kujera qafa daya kan daya kamar yadda ta saba zama kenan cikin izza
da nuna ita watace,gama share falon da mopping dinta kenan ga zauna don ta huta,duk
wanda ke da girki shike wannan aikin,ba laifi zainab din nada tsafta dai dai
gwargwado.

          Sallamar da ake zabgawa daga harabar gidan shi yaja hankalinsu,zainab ce


ta miqe tare da ajjiye remote din hannunta ta bude qofar ta fita,fadima ce ita da
jamila diyar yaya yahanasu,bakinsu a washe suka soma takowa zuwa inda take
"Ku tsaya daga nan da Allah ku cire takalmanku kada ku batawa mutane waje yanzu na
gama mopping" da fari jamila tayi dum amma ganin fadima ta tsugunna ta cire nata ya
sanya itama dole ta cire,juyawa tayi fuska a cusgune su kuma suka bi bayanta.

           Zama tayi kan kujerar ta maida qafarta yadda take,suna shirin zama saman
kujerar da sauri tace
"A'ah,da Allah ku zauna a qasa,ai carfet ne,idan kuma baku iyawa ku tafi can ga
nata kujerun can ku zauna a kai" tsabar qin da suka yiwa sumayyan suka gwammaci
zama a qasa,suka gaidata ta amsa da qyar,ko kusa baau dubi sumayya dake guga
ba,haka suma ko qurar data kwasosu bata kalla ba
"Dama yaayaa ce ta aiko mu gun yaya muntari" inji fadima,wani kallo ta watsa musu
"Bacci yake,ku fadi saqon sai na gaya masa idan ya tashi" shiru suka dan yi sannan
suka dubi juna alamar basu son fada,hakan yasa ta dubesh kai tsaye
"Sai ku tashi ku koma da saqonku,ko kuma wadda ta aiko kun tazo da kanta"
"Yaaya yahanasun?" Suka fada tare cikin mamaki
"Eh,ita din mana,to meye?,kunga ku tashi ku bani guri da Allah,muta ne sai shegen
binbinin tsiya haba" ta fada tana jan tsaki tare da mai da kanta gun t.v.

         Zuciya ce ta zowa jamila wuya,bayan sun miqe sai ta kasa shiru


"Kema halin fa'izan gareki?,lallai akwai butulu a duniya da yawa,to wlh bari
kiji,baki isa ki shiga tsakaninmu da dan uwanmu ba wallahi"kallon banza ta yi mata
sannan ta saki murmushi tana kada qafa
"A'a'ahhhhhh.....yaro man kaza,quruci dangin hauka"
"Ke za'a gayawa wannan ai mahauk......."
"Idan kika sake bakinki ya qarasa wallahi sai na tashi na tsitstsinka maki mari,na
kuma tattaka ki naga wanda ya tsaya miki...." Ganin yadda ta yunquro kamar zata
sanya musu dukan ya sanya fadima ta janyeta suka fice jamilan na ciccika baki tana
cewa "ai umman zata zo naga uban da ya isa ya hanata ganin dan uwanta,mata duka sai
shegeb butulci duk wadda ka yiwa rana sai ta yi maka dare" itakam sumayya na
gefe,ci kanku bata ce ba balle ta dago ta dubi abinda ke faruwa,tana jin zainab din
na ci gaba da banbaminta mai kama da jirwaye da kamar wanka
"Ni wallahi babu wata yar miji da zata shiga rayuwata tunda ba ita ke aurena
ba,idan da can an saba muku toni wallahi bazan lamunci a dinga tatsemin miji ba"
ita dai ko kallo bata isheta ba,cikin hakan mukhtar ya fito sanye da doguwar riga
jallabiya
"Ke dawa haka ina daki ina jiyoki?"
"Ni da danginka mana,haka akeyi basu da aiki sai zuwa roqo tsakani da Allah?"
Zancan sai ya baiwa sumayya mamaki,iko sai Allah,ke kudin nan ba naki bane,kuma
wanda suka roqa din ai dan uwansu ne ko?.
Tsaki yaja yana zama kan daya daga cikin kujerun
"Kudi take so zata biya kudin makarantar yara,na kuma gaya mata tayi haquri ribar
hannuna na baki zaki fara saida mayafai,kasuwa kuma yanzun sai a hankali ba kamar
da ba amma ta qi yarda,gwara da suka tafi din don ko sun sameni ba ni babu abinda
zan iya bayarwa"
"Ato nidai na kora musu jawabi" ta fada tana tafa hannuwa
"Samamin ruwan zafi du Allah" ya fada yana kashingida.
"Gaskiya muntari na fara gajiya,aikin gidan nan fa akwai wuya kawai ka sama min mai
aiki" ta fada a shagwabe,murmushi ya danyi sannan yace
"Kada ki damu,kafin a kama azumi za'a samar mikin ki bada cigiya"fari tayi da ido
cikin salo" kai dear na ko gode....bari na kawo maka"miqewa tayi tana wani rangwada
tare da sakin wani dan qaramin fito na jin dadi,a duniya bata da burin wulaqanta
sumayya,tunda ita taqi samuwa to ko ta hanyar mukhtar din kawai ya isheta tunda
tana cimma burin cusguna mata.

          A hankali idanunsa ya sauka kanta,tana gefe daya tana guga abinta,sai ka


rantse bata cikin falon ko batasan meke faruwa ba,saidai can qasan zuciyarta ita
kadai tasan meke nuqurqusar zucida da gangar jikinta baki daya,baki daya ba mukhtar
dinta take ganin ba a yanzun,siffar ce kadai tasa,rabon da ta sanya shi idaunta
kwanaki uku kenan,idan yaso yana iya daukar kwananta ma ya kaiwa zainab din,saidai
ci kanka bata taba ce masa,ta debo idanu kawai ta sanya musu.

        A nutse yake nazarinta wani abu na fisgarsa,sosai yaga ta fada ta sake


haske,qirjinta ya sake cika sosai sai hancinta da ya sake fitowa saboda rama,riga
mai dogon hannu da skert ne a jikinta na wani yadi mai roba,kanta na kame da ribbom
don ta jima rabonta da kitso
"Sumayyah" ya furta a hankali ba tare da ya san kalmar ta fito ba,sarai ta jishi
amma sai tayi zaton gizo kunnenta yake mata,saboda haka tayi banza da shi
"Sumayya ba zaki kula ni ba?" Ya kuma fada a tausashe,sosai muryar ta bugeta,murya
ce irin wadda yake mata amfani da ita a zamanin BAYA,hakan ya sanya ta gaza
daurewa,sai ta daga idanunta da suka cika taf da qwalla ta azasu kansa,kallon kallo
suka farayi kowa zuciyarsa da gangar jikinsa na shirin motsa masa soyayyar dan
uwansa da suke tunanin sunyi bankwana da ita.

         Muryar zainab dake takowa daga kitchen ta raba tsakaninsu,sai ta gaza ci


gaba da gugar ta zare socket din ta tattara kayanta ta wuce dakinta,kan gado ta
fada ta saki wani marayan kuka,zuciyarta da jikinta na azabtuwa da qaunar mukhtar
da kewarsa.

         
       ****     ****      ****

       Da izzarta da bacin rai ta diro gidan tun qarfe tara na safe,saidai ga


mamakinta tana qarasowa cikin falon ta qwala sunan zainab din wadda ta fito cikin
kayan bacci sai ta nemi duk wani bala'i da ta tanada ta rasa,hasalima ma sai ta
fara gaida zainab din,sheqeqe tace da ita
"Lafiya?,me kika zo yiwa mutane a gida tun farar safiyar nan,ko farkawa masu gidan
basu yi ba?"
"Haba ko hutawa ai nayi ko zainabu abu"
"Hutu kika zo yi gidan da ba naki ba?" Ta fada tana rungume da hannunta a qirji
"A'ah....to....to daka jiya na aiko yara zasu karbi kudin makarantarsu ne sai kuma
basu samu ganin kawun nasu ba,shine ni na biyo sahu,saboda koda yaushe za'a iya
korarsu daga makaranta" gyara tsaiwarta tayi
"Au basu gaya miki rashin mutunci da rashin tarbiyyar da suka zo suka yimin ba?"
Duk da cewa tasan komai amma sai ta samu kanta da gaza nunawa
"Su su fadiman?"
"Eh su din fa,don haka ina mai sanar miki cewa sun jaza miki,ba zaki samu damar
ganin mukhtar ba,bacci yake koma ba haka ba wallahi ba zaki ganshi ba,ki tashi
sawunki a likkafa ki tafi,babu mai matsawa mijina da shegen roqe roqe" idanu yaya
yahansun ta zuba mata,tana so tayi masifa amma ta kasa,kamar an wanke zuciyarta
haka takeji.

      Tunda ta idar da sallar walha ta bingire da baccin da batasan sanda ya


dauketa,muryar zainab din ta dinga jiyowa sama sama wanda shi ya farkar da ita,bata
da niyyar fitowa amma tilas ta fito din sabida yunwar da ta tashi da ita.

         Zainab din na tsaye kan yaya yahanasun tana zubda shika shikan rashin
mutunci,yaya yahan tayi muqus kamar ba ita ba sai idanu da take bin zainab din cike
da mamaki ba tare da ta iya tankawa ba,fes sumayyan ta fuskanci meke faruwa tunda
na jiya ma gaban idonta akayi,sosai taji ranta ya baci,a rayuwarta ta tsani
wulaqata babba sam,a kwanakin quruciyarta har kuka idan taga babba cikin wata
iriyar rayuwa,ko ba komai ko bata girmesu ba yaya yahanasun ai tsatson mukhtar ce
duk lalacewarta,ranta taji yana baci hakan ya sanya ta gewaye ta bayan kujerun ta
bude qofar da zata sadata da falon mukhtar zuwa dakin baccinsa kai tsaye ta
shige,wanda hakan shi ya ja hankalin zainab,da sauri ta fara kiranta da niyyar
tsaidata saidai ko qurar data kwaso bata kalleta ba bare ita,hakan ya sanya ta rufa
mata baya,tana shiga falon ta bame qofar dai dai lokacin da zainab din ke qoqarin
sanya qafarta a falon,tana iya jiyo hayaniyarta akan ta bude qofar kada ta tasar
mata miji,banza ma ta fita saboda haka ta nufi dakin gadon.

           Kan side bed drower idaninta ya fara sauka sanda take qoqarin isa ga
mukhtar din wanda ke daga can saman gadon yana barci,garwashi ne tare da wani
qullin tsumma a kai,a hankali ta taka zuwa inda kayan suke,idanu ta zuba musu tana
nazarinsu,babu alamun turaren wuta zata sanya don bata ganshi ba,hakanan taji bata
aminta da qullin ba musamman da taga launin wani irin tarkace dake ciki,sai ta
kunce qullin bakinta dauke da addu'o'i ta tura bandakin mukhtar din ta shiga,cikin
masai ta zazzage dukkan maganin tayi plushing dinsa.

        A hankali ta soma ambaton sunansa hannayenta harde a qirjinta fuskarta a


dinke tsaf,idanunsa ya soma warewa kanta kafin ya gama budesu baki daya cike da
mamaki,ya manta rabonsa da ya ganta cikin dakin,zai ambaci sunanta ta dora yatsanta
kan lebanta sannan kai tsaye tace
"Tashi" ba musu ya yaye bargon ya tashi,sai ga taka zuwa gefansa ta zauna,idanunta
sosai cikin nashi ta soma magana muryarta can qasa
"Wacece yaya yahanasu a gunka?" Cikin rashin fahimta yake dubanta,sai kuma ya bude
bakinsa a hankali
"Yayata ce"
"Zainab kuma fa" hade rai yayi yana jin qin wani abu da zai taba martabarta cikin
ransa
"Mata ta ce"
"Cikinsu wa zaka iya sauyawa" take yaji zuciyarsa ta harzuqo
"Kinga....bansan....."
"Riqe maganarka tukun" itama ta katse shi
"Ka tashi ka wuce kaje tana son ganinka yanzun nan" ta fada kanga tsaye cikin bashi
umarni tare da miqewa abinta tana shirin ficewa,binta yayi da ido cike da mamakin
yadda yau ta dumfareshi kai tsaye a yau din tana kuma bashi umarni,hakanan yaji ya
kasa musanta mata,sai ya sauko da hanzari ya zura takalminsa yabi bayanta.

         Bakin qofa suka tadda zainab,ga mai hankali kallo daya zaya yi mata ya
gane hankalinta a matuqar tashe yake,ita kadai tasan wahala da kuma kudin da ta
kashe kafin samuwar maganin,a yau akeso ta yiwa mukhtar din ya kuma shaqi hayaqin
sosai,kusan sai yau ta samu wannan damar,amma ta fuskanci tana naman bare
mata,saboda haka suna fitowa ta fada dakin don duba abinda ke wakana ba tare da ta
kuma bi ta kan su yaya yahanasun ba.

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖
*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

2⃣7⃣

______________________________________
*Bismillahir rahmanir rahim*

*wa may yattaqil laha yaj'al lahu makhraja,wa yarzuquhu min haisu la yahtasib*

_duk wanda yaji tsoron Allah to Allah zai sanya masa mafita(cikin lamuransa),ya
kuma azurtashi ta inda baya zato_

*ya Allah kai mana baiwa da jin tsoronka,ka azurta mu da dukkan kyakkyawa*

___________________________________

         Tana bayansa har suka qarasa inda yaya yahanasu taje zaune tana kallon
ikon Allah,a mutunce sumayyan tace
"Yaya ina kwana?"
"Lafiya" ta amsa babu yabo ba fallasa,tana son ganin kyawun kyautatawar data mata
idan da hali ta mata godiya amma sai ta kasa,dama sumayyan ba domin ita tayi
ba,tayi ne domin girman Allah da kuma girman da zumunci ke da shi a wajen
ubangiji,hakanan ko ita ba zata so ace yau yaya abbakar ya auri wata da zata
rabashi da su ba,ko ita ta haifa ya auri wadda zata rabasu din,kitchen ta wuce ta
soma hadawa kanta dan abinda zata iya ci,ko kafin ta kammala ta fito ma falon babu
kowa da alama ta tafi,sai ta zauna ta fara kurbar ruwan shayinta.

         Kamar daga sama zainab din ta fito tana banbamin masifa kamar zata ci baki
mukhtar na biye da ita yana son shan gabanta amma ya gaza cimmata,qerere tayi a kan
sumayya wadda ko mutuncin kallonta bata samu ba
"Uban wa ya saki ki tabamin turaren wuta na?" Sosai abun ya bata mamaki,har tana
iya bude baki tayi cigiyar kayan data tabbatar ba na Allah bane?,qare matsota tayi
tana huci ta kuma maimaita tambayar tata,ganin zainab din na qoqarin kai hannunta
jikinta ya sanya sumayyan dubanta
"Kada ki soma,don fankan fankan bata kilishi wallahi kika dakeni bazan dubi
girmanki ba tsaf zan rama" idanu ta zaro tana nuna qirjinta
"Ni zaki daka don ubanki,to dokeni din"
"Wai meye haka ne zainab ba tun cikin daki nake miki magana ba?,ke sumayya tashi ki
koma dakinki" wani kallo ta watsa masa sannan ta dakata da shan tea dinta
"Kayi haquri amma bata isa ba wlh don yanzu na fito ban kuma kammala uziri na
ba,kana iya janye matarka idan na gama na tafi ita ta fito" ta fada tana ci gaba da
kurbar shayinta duk da wata iriyar tafasa da zuciyarta ke mata,jinta take dai~dai
sa su baki dayansu,banda daraja da girman sa da take gani babu abinda zai hana ta
yayyaba masa baqaqen maganganu masu zafi
"Muje nace zan biyaki kudin ko?" Sai ta sauke ajiyar zuciya,dama abinda yafi
damunta kenan,don sake samun wani maganin wannan da sauqi  
"Allah ya ceceki" ta fada tana huci sannan ta juya tabi mukhtar din,cak shayin ya
tsaya mata a wuya,ambaton sunan Allah ta dinga yi don ya kawo mata dauki,tabbas sai
yau ta tabbatar mukhtar dinta ba cikin hayyacinsa yake ba,kayan karin da bata gama
ci ba kenan.

**** **** *****

         Wani nannauyan bacci ne ya dauketa tun bayan kammala sallar asuba,hakan ya


sanya bata tashi ba sai wajen sha daya saura na rana saboda zafin rana da ya fara
hudo labule.

            Da wata mahaukaciyar yunwa ta farka,saboda haka bandaki kawai ta shiga


ta wanko bakinta ta shiga kitchen don samarwa kanta abinda zata ci,don bata sa aka
ba tasan ba samun abun kari zata yi ba,haka ne yake faruwa duk ranar girkin zainab
din,shi kansa mai gidan wani lokaci sai dai ya fita haka.

          Sam bata lura da meke faruwa ba sai data shiga cikin kitchen din
sosai,nafi'u ne yaron zainab tsaye dare dare kan stool yana sauke dukkan farantanta
na tangaran dake jere cikin glass drower dinta yana sakinsu qasa daya bayab daya
suna tarwatsewa.

        Da sauri ta qarasa ciki tana kiran sunansa cikin tsawa,ko gezau baiyi ba
bare ya fasa aikata abinda yakeyi din,hannunshi ta riqe gam kana ta saukeshi daga
kan stool din tana dubansa ransa a bace
"Baka da hankali?,ko bakasan me kake yi ba?,ko bakasan abin amfani kake lalatawa
ba?",cikin rashin kunya yace mata
"na sani mana"abun sai ya bata haushi ta kama kunnansa ba tare da ta murde ba tace
" wato tsabar rashin ji ne kenan ko?"
"Sakarmin kunnena ai kema bake kika siya ba,kuma Allah ya isa na da tabamin kunne
da kikayi" sosai yaron ya bata haushi da mamaki,ta sanya tafin hannunta ta buge
masa baki,wata qara ya saki kamar wanda aka sanya wuqa aka yanke masa maqogaro yana
fadin "wayyo bakina wayyo mama ta fasamin baki".

         A hautsine ta fado kitchen din dama tasan hakan na iya faruwa,don ita ta
sanyashi,saboda har yau bata huce takaicin asarara maganinta da sumayyan ta jawo
mata ba,duk da mukhtar din sai da ya biya ninkin kudinsa,da sauri ta qarasa inda
suke tsaye ta ture sumayya tana fadin
"me kika yi masa?,me tayi maka nafs(da yake haka take kiransa)"
"Bakina ta dakarmin mama duba ki gani"hannunsa ta sauke tana duba bakin,babu wani
abu da yayi tunda duka duka dukan data masa ba wani mai zafi bane,waiwayawa tayi ta
dubi sumayya dake tsaye rungume da hannu tana dubansu
" dukarmin yaro kikayi saboda bakisan ciwon haihuwa ba ko?,to wallahi sai na rama
masa"sai kuwa tayo kan sumayyan gadan gadan.

         Ko alama bata motsa ba har ta qaraso inda take,ta daga hannu da niyyar
zuba mata mari caraf ta kama hannun nata ta yarfar da shi gefe,sannan cikin bacin
rai tace mata
"Bansan ke din wace iriyar uwa bace,ban kuma san irin tarbiyyar da kika bama
yaronki ba,amma bari na gaya miki,matuqar irin wannan tarbiyyar ita kika bashi to
ba shakka kin cuci kanki,abu na gaba duk iya zaluncin da zaki aikata cikin gidan
nan kiyi,Allah na sane da ke,amma kada ki soma gigin daukar hannu kice zaki dake
ni,don baki haifeni ba,ba kuma kisan ciwo na ba kamar yadda kika ce bansan ciwon
haihuwa ba,kuma kema ba Allah kika yiwa fadanci ba ya baki,ganin........".ihun da
zainab din ta qwalla gami da dora hannu bisa ka ya dakatar da ita daga maganar da
takeyi,sai tayi sororo tana dubanta tare da tunanin ko zainab din nada ciwon hauka
ne dake tashi lokaci bayan lokaci?.

         Sam bata fahimci tarko bane ta dana mata sai data ga shigowar mukhtar
cikin kitchen din a rude,ashe tuni taga giftawar inuwarsa ita zainab din,binsa tayi
da kallo sanda ya nufi zainab,ta manta kwana nawa rabon da ta sanyashi cikin
idanunta,ranar qarshe kawai zata iya tunawa da bata kuma ganinsa ba sai yau,itace
randa ya rufeta da fada tamkar zaya daketa,sabida tayi dan wake abincin dare,ita
kuma zainab tace sam bazata ci ba ai dan wake ba abinci bane,ya umarceta ta shiga
kitchen ta yiwa zainab din shinkafa da miya qarfe goma na dare,umarnin ya yi mata
tsauri saboda haka bata ko tanka ba ta wuce dakinta tayi kwanciyarta bayan ta kulle
qofarta,don tana da yaqinin zaya iya biyota,ilai kuwa ya biyo sahun nata,yayi bugun
duniya taqi ta bude masa,hakan ya sake harzuqa shi,haka ya koma tare da ci mata
alwashin sai ya sabar mata,to tun daga ranar rabon data karbi girki ma cikin
gidan,saidai idan sun kammala a barshi a kitchen,idan tana da sha'awarci ta
diba,idan bata ga dama ba ma ko kallo bai isheta ba.

       "Wato ke kin zama 'yar iska mara mutunci ko?" Ya fada yana nufota cikin huci
bayan zainab ta gama tsara masa qarya kan abinda ya faru,hannu tasa ta toshe
bakinta saboda yadda taji kanta ya mata dummm,kalmar ta yiwa qwaqwalwarta tsauri
haka nan ta yiwa kanta nauyi,ita mukhtar ke kira da 'yar iska?,kalmar da babu wani
mahaluqi da ya taba jifarta da ita?,da sauri ta juya ta fita daga kitchen din cikin
sassarfa saboda kukan dake shirin qwace mata ba wai don mukhtar din dake nufota ba.

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

2⃣8⃣
_________________________

*Bismillahir rahmanir rahim*

*lillahi mulkus samawati wal'ard,yakhluqu ma yashaa,yahabu limay yasha'u inasan


wayahabu limay yasha'uz zukur,au yuzawwijihum zukranaw wa inasaa,wa yaj'alu may
yasha'u aqima*

_mulkin sammai da qassai lallai na Allah ne,yana halittar abinda yaso,ya bawa wanda
yaso kyautar(d'a) 'ya'ya mata ya bawa wanda yaso kyautar 'ya'ya maza,ko kuma ya
cudanya musu maza da mata,ya sanya kuma wanda yaga dama ya zamo bakarara(wanda baya
haihuwa)_
*ya Allah ka azurtamu da managartan zuriyya shiryayyu saboda annabinka S A W*
__________________________
      Yau babu tantama abinda ke mata kaikawo a zuciya ya tabbata,mukhtar ya daina
sonta ya daina mararin ganinta,wannan wacce iriyar rayuwa ce?,haka mata keji duk
sanda suka samu juya baya daga wajen mazajensu ba tare da haqqinsu ba?,me yakai
wannan zunubi shiga tsakanin ma'aurata?,shiga tsakanin masoya?,masoyan da suka gina
zuciyoyinsu da qaunar juna,tsaftatacciyar qauna ta fisabilillahi. Wani mugun amai
mai zafi taji yana taso mata,da qyar ta samu ta isa bandaki,ta dinga kakarin aman
tamkar hanjin cikinta zai fito,saidai banda wahala da yunquri babu abinda abinda ya
fita din saboda babu komai cikin cikin nata,don a yanzu ba kowanne lokaci take
yarda da abincin zainab ba. Haka ta gama wahalarta sai yawu kawai data fitar ta
sakarwa kanta shower tana wanka tana kuka har ta kammala sannan ta dawo cikin dakin
iska na dibarta ta zabi doguwar riga ta sanya ta koma saman gadonta tayi dai
dai,jinta take wani iri daban,zazzabi taji na son rufeta,haka ta yunqura ta sha
paracetamol ta dawo ta kuma kwanciya,tunani ta shiga mai zurfi lokaci lokaci tana
dauke hawayen dake bin kuncinta.

       Kamar daga sama ta dinga jiyo sallamar zainab qanwarta,daurewa tayi ta miqe
ta dawo bakin qofar dakinta don ta sanar mata tana ciki kada zainab tayi qaryar
bata nan,sai data tabbata zainab din taji sannan ta koma bakin gadonta ta zauna har
ta shigo. Kallo daya ta yiwa sumayyan tace
"Lafiya kike kuwa anty" qoqarin qaqalo murmushi tayi sannan ta dan ja tsaki
"Qalau nake,yau ne kinga na tashi bana jin dadin jikina da bakina gaba daya"
"Yaya kamar fa kuka naga kinyi" sai ta basar ta hanyar fadin
"Barni kawai,nida mukhtar ne ya matsan sai da nasha magani,ni kuma kinsan bana son
qwayoyi" sai zainab din ta gamsu da maganarta ta zauna tana fadin
"Kamar kuwa mamanmu ta sani kinga tace sai na tsaya tayi dambu mutuminki na kawo
miki",ba jira kuwa ta sanya hannu ta janyo flask din ta bude ta soma ci. Sosai taji
dadinsa cikin bakinta,sai data ci fiye da rabi sannan ta ajjiye.

      Bata sake fitowa daga dakin ba ranar,kusan yini sukayi ita da zainab tana
mata 'yan gyare gyare cikin dakin,koda ta yunqura don sama mata abinci sai tace
azumi ma takeyi,a nan take gaya mata mama tace taje ta yiwa anty dije sallama zasu
koma abuja ita da mai gidanta,gwamnatin tarayya ta qara masa matsayi,duk sai
jikinta yayi sanyi,bata son rabuwa da anty dijen,idan ta tafi bata da gun wanda
zata je su shawarta matsalarta kenan,anty dije zata tafi ta barta a sanda alamu ke
nuna matsalolinta qara qarfi suke. Sai taji zuciyarta na neman raurawa amma sai ta
aro dakiya da juriya ta yafa wa kanta gudun kada zainab din ta fahimci wani abu.

          Sai yamma lis zainab ta tafi ko banza ta debe mata kewa sosai kuwa,a
ranar ta sanar da mukhtar tana so taje wajen anty dijen washegari,saboda jibi zasu
tafi,Allah ya dorata a kansa ranar tambotsan nasa da sauqi,don a dakinsa ma ta
kwana duk da zaman kurame sukeyi.

     ****      ****      ****

      Tun goma na safe ta kammala shirinta tsaf cikin shadd ja wadda aka yiwa adon
stone work baqi,ita kanta sai data tsaya ta kalli kanta,duk damuwar da take ciki
amma sai taga ramarta bata fito kamar baya ba,mamakin yadda ta qara haske da cika
takeyi,haka ta yafa baqin mayafi a kanta ta saqala baqar jaka ta fito.

          A harabar gidan sukayi clashing da su kasancewar harabar ba mai girma


bace,tilas idan zata wuce din su ganta,yana zaune cikin mota zainab na tsaye riqe
da murfim mota,kudade ta yanka masa zai bata shine ta biyoshi amsa,tana karba ta
juya tayi ciki abinta,zuwa lokacin sumayyan ma har takai ga ficewa daga gidan.

         A hankali yake bin bayanta,sosai ya rage gudun motar yana tafiya a hankali
don baison ya wuceta,tafiya take cikin nutsuwa,idan ka kalleta sai ka rantse da
Allah bata taba aure ba,sosai shaddar ta haska jar fatarta,ga komai nata yayi mata
cif a jikinta duk da da shigarta babu inda ta bayyana tsiraici,a haka har suka kai
bakin titi,yana so yace ta shigo ya kaita amma kamar an masa shamaki da ita haka
yakeji,haka ya karya kan motarsa ya wuceta ya hau kwalta sosai. Itakam sai a
lokacin ne ma ta lura da shi,da idanu ta rakashi sannan daga bisani ta dauke kanta
tana hadiye wani abu mai d'aci.

          Sosai ta lula tunani tsaye a bakin titin wanda hakan ya sanya ta kasa
ankara da horn din da yake ta zabga mata,murmushi tayi ta qaraso gaban motar bayan
ya sauke glass din
"Wa nake gani kamar abdur rahman cikin mota?"ta fada tana duban motar samfurin
*vibe* fara qal da ita,sosai motar ta mata kyau
Murmushi yayi yana fadin
"Eh mana,ya son ranki?" Cikin dariya tace
"Fes wallahi"
"Ina zuwa haka da safe?"
"Zani gidan anty dije ne zamuyi sallama suna shirin bar mana kano su gudu abuja"
"Shigo ciki ma qarasa maganar ai hanya ta ce indai gidan da take har yanzu shine"
ya fada yana bude mata mazaunin gaba
"Rufan asiri nan ai na qanwata ne,nan ma ya isa" ta fada tana shiga baya
"Yayarki dai,kina nufin nidin ban girme miki da wajen shekara uku ko hudu ba?"
"Jimin mutum da shegen son girma,shekara hudu kakar wata shekara arba'in,kai uku ne
ma"
"Ko second daya ne dai na fiki ko?" Ya fada yana dariya,don sun saba da wannan
caftar indai shi da sumayyan ne,itama dariya ta saki sannan suka shiga gaisawa a
mutunce,ta tambayeshi mutanan gidan da kawunsa wanda qani ne ga mahaifin mukhtar.

"Kinsan tun ranar nan naso kawowa yaya mukhtar mota ta ya gani da kuma
takardar zanen filin da zamu fara gina islamic clinic to ban samu dama ba"
"Da kyau masha Allah abdhr rahman,Allah ya sanya alkhairi ya kade fitina,kace yanzu
sai bude asibiti"
"In sha Allah duk da aikin ginin ba qaramin abu bane,har kwantarwa nake sa ran zamu
dinga yi,zamuyi amfani da likitancin musulunci da kuma na'urorin bature"
"Kace mun kusa fara kiranka alhaji abdur rahman"
"Da ba alhajin bane?,mijinki zaki cewa haka,gashi har yau ya kasa zuwa ko ina,ya
zama sai a hankali wallahi" sai ta danyi shiru tana sauke boyayyar ajiyar zuciya
don ha taba mata inda yake mata qaiqayi
"Ina fata kina ci gaba da addh'o'inki ko?"
"Babu abinda na fasa abdur rahman,sauqin ne sai a hankali"
"Haka ne,kada ki gaji,kinsan ita cuta farad daya take shiga sauqi kuma samuwarsa
sai a hankali,Allah ya yaye ma dukkan musulmi baki daya"
"Amin abdur rahman,na gode" haka suka ci gaba da hira jifa jifa yana kwasarta da
tsokana,har qofar gidan anty dije ya sauketa sanna ya mata kyautar dubu uku,da fari
taqi karba sai da ya bata rai sannan ta amsa tayi godiya tare da bashi saaon
gaisuwa gun qanwarsa bahijja da mamarsu.

Anty dije taji dadin ganinta sosai,nan suka wuni suna hira,ta tayata hada
ragowar kayayyakin da bata kammala hada kansu ba,tuni yaranta sunyi gaba don su
qarasa kammale gidan kafin isowar maman tasu. Suna hada kayan tana mata nasiha mai
ratsa jiki,idanun sumayyan ya hada qwalla har ta kai ga gangarowa,ta share qwallar
tana fadin
"Yanzu shikenan anty?,gurin wa zan dinga zuwa" sosai ta bata tausayi,yarinyar da
dududu bata wuce shekara sha tara ba amma ta hadu da kaidin kishiyoyi kala kala,sai
ta saki abinda take ta koma gefanta ta zauna
"Kina da Allah sumayya,baya ga haka akwai waya hannunki,duk abinda ya shige miki
duhu ki kirani ki tambayeni,koda babu kudi a ciki kimin plashing zan kiraki da
yardar Allah,ki ninka haqurinki kawai,domin duk wata mace da kika ga ta zama wata
gidan mijinta ki tambayeta wanne irin haquri ta hadiya kafin ta kai ga cimma wannan
matakin"
"To anty na gode"
"Babu godiya,ke diyata ce kamar su yasmin kike a gurina.....amma sumayya yanayin
jikinki kamar ya sauya?,ko baki kula ba?" Ta fada tana kallonta
"Me kika gani anty?"
"Bakya jin wani sauyi a jikinki?"
"Babu abinda nake ji" ta fada tana kallon anty,shiru ta danyi sannan tace
"Shikenan.....koyaya kika ji wani abu kada ki zauna,kije asibiti"duk da bata
fahimci abinda take nufi ba amma ta amsa mata da to.

Ana gab da sallar magariba ta koma gida,a gajiye ta koma,bandaki kawai ta


fara shiga tayi wanka ya daura alwala,sai da ta kammala sallahr magariban sannan ta
fita,cikin kitchen taji motsinta sai ta tura qofar ta shiga,tana tsaye tana hada
food flask na abincin mukhtar,qarasawa tayi kusa da ita ta mata sallama,kai kawai
ta daga ta dubeta ta maida kai taci gaba da abinda take ba tare data amsa ba,ita
din ma bata damu data amsa ba kai tsaye ta jeho mata tambayar da ta fito da ita
"ina abincina zainab,banga flask dina ba"
Dagowa tayi sosai ta sake kallonta,sai ta saka wata dariya data sanya dole sumayyan
ta tsaya tana kallonta cike da alamar tambaya,sai da ta tsagaita don kanta sannan
tace
"Ince ko baki samu labarin baki da abinci a gidan nan ba" jin maganar tayi
banbarakwai,ba kuma ta fahimci inda ta sa gaba ba,saboda haka taci gaba da
kallonta,dauke kai tayi daga bisani sai ta nufi dan qaramin store din dake kitchen
din da niyyar fiddo da ko indomie ce ta tafasa,sai ta tarad da store din a garqame
da kwado,waiwayowa tayi ta sake duban zainab din
"Naga alamun baki fahimta ba,amma bari nayi miki bayani dalla dalla,mukhtar ya soke
baki abincinsa,walau ni na dafa ko ke kika dafa kin fahimta ai yanzu ko?" Sosai
maganar ta daketa,sai ta kasa furta komai baya ga wani abu da ya tokare
maqoshinta,bata fahimci me hakan ke nufi,tilas ta jira dawowarsa tunda shi ya
ajiyeta ba zainab ba,wannan maganar ba tata bace. Wuce zainab din tayi ta nufi
sashenta ta dauki tukunya ta tari ruwa ta dora kan gas tare da jefa lipton,tilas ta
sanya wani abu a cikinta ba don haka ba abinda take ji cikin zuciyarta bata jin
wani abu mai suna abinci zai iya wucewa ta maqogoronta.

Hannayenta ta harde saman qirjinta tana jiran ruwan ya tafasa,tamkar zata


fadi haka take ji,ga yunwa ga bacin rai,tana kammalawa ta juye a cup ta nufi
daki,bata ko bi ta kan qananun habaicin da zainab keta jefawa cikin waqe,don yanzu
bata ita take ba ta kanta take. Tea ta hada da kayan shayinta wanda dama a dakin
suke.

Ko rabi bata sha ba ta soma yunqurin dawo da shi,sai data amayar da shi tas
sannan ta dawo ta zube qasan carfet din dakin cikinta naci gaba da juyawa,rasa
abinda ke mata dadi tayi,fashewa tayi da kuka tana kiran sunan Allah.

*mrs muhammad ce*👑


📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

2⃣9⃣
_________________________

*Bismillahir rahmanir rahim*

*Bismillahir rahmanir rahim*

*kullu man alaiha faan,wa yabqa wajhu rabbuka zuljalalu wal ikram*

_dukkan wani abu dake kanta(duniya)qararre ne,zatin ubangijinka mai girma da


daukaka ne zai dawwama_
_________________________

*Na sadaukar da wannan page da dukkan wani makarancin littafin KUNDIN


QAgDDARATA,haqiqa zan so ace ina da lokaci da zan iya binku daya bayan daya na amsa
commenta naku,saidai ina fatan wannan shafi ya isar muku,na gode qwarai*

_masu qorafe qorafe kuyi haquri,ku karbi littafin a duk yadda yazo muku,da fatan
kunyi duba da ayar da tazo a farkon shafin,ita kadai ta isa ku fahimci me nake
nufi,godiya nake_

        Kwananta biyu kwance cikin dakin babu abinda take iya hasalawa,daga
kwanciya sai bacci,ga wani shegen zazzabi da yaqi sauka daga jikinta,duk lokacin da
ta yunqura ta yiwa kanta duren shayi tofa qarshensa ya dawo baki daya,abinci kuwa
ko kadan bata da sha'awar cin komai,hakan ya sanya ta haqura ta zubawa sarautar
Allah ido,banda ruwa babu abinda take kurba,roqon Allah take ya sassauta mata ko ya
jefo mata wanda zaya taimaketa,hatta da wayarta bata san inda ta cillata ba,a haka
ta shafe kwana hudu cur bata ga kowa ba rana gurzar ciwnta ita daya,duk da cewa
taci ranar girkinta har ta fita amma bata ga idon mukhtar ba,to idan da sabo dama
ta riga data saba da hakan,data ga irin hakan tasan an karbi kwananta ne an qarawa
zainab.

      ****     *****     *****

     Cikon kwana na biyar din cikin ikon Allah ta ji sauqi sauqin jikinta,tana jin
qwari qwari a jikinta,har ta iya shiga da yammaci gab da magariba bandaki tayi
wanka,tana fitowa ta soma laluben wayarta,can cikin jakar da ta dawo daga gidan
anty dije ta ganta,a nan taci karo da dubu ukun da abdur rahman ya bata,sai taji
dadin kudin don bata da ko siai a hannunta,to ina ma taga mai batan tunda ita ba
sana'a take ba,caji ta sanya a socket din dake daura da madubinta,ta dawo bakin
gadonta ta zauna ta soma shafa mai,daga inda take zaunen tana iya hango kanta sosai
cikin madubi,ta rame sosai tayi wani fayau da ita,sai uban fari da ta qara kamar
wadda ta hadiyi qwayar qara hasken fata.

        Tura qofar dakin nata da akayi shi ya maidota cikin hayyacinta,ta dubi
bakin qofar,mukhtar ke shigowa,sanye da yadi tissue na maza orange wanda ya
ciza,yayi kyau sosai amma sai taga kamar ya rame,duj da bata sani ba ko idanunta
ne,don idan ba makuwa tayi ba rabonta da shi yau kwanaki shida cif. Kanta ta dauke
don bata ga dalilin ci gaba da kallonsa ba,ta soma lalubar mayafinta ta lullube
jikinta saboda guntun towel ne kawai daure a qirjinta.

       Shikam kallonta yake ci gaba da yi yana son lalubar sonta cikim zuciyarsa
amma ya rasa duk da dumbin qaunar da yake jin tana zanga zanga cikin zuciyarsa
wadda ya azata a bigiren tausayi,uban haushinta da yake ji yau babu shi kamar yadda
bai jin soyayyarta cikin zuciyar tasa. Bata sake bi ta kansa ba har ta gama shafa
manta,ta bude drower dinta ta fidda kayan da zata sanyasai a lokacin ta kuma
dubansa
"Ka fita don Allah zan sanya kaya" ta fada idanunta tsakar nashi
"Me ya sameki haka sumayya naga kin rame?,ko duk shegen kishin da kika sanyawa
ranki ne kamar yadda zainab ta fada?"ya fadi ba tare da yayi duba ga qorafinta na
farko ba
"Kan bala'i" ta fada cikin zuciyarta,wani baqinciki na takore mata qirji,wannan
rainin hankalin da me yayi kama?,ita yake tambaya ma meke damunta?
"Ba wannan ne a gabana ba,ka ficen a daki" ta fada ranta na suya,sai ya fara takowa
inda take,wani shauqinta na fusgarsa,son kasancewa kawai yake da ita,yayi kewarta
kwanakin bakwai din nan da bai ziyarceta ba
"Bari na qaraso ki gayamin nawa muka hada muka gina gidan da har dakin ya zama
naki". Qarasowarsa ke da wuya qamshin turarensa ya daki hancinta,wani tashin
hankali ya ziyarceta,take ta saki kayan hannunta ta buqaci bandaki,nan ta fara
kelaya aman da yayi sanadiyyar ficewar ruwan tea din data samu yau ya zauna mata.

       " lafiya sumayya?,meke damunki?,me ya sameki?"haka ya dinga fadi yana riqe


da ita,dukkan alamun tashin hankali sun bayyana a fuskarsa wanda hakan yayi matuqar
daurewa sumayya kai,mukhtar din tamkar wani bugun jinnu haka ya koma,idan yaso ya
dinga gasa mata aya a hannu shi da matarsa,amma wani lokaci sai ya dinga yunqurin
juyewa ya koma mata yaya mukhtar dinta sak wanda ta sani a can baya.

       Ganin qamshin turaren ke sake dugunzuma tunaninta ya sanya ta buqaceshi da


ya matsa ya barta bata so,haka ya koma baya ya zuba mata ido har ta kammala ta
gyara wajen ta dawo bakin gadon ta zauna tana maida numfashi
"Kishirya na kaiki asibiti,ni bansan baki da lafiya ba" duk da yadda take fidda
numfashi dai dai amma hakan bai hanata maida masa magana ba
"Bani buqata,me magani zaya yimin?,shin wai damuwa kayi ma da wata sumayya?,na
tabbata bakaqi na mutu ba,tunda har zaka iya hanawa a bani abincin gidanka ina a
matsayin matar ka" ta qarashe maganar tana sakin kuka don sosai batun ke ci mata
qoqon zuciya,ba wai don ta damu da abincin ba,a'ah,ta dauka tafi qarfin komai a
gidan mukhtar din,ta dauka ita din mai iya dauka ce ta bayar ma kyauta,sai gashi
ita ake hanawa abinci
"Wallahi ni bansan lokacin da akayi hakan ba,waye ya gaya miki ni na
hana?"maganarsa ta ratsa kunnenta,sai ta daga ido tana dubansa tana daga
kwancen,gani take kawai raina mata wayau zai yi,aljanu gareshi ko farfadiya ce ta
kamashi lokacin da ya bawa zainab din umarni?,baqinciki ne ya hanata magana,ganin
tayi shiru ba tare da tace komai ba sai kukan ta data ci gaba da yi yasa yace
" duka mubar wannan maganar muje asibitin a dubaki tukun,zanje nayi sallah ma
dawo"ya fada yana ficewa.

        Da fari taso taqi yarda,amma jin tsaiwa na niyyar gagararta sanda zata bada
faralin sallar magariba yasa ra taushi zuciyarta ta amince,ita kanta zata so taji
meke damunta bawai tayita zama da ciwo ba,tunda tunda take bata taba jin irin hakan
ba.

        Ba jimawa da idar da sallar sai gashi ya dawo,zuwa lokacin da qyar ta samu


ta gama tata sallar aman ya sake tsinke mata,jikinta yayi laushi tubus sai numfashi
da take maidawa,yaso taimaka mata wajen fita amma tace bata buqata,haka ta dinga
bin bango har suka isa cikin motar.

         Wani private hospital dake cikin unguwar tasu ya kaita,bayan taga likita
ya bata takardar gwaji taje lab,minti goma ta karbi sakamakon ta koma dakin ganin
likitan ta kai masa
"Alhamdulillah,sai ka godewa Allah,madam na dauke da juna biyu"baki dayansu wuta ce
ta dauke musu kada ma sumayya taji labari,sai ta fara girgiza kai hawaye na sauko
mata,magana take son yi amma bakinta ya gaza furta komai
" likita don Allah ka daina mana irin wannan wasan sai ka dauki haqqinmu"ta fusgi
kalaman da qyar,sau ya dago kai ya dubeta
"Bama yiwa patient wasa cikin abinda ya shafi lalurar da ta kawo su,ki baki yarda
bane hajiya,ai muna da na'urar daukan hoto bismillah ga gado can hau in nuna miki"
kasa tashi tayi baki daya,ga rashin qwarin jiki ga luguden da maganar tayi
mata,mukhtar dake son tabbatar da gaskiyar labarin shi ya taimaka mata har suka isa
bakin gadon.

       Cikin qwarewa ya shiga nuna masu dan qaramin tayin dake cikinta wanda duka
baifi wata biyu da rabi ba,basu iya ganewa amma sun lura da wani dan digo wanda
shike alamta yaronsu kenan,wata doguwar ajiyar zuciya ya saki tare da lumshe ido
yana jinsa cikin wata sabuwar duniyar,yayin da sumayyan ta fashe da kuka,jikinta
baki daya rawa yake,ashe tana daga cikin mata masu haihuwa?,ashe akwai rabon zata
ga yaron kanta?,ashe ita ma din watan watarana zata zama uwa?,zata yi raino ta kuma
bada tarbiyya?,lallai ubangiji babu wanda ya kaishi iyawa cikin mulki da
kyauta,babu ko shakka ubangiji baya bacci,baya mantawa da duk wanda ya ambaceshi ya
kuma nemi agajinsa.

        Barinsu likitan yayi suka gama murnarsu,don ya fahimci dukkansu ba'a cikin
hayyacinsu suke ba sannan ya sanarwa mukhtar din jikin sumayyan ba qwari,zasu
riqeta su sanya mata drip(ruwa)har zuwa safiya ko zata ji karsashi,sannan ya rubuta
magungunan da zatayi amfani da su wadanda zasu taimaka mata ita da abinda ke
cikinta,sannan ya jadda masa alfanun cina abinci mai kyau da gina jiki da qara
kuzari a gareta,karba yayi saida ya tabbatar an gama komai an sanya mata drip din
sannan ya fita siyo magungunan.

       Ya jima zaune cikin mota ya kasa tayar da ita,ina zaikai wannan kayan
farincikin?,da wa ya kamata ya raba wannan farincikin kada ya masa yawa ya masa
illa?,da sauri ya zaro wayarsa daga aljihu ya soma daddanna wasu lambobi kyakkyawan
murmushi kwance a kan fuskarsa,jinsa yake cikin wata duniya mai dauke dimbin
farincikin da ya jima bai jishi ba,jinsa yau yake wani na daban.

     ****      *****     ****

        Ji take idan ga zauna gu d'aya tamkar wani mummunan abu zai faru ne tare da
ita,tana jin qwaqwalwarta ko zuciyarta daya daga ciki zai iya tarwatsewa,tunda take
bata taba cin karo da mummunan labari da ya firgita duniyarta ba irin wannan
labarin,idanunta basu taba mummunan gani ba irin na wadan nan kwanakin,sumayya
kishiyarta da ciki?,ita kuwa tana me?,wanne shirme take?,wanne baccin asarar tayi
har mukhtar ya yiwa sumayya ciki duk da uban takatsantsan din da take?,duk da raba
tsakaninsu da tayi ya daina sha'awarta?,tabbas idan har ta bari sumayyan ta rigata
haihuwa cikin gidan ta dibga babbar asara,hakazalika bata ci sunanta,gidan da take
da buri a cikinsa,gidan da take so shi da mamallakin gidan duka su zama qarqashin
ikonta shine wata zata riga ta fara ajjiye iri?,tun yanzu ta fara ganin manya
manyan sauye sauye ina ga ta haihu?,tun yanzun mukhtar ya ruguza dukkan wani plan
data yi cikin gidan,wani kukawa yake bawa sumayyan wanda hakan ke nuni da qiris ya
rage sun koma su dinke kamar daa koma sufi daa dinkewa,abinda idan har ya faru ba
zata taba gafartawa kanta ba,lallai ko zatayi yawo tsirara sai ta tabbatar ta kawar
da duk wata barazana dake shirin tunkaro ta.

      Kamar mahaukaciya haka ta suri wayarta ta soma laluben lambar wayar


aminiyarta qawarta,wadda bata aiwatar da komai sai da shawarat,zama tayi dabas
gefan gadonta jin wayar ta shiga,cikin qananun sakanni mamallakiyar lambar ta
daga,ko ta kan gaisuwar da take jefo mata bata bi ba ta soma zayyano mata abinda ke
gudana cikin gidan.

      Tsawon minti talatin ta dauka kan layin wayar suna qulla saqa a mugun
zare,sosai taji dadi da shawarar data baga,shi yasa bata da kamarta,shawara ce mai
sauqi wadda babu zuwa gun boka ko malami,hakanan babu barnar kudi,amma fa buqata
zata biya,don dama babbar matsalarta yanzun duka jarinta ya karye warwas,saboda
ribar da uwar kudin duka sun tafi gun 'yan tsubbu,bata kwana arba'in bata je an
mata service ba,tun tana tsoron hadisin data taba tsintar wasu yaran 'yan
makarantar islamiya na karantawa na cewa duk wanda yaje gun boka ko dan duba,to
sallarsa ta kwana arba'in Allah bazai karbeta har tazo ta dake tama manta da
hadisin baki daya bare ta tunoshi ya zame mata birki. (daya daga cikin abinda Allah
ke jarabtar masu biye biyen malamai kenan,basu taba tara abun hannunsu,kullum suna
kan hanyar rabawa matsubbata da 'yan duba,ko kishiya gareki mai irin wannan biye
biyen ki lura da kyau,duk abinda miji zai baku sai ki nemi nata ki rasa,kullum
cikin babu da bani bani take,ba zaki taba ganin burbushin abun ba ko a dakinta ko a
jikinta ko a jikin yaranta,Allah ka kiyashemu ka tsare mana imaninmu).

       Tana kammala wayar ta saki murmushi ita daya take magana da kanta
"Kissa ai tafi magani,ba shakka quruciyarki ta yimin rana,zan amfana da ita sosai"
ta fada tana ficewa a dakin inda kai tsaye ta nufi dakin sumayya.

        Tana kwance saman carfet din dakin nata tayi matashin kai da pillow,duk da
ba yadda mukhtar baiyi ta dora kan nata saman cinyansa ba amma ta qiya,yana zaune
dirshan gabanta da faranti a tsakiyarsu wanda ke dauke da kankana da tuffa da
gwanda,ayaba yake bare mata yana miqa mata tana daga kashingide take amsa tana
ci,dubansa take kawai cike da mamaki,yana son dawo mata mukhtar dinta,"Allah yasa
ba yaudara bace,ya Allah kasa kada ya juyan baya"haka ta dinga fada cikin ranta
tana binsa da kallo wanda shi sam bai ma kula ba,hannu ta sanya ta shafi cikinta
wansa daga can qasa ta fara jin dan tudu kadan,lumshe idonta tayi tana jin qauna
cakude da farinciki na ratsata,duk kwanan duniya takan shafa cikin sau babu
adadi,wani lokaci takan tsaya gaban madubi ta dage rigarta tayita kallon fatar
cikinta tana mamaki yau ita ke dauke da juna biyu,idanu ya zuba mata shima yana
kallonta farinciki na bibiyar duk wara gaba ta jikinsa,a haka ta bude idanunta
karaf cikin nashi,sai kunya taso kamata,murmushi yayi sannan yace
"Bakiyi laifi ba sumayya ki qaunaceshi yadda ya kamata,wallahi Allah a duniya ban
taba jin son wani abu a rayuwata ba kamar yadda nakejin son cikin dake jikinki
ba,zan iya rasa komai sabida shi,zan iya rabuwa da komai saboda shi,don Allah ki
kularmin da kanki da abinda ke cikinki komai runtsi" ko bai fadi ba tasan zancan
daga zuciyarsa kai tsaye yake fitowa,ita kanta bata san irin son da takewa cikin
ba,kai ta sunkuyar tana murmushi tare da furta
"In sha Allah ya mukhtar".

       Dukkan wannan maganganun cikin kunnen zainab suka yisu wadda ta sawo kai don
shigowa dakin
" ka nunawa kucciya baka"ta fada sannan ta shigo dakin da sallama tana sake sai
saita nutsuwarta,gaban sumayya ya fadi har sai data runtse ido cikin zuciyarta tana
fadin
"Allahummakh finihim bima shi'ita(Allah ka isar min da su da abinda kaso)(addu'a ce
mai kyau ga wanda yaji tsoron zaluncin wasu mutane)" murmushi taje jifarsu da shi
wanda shi kansa mukhtar din sai da yayi mamaki
"Ashe kana gun uwar gidanmu my mukhtar" ta fada tana zama kusa da shi,amsa mata
yayi sannan ta dora
"Gwara ai ka kular mana da ita sosai musamman da take dauke da cikar
muradinmu,Allah mun gode maka daka nuna mana wannan lokaci" ta fada tana maida
hankalinta ga sumayya,hannunta tasa ta riqe nata hannun,ji take kamar ta kama
garwashin wuta amma sai ta dake
"Sannu sumayya ya jikin naki?" Da qyar ta bude labbanta tace
"Da sauqi"
"Allah ya inganta ya qara miki lafiya kinji,na godewa Allah da zaki samarwa mukhtar
sanyin idaniya,naji dadi qwarai dama ke ya cancanta ki fara samun wannan
matsayin,don Allah duk abinda kike da buqata ki sanarmin kada kice zaki yiwa kanki
wani abu,kada ki duba duka wasu abubuwa da suka faru a baya,sharrin shaidan ne da
kuma zuciya wadda bata da qashi,in sha Allah ba zasu sake faruwa ba,sai yanzu na
fahimci kyakkyawar zuciya da kuma haqurin da kike da shi,don Allah mu hada kai mu
zauna lafiya kinji?" Duk da bata gama gamsuwa ba amma taji dadin maganganun zainab
din,ko babu komai wake son tashin hankali?,ai babu abinda yafi zaman lafiya dadi
"Ba komai maman nafi'u,Allah ya sake hada kanmu"
"Ba amin ba,don wallahi da kai na ya hadu da na kishiya gwara na qare rayuwata kan
nawa na ciwo" ta fada a zuciyarta,amma afili sai ta saki murmushi tana fadin amin.

        Sake matsowa tayi ta karbi bare ayabar daga hannun mukhtar din,ita ta dinga
barewa sumayyan tana miqa mata,tanayi can qasan zuciyarta na mata suya,amma
fuskarta kuwa murmushi da kulawa ne kwance a cikinsu.

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

3⃣0⃣

___________________________________
*Bismillahir rahmanir rahim*

*iy yansur kumullahu fala gaaliba lakum,wa iy yakzulkum faman zal lazi yansur kum
min ba'a dih,wa'alal lahi fal yatawakkalil mu'uminin*
*_idan ubangiji ya taimakeku babu wanda ya isa yaci nasara a kanku,idan kuma Allah
ya qyaleku(ya fita daga sha'aninku) waye zai taimakeku bayan shi?,ga Allah kawai
muminai na qwarai suke dogaro_*

*Ya Allah ka taimakemu cikin dukka lamarun mu*


_________________________________

       Kulawa ta musammanzainab ke bawa sumayya wadda zata kwantar da hankalin


dukkan wani mai zargi,ta hanata komai,babu abinda sumayyan keyi cikin gidan banda
wanke goma ta tsoma biyar,hatta da ruwan wanka ita ke dafa mata ta ajjiye mata a
bandaki,girki kowa saidai kawai taci kuma mukhtar ya kwana dakinta,sau tari zainab
din kan yafewa sumayya kwananta a zuwan yaje su kwana tare tafi samun kulawa,ta
dauke dukka ayyukan gidan bisa wuyanta,ita kadai tasan me take ji cikin
zuciyarta,wani lokaci zuciya kan raya mata ta shaqe sumayyan kawai ta mutu ta huta
da ganinta da ganin abinda ke cikinta,saidai mardiyya qawarta kan yawaita ja mata
kunne da cewa,matuqar ba zatayi haquri ba to kuwa ba zata cimma nasara ba,hakan
shike yawaita taka mata burki tana jira har zuwa lokacin da zata kammala qudirinta.

        Qwarai mukhtar na jin dadin yadda take kula da sumayyan,yana yaba mata
sosai,hankalinsa ya kwanta,duk da cewa har ya zuwa yanzu akwai tasirin ragowar
sihirinta a jikinsa,a duniya yanzu babu abinda yake so irin cikin jikin
sumayyan,shi yasa hakan da takeyi yake sake saka farinta a idonsa,shi din ma ba'a
barshi a baya,hidima da tattali yake mata kan jiki kan qarfi,duk da sai data masa
tutsun abinda ya dinga mata a baya,saidai abun mamaki yaje bashi,ya sanar mata sam
baisan sadda hakan ta dinga faruwa ba,kallon ya raina mata hankali ta dinga
masa,hakan da ya lura da shi ya sanya ya karbi lefin kawai ya kuma bata haquri.

        Ita din ma sumayyan ba'a barta a baya ba wajen tattalin kanta da abinda ke
cikinta,duk wani abu da tasan zaya kawo tarnaqi ga lafiyar cikinta tana kauce
masa,har yau bata bar mamaki ba wai itace yau da ciki bayan shekaru kusan takwas
cikin na tara da aurenta,bayan da ta riga ta debe haso?,lallai rabon kwado baya
taba hawa saka ko ya hau din ma rabi zaya sauko da shi,babu ranar da zata fito ta
fadi bata godewa ubangiji ba.

      Mama mahaufiyarta kuwa kullum cikin kiranta a waya take da turowa a duba mata
ita,duk sanda zata aiko da abinda zata kawo mata na kayan qwalama na masu ciki,ita
kanta yaya yahanasu da taji labarin laqwas jikinta yayi,sai ta rasa me take ciki
farinciki ko baqinciki,amma jikinta yayi sanyi ta kuma taya mukhtar din
murna,saidai har yau bata je ta ganta ba,tanq gudun wulaqancin da zata taras a gun
zainab,don ta yanka musu gargadi kan zuwa gidan duk sadda suka ga dama.

*.........KAYAN KWALABA*
          _MAFARI_

        Zaune yake gefan gadon dakinsa yana sanya maballan rigarsa a shirin sa na
fita kasuwa. Ahankali zainab ra bude qofar dakin ta turo ta a hankali kamar wadda
qwai ya fashewa a ciki,kujerar madubu ta janyo ta zauna tana fuskantar mukhtar
idanunta a kansa,shi ya soma magana
"Lafiya dai ko?,na lura tun jiya jikinki a sanyaye yake,mu da muke cikin farinciki
a kwanakin nan"
"Kake cikin farinciki dai,kuma na kusa datse igiyar farincikin". A zahiri sai ta
soma goge qwalla da ta fara sakkowa a idanunta tana kallon mukhtar din
" mukhtar,wannan farincikin da muka samu idan bamuyi wasa ba yana gab da qwacewa
daga cikin gidan nan,bansan me yasa take ta qoqarin aikata haka ba,bansan me yake
damunta ba"barin sanya takalman da yake qoqarin yi yayi,ya dago ya dubeta idanunsa
cike fal da tambaya,har ya gaza boye hakan sai da ya furta
"Kamar yaya fa?,me yake faruwa ne?" Kai ta shiga girgizawa cike kirsa
"A'ah mukhtar,barin maganar nan shi yafi alkhairi,don bansan ya zaka dauketa ba"
"Idan kina tunanin wani abu ne da zai cutar da ni qauna ce ki boyemin kiqi
gayan,gaya min zainab" dan shiru tayi a zahiri fuskarta dauke da tashin
hankali,yayin da zuciyarta ke cike fal da murna da farinciki tare da fata da
addu'ar samu nasara tamkar wata wadda zata aikata abun arziqi,bata kuma magana ba
har sai da mukhtar din ya jaddada sake tambayarta,taba goge qwalla tace
"Mukhtar,sumayya ce......sumayya ce naji tana magana da wata baquwa da
tayi,bansanta ba,ina tunani ko qawarta ce ko qanwarta ko 'yar uwarsu,wai wallahi
sam batayi farinciki da samuwar wannan ciki ba,ina ita ina haihuwa bayan ko shekara
ashirim baga gama rufawa ba,dama ita can kawai nunawa take tana son haihuwa amma
wlh sam bata qaunarta,bare wai ta lura ba wani kulawa take samu yanzu daga gareka
ba,tunda kwanakin baya ka juya mata baya yanzu haka data haihu qila ka sake komawa
halayyarka,yanzu haka maganar da nake maka har ta bata shawarar ta sha maganin da
zai barar da cikin kawai ta huta".

         Tamkar guduma zainab ta sanya ta daki qahon zuciyarsa haka yaji,take


maganar da yaya yahansu ta ta sha gaya masa shekarun baya suka bijiro mada suka
cakudu da wannan sabon batun
" kai idan zaka farka gwara ka farka,matarka fa ba son haihuwa take ba,bata ma
sha'awarta,tunda kuke ka taba gani ta sha wani magani don ta haihu ko ta taba maka
maganar kuje asibiti a dubaku?,ina kyautata zatan ma ita tasha maganin da zata hana
kanta haihuwa,banda haka yarinyar dake da quruciya mai zai hanata haihuwa a irin
wannan lokacin?". Wani fushi da bacin rai mai tsanani ya sauko masa,sai kawai ya
miqe,burinsa kawai yaje ya samu sumayya yanzun nan,da sauri ta riqeshi don ba yanzu
take da muradin nakiyar ta fashe ba
" a'ah mukhtar ina kuma zaka?"
"Sakeni zainab,sakeni naje na sameta" wani mugun marairaicewa tayi sannan tace
"Shi yasa fa naqi gaya maka tun jiyan,yanzu me zakaje ka yiwa yarinyar mutane kana
cikin fushi haka?,idan baka iya kama barawo ba sai shi barawo ya kamaka,zauna muyi
magana akwai mafita" babu musu ya koma ya zauna yana maida numfashi
"Mukhtar,kada ka damu,ni mai qaunarka,ina son abinda kake so,idan baka manta ba
nike kulawa da sumayya...to kada ka damu,zan sanya ido sosai a kanta,sannan zan
hana duk wani abu faruwa har Allah yasa ta haihu lafiya na maka alqawari" hakanan
yaji kalamanta sun kwanta masa a rai,sai ya sauke ajiyar zuciya
"Na gode zainab,don Allah na roqeki ki kula da ita,a duniya yanzu babu abinda
nakeso sama da cikin nan don Allah" wani shegen kishi ya takore mata,cabdi,a haka
zata bari sumayya ta fara haihuwa,ai ba zaya yiwu ba,a fili tace masa
"Na maka alqawari tare ma zamu dinga wuni insha Allahu kada ka damu" jikinsa a
sanyaye ya gama shirin zuciyarsa na bugawa,mamaki da haushin sumayya ne fal cikin
zuciyarsa,da kamar ya wuce abinsa ba tare da ya mata sallama ba zainab din ce ta
tursasashi kan sai ya shiga din,koda ya shiga sumayyan sai taga yanayinsa ya sauya
sosai,ba kamar yadda ya saba mata ba,gabanta ne ya dinga faduwa tana fatan ba
halayensa na baya bane zasu dawo,don ko kusa bata da buqatar wannan yanayin.

       Har ya juya zai fita sai ya sake waiwayowa ya dubeta


"Ki kularmin da cikina,din bazan iya jurewa ko yafiya gareki ba ga duk wani abun qi
da zaya samu cikin nan ba" dai ya juya ya fita,kanta ne ya daure sosai,me yake nufi
kenan,ta jima tana qoqarin lalubo amsar,daga qarshe abinda qwaqwalwarta ta bata
shine tsabar son cikin da mukhtar din keyi ne haka ta barwa ranta taci gaba da
sabgoginta.

      ****     ****     ****

    Bata gushe ba tana ci gaba da cusawa mukhtar tunani kala kala kan zub da ciki
sumayya ke qoqarin yi,amma ta nuna masa tana bala'in takatsantsan akan faruwar
hakan,sosai ya shiga damuwa da tashin hankali,mamakin sumayyan yake yi,da ya
matsanta kan sai ya mata magana yana son daukar mataki,bazai iya jura ba idan wani
abun ya samu cikin sai ta masa alqawarin zata nuna masa da idanunsa zai gani saboda
hukunci da hujja yafi.

*KUNDIN QADDARA*

*_BAQAR RANA_*

Tun da safe ta hada mata shayi kamar yadda ta sabarwa kanta,duka yana
cikin qudurinta da tsarinta. Ranar kusan da wuri mukhtar ya fita,tana kwancan har
ya fita din ko abin kari ma bata masa ba saboda mugun qudirinta data qulla
aiwatarwa a yau din nan ko farkawa bata nuna tayi ba,hakan ya sanya data shiga da
shayin ta zauna tana jan sumayyan da hira,bata bar dakin ba sai data tabbata ta
kammala shan shayin,sannu a hankali ta soma hamma,zainab din ta dubeta fuskarta
qunshe da murmushi wanda ke dauke da manufofi uku,manufar cimma nasara da manufar
mugunta,sai kuma dadi daya kamata saboda tafuskanci magungunanta zasu soma aiki
lokaci guda yadda take so
"Kwanta ki huta qanwata na fuskanci kamar bacci kike ji"
"Wallahi kuwa,duk jikina ya mutu" ta fada tana jan pillow ya yada kai saboda nauyi
da taji kanta ya soma yi sakamakon bacci mai nuyi daya lullube idanunta. Leqa
fuskarta tayi ta tabbata ta soma baccin sannan ta sake sakin murmushi,a nutse ta
nufi drower din gefan gadon sumayyan ta fiddo magungunan da suke soke cikin rigar
mamanta,magunguna ne har saches uku dukka na zub da ciki ne,saches daya aka balla
guda gudu wanda ita tayi amfani da shi ta zubawa sumayyan cikin ruwan shayin data
kammala sha yanzu,sai wata 'yar qalamar kwalba da wani saches din wanda duka
maganin dake bugarwa ne da saka bacci wanda yawanci 'yan shaye shaye aka sani suna
ta'ammali da shi. Dorasu duka tayi kan drower din sannan ta fice.

Kitchen ta shiga ta samo kofi cikin kayan sumayyan ta zuba ruwa ta dawo
kusa da magungunan ta ajjuye,ta bude kwabar kayanta ta ciro hijabi ta ajjiye saman
kanta sannam ta nufi ma'ajiyar takalmanta ta ciro ta sanya mata daya daga ciki a
qafafunta,sai data qare mata kallo ta tabbatar komai ya kammala sannan ta saki
dariya ta fice zuwa dakinta.

Tazarar mintina goma ta bada kamar yadda aka ce mata magungunan zasu fara
aiki amma maganin baccin zai sa ba zasu tashi aikinsu gadan gadan ba sai bayan
minti ashirin,dakin ta sake nufa ta leqata sai ta tarar har yanzu baccin take amma
tana motsawa akai a kai,jinjina kai tayi ta sake komawa dakinta.

Kai tsaye ta dauki wayarta ta laluba lambar mukhtar,bugu uku ya daga tare da
yin sallama,bata bi ta kan amsawa ba ta soma magana cikin yanayi na matuqar rudewa
qwarai da gaske
"Wayyo Allah mukhtar mun shiga uku,mukhtar na kasa riqe amanar da ka bani" cikin
wani mugun tashin hankali ya miqe tsaye daga inda yake zaune sannan ya fara
tambayarta
"Lafiya zainab yi magana mene ne?"
"Kasan ka barni a daki ina kwance ina bacci,to ina tashi naga lokaci ya ja,sai na
tuna sumayya na barta bata ci komai ba,da sauri na shiga kitchen na hada mata abun
kari na nufi dakinta,ina shiga naga babu kowa na duba gidan baki daya ban ganta
ba,ina falo ina taraddi ina ma shirin kiran wayarka ko kasam zata fita?,kawai sai
gata ta dawo dauke da wata baqar leda ita da wannan 'yar uwar tata,da nayi mata
magana ma kallon banza ta yimin tayi tsaki ta wuce daki,sai ma qyaleta sabida nasan
masu ciki da fushi,sai daga baya na sake leqata sai na tarar tana shan wani
magani,na mata zancan abinci tace ta qoshi bata buqata taci a waje,na qyaleta na
dawo ina hidimar gida,bayan wajen minti talatin sai na fara jiyo ihunta tana wayyo
cikina wayyo bayana inzo in taimaketa" sai ta fashe da kuka kamar gaske,ya gaji da
dogon jawabi kawai jira yake azo gurin
"Ki gayan me ya faru?"
"Jini ma gani daga jikinta mukhtar yana fita wanda ke nuna kamar bari tayi"
"Me!" Ya fada da madaukakin sauti,kafin ta kai ga amsawar ta soma jiyo kumar
sumayyan na kiran sunata,dadi ya kamata komai yazo a daidai kenan?,sai ta sake
dububurcewa
"Tana kirana mukhtar don Allah kayi sauri kazo mu kaita asibiti kada mu rasa cikin
nan" sai ta katse kiran kawai cikin gaggawa ta nufi dakin sumayya.

Murququsu ta cimmata tana yi da malelekuwa daga saman gadon har qasan carfet
din dakin,tun daga kan gadon jini ne har qasan dakin,wata azaba ke ratsata ilahirin
jikinta,duk da azabar da takeji bai hana hankalinta tashi ba,tasha jin ana cewa
zubar jini hadari ne gun mace mai ciki tun daga shigar ciki zuwa haihuwarsa,tsoro
fal da fargaba ke zaga zuciyarta,tsoron rasa cikin jikinta,tsorom rasa gudan
jininta
"Ki taimaka kin don Allah amarya kada na rasa baby na" ta fada hawaye da gumi na
hade mata saboda tsabar azabar radadin da mararta ke mata,ga tarin mamakinta sai
taga zainab din ta sheqe da dariya
"Kadan kika gani,ci gaba da karbar gashin ciwon rasa d'a kafin ki rasa mijinki ma
baki daya,nice sila ba zan iya taimaka miki da komai ba,burina nake so ya cika" sai
ta sake takowa zuwa gabanta ta ranqwafo
"An fada miki akwai ranar da kishiya zata so kishiyarta ne?,an gaya miki ni sauna
ce da zan dinga miki bauta?ko an fada miki wawiya ce ni bansan me nake ba?,lallai
dukkan wanda ya riga ka kwana tilas ya rigaka tashi,wannan ya isheki ishara game da
kaidin kishiya,ke yarinyace,bakisan komai ba sumayya,daga yau zaki shaidi kaidin
kishiya" ta fada tana juyawa ta fice ta barta a dakin tare da komawa falo tayi
zamanta.

Runtse idanunta tayi wani abu na dawafi kan qwaqwalwarta,babu shakka


ayanzun maganganun da zainab ta furta mata sunfi mata ciwo fiye da ciwon dake
nuqurqusarta,tana nufin ita ta mata silar abinda ke faruwa yanzun da ita?,me ta
aikatama zainab din haka mai muni da zata zama silar rabata da abinda ta jima tana
dakon isowarta gareta?,don kawai sun hada miji?,saboda kawai suna qarqashin inuwa
daya?WANNAN ITACE KAWAI HUJJAR?dafe mararta tayi tana ci gaba da kallon yadda jini
ke kwaranya yanabin qafafunta tare da bin lafiyar carfet dinta.

Tana jin qarar tsaiwar motarsa ta miqe da hanzari ta shige dakin


sumayyan,kanta tsaye ta nufi kan drower din ta kwaso magungunan dake ajjiye a kai
ta riqe a hannunta tana kallon sumayyan taba murmushi sannan tace
"Yanzu zaki ga babban kaidina don na tabbatar bakisan da zaman wadan nan magungunan
ba,baki ta saki tana kallonta tare da jijjuya kai cike da azaba,ko magana ma ta
kasa yi,sai da taji takun shigowarsa yana qwala musu kira ta saki kuka tana
jujjuyasu tare da matso hawaye tana fadin
"Me yasa kika aikata haka sumayya?,me yasa zaki raba shi da farincikinsa?,abinda ya
jima yana nema sumayya shine yau zaki zama silar rabashi da shi,ina ma ni Allah ya
bawa sumayya kin cika butulu ta gaske,wayyo Allah yau mun rasa yaronmu"sai ta rushe
da kuka,wani duka zantukanta suka yiwa dodon kunneta,sai ta daga kai tana duban
baki qofa saboda ganin inuwar mutum,take idanunta suka sauka cikin na mukhtar wanda
ke dauke da tsantsar bala'in da bata taba katarin ganinsa cikin idanun nashi
ba,tsaf mukhtar yaji duka abinda zainab din ke fada,yi tayi kamar bata ganshi ba
taci gaba da cewa
" yanzu har da maganin 'yan shaye shaye sumayya da tarbiyyarki da komai......
"Kasa ci gaba da daukar batun kunnuwanta sukayi,dummmm taji sunyi mata,a hankali ta
soma jin jiri na kwasarta tana daga zaune,cikin 'yan sakanni wani duhu ya mamaye
idanunta ta daina gani ta daina ji.

**** ***** *****

Sannu a hankali ta soma yunqurin bude idanunta har taci nasara ta kammala
budesu baki daya,idanunta suja sauka kan ruwan dake rataye yana shiga jikinta sannu
a hankali,take abinda ya faru da ita ya dawo mata tar,tayi hanzarin fadin
" la'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minaz zalimin"bakinta ya furta
"Hmmmm,kamar gaske" muryarsa ta daki dodon kunnuwanta,da sauri ta waiga ta dubi
bangaren da sautin ke fitowa,mukhtar ne tsaye hannayensa nannade a qirjinsa,duba
daya zaka yi masa ka fuskanci a yamutse yake,har yanzu idanunsa jajur suke tamkar
an badesu da barkono,kafin tace wani abu ya tako zuwa gaban gadon da take. Babu
shakka da zata iya da tashi zata yi ta arta ana kare saboda yadda kamanninsa suka
sauya baki daya kamar wani mayunwacin zaki
"Sumayya,ban taba zaton soyayya zata juye ta koma qiyayya ba sai yau,babu shakka
kin cuce ni kin zalunceni,kuma Allah ya isa tsakanina dake,don bazan taba iya yafe
miki ba,na zauna da ke tsawon shekaru ina kare martaba da mutuncinki,ina tattalin
farincikinki ashe ni nawa kike rusawa,meye aibuna da bakison ki haihu da ni?,me
yasa baki gaya min ba tun wuri nayi nesa da rayuwarki?,a yau na tsaneki tsanar da
ban taba yiwa wata halitta makamanciyar irinta ba,na gani da idona ba gaya min
akayi ba"zuciyarta na mata wata iriyar muguwar suya ta bude baki don kare kanta duk
da rashin qwarin gwiwar da take da ita,sai ya watsa mata magungunan da kuma
sakamakon gwajin da ka yi mata na dalilin barinta wanda ya nuna maganin zub da ciki
ta sha
"Allah ya saka min sumayya na dora buri kanki amma kin zalunceni" abun mamaki kawai
saiga hawaye na fita a idonsa,abinda bata taba tsammanin ganin ba agreshi
"Zan bar rayuwarki kije kiyi duk yadda kika ga dama da ita,KIJE NA SAKEKI SAKI UKU
don bazan tab iya ci gaba da rayuwa da ke ba" wani tashin hankali ya rikito
mata,sai ta ware baki daya idanunta tana son tabbatar da gaskiyar lamarin,ko dai
barin da tayi ya shafi awaqwalwarta da jinta?.

"Haba my dear wannan danyan hukunci haka?,ai yayi tsauri" ta fada tana isowa
gareshi cike da kisisina
*Dakata da Allah!"ya katseta cikin kakkausar murya,gabanta yayi mugun bugawa saboda
ta tuno da sharadin da malam ya gindaya mata nacewa kada ta kuskura tace komai har
a qare lamarin,saboda ba qaramin so yakewa cikin ba hakanan har yau duk da daurin
da aka yiwa zuciyarsa da sanya masa ganin baqin sumayya har yau sonta na da sauran
tasiri cikin zuciyarsa,itadai kawai ta sanya layarta cikin bakinta tayita
taunawa,jajayen idanunsa da suka firgitata ya zuba mata
"Tunda sumayya ta iya yimin haka a rayuwa,to babu macen da zan aura ta kasa aikata
min haka,saboda haka kema kije na sakeki saki uku!"
"Iyeee!" Ta fada cikin madaukakiyar murya fitsari na kubcr mata take ya fara bin
qafarta saboda azabar rudewa,kai ya sanya ya fice daga dakin,wanda kammala fita su
mama(babar sumayya) suka sanyo kai da alama dama suna cikin asibitin.

_kuyi haquri fa kawai ku ci gaba da bibiyata don cimma darasin dake cikin labarin
da kuma rayuwar sumayya_
*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

3⃣1⃣
________________________

*Bismillahir rahmanir rahim*

*wa bashshiris sabirin,Allazi a iza asabathum musibatun qalu innalillahi wa inna


ilaihi raji'un*

_ka yiwa(ya annabin Allah) masu haquri bushara,sune wadanda idan musiba ta samesu
suke fadin daga Allah muke kuma gareshi zamu koma_

*Allah ka sanya mu cikin wadanda zaka yiwa kyakkyawan sakamako sanadiyyar fadan
wannan kalma*
_________________________________

   

      Zainab qanwarta ce akan gaba,sai mama da yaya abubakar halima na biye da


shi,umma sadiya qanwar babansu na biye da su
"Yaya sannu yanzu muka ga ya mukhtar din ma ai ya fita" ta fada ba tare da sun
ankara baki daya da yanayinda take ciki ba,haka ma basu lura da zainab dake tsaye
gefe ba tana tsuma tare da kallon fitsarin da ya gama wanke mata qafafu. Kallo daya
mamanta ta yi mata ta fuskanci ba dai dai taje ba duk da cewa akwai ciwo tattare da
ita.

        Da idanu kawai take binsu tana fata ta farka daga mummunan mafarkin da
takeyi,sai da maman ta qarasa gefan gadon ta zauna ta soma yi mata sannu sannan
sumayya ta tabbatarwa kanta idanuntq biyu,a zahiri komai ke faruwa,wata cukuikuya
ta yiwa maman nata tana sauke wata ajiyar zuciya tare da fadin
"Ya sakeni mama,ya rabu da ni bayan bani da wani laifi",cikin rudani suke kallonta
duk suna zaton zafin ciwo ne
"Sumayya zafin ciwo ne duka hakan?" Sai ta fashe da wani kuka mai azabar cin rai
tana maimaita fadin
"Walllahi mama ya sakeni,yanzun nan da kuka ganshi ya fita sakina yayi mama" salati
suka saka baki daya wanda ya dawo da zainab hayyacinta
"Allah ya isa 'yarku ta jawo min masifa,ta jawo min zawarci kashi na biyu garin
qoqarin zubar da cikinta" ta fada tana wucewa fuuuu ta bar dakin.

       Shiru ya ratsa dakin,babu wani abu dake tashi sai shashsheqar kukan sumayya
wanda zainab da halima ke tayata saboda tsantsar tausayin 'yar uwarsy,yayin da
zuciyoyin sauran ke quna,zancan zainab kuma ke musu kai kawo
"Mama har saki uku yaya mukhtar ya yimin,mama wallahi ban aikata ba,na fishi son
naga na haihu mama ki......." Sai ta fara jan numfashi da qyar wanda hakan ya sanya
su sake rudewa,da sauri yaya abubakar ya nufi reception don kiran nurse ko
likita,cin qanqanin lokaci sai gashi tare da likita wanda yake gab da tashi Allah
yasa bai fita ba,waje ya fid dasu baki daya sannan ya rufe dakin,take suka rude da
koke koke cike da tashin hankali.

       Kusan mintina talatin sannan likitan ya fito bayan ya gama dubata ya mata
allurar bacci tare da sanya mata wani ruwan,ya sanar musu bata buqatar
hayaniya,sannan don Allah su guji tada mata hankali idan baso suke ta hadu da hawan
jini ba,don ko a yanzun jini nata ya fara sama,bugu da qari kuma ta zubda jini mai
yawa,godiya suka yi masa sannan suka koma dakin kowa ya samu gu ya zauna
zugum,dukkansu da abinda suke saqawa zukatansu,daga bisani yaya abubakar ya fice
dan yi musu siyesiyen abubuwan da zasu buqata kafin suga yadda hali zaiyi.

       Tun a hanya take sumbatu,ko da wasa bata taba zaton ramin da ta haqa zai
rufta da ita ba,bata taba ganin masifa irin wannan ba,taga samu taga rashi,gidan da
takewa kanta hasashen samun abun duniya yau dare daya an rabata da shi
"Ina!!!,wlh sam bazai yiwu ba,mukhtar ko baka qaunar Allah sai ka ci gaba da zama
da ni,babu wanda zan sanarwa ma ka yimin saki uku,wallahi yanzu na fara aurenka"
maganar da tayi kenan wadda ta sanya mai adaidaitam juyowa ya dubeta,banda kayan
jikinta da basu nuna alamun akwai hauka tattare da ita ba da babu abinda zai hana
yace mahaukaciya ce,a qofar gidansu ya sauketa ya juya ya kama gabansa.

        Tunda ya bar asibitin gida ya wuce kansa tsaye tamkar wani mahaukacu,kuka
yake wiwi da haka ya kashe motarsa qofar gidan ba tare da ya samu qwarin gwiwar
tura dan matsakaicin get din ba bare ya iya shiga da ita,dakinsa ya wuce ya fada
saman gado yana dafe da kansa,me yasa sumayya zata yi masa haka?,wanne abu ya mata
da zata saka masa da wannan?,zata rabashi da gudan jininsa,sata rabashi da burin
rayuwarsa,shin ta manta cewa samun d'a shine CUKAR BURINSU shi da ita?,wani kukan
ya sake saki kamar qaramin yaro,sai a lokacin ya fara ambaton sunayen Allah daya
bayan daya,sannu a hanakali nutsuwa ta fara saukar masa,yabar tumurmusa gadon da
yake yayi luf saman gadom cikin yanayin na kwanciyar rub da ciki idanunsa na ci
gaba da fidsa qwalla masu zafi.

      ****    *****   *****

       Kwana daya rak amma sunfi kwanaki dubu ciwo da wahala a rayuwarta,baki daya
ta sauya kamar ba sumayya ba,tayi wani mugun dashewa wanda ya sanya nurses suka
soma tunanin tana buqatar qarin jini ko babu jini jikinta,da likita ya duba sai
yaga magungunan qarin jini ma kadai sun isheta sai maida kai gun cin abin mai
lafiya.

       Ko kallon abincin bata yi bare ta kai ga ci,ko ruwa bata iya kurba a
bakinta,ki da yaushe tana kwance idanunta rufe kamar mutum mutumi,sai da malam yazo
shi daya ya shiga dakin sukayi magana ta tsawon mintina kusan ashirin shi da ita
sannan aka fara samun salama,takan karbi duk abinda aka bata taci koda zata yi
amansa,hakan ba um ba um um sai zubda hawaye tamkar qwayar idonta zai tsiyaye,kusan
kowa tausaya mata yake tare da girgiza da al'amarin,duk da cewa har yau malam kawai
ta iya yiwa bayanin abinda ya faru shi kuma ya sanar da abubakar da umma
sadiya,sosai umma sadiyan ta fusata qwarai tace sam ba zasu yarda ba tilas su maka
mukhtar a kotu shi da zainab din baki daya,baisan halin sumayyan bane?,yarinyar da
kusan shi ya qarasa yi mata tarbiyya,malam ne ya hana yace sam hakan baida
amfani,tunda koda sun aikata hakan ba zasu iya maida hannun agogo baya ba,ba zasu
iya gyara lamarin ba tunda abinda zai faru ya riga da ya farun,da wannan zancan
suka rufe batun suka maida hankali wajen kula da lafiyar sumayyan.

         Da wani yammaci sumayyan na zaune jingine da bango,bata jima da yin wanka


ba tana sanye da atamfa,mamanta ne da zaina da halima sai khadija da hajara cousing
dinta zauneba dakin suna dan taba hirarsu,sallama akayi suka kalli bakin qofar baki
daya suna amsawa,haj salamatu ce wato umma mahaifiyar abdur rahman ita da qanwarsa
bahijja,duk da quncin da zuciyarta ke ciki saida sumayyan ta washe haqora ta sake
gyara zama tana mata sannu da zuwa.

      Cikin mutuntawa suka gaisa su halima suka gaidata tare da miqewa suka fice
don zuwa karbo canjin ruwan da suka siya cikin shagon asibitin a dazu
"Sannu sumayya ya jiki?,ya kuma mukaji da wannan abu" umma ta fadi fuskarta dauke
da alhini da tsantsar tausayi,qasa tayi da kanta hawaye na zirarar mata
"Alhamdulillahi umm" ta fada muryarta a karye
"Ki yi haquri kan haquri sumayya,duk da na sanki dama ke gwanar haqurin ce,haqiqa
Allah ba azzalumin sarki bane,ni sam bansan meke faruwa ba,abdur rahman da bahijja
dai sunje zasu miki sallama da yake zai sake koma wa jami'atu ummul quraa zai hado
masters dinsa,to da suka dawo sai suka ce sun tadda gidan naku a kulle,babu wanda
ya kawo komai don har mukhtar din ya kira ya masa sallama baice da shi komai ba,sai
jiya da safe saiga mukhtar din yazo gaida kawun nasa,a nan yake gaya masa duk
abinda ya faru,wallahi mama ina jin batun na tabbatar sharrin kishiya ne da asiri
ke dawainiya da yaron,cikin kwana uku tal da faruwar lamarin kada kiso kiga yadda
ya fige ya lalace,babban abun haushin ma duk yadda muka so tunatar da shi wace
sumayyan wallahi yaqi fuskanta yaqi gane wacece ita,har yau da haushi da zargin
abun a ransa,amma babu komai mai gaskiya yana tare da Allah,kuma in sha Allahu
Allah zai miki KYAKKYAWAN SAKAMAKO".

       " babu komai ai umma,kowanne bawa da irin tasa QADDARAR,kuma shi aure rai ne
da shi,da zarar zaman ya qare sai kiga ko babu sanadi an rabu".hawaye ne kawai ke
ci gaba da tsiyaya idanun sumayya,tamkar ta zura a guje haka take ji,bata qaunar
jin duk wani zance da ya danganci mukhtar din,tunda mukhtar ya yi mata haka a
duniya yaqi bata dukkan yarda da amincinsa bayan yasan wace ita to babu wanda bazai
iya cin zarafinta ya ha'inceta ya wulaqanta ta ba.

     Maganganu masu sanyi umma ta dinga fada mata masu kwantar da rai wadanda suka
sauke kaso mai yawa na bacin rai baqinciki da firgicin da take ciki,sosai taji
sukuni cikin zuciyarta,sai wajejan la'asar sannan umma ta musu sallama ta tafi
bayan ta ajjiyewa sumayyan dubu uku tace tasha lemo.

**** ***** ****

Cikin kwana biyar jikinta yayi sauqi sosai,hakan ya sanya likita ya bata
sallama tare da gargadarta ta rage damuwa ta kuma kula da lafiyarta.

Sosai take samun kulawa daga dukkan wani da yake cikin gidan nasu,kowa haba
haba yake da ita,dakinta daban wannan karon malam yasa aka ware mata don kada su
takura mata,amma duk da hakan wani lokaci cikinsu haliman take kwana,ganin yadda
kowa ke son farincikinta ya sanyata warewa,tayi qoqari qwarai wajen fidda damuwa
daga ranta duk don saboda su,duk da abadini hakan ba mai yiwuwa bane gareta.

Watanta guda da komawa yayanta abubakar ya siya kata foam na wata


makarantar koyon sana'o'in hannu na mata don rage mata kewa da dauke kaso mafi
tsoka a cikin lokacinta wanda hakan zai taka rawa matuqa da gaske wajen hanata
tunani ko damuwa,kama daga dinkin labulaye,zannuwan gado,suturu kayan sawa,carfet
zuwa saqa,hadin su humra,sabulu,man shafawa man kitso da sauransu dukka suna
koyawa,sosai take jin dadin makarantar hakanan ta maifa hankalinta sosai tana dauke
duk wani abu da aka koya mata,har ya zuwa lokacin ba'a debo kayanta daga gidan
mukhtar ba din baki daya ta tsane su ta tsani ganinsu,hakan ya sanya umna halima
tace idan an tashi daukosun a wuce da su gun masu saida furniture a siyar kawai.

*ZAKARAN DA ALLAH YA NUFA DA CARA*

Kusan a yanzu ya zame mata al'adarta,takan kwashi lokaci mai tsawo kwance
cikin nazarin da tunani kafin bacci ya samu nasarar daukarta.

Yauma kamar kullum tana kwance ruf da ciki,duk da cewa dakin babu hasken
fitila amma idanunta a bude suke tar,kwanyarta na aikin sarrafa tunane tunanen dake
bijiro mata daya bayan daya.

Zumbur ta miqe sakamakon motsin da take ji can qasan mararta,wanda wannan


shine karo na barkatai da take jin hakan cikin wannan satin,sau tari takanyi kasaqe
tana sauraran motsin har zuwa sanda zai lafa mata,hakan ce ta faru wannan
karon,bayan motsin ya lafa sai ta koma ta kwanta rigingine tana mai lumshe
idanunta,tana tunanin gobe zata sanarwa mama don tana zaton ba lafiya saboda bata
taba jin irin hakan ba.

Qarfe takwas na safe tana tsakar gidan tana shara bayan ta kammala duk wani
aiki na gidan qannanta sun wuce islamiyya wadda suke shiga tara zuwa biyat da rabi
na yamma,tunda tazo ta koma al'adarta ta da,tun kafin tayi aure ita ke hidimar
gidan duk da qarancin shekarunta a lokacin,sai abinda yafi qarfinta ne kawai wanda
ba zata iya ba take barma maman nata shi,to hakan ce ta kasance wannan karon,duk da
maman na hanata kai bama ita ba har su haliman idan suna nan basa yarda tayi
komai,amma takan qiya saboda hakan na matuqar debe mata kewa da sata jin qwarin
jikinta.

Tana daga rumfarta zaune amma tana iya hango duk abinda ke faruwa cikin
tsakar gidan kasancewar labulen falon a dage yake don ta samu iska ta shiga inda
take,da idanu take bin duk wani motsi na sumayyar da kallo,tausayi da qaunar
yarinyar tata na ratsata,sai kima wasu sauye sauye da take ci gaba da gani dangane
da ita,har sai da ta kammala komai sannan ta shigo falon
"Wash" ta fada wanda hakan ya sanya maman juyawa ta kalleta
"Lafiya dai ko?"
"Lafiya lau,kawai gajiya nake ji da kasala mama" shiru ta danyi sannan ta sake
dubanta,tunani ne fal cikin zuciyarta amma bata aminta da abinda zuciyarta ke kawo
mata ba don bata jin hakan zai yiwu
"Bakijin komai a jikinki sai kasalar kawai?" Dan shiru tayi sannam tace
"Ummmm,wani lokaci inajin motsi mama har nace zan gaya miki ko zanje asibiti,sai
kuma naji motsin ne kawai baya ko ciwo cikin nawa" ta fada cike da quruciya dake
nuni da rashin sanin abinda ke faruwa da ita
"Tun wajen yaushe kike jin hakan?" Ta tambayeta tana dubanta da saka ran jin amsa
"Eh wajen kwana goma kenan"
"Lallai kuwa ya kamata mu koma asibiti" maman ta fada tana jinjina kai cikin
qarafafawa wanda hakan ya bawa sumayyan tsoro,take hantar cikinta ya kada,kodai
wani babban ciwo ke shirin samunta?,gaza yin shiru tayi saboda tsabar tsoro
"Mama!......bani da lafiya ko?" Ta fada kamar zata saki kuka,murmushi ta saki don
kwantar mata da hanakali,bugu da qari itama bata da tabbas din abinda take zato
kansa
"Lafiya lau kike,dauko min wayata na kira malam in sanar da shi idan yaso sa muje
kiga likitan"
"To" ta fada jikinta a sanyaye qirjinta na bugawa duk da maman tace mata lafiyarta
lau,dakin gadon maman ta shiga ta fiddo wayar ta dawo ta miqa mata sannan ta samu
gefe ta koma ta zauna.

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

3⃣2⃣
_________________________

*Bismillahir rahmanir rahim*

*wa iyyamsaskallu bi durrin fala khashifa lahu illa huw,wa iy yuridka bi khairin
fala raadda li fadhlih,yusibu bihi man yasha'u min ibadihi wa hul azizul gafur*

_"idan Allah yaso ka da cuta(lalura,abubuwa marasa dadi)babu wanda zai yaye maka
face shi,idan kuma ya soka da alkhairi babu wanda ya isa ya maida falalarsa,yana
sowa ga wanda yaga dama cikin bayinsa,haqiqa shi madaukaki ne mai gafara"_
_____________________

       Cikin abinda duka bai wuce awanni biyu ba isar su asibitin da shiga dakin
ganin likitan,umartar ta yayi da tahau wani dan gado wanda kusa da shi na'urar
daukar hoton ciki ne.

       "Allahu akhbar" shine abinda likitan ke fadi yana jinjina kai tare da
girmama iko na ubangiji,yaro ne kwance cikin mahaifarta ga motsi nan yana yi ga
bugun zuciyarsa da komai,dukkansu ba wanda idonsa bai gani ba daga sumayya har
mama,mamaki fal zukatansu tare da girmama lamarin buwayi gagara misali,sai da ya
kammala komai har EDD sai da ya duba mata sannan yace ta sauko ya koma kan tebur
dinsa ya soma rubuce rubuce.

       Magunguna ya rubuta mata wadanda zasu qara mata lafiya sannan ya bata wasu
gwaje gwaje da ya kamata ace a wannam stage din da cikin ke da watanni hudu da sati
uku tayi su
"Likita lafiyarsa qalau"furucin ya subuce ya fita daga bakinta jikinta a
sanyaye,murmushi yayi yana dubanta
" lafiya qalau komai yake,babu wata damuwa tattare da shi"sai da ya bata amsar
sannan kunya ta kamata ta sadda kai qasa,batasan cewa tana bala'in qaunar abinda ke
cikin nata ba sai yanzu,wani qwarin gwiwa karsashi da soyayya take ji cikin
ruhinta,banu shakka wannan karon tanajin zata iya yaqi kan cikinta a shirye take.

       Basu bar asibitin ba sai da suka kammala duk wani gwaji suka siyi magungunan
suka nufi gida.

        Har yanzun maman ta kasa cewa komai kamar yada sumayya ta kasa magana,sam
basuyi zato ba,basu tsammaci akwai sauran ciki jikin sumayyan ba,ZAKARAN DA ALLAH
YA NUFA DA CARA ko ana muzuru ana shaho sai yayi kenan. Hakanan sumayyan ke jin
zuciyarta fes da ita,bini bini ta saki murmushi tare da shafa cikin nata,maman na
ankare da ita,tausayinta ya dinga ratsata,haqiqa babu dan halak din da zai guji
haihuwa,babu wata halitta da bazato ganin jininta ba,dole dan adam ya koka idan ya
rasa baya wato 'ya'ya,abu ne mai ciwo da cin zukata,Allah kuma maji roqo da addu'ar
bayinsa ne,a yau gashi duk yadda akaso rabata da rabon da Allah ta bata amma hakan
bai yiwu ba,ya riga ya QADDARA yana cikin QADDARARTA haihuwarsa da dadi ba
dadi,saboda hikimarsa sai ya bawa yaron kulawa ta musamman,ya boyeshi daga kallon
idanuwa,ta yadda ko mahaifiyarsa bata san da zamansa ba sai yanzu da buwayin sarki
yaso ta sanin.

       Tun daga sanda suka koma gida daga asibitin maman ta fara bata kulawa ta
musamman,ta hanata yin komai komai qanqantaraa,duk da babu wani ciwo ko laulayi da
sumayyan keji,lafiya qalau take jin jikinta. Malam na dawowa maman ta sanar
masa,sosai shima ya jinjina lamarin yana qara girmama isa da buwaya ta ubangiji,to
ita kanta sumayyan ma alokacin ba'a zaci zata kai ba bare d'an dake cikinta
"Yanzu ya zama dole a sanarwa uban yaron saboda yasan da zaman cikin" inji mama.
"Wannan ya zama dole ai,zan sanya abubakar yayimin kiransa ko zuwa gobe ne" cewar
malam.

       ****      ****    ****

      Kansa na duqe amma gumi tsatstsafo masa yake har ta kafar farcensa,babu
shakka baya ga girman tsohon da yake gani da kuma farin sani da yayi masa kan wane
shi da tashin farko zai qaryata batun da a yanzun yake gaya masa.
"Amma ga wadan nan ka duba hoton cikin ne da aka yi mata a jiya,idan ma duka basu
gamsar ba kana iya zuwa gobe sai kuje da ita da su halima wani asibitin a sake
gwada maka har da watannin cikin" malam ya fadi yana zube takaddun scanning da
komai da komai a gabansa,jikinsa na rawa ya dauka ya soma dubawa,tsaf daya lissafa
watannin cikin zuwa yanzu dai dai suke,sau taji wani abu na zaga shi,madaukakin
farinciki ya wadatu a zuciyarsa
"Na gode maka ya Allah da baka bata damar salwantar min da ciki ba" ya fada cikin
zuciyarsa idanunsa a lumshe,duk da zuwa yanzu yana mamakin me yasa ta aikata masa
haka?,zuciyarsa kuma na kokwanton ita din ce da kanta?,wani sashi na zuciyarsa kan
gaya masa ita dince mana,tunda kaga shaidu na magungunan cikin dakinta,kuma a baya
likita ya tabbatar da ta sha din.

      Sallamarta ita ta katse dogon nazarin da yake,sanye take da dogon hijabi har
qasa mai hannu wanda idan zata shigo wajen malam din haka take sanyashi,din yanzu
baki daya irin wannan shigar tafi mata armashi,duk da dama yana daya daga cikin
dressing dinta tun a da,sam bata ma san da zuwansa ba,tazo ne karbar rubutun da
malam din yace mata zata dinga sha daga tsakanin magariba zuwa isha'i,gefe ta samu
kusa da malam din ta zauna har ya zuwa yanzu bata luta da mukhtar din ba dake satan
kallonta,abu biyu yake ji dangane da ita,haushin yunqurin zub da masa ciki da kuma
qaunar jininsa da take dauke da shi.

       "Ka duba su da kyau gasunan" inji malam,wanda maganar da yayi ce ta ja


hankalin sumayyan ta lura da mukhtar din,da sauri ta dauke kanta bayan sun hada
idanu,qasa qasa tace
"Ina yini" kamar wadda aka tilasta ta fada,tasan dole ne ma ta gaidashi saboda
malam dake gun
"Lafiya qalau,ya jiki naki"
"Alhamdulilla" ta fada da qyar tana jan tsaki cikin zuciyarta tare da fadin
"Me ya shafeshi da jiki na ji da nake mai laifi"
"Malam rubutun nazo karba" ta fada a hanzarce don so take ta bar falon ba zata juri
zama cikinsa ba
"duba gefan akwatincan ki dauko min farar gorar can" ya fada yana nuna mata,ta miqe
ta isa gun yayin da idanun mukhtar din ke kanta,baki daya yanayinta ya nuna mace
mai ciki ce,cikin ma da ya soma qwari.

      Cikin wata silver mai dauke da rubutun yasin da ayatul kursiyyu ya fara zuba
rubutun ya bata ta shanye sannan ya dura mata wani cikin jarka ya miqa mata,a
hanzarce ta karba ta fice a dakin.

        Kasa tsaiwa tayi a falonsu sai data dire zuwa dakinta ta ajjiye rubutun
gefe ta zauna saman gado dafe da kanta,kuka ne ya kubce mata wanda ba zata iya
fadar dalilin sa ba,sosai ta koka sai data ji sanyi cikin ranta sannan ta rarrashi
kanta.

        Cikin kunya da nuyin da ada bai jisu ba sai yanzu suke saukar masa ya dubi
malam bayan sun gama tattauna abinda zasu tattauna din
"Malam ina son jin abinda ake da buqata wanda zatabyi amfani da shi" kai malam din
ya gyada yana nazarinsa,duk ya fara qarewa kamar wani kudin guzuri,addu'a yake masa
cikin zuciyarsa Allah ya yae masa abinda ke damunsa
"Babu wani abu da muke sa buqata,yadda sumayya take diyata kaima d'a na nae,tunda
ko babu komai alaqa ta sake qulluwa darajar abinda take dauke dashi" nauyinsa ya
sake kamakashi,ya sadda kai qasa
"Na sani malam,amma ka fini sanin haqqina ne yanzu in ci da ita har ta haife abinda
take dauke da shi,don Allah a fadamin na sauke haqqin da ya rataye a wuya na" dan
shiru malam din yayi sai daga bisani ta numfasa
"Shikenan,kaje ka kawo duk abinda kasan zaka iya"
Kanshi a qasa ya masa godiya sosai,karamcinsa na sake daureshi,yadda malam din ke
mu'amalantarsa kamar ba wanda ya sakar masa diya ba,sakin ma kuma mai kankat.

       Cikin mota jikinsa yayi sanyi baki daya,da qyar yake iya tuqi,a yau ji yake
ina ma bai saki sumayya ba duk har yanzun akwai haushi da zargin yunqurin zubar
masa da ciki da tayi,mai yasa baiyi haquri ba ko ya dauki mataki wanda bai zama na
rabuwa ba,a lokacin baisan me ya sanya yaji rabuwa da ita ne kawai maslaha a
rayuwarsa ba tunda har bata da buqatar hada zuriya da shi
"Ke kika jawo sumayya,me yasa?,me yasa kika aikata abinda ya zama silar datse
alaqarmu?" Haka ya dinga fada yana tafe yana tambayar kansa.

        Tamkar wanda qwai ya fashewa a ciki haka ya faka motar sannan ya rufeta ya
nufi cikin gidan,sosai yayi mamakin ganin qofar falon a bude sabanin dazun da take
a kulle,sai yayi zaton ko 'yan uwan zainab sunzo kwasar kaya bayan fitarsa a gidan
saboda har yau sunqi kwashe kayanta
"Sannu da zuwa my mukhtar" yaji muryar zainab na ambata,da sauri ya maida idomsa
inda yake jiyo muryat,zainab din ce ta qure ado sanye sa wata matsiyaciyar doguwar
riga wadda ta bayyana suffarta baki daya,fari take masa tana sake takowa kusa da
shi,da sauri ya daka mata tsawa
"Ke wacce iriyar maca ce,wato da na hanaki bina kasuwa shine kika sauya salon
biyoni gida,to ina gargadinki wallahi ki gaggauta ficewa daga gidan nan don
gamuwarmu ba zata yi kyau ba,don na tsani kowacce mace tunda sumayya ta ha'ince ni
taso cutata ba don Allah ya riga ya rubuta mai taka doron qasa bane" maganar sa ta
qarshe ita ta girgizata,idan har tayi dogon nazari da tsinkaye yana son ce mata
cikin sumayya yana nan zata haifeshi nan gaba?yana nufin ita ta tashi banu
riba?,ita tayi biyu babu ko daya?,bata samu sukunin tambayarsa ba ya daka mata wata
tsawa wadda ta dawo da ita hayyacinta ta soma dubansa tana kada kai
"Wallahi bazanyi biyu babu ba mukhtar,kana nufin taci riba?" Sam tunaninsa bai kai
ga fassara maganarta ba,burinsa guda kawai ta fice masa a gida a yanzun kadaici
yake da buqata,ganin zata bata masa lokaci ya sanyashi fincikar hannunta ya watsa
ta waje,sannan ya dawo ya yibi mayafinta da jakarta ya wurga mata har kan fuskarta
ya kulle gidan. Dawowa yayi ya zube saman kujera yana maida numfashi zuciyarsa na
ci gaba da tuhumar sumayya,ta zamo silar yankewar duk wani jin dadi nasa,wayarsa ce
ta soma takura masa da ruri ya dagata ya duban sunan mai kiran,yaya yahanasu
ce,baya da buqatar qarin matsala akan wadda yake ciki,saboda haka ya kashe wayar
baki daya ya ajjiye
"Wallahi ban tafi kenan ba zan dawo,na dinga bibiyar rayuwarka kenan saboda ni da
kai kadai zan rayu" ya jiyi zainab na aiko masa da maganar daga inda take,tsaki ya
ja don ya fara daukarta a matsayin mai matsalar qwaqwalwa

    ****    ****    ****    ****

      Siyayyar dukkan wani abun buqatuwa ga sumayyan shine abu na farko da ya soma
yi a safiyar washegerin ranar,kai hatta da man goge baki bai rage ba cikin
siyayyarsa,sannan ya dora kudi dubu goma akai.

       Sanda kayan suka iso gidan tashi tayi ta bar wajen ma baki daya ta koma
daki,yadda bata da buqatarsu haka bata da buqatar ganinsu,kuka ne sosai ya kubce
mata,har yanzu mamakin mukhtar take da har ya iya amincewa da ta aikata mummunan
laifi irin wannan,ba wannan take buqata ba,baki daya mukhtar ya gaka rushe duk wani
tanadi na raino da suka ciwa yaran da zasu haifa buri,itakam mai yayi saura,ba
gwara ya qyaleta ba baki daya tasan cewa ta rasashi har abada?,dukkan wata kulawa a
yanzun da zai nuna babu wani zaqi da zata mata ballantana ta burgeta.

       Tun daga lokacin ya zamto duka qarshen wata zai mata siyayyar dukkan wani
abu,tun daga na ci zuwa na buqata,duk da malam na hana wasu abubuwan amma sam bai
yarda ba,yana jin haqqi ne a kansa kuma nauyi ne da ya rataya wuyansa ya kula da
ita saboda yaronshi da take dauke da shi.

       Kusan duk zuwansa yakan tsaya ne daga sori,su gaisa da mama da sauran yaran
ya bada saqon ya juya,baki daya gashi nan dai a tafe ne,amma sam babu wani abu dake
faranta masa illa idan ya tuna ya kusa daukan 'yarsa ko dansa.

        Ta bangaren yaya yahansu kuwa sanda taji labarin sakin,sosai na zainab ya


faranta mata,sai a lokacin ta dinga tuna abinda zainab din ra dinga yi musu,ta
tabbatar har su ta hada ta asirce shi ya sanya suka gaza tabuka komai,jikinta kuma
yayi sanyi da sakin sumayya,ita kanta ta dunga tunanin anya abinda mukhtar ya gaya
mata ya faru ba tuggun zainab din bane?,tilas ta bar batun tunda abinda ake gudu ya
riga da ya faru,amma lokacin da ya sake dawo mata da batun cikin na nan wani
farinciki taji ya mamayeta,tana da muradin zuwa taga sumayyan amman kunya ta
hanata,tana ganin kowa yasan gallazawar sa ta yiwa sumayya,da wanne ido 'yan uwanta
zasu dubeta?,sai a yanzun take sake tausayin dan uwan nata ganin yadda ya sauya
kamar ba muntarinsu ba.

    ****      ******    *****

      Hakanan yau ya tashi da muradin ganin cikinsa,amma ya kasa tantance cikin


yake son gani ko sumayyar duk da zuciyarsa tafi afuwa ga cikin yake son gani,don
rabonsa da ganinta tun randa malam ya gaya masa zancan cikin na nan a falonsa.
         Saura kusan kwanaki bakwai lokacin da yake mata siyayyar ya cika,amma duk
da haka da yammacin ranar ya shiga store din da ya saba siyayyar,shugaban gurin na
ganinsa ya san me dame yake buqata,shi ya sanya aka hada masa komai sannan akayi
total ya biya ya karba ya fice.

         Qarfe biyar a qofar gidan tayi masa,yana sanye da wani yadi mai qarancin
kauri ruwan bula mai haske wanda aka yiwa aiki da ruwan bula mai turuwa,duk da
sauyawar yanayinsa da rama amma hakan bai hanashi kyau ba,sam rayuwar gidan bata
masa dadi saboda a yanzun shikewa kansa komai,hakan ya sanya ya nemi wani saurayi
wanda ke zuwa ya masa share share.

         Halima ce ta soma ganinsa,ta yiwa mamansu magana aka bashi izini ya


shiga,duk da yaran yanzun basa sakewa da shi kamar da,hakan baya masa dadi sam don
baiga abinda su ya shiga tsakaninsu ba.

        Cikin girmamawa ya gaida maman ta tambayeshi su yahanasun ya amsa mata duk


lafiya qalau shi kuma ya tambayi masu jiki(wato sumayya),ba wata hira dama tun da
can ke shiga tsakaninsu ba daya wuce gaisuwar,hakan ne ya sanyashi ya miqe bayan an
gama shigo da kayan ya musu sallama ya fice.

        Sai ya kasa tafiya ya tsaya a soron,yana da muradin ganin cikinsa gashi ko


gilmawarta bai gani ba bare yaji muryarta,hakan babu wanda ya masa zancanta,jingina
yayi da bangon soron hannunsa harde a qirjinsa yana tunanin ta yadda zai ganta
din,cikin ikon Allah sai ga zainab ta fito tana sanya hijabinta zata shagon kusa da
gidansu ta karbo klien zata wanke kwanukan da suka kammala abincin dare da su
"Yauwa zainab,don Allah taimaka min ki fito min da yayarki mu gaisa" ya fada yana
gyara tsaiwarsa,mamaki ya cikata,kamar tace wani abun kuma sai ta fasa ta juya ta
koma ciki.

         A dakin sumayyan ta tarad da maman tsaye kanta tana mata fadan rashin
fitowa su gaisa da mukhtar,tundanko banza dai ai uban d'anta ne,abinda ya faru kuma
babu wanda ya ruga ya gogeshi cikin KUNDIN QADARARTA,hawaye ta soma gogewa abinda
maman bata so kenan
"Amma mama meye amfanin fitar tawa mu gaisa,tunda dai lafiya qalau nake"
"Na san da wannan,ko banza ai ko baya ta taki zai so ya tabbatar da lafiyar abinda
ke cikinki ko" maman ta fadi
"Shikenan kiyi haquri mama zan dinga gasheshi" tausayinta ya kamata,tana shirin yin
magana zainab din ta shigo ta fada mata abinda mukhtar din ya buqata
"Kin gani ai,sai kije ku gaisa" ta fada ta juya tana ficewa,hajibinta ta janyi dake
rataye jikin sif ta zura sannan tayo waje.

       Tunda ta fito ya zuba mata ido yake kallonta,sosai wannan karon cikin ya
fito fiye da waccan karon,hatta tafiyarta ta soma sauyawa,kanta ma qasa din bata
son hada ido da shi har ta qaraso,daga can gefe guda ta tsaya sannan tace
"Ina yini" ba tare data daga kai ta dubeshi ba
"Lafiya lau,ya jikin naki"
"Alhamdulillah" ta fada cikin sanyi,sai shiru ya biyo baya kowa da abinda ke saqawa
cikin zuciyarsa,tsaiwar ta fara mata tsauri har ya lura da haka,sai ya waiwaya ya
gangaro mata wani dutse da suke tokare qofa da shi ya furta
"Ga guri zauna" bata musa ba ta zauna din don tana da buqatar hakan
"Me yasa sumayya?,why?,kinga ayanzun kin zama silar da zamu raini yaronmu a
mabanbanta gurare abinda ko a mafarki ban taba hasashen faruwarsa ba"ya furta wani
daci na zagaya harshensa,idanuwansa na sauya launi,da sauri ta daga kai ta watsa
masa fararen idanuwanta,take wani bacin rai ya soma bijiro mata,wato har yanzun
zarginta yake kenan?,dama abinda yake son gaya mata kenan da har ya fiddo ta tana
zaman zamanta tana lallaba rayuwarta.

       Qin tankawa tayi sai ma yunqurin miqewa da ta soma yi saboda bata ga alfanun
ci gaba da tsaiwa a gabansa ba,ganin tana niyyar wucewa ba tare da ya gaya mata
abinda zaya fadi ba yace
" idan nayi lissafi dai dai cikin ya kusa shiga wata na tara,zuwa yanzu ya kamata
ace anyi siyayya,ki rubuta duk abinda kike da buqata jibi zan dawo na karba in sha
Allah"
"Ka kawo duk abinda kake ganin zaka iya" ta fada tana mai shigewa gidan ba tare da
ko ta waiwayoshi ba zuciyarta na suya,idanunta na zafi.

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ KUNDIN QADDARATA✍
📖📖📖📖📖

NA
SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA

WATTPAD:HUGUMA

HASKE WRITERS ASSO


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

3⃣3⃣

Zuwa ga marubuciyya safiyya abdullahi musa huguma mujin shuru kwana muna ta xuba
ido mu masoyanki Allah yasa dai lafiya dan Allah ki taimaka ki cigaba da post muna
jin dadi littafin sosai.
Na gode daga masoyarki.
Aysha M Adam ( maman muneepha)

Dan Allah duk wanda ya gani ya tura gaba har ya isah garaita plx.
👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

3⃣4⃣
______________________________
*Bismillahir rahmnair rahim*

*tsarki ya tabbata ga Allah wanda mulki ke hannunsa kuma mai iko ne akan
komai,wanda shi ya halicci rayuwa da mutuwa,ya halicci cuta da lafiya*

*haqiqa kalmomin bakina sunyi qaranci wajen nuna tsantsar godiya ta ga ubangiji
bisa alfarmar samun lafiya da yayi min,bani da abun cewa face roqonsa ya bani ikon
morarta ta hanyar bauta masa da yi masa biyayya*

*godiya ga iyaye na,babu shakka soyayya irin ta mahaifa babu kamarta duk fadin
duniya,naga zallar ta a idanuwa da ayyukansu,ban da abin biyansu,saidai bazan gaza
ba wajen yi musu addu'ar ubangiji ya musu kyautar Aljanna madaukakiya,ya musu
kyakkyawan qarshe,yasa su cika da kalmar shahada,ya jiqan magabatansu,ya cika musu
burikansu duniya da lahira,ya cika rayuwarsu da farinciki lafiya wadata da
kwanciyar hankali*

*fans ina matuqar godiya a gareku,'yan watpadd bani data cewa sai fatan Allah ya
muku kyakkyawan qarshe,'yan watsapp bazan manta karamcinku a gareni ba,ubangiji ya
hadamu cikin jannatul firdausi,addu'o'in alkhairinku gareni fans ina roqa muku
ninkinsa wajen ubangiji*

*_wannan shafi sadaukarwa ne a gareku_*

*mariya SB*

*aysha abubakar(maman khalipha)*

*mariya yola(mamam shuraim)*

*mommy maimuna musa*

*Allah ya saka da alheri ya qara zumunci*

______________________________
Hakanan yau ya tashi da muradin ganin cikinsa,amma ya kasa tantance cikin yake son
gani ko sumayyar duk da zuciyarsa tafi afuwa ga cikin yake son gani,don rabonsa da
ganinta tun randa malam ya gaya masa zancan cikin na nan a falonsa.

         Saura kusan kwanaki bakwai lokacin da yake mata siyayyar ya cika,amma duk
da haka da yammacin ranar ya shiga store din da ya saba siyayyar,shugaban gurin na
ganinsa ya san me dame yake buqata,shi ya sanya aka hada masa komai sannan akayi
total ya biya ya karba ya fice.

         Qarfe biyar a qofar gidan tayi masa,yana sanye da wani yadi mai qarancin
kauri ruwan bula mai haske wanda aka yiwa aiki da ruwan bula mai turuwa,duk da
sauyawar yanayinsa da rama amma hakan bai hanashi kyau ba,sam rayuwar gidan bata
masa dadi saboda a yanzun shikewa kansa komai,hakan ya sanya ya nemi wani saurayi
wanda ke zuwa ya masa share share.

         Halima ce ta soma ganinsa,ta yiwa mamansu magana aka bashi izini ya


shiga,duk da yaran yanzun basa sakewa da shi kamar da,hakan baya masa dadi sam don
baiga abinda su ya shiga tsakaninsu ba.

        Cikin girmamawa ya gaida maman ta tambayeshi su yahanasun ya amsa mata duk


lafiya qalau shi kuma ya tambayi masu jiki(wato sumayya),ba wata hira dama tun da
can ke shiga tsakaninsu ba daya wuce gaisuwar,hakan ne ya sanyashi ya miqe bayan an
gama shigo da kayan ya musu sallama ya fice.

        Sai ya kasa tafiya ya tsaya a soron,yana da muradin ganin cikinsa gashi ko


gilmawarta bai gani ba bare yaji muryarta,hakan babu wanda ya masa zancanta,jingina
yayi da bangon soron hannunsa harde a qirjinsa yana tunanin ta yadda zai ganta
din,cikin ikon Allah sai ga zainab ta fito tana sanya hijabinta zata shagon kusa da
gidansu ta karbo klien zata wanke kwanukan da suka kammala abincin dare da su
"Yauwa zainab,don Allah taimaka min ki fito min da yayarki mu gaisa" ya fada yana
gyara tsaiwarsa,mamaki ya cikata,kamar tace wani abun kuma sai ta fasa ta juya ta
koma ciki.

         A dakin sumayyan ta tarad da maman tsaye kanta tana mata fadan rashin
fitowa su gaisa da mukhtar,tundanko banza dai ai uban d'anta ne,abinda ya faru kuma
babu wanda ya ruga ya gogeshi cikin KUNDIN QADARARTA,hawaye ta soma gogewa abinda
maman bata so kenan
"Amma mama meye amfanin fitar tawa mu gaisa,tunda dai lafiya qalau nake"
"Na san da wannan,ko banza ai ko baya ta taki zai so ya tabbatar da lafiyar abinda
ke cikinki ko" maman ta fadi
"Shikenan kiyi haquri mama zan dinga gasheshi" tausayinta ya kamata,tana shirin yin
magana zainab din ta shigo ta fada mata abinda mukhtar din ya buqata
"Kin gani ai,sai kije ku gaisa" ta fada ta juya tana ficewa,hajibinta ta janyi dake
rataye jikin sif ta zura sannan tayo waje.

       Tunda ta fito ya zuba mata ido yake kallonta,sosai wannan karon cikin ya
fito fiye da waccan karon,hatta tafiyarta ta soma sauyawa,kanta ma qasa din bata
son hada ido da shi har ta qaraso,daga can gefe guda ta tsaya sannan tace
"Ina yini" ba tare data daga kai ta dubeshi ba
"Lafiya lau,ya jikin naki"
"Alhamdulillah" ta fada cikin sanyi,sai shiru ya biyo baya kowa da abinda ke saqawa
cikin zuciyarsa,tsaiwar ta fara mata tsauri har ya lura da haka,sai ya waiwaya ya
gangaro mata wani dutse da suke tokare qofa da shi ya furta
"Ga guri zauna" bata musa ba ta zauna din don tana da buqatar hakan
"Me yasa sumayya?,why?,kinga ayanzun kin zama silar da zamu raini yaronmu a
mabanbanta gurare abinda ko a mafarki ban taba hasashen faruwarsa ba"ya furta wani
daci na zagaya harshensa,idanuwansa na sauya launi,da sauri ta daga kai ta watsa
masa fararen idanuwanta,take wani bacin rai ya soma bijiro mata,wato har yanzun
zarginta yake kenan?,dama abinda yake son gaya mata kenan da har ya fiddo ta tana
zaman zamanta tana lallaba rayuwarta.

       Qin tankawa tayi sai ma yunqurin miqewa da ta soma yi saboda bata ga alfanun
ci gaba da tsaiwa a gabansa ba,ganin tana niyyar wucewa ba tare da ya gaya mata
abinda zaya fadi ba yace
" idan nayi lissafi dai dai cikin ya kusa shiga wata na tara,zuwa yanzu ya kamata
ace anyi siyayya,ki rubuta duk abinda kike da buqata jibi zan dawo na karba in sha
Allah"
"Ka kawo duk abinda kake ganin zaka iya" ta fada tana mai shigewa gidan ba tare da
ko ta waiwayoshi ba zuciyarta na suya,idanunta na zafi.

      Babu kowa cikin tsakar gidan nasu kai tsaye ta fada dakin tana jan
numfashinta tana jin zuciyarta na mata nauyi,qwalle ke layi kan kuncinta daya na
bin daya,a addafe ta nemi gefan katifa ta zauna tana jujjuya kanta cikin zuciyarta
tana addu'a wadda bata tantance mai take roqa ba,abu daya zuwa biyu zata iya
tantancewa shine haushi da tsanar mukhtar dake mata yawo cikin zuciya,sai kuma
zainab wadda take jin ba zata iya yafewa karan tsayen da ta tiwa rayuwarsu ba
musamman ita din,wanda gangar jikinta da zuciyarta bata saba da kowa ba sai mukhtar
din tun zamanin quruciya zuwa girma.

      Ta dauki a qalla mintuna talatin a haka kafin sautin qarar wayarta dake yashe
gefe ta katse mata yanayin da take ciki,sunan anty dije ke yawo bisa screen
din,tamkar an kwance qullin dake zuciyarta taji zuciyar ta karye hawaye ya sake
balle mata tun kafin ta kai ga daga wayar.
      Muryarta kawai anty dije taji jikinta ya bata akwai damuwa,fada ta shiga yi
tun kafin taji matsalarta akan kan mene ne za'a dinga bata ranta,ta gaya mata me
aka mata waye ya bata mata,ganin ta gaza bata amsa yasa ta katse kiran ta nemi
layin maman,tana daga daki ta juyo muryar maman da alamu anty dijen ta
sameta,jikinta ta komar ta jinginar a bango ta lumshe idanunta tana matse hawaye.

     Batasan ya sukayi da mama ba daga bisani ta kirata ta gaya mata idan har taga
ba zata iya ba tayi tahowarta abuja gurinta ta zauna ta haihu a nan,godiya ta mata
tare da ce mata to ba don tana jin tafiya can din ba,maida kanta tayi ta kwanta
sosai saman katifar tana maida ajiyar zuciya

  ****     ****    ****   ****

    La'asar ce sosai misalin qarfe biyar na yammacin,tana zaune saman kujera 'yar
tsuguno tana tsinke danyan zogale,halima na bakin kurfeti wanda take kwashe tuwon
dare,mama na saman tabarma daga gefen sumayya tana daka gyada da daddawa,sai zainab
wadda ke wankin kayan sumayyan wanda basu wuce kala hudu ba,hira suke irin wadda ta
shafesu,sosai hirar kewa sumayya dadi don har qyaqyata dariya take.

        Sallamar yaro ce ta katse musu hirar wanda ya sanar musu mukhtar na


gaidasu,mama ce ta fadawa yaron yace ya shigo wanda hakan ya sanya sumayya sakin
zogalen hannunta ta dafa qasa tare da yunqurawa ta miqe,bat fara'ar dake fuskarta
ta bace,a hankali ta juya ta shige dakin yayin da maman ta bita da kallo lokacin da
take qoqarin zura hijab a jikinta.

        Yara ne suka fara shigo da kaya,akwatu ne har seti uku matsakaita masu
kalar ruwan hoda da ruwan toka(ash and pink)masu azabar kyau,sai da suka ajjiyewa
suka fice sannan mukhtar din ya shigo.

        Sanye yake da shadda ruwan madara(milk)dinkin tazarce wadda tayi masifar


masa kyau,sosai ta dace da shi duk da irin ramar da yayi,kamar ko yaushe ya gaisa
da maman cikin kunya da nutsuwa kafin shiru ya biyo baya na 'yan daqiqu sannan yace
"Kaya ne mama gasu nan,idan akwai abinda babu ciki sai a sanarmin don Allah mama"
addu'ar fatan alkhairi tayi sannan daga bisani ya miqe bayan ya ajjiye wasu kudi
gaban maman ya fice yana kiran halima.

        Kusan duk cikin kunnenta komai ya faru,idanunta na a rufe har ya fice daga
gidan,wani gudu gudu zuciyarta ke mata tare da wani zafi,duk sanda ta tunashi kota
jishi ko ta ganshi wani miki ke motsawa cikin zuciyarta,har yanzu cikin jin
haushinsa da zarginsa babu abinda ya ragu cikin zuciyarta,a ko yaushe zuciyarta na
gaya mata tunda mukhtar ya zargeta aduniya waye zai gasgata ta?,waye zai yarda da
gaskiyarta,a haka ta zame ta kwanta ko zata samu sauqin zugin da zuciyarta ke mata.

      Bayan sallar isha'i mama ta nunawa mallam akwatunan,bai buda ba yayi addu'a
dai kawai,cikin sauri halima da zainab da suka qagu suga meye a ciki suka matso
gaban akwatim suka soma budewa,sumayya na daga saman kujera wadda tunda ta yiwa
malam sannu da zuwa bata sake cewa komai ba,sanye take da hijabi hannunta riqe da
qaramin alqur'ani tana karantawa qasa qasa,sam idanunta bai kansu karatunta kawai
take kamar batasan meke faruwa ba.

        Ba qaramin tafiya da su halima kayan sukayi ba,kallo daya zaka musu ka


tabbatar mukhtar yayi rawar gani,kaya ne masu dan uban kyau da tsada unisex,takalma
huluna,riguna fidoji,tarkace dai kala kala wami abun ma basu san sunanshi ba,akwati
biyun duka na jarirai ne,yayin da ta qarshen atamfofi ne super biyu,lace daya
shadda daya,sai materials masu kyau guda biyu jaka takalmi da mayafi sai sarqa da
awarwaro,kana kallonsu kasan na uwar yaro ne na fitar suna
"Masha Allah,wannan yaro ko yarinya anyi dan gata,don Allah anty sumayya dago ki
gani" zainab ta kasa shiru ta fadi haka. A hankali ta daga idanunta ta watsawq
zainab din wanda ya sata dawowa hayyacinta,sai tayi shiru ta sadda kai yayin da
sumayyan taci gaba da karatunta ba tare data sake tofawa ko dubansu ba.

       Qememe taqi yarda a ajjiye kayan a dakinta kusa da ita,tun yaya abubakar na
tsokanarta suna dauka wasa ne har suka gane bil haqqi da gaske take,don kuka ta
fashe musu da shi,tilas ya abubakar ya karbi kayan ya musu ma'ajiya a dakinsa.

  ****   ****   ****   ****

    Tunda ta idar da sallar isha'i ta kwanta bayan taci tuwon dare,wani mugun ci
tayi masa har halima na mata dariya tana tsokanarta duk da yadda take jinta a
takure saboda yadda baya da mararta ke ciwo kadan kadan. Bacci taso ya dauketa
saidai yaqi zuwa juyi take lokaci bayan lokaci saboda yadda kwanciyar taqi mata
dadi duk da cewa idan da sabo ta saba tunda cikinta ya fara nauyi,a haka har su
halima suka gama bidirinsu suka shigo suka kwanta bacci ya kwasheta idanunta biyu.

       Sannu a hankali taji ciwon yana ci gaba da qaruwar mata daga mararta zuwa
baya,sai ta miqe a hankali jin motsin mama da tayi a tsakar gida tana rufe kitchen
da alama bata kwanta ba,tana qoqarin shiga daki sumayyan ta kira sunanta,waiwayowa
tayi cikin mamaki ta amsa don a tunaninta ta jima da yin bacci tunda ta riga kowa
kwanciya.
"Mama marata da baya ne kemin wani irin ciwo,gashi na kasa bacci" idanu ra zuba
mata tana nazarinta sannan tace
"Tun yaushe ne?"
"Tun dazu" ta fada tana cije lebe saboda yadda aka mintsineta,kai ta gyada sannan
ta juya ta bude dakinta maimakom dakin malam da take niyyar shiga tace da ita
"Shiga ki kwanta anan ina zuwa" ta fadi tana sake juyawa zuwa dakin malam din.

        Koda maman ta dawo bakin gado ta sameta zaune saboda kwanciyar ta


gagareta,ji take kamar ana tsaga mararta ana karya gadon bayanta,tuni gumi ya fara
yi mata sallama,yarfa hannu take tana kiran sunnayan Allah tare da mirgina kai hagu
da dama,kofin hannunta maman ta miqa mata cike da tausayi tace ta shanye,kallo daya
tayi mata ta tabbatar naquda take,daga kai tayi ta shanye baki daya sannan ta dire
kofin a wahalce,cikin mintina qananu ciwon ya sake yin gaba.

       Awa daya ta wuce shiru biyu shiru hakan ya sanya mama ta sake komawa gun
malam ta kuma karbo mata wani rubutun ta sake shanyewa,tun tana daurewa har hawaye
suka qwace mata ba tare data shirya ba,ba shakka zamantowa uwa ba qaramin abu bane
haka ta dinga rayawa cikin zuciyarta.

         Qarfe biyar saura na asubahin ranar talatar ya zamanto mata ranar tarihi a
gurinta,dai dai lokacin da yaron cikinta ya shaqi iskar duniya,kukansa ya karade
ilahirin gidan wanda ya sanyawa ilahirin wanda ke gidan yana bacci farkawa,malam
kuma dake zaune dungurgur yayi hamdala ga ubangiji yana qarawa.

      Ware idanunta tayi sosai sanda iskar sanyin asuba ke busata,tana son
tabbatarwa kanta da gaske ne abinda ke cikinta ne ya iso duniya yake cala kuka
haka?,da gaske ne a yau itama ta zama uwa?,ta shiga sahun iyaye?,da gaske yau itama
zata riqe ta kalla ta kuma raini danta na cikinta?,ta fita daga sahun juya?,wannan
kalma ta zama tarihi cikin rayuwarta?,a yau ta haifawa mukhtar da wanda yake buri
gareta buri gareshi,sai dai kash,ba zaya samu irin tanadin da suka yiwa rainon da
zasu bashi ba,wata qaqqarfar QADDARA ta shigo ta farraqa kasancewarsu tare,a yau
zasu raineshi ne a mabanbantan gurare,sai ta saki kuka a fili wanda cikin zuciyarta
tana tasbihi ne ga ubangiji,cikin mamaki mama ke dubanta
"Lafiya ko wani guri ke miki ciwo kuma?" Ta tambaya sanda take tsaka da qoqarin
dauke yaron da gyara gurin,kai ta girgiza tana ci gaba da kuka,tuni maman ta gano
kukan me take saboda haka taci gaba da aikinta tana cewa
"Godiya ya kamata ki yiwa ubangiji ai".

       Kafin gari ya waye tuni komai yayi tsaf daga uwar har dan har gurin da akayi
naqudar,maman ce ta shigo da yaron dake nannade cikin shawul ruwan sararin samaniya
bayan sunqufe shi da akayi cikin lallausan kayan sanyi suma ruwan bula din,malam ta
kaiwa shi bayan ya dawo sallar asubahi ya ganshi,ya sha addu'a kuwa bayan wasu
sirrika da ya hada ya dangwala masa a baki,sumayyan na gefan gadon mamam riqe da
kofin shayi mai kauri da maman ta hada mata kan ta fita da yaron,har yanzu ta gaza
shanyeshi saboda bacci dake dibarta
" karbeshi ki ganshi sumayya ki masa addu'a"maman ta fada tana dora mata shi saman
cinyarta bayan ta karbo kofin shayin data samu ta shanye.

     A hankali kamar mai tsoron tabashi ta sanya hannu ta tallabeshi,take idanunta


suka cika taf da qwalla,a sanyaye ta sanya hannu ta yaye rufin fuskarsa idanunta
suka sauka kan fuskar tasa wadda idanunsa ke rufe ruf yana ta sheqar bacci cikin
lumana da kwanciyar hankali,kallo daya tayi masa ta hango kamanni na kai tsaye da
yaje da babansa duk da ba idanunsa biyu ba,a kallon farko taji wata iriyar qauna da
soyayyar yaron ta mamayeta,irin qauna ta da da mahaifi,tausayinta kuma ya samu
gurbi cikin zuciyarta karon farko data tuna irin siradin da rayuwarsa ta tsallake
kafin ya kai ga isowa zuwa ga wannan fili da muke kira da duniya,sai gashi Allah ya
nuna ikonsa,yaro qato kyakkyawa mai cike da qoshin lafiya,wanda ko cikin mafarkinta
bata taba tunanin zata haifi kamarsa ba
"Bawan Allah" ta furta ba tare da tasan a fili ta ambaci hakan ba qwalla na
kwaranyo mata,daga shi tayi zuwa fuskarta ta karkata kunnensa na dama ta karanta
masa kiran sallah ta karkata na hagu ta karanta masa iqama sannan ta ambata masa
sunansa *ABDALLAH* bawan Allah.

     Murmushi mama tayi ta dubeta


"Amma kya jira babansa yazo ya zaba masa suna ko?" Kai ta girgiza
"Kiyi haquri mama,ni yafi kamata mama na sa masa suna,ni kadai nasan wahalar da
nasha,daga ni sai ubangiji na ma......." Sai ta kasa qarasawa saboda karyewa da
zuciyarta tayi
"Kukan ya isa haka,yau ranar murna ce,ajjiyeshi kusa da ke,maza so nake ki kwanta
kiyi bacci sosai" bata musa ba din tayi yadda maman tace,tun tunaninnika na bijiro
mata har wani nannauyan bacci mai dadi yayi gaba da ita.

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

3⃣5⃣

_______________________

*Bismillahir rahmanir rahim*

*wallazi yumutuni summa yuhyi,wallazi adma'u ay yagfirali khadi aty yau maddin*
______________________________

A makare ya tashi yau wanda hakan ya sabba ba masa yin sallar asubahi cikin
gida,tunda ya idar da sallar yake zaune saman daddumar bai tashi ba kamar yadda bai
aiwatar da komai ba,tunanin sumayya ne fal zuciyarsa yau ya wayi gari da
shi,hakanan yake jin wunin yau ba zai iya qarewa ba ba tare da yaje ya ganta da
lafiyar abinda ke cikinta ba,kusan tunda ta shiga watan haihuwarta da ita yaje
kwana yake tashi.

Qarar wayarsa ce ta katse masa hanzari,ya juya bangaren da take ya jawota ya


duba,baquwar lamba ce,ya latsa sannan ya kara a kunnensa,runtse idanunsa yayi
zuciyarsa ta soma quna saboda muryar wadda yaji,bai taba jin ya tsani wani abu
tsana mai tsanani ba irin na mamallakiyar muryar,zainab ce take magana cikin maqale
murya da wani irin salo nason tafiyar da hankali,tun a daren jiya bokanta wanda
take kira da malam ya bata wannan sa'ar ya kuma tabbatar mata bayan sallar asubahi
ne zata sameshi,sanda ya daga wayar zuciyarta sai ta cika da farincikin samun
nasara,don dama ya sanar mata bayan sallar asubar a gobe bazai koma bacci ba,jin
tana ta magana ya mata shiru ya sanya ta fashewa da wani makirin kuka
"Habaa my mukhtar,dama laifin wani kan iya shafar wani?,mene laifina ni a ciki?,duk
iya yina nayi don inga abinda ke cikin yarinyar nan ya kubuta,duk tarin hidima dana
dinga yi da ita rana daya duk ka mance ka watsar da alkhairi na a gareku ka
sakeni,kuma ma tunda an samu cikin na nan ba shikenan ba komai ya wuce sai ka
maidani daki na ko?".
Kamar garwashin wuta haka yaji kalaman nata,cikin harzuqa ya dakatar da ita
" ke wacce iriyar jahila ce wai?,shin kin manta zama ni dake a yanzu ya haramta ne
sau nawa zan nana ta miki,ke koda kuwa ma zamanmu ya halatta bazan iya zama da
kowacce mace ba a yanzu,tunda sumayya da na raina da kaina ta iya min haka babu
wata diya mace da ba zata iya aikata min makamancin haka koma fiye da shi ba,saboda
haka gargadina dake na qarshe,kada ki sake gigin kiran layi na ko tarar hanyar da
kika san zan bi,idan kuma kinqi ji ba zaki qi gani ba"daga haka ya katse kiran ya
ajjiye wayar a fusace.

Daga daya bangaren nata itama ajjiye wayar tayi tana huci sannan ta dubi
qawar tata
"Wannan wanne irin mutum ne haka?,duk zama da wuyar da muka sha wajen malam ta
tashi kenan a banza,kinji maganganun banzan da yake gaya min?,to wallahi wannan
karon babban aikin zan saka a masa koda duniya zata zageni,ko zanyi yawo babu zanin
daurawa" kafada ta daga tana fadin
"Au ho sai yanzu kika gane kenan?,tuntuni ai malam din ya gaya miki ki saki naira
kiga aikin da ko uwarsa dake kabari ba zai ganta a gabansa ba sai ke" miqewa tayi
ta fice daga dakin fuuu tana fadin
"Ai anzo gurin kuma".

A hasale ya kuma waiwayowa ga wayar tasa jin ta sake tsuwwa a karo na biyu
yana zaton ita din ce ta sake kiransa,sai jikinsa yayi sanyi gabansa ya fara faduwa
ganin sunan abubakar kan screen din,cikin sanyi da sallama ya amsa wayar,lumshe
idanuwa yayi wata rahama na sauka cikin zuciyarsa lokacin da abubakar ke furta masa
albishir mafi dadi da ya taba sauraro tsawon rayuwarsa,sumayya ta haihu ta haifa
masa yaro,baisan adadin lokacin da ya dauka ba cikin duniyar madaukakin farinciki
shidai ya farka yaga har kiran na abubakar ya katse.

Faduwa yayi saman a bin sallar yayi sujudush shukur yana mai tasbihi ga
ubangiji,bai wani jinkiri ba ya miqe ya fada makewayi ya shiga wanka,cikin mintina
talatin ya fito,kai tsaye gaban sif dinsa ya isa bayan ya tsane jikinsa,ya bude
yana kallon kayan,a sanyaye ya sauke hannayensa yana duban kayan kala bakwai da
suke sababbi dukkansu,ba zai manta randa ya bada dinkinsu ba,tun cikin sumayya na
da wata uku a lokacin tana gidan,musamman ya tanadesu ya dinkasu saboda ya sanyasu
tun daga rana ta farko da aka haifa masa yaronsa har ranar suna,baya iya manta
lokacin da take dariya tana tsokanarsa da cewa gandoki,sai ya koma bakin gadon ya
zauna yana yarfa hannu,yana jin yadda bacin rai ke taso masa yana son danne
farincikin da yake ciki,baisan mai yasa har yau zuciyarsa ta kasa daina jin ciwon
abinda tayi masa ba duk da cewa an cimma nasarar tsallakewar cikin gashi har yau
Allah ya nufa ya iso duniya.

Da qyar ya samu ya hadiye wani dunqulen abu mai daci sannan ya miqe ya
shirya cikin wani yadi mai kyau na maza fari sol wanda ya masa kyau sosai,ko abinda
zai sawa cikinsa bai nema ba ya fito don dama ba ko yaushe yake samun damar
karyawar safe ba,yana shirin tada motarsa ya kira ya yahansu ya shaida mata,hamdala
ta dinga yi matiqa da gaske tana jin dadi a zuciyarta,ta kuma shaida masa lalle ya
biyo gidan nata kafin ya wuce.

Kafin sha daya na safe tuni gidan ya cika da jama'a 'yan uwa da abokan
arzuqi,kowa barka yake mata tare da tayata farincikin wannan rana da aka jima ana
saka ran zuwanta,sam ita bata san me ake ba ma,bacci take sosai ita daya a
dakinsu,yaron shima nashi baccin yake,sai da ya farka ya fara kuka alamar yunwa
sannan mama ta baro dakinta wanda suke zaune da mutane ta shigo dakin ta
tasheta,sai data sake hada mata shayi mai kauri ta sake sha sannan ta dora mata shi
saman cinyarta ta fara koya mata yadda zata shayar da shi,runtse tayi sannan ta
fara qorafin zafi maman tace
"A haka zaki daure har ki saba".

Sallamar da kunnuwanta ya jiyo shi ya sanya jikinta saki,sai ta zubawa


bakin qofar dakin ido tare da barin qorafin da takeyi,halima ce ta shigo
" mama ga yaya mukhtar"
"To ya shigo mana" ta fada tana gyara mayafin jikinta,qasa sumayya tayi da kanta
tana duban yaron dake saman cinyarta yana tsotsar nono a hankali,sallama yayi cikin
dakin sannan ya qaraso a nutse hannunsa dauke da qatuwar baqar leda,baki daya
idonsa na kan sumayya da yaron wadanda kowannensu yake jin mabanbantan yanayi a
kansa cikin zuciyarsa,wata qauna ta musamman yaji ta dirar masa tun kafin yayi
tozali da gudan jinin nasa,yayin da tausayi da kuma wata daraja ta sumayya ta daban
yaji ta ginu a ransa,a mutunce suka gaisa da maman sannan ta miqe ta fice,shiru ya
ratsa dakin bayan ficewar tata,shi yana zaune yana aukin kallonsu ya rasa daga inda
zaya fara,yayin da itama taqi motsin kirki dukkan idanunta na kan yaron nata tana
dubansa,tana jin yadda yake zuqar mama har cikin ranta,ci gaba yayi da dubansu wani
yanayi na ratsashi,sai suka burgeshi sosai,karo na farko da yaji zai iya yafewa
sumayyan kome tayi masa,yana ji a yanzu ta cancanci yafiyarsa.

Cikin qwarin gwiwa da karsashi yayi gyaran murya tare da muskutawa yace
"Sannu sumayya"ta dan cije lebe kadan sannan ta amsa can qasa
" yauwa"
"Sannu da qoqari,Allah ya saka miki da alkhairi,na yafe miki sumayyan duk wani abu
da kika yimin" da sauri ta daga kai ta dubeshi sannan ta kau da kai
"Bana buqatar yafiyarka tunda ni din ban aikata maka ko wanne laifi ba,hasalima ni
nafi cancanta da a nemi yafiya ta" mamaki kalaman nata suka bashi,bai kai ga furta
komai ba mama ta sake shigowa hannunta dauke da kofi cike da kunun kanwa yana
tururi
"A'ah,baki bashi shi ya ganshi ba,ki cire shi haka idan ya gama ganinsa yaci gaba
da sha ko" ta fada tana dire kofin tare da ficewa.

Bata kammala ficewar ba ya taso da kuzarinsa ya qaraso gabanta sanda ta cire


maman daga bakinsa tana gyara masa rufa,ya miqo hannunsa ta dora masa shi saman
hannun nasa tana fadin
"Ga abdallah nan"sai ya cira kai ya dubeta,tabbas suna ne mai kyau da asali,ko shi
din ma sunan yayi masa,baice komai ba ya koma da baya ya zauna inda ya tashin yana
kallon yaron,baisan fuskarsa ta wadata da murmushi ba,baisan hawaye na bin fuskarsa
ba sai da yaga digarsu kan kuncin yaron wanda hakan ya sanya yaron bude idanunsa
yana kallonsa,wata qaunar sumayyan ke son dawowa cikin zuciyarsa,ko babu komai koda
ta aikata laifin tayi fama da dakon wannan qaton babyn cikin cikinta tsawon watanni
tara ta kuma yi naqudarsa ta haife masa,rana da wani matsayi na daban wanda babu
diya macen da ta takashi cikin rayuwarsa,ita din ma dubansu take tana daga
zaune,wani wawan rauni keson ziyartar zuciyarta,saidai zargin saurin yanke hukunci
na mukhtar da rashin bincike ke naushin zuciyarta,sai ta dauke kai daga dubansu
tana jin kuka nason qwace mata tana qoqarin maida shi.

Ya jima zaune yana aikin kallon yaron da yi masa addu'a tamkar zai maidashi
ciki,sam kamar ma bashi da niyyar tafiya,har sai da aka sake yin baqi sannan ya
miqe ya dora mata shi saman cinyarta,ya sunkuya ya sumbace har tana jin hucin
numfashinsa wanda hakan ya sanya ta ja da baya,ya dago yana dubanta bayan ya ajjiye
ledar da ya shigo da ita a gefanta ya dora kudi a sama
" ga wadan nan ko zakuyi amfani da su,ban yarda a dorawa kowa wani nauyi wanda yake
nawa ne,Allah ya qara muku lafiya"ya fada yana juyawa ya fice daga dakin a sanyaye
tamkar bai son tafiyar

**** ***** **** ****

Cikin kwanakin hidima aka dinga yi sosai cikin gidan,duk wani dan uwa na
jiki ko aboki babu wanda baizo ya tayasu murna ba,mukhtar kuwa kullum qafarsa na
gidan babu ranar da bazaizo ganin fuskar Abdallah ba,sau tari saidai sumayyan tasa
a miqa masa shi tana daga cikin gida.

Yaya yahanasu tazo a kunyace saidai ita daya don sauran duk sun kasa
zuwa,atamfa ta kawowa sumayya turmi biyu sai dan qaramin akwati na qarshen wanda ta
cikoshi da kayan baby,ba wanda ya nuna mata komai suka karba suka mata godiya.

Suna akayi na gani na fadan tamkar tana gidanta,hatta anty dije dake abuja
ba'a barta abaya ba sai data halarta ita da yaranta baki daya,duk da cewa suna
tsaka da zangon karatu amma sai da suka dauki uzuri suka zo,rago da saa mukhtar ya
yanka masa,sosai abdallah yaga gata,yaron yazo da farinjini da goshi mai yawa,qauna
da soyayya ko ta ina,kowa gwada masa kalar tasa yake yi.

**** ***** *****

Jego take sosai irin na daa shi mama take mata,sosai take gasata ta kuma
cikata da cimaka,irinsu romon nama,tuwon dawa kunun kanwa kunun gyada da
sauransu,hakanan babu fashin wankan ganye safe da yamma take yinsa har sai data
cika kwanaki arba'in harda doriyar kwana biyar,zuwa lokacin ta murje ta dada
kyau,idan ka dubeta ba zaka taba cewa ita ta haife abdallah ba,yayin da abdallahn
yayi wani irin wayau da qiba dauka da nishi ajjiyewa da nishi,kullum mukhtar na
hanyar gajin yaronsa,sau tari yakan bawa mama da malam tausayi yadda baya ko
gajiya,duk sanda zaizo hannunsa dauke da wani abu yace na abdallah ne,har da abinda
bazai yi masa amfani a yanzu ba saidai ko nan gaba,itakam sumayyan bata ma yarda su
hadu bada yaron take ta shige daki,yakan jima yana yiwa yaron wasa tare da jin
qaunarsa da kewar mahaifiyarsa cikin zuciyarsa.

**** ***** ***** ****

Rayuwa ta mata kyau saboda ta samu gata yadda ya kamata,cikin watanni uku
abdallah ya soma iya zama,wata na biyar rarrafe ya miqa,sosai yaron yake da shiga
zuciya da daukan hankali,saboda tsafta da kukawa da yake samu,ko yaushe zaka ganshi
tsaf cikin shiga ta gayu kamar wani saurayi,idan manyan kaya ta sanya masa kai kace
babban mutum ne,idan kuma qananun kaya ne sai ka dauka saurayi ne,baya rabo da
qamshi shi yasa har maqota aikowa suke daukarsa,zuwa wannan lokaci mukhtar wani
lokacin yakan zo ya daukeshi ya jima wajensa wani lokaci har kasuwa yake leqawa da
shu,tun tana bata rai mama na mata fadan na zata raba da da uba ba har ta saki
ranta ta haqura,wata goma ya qware a tafiya sosai,idan ka ganshi sai ka zaci yayi
shekara daya da rabi ne.

A lokacin yaya abubakar ya sama mata foam na wata makaranta dake koyar
sana'o'i,ta zabi ta koyi yadda ake saqa da humra turaren wuta da na kaya da na
tsugu no,hankali kwance take zuwa makarantarta ta dawo don bayan layinsu
take,abdallah kuwa bai cika rigima ba sai idan yaso,saboda haka a gida take barinsa
taje abinta ta dawo,koda ya sa rigima ma zainab ko halima kan daukeshi su kai mata
shi,a lokacin ta sake wani kyau da cika,saika rantse da Allah bata taba aure ba
balle har ta haifi yaro.

***** ****** ******

Qarfe hudu da mintuna ta iso gida a gajiye,tana sallama abdallahn ya kubce


daga hannun zainab dake shafa masa hoda a wuya da alama wanka aka sake masa,riga ce
mara hannu a jikinsa sai wando three quater,yayi kyau sosai,da gudunsa ya taho ya
tareta yana mata gwalantu wanda ke nuna alamar fara koyon magana,daga shi sama tayi
tana juya shi suna qyalqyala dariya sannan ta direshi tana amsa maganar zainab
wadda ke mata qorafin yau abdallah ya bata kaya sunfi uku
"Kunfi kusa ai,bake ke kareshi ba idan za'a masa fada" tayi maganar tana qarasawa
bakin fanfo don daura alwala tana sake fadin
"Mama fa?,naji gidan shiru" zainab dake tattara kayan kwalliyar abdallah ta amsa
mata
"Eh sun fita ita da ya halima gidan maman shafa'atu ganin salima"
"Kice biki ya kusa kenan"
"Wlh saura 'yan satittika basu wuce uku ba"
"Allah ya sanya alkhairi" ta fada tana gyara daurin dankwalinta ta shige daki
donyin sallah abdallah na biye da ita a baya yana mata surutu.

Tana kammala sallar abdallah na saman jikinta yana faman qiriniya da


nuqurqusarta taji sallama kamar ta bahijja,kafin ta yunquro taji ana tambayar tana
nan zainab ta amsa da eh,bahijjan ce kuwa,hannu bibbiyu ta karbeta sai da suka fara
gaisawa ta sanar mata tare da abdur rahman suke yazo ganin abdallah,idanu ta zaro
tana dariya
"Iyeee,kice da tare da larabawan madina kuke kada kai ace har an gama karatun?"
Cikin murmushi bahijja tace
"A'h,yadai samu hutu ne yace tunda ya shekara bari yazo yaga gida"
"Da kyau.....zainab zoki dauki carfet ki shimfida masa a zaure(soro)"ta fadi tana
murmushi tare da qoqarin miqewa.

Tare suka fito da bahijjan saboda abdallahn na hannunta,ji take kamar kada ta
ajjiyeshi yaron ya shiga zuciyarta sosai.

Tun kafin ta qarasa soron wani kalar qamshi na daban ya ziyarci


hancinta,zaune yake ya hakimce kan carfet din,yana sanye da shadda ruwan siminti
sai qyalli take,kansa saye da baqar hula,baki ta riqe tana murmushi,sosai abdur
rahman din ya sauya,ya zama wani babban mutum lokaci daya,kai bakace abdur rahman
din dake tayata zama bane sanda tana amarya mai qarancin shekarun da basu gaza goma
sha uku ba,ya zama mai cikakkiyar kamala da haiba,fatar nan tayi fresh da ita,duk
yadda taso ta zolayeshi da tsokana kamar yadda suka saba sai ta kasa sanda shi yake
tsokanarta da iyeeem ba,yarinya ta girma gata da yato ta zama mama,bayan sun gama
barkwancinsu kasancewarsa mutum mai yawan son barkwanci sannan ya shiga jajanta
mata abinda ya faru tun daga samuwar cikin abdallan zuwa haifeshi,suna tattaunawa
yana wasa da abdallahn har bahijja ta gaji ta tashi ta koma ciki wajen zainab ta
barsu a nan.

Sosai yaron ya masa ya tafi da shi har ya gaza boyewa sai da ya


furta,murmushi kawai tayi suka ci gaba da hirarsu a haka mama ta cimmasu,a mutunce
suka gaisa tana mamakin ganinsa da sauyawarsa ta tambayeshi mutanan gidan ya amsa
duka lafiya ta dubi sumayya
"Amma ai abdur rahman ba baqo bane da zaki barshi a soro,maza tashi ka dawo tsakar
gida" cikin tsokana yace
"Atoh mama na sani ko rowar gidan ake min,ni kuma naga gun hira kuwa har na
koma,tunda nayi aboki" hararar wasa sumayyan ta masa tana cewa
"Dadinta ai na maka tayi kace a'a tunda mama bata nan nan zaka zauna" ta fada tana
shigewa cikin gidan.

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

3⃣6⃣

_____________________________
*Bismillahir rahmanir rahim*

*huwallazi yuhyi wa yu miit*

*sannan shi (Allah) shi yake rayawa yake kuma kashewa*

______________________________

       A tsakar gida zainab ta sake shimfida musu wata tabarmar suka koma ciki.

       Hira sosai suka dinga yi har da mama,abdur rahman na basu labarin garin
ma'aiki madinatul munawwara har aka kirayi sallar magariba,tare suka fita sallar
shi da malam da yaya abubakar,koda suka dawo ma bai tafi ba tare suka ci abincin
dare sannan ya musu sallama.

         Hannunsa dauke da abdallah ya fito daga gudan,bahijja da sumayya na


bayansa wadda ta fito don ta dan taka musu,a bakin motarsa sabuwa da ya sauya qirar
range rover yaja burki yana duban sumayya
"Tsarabar abdallah bata qaraso ba,ko zaki dan rakamu waccan titin dake gabanku naga
akwai wami super market na dan masa siyayya kafin su iso?". Kai ta kada tana
dubansa
" haba sabida dorawa kai wahala,mun yafe duk sanda suka iso ma amsa".kunu ya dan
sha yana dubanta
"Dorawa kai wahala kuma?,niba babansa bane?,ko kina so kice ba yarona bane?" Baki
ta bude tana dariya tare da dubansa tace
"Ni na isa in fadi haka,kai matsala ta da kai son girma fa"
"Ban kai naso girma ba ko sumayya?" Ya fada cikin wani irin salo da ya sauya
yanayin muryarsa idanunsa cikin nata,wanda ya haifarwa da sumayyan rage farashin
dariyarta,karon farko da taji duban qwayar idonsa ya mata nauyi,sai ta janye idonta
tana cewa
"A'ah,ai ko da sakan daya mutum ya girmeka ya girmemaka har abada" dan shiru yayi
sannan ya gyara tsaiwarsa yana miqa mata abdallah
"Karbeshi yau mun wunar muku,sai kuma gobe idan Allah ya kaimu" ta amsheshi tana
cewa
"Allah ya nuna mana goben" cikim zuciyarta ta dauka da wasa yake,hannun abdallahn
ya bude ya sanya masa 'yan dubu dai dai guda uku yana cewa
"Kasha sweet my son"
"Habba abdur rahman...."
Katseta yayi ta hanyar cewa
"Shshshshsh!,ai bake na bawa ba ko?,kuma wai bakijin kunyar fadar suna na haka
gatsal?" Galala ta saki idanu ta bishi da kallo
"Kunyar kamar yaya?" Ta fada tana dubansa,murmushu kawai yayi ya bude gaban motarsa
ya zauna sannan yace
"Sai goben ko 'yamma ta?" Murmushi ta saka mamakin abdur rahman din na kuma kasheta
"Nice kuma yau 'yammata abdur rahman ga yaro na a hannu?"
"Oh,kuma fadar sunan nawa dai kika yi?" Ya tambayeta yana kada kai,shuru ta masa
tana zagayawa wajen bahijja ta dubeta
"Bahijja ki gaida mama kinji,naga alama wannan yayan naki bayan karatu sa ya tafi
qarowa ya qaro yadda ake canjin hali" dariya bahijjan tayi tana amaa mata da zata
ji,shima dariyar yayi sannan ya tada motar tasa yayin da sumayya ta shige gida.

        Tunda ya shigo da motarsa layin su sumayyan ya hagi tsaiwar wata motar a


qofar gidansu,har zuwa yanzu da motar tazo ta wuce ta gefan tashi yana binta da
kallo tare da qoqarin tantance waye a ciki,saidai duk qwaqqwafinsa ya kasa gane
waye a ciki saboda glasa din motar mai duhu ne,hakanan sai yaji wani abu mai tauri
ya riqe masa wuya,rabin 'yar walwalar da ya samu wunin yau ta kau baki daya,a sannu
yaci gaba da tuqa motar tasa har ya qaraso qofar gidan ya tsaya ya fito ya samu
yaro ya aikashi ciki,ba jimawa yaron ya fito dama sun riga da sun saba duk sanda
aka aika akace ana gaida mama to mukhtar din ne kuma sun san me yazo yi,sai halima
ko zainab ta kawo masa abdallahnsa,nan cikin mota yake zama da shi su qaraci wasan
su sannan yayi horn su fito su karbeshi da abinda ya kawo masa sannan ya wuce,sau
tari yakanji sha'awar ganin sumayyan saidai babu wannan damar,rabon da ya ganta ma
bazai iya tantance adadin kwanakin ba,tilas yaje danne komai don ya sani a yanzu ta
fita a huruminsa.

        Yau din ma kamar kullum hakan ce ta kasance,abdallahn nata masa gwalanto


saidai bai gane me yake cewa ba biye masa kawai yake,bai wani jima ba ya maida shi
ya tafi zuciyarsa na sakutarsa kan motar da ya gani,ya mance cewa a yanzun sumayyan
rabon mai rabo ce ba mallakinsa bace

  ****    *****   ******  ****

          *BAYAN KWANA BIYU*

      Tun daga ranar abdur rahman ya maida gidan gurin hirarsa,wani lokaci yazo shi
kafai wami lokaci ya taho da bahijja,da yake su biyu Allah ya bawa mamansu,sukan
dauki lokaci da sumayya suna hirarsu,yayin da wani lokaci idan ya furta wata
maganar sai ta sanya ta a duhu,wani sa'in takan yi murmushi ta alaqanta hakan da
girma da abdur rahman din ya sake yi,ya fara zama babban mutum shi yasa yanayin
hirarrakinsa suke sauyawa,bata taba kawo komai cikin zuciyarta ba saboda ita din
rainon mutum daya ce da mutum daya ta taba gina duniyarta wato mukhtar,ba komai
take iya ganewa ba ko fahimta game da wasu baqin al'amura a gun d'a namiji ba.

     Sau biyu mukhtar na katarin ganin motar na tasiwa daga qofar gidansu ta fice
daga layin,saidai har yau bai samu nasarar gano waye ba,lamarin ya tsaye masa a
zuciya,duk da yasan baida hurumin hakan amma zuciyarsa ta gaza daurewa,hakan ne ya
sanyashi cin washin zuwa ya tadda ko waye.

    Tunda ta fito daga makarantar tasu ta lura yake bin bayanta cikin mota wanda
hakan ya matuqar tsorata ta musamman data lura yau unguwar tasu babu yawaitar
jama'a,hakan ya sanya ta qarawa qafarta sauri.

      Ganin tana neman bace masa ya sanya shi faka motar sannan ya fito ya biyo
bayanta,gabanta taga an sha wanda ya hakan ya dan tsorata ta taja baya taba
dubansa,matashi ne wanda a qalla zaiyi shekara arba'ain da biyu,dogo ne baqi maras
jiki sosai,za'a iya karansa da chaculet colour,babu laifi yana da kyau dai dai
gwargwado,kana kallonsa kasan yana cikin rufin asiri da wadata dai dai gwargwado
"Assalamu alaikum" ya fada yana murmushi wanda sallamar ta dauke kaso mafi yawa
daga cikin tsoron da ya cika zuciyarta,cikin qarfin hali ta amsa masa
"Don Allah kiyi haquri,nasan ban tsaidaki a yanayin da ya dace ba,nidai suna na
lukman,na gaza daurewa zuciya ta ne shi yasa ni aikata hakan,na lura kamar a darare
kike da ni,idan ba zaki damu ba ki bani lambar wayarki sai muyi magana" kamar kuwa
ya sani a takuren take,saboda wannan shine karo na farko da ta fara tsaiwa da wani
namiji,ga masu shugewa jifa jifa suna faman binta da kallo,hakan ya sanya cikin
rudewa ta karanto masa lambar halima don bata da niyyar bashi tata,yayi serving
yana murmushi gami da yi mata godiya,bata ko jirayi amsa masa ba tayi gaba da sauri
shima ya wuce ya tada motarsa ya fice a layin.

        Tun daga nesa take hangowa kamar shine sabe sa abdallah ya zuba mata
idanu,sai data qaraso gab da shi ta tabbatar shi din ne kuwa,hannunsa dauke da leda
wadda ta tabbatar abdallah ya yiwa siyayya kamar yadda ya saba
"Waye wancan?" Ya tari numfashinta ya furta fuskarsa a dan daure ta hanyar riga ta
yin magana,dan galala tayi tana dubansa cikin mamaki,sai kuma ta basar ta saki
dariya cikin tsokana tace
"Bazawari na ne"
"Bazawarinki?" Ya tambaya cikin nanatawa har sau uku yayin da ta tsaya tana sake
dubanshi
"Eh mana" ta fada kanta tsaye,shiru yayi kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa ya
sauya akalar abinda zai fada din da cewa
"Ok,muje qofar gida akwai maganar da nakeso muyi" ya fada cikin magana ta gaske
yana yin gaba,kamar an qulle bakinta sai ta ja qafafunta ta bishi.

      Qofofim gaban motar ya bude ya shiga nashi mazaunin yana dauke da abdallah
wanda baiko damu da ganin maman tasa ba,ya wani lafe jikin abdur rahman din yana ta
fama da biscuite,dubanta yayi ganin tana tsaye qiqam a waje
"Bismillah shigo ki zauna" kafadunta ta daga
"Haba,ai kaima kasan bai kamata ba,mu shiga cikin gida kawai ko meye ai ina ga sai
yafi dadin tattaunawa ko ba cikin mota ba"
"Ai nasan da cikin gidan,amma maganar bata cikin gida bace,idan kuma kina da wani
gu da zamu mu tattauna kuma to" kanta ya daure tana mamakin wacce iriyar magana ce
haka da yakeso suyi da sai su kadai?
"To amma kuma malam fa,idan ya dawo ya ganni cikin motarka"
"Indai malam me baki da matsala,na gaya miki hakan da gaske" dan shiru tayi sannan
ta sake bude murfin ta shiga ta zauna ba tare da ta maida murfin ta rufe
ba,abdallah ne ya soma yunqurin tahowa gunta hakan ya sanya ya miqa mata shi,sai da
ta zaunar sa shi sosai ya nutsu a gunta sannan ya soma magana
"Sumayya..."
Yadda yayi kiranta ya sanya ta daga kai ta dubeshi
"Kinsan cewa tun kafin a haifemu Allah ke rubuta mana dukkan wani abubda zai faru
da mu har ya zuwa ranar mutuwarmu ko?".kai ta jinjina tana bashi dukkan nutsuwarta
" a gaskiya sumayya bazan cuci kaina ko na zalunci kaina ba,sumayya.....haqiqa na
ga dukkan wasu halayya na mace ta gari,naga dukkan wasu dabi'u na macen da za'a iya
aure ta zama uwar 'ya'ya,na gamsu na nutsu,nagano alkhairai a tattare da ke
sumayya,da haka zuciya ta ta fara qaunarki sumayya,zuciyata ta gamsu da ke a
matsayin wadda zamu rayu tare,ina sonki ina qaunarki,ina buri ki zama mata ta,ina
kuma fatan zaki amince da maganganuna,kin san ko waye abdur rahman sumayya tun ba
yau ba,saboda haka mene ne ra'a yinki a kaina?"
Dariya dariya ta saki duk da tarin mamakin dake cunkushe cikin zuciyarta
"Kai abdur rahman,Allah ka iya wasan kwaikwayo,kyanka dramer"
"Sumayya!" Ya kira sunanta da dan qarfi wanda shi ya sake jan hankalinta gareshi
"Dubeni da kyau!,kinga wasa a idanu na da fuska ta bare kalamaina?,wallahi billahi
babu wasa cikin lamari na,da qarfina nazo gareki sumayya ko yau kika amince a
shirye nake da a daura min aure da kai".

      Sosai maganar ta daki qirjinta,sai ta shiga kada kai kamar qadangaruwa,da


qyar ta qwaci kalmar
" haba abdur rahman,ka rufamin asiri mana,ka manta kai waye ne?,kai dan kawun
mukhtar ne fa,ko ka manta mukhtar kamar yaya yake a gare ka?,baya ga haka ma so
kake duniya ta zage ni?,nifa bazawara ce har da yaro na,kai kuwa matashin saurayi
ne da ko auren fari baka yi ba"murmusawa yayi yadda yaga tsantsar tashin hankaki
kan fuskarta kamar wadda aka ce za'a yanka,sai maganarta ta biyu data bashi
dariya,dududu ita din ma nawa take,'yammata da yawa wasu masu shekaru irin nata ma
ba'a fara zancan aurensu ba,wasu kuwa sai a lokacin suka isa auren ma,shekara
ashirin kacal da take da su din,idan ba ita ta fada ba babu mai yadda tayi auren
fari ma bare haihuwa,kai ya kada da ya tuna ita din farin shiga ce,baki daya ta
rude,dole ya bita a hankali har ta sake da shi
"Dukka wadan nan basu isa hujjoji a gareni ba sumayya,jeki gida ki nutsu kiyi
shawara,na baki nan da sati guda,amma kada ki manta ni din ina sonki kuma in sha
Allahu sai na aureki". Har wani tsoro ta dinga ji haka taja qafafunta da sukayi
sanyi tamkar an buge mata su ta fita daga motar ta rufe masa ita,sai ta kasa motsi
har yaja motar ya soma fita a layin tana jin motar da idanu.

       Horn din da aka danne shi ya sanya ta dawowa daga karanta wasiqar jakin data
tsaya yi a qofar gida,abdallah na kafadarta duk ya bata mayafinta da nashi bakin da
burbushin biscuite amma sam bata ma ankara ba,idanunta ta juya zuwa gabanta,mukhtar
ne zaune cikin motarsa yana dubanta,fuskarsa a hautsine kamar wanda aka kikkifawa
mari,a hanzarce ya fito daga motar ya zagayo zuwa inda take yana fidda wani huci
" waye waccan?"ya tambaya yana mata nuni da motar abdur rahman dake gab da qulewa
zuwa kan babban titi,sai tabi inda yake nunin da kallo kamar bata san motar da yake
nunawa din ba,mamakin tambayarsa da dalilin fusatarsa ya taru ya sake daskarar sa
qwaqwalwarta,cikin qarfin hali tace masa
"Gurina yazo,sai me?", mamaki ya kamashi,shi sumayyan ke gayawa haka,zuciya ta taso
masa iya wuya,hannu yasa ya fincike abdallah daga hannunta har ya dan tsorata ya
tabe baki zai sa kuka,sai ya rungumeshi a aqirjinsa,yayi luf kuwa abinsa don tuni
ya jima da gane shi,akwai sabo da shaquwa sosai tsakaninsu,cikin tsantsar bacin rai
yace da ita
" sai me kuwa?,ba damuwata bace,saidai ki sani bashi da alaqa ya yaro na,kiyita
fitowa gunsa amma badai da yaro na ba"sai ya juya ya bude motarsa ya shige ya tada
ta ya bar layin.

      Kuka ta saki ta shige cikin gida da gudu wanda ya ja hankalin mama dake bakin
qofar madafi zaune tana gyara kwanukan abincin daren malam,tsaye ta miqe tana
tambayarta lafiya
"Mama ya karbe abdallah ya tafi da shi"
"Waye?,waye ya tafi da shi" ta tambaya cikin rudewa
"Mukhtar mana" ajiyar zuciya ta saki hankakinta na kwanciya,tayi zaton wani ne ma
daban,harara ta  balla mata
"Sai aka ce miki saceshi yayi?,ko ce miki akayi bazai dawo da shi ba?".kai ya gyada
" bazai dawo da shi ba mama"harararta ta sake yi
"Maras kunya,idan bai dawo da shi din ba sai me,ba ubanshi bane,ke yanzu akan dan
farin kika tsaya kina min kuka?,matsa ki bani guri"janye jikinta tayi ta shige daki
tana ci gaba da matsar qwalla,ta yadda lallai har yau akwai sauran quruciya akan
sumayyan,ko tsabar tabara ce oho.
     Har maman ta gama abinda take bata iya yin shiru ba,ji take kamar ta fita ta
karbo yaronta,ganin bilhaqqi da gaske kukan take ya sanya maman binta daki ta
kwantar mata da hankali,ita dai jin maman take kawai,gani take bazai dawo mata sa
shi ba,da qyar ta fita ta dauro alwalar sallar magariba ta dawo ta tada sallar tana
kasa kunnen ta inda abdallanta zai bullo,abun sai ya hadu ya dagule mata,ga zancan
abdur rahman ga kewar yaronta.

_tofa masu karatu,nasan yanzu zamu fara raba team,ga team ABDUR RAHMAN,ga MUKHTAR
ga kuma wata sabuwa LUKMAN_

*MRS MUHAMMAD CE*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

3⃣7⃣
_____________________________

*Bismillahir rahmanir rahim*

*wa'iza sa'a laka ibady anny fa inni qarib,ujibu da'a watad da'i iza da'aan*

*_idan bayina suka tambayeka game da ni kace ni makusanci ne(ina kusa da bayi
na),ina amsa addu'ar mai addu'a idan ya roqeni_*

_______________________________

      Har ta idar sallahr isha'i babu abdallah ba mukhtar,sai ta rushe sa kika


ganin qarfe takwas na neman gotawa,komawa tayi ta jingina da jikin katifa tana
maida numfashi tare da sakin ajiyar zuciya.

        Kamar daga sama taji muryar mukhtar din kamar daga can soro suna magana da
yaya abubakar,sai ta miqe zumbur ta zauna tana saurare har zuwa sanda abubakar din
ya daga labulen qofar dakinta ya leqo
"Kije ki karbi abdallah,wai yau ni zaiwa rashin m yaga babansa yaqi yarda na
karboshi" ya qarashe zancan yana sakin labulen,tana ji yana ma mama qorafi tana
musu dariya,zumbur ta miqe kamar mai jira,dama tun hijabin da tayi sallah shine a
jikinta bata cireshi ba.

       A soron ta tadda su tsaye yana rungume da abdallan,tana zuwa ta miqa hannu


alamar ya bata shi,banza yayi kamar bai gane me take nufi ba,ya dubeta fuskar nan a
dinke tsaf
"Duk randa kika sake gigin fitowa gun bazawarinki da yaro na,idan har na tafi da
shi ya tafi kenan har abada" ya qare maganan sannan ya miqa mata shi wanda tuni
bacci ya fara dibansa,hannu tasa cikin azaba ta karbeshi,cikin hanzarin ta shige
gida kamar wanda zaice mata dawo da shi,binsu yayi da kallo har suka shige,ya jima
tsaye cikin soron ba tare da ya iya tafiya na a haka abubakar ya cimmasa sannan
sukayi sallama ya tagi,har yanzu bai cimma burinsa na ganin wanda ke zuwa gun
sumayyan ba,amma babu shakka ba zai guahe ba har sai ya gano waye.

        Dare ya fara miqawa amma tana kwance idanunta biyu,abdallah na jikinta yana
ta barcinsa,a haka halima ta daga labulen dakin ta shigo
"Yaya sumayya wani ne keta kira tun dazu yana cewa sumayya yake nema,nace masa ba
ita bace amma yace ita ta bashi number din "
"Wani?" Ta tambaya cikin mamaki,don har ga Allah ta mance shaf da luqman.
"Eh,yace dazu da yamma" sai a lakacin ta tuna da shi,don baki daya abdur rahman ya
hargitsa tunaninta,maganar sa ta mata girma,ga mukhtar shima da yaso hautsina
ta,kafin tace komai wayar ta sake ruri,haliman ta kalleta
"Yaya gashi,shi ya sake kira" tsaki ta dan ja tana ganin baiken kanta tun farko da
bata bashi lambar bogi ba,kanta ta maida kan filo sannan tace
"Kice da shi nayi bacci"
"Amma yaya....." Haliman taso yin qorafi saboda ba sabonsu bane yin qarya
"Don Allah ki fita ki bani guri ki gaya masa yadda nace din ko kisan me zaki gaya
masa" ganin sumayyan ta harzuqa har haka wanda basu saba ganin hakan tattare da ita
ba ya sanya ta juya ya fice ba tare data amsa wayar dake ta faman kururuwa ba.

*****     ******    *******

       Cikin kwanakin da suka biyo baya gaba daya haka take wuni sukuku,ga maganar
abdur rahman dake mata amsa kuwwa a kai,gefe guda kuma ga luqman daya matsanta da
kiran waya ba dare ba rana,duk da ko daya bata taba amsa wayarsa ba amma hakan bai
sanya ta gajiya ba.

        Gani take baki daya abdur rahman ta shigo da maganar ne don ya dagula
lissafinta,domin shi kansa yasan yana magana ne kan abinda bashi yiwuwa,ta yaya
zata aure shi bayan ta auri dan uwansa?,ta yaya zata yadda ta sake maida kanta
cikin ahalin da bata da farinjini ko sau daya a gunsu?,ahalin da tasha wahala tasha
jinyar zuciyarta duk a kansu,ahalin da basu ganin alkhairi tattare da ita?,duk a
ture ta wannan ma yaushe zata aure musu abdur rahman?,matashin saurayin da ko auren
fari baiyi ba?,sam bata jin zata iya wannan abu koda a mafarki ne ballanta na kuma
a gaske.

        Ranar da ta fara amsa wayarsa suna zaune ne baki dayasu a falon maman suna
cin tuwon dare wayar haliman ta sake tsuwwa karo na wajen uku kenan,mama ce da
ringing din wayar ya soma damu ta dubi halima
"Wai halima idan ba zaki daga wayar nan ba ki kashe ta mana haba"
"Mama bani ake kira ba yaya ake kira,yau kusan kwana hudu kenan wlh taqi ta daga ko
sau daya" sai maman ta juya tana suban aumayya wadda ta cika tayi fam sabida halima
ta gayawa maman
"Ke sumayya wake kiranki" cikin murya mai kama da shagwaba wanda sau tari idan
ranta na bace bata aon magana haka yanayin muryarta ke komawa tace
"Wani ne nima mama ban sanshi ba"hade rai maman tayi sannan tace
"Ha'aa,baki sanshi ba kamar yaya?,ina cewa ke kika bashi lambar ko?" Dan jim tayi
sannan ta gyada kai
"To maza bana son shashanci karbi ki amsa kirab,na gane take takenki sarai,kuma
kinfi kowa sani malam ya fara maganar baiga kina magana da wani ba,kinsan halinshi
sarai tun da can baya ma shi ba mai barin yara su girme a gabanshi bane,su kansu su
halima rashin tsayayye ye ne ya sanya har suke gida iwar haka" gabanta ya fadi
fargaba ta lullubeta,wani irin aure kuma?,duka duka mutuwar auren nata da bai wuce
shekara biyu ba?,tilas ta karbi wayar ta miqe ta shige daki.

        Sun dan dauki lokaci kan wayar yana qoqarin shigar da kansa a gunta,ba yabo
ba fallasa ta amsa masa duk wata magana da yayi mata,da qyar ya shawo kanta ta
bashi lambarta,yayi murna da godiya sosai tare da alqawarin zai kirata gobe,tabe
baki tayi tana bin wayar da kallo bayan sun gama wayar,sai ta miqe nan saman katifa
tayi kwanciyarta taqi komawa falon don koda ma mama ta sake baro wata maganar.

   *****    ******     ******

     Kullum ta Allah baya fashin kiranta,koda kuwa bata dauka ba zai mata
tex,qoqarin kafa kanshi yake sosai da gaske,duk da gaya masa ita din fa ba budurwa
bace har da yaronta,yace babu komai shi hakan ma yake so,a haka har sati dayan da
abdur rahman ya diba mata ya cika,satin guda cif bai sake nemanta ko takowa gidan
ba har cikar wa'adin kwanakin.

       Tun safe take addu'ar kada Allah ya dawo da shi,a haka har lokacin tafiya
makaranta yayi ta shirya ta tafi tare da abdallah wanda yau ya tubure sai ya bita.

      Yau sai kusan biyar suka taso,tun daga qofar gidan ta hangi motarsa,a hankali
ta dinga takawa jikinta a sanyaye har ta isa gab da motar,qofar mazaunin direba a
bude take alamun mamallakin motar yana ciki,tuni abdallah ya gane motar waye,ya
zame daga jikinta yayi wajen motar yana kiran abba,hankalin abdur rahman yayo wajen
ya waiwayo yana murmushi sannan ya fito ya dage shi sama ya cafe suna dariya,sanye
yake da yadi irin na maza blue black,hula da takalminsa sau ciki duka baqi,yayi
kyau sosai. Ya sauke idanunshi a kanta yana kallonta
"Yau kam kin dade,kinsan tun nawa nake nan ina jiranki?" Kai ta girgiza ba tare da
tace komai ba,yatsun hannunsa ya daga guda hudu ya nuna mata,sannan ya dora da
fadin
"Shine yau kika dauke abokin hirar ko?" Kai ta sake kadawa sannan tace
"Shine ya nace yau sai ya biji,nima bana son tafiya da shi"
"Mukam muna maraba da shi ko yaushe,shiga ki kintsa kafin naje can qasan layinku na
dawo na baki minti talatin"
"Amma dai da ka shigo ciki ko?"
"Amma dai kinsan gunki nazo ko?"ya bata amsa da salon yadda tayi tata maganar,ta
lura jan magana yake ji saboda haka ta sanya kanta gida tana fadin
"A dawo lafiya".

       Salla kawai tayi wadda lokacinta ya kubce mata,ko abincin ta kasa ci tanaa
zaune tana nazarin hanyar da zata bi abdur rahman ya janye zancansa salin alin ba
tare da an kai ruwa rana ba,don gaskiya bata jin zata iya maida kanta cikin familyn
su mukhtar,an gudu ba'a tsira ba kenan,ko kuma tsugune bata qare ba?,cikin haka
zainab ta shigo dakin ta gaya mata taje ya abdur rahman na waje ta karbi abdallah.

      Kamar wancan karon wannan ma haka ya tilasta mata shiga motar tasa,shuru ya
ratsa motar na wasu daqiqu ba wanda ya sake cewa uffan bayan abdur rahman ya gama
jaddada bayanansa a gareta
"Da farko abinda zan fara cewa shine na gode na gode matuqa,na yaba da qaunata da
kace kana yi,har ka nuna sha'awar zamantowa abokiyar rayuwarka duk da ban cancanci
wannan darajar ba,amma abdur rahman kayi haquri,bazan iya aurenka ba,saboda wasu
dalilai wadanda ni da kai duka mun sansu wasunsu kuma ni da ubangiji na ne kawai
muka sansu" kai yake jinjinawa yana dubanta sannan yace
"Ban gamsu da baya nanki ba ko kadan,babu wani abu da zai sanya ni janyewa daga
batun neman aurenki sumayya,ina sonki babu wanda zai hanani"so take ya fahinceta
bilhaqqi don su bar maganar sun wuce gun,sai ta sake fuskantar sosai wani abu na
taba zuciyarta na daga abubuwa da suka faru da ita a baya
" ta yaya abdur rahman kake so na sake komawa cikin danginku,bayan kaima kana daya
daga cikin mutanan da zasu shaidi irin rayuwar da nayi a cikinsu,ya kake so ka sake
maidani rayuwar baqincikin da nayi bankwana da ita?,ko kuwa zaka sauya dangi ne
saboda zaka aureni ni sumayya 'yar gwal,ko ka manta waje mijina na baya,ka manta
alaqar da take tsakanin ku,don Allah abdur rahman muci gaba da mutunci mu ajjiye
zancan soyayya a gefe"ta qarashe maganar tsohon mikin dake zuciyarta na taso
mata,sai ta sanyo qafafunta waje ta fito daga motar,da sauri shima ya fito ya
zagayo inda take tsayen,kafin yace mata komai suka ji tsaiwar mota,waiwayawa sukayi
dukkansu don ganin waye.

       Mukhtar ne,tun yana cikin motar tasa yake qarewa motar kallo,babu shakka
wannan motar yake tawan gani a qofar gidan su sumayyan,kenan yau zai ga waye
mamallakinta zaiga wake zuwa gunta,amma idan idanuwansa na nuna masa dai dai kamar
abdur rahman yake gani tsaye tare da sumayya,to meye yake haka a gidan?,meyw
hadinsu?,shine mai motar da yake gani kullum na ficewa daga layin?,don samun
amsaoshin tambayoyinsa sai ya balle murfin ya fito bayan ya kashe motar ya nufosu
idanuwansa a kansu zuciyarsa na azalzala tare da ayyana masa wani abu wanda baya
fatan kasancewaraa.

        Sallamarsa ita ta katse abdur rahman daga kallon sumayya da tuni idanunta
suka cika da qwalla,sannan suka katse shi dag fadar abinda yake shirin
fada,dukkansu waiwaya suka yi suka dubeshi,fuskar abdur rahman din dauke da
murmushi ya miqawa mukhtar hannu yana fadin
"Ah,ya mukhtar kai ne?" Baiqi miqa masa nasa hannun ba suka yi musabaha yana fadi
tare da tsareshi da wani irin kallo
"Eh,ya kawu da sauren mutanen gidan"
"Duka lafiya alhamdulillahi" ya fada yana sakin hannun mukhtar din sannan ya juya
ga sumayya
"Ki nazari a nutse,kada ki ruda kanki,kada ki cuci kanki ki cuceni,gobe in sha
Allah zan dawo" ya fada yana juyawa zuwa wajen motarsa,dukkansu ita da mukhtar din
suka yi masa rakiyar idanuwa,saidai kowa da abinda ke kai kawo cikin zuciyarsa,ya
bude motar ya shiga bayan ya bawa abdallah 'yar madaidaiciyar baqar leda cike da
biscuite da choculet ya saukeshi ya tada motar ya wuce.

Busy kuyi haquri da wannan

*mrs muhammad ce*

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)
3⃣8⃣

____________________________
*Bismillahir rahmanir rahim*

*wala taqulanna li shai'in inni faa'ilun zalika gada,illa ay yasha Allah,wazkur


rabbaka iza nasit*

_kada kace ni zan aikata wani abu gobe,face sai ubangijinka yaso,ka tuna
ubangijinka idan ka manta_

______________________________

        Wani abu ne ya tokare masa wuya yana jin wani irin bacin rai na taso
masa,sai yayi qoqarin dannewa ta hanyar daukar abdallah da ya nufo gunsa kai tsaye
yana fadin daddy daddy,motsawa sumayya tayi don shigewa cikin gidan cikin hanzari
ya sha gabanta
"Me abdur rahman ke zuwa yi gunki?" Idanunta ta dora a kansa kanta tsaye tace
"Alheri"
"Alheri wanne iri?,kada kice min gonata yake son shigowa?"wani irin kallo ta masa
"Yaushe ka fara noma?,dama kana da gona ne?,alheri kuma duka alheri ne babu wani
banbanci" ta fada tana rabeshi zata wuceshi ranta a bace,baisan ya riqo gefen
hijabinta ba hakan ya sanyata waiwayowa tana dubansa a mamakance
"Me yasa kike cutar da ni haka sumayya me na miki a rayuwa da zafi?" Ya fada
zuciyarsa na zafi yayin rauni ya bayyana qarara a fuskarsa
"Cutarwa?,ni nake cutar da kai ma mukhtar!" Ta fada tana nuna qirjinta da yatsa
cikin mamaki,sai ta juyo baki daya tana dubansa sosai
"Bance ka cutar da ni ba mukhtar ni da ka saka saki uku ina kwance?,bance ka cutar
da ni ba ni da ka yanke min hukunci kan zato da zargi,ka yanken hukunci ba tare da
kayi bincike ba?...."
"Wanne bincike sumayya bayan ba labari aka bani ba,na gani da ido na,sannan bincike
na likita ya sake tabbatar min da kinsha din wanne bincike kike da buqata nayi
bayan wannan" a kaikaice takw dubansa sannan tace
"Ok ko?,to shikenan,yayi kyau hakan ai,amma shawara zan baka ka fita daga dukkan
harkoki na,ko da maza dari zaka ganni da su wannan ba damuwarka bane,tunda dai a
yanzu ba qarqashin ikonka nake ba,gashin kaina nake ci sai ka shafamin lafiya" tana
gama maganar ta juya tayi shigewarta cikin gida ta barshi da abdallah.

     Binta yayi da kallo,taushe sunayya ta koma haka,yaushe bakinta ya bude da


magana haka?,saidai batayi laifi ba yana ganin baiken kansa,tabbas ba shakka
gaskiya ta fadi yanzun ita din ba huruminsa bace,baisan me ya sanya ya shishshigewa
lamarin rayuwarta har haka ba,jiki ba qwari ya koma mota ya dauko siyayyar abdallah
ya riqoshi har bakin qofar da zata sadaka da tsakar gidan ya ajjiyeshi ya
wuce,cikin mota yana tuqi yana tunanin yadda zai raba kansa da shiga lamuranta,don
bisa gaskiyarta take,wani sarawa kansa yayi wanda hakan ya sanyashi yin parking
motaraa gefan titi ba shiri,ya dauki a qalla sama da mintuna talatin kafin yaci
gaba da tafiya.

   *****    *****    *****

    Duk yadda taso abdur rahman ya fahimci abinda take nufi yaqi fahimta,sai ta
tattarashi ta janye masa jiki,sau tari takan qi dawowa daga makaranta akan
kari,tana kuma dawowar lokacin sallar magariba ne,daga nan kuma suna zama karatu da
malam wanda ya sanya musu wasu litattafan addini wanda suke hadda ce wasu abubuwa a
ciki,sam ta daina bada wani gaf ko wata dama da zasu kadaice har suyi magana,idan
ana tare cikin jama'a zasu yi magana da shi kamar kowa.

      Ta bangare daya kuwa luqman shima ya matsa lamba,tilas ta bashi dama yazo
gidan sau daya,a ranar malam ya dawo ya ganshi suka gaisa,saidai malam din baice
mata komai ba kamar yadda ta zata,hakanne ya sanya ta saki jiki har ta sake bashi
wasu damammakin yazo wai koda hakan zai sanya abdur rahman ya janye daga
qudirinsa,saidai duk da hakan babu abinda ya girgiza shi,har mamaki abun ke
bata,cikin lokaci qarami ya sanyata ta saki jikinta da shi,mutum ne mai barkwanci
da yawan bada labarai,ko bata son magana sai ya sanyata dariya.

       Abinda bata sani ba malam din na sane da komai,bata san da hakan ba sai
ranar da aka kai kudin auren abubakar da saka rana wanda baki daya aka tsaida
watanni biyu,washegarin ranar malam din yayi kiranta falonsa,bayan ya kammala duka
abubuwan da yake ya dubeta
"Am sumayya,nasan cewa kinsan tsarina da al'ada ta gidan nan,sannan alhamdulillah
kin san mutuncin mace dakin mijinta,baki da inda yafi nan daraja,dukkan wani abu da
ya faru a baya mu ajjiyeshi gefe haka Allah ya tsarama rayuwarki,cikin KUNDIN
QADDARARKI yake,babu wanda ya isa ya goge miki ko ya kautar miki da shi"
"Haka ne malam" ta fada kanta na duqe zuciyarta ba bugawa kamar zata bullo,addu'a
take kada Allah yasa malam ya bullo mata da zancan da bata da buqatar jinsa a yanzu
"Sumayya,yaron nan abdur rahman yazo guna ya gabatar min da kansa a matsayin
manenin aurenki,to amma kasancewarki bazawara a yanzu addini ya baki damar zabawa
kanki mijin aure ya sanya nace sai na tambayeki naji mene ne ra'ayinki,kada ki
zalunci kanki a yanzu kina da dama,sannan zaman aure zama ne bana yau ko gobe kawai
ba,zama ne na har abada". Wani tashin hankali ne ya rikito mata,abubuwan da suka
dinga faruwa da ita zamanin tana auren mukhtar tsaf suka dinga dawo mata,a hankali
ta bude bakinta muryarta na rawa
"Kayi haquri malam,abdur rahman dan uwa ne ga mukhtar dan wan babansa ne nasan
kasan haka malam" murmushi ya saki
"Sumayya,sumayya kenan,wannan duka ba abun damuwa bane tunda dai aure ya halasta a
tsakaninku ba haramun bane" tashin hankali ta fada cikin zuciyarta,'yan uwan
mukhtar fa sune dai 'yan uwan abdur rahman,ba'a canzawa tuwo suna
"Malam,ina tsoron sake kasancewa da ahalin su mukhtar...." Sai tayi shiru ta kasa
qarasawa,shima shirun yayi yana nazarin maganarta,tabbas sumayya yarinya ce mai
matuqar zurfin ciki,a iya zamanta na aure bazai iya fadar ranar data kawo
matsalarta ba,saidai idan an fahimta a maganta mata.
"Ke kike da zabi a hannunki ai,ba zan miki auren dole ba"
"Malam,ina so abdur rahman ya janye daga qudurinsa,bana son sake shiga ahalinsu" ta
fada zuciyarta na raurawa muryarta na rawa
"Shikenan zancansa ya wuce,sai ki fidda miji ina son hada aurenki da na yayanki
abubakar idan ta kama har da su halima baki daya"
"Amma malam ba......."
"Sumayya,bana son qorafi ko wata magana,kinsan ba zaiyiwu kici gaba da zama a gida
ba,shekara nawa,shekara daya ana gab da cika ta biyu" shuru tayi don tafi kowa
sanin waye malam,amma ina mafita meye mafitarta?,
"Sumayyan luqman fa?" Taji ya jefo mata tambayar wadda ta sanya dago kanta ta
dubeshi,murmushi ya kuma yi yana dubanta
"Mamaki kike yadda na sanshi?,ya fara zuwa gunki ba da izini ba ya karya doka
ta,hakan ya sanya nayi bincike a kansa,na samu gamsassun bayanai a kansa,mutumin
kirki ne bakin gwargwado" sai ya dan ja fasali yana dubanta kafin yaci gaba da
cewa.

_yauma dai amin uziri_

*mrs muhammad ce*👑


📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

4⃣0⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

*innal laha la yugayyiru maa bi qaumin hatta yugayyiru ma bi'an fusihim*

_haqiqa Allah baya canzawa mutane(halin ko yanayin da suke ciki)har sai sun canza
da kansu_

______________________________

        Ungawa ce mai matuqar kyau da tsari,akwai nauikan mutane daban daban


cikinta,saidai akasarin mzauna cikinta din masu hannu da shuni ne da kuma masu
rufin asiri ko wadanda suke ma'aikatan gwamnatin tarayya ta basu gida su zauna
kamar su anty dije.

       Sai da mansur ya fidda kayanta baki daya ya shigar mata cikin gidan ta masa
godiya sosai sannan ya ja motarsa ya shige wani katafare kuma hamshaqin gida dake
kallon nasu.

         Dukka yaran gidan na nan kasancewar ranar qarshen mako ce,laila ita ce
babba,sai hafiz mai bi mata,sannan khalifa sai nasir sai auta amina minal,a qalla
laila zata yi shekaru goma sha hudu,ita ta fara ganin shigowar sumayya falon,ihu ta
sanya wanda ya janyo hankalin 'yan uwanta ta nufi sumayya ta rungumeta,haka sauran
suka baibayeta wanda ya janyo musu faduwa a qasa dukansu suna dariya,da qyar ta
samu suka dagata suka koma saman kujera sannan ta soma tambayarsu anty dijen don
bata ji motsinta ba,dining laila ta nuna wa sumayyan tana cewa
"Kinga yaya sumayya can duka abincinki ne,tun dazu mama ke jiranki baku iso ba har
ta gaji ta shiga gidan daddy prof,amma bari naje na kirata" ta fada tana yafa dan
yalolon mayafinta tayi waje da sauri,khalifa sumayya tasa ya fara nuna mata toilet
ta shiga tayi alwala,tana kammala alwalar anty dije na shigowa
"Sai yanzu?,gaskiya kunyi nauyi a hanya kamar wadanda suka hau motar haya inji
hajiya bilki" murmushi sumayya tayi tana duban anty dije wadda ta sake gogewa bisa
dukkan alamu zaman garin ya karbeta matuqa,ta kuma zama 'yar gayu ita da yaranta
baki daya
"Wallahi anty sai da muka biya kasuwa muka karbo wasu kaya sannan har mun dau hanya
wani oga ko yallabai ya maida ku zoo road karbo dinki"
"Eh inaga man ne dinkunan su'ad ce,maza yi sallar kizo kici abinci kafin mu zauna
hirar yashe gamo" ta fada tana sanya su laila dauke akwatunta zuwa wani daki da aka
tanada saboda baqi irinta.

      Sai da taci ta qoshi sannan suka baje a falon ana hiran yaushe gamo,kusan
haka suka qarar da wunin ranar,ko da malamar lesson din yaran ma tazo guduwa sukayi
suka qi zuwa sai tafiya tayi,da dare ma yayi da qyar suka tafi dakinsu don cewa
sukayi tare da sumayyan zasu kwana,saida anty dije ta korasu saboda tana son suyi
zance,sosai suka sake kuwa don mai gidan ta baya nan sun tafi semina lagos,sosai
anty dije ta sake kwantar mata da hankali tare da bata shawarwari ta rufe da fadi
cikin sigar tsokana
"Duk da nasan sumayyan tawa zuwa yanzu ta fara girma,hankali ya fara zuwa mata"
itama dariya tayi,sai wajen sha daya da rabi sannan ta fita ta barta,to nan din ma
lukman bai barta ba da hira sai data ce tana jin bacci sannan yace
"Ki kula min da kanki to na baki amanar kanki my dear kinji"ajiyar zuciya ta saki
sannan ta amsa masa ta katse kiran,taso kiran halina taji ya abdallah yake,amma
ganin dare yayi nisa ya sanyata ta haqura ta barwa gobe,duk sai taji tana kewar
yaron nata.

   ******     ******     ******

      Kwanakin da tayi a garin kwanaki ke da suka yi mata dadi sosai,kullum yaran


na nanuqe da ita suna hira,sauqin abun sun gama jarabawa hutu kawai suke jira,wani
lokaci da yammaci anty dije kan debe su da motar mai gidan da ya barta a gida ta
kaisu park su dan sha iska suyi ciye ciye su dawo,hakan na yiwa sumayya dadi,lallai
ko yaya ka motsa daga wani gu zuwa wani gu zaka samu sauyi zuciyarka zata yi dadi.

        Duk wani abu da ya kamata a yiwa amarya anty dije da kanta ta yiwa
sumayya,cikin kwana goma ta hadata tsaf.

       Ana ya gobe zasu koma kanon laila na kwance kan cinyar sumayya sumayyan na
tsefe mata kitsonta zasu wankin gashi da yamma anty dije ta fito ta dubesu
"zan dan shiga gidan daddy prof zamuyi sallama da su,Allah baiyi da ni za'a yi
sunan nan ba"sumayya ta daga kai ta dubi anty dije
" au haihuwa akayi halan?"
"Sai yau zaki tambaya kenan,kwana na nawa ina leqa su amma baki taba karar ki shiga
ku gaisa da mutanen ba,direban gidan ya dauko ki daga kano fa,surukar gidan ce ta
haihu" murmushi sumayya tayi
"To ai ban sansu bane anty"
"Ni ai na sansu kuma gashi na gaya miki,mutanen akwai tsabar mutunci da karrama
mutum,duk yadda Allah ya musu tsabar arziqi amma basu raina na qasansu,mai gidan
bakiga yadda ya dauki abban khalifa ba kamar dan cikinsa,su khalifa kuwa ya maidasu
tamkar jikokinsa" jinjina kai sumayya keyi sannan tace
"Allah ya saka musu da alkhairi,kice ina musu barka"
"Zasuji tunda ba zaki din ba" inji anty dije ta fice tana mita sumayya ta bita da
dariya.

       Basu jima da kammala tsifar ba anty dijen ta dawo hannunya dauke da baqar
leda,ta cillar kan cinyar sumayya
"Da baki iya zuwa gaida mutane ba gashinan haj bilkisu tace na kawo miki kiyi fitar
biki,ta yaba da zabin leshin ki wai kin iya zabar kala,ashe tare kuka shiga shagon
da mansur din". Baki ta saki sanda ta fiddo leshin taga daya daga cikin wadanda
suka siya dinne
"Anty kinsan kuwa nawa ne farashinsa duk guda daya?". Dariya anty dijen tayi
"Hmmmmm,bakisan mutan gidan bane sumayya,kinga ku tashi ku shirya ku wuce wankin
kan nan kada dare yayi muku hanya"ta furta tana miqewa ta nufi kitchen.

   ******    *******    *******

      Sanda suka isa kwanaki biyu sukayi saura a daura aure don babu wani event da
sumayyan ta tsara yi,yaya abubakar ne kawai zaiyi walima bayan an gama daura aure.

       Kusa awa guda kenan da shigowarta gidan amma bata ga wulgawar abdallah
ba,tun tana kawaici bata tambaya ba har sai data magantu
"wai nikam ina abdallah ne?" Maimakon maman ta amsa mata sai tace da ita
"Kije malam nason magana da ke" hakanan taji jikinta bai bata ba,ta miqe ta zura
hijabinta ta fice.

      A ladabce ta gaisheshi ya amsa yana tsokanarta abuja ta karbeta,sai ya bata


kunya ta sunkui da kai tana murmushi yayin da tausayinta kuma ya darsu a zuciyar
malam din
"Sumayya maganar da zamuyi da ke nasan ba zata miki dadi ba,domin raba da da uwa
sai Allah,saidai babu yadda muka iya,bayan tafiyarki mukhtar yazo ya karbi
yaronsa...." A firgice ta dago ta dubeshi muryarta na rawa idanunta na fidda ruwan
hawaye
"Amma malam me yasa zaimin haka,rabamu ken......."kaaa qarasawa tayi tayi qas da
kanta
" kiyi haquri sumayya,shi ya fiki a haqqu da shi,sannan ya riga da yace baiso yaron
yayi zaman a golanci gidan wani kamar yadda shima yayi,kiyu haquri nasan ba wai ya
rabaku bane na har abada saboda yadda yazo mana bada nuna isa ko qarfa qarfa
bane,abinda na lura shine bazai iya jurar rashin ganin yaron bane,tunda idan har
kika tafi da shi bashi yiwuwa ya dinga binki gidan mijinki da sunan yazk ganin
dansa,kiyi haquri babu komai ai kuna tare,na tabbata za'a dinga kai miki shi"malam
ya fada cikin tausasawa. Haka malam din ya dinga lallashinta yana bata kalamai har
ta samu ta danji sauqin zugin zuciyarta,saidai abinda take ji na game da kewar
yaron har yau bai sauya ba.

       Data koma daki taga sauran kayayyakinsa kasa ci gaba da daurewar tayi,ba
shakka raba da da uwa ba qaramin abu bane,shi yasa aka ce ko mutuwa tana shakkar
idon uwa,yaya wadanda suka rabu da 'ya'yayensu suke ji rabuwa ta har abada?,ashe da
sauqi ita tunda yana nan cikin duniyarta kusa da ita amma duk da haka ta gaza
daurewa,kuka tayi mai yawan gaske wanda shi ya haifar mata da zazzabin da ciwon kai
mai tsanani har ranar da aka daura auren,haka nan aka tattarata aka kaita dakinta
tana mai ci gaba da kuka mai qunshe da abubuwa iri daban daban

     **** *9:30 pm*  *****

      Lukman Bashir shine asalin sunansa,haifaffen garin kano cikin qaramar hukumar
kano municipal,yayi karatunsa iya N.C.E sai ya fada kasuwanci gadan
gadan,mahaifiyarsa hajiya kubra shi kadai tallin tal ta haifa,hakan ya sanya ta
dauki so da qauna da kulawa ta dora masa,wannan shine dalilin da ya sanya duk
lokacin da yayi aure ta fuskanci yana mutuwar son matar take rabasu don wai ba zata
bari a mallake mata yaro ba tana kallo,kasancewar gidansu daya part guda yayi mata
da ya tashi ginin gidansa,a haka a haka ta sanya lukman ya rabu da mata kusan hudu
kenan duk da cewa yana dacen matan aure masu matuqar haquri da biyayya saidai ita
sam bata gani,haquri da biyayyar da sukewa lukman din ita ke jawo musu qauna
gunsa,amma ita gani taje tsabar asiri ne matan suke yi,sam matan basu da
sukuni,hatta zanin daurawa idan zai musu ita ke karbar kudin ta siyo ta bada adinka
musu ita kuwa sai wanda ta zaba zata sanya,hakanan duk cikin matan da yake aurowa
mutum daya ce ta haihu da shi don na wani dadewa take bari suyi ba,ita din ma a
gidansu ta haife sai da ta yaye hajiyan tasa aka karbota,'ya mace ta haifa wadda
ake kira da nuwaira.

       Hausawa suka ce alhaki kwikuyo ne,a irin haka ne Allah ya hada lukman da
KARIMA gogaggiya mai idanu a tsakiyar kaa wadda ita ta haifa masa yara uku dukka
mata zaitun marwa da radiya,da fari kariman lumbu lumbu ta yiwa hajiyan har ta saki
jiki da ita,sannan daga bisani ta sanya gaba daya daga lukman din har hajiyan aka
sanya su qarqashin ikonta,daga lukman din har hajiyan umarni suke karba daga
wajenta,babu wanda ya isa ya tsallake abinda ta shimfida masa,sai a bayan idonta su
yita takaici da jimami amma a gaban idonta ko tari ba wanda ya isa yayi,mutane da
yawa sunyi murna sunyi shewa da wannan sauyi domin ya zamewa hajiya kubra izina.

       Tun bayan da ya auri karima bai kuma gigin qara wani auren ba sai a yanzu da
yake KUNDIN QADDARArsa na rubuce da auren sumayya,sanda yake gaya mata zai qara
aure a tsorace yake,ita kanta tayi matuqar mamaki,a fusace ta shiga dakinta ta kira
wayar malaminta ta sanar masa,wayar tace ya kashe zaiyi bincike nan da awa guda zai
nemeta,ya kuwa nemetan ya sanar mata wannan aure ba makawa sai an yishi saboda
yarinyar nada addu'a hakazalika 'yar gidan malamai ce,wannan kalma ta sake tunzura
karima ta sanya aka sake sabunta aiki mai kyau akan hajiya da lukman don kada
sumayyan ta samu kafar rusa mata shirinta wanda ta riga ta qudurceshi cikin
ranta,haqura tayi saidai duk wani harkar biki kama daga lefe da sauransu ita tayi
su,komai sai data ninka kudinsa sannan kuma ta zuba abinda ranta yaga dama,sauqin
daya gidansu sumayyan gida ne na dattako babu wanda ya damu dabtsada ko yawan
abinda aka zuba cikin lefen.

         Qarfe tara da rabi na daren bayan an kaita gun hajiya an gabatar da ita
yayin da ita kuwa hajiyan ke fadin tabi karima wanda ya baiwa kowa mamaki sannan
aka dawo da ita dakinta wanda falo ne guda daya makeke sai dakunan bacci na kowacce
mace da bandaki a cikinsa,sai dakin yara da mai gida kitchen da bandaki duk cikin
babban falon,cikin falon dai ya kira sumayya don dama ita karima na zaune a falon
tun kan a kawo sumayyan har kowa ya watse
"To sumayya wannan itace uwar gida na uwar 'ya'ya na,idan kika bita kamar kin bini
ne,na auroki ne ba don bana sonta ba,bana so kuma ki raina min ita,hatta hajiya
farincikinta shine farincikin karima da fatan kin gane" kanta ta cira a hankali
tana dubansu baki daya,cikin zuciyarta ta furta
"Ikon Allah,yau kuma da wacce kalar Allah ya hadani?".
Miqewa kariman tayi cikin izza tana yatsina
" idan ka gama ka sameni a daki,kada ka wuce minti biyar"
"To....to to" ya amsa cikin inda inda tare da binta da kallo har ta wuce dakinta,da
sauri ya dubi sumayya
"Amarya ta muje na rakaki daki kinji" ya fada cikin kwantar da murya,ba musu ta
miqe tayi gaba mamaki na kasheta,wai dama haka lukman din yake?me yake shirin
faruwa ne?.

      Bakin gado ya zaunar da ita yana duba agogo don kada yayi laifi
"Zauna bari naje,in Allah ya yarda zanyi qoqarin dawowa,ga kaxarki nan idan kina
jin yunwa kici kafin na dawo" ya fada yana juyawa ya fice da sauri,binsa tayi
dakallo baki daya qimarsa da mutuncinsa da take dan gani a da suna ficewa fit daga
ranta,hawaye suka soma fita daga kuncinta data tuna rayuwar gidan mukhtar
makamanciyar wannan,saidai sam da alamu bata kai qazancewar wannan ba,ita kuma nata
salon QADDARAR kenan?. Juyawa tayi ta kwanta tana faman zubar da hawaye.

       Har bacci ya soma fusgarta taji yana ambaton sunanta sama sama,ta bude
idanunta tana dubansa,murmushi yake yana kallonta shima tare da duba bakin qofar
dakin kamar wani ya biyoshi,ganin ta tashi ta zauna ya sanyashi maida qofar dakin
ya murza key,kamar wanda ke sauri jirgi zai tashi ya barshi yake magana
"Tashi maza ki dauro alwala,ina fatan dai kinci abincin ko?.....kinyi sallar
isha'i?.....dauro alwala sumayya babu lokaci...."ya fadi yana satar kallon qofar
dakin
Cikin mamaki take dubanshi duk ya wani firgice,lokaci kada ya qure kamar yaya take
tambayar kanta
" don Allah tashi mana sumayya kada ta....."bai qarasa fada ba aka fara dukan qofar
kamar za'a ballata
"Innalillahi wa inna aihi raji'un" ya fada yana dafe kansa.
"Zaka bude ko sai na sassaba maka,maci amana" inji mai buga qofar,jiki ba qwari ya
nufi qofar ya bude mai bugun ta fado dakin tana raba idanuwa,kubra ce sai data
qarewa dakin kallo ta fuskanci babu abinda ya faru sannan ta kalleshi
"Ni zaka ci amana ka karya alqawarin daka yimun?,to wallahi ko kwana a dakin baka
yi butulu kawai,maye,tunda ni ban isar maka ba,wuce muje nace ka tsaya ka kafeni da
idanuwa" sai ya waiwaya yana duban sumayyan har sai data ingiza qeyarsa sannan ya
fice yana waiwaye.
     Kan sumayya ta dawo da kallonta"da sauran quruciyarki amma kin zabi nakasta
rayuwarki,idan don kwanciyar aure kika zo gidan nan to kinyi babban kuskure don
yadda kika zo haka zaki koma,don babu wasu 'ya'ya da za'a haifa a gidan nan sai
nawa yaran,itama wadda aka haifa din don uwarta ta rigani zuwa ne,wlh da ni na
rugata zuwa da bata isa ta haifeta ba,keda lukman kuwa saidai kallo"
"Ke lukman ya dama,kuma ta Allah ba taki ba,ni an bani ilimin yarda da QADDARA mai
kyau ko akasinta,hikinar ubangiji kuma yawa gareta,hakanan sanin gaibu sai
Allah,duk kuma nisan jifa wataran qasa zai fado,mai yiwuwa ma idan ya tashi fadowar
ya dawo tsakiyar kan wanda yayi jifan"
"Ke ki iya bakinki wallahi idan baso kike kiyi kwanan gidanku ba"
"Idan kinso kina iya karbe aron numfashin ma da kika bani idan yaso nayi kwanan
kabari baki daya" sumayya ta fada hankalinta kwance,don ya zuwa yanzu tana jin ta
gama daukar haquri da rainin wayon kishiya,bata cuce su ba don me su zasu dinga
cutar da ita,tabbaa dafi da gubar zainab har yau bata bar illata zuciya da gangar
jikinta ba,don kusan ita ta zama silar data sake cillota wannan muhalli da take
ganin wata rayuwa miji ke biyayya wa mata. Mamaki ya cika kariman don ta jima rabon
da a mayar mata da magana haka,sai zuciyarta ta tuna mata daga inda sumayya ta
fito,take gumi ya fara tsatstsafo mata,tabbas sai ta sake shiri a kanta,qwafa taja
sannan ta juya tana fadin
"Da karimatu kike zancan lallai bakisan wace ni ba"bata yi nauyin bakin maida mata
amsa ba don kada ma ta fita bata ji ba
"hakanan bakisan wace sumayya ba,ki zuba ido kisha kallo". Bayan fitarta muqulli
sumayya ta sanyawa qofarta ta shiga toilet ta daura alwala,sam bata ji wata damuwa
na barinta da angonta yayi ita daya a dakin ba,kaya ta fiddo ta sauya wadanda zata
sake a cikinsu sannan ta sanya hijabi ta tada sallah,kyawawan nafiloli ta raya
daren sosai da su kafin bacci ya rinjayi idanuwanta.

*asuba ta gari amaryar lukman*

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

4⃣1⃣

*Bimillahir rahmanir rahim*

*wattaqu yauman turja'una fihi ilallah,summa tuwaffa kullu nafsin ma kasabat wa hum
la yuzlamun*

*_KUJI TSORON WATA RANA DA AKE KOMAR DA KU IZUWA GA ALLAH A CIKINTA (RANAR
LAHIRA),SANNAN A SAKAWA KOWACCE RAI ABINDA TA AIKATA (SHARRI KO ALHERI)ALHALIN SU
BA'A ZALUNCESU BA(BA WANDA ZA'A ZALUNTA DUK ABINDA KA AIKATA SHI ZAKA GANI)_*
______________________________

Qarfe tara na safiya tayi wankanta,ta shirya cikin atamfa dinkin riga da
zani,ba wani kwalliya tayi ba amma tayi kyau,dakin ta sake karkadewa ta goge sannan
ta koma bakin gadonta ta sake kwanciya,idanunta ta lumshe tana saqa da
warwara,kewar abdallah take ji sosai cikin zuciyarta har qwalla na shirin kawo
mata,tunani ne fal zuciyarta tana wassafa yaya rayuwa zata kuma kaya mata cikin
wannan gidan.

Hayaniya ta dinga jiyowa cikin falon da surutai,ta bude idanunta ta kalli


agogon dakin,goma tayi har da mintina arba'in da biyu,saita bude sif dinta ta ciro
hijabi ta zura kana ta sanya silifas dinta ta murda qofar dakin ta fito.

Duk uban hayaniyar da take ji yara hudu ne cikin falon,yarinyar farko


wadda ita ta sake hautsina yanayin falon ma hakimce kan kujera kamar wata babbar
mace duk da du du du ba zata wuce shakara sha uku ba,kallo take a tashar mbc three
ta qure volume kamar ita da mutum dari suke kallon,sai yarinya ta biyu wadda batafi
shekara uku ba dake zaune qasanta kan carfet taci uban indomie ta hadeta da ruwan
shayi tana wasa da ita,daga can wajen step na dining kuwa wasu yaran ne su
biyu,daya shekarunta goma daya takwas suna karyawa,su biyun kadai sun dame gurin
kamar qanwar tasu dai,ta sake wurga idanunta,wata yarinya ce data tasamma zama
matashiya wadda ta kusa shekara goma sha hudu takure a saqon kujeru,kallo daya zaka
mata kasan daban take kamar yadda kamanninsu ya bambanta da sauran yaran dake
falon,don dukkansu kamarsu daya ita kadaice kamarta daban kamar yadda ta fisu kyau
baki dayansu.

Dukkansu sun ga fitowarta saidai babu wanda ya kulata,ta dubi qofar dakin
karima wanda ke garqame ta sake dauke kai
"Ina kwana anty"
Taji an ambata daga bayanta,saita waiwaya,yarinyar dake zaune ce saqon kujera ta
gaidata tana murmushi,maida mata murmushin itama tayi tana mamakin zarnin dake
tasowa daga jikinta
"Lafiya qalau,an tashi lafiya?,me sunanki?"
"Nuwaira"
"Sunan mai dadi" sai tayi murmushi tana cewa
"Na gode anty".
"Ko zaki rakani wajen kakarku?"
"Wa?,hajiya"
"Eh"
"Muje in rakaki anty" ta fada tana wucewa gaba sumayya na rufa mata baya.

"Wallahi bari umma ta fito sai na gaya mata duk abinda kika yi,bata ja mana
kunne ba?" Yarinyar daje saman kujera ita ta ambaci hakan tana jijjiga kai,cak
yarinyar ta tsaya kamar an ambata mata mala'ikan mutuwa,idanunta na tara qwalla
tace
"Kiyi haquri don Allah kada ki gaya mata"
"Wallahi sai na fada saidai ta kasheki" ta fada tana buga hannu alamun babu
fashi,wani abu ya tsayawa sumayya a wuya,takaici da mamaki suka cikata,sai ta janye
nuwaira tana fadin
"Muje babu abinda zai faru dake kinji kada ki damu" jikinta babu qwari ta bi
sumayyan suka fice.
Kafin su qarasa gun hajiyan sumayya ta dubeta
"Me yasa kinsan kina fitsarin kwance da kika tashi baki sauya kayanki ba
nuwaira?,kinsan fa ba'a son mace da qazanta" sai yarinyar ta fara qwalla ta soma
sharewa tana cewa
"Wallahi anty tunda bana fitsarin kwance,saddiqa keyi sai a hadamu kwanciya gado
daya,idan tayi duk sai ya jiqani,idan ta tashi ita sai nuratu ta sauya mata kaya,ni
kuma ba zan canza ba har sai umma ta gama bacci tayi wanka ta fito sannan zata
nunan wadanda zan sauya din,koda asuba bana samu nayi sallah sai rana ta fito" ta
fada da alamu abun na ci mata tuwo a qwarya,shiru sumayya tayi tausayin yarinyar na
kamata,wannan wanne irin zalunci ne,tun kallon farko da ta yiwa yarinyar ya nuna
tana jin jiki a gidan,amma tana tunanin kamar ita ce yarinyar nan daya da karima
jiya ta gaya mata uwarta daban,don ta tabbatar sai ta tambayeta
"Ina mamarki to?"
"Mama na tayi aure a wani gidan,tun kafin a yayeni aka karboni aka bawa hajiya
ni,to da abbanmu ya sake aure ya auro umma sai umman ta karbeni nake gunta"take
tsanar karima ta darsu a zuciyar sumayya,lallai ba shakka bayan shirkar tsafi ma
harda azabtar da yarinyar da bata ji ba bata gani ba,wai me mutane suka dauki
duniya ne?,kowacce mace son kanta ya mata yawa?,burinta ta mallaki miji ta rabashi
da kowa nasa?,ta rabashi da 'yan uwansa da tazo ta samesu tare,'yan uwa da suka
zamar masa bango marufar asiri tun yana zanin tsumma har kawo yau,ta rabashi da duk
wani alkhairi uwa uba ta rabashi da mahaliccinsa,ta sakashi a musibar da ranar gobe
qiyama bazai iya tsallaketa ba,ta rabashi da hankalinsa bare ya kula da
addininsa,wanda ya cancanci a bashi haqqinsa ta hana ya basu yanzu duka wannan
qauna ce?,sai tace sonshi take shi yasa ta aikata haka,wannan ko babban maqiyinka
ba shakka iya cutarwar da zai maka kenan,da irin wannan tunani suka isa bangaren
hajiyan.

A duqe suka sameta tana share falon nata dake malale da carfet,kallo daya
sumayya tayi mata ta fuskanci shekarunta basukai ace tayi tsufar da tayi a yanzu
ba,da sallama suka shiga ta dago tana amsa musu riqe da qugunta wanda bisa dukkan
alamu ciwo yake mata,nuwaira ce ta gaisheta ta amsa babu yabo ba fallasa yayin da
sumayya ta qarasa tana amsar tsintsiyar hannunta tana gaidata,amsawa tayi tana
dubanta yayin da sumayya ke qarasa mata sharar har ta kammala sannanbta dawo inda
hajiyar ke zaune tana yiwa nuwaira masifar sai zuba zarni take taje bandakinta ta
wanke jikinta,mamaki ya cika sumayyar,to ko batasan meke wakana bane cikin
gidan?,batasan ba laifin nuwairan bane karima ce ta cancanci fada idan da duka ma
ayi mata?,tashi yarinyar tayi ya shige bandakin hajiyar sannan hajiyar ta maido
kallonta ga sumayyan
"Ban gane fuskar ba wace ce ne?" Murmushi kawai tayi ta dan sad da kai
"Oho,ko amaryar lukman ce" kai sumayyan ta gyada.

Shiru ne ya biyo baya,hajiyan na dan satar kallon sumayyan,sai taji ta dan


sake da yarinyar duk da ba hira suke ba zaman kurame ne,a haka har nuwaira ta fito
daga bandakin sanye da jiqaqqun kayanta wadanda ta wanke bayan ta dauraye jikinta
ta maida su a haka
"Wani nuwaira nikam bakuyu abin kari bane yau,gashi har sha daya na shirin gotawa
yau ba'a kawo kin komai ba,ko luba mai aikin bata zo bane?"cike da madaukakin
mamaki sumayya ke sauraron zancan
"Tazo hajiya,bansan ba'a kawo miki ba,don ko nima yau ban karya ba,naga dai su
nuratu na karyawa ni ma ba'a bani nawa ba"ta fadi babu alamun damuwa tattare da ita
bisa dukkan alamu ta riga da ta saba da hakan,yamutsa fuska hajiyan tayi
"gaskiya na fara jin yunwa wlh,wannan abu Allah kayi mana maganinsa"
"Amma hajiya ai naga kina da sauran kayan abincinki da kika ce bazaki iya ci gaba
da girki ba ai abba bai debe su ba ko?"
"To idan banda abinki ina fama da lalura ina zan iya,sharar ma don bazan iya zama
cikin qazanta bane nake daburtawa nake yinta" ta fada ta muskutawa da alamu yunwa
na sakadarta,tausayinta duka sai ya kama sumayya ta dubeta
"To hajiya idan ba damuwa sai na shiga na girka miki ai ko?"haba ta riqe
" a'a,har kya fara shiga madafi ta sanadina?,ki barshi babu komai idan da sabo ai
mun saba da irin wannan gashin,ke dai kawai Allah yayi mana magani"murmushi tayi
kawai ta miqe tana tambayar nuwaira inda kitchen din yake.

Sallamar karima a gadarance ita ta maida hankalinsu bakin qofar,ita ke gaba


gogan na binta a baya riqe da wani dan qaramin flask wanda bako shakka abun karin
hajiyan ne a ciki,idanunsa na kan sumayya yana faman sakar mata murmushi ,wani
takaici da haushinsa suka qumeta saita dauke kai tana jin kamar taje ta
shaqeshi,haka nan kawai taji jarumin namiji yana burgeta,sai ta tuna sanda zainab
ta fara murza kambunta lokacin tana gidan mukhtar,tabbas ko a lokacin mukhtar din
kan tauna tsakuwa wani lokaci.

Hajiyan da za'a yiwa sannu a gaisheta ita ke faman yiwa kariman sannu tare da
gaisheta,lukman ya koma gefan hajiyan yana gaidata cikin dari dari suke gaisawar
kamar suruki da suruka duk don kada su batawa karima rai,baki sumayya ta saki tana
kallon abun mamaki bayan hajiya ta bude flask din da aka kawo mata,wani gantalallen
soyayyen dankali ne da rabin wainar qwai babu ko tea amma hajiyan sai godiya da
sannu take mata
"Saidai yau kici haka hajiya don kafin na fito jikokin naki sun shanye shayin"
"Ai babu komai,idan baka yiwa jikanka ba wa zaka yiwa" ta fada fara'a kamar gonar
auduga.

Kallon sumayya karima tayi bayan sumayyan ta gaida lukman wanda ke faman
binta da kallo kamar tsohon maye
"Ke baki iya gaida mutane ba" ta fada fuska a tsuke kamar wata uwarta,waigawa
sumayyan tayi ta watsa mata kallo
"Su waye mutanen?" Ta tambayeta bayan ta tsareta da ido,sai kawai taji sumayyan ta
mata kwarjini da irin kallon da take mata,janye idonta tayi ta dubi hajiya
"Hajiya kina gani dai a gabanki ko?" Ta fada cikin zafin rai,lukman yayi saurin
karbewa
"Bana son rashin zaman lafiya fa sumayya a gida na kinji ko?" Kallon da wa kazo ta
watsa masa sannan ta dauke kai,hajiya cikin rawar jiki tace
"Ke yarinya,farincikinmu shine farincikin karima,saboda haka dole ki mata biyayya
ki kiyaye" girman hajiyan take gani,saboda haka ta dan rusuna
"Insha Allahu hajiya kiyi haquri" ta fadi da sauri tana shigewa kitchen din hajiyan
don bata son ma ta sake kallon fuskar lukman bare ta karima.

Tana kitchen tana hada girkin duk da wasu kayan buqatun babu,mamaki da
tunani fal ranta,a haka taji sallamar hajiyan,ta juya tana amsa mata,qarasowa
hajiyan tayi ta kama hannun sumayya kamar zata saki kuka
"Kiyi haquri sumayya da abinda nayi miki dazu,yarinyar nan idan ta umarcemu da abu
daga ni har lukman bama iya musa mata,amma nasan alhakin yaran jama'a ne yake
bibiyata,haka kawai naji kin kwanta min sumayya zan gaya miki wace ni me na aikata
ga rayuwata da rayuwar yarona"
Kafin sumayyan tace wani abu tuni hajiya ta fara bata labarin dukka aure auren da
lukman yayi wanda ita ce sila,da fari haushin hajiyan ta dinga ji,amma daga bisani
sai tausayinta ita da lukman ya baibayeta baki daya,tabbas abu na farko data
fuskanta ya janyo wannan matsalar sakaci da rashin riqe ubangiji hannu bibbiyu,har
qwalla sai data yiwa hajiya da lukman din saboda aikin kariman ya shallake hankali.

Cikin sanyin jiki ta riqe hannun hajiyan ganin tana zubda qwalla
"Kiyi haquri hajiya ki fawwalawa Allah lamarinki,ba shakka inna idan ma alhakin ne
ba mamaki,Allah na sonki shi yasa zai hukunta ki tun a duniya,din hukuncin lahira
da shi gwara na duniya sau babu adadi,in sha Allahu ni zanyi iya bakin qoqarina
wajen ganin na daidaita lamarin iya abinda Allah ya huwace min,ina so daga yau kisa
a ranki ba zaki qara jin tsoron karima ba,ba zaki sake bin umarninta ba sai abinda
ya dace shi zakiyi,a duk sanda kika ganta idan kika ji faduwar gaba ko tsoro ki
karanta ALLAHUMMAKH FINIHIM BIMA SHI'ITA matakin farko kenan,sannan daga yau kada
ki sake cin duk abinda ya fito daga hannunta,ki umarci lukman ya kawo miki kayan
abincinki a zuwan zaki ci gaba da girki,ni kuma in sha Allahi zanci gaba da dafa
miki" kai take gyadawa cike da gamsuwa tana jin tamkar damuwarta na gab da yayewa
"Sannan lukman danki ne hajiya,bakin uwa kaifi gareshi,ki dage da yi masa
addu'a,Allah ya yaye masa bala'in da ya fada ta sanadin abinda ke kika aikata
shi,bashi kadai ba,har ke dinma saikin dage da addu'a wa kanki na neman tsari"
Kai ta sake jinjinawa
"Har na manta rabon da na sashi a addu'a ta,na gode da tunatar da ni da kikayi,na
gode sosai"
"Sannan hajiya,kinsan rayuwar da nuwaira take cikin gida kuwa?" Ta tabo inda yafi
mata qaiqayi
"Na sani sumayya na sani,saidai bani da ikon magana bani da ikon gyarawa" ta fada
cikin jimami,don har ga Allah duk cikin jikokinta tafi qaubarta,din ta fita daban a
cikinsu,nutsuwarta da komai da komai,shiru sumayyan tayi sannan tace
"Babu komai,zanyi iya bakin qoqarina itama akanta kafin Allah ya kawo qarshen
lamarin"
"Na gode sumayya na gode,haqiqa kin zamo *HASKE* cikin gidan d'ana cikin kwana daya
tal,ina miki fatan alheri sannan kuma ina miki fatan samun nasara,Allah ya
albarkaci rayuwarki da alkhairi masu tarin yawa,ya tsareki" amin sumayya ta dinga
cewa tana jin dadin addu'ar har cikin ranta,ko da can ita din mai son wani na gaba
da ita ne ya albarkaceta,kusan tare suka gama aikin ta kammalewa hajiyan cikin kula
yadda tasan zai ishesu ita da nuwaira,tace zata turo mata ita taci na rana dana
dare,don ta lura bata samu albarakacin cin na safe ba,sai na hajiyan da suka
yayyafita.

Nan tayi zamanta gun hajiya,ita kanta hajiyan sai ta dinga jin dadi cikin
ranta,nuwaira ma ta dinga sato jiki tana leqowa har sanda sumayyan ta koma
bangarensu.

***** ****** ******

Cikin kwanaki hudu rak sumayya ta gama dukkan wani shiri nata na tunkarar
wakeken qalubalen data fuskanci yana danqare a gidan,ita kanta mamakin kanta take
yadda zuciyarta ta taurare baki daya har take ganin zata qalubalanci karima wadda
baki daya ta rusa rayuwar gidan ta dora ta kan turbar da take so,sam sam yaranta
irin yaran nan marasa tarbiyya ko qanqani,su zagi babba duk girmansa ba komai bane
a gunsu,sam sam sumayya bata shiga shirginsu ko sakar muau fuska tunda ta fuskanci
inda tarbiyyarsu tasa gaba,hakan ya sanya suka fara shakkarta,sai kuma mai biwa
babbar da ta soma son kula sumayya,sau tari takan qwanqwasa qofarta idan ta bude
mata tace ta shigo kuma sai taqi,sai ta fuskanci shakkar mamarta take,hakan ya
sanya ita sumayyan ta fara qoqarin janyota a jiki,ga shegen gulma munafunci da iya
kawo labari,hatta da mahaifinsu suna iya dauko gulmarsa su kawo mata ita kuma ta
tuhumeshi kan haka,sumayyan na sha'awar hatta da tarbiyyar yaran ta saisaita musu
ita,don ta kula sam daga makarantar boko babu kuma wata makaranta ta biyu da yaran
ke zuwa wadda ake kira da makarantar addini ko islamiyya,baki daya idan ka dauke
sumayya banu mai rayuwa kan ra'ayinsa sai abinda ta shinfida,tun abun na bawa
sumayya haushi har ya koma bata tausayi,ita sam ma baki daya bata ta angon ko
kadan,wanda zuwa yanzu hatta lokacin fita da dawowarsa gida karima ta sauya masa
duk don kada su hadu da sumayyan,ta saka an qara narka masa aikin mantau akan
sumayya wadda ko gefen silifas dinta lukman din ma baije ba,sau tari takan tambayi
kanta me yasa ta auri lukman sai ta rasa dalili,amsa daya ke zuwa kanta
"Qila don kizo ki ceci rayuwar 'yar gidan ne" ita kanta tafi gamsuwa da wannan ce
sahihiyar amsar

****** ******* *******

Cikin satittika qalilan shaquwa ta fara shiga tsakaninta da hajiya,kusan koda


yaushe can take wuni,ta yima haijan aikace aikace sannan suyi girkinsu abinsu,sannu
a hankali sauyi ya fara samuwa tattare da hajiyan,sumayya ta zaburar da ita ta kuma
koya mata addu'o'i sosai,rana ta farko da suka fara fuskantar zuwan sauyi shine
randa kariman ta shigo da abincinta wanda aka saba sanwa hajiyan don bazance bata
ba,duk da hajiyan ta jima bata ci amma sumayya tace ta dinga karba kada ta gaya
mata idan yaso saita dinga bayarwa,tunda ta shigo ta lura hajiyan sam bata rawar
qafa yadda ta saba idan ta shigo gunta,abu na biyu tana jiran taga hajiyan ta
gaidata yadda ta saba sai taga tayi fuska,ta maida hankalinta gun sumayya dake
shafa mata man zafi a gwiwarta data riqe mata take mata ciwo,wanda abaya bata da
wannan gatan saidai taci ciwonta ta warke don dolenta.

Kanta yayi masifar daurewa,abu na farko da yazo kanta aikin hajiyan ya fara
sako sako don dama kwana biyu tafi maida kai a kan lukman din
"Ga abinci nan" kariman ta fada a wulaqance,juyowa hajiyan tayi tana duban flask
din ranta cike da takaicin yadda ma ta dinga karbar wannan abincin
"Wai ni?,ai da kinyi gaba da abinki don na jima banci abincinku ba,'yata na
girkamin kullum" ta fada tana duban sumayya,take tsoro ya shigi karima,ashe tayi
sake har haka?,ashe fa diyar malamai wannan karon lukman ya kwaso mata,lallai ba
shakka shi yasa taga bata taba tambayar abincinta ba a gidan duk yadda ta sha
alwashi akan yi mata kaca kaca duk sanda ta tambayi a bata abinci.

Hankalinta tashe ta fito daga bangaren ciken da tsoron lallai idan ta gama da
hajiya babu shakka lukman zata dawowa,kacibus sukayi da nuwaira wadda ke dawowa
daga gidan kitso da sumayya ta turata tayi saboda ba zata iya mata ba jiya ta yanke
da wuqa a hannunta,baki ta saka tana duban nuwairan yadda ta canza cikin sati biyu
kacal da kariman tayi bata nan,ta tilasta lukman ya biya musu umra ita da shi don
har sai da yaci bashin wajen dubu dari biyar sannan ya cika musu,su kuma yaranta da
zata tafi ta tattarasu ta maida su gidan iyayenta ta bar nuwaira ko oho,don dama ta
saba yi mata irin hakan,tsoro ya kama nuwairan sai ta rabe gefe sannan ta tattakura
ta sheqa da gudu sai bangaren hajiya,don kayan dake jikinta na waccar sallar ne
shekara uku da dinka su,bata barinta ta sanya su sai wani abun ya tashi duk da cewa
suna da lodin kaya harda wanda bata taba sawa ba ma sababbi,ta riga ta saba kayanta
koda yaushe haka suke tamkar tsummokara,a haka ma sai an bata umarnin wadansa zata
saka,bayan 'yan uwanta kullum cikin saka mai kyau suke.

Bata bi ta kan nuwaira ba don ba ita ce yanzu a gabanta,bangarenta ta wuce


hankalinta a matuqar tashe,tabbas lallai babu shakka idan batayi wani abu ba ta
lura duniyar rayuwarta gab take da girgiza koma rugujewa baki daya,dole ne gidan ya
koma yadda yake,dole kowa ya koma yadda take so ciki kuwa harda sumayyan

****** ******* ******

Tunda ya karbeshi kusan shi ua zame masa uwa da uba baki daya,yana matuqar
debe masa kewa,yana sanyashi nishadi,wata qauna ta yaron nasa yake ji cikin jikinsa
da jininsa,sau tari ya kanyi mamakin kansa yadda yake zama yayita kallon abdallan
kamar babu gobe,babu yadda yaya yahansu batayi ba akan ya bata shi amma ya qiya,ya
bata haquri don bazai iya bata shi din ba.
Da safe tare suke shiryawa ya bashi abinci su fita kasuwa tare da shi,zuwa
azahar zai bar kasuwa ya dan fita da shi su zaga gari su dawo da la'asar,qarfe
shida subar kasuwa su dawo gida,har gado ya siya na yara ya sanya masa can cikin
shagon,nan ma idan sun dawo sunyi wanka sannan suci takeaway din da ya tsaya hanya
yayo musu,daga nan ya zube masa kayan wasansa yana tayashi yana kallon t.v har
yaron yayi bacci,wani lokaci yakan bata lokaci saman abun sallah yana wa yaron nasa
addu'a tare da yiwa kansa,wanda hakan ya sake samarwa da ruhinsa nutsuwa,shikewa
Abdallahn komai,dai dai da rana guda mukhtar bai taba jin ya qosa koya gajiya
ba,kai kanka idan ka kalli yaron ba zakayi zaton bai tare da mahaifiyarsa ba,kusan
kullum sabon kayan mukhtar zai sanya masa,ado yake masa sosai,hakanan idan shadda
zaya sanya ko yadi anko suke abinsu,duk wanda ya gansu a hanya zasu burgeshi,wata
qauna ta musamman ce tsakanin d'a da ubansa,wani lokaci idan ya soma rigiman
mamansa sai ya kaishi gunsu halima ya wuni don bai iya barinsa ya kwana,da dare
yazo ya dauki abinsa su wuce.

Sau daya yaya yahansu ta taba tuntubarsa da batun bazayayi aure


bane,murmushi kawai yayi mata yace tabar batun don ko sha'awar sa bayayi,tilas ta
ja bakinta ta tsuke,domin har yau tana tuhumar kanta da cewa ita ce sila,zuwa yanzu
itama ta fara gani,don kuwa yaron da jamila ke ao kamar ta mutu shima yayarsa ta
hana auren sam tace bata yarda ba,ga fatima nan ma a gabanta babu wani
bayani,fiddausi kuwa uwar miji ta sakota gaba,yau tana gidanta gobe tana gidan yaya
yahanasun

*_KOMAI NISAN JIFA_*

Tunda dukka ayyukanta suka kammalu wajen malaminta data bawa hadin kai
wanda har ta kaita da kwanciya da shi,ki a jikinta babu abinda taji tunda har ya
mata alqawarin tabbas tamkar ta samu kukhtar ta gama koda kuwa zata sanar masa ita
ta shirya duk abinda ya faru a baya da sumayya,babu abinda zai iya aikatawa ba
zaiga aibunta ba face sabuwar soyayya da zata sake ballewa a tsakaninsu.

Ranar lahadi ta shirya zuwa har gida saboda ta tabbatar a ranar bai fita
kasuwa,dinki na musamman tayi sabo,baya ga sabon kitso da gidan kwalliya da taje
duka aka sauya halittar Allah,saboda tana rayawa matuqar ciniki ya fada tofa ba
lallai bane ma ta dawo gidansu ba saidai a biyota da kayanta,tunda har yau a
matsayin saki daya yayi mata haka ta sanarwa mamanta,wanda koda sakin ukun tace an
mata ta kuma ce zata koma babu abinda uwar ta isa tayi don ba a bakin komai take a
gunta ba.

Qarfe sha goma na safe ta kammala komai,a nan cikin shagon masu kwalliya
wadda ta sanya fitowa tunda safen tayi mata ta sauya kaya,double ta biya kudin
makeup din hakan ya sanya ta yiwa jakarta qarqaf,bata da damuwa tunda tana saka ran
kome wanda zata fanshe dukkan abinda ta kashe gun mukhtar,ba shakka sai ta rama
wahalar da ya bata ba zata sassauta masa ba.

Qarfe goma sha daya saura mintuna goma ta sauka qofar gidan mukhtar din,wani
farinciki ya lullubeta ta soma shaqar iskar komawa cikin gidan,cikin sa'a tana tura
qofar gidan ta taddata a bude,a hankali take takawa saboda cogen dake qafarta har
ta sada kanta da falon gidan,a hankali take qarewa falon kallo yadda ya sake
maidashi ya gyarashi bayan barinsu gidan,sai abun ya sake burgeta,ko ina tsaf kamar
akwai mace a ciki kasancewar yana da mai share share da goge goge,cikin kallon da
takeyi ne idanuwanta ya saukan kan abdallah dake zaune tsakiyar falon,sanye yake da
jallabiya fara tas ta yara wadda ta masa kyau kamar dan larabawa,wasansa yake da
kayan wasa turmus a gabansa nau'i daban daban.

Idanuwa ta zuba masa kamar yadda shima ya zuba mata idanuwa yana kallonta
tamkar ya santa,karkata kai take tana gano kamannin mutum biyu tattare da
shi,sumayya sumayya mukhtar mukhtar,ci gaba tayi da kallon nasa tana son tantance
dan waye?,miqewa yaron yayi yana ci gaba da kallonta sai kuma ya saki kuka tare da
juyawa a guje ya shige bangaren baban nasa wanda ke ciki.

*mrs muhammad ce*

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

4⃣2⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

*wala tahsabannal lazina qutilu fi sabilillahi amwaataa,bal ahya'u inda rabbihim


yurzaqun*

*_kada ku zaci wadanda aka kashe ta hanyar Allah(shahidai)matattu ne,rayayyu ne a


gun ubangijinsu ana azurtasu_*
_______________________________

Mukhtar dake falo zaune saman abun sallah yayi saurin sallame raka'arsa ta
qarshe wadda dama zaman tahiya yake,qarasowa abdallah yayi yana kebe baki ya fada
jikin mukhtar,tambayarsa yake menene kamar wani babba,babu baki sai gwalanto da
yake masa wanda bai gane mai yake cewa,miqewa yayi da sauri sabe da shi a kafadarsa
sabida tunawar da yayi dazu da ya fita siyo ma abdallan alawa ya manta ya bar qofar
gidan a bude.

Tana zaune qafa daya kan daya tana kadasu hankalinta kwance,tana jin ba ma
sai taje nemansa ba da kanshi zai fito,qamshin turarensa da ta ji shi ya maida
hankalinta zuwa qofarsa,shi dinne dauke da abdallah sanye da jallabiya sak irin ta
abdallan,har ga Allah bai lura da ita ba sai da yaji an ambaci
"Ranka ya dade" cak ya tsaya sannan ya waiwayo ya dubeta,idanunta ya dan juya don
tabbatar da cewar ita din ce?,ita ce don kuwa zuwa yanzu gabansa take takowa,dab da
shi ta qaraso tamkar zata shige jikinsa,cikin narke murya ta soma magana
"Haba my mukhtar,ka riga da kasan irin kamun da soyayyarka tawa zuciyata,ta yaya
kake tunanin nisanta kanka da ni bayan kasan cewa ina mutuwar sonka,a yau ina so ka
maidani dakina ba sai gobe ba domin shine burina kaji" ta qarashe maganar ta sigar
bada umarni.

Wani bala'i ke cinsa,ya tabbata cewa idan har baiwa zainab akuyanci ba ba
zata taba barin rayuwarsa ba,yarinyar da kullum kwanan duniya ya zauna tunani yake
tare da tambayar yaya akayi ya aureta ma wai?,mene ya ja hankalinsa,ko da yaushe
yakan godewa Allah da bai QADDARA rabon zuria a tsakaninsu ba.

Cikin tsantsar bacin rai ya soma nuna ta da yatsa kamar zai tsone mata
idanuwa
"Cikin halittun dabbobi ke wacce iriya ce a cikinsu?,bakiji gargadin da na miki ba
kenan?,tunda nake ban taba ganin ballagazar mace irinki ba,sha sha sha kawai
wawiya,to wallahi zan miki gargadi na qarshe,duk sanda kika sake shiga rayuwata sai
na miki abinda ko hanyar da nake bi aka ce kibi ba zaki biba,bace min da gani banza
qazama kawai" ya fada kamar zai hankadata.

Tsantsar tashin hankali da baqinciki suka taso suka tokareta,amma data tuna
yadda bokanta ya jaddada mata kyawun aikin da yayi mata sai taga bari ta sake gwada
sa'arta
"Wai mukhtar me na maka da zafi haka,nina shiryawa sumayya dukkan wata gadar zare
kuma a idanunka sumayya ce ta aikata laifin,to amma na lura tsanar da ka yimin baka
yi mata koda rabinta ba" sosai maganar ta daki kunnensa gangar jiki da zuciyarsa
duka lokaci daya,wani abu yaji yana zagaya kansa,wani irin sanyi jikinsa yayi ya
zubawa zainab ido har baisan sanda yace
"Kika shirya mata gadar zare kamar yaya?" Wani fari tayi da idanuwa tana ci gaba da
kallonsa,a tunaninta sanyin da jikinsa yayi aikinsu ya fara shiga jikinsa ne,sai ta
kama hannunsa babu musu ya bita zungui zungui,don baya gane komai a yanzu,abinda ke
yawo kansa kawai shine irin abubuwan da suka dinga faruwa tsakaninsa da sumayya a
lokacin,sai da ta kaishi gefan kujera ta zaunar sannan ta zauna gefansa.

A hankali ta dinga warware masa zare da abawa tamkar wadda ake umarta,ko da
yake umarni ne na rabbil izzati da yaso ya fidda bayinsa daga wani mummunan
sharri,ta qare da cewa
"Dukkan wannan saboda tsananin qaunarka da kishinka da nakeyi ne ya janyo na aikata
hakan,kuma babu abinda bazan iya aikatawa duk don saboda kai saboda na mallakeka ni
kadai,a shirye nake na sadaukar da dukkan abinda na mallaka" ta fadi tana karya
wuya tare da sakin murmushin alamun samun nasara a tunaninta.

Gaba daya daina zagayawa jini yayi a jikinsa,kansa ya masa nauyi,cak


qwaqwalwarsa ta tsaya da aiki,wani duba yakewa zainab din mai cike da tsantsar
tsana,daki daki musgunawa da zargi da kallon tsana da ya dinga yiwa sumayya ya
dinga dawo masa kamar bitar karatu,yanzu duk baki daya ba bisa laifinta bane
ashe?,ashe ita din bata aikata komai ba kamar yadda tasha sanar masa?,bai taba jin
ya tsani wata halitta a duniya ba kamar yadda yake jin tsanar zainab na yawo cikin
jininsa da ruhinsa ba,sai da wuta ta dauke masa na wasu mintuna kafin ya fara
tunaninsa ya fara dawowa kan hanya.

Yana jin yau idan bai ci uban zainab a duniya ba yayi asarar rayuwarsa,baisan
wanne ne hukunci na qarshe da ya cancanci yayi mata ba,miqewa yayi da hanzari ta
ruqo hannunsa
"Ina zaka?" Wani kallo ya juya ya watsa mata wanda ya sata sanqamewa,fargaba ta
lullubeta tana fatan ba abinda take tunani bane ke shirin aukuwa
"Gidan uwarki da ubanki zani,zauna ki jirani" ya fada a tsawace yana tsige hannunsa
daga nata,wani malolon takaici ya cika zuciyarta,kada dai ace mukhtar din na cikin
saitinsa tayi wannan barin zancen?,yana nufin aikinta baiyi tasiri a kansa
ba?,waishin wani irin mutum ne mukhtar din?,yana nufin dukka kashe kudi bata lokaci
da sadaukar da jikinta da tayi ya tashi a banza?,to wallahi wannan karo kam bai isa
ba,bai isa ya sanyata ci gaba da yin asara ba,kota hanyar tsiya kota arziqi,tsaye
ta miqe a zafafe tana dubansa
"Kai mukhtar,na gaji,na gaji da asarar lokacina da kudina a kanka,me yasa bakasan
darajar soyayya ba?"
Dauketa yayi da wani zazzafan mari wanda ya haddasa mata ganin wulgawar wasu
taurari tare da zubewa warwas a qasa,lokaci guda jini yayi kwance gefan qwayar
idanuwanta,kafin ta kai ga dawowa hayyacinta tuni ya garqame qofar falon sannan ya
wuce ciki cikin matsanancin sauri,bedroom dinsa ya shiga ya kwantar da abdallah da
bacci ya daukeshi kan fadar mukhtar din sannan ya fito ya rufe qofar dakin baccin
ya rufe ta falo baki daya don bai fatan yaji ko yaga abinda yake shirin
aikatawa,wani irin suya qirjinsa yake a fuskarsa yana jin wani hucin zafi na fita
kamar wanda aka cilla cikin rumbun gasa biredi.

Nan saman kujerar ya sameta zaune tana shafawa tare da jajjabin kuncin da ya
mareta wanda lafiyayyun yatsunsa suka fito rada rada tamkar an zana su,bata lura da
fitowarsa ba sai da flower vase din dake kan t.v stand ta fado ta fashe saman tiles
sanadiyyar finciko wayoyin dake jikin kayan kallon ta ankarar da ita,nufota ya soma
yi wanda hakan yayi matuqar firgitata,gaba daya kamanninsa sun sauya mata,ganinsa
take kamar wani mayunwacin zaki yaga abun farauta
"Me kake shirin yi mukhtar,kada dai kace dukana zakayi"
"Idan akwai abinda yafi duka yau zaki dan dana shi,inaso gangar jikinki ta fara
dandana azaba kafin na kai ga ruhinki,yau zakiyi dana sanin raba masoya,daga yau ko
a shirin film aka ce ki fito a matsayin jarumar dake raba masoya ba zakiyi marmari
ba"
"Amma dai kasan......." Sai maganar ta katse sakamakon ihun da ta tsala saboda
kyakkyawan masauki da wayar ta samu a gadon bayanta,duka kota ina ya dinga kai
mata,baki daya ya fice hayyacinsa kamar yadda itama ta fara dan dana kudarta,duk
duka daya da zai kaimata sai ya tuno baqar azabar da sumayyan ta sha a wancan
lokaci,tun zuwan zainab din gidan har ya zuwa ranar data kwanta gadon asibiti,ranar
data zamto rana ta qarshe a tarihin zamantakewar rayuwar aurensu.

Duk inda ta nufa da nufin samun mafaka ko maboya sai ya bita,tuni takalman
qafarta sukayi nasu guri daban,haka dankwali da mayafinta,ganin abun nasa na gaske
ne babu alamun sassauci yasa ta fara bashi haquri,saidai sam baya fahimtar me take
fada,sai bada haqurin ya zamo tamkar tana qunduma masa zagi ne a gurinsa.

Tun zainab na iya ihu da neman agaji har muryarta ta dakushe,tuni fuskarta
ta cabe baki daya,kwalliya tayi nata guri,baka iya tantance ina kwalliyar tata bare
fuskarta,babu inda bai fasa ba ajikinta har wani sashe na kayan jikinta ya yage
saboda tsantsar dameta da kayan sukayi,jagaf ta jiqa kayanta da gun da ta dinga
malelekuwa da fitsari,wurgar da bulalar yayi gefe kamar yadda zainab ke yashe gefe
daya tana fidda qwalla hadi da numfashi,sai yau ta yarda da maganar hausawa na cewa
kuka ma rahama ne,gashi a yanzun bata da qwarin ma fidda sautin kukan,azaba take ji
na shigarta takowacce kafa ta jikinta,dukan da tunda tazo duniya ba'a taba yi mata
kwatankwacinsa ba duk da kasancewarta yarinya gagararriya tun a wancan lokacin,yana
haki numfashinsa na fita da qarfi saboda tsananin bacin rai,ji yake kamar ya
shaqeta ta mutu ya daina kallonta,duk duba daya da zaiwa fuskarta tsanarta ke
ninkuwa cikin ruhinsa,ba shakka wannan duka babu abinda ya rage cikin zuciyarsa na
daga bala'in da yake ji,qafarta daya ya kama ya bude qofar falon ya dinga janta
tamkar kayan wanki,bai direta ko ina ba sai bakin qofar gidan,ya koma ya kwaso
tarkacen takalmi jaka da mayafinta ya watsa mata,yana tsaye a kanta ya nunata da
yatsa
"Ba qarshen hukuncinki kenan ba,ki jirayi abinda zai biyo baya" ya fada yana juyawa
cikin gida.

Wani irin jiri ya dinga kwasarsa,da qyar ya kai kansa cikin dakin baccinsa
inda abdallah ke baccinsa lakadan baisan meke faruwa ba,gefansa ya zauna ya zuba
masa idanu yana kallonsa cike da tausayinsa tausayin kansa da kuma tausayim sumayya
baki daya,tambayar kansa yake ta yaya ya yarda sumayya zata iya aikata haka ma
wai?,sumayyarsa ce fa?,rainonsa ce,tarbiyyarsa ce,yaya akai har ya gaza bincike
tashin farko ya yarda ya dora zarginsa kan halittar da bai taba samunta da cutar da
wani qwaro ba ballanta na mutum dan adam mutum din ma shi mukhtar,mukhtar
dinta,wannw iri kaidi ne mata suke da shi haka?,wanne irin halakakken kishi ne
wannan?,yunqurin kisan kai fa kenan a taqaice,ta yaya zai ga sumayya?,ta ina zai
fara neman yafiyarta?,da wanne ido ko fuska zai kalleta?,shi kansa baisan amsar
dukkan wadan nan tambayoyi ba,haqiqa ya cutar da ita,ya cutar da zuciyarta,babu
shakka shi yasa tun daga ranar da ya saketa bai sake samun sukuni nutsuwa ko
farinciki cikin zuciyarsa ba,ya sani haqqinta ne Allah bazai taba barinsa ya huta
ba bayan ya cutar da ruhin dake masa qauna ta domin Allah,sai kawai ya dafe kansa
da hannu bibbiyu wanda yakejin kamar zai tsage,kuka ya saki mai tsuma zuciya hawaye
na bin fuskarsa,fata yake ya samu sauqin azabar da zuciyarsa ke masa,fata yake ya
samu salama qirjinsa ya bar suya,baisan wanne hukunci ya dace ya sake yiwa zainab
ba,ba shakka wannan hukunci yana ji har cikin zucuyarsa bai gamsar da shi ba yayi
kadan.

_kuyi haquri da wannan_

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*
*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

4⃣3⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

*fazakkir fa innaz zikra tanfa'ul mu'uminin*

*_KA TUNATAR DOMIN TUNATARWA TANA AMFANAR DA MUMINI_*

_______________________________

         Nan gefan abdallah ya kwanta yana ci gaba da kuka tamkar wani qaramin
yaro,jin zuciyarsa yake kamar zata fashe,janyo abdallah yayi cikin jikinsa yana
magana qasa qasa mai cike da kalmomin nadama yana ci gaba da kuka.

          Sai da rana ta soma bugun naman jikinta sannan ta iya miqewa a daddafe ta
yafa mayafinta,takalmi kuwa basu sakuwa a hannu ta riqesu hadi da jakarta,da qyar
da jan qafa ta kai kanta titi ta tari adaidata sahu ta hau duk da cewa bata da
qwadalar da zata bashi,qofar gidansu ya sauketa tace ya jira ta miqo masa
kudin,tana sallama ta zube a tsakar gidansu tana maida numfashi,mamarta dake wanki
bakin fanfo ta dago tana dubanta,mamaki ya cikata saidai bata da ikon tambayar ta
abinda ya sameta,murya can qasa da qyar ta qwalawa qanwarta kira
"Idan akwai naira dari jakarki fita waje ki bawa mai adaidaita sahu,mama dora min
ruwan zafi" kowannansu da to ya amsa mata,maman ta saki wankin ta shiga kitchen.

      Gashi tayiwa kanta sosai tamkar kai jego,tanayi tana runtse ido zuciyarta na
zafi da quna,tana tuna yadda mukhtar ya dinga jibgarta kamar wanda ya sayi jaki mai
taurin kai,dakinta ta koma ta shafe jikinta da man zafi ta samu ta kwanta sannan ta
janyo wayarta tayi kiran abokiyar shawara da shaidancinta zinatu,tana dagawa ta
buqaci ganinta,cikin sa'a kuwa tana kusa.

      Cikin mintuna qalilan zinatun ta iso,suka gaisa da maman wanda ke zaune


tsajar gida tana shirin dora abincin rana,da kallo tabi zinatun har ta shige dakin,
"Lafiya?,na zaci zaki cemin gaki gidan mukhtar anyi kome sai nazo na sameki kina
tashi da qyar haka?"baqinciki ya sake tokare zainab,cikin bacin rai ta soma fadin
" ni malam zai ciwa kudi zinatu,ni zai ha'inta?,kalli jikina ki ga abinda mukhtar
ya yimin duba zinatu"
"La la lal" shine kawai abinda zinatu ke fada tana gyada kai
"Garin yaya haka zainab" tas ta kwashe yadda komai ya faru ranta na quna ta qunduma
ashar sannan ta dora
"Ba sai na warke ba gobe gobe zamu koma wajen malam,wallahi sai na nuna masa ni
'yar tasha ce,duk abinda ya buqata nayi masa,kwana nayi yana sasukata duk warin
dake tashi a jikinsa amma ban damu,shine ni kuma zai rainamin wayo an gaya masa ni
gara ce,to wallahi Allah ya nuna mana gobe shege ka fasa" haka ta dinga bambami
zinatu na tausarta da haka sukayi sallama da niyyar gobe da sassafe zasu dirarwa
malam

  *******  *******   ******

       Tana zaune bakin gadonta tana ninke kayan sawarta a hanakali,tunanin


abdallah na kai komo cikin ranta tun safe,tunda ta haifeashi basu taba rabuwa
daidai da kwana guda ba banda sanda ta yayeshi sai wannan lokacin,yanzu haka
watanni kusan shida kenan bata sanyashi a idanunta ba,gidan nasu yau shiru yake tun
safe har yammaci,hajiya na bangarenta yau bata jin dadi,tunda ta kammala mata girki
sai ta barta ta dan kwanta ta huta,karima ta hada kan yaran sun tafi sunan qanwarta
data haihu,bata kuma bar nuwaira ba haka ta kada ta suka tafi tare,yaran baki daya
sunci ado banda ita,a haka da sauqi tunda sumayya ta tattara dukkan yagaggun
kayanta ta boye ta hanata sakasu tafiddo mata da wasu,haka karima ta haqura bayan
sa'insar da suka sha da sumayyan,a yanzu bata da goyon bayan hajiya lukman kuma bai
gari yayi tafiya bare ta hadata da shi.

        Hudu da rabi na yammacin taji sallamarsa bakin qofar dakinta,a hankali ta


daga kanta tana dubansa,ta mance yaushe rabon data sanyashi a idanuwanta tun kafin
yayi tafiyar nan wadda ita kanta satinsa biyu kenan baya nan,sanye yake da shadda
dinkin tazarce da hula saman kansa sai takalmi sau ciki,kafadarsa rataye da jaka ta
matafiya,kallonta yake yana mata murmushi
"Sannu da zuwa" ta fada tana gyara daurin dan kwalinta
"Yauwa sumayya,ya gidan?" Ya fada yana zama gefanta yana mai ci gaba da kallonta
"Lafiya qalau" ta fada tana hada kayanta waje guda tare da miqewa ta zura hijabinta
tana shirin ficewa
"A'ah,ya haka kuma,ya zaki fita ki barni"
"Au da dawa nake barinka" ta fada tana gyara zaman hijabinta gami da kallonsa
"Amma dai ai yau gidan babu kowa ko?,wa zai kula da ni?"
Qugu ta riqe tana duban idanuwansa
"Sai babu kowa cikin gidan sannan nake da amfani a gunka?,to gun hajiya zani na
dubata na barota bata jin dadin"damuwa qarara ta gani ta bayyana kan fuskarsa karo
na farko kan maganar da ta shafi mahaifiyarsa
" subhaballahi tun yaushe?,muje na ganta"ya ajjiye jakarsa ya miqe yabi bayanta.

       Ganin yadda ya damu qwarai ya sanyata cewa


"Ba wani ciwo me mai zafi ba,qafarta ce kawai ta motsa"tayi furucin tana kallon
gabanta,ajiyar zuciya yayi bai sake cewa komai ba har suka qarasa dakin hajiyar.

      Tana kwance a falo da alama sallah ta idar,sosai tayi mamakin ganin lukman
din wai tazo dubata,saidai bata nuna masa ba,suka gaisa fuskarta a sake,shi da itan
duka wani dadi suke ji,sai gashi suna hira kadan kadan,hatta da sumayya sai data
dinga jin dadi,ta dade da sanin dadin da iyaye ke da shi a gun d'a,hakanan zuwa
yanzu tasan yadda uwa ke jin dadi a duk sanda ta daga ido ta kalli danta ko diyarta
cikin kyakkyawan yanayi.

     " kaje ka huta lukman ka dawo daga baya idan hirarce"hajiyan ta fada qasan
zuciyarta a karye,don tasan ita kanta fada kawai tayi,saboda babu lallai ya sake
zama da ita irin haka matuqar karima baqar daga ta dawi cikin gidan,ta fada ne don
kawai kada ta shiga haqqinsa shi da iyalinsa,saboda zuwa yanzu ta yarda kura kuran
da ta tafka a baya zunubinsu ke bibiyarta,amsawa yayi da to don shi kansa yanason
kasancewa da matarsa,miqewa yayi yayi gaba wanda tilas sumayyan tabi bayansa don
tana kunyar hajiya da ganin girmanta,bata son ta fuskanci komai daga gareta.

        Gaba ya sanyata har zuwa dakinsa,karo na farko data fara taka dakin tun
zuwanta gidan,kan gado ya zube yana dubanta
"Hadamin ruwan wanka na gaji sumayya,sai ki yo alwala idan na fito zamuyi sallah"
"To" kawai tace masa tana tunanin lokacin sallar magaribar ai baiyi ba aqalla akwai
kusan awa guda nan gaba,sai daya shiga wankan sannan tayi alwalar kamar yadda ya
buqaceta,a nan gabanta ya shirya duk da dauke kai da tayi sannan ya umarceta da
tatashi suyi sallah,bata fuskanci abinda yake nufi ba sai suka idar da sallar taji
yafara addu'a,take jikinta yayi sanyi,tsoro kuma ya cikata,tana jin ta yaya zata
sake wata sabuwar rayuwar da wani sabon mutumin na daban ba wanda ta saba da shi
ba?,saidai babu yadda ta iya din saboda tana da cikakkiyar masaniyar cewa da
mijinta take tare wanda ya biya sadakinta shaidu kuma suka shaida,to shi kansa
kamar baqo haka ya bijiro mata,sai daga bisani ya fara warewa a hankali,hawaye ne
suka dinga gangaro mata,ambaton Allah ta dinga yi cikin zuciyarta.

        Tana gaban madubi tana gyara gashin kanta bayan ta gogeshi tare da maida
masa ribbom dinsa,shi kuma na zaune bakin gado yana kallonta,tabbas babu shakka
kyauta Allah ya masa,a cikin mata hudu da ya aura har da karima cikon ta biyar din
bai taba cin karo da mace kwatankwacin sumayya ba cikin duniyar ma'aurata,babu
abinda ke kai kawo cikin qwaqwalwarsa sai yadda ya samu sumayyan cikin sahun mata
na musamman wadanda suke 'yan kadan ne cikin daruruwan mata,amma sai ya fuskanci
babu wata fara'a ko walwala sam a fuskarta,wanda hakan sai yaji sam bai masa dadi
ba,a hankali ya kira sunanta ta amsa gami da waiwayowa tana daura dankwalinta ba
tare da ta dubi qwayar idonsa ba
"Sumayya,naga kamar bakya farinciki da ni ko?,nasan fushi kike da ni haushina kike
ji,nasan dole kiji haushi bake bama koma wacece,don Allah don annabi kiyi haquri
sumayya,wallahi ba laifina bane,bansan dalilin da ya sanya idan karima ta bani
umarni ba nake kasa bijire mata,bansan me ya sanya ba nake tsananin tsoronta,duk da
cewa a yanzu cikin kashi dari inajin babu kashi hamsin yana raguwa sosai,kiyimin
haquri sumayya ina saka ran in sha Allahu komai ya kusa dai daita,ina miki godiya
kan namijin qoqarin da kike kan gyaruwar gida na,ina sane kuma ina lura da
komai,wasu kuma karima ta sanarmin sa niyyar na na taka miki birki,wallahi sumayya
ban taba ganin mutumin dake taka karima itama kuma take shakka shakkarsa ba
saike,kiyi haquri kici gaba da yin haquei komai mai wucewa ne in sha Allah" yanayin
yadda yake maganar kawai ya isa ya sanar mata bilhaqqi da gaske yake,sai taji
tausayinsa ya kamata,mutum cikakke kamar lukman amma sharrin mace ya maidashi wani
iri
"Babu komai,kowanne bawa da irin tasa QADDARAR  a rayuwa,Allah ya mana magani ya
shige mana gaba,ka riqe addu'a kaima insha Allahu HASKE na nan zuwa....".

      Bai kai ga bata amsa ba suka soma jin bugun qofa mai tsananin qarfi
"ka bude lukman bude,ina fatan ba abinda nake zargi bane,wallahi idan har shine ka
kuka da kanka"idanuwansa ya runtse gabansa na faduwa,sumayya dake zaune a nutse
abinta ta soma nazartarsa da nazartar yadda ya tsorace,babu laifi da sauqi,tunda
idan da dane da tuni ya arta da gudu yaje ya bude din
" ka ambaci Allah cikin ranka hakan shi zai cire maka tsoron dake cikin ranka"
"Allahumkhfinihim bima shi'ita"ya fara ambata daya daga cikin addu'ar da yaji
hajiyansa na ambata tun bayan zuwan sumayya gidan aduk lokacin da taga karima.

      Sumayya ce ta tashi ta isa bakin qofar dakin ta murza key din ta bude,karima
ce tsaye bakin qofar rataye da jaka,shigowarta gidan kenan ta hangi motar lukman
fake,ta tambayi mai gadi ya sanar mata kusan awanshi biyu da kenan da dawowa,dama
tun tana gidan sunan taji hankalinta yayi gida,abun mamakin shine dukka yaranta na
tsaye bayanta harta da qaramarsu,abinda ya sake daurewa sumayya kai kenan,nufinta a
gabansu zata tijara babansu?,da yanayin da tazo mata taso itama ta tarbeta,amma
ganin yaran ya sanya sumayyan murmushi
"A'ah,maman nuratu,kece kuma da yaran baki daya haka?"harara ta balla mata sannan
tace
" munafukar Allah bake nake nema ba,babban magulmacin nake nema,matsamana mu
shige"murmushi ta kuma yi tana gyada kai
"Mai zai hana na barki ki shiga,ke da dakin mijinki,amma bai kamata ku dunguma baki
daya ba,saboda bakisan a yanayin da zaku ruskeshi ba" ta fadi maganar tata ta
qarshe qasa qasa yadda kariman ce kawai zata iya ji
"Bismillah" sumayyan tace sa ita bayan ta janye mata jiki,sai data ja tsaki sannan
ta wuce kamar zata bangajeta,yaran suka yunquro zasu shiga ta sha gabansu,ta dubi
nuwaira wadda ta tabbatar itace mai hankalin cikinsu
"Nuwaira,maza ku tafi dakinku ku sauya kaya,mamanku na fitowa,kama hannun basma ku
wuce ko?"
"To anty" ta fada tana kama amma da nuratu sukayi gaba,tsare sauran tayi da idanuwa
tilas duk rashin kunyarsu suka bi bayan nuwaira daidai sanda maganganun karima
cikin ihu suka soma tashi
"Na shiga uku na lalace,yanzu lukman sai da ka kwanta da matarnan,lallau namiji
d'an kunama ne,wayyo Allah yau naga ta kaina" ta fada tana dora hannu a ka tare da
qarewa gadon nasa kallo,tsaye sumayya tayi harde da hannayenta tana kallonta,wato
badon ta kora yaran ba nufinta gabansu zatayi wannan tambelan?,gaskiya ne dole wasu
matan su janyo a dinga kiran mata masu naqasun hankali,takawa tayi ta dafa
kafadarta wanda ya sanya karima waiwayowa tana dubanta
"Meye na tashi hankali haka?,tun ranar farko kenan?,bakisan somin tabi bane yanzu
aka soma?,ki godewa Allah ma da bakizo kin samu ana third round ba" ta fada tana
kewayeta tare da komawa bangaran gadon ta soma gyara bedsheet din tana murmushi.

       Ashar ta lailayo ta danqarawa sumayyan irin wadda bata taba jin irinta ba
"Wallahi kinyi qarya kin kwana da yunwa duk malantar ubanki baki isa ba,duk wanda
yaci tuwo da ni miya ya sha,wallahi sai kin gane kurenki,saikin gane shayi ba komai
bane face ruwa,sai na cusa miki baqinciki fiye da wanda kika cusa min" sai ta
waiwaya inda lukman ke zaune,tayi tsammanin ganin tashin hankalinsa qarara yadda
aka saba sai ta ganshi zaune ko gezau
"Kai kuma tashi mu wuce dakina" ta fada a tsawace
"Ba inda zanje" ya fada yana jin shakka shakka na tasowa can qasan ransa yana
qoqarin danneta,idanuwa ta zaro,jikinta ya soma bari,ba shakka alqadarinta gab yake
da karyewa,kasa magana ma tayi sai kallonsa da takeyi
"A'ah,ki wuce mana kije tunda dai shi din yace bashi zuwa" a fusace ta waiwayo ta
tunkuda sumayyan wadda bata zata ba,hakan yayi sanadin da tayi taga taga zata fadi
lukman din ya tareta,sai ta miqe daga jikinsa tana murmushi kamar ba ita aka yiwa
ba
"Babu komai,duk cikin haushi ne" qwallar baqinciki ce ta fara qoqarin zubo mata,da
hanzari ta juya ta fice a dakim saboda batason sumayya ta gani har ta gane ta soma
samun rauni,qofar sumayyan tabi ta kulle sannan ta dawi ga lukman wanda ta lura
hankalinsa ya soma tashi,sosai ta zauna gabansa tana karanta masa abubuwan da suka
dace har ya soma daidaita,sannan suka tashi suka sake komawa duba jikin hajiya
wadda mamaki ya sake kamata ganin sun sake dawowar duk da taji shigowar karima
gidan.

     Qarfe goma da rabi suna dawowa daga wajen hajiya suka ratso ta falon,islam
suka gani na matse hawaye ta tari gaban uban tana cewa
"Abba kaga kasa mamanmu ta hada kayanta ko ta tafi,kuma tace ba zata dawo ba" wani
matsanancin faduwar gaba ya ziyarce ya zaro ido yana dubanta
"Tun yaushe?"
"Dazu,naje dakinka baka nan" duk sai sumayya taji babu dadi,kada dai abinda ya faru
dazun ya sata bar musu gidan,sai ya kama hannun yarinyar yana fadin
"Ya isa,kada ki damu mamanku gobe zata dawo kinji,sumayya jeki da su suna dakinsu
ina zato" amsa masa tayi,saidai qememe yarinyar taqi yarda ta kama hannuwanta haka
suka tafi,koda ta shiga dakin suna zaune baki dayansu tsuru tsuru,duk sai taji
tausayinsu ta dinga jin babu dadi,da fari duka qin sakin jikinsu sukayi da ita sai
nuwaira kawai,amma ganin nuwairan ta saki jiki sai basma qaramar cikinsu itama ta
ware,daga baya nuratu ta sake itama,sai islam kawai da tayi kicin kicin taqi shiga
sabgarsu,ba ita ta barsu ba sai da taga sunyi bacci sannan ta musu addu'a ta bar
dakin.

Sumayya na wucewa wayarsa ta dauki ruri,lambar karima ce hakan ya sanyashi


dagawa cikin hanzari yana cewa
"Haba karima,haba karima,meye haka din da zaki bar yaranki ki kwashi kaya,yaji da
girmanki da komai"
"Saurara ba wannan na kiraka ka gaya min ba,kiranka nayi na gaya ma ka sanar da
wannan matar taka diyar malamai masu kwanan buzu cewa,ta bar murna karanta ya kama
kura,babu inda zani ina nan dawowa,kuma dawowata ba zata yi mata dadi ba wallahi
wallahi sai ta gwammace kida da karatu,don babu wata 'ya da zan bari ta shigarmin
rayuwa ba tare da na nuna mata kuskurenta ba,kuma kada ka soma wahal da kanka kace
zaka nemeni don ba samuna zaka yi ba,har sai randa na dawo da karan kaina,ina fata
ka gane"qit ta datse kiran sai yabi wayar da kallo yana kada kai aljihu ya maidata
yana amsa sallamar da sumayya tayi masa.

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

4⃣4⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

*innal laha la yazlimu misqala zarrah*

*_haqiqa Allah baya zalunci daidai da qwayar zarra(ko qasa ma da abinda yafi qwayar
zarra qanqanta)*_

_______________________________

     Gefansa ta zauna cikin rashin jin dadi,tana jin kamar ta raba yaran da mamansu
ne,ta dubi lukman
"Ya kamata zuwa gobe kaje ka dawo da mamarsu islam,kada a ja abun yayi nisa don
Allah,yaran na buqatar mamarsu" kai ya kada baison gaya mata wani abu da zai daga
mata hankali,a yanzun da karima ta dan tura ta bar gidan sai yake jin kamar an zare
masa wata qaya data tsaya masa a maqoshi
"To naji" kawai ya fada.

     Kwana biyu tana masa mitar yaje ya dawo da karima arana ta uku yace kada ta
sake masa maganar baiso,idan lokacin dawowa yayi zata dawo,ai ta saba ba yau farau
ba,hakan ya sanya ta tsuke bakinta,hankalinta ya dan kwanta ganin yaran basu tada
hankali sosai kan rashin dawowar mamansu ba.
       Cikin kwanakin da suka biyo bayan tafiyar karima baki daya gidan yayi
dadi,kada ma lukman hajiya da nuwaira suji labari,da fari sumayya ta fara fuskantar
matsala daga yaran saboda qarancin tarbiyya da suke da ita,amma sai ta jure tayi
amfani da hikima irin tata,a hankali ta fara janye qananan,nuratu basma da
syyada,islam ce kawai ta taqi biyuya,ta soma kwaso halin uwarta tsaf,hakan yasa ta
tattarata ta watsar gefe,zasu hadu suci abinci tare,suyi karatu,ta basu labarai na
annabawa da sahabbai,suna bala'in so ta basu tarihi,har rigima suke idan tace ta
gaji,sosai ta shiga jikin yaran suka soma shaquwa da ita,ta koya musu abubuwa da
dama wadanda ya kamata ace sun iya amma basu iya ba,kamar alwala,sallah,sallama
idan zasu shiga guri,addu'ar sanya kanya,addu'ar bacci da tashi daga bacci,addu'ar
shiga bandaki data fitowa,addu'ar fita daga gida da ta shigowa da yin bismillah da
hamdala kafin da bayan gama cin abinci,su kansu yaran dadi sukeji,nuwaira tafi kowa
murna takance
"Anty dama tuntuni kema 'yar gidan nan ce,ai da tuni nayi saukar qur'ani ko?"
Dariya takanyi tace
"To ai yanzun ba gashi na zo ba?,kuma zakiyi ne in sha Allah",tarbiyya take basu
sosai mai wuyar bari ko mantawa,tana musu ne bilhaqqi fisabilillahi,don har ga
Allah tana son yaran,ko ba komai babansu da kakarsu na gwada mata qauna.

      A hankali sai itama islam din ta fara biyuwa,ta shige cikinsu,idan kaga
sumayya da yaran zakayi zaton qannenta ne,dama gata gwanar son yara,abun ya yiwa
hajiya dadi,wani lokaci har takan tsinci kanta da addu'ar kada Allah yasa karima
dawo,don ita kanta yanzu anan bangaren take wuni sai dare zata kwashi jikokinta
suje su kwana tare da ita a can,a yanzu sumayya ta koya musu qaunarta da ganin
girmanta,ta bangaren lukman kansa yana mamakin yadda hankalinsa yake a kwance,sau
tari ma sai ya mance da wata karima,kwanciyar hankali da nutsuwa ya samu sosai irin
wadda bai taba samun irinta ba tunda ya fara aure,ba shakka sumayya ta dabance,zai
kuma yi fatan kasancewa da ita har qarshen rayuwarsa,hatta da mai gadi da mai aikin
gidan sunga sauyi,sun kuma ga banbanci,suma sun samu 'yanci.

       Kwanci tashi har aka kusa shafe wata biyu ba motsin karima,sam sun mance ma
basa maganarta,banda yaran da wani lokaci zasu dan tada zancanta shikenan an wuce
gun,ta maida qaunar dake tsakaninsu baki daya saboda haka nuwaira ta samu
matsayinta na babba a gidan,a yanzu takan iya tsawatarwa dukkaninsu sabanin daa da
bata isa ba,basma ma na iya dungurinta ta wuce,da tace musu abu babu kyau zasu
daina saboda ta gaya musu wanda keyin abinda babu kyau Allah zai sashi a wuta,ta
wassafa musu yadda wuta take dai dai da tunaninsu yadda zasu gane haka ma
aljanna,don haka da tace abu da kyau tofa zasu shiga yi saboda sun san aljanna sun
san wuta.

       Da kanta ta nemi lukman kan ya sanya yaran islamiyya,saboda duk wanu ilimi
da zai basu matuqar babu karatun addini aikin banza ne,ya yarje mata kan ta nema
musu ya amince,da kanta ta duba islamiyar dake qarshen layinsu,ta gamsu da yanayin
karatunsu saboda haka ta yankar musu foam,cikin kwanakin da basu wuce uku ba aka
gama musu komai har dinkin unifoarm suka fara zuwa,su kansu yaran murna suke da
fara zuwa makarantar,idan suka dawo tare suke bitar dukka karatuttukansu,wani dadi
hajiya da lukman din ke ji,sai yanzu suka gane tabbas ashe da rayuwa suke cikin
duhu sai da Allah ya kawo musu SUMAYYA HASKE.

    *KUNDIN QADDARARTA*

      Ya sake bude mata shafi ne daga lokacin da karima ta cika wata biyu da rabi
da barin gidan,sauyin data fara gani daga lukman din,kusan tun bayan tafiyar karima
sumayya ta dorashi kan ibada saboda gunewa faruwar wani abu,cikin sati gaba daya ta
fuskanci ya zama mai son jiki da wata muguwar kasala,da qyar yake iya sallolinsa na
farilla balle akai ga na nafila,idan qur'ani suka dauko zasuyi tilawa yadda suka
saba sai ya soma gyangyadi daga nan sai bacci,idan sallar asuba ce kullum sai ya
makara sai tayi da gaske,duk wani abu na ibada ya zama very lazy akansa,tun abun na
bata mamaki har ya soma bata tsoro,hakan ya sanya ta samu hajiya da maganan,sam
bata kowa komai ba tace sumayyan taci gaba da haquri da kuma qoqarin ci gaba da
dorashi a hanya har ya daina,kuma itama zata yi masa fada
     A hankali sai abun ya soma cin tura,hatta idan yana bacci bai da aiki sai
kiran sunan karima,idan ya tashi kuwa washegari haka zai yini babu wannan walwalar
sam.haka kawai yake jin rayuwarsa da zuciyarsa cikin takura da qunci,ji yake kamar
yana cikin wata kurkuru,burinsa kawai yaga karima cikin gidan,saidai duk da haka
bai taba furtawa sumayya ba.

      *_Bayan sati d'aya_*

         Bayan sallar isha'i ne dukkansu suna zaune a falom gidan banda hajiya dake
bangarenta saboda yau da wuri ta kwanta,sumayya da nuratu da nuwaira na zaune tana
koya musu aikin gida(assigment)da aka basu a makaranta,basma na saman kujera tana
bacci tun sanda suka gama cin abincin dare,sai islam dake kwashe kwanukan da suka
ci abinci da su tana shigarwa kitchen.

       Lukman ne ya fito falon a gaggauce wanda tunda ya dawo daga kasuwa yana
cikin daki bai fito ba sai yanzu,hannunsa riqe da dan mukulli,daya hannun nasa kuma
riqe da hularsa,kana ganinsa kamar wanda aka jefo ko aka tunkudo,daga kai sumayya
tayi tana dubansa sanda ya giftasu zai fice ganin bai cewa kowa komai ba
"Abban nuwaira" waiwayowa yayi yana dubanta tare da amsawa
"Ina zaka fita haka tara na dare?" Ta fada a marairaice
"Sorry airphort zani,yanzu zamu dawo" ya fadi yana ficewa da sauri jin wayarsa na
ringing,kanta ta maida suka ci gaba da assigment din da yaran,hakanan taji gabanta
na yawaita faduwa,hasbunallahu wa ni'imal wakil ta dinga maimaitawa,suna gamawa ta
tattara yaran duka suka tafi dakinsu,sai da kowa ya sanya kayam baccinsa ya karanta
addu'ar kwanciya bacci suka kwanta sannan ta rufo musu dakin ta koma nata
dakin,alwala tayu tayi shafa'i da wutirinta sannan ta zauna ta karanta suratul
mulk,har ta gama abinda take bata ji shigowarsa ba,saboda haka ta sanya hijabinta
ta nufi bangaren hajiya.

      A kashingide ta sameta riqe da carbi,ganin sumayyan ya sanyata zama tana


murmushi
"Yanzu kuwa nake zancanki a zuciyata" itama murmushin take tana cewa
"Hajiya baki bacci ba?"
"Kin ganni nan wlh banyi ba,gabana ne yake ta faduwa sai na tuna dazu banyi
waraddallahu ba,sai nake yinta yanzu (waraddallahul lazina kafaru bi gaizihim lam
yanaluu khairaa,wa khafallahul mu'umininal qital,wa kanallahu qawiyyan aziza,ana
karanta ta ne qafa dari bayan sallar asaba kariya daga dukkan kaidin wani maqiyi
dake nufarka da shi in sha Allah)"
"Ai gwara hajiya" ta fada tana tunanin faduwar gaban da itama take ji tayi dai dai
data hajiya kenan
"Ina lukman din kuma?"
"Ya dan fita ne hajiya yara kuma sun kwanta saboda makaranta goben"
"Sannunki kedai sumayya,Allah yayi albarka" "amin hajiya"ta fada tana murmushi
kanta a qasa,shiru ne ya biyo baya kafin su soma taba hira kadan kadan,ganin har
sha daya na dare tayi ya sanyata yiwa hajiyan sallama ta koma sashenta.

      Tana zaune har sha daya da rabi sannan taji muryar lukman,a hankali ta tashi
ta leqa,shine a gaba janye da akwati daya hannun jaka,sai KARIMA dake biye da shi a
baya,da sauri ta saki labulen ta koma da baya tana kiran sunayen Allah,sannu a
hankali nutsuwa ta saukar mata,sai ta daura alwala ta kwanta,don jikinta na bata
lukman ba zaya nemeta a yau ba.

      Ilai kuwa bata sake jin motsinsa ko na karima ba har bacci yayi awon gaba da
ita.
   ******    *******    *****

      Washegari yadda suka saba haka tayi bata fasa ba,ita ta tashi yaran baki daya
sukayi sallar asuba,sannan ta dafa ruwa mai zafi islam ta fara yi sannan nuwaira ta
dinga yiwa qananan tana tura su islam na shiryasu ita kuma tayi daga qarshe,sumayya
kuma na kitchen tana hada breakfast da wanda zasu tafi da shi makaranta,abinda
dukka a da basu saba yi ba amma a yanzu ya zame musu jiki.

       Sun shirya tsaf suna karyawa ya zagaya ta buga dakin karima don taga idan
sun tashi ta tura yaran su gaida mamansu kan su wuce,saidai har ta gama bugunta ko
tari bata ji anyi ba,abinda bata sani ba lukman na jin bugun,ya kuma san sumayyarsa
ce,kamar ya zura a guje ya bude saidai ina sam bai isa ba,saboda bai samu umarni
ba,tunda ta dawo a jiyan qasan zuciyarsa ke a cunkushe cike da baqinciki bacin rai
da tsananin tsoronta,amma a fili tsantsar farinciki ne da tsananin biyayya bayyane
a fuskar tasa,abinda zai baka mamaki tunda ta dawo bai taba kwatanta tambayarta
inda ta tafi da aurensa a kanta ba kuma ba tare da izininsa ba har na tsawon wata
biyu ba,a lokacin ma yana bandaki yana wanke mata tana son shiga wanka saidai ya
hada qura a tsawon wata biyu da bata nan tunda ba wani ke shiga ba gun nata na a
rufe ne.

       Dawowa tayi inda suke kowa ya kammala mai adaidaitan dake kaisu ma ya iso ta
dubesu
" mamanku fa ta dawo jiya da daddare"ta tsammaci zata ga tsantsar farinciki a
fuskokinsu,sai taga babu yabo ba fallasa,babu wani zumudi ko doki,nuwaira kuwa
tsoro da fargaba ne ma ya mamayeta,a haka ta rakasu suka fice sannan ta dawo ta
gyara falo zuwa kitchen ta barwa mai aikinsu wanke wanke idan ta iso tayi wanka ta
leqa bangaren hajiya,sai ta sameta tana bacci,saboda haka ta mata 'yan gyare
gyarenta ta fito ta barta ta dawo falo ta zauna tana jira sha daya da rabi tayi ta
karya,sai ta kunna t.v tana kallon arewa 24 don ta debe mata kewa,zuwa yanzu sum
shaqu sosai da yaran,idan basa tare duk sai taji babu dadi kasancewarta mai son
yara.

       Tana jiyo qarar bude qofar karima amma bata maida hankalinta kai ba har sai
da taji cikin taqama tana fadin
"Ina yara na" cikin ladabi kamar bawa da uban gidansa taji lukman na cewa
"Eh sun tafi makaranta ai sumayya ta turasu" cikin harzuqa tace
"Eh wato suma an shige musu za'a shanyesu a rabani da su kenan?" Sai ta saki wani
shu'umin murmushi tana kada kai
"Mu zuba mu gani,muje ka rakani naga hajiya nata salon ita kuma" ta fada tana yin
gaba,jiki na rawa yana tafe yana waiwayen sumayya yabi bayanta,kai ta jinjina bayan
fitarsu
"Innalillahi wa 'inna ilaihi raji'un" ta fada tana kada kai ganin hannun agogo
nason komawa baya game da lamarin lukman din.

Zuwanta gun hajiyan ta taddata fiye da yadda ma ta barta,don fada hajiyan ma


ta mata kan dalilin tafiyarta wani gu bayan tana da aure,sosai hajiyan keji qarfin
zuciyarta sam babu wani dar da taji balle taji tsoron karimar,sai lokacin ta yadda
lallai idan kayi sakaci da addu'a babu abinda ba zaya iya faruwa da bawa ba duk da
cewa akwai QADDARA amma babu abinda ke sauya qaddarar irin ADDU'A.

Ko da rana da yaran suka dawo sun gaidata,baki ta saki tana kallon yadda suka
sauya baki daya,tana kallon yadda suke girmama nuwaira da islam,lallai sumayya ta
sauya mata yara,ya akayi bata sanya an musu farraqu ba ita da au ta barsu suka
shaqu haka,tana gani suka sauya kayansu zuwa na islamiya bayan sunci abinci,suna
sanya hijabansu sumayya na tsakiyarsu tana hada musu litattafan islamiyar su
kariman ta banko qofar dakin tana huci,tsayawa tayi tana dubansu fuska a
tsuke,sumayya data kalleta saita maida kai taci gaba da abinda take
"Laaa,mama bakiyi sallama ba fa,kuma babu kyau shiga gu ba sallama" nuratu ta
fada,mamaki ya kama kariman sai ta waiwaya tana kallonta amma sai ta wayance da
cewa
"Ku cire kayan nan,babu wata makaranta da zaku sake zuwa daga dawowarku daga boko
ko hutawa bakuyi ba" islam ce ta maqe wuya tana cewa
"Mama ki barmu muje,idan mun dawo ma huta din,idan kana fashi fa ana wuceka a
karatun" ido ta kuma zarowa mamki na sake kasheta,lallai sumayya tayi amfani da
irin surkullensu ta rabata da yaranta,tsawa ta daka musu tana cewa
"Don ubanki da ni kike jayayya,ku cire kayanku nace babu inda zaku" sumayya ce ta
bar abinda take ta tako zuwa inda take tana cewa
"Haba maman nuratu,meye na zagi har haka?,ina cewa ke zaki fi kowa farincikin zuwan
yaranki makaranta,ba girmanki bane" sai ta waiwaya ga yaran da sukayi carko carko
suna kallon karimar
"Maza ku wuce ku tafi mamarku ta haqura" da sauri suka fice kuwa daya bayan
daya,sai da suka kammala ficewa tas sannan karima ta kalli sumayya
"Yaro man kaza,ke da su baki daya baku da bambanci a gurina,lokaci na baki shi nake
jira" tana gama fada ta fita
"Allah ya fiki,Allah ya isar min da ke akan dukkan wani nufinki,alkhairin ubangiji
nake nemawa rayuwata" ta fada tana gyara dakin yaran da suka bata tare da killace
kayan makarantarsu gu guda kafin su dawo su wanke

Baki daya sai aka koma 'yar gidan jiya kan halayen mukhtar,yayin da bangare
guda sauyawar yaranta da hajiya ke ciwa kariman tuwo a qwarya,saidai ta kammala
dukkan wani shirinta na maida hannun agogo baya ranar kawai take jira,wanda hakan
ya sanya ta sanyawa kowa ido,wannan kuma ya bada damar da shaquwa mai qarfi taci
gaba da gudana tsakanin sumayya yaran da hajiyar.

****** ******* ******

Qarfe daya na rana ne wanda saika dauka qarfe takwas ne na safe saboda yanayin
sanyin da ake zabgawa a garin,tuni ta kammala abincin rana ita da mai aikin gidan
qwaya daya saboda biyu na rana yaran zasu dawo ta baiwa kowa haqqinsa,kasancewar
tunda karima ta dawo gidan bata ko dubi kitchen ba.

Tayi sallar azahar dinta sai ta qudundune kan gado kafin yaran su dawo,bude
qofar dakin nata da akayi shi ya sanyata daga kai ta kalli qofar,karima ce cikin
kwalliya da daurin ture kaga tsiya,jambaki kamar zai digo daga bakinta,itace a gaba
lukman na biye da ita janye da trolly,sallama kariman tayi wadda ta bawa sumayya
mamaki,qarasowa tayi bakin gadon tana duban sumayya
"Mijinki ko mijina?....oho koma meye,shi na rako ya miki sallama zaiyi tafiya,wadda
itace zata kasance sallama ta qarshe tsakaninku" ta qarashe tana dariya dariya,ta
waiwaya ta dubi lukman dake tsaye,fuskarnan tamkar zai sanya kuka ,amma tana
dubansa sai ya saki murmushi
"Bari na baku guri ko don kuyi sallama sosai" sai ta juya ta fice.

Sakin akwatin yayi ya qaraso inda take ya zauna gefanta,sai ta tashi daga
kwanciyar ta zauna sosai tana kallon fuskarsa gabanta na faduwa
"Kiyi haquri sumayya,kiyi haquri don Allah,ba laifina bane sumayya,haka nan nake
jin bazan iya ci gaba da ke ba,haka kawai nake jin idan naci gaba da zama da ke
akwai cutarwa,sumayya ki yafemin akwai QADDARAR dake bibiyar rayuwata,ina sonki har
cikin zuciyata amma bazan iya zama da ke ba...."
"Ya isa lukman,ka fadi abinda kake son fada,ka fadi a wuce gurin" ta fada cikin
rawar murya,bai kai ga cewa komai ba karima ta sake shigowa dakin,cikin daga murya
tace
"Wai me kakeyi ne hakan har yanzu,kasan dai jirgi baya jira saidai a jirashi ko?"
Ta fada tana tsareshi da ido,cikin sanyi jiki ya sanya hannunsa a aljuhunsa ya
fiddo takarda a ninke ya miqa mata,hannu kawai ta sanya ta karba,koda baiyi mata
bayani ba tasan takardar meye,saboda haka bata da buqatar budeta,kamar kazar da
qwai ya fashewa a ciki haka ya miqe yaja akwatinsa yana waiwayenta har ya fice
karima ta rufa masa baya.

Cikin dogon tunanin da batasan tsawon lokacin data dauka cikinsa ba taji
islam na girgiza kafadarta
"Momy,tun dazu muke sallama shiru baki amsa mana ba" sai ta daga kai ta
kallesu,dukkansu suna tsaye gabanta suna kallonta cirko cirko,alamun damuwa duka
sun bayyana kan fuskokinsu,tausayinsu sai ya lullubeta duk da a yanzu tafi jin
tausayin kanta,don nasu mai sauqi ne,qwalla ta cika mata idanu amma sai tayi ta
maza ta hadiyeta,ta qaqalo murmushi tana cewa
"Wa'alaikumus salam warahmatullahi wabarkatuhu,banjin sallamar taku bane,muje maza
a shirya yau kun dawo a makare ko?" Ta fadi tana saukowa daga kan gadon,biyo
bayanta sukayi kowa na bata labarin yau na makaranta,tana shiryasu tana biye
musu,yayin da qarqashin zuciyarta ke a cunkushe,tausayinsu naci gaba da lullubeta
musamman nuwaira,duk da tana da yaqinin insha Allah ba zata tozarta kamar baya ba
tunda a yanzu an samu kan 'yan uwanta da kakarta,sosai tayi jarumtar danne
damuwarta,saidai duk da haka nuwaira sai da taso dagota,don ta saci kallonta sai
daya taga tana dauke qwalla,duk sai yarinyar ta tsargu taqi sakin jiki,duk inda
sumayyan tayi tana biye da ita da idanu,har suka gama dabdalarsu bataji motsi ko
giftawar karima ba,da haka ta shiryasu suka fice,ko sanda zasu fita din sai data
juyo ta sake kallonta ita kuma ta rakata da murmushi.

Sai data fara hada kayanta sannan taji kuka ya qwace mata,bakin gado ta koma
tayi kuka san ranta sannan ta hada duk abinda zata buqata cikin akwati ta zira
hijabinta ta janyo akwatin nata bayan ta saka takalmanta.

Sallama tayi bangaren hajiyan ta amsa mata tana murmushi tana tsokanarta
"Yau sanyi ya boyeki ko sumayya" ganin yanayin fuskar sumayyan ya katse fara'ar
hajiyan,gefan hajiyan ta zauna kanta na a qasa
"A'ah lafiya kuwa sumayya?" Cikin rawar murya tace
"Zuwa nayi muyi sallama hajiya zan tafi" cikin tashin hankali tace
"Sallama,tafiya zuwa ina?" Kasa bata amsa tayi saita miqa mata takardar dake nade a
hannunta,da sauri hajiyan ta karba tana dubawa,salati ta saki."yaushe hakan ya
faru?,me yasa ban gaya min ba dazu yamin sallama zai je ghana,sumayya...."sai ta
rasa abinda zata fada
"Haka lukman zaimin?,to wallahi nima bani zama a gidansa,yaci gaba da zama da
karima ita kadai" Cewar hajiyan,sai kuma ta saki kuka,da sauri sumayya ta goge nata
hawayen ta kama hannun hajiyan tana girgiza kai
"A'ah hajiya don Allah ki daina masa kuka,zaki sake jefashi cikin wani bala'in
bayan bai fita daga wanda yake ciki ba,hajiya,lukman danki ne ke kika haife
abinki,ke kika san zafinsa,idan bakiyi yaqi a kansa kin saita rayuwarsa ba duk
duniya wazai miki wannan aikin,hajiya ke zaki zauna kici gaba da aikin da na
fara"wajen mintuna ashirin ta kashe tana yiwa hajiyam bayani tare da jan hankalinta
sannan ta fara samun nutsuwa
" naji sumayya,nan zaki zauna gurina,tilas na nemo lukman duk inda ya tafi,dole ya
dawo da ke,akwai sauran igiya daya tsakaninku"kai ta kada tace
"A'ah hajiya,kada ki tilas ta shi wanda hakan zai iya haifar da wani abun
daban,babu abin buqata a yanzu fiye da dawowarsa kan hanya,Allah ne mafi sani kan
dalilin faruwar hakan,na yadda cewa wannan ma na cikin QADDARAR rayuwa ta,koda
yaushe Allah nake miqawa zabi kan rayuwata ya zaba min abinda yake gani shine dai
dai ba abinda ni nake ganin shine dai dai ba,na gode masa ma da ya bani ikon
fiddaku ke da su islam daga halin da na riskeku,abun da nake so hajiya kimin
alqawari shine,ba zaki sake zubda masa qwalla ba,ba zaki saki addu'o'inki ba,ba
zaki bar su islam su koma irin rayuwarsu ta baya ba,sannan ba zaki gaji da nemawa
lukman kubuta da tsiraba,wannan yaqin naki ne,duk na dora miki hajiya zan kuma
tayaki da addu'a"
"Insha Allahu sumayya in sha Allahu,Allah ubangiji ya albarkaci rayuwarki,kuma in
sha Allahu ina mai tabbatar miki da yardar Allah zaki sake dawowa gidan nan,duk
inda lukman yake zan nemeshi zan nemeshi ya dawo da ke" ta fada zuciyarta a
raunane,cikin irin wannan yanayi mai ban tausayi sukayi sallama.

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

4⃣5⃣
_____________________________
*wa asa an takrahu shai'an wa huwa khairul lakum,wa'asa an tuhibbu shai'an wa huwa
sharrul lakum,wallahu ya'alamu wa antum la ta'alamun*

*_SAU DA YAWA ZAKU QI ABU AMMA ALKHAIRI NE A GURINKU,SAU DA YAWA ZAKU SO ABU AMMA
SHARRI NE A GURINKU,HAQIQA ALLAH SHINE YA SANI AMMA KU BAKU SANI BA_*

______________________________

*ZAINAB*

Kamar yadda suka tsara ita da zinatu hakan ce ta kasance,qarfe goma na


safiyar washe gari a gidan malam ta yi musu,duk da dan uban ciwon da jikinta ke
mata amma sam bata kula ba,burinta kawai ta ganta gaban malam din,da yake safiya ce
bata taras da mutane da yawa ba a gidan mutum daya ne ya fito suka shiga.

Kamar ko yaushe mutumin da suke kira da malam ya kuma shiga rigar malamai yayi
bake bake yana zaune kan buzu,yaci babbar riga da rawani gefe litattafan addini
jere wadanda ko zaka kasheshi layi guda bazai iya karantawa ba balle har ya iya
gane me ya karanta din.
"Zainabu abu,ina fata buqata ta biya don na ina nan ina ta kewarki,ban manta
daren mu ba na......"
"Dakata dalla malam,ni zaka yaudara?,kayimin aikin banza lalataccen aiki da tunda
na fara yawon bin malamai ba'a taba min matsiyacin aiki irinsa ba,to wallahi da
sake bazai yiwu ba"turbune fuska yayi ainun yana dubanta
" ke kisan fa agaban wa kike,bana son tsiya"sake harzuqa tayi tana cewa
"Eh dole mana ka fadi haka,bayan ka gama amfana da albakatun jikina ko?"
"Ke sha shashasha,ai ba kanki farau ba,kuma ke kika kawo kanki,dama tunda kika rabu
da Allah babu irin qazantar da ba zaki fada ba,kinga ki fadamin abinda ke tafe dake
kada ki batamin lokaci customers na tafe a hanya kada ki bata min aiki" cikin
masifa ta sake takowa gabansa tana dubansa
"Amma malam bansan kai ba qaramin dan akuya bane sai yau,to wallahi baka isa kaci
bulus ba,ni babu wanda ya isa ya takani wallahi na qyaleshi ban dau fansa ba ko
uban waye kuwa" dariya ya barke da ita ya dinga qyaqyatawa har suka saki baki suna
kallonsa
"Saidai cin bulus na gaba,bulus kuma ai na gama cinta tunda na hadaki da CUTA MAI
KARYA GARKUWAR JIKI?" wata saukar guduma sukaji bisa kawunansu,ba zainab kadai ba
hatta da zinatu
"Cuta mai karya garkuwar jiki!" Zainab ta tambayeshi cikin qaraji,dariyarsa ya ci
gaba da yi yana kada kai
"Qwarai kuwa,wannan tsaraba ce da muke baiwa dukkan macen data bijirewa Allah,ta
zabi biyan buqatar duniyarta akan ta lahira" sulalewa kawai tayi a gun,zinatu ta
fasa kuka tayi kanta,ganin suna neman tara masa jama'a ya sanyashi samo mai
adaidata sahu ya dorasu ya saita musu hanyar asibiti.

*MUKHTAR*

Tun ranar da sirrin ya yaye masa baki daya ya sauya,tamkar ba mukhtar


ba,hatta da abdallah sai da ya samu sauyi da naqasu wajen kulawar da yake samu,ya
kusa wata bai zuwa ko ina yana gida,sai abdallah ya matsa da rigima yake fita waje
ya dan tattaka da shi a qafa ya dawo,babu abinda ke bijiro masa sai tausayin
sumayya da tunanin da wanne ido zai kalleta?,ko wane minti daya tana dawo masa ne
da irin abubuwan da ya aikatawa sumayyan,tun daga auren zainab zuwa ranar
rabuwarsu,wasu abubuwan gani yake tamkar a mafarki suka faru ba a zahiri ba,kuka
kam ya yishi sau babu adadi,baisan iyaka ba,yana so yaje ya warwarewa su malam
komai amma yana jin wata 'yar banzan kunya da nauyinsu wadda a da bai jita ba,kusan
ya mance kwanansa nawa rabonshi da gidan,saidai ya zame masa dole yaje gidan don
sauke nauyin dake kansa.

**** ****** *****

Zaune take gefan gado sanye da hijabinta tana ci gaba da sharce


hawaye,tsahon kwana biyu da faruwar lamarin amma ta kasa tsaida hawaye a idanuwanta
wanda ita kanta ta rasa dalilin haka,kukan nata ya dadu ne tun bayan gama wayarsu
da anty dije wadda kejin tamkar a kanta hakan ya faru.

Halima ce ta shigo dakin


"Yaya sumayya kije inji malam" jikinta ya qara sanyi a zatonta magana a kanta ne
bata qare ba,duk da cewa babu abinda ya fada face yi mata addu'a bayan ya gama
saurarar rayuwarta a gidan mukhtar,fada daya yayi mata na rashin neman taimako daga
wanda tasan ya fita gogewa da sani kan irin wadan nan lamuran,al'amura ne da kake
buqatar addu'a koda daga wajen iyayenka ne daga bakunansu,tunda addu'ar tasu
karbabbiya ce a wajen ubangiji.

Cikin sassanyar murya tayi sallama a falon nasa,da abdallah idanunta suka
soma tozali,ko kadan batayi tsammanin ganinsa a lokacin ba shi ko mahaifinsa,ai da
gudu ya baro jikin mukhtar din ya iso inda take tsaye ya riqeta yana kiran amma
na,jikinta da zuciyarta baki daya a raunane suke,hakan ya sanyata zubewa shima ya
fado jikinta,sai ta rungumeshi a jikinta tayi qas da kanta hawaye ya balle mata a
boye,cikin dabara take shareshi.

"Sumayya" taji malam ya kirata


"Na'am" ta amsa murya a sarqe
"Ga mukhtar nan yazo neman gafararki kan abunda ya faru tsakaninki da shi a
baya,wanda mu nasan ya riga da ya wuce a gunmu saidai tsakaninku dai" ya fada yana
miqe ya fice ya turo halima ta zauna da su tunda ya sani a lokacin bai halatta ya
barsu su kebe ba,har a sannan tana matsayin matar lukman har zuwa sanda ta kammala
idda.

Dauke idanunsa yayi da sauri daga kanta saboda tunawa da yayi matar wani
ce,rabonsa da ya sanyata a idanunsa ya mance,tun kafin aurenta.
"Sumayya,nazo gareki a matsayina na mutum mai tarin laifi,a matsayina na mutumin da
yafi kowa laifi duk duniya a gurinki,nasan cewa kalmomina basu isa su haqurqurtar
da ke kan abinda na aikata a gareki ba cikin jahilci,gaggawa da yanke hukunci cikin
rashin bincike,tun ranar da na san gaskiyar lamarin naso neman gafararki amma hakan
bazai yiwu ba saboda kina gidan wani,yanzun ma mama da malam mazo sanarwa ya gayan
kina kusa,don girman Allah sumayya na roqeki ki yafemin,koda kuwa wannan ne alfarma
na qarshe da zakiyimin,babu shakka zainab ta zalunce ni ta zalunceki ta kuma
zalunci danmu,kimin afuwa don Allah" tsam ta miqe ba tare da tace komai ba ta dauki
abdallah ta fice daga falon,sai yayi qasa da kansa zuciyarsa na masa zafi,yayin da
nauyi ya kama halima,sai ta miqe tabi bayan sumayya itama.

Ranar bacci barawo ne kawai ya dauketa,zafi goma da ashirin ke bugun


zuciyarta,ta duba ta laluba kaf rayuwar aurenta babu wanda ya ruguza farincikinta
sai mata 'yan uwanta,babu abinda ta aikata musu don kawai sun hada miji?,me yasa
kishiya ta zame mata qalubale cikin rayuwarta baki daya?.
        Sannu kwanaki suka dinga hada satittika,satittika suka hadu suka bada
watanni,ta miqawa Allah dukkan lamarinta baki daya,ta yadda babu bawan da ya isa ya
gujewa qaddararsa,watanni uku cif cif iddarta ta cika,ta godewa Allah bisa baiwa da
ni'inar lafiya da ya bata,ta watsar da dukkan wani abu ta rungumi rayuwarta,riqon
Abdallah ya dawo wajenta,hakanan taci gaba da makarantarta na koyon sana'o'i,wanda
zuwa lokacin ta qware sosai wajen iya humra kwalakca da turaren daki na kaya da na
tsuguno,ya abbakar shi ya bata jari ta soma gwadawa,Allah kuwa ya sanyawa abun
albarka don ciniki take sosai,don kana shigowa gidansu zakasan ana saida humra
balle kuma jikinta,nutsuwa sosai ta sake zuwa mata,wani girma da hankali na
musamman ya soma gameta,mukhtar kuwa har yau bata yarda ta sake ganinsa ba ma bare
ya dagula mata lissafi.

    ****   *****   ******   *****

      Qarfe bakwai na bayan sallar magariba ta gangaro cikin layinsu abdallah na


sabe a kafadarta,tun daga makaranta ta wuce gidan anty maryam qanwar mama sai gab
da magariba ta fito.

       Tana gab da gidan nasu ta kula da motar wadda ko daga bacci ta tashi zata
iya ganeta,motar mukhtar ce,sai ta dauke kai tana qoqarin wucewa cikin gidan,saidai
abdallah dake kafadarta wanda ya soma zillo ganin babansa yaqi bada hadin kai,tilas
taja tunga ta saukeshi da niyyar ta wuce ta barshi a gun,saidai tana dagowa daga
durquson da tayi ta tsinci mukhtar din tsaye a gabanta
"Zan wuce malam" ta fada ranta a hade
"Kiyi haquri malama" ya fada da irin salon muryarta,kicin kicin tayi ganin yadda
yake son maida lamarin wasa
"Ka bani hanya da Allah kana batamin lokaci bana son shirme" tsit yayi yana
kallonta,ita kanta sai taji kalma ta mata nauyi,don haka ta basar ta hanyar gyara
hannun hijabinta
"Sumayya" ya kirata da wani irin salo wanda ada can yake kiranta da shi,kira ke da
idan yayi mata take jinsa har cikin jikinta
"Ki yafemim sumayya,a kullum tsahon wata biyar kenan cikin neman yafiyarki
nake,idan na kira baki dauka,idan nayi miki saqo baki reply,kiyi haquri ki
yafemin,na yadda nayi babban kuskure a rayuwata amma na girbe abinda na shuka ai,na
rasaki na tsahon wasu shekaru,ban taba tunani a baya akwai abin zai rabani da ke ba
idan ba mutuwa ba,tunda na rabu da ke sumayya ban taba samun nutsuwa ta minti guda
ba,Allah ya hukuntani tunda har kin shiga gidan wani sumayya,ki zama mai afuwa da
yafiya kamar yadda na sanki nasam halinki a baya,mukhtar dinki ne sumayya bazan
daina neman yafiyarki ba matuqar baki yafemim ba har sai ranar da numfashina ya bar
gangar jikina...."da sauri ta katseshi don yana neman karya mata zuciya
" don Allah ka bani hanya,na gaji da jin kalaman bakinka"murmushi ya saka yana kada
kai
"Shikenam sumayya,idan kinso ma ba zaki sake gani na ba tunda haka kika buqata,amma
bazan daina neman afuwarki ba,na barki lafiya"ya fada yana juyawa ya danqawa
Abdallah wani dan madaidaicin kwali ya wuce motarsa,sai ta samu kanta da tsayawa
cak a gun ta kasa tafiya har ya bar layin,tausayinsa nason rinjayar zuciyarta,tuna
wahalhalun da tasha shi ya bijiro mata ya taurarar da zuciyarta,kama hannun
abdallah tayi suka shige ciki.

   *****   ******    ******

      Tunda ya bar gidan yaso tilastawa kansa cireta daga zuciyarsa saidai ya gaza
hakan,wata sabuwar soyayya da qaunarta ke yawo ko ina cikin jinin jikinsa fiye da
irin qaunarta da yake ji a da,sai ya soma komawa wani iri,ko da yaushe cikin
tunani,ga wani matsanancin ciwon kai dake matsanta masa wanda ke kwantar da
shi,yana mamakin yadda ya kasa haqura da ita,ji yake tamkar idan ya haqura da ita
din zai rasa numfashinsa,hakan ya sanya ya shirya da kansa wani dare bayan ya yiwa
abbakar waya ya sanar masa ya gayawa malam zaizo zasu tattauna,idan da hali
abubakar din ma ya zauna.

        Qarfe takwas yana sitring room din malam din dake qofar gidansu,hakan ne ya
sanya babu wanda yasan da zuwansa a cikin gidan

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*
*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

4⃣6⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

*wa yuhazzirikumul lahu nafsah*

*_Allah yana tsoratar da ku game da kansa_*

_______________________________

       Duk yadda ta kai ga tunanin duniyar gidanta zata sameta yadda takeso ba haka
abun yazo mata ba,komai na neman lalace mata bayan ta tabbatar da cewa tayi nasarar
tuge sumayya daga gidan,gaba daya yaranta yadda ta sansu a yanzu ba haka suke
ba,baki dayansu kansu a hade yake,qarami na girmama babba,haka babba na tausayin
qarami,nuwaira na cikinsu tamkar cikinsu daya da ita,ita ke jagorancin ragamar
sauran a matsayinta na babba,duk yadda taso ga sake raba kansu abun yaci tura,duka
ne a yanzu basa tsoron dukanta,da tayi abu zasu ce mama babu kyau fa abu kaza,ko
daya daga cikin tarbiyyar da sumayya ta dorasu babu wadda suka watsar,a yanzu haka
sunfi qaunar zama wajen hajiya akan wurinta,saboda babu abinda ke shiga tsakaninsu
sai duka hantara da tsawa saboda basa mata yadda takeso,babu mai bin umarninta
cikinsu matuqar ba kan dai dai bane hatta da qaramarsu basma,bata fuskanci sumayya
ta gama da rayuwar gidanta ba sai da yaran suka dinga gudunta,idan ranar makaranta
ne ba zata sanyasu a idanunta ba sai dare,don idan suka dawo daga boko don kada ta
hanasu zuwa uslamiyya gun hajiya suke togewa su shirya su wuce abinsu,ranakun
qarshen mako kuwa gun hajiyar suke wuni,idan ka gansu a bangarensu to wani abu suka
zo yi suyi su sake komawa.

      Lukman kuwa mallakar data yi masa sai ra soma damunta,ba irinta take buqata
daga gunsa ba,ya zama kamar irin dolayen nan,komai tace sai yace to,ya zama kamar
qaramin yaro,hatta wanka da cin abinci sai tace yayi,sai ya zame mata qarin nauyi
cikim rayuwarta,bashi da wani tunani ko kadan,ko wuta tace ya sanya hannunsa ba
musu zai tsumbula,abinda ta fuskanta har yau sumayya na maqale cikin zuciyarsa,sau
tari zai zauna ya yita kallon qofar dakinta babu qaqqautawa har sai tazo ta
koreshi,hakanan ko sunan sumayya yaji an kira koda a hanya ne sai yayi firgigit
kamar wanda aka tasa daga bacci,idan kuwa su nuwaira na zaune suna hirarta sai ya
zauna daga gefansu yana saurararsu yana tambayarsu kan wasu abubuwa ko sanya musu
baki,a kan hirarta da suke zama suyi sai da karima ta tara su ta musu dukan
tsiya,ta kulle nuwaira kuma a daki sai da hajiya ta shigo taci mata mutunci ta bude
ta tace kada kuma ta sake dukar mata jikoki itace abar a daka ai basu ba,nan ta
saki baki ta dinga caccabawa hajiyan magana,bata bu ta kanta ba ta kada kan
jikokinta suka fice.

Wannan shine halin da karima ke ciki.

*******   *******    ********

      Kansa na sunkuye a qasa yana mai jin nauyi da kunyar abinda zai fito daga
bakinsa,saidau tilas ya furta din saboda yana mai cike da fata da burin inganta
rayuwa ne ta mutum uku,shi abdallahnsa da sumayyarsa,kasa magana yayi har sai da
malam ya maimaita fadin ina jinka,yayin da ya abubakar ya gyara zamansa,kawu
sulaiman wanda yake qani ga malam ma yazo kawowa malam ziyara suyi hira kamar yadda
suka saba kasancewar su biyu suka rage raye a duniya ya tadda zuwan mukhtar din
"Malam,ina mai jin kunyar neman wannan alfarma daga gunku,nasan cewa na muku laifin
da dukkan iyaye zasu ji babu dadi a cikin ransu,saidai malam wannan alfarma da zan
nema ina fatan zata shafe dukkan wani abu mara kyau da ya faru a baya,sannan zata
inganta rayuwar mu baki daya" dan shiru yayi sannan daga bisani ya dora
"Malam,don Allah don annabi ina son ka bani auren sumayya karo na biyu" shiru dakin
ya dauka kowa da abinda yake saqawa cikin zuciyarsa,tsawon wani lokaci babu wanda
yayi magana,jinjina kai malam yake kafin ya motsa
"Mukhtar,babu shakka kai mutum ne na qwarai,wanda shine babban abinda yaja
hankalina karon farko na baka auren sumayya,na sani na shaida cewa dukkan wani abu
da ya faru tsakaninku sharri ne da makirci wanda babu wanda bazai iya fadawa
cikinsa ba,abu na biyu kuma sakaci da addu'a,na ukunsu rashin game hankali guri
guda tare da yin dogon nazari da bincike kan lamura,ammm....mukhtar"
Sai ya dago yana mai amsawa zuciyarsa na gudu daya bayan daya,duk da cewa yana da
cikakken fata na cewa zai cimma nasara
"A qa'ida ta addinin musulunci bazawara ita ke da ikon zabawa kanta miji,saidai
idan har anga tana neman jefa kanta wajen wanda bai cancanta ba bayan ga wanda ya
cancanta a gefe,kada ka manta sumayya bazawara ce ita ke sa ikon zabawa kanta miji
duk da nasan cewa ko a yanzu nayi mata zaben miji ba zata musanta min ba,to amma
dai zan bata damarta,mukhtar,bazan hanaka neman sumayya ba,amma kadai zan amince ne
idan ta yarda da aurenka".

       Shiru yayi kafin daga bisani yace


" malam,na gode da wannan alfarmar da ka yimin,amma ina mai neman alfarma ta gaba"
"Uhmmm,ina jinka"
"Malam,don girman Allah ina neman alfarma a gunka da ka karbi sadakin sumayya daga
gurina,nayi maka alqawari tsakanina da ubangiji na matuqar sumayya taqi aminta da
ni zan karbi sadakina zan haqura,na maka wannan alqawarin" shiru ne ya sake biyowa
baya,kowa da abinda yake nazarta qasan ransa,malam na gudun shiga haqqin
sumayya,yayin da ya abbakar ke tunanin tabbas dama ce wannan,don shi kadai yake iya
fahimtar yaren sumayya,saidai ya hango alamun rashin amincewa qarara a fuskar
malam,yayin da mukhtar ke duqe yana mai cike da fatan samun nasara,ya abbakar ne
yayi saurin yankan hanzarin malam din
"Malam,ina ga ka bawa mukhtar wannan damar,domin ni na shaida cewa sumayya na son
mukhtar,hakanan na tabbata ba za'ayi nadamar karbar sadakin nan ba in sha Allahu
gyara ne zai tabbata a tsakaninsu" kusan abinda kawu sulaiman ke ayyanawa cikin
ransa kenan,don ko shi yana tausayin sumayya da abdallah,saboda haka ya ari bakin
malam ya ci masa albasa
"Kaje muntari,an baka wannan damar,kaje ka kawo sadakin amma tare da manyanka zaka
dawo". Jinsa yayi kamar ba a duniya yake ba,godiya ma rasa wacce iriya zaiyi,ya
tabbata yana jin karsashin samun nasara da shawo kan sumayyansa.

            **************

       Kasancewar juma'a ce ta zamo washegarin ranar,qarfe hudu bayan sallar


la'asar mukhtar ya iso gidan shida kawunsa wato mahaifin abdur rahman da kuma
baffansa wanda yake wa ne ga innarsu da qanin innar yasu su hudu kenan,kawu
sulaiman da babban dansa sai yaya abubakar su suka sake karbar sadakin sumayya karo
na biyu,wanda ita wadda ma ake batun sam batasan ana yi ba,don a lokacin ta tafi
kitso,ta dawo dai ta tadda mutane cikin sitting room din malam,saidai batasan ko su
waye ba tunda bata shiga ciki ba cikin gida ta zarce,bayan malam din ya sallami
kowa ya shigo cikin gida ya tadda mama ya buqaci ganinta sannan ya sanar mata tare
sa gaya mata baya son ta sanrwa kowa har sai sun hada kansu da kansu,to ita din
macace,kuna tasan burin kowacce mace ta zauna da uban 'ya'yanga,hakanan kowa ya san
nagarta da kyawun halayen mukhtar tun kafin wannan qaddarar ta afkowa rayuwarsu.

              *ZAINAB*
       Tunda ta farka daga suman da tayi take qaraji tana kuka,sai data tada
hankalim duk marasa lafiyan dake dakin,babu yadda zinatu batayi kan ta lallabata ba
amma taqi yin shiru,duk yadda take jin dadin halin da taga zainab din a ciki amma
ji take kamar ta zura da gudu,dadi take ji sosai da wannan labarin na samuwar cutar
qanjamau jikin zainab din,ganin yadda zainab din ke firgita musu marasa lafiya  ya
sanya suka canza mata daki.

      Kusan kwana tayi a haka kafin daga baya ta fara sassauta qugin da takeyi
saboda ta fara jin sassaucin radadin da take ji a zuciyarta.

      Tana jingine a bango har zinatu ta gama bata shayin,saidai har a lokacin bata
ce komai ba sai faman jinjina kai da take,kanta ta daga ta kalli zinatu da jajayen
idanuwanta kamar na maza murya a kausashe tace
" kin gayawa wani a gidan mu abinda ke faruwa ne"kai ta kada tana ajjiye kofin
hannunta
"A'ah,babu wanda na gayawa"
"To bana buqatar kowa ya sani"
"To" kawai zinatun ta fada tana dariyar mugunta cikin zuciyarta.
"Cutar qanjamau zinatu" tayi furucin tana kallon zinatu tamkar mai neman tabbaci
kan wata magana,cikin fuskar tausayin qarya tace
"Don Allah ki bar daga hankalinki zainab,mutum nawa ne masu irin cuwin ke rayuwarsu
hankali kwance"
"Dalla can malama daqiqiya kawai,bani da dama kenan ta komawa mukhtar ko kin
manta?" Shiru zinatu tayi zagin da tayi mata yana mata ciwo amma ba zata iya
maidawa ba
"Zinatu,hakan fa yana nufin mutuwata gab take da ni kenan"
Kallonta kawai zinatun tayi ba tare da tace komai ba,kamar zararriya sai ta miqe
tsaye tana girgiza kai
"Inaaa,wallahi bazai yiwu ba,wallahil azim bazan mutu ni kadai ba,kai ka zama silar
kasancewata cikin wannan hali,kaine sila,kai ka jawo min" ta fada tana zarya cikin
dakin,mayafinta ta figa ta yafa tana fadin
"Ki nemo kudinsu ki biyasu ki sameni a gida zamu warware" tayi maganar tana ficewa
daga asibitin.

*tofa,muje zuwa masu karatu*

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

4⃣7⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

_____________________________
*wa may ya'amal misqala zarratin khairan yarah,wa may ya'amal misqala zarratin
sharran yarah*

*_duk wanda ya aikata dai dai qwayar zarra na alkahiri zai gani,duk wanda kuma ya
aikata dai dai da qwayar zarra na sharri zai gani_*
_______________________________

*Gaisuwa da fatan alkhairi gareku*🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽

*sis farida muhammad abbas*

*sis rabi'ah haroun*

*sis dada*

*Bilkisu mai gadon zinare*

*mrs alqali*

*maman sayyid*

     Bayan sallar isha'i ne,idarwarta kenan abdallah ya soma rigima tilas ta


kwantar da shi gefanta ta soma lallabashi,don kwanakin abinda ya koya kenan rigima
idan zaiyi bacci,ya Abbakar ne dake shirin wucewa gidansa ya leqo
"Kinyi baqo sumayya"
"Baqo?,baqo kuma ya abbakar?" Ta tambaya cikin mamaki da faduwar gaba,waye yake son
jawo mata jarfa tana zamanta lafiyar Allah
"Eh baqo,kiyi ki fito kada ki zauna" ya fada cikin halin ko in kula da yanayinta
yana sakin labulen ya fice,magabar tayita juyawa cikin ranta,sai ta banzatar da
zancan jin yaya abbakar din na yiwa mama sai da safe ya wuce gidansa.

     Minti kusan goma da fitar tasa mama ta dago labulen ta shigo


"Wai ba yayanki ya fada miki kina da baqo ba" kamar zata saki kuka ta dubeta
"Mama ban fa san ko waye ba"
"Idan kinje kya ga ko waye din yana sitting room din malam,tashi maza ki wuce kuma 
saura kije ki yiwa mutane sakarci",tilas ta miqe bayan ta kwantar da abdallah a kan
gado ko hijabin jikinta bata cire ba ta fito zuciyarta fal quna.

       Turus tayi bakin qofar ragowar sallamarta ta koma ciki,da hanzari ta juya
tana mai neman fita,cikin zafin nama ya sha gabanta wanda saura kadan jikinsu ya
hadu,sai ta ja baya tana dubansa,mukhtar ne sanye da dinkim shadda ruwan sararin
samaniya babu hula kansa,ta masa kyau sosai saidai ramar da yayi ta
bayyana,hancinta ya cika da qamshin turarensa ya dinga tuna mata baya,saboda haka
da sauri tace
" matsamin na wuce"
"Babu inda zakije sumayya yau sai kince wani abu game da ni,kin yafe min ko baki
yafemin ba,sumayya ya ina kike so na dora raina?,laifi ne na aikatashi na nemi
afuwarki sumayya amma kinqi kice komai,kinsan kullum ya nake kwana ya nake tashi da
rashin cewa komanki?,kinsan me nakeji cikin qirji na" sai kuma ya sassauta murya
cikin sanyi
"Kinfi kowa sanin wane mukhtar sumayya,kinfi kowa sanin wane irin zama mukayi a
baya,sumayya ki tausaya min koda ba zaki tausayamin ba ki tausayawa
abdallah,abdallah ya zama marayan qarfi da yaji,abdallah na buqatar mu ni da ke a
tare,idan baki tausayawa mana ba sumayya waye zaiji tausayinmu duk duniya?,taba
qirjina sumayya kiji" ya fada yana fincikar hannunta zuwa qirjinsa,sosai taji
zuciyarsa na bugawa,gaza cire hannunta tayi sai da taji ya ambaci wash,da sauri ta
dubeshi sai taga yana dafe da kansa yana layi,batasan sanda ta riqeshi ba a rude
tana cewa lafiya?,ganin yana neman gun zama ya sanya ta zaunar da shi tana masa
sannu,tsahon mintina biyar sannan ya sauke numfashi ya gyara zamansa tana zaune can
nesa da shi ya dubeta
"Ciwon kai nake fama da shi,amma wannan duka ba damuwata bace burina kawai ki
yafemin" ya fada yana duban qwayar idanunta,a hankali ta janye idanuwanta zuciyarta
na mata bitar waye mukhtar agurinta,
"Na yafe maka" ta furta murya can qasa
"Allah ya yafe mana baki daya" wani wawar ajiyar zuciya ya saki,baki daya jikinsa
ya saki,wani farinciki yaji yana ratsa kowacce gaba ta jikinsa,yana so yaje ga
sumayyan amma sam jikinsa babu qwari ko kadan,sai ya miqa mata hannu
"Taso sumayya kizo kusa da ni don Allah" sai ta girgiza kai ba tare data motsa
ba,tilas ya tattaro duk wani ragowar qarfinsa ya kiqe ya isa gareta,kusa da ita ya
zauna har tana gogar kafadarta,hakan ne ya sanyata ta janye da sauri tana hada rai
"Meye haka,don nace na yafe maka ai hakan ba yana nufin kai mijina bane ko zan sakw
aurenka ba" da sauri ya sake matsawa kusa da ita babu gun matsawa a gunta don ya
kaita qarshen kujerar sai ya kama hannunta ya matse cikin nashi
"Sumayya,na sake miki wani laifin don na bada sadakinki,amma bisa sharadin matsawar
baki amince ba zan karbi kaya na na haqura"
Wani abu taji yana ratsa zuciyarta mai kama da farinciki,zuciyarta ta karye hawaye
ya biyo kuncinta,cikin raunanniyar murya ta kwabe fuskarta
"Ni nace maka ka kai sadakina ba tare da sani na ba?,ai kuwa sai kaje ka karbi
abinka don ni ban amince ba,kuma......" Bata ankara ba ya hade bakinsu waje daya
wanda hakan yayi sanadiyyar katsewar maganarta,sun dauki kusan minti goma a haka
sannan ya janye yana dubanta,qasa tayi da kanta kan fuskarta qaramin murmushi na
fita a fuskarta
"Magana ta qare,na sanki tun ba yau ba,dukkan abinda zaki fada a yanzun nasan aji
ne kawai za'a jamin ko ba haka ba" sake hade fuska tayi kamar gaske
"Nidai na fada kaje ka karbi sadakinka,bana yi"
"Ok to bari na kira ya abbakar na sanar masa" ya fada yana fiddo wayarsa daga
aljihun gaban rigarsa,ganin da gaske lambar ya abbakar yake nemowa ya sanyata qwace
wayar
"A'ah,ki bani mana na isar mishi da saqonki"
"Ni bance ba" ta fada a shagwabe,sai yayi jagale yana kallonta saboda tuna masa da
baya da tayi ta salon yanayin maganar da tayi
"Kada ki hanani fa tafiya gida yau na kwana a nan"
"Bismillah mana ai ga guri nan" sai yayi kalar tausayi yana dubanta
"Yaushe za'a tara shaidu sumayya ki koma dakinki" idanu ta juya ta dan murguda baki
"Sai shekara iwar haka" qirjinsa ya dafe yana kallonta
"Mutuwa kike so nayi kafin lokacin sannan ko?" Rai ta hade
"Ka daina fadin haka mana ya mukhtar,ni kunya nake ji gaskiya ka bari idan ja
shirya zan fada maka ka sanarwa ya abbakar" hannunta wanda ke cikin nashi ya
sumbata yana fadin
"Na gode,na gode,na gode sumayya,na gode da karamcin da kika nuna min a rayuwa,na
gode da kika nuna ke mai qaunata ce har yanzu" sai ya dakata yana fidda zoben
azurfan dake yatsansa ya zura a nata,ya mata yawa hakan ya basu dariya baki
dayansu,sai ya cire ya sanya mata a yatsan tsakiya duk da haka ya mata yawa
"Ina son zoben nan sumayy,amma sai naga yafi kyau a hannunki,ki ajiyemin zan karba"
"Idan kuma naji dadinsa bazan maida maka ba"
Dariya ya danyi sannan yace
"Babu komai,ai da kai da kaya duka mallakar wuya ne" sallamar halima ta sanya
sumayya miqewa,shigowa tayi dauke da abdallah tana fadin
"Wallahi yaron nan ya koyi rigima,tunda ya tashi yaje zunduma ihu nayi tsammani ma
kin jiyo shi"
"Ina zata jiyoshi ta shiga kogin qauna" mukhtar ya fada cikin salon zolaya yana
miqa hannu ya amshi abdallah dake ta dokin zuwa gunsa yana kiran abba na,murmushi
halima tayi tana yiwa sumayya kallon tsokana ta fice,ita kanta wani dadi taji don
babu wanda yaji dadin rabuwarta da mukhtar,qafarta har qaiqayi take taje ta bawa
zainab labari.

     'Yar kallo sumayya ta koma sanda mukhtar suka soma wasa da abdallah,bata taba
ganin d'a da uba irin haka ba,sai wajen qarfe goma ya fito zai tafi,qin tafiya yayi
har sai data masa rakiya bakin mota,har ya shiga ya fito ya sake kallonta
"Ban son tafiya sumayya,banqi ace tare da ke zan tafi ba,don Allah ki taimaka ki
gama shirye shiryen da duk zaki da wuri,ni na amince ma duk abinda baki qarasa ba
ki qarasa shi a gida na zan baki wannan damar,ji nake kamar lokaci na qure mana"
murmushi tayi tana jin maganar tasa na sauka sosai cikin zuciyarta
"Kada ka damu ya mukhtar,ka qarasa gida dare yanayi" ta fada tana taka masa,sai da
yaja motar ya bar layin sannan ta koma cikin gida.

   *******     *******   ******

     Cikin abinda bai gaza sati biyu ba mukhtar ya sabunta soyayyarsa baki
daya,kullum yana tare da ita idan baizo ba kuwa ranar katin waya zaici ubanshi,har
tsokanarta su halima sukeyi,wai sai kace wasu masu auren fari,ya dawo mata ya
mukhtar dinta sak,sai ta samu kanta da dokanta wajen ganin ta a gidanta cikin
sabuwar rayuwa ita da mukhtar dinta da yaronta.

        Sati na zagayowa aka maida auren sumayya da mukhtar karo na biyu ranar
jum'a bayan an sauko daga masallaci,a ranar mukhtar ya matsanta mata sai ta sanya
ranar tariya,sati biyu tace ya tuburr mata kan ya masa yawa,tilas ta haqura ta
maida shi sati dayan,don dama tana jiran aiken da anty dije tace zata yi mata nan
da kwana goma.

  *******    ********   *******

      Juma'a asabar lahadi litinin kwana hudu da mai da auren ran litinin mukhtar
yace ta shirya da daddare zata masa rakiya zai yi siyayyar kayan da yake son
sauyawa cikin gidan,mama ta sanar,Allah ya tsare sai kun dawo abinda maman tace
kenan.

     Tana idar da sallar magariba ta soma shiryawa,kwalliya tayi wadda rabonta da


yin kwalliya irinta har ta manta,tsaf ta shirya cikin material na one million stone
peach ne da adon mint green,fitted gown aka mata da shi,ya masifar yi mata
kyau,zainab ke dubanta tana cewa
"Kai yaya sumayya,sai kace zaki dinner,ai kya bari sai nan da kwana hudu wannan
kwalliyar,karfa ki sanya ya mukhtar yaqi maidoki" daquwa sumayya tayi mata tana
cewa
"Ni sa'arki ce,naga alama kin soma rainani" dariya ta sanya
"Yi haquri yayanmu,amma dai ba hijabi zaki sanya ba ko?,naga kina da mayafi kalar
kayan"
"Kyaji da shi" sumayyan ta fada tana feshe jikinta da turaruka,ita kanta tasan cewa
tayi kyau,sai da tazo fitowa sai taji kunyar wuce mama a haka,da qyar ta fice kanta
na sunkuye mama bayan ta barwa zainab abdallah wanda yau yayi baccin wuri.

      Baki kawai mukhtar ya saki yana kallonta har sai data hure masa idanu,dariya
sukayi baki daya
"Ki amince kawai yau mu wuce gida my sumy"kicin kicin tayi
" amma dai unguwa kawai kace zan raka ko?"murmushi ya saki
"Afuwa ranki shi dade,na tuna,muje" suna tafe yana tuqi amma baki daya ya wani
narke mata bini bini ya kalleta har suka isa gun ya kashe motar ya zuba mata ido ba
tare da ya fita ba
"Sumayya,ina jin wata sabuwar qauna taki na dasuwa cikim zuciya ta,da ace a yanzu
ne wani ya aureki mutuwa zanyi wallahi,ina sonki sumayya ina fata mu kasance tare
har ABADAN" murmushi ta saki tana kada kai
"Nima ina fatan haka ya mukhtar"
Sai da ya sumbaci goshinta sannan ya bude motar suka fita.

     Kayayyakin amfanin gida suka siya sosai,harda kayan kitchen sai da ya siya
wasu abubuwa daga ciki,motarsa ta cinye kayan a ciki aka zuba masa sannan suka
fito,sake tsayawa yayi a wani gu da saida kayab qwalam da maqulashe ya sayi kaji
biyu gasassu da ice cream,sai damammiyar fura ya dawo ya tada motar yana
dubanta,hira suke qasa qasa duk ya wani sukurkuce,wani kallo yake jifanta da
shi,sai taga ya dauke kan motar ya sauya hanya,shuru tayi ta kasa tambayarsa
hakanan sai ta biye masa har suka isa qofar gidansu,gidanta ne a da wanda a yanzu
ma ya sake zama mallakinta
"Bismillah muje ciki ko?"
"Ya mukhtar na bar abdallah a gida fa"
"Babu komai,minti talatin kawai ina son ganinki ne sumayya" nan ma bata ce komai ba
ta fita suka shiga gidan,tayi mamakim ganin komai a tsaftace a killace,bai tsaya ko
ina ba sai dakin gadonsa,ya dubeta sanda yake cirw hularsa tare da tattare hannun
rigarsa
"Nasan bakiyi sallar isha'i ba ki daura alwala muyi sallah sai mu wuce ko?" Cikin
shagwaba tace masa
"Wai nikam bansan gaggawar me kake ba ya mukhtar,saura kwana hudu fa na dawo gidan
baki daya" murmushi kawai yayi bai amsa mata ba ya shiga bandakin.

       Bayan sun idar ya matso inda take,hannunsa ya sanya cikin nashi yana kallon
qwayar idonta
"Sumayya,Allah ne kadai yasan yadda nake jin sonki a zuciyata" murmushi tayi tana
girgiza kai."ya mukhtar,sai kace yau kasan sumayya,sai sake jaddada qaunarta kake
bayan ta riga da tasan hakan"murmushin shima yayi
"Hakane fa ko sumayya,amma wannan karon wata qauna ta daban nakeji,sumayya,ina so
ki kasance tare da ni har qarshen rayuwata"
"Na maka wannan alqawarin"
"Na gode"
Sai kuma shiru ya biyo baya har ya qosa taji me zai sake cewa,sai daga bisani yace
"Sumayya,zaki yimin alfarma na kasance tare da ke cikin wannan daren?"idanu ta daj
fiddo
"Ya mukhtar,kwana hudu fa ya rage"
"Na sani sumayya,amma so nake kimim wannan alfarmar indai ban keta iyakar ubangiji
ba"
"Na maka ya mukhtar" ta fada kanta tsaye
"Allah yayi miki albarka" ya fada yana janyota ta fada jikinsa kowannansu cuke da
kewar dan uwansa,kada ma mukhtar yaji labari,ji yake kamar an masa bushara da
aljanna.

       Qarfe goma saura na dare ta fito daga bandaki,mukhtar tuni ya kammala


shiryawa yana zaune yana jiran fitowarta,binta ya dinga yi da kallo,ji yake tamkar
ya hadiyeta ya maidata ciki,har yanzu baiwar nan da ya santa da ita na tattare da
ita,ganin ta kammala ta yafa mayafi tana saba jaka ya sashi saurin cewa
"A'ah,amarya guda bai kamata ace bata ci komai ba" sai ta saki murmushi cikin jin
kunya
"Ya mukhtar yau ka manta da abdallahnmu?,munfa barshi a gida"miqewa yayi da sauri
yana fadin
"Kai kai hakane fa,jikina ya bani ma fa ya farka" dariya ta saki
"Uhmmm,sannu masu 'ya'ya"
"Wallahi kuwa,d'a ba wasa bane" ya fada yana kama hannunta suka fice.

       Ihu take so ta kwarara ko zataji sanyi a ranta amma zinatu ta hanata don
kada ta tara musu mutane,wadda ita ta kawo mata labarin komawar auren sumayya da
mukhtar,maimakon haka saita maida dubanta ga zinatu cikin daga murya
"Wallahi wallahi sai na aikata abinda na qudurta babu mai hanani aikatashi
wallahi,mukhtar nawa ne,nawa ne ni kadai,bazan juri ganinsa da wata ba ba ni ba" ta
fada kamar zararriya tana mai ficewa daga layin cikin qunar zuciya kamar zatayi
aman zuciyar tata.

Ko da ya sauke ta ma sai da ya sake tsareta,kamar bazaya tafi ba har sai


dayaga giftawar malam da alama ya shigo gida kenan sai da safe sannan sukayi
sallama bayan ya cikata da kalamai masu tsayawa a zuciyar wanda ake so.

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

4⃣8⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

*kullu nafsin za'iqatul maut,summa ilaina turja'un*

*_DUKKAN RAI SAI TA DANDANI MUTUWA,SANNAN IZUWA GAREMU ZAKU KOMO_*

_________________________________

Tana shirin kwanciya wayarta ta dauki ruri,mukhtar ne sai ta kumahe idanu


tana murmushi
"Na kasa bacci my sumy,ganinki nake kusa da ni".'yar qaramar dariya ya tasa tana
fadin
" baban zumudi ka zama ya mukhtar ne?"shiru ya danyi sannan ya saki ajiyar zuciya
"Bakisan me nake ji ba game da ke sumayya". Hira suka kashe lokaci suna yi,a nan
yake gaya mata ran rakota tare da yaya yahanasu za'a zo,har mamaki take idan taji
yadda yaya yahasun ta sauya take nuna mata qauna,basu suka rabu ba sai daya na
dare,ta dubi agogo tana zaro ido ganin lokacin da suka shafe tare,sai ta fita ta
daura alwala tayi sallah raka'a biyu sannan ta kwanta.

****** ******** *******

Shirye shiryen tariya sun kankama sosai,tayi gyaran jiki hadi da qunshi da
kitso,kayanta baki daya ta kammalesu.

Ranar alhamis ana ya gobe zata koma,da azahar suna falo ita da halima da
zainab suna hira ita kuma tana gugar ragowar kayan abdallah da bata gama shiryawa
ba,sai anty salma qanwar mama wadda anam zata kwana,wayarta dake daki ta soma
burari,abdallah ne ya miqe da gudunsa ya dauko ya miqa mata,anty salma ta talle
masa qeya tana cewa
" kaji dan jakar uba wai yasan kayan uwarsa,sai kace wani yace zai dauki wayar
ne"dariya sukayi dukansu halima tace
"Indai Abdallah ne kadan kika gani anty" ita kuwa sumayya miqewa tayi ganin lambar
mukhtar ce ta fita ta koma dakinta
"Lafiya abban abdallah naji muryarka can qasa?"murmushi ya saki sannan yace
" lafiya qalau,a yanzu ma ina gida kwance ina hutawa,babu abinda nayi amma wata
gajiya nakeji sosai a jikina,kewarki nake sumayya goben nan kamar ba zata zo
ba"tamkar yasan abinda take ji jikinta itama kenam,sai ta saki ajiyar zuciya tana
masa murmushi
"Au dariya ma kike min?,naji na gode,amma da zaki taimaka min da kinzo na ganki
kinji my sumy" sai ta kasa musa masa,dama suna da agender fita karbo dinkunan
sumayya gidan wata mata bayan sallar la'asar ita da anty salma
"Babu damuwa ya mukhtar,amma sai bayan la'asar"cikin zumudi yace
"Da gaske sumayya ta?,kada fa ki shirgani"dariya ta qyalqyale masa da ita
" da gaske nake mana abban abdallah,ka jirayeni,amma fa gobe ba za'a rakoni da wuri
ba tunda yau ka sake gani na"
"Babu komai,ai goben ta Allah ce,Allah yayi miki albarka sumayya ta" tana jin dadi
ya sanya mata albarka don haka da sauri ta amsa da amin.

A gidan mai dinki ta bar anty salma tace zata je ta dawo,ta riga da tasan
inda zata din saboda haka tayi tayi abdallah ya zauna qememe yaqi har da kukansa
ammi zai bi tace madallah yayi ta binta din sai sun dawo.

A qofar gidan mai adaidaita sahu ya sauketa,ji tayi ana malam ga kudinka,tana
waiwayowa sai taga mukhtar ne,cikin mamaki take tambayarsa
"Ya akayi kasan na qaraso"
"Jikina ne ya bani" ya bata amsa yana amsar abdallah daga hannunta yana masa
cakulkuli suna qyalqyala dariya tana biye da su har zuwa falon gidan,kallon gidan
take ya sauya komai kamar wanda zai kawo budurwa,komai fes gwanin sha'awa,zubewa
sukayi kan kujera mukhtar na biyewa abdallah suna ta wasanninsu yayin da sumayyan
ke zaune gefe guda
"Wai nikam 'yar kallo kuka maidani ne,nazo amma ba'a tani,bayan nemana akayi" ta
fada tana murguda baki,dariya mukhtar din ya saki yana duban abdallah."lah,abdallah
kaga mamanka na kishi da kai"sai ya kada kai kawai yaron don bai fahimci me yace
ba,juyawa yayi gunta
"Dama taimaka mana kika yi kika dafa mana wani abun madam"
"Kamar me?" Ta tambayeshi
"Abinci mai sauqi da dadi"
"An gama" ta fada tana miqewa
"Ammm,madam,amma da kin taimaka kin cire wannan hijabin tunda gaban mijinki kike
ko?" Dariya ma ya bata yadda yayi maganar a dake,bata ce komai ba ta cire din,sai
ta miqawa abdallah hannu
"Muje kayi fitsari sai ka dawo ko?" Lafewa yayi jikin mukhtar din qememe yaqi yarda
da ita
"Barmin yaro na ana dole ne,yayi fitsarinsa babu komai cinyar babanshi ce".don haka
ta juya zuwa kitchen ta barsu nan.

Tana tsaka da girkin mukhtar ya shigo goye da abdallah,saura qiris ta dona


hannunta cikin gas garin dariya
" ka ganka kuwa da goyon nan,don Allah tsaya na maka hoto"shi din ma dariya yake,
"To ya zanyi,yaqi yarda na kwantar da shi kwata kwata"hoto ta musu wajen kala biyar
ta nuna masa suka dinga sheqa dariya,tex din da ya shigo wayarta ya katseta,anty
salma ce ke gaya mata ta wuce gida uta kam sai ta taho,tana niyyar kiranta tace ta
jirata tana tahowa mukhtar ya riqe hannunta
" qyaletq ni da kaina zan maidaki".qarshe tare suka gama girkin wajen sallar
magariba sannan ta karbi abdallah da qyar zata kwantar,sai ya farka ya riqe mukhtar
gam gam yana sakin kuka,tilas yace ta qyaleshi suka dauro alwala sukayi jam'in
sallar magariba tare sannan ta gabatar masa da abincin.

Tare suke ci baki dayansu,saidai duk daga kan da zatayi idanuwansa na


kanta,saidai ya sakar mata murmushi ta maida masa martani,sake hada idanuwa sukayi
karo na barkatai,sai ya kauda kallonsa ya maida kan abdallah
"Na godewa Allah da ya sake gwadamin wannan lokaci cikin rayuwata,lokacin da zan
zauna ni da matata abar sona da kuma diyan cikina,ina fata Allah ya rayamin kai" ya
fada yana shafa kan abdallah,sai yaron ya dago kai yana kallonsa kamar yasan
ma'anar abinda yake cewa
"Ina da buri kanka abdallah" ya sakw fadi,sai ya dubi sumayya
"Ki taimaka min wajen tarbiyyar abdallah don Allah" murmushi ta saki zuciyarta na
bugawa kadan kadan
"Banda abinka ya mukhtar ai saidai mu taimaki juna tunda tare zamuyi tarbiyyarsa"
girarsa daya ya dage
"Haka ne fa,to Allah ya bamu aron rai"
"Amin ya Allah" ta fada tana ci gaba da cin abincin,sai daga bisani ta lura ba wani
cin abincin sosai mukhtar din keyi ba sai aukin kallonsu
"Ai bama cin abincin kake ba fa yaya,wannan kallon duka na meye?"
Murmushi ya kuma saki."kallon so da qauna nake muku"dariya ya bata sosai
"Naga alama sai na maka dura" ta fadi tana debo abincin da spoon tana bashi,qarshe
ita ta qarasa basu abincin dukansu sannan ta gyara gun,kayan wasa taga yana ta
hadawa abdallah sannan ya janye ta bedroom yace zata tayashi wani aiki,bata fahimci
wayo yayi mata ba sai da labari ya soma shan banban.

Daf da kammaluwar komai sai ta tsinci hawaye na diga idanunsa,tasa hannu ta


shafo sai taji itama nata idanun na fidda ruwan qwallar da batasan dalili ba
"Ya mukhtar ko na yi ma laifi ne?" Ta tambayeshi cikin sanyin jiki,sai ya sake
qanqameta yana sakin ajiyar zuciya tare da murmushi
"Babu abinda kika yimin,tsakani na da ke sai fatan alheri,Allah ya haskaka
rayuwarki,qwallar farinciki nake musamman idan na tuna gobe zamu sake sabon zama
sumayya" dariya tayi tana kwantar da kanta a qirjinsa
"Na gode ya mukhtar"
"Nine da godiya sumayya,ina so ki sake yafemin ki dauka tamkar babu abinda ya taba
faruwa tsakaninmu mara dadi" cikin shagwaba tace
"Ni na manta ma fa ya mukhtar,ni babu abinda ya taba faruwa tsakanina da kai,kai fa
uban 'ya'ya na ne".

Da qyar ya yarda zai maidata gida,da sdrd yayi tayi zamanta meye marabar yau
da goben,ko a motar ma sai da ya gama yawo da su guri guri ya loda uban siyayya
sannan ya kaisu gida,riqe hannunta yayi sanda take shirin fita ya sumbaci bayan
hannun nata,itama sai ta maida masa martani,ta jima tsaye a soronsu tana leqensa
ganin ya tsaya bai tafi ba,sai daga bisani taga ya ja motar ya tafi.

*JUMA'A*

Tun mafarkin da taji daren jiya jikinta a mace yake,tana farkawa ta kira
mukhtar din ta tabbatar da lafiyarsa,har yana zolayarta kodai ta qagu ne kawai a
kawota,shi bacci ma yakw ta tasheshi,dariya tayi cikin jin kunya sukayi sallama,har
zuwa wayewar garin juma'ar jikinta a mace yake,tun safe take kwance ta kasa
katabus,tana jiyo koke koken abdallah da yau ya tashi da rigima amma ta kasa cewa
komao,har ya shigo dakin ya gama kukansa da kawo mata qarar walida 'yar anty salma
ya gaji ya fice ba tare da tace masa komai ba.

Qarfe hudu na yammacin ranar tana tsaye tana shiryawa cikin dinkin atamfa
riga da zani anty salma na tsaye kusa da ita tana bata turare wayarta ta dauki
kuwwa,sunan mukhtar ne ya bayyana gabanta yayi mummunan faduwar har qafafuwanta
taji sunyi sanyi,sai ta koma bakin gado ta zauna tana amsa wayar cikin fargaba
"Assalamu alaiki amarya ta" muryar mukhtar ta ratsa dodon kunannata,sai ta amsa
masa tana lumshe idanuwanta,cikim salon soyayya suka gaisa sannan yace
"Ina fatan kin fara shirin tahowa gidanki" dariya ya bata ta murmusa
"Yanzun haka ma shirin nake angom doki"
"Eh naji na yarda ina abdallah"
"Yana waje,yau tun safe yake ji da rigima wallahi" nemo min shi mu gaisa"
"Bai kusa fa ya mukhtar" ta fada a shagwabe,tuburewa yayi tilas ta qwalawa zainab
kira ta kawo shi ta hadasu da wayar taci gaba da shiryawa,sai da ta gama sannan ta
karbi wayar
"Nima ina gun masu dinki zan karbi dinkuna na,SAI KIN TAHO?"
"To ya mukhtar,ka kularmin da kanka"
"To my sumy". Ajjiye wayar tayi tana sakim ajiyar zuciya.

Bayan sallar magariba 'yan rakiyar nata sukayi mata sallama kowa ya kama
gabansa,ganin har isha'i tayi shiru sai ta daura alwala tayi sallar isha'inta,sam
gidan ba,gabanta ke yawaita faduwa tana ambaton hasbunallahu wa ni'imal wakil,ga
abdallah na tare da mukhtar tare zasu taho da shi,ganin shirun yayi yawa sai ta
miqe ta kunna saudi qur'an Allah ya taimaketa ma akwai wutar nepa ta zauna tana ci
gaba da saurara zuciyarta na mata wani iri babu dadi.

Firgigit ta dawo hayyacinta tana duba agogo,goma na dare ta dubi wayarta


dake ta faman ruri,sunan malam ta gani kam screen dinta,sai taji gabanta yayi
mummunan faduwa har sai da ta furta hasbunallahu wa ni'imal wakil a bayyane sannan
ta kara wayar a kunnenta
"sumayya kina ina?" Abinda taji malam ya fadi kenan,sai tambayar ta bata mamaki
"Ina gida na malam"
"Yauwa to maza kashe wayarki ki fito qofar gida abubakar na jiranki,yace yana ta
bugu bakiji ba"sai ta amsa da to kawai tare da bin umarnin malam din kawai tana jin
wani yanayi nabin fata da tsokar jikinta,hijabin data idar da sallah ta zira ta
fito kai tsaye qofar gidan ba tare data rufe gidan ba.

Ya abbakar ne tsaye jikin adaidaita sahu kansa a kife,qarar bude gidan ya


janyo hankalin sa,sai ya kalleta
"ya baki kulle gidan ba,malam ke son ganinki"
"To" kawai ta kuma cewa ta koma ta jajjanyo qofofin,tana fitowa ta miqawa ya
abubakar wayar tata don ji tayi ta fara yi mata nauyi a hannu,kallonta kawai yayi
ya sanya hannu ya amshi wayar ya sanya a aljihunsa suka shiga adaidaita sahun ya
jasu suka bar qofar gidan ba tare da kowa ya sake cewa komai ba.

Cikin harabar asibitin mai adaidata ya faka ya abbakar ya biyashi suka


fito,binsa kawai take a baya ba tare da tasan inda take jefa qafarta ba,tarin
tambayoyi ke yawo kan kwanyarta amma ta gaza furta koda guda?,shin waye a
asibiti?,me ya faru ko meke faruwa?.gab da zasu haura saman asibitin ta iya
tambayarsa
"Ya abbakar,wai me yake faruwa?,waye ba lafiya?"
"Babu komai muje kawai"
Tun daga farkon barandar ta fara cin karo da mutane,yaya yahanasu,malam,kawu
mahaifin abdur rahman da hajiya mahaifiyarsa,jamila yarinyar yaya yahanasu,sai
mamanta da wasu mutane uku da batasan su waye ba,tunda taga yaya yahanasu mukhtar
ko abdallah ne suka fado ranta,jikinta ya fara rawa sai ta fara qoqarin faduwa
sanda suka had ido da yaya yahanasu taga ta saki kuka,da sauri hajiyan abdur rahman
ta qaraso ta tareta ta zaunar da ita kan kujera tana fadin
"Yi a hankali sumayya,babu komai in sha Allah Allah zai bashi lafiya,kiyi masa
addu'a"
"Waye hajiya me ya sameshi" malam ne ya qaraso yayi mata bayani,hatsari mukhtar din
ya samu yana hanyar tahowa gida shida abdallah gab da sallar magariba,yanzu haka
mukhtar din na tare da likitoci amma sunce yanzu zasu fito da shi saidai ICU zasu
kaishi,wani irin tauri taji zuciyarta tayi
"La haula wala quwwata illa billah" ta dinga maimaitawa,jin jikinta take kamar ba
nata ba.

Bata ce komai ba har zuwa sanda aka bude qofar wani daki aka turo
gadon,mukhtar ne kwance tamkar gawa,babu abinda ke aiki a jikinsa sai numfashinsa
dake fusga duk bayan wasu daqiqu,kansa nannade da bandeji fari wanda jinin da ya ci
gaba da ratsowa ke barazanar sauya masa kala,a haka ma sun gyarashi sun dan
gogeshi,wani kalar tashin hankali ya ruftowa sumayya,sai ta miqe tsaye har suka
wuce da shi intensive care unit din,kukan yaya yahansu na haduwa da nata tashin
hankalin yana yamutsa qwaqwalwarta,qunshe bakinta tayi cikin hijabi ta saki wani
irin kuka qasa qasa ta soma furtawa
"Ya ubangiji na,na roqeka kada ka sanya wannan ya zama cikin KUNDIN QADDARA
ta,Allah na tuba,na tuba ubangiji na" abinda ta dinga maimaitawa kenan qasa
qasa,hajiyan abdur rahman ita ta dinga lallashinta,saidai babu abinda ke qara mata
sai tashin hankali ahaka sha biyu na dare ya cimmasu dai dai lokacin da likitocin
suka fito,bayani suka yi masu kan dakin bai buqatar shigar mutane ciki,haka nan
mutum daya suke da buqata wanda zai zauna da mara lafiya
"Don Allah don annabi malam ku qyaleni na kwana,wallahi bazan iya tafiya gida ba"
sumayya ta fada tana fashewa da kuka,babu wanda tausayinta bai kama ba anan,ganin
babu yadfa za'ayi a barta ita daya kawu da ya abbakar zasu kwana cikin asibitin,ita
kuma ta kwana gun mukhtar din.

A hankali ta dinga takawa har gaban gadon da mukhtar din ke kwance,ko ina
na'ura ce ke aiki a jikinsa,baki daya fuskarsa ta sauya kamar ba mukhtar ba,kallo
daya zaka masa kasan lallai ya bugu sosai a kansa don tuni har ya kumbura kan
nasa,kujera ta ajjiye bakin gadon tana qoqarin danne zuciyarta tare da tuna nasihar
da malam yayi kata kafin su tafi
"Kuka baya maganin komai,addu'a ita ke magani" abinda ya gaya mata na qarshe
kenan,kanta ta girgiza tana sake baiwa kanta qwarin gwiwa,sai ta kama tafin
hannunsa ta sanya cikin nata,a hankali murya can qasa mai cike da rauni ta soma
karanto ayoyin qur'ani wadanda su suka dinga debe mata kewa tsawon daren,saidai
abinda ke daga mata hankali dai dai da second daya babu wani abu da taga ya motsa
daga jikinsa,wanda likitocin sunce ta kula ko yaya taga ya motsa ta sanar musu,duk
da lokaci bayan lokaci suna shigowa suna sake dubashi.

Sai da suka saitu sosai kan hanya sannan mama tace


"Ina abdallah" tofa,sai lokacin hankalin kowa ya dawo jikinsa,duk cikinsu babu mai
amsar tambayar,don hatta jama'ar da suka ceci mukhtar dim babu wanda yace yaga
yaro,take wani sabon tashin hankalin ya samesu,mama kam kasa daurewa tayi saboda
tsananin tausayin sumayya sai kawai ta sanya kuka,kai tsaye malam ya nemi alfarmar
mai abun hawar ya canja akalarsa zuwa policestation wanda tafi kusa da inda
al'amarin ya faru don si shigar da report cike da matsanancin tashin hankali.

Kiran sallar asubar fari sanyi ya fara busowa,sam bata lura ba tana gyara
zamanta,tana daga kai suka hada idanu,ya bude idanuwansa tar yana kallonta,wani
farinciki ya dinga zagaya ta,ga mamakinta taji sai taji ya kita sunanta,cikin
matsanancin farinciki ta amsa
"Qarfe nawa?"
"An kusa sallar asuba"
"Daura min alwala sumayya banyi sallar magariba da isha ba" girgiza kai tayi
"Ya mukhtar jikinka duka kayan aiki ne,ka bari likita yazo sai ayi maka" tubure
mata yayi hakan ya sanya ta lallaba ta shashshafa masa ruwan iya inda zai yiwu,yana
daga kwancen ya dinga halarto da sallar yana yi har ya kammala baki daya tana zaune
tana kallonsa,yana sallamar qarshe kansa saitinta ne sai ya zuba mata
idanu,murmushi tayi tace
"Sannu ya mukhtar" kai ya kada mata sannan yace
"Ina abdallah" abdallah,ta dinga nanatawa,idan kunnuwanta basuyi mata qarya ba ance
tare suke da abdallah,to ina yake ina yayi?
"Ina fata lafiya yake babu abinda ya sameshi" tabbas lafiya yake idan da ba lafiya
ba da sun gaya mata
"Lafiya yake ya mukhtar" ta fada cikin salon son kwantar da hankalinsa
"Alhamdulillah" taji ya fada sai ya maida kansa,cikin farinciki da tada sallah
itama.

Shaquwa taji ya soma yi wadda kan ta idar da sallar ta qara yawa,tana


sallamewa tayi kansa tana masa sannu,da hanzari ta dauko ruwan roba ta bude ta fara
bashi a hankali,sosai ya sha ruwan kuwa sannan ta cire roban daga bakinsa ta qulle
tana masa sannu,minti biyar tsakani shaquwar ta dawo,ta sake matsawa gunsa tana
riqe da hannunsa tana masa sannu cikin tashin hankali ganin yadda qirjinsa ke
dagawa wannan karon
"Bari na qara maka ruwan" ta fadi tana shirin juyawa inda gorar ruwan take,sai taji
ya damqe hannunta,juyowa tayi tare da tsayawa cak kamar an kafeta,idanuwansa taga
sun fara juyewa,jikinta ya hau rawa ta qanqame hannunsa tana fadi a fili
"La'ilaha ilallah,muhammadur rasulullah" abinda ta dinga maimaitawa kenan a fili
babu qaqqautawa,a hankali taji ya kama yana maimaitawa,kusan minti biyu yana fada
shima cikin fusgar numfashi sai taga idanunsa na lumshewa,riqon da ya yiwa hannunta
tsaurinsa ya sassauta
(Abinda ake so ga kowanne majinyaci kenan,mutuwa na da sa gigita da daga
hankali,amma gata ake so ka yiwa mamaci wanda shine qarshen qaunar da zaka nuna
masa,a yayin daka fuskanci wasu alamu na fitar ruhi daga gangar jikin
majinyaci,bakinka ya dinga ambaton la'ilaha ilallahu muhammadur rasulullah ko za'a
dace mamaci ya kama,ba cewa ake fadi abinda na fada ba,ko kuma cene la'ilaha
ilallah,a'a ka dinga fadi yadda kunnuwansa zasu iya ji,idan Allah ya qaddara
bawansa ne na gari sai ya kama ya kuma cika da ita,Allah kasa mu cika da wannan
kalma mu da daukacin musulmi baki daya,amin).

Hannunta ta zare qirjinta na fat fat fat,hawaye ne ke bin kuncinta,wasi wasi


ya cika zuciyarta,fata take ba abinda take zato bane,wannan tunani ya sanyata fita
da gudu tayi ofishin likitan.

*mrs muhammad ce*

*Fatan alkhairi ga*

*oum imaan*

*mmn husna*

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

4⃣9⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

*assalamu alaikum*
*da fari ina neman afuwa ga wadanda na sanya kuka,Allah yayi mana kyakkyawan
qarshe,haka rayuwa take zaqi da madaci*

_abu na biyu da nake so makaranta su gane shine,haqiqa Allah baya barin wani don
wani yaji dadi,ko kuwa don kuna tsaka da farinciki sai Allah ya kasa dauke bawansa
alhali ajalinsa yazo?,na tabbata ni ke ko kai an taba dauke mana masoyanmu,uwa,uba,
'ya'ya,qawaye maqwafta ko dangi,wala allah muna tsaka da jin dadin rayuwarmu bamu
zatan musu mutuwa ba,ba kuma tare da sunyi sallama da mu ba,amma Allah ya daukesu
saboda lokacinsu yayi kamar yadda Allah madaukaki ke fada a alqur'ani_
_(iza ja'a ajluhum la yasta'akiruna sa'atan wala yastaqdimun/idan lokacinsu yazo
ba'a jinkirta musu sa'a daya kuma ba'a gaggauto da ita ma'ana su tafi alhalin suna
da sauran minti daya cikin duniya)_
_(kullu nafsin za'iqatul maut)_
_(kullu man alaiha faan)_
_duk abinda ke kanta(qasa)qararre ne_
_mutuwa dole ce idan tazo sai an tafi,babu wanda zai dawwama cikin duniya ko
shekara miliyan nawa zaiyi sai ya tafi,cikin dadi ko wuyar da kake ciki babu ruwan
ubangiji,na tabbata babu wanda ba'a taba yiwa mutuwa ba,babu wanda bai taba rashin
wani nasa ba,fatanmu Allah yasa mu cika da kyau da imani_
*sannan ina cewa masu karatu sun manta sunan littafin kenan KUNDIN QADDARATA?,kowa
ya san rayuwa tafe take da qaddara,cikar imanin mumini kenan a
jarrabceshi,jarrabawa na zamowa kankarar zunubi ga mumini,Allah ya bamu ikon cinye
jarabobinmu*

*wa bash shiris saabirin,Allazina iza asabathum musibatun qalu innalillahi wa inna
ilaihi raji'un*

*_KA YIWA MASU HAQURI BUSHARA,SUNE WADANDA IDAN MASIFA TA SAMESU SUKE CEWA MU DAGA
ALLAH MUKE KUMA MU GARESHI NE ZAMU KOMA(innalillahi wa inna ilaihi raji'un)_*

________________________________

       A rude ta fada ofishin likitan tana kiransa,likita ne mai kirki,ya gane ko


wacece saboda haka ya miqe kawai ya biyota,zata fada dakin ya dakatar da ita yace
ta jira a waje
"Sumayya,jikin muntarin ne?" Kawu wanda idar da sallarsu kenan daga masallaci suka
yo cikin asibitin suka tambayeta
"Kai kawai ta iya daga musu hawaye na bin kuncinta,don bata jin zata iya cewa
komai,jiri ta fara ji yana neman kayar da ita saboda tashin hankali da mintinan da
suka kwashe a tsaye,sabida haka sai ta daddafa ta zauna kan kujerar sake barandar
dakin.

      Likitoci biyu ne suka zo suka sake shigewa dakin suna nan zaune,awa guda ta
kusa shudewa dai dai lokacin da mama halima da zainab suka iso,yayin da malam ya
fara biyawa ta police station ko an samu labarin abdallah,jikin mama ta jingina
kawai ta kwantar da kanta a kafadarta ba um ba um-um,sannu maman ke mata tana
tambayar jikin mukhtar din,kawu ne ya amsa mata da cewa da sauqi don baki dayansu
hankalinsu bai jikinsu.

       Budewar qofar dakin ne ya ja hankalinsu,likita na farko ya wuce baice musu


komai ba,na biyu ma haka,na ukun ne ya tako gabansu a hankali sannan ya dubesu
" dukkan mai rai mamaci ne wannan alqawarin Allah ne babu mai zama cikin duniya sai
ya tafi,ina mai baku haquri,Allah ya yiwa mara lafiyanku cikawa,sai kuyi masa
addu'a",kuka ne da salati ya gauraye wajen,wani dogon numfashi sumayya ta ja,cikin
daga murya wadda bata san ta yita ba ta furta
"INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN,ALLAHUMMA AJIRNI FI MUSIBATI WA AKHLIFNI
KHAIRAN MINHA" tun daga haka bafa dada ba bata rage ba,don ba sosai take ganewa
ba,bin kowa kawai take da idanuwa.

     Isowar yaya yahanasu shi ya sake ruda gurin,zubewa tayi a qasa tana kuka kamar
ranta zai fita,daga bisani ta sume a nan,sai da aka bata taimakon gaggawa sannan ta
dawo hayyacinta,zuwa lokacin an kammala settling na tafiya da gawar mukhtar,motar
asibiti suka basu a kaishi ciki(ambulance)itakam sumayya ido kawai take bin kowa da
shi,sai ajiyar zuciya da take ta faman saki har suka isa gidansu na aure,gidan da
suka tanada domin sabunta rayuwar aurensu,gidan da suka ciwa burin sake gina
kyakkyawar alaqa da danganta har gaban ABADAN,ashe wannan mafarki nasu bazai cika
ba,ashe wannan buri nasu yankakke ne,ashe sunyi zaman qarshe da mukhtar kenan a
daren jiya?,abinda ya dinga bijiro mata kenan,kallon mutane take suna kuka,sai ta
dinga jin dama itace su,dama itama zatayi kuka,domin kuka ya fiye mata sau dubu
akan bala'i da sukar da take ji a qirjinta.
        Cikin uwar dakanta aka wuce da ita aka zaunar da ita,har lokacin babu um ba
um um sai ido kawai,a falo aka kwantar da mukhtar,aka bawa makusantansa dama suka
wanke shi aka maaa suttura sannan aka buqaci 'yan uwansa suje suyi masa
sallama,take gidan ya sake rudewa da koke koke,hakanne yasa anty salma tace a bar
kowa ya gama shiga sannan sumayya ta shiha daga baya,da qyar aka fidda su yaya
yahanash,kuka take tana ya yafe mata,itakam ta yafe masa dan bai taba saba mata
ba,tsakaninsu biyayya ce irinta d'a da uwarsa tunda ta fara riqonsa har ta aurar da
shi.

      A hankali take takowa cikin falon da taimakon hajiyan abdur rahman wadda ta
riqeta,gaban gawar mukhtar ta durqusa wadda ke lullube cikin likkafani aka sake
rufeta da wani mayafin,kanta ta duqar zuciyarta na suya tana jin zafin yana ratsa
dukkan sassan ilahirin jikinta,tana daga kai suka hada idanu da malam,da idanu ya
mata nuni ta masa addu'a,hakan ya qwarara zuciyarta,a hankali ta soma fadin
"Allah ya jiqanka ya mukhtar ya gafarta maka,ya Allah ka tsareshi daga azabar
qabari da fitinarsa,ya Allah gashinan yana mai buqatuwa izuwa rahamarka,kai
mawadaci ne daga barin azabtar da shi,idan ya kasance mai kyautatawa ya Allah ka
qara masa kan kyawawan ayyukansa,idan ya kasance mai sabo ya Allah kayi masa
afuwa,ya ubangiji ga mukhtar nan,bawanka ne Allah ka gafarta masa kayi masa
rahama,ka yalwata masa makwancinsa,ka wankeshi daga laifuffukansa da ruwa da
qanqara kamar yadda ake tsaftace farin tufafi daga dauda,ka sauya masa gida wanda
yafi gidansa,da iyali wadanda suka fi nasa,da mata wadda tafi tasa......."sai ta
sake yin qasa da kai,karo na farko da hawaye ya samu gurbi cikin idanuwanta,babu
wanda bata burgeshi ba a gun da irin jarumtarta,kamar yadda babu wanda tausayinta
bai ratsa shi ba,alfaharin haifar diya irin sumayyan ta kama malam,Numfashinta ne
ya yanke,duhu ya fara mamaye idanuwanta,kunnenta ya daina jin komai,daga nan ta
daina gane komai sai daukarta akayi aka fita da ita,kamar yadda aka dauki gawar
mukhtar zuwa gidansa na gaskiya,gidan dake jiran kowanne bawa.

       Bata sake sanin inda kanta yake ba sai gab da sallar la'asar,har ana
shawarar kaita asibiti idan aka kammala sallar la'asar din bata farfado ba,da
kalmar shahada ta farka,daga bisani kuka ta sake qwace maga,qanqame anty salma tayi
tana rusa kuka mai tsuma zuciya,wanda hakan ya sake sanya wadanda ke dakin fashewa
da kuka,babu wanda bai tausaya mata ba,ba shakka mutuwar miji babban al'amari ne
gun diya mace,mijin ma irin mukhtar,shiru kam yaqi ywuwa a gurinta,har sai da malam
ya shigo da kansa ciki wanda basu jima sa dawowa daga wajen 'yan sanda
ba,hankalinsu a tashe yake don babu labarin abdallah,baiso wannan labari ya kai
kunnen sumayya,so yake kafin komai ya lafa a ga abdallahn a duk inda yake,ya jima
da ita a daki kafin ya fito,tayi shiru amma har hanzu hawaye basu bar bin kuncinta
ba,haka nan bata fasa ambatar innalillahi ba cikin zuciyarta.

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*
*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

5⃣0⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

*fasbir sabran jamilah*

*_kayi haquri haquri mai kyau_*

_________________________________

     Cikin kwana daya tal amma ji take duniyar ta mata daurin huhun goro,babu
abinda qwaqwalwarta keyi sai bitar rayuwarta da mukhtar,idanunta sunqi dakatawa da
zubda hawaye dai dai da second d'aya,cikin kwana gudan tal ta rame ta fige ta fita
hayyacinta,ba ta cewa uffan sai ido kawai,ko gaisuwa aka yi mata saidai ta amsa da
ka,daga jiyan zuwa yau babu abinda ta kai bakinta illa ruwa da take kurba lokaci
zuwa lokaci idan an matsa mata,sam abincin bai iya wucewa ta maqogaronta balle ya
kai ga uwar hanjinta,a washegarin ranar anty dije ta iso hankali tashe,sai sabon
kuka ya balle tsakaninsu,ba qaramin tausayawa sumayya take ba,yarinya qarama amma
taga jarabtar rayuwa iri iri,da qyar aka sha kansu.

      Bayan sallar la'asar tana saman abun sallah tana lazumi cikin dakin
gadonta,anty salma ya yahanasu antu dije da mama ne zaune a dakin sai ita ta
biyar,sai yaran 'yan uwa dake gefe suna wasa,idanuwanta da hankalinta na kansu
"Abdallah" sunan da ya fado kanta kenan,cak ta tsaya da lazumin tana lissafin ina
abdallah yake?,bata ga abdallah ba duk cikin kai komon yata,haka bata ganshi gaban
gawar mukhtar ba
"Ina Abdallah" lokaci na farko da tayi magana tun bayan tsawon awanni kusan
talatin,dif dakin sukayi don babu mai amsar bata,tuni hawaye ya cika idanuwan anty
dije ta sanya mayafinya ta soma sharewa,mama tafi kowa shiga cikin taraddadi,don
ba'ayi minti goma ba malam ya kirata yace suna gun 'yan sanda,sumayyan dai bata yi
maganar sa ba ko?tace masa eh
"Ina abdallah yake?" Ta kuma tambaya wannan karon tana dubansu hawaye na bin
kuncinta
"Don Allah kuce min wani abu kunyi shiru,ko shima ya mutu ne?,shima yabi sahun
mukhtar?,ku daina boyemin ku gaya min don Allah"
"Abdallah na nan a raye bai mutu ba,kiyi haquri kinji sumayya" inji yaya yahanasu
ta fada tana share hawaye,murmushi mai dauke da hawaye tayi wanda ya sanyasu yin
jagale suna kallonta
"Meye na boyemin idan shima ya mutun,ban isa nayi komai ba saidai nayi haquri,ku
fadan don Allah na sashi cikin addu'ata idan har ya mutun" mama ce cikin hawaye ta
taso ta iso gabanta ta soma share mata qwallar
"Haka ne sumayya,kiyi haquri kan wanda kika yi,a iya binciken da jami'an tsaro
sukayi abdallah bai mutu ba,saidai ya bata an rasashi ba'a san inda yake ba,amma in
sha Allahu ana gab da samunsa 'yan sanda na nan suna bincike kan inda yake" shiru
sumayyan tayi tana duban maman,sai ta sake qas da kanta bata sake cewa komai ba sai
taci gaba da jan carbinta,ta riga ta sallama abdallah ya riga ya tafi kamar yadda
mukhtar ya tafi ya barta,kasa zama anty dije tayi sai ta miqe ta fice tana
hawaye,ba'a yi sallar magariba ba wani zazzafan zazzabi ya rufeta.

      Zazzabin shi yaci gaba da jigata ta da wahal da ita tsahon kwanaki biyu har
ranar sadakar bakwai,qarin ruwa kam ta shashi har ta godewa Allahi,idan ka ganta
baka cewa itace sumayya,ita kadai tasan me take ji a gangar jikinta da zuciyarta,ta
riga data sallamawa rayuwa baki daya.

     *****   *******  *****

     Zaune take a falon gidan sanye da hijabi da carbi,idarwarta kenan daga sallar
walha,gidan ba kowa sai yaya yahanasu wadda ke zuwa kullum ta wuni ta tafi anty
dije halima da matar kawun abdur rahman,tun shekaran jiya da akayi sadakar bakwai
kowa ya watse aka barta da su.

     Anty salma ce ta fito daga kitchen dauke da cup ta qaraso inda sumayya ke
zaune
"Ungo ai kin idar da sallar karbi kisha" kai ta gigirza hawaye fal idanuwanta
"Bazan iya sha ba anty salma,babu dadi,tsayamin yake a wuya"
"Haba sumayya,haba sumayya,ana yabonki sallah kuma ya haka,kowa na yabawa
tawakkalin da kikayi,akwai ciwo rashin miji da batan da'a,amma kinsan babu yadda
za'ayi rayuwa ta yiwu ba abinci,tunda abun nan ya faru baki sake sanya abu cikinki
ba,mu kanmu da muke tare da ke kinsan ba zamu ji dadi ba,daure ki karba kisha don
Allah ko kurba uku ce" hawaye na bin kuncinta ta karba ta kafa kai tare da rintse
ido kamar wadda zata sha guba,kurba uku tayi masa ta dire kofin tana maida
numfashi,dai dai lokacin da aka yi sallama bakin qofar falon amsawa sukayi halima
ta duba tace 'yan sanda ne,anty dije tace eh abban laila ne ya turosu su shigo suke
bincike kan batan abdallah da musabbabin hadarin mukhtar,gaban sumayya yayi
mummunan faduwa idanuwanta kan qofar falon har suka shigo,suka samu gu suka
zauna,tambayoyi suka yiwa sumayyan suna saurarenta har ta gama,daya daga cikinsu
wanda da alama shine babbansu ya fiddo wata leda wadda kana iya hango abinda ke
ciki ya miqo musu
"Kince gab da lokacin da abin zai faru kunyi waya,munga komai nashi cikin motar
saidai bamu ga wayar tasa ba,ko akwai wanda yayi kiran lambarsa tun bayan rasuwar?"
Anty yahanasu dake zaune gefe tace
"Gsky a'ah"
"Ok,ko zamu iya samun lambar wayar tasa?"
"Eh" anty dije tace,ita ta karanta masu lambobin yana rubutawa,ya kammala rubutawa
sannan ya latsa kiran,cikin second uku kiran ya shiga,tsit dakin yayi kamar babu
wani mai numfashi suna sauraren shigan kiran wayar
"Waye me magana" wata murya ta fada daga can bangaren
"Am,mukhtar nake nema don Allah" wata dariya aka saki wadda cika falon kasancewar a
hands-free ya sakata
"Ai mukhtar ya dade da wulawa barzahu,idan ma qarin bayani ake nema bari nayi
maka,mun kashe mukhtar,hakanan d'ansa yana hannunmu mun daukeshi,zamuyi masa irin
tarbiyyar da muka ga dama mu kuma moreshi sannan mu aikashi inda babansa ya tafi,na
tabbata wannan ya ishi babbarsa itama tabi sahunsu" qit aka katse kiran,salati suka
dauka baki dayansu,basu ankara ba sai ganin sumayya sukayi ta sulale a gurin,tashin
hankali sabo,a rude baki dayansu sukayi kanta.

      A hankali ta bude idanuwanta tana fadin


"Allahumma la sahla illa ma ja'altahu sahla,wa anta taj'alik hazna iza shi'ita
sahla" idanunta ya sauka cikin falon,wannan karon mutane sun dadu sabanin
dazu,malam ya abbakar kawu da mijin anty dije wato umar farouq duka suna cikin
falon,sai ta sanya kuka tana kiran sunan Allah,tausayinta ya kama kowa,wannan karon
babu wanda ya hanata,don sunsan cewa abun ya mata yawa,dole ta zubda hawaye ko zata
samu sauqin radadin dake cikin zuciyarta,a qalla kimanin minti goma tana kukan mai
fidda sauti kafin ta koma yin na zuci,sai a sannan 'yan sandam suka samu damar yin
magana,wanda yayi magana dazun wannan karon ma shi ya maganta
"Alhamdulillahi mun gode Allah,ba shakka wannan bincike ya zo mana cikin
sauqi,cikin ikon Allah sun sauqaqa mana wahalar bincike"
"Haka nace cikin zuciyata ASP,yanzu me kake ganin za'ayi,don ya kamata cikin
gaggawa a nemo yaron kada  su samu nasarar cutar da rayuwarsa" cewar mijin anty
dije cikin tsananin takaici da zaquwa
"Hakane alhj farouq,ina ganin zamuyi amfani da hikimar tracing layin har don mu
gano indo suke"
"Good,hakan yayi,kamar zuwa yaushe kenan ?"alh farouq ya sake fada
" daga yau zuwa gobe in sha Allahu zamu aiwatar da komai"
"Na gode ASP,na gode qwarai" alhj farouq ya fada yana bawa ASP hannu,sukayi sallama
daga nan suka fice.

     Hankalinsa ya maida ga su malam


"Malam,sai mu dage da addu'a,Allah ya bada nasara a gano ko su waye,ba shakka idan
aka ganosu ba zamu qyalesu ba,sai mun bi haqqin ran mukhtar da yardar
Allah....sumayya saiki qara haquri,Allah ya baki juriya ya baki ladan haqurin da
kikeyi". Godiya sosai su malam ya yiwa farouq gajin yadda yayi uwa yayi makarbiya
kan lamarin,bai gari ma sanda abun ya faru amma ya dawo ya karbi ragamar
al'amarin,a nan sukayi sallar azahar sannan suka tafi bayan ban baki da suka sake
yiwa sumayya.

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

5⃣1⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

_______________________________
*Innal laha ma'al lazinat taqau wallazina hum muhsinun*

*haqiqa Allah yana tare da masu jin tsoronsa,kuma yana tare da masu kyautatawa*
____________________________

    A hankali jerin gwanon motocin jami'an tsaron suka dinga kutsa kai cikin hanyar
don baza'a kirata layi ba,saboda sabuwar unguwa ce wadda ba'a kammala ginin nikan
dake cikinta ba balle a samu sukunin gabe layuka,kana iya bi ta ko ina,cikin gonaki
ko filayen dake daura da wajen wucewarka,motar dake gaba mutumin dake kusa da
mazaunin direba wanda shine shugaban 'yan sanda shi ya dauki wata waya da jami'an
tsaro suke magana don bada umarni zuwa sasanni dabaj daban ya kara a bakinsa yana
bada sanarwa ga sauran motocin dake biye da su a baya a kan su kashe jiniya,sannan
ko wannensu ya shrya don suna gab da qarasawa gidan da na'ura ta musu nuni cewa a
wannan gun layin wayar mukhtar ke aiki.

      Sosai suka dinga rage gudu har suka qaraso daura da gidan inda suka faka
motocinsu,ogan nasu ya sauka ya bawa kowanne umarni kan inda zai tsaya,kafin wani
dan lokaci sun zagaye gidan baki dayansa,daya daga cikinsu wanda ke sanye da kayan
gida saidai akwai qaramar bindiga boye a aljihunsa ya nufi qofar gidan kai
tsaye,yayi bugu kusan sau goma kafin ya jiyo wata kakkausar murya na tambayar
wane,nine yace aka sake maimaitawa da cewa kai wane
"Gun oga nazo,idan na baza'a bude ba ai harkar ba dole bace sai na koma akwai masu
jira na"ya fada cikin zafi zafi
" bari na sanar masa"mai maganar yace yana mai juyawa zuwa cikin gidan,a falon
gidan ya samesu harda ZAINAB dake zaune tana dakon zuwan mutumin da zata saidawa
abdallah da shi,wanda abdallah ke zaune gefe daya a falon cikin kashi da
fitsari,kwanukan da yake cin abinci da su suma sun gauraya cikin qazantar,yana
sanarmusu baqo yazo oga ya bada umarni a bude masa ga zatonsu mao siyan yaron ne
yazo.

      Yana kammala bude qofar yayi caraf ya damqeshi,bindiga ya nuna masa saitin
kansa yana cewa
"Duk wani motsi da zaka yi wanda zai alamtawa abokan aikinka akwai matsala dai dai
yake da harba alburushi cikin kwanyarka,muje ka nuna mana inda suke" kai ya kada
idanuwa a warwaje kamar an shaqe mujiya,alama ya yiwa sauran jami'an tsaron da zasu
shiga ciki suka biyo bayansu.

       Kusan su biyar ne a falon,ganin an taso dan uwansu da bindiga ya sanyasu


saita tasu
"Ku ajjiye makamanku,idan ba haka ba ku baqunci lahira" cewar wani gabjejen dan
sanda cikin kakkausar murya,da fari sun so suyi gardama,amma daga bisani da suka ga
yawan jami'an tsaron ya sanya su ajjiye makaman nasu aka tattarasu gu daya sannan
aka fara aikin daure musu hannayensu don yin gaba da su.

      Tuni cikin zainab ya duri ruwa,ta tabbatar cewa matuqar batayi wani abu da
zata wanke kanta ba tun anan babu shakka tata ta qare,saboda haka tayi hanzari ta
faki idanuwansu ta zagaya inda abdallah ke zaune cikim qazanta yana kallon kowa ta
kunceshi ta qanqameshi a jikinta duk wari da zarnin da take shaqa ta hadiyeshi,sai
ta saki kuka mai gunji tana fadin
"Allah na gode maka da ka kubutar da mu daga hannun wadan nan azzaluman,Allah abin
godiya" kukan nata na qarya yaja hankalinsu,wannan kakkauran dan sandan daya gama
qullesu ya kalleta yana zare ido,cikin daga tsawa yace
"Kefa?,daga ina?"ance mara gaskiya ko cikin ruwa gumi yake,take jikinta ya kama
rawa cikin rawar murya tace
" nice....nice uwar dannan,sato mu sukayi"baki dayansu 'yan sanda suka zuba mata
ido,kowa dai yasan case din rasa abdallah,hakanan sunsan uwa da ubanshi,to ita
wannan din wace da zata ce uwarsa ce
"Wallahi qarya take yallabai,ita ta bamu kwangilar kashe......." Wanda ya bude musu
qofa wanda da alama duk ya fisu tsoro ya fara rattabo bayani cikin rawar jiki
"Qarya ne sharri zai min" zainab ta fada cikin daga murya tare da yunqurin hanashi
tona mata asiri,take sai musu yaso ya balle tsakaninta da shi,shi yana son
bayyanawa ita tana son hanawa,yayin da ogan nasu haushin zainab ya tsaya masa a
wuya,ya tabbatar koma meye wannan kama sun yana da alaqa da aikinta da suka aiwatar
mata,ji yake ina ma bai ya da bindigarsa ba,da babu shakka sai ya fasa mata kai da
harsashi a take,amma babu komai,idan kere na yawo zabo na yawo zasu hade,tsawa
shugan 'yan sandan ya buga musu wadda ta sanyasu yin tsit
"Lawan,dauke abdallah,idris ka sanya mata ankwa itama,ko meye ma ya kawota nan din
muje bincike zai nuna" ya fada yana ficewa tare da yi musu umarnin su tafi,zainab
na zare ido na komai aka buga mata ankwa aka hadata da tsagerun aka tura cikin
mota,sun fara tafiya kenan ogan ya faki idon dan sandan dake tsare da su ya daga
kafceceyar qafarsa ya daki ta zainab cike da jin haushinta da ganin ta jaza musu
masifa,ji kake qasssssss zainab din ta saki wata razananniyar qara ta sume,shugaban
'yan sanda shi yace aci gaba da tafiya kada a tsaya idan anje station a mata duk
taimakon da za'ayi,yayin da yasa suka qara dora kula a kan oga don gudun kada ya
subuce musu.

Tun safe da taga fitar malam alhj farouq da kawu hankalinta ya kasa
kwanciya,duk da cikin damuwa take sai damuwar tata ta ninka ta da,jan carbi take
wanda shi ya zamo mata abokin hirarta tana share hawaye,har aka yi sallar la'asar
babu labarinsu,abunda ta kula da shi shine lokaci lokaci anty dije na daga waya
tana kiran mai gidanta,saidai babu wanda ta tambaya kamar yadda babu wanda ya
yimata bayani.

Cikin dakinta tayi sallar magariba tana jiran isha'i,ta zurfafa a cikin
tunani anty dije ta shigo
"Kizo inji su malam"
"To" ta fada ba tare da ta iya motsawa ba,gabanta ne ya tsananta faduwa,zuciyarta
ta ta cire tsammani ,wala'alla ba'a samu nasara ba,wala'alla ta rasa abdallanta
kamar yadda ta rasa mahaifinsa,shikenan haka Allah ya tsarama rayuwarta,sai ta kife
kanta jikin gado ta saki kuka
"A'ah,subhanallahi sumayya kuka dai?,ke da nace kije su malam da abban laila(alhj
farouq)na jiranki,tashi don Allah ki bar kukan nan haka" anty dije ta fada tana
qoqarin dagata,ita ta dafa don ba cin abinci take ba balle ta samu qwarin jikinta a
haka har suka isa falon.

Bata san ta saki anty dije ba,bata san kan qafafunta take tafiya ba sai data
isa gaban abdallah ta zube wanda ke kan cinyar ya abbakar,wani sabon kuka ta saki
tana yunqurin daukar yaron ganin yadda ya sauya cikin kwanakin da basu wuce goma
ba,yayi baqi ya rame goshinsa har da ciwo,a haka ma sai da aka kaishi wajen mama
tayi masa wanka ta bashi abinci yaci aka sauya masa sababbin kaya,qanqameshi tayi
tana sake sakin kuka mai cin rai,kowa tausaya mata yake tare dayi mata kyakkyawar
addu'ar yankewar qaddarorinta haka nan,a hankali alhj farouq ke bayani
"Alhamdulillahi an kama Abdallah tare da wasu wadanda babu shakka su sukayi sanadin
mutuwar mukhtar kamar yadda sukayi iqirari da kansu,tunda an kamasu da wadansu
abubuwa dake sake bayyanar da hakanne,cikin wadanda aka kama harda wata ZAINAB
wadda da fari ta musu iqirarin cewa itace mahaifiyarsa" da sauri sumayya ta dago
kai tana maimaita zainab cikin ranta gabanta na ci gaba da faduwa,alhj farouq ya
dora
"Amma abinda su yaran suka ce shine ita ta dauki ta basu aikin kashe mukhtar,sannan
daga bisani da taga ba zata iya biyansu sauran kudin ba ta sauya shawarar daukar
abdallah ta tafi neman kudi da shi,taga gwara su saida abdallah ta biya kudin
sauran tayi harkar gabanta" ba sumayya ba wannan karon,baki daya jama'ar dake falon
ba qaramin girgiza sukayi ba,wannan waccw iriyar masifa ce,tamkar ba diyar musulmi
ba,tamkar babu digon musulunci a jikinta,wannan karon cak kukan sumayya ya
tsaya,sunayen Allah ta dinga kira,tsoron zainab na kamata kamar tana wajen,kisa
zainab,kisa?,kisan mukhtar?,daga bisani wani hawayen ya sake subuce mata,har ta
gaji da kuka haka nan,ko da yaushe idanunta zafi suke mata saboda kuka,har wani
lokaci take gani hatsa hatsa,sai ta rufe idonta tana godewa Allah daya QADDARA mata
sake rayuwa da d'anta,ya kubutar mata da d'anta cikin aminci da salama,bata san da
wanne baki zata godewa uncle mukhtar mijin anty dije ba,ta sake jinjina masa da
yadda yayi zumunci irin haka sanda taji yana fadin idan aka kammala bincike cikin
'yan watanni qalilan insha Allah za'a soma shari'a,don dole abi kadin haqqin rai a
kuma hukunta duk wanda ke da hannu cikin lamarin,tabbas babu shakka indai har da
zainab cikin wadanda suka aikata wannan aiki mutum ya zama abun tsoro,to idan babu
sa hannunta shin me ya kaita wajen?,har tana iqirarin abdallah danta ne?,ita ce
mamarsa?
"Ya Allah ka yimin gata,ka shigemin gaba,ka yimin jagora cikin al'amuran rayuwa ta"
abinda ta dinga fadi kenan tana maimaitawa rungume da abdallah a jikinta,shi kansa
yaron kallonta yake tayi yana kiran ammi lokaci zuwa lokaci,haka yayi luf a jikinta
jikinsa a sanyaye yana jin dumin mahaifiyarsa.

****** ******** ******

*wai ina lukman ne?*

*kuyi haquri da wannan sabgogi sun sha min kai,ku tara gobe in sha Allahu*

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽

✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

5⃣2⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

_________________________________
*Allahu waliyyul lazina amanu yukrijahum minaz zulumati ilannur*

*haqiqa Allah shine majibancin lamarin wadanda sukayi imani yana fitar da su daga
duhu izuwa haske*
_________________________________

*ina muku fatan alkhairi baki dayanku kafatanin groups dake karanta KUNDIN
QADDARATA*

*GIDAN LUKMAN*

Baki daya rayuwar gidan ta yiwa karima baqi,kusan ita kadai ke rayuwarta
cikin gidan,yaran baki daya sun kwashe kayansu sunyi qaura zuwa bangaren
hajiya,tsakaminta da su kallo daga nesa,suna dai shigowa su gaidata su kuma
tambayeta mai zasuyi mata na aiki,hakanan duk abinda tace suyi matuqar bai sabawa
addini ko al'ada ba hajiyan na umartarsu suyi mata,lukman kam tunda ya hada kayansa
yayi tafiya zuwa legos tsawon watanni rabonsa da gida,saidai yakan kira wayar
hajiya wanda ya siya ya ajjiye musu a bangaren hajiya,yana kira suyi hira da yaran
ya kuma gaisa da hajiyan,sau tari idan tace ba zai dawo ba haquri yake bata,yace
sam yaji gidan ya fice masa ne a rai tunda sumayya ta bar gidan,hakanan yana zama
yana bata ran hajiyan,amma tayi haquri lokaci ne idan yayi zai dawo,sam karima bata
san ya sauya lamba ba saidai idan ta kira tayi ta jin is switch off,hakanan a yanzu
ba zata iya cewa ga inda lukman din yake ba,sai dai lokaci lokaci tana jin alert na
transper din kudi daga account dinsa zuwa naga,kudin buqatunta na yau da
kullum,sannu a hankali hankalinta ya fara tashi,wannan karon saboda rashin lukman
din a kusa bata da isashshen kudi gunta da zata koma wajen malaminta.

******** ***** ********

Sannu a hankali rayuwa ta dinga juyawa,kwanakin takabarta na raguwa,ta


fawwalawa Allah lamarinta baki daya,hakanan ta karbi QADDARArta hannu
bibbiyu,saidai ba'a raba zuciya da tuna abubuwa masu d'aci da suka gabatar
mata,yanayin sumayya ya sauya baki daya,ta sake zama mai yawan shiru shiru,sai
kallo da idanuwa,har yau jikinta ya kasa komawa dai dai,ta rame,sai uban fari data
sake yi sanadiyyar ramar da tayi,anty dije ta koma sai ita a gidan da zainab da
halima,su kawu sukace ta zauna tayi iddarta a dakinta don haka addinin musulunci
yafi so,lokaci lokaci ya abbakar da matarsa da suke kira anty sukan leqosu.

Ranar wata asabar wanda ya kama wata biyu da rasuwar mukhtar alhj farouq ya
iso kano,cikin falon sumayya suke zaune kamar yadda suka saba idan zama irin wannan
ya kamasu,bayan gaishe gaishe da qarin wani jajen alhj farouq ya soma gabatar da
maganar data tarasu
"Bayan dukkan wani bincike da jami'an tsaro suka gabatar ya bayyana cewa zainab ita
ta dauki nauyi ta kuma bada umarnin kisan mukhtar" duk sa suna zargin hakan amma
sai da maganar ta sake razanasu,kuka yaya yahanasu ta sanya tana salati da kalmar
shahada tare da ambatar sunan zainab,alhaj farouq bai kula ba ya dora
"Ta bayyana dalilinta na yin hakan da cewa bacin ran wulaqancin da mukhtar ya mata
ne na saki uku kuma yaqi maidata bayan kaahe kudaden da tayi wajen bin malamai amma
babu nasara,qarshe ma ya bita da dukan kawo wuqa,daga bisani kuma ta tsinci labarin
ya maida aurensa da sumayya bayan ita ta kamu da cuta mai karya garkuwar jiki ta
sanadinsa,tunda taga haka ta tabbatar bazai mayar da ita ba,sai taga gwara ayi biyu
babu kowa ya rasa,baya ga haka dama tana jin haushin sumayya na tsallake rijiya da
baya da tayi har ta haifi abdallah"alhj farouq ya saurara yana maida numfashi cike
da bacin rai,ji yake kamar ya shaqe zainab a lokacin da take wannan bayanin,tun
asali shi mutum ne mai tausayi da jin qai,baya qaunar zalunci sam a rayuwarsa
"La ilaha illa anta,yanzu sakayyar da zainab kika yi mana kenan,ashe kece ajalin
muntari?" Yaya yahanasu ta fada tana sakin kuka mai qarfi har da sheshsheqa,tana
jin cewa itace da alhakin mutuwar mukhtar,durqushewa tayi sannan ta ja jikinta da
qyar ta isa gaban sumayya wadda abdallah ke zaune a kan cinyarta tana
dubansh,idanuwanta sun gaji da kuka sai na zuci take wanda yafi ciwo
"Sumayya,don girman Allah,don darajar ma'aiki da iyayenki ki yafemin,babu shakka
ina ji a raina nice sikar ajalin muntari,Allah ya bawa muntari mace ta gari,ta daga
hankalina na hanaku zaman lpy don kawai baki samu abinda Allah ne kadai ke da ikon
bawa bawa ba,na yi masa aure na farko suka rabu bai isheni ishara ba,na sake dauko
masa wata na tsaya kai da fata sai da ya kawota cikin rayuwarku,ashe ita ce
ajalinsa,itace silar tarwatsa rayuwarku,nayi gaggawa na shiga hurumin ubangiji,idan
da na haqura ashe akwai rabon mukhtar bazai taba barin duniya ba sai ya haifi
abdullahi,sumayya ki yafemin,kimin afuwa,wallahi na tabbatar idan baki yafemin ba
haqqinki bazai taba barina cikin rayuwa ba....." Sai ta kasa qarasa abinda take da
niyyar cewa muryarta ta sarqe kamar idanuwanta zash tsiyaye saboda kuka.

Dubanta sumayya keyi kawai,ita yanzu a rayuwa me ya rage mata?,me zai bata
mata rai?,mene ribar taqi yafewa yaya yahanasun tunda mai afkuwa ta afku,babu mai
goge abinda ya faru,idan ta qullaceta mai hakan zai maganta mata?,koba komai taci
darajar mutum biyu MUKHTAR da ABDALLAH
"Allah ya yafe mana baki dayanmu" abinda ta fada cikin raunin murya,babu wanda
hakan bai burgeshi ba,godiya ta dinga jerawa sumayyan tare da binta da kyawawan
addu'o'i sannan ta juya ga malam
"Malam kaima ina neman afuwarka,abinda na yiwa diyarku da kuka bamu ita cikin
aminci da amana tun tana shekara sha uku amma naci amana,na bada gudun mawa wajen
mutuwar mijint...." Nan ma kasa qarasawar tayi saboda yadda lamarin ke mata ciwo
cikin zuciyarta
"Ya isa yahanasu,babu mai rayawa ko kashewa sai ubangiji,komai akwai sanadiyya amma
kuma Allah ya riga ya tsara komai,abinda ake so ga bawa dama shine,a duk sanda ya
fahimci yayi wani kuskure to ya nemi afuwa ya kuma guji aikata laifin a gaba,Allah
ya bamu dacewa baki daya"
"Amin ya Allah,amin" duka suka amsa,sumayya ta miqe don komawa ciki,haka take bata
son zama cikin jama'a balle tayi doguwar magana,a nan alhj farouq ya sanar musu
cewa ranar litinin za'a miqa zainab da sauran yaran kotu,amma basai sumayyan taje
ba insha Allahu tunda sun amsa laifinsu ba wata doguwar shari'a za'ayi ba.

******* ****** ********

Kwana goma ya rage mata ta kammala takabarta aka gama shari'ar wadda ta dauki
wata biyu ana yinta,bincike ya nuna zainab na da hannu dumu dumu wajen mutuwar
mukhtar,ita ta biyasu suka kunce tayar motar mukhtar a sanda yake shagon dinki zai
amso kayan dinkin sa,yayin da yaran data dauka aiki anjima ana nemansu,irin mutanen
da ake hayarsu ne suyi kisa,sun kashe mutane da dama hakan ya sanya aka yanke musu
hukuncin kisa ta hanyar rataya,zainab kuwa aka yanke mata hukuncin daurin rai da
rai,aka fara wucewa da ita asibiti,sabida a lokacin cuta mai karya garkuwar jikin
dake jikinta ta fara mata tasiri,zaman gidan kurkuku da tayi ba tare data fara shan
magani ba ya sata bayyana lokaci guda,alamominta duk sun gama bayyana,sannan
qafarta da oga ya daka ta karye aka mata dori dorin baiyi kyau ba,don da aka kwance
gun har ya fara ruwa yana neman lalacewa......

****** ****** *******

Ranar da ta kammala takabarta a washegari malam yace su dawo gida,kawun abdur


rahman shi ya nemi alfarma gun malam din yayi haquri a gama tattara dukiyoyin
muntari a raba gado,shikam yace babu komai duk abinda suka zartas dai dai ne amma
kawun yace a masa alfarmar dai,cikin qanqanin lokaci aka kammala hada komai na
mukhtar din,aka raba gadon kamar yadda ubangiji ya tsara,kusan dukiyar baki daya
abdallah ya cinyeta kasancewarsa d'a namiji qwaya daya tal wajen mahaifinsa,kawu ya
tattaro dukiyar baki daya ya kawo gaban malam,sam malam yace yaje ya riqe ya kula
da ita amma qememe kawun yaqi,daga qarshe suka yanke shawara aka danqawa ya
abubakar ya juya masa cikin kasuwancinsa da yake na saida atamfofi,addu'a sosai
suka yiwa abubakar din kan Allah ha tayashi riqo

*SABUWAR RAYUWA*

A kullum ta kebe kanta ita daya tunani take yi yaya rayuwa zata kaya
mata?,meyw kuma kundin qaddararta na gaba?,wanne shafi kundin zai bude mata
kuma?,amma a zahiri ta saki jikinta ko don yadda 'yan uwa da iyayenta suka damu da
ita,burin kowannansu ya faranta mata ya sanyata dariya,kowa tausayinta yake,tana
ganin bai kyautu ba taci gaba da zama cikin damuwa har ta sanya wasu,mukhtar dai ya
riga ya tafi ba kuma zai taba dawowa ba har abada duk kuwa yadda take
qaunarsa,qauna daya ce tsakaninsu kada ta manta da yi masa addu'a,hakan yasa ta
rungumi rayuwarta ta kuma rungumi danta,a lokacin cikin kudinta na tumunin takaba
ya abbakar ya ware mata wani abu yace ta fara sana'a,dama can sumayya ta iya
sana'arta,saboda haka babu bata lokaci ta shiga kasuwar kurmi ta saro kayan humta
turaren wuta na daki kaya dana tsugunno sai kwalakca ta koma tsohuwar
sana'arta,mutum ce ita mai nasibin sana'a,duk abinda ta sanya kanta ta fara saidawa
sai Allah ya kama mata,cikin ikon Allah kuwa sai wannan karon abun nata ya sake
bunqasa,cikin abokan ya abbakar akwai mutum uku da iyayen gidansh ke da
supermarket,suka buqaci ta kawo su gwada cikin shagon,ta samu kwalabe masu kyau da
tsari ta zuba,ba'ayi sati ba suka qare suka kawo mata kudinta suja sake nemam
wasu,cikin lokaci qanqani abun ya habaka,sai ta sanya halima da zainab ciki sukeyi
tare,tunda ta aikama anty dije itama take karba ta amfanin gida,wani lokaci ta
saida ko tayi kyauta.

Sana'ar da take yi ta dauke hankalinta sosai,ta rage mata zaman tunani da


kuka,saidai duk da haka babu wani abu da ya ragu na tunanin mukhtar cikin
ranta,hakanan duk dare kafin bacci ya dauketa sai tayi kuka mai isarta.

****** ***** ********

*_Bayan shekara daya_*

Koda kwana daya ne ya ratsa cikin rayuwar bawa ta iya yiwuwa kaga sauyi
tattare da rayuwar nan tasa,walau a sarari ko a boye,hakan ce ta kasance ga rayuwar
gidan su sumayya,wanda a wannan shekara guda din an sauya fasalin gidansu san sake
musu gini mai kyau da tsari cikin ribar kudin abdallah sumayya tasa aka yi wannan
aiki,sun sake samun rufin asiri sosai,babu abinda ta nema a rayuwarta ta rasa,ci da
sha da sutura baki daya,don har taimako takanyi cikin ribar sana'arta wanda bai
gaza dubu hudu zuwa qasa ba,an kawo kudin auren zainab wanda ba'a sanya rana ba ana
jira zuwa wani lokaci kafin na halima ya gama shiryawa kamar yadda yace a bashi
lokaci.

***** ********** ******

Sanye take da dogon hijabi mai hannu wanda har jan qasa yake,qafarta na sanye
da safa sai niqabi daure a fuskarta,wannan itace shigar data koma yi tun randa ta
taba fita wani ya biyota ta yiwa kanta alqawarin canza shiga,duk da dama can
ma'abociyar sanya hijabi ce,daga ranar ta bada kudi aka dinka mata su kaloli masu
kyau har kala biyar,ko ina zata su take sanyawa duk tsadar suturar dake jikinta,ko
yaushe kar suke a goge cikin tsafta da qamshi,shigar na matuqar yi mata kyau qara
mata kwarjini da kuma boye kyawun sufarta baki daya,dawowarsu kenan daga gidan anty
salma ita da halima ta kai mata humra da turaren wutar da ta yiwa wata amarya da
za'a yiwa aure 'yar maqotanta,daga nan ta tsaya aka musu lalle ita da haliman bayan
ta shiga kasuwa ta sayi kayan humra,saboda anty dije tace sati na sama tana nan
zuwa kano,har tana tsokanarta da ita zata koma abuja don ta fuskanci bata qaunar
zuwa abujan ko kadan,dariya sumayyan ta dinga yi tana tsokanar anty dijen itama da
cewa zaman garinku sai wanda ya saba,haka kawai kaje a qunsheka cikin gidan ba
motsin yara bana maqota saidai idan kai ka shiga.

Sam bata damu da sabuwar motar da ta gani ajjiye qofar gidansu ba suka wuce
zuwa cikin gidan ita da halima suna 'yan hurarrakinsu,tun daga soron gidan su
qamshin turare ke dukar hancinsu ba kuma irin turaren humrarta ba da ya kama
gidan,daga bakin qofar falonsu ta hangi takalma sau ciki na maza bata kawo komai a
ranta ba tadage niqaf dinta tayi sallama cikin falon.

Abdur rahman ne zaune cikin daya daga cikin kujerun falon sanye da shadda
ruwan madara wadda ta haska fatarsa,kansa hula ce zanna,hankalinsa na kan mama suna
taba hira da alama labari yake bata,sallamar su ce ta maido hankalinsa bakim
qofar,baki ya saki yana kallonta cikin mamaki kamar yadda ta saki baki itama tana
kallonsa cike sa mamakin yaushe ya diro nijeria
"Kai kam baka da aiki sai zuwan bazata?"
"Kawai kice yaushe a gari inji maqi baqo" ya fada yana murmushi,sai data samu gu ta
zauna sannan ta dubi mama
"Wai don Allah mama yaushe yazo?"
"Fitarku ba dadewa" sai tayi murmushi tana gaida shi,amsawa yake shima cikin sakin
fusakar suka fara dan tsokanar juna yadda suka saba,halima ce ta shigo wadda sai da
ta tsaya ta daura alwala,a ladabce ta gaidashi ya amsa yana dubanta
"Wai shekara daya tal naga duk kum qara girma,halima ke kam ashe ke kika debo kamar
sumayya"dariya tayi ta shige daki don tada sallah,mama ta miqe jin zainab na
kiranta tazo taga ruwan miyar tuwon daren data tsayar ya isa.

Maida dubansa yayi ga sumayya


"sumayya ya kuma bayan saduwa,bayan tafiyata lamura masu yawa sun wakana,Allah ya
jiqan yaya mukhtar,ya gafarta masa ya masa kyakkyawan masauki a aljanna yasa ya
huta"
"Amin ya Allah" ta fada wani miki na neman motsuwa a zuciyarta,zuciyar na son
karyewa hawaye na neman zuba,shuru ya ratsa dakin yana nazarinta,ya fuskanci ya
taba mata mikin dake zuciyarta
"Tunda nazo nake tambaya ina mutumina ashe yana gidan gwaggwo yahanasu,da yake ban
leqa gidan ba,jiya na shigo qasar" sai ta murmusa tana cewa
"Ayyah,ai da ya samu hutu sai tazo ta daukeshi da kanta" idanu ya zaro
"Kice abdallah an fara makaranta,lallai an girma"murmushi ta kuma tana bashi amsa
sanda mama ke dawowa cikin falon
"eh,ai yana cika shekara ya abbakar ya sanyashi"
"Wacce makaranta ce?"
"New egypt international" kai ya kada
"Masha Allah" hirar sai ta koma gun mama sai ta miqe itama tayi sallar
la'asar,bashi ya bar gidan ba sai da yayi magariba suka gaisa da malam sannan ya
ajjiye musu tsaraba dangin alawoyi da jallabiya ta maza data mata tasu sumayya
zainab da halima,sai tarin qananan kaya na abdallahnsa.

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*
*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)
5⃣3⃣
*Bismillahir rahmanir rahim*
_________________________________
*Allahu waliyyul lazina amanu yukrijahum minaz zulumati
ilannur*
*haqiqa Allah shine majibancin lamarin wadanda sukayi
imani yana fitar da su daga duhu izuwa haske*
GAISUWA MAI TARIN YAWA DA FATAN ALKHAIRI GAREKU
'YAN WATTPAD,BA SHAKKA INA JIM DADIN COMMENT
DINKU,HAKA INA GODIYA DA ADDU'O'INKU.
_________________________________
*GIDAN LUKMAN*
Baki daya rayuwar gidan ta yiwa karima baqi,kusan ita
kadai ke rayuwarta cikin gidan,yaran baki daya sun kwashe
kayansu sunyi qaura zuwa bangaren hajiya,tsakaminta da su
kallo daga nesa,suna dai shigowa su gaidata su kuma
tambayeta mai zasuyi mata na aiki,hakanan duk abinda tace
suyi matuqar bai sabawa addini ko al'ada ba hajiyan na
umartarsu suyi mata,lukman kam tunda ya hada kayansa
yayi tafiya zuwa legos tsawon watanni rabonsa da
gida,saidai yakan kira wayar hajiya wanda ya siya ya ajjiye
musu a bangaren hajiya,yana kira suyi hira da yaran ya kuma
gaisa da hajiyan,sau tari idan tace ba zai dawo ba haquri
yake bata,yace sam yaji gidan ya fice masa ne a rai tunda
sumayya ta bar gidan,hakanan yana zama yana bata ran
hajiyan,amma tayi haquri lokaci ne idan yayi zai dawo,sam
karima bata san ya sauya lamba ba saidai idan ta kira tayi ta
jin is switch off,hakanan a yanzu ba zata iya cewa ga inda
lukman din yake ba,sai dai lokaci lokaci tana jin alert na
transper din kudi daga account dinsa zuwa naga,kudin
buqatunta na yau da kullum,sannu a hankali hankalinta ya
fara tashi,wannan karon saboda rashin lukman din a kusa
bata da isashshen kudi gunta da zata koma wajen
malaminta.
******** ***** ********
Sannu a hankali rayuwa ta dinga juyawa,kwanakin
takabarta na raguwa,ta fawwalawa Allah lamarinta baki
daya,hakanan ta karbi QADDARArta hannu bibbiyu,saidai ba'a
raba zuciya da tuna abubuwa masu d'aci da suka gabatar
mata,yanayin sumayya ya sauya baki daya,ta sake zama mai
yawan shiru shiru,sai kallo da idanuwa,har yau jikinta ya kasa
komawa dai dai,ta rame,sai uban fari data sake yi sanadiyyar
ramar da tayi,anty dije ta koma sai ita a gidan da zainab da
halima,su kawu sukace ta zauna tayi iddarta a dakinta don
haka addinin musulunci yafi so,lokaci lokaci ya abbakar da
matarsa da suke kira anty sukan leqosu.
Ranar wata asabar wanda ya kama wata biyu da rasuwar
mukhtar alhj farouq ya iso kano,cikin falon sumayya suke
zaune kamar yadda suka saba idan zama irin wannan ya
kamasu,bayan gaishe gaishe da qarin wani jajen alhj farouq
ya soma gabatar da maganar data tarasu
"Bayan dukkan wani bincike da jami'an tsaro suka gabatar ya
bayyana cewa zainab ita ta dauki nauyi ta kuma bada
umarnin kisan mukhtar" duk sa suna zargin hakan amma sai
da maganar ta sake razanasu,kuka yaya yahanasu ta sanya
tana salati da kalmar shahada tare da ambatar sunan
zainab,alhaj farouq bai kula ba ya dora
"Ta bayyana dalilinta na yin hakan da cewa bacin ran
wulaqancin da mukhtar ya mata ne na saki uku kuma yaqi
maidata bayan kaahe kudaden da tayi wajen bin malamai
amma babu nasara,qarshe ma ya bita da dukan kawo
wuqa,daga bisani kuma ta tsinci labarin ya maida aurensa
da sumayya bayan ita ta kamu da cuta mai karya garkuwar
jiki ta sanadinsa,tunda taga haka ta tabbatar bazai mayar da
ita ba,sai taga gwara ayi biyu babu kowa ya rasa,baya ga
haka dama tana jin haushin sumayya na tsallake rijiya da
baya da tayi har ta haifi abdallah"alhj farouq ya saurara yana
maida numfashi cike da bacin rai,ji yake kamar ya shaqe
zainab a lokacin da take wannan bayanin,tun asali shi
mutum ne mai tausayi da jin qai,baya qaunar zalunci sam a
rayuwarsa
"La ilaha illa anta,yanzu sakayyar da zainab kika yi mana
kenan,ashe kece ajalin muntari?" Yaya yahanasu ta fada tana
sakin kuka mai qarfi har da sheshsheqa,tana jin cewa itace
da alhakin mutuwar mukhtar,durqushewa tayi sannan ta ja
jikinta da qyar ta isa gaban sumayya wadda abdallah ke
zaune a kan cinyarta tana dubansh,idanuwanta sun gaji da
kuka sai na zuci take wanda yafi ciwo
"Sumayya,don girman Allah,don darajar ma'aiki da iyayenki ki
yafemin,babu shakka ina ji a raina nice sikar ajalin
muntari,Allah ya bawa muntari mace ta gari,ta daga hankalina
na hanaku zaman lpy don kawai baki samu abinda Allah ne
kadai ke da ikon bawa bawa ba,na yi masa aure na farko
suka rabu bai isheni ishara ba,na sake dauko masa wata na
tsaya kai da fata sai da ya kawota cikin rayuwarku,ashe ita
ce ajalinsa,itace silar tarwatsa rayuwarku,nayi gaggawa na
shiga hurumin ubangiji,idan da na haqura ashe akwai rabon
mukhtar bazai taba barin duniya ba sai ya haifi
abdullahi,sumayya ki yafemin,kimin afuwa,wallahi na tabbatar
idan baki yafemin ba haqqinki bazai taba barina cikin rayuwa
ba....." Sai ta kasa qarasa abinda take da niyyar cewa
muryarta ta sarqe kamar idanuwanta zash tsiyaye saboda
kuka.Dubanta sumayya keyi kawai,ita yanzu a rayuwa me ya
rage mata?,me zai bata mata rai?,mene ribar taqi yafewa
yaya yahanasun tunda mai afkuwa ta afku,babu mai goge
abinda ya faru,idan ta qullaceta mai hakan zai maganta
mata?,koba komai taci darajar mutum biyu MUKHTAR da
ABDALLAH
"Allah ya yafe mana baki dayanmu" abinda ta fada cikin
raunin murya,babu wanda hakan bai burgeshi ba,godiya ta
dinga jerawa sumayyan tare da binta da kyawawan addu'o'i
sannan ta juya ga malam
"Malam kaima ina neman afuwarka,abinda na yiwa diyarku
da kuka bamu ita cikin aminci da amana tun tana shekara
sha uku amma naci amana,na bada gudun mawa wajen
mutuwar mijint...." Nan ma kasa qarasawar tayi saboda
yadda lamarin ke mata ciwo cikin zuciyarta
"Ya isa yahanasu,babu mai rayawa ko kashewa sai
ubangiji,komai akwai sanadiyya amma kuma Allah ya riga ya
tsara komai,abinda ake so ga bawa dama shine,a duk sanda
ya fahimci yayi wani kuskure to ya nemi afuwa ya kuma guji
aikata laifin a gaba,Allah ya bamu dacewa baki daya"
"Amin ya Allah,amin" duka suka amsa,sumayya ta miqe don
komawa ciki,haka take bata son zama cikin jama'a balle tayi
doguwar magana,a nan alhj farouq ya sanar musu cewa ranar
litinin za'a miqa zainab da sauran yaran kotu,amma basai
sumayyan taje ba insha Allahu tunda sun amsa laifinsu ba
wata doguwar shari'a za'ayi ba.
******* ****** ********
Kwana goma ya rage mata ta kammala takabarta aka
gama shari'ar wadda ta dauki wata biyu ana yinta,bincike ya
nuna zainab na da hannu dumu dumu wajen mutuwar
mukhtar,ita ta biyasu suka kunce tayar motar mukhtar a
sanda yake shagon dinki zai amso kayan dinkin sa,yayin da
yaran data dauka aiki anjima ana nemansu,irin mutanen da
ake hayarsu ne suyi kisa,sun kashe mutane da dama hakan
ya sanya aka yanke musu hukuncin kisa ta hanyar
rataya,zainab kuwa aka yanke mata hukuncin daurin rai da
rai,aka fara wucewa da ita asibiti,sabida a lokacin cuta mai
karya garkuwar jikin dake jikinta ta fara mata tasiri,zaman
gidan kurkuku da tayi ba tare data fara shan magani ba ya
sata bayyana lokaci guda,alamominta duk sun gama
bayyana,sannan qafarta da oga ya daka ta karye aka mata
dori dorin baiyi kyau ba,don da aka kwance gun har ya fara
ruwa yana neman lalacewa......
****** ****** *******
Ranar da ta kammala takabarta a washegari malam yace
su dawo gida,kawun abdur rahman shi ya nemi alfarma gun
malam din yayi haquri a gama tattara dukiyoyin muntari a
raba gado,shikam yace babu komai duk abinda suka zartas
dai dai ne amma kawun yace a masa alfarmar dai,cikin
qanqanin lokaci aka kammala hada komai na mukhtar
din,aka raba gadon kamar yadda ubangiji ya tsara,kusan
dukiyar baki daya abdallah ya cinyeta kasancewarsa d'a
namiji qwaya daya tal wajen mahaifinsa,kawu ya tattaro
dukiyar baki daya ya kawo gaban malam,sam malam yace
yaje ya riqe ya kula da ita amma qememe kawun yaqi,daga
qarshe suka yanke shawara aka danqawa ya abubakar ya
juya masa cikin kasuwancinsa da yake na saida
atamfofi,addu'a sosai suka yiwa abubakar din kan Allah ha
tayashi riqo
*SABUWAR RAYUWA*
A kullum ta kebe kanta ita daya tunani take yi yaya
rayuwa zata kaya mata?,meyw kuma kundin qaddararta na
gaba?,wanne shafi kundin zai bude mata kuma?,amma a
zahiri ta saki jikinta ko don yadda 'yan uwa da iyayenta suka
damu da ita,burin kowannansu ya faranta mata ya sanyata
dariya,kowa tausayinta yake,tana ganin bai kyautu ba taci
gaba da zama cikin damuwa har ta sanya wasu,mukhtar dai
ya riga ya tafi ba kuma zai taba dawowa ba har abada duk
kuwa yadda take qaunarsa,qauna daya ce tsakaninsu kada ta
manta da yi masa addu'a,hakan yasa ta rungumi rayuwarta
ta kuma rungumi danta,a lokacin cikin kudinta na tumunin
takaba ya abbakar ya ware mata wani abu yace ta fara
sana'a,dama can sumayya ta iya sana'arta,saboda haka babu
bata lokaci ta shiga kasuwar kurmi ta saro kayan humta
turaren wuta na daki kaya dana tsugunno sai kwalakca ta
koma tsohuwar sana'arta,mutum ce ita mai nasibin
sana'a,duk abinda ta sanya kanta ta fara saidawa sai Allah ya
kama mata,cikin ikon Allah kuwa sai wannan karon abun
nata ya sake bunqasa,cikin abokan ya abbakar akwai mutum
uku da iyayen gidansh ke da supermarket,suka buqaci ta
kawo su gwada cikin shagon,ta samu kwalabe masu kyau da
tsari ta zuba,ba'ayi sati ba suka qare suka kawo mata
kudinta suja sake nemam wasu,cikin lokaci qanqani abun ya
habaka,sai ta sanya halima da zainab ciki sukeyi tare,tunda
ta aikama anty dije itama take karba ta amfanin gida,wani
lokaci ta saida ko tayi kyauta.
Sana'ar da take yi ta dauke hankalinta sosai,ta rage mata
zaman tunani da kuka,saidai duk da haka babu wani abu da
ya ragu na tunanin mukhtar cikin ranta,hakanan duk dare
kafin bacci ya dauketa sai tayi kuka mai isarta.
****** ***** ********
*_Bayan shekara daya_*
Koda kwana daya ne ya ratsa cikin rayuwar bawa ta iya
yiwuwa kaga sauyi tattare da rayuwar nan tasa,walau a sarari
ko a boye,hakan ce ta kasance ga rayuwar gidan su
sumayya,wanda a wannan shekara guda din an sauya fasalin
gidansu san sake musu gini mai kyau da tsari cikin ribar
kudin abdallah sumayya tasa aka yi wannan aiki,sun sake
samun rufin asiri sosai,babu abinda ta nema a rayuwarta ta
rasa,ci da sha da sutura baki daya,don har taimako takanyi
cikin ribar sana'arta wanda bai gaza dubu hudu zuwa qasa
ba,an kawo kudin auren zainab wanda ba'a sanya rana ba
ana jira zuwa wani lokaci kafin na halima ya gama shiryawa
kamar yadda yace a bashi lokaci.
***** ********** ******
Sanye take da dogon hijabi mai hannu wanda har jan
qasa yake,qafarta na sanye da safa sai niqabi daure a
fuskarta,wannan itace shigar data koma yi tun randa ta taba
fita wani ya biyota ta yiwa kanta alqawarin canza shiga,duk
da dama can ma'abociyar sanya hijabi ce,daga ranar ta bada
kudi aka dinka mata su kaloli masu kyau har kala biyar,ko
ina zata su take sanyawa duk tsadar suturar dake jikinta,ko
yaushe kar suke a goge cikin tsafta da qamshi,shigar na
matuqar yi mata kyau qara mata kwarjini da kuma boye
kyawun sufarta baki daya,dawowarsu kenan daga gidan anty
salma ita da halima ta kai mata humra da turaren wutar da
ta yiwa wata amarya da za'a yiwa aure 'yar maqotanta,daga
nan ta tsaya aka musu lalle ita da haliman bayan ta shiga
kasuwa ta sayi kayan humra,saboda anty dije tace sati na
sama tana nan zuwa kano,har tana tsokanarta da ita zata
koma abuja don ta fuskanci bata qaunar zuwa abujan ko
kadan,dariya sumayyan ta dinga yi tana tsokanar anty dijen
itama da cewa zaman garinku sai wanda ya saba,haka kawai
kaje a qunsheka cikin gidan ba motsin yara bana maqota
saidai idan kai ka shiga.
Sam bata damu da sabuwar motar da ta gani ajjiye
qofar gidansu ba suka wuce zuwa cikin gidan ita da halima
suna 'yan hurarrakinsu,tun daga soron gidan su qamshin
turare ke dukar hancinsu ba kuma irin turaren humrarta ba da
ya kama gidan,daga bakin qofar falonsu ta hangi takalma
sau ciki na maza bata kawo komai a ranta ba tadage niqaf
dinta tayi sallama cikin falon.
Abdur rahman ne zaune cikin daya daga cikin kujerun
falon sanye da shadda ruwan madara wadda ta haska
fatarsa,kansa hula ce zanna,hankalinsa na kan mama suna
taba hira da alama labari yake bata,sallamar su ce ta maido
hankalinsa bakim qofar,baki ya saki yana kallonta cikin
mamaki kamar yadda ta saki baki itama tana kallonsa cike
sa mamakin yaushe ya diro nijeria
"Kai kam baka da aiki sai zuwan bazata?"
"Kawai kice yaushe a gari inji maqi baqo" ya fada yana
murmushi,sai data samu gu ta zauna sannan ta dubi mama
"Wai don Allah mama yaushe yazo?"
"Fitarku ba dadewa" sai tayi murmushi tana gaida
shi,amsawa yake shima cikin sakin fusakar suka fara dan
tsokanar juna yadda suka saba,halima ce ta shigo wadda sai
da ta tsaya ta daura alwala,a ladabce ta gaidashi ya amsa
yana dubanta
"Wai shekara daya tal naga duk kum qara girma,halima ke
kam ashe ke kika debo kamar sumayya"dariya tayi ta shige
daki don tada sallah,mama ta miqe jin zainab na kiranta tazo
taga ruwan miyar tuwon daren data tsayar ya isa.
Maida dubansa yayi ga sumayya
"sumayya ya kuma bayan saduwa,bayan tafiyata lamura
masu yawa sun wakana,Allah ya jiqan yaya mukhtar,ya
gafarta masa ya masa kyakkyawan masauki a aljanna yasa
ya huta"
"Amin ya Allah" ta fada wani miki na neman motsuwa a
zuciyarta,zuciyar na son karyewa hawaye na neman
zuba,shuru ya ratsa dakin yana nazarinta,ya fuskanci ya taba
mata mikin dake zuciyarta
"Tunda nazo nake tambaya ina mutumina ashe yana gidan
gwaggwo yahanasu,da yake ban leqa gidan ba,jiya na shigo
qasar" sai ta murmusa tana cewa
"Ayyah,ai da ya samu hutu sai tazo ta daukeshi da kanta"
idanu ya zaro
"Kice abdallah an fara makaranta,lallai an girma"murmushi ta
kuma tana bashi amsa sanda mama ke dawowa cikin falon
"eh,ai yana cika shekara ya abbakar ya sanyashi"
"Wacce makaranta ce?"
"New egypt international" kai ya kada
"Masha Allah" hirar sai ta koma gun mama sai ta miqe itama
tayi sallar la'asar,bashi ya bar gidan ba sai da yayi magariba
suka gaisa da malam sannan ya ajjiye musu tsaraba dangin
alawoyi da jallabiya ta maza data mata tasu sumayya zainab
da halima,sai tarin qananan kaya na abdallahnsa.
Mrs muhammad ce✍
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

5⃣3⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

*innash shaidana lakum aduwwun fattakizuhu aduwa*


*HAQIQA SHAIDAN ABOKIN GAABARKU NE,KU RIQE SHI ABOKIN GAABA*
___________________________

*Afuwan nayi mistake na number,yau ne zamu tashi page na 53*

___________________________________

        Yanayin sanyi ya fara ja baya,yayin da zafi ya fara sako kai,wannan shike


nuna alamu na tahowar damuna,mafi yawanci lokutan zafi bata iya bacci mai
yawa,hakan shi yake sanya ta tashin wuri,qarfe goma tuni ta kammala ayyukan
gidab,bata ma jirayi tashin zainab ko halima ba,wanka tayi ta sanya kaya sa'annan
ta debi kayan kari daga kitchen ta shiga falon mama,a zaune ta sameta itama tana
gyara mafitai tunda lokacin amfaninda su ya zo,kasancewar ba ko da yaushe ake samun
wuta ba,nan ta zauna tana karyawa suna hira da mama,bayan ta kammala ta dauko kayan
hadin humrarta tana fadin
"Mama bari kiga na fara hadawa anty dije tata,saura kwana biyar tazo kada lokaci ya
quren"
"Ai kam don idan tazo baki matan ba ke da ita,ya taku kada ku sakani ciki" dariya
sumayyan ta danyi tana bude robar ruwan turare
"Ai ba'a shiga fadan uwa da d'a mama,Allah mama tun ina mamakin irin qaunar da anty
dije kemin har naxo na daina" murmushi mama tayi
"Ko sanda muna gida tamu tafi zuwa daya ai,dana haifi abubakar lokacin bata yi aure
ba cewa tayi da sai ta karbeshi,sanda na haifeki kuma basa garin nan ita da farouqu
da tuni gunta zaki tashi,kinga kuma kina da shekara sha uku aka aurar da ke" kai
take jinjinawa tana hadin humrar tare da jin dadin labarin da mama ke bata.

      Halima wadda bata jima da tashi a bacci ba ta shigo dauke da wayar dake
burari sumayya wadda gunta wayar ta kwana tana miqa mata
"Yaya ana kiranki" kanta ta daga ta dubeta
"Waye?"
"Baquwar lambace" ta daga mata kiran sannan ta miqa mata,karawa tayi a kunnenta
tana mai sallama daga daya bangaren aka amsa mata sannan ta buqaci sanin
waye,ajiyar zuciya ya saki yana lumshe idanuwansa
"Amma kam banji dadi ba da har cikin sauri haka kika manta da ni sumayyah" gabanta
ne ya fadi,idan ba gixo kunnenta ke mata ba muryar lukman ce,dakewa tayi cikin
qarfin hali tace
"Ba abun mamaki bane don na mance muryar wanda ban sani ba" dariya ya dan saki
sannan yace
"Lukman ne sumayya,lukman tsohon mijinki wanda kuma yake fatan sake zamantowa
mijinki a karo na biyu" jikinta ne ya dauki bari,sai kawai ta katse wayar tana
duban halima da ta zuba mata ido tana kallonta,mamanta shiga uwar daki maida
mafitan
"Halima lukman ne wai" ta fadi muryarta na rawa
"Mene?,me ya gaya miki?"
"Ba komai"
"Shine kuma duk kika bi kika rude yaya,har yau kamar mune yayun kece qanwar
wlh,kinga,ki tsaya kiji me zai fadi bawai ki katse waya ba"
"Cewa yayi tsohon mijina mai kuma fatan sake zama mijina"
"Dole aka ce haka ce zata tabbata?" Ta tambayeta tana kallonta,shiru tayi bata amsa
mata ba,ganin bata da alamar ansawa ya sanyata juyawa zata fice,sai sumayyan ta
niqa mata wayar tace ta tafi da ita.

       Gabanta ne ya dinga faduwa,sai aikin nata ya koma sukuku sabanin dazu da


take yinsa cikin karsashi,har mama ta ankara saidai bata tambayeta ba,tana zaton ko
mukhtar ta tuna,da yake yawancin lokuta haka na faruwa da ita idan ta tuna shi,tana
shirin miqewa ta adana kayan haliman ta sake shigowa riqe da wayar,idanuwa ta
tsareta da shi
"Ya aka yi?"
"Ba lukman bane wannan karon ya abdur rahman ne" tsaki ta ja tana ci gaba da
ayyukanta,ta gama lura da take takensa
"Duk kanwar ja ce,dauki kice bana kusa"
"To" haliman ta fada tana daga wayar gami da ficewa daga dakin.

      Sai bayan kusa awa daya sannan ta dawo dakin tana dariya ta dubi sumayy
"Wlh yaya kin ban kunya,kinga ya abdur rahman ya gane fa,cewa yayi har da ni a yi
masa qarya ko,yace zaya zo anjima zamu hadu" shiru tayi ba tare da ta ce komai
ba,bata fata ko buri abdur rahman ya dora daga inda ya tsaya wajen yada
manufarsa,domin a yanzu bama abdur rahman ba,bata buri kowanne namiji ya sota,don
kwata kwata bata ji a rayuwarta zata iya sake yin aure,idan tayi tana jin kamar
taci amanar mukhtar ne,gwara taci gaba da rayuwarta a haka har itama tata tazo ta
tadda ita ta hadu da mukhtar dinta a jannatul firdausi.

      Idanu ta dinga zubawa tana addu'a kada yazo,addu'arta kuwa taci don baizo ba
din har suka kwanta,saidai washegari da yammaci ta gama wanka kenan tana shafa mai
taji muryarsa a tsakar gida,yau duka a kasalance ta wuni cikin mutuwar jiki,saboda
yadda lukman ya matsanta mata da kira da turo saqonnin ban haquri yafiya da kuma
yunqurin dawowa gareta,baki daya ya birkita mata kwanya,baisan yadda ta tsani batun
aure ba yanzun,sam ya fice mata a kai,ta yaya zatayi marmarin abunda tasha wuya
cikinsa,baki daya tarihin rayuwarta wahalar aure ce wadda ta cimmata ta jigata ta
cikin qananun shekaru.

      Ta kammala sanya kayanta tana shirin tada sallah wadda zata yita ne a makare
don lokacin ya fita zainab ta shigo wadda ta gama shiryawa zasu yinin biki ita da
mama
"Ya sumayya kizo inji yaya abdur rahman"
"Ina zuwa" tace tana yunqurin tada sallah
"To mu mun tafi inji mama,tace ki kula da yadfa halima zata sa sanwa kada tayi yawa
tunda yau banda malam" kai ta gyada mata don ta riga ta tayar din.

       Falo zuwa tsakar gida ta duba duka baya nan,hakan ya sanya ta leqa soronsu a
bakin sitting room ta hangi takalmansa,sai ta sanya silifas ta fita zuwa can,da
sallama ta shiga ya daga kamsa daga wayar da yake daddannawa ya dubeta,gefe can ta
samu ta gaidashi ya amsa idanuwansa na kanta,kallon ya fara mata yawa saboda haka
ta kau da kai tana shirin magana sai kuma ya rigata
"Nima sai an ja min aji sannan za'a fito?" Idanu ta watsa masa wadanda suka
sanyashi lumshe nashi idon,sau tayi murmushi ba tare da ta dubeshi ba tace
"Wanne irin jan aji kamar saurayin da yazo zance gurin budurwarsa"
"Ai hakanne,saurayin ne yazi zance gun budurwarsa ko kin manta?" Sai ta sake
dubansa,Maganar ta taba ta duk da ta tsammaci haka,shima ita yake kallo,cikin son
maida maganar wasa tace
"Ah ko?,to ai kayi kuskure,ka manta ni din ba budurwa bace,saboda haka saidai
bazawari yazo guna ba saurayi ba,saurayi sai budurwa ai"
"A haka na gani nake kuma matuqar so" shi kuma ya fada ba tare da alamun wasa
ba,ganin yanason maida zancen gaske sabanin yadda take son maidawa saita waske da
cewa
"Yau kuma tsurfa ce ta tashi daga toge a sitting room maimakon ka shiga ciki yadda
ka saba?"
"Neman aure nazo,kinga bai kamata naci gaba da shiga cikin falom surukai ina zama
ba" sai ta danyi dariya duk ason bagarar da zancan
"Ah wai...auren halima ko?"ya fuskanci da gangan take watsi da manufofin da yake
son yadawa,hakan ya sanya ya kira sunanta wanda ya tilasta mata dubansa
"kinsan ko a da idan na fadi magana irin wannan da gaske nake ko?,to har yau din ma
hakan take,da gaske sumayya na dawo neman aurenki ke karo na biyu babu wasa,kuma
ina fata wannan karon ni zan jefa qwallon"shuru tayi tana jin yadda zuciyarta ke
bugawa,mukhtar dinta ta tuna,ta daga kai tana kallon abdur rahman idanuwanta fal
qwalla
"yanzu kaima sai ka yarda naci amanar ya mukhtar?" Cikin rashin fahimta ya tsuke
gira
"Cin amana kamar yaya,da aurensa ne a kanki?,ina cewa koda yana raye halas ne na
aureki bare ya rasu?"
Kalmar ta mata ba dadi sai ta miqe
"A gunka mukhtar ya rasu amma ni a cikin zuciyata rayayye ne tamkar yadda kake a
raye" sai ta juya ta fice kuka na qwace mata,sam bayi tunanin wannan maganar ta isa
bata rai ba,amma da ya tuna cewa har yau tana cikin zafin mutuwar uban danta sai ya
mata uziri,hakan ya sanya daga sitting room din ya wuce ba tare da ya dawo ciki
ba,har dare ranta na a jagule,tana zaman zamanta yana neman jagula mata
lissafi,tana ganin kiransa ta share shima da yaga bata daga ba sai ya tura mata tex
ya qyaleta.

  *******    *******   ********

      Batasan cewa ana shirin jagula mata lissafi ba sai washegari da azahar data
tsinkayi sallamar su nuwaira a tsakar gidansu,baki daya yaran ne cikin kyakkyawar
kaka data bayyana mata har yau basu sauya kan turbar data dorasu ba,zuciyarta ta
dinga bugawa tsoro ya cikata,duk da a bangare guda tayi farinciki da ziyarar tasu.

       Sosai taji dadin zuwan yaran,basma ta dubeta


"Anty abbanmu ne ya kawo mu,yace wai kema zaki dawo gidanmu ko?" Yarinyar ta
tambayeta,murmushi tayi tana shafa kanta
"Basma,har yau surutu na nan kenan" ta fada da sigar son bagarar da maganar,tare
suka wuni da ita,suna zagaye da ita suna bata labarun gidansu da yadda lamura suka
sauya,inda sukayi dai dai ta yaba musu,inda suka kuskure ta gyara musu ta nuna musu
yadda akeyi.

     Da yamma bayan sun gama sallar la'asar sun sake cin abinci nuwaira ta dubi
sumayya
"Anty,don Allah ki daure ki dawo gidanmu,abba yace mu roqeki,muna sonki wallahi
anty,baki ga yadda hajiya ma ke son ki dawo ba,naji tana cewa ne ba zata sanya baki
ba tun yanzun,kada nauyinta ya sanya kiyi abinda bakiyi niyya ba ta shiga
haqqinki,don Allah anty ki dawo" ta fada tana karkatar da kai,sai islam ma ta matso
"Eh wallahi anty tunda kika tafi baki daya gidan babu dadi,ko abba ma barin garin
yayi,baifi wata daya da dawowa na,da ya dawo kuma kullum masifa suke da mama,gidan
ba dadi muna gun hajiya ko yaushe,ki dawo anty don Allah kinji" kasa magana tayi
baki daya,wato lukman kwaso mata yaransa yayi kenan su masa campaign ko su daure ta
da jijiyar jikinta?
"Anty baki ce komai ba" cewar nuwaira wadda ta qagu taji sumayyan ta amsa,murmushi
ta sanya ta kama hannayensu ta hade waje guda
"Kunsan komai nufin Allah ne,kuma ko wanne bawa da irin tasa qaddarar,to ku yita
addu'a idan akwai alkhairi zan dawo in sha Allah kunji?"
"To anty" suka fada jikinsu a sanyaye,duka sai suka bata tausayi,babu shakka yaran
abun tausayi ne,su masu uwa ma kenan bare mara uwa a gidan,ko da yake dace da uwa
ta qwarai shine jigon farinciki da jin dadin rayuwar 'ya'ya duniya da lahira.

       Qarfe biyar saura yaro yayi sallama gidan yace su nuwaira su fito,tuni basma
ta sheqa da gudu ta gano abban nasu sannan ta dawo
"Abba ne,yace ku fito",kyautar humra da kwalakca ta yiwa kowannansu,sannan ta zuba
wata da yawa ta hada da turaren wuta tace su kaiwa hajiya.

       A bakin qofar soro ta ja tunga tana musu sallama,nuwaira ta dubeta tana


narai narai da idanuwa
"anty iya nan ko qofar gida ma ba zaki rakamu ba?"dariya tayi,ta fuskanci wayo wai
yarinyar keson yi mata
"shikenan muje"ta fada don faranta musu,yana tsaye bakin mota ya bubbude qofofin,da
dai dai yaran suka dinga shiga tana musu sallama sannan ta rufe musu qofar
motar,tana dagowa suka hada idanu
"Ku gaida gida ku gaidamin hajiya" ta fada tana juyawa da niyyar shigewa ciki,da
sauri ya tari gabanta
"Haba mana sumayya,ko gaisuwa ai kya tsaya kuyi ko?" Ta tabbata idon yaran yana
kanta hakan ya sanyata tsayawa tana dubansa
"Don girman Allah sumayya kimin alfarma ki koma gida na,kimin alfarma ko don
rayuwar yara na"
"Ni kuma tawa rayuwar fa?" Ta masa tambaya kai tsaye
"Sumayya gida na ya sauya a yanzu,da qafafuna nake tsaye,hijabin dake lullube da
idanuwa Allah ya yamin shi,ki taimaka ki koma gidana ki sa cikasa mana sauran haske
da farincikin da muke da buqata,kowa a gida na na buqatarki sumayya,don Allah kada
ki gujemu". Kai ta kada
" lukman,bani da buqatar nayi aure har na koma ga mahalicci na,domin ina fata naje
na hadu da mijina uban 'ya'yana,ina mai baka shawara tun wuri kayi haquri da ni"ta
qarashe zancan zuciyarta na raurawa ta kewayeshi ta wuce ciki,jiki babu qwari a
sanyaye shima ya koma cikin motar ya tada ita ya bar layin.

Tana shiga zainab na miqa mata waya,bata san ko waye ba haka bata tambaya
ba,tama yi tsammanin anty dije ce don tace anjima zata kira ta,wayar ta maqala a
kunne,muryar abdur rahman ta mamayi dodon kunnen nata
"Ba mukhtar kadai ba,ashe har lukman ma na raye a zuciyarki?" Tambayar da ya fara
jefo mata kenan wadda ta sanyata saurin janye wayar daga dodon kunnenta,yaushe
abdur rahman ya ganta da lukman?,tambayar data yiwa kanta kenan,kawai sai ta tsinci
kanta da fashewa da kuka,saman katifarta ta fada tana kife kanta a saman filo,baki
daya cikin kwanaki hudu zuwa biyar kacal suna son lalata zaman lafiyar zuciyarta
ruhinta da ma gangar jikinta?,wa yace musu tana da buqatar aure a yanzu?,wa yace
musu tana buqatar wani daga cikinsu?,akan me zasu yi mata kutse cikin rayuwar data
lallabata ta fara samun nutsuwa da dangana?su suke suce ta mance da mukhtar ta fara
sabuwar rayuwa da su?,ta mance da mutumin da shi ya fara gina tunani da zuciyarta?.

Qarar wayarta karo na biyu ya sake katse mata tunanin da ya karade ilahirin
qwaqwalwarra,kamar ba zata daga ba sai taga lambar anty dije ke yawo bisa fuskar
wayar,qara fashewa tayi da kuka da taga sunanta,zuciyarta ta sake karyewa,tasan a
irin wannan yanayin babu wanda take budewa damuwarta irin anty dijen,taso ace a
yanzu tana kusa da ita,sai ta daga kiran da sauri,saidai maimakon sallama da anty
dijen ta tsammata sai taji sautin kukan sumayya ya karade kunnuwanta.

*mrs muhammad ce*👑

✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)
5⃣4⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

*Rabbukum a'alamu bima fi nufusikum*

*(haqiqa)ubangijinku shine mafi sani ga abinda yake cikin zukutanku*


_________________________________

       A rude anty dije ta soma tambayarta


"Lafiya sumayya?,me yake faruwa?,ko wani ne ya mutu?" Ta jero mata tambayoyin baki
daya,jin tayi shiru bata tanka ba ya sanyata itama shirun tana sauraren kukanta,ta
tabbatar wata matsalarce ta taso mata haka jikinta ya bata,tausayin yarinyar take
ji,sai yaushe ne zata fita daga matsala,sai data dauki a qalla minti goma sannan ta
soma magana cikin karayar zuciya
"Anty,lukman da abdur rahman"
"Me ya samesu?"
"Anty......dukkaninsu sun dawo,kowanne so yake na aureshi,fisabilillahi anty ni
bazan huta ba?,duka duka yaushe na soma samun nutsuwa?,anty bana buqatar sake wani
auren yanzu,tsoro nake ji kada su nufi malam da maganar,idan malam ya umarceni anty
bazan iya bijire masa ba" sai ta fashe da kuka,tsaki anty dijen tayi sannan tace
"Zancan banza,kema kin riga da kinsan cewa malam yasan haqqinki na hannunki
yanzu,ke zaki zabawa kanki miji ko?,sannan tsakanin lukman da abdur rahman akwai
wanda ya isa ya aureki ne bada amincewarki ba da zaki tadawa kanki hankali ki dinga
zubda hawayenki?,duk wanda kika zubar a baya bai isheki bane sumayya?,ko so kike
wani ciwon ya sokeki?,to nikam na gaji da ji da gani,kishirya da gaske idan nazi
tare zamu koma,idan yaso naga wanda zai qara bata ranki" ta fada tana katse wayar.

       Shiru tayi tana juya wayar a hannunta,ba haka taso anty dije tace ba
shawarar yadda zata kubuce daga tsakanin da lukman da abdurrahman suka sanyata take
so ta bata,amma da tayi tsai sai ta lura lallai babu hanyar da zata zille musun
idan ba barin garin kanon zata yi ba kamar yadda anty dije tace,sai ta sauke ajiyat
zuciya tana goge hawayenta,tana qiyasta idan ta bar kano koda na tsawon wata daya
ne itama ta samu hutu,ta samu ta manta da wasu lamuran ta manta da damuwoyinta.

  *******  *******   *******

  Washegari ta shirya don zuwa gidan yaya yahanasu ta dauko abdallah tunda duka
duka saura kwana biyu anty dije tazo,tana tsaye a falon mama tana sanya hijabinta
tare da yiwa mama sallama suka ji sallamar abdur rahman,kamar ta juya ta shige daki
amma tasan idan tayi hakan kamar ta nunawa mama akwai wani lamari tsakaninsu irin
wanda ya faru a baya,abinda bata da buri ko fatan kowa ya fahimta kenan
"Ina yini" sumayyan ta gaisheshi tana shirin ficewa bayan sun gaisa da mama
"Lafiya......ina zuwa haka?" Ya tambayeta yana dan dubanta,cikin hanzari ta soma
sanya takalmanta tana bashi amsa
"Zan dauko abdallah he gidan ya yahanasu"
"Yauwa,nafi jin dadin tafiya,dama jiya da naje na yiwa abdallah alqawarin yoghourt"
ya fada yana miqewa tsaye,kamar ta zura da gudu haka taji,take yanayin fuskarta ya
sauya wanda tashin farko ya fahimci bata ji dadin shishshigin da ya mata ba,saidai
sam bashi da damuwa matuqar zai kasance da ita,inda zata iya zata ce masa bata so
amma idanuwan mama ya sanya ta kasa cewa komai
"Sai mun dawo mama"
"Allah ya kiyaye hanya ku gaida min yahanasun"maman ta fada ba don son ranta ba,don
ba kasafai take barinsu suna shiga motocin gida ba koda na 'yan uwa ne,tafi ganewa
su hau ta haya
"Zataji" inji zainab wadda ita ce 'yar rakiyar.
      Gaban motar ya bude mata da kansa,sai da yaga ta shiga ta zauna sannan ya
zagaya nashi mazaunin ya tashi motar suka tafu,shiru ya ratsa motar,babu mai magana
tsakaninsu,sai ya sanya hannunshi ya dannan plate jikin redion motar,cikin sakanni
lacture malamin dake cikin fefan ta fara tashi,ya daj qaro volume din sannan ya
dauke hannayensa ya maida kan sitiyarin motar
"Nikam bansan wanne irin baqin jini ne da ni ba" ya fada qasa qasa yadda ita da shi
ne kawai zasu iya jin me yake fadi,ta gefen ido ta kalleshi don ta tabbatar da ita
yake ko kuwa,sai ta gane da ita din yake saboda yadda yake kallonta kadan
kadan,shiru tayi bata da niyyar tankawa saboda bata fuskanci ma inda zaurancen nasa
ya sa gaba ba
"Sumayya me nayi da jiya baki sona,yau ma kinqi karbata,ko na aikata miki wani
laifi ne?,ko ina da wani aibu da ban cancanci a soni ba?" Ya tambayeta yana mai
muradin jin amsarta
"Baka aikata komai ba,amma don son annabi mubar maganar nan,kada ka manta har yau
jinyar zuciyata nake bata warke ba,ban kuma san ranar warkewarta ba" ta fadi tana
duban gabanta ba tare da ta dubeshi ba.

     Shuru yayi yana jin yadda ransa ya quntata,karo na farko da ya soma jin kishin
nukhtar har cikin ransa,mukhtar jininsa ne wanda har ya mutu babu wani abu mara
dadi da ya taba hadasu,hakan ya sanya bai sake tofa komai ba har suka iso gidan
yaya yahanasun,tayi zaton zai shigo ne da ya ajjiyesu,sai taga ya juya kan motar
yayi gaba.

      A tsakar gida suka samu abdallan,yana ta wasa da dan qaramin keke da yaya
yahansun ta siya masa,jamila na faman binsa tana sauya masa kayansa da yayi kaca
kaca da su da miya amma yaqi yarda,ya maidata abar wasansa sai zagaye suke yana
dariya,yana ganinta yayi cilli da keken ya taho a guje ya dafeta yana dariya,itama
dariyar take,sai taji sanyi a cikin zuciyarta,yaya yahanasu da taji muryarsu ta
fito cikin fara'a tana musu sannu da zuwa.

      Ina ka saka ina ka ajjiye take tayi da su,kamar zata goya sumayyan,abdallah
ya wani ajiye kumatu,abinda yakeso kawai yake cikin gidan,sai bayan sallar magariba
sannan suka shirya tafiya,qeme me abdallah yace ba zai bisu ba,saidai sumayyan
itama ta dauko kayanta ta zauna anan,dariya suka dinga yi,ganin haka ya sanya
sumayyan tace a barshi,duk sanda ya gaji ya dawo.

      Ga mamakinta suna fitowa ta tadda abdur rahman tsaye qofar gidan,qofa bude
yana kallonta,ta fuskanci me yake nufi saboda haka babu musu ta shiga,zainab ma ta
bude gidan baya ta shiga,sau daya rufe sannan taga ya shiga gidan,baifi mintina
biyar ba ya fito suka tafi,har suka je gida baice uffan ba,ya saukesu ta masa
godiya ta wuce,tana shirin kwanciya saqonshi ya shigo wayarta,saqo ne dake dauje da
kalamai masu nuna tsantsar qauna,da nuna ba za'a rabu da abinda ake so ba,tana gama
karantawa ta goge ta kwanta,tana ayyana ta kusa nesa da dukkan wadan nan rudanin.

  ******   *********   *****

   *BAYAN KWANA BIYAR*

   Anty dije suka iso kano ita da yaran da mai gidan baki daya,gidansu na da anan
suke masauki duk sanda suka zo din,bata samu zuwa gidansu sumayyan ba sai bayan
kwana biyu da zuwan nata.

       Sha daya da rabi na rana suka iso baki dayansu,sun sauya baki daya daga anty
dijen duka sunyi kyau da wata irin gogewa,kana ganinsu kasan kwanciyar hankali da
hutu sun samu wajen zama,duk suna falon mama,maman da anty dije suna hirarsu ta
zumunci,yaran duka sun kewaye sumayya suna ta bata labari,mutuniyar tata minar na
zaune dare dare kan cinyarta,laila ce ta soma tambayar Abdallah wanda hakan ya
janyo hankalin anty dije
"Nima fa ban ganshi ba" injita,murmushi mama tayi
"Mu zai nunawa 'yan ubanci ai,tunda yahanasu ta daukeshi kinga yaqi dawowa,uwar ma
taje da kanta yaqi biyota" haba anty dijen ta riqe tana dariya
"Yanzun haka zamu tafi ki barshi a kano?" Tayi maganar ta sigar tambaya tana duban
sumayya,dariya sumayya tayi
"Wai da gaske anty sai na bikin?,to idan naje ma kwana nawa ne zan dawo ai ba
dadewa zanyi ba" dubanta anty dijen tayi cikin mamaki
"Wai meke damunki da baki son abuja ne kamar ana gutsurarki" tabe fuska tayi kamar
qaramar yarinya
"Garin ne ni banjin dadinsa anty haka kurum" kanta ta dauke daga kan sumayyan tana
cewa
"Sai kiyi kuma,mu me ya cimu?,"
"Yaya asama'u(sunan mama na asali)Allah yasa dai malam na gari,don tun yau nakeson
sanar masa da sumayyan zan tafi,na lura kamar ku din a nan bata samun kwamciyar
hankali da nutsuwar data dace,dama can baya kun yimim alqawarin bani ita kuma aure
ya fado mata da wuri,kinga yanzu sai a cikamun alqawari na"dariya mama tayi tana
cewa
"Malam yana nan ya fita ne taron bude wani sabon masallacin juma'a da aka gina,amma
nan da biyar ko shida na yammaci zai dawo"
"To Allah ya dawo dashi lpy,ina nan har ya dawo"
"Amin" inji mama.
"Momy,wai anty da ita zamu tafi?" Khalipha ya fada cikin murna da doki yana dora
hannunsa hannunshi kan cinyar anty dije
"In sha Allahu" ta bashi amsa,
"Yeeeeeyyyyyy" yaran suka sanya ihu baki daya har suka sanya sumayyan ta tuntsire
da dariya duk da yadda jikinta yayi sanyi da zancan tafiyar tata.

Anty dije ko bata tafu din ba har sai da malam ya dawo,sanda ta tuna masa
tsohon alqawarin da suka mata dariya ya saka sosai,don shi sam ya manta da maganar
ma baki daya,shi kansa cikin yaransa yana son sumayya,tana da baiwa da wasu halaye
na daban da ba kowa ke da su ba,amma babu yadda ya iya,tilas ya cika alqawarin da
ya dauka duk da cewa tsoho ne,yace ya basu sumayya halak malak indai suna so,da
yake gaban alhj farouq akayi shima yaji dadi sosai,har da shi a godiya,don shima
yasan halayen sumayyan,ya tabbata ko zama tayi cikin yaransa zasu qaru da
ita,hakanan zata taimaka ma matarsa zasu dinga ganin nasu na gida a kusa da su saji
dadi.

Sanda labari ya iske sumayyan sai jikinta yayi sanyi saidai a fuska bata nuna
komai ba ko don darajar yaran dake ta munnar zata koma gidansu,ya zata iya rabuwa
da mahaifarta?,inda ta taso tayi wayo ta gabatar da rayuwarta baki daya?,inda anan
dukkan wani tarihi na rayuwarta ya samo asali ya kuma kafu?,zata bi anty dije amma
bata jin zata iya zama a garin din din din,zainab ce ta zungureta tana fadin
"Wai nikam wacce iri ce ke yaya sumayya don Allah,ina ma nice anty dihe tace zan
koma gurinta,wallahi da kinga yadda ake abu" harara ta watsa mata
"Yanzun ma ki gayawa Abdulmalik kin fasa aurensa sai kizo ayi musaya da ni ke ki
bita ni na zauna" dariya ta tuntsire da ita,tana son taga yaya sumayyan tata na
masifa,sai tayi mata wani iri saboda bata saba ba ba al'adarta bace
"Bazan iya ba wallahi,ni da abdul malik jini da hanta ne"
"Madalla" ta fada taba juyawa taci gaba da abinda take cikim zuciyarta tana musu
kyakkyawan addu'a da fatan dacewa da rayuwar aure mai inganci ba irin tata ba data
kasance farkonta zaqi,qarshenta madaci wanda har yau take fama da taunarsa dacin
bai bar bakinta ba,har yau duk farincikin da take ji idan ta tuna mukhtar sai ya
gushe,duk sukunin da take ciki idan ta tunashi sai ya tarwatse,ko a yanzun data yi
wannan tunani sai da hawaye suka biyo kuncinta.

To sati daya anty dijen ke da niyyar yi,siyayya dama zasuyi kasancewar ba


zasu sake dawowa kano ba sai bayan qaramar sallah,haka ta dinga zuwa tana daukan
sumayyan suna shiga kasiwa siyayya,a kwanakin baki daya sumayya bata zama bata da
sukuni,hakan ya sanya abdur rahman ko lukman babu mai sukunin ganinta,saidai kullum
ta Allah saqonninsu na tafe ta ma'adanar saqonnin na wayarta,wani lokaci har da
tarin misscall na kiran da bata daga ba,taso sumayyan ta dauki kayayyaki amma tace
bata buqatar komai,data matsane ta yanki sababbin yadin hijabai da zasu kai mata
har qasa ta bayar a dinka mata,anty dijen nata tsokanarta mai hijabai bqta ce komai
ba ta dai yi dariya don ita a yanzun babu shigar dake mata dadi irin ta hijaban.

Ana ya jibi zasu tafi bayan sun dawo daga kasuwa,suba zaune falon anty dije
sumayya na tayata hada kaya wayar anty dije daga hannunsu laila ta dauji ruri,da
sauri lailan ta sauko saga kan kujera ta nufi anty dijen tana cewa
"Hajiya mama ce take kiranki"
"Kamar kuwa tasan suna raina" anty dijen ta fada tana karbat wayar,sumayya nata
shirya kayan ita kuma na wayar har ta kammala tana fadin
"Komawa kasuwa ya kama mu fa gobe sumayya" tana zuge zif din jakar matafiya ta
trolly ta dago kai ta dubeta
"Naji kamar dazu kince kin kammala siyayya ko kinyi mantuwa ne?,nikam ma gaji da
shiga kasuwan nan wlh kinsan ban taba shiga kasuwa haka ba?"tana zama gefan kujera
tace
"Nima kaina na gaji sumayya,amma hajiya mama ce tafi qarfin komai gunmu,ko abban
laila sai da ya soma qorafi jiya wai kasuwannin kano zamy siye ne baki daya har yau
bamu gama siyayya ba?" Ta qarashe tana dariya sumayya na tayata
"Amma idan nace masa hajiya mama ce nasan bazai hana ba,ki kwana nan kawai gobe sai
muje,atamfofi take so supers zatayi barka"idanuwa sumayya ta zaro
"da super zatayi barka?"murmushi anty dije tayi
"hajiya mama ce fa?,akwai yin harkar girma" shiru sumayya tayi sai data gama ta
ture jakar gabanta sannan tace
"Nikam bazan kwana a nan ba,ni da ku ganni sai randa zamu tafi ku biyo
daukata,zanje na qarasa jin dumin tsohuwata" hararata anty dije tayi
"Kome zaki fada saidai ki fada an riga an bamu ke kuma kin badu,so kike kice zaki
ji duminta kafin jibi mu rabaki da ita ko?" Dariya ta qyalqyale da ita
"Ni ba haka nake nufi ba anty"
"Koma hakanne gobe da yamma kizo muje"
"To" ta amsa tana dan miqewa saboda bayanta da ya qage,kiran abdur rahman ya katse
mata hutun nata,da kamar ba zata daga ba sai kuma ta kasa
"Gimbiya sumayya,ni yanzu lallabawa nake,naga alama ganinki sai an cike foam"
"Baka fara cike foam din ba ka dai kusa ka fara cikewa" ta fada a zuciyarta,a fili
kuwa sai tayi 'yar qaramar dariya data sanyashi lumshe iso saboda yadda sautin ya
ratsashi
"Ko kadan,sabgogi ke sukayi yawa,ina tare da anty dije kasan jibi zata koma"
"Ayyah,amin gaisuwa gurinta don Allah,naso in shigo mu gaisa na fara kamun qafa
saidai yanzun haka ina sokoto,baki ma sani ba saboda baki damu da ni ba" murmushi
kawai tayi mishi,a ranar ta sake masa sun taba hira,hakan ya masa dadi sosai,itama
sai ta danji dadi a ranta,saboda rabon tayi hira haka da wani har ta mance,sanda ta
gama taga misscall din lukman kusan goma,bata bi ta kaiba ta kashe wayar,anty dije
ce ta dinga tsokanarta kodai ta barta kanon kawai,murmushi tayi wanda baikai zuci
ba,don har ga Allah bata son ayi mata maganar aure,sai magariba sannan ta koma
gida.

IDAN NA SAMU LOKACI WATAQIL ANJIMA KU SAMU WANI,IDAN KUMA KUNJI SHIRU TO BAN SAMU
DAMA BA.
*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

5⃣5⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

*wa lillahi Aaqibatul umur*

*qarshen al'amari mallakar Allah ne*

__________________________________

*WANNAN SHAFIN SADAUKARWA NE GAREKI*

*UMMU RAMLAT(meena slimzy novel group)*

Qarfe sha daya na safiya su Anty dije ta qaraso da motar su wadda drivern su
ne zai ja motar kamar yadda suka zo,alhj farouq tuni shi ya riga su komawa saboda
kira da ya samu daga wajen aikinsu.

Tuni aka sanya kayanta a mota saidai ta tsaya sallama da mama,hawaye ne ya


balle mata sanda suke sallaman,dariya maman tayi
"Saikace wadda aka ce idan ta tafi ba zata dawo ba,jeki don Allah sunata jiranki
kada ku bata lokaci a hanya" halima da zainab ne suka rakota har bakin motar,tana
shirin shiga halima tace
"Yaya sumayya,me za'a cewa yaya abdur rahman idan yazo,baki sanar masa ba fa,sannan
baki bar saqo ba"
"Ki fada masa duk abinda kika ga ya dace" dariya sukayi don sun fuskanci gatse take
musu,tana shiga yaran suka fara raba gardama,kowa na fadin kusa da shi zata
zauna,motar akwai yalwa,sit uku ne da ita harda gun mai tuqi na hudu,hakan ya
sanya ta tattara ta koma sit din cab qarshe ita da laila da minal,khalifa da hafiz
na sit na biyu,anty dije ita kadai na sit na uku wanda ke kusa da driver tana
rubuce rubucenta da lissafi na siye siyen da tayi don ta taba kudinta sosai har ta
so shiga kudin abban lailah shi yasa tace su barta tayi lissafi,saidai duk da ita
daya ce a sit dinta hayaniyarsu bata barta tayi aikin da take so ba,sun cika motar
da karadi sumayya na biye musu,duk da zuciyarta babu dadi amma haka ta dinga biye
musu har suka hau kwalta sosai,minal ita ta fara bacci sannan hafiz da yake bashi
da son hayaniya sosai,khalipha shima yabi sahu sai laila ta dinda dariya tana cewa
"Yauwa kwa qyalemu ni da anty sumayya ta muyi hirarmu",su biyu suka dinga hirarsu
tafiyar tasu naci gaba da gangawarawa,kafin a kai zaria sai ya zamto motar babu
kowa sai sumayya da anty dije wadda sai lokacin ta samu sukunin yin aikinta.

Suna shiga kaduna suka farka baki dayansu,nan anty dije ta sanya salihu
direban nasu ya wuce da su wani gidan cin abinci (restaurant)da sukan tsaya suci
abinci duk sanda zasu taho kano ko zasu koma abuja,cikin mintina qalilan suka isa
da yake kamar kan hanya yake,sai da suka fara shiga masallacin dake daura da wajen
suka bada farali sannan duk suka fito sumayya na dauke da minal take ta saje da
'yan garin,tun a hanya ta dinga qarewa yanayin garin kallo,akwai yawaitar mata masu
dogon hijabi da niqab kamar nata,sai kuma qabilu data lura suna da wani kaso na
musamman cikin garin,baka tafiya daya biyu baka gansu ba cikin irin nasu
shigan,hakan ya sanya ta yiwa garin hasashen gari mai tarin mabanbantan qabilu da
yare.

Table biyu suka kama kowanne nada kujeru uku uku,daya sumayya laila da
minal,sau dayan kuma anty dije hafiz da khalipha,salihu kuma na can wajen wani
tsohon abokinsa ya karbi nashi abincin yana ci suna hira.

Kowa cin abincinsa yake cikin kwanciyar hankali,saidai sam ita ta kasa cin
nata,hasalima jinta take a takure tamkar ita kowa yake kallo saboda bata taba zama
gu irin wannan taci abinci haka cikin guri dake cakude da maza da mata ba,ko da can
ita mai kunya ce rashin sabo da rashin saurin sakin jiki,don haka minal kawai take
ta bawa abincin idanuwanta na kan minal din duk motsin da take,don a tsarge take.

tunda ta shigo gun ya zuba mata na mujiya,sau biyu suna hada idanu yana
jifanta da murmushi,hakan ya sanya ta saka hannunta ta maida niqabin fuskarta,duka
anty dije na ankare da yadda take a takure,saidai bata san dalilinta na sakin niqab
din ba,ta dai dauka rashin sabo ne na shiga irin wadan nan wuraren,laila ce ta
dubeta tana dariya
"Wai anty sumayya anan din ma sai kin rufe fuskarki,wurin cin abinci ne fa kowa
abinci yake ci,duba ki gani" ta fada tana waiwayawa tare da yi mata nuni da ido,sai
itama lailan idanuwanta ya kai kansa,matashine wanda zaiyi shekara talatin da
biyu,fari ne sosai,yana sanye da shadda ruwan madara dinkin yarbawa,kansa babu
hula,kallo daya zaka masa kasan cewa hutu ya ratsa jikinsa,su uku ne saman
teburinsu shi da wasu matasan da aqalla zasuyi shekaru daya,biyun cin abincinsu
suke suna duba wayar da take hannun na kuaa da shi,sam basu ma lura da yanayin da
dan uwansu ke ciki ba
"Anty sumayya,kinga wani sai kallonki yake ya sanki ne?" Laila ta fada cikin sigar
gulma murya qasa qasa taba ranqwafowa kan teburin
"Ku da kuke wucewa ta gun baki sanshi ba sai ni da yau na fara zuwa" sumayya ta
fadi tana gogewa minal baki da tissue bayan ta gama bata abincin
"Ku taso mu wuce ko?" Anty dije tace tana daukar minal don ta ragewa sumayya tayi
gaba suka bita a baya,da kanta taje wajen biya da yake har sun saba da su
sosai,tasa aka hado takeaway saboda sumayya don ta lura bata ci komai ba ta amsa
sannan suka wuce.

Suna shiga motar laila tace


"Lah,wallahi anty sumayya kinga har ya biyo mu ya koma,ta fada tana qyalqyala
dariya"
"Waye ya biyo mu" anty dije ta tambaya tana qoqarin maida atm dinta jaka
"Ba kowa" sumayya ta fada da sauri sannan ta juya tana kallon laila,harararta tayi
sannan tace
"Bana son surutu komai kika gani kiyi magana kai,idan ba haka ba bazamu shirya ba"
"Sorry anty sumayya" ta fada tana narke fuska don ta cikawa su hafiz baki ita ce ta
gaban goshin anty sumayya bata son su gansu a rana
"Shikenan" ta fada tana gyara zamanta,sai da suka sake daukar hanya sosai sannan ta
lalubi wayarta da niyyar kiran yaya yahanasu,sai taci karo da misscall din abdur
rahman,sai kuma saqon SMS
_garin masoyi baya nisa,ina miki fatan alkhairi_ abinda kawai ya rubuta kenan,bata
fahimci zaurencen nasa ba saboda haka ta share ta lalubi lambar yaya yahanasun ta
danna kira,ringing biyu ta daga,cikin mutunci suka gaisa sannan aka nemo mata
abdallah aka hadata da shi,hira ya dinga mata wani shirme wani abun dariya haka ta
dunga dariya,daga bisani su laila suka amshe wayar suka yita shirmensu su da shi
sai da suka cinye nata credit dinta tatas sannan suka haqura,bayanta ta maida
makarin kujerar ta lumshe idanuwa zuciyarta fes tana jin dadi da jin muryar
abdallah da tayi,tabbas d'a ba wasa bane,ababe ne masu wanke zukatan mahaifansu
koda da shirme da quruciyarsu kadai,tunanin mukhtar shi ya ratso cikin farincikinta
ya gusar da shi cikin yab sakanni qalilan,taje fuskarta ta sauya,damuwa ta lullube
zuciyarta,taso abdallah ya rayu da mahaifinsa,yaci gaba da cin gajiyar gata da
mahaifinsa ya tanadarwa rayuwarsa saidai ina,tsarin ubangiji shine daidai,tana jin
hayaniyar su laila amma tayi fakare kamar mai bacci,bata sake bude idanuwanta ba
har suka shiga garin abuja.

Qarfe biyar da rabi suka isa garin,bata mance yadda unguwar tasu take ba saidai
an sake samun sauye sauye,sabbin gine gine da kuma sabunta tsoffin.

A falo suka zube baki dayansu wanda basu tashi ba sai da lokacin sallar
magariba yayi sannan kowa ya debi kayansa zuwa daki,a dakin laila da minal ta zabi
zama,kasancewar gado uku ne a dakin,daki ne madaidaici wanda ke shimfide da tiles
da labulaye sai fenti dukkansu kala daya,wardrobe ce irin ta jikin bango wadda ta
cinye bango guda,sai madubi a wani bangon daban,daya bangaren kuma gun ajitar
takalma ne zuwa su jakankunan makarantarsu,daura da nan kuma qofar bandaki
ne,sallah ta sanyasu suka fara yi sannan suka bude kayansu suka koma maidasu
muhallinsu,a wanke a goge suke dawo da kayansu kamar yadda suka tafi da su.

Anty dije ce ta turo qofar dakin ta shigo,wannan karon ta sauya kayan jikinta
da alamu ma wanka tayi don sai qamshi take zubawa ta dubesu tana zama gefan daya
cikin gadajen dakin
"Sannunku da himma,hala ma ko wanka ba wanda yayi a cikinku ko?"
"Ummi sai mun gama gyaran kaya"inji laila
"eh kam bakwajin yunwa ne" anty dije ta sake fada,murmushi sumayya tayi din itakam
ba yunwa tattare da ita,miqewa anty dije tayi
"Idan kun gama ga takeaway can da abban laila ya shigo da shi sai ku dauka
kuci,nikam ina ga sai da safe zamu sake haduwa da ku"
Minal ce ta miqe da sauri
"Ummi zani gun abba"
"A'ah,ya shiga daki shima a gajiye ya dawo,abba sai da safe ki kwanta ga anty
sumayya nan sumayya sai da safe,ayi kwanan baqunta lafiya" dariya duka sukayi
sumayya tace
"Allah ya bamu alkhairi anty"
"Amin" ta amsa tana ficewa.

Kamin wani lokaci sun gama kintsa komai,sai da suka ci abincin sannan suka yi
wanka kowacce tayi shirin kwanciya,tana saman gadonta lullube da bargo saboda ac da
laila ta kunna wayarta ta soma haske sabida ta maidata silent,abdur rahman ne kamar
ba zata daga ba saboda bacci take da buqatar yi,amma sai taga hakan bai dace ba,a
mutunce ta gaida shi ya shaida mata ya kirata dazun kiran bai shiga,ta sanar
masa,mai yiwuwa lokacin suna kan hanya ne ba service,qorafi ya shiga yi mata kan
dalilin tafiyarta bata sanar masa yace
"A qalla ko addu'a sumayya na miki ko?,har yau kinqi gayan dalilin da ya sanya baki
sona" baki ta bude kamar yana ganinta
"Ni bance ma bana sonka ba abdur rahman,kawai dai ina da buqatar hutu ne cikin
rayuwata,har yau zuciyata da qwaqwalwata basu zama fresh ba,kuma ko baya ga haka ma
banson na zalunceka,don banajin akwau mahaluqin da zanso kwatankwacin mukhtar,zanfi
so na qarashe rayuwata a haka naje na tadda shi a inda yake" shiru ya ratsa wayoyin
nasu kafin daga bisani ya sauke ajiyar zuciya
"Wannan ba hujja bace,amma har zuwa yaushe kike ganin qwaqwalwarki zata zama fresh
din na daga miki qafa zuwa wannan lokacin?"
"Ban sani ba nima abdur rahman,ban da masaniya" ta fada da alamun ta fara
karaya,shuru ya sakeyi,ta tabbata sumayya abar tausayi ce,hakanaj dole ayi mata
uziri,amma ya ya iya bazai iya rabuwa da ita ba,tsakanin jiya da yau kawai
lissafinsa ya dagule,aikin da ya tafi sokoto domin shi ya gaza aiwatar da komai
"Zan bar miki maganar da baki so har zuwa sanda zaki buqaci haka,saidai ina son don
Allah mu maida dangantakar mu ta baya ta wa da qanwa,idan na kiraki ki amsamin
kamar dan uwanki kin yarda?"
"Anya hakan ma zai yiwu?"
"Mai zai hana kin manta abdur rahman ne dan zaman dakinki?" Dariya ya sanyata wadda
ta taho da hawaye,ya tuna mata wani abu can baya,wani abu da bazai taba goguwa
cikin KUNDIN tarihin rayuwarta ba,dadi yaji cikin ransa da ya fuskanci ta sake,bai
wani cikata da surutu ba sosai yace ta kwanta tayi bacci zaya kirata gobe yaji yaya
kwanan abuja.

*WAI INA ZAINAB NE?*

Tun sanda aka kaita asibitin ta soma gane Allah da girma yake,ga cutar qanjamau
dake cin kowane sashi na jikinta,ga qafa wadda ta tasamma rubewa koma ace ta
rube,ga hannu daya kullum daurw da ankwa jikin qarfen gado,gwajin farko aka gano
cancer ta shiga ciwon saboda haka tilas a yanke qafar kada dayar ma ta harbu,kuka
ta dinga yi wiwi da idanuwanta sanda aka nemi kudin da za'a biya ma a samu a yanke
qafar aka rasa,ita ta shawarci mamarta da cewa
"Mama,ko kadarorina dake cikin dakina za'a diba a saida a biya tunda ku kun kasa
biyamin,bakusan bala'in da nake kwana nake tashi a cikinsa ba" kallon banza maman
tayi mata ganin cewa har yanzu bakin zainab din bai gama rusuna ba,duk da halin da
take ciki
"Wadanne kadarori kuma kike da su,bayan wadanda kika aiko zinatu ta diba ta saida
miki ta kaiwa alqali kudin don ki samu nasara kan shari'arki,da yake Allah ba
azzalumin bawa bane gashinan abinda kika aikata yana bibiyarki" ihu ta kwarara
wanda ya janyo hankalin jami'an tsaron dake gadinta,wadanda basa rabuwa da ita koda
tayi bacci,rantse rantse ta shiga yi kan cewa ba ita ta aiko zinatu ba,maman taje
ta nemota duk inda take damfararta tayi,kudin da take sa ran za'a dinga juya mata
ana aiko mata da su don tayi rayuwa mai kyau da'yanci cikin kurkuku(kujifa,ita da
aka yankewa hukuncin daurin rai da rai amma zuciyar da sauran buri har wata rayuwa
mai kyau take hangowa kanta),rirriqeta ta jami'an tsaron sukayi sannan suka sanya
likita yazo ya danna mata allurar bacci maman na kallo,a hankali jikinta ya saki
har bacci ya dauketa,kuka maman ta sanya bayan 'yan sanda sun aikata waje don basa
bari ma a ga zainab din,tausayin 'yar tata kuma sai ya kamata,duk da irin tsiyar da
zainab din ta shuka tun tana budurwa kawo yanzu,asirin data yiwa maman ma kusan sai
da aka daureta gidan yari ya saketa, ta sani cewa maiyiwuwa zaluncin da itama ta
tafka tsakanin kishiyoyi zamanin mijinsu na raye shine alhakin ke bibiyarta Allah
ya sauko mata da wannan jarabawar,wato shi sharri kare ne maishi yake ba,hakana
sharri dan aike ne,duk inda yaje gun wanda ya aikeshin yake dawowa.
******* ******** *******

Washegari da gyaran gidan suka tashi kasancewar 'yar aikin anty dijen itama ta
tafi garinsu,babu tabbacin dawowarta ma don suna tsammani aure za'a yi mata,basu
samu kansu ba sai la'sar sannan suka kammala komai,daki sumayya ta shiga tayi wanka
sannan ta fito ta shirya cikin riga da zani na atamfa,ta zura hijabinta kenan zata
tayar da sallah wayarta ta dauki ruri,mama ce sai ta koma bakin gado suka
gaisa,sannan daga bisani ta buqaci ta kaiwa dije zasuyi magana ta kira nata layin a
kashe,kiran ta katse sannan tayo falo don ta haura sama ta miqawa anty dijen wayar.

Kyakkyawar budurwa ce tsaye a bakin qofar falon,farace mai matsakaicin


tsaho,sanye take da yadin material plain mai santsi da kauri ruwan
makuba(maroon)tayi rolling da mayafi ruwan hoda wanda ya sauka iya
kafadunta,takalmin qafarta mara tudu(plate)ne shima ruwan hodar,fuskarta fayau babu
kwalliya sai kwalli kawai,kallo daya zaka yi mata kasan cewa akwai hutu kwainane da
boko zalla a gun,a qalla zasuyi sa'anni da sumayya,minal na tsaye gabanta tana ta
tsalle,yayin da budurwar ke qoqarin budewa minal choculet data shigo mata da
ita,daga kai tayi suka hada ido da sumayya,sai ta maida kanta ga minal,hakan ya
sanya sumayyan itama dauke kanta don bata santa ba ta nufi matattakalar benen don
ta haura sama,sai muryar anty dije dake saukowa ta dakatar da ita
"A'ah amira ya kike tsaye,samu gu ki zauna mana"
"Ba komai umman khalipha,sauri nake zamu fita ne da anty su'ad,sai malam alqasim
yace min yaga dawowarku na shigo inga mutuniya ta" dariya anty dijen tayi tana
qarasa saukowa
"Mutuniyarki kam ai gata nan,yasu maamaa"
"Maamaa lafiya tace in gaidaki"
"Ina amsawa,kice su'ad anzo kenan" dan murmushi tayi
"Eh wlh,bari na wuce umman khalipha"
"Af tsaya mana na baki saqo wajen maamaa"
"Umman khalipha sauri nake,amma may be idan mun dawo da wuri zan biyo na karba
mata,banso ma akai su'ad na nan" ta fada a shagwabe kamar wata qaramar
yarinya,dariya anty dije tayi don tasan dawar garin
"To shikenan,sai kun dawo"
"Tom" ta fada tana jan kumatun minal tana mata bye bye bayan ta dan sake duban
sumayya dake danna wayar ta tana laluben mama don ta kira ma anty dije ita sannan
ta miqa mata wayar,karba anty dije tayi tana fadin
"Kun gaisa ne da amira" kai kawai ta kada
"Kai amma dai baki kyauta ba,da na ganku tare ai na zaci kun gaisa sumayya"
"Bansanta ba anty,kuma ko da na fito bata min magana ba,hasalima dauke kanta tayi"
"Qaniyarki,ba gidanku tazo ba" dariya tayi cikin tsokana tana rufe baki
"Af,na manta gidanmu fa tazo afuwa umman khalipha" itama ta fada,sai ta baiwa anty
dijen dariya,saboda kusan da wuya kaga sumayyan na zolaya ba al'adarta bace sai
lokaci zuwa lokaci,daki ta juya ta shige tana fadin
"Idan kin gama anty ki bawa laila don Allah ta samun chargy"
"To" anty dijen ta amsa tana amsa kiran wayar.

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

5⃣6⃣

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*Wa wassainal insaana bi walidaini ihsaanaa*

*mun yiwa mutum dan adam wasiyya/umarni da kyautatawa


iyaye(uwa/uba)kyautayawa(matuqar kyautatawa)*
________________________________

      Tana idar da sallar minal ta shigo dakin da gudu


"Anty kizo ana kiranki a waya"
"Waye yake kirana?" Bata amsa mata ba yarinyar sai jan hannunta da ta soma tana
nuna qofa da yatsarta,murmushi tayi don tasan halin minal din,sai kawai ta miqe ta
bita,tayi tsammanin wayarta dake gun anty dije ake kira,saidai bata tsaya ko ina ba
sai kitchen,ta dangana da ita zuwa bakin wayar su ta landline
"A nan ake kiranki" cikin mamaki tace
"A nan kuma,ba wayarku bace ta gida,saidai ko anty ake kira ko?"
"A'ah sumayya suka ce" inji anty dije dake shigowa kitchen din,cikin shakka da ko
kwanto ta daga bayan wayar ta sake sakin qararrawa.

      Nemam wajen zama ta soma yi jin muryar namiji,gabanta ya yanke ya fadi tsoro
ya kamata,ta tsani abinda zai hadata da namiji,ta amsa gaisuwar da ake mata sannan
mamallakin muryar ya soma magana
"Nasan baki sanni ba duk da kin taba ganina sau daya,amma nasam zaki iya
tunani,shekaran jiya na ganku a wani restaurant dake kaduna ke da qannenki da
yayarki,so naso na tare ki na miki magana sai kuma kunyar idon mamanki ya hana,na
lura akwai sanayya tsakaninku da masu wajen,gurinsu na amshi lambarku ta gida"
"To sai kuma akayi yaya?" Ta fada gabanta na faduwa tana neman wajen zama saboda
sanyi da jikinta yayi,tana mai fatan alaqar ta yanke daga nan,murmushi yayi wanda
har sai data jiyo
"Haba yi a hankali mana beauty,ni da nake so mai qulla dangantaka da alaqa mai
kyau?"
"Me kake nufi?" Ta tambayeshi gabanta na faduwa
"Kin gane,tun ranar da na dora idanuwana a kanki Allah ya dora min qaunarki,duk
duniya naji babu wata diya mace da zuciyata ke so da qauna sai ke,hakan ya sanya na
kasa haquri da ke,ina kuma fatan zaki karbi maganar da hannu bibbiyu"
"Hmmmm,Allah sarki" tayi qarfin halin fada tare da kife kan wayar ta miqe ta fice
daga kitchen din,baki daya jin zuciyarta tayi ta quntata,itakam duk yadda take
qoqarin killace kanta bata tsira ba?.
       Kusan ragowar ranar baki daya a daki tayi ta,dadin abun ma suna tare da su
laila,kwanakin qarshen mako ce,sai jibi litin zasu koma.

  *******   *******   *******

      Washe gari tana zaune falo ita da hafiz da minal suna kallo,hafiz kuma na
goge musu uniform dinsu,da yake da kansu suke wankinsu saboda suna da inji
wanki(washing machine),sumayya ke girkin dare suna ta murna yau zasu ci tuwo saboda
haka hankalinta ta rabashi gida biyu,anty dije ce ta sauko daga sama laila na binta
a baya hannunta riqe da turamen atamfofi guda biyar,har suka qaraso falon laila na
wa anty dujin rakin kayan sun mata nauyi
"To hafiz guga yake muku da ya rakaki,khalipha kuma nasan idan ya bikin ba dawowa
zaiyi da wuri ba,kuma aiki ne da shi zaiyi gyaran jakankunan makaranta,idan kinje
bakin get baba haruna ya karba miki ku qarasa ciki"
"To" lailan ta fada tana nishi ta fice,dariya sumayya ta dinga yi mata tana
tsokanarta wai taji kunya.

      Minti kusan ashirin shiru laila bata dawo ba har sumayyan ta kammala abincin
dare,anty dije dake shirin shiga wanka ta sauko qasa tana duban sumayya
"Kinji lailan itama shiru kamar an aiki bawa garinsu?"
"Ko a tura khalipha ya ganota tunda har yanzu hafiz bai gama gugar ba?"
"A'ah,ai duk kanwar ja ce,sanya mayafinki don Allah ya rakaki ki gano min ita"
fuska ta yamutsa
"Banson fita anty wlh"hararata tayi
"ke kam ko gajiya da zama a gida bakiyi,tun jiya da kika shigo ko waje baki leqa
ba,to ba wani gu bane gidan Baabaa prof ne,gashinan yana kallon gidan nan" dan jim
ta sake yi,haka kawai bata son shiga gidan,don tun daga qofar get din zaka ga
banbamci qarara da sauran gidajen da ke dukka layin da kewayen unguwan,ba yadda ta
iya ta shiga daki ta fiddo dogon hijabinta ta dora saman riga da skert na atamfa
dake jikinta ta zura silifa ta fito khalipha ya biyo bayanta.

Khalipha na gaba tana biye da shi har bakin tamqamemen get din
gidan,qwanqwasawa ya shiga yi a hankali,daga ciki taji ance cikin wata dattijuwar
murya
"Kai,waye a nan"
"Khalipha ne"
"A'ah,khalipha khalipha 'yan kano" taji ana fadi kafin taji motsin bude
qofar,dattijo ne wanda a qalla zaiyi shekaru sittin tsaye a gabansu hannunsa riqe
da buta yana murmushi
"Ina wuni baba halliru"
"Lafiya qalau khalipopi,dazu naga laila ta wuce ai tana tafiya da qyar da kaya a
hannu,sai haruna ne ya qarasa mata da su" baban ya fada yana basu hanya su
wuce,russunawa rayi cikin girmamawa kamar yadda halayyarta take ta gaidashi amsawa
yayi cikin fara'a,khalipha uban 'yan surutu yayi caraf yace
"Yayarmu ce baba daga kano muka taho da ita"
"Sannu da zuwa" baban yace ta amsa da yauwa sannan ta ja khalipha suka wuce ciki.

A darare taki bin bayan khaliphan wanda yayi gaba abinsa da alamun sabo da
gidan a tattare da shi,girma da kyawun gida ya ratsata tare da bata mamaki,zata iya
cewa kaf rayuwarta bata taba ganin gida kwatankwacinsa ba,ko ina ka kalla qasan
gidan a shimfide yake da grass carfet,babban gida ne wanda aka tsara gininsa,sannan
aka baje fasaha aka fidda sassa sassa a gidan a zamanance masu kyau da kama da
juna,gidan na dauke da sassa biyu manya,kowanne sashe akwai sasanni a cikinsa guda
uku masu yalwa da tsari kuma kowanne ma dauke da bene,babban sashin dake hannun
dama sashi ne na mai gidan da matansa guda biyu,daya sashen kuma sashe ne da tun
usuli yake mallakar yaransa maza su uku tun zamanin samartakarsu har ya zuwa yanzu
da dukkansu sukayi aure mallakarsu ne suna amfani da shi lokaci zuwa lokaci,kallo
daya zaka yiwa gidan ya burgeka saboda tsarinsa da yanayinsa,komai luf luf a
tsaftace a killace,kama daga wajen hutawa dake gefe guda,gun ajiyar motoci wajej
wasannin motsa jiki da lambun dake daga bayan gidan.

Sashen dake hannun dama khalipha ya dosa,ganin sun tunkari wata qofa ya
sanya sumayya riqeshi
"Kai,wai ina zamu?" Dariya yayi
"Kiran anty laila mana"
"A wanne guri?"
"Gun ummee ko gun anty maamaa" sakinsa tayi tana kokwanto kafin daga bisani ta
bishi.

Shi ya tura qofar falon da sallama kafin itama tayi tata,saka kanta kawai ya
sanar mata akwai sauyin yanayi sosai tattare da gun,falo ne na alfarma wanda ya
ginu ya kuma tsaru abun burgewa da sha'awa ga idanuwa,tsit falon yake babu kowa sai
tafkekiyar t.v plasma dake barazanar mamaye bango dake manne tana aikinta a tashar
sunna t.v,carfet ne mamaye da falon duk girmansa a maimakon tiles,labulaye da
kujeru na alfarma kalar carfet din mai azabar taushi,flower vase ce masu kyau qirar
qasar chaina a sakaye a kowacce kusurwa ta falon,sai tarin kayan turaren wuta da
humra dake ajjiye cikin tsari gu guda,da qananun centre table dake tsakanin kujeru
don ajjiyewa baqo abin sha,ba wani tarkacen qyale qyale bane a falon amma ya
tsaru,hakanan duk abinda ke cikinsa mai kyau ne da tsada,qamshi da sanyin da falon
ke bayarwa kadai ya ishi zuciya samun nutsuwa.

Sallama ta qarayi tana wuwwurga idanuwa cikin falon jin shuru ba motsin
mutane duk da tana iya jiyo qamshin girki dake tasowa bisa dukkan alamu kitchen din
na cikin falon duk da bata iya gano qofar da kitchen din yake,jin still shiru yasa
ta juya ta dubi khalipha
"Wai ina ka kawo mu nan ne khalipha,kasan dai nan babu alamun laila,inda tana nan
da tuni ka jiyo ka......." Qarar takalmi da ta jiyo alamun ana saukowa daga saman
benen ya sanyata yin shuru ba tare da ta qarasa fadar abinda takeson fadin ba
"Ha'an,khalipha ne?" Taji ana fada wanda hakan ya sanyata daga kai.

Farar mace wadda a qalla za'a kira da mai matsakaitan shekaru wanda hutu da
tsabta suka kwakwashe shekarunta suka boye,a zahiri ta tasamma shekara hamsin da
uku amma kai baka ce haka ba,fara ce tas kamar yadda nace a baya wanda har wani
yellow takeyi,kallon farko zaka san cewa zamanin quruciya an kasa maza da yawa a
kanta,akwai kyau da kansa zaune a fuskarta,duk da shekarun da take da su amma basu
ci nasarar boye kyawun nata ba wanda hakan ke nuna na asali ne ko kuma ace na gado
ne,tana da matsakaicin tsaho yayin da jikinta ke a murje,sam babu rama ko qiba
tattare da ita,fuskarta a sake take saukowa daga saman tana sanye da jar atamfa da
ta haskata dinkin riga da plain zani
"Ummee ina kwana" murmushi ta saki har sai da fararen haqoranta suka bayyana
"Ina kwana ko ina wuni khalipha sarkin shirme,ku zauna mana sai mu gaisa ko?,baquwa
mukayi" an aosa masa inda ke masa qaiqayi
"Eh yayarmu ce muka taho da ita ummee,itama ta dawo nan ta zama 'yar gidanmu"
dariya sosai ya bawa ummeen duk da kasancewarta mara son hayaniya,gu ta samu ta
zauna,hakan ya sanya sumayya dake qame gu daya ta qaraso a hankali kanta a qasa ta
samu gefan kujera ta zauna,hakanan take jin matar ta mata wani kwarjini da girma
"A'ah tashi baquwa ki koma saman kujera... Me sunanta khalipha?"
"Anty sumayya"
"Tashi sumayya ki koma sama" kai ta girgiza don ta qagu ta koma gida
"Yanzu zamu koma laila muka zo dubawa anty taji shiru" ta fada sannan ta soma
gaidata,amsawa tayi tana cewa
"Na tsammaci ai ta koma tun dazun data kawomin aiken ta fita,amma ba mamaki suna
wajen maamaa bilkisu,don nayi hayaniyan yaran gunta"
"To sai anjima" ta fada tana miqewa
"Yauwa rakata khalipha wajen maaamaanku,ki yiwa khadijan godiya naga sautu sunyi
kyau"
"To zataji" ta fada suna nufar qofar fita daga bangaren nata,saidai kafin sukai ta
shigo,budurwar rannan ce sanye take da gown mara nauyi wadda take armless bata da
hannu,sai siririn mayafi data yane tulin tsefaffen gashin kanta da shi ,kumatunta
duka biyun da hannunta jagale suke da wani abu kamar butter,sallama tayi tana
dariya idanunta a kan ummee dake dubanta itama,harara ta watsa mata
"Da kyau,sannu shugabar masu shiririta,shine kika dora mishi girki sannan kika tafi
kika tara yara kuna wani birthday din shirme,to sai ki wuce ki duba Allah yasa ya
qone,wallahi ya shigo kada ma ki dosheni don baxan qwaceki ba a hannunshi" idanuwa
ta qwalalo cike da tsoro,sannan ta kwashi sauri ta nufi hanyar kitchen din fuska a
kwabe kamar zatayi kuka tana cewa
"Wayyo ummee na banu don Allah kada kicemin girkin ya qone"
"Ke kika sani" ummin ta fada.

Shikam khalipha fuska ya bata bayan sun fito


"Ina ga yau bithday din siddiqa shi yasa ma anty laila taqi dawowa gida tunda aka
aiketa,tunda naga anty amira ma nasam da qyar idan ba yau bane,dama tun kafin mu
tafi kano anty amira tace an kusa,wayyo mami duk ita ta hanamu zuwa" ya qarashe
kamar zaiyi kuka,itakam sumayya bata ce komai ba,duban hanya take ganin sun nufi
wani sashen na daban.

Tun kafin su shiga ta tabbatar akwai banbanci tsakanin waccen sashen da


wannan,tun a qofa ta fara jiyo hayaniya da ifce ifcen yara,da banbancin kam,don
wannan falon cike yake da yara sun kusa su goma sha biyu,qananu da matsakaita,baki
dayansu sanye suke da gown suma mara hannu,dukkan rigunan irin daya ne,hatta
safunan qafafunsu(socks)iri daya ne,yaran sunyi kyau gwanin sha'awa,tsakiyar falon
qaton cake ne wanda suka dora kan center suna ta wadaqarsu da shi,da alamu shi ya
bata jikin budurwar data gani dazu,kusan ba wanda yaji sallamarsu sai wata mata
dake tsaye daura da su tana kallonsu idan zasuyi ba dai dai ba ta gyara musu,ita ta
juyo murmushi dauke a fuskarta tana amsa musu sallamar idanuwanta kan
sumayya,gaidata tayi tana duban laila da ta nufo gun saboda taga shigowarsu
"Wuce muje" sumayya ta fada tana mai juyawa tare da cewa sai anjima tasa laila a
gaba.

Daf da zasu fice taji matar na fadi cikin daga murya


"kuyi maza ku kwashe kayayyakinku zansa a gyara gurin kada uncle ya shigo ya tadda
wajen haka...." Bata qarasa jin me suke cewa ba don sun fice.

Suna gab da fita daga gidan baba halliru cikin gaggawa ya budewa motar wadda
aketa faman danna horn kamar za'a tashi unguwar,baqar motace wadda ke dauke da
baqaqen glass baqi wanda har baka iya hango wanda ke ciki ta danno cikin gidan a
guje wanda badan grass carfet dake harabar gidan ba da anga tashin qura
"Hmmm,gata nan ta dawo Allah yasa an tashi ma" laila ta fada tana hararar motar
sanda suke qoqarin fita
"Anty su'ad ko?" Inji khalipha ya tambaya yana kallon laila tare da tabe bakinsa
"Itace mana,nifa shi yasa idan tana garin bana son shiga gidan baabaa wallahi anty
sumayya" ta fadi tana duban sumayya tana son bata labari,saidai hararar ta sumayyan
tayi
"Ke kam laila ke da khalipha bansan wanda yafi wani surutu ba wallahi"
"Wallahi ya fini" inji laila tana dariya,take musu ya sarqe tsakaninsu da khaliphan
har suka qarasa cikin gidan.
Shigarta ta tadda wayar gidan nata faman ruri anty dije na kuma saukowa da
alama fitowarta kenan daga wankan
"Qarar wayar nan ce ta isheni,tunda kika fita aka dinga kira,hafiz ya daga akace ke
nema ya gaya musu baki kusa amma basu daina kira ba,don Allah jeki daga ko
kunnuwanmu sa huta" bata fuska tayi ranta na baci,jikinta ya bata mai kiran jiya ne
wanda ya kira kansa da alqasim
"Ni wa na sani anty da zai kirani da lambar wayar gidanku,na gaya musu bani bace
amma anqi daina kira"
"To amma ya akayi haka?,shikenan....bari na daga na musu bayani" antyn ta fada tana
nufar kitchen,sai sumayyan tayi saurin barin falon ta shige dakinta haushinsa na
kamata,haka kawai don musiba yana son ya zame mata jarfa,ta bar kanon amma don ta
samu hutu ta nutsu amma bata samu nutsuwar ba,ina dalili,su qarke qalau da anty
dijen.

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

5⃣7⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

*wallahi tallahi billahil azim duk wanda baibi Allah ba ya shiga uku,duk wanda
baiji tsoron Allah ba ya kade,duk wanda tsoron Allah bai hanashi bin son zuciyarsa
ba yana cikin babbar musiba,dan adam ba kowa bane hakanan ba komai bane shi,kaji
tsoron ubangijinka kayi biyayya a gareshi KAJI TSORON AZABARSA KAYI KWADAYIN
RAHAMARSA sai ka samu rabauta,ka guji duk wani abu mara kyau,kayi riqo da kyawawan
ayyuka, 'YAR UWA,KI KARANTA YADDA UBANGIJI DA MA'AIKI SUKA WASSAFA MANA
JAHANNAMA,ALLAH KAYI MANA TSARI DA ITA BADON HALAYENMU BA,KADA KA NUNA MANA ITA KO
NA QIFTAWAR IDO NE,KA BAMU IKON YIN BIYAYYA A GAREKA,KA KADE MANA ZUKATANMU DAGA
TUNANI KO AIKATA DUK WANI SABO KO ZALUNCI*

______________________________________

Kwanaki nata tafiya,tun tana a takure da zaman garin har tazo ta fara sakin
jiki,abu daya ke damunta kewar abdallah,tausayinsa take hakanam tausayinsa ya ninku
a zuciyarta tun daga randa ya rasa mahaifinsa,kullum takan kira a bata shi su gaisa
susha hirarsu,abinda ya sake kwantar mata da hankali a nan ba inda take zuwa bare
ta gamu da wani yace mata yana sonta,hakanan kiran waya ma da ake ana nemanta tun
ranar da anty dije tayi magana aka samu sauqim kiran,sai jifa jifa shi din ma ba
dagawa take ba,abdur rahman ne kadai ke kiranta su sha hirarsu har ta riga da ta
saba,babu wata rana da zata fito ta fadi bai kirata ba,ta sake sosai don bai qara
yi mata wata magana daban ba banda ta zumunci,anty dije tayi ta mata tsiyar batasan
muguwar kifin rijiya bace ita sai yanzu,bata son zuwa ko ina,ko gidan baabaa prof
shigarta biyu kwata kwata shima da dalili na farkon kiran laila da taje,na biyu
kuma da sumayyan tayi dambu gidan ba yara ta sata ta kaiwa anty maamaa da yake ita
mai son dambu ce,kota shiga din ma bata wuce minti biyar ko goma ta fito,hakan ya
sanya anty dije ta bada sautun kayan turare da humra aka kawowa sumayyan ta soma yi
a nan,cikin designers kwalabe take zubawa,nan take kuwa ta soma ciniki,duk da wani
gu ake kaiwa,'yan unguwar ne kawai ki zuwa siya cikin gida.

Yau ma kamar kullum babu yara a gidan suna makaranta,gab suke da fara
jarabawa ayi musu hutu saboda gabatowar wata mai alfarma na azumin watan
ramadan,suna zaune da anty dije a kitchen tana anty dijen ke girki yau sumayya na
ganin yadda take yi din don bata iya irinsa ba,iya zamanta da anty dijen ta qaru da
abubuwa da dama ta fannin zamantakewar gida,girki iri iri,gyaran jiki da kuma uwa
uba iya gayu,wayarta anty dijen ta daga wadda ta fara ruri ta kara a kunne,ganin
haka sumayya ta karbi yankan cabbage din da takeyi taci gaba,sai data gama sannan
ta dubi sumayyan
"Sumayya,inaga fa ke zaki miqawa anty maamaa humrar nan,kaya take hadawa kuma kinga
yaran basu dawo ba" kasaqe tayi,sarai anty dijen ta gane bata son zuwa ne,bata san
me yasa bata qaunar shiga gidan ba amma sai ta shareta,ta gane mai anty dijen ke
nufi tilas ta miqe tace to,dakinta ta shiga ta sanya dogon hijabinta har qasa
sannan ta jawo ledar data jera humrorin wadda anty maamaa ta bata tayi mata,saboda
umrar azumi da zasu tafi ita da maigidan da kuma ummee,sai babban yaron gidan shi
da matansa biyu sai qaninsa da tashi matar,sai manyan jikokin gidan su biyar duk da
basu wuce shekara sha hudu zuwa qasa ba,duk laila aku(sunan da idan taso take
kiranta da shi kenan kusamman idan tayi hali ) ke bata wannan labarin tunda ita ba
shiga take ba ballantana ta sani.

Kamar kullum a hankali ta dinga ratsa gidan bayan sun gaisa da mai gadin
dake gadin wannan qofar sa suke shigowa da yake akwai wata qofar ta baya,mutumin ya
haifeta shi yasa take ganin girmansa,mutum me mai faran faran da son jama'a,duk da
ganinsa da sumayyan baifi uku ba amma yana yabawa hankalinta yadda take rusunawa ta
gaidashi,duk da yasan iyalan gidan alhj umar farouq ba baya bane wajen tarbiyya.

Kanta a qasa qirjinta na bugawa ta dinga kutsawa cikin gidan,batasan me yasa


take yawan faduwar gaba ba idan ta shigo gidan,ko don tana ganin kamar akwai
banbancin matsayi tsakaninsu bai kamaci ta dinga shiga musu gida ba.

Tazo mararrabar sashin anty maamaa data ummee sai taso ta manta wane waje ne
na anty maaman don bata rarrabewa da sunayensu,a hankali ta juya idanuwanta tana
canki canki,karaf idanuwanta suka sauka a kansu,zaratan samari ne ke tsaye su biyu
suna magana da junansu,dukkaninsu dogaye ne saidai daya yafi daya masu matsakaicin
jiki,kowannensu na sanye da t.shirt da trouser masu mabanbantan kaloli kowa da
kalar nasa,farare tas da su kamar yadda ta dan fahimci haka kalar fatar masu gidan
take,fuskar daya kawai taje gani bata ganin ta dayan kasancewar ya juya baya ne
yana magana da dayan,da alamu kuma duk hankalinsa na kanshi,shima ya ganta,idanu ya
sanya yana kallonta har waccan ya kammala fadin abinda zaice yayi gaba ya shige
daya sashen.

Rudewa tayi kamar mara gaskiya,jikinta ya soma rawa ta fara qoqarin juyawa ta
koma inda ta fito ganin kamar yana takowa inda take
"Wa kike nema?" Ya tambayeta fuskarsa ba yabo ba fallasa,cikin qoqarin daidaita
nutsuwarta ta hada kalmar
"Sashen anty maamaa nake nema"
"Ko gun amira kika zo?" Ya sake tambayarta yana kallon ledar hannunta,bata ma gane
wace amirar ba,sai tave masa
"A'ah,saqo na kawowa anty maamaa" sai taga ya saki murmushi
"Yauwa,muje ma na rakaki,Allah yasa wannan turaren mai dadi aka kawo mata wanda
tamin alqawari" ya fada yana yin gaba cikin mishadi,ta bishi a baya tana cike da
mamakin sauqin kai irin nasa,batayi tsammanin haka ba.

Falon suka shiga yana sallama cikin daga murya,wannan budurwar da take zaton
ita ce amirar ta fito da sauri daga kitchen tana dariya,bata lura da sumayya dake
bayansa ba,ganinsa ya sanyata tsaya tana dubansa tana qyalqyala dariya,da alama
wani abu da ya faru dazun tsakaninsu taje tunawa
"Ya akayi yaya mahmoud?" Ta fada tana sake tuntsira dariya
"Zaki zo hannu ai kin sani.....yanzu ba wannan ba ga baquwa nan tazo wajen anty
maamaa" dan leqowa amiran tayi inda sumayya ke tsaye,sai tayi murmushi
"Ba baquwa bace a gidansu umman khlipha take,duk da dai baquwa ce a gidan nan
saboda na fuskanci bata son mutane" ta fada tana murmushi
"Ke kuma gaki da shegen kwashe kwashe ko,ki bata guri parrot tukunna,ki gayawa anty
zan dawo anjima,yanzun yaa man ya aikeni ne" ya fada yana juyawa zai fice,ganin
haka yasa amira daga murya
"Don Allah ya mahmoud ka siyo min na tuba" ta fada a shagwabe tana kama kunnuwanta
guda biyun,harara ya watsa mata yayi ficewarsa,sai ta narke fuska kamar zata yi
kuka har ya bace a falon kafin ta maida kanta wajen sumayya.

Murmushi tayi mata sannan tace


"Ga waje zauna,amma sai kin dan jira antyn don tana wajen dan tsohon mijinta,kinsan
ba'a kiranta idan ya shigo sai mutum ya jirata" ta fada cikin salon tsokana tana
dariya,itama sumayyan sai ta saki murmushi,kusan haka halayyar anty dije take,take
mukhtar ya fado mata,a hankali sai murmushin nata ya soma gushewa damuwa ta fara
bijiro mata,take ta fada kogin tunani tana tuna wasu lokuta masu dadi daga cikin
rayuwar da sukayi tare da shi.

"Ga lemo bismillah" amiran ta fada tana ajjiye tray data dora lemo da kofuna
a kai,kai sumayya ta kada cikin murmushin yaqe tace
"Alhamdulillah,a qoshe nake"
"Al'adar gidan anty maamaa ne,dole kisha wani abu kafin ta fito" ta fada tana
tsiyaya mata a cup,kallonta sumayya tayi tana yaba karamcin hakan,sai a sannan taga
kamanni da wanda ta kira mahmoud a dazu,da alama kwai dangantaka ta jini mai qarfi
tsakaninsu,hannu ta saka ta karba tana fadin
"Na gode"
"Ba komai,bari na duba girki kada ya kama"
"To" sumayyan tace,kurbe daya tayi masa ta ajjiye damuwa ke sakadarta,a haka taji
an bude wata qofa dake can wani sashe daban na falon,anty maaman ce ta fito tana
cewa
"Ayyah tun yaushe kika zo" murmushi tayi
"Ban jima ba,ina yini" ta gaidata amsawa tayi tana zama tare da amsar ledar
humrorin,budewa tayi tana shanshanawa tare da yaba yadda sukayi bala'in
qamshi,godiya tayi mata sosai tamkar ba biyanta tayi ba,miqewa tayi tana shirin
tafiya
"Umhmmm,za'a gudun ne?" Amira take baro kitchen ta fada tana dan murmushi,waiwayawa
tayi tana dubanta itama fuskarta qunshe da murmimushin,sam batayi zaton zata yi
sauqin kai haka ba
"Na baro aiki ne a gida shi ya sa"
"Ayyah to sai yaushe?,ko sai na shigo?"
"Allah ya kawoki lafiya"
"Amin,ni sunana sumayya na gaskiya,sunan mamar babanmu ce ake kirana amira,kefa?"
Murmushi ta saki
"Nima suna na kenan?" Idanu amiran ta zaro gami da rufe baki
"Kai kai,dama baabaa na kusa ya ganki,yaga mai sunan mamarshi,yana son mai sunan
mamarsa wallahi,me ake ce miki to?"
"Shi ake gayan" kai ta kada sannan tace
"Gaskiya ni bazan fadi haka ba,zan dinga kiranki kema da amira,amiran umman
khalipha" dariya sosai sumayya tayi
"Shikenan to" ta amsa mata sannan sukayi sallama ta juya da niyyar fita tana dariya
amiran,kusan zasuyi shekaru daya da ita,saidai yanayin inda ta taso da gata sai
take ganin kanta kamar qaramar yarinya,duk da aqalla zasuyi shekaru ashirin da
daya.

A bakin qofar shigowa falon taji tayi karo da abu har yana bangazar
kafadarta,da sauri ta ja baya tana fadin
"Subhanallah"
"Mtsweeeeww" taji an tsaki,baya ta sake ja tare da daga kanta tana kallonta wanda
ita dinma kallonta take,saidai nata kallon yasha bamban da wanda sumayyan ke
mata,kallon farko ta fahimci macace mai izza da jin kanta,haka yake don sumayya
bata yi qarya ba,matashiya ce dake jin duniyarta dai dai,wadda a qalla ta doshi
shekara ashirin da takwas a duniya,doguwa ce sosai hakanan siririya ce,fara ce
itama sosai kamar yadda sauran suke,sanye take da wani baqin hight rise slim leg
jeans da v neck t.shirt mai gajeran hannu,hakan shi ya fiddo surar ta da shape
dinta baki daya,kanta yane da wani dan kwali mai santsi don ba za'a kirashi mayafi
ba,idanunta saye da sun glases da ya kusa cinye rabin fuskarta,wani kallo take wa
sumayyan na sama da qasa cikin izgilanci kafin ta zare gilashin nata,tsaki ta ja
kafin ta wuce tana taku dai dai tana duban amira
"Maamaa fa?" Ta tambayi amira kamar bata son yin magana
"Ta haura sama" ta fada tana nufo sumayya dake gab da ficewa daga falon,da sauri ta
daga murya
"Kiyi haquri sumayya" amiran ta fada cikin damuwa,sai ta waiwayo tana sake mata
murmushi tare da fadin
"Kada ki damu", sai da sumayyan ta fice sannan ta dawo da kallonta cikin falon ta
saukesu kan wadda ta shigo din,sai ta kada kai kawai ta shige kitchen ganin ta
zauna saman kujera tana jiran saukowar maamaan,ta sani sarai ba zata iya haurawa
saman ba dama idan ba da wani qwaqqwaran dalili ba,shi ya sanya tayi saurin komawa
kitchen don kada ma tace zata aikata.

Tana hanya tana tuna irin kallon da ta yi mata,a qa'ida ita ta bigeta,ranta
yaao baci amma sai ta dorama kanta laifin,ko ba komai ita tazo musu gida,tana isa
gidan ta bawa anty dije labarin amiran,
"Amira kam akwai son mutane ai haka take ita da mahmoud ai mutane na ne"
"Eh kam na ganshi shine ma ya rakani wajen anty maamaa,yana da kirki sosai"
"Shine d'a na uku a wajen ummee"
"To ita amiran 'yar waye ne anty,yau tana can gobe tana nan"
"Itama d'iyar ummee din ce"
"Ita ummin bata da yara ne?" Hararta tayi tana cewa
"Yau kin zama 'yar jarida,to ban sani ba,ai baki son jama'a ne,banda haka watanki
nawa a gidan nan yaci ace kin gama saninsu,tunda alhamdulillah mutane ne masu kirki
karamci da son jama'a" dariya sumayyan tayi tana kame bakinta da yatsunta
"Ni dama amiran nake son na san 'yar ina ce kuma an gayan" sai suka yi dariya anty
dije na qorafin qib sakin jiki na sumayyan.

Da daddare dukkansu suna zaune a qasa suna cin abincin dare har da mai
gidan,sumayya ce kawai ke zaune can gefe tana cin nata,babu yadda anty dije da
uncle farouq baiyi ta dinga cin abinci cikinsu ba amma ta kasa,kunya gareta,bata da
sabo sosai idan ba wajen yara qananu ko mutanen gidansu da suka taso tare ba,tun
suna qorafi har suka suka haqura suka zuba ido a haka suka saba saboda sun lura
halittarta ce ba zata sauya ba.

Sai da suka kammala baki dayansu sannan hafiz yace cikin doki
"Abba,wanne albishir ne da kace sai mun gama cin abinci zaka yi mana?"idanu ya zaro
yana murmushi yana duban hafiz din
" ummm,wannan zumudi haka?"
"Eh wallahi abba nima na qagu ya rigani fada ne kawai a baki" juyawa yayi yana
kallon lailan,wannan karon dariya ce ta subuce masa
"Au kema?"
"Eh abba" ta fada itama tana dariyar,sai ya dubi anty dije
"Kefa madam?" Murmushi tayi tana gyara zama
"Ai yara sun gama magana,nima na zaqu inji wanne albishir ne?" Dariya ya sake yi
"Uhmmm,shine kenan to tunda bakinku yazo daya" ya fada yana gyara zamanshi,sumayya
na gefe tana satar kallonsu,yanayin rayuwarsu tana burgeta,soyayya dake tsakanin
uncle farouq da anty dije kullum kamar wasu sabbin aure,waiwayawa yayi ya fito
sumayyan da hannu
"Taso kema ya shafeki" sai tayi qasa da kanta sannan ta miqe ta qaraso tana
murmushi,gefan laila ta samu ta zauna,duk sukayi shiru suna sauraronsa.

"Alhamdulillah,Alhamdulillah" ya fara cewa


"Wato a yau labari ya iskemu gwamnatin tarayya ta aiko da takarda ma'aikatarmu,ta
zabemu mu goma zamu tafi london bayan sallahn nan mai zuwa da sati daya,zamu qaro
karatu don samun qwarewa kan aikinmu na tsawon shekara guda" ya fada yana sauke
numfashi,duk sai fuskokinsu suka sauya,kowa da abinda ya fara yawo cikin
zuciyarsa,suna wassafa yadda zai tafi ya barsu da yadda zasuyi kewarsa,dariyan da
ya saki ita ta maido hankalinsu kanshi
"Jibi fuskansu,to gwamnati ta bamu daman tafiya da iyalanmu amma kada su wuce mutum
hudu,shine babbar matsalar,gashi mu mun kai mu shida,tunani daya wa za'a bari da wa
za'a tafi?" Shuru dakin ya dauka,murna ta soma komawa ciki,kowa na zulumin kada ace
shi za'a cire,banda sumayya da farinciki ya mamayeta zata koma kano kenan har
tsawon shekara daya,don dama ko a mafarki bata zaci ma zata bar state dinta ba
balantana akai ga qasarta,ganin ba wanda yace komai sai sumayyan tayi gyaran murya
don fidda abinda ke cikinta,dubanta uncle farouq yayi yace
"Ummm,me zaki ce?" A ladabce tace
"Dama uncle.....cewa nayi.....ni mai zai hana a cireni a lissafi sai na koma kano
kafin dawowar taku?"
"Shawara bata karbu ba" anty dije ta fada kanta tsaye,sai ya saki dariya yana
kallon sumayya
"To kinji abinda antynki tace" yana maganar tare da mai da hankalinsa kan anty dije
"To ke hajjaju mai zai hana cikin taskarki din nan da ake boyo ki dauki nauyinmu
baki daya?" Ya fada cikin zolaya wanda hakan ya sanyasu dariya baki dayansu,sai da
suka nutsa sannan yace
"Ni a binda nake gani,hafiz,kai zakayi haquri saboda karatunka a yanzu yake buqatar
nutsuwa da dagewa,kai zamu bari a nan garin,sumayya kuma kema 'yar mu ce,kinga kuwa
mai 'ya mace bazai dinga barinta wani gu ba,ni zan yi mata passport da visa a
kudina,shikenan madam?"murmushi ta saki
" yayi yallabai,mun gode Allah ya saka da alkhairi ya qara arziqi"hafiz wanda sam
baiji dadi ba har cikin ranshi,amma da yake yarone mai hankali da haquri,da wuya ka
gane bacin ranshi sai yace
"A wanne gida abba Zan zauna?"
"Duk inda ka zaba,ko gidan inna(kakarsu da yake nan ya dawo da ita,ba wata tazara
bace mai nisa tsakaninsu),ko gidan baabaa prof,kayi haquri kaji hafiz,girman kenan
kaji?"
"Ba komai abba" ya fada,sai ya baiwa antu dije tausayi
"Ni har ka tunan ma abban laila,ina zuci zuci sukai sumayya ta gaidata,innan tace
wai ba zata iya gane sumayyan yanzu ba"
Yana miqewa yace
"Kinsan tsufa sai a hankali,ai babu damuwa ko zuwa gobe ko jibi sai suje"
"Allah ya kaimu" injita,miqewa hafiz din yayi yabi bayan abban nasa da ya kirashi
yace yazo ya karbi wani abu,take falon ya sarqe da murna,laila anata wassafa kai a
jirgi,sumayya na dubanta tana dan murmushi duk da hankalinta ya kasu kashi biyu,ran
qwashi anty dije ta zuba mata tace kota nutsu ko ta saka a cire sunanta a saka na
hafiz take ta kame bakinta duk da bata fasa mutsu mutsun murna ba.

*mrs muhammad ce*👑


📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

5⃣8⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

*KO KUNSAN ACIKIN 'YAN WUTA WAYE MAI QANQANUWAR AZABA MAFI SAUQI?,WANDA AKA FI
SAUQAQAWA??*

*Shine wanda za'a sanya garwashin wuta a tafin qafafunsa guda biyu,kowanne tafi
daya garwashi daya,sai qwaqwalwarsa ta dinga tafasa*

*ALLAHUMMA AJIRNA MINANNAR*

__________________________________

      Falon anty dije ta basu tana fita laila ta dora daga inda ta tsaya,har gwada
irin shigar da zata dinga yi take idan suka tafi,sumayya na gefe tana kallonta tana
dariya,can qasan ranta kuwa tana ta jujjuya maganar,wai itace zata wata qasa wata
uwa duniya a jirgi har london?.

       Suna haka hafiz ya fito daga wajen uncle farouq,fuskarsa qunshe da murmushi
hannunsa dauke da laptop sabuwar qar,idanun laila suka fara kaiwa kai
"Laaah,ya hafiz sabuwar laptop abba yayi ne?"
"Wannan ba ta abba bace,tawa ce wanda ba za'a london da shi ba" ya fada yana zama
tare da budeta ya kunna,tuni laila aka fara raba ido,ta matso kusa da shi
"Da gaske kake ya hafiz" hararta yayi
"Da da wasa nake miki" shiru tayi sannan daga bisani tace
"Allah ko nima na fasa zuwan ne a siya min,kada muje mu dawo dadi ya qare kai kuma
ga abarka nan kama mora?" Dariya ta qwacewa sumayya,tana niyyar cewa wani abu anty
dije itama ta fito daga dakin hannunta dauke da wata laptop dim,gefansu sumayyan ta
zauna tana kallon hafiz
"Tofa,an samu nayi ko?" Murmushi yayi kawai yana danne dannensa dadi ya
cikashi,sumayya ta miqawa laptop din tana cewa
"Ungo wannan" amsa tayi tana duban antyn
"Daki zan kai miki?"
"A'ah taki ce,abba laila ya siya miki yace zai miki bayani,akwai abinda ya shirya
miki kan bunqasar karatunki yana so kiyi karatu ne da ita,idan mun tafi ina
tsammanin akwai makaranta da zai sama miki da zaki koyi karatu ma shekara
gudan,nasan baki da matsala ta karatu da rubutu duka kin iya,hakanan turancinki ba
laifi zaki iya karantawa ki fahimci wasu abubuwan,fahimtar sosai da maidawa yadda
ya kamata ne kawai matsalarki" qamewa tai a gun tana mamaki,to ita ya zata iya da
wannan aba da uncle din ya mallaka mata,kasa magana tayi har sai da laila ta saki
dan ihu tana karbarta daga hannunta
"Wayyo!,muma munyi computer,ya hafiz ka daina mana kallon banza" cikin sanyin murya
da sake gasgata qaunarta da anty dije tace
"Anty na rasa wacce iriyan godiya zan muku,na gode na gode Allah ya saka muku da
alkhairi,ya biya muku dukkan buqata ya jiqan magabatanku,ya hada kan zuriyyarku
baki daya"
"Amin" anty dijen ta amsa tana shigewa ciki.

        Da sauri laila ta miqe ta jona mata chargy hadu da kunnata,tana da rawar


kai hakan ya sanya ta iya laptop din kamar wadda ako koyawa,don suna game sosai a
cikin ta muhsina daya daga cikin qawayenta jikokin gidan baabaa prof,nan ta fara
duba games din ta ta tarar a ciki,ta zabi daya ta fara bugawa minal ta matso tana
kallo.

        Daga bakin qofa akayi sallama,dukkansu hankalinsu na kan laptop din sai
sumayua wadda ta amsa yana waiwayowa,amira ce ke shigowa fuskarta qunshe da
murmushi,sanye take da black gown brided tube midi mai adon zane orange a jiki mai
dogon hannu,kanta yane da mayafi medium orange haka plate shoes dinta,hannunta riqe
da wayarta,fuskarta ba makeup saidai akwai alamun hoda da lipstic,bayanta wata
matashiya ce,sanye da baqin skert da t.shirt ruwan omo dukkansu na yadi,sai dan
madaidaicin hijab dake wuyanta,kallon farko zaka gane 'yar aiki ce,eh tana daya
daga cikin ma'aikatan gidan baabaa prof,qarasowa tayi cikin falon wanda hakan ya
ankarar da su laila
"Anty amira ina wuni" suka gaisheta baki dayansu ta amsa tana zama gefan sumayya
"Kin ganni da daddare ko?" Murmushi kawai tayi tana janyo lemo da ruwa nata wanda
tun dazun bata sha ba da suka gama cin abinci ta ajjiye gaban amiran tana cewa
"Bismillah"
"Um_um,a qoshe nake,shopping naje nayo sai nace bari na shigo,ina so dama na baki
haquri ne kan abunda ya faru dazu" kusan ta mance ma ma ya farun
"Mefa?" Sumayyan ta tambayeta
"Bigeki da antynmu tayi dazu,kiyi haquri don Allah,antynmu ce saidai bata da kirki
sam,kiyi haquri" murmushi ta kuma yi har fararen haqoranta na bayyana
"Babu komai,ai karo mukayi"kai amira ta girgiza
" duk da haka,nasan halinta ai,kiyi haquri"
"Bafa komai" ta sake maimaitawa,maida dubanta tayi ga wadda suka shigo din
tare,tana tsaye har yanzu
"Ki zauna mana" sumayya tace mata,murmushi tayi tace
"No madam,na gode". Kan ta sake cewa komai wayarsu ta tafi da gidanka dake  kitchen
ta fara burari,laila ta subi khalipha
" jeka duba khalipha"kanta na ga laptop don bata son a mata game over,da sauri ya
miqe ya shige kitchen din minti daya tsakani ya fito
"Anty sumayya ke ake nema" yana fada alqasim ya fado mata,fuska ta tsuke
"Kace bana nan"
"Yace don annabi ki daure ki daga" khaliphan dake tsaye bakin qofar kitchen din ya
fada,goshinta ta dafe da tafin hannunta,bata so a hadata da ma'aiki taqi yin
abu,amira ta miqe tana dubanta
"Kije ki amsa mana namecy,zan tafi sai da safe ki gaida umman khalipha" ta fadi
tana murmushi
"Sai da safe ki gaida gida" sumayyan ta fadi itama tana miqewa,ita tayi kitchen su
suka fice ita da mai aikinta.

      Murya a sanyaye ya mata sallama,a dake ta amsa


"Bakisan halin da zuciyata ta fada sanadinki ba sumayya,please don Allah ki daure
ki dinga daga wayata ko ba zaki ce min komai ba"shiru ta danyi ta rasa me zata ce
da shi,zuwa yanzu yaci ace yayi zuciya ya bar nemanta
"me kake so nace mai kake buqata?"
"Yauwa beauty,a qalla ko gaisuwa ma ta wadatar" kusan wannan ne abinda abdur rahman
ya gaya mata,gashi yana neman jefata cikin tarkon sabo da jin muryarsa,wannan wanne
irin wayo ne,ba zata yarda ba kam
"Sai anjima" tace masa tana kife kan wayar ta fito daga kitchen din tana sauke
numfashi,inda ta tashi nan ta koma ya zauna ta janyo wayarta tana laluban lambar
mamanta tana son jin muryar abdallah.

******    ********    ********

       Ramadan ya rage saura kwanaki uku,nan sumayya taga tsari,yadda anty dije ke
tsara gidan nata tare da sauya abubuwa sabida shigar watan,baki ta sake tana mamaki
don su duk basu irin wannan,dariya anty dije tayi
"Da kike mamakin nawa gyaran kice idan kika ga na gidan baaba prof saikin yada
idonki?"ido ta qwalalo
"duk kyau da tsaruwar wannan gidan sai an sake masa wani tsarin?"
"Duk shekara iwar haka sai dukka gidan sun sake komai nasu,sai su rabar da
tsofaffin ga 'yan aikinsu,wasunsu har kayan sawa da yayi shekarar nan ake canza
wardrobe baki dayanta" baki sumayya ta sake tana duban anty dije kamar ita ce ke
sanya su
"Gaskiya mutanen nan mabarnata ne,yanzu wannan gidan ba ya isheka har qarshen
rayuwarka ba,wani ma idan yana wani gu baisan da wani ba,har meye ne zai tsufa a
shekara a sauya shi?"dariya sosai anty dije tayi
" lallai har yau bakisan wannan familyn ba,kowa da irin matsayinsa fa,ita rayuwa
kowa da inda Allah ya ajiyeahi,idan kaga rayuwar wasu kai a gunka barna ce da
almubazzaranci,ko kaga tsabar warya ce ko bazata yiwu ba,amma kaima da Allah zai
kaika irin wannan matsayin babu shakka sai kayi kamar ko fiye da abinda
yakeyi,yanzu kamar ni din nan,da wasu zasu ga abinda nake cewa zasuyi nima
almubazzaranci bane,amma ba haka bane,idan Allah ya wadataka kana da shi ka sauya
to ka bawa na qasa da kai wancan su amfana suma,ba ka qanqame ba ka qanqame jama'a
ba,amma.....zauna na gaya miki su waye wadan nan family din kinji"ba musu sumayyan
ta zauna tana baza kunne,itama anty dijen zama tayi,kafin tace komai laila ta shigo
tana sanar mata tayi baquwa tilas suka katse hirar ta fita wajensu,sumayya ta tashi
ta kama mata aikin da ta tafi ta bari.

  *********  ******  ********

      Baki daya a yanzu rayuwar gidan bata yiwa karima dadi,bata da buri a yanzu da
ya wuce taga yaranta da mijinta kusa da ita amma abu ya gagara,kowa tsoro da
haushin zama kusa da ita yake,hatta da lukman din ma kwanciyar bacci kadai ke
kawoshi bangaren,ya sauya mata irin sauyin da bata taba zata ba,bai shiga shirginta
indai ba haqqinta na aure zai sauke mata ba,wanda shima yasan idan ya take mata sai
Allah ya tuhumeshi,a nan takan so jan ra'ayinsa amma abu yaci tura,da ya gama yake
wanka idan an kusa asuba ya zauna karatun qur'ani da addu'o'i har sai an kirayi
asuba ya fita yayi sallah,idan ya dawo ya zarce wajen hajiya su hafu da yara suyi
karatu sannan su shirya ya miqa su makaranta,idan ya dawo shine zai shigo mata yayi
wanka ya fice ko sauraron abincinta baiyi gun hajiya shima yake ci,hakan shi ya
sake taka muhimmiyar rawa wajen rugujewar duk wani aiki da zata masa,walau na
abinci ko na jinnu,ya tsayawa addu'a abincinta kuwa baici bare ya dameshi,bata gane
bata da wayo ba sai sanda taso ta gwada yi masa tawaye kan yadda yake maganar
sumayya da daukar yaranta ya kaiwa mama su,ranar taga tijarar da tunda Allah ya
hadata da shi bai taba yi mata ba,tayi kuka na fitar rai,a hankali kuma sai ta soma
tunanin me yafi zaman lafiya dadi?,me zaisa ba zata haqura da komai ba ta kawo
qarshen wannan zaman fagen yaqin da sukeyi,abinda bata sani ba tanqwara busashen
itace abune mai wahala,ta riga da ra yiwa kanta mummunar lamba wajensa.

      Duk sanda yaje yakanyi yunqurin karbar adreas din sumayya wajen zainab ko
halima,saidai duk sanda yaso yin hakan sai ya taras basa nan suna tahfiz,ita kuwa
mama ba wani riqe adress din tayi ba,yaciji yatsa yaji ciwon abun da tun lokacin
aurensu da tace zata gidan anty dijen lokacin da shima zaije abujan bai bita ba
yaga gidan,da tuni yanzu bakinsa alekum sai ya kama hanya,wayarta kuwa idan ya kira
sau biyar idan yaci sa'a zata daga sau daya su gaisa ta tambayi yara,daga haka zata
katse kiran sai kuma wani lokacin.

******   ********   ********


       Ranar lahadi da daddare watan azumi ya bayyana,hakan ya sanya litinin
daukacin al'umar musulmin duniya suka tashi da azumi a bakinsu,duk gidan kowa na
azumi banda minal saboda shekarunta basu qarasa ba,ta fara gwadawa zuwa sha biyu
anty dije ta bata abinci,kafin azahar su laila anyi laqwas saman kujera,khalipha an
fara mutstsuka idanuwa,dariya sosai sumayya ta dinga sheqa musu yayin da anty dije
tayi kicin kicin da fuska don kada ma wani yaga fuskar da zaice zai karya,hafiz ne
kadai da qwarinsa da yake shine babba.

       Biyu da rabi bayan sumayya ta kammala sallar azahar tana tilawar qur'ani
anty dije ta taddata da hijabi jikinta itama da alama bata jima da gama sallarta
ba,gefe ta zauna hakan ya nunawa sumayya magana tazo yi da ita saboda haka tana
kaiwa qarshen shafin ta rufe tayi addu'a ta shafa ta waiwayo ga anty dijen
"Ya ibada,ke kam azumi nasaj gwaninki ne,tunda kina na litinin da alhamis dama"
murmushi tayi
"Wallahi kam anty"
"Allah ya kawo min sauqi wannan karon shi yasa nace bari nazo na sameki,kinsan duk
watan azumi nike wa baabaa prof abinci har a kammala azumin,abban laila ne yasa a
dinga yi saboda karamcin dattijon,yana son abinciccikan gargajiya duk da
kasancewarsa dan boko,to su mutan gidan sun fishi boko,da azumi basa wani abincin
azo a gani sai abinciccikan zamani,ummee ce ke masa lokaci lokaci don itama tana
so,to wannan karon ummee sun tafi umra mazan ne kawai suka rage a gidan,duk da kowa
na da mai aikinsa amma shima baabaan baison girkin ma'aikata shi danshi ya gado" ta
fada tana dariya data tuno shi
"nasa gwanar girkin gargajiya ce ke,ni ki barni da girkin gida ki dinga na baabaa"
murmushi tayi
"To ai zan iya ma anty duka,haba,sai kace ba mace ba"
"Nasan zaki iya,ai ranon mama ce,amma kya dai tayani na gidan"
"Tom anty" miqewa anty dijen tayi
"Naga yau garin kam masha Allah akwai hadari,ko yau zamu samu ruwan farko a ranar
farko?"
"Allah yasa anty,dama tun muna kano naga irin garuruwan nan kunfi ko ina samun
ruwa,ga damunarku itace qarshe wajen tafiya"
"Wallahi masha Allah,muna shan ruwa kam,saidai zafi"
"A hakan anty,duk wannan ac da kuke kwankwada"
"Saikin fita ai sumayya zakiji a jikinki"
"Saidai haka" ta miqe itama tana nannade abun sallahr ta don shiga kitchen saboda
su kammala komai kan lokaci.

      Ana la'asar kuwa ruwan farko ya soma sauka zuwa qasa,tana kitchen din a
lokacin,sai ta zuge glass tana kallon yadda ruwan ke juqa shukoki yana tayar da
qamshin qasa,a rayuwarta tana son damina,murmushi ya subuce mata data tuna sanda
suna tare da mukhtar,duk sanda baya gida takan fito ita da yaranta dake tayata zama
susha wankansu a ruwan sama,kafin ya dawo ta share gidan ya sauya kayanta kamar
bata shiga ruwa ba,amma kallon farko idan ya mata yake gane ta shiga ruwa,musamman
gashinta dake saurin fallasata saboda cikarsa da tsahonsa bai bushewa da
wuri,abinka da quruciya a lokacin yaron da bai saba qarya ba idan yayi ma sai an
ganeshi,sai ta fitittike tace masa wankan tsarki tayi
"Wanne wankan tsarkin,me ya sameki bayan fitata da zakiyi wankan tsarki?" Narai
narai take da ido tace itadai wankan tsarki tayi a tunaninta shi kadai ne mafitar
da zai yadda ba wasan ruwa tayi ba tunda wankan tsarki ne kadai ake jiqa kai idan
za'ayi,idan yaga ta dage sai kawai ya qyalqyale da dariya ita kuwa ta sake hade rai
don kada ya gano,tilas yake sakin murmushi yace ya yadda,tana kawowa nan a
tunaninta ta saki itama murmushin qwalla na bin kuncinta
"Allah ya gafarta maka ya mukhtar,ya kyauta makwancinka" tayi furucin tana goge
hawayen da tafin hannunta,baki daya sai walwalarta ta tafi kamar yadda hakan ke
faruwa yawancin lokuta idan ta tunashi,girkin take amma zuciyarta babu dadi,duk da
haka hakan bai hanata hanzari ha,kafin kace me wannan ta gama girkin baabaa
prof,dashishi ta masa da miyar ganye,wanda kallonta kadai ya isa ya tsinkar maka da
yawu,tun ba yau ba tun tana qaramarta haka hannunta yake da iya sanwa,ballantana a
shekaru takwas zuwa tara da tayi gidan aure ya sake maida ta gwana fagen iya girki.

      Ko da anty dije tazo tayi mamakin saurin girkinta,don tuni suma ta musu
miya,miyar qwaice da alayyahu tayi shar tayi kyau sosao,gun any dijen ta koya amma
sai take ganin kamar ta fita ma iyawa,kasancewar sumayya bai bala'in qwaqwalwa da
saurin dauke abu,cewa tayi ta bar mata sauran ta qarasa tunda tayi kusan rabin
aikin gidan bayan na baabaan.

      Daki ta shiga tayi wanka,saura kusan awa guda kafin a sha ruwa,ta fito ta
shirya kanta cikin atamfa riga da zani,kanta ta daure da dan kwali ta dauki
carbinta ta fito falo,dariya ta zo mata ganin yadda laila ta sake bajewa saman
kujera,khalipha kuwa tuni bacci yayi awan gaba da shi,bata ce musu komai ba ta
sauya tasha zuwa sunna t.v wanda suka sako tafsirij shehun malaminta sheik Ali
ibrahim isah fantami,sosai take jin dadin tafsir din har zuwa wani lokaci data koma
kitchen din ta tadda anty dije ta kammala komai,ita ta dinga kwaso kayan tana
shiryawa saman dining anty dije kuma ta shiga wanka ganin saura mintuna akira
sallah.

     Lokaci qalilan gidan ya kacame,kowa na kaiwa baki,daga nan uncle farouq ya


kada kansu zuwa masallaci sukayi sallar magariba.

     Babu kowa gidan duka sun fita sallar asham tarawih,ta sanya hijabinta zata
tada tata kenan cikin gidan anty dije ta shigo itama sanye da hijabi
"Sumayya,yanzu abban laila ya kirani,yace ki miqa abincin baabaa prof,ga driver nan
yana waje zai amshi nashi abinci sai ya riqe miki wasu kwanukan" babu musu yau kam
sai faduwar gaba jin an ambacin gidan tace to,dirvan nasu shi ya dauki kwandon ita
kuma ta dauki flask daya da ya rage.

     Tana gaba yana binta a baya har suka isa bakin qofar,a mutunce suka gaisa da
baba harunaya bude mata qaramar qofar suka shiga,harabar gidan tarwai take da haske
da fararen qwai,ko ina a haskake tamkar rana,ma'aikatan gidan sanye da unifoarm
nata kaikawo kowa na aikinsa,grass carfet da shukokin dake jere a tsare sun samu
ruwan sama sunyi kyau gwanin sha'awa,kamar yadda garin yayi dadi,iska mai dadi mai
cakude da qamshin qasa na kadawa,sai ta dinga jin wani mishadi na shigarta,tana
shaqar iskar tana mata dadi har cikin qirjinta,ta dinga takawa a hankali har zuwa
tsakiyar harabar gidan,su biyu ta fara hangowa tsaye da alama magana suke kamar
rannan,mahmoud din kawai ta iya ganewa saboda shike fuskantar qofar shigowar,kamar
wancan karon dai dayan na fuskantar mahmoud sai bayansa kawai ta iya hangowa,yana
sanye da jallabiya ta maza fara sol da silifas farare a qafarsa,hannunshi riqe da
dadduma,tana gab da isa garesu ya juya ya shige ta wata qofa da zata iya sadashi da
waje,yayin da mahmoud har ya juya sai ya hangeta,tsayawa yayi yana murmushi har ta
qaraso,hanmunsa ya miqa zai amshi flask din hannunta yana fadin
"Bisa alamu abincin baabaa ne" murmushin itama tayi tana miqa masa
"Eh shine"
"Masha Allah,a gaida umman khalipha" sai ya dubi drivan yana miqa masa hannunshi
alamar ya bashi ,rusunawa yayi cikin girmamawa ya miqa masan sannan ya juya zuwa
qofar fitan,dubanta yayi
"Muje nayi sauri na rakaki kada liman ya tada salla na rasa wata raka'ar,don na
tabbata ya isa masallaci saura minti biyar a tayar" dan baya ta ja kadan
"Ai ba sai na shiga ba ma,ina cewa ma duka masu gidan basa nan,ka kaima baaban
kawai kace ina gaidashi" murmushi yayi
"Kamar ya sanki,na tabbata baki taba zuwa kin gaidashi ba,sannan ko ba kowa a gidan
su anty farida da sauran yara na nan" murmushi ta sake yi
"Zanzo na gida baabaa in sha Allah,su anty farida kuwa ka gaishesu na tabbata suma
basu sanni ba,amma kace ina gaishesu,nima sallah zanje nayi"
"Is ok,ki yiwa umman khaliphan sannu"
"Zata ji" ta fada tana juyawa a hankali ta fice daga gidan.
      Tana shiga ta isarwa anty dije saqon,sannan ta shige dakinta,da hanzari ta
tada isha jin an fara kiran sallar tarawih don sun gama isharsu,cak ta tsaya
lokacin da limamin ya fara karanta fatiha,daina aiki qwaqwalwarta tayi na wucin
gadi,babu abinda kunnuwanta ke ji sai karatun dake fitowa daga lasifiqar yana
karade unguwar kasancewar masallacin na daura sa su ne,muryar da bazata iya mancewa
da ita ba komai tsawon zamani,komai sauyawar yanayi,komai dadi komai wuya,muryar
MUKHTAR dinta take ji tana karade kunnuwanta,wani irin faduwa gabanta ya dinga yi
har ya haifarwa da gabban jikinta yin sanyi,tana so ta zauna amma ta kasa,jin
kunnuwanta take kamar zasu zaunce,hannunta ta sanya ta toshe kunnen nata ko zata
daina jin amsa kuwwar karatun amma hakan ya gagara,kanta ta shiga girgizawa
"A'ah,ba mukhtar bane,wanda ya mutu baya dawowa" ta fada tana ci gaba da girgiza
kanta hawaye na shirin soma sauko mata,a sukwane ta juya ta fito zuwa falon gidan
ba tare da tasan me zata aiwatar ba.

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

5⃣9⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

*KO KUNSAN RANAR QIYAMA ANA DAURE DAN WUTA DA SARQA MAI TSAHON ZIRA'I SAB'IN KAFIN
A JASHI ZUWA JAHANNAMA*

*Astagfirullah wa'atubu ilaih*

___________________________________

     Birki ta ja a falon zuciyarta na wata iriyar bugawa,idanu ta shiga rarrabawa


qwaqwalwarta ta daure tamau,muryar na ci gaba da ratsa kunnuwanta cikin daddadan
sautin karatun mai qunshe da muryar mukhtar,me zata aikata?,abinda ta kasa baiwa
kanta amsa kenan
"Ya mukhtar,ya mukhtar" ta soma fada hawaye na zubo mata,shigowar laila a guje
wadda fitsari ya korota daga wajen sallar ya dawo da ita hayyacinta,bata jirayi
qarasowar lailan ba ta isa gareta ta riqe kafadarta
"Laila,wake karatun sallah a masallaci?,mukhtar ne?"dariya ta saki tana kallonta
tare da yin tsalle alamar fitsarin ya matseta
"A'ah,yaya ne fa,duk azumi shi yake jan sallah" ta fada tana zillewa ta ruga
bandaki,sam bata fuskanci bayanin laila ban ta ji anty dije na cewa
"Shike limanci fa,nan da goman qarshe zai tafi a saudiyya yake sallah sai dai malam
usman ya qarasa" firgigit tayi tana duban anty dije,sai ta kada kai kawai ta juya
jiki a sanyaye zuwa cikin dakin nata ba tare da ta furta komai ba,zama tayi bakin
gado tana jingina da jikin gadon,tamkar wadda aka zarewa laka,ta kasa kowanne irin
tunani,muryar ce kawai ke ratsa dodon kunnenta tana mata shawagi,runtse idanunta
tayi ta koma ta kwanta a gefan hannun damanta,wani abu take ji yana yana zagaya
kanta kamar ana yamutsa qwaqwalwarta,haka hawaye yaci gaba da tsiyaya ta gefan
idanuwanta.

        Sallar da bata iya yiba kenan har aka kammala sallar laila ta shigo kiranta
tazo suci abinci,can qasa ta amsa mata data qoshi sai anjima zata ci,haka taci gaba
da kwanciya,tana ganin tarin misscalled din abdur rahman amma ta kasa dagawa har ya
gaji ya bar kiran ya turo mata texs,baccin dole ne ya dauketa,bata wani jima ba ta
farka,har a lokacin tana jin wata iriyar damuwa na ratsata,sallar isha'in da bata
yiba tayi,sannan tayi tarawih din raka'a bakwai har da wutiri.

  *******   ******   *******

       Daga ranar karatun shi ya zame mata abun sauraronta daga sallar isha'i har a
kammala,sosai karatun da muryar ke debe mata kewa ya sanyata nutsuwa,wani lokaci
tana ji tana hawaye don ba qaramin tuna mata mukhtar yake yi ba,babu wanda yasan
halin da take ciki sai ita kadaj,kawai dai anty dije taga ta rage walwala,bata kawo
komai ba ta dauka ibadar da ake ciki ne.

       A haka aka kammala azumi ashirin cif,ranar ashirin da daya sai taji ba
waccan muryar bace,duk sai taji ta damu,ji take kamar ta fita ta gano me ya kawo
wannan sauyin,daga bisani ta tuna anty dije ta gaya mata goman farko da na tsakiya
kawai yake jan sallah,to wannan wane ne?,babu shakka ba don anty dije ta sanshi ba
babu abinda zai hana tace mukhtar dinta ne,baki daya sai ta jita sukuku,ba qaramin
dadin jin muryar take ba,a ranar uncle farouq ya shigo musu da kayan
sallarsu,kowannensu kala shuda shida a dinke,sumayya laila da anty dije kam harda
mayafai takalma da jakankuna,daga mayafin kawai sumayyan tayi ta ajjiye gefe,tun
mutuwar mukhtar ta sake qanqame hijabi duk da cewa dama al'adarta ne sanyashi,sai
dai a baya tana sanya mayafan lokaci lokaci,anty dije ta lura sai ta bada sautun
yadin hijabai masu kyau aka yi mata irin wadanda take so,anty dijen ita ta sanya
kudinsu ta saya musu dan kunnaye da awarwaro da sarqa fashion designers masu kyau
kala uku uku.

         Washe gari akayo aike daga gidan baabaa prof,duk da cewa a jiya ya daga
saudiyya shima zasu dawo tare da iyalansa a ranar sallah,a qasarsa yake nashi bikin
sallah saboda ziyara da ake kawo masa tako ina,abokai 'ya'ya jikoki 'yan uwa da
abokan arziqi,daya daga cikin ma'aikatan gidan ne,sanye da unifoarm dinsu,a mutunce
ta gaida anty dijen sannan ta miqa mata wata qatuwar baqar leda dake dauke da
tambarin wani company dake dubai,company ne da yaje mallakin daya daga cikin iyalin
baabaa prof din,shahara da daukakar company din ya sanya wasu suma saka jarinsu a
ciki
"Kiyi haquri umman khalipha,tun jiya baabaa ya bada saqon,sai yau na samu sauqin
aiki,munata ayyuka ne"
"Babu komai shema'u,baabaa dai kam bai gajiya,Allah yasa a gama lafiya" murmushi
tayi
"Baabaa badai alkhairi ba,ko mu bai mana mu kadai har 'yan uwa na kusa alherinsa
bai barsu ba,ina zaton wannan karon har baquwarki da nata kayan,naji kamar ita
taiwa baabaan abincin kwana ashirin ko?" Dariya anty dije tayi
"Sumayya,eh itace"
"Ai baabaa na jin dadin abincin nan kam qwarai,rannan har yasa a kira ta su gaisa
sai yayi baqi kuma ya sha'afa"
"Allah sarki,ai idan suka dawo da kaina zan tura ta ta gaidashi,Allah ya saka masa
da alheri,yaci gaba da shirya masa zuria"
"Amin ya Allah"
Shema'u ta fada tana ficewa.

       Juya ledar anty dije tayi tana murushi,tambarin kamfanin kadai data gani
tasan ba kaya bane masu qananun kudi,bude ledar tayi ta fara zarosu,diguwar riga ce
irinta mata mai bala'in kyau da tsari wadda aka zauna aka yiwa aikin duwatsu daga
sama har qasa,iya dutsen kadai idan ka kalla kasan ba qaramin kudi zaka sanya ba
kafin ka mallakesu,yadin kansa abin kallo ne bare dutsen,guda daya baqa ce,sai
dayar fara ce qal da aka yiwa aikin baqaqen duwatsu,dayar kuma ruwan jinin kare ja
ba dau ba ya dan rusuna amma baikai duhun maroon ba,tana duba size din rigar ta
gane sune na sumayya,kowacce akwai vail da ya dace da ita,murmushi tayi don tasan
aikin amira ne wannan,wani shegen fashion mai zubin gwal guda daya da banguls
dinsa,haka na lailaa suke saidai banbancin tsaho da kala,tasan laila kam za'a sha
murna,duk shekara ya saba haka yake musu,duk cikin kayan sallarta tafi ji da kayan
gidan baabaa prof,mazan ma baki dayansu jallabiua ce irinta maza mai tsada,sai
gezna wadda kana mata kallon farko itama kasan ansha kudi kala bibbiyu duka kalolin
iri daya,sanda aka kawo su sumayya basanan sun tafi wankin kai,da suka dawo baki
sumayya ta saki,zata iya cewa banda lace din da aka bata taba kaya masu tsada haka
ba,ko lace din ta tabbata baikai kudin wadan nan ba,yana ajjiye ma bata dinkashi
ba,godiya tayi sosai kamar suna wajen tare da yaba dimbin karamcin ahalin gidan.

      Cikin ranakun goman qarashen so kadan bata yi sanya wajen zabga addu'a gareta
da d'anta da sauran yaran musulmi ba da al'umma ba,musamman ranakun da suke
mara,wato ranakun da ake tsammacin dare lailatul qadr,tayi addu'ar samun kyakkyawar
rayuwa da kuma kyakkyawar QADDARA,sai ta dinga jin nutsuwa da kwanciyar
hankali,tsoro da damuwarta suka dinga raguwa a hankali.

        Ran ashirin da tara ga wata aka tabbatar da ganin watan sallah waahegari
idin qaramar sallah kenan,a gajiye ranar suke don wuni sukayi gidan qunshi,da cewa
sumayyan tayi ma bata yi,anty dije ce ta matsanta mata tilas ta bisu,ga wainar
shinkafa da ta tsara zata yi musu a ranar sallah,Allah ya taimaka kafin ta kwanta
tayi miyarta,zumudin zuwan sallar take sosai wannan karon,saboda uncle farouq yace
sallah da kwana biyar zasu tafi kano,a qalla zasuyi sati guda sannan su dawo su
fara shirin tafiya london.

*******   ******    *********

        Qarfe goma na safe tuni an sakko daga sallah,zuwa lokacim sumayya ta


kammala aikinta,wankanta tayi ta shirya cikin daya daga cikin dinkin da abban laila
ya musu,ba wani makeup tayi ba amma kayan sun mata kyau,rabon abincin sallah anty
dijen tayi kamar yadda ta saba.

       Da yammaci su laila da khalipha nata hada barka da sallah sabbin kudi baki
yaqi rufuwa,sai shigowa suke suna bawa sumayya labari su wance sunzo gidan baabaa
su wane sunzo,itakam kusan bata sansu ba saidai tace musu to,dariya anty dije tayi
"Abokansu ne jikokin baabaa prof, 'ya'yan babban dansa da me bi masa,kinsan duk
wani da nashi da jika dake nesa a gida yake sallah". Abban lailan nata baqi,wasu na
zuwa wasu na tafiya kusan haka suka wuni.

        Wajen biyar tana sama dakin anty dije tana gyara mata,saboda yau baki daya
ta kasa zama saboda baqi,hayaniya ta dinga jiyowa da qarar motoci,sau ta miqe a
hankali,ta yaye labule tare da bude qofar da zata sadaka da balcony din anty dije
dake saman,bata fiya budeshi ba sai lokacin zafi ko kuma idan ta kama saboda idan
ka fita kana iya hango jama'an waje suma suna iya ganinka musamman da yake yana
center din tafkeken get din shiga gidan su amira,duk da cewa waccar babbar qofar da
akafi shiga  wadda jami'an tsaro ke gadinta tana daya daya layin nasu,wannan a nan
suka fi harkokinsu.

      Motocine na alfarma qirar zamani,wanda ke dauke da lamba mai tambarin sunan


baabaa prof,wanda hakan ke alamta mallaki ne na ahalinsa,kimanin mota shida kowacce
na qoqarin shiga gidan ba tare da wata ta gogi wata ba,sai da suka kammala shiga
baki daya sannan wadanda suka wangame get din suka rufe shi,ajiyar zuciya ta saki
sannan ta juya ta koma cikin dakin wanda hakan yayi dai dai da shigowar anty dije
"Kai,har kin gama?" Tana duba yadda ta gyara kayan
"Na gama anty" inji sumayya tana dan kashingidewa
"Kinga yanzun abban laila ke gayan su baabaa sun dawo,amma dai wannan karon zaki ki
masa sannu da zuwa ko ku gaisa"dan murmushi ta saki yana yamutsa fuska
"Eh anty,amma dai ba yanzu ba ko?"
"Nima ai bance yanzu ba,kinji an ambaci maqiyinki shiga gidan baabaa ko?" Dariya ta
tuntsire da ita har tana kwanciya ganin irin yadda antyn tayi maganar.

  *****  ********    ******

    Washe gari da yammaci hudu da ashirin bayan ta gama yima anty dijen komai,sai
ta shirya cikin wasu kayan nata,swiss ne mai asalin tsadar wanda aka tsara mata
dinki na riga da skert,babu kwalliya a fuskarta kamar ko yaushe tun bayan rashin
mukhtar cikin rayuwarta illa hoda jagira da liptsic,sabon hijabinta mai hannu
wannan karon iya gwiwarta ta zura wanda yayi marching da lace din jikinta,tayi kyau
sosai kayan sun haska ta,tun dazun take laqai laqai na zuwa gaida baaban,hakan ne
yasa ma ta tsiri yi masa dambun zallar tsokar kaza.

       Anty dijen ita ta sake turo qofar dakin karo na biyu tun bayan shigarta
wanka
"Baki gama bane har yanzu?"
"Na gama anty" ta fada tana fesa turare
"To,saidai fa ki shiga ke daya kya tadda lailan acan,don duka suna can gidan,ta
kasa jiranki,don naji tana kamar zasu park ne"
"To" ta fada badon ranta ya so ba,takalmi ta zura mara tsahon dunduniya sannan ta
fito.

        Daga qofar gidan baka gane gidan na qunshe da baqi ba sai ka kai ga shiga
harabar gidan,yara ne da 'yammata kala kala,wadanda kana duban yanayin shigarsu
zaka tabbatar da cewa lallai boko ya ratsasu,wayewa da kuma sanin kam duniya,kamar
yadda group group ya rabu haka kowacce da irin tata shigar,ta wannan tana wace
wance,nan da can zaka ga mutum biyu uku har hudu ma a tsaitsaye,kowa na sabgar
gabansa saboda wadatar guri da kujerun zama a ko ina,wanda suke nuna lokaci irin
wannan ake fiddo su ayi amfani da su.

       Sai taso ta rude baki daya,ta dinga takawa a hankali tana tunanin inda zata
shiga
"Muje na rakaki,naga alamar ko yaushe tsoron shigowa gidan nan kike,ko wani ne zaya
kamaki?" Taji an ambata daga gefanta,waiwayawa tayi a hankali,mahmoud ne,yayi
adonshi cikin shadda ruwan sea blue,ta masa kyau sosai ta fidda ainihin
surarsa,murmushi ya subuce mata,sai ta girgiza kai kawai tana gaidashi,ya amsa mata
suka fara takawa zuwa ciki
"Naga kowa tun daga ranar sallah da muka dawo zuwa yau,amma ke kam ban ganki ba,su
laila tun dazu suna gidan nan,zaman gida bai damunki ne?" Murmushi ta sake saki
tana kada kai
"To ina zanje,ba wanda na sani"
"Nan fa,nan ma gidanku ne,ko bakiga yadda su laila suka maidashi gidansu ba?"
"Haka ne" ta amsa masa don batasan me zata ce ba,shima shirun yayi suka ci gaba da
takawa,suna gab da shiga bangaren anty maamaa yace
"Dama dai wani abun dadi kika kawowa baba,yau a gunsa zan maqale,kinsan ni da yaa
man bamu cin abinci idan akayi buda baki har sai an kawo na gidan umman
khalipha,yace shikam bai gane mana wannan wayon namu ba da muke maqale masa a
kwanon,har gwara ni gauro ne shifa yaayaa fa" dariya ya bata har sai data
murmusa,ta fuskanci mahmoud irin mutanen nan me masu barkwanci faran faran da
saurin sabo da mutane.
        A falon anty maamaan suka ci burki,wasu 'yammata ne zaune a falon biyu na
saman kujera biyu na qasa,kowacce ta baje kayan kwalliya suna makeup,baki daya sun
cika falon da hira da karadi,kayan sawarsu na aje gefe da alamu fita zasuyi wata
unguwa,kana dubansu zakasan suna daga cikin baqin da gidan ke karba a irin wannan
lokaci,sallamar mahmoud ita ta janyo hankalinsu
"Anty maamaa" kawai ya fadi,daya daga cikinsu wadda ke qoqarin daura dankwalinta
tace
"Tana G-kitchen" juyawa yayi ya dubi sumayya
"Idan baki gaji ba muje bata cikin nan" bata ce komai ba tabi bayansa yayin da
'yammatan suka bishi da kallo,wadda ke daura dankwalince ta tabe baki,kishi ne fal
bayya ne a fuskarta,ta kusa da ita ce ta zungurota ganin yadda take binsu da kallo
"Uhmmm,yadai?" Qaramin tsaki ta ja
"Nikam baisan me yasa Allah ya zubawa mazan gidan nan girman kai ba,suna jin kamar
su kadai ne halittar maza da Allah ya qirqira a ban qasa,jibi,kamar baisan wace ni
ba" dariya wadda ke shafa powder ta qyalqyale da ita sannan ta tsaya da abinda take
yi
"Kema kinsan su isa sun kai suyi girmankan,karfa ki manta su su waye?,kina zaton
samunsu a bagas ne,nikam banga laifi ba don sunyi girman kai sun kai suyi ne,kibi a
sannu idan da rabonki zaki shiga familyn prof,nikam tuni na sallama" ta fadi tana
ci gaba da murza hodarta,shiru tayi bata sake cewa komai ba sai taci gaba da gyara
daurin dankwalin nata cikin sanyin jiki.

      Bayan suka zagaya sai gasu cikin wani qaton kitchen wanda idan ba wajajen
kayi ba ba lallai kasan da zamansa,kitchen ne babba mai dauke da electrics kala
daban daban da manyan tukwane,kayan girki nau'i daban daban,kitchen ne da
ma'aikatan gidan ke haduwa suyi amfani da shi duk lokacin bikin sallah irin
wannan,biki ko suna na gidan idan ya tashi,gaidasu sumayyan tayi tare da yi musu
sannu da aiki,antyn na tsaye sanye da jar shadda wadda keta maiqo da qyalli dinkin
bubu da aka yiwa adon baqin zare,duk da ta tasamma shekara arba'in da kusan biyar
amma sai ka zaci 'yar talatin ce,anty mama kam badai ado ba,tana sabe da wata
kyakkyawar yarinya wadda aqalla zatayi shekara daya,an mata kwalliya cikin riga da
wando,gashin kanta kuwa adin ribbom ne kala kala,ma'aikatan take sanarwa mai za'a
dafa a mazaunin abincin dare a gidan baki daya
"Ah mahmoud yadai?,kun fasa tafiyar ne?" Ta fada bayan sun gama gaisawa da
sumayya,shi kuma yana jan yarinyar dake kafadarta din da wasa wadda da alama itama
jikar gidan ce,sumayyan na tsaye gefanta antyn riqe da hannunta daya
"A'ah,wannan mai tsoron shigowa gidan nan din na rako zata gaida baabaa" murmushi
tayi ta juya tana kallon sumayya,haka nan sumayyan take burgeta tun ganin farko,da
alamu zatayi nutsuwa,bata da rawar kai da fi'ili irin na 'yammatan zamani,shigarta
kadai ta tabbatar mata da cewa daga babban gida ta fito,koda ba gidan da suke da
kudi da ababen more rayuwa ba,a'ah,babban gida na nufin gidan mutunci da
karamci,gidan da aka san dattako,gidan da usuli ilimi tarbiyya da wadatar
zuci,gidan dake cike da tarbiyya da daraja
"Ba tsoro bane,baqunta ce" inji antyn tana murmushi,kusa da antyn ya matso bayan ya
ajjye mata kwanon
"Nidai anty gashi nan,a tuna da ni idan baabaa zaici abinda ke cikin kwanon nan"
hararsa tayi
"Haka fa,anqi aure anbi an takura mana miji,kunqi barinsa yayi auki,komai zaici sai
kun tayashi" dariya ya sanya yana ficewa tare da fadin
"Wannan tsohon mijin naki anty ana ji da shi" itama dariyar tayi sabida tasan halin
zolayar mahmoud,qarasa lissafa musu abinda ya dace tayi sannan ta dubi sumayya tace
"Bismillah" ta soma qoqarin tafiya tare da daukar kwanon,ganin haka ya sanya
sumayyan matsawa kusa da antyn ta miqawa yarinyar hannu,zubawa sumayyan ido tayi
tana kallonta,dariya anty tayi
"Wannan uwar qyuyar,Allah yasa ta yarda,uwarta na can ta tafi yawon saloon din da
ba'a yishi ba sai yau ta barni da rigimamma" kamar taji kuwa abinda antyn tace sai
ta miqawa sumayyan hannu alamar ta dauketa,ba antyn ba har masu aikin ta basu
dariya,saboda kowa yasan qyuyarta ba da kowa take yarda ba
"Lallai kin ciri tuta mai sunan umma" ta kira sumayyan da haka saboda tuna sunan
wace garesu,murmushi ta danyi tabi bayan antyn tana duban yarinyar,sai ta tuna mata
abdallahnta,ko yanzu me yake?,tana kewarsa sosai,ta qagu lahadi tayi ta ganshi,sai
kuma ta tuna yaranta wadanda ke tayata zama tun suna tsohon gidansu da mukhtar,su
naana kam tasan yanzu sun girma,tana saka ran in sha Allah da zarar ta koma zata
ziyarcesu,itakam tasan cewa son yara a jininta yake haka halittarta take,duk inda
taga yaro ya dinga burgeta tana kallonsa kenan.

A hankali suke ratsa gidan anty maamaan na janta hira kadan kadan,jefi jefi
suna gaisawa da mutane a kan hanya wanda da alama basu hadu bane tun safe sai
yanzu,ba mamaki saboda girman gidan wanda ya iya hadiye duka baqin dake ciki,tun
daga farkon sashen ta tabbatar da cewa akwai banbanci da sauran sasannin
gidan,antyn dai na gaba tana bin bayanta,yarinyar na ci gaba da kallon sumayya tare
da yi mata shirmen surutu irin na yaran dake son koyon magana ita kuwa na biye mata
anty na binsu da murmushi har suka isa qofar da zata sadasu da babban falon dake
mallakin mai gidan ne.

     

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

6⃣0⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

*SHIN KO KUNSAN DUK LOKACIN DA AZABA TA TSANANTA GA DAN WUTA,FATAR JIKINSA TA


KWASHE TA QONE,ANA SAUYA MASA WATA FATAR NE SANNAN ACI GABA DA GANA MASA AZABA*

*Allahumma la tada a lana zanban illa gafartah*

____________________________________

        Dattijo ne mai kimanin shekaru sittin da biyar zaune kan daya daga cikin
kujeru na alfarma dake zagaye da falon,haiba kwarjini da kamala sun bayyana qarara
kan fuskarsa,Allah yayi masa baiwar furfura tun daga gemu zuwa kansa,farin gilashi
ke saye a fuskarsa baya ga shaddar dake jikinsa fala sol,dogon wando da riga mai
gajeran hannu iya gwiwa,da alamu akwai babbar rigarsu wadda bai sanya ta ba,gefensa
daga hannun dama samari ne guda uku,wanda ke daura da shi yana fuskantarsa
sosai,bisa alamu magana suke mai muhimmanci,kyakkyawan matashine mai cike da kyau
kwarjini izza da haiba,sanye yake da irin kayan tsohon bisa dukkan alamu anko
sukayi,shi dinma fuskarsa sanye take da gilashin,daya hannun nashi ma wasu
matasanne su biyu sai mata guda biyu.

     Tunda suka shigo falon gabanta ke mugun faduwa,sosai ta dinga qoqarin baiwa
kanta qwarin gwiwa saboda haka sai ta sadda kanta qasa har suka qaraso cikin falon
suna sallama,dattijon ne ya amsa da wasu daga cikin mazauna falon,idonsa na kan
antyn da sumayya har suka qaraso,gefe ta samu ta zauna daga qasan carfet din,da
sauri baabaa yace
"A'ah,tashi ki koma saman kujera mana" murmushi tayi kanta na qasa,ta soma gaidashi
tare da yi masa sannu da zuwa,fuska sake tamkar ya santa ya amsa mata,anty ta
dubeshi
"Nasan baka santa ba" sake dubanta yayi yana gyada kai
"Gaskiya kam,koda na santa to ta kwanta min,kinsan shekarun sun fara turawa sai a
hankali" sauran dake zaune sukayi danyi dariya banda mutum daya da tun shigowarsu
ya dauke kansa ya maida hankalinsa kacokam kan wayarsa yana tura saqonni,hakanan
ransa yake a bace.
"Itace wadda ka dinga bamu labari ka kwashi girki na kwana ashirin ka dinga zabga
santi" baki daya dariya suka kuma saki wanda hakan ya dan ja hankalinsa,har ya
sanyashi daga kai ya mata kallo daya tak ya sake maidawa kan wayarsa yaci gaba da
abinda yake
"Masha Allah,Allah yayi albarka,naji dadin abinci kam qwarai da gaske,Allah yayi
albarka"
"Amin baabaa,na gode" ta fada cikin jin dadi bisa dabi'arta ta son na gaba da ita
wanda take saka ran addu'arsa zata iya binsa ya sa mata albarka,hannu ya miqawa
husna wadda ke hannun sumayya,ta kuwa lafe a jikinta tamkar ta santa,qememe taqi
zuwa,sai ya zura hannunshi cikin aljihun rigarsa ya zaro alewa,kasancewarsa mai
yawan kyauta,musamman a irin wannan lokaci da jikokinsa ke kasancewa a gidan tare
da shi,hakan ya sanya baya rabo da alewa da sabbin kudi,miqa mata yayi take kuwa ta
tafi gurin nasa,hannu yasa ya dagata yana dariya jama'ar falon na tayashi,tsaki ya
ja qasa qasa yana miqewa,shikam bai san me yasa abun dariya bai yiwa su mu'azzam
wuya ba,shi baki daya ma baiga abun dariya ba,yarinyar ma tunda ta shigo baki daya
ma yaji ransa ya baci,musamman katse musu hanzarin da tayi kan muhimmin batun da
suke tattaunawa,tun dazun dama yake addu'ar kada wani ya shigo saboda baison abinda
zai katse masa bayanin da ya daukowa baban,ya san mutum ne shi mai mutunta
baqo,kome yakeyi yana iya katsewa ya saurari baqonsa,sarai baaban ya ganshi amma
sai ya qyaleshi,yasan halin kayansa sarai,da idanu ya rakashi har ya fice,ganin ya
fita ya sanya sauran miqewa
"Baabaa kada fa ya tafi ya barmu"
"Jeku,don tsaf zai iya aikatawa,musamman da kun zo da tsarin da baiyi masa
ba"dariya suka yi sannan sukayi sallama da baban suka fice,tattambayarta baabaa
yayi kan wasu abubuwan tana amsa masa,har alokacin kanta na duqe,ta miqe bayan wasu
mintuna ta masa sallama,sai anty ta ajjiye masa kwanon tana masa bayani,qwarai da
gaske yaji dadi,domin shi mutum ne da baya raina alkhairi komai qanqantarsa,koda
yafi qarfin abu ka bashi shi yana ganin girmansa abun agunsa,dakatar da ita yayi
yana fadin
"bari na baki zamzam da bagaruwa ko"
"To" ta fada tana murmushi,antyn yama kwatance cikin dakinsa,cikin sakanni ta shiga
ta fito da wata jarka
"Ba ita ba,zamzam din da nayi dawafi da shi" mamaki antyn tayi,don irin wannan zam
zam din ba kowa yake bawa shi ba,dashi yaje dawafi da addu'o'i,yakam zama magani
cikin ikon Allah ga duk wanda ke jin lalura ya bashi yayi amfani da shi,duk da
kasancewarsa tantagaryar dan boko amma akwai ilimin addini mai yawa tattare da
shi,jarka ce guda tayi tsawon ta faro qarami ya zuba mata,sannan ya cika mata leda
da bagaruwa da dabino,godiya tama baban sosai ta kuma ji dadin kyautar tasa,tare
suka fito da antyn
"Anty zan koma"
"Haba daga shigowarki,kodai tsoron kike ji kamar yadda mahmoud ya fada,naga ko
mutuniyar taki amira baki gani na,bayan ita tunda muka dawo take maganarki,na
tabbata baqi ke suka hanata fitowa da tuni kin ganta,sannan baki shiga kin gaida
ummee ba" sam bata so antyn ta debo mata wannan bayanin ba,amma sai ta sadda kai
tace
"To,bari na shiga"
"Yauwa,ki gaida ummam khalipan don Allah idan kin koma,nasan itama baqi ke suka
hanata leqowa,dukkanmu irin wannan lokacin sai haquri baqi muke ba dauke qafa"
"To zataji" ta furta sanda antyn ke yunqurin amsar husna,nan ma qi tayi,dariya
antyn ta dinga
"Shikenan kuje da ita kin samu qanwa,idan tayi kuka ko laila kaya bada ta kawota"
"To anty" tafada tana dariya tare da yin gaba.

        Baki daya falon ya sauya ba kamar waccan karon data shigo shi ba,da alama
gyaran azumin ne,komai ya canza a falon,saidai tun kafin ka kai ga qarasowa cikin
falon zaka jiyo muryarta,tana tsaye tsakiyar falon hannunta riqe a qugu tana zuba
masifa,bisa alamu da 'yanmatan dake zaune a falon take,sun kusa su hudu harda amira
dake gefe tana shan ice cream hankalinta kwance kamar ma bata falon
"To bani cike da iskanci,ran kowa sai ya baci wallahi,bazan dauki raini ba,kuma
wanda ya fasa karbo greeting cards na 'yammata yana kawowa bai cika ba mu zuba ni
da ku,aikin banza kawai" tana gamawa ta juya a fusace tana taku kan tsireren
takalminta mai igiya,kowa sanye da suturar al'ada banda ita,wando ne a jikinta irin
straight leg din nan,sai riga one shoulder a jikinta,gefe sumayyan ta janye tana
dubanta,dariya taji 'yammatan suka saki bayan fitar tata banda amira fake ci gaba
da abinda take,daya daga cikinsu tace
"Duk wayon amarya wallahi sai an sha manta"sai a lokacin sumayyan ta maimaita
sallamarta,amira ce ta amsa cikin fara'a ta miqe
"amiran umman khalipha kinsan kina raina,sannu ga guri zauna" tana mata nuni da
wata kujera dake can gefe babu kowa,qarasawa tayi tana zaman amira ta sake cewa
"Ina kika tsinto wannan uwar qyuyar,daina kallona kina wani saukar da kai ban
daukanki zanyi ba nima" ta fada tana dan daga murya da zaro ido da alamu tana jin
haushin irin qyuyar husnar,murmushi sumayya ta saki tana dafe kan husna wadda ta
kwantar da kanta aqirjinta
"Dole fa ta miki qyuya,kina mata irin haka"
"Allah bata da kirki" gaisawa sukayi ta mata sannu da zuwa sannan ta tambayi ummin
"Ummi na sama,bari na miki kiranta"
"To" ta amsa,satar kallonta 'yammatan suka ci gaba da yi itakam hankalinta na kan
husna tana mata wasa a haka amira ta dawo ta tadda su,ba dadewa ummin ta
sauko,abinda sumayya ta dan lura da shi shine,ummen irin mutanen nan ne da basu son
hayaniya da yawan surutu.

       A mutunce ta gaidata ta amsa mata fuska a sake itama tana son daukar
husna,saidai itama husnar ta watsa mata qasa a idanu kamar sauran,tilas ta barta
sumayya na mamakin qyuyar yarinyar,bata wani jima ba tayi musu sallama ta fice
sabida yadda 'yammatan ke kallonta.

       Anty dije ma tayi mamakin ganinta da husnar,goyata tayi bayan ta bata


abinci,ba jimawa kuwa tayi bacci a bayan nata,gab da magariba sukaji sallama a
falon,sumayyan ce ta fito goye da husnar tana amsawa,magidanciya ce wadda zata
doshi shekara talatin da hudu,fuska a sake sumayya tayi mata sannu da zuwa,leqa
bayan sumayyab tayi tana riqe baki cikin fara'a
"Wai lallai raino yayi dadi,ashe kam da gaske tana nan din,ni ina can hankalina na
kanki uwar qyuya ashe ke kin haye bayan mutane kina bacci abinki" dariya sumayya ta
danyi sai alokacin ta fuskanci mamarta ce,yunqurin saukota tayi tana fadin bari ta
bata ita
"A'ah,barta mana idan ba'a matsa miki ba,haba sai kace bare,da nan da gidan baabaa
ai duka daya ne,kawai dai idan ta tashine nasam zata taba miki darunta,sai azo a
dauketa"
"To" ta amsa tana gyara goyon
"Ina anty dije" ta ambaceta da sunan da suke kiranta a kano sabanin yadda taji
mutan gidan na kiranta da umman khalipha
"Yanzun nan ta shiga wanka"
"Sarkin kwalliya wa miji,idan ta fito kice ina gaidata" ta fada da sigar
zolaya,bisa alamu sun saba sosai.

      Bata farka ba sai bayan magariba sumayyan ma na shirin tada isha'i,daukota


tayi daga kan gadon ta cire mata pampers tare da zuba abinci ta bata,sai da taga ta
qoshi sannan ta sabata a kafada ta zura hijabin sallarta wanda ke kusan sharar qasa
tace khalipha yazo ya rakata.

        Tarwai gidan da haske kamar kowanne lokaci,saidai yau akwai yawaitar mutane
a harabar gidan,sashen anty maamaa ta shiga tacu sa'a ko ta tadda maman
husnar,amsarta tayi tana yiwa sumayyan sannu tare da godiya.

       Tunda ta tako daga sashen anty maaman ya zuba mata idanu,haske gidan kadai
ya wadatar masa ya gane wace ita,mahmoud da ya gaji da yi masa magana ya dafa
kafadarsa wanda hakan ya sanyashi daga kai da sauri yana dubansa
"Mahmoud,sumayya ta nake gani a gidanku" waiwayawa yayi zuwa inda yaga alqasim din
na kalla,tabbas sumayya ce ke tahowa
"Wannan sumayyan ce sumayyarka dama?"
"Wallahi itace" alqasim ya fada a rude,dariya mahmoud ya saki
"Ai tazo gidan sauqi,amma fa ba abune mai sauqi ba shawo kanta haka na fuskanta"
"Please mahmoud" alqasim ya fada cikin damuwa yana hade hannayensa ganin sumayyan
na gab da su
"Don't mind"mahmoud ya furta yana waiwayawa yadda zata iya ganinsa idan ta
qaraso,sam bata lura sa su ba duk da hasken da ya wadatar da gidan tamkar
raba,hanakalinta na gefe can inda wasu 'yammata ke zaune suna hira,kusan basu suka
dauki hankalinta ba ma yaran dake wasansu kusa da su ne,wanda daya daga cikinsu
keta kiran abbanaa da alama labarin abban nasu yake basu,tana ganin sa'o'in
abdallah a ciki,cikin ranta ta raya suna cikin farinciki da gata,sabanin abdallah
da take fatan zai tashi cikin farinciki saidai baisan dadin uba ba,qwalla ta taru
idonta sai tayi hanzarin sadda kai da qara sauri a tafiyarta don ficewa daga
gidan,tun jiya ranta a jagule yake,hakanan ta wuni da tunaninsa cikin ranta,wanda
ya haddasa mata kasala da mutuwar jiki wunin baki daya,shi ya qara mata qyuyar
fitowa waje
"Yi a hankali kada ki fadi" mahmoud ya fada yana dubanta,cak ta tsaya tana dubanshi
tare da qaqaro murmushi
"Hala sauri ake a fice daga gidan namu"dariya ma yaso bata saidai bata yin ba sai
murmushi saboda damuwar da zuciyarta ta shiga daga tuna mukhtar
" kadai camfani"
"Ko kadan,to daina saurin,ga baqo kinyi,yanata nemanki wata da watanni sai yau
Allah ya qaddara haduwarku" a zabure kamar wadda ta yiwa sarki qarya ta daga
kai,suka hada idanuwa da alqasim,farinciki yake ji sosai cikin ransa,takowa yayi
gefanta yana dubanta
"Zakaran da Allah ya nufa da cara sumayya,mai yiwuwa Allah ya qaddara wani lamari
ne mai girma tsakaninmu,shi yasa ya kado hankalina abuja gidansu abokina
mahmoud,ashe rabon na ganki ne" ba shakka tana ganin girma da qimar mahmoud,tunda
shi ya soma tsaidata,banda haka da tuni ta yankawa alqasim warning cikin daqiqun
nan tare da kaucewa.

        Saye yake da quater zip sweater mai dogon hannu ta kamfanin armani maroon
colour saboda sanyin da ya soma busawa sakamakon hadarin da ya hadu dazu bai zub da
ruwa ba sai ya bada sanyi wa garin baki daya,wandon jeans baqi,sai high top
sneakers,hannayensa saye cikin aljihun wandonsa ya fito zuwa harabar gidan yana
duddubawa,kusan al'adarsa ce wannan a lokaci irin wannan,kafin yaje ya kwanta sai
ya dudduba ko ina saboda baqin dake gidan,ya tabbatar babu yarinyar data fita yawo
balle akai ga zuwan saurayi zance gidan,yace duk mai buqatar hakan ta bari idan ta
koma gidansu tayi abinda taga ya mata amma ba cikin gidansu ba,tsarin ya yiwa
baabaa prof saboda haka baice komai ba,a irin hakan wasu daga 'yammatan wadanda
suke zaton wayewa ce garesu,iliminsu da gogewarsu ta kai wani mizani,sukan fita
ciye ciye ko siyayya da samarinsu,wani lokaci sukan kai goma ko tara na dare basu
dawo ba,yayin da wasu sukan maida harabar gidan filin baje kolin gayyatar saurayi
suyi zance,hakan ne ya sanyashi sanya wannan doka wadda ta yiwa manyan dai dai
saboda tsaron tarbiyyar kowacce yarinya har ta koma gidansu,hakanan duk wanda ke
kawo ziyara gidan a irin wannan lokaci ya san da dokar,walau mace ko namiji.

Cikin izza da ginshira yake takowa tsakiyar harabar gidan yana qarewa
kowacce kusurwa ta gidan kallo da idanunshi,tuni hayaniyar wajen ta soma raguwa
kowa ya soma shiga taitayinsa,wasunsu suka shagala da kallonsa,masu gulmarsa qasa
qasa nayi.

Kamar ta sanya kuka haka sumayyan keji,yayin da alqasim kuma ya dage wajen
ganin komai ya daidaita kafin barinta wajen,idanunsa ya sake wurgawa wani sashen,a
can saka masa kamu,maca ce tsaye da hijabinta har qasa da wani saurayi tsaye a
gabanta,sai wani saga gefanta,ranshi ya matuqar baci,ya tsani ya sanya doka a karya
masa,a ganinshi wannan daya ne daga cikin alamun raini,idanu ya zuba sosai sai ya
dinga hango kamar mahmoud ne dayan dake gefe,cikin bacin rai ya soma takawa
idanuwansa na wajen,sam mahmoud bai ankara da fitowarsa ba shakka da tuni ya
sallameta,ya riga da yasan halinsa sarai mutum ne mai doka da qa'ida,bazai karya
dokar wani ba so shima kada a karya tasa shine zaman lafiyar mutum.

"Mahmoud" ya ambaci sunanshi bayan isowarshi gun,wani abu taji ya caketa tun
daga tsakiyar kanta zuwa tafin qafarta da taji muryar mukhtar gab da ita,kuma a
bayanta,kamar mai ciwon wuya haka ta dinga waiwayawa a hankali har ta kammala
juyawa baki daya,tsaye yake harde da hannayensa yana yiwa mahmoud da alqasim magaba
cikin bacin rai,idanuwansa na kansu,wanda sam bata iya jin abinda yake gaya musu
illa bakinsa da take gani yana motsawa,muryar ce taci gaba da yi mata amsa kuwwa
cikin kunnuwanta,a hankali ya dinga juye mata zuwa mukhtar dinta,sannu sannu
jikinta ya soma rawa tamkar wadda aka tsoma cikin ruwan sanyi,bata ankare ba taga
yana qoqarin juyawa ya bar gurin,batasan lokacin da ta daga murya cikin qaraji daya
sabbaba har wadanda ke daura da su jin sautinta ta ambaci
"Mukhtar!" Cak ya tsaya tare da waiwayowa yana dubanta,kallonsa take tana takowa
zuwa gurinsa a hankali,tsayawa kawai yayi yana dubanta,tun dazun haushi ya tsaye
masa a wuya,tunda ya tsaya gun ya lura da yadda ta zuba masa udanuwa,abinda ya
tsana kenan cikin kafatanin halayen 'yammatan wannan qarnin,kallon tsiyawa d'a
namiji,babu wata kunya tattare da su
"Mukhtar kai ne?,kaine mukhtar!,dama kana nan,dama baka mutu ba?" Cikin bacin rai
da yi mata kallon mai tabin hankali ya dubi mahmoud
"After All ma ashe da mai lalurar tabin hankali kuke tsaye?,sai kuzo kusan yadda
zaku fidda ta tun kafin ta soma yiwa mutane barna"
"Mukhtar nice fa,sumayyarka ce mukhtar,nike da tabin hankali?" Har yanzu bai
gasgata mai hankali bace,amma sai ya nutsu tsaf ya dubeta,babu alamu na hauka
tattare da ita,ayyanawa yayi kawai tsabar rainin wayo ne da son samun guri,wanda ba
tun yau ba ya gama haddace kissa ta son samun guri na 'yammata masu cusa kai kala
daban daban,wani tsaki ya ja,sannan cikin dakakkiyar muryarsa wadda ta sake
taimakawa wajen sawwara mata surarsa zuwa ta mukhtar yace
"Ban ciki da hauka da gidadanci kinji ko,ki kama kanki tun bai gudu ya barki
ba,kama hanyarki ki koma inda kika fito" ya juya yana yunqurin barin wajen,a zabure
ta bishi har ta samu nasarar riqo dantsensa,cikin tsananin bacin rai ya juyo yana
dubanta cikin ido,wani kallo ya jefe ta da shi wanda tabbas da cikin hayyacinta
take tuni ta sake shi saidai sam ko a jikinta
"Sake tafiya zakayi ka barni?"
"Sakeni!" Ya daka mata tsawa
"Bazan sake ka ba" itama ta fada cikin tsawa da bacin rau,take zuciya
tanzuroshi,marinta yaso yi amma yaga rashin dacewar hakan,maiyiwuwa akwai tabin
qwaqwalwar da batasan tana da shi ba,yaga kuma alama matuqar yaci gaba da tsaiwa
zata iya ma rungumeshi kaban wadan nan yaran ta zubda masa mutunci,saboda haka sai
ya fincike hannunshi tare da tunkudata yayi gaba,wani irin zafi yake ji da
haushinta,baya tayi cikin rashin qwarin jiki,sun tsammaci zata turje ta tsaya sai
kawai suka ga ta sulale ta zube baki daya,cikin firgici da tashin hankali mahmoud
ya soma qwalawa amira kira don babu damar taba ta wadda fitowarta kenan shan iska
batasan ma meke faruwa ba,ganin sumayyan kwance ya daga hankalinta ta koma ciki a
sukwane,nan sukayi kacibus da anty farida mamar husna ta kamo hannunta suka yo
wajen.

Ba amira da anty farida ba,hatta mahmoud da alqasim hankalinsu tashi


yayi,kowa mamaki yake,meke faruwa ne haka,abu kamar dramer cikin sakanni
qalilan,tana ta faman kiran mukhtar shi kuma wannan ALMUSTPHA ne abinda suke tunani
kenan,cikin hanzari anty farida ta soma yunqurin dagata da taimakon amira,idan ka
dubi fuskar wasu dai daikun 'yammatan dake gun jimami da tausayi ne bisa
fuskrsu,addu'a suke mata kan Allah yasa ba qoshin wahalar da suka afka bane itama
ta afka cikinsa,yayin da wasu dadi ya rufesu kamar su taka rawa,ko banza basu zama
su kadai ba cikin wadanda suka rasa wannan damar.

A hankali ta ja numfashi tana ambaton sunan Allah,idanunta ta bude,jinta


take kamar wadda ta tashi daga bacci,idanuwanta ta sake lumshewa take abun ya sake
fado mata,kalamansa da muryarsa suka fara yi mata amsa kuwwa cikin kunne,take
idanuwanta suka tara hawaye masu dumin gaske suka soma bin gefen kunnenta,sake
rintse idanuwanta tayi,kamanninsa suka fara dawo mata ganin farko data yi masa
kafin idanuwanta su rudeta,da sauri ta bude idanuwanab tana girgiza kai,tabbas ba
mukhtar bane,babu kamannin mukhtar ma tattare da shi idan ka dauke murya,me ya
shiga kanta ta aikata haka sai kace wadda jinnu suka juyawa tunani?.

Saitin fuskarta taga an turo screen din waya,idanuwanta ta bude kan screen
din,shine,shine wanda ta gani dazun,sanye yake da qananun kaya kyakkyawar fuskarshi
qunshe da murmushi,hotonsa ya cika fuskar wayar baki daya,a yanzun ta sake
tabbatarwa bata ga kama tsakaninsa da mukhtar dinta ba,sai ta waiwaya don taga
wanda ke haska mata hoton,amira ce zaune gefanta,idanuwa suka hada sai ta janye
wayar tata ta kasheta tana duban sumayya
"Wannan yaya nane,mama da baabaanmu daya,ummee ita ta haifemu,sunanshi MUSTAPHA ko
ALMUSTAPHA duk daya ne,anty dije ta bani labarin waye mukhtar a gunki,matuqar suna
kama da mukhtar kuma yayi miki na miki alqawarin zaki zama mallakinsa,duk da nasan
babban aiki na daukawa kaina saboda sanin waye YAYA MAN,amma abinda yayi miki ya
bata min rai,ina jin tamkar ni aka yiwa,ko don saboda wannan indai kina sonshi
amiran umman khalipha na miki alqawarin aurensa".
*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

6⃣1⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

*SHIN ko kunsan RUWAN DAN WUTA,RUWAN MUGUNYA NE(KAMAR RUWAN CIWO QURJI)TAFASASHSHE
MAI AZABAR ZAFI DA TURURI,A DUK LOKACIN DA YA BUQACI SHAN WANI ABUN SHA SABODA
TSANANIN QISHIRWAR DA YAKE JI SHI ZA'A BASHI YA SHA,YAYIN DA YAKE SHA DIN SABODA
TSABAR ZAFI DA TAFASA HAKA ZAI DINGA YAYYANKA DA TSITSTSINKA MASA HANJINSA,YANA
ZAGWANYEWA*

*Subhanallah,muji tsoron azabar Allah 'yan uwa*

____________________________________

Shuru amiran tayi tana duban sumayya cike da qwarin gwiwa da kuma yaqini
cikin zancanta,itama dubanta sumayyan keyi kafin ta saki murmushi sannan ya kada
kai
"Ni nayi kuskure amira,ni na yi masa kallon mukhtar dina bayan bashi bane
kamanceceniyar iya murya ce kawai,koma waye zaiyi zaton ba lafiya tunda baisan
farkon lamarin ba,amira,bana jin so ko qaunar ko wanne namiji bare na yi sha'awar
zaman aure da shi,banqi a ce nabi mukhtar ba muyi zamanmu cikin rahamar
ubangiji,abunda kawai nake tausayawa abdallah na" ta fadi cikin karyewar murya da
rauni,duk da qoqarin kaucewa hakan da takeyi,tausayinta ya sake kama amira
"Da gaske amiran umman khalipha kin taba aure kuma ma har da boy?" Ta tambaya cikin
zumudi,kai ta gyada mata tana murmushi
"Zanso naga boy din nan,na tabbata zaiyi kyau kamar mamarsa" wannan karon har
dariya taso sara,saboda ta tabo gudan jininta,yaron da shima tun kafin ya shaqi
iskar duniya ya fara fuskantar gwagwarmaya da matsalar rayuwa,koda ya shigo cikin
duniyar ma ba'a barshi ya huta ba sai da aka so saida rayuwarsa,zainab ta fado
mata,ko yanzu tana wacce duniya,baki daya sai taji son aure ya sake fita daga
zuciyarta,itakam yanzu me zata ci da aure
"Amma zanso amira ki amincewa qudirina,na tabbata cewa rayuwar yaya man zata sauya
zuwa yanayin da muke masa fata da hange,zan iya cewa ANTY SU'AD bata da wani amfani
a rayuwanshi" cewar amira tana duban sumayya,kai ta shiga girgizawa
"Duk mai qaunata amira ba zai sake min sha'awar aure ba a yanzu,nikam me zanci da
aure,auren ma na mai mata"
"Me kike cewa ne?,amira zanso sanin wace ke,na tabbatar akwai wani abu a rayuwarki
ba wai mukhtar bane zalla" miqewa tayi a hankali ta zauna tana duban amiran
"Babu lokaci,duba kiga goma na dare"
"Ko zan kwana anan nasan babu damuwa,ina son ki ban labarinki don Allah,naji anty
dije na fadin wasu abubuwa da ban gane ma kansu ba"murmushi tayi
"Me zakici da labarina banda kayan sanya hawaye a ciki,babu komai a labarina face
wuya da naci game da kishiyoyi da abokan zama na" idanuwa amiran ta zaro
"Kina nufin bama aure daya kika yi ba amiran umman khalipha?,ina cewa zamuyi
sa'anni dake fa?" Dariya tayi wannan karon
"Hala mass com kika karanta ko,ina ce miki dare yayi amma baki damu ba?"
Dariya itama ta saki tare da miqewa ba don taso ba
"Zan tafi,amma zan dawo ki bani labarinki"
"Sai kinzo,sai da safe na gode"
"Nice da godiya kuma kiyi haquri da abinda ya faru"
"Babu komai QADDARA CE!" ta ambata wani abu na taba ranta,juyawa amiran tayi ta
fice tana murmushi

****** ******* *******

Sukuku haka ta wuni washegari,duk da ba wani abu take ji na ciwo a jikinta ba


amma baki daya bata da kuzari kamar wadda aka zarewa laka,da yammaci tana kwance a
falon,babu kowa gidan daga ita sai anty dije,su laila sun tafi gidan kakarsu,itama
rashin qwarin jiki ne ya hanata zuwa taji muryar amira tana sallama,miqewa tayi
daga kwanciyar tana amsawa tare da maida daurin dankwalinta da ya zame,sai taga
ashe su biyu ne ita da anty maamaa,miqewa tayi fuskarta qunshe da fara'a tana musu
sannu da zuwa,kitchen ta juya ta dauko lemo saman tray ruwa da kofuna ta ajjiye
musu sannan ta haura sama don kiran anty dije.

Tare suka sauko,fuskarta dauke da fara'a itama take musu lale da zuwa,ta
zauna suka gaisa sannan sumayya ta gaida antyn kafin ta waiwaya ga amira suka gaisa
"Zuwa nayi dubiya,jiya muna cikin gida ashe haka abu ya faru,sam ban sani ba sai
dazu da mahmoud ya shigo yake gayan,sai kuma farida itama ta sanarmin su suka
kawota gida"
"Wallahi kuwa,abin sai addu'a,damuwar dake ranta ce ta mata tasiri har ta haifar da
hakan"
"Allah ya kiyaye gaba,baki daya ma banga mustaphan ba yau,yana ta shirye shiryen
komawa,inason tambayarsa ya akai hakan ta faru,banji dadi ba sam bai kyauta ba,ai
ba'a haka.....sannu sumayya ya jikin?" A kunyace kanta na qasa tana murza yatsun
hannunta,tana jin tamkar ta jawowa kanta wani babban abun kunya ne,kada ma wasu su
tsammaci saboda shi ta suma tace
"Na warke ai anty"
"Allah ya sawwaqe ya qara afuwa"
"Amin anty dije ta amsa,amiran ce ta dubi sumayya
"muje ina son in ganki"tana dariya,sai ta miqe tayi gaba amiran ta biyo bayanta.

Bakin gado suke zaube baki dayansu amiran ta kalleta


"ina alqawarina?"
"Labarina bazai yiwu ba yanzu amira,ki bari na sake samun sauqi ko?"shiru ta danyi
tana kada kai
"To shikenan,Allah ya qara baki lafiya"
"Amin" ta fada tana murmushi,jefi jefi amiran ta dinga sako mata hita,wata ta 'yan
uwa wata ta qawayenta wata ta gidansu duk don ta sake sakin jiki,yawanci duka bata
sansu ba,amma abun yana burgeta,saidai tayi murmushi kawai,a nan ta fahimci su'ad
itace matar mustapha.
Suna zaune anty dije ta leqo tace anty zata tafu,miqewa tayi tana cewa
"Nima tafiya zanyi,zamu je unguwa ne yau duka 'yammatan,sai na dawo"
"Allah ya tsare,na gode ki gaida ummee"
"Zataji kuwa,don batasan abinda ya faru ba,da yau ya man ya shiga uku wallahi,inaga
ma sai na guntsa mata batun" ta fada tana dariya gami da ficewa,sumayyan nason ce
mata kada tayi amma tuni tayi gaba abinta.

Kiran wayar bdur rahaman ita ta qarasa tayata hira har sha biyu na dare
sunata hira,yana ta bata labarin yadda shirye shirye suka kankama na bude islamic
clinic dinshi,yana so ya soko mata maganar yadda yayi missing dinta da kuma yadda
yake son ganinta saidai yana tsoron kada damar da ya samu ya rasata,sam bata gaya
masa zata zo kano ba har sukayi sallama.

******* ******* ********

A hankali ya dinga takowa cikin tafiyar sa ta qasaita har cikin falon baabaa
prof din,sanye da short sleev polo t.shirt jaa da touches na baqi,straight leg
trouser sai safa a qafarnshi,hannunsa soke a aljihun wandonsa,wanda ya zame masa
al'ada idan ya sanya qananun kaya,idan ba waya hannunshi to zaka samu hannayen
cikin aljihu ko harde a qirji.

Sallamarsa ce ta sanya baabaan dago kai yana dubansa,mai hali bai sauya
halinsa,wasu daga al'adar turawa har yau sunqi barin mustaphan,ko da yake ta yaya
zasu barshin bayan har yau shima bai bar cikinsu ba,sam baison manyan kaya,da wuya
ka ganshi da su,cikin girmamawa ya qaraso ya duqa gaban baabaan yana gaida
shi,amsawa shima yayi saidai fuskanshi sam babu walwala sabanin yadda ya saba
ganinsa
"Yaushe ne zaka koma" hannayensa soke cikin juna ya amsa kamar wanda baison yin
maganar
"Cikin wannan satin in sha Allah"
"Allah ya lamunce"
"Amin ya Allah". Shiru ne ya dan ratsa tsakaninsu,shi mustpha na sauraron me baaban
zai gaya mishi tunda shi ya aikata takanas sashensa aka kira shi,yayin da shi kuma
baaban yayi banza da shi,yana so yau ya qure miskilancinsa,yaci gaba da bude
shafukan jaridar dake hannunsa,sam baka rabashi da duba jaridu,duk da bai cikin
sabgogi da al'amuran gwamnati a bayyane amma a badini gangar jiki da zuciyarsa na
tare da su.

Har ya kammala karatun jaridarsa baiji yace komai ba,hasalima da ya daga


kansa sai yaga ya jingina bayansa da jikin kujera gami da miqe qafafunsa idanuwansa
a lumshe,ajjiye jaridar yayi yana sauke ajiyar zuciya,glass dinsa ya zare shima ya
ajjiye gefe yana dubansa
"wato ba zaka iya tambayar dalilin da ya sanya na kiraka ba kenan"miqewa yayi ya
zauna sosai yana duban baaban
"nayi zaton baka kammala abinda kake bane,banson kuma katse ka"shuru yai ya jinjina
kai,duk cikin 'ya'yansa bai haifi kamar mustapha ba har yau ta kowanni fanni ya
tsrerema 'yan uwansa maza da mata
"me ya kaika ture yarinyar mutane har ta suma"
"Yarinyar mutane har ta suma?" Abinda ya dinga maimaitawa ciki kwanyarsa kenan,sam
ya mance wace ce,wa baabaa ke fadi ya ambata cikin zuciyarsa
"Yarinya baquwa 'yar gidan alhj farouq" har ga Allah bai fuskanci kan wa baba ke
magana ba,don shi baki daya ya mance lamarin,baaban ya kalla kamar yanason qarin
bayani kan abinda yake cewa,baabaan yasan irin kallo,indai mustaphan yayi ba shakka
yana buqatar qarin bayani
"Tashi kaje,ka kyauta ka kuma yi abinda ya dace,nima zanyi abinda ya dace din" duk
da bai gane da wa yake nufin ba amma ya miqe kasancewar ya riga ya bashi
umarni,cikin girmamawa ya rusuna yana cewa
"A huta lafiya" baban bai amsa shi ba har ya miqe ya juy,har ya taka daya biyu sai
kuma ya juyo ya dawo ya sake rusunawa aladabce
"Dambun naman naka ya qare?" Ya fahimci me yake nufi,dambun naman da sumayya tayi
masa ne,ya ganshi yana ci ya tsokaneshi da cewa gun saidawa aka siyo masa don yasan
baison cimar siyarwa,yace idan ya qare zai masa magana ya sake siyo masa a inda aka
siyo
"Bai qare ba" baban ya bashi amsa idonsa akanshi har ya miqe,baiyi qarya
ba,mustaphan daban yake cikin yaranshi,kamar yadda yake da wasu baqin halaye haka
dabi'unsa na kula da iyayensa suke,daban ya daukesu,martaba da darajarsu bai hada
ta daya data wani halitta ba,cikin kowanne yanayi ko motsi nashi yakan sanya shi
gaba,fatarshi da addu'arshi daya Allah ya azurta shi da zuriyya dayyiba
saliha,wadda zata ji qansa yadda yake jin qan nashi iyayen.

***** ****** ****** *****

Daren da zasu tafi kanon kasa bacci tayi baki daya,tsaf ta gama hada
komai,hatta da kayan da zata sanya goben ta waresu gefe,cikin irin wannan zaman
taji kuwwar wayarta,ta janyota tana dubawa,baquwar lamba cr,maidata tayi ta aje don
a yanzun tsoron daga baquwar lamba take,sai data fuskanci wayar na neman hanata
sakewa ya sanya ta dagawa,muryar alqasim ce ta bayyana,yasan kadan daga aikinta ta
datse wayar wanda baya fatan haka,saboda yaci wahala kafin ya kai ga samun
lambarta,hakan ya saka ya cikata da magiyar ta tsaya ta saurareshi,bai kyautu ta
watsa masa qasa a ido bo saboda qimar mahmoud,hakan ya sanya ta tsaya tana
sauraronsa zuciyarta fal da mamakin inda ya samu ainihin lambarsa,gaisuwa sukayi ta
mutunci ya sake mata sannu da jiki ta amsa masa,shiru yayi kamar ba zaice komai ba
hakan ya sanya ta buqaci kashe wayarta,wanda shi ya zaburar da shi ya soma
magana,tatsuniyar gizo dai bata wuce ta qoqi,
"Alqasim,ni bazawara ce na taba aure,ko da ina da ra'ayin aure banda ra'ayim auren
saurayi,ballantana ma mi ban hango shekarun da na tsara ba kafin na sake aure,babu
lokaci,saboda haka ina mai godiya bisa qaunar daka nunan,kuma ina mai baka haquri
tare da addu'ar ubangiji ya baka wadda ta fini" ta kaiwa qarshe ta kashe wayar ta
cillar gefe tare da mirginawa ta kwanta ta runtse ido tana son bacci ya dauketa ko
zata samu damar tashi gobe da wuri ta shirya.

******** ******* *******

Qarfe sha daya na rana dukkan shirin tafiya ya kammala,wannan karon har da
abban laila zasu tafi a mota daya,sun gama komai har motar ma drivern ta faka ta
bakin get din gidan,duka suna ciki zaune,abban laila kawai da ya shiga yiwa baaba
sallama suke jira,wanda sabonsa ne baiyin kowacce tafiya bai sanarwa baban
ba,saboda ya daukeshi a mazaunin mahaifi.

Anty dije ce tayi mantuwa cikin gidan,botiki ne data zubawa mama sabulun salo
mai yawa a ciki wanda su zainab zasu hada sabulun gyaran jiki,sau biyu tana aiken
laila bata ganshi ba,ganin zata bata mata lokaci kada abbansu ya fito ba'a dauko ba
ya sanyata tura sumayya.

Kunnenta maqale da waya suna waya da abdur rahman,yayin da daya hannun ke


riqe da dan botikin,ta sanyo qafarta waje kenan kunnenta ya jiyo mata muryar tasa
ginshira yana fadin
"Amma why not kubi jirgi,akwai jirgi daga nan zuwa kano 12"dariya uncle farouq yayi
"wannan kam ai su ku manya,ba damuwa,awa biyar ne ba dadewa zamuje" hannu ya bashi
yana fadin
"Allah ya tsare"
"Amin amin,wataqil kafin mu dawo kun koma,sai gani na gaba" murmushi kawai yayi ya
juya,har a lokacin tana labe bakin qofar,hakanan jikinta ke rawa har wayar hannunta
ta subuce ta fadi bata sani ba
"Ah ah,ashe kin dauko me kuma kike a tsaye a nan?" Anty dije ta tambayeta wadda ta
biyo sahunta jin shirun yayi yawa
"Ba komai...fitowa zanyi dama" ta fada muryarta na rawa tana durqusawa tare da soma
tattare wayarta data watse a gun,bin wayar anty dije tayi da kallo cikin ranta tana
tambayar kanta me ya faru har ta kammala tattarewar ta juya tabi bayanta bayan ta
rufe gidan.

TOFA!

*Mrs muhammad ce👑*

📚📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

6⃣2⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

*KO KUNSAN SABODA BALA'I DA JAHANNAMA KE DA SHI HAR WANI SASHE NATA YANA NEMAN
TSARI DA WANI SASHEN?*

*Allahumma ajirna minan nar*

_________________________________

        Luf tayi cikin motar idanuwanta a lumshe,duk da hayaniya da karadin da suke


tayi cikin motar amma babu ita,bata san me ya haddasa mata mutuwar jiki ba,batasan
me take tsoro ba,abu daya ta sani muryar na daga mata hankali,muryar na sanyata ta
tuna da mukhtarinta,anty dije ma tayi tsammani bacci take saboda ta san jiya batayi
wani isashshen bacci ba,yau kuma ta riga kowa sammakon tashi,tun tana jin
hayaniyarsu sama sama har bacci barawo yayi awon gaba da ita.

      Kamar kullum yau ma sun tsayawa wannan restaurant din don cin abinci saidai
banda ita,zaman ta tayi cikin mota sai takeaway sukayi mata sannan suka wuce.

      Yamma lis suka isa kano ta dabo tumbin giwa,ko da me kazo an fika,gari ba
kani ba dajin Allah,wani farinciki ya dinga shigarta tun kafin su qarasa gida,iskar
garin na kano take shaqa sosai,taje farinciki ya lullube zuciyarta,doki ya mamaye
zuciyarta,kewar mama malam abdallah dama su zainab suka dawo mata sabuwa fil,kamar
kuwa uncle farouq ya sani yace a fara biyawa gida a sauke sumayyan,anty dije zatayi
qorafi kan ba haka ba su wuce gida idan sun huta baki daya sazo gobe yace a'a sam
tana son taga mamanta,hakan ya mata dadi matuqa duk da ta boye dokinta,suna sauketa
kuwa suka wuce kan sai gobe zasu shigo,tana fara'a ta daga musu hannu sannan ta
sanya kanta cikin gidan yaran maqota na shiga mata da jakarta.

      A tsakar gidan ta ware muryarta tana kwada sallama,abdallah ne ya soma fitowa


da gudu halima na biye da shi,da gudu ya qarasa wajenta yana kiran
"Mami na"
"Abdallah na" itama ta fada cike da kewa ta durqusa tare da ware hannayenta ya fada
ciki ta miqe rungume da shi tana dubansa fuskarta fal murmushi,ya qara kyau wayo da
girma kamar ba abdallahnta ba,kallo daya zakayi masa ka tabbatarwa kanka yana cikin
kwanciyar hankali tare da samun cikakkiyar kulawa,yayi bul bul da shi,fes
kamanninsa da babanshi kan fuskarsa.

       Dakin mama ta shige tare da su halima da maman,tana sanya kanta falon taga
amina zaune matar abubakar ciki a gaba,baki sumayyan ta bude tana kallonta
"Antynmu kice kema kina gidan namu yau?"
"Gidanku ko gidanmu,aike kam yanzu baquwarmu ce" dariya sumayya tayi
"Allah sarki anty amina,kice kinyi nauyi shi yasa kika kasa tasowa ki tarbeni"
dariya aminan tayi a dan kunyace saboda mama na gurin,gaban maman sumayya ta qarasa
idonta a kanta tana jin wani dadi na gajin mahaifiyar tata,itama maman kallonta
take,a gabanta ta durqusa ta gaidata,cikin farinciki maman ta amsa tana tambayarta
ina dijen kuma,nan ta sanar mata sai gobe zasu shigo,hira ce ta barke babu
qaqautawa tsakaninsu abdallah na kan cinyarta,yaqi yarda ko nan da can yaje,halima
ke dungureshi tana cewa
"Zata tafi ta barmu da kai ne mai qaton kai da kaqi zuwa wajen kowa" amina ke
kareshi
"Barshi malama,yaro da uwarsa,ai yayi qoqari ma,yaushe rabon da ya ganta?" Har
magariba suna hira,sai da aka gama sallah magariba sannan sumayya ta cewa zainab ta
hada mata ruwa zata yi wanka,dariya zainab tayi
"Wankan lafiya da daren nan?"
"Bazan iya bacci ba sai nayi wallahi" dariya ta kuma yi
"Kice ba banza ba yaya sumayya kika dad wannan dan banzan kyan,wallahi abuja ta
karbeki,baki ga yadda kika koma 'yar gayu ba"
"Hada min ruwan sai kizo kici gaba da sharhin naki" sumayya ta fadi tana
dariya,anty amina ce ta karbe
"Gaskiya ai ta fadi,wallahi garin ya amsheki sosai"
"Kin biye mata kenan antynmu" ta fada tana dariya anty aminan na tayata.

       Bayan tayi wanka ta sake shiryawa cikin doguwar riga ta wani cotting din
yadi mau gajeran hannu,ta yane kanta da dan qaramin mayafi ta dawo falon mama,a nan
suja zuba tuwon dare baki daya idan ka dauke maman,suna ci suna ci gaba da hira,har
yanzun idanuwan maman ma kanta,ita kanta tasan diyar tata ta soma sauyawa kamar ba
ita ba,ta tabbatar sauyin rayuwa ya fara samuwa a gareta,cikin zuciyarta ta dinga
mata addu'ar Allah ya azurta ta da miji na gari,wanda zaici gaba da dawainiya da
ita cikin ingantacciyar rayuwa.

      Suna gab da kammala cin tuwon malam da yaya abubakar sukayi sallama,amina
tayi saurin janyo hijabinta ta sanya,yau malam da kanshi ya shigo falon
maman,fuskanshi shina dauke da farincikin ganin diyar tasa,cikin girmamawa ta gaida
malam din ya amsa yana tambayarta mutan abuja,tace kowa lpy suna gaida ka,amma gobe
su antyn zasu shigo,madallah malam din yace sannan ya fice yana cewa bari ya barta
ta huta da gajiyan hanya,murmushin jin dadi kawai tayo ganin yadda kowa cikin 'yan
uwanta ke qoqarin nuna mata qauna da kulawa.

       "Hala nan gaba kadan zamu kasa ganeki sumayya,irin wannan kumatu haka" sosai
ya bata dariya,bama ita kadai ba duk jama'ar falon,don babu wata qiba da tayi
tsabar tsokana ce,saidai duk wanda ya kalleta zauga yadda fatarta ta murje tayi
kyau,hutu da wayewa suka sake bayyana a jikinta,sai da ya gama tsokanar tasa sannan
yace
"Dazun dama nake cewa ko baku zo ba cikin satin nam zaki ganni kafin ku wuce
london,inaso muyi maganar kudin abdallah dake hannuna,sun fara yawa gaskiya ya
kamata kuma ayi tunanin sake fadada wani kasuwancin da su" dubanshi tayi
"Haba ya abbakar,kaima fa kamar uba kake gunsa,duk abinda ka yanke dai dai ne,baya
ga haka ga malam ga mama ga yaya yahanasu ko su sun isa kayi shawara da su ku
zartar da duk hukuncin da ya dace ko?"
"Eh duk munyi magana da su kuma su suka ce aji ta bakinki,amma koma me ake ciki kan
ki koma zamuyi magana,yaushe zaku koma?"
"Ba zamu wuce sati daya ba"
"To ba damuwa....ke taso mu tafi" ya fada yana miqewa,amina tasan da ita yake,sai
ta shiga yunqurin miqewa
"Dakata mata mana,yanzu fa ta gama cin abinci ko fada mata baiyi ba,koma ki zauna
ki shirya a nutse" cewar mama tana hade rau,dariya ta kama sumayya,ba shakka idan
da duka haka surukai suke da ba'a dinga samun baraka tsakanin surukai ba.
"Idan kin gama ki kirani a waya,zan je ayimin aski" ya fada yana ficewa ta amsa da
to.

      Halima ce ya shiga tsokanarta kan tafiyarsu london


"Yaya sumayya dama nice,ki barmim don Allah" haka ta dinga fada,murmushi kawai tayi
tana kallonsu,abinda basu sani ba ita din ce ke jin dama ita ce su,basu taba
fuskantar wata matsala ba,ko yaushe suna tare da mamarsu da babansu,suna cikin
garinsu,basu da wata damuwa da ke hanasu bacci ko ta sanyasu a halin tunani,tana
ganin quruciya ce kadai ke sasu sha'awar zamowa ita.

        Sai takwas na dare amina suka tafi da ya abubakar,zuwa lokacin itama bashin
baci da gajiyar hanya sunyo mata kabbara,tilas ta musu sallama ta dauki abdallah da
yayi bacci kan kafadarta suka nufi daki.

  *******   *******   *******

     Washe gari kusan tare sukayi aikin gidan ita da mama,kasancewar qarfe shida da
rabi su halima na fita makaranta sai goma na safen suke dawowa a irin wadan nan
ranakun,a yanzu haka ma shirin tafiya musabaqa suke wanda suna daya daga cikin
wadanda aka zaba,sunayi suna hira irin ta tsakanin da da uwa,zuciyoyinsu
fes,sumayya na jin gata ga mamanta kamar kar ta sake tafiya,yayin da maman ke
farincikin sauyawar diyar tata,tara da rabi suka kammala har karin kumallo,wanka
sumayyan ta shiga tayi sannan ta shirya cikin atamfarta super wadda tayi mata kyau
ainun,ta dan taba kwalliya kadan sannan ta sanya hijabinta ta nufi dakin malam.

     Karyawa take sanda ya shiga,ta gaidashi ya amsa mata yana fara'a


"Mutanen abuja yau anyi kwanan kano" kanta tai sunkuyar tana dariya
"Ai malam,duk wanda ya bar gida gida ya barshi" tace tana wasa da yatsunta
"Wannan kuma gaskiya ne" labari take bashi kadan kadan game da abinda ta fahima kan
rayuwar garin har mama ta cimmasu a haka
"Qarfe sha daya ne daurin auren fa malam" maman ta tuna masa,a gogo ya duba sannan
ya miqe
"Au,au,ai kuwa na manta,gashi sha daya saura kwata,hira ta dauken hankali,idan na
dawo ma qarasa ko?"dariya tayi." To,a dawo lafiya"
"Allah yasa".

      Falon mama ta koma don ta karya itama,tana tsaka da hada tea abdallah ya
tashi,dole ta bar karyawar ta yi masa wanka ta karbi kayansa wajen mama ta sanya
masa
"masha Allah"ta fada tana dubansa tana murmushi ganin yadda yayi kyau,shima sai ya
maimaita abinda tace din,dariya ya bata dai dai sanda mama ta shigo bayan ta
sallami malam
"gaskiya mama bakin yaron nan ya kuma budewa"
"Ba dole ba,yaron dake zuwa makaranta me zai hana bakinsa budewa", su halima ne
suka shigo hakan ya sanya ya qyaleta yayi wajensu can yana buga musu rigima,gefe ta
koma ta soma karyawa tana jinsu tana dariya cikin ranta.

        Sallamar abdur rahman data jiyo ita ta sanya ta kusa qwarewa,da sauri ta
dauki ruwa ta sha,tare da janyo mayafi ta yafa kafin a amsa iso,yana sallama cikin
falon ta soma tattare kayan breakfast din ba tare data kammala karyawa ba ta maida
kitchen,tunda ya shigo idanuwansa na kanta,don bai tsammaci tazo garin ba,bayan sun
gama gaisawa da mama ta miqe ta fice,su halima ma suka gaidashi sannan suka fice
don sauya unifoarm da kama aikin abincin rana na gidan.

       Idanu ya zuba mata har sai da taji nauyinsa ta kau da kai


"kin kyauta qwarai,tunda har baki iya gayamin cewa zaki zo kano,matsayin yaya ma da
nake tunani an bani ashe ba haka abun yake ba na bar murna" murmushi ta saki tana
kada kai
"Ba haka bane,afuwa,suprise naso baka"
"Da shi dai kike so ki fake,amma inda hakanne ai da a yau da safe zaki kirani ki
gayan,ko kuma tun a jiyan ki sanarmin kina zuwa kano ko?"
"To nayi laifi babban yaya ayi haquri" ta fadi cikin raha,numfashi ya dan dauke
kadan,kwata kwata baison sunan,wannan sunan bai masa ba,so yake yaji ta kirashi da
wani suna dake qunshe ko yake nuni da zallar qauna,kai ya gyada kawai yana
murmushi,sabida ya lura idan baiyi wasa ba wankin hula na neman kaishi dare
"Ina abdallah?" Sai ta dan ware idonta kamar tana nemansa
"Yanzun na masa wanka na bashi abinci,ina zaton ya fita"nashi idanun shima ya waro
" kan me zaki dinga barmin yaro yana fita waje?"dariya ta danyi
"To duka ma yaushe na dawo garin ni?,abdallah ya riga ya saba da fita tunda ya
tashi gidan yara" halima ya kira yasa ta dauko masa abdallahn,ba dadewa ko ga dawo
da shi,yayi budu budu da qasa da alama ya sha wasan qasansa ya qoshi,kicin kicin da
fuska abdur rahman din yayi ya hau fada,tilas ta tashi ta sake gyarashi.

       Sai da ya tabbatar ta gyarashin sannan ya miqe yana dubanta


"Har zaka tafi?" Ta rigashi fadi
"Eh,dama ai zuwan ba naki bane,tunda ba'a gayan zuwan ba,amma zan dawo ko zuwa
gobe,idan ba gobe ba jibi,akwai muhimmiyar magana da nake so mu tattauna" shiru ta
danyi
"Allah ya nuna mana,ka gaida bahijja da hajiya don Allah"hararar wasa yayi mata
"bazan gaya mata ba,maruqar ba zaki je ki gaidata ba,ko kara ma sumayya fa baki da
ita"dariya tayi a kunyace,ita kanta tasan bata kyauta ba
"Kayi haquri in sha Allah bazan koma ba sai naje na gaida hajiya" kafada ya daga
yana fadin
"Da dai yafi" sallama ya musu ya danqawa abdallah kayan qwalama kamar yadda ya saba
sannan ya wuce.

       Kwanakin ta a kano jinta take kamar wata sabuwar duniya,wuni suke


hira,hakama anty dije idan ba wani gu zata ba tana gun mama,ranar da abdur rahman
yace zaizo har yammaci taji shiru,hakan ya sanya ta shirya don zuwa tsohuwar
unguwarsu kamar yadda tayi alqawari,halima da zainab ne 'yan rakiya,sai laila wadda
a gidan ta kwana,sumayyan tayi kyau cikin wani leshi wanda daya ne daga cikin kayan
sallarta da uncle farouq ya siya mata,mayafi ta yafa bisa matsantawar halima,duk da
babba ne amma tayi kyau matuqa,talkalmi da jaka komai da tayi amfani da shi ya dace
da kalolin jikin lace din,sai oga abdallah shima da tayi masa kwalliya cikin
qananun kaya,da rufaffen takalmi irin na maza.
      Tana tsakar gida suna sallama da mama suka ji sallamarsa a soro kamar yadda
ya saba bai shigowa har sai an masa izini,maganar da suke da mama ta katse tana
duban soron,sai da maman ta sanya hijabin sannan aka masa iso,tunda ya shigo
idanuwansa na kanta,tayi masa kyau fiye da duk lokutan da ya saba ganinta,yai yayi
kamar yayi sallama da mama ya fito saidai ita tasan ba tafiya yayi ba,suna fitowa
suka ganshi hakimce jikin mota,shi din ma yayi kyau cikin wani yadi mai taushi
ruwan qwaiduwar qwai,gaban motar kawai ya bude mata tare da cewa
"Bismillah" kai ta rausaya ganin yadda ya tsareta da idanu kawai ta shige,su laila
suka shiga baya sannan ya shiga ya tada motar.

        Sai da suka fice daga layin sannan yace


"Ina zuwa ranki ya dade?" Kanta ya sake rausayarwa tana murmushin sunan da ya
laqaba mata
"Tsohuwar unguwar da muka zauna ni da ya mukhtar" wani kishi ne ya soki
zuciyarsa,amma sai ya danne ba tare da ya nuna ba,kamar ta fahimci mekw
tsinkulinshi sai tace
"Zanje mu gaisa da yara da iyayensu da muka zauna tare"
"Hakan nada kyau" ya bata amsa,da fari motar tayi shiru,sai daga bisani abdur
rahman din ya sako hira,kadan kadan suke tabawa har suka isa unguwar.

      Unguwar na nan kamar yadda ta santa,saidai tsohon gidansu da suka zauna wanda
mutanen da suka siyeshi suka masa kwaskwarima,gidan maman naana suka fara
shiga,taso ta kasa gane sumayya sai da naana ta fito daga daki,da gudu ta nufi
sumayyan tana ihun kiran sunanta,rungumeta tayi tana dariya itama tana kiran
sunanta,daga nan maman naanan tayi mata iso zuwa falo
"Wallahi sam fuskarki taso bacemin sumayya saboda canzawar da kika yi,kin sake zama
babbar mace?" Maman naanan ta sake fada cikin mamaki,murmushi kawai sumayya tayi
sannan suka fara gaisawa,naana na gefe bakinta yaqi rufuwa,tashi tayi taje ta siyo
wa sumayyan pure water mai sanyi da lemo,dubanta sumayyan tayi tana murmushi,ba
zata manta ba wannan na daya daga cikin rainon da ta yiwa yaran na girmama
baqo,ashe har yau basu manta ba,ita kanta nanan ta girma ta sauya,nan sumayyan ta
dinga tsokanarta na ganin girman da tayi.

      Kafin ta bar gidan sai ga yaran na shigowa daya bayan daya,da alama nana ke
shiga gida gida tana gaya musu zuwanta,dui wadda ta shigo rungume sumayyan take
cikin jin dadi,itama mamakin girman yaran take,kusan awa daya da wani abu tayi a
gidan sannan ta dinga shiga gida gida yaran na rakata,kowa mamakin sauyawarta yake
inda ita kuma sam bata ganin sauyawar da tayi,duk gidan data shiga sai ta ajjiye
musu dubu daya,cikin kudin da ya abbakar ya bata jiya a ribarta na kudinta da ake
juya mata,sunyi murna kuwa sosai,sai magariba sannan suka bar unguwar duka abdur
rahman na cikin mota yana jiransu.

        Sai wajen isha'i suka koma gida,don daga qofar gida da ya ajjiye motar
masallaci ya tafi sallar isha'i,sai da ya dawo yayi kiranta a waya kan ta fito ya
dawo,sanda ya kira din fitowarta kenan daga wanka,don ranar ta gaji da wuri take
sonyin bacci.

        A sitting room dinsu ta sameshi wanda halima ta bude masa ta masa masauki a
can,kamar kuwa tasan sumayyan bata son komawa cikin motar,kallonta yake sake
yi,komai ta sanya kyau yake mata,rigar data sanya ba wata ta azo a gani bace amma
ta mata kyau duk da hijabi ne a jikinta saidai qarami ne.

       "Sumayya,zuwa yanzu na gaji da zaman kare a karofi da nakeyi,lokaci yayi da


zamu fukancu gaskiya baki dayanmu,ni na sani cewa bazai yiwu naci gaba da biye miki
a yadda kike so ba,kamar yadda kema kika sani cewa indai da rai da lafiya malam
bazai taba barinki babu aure ba" abdur rahman yayi shiru yana maida numfashi tare
da nazartar yanayin da sumayyan ta shiga sannan ya dora
"Ko baki so sumayya dole a ce mukhtar ya koma ga Allah,kin sani na sani haka ma
duniya ta shaida,don wani wanda kake so ya rasu ba shine zaisa kace kai kuma ka bar
yim taka rayuwar ba,yin hakan dai dai yake da gayawa Allah bai maka dai dai ba
kenan,tunda ya dauke wanda yaga dama ne ya kuma bar wanda yaga dama babu wanda ya
isa ya tilastashi,gata daya zaki masa shi da yaronshi ki killata kanki a gidan
aure,ki bani dama sumayya na cike miki gurbin farincikin da kika rasa"
"Sumayya!" Ya kira sunanta cikin kaurara murya
"Inason yau ki gayamin matsayina,mu bar wannan zaman qaryar,zaki iya aure na ki
zauna da ni?" Shiru tayi maganganun abdur rahman na ratsata,babu shakka gaskiya ya
fada mata,wanda shine ya fara gaya mata karo na farko tun bayan rashin mukhtar idan
ka dauke malam da mama
"Idan har kin yarda ki barni na yiwa malam magana,tunda a yanzu yana tunanin na
janye tunda har kin sake wani auren,ya taba gayan hakan cikin wasa,saidai ni sam
cikin zuciyata ba haka bane,har yau sumayya sumayya ce bata sauya ba a idanuwa na"
Shiru ya sake yi don ya bata damar fadin ra'ayinta da abinda ke zuciyarta.

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

6⃣3⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

*MANZAN ALLAH S A W YANA CEWA,KUJI TSORON WUTA KODA DA TSAGIN DABINO NE*
_____________________________________

      "Ka yimin afuwa,a yanzu haka tafiya zanyi ta shekara daya,ka barni har na
dawo don Allah,na sani cewa ka cika mutum,kuma ka nunan dukkan wata qauna da
halacci,amma ina son ka barni har zuwa sanda zan dawo daga wannan tafiyar,wala'alla
zuwa sannan zuciyata ta sake sanyaya daga rashin da nayi,ka sani abdur rahman yadda
mutuwa ke da ciwo da wuyar barin zuciya,kayi haquri da ni don Allah" ta qarashe
maganar muryarta na rawa idanuwanta na tara hawaye,tausayinta ya kamashi,ya sani
cewa raba zuciyar sumayya da mukhtar ba qaramin abu bane,a kanshi ta fara sanin so
da qauna,a kansa ta fara sabawa da wani namiji baare,ta soma iya magana da d'a
namiji,tilas yaci gaba da haquri kafin ya cimma burinsa,zaici gaba da addu'ar samun
zabi mafi alkhairi,kafin lokacin dawowarta ya tabbatar shima duk wasu burikansa sun
gama cika,ya kammale hankalinsa guri guda,dubanta yayi cikin sigar lallashi
"Na sani cewa shekara daya ba kwana daya bace,amma gurin Allah ba komai bace,Allah
ya nuna mana,amma kema sai kinyi yaqi da zuciyarki,sannan kada ki bawa wani dama
bayan ni,kinyi alqawari?" Murmushi tayi saboda maganar ta bata dariya,to shi dinma
tanqwara zuciyarta take qoqarin yi ina ga ace ta bawa wani dama,ko ya mance
zuciyarta ba lafiyayya bace?
"Baka da wannan damuwar" ta fadi tana kada kai,maganar tayi masa dadi sai yayi
murmushi ya soma janta da hira,bai tafi ba sai da ya rage mata damuwa sannan sukayi
sallama.

       A daren kasa bacci tayi baki daya,juyi ta dinga yi daga farkon gado zuwa
qarshensa,tunani fal zuciyarta,zuciyarta sam babu dadi,rayuwa kenan,yau zaqi gobe
madaci,abinda ya dinga yi mata kai kawo kenan har bacci barawo ya dauketa.

       Kwanakinsu a kano sunyi mata dadi qwarai,ana ta gabatar da hawayan sallah


irin na al'ada don ma saura suka tarar,garin cike yake da baqi cikin kowanne sassa
na duniya masu zuwa kano daga qasashe daban daban,kama daga qasashen turawa har na
larabawa don ganin hawan sallahr garin kano,wanda babu irinshi kaf arewa saidai a
kwaikwayeshi,ta yadda tabbas kano nan ake morewa bikin sallah ba kamar sauran
garuruwa ba da basusan ana yiba ma,tayi hira da mama malam da qannenta iya son
ranta,abin dadin uncle farouq ya qara musu kwanakim yace su cikashe kwana
goma,randa suka cika sati suka soma zaga 'yan uwa da qawayen anty dije suna musu
sallama,kusan ko ina da sumayyan aka je don itama ta yiwa dangi sallama,kwana biyu
suka kammala ya rage musu kwana biyu su koma abuja don fara shirin tafiya uk
london.

     Washegarin ranar da zasu tafim bayan ta gama hada kayanta baki daya ta shirya
tsaf ta shirya abdallah,ta riga data yiwa driver magana zata unguwa,gidan yaya
yahaa take son zuwa don yi mata sallama,anty dije tace zaya zo ya kaita,qarfe sha
biyu na rana ya iso,ta yiwa mama sallama ta dauki abdallah suka tafi.

       Daga falo suke amsa sallamar tata,yaya yahanasun ce kawai ta dauki


murya,jamila fatima da fiddausi nr zaune duka a falon,gefe kwanon koko ke da kofuna
da alama shi suka gama sha,baki daya fiddausin ta fige ta fita kamanninta tayi baqi
kamar ba ita ba,yaranta uku a yanzu (banda yaran data haifa wanda sumayya taje
sunansa)har yau tana gida babu wani ci gaba,uwar miji tace ba zasu iya ba ta cika
haihuwa,danta ba qarfi gareshi ba,sai su fatima da rashin aure kan lokaci yasa suka
soma tsotsewa,jamilan ta qwallafa rai kan wanda takeso shi kuma yayarsa ta hana
tace auren gida zaiyi,fatima ma kuwa babu maganar kowa,baki dayansu anty dijen ke
riqe da su,abun akwai tausayi,mataimakin madogarar dama qwaya daya ne MUKHTAR,a
yanzu da babu shi kuwa babu wani mai dubansu,dukkaninsu washe bakin ganinta suke
itama tana amsa musu fuska sake har tayi matsugunni kan daya daga cikin
kujerun,tuni abdallah yayi wajen yaya yahanasu,ta rungumeshi tana shafa kansa tare
da duban fuskarsa,qwalla ta cika mata idanuwanta har ta soma gangarowa,duk sanda
taga yaron mukhtar yake tuna mata,kamanninsu daya,tana jin kanta a mai laifi,a
wadda tayi silar maida shi maraya,kullum kwanan duniya sai ta yiwa zainab Allah ya
isa.

      Baki dayansu jikinsu yayi sanyi ganin yadda yayan ke share hawaye,tuni itama
sumayya ta fara goge tata qwallar,tsawon mintuna kafin su bawa zukatansu haquri
sannan suka shiga gaisawa,baki dayansu kunyar sumayyan sukeji,ga wani girma da suke
bata na daban,ranar anan ta wuni,har la'asar,sai ina kasa ina ka ajjiye suke da
ita,sai da tayi sallar la'asar sannan tayi sallama da su bayan ta ajjiye ma yaya
yahanasun sabulai klien da su maggi cikin leda mai layi layi,sannan ta baiwa fatima
da jamila dari biyar biyar,fiddausi dubu daya duk cikin irin kudadenta.

       Hakanan ta tsinci kanta bayan fitowarta da yiwa mai a daidaita sahun data
tsaida kwatancan gidanta,ma'ana gidan qarshe da suka zauna da mukhtar,wanda tun
wajen raba gado ya shigo cikin kasan su,daidai madaidaicin get din gidan ya
ajjiyeta,ta sallameshi ta dauki abdallab,jakarta ta laluba cikin sa'a muqullan na
ciki ta sanya ta bude fa shiga.

      A hankali ta dinga takawa tana duban gidan,duk taku guda na dawo mata ne da
duk wata rayuwa tata da ta shude can baya,sannu a hankali zuciya da gangar jikinta
suka raunana,ta dinga takawa a sannu har ta kai ainihin falonsu,duk kayanta na jere
ma ciki babu abinda ta fitar,saidai gidan yayi qura sosai saboda rashin kasancewar
kowa a ciki,shimfide abdallah tayi saman kujera wanda ya soma bacci tun cikin
adaidaita,idanuwanta suka wurga zuwa qofar da zata sadaka da bangaren mukhtar,sai
ta miqe tana duban qofar harta sada kanta da ainihin dakin gadonshi,babu komai ciki
kamar yadda mamallakin gun bai duniya,sai ta gaza riqe hawayenta suka fara sintiri
kan kumatunta,gefe guda ta duqe tana bin bango saboda rawar da jikinta keyi ta
rushe da kuka mai tsuma rai da zuciya,ta jima tana kokawa sannu a hankali har
nauyin dake cikin zuciyarta ya soma raguwa,ta share qwallar tata ba don ta qare ba
ta juyo da niyyar miqewa,abdallah ta gani tsaye bayanta yana kallonta
"Wa ya saki kuka ammi?"hannu ta miqa masa alamar ya taho,ya taho din kuwa ya fada
jikinta ta rungumeshi tana ci gaba da goge hawaye.

       Sai data samu nutsuwa cikin ranta sannan ta qarasa zagaye gudan,duk inda ta
taka da abinda zau tuna mata,a haka ta kai har biyar da rabi sannan ta lalubo
abdallah dake can wani gu yana wasansa ta sauya masa kaya ta rufe gidan suka fito
idanu jajur na kukan da ta sha.

       Washegari suka kama hanyar abuja,hankalinta yasi dagawa na barin abdallah da


zata sakeyi,bata so yayi maraici irin na mahaifinshi,babu uwa babu uba,saidai ganin
yadda sam bai damu ba shi ya kwantar da hankalinta,da fari ya soma maqale maqale
amma daga bisani sai ya ware har da shi a masu daga mata hannu,ajiyar zuciya ta
saki bayan sun hau hanya sosai ta maida idanuwanta ta rufe,sam bata son komawa
abujan nan,tafi qaunar garinta kano,koba komai kowa nata yana can,da zata iya data
roqi su anty dijen su barta a can din,saidai yin hakan tamkar butulci ne ga qaunar
da anty dijen ke nuna mata fiye da dukkan wata 'ya dage cikin danginsu,duk da 'yan
maganganu da ke fara tsowa na hassadar riqon nata da antyn keyi.

       Kasancewar basu taso da wuri ba shi yasa basu suka isa gida ba sai takwas na
dare,a gajiye kowa yake,saboda haka kowa gun kwanciya ya nema idanuwa cike da
bacci,dama tuni sunci abincin darensu kan hanya.

       Washe gari da gyaran gidan suka tashi,suka kintsa ko ina,kafin wani lokaci
gidan ya dawo hayyacinsa,basuyi dai break da wuri ba saboda aiki.

        Zuwa la'asar har abincin dare sun gama,su khalipha na dakinsu suna gayaran
kayayyakinsu tare da fara ware wanda zasuyu tafiya da shi,sumayya na zaune falon
tana hutawa,hannunta riqe da waya tana neman lambar mama don su gaisa ta kuma ji ya
abdallah yake,sallamar amira ita ta katse mata abinda take shirin yi din,ta shigo
sanye da yadin sartin baqi sidik wanda aka yiwa doguwar riga,sai dan madaidaicin
jan mayafin data yane kanta da shi,cikin fara'a sumayyan ke dubanta har ta qaraso
ta samu wajen zama
"Mutanen kano ta dabo,sauka ba sanarwa?"
"Kada ki qorafi,saukar dare ce,har yanzun kuma bamu gama watstsakewa ba,sai dazun
muka gama saita gidan"
"Gaskiya kam,ko mu muna nan muna hutu,baqi sun tafi sun barmu da kewa,gidan ba kowa
duka ba dadi,kowa ya koma inda ya fito,dadin abun daya nima next week zamu koma
school" murmushi kawai tayi,suna hutawa tamkar sunyi hidima da baqin,bayan komai
akwai masu aiki dake gudanarwa
"Gaskiya kam ansha baqi,saidai Allah ya bada lada"
"Amin" amira ta fada tana lalubo wata number cikin wayarta qirar iphone 7
"Ki duba dakina can wajen bedside drower akwai black bag ki kawomin gidan umman
khalipha" abinda tace kenan cikin salo na bada umarni ta kashe wayar,sumayya ta
ajjiye lemo da ruwa gaban amiran tana tambayar maman husna,murmushi tayi tana
daukar gorar ruwa
"Husna mutuniyarki,sun koma inda suka fito" idanuwa sumayyan ta dan fiddo
"Suma ba nan suke ba?"
"Eh,mijin anty farida custume ne,basu zama gu daya,yau suna can gobe suna nan,amma
lokaci lokaci suna zuwa hutu da kuma lokacin bikin sallah kamar haka" kai ta
jinjina
"Allah ya taimaka"
"Amin"hira suke tabawa kadan kadan har ta shigo bakinta dauke da sallama.

     Sumayyan ta ganeta tare hadimar amiran ce,tare suke shigowa,isa da qasaitar


gidan baabaa prof kusan kowa dame masa aikinshi shi daya,gaida sumayya tayi saidai
ta kasa amsawa ta maida mata gaisuwar suka gaida juna,kusan zata dan girme musu
saidai ita din yare ce,sannan ta rusuna cikin girmamawa ta miqawa amira jakar mai
kyau,amsa tayi sannan tace
"zaki iya tafiya,idan ummee ta tambaya kice ina gidan umman khalipha"
"To madam" ta amsa ta fice,miqawa sumayya jakar tayi tana fadin
"Ga tsarabarki ta saudiyya,babu yawa a karba da haquri" murmishi ta saki tasa hannu
ta karba tana godiya tare da fadin
"Mai yawan kenan" tana fidda kayan ciki,turaruka ne designers masu kyau guda
uku,agogo cikin dan akwakunsa,sai hijabai saqar qasar oman suma guda uku masu
azabar kyau,sun burge sumayya qwarai har sai data fidda murmushi saman lebanta
"Naga kina sonshi ne sosai"
"Naji kuwa dadin kyautarsa fiye da komai cikin kayan nan"
"Ina fata kin yaba"
"Qwarai da gaske" suka sa dariya baki daya,a nan anty dije ta fito,gaisawa sukayi
sumayya ta nuna mata kayan ta gani ta tayata godiya.

Wayar amiran ce ta dauki qara,dagawa tayi tana dubawa,idanu ta zaro,a fili ba


tare da tasan ta fadi ba
"Na shiga uku ya man yau kuma?" Da hanzari ta daga kiran ta kara kunnenta
"Ok,to yaya" ta fada tana miqewa
"Amiran umman khalipha na wuce,ya man ya aikeni na kaiwa umme waya kada ya qara
kira ban je ba,ya kira wayarta taqi shiga haka land line din part dinta"
"Ok,muje na taka miki" sumayya ta fada tana miqewa
"Na gode" ta fada tana murmushi,don haka nan Allah yasa mata qaunar sumayya,burgeta
take sosai.

Jerawa sukayi suka fito,suna gab da kaiwa qofa amira tace


"Uhmmm,ko ki tambayi ma mutuminki ko?"
"Ayyah,ya mahmoud,ki gaidashi don Allah nayi laifi kam"
"Um um,ni ba ma shi nake nufi ba,ya mustapha mana" shiru ta danyi gabanta na duka
tunda ta ambaci sunam nashi,da ido amiran ke karantarta ganin bata ce komai ba har
tana shirin fita ya sanya ta bar zancan ta soko wani
"Yaushe zaki shigo gaida baabaa,yana ta maganan baiga mamanshi ba" dan qaramin
murmushi ta saki,sai taji tayi kewar tsohon duk da ba sabawa sukayi ba,amma saidai
ko kadan bata sha'awa ko marmarin sake shiga gidan,tun daga randa abun ya faru.
"Ki gaida min baabaa da kyau don Allah,zan shigo idan Allah ya yarda" ta fada da
siga biyu don bata da niyyar zuwa din
"Allah yasa da gaske ne,saikin shigo din na gode"
"Nike da godiya,ki gaidamin su ummee ma"
"Zasuji" ta fada tana ficewa tare da jin dadin yadda sumayyan ta nuna kulawa ga
ahalinta.

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

6⃣4⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

*haqiqa Allah yana son masu yawan tuba*


___________________________________

       Cikin sati guda suka kammala duk wani shiri nasu na tafiya,ya kama ranar
lahadi zasu tashi zuwa uk,hafiz ne kadai abun tausayi,don su kansu su laila sun
daina dariya da tsokana sai tausayinsa,ranar asabar da daddare abbanshi da anty
dije suka kaishi gidan kakarshi sannan suka dawo.

        Da daren ana ya gobe zasu tafi tana zuge jakar matafiyanta wayarta ta dauki
qara,bata duba ba ta dauka ta kara kunnenta,sai taji muryar lukman,murya a sanyaye 
bayan sun gaisa ya soma fadin
"Da gaske sumayya baki damy da ni ba baki damu da yaranki ba,kizo kano kiyi kwanaki
har goma ki kasa gayan,bare kice zaki ki gaida hajiya,sumayya me muka yi miki
haka?" Sai a lokacin ta tuna ma tace zata gaida hajiyan abdur rahman,baki daya ya
mance,ta kuma san shima yana sane shiru kawai ya mata ya zuba mata na mujiya
"Kayi haquri,babu abinda kuka yimin,tunda naje ban zauna ba munata shiga kasuwa da
sallamawa 'yan uwa da dangi?"
"Sallama wacce iri" dan jim tayi tana jin nauyin fada masa,saidai dole ne ya sani
din yanzu
"Gobe in sha Allah zamu tashi zuwa uk,sai bayan shekara daya zamu dawo" baki daya
jikinsa ya saki,jijiyoyinsa suka yi laushi,idanunsa ya lumshe wadanda ke masa
zugi,ya budesu da qyar muryarsa kamar wanda zai saki kuka yace
"Da qyar ne idan ban rasaki ba sumayya,burinsu nuwajra na ki dawo musu bazai cika
ba,na saddaqar sumayya kin subuce min" ya fadi yana kada kai tamkar yana
gabanta,shuru tayi ba tare data ce komai ba,don batasan me zata ce din ba,itama sai
ya kashe mata jiki baki daya,tausayin yaran ya taso mata,nannauyar ajiyar zuciya y
saki
"Shikenan sumayya,ina miki fatan alkhairi,Allah ya tsare ya dawo daku lafiya,saidai
hakan bai nuna na miqa wuyan rasaki,bazan fidda da rai da rasakin ba sai randa naga
an daura miki aure da wanu wanda nake fatan wanin ya zamanto nine" ya qarashe
muryarsa na dan rawa,sabida ba zaya taba mance kulawa da kwanciyar hankali da
farincikin da ya samu a aurenta ba,duk da cewa baki daya zaqin da dadin na wasu
taqaitattun watanni ne,amma hakan ba zai taba barin kwanyarsa ba har ya
mutu,sumayya ba irin matan da kake saurin mancewa da rayuwar da kayi da su
bane,tana da wata iriyar baiwa ta musamman mai tsayawa a wuya
"Na gode,a gaida yaran"
"Zasuji,da fatan zan samu number dinki ta can idan kun isa ko don ku dinga gaisawa
da yara"
"In sha Allah" ta fada tana datse kiran,jikinta a sanyaye ta sauke wayar,tana
mamakin yadda ta shiga rayuwar wasu mazaje,har suke iya bata muhimmanci mai yawa
haka a rayuwarta,bayan ita din bata ga wani abu da take da shi ba wanda za'a
kwadaitu wajen zama da ita,da wannan tunanin taci gaba da aikinta har ta kammala ta
kwanta don ta huta.

     *RANA BATA QARYA*

     Dukkansu sun hallara cikin lafiyayyar zungureriyar motar data dauke kayansu
baki daya,wanda baabaa prof shi ya bada ita yace a kaisu a cikinta,anty dije data
shiga sallama da su ita da uncle farouq suke jira.

        Harara anty dije ta aika mata da ita bayan sun fito wadda batasan ta mece
ba har sai data bude baki tayi magana
"Kinji dadi a ranki ko?,ai yanzu sai ki shiga ki musu sallamar tunda mai gidan da
kansa ya nemeki" sosai taji kunya da har baabaa prof ya cigiyarta,bata son shiga
gidan sam,haka ta sauko a hankali ta nufi gidan cikin shigar wata iriyar gown mai
dogon hannu A shape,wadda anty dijen ce ta siyo musu tace ita zasu sanya,tayi
rolling da dan madaidaicin mayafinta,kayan sun mata kyau matuqa,saidai baki daya
jinta take a takure saboda rashin sabo,ta riga ta saba ta adana jikinta cikin
hijabi.

        Gabanta na faduwa ta sanya kanta zuwa sashen baabaan


"Laaah ilah" taji an ambata a bayanta,da sauri ta juya,amira ce ke tsaye tana
kallonta,fuskarta dauke da dariya hannunta riqe da mayafi
"Ai yanzun nake sauri naje rakiya kada ku tafi ki barni,na lura sam wlh amiran
umman khalipha baki damu da ni ba,nike ta taki"
"Kiyi haquri don Allah kada kice haka,yimin jagora na yima baabaa sallama"bata amsa
ba face gaba data soma yi wai ita taji haushi sumayyan tabi bayanta tana
dariya,saidai kafin su qarasa din bakin amiran ya kasa shiru
" gaskiya dole amiran umman khalipha ki dinga boye jikinki cikin hijab,dama haka
kike?,wannan idan muka jera ai sai ki kashe mana kasuwa,haka kika hade?"ta fada
cikin sigar wasa da mamakin irin kyawun sumayyan,wani irin kyau me tsari da ban
sha'awa,dariya sosai ta baiwa sumayya har ta kai mata duka ba tare data shirya
ba,itakam babu wani kyau sam data gani daga gareta,ita amiran bata kalli kanta
ba,kyau hutu wayewa da kwalliya duka,ta ina zata kashe mata kasuwa,ita bama neman
kasuwar take ba don haka taci kasuwarta hankali kwance,ta qarashe sauran maganar a
fili,dariya sosai ta baiwa amiran
"Wai kina nufin ba zaki sake aure ba?" Wani abu ne ya soki sumayya sai ta kasa
amsawa,kai kawai ta kada mata ba tare da tace komai ba,ganin hakan ya sanya amiran
jan bakinta tayi shiru,don dama ko can ita ba mai yawan bin qwaqwqwafi bace har
suka isa sashen baban.
       Yana falonshi zaune kan kujerunsa na alfarma,idanunsa saye da gilashi yana
kallon tashar VOA,gefansa jarida ce,daya barin kuma damammiyar furarsa ce da umme
ta gama dama masa yanzun nan,don ko falon bata kai ga ficewa ba.

       Cike da kunya girmamawa da mutun tawa ta isa gabanshi kanta a qaaa,kwarjini


dattijon yake mata kamar malam dinta,cikin ban girma ta gaidashi sannan ta gaida
ummee dake zaune gefansa,ta amsa itama fuska sake,hakanan take jin nauyin
mutanen,duk da baki dayansu baifi gani biyu zuwa uku tayi musu ba
"Da tafiya zaki mama na bakimin sallama ba?,haba,shekara daya ba nan kusa bace
bafa?,kika sani ko kafin ki dawo ta Allah ta kasance a kanmu" sai taji ba dadi,ita
din saurin karayar zuciya,zuciyar tata ta karye,duk sai taji babu dadi har sai data
dago ta dubeshi,ya tuna mata da mukhtar dinta yayin da mutuwa ta daukeshi a ranar
da yake shirin sake angwancewa da ita,tabbas mutuwa bata da sabo,amma bata fatan
hakan ta kasance kan dattijon,tana jin qaunarsa a ranta kamar malam dinta,duk sanda
ta kalleshi yana tuna mata da malam din
"Bama fatan haka baabaa,Allah qara muku tsawon kwana da lafiya mai amfani"
"Amin amin" umme amira da baban suka amsa baki daya,amira ke turo baki tunda baban
ya fadi maganar,ta kasa shiru sai data tanka
"Wai baabaa fata kake ne ka mutu ka barmu,kullum sai kayi zancan mutuwa,bayan ko
aurena ni auta baka gani ba,ga yaya mahmoud da usama" dariya yayi irinta dattawa
sannan yace
"Mama na kenan,banda abinki ita mutuwa ina ruwanta da wanu tsari naka,duk sanda
tazo daukarka zata yi bafa zata fasa ba,ko babu ita akwai rabuwa,zaka rabu da mutum
wanda ba lallai ka sake ganinsa,kamar yadda har yau nake burin ganin wani tsohon
abokina da mukayu rayuwa a karkara tare,har yau Allah bai nufi zan ganshi ba,har
yau kuma yana raina" tuni idanunta ya soma digar hawaye kanta na a qasa,baabaa yayi
mata fami sosai,baima lura da ruwan hawayen nata ba,ya ciro wasu kudade irin na
qasar engaland din masu kauri ya miqa mata
"Ungo wannan mamana,kiyi amfani da su kinji sune tsarabata" bata son ta daga kai
yaga hawayenta,sabida haka ta sanya hannu bibbiyu ta amsa tana masa godiya mai cike
da fatan alkhairi sannan ta miqe ta juya ta fita,amira ce ta kalli baabaa
"Baabaa,zan rakasu airphort don Allah" umme ce ta cafe zancen
"Umhummm,wato zaki raka qawarki ko?,ina cewa nan su'ad tayi tayi ki rakata randa
zasu tafi kika qi,sai yanzu jikinki na rawa zaki ce zaki,to ba inda zaki din"
"Saurara KILISHI,Allah shike hada qauna tsakanin mutum da mutum,haka kawai Allah ya
hada jininta da yarinyar,barta taje,mama na sai kun dawo,daga nan kada ki biya ko
ina,ki dawo kizo kimin lissafin me kike buqata na komawa makaranta kinji" cikin
murna kamar qaramar yarinya tace
"Yauwa baabaa na,na gode"ta juya da sauri don ta ruski su sumayya.

       Cikin motar amiran ke basu labarin yadda garin yake,duk da yake akwai
banbancin gari,garin data zauna su ba nan zasu zauna ba,su laila an kasa kunne ana
kwashewa,murna da doki sun cikata burinta kawai su isa.

       Cikin qanqanin lokaci suka isa filin sauka da tashin jiragen sama na Nnmdi
azikwe dake garin abuja,bai wuce mintuna talatin ba lokacin tafiyarsu yayi,sabida
haka uncle farouq ya sallami driver din wanda ya tilasta amira yiwa sumayya sallama
saboda tare zasu koma,duj fuskarta ta nuna rashin jin dadin tafiyar tasu,kai kace
sunyi mugun sabo da juna
" nikam irin wannan qauna haka da amira ke gwada miki,bata da saurin sabi da sakin
jiki wa mutane fa,amma ke naga ta sake miki"murmushi sumayya tayi kawai tana miqawa
anty dije kudaden da baaban ya bata,kanta qulle tamau da mamakin wanne irin arziqi
baabaa ke dashi haka,duk da batasan kan kudaden waje ba amma tana jin labarin
darajarsu fiye da namu na naija,kuma yanzu haka wadanda ke hannunta ba daya biyu
uku biyar bane,sunfi haka,ido itama ta zaro
"Wa ya miki kyautar wadan nan kudin?"
"Baabaa ne"
"Kai baabaa,baabaa,alkhairinsa yawa gareshi,Allah ya saka masa da alkhairi"
"Amin,amma anty su basujin kyauta haka" murmushi ta kuma
"Haka suke,hannun kyauta garesu,suna da mutunci da karamci,yaci ace kisan ko su
waye su din,amma bari mu shiga jirgi zan gaya miki su waye su" bata kai ga amsawa
ba wayarta da zuci zucin ta kashe ta soma ruri,number amira ce,cikin mamaki ta daga
"Ya mahmoud ne zai magana da ke" ta fada tana hadata da shi
"Babu fada me ya kawo gaba gimbiyarmu,yanzu fi sabilillih zaki bar naija amma ko ki
sanar da abokina why?" Murmushi ta danyi
"Tunda ka sani ka wakilceshi ya mahmoud,kaa gaya masa"
"A'ah,wannan saqon ai na masoya ne,amma tunda kince haka zan gaya masa,ta inda kuma
zaki wanke kanku guna indai ni yayanne ki bada num dinki idan kun isa na bashi"
dariya ma ya bata,saidai yana da qima idanuwanta,shine mutum na farko da ya fara
tararta cikin fara'a da girmamawa sanda ta tsoma qafarta gidan baabaa prof
"Babu matsala"
"To ina godiya,inawa umman khalipha fatan alkhairi ki sanar mata" ya datse
layin,tana shirin maida wayar jaka saqon fatan alkahiri daga abdur rahman ya shigo
mata,ta karanta a gurguje ta mayar masa da reply.

       Idanu sumayyan ta shiga bazawa bayan tsintar kanta da tayi cikin jirgi ya
soma dagawa da ita zuwa sararin subhana,bata samu nutsuwa ba sai bayan shudewar
wasu lukatai sannan,anty dije ce a damanta
"Bari na cika alqawa ko,na gaya miki tarihin gidan baabaa prof"
"To anty ina jinki"

  *IYALAN GIDAN BAABAA*

     BAABA prof ba shine asalin sunanshi ba,suna ne da ya samu ta dalilin zuzzurfan


ilimin boko da yayi har ya kaishi ga zama professor,cikakken sunansa shine MUKHTAR
MUHAMMAD ADAM GWAMBE,haiffen wani qauye da ke cikin pantami,mahaifinsa Adamu wanda
aka fi sani da mai dabba,wanda ya ci sunan nashi ne sabida yadda Allah dora masa so
da iya kiwon dabbobi tun yana qanqaninsa,ga tausayi ga dabbobi,bama dabbobi kadai
ba hatta da mutane,ana amfana qwarai da tarin dukiyar da Allah ya huwace masa,wajen
taimako ga mabuqata,bafulatani ne gaba da baya,ma'abocin iya kiwo,wanda kuma Allah
ya albarkaceshi da tarin dabbobi,kama daga tumakai awakai raguna tinkiyoyi da shanu
bila addin,wand kaf qauyensu da kewayenshi babu wanda ya kaishi yawan
garke,matarshi daya khadijatu,ita ta haifa masa muhammadu da yayyensa guda
biyu,dukkaninsu suna ganiyar samartaka suka rasu sai muhammadun kadai da Allah ya
bar masa,yaro ne da yafi shiga ransa duk cikin yaranshi,ya debo kyawawan halayensu
tsaf har da ma qari,sannu a hankali muhammadu ya girma aka hadashi aure da wata
yarinyar wani malami maqocinsu mai suna naja'atu,cikin watanni tara kacal Allah ya
albarkaceta ta haifi MUKHTAR baabaa prof,wanda ba'a jima da haihuwarsa ba Allah ya
yiwa mai dabba rasuwa,ya rasu ya bar matarshi,bayan share makoki aka raba gado aka
baiwa khadija matarsa da dansa muhammadun,ya karbi dukiyar mahaifinsa kuwa a sa'a
don habaka tayi tayi,abu ya dinga dad gaba,saidai daga baya ya fuskanci kamar kiwon
wahala ce kawai,ya saida shanun ya rage wasu daga ciki ya barwa mukhtar kyauta
halak malak,yace shima ya taba aikin gado,dama can shi mai son kiwo ne,tare suke
fita da shaqiqin abokinsa wanda tun yana da shekara daya a duniya baida aboki sama
da SULAIMAN sule,babu abinda ke rabashi da sule,hatta bacci ma wani sa'i tare
suke,musamman idan matar babanshi taso tsiyar tata,tausayinsa yake,qaunarsa yaje
fusabilillah,mahaifiyarsa ta raau tun randa ta haifeshi ko waiwayowa batayi taga
abinda ta haifa din bata yi ba,sai suka qulle sosai,muntari baida qani balle ya
debe masa kewa,haka sule ma baida dan uwa sai hashimu,shi kuwa bai isa ya rabeshi
ba don tuni altine ta shiga tsakaninsu ta raba zumuncin Allah qarfi da yaji,duk da
hashimun na qaunar dan uwansa,tare suka dinga fita kiwo shi da sule,yayin da
babansa muhammadu kuma ya soma saida zannuwa a cikin garin gwambe,dukkaninsu Allah
ya sanya musu albarka baki dayansu,har mamakin yadda dabbobin muntarin keta habaka
babansa muhammadu keyi,shida sule kiwo suke haiqan,duk da babu dabbar sulen ko daya
a ciki amma sabida qaunar dake tsakaninsu wani lokaci a shike fitar ma muntarin da
su,altine tayi dukan,tayi dukan don ta raba tsakninsu saboda yadda taga suke na
samun kulawa a gidansu muntarin amma a banza wai man kare,saboda tare malam
muhammadu ke musu komai,bai rasa ci ko sha ba balle sutura,ba'a rabasu a gidan sule
dai dai yake da muntaru,data gama dukan zata kuma gansu tare,abun ya tsaya mata a
rai,sai ta koma ziga gun babansa,to shi din ma baici nasarar rabasu din ba,saboda
yadda qauyen aka soma zaginsa shi da matarsa kan yadda suka qwallafawa dan marayan
Allahn.

Cikin haka turawa suka shigo qauyen nasu,suka kawo musu makarantar boko har
cikin garin nasu,kowa ya tsame dansa yace babu shi a wannan batu,muntari na bala'in
sha'awar karatun,ya samu babansa ya sanar masa kan ya sanyasu shi da sule,da fari
shima yace sam kada muntarin ya sake wannan magana,bayan dogon nazari da malam
muhammadun yayi sai ya amince,ya hadasu da sule ya kaisu amma yace saidai suyi jeka
ka dawo(day),altine zani a hannu ta shaidawa mahaifin sule abinda malam mahammadu
yayi,ai kuwa ya wanke qafa yaje har gida ya ciwa malam mahammadu mutunci,a lokacin
sule na gidan tare da muntari,kuka ya dinga yi yana jan baban nasa kan ya daina
zaginsa amma ya mangareshi ya qara gaba,tilas malam ya lallashi sule kan yayi
haquri tunda babansa baya so,haka ya haqura ba don rai naso ba,ya ci gaba da fitar
da shanun muntari kafin ya dawo daga makaranta sai ya taddashi a jeji suci gaba da
kiwon tare da yammaci su dawo gida,malam muhammadu yace ya ya daina,ya bari idan
muntarin ya dawo sa fita tare su dawo tare,amma sam yace a'a,ai shi da muntarin
duka daya ne,duka a lokacin basu wuce shekara goma sha uku uku ba.

A haka shanun muntari suka sake yawa,ga cikakkiyar lafiya dake garesu,ganin
haka ya sanya muntari ya shawarta da malam muhammadu zai raba dabbobin biyu ya
baiwa sule rabi,saboda wahalar da yake da su ko shi sai haka,ba musu dukka suka
amince har da mahaifiyarsa,randa ya sanar da sule cewa yayi bazai karba,shi don
Allah don qauna da amincin dake tsakaninsu yake masa,tilas daga qarshe malam
muhammadu ya tilas ta shi ya karba,godiya ya dinga musu harda hawaye,din suna da
yawa baiyi tsammanin mallakar wani abun duniya kwatankwacin haka ba.

Randa yaje da maganar gida da yammaci ne,altine kasa bacci tayi sai data
dangana da bokanta,kafin wayewar gari ya yiwa sule kurciya,kurciyar data kawo
rabuwarsa da muntarinsa,rabuwar da har yau fuskokinsu basu qara ganawa ba,duk da
yadda muntarin keta nemansa ko ina loko da saqo na garinsu saidai babu
labarinsa,tun da quruciya yake nemansa har girmansa,har yau yana kewar dan uwansa
kuma amini shaqiqinsa sule saidai har yanzu Allah baisa an dace ba.

Muntari yayi kuka yayi kuka har wasu ma suka tayashi kokawa,da qyar aka samo
kansa,amma shima daina kiwon yayi ya haqura ya kama karatunsa gadan gadan,bayan
rasuwar khadijatu mahaifiyar malam mamman kaka ga mukhtari baabaa prof,garin ya
daina musu dadi baki dayansj,sai ya tattara ya koma cikin ainihin garin gombe inda
dama kasuwancinsa ya riga yayi qarfi qwarai a can,ya saida dabbobin muntari saidai
muntarin yaqi a saida wanda ya baiwa sule,ya samu fili daya na babansa ya zubasu ya
maidashi kamar dan qaramin gidan gona yaci gaba da kiwata masa su,yayi alqawarin
duk randa Allah ya sake hada fuskokinsu matuqar yana raye saiya cika wannan
alqawari.

A kasuwa mahammadu ya zuba kudin muntarin,suka ci gaba da juyawa tare,gefe


guda kuma ga karatunsa bai fasa ba,kafin wani lokaci muntarin ya zama dan birni
sosai,ya goge,ilimi ya ratsashi,ya zama saurayi wamda har ya kammala secondry dinsa
ya soma jami'a.

Kyau tsantsa irin na usilin fulani Allah ya baiwa mukhtar shi,tsantsar farin
jini kamun kai kamala da kwarjini wanda shi ya janyo masa tarin masoya maza da
mata,yana faran faran da son jama'a,'yammata kuwa ba'a cewa komai,duk da 'yamata ne
irin na da,masu tsananin kunya da kamun kai,da wuya kaji tace tana sonka,saidai ka
gani a ayyukanta,a hakan ma ana ganin kansu ya bude suna jami'a,a jami'ar ma babu
yawan matan,sabida har lokacin jama'a basu karbi karatun boko ba sam sai daidaiku.

Zuwa lokaci dukiyarsu ta sake ninkuwa,irin dukiyar da a lokacin tsoro ma


kake asan kana da ita saboda yawanta da rashin hanyoyin boyeta da sarrafata kamar a
wannan zamanin,tuni malam muhammadu ya tashi daga malam ya koma alhaji,ya tamfatsa
gida irin na masu kudin da,irin gidan da a da saidai gida na sarauta,mai sarautar
ma wanda ya isa,kamar sarki ko waziri,gwamna ko shugaban qasa,tun mota da babur da
handset sai wane da wane mukhtar yake hawa yake riqewa,arziqi ya zauna musu na ban
mamaki,gefe guda bai fasa kiwata dabbobin sule ba,wadanda sukayi albarka suka zama
hamshaqin gidan gona,wanda ke fidda kaji,madarar shanu,qwai,a kuma sarrafa yoghourt
wanda yayi sunan ba gombe kawai ba har a arewa a wannan lokacin,duk abinda aka
saida yana tara kudin a gu na daban yana ajjiyewa sule,har lokacin bai fasa nemansa
ba,bai fidda ran kuma ganinsa ba,yakan ce IDAN DA RAI DA RABO.

Kaf qauyensu babu wanda baici arziqinsu ba,mutanen da suka kai maka Allah
yayi yawa sa sh,tun a lokacin mai zuwa maka a jirgi sai wane da wane,hatta da
mahaifin sule wanda altine ta yashe ta gudu ta barshi cikin tsananin talauci da
yunwa,mkhtar ya fidda kudi cikin kudin sule ya biya masa hajji,kafin ya dawo aka
buge gidan sa aka sake masa gini da ya dace da irin wancan zamanin,kuka ya dinga yi
yana shiwa muntari albarka yana roqon Allah ya bayyana masa dansa,don hashimun ma
ta gudu da shi baisan inda yake ba,sosai baban sulen yaci arziqinsa kafin Allah
yayi masa rasuwa.

Muntari baabaa prof sun hadu da matarshi ta farkoZUWAIRIYYA wadda ake kira
KILISHIa makaranta,a lokacin yana karatun degreed dinsa na biyu a jami'ar bayero
dake kano,diya ce sarkin rano,yarinya ce mai kamun kai,miskilanci da haquri,akwai
dan jin kai tattare da ita dan kadan wanda jinin sarauta dake yawo jikinta ya
haddasa hakan,saidai akwai fada da tsiwa idan ka tabota,kusan abinda ya zama silar
qulluwar alaqarta da mukhtar kenan,haduwarsu wajen cin abinci dake makaranta,sukayi
fada daga qarshe ya nemota ya nemi soyayyarta,ta dan garashi sannan daga bisani ta
amince ta yarda da aurensa,ba wani lokaci aka dauka ba kasancewar akwai sanayya
tsakanin alhj muhammadu da mahaifin kilishi,saboda shahararsa a kasuwanci,zaka samu
wani lokaci akwai alaqa ko abota tsakanin masu sarauta da 'yan kasuwa.

Babu bata lokaci akayi komai aka gama,alhj mahammadu ya danqarawa tilon
dansa gida cikin kano da kudinsa da kansa a daura da jami'ar bayero,wanda a sannan
ba unguwa bace face irin unguwannin nan marasa gidaje sabbin unguwanni,a nan suka
tare cikin qauna da aminci da kula da juna,shi yana nashi karatun itama tana nata
hankali kwance,da ya gama ya juya masters ita kuma data hada degree ta tsaya
hakanan ta maida hankalinta kan kula da gidanta,macace data iya zaman aure,tsantsar
kula da miji,iya tarairaya da nuna qauna,shekara uku da aurensu suka samu qaruwar
d'a namiji,ba bata lokaci mukhtar baabaa prof ya sanya ma yaron sunan kakansa wato
adam,shekara na zagayowa kilishi ta sake sambalo d'a namiji wanda C.S aka yi mata.

Abinda basu taba gani ba wato alhj muhammadu yazo gidansu,da kansa wannan
karon yazo ganin jariri bayan sallamarsu daga asibiti zuwa gida,tun a daren kilishi
da adam ke kira ummee ta dinga dariya tana fadin lallai wannan yaro yayi
goshi,sanda aljh ya daukeshi kallonshi ya dinga yi yana murmushi,yayi wata magana
data sanyaya jikinsu ta kuma basu dariya
"Inama rai zai bani aron lokaci da rayuwa naga girman wannan yaro,ba shakka na
tabbatar akwai wani lamari tattare da shi,shi na daban ne cikin yaran da nake
gani,tun a daren da aka ciroshi jikina ya bani haka" kilishi da ta maida abun wasa
dariya tayi
"Alhj ya akai ka sani" da yake shi wasa yake musu tamkar jikokinsa,dariyar shima
yayi
"Zaku ce na gaya muku,lokaci zai nuna,ba shakka shi MUSDAFA ne,zababbe ne"
"Shikenan baaba,ka sanya masa suna,dama sunanka nakeso na saka wannan
karon,MUHAMMAD MUSTAPHA" yaji dadi qwarai a zuciyarsa,har ya gaza boyewa,ya daga
mustapha yadinga masa addu'o'i,wasu cikin kunne wasu cikin baki wasu cikin
ido,addu'o'i ne wadanda ko diyan cikinsa mukhtar bai masa su ba,yana son yaron,yana
jinsa har cikin zuciyarsa,sosai ya roqa masa albarkar rayuwa duniya da lahira.

Mustapha bai cika wata ukuba duniya ba Allah ya yiwa alhj muhammad
rasuwa,dan kasuwa mai gaskiya da amana,tausayi da taimako,kowa nashi ne,kowa cin
arziqinsa yake,ba iyalansa kadai sukayi rashi ba hatta da kano da gombe baki
daya,mukhtar ya dauko mahaifiyarsa ta dawo gidansa dake kano da zama,ya sake yiwa
gombe nisa,abinda ya sake sakashi kenan ya rage zuwa gomve,sai yayi wata shida ko
shekara baije ba,hakan ne ya sanya har sule yaje ya tafi basu hadu ba,sanda yaje
aka gaya masa kamar zaiyu hauka,sai ya koma zuwa akai kai amma har ya gaji ya
watsar sulen bai kuma dawowa ba,da alama har yanzu baqin abun da aka yi masa na
cikin jikinsa.

Nauyi sai ya sake yiwa mukhtar yawa,ga dukiyarsa ga wanda mahaifinsa ya bari
aka raba musu,mahaifiyarsa ta dauki tata ta damqa masa,don bata da wani itama sama
da dan nata,haka duka ya hada,ga karatu da ya kasa haquri ya bari saboda yadda yaji
dadinsa,ga kasuwanci ya sakoshi gaba,bayan shekara biyar da haihuwar mustapha
kilishi ta sake haihuwar 'ya mace wadda taci sunan farida,zuwa lokacin sun fara
ganin abinda alhj muhammadu ya fada akan mustaphan,ba shakka shi na daban ne
tsakaninsa da dan uwansa,akwai banbance babance sosai,bayan haihuwarta ba dadewa
itama innar mukhtar ra rasu tabi mijinta bata cika shekara ba aka haifi mai sunanta
naja'atu suna kiranta da huda,haka suka ci gaba da gudanar da rayuwarsu,ko yaushe
arziqinsu bunqasa yake albarkacin taimako da suke yiwa bayin Allah da nemanta sa
suka ci gaba da yi ta hanyar Allah.

Mukhtar bai bar karatunsa ba sai da ya zama farfesa,a lokacinne suka hadu
da ABDUS SAMAD wanda ya zame masa aboki,kusan bai qara amini tun bayan rasa sulensa
da yayi sai a kan abdus samad,abdus samad na qaunar baabaa prof qwarai da gaske,a
lokacin ya fara taba siyasa,ya shigeta da qafar dama,ko ince ya shigeta da gaskiya
da amana,da magana daya tak idan ya fadeta,abinda yawancin 'yan siyasarmu suka
rasa,ba wani abu yake nema cikinta ba sabida babu abinda ya nema ya rasa a
duniya,arziqin duniya da dukiya Allah riga da ya bashi saidai ya nemi na
lahira,wanda yana amfani da dukiyarsa yana nema saidai Allah ya karba masa,ba
takara ya tsaya ba,amma yana supporting gwanatin dake nema sabida yadda da yayi da
ingancinta da,cikin ikon Allah kuwa ta samu nasara,hakanne ya sanya aka bashi
matsayin AMBASSDOR jakadan nijeria a merica,sosai abdus samad yayi farinciki,don
shima iyalinsa na can,matarshi daya alokacin hajiya khaulat,abinda ya zaunar da ita
can acan abdus samad ya ganta ya aureta sabida mahaifinta pharmacist ne acan a wani
asibiti yake aiki,,itakam tace ba zata bishi nijeria ba,tilas ya yadda ya aureta a
can suka zauna a can,bai wani damu sosai ba,don shima acan yake nashi aikin irin ma
surukinsa,damuwarsa kawai yaran da zai haifa kada su tashi da tarbiyyar can.

Gidan da abdus samad suke zaune me block biyu ne,hakan ya sanya yace muntari
ya zauna a nan,amma yace a'ah,saidai abdus samad yazo su zauna qyatacce kuma
yalwataccen gidan da gwamnatin tarayya ta bashi ya zauna iya wa'adin aikinsa,hakan
suka tattaro suka dawo,duk da khaulat bata so ba,saboda macace mai tsananin izza
girman kai da ji da kai,macace dake son taga kowa a qasanta ita ce a sama,hakan ya
sanya jininsu yaqi haduwa da kilishi ummee,saboda sam bata da wulaqanci,barta da
miskilancinta fada da rashin son raini,sam ta tsanu halayen khaulat,duk da yadda
ita khaulat din ke maqale mata,saboda tasan daga babban gida ummeen take,bugu da
qari girma ne da cinyewa a wajenta ace tana hulda da mace irin ummeen,mata a wajen
ambassador muhammad mukhtar muhammad adam,kuma diyar gidan sarauta.

Komawarsu america ummee bata saki tarbiyyar yaranta ba,basu fi shekara guda ba
Allah ya hada baabaa prof da Bilkisu,yarinya mai tarbiyya hankali faran faran da
jama'a,sanda ya zowa ummee da zancan tasi tayi bore,amma tilas ta haqura da
mahaifinta ya tsawatar mata,yace a nijeria ma bilkisun zata zauna,sosaj khaulat
taso zuga ummee,saidai ko kallo bata isheta ba,don jininsu bai gama haduwa ba,ita
dinma tana da hankali,bata da shegen kishi da iskanci irin na 'yammatan yanzu da
zasu nemi tasarwa uwar gida hankali,tun kafin ta shigo ma sai suka fahimci
juna,tana yawan kiran ummee a landline tasu suna gaisawa,tun ummin na basarwa har
ta saki jiki,sai Allah yasa mata qaunar bilkisu har akayi auren,shekara guda ta
haifi danta na fari mahmoud,baki daya suka je nijeria suna da yaranta baki
daya,sukayi sati suka dawo.

A lokacinne kaulat ta samu ciki,bata taba haihuwa ba,wannan ita ce haihuwar


fari da zatayi,ita ta dakatar da haihuwar a cewarta bata da buqatarta a kusa,bayan
wasu watanni ta haihu,ta haifi SU'AD,tun a sabitin tasa aka juyar da
mahaifar,wannan wuya wai ba zata iya ba,da yake turawa ne ba ruwansu suka yi mata
abinda take so.

So da qaunar duniya ita ta dauka ta dorawa su'ad,yarinyar ta taso a


sangarce,abinda take so shi take yi,babu kwaba babu hantara,kallon banza kayi mata
sai ta saka ihu tun tana qanqanuwarta,hakan ya sanya sam tasu bata zo daya da yaran
ummee ba musamman mustapha,miskilin yaro wanda jinin sarauta ke yawa a jikinsa
kamar uwarsa tun yana da qananun shekaru,ko kallo yarinyar bata isheshi ba,idan
tana gu bai zama,shu kadai ke iya bugunta ta haqura ta shanye bata kai qara ko ta
tashi hankalin gidan ba,shi kadai ke hukuntata yadda yaga dama,hatta babanshi da
shi yake hadata idan ta addabeshi,bala'in tsoronsa Allah ya dora mata da
qulafucinsa,bai damu da ita ba amma idan ta wuni bata ganshi ba ta dinga binbini da
tambotsan nemansa tana yiwa uwarta rigima,kota shigo wajen ummee ta liqe mata tana
buga rigimarta,da ya shigo kuwa kallo daya zai mata ta shiga taitayinta.

Kai kai,yau nayi abun kai,4932 words?,ku biyoni a gaba don jin qarashe wannan
family.

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*
*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

6⃣5⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

*innalillahi wa inna ailaihu raji'un*

*Allah subahanahu wata'ala yana cewa cikin qur'aninsa*

*RANAR DA ZAMU CE DA JAHANNAMA SHIN KIN CIKA?,SAI TACE AKWAI QAARI NE?(na mutanen
da za'a zuba mata)*

*subhanallah,Allahumma ajirna minan nar*

____________________________________

       Ba yadda ummee ta iya wani lokaci haka take biyewa tsiyar su'ad,ta
lallabata,takan yiwa mustapha fada idan ya mata tsawa ko ya niyyaci dukanta,sam bai
son sangartarta,bai shiga gidansu ma sabida halayyarta data uwarta da bata yi masa
ba,ummee bata son yadda yake mata,takan ce yarinya ce fa mustapha su'ad har
yanzj,cikin zuciyarta kuma bata ganin laifin kowa sai na uwarta,tunda ance ice tun
yana danye.....,haka nan barewa bata gudu danta yayi rarrafe.

        Tun yana qaraminsa Allah ya zuba masa miskilanci,halinshi ne,halittarsa ce


haka gado yayi,yaro ne shi mai zubin gidan sarauta,yana qaunar doki,kayan sarauta
da duk wani abu daya danganci hawa doki,kusan yadda halayyarsa take tamkar babban
mutum ya sanya abokansa yaran turawa ke tsokanarshi da sunan MAN,mukhtar baabaa
prof shima yakan tsokaneshi lokaci lokaci,daga haka sunan ya bishi,son dokinshi ya
sanya baabaa prof tun a lokaci yakan siya masa ticket yaje kallon wasan polo tun a
american,yawan kallon wasan polo ya sanya su'ad itama wasan ya soma burgeta,bai da
abokin tafiya duk sanda zashi kallon,sai ita ke nacewa zata rakashi,tun yana daka
mata tsawa yana korarta yana cewa ba zata rakashi ba har ya fara barinta tana
binsa,saidai har suje su dawo bai tanka mata,ita kuwa ta cikashi da surutu,abinda
baiso kenan,yanzu kansa zai hau ciwo,don ciwon kai bai masa wuya.

        Tsabar qwaqwalwa da Allah ya zuba masa ya sanya aka daukeshi daga nursery
zuwa primary,a can din ma suka fuskanci basirarsa ta girmewa gurbin da suka
bishi,tilas aka sake turashi ajin da zasu kammala secondry a shekarar,

       A shekarar ne baabaa yaga dacewar ajjiye aikinsa ya dawo gida ya tattara kan
iyalinshi baki daya,anty maamaa dake abuja da ummee dake tare da shi a
america,maida hankalinsa sosai yayi ya tasamma gina katafaren gidanshi a
abujan,gini ne dashi kansa yasan cewa ya kashe masa maqudan kudade duk da ba komai
bane abinda ya cira wajen ginin cikin irin dukiyar da Allah ya hore masa,a yanzu ya
tabbatar baida wasu family na jikinsa sosai baya ga sauran dangi tsiraru da suka
rage banda yaransa da ya haifa,wanda a yanzu sun zama su bakwai,ummee na da biyar

ADAM
MUSTAPHA
FARIDA(UMMAN HUSNA)
HUDA sau auta
SUMAYYA(AMIRA)

Bilkisu anty maamaa na da yara biyu duka maza

MAHMOUD da
USAMA

       Gini yayi yana mai hasashen gaba,yana son yaransa maza su zauna da shi idan
Allah ya hukunta hakan cikin gida daya,hakan ya sanya yayi sassa biyu,ko wane sashi
akwai wasu sassan ciki,duk a lokacin ma adam da yake babba a lokacin yake ss two a
can american,sanda suka tashu tafiya aka bar adam ya kammala secondry dinsa,yayin
da uncle abdus samad mahaifin su'ad ya nemi alfarmar a bar masa mustapha,saboda ya
lura da yadda su'ad ke daga hankalinta daga jin labarin tafiyarsu,da fari mustapha
yaqi ya murje idanunsa,sabida asalan shi mutum ne da bai boye abinda ke ransa koda
ba zai maka dadi ba,gaskiya ce zaya fadeta komai dacinta,saida baabaa prof ya jashi
yayi masa fada kaca kaca,ya gaya masa abdus samad babansa ne kamar yadda shima yake
babansa,yarone mai biyayya da bin umarnin iyayensa komai tsaurinsa,baison bata musu
ko yaya,hakan ya sanya ya sunkuyar da kai,bai sake cewa qala ba har akayi aka gama
suka tafi suka barshi hannun abdus samad da matarsa khaulat,murna cikin khaulat
kamar tayi me,a take ta dinga hasasowa ranta hada mustapha da su'ad,tabbas ba zata
bari 'yarta tayi asarar babban gida irin wannan ba,zata so hada alaqa da gudan
professor mukhtar muhammad,tabbas ba qaramin kankaro mutunci bane ku samu relation
da attajirai irinsu,shu'umin murmushi ta saki,kusan ita ta qara kitsawa su'ad
soyayyar mustapha,tunu yarinya ta hau turba,dama gata cikin turawa,batasan kunya ba
ko kadan,a shekarun har tasan wani soyayya da i love you,a haka shekaru suka fara
tafiya,adam ya kammala karatunsa yana niyyar komawa naijeria,yana son qasar tayi
masa,ba kamar mustapha ba da ya lura tunda aka tafi aka barshi bai kuma zancan
qasar ba,fushi ne ko ameriacn tafi yi masa oho?.

      Koda ya koma nijeria adam makarantar gaba da secondry aka sama masa ya sake
komawa,yayin da mustapha tuni ya shiga secondry,yana aji biyu junior suka daukeshi
suka maidashi senior aji biyu saboda gifted ne na tashin hankali,kishinsa classmate
dinsa suka musamman turawan nan,suna ganin bai isa ba yana asalin dan nijeria yace
zaizo ya dokesu,kunsan mai jan kunne da shegen kishi da ganin kai baqar fata baka
isa ba,to indai mustapha ne basu isheshi duba ba,karatunsa yake haiqan,babu wanda
ya isa yayi gigin tabashiduk iskancinau,sunsan waye ubansa,ko baya ga haka ma suna
sane da halin jarumta irin tashi,sau da yawa abubuwa na tsoro sai su kasa shike
gabatar da su,baison raini ko kadan yana da zafi,bai shiga sabgar da bata shafeshi
na,wadda ta shafeshin ma ba lallai ya bata muhimmanci ba,karatu ya zaunar da shi
kuma shi yakeyi,tilas suma suka sallama masa,cikin qanqanin lokaci yayi fice yayi
suna cikin makarantar,tare ake kaisu a daukosu shi da su'ad,saidai ko kadan basa
shiri saboda yadda ta cika rawar kai da kule kulen maza,amininshi daya ne tal a
duniya har ya zuwa yau din nan,HAMZA ABUBAKAR JAHUN,babansa aiki ne ya kawoshi
qasar suke zaune,shi daya yasan ta kan mustapha,ya iya zama da shi hakan ya sanya
tasu tazo daya.

        Duk da wannan halayya tasa mutum ne shi mai tausayi,yana da tausayi ga mata
tun asali yasan su masu rauni ne,sannan qananan yara musamman idan aka ce wannan
maraya ne,Allah ya zuba masa tausayin maraya walau uwa ko rasa ko uba,ko kuma dukka
baki daya,tun a sannan ya yiwa kansa alqawarin gina gidan marayu idan ya
girma,yasan idan ya yiwa babansa maganar shi mai ginawa ne,to amma yafison ya gama
karatu ya kama aiki,ya ginda da kudinsa daya nema da guminsa.

     A can mustapha ke halartar wata makaranta,duk da yake aji guda ne saidai kowa
da inda ake masa qari,alqur'ani ake koya musu da littafan addini wanda ya shafi
fiqhu,tauhid/aqida,da kuma hadith,mutumin dan qasar pakistan ne,da fari su'ad na
binshi suje,duk da ba wani abun arziqi take koyowa ba,daga bisani bayan shekara
daya ta watsar,saboda a ganinta ta girmi zuwa makarantar islamiyya,tayi zamanta da
jahilcinta tana yiwa wasu kallon gidadawa kidahumai,mustapha bai gushe ba yana zuwa
makarantar har ya sauke bayan haddar izifi talatin cif da ya samu,wanda har zuwa
yanzu tana nan a kanshi.

A hankali shekaru suka fara ja,girma yazo wa kowannensu,su'ada an zama


budurwa,tana ss 2 a lokacin,yayin da mustapha ke universty,a duniya baida sha'awar
kowanne karatu irin karatun likita,yana son karantar bangaren cututtukan yara,sai
aka samu akasi kasancewarsa ba mai magana ba,uncle abdus samad ya cike masa fannin
mata,wato gynocology,sam wannan fannin bai burgeshi ba,amma da sukayi magana da
ummensa,ta nuna masa cewa bangare ne mai muhimmanci da irin adadin matan da zai iya
taimaka,sai ya gamsu ya karba hannu bibbiyu,ya shiga karatu ka'in da na'in,kowa ya
sani cewa karatun likita ba abu bane mai sauqi kamar sauran bangarorin,balle agun
mutum mai daukan lamuransa da gaske irin mustapha,bashi da lokaci komai sai na
karatunshi,fanni guda suke karanta shi da abokinsa hamza,a hankali suka hadu da
abokai daidai su,wadanda karatu kawai suka saka gaba,cikin qanqanin lokaci group
dinsu yayi shura,su shida ne cif,dukkansu babu baya cikinsu,ta fannin kyau,nasaba
da dukiya,mustapha,hamza,usman,musaddiq,lamin,huzaifa,suna da ra'ayoyi iri guda ta
wani fannin,yayin da kuma suka saba ta wani bangaren,abu guda dai wanda sukayi
tarayya a kai shine,aqidun turawa da sukayi tasiri cikin gangar jiki da
zuciyoyinsu,sakamakon dadewa da kowannansu yayi cikin qasar,lamin me kawai da
musaddiq karatu ne ya shigo da su,ba wanda ke harkar banza a cikinsu anutse
suke,saidai kama daga abinci,sutura zabi na irin matar aurensu,doka da qa'ida da
mu'malaolinsu na yau da gobe dukka aqida da halayen nasara ya shiga cikinsu yayi
kane kane.

SU'ADAH

Yarinyar da tun tana qanqanuwarta aka nuna mata ta ginu ta kafu kan raina
talaka,dukkan wanda bai da shi bai da qima baida daraja a idanuwanta,kai hasalima
bata masa kallon cikakken mutum mai 'yanci,yarinya ce mai yawan izza da jin
kanta,yarinyar da bata mu'amala da dukkan mutumin da bai fisu arziqi ba,matuqar
kina so ko kana so kuyi qawance ka tabbatar ka fito daga gidan da yafi nasu arziqi
ko kake dai dai da ita,ta dauki kanta da girma,ta ajjiye kanta can nesa sama
qololuwa,komai nata high class ne,komi da zata mallaka sai ta tabbatar yasha banban
da na kowa,bata taba yadda wani ya fita ko ya shalle mata,bata lamunci kallon banza
ba bare ka furta mata maganar banza,taku take iya qarfinta,jin kanta take tamkar
diyar DONALTRUMPH ko kuma BILLGATE,kallon da takewa mutane ma dabanne,duban farko
ga mai hankali zai fuskanci kallo ne na qasqanci da ganin kowa bai isa ba face ita
din nan dai,masu hidimawa gidansu kallonsu take tamkar bayi da suka siyesu,babu
wanda baifi qarfin ta takashi ba matuqar arziqinka ya gaza nasu,wayewarta ta wuce
iyaka,ta wuce tunaninka,duk wani abu da baturiya zatayi shi a matsayinta na farar
fata wadda bata da cikakken addini bare kunya shi su'adah zata yi ba,babu uban
wanda take jin kunya,abu guda ne bata taba yiba bada mutuncinta,saboda ta riga ta
sanyawa ranta bata da miji daya wuce mustpha,har yau batayi katari da namiji kamar
mustaphan ba,duk wanda ta kalla sai taga mustaphan ya masa fintikau,tamkar yadda
sama ta yiwa qasa nisa,bugu da qari ta tabbatar ta jewa mustapha a fanko babu
abinda zaya hana wulaqanta duniyarta,babu abinda zai hana yayi fatali da dukkan
wata qauna da take masa ya hukuntata mafi tsananin hukunci,tana yarfa tare da
wulaqanta maza da yawa,kama daga hausawa har zuwa turawan,idan har kaga ta tsaya ta
kulaka tofa ka tabbatar babanka an sanshi ya san wani shima,sunansa ya zama tambari
a duk qasar da kuke da zama,su'adah bata san sanya atamfa ba balle daurin
zani,dankwali kuwa saidai ta gani a kan wasu,yadda americans ke shigarsu itama haka
yake,ta sanya rigarta da wando,ta fito da gashi ta fice abinta haka,a da har ra
tsiri saka mini skert,mustapha yaci ubanta ya taka mata birki,tana qwafa tana
kumburi bayan fitarsa tana ba zata daina ba,kaulat da take kira mom ta mata fada,ta
fuskanci sam a cikin kaso dari na rashin nutuncin su'adah itakam ko arba'in bata yi
ba,dama wai ance sai mai koyo yafi qwararre qwarewa
"Ke da kike son aurensa,ta yaya zaki qi yin abinda yake so,idan dai baso kike ki
jawo mana asara ba,jira nake kawai ki gama secondry na qyasawa babanku maganar,don
kada ma ya hango wata ya jawo mana asara" kan haka ya sanya ta daina sanyawa,ta
kuma nemi dankwali take sanyawa akanta don dole wanda data fice yawonta zata
figeshi sai kuma idan zata dawo gida.

A irin zaman hostel da sukeyi idan jarabawa ta kusa,suna zaune su shidan


bayan kowanne yayi karatu ya gaji,sai kuma suka barke da hira,mustapha dake
kashingide gefansu yana duba handout,shi kadai ne bai ajjiye tasa ba,sun riga kusan
da sun saba da irin wannan halayya tasa,yadda yake na daban komai nashi dabanne,bai
gajiya sam da karatu,iskar gun nayi mishi dadi qwarai,saboda wadatar shuke shuken
dake wajen,a hankali suka gangaro kan hamza,shi sukewa tsiya kan yaci baya,ya rasa
wadda zaya aura sai 'yar afrika,afrikan ma nijeria,nijeria ma yarinyar da kwalin
secondry school kadai gareta,ra'ayinsa ne,don duk cikinsu ya fisu sassauqan
ra'ayi,baiga dalilin da zai daukarwa kansa jangwam ba,yana mamakin yadda 'yammatan
da idanunsa ke bude tarwai suke burgeshi,shikam ya sheqa yaga babu qwaya gwara ya
auri local ya wayar da abunsa,kusan mustapha yafi kowa jin baqincikin batun,shi
gaba daya atsarinsa ma baijin zai iya auren matar da bata da kwalin degree zuwa
sama,matar da tasan abinda take yi,yana jinsu suna ta kumfar baki,daga bisani da
yaji sun fara cikashi ya miqe zai bar gun,don kada ma ranshi ya baci kan
lamarin,bai son cewa komai,haka ya kwashe litattafansa ya sauya gu yana ganin
baiken hamza,tare da mamakin meye amfanin wayewa da karatunsa da zai dauki irin
wadan nan yaran a matsayin matar aure,wadda babu wayewa tattare da su,a ganinsa
saidai kawai kasha kayan haushi,babu wata kulawa da zallar soyayya mai maqalewa
zuciya da zasu iya yi ma,a yadda yake din nan mayen soyayya ne,mutum ne shi mai
burin samun macen da zasu baje kolin soyayya,ta soshi tamkar ranta,ta kula da shi
kamar sabon jinjiri,ta shagwabashi kamar dan auta,ta bawa lamuransa muhimmanci ta
fifitashi fiye da kowa ina zaya samu wannan ga irin wadancan matan?.

Lokacin da mustaphan ya gama karatunsa baki daya har ya samu aiki a wani
babban asibiti dake garin,wanda da gudu suka daukeshi,sun jima dama suna bibiyar
irin qwazonsa,don a daliban da jami'ar ta yaye a shekarar banu dalibin da ya kai
qwazonsa,ranar baabaa prof yayi farinciki da samun d'a kamar shi,ya runa kalaman
mahaifinsa muhammadu,ba shakka suna ganin abinda malam ya gaya musu
zahiri,mustaphan daban yake tun daga haihuwarsa zuwa yau,haka ma ummee don baki
daya suka rankayo harda anty maamaa suka zo bikin yaye su din.

  familyn tun a lokacin family ne mai ban sha'awa da burgewa,cike yake da


qaunar juna da hadin kai,dukkansu daga ummee har anty maamaa sun tsarkake
zukatansu,kowacce ta riqe 'yar uwarta fusabilillab,sai Allah ya shiga lamarinsu ya
kade musu dukkanin abun qi.

Ana ya gobe su baabaa prof din zasu koma uncle abdus samad ya sanarwa
baabaan niyyarsu ta hada auren mustapha da su'adah,ba qaramin farinciki baban yayi
ba,yana ganin lokaci ne na qara danqon aminci da zumuncin dake tsakaninsu,ko a
lokacin sai da ya tuna da sulenshi,inama ace diyar sulenshi ce zai aurawa
mustapha?,kowa yayi na'am da batun sabanin mustapha daya shiga tashin hankali da
bacin rai,tunda shi kam babu wata alaqa ta soyayya data taba shiga tsakaninsa da
yarinyar sam,hasalima bata cika sharadan da yake so ba,don candy kadai tayi,kawai
dai ya dauketa ne matsayin qanwarsa,amma da batun yaje kunnen abokan nasa su suka
kwantar masa da hankali,a ganinsu babu komai,a daura auren taci gaba da
karatunta,shima yaci gaba da aikinsa,idan yaso sai yayi rainonta har takai matakin
da yake so ta kai,ya dorata kan dukkanin tsarinsa,tunda babe din ta hadu,abinda
basu sani ba dukkansu shine su'adan ta girmi tunaninsu,shi sam shawarar ma bata yi
masa ba,abu guda da ya sanyashi amincewa shine ranar wata lahadi da ya jiyo muryar
kaulat na kururuwa,su'adah din ya dirki guba saboda ta lura mustaphan baya
sonta,abun ya tsoratashi,ta dauki halayen yahudawa baki daya na rashin yadda da
qaddara,ko data farfado cewa tayi zata kashe kanta,roqon sa da uncle din ke masa
kan ya aureta shi ya masa nauyi,ba tare da bata lokaci ba ya amincewa aurenta,yana
tunanin yayi amfani da shawarar abokansa kawai.

Cikin iya duniyanci da gogewa sannu a hankali ta soma jan ra'ayinsa,sai ya


sakar mata ya zuba mata ido,cikin kaffa kaffa take lamuranta,don tasan halinshi
sarai bai daukar wargi,a hankali ta soma bude wata qofa daga cikin zuciyarsa,wanda
hakan ya sanya ya dan sakar mata kadan,a wannan bigiren sukayi aure.

Baki daya ta bata tsarinsa na yayi rainonta,abu guda ne ya dore ci gaba da


karatu da tayi,don itama tana masifar son karatu,tana son tayi karatun da zata zama
wata,watan da duniya zata dinga maganarta da kwatancenta,ta riqi karatunta da
masifar muhimmanci,tana ganin shine tsanin mataki na biyu da zai sanya ta zama wata
a duniya,bayan zamantowarta daya daga cikin iyalin PROFESSOR MUHAMMAD MUKHTAR
MUHAMMAD ADAM GOMBE.

Rayuwar gidan aurensu rayuwa ce irin wadda suka ga mazauna qasar


nayi,rayuwar 'yanci,kowa yana da right,har wani lokaci mace tafi namiji dama,saidai
a wannan bangaren mustaphan ya riqe kambunsa,yayi riqo da bahaushiyar al'ada,ya
bata damarta,saidai fa bata isa ta tsallake umarni qa'ida ko dokarsa ba,wannan
kadai take gani ya takura ta,shike bata mata rai,to amma ba komai bane a gunta
saboda masifaffen son da takewa mustaphan,tanaji a acikin ranta ko ummee da tayi
naqudarsa bata kama qafar son da takewa mustaphan ba.

Tsakaninta da mustapha ya biya mata buqatarta,ta aure kota kudi,taci sa'a


kuwa gwanin kyautatawa iyali ne,bata san cinsa ko shansa ba,batasan tsaftar muhalli
data tufafinsa ba,suna da kuku suna da mai share share suna da mai wanki da
guga,sam ita a rayuwarta ma baki dayanta bata taba shiga kitchen ba,shege ruwan
zafi saidai ta ganshi kawai,rayuwa ce irin ta banasaren mutum zallah suke
gudanarwa,shima bai damu ba,amma wani lokaci sai yayi mamaki idan yaje nijeria yaga
yadda su umme ke dawainiya da majinsu,basu duba tsufansa ko girmansa ko kuma yawan
ma'aikatan dake gidan,wanda duk abinda kake so daka fada ta cikin waya za'a gabatar
maka da shi,sai ya watsar tare da dora hakan kan mizanin banbancin al'ada da
dabi'a.

Yana tsaka da aikinsa wani babban asibitin kudi suka yi masa tayin aiki a
asibitinsu,ya duba yanayin asibitin yaga yayi masa,akwai nisa sosai tsakanin jahar
da suke da jahar da asibitin yake,hakan ya sanya ya duba gida mai kyau a can ya
siya,bedroom biyu falo sai kitchen ya koma can da aiki,yayin da ya bar su'ada a nan
tana ci gaba da karatunta,don cewa tayi ba zata bishi ba gaskiya taba tsaka da
karatunta,shima bai wani damu ba yayi tafiyarsa,saidai sam baida lokacin zuwa inda
suke,ita dince idan ta motsa mata zata kwashi kayanta ta bishi,tayi masa weekend ta
dawo taci gaba da sabgoginta.

Tafiya ta fara nisa,babu haihuwa wajen su'adah ba dalilinta,bata yi mamaki


ba,don tuni ta jima da fara hadiyar qwayoyin tsaida haihuwa tun satin farko na
aurensu,kusan tafi uwarta iya shege,don daga bisani ma zuwa tayi ita aka juyar da
mahaifar,don tace bata ga me zata ci da haihuwa ba,ita da iyayenta suna da arziqin
da basai ta nemi taimakon da ba,tunda dama don ya taimakeka kake haifarsa(a
tunaninta),sam mustaphan bai san da wannan badaqalar ba ko kadan,ya dauka kawai
Allah ne bai kawo ba,baya ga aikin da yakeyi yana kasuwanci sosai,wanda har yaso
yafi baabaa prof qashin arziqi,cikin qanqanin lokaci dukiyarsa tayi haukatar ban
mamaki,hakan ya sanyashi diban maqudan kudade ya zo nijeria,kowacce state din nan
da muke da ita ciki harda abujan ya danqara asibiti,wanda idan da na private ne sai
ka isa ma zaka iya zuwanshi,amma yace kyauta komai za'a dinga yi ciki,shi da kansa
idan ya samu lokaci yazo nijerian yana zabar states din da yake ga zai iya zuwa
ciki harda gombe wadda bai fashin zuwanta sabida tuna asali da tushe ya ziyarci a
asibitocin,ya karbi cases masu girma da asibitin ya samu ya zauna yaga marasa
lafiyan yayi musu abinda ya dace,asibitin abuja kuwa sati biyu yake yi yana ganin
marasa lafiya kowanne iri matuqar lalurar ta shafi mata,hakan ne ya sanya kaf fadin
najeria babu asibitoci mafiya inganci taimako da kula da marasa lafiya irin nasu
asibitocin,girmamawa ta musamman gwamnati ta yi masa saboda taimako da gudun mawar
da ya baiwa al'ummarsa.

Baya ga wannan ya gina gidan marayu,kano daya gombe daya abuja daya,gidan
marayu mafi girma da baiwa marayu tallafi da kulawa a nijeria,shike daukar nauyi da
dawainiyar komai nasu,yana daga can yana turo duk wani abun buqata nasu,ya sake
samun bunqasar arziqinsa ne lokacin da ya zuba hannun jarinsa cikin wani company
dake dubai wanda ke saqa nau'in dogayen riguna na maza da mata masu tsada da kuma
masu matsakaitan kudi,daga bisani masu hannyen jarin kowa yaso janye nasa,shi ya
biya kowa ya mallakin company,ya zauna tare da taimakon hamza,musaddiq lamin da
usman suka sake yiwa companyn garambawul ya sake tashi a aiki,suka sauya masa suna
wanda yake amfani da tambarin MM mustapha mukhtar,sai gashi ya zama company mai
daraja ta daya dake sarrafa dogayen rigunan dai nau'i daban daban,kaloli daban
daban,companyn na daya daga cikin zuciyar arziqin da ya mallaka.

Rayuwa ta yiwa su'adah dadi,sai yanzu take sake kallon irin gatan da mamanta
tayi mata na maqalewa tare da naqalta mata auren mustapha,tana jin dadi tana
alfahari ta juya a duniya tace itace matar MUHAMMAD EL-MUSTAPHA,wanda ya kasance
cikin jerin sahun farko na matasan shahararrun masu arziqin da nijeria ta mallaka.

Rayuwa ta yi masa kyau,burikansa suna dab da cika,wannan karon yana yawan


waiwayar nijeria,idan azumi ya kusa kamawa a nan zaizo yayi guda ashirin,goman
qarshe su wuce umra shi da duk wanda Allah tsaga da rabonsa ko wanda baabaan shima
ya biyawa,duk shekara bai dauke sunan ummensa babanshi da anty maamaa,sai autarsu
sumayyatul amirah,shike biya musu,bai yadda suyi amfani da kudinsu wajen biyawa
kansu ba saidai wanda suka ga dama cikin 'ya'ya dangi ko surukai,idan ta rayawa
su'adah tace zata bismillah,idan kuma 'yan abun basa kusa taqi zuwa,wani lokaci da
taje can ta gwammace ta siyawa kanta da qawayenta tikiti na maquden kudade su tafi
kallon wani wasan a can wani shahararren gun kallon wasa duk inda yake a duniya
saidai idan ba'a ginashi ba,hakanne ya sanya take matuqar qawance da qasar
DUBAI,daga bisani Allah ya hukunta mustaphan aikinsa ya dawo dubai din,hakan ya
masa dadi saboda yayi masa kusa da company dinsa,duk da dama bai da damuwa yana da
abokai masu kama da 'yan uwa dake kula da shi,kasancewar dukkansu basu kai budin
mustaphan ba,sai dubai ta sake zamewa su'ad din gida,tana iya baro karatunta ta
taho dubai din takanas kallon film ko wani wasan,daga nan ta shargalle agun
mustaphan idan taga dama ta wuce,hakan ya sanya karatun nata ke kwan gaba kwan
baya,har yau yaqi ya qare.

Sukan dawo daga umra ranar sallar,daga nan idan baijin gajiya zai sake hawa
jirgi a washegari ya taho rano wajen kakanninsa,da shi ake hawan sallah,abun na
qayatar da shi,kusan tawagarsa daban take,duk sanda zai wuce sai ya ja hankalin
mutane saboda kwalliyarsu daban take,bayan ya gama hawan sallah sannan ya dawo ya
koma kan ayyukanshi,haka rayuwarsa take,kusan baida wani lokaci na banza a
rayuwarsa,duk daqiqa daya mai amfani ce a wajensa,yana tafiyar da ita wajen
ayyukanshi,hakan bai damu su'adah na wai bata samu cikakkiyar kulawa ba,arziqi
dukiya da rayuwa mai aji da tsada take buri kuma ta samu,buqata ce idan ta taso
mata duk inda yake zata siyi ticket ta bishi ta fansheta ta dawo.

Hakanne yasa a hankali qannensa mata suka fara lura da irin rayuwar da
yayansu yake,rayuwa ce mai kama data gauro,bai da wata mace a gefansa da zai dafa
ta aduk sanda wani abu ya taso masa na gaggawa,bashi da wata mace dake tare da shi
kullu yaumin da zata tsara masa lamuransa,lokutansa da rayuwarsa,ko da yaushe yana
cikin aiki,aiki dai,shi yana gabas kasuwanci da aiki matarsa tana yamma karatu,sam
baida wani family da zai nuna nashi kamar yadda sauran 'yan uwansa ke da shi.

Misali: babban wansu adam a yanzu haka yana da matan aure biyu,ta farko
na'imah Allah bai bata haihuwa ba ya sake aure ya auri fahriyya,yanzun haka yana fa
yara hudu,biyu maza biyu mata,yana aiki a legos cikin shima nashi company na qashin
kansa,yana zuwa gida da su baki daya idan ya faru ko kuma daya tazo a bar daya a
can,qanwarsa farida tayi aure,tana da yara uku,mai bi mata huda itama tayi aure
yaranta biyu,mahmoud ya kammala karatunsa,yana juya dukiyar baabaa prof shi da dan
uwansa usama,baaban baya komai sai kula da gidan gonan sulensa,har yau sule yana
ranshi yana saka ran haduwarsu kafin mutuwa da ruski dayansu,gidan gonan da zuwa
lokacin yayi rassa jahohi daban daban har nan abujar,duk da cewa usama akwai sauran
nauyin karatu a kansa da bai kammala ba,amma daga can inda yake yana
kasuwancin,thailand ne,shi da mahmoud din ke shigo da kayan su rarrabawa 'yan
kasuwa,kowannensu ya fidda macen aure,lokaci kawai ake jira,sosai baabaa yaga
alfanun yiwa yaran nasa sashensu,don ya zame musu tamkar mahada ko masauki duk
sanda suka baro wajajensu kowa nada bangarensa da zaya sauka cikin gidan kusa da
babansu,akan ga kowa a gida akai akai amma ganin mustapha yakan zama aiki,balle
madam din nasa,wadda lokacin bikin sallah ne take biyoshi don ta san cewa gidan
nasu kan kasance cikin baqi 'yammata da samari,takan biyoshi ne ta kasa ta
tsare,abinda har yau bata sani ba kenan halayyar mijinta,itace shaida ta farko da
zata fadi kan mustapha baida idanuwan kallon mata baki daya,amma ita sai take ganin
hakan isarta ce tasa har yau ita kadai yake gani,ta sani cewa mustaphan nata irin
mazan nan ne dake tsada,mazan da mata ke marmarin samu,ba wai saboda tsurar kyau
kawai ba,a'ah,kwarjini haiba kamala da cikar zati da halitta,ita kanta ta tabbata
Allah ne kawai ya kashe ya bata,tana sane da yadda ake farautar mustaphan,kama daga
yammata kyawawa masu taqama da kyau da arziqi irin nata ko fiye da natan ma,zuwa
manyan hajiyoyi masu juya naira,abun yakan bashi mamaki ganin yadda mata ke
farautar d'a namiji,yakan jima yana jinjina lamarin,wasu na roqon aure ya
hadasu,yayin da wasu ke roqo ko da harkar banza yazo suyi,son so ace yadda haduwar
mustaphan take baida komai,da sun yaudareshi koda da dukiya ce,saidai kash,sai suka
sameshi da arziqin da zai iya daukar nauyin danginsu ma baki daya.

Sirrin samuwar nasararsa ta ta'allaqa ne ga biyayya da tsananin kyautatawa


iyaye,bai iya tsallake umarninsu,uwa uba kuma tausayi da taimako.

Wannan shine familyn baabaa prof.

TOFA ADDU'RKU TACI,YAUMA NA KUMA KO?


*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽

✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

6⃣6⃣
*Bismillahir rahmanir rahim*

*Allah s w t yana cewa*

*HAQIQA SAI NA CIKA JAHANNAMA DA MUTANE DA ALJANU BAKI DAYA*

*Ya Allah ka yi mana tsari,ka suturta mu*

__________________________________

     "Wannan shine cikakken tarihin familyn baabaa sumayya,na tabbata zuwa yanzu
kin fahimci komai" murmushi sumayyan keyi tana gyada kai,sosai labarin asalin
zuriyyar ya burgeta ya qayatar da ita,very interesting,ta tsinci darussan masu yawa
a ciki,sunyi gadon karamci mutunci da halacci,qasan ranta take raya amma shi kam
bata san inda ya tsinto nashi halayyar ba,tana masa duban mutumin da bai girmama
mutuntaka ta dan adam,mutum mara saurin fahimta da dogon tsinkaye da bada hanzari
"Wa kenan"ta tsinci muryar anty dije na tambayarta
"Na'am"sumayya ta waiwayo da hanzari tana tambayarta,don bata tsammaci da ita take
ba
"Idan na canka dai dai mustapha kike wa wannan yankan hanzarin ko?" Da sauri ta
kada kai
"Ko kadan,me kika ji nace?" Murmushi antyn tayi ganin tana son musanta mata,cikin
sigar tsokana tace
"Kiyi dai a hankali,kada kema ki fada tarkonshi,naga ba wuya 'yammata sun zurma
cikin komarsa" wata matsananciyar faduwa gabanta yayi,kai ta soma kadawa
"Allah ya sawwaqe anty,ya rufamin asiri duniya da lahira,yanzu kyamin wannan fatan
haba anty?,na kai su'adah ina,baya ga haka ma wallahi baiyimin ba ko kadan,banga
abun burgewar ba anan wajen" dariya antyn tayi sosai har su laila dake sit din gaba
suka waiwayo suna dubanta sai data ce su juya
"Dukka yadda akayi kallon tsoro kika yi masa,kece mutum ta farko da naji kin ambaci
haka,ko minal dake da qarancin shekaru cemin take,mami uncle man yana da kyau kamar
na 'yan india,ta yaya ma zaki gane shi bayan kallon mukhtar kika yi masa ba ainihin
kamarsa kika gani ba,kuma ma meye na saurin rantsuwar baiyi miki ba?,kika san inda
rana zata fadi?"
"A inda ta saba faduwa mana anty,komai kyansa bazan gane ba anty daga kan mukhtar
an gama namiji" ta qarashe zancan fuskarta na nuna rauni da karaya da zuciyarta
tayi,hakan ya sanya antyn yin shiru,yayin da itama tayi shirun tana maida numfashi
tare da hadiye yawu da qyar.

        Kai ta girgiza bayan ta gama wassafa ta yaya zata zauna zaman aure da wani
bayan mukhtar din,sam,ji take ba zata iya ba,babu wannan mafarkin cikin
rayuwarta,kamar soyayyar da take nuna masa bata cika ba kenan.

        Cikin hukuncin Allah suka isa qasar lafiya,tun daga airphort sumayya ta
soma gane banbanci baro baro da tata qasar,haka tayi ta kalle kalle sanda taxi ke
dauke da su zuwa masaukinsu,sai ta samu kanta da yiwa qasarta addu'a tare da fatan
samun ci gaba kamar wannan qasar.

         Da suka isa a gajiye suke,gida ne wanda ke dauke da falo guda daya,sai


kitchen,bedroom uku,kowanne da manne da toilet,sallolinsu kawai suka rama kowa ya
kama makwancinsa,kusan ita ce qarshen bacci a gidan,ta jima tana juyi kan
gadon,hakanan take da tsananin baqunta,duk sanda ta sauya muhallin data saba da shi
tana dadewa kafin bacci ya dauketa.

       Tunda suka je uncle farouq bai zauna ba,yana ta zirga zirga kan abinda ya
kawoshi tare da yi musu siyayyar abubuwan da zasu buqata na gida,sai da suka ci
sati guda cur kafin komai ya daidaita,ya miqa laila da khalipha wata makaranta
wadda ke nan cikin unguwar,yayin da ya samawa sumayya wata center ta manya dake
karantar da su dukkan wasu karatuttuka irin na 'yan secondry tun daga matakin farko
cikin shekara guda su baka certificate dinka,itama babu nisa tsakaninsu,ko a qafa
zaka iya zuwa,idan kana da buqata kuma kana fita bus zata zo ta daukeka ta qarasa
da kai,da fari sumayyan ta tsure,tsoro take ji,tana tunanin ta yadda zata dinga
zuwa wajen ita daya,ta zauna cikin baqin fuska,fararen fata,wadanda akwai banbancin
addini harshe da al'ada tsakaninsu,kamar tayi qwalla saboda tsoro,anty dije ta
dinga tuntsira mata dariya
"To ko ni zan dinga rakaki?" Ta zolayeta
"Dole fa ki saki jikinki sumayya,nan qasar babu ruwan wani da wani ce,kowa abinda
ya kawoshi shi yakeyi,ki zama mai budadden kai,so nake a kasa ganeki duk sanda muka
koma gida" da irin wadan nan kalaman ta qarfafi gwiwarta.

       Ranar farko gabanta na dukan uku uku  haka taje,tayi tsurutsuru cikin
ajin,sam bata fahimtar me suke fadi bata fahimtar turancinsu,a wani hade yake bare
ta iya tsintar abinda zata iya tsinta din,tana nan zaune tsuru taji an dafa ta,ta
waiwaya tana kallonta
"Sannu,ke baquwa ce ko?" Sai ta sake kallonta sosai,baqar fata ce 'yar uwarta wadda
a qalla zasuyi shekaru daya,amsa mata tayi,fuskarta sake ta nemi wajen zama kusa da
sumayyan tana gabatar mata da kanta,kusan ita tayata zama har aka tashi suka taho
tare,ashe basu da nisa saboda haka ta samu abokiyar tafiya tare suka taho,sunanta
zulaiha ta sanar mata,itama baquwa ce a qasar bata kai shekara guda da zuwa ba.

       Cikin satittika suka soma sabawa da zulaihan,anan take gaya mata dan uwan
mahaifiyarta ke ruqonta,mamanta na aure ne a kano qauyen sumaila,itace autarsu,tana
da shekara sha takwas mahaifiyar tata ta rasu,babanta na son yi mata auren
dole,yayan mamanta shi yaji labari yazo ya dauketa,ya taho nan da ita inda yake
sana'ar drivern taxi,da yake qasa ce ta neman arziqi,jama'armu da yawa musamman
daga qasashe na afirka kan tafi neman kudi irin wadan nan qasashe,idan zamanta ya
karbeka duk sana'ar da kake sai kaga albarka cikin arziqinka,sam ba zaka ce yana
tuqa taxi ba anan musamman idan yazo gida nijeria,matarsa daya dansu daya.

      Akwai banbanci tsakanin sumayya da zulaiha,zulaihan ta fita wayewa da gogewa


qwarai,idan ka ganta ba zakayi tsammanin ga daga inda ta fito ba,mutumce mai son
jama'a da faran faran,hakan ya sanya take da qawaye sosai,sai a lokacinne sumayyan
tasan alfanun qawa da dadinta,musamman idan ka hadu da mai kyakkyawar halayya irin
ta zulaiha mai sonka da zuciya diya,da fari sumayyan ta fara tababa kan yadda
zatayi shiga ta fita ba irin wadda ta saba ba,zulaihan ita ta karbi kudi wajen anty
dije ta rakata ta siyo irin sutturun qasar,wanda zaki sanya basu fidda tsiraicinki
ba,wadanda zaka dace da zamani ba kuma tare da ka fidda tsiraicinka ka sabawa
al'adarka ba da addininka baki daya,sau tari idan ta shirya zata makaranta laila
kan tsokaneta
"Wallahi anty sumy kin canza cikin watanni kadan,bakiga yadda kayan nan ke miki
kyau ba,kamar ba sumyn malam ba,maman abdallah" anty dije na tayata
"Kin rigani a fili na rigaki a zuciya,ta koma wata qaramar baturiya,haskenki ne
kadai ba qarasa nasu ba,inaga ma kafin mu koma fa kim saje da su,kayan sun amsheki"
ita kanta ta sani amma sai ta saki dariya
"Ina wani kyau a kayan banasaren mutum anty,dadinta daya kawai basa fidda tsiraicin
mutum" duk da haka bata bar hijabinta ba,don babu sutura mafi daraja a gunta irin
hijabin,saidai duk sanda ta sanya kafin ta kai makarantar suna shan kallo ita fa
zulaiha,har zulaihan kan ce
"Ke kuwa sumayya ki haqura mana"
"Babu abinda zai rabani da hijabi sai mutuwa,sai randa likkafani ya zama sutura ta
ta qarshe" dariya zulaihan keyi
"Nima wasa nake miki".

       Wata baiwar qwaqwalwa Allah ya baiwa sumayyan,cikin wata biyu kacal


harshenta ya fara juyewa,su kansu uncle farouq da anty dije mamaki suke,ganin tana
ganewan ne ya sanya ya yanke shawarar sanyata wata makarantar dake training wa mata
zamantakewar rayuwa,ciki harda nau'in girke girke na kowacce qasa,duk randa zakuyi
girkin wata qasa tofa malamar 'yar asalin qasar ce,makarantar akwai tsada don ko
ita anty dije ta burgeta,ba don tayi tsada da yawa ba itama taso shiga,amma tunda
'yarta ta samu tace ba komai ta dinga koya mata.

        Watansu biyu da daddare uncle farouq ya kwashesu suka fice suga gari karon
farko tun bayan zuwa,don sam bai da lokacin zama a gida,awa biyu kacal sukayi suka
dawo saboda yana da aikin da zaiyi,suna gab da shiga gidan ya tuna dawowar qanin
abokinsa wanda gidansa ke daura da nasu,sunje ganin gida ne shi da matarsa sai
shekaran jiya suka dawo,baki dayansu suka nufi gidan don a gaisa,anty dije ta riga
data sansu dama,mai gidan na girmama uncle farouq kasancewarsa abokin yayansa.

       Gidane qarami kamar nasu,ga mamakin sumayya matar gida matashiya ce wadda
kusan zasuyi sa'anni da ita,yaronta daya itama wanda ya kusa shekara hudu,nafisa
asalin shuwa ce,tana aure da mijinta Dr auwal wanda qarin karatu ya kawoshi
qasar,shekararsu biyu kenan,shekara biyu ya rage musu su koma gida,shekararsu hudu
da aure,yaransu daya khalid wanda shima shekararsa hudun dai dai da shekarar
aurensu,saidai har yanzu bata qara wata haihuwar ba,ita din ma karatu take,yanzu
haka ta kusa hada degree dinta a fannin kasuwanci,abinda tafi sha'awa kenan tun
tana yarinya,kusan gado tayi,sabida kasuwanci shine sana'ar mahafinta .

        Ba qaramin dadi taji ba da ganin iyalan uncle farouq din,sai ta jita kamar
a gida nijeria,nan kusa da su dama babu wani dan nijeria,duk a tsakiyar fararen
fata 'yan asalin qasar take,tun kafin su tafi ganin sumayya sa'a take a gunta ta
dinga fadin
"Na samu 'yar uwa"
"Lallai kam,wannan,ai sai kinyi da gaske nafisa,bata da son mutane,ga shegen
qulafucin zaman gida,makaranta kadai ki fidda ta"
"Zamu saba ai ko sumayya,zaki zama qawata" ta fada tana kallonta,tashin farko taji
sumayyan tayi mata,nutsuwarta ta burgeta,murmushi sumayyan tayi
"Insha Allah maman khalid"
"Kamar gaske" cewar anty dije
"Haba umman khalipha kada ki sage mana gwiwa mana" inji nafisan.

        Sumayya kam ta gwada mata halinta,mutum ce mai yawan janye jiki ga baqin
mutane,musamman wanda ta fuskanci rayuwa bata ajesu bigire guda ba,bata son sanya
kanta inda zai zame mata matsala ko dana sani a gaba,ko kuma inda ya fi
qarfinta,qwarya tabi qwarya haka nata ra'ayin yake,wanda ta gada ne daga wajen
mahaifanta,mutane masu sanin daraja da qimar kansu,masu wadatar zuci da yakana,bata
manta nasihan mama da kullum take gaya musu,kaso duniya mutane su qika,ka qi duniya
mutane sai su soka,ka guji kwadayi,don shi din mabudin wahala ne,matuqar ka hau
motar kwadayi to la shakka babu inda za'a saukeka sai tashar wulaqanci,mutunci yafi
kudi,mutunci abu ne da idan ya zube qasa bai yiwuwa ka kwasheshi,mutunci abu ne da
kudi ko wata isa basu iya siyanshi,ire iren wadan nan maganganu ke mata
tasiri,takan zama mai tsantseni duk inda ta samu kanta,takan koma dora mutuncinta
gaban komai nata.

        Nafisa 'yar gata ce gaba da baya,itace auta a gidansu baya ga maza yayye da
take da su guda hudu,ita daya ce diya mace qwal daya tilo da iyayenta suka
haifa,hakan ya sanya take ganin gata,baya ga arziqi da Allah ya yiwa
mahaifanta,nafisa irin mutanan nan ne masu son jama'a,sakin fuska da jan mutane a
jiki,ko kadan ba zata taba yin wani aiki da zai nuna maka ga daga inda ta fito
ba,saidai idan kai idanuwanka suka kai ka gani,tunda taga sumayya taji tayi
mata,take jin ta samu 'yar uwar data rasa a baya,duk da cewa tana da tarin qawaye
amma sai taji sumayyan ta zame mata daban.

        Tun sumayyan na janye jikinta har ta saki jiki,nafisan ita ta soma koya
mata cumputer,ta naqalceta sosai,itama halayen nafisan sun burgeta,yadda ta
tsammaci halin masu kudi duka guda ne ashe ba haka abun yake ba,taga misali daga
kan nafisa da kuma amira,a yanzu haka amiran ko yaushe na kan kiran sumayyan,har
tana mamakin bata ganin kudin da take qonewa wajen kiran nata?,kullum nafisan na
kan qorafi da mitar yadda sumayya taki sakin jiki da ita bayan ta dauketa 'yar
uwa,kan hakan har tasowa sukayi takanas ita da mai gidanta suka zo suka kawowa
uncle farouq qarar sumayya wai bata sonsu,wanda tilas hakan ya sanya ta soma sakin
jiki da itan,shima mijin nata auwal da yake dan taya bera bari ne ya biye
mata,akwai tsantsar qauna shaquwa da fahimtar juna tsakaninsa da matarshi,qauna ce
mai yawa da tsafta tsakaninsu,wani lokaci idan sumayyan taje taga yadda ake zuba
soyayya kunya kamata take,takan ce bari naje gida,bazan iya wannan badalar taku
ba,dariya nafisa ke saki
"Wallahi sister(haka take ce mata)sai kin fini tsula tsiya,bari kiyi auren" kyabe
baki sumayya keyi
"Wane aure,ai mu mun bar muku shi,mu da shi sai a qiyama" kalaman da sun jima suna
daurewa nafisa kai,ga tsammaninta sumayyan budurwa ce bata taba aure ba,sau tayi
yunqurin tambayarta sai kuna taja bakinta ta tsuke,ba kasafai take son yiwa mutum
shishshigi cikin lamuransa ba,randa taga sumayyan na waya da abdallah a ranar ta
kasa daure tarin tambayoyinta
"Ke wallahi baki isa ba,kullum ki sani a duhu ki gudu,to yau kam sai kin gayan wace
ke" nafisan ta fada cikin yin kicin kicin,dariya tayi mata
"Wace kuwa ni din bayan sumayyan da kika sani" sakinta nafisan tayi tayi baya ta
zauna
"Shikenan tunda haka kika ce,na fuskanci baki daukeni yadda ni na daukeki ba,inda
kin daukeni yadda na daukeki da ba zaki boyen komai dangane da ke ba,tunda dan uwa
bai boyewa dan uwansa sirrinsa,naga har shawara nake dake sumayya kuma ina ganin
haske cikin dukkanin shawarar da kika bani" shiru tayi ganin yadda fuskan nafisan
ta nuna rashin jin dadi qarara,babu shakka dukkan wata qauna ta fisabilillahi
nafisan ta nuna mata,bata shayi ko shakkar yin kowacce shawara da ita,ajiyar zuciya
ta saki
"Shikenam kiyi haquri mom khalid,yanzu ki bari naje gida na yiwa anty abincin dare
kinga bata nan sun fita da uncle,amma na miki alqawarin idan na kammala zan dawo na
baki labari na" sake hade rai tayi don ta nuna mata gaskiyan abinda take fada
"Na amince saidai da sharadin idan kinzo nan gidan zaki kwana,tunda kin sani yau
dadyn khalid bai gida kwanan makaranta zaiyi" dariya sumayyan ta bushe da ita ganin
yadda ta hade rai tana mata muzurai kamar wadda ta hadiyi kunama
"Idan anty ta barni zan kwana"
"Zata ma barki saidai baki so ba" bata qara cewa komai ba ta miqawa khalid hannu
dake kallonta,jira dama kawai yake tace su taho,wani shaquwa sukayi sosai da
yaron,ganinsa take kamar abdallanta,ta sabi khalid din suka fice nafisa na binsu da
kallo,murmushi ta saki tana jin dadi,jin sumayya take kamar ciki daya suka
fito,Allah shike hada qauna da soyayya a tsakanin mutane har ma da jinsin
dabbobi,haduwar jini wani abu ne na daban daga Allah.

      Tana zaune kan sofar dake dakin baccin nafisan sanye da nata kayan bacci
cotton masu kauri riga da wando wadatattu,khalid na saman cinyarta yayi
bacci,hannunta na saman sumar kanshi tana shafawa don bai jima da yin baccin
ba,lokaci lokaci takan daga kai ta dubi nafisa dake tsaye gaban madubi tana ta
faman shafe shafe da goge goge bayan fitowarta daga wanka,mamaki duka ya cikata
bacci akewa wannan hidima haka,gaskiya mana ko yaushe fatar nafisan kamar ta dan
jariri,duk da fara bace choculet ce,har haqurin sumayyan ya qare ta tanka
"Wai duka wannan wankan naki meye amfaninshi bayab wanda ake mawa baya nan mrs
auwal kamar zaki sauya fata?" Murmushu tayi tare da ajiye body mist da ta fesa ta
dubi sumayyan
"Au sai noor yana nan sannan zanyi haka,ai ya riga da ya zame min al'ada ta"
"To ai saiki bada himma,nikam na fara jin bacci,ina jin labarin nan bai yiwuwa sai
gobe" ta fada tana gyarawa khalid kwanciya saman gado,da sauri ta zura 'yar saman
rigar baccin nata ta qaraso inda sumayyan take itama ta haye gadon tana cewa
"Sorry,na kammala,kema dab kike daki fara wannan sanaben ai" baki ta kama
"Niii,rufan asiri,ku din dai sai kuyita yi,haka naga laila ma 'yar qwailarta da ita
ta fara daukan course" dariya nafisa tayi
"Wallahi da gaske nake,jiya na hau internet,naga D&G sunyo sabbin mai na gyaran
fatar fararen mata,set ne harfa perfume,sure,da subulunshi,na riga ma da na siya
miki,jiran isowarsa kawai zamuyi,a yadda suka ce gobe zasu kawo min" shiru tayi
tana saurarenta,wannan wace irin qauna nafisan ke mata haka?,daga ganin abu babu
wanda ta tuna sai ita din?
"Am ready fa,ke nake jira" ta katsewa sumayyan tunani tana dubanta.

       Gyara zamanta tayi bayan ta jingina jikinta da bango,a hankali ta soma


warware mata wace ce ita,babu abinda ta boye mata,sumayya kuka nafisa kuka,babu
wanda zai rarrashi wani,bala'in tausayin sumayyan ya kama zuciyar nafisa,yayin da
sumayya ta tsokano wani danqararren tabo da dama har yau bai ida warkewa ba,janyo
sumayya tayi ta kifa kanta saman cinyar nafisan tana ci gaba da kukan tana bubbuga
bayan itama tana tayata ba tare da ta tsaidata ba,cikin zuciyarta taba cike fal da
mamakin irin rayuwar da sumayya tayi,bata taba hasashen zata iya yin rayuwa irin
wannan ba,shi qunci da matsin rayuwa gami da QADDARA hadi da JARRABAWA kenan babu
ruwansu da girma ko qanqantar shekaru?.

Sai da zuciyarta ta samu salama sannan nafisa ta soma magana


"Ashe akwai irin wannan rayuwar a duniya?,rayuwar da mutum mai kimanin shekaru
kwatankwacin nawa zaya fuskanceta da tsanani har kamar haka?,na jinjina miki
sumayya,Allah ne kadai yasan me ya tanadarwa rayuwarki,irin wannan yarda da qaddara
da karbarta hannu bibbiyu bau tashi a banza,Allah ya jiqan mukhtar ya raya mana
abdallah,kici gaba da haquri,amma kada ki sake hasashen ba zaki sake yin aure ko
jin dadin rayuwarki ba,kin sani kowanne bawa da yadda Allah ya tsara masa zai
rayu,dole kowa ya rayu bisa tsari da doron da mahalicci ya QADDARA,kici gaba da
addu'a,zan tayaki da yardar mai duka,yayi miki zabin kyakkyawar rayuwa,ya cire
dukkan qunci da damuwa da kika taba tsintar zuciyarki a ciki",ta jima tana fidda
hawaye masu dumi wadanda suka dinga wanko zafi da radadin dake cikin zuciyarta
maganganu ta dinga bata masu kwantar da hankali har ta samu nutsuwa cikin
zuciyarta.

Washe gari ta tashi fuskarta ta dan tasa saboda kukan data raba dare jiya
tana yi,baki daya nafisa sai ta damu tana ganin kaman laifinta ne,murmushi sumayyan
ta dinga tana girgiza kai tana qoqarin nuna mata ba laifinta bane,dole ne ga duk
mutumin da yake da miki cikin rayuwarsa ya koka duk sanda wannan ciwon ya motsa.
*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

6⃣7⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

Allah madaukaki yana cewa

*duk wanda ya sallamawa Allah dukkan lamuransa alhali yana mai kyautatawa haqiqa
yayi ruqo da igiya qaqqarfa wanda bata tsinkewa(yankewa/rabewa)*

_____________________________________

        Wuni nafisa tayi ta kasa sukuni da tausayin sumayya,a haka auwal ya dawo ya
taddata,baki daya wani qaunarta na sake shigarta,haqiqa bata yi zaben tumun dare na
aminiyar qwarai ba.

         Washegari da kanta taje gidan anty dije dauke da ledar mayuka da turarukan
data siya matan,dariya sumayyan ta dinga tana kallon tarkacen kayan,ko ba'a fada
mata ba tasan cewa sunfi qarfin mai rangwamen gata irinta,saboda zuwa yanzu kanta
ya soma budewa,tana iya gane abu mai tsada,balle ta san nafisan sarai,komai nata
designer ne,kuma komai nata a set dinsa take amfani da shi
"Wai kina nufin ni kike so na dinga amfani da wannan kayan?"
"Qwarai kuwa da wace?" Kai ta kada tana dariya
"So nake naga kin sauya sis,so nake naga kin fara sabuwar rayuwa" kai taci gaba da
kadawa tana dubanta,kafin tace wani abu anty dije ta shigo dakin,kayan ta dinga
dauka tana dubawa tana dariya
"Allah yasa a baki hadin kai"
"Idan ma taqi ina kallon fatarta zan gane,don sun tabbatar min suna da kyau,suna
gyara fararen mata" itama ta fadi tana dariyan,godiya anty dije ta taya sumayya,sun
jima suna hira kafin nafisan ta koma gida don dora abincin dare,don auwal baison
take away idan ba lalura ba ta kama.

        Anty dije ke jinjina tsadar kayan


"Bansan ya zata kaya ba idan kayan suka karbeki ba,suna da kyau amma akwai tsada"
cewar anty dijen.

Kiran wayar daya shigo wayar sumayya ita ta katse hirar da sukeyi
din,fuskar ta washe baki bude take fadin
"Amiran baabaa ce anty"
"Kice ina gaidata" inji anty dije tana miqewa don ficewa daga dakin ta fara jiyo
hayaniyar minal da khalipha da alama rigima suke shi da ita
"Autan baabaa(haka take kiranta idan taso tsokanarta)"
"Mutanen uk,wai nikam yaushe zaku dawo,nifa na gaji wlh daga gida sai makaranta,ni
daya kamar mayya,idan bakuyi wasa ba fa zaku ganni wlh na biyo sahu" dariya sumayya
ta dinga yi ganij dududu watansu nawa ma da tahowa
"Kamar yaune fa zaki ga mun dawo din,yi haquri takwara" dariya sukayi baki daya
sannan suka soma taba hira,amiran na bata labarin abubuwan da suka faru bayan
tafiyarsu
"Amiran umman khalipha,baabaa fa ya karbi kudin aurena har da sa rana watanni shida
masu zuwa dai dai sanda zan kammala degree dina" ta fada cikin nuna farinciki,cikn
zumudi sumayyan tace
"Kai haba dai takwara"
"Wallahi amira,amma nikam tsoron yin auren nan nakeji takwara,duk da saifullahi na
matuqar sona da qaunata,hakanan na amince da tarbiyya da halayyarsa" gefe daya na
zuciyar sumayya itama jimamin da take mata kenan,saidai ba lallai abinda ya samu
dan uwanka kaima ya sameka ba,kowa da tashi kalar qaddarar,bare amiran ita ba mai
mata zata aura ba,ita daya ce a gunsa
"Meye wani abun tsoro?misali su ummee da sukayi auren su wani abu kika ga ya
samesu?" Kai ta kada kamar tana kusa da ita
"Um um,kawai banson rabuwa ne da gida,ina son family na"
"Ba shakka familynki abunda zaka yi marmari da begensu ne idan ka barsu,duk wanda
ya kalli yadda kuke son juna ba zaiyi mamakin haka ba" sumayya ta zantawa
ranta,amma afili sai ta bagarar da zancan da nuna rashun muhimmancinsa
"Duk mace 'yar wani gidan ce,ko su su ummeen ce miki akayi gidanku ne gidansu,suna
nasu familyn fa suka baro ko?" Sai amiran ta qyalqyale da dariya
"Kinji umme tace ah to,ashe taji me kika fadi,kinsan abinda anty maamaa ta gama
gayan kenan dazu" itama dariyan tayi,ta shiga tsokanar amiran
"Kawai kice mu fara shirin baki,ina ga ba zamu wuce wata guda da dawowa ba zamu
shiga hidima,ummm,bari na gayawa anty dije mu fara taru"
"Ahto,don kune amarori,shi yasa na dage saidai asanya wata shidan,daa qasa da haka
za'a saka,nasan kafin sannan kun dawo"ci gaba da tsokanarta sumayya tayi a haka
suka rabu cikin barkwanci.

Bayan ta aje wayar ta samu anty dije na sauyawa minal kaya da alamu bata
wadancan tayi don ba'a jima da yi mata wanka ba
" nikam saura qiris na sauya qawa,wannan qawa tawa qazamiya ce"sumayya tayu maganar
tana duban minal tare da yamutse fuska
"Yadai fi wallahi,duk gidan nan babu mai bata kaya kamar nata"inji anty dije,fuska
ta kyabe tana shirin sakin kuka
" na daina anty,wayyo Allah na"ta fada tana bubbuga qafafunta zata hau bori
"To shikenan,ya isa,ai ke qawata ce ta amana,babu mai rabamu,uwata ce fa ta kaina"
sai ta soma dariya tana tsallen murna sumayya na dubabta tana murmushi,duk yaron
data gani tuna mata yake da abdallahnta,dauke kanta tayi ta maida ga anty dije
"Anty an sanya bikin amira fa,wata shida mai zuwa" sakin maballin da take ballewa
minal tayi dama ta kusa gamawa ta juyo tana duban sumayya
"Tabdijan,kice akwai gangami kenan,bikin auta guda?,bikin amira ni 'yasu?" Antyn ta
fada cikin jinjina lamarin,kai sumayya ta gyafa tana nade qafafunta saman gado tana
murmushi
"Jar uba,kice abuja zata motsa,familyn baabaa prof za'ayi bikin da aka jima ba'ayi
kamarsa ba,to ai ina ga da na su mahmoud za'a hada tunda suma wata bakwai ne inaga
yayi saura cikin ranar auren da aka sanya musu ko,Allah ya nuna mana,sai mu fara
shiri tun yanzu,sumayya kuna da biki" inji anty tana murmushu gami da jinjina kai
"Wallahi anty haka tace,ni kam mai zan iya cikin hidimar,ni da ban taba bikin qawa
ba?"
"Aikuwa dole ki ware ayi komai da ke,yadda amira ta daukeki kada kuce zaki watsa
mata qasa a ido,nasan halayyarki sarai" dariya sumayya tayi ganin yadda antyn ta
camfata tana kwantar da kanta saman filo
"Allah ya bamu iko to anty" kan ta gama rufe bakinta kira ya shigo wayarta,lambar
alqasim ne,tana mamaki da har yau bai rabu da ita ba,bayan ta zayyana masa ita din
bazawara ce har da yaro,sai ta latse wayar ta kasheta baki daya tana jan qaramin
tsaki ta gyara kwanciyarta abunta,ita yanzun babu mai daga mata hankali,ko lukman
idan ya kira sai taga damar dagawa,darajar yaranshi dake sonta kawai take
dubawa,badur rahman je kadai ke da wannan qinar na daga kiransa a duk yayin da ya
kira din.

        Cikin qanqanin lokaci da fara amfaninta da mayukan da sabulan taga


banbanci,ita a karan kanta taga sauyi,wani laushi da santsi fatarta ke sake yi
tamkar wadda ke zuwa gyaran jiki,baki daya qamshin jikinta ya sauya zuwa wani
qamshi na musamman ma daban wanda ya kama kayanta sabida turaren da take amfani da
shi set na man da sabulun,cikin watannin da basu gaza biyu ba sumayya ta sake
komawa wata ta daban,komai nata ya sauya,sau tari laila na tononta tana cewa
"Wlh anty sumayya kin koma 'yar gayu" hakan ya yiwa nafisa dadi qwarai a ranta,bisa
dukkan alamu zata cimma qudurinta cikin sauqi kan sumayyan,tana son sumayyan ta
zama wani sashe na familynsu,dukkanin halayyarta sun mata babu na yarwa.

*******     *******    ********

         Yau da gobe kayan Allah,sannu a hankali kwanaki ke mirginawa suna wawasar


kwanukanmu a duniya,da kuma kwanakin dukkan wani abu da muka sanya masa lokaci,zuwa
yanzu su sumayyan na da watanni takwas cikin qasar ta uk,ba qaramin karba qasar ta
yiwa sumayyan ba,bugu da qari kuma ga nafisa daga gefe data kafe kai da fata zata
sauya sumayyan malam din zuwa wata sumayyan ta daban,sumayyan uk,qudirinta kuwa ya
karbu,a yanzu idan kaga sumayyan zaka sha mamaki,komai nata ya sauya,wani irin kyau
da da can yake boye a yanzu ya soma bayyana kansa,hutu jin dadi da kwanciyar
hankali suma na bada tasu gudun mawar,hatta da anty dije kan kalleta mafi yawancin
lokuta,dadi take ji cikin ranta da ta sanadiyyarta sumayyan ta soma samun canjin
rayuwa,ashe da can damuwa rashin kwanciyar hanakali da tension ita ta tasamma
kassara sumayyan da gurgunta tunaninta,a yanzun kai baka ce sumayya bace wadda ta
taba aure,'yar shekara ashirin da biyu har da yaro ba,sai kayi zaton tana cikin
shekararta ta sha shida ne,tun da can Allah ya bata sanyin murya nutsuwa da iya
magana,sai abun ya sake zame mata ado,zakayi zaton daga wani babban gida ta fito.

       Gefe daya karatun ta ya kankama haiqan,turanci ba damuwarta bane a yanzu


bare hausa,mai gaba dayan larabci dama ya jima da zama kan harshenta tun tana
qanqanuwarta,tana daya daga cikin zaqaquran ajinsu a yanzu,zaka yi mamakin yadda
harshenta ya karye,tana karbar karatunta da kyau,tuni wata daya baya ta kammala
makarantar koyon girki da mu'amalar yau da kullum,ta fita da cetificate mai kyau,a
yanzu kusan anty dije ta zama 'yar kallo ta fannin kitchen,kowacce rana da kalar
abincin qasar da sumayyan zata girka,uncle farouq da taya bera bari shike basu kudi
suje suyi siyayyan kayan da za'a buqata a ranar tunda shi bai sansu ba,laila ce
'yar rakiya,kai na rawa zata bita suje,zuwa yanzu ta sake tana iya zuwa gurare
wadanda ke kusa da su ba nisa can ba,idan kuma suka so yin nisan nafisa ce
jagora,zata debesu guri guri da yake ita din tamkar 'yar gari ce a garin,ranar haka
zasu wuni a waje,sau tari sumayya na noqewa saboda ganin yadda nafisan ke kisan
kudi idan sun fita amma taqi bata dama,duk abinda ta siyawa kanta sai ta saiwa
sumayyan duk tsadarshi,dole tayi surrender ta tabbatar Allah ne yayi wannan hadin
tsakaninsu.

*******     ********    *******


     Kamar ko yaushe yau ma tafe suke su shida,nafisa,sumayya,laila,khalipha,sai
minal da kuma khalid dake riqe a hannu,ganyayyakin abinci suka sayo daga can suka
wuce suka sha coffe a wani gun shan coffee dake daura da gun,zasu hau bus nafisa ta
hana,a qasa suka dinga takowa tana nuna musu gurare tana musu bayani,sosai yanayin
ya yiwa sumayya dadi qwarai,murmushi kawai ke tashi a fuskarta,sanye take da dubai
abaya wadda tayi mata cif a jiki,ja ce mai dan turuwa kadan,bata yi amfani da
mayafin rigar ba saboda yayi mata qanqanta,sai ta yafa wani medium vail dark blue
wanda ya lullube har kafadarta.

      Idan ka kalleta dole ta burgeka,murmushin dake tashi kan fuskarta kawai abun
sha'awa ne,kayan sun haskata matuqa,khalipha da minal da laila sunyi gaba abinsu
suna ta tsalle tsallensu laila na qoqarin saitasu,ita da nafisan ke ci gaba da
takawa a hankali suna hira tana bata labarai.

       Maganar da nafisan ta fada ta sanyata juyawa tana kallonta dariya ta kubce


mata,sam bata lura da gabanta ba ji tayi ta bangaji abu,taga taga tayi zata fadi
murya a sama taji ance
"Hey!" Tare da riqo hannunta,tashin farko ta gigice,abubuwa biyu cikin lokaci daya
suka hargitsa ta,walainiya idanuwanta suka shiga yi zuciyarta na bugawa,man
ne,mustapha,sanye cikin three pieces slim fit suit navy blue wadanda sukayi matuqar
yi masa kyau tare da fidda sigar kyawunsa,idanuwansa saye cikin sun glasses,ya
kafeta da tsinin idanuwanshi duk da bata iya hangosu fes amma tana ganin
alamunsu,jikinta ya soma rawa sanda ya saketa sai ta sake tafiya zata fadi nafisa
ta tarota tana fadin sunanta,tsaye yake qyam yana dubanta,duba mai dauke da bacin
rai,tuni baturen dake tare da shi ya kammala tsince wayoyinshi da suka zube qasa
yana masa sannu cikin harshen nasara,dauke idanuwanshi yayi ya maida kan wata
rantsatstsiyar baqar mota data faka a gabanshi,qaramin tsaki ya ja sannan ya juya
cikin takunshi ya nufi inda motar take,da alama dama ita yake jira,baturen ya mara
masa baya cikin hanzari ya bude masa mazaunin baya kafin shi kuma ya shiga gaba,jan
nafisa ta soma yi jiki na rawa tana waiwaye har suka shige motar suka tayar suka
bar wajen.

Waiwayowa tayi inda nafisa ke tsaye bayan ta cikata,sai ta tsinci nafisan na


kallonta
"Waye wannan sumayya?" Ta jefo mata tambayar ba tare da ta shirya ba,boyayyar
ajiyar zuciya ta saki gabanta na bugawa,hakanan Allah ya dora mata wani tsoronsa
"Nima ban sanshi ba" ta fada tana ci gaba da jan nafisan don su bar wajen,batasan
me zata ce mata din ba,saidai baki daya gwiwoyinta sun sare kamar an doke mata
su,kamar qafarta ba zata iya kaita gida ba
"Taya zaki ce baki san ko waye ba bayan na shinshino alamun sanayya tattare da ke?"
"Kiwa Allah kada ki qara tambayata,don ban sanshi din ba"
"Ala kyauta" nafisan ta fada ba tare data sake tambayar tata ba,haka suka isa gida
tamkar kurame.

Cikin sanyi jiki ranar baki daya ta wuni,girkin ma data fita ta sayo
ingredient din bata iya yinshi ba,ta cewa anty dije bata jin dadi,sai ta koma daki
ta kwanta kawai lamo,bata fadawa anty dije ga wanda ta gani,to tace mata me?,tace
taga wa?,meye hadinta da su da zata sanar mata haduwarsu?,ta tabbata su laila basu
ganshi ba tunda bata ji sunyi maganarsa ba.

******* ****** ********

Sannu sannu kwana nesa,yau da gobe kayan Allah,sai gasu sumayya sun fara
hada komatsansu waje guda,wasu suna aikowa da su nijeria wasu kuma suna faka su
waje daya,wata daya ne ya rage musu wa'adin zamansu a qasar ya qare,wato sati hudu
zuwa biyar masu zuwa zasu bar qasar,tuni nafisa ta soma qaguwa suma su koma gida,ta
fuskanci lallai idan su sumayyan suka barsu qasar sam ba zata ji dadin zama
ba,zulaiha ce abar tausayi,wadda Allah ne yasan ranar komawarsu,zata yi kewa ba
kadan ba,saidai tilas ta haqura.

Hutun sati guda uncle farouq suka samu,hakan ya sanya suka zauna sukayi
dukkanin lissafinsu na abinda zasu saya wanda zai musu amfani,ranar da daddare suka
shirya zuwa wani katafaren mall wanda ke saida dukkan wani abun buqata,kama daga
mai qaramin kudi zuwa mai babban kudi,duk wani abu na amfanin dan adam,sutura zuwa
abinci da abunsha suna saidawa a wajen,basa bude gurin sai qarfe shidda na magariba
har zuwa tsakiyar dare.

Uncle farouq ya kira ya buqaci taxi da zata kaisu ya bada adress dinsa,cikin
mintuna qalilan ta iso,shine zaune a gaba shi da minal,su kam suna baya,hira suke
sosai cikin motar,wanda ita bata ma san me suke cewa ba saboda tana amsa wayar
abdur rahman ne,bayan ta kammala ta maida wayar jaka,dubanta anty dije tayi cikin
salon tsokana
"Nafa lura kwanaki biyun nan ana dasawa da abdur rahman,ko yaushe cikin waya,ko dai
da shi za'ayi ne?" Kunya ta bata saboda uncle farouq dake cikin motar,sai ta kasa
magana ta saki murmushi kawai,dariya ya danyi yana daga gaban motar yace
"Allah dai ya zaba abinda yafi alkhairi kurum"
"Amin" cewar anty dije.

Ta kai kimanin aqalla minti ashirin tana nemansu cikin katafaren shagon bata
gansu ba,ta duba anty dije da uncle farouq babu su ba alamunsu,tuni ta soma
tsurewa,ta ajjiye kwandon dake hannunta ta soma laluben hanyar fita nan ma ta kasa
ganeta,qwalla ta cika idanuwanta jikinta ya soma rawa,ina yaran sukayi?,ina su anty
dijen suke?,idan ta rasasu ta yaya zata iya komawa gida?,wannan tunanin ya sanyata
qara sauri,data fita daga wannan bagaren saita fada wancan saidai ko qyallinsu bata
gani ba.

Wani irin burki ta taka wanda ba don tayi saurin dakatawa ba babu abinda
zai hana su yin karo da juna,dubanta yake kamar yadda take dubansa,kamar ko yaushe
fuskar nan a murtuke babu walwala,kai kace bai taba dariya ba a duniya,gabanta ya
shiga faduwa kamar kullum,ji take kawai tata ta qare,ta rasa da mutumin da zata
hadu sai da wannan?,kamar yadda al'adarsa take,saye yake da suit qirar company
dolce anda gabbana baqaqe,hannayensa saye cikin aljihunsa kai kace babu abinda yazo
siya,daga ita har shi babu wanda ya motsa,ita bata wuce ba tana kallonshu,yayin da
shi kuma ke duba turarukan dake jere reras yana karanta sunayensu daya bayan
daya,tuni hawayen da take adanawa suka soma samun hanya da zuciyarta ta raya mata
su anty dijen sun bace mata fa,wata qila ma sun bar mall din suna nemanta
suma,tattaro ragowar qarfin ta tayi da niyyar rabewa ta wuce don yana tsaye ne
tsakiyar hanyar,ya raba hanyar gida biyu.

Hannunta guda daya taji an riqo,wata zabura tayi ta waiwayo qirjinta kamar
zau fado,taushi da laushin tafin hannun nashi na ratsa jiki da jijiyoyin
jininta,bai ko dubeta ba ya soma jan hannun nata,bata da wani qwarin gwiwa da
qarfin da zata qwace,ko wacce gaba ta jikinta an zare mata laka,abu daya zuciyarta
ke raya mata,yau tata ta qare,don wannan mutumin babu alamu na imani ko tausayi
tattare da shi,Allah ne kadai yasan me zai aikata,hawayenta suka qaru tana biye da
shi tamkar raqumi da akala.

Wani farin ciki ya mamayeta saboda hango su anty dije da tayi su da yaran
bangaren kayan yara,a hankali ya zare hannunshi cikin nata tare da juyawa ya barta
a wajen,sai ta waiwaya tana duban yadda yaje tafiyarsa ba tare ko ya sake waiwayowa
ba
"Laaaaah,ga anty sumayya can,yaa mustapha ne ya kawota" cewar khalipha wanda shi
daya ta hangi isowarsu gun,tuni mustapha ya bace a gun,anty dije ta dago tana
dubanta,sai kuna tayi turus ganin hawaye fuskar sumayyan
"Lafiya?,ke kuma me aka yi miki?"
"Amma anty nayi tsammanin kun tafi fa,idan na bace nan gun wa zai maidani gida?"
Dariya ma ta baiwa anty dijen ganin yadda sabbin qwalla ke sake saukar mata
"Kina nufin har yau da sauranki sumayya?,ta yaya zamu taho da ke mu koma babu
ke?,bakiji sanda nake gaya miki kici gaba da siyayyarki ba zamu zo nan gun ki
samemu wajen biyan kudi?,to don Allah ya ma za'ayi ki bace wajen da duka ko ina
cctv camera,an fada miki nan irin nijeria ce?,ti waye ya rakoki?" Ta rufe maganar
tana dariyar wautar sumayyan ciki ciki,kafin ta amsa khalipha ya bata amsar
tambayar
"Hala yaganki kenan kina kuka kamar qaramin yaron da ya bata" laila sau ta sanya
dariya,harara sumayyan ta maka mata don kusan itace ta sanya bata ji sanda anty
dijen tace mata suna zuwa ba,isowar uncle farouq yana dariya ita ta tsaida dramer
da akeyi
"Tom,musty yace mu kula,ya lura yarinyar nan sakarai ce,kada ta janyo mana abinda
za'a kamamu kan mu bar qasar nan,kinsan su mai jan kunnuwa akwai kula da haqqin dan
adam" dariya suka sanya shi da anty dijen yayin da wani abu ya tsayama sumayya a
wuya,ita za'a kalla a cewa sakarya?,aikin banza ita tace ma ya kawota da zai gaya
mata magana,ita kadai ke masifarta cikin zuciya ta qulu ta cika tayi fam,siyayyar
da bata qara darawa nan da can ba sai anty dije ce ta qarasa zabar mata abinda taga
ya dace,gani take ko ya ta matsa zasu sake yin clashing da shi.

Sai da suka shiga mota sannan ta dubi anty dije,shaf ta manta cewa sunyi
zata bata kudin da baabaa ya bata randa zasu taho zata siyawa amira wani abun a
gift din biki
"Anty,banfa daukawa amira komai ba"
"To me za'a siya mata,su fa irinsu komai suna da shi,amma ki bari idan mun koma
gidan kwayi shawara da nafisa sai ki siya mata abinda ya dace"
"To" ta fada tana jingina da kujerar cikin mutuwar jiki hannayenta runguma a
qirjinta.

Da sukayi shawara da nafisan sai taga kawai tayi mata danginsu


humra,turaren wuta na daki kaya dana tsuguno,collucture tana ganin zasu
burge,shawara kam tayi mata,tasan amiran kuwa da jarabar son humra,akwai wani
company wadanda ke qera crystal kala kala masu azabar kyau,nafisan tayi oder din
kwalaben da sumayyan zata zuba kayan idan tayi,batasan da su ba sai kiranta nafisan
kawai tayi ta nuna mata bayn an kawo,kwalaben humra kadai saiti uku uku sai data
siya saiti bakwai kusan kwalaba ashirin da biyar,haka ta turaren wuta da wasu
dogaye da za'a zuba collucture,kwalaben kansu abun kallo ne,wani irin design aka yi
masu masu matuqar tafiya da hankali,kasa magana sumayya tayi,karamcin nafisa ya
girmi qwaqwalwarta,sai ta zauna akwai tana kallon nafisan ita kuma tana
murmushi,baki ta bude da niyyar hada kalmomin godiya sai tayi hanzarin tararta
"Kada kice komai,kada ki godemin,nima gudun mawata na baki ki baiwa qawarki,duk da
bamu taba haduwa da amira ba amma tana da kirki iya gaisawar da muke,kuma taci
darajanki sister", anty dije kanta rasa me zata ce tayi,sai albarka take sanya mata
tare da fatan dorewar zumuncinsu da addu'ar kade fitina,cikin kaya suka shirya
kwalaben yadda ba zasu fashe ba.

********* ****** ********


Randa zasu koma nijeria nafisa na tare da sh,ita da auwal suka suka rakasu har
airphort,jirgin dare zasu bi,batasan me ya sauya lokacin tashinsun ba,don da taji
uncke farouq na fadin jirgin safe ne,tuni sukayi sallama da zulaiha,har kuka sai
data yi,ji take kamar tabi sumayyan,to itama din nafisan tuni ta narkewa auwal ta
soma masa qwalla,khalid kuwa ba'a magana jiki duka ya mutu,ya fuskanci anty
sumayyan tafiya zata yi ta barsu,ai kam ashe kuka na gaba,sai da suja zo tafiya
auwal ne ya janyeta yana rarrashinta
"Is ok dear,muma fa nan da wata daya zamu koma keye ya rage ne?,wata dayan kwanaki
nawa ne?,haba momyn khalid,goge qwallar khalid na dubanki" da qyar ta tsaya sukayi
sallama auwal yayi dabarar dauke khalid sannan nafisan ta biyo bayansu.

Mamaki ne ya kama sumayya ganin su a VIP wannan karon,tasan dai ba'a VIP din
suka zo ba,sai tayi zaton ko daga gwamnatin tarayyar ne,abinda ta lura kuma da shi
shine iya su kadai ne,baki ta tabe don batasan meke faruwa ba ta fiddo wani littafi
da nafisan ta bata ta fara duba shafin da take,don son bata sha'awar yin hira
yau,kewar zulaiha da nafisa take,ba shakka sabo turken wawa,karatun ya soma yi mata
dadi,yayin da wani qamshi mai taushi ya dinga shiga hancinta,qamshin yayi mata,sai
ta lumshe ido tana jin yadda ke ratsa qofofin hancinta,sai tayi tsammanin wani abun
ne a cikin jirgin,lol
"Barka da dare uncle" taji su laila na fada,cikin mamakin yadda lailan mai shegen
rawar kai da surutu ke magana a kintse ya sanyata ajiye littafin ta dago kai da
niyyar tsokanarta,so tayi tace
"Allah ya nuna mana ma'aiki yau laila ke magana cikin nutsuwa irin haka?"sai
maganar ta maqale mata,zaune yake kujerar dake bayanta wadda ke daura da mazaunin
uncle farouq,magana suke qasa qasa da uncle farouq din,idanu suka hadu,da hanzari
ta juya ta maida idanuwanta mazaunin gabanta,qirjinta na bugawa da sauri,ta rasa
wannan wace iriyar masifa ce haka,ba dama ta ganshi yanayinta ya burkice,anya ma ba
maye bane wannan mutumin,sanye yake da fararen suit qal wadanda suka dace da
takalminsa,yayi kyau cika da wani irin kwarjini,bata san me ya shigo da shi jirgin
da zashi nijeria ba,idan bata manta ba anty dije ta gaya mata gun aikinsa na dubai
" matsa man sumayya,ina ta magana tun dazun kamar wata kurma"anty dije ta fada tana
tsaye kanta,jiki babu qwari ta matsa din anty dijen ta zauna tana bude zip din
jakarta tace
"Kun gaisa da mustapha ne?,wannan karon zashi nijeria ba lokacin zuwansa ba,nasan
baabaa zaiji dadi,dan gaban goshi zaizo,diyar ambassador din nijer anan ya dubawa
aikin da yayi mata a dubai,baban nata abikin baaba prof ne sun taba aiki tare"
kanta kawai ta kada ba tare data iya amsawa ba,bata ma ga mai ya hadata da wannan
sharhin ba,giyar qaunar ahalin baabaa ta kama su anty dijen sosai,ko da yake babu
abinda KARAMCI baya iya maida maka mutum ta raya a qasan zuciyarta
"Kinga muma yau mun dana,gamu a VIP,mustapha yayi abinda ya saba" ta fada tana
dariya tare da qoqarin kashe wayarta,duk maganar da anty dijen keyi bata
fahimtarta,zaune take kurum,ta rasa abinda yasa jikinta sam baison hada inuwa daya
da shi,ta tabbatar da cewa taqi jininsa ne tun ranar da ya yarfa ta gaban tarin
jama'a,har yanzu tana iya jin zafin abunda yayi mata,baka san waye mutum ba,bakasan
wanne yana yi yake ciki ba amma kayi masa haka amatsayinshi na dam adam
irinka?,itakam jin anty dije kawai da take yaba kyawun halayensa,eh,ta yadda da
mutunci da karamcin ahalinsu amma bata jin shi yana ciki.

Laila ta sake taimakawa wajen dagula lissafinta data nace da tabata kan sai
ta juyo taga abinda take nuna mata cikin laptop dinta
"Idan ba zaki iya kalla ke daya ba zan karbi abata kinji ko?" Hakan data gaya mata
shi ya sanya ta sarara mata.

Mintuna arba'in kowa ya nutsu a kujerarsa yana abinda zai fishsheshi,duk yadda
ta kai ga matse fitsarin da take ji amma yaqi sarara mata,ta fuskanci ya zame mata
dole tayi,ko kusa bata son tashi daga inda take,saboda matsawar zata shiga bandakin
tofa sai ta gifta ta kusa da su,a hankali ta waiwaya sai taga baki daya ya aza
hankalinsa ga system,hakan ya bata qwarin gwiwa ta miqe anty dije ta matsa mata ta
wuce,cikin sanda kamar wata barauniya haka ta wuce,baima san da wucewar wani a gun
ba har ta gama fitsarin ta dawo.

Daidai lokacin da yake magana da uncle farouq cikin nutsuwa,muryarsa ta


shiga dodon kunnuwanta,ya salam,muryar mukhtar take ji muraran cikin tashi
muryaf,ya ilahi wannan kamanceceniyar murya dame tayi kama?,ta tabbata abinda take
ji yana da nasaba da muryar mukhtar dinta wanda ko wanne lokaci yayi magana tuna
mata da shi yaje,ji take kamar shine a raye a kusa da ita,har marmari take taji ya
furta wani abu.

Dumi da taji yana ratsa rigarta da qarar fasgewar cup shi ya ankarar da ita
karo da tayi da daya daga cikin 'yammatan ma'aikatan dake kara kainam baiwa kowanne
passinger abinda yake da buqatar ci ko sha,baya tayi jikinta na rawa yayin da itama
budurwar tayi baya tana baiwa sumayyan haquri cikin harshen nasara,a qa'ida
sumayyan ke da laifi,saboda tayi qoqarin kauce mata amma sai data bugeta,iya tafi
da custumer nasu ya sanya take bata haquri tare da bata hanya ta wuce ko kuma ta
koma toilet ta wanke hadaddiyar doguwar rigar shadda dake jikinta wadda sabuwa ce
kar ranar ta soma sanyata,lemon green da aka yiwa adon orange,mayafin data nannada
saman kanta shima orange ne,ba tare da wani dogon tunani ba ta wuce zuwa mazauninta
sabida ta kasa tantance me ya kamata ma tayi.

Qarasawa tayi dauke farantin da pieces glasses din cup din tana baiwa
mustapha haqurin bari ta sake kawo masa wani,sai a sannan ya daga kansa daga abinda
yake yi din,kallon da yayi mata ya rudata,sai ta fara yi masa bayanin ta kawo ne
sukayi karo da madam ya zube,da hannu ya tsaidata yace taje kawai bai buqata,haquri
ta bashi sannan ta juya,ya fahimci me ya faru,don yana iya jiyi anty dije na
tambayar bata qone ko taji ciwo ba ko?,tsaki yaja qasan ranshi yana ayyana anya
tana da lafiyan qwaqwalwa kuwa,haduwarsu ta farko ya tuna,sannan ya gangaro
haduwarsu ta biyu,haduwarsu a mall da girmanta tana wani hawaye shabe shabe kamar
'yar yaye,sai kuma yau,yaso tambayar alhj farouq sai kuma ya tuna ba abunda ya
shafeshi bane yaci gaba da harkansa,amma ya barwa ransa akwai wani abu a
qwaqwalwarta don bai taba ganinta a nutse ba.

#mrs muhammad ce

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*


*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

6⃣8⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

Allah yana cewa


*(RANAR QIYAMA YAYIN DA AKA BAWA DAN ADAM LITTAFIN DUKKAN AYYUKANSA ABINDA YA
AIKATA SANDA YANA RAYE ZA'A CE DA DAN ADAM)KA KARANTA LITTAFINKA!!!,YA ISHEKA AKAN
KANKA KA YIWA KANKA HISABI*

ya subhanallah,ya rahmanu kada kayi mana hisabi ka yafemu.


____________________________________

TEAM ABDUR RAHMAN YA DA SAURIN KARAYA IRIN HAKA NE,NAGA HAR KUN FARA SAREWA FA,ITA
FA MACE ALLURAR CIKIN RUWA CE MAI RABO KA DAUKA,KADA 'YAN ADAWA SUYI MUKU DARIYA
FA,TAM.
_____________________________________

Bata sake yunqurin tashi ko motsawa daga wajen ba har zuwa sanda suka iso
qasa nijeria,anty dijen na lura da ita,ta kuma kusa ankarewa da dalilin gushewar
nutsuwarta,daya daga cikin motocin alfarma dake mallakar mustaphan ita tazo ya
kwashe baki daya,kallo daya zaka yi musu ka tabbatar sabuwa ce dal,laila sai bude
baki take saboda yadda motar tayi mata dadi,qasa qasa take cewa da sumayya
"Anty sumayya dama kada aje gida don kada mu sauka daga motar nan,dadi wallahi"
dariya ta baiwa sumayyan har sautin murmushinta ya fito,hada idanuwa sukayi sanda
ya waiwayo yana tsammanin ko wani abun ne ya sake faruwa,da sauri ta kawar da kanta
tana gintse dariyar.

Kowa na ficewa daga motan yayin da yake zaune baiko da niyyar


motsawa,amma ta danganta hakan da cewa shi za'a shige da shi cikin gida ne tunda su
zasu sauka ne su shiga nasu gidan,tsoron ta yadda zata giftashi ya kamata,duka sun
fice saura ita daya,a hankali ta durqusa zuciyarta na bugawa har ta isa bakin qofar
inda anty dije ke tsaye tana tsumayin fitowarta din cirar maqullin gidan dake jakar
sumayyan,daidai sanda ya fara magana cikin izza da nutsuwa yana baiwa driva umarnin
su wuce ciki,kadan ya rage ta fadi anty dije ta tallafeta tana dubanta cikin salon
tuhuma
"Wai mene haka sumayya lafiyanki kuwa"
"Bab....babu komai,qafata ce ta harde" bata ce komai ba ta karbi maqullin sannab
suka jera zuwa cikin gidan
"Ya kamata ki sanyawa ranki nutsuwa,na fuskanci duk sanda mustapha yayi magana
saiki rasa sukuni da nutsuwarki,bafa mukhtar babe,bai kuma san mukhtar ba,kada ki
sake ki sake aikata irin gangancin da kika aikata" da sauri ta dubi anty dijen,ya
akayi ta karancin halin da take ciki,itama bata sani ba,batasan dalilin da yake
sanyawa take kasa controlling kanta ba aduk sanda taji muryarshi wadda ke zubi sak
data mukhtar dinta,abinda kawai zai banbanta tashi data dan fi ta mukhtar
laushi,bata da bakin magana saboda haka bata ce komai ba jikinta a sanyaye suka
qarasa cikin gidan.
Washe gari haka ta tashi jiki duk a mace,ba dadi haja take ji cikin
ranta,bata so anty dije tayi mata wani duba na daban,ba ita ta dorawa kanta ba
tasani daga Allah ne,muhimmancin da mukhtar ke da shi a rayuwarta zaiyi wuya tayi
saurin mance duk wani abu da yayi kamanceceniya da tashi rayuwar,ba abunda ta iya
tsinanawa daga wanka sai kwanciya,ita kanta anty dijen ta lura,sai itama taji ba
dadi,tana tsammanin ko fadan data yi mata ne ya sanyata zama haka?.

Wajen sha biyu ta sameta dakinta tana fitar da kayan da suka dawo da su
tana kuma shirya wasu cikin wata jakar daban
"Sumayya,meke damunki?,ko don na miki fada jiya" kamar mai jira sai taji qwalla ta
cika mata idanu,kai take girgizawa tana duban anty dijen
"Ba don wani abu yasa na miki magana ba,na fuskanci abinda ke faruwa da ke ne,ina
so ki sauya kanki ne" da sauri ta tareta
"Ki daina fadar haka anty,wlh ba haka bane,ke uwa ce a gareni,kina da ikon zartar
da duk hukuncin da ya dace da ni,nima bansan me yasa a duk sanda yayi magana nake
zamowa haka ba,mukhtar dina nake tunawa anty har yau yaqi barin zuciyata,muryar
mukhtar nake ji cikin tasa,sai na dinga jin kamar shine tare da ni" tausayin
sumayya ya kamata,ta kama hannuwanta tana duban idanuwanta tana murmushi
"Na fahimceki sumayya,amma shi baisan da haka ba,bana son ya raina min ke ko yayi
tunanin wani abu na daban,nafa ji zafin abinda ya miki da fari,ban fadi miki bane
saboda yayi ne cikin rashin sani......ki zama jaruma pls,ki dinga tunawa ba shine
mukhtar ba....any way,mu ajjiye wannan maganar a gefe,me zakiyi da wadan nan kayan
da kike shiryawa a jaka?" Hawayen take gogewa da tafin hannunta itama tana murmushi
"Kano nake so gobe na tafi" idanu ta zaro
"Kano sumayya gobe daga dawowarmu jiya,ko dai wani abun daban aka yi miki?"
Marairaice wa tayi
"Don Allah umman khalipha ki daina cewa an min wani abu,kin taba gani uwa ta yiwa
'yarta wani abu ba dai dai ba,kuma diyar ranta ya baci?"
"To idan ba haka ba ai kya bari ko zuwa next week ne atleast ko?,zuwa sannan kin
warware gajiyar tafiya kin fidda tsarabar su malam"
"Anty inata kara amma baki gane me nake nufi ba,na qagu any naga abdallah,i missed
him alort anty,shima kuma nasan haka ne" kama baki tayi taja dariya
"Iyeeee,lallai yarinya,ga malam ga mama duka su bakiyi missing dinsu ba sai yaronki
gaskiya ne" kunya ta kama sumayyan ta kifa kanta saman hannun anty tana dariya qasa
qasa,ba zata iya boyewa ba,tabbas tayi missing yaronta
"Shikenan,Allah ya kaimu,amma fa saidai ki bari sai jibi,zamu bude jaka afidda
kayan su malam" duk da cewa ba hakan taso ba amma anty dije tafi gaban tayi jayayya
da ita haka ta amsa mata da to.

Misalin uku na rana suna zaune suna cin abincin rana amira ta shigo,bisa
dukkan alamu daga makaranta take,don ga handout nan a hannunta da key din
motarta,wani daj ihun farinciki ta saki tana qarasowa kusa da sumayya,gaisawa
sukayi da anty dije tana tsatstsokanar su laila khalipha da minal,baki daya tace
sun sauya,lallai garin ya karbesu,sai ta maida dubanta ga sumayya
"Umman khalipha wai wannan amiran umman khalipha ce ko wata kuka samo a can?"
Dariya suka saki baki daya kowa ya gane me take nufi,cikin salon zolaya itama
sumayyan tace
"Sun baro waccar a can,wannan musanyota sukayi" dukan cinyar sumayyan amira tayi
tana fadin
"Kina kallon mudubi kuwa?,wallahi kin bala'in zama wata queen namesake,ni zan fara
yiwa alqasim wannan albishir din" harara ta aika mata tana murmushi
"Ban aikeki ba,bismillah sa hannu muci abinci" idanuwanta ta maida kan abincin
wanda saura duk da miya suke ci banda ita,fara da man take jin ci don an dade ba'a
hadu ba
"Wai wai,an kuwa zanci,shinkafa da wake da manja ne da yaji ko?,ga kuma
salad,rabona da abincin nan da dewa,ina son fara da mai da yaji,su kam saidai suyi
miya,musamman idan waccan baturiyar tazo,bama tasan fara da mai ba,idan taga wani
yana ci har kyabe baki take wai muna cin abinci gaya" ta fada itama tana tabe
baki,murmushi anty dije tayi
"Dan gidanku yayarki ce dai,kuma kinsan baki isa ku fadi ba gaban maigidanta" amsa
mata ta soma bayan tayi cokali daya
"Me ruwa na da su,shima shi yaga zaya iya,haka kawai mutum bashi da maraba da
gauro,kowa yana ci gaba ta fuskan family amma banda shi,haka kawai jiya har na
kwanta ya tada ni wai na hada mishi fruit salad baturen kawai ga abinci ba zaya ci
ba wai yayi masa nauyi"
"Ke amira,zakici gidanku,ba yayanki bane?" Saki tabe fuska tayi kakar zata saki
kuka
"Ni umman khalipha bama wannan bane ya qonan raj,Allah anty su'adah 'yar rainin
sense ce,na shiga kai mishi naji suna waya,ta baro america ta biyoshi dubai wai
bata tadda shi,yace bai nan yana naija wai gobe zata biyoshi,wannam ai ba matar
aure bace matar yawo ce,kuma kowa yw zuba mishi idanu wai matarshi ce haka suka
tsara rayuwansu,to wallahi aure zamu masa" baki daya ta basu dariya saboda salon
yadda tayi maganar bilhaqqi,har sumayya na qwarewa sai data kurbi ruwa
"To ba sai ki masa ba tunda kece gaba da shi,kijimim tsaurin ido,musty zaki ma
aure?,yo ko adam ai bai usa yace zaya yi masa aure ba bare ke" tsaki sumayya ta ja
bayan ta samu tarin ya tsaya tana dan dukan cinyar amiran
"Kinga malama,ki dinga maganar da zata amfanemu,juyo muci abinci" waiwayowa tayi
tana duban sumayya
"Uhmmmm,wallahi kuwa,don wannan babu ranar sauyawarsu" sai tayi qasa qasa da murya
"Kefa kawai nake jira ki dawo a fara tsara mai yiwuwa,jibi za'a kawo lefe fa,kuma
da sati uku zasu zo kwanakin bikin"
"Komai kika tsara dai dai ne,amma ni jibin zan wuce kano" idanu ta zaro tana tsaida
cin abincin da take
"Me kika fada namesake,ina ce miki jibi kawo lefe kina cemin jibi zaki tafi kano,a
satin nan fa zamu je dubai siyo kayan kitchen,tare da ya musty zamu koma,shigowar
nan da nayi passport naki nazo karba za'a buga mana visa" cabdi,wane musty
din,mustaphansu?,ta godewa Allah da ya bata idea din tafiya kano,don ko ana yankan
jikinta ba zata bisu ba,wannan dan jin kan?,dan wulaqancin dan rainin wayo?
"Kice wani abu mana kinyi shiru,duk kin rusan plan,wallahi idan baki je ba da
wannan matar tashi zaya hadanu siyan kayan kitchen,bayan babu abinda tasan
amfaninsa a kitchen saidai ta ganshi da ido,sai shegen izza da dagawa,zata siya min
kayan shirme ne masu dan banzar tsada tana ganin kudin mijinta ne,kamar an gaya
mata shi mai kudi baisan ciwo da zafinsu ba" ajiyar zuciya ta saki
"Banji dadi bane amira,amma zuwa kano ya zame min dole jibi,malam na son ganina" ta
hada da qarya,sai anty dije tayi saurin tashi ta doshi kitchen don kada amira ta
roqeta ta hana sumayyan zuwa,don qaryan sumayyan ta mata dai dai,koda tana abuja ba
zata barta taje ba,don ta fuskanci inuwa daya bata zaunuwa tsakanin sumayyan da shi
uban gayyar,bare tafiya ma wata uwa duniya babu muharramin sumayyan ba zata yarda
tayi ta ba.

Shuru amira tayi wanda hakan ke gwada baki daya bata ji dadi ba,jikinta a
sanyaye taci gaba da cin abincin,sai da daqiqa kusan biyar ta shude sannan ta iya
cewa
"Malam yafi gaban komai amira,sai kin dawo Allah ya kiyaye,amma don Allah ki dawo
da wuri,sannan kimin alqawari zaki shiga ayi komai da ke,zaki dauki kanki kamar
diyar baabaa,wallahu tun wancan satin baabaa ke tsokanata,wai idan baki dawo ba
baisan ya zanyi ba,qila saidai ya daga bikin ko?" Murmushi tayi,alqawarin yayi mata
girma da yawa,amma tilas ta dauka,anayi da kai yafi ba'a yi da kai,masoyinka kuma
yafi maqiyinka
"Kada ki damu,nayi alqawari in sha Allah"
"Amma kafin ki wuce zaki shigo ki gaida su ummee,daga nan kiga ankon da aka fitar
ko,ku hudu amma kalar naku daban,ke da qawaye na su uku"
"Me zai hana,in sha Allah" ta fada kawai din a wuce gun,amma mai zai kaita gidan a
irin wannan lokacin da wannan mutumin ke qasar,daga haka ta ware suka ci gaba da
hirarsu.

******** ******** ********

Tun dare ta kasa bacci,gani take kamar gari bazai waye ba,bata ji kwanciyar
hankali ba sai data ganta a mota sun dauki hanya,babu wanda ta gayawa tana zuwa don
so take tayi masu ba zata.

Qarfe daya da minti ashirin na azahar a qofar gida tayi musu kasancewar sun
fito ne da wuri,ita ta fara shiga kafin driver din su anty dijen ya soma shiga mata
da akwatunta da qatuwar jakar dake dauke da kayan tsaraba.

Halima ce a kitchen,mama na bakin fanfo tana daura alwalar sallar


azahar,yayin da zainab ke mopping falon mama wanda ta dage labulensa,hakimin
abdallah na kwance abinsa saman kujera yana kallon cartoon,zainab na mopping din
tana mitar ya hanasu kallon kowacce tasha sai ta 'yan aljanu,mama na fadin ai
yafi,sunfi son suyita kallon waqe waqe da raye rayen banzan nan da wofi.

Tana sallamar halima ta saki kwashe miyar da takeyi ta fito,zainab ta saki


mopper,yayin da mama tayi tsaye tana dubanta tare da amsa mata sallamar fuskarta
dauke da madaukakin murmushi,kusan a tare suja ruqunqumeta suna ambatar
sunanta,dadi ya cika kowannansu,sam abdallah bai fahimci me ake ba sai da suka
shigo falon,dirowa yayi daga kan kujerar yayi kan sumayya yana kiran
"Mamiiiiiiii naaaaaaa" baki daya ya cukuikuyeta kamar zai shige jikinta,itama tsam
ta rungumeshi tana dariya farinciki fal zuciyarta kamar an wanketa da ruwan
qanqara.

Baki daya sun baibayeta,idanuwanta na kam abdallah,photocopy na mukhtar take


kalla,cikin shekara guda tal ya sake wani girma da wayo na ban mamaki,ya fara zama
dan saurayi,shekara kusan biyar ba wasa bace,girman dan mutum babu wuya,duba daya
ya wadatar da kai ka gane yaron na samun gata da kulawa,don suturar jikinsa ma
kadai amsa ce,zainab da halima kowa da abinda zai fadi
"Yaya sumayya kin ganki kuwa?,kamar irin hajiyoyin nan"
"Yaya sumayya kin zama budurwa wallahi,irin 'yammatan abujan nan,gaskiya tafiyan
nan ta karbeki,kaman an canjoki baki daya" dariya take ta rasa abin cewa,tunda ta
sauko daga mota ta lura da kallon da jama'ar unguwar tasu ke mata wasu ma kamar
basu ganeta ba,haka su halina suka cikata da surutu har sai da mama ta korasu
halima taje ta zubo abinci ta kaima driver a waje din da yayi salla zai koma,sannan
ta zubowa sumayyan ma, zainab kuma ta kai mata kayan daki,sai bayan fitarsu sannan
suka ji kunnuwansu,abdallah na maqale jikinta yana ta bare choculets yana gama musu
aiki.

Haka suka wuni ba wanda ya fita a gidan,sai maqota dake shigowa jifa jifa yi
mata sannu da zuwa,wanda wasunsu labarin yadda sumayyar ta koma suka ji suka zo
ganewa idanuwansu.

Koda ya abbakar yazo shima baki ya saki


"Lallai nasan gobe mutuniyar anan zata wuni"
"Ni ya kamata naje yaya,ina babymu nasan ta fara wayi bata san mamarta ba(da yake
matarsa ta haihu)"
"Ke dai kawai sai kin ganta,na tabbata ba zata iya haquri har kizo ba", malam ne
kawai bai shigo da wuri ba amma ta gaza bacci sai da taga shigowarshi,kusan raba
dare sukayi suna hira da shi,zuciyarsa na masa dadi duk sanda ya kalli diyar
tashi,babu shakka rayuwa ta soma yi mata kyau,saidai a yanzun yana ganin ya kamata
ta fidda abokin rayuwa ta sake aure,ko bai mata maganar yanzu ba zai fara yi mata
jirwaye mai kama da wanka,zai tashi haiqan wajen yi mata addu'ar katari da miji na
gari ita da 'yan uwanga baki daya,sai wajen sha biyu da rabi na dare suka rabu taje
ta kwanta.

******** ******** *******

Washe gari a dakin malam din ta karya,ko wanka bata yi ba kayan bacci ne
jikinta rida da dogon wando masu kauri,ta dora dogon hijabinta mai hannu,bayan sun
kammala suka ci gaba da taba hirarsu,gayaran murya malam din yayi
"tunda gaki Allah ya dawo dake auren 'yar uwarki ina jin ba zai wuce wata biyu
ba,dama su suka matsa da magiyar a bari ki dawo,basa son ayu bikin wai
bakyanan,shima kuma abubakar ya goyi bayansu" murmushi tayi ta dan sadda kai a
zuciyarta tana lissafin bayan bikin amira da sati hudu kenan?
"Alhamdulillahi,Allah ya tabbatar mana da alkhairi"
"Amin ya Allahu,gwara ayi,hankalina sai yafi kwanciya,burina naga kowacce dakin
mijinta,shine cikakken mutuncin 'ya mace,duk inda kika kai ga isa da dukiya nasaba
da ilimi matuqar baki da aure baki kammala zama cikakkiya ba,don shine rabin,sai
muyita addu'a,shi dama ibada ne,idan ka dace ka godewa Allah,idan ya jarabceka kayi
haquri ka kuma nemi lada a wajensa"
"Haka ne malam,Allah ya tabbatar da dukkan alkhairi" kai ta sunkuyar,jikinta yayi
sanyi,ba shakka ta fuskanci zaurencan malam,gugar zana yake mata,ita kam ina zata
tsomala rayuwarta a yanzu idan malam ya taso mata da batun aure,da sauri ta nemi
tsari kada Allah ya karkato da hankalinsa.

Cikin siyasa da qwarewa ta cikim hirar da suke yake jan hankalinta dangane
da halayen rayuwa,babu shakka dukkan maganarsa izina ce kuma abar dauka,sosai taji
dadin hirar da shi saboda yadda yayi mata tuni sosai game da wasu lamura masu
matuqar muhimmanci ga rayuwar diya mace,ranar malam bashi ya fita ba sai sha biyu
na rana,tun mama na leqosu taga ko ya gama shirin fitar har ta gaji ta barsu.

Sanda ta fito zuwa falon mama ashe anty amina matar yaya abubakar har
tazo,dariya ta saki tana dubanta
"Tab,wlh anty kwata kwata banji shigowarki"
"Ina zakiji 'yar gaban goshin malam" zainab tayi caraf ta karbe
"Wallahi anty kema kya fada,baki daya faadar malam tata ce" karyar da wuya amina
tayi
"Dole malam yaji da sumayya don gaskiya ba daya kuke ba,kun manta yadda rayuwa tayi
da ita ne,QADDARA ta wajiga ta?"
"gaya musu dau matar yaya" ta fada tana amsar babyn fuskarta qunshe da fara'a tana
cewa
"Ga babbar jika,ga babbar jika a mata" yarinyar kuwa dariya ta dinga bangalawa
kamar ta gane wace sumayyan a wajenta,yarinyar kyakkyawa sosai ta biyo jinin
gidansu sumayya.

Amina ke ta bin sumayya da kallo har sai data tanka


"Wai sumayya me anty dije ke baki haka,kinga yadda kika koma kuwa?" Dariya ta saki
"Haka kowa ke fada anty"
"Wallahi kin sauya baki daya masha Allah,boyayyen kyawun nan duk ya fito,yau dai na
yarda kinfi abban yusra kyau" dariya ta tuntsire da ita,sabida sau da dama suna
musu kan hakan amma taqi yarda,sai gashi yau ta sallama.
******* ****** ******

Washe gari qarfe sha biyu na rana ta shirya tsaf cikin african abaya,abaya ce
me mix da atamfa wadda tasha kwalliyar duwatsu,tayi kyau qwarai,jaka da takalminta
duka marching colour,gidan hajiya tayi niyyar zuwa yau,hajiyan abdur rahman,so take
ta wanke kanta,don tasan sam bata kyauta ba,shiru kawai wancan karon abdur rahman
yayi mata.

Ita da halima zasu je,saboda zainab ita yau ke da girki,suka yiwa mama
sallama suka fice bayan tace su gaida mata hajiyan da bahijja,don shima abdur
rahman din kwana biyu kenan bai leqo ba,abinda idan yana gari bai taba tsallake
kwanaki biyun bai leqo ba,ba wani tazara ce mai yawa tsakaninsu ba,hakan ya sanya
cikin mintuna arba'in mai adaidaita sahu ya saukesu bakim get din gidan suka
sallameshi suka nufi gidan.

Tun kafin su shiga abdallah ya soma fadin


"Zamu gun daddy A ko?,gun hajiya da bahijja" kallon mamaki sumayya ke masa kafin ta
maida dubanta ga halima
"Kai,wai yaron nan har gidansu abdur rahman ya sani?" Murmushi halima tayi
"Me zai hana,yaron dake wuni a gidan" shuru kawai tayi tana kada kai har suka shiga
gidan.

Daga can bakim setting room ta hangi takalma,wanda hakan ke alamta masu gidan
na da baqi maza,babu kowa falon sai bahijja dake kwance kan doguwar
kujera,sallamarsu ita ta sanyata miqewa zaune,fuskarta taf da fara'a takewa sumayya
sannu da zuwa gami da miqewa tsaye saboda murna da mamakin ganin sumayyan,ana haka
hajiyan ta fito daga dakin da yake mallakin bahijja hannunta dauke da
magunguna,lale marhabin ta shiga yiwa su sumayya suna gaisawa da halima,yayin data
ja abdallah jikinta tana fadin
"Matso mai gida na,kwana biyu ban ganka ba,daddynka ya shiga rububi bude asibiti ya
hanashi sukuni,hala ma kun ganshi?,don yana sitting room tare da baqi" murmushi
sumayyan tayi a aladabce
"Bamu ganshi ba,amma kamar akwai mutane a wajen"
"Masha Allah,mutanen uk,tafiya ba sallama" ta fada cikin zolaya,sai kunya ta kamata
ta sadda kai
"Wallahi hajiya,shirin tafiyar duk shi ya cinye lokacin amma naso zuwa"
"Babu komai,ai komai sai Allah ya nufa,kun dawo lafiya yasu dijen,kina wajenta ko?"
Kai ta kada tana fadin
"Eh,lafiya qalau suna gaisheku"
"To madalla muna amsawa,bahijja miqe ki sama musu wani abu a kitchen kafin a gama
abinci"
"Halan bata da lafiya ne hajiya?" Sumayya ta tambaya tana duban bahijja
"Bata jin dadi,kuma saboda wani iya shege bata da lafiya amma taqi shan magani,ta
ina lafiya zata samu"
"Gaskiya kam" sumayya ta fada,ita da halima suka shiga,haka suka fito da snacks
ruwa da lemo,yayin da hajiya ta ajjiye maganin ta basu wuri tana dauke da abdallah
ko nauyinshi bata ji,yaron itama yana tuna mata mukhtar,akwai tsantsar kama mai
yawa tattare da su.

Suna zaune suna hira bayan sun idar da sallar azahar suka ji
sallamarsa,sanye yake da jallabiya ruwan madara mai haske,kanshi babu hula sai
takaddu masu yawa dauke a hannunshi,idanu suka hada da sumayya wadda ke amsa
sallamarsa
"Hala batan hanya kika yi?,ko ba sumayya bace?" Ya fada tamkar da gaske yake,dariya
suka bushe da shi baki dayansu har ita,ya qaraso ya samu gefan hajiya ya zube cikin
gajiya yana ajjiye tarin takardun hannunshi abdallah ya maye gurbin takardun ya
haye masa cinyar,surutu ya fara yi masa yana biye masa yayin da yake amsa gaisuwar
halima
"Hala ke kika tuna mata da mu ko halima?matar da ko ki sanarmin zaki dawo nijeria
banyi wannan matsayin ba" Ya fada yana dubanta,hararar wasa tayi masa sabida hajiya
ta bar wajen
"Tunda ita ta tunamin sai na tafi sai na tuno don kaina sai na dawo"
"Ni kike harara?,lallai idanunki sai isa yanka" dariya ya bata suka dara sannan ya
soma tambayarta gajiyar tafiya mutanen abuja da sauran abubuwa tana amsa
masa,saidai ta kasa sakewa saboda wani kallo da yake binta da shi,hakan ya sanya
babu shiri qarfe uku na rana tayi haramar tafiya,ko ya lura a takure take ya sanya
ya sauke abdallah bayan ya kammala cin abinci yace
"Bari na shiga na watsa ruwa sai na zo na kaiku" kai kawai ta daga ba don taso
ba,ta sani dole a yau akwai abinda zai faru,tana tsananin kunya da jin nauyinsa a
yanzu,ba yadda ta iya tilas suka jirayi fitowarshi.

Cikin wani yadi ruwan omo ya fito,yayi kyau sosai,yace su sameshi mota sanda
suka tsaya yiwa hajiya sallama,ta ajjiyewa hajiyan turare da turmin atamfa data
siyo mata,sai wata qaramar jaka mai kyau mai garai garai wadda ke dauke da set na
kayan makeuo data siyawa bahijja,murna sosai bahijja ta dinga yi,yayin da ta dauki
mayafinta tace zata rakasu dama ta gaji da kwanciya ko zata ji qwarin
jikinta,godiya sosai hajiyan ta dinga mata tamkar bata fi qarfin abun ba,dama shi
alkhairi dadi gareshi koda wanda ka yiwa din yafi qarfin abun indai yasan karamci.

Duka baya suka shiga ita da shi ne a gaba,bini bini ya juya ya kalleta,wani
lokaci su hada ido wani lokaci ta basar,bai dai ce komai bar zuwa sanda wani go
slow ya riqesu,wasa wasa sai gashi suna shirin cin mintuna goma bai motsa ba,ga
hadari ya soma haduwa ya sanya garin yin duhu duk da har yanzu bai fara zubda ruwan
ba sai zafi da ake fama da shi,bata mantawa lokaci iwar haka suka bar nijeria
lokacin damina sai gashu sun sake dawowa sanda take shirim kamawa.

Baki daya motar dake gefansu wajen guda uku sun rufesu kasancewar sunfi
nasu tudu,sai ta sauke glass din motar qasa,abdallah dake sit din baya ya zuro
hannunsa yana qoqarin sanya mata yoghourt a bakinta wanda hajiya ta bashi wai
tasha,bata kai ga sha din ba ya zuba mata a jiki,baki daya ya bata saman cinyoyinta
"Ya salam,ya salam abdallah ka bata min kwalliyar mata" abdur rahman ya fada yana
laluba gefanshi ya dauko ruwa a cikin jarka ya miqa mata
"Budr murfin motar ki dan wanke gefan da ya baci kafin mu qarasa gida" karba tayi
ta balle murfin motar ta dan zura jikinta waje zata soma wankewa,ganin mayafinta na
niyyar shiga ya shafa shima ya sanyashi sanya hannu yana janye mata,dai dai lokacin
da motar dake daura da su aka sauke nata glass din wanda zafi ya ishi wanda ke
zaune sit din baya,tsaki yaja mai qarfi saboda ko kadan baisan a.c din motar ta
lalace ba,driven bai gaya masa saboda sabbabi ne ko wata daya basuyi ba,wannan ne
kuma hawanshi na biyu zashu rano,yayi niyyar hawan jirgi kuma babu jirgin da zai
tashi kano to abuja a irin lokacin da yake son ya taho din,hakan ya sanyashi hawa
mota.

Kyakkyawan gani idanunshi suka yi masa,da fari ya dauke kanshi kasancewarsa


wanda baison shiga sabgar da ba tashi ba amma sai qwaqwalwarsa ke gaya mishi kamar
ya santa,sake maida idanuwansa yayi wajen,ita dince,gaban motar wani yana janye
mata mayafi,ci gaba da kallon wajen yayi har ta kammala ta ta maida kanga ciki taja
murfin ta rufe
"Yammatan yanzu?,duka sammakal suke ne?" Ya tambayi kanshi,sai ya danna madanni
glass din ya koma ya rufe yadda yake,wani tsakin ya kuma ja,gwara ya yita shan
zafin da idanuwansa su dinga shishshigi kan lamuran da ba huruminsa bane.

Sam bata ma san abdur rahman ya janye mata mayafin ba,ta kammala ta kiqa
masa gorar tana masa godiya
"Ai yiwa kaine" ya fada yana murmushi,itama murmushin tayi don a yanzu ita ba
qaramar yarinya bace ta fuskanci me yake fadi.

Fita sukayi dukansu har bahijja tace zata shiga ta gaida mama,bai hanata ba
don yana da buqatar sararin da zaiyi magana da ita,kallonta yake har ta gaji ta
tanka
"Kada fa ka cinyeni"
"Da hakan zai yiwu da nafi kowa farinciki,kinga idan ma cinyeki kin tabbata
mallakina ni kadai har abada,wani ma bazai ganki ba bare ya qyasa" kunya kalamansa
suka bata,saita maida kanta daya barin tana sauke murmushi
"Naga ma sai wani shamin qamshi ake,ko da yake girmanki ne,shekara kwana inji 'yan
magana,ina maganarmu ta kwana sumayya?,nayi haquri sosai fa,dukkan kuma wani abu da
nake saka ran kammaluwarshi ya kammala,jibi in sha Allah za'a bude asibiti,ya muke
ciki,ko baki yarda ba wannan karon inajin ta qarfin tuwo zan qwace ki"
"Amma dai kasan ko budurwa bai halatta ayi mata auren dole va bare bazawara" ta
fada tana dariya qasa qasa
"Kada ki yimin haka sumayya" ya fada a marairaice,ta jima tana nazarin abdur rahman
din,bata da wata mafita yanzu,babu hanyar tsira,koda bata auri abdur rahman ba dole
ta auri wani a gaba wanda bata san wayeshi ba,ta tabbata malam bazai barta ta rayu
haka ba tunda har ya fara yi mata gugar zana,zata tanqwara zuciyarta,ta kwatanta
karbarsa taga ni,bata san me gaba zata haifar ba,amma me mutane zasu ce idan sukaji
zata auri dan wan baban mukhtar,wanda shi saurayi ne ita din bazawara ce?,wacce
iriyar fassara zasu masu,meye matsayar hajiyarshi?,da wace fuska zata kalli batun
"Ka cancanta abdur rahman,bazan hanaka damarka da Allah ya baka ba,amma kamim
haquri kada ka sanar da malam har zuwa sanda za'a kammala bikin zainab,na tabbata
idan ka gaya masa yanzu zaice zai hada da ni ne,wanda ya kamata kafin sannan ace
mun sake fahimtar juna kan zaman da zamu tukara da tsara abinda ya dace" hannunshi
ya dunqule kawaj saboda tsabar farinciki
"Amincewa da yardarki kawai ta isheni farinciki,na godewa Allah,bazan takura ki ba
ki kammala shirinki a nutse,amma don Allah a yimin alfarma nayi azumim bana a
dakina"ya fada a marairaice,dariya ya bata har sai data qunshe bakinta,wai a
dakinsa sai kace wani mace
"Allah ya zaba mana abinda yafi alkhairi"
"Amin ya Allah,ki shiga ki sauya kaya ki huta naga kaman yoghourt din dake jikinsu
ya hanaki sakewa,bazan iya shiga gun mama ba kunyarta nakeji kinsan ta zaka
suruka,sai gobe insha Allah zan kawo musu katin gayyatar bude asibitin shi da yaya
abbakaf,ki turon bahijja" ya fada yana sanya mata kudade a jakarta,kudi sam ba
matsalarta bane yanzun amma tun kafin tace komai yace baiso tace komai din,tilas ta
dauki jakar tana masa godiya ya bita da kallo har ta shige gidan wani madaukakin
farinciki na ratsashi.

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖
*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

6⃣9⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

*KU SHIGO CIKI KUJI*

*ALLAH YANA FADA CIKIN QUR'ANINSA MAI GIRMA*

*MISALIN ALJANNAR DA AKA YIWA MASU IMANI ALQAWARI,A CIKINTA AKWAI QORAMU  NA RUWA
WANDA BAI JIRKITA BA,DA QORAMU NA NONO WANDA DANDANONSA BAI SAUYA BA,DA QORAMU NA
GIYA WADDA TAKE MAI DADIN DANDANO GA MASU SHA(WADDA BATA SAKA MAYE KO TAMBELE),DA
QORAMU NA ZUMA TATACCIYA,KUMA A CIKINTA SUNA DA(SU 'YAN ALJANNA)NAU'IN KOWANNE IRIN
KAYAN MARMARI(DAN ICE)*

*kai jama'a wannan ni'ima da yawa take,idan kaso ka zama TATACCEN QASAITACCEN DAN
GIYA AMMA FA NA ALJANNAH,ya Allah ka sanyamu cikinta don rahamarka*
________________________________________

       Kafin su kai ga fita daga airphort din ruwan sama ya sauka,hakan ya hadu da
duhun magariba ya kawo qarancin jama'a bisa titi,idanuwan sumayya qur bisa kwalta
yadda ruwan ke sauka yana wanketa,a duk sanda ruwam sama zai sauka sai ya mata
tunin mukhtar kamar ko yaushe.

      
        Rashin daukewar ruwan har suka isa gida shi ya sabbaba driban ya shige da
su baki daya cikin gidan baaban ba tare da sumayya ta samu damar sauka ba kamar
yadda taso,saboda Abdallah wanda ya jima da yin barci kan cinyar amira,ruwan na iya
tabashi,da ita daya ce da da sauqi.

       Lema kubra ta shiga ta dauko musu sannan suka fito,suka taka har cikin
gidan.

     Lallai kam wannan biki ba qarami bane,baki daya harabar gidan ko ina an kafa
tempol,duk da gidan bai wani cika rana ba,duk da ruwan da ake tsulawa hakan bai
hanaka ganin mutane na kai kawo daga wannan sashi zuwa wancan sashi ba,a haka suka
qarasa bangaren ummee,falonta cike yake da baqi,yan uwa qawaye da abokan arziqi,ga
'yan rano nan wanda ko ba'a gaya ma ba kana kallonsu kasan jinin ummee ne,jinin
sarauta,ga 'yammata nan ko ina zazzaune kowa na nashi harkan,shigar amiran ya sanya
hanaklin sh dawowa kanta,masu tsokana nayi masu mata barka da dawowa nayi,da qyar
ta yakice suka hau falon sama na ummee wanda tana can.

       Karon farko da sumayyan ta taba shigarshi,falo ne dan gaske,wanda ya mallaki


duk wasu kayan alfarma,baki daya kwalliyar falon ta da duk abinda aka zuba mishi na
sarauta ne,kama daga royal chairs zuwa fentin falon,yayi matuqar burge sumayyan ba
kadan ba,ummen ma zaune kan daya cikin kujerun falon tana irga sabbabin kudi wanda
suke daure a rafarsu,ita da wasu mata ne wadanda kusan cousin dinta ne da suka taso
tare tun zamanin 'yammatanci,qarasawa amira tayi ta kwantar da abdallah kan daya
cikin kujerun,ummee ta dubeshi tana musu sannu da qarasowa ita da sauran 'yan
dakin,a ladabce sumayya ta qarasa gabanta ta duqa tana gaidata,ta amsa fuska sake
tana cewa
"Amira ta hanaki sakat ko sai data daukoki" murmushi tayi kawai amiran tace
"Ummee ba'a shiga tsakaninmu"
"Au ai dama itaku amira" ta fada tana kiran daya daga cikin ma'aikatanta ta wayar
hannu tana tambayarta an gama gyara dakin da tace,sai data gama wayar ta dubi amira
"Kije an gama gyara muku dakin,saiki sanya a kawo muku abinci,ki duba abinda kuke
da buqata ki kira mama uwani ki sanar mata,su ummu salma ma ina zaton suna dakin
tun dazun suke qorafin rashin dawowarki gashi gobe kamu"
"To ummee na" amiran ta fada tana miqewa
"Muje,ummee idan abdallah ya tashi ki bada shi a kawo mana shi" ta fada tana nuna
abdallahn dake kwance yana baccinsa lakadan,kai ummim ta daga don bata son yin
magana ta sake bata a lissafin.

        Dakina babba sosai wanda ya babu komai cikinsa sai carfet da aka malale shi
da shi,katifune saman carfet din ko ina aka kwakwkwantar,yayin da aka lullube
kowacce katifa da zanin gado abun rufa da filo qwaya daya alamar kowacce ta
kwanciyar mutum guda ce,sai toilet qwaya biyu cikin dakim,da qaton madubi da ya
kusa cinye rabin bango,mutum biyar suka taras a dakin,wasunsu na hira wasu na cin
abinci,shewa suka sanya da ganin shigowar amaryar,kowacce da abinda zata fadi,nan
suka zube aka gaisa suna ci gaba da surutaj,itakam sumayya na gefe tana
kallonsu,rayuwar wayewa kawai ake a wannan familyn,kowacce ka gani tana ji da
wayewa kyau da arziqin gidansu,akwai alama dake nuna suna da zumunci da kara,sannan
akwai sabo da fahimtar juna tsakaninsh,wanda hakan baya rasa nasaba da yadda baabaa
prof ya hadasu baki daya ya rungume kowa,duk sallah babba da qarama duk 'ya'yan
'yan uwan na gidansa,baya banbantawa da nashi dangin dana matansa,shi ya sanya kowa
yasan kowa,'yammata ne hadaddu wannan na wace wancan ta fada a ranta tana murmushi.

       Agogon fata na kamfanin gucci purple dake daure a hannunta ta duba ganin
ruwan ya tsagaita sai yayyafi wanda take iya gani ta window din dakin albarkacin
hasken lanatarkin da yake tarwai kowane lungu da saqo na gidan
"Zan wuce fa amira" inji sumayya ganin yadda amiran ta bararraje tana kwasar
hira,duka sai hankalin su ya dawo kanta har taji nauyin yadda kowa ya dora mata
idonshi
"Wasa fa kike amirah,kin manta alqawarinmu,ai ga gun kwanaki nan har na bar gidan
nan" sai ta karyar da wuya tana murmushi
"Amma dai ai kya bari naje naga anty ko?"
"Eh,wannan kuma,kuma ai ban ma gama ganinki ba,muje part din anty maamaa akwai
abinda zaki gani idan kin dawo na nuna miki sauran" ta fada tana miqewa,itama
tashin tayi suka fito,har sun kai qofa tace
"One minute don Allah sis,bari na dauko kayan waccan jarababbar na kai mata,Allah
yasa ya musty bai nan" kafin tace komai har ta juya da sauri ta koma,tsayawa tayi
tana jiranta gabanta na faduwa,tana addu'an kada Allah ya sa tace sai ta
rakatan,don gaskiya ba abinda zai hanata ce mata ba zata ba.

        Tana shiga ummu salma tace da ita


"Amira wai ina kika samu wannan babe din haka mai shegen class,wallahi tamun,ta
burgeni da ganinta akwai nutsuwa"
"Ga kyau,muryarta ce ni kuma ta burgeni" inji hafsat,dariya suka bata,dukkansu
'ya'yan yar ummee ne,tasu ta bala'in zuwa daya da amira saboda halayyarsu kusan
daya ce,ba ruwansu suna da matuqar kirki
"Nan fa gidan anty dije wadda ta muku fried rice da sunan hanan,a nan take"
"Masha Allah wallahi tayi"
"Ai baku ma san tayi ba sai mu da muka je gidansu...." Eesha da hassada ta cikata
tace
"Me tayi,mr suke da shi a gidan nasu" amira wadda har ta sanya qafarta zata fita ta
fasa ta dawo jin abinda eesham tace,dama tana lura da take takenta akan
sumayya,wadda bata ga ita sumayyan abinda ta yi mata ko ta tsareta mata ba
"Basu da komai,amma suna da rufin asiri,suna da wadatar zuci,basu taba kuma roqon
wani ba,baya ga haka suna da karamci kyautatawa da girmama baqo,wadan nan abubuwa
sun basu komai na rayuwa koda basu da shi din" inji amira ranta a bace sannan ta
juya ta fita ranta a bace,humaida ce wadda itama ke jin haushin abinda eeshan keyi
ta dora
"Arziqi ba kudi bane eesha,wadatar zuci sanin darajar kai,mutunci yakana da karamci
sune arziqin,kana da cin yau kana fa na gobe jibi wata ko shekara ma,kana sanya
suturarka ta mutunci,baka taba roqa a baka ba,baka tashi ka rasa abin kaiwa baka me
kake nema?"
"Kinga malama,ni ba wani nace mata ba da zaku isheni da dogon wa'azi,ha'an..." Ta
qarashe tana jan tsaki,caaa suka mata sun fita yawa ala tilas tayi shiru.

A inda ta barta a nan ta taras da ita,suka ci gaba da takawa ba tare data


nuna wa sumayyan akwai wani abu ba,bangaren anty maamaa suka soma shiga,itama
bangaren nata masha Allah da mutane,suka gaisa sannan taja hannunta suka tsallake
zuwa kitchen dinta,suna shiga tana yunqurin fitowa hannunta dauke da tray wanda aka
jera tangaran mai garai garai guda daya wanda ke dauke da hadin salad mai kyau,sai
wata qaramar butar shayi irin ta larabawa da cups dinta wanda ke dauke da baqin
shayi wanda yasha kayan qamshi iri iri,su'ad ce,fuskar nan a hade tana faman
kumburi,ko kunyar idon mutane bata ji,ta zama baturiyar qarfi da yaji,sanye take da
dogon wando wanda ya kama jikinta da t.shirt mai gajeran hannu,kanta babu dankwali
sai uban qarin gashi wanda aka dasa shi kamar nata na ainihi,ta sanya ribbom ta
kameshi,takalmin qafarta kuwa irin mai igiyar nan je,wanda tsininsa ba kawai abun
kallo ne,amma akace sabo da yi gawa da gatsine,da yake ta saba tafiya da abunta sam
bai dameta ba,hannyenta kuwa farce ne wanda tasha nail polish,gefe suka janye bata
ko kallesu ba ta wuce abinta,da kallo amira ta bita tana tabe baki kafin ta maida
kallonta ga anty maamaa
"Kumburin banza kawai,shi wanda kike ma kumburin ma baisan kina yi ba,ba kuma ki
isa kiyi masa a gabanshi ba,abincin ba bake zaki girki ba ki karba ki kai masa yaci
kina baqinciki kamar da kudinki aka sarrafa,wallahi ni yanzu baiken ya musty ma
nake gani,kana aure amma kamar ba magidanci ba,babu wani ci gaba da ka samu ko
sauyi dangane da tsohuwar rayuwarka" daquwa anty maaman ta jefeta da ita tana fadin
"Sau nawa zan miki magana kan dauke ido daga rayuwarsu?,ke ke zaune da ita?,ko
kinga ta kulaki sansa zata fita" shigin shagwaba amiran ke kumbure kumbure tana
fadin
"Duk ku kuke sake bata su wallahi,ni da ganin wannan takacin gwara kayi aurenka ma
kayi gaba a barku da su" dariya ma ta baiwa anty maaman sai ta dauke kanta tana
duban sumayyan
"Qaraso amiran umman khalipha mu gaisa ki qyale wannan tuburarriyar qawar taki,rana
iwar haka dai naga wanda zata yi mawa" dariya sumayyan ta saka itama tana qarasowa
inda anty maman take,a ladabce ta gaidata tana tambayar yadda ta baro mutanan
gidan,sai da suka gama gaisawa sannan tace
"Anty mama,bedroom dinki na bude,zamuga wadan nam kayan" kai ta kada mata suka juya
suka fice.

Har bedroom din ta dangana da ita,aljannar duniya sumayya ta kira


dakin,cupboard din antyn ta bude ta jawo wata akwati ta ajjiye gaban sumayyan,ta
sake janyo wata ta ajjiye sannan ta fara hudewa tana fadin
"Ga kayan da zaki saka na biki baki daya,komai da komai,sarqa kawai zaki buqata
bansan choice dinki ba" baki kawai sumayyan ta sake tana kallonta,ta soma ware mata
wanda zata sanya gobe kamu,wani dandatsetsen lace ne brown mai yarfin milk wanda
aka yiwa dinkin fitted gown,rigar ta dinku iyaka,sai takalmi milk na companyn vinci
wanda ke da tsini dunduniya,sake dago wata doguwar riga tayi wadda ta tafi da
imaninta,ire iren rigunan da baabaa ya basu da salla ita da laila mai dauke da
tambarin companyn MM,itama da takalminta ruwan kwalliyar duwatsun dake jikin rigar
tace wannan ta jibi ce ranar arabian night,sake janyo wani shegen yadi tayi wanda
bata tantance wanne ba,baqi ne baki dayansa an masa ado da milk din zare tsalli
tsalli da milk din qulalai a jiki,shima fitted gown ce,har tafi ta farko
fitinuwa,sai wani shegen hill shoes mai igiyoyi ruwan adon jikin yadin da jaka
purse mahadin kayan ga
"ankon dinner dinki" amira ta fada tana murmushi,rasa bakin magana kawai tayi tana
duban amira,dariya ta sanya sanda ra motsa zata yi magana
"Wallahi idan kika ce wani abu sai mun bata,baabaa ne duka ya bada yace na zabi na
dinkawa babbar qawata" kai kawai ta dinga kadawa kafin ta furta kalaman
godiya,kunnuwanta ta tasihe da nufin bata son ji.

Daya akwatin kuwa baki daya kayan amarya ne da zata yi fitar biki,fadin irin
kyawunsu ma bata baki ne,sai data daga mata su daya bayan daya sannan ta rufe ta
maida ma'ajiyarsu tana cewa
"A nan zamu dinga shiryawa,don haka anan zamu bar kayanmu,sai muje kiga lefe dama
baki gani ba" dariya tayi
"So kike dai dare yamin banje naga anty ba,ai basai na gani ba amira".
" shikenan,muje ki rakani na miqawa waccan kayanta,sai na rakaki qofa kije ki dawi
din"fuska ta narke,ta langabe kai duk don amiran ta haqura da wannan rakiya
"Habbaaa amira,muje dai ki wuce ki kai mata ni kuma na wuce gida"
"Ke kika ce sai na amso mata dinkin ina zaman zamana,saboda haka dole ki rakani"
tayi maganar tana gyara nadin mayafinta,miqewa tayi jikinta babu qwari tabi bayan
amiran suka fice.

Daf da zasu shiga bangaren wanda ta baya suka biyo da yake qofofi biyu
garesu,akwai qofar gaba wanda zaka shiga ta falo,akwai qofar baya wanda zaka shiga
ta kutchen wannan qofar suka biyo,daga hannun hagu na bakin qofar,a qawace yake da
wasu irin nau'in furanni da shukoki masu kaloli daban daban da kuma kyau,baki
dayansu kansu daya babu wadda tafi wani tsaho,an qawata gun tamkar wani dan gurin
hutawa,kaf gidan nan dinne kadai ke da irin wadan nan shukokin,wanda qilan
mamallakin bangaren ne ya siyi abunshi yasa aka tsara masa su a haka,yara ne kusan
su hudu,maza biyu mata biyu,a qiyasce zasuyi sa'annin juna baki dayansu,kowanne
qananun kaya ne a jikinsa,sun kunna fanfunan suna ta faman wasan ruwa,amira ita ta
fara hangosu,sai ta dakata tana daga murya
"Hibba!!,yayi muku kyau da wasan ruwa kunji ko" baki daya suka waiwayo suna
dubanta,kyawawan yara ne wanda kallo daya zaka yi musu ka tabbatar jinin gidan
baabaa prof ne,wadda aka kira da hibba ita ta matso
"Anty amira,gasar yin alwala muke,su hibban duk basu iya ba,zo kiga na fisu iyawa"
"Matsa ki ban gu,yanzu ban da lokacin shirmenku kinji,tawa ta isheni" sai ta karyar
da kai fuskarta kamar mai shirin yin kuka tace
"Don Allah anty amira kizo ki gani" idanunta ta zaro tana dubanta
"Ina wasa dake ne,bakiga ina cikin hidima ba,matsa a wajen nace" sumayya na tsaye
tana murmushi tana dubansu,yarinyar ta burgeta,zuciyar son yaranta ta motsa
mata,dauke idonta yarinyar tayi daga duban amira ta maida kan sumayya
"Tunda ba zaki ba ai ga wata antyn ko?anty zaki je ki gani?"
"Me zai hana" sumayya ta fada tana murmushi,tsalle ta fara wanda hakan ya sanya
sauran yaran qarasowa din jin me ya faru
"Ba inda zata,Allah hibba kin baci da yawa,itama tana da abunyi"
"A'ah,nifa sai naje" inji sumayya wadda dama hanyar kubuta take nema
"Kije ki fito kya sameni a nan" ta fada tana yin gaba din tuni yarinyar ta riqe
mata hannu
"Anty muje waccan fanfon,wannan na uncle man ne,zai zanemu ya ganmu a gurin,amma
idan mukayi kuka sai ya bamu chaculet yace mu daina" murmushi tayi kawai tace
"Allah"
"Allah anty,kuma duk yafi sona" hibba ta fada suna qarasowa wani waje wanda shima
akwai fanfo saidai baikai wancan kyau ba.

Jin muryar yara ya sanyashi daga idanunshi daga kan laptop din dake
gabanshi yana duba wasu sababbin design na dogayen riguna da kamfaninsa ke son
fitarwa a sabuwar shekara,gefanshi butar shayi ce da cup qwaya daya,a rayuwarshi
yana son ababen nan,yanayi na damuna irin wannan bayan gama saukar ruwan sama,da
guri wanda ke da wadatar korayen tsirrai,iskar wajen mai dan sanyi sanyi kadan hade
da qamshin qasa da qamshin furanni na masa dadi qwarai,ganin yaran tare da wata ya
sanyashi maida kanshi yaci gaba da abinda yake.

Daya yaron ne ya tabe fuska yana cewa


"Qarya ne anty,yafi sona,ko za'a tambaya ma" yatsanta ta dora kan lebenta tana zaro
masu idanu alamun yayi abunda ba mai kyau ba
"Bakasan ba'a cewa babba qarya yake ba,lala ba kyau,kace Allah na tuba" kan
kunnensa kalaman suka sauka sai ya daga kai ya sake duban inda suke tsaye,har yanzu
bai gane wace ba,amma yana iya gane yaran saboda baki daya yasan
muryoyinsu,hannunshi ya sanya ya tsiyayi shayin ya kai bakinsa yana ci gaba da
sauraronsu,a rayuwa Allah ya zuba masa qaunar yara,zama cikinsu yana debe kewanshi
a duk sanda ya samu kansa cikin kewa,hakan ya sanya wani lokaci yakan bata lokaci
cikin gidan marayunshi,akwai yaran da suka shiga ransa da dama a gidan,baisan so
yaushe ne zai daina rayuwar kadaici ba.

Murmushi tayi ganin yaron yayi saurin rufe bakinsa yana cewa
"Allah na tuba"
"To yanzu muje mu gwada inga alwalar kowa din,duk wanda yafi iyawa shi ya m....."
Sai ta kasa qarasa sunan
"Wanda duk yafi iyawa shi aka fi so" ta sauya salon maganar tata,tsalle suke har
suka isa gaban fanfon,tana tsaye tana kallon kowa daya bayan hannayenta harde a
qirjinta,kamar yadda yake zaune saman kujera yan kurbar tea mai zafi yana
kallonsu,sai da suka kammala tsaf,tabbas hibba ta fisu iyawa,amma ita dinma akwai
gyare gyare,a hankali ta yaye yalwataccen mayafin data suturce jikinta da shu,wanda
hakan ya bayyana shape dinta sosai kasancewar riga da skert ne a jikinta,tun bayan
zuwanta abuja kayan suka dan kamata kasancewar ta murje ta cicciko,idanuwanshi ya
lumshe saboda gujewa kallin haramun dinshi,sai ya kasa sake bude idanuwan mashi ya
barsu a lumshe yana sauraron ta tana fadin
"Sai kuyu haka,yauwa haka,haka" bai bude ba har sai da yaji tana fadin
"Idan kayi haka,kayi alwala mai kyau" a hankali ya bude idanuwan nashi,wannan karon
fuskarta tarwai take ta haske qwan lantarkin da ta tsaya saitinsa,ya dan qura mata
idanuwa yana son tuna inda yasan fuskar
"Mai kuka a uk mall" qwaqwalwarsa ta birkito file dinta,qaramin murmushi ne ya
subuce masa,wanda idan baka kula da kyau ba na zaka gane hakan ba,saboda cije leban
qasan bakinsa da yayi
"Tana acting kamar wata babba" ya raya hakan a ransa.

Riqeta yaran suka sake yi,nurain daya daga cikin yaran yace
"Anty ki mana tatsuniya,baabaa lami mai aikin momi tana mana" murmushi ta saki,ta
lura suma lallai yaran masu son mutane da sabo ne,saidai suna son riqeta gashi tana
son tafiya gida ne
"Ban iya tatsuniya ba saidai na baki tarihi"
"Laaaah,irin wanda uncle man ya taba yi mana rannana?" Zaitun daya yarinyar ta
ambata da salon tambaya,duk da bata sani ba amma sai ta daga kai
"Ita,amma yanzun inaso naje gida na gaida anty na,sai wani lokacin na muku ko?"
"Yaushe?" Inji hibban,kai ta girgiza qaramar dariya na son subuce mata,yaaraan
akwai wayo,tana som tana yaro mai wayo da kaifin qwaqwalwa irin haka,ta tabbatar
basirar da wayon bai tashi a banza,zai zama abu ne mai amfani a nan gaba
"Wataran in sha Allah".

A hankali ya janye idanuwanshi daga kansu jin qarar wayarshi,ya cirota daga
aljihun black trouser din dake jikinsa yana duba mau kiran,su'ad ce,dan qaramin
tsaki yaja,ba matsala yake so ta qara maishi ba,ya riga da ya yanke magana,ya gaji
da auren asha ruwan tsuntsaye da sukeyi,ita tana kano shi yana daura,kusan tun jiya
bayan isowarshi garin da yaje gidan hamza abun ke dawainiya da shi,kasancewar wanda
amiran zata aura cousin suke da hamza,wata rayuwa ya gani ba irin tasu rayuwar
ba,ba irin rayuwar gidanshi ba,yana iya tuna sanda hamza ya dagewa auren yarinyar
suna ganin baikensa,ashe akwai abinda ya gano?.

Rejecting call din nayi sannan ya maida kansa kan laptop dinshi da niyyar ci
gaba da aikin da yakeyi,wani tsakin ya kuma ja ganin lokacin da ya bata yana kallon
sha'anin da bai shafe shi ba,yayi asaran time dinsa a banza,saidai yadda take
kiranshi a jejjere ya hanashi aiwatar da komai,wani wawan tsakin ya sake ja,a
rayuwarshi ya tsani abinda zai takurashi,sai ya ciro wayar a fusace ya daga ya kara
a kunnenshi,cikin shagwaba da karyar da murya ta soma fadin
"haba my man,please....please kada muyi haka da kai,ka duba fa ka gani duka duka
shekara daya ya rage min na kasance tare da kai fa?"
"Keep quite su'adah please....na riga da na gama magana,idan zaki iya zama gu daya
fine,idan ma ba zaki iya zama ba duk daya,amma kada ki zargeni nan gaba" ta
tabbatar da cewa shi din kaifi daya ne,baha magana ya sauyata,mutum biyu ne tal a
duniya ke sauya masa ra'ayi koda baiyi daidai da mizanin mashi ra'ayin ba,baabaa
prof sai ummee,sanin baya qaunar kuka ko misqala zarratin,koda na qaramin yaro ne
ya sanyata saka kuka har da sheshsheqa,sai ya lumshe idanuwansa yana sauraren
sautin kukan nata,a hankali ya zame wayar daga kunnenshi sannan ya kasheta baki
daya ya cillata aljihu,shutting down din system din yayi sannan ya miqe tsaye yana
jira ta qarasa mutuwa,ya laluba aljihunsa yaji muqullansa na jiki,ya dauke system
din sannan ya dinga takawa a hankali ya nufi inda yayi niyya,baki daya baya
marmarin komawa bangaren bare taci gaba da jagula masa lissafi,saboda haka ya isa
ga qarama cikin motocinsa ya bude ya ajjiye kayanshi ciki ya tada ta ya fice ba
tare da ya nemi kowa ba.

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

7⃣0⃣
*Bismillahir rahmanir rahim*

*HASBUNALLAHU WA NI'IMAL WAKIL*


___________________________________

Mamaki ya kama anty dije ganin sumayya,dariya ta dinga yi tana cewa


"Maganinki,da kika qi dawowa ga mai gaba daya nan taje ta taho mana da ke ai" itama
sumayya dariya take
"Hmmm,amira,amira rigima amira tabara,sai ganinta kawai nayi wallahi"
"Ina sane ban gaya miki ba ai" guri sumayyan ta samu ta zauna tana ci gaba da
dariya.

Nan ta shantake suna ta hira da anty dijen,bata tashi farga ba sai taga har
sha daya tayi,hakan ya sanya ta bude dakinta tayi kwanciyarta,anty dije je cewa
"Abdallah fa?"
"Barshi anty,babu lallai yayi rigima"

****** ****** *******

Qarfe goma na safe tayi wanka bayan ta gama hada breakfast ta barwa anty
dije sauran aikin gidan,doguwar riga ta saka ta wani irin yadi mai talewa,hijabi ta
zura wanda ya saukar mata har saman tafin qafarta,niqabinta ta daura sannan ta fita
ta tadda anty dije na goge kayan kallo a falo
"Anty zan wuce,nasan amira tana can ta cika fam,fashewa kawai take jira tayi" ta
fada tana qyalqyalewa da dariya,dariyar itama tayi
"Ato,yau mai rabaku sai Allah" tana dariya ta saki niqab din nata ta fice a gidan.

Ya kusan a qalla mintuna talatin zaune cikin corridor din dake saman
benanshi,bata san sanda ya shigo ba,tun daren jiyan taje zaman jiran shigowarshi
taji shiru,ta kira wayar babu adadi saidai duka amsa daya ce wayar a akashe
take,tun tana kumbura har zuciyarta ta fara saukowa,ta sani cewa fushinsa bashi da
dadi,tana shan wuya a duk lokacin da yayi fushi,hakan ya soma daga hankalinta,kusan
ranar bata yi cikakken bacci ba,saidai duk da haka bata san shigowarshi cikin gidan
ba.

Cikin qanqanin lokaci zuciyarsa tayi fes,fuskarsa ta soma washewa,yaran


dake shawagi kan idanunshi a harabar gidan,yaro daya tak yake hangowa cikinsu wanda
bai sanshi ba baquwar fuska ne,saidai a yadda wasan da yaran ke gudana duka ya fisu
kuzari da wayo,motsin yaron ya dinga bi da kallo yana sakin murmushin gefan baki.

Sai data tsaya suka gaisa da baaba mai gadi kamar yadda suka saba sannan
ta sanya kanta cikin gidan,tunda ta shiga gabanta ke wani irin faduwa,kusan yara
sunfi yawa a harabar gidan suna wasanninsu,jifa jifa mutane na kai kawo,juyiwar da
abdallah zaiyi ya hangota,duk da niqabin dake fuskarta da hijabinta hakan bai sanya
ya kasa ganeta ba,da gudu ya tafi yana kiran
"Ammiiiii....amminaaaa" cak yaran suka tsaya suna kallonshi ganin suna tsaka da
wasa ya bar gun.

Da idanuwa yabi yaron ganin yayi wani guri da gudu,hannayenta ta bude baki
daya duk da har yanzu niqabin na kan fuskarta amma murmushi ne kan
fuskarta,durqusawa tayi ta daga shi tana nishi saboda nauyin da abdallahn ya dan yi
mata sannan ta dage niqaf din,fararen jerarrun haqoranta a waje
"Wai abdallah,na kusa fara kasa dagaka,me kaci yau ka qara nauyi?" Dariya ya saki
irin ta quruciya sannan yace
"Ammi,wata ummi ce,na kwana a dakinta,ta yimin wanka ta bani chips da qwai ni kadai
na cinye,harda tea da suger sosai" dariya ta kamata,har sai data dora tafin
hannunta kan bakinta,kafin tace wani abu hibba tayo gaba da gudu itama sauran yaran
suka biyota,bata ankara ba taji an ruqunqumeta ana fadin
"Anty,kin dawo zaki mana labarin?" Waiwayowa tayi tana dariya,ta sauke abdallah
tana fadin
"Kin manta yau ana bikin anty ameeraa?,sai idan an gama zan muku,muje ku rakani
inda anty amiran take" gaba tayi yaran na binta a baya wannan ya riqe hannunta
wannan ya riqe hijabinta a haka suka tafi.

Baisan yana binsu da kallo ba sai da suka bacewa ganinsa,ya lumshe idanunsa
sannan ya bude a hankali,abun ya burgeshi ya bashi sha'awa,yana son yara har cikin
zuciyarsa,bayansa ya jinginar jikin kujerar yana fidda zazzafan huci daga bakinsa
"My man" yaji an ambata a tausashe,yasan ko wace hakan ya sanya yaqi
waiwayawa,sannu a hankali ta tako gabanshi,sanye take cikin riga da wando,ire iren
shigar da tasan yana muradi suna burgeshi qwarai idan tayi,jikinta na fidda wani
irin qamshi mai dadi,duka hannayenta ta zuba a kafadarsa,cikin shagwaba salon da
tasan yafiso tace
"My man,ka sanyani a damuwa jiya,kasan cewa ina buqatar ka,baki daya kwanakin da
zamu kasance tare ba masu yawa bane,amma man ka qauracemin" ko kadan bai da buqatar
maganarta,hakan ya sanya ya saka hannunshi ya sauke hannayenta dake kafadarsa
sannan ya ture kujerar ya miqe tsaye ta juya yana shirin barin gun,ranta ne ya
baci,hankalinta ya tashi,ta tabbatar cewa ya hau bigerin da shawo kansa zaiyi
wuya,bata kuma isa ta sha gabanshi don hakan zai iya jawo mata wata matsalar,tilas
ta janye jiki tana kallonshi ya wuceta,hannayenta ta saki zuciyarta na
zafi,idanuwanta na neman tara qwalla,babu shakka idan banda mustapha mustapha ne da
babu namijin da zata zauna a duniya yayi mata haka,saidai mustaphan na dabanne
kamar yadda yake daban a zuciyarta,mafita daya gareta ta kaishu gaba inda za'a
sashi tilas yayi mata abinda take so din,bama inda ta saba kaishi ba wannan karon
na can zata kaishi ba,sai ta juya da dan sassarfa ta ratsa ta dakinsa zuwa falonsa
ta sauko qasa ta nemi hanyar ficewa ba tare data damu da sauya kaya ko daukar
babban mayani ta suturta jikinta ba ko don girman wanda zata gurinsa.

A dakinsu na jiya sumayyan ta tadda su,tana qunshe dariya ta qarasa,dariya


amiran ta saka tana harararta
"Wallahi kin maida ni wata iri amira,godiya nake"
"Afuwa namecy,afwa"ta qarasa ciki suna gaisawa da 'yammatan dake ciki,gira ta daga
" to ya zanyi da ke,ni na kai kaina inda ba'a damu da ni ba,muje kimin rakiya wajen
baabaa"
"Ya kamata,don nima ina son inje in gaidashi" eesha dake shan tea ta ajjuye cup din
tana yiwa sumayyan duban ita kuma a wa?,kamar zata furta sai kuma ta fasa,ta miqe
itama tana yafa dan yalolon mayafi kan kayan baccinta tana cewa
"Muje nima nayi rakiya"
"Owk" amira ta fada ta dubi su hibba
"Oya,ku wuce ku tafi wasanku" juyawa sukayi hibba ta tsaya ta karbi abdallah suka
wuce.

Sai da suka shiga wajen anty maamaa da ummee ta gaidasu sannan ta suka wuce
zuwa sashen tsohon.

Zaune yake gefan umminsa daga shi sai itayana kurbar coffee,idan da kowa
a gun ta tabbata bazai sha ba,wanda ta shiga kitchen da kanta ta hada masa,dubanshi
take qasa qasa,ita daya take iya gane mustaphan,tayi tsammanin idan yayi aure
shikenan komai ya qare,matarsa zata fahimceshi fiye da kowa,saidai kash,sabanin
haka ne ya faru,matarsa itace wadda bata fahimceshi ba fiye da kowa,a yanzun kallo
daya tayi masa ta fahimci yunwa yake ji,bazai iya gaya mata ba,zai iya ci gaba da
zamansa haka har sai an bashi,idan ya gaji ya kuma yana iya fita can wani wajen cin
abincin yaci abinshi,time to time yakan sanya matarsa tazo ta karba masa idan
yunwar taci tura,hatta da amira tafi matarsa sanin ko shi waye,wani irin mutum ne
shi mai wuyar sha'ani,ba kowa ke iya fahimtarsa ba,bai iya sharing damuwarsa ko
shawararsa da kowa idan ka dauke ummeen da baabaansa,tayi zaton idan yayi aure
wannan zai zama aikin matarsa,saidai ina ma yaga matar bare ta dauki wannan
responsibility din,saidai komai tana ganin ya kusa zuwa qarshe tunda gaf su'adan
take da kammala karatunta,tana zaton idan ta gama din zata nutsu ta tara hankalinta
waje guda ta kula da mijinta kamar kowacce matar aure.

Yana tsaka da amsa waya ta shigo falon kai tsaye tare da sallamarta,a
hankali ya daga kanshi don ganin waye,kansa ya kawai gefe yana jin kunyar ganinta a
haka a matsayin surukarshi,baki daya babu al'adar bahaushe ko digi cikin jini da
jijiyarta,komai nata na mai jan kunne ne,ko qanqanin bata jin kunyar keta gidan a
haka,duk da tarin baqi dake gidan,yana yiwa yaronshi sha'awar sauyin rayuwa,duk
abinda ke faruwa cikin rayuwar yaron shi da yakeso fiye da kowa cikin yaransa idan
ka dauke amira yana sane,saidai baison jefa kanahi cikin sha'anin da ba'a nemi
agaji ko tallafinsa,dattijon suruki ne wanda yasan ciwon kanshi da mutucinsa,amma
tabbas mustapha ma cikin wani wadi daya cancanci a tallafeshi,tun fari laifinshi ne
da bai ganin aibun rayuwar mai jan kunne,gani yake rayuwa ce ta burgewa,baisan babu
komai cikinta face tsantsar wahala da rashin nutsuwa.

Cikin sheshsheqar kuka ta zube a gabansa


"Baabaa don Allah kayi masa fada,ka masa magana,yana son takurani,yana son tauyen
'yancina" sosai yake dubanta,a nutse yace
"Nutsu su'adah,zauna,zauna sosai,gayamin,me ya faru?,me ya hadaku" zama tayi
gabansa tana goge hawayen nata da tissue,don ko dan mayafin da zata kama ta goge
hawayen babu a jikinta
"Baabaa,mustapha ne,haka kawai muna zamanmu yadda muka saba,shekaran jiya yaje
gidan hamza,ya gano wata zamantakewa ta daban yace dole muma irinta zamuyi,bayan
zamantakewar tasu sam babu 'yanci ko walwala a cikinta,sai dinbim takura kai da
rayuwa cikin duhu da rashin wayewa,lallai wai saidai na dawo nan qasar na zauna
daku na qarasa karatuna don bai amince da duk qawaye na da abokaina ba,sannan wai
idan na kammala na bishi dubai mu zauna tare na dinga kula da shi,don Allah baaba
wannan ba takura bace,ni ban taba ganin inda da quruciyarki kike rayuwa irin haka
ba,a gun africans kawai nake gani suma rashin wayewa ce da duhun kai" idanu baban
ya runtse kafin ya bude,duka ta hadu ta zagesu su da iyayensy,babu shakka ba
qaramin tasiri rayuwar yaro take ba a duk inda aka haifeshi ko ya taso,sai Allah ya
taimaka iyaye sunyi tsaiwar daka sannan za'a samu yaro ya tashi da dabi'a halayya
da al'adunshi.

Cup din ya dire dai dai sanda wayarshi tayi tsuwwa,ya duba yaga kiran daga
baabaa ne,tun kafin ya daga ranshi ya raya masa mishkilar su'adah ce,daya daga din
kuwa ce masa baabaan yayi
"Kana ina?,duk inda kake kazo ka sameni a falo,ina jiranka" daga maganar tasa kawai
ya fahimci mawuyaci ne ba qararsa ta kai wajen baabaan ba,duk da cewa hakan ba
baqon lamari bane wajensa,amma abun yayi masa ciwo fiye da kullum,ranshi bace ya
maida wayar aljihunsa yana duban ummee
"Baabaa na kira" ya fadi a taqaice
"Ok,ka qoshi kenan coffee kawai ya isheka,bayanshi banga kaci komai ba?"
"I'm ok ummee" ya fadi yana takawa ya fice daga dakin.
Cikin sanyi da qasaita yayi sallama cikin falon baaban,wani kallo yajefa
mata wanda ya sanyata sadda kanta qasa,take jikinta yayi sanyi,nadamar kawo qarar
ta baibayeta,kwarjininsa kadai ya ladabtar da ita,cikin girmamawa ya isa gaban
baaban ya zauna gami da lanqwashe qafafunsa,ajjiye takaddun hannayensa yayi sannan
ya maida hankalinsa gareshi
"Mustapha,me ya shiga tsakaninka da matarka" shiru yayi na wasu daqiqu kanshi na
qasa,idanunshi bisa carfet din dake dakin,a hankali ya motsa bakinsa
"Baabaa,ina da buqatar mata ta ne kawai kusa dani,na buqaci ta ajjiye karatunta ta
zauna tare da ni" yasan a rina,mustaphan ba mai boyon abu bane cikin zuciya,komai
tsaurin gaskiya ko dacinta sai ya fadeta,tabbas mustaphan bashi da laifi cikin
maganarlaifinshi daya tun fari a haka ya tarbiyyanci matarsa,amma kowanne magidanci
zaiso kasancewa da iyalinshi,bawai kowannansu da inda ya sanya kanshi ba sannan ace
wai a haka za'a rayu,tausayinshi ya kama shi,yana jin wannan karon ya kamata yayi
wani hobbasa cikin rayuwar yaron nashi
"Baka kyauta ba mustapha" maganar data sanyashi daga ido cikin mamaki ya tsare
babaa da kallo,yayi zaton shine na farko da zai goya masa baya?,ya zaci shima yasan
ba haka rayuwar ma'aurata take ba
"Tun farko haka ka dora bigiren rayuwarku kai da ita,ka manta ice tun yana danye
ake tanqwarashi,basai ya bushe ba sannan kace zaka tanqwarashi" kai su'adah ke
kadawa cike da jin dadi tare da alamun samun nasara cikin zancan baban ba tare data
fuskanci dungun dake cikin maganar ba
"Mustapha,komai ya kusa qarewa,ka qyale matarka ta kammala karatunta a inda ta
fara,shekara guda ya rage mata ta kammala,idan yaso koma meyw zai biyi baya sai ka
zauna ku yanke" shiru ne ya ratsa falon,kowa da abinda yake saqawa cikin
zuciyarshi,zuciyar su'adah ciki fal da fatan samun nasara.

Bayajin a duniya akwai wani umarni da baban zai bashi ya tsallakeshi,ya


numfasa a hankali sannan ya furta
"Na barta baabaa"
"Yes dad,thank you" sa'adah ta fada cikin daga murya,murmushi ya subucewa
baabaan,addu'a yaje da fatan saisaituwar halayen su'adah ko kyakkyawar rayuwa zata
samu ga diyansa,miqewa tayi cikin farinciki ta fice,fes taje jin ranta,don ta
mustapha tana tunanin tasan yadda zata shawo kansa,don ko kadan bata jin zata iya
tabbata cikin nijeria tayi rayuwa a cikinta.

Fitarta sukayi kacibus da su amira na niyyar shigowa,babu wanda ta kalla


cikinsu tayi gaba abinta,yayin da eesha ta bita da harara kamar idanuwanta zai
fado,babu wanda ta tsana a duniyarta sama da su'adah din,tana ganin baki daya ta
kanainaye rayuwar mustapha,ta hanashi duban kowacce mace da qima,bayan ita din ba
wata uwa take tsinanawa gareshi ba,abinda bata sani ba,abun a jininsa yake,tsaki ta
ja wanda ya sanya amira waiwaya ta dubeta,tasan meke kai kawo a zuciyarta,saidai
koma mene bata fatan Allah ya ida nufi,don qwaryar sama ke dukan ta qasa,banbancin
ita da itan kadan ne.

Bayan sallama da tayi ganinsa shine abu na biyu daya biyo baya bayan
shigowarta falon,nutsuwarta yaji na nemam gushewa
"Bafa mukhtar bane,ba kuma zai taba zama mukhtar ba" wannan shine kalaman sa suka
dawo mata cikin kwanyarta,sai ta lumshe ido taja dogon numfashi kafin ta ajiye
nunfashi ta kuma daidaita nutsuwarta.

Fuskarsa dauke da fara'a yake dubansu


"Mommies dina ne da kuma mai sunan uwar mumunai" ya furta cikin fara'a,su dinma
fuskarsu washe take suka samu waje gefe da shi suka zauna,yayin da eesha tafi daura
da mustapha,satar kallonshi take,baki daya man din ya sake tafiya da tunaninta,
"Allah ka mallakamin shi" ta fada cikin zuciyarta tana lumshe idanuwa tana ci gaba
da satar kallonshi,wanda sam shi baisan ma tana yi ba,abinda ke gabansa kawai shi
ya dameshi,gaisuwansun ma bai dago kai ba bare ya gane su waye ya amsa musu baki
daya kudin goro,ba haka eesha taso ba,gaida baabaa sukayi baki daya ya amsa cikin
fara'a
"Mutan kano,gaki ga mutuniyar dai,bata qyaleki ba,nan ta addabeni sai da na siya
musu ticket ta taho" dariya suka dan saka baki dayansu.

A hankali ya miqe yana shafa sumar kanshi,jin maganansu yake kamar a


tsakiyan kanshi kasancewar bai son hayaniya,baabaan ya fuskanci me yake son
fadi,saboda haka yace
"Shikenan,kana iya tafiya" juyawa yai a hankali ya fice a falon fuska a daure kamar
ko yaushe,eesha ji take kamar ta bishi ta rungumeshi,saboda yadda kullum kwanan
duniya yake sake tafiya da ita,yayin da sumayya kanta ke qasa tana wasa da yatsunta
zuciyarta na bugawa,amira ta bishi da kallo kamar yadda baaba shima ya bishi da
kallo,shiru yaci gaba da ratsa falon har ya fice din sannan baabaa ya dauke
idanuwansa daga kanshi ya maida kansu,ya dubi amira
"Aishatu ta rakaki amira kuje ku amso min saqo wajen ummenku"
"To abba" ta fada tana miqewa,tasan babanta sosai,hakan ya sanya bata ce sumayya ta
taso na,tunda taga haka tasan akwai manufarsa na aikensu su biyu,baki daya taji
wani nauyi ya sake kamata bayan fitar tasu,falon yayi shiru ta kasa motsawa sai
kanta dake qasa har yanzu
"Mamana,ki saki jiki mana,nima fa babanki ne ko ba haka bane" murmushi tayi
"Haka ne abba" shiru ya sake ratsa falon na wasu sakanni kafin ta sake jin muryarsa
"Mama na,wata alfarma nakeson na roqeki,saidai ina jin nauyin haka" mamaki ya
kamata,ita din wace?,wacce alfarma babban mutum kamar baabaa prof din zai nema daga
gareta,bayan ita din ba kowa bace,bata kuma mallaki komai ba
"Baabaa,yanzu kace kai abbana ne,kuma na yarda haka ne,me yasa uba zaiji nauyin
bawa diyarsa umarni" sosai wani irin qima da darajarta ya qaru a idanuwanshi,ya
jima baiga nutsuwa da hankali tattare da yarinya mai makamancin shekaru irin nata
ba,nutsuwarta da kaifin hankalinta shine abu na farko daya fara bashi mamaki
tattare da ita,tana da wani irin dattako kunya nutsuwa da ganin darajar manya,wanda
zaiyi wuya a wannan zamani ka samu mace kamarta da wannan qualities din
"Allah yayi miki albarka maman,haqiqa iyayenki sunyi nasara wajen tarbiyyarki,sun
rabauta da diya ta qwarai,mamana.....kinga yayankun nan da ya fice yanzu?" Gabanta
ya buga,sai ta kasa daga kai ta kalli baabaan,Allah yasa ba wani sharrin yayi mata
wajen baban ba,kai kawai ta kada
"Mamana,zaki taimaka min ki taimaka masa wajen inganta rayuwarsa?" Duburburcewa
tunanunta yayi,sam bata gano me baban ke nufi ba,inganta rayuwarsa kamar yaya,ya
manta bata da komai ne qarqashin wasu take itama,duk yadda taso ta fassara maganar
tsakaninta da qwaqwalwarta ta gaza gano ainihin ma'anar maganar,har rudun hakan ya
bayyana saman fuskarta.

Murmushi baaban ya saki,ya yadda har yau ita dinma akwai sauran quruciya
tattare da ita,baison rudata,saboda haka yace
"Baki fahimci baaba ko,shikenan,tashi kije kuci gaba da sabgoginku,idan kika
fahimci ma'anar maganar ina son ganinki a lokacin,amma fa kada ki zurfafa
tunani,kune qawayen amarya,kusha bikinku kinji mamana,Allah yayi miki albarka"
"Amin baabaa,na gode" ta fada tana miqewa,hakanan taji jikinta yayi wani mugun
sanyi,rashin jin dadin kasa fahintar maganar baban ce har ya dago haka ko kuwa
mene?.

Naso yafi haka but am busy fans.

#mrs muhammad ce
*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

7⃣1⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

Allah S W T yana cewa

*"DUK INDA KUKE SAI MUTUWA TA RUSKEKU"*

Allah kasa mu cika da imani

____________________________________

     Qarfe biyar na yammacin ranar baki daya gidan ya sake dinkewa da jama'a saboda
shirin fara gabatar da kamun amarya,sumayya na tare da amiran duk inda ta sanya
qafarta sai ta janyota,kamar yanzu da suke can uwar dakan anty maamaa suna
shiryawa,daga sumayyan sai amira sai humaida da humaira,amiran akewa kwalliya an
kusa kammala mata,tayi kyau qwarai da gaske cikin wani irin yadin saqi na fulani
mai azqbar kyau da daukan hankali,saqin fulani je wanda aka zamanantar da shi da
kayan ado dana qawa,maroon ne sosai da yarfin kwalliyar golden a jiki,walwali kawai
take zubawa,ta lura da yadda sumayyan ke yawaita shiru,saka bakinta cikim hirarta
yayu qaranci sosai,hannu ta sanya ta tabota,ta daga kai ta dubeta tana murmushi,da
hannu ta yi mata alamar lafiya,sai kawai ta girgiza kai ba tare data ce komai
ba,duk yadda taso barin zancan da baabaa yayi mata abun yaqi barin
kwanyarta,zuciyarta ta nace da son gano ainihin me maganar tashi ke nufi
"An gama min,saura ke" inji amira tana isa bakin mudubi tana duba kwalliyar
tata,kai ta kada
"Powder kawai za'a shafa min a jamin jagira sun isa" idanu amira ga watso mata
"Bazaiyiwu ba wallahi,kina babbar qawar amarya?"
"Ki barni ayimin hakan don Allah,naga dai yau aka fara abin nan ko?,gaba a yimin"
ta fada tana zama gaban mai kwalliyat,dariya humaida ta saka,yanayi da halayen
sumayyan ke qara bata sha'awa,sam bata da rawar kai ko iyayi irin na 'yammata.

       Duk da cewa ba wani kwalliyar azo a gani aka mata ba amma tashi daya ta
sauya,tayi wani sihirtaccen kyau mai sanyi wanda babu hayaniya a cikinshi,su kansu
sai da suka yaba,biyar da kwata kiran ango saifudden ya shigo wayarta,yake sanar
mata sun iso,da yake tare za'a kama su shi da ita,falon anty maamaan suka sauko
sannan suka hadu sa sauran qawaye da 'yan uwa suka fito.

       Qyashi da hassada fal ran eesha,duk yadda taso taga ta wuce sumayyan a
kwalliya abun yacu tura,ira kadai ta tsone mata duk taton 'yammatan nan,saboda kaf
cikinsu bata ga wadda tayi ya kyawunta ba,duk da yake akwai wadanda suka saka
suturar da suka fi nata kayan qaawa da tsada,amma ba'a nan take ba wai aj dannewa
bodari kai,abinda bata sani ba baki daya sumayyan jinta take a wani mugun
takure,karo na farko a rayuwarta data taba shiga makamanciyar wannan,qememe amira
ta hanata sanya mayafi sai ratayashi kawai tayi gefan kafadarta guda daya,kayan
sunyi masifar amsarta kamar wanda ya saqa su ya saqasu ne musamman saboda
ita,takalmin ne kawai ya gagareta tafiya,subaleshi tayi ta nemi plat cikin na
amiran ta saka,a ranar tayi adon gashinta wanda yasha gyara aka fito mata da shi
cikin daurinta sai sheqi sa walwali yake,ta saje cikin 'yammatan amaryar har ta
zama kamar wata fitila ta daban cikinsu.

        Bata gane wautar data tafka ba sai bayan da suka iso gurin taron,wanda a
cikin gidan aka shirya kujeru rumfuna da decoration na alfarma da kece raini,saika
rantse da Allah wani event center ne mai tsada aka kama,ita ke riqe da amiran amma
sai ta kusa faduwa saboda yadda idanuwa suka mata caaa,idanunta ta lumshe tana
kiran sunayen Allah,ko ina abokan ango ne gogaggu kuma wayayyu tsaitsaye suna jira
a qaraso musu da amaryar,hannun anty huda ta danqa ta sannan ta juya har tana
hardewa saboda ido ta juya,su'adah na tsaye gefan huda din,india ta tafi baki
daya,sari ne a jikinta wanda ya amsa sunansa,sak irin dinki 'yan qasar hindun ne
jikinya skert da 'yar fingilar riga,sai mayafin kayan a jikin skert din ta nannade
jikinta,yayin da kanta ke a bude kamar nasu,sai gashin dokin da aka dinkeshi da
ainihin nata ya tashi tamkar nata,ta rabashi kafadar hagu da dama kakar yadda 'yan
qasar hindun keyi.

     Tana juyawa suka ci karo da anty farida umman husna,bakinta a washe take duban
sumayya
"Wai wai,kunyi wuyar gani,ko diyarki baku hadu ba" murmushi sosai kan fuskarta
cikin girmamawa ta gaida anty farida sanan ta wuce ummee dake cikin gida bata fito
ba ta aikota wajen amiran.

       Wayarta dake hannunta ta dauki vibration sanda amarya ta samu zama a


gurbinta ita da angonta,sunan nafisa ta gani,mamaki ya cikata ganin number dinta ce
ta nijeria,qarar lasifiqan wajen bazai barta taji ba,hakan ya sanya ta soma takawa
don barin wajen tana duban kiran,can baya inda zata iya jin ta ta tsaya ta soma
lalubarta saboda kiran ya riga da ya katse
"Am at home sisi" idanu ta fiddo waje
"Da gaske?"
"Suprise wlh naso baki,shigo gidan anty ki shigo dani yau traditional setting na
amira ina lissafe dama"
"Wayyo sis,gani nan" ta fada cikin zumudi da murna ta kashe wayar,daidai sanda kida
ya soma tashi daga inda ake gabatar da bikin,tsalle ta dan saki kadan farinciki fak
ranta
"Yi a hankali gimbiya kada ki fadi ki batan kwalliyar" abinda taji an ambata
kenan,da sauri ta waiwayo,alqasim ne tsaye sanye da shadda ya kawo hula gaban
goshinsa yana qare mata kallo yana murmushi,daidaita natsuwarta tayi sannan ta juya
da niyyar ci gaba da tafiya,saurin shan gabanta yayi,ya wani karyar da kai
"Haba sumayya,ko gaisawa i kya tsaya muyi ko?" shiru tayi tana dubansa ba tare data
ce komai ba,ji take kawai zai bata mata lokaci ne,bata da buqatar wani abu a
yanzu,tana cewa ta gama da babinsa,tunda tuni ta gaya masa ita din ba budurwa bace
bare ya saka ran zata biye masa,idanunta tarufe tare da yin banza da shi,tana
jinshi yana magana ci kanka bata ce masa ba.

       Tunda suka fara tashin kidan ya tashi ya shiga bathroom ya sake wanka,jin
kidan yake kamar a tsakiyar kanshi,duk wani abu da zai zama tamkar hayaniya bai
qaunarsa,ko qwaqwaran motsi ne ya fiya yawa yanzun zai dameshi,sau tari babban
wansi adam kance
"Kai ko mustapha kamar mai aljanu,koyaya motsi yake sai ya dameka" amma hakan bai
rasa nasaba da ciwon kan da yake fama da shi tsawon shekaru,wanda idan ya tayar
masa baya masa ta dadi.

         Ta baya yabi don bai muradin haduwa da kowa bare a tsaidashi a cikashi da
suruti,baki daya yau zucuyarsa a quntace take,saidai ko kai daka sanshi baka isa ka
fadi hakan ba,sakamakon yadda ko yaushe haka fuskarsa take a daure koda cikin
farinciki yake indai ba girmama farincinkin yayi ba shine zaka ga fuskar ta sake
washewa fiye da yadda take da,yatsanshi saqale yake da maqullin motar da yake
sha'awar fita cikinta,tun kafin ya shiga wankan ya turawa P.A dinsa ya shirya
haduwarsa da mutanen da yace jiya bazai samu damar ganinsu ba qasa da awa daya yana
hanya kada su wuce haka,sannan ya turawa driver dinsa shima ya shirya motar da zai
fita,kanshi a qasa yake takowa cikin shigarsa ta qa'ida trouser da t.shirt v neck
wanda ta fidda structure ta jikinsa sosai,kwata kwata saka manyan kaya bai cikin
tsarinshi,duk wanda yasan mustapha cikin duniyarsa yasan ba ma'abocin sanya manyan
kaya bane,kana iya gama mu'amalarka kaf da shi baka ganshi da manyan kaya ba,daidai
gun da jiya suka zauna wasa ya tuna,yaron ya fado masa,ya tuna shegen wayonsa,wani
qaramin murmishi da bai shirya masa ba ya kubce masa,a hankali ya daga kanshi sai
ya hangosu,tsaye yake a gabanta yayi kane kane kamar zai hade gaf din dake
tsakaninsu,yayin da take tsaye hannayenta harde a qirji tana dubanshi,rashi ya
baci,dan salaman da ya samu ta gushe,yana daya daga cikin abinda yasa kenan baison
baqin 'yammatan cikin gidansu,yana zaton daga daga cikin 'yan matan family din nasu
ne,sauya akalar tafiyar tasa yayi zuwa wajen,sai da yaje dab ya lura alqasim ne
"Itakam haka take,gobe wancan mutumin jibi wannan?" Ya qarasa bayansu,daidai sanda
take fadin
"Na riga na gama magana da kai ko?,ba zaka taba samun abinda kake so ba,so don
Allah ka qyale rayuwata" ta kammala fadi sannan ta juya a hankali ta soma barin
wajen,burinta kawai ta isa ga nafisan gashi ya bata mata rai da lokaci baki
daya,binta yayi da kallo har sai data bacewa ganinsa sannan ya juyo yana sakin
ajiyar zuciya,sai suka hada idanuwa da mustaphan yana kallonshi,kunya ta
kamashi,yana bala'in ganin girman almustapha da mutuncinsa,girmama shi yake qwarai
da gaske,ya dan diririce yana fadin
"Barka da fitowa yaya" bai amsa ba ya qara taku zuwa inda yake yana dubanshi,haushi
yakeji,hashi ya kamashi,ji yake kamar shi akawa haka
"Kan me ka tsaya mace na gaya maka irin wannan maganar ibrahim?,kai namiji ne ka
manta?,so kayi maintaining dignity dinka,akwai mata da yawa a gari ka zabi wata
mana,kar ka cusa kanka inda ba'a sonka,ba'a so dole,i hope ka fahimta?,ba ita daya
bace mace akwaisu da yawan gaske" kai ya rusuna yana gyadashi alamun gamsuwa,cikin
zuciyarshi yana cewa
"Ya mustapha kai baka hango abinda na hango ba,baka hango personalityn dana gani
tattare da ita ba,hmmmm ke ka ganin so wani abu mai sauqi ne tunda kullum cikin
neman son ake a wajenka"amma a fili sai yace
"na gode,Allah ya qara girma" kai ya jinjina ba tare da yace komai ba ya juya ya
bar wajen.

      Kamar ta goya nafisa haka taji lokacin data ganta,tayi ado sosai tana rungume
da khalid,ta amshi khalid din kai tsaye suka koma wajen da ake kamu,sanda suka je
tuni al'amura sun fara nisa,bayan gabatar da abubuwan da suka dace sannan aka kama
amira kafin daga bisani a bada damar yiwa amarya da ango liqi,basu suka tashi daga
kamun ba sai qarfe takwas na dare,kamu ya qayatar matuqa da gaske,tafiya nafisa
tayi bayan sun gaisa da amira sama sama,taso riqeta tace a'ah tayi haquri abban
khalid din ya iso,saidai zata zo dinner insha Allah wanda za'ayi ranar alhamis.

       Washegari akayi arabian night wanda aka gabatar da ita itama cikin gidan
baabaa prof,gidane gari guda hakan ya sanya basu da damuwar sai sun kama waje,ba
qaramin qawata wajen akayi da kayan ado ba,ranar duk wani ahali da ya shafi baabaa
prof sanye yake da abaya ta mata,maza kuma doguwar riga ce da hirami,kai ka rantse
a ranar baqin larabawa aka yi a unguwar.

 ******* ****** ********     

Washegari tana kwance tana baccin gajiya,kasancewar alhamis ce ranar babu event din
da za'a yi sai gobe idan Allah ya kaimu,ji tayi an daka mata duka,tilas ta farka
tana mutstsike idanu,amira ce zaune gefanta
"Sannu,ai wallahi bacci bai ganki ba bai kuma kamaki ba,qarfe hudu zamu lunching na
maman saifullahi,kuma ba kowa ne zashi ba,bamu da yawa" zama tayi sosai tana hamma
hannunta kan bakinta
"Shine zaki dakamin wannan dukan,badon inajin kunyar idanun saifullahi ba sai na
rama" dariya ta qyalqyale da ita
"Ato bismillah,ni kinga ina da mai ramamin,ke kuwa nasan ko na dakeki na daki
banza,waccan mutumin da na gani a kano babu abinda zaya iya" ta sani sarai da abdur
rahman take,bata san meye hadinta dashi ba data saka masa tsama haka da yawa,harara
ta jefa mata sannan ya shiga bandaki ta wanke bakinta ta dawo ta amshi katin tana
dubawa,komai a tsare yake harda dress code na maza da mata,mata shigan baqi zasuyi
maza shigan fari.

        Kusan baki daya kayanta sai data baje su saman gado,ta rasa wanda zata
zaba,a haka anty dije ta cimmata,dariya ta dinga yi mata
"Ato wallahi gwara ki qure adaka,don suma dangin saifullahin ba baya bane"sai data
gama ruwan idonta sannan ta zabi wani shegen lace a cikin kayan wanda yake baqi ne
an masa adon ja mai daukar idanuwa,zuba kayan tayi a jaka don ta nufi gidan baabaa
don amira na can na jira,sanda ta isa an gama mata kwalliya,tayi masifar kyau cikin
baqar wedding gown,sumayyan zama tayi itama aka soma yi mata tata.

         Wani irin sihirtaccen kyau ke fita daga kwalliyarta hadi da tsumammen


qamshi,kunya ta kamata da mamakin kanta,riga da skert ne wanda suka fitar da baki
daya qirarta gaba da baya
" wow"abinda amira ta dinga fada kenan tana qarewa sumayya kalo
"Haka baqin kaya ke miki kyau amiran umman khalipha?,ya Allah" kai ta kada
"Ai kam cire kayan nan ya zamemin wajibi,ina zan iya fita cikin jama'a haka amira"
ta fada tana yunqurin cire daurin dankwalin da aka bata lokaci ana mata shi,da
sauri amiran ta riqe hannunta tayi kicin kicin da fuska
"Allah idan kika cire sai mun bata,ke komai ma bakison ya miki kyau,kina da kyau
kina da aji kina da isar da za'a dama dake,kibar yin haka don Allah" yanayin yadda
tayi maganar ta bata dariya,sai ta zame hannunta tana hada mata kayayyakinta data
yi amfani da su kasancewar yau cikin dakinta ta shirya
"Bari na maida su sashin anty maamaan ko"
"Godiya namescy na" murmushi tayi ta fice a dakin.

       A shirye ta tadda anty mamman,kasancewar ita zata yiwa amiran rakiya,wani


irin biki suke a tsarin familynsu,suna gayyatar amarya ne da manyan yayyenta da
iyayenta,inda zasu kawo musu ita suyi mata nasu bikin ma musamman haka sukeyi,ta
ajjiye kayan tana saukowa suka sake kacibus da anty maamaa wadda ke kai kawon
hadawa baabaa kunun alkama,haka matan suke,duk rintsi basa wasa da cikin mijinsu
"Amiran umman khalipha zo don Allah ki kulamin da kunun nan in qarasa hadawa
babanku hadin salad din nan"aladabce ta asawa ta bita kitchen din,cikin sauri sauri
take hada komai saboda lokacin tafiya yayi,sau uku amira na aikowa sumayyan tazo su
tafi,antyn bata sani ba,sai ana hudu taji aiken da ake mata ta dubeta
"Jeki amira,na qarasa na biyoku daga baya" murmushi tayi tana noqe kafada
"A'ah anty suje kawai,ma taho".

     Cikin mintuna talatin suka gama,babu abinda jikinta yayi,saboda haka goge
hannunta kawai tayi,sannan ta fidda kwalakcarta ta goga a hannayenta,ta sake shafe
jikinta da turaren humrarta mai fidda wani sihirtaccen qamshi,wayarta dake ruri
anty maman ta daga ta kara a kunnenta sannan tace
"Eh na gama,gani nan" ta dubi sumayya tana maqala kyakkyawar jakarta
"Muje ko amira" ta amsa.

       Tuni maman ta rigata yin gaba saboda hill shoes din dake qafarta wanda ya
sake sauya yanayin tafiyarta,sannu a hankali take takawa,sai ka dauka wani salon
tafiya ce ta daban,koko tsabar yanga ce da iyayi ga wanda baisan takalmin ne ya
takurata ba,baqar rantsatstsiyar mota ce wadda har sheqi take da daukan ido saboda
tsabar sabunta da kyau,ita daya ta rage tsaye a wajen,da alamu dukka an tafi,baya
anty mamaan ta bude ta shiga,yayi kyau cikin farin qal din trouser da lallausar
short sleeve t.shirt baqa mai adon fari a jiki,wadda ta fidda sirrin hannunshi na
tarin gargasa wadda ta kwanta har saman tafin hannunshi,da wani sashi na murdadden
dantsensa wanda kana gani kasan ya saba daga qarfe,daya daga cikin abinda ya sanya
kenan bai fiya saka kaya masu gajeran hannu ba,black hight top snickers ne a
qafarsa,tsintsiyar hannunshi daure da agogon fata na kamfanin gucci mai matuqar
tsada da kyau,yadda jikinsa ke fidda wani sihirtaccen qamshin wani turare da
mawuyacine ka gane wani iri ne haka motar ki fidda sanyayyan qamshin freshner,komai
nasa mai kyau tsafta da aji ne,jin yana niyyar tayarwa ya sanya tace
"Tsaya,akwai mutum daya" a kasalance ya kashe motar,ka kadan baison tuqi da kanshi
idan ba kamawa tayi ba kamar irin hakan,qarasowa tayi tana niyyar bude bayan anty
maamaa tace
"Koma gaba amira" don tasan halinshi sarai,ya tsani ya dauko mutane su shiga baya
baki dayansu,yana alaqanta hakan da sai driver,jin an ambaci sunan amira ya
sanyashi juyowa,daidai sanda take daidaita zamanta gaban motar suka hada
idanu,idanuwanta suka fada cikin nashi,tashin farko kowanne ya janye
idanunshi,qirjinta na bugawa,qamshin turarenshi na ratsa qofofin hancinta,idanunta
ta ragewa girma tana duban gaban motar,tana ji kamar ta zura da gudu ta bar
motar,wani dabaibayi taji na daureta,kwarjininsa ya mata yawa,tana jin zamanta a
bigiren bai dace ba,a kasalance ta sanya hannu zata rufe murfin motar taji kamar
muryar laila na kiran sunanta,itace tafe riqe da hannun abdallah da yayi kyau cikin
baqaqen suit na yara,sai baqin sau ciki na yara da baqar safa baki daya,suka qaraso
bakin motar inda take zaune
"Anty,mami tace na kawo miki shi,kuka ya soma yaqi zama" dubanshi tayi cikin sigar
lallashi
"Abdallah,ina cewa na gaya maka tun dazun bazanje da kai ba,ka koma gida ka zauna
da su laila,yanzu zan dawo bazan jima ba" qafafunshi ya sa bubbugawa yana sakin
kuka sosai kamar wanda ake yanka yana fadin
"Allah ni sai naje" ranta ya baci ganin yadda yake tsala kuka kamar tayi mishi wata
uwa,sake lallaminshi tayi baiji na,maimakon haka ma sai ya buge hannun laila ya
taho inda take ya shigo sit din da take,abinda bai taba yi ba kenan,yana qarasowa
kuwa ta daga hannu ta kai masa mari,ta kuwa sameshi gefan fuskarshi,kafin anty
maama ta furta maganar daga bude baki zata yi wata tsawa ta karade motar,tuni laila
ta ja baya a tsorace,hannunshi ya miqo inda suke ya janyo abdallah wanda ke sakin
kuka cikim jim zafin marin ya dorashi kan cinyarshi yana shafa inda ta mareshin
"U r very stupid,how dare you zaki mari qaramin yaro har haka?,saboda bakisan
ciwonshi ba?,bakisan ciwon haihuwa ba?,idan baki iya riqeshi mai ya sanya ba zaki
sa a maidashi wajen mamarshi ba,fice min a mota!" ya fada cikin bacin rai da zafin
rai,bata ankara ba taji hawaye sun soma layi bisa kuncinta,ji take kamar mukhtar ke
mata fadan,me ya fusata ta ta mari abdallah itama bata sani ba,hannunta ta sanya
kan mabudin motar ta tura da niyyar fita anty maamaa ta dakatar da ita
"A'ah zauna,kuyi haquri mutapha,baki kyauta ba amiran umman khalipha,saurin hannu
wa yaro bai kamata ba,ki kiyaye gaba"
"To maamaa" ta fada ba don taso ba ta koma ta zauna,so tayi ta qyaleta ta fita,wani
nauyi taji zuciyarta tayi,tana jin hucin numfashinsu su biyun.

      Luf abdallah yayi kan cinyar mustapha wanda ya zaunar da shi suna facing juna
ya rungumeshi cikin jikinshi yana ci gaba da shafa inda tayi marin,ci gaba da
kallonshi abdallahn yayi,a hankali ya furta
"Abba!" Sannan ya sake narkewa cikin jikinshi,wani nauyi zuciyarta ta sake yi,sai
ta kasa daurewa ta sanya kanta a tsakiyar qafafunta,tausayin abdallahn yasake qara
yawan hawayen dake fita a idanunta.

        Bubbuga bayan abdallahn yaci gaba dayi kadan kadan har sai da yaji alamun
ya huce,hannun ya sanya gefanshi ya ciro gorar ruwan da ya dauko da niyyar sha ya
bude mishi ya saka mai a baki,sai da yasha sosai sannan ya rufe ya maidata
gurbinta,ya sake zaro wayarsa ya latso wasu lambobi ya kara a kunnenshi yayi magana
a taqaice
"Eh,ka sameni gidan,ka tambaya adress din" ya katse kiran ya ajjiye,tada motar yayi
sannan ya ya jata a sukwane abdallah na kwance jikinsa.

        Shiru ne ya ratsa motar ba wanda ya sake magana,sumayya na kife har yanzu


kan cinyarta tana qoqarin control din hawayenta,ambaton sunayen Allah ta dinga yi
daya bayan daya har ta samu hawayen suka tsaya saidai bata iya dagowa ba har suka
isa wajem,anty maamaa ce ta soma fita,tuni tayi gaba saboda suna isowa taji ana
nemanta ta lasifiqar dake cikin wajen taron.

       A hankali ta daga kanta ta gyara yafen mayafin dake kanta sannan ta bude
murfin motar ta fice,ta gefan ido yake dubanta har ta bace a wajen,gajeran tsaki ya
ja,yana jin bazai iya ci gaba da zama a wajen ba,daga yarin yayi ya dubeshi har ya
soma bacci,sai yaji tausayinshi ya kamashu,haushinta ya sake qumeshi,cikin
zuciyarshi ya dinga masifa shi kadai,bude motar yayi ya saba abdallah a kafadarsa
suka koma sit din baya,kwantar da shi yayi sannan ya zauna gefansa.

       Tana tsaye bakin get din gidan jingine jikin motarta hannunta harde a
qirjinta,sam wajen bai dace sa tsarinta ba kasancewar a gargajiyance suka tsara
komai,bugu da qari ranta a jagule yake,yadda almustapha ke ninka nuna hakin ko in
kula da lamuranta,shigowar motar yaso ya dan ja hankalinta kadan,saboda irin motar
mustaphan da take mutuwar so,wadda a yau ita taso hawa amma yaqi bata hadin
kai,dauke kai tayi daga kallon motar don kada ta zubda ajinta,a dauka 'yar
matsiyata ce kamar yadda take rayawa a ranta,ganin fitowar anty maamaa daga ciki
shi ya sake maida hankalinta kan motar
"Kada dai ace almustaphan ne?,yazo ya dauko maamaan a ciki amma ni ina matsayin
matarsa ya watsan qasa a ido?" Take raya haka a ranta tana qarewa motar kallo,bata
jin mustaphan ne,don tunda itama yaqi daukota ya kawota tabbas babu wanda zai kawo
koda kuwa iyayenshi ne(a tunaninta),ita kanta motar bai taba hawanta ba sai
yau,hakan yasa ta yin kwadayin ace ita ya fara dauka a ciki,mutum ce ita mai son
taga tafi kowa,komai a gunta aka fara ganinsa,bata gama wannan tunanin ba sumayyan
ta bude murfin motar itama ta fito cikin salon wata tafiya da zaka tsammaci ta
yanga ce,saidai tsabar kasala quncin zuciya da tsinin takalminta ya haifarwa da mai
kallonta ganin cewa yanga take kai tsaye,wani bala'i ne ya dirarwa zuciyarta,take
ta tattara kallonta baki daya a wajen,ci gaba tayi da kallon sumayyan wadda sam
hankalinta bai wajen taci gaba da yi har ta wuce,zuciyarta na tsaka da bata
shawarar zuwa ta duba matuqin motar don tabbatar da cewa mustapha dinta ne cikin
motar ko wani ne daban mai farcen susa ya yaci nasarar mallakar irin motar mijin
mata,hutassheta akayi saboda fitowar da yayi ya koma gidan baya yana sabe da
abdallah,ta gane yaron,yaron data cuccusawa zagi jiya da daddare saboda ya gyara
mata gyaran alwalarta,huci ta soma fitarwa saboda wani zafi da taji qirjinta yana
yi,me kenan?,me hakan ke nufi?,ba bata lokaci ta soma takawa zuwa bakin motar.

      Bude murfin motar tayi sannan ta cusa kai cikin motar kai tsaye,hannunshi na
saman kan abdallah yaji shigowarta,juyowa yayi ya dubeta sannan ya dauke kai yaci
gaba da abinda yake kamar bai santa ba,ta sani sarai bazai tanka mata ba idan in
zata shekara matuqar ba ita tayi magana ba,ko ita din tayi bata da tabbacin amsarsa
"Tsakani da Allah ka kyauta kenan man,naci burin hawa motar nan ka watsan qasa a
ido amma sai naga ka kawo wasu,har wata banza can ka baiwa damar zama gefanka wanda
ni kadai ke da wannan matsayin?" Ta fada cikin son dai daita fushinta don kada ta
fita daga hanya ta jawa kanta wani sabon lamarin,ta san duk sabida zancan qarasa
karatunta ya sake zame mata wani badadde,ilai kuwa shiru ne ya biyo baya,kishin
sumayya data gani yaci gaba da mintsinin zuciyarta
"Wai shin ma meye alqarka da ita waccan yarinyar da har ta samu matsayin daukota
cikin motar da koni ban taba shigarta ba,sannan ko kai kanka yau ka fara shigarta?"
Bai da ko niyyan waiwayowa ya dubeta bare ta saka ran samun amsa,wayarsa ce tayi
tsuwwa ya saka hannu inda ya ajjuyeta ya dauko yana dubawa tare da amsa kiran da ya
shigo din
"Bude ka shigo a bude take" ya gayawa drivern nasa a taqaice,dama shi yake
jira,sauke wayar yayi still bai dubeta ba yace
"Idan kin gama kina iya sauka ko?"wani abu ya tokare mata wuya,sai ta zuba ido tana
kallonshi,sonshi kamar ta lasheshi,haushi kamar ta hafiyi zuciyarta,idanunta ya
cika taf da qwalla,cikin rawar murya da son karya lagonsa da kuka ta soma cewa
" ni kake ma haka mustapha?"hannu yayi saurin daga mata wanda dole ta shanye sauran
maganarta,sai ta bude murfin ya fice da hanzari,budewa drivan yayi ya shiga cikin
girmamawa ya russuna bayan ya zauna ya gaidashi,a taqaice ya amsa mishi,sai da ya
tayar da motar suka bar layin suka hau kwalta sosai sannan cikin girmamawa yace da
shi
"Ranka ya dade ina zamuje?"
"Maitama" ya bashi amsa a taqaice,baice komai ba ya qara gudun motar suka lula
titi.

         Sosai lunching din ya qayatar,ba qaramin qauna iyalin saifullahi suka


nunawa amira ba,basu tashi ba sai qarfe bakwai na dare,wannan karon tare da su
amiran suka koma,saidai ko kadan bata da walwala,a takure take jim zuciyarta baki
daya,hatta da amiran ta lura,amma bata ce mata komai ba saboda ta tambayi anty mama
abdallah taje gaya mata abinda ya faru,ana saukesu ta dubi amira
"Kimin afuwa zan wuce gida sai gobe,kaina ke mij ciwo sosai" ba qarya take ba da
gaske kan nata ciwo yake mata,sai ta daga kai
"Na miki,Allah ya bada lafiya,ya tashemu lafiya" ta bude murfin motar ta fice.

        Wanka ta fara yi sannan tayi sallolinta,anty dije tace mata ga abinci tace
sai anjima,duka abinda take hankalinta bai wajen yana wajen abdallah,ina yake?,ina
ya kai mata shi,tun tana kasa kunne da ido har ta kwanta saidai shiru kake ji,kasa
haquri tayi ta miqe da hijabin sallarta ta qwanqwasa dakin anty dije ta mata izinin
shiga,kwalliya ta tadda ta tanayi
"Uhm,ya akai amara qirjin biki" murmushi ta danyi wanda yafi kama da yaqe
"Anty wannan yayansu amiran ya amshi abdallah tun dazun,har yanzu ban ganshi ba
bashi ba abdallahn" cikin ko in kula tace
"Wa?,wai musty,kada ki damu kisa a ranki kamar kina tare da abdallah ne,ai mayen
yara ne,indai mustapha ne a rina" hankalinta ya dan kwanta da jin hakan,sai ta koma
daki tayi shirin kwanciya,don ita kadai take da buqata a yanzh,tun tana sauraren ta
ina abdallahn zai shigo har bacci ya sureta.

         Washe gari sam bata shiga gidan ba ma sai da yammaci tayi aka soma shirin
tafiya dinner,nan ka bata ga abdallan ba,ba kuma wanda ya mata maganarsa,haka taci
gaba da daurewa har sanda anty maamaa ta dan tsokaneta
"Abdallah kam anyi wuyar gani anyi sabon daddy" murmushi kawai ta danyi ta basar.

       Wani qayataccen event center suka kama,hmmm masu abu da abinsu,kada kaso
kaga yadda gun ya qawatu yayi matuqar tsaru,ranar sumayya anyi abun gani,ita ta
zauna mazaunin babbar qawar amarya,tayi komai yadda zata faranta ran amiran duk da
a takure take matuqa,idanuwan maza bisa kanta sunyi yawa,kai har ma wasu daga cikin
matan,sai da guri ya gama tumbatsa sannan su'adah ta iso,a nan tayi burgar data
saba,tsakiyan abokan ango cikin dinkim riga da skert na wani shegen leshi mai
azabar tsada wanda aka ci mutuncin tsadar tasa aka yi masa dinki na ganin
dama,tsagar skert din har kusan gwiwarta,dinkin ya kamata dam,banda dankwalin da
aka tsarawa dauri babu komai a kanta,don ko tuna sunan mayafi bata yi ba,liqi ta
shiga yi da 'yan dubu dubu sabni kar wanda ita kanta bata san nawa ta barar ba,abin
nema ya samu ta dauki idanuwan jama'a,ta kuma qona zukatan 'yan baqinciki wadanda
bas son tarayyarta da mustapha,to su gani ya tsaya mata,sai data yi mai isarta
sannan ta sauka daga step din ta koma mazauninta.

Sai sha daya na dare aka tashi kowa ya koma inda ya fito.

*******    *******    ******

        Tun qarfe goma na safe layin nasu ya tumbatsa ya dinke da jama'a kasancewar
goma da rabi ne daurin auren,bacci ranar tayi sosai dakin anty dije,bata tashi
farkawa ba sai qarfe tara da rabi na safe,tarin missed call ta taras duka na
amira,da hanzari ta miqe ta fada toilet tayi wanka,a gurguje ta fito ta shirya
cikim shaddar da sukayi anko wadda tayi masifar haduwa,kamar yadda dinkin doguwar
rigar ya dace da jikinta,komai da tayi amfani da shi kalar zaren da akayi aikin
shaddar da shi ne,ta fito fes mashaAllah,daidai sanda laila ta shigo,baki ta sake
tana kallon sumayyan,ta qaraso dakin ta samu bakin gado ta zauna
"Wai dama don Allah anty sumayya haka kike da kyau" dariya yarinyar ta bata saboda
bihaqqi ta fada
"Sai an tambayo" ta fadi hankalinta ka can gidan baba,saboda hayaniyar data dinga
jiyowa na tashi ta tabbatar layin yayi tumbatsar da babu damar ta fita,valcony din
saman benan anty dije ta bude ta fita ciki,layin ya shaqara da mutane ya cika masha
Allah,kai ta dinga kadawa don tasan dole ta haqura har sai an ragu.

Kujeta ta ja ta zauna daga gefe yadda zata iya hango komai,ta bude wayarta ta
soma lalubar lambar amira don ya bata uzurinta,hakanan taji yana yinta ya soma
sauyawa kamar ba ita daya bace a gun,kamar fisgar mayen qarfe haka idanuwanta suka
jata zuwa inda yake tsaye tsakiyan wasu zaratan samari kamarshi.

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

7⃣2⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*


*ALLAH YANA GAFARTAWA WANDA YASO YA KUMA AZABTAR DA WANDA YASO*

YA ALLAH KA GAFARTA MANA


___________________________________

*TAB,BIGI SAI BIGI,BABBAN GORO SAI MAGOGIN QARFE,IDAN KAJI WANE BA BANZA BA,INA
MA'ABOTA KARATUN LITATTAFAN HAUSA,KAMA DAGA NA QUNGIYAR HASKE HARMA WANDA BA NA
HASKE BA,SHIN KUNA DA BUQATAR JIN WANI SABON KUNDI WANDA YA TATTARE LABARAI NAU'IN
DABAN DABAN WADANDA SUKA SHAFI AL'AMURA NA ZAHIRI DAKE FARUWA CIKIN RAYUWARMU TA
YAU DA KULLUM?.......TO MAZA KU GARZAYA KU NEMI LITTAFIN KUNDIN HASKE,WANDA KE
QUNSHE DA LABARAI DAKE DAUKE DA NAU'IN RAYUWA IRI DABAN DABAN,LABARAI NE WANDA KE
DAUKE DA DIMBIN DARUSSA MASU RATSA ZUKATA,DUMBIN ILIMI MAI JAWO HANKALIN DAN ADAM
ZUWA SAKE LURA DA GYARAN RAYUWARSHI,MAZA KA/KI GARZAYA KADA A BAKI LABARI,BA SHAKKA
ZA'A CI DA RABONKI MATAUQAR KIKA BARI YA WUCEKI,AKWAI SHI A WATSAPP DA APP DIN
WATTPAD BAKI DAYA*

*SADAUKARWAR WANNAN SHAFIN GA:*

*SADIYA ZABURA*
*UMMU RAMLAT*
*MAMAN SAYYID*

*DA MARUBUCIYA*

*AYSHA DAN SABO*

*RABBI YA BAR QAUNA*🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽😍😍😍

       Kyawawan idanuwanshi wanda suka wadatu da gashin idanu kamar yadda girarsa
take masu kama da na wanda ke jin bacci suke kan ta,shi daya ne tak sanye cikin
qananun kaya sabanin dukka sauran wadanda suke tsaye tare,baki dayansu shadda ce
jikinsu dinkin tazarce kaloli daban daban,kusan tare suka janye idanuwansa,gabanta
ya shiga faduwa,kasa zaman wajen tayi,batasan ana iya gajin mutum ba,gashi ko
mayafi babu a jikinta,sai ta miqe jikinta na rawa gabanta na faduwa ta bar wajen,ta
tura qofar ta kulle ta dawo cikin bedroom din anty dijen.

      Gefan gado ta kwanta rub da ciki tana sauke numfashi,maganganun baabaa suka
soma dawo mata,har yau ta kasa gane me yake nufi,tana da buqatar qarin bayani,tana
buqatar taimako wajen wanu ko zata fahimci me yake nufi,amma ta taimaka masa wajen
gyara rayuwarsa kamar yaya kenan,wanu mummunan abu yake mara kyau yakeso ta saka
baki?,amma ita a wa?,bata da wannaj power din,ganin qwaqwalwarta na neman daurewa
yasa ta kada kai tare da yin watsi da maganar,maimakon ci gaba da tunani sai ta
sake daukan wayarta ta lalubi zainab ta kirata,din jiya suna wajen dinner taga
misscall dinta baya kuma samu ta bita ba.

        Bayan sun gama gaisawa da mama ta musu Allah ya sanya alkhairi zainab ta
karba,nan take gaya mata jiya aka kawo lefe sati uku kuma aka sanya,murmushu
sumayya ta saki tana tsokanarta
"Kice mu fara shirin tahowa kano ko?"
"Wallahi yaya,kizo ayi tsare tsare masu kyau"
"Insha Allah,ina huce gajiyar wannan bikin zaki ganni,Allah ya nuna mana da rai da
lafiya"
"Amin yaya,ina abdallah na"
"Uhmm,ni kaina bansan ina yake ba,yana gidan biki"
"Ki gaisheshi tunda ya manta da mu" dariya ta danyi
"Zaiji,ki gaidan halimaty,wayarta bata shiga"
"Zata ji" suka katse wayar.

       Tana sauke wayar ta jiyo muryar abdallah yana karadi daga qasa shi da sh
hafiz,sauka tayi daga gadon ta sauko qasa,yayi masifar kyau cikin wata arniyar
shadda ash wadda batasan inda ya samota ba,hulace kanshi zanna wanda sau faman zuba
qyalli take,qafafunshi saye da takalmi sau ciki,abinka da uwa da da,yana ganinta ya
tako da gudu ya daneta,murmushu tayi ta zube saman kujera yana faman zuba mata
surutu da bata labari.

        Ganin sha daya tayi ga gidan babu kowa sai ita ya sanyata yin shahada ta
yafa mayafinta ta fito,kamar zata nutse haka ta dinga ratsa mutane a darare tana
wucewa har ta kai ga cikin gidan bayan ta kira humaida ta gaya mata inda suke,ko
ina harabar gidan 'yan uwa da abokan arziqi ke kai kawo,kowa ka ganshi cikin
kwalliya da walwala,daga gefe guda ta hango mahmoud da tarin abokansu ciki har da
alqasim,suma sun ganta saboda haka ta qara sauri don kada su rusketa.

       Batayi aune ba sukayi karo kanta ya daki qirjinsa,tayi taga taga ta komo ta
fada qirjinsa,zuciyarta kamar zata fito saboda tsoro,tayi yunqurin janyewa,ta samu
nasara saidai hannunta na cikin nashi hannun yana duban qwayar idanuwanta,sai yanzu
ya samu amsar inda ya samu qamshin da ya buwayeshi tun shekaran jiya,wanda har kuka
su'adah tayi sabida jin qamshin,don ta tabbatar hadin humra ce ta mata ta musamman
ba turaren namiji bane,gaba ta tusashu tana tambayarsa ina ya samu turaren,baki
daya zuciyarta ta gama zayyana mata yana neman wata ne,idan banda haka ina zai samo
turaren mace a hannunshi?baya ga haka ta lura wannan karon sam baya marmarinta,baya
nemanta idan ba ita ta buqata ba,bayan a baya ta sani cewa duk sanda suka hadu har
sai ta gaji ta hada kayanta ta gudu yake qyaleta,amma wannan karon sam ba haka
bane,yana jinta yayi mata banza ya gama shirin baccinsa ya kwanta tare sa juya mata
baya,don bashi da amsar bata,shi kansa yana jin qamshin cikin hancinsa amma baisan
inda ya sameshi ba,baijin zai iya bata lokacinsa ya mata wannan bayanin tunda har
tana zarginsa,to ta dauki duj hukuncin da take gani zata iya dauka,hakan ya sake
hassala zuciyarta,itama ta shiga fushi da shi gadan gadan miqe ta fice ta sauya
dakin kwana,bata san cewa ba shi ta yiwa ba kanta ta yiwa,tunda ba yau farau ba da
yake kwana shi daya tamkar gauro,idan da sabo ai ya saba.

       So take ya sakar mata hannu ko don idanuwan mutane da ke kai kawo a


wajen,uwa uba ga haramci na riqe mata hannu da yayi,tayi yunqurin zame hannun nata
amma abu yaci tura yana tsaye qyam yana dubanta,babban goro sai magogin qarfe,ya
kusa lullube tsahonta baki daya,dududun nata tsawon bata fi iya qirjinsa ba,ga wani
kwarjini daya cika wajen,ganin masu wucewa sun soma ankara ya sanyata cewa
"Ka sakar min hannu" cikin izza da motsa labbansa
"Saikin gayan abinda ke baki tsoro,me ya koroki bayan kowa na kai kawo a nutse amma
banda ke?" Daga fararen idanunta tayi ta watsa mishi su,duk da yadda qirjinta ke
bugawa,lumshe idonsa yayi ya bude ya janye nashi idanun daga kallonta,bai taba
ganin mace mai farin qwayar idanu ba kamar haka ya raya a ransa,tsaki yaja a fili
sannan ya saki hannun nata
"Ki kula next time,ban son irin wannan shirmen" ya fada yana duban gefanta,ita ke
shirmen ma?,abun ya bata haushi,sai ta banka masa harara ta gefan ido duk da yadda
gabanta ke faduwa qasa qasa tace
"Kaima sai ka kula tunda kana da idanu ai ba ni kadai ke da idanuwa ba" batasan
tayi kuskure ba saboda kaifin ji da Allah ya hore mishi,ko yaya magana take yana
iya jiyota,yana daya daga cikin wadanda Allah ya yiwa baiwar ji,har wani lokaci
ba'a iya gulmarsa matuqar yana cikin gidan,har yayi gaba ya juyo a mamakance yana
dubanta,karo na farko kenan da wata 'ya ta taba maida masa magana,bakinta ta
murguda duk don ta sake bashi haushi tayi gaba abinta,wani abu ya tsaya mishi a
rai,ranshi ya baci,yau shi akewa rashin kunya?,abinda yafi tsana kenan a rayuwarsa
tun lokacin quruciya,abinda ya fara hadashi kenan da su'adah tun tana
qaramarsa,lallai zaiyi maganinta,wace ita da har take jin karanta ya kai
tsaiko,babu shakka sai ya hukuntata.

      A bangaren anty maamaa ta tadda su,tana zaune tsakiyar yayunta anty farida da
anty huda da matan yayyen ta ni'imah da fahariyya,sai qawayenta da cousins dinta
irinsu eesha humaida ummu salma da sauransu,a hankali ta qaraso saboda lasalar da
take ji cikin jikinta tana karbar saqon harara daga amira,duk da haka murmushi ne
kan fuskarta,ta riga da ta sani itace mai laifi,sauran da suka san mekw faruwa
dariya suka dunga yi sunsan za'a kwashi daramer,amma sai sumayya ta kashe mata
gwiwa da fadin
"Ta zama ta saifullahi,ayya yarinya zata bar gida" ai kuwa sai ta soma qwalla,tana
dariya ciki ciki ta qaraso ta zauna gefanta ra mata rada a kunne ma tsawon minti
biyu,sau gani sukayi ta saki dariya tana share hawayen,huda ce taja tsaki
"Au qaryar banza,dama fa son aurenta take 'yar banza bansani bane,saifullahin da
ake ji da shi kamar a lashe mishi mazaunai" dariya ta kamasu baki daya,dqi dai da
dai dai sumayya ta bi ta gaida kowa,batasan matan yaya adam ba sai lokacin ni'imah
da fahariyya,fahariyya ita ta fara tahowa ni'imah ta jira maigidan sai jiya suka
taho tare da daddare,bata ga fahariyyan ba saboda 'yar jin kaice itama kamar yadda
amira ke gaya mata,ni'imah din ce babu ruwanga,hakanan take haquri da halayyar
fahariyya na goranta mata da take lokaci lokaci akan rashin haihuwa,saidai zaman
nasu babu yabi ba fallasa,rashin mutuncin fahariyyar da sauqi sakamakon cewa adam
din tsayayyen namiji ne,bai yarda a wulaqanta masa uwar gida ba,sam basa shiri da
su'adah da fahariyya saboda kowacce na jin kanta da jin cewa ta isa saidai daya
tabi daya,duk da a zahiri duk cikin yaran gidan babu wanda ke da dukiyat
almustapha,wannan ya qara kishin su'ad cikin zuciyar fahariyya,itakam ni'imah 'yar
babu ruwa na ce,ta kama mutuncin kanta,don iyayenta ba wasu bane rufin asirin Allah
ke garesu,sai a yanzu da tayi dace da miji na qwarai suke samun sauyin rayuwa
sanadiyyarsa,duk da haka dama tana da managartan halaye wadanda su suka fusgi adam
zuwa gareta,duk da tarin yaran masu kudi dake sonshi a lokacin,ta kasance ta daban
a gunsa har a yanzun duk da bata taba haihuwa da shu ba,sakamakon haquri biyayya da
tsantsar iya zamantakewa da miji mai tafiyar da hankali.

        Da daidai suka miqe suka fice ya rage saga sumayyan sai anty ni'imah sai
humaida,suma sun maqale ne saboda suna kwasar wasu sirrika da lacture da anty
ni'iman ke bawa amira,wanda baga fara ba sai bayan da wadancan suka fita,ba amira
ba hatta su sumayya sun qaru da ita sosai,a nan suka zauna suka ci gaba da
hirarsu,ni'imah ba dai sauqin kai ba,kamar qannenta haka ta daukesu,aqalla zata
girme musu da kusan shekaru goma,amma sam hakan bai wani nuna ba sosai sabida
tsabar gayu.

      Qarfe bakwai na magariba aka tafi kai amarya,babu wani takura ko neman mota
kasancewar kusan kowa ya mallaki motar hawanshi,wanda ya taho daga wani garin ne
bai taho da abun hawanshi ba sukayi amfani da motocin gidan baabaa,ga kuma ta
familyn saifullahi.

       Ba shakka wannan shi ake kira qwarya tabi qwarya,ba shakka amiran ta shiga
gidan da yayi dai dai da ita,gidane na alfarma wanda ke tafiya da tunanin mai
tunani,sanda aka fara tafiya amiran ta riqe sumayya gam kan sai ta jira anzo an
sayi baki,sun riga da sun gama tsarawa babu batun siyan baki,ko akwai din ma ita
batajin zata tsaya,saboda mutum biyu daga cikin abokan saifullahi da suka uzzurawa
rayuwarta tun ranar kamu,ta musu qaryar a niger take,saboda haka bata son su hadu
bare su takura ta,dabara tayi mata cewar bari taje tayi fitsari daga haka ta arto
gida.

      Biki ya tashi lafiya,ummee da kanta ta yi ma sumayyan godiya tare da godiyar


kayan humra data yi mata wanda su aka jerawa amiran ma,kunya ce ta kama
sumayyan,duka duka me tayi,su basu duba tarin karamcinsu wanda ya kai ga
cancantarsu kan yi musu komai.
       Tun a daren ta kashe wayarta kwata kwata,don ta tabbatar cewa gobe kamar da
qasa sai amira ta nemeta,jikinta ya gaji tubus irin gajiyar da bata taba yin irinta
ba,lallai biki ba wasa bane,tunda ta kwanta bata tashi ba sai da gari ya waye,ta
makara sallar asuba,don sai shida da rabi ta yita,tana gamawa ta koma ta sake
kwanciya,ba ita ta farka ba sai sha biyu saura na rana,yunwa ta sadakarta,a guje
tayi kicin ta tadda anty dije na soya miya qamshinta ya cika gidan baki daya,ba
magana ta mata nuni da kayan break dinta dake ajjiye gefe,tana kaiwa baki daya yiwa
antyn sannu da aiki
"Ai ke zanwa sannu,yaran nan sunso tadaki badon ma hanasu ba,shi yasa da abbansu
zai fita na hadasu da shi ya kaisu wajen inna(kakarshi)"
"Kai kina ji da ni anty na" ta fada tana jan kujera don ta ji dadin cin abincin
sosai
"Ba dole ba,kece fa babbar diya" suka sanya dariya baki daya sannan suka ci gaba da
hira suna tattauna wasu daga lamuran da suka faru yayin bikin,antyn na juye miyar
cikin warmer tace
"Ai ke kam bakiga hutu ba,saura sati uku a shiga wani bikin"
"Wallahi anty shi yasa nakeso nayi kamar kwana uku haka ina bacci,don so nake next
week na wuce kano" hararata antyn tayi
"Dama na sani ai,ke kam garin nan kamar yana mintsininki,gidan fa baki daya baya
dadi wallahi idan kika tafi,hatta da abbansu ya dinga mitar kin dade,amma wani
lokaci sai na rayawa a raina dole fa mu saba tunda wataran zaki aure,idan kika tafi
kuma ya zamuyi" shiru sumayyan tayi taci gaba da kurbar tea,saboda anty dijen ta
kawo zancan da bata qauna cikin hirar tasu,sai data gama sha ta sure cup din tana
goge hannunta sannan tace
"Anty,wata tambaya ce da ni"
"Uhmmm,Allah yasa na sani" shiru ya danyi tana tsara yadda zata jefa mata tambayar
kafin tace
"Wai idan wata ko wani yazo ya cewa budurwa ki taimaka ki gyara rayuwar wane,wai me
hakan yake nufi?" Waiwayowa tayi ta kalleta har sai da gaban sumayya ya fadi,Allah
yasa ba wani mummunan abu bane,kamar antyn ta tambayeta wa ya fadawa wani hakan sai
kuma ta fasa,taci gaba da aikinta tana bata amsa
"Maganar na da ma'ana bangare biyu,nq farko idan har aka fadi haka ga wani ko wata
makusanciya ta mutum ana nufin ta dinga bashi shawara da hanashi aikata wasu
abubuwa,ko kuma wani abu na son faruwa da shi ana son ka taimaka kada ya fada cikin
wannan abun,sannan ma'anar na iya daukan AURE ko SOYAYYA,abun nufi.......shi wanda
ya gaya miki maganar yana ganin kamar kina da wasu qualities da wani namiji ke
buqata,wanda wannan qualities din zau taimaka masa wajen gyaruwa ko ingantuwar
rayuwarsa,babu kuma hanyar da zaki gyara ko ki inganta rayuwar tasa sai ta hanyar
AURENSA ko yin SOYAYYA da shi,to sai a baka maganar a dunqule" tunda ta dauko
maganar gaban sumayyan ke faduwa
"Da gaske baba na nufin kenan ta auri almustapha?,abinda baabaa ke son fadi mata
kenan" kai ta shiga girgizawa cikin zuciyarta ta soma furta
"La haula wala quwwata illa billah,Allah ka sani ina ganin qima da darajar wannan
bawa naka,ya Allah ka fidda masa wannan tunanin daga zuciyarsa a kaina,ka jefa masa
tunanin wata,Allah kada ka bashi iko ya tambayi abinda bazan iya masa ba"
"Ke sumayya meye haka?" Inji anty dije ganin yadda take kada kai tana mus mus da
baki,murmushin yaqe na musamman ta qaqalo sannan tace
"Ba komai,kawai ina mamakin yadda muka kasa fassarar maganar,wani ne ya gayawa
wata" ta fada tana miqewa tsaye sannan ta fice daga kitchen din,da kallo anty dije
ta bita,cikin zuciyarta tana addu'a,Allah ubangiji ya sanya sumayyan tayi gamo da
miji ne dan gaske,wanda zata huce takaicinta,babu shakka zata so za kuma tayi burin
sumayyan tayi auren da zata huta ta sanadiyyarta,juyawa tayi taci gaba da aikinta
tana addu'a cikin ranta.

        A sanyaye ta zauna bakin gado maganar na sake y mata yawo,indai haka ne ba


shakka dole ta qauracewa haduwar ta da baabaa,kai ya zame mata jazaman tafiya
kano,kuma bata jin zata dawo nan kusa idan ta tafi din,zata yita qirqiro dalilai ne
wadanda zasu zaunar da ita a can.
       A daddafe ta haqura ta kai ranar alhamis kamar yadda ta gayawa anty
dije,sannan ta shirya tafiya,wanda ya rage sauran kwanaki goma sha hudu bikin,anty
dije ta bata saqonni gun mama sannan tace suma nan da kwana bakwai suna tafe,wannan
karon saboda tsabar zaquwa ta tafi bata iya jira abban laila ya dawo daga kaduna da
yaje ba ya hadata da driver,motar haya ta hawo ta tafi,ba yadda anty dije bata yi
ba amma ta kasa daurewa ta jira.

        Tana hanya taji kira,lambar amira ce,tun kafin ta daga ta saki murmushi
"Amaryar saifullahi bada kanki a sare" kamar wadda ke shirin sakin kuka ta soma
mata qorafin kota nemeta ko?,sun hada baki da saifullahi sun sace mata wayarta,shi
din ma ya rufe gidan ba shiga ba fita wai sai sun huta,ya kuma hanata wayarshi sai
yau ya bata wayan,dariya ta dinga mata din yasan da wannan plan din,sai da ta gama
qorafinta sannan suka gaisa tace yaushe zata zo don Allah
"Kin ganni hanyar kano,wani bikin ya sake kira na,bikin zainab dita"
"Wayyo,dama a kusa da namu ne,naci burin zuwa fa namecy" dariya tayi
"saidai ki tara ana halima idan Allah ya kawo"haka nan suka gama hirarsu ta baiwa
saifullahin suka gaisa sannan sukayi sallama.

   Kamar ko yaushe sunyi murna da zuwanta,mama nata tsokanar abdallah wai ya qara
qiba
"Amma dai zaka koma ko?" Wuya ya maqale a kafadarsa
"Nan yafi dadi,can kullum kuna rufe a gida" dariya suka saki don abdallahn badai
son yawo da wasa ba,hararshi sumayya tayi
"Nima babu inda zaka bini,rigimammen kawai" ko a jikinsa dariyarsa ma ya sanya
abinsa,washe gari yaya yahansu tazo ta daukeshi ma sukayi tafiyarsu,sai ranar kamun
zainab tace zata dawo da shi.

       Tunda tazo babu zama suna ta shirye shirye ba kama hannun yaro,ita da anty
salma qanwar mama da anty amina matan yaya abubakar,sunyi waya abdur rahman bai nan
amma zai dawo da shi za'a yi daurin auren shi yasa take hidimarta hankali kwance ba
wani damuwa ko takura,cikin ikon Allah da baiwarsa komai yana tafiya daidai,sumayya
taga yadda ake komai cikin tsari saboda haka ta dage ta tsarawa 'yar uwarta komai
yadda zai qawatar ya kuma burge,kudi sosai tasa yaya abubakar ya bata bayan wanda
anty dije da uncle farouq suka bata,dinkuna sosai ta yiwa mama,atamfofi masu tsada
da kyau,harda mayafai da takalma duk da yaya abubakar yayi musu amma tace wannan
nata ne,sannan ta siyawa malam gezna ta asalin wadda zai sanya ranar daurin
aure,takalmi mai kyau harda agogo da turare da sabon rawani fari qal,kasancewar
malam din ba baya bane wajen tsafta shi yasa kusan kayansa galibi farare ne,aka yi
masa dinkin babbar riga 'yar ciki da wando,ita kam dama bata da matsalar sutura sai
anko kawai data yi,sai abdallah data masa shaddar daurin aure duk da dumbin kayan
da yake da su,saura kwana tara biki kuwa saiga anty dije da iyalinta,nan aka shiga
hidima sosai.

      Kan hanyarsa yake ta dawowa daga airphort bayan ya kai anty dije da yaranta
sun tashi zuwa kano,tun daga nesa yaga kamar motar baabaa prof a tsaye,hakan ya
sanya ya rage gudun motar ya qaraso a hankali ya faka tashi motar bayan tasu sannan
ya bude ya fito.

      Baabaan ne tsaye gaban motar,kana dubanta kasan matsala ta basu,qarfen nasara


da bashi da tabbas,motar kwata kwata shekararta guda,ba yadda mustapha baiyi kan a
canzata ba kamar yadda ya saba sauya masa motocin hawanshi amma yace a sauya sauran
amma ita banda ita,yana jin dadin motar,da ita yake zuwa gidan gonan sulensa duk
qarshen sati,duk randa zai tafin baya tafiya da wasu motocin face wadda ita kadai
zai hau,kuma daga shi sai druvansa,yana jin dadin zama gidan gonar,ya zazzaga yaga
gidan gonar sosai,yanajin nishadi da farincikin yadda dukiyar sulensa ke
habaka,fatanshi Allah nuna masa ranar da zaiga sulenshi,a irin haka ne yau motar ta
tsaya musu a hanya.
       A aladabce uncle farouq ya qaraso
"Subhanallah,baba kada dai ace qarfen nasara ya muku tsiya?" Cikin murmushi mai
dauke da dattako yace
"Wallahi kuwa,to ya za'ayi,yau da gobe ai sai Allah,babu wani abu dake matabbaci"
"Gaskiya ne" inji uncle farouq yana fidda waya daga aljihunshi yana fadin
"Bari a kira gida to a turo wata ko baabaa,tamu motar ba lallai ka iya shiga irinta
ba" murmushi ya kuma subucewa baban,har ya sanyashi ya juya ya sake kallon motar
duk da ya santa,motace mai lafiya wadda bata da wani aibu ko makusa,ko kai waye
zaka iya hawanta,amma ya sani cewa irin motocin da mustapha ke ajjiye masa yana
hawa shi ya sanya farouq din tunanin yafi qarfin wannan
"Haba faruqu,saidai kawai idan rawar hawa motar take kake min,amma ni din waye da
bazan hau wannan motar ba" ya fada yana dariya,bakinsa ya rufe shima yana dariya
"Afuwa baabaa" ya fada yana bude masa gaban motar,kafin ya shiga ya waiwaya ya dubi
drivan nashi
"Kada ka tsawaita tsaiwa a nan,ka kira bakaniken nan,idan bakaniken ya iso ka bashi
muqullan ka taho gida" a ladabce yace
"Yallabai man yace kada a sake barinka ka hau motar da baniken hanya ya tabata
ranka ya dade" murmushi ya saki
"Qyale wannan,idan na biye masa ma a jirgin sama zan dinga yawo,ni waye da
bakaniken hanya bazai taban mota ba,shi yasa na hana a kira gida agaya musu motarmu
ta tsaya nasan zai iya jin zancan ya damu mutane da batub sauyan motoci,bayan ni
din duka kwana nawa ya rage mana a duniya,kayi yadda nace kawai"
"To ranka ya dade" inji drivan,baban ya juya ya shiga motar faruqun ya rufe ya
zagaya shima ya shiga ya tadata suka fara tafiya.

       "Asalina daga qauye na fito faruqu,kiwon dabbobi  na dinga yi ni da


aminina,da can ko jaki bani da shi na hawa bare a kai ga mota,din me zan dinga
manta asalina,ita duniya gaba dayanta yadda ka dauketa haka take zuwa maka,mafi
daraja cikin mutane shine wanda a zahiri ya isan amma yake daukan kanshi ba'a bakin
komai ba,girman kai rawanin tsiya ne,wanda ke zaton ya isa kuma sai Allah ya
qasqantar da shi a duk inda baiyi zato ba" kai uncke farouq ke gayadawa cike da
gamsuwa,tsohon dattijon qwarai ne,yana bala'in son zama da shi saboda dole ka dauki
darasin rayuwa,idan ya shiga cikin wasu baka isa kace shine wannan professor din
ba,kuma tsohon jakadan nijeria a qasar amurka.

      Danja ta tsaidasu uncle farouq yaci burki da sauri saboda yana dan gudu,wanda
hakan ya sanya katinan dake zube gaban motarshi suka zubo,jiya ya karbosu shi yasa
aka yiwa malam su na daurin auren zainab ya baiwa anty dije ta tafar mai da su
ragowar ya ajjiye wajansa zai bawa kawunshi
"Bismillahi" malam ya fada yana cewa
"Kaima ashe kana dan taba irin tuqin almustapha kenan ko?" Ya fada yana murmushu
tare da duqawa yana kwaso katinan sa sukw zube din.

       Caraf idanunshi suka kai kan sunan dake jikin katin wanda ke qunahe sa
sanarwar daurin auren SULAIMAN AMINU DAHIRU GOMBE,sake maimata sunan yayi,sunann da
ya kasance sak irin na tsohon amininshi sule,tsohon aminin da kullum zuciya ke
begen ganawarsu,maimaita sunan ya dinga yi tare da kallon rubutun da aka tsarashi
kalar golden,tamkar zai gano masa da zargin da zuciyarshu ta fara yi,uncle farouq
ya lura da hakan sai yace
"Bikin qanwar mai sunan mama ne,wato 'yar yayar khadija" wawiyar ajiyar zuciya ya
sauke ya maida dubanshi ga farouq
"A ina suke faruqu"
"A kano suke"
"Kano?,meys asalin mai gidan" kai ya girgiza cikin kokwanto
"Bamu taba zancan gaskiya da ita ba,amma dai a kano na sansu,wani abu ne baabaa?"
Kai ya kada yana maida katinan mazaunansu
"Sunan ne kawai ya yimin kama da na wani tsohon aminina wanda har yau nake neman
bayan ya bata tsahon shekaru"
"Ayyah,Allah ya bayyana shi"
"Amin amin faruqu". Bai bar babaan ba sai daya dangana da shi har cikin gidan
sannan baabaan ya sauka yaba masa godiya,kunya duk ta kama faruqun,a rayuwa babu
wani abu da zaiwa baban da har zai masa godiya,bayan babu wani nau'in karamci da
kyautatawa da baban bai masa ba tun daga sanda ya sanshi har zuwa yau.

      Tunda ya koma gidan baki daya ya kasa sukuni,katinan da sunan sun tsaye masa
a rai,daren ranar kasa cikakken bacci yayi,yayi salloli sosai kafin ya samu bacci
yayi awon gaba da shi,da asuba da ya tashi da abun ya tashi cikin ransa,har gari
yayi haske,sai kawai ya tsinci kanshi da jawo kiran wayar uncke farouq ya buqaci
adress din gidan mamallakin sunan da ya gani jikin katin,babu haufi ya tura masa
don baya shakka cikin nagartan baabaan,yasan cewa koma mene alkhairi ne IN SHA
ALLAH.

        Waya kawai ya sake dagawa,ya lalubi lambar mahmoud ya buqaci ganinsa,ba


bata lokaci ya iso kasancewar yana cikin gidan,sanar masa yayi ya laluba idan akwai
jirgin da zai tashi daga abuja zuwa kano ya yankar masa ticket guda hudu,shi daya
mahmoud din daya mus'ab wanda yazo biki bai koma thailand ba,da kuma drivansu,bai
wani mamaki ba saboda yasan lokaci zuwa lokaci baaban nasu nayin tafiya kota ziyara
ko duba gidajen gonar wannan babban aminin nashi da tunda suka taso suke jin
sunanshi suka kuma haddaceshi,tare da riqe girma da matsayinsa wajen babansu,lokaci
lokaci sukan yi bita da tilawarsa,saidai har kawo yanzu idanuwa basu taba ganinshi
ba,cikin sa'a aka samu jirgin azaman wanda zai tashi ne da la'asar qarfe hudu na
yamma,ba haka baban yaso ba amma haka ya karba.

        Qarfe hudun jirgin ya lula da su sararin subhana zuwa kanon dabo,wanda


cikin mintuna suka isa cikin yarjewa da ikon ubangiji tare da sahalewar ci gaban
zamani irin na yanzu,kano tamkar gida take wajen baaban,saboda haka suna sauka suka
tarar da motoci guda biyu suna jiran isowarshi,ba bata lokaci suka shiga suka fice
daga airphort din.

       Wayarsa baban ya ciro,ya lalubo adress din ya soma karantowa


drivan,kasancewarsa dan kano ne tuni ya fahimci wajen,sannu a hankali suka dinga
keta unguwanni har suka qaraso unguwar da ya buqata,a bakin qofar gidan sukayi
parking,drivan ya sake tambaya aka tabbatar masa nan ne gidan malam sulaiman,yaron
ya aika ciki ya tambayo yana nan kamar yadda baabaa ya buqata,saidai yaron ya sanar
musu baya nan amma bayan sallar isha'i yana gida,ya sake aika yaron yace idan ya
dawo a gaya masa yayi baqo,amma zai dawo bayan sallar isha'in ya tsumayeshi don
Allah,sai da ya isar da aiken sannan suka tada motocin suka bar layin yaron na bin
motocin da kallo saboda yadda suka yi masa kyau.

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)
7⃣3⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

*HASBUNALLAHU WANI'IMAL WAKIL*

__________________________________

       Baabaa prof ji yake kamar isha'in ba zata yi ba,fata yake cikin ransa Allah
ubangiji ya sanya sulensa ne,Allah ya qaddara saduwarsu,haka kawai yake jin zumudin
zuwan sallar isha'in yayi yaje yayi tozali da mai wannan suna.

       Kai tsaye gidansa daya fara zama cikin garin kano tun zamanin quruciya can
aka wuce da shi,gidan har yanzu yana nan da kyansa da daukar hankali,kasancewar bai
bar gidan ya lalace ba,ko yaushe sake sabunta shi ake saboda ba'a rasa cikin
iyalansa mash zuwa kanon,gida take kano a gun kowa,ko baka shigo ka zauna cikinta
ba baqunta ko kasuwanci ya kawoka,ko ba haka ba ma hanya ta wuce da kai ta
cikinta,wanka yayi ya sauya shiga sannan suka wuce masallaci shi da mus'ab da
mahmoud baki daya kasancewar dab ake sa fara sallar magariba.

       Basu suka baro masallacin ba sai da akayi sallar isha'i,kai tsaye hassan
driver ya koma gida ya fiddo motar ya kawota bakin masallaci suka shiga,tafiya ce
da bata wuce minti talatin ba ta maidasu unguwar,guri suka samu sukayi parking
sannan suka aika yaro yaje ya sanar da malam ana sallama,cikin sakanni ya dawo ya
gaya masa yana fitowa.

      Tsaiwar mintuna biyar kacal ya hangoshi,idanuwa ya zuba masa baki daya ko


qwaqwaqwaran motsi baya yi,tun kafin ya kai ga qarasowa inda suke ya
shaidashi,girma ko tsufa baiyi isar da zaya sanya ya kasa gane sulenshi ba,dadi ko
wuya babu abinda zai mantar da shi sule,shima takowa yake saidai sam bai kula da
wanda ke gabansa,kasancewar yafi ganin mahmoud da musa'ab dake tsaye gaban baabaa
prof din,a hankali ya qaraso ya dubi su mahmoud a nutse
"Yan samari kuke sallama da ni?"
"Basu bane,muntarinka ne,muntarinka ne sule,suken mai gado" da hanzari ya daga kai
shima din gani waye?waye wannan dake ambatarsa da sunan nan qwaya daya jal da yasan
duk gadin karkararsu shi kadai ke kiransa da shi,ya sanya masa sunan me tun daga
lokacin da malam muhammadu(mahaifin baabaa prof) ya basu tarihin annabi sulaimanu
da nana bilkisu,kutsawa yayi tsakiyar su mahmoud yana fatan kayalinsa ya zama
gaskiya,ya tabbata kuwa,muntarinsa ne,muntarin da kullum matuqar rana zata fito ta
fadi walau yana da cikakkiyar lafiya koko babu ita sai ya tunashi,sai yayi begen
ganinsa,da sauri suka qarasa zuwa ga juna suka rungume juna kowa na ambatar sunan
dan uwanshi,kowannansu jikinshi na rawa,lamarin ya yiwa su mahmoud nauyi ganin
yadda dattawa ke fidda ruwan hawaye,yara masu wucewa suka soma tsayawa suna tunanin
wani abu ne ya faru ga malam din,mus'ab ne yayi qarfin halin cewa
"Amm,baabaa yara fa sun fara tsayawa" abinda ya fargar da malam kenan ya saki
muntari yana kallonshi,ji yake kamar zai sake bace masa bazai kuma ganinsa ba,ko
kuma mafarkin da ya saba ne yake yi
"Ina zuwa" malam ya fada cikin sauri har yaja tuntube ya shiga gida a gaggauce ya
karbi muqullin sitting room wajen mama yana shaida masa yau ga muntarinsa a
gidansa,muqullin kawai ta bashi tana tantama,muntarin da tunda suka hadu take jin
sunanshi daga bakinsa amma bata taba ji sun hadu ba shine tau aka ganshi?.

       Jikinsa har rawa yakeyi ya bude sitting room din suka shiga,har yanzu
kowannansu gani yake kamar almara
"Sule kaine?,ko almara ce?"
"Nima haka nake ji muntari,saidai lamarin ubangiji yafi gaban haka,shi sami'ud du'a
ne"
"Qwarai kuwa ba shakka"doguwar gaisuwa sukayi bayan sun gama sumbatun ganin
juna,sam sun mance ma da wani mus'ab da mahmoud a wajen,har sai da mahomud da
mus'ab din suka matso suna gaida malam ya amsa fuskarshi na fitar da annuri,dukkan
wani nauyi dake cikin zuciyarsa ya yaye,a yau ya tabbata farinciki bazai barshi
yayi bacci ba
" wadan nan 'ya'ya na ne sule,gasunan,akwai biyar a gida,baya ga jikoki da suka
kusan tasamma guda goma matan aure biyu,kaifa sule?,ya rayuwa ta kasance?"ya fada
yana dubansa,wani sashi na zuciyarsa na masa susa ganin alamun sulen bai kama koda
kaso daya cikin goma na arziqin da shi yake da shi ba,bayan kusan tare suka sha
wuyar tattala da tara dukiyar,saidai alhamdulillahi kana ganinsa kasan baya cikin
wahala,yana cikin matuqar rufin asiri,miqewa mahmoud sukayi shida mus'ab suka koma
qofar gida don bash waje suji dadin ganawa sosai,gyaran murya malam yayi sannan
yace
"Bayan barina garinmu muntari na jima bansan inda hankalina yake ba,da na tashi
kawai na tsinci kaina cikin makarantar allo ta almajirai,wani malami dake yawon
rarraba almajirai ya tsintoni ya hada da yaran da zai kawo kano,sai na karbi
rayuwar a yadda na ganni,na riqe karatuna da hannu bibbiyu,na zama daya daga cikin
hamshaqan dalibai haziqai da malam ke ji da su,gefe daya kuma kasan tun asali bani
da matacciyar zuciya,a duk lokutan da ba na karatu bane nakan fita neman na
kaina,duk aikin da na samu zanyi kowanne iri indai na halal ne,batun gida kam baki
daya na manta ma ni din dan wanne gari ne,tun malam na damuwa yana qoqarin
tambayata har ya haqura ya watsar a haka rayuwa taci gaba da turawa,na samu
cikakkiyar haddar alqur'ani mai girma,na zama daya daga cikin amintattun malam,'yan
gaban goshinsa,muntari ban tashi tunawa da garinmu ba sai sanda Allah ya yiwa
mahaifina rasuwa,naje na tadda rasuwarshi,na kuma samu labarin dukan abun arziqin
da kake yi,na tambaya saidai kash ko daya ba wanda yasan inda kuka koma acikin
gari,suce zuwa musu kake ka koma,da haka na isa ga dangin mahaifiyata wadamda suma
mutuwa ta daddaukesu sai 'yan ragiwa,muka gaisa na dawo cikin gari na hau
cigiyarka,wasu suce min sun sanka amma basu san matsugunninku ba,wasu suce ma basu
sanka ba,da haka na haqura da dawo kano bani qwarin gwiwa,bayan wasu shekaru ban
haqura ba na sake komawa,sai naje na tadda ma baki daya kunyi qaura daga gombe kun
dawo kano,naji dadin hakan saboda ina zaton zan sameka ta sauqi tunda muna gari
daya,saidai na manta cewa kano nada girma da fadi yawan al'umma da yawan
qabilu,akwai tarin qananan hukumomi qarqashinta,haka na qaraci nemana tsawon
shekaru,tun inayi tuquru da qarfina har na haqura.

       Uwar 'ya'yana a yanzu diyar malam ce,wanda saboda yadda da gamsuwa da yayi
da kyakkyawar halayena da dabi'una ya bani aurenta,na samu tarin ilimi daga wajen
malam har bayan rasywarshi sunan malam ya dawo kaina,duk da ban iya ci gaba da kula
da almajiran ba kowa ya koma garinsu,amma ban fasa bada karatu ba wa dalibai masu
zuwa su tafi,a yanzu haka muna da yara hudu da jikoki biyu,sannan cikin qarshen
wannam satin zan sake aurar da yarinyata ta uku,kazo a daidai muntari,ko yaushe ina
bege idan wani abu da ya shafi iyalina ya taso,inama ace muntarina na nan"cikin
farinciki baabaa ke dubanshi
"Allah ya amsa addu'armu sule,Allah shine abun godiya" a hankali baabaan shima ya
soma zayyane masa yadda yayi tashi rayuwar,gyada kai kawai malam yake yana kallon
muntarinsa yana jin dadi,baabaa prof din ya qare da cewa
"A yanzu haka sule na kaima kana da taka dukiyar ta kanka,kyautar da nayi maka ban
fasa ba sule,itace naci gaba da kula maka da ita har kawo yau,a yanzu haka duk wani
gidan gona ko yoghourt ko fresh milk dake dauke da tambarin S.A.D mallakinka ne"
mamaki ya kama malam,girma matsayi na muntarinshi ya sake ninkuwa cikin
idanunshi,samun mutum mai amana irin haka a wannan zamani abu ne mai wuya,samun
aboki irin muntarinsa a zamanin nan tashim hankali ne,bai manta wani waqe da wani
balaraben mawaqi ya tabayi yana cewa'a yanzu zaka samu cewa,zukatan abokan gaba
sune a jikkunan abokai'ma'ana a fili a bokai suke a idanun kowa,amma a badini
kowannensu gagarumin abokin gaba ne ga dan uwansa,bai qaunarsa,bai son ganin ci
gabanshi,burinsa kawai yaga faduwa hasara sa damuwa tattare da shi,kai malam ya
kada
"Duka wannan ba shine abun damuwa ba,haduwata da kai kafin Allah ya zare numfashi
daga jikina shine babban abu,kuma Allah ya cika mana wannan burin" shima kai
baabaan ke kadawa
"Dukkan abunda muntari ya mallaka na sule ne,yana da iko da shi,bare wata qaramar
kyauta da ya masa tun zamanin quruciya?,haqqinka ne sule dole ka karba,munyi haka
tun a gaban idanuwan malam,A yanzu bayan qaaa ta rufe idanunshi sai mu sauya?,sam
haka bazai faru ba" inji baabaa.

        A daidai qofar gidan kai napep ta saukesh,ita ne da zainab da halima,a


gajiye suke matuqa,don sunyi yawo sosai gidan 'yan uwan mamanta rabon chewing
gum,burin sumayya kawai ta samu inda zata jefa haqarqarinta ta kwanta,don ko ta
abinci bata yi,Allah ya sota tayi sallolinta baki daya.

       Kamar ance dubi can ta hangi mahmoud zaune saman motarsu yana jajjefa qafa
yana murmushi,bisa dukkan alamu yana jin dadin yanayin,haka sauyin waje zuwa
unguwar da bai santa ba bai taba zuwanta ba hakan yayi masa dai dai,idanu ta zuba
sosai wai ko idanuwanta ke mata gizo,ta sake matsawa wajen,tabbas shine,daidai
sanda ya waiwayo shima,baki ya bude yana mamaki
"Wa nake gani haka?,me ya kawoki unguwarnan?" Ya fada yana murmushi tare da saukowa
daga saman motar
"Da gaske kai ne?,to me kake yi a kano kuma a unguwarmu a qofar gidanmu?"
"Kina nufin nam shine gidanku?" Ya fada yana nuna gidansu da yatsa
"Qwarai kuwa,nan aka haifeni"
"Malam shine aminin baabaa dama,sulen muntari?" Wannan magana ce kawai ta kasa gane
me yake nufi,sai ta dubeshi tana neman qarin bayani,baisan ta yadda zai fasaara
maga zancan ba sai ya dora da cewa
"Tare da baabaa prof muke fa sumayya,babanku shine tsohom aminin nan masa da yake
yawan ambata,wanda ba yadda zakuyi magana da shi ta awa daya bai sako zancansa ba"
ya fada yana murmushi har cikin zuciyarsa yana jim dadin yadda a yau burin
mahaifinsu na tsahon shekaru ya cika,mamaki ya kamata qwarai,tabbas babu shakka
zata iya tunawa ko ita yana sako mata zancansa lokaci lokaci idan hira ta dan
hadasu
"Malam dinmu?,baaba yanzu yana ciki?" Duka tayi tambayar a tare lokaci guda cike da
dimbin mamaki,wai babanta shine tsohon aminin baabaa prof,bugu da qari kuma wai
baban ne yau a gidansu
"Qwarai kuwa,mun fito mun nasu guri ne din kinsan tsaffin abokai idan aka hadu ba
dama,kada a tuno wata quruciyar aji kunya a gabanmu" ya fada cikin irin salonshi na
tsokana,dariya ya basu baki daya
"Allah mai iko" sumayyan ta fada har yanzu abun nata na bata mamaki
"Bari naje na gaida babanmu" ta fada tana yunqurin wucewa
"Wannan qani na ne,shike bi mini,mus'ab dake thailand,gashi nan ku gaisa" ya fada
yana dukan kafadarsa,a mutunce suka gaisa sannan ta sanya kai zuwa cikin gidan cike
da zumudi da mamaki.

       Sai da tayi sallama biyu aka bata izini sannan suka sanya kai cikin
dakin,suna zaune irin zaman da kama dubansu kasan muhimmiyar ganawa suke,ganawa
kuma mai dauke da qauna da fahimtar juna,duk da ruwa dake lemukan gaban baabaa prof
babu wanda ya taba,ganin sulenshi da sauraron labaranshi ya fiye masa komai,daga
kai baaban yayi cikin mamaki yana dubanta
"A'ah,mama na,daga ina haka" kanta a qasa cikin murmushi ta qarasa gabanshi ta duqa
"Baabaa,yau kaine a gidanmu?" Sai ya maida dubanshi ga sule yana fadin
"Kada dai kace min sumayya diyarka ce?" Cikin murmushi ya daga kai
"Tabbas,ita ce diya ta tabiyu,ita ce kuma ta haifamin babban jika na" kai baabaan
ke dagawa,wani madaukakin farinciki na mamayarsa,tabbas Allah na sonshi,Allah na
duba ga zukatan bayinsa ya musu taimako cikin ayyukan alkhairin da suka sanya
gaba,a ladabce sumayya ke gaidashi da su zainab ya amsa cikin farinciki yana sanya
musu albarka.
       Sosai wani irin farin ciki ke shigar shi,ji yake tamkar babu wanda ya kaishi
farinciki yau a duniya,mamanshi cikin zuriyyar sulenshi?,babu ko tantama Allah yana
nufinsa da alkhairi,sosai yake jansu da hira abinshi,tun su zainab na dari dari na
rashin sabo har suka saki jiki
"Ba don bikin da za'a yi ba shakka sai na daukeku baki daya,dama ita mama na 'yar
gida ce" baabaa ya fada yana murmushi,dariya suka sa baki daya suna sake jinjina
girman qaunar dake tsakanin iyayensu,sumayya ce ta janyesu tace bari su shiga ciki
suma don su sake basu waje sosai,murmushi ne dauke a fuskar baabaa prof har suka
fice sannan ya maida idanunsa kan malam.

    "Sule,dama sumayya diyarka ce?,wannan abu ya faranta min fiye da yadda kake
zato,tun sanda naga yarinyar naji ta kwanta min,na yaba da halayyarta,haka naji ina
qaunarta kwatankwacin yadda nake qaunar amira,ashe jininmu ce,jinin sulenmu ce"
murmushi malam keyi sannan yace
"Mai sunan inna daban take muntari cikin 'ya'yana,Allah ya yi mata baiwar ilimi
hankali haquri da nutsuwa,zakayi mamaki odan na baka labarin irin rayuwar data
fuskanta,da irin qaddarorin da suka fuskanceta,cikin ikon Allah ta cinye
jarrabawarta,dubeta,yanzh waye zai ce ta taba fuskantar matsi da qunci makamancin
haka,waye zai ce harda maraya gareta?" Dubanshi kawai baabaa keyi,don shi bai san
sumayyan ta taba aure ba
"Kana nufin kace mama na ta taba aure?" Kai malam ke kadawa don tabbatar masa
"Qwarai kuwa,har da yaro" gaban baabaa na faduwa cike da faata yace
"Ina fata amma a yanzu bata da aure ko maganar wani kanta?" Cikin mamakin gambayar
da muntarinsa ya masa ya amsa masa da eh,sauke ajiyar zuciya baabaa yayi yana furta
"Alhamdulillahi,sule,ko zaka iya taimakamin ka bani auren mama na?" Dubanshi yake
alamun bai fahimta ba
"Ina nufin ka bani auren mama na na karbawa d'aana mustapha?" Murmushi ya subucewa
malam din,amma sai ya gaza cewa komai,baaba ya dora da bayani
"Mustapha na cikin yara mafi soyuwa a wajena kamar yadda mamana take,tabbas da dan
adam keda ikon tsarawa dan uwanshu rayuwa bazan zabawa almustapha rayuwan da yake
yi ba a yanzu,taimako nake da buqata ka yiwa yaronka mustapha,don Allah kada a
hanashi,bari na gaya maka wanne irin rayuwa mustapha keyi da iyalinshi" hankali
kwance baabaan ya zayyanewa malam komai,kai kawai malam ke kadawa,shi kam bai ma
tabajin rayuwar aure ta tsantsar nasaranci ba irin wannan,baiyi yawon duniya ba
bare ya santa,wadda tazo cikin qur'ani da sunna da wadda akeyi cikin kowanne gida a
society dinmu kawai ya sani,shi da ko karatun boko bai bari anyi a gidansa ba banda
zamani daya tilastashi ya bar halima da zainab sukayi candy,
"tabbas wannan wani taimako da jihadi zakayi sule,saboda yau da gobe tafi qarfin
wasa,almustapha lafiyayye ne,yana da tarin dukiya wadda tafi tawa,kai duka cikin
zuriyata babu mai dukiyarshi,'yammata na qasashe daban daban na sonshi koda ba
soyayyar aure ba,yana da iko da 'yancin yin komai,WA YASAN GOBE?,wa yasan gobe mai
zata haifar,gwara tunda ina da ikon kawo gyara na kawowa rayuwarsa gyara ta hanya
halastacciya" mamaki ke ci gaba da ratsa malam wamda ya haddasa masa kasa
magana,wannan wace iriyar mace?,ita zata iya daga hannu tayi tutiyar ita din matar
aure ce?,murmushi ya saki ganin yadda muntarin ya zuba mishi idanu yana jiran
amsarsa,irin kallon wanda ke tsoron jin fitowar amsa mara dadi daga bakin wani
"Ba qaramar kunya ka sanya naji ha muhtari,yanzu don Allah ka cancanci ka roqeni
kan neman auren mai sunan inna?,ashe ma ba daya muke ba,ashe ma yadda ka daukeni
ban kai nan ba,sannan baka amince da yadda matsayinka yake a guna ba,har kwanan
gobe muntarim ban sake aboki ko amini wanda nake jinsa kamar ni da shi tagwaye muke
ba tunda muka rabu da kai,muhtari,ba almustapha ba,ko kai keson sumayya na baka ita
halak malak bare tsatsonka,kai,ko moqocin maqocinka kesom sumayya wlh yaci
albarkacinka,kana iya aurar da ita ma ba tare da na sani ba,NA BAWA ALMUSTAPHA
SUMAYYA HALAK MALAK,amma wani hanzari ba gudu ba,sumayyan tayi aure ba guda daya ba
har biyu harda yaro,kana ganin hakan ba matsala bace?" Kai yake kadawa
"Naji dadi sule,na gode da wannan karamcin naka,sumayya ko aure dubu tayi matuqar
nace wa mustapha ina so ya aureta babu musu sai ya aureta,baaga auren budurqar ba
anyi meye ne a ciki?,bazawara nada tata baiwar ta musamman kuma ta daban matuqar ta
tsare mutuncin kanta tasan ciwon kanta,hankalinta da na budurwa ma kadai akwai
banbanci,nasan mustapha cikin 'ya'yana,ni inda nake kokwanto mamana,kada muyi
abinda zai sabawa ra'ayinta" dariya malam yayi
"Muhtari kenan,wacce maman namu?,yadda kake da tabbas kan danmu almustapha haka
nake baka tabbas kan maman taka" cikin farinciki suka saki dariya
dukansu,hannayensu damqe cikin juna farinciki na shawagi da su cikin
duniyarshi,tamkar baabaa ya tashi ya taka rawa haka yake ji,yau Allah yayi mishi
baiwa manya manya guda biyu,ko yau Allah ya dauki ranshi tabbas ya cika masa
burikansa,a hankali malam ya warwarewa baabaa labarin sumayyan da irin gwagwarmayar
da tasha,tausayi da qaunarta ta sake yawa a ranshi,qimarta ta dadu,tabbas wannan
itace macen aure,ba shakka irin wannan matar ita ta dace da a nema,ya godewa Allah
data kusa zama halak malak din familynsa,wannan shi ya sake motsa baabaa ya dubi
malam
"Sule,idan zai yiwu ina son a hada auren nan da na 'yar uwarta,idan yaso bayan an
daura a nutse sai ta tare ko bayan kwanaki nawa ne,ji nake kamar wannan damar zata
subucewa mustapha" dariya ta subucewa malam
"Haba muhtari,tunda na bada sumayya wa almustapha duk duniya banga wanda ya isa ya
maida wannan alqawarin ba,kawai ina ganin shi kansa yaron bai sani ba tunda naji
kace yana can dubai wajen aikinshi,amma tunda sai kafi nutsuwa da hakan hakan
za'ayi,za'a hada da zainab din in sha Allah,ubangiji ya tabbatar mana da dukkan
alkhairi yasa wannan hadin ya zamo abun alfahari da farinciki wa zuri'ar ta da
taka"
"Amin ya rahmanud dunya wal'aakhira" cikin madaukakin farinciki baabaa ke
amsawa,shigowar mus'ab sitting room din shi ya katse sauran maganar da sukeyi,ya
dan rusuna yana fadin
"Afuwa,baabaa sha daya na dare,nace ko nan zaka kwana mu mu wuce?"ya fada cikin
salon tsokana,daquwa baabaan ya watsa masa
" baka gama fahimtar waye sule a gurina bane,da da hali kwanan zanyi,amma na
tabbatar idan na kwana din kwanan zaune zamuyi ni da shi,don hira tsakaminmu ba mai
qarewa bace,ni sai naga ma kamar daren yana gudu"dariya ya basu don babu wani gudu
da dare keyi,idanuwanshi ne kawai,har bakin motarsu malam ya takowa aminin nashi
masoyinshi,gab da baabaa zai shiga motar ya dubeshi
"Gobe ya kama saura sati guda kenan daurin auren ko?"
"In sha Allahu"
"To madalla,ina zaton gobe zan koma gida na sanarwa da mutanen gida muma mu fara
shiri,don wancan auren da yayi ba'a qasar nan aka daura ba,hakan yasanya daidaiku
ne suka je masu ikon zuwa,amma wannan karon d'aana zai auri diyata sai inda kati ya
qare" dariya sukayi a tare,malam ya rufe mishi murfin motar yana mausu fatan
alkhairi da fatan wayewar gari lafiya.

       Sai da suka fara tafiya a titi sannan mahmoud ya dan zunkuda kadan,tun dazun
daya tsinci maganar ake mintsininshi,so yake yaji shin abunda yake zato ne?
"Am....baba daurin auren waye kuma nan da sati guda?" Waiwayawa baabaan yayi ya
dubeshi sannan yace
"Yayanku almustapha in sha Allahu" idanu suka waro mahmoud yace
"Shi da wa?"
"Diyar sule aminina sumayya mai sunan mama na" ya basu amsa kai tsaye,duk sai kasa
furta komai,babu abinda ke yawo kansu irin halaye da tsare tsaren yayan nasu
almustapha wanda babu wanda baisan halayyarshi ba,shin baabaa na shirin daura masa
aure kenan baida masaniya da yarinya 'yar afrika?,
"Yarinyar tayi,tayi wlh bata da makusa,ga nutsuwa ga hankali,koni a lokacin da na
soma ganinta don dai kawai akwai alqawari tsakanina da rahma da tuni na saka kai"
ya fada yana dan kauda ido waishi kunyar baabaa,murmushi baban ya saki,idan da sabo
ya saba da irin wannan barkwancin tsakanin mus'ab da mahmoud,yaso ace haka halayyar
mustaphanshi take kan barkwanci,saidai kowa da yadda Allah ya tsara masa
halittarsa,suna hira da raha sosai da shi,sun maida shi tamkar kakansu,yabon da ya
sake yi kan sumayya ta sake faranta masa rai,kafin ya sake cewa komai mus'ab ya
muskuta yace
"Hmmm,dan gaban goshi,auren gata wannan karon za'a masa,yana can yana harkokinshi
an nema masa aure,mu kuwa gamu nan tamu maganar ma ko ya ake ciki ne mahmoud?" Ya
maida tambayar kan mahmoud,dole dariya ta qwacewa baabaa saboda salon yadda mus'ab
din yayi furucin,daquwa ya watsa masa sannan ya dafa kafadarshi
"Kai ka jawo tsaiko da karatunka bai gama kammala ba,amma ku din ma ba zaku wuce
nan da wata biyar ba" sai suka saki dariya kuma suna jin kunya,su kamsu sunsan
yayan nasu yana buqatar dauki,sunsha rayawa a ranau idan sune ba zasu iya wannan
auratayyar ba,saidai da yake maza ne babu wanda ya gayawa dan uwanshi ko suka zauna
suka tattauna batun,saidai kowa yayi shida zuciyarshi,da haka suka qarasa gida ko
zuciyarshi fes.

   ******   ********    ******

       Washe gari tun tara na safe suka gama shirin fita ci gaba da shirye
shiryensu,sabida a yau sumayya keson su gama rabon i.v saboda ta gaji,gashi uwa uba
kuma so take da anfarawa zainab din gyaran jiki kada ta sake fita,tuni anty dije
wadda yau tare zasu fita ta iso,tana wajen malam suna hirarsu ita da shi da yaya
abubakar wanda yau bazai fita kasuwa ba ya taho gidan hira,amina ma na nan zuwa
anjima don kusan gidan take wuni tunda satin bikin ya kama,sai da suka kammala
sumayyan ta leqa falon malam din tana fadin anty dijen ta taso su tafi sun gama
shiryawa don ma nafisa ta tsaidata ta tsaya amsa kiranta wadda ta tabbatar mata
zata halacci bikin zainab,don zata zo kano dama gaida iyayen mijinta mahaifan auwal
"Jeki ki kira min babarku ku taho tare ke da ita" inji malam,haka kawai taji
qirjinga ya buga,tashin farko jikinta yayi sanyi,ta juya zuwa bakin fanfo inda
maman ke daura alwalar sallar walha ta gaya mata,qafafunta kawai ta kammala wankewa
ta bita suka nufi dakin.

       Sai da suka samu gu suja zauna suka nutsu sannan malam din yace
"Haqiqa na tabbatar da cewa duk wanda ya kwana ya tashi cikin gidan nan yasan abun
farincikin da muka kwana da shi na bayyanar aminina,to bayan mun gama farinciki na
ganin juna muna hira bayan ke sumayya kun shigo kun fita ya bijiromin da wata
buqata,na sani kun san cewa duk da baku taba ganin muhatari ba amma kunsan
muhimmancinsa gareni da irin shaquwa da halaccin da yake tsakanina da shi,ya
bijiromin da wata buqata wadda na tabbatar yagi qarfinta a wajen iyalina,duk da
nasan cewa haqqin sumayya ne amma na amshi buqatar hannu bibbiyu saboda nasan cewa
na isa da ita sannan ba zata taba watsan qasa a ido ba" tun kafin yaci gaba
qirjinta ya fara wata iriyar sukuwa,kanta yayi nauyi ta kasa dagashi,maganar da
sukayi da shi kafin tahowarta kano da fassarar da anty dije tayi mata suka fara
dawo mata daki daki
"Ya nemi na bawa yaronshi auren sumayya bisa wasu hujjaoji daya zayyanamin wadanda
sun isa sun kai baya ga matsayin muhtarin a gurina a bashi auren ita sumayya,saboda
haka na bada auren sumayya ga yaron nashi wanda za'a daura auren ranar juma'a tare
da na zainaba insha Allah" wani kuka ne ya qwace mata wanda sautinsa yaso fitowa
tayi hanzarin sanya hannu ta rufe bakinta,
"Alhamdulillah" kawai anty dije ke jerowq,kamar ta tashi ta taka rawa haka ta dinga
ji,ta kasa zama waje daya sabida farinciki,ba shakka tana mai tabbatarwa kanta
sumayyan tayi kyakkyawan gamo mai dauke da dumbin alkhairai
"Kiyi jaquri sumayya,na miki shishshigi,saidai ina mai baki haquri tare da neman
alfarma kan ki yimin wannan alfarmar kada ki watsan qasa a ido" maganar malam din
ta hadu ta sake yi mata nauyi a ka,duk da halin ha'ula'in da take ciki amma haka ta
tattara kalaman
"Don annabi ka daina fadan haka malam,ka daina bani haquri,ni bani da wani da na
cancanci a nemi alfarmata a kansa,kaine silata kai ka haifeni,duk yadda kayi da ni
malam daidai ne,na tabbatar ba zaka taba cutar da ni ba,na amince na miqa wuya a
gareka,roqon da nake maka kadai shine malam ka bini da addu'a,ka sakani cikin
kowacce addu'a taka,Allah ya qarfafeni,ya hanani gazawa bare na watsa maka qasa a
ido,na samu juriya mai yawa da zata kaini ga cika burinka" tana kaiwa nan ta gaza
dairewa,sai ta fashe baki daya da kuka zucuyarta na tuna mata abubuwa masu
yawa,wadanda suka faru da wadanda kan iya samunta a gaba,fata take Allah yasa
SHAFUKAN KUNDIN QADDARARTA sun qare ashe akwai wasu sabbin shafukan kar a gaba,sai
yaushe ne zata kammala bitar wannan kundi mai dan karen wuya da sanya zuciya da
gangar jiki yin rauni,rauni kuwa bana wasa ba,ya barwa zuciya da rayuwa tabbai masu
wuyar warkewa,masu wahalar sha'ani da sarrafawa tare da tanqwara zuciya a kansu,duk
wanda ke dakin jikinsa yayi sanyi,sunsan mai take tunawa
"Insha Allahu sumayya daga wannan karon ba zaki sake kuka ba,da yardar ma duka
lokacin dariyarki ne yayi,na tabbatar da cewa ban kaiki imda zaki wulaqanta ba,na
kaiki ne cikim ahalin da suka gaji karamci da mutunci tun daga tushe,ko bana raye
ina da yaqinin muhtari ya isheki uwa da uba ma baki daya,addu'a kuwa kullum kina
cikin addu'o'ina,zaki rabauta sumayya da yardar Allah,tashi kije,Allah ya
albarkaceki da dukkan wani abu da ya shafeki"
"Amin" baki daya mazauna dakin suka amsa,sai ta kasa tashi saida anty dije ta
kamata,kai tsaye dakinta ta kaita ya zaunar da ita sannan ta zauna gefanta tana
kallon yadda take kuka kamar hawayenta zai qare,bata cemata ta tafas ba har sai
data soma tsagaitawa don kanta,bawai don ta gaji bane ko ta samu sassaucin da take
son samu,ta tsagaita ne saboda yadda idanunta suka soma radadi da kuma yadda ta
fuskanci antyn nason tayi magana da ita
"Sumayya kuka kike saboda auren almustapha?" Ta jefa mata tambayar kamar wadda
batasan batun ba
"Na tabbata bakisan waye almustapha ba,banda haka da sai nace kukan da kike kin
yiwa Allah butulci" jajayen idanunta ta daga ta kalleta alamar tamabaya,ciki yaqini
anty dijen ke kada kai
"Tabbas abinda na fada hakan yake,kinsan irinsu mustapha suke tsada a wannan
lokaci?,kinsan yadda mustapha ya tara managartan halaye kuwa?,kin taba tambayar
kanki me yasa su'ad ke tsananin kishinsa duk da kishin banza take tunda batasan
yadda zata riqeshi ba?,kin manta waye baabaa da karamcinsu?,kina zaton idan kika qi
aurensa zaki ci gaba da zama haka ba tare da kinyi aure ba?,kinwa kanki wadan nan
tambayoyin?" Kai take girgizawa bayan ta gama sauraronta,cikin rawar murya ta soma
furta
"Anty a fuskata almustapha bashi da kirki,bai taba kyautata min ba ko sau
daya,anty...kin manta yadda auren soyayya ke kayawa a wannan zamanin ina ga irin
wannan?,baki daya almustapha anty ba ajina bane kamar yadda nake nima ba ajinsa
bace,babu dacewa tsakanina da shi anty,komai nawa da nashi ya sha banban,ra'ayi
yanayi al'ada wayewa da dabi'u,ta yaya zamanmu zaiyi daidai,baya ga haka ma baki
daya anty KISHIYA!,kishiyar ma irin su'adah,kin manta anty ina kika baro
wannan?,kin manta kishiya duk inda na shiga itace babbar qalubalena,bayan bansan me
na musu ba,ko don ni yarinyace?,ko din bani da qarfin qwatarwa kaina 'yanci,ko don
ban iya mugunta da baqin hali ba,wadan nan sune dalilan?" Ta fada wasu hawayen masu
dumi na bin kuncinta,hannunta anty dije ta riqe tsam cikin nata,madadin taga tashin
hankali bisa fuskarta sai taga murmushi ne ma kwance kan fuskarta
"Almustapha?,ko ba haka bane sunanshi?,kin manta shi namiji ne?,namiji kuwa ko
wayeshi ta bangaren zamantakewar auratayya dole ya sakarwa mata,ki manta da wannan
ki cire rashin soyayya a tsakaninku a matsayin matsala,kishiya ita kike tsoro?,ina
zaton zuwa wannan lokacin kin horu sumayya,meye yayi saura meye bakiji baki gani
ba,sai d'ai d'ai,wannan karo ki sama ranki cewa kishiya ga gama yin nasara a kanki
da yardar Allah,waccan karon ma dan dai kawai yana cikin KUNDIN QADDARARKI ne,ke
mai bawa wata labari ne,dame kishiya zata tsorataki sumayya,bayan kina da
Allah,kina da tsarkakakkiyar zuciya,ke matuqar su'ad ma ta baki tsoro sumayya ke
kika so,ki kwantar da hankalinki damuwa ba taki bace,bakisan sirrin da Allah ya
boye ba har ya turo baabaa dai dai wannan lokaci,bana son qara ganinki hawayenki
daga yau" Kai kawai ta gyada mata ba don tana tsammanin samun salama cikin ruhinta
ba,komawa tayi kawai ta lafe kan gado kanta na sarawa,ita kadai tasan me take
ji,kai kawai take mirginawa tana jin nauyi da girmam zancan a qirjinta,su halima da
zainab ne suka shigo a sanyaye saboda ganin yanayin sumayyan,antyn tace suje kawai
ba zata samu zuwa ba ita da sumayyan,bata son ta tafi ta barta a yanayin da take
ciki,wayarta dake gefanta tayi ruri,kiran abdur rahman ne,idanuwanta ta runtse tana
kiran sunayen Allah,sai a sannan ya fado mata,me zata da shi?,me zata gaya masa ya
yarda da ita,tabbas bata da abinda zata ce masa,hakanne ya sanya ta qyale wayar
taci gaba da rurinta har ta katse don karan kanta,qarar wayar kawai qara mata ciwon
kai yake,wanda zuwa lokaci wani zazzafan zazzabi ya rufeta ta kwanta sosai,saidai
bata bari kowa ya gane ba.

****** ******* ********

Tunda ya isa gida kafatanin al'umar dake cikin gidan suka fuskanci akwai
wani gagarumin al'amari na farinciki da ya faru da mai gidan,tun daga manyan
ma'aikata na gidan har qananu,take ya yiwa kowa qarin albashi sabida tsananin
farinciki da nuna tsantsar godiyarsa ga Allah.

Bai samu ganawa da matan gidan ba sai bayan sallar magariba,ya warware musu
komai,babu abinda ummee tace,ita kanta tasan yaron nata yana da buqatar sauyin
rayuwa,kawaici kawai irin nata yasa basa tsomala baki cikin lamuransa,saidai sauyi
wanne iri?,sauyin zai yiwu kuwa ta wannan bangaren,bayan kowa yasan ra'ayim
almustapha wajen zabar matar aure?,kai hasalima kaf tarihin rayuwarshi bashi da
muradi ra'ayi ko sha'awar yin mata biyu sam sam,bata manta yadda ya dinga qananun
maganganu sanda yayansu adam zai sake aure na biyu,saidai a tarbiyyarsu sam babu
musu ko jayayya kan duk hukuncin da jagoran gidan ya yanke,saidai su tayashi bin
dokarsa ko hukuncinsa,bangaren anty maamaa ma tayi farinciki,don a dan zamanta da
sumayya ta karanci halayenta,ta kuma san ta sha banban da halayyar su'ad,saidai
itama tata fargabar ta yaua almustaphan baqin bature dan ra'ayin riqau mai doka da
qa'idoji zai amshi wannan lamarin,gashi uwa uba baban yaja kunnen kowa da kada
wanda ya sanarma almustapha maganar shi da kansa zai sanar masa,kome meye tasan na
dan lokaci ne zai wuce,to baki dayansun masu biyayya ne gareshi,sannan babu wanda
baida burin ganin farinciki cikin rayuwar mustaphan.

Anty farida da huda kam da suka ji lamarin har wani ihun farinciki suka
saki,kasa zama sukayi sai da suka dangana da baabaan suka yi masa godiya tamkar su
ya yiwa,murmushi kawai yayi yasan lamarin na damun kowa,koma dai meye shi ya fisu
farinciki da shigowar jinin sule cikin tashi zuriyar.

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*
*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

7⃣4⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

*Allah S W T yana cewa*

*KACE HAQIQA MUTUWAR DA KUKE GUJE MATA MAI RUSKARKU CE,SANNAN KUMA KU KOMA IZUWA GA
MASANIN ABINDA KE FILI DA NA BOYE YA BAKU LABARIN ABINDA KUKE AIKATAWA*

Ya Allah kasa ta ruskemu kana masu farinciki da mu,muna masu farincikin haduwa da
kai

______________________________________

       Gaba daya ta koma ta zama wata irin cikin kwana biyu kacal,duk wani kuzari
da buri data ci na bikim zainab yayi nashi wuri,tsantsar tashin hankali take shiga
a duk sanda ta tuna lamarin dake tunkarota,ko ya zata qare?,ko meye zai faru da ita
wannan karo?,shine tambayar da take yawaita yiwa kanga,uwa uba Abdallah da ya tsaye
mata a rai,ana ya gobe kamu nafisa ta iso gidansu,wani kallo take binta da shi tana
tabe baki
"Ke yanzu sai kace wadda zatayi auren fari kamar wadda yau zata fara zama da
kishiya shine kika bi kika susuce haka?,a haka zaki qwaci kanki duk kin fafa
zabgewa kina ramewa?,amma wallahi kin bani kunya" cewar nafisa,daga kai tayi tana
kallonta tare da mamakin wanda ya gaya mata zancan
"Me kike kallo na,munyi waya da amira ta gayan komai,ta kuma ce tana kiran wayarki
amma kullum switchoff,na gaya mata zan shigo kanon tace na duba mata ke don Allah"
ta sake fadi tana duban sumayya,fada ta zarce da yi maga,kuka ya qwacewa
sumayyam,wau su don Allah ita kadai take gano abinda take ganowa,su basu hangen
komai,ta gama fadanta sannan ta koma lallashinta,inda daga qarashe ita ta tilastata
ta miqe tayi wanka tace zata rakata siyayya,jiki babu qwari haka ta shirya,ga
zazzabin dake sakadarta a hankali,bugu da qari ga wani ciwon mara da ya saukar
mata,wanda bata sani ba ko tashin hankalin da take ciki ne ya jawo shi oho.

       Wani katafaren shago wanda ke saida kayan jiki na zamani nafisa ta kaisu,da
idanu sumayya ke kallonta sanda take loda kayan tana zaba,harda wanda sumayyan
yanzu ke amfani da shi tun wanda ta taba siya mata a uk har yau da shibtake amfani
da yake ya karbeta,suna cikin mota take shaida mata yadda zata yi amfani da
sauran,haushi ya kama sumayyam,yamzun suna nufim wami namiji zata yiwa hidimawa
jikinta saboda za'a daura mata aure da shi
"Wallahi da kin gayan ni kika  siyawa bazan barki ba,sabida asarar kudinki kawai
kika yi babu abinda zanyi amfani da shi cikinsu" a fusace nafisan tace
"Wallahi baki isa ba kinyi kadan,amfani da su wallahi ya wajabta a kanki" ganin
yadda nafisan ta hasala ya sanyata yin shiru,saboda ko qwaqwaqwarar magana bata
sonyi yanzu kanta zau fara sara mata.

       A bangaren baabaa kuwa shirin daurin auren yake babu kama hannun yaro,kai
kace wannan shine karon farko da za'a yi daurim aure cikin familyn baabaa prof
din,ana ya gobe daurin aure suka baro abuja suka sauka gidanshi dake kano,saboda ya
kasance kusa da abokinsa,duk wanda ya dace ya san da daurin auren babu wanda baabaa
bai aikawa ba.

       Duk abinda ake idanu ne nata sai ta koma 'yar kallo sabanin daa da itace
amara,katunan daurin aure masu dan karen kyau tsari da tsada baabaa ya sanya aka
buga ya baiwa malam wani shima ya raba wani,duk wanda yaji daurin auren ya zama na
mutum biyu harda sumayya sai yayi mamaki,saboda kowa yasan babu ita a batun,da
kansa baba ya sanya cikin kwanaki hudu aka yima sumayyan akwatu uku na suttura
wadanda zata sanya kawai bawai lefe bane,lefanta yace sai almustaphan yayi kamar
yadda ya yiwa su'ad,kaya ne masu kyau da tsada dinkakku,kama daga shadda laces
atamfa material sa sauransu.

        Da ido kawai take binsu lokacin da aka zo yima amarya zainab lalle,almara
kawai take ganin komai,wai ita za'a daurawa aure nan da kwana uku?,abinda ko cikin
mafarki bata taba hasashensa ba,qememe taqi bada hannunta ayi mata komai,anty dije
tace a barta kada a matsa mata,tasan cewa akwai lokacin da ita anty dijen da kanta
zata sanya ayi mata kuma dole ta bada hannunta.

        Ana ya jibi daurin aure kwana tayi tana kuka saboda nasihar da mama tayi
mata,ta gaya mata duk wanii motsi da zata yi wanda bai dace ba tamkar ta watsawa
mahaifinta qasa a ido ne,ga gidan ya fara amsar baqi,haka ta tashi washegari da
zazzabi da ciwon kai amma haka ta dinga cijewa tana shiga jama'a,wanda hakan bai
amfana mata komai ba face sake qaruwar ciwon kanta.

          Bayan sallar isha'i tana kwance cam uwar dakan maman kan abun
sallah,hasbunallahu wa ni'imal wakil kawai take ambata babu qaqqautawa saboda yadda
taji nugun zuciyarta na daduwa,sallama taji anayi tsakiyar gidansu wadda ta sanyata
miqewa dungur gur ta zauna tanq raba idanu kamar wadda aka ritsa da wuqa a
maqogaro,muryar abdur rahman ce,sai gabanta yaci gaba da faduwa ta fashe da kuka
qasa qasa tana cusa kanta tsakanin cinyarta.

         Daga airphort direct gidan ya zarto ko gida bai nufa ba sakamakon mummunan
labarin da ya sameshi ta bakin bahijja,kai tsaye aka yi masa iso falon malam wanda
shigowarsa gidan kenan,a mutunce suka gaisa saidai kallo daya malam yayi masa yaga
sauyi tattare da yanayinsa
"Ina fata lafiya malam abdur rahman" cewar malam din,kai ya girgiza cikin sanyin
murya
"Malam,na jima ina neman yarda da amincewar sumayya tun kafin rasuwar yaya mukhtar
har kawo yau din nan,na fara samun hadin kanta a kwanakin nan,saidai ta nemi
alfarmar na bar maganar har ka kammala aurar da zainab,kwatsam sai jiya na samu
labarin wai za'a aurar da sumayya malam haka ne?" Kai ya jinjina kafin yace
"Wannan haka yake abdur rahman,zan aurarwa dan aminina sumayya,sam banyi tunanin
kana ci gaba da neman sumayya ba abdur rahman,ban kawo haka a raina ba" sosai ya
girgiza da jin amsar malam din,idanunsa suka kada ya dubi malam din
"Malam ni nafi cancanta da sumayya,ka yimin alfarma ka aurar min da ita" cikin
tausayawa malam din ke dubanshi
"Kayi haquri abdur rahman,wannan wanda zan baiwa sumayya wa familynsu sunfi qarfin
na musu haka,idan da wani ne can daban babu abinda zai hana na maida auren
kanka,amma zan gaya maka kadan daga labarin muntari,zan gaya maka kadan daga cikin
waye muhtari a gurina" warware masa yayi DANGANTAKAR dake tsakaninsa da baabaa
prof,dangantakar kuma da suke fata da burin ba zata sake katsewa ba har
ABADAN,wanda hakan suna burin ya zama hanyar ci gaba da yado da qarfafa zumunci da
dangantakarsu.

        Cikin gamsuwa abdur rahman yakw gyada kai,babu shakka irin wannan
dangantaka dake tsakanin malam da muhtari ko shine idan yana da diya abinda zai iya
faruwa kenan,ba zaiso ya zama silar datse wannan kakkaurar tsohuwar igiya ba da ka
qullata tun duniya na kwance,tun basu gama sanin su waye su ba kawo yau,saidai
rabuwa da sumayyan ba abu bane mai sauqi tattare da shi,wani mugun ciwo ne da zai
ci gaba da illata shi
"Shikenan malam,ina muku fatan alheri,saidai mu a tayamu da addu'a,Allah ya bamu
haqurin jurewa" ya fada cikin karyewar murya
"Allah ya yi maka albarka,ya sanya juriya a zuciyarka,ya musanya maka da wadda ga
fita alkhairi a gareka"
"Amin malam,na barka lafiya" ya fada yana mai miqewa,cikin tausayawa malam din ya
bishi da kallo,har ya kai qofa ya kirashi ya dawo ya tsugunna kansa a qasa
"Abdur rahman"
"Na'am malam"
"Idan har babu takura kuma ba zaka damu ba,mai zai hana ka nemi halimatu 'yar uwar
sumayyan,a tunani kamar zata iya maye maka gurbinta"
"Indai malam kana ganin hakan yayi daidai bazqi haifar da wata matsala ba na
karba,ina kwadayim zuriyarka ne malam,na tabbatar akwai alkhairi ga dukkan wani
d'aa da ya fito daga gidan nan" murmushi malam din ya saki cikin jin dadi
"Kayi tunani a nutse,kada kayi abinda kasan zaka takura,idan halima tayi maka ka
dawo zan baka ita,idan bata yi maka ba babu komai zan biku da kyakkyawar addu'a"
"Ta yaya malam zanqi jininka,halima jininka ce jinin sumayya,na karba malam,kuma in
sha Allahu a gobe zan bada sadakina nima kada itama na rasata"murmushi ya subucewa
malam,sosai ya sanya musu albarka tare da jan doguwar addu'a ta fatan alkhairi a
garesu baki daya,yace yaje sitting room a bude yake zai turo masa haliman,miqewa
yayi kansa a qasa yana yiwa malam din godiya,abun mamaki cikin qanqanin lokaci
tashin hankalin daya tsinci kamsa kaso dari sai yaji babu hamsin ciki,ya taka ya
fice sitting room din gidan yana jiranta.

      Malam yana daga falon ya qwalawa haliman kira,gama cire lallenta kenan taji
kiran malam din,ta goge hannum nata ta sanya hijabinta ta shiga dakin
"kije sittin ro abdur rahman na jiranki" jin maganar tayi banbarakwai sai ta daga
kai ta dubi malam
"Ni ko yaya sumayya dai?" Daquwa ya mata
"Dan gidanku na kasa gane sumayyan sai ke zan kira?,ke nace ba sumayya ba" bata
sake cewa komai ba ta miqe ta fito ta nufi sitting room din gabanta na faduwa.

      Tsaye yake tsakiyar sitting room din hannayensa goye a bayansa ya zubawa
qofar shigowar idanu,tana sallama suka hada ido,karom farko taji wata faduwar gaban
da bata taba jin irinta ba don ta kalleshi,idanu ya zuba mata yana amsa
sallamar,sai yake hango yanayinta da sumayya muraran,ya taba kula da hakan shekarun
baya amma ba kamar yanzu ba,ga mamakinsa murmushi sai ya subucewa lebansa,ya zuba
mata ido yana ci gana da kallonta har ta qaraso gabanshi,cikim diriricewa tace
"Ya abdur rahman gani.....malam yace wai.....kana jira na"
"Bismillah zauna" babu musu ta taka ta zauna kan daya daga cikin kujerun,gabanta ya
iso a hankali ya zube a gabanta wanda hakan ya sake haddasa mata faduwar gaba
da,sai ta jita ta takura sabida basu taba zama gab da gab irin haka na,duk a qasa
yake zaune a gabanta amma yana kusa da ita
"Halimatus sa'adiya,malam baice miki komai ba?" Kai ta gyada da sauri sabida ta
gaji da yadda gabanta ke faduwa,murmushi ya dan saki,wato shi zai yiwa kansa yaqi
kenan ko?,daga idonsa yayi ya zubesu a kanga,sai ta janye nata idanuwan
"Halimah kina sona zaki iya aure na?" Taji tambayar babu zato na tsammani,ido ta
zaro tana dubanshi,kasa cewa komai tayi har sai da ya maimaita,bakinta na rawa tace
"Yaya abdur rahman.....yaya sumayya.....ita yaya sumayya fa?" Murmushi ya saki
"Bakya gidan ne?,bakisan malam ya bata wani ba?,ni kuma a yanzu malam ya bani ke
zaki iya aure na?" Shiru tayi gabanta na faduwa,yayin da kunya ta kamata ta sadda
kai qasa qwalla na taruwa a idonta,hakan taji tsoro ya kamata,malam zai aurar da
ita kenan itama,jin shiru ya sanyashi sanya yatsunsa ya daga fuskarta,kallo daya
tak yayi mata ya fuskanci ta karbi lamarin duk da bata bayyana ba muraran sabida
kunya da tsoro
"Kice wani abu mana halimah,koda baki sona ki amince min zan saki ki soni
kinji,kada nayi asarar zuriyar malam baki daya ace na rasa ko daya,da wallahi barin
garin zanyi" dariya taso qwace mata saboda yadda ua shagwabe mata,kunya ta
lullubeta saita qudundune kanta cikin hijabi,dariya ya saki
"Iyeeee,ko baki ban amsa ba ma na gano a bata,ashe dai har kunyar abdur rahman din
akeji,lallai na samu karbuwa,koba haka bane?" Shiru tayi taqi amsa masa
"Shikenan tunda ba zaki ce komai ba bari na haqura na tafi,kuma ba zaki sake ganina
ba,zan kuma gayawa malam baki amince ba sai na haqura" ya fada kamar mai tafiyar,da
sauri ta daga kanta tana shirin cewa wani abu,sai ta ganshi tsaye a gabanta,kunya
ta sake kamata tayi qasa da kai suna dariya baki daya.
       Komai na Allah ne haka komai nufin Allah ne,sai gashi ya shantake har qarfe
tara da rabi yana gidan,halima akwai kunya saidai alamu baki daya sun nuna ta
karbeshi,sai goma saura sannan yayi mata sallama,ya zuba hannayensa a aljihu yana
dubanta
"Ina wayarki" cirota tayi daga hijabinta,karba yayi yana qoqarim cire layin ciki ya
zura a aljihunaa sannan ya ciro daya daga cikin layukansa ya saka mata yana cewa
"Gashinan,ni kadai zan dinga kiranki kafin na siya miki wani layin,ina da kishi
bana son wani ya sake jimin muryar mata ta,sai da safe muje na rakaki" har bakin
qofar shiga tsakar gida ya rakata sannan ya juya ya fice,zuciyarsa fes yana mamakin
lamarin Allah,ya riga ya qaddara sumayya ba matarsa bace shine masanin GAIBU mai
rubuta QADDARAR BAYINSA,Allah kenan mudabbirul amri mai jujjuya al'amura a lokaci
da baka zata ba,ya shigo gidan cikin tashin hankali da jimami ya fita cikin
farinciki da annushuwa,babu abinda zai cewa dattijon arziqi mai karamci sai godiya
tare da yi masa fatan kyakkyawan qarshe.

        Tana shiga tsakar gidan taga shigar zainab dakin mama wadda ta fito daga
kitchen ta dafawa sumayya tea,da sauri tabi bayanta don fatinciki ke cinta,bata da
'yar uwar da take sharing sirrikanta da ita kamar zainab din,tsaye ta taddata tama
fifitawa sumayya tea din,sam halima bata kula da sumayya dake dakin ba ta dane
bayan zainab wanda hakan ua sanya tea din hannunta tangal tangal zai zube
"Wayyo zainab,yau Allah nima ya bani yaa abdur rahman,zainab mallam ya bawa abdur
rahman ni,a gobe nima zanbi sahunku zan zama matarshi" sak sumayya tayi tana
dubanta,tun dazun take jira taji wani abu daga wajen abdur rahman din ko malam amma
taji shiru,gani tayi zainab tayi shiru kawai saita sake kallonta
"Baki ce komai ba ya kikayi shiru" da idanu tayi mata alama da wani na gun,ta wurga
idonta saita hangi sumayya,da sauri cikin jin nauyinta ta juya zata fice,cikin
kasalalliyar murya tace
"Zo yaki halima" cikin jin nauyinta ta iso inda take ta zauna,ta karbi tea din da
zainab ke miqo mata ta aje gefanta
"Meye na jin kunyata halima kamar wadda ta aikata haramci,wallahi har ga Allah naji
dadi da wannan hadin da malam yayi,sannan abdur rahman ya cika mai sonmu tsakani da
Allah da son iyalan gidan nan,ki saki jikinki ni yayarku ce har abdur rahman din ba
tun yau ba dama,ki manta da cewa abdur rahman ya raba sona,Allah shine dama yasan
abinda ya boye shi yasa bai taba darsamin soyayyarsa ba ko qanqani,illa ganin girma
da mutuncinsa da nake,babu wani abu da ya isa shiga tsakaninmu,dan uwa ba wasa
bane,idan banda Allah babu wanda ya isa yayi maka kyautar dan uwa,Allah ya baku
zaman lafiya ya tabbatar da alkhairi"
"Amin" suka amsa baki daya,taji dadin addu'ar sumayyan sosai,to tsakanin daren zuwa
wayewar gari sun sake wata qwaryar
qwaryat shaquwa,kusan kwana sukayi suna waya sumayya na jinsu,wadda tuni ta goge
duk wani abu da ya shafi abdur rahman daga wayarta,tayi lamo bisa gado,kewa ta
kamata,ta dinga matse hawaye tana tuna mukhtar,mutuwa mai tonon silili,idan banda
mutuwa ta dauke mata shi da tuni sun jima da shimfida sabuwar rayuwa,wataqila ma da
tuni ta sake haifa masa 'ya'ya,saidai tsarin Allah shine tsari,(Allah kasa mu dace
ka cika mana burikanmu kasa mu cika da imani don alfarmar sayyadina rasulullahi S A
W)amin.

Washe gari kawu da wansa da qaninsa mahaifin abdur rahman sai gashi da safe
yazo nemawa abdur rahman din auren halima,wanda ya bawa malam dariya,yace ai da
abdur rahman da halima duka nashi ne,ko basu zo ba sai ranar daurin auren ya riga
ya bashi ita,a nan kawun yayi godiya qwarai suka tafi,a nan suka bar abdur rahman
ya sake baje kolin soyayyarshi,sai da aka soma nemansa a asibiti sannan ya
tafi,binsu sumayya take da kallo,wato bawa bai gujewa Qaddararsa.

*KUNDIN QADDARA*
Rana bata qarya saidai uwar diya taji kunya inji malam bahaushe,wannan haka
yake,domin yau take juma'a wadda ta kasance rana ce mai girma da muhimmanci da kuma
dumbin tarihi wajen malam sulaiman gombe,wanda zai aurar da duka diyoyinshi mata da
Allah bashi cikin mutunci da rufin asirj,wanda abun farinciki ne da godewa
mahalicci a irin wannan zamanin namu mai cike da rudi da abubuwan firgici ga 'ya'ya
mata Allah ya yi maka baiwar aurar da diyoyinka mata baki daya hannun nagartattun
maza da kake saka musu ran zasu musu riqo na mutunci,ta hannu daya baabaa prof
shima cike yake da farinciki,domin kuwa tun qarfe tara ya iso wajen a maimakon
qarfe goma da za'a daura auren.

Daga cikin gida kuwa tuni zainab ta yi wanka kwalliya irin ta amare,tana
sanye da wani lace mai azabar kyau wanda sumayya ce ta siya musu,haka amarya halima
na sanye cikin shadda wadda ready made ce abdur rahman ya aiko mata da ita,tayi
mata kyau ainun,dukkaninsu idan ka dubi fuskokinsu qunshe take da fara'a sabanin
sumayya dake kwance ko wankan ma bata kai ga yi ba,binsu take da idanu tana rayawa
cikin ranta,kowa yana rayuwar farinciki banda ita,ita kadai ke fadawa halin
jarrabawa cikin yaran gidan nasu?,nafisa ce ta sanyata a gaba wanda tilas ya
sanyata tashi tayi wanka ganin tana son qara mata ciwon kai,ta fitar mata da wani
dan banzan lace cikin kayan da aka kawo mata dinkin skert da riga mai dogon
hannu,kamar yadda ya qawatu lace din haka ya qawatata ta,babu abinda ta shafa banda
turare mai da hoda amma sai ta fito cas gwanin sha'awa,fuskar ta tayi fayau ta
dashe tare da ramar da tayi,naji ance amarya daban take ko batayi kwalliya ba,to
kusan hakanne ya tabbata ga sumayya,komawa tayi ta kwanta abinta,don hayaniyar data
cika gidan kadai ma damunta take bare ta waje,wanda tuni layin ya soma dinkewa,tana
iya jiyo kwaroroto da muryar maroqa iri daban daban,sun baje hajarsu kowanne yana
kwasar rabonsa,basa wasa da bikin daya shafi gidan professor mukhtar muhammad
adam,don idan kazo a sa'a wani daga ranar ya daina roqo sai ya samu jarin da zai
isheshi sana'a,ballantana yau da sunan almustapha ya bayyana baro baro na cewa shi
zai sake aure.

Cikin qanqanin lokaci layin ya cika ya tumbatsa da jama'ar baabaa


prof,jiniya iri iri ke tashi wadda ta qusoshin gwamnati ne da jami'an tsaro,kowa
yana iya jiyo yadda daurin auren ke kayawa sakamakon maroqan dake bayyana dukkan
abinda ke faruwa a wajen,auren zainab sulaiman gombe aka fara daurawa da angonta
abulkhairi muhammad bala kan sadaki dubu talatin,sannan aka daura na halimatus
sa'adiya sulaiman gombe da angonta abdur rahman Ahmad yusuf kan sadaki naira dubu
hamsin,daurin auren qarshe shine na doctor muhammad almustapha professor mukhtar
adam gombe wanda aka daura kan sadaki naira dubu ashirin,sai kuma kyautar mota duka
cikin sadakinta take,daidai kunnenta nafisa tazo ta rangada guda,jin gudar take
kamar ana zaqular qwaqwalwarta,saita dunqule ta cure waje daya,ta saki wani marayan
kuka wamda bai fidda sauti,ita kadai yasan me take ji cikim zuciyarta,shikenan yau
din ta sake zama mallakim wani bayan mukhtar?,wanin ma da baisan daraja ko qimarta
ba,ya zata kaya musu?,ya zata kasance?,bata da amsar wannan.

Kusan ranar haka ta wuni,da daddare ta dauki kayan sawarta kala uku ta gudu
gidan anty dije,a can ta barje kukan ta son ranta,saboda a can babu dama saboda
idon mutane,itama antyn batasan tana nan ba,sai wayar mai gadinsu ta ara ta
gayamata don kada su nemeta,washe gari aka sha yini sosai,duk abin nan da ake
sumayyan na gidan anty dijen,haka ta wuni kwanciya don mai gidan baya nan,ita kuma
antyn a can gidansu ta kwana,sai gobe zata dawo idan an kai amarya,halima itama sai
next week za'a kaita,kafin nan an kammala yi mata tata siyayyar.

******* ****** ********


Zaune take a uwar dakan anty dije wadda jiya bayan kai amarya ta dawo
gida,tana ta faman shirya kayansu cikin trolly abinta,sumayya na zaune daga
bayanta,sanye take da doguwar riga 'yar kanti mai qaramin hannu,kanta ba dankwali
sai gashinta mai baqi da santsi data hade cikin ribbom,jingine take da kujerar dake
dakin qafafunta amiqe,hannunta riqe da cup din tea wanda tun dazun aka hado mata
shi har yana gab da hucewa bata yi masa kyakkyawan shaa ba,idanuwan nan a kode
tamkar danyen nama kamar yadda fuskarta take a kode alamun ko yaushe cikin kuka
take,sam anty dije taqi bata fuskan kawo wani qorafi ko wata magana kan auren,tunda
dai an riga an daura ta riga data zama matar almustapha,abu guda ne kawai yanzu a
gaban anty dijen yadda zata shirya diyar tata fes ta iya shiga kowanne bigire na
rayuwa,abinda ke sake karya zuciyar sumayya yadda taga ita antyn ma murnarta
take,hannunta tasa ta shafa gashinta hadi da lumshe ido tana kiran sunan Allah qasa
qasa,ita kadai tasan meke yawo cikin kwanyarta,kamar ta cire qwaqwalwar ta huta
haka take ji,waiwayowa antyn tayi tana cewa
"To zaki bimu abujan ne ko kuwa sai munzo daukar amarya?" Mai neman kuka ne aka
jefeshi da kashin awaki,aisai kawai ta saki kukan ta sosai ta dire cup din tea
din,baki anty dije ta kama dariya na subuce mata
"La'ilah,ku jimin yarinya,wai ita bilhaqqi da gaskiya bata son almustapha,mutumin
da ake so ko kallon arziqi ya yiwa wasu,to wallahi saidai kiyita kukanki kada ki
fasa bazan lallasheki ba,tunda kinqi jin lallashi ballantana shawara,da kinsam tun
usilu ba zaki iya biyayya wa su malam ba ai da kin gaya musu tun sanda suka tasamma
hada auren,sai yanzu saboda yankan baya zaki tasani gaba da kuka me zan miki,haka
zakije ki yi gaban su'ad din,tabdi wallahi da kuwa kin jawa kanki,idan kin gama
kukan kya tashi kiyi abinda ya dace,don tun jiya malam ke tambayarki bai gqnki ba
zai damqa miki sadakinki" anty dijen ta juya tana ci gaba da aikace aikacenta har
sanda laila ta shigo da wayar sumayyan hannunta tana fadin
"Anty amira ce a layi" ta miqawa sumayyan,harara ta danqara mata hakan ne ya sanya
anty dije karbar wayar ta kara a kunnenta bayan ta sanyata a handsfree tana fadin
"Ai amira kema ta shafeki ba zata amsa wayarki ba,ke da jin muryarta sai bayan wani
lokaci"dariya ta qyalqyale da ita
" don Allah anty matsa kusa da ita nayi kata waqar ta zama ta zama,nima haka ta
yimin,ranki ya dade amaryar yayanmu ayi mana haquri,amma dai ya musty ne ya riga ya
zama mijin sai haquri,anty barta ko bata yi magana ba yanzun zata yi idan muka zo
sayan baki"dariya suka sanya baki daya,hakan ya sake qular da zuciyar sumayya,sai
ta miqe ta fice tana kuka muraran kamar wata qaramar yarinyar,binta anty dije tayi
da kallo tana dariya,har yau da sauran quruciya sosai tattare da sumayyan,gata nan
a zahiri ta bayyana.

Tunda aka daura auren ranar juma'a baabaan bai bar kano ba har zuwa yau
litinin,misalin qarfe takwas na dare bayan ya gama cin abincin dare ya dauki
wayarsa ya soma lalubar musty man.

Dawowarshi kenan daga asibiti,yau a gajiye yake saboda mutum uku ya yiwa
c.s,kayan jikinsa kawai ya cire ya rataye suit dinshi a inda yake rataye kayan da
za'a wanke masa,ya zaluqo daya daga cikin towel daga ma'ajiyar towel ya daura
sannan ya shiga wanka,kwanciyarsa yayi luf cikin ruwan wankan mai azabar dumi da
qamshi,duminsa na ratsa kowacce gaba ta jikinsa,idanunsa na alumshe sai ka rantse
da Allah bacci yake saidai idanunshi biyu,tunani ne kala kala kan kwanyarsa yake
yawo,ya soma gajiya da zaman wannan hotel din wanda kusan a ciki yake rayuwa,duk da
yana da gida mallakinsa cikin qasar,saidai hakanan yafi sha'awar zamam hotel din
yana ganin kamar ya fi masa sauqi,idan gidan ne dole sai ya nemi ma'aikata da zasu
zauna cikin gidan su kula masa da tsaftarsa da komai da komai wanda shi ba kasafai
yake son ma'aikata haka barkatai ba,musamman a qasar da ba taka ba,tun yana cikin
bayin ya dinga jin rurin wayarshi,data katse wani kiran ke shigowa,sai ya saki
tsaki ya sake gyara kwanciyarsa ba tare da koya bude idanunshi ba bare yayi haramar
fitowa,ga tsammaninshi su'ad ce don kimanin sati guda rabon da ya nemeta,ta kirashi
dazu zai shiga thiather ya dakatar da ita,saboda abu na farko data fara da shi
shine mitan ya watsar da ita sabida ta koma zata qarasa karatunta,shikam a yanzun
yana ganin matsalarta ce,shi ya gama da wannan issue din,sabgogin dake gabansa ma
kawai sun shasa masa kai,sai da ya kammala wankansa a nutse sannan ya fito ya daura
towel dinsa a qugu wanda hakan ya fito da dukkan suffa da zatinsa na cikakken
namijin da ya amsa sunanshi,ya qarasa wani sashi daban ya daura alwala ya fito.

Zai gifta wayar kenan ta sake ruri,ya waiwaya kadan ya dubeta sai yaga
sunan abbu na yawo saman screen din,sunan da ya sanyawa baabaa prof kenan,da
hanzari ya fasa abinda yake ya isa ga inda wayar take ya daga cikin girmamawa
tamkar yana gabanshi cikinnn nutsuwa da sanyin murya
"Barka da warhaka" ya fadi
"Barka kadai,ina ka shiga ne haka tun dazun ina kira ko kana asibiti ko company?"
"A'a wanka nake" ya fada a taqaice,don a tsarinsa bai fiya doguwar magana ba,kadan
ce mai ma'ana
"To madalla"
"Lafiya kuke baabaa ya kowa da kowa?"
"Kowa lafiya qalau yake almustapha"
"Masha Allah"
"Ammm,almustapha kawai tsarin zuwanka gida ne nan kusa?" Dan jim yayi kafin ya amsa
"A'ah,saidai ko idan kana son ganina ne?" Yana mamakin yadda yake da kaifin
qwaqwalwa da cimma abun tun kafin ka kammala bayaninka,sau tari suna fara magana da
baabaan yake gane mai yake da buqata tun bai qarasa ba
"Tabbas,ina buqatar ganinka,wani muhimmin batu ne ya taso ma rayuwarka nake so mu
gana a kai,yaushe kake da chance din zuwa?" Duk da maganan ta dan sanyashi a duhu
amma bai da niyyar tambaya
"Yaushe kake son gani na?"
"Eh to,ko kamar nan da sati biyu haka"
"Sati biyu masu zuwa ina zuwa da yardar Allah"
"To masha Allah,Allah yayi maka albarka,sai kazo"
"Amin,na gode" a hankali ya ajjiye wayar yana binta da kallo,zuciyarsa na son
sawwara masa muhimmin batun da baabaa yace ya taso wa rayuwarshi,duk iya hasashensa
bai canka ba,hakan ya sanya ya dage kafadunsa biyu na rashin damuwa ya nufi inda ya
ajjye kayan shafarshi a tsare kamar wata mace,komai nashi mai aji da tsada irin
wanda maza ke amfani da shi,yana shiryawa yana tunanin yadda tafiyan zata
kasance,dama yana son zuwa daya daga cikin asibitocinsa dake kano kwana biyu bai
leqa yaga maike faruwa ba shu da gidan marayunsa,duk da yana da wakili dake gano
duk abinda ke tafiya kuma a kai duk abinda ake da buqata wuraren,amma bai saki
komai ba balle kowa yayi mishi yadda yaga dama,mutum ne shi mai doka da qa'ida
baison kuma a saba masa ko a taka mishi kamar yadda bai taka dokar kowa.

Yana shiryawa yana kiran lambobin da ya saba kiran idan yana buqatar
abinci,duk da sun san kusan cimarsa ta dare,ba wani abu mai nauyi yake ciki ba,a
ladabce suka amsa buqatarsa ya kashe wayar,wanda kamar jira ake ya kashe wancan
kiran wani kiran ya shigo,su'ad ce da layinta na america,yana kallon kiran yayi
banza da shi har sai daya gaji ya katse,haka ta dinga kira har ta hada masa wajen
miscal biyar,wanda tuni ya maida wayar silent don baison hayaniya,daga qarshe saqon
tex ya shigo yasan kuma daga ita ne,baibi ta kai ba ya share ya tada shafa'i da
wuturi,da wuri yake son kwanciya yau ya huta sosai saboda gobe yana da meeting da
ma'aikatan companynsa na saqar abaya.

To masu karatu yanzu fa kusan aka soma ko?,saidai gobe kumin uziri idan ina da
sabga idan kun samu to ba lallai ya kai na yau ba,idan kuma kunji shuru sai
uziri,kasancewar duk sanda kuka ji shiru daga wajen marubuci uziri ne ke kama shi
irin uzirin dake kama kowanne dan adam,babban nauyi marubuci keji cikin kansa da
qirjinsa idan ya soma rubutawa jama'a labari,baya jinsa fayau sakayau har sai randa
ya kammala,Allah ya bar zumunci.

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

7⃣5⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

*ALLAH S W T YANA CEWA*

*ALLAH BAYA JINKIRTAWA WATA RAI IDAN AJALINTA YAZO*


______________________________________

        Wannan karo anty dije daga ita sai yaranta suka koma abuja cike da
kewa,kowa cikinsu sai yaji babu dadi,kasancewar sumayyan ta riga ta shiga jikinsu.

         Sati guda malam ya yiwa baabaa maganar ya za'a yi da jeran sumayya,ce masa
yayi babu ruwanshi wannan ba huruminsa bane,murmushi kawai malan din yayi
"Ku qarata kai da 'yar taka" ya fada yana dariyaanty dije ce ta matsa kan ko daki
daya abasu su saka mata kaya,tilas baabaan ya sanya aka bude daki daya dake saman
aka basu shi suka saka kayan gadon da malam ya siya mata,idan baku manta ba gidan
baabaan na da sashe biyu ne,ko wanne sashi akwai sassa a ciki,sashin daya barwa
yaran nashi daya na wansu ne adam da matan shi,daya nasu mahomud ne da mus'ab,daya
na almustapha ne,kowanne sashi yana dauke da balcony sama da qasa,sannan babban
falo da dakunanan bacci manya manya wanda zasu iya cinye kayan gado set
biyu,bedrooma din cikin corridor suke wanda ke hagu da daman falon,sai ka fito daga
ciki zaka samu falon,sai qofar kitchen daga can gefe wanda qofa daya ce amma idan
ka shiga zata tadda qofofin kitchen biyu biyu,akwai wata qofar daban da zaka fita
vantilation,kusa da kitchen dining area ne,saman babban falo ne shima da dakunan
bacci guda uku,daya ne makeke wanda a ciki mustaphan yake,kowanne sashe nada girma
da yalwa,duk yadda ka kai ga son jin dadinka.
        Dakunan baccin duka guda biyun again dake qasa baabaa yasa aka shirya mata
su ba tare da sanin kowa ba,illa ya yiwa kamfani waya ya basu adress,royal beds ne
set dinsu masu azabar kyau da tsada,hakanan kitchen din aka zuba qawata shi da
dukkan wani kayan qawa da kayan amfanin buqata na kitchen,falon ma ba'a barshi haka
ba,sai da ya sanya aka sauya duk wani abun amfani,a taqaice dai tashin farko sashen
ya sake sauyawa sosai,duk da dama sashe ne wanda ya tsaru ya qawatu tun da can,yafi
kowanne sashe kyau da qyale qyale,kasancewar mai sashin mai son tsafta da
gyara,yayin da matar sashen ta zama mai dagawa da son nuna iyawa da kuma qaunat
ganin tafi kowa.

       Ba wai don almustapha bai da wani gida ba,yana gidan daya kusa a qalla
shekara hudu ana gininshi yana narka masa kudi,har rade radi aka dinga yi a rean
cewa da qyar idan ba gidan wani shugaban wata qasar vane,babu abinda bai zuba ba a
cikin gidan,dai dai da cokali gidan baya buqata,hatta da kayan sangawa baki daya
cupboard din gidan a cike take,wani irin tsari aka yi masa mai bala'in kyau da
daukar hankali,hatta da qasashen da suka ci gaba samun irin wannan gidan sai an
tona,to saidai babu wanda yasan da gidan do ba wanda ya gayawa,shi wani irin mutum
ne da bai fiya son fadin abubuwan da yake yi ba,da fari yaso maida su'ad
ciki,saidai irin rayuwar da yake so ya shimfida cikin gidan ba ita ta shiryawa yi
ba,rayuwar soyayya da kulawa zalla tsagwaronta yakeson shimfidawa cikin gidan wanda
dama ya ginashi ne don ya morewa rayuwarshi da arziqin da Allah ya mallaka masa,duk
sanda ya kalli gidan yana sanyashi nishadi da walwala,ya zuba ido yana jiran yaga
ranar da su'ad zatayi daidai da tsari da ra'ayinsa,ta shiryar karbar irin rayuwar
da yake so,to a lokacin yake saka ran maidata gidan wanda har yanzu hakan bata samu
ba,a qalla kusan watanni shida kenan da kammala komai na gidan,saidai lokaci lokaci
idan yana buqatar kebewa ko hutawa yaje ya wuni ko ya kwana daya ya dawo,cikin
dribobinsa ma mutum daya kacal yasan da gudan kasancewar shi ke kaishi.

  *******  *******    *******

      Duk yadda taso kauda da damuwa cikin ruhinta ko don saboda malam abun yaci
tura,a yadda take yaqe da qoqarin zama cikin mutane duk da gidan nasu yanzu sun
sake raguwa,daga ita sai mama,abdallah ma yaqi zama kasancewar gidan yayi shiru da
yawa,ya gudu wajen yaya yahanasu don acan yake baje kolin tabararsa yayaan da su
jamila na biye masa,ga yara 'yan wasa kamarshi,kana duban sumayyan kasan akwai
kwantacciyar damuwa a zuciyarta,a hankali ciwon marar ke sake matsanta mata wanda
ta kai ga cewa har sai ta sha paracitamol wani lokaci yake barinta tayi bacci.

         Sati guda cif da daura aurensu malam baice mata komai ba,itama bata
tambaya ba bata ma damu taji komai ba,addu'a ma take Allah yasa tayi zamanta a
haka,kan me zata damu?,ta damu da mijin da batasan haqiqaninshi ko wani abu nashi
ba?,da zaiyita zama bai nemeta ba ma ita haka take so,ko banza sunanta matar aure
ba za'a matsanta mata kan aure ba tunda akwai igiyar wani a kanta.

      Ranar da suka cika kwana takwas ranar litinin abdur rahman zaizo daukar tashi
amaryar,tun rana halima ke faman shiri duk da cewa jikinta a sanyaye yake,kusan
sumayya ce qarfin shirin duk da ciwon marar dake tsunkulinta haka ta dinga shirya
ta tana mata hira da gaya mata abubuwa masu amfani duk don ta saki jikinta,zuwa
sanda aka idar da sallaf magariba ta kammala shiryata tsaf sai tashi qamshi take
mai sanyi wamda duka cikin taskar hadaddiyar humrar sumayyan ce,sumayyan ce ta raka
haliman har zuwa falon malam,gabanshi suja zauna kan haliman a duqe,a hankali malam
din ya dinga yi maya nasiha mai narjar da zuciya wadda kusan dasu yake baki
daya,hatta da sumayyan sai data yi qwalla,ta sake taqinin duniya ba'a bakin komai
take ba,hakanan mace bata da wata riba a rayuwa indai bata yi biyayya wa mijinta
ba,ta ina zaki ci rina bayan aljannarsa na qasan qafarki idan kika saaba masa ya
take fa?,da qyar halima ta iya roqon gafarar baabaa sabida kukan da yaci
qarfinta,tashi sumayya tayi ta basu waje jin baabaa na yiwa abdur rahman izinin
shigowa wanda ta tabbatar shina nasihan baabaa zaiyi masa,fuskarsa sai qyalli da
annuri take,yana sanye da wata danyar shadda fara qal dinkin 'yar ciki da babbar
ruga,kana kallonshi kaga ango sak,dakinta ta shigi ta samu gefan gado ta zauna tana
fidda hawaye bayan taji tafiyarsu,shikenan,kowa ya fashe ya barta,kowa ya tafi
wajen nashi masoyin,saura ita,ko ya zata qare?(nidai huguma nace Allah A'alamu).

      Babban dakin taron wanda ke cikin qasaitaccen kamfanin na MM dauke yake da


ma'aikata wanda a qalla sun doshi su arba'in,manyan ma'aikata daga qasashe daban
daban wanda ya qunshi naijeria,pakistan,china,gahana da india,kowanne zaune cikin
tsari kan tashi kujeran wanda suke a jere hagu da dama,tsakiya kuma dogon tabureni
wanda kana kallonshi kasan cewa kamfanin da suka qerashi ba qaramjn fasaha garesu
ba,shine teburin wadan nan kujerun da ma'aikatan ke kak,gaban kowanne dauke da ruwa
da lemo,saidai baki dayansu ba wannan ne gabansu ba,sun tattara hankalinsu ne kan
ogansu wanda ke hakimce a kujefa qwaya daya tal dake tsakiyar teburin,sanye kowa
cikinsu yake da suit baqi da fari sabanin shi dake sanye da tashi tsumammiyar suit
din ruwan sea blue mai dan turuwa,ta sake fidda sigar kyawunsa da zatinsa,wadda
kana kallon suit din kasan tasha banban data duk wani mahaluqi dake dakin
taron,jikinsa na jingine ne da  makarin kujerar yaja juyawa kadan kadan hagu da
dama tamkar mai hutawa abinsa,saidai ina,bayani yake cikin gamsarwa da hikima da
fasaha ta iyawa da qwarewa a kasuwanci,kusan sun gama tattauna komai conclusion
yake musu,tafi kowannensu ya sanya bayan ya gama yana rufewa da idan akwai mai
tambaya yayi,minti uku ya bada babu wanda yace komai kasancewar ya gama hadiye
komai cikin jawabansa,ya duba agogon fata na kamfanin gucci dake daure tsintsiyar
hannunshi,awa biyu ya rage jirgin fly emirate da zaibi zuwa nijeria,hakan ya
sanyashi miqewa,wanda ke tsaye kusa da shi cikin baqin kaya da baqin glass ya soma
tattare dukkan wasu files da takardu ya dauka masa yayin da ya bishi a baya zuwa
office dinsa.

      Yana gab da shiga elavator ya jiyi muryar hamza na qarasowa,hakan bai sanya
shi ya tsaya ba ya shige ciki abinsa,da dan gudu hamzan ya qaraso ya shige ta rufe
da su bayan ya amshi files dinsa dake  hannun wannan mutumin,harara ya juya ya
gallawa almustapha
"Maan,nifa banson wulaqanci da iskanci,nidin macace da zaka wani jaamin aji,idan
ban narka maka dundu ba kace ba nine hamza ba" hararar shima ya watsa masa
"Haka kawai don ka zubda mana mutunci sai ka dinga ma mutane wannan kiran
mafarautan kaman zan bar garin,sai kace bakasan inda office dina yake ba,baka ganin
yadda ka taramin jama'a suna kallona wadancan yaran sun wami qwalolowa mutane idanu
kamar zasu cinyeshi danye" dariya hamza ya bushe da ita ya dunqule hannu ya daki
kafadarsa yana fadin
"Shege man,ashe kana kula,banda abinka kai da keson yaran wata qasar mai zai hana
cikin indiyawan nan ka qara da daya" ya fada cikin salom tsokana sanda akwakun
qarawa tafiya hanzari (elavator) ta iso da su block din da ofishinsa yake,bai kula
shi ba shi kuwa hamza yabi bayanshi yana sheqa dariya abinsa,kusan duk duniya su
kadai ke iya taba musty su dinma ba kowanne lokaci ba,bai tanka masa ba har ya
sanya kati qofar lafiyayyen office dinshi ta bude wanda ya wadatu da tsafta qamshi
da sanyi ya shige hamzan ya biyoshi,freezer ya bude ya fidda lemonsa da yake
matuqar so ya daga ya soma sha yana takowa inda hamza ke zaune yana masa
shaqiyanci,ya kammala sha ya jefa kwalin dustbin yayi kamar zai wuce sai ya
shammaci hamzan ya damqo shi sosai ya riqe wuyan rigarsa yana dubanshi
"Ni kake ma shaqiyanci yau zaka gane kuranka" dariyarsa yaci gaba da yi don time to
time sun saba haka da mustaphan wanda a wannan fage shi daga suke hakan koda su
lamin bai sake musu haka,hannunshi hamza ya ware yana ci gaba da diyarsa yace
"Ah to,laifi nayi,wallahi aure ya kamaceka ka qara musty kowa yasan hakan" tsaki ya
ja ya saki kwalarsa yana komawa da baya
"Allah ya sawwaqe,ni na gaya maka ina da buqatar aure don ubanka"cikin sin ya
tunzurashi yace
"Basai ka gaya min ba,last night naje wajenka a hotel na taddaka kana mafarki,har
wawurata kayi da qyar na sha" ya qarasa cikin matsananciyar dariya,naushi ya kawo
masa ya kauce,sumarshi mustaphan ya shafa,ya fuskanci caakar da shi hamza ke son
yi,qarancin suruti da yake da shine ya sanya bai iya maida raddi ko wasu amsoshi
masu zafi ba matuqar ba cikin bacin rai yake ba,yanzun ma lalubar mai zai maida
masa yake
"Kai zaka qara aure bani ba mayen mata"
"For what?,Nikam alhamdulillah,abida ta tsaren gaba ta tsaren baya,tun jiya wayarta
ke damuna ma tayi missing dina tana buqatar na dawo gida,cikin satin nan kuwa zan
gudu tunda mun gama daidaita komai samfuran kawai zamu fara saqawa,kai ke buqatar
aure har yau aurenka babu riba,nan da few months za'a soma kirana da daddy" maganar
ta daki mustapha,sai yayi shiru bai iya nada amsa ba,komawa yayi saman doguwar
kujera ya kwanta gami da miqe qafafunshi bayan ya cire sau cikinshi da safar sa,duk
da hamza baiyi da niyyar cin fuska ba tsokana ce kawai irin tasa sai ya dinga ji
kamar bai kyauta ba,kamar ta bata ran abokin nashi,shima sai ya koma ya zauna yana
fadin
"Am sorry musty,i dont mean to hurt you"
"Is ok" ya fada can qasa idanunshi a lumshe yana shafa fuskarshi da tafin
hannunshi.

       Tsawon minti talatin suja zaune a haka hamza na shan lemo bayan ya gama amsa
wayar abida mustaphan na sauraran duk abinda suke cewa,duk da shi ba mutum bane mai
sanya idanu kan lamuran wasu ba ba ruwanshi amma wannan karon kunnenshi sun kasa
haqura,soyayyar ta burgeshi qwarai,shi mutum ne mai son yaga ana nuna damuwa da
kulawa a kansa,zumbur ya miqe daga kwanciyar kamar wanda aka tsikara ya janyo wata
sabuwar safar yana sanyawa cikin wani dan abu dake gefanshi don ya gama da waccar
da ya cire yana fadin
"Muje ka saukeni airphort,sauran awa daya da rabi jirginmu ya tashi"
"Zuwa ina?" Hamza ya tambaya
"Nijeria" ya bashi amsa a taqaice kamar yadda ya saba,baki hamzan ya sake yana
kallonshi,wani irin mutum ne mustaphan,yanzun suna tare zai tafi nijerian amma ya
kasa bude baki ya gaya musu?,yasan halinshi sarai yafi gaban haka ma indai mustapha
ne.
"Me zaka yo bayan ba time din zuwanka bane"
"Baabaa ke nema na" cikin son ya tsokaneshi yace
"Allah ya sanya wata 'yar naijan ya nema maka aure kai Allah yasa ma har an daura
muga ya zakayi da 'yar africa tunda wadan da ba african ba ma kaqi" wata muguwaf
harara ya watsa masa,haka kawai ya dinga ki kamar hamza ya masa baki ne
"Da kuwa sai na nada maka duka mummunan fatan da ka yimin,kafin na sanyata da
qafafunta ta koma inda ta fito,na maka kama da wanda zai tara mata?,mace daya ta
isheni rayuwa,dayan ma da ana bada rabi karba zanyi" sosai maganar mustaphan ta
bashi dariya,yasan yaddq zai tsinkuleshi sosai.

      miqewa yayi ya dire cup din yayin da mustapha ya gama gyara wuyan suit dinshi
ya kwashi wayarsa da sauran abinda yake da buqata ya kashe duk wani electric dake
office din suka fito,
"Kwana nawa zaka yi?"
"Ban sani ba nima" ya fada yana maida wayar aljihun suit dinshi
"Wacce iriyar masa ce haka kai har abada bayani wa mutane wuya yake maka?"
"Oh god,ka fiya tambaya,ka sanyani magana da yawa,bayan kana gani yanzu muka gama
meeting nayi maganar da ba adadi,zaka sanya qirjina ciwo fa?"
"Bari na rufa maka asiri nayi shiru,don idan ya soma cuwon baka da mai jinyarka ko
kwantar ma da hankali,amma ka sani this week nima zanyo gida"
"Sai ka iso" ya fada a taqaice,don yasan idan ba haka yayi masa ba bazai barshi
ba,murmushi hamza yayi yana yiwa abokin nashi addu'ar Allah ya hadashi da mace ta
gari wadda zatasan zafinsa da darajarsa,yasan dama bazai hana shi tafiya ba mutum
ne mai kula da haqqin iyali ko na nashi ba.

*******    ********    *******

        Kano ta yiwa baabaa dadi,tunda ya baro abuja lokacin daurin aure bai koma
ba,har yau rana irin ta yau da mustapha ke isowa nijeria wajenshi wanda a yau
yammacin yau ne yake saka ran zai koma abuja shida matan nashi guda biyu,kullum
yana kusa da abokinshi har yau labarin bayan saduwar bai qare ba.

      Bayan gama shirin nashi cikin qaton dakin nashi falle daya dake dauke da
faffadan gado da malalen carfet,wanda shine dakinshi na farko daya tabayi kuma shi
dinma har yau ba rabu da shi ba,anty maamaa ta aiko mishi da abinci yaci sannan ya
fito don ya gaisa da su.

     Bangaren ummensa ya fara shiga,ya taddata zaune a falo tana gyaran


farcenta,gefe da ita kadan ya samu ya zauna sosai ya tanqwashe qafafu,fuskarta
fadade da fara'a take dubanshi,gashi mutum zam sak amma rashin iyalin qwarai na
wasa da nutsuwarshi
"Barka da rana ummee,na sameku lafiya?"
"Lafiya qalau almustapha,ya hudimomi da sabgogi?"
"Alhamdulillahi ummee" ya fadi yana shafa suman kanshi
"Ya kowa da kowa?"
"Duk suna lafiya" ta bashi amsa,tasan da su amira huda da farida wanda ke dakin
aure yake,yakan yawaita tambayarta yanayin zamansu,shiru ya dan ratsa
tsakaninsj,shi bai da abin cewa kasancewarsa ba mai yawan magana ba,yayin da ummee
ke kai kawon yadda almustaphan zai amshi maganar aurenshi,don ta tabbatar da cewa a
yau baabaa zai gaya masa maganar
"Kunyi waya ne da yayanku?" Kai ya girgiza alamar a'ah idanunshi cikin na ummeen,ya
gama karantar akwai wani lamari tattare da ita,bai wasa da dukkan lamuranta hakan
ya sanya bashi wuya wajensa karantar yanayinta
"Okey,zaka wajen mahaifinka zakuyi magana da shi,abinda nake son gaya maka
mahaifinka mahaifinka ne kafi kowa sani,bani da buqatar kayi jayayya ko mujadala da
shi,tashi kaje nasan yana can yana jiranka" miqewa yayi yana amsa mata da to,yayin
da zuciyarsa ke wassafa masa meye wannan wai da ya faru haka da shi wamda shi bai
sani ba?,bai wuce ba sai da ya shiga ya gaida anty maamaan,cikin kulawa itama ta
amsa masa,saidai ya lura itama tana masa irin kallon da yaga ummee na masa,yayim da
tace masa sanda zai fita
"Almustapha,ka daure ka dore kan halinka na biyayya kaji?" Itama to dince amsar,sai
ya samu kansa da hanzarin isa wajen baabaan don yaji koma mene,don shi mutum ne da
baison boye boye,sak yake,fadin gaskiya komai dacinta.

       Da murmushi baabaa ya masa nuni ya iso har gabanshi,ya sanya masa ludagi
cikim furar da yake sha,kasancewarsa yasan almustaphan da son fura,kadan ya sha
saboda qagara da yayi da jin dalilin zuwanshi nijeria cikin qanqanin lokaci,sai da
baban ya kammala ya kira anty maamaa ta kawo masa wayarta ta fita sannan ya soma
magana da shi
"Almustapha,kowa na da labarin bayyanar tsohon abokina sule ciki kuwa har da kai
nasan labari ya isa gareka" qaramin murmushi ya saki don har ga Allah ya taya
mahaifin nashi murnar ganin wannan amini da tun haihuwarsu suke ji labarinsa sai a
yanzu ya bayyana,kai yake jinjinawa yana murmushi,yana zaton malam zaice ne yaje ya
gaidashi
"Almustapha ungo nan" ya fada yana miqa masa wayar anty mama,babu musu ya sanya
hannu ya karba yana duba wayar,hotonta ne,daya daga cikin hotunanta na bikin
amira,ta fito tayi tar ta cika screen din wayar fuskarta qunshe da murmushu da ya
sake fidda sigarta mai sanyi da kyau,janye wayar yayi daga fuskarshi yana duban
baabaa,gabanshi na faduwa yana addu'ar kada Allah yasa baabaan yace ya auri wannan
'yar mitsitsiyar yarinyar ne,amsar wayar baabaa yayi sannan ya dora
"Nasan maiyiwuwa zaka iya ganeta,yarinyar dake gidan farouq maqotanmu na abuja,diya
ce ga aminina sule?,almustapha" ya sake kiran sunanshi cikin yanayi na
gaske,fararen idanunshi kawai ya daga ya dubi baaba
"Na nema maka aurenta saboda mutuncinta,na nema maka aurenta saboda nutsuwarta,na
nema maka aurenta saboda addininta,na nema maka aurenta saboda daga gidan data fito
daga tsatson data fito,uwa uba na nema maka aurenta saboda TA DACE DA KAI!" baki
daya kalmar baabaan ta qarshe taso tafiya da majiyar kunnensa,bai gama lalubo
duniyar da yake ciki ba yaji wani sautin na cewa
"Ta taba aure tana da yaro daya,tana da hankalin da zata iya zama da kai ta baka
dukkan abinda ya kamata" ai wannan karon bansan sanda ya daga kai ya dubi baabaa
ba,take wasu irin jijiyoyi suja fito a goshinsa,qoqarin danne zuciyar tasa yake da
irin bala'in da yake ji cikinta amma bakinsa yaqi bashi hadin kai
"Baabaa,ban santa ba,bata sanni ba,bata sona bana sonta,baabaa aure yanzu?,auren ma
na bazawara da d'aa baabaa,please baabaa i beg you idan na maka wani laifin ne ka
yimin duk wani hukunci da ya kamata amma banda wannan"murmushi baban ya saki
" ba hukunci bane mustapha gaata ne na maka"
"Gaata baabaa" ya fada cikin nuna shakku da taraddadi
"Baabaa ba wannan gatan nake so ba baabaa ka sauyan wani umarnin zanbi amma banda
wannan" nan ya shiga roqo iri iri yayin da baabaan ya zuba masa idanuwa yana
kallonsa,yasan dole za'a samu rudani amma bai tsammaci abun zaya kai haka ba,ganin
yanata zuba ya sanya baabaan daka masa tsawa
"Muhammad almustapha!" Sunan da ya kira shi da shi yasanya hankalinsa dawowa
jikinsa
"Ni muhammad mukhtar!,indai ni na haifeka na baka umarni ka karbi auren sumayya
umarni ba shawara ba,tashi ka bani waje!" Da qyar ya iya miqewa kamar wanda ya sha
abun maye ya lalubi hanya ya fice.

     Ya jima zaune gefan gadonshi aqalla awa guda yana yamutsa hannayensa cikin
kwantacciyar sumarshi mai santsi da laushi,gumi ko ina yana keto masa,miqewa yayi
ya soma zare kayanshi yana jefarwa cikin dakin,sai da ya rage saga shi sai boxer
sannan ya fada bandaki,ruwan sanyi ya sakarwa kansa tsakiyar shower,ya jima tsaye
sanyinbruwan na ratsashi tare da qoqarim control din kansa,ya sake barnatar da awa
guda cur a haka har sai da tunaninsa ya dawo yadda ya kamata,qwaqwalwarsa ta fara
yi masa bita,ya tabbatarwa kansa bai yi kalaman da suka dace ba ga
mahaifinsa,baabaa ne,masoyinsa,wanda qaunar da yake masa ta daara ta dukkan wani
daa ko jika dake cikin zuriyarshi,dakin gadon ya dawo ya sake lalubar wasu kayan ya
sanya,wannan karon jallabiyya ce,ya gabatar da sallar la'asar,zama yayi kawai yana
karanta yadda wannan QADDARAR ta fadowa rayuwarshi a lokacin da bai zata ba,yana
nan a haka bai ankara ba yaji kiran sallar magariba,a nan gun itama ya yita a haka
isha'i ta ruske shi,sai a sannan ya samu qwarin gwiwar miqewa ya sake daura alwala
ya sanya hular tashi ka fiya naci ya nufi masallaci.

       Sahunsu daya da baabaa,har aka idar bai motsa ba sai da ya ga baabaan ya


gama addu'o'inshi ya miqe zai fita sannan ya mara masa baya,yana gaba yana binshi a
baya,baban ya san da haka amma yayi banza da shi bai ko nuna ya ganshi ba,sai da
zai bude qofar gidan yayi sauri ya bude mishi yaci gaba da binshi har sanda ya isa
falonshi sannan ya waiwayo yana sake tamke fuska duk da yasan dama hakan zata
faru,yasan halin mustaphan zai sake waiwayowa a duk sanda nutsuwarshi ta dawo
jikinsa
"Lafiya kake bina,zan shiga na kwanta ne idan akwai bashin da kake bina ban kammala
biyanka ba sai ka gayan ko?" Kai ya sadda yana jin nauyi da kunyar maganar da
baabaan ya fada,qarasawa yayi gabanshi sannan ya zube kan gwiwarsa
"Kayi min afuwa baabaa kayi haquri kan baata makan da nayi,nayi kuskure wanda bana
fatan sake yinsa,na amshi dukkan hukuncin daka yanke me kake buqata yanzu daga
gareni" dawowa yayi ya samu waje ya zauna sannan yayi masa nuni da ya dawo kusa da
shi ya zauna,sosai baabaan ya dinga kwatanta masa manufofi da hujjojin da yake jin
sun isa su sanyashi qara aure,daga bisani ya rufe
"Ka gwada zama da ita mustapha na cika maka baki tare da kurin samunta fiye da
yadda kake zato ko tsammani,nasan jinin sule ba zai taba kasa gadon halinshi
ha,mustapha,ka riqemin sumayya da mutunci da amana,idan ka wulqantata ka dauka ni
ka yiwa,haka idan ka bata daraja,bazan iya maka afuwa ba aduk sanda na sameka da
lafin wulqantata ba bisa haqqi ba"
"Na yi maka alqawari insha Allahu"
"Allah ubangiji ya albarkaceka,yq cika makq burikanka,ya kyautata rayuwarku kai da
ita baki daya,kiran da nayi maka kenan zuwa nijeria,yaushe zaka dauki
matarka?,sannan a ina kake son ajjyeta?"
"Duk yadda kace baba haka za'ayi" murmushi ya saki yana dukan kafadarsa
"Kaine fa mijin kuma kai ke aurenta bani ba da zaka turon zabin"
"Ka isa damu ne baki daya baba"
"Idan ta nine ko yau kaje ka dauko matarka,sannan ka wuce da ita dubai,don nima ina
son naga daana ya fara dandanar zaqin aure" duk da rudin da yake ciki maganar baban
ta qarshe sai data sanyashi jin nauyi
"Zanyi yadda kace,amma amin afuwa zuwa gobe"
"Ba lallai bane ai,kana iya barinta abuja idan kaso,amma sai bayan kun gama
fahimtar juna da ita kun fara sabawa,fatana ka riqeta da mutunci"
"Insha Allah baaba" addu'a yayi masa mai kyau da tsaho,wanda tilas mustapha ya
dinga lallaba kansa da zuciyarsa ya zauna sukayi hira da malam din na wasu mintuna
sannan ya tashi ya wuce.

       Kamar zai zauce cikin dakin shi daya haka ya dinga ji,kiran hamza ya shigo
wayarshi,wata bahaguwar harara ya ballawa wayar,ganu yake hamzan ne da shegen
bakinsa ya masa wannan fatan,to amma ai ba fatan hamza bane tunda baifi awanni da
yi masa shi ba,anya kuwa hamza baisan da wannan maganar ba ya munafunceshi?,yana
kallon kiran har ta ya gaji da kiran nasa ya haqura,yana tsagaitawa lambar su'ad ta
danno kai,wanda shi sam yama mance da ita,ya kuma mance rabon da suyi waya,hannu ya
sanya cikin mutuwar jiki ya daga kiran ya kara akunnensa,tun kafin yace wani abu
sheshsheqar kukanta ta cika kunnuwansa wanda hakan ya hadu da tashin hankalin da
yake ciki take suka saukar masa da ciwon kai,sai ya runtse idanu yana saurarenta
"Almustapha,ni zaka ci amana?,ni zaka yaudara almustapha,dama zakq iya kqllon wata
mace macen ma 'yar afrika bayan ni?,almustapha kana jina kayimin banza da kai nake
musty!" Ta fada cikin qaara da qaraji,tasan sarai yana jinta tafi kowa sanin
halinshi na rashin son hayaniya da kuka,shirunsa ya sake tunzurata,mamanta dake
gefe ta rada mata abinda zata yi,itama a ganinta hakanne ya dace tunda da irin
wannan taci nasarar aurenshi
"Wallahi almustapha sai na kashe kaina,sai nasha poison don bazan iya hada ka da
wata can ba,wallahi sai na kashe kaina....." Ga mamakinta tun kafin ta kashe wayar
shi ya kashe,bama kashewa kadai ba sai da yaja mata wani mugun tsaki sannan ya
kasge wayar baki daya ya cillar,miqewa yayi cikin tangadi ya sauya kayan bacci ya
koma gado ya duqunqune cikin bargo,yayin da qwaqwalwarsa ta kasa aikin komai a
tsaye take cak.

   ******   ******   *******

      A shirye ya fito cikin baqaqe sidik three pieces slim fit suit,ba qaramin
kyau suka yi masa sun haskashi matuqa,saidai shi kadai yasan izayar da yasha daren
jiya,tilas ya dauki sun glases wada ya dace da shigarsa ya sanya,tamkar don ado ya
sanyashi ba don kare idanunshi da suka sauya launi ba saboda rashin wadataccen
bacci yayi masa kyau sosai shima,ya yanke shawarar gwara yaje asibitinsa ko wasu
daga cikin marasa lafiyan da zai iya dubawa ya duba ko hakan zai rage masa zafi da
radadin da yake ji.

     bai samu baabaa ba saboda ya fice wajan aminin nashi malam kan maganar yadda
zai gabatarwa da malam dukkan gidajen gonanshi wanda yakeao a yanzu su dawo
hannunshi ya karbi dukiyarsa,yaga kamar malam din yana bagarar da zancan yaqi
tsayawa su tattaun,yau yake so ayita ta qare,saboda haka anty maamaa maan kawai ya
gaisar ya wuce wajen ummee,tana kwance ta fito ya gaidata ta amsa tana
dubanshi,basai an gaya mata ba tasan da walakin goro a miya,ta gabatar masa da
break fast,bai iya cin komai ba sai coffe da yayi qoqarin sha don kada ya daga
hankalinta,yana sha tana gefansa a hankali tace da shi
"Dukkanin mai biyayya zaici ribarta a gaba,bijirewa iyaye koda kan gaskiyarka ne
bashi da wani alfanu,zaiyi wuya idan baka ci karo da tashin hankali ba a gaba
sanadiyyar wannan bijirewar,almustapha,na roqeka ka riqe musu yarinya da mutunci,ka
fiddani kunya kada ka watsan qasa a ido,yanzu ne lokacin da zaka nuna irin
tarbiyyar daka samu daga gareni" jikinsa duk sai yayi sanyi,shi wai iyayensa da
suka isa da shi ke roqo?,akan me?,duka akanta?,akan yarinya qwara daya tal,cup din
ya dire yana fadin
"In sha Allah" cikin sassanyar murya sannan ya fice yana dauke da brief case,tuni
drivanshi ya gama shirya komai,maimakon baya da yake shiga wannan karon gaban motar
ya shiga,baice komai ba don shima ya lura akwai abinda ke faruwa da ubangidan nashi
ya shiga ya tada motar masu tsaron qofa suka bude masu wakekem get din suka fice.

       Daga kadan kadan ciwon marar ke sake yawaita mata,wanda hakan ya sanya maama
ta takurata kan lallai yau sai taje taga likita,itakam baki daya bajin dadin
rayuwar ma take ba,amma tilas ta shirya zuwa don cika umarninsu da samun kwanciyar
hankalinsu,qarfe tara ta gama shiryawa bayan sun gama waya da anty dije ta bata
adresa din wani asibi,ta gaya mata komai kyauta ake saidai akwai tsantsar kulawa
tamkar asibitin da ka fidda kudinka ka biya,ba kyautar ce zata kaita ba,kulawar
data fada shi yasa zata,don bata da matsalar kudi,don baabaa ya ajjiye mata su
tamkar baisan zafin su ba,hatta da abinda zata ji bai yarje taci na gidan ba,sabida
yace yanzun ba dolensu bace.

        Sai data shiga ta gaida baabaan a kunyace sannan sukayi sallama da malam
kan zata asibitin da yake baaban yace izinin fitarta ya damqawa malam din kafin
qarasowa mijinta,dakatar da ita baaba yayi ya fidda wayaraa ya kira daya daga cikin
direbobin dake dakon fitowarsa ya bashi umarnin kaita ganin likita,cikin girmamawa
ya amsa,shiru tayi cikin lafiyayyar motar wadda idan ba gargada ta kai gargada ba
ba lallai ka fahimci ana tafiya ba,ire iren motocin da suke mallakin familyn
professor mukhtar,motar da ada ko a mafarki bata darsa shiga irinta ba,ajiyar
zuciya ta saki sannan ta fidda wayarta ta duba kiran dake shigowa amira ce,murmushi
ta saki duk ciwon marar dake neman sake tsananta mata,amsa wayar tayi ta kara
akunnenta.

Masu karatu muje zuwa,wanne asibiti sumayya zata????.

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

7⃣6⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

*la haula wala quwwata illa billahil aliyyul azim*


_____________________________________
        Cikin babbar haraban asibitin motar ta ajjiyeta a muhallin da aka tanada
saboda ajiyar motoci,cikin rashin qwarin jiki ta bude murfin motar ta fita sanda
drivan ke kashe motar yana sake daidaita tsayuwarta,kai tsaye reception ta isa,aka
bude mata file kasancewar komai kyauta ne,tayi mamakin kyau da tsaruwar
asibitin,wanda ta tabbatar da cewa inda mamallakin asibitin yayi shine saboda kudi
ba shakka ba qananun kudi zaya samu da asibitin ba,tsarin ya burgeta,ba qaramar
dabara yayi ba,saboda tasan ladan da zaya samu ba kadan bane,d'aya daga cikin
abubuwan da masu kudinmu basa ganewa kenan,sun gwammace suyi saboda kasuwanci,ba
don ya zame musu sadaka mai gudana ba wadda zata yita bibiyarsu har bayan rayuwarsu
ba,abune wanda koda sunyi ba komai bane cikin dukiyar da Allah ya basu ba,Allah
madaukakin sarki yana cewa
"Yaku wadanda kuka bada gaskiya da Allah ku ciyar daga abinda muka azurtaku tun
kafin ranar da babu fansa a cikinta(da zata yi maka amfani),ba abokantaka (a
cikinta da zata yi maka amfani),ba ceto(sai da izinin ubangiji)tazo muku(wato ranar
qiyama",bayan mai bada katin ya gama cike mata ya miqa mata yana nuna mata inda
zata kai a saka ta a layi yana fadin
" kinyi sa'a kuwa malama,yau oga ne da kansa ya zauna,ba kowa ke samun sa'a irin
haka ba ranar garkonshi"ya fada yana washe baki,don tunda ta shigo tayi masa,duk da
kasancewarta cikin zabgegen hijabi har qasa amma hakan bai gaza bayyana kyawunta ba
"Na gode" kawai ta fadi ta amshi folder din ta kai inda yace mata,akwai mutane
kusan goma sha biyar a gabanta,saboda haka dole ne tayi zaman jira,bata jima da
zaman ba kiran nafisa ya shigo wayarta,wanda shine ya sake dauke mata hankali da
radadin da take ji,don a qalla sun bata kusan minti talatin suna waya kafin su
rabu.

       Sannu sannu suka soma raguwa,duk wanda ya fito fuskanshi qunshe take da
fara'a saboda an duba shi yadda ya kamata,uwa uba zai samu magunguna masu kyau fiye
da kullum,wanda kusan yawancinsu masu ciki ne,duk na gabanta suka qare layi yazo
kanta,wanda bayan fitowar matar qarashe ta miqe ta isa qogar office din ta tura ta
shiga.

      Lafiyayyen office ne wanda yake a tsaftace sannan a tsare kamar yadda


ilahirin asibitin yake,office ne mai girma wanda daga hannun hagu ke dauke da
rukunin wasu irin kujeru kusan guda hudu da table dinsu a tsakiya,kana shigowa kuma
table din likitan ne wanda ke dauke da tashi kujerar da kuma kujeru guda biyu a
gaban table din suna fuskantar juna wanda anan patient ke zama yayi bayani,daga
bayan tashi kujerar wami dan katako ne a tsaye wanda yake rataye 'yar saman suit
dinshiba jiki,sannan gaban table din kadan dan gado ne wanda ke hade da na'urar
sacanning ta musamman da sauran tarkacen likitoci,daga hannun dama kuwa qofofi biyu
ne kulle,daura da su freezer ce girke a kanta akwai set na warmers da cups na tea
da na ruwa,sai coffe maker daga gefe.

      Tsaye yake gaban gadon scanning din inda ya baiwa qofa baya,hannunshi dauke
da takardar da ya gama yiwa wata mata scanning yana dubawa,ranshi a bace yake sosai
har hakan ya nuna saman fuskarshi,yana mamakin yanda a yanzu maza ke wasa sa
haqqunanau kan matayensu,kana da mata tana dauke da cikinka,wanda rayuwarta na
cikin qila wa qaala ne,ko ta mutu ko dan ya mutu ko a rasa su baki daya idan kuma
ta kasance daga cikin masu sa'a su rayu baki daya,amma ka kasa tsayawa ka bata
kyakkyawar kulawa?,abincin da zata ci mai kyau ya gagareta?,kullum tana cikin
tashin hankali da masifa,tayi wahalarka tayi ta yaranka?,akan me?,saboda me?,duka
cikik zuciyarsa yake wannan maganan.

       Turo qofan tayi sallama a bakinta,ya amsa ba tare da qwaqwalwarsa ta bashi


wace ba,dan tsayawa tayi saboda batasan inda zata zauna ba,ga faduwar gaban sata
rusketa lokaci daya sai daga bisani ganin ba'a ce mata komai ba sannan ta taka ta
isa gun kujerun ta zauna.

        Takardar ya nade ya ajjiyeta gefe yana sakin tsaki sannan ya juyo a hankali
ta tako zuwa nashi muhallim ya ja kujerar ya zauna ba tare da ya dubi wadda ke
zaune din ba,duk da yana shaqar wani qamshi da kamar yaso ya sanshi,ya jawo file
dinta ya bude,ganin sabo ne alamun zuwanta na farko ne ya sanya shi fadin
"Uhm,meke damunki?",ita din ma bata dubeshi ba har sai da sautin muryarshi ya daki
kunnenta,da sauri ta daga kanta idanunta suka sauka kanshi,tsabar ciwon dake murda
mata ya hadu da firgitar da tayi ya so riqe numfashinta,qoqarin miqewa take amma ta
kasa,har ya kammala rubuta date din da zaiyi baiji an amsa ba,hakan ya sanyashi
daga kansa yana tsammanin ko kurma ce,idanunshi ya dan ware a kanta,kafin yq
maidasu yadda suke,wanda hakan ya taimaka wajen sanyata miqewa da hanzari dom barin
ofishin,ta gwammace ta haqura da ganin likitan baki daya,cak ta tsaya jin sautin
muryarsa kuma muryar mukhtar yana bata umarnin dawowa inda ta tashi din,har cikin
zuciyarta tana jin ba zata iya tsayawa ba,a inda daga shi sai ita?", sai ta sake
daga qafarta don cikin yunqurin cimma ficewa daga office din ba.

       Batasan ya akai ba,yaushe ya iso inda take?,sai kawai ji tayi an tado


qafafunta,wanda hakan yayi sanadiyyar wancakalar da jakarta sannan ta tafi zata
fadi dama jikin babu qwaru,tuni ya tarota da hannayenshi,bai cikata ba har sai da
ya kaita kan rukunin kujerun nan guda hudu ya zaunar da ita,tsaye yayi a kanta
hannayenshi harde cikin qirjinsa yana dubanta,qare mata kallo yake yana sake
shaidawa kansa cewa matarka ce,duk abinda zakayi kayi controlling kanka,duk da bai
iya kallonta yadda ya kamata sakamakon hijabin da ya lullube dukkan jikinta,tafin
hannayenta kawai yake iya gani sai fuskarta wadda itama bata fita ba saboda kanta
na sunkuye ne a qasa,so yake ya gani ta inda ta dace da shi,so yake ya gani yadda
zaiyi ya zauna da ita,ya kuma gano ta inda zata iya taimakonsa ko amfanarsa,bai
gani digon wayewa ko dis tattare da ita ba,hasalima shi tunda ya santa cikin hijabi
yake ganinta,sau daya ya taba ganinta ba cikin hijab ba ranar bikin amirarsa,wannan
itace zata iya zama da shi ta samaasa farinciki wanda ita kanta bata samawa kanta
ba?,ya tabbatar gwara su'ad sau dubu da ita,wanda ko ita su'ad dinma data san ta
kan duniya ta kasa iya tafiyar da shi,ta kasa shayar da shi soyayya mai zafi irin
wadda yake muradi balle wannan da kullum take a qunshe?.

       Idanuwansa ya lumshe sannan ya hadiye wani abu mai tauri daya tsaya masa a
wuya sanda ya fuskanci kuka take,qaramin tsaki ya ja cikin zuciyarsa yana cewa
"Ko uban me nayi mata oho?" Motsa bakinsa yayi da niyyar daka mata tsawa sai kuma
ya tuna ita din wacece wajen baabaa?,me baabaa ya gaya masa game da ita,hannunsa ya
dunqule ya daki daya tafim hannun nasa wanda hakan ya darsa tsoro a ranta,sai ta
runtse idonta tana jira taji mai zai faru.

      A hankali ya tako zuwa gabanta bai gushe ba sai sa ya zo gab da gwiwoyinta


sannan ya durqusa,dora hannunshi guda daya yayi  saman kujerar gab da inda cinyarta
take saidai basu hadu ba,ya sake motsa bakinsa zaiyi magana aka soma knocking
qofar,dauke fuskanshi yayi ya maida qofar yana cewa
"Yes" wanda hakan ya baiwa mai son shigowar daman budewa ya shigo,daya daga cikin
ma'aikatan asibitin ne,cikin mamakin ganin ogan nasu a haka yayi saurin cewa
"Am sorry sir" ya juya da niyyar ficewa,cikin sanyin murya yace
"Baka da damuwa,ya ake ciki?" Jin haka ya sashi dawowa yana satar kallon sumayya
wadda kanta ke qasa,tuntube yayu da rug din dake shimfide wajen bai kula ba saboda
kallon da yake matan,da sauri yace subahanalla sannan yayi hanzarin maida idonshi
ga mustapha,wata muguwar harara ua watsa masa wadda ta sanya hanjinsa kadawa,ba tun
yau ba yasan murtala mayen mata ne,ya sha bashi warning akan yadda yaje zuwa ya
taddashi da mata suna hira suna qyaqyata dariya,cikin rawar jiki ya miqa masa wasu
takaddu
"Gasu yallabai,mun gama komai mun bata gado,an gayara dakin thierther din"
"Good,kun tabbatar tun jiya bayan isha'in bata sake cin komai ba?"
"Eh yallabai"
"Ok,nan da one hour zamu shiga in sha Allah"
"To yallabai" ya fada yana juyawa,har ya kai qofa mustaphan ya sake tsaidashi
"Ban amince ku bad mijinta ya shiga dakin ba koda yazo,sannan ku san yadda zakuyi
da sauran patient din dake jira,kwashe wadan can files din ka fita da su"
"To" ya amsa cikin rawar jiki ya tattare ya fita da su saboda yadda yake ta faman
jifansa da wani irin kallo.

       Da idanu ya rakashi har sai da yaga fitarsa sannan ya dauke idonshi ya sake
maidawa kanta ya kafeta da su
"Da ba sai kinzo ba ma,ko baki zo ba dole baaba yace yau nazo" da sauri ta watsa
masa idanunta wadanda ke jiqe da hawaye,me yake so yace?,biyoshi tayi?ciwon da take
ji ita shi ya dameta,amma dole ta fahimtar da shi don bazata lamunce tana ji tana
gani ya mata wata fassara ba
"Allah ya sawwaqe...i bab...ba kai na biyo ba,bansan ka ba bare....." Takaici ya
turnuqeta ta kasa qarasawa
"Idan ba haka bane mai ya kawoki?,na tambayeki baki amsa ba,tabbacin maganata tana
kan gaba kenan" banza tayi da shi tana digar hawaye,yayin da shi kuma yaci gaba da
kallonta yana nazarinta,sai a sannan ya lura da hannunta wanda ke zaune saman
mararta,hannun yabi da kallo sannan ya maida dubanshi fuskarta
"Tashi ki cire hijabin na duba miki" ya fadi yana matsawa da baya sannan ya miqe
tsaye,shiru tayi masa kamar bata jiba,don bata ga dalilin da zai sanyata cire
hijabinta ba,ransa ya soma baci da shariyarta,abinda bai qauna tsawon
rayuwarsa,uhmmm wanzami dama hausawa suka ce baya son jarfa,sake matsawa baya yayi
hannayensa zube cikin aljihunsa yana dubanta
"Ko kaxa baaba ya bani da hannunshi yace na kula da ita daga ranar tafi qarfin
wulaqanci ko tozarci a wajena,kina neman ki hasalani nayi miki abinda banyi niyya
ba ko?,kada ki yarda raina ya baci,idan kuwa ba haka ba bazakiji da dadiba,kina iya
tashi ki tafi idan har ba zaki bari baaban yasan asibitina kuma gurina kika zo
ba,kiyita zama da cutarki wannan ba damuwata bace" ya qarashe maganar yana daga
kadunshi,hakan ya bata qwarin gwiwa ta muqe da hanzari duk da ciwon da takeji na
tsikarinta,ta isa ga jakarta ta tattare kayanta ta maida ciki cikin hanzari,wanda
hakan ya sabba ba mata manta hotunan mukhtar guda biyu qananu wanda suka zube ta
doshi qofa abinta.

       Wata zuciya ta taso masa,tana jin bata da kunya kenan?,ita din wace?,bai
manta rashin kunyar data yi masa ba randa ta bigeshi duk don yace ta dinga kula,me
take da shi da take wani qunshe qunshe,taku daya biyu ya isa inda take,hannunshi ya
sanya ya finciko hijabin baki daya ya fiddashi daga jikinta wanda hakan ya sanya
gashin kanta warwarewa baki daya,dama daureshi kawai tayi ba tare data sanya komai
ba,hakan ya tilas ta mata tsayawa cak,waiwayowa tayi da niyyar sauke masa magana
kwarjininsa ya cika idanuwanta
"Mijinki ne",kalaman malam suka dawo mata,ita din ba mai tsiwa ko rashin kunya bace
tun da can baya,tun daga aurenta daga mukhtar zuwa lukman,bata iya kallon tsabar
idon wanda ya girme mata tayi masa rashin kunya ba,sai yanzu zata fara?,a kan dan
mutumin dake qaunarta,uba a gareta babban masoyi amini ga mahaifinta,sai ta runtse
idanuwa,yayin da juyawar tata ya tilastawa mustapha kau da idamuwansa daga
kanta,skert ne a jikinta da riga 'yan kanti,irin masu robar nan wadanda suke bin
jikin mutum,gajeran hannu gareta,wuyanta kuma v.hape ne wanda ya fidda kyawun
wuyanta zuwa qirjinta
"Idan ka wulqanta sumayya ka tabbatar wa kanka ni ka wulaqanta" maganar baabaa ta
dawo mishi shima kwanyarsa,dukkaninsu lokaci guda umarnin iyayensu ya yi musu
linzami,lokaci guda ya sauke dukkan wani abu da kowannansu keji game da dan uwansa
a zuciyarsa,hijabinta ya wurga mata ba tare da ya dubeta ba,da yatsa yayi mata nuni
da gadon dake bakin na'urar scanning,bata ce komai ba ta maida hijabinta jikinta,ta
taka a hankali zuwa bakin gadon ta hau,sai da ya bada wasu mintuna sannan ya soma
takawa zuwa kan gadon
"Kwanta" yace mata,idanu ta fiddo har sai da ya sake dubanta,da baya ta koma ta
kwanta saman gadon
"Janye hijabin da rigarki" ya sake fada yana duban wani gurin,hijabin ta janye amma
sai ta kasa janye rigar,sake waiwayowa yayi yaga abinda tayi,bai ce mata komai ba
ya sanya hannunshi ya dage rigar,idanunta ta runtse zuciyarta na bugawa,da sauri ya
sake rigar ya koma da baya,bai iya tuna mata nawa yayi wa scanning tun daga
farawarsa aikin likita kama yau,mata daga nau'in yare jinsi da qasashe daban
daban,amma haka kawai yake jin wannan bazai iyaba.
        Bakin teburinsa ya isa ya soma qoqarin kiran reception ta wayar landline
yana tambayarta
"Duk wata kina period dinki?"
"Eh" ta bashi masa murya can qasa cikin jin haushi da kunya
"When last kika ga period din" shiru tayi tana tunani,a qalla kusan watanni biyu
kenan baizo mata ba
"Wata biyu"tabe baki yayi yana mamakin rashin damuwa da kai da har zakayi wannan
watannin baka ga al'adarka ba kana zaune.

       Wata nurse ce ta shigo wadda a qalla ta kusa shekara arba'in,cikin harshen


nasara da tataccen engishinsa yake gaya mata abinda zata yi duka sumayyan na jinsu
sai,a ladabce ta amsa ta qarasa inda sumayyan ke kwance,yayin da shi kuma yayi lamo
cikin kujerarsa idanunshi a lumshe,yanajin yadda wata gajiya da kasala ke saukar
masa,bai sake motsawa ba har nurse din ta kammala ta masa bayani idanunshi na arufe
yana gyada kai,idanuwa sumayyan ta fiddo jin tana zancan scanning din da ake ta
qasa za'a yi mata wanda nurse din bata iya ba,qirjinta ya dinga bugawa,ta soma
ayyanawa a ranta yadda hakan zata kasance,sai data bayyana bayaninta tsaf sannan ya
bude idanunshi wanda suka sauya launi kadan,ya jawo wata paper yayi rubutu da baifi
layi hudu ba ya miqa mata yace ta karbo masa yanzu yana jira,karba tayi a ladabce
ta fice.

       Shiru ya ratsa office din sai qarar a.c dake buso sanyi tare da wani
ni'imtaccen qamshi dake gauraye da office din,tana kwance wajen zuciyarta na bugawa
"sauko"ya fadi yana miqewa tsaye ya shige toilet,da hanzari ta sauko ta sanya
takalmanta sannan ta dauki hijabinta ta nufi qofar,sau uku tana murzawa taqi
buduwa,dole ta dawo ta zauna,wanda tana zama nurse din ta sake turo qofar ta
shigo,saman teburin kawai ta dora maganin ta fice.

       Fitowa yayi daga toilet din fuskarsa da hannayenaa wanda ya nannade hannun
'yar cikin suit dinsa jiqe da lema,da alamu alwala ya daura duk da ba lokacin yin
sallah bane,bai dubeta ba ya isa gaban teburin ya fidda magungunan ya dudduba
sannan ya koma gaban freezer din ya ciro ruwan roba,ya balli magungunan ya zube
gabanta tare da ruwan sannan ya juya ya bude daya qofar wanda ke kusa data toilet
ya shige bayan ya sanyawa qofar office din baki daya key,ba musu ta kwashi
magungunan ta zuba a bakinta baki daya ta kora da ruwa ta hadiye,duk yadda taje qin
magani haka ta hadasu baki daya ta hadiye,wannan karon ma ta sake jarraba bude
qofar don bata ga mai zai zaunar kuma da ita na saidai taqi buduwa,a gaban idanunta
ya rufe ba kuma tasan yanda zata bude din ba.

       Fitowa yayi sanye da kayan da likitoci ke sanyawa duk sanda zasu shiga yin
c.s,saidai nashi sun dan banbanta,saboda ash ne nasa,wanda suke a wanke fes da
karin guga muraran a jikinsu,riga ce iya cinya mai qaramin hannu,sai dogon wando da
hula,kamar ba kayan aiki ba sun masa kyau,qafanshi sanye takalmi plate sabanin dazu
da yake sanye da ciki,qwanqwasa qofar aka soma yi baki dayansu suka dubi qofar,yana
qoqarin sanya abun hanci yace
"Waye"
"Ranka ya dade Dr maqarfi ne" aka fada daga waje,takawa yake zuwa bakin qofar yana
fadin
"Ki koma wancan dakin,ki dauki jakarki"
"Gida zan wuce,me zanyi a ciki?" Ta fada cikin zafi zafi,bai gasa nufar qofar ba
bai kuma juyo ba yace
"Ba shi na tambayeki ba,kada ki yarda ya shigo ua ganki a nan"cikin qunan rai ta
miqe ta dauki jakar tata,tana gunguni cikin zuciyarta ta tura qofar ta shige.

     Baya yi zaton ganin dakin ba haka,daki ne sosai mai dauke da madaidaicin gado
wanda ya wadatu da shimfidar bedsheet fara qal bayan lallausar katifar dake
kai,shimfide dakin yake da carfet maroon sai fararen labulaye,daga daya bangon
kwaba ce ta glass wadda aka tsarata cike da littattafai da suka shafi aikin
likitanci,saj wata iriyar hanger kai kyau ta silver ta rataye kaya,qamshi dakin
yake kamar ba cikin asibiti yake ba,gefan gadon ta qarasa a hankali ta yiwa kanta
mazauni gefan gadon tana kalle kalle tana jiyo maganan mutumin da ya kira kanshi da
dr maqarfi a cikin office din,magana suke kan tiyatar da zasu shiga yanzu.

       Sauka idanuwanta sukayi kan wani dan qaramin frem dake zaune kan wata 'yar
bedside,idanu ta saka sosai sai ta gane su'ad ce,sanye take cikin qananun kaya masu
fidda sura,tayi makeup sosai tana dariya cikin hoton,kanta ta dauke tana wassafa
yaya zama zai kasance tsakaninsu,tun tana karanta wasiqar jaki har bacci ya fara
rinjayar idanuwanta,batasan sanda ta jingina da fuskan gadon ba yayi awon gaba da
ita.

       A qalla kusan awanni biyu suka share dakin c.s din saboda mutum biyu suka
yiwa,kowanne anyishi successfull,a gajiye yake saukowa daga sama inda sukeyi aikin
zuwa qasa,ya sanya maqulli ya bude,ya sanya qafafunshi masinjanshi na biye da
shi,da sauri ya dakata sabida tunowa da yayi tana ciki,ya karbi kayansa dake
hannunshi ya sallameshi sannan ya shiga ya rufe office din,sai da ya sanya wani
sabulu ya wanke hannunshi cikin wani dan sink kana ya doshi qofar dakin,yana tura
qofar ta farka,idanunta ta bude baki daya wadanda suka qara girma sakamakon baccin
da tayi ta zubesu fes cikin nashi,sai ya janye nashi idanun yana fadi cikin
zuciyarsa
"Kaman mayya" bai taba ganin idanun da yake jin nauyin sanya nashi ciki ba ko na
waye irin wadan nan idanun,hakan ya sanya yake jin haushinsu,da hanzari ta gayara
zamanta daga kashingidar da tayi saboda ganinsa da ya tuna mata inda take,wuceta
yayi ya nufi inda kayanshi suke da alama zai canza ne hakan ya sanyata miqewa ganin
lokacin azahar yayi,da sauri ta koma ta zauna inda ta miqe din zuciyarta ba
bugawa,jini ne digo digo a inda ta tashin
"Yaya akai haka?,yaushe al'adan har tazo mata bata sani ba,bayan dazun nan ta
lissafa wata biyu bata ganta ba" kamar wadda aka daure haka take jinta,bayansa tabi
da kallo sanda ya kwashi kayansa yana yunqurin ficewa,tamkar ta tsaidashi haka take
ji,ya zatayi  da jikinta?,ya zata yi da wajen?,abinda ta dinga fada kenan har ya
fice,tana jiyo sanda aka ja waccan qofar ta office dim,wanda hakan ke nuna mata ya
sake ficewa ne baki daya,hakan ya bata damar miqewa da hanzari,yaye zanin gadon
tayi cikin sanda ta shige toilet din dake cikin dakin da shi,bandaki ne madaidaici
wanda aka qawatashi,akwai komai a ciki na amfani harda soson wanka da nau'in
sabulai ma ruwa da daskararre,wata roba dake manne da tambarin klien ta bude ta
zazzaga ta soma wanke wajen,sai data tabbatar ya fita sannan itama ta gyara
jikinta,fitowa tayi da zanin gadon ta baje shi saman katifar don ya matsu
sosai,tana qoqarin maida hijabinta ta juyo sallama cikin office din,a hankali cikin
sanda ta fito,nurse din dazu ce,cikin fara'a ta miqa mata wata leda wadda ke dauke
da tambarin sunan gidan abincin seven thirty tana cewa
"Gashi inji yallabai" murmushi itama tayi mata da alama matar na da kirki ta amsa
tana fadin
"Na gode" har ta juya zata fita ta dawo
"Ammm,ranki ya dade ba don kada nayi shishshigi ba da na tambayeki,don Allah
matarshi ce ke?" Girma tambayar tayi mata,amma saita waske tana murmushi
"Qanwarshi ce" cikin murmushi ta sake miqa nata hannu
"Naji dadin haduwa da ke,suna na nurse barira" miqa mata yi itama tana murmushin
"Ameera" sakin hannun nata tayi sannan ta fice tana murnar ganin jinin gidansu
doctor almustapha.

      Ledar ta bude qamshin da ya daki hancinta shi ya tabbatar mata abinci ne,sau
wata ledar wadda tana budewa taga always ce a ciki,idanu ta zaro tana mamakin yadda
akayi yasan tana buqatarta,bata wani tsawaita tunani ba ta dire abincin ta ciri pad
din ta shiga bandaki ta saka ta jefa saurar a jakarta,gyara zaman hijabinta tayi
sannan ta rataya jakarta ta fice a office din.

       Rufe laptop din yayi cikin dakin hutawarshi dake asibitin bayan ya gama
kallon duk abinda tayi din,yana iya ganin kowane sashi na asibitin a dakin hutawar
tashi ta na'urar cctv camera dake asibitin,ya dire cup din coffen da ya gama sha
sannan ya tattare kayanshi ya sauko zuwa qasan.

       Idanu ta shiga rabawa ganin babu motar data kawota babu alamarta,da alama ya
gaji da jiranta kenan ya tafi,babu mamaki,tun qarfe tara na safe suke gashi yanzun
har uku tan gab da yi,bata ga laifin drivan ba ba,haka kawai ya wani tsareta bayan
bata ga alfanun tsaretan da yayi ba,hakan ya sanya ta soma takawa a hankali don
taje titi ta samu abun hawa gangar jikinya da zuciyarta duka a gajiye.

Tana yunqurin fita mai tsaron qofar wanda yake dattijo ne ya qaraso cikin
girmamawa fuskarsa qunshe da fara'a
"Ranki ya dade,ai ya tafine wanda ya kawoki,yallabai yace ya tafi zaku tafi
tare,yace ki tsimayeshi idan kin fito" murmushi tayi cikin gajiyawa
"Babu komai zan samu abun hawa,ina sauri ne kuma bai kammala abinda yake ba" ta
sake sanya kanta zata fice sai ta kuma jiyoshi yana cewa
"Ranki ya dade gashinan ya fito ma ai" ya tunkaro get din yana qoqarin bude
masa,tilas ta ja birki ta koma da baya ta soma takawa zuwa wajen get din saboda
yadda idanuwa suka yi mata yawa,batasan me mutanen ke kallo tattare da ita ba haka.

Gidan baya ta sanya hannu ta bude ta shige ba tare da tayi tsammanin a bayan
yake zaune ba,sai data rufe qofar sannan ta ankara da shi,yana zaune hakimce
abinsa,maimakon suit dake jikinsa dazun yanzun shadda ce jikinsa mai gajeran
hannu,iyakarta gwiwa da dogon wando
"Zaki ci wuyar zama da ni matuqar zaki kasance mai taurin kai da rashin jin magana"
ya fada cikin muryarsa qasa qasa,ta gefan idanu ta kalleshi wayarshi yaje dannawa
kafin ta maida idanunta kan titi,wayar ya ajjiye gefansa ba tare da ya sake cewa
komai ba.

A tunaninta zasu maidata gida ne sai taga sun canza hanya,dubanshi tayi
tana sake kallon titin
"Ba nan bace hanyar" ta yi magana tana kallon titin,sai da ya shaqi isaka sannan ya
amsata
"Wacce hanya kenan?"
"Gidanmu mana"
"Baki da abinda zaki koma gidanku kuyi,so kin taho kenan" idanuwa ta zaro tana
kallonshi cikin mamaki,wannan wacce iriyar magana ce haka?,me hakan ke nufi?,kallon
mamaki taci gaba da yi masa kafin tace
"Ban gane ba,kawai daga zuwa asibiti sai ka zarce wani gun da ni haka akeyi?"
"Haka baba yace nayi,idan kuma ni din kwartonki ne sai ki gayan" ya fadi yana balle
kwalin lemo ya kai bakinsa,ci gaba tayi da kallonsa baqinciki fal zuciyarta,so yake
ayi abunda ba'a taba yinshi ba cikin tarihi kenan,idan wani ya fahimta wani bazai
fahimta ai,wani zai iya dauka ita ta kai kanta
"Amma ba haka al'ada ta tanadar ba ai"
"Addini fa?,me ya tanadar?" Ya maida mata amsa cikin yanayin ko in kula,bata haqura
ba dai duk a qoqarinta na fahimtar da shi,duk da yadda ranta ke baci
"Ko 'yar tsana ce ai tayi sallama da mu......"
"Shut up,idan kika sake magana zaki fitarmin a mota!" Ya fada cikin hargagi wanda
ya tsoratata ya sanyata yin shiru,kanta ta kwantar jikin kujerar motar,bata ankara
ba hawaye suka fara bin kuncinta tana daukesu,wai me yasa ba tun fari bata zabi
abdur rahman ba?,ta tabbatar da cewa koba komai da tuni tana can cikin
farinciki,itakam gaskiya bata jin zata iya da wannan mutumin mai shegen girman kai
izza da taqama.

Bata fahimci airphort suka zo ba sai da motar ta tsaya ya fice yana bata
umarnin fitowa,binsa kawai take jiki a sanyaye baki bude,qarar wayarta ta dawi da
ita hayyacinta,number malam ta gani cikin hanzari da daga
"Jirgin naku bai tashi bane sumayya?" Cewar malam din,mamaki ya cikata,me
kenan?,malam ya sani ne dama,kamar yasan me yake kai kawo a ranta yace
"Drivan muntari da ya dawo ya sanar mana shi mustaphan yace abuja zaku wuce,Allah
ya tsare hanya,ki riqe aurenki da kyau mamana,kiyi biyayya kiyi kuma haquri,ki
kauda kai ki zama mai kara,ki ninka haqurinki,in sha Allah ba zaki tozarta ba,ni
nasan ba zaki taba wulaqanta ba gidan muhtari,Allah ya tsare hanya ga mamanki"
"Daga zuwa ganin likita sai ki gudu abinki kuma?" Cewar mama cikin salon tsokana,a
zaton sumayya da gaske maman take sai ta sanya kuka
"Wallahi mama ban san shine ba,bansan tafiya zaiyi da ni ba"
"Keee,a kul na sake jin kukanki,wanne irin shirme ne wannan daga tsokana?,to dama
me zaki dawo kiyi?,dukka qannanki fa kowa ta tafi nata gidan"
"Amma mama ni kadaice ba'a rakani ba,banyi muku sallama ba babu"
"Sallamar me zaki mana,sannan abujan baquwarki ce da sai an rakaki,mu kuma ba gashi
muna sallama ba,kibi mijinki sumayya kiyi biyayya,yi nayi bari na bari,ki
girmamashi ki tuna waye shi a wajen mahaifinki,kada ki sake yayi kuka da ke" nasiha
tayi mata qwarai mai ratsa jiki,duk sai ta tafiyar da wani zafi da take ji cikin
zuciyarta,kafin suyi sallam ta wanke mata zuciyarta fes da kyawawan kalamai sukayi
sallama,bata ajjiye wayar ba sai data kira nafisa ta gaya mata tahowarra,jin ta
fara cikata da tsokanar amarya ya da biyo miji haka babu ko 'yan rakiya,sai tazo
tsuma amarya wai,sai ta kashe tana kada kai,tsokana cikin nafisa ita da amira tana
da yawa,anty dije ta sake laluba ta kirata ta gaya mata,bata damu ba itama da jin
tahiwarta ita da shi,saima farinciki daya cikata ta musu addu'ar isowa lafiya tare
da shirin tarbar sumayyan,tayi niyyar kiran amira amma ta fasa,sai kawai ta tura
mata tex ta kashe wayar.

Bayan ya gama sallamar drivan ya tako a hankali zuwa inda take tsaye don
batasan abunyi ba,wayarshi dake aljihu ta dauki tsuwwa,ya laluba ya cirota yana
duba mai kiran,su'ad ce,shafa wajen ansawar yayi ya daga ya kara kunnenshi
"Mustapha ina tafe zuwa abuja a daren yau ba sai gobe ba,ina son kafin na qaraso ka
tabbatar ka saki wannan kidahuma bagidajiyar yarinyar mai yawo a hijabi,idan ba
haka ba wallahi sai na tashi abuja" tsawa ya daka mata cikin matsanancin bacin rai
tamkar tana gabanshi
"Kin manta da waye kike magana?,kin manta waye almustapha?,ok.....naga alamun kin
manta,amma ina jiranki idan kika iso zan tunasar dake waye muhammad almustapha" ya
datse kiran cikij bacin rai,ya zuqi iska mai zafi yana fesarwa,ya kashe wayar baki
daya ya jefa aljihu yayi gaba,yana jin lallai wannan karon idan su'ad batayi wasa
ba zai juna mata qaramin hauka ta iya ga inda ake babban,zai koya mata darasi mai
girma,binshi tayi cike da tsoro da taraddi,haka yake da fada?,haka yake da saurin
hawa?,wace tayi kiransa ya dugunxuma haka?,baki ta tabe tana biye da shi koma meye
ba sabgarta bace.

Wayar ta sauke daga kunnenta tana duban mahaifiyarta dakezaune gefanta,wadda


itace ta karanta mata dukkan abinda zatayi din
"Nifa mom gaskiya ina jin tsoro,ina son mijina kada naje nayi abinda zai zame mana
dana sani,nasan halin almustapha sarai baya daukar raini" harara ta galla mata tana
huci tamkar ita aka yiwa kishiyar
"Ai sai ki zauna dan ubanki,ke yanzu ba abun kunya bane gareki ace wai an miki
kishiya?,uwarki ma har ta qaraci quruciyarta har zuwa tsufanta bata zauna da
kishiya ba?,ki tashi ki masa hauka ki qwaci 'yancinki,rashin qwatar 'yancin naki
shi zai haifar da abinda kike tsoron na rasa mijin naki,kishiya bala'ice masifa ce
annoba ce,ke kishiya ta wuce duk inda kike zatonta,ki tabbatar ya zaba ko ke ko
ita,ke yarinya ce baki sani bane,inda ina da ita 'yancin da kika samu a rayuwarki
da baki same shi ba,ban taba sanin hajiya kilishi da gaske har yau bata qaunata ba
sai yanzu,daboda ita ta zauna da kishiya shine suka hada baki suka yi miki,dama can
ba jituwa muke ba,aurenki da danta ne ma ya sake sawa muke hulda ta dole,to wallahi
zata ga tsantsar rashin arziquki,ki tashi tsaye kada ki raga mata har sai kin raba
tsakaninsu,sannan duk wanda ke gidan kada ki raga masa ciki harda hajiya
kilishin,ku juye rashin mutuncinki son ranki,har sai kowa yayi laushi ya nemi
daidaito da ke,indai nonon khaulat kika sha rainon america ce ke" kalamai masu
nauyi ta dinga amfani da su tare da nuna mata cewa ba zata taba mallakar almustapha
ba matuqar yana da wata matar,kalaman sunyi tasiri matuqa a kunne zuciya da gangar
jikin su'ad,hakan ya sanya ta soma hada kayanta haiqan don isowa nageria ta bashi
zabin zama da ita ko zama da amaryarsa,wanda baki daya haushin jama'ar gidan takeji
musamman data samu labarin diyar aminin baabaa prof ce,tana jin dama can suna adawa
da ita,suna adawa da zamanta da mijinta,saboda ya dauke mata komai tana juyawa da
takunta yadda taga dama,ba shakka ba zata raga ma kowa ba indai akan almustaphanta
ne.

To masu karatu,ku biyoni muje.

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

7⃣7⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

___________________________________

      Bayan sun shiga cikin jirgi bata sake ganinshi ba,batasan inda ya zauna ba
sai da suka sauka,cikin motocin gidan aka zo daukarsu,tana tsaye har ya shiga
sannan itama ta bude ta shiga,yana zaune daga daya bangaren itama haka,motar
tsit,shi yana danne dannen wayarshi yayin da ita kuma ta bige da kallon titi tamkar
yau ta soma ganin garin a haka har suka qarasa.

       A hankali motar ke kutsawa cikin unguwar tasu,tana kallo suka wuce qofar
gidan anty dije,kamar tayi tsalle ta fita haka take ji,saidai ba yadda zata
yi,yanzun a qarqashin wani take dole,ajiyar zuciya ta saki tana sauke jumfashi,a
yau a kuma wannan lokacin gata ta sake dawowa cikin gafin,saidai cikin wanu matsayi
na daban,ta dawo cikin garin a matsayin matar wani kuma surukar gidan baabaa
professor,ma'ajiyar motoci motar ta tsaya bayan mai gadin ya bude masu wakekiyar
qofar gidan,a hankali ta sanya hannunta ta bude murfin motar bayan tsayawar
motar,qafarta ta zura guda daya waje ihun amira ya karade kunnuwanta,kafin tace
wanu abu tuni ta ruqunqumeta
"Wayyo amaryarmu oyoyo oyoyo" murmushi ya subucewa sumayya,da ido takewa amiran
nuni da bayanta,sam bata ankara ba karadinta kawai take
"Ke matar nan kiji tsoron Allah,har an fara sanin dadin miji ko?,anty ta bani
labari daga zuwa ganin doctor sai kawai ayi mai gaba daya,kodai......" Bata kai ga
qarasawa ba ya fito daga cikin motar,wanda hakan ya tilasta mata sanyawa bakinta
fulasta sabida kallon da ya jefeta da shi,magana ce fal cikinta amma tilas ta saita
kanta,a ladabce tace
"Barka da isowa yaya"
"Sake mata hannu ko?" Ya fadi ba tare da ya damu da amsa gaisuwar tata ba,hannun ta
saki tana baata fuska ta janye gefe,kafeta yayi da idanu yana mata alama data wuce
yana yin gaba,binsa tayi a baya amira ta rufa musu baya,duk da haka bata haqura ba
sai data tsaya saitin sumayyan murya qasa qasa
"Wannan hadi yayi kyau,Allah ka nunamin idanuwan su'ad naga ya zata yi" ta gefan
idanu ta jefa mata harara amma hakan bai sanya ta fasa ba,waiwayowar musty din ne
ya sanyata ja da baya tana raba idanu.

      Kai tsaye bangaren ummee suka soma shiga,a hankali suke takawa jere da
junansu tamkar wasu shaqiqan masoya,su biyun ke zaune a falon ummee da maamaa,da
alama suna tattauna wani abu ne,amsa sallamar sukayi kowacce fuskarta a sake,idanun
umme bisa fuskarshi,shi ya soma yiwa kansa matsuguni kan daya daga cikin kujerun
falon kafin ta qarasa takowa a ladabce zuwa cikin falon,kanta a qasa a kunyace ta
qarasa amira na gefanta,wata kunya da nauyinsu take ji a yanzu wadda ta ninka ta
da,musamman ummee wadda dama can ba wani sakewa ko sabo sosai tsakaninsu,gefe ta
zauna qasan carfet kan ta a qasa
"Tashi ki koma saman kujera mana,wacce irin tafiya ce haka almustapha?" Ta
tambayeshi tana dubansa,kanshi ya shafa yana yana yiwa ummeen magana da idanu zuwa
sashen da su sumayya suke,ta fuskanci mai yake son fadi amma duk da haka bata fasa
sake magana ba
"Babu sanarwa ba komai,halan ma baka barta ta kintsa ba ka tattago ta ko?" Inji
ummeen tana bata rai,don tuni amira ta fesa mata yadda ya dauko sumayyan,cikin
salon bada uziri yace
"Ummee,umarnin baba ne"dauke idanunta tayi ta maida kan sumayyan wadda suke gaisawa
da anty maamaa,cikinnurmushi ta soma gaidata
"Ummee ina yini"
"Lafiya qalau ya gajiyan hanya"
"Alhmdlh" ta fadi cikin ranta tana fadin wacce gajiya gurin mutumin da yayi tafiya
a jirgi
"Anty kun yini lpy?" Cewar almustapha yana miqewa tsaye
"Lafiya qalau almustapha,ashe kuna hanya babu sanarwa bare ayi abun tarbar baqi"
qaramin murmushi kawai ya saki na gefan baki,bai amsa ba sai ya jefo tambaya
"Baabaa fa?"
"Ya fita,yana can suna lissafin gidajen gonar nan"
"Ok" ya fada a taqaice yana takawa zuwa hanyar barin falon,ko motsawa sumayyan
batayi ba,wanda hakan ya burge ummee da anty maamaan baki daya,ta tabbatar da cewa
da su'ad ce da tuni miqe ta rufa mishi baya
"Kada ka rufe sashen idan ka shiga,anjima zamu kawo amarya" inji anty mama
"Ok" kawai yace yana ficewa a sashen,kamar jira amira takeyi ta buga tsalle ta iso
gaban sumayyan
"Tashi muje namecy" harara ummee ta buga mata
"Saura ki hanata sakewa kuma bare ta huta gajiyan data kwaso ko?" Dariya amira tayi
yayin da sumayya ta miqe ta bita tana murmushi kanta a qasa.

Hira ce sosai ta barke tsakaninsu,sumayya kallon amiran take,da alama auren


ya karbeta qwarai,ta sake haske ta murje,tsokanan da amiran keyi mata ya soma
isanta hakan ya sanya itama ta soma tsokananta kodai ta samo musu baby,wannan ya
taqaita tsokanan da take mata ta barta ta sarara mata,sai da akayi sallar magariba
amira ta shiga alwala sannan ta kira antyn ta shaida mata isowarsu,ta soma roqonta
ta turo mata laila
"Madalla amarsu,su laila zasu zo amma ban fadi yaushe ba,ke ke da ki gansu ma sai
na gamsu da yadda kike zamantakewarki" kai ta langabe kamar tana gabanta
"Kai anty,haka zamuyi dake?"
"Har ma fiye da haka idan baki zama jarumar mace ba,baki kuma yi fiye da yadda nake
son gani ba" ta fada tana datse layin,dariya ma maganar anty ta bata,bayi ta shiga
itama don sauya pad din jikinta bayan fitowar amiran.

Gefan gado ta kuma zama ta lalubi lambar yaya yahansu don taji abdallah,bugu
uku aka daga,shi din ne ma ya daga,murmushi ta saki kan yadda yayan ke shagwaba
abdallah
"Amminaaa" ya fada cikin muryar quruciya
"Abdallah na,kai baka damu kaga amminka ba ko?" Dariya ya qyalqyale da ita yana
cewa
"A nan ma ai ina da wasu ammin,ga mama ma,ga anty jamila,ga anty yaya(yaya
yahanasu)"taji dadi qwarai cikin ranta jin bai tare da wata damuwa,amma sai ta dan
tsokaleshi
"Shikenan na sake komawa abuja na barka ai"
"Nima bana son zuwa,su kullmun ana gida,nan kuwa zamuyi wasa da su walid,amma
kicewa daddy na wannan wanda ya daukeni a motarsa ina gaisheshi" sarai ta gane
almustapha yake nufi,sai tayi murmushi kawai ta kauda zancan
"Me kake so a kawo maka yanzu"
"Ba komai ammi,dazu ma da inason indomie anty jamila ta dafa min naci na qoshi,ta
kuma bani bobo"
"To an gaida anty jamila,ayi karatu da kyau abdallah,banda rigima"
"Ai bazanyi ba,tunda ga malam dina dazu ma naje wajensa" dariya ta saki sannan tace
"Ok ilove you my abdallah"
"I love you too ammina"tayi hanzarin datse layin jin yaya yahanasu na qoqarin
karba,nauyinta take ji sosai bata jin a irin wannan yanayin zata iya magana da ita
" ki gama cin amarcinki zuwa zamuyi mu dauko abdallahn mu"cewar amira,murmushi
kawai tayi din bata jin mutanan kano zasu iya basu abdallah,musamman yaya yahanasu
da take jinsa kamar mukhtar,bata son ya motsa ko nan da can,shima kuma yaron kamar
yasan yadda aka rabu da mahaifinsa cikin kewa baya yadda ya yiwa gida nisa,bai wuce
gidansu ko gidan yaya yahanasun ko na wuni daya kuwa.

Bayan sallar magariba suna hira sama sama anty maamaa ta shigo dakin
"Amarya taso baabaanki na fada yace na miqa ki dakinki" a kunyace ta motsa ta
miqe,gabanta na wani irin faduwa,fargaba ta cikata,haka ta fito antyn na riqe da
hannunta amira na biye da su,a falo suka samu ummee,antyn ta dubeta
"Ummeen yara zaki rakamu ne?" Ta fada cikin salon tsokana,wanda tasan ba zata din
na,baki ta tabe tana murmushi gami da girgiza kai
"Um um,sai kun dawo,ki dai jawa d'anki kunne idan yana nan" ta fada tana miqawa
sumayya wani babban kwali,amira ce ta qaraso ta amsa tana taya sumayyan godiya
sannan suka fice.

Karon farko data fara shiga sashen tunda take zuwa gidan,kamar sauran sassan
gidan haka yake saidai duka ya fisu qaawa da burgewa,biye take da anty maamaa
jikinta asanyaye,kai tsaye anty maamaan ta miqawa amiran muqullan hannunta ta bata
umarnin bude dakunan,sannan ta jiya da ita kafin amiran ta bude dakin suka nufi
qofofin kitchen,nata ta bude mata ta nuna mata,komai na a tsare masha Allah,babu
abinda ba'a tanadarwa kitchen din ba na kayan amfani,dakin farko ta fara nuna mata
sannan na biyu,a nan ta zaunar da ita gefan gado sannan itama ta zauna kan kujerar
dake fuskantar gadon
"To mamanmu,ga gidanki nan ga dakunanki nan,daya dakin naki yana sama saidai naga
kamar mai gidan kamar baya nan shi yasa bai kanki can ba,nasan zaya nuna miki idan
ya dawo,duk abinda zan gaya miki nasan tuni an fada miki tun daga gida,almustapha
dai mijinki je biyayya gareshi wajibi ne a gareki,kamar yadda tilas ne ya kyautata
miki,bari na fada miki wani sirri na mallakar miji cikin sauqi,yi nayi bari na
bari,ma'ana biyayya da kyautatawa,haquri da kai zuciya nesa,wannan shine kadai
abinda zan qara miki a kai,Allah ya baku zaman lafiya ya hada kanku baki daya,ga
kayan lefanki can kusan fiye da rabi a dinke suke,nasan baki taho da abubuwan
buqatarki ba saidai kina iya amfani da su,amira ki tayata ku sanya kayan cikin
wardrobe amma kada ki wuce awa daya,kema wucewa zakuyi keda saifullahi kada yazo
yayita jiranki"
"To anty" ta fada tana miqewa,kusan sumayya bata da kuzarin da zata yi aikin,amiran
ce ta shirya mata duo kayan dake a dinke,sai data gama ta dubeta cike da tsokana
tana mata nuni da cikin sif din
"Wadannan kayan gida ne,nan bangaren qananun kaya ne na zaman falo,don bance ki
raga ba wajen sanyasu,can sashin kuma kayan daukan magana ne na zuwa turaka kin
gane ai?" Ta fada tana daga gira,duk yadda take ji a zuciyarta sai data bata dariya
"Kin fara rainani amira,kada ki manta nifa yayarki ce yanzu"
"Eh wallahi afuwa,amma sai mun fadi gaskiya,sai ma nan da kwana hudu zamu dawo ni
da nafisa,sai mun baje miki aiki" ta fada tana ficewa daga sashen da gudu tana
dariya,da idanu sumayya ta fita kafin daga bisani ta dauke idanunta tana girgiza
kai,tana ji dama itace amiran,ba shakka babu abinda yake rayuwa cikin farinciki ba
tare da matsala ba dadi.

Kowanne huduba da ta samu daga kowanne sashi tayi tasiri cikin ruhi da
zuciyarta,ta fuskanci kowanne sashe dake da muhimmanci a rayuwarta na supporting
wannan aure,wanda ita har yau zurfin tunaninta baikai ga hango abinda su suka hango
din ba,a hankali ta bude qofar toilet din dake maqale cikin bedroom din,bandaki ne
wadatacce wanda aka qawatashi da dukkan wasu kayayyakin amfani na bandakin
zamani,ruwan zafi dana sanyi ta hada yadda take buqata ta shower don bata fiya son
shiga bathtube ba.

Ta jima gaban kayan tana kallon yadda amiran ta shirya mata su,kai kawai
take kadawa,batasan wacce iriyar qauna amiran ke mata ba,bata da abinda zata saka
mata da shi qauna ce daga Allah,da hannu ta dinga taba kayan baccin har ta ciro
wasu cotton masu kauri,riga da wando ne dogon wando,iyakar rigar cinya saidai
hannun nata dogo ne,bayan ta sanya ta isa gaban mudubi,ga mamakinta irin mayukan da
take amfani da su ne da turarukanta,ta tabbatar da cewa wannan aikin amiran ne
shima,murmushi ta sake saki tana fadin
"Amira?,amira?,hmm"sai data hade gashinta waje daya sannan ta soma mutststsuka mai
bayan ta feshe jikinta da turarukanta.

A fujajan haka ta shigo gidan tamkar wadda aka koro,akwatinta qwaya daya
aharabar gidan ta barshi tana baiwa hadiman gidan umarni da su biyota da shi,babu
kowa a falon,sauyin da falon ya sake samu kawai ya tabbatar mata ba shakka a yanzun
ba ita daya bace mamallakiyar sashen,hakan ya sake tabbatar mata da cewa almustapha
zai zama nasu ne su biyu ita da wata,kamar zautacciya haka ta shiha karkada kai ita
daya tana fadin
"Ina!,sam wallahi zuciyata ba zata jure wannan ba" ta fada tana haurawa sama cikin
hanzari,zuciyarta nata mata saqe saqen irin yanayin da wai zata iya zuwa ta tadda
almustapha shi da amaryarshi,kishinta na hauhawa zuciyarta na sake haukata idanunta
na kuma rufewa.

Tsaye yake bayan ya fito daga wanka yana sanya kayan baccinsa,a gajiye yake
matuqa,so yake ya kwanta ya huta hakanan ko qwaqwalwarsa zata samu irin hutun da
yake fata,sashe daya na zuciyar nashi na masa tunanin me zaya bata taci kafin ta
kwanta?,tilas dunsa ne cinta da shanta na a wuyanta,duk da ya tabbata baza a rasa
abinci cikin gidan ba amma shi kam bazai tambaya a kawo din ba,mutum ne da tun
asali ba mai roqo ba,hakanan baison roqo,dalili da yasa har yau yawan roqo irin na
sy'ad ke bashi mamaki,a hankali ta tura qofar zuciyarta na bugawa tamkar zata fito
waje,wata wawiyar ajiyar zuciya ta saki ganinshi tsaye shi kadai sanye da kayan
bacci,da gudu ta banko dakin wanda kafin ya kai ga waiwayowa ta ruqunqumeshi ta
baya tana sakin kuka,bai ce mata uffan ba bai kuma juyowa ba,saidai yana sauraren
sautin kukan da take fitarwa,tuni kukan ya soma hawa masa ka,ta sani ya tsani kuka
amma hakan bai hanata rerashi ba aduk sanda tayi niyya,da faru baiyi niyyar
lallashinta ba ko kadan saboda maganganun data gaya mishin dazu,amma tunawa da yayi
yasha jin mata na fadin irin qunci da bacin ran da suke fuskanta takura da kuma
kishi shi ya sanya shi zagaya hannunshi ya dawo da ita gabanshi suna fuskantar juna
sannan ya zaunar da ita gefan gado kafin shima ya zauna,hakan yayi mata kyau da
dadi qwarai,zuciyarta ta shiga gaya mata cewa ba shakka tana da nasara
"Ya kamata ki nutsu kiyi controlling kanki,aurena bai nufin konai zai sauya
tsakanina da ke"cikin sheshsheqar kuka tace
"Almustapha,wallahi bazan iya zama da kowacce diya mace ba amatsayin wai itama
matarka ce bazan iya ba wallahi,ya zama tilas ka saketa wannan dole ne" fubanta
yake yana qoqarin controlling kansa jin yadda take bashi umarni kai tsaye tamkar
uta din ita tayi naqudarsa kafin daga bisani yace
"Look su'ad,bana so ki sake tada wannan magana,kada ki sake ambaton saki cikin
maganarki don babu shi duka ciki qwaqwalwata,ki iya bakinki ki san me zaki furta"
ba qaramin hasalata kalaman sukayi ba,tuni zuciyarta ta dinga gaya mata tsananin
sonta yake,qaunarta yake shi ya sanya har yake gaya miki hakan a kanta,take kalaman
mom dinta suka fado mata na kada ta ragawa kowa,tayi hauka sosai don ta qwatarwa
kanta 'yanci,miqewa tayi tsaye tana qanqan da idanunta,hannayenta riqe a
qugunta,karo na farko data shirya kallon tsabar qwayar idanunshi ta masa rashin
kunya
"Ai dama namiji ba dan goyo bane,gaskiya mana naji kidahuman matan africa na fadin
haka,mu dama mun jima da sanin haka,to wallahi almustapha bari na gaya maka wani
abu,duk eani qulla qulla da munafuncin da aka hada kan auren nan tilas ya rabu,don
ni bazan taba zama da kishiya ba wallahi bata isa na hada miji da ita ba,wallahi
dole ka saketa idan ba haka ba zan dauki mafi munin mataki wanda bazaiw kowa dadi
ba,zan iya kashe...." Wata gigitacciyar tsawa ya daka mata wadda ta sanya ta yin
shiru,cikim zafi da fushi wanda suka bayyana muraran a fuskarshi ya soma nuna ta da
yatsa
"Kada bakinki yayi ganganci ko kuskuren zagar min iyaye,idan kuwa kika aikata hakan
ki lissafashi cikin ganganci na farko da kika taba yi cikin rayuwarki" cikin tsiwa
da bushewar zuciya tace
"A daki mutum a hanashi kuka,na fuskanci almustapha baka qaunata har yanzu?"cikin
fushi da son cusa haushi shima yace
" ke sai yau kika sani?"baki ta saki galala tana dubanshi hawaye na malala bisa
kuncinta,q maimakon ya qasqantar da kai ya lallasheta shine yake gaya mata wannan
baqar kalmar da ya raba fada mata can wasu shekaru baya da shka wuce,tuni ya miqe
yaci gaba da daura zaren kayan baccin dake jikinsa,kai ta shiga girgizawa zuciya na
tunzurata,juyawa tayi ta sauka qasa da gudu,yabi bayanta da kallo yana jan wani
mugun tsaki,kai tsaye kitchen ta nufa ta zari daya daga cikin setin wuqaqenta wadda
sabuwa ce dal,bata taba amfani da ita ba kasancewar babu abinda ta taba shiga
kitchen din tayi tunda aka tanadar mata sji,saidai ta karbo musu koma meye wajensu
umme in har ma tazo qasar,saman ta koma ta banka qofar dakin sanda yake qoqarin
zama gefan gadon ta qaraso gabansa ta tsaya
"Almustapha,wallahi gwara na kashe kaina da naci gaba da sauraron kalaman qi daga
gareka,gwara na kashe kaina dana zauna da wata" ta fada tana daga wuqar da niyyar
dabawa cikinta,cikin wani irin zafin nama ya sanya hannunshi ya riqe wuqar,wanda
hakan yayi sanadiyyar yankewarsa jini ya soma diga,bai kula da wannan ko ya damu
ba,don ya lura su'ad mahaukaciya ce wadda aqidar yahudawa ta gama ratsata,wannan
shine karo na biyu da tayi yunqurin hallaka kanta saboda shi
"Ke wacce iriyar dabba ce mara hankali,shashashar banza mahaukaciya kawai"zuge
wuqar tayi daga hannunshi wanda zafin sai da ya ratsashi har cikin kwanyarsa
"Kome zaka fada saidai ka fada,amma almustapha amma yau ko ban kashe kaina ba zanje
na kasheta idan yaso nima a kasheni" ta fada tana juyawa da sauri ba tare data damu
da ciwon data ji masa ba,da hanzari ya fincota tana waiwayowa zata sauke masa
rashin kunya ya zabgeta da wani irin lafiyayyen mari daya tarwatsa tsarin
qwaqwalwarta sannan ya hankadata ta fada saman gado,yasanya qafarshi ya take
hannunta wanda hakan ya tilasta mata sakin wuqar ya zareta
"Ban taba dana sanin saninki ba su'ad sai yau,ashe ke din ba mutum bace har kike
ikirarin kashe kanki ki kashe wani?,banza wawiya kawai mara hankali" ya fada yana
nufar qofa zai fice,wannan ya watstsakar da ita daga marin da yayi mata ta yunqura
tana fadin maganganu cikin ihu da zummar binsa,tuni ya fice dauke da wuqar,ya sanya
key ya rufe qofar sannan ya qarasa kan kujerun falon ha zaune yana dunqule da tafin
hannunsa,yana iya jiyo surutanta wani cikin hausa wani cikin harshen nasara tana
bugun qofar,daga bisani ya dinga ji qara ta gilasai wanda da alama barna ta soma
masa cikin dakin,hakane kuwa,don duk wani glass na dakin ka daga t.v
palsma,mirrow,bedside lamp babu wanda bata hada ta kwankwatse ba,cikinbqanqanin
lokaci itama ta jiwa kanta ciwo,zuciya ke tunzurashi ya bude qofar ya shiga yayi
mata dukan kawo wuqa yana qoqarin danne fushinsa,ya tabbatar idan yaci gaba da zama
komai zai iya faruwa,zai iya gaza ci gaba da yin haquri ya bude dakin wanda ya
tabbata gamuwarsu a wannan lokacin bazai haifar da d'aa mai ido ba,hakan ya
sanyashi ya miqe ya gwammace ya sauko qasa,don baiga abinda zai kashi nata dakin
ba.

Kwance take lamo bisa gadon nata tana iya jiyo hargowa saman gidan,tuni ta
dauke muryar su'ad ta kuma tabbatar itace,fargaba da tsoron irin hayaniyar data
dinga ji ita ta kamata,sannu a hankali ta dinga kiran sunayen Allah,sannu sannu
fargabarta da tsoronta suka gushe,kalaman anty dije suka dawo mata sanda zata taho
abuja
"Idan har su'ad ta tsorataki kinyi asara,wacce kalar kishiya ce baki gani ba,kada
ki yadda ki kasa kyautatawa mijinki saboda wata,zaku taru ne dukanku ku zama
daya,don qwace goruba hannun kuturu ba abu bane mai wuya,samun almstapha a tafin
hannunki saidai idan baki so ba" tabbas haka maganar anty take,ya kamata zuwa yanzu
ace ta tsike,ya kamaceta ace ta fara qwatar 'yancinta hannun kishiya,su dinma fa
mata ne kamarta,don me zata zauna suna garata daga wannan waje zuwa wannan?,akanme
zata zuba musu ido su dinga yin yadda suka ga dama da rayuwarta,'yanci shi take
buqata wannan karon,ta kuma bawa kanta tabbaci da qwarin gwiwar tabar bari ana
cutarta yadda itama ba zata cuci kowa ba to a zauna lafiya,tana buri da fatan
wannan ya zame mata gidanta na qarshe koda banu soyayya da shaquwa tsakaninta da
mai gidan,amma akwai da dama masu zamansun a haka girmamawa da kyautatawa ita ke
musu jagora.

Sallamar data ji cikin falon nasu anata yi ita ta sanyata miqewa ba tare da
shayi ko fargaba ba ta zira hijabinta ta bude qofan ta fito,biyu daga cikin
ma'aikatan gidan ne dauke da kwanduna guda biyu,cikin girmamawa suka dan rusuna
wanda hakan ya bata kunya suna gabatar da kansu sannan suka ce
"Abincin dare ne maamaa tace a kawo muku,wannan kwandon abincin yallabai ne,saidai
ummee tace don Allah a sashi yaci kada yasha coffee yace zaya zauna haka" murmushi
ya subuce mata wanda hakan ya bayyana fararen haqoranta,kunyar ummeen ta kamata duk
da bata wajen,masar kwandunan tayi tana cewa ayi musu godiya da sannu,shka juya
suka fice zucuyarsu fal mamaki da murna,ganin sauyi muraran yau a sashen
yallabai,abinda ba'a taba yi musu ba,sau tari idan suka kawo abincin ma tana
yatsina zata sanyasu su shiryashi saman tebur,idan kuma bai mata ba tana masifa
zata basu umarnin abinda zasu dafa din komai dare.

Tunda ma'aikatan suka shigo yana kwance saman kujerar yana dubansu,saidai su
ba zasu iya ganinshi na sakamakon nutsewa da yayi tsakiyar kujeru runtse da
hannunshi,wuqar na ajjiye saman center table dake daura da shi,to ita din ma bata
lura da shi na,a nutse ta wuce taje ta shirya abincin kai dining,sannan ta sauko a
hankali tana tunanin yadda zata cika roqon da umme tayi mata,ta yaya zata tasoshi
kenan?,wani adon dan qullutu dake jikin kujerar da yake kwance shi ya riqe gefan
hijabinta,ta waiwayo da niyyar cirewa sai ta gashi kwance,cikin dakewa da boye
rudunta ta cire hijabin nata sannan ta qaraso inda yake kwancen
"Ga abinci an kawo umme tace kaa......" Sai ta gaza qarasawa sakamakon ganin irin
yankar dake hannunshi,gefe kadan sharbebiyar wuqar da jini ke kwance jiki,take ta
tsorata,ta sanya tafin hannunta baki daya ta rufe bakinta
"Ya salam,subhanallah,me yake faruwa?"ta ambata cikin rawar murya da tsorata,baiko
motsa ba yana kwance ya zuba idanunshi a kanta,yanayim yadda ta firgita ya sanyashi
ya miqe ya zauna wanda hakan ya sanyata zabura data hangin jinin da ya zubar wanda
ya kwanta saman tiles
"C'mon,kada ki taramin jama'a" ya fada cikin dakiya
"Amma haka ka zauna bai da kyau fa ga lafiya zubar jini irin haka" ta fada tana
kama hannun cikim rudewa ba tare da yasan ta riqe din ba,hannunshi yayi hanzarin
janyewa,itama da sauri ta janye nata hannun tana zaton zafi yake ji,wannan wanme
irin yanka ne daya shiga hannunshi sosai haka
"Sannu zafi ko?dame za'a tsaida jinin?"tilas ya soma gaya mata inda first aid boxs
dinsu yake,sai kuma ya tuna yana dakinsa ne su'ad kuma na qulle ciki
"jeki kawai bai kusa" ya fada yana lumshe idanunshi tare da tunanin mai zai saka ya
tsaida jinin,tunawa tayi dazun kamar taji qamshin na'a na'a da suka shiga kitchen
dinta,da sauri ta shiga ta bude kitchen din,cikin sa'a ta sameta kuwa,ta debo a
tafin hannunta ta sake dawowa inda yake din,har yanzu idonsa rufe yake,baisan me
ake sawa atsaida jini ba bayan kayan aikin su na likita,a tausashe yaji an riqe
tsaintsiyar hannunshi,ya bude idanuwansa ya zubesu a kanta,tana duqe bayan ta cire
hannayen hijabinta ta sanya tissue da kwalinta ke saman table din ta goge jinin
sannan ta shiga jera barbadata a saitin wajen ciwon,sai data kammala sannan ta
tsaya na wajen minti hudu taga jinin ya tsaya sannan ta saki ajiyar zuciya ta saki
hannun,miqewa tayi ta koma kitchen don dauko mopper bayan ta dauke wuqar,wadda har
tashi tsigar jikinta keyi idan ta kalleta,da idanu ya bita kafin ya dauke idonsa ya
dawo dashi kan hannun nashi yana duban abinda tayin kafin daga bisani ya maida
idanuwan nashi ya sake lumshewa,ya akayi tasan wannan hanyar ta tsaida jini?,mopper
da dettol ta dauko gyara wajen tas,baki daya zuciyarta a jagule take,ta tabbatar
wannan ciwon na da nasaba da hayaniyar data ji na tashi dazun,wannan wane irin
ta'addanci mata keyi?,mace mai laushi da taushin zuciya mai cike da tausayi ce ke
iya aikata haka?,tabbas idan har ita ta aikata hakan ba zata saurara mata ba
ballantana ta samu damar gwada hakan a kanta ba.

*mrs muhammad ce*👑

✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

7⃣8⃣
*Bismillahir rahmanir rahim*

___________________________________

         Kayan ta koma maidawa kitchen,sai ya bita da kallo yana duban hannun nashi
har ta shige kitchen din,a hankali ya miqe ya haura saman,a yanzun falon tsit yake
da alamu ta gama haukan nata ko gajiya ce ta sata sadudar dole ganin babu wani
alamu na zaya bude qofan.

       Falon ta dawo da niyyar gabatar mai da abincin kamar yadda ummee ta roqi
alfarma saidai bata taddashi ba,ta danyi jim don batasan inda zata sameshi ba,tilas
ra juya ta koma dakinta ta sakaya qofar sannan ta haye kan gadon bayan ta sauya
hasken dakin zuwa na bacci,baki daya bata da sha'awar cin komai,tunani ne fal
zuciyarta,tana so tasan ta yaya haka ta faru a gidan nasu,dama su'ad din tana cikin
gidan me koko yaya?.

        A hankali aka turo qofar dakin sanda take tsaka da tunanin,sai ta sake lamo
tana son taga waye,almustapha ne,cikin takunshi na nutsuwa ya qaraso ciki a
hankali,da idanu ta dinga binsa har ya isa kan doguwar kujerar dake dakin ya zauna
akai tare da miqe qafafunsa,bayansa na jingine da hannun kujerar yayin da qafarsa
ke tokare da daya hannun,duk tsawon kujerar ya cinyeta tsaf da nashi tsahon,hannun
nashi na ajjiye saman cinyarshi,idanunsa ya maida ya lumshe yana jin yadda zugin
ciwon ke ratsa ko ina ajikinsa,bai san wanne irin hukunci ne ya dace ya yankewa
su'ad ba,wacce iriyar yarinya ce haka?,wadda batasan darajat rai ba,bata san
darajar al'ada da mutunci ba?,wanne irin raino ta samu wacce iriyar tarbiyya
ce?,iliminta me ya amfana mata da shi?,wadan nan tunanukan su suka jagoranci
qwaqwalwarsa,suka hana idanunshi runtsawa,lokaci lokaci yana tashi ya sauya yanayin
zaman nashi,dukka abinda ke faruwa a idanun sumayya ne,duk wani motsinsa tana lura
da shi,karon farko taji tausayinsa ya kashi,wacce iriyar mace yake aure?,rashin kan
gadon nata har ya kai ta sanya makami ta yanki mijinta,mijin da take ji duk duniya
tafi kowa sanshi?,ita dinma kusan duka juye juye ta dinga yi saman gadon,wanda
hakan yaso ankarar da shi idanuwanta biyu,a hankali ya miqe yana tsurawa inda take
kwancen ido cikin duhu duhun dakin,qarasawa yayi inda makunnin dakin yake ya sanya
hannunsa ya kunna qwan,take haske ya gauraye dakin wanda hakan ya sanya ta cikin
hanzari ta runtse idanunta,ido ya zuba mata yana kallonta,jikinsa ya bashi idanunta
biyu,cikin dakewa murya can qasa yace
"Saiki tashi ki zauna,don ba dolen yin baccin aka yi miki ba" shiru tayi ta sake
yin likimo kamar mai baccin gaske,sai kawai ya qyaleta ya kashe qwan ya sake komawa
inda ya taso din,kusan bacci barawo ne kawai ya fauci idanuwan kowannansu.

       Tana motsawa ya farka,sai ta tsaya sak sai data ga bai sake motsawa ba,yana
kallonta ta shige bandaki,pad din jikinta ta cire ta sauya wata bayan tayi tsarki
da ruwan dumi,sannan ta wanke bakinta ta daura alwala ta dawo cikin dakin,gadon ta
sake komawa,saidai wannan karom maimakon ta kwanta sai ta zauna sosai ta jingina da
fuskar gadon idanunta alumshe tana karanta azkar,ta riga data saba koda tana al'ada
ne sai tayi wannan alwalar sannan ta karanta addu'o'inta,wannan na daya daga cikin
sirrin nasararta na kubcewa kamuwar sihiri a jikinta.

       A hankali ya miqe ganin ana gab da sallame sallar asubahin ya nufi qofa ya
fice a dakin,kai tsaye ya sake nufar saman,ya sanya muqulli ya bude dakin,kallo
daya zaka yiwa dakin ka rabbatarwa kanka an masa barna ba kadan ba,don kusan duk
wani abu da zai iya fasuwa an sauya mishi kamanni,a hankali yake takawa saboda
kwalaben dake dakin dai dai ko ina,wanda idan baka kula ba kana iya takata,zaune
take dirshan a can lungun gadon ta hade kanta da gwiwa da alama a haka ta
kwana,baki daya gashin dokin dake kanta ya wargatse kai kace anyi barin shinkafa
bisa kwalta,bakin gadon ya qarasa ya zura takalman da yake amfani da su idan yana
cikin bedroom ya nufi toilet,a bakin toilet din ya cire wannan ya saka na shiga
bandaki ya murda qofar ya shige,wanda warar bude qofar shi ya farkar da ita daga
baccin da ya saceta,da hanzari ta duro daga gadon wanda hakan yayi sanadiyyar
yankewarta da kwalbar dake tsakar dakin,bata damu ba ta isa bakin toilet din ta
tsaya yana kiran fitowarsa,wanda badon shakkar kada ya aikata mata wani mummunan
abu ba afkawa kawai zatayi.

       Ruwa ya hada mai dumi yayi wanka sannan ya daura alwala,ya zira rigar towel
ta wanka ya fito,bai kula da ita ba har sai data ce
"Almustapha!" Wani kallo ya juyo ya watsa mata wanda ya sanya ta nemi iskancin data
tsara yi masa ta rasa,bai sake waiwayarta ba sai ya wuce ma'ajiyar kayansa ya
bude,bin bayansa tayi ta tsaya tana qoqarin bawa kanta qwarin gwiwar yi masa wata
tijarar,fidda jallabiya ruwan madara yayi ya sanya da hular tashi ka fiya naci
bayan ya feshe jikinsa da turare,sannan ya dauki darduma yana niyyar wucewa,gabansa
ta sha cikin gunjin kuka
"Almustapha ni zaka wulaqanta?,wallahi wallahi nafi qarfin wulaqancin namiji,kuma
wallahi yau sai na tashin hankalin kowa a gidan nan"hannu ya sanya janyeta gefe
guda ya wuve,don ya tabbata matuqar yaci gaba da saurarenta hannunshi zai kai ga
tumurmusata cikin fasassun kwalaben dake dakin.

      A guje ta fito daga bangaren nasu ba tare data damu da suturar dake jikinta
ba ko ciwukan data ji ba,kai tsaye bangaren baabaa ta nufa wanda gab da zata shiga
suka kusa karo,da sauri ya ja da baya a tsorace yana ambatar
"Subhanallahi waye haka?" Kuka ta saki iya qarfinta wanda duk mutumin dake daura da
su zai iya jiyota
"Baabaa kun jawo min masifa da bala'i ina zaman zamana,me nayi muku haka kuka
bibiyeni da irin wannan sharrin?" Sam bai ma fuskanci me take fadi ba,don sai da ya
gyara gilashin idanunsa sosai ya iya gane wace,duk da hasken ya fara gauraye
garin,kasancewar babu wanda yasan da dawowar tata
"Wuce ciki muje kada ki tara jama'a da sassafen nan" cewar baaban yana mai juyawa
zuwa ciki lura da irin shigar dake jikinta,ba zaya so ma'aikatan gidan maza su fito
su ganta haka ba,dole ta bi bayansa tana jin kamar ta danna masa ashar,dole tabi a
sannu don ta sha kansa ya sanya mustapha ya saki wannan auren.

      Ummee na tsaye falon tana kintsa shi kasancewar su ke masa gyaran da


kansu,sanye take da doguwar riga da hijabinta wanda sallah ta idar ta fito falon
"Bata hijabi kilishi ta sanya" cewar baabaa yana wuce bedroom dinsa,waiwayowa tayi
cikin mamaki tana duban su'ad,mamakin irin ciwukan dake jikin su'ad din wanda duka
kusan yanka ne,itama idanun su'ad din qyar cikin nata,wata tsanar ummen take
ji,tana jin laifinta ma yafi na baabaan yawa,tunda uwarta ta gaya mata tun usuli
ummeen dama bata qaunarta,bata furta komai ba kamar yadda su'ad din bata ce ba ta
juya daki ta fiddo hijabin ta kawo mata,kamar wadda aka bawa kashi haka ta sanya
hannu ta amsa,bata tunanin kaf rayuwarta ta taba sanya hijabi,amma ya zata yi da
wannam tsohon dole ta saka don cikar burinta,yanayinta kawai da ummee ta gani ya
sanya ta sake tsare gida taci gaba da aikace aikacenta,ta tabbatar akwai wata a
qasa,don dama can macace da bata daukar raini a hakan baabaan ya fito.

       Cikin sheshsheqar kuka bayan ya sake tambayarta ta soma magana


"Yanzu an kyauta min kenan baabaa an yimin adalci,haka akeyi bada sani na ko yarda
ta ba kawai a yimin kishiya(nace hmmmm ko ta dauka a america take)?" Murmushi ya
dan sake kafin yace
"Banda abinki su'ad ai ita kishiya lokaci ce,idan lokacinta yayi sai tazo ko ka
yarda ko baka yarda ba,zancan sani kuma mai gidanki shine a haqqu da ya sanar da
ke"
"Amma ai bakinku daya shi yasa shima bai gaya min ba,gaskiya baabaa ni dai idan ana
son zaman lafiya tofa a raba auren nan,ka duba jikina baki daya daga jiya zuwa
yau,nan gaba abun sai yafi haka" a nutse baabaa ya soma yi mata bayani da kwantar
mata da hankali tare da bata kyawawan misalai na kishiyoyin dake zaune lafiya,ciki
kuwa harda su ummee,ga zatonshi tana saurarenshi ne amma kafin ya kai qarshe sai
kawai ta saki ihun kuka,miqewa ummee tayi tana tabe baki sabida baabaa ya hanata
magana,ficewa tayi don ba zata iya ganin wannan iskancin ba,itama miqewar tayi
"Wallahi ni bazan zauna da shi ba" ta fada tana yage hijabin jikinta ta wurgar ta
fice,miqewa baabaan yayi cikin nutsuwa ya taka a hankali yabi bayanta zuwa sashen
nasu,karo na farko da  ya soma zuwa sashen.

         Yanayin tafiyar tasu ba daya ba,hakan ya sanya ya cimmata a falo sanda


take yunqurin haurawa sama,kiran sunanta yayi tare da bata umarnin tazo ta samu
waje ta zauna,kwarjini yayi mata amma da niyyarta ko 'yar harara ta banka masa,sai
ta kasa haka ta dawo ta zauna din tana rusa kuka.

       A hankali cikin nutsuwa ta bude qofar dakin nata ta fito,gama tilawarta


kenan tana rufe alqur'anin da niyyar sake kashingida kasancewar lokacin bakwai na
safe tayi sai taji kamar muryan baabaan,fuskarta qunshe da murmushi kunya da
girmamawa ta qaraso inda yake tsaye,ta rusuna har qasa tana gaidashi,shi din ma
fuskarsa sake take,farinciki na ratsashi ya amsa gaisuwan nata
"Yaya kwanan baqunta?" Ya tambayeta,kunya ta kamata ta sadda kanta qasa
"Maza kiramin almustapha" cewar baabaa,miqewa tayi cikin ranta tana taraddadin inda
zata nufa,shahada kawai tayi ta nufi saman yayin da su'ad ta bita da kallo mai
dauke da harara zuciyarta na zugi
"Banza kawai 'yar qauye" take ambatan hakan cikin zuciyarta,fata take barazanarta
ta kafu cikin zukatansu,addu'a take Allah yasa almustaphan na saukowa baabaa ya
sanyashi ya sallameta ta huta.

       Idanu ta shiga rarrabawa tsakanin qofofin,ta tsaida idonta kan qofar da tafi
kowacce fadi cikin qofofin dakunan dake saman,nan ta nufa ta sanya hannunta cikin
fargaba da runtse ido ta tura qofar,tashin farko ta taka daya daga cikin kwalaben
dake dakin,zafin ya ratsata har qwaqwalwarta
"Wash" ta furta wanda hakan yayi sanadiyyar dago da kanshi daga kallon dan qaramin
qur'anin dake hannunshi,wanda tun bayan daya kammala sallar asubah yake tilawa duk
don nemawa kanshi sauqin zugi da radadin da zuciyarsa keyi,babu shakka sai ya
hukunta su'ad din hukunci mafi tsanani don gayara mata zamanta,ba'a taba nuna masa
raini irin wannan ba,ya fuskanci ya sakar mata mara ne da yawa,bai fuskanci illar
sakar mata din ua yayi ba kamar yadda su hamza ke nusasheshi ba sai yanzu,to ba
zaya lamunci wannan iskancin ba,idan taga zata iya zama bisa doka da tsarinsa ta
zauna,idan kuma ba zata iya ba tana iya yanke duk hukuncin da take so,amma tilas
idan tana son zama da shi tabi dokarsa,idanunshi ya maida kan qafarta data dage
sannan ya sake maidawa kan fuskarta,yaso ya share sabida yana ganin duk sune silar
damuwarsa cikin satin musamman tsakanin daren jiya zuwa yau,sai kuma ya gaza
daurewa kasancewarsa mutum mai tausayi,uwa uba kuma kulawar data bashi daren jiya
har yau tana yawo tsakanin idanunshi
"Tsaya a nan" ya fada yana ajjiye alqur'anin hannun nashi,a hankali ya tako zuwa
inda take tsaye ya duqa,yana son kama qafar saidai ya rasa ta inda zaya fara,yayin
da ta runtse ido sabida zafin da take ji,a hankali ya sanya hannun shi dai fai idon
sahun ta,ya sanya yatsunsa uku ya zaro ragowar kwalbar ya cillar gefe,mitsa qafar
tayi da alama taji zafin haka,a hankali ya saki qafar sannan ya miqe tsaye,wanda
hakan ya zamanto suna tsaye dab da juna,idamunsu suka hadu da sauri ta janye
idanunta tana ja da baya saboda yadda taga yayi dab da ita,caraf taji ya kama
hannunta cikin daga sauti yace
"Kula!" Ta dan tsorata,ta waiwaya baya sai taga madubi ne fasashshe dab da qafar
tata saura kadan ta taka,hannun ya saki tayi qoqari tsayawa daidai
"Baabaa yana kiranka,yana jiranka a qasa" idanuwanta na qasa bashi take duba ba,sai
ya gewayeta zai fice,har ya murda qofar cikin sanyin murya tace
"Ya hannun naka?" Waiwayowa yayi cikin sa suka sake hada idamu,wannan karon shi ya
fara kauda kanshi,a gajarce yace
"Alhamdulillah",ya ambata yana qarasa ficewa daga dakin,maida idanunta tayi cikin
dakin,mamaki ya kamata na ganin yadda dakin ya zama kamar wata bola ta
gilasai,komawa tayi ta lalubi tsintsiya da paka ta soma tattare kwalaban cikin taka
tsantsan da tsantseni.
Cikin lokaci qanqanin ta kwashe duka kwalaban tsakar dakin wanda ta
gani,ta zuba cikin wani dan kyakkyawan kondon shara dake bayan qofa,ta dago kenan
aka banko qofar wanda hakan ya sanya goshinta bugewa duk da bata wani buge sosai ba
amma taji zafi,dafe wajen tayi tana dubanshi,ko baka sanshi ba kana duban fuskarshi
kasan ya kai qarshe wajen fushi da bacin rai,su'ad ce biye da shi wadda dukkan
hudubar da baabaan yayi musu ta bayan kunne tabi,wanda badon tsoro da tsinin idon
almustapha ba saita gaggaya masa magana,biye take da shi tana ambatar sunanshi
wanda ya wuce kai tsaye zuwa ma'ajiyar kayanshi ya fidda suit ash and pink ya
ajjiye yana lalubar tie din da zai daura,bayanshi ta tsaya cikin kuka da masifa
tace
" wallahi almustapha sai na tafi ko baka so,ba kuma zaka sake gani na ba"a wani
fusace ya waiwayo yana mata kallon banza,cikin masifa tamkar wanda zai fidda
garwashin wuta daga bakinsa yace
"Wa ya riqe qafafunki?,kina mafarkin ni mustapha zan tsaidaki na hanaki
tafiya?,idan kinso kifi iska ko guguwa gudu,amma ina son kisan abu daya,ni muhammad
almustapha kada ki damo zaton cewa zan biyo sahunki,kada ki soma mafarkin zan taka
qafata muhallinku da sunan biko,zaki gane cewa ni din cikakken dan halak
ne,jinin......." Da hanzari ta ajjiye fakar da tsintsiyar ta fice zuwa falon,don
bata da hurumin sauraran wannan case din,yana kammala fadin haka ya ci gaba da
abinda yakeyi,cikin zafi zafi ya soma shiryawa,juyawa tayi da wani irin sauri ta
fice tana sakin kuka,bata taba zaton cewa ita din ba kowa bace bata kai matsayin
kowa ba wajen almustaphan sai yau,ta tabbatarwa kanta sai tayi nisan da zai mance
wace su'ad,ta hakanne kadai take ganin zata iya hukuntashi,yadda idanunta suka rufe
ya sanya bata kula sam da sumayya ba har ta sauka qasan a gurguje tana kuka.

A gaggauce ya fito daga cikin dakim zuwa falon,jeat da shi ba qaramin kyau
shigar tayi masa ba,saidai zuciyarsa a hargitse take sabanin yadda shigarshi take a
tsare,inda take din ya qaraso a gaggauce,hannunshi ya sanya ya daga nata hannun
wanda take dafe da goshinta saboda dan zugi zugin da yake maga,kalla yayi sannan ya
saki hannun nata,hannunshi ya zura aljihunsa ya fiddo takarda da kudi ya ajjiye
mata yayi gaba yana cewa
"Kada ki damu da cewa sai kin gyara dakin,ga number nan da zaki kira wanda zai kawo
miki dukan abinda kike buqata,if kinason kiyi breakfast a wani waje ki kira duka
za'a kaiki" ya qarashe maganar yana ficewa yayin data bishi da kallo,cikin qanqanim
lokaci ta fuskanci tabbas akwai wata hargitsatstsiyar rayuwa da dangantaka cikin
duniyarshi,har ga Allah taji tausayinshi ya tsarga mata,ta jima kafin ta miqa
hannunta ta dauki takardar,rubutu ne a tsare wanda kana kallo kasan gwanin iya
rubutu ne ya tsarashi sabanin rubutun likitoci da mafi yawa bai da kyau,ajjiye
takardar tayi saman kudin ba tare data damu taga ko nawa bane,dakin ta sake komawa
cikin nutsuwa ta kintsa komai ta goge ko ina,cikin qanqanin lokaci ya dawo
hayyacinsa,sai rashin kayan qawa kawai da yayi.

Qarfe goma saura ra sauko,falon babu kowa,saidai tana iya jiyo motsi mai
qarfi wanda yake tabbatar mata daga sashen su'ad ne,dakinta ta koma tayi wanka ta
shirya cikin dinkin atamfa riga da zani plain,mai powder lipstic su kadai ta
buqata,sannan ta feshe jikinta da turare,mayafi ta samu wadatacce ta yafa saman
kanta wanda ya dace da shigarta ta fito matar bahaushe zam,plat din takalmi tayi
amfani da shi sannan ta rufe dakin ta fice baki daga sashen.

Bangaren ummee ta nufa kai tsaye,tana gab da zata shiga ta jiyoshi


"Matar yayanmu" waiwayowa tayi fuskarta qunshe da murmushi,mahmoud ne shima dariya
yake ya qaraso inda take
"Allah ya taimaki matar yaya,an tashi lpy,ni qi bansan da isowarku da gurinku zanci
abincin dare" dariya yaso bata,wanne gu zaici abinci,gidan da tunda suka shigoshi
zuwa yau babu cikakken nutsuwa da kwanciyar hankali,koshi mai gidan bata tsammani
yasanya wani abu cikinsa daga jiya zuwa yau din,tare suka jera suka taka zuwa ciki
tana amsa masa yana zolayarta.

Ummeen na zaune a falon tana karyawa,a hankali ta qarasa gabanta ta zube tana
kwasar gaisuwa,ajjiye cup din ummen tayi tana dubanta,lokaci guda yarinyar ta soma
burgeta,tana hango tsantsar nutsuwa hankali da tarbiyya irin na diyan bahaushen
asali tattare da ita,zata iya cewa kaf DANGANTAKAR da suka taba da su'ad bata taba
gani ta ko russuna ba wajen gaida daya daga cikinsu,gaisuwa take musu irin ta
turawa,a tausashe cikin qauna ummeen ta masa kafin tace
"Na aika a kai muku abun kari,su kuma gyara sashen halan kunyi sabani ne"
"Eh ummi,amma na kammala gyaran sashen ma"
"Masha Allah" ummin ta fada cikin farinciki gane da sauyin da ya fara samuwa shiru
ya biyo baya saboda ficewar mahmoud bayan ya gama tsokane tsokanenshi
"Kije ku gaisa da maamaa ko,idan kun gama ki hawo sama ina so muyi magana" a
ladabce ta amsa mata kana ta miqe a nutse ta fice.

Bata jima wajen anty maman ba ta dawo,a darare ta haura saman,ta tura
qofar dakin ta shiga bayan ta nemi izini wajen ummeen tayi mata,nuni tayi mata da
gefanta inda take zaune gefan gado,a kunyace sannan a darare ta zauna,hannayenta
baki daya ummee ta kamo cikin nata
"Ki saki jikinki amiran umman khalipha,ki daukeni kamar mamanki kamar yadda na
daukeki tamkar tawa amiran" kai ta gyada alamun to
"Ina fata jiyan kin min alfarmar dana roqa wajenki ko?" Ta jefo mata tambayar,nauyi
ya saukar mata,ta yayq zata gaya mata baici abincin ba sabida abinda ya faru a
sashen nasu?sai data gama karantarta sannan tace
"Kada ki damu,na tabbata jiya akwai abinda ya faru mara dadi a bangarenku,tunda yau
naga ya fice ba tare da yazi gurina ba,yakan yi hakanne matuqar akwai matsala,baya
son yazo naga damuwa kan fuskarshi bare hakan ya shafi tawa walwalar......sumayya"
"Na'am ummee" ta amsa kanta a qasa
"Ta iya yiwuwa baki son almustapha,ta iya yiwuwa bai miki ba,ni da baabaanshi duka
shaidane biyayya ce ta hadaku kuke zaune,ban sani ba ko zan iya neman wata alfarma
wajenki"
"Ummee ki fadi ko meye,in sha Allah ni mai biyayya ce a gareki" ajiyar zuciya ta
saki
"Sumayya,ina son don Allah don annabi ki dauka min alqwarin bawa almustapha dukkan
wata kulawa da macen qwarai ke baiwa mijinta,ki taimaka ki zama sikar dawowar
walwala da jim dadinsa,rashin kyakkyawar zamantakewar auren mustapha ta jima tana
cimin rai,ba tonon asiri ba sam almustapha baisan dadin aure ba,bashi da abun fada
game da aure tsawon shekarun daya kwashe,yana da buqatar samun wata mace a
gefansa,macen data kasance ba uwa bace,macen da zata karbi sunan abokiyar rayuwa
mai tallafar damuwa farinciki nasara dama asara,macen da zqi jingina da ita ya
sauke damuwarsa,macan da zata iya daukar role na mahaifiya a bigiren da mahaifiyar
tayi nisa ko babu ita,macen da zata kasance ko yaushe daura da shi,zaki iya zama
dukkan wadan nan abubuwa a rayuwar mustapha?,zaki iya min wannan alfarmar wadda ni
ban isa na yiwa rayuwar tasa ba?,zaki taimaka wajen gyaran rayuwarshi kamar yadda
baabaa ya taba roqa daga gareki?" Nauyi kunya da tausayin ummeen suka
dabaibayeta,babu shakka kowacce uwa tana qaunar danta,tana buri da fatan ingantuwar
rayuwarsa,don me ba zata yiwa wadan nan mutane masu karamcin wannan karamcin ba?
"Nayi miki ummee nayi in sha Allah,saidai ki yimin afuwa aduk sanda aka samu gazawa
kan hakan" madaukakin farinciki ya kama zuciyar ummeen,lallausan murmushi shinfide
kan fuskarta tace
"Ina roqon ubangiji ya albarakaci gabaki da bayanki,damaki da hagunki,samanki da
qasanki,ya faranta miki yadda kika saka farinciki a zuciyata,kike kuma da burin
sakawa a nan gaba cikin ruhin daana,ba shakka bana zaton za'a samu kasawa,zan tsaya
miki sumayya da dukkan tsayawa wadda ta dace suruka tayi cikin rayuwar
surukuwarta,na gaya miki waye mijinki almistapha?,me ye tsarin rayuwarsa?,me yafi
so me kuma yafi qi?" Kunya ta dabaibaye sumayya,tayi qas da kanta tana
murmushi,haqiqa bata taba cin karo da uwar miji ba a tarihin rayuwar aurenta irin
ummen
"Daina kunyata,ni uwace amira,ni da nake tsammatar zuwanki gareni neman shawara
idan abu ya shige miki duhu"murmushi ta sake saki kawai ba tare da tace komai ba,a
hankalu ta dinga gaya mata ra'a yoyin almustaphan,wasu su bata mamaki,wasu taji
sunyi mata tsauri,sannan ta rufe da cewa
"ina fata zaki rufe tarihin kaiwa mijinku abinci a duk sanda yake qasar nan,kamar
yadda duk lokacin da adam ke gari babu wanda ke aikawa da abinci sashinsa"
"In sha Allah ummee"
"Da kyau,saiki fara daga yau,duk da nasan cewa mawuyacine yadda ranshi ke bacan nan
idan bai tsiri komawa dubai ba a gobe,a duk sanda hakan ta hadashi da ita yakan
dauki wannan mataki me don ragewa kansa bacin rai,saboda bashi da wani abu da zai
iya kawar masa da wannan bacin rai a ganinsa sai nisantar inda ran mashi ya
baci,tun yana qarami haka yake,rashin tsayyar mace kusa da shi ya zame masa
al'ada,ina kuma fatan nan da lokaci kadan zaki maida wannan al'adar tasa ta zama
tarihi,kada ki damu,sannan kada ki hanashi,hakan ma wata dama ce da zaki sake bitar
halayensa da shirya yadda zaki bullo"
"To ummee"
"Allah yayi miki albarka" ranta qal take amsawa,tana jin cikim zuciya da gangar
jikinta wani muhimmin taimako da sadaukarwa zata yi,karo na biyu a rayuwarta tun
bayan barinta gidan lukman
(Gareku iyayenmu mata,wallahi na qaramin lamari banr roqawa yaronki mace ta gari
cikin addu'arki tun yana qaraminsa,MACEN JARABA ba qaramin hatsari bace cikin
rayuwar d'aa namiji,babu babban dacewa da jin dadin rayuwa ga namiji irin samun
MACE TA GARI,manzan Allah S A W yana cewa mafi jin dadin duniya shine mace ta
gari,rayuwarshi zata iya tarwatsewa ya rasa walwala har ya koma ga Allah a dalilin
rashin mace ta gari,Allah kasa mu dace,ka hada 'ya'yanmu,'yan uwanmu,iyayenmu
qannenmu yayyenmu mazajenmu da mata na gari).

Kusan yadda ta dawo qasar bada sanin kowa ba a gidan haka ta hada kayanta ta
nufi airphort da zummar komawa america,tana jin wannan karo duk son da takewa
muhammad almustapha zata yakiceshi gefe ta hukuntashi,ta azabtar da zuciyarsa ta
hanyar yin nesa da shi da hana shi ganinta,sai ta rama ninkin wulaqancin da yayi
mata.

Wannan kenan.

*mrs muhammad ce*👑

✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)
7⃣9⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

*Allah S W T yana cewa*

*RANAR DA WASU FUSKOKI ZASUYI HASKE,WASU FUSKOKI KUMA SUYI BAQI(RANAR QIYAMA)*

___________________________________

         sai la'asar sannan sumayyan ta koma bangarenta,sosai taji dadin zama


wajen,sunyi hira mai muhimmanci da ummee,wanda tun tana jin kunya da d'ari d'ari
har ta soma sakin jiki,ta sake qwarai cikin ma'aikatan gidan,wucewa tayi bangarenta
tana tunanin me zata tanadar masa,kasancewar baison cin abun mai nauyi da
daddare,yayin da itama ummee ta shiga tata sabgar tana tunanin yadda zata bullowa
mustaphan matuqar ya tada maganar tafiya dubai,wanda tasan mawuyacine bai ambaceta
ba.

       Qarfe takwas na dare da mintuna ashirin ya tako cikin falon wanda babu
motsin kowa sai na na'urori da kuma hasken qwayaye,samanshi ya nufa kai tsaye yana
furzar da hucin iska daga bakinsa,shi daya yake tuno gamonsa da su'ad lamarin na
sake bata ranshi,ya tabbatar da cewa ta tafin kamar yadda ta fadi,hakanan shima
yana kan nashi qudurin na baiga abinda zai sanya shi nemanta ba koda zasu shekara
dubu a haka,turus ya danyi yana mamakin yadda dakin ya dawo hayyacinshi bayan yasan
me gayaran dakinshi baya nan,don bai gaya mishi zuwanshi abuja ba,da yake idan ba
kowa a sashin sallamarsu yake har sai randa suka zo,a hankali tamkar mai ciwon qafa
yake takawa yana duban yadda komai ya zama neat kamar ba'a yi waccar barnar ba
ciki,a haka har yaqarasa bakin gado ya soma fidda kayan jikinsa yana mamakin wanda
ya aikata hakan,bandaki ya shige yana niyyar hada ruwan wanka,tsayawa yayi cike da
shakku yana tunani ta ina aka samu ruwan wanka haka?,mai dumi da qamshi,cikin
kokwanto ya sanya hannunshi cikin ruwan,anya ba jinnu ke neman yi masa wasa da
hankali ba,take sha'awar yin wankan ta sake kamashi,saboda ruwan yayi masa dai dai
irin yadda yake so,bai bata lokaci ba kuwa ya shige kwamin wankan abunshi,ya kwanta
luf a ciki gajiya na warwarewa daga jikinsa yana zaton anya ba ummee bace tayi masa
duka wannan hidiman,yasani cewa ita kadai duk duniya tafi kowa sanin abunda yake
so,saidai a iya sanshi ummen bata taba takowa sashen nasu ba,a hankali zuciyarsa ta
shiga masa tariyar awannin da suka shude dazu,sanda ya cimmata tana tattare
kwalaben dakin,anya ba ita tayi wannan aikin ba
"Ba ita bace,me zata iya wannan,bai tunanin tana da fikirar da zata iya duka wannan
aikin,ita dinma bata ma yi masa kwata kwata kalar masu kuzari a jikinsu da zasu iya
wannan aikin ba daga safe zuwa yanzu(nace lol saboda baka saba gani cikin gidanka
ba)" hannunshi ya daga ya kalla inda yankan yake yana kallo,har yanzu wajen jazur
yake abinka da farar fata,yayi mamakin yadda wajen ya kame haka da wuri,sannan
zugin ya ragu sosai,ya tuna yadda tayi masa treating hannun,bai taba dauka ana irin
hakan ba a gaske,yasan dai a fina finai hakan na faruwa,ko kuma ga matan turawa wa
mazajensu ko samarinsu,tunanin ya dauka ya ajiye gefe,yana da buqatar barin qasar
nan a  gobe ko zai samu nutsuwar zuciya,yana jin bai da wani abunyi a
cikinta,wannan tunanin ya sanyashi miqewa daga cikin ruwan wankan ba don ya gama
awannin da ya sabayi ciki ba,ya saba kunfa ya qarasa wanke jikinsa ya daura towel
ya fito.

       Bakin madubinsa ya tsaya da niyyar yin shafa,sai a sannan ya lura madubin


nashi ya koma babu komai a kai saboda haukar daya fuskanta a daren jiya,wani mugun
tsaki ya ja,yana sake jin zafinta da haushinta,tana kuma sake fice masa a ka,wani
dan abu ya danna gefan gadonsa ya janyo wata qaramar locker,take dukkan wasu kayan
shafe shafensa suka bayyana,ya kwasosu ya watsa saman madubin yana dauka daya da
daya yana amfani da kowanne a muhallinshi,bayan ya kammala ya fitar da qananun kaya
ya saka sanann ya sanya takalmi wanda ya dace da kayan.
       A nutse yake saukowa qasa,har yanzu falon shiru yake
"Me taci tun safe zuwa yanzu bayan lawal yace ba wanda yayi kiransa" yake rayawa
cikin ranshi,mutum ne mai qoqarin sauke haqqin da ya rataya wuyanshi,hakan ya sanya
ya taka a hankali ya isa cikin corridor da dakunanta suke,ya murde qofar ya
tura,tsaye take cikin nutsuwa saman abun sallah,sanye da yalwataccen farin hijabi
wanda ya saukar mata har saman qafafunta,hannayenta na hade saman qirjinta kanta a
sunkuye tana karatun sallah murya qasa qasa,sakin qofar yayi ya koma da baya
idanunsa a kanta kafin ya juya baki daya ya fice,idanunsa ya lumshe kana ya budesu
yana ficewa daga sashen ba tare da ya iya tuna komai ba.

     Ummeen na zaune gefan baabaan yana cin abincinsa,yayin da bangare guda kuma ya
bata dukkanin kunnuwanta yana saurarenta cikin gamsuwa,sai data kammala tsaf sannan
yace
"Wannam shawarar taki tayi dai dai,don nima abinda na yanke kenan cikin raina....."
Sallamarsa ita ta katse hirar tasu,baki dayansu idanuwansu na kanshi wanda hakan ya
tabbayar masa maganarshi suke,cike da girmamawa ya qaraso gurin,ya zauna a gabansu
kamar yadda suma suke zaune saman rugs din dake wajen ya lanqwashe qafafu
"Barkanku da warhaka" kusan lokaci guda suka amsa mishi,sama sama suka fara hira da
baabaa ummee na gefe tana kallonsu tare da karantar yanayinsa,tana hango irin yadda
mustaphan zai koma matuqar tsarinsu ya cimma gaci,mustphan irin mutanen nan ne da
basu iya so kadan ko qi kadan ba,hakanan idan abu ya fita a kanshi zaiyi wuya ya
kuma waiwayarsa
"Baka son abu mai nauyi at night,gashi naga kaman kana son tuwo...."
"Barshi baabaa.....matarshi tayi masa kalar abinda yafi wayo a gun" ummee ta tari
numfashin baabaa,waiwayowa yati fuskarsa qunshe da murmushi yana duban
almustapha,farinciki yaji,wato hakan na alamta fara samun sauyi kenan cikin rayuwar
mustaphan
"To kaji abinda ummenka tace,sai ka barmin abincin tsaffin mata na" kansa ya dan
sadda qasa yana sakin murmushi
"Baabaa,ina tunanin gobe in sha Allah nakeso na wuce dubai,na baro company kan
aiki,mun fara fidda sababbin design da wasu companies keso na sabuwar
shekara,wannan karon harda vails mukeso mu fidda" kai baba ke kadawa cike da
farinciki da kuma alfahari kan irin qwazon da Allah ya bawa almustaphan
"Masha Allah,Allah yayi albarka ya kuma taimaka,saidai ita mai dakin naka ai bata
da visan shiga dubai ko?" Addu'a ya soma cikin ranshi kada baban ya ballo masa ruwa
"Baba ai nan da nakeso ta zauna......"
"Ban yarda ba,ka daga tafiyarka sai jibi ko gata zuwa lokacin na sa an buga mata
visa,and then bana son zaman hotel,ina son zaman hotel ya qare maka,ka koma naka
gidan" kanshi a qasa yana dawurwura,da zai iya da ya nemi alfarma wajen
baaban,saidai bazai iya musu da shi ba
"Shikenan,za'ayi yadda kakeso din in sha Allah,amma baba gidan zai dauki a qalla
wata uku kafin ya zaunu,saboda akwai wearing na abubuwa da za'a yimishi,kasan komai
na qasarsu a tsare yake saida amincewar gwamnati zaka yi"
"Ba komai,sannan gobe ka zauna gida ka huta hakanan,ko don ciwon hannunka" baisan
me zai zauna yayi a gida ba,amma ko bazaiyi komai din ba babu musu tsakaninsa da
baba
"In sha Allah"
"Kira maman tawa ta kawo passport dinta idan yana kusa" rasa yadfa zaiyi yayi din
bashi da numberta,baiso kuma ya fada hakan ya bata ransu,iyaye ba wasa ba tuni
dukkaninsu suka fahimci hakan
"Ka amshi number wajen mamanka tunda sai an gaya maka abinda ya dace,tashi kaje ka
kirata" ba musu ya miqe yayi hanyar waje,da idanu suka rakashi,kowannansu zuciyarsa
cike da farinciki tare da cikakken alfahari da shi,mustapha na dabanne cikin
zuriyar gidan,tsananin biyayya da qaunar iyayensa na dabanne cikin zuciyarsa.

       Riga da skert ne a jikinta na atamfa wadanda suka zauna cas a jikinta,ta


rasa wanme mayen tela ne har ya iya fidda qirarta haka,ta tabbatar sharrin amira
ne,gashinta ta ware bayan ta gama feshe jikinta da turaren jiki da na gashi,dariya
ta subuce mata sanda take taje kan,tana kwatanta zata iya tunkarar mustapha kenan
zuciyarta ke nufi.

     Turo qofar da akayi shi ya sanyata juyowa da hanzari,tsaye yake a bakin qofar
hannunshi riqe da handle din qofar,janye idanunshi yayi daga cikin nata idon ya
maida kan gashinta wanda ya sauka har qasan kafadunta,baki ya tabe a zuciyarsa,wato
itama tana jona gashi irin wanda su'ad keyi kenan,wanda sunsha kai ruwa rana da shi
akan gashin dokin,duk sonshi da gashi bai son attachmen
"Ki fito ki sameni a falo tare da passport dinki,wannan abun kuma da kika qarawa
kanki ki tabbatar kinje an cire miki shi" ya nuna kanta da bakinshi,a hankali ta
daga hannunta ta dora saman kanta don taji me yake nufi,itakam idan banda gashinta
bata ji komai ba,bata fahimceshi ba bata kuma zurfafa tunani ba ta daure gashin
nata ta zari hijabi ta zura,sannan ta janyo jakar hannunta ta fiddk passport din
nata wanda dama tunda suka dawo daga uk yana ajjiye a ciki ta fito falon cike fal
da mamakin me zaiyi da passport dinta kuma?.

       A tsaye ta taddashi hannayensa cikin aljuhunshi,da idanuwa yayi mata nuni ta


wuce gaba,kanta a qasa tayi gaba ya bi bayanta,tamkar wanda aka sarqafe idanuwanshi
haka ya dinga bin duk wani takunta da kallo,tamkar wadda ke rangaji haka take
ajjiye takunta anutse,duk jin kan su'ad da jin ita din wata ce wajen iya gayu
maqale magana da tafiya bai taba ganin tayi irin wannan salon ba,ko don bai kallon
mata banda su'ad ne oho,shi a nashi tunanin ko wacce mace tana sane take nau'in
waccan tafiyar saboda tashi madam din kawai ya sani,baisan komai da ya shafi
shirgin mata ba,tsakaninshi da su ya duba su idan lalaura ta taso.

      "Wait" ya ambata sanda take gab da shiga sashen,ya qaraso a hankali ya


daidaita da ita sannan suka shiga,kamar ko wanne lokaci haka ta gaida baabaan,ya
miqa hannu ya karbi passport din nata
"Ki shirya in sha Allah zaku wuce dubai gun aikin mijinki,ina ga kamar hakan zaifi
ko?" Kanta sunkuye cikin fargana da gaduwar gaba tace
"Duk yadda kace baba yayi" murmushi ya saki don dama yasan ba matsala tattare da
ita,yana fatan hakan zai haifar da alaqa mai tsafta kyau da danqo a tsakaninsu,kai
yake gyadawa cikin farinciki ya sanya musu albarka kana ya sallamesu yace su wuce
sai da safe,tare suka sake jerowa,saidai suna zuwa gab da sashen ya ja da baya ya
koma ya yiwa kansa mazauni kan daya daga cikin kujerun hutawar daya qawata wajen da
su,daura da inda fanfunan nan suke,hannunsa ya sanya ya fidda wayarshi dake
burari,hamza ke kira,dora wayar saman tebur yana kallonta har ta qaraci kukanta ta
katse,sai da ya hada misscall wajen biyar sannan ya dakata,bai bi takansa ba,yana
ciki da shi,ji yake kamar shi ya masa bakin da ya bishi sanda zai taho daga
dubai,sai da ya mula don kansa sannan ya daga wayar ya kirashi,bai iya fushi da
hamzan amini ne na qwarai
"Maan,ina ka shiga ne inata kira,ko ana angonci mode" ya fada dariya na son subuce
masa
"Allah ya isa tsakanina da kai wallahi hamza shege mai mugun baki" dariyar da yake
son dannewa bata barshi ba sai data subuce,wanda har sai da mustaphan ya dage wayar
kadan daga kunnensa sabida dariyar da yake zabga mishi,tuni hamzan ya samu labarin
komai
"Me kuma nayi,sunnar ma'aiki na maka fatan sake rayawa fa kuma ta tabbata"
"Na rantse idonka idona sai na karkatar maka da baki,idan yaso tayi jinyarka da
kyau waccar 'yar kazar taka"
"Qarya kake wallahi abida ta wuce kaza a wajena giwa ce,kuma zaka bada bayani dalla
dalla duk sanda ka shiga hannu wallahi,gwara ka fara saita kanka tun yanzu,ni nasan
me nake aure shi yasa na sallamawa matan africa espicially na nijeria,nijerian ma
AREWA,they are special over wlh"
"Close your mouth malam...yaushe zaka koma,kayan dake warehouse sunyi qasa fa
sosai"
"Kai barni,haka kawai ina tsaka da shan amrcina,mun shigo abuja ni da madam dazu da
zahar,gobe ma in sha Allah da yammaci zamu kawo muku ziyara daga nan muga amarya"
"Ganin amarya ko gulma?" Ya fada yana datse kiran,dariya hamza ya dinga yi
abunshi,yq riga ya saba da dukka halayen mustphan,tex ya tura masa na musaddiq(daya
daga cikin abokanshi)na neman wayarshi bai samu ba,pls ya kira shi,tsaki ya
ja,yasan tsiya ce zasuyi mishi,don sarai yana da yaqinin hamza ya baza labarin wai
an masa auren dole,kamar yadda yake tsokanarshi kenan,kiran daya daga cikin MD na
kamfanonin da suke karbar riguna a wajensu ne ya shigo,nan ya jima wajen zaune suna
waya,wanda sai da suka bata tsahon awa biyu kafin suyi sallama.

  *******    ******    *******

     
       Qarfe hudu saura ya sauko daga saman cikin sassarfa wanda tunda gari ya waye
bai sauko ba din sai yanzu,sau uku tana hawa cikin fargaba tana dubashi sai ta
tadda yana bacci,hakan ya sanya ko breakfast data shirya masa su daukewa tayi bai
ci ba,tunda ta ganshi kwance tasan baida niyyar fita,hakan ya sanya ta quduri
aniyar shirya abincin rana,sam bata ma san da zuwan baqi gidan ba.

      Yana sanye da long sleeve t.shirt baqa mai dauke da logo din armani,slim fit 
jeans din jikinsa baqi ne shima,kamar yadda hight top sneakers din qafarshi yake
baqi,baki daya shigar saita haska farar fatarshi sosai kamar wani jinsin ba hausa
fulani ba,da sassarfa yake saukowa don bada oder na abinda za'a kawo ma su hamza
idan sunxo,ya saba,ta zame masa al'ada matuqar zaiyi baqi saidai ya siya musu abin
fitar kunya,masu aiki su shirya shi a gun cin abinci,yana step din qarshe wayarsa
ta dauki ruri,lambar hamzan ce
"Munfa iso,a zo a qaraso da mu" inji hamzan,wayar ya mayar aljihu yana furzar da
iska tare da shaqar daddadan qamshin abincin da yafi zaton kodai daya daga matan
adam tazo abuja ne?,ya taka a nutse ya fice zuwa parking space.

         Suna tsaye shida abida,wadda itace matarshi,matashiya mai matsakaicin


kyau,nutsuwa cikakkiyar tarbiyya da iya mu'amala,cikin shigarta ta bahaushiya zam
suna tsaye da hamzan ta dan jingina da mota saboda cikinta daya soma nauyi,kana
dubansu kasan akwai kyakkyawar DANGANATAKAR ZUCI data fili a tsakaninsu,a haka ya
iso ya taddasu,tana matuqar jin nauyin mustapha yana mata kwarjini,hakanan tana
girmamashi,saboda haka abayansu ta tsaya tana biye da su fuskarta washe da murmushi
tana duban yadda take wakana tsakanin hamza da almusphan.

       Baki dayansu suna shiga suka san akwai wani gagarumin sauyi dake shirin
faruwa a rayuwar mustaphan,duk da basu fiya zuwa gidanshin ba kasancewar ko kadan
su'adah bata mu'amala da matan abokanshi,a cewarta duka basu waye ba,ta raina
ajinsu,bata qawance da diyoyin africa masu duhun kai,idan kika ga tana harka dake
to matar wani hamshaqin ne wanda yake babban abokin kasuwancin kamfanin MM
abaya,mazauni kowanne ya yiwa kansa a inda ya dace hamza naci gaba da takalar
almustapha wanda ya daure gira acewarsa ya fita daga shirginsa,a mutunce abida ta
gaidashi sannan tace
"Amaryar fa?"
"Barshi my wife,rowa zai mana halan" bugu ya kai masa da qafa sannan ya miqe yana
tunanin inda zai samota,jin qarar kwanuka a kitchen ya sanyashi nufar can kai
tsaye,tsaye take tana goge sink bayan ta kammala girkin ta zuba komai cikin
kyakykyawan mazubi,hatta da kwanukan baki daya ta wankensu goge wajen kawai take.

       Atamfa ce a jikinta kasancewar tafi son sanyata,saidai baki daya dinkin na


falle biyu ne,tana mutuwar son atamfar sanda ta ganta,falle biyu ta rage agun
saidawar aka dinka mata,bata taba sanya kayan ba sai yau,hakan ya sanya dinkin ya
mata dam,eight pieces ne skert din ya fidda shape din qugunta qwarai,rigar kuwa
baki dayanta iya karta qasan cibiya,gashinta na fake tsakiyar kanta jelar na reto
gadon bayanta,bata daura dankwali ba kasancewar tasan cewa ita daya ce a gidan,tana
da yaqinin koda ya tashi baccin babu abinda zai kawoshi kitchen din,Allah Allah
take ta kammala girkin taje ta cire kayan saboda sun takura mata,saidai ta barwa
zainab ita zasu fi yiwa,tun jiya data ji labarin tafiyar take cikin fargaba,yaya
zaman zai kasance musu?,wannan shi take yawaita tambayar kanta.
       Safa(socks)din dake qafarsa ita ta hanata jin takunshi,idanuwansa na bisa
bayanta tana ta goge goge abinta ba tare da kawo komai cikin ranta ba,zaj iya cewa
bai taba ganin hips zaunannu jikin mace irin haka ba,da gaske matan africa sunfi
matan kowacce shiyya structure ta jiki?,ya taba jin haka daga bakin hamza sanda
yana kan ganiyar neman auren abida,wata kasala ta saukar masa sanda ta sake motsawa
kadan ta gyara tsaiwarta,wanda hakan ya sake fitar da shape dinta,idanunshi ya
dauke,sai ya tsaya cak yana tunanin yadda zai mata magana,kawai sai yaja ya tsaya
gami da jingina da bango hannunsa cikin aljihunsa yayi crossing qafafunshi tare da
maida idanunshi wani sashe daban,haka nan yaji yana son ya duba yaga ta gama,ta
gama goge wajen,kwanukan take gogewa da tsaftataccen towel na kitchen tana jerasu a
ma'ajiyarsu,dakin girkin na da tsaho da fadi hakan ya sanya zaiyi wuya kayi saurin
ganin wulqawar mutum,sai yaci gaba da kallonta jikinsa na mutuwa,karon farko da ya
taba ganinta a haka cikin rufin daki guda da 'yar qaramar tazarar dake tsakaninsu
cikin muhalli guda,idanunsa ya lumshe yana son sake yiwa kansa shamaki da kallon
nata,da hanzari ya tashi daga jikin ginin ganin bazai iya jira har ta ganshi ta
kanta ba,freezer ya nufa ya bude wanda qarar taba tan ya sanyata juyowa a razane
don tayi matuqar tsorata,hakan ya sanya plates din biyota suka fado suka tarwatse
saman tiles din kitchen din,inda Allah ya taqaita na plastic ne da robobi,yadda ta
tsoratan qwarai ya qawatar da shi,kamar wata qaramar yarinya,yana son mace mai
tsoro wanda har ya manta akwai wannan halayyar wajen diya mace,su'ad nada dakiya da
taurin zuciya irin ta wasu matan turawan,ba komai ke sanyata firgici ba tunda sun
saba ganin bindiga da sauran makamai a banza,ruwan ya maida ya tako a hankali zuwa
gabanta wanda taqin dake tsakaninsu bai da yawa,duqawa yayi ya soma tattare
kwanukan tana tsaye jinkine da kantar hannayenta dafe ita tana maida numfashi cikin
tsoro,ko bata fada ya tabbatar taji zafin yadda kwanukan suka zube mata saman
qafa,sqi da ya gama tattarawar sannan ya tuna da kwalbar data taka itama jiya,ba
zato taji ya daga qafar tata,ya sanya yatsanta guda daya yana shafa wajen data
yanka din,idonta ta runtse tsam,yayin da ya kai ya kawo a gurin wajen sau biyar,da
sauri ya saki qafar saboda tuna qafan wace a hannunshi da kuma wadanda ya bari a
falo,tsaki yaja yana jin haushin kansa me ya zaunar da shi,bai bata umarnin ta fito
ba kawai ya wuce,me ya kaishi tattare mata kwanuka bayan ita ta barar,me ye
damuwarsa da ciwonta
"Saboda itama ta nuna kulawa da naka ciwon" ya amince da amsar,mutum ne mai nuna
kulawa ga wanda ya kula da shi,miqewa yayi yaja da baya
"Me jiya na gaya miki game da wannan gashin dake kanki,bance ki cire ba?"ya tambaya
cikin dakakkiyar murya da tsare gida,kai ta girgiza ba tare data iya duban idonshi
ba saboda yadda yau yayi mata wani kwarjini
"ba saka nayi ba,nawa ne"hannu ya zura har qirjinsa yana gogar nata ya kama jelar
da niyyar fincika,saidai lushi santsi da taushinsa kadai ya bashi amsar mallakinta
ne tun kafin ya fincika din,da sauri ya saki saboda wani shock da yaji a
jikinsa,haushin kanshi ya kamashi,me zaisanya jikinsu ya dinga haduwa haka?,da
hanzari ya juya yana fadin
"kada ki bata musu lokaci"
"Amm,don Allah ka taimakamin da hijabi a daki?" Waiwayowar da yayi ya sanyata
sunkui da kai,kallo ya qare mata tun daga qafarya har kanta,yayin da ya dawo ya
tsaida idanunsa saman qirjinta wanda matsewar rigar ya takurasu suma,haka kawai
yaji ya gamsu dari bisa dari da dauko hijabin,baice komai ba ya fice.

       Yanayin qamshin dakin daban yake da saura,komai na kintse a muhallinsa,kan


gado ya hangi hijabin,saidai akwai littafi kan hijabin,hannu yasa ya dauki littafin
yana jujjuyashi,littafine dake qunashe da qananun hadisai guda d'ari saboda
hadda,maidashi yayi saman bedside drower din ya fito,daga bakin qofar ya cilla shi
ya fito.

      "Haba malam,tsakani da Allah ka kyauta,ka barmu ni da madam daga kiran amarya


saika tsaya yada manufa,ai ka bari mu baku waje ko?" Inji hamza dake fadi qasa qasa
yadda abida ba zata ji ba,yatsunshi ya kama wanda saida hamzan yaji a jikinsa
sannan ya sakar masa,bai damu ba tunda yasan shi ya tsokano.
       A nutse take takowa hannunta dauke da farantin wanda kansa ke dauke da
lemukan kwali da kofuna sai kuma ruwa,sallama tayi musu hamza da abidan suka
amsa,abida ta miqe ta rage mata wasu sumayyan na murmushi tace
"Kai,dama kin barshi"
"Babu komai,ai sunyi miki yawa"
"Ai kuwa da kin qyaleta,aikin wannan mutumin ne" inji hamza da bai daddara ba,da
idanu mustapha yayi masa gargadi sannan ya sake tsare wuri.

       Bata zauna ba sai data jera dukkan wani abun ci da nasha wajen,lamo yayi
cikin kujera ya wani lafe yana binta da kallo,abun yayi matuqar burgeshi,irin
abinda yake gani gidan wasunsa kamar su hamza yau gashi gidansa,sai yake ji wani
izza da girma na shigarshi
"Kai nifa abincin zan fara ci gaskiya hirar nan bata yiwuwa,my abida
bismillah,sumayya sai kiji kema da angonki" kunya ta kama sumayyan sai ta saki
murmushi tana sadda kanta,ya dan saci kallonta wanda zakayi tsammanin idanunshi a
lumshe suke,tuni abida ta qarasa kusa da shi,wanda hakan ya tilastata miqewa,daura
kadan da shi ta qarasa,wanda tana iya jin qamshin turarenshi kamar yadda yake iya
shaqar humrarta,ta kiyaye tsarin cin abincinsa tsaf,qasa qasa gake dubanta yana
mamakin yadda har ta iya gane ra'ayinshi da qa'idarsa,duk da sam baijin zai iya
sanya komai a bakinsa,idanuwan hamza da abidan kawai ya sanyashi yayi shiru
"Barakallahu fiki" cewar hamza bayan ta gama zuba masa,kusan tare suka miqe sukayi
dakin sumayyan don su basu waje.

      Tuni hamza ya soma kaiwa cikinsa,ko ba'a fadi ba ya tabbatar ba'a qasa ta
tsinci qwarewarta wajen girki ba,gyara zamansa yayi duk da yadda qamshin ya buwayi
hancinsa,taba shi yayi
"Ya dai?,ko soyayya ta cika maka ciki?" Ya zolayeshi,miqewa yayi sosai ya
zauna,wanda yanayin zamanshi kadai ya alamtawa hamza magana zasuyi mai
muhimmanci,yana jin zuwa yanzu yana buqatar abikin shawara,wanda babu mutumin da
yasan cikinsa irin hamzan,kasancewarsa mutum mai yawan zurfin ciki
"Hamzah"ya kira sunanshi da gaske
"Na'am"
"Hamza,bana jin yarinyar nan ta dace da ni,bana jin zamanmu zai yiwu,hamza komai
namu ba iri daya bane,ban hangi abinda zai kawo dacewar zamanmu ba,amma na fuskanci
tana qarqashin goyon bayan baba,kasan yanzu haka ya matsa sai mun wuce dubai tare?"
"Ka manta hausawa sunce duk abinda babba ya hango yaro ko ya hau dala da gauron
dutse bazai hangoshi ba?,akwai wani abun qyamata guda daya tak daka gani tattare da
ita iya awannin da kuke tare?"
"Ta yaya zan gane?,bayan duka awananin da mukayin baifi ka qirgesu da yatsun
hannunka ba,kawai ban son raini hamza kai ka sani"
"Duka macen data samu cikakken tarbiyya daga gidansu ba zata taba raina duk wani
namiji da ya amsa sunan mijin aurenta ba,amma tunda haka ne kasan me yafi?" Kai
kawai ya kada
"nisantarta duka bazai daidaita komai ba,ka zauna da ita,ka mu'amalanceta kamar
mu'amalar yaya da qanwarsa,ta nan ne zaka karanceta,zaka gane halayyarta,,zaka dasa
mata girman da kake so ta gani naka(yayi dariya cikin zuciyarsa shi yasan kan
tsiyar shi yasa ya gaya masa haka)"shiru yayi ya koma ya lafe idanunsa a qulle yana
nazarin maganganun hamza.

        Cikin 'yan awanni suka saba sosai da abida,tana da kirki da son


jama'a,sunyi hira mai amfaji qwarai,wanda hakan ya sake sanyawa sumayya wasu
mafarke mafarke da hange mai tsaho kan zamantakewar gidanta.sai da sukayi sallar
magariba sannan suka wuce.

          Da daren ya shaida mata ta shirya da wuri gobe akwai inda zasu,bata san
ina zasun ba har sai data gansu garin kano,murna da farinciki kamar zara yi me?
kamar wadda ta shekara bata ga kowa ba,saidai bata samu ganin kowa ba,amma taga
abdallahnta,don wunu sukayi tare,ta tabbatar abdallah ya samu iyaye fiye da nashi
na asali,sauketa kawai yaayi suka wuce ahida driver,batasan ina yayi ba,bai shigo
gidan ba sai da yammaci da zasu tafi,a lokacinne ya shigo suka gaisa da malam da
mama,satar kallonshi take kawai,wato mutum me shi da yasan darajar iyaye koda ba
nashi bane,sallama ya yiwa malam kan zasu wuce dubai,addu'a sosai malam din yayi
musu.

      Cikin mota ta tsinci kanta tana kuka,a hankali ta dinga share hawayenta da
gefan hijabinta,ji take kamar idan ta tafi ba zata dawo ba,waiwayowa yayi ya dubeta
sai ya dauke kai yaci gaba da abinda yake,fata yake kada tayi mai sauti yadda zai
dameshi,to kukan ma baiyi tsaho can ba sabida yadda ta tilastawa kanta yin
haquri,tayi lamo tana tilawar nasihan mama.

        Duk da yadda ta gaji bata kwanta ba sai data gama shirya dukkanin
kayanta,haka kawai ta tsinci kanta da sauya yanayin kayanta baki daya,hijabi biyu
kawai ta dauka madaidaita saboda sallah,ita kanta batasan manufar yin hakan ba
batasan me yasa tayi haka ba,wanka tayi bata huta ba ta shiga kitchen,tana son
gabatar da duk abinda ummen ta sanar mata,tukunya ta dora bayan ta zuba ruwa,ta
duba inda suke ajiyar kayan hade haden shayin su tayi wani hadi na musamman wanda
ya bada qamshin shayin wata qasa,cikin qanqanin lokaci ta juye cikin cup mai plate
ta sake dorawa kan wani plate din tayi shahada ta haura sama,motsin ruwa data ji a
toilet ya sanyata ajjiyewa ta sauka qasa bayan taja qofar tana fatan ya sha kada ya
barshi kamar yadda yake barin sauran kayan abincin,tunda ya fito a bandakin ya
dinga neman inda yake jin wannan qamshin shayin,qamshin da ya san a dubai kadai
yake samunshi,sai da ya gama komai na kwanciya sannan ya qarasa gadon,a lokacin ya
lura da shi sanda yake qoqarin kashe fitilar gefan gado,a hankali ya sanya
hannunshi ya dauka,kamar wanda ke tsoron kurba haka yakai bakinsa ya
kurba,idonsanya lumshe na tsawon mintuna dadin shayin na ratsashi,sai ya jishi ya
koma qasar dubai,kadan kadan sai gashi ya tashi da cup din,saidai bai gamsar da shi
ba,hakan ya sanya ya soma qoqarin sauka daga gadon don ya samo qari.

       Da dan sassarfa ya sauko qasan ya nufi kitchen kai tsaye,babu komai cikin
tukunyar da alama kai da kai aka dafa,sai ya bude locker bayan ya kunna gas ya
maida tukunyar cike da karambani don bai taba yi ba,canke canken ganyayyakin ya
dinga yi,haka ya hadasu ya zuba suka tafasa ya juye,kurba daya yayi fatali da cup
din ya furzar da na bakinsa yana yamutsa fuska,tilas ya wanke bakinshi ya fice daga
kitchen din ya koma saman,zuciyarsa na son yasha amma baijin zai iya sanyata ta
sake mishi.

To masu karatu,ga Almustapha ga sumayya zuwa wata qasa,koya zaman zai kasance.

*SADAUKARWAR WANNAN SHAFIN GA ZAMA NA AMANA GROUP DAKE FACEBOOK,ina godiya da fatan
alkhairi ga dukkan wani member dake group din,haqiqa comment dinku na qayatar da
ni,Allah ya qara zumunci,LOVE YOU ALL*

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*


*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

8⃣0⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

Wannan page sadaukarwa ne ga

HUGUMA CONVERSATION GROUP

HUGUMA NOVELS GROUP

ZAUREN BIEBIE ISAH ZBI

MAMAN HANEEF NOVELS

MAMAN AYSHA NOVELS

INSPIRING STORIES

HASKE WRITERS FANS GROUP

KUNDIN HASKE GROUP

KUNDIN QADDARA NOVEL GROUP

DA KUMA IYAYEN GAYYAR

HASKE WRITERS ASSO

DA KUMA

FOLLOWERS DINA NA WATTPAD MUSAMMAN MASU KANKARO MUTUNCI(LOL) DA COMMENTS DINSU

ALLAH YA QARA ZUMUNCI,INA GANIN COMMENTS INA GODIYA,SOMETIMES ZAKUGA NA AMSA WASU
WASU BAN AMSA BA SABODA YAWAN MUTANEN,SAIDAI GASKIYA ALQALAMINA BAI IYA TSALLAKE
KYAWAWAN ADDU'O'INKU NA FATAN GAMAWA DA DUNIYA LAFIYA DA KUMA SAMUN ZURI'A
DAYYIBA,INA GODIYA.

___________________________________

Sha daya ne na safe,tana zaune cikin girmamawa a gaban baabaa,sanye da daya


daga cikin baqar abaya wadda aka yiwa adon fari,tun daga zare kama duwatsu,tayi
rolling da mayafinta wanda ya fidda shape din fuskarta da sirrin kyawunta,hill
shoes ta sanya fari qal da 'yar madaidaiciyar jaka wadda mariqinta bai wuce ka
saqala shi a gwiwar hannu ba,tsintsiyar hannunta daure take da farin agogo na fata
mai baqar fuska,qamshi jikinta ke fiddawa mai sanya nutsuwa da kwantar da
hankali,gama shirinta na tafiya kenan tayi burki a bangaren baban,nasiha baban yake
mata mai ratsa jiki,wadda tabi kowacce gaba ta jikinta,yana sake tunasar da ita
haqqin daya rataya a wuyanta,cike da gamsuwa cikin sanyin jiki ta soma yi masa
godiya,a daidai sanda uban tafiyar ya shigo,cikin shigarsa tako yaushe ta
suite,baiyi tsammanin zai tadda ta a nan ba,sallama yayi dai dai lokacin da baban
yake cewa
"Goge hawayen,duka abun bana kuka bane ai" ta gefan idanu ya kalleta,karon farko da
irin wannan shigar ta soma burgeshi,kwata kwata ba shigar su'ad bace wannan,bai
taba ganinta sanye da abaya ire iren wadan nan ba,a hankali ya kau da kanshi yana
maidawa kan baban,ya isa gabanshi nesa da ita ya duqa yana masa sallama,sanda ta
yunqura zata tashi don basu wuri baban ya dakatar da ita
"Almustapha ga amanar sumayya nan na danqa maka,kada ka cutar da ita don kana ganin
kunyi nesa da gida,kasan muhimmanci amana,ko ban gaya maka ba aure amana ce ta mace
da ake danqawa namiji,wanda duk kuma yaci amana Allah bazai qyaleshi ba,na tabbata
diyata bata da matsala,idan naga wata matsala to daga kaine,ka kuma kuka da kanka
don bazan taba daga maka qafa ko baka uziri ba,ki kiyaye" kowa amana dai amana duk
saboda ita?,abinda ummee ta gama gaya masa kenan yanzun daya fito,tana jaddada masa
cewa ko rama taga tayi to shi zata tuhuma
"Insha Allahu zan kiyaye,Allah ya qara girma,ya qara lafiya da nisan kwana"
"Ameen summa ameen,Allah yayi muku albarka"inji baban,sannan yaja musu addu'a suka
shafa.

Su biyu ne zaune bayan motan sai driver a maxauninshi,hawaye ya ziraro


mata sanda suke gifta gidan anty dije,ta tuno sallamarsu ta jiya,ita kanta antyn
wannan karan ta kasa daurewa sai da tayi qwalla,gefe tayi da kanta tana damqe
littafin da antyn ta bata wanda har yanzu bata kai ga budewa ba
"kowa amana yake bani,ni me yasa ba'a bada tawa amanar ba?"kunnuwanta suka jiyo
mata shi yana fada cikin mafi soyuwar sauti a wajenta,kamar zata juya kuma sai ta
fasa,taci gaba da barin kanta a inda yake,ya motsa bakinshi kamar zaice wani abu
sai kuma ya fasa ya ciro wayarsa dake ruri,yanayin yadda taji yayi sallamar kawai
tasan hamza ne,bisa dukkan alamu shima bai wuce wannan satin zaya koma,wayar bata
qare ba har suka isa airphort din wanda hakan ya sanya bai samu damar qarashe
maganar da zaiyi ba.

A baya take biye da shi cikin nutsuwa,yau airphort din ba laifi akwai
yawaitar jama'a,hakan bai rasa nasaba qila da yawan matafiya masu sauka da masu
tashi a safiyar yau din,sai taga ya fara rage saurinsa har ta cimmasa,da idanu yayi
mata nuni kan tayi gaba,wucewar tayi kamar yadda ya umarcetan suka ci gaba da
tafiya a hakan,idanunshi ne biye da ita duk inda ta taka qafarta tamkar mai
qididdige adadin takun nata,a jikinta takejin akwai idanuwa a kanta baya ga idanun
jama'ar dake kai kawo wajen,hakan shi ya sanyata ta fara jin rudewa,tun baya can
mutum ce da aka raineta cikin tsaftataccen yanayin da bata iya cudanya da
ajnabiyyanta ba,bata sakewa da kowa a lokacin idan ba malam ko yaya abubakar
ba,koda wani taro ne na dangin mama matuqar ya hada da maza kamar daurin aure da
sauransu bata sakewa,hakan na daya daga cikin dalilan da suka ja ko bikin amira da
qyar ra iya sakewa(gareku iyaye mata,wannan dabi'a ce mai kyau,ana son a dasawa
diya mace dabi'a ta rashin yarda da sakewa,dari dari da takatsantsan da duk wani
jinsin d'aa namiji,wannan dabi'ar na taimakawa qwarai da gaske wajen dakusar da
sharrin mai sharri cikin jinsin maza,misali masu baata yara da sauransu,ko da yayye
gareta ko qanne maza ki nuna mata yadda zata dinga kamewa a cikinsu,to balle wani
d'aa namijin a wajen,idan yayanta ne namiji ki nuna mata girmama shi zata dinga
yi,bawai su dinga wasu wasa don tana qanwarshi ba,ko zama a jikinsa kada ki yarda
ta yawaita yi don yana wanta,wannan dalili ne yasa ma'aiki yace mu rabawa yaranmu
maza da mata wajen kwanciya da zarar sun fara wayo,idan qannenta ne kuma ki koya
mata kama girmanta,bata shiga suyita wasu wasanni ba,koya mata sanya hijabi
kallabi,saka sutura mai rufe jiki,kada kiyi tunanin ai yarinya ce babu
komai,a'ah,ita rai dabi'antar da ita ake akan abu,ta yadda komai tsahon zamani zata
dawwama a kan wannan dabi'ar).

Ba tare data ankara ba taji ta harde tana yunqurin kaiwa qasa,cikin


matsanancin zafi ya tarota ta fada a qirjinsa idanunsu suka harde cikin na juna
"Sannu,da fata dai bakiji ciwo ba ko?" Cewar wata dattijuwa cikin mutanen dake kai
kawo a wajen ita samarin yaranta su uku
"Eh banji ba mama"
"To Allah ya taqaita"
"Amin na gode" ta fada cikin siririyar muryarta data ratsa kunnenshi,idanunshi ya
daga yaga yadda idanuwa sukayi caaa a kansu,hakan yasan baya rasa nasaba da
kasancewarshi sananne cikin fadin nijeria,wani abu yaji ya taba ranshi na yadda
dukka idanuwa ke kanta,haushin ta jawo musu kallo ne kokuwa meye ne oho,sai ya fasa
sakinta,ya jata sosai cikin qirjinsa ya rungumeta baki daya tamkar mai duba
qafartata
"Ki nutsu kada ki sake jawo mana idanuwan jama'a" ya fada cikin kunnenta yana
sabule jakar dake hannunta,jikinta taso janyewa,ya fuskanci hakan sai ya daga
lumsassun idanuwansa ya watsa mata su cikin salo na harara a fakaice,baki daya ta
qarasa gigicewa kamar yadda yakejin sauyin yanayi tattare da shi yana qoqarin
kokawa da feelings din,da da hali sakinta zaiyi saidai idan yayi hakan kan idanun
jama'a kamar ya tona sirrinsu ne,jikinta ya saki qirjinta na wata iriyar bugawa
sanda ya kewaye hannunshi a bayanta zuwa daya kafadar tata yaci gaba da tafiya da
ita jakarta na hannunshi,tsoro da firgici duka suka kamata,zuciyarta ta dinga
bugawa,yayin da gefe guda qamshinta ke neman buwayar hancinsa,nan da nan suka sake
zama abun kallo ba tare da sun ankara ba,abinka da irin yanayin tamu qasar
kenan,kanta na jingine a kafadarsa cikin kasala idanubta a qasa saboda kunya da
nauyin jama'a data dinga ji,dai dai sanda zasu wuce eesha ta fito,baki ta saki tana
dubansu,ya man ne wata?,tamkar taso kuma tasan fuskar,sam ba su'ad bace,kodai gaske
ne labarin da humaida ta gaya mata ta zaci tsabar hassada ce?,abinda ya barota daga
gida kano kenan ta taho abuja da safiyar nan tazo ta tabbatar,ko gida bata je ba
daga hostel direct sai airphort,don bata son taje gida ma a bata labari gwara ta
tabbatarwa idanuwanta,tunda ta samu labarin yana abujan,tuni ta zare sun glasses
din idanuwanta ta maidashi saman goshinta,sun riga sun wuce shingin bincike tilas
ta juya ta fice a sukwane jikinta na rawa,tana fatar samun mota da wuri don isa
gidan baba prof,bata jin zata iya yiwa ummee waya har ta jira driver yazo
daukanta,wace ce haka take tunanin ta mata shigar sauri?,wace take son sake sanya
nisa mai tsaho tsakaninta da muradin ranta?,ta tabbatar da cewa koma wace ba
qaramin kamu tarkonta yayi ba,tunda har cikin dumbin jama'a ya man da ko matarsa
yake dake mawa amma ya iya rungumarta cikin jikinsa hannunshi dauke da jakarta.

Wani zama ne sukayi cikin jirgi,tunda suka shiga wani babban yaron abokin
kasuwancinsa yayi masa magana taga ya sake tsare gida,mutum ne shi da baison
shishshigi,mu kuma kusan tamu al'adar kenan,sau tari wasu basa tashi yiwa mutum
magana ko kulashi sai sun ganshi tare da iyalinsa,to bare wannan yasan cewa su'ad
kadai ya sani,mai yiwuwa wannan yana masa kallon ko ya soma hutawa da 'yammata
kamar yadda su sukeyi,kujerunsu na jere da juna,hakanan ya sanya tafin hannunshi
cikin nata yana sake matsowa kusa da ita yana magana qasa qasa,idan daga nesa ne
zaka rantse shauqin soyayya ke yawo da su duka su biyun sararin samaniya,amma idan
a tsakanin kujerun nasu kake idan ka qware wajen iya gulma zaka ji yana fadin
"Banson kiyi komai sai nace kiyi,idan nace kiyi din kuma kiyi babu musu ko
tambaya,kibi a hankali" kai ta gyada zuciyarta na bugawa,laushi da taushin tafin
hannunshi kadai ke ratsata,yayin da shima ya sauke boyayyar ajiyar zuciya yana jin
wani dumi cikin tafin hannunta yana bin kowacce jijiya ta jikinsa.

Gulma ta hana mutumin da yaji ya ambata da bashir zama,ya taso daga tashi
kujerar ya nufosu,ya ganshi hakan ya sanya da sauri yace mata
"Kwantar da kanki a kafadata,bance ki dago ba har sai na gaya miki" idanunta ta
daga ta dubeshi,saidai ba itama yake kallo ba,yanq danne dannen waya ne da yake
qoqarin kashewa yaga tasowar bashir,a hankali ta dora kan nata saman
kafadarsa,dumin jikinsu ya soma gauraya,taja wani numfashi wanda ya zuqo dukkan
tattausan qamshin jikinsa,kana ta sauke numfashin a hankali tana lumshe ido qamshin
nayi mata dadi,gab da zai qaraso ya lura da yanayin almustaphan,ya sanshi
sarai,hakan ya sanya ya koma da baya,haushi ya cikashi,baison me ya hanashi zaman
VIP ba wannan karon,irin wannan shishshigin ne da takura baiso,shi yasa yake zama
can.

Jin baice mata komai ba ya sanya bata bude ido ko daga kanta ba,tayi lamo
tana sheqar daddadan qamshinsa,a hakan batasan sanda bacci yayi awon gaba da ita
ba,shi dinma ya sha'a fa,sai da jirgin ya lula zuwa sama yana niyyar gyara zamanshi
sannan ya tuna,juyawa yayi ya dubeta,yana iya jin yadda zuciyarta ke bugawa a
nutse,wanda hakan ya tabbatar masa bacci take,zai janye kafadarsa me ya tuna sai
kuma ya fasa,ya jingina da kujerarsa shima yana lumshe idanuwansa.

Cikin tsari da nutsuwa fasinjojin ke sauka daya bayan daya daga


jirgin,waiwayawa yayi yana kallonta,bata motsa ba bai kuma san ta yaya zai tayar da
ita ba,a hankali kamar wadda aka bawa umarni ta bude idonta,fes suja sarqe cikin
nashi,cikin hanzari ta daga kanta daga jikinshi tana jan mayafinta daya zame,baice
komai ba ya miqe ya soma takawa,itama miqewa tayi tana biye da shi,gab da
matattakalar ta lura babu jakarta
"Jakata" ta ambata qasa qasa,sai ya waiwayo yana dubanta da idanunshi,ya kafeta da
su kafin ya furta
"Ohhh,u mean naci gaba da yi miki dako?" Bata ce komai ba ta koma ta baya ta
dauko,zuwa lokacin har ya gama sauka yana farfajiyar a tsaye.

Motar dake mallakinsa ce tazo daga company daukarsu,lafiyayyar mota ce dake


da sit daban daban kusan hudu,sarai yaga bashir din,haka ya sanya shi saka hannu ya
bude mata motar,yana tsaye ta shiga dai dai sanda ya qaraso yana murmushin gulma
"Yallabai,ko zaku saukeni hanya?"
"Babu waje" ya fada cikin dakiya ya shige shima tare da rufe motan ya bawa drivan
umarni yaja suka tafi.

Tun daga hanya take kallo har suka isa qawataccen hotel din,wanda hotel ne
na isassu sai kaci ka tada kai kake iya zama cikinsa,hotel ne mai kyau da tsari,duk
wani mazaunin cikinsa da ya kama daki yana jinsa ne kamar a gidansa,saboda babu
ruwan wani da wani,hakanan babu abinda zaka buqata ka rasa,saidai tun a nan ta
fahimci bisa dukkan alamu akwai na matan da mazan dake kai kawo ciki masu wata
mu'amala ta daban,hakan baya rasa nasaba da yadda taga almustaphan na riqe da
hannunta har suka cimma dakinsu.

Komai a gyare yake neat a dakin,kasancewar ya bada sanarwar


dawowarshin,hannunta ya sake da sauri don dama Allah Allah yake su isa ya saki
hannun,tsaye take a gefe,baquwa zam tana dan kalle kalle,yayin da yake tsaye gaban
gado yana qoqarin sassauta tie dinsa,da alama daya daga cikin rigunan jikinsa yake
son ragewa,wayarshi dake saman gadon ta dauki ruri,sai data katse bayan ya gama
sassauta tie din sannan ya dauka yana dubawa,hannunshi daya riqe a qugunshi yana
takawa zuwa bakin window din hotel din,ya bude yana kallon harabar shi,magana yayi
wadda bata wuce ta minti daya ba taga ya dawo da hanzari ya maida safarshi da
takalminsa,ya maida tie dinsa ya matse,wayarshi kawai ya dauka da maqullin dakin
nasu ya fice da hanzari ya rufe qofar.
Ajiyar zuciya ta saki bayan ficewar tasa,wanne irin mutum ke shi da bai
hutawa rayuwarshi?,baki daya ko minti goma cikakke basuyi da shigowa dakin ba amma
har ya sake ficewa,ta yaya matarshi zata samu kulawar da take so?,Allah ma yaso ba
soyayyarshi cikin ranta bare hakan ya baqanta mata,ta fada cikin zuciyarta tana
daga kafadarta tare da yarfe hannaye.

Gefan tattausan gadon ta zauna tana duban dakin,falle daye ne dauke da


makeken gado,sai kujera doguwa guda daya da qananu guda biyu ajiye daga can wani
sashen daban,babbar ma'ajiyar zuba kayan sawa,madubi bedside da kuma qofar
toilet,daki ne mai matuqar fadi da yalwa,ta dauki lokaci zaune har sai data duba
taga lokacin sallar azahar yayi sannan ta miqe ta shiga toilet din kasancewar dazu
da asuba ta samu tsarki,bandaki ne mai tsari,komai neat yake,ko ina qamshi ya
kama,qamshin duka abinda yake mu'amala da shi,kama daga turare sabulu turaren gashi
da sauransu,sai data kammala sallar sannan ta janyo kayanta ta fiddosu daya bayan
daya ta fara jerawa ganin cewa babu abinda zata yi,akwai makekiyar t.v plasma dakin
saidai batayi sha'awar kunnawa ba bare ta debe mata kewa,bayan ta gama jera nata ta
janyo nashi,ta zuge a hankali,a jere kayan suke gwanin sha'awa suna fidda qamshi
mai sanyi,haka ta dinga fitar da su tana jerawa daga daya side din a tsare,komai ta
sanyashi a muhallinsa sannan ta sanya jakankunan nasu a wani bangare daban na sif
din,zuwa lokacin sallar la'asar yayi,ta soma jin yunwa,saidai babu komai a dakin na
ci,hatta freezer dake dakin babu komai ciki,idan zaiyi tafiya yakansa ma'aikatan su
kwashe duk wani abu dake cikin freezer din,alwala ta sake daurawa ta dawo ta
gabatar da sallar la'asar din,sai ta kwanta lamo saman abun sallah yunwa na
nuqurqusarta,dama bata karya ba suka fito,haka cikin jirgi babu abinda taci saboda
bacci da ya dauketa.

Wasa wasa a wanni suka shiga shudewa,duhu ya fara sako kai,lokacin magariba
yayi,a daddafe ta tashi tayi sallar magariba ta dawo ta kwanta,a haka akayi
isha'i,zuwa sannan ta fara raina kanta,tuni ta fara fidda ruwan hawaye,tunanin da
gayya al mustapha yayi mata haka ya cika zuciyarta,tana daga kwancan amma jiri take
ji saboda tsabagen yunwa,ta dinga share hawaye tana juyi saman abun sallah,tuni
idanunta suka sauya launi saboda kuka da yunwa.

Tunda ya fita wunin baki daya bai zauna ba,gagarumar matsala ce ta taso
cikin companyn tsakanin qananun ma'aikata ta qabilanci,wanda hakan har ya kai
kunnen hukumar qasar,tun jiya abun ya faru amma ba'a sanar masa ba sai yau yana
sauka qasar,kasancewar akwai jinsin daban daban kuma 'yan qasa kala kala dake aiki
qarqashin company,tunda ya fita banda coffee cup biyu babu abinda ya sanyawa
cikinsa,shaf har ga Allah ya manta da ita baki daya,har sai da aka idar da sallar
magariba cikin masallacin dake cikin kamfanin,yana tsaka da azkar ya tuna,katsewa
yayi cikin hanzari ya soma lalubar wayarshi,sai ya tadda ya barota a office,cikin
hanzari da sassarfa ya miqe ya nufi office din,inda yake rataye keys yaga key din
dakin,sai a sannan ya tuna da rufeta ma yayi,hakan ya sanya babu shiri ya kira P.A
dinshi yace ya sallami kowa sai gobe zasu qarasa zaman,yayi kiran drivansa yace su
hadu a parking space.

A gaggauce suka tsaya wani gun saida abinci da bashi da tazara da


kamfaninsa inda anan yake order din abincinsa yayi musu takeaway,sunyi mamakin
ganinsa saboda kiransu yake kawai su kai masa yau sai gashi da kanshi,bazai iya
jira bane kawai shi yasa yayi hakan,abinda ya saba ci da dare tayi order,ita din
baisan me take so ba sabida haka kawai ya saimata abinda yaga amira tafici idan
tafiya irin wannan ta kama,tafiyar minti arba'in cif tsakanin companyn da hotel din
suka isa,ficewa yayi daga motar dauke da kayan yana bashi umarni cikin harshen
nasara kasancewar dan india ne ya gyara parking din motar ya bada key din a
reception.

Tana daga kwancen taji ana yunqurin bude qofar,sai ta sake tsurewa ta zaro
ido tana duban bakin qofar,a nutse ya turo qofar ya shigo kana ya maidata ya rufe,a
kanta idanunshi suka fara sauka,sai ya tako a hankali zuwa inda take kwance wanda
tuni ta runtse idonta da hawaye ya jiqe zara zaran gashin idonta,durqusawa yayi ya
gabanta yana sauke ledojin tare da cewa
"Na manta da ke ne,tashi ga abinci kici" haushi ya qumeta,ya manta da itama kenan
tsahon awanni sabida rainin wayo,sai ya miqe bayan ya gama bude mata ledojin yana
cire suit din sama
"Wannan amanar da kace zaka riqe ce?" Ta furta cikin subutar baki muryarta na
rawa,batasan zai fito ba maganar,abinda ke zuciyarta ne kawai,cak ya tsaya da
abinda yake,ya sake takowa a hankali bayan ya janyo wata kujera mai siffar zero
wadda jikinta baki daya cushion ce katifa ce baga da nauyi ya ajjiye gabanta
"Am so sorry" ya furta yana janyo ledojin gabanshi,da mamaki ta daga idanunta ta
dubeshi,batayi zaton jin kalmar daga bakinsa ba,bai dubeta ba ya fito da soyayyar
shinkafa da gasashshiyar kaza,bayan ya ajiye robar fresh milk data tataccen ruwan
inibi,kusan wadan nan sune abun shansa,cikin park din akwai wani dan plate na qarau
mara qwari,a kai ya juye mata ya sanya cokali sannan ya daga kai ya dubeta
"Tashi kici" tazarar sakan uku kafin ta miqe cikin rashin cikakken kuzari tana goge
qwalla,idonsa ya dauke daga kanta,ya tsani kuka,musamman wannan kukan da yake jin
shi ya zalunceta,baison zalunci shi yasa yake jin kukan har ranshi,kaman fushin
baba zai sauka a kansa haka yake ji,can qasa bayan ya kauda kansa wani sashe yace
"Stop crying" bata amsa ba illa jan plate din data yi ta soma tsakuran
abincin,baifi loma biyar ta kai cikinta ba taji cikinta ya dunqule waje guda,take
ta soma yunqurin amai,almustapha dake gaban t.v ya waiwayo yana dubanta,kafin yace
wani abu tuni ta fara kelaya aman,a gaggauce ya qaraso ya tsaya kanta,baisan ya
akeyi ba,baisan me ake cewa ba,sai data gama tsaf sannan ya miqa mata ruwa ta
kuskure bakinta,ta rasa inda zata zuba yace
"Zuba anan" yana danna waya,jikinta ta janye gefe tana maida numfashin
wahala,magana yayi a recption,cikin qanqanin lokaci saiga leburori,ya matsa musu
yana tsaye harde da hannaunshi a qirji har suka kammala gayarawa,jifa jifa yana
dora idanunshi a kanta,suna yunqurin ficewa wani ma'aikacin ya sake shigowa da
butar shayi da qananun cups,sai da suka fice ya maida qofar ya rufe sannan ya nufi
inda butar shayin take,ya tsiyaya cikin daya daga cikin kofunan ya qarasa inda take
ya miqa mata
"Karbi" ya fada a taqaice,hannunta na rawa ta amsa sai ya bita da kallo,sai da yaga
ta shanye baki daya sannan ya miqe ya shige toilet.

Tsahon awa guda sannan ya fito daure da rigar towel wanda da kadan ta zarta
gwiwarsa,hakan ya sanya kwantacciyar gargasarsa data sha ruwa kwanciya luf,idanu
suka hada sanda yake fitowa,ta dauke idanunta da sauri ta maida idonta ta rufe,tana
jin yadda ruwan dumin ke warware hanjinta,gun jakar kayansa ya nufa sai yaji babu
komai ciki,hakan ya sanya y nufi drower din ya bude,cikin mamakin yadda kayan ke
jere a tsare yake kallonsu,kadan ya waiwaya yana son satar kallonta sanda ransa ya
raya masa ita ta gyara,tunda dakin na rufe bare yace wani ne yayi,kayansa ya diba
ya koma toilet ya saka sannan ya fito,pyjamas ne na maza me v.neck wanda igiya ce
ke daure da su,wani sashi na gashin dake cike a qirjinsa kwance luf ya
bayyana,dogon wando ne da ita sai takalmi slippers a qafarsa,gun ya sake dawowa ya
janyo abincin ya miqa mata,da idanu ya mata nuni data ci,fuska ta soma yamutsewa
tana tsoron kada ya sake dawowa,kafeta yayi da idanu wanda hakan ya tilastata yin
yadda yake so din,baki daya cin abincin kawai take saboda yadda ya rutsata da
idanunshi yana bibiyar motsinta,qarar wayarshi ce kawai ta ceceta,miqewa yayi daga
gun ya koma gefan gado bayan ya dauki tashi ledar ya janyo center table ya
dora,baki daya abincin daren nasa chips ne da hadin salad kamar ko yaushe da ruwan
inibi,sai fresh milk wadda ya jima bai shata ba saboda wasu dalilai,baya kuma sha
din sai ya tabbatar bai da matsala,sai da ya zauna sosai sannan ya fara amsa wayar.
Ya jima yana wayar wanda har batasan sanda ya kammala ba sakamakon gyangyadi
data soma a wajen data gama cin abincin saboda wata mutuwar jiki da kasala data
rufeta,wutar dakin na akashe sai hasken wasu qwayayen bacci guda biyu masu
duhu,jikinta ya bata yayi bacci saboda haka ta miqe ta kunna haske wayarta ta fidda
doguwar rigar baccinta wadda keda santsi,silk ce sosai mai bin jiki ta wuce
bandaki,cikin sanda take takawa don kada ya motsa har ta shiga,saidai abinda bata
sani ba idanunshi biyu,hakanan yana iya ganintar tar sakamakon ya jima cikin duhun
dakin shi yasa bai ganin duhun sosai,so yaje yayi bacci amma abun ya
gagareshi,dalilin da yasa baya shan irin wadan nan abubuwa kenan,duk sonshi da
fresh milk da yoghourt ya haqura da su don ya zauna lafiya,yana son kunun aya
matuqa haka shima ya ajjiye shi gefe,koda yaje gida ya tadda ummee tayi saidai yace
baisha,acan ta wanke hannunta,sannan tayi brush ta sauya kaya sannan ta fito.

A hankali ta ja qofar toilet din ta rufe,idanunshi suka sauka a kanta,haske


pink din rigan baccin na yawo cikin dakin,binta yaci gaba da yi da idanu har ta
qarasa bakin mudubi ta dauki turarenta ta mutsetsike jikinta duk idanunshi na biye
da ita,take qamshin humrar ya karade dakin ya isa har inda yaje kwance,bai san mai
yaje sake jansa ga kallonta ba har ta kai saman doguwar kujerar ta haye tana
karanta addu'o'i tana shafe jikinta da su,bayan ta yane jikinta da mayafi ta kwanta
tana rufe idonta,baki daya abincin data ci ya sanya mata mutuwar jiki,bacci kawai
take da buqatar yi.

Sai a sannan ya dauke idanunshi yana sauke numfashi hadi da ambatar sunan
Allah,wani irin juyi yayi ya sauya yanayin kwanciyarsa idanunsa a rufe yana son
tilastawa kansa yayi bacci,saidai yasan yaci qarya,ba kasafai a irin wannan yanayin
yake iya bacci ba,yayi juyi yafi sau arba'in,take ya soma ganin baiken kansa,mai ya
kaishi shan abunda yasan zai zame masa damuwa,sannan ya bige da kallon abinda baiji
cikin ranshi har yanzun nashi ne,a qalla ya kwashe kusan awanni biyu a haka kafin
ya fara samun sassauci,gumin da yaji yana yi shi ya tabbatar masa da komai yazo
qarshe,kimanin minti talatin sannan ya miqe ya kunna qwan dakin ya shige bandaki.

Fitsari ne ya farkar da ita,ganin saman gadon wayam ba kowa ya sannan ga


motsin ruwa a bandaki ya sanyata zaman jiran fitowarsa,minti biyar tsakani ya turo
qofar ya fito daure da towel jikinsa jiqe da ruwa,baiyi tsammanin farkawarta
ba,dauke kai yayi cikin dakewa da daure fuska tamkar ita ta kar zomon ya bude
ma'ajiyar kaya,yayin da ta miqe wuf ta fada bandaki saboda wani nauyi da kunya da
suka lullubeta,ganinshi a haka yayi matuqar yi mata tsauri,bata fito ba sai data
bada tazarar minti goma sannan,saman abun sallah ta ganshi yana salla,da sauri ta
koma saman kujerar ta qudundune bayan ta duba agogo ta tabbatar tsakiyar dare ne,ya
bata aqalla awa daya kafin ya koma saman gadon ya kwanta bakinsa dauke da tasbihi a
haka bacci ya daukeshi.

*mrs muhammad ce*👑


📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

8⃣1⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

*ya hayyu ya qayyumu bi rahmatika astagis,aslih li sha'any kullahu,wala takilni ila


nafsy darfata aynin*
___________________________________

Qarfe takwas na safe ta farka bayan baccin data koma bayan ta kammala sallar
asuba,babu kowa a dakin sai ita daya,alamu sun nuna ma ya fita,gefe daya ta tarar
da kayan break fast,komai da komai irin wanda zata iya ci,toilet ta shiga tayi
wanka ta dawo ta gyara dakin sannan ta sanya kayan taja kayan ta karya,kwanciya ta
sake yi bayan ta gama,ba dadewa wani baccin yayi awon gaba da ita,bata farka ba sai
data ji ana knocking qofar,ta miqe ta isa ga qofar,ga mamakinta a bude take
muqullin ma na jiki yau bai rufe ba kenan.

Matashiya ce sanye da kayan ma'aikatan hotel din,cikin murmushi ta dubi


sumayya ta gaidata da harshen larabci cikin kokwanto,don bata da tabbacin zata
ji,murmushi ta saki tana mamakin jin larabci mai kyau a bakin matar,tasan yawanci
larabcinsu ba irin wanda ake mana amakarantu bane ta maida mata,sai ta sake fadada
murmushinta ganin cewa tana jin yaren,ta miqa mata wani abu a nade da wata leda mai
qyalli tana shaida mata abincin ranarta ne,sannan ta nuna mata tarin lemuka da ruwa
tace idan ba damuwa zata sanya mata a fridge,matsa mata tayi tana fadin
"La ba'as,tafaddal" ta koma ciki ta biyota,tana tsaye ta gama shirya komai sannan
ta maida qofar ta rufe bayan tayi mata godiya,sai data fara sallar azahar sannan ta
bude,gasashshiyar kaza ce da soyayyar taliya sai hadin coleslow,ba wani da gawa
taci ba ta rufe kasancewar bata jin yunwa.

Kusan haka ta wuni ba cas ba as,har kwanciyar ma ta isheta,ita ba sanin kan


hotel din tayi ba ballantana ta fita,sai daga bisani ne ma ta koma bakin window din
dakin tayi zamanta kasancewar tana ganin mutanen dake kai komo ta nan.

Kusan haka zaman nasu ya kasance har kusan kwanaki goma,da safe zata tadda
ya fita amma ga breakfast dinta,da rana wannan matar zata kawo mata lunch,da
yammaci ta dawo ta tambayeta koda wani abun,sai kuma na dare zata sake kawo mata
shima,sau tari kafin ya dawi tayi bacci,sai haduwa tayi wuya a tsakaninsu idan ba
da asubahi ba,sai data ta farka taga an fidda abincin da bata cinye ba a ajjiye
mata wani,abinda ta fuskanta shine shi din mutum ne wanda bai san dadin jikinsa
ba,mutum ne da ya baiwa sana'a da business muhimmanci mai tsoka cikin
rayuwarsa,bashi da wani lokaci sai na kasuwancinsa,bugu da qari kuma ta lura da
yadda matsalan kamfanin ta sanyashi a gaba,sam ba haka rayuwarsa ya kamata ta
kasance ba,ya qare qarfinsa wajen kasuwanci ba kawai,tana ganin hakan bai dace
ba,ita kanta ta soma qosawa da zaman garin,don baki daya bata ga wani amfani da
zamanta ke da shi ba,tunda bata ganin wanda take zaunen saboda shi,saidai kullum
taci ta sha ta kwanta,hakanne ya sanya yau ta qudurce ba zata yi bacci ba har sai
ya dawo,tanas son tayi waya da 'yan gida,mama,malam abdallanta,zainab da halima
baki daya,ga anty dije,layinta tunda suka shigo qasar ya daina amfani,kuma batasan
inda zata samu wani layin ba bare fa nemesu.

Tana idar da sallar magariba ta shiga tayi wanka,zama tayi bakin mudubi bayan
ta fito ta mutstsike jikinta da turaren humra bayan ta shafa mai,ta goge fuskarta
da powder sannan ta wadata lebbanta da man lebe mai taushi da qyalli,kwalli ta
zizarawa fararen idanuwanta wanda hakan ya sake fito da kyawunsu sannan ta gyara
jagirarta,kai tsaye ta wuce gun kayanta ta fito da atamfarta,holland ce dark brown
ne jikinta,yayin da aka yi maya ado na mint green da yarfi yarfin fari,riga ce da
zani simple,saidai rigar tayi maya cas a jikinta,daurin ture kaga tsiya tayi saidai
baiyo gaba sosai ba,wanda yake fitar da kyan fuskarta da tulin gashinta dake
daure,takalmi ta sanya plate fari qal,sabone shima kamar yadda kayan jikinta suke
sabbi,wani masifar kyau tayi,kallo daya zaka yi mata ya tabbatar maka cikakkiyar
BAHAUSHIYA CE,a qalla tasan zata iya kashe awa biyu kafin ya shigo,hakan ya sanya
ta yanke shawarar fita waje ko hakan zai ribaci idanunta har ya dawo.

Karo na farko data fara fitowa tunda suka shiga dakin,doguwar corridor ce a
qawatacciya mai kama da falo wadda ke dauke da dakuna ajere reras cikin tsafta
qamshi da tsari,kamar zaka zuba abinci a qasa kaci,a hankali ta dinga takawa,har ta
fice daga corridor din bata ga kowa ba,ta karya kwana ta fita wata varender wadda
aka tanadeta saboda hutawa,an tsarata da kujeru da 'yan shukoki cikin qananun
tukwane masu kyau,daga nan kaya iya ganin harabar hotel din sarai da dukkan abinda
ke kai da kawowa,ta nan zaka iya sauka zuwa qasa ko kuma ka wuce zuwa ciki,hakan
yayi maga,sai ta jita sakayau,ta tsaye dafe da makarin varender wanda yake na
silver ne tana kallon komai daidai fuskarta a washe tana more iskar gun da kalle
kallen da takeyi.

A qalla sai data share awa biyu sannan taji ta soma qosawa,hakan ya sanya
ta juya a hankali ta koma ciki,har yanzu bata jin bacci,saboda haka ta koma bakin
window din dakin ta sake tsayawa hannunta harde a qirjinta bayan ta cire mayafin
dake lullube a kanta ta ajjiye.

A gajiye ya turo qofar dakin,sam baiyi tsammanin samunta ido biyu ba kamar
ko yaushe,amma duk da haka bai fasa sallama,jin an amsa masa ya sanyashi daga
idanunshi cikin mamaki yana dubanta,itama nata idanun cikin nashi suke,sai ta saki
hannayen nata ta ta ko a hankali tana janye idanunta daga nashi
"Sannu da zuwa" ta furta cikin sanyin murya lokacin da take yunqurin karbar jakar
hannunsa,sai ya sakar mata cike da mamaki karo na farko da wata ta soma yi masa
hakan ba masinjansa ba,juyawa tayi cikin nutsuwa ta nufi inda taga yafi ajiye jakar
don yi mata mazauni,sai ya tsinci kansa da binta da kallo da idanunshi,ta zama
cikakkiyar bahaushiya zam,karo na farko daya taba tsayawa ya dubi wata matashiyar
bahaushiya cikin shiga ta atamfa,ashe atamfa sutura ce har haka dake fidda ainhin
mutuncin BAHAUSHIYA HAUSA DA HAUSAWA?,ganin tana niyyar juyowa ya sanyashi saurin
janye idanuwanshi ua soma ragewa kanshi rigar samanshi yana ratayeta a mazauninta
"An dawo lafiya?" Ta kuma ambata cikin yin qas da murya wanda hakan ya sanyashi jin
wani yam a jikinsa,bata tsaya sauraren amsar sa ba,don tuni ta wuce toilet,ruwan
wanka ta hada masa mai dumi bayan ta wadatashi da irin turarukanshi na wanka da
yake amfani da su,ta jawo lallausan towel mai yalwa ta rataye masa sannan ta fito.

Yana zaune ne bakin gado yana cire agogon hannunshi bayan ya rage riguna
biyu dake jikinsa,saura wandon coat din da t.shirt mai dogon hannu dake can
ciki,jira yake ta kammala nata uzirin ta fito ya shiga yayi wanka,yana ganin
fitowarta ya moqe yana balle botiran rigarsa tare da shigewa.

Kan kujera ta koma fa zauna tana janyo littafin da anty dije ta bata wanda
sam ta manta da shi sai yanzu,shafin farko ta soma budeww,rubutu ne kamar haka
"A sanda kake son ganin rashin isar namiji duk kuwa isarshi,d'ana masa tarkon mace"
"Matuqar kin amsa sunanki na mace zaki iya sauya mijinki a duk sanda kika so ko
kika ga dama,domin kuwa su din tamkar qananun yara suke" murmushi ya subuce
mata,kunya ta kamata kamar antyn na gabanta,sai ta janye littafin wani tunani ya
fado mata
"Da gaske haka yake?,indai kuwa hakanne zata yi gwaji koda kuwa a gobe ne,sai ta
miqe ta lalubo takarda da biro inda ta fuskanci yana ajiyar abubuwan rubutu,ta koma
saman kujerar ta soma tsara rubutu,tana yi tana murmushi saboda tunanin ta yadda
zata isar da takardar da kuma saqon.

Dai dai fitowarshi kenan idanunsa ya fada kanta,dan zuba ido yayi yana
dubanta,fararen haqoranta a waje,me take rubutawa da ya sanyata nishadi?,bayan ban
bata wani abu da ya cancanci tayi farinciki haka ba?,wannan ne karon farko da yaga
murmushinta muraran haka,sai ya janye idanunshi yana qarasowa cikin falon,baisan me
yasa duk sanda ta hada masa ruwan wanka yakeji dadinsa fiye da wanda zai hada
kanshi ba,dumin yana masa daidai,qamshin yana burgeshi,gajiya na saurin sauka daga
jikinsa,tayi nisa a rubutunta bata ji fitowarshi ba sai qarar bude sif,da sauri ta
maida kanta ganinshi sanye da rigar wanka.

Har ya kammala shiryawa bata gama ba har sai daya zauna cin abinci sannan ta
gama,ta ninke takardar tana murmushi ta daga pillow dinta dake saman kujera ta saka
a qasa,yana cin abincin amma a zahirance hankalinsa duka na kanta,baisan me yasa ya
damu da abinda takeyi din ba,bayan shi mutum ne da bai damuwa da lamuran da ba
nashi ba,sai ta nade qafafunta saman kujeran ra rungume pillow a qirjinta tana
satar kallonshi,sau uku suna hada idanu kowa yana basarwa,a na hudun suka kama
juna,sai ya gyara zamanshi,cikin yanga kamar wata mace ya soma magana a hankali
"Ina fatan ba damuwa bace ta hanaki bacci kamar yadda kika saba ba?" Kai kawai ta
kada masa idanuwanta na duban bezar da aka yiwa filon ado bayan ta dauke idaon nata
daga kan abincin da yake ci,tana mamakin ta yadda mutun zai dinga cin wadan nan
abunuwan da dare kadai wai sune abincin darensa,banda hutu da kudi da yasa jikinsa
da fatarsa murjewa da babu abinda zai hana ya shiga sahun ramammu,saidai babu qashi
a jikinsa wanda zai nuna maka ramarsa,amma idan ya samu kulawar data fi haka ba
shakka jikinsa sai yafi haka cika,ajjiye spoon din hannunsa yayi
"To me ya hanaki bacci as usual?"motsa bakinta tayi itama a yangance tamkar bata
son yin maganar ta maida masa
"nothing"yanayin yadda labbanta da suka sha lips balm suka motsa ya sanyashi tsaida
idanuwanshi kansu,sai kuma ya janye yana ci gaba da cin abincin a nutse
"sai haquri,haka nake haka aikina yake"ya sake fada
"ba matsala"ta amsa a taqaice itama,duk da yayi mamakin yadda ta amsa din amma bai
nuna ba,zai iya tuna duk sanda su'ad ta kawo masa ziyara ta sameshi cikin aiki haka
har ta koma tana mita da qorafi,shi a kan kansa yasan yana hora kanshi da aiki
over,saidai yana ganin hakanne ya dace da shi,baiso ya baiwa kansa wata kafa da
zaiji wani feeling a jikinsa da zai hanashi sakewa,dubai qasa ce ta cin gashin
kai,zaka iya duk harkokin da kaga dama,mata sai kalar wanda ka zaba babu qabilar da
babu,mai ko wanne irin kyau kuma,musamman idan kana da abun hannunka har inda kake
sana'arka za'a kawo maka tallarsu,kai ko ba'a kawo maka ba su da kansu idan suka
samu wargi zasu kawo kansu,musamman idan kayi musu koda ba zaka biya ha zasu iya
kasancewa tare da kai,bazai iya tuna adadin mutanen da ya daina hulda da su ta
sanadiyyar haka ba,idan kuma yana ganin qimarka ya yanka maka babban warning,(da
wannan nakeson jan hankalin matan da mazansu ke tafiye tafiye,ku tsaya tsayin daka
ku kula da mazanku,na tabbatar babu kalad matan da basa gani,wadanda sun fimu
komai,matuqar akwai fahimtar juna tsakaninki da mai gida kuka zauna yana bakin
labarin qasashen da yake zuwa zaki ji irin wadannan labaran,wanda da dama marasa
tsoron Allah sun fada harkar neman mata saboda suna ganin suna wata duniyar babu
mai ganinsu,ko kuma ke kinyin sakacin da har yaga wata mara kintsin ta
burgeshi,wanda tsoron Allah da irin kyautatawar da kike masa shi kadai zai
tsallakar da shi,Allah ka tsare ka kiyaye mana musulminmu a duk inda suke).

Kana dubanshi zai yi wuya ka dauka ba bacci yake ba,sakamakon lamo da yayi
saman gadon cikin tattausan bargo yana sauraren wani recording na tattaunawar sirri
da hamza yayi da qananun ma'aikata yayi recording bada saninsu ba ya turo masa don
gano bakin zaren matsalar dake shirin kunno kai a companyn,a tunaninta yayi bacci
saboda haka ta miqe ta ajjiye littafin hannunta ta dauki kayan baccinta ta shiga
toilet ta sauya
"La haula wala quwwata illa billah...." Ya fada qasa qasa yana jan numfashinsa tare
da kulle idanuwansa,ba wani tsiraici bane da rigar baccin saidai yadda ta lafe a
fatarta ya fitar da sigarta ya kuma haskata,daga sanda ta fito bai sake fahimtar
audion din da yake saurare ba,sai yaci gaba da binta da idanu har ta kai ga yafa
mayafin ta kwanta abunta bayan ta gama addu'o'inta,saidai a banza,tamkar bata yafa
ba haka yake gani,ya tabbatar bazai sake samun nutsuwa ba matuqar tana a
haka,zumbur ya miqe zaune saman gadon,ya miqa hannunshi ya kunna qwan dakin bayan
ya rufe jikinsa da bargo,hasken da ya mamaye dakin shi ya farkar da ita
"Nemi hijabin sallarki ki saka,wannan kayan sam basu dace da ke ba" ya fada cikin
dakiya yana kau da kai sannan ya gayar filonsa ya maida kansa ya ya kwanta bayan ya
kashe wutar dakin,ba musu ta ja hijabin ta zura tana mamakin me maganarshi ke
nufi?,ita dai tasan ba aibu a kayanta,asali ma suna da kaurin da yawonta a dakin
zata iya,baya ga haka ga mayafi data lullube jikinta da shi,ture tunanin tayi gefe
absa dole saboda bacci da yaci qarfinta.

******** ****** *********

Yau kan idanunta aka kawo break din,tana zaune saman kujera lokaci lokaci
tana satar kallonshi bayan ta tabbatar ta sanyabtakardarva muhallin da zai fara
karo da ita a duk sanda ya buqaci aiki da jakar,hannunta riqe da cuo din tea data
hada bata kai ga sha ba,ya fiya ado kamar mace,haka take gulmarsa cikin ranta,tsaf
ya kammala shirinsa ya dauki wayoyinshi da jakarsa,da sauri ta isa gabanshi,sai
kuna ta rage saurin bayan ta isa dab da shi,cup din ta miqa masa tana
kallonshi,shima ita yake kallo,ummee,ummee ce ta fado masa a rai,ita kadai duk
duniya har yau ke masa haka,tunawa yayi da wace ita wajen ummee da baba,sai yasa
hannun damanshi ya karba sannan ya koma gefan madubi yadan jingina kadan daukar yin
hani da shan abu a tsaye daga ma'aiki S A W,a nutse yake kurba yana dubanta kadan
kadan inda take zaune tana wasa da yatsun hannunta,baifi rabi ya sha ba ya tako a
hankali inda take,wanda bata ji takunshi ba sai qamshinsa gab da ita,ya dire cup
din a teburin dake kusa da ita,murya qasa qasa ya furta
"Thanks" ya juya yana niyyar fita
"Ina zan samu layi ina son yin magana da 'yan gida" tsayawa yayi cak,kafin ya daj
dawo da baya kadan,ya fidda wayoyinsa dake aljihunsa ya zari daya ya sake dawowa
kusa da ita ya ajjiye
"Aro" ya fadi a taqaice kafin ya fice.
Bin wayar tayi da kallo,fara ce qal kamar hannu baya tabata,wayar kanta sai
tayi mata kwarjini,saka hannu tayi ta dauka,qamshinsa daya ratsa dukkan wani abu da
yake mu'amulanta shi ya kama wayar ita kanta,bata taba ganin waya mai kyau data
burgeta haka ba,tasa hannu ta shafa screen din ya bude,kasancewar babu password a
kai.

Murmushi tayi ta ajjiye wayar gefe,sai data yi wanka ta karya sannan ta zauna
sosai saman kujera ta soma kiran duk wanda zata kira din daya bayan daya ciki kuwa
har da ummee wadda ba qaramin murna tayi da jinta ba,ta sake jaddada qorafinta na
kullum ta kira almustapha kan ya bata sai yace yana company shin bai hutawa ne
shi?.

Tafe yake yana duba wani file da daya daga cikin manyan ma'aikatansu
wanda shine mataimakin hamza a sashen da suke kula da irin auduga da zararrukan da
suke siya daga wasu kamfanoni,takardun jimillar audugar da suka shigo da su ne yake
dubawa,dab da zai shiga elevator sukayi kacibus da hamzan,sai ya miqawa wancan da
ake kira ramadan yace anjima ya kawo mishi ya qarasa dubawa,don su kammala lissafin
dukkan kudin da suka fita ta wannan fannin.

"Ya dai yau naga kamar kadan so makara baka shigo da wuri ba"
"Jiki da jini ke kawai"
"Gaskiya ne,me kake tunani kan audion daka saurara jiya?"
"Mu qarasa na yi maka bayani", a haka suka qarasa office din.

Kan kujerarsa ya nufa kai tsaye ya zauna yana dora jakarsa saman
teburin,yayin da hamza ya fara bude fridge ya dauko ruwa yana sha,qoqarin bude
jakar ya fara yi amma mazugin ya cije,ya daga jakar don ganin mai ya hanashi wucewa
sai yaga takarda lanqwashe a jiki,cikin mamaki ua ciro takardar ya soma
warwareta,rubutu ne a tsare tamkar da injin buga rubutu aka tsara shi,sannu a
hankali ya soma bin rubutun yana karantawa,yana karantawa kanshi na shiga
duhu,shawarwarine a tsare game da yadda zai warware matsalar kamfanin cikin
sauqi,daya bayan daya kowacce kalma dake qunshe cikin takardar mai muhimmanci
ce,kanshi bai fita daga duhu ba sai da yazo layin qarshe
"ina fatan alkhairi tare da fatan warwarewar matsalar cikin sauri,saboda ka dawo
nutsuwarka,iyalinka na da buqatar zamanka waje daya da kuma samun cikakkiyar
nutsuwarka,kulawar ubangiji ta tabbata tattare da kai" sosai kalaman suka dinga
ratsashi,sai ya samu kanshi da maimaita kalaman,karon farko a rayuwarshi da ya taba
samun wadan nan kalamai masu kyau da tsari daga wajen wata mace dake qarqashin
ikonshi,a hankali murmushi ya subuce masa sanda ya kammala karanta sadarar karo na
biyar
"Lafiyanka qalau kuwa zaka zauna kana dariya kai kadai,mutumin da murmushin naka ma
wataran sai anyi kamar za'a biya kafin a ganshi?"
"Hauka nake" ya bashi amsa kai tsaye cikin gatsali yana gintse fuskarsa tare da
miqewa tsaye,takardar ya dunqule zaiyi jifa da ita yana jan tsaki sai kuma ya
fasa,ya daga takaddun dake gabanahi ya saka ta a tsakiyarsu,hakanan sai yaji wani
sashe na zuciyarsa na bashi qwarin gwiwar gwada amfani da shawarwarin dake qunshe
cikin wasiqar,jawo wayar land line yayi dake gabanshi ya fara latsawa,cikin
qanqanin lokaci ya bada umarnin tara dukkan ma'aikatan dake cikin kamfanin a babban
dakin taro dake kamfanin,freezer ya isa ya ciro ruwan shima yana kurba a
hankali,binsa hamza yake kallo kafin yace
"Wai meke faruwa haka musty?"
"Zaka gani" bakinsa yaja yayi shiri,yasan tunda ya fara magana haka a taqaice ba
mai sanya shi fadadawa,tilas yayi shiru har sanda aka isar masa da saqon gama
haduwar ma'aikatan baki daya sannan ya dubi hamza
"Taso muje,meeting ne na qarshe".

Cike dakin taron yake da baki daya ma'aikatan kamfanin,kowanne zaune kan
mazauninshi cikin tsari,shigowarsa ya sanya kafataninsu miqewa cike da girmamawa,ba
wanda ya zauna sai da ya zauna kan tashi kujerar ta musamman wandda ke a
center,hamza ya zauna kan wadda ke daura da tashi sannan suka zauna,kowa ya shiga
taitayinsa don sun san kan matsalar da har yau ake tattaunawa,musamman da
kowannensu yasan halayyar ogan nasu,sosai ya kashingida tare da lafewa cikin
kujerarsa yana duban kowa daya bayan daya,wanda hakan ya sake ladabtar da su,a
hankali ya soma jefa bayani daya bayan daya yana karantar yanayin kowa cikin
tataccen turancinsa,cikin qanqanin lokaci dakin ya soma rudewa,wata uwar tsawa ya
daka tare da dukan table din dake gabanshi,shiru dakin taron ya sake yi,kowa ya
sake shiga taitayinsa,dorawa yayi da bayanin wanda cikin qanqanin lokaci gaskiya ta
fara fitowa,tsawon sa'a biyu sai gashi komai ya bayyana,ya bawa kowa hukuncin daya
dace da shi,wadanda suka cancanci ya dakatar ya dakatar da su saboda ya zama jan
kunne a guresu,tare da kafa sabbin dokoki masu tsauri sannan ya sallami kowa.

A hankali yake jin nutsuwa da kwanciyar hankali sanda yake takawa don komawa
zuwa office dinshi,bai taba tsammanin shawarwarin dake rubuce zasu warware damuwar
cikin sauqi haka ba
"Wai maan,ya akayi komai yazo da sauqi haka"
"Daga Allah ne......inaso mu zauna mu tattauna kan yadda ya kamata mu fara noman
audugar da muke amfani da ita da kanmu.....but amma yanzu zan wuce,zamu hadu gobe
in sha Allah" binshu yaje da kallo,yau almustapha ne zai bar office tun la'asar?.

Shirt ce a jikinta irinta mata wadda ta fidda shape din jikinta mai gajeran
hannu,sai wrapped skirt mai roba wanda ya zauna mata daidai jikinta,kanta ba
dankwali tunda ta idar da sallah ta cire hijabin sallar tata ta ajjiye gefe,kwance
take rigingine saman kujera riqe da wayar tana duba hotunan ciki,zaman kadaicin ne
ya isheta,hakan ya sanya bayan ta kammala sallar la'asar ta sake daukar wayar tana
duba hotunan don debe mata kewa,don tunda ta gama kiran da zatayi ta ajjiye wayar
bata kuma tabata ba sai yanzu.

Kusan duka hotunan shi ke ciki,wanda da alama ba'a cikin wayar aka
yiba,turasu akai kawai,babu hoton da baiyi kyau ba ciki,da yawa daga ciki da alamu
baisan am daukeshi ba,baki daya sanye yake da suit,bata taba ganinshi da shigar
manyan kaya ba tunda take,tamkar bature haka yake wajen sanya sutura,ta shagala
sosai wajen kallon hotunan,daya bayan daya,sannu a hankali ta soma sakin
murmushi,ko cikin hotunan halayyarsa tana fitowa,kusan duka adake yake cikin
hotunan wani kuma zaka sameshi cikin aiki yake ko yana bada umarni.

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*


*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

8⃣2⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

*Allah S W A yana cewa*

*BAMU KASANCE MASU AZABA BA HAR SAI MUN AIKO MANZO(MAI GARGADI DA BUSHARA)*
______________________________________

*nasan zan wanke muku zukatanku with dis longest page*❣☺


*i wish za'a wanken tawa with ur beautiful prayers duk da dama sabonku ne,ina
godiya,shukran lil jamiii'i*

Gyara kwanciyarta tayi haka fuskarta dauke da murmushi,hakanan take jin dadin
kallon hotunan,tunda ya shigo hotel din har ya kai ga qarasowa dakin ya jima kanta
tsaye bata sani ba
"Wannan mutum" ta fada a fili qasa qasa
"Fuska kaman an maka mutuwa,smile sunnah ne fa" ta kuma fada tana wucewa zuwa hoton
gaba,kowanne hotu da irin yanayin da aka yishi,ta yadda ta kuma sake tabbatarwa
yanayinsa daga Allah ne kurum
"Ya salam" ta furta a hankali sanda tazo kan wani hoto nashi da yayi cikin kayan
sarauta baki daya harda alkyabba,wani dan banzan kyau yayi ba na kadan ba,wannan ne
karo na farko data ganshi bata suit ba,tashi tayi zaune tana gyara zamanta,sai ta
hangi kamar inuwar mutum,wani tsoro ya shigeta zuciyarta ta fara gudu,wani yunquri
tayi ta miqe zatayi bayan gado da gudu taji an cafketa,sai ta bude baki zata saka
ihu,cikin hanzari ya dora bakinsa kan nata ya rufe nata bakin,idanu ta qwalalo tana
son fahimtar meke faruwa da ita tare da daga idanunta sama don son ganin waye,da
sajen gefan fuskarshi ta gane,sai yanayinta ya sauya daga firgici zuwa tsoro,bugun
zuciyarta ya sake qaruwa ta dinga yunqurin janye bakinta amma batasan me ya hana
hakan tasiri ba.

A hankali ya zare bakinsa yana janye jikinsa baya,yana jin yadda feelings
dinsa ke sauyawa,fuska a hade yana tuhumar kanshi,juyawa kawai yayi ya soma cire
takalmin qafarshi da safarsa sannan ya shige toilet kai tsaye,ragwab ta fadi saman
kujera tana dafe da kanta,ta rasa me zata iya tunawa cikin abu biyu,ruqon da yayi
mata da tsoron da ya bata,ga wani mutuwar jiki sakamakon tsoratar da tayi tun da
fari,tana naj zaune dafe da kanta har taji bude qofar toilet din,idanunshi ya sake
sauka kanta,hargitsatsen gashinta da rigarta data cukuikuye ya kalla,hakan ya tuna
mata kayan dake jikinta,sai tayi hanzarin saka hannu ta janyo hijabinta ta
zura,idanunta a qasa ra furta
"Sannu da zuwa"yana takawa zuwa gaban madubi ya amsa
"yauwa..." Shuru ya sake dan ratsawa kadan,ba wanda ya sake furta komai har sai
daya kammala shafa mai sannan yace da ita
"Ki shirya zamu fita" ya fada a taqaice,bata tsaya fahimtar komai ba ta fada
toilet,don dama neman mafaka take,ta jima ciki tana sauke numfashi kamin ta soma
wanka,batasan me yasa abun ya tsaye mata a rai ba.
Yana tsaye gaban mudubi yana gyara sumarshi tare da duban kanshi,ya kalli
labbansa a hankali ya sanya harashensa ya kasheshi,qwaqwalwarsa ke qoqarin bijiro
masa taushin da yaji saman lips dinta yana qoqarin fada da hakan,tsaki ya saki
bayan ya gama gyara sumar tashi yayi jifa da cumb din sannan ya nufi wajen kayan
sawarshi ya fidda shirt da trouser baqi da ja ya shirya,ya sanya takalma high top
tare da maqala sun glasses don sakaye idanuwanshi ya bude qofar ya fice.

Sanda ta fito baya nan,tunani take ina zasu haka?,duk da batasan inda
zasun ba amma hakan ya mata dadi,koba komai zata fita waje tasha iska,tsaf ta
shirya cikin abaya maroon data fito da hasken fatarta wadda samanta ke a tsuke
qasan a bude qwarai akwai yalwa,ta gyara sumarta ta daureta da band sannan yi
rolling da mayafinta,ta daura agogo kana ta sanya zoben dake mahadin agogon ne
tsakiyar yatsanta,takalmin data sanya mai tsini ne duk da bata saba sanya irinsu ba
amma ta yiwa kanta alqawarin koyar saka su,wani fitinannen kyau tayi tamkar wadda
ta fito daga jinsin larabawa,bakinta yasha jan janbaki radau ya sake fitar da sigar
dan qaramin bakinta,dududu bata fi sati uku ba cikin qasar amma fatarta ta sake
haske da gogewa kamar wadda ta shekara,tana tsaye gaba mudubi tana shafe jikinta da
humra ya turo qofar,tsayawa yayi kadan yana dubanta,ko yaqi ko yaso tayi masa
kyau,dalili kenan da ya sanya yake jibgowa amira abaya tun a gidan,shigar tana
burgeshi,mutum ne mai son kwalliya matuwa da gaske,hakan ne ya sanya tasu ke zuwa
daya da amira kota wajen siyayya,saboda tafi farida da huda ado,ganin tana yunqurin
waiwayowa ya sanyashi dauke kai,ya qaraso cikin dakin yana daukan wayarsa
"Bani wayata idan kin gama min kallon qurillar da kuma gulmar" mamaki ya
kamata,wato dazun dama tsayawa yayi yana ganinta taba kallon hotunanshi?,kunya ta
kamata sai ta zunbura baki cikin harshen larabci da take tsammatar ba zqiji abinda
take fada ba qasa qasa tace
"Gulma?wai kallon qurilla,to me zan kalla?" Dagowa yayi yana murmushi qasan ransa
ba tare da bayyana saman fuskarshi ba,yasan tayi maganar ne ga tunaninta baiji ko
bazaiji me zata ce ba,hannunshi ya harde a qirji yana dubanta har ta dauko wayar ta
sake nufowa wajensa ta miqa masa,ya kafeta da mayun idanunshi yana mata kallon
qurilla,baiko bi ta kan wayar da take miqo masa ba,ya motsa bakinsa kamar wanda
baison yin magana
"Qarya nayi kenan?,na gaya miki me kike kallon ko zaki iya tunawa da kanki?" Cikin
mamaki ta daga kai ta dubeshi,saidai nauyin da idanunsa suka yi mata ya sanyata
sadda kai ba shiri,ashe yana ji?,ta shiga uku ita kam,me ya kita kallonsa koda a
waya ne bare tayi masa qunquni?,sake matsowa yayi gab da ita yana son hade tazarar
datayi saura tsakaninsu yana duban lips dinta,haka kawai yaji ya bashi sha'awa
yadda jambakin ya kwanta saman farar fatarta
"Uhummm,ki bani amsa ko ni na amsa miki,na lura kamar baki da kunya fa sosai"
gabanta ya fadi,jikinta yayi sanyi,ba'a taba mata shaidar rashin kunya ba sai
yau,yanzu idan da malam ko ma zasuji ya fadi hakan Allah ne kadai yasan fadan da
zata sha,sai idanuwanta suka tara qwalla,bata so yayi mata wannan shaidar
ba,muryarta na rawa alamun fara kuka ko da yaushe tace
"Kayi haquri,bada niyya bane?"
"Kika yi me?," ya fada yana sake takowa saura kadan ya hade jikkunansu,tsoro ya
hajata daga qafafunta bare taja baya,gani take yau Allah ne yasan me zaya yi mata
"Komai ma" ta fada tana dauke qwallar data ziraro mata ta ido daya ta daya idon
tana shirin fitowa itama,hakan yaji tausayinta ya kamashi,a yau din nan fa ita ta
fiddashi daga matsalar daya kusa sati biyu ciki,bata cancanci tayi bacin rai a yau
din ta sanadinsa ba,bata da kowa a qasar saishi,kwananta kusan ashirin da wani abu
tana wuni cikin kewa ita daya qulle a dakin,zaya so a yiwa amiransa haka?,bai manta
ba hamza yace ya dauketa tamkar qanwarshi sai a yanzun yaji zai iya hakan.

Ga mamakinta sau taji ya kama fuskarta da hannayenshi biyu ma'ana fuskarta


da tsakiyar tafin hannunsa
"Shshshshsh....ya isa,ba laifi kika yi ba,amma indai kika bar daya hawayen ya zuba
to zan miki hukunci,maza hadiyeshi" maimakon ya koma din sai ya qarasa
silalowa,idonsa ya runtse yana jin ba dadi,baya son kuka ko kadan,sai ya sanya
hannunshi a aljihun trouser dinsa ya ciro handkherchief ya goge mata hawayen ta
yadda kwalliyarta ba zata baci ba,sannan ya dora shi saman lebanta ya soma rage
mata janbakin
"Yayi yawa,kadan ya isa" ya fada yana kallon lips din nata tare da maida
handkherchief din aljihunsa,itakam bata ga wani yawa ba da yayi
"Is ok,kada ki sake kuka,ki riqe wayan saboda gida before ki samu wani layin,muje"
ya fadi yana dubanta,gaba tayi cikin mamakinshi,wane sabon halayya ne haka?,shi
kuma ya take mata baya har suka fice daga dakin ya rufe.

A reception ya tsaya ya karbi muqullin motar sannan suka fice tana gaba
yana bayanta.

  A hankali suke takawa suna wucewa zuwa gurin ajiyar motoci,abun mamaki duk
inda suka gifta tun daga cikin hotel din sai sun dauki hankali,tsammata ake wasu
shaqiqan masoya ne,yanayin shigar kowannensu ya dace da shi,a haka har suka qarasa
wajen motar,da kanshi yau zaiyi driving din saboda haka kai tsaye ya wuce mazaunin
driver.

         Wani nutststsen tuqi yake yi wanda ke qarawa zuciya da ruhi


nutsuwa,bazaiyi qarya ba kam yau wani annushuwa yake ji,hakan kuma yaba tunanin bai
rasa nasaba da warwarewar matsalarsa cikin sauqi,shiru kake jin motar,idanunta na
bisa titi a fakaice tana qarewa garin kallo,haqiqa yayi matuqar tafiya da ita fiye
da uk da ta je,gari ne mai cike da qyale qyale da kayan qawa masu matuqar jan
hankali,dan satar kallonta yayin kafin ya maida kanshi bisa titi
"Thanks" taji ya ambata,a hankali ta maida idanunta kanshi wanda titi yake kalla
kafin ya dauke kanta,murya qasa tace
"Dame fa?" Shiru ya biyo baya kamar bazai amsa ba,har tayi zaton ma ya bar zancan
sai taji ya kuma cewa
"Shukhran alat taujih" sake daga kanta tayi tana dubanshi murmushi na son subuce
mata,ta rasa ya akayi yaji larabci haka,wati dazun tayi shuka ne idon makwarwa,ta
gode Allah da ba wata magana ta fadi ba,sai ta kauda kanta
"Babu komai,abinda ya kamata ne nayi shi" sosai maganar ta burgeshi,kusan shi daya
yake warware matsalolinshi idan sun taso mashi ya riga ya saba,shi yasa wannan
karon yake jin tayi mishi wani gagarumin aiki data cancanci a gode mata,ba shakka
samun abokin shawara da yin shawara a kuma baka shawarar yana da matuqar muhimmanci
kamar yadda ummee ta saba gaya masa
"Ko zaiyiwu na riqeki personal adviser?"
"Aikin kowacce macen gida ce matuqar an lamunce mata hakan" itama ta fada ba tare
data dubeshi ba,tana jin qarin mamakinsa cikin ranta,kamar yasha wani abu
ne?,wannan ne karon farko tsawon sanayyarta da shi da suka taba zance mai tsahi
makamancin hakan,ta nashi bangaren mamakin irin tata baiwa da fasahar yake,yana
ganin matan arewa basu da wannan fikirar amma a yanzu yaga guda daya?,haka suke ko
kuwa wannan ce kawai?(hmmm,mun wuce haka ma malam almustapha,muje dai zuwa).

        Bai tsaya ko ina ba sai zabeel park,tunda suka shiga wajen yayi matuqar
qayatar da ita,karon farko a rayuwarra data taba shiga wani park,guri ne da family
kan iya zuwa,miji da mata da yaransu,koma miji da mata kawai,a hankali suke takawa
jere da juna,saidai idanuwanta na wulqawa ko ina tana kalle kalle abinta cikin
hikima ba tare daka fuskanci ta matowa gurin ba,wani sashe daban suka nufa wanda ke
dauke da wasu rubuce rubuce na SEASON four dubai garden glow,hakan ke nuna lokaci
lokaci wajen ke a bude,gurin biyan kudin shiga ya biya aka nasu ticket sannan suka
shige.

        Bata taba ganin abubuwan data gani cikin garden din ba,wani irin garden ne
da aka baje fasaha wajen yinsa,kowa na harkarshi cikin wajen,kama da yara qananu da
matsakaita,maza da mata,masoya gasunan birjik kowa na baje kolin tashi
soyayyar,wani guri na musamman suka yi mazauni sanda wayarshi ta fara ruri ya
cirota yana qoqarin amsawa yayin da ita kuma taci gaba da bawa idanunta abinci,a
hankali idanuwanta suka sauka kan wani family,miji da mata ke sai yaransu uku,mace
babba sai mai bi mata namiji sai qaramin shima namiji,a yadda suke raha kana
kallonsu kasan banu abinda ya shafi rayuwarsu,sisai yaron suka burgeta kasancewarta
mutum mai son yara qwarai,suna ta wasanninsu suna kaiwa suna kawowa wajen
iyayensu,ta sake dauke idanunta ta maida kan wasu matasa biyu mace da
namiji,namijin ke bawa macen ice cream yana ta faman lallabata ya kasa ya
tsare,tayasu dariya tayi ta hanyar sakin murmushi sanda ya dangwala kata shi kan
hancinta sanyinsa ya ratsata ta fidda idanuwa,abinda bata sani ba duk abinda take
almustaphan na ankare da ita,har ya kammala wayar bata sani ba,maidata aljihu yayi
ya hade hannayensa waje guda yana nazarin yadda annuri ke fita daga fuskarta,take
ya sake karantar yanayinta na tsantsar son yara,ta sake maida idanunta wajen wasu
yara dake daura da su wajen su biyar da wata 'yar matashiya tsakiyarsu da alama ita
ta kawosu,wasa sukeyi abinsu na buya,yarinyar dake cikinsu wadda bata wuce shekara
uku ba ta taho a guje ba tare data lura da sumayyan ba ta boye bayan kujerar da
take zaune tana fadi cikin harshen larabci
"Ki boyeni",murmushi ya qwacewa sumayyan sai ta sake bude doguwar rigarta ta boye
yarinyar ga sake lafewa tana sakin dariya irinta quruciya,nemanta suka shiga yi
wanda dariyar da take qyalqyalawa ya sanya suka gano inda taje,sai ta cukuikuye
sumayya tana dariya tare da kifa kanta acinyarta,daukanta tayi itama tana murmushi
sannan ta miqe sanda yaran suka qaraso ta ajjiye musu ita,sake diba sukayi da gudu
ta koma ta zauna tana binsu da kallo tana murmushi.

  
          A nutse suka ci gaba da takawa suna qarewa kyawun wajen da tsarinsa
kallo,har yanzu murmushu bai bar fuskarta ba,zuciyarta fes,Allah ya sani tana son
yara
"Allah ka bani yara da yawa"ta furta can qasa sosai lebanta na motsawa
"Da wa?" Zuciyarta ta tambayeta,,matuqar yaran takeso saidai tare da mustapha fa
kenan,a hankali ta daga kai ta dubi mustapha,sai suka hada idanuwa,tare kowa ya
dauke kanshi,kaifin ji gareshi kamar me,yaji sanda tayi addu'ar,shirun minti wajen
biyar tsakani taji ya jeho mata tambayar da bata san amsarta ba
"Haihuwa kike so kenan?" Sosai tambayar ta doketa,ya akayi tayi maganar yadda zaya
ji,sai ya tsaya cak da tafiyar ya kafeta da idanu ta cikin gilashinsa,bata ce komai
ba sai dauke kanta da tayi
"Uhummm,ki amsa mana,kina so ki samu ciki ne ki haihu?" Gani take kamar ma wani
nishadi yake yana son qureta,hakan ya sanya ta cire kunya ba tare data dubeshi ba
tace
"Kuskure ne?,kai din baka so?,shekarunka nawa a duniya?,ina tsammanin zuwa yanzu
zaka yi kwadayin samun diyan kanka" shi din ma ba qaramin dukanshi furucin yayi
ba,amma ya sai ya tsinci kansa qaramin murmushi na subuce masa,ya lura qarfin hali
tayi ta furta maganar,yana son mutum mai confidence qwarai,zaya so kacici kacicin
nasu ya dore saboda haka yace
"Why zan qi hakan,ina so,but bani da matar da zata haifa min.....ko ke zaki iya?"
Waiwayowa tayi da hanzari ta dubeshi,sai ta sake kasa ci gaba da jurewa kallon
nasa,ta kuma juya baya tana harde da hannayenta a qirji,yayin da,nashi hannayen ke
zube a aljihu yana dubanta,yana son qure confidence din da take ji tana da shi,kai
ta girgiza bayan ta samo amsar bashi
"A'ah ni a su wa,ban shirya ba,after all ma bazan iya ba" ta fada tana watsa
hannuwanta,dariyarshi ya danne don ya hango karaya muraran a kalamanta
"Me zaya hana ne wai?,ai sai an gwada aka san na qwarau,if u can try u can do it"
ya fada yana kama qugunta da hannayenshi tare da mannata a jikinsa,har ga Allah
yayi da wasa don kuma ya qureta,saidai yaji a jikinsa fiye da yadda ita taji,don
ita tsoro ne ya lullubeta,dakiya da taurin zuciya ya hanashi sakinta,sai da yace
"Tunda kika fada dole ki gwada,sai an banbance aya da tsakuwa tukunna" sannan ya
saketa,da hanzari tayi baya tana jingina da jikin wasu qarafuna dake tsaye wanda
aka yiwa ado saboda yadda qafafunta sukayi sanyi,tsahon mintina qirjinta na bugawa
ta rasa ta cewa,batasan sanda ya sayi ice cream din ba ta dai ga yana miqo mata,a
sanyaye ta saka hannu ta amsa.

        Basu bar wajen ba sai wajen takwas na dare,duj wata kewa da takura na
tsahon satittikan sun baje sunyi nasu guri a park din,don ma baki daya ta kasa ci
gaba da sakewa tun maganar da sukayi da shi,kunya nauyi da tsoro sun cikata duk da
bai sake dubanta ba bare yace mata wani abu,har suka koma gida yayi wanka yayi
shirin bacci tana takure guri daya,tuni yayi luf saman gado,ta qididdige lokutan
data saba bashi ja zatonta cewa yayi bacci sannan ta miqe ta shiga toilet tayi
wanka ta sauya kayan baccinta,kusan tuni ya haddace sanda take sauya kayan,hakan ya
sanya ma yau bacci bai daukeshi ba,tamkar mai jira yaga fitowarta din kuwa sai gata
ta fito,a gajiye take don haka a sannu take takawa cikin kayan baccin riga da wando
ne,rigar iya cinya wando kuma ya wuce gwiwarta iya qauri,idanunsa ya lumshe yana
ajiyar numfashi kadan kadan,kansa ya wani sara mishi,sunan Allah ya ambata tare da
addu'ar kada ya zamana ciwon kansa ke shirin tashi,yau yayi surutu ta waya da
yawa,ga inda suka je din akwai hayaniya ba laifi,bugu da qari jiya bai samu
isashshen bacci ba saboda wannan matsalar,a haka ciwon kan ya dinga sakadarshi har
kuaa da asuba kafin ya samu bacci.

  ******      ******    *******

         Qarfe tara na safiyar washegari ta fito daga toilet bayan ta wanke


bakinta,yana zaune gefan gado yana amsa wayar hamza,kallo daya ta yi masa taga
sauyi a idanunshi,sun sauya sun fada kadan ba kamar yadda suka kwanta daren jiya
ba,ta daya bangaren hamza ke ce masa
"Muna da baqi fa maan,ka shirya kasan yadda za'ayi"yadan motsa fuskarshi
"Su wafa kenan?"
"Usman,huzaifa,musaddiq,lamin,on their why to dubai tomorrow in sha Allah(abokan
asali su shida tun suna universty a america idan kun tuna)" miqewa yayi a hankali
ya fice a dakin sannan yace
"Kaifa dan iska ne wallahi hamza,ka girma amma bakasan ka girma ba,sai kasan yadda
zakayi don nasan gulma ce zata kawo su ka sanar musu komai ko?" Dariya hamza ya
dinga harda qwalla
"Wallahi baka isa ba,ai baqinka ne,congratulating dinka zasu zo suyi sai kace min
kuma nasan ya zanyi da su,can ta matse maka" ya fada yana katse kiran,lalubar
hamzan ya soma yi,yasan kadan daga iskancinsa yasanyasu suzo mishi daki haka
kawai,bugu daya ya daga tunda yana kusa da ita yasan sarai zai kirashin
"Ya akayi?" Inji hamza
"Ya kake ganin za'ayi?"
"Kafi kowa sanin halin guys din nan zuwa daram wllahi"
"Jokes apart don Allah,ka saukesu gidanka,idan yaso sai muzo nan"
"Ka nemi maslaha,tunda kai kafi ganewa zaman hotel,Allah ya sawwaqa"
"Ka rufen baki malam,ka cuci mutane kawai..."ya katse wayar yaja jan tsaki tare da
furzar da iska daga bakinshi,hamza bai da mutunci amma sai ya rama zaiji dadi,ya
tabbata shi ya gaya musu don bai manta abinda suka dinga masa sanda zai auri abida
'yar africa,juyawa yayi ya koma dakin yana tunanin da me zasu karya,kadan kadan
yake jin shima ya soma qosawa da zaman wajen,shekarunshi nawa yana siyan abinci gun
saidawa,da a gidane ya tabbata ko coffee zaya samu yasha tunda yaji ta iya dafa
shi.

*******    ******    ********

        Washegari bayan fitarsa office ta wayarshi dake hannunta ya tura mata texs
ta shirya ga driva nan zai kaita gidan hamza,cikin murna ta hau shiryawa,ko banza
yauma zata miqe qafarta,minti talatin kacal ta gama shiryawa cikin african abaya
wanda tayi masifar karbarta,ba wani makeup ta yiwa fuskarta ba amma saida duk
abinda tayi amfani da shi ya dace da shigarta,hakan shi ya qawata kwalliyarta,dakin
ta rufe cikin zumudi sannan suka wuce.
       Gidajene wadanda ke dauke da qawatattun madaidaitan apartment daidai
rayuwarku ku babu matsi balle takura,wanda ke nuna na haya ne,falo ne madaidaicin
mai kyawun tsari wanda ke dauke dining mai kujeru shida baya ga kujeru set daya,sai
dakunan bacci guda biyu kowanne da toilet,sai kitchen daga can daban wanda ke da
vantilation,cikin murna da farinciki abida ta tarbeta,wanda ta sauketa da drinks da
kayan snacks,abun yayi mata sosai,duk sai taji rayuwar hotel din baki daya bata yi
mata ba,bayan sun dan taba hira abida tace
"Ina fata kinzo da shirinki,ogogi na da baqi,kitchen zamu nufa yanzun" baki ta tabe
cikin mamaki
"Nikam yace min kawai ja shirya a kawoni wajenku" murmushi abidan tayi
"Almustapha,har yau bai sauya ba miskilancinsa na nan" miqewa sumayya tayi tana
dariya
"Muje kawai ki tayani hira,don ke da wannan cikin ai idan ba'a hutashsheki ba ba'a
saki wahala ba" miqewa tayi tana gaba sumayya na bin bayanta tace
"Ke!,waya gaya miki?,irin wadan nan mazan namu da suke ganin mata kala kala aisai
da miqe tsaye,babu abinda na fasa in gaya miki,daka saki baki saidai ayi babu ke"
dariya ta kama sumayya,yayin da maganar ta dan maqale mata a rai.

       Kusan abida 'yar kallo ta zama duk qwarewarta a girki tana daukan style
wajen sumayya,kafin wani lokaci komai ya kammala abinka da na'ura,sumayya na zaune
gefan gadon abida sanda abidan ta shiga wanka,wayar almustapha dake jakarta ta
dauki kidan wani sassanyan ringing,ta ajjiye littafin da take dubawar ta ciro wayar
MY SU'AD shine sunan da ya bayyana saman screen din hadi da hotonta,ta jima tana
kallon wayar har kiran ya katse,wani kiran ne ya sake shigowa ta sake daga kai ta
zubawa wayar ido,batasan me take ji ba a qirjinga saidai tana jin wani abu na neman
cushe mata wuya,a haka abida ta fito ta taras da ita
"Ah ah,waya nata ringing fa"
"Bani ake kira ba" ta fada tana dauke kanta daga saitin wayar
"To wayar wane?"
"Wayarshi ce"
"Ki daga to ki gayawa mai kiran bashi kusa ko wani abu mai muhimmanci ne ya....."
Sai maganar tata ta katse sanda taje kusa da wayar don daukar bargon da zata tsane
jikinta da shi ganin sunan su'ad
"Bar shegiya wallahi kada ki daga" cewar abida cikin tsantsar kishi,dubanta sumayya
tayi ganin yadda abidan ya sauya maganarta lokaci daya,bata dubi sumayyan ba ta
nufi bakin mudubi abinda ta soma shafa mai,har kiran ya katse babu wanda yace uffan
sai daga bisani abidan tace
"Sumayya,Allah ne ya hada jinina dake,wlh kinga baifi sau biyu muka taba haduwa da
su'ad ba amma baki daya bansan me yasa jininmu sam baizo daya ba,bana son mutum mai
dagawa da jin kai,don Allah kada ki sake komi bari taga wallenki bare ta rainaki,ki
zame mata dodo,ki daukaka darajar almustapha a idanuwanga tasan cewa ba kowane ke
iya jefar da daimond ya dawo ya tsinceshi ba awajen,ba taba ganin sakaryar mace ko
a labari ba irin su'ad wallahi" ajiyar zuciya sumayyan ta saki ta furta
"Na gode,Allah ya bar qauna" daga haka suka rufe chapter din suka shiga wata hirar
daban,yayin da wayar tacu gaba da burari aqalla sai data hada miscal goma sha biyar
sannan ta haqura ta bi bayansu ta tex wanda bata sake taba wayar ba ma balle taga
me ta rubuta din.

        Bayan idar da sallar la'asar baki dayansu suka iso cikin lafiyayyar motar
almustapha wadda ta cinyesu baki dayansu,hira da musu ta cika motar baki daya,baka
jin komai sai muryoyinsu,yayin da almustapha ke daga zaune yana dariya,ya jima
baiyi dariya irin wannan ba,ba shakka aboki wani abu mai muhimmanci ne a rayuwar
mutum,musamman idan kayi dace da samun aboki na gari,hamza shine kan gaba suna
bayansa,da irin wannan hirar suka shigo falon wanda ya wadata da qamshin turaren
wuta wanda sumayya ce ta mata kyautarsa irin wanda tayi da hannunta,sosai yanayin
falin ya yiwa almustapha,haka qamshin dake tashi,take ya soma wassafa komaea nashi
gidan yana tsara yadda hakan zaya kasance.
       Dukan cinyarsa musaddiq yayi bayan hamza ya wuce dakin abida
"Maann,Allah na qagu naga wacce 'yar afrika ko ince arewar ce tayi nasarar sace ka
haka?" Dariya suka sanya baki daya,usman yace
"Ai wallahi tunda maan ya sallama kowa ma ya sallama,nikam dama tuni na miqawa
sahar kaina,wallahi na sallama"
"Bare ni da naga zuhra" cewar huzaifa yana latsa waya yana dariya,harara dukka ya
watsa musu,yasan baki dayansu hamza ya kwaza musu yadda akai auren
"Ina fata har yau baku manta waye maan ba ko?,kubar ganin kun fara neman aure har
yau baku girmi na daddaki bakinku ba wallahi qattin banza" ihu suka sake sanyawa
"Allah ya shiryeka,mata biyu amma har yau basu sanyaka ka girma ba" haka suka dinga
fadi,ganin fitowar hamza ya sanya su nutsuwa yana sanar musu gasu nan fitowa,yadda
suka nutsu suna jiran ganin fitowar tasu hakanan mustapha ya dinga jin kamar yace
kada su fito suyi zamansu.

       Wani abu ya dinga motsa masa sanda suka fito,abida na kan gaba dauke da try
sumayya na bayanta dauke da wani try din me snacks a ciki,sai yake ganin duk cikin
shigarta ta yau kamar ta musamman tayi,ganin abida ta nufi gaban hamza ta dire
itama ya sanyata isa gabanshi ta dire
"Amma wannan tsabagen son kaine,mazanku kurum kuka sani?" Cewar musaddiq idanunshi
na kan sumayya wadda ta saki murmushi idonta a qasa,baki daya wanu nauyi take ji
bata saba shiga cikin maza haka ba,idanun almustaphan shima na kanta,can qasan
murmushin nata yake hango damuwa kadan kadan,almustaphan ne ya sanya qafarshi ya
tura plate din gabansa
"Gashinan malam sai ka saurara haka ko?" Ya fada cikin dakewa,dariya ya tuntsire da
ita,kusan halinsu daya da hamza,yaci alwashin yau sai ya wana almustapha ya manna
masa hauka,dama an dade ba'a hadu ba
"Amma dai da ka barta ta kawo da kanta a matsayinmu na baqinsu" ya fada sanda suka
gama gaisawa suka koma kitchen don shirya musu abincin saman tebur,wani banzan
kallo ya watsa masa
"Tunda tare muka hada muka biya sadakin ko?" Ya fada cikin subul da baka,dariya
suka sake kwashewa da ita,lamin ke nuna shi da yatsa,hamza na danne dariyarshi ya
sauka qasa ya soma zuba musu kunun aya da sumayya ta hada mai sanyi da yasha madara
da flavour cikin cups yana miqawa kowa,ya zuba na qarshe ya miqawa almustapha,sai
yaqi masa ya zuba ma hamzan ido yana aika masa da gargadi
"Karbi mana malam ka sanya min ido haka?" Wannan maganan ita ta ja hankalin
sauran,musaddiw yace
"Wai man har yau kana kan bakanka baka shan irin wadan nan abubuwan,ina cewa komai
ya sauya tunda now u r married baka da case"
"Keepquite malam,ni na gaya ma haka?" Ya fada yana amsar cup din daga hannun hamzan
don baison suyi masa dogon sharhin nan nasu,ya kai bakinsa ya kurba,sosai abun yayi
masa dadi,ya lumshe ido yana jerowa hamza Allah ya isa cikin zuciyarsa,ya tabbatar
yau ya jefashi a masifa ne kawai,usman ne da yake shi ya dan biyo almustapha kadan
"Kai maaaan,wallahi ko cikin larabawa ka samu yarinyar nan ka more,idan zaka saki
jiki ka kwashi gara tun lokaci bai qure maka ba ato"
"Gaya masa dai mutumina,komai fa yaji wallahi,gaba da baya duka babu makusa" wanu
abu yaji ya soki zuciyarshi,ranshi ya baci wanda ko a wasa bai taba zaton zai baci
ba,dukkaninsu suka lura da hakan saidai basu fasa dariyarsu ba
"Koma ciki!" Almustaphan ya fada cikin dakakken sauti da daga murya sanda take
fitowa daga kitchen dan kawo kayan abincin saman dining,sosai maganar ta
ratsata,sai ta koma da abincin ta samu wajen cikin kitchen din tayi zamanta,sai a
sannan suka lura da sauyawar yanayinsa,hakan ya sanya suka rage tsokanar suna yiwa
juna magana da ido tare da danne dariyarsu, don duk basu dauki abun zaiyi tasiri
haka ba.

       Hamza shi ya qarasa shirya komai,yayin da suka shiga wata hirar,shi dinma
dannewa ya dinga yi yana sin tabbatarwa kansa ba wani abu bane ya faru,har sanda
suka zauna kan dining hamza yayi serving kowa sannan suka fara kaiwa baka,take kuma
sai aka koma santi,suka soma tambayar inda suka siyo abincin,shikam yasan ba taste
din abincin abida bane,duk ita gwanar girki ce,sai ya ciro waya yasanya handsfree
ya kirata yana tambayarta inda suka siyo abinci,dariya ta qyalqyale da ita
"Dear ba wani gidan abinci,girkin sumayya ne,taga nayi nauyi ne ta amsar min aikin"
"To masha Allah" ya fada yana katse kiran ya dubesu yana kai wata lomar bakinsa
"To kunji girkin amaryar musty ne" take kowa ya soma yaba girkin,lomar da yayi ta
tsaye masa a wuya,sau kawai ya dauki ruwa ya kora ya miqe tana duban hamza fuska a
dinke
"Tashi ka kiramin ita mu wuce" dubansa yayi yana qoqarin hadiye abinci
"A'ah man,bamu tattauna komai bafa,dududu ko awa bamuyi ba agidan nan"
"Zaka kira min ita ko sai na shiga dakin da kaina" dariya suke qasa qasa,lamin ne
ya dake ya soma masa bayani ba wani abu suke nufi da matarshi ba tsokanarshi kawai
suke,hannu ya saka ya daki teburin
"Ce muku nayi wannan ne ya bani haushi,shut up da Allah"yau sunga bala'i sai suka
sanya masa ido,miqewa hamza yayi ya isa kafadarshi ya dafa shi ya soma masa magana
wanda basa jin me yake ceww,ajiyar numfashi yayi ya juya ya dubesu,sau ya saki
qaramin murmushi
"kunci bashi wlh zakusan kunyi da musty,amma kiramin ita mu wuce din kawai na riga
da na tashi,after eight zamu hadu a masauki ba case"dariya suka saki baki
daya,cikin minti biyi sumayyan ta fito
"amarya ki gaida gida"suka ce mata ta amsa da to tabi bayanshi.

      Tuqinsa yake a hankali saidai har yau abinda ke tokare a zuciyarshi bai baje
ba,sau biyu yana satar kallonta,har yanzu mode din damuwa yake iya gani kan
fuskarta,ya lura da wayarshu dake ta haske a jakarta amma baice komai ba kamar
yadda bata ce masa ba,a zaman kuramen suka isa gida.

       A waje yayi magariba da isha'i,sanda ya dawo da zummar yin wanka sai ya


sameta nannade saman doguwar kujera,ko t.vn ma da ya kunna kafin ya fita a kashe
take,hakanan yaji ya fasa fita,wayoyinsa biyun da suke gunsa ya kashe ya shiga yayi
wanka ya dawo ya sanya pyjamas masu taushi farare qal bayan ya wadata jikinsa da
turarensa kamar ko yaushe,tana kwancen bata motsa ba,jikinta duka na arufe sai
kanta dake a waje,qwayayen dakin ya kashe ya kunna na bacci duk da a sannan dududu
qarfe tara na dare,gadonsa ya haye yaja lallausan bargonsa ya rufa iya qirjinsa
bayan ya zauna sosai saman gadon yana karanto addu'o'i,sai yaje yayi bacci da wuri
tun kafin abinda ya sha ya soma taso masa.

       Wayar dake saman kanta ta soma haske,hannu ta sanya ta duba,miscal ne da


qarin saqonni,tsaki ta ja kamar ta maidata ba tare data gaya masa ba sai taga hakan
bai dace ba,mai kiran zatayi tsammanin ya ganu ne bai kula ba,kuma ko banza
matarshi ce,motsa bakinta tayi murya can qasa a tausashe kamar maijin bacci tace
"ana kiranka akwai kima sms"
"Tun yaushe?"
"Rana"
"Waye?" Dan jim tayi sannan tace
"Su'ad na gani" shiru yayi yana ci gaba da addu'arsa har sai daya kammala sannan
yace
"Me saqon yace?" Kai ta girgiza tana daga kwancen
"Ban duba ba"
"Me yasa?"
"Ba saqona bane,ba kuma hurumina bane" amsar tayi masa,wannan itace cikakkiyar
amana
"Ok,karantomin naji" shiru tayi don bata da muradin karantawar har ranta,sai da ya
sake maimaitawa,janyo wayar tayi ta bude,a hankali ta isa ma'ajiyar saqonni wanda
tunda wayar ke gurinta ko gefan bata je ba,ta dannan saqon daya fara shigowa da
fari ta soma karanta masa,idanu ya lumshe muryarta da tayi low tayi sanyi na
ratsashi,har ta qare kusan bai fahimci me ta karanta din ba,sai da yaji shiru
alamun ta gama karanta saqonnin sannan ya farga,gyara zamanshi yayi tare da bude
idanuwanshi
"Banjin me kike karantawar,dawo nan kusa" ya fada yana mata nuni da gefansa,duk da
babu wadatar haske amma tana iya ganinsa,ba tare da tunanin komai ba ta miqe
tsaye,ta nufoshi tana maida mayafinta daya zame daga kan tulin gashinta dake daure
cikin ribbom,a hankali ta zauna daga gefan gadon da tazara mai yawa tsakaninsu
qafafunta na zube a qasa ta jingina da fuskar gadon sannan ta sake bude saqon da
nufin maimaita masa.

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

8⃣3⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

___________________________________

      Idanunsa lumshe murya can qasa ya mata nuni da filon dake daura da shi
"Nan zaki dawo" daga kai tayi ta dubeshi,ganin idanunsa a rufe yake ya sanyata
matsowa ta sake rage muryarta ganin tana kusa sosai da shi babu buqatar daga
murya,don har tana iya sheqan daddadan qamshin turarensa
"A daga wayata,nasan cewa kana kusa,kana shirin wulaqantani ne kawai,kafi kowa
sanin zuwa yanzu zan iya rasa kudi hannuna,naji kuma ka share baka da alamun sauke
nauyin dake kanka" cikin harshen turanci ta turo wannan saqon,salon yadda take
karanta saqon da tataccen engilishinta ya matuqar burgeshi,ta karya harshe sosai
tamkar yarenta,sautin muryarta ya dinga ratsashi ya hanashi sukuni,jin tayi shiru
yasa yace
"Uhmmm,ci gaba" ba tare da ya bude idanunshi ba,sake bude dayan tayi wanda shi kuma
da hausa ne
"Kana wacce qasa?,ina son nazo na sameka mu warware sabanin dake a tsakaninmu,kafi
kowa sanin bazan iya jurewa rashinka ba......"
"Is ok" ya fada yana amshe wayar daga hannunta,don bashi da lokacin saurarar
shirmen su'ad din,ya lura ta maidashi wani qaramin yaro,ya tabbata buqatarta ce ta
taso,mai hali baya fasa halinsa,ba zata taba canzawa ba,a hankali ta soma motsawa
da niyyar sauka daga gadon,caraf taji an ruqo hannunta,da sauri ta waiwayo,still
har yanzu idanunsa na rufe
"Ina zaki?"
"Kwanciya zanje nayi bacci nake ji"
"Ni kuma bana jin bacci so ya za'a yi dani?" Ya qarashe fada bayan ya ware manyan
idanuwansa fes a kanta wadanda suka sauya launi,sunkui da kai tayi saboda wani abu
da taji yana fisgarta,hannunta ya saki yace
"Dawo ki zauna" bata musa ba cikin mutuwar jiki ta sake dawowa gurbin data
matsa,saidai wannan karon baki daya a takure take,saboda waiwayowa da yayi yana
fuskantarta gami da zubo mata ido,baisan me zaya ce mata ba,baisan ta ya zai
fuskanceta ba,bai taba tsammani akwai wata rana da d'iya mace zata yi masa kwarjini
ba,shi kadai yasan me yake ji cikin jikinsa,meke zagawa jini da jijiyarsa,tabbas
yana buqatar dauki,ya godewa Allah daya kasance akwai halalinsa a kusa,da ya
tabbatar yau babu abinda zai hana ya yanki ticket zuwa america,zuwa yanzu nauyin da
yake ji ya fara guduwa,ya soma daina fahimtar kunya nauyi izza da isa dake tattare
da shi,zuciyarsa ta fara kaiwa maqura,ajiyar zuciya ya sauke
"Bani labari.." Ya fada yana dubanta,a wannan karon yadda mamaki ya kasheta shi ya
hanata motsi bare ta dago kai
"Bani da labari" ta yanke masa hanzari tun kafin taji me yake shirin fada,shiru ya
ratsa tsakaninsu,yayin yaci gaba da qare mata kallo ta cikin lullubinta wanda
mayafin ba wani kauri gareshi ba,numfashi ya fitar da qarfi sannan yace
"Shekaran jiya kin yimin tayin samun 'ya'ya ko?" Ya fada yana duban sumarta wanda
mayafin ya zame ba tare data sani ba,sai a sannan ta dago ta dubeshi tana mamakin
me ya maido wannan maganar,kanta ta maida qasa tana murza tafin hannunta
"Ta wuce ai,tunda baka da matar da zata haifa maka din"
"Idan kuma ya kasance kece matar fa?" Gabanta ya fadi tsoro ya kamata
"Idan kuma bazan iya ba fa?"wani salon murmushi mai fidda qaramin sauti ya fitar
yana matsowa dab da ita
"qarya ne,wanda kika taba haifa fa a baya?"wannan karon ma sai data dubeshi,ya
akayi yasan ita ta haifi abdallahn?duk da ya gansu a tare amma ta tabbata baisan
itace mamarshi ba,duba da tsawan daya taba yi mata sanda ta mareshi,tsareta yayi da
idanuwanshi yana karantarta,tuni tsoro ya mamayeta,idanuwanshin kadai sun karantar
da ita me yake nufi,to amma da wacce siga yake son kasancewa da ita,mutumin da bai
gama aminta da cewa matarsa bace ma?,mutumin da bai taba cewa yana sonta ko yana
qinta ba,ita kam wai a haka rayuwarta zata kasance,ta zama rabon mutum uku kenan
nan duniya?,zuciyarta ta karye tana jin wannan karon ba zata iya ba har sai ta
tabbatar da matsayi ta,da azama ta sake motsawa da niyyar sauka,saidai ina halittar
ba daya bane,cikin zafin nama ya danne rigar baccin tata ta gefe daya ya aza duk
nauyinsa,tilas ta durqushe,jikinta ya fara rawa idanunta suka tara qwalla
"ka yima Allah ka barni matuqar kasan ba zaka iya ci gaba da zama da ni ba har
qarshen rayuwarmu,kada ka shiga rayuwata daga baya ka fice ka barta" ta fada kuka
na qwace mata,baki daya jikinsa sai ya mutu amma hakan bai kashe kaifin abinda yake
ji cikin zuciya da gangar jikinsa ba,tabbas ya sani ta taba aure amma baisan me ya
rabata da gidajenta ba,abu daya kawai ya sani ya kuma yarda da shi,baban bazai taba
zaba masa macen da bata kamaci rayuwarsa ba,tafin hannunshi ya sanya tsakiyar nata
yana murzawa a hankali idanuwanshi a kanta,ya tabbatar koma mene wani miki ne dake
zuciyarta me yiwuwa take amayar da shi ta hanyar hawaye,a hankali yaci gaba da
mutstsuka tafin hannunsu dake hade waje guda,wani abu na yawo cikin jikinsa,sannu a
hankali kukan nata ya soma tsagaitawa,har cikin jininta take jin mutstsutsukawar da
yakewa tafin hannunta,cikin sanyi ta daga kanta sai ta tsinci idanuwanshi na
kanta,kai ya girgiza mata alamun a'ah,sai ta maida sabuwar qwallar dake shirin
zubowa,hannayensa ya bude mata baki daya alamun ta taho,haka nan wani shauqi ke
jansa zuwa gareta,kai ta kawar gefe alamar ba zata iya ba,birkitota yayi baki daya
tayi masauki saman faffadan qirjinsa,jikinsa ya hadu da nata,lallausan fatarta ta
sake bashi gudun mawa wajen samun himmar aiwatar da abinda da kaikawo cikin jiki da
zuciyarsa,tamkar wanda ake kadawa gangi haka ya dinga tsuma,cikin zafi zafi yaje
aika mata da saqonni masu nauyi,wanda har suka nauyaya cikin qirji da
zuciyarta,tsoro ya kamata,tunda take bata taba tsintar kanta cikin duniyar daya
jefa ta ba,saqonni ne masu rikita qwaqwalwa da kashe gangar jiki,data rasa abunyi
sai kawai ta sake masa kuka,sam baya son abinda zai kawo cikas ga abinda ya
nufata,yayi nisan da bai tsammanin kira zai dawo da shi,bai buqatar kukanta a
wannan lokaci,sai ya hade bakunansu waje guda tare da sake jefata a wata duniya mai
nisan gaske wadda bata taba tsammatar akwaita ba.

      Tana kwance saman faffadan qirjinsa duk da kusan shudewar awanni biyu suna a
haka amma hakan bai dameshi ba,shauqi ke shawagi dashi cikin sabuwar duniya kamar
tsuntsun daya samu sararin sama,abunda bai taba faruwa ba tsakaninsa da su'ad
ba,hasalima Allah Allah yake ya tashi ya tsaftace jikinsa,saidai wannan karon jinsa
yake wani daban,ya kasa rabata da jikinsa,ya kasa tashi,hakanan ya kasa lallashinta
kukan da take fitarwa,saboda yana da yaqinin idan ya lallasheta din akwai wani
lallashin a gaba,saboda baijin zai iya barinta aziyara daya,anya daidai kunnensa ya
jiyo masa sanda baban ke fadin bazawara ce da yaro guda daya tsaga jikinta ya
fito?,har yau ya kasa tantance ainihin duniyar da yake,duk yadda yaso sake koyi da
sunna wajen yin alwala amma ya gaza samun wannan qwarin gwiwar,burinsa kawai shine
ya koma duniyar da ya fito,kuka ta sake saki sanda ya sake maidata jikinsa,tana
tunanin rayuwarta kawai yau yake nema,maganin kukan ya sakeyi karo na biyu sanda ya
rufe bakinta gaba daya da nashi.

  ******    *******    ********

      Ya jima zaune saman abun sallar da suka idar da sallar asuba yana
dubanta,yayin da take takure waje daya itama kan abun sallar tana zub da
qwalla,tasbihi kawai takewa ubangijinta tare da godiya a gareshi,tasan shi kadai ke
yadda yaso da rayuwar bawa,sosai kukan nata ke sukarshi,ya rasa ta yadda zai
lallasheta,yana jin tamkar bai kyauta mata bane,don me ya gaza haquri ya shiga
gonarta ba tare da amincewarta ba,sai ya jingina da gadon yana qarasa azkar
dinshi,ya kammala ya shafa,har yanzu bata sauya zani ba,wani mugun firgita tayi
sanda taji ya sureta gaba daya,karon farko data yarda suka hada idanuwa tun daren
jiya bayan faruwar abun,baki daya idanuwanta suyi luhu luhu sunyi ja,hawaye ne cike
da idanun,ya fuskanci me take nufi,tana tsoron ko wani abun zai sake,shi kansa yayi
makin yadda taji jiki haka,yadda ya saba tafiyar da su'ad haka yayi mata,dauke
kanshi yayi yana ci gaba da takawa har kan gadon,gyara filo yayi ya kwantar da ita
"Ba abinda zan sake miki,bacci kawai nakeso kiyi" ya fada yana ja mata bargo zuwa
kafadunta,luf tayi tana sharar qwalla gami da fitar da ajiyar zuciya
"I hate crying" taji ya fada
"Idan baki daina ba kuma zan miki abinda bakyaso" har ga Allah tsoronsa take
ji,bata marmarin sake gamuwarsu,sai ta rage jan hancin da take,kashe qwan dakin
yayi tana jinsa ya bude qofar ya fice ba tare da tasan inda zashi ba,a hankali
idanuwanta suka fara nauyi,bacci mai dadi ya sureta wanda batayi tsammanin zuwanshi
nan kusa ba.

         Minti talatin ya dawo a sanda yake zaton tayi bacci,sai ya janyo kujerar
soso ya dawo da ita gabanta bayan ya kunna qwan dakin,qaramin qur'ani ya dauka
cikin ma'ajiyarsa ya bude ya dora da tilawarsa daga inda ya tsaya cikin zuciyarsa
yake yi,saidai lokaci lokaci yakan daga kai ya dubeta,fuskarta ta sake wani
haske,kamar yadda kan hancinta da saman idanuwanta suka yi ja sabida kukan data
sha,hakanan tausayinta ya dinga ratsashi,baisan tausayin na meye ba,ya dinga tuna
wasu abubuwa da ya gani game da ita tun daga sanda igiyar aurensa ta hau kanta zuwa
yau,yasan dai koma me yayi halalinshi ya karba,amma baisan me yasa yake jin wani
bawai ba,ganin bai fahimatar karatun sai kawai ya rufe qur'anin yaci gaba da
kallonta,har yanzu akwai lema kan zara zaran gashin idanuwanta,dan qaramin bakinta
wanda kalarshi take pink ya kalla,sai ya lumshe ido yana jin wani sabon shauqi na
taso masa,ba shakka tilas su bar hotel din nan su koma gidansa kowa ya kama
dakinsa,idan ba haka bai baijin zai iya jure ci gaba da zamansu a muhalli daya ba
tare da faruwar wani abu ba,bazai iya kallon giftawarta ta gabanshi ba tare da yaji
komai ba,murmushi ya kufce masa sanda ya tuhumi kansa yaushe ka koma haka
almustapha?,bai mancewa yakan jima baiji wani abu akan su'ad ba,wani lokaci har sai
ta nemeshi sannan zaiyi ashe akwai feeling tattare da shi,har qorafi take masa bai
zuwa wajenta saidai idan ita ta matsu ta biyoshi,hannunsa ya sanya qasan gadon ya
ciro wayarshi wadda tun jiya ta fada,yama manta da su hakanan baibi ta kansu ba sai
yanzu,kunnasu yayi baki daya har ta hannunta wanda ta soma karanta mishi
saqo,murmushi ya sake saki sanda ya tuno yadda take karanta saqon a tsare cikin
muryarta mai dadin amo,yadda kowanne harafi take furtashi cikin qwarewa,baisan
yaushe yakai gareta ba,murmushi ne kwance saman fuskarshi yana zancan zucinsa shi
kadai,saqonnin su hamza lamin musaddiq ne suka dinga shishshigowa a jajjere,dan
qaramin tsaki ya ja,baki daya ya mance da cewa ya musu alqawarin zasu hadu a
masaukinsu jiya da daddaren,baibi ta kan saqonnin nasu ba ya soma lalaubar lambar
kamfanin da suka yi mishi aikin ginin gidansa,ba bata lokaci suka daga ya basu
umarnin qarasa dukkan sauran abinda ya rage cikin gidan tare da basu kalolin
furniture din yake so a zuba dakinsa da daya dakin
"Sir sauran dakin fa?" Waiwayawa yayi ya dubeta,baison wanne kala tafi so ba,dauke
kanshi ya sakeyi
"A sanua orange da fari" ya amsa musu,bai ajjiye wayar ba sai da ya musu transfer
na dukka kudin da ya rage.

      Yana shirin ajjiye wayar kiran baba ya shigo,a ladabce ya daga kiran yana
gaida baban,yayin da yake amsawa shima tare da tambayarsa harkokinsa,ya tabbatar
masa komai lpy
"Masha Allah,ina fatan komai yana tafiya dai dai ko?"
"Komai lafiya baba"
"To madalla,kadai kula da amana,Allah yayi maka albarka ya sake hada kanku"
"Amin ya Allah,Allah ya qara girma,ya jiqan mahaifa ya saka da alkhairi" ya samu
kanshi da kwararowa baban addu'o'in
"Amin ya Allah,ga umminka ita keson magana da kai" ya fada yana miqawa ummeee
wayar,cikin girmamawa ya gaidata ta amsa tana fadin
"Ina amirata?" Sake dubanta yayi,tana baccinta cikin nutsuwa,karon farko daya taba
ganin wani mutum wanda bacci ya yiwa kyau irin haka
"Nace ina amira?" Ummen ta sake maimaitawa jin shiru bai amsa ba,sam ya mance tan
kan layi
"Tana bacci ne ummee"
"Ba rana ta soma fitowa ba nan?,Ina fatan dai lafiyarta qalau ko?" Kunya ta
kamashi,yana ganin kamar ummeen zata fahimci wani abu,cikin qoqarinsa nason boye
komai yace
"Lafiyarta qalau,kawai batai isashshen bacci bane jiyan....." Da hanzari ya katse
maganar da yake sanda ya soma fahimto zaiyi baran barama
"To madalla,ka gaisheta idan ta tashin,anty maamaa tana gaidaku"
"Zataji insha Allah" ya fada yana datse layim cikin hanzaei,idanuwa ya fitar waje
yana furzar da iska daga bakinsa.

       Daya wayarce ta soma ringing,da sauri ya amsa kiran yana duban sumayya dake
kwance,haka kawai baya son ta tashi,hamza ne tashi yayi ya koma saman doguwar
kujera ya miqe a can sannan yace
"Lafiya malam da zaka damu mutane da kira da sassafe haka?" Dariya hamza ya bushe
da ita
"Wai ko ba musty na kira bane?"
"Ban sani ba dan iska,da bakasan waka kira ba?"
"Dole na fadi haka,amazingly na kiraka kana na tasheka da sassafe,naga kai din baka
da lokacin kira,any time ur available" yasan tabbas magana ya gaya mishi don hakan
yake,su din ne har basu so a fiddasu daga gida da daddare ko a sasu tashin
wuri,hakanan yau yake jin kansa shima as magidanci ,yake jin kansa wani na
daban,ashe haka suke ji idan aka kirasu da sassafe haka,shi daya ne baya damuwa
saboda baisan ana jin haka ba idan aka kira mai iyali da wurwuri ko idan dare ya
fara turawa ba
"Naga alama ka fara rainani wallahi hamza,ni kake gayawa am available always?"
"To qarya nayi,idan banda rainin wayo jiya saika shanyamu muna ta jiranka har sha
daya na dare na baro abida ita daya a gida?"
"Sannu tattabara sarkin aure,to nima fitarce bazan iya ba na bar....." Idanunshi ya
dauke ya dora a kanta yana ware mata kallo,sai ya rasa sunan da zaya kirata da
shi,dariyan da hamza ya qyace da ita ta sanyashu runtse ido,hayaniyar har tsakiyar
kansa
"Hey,ar u mad,a kunnena kake wannan gadar?"
"Aci amarci lpy my maan,sai ka fito" ya fada yana datse kiran,maimakon yaji haushi
yadda suka saba yi da hamzan sai murmushi ya subuce masa,ya sauke wayar daga
kunnensa yana kwanciya rigingine yana kallon saman dakin,hannunshi kan sumarshi
yana shafata a hankali,jinsa yake fresh tamkar wani sabon mutum,wani farinciki ke
ratsashi
"Iyalina,matata,mata ta na bar ta ita kadai,matata bata son wannan,mata ta tana son
abu kaza,mata ta tana buqata ta,mata ta ce ta kirani,mata ta ce ta yimin,ina son
naji muryar mata ta,nayi kewar mata ta,iyalina sunyi kewata,mata ta zan siyawa,mata
ta tace na siyo mata,mata ta tana neman izini na" dukka wadan nan lafuzan a bakin
hamza da sauran abokai yake ji,dai dai da kalma daya cikin jerin gwanin wadan nan
kalmomi baisan da zamansu ba aduniyar ma'aurata,duniyar zamantakewar aure,sai gashi
cikin watanni hudu ya soma sanin wasu daga cikin kalmomin,kamar jiya da ya kasa
fita saboda karantar wani yanayi na takura da rashin sakewa tattare da ita,ajiyar
zuciya ya saki yana sake maida idonshi kanta,maganganun da baba ya gaya mishi ke
masa bita daya bayan daya cikin qwaqwalwarsa.

          Cikin jin kunya da nauyi take komai,duk inda ta motsa tana jin
idanuwanshi a kanta,har ta kammala azkar dinta ta miqe ta nade sallayar bata
dubeshi ba,rabonta da kallonshi kwanaki hudu kenan,duk abinda zaice mata saidai ya
fada tana duban wani gun,sauqin abun ma kwana biyu suna wani taro na mutanen da
suka mallaki kamfani a qasar,bai shigowa sai bayan magariba,takanyi qoqarin yin
bacci ko na qarya ne kafin ya shigo din,bata san me ya sanya take jin kunya da
nauyinshi ba,irin nauyin da bata taba jinsa ba tattare da sauran mazan data
aura,shima qoqarin tura mata saqo sau biyu a rana najin lafiyarta,duk don kiyaye
amanar da aka bashi,bata bata dubawa ba sakamakon tana tunanin duka saqonnin nashi
ne,saidai abu daya daya tsaye masa a tunaninsa wanda ya rasa dalilin haka,dare
qwaya daya tak wanda yayi karen tsaye a tunaninsa,har yau yaqi goguwa daga
idanuwanshi,sau tari tunanin wannan dare yakan wafci duk aikin da yake ya fado
ciki,saidai ya tsinci kansa ya saki murmushi yana girgiza kai,yayin da hamza aka sa
masa ayar tambayar wai me ya maidashi haka?,harara yake watsa masa yace zai daddaki
hancinsa idan bai fita sabgar rayuwarshi ba,dariya yake masa tuburan ya bashi
waje,yasan dai tabbas ruwa baya tsami banza,haka nan ya samu kansa da yin addu'ar
Allah ya sanya canjin da suke fata ne ya soma samuwa.

      Qoqari yake su hada idanu amma abun ya faskara taqi yadda,duk inda ya kalla
sai ta kauda kai,tun daga ranar taqi yadda ta dubeshi,har abun ya zame musu tamkar
game,shi ya dage sai yaga qwayar idonta ita kuma qememe taqi,kamar yanzun data
gwammace ta zubawa t.v idanu,wanda yasan hakan ba al'adarta bane,tunda suka zo bata
taba kunna tv don radin kanta ba,dan qaramin murmushi ya saki na gefen baki,sai ya
miqe ya isa ga makunnin tv ya kashe,janye idanuwanta tayi,ta rasa inda zata tsoma
ranta,yayin da shi kuma bai fasa kallonta ba,shigarta qarewa kallo yana ambatar
bahaushiya cikin ranshi,atamfa ta sanya dinkin zani simple,sannan ta saka riga halp
buba wadda iyakarta gwiwa,kayan sun mata kyau duk da cewa baki dayan dinkin simple
ne
"Miqo min ruwa" ya fada wai ko zata kalleshi,miqewa tayi tsam ta isa ga freezer
tana mamaki,don bai taba sata yin wani abu ba saidai idan tayi niyya don radin
kanta.

       A hankali take takowa zuwa inda yake yana satan kallonta har ta qaraso ta
tsugunna ta zuba cikin cup ta miqa masa,sai ya hade cup din da hannunta baki
daya,sai a sannan ta daga kai da sauri ta dubeshi jin yadda ya matse hannun jikin
cup din sanyin na ratsata,da hanzari ta maida idanun wani wajen,baisan sanda
murmushi ya subuce masa ba,ashe haka kunya ke yiwa mace kyau?,abar data sanya auren
'yan arewa ya fice masa a kai kenan da fari,jin cewa kunya ta sanya sun zama wasu
iri,basu iya nunawa miji zallar qauna,sai gashi yau yaga kunya a muhallin data
burgeshi
"Tashi ki tafi,tunda tsoron kallona kike" kunya ta sake kamata,sai ta miqe zata bar
wajen,qafa ya sanya mata ta dawo da baya baki daya ta fadi jikinsa,sai ya lullubeta
da hannayensa gaba daya ya soma yamutsata yana sane,so yake yaga ya zata yi,ai kuwa
tuni ta bare baki zata saki kuka,har yanzu cinyoyinta basu bar ciwo ba hakan
yasanya ya sake ta babu shiri,idanunta sun cika da qwalla,sai ya sake sakin
murmushi,yanayin kawai ya burgeshi,ya motsa bakinsa da niyyar tambayarta shekarunta
saboda yadda quruciya ke bayyana aduk wani motsinta sai kuma ya fasa,hannunsa ya
sanya ya dauki wayar da ya batan wadda ke daura da shi,a nan yaci karo da dukka
saqonninsa da yake turowa ba guda daya data taba
"Wannan fa?" Ya fada yana haska mata wayar,duban wayar tayi na wasu 'yan sakanni
kafin ta dauke kai
"Ban zaci nawa bane" dauke idonshi yayi daga kanta ya maida kan wayar,deleting din
saqonnin yayi baki daya sannan ya kashe wayar ya sanyata cikin aljihunsa.

****** ****** *******

Zaune yake cikin ofice dinsa,aika saqo yake cikin zafin nama qwarewa da kuma
gaggawa saboda yana son ya gama ya saurari hamza dake zaune yana jiransa
"Kuskure ne?,kai din baka so?,shekarunka nawa a duniya?,ina tsammanin zuwa yanzu
zakayi sha'awar samun diyan kanka" magan ganunta suka fado masa ya tuna yadda
qaramin bakinta ke motsawa sanda takw furucin,murmushi ya subuce masa yana girgiza
kai,tana da confidence,saidai akwai tsoro da kunya tattare da ita
"Man anya lafiyanka daya kwana biyu kuwa?" Maganar hamza ta katseshi daga duniyar
tunanin da ya tafi,idanunsa ya zubawa hamza baki daya gami da dauke hannayensa daga
kan madan nan cumputer din ya dafe kanshi da su
"Tambayarka nayi lafiya kake?"
"Na haukace" yayi furucin kansa tsaye yana ci gaba da kallonsa,dariya hamzan ya
saki
"Kana gab dai da haukacewar,don iya sanina da kai ban taba ganinka kana murmushi
kai daya ba tsawon rayuwarmu sai wannan qarnin,anya baka fada tarkon soyayya ba?"
"Ba tarko na fada ba rami na rufta qaramin mara mutunci,sau nawa zance ka fita
harkata hamza?"
"Anqi a fita din,idan kaji haushi ka bayyanawa duniya ka soma son wata diya mace
sai ka huta da binbini na" apple din dake gabansa ya dauka ya jefa masa ta sameshi
a qirji ya cafe yana dariya
"Na gaya maka zuciyata ba'a halicceta don tayi soyayya ba,kudai da kuka afka sai mu
tayaku da addu'a Allah ya......" Zancansa ya katse sanda wayarsa ta soma ruri,umme
ce ke kira,saboda haka ya saki duk abinda yake ya amsa kiran,cikin girmamawa ya
gaidata ta amsa mishi sannan ta dora da cewa
"Na kira ne na shaida miki bikin qannenka nan da three weeks,so nasan ba lallai kai
ka samu zuwa ba qila sai ana ya gobe daurin aure,so ina so ko nan da sati daya ka
turo sumayyan ta fara yo gaba,taje gida ta musu sati idan yaso satin bikin idan ya
kama sai ta taho nan"
"Hakan ya miki ummee?"
"Eh idan ban takura muku ba"
"Yadda kika ce haka za'ayi,Allah ya sanya alkhairi"ta amsa tana sanya masa albarka
sukayi sallama,idanunshi ya maida kan cumputer din yana ci gaba da danne danne
"yaran nan sun dage sai sunyi auren nan daga kammala karatunsu hamza"
"Sai aka ce halinku sai ya zama daya dole,me yafi ransu,dai dai kenan,to me zasu
jira?"
"Allah ya taimaka" ya fada yana ci gaba da aikinsa.

Sai da ya gama ya saurareshi,rigunan da aka gama hadawa ya kawo masa yaga


irinsu
"Na bawa wadancan guys din zasu zuba lefansu"
"Ba laifi" ya fada yana ajjiye rigar
"Ya sunyi?"
"Kasan ba ganewa nake ba, abawa stores din samfuran su gani idan design din yayi"
daya hamza ya fidda yana ajjyewa gabanshi
"Wannan karon zaka gane idan ka ganta a gidanka tunda ba'a saba sawa ba,ka kaima
sumayya ta gwada maka sample ka gani yadfa abida kemin" baki almustapha ya tabe
yaba dubanshi
"To sarkin abida madalla"
"Zakayi bayani ne" inji hamza yana dariya tare da ficewa.

***** ***** **** *****

Cikin kwana hudu ya gama shirya mata tafiyar ba tare data sani ba,randa komai
ya kammala ya tashi office qarfe shida na yammaci saboda baqi da sukayi,yana
tattare files dinshi yaci karo da rigar da hamzan ya bashi tun rannan,jefata yayi
cikin jakarshi ya dauka ya fice.

Sai daya tura qofar yayi sallama,tana zaune saman abun sallah tana
karatu,yana mamakin yadda bata gajiya,bayan kowacce sallah sai ta zauna tayi
tilawa,karatun ta katse kanta na gefe tayi masa sannu da zuwa,ga mamakinta yau bai
amsa ba,safa takalmi 'yar saman suit dinshi duka ya cire ya shige bandaki,wanda
dama yana dawowa wanka yake fara yi kafin ya saurari abinci,wanda sunsan lokacin da
suke kawo masa dama daga wani wajen saida abinci dake daura da hotel din,duk sai
taji ta wani iri saboda rashin amsa matan da baiyi ba,qur'anin ta rufe kamar yadda
ta saba ta dauke socks da takalmin ta musu waje,haka suit din ta ratayeta sannan ta
samu waje ta zauna tana jiran fitowarshi.

Kanta ta sake daukewa sanda yake fitowa daga bandakin daure da towel a
qugunshi,wanda hakan ya bayyana uban albarkar gargasar dake ilahirin jikinsa,abinda
bai taba yi ba fitowa haka,saidai ya fito da rigar wanka,nauyinsa taji ya
kamata,sai ta miqe a hankali tana maimaita yi masa sannu da zuwan tana nufar qofa
"Dawo ki zauna" ya bata umarni ba tare daya amsa sannun tata ba,cikin jin nauyi ta
koma da baya ta zauna,ya isa gaban mudubi ya soma tsane jikinsa yana qare mata
kallo ta cikin mudubin,baki daya a takure take kamar zata zura da gudu,dariya ta
taso masa amma ya danneta,ta maidashi kamar wani dodo tun daga ranar da suka hada
shimfida,baki daya bata iya masa wani cikakken kallo
"Yau zanga qarshen kunya" ya fada a ransa
"Zo nan" yace da ita
"Ni?" Ta tambaya tana raba idanu,kicin kicin yayi
"Da wa?" Miqewa tayi tana takawa a hankali har ta iso bayanshi ta tsaya,towel ya
miqa mata cikin halin ko in kula
"Jikina zaki tsanemin" sakato tayi kamar zatayi kuka,baice uffan ba ya kafeta da
ido,a sanyaye ta karbi towel din,cikin sanyin jiki,sai ta gaza motsawa tayi tsaye
riqe da towel din
"Uhm,bismillah ina so na shafa mai ne fa"qwal qwal tayi da idanu sannan ta matso
tana dauke idonta daga kallon jikinsa saboda yadda yayi mata kwarjini,bugu da qari
sai tq zama wata 'yar cukul a gabanshi,sai da ya wanata,dariya a cikinsa kuwa kamar
zata fito amma yana maidata,wanda a zahiri fuskarsa ba haka take ba sannan ya amshi
towel din yana fadin
"ba abinda kika iya ma"baki ta tura cikin ranta tana qunquni
"Haka kawai dama mugunta ce tasa kace sai nayi,kai ko kunyar abinda ka aikata ma
baka ji" bude jakarshi yayi ya fito da abayar ya miqa mata sannan ya zuba mata
shanyayyun idanunshi.

Kuyi manage da wannan,ina da uziri,koda gobe baku jini ba kuyi haquri,idan kuma ya
samu falillahil hamdi,na gode.
*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

8⃣4⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

*Allah madaukaki yana cewa*

*HAQIQA ABINDA AKE YI MUKU ALQAWARI/ALWASHI(NA ALQIYAMA)MAI ZUWA NE,KU BA MASU


TSEREWA ALLAH NE BA*

Allah ka sanya farinciki a zukatanmu a wannan rana,ka sanyamu qarqashin inuwarka.


_____________________________________

*WANNAN SHAFI SADAUKARWA NE GAREKU,HAQIQA ALKHAIRINKU GARENI BAZAN MANTA BA*

*SISTER AINA'U(HUGUMA CONVERSATION)*

*TASH (INSPIRING STORIES GROUP)*

       Hannu biyu ta sanya ta karbi rigar tana kauda kai daga kallon da yake mata
wanda sam bata sonshi,yana sanyata jin wani irin abu da nauyi cikin jikinta
"Inji hamza" ya fadi yana juyawa gaban madubi yana ci gaba da taje sumarshi hankali
ta furta
"Na gode,Allah ya saka da alkhairi" bai amsa ba saici gaba da kallonta da yake ta
cikin mudubi,bai tsammaci jin wata addu'a ko godiya daga bakinta ba,don hamzan
yasha yiwa su'ad kyauta wanda ta ninninka haka saidai ta karba ayatsine,wani lokaci
idan ta duba ma takance
"Shikam baisan me yasa bai iya kyauta ba,yana qarqashun mijina yana aiki yana cin
arziqinsa ya rasa mai zai bani sai wannan?" Harara yake jifarta da ita almustaphan
sannan yace
"Ki shiga hankalinki su'ad,hamza ba aiki yaje qarqashina ba kafada da kafada muke
aiki,ba tilas sai ya miki kyauta ba don ba qasanki yake ba,ki gyara bakinki" hakan
na mata ciwl,don ita a duniya ba abijda ta tsana irin a daidaita matsayinta dana
wani,wanin ma dake gain kamar bai isa komai ba.

      Wayarshi ce ta fara tsuwwa,ga zatonshi ma umme ce zata ce ya hadata da


sumayya,saboda haka bai ko dubaba ya daga yana karawa akunnensa,ya maqaleta a
kafadarshi yana ci gaba da shafarshi,muryar su'ad ce cikin bacin rai da kwantar da
murya cikin harashen nasara
"Ashe da gaske ne abinda akefadi idan namiji yayi aure wulaqantaki yake?,yanzu a
haka kakeso na yarda na karbi kishiyar da ka yimin mu zauna tare?"shiru yayi tamkar
bai kam layin har sai data kira sunanshi,kawai sai ta saki kuka harda
sheshsheqa,cikin harshen hausa da son dawo da qauna cikin zuciyar wanda kuke magana
tace
"almustapha kasan duk duniya babu wani abu da nake qauna sama da kai don me zaka
yimin haka?"
"Look su'ad,wannan baki daya matsalarki ce ni ban da case da duka zantukanki,i
think na gaya miki dukkan wani rules nawa ko?,so pls idan zaki iya bi bismillah,if
not ki qyaleni na huta hakanan"
"Ni kake wulaqantawa haka maan?"cikin fushi yace
"if u dont like how things are,take control,decide how u ar going to change it,kada
ki sake nema na daga yau,take me as iam,or leave me as iam"katse layin yayi ya jefa
wayar gefanshi,cikin bacin rai yaci gaba da shiryawa sauri sauri,sumayya kam tunda
taji ya ambaci su'ad ta miqe ta shige toilet,dama wanka take sonyi wanda yau bata
samu tayi da wuri ba tun na safe da tayin.

         Cire wayar su'ad tayi daga kunnenta sanda ta fahimci ya katse kiran
nata,duk da ba yau ne farau ba idan tazo masa da shirme amma wannan yayi matuqar
baqanta mata,gani take kawai saboda ya sake aure ne ya sake qaro wulaqanci fiye da
wanda ta sanshi da shi,hawaye na bin idanuwanta ta dubi mamanta,sannan ta dubi
qanwar maman nata anty kubra dake zaune tana kallonta wadda ke zaune ita mijinta a
south africa,ta zo ne american wajen yayarta ta tadda wannan cakwakiyar
"Ba sai kince komai ba naji komai,ai wallahi laifinki ne khaulat,ta yaya har zaki
bari su'ad tayi wasa da damarta,kunfi kowa sanin samun damar auren irin su
mustaphan sai wanda Allah ya zaba nan gidan duniya,tun tuni kallonku kawai
nake,yarinya tana gantalinya da sunan karatu,karatun uwar me?,me zata ci da
karatun?,me take nema da shi?,dame mijinta ya rageta?,bata taba tambayarsa abu
komai yawansa yace mata babu ko bazai bayar ba saidai ma ya ninka mata,kuna zaton
miji irin mustapha wanda Allah ya yuwa baiwar kyau da kudi zai zauna bai sake
aureba bayan yana da mace irin su'ad?,to ta godewa Allah ma daba neman mata yake ba
ya kwaso wata cutar ya laqaba mata,kinga idan zaki zubar da wannan gantalallen
karatun naki kije ki kwashu makaman qwatar mijinki kije ku buga ke da ita mai rabo
ka dauka to,ta taki qatuwar sa'ar samun auren elmustapha bayan gwagwarmayar da aka
sha,duk da tasan cewa ba sonta yake ba amma tausayi da qaunar da take masa ya sanya
ya amincewa aurenta" ta fada tana maida numfashin takaici
"To kuma kubra me ya kawo tonon silili haka?,abinda ya wuce ai ya riga ya wuce
ko?,kawai shawara muke da buqata"
"Ki tattarata ta koma gidanta,ko a kango yace ta zauna ba nijeria ba ta zauba,bare
ma meye marabar gidan nata da nan din?don kawai tana cikin family house,kowa ya
sani qaryarka kace gidan mutum kamar almustapha an rasa jin dadi da walwala da
dukka wata qawar duniya,idan zata koma taje kowa ta qwaci mijinta to,idan kuma zama
zatayi bismillah saikici gaba da dorata akeken bera ki kuma share mata wajen
zama,kinsan dai ko auren ta kaso wallahi duk yadda takejin kan nan nata a sama ba
zata samu wanda ya koda kama qafar doctor mustapha ba"
"Ya isa kubra don Allah,ke dole sai kin zagi mutum zakiji dadi" waiwayawa haj
khaulat tayi ta dubi su'ad dake zaune hawaye shabe shabe,har cikin qirjinta taje
jin kishin mustapha,tamkar ta dauki ran wadda ta aure mata shi haka take ji,kullum
kwanan duniya ji taje kamar ta yanki ticket ta koma masa,don tun kafin a kai ko ina
ta soma raina kanta,ta tabbatar rabuwa da mustapha kamar yadda tayi iqirari ba mi
yiwuwa bane a rayuwarta,ko sakinta yayi tana jin ba zata iya qara aure ba har ta
mutu,don gani take nan duniya babu kamar yashi
"Zaki shirya ki koma wajen mijinki,daga yau so nake kada ki saurara kada ki daga
qafa,duk inda ya sanya qafa ki bishi,sai kin tabbatar kin mamaye rayuwarshi,sannan
cijin gidan bance ki saurarawa uban kowa ba,fin baki dayansu munafukai ne,suna da
masaniyar qara auren nasa su suka hada,ki taka uban kowa koda kuwa hajiya
zuwairiyya ce uwarsa kinji na gaya miki,ki fara shiri,naji labarin biki ya tasi a
gidan,zaki isa ranar daurin aure don kiga idon uban kowa,uban kowa yaga naki idon
ihee"kai su'ad ta gyada cike da gamsuwa da samun qwarin gwiwa,itadai kubra na gefe
tana kallonsu tana tabe baki,ta tabbatar zamansu bazai taba daidaita da mustaoha ba
matuqar tace zata taba iyayensa,kai ta dauke tana qissima yadda dramer zata kwashe.

        Minti talatin cif ta fiti daga bandakin,ba kowa cikin dakin alamar ya
fita,hakan ya sanya cikin nutsuwa ta fara shiryawa bayan ta kulle qofar,sai data
gama komai tsaf sannan ta bude ledar daya bata ta zari rigar ta wareta,sosai rigar
tayi mata bata taba ganin irin desing dinta ba,bisa dukkan alamu sabuwar design ne
dako kasuwa bata kai ga fita ba,sai taji tana sha'awar sanyawa,saboda haka kai
tsaye ta zirata ta daidaita ta ajikinta,cif cif tayi mata har fadin tamkar an
gwadata,ta fidsa shape din qirjinta sosai zuwa faffadan qugunta,qila hakan baya
rasa nasaba da tsahonsu da ya kusa zuwa daya da abida,saidai abidan ta fita
jiki,don sake qawata rigar a jikinta sai ta bude inda take ajiyar dankunnayenta,ta
sanya dankunne da 'yar sarqar hannu wadda ta dace da kalar dutsen da aka qawata
rigar da shi,yafa mayafin kawai tayi bayan ta daure gashinta,sai ta fito tamkar
wata balariyar qasar,murmushi ta saki sanda ta kalli kanta a madubi,ba shakka tayi
amsheta rigar,wayar dake gefanta ta jawo ta dauki hoto guda biyu,zata qara sai ta
tuna ta almustapha ce,ajjiyeta tayi inda ta dauka ta wuce zuwa saman kujera kuma
gadonta ta koma ta zauna ta janyo littafin wajen anty dije taci gaba da karantawa
karo na biyu tunda ta bata shi.

       A quntace yake takowa zuwa qofar dakin nasu cikin tafiyarshi ta


qasaita,ranshi har yanzu a matuqar bace yake,hannunshi ya sanya ya murda handle din
da niyyar turawa ya shiga sai yaji qofar a rufe tanke,ranshi ya dan baci,ya soma
knocking a zafafe,littafin ta ajjiye cikin fargabar yadda ake qwamqwasa qofar,ta
isa bakin qofar cikin siririyar muryarta tana fadin
"Ana zuwa" ta janyo qofar baya,idanunshi suka fada kanta ba tare da ya shirya
ba,kallo ya shiga qare mata tun daga yatsun qafarta zuwa kanta,ya dawo ya dire a
qirjinta,boyayyar ajiyar zuciya ya saki,bai taba tsammanin rigar da suke fitarwa ta
kai kyawun haka ba duk da yasan yadda suke zuba fasaha wajen saqata ba sai
yau,dalili kuwa bai taba tsayawa ya qare mata kallo jikin wata ba sai yau din,koda
ya kawowa su'ad bai taba gani ta saka ba,hasalima saidai ta bayar ko tayi kyautar
neman suna,ita dole ace mijinta ke da MM VAIL AND ABAYA INTERNATIONAL COMPANY,amma
bata taba rabata a jikinta ba,a cewarta tayi mata nauyi ko zata bata mata tsarin
shigarta duk kuwa da yadda abayar ta kai ga kyau da tsada,sosai shigar abaya ta
sake burgeshi duk da dama can yana sonta,da sauri ya hade fuska sanda suka hada
idanu ta kama shi yana kallonta,baya taja a hankali cikin tsoron irin kallon da
yake kata,takowa ya soma yi zuwa ciki murya a dake yana fadin
"Idan da wani ne kuma kr bugawarfa,kawai saiki bude ba tare da kin tambayi waye
ba?"
"Ai nasan kai kadaine zai shigo"
"Ba tabbas,hotel ne dont do this again"
"In sha Allah" ta fada kai tsaye kuma cikin sanyi,sai amsar tata tayi masa dadi,a
hankali sai ya dinga lalubar bacin ran nashi yana rasawa har zuwa sanda ya dubeta
sanda take nannade saman kujera tana ci gaba da duba littafin
"Ki shirya kayanki,nan da gata zaki je naijeria" a ba zata maganar tazo mata,sai ta
dago kai tana ware fararen  idanuwanta a kansa tana bude baki cikin tsananin
farinciki har batasan sanda tace
"Da gaske?,da gaske kake don Allah"
"Ni abokin wasanki ne" ya fada yana mai fatan ta janye fararen idanuwanta daka
kanshi,wani feelings akanta ke son kamashi,idanuwa ya lumshe sanda ta girgiza kai
alamun a'a ta janye idanuwan nata daga kanshi,saidai murmushin dake saman fuskarta
yaqu boyuwa,sake bude idanuwan nashi yayi a hankali ya azasu kanta,wanda ita bata
ma sani ba ta tattara hankalinta ga littafin duk da ba karantawa take ba,zai iya
cewa bai taba ganinta cikin farinciki haka ba,sai ya sake maida su ya rufe
again,baya son abinda yake ji a kanta yaci gaba da tasiri a kanshi,don matuqar yaci
gaba da tasirin to zai jagoranceshi ya aikata koma mene,tun wancan daren zuwa yanzu
bai taba samun sukuni ba duk sanda tunanin moment na daren ya fado masa,sai yaji
kamar ana mintsini ko tsikarinshi,baiso ya karya alqawarin da ya daukarwa kanshi a
kanta,hakan ya sanya tilas ya kwanta duk da baijin bacci,da qyar ya samu bacci ya
daukeshi.

*******   ********    ********

      Baki daya ta kasa sukuni tunda ya shaida mata tafiyar,ji take kamar tayi
tsuntsuwa ta ganta a gida,har ya fura lura da irin dokin da takeyi,ana ya jibi zata
tafi kuwa ta kwashe kusan duk wani abu nata mai muhimmanci tayi parkinga nasa waje
guda.

       Ana ya gobe kuwa zata tafi har ya kwanta tana ta zirga zirgan hada komai
nata,ya jima kwance cikin bargo yana kallonta cikin kayan bacci,wanda ita har ga
Allah ta tsammatar masa bacci,mamakin irin zumudin da take kawai yakeyi,sai tayita
sakin murmushi ita kadai.

        Shi da kanshi yake tuqa motar zuwa filin sauka da tashin jirage na
qasar,yayin da m'aikatansa biyu ke binsu a wata motar ta daban dake bayansu,har
suka isa airphort din wani farinciki na ratsata,musamman data duba ticket dinta
taga jirgin zai sauka kano ne,hakan na nuna cewa gida zata fara isa,waiwayowa tayi
sanda aka fara kira matafiyan da zasu tashi zuwa nijeria ta dubeshi,sai ta sadda
kai ta rasa me zata ce
"Allah ya tsare,ki gaida su"ya fada hannayensa zube cikin aljihunsa,wani yanayi ke
ratsashi wanda baisan na meye ba,kamar wani abu na neman gushewa daga gareshi wanda
ya jibanceshi,ranshi a bace yake haka kawai baijin duk wani karsashi da
farinciki,dagowa tayi ta dubeshi suka hada idanu
"zasu ji,na gode"
"Ba case" ya fada yana ci gaba da dubanta ba tare da ya janye idanuwanshi ba,a
hankali ta daga qafafunta tana takawa,tana jin idanuwanshi a kanta,ita dinma sai
taji karsashinta da murnarta na dan raguwa,sabo ne take zato wanda hausawa ke cewa
turken wawa,ko dabba ce kana tare da ita randa kuka rabu sai kaji wani iri,yana nan
tsaye hakanan ya kasa tafiya har ta bacewa ganinshi sannan ya juya a hankali ya bar
wajen,kwance yayi cikin salo na kashingida abayan motar drivan ka janshi wanda ya
kama tashar gidan redion dake qasar,umarni mustapha ya bashi kan ya kashe,baison
hayaniya,
"Sorry sir" ya fada yana kasheta.

     Cikin awannin da basu da yawa suka iso qasata nijeria,tuni mota daga gidan
baba prof dake kano ta iso tana jiran ta,tamkar jira wayarta take ta soma ruri
network ya dawo,ta laluba aljihun jakar na baya ta zaro wayar tana dubawa,amira
ce,murmushi ya subuce mata tana mirgina kai
"Wohoho amira,i missed you wallahi so much" ta fada a fili sanda take shigewa bayan
motar sannan ta daga wayar,wani ihu da amiran ta sakiwa kunnuwanta sai data rufe
ido
"Kunne na amira kunne na"
"Wallahi kaman a mafarki namecy ashe kin iso,last week muka je umra na takurawa my
saif sai munje wajenki wallahi yaqi wai nauyin ya musty yake ji,wayyo namecy kina
ina?"
"Saukata kenan ko gida ban qarasa ba,ina mota a kani na sauka,next week insha Allah
zan qaraso"
"Qarasa gida namecy ki huta akwai labarai wallahi" ta fada tana dariya,murmushi
sumayya ta saki
"To ba damuwa"
"Ki gaidan mama,amma fa idan naga ba dama zan biyoki na zaqu wallahi naga matar
yaya na" dariya suka sa baki daya sumayya ta kashe wayar,har yau amira halin dai
bai sauya ba.

        Saboda murna bata iya tsayawa an shiga mata da kayanta ba,wanda itama
batsan da kayan bama sai da suka sauka ta gansu,da sallama ta kutsa kai tsakar
gidan,wata dake shirin shiga kitchen ta dakata ta juyo,halima ce,ta zama wata
babbar mace,haliman da ake zaton ba zatayi qiba ba saiga kumatu a fuskarta,da gudu
ta nufo sumayya suia rungume juna kowa na ambatar sunan dan uwansa,hayaniyar ita ta
sanya mama dake falon ta daga labule ta leqo
"Kada dai kicemin gudu kike halima me yasa kike da kunnen qashine wai?" Sak maman
tayi sanda sumayya ke dagowa,bakinta har kunne,da hanzari sumayya ta saki halima ta
nufi mama tana kiran sunanta,hannayen mama ta kama ta riqe gam qwalla na taruwa a
idonta
"Me kuma na kukan ne sumayya?" Maman ta fada cikin farinciki sanda sumayyan ta fada
jikinta,dakin suka shige baki daya farinciki zuciyar kowannansu ba magana.

        Nan da can kowa ya kasa motsawa cikinsu,anata hirar yaushe rabo,mama nata
kallon sumayyan,farinciki na zagayata,bata taba ganin diyar tata cikin kyakkyawan
yanayi makamancin wannan ba tunda take aure,wani kyau haiba da cikar kamala,ta sake
zama babbar mace qwarai,da alama hankali ya fara gameta,ita kuma sumayyan na duban
halima sannan ta dubi mama
"Wai dama mama halima zatayi qiba?" Murmushi ya subucewa maman
"Gata nan kuwa sumayya"
"Masha Allah,lallai abdur rahman ya iya kiwo"
"Har ya kai yayanmu,wai baki kallon madubi ne yaya,wallahi sanda kika shigo na zaci
baquwar balarabiya mukayi Allah kuwa kada ki dauka sharri ne ko mama baki gani ba?"
Murmushin jin dadi maman ta saki
"Masha Allah kam" sai kunya ta kama sumayya tadan rausayar da kai,idanunta ya sauka
kan abdallah dake kwance yana bacci,baki ta bude
"Kai dama mama yaron nan na gunki?" Dubanshi sukayi baki daya
"Sunzo dai tare da mamarshi halima,abdur rahman yayi uwa yayi makarbiya ya karbe
abdallah daga gunmu baki daya,baki ga dambun tsiyar da aka dinga yi tsakaninsa da
yahanasu ba amma yace saidai tayi haquri shida mu saidai ziyara" kai take gyadawa
taba duban halima,dariya ta saki
"To ai koni bazan bada abdallah ba Allah yanzu ko kece saidai ki haqura" dariya ta
saki
"Ni meye mawa,dama abdallah ai danku ne,kuyi duk yadda kuka ga dama da shi,Allah ya
qara zumunci" miqewa mama tayi ta basu waje don sauke tukunyar abinci,wanda halima
ba zata iya ba sabida an hanata duk wani motsi mai qarfi sabida juna biyun da take
da shi wanda bai wuce wata daya da rabi ba,a nan haliman ke gayawa sumayya da kuma
barin da zainab tayi wanda ita taje dubawa ma ta biyo ta gida,baki sumayya ta saki
tana dariya tare da duban halima
"Kai halima ko kunyata bakiji,Allah ya inganta mana ya raba lafiya" cikin jin 'yar
kunya ta amsa.

        Sosai sumayyan ta zage ta daki abincin,ba qaramin missing abincin gida tayi
ba,wanda kullum suna fama dana hotel,wanda idan ba fried rice ba bata iya cin wani
abu sosai saidai kawai ta taba sama sama,da qyar ta yakice ta kira nafisa ta shaida
mata zuwan ta,kamar ta ballo itama tazo haka take ji,amma sumayyan ta gaya mata
satin sama tana tafe,tace tana nan tana jiranta,daga nan anty dije ta kira,bakin
antyn har kunne,itama ta zaqu taga sumayyan,sun dan jima kan layi kafin suyi
sallama,sun sha hira qwarai,a nan mama ke bata labarin irin gidajen gonar da baba
prof ya damqawa malam yace nashine,tun tsohuwar dukiyarsa da bai tsaya da juya masa
ba,irin hayayyafar da tayi,kai kawai sumayyan ke kadawa,babu shakka samun abota
irin wannan tana da wuya a wannan zamanin,wani qima da mutuncin baba ke sake
hauhawa cikim zuciyar sumayya,qaunarsa na sake kamata,qauna ta fisabilillahi wanda
tun kafin tasan matsayinsa wajen mahaifinsu take masa ita
"Allah ya saka da alkhairi ya cika masa burikansa duniya da lahira" amsawa itama
maman tayi,tana sake gaya mata ci gaban da aka samu,kwanaki kadan ya rage subar
wannan gidan zuwa wani sabin gidan da malam din ya saya,wanda da baba ne zai biya
malam din yaqi,dawainiyar da karamcin tayi yawa inji malam.

       Farincikin da malam yaji sanda yaga diyar tashi ba mai misaltuwa bane,ido ba
mudu ba yasan kima,yasan cewa bisa dukkan alamu addu'ar da yake binsu da ita dare
da rana zatayi tasiri a kansu,sun jima sosai suna hira da malam har kusan sha daya
na dare,shi da kansa ya sake warware mata abinda ya faru na danqa masa gidajen
gonakinsa da baba yayi,wanda har yau basu ma je na wasu garuruwan ba,addu'a sosai
ta yiwa baban malam na amsawa.

        Washegari tare suka karya ita da malam din da abdallah,wanda abdur rahman
yace a barshi yaga mamanshi har sanda zata tafi,shi kansa abdur rahman din
tsokanarta ya dinga yi yana cewa manyanmuyaya sumayya,raha suka yi sosai kamar babu
wani abu da ya taba faruwa tsakaninsu,dariya ta dinga kawai,shi kansa ya sauya ya
sake zama magidanci,alamun hutu da kwanciyar hankali baki daya sun bayyana tattare
da shi,cikin zuciyarta tana gode ma Allah,tasan ko ba komai 'yar uwarta na cikin
rayuwar jin dadi da walwala kamar yadda take fata.

       Kwalayen jiya ta bude ta duba,uwar tsaraba ce a ciki,akwai wasu dake nannade


da sunayen malam da baba,bata taba ba ta miqa musu cikin mamaki,sai take jin wata
qimarsa cikin ranta
(Gareku maza,abune mai kyau ka dinga kyautatawa iyaye da 'yan uwan matarka,don haka
na qara qimarka a idanunsu da idanun matar taka gaba daya,ko yaya alkhairi yake
dadi gareshi,Allah ya hore ya kuma bada iko amin),sai data gama sannan ta shirya
zuwa gidan zainab,ranan can ta wuni baki daya,ta sameta cikin kyakkyawan yanayi
itama kamar 'yar uwarya,jikin nata ma ya warware gaba daya,washegari kuma gidan
yaya yahanasu ta wuni,kallonta yayan ta dinga tana qarawa,har sai data kasa shiru
"Allah qadiran ala may yasha'u,ashe sumayya ke din rabon wani ce da muntarinmu
ba,kowanne bawa da kalar tashi qaddarar" ta fada tana matse hawaye,hakan ya sosa
tabon dake zuciyar sumayyan,duk da haka sai ita ta lallashi yaya yahanasun,sai
la'asar taje ta gaida hajiyan bahijja da abdur rahman,sosai taji dadin ganin
sumayyan,ita ta tsaidata ma bata wuce gida ba sai magariba.

         Again washegari kuma gidan yaya abubkar ta wuni,amina ta rasa inda zata
sanyata saboda murna,itama dubanta take kamar yadda kowa kallonta,sosai sumayyan ta
sauya mata cikin 'yan watanni
"Masha Allah sumayya masha Allah,dama haka almustaphan naki ya iya kiwo?"
"Kai anty kai" ta fada tana qyalqyala dariyar irin yadda meena tayi maganar.

   ******   *******   *******

        Qarfe sha daya na dare ya dawo daga office din,baki daya ranar ya maida
kanshi busy,sosai ya tsaya da kanshi cikin kamfanin yana zagayawa waje waje yana
ganin yadda ma'aikatan ke gudanar da aikinsu,abinda tunda suka taho tare da
sumayyan baiyi ba,baisan me ya hanashi ba,daga qarshe ya tuqe a warehouse
nasu,hamza ne ya dubeshi a gajiye
"Gaskiya maan na gaji gida zan wuce,magariba fa ta gota,na tabbata abida na can na
zuba ido" cikin ko in kula yana duban bangaren da suke ajjiye kayan aikinsu yace
"Wani ya hanaka tafiya?"
"Ok,dama kai na tsaya,na lura kuma kai yau aikin naka ba mai qarewa bane,ko don yau
gauro kake?" A nutse ya waiwayo ya maka masa harara
"Ba yau na fara ba bare ka gaya min ba dadi" dariya hamza ya saka
"Gaskiya ne wannan,ko zaka zo mu wuce tare kaci abinci wajena?"
"Bana buqata" ya fada yana ci gaba da takawa hannunsa zube a aljihu,haka kawai yake
jin sam baida sha'awa ko karsashin komawa hotel din,a haka hamza ya juya ya fice ya
barshi a wajen,yasan tunda yace bashi zuwa to bazashi din ba.

         A hankali ya tura qofar dakin,babu haske a dakin kasancewar babu kowa,ko


ina dumdum yake da duhu,kunna qwai yayi yabi ko ina na dakin da kallo,sai yaga
dakin tamkar bashi ba,komai ya canza,wani fili yaga dakin ya sakeyi kamar an dauke
wani abu,wata gajiya ta musamman ta saukar masa,ya taka zuwa cikin dakin ya zauna
gefan gadon idanuwanshi na kan doguwar kujerar data saba zama,yana fidda takalmin
qafarshi da safa yana jefarwa,gadon ya fada baki daya yana fidda iska daga
bakinsa,a qalla ya kai kusan minti goma a haka kafin ya miqe ya zauna dai
dai,wayarsa ya fidda ya kira ya bada umarnin a kawo mishi dinner sannan ya miqe ya
cire kayan jikinsa ya fada toilet,turus yayi yana duban bathtube wanda yake wayam
babu komai a cikinsa,sabanin watannin baya da idan ya dawo yake tadda shi cike da
ruwa mai qamshi da dumi,cikin kasala ya soma tara ruwan kafin ya shige cike,qaramin
tsaki ya ja,baki daya ruwan bai masa ba,sabanin nata da yake jin baison fita a
ciki,a gurguje yayi wankan ya fito yana tsane jikinsa da towel aka yi knocking,sai
daya sanya doguwan riga sannan ya bude ya karba,shafa'i da wutiri yayi kafin ya
dauko computer dinsa ya kunna bayan ya jonata chargy,sosai ya zauna a qasa ya bayan
ya janyo abimcin ya bude ya soma kaiwa bakinsa,lokaci lokaci yakan daga kai ya
kalli inda ta saba nadewa duk lokaci irin wannan da yake zama cin abinci ko yin
wani aiki,lokaci lokaci yakan kamata tana satan kallonshi da fararen idanuwanta,ko
ita wani lokacin ta kamashi ko su kama juna,kowa yakan dauke kai da sunan ba kallon
dan uwanshi yake ba,qaramin murmushi ne ya subuce masa,ya ture abincin dake
gabanshi,yana tuna sanda tayi yajin aikin daina kallonshi tun faruwar lamarin a
wannan daren,kai yake girgizawa yana sake tuna duk wani minti daya daya gifta musu
a daren,cikin hanzari ya soma kokawar kauda tunanin,ya jawo computer din ya soma
kunnata cikin bawa zuciya da gangar jikinsa karsashi da qwarin gwiwa,saidai duk
yadda yaso da nuna jarumta lamarin yaci tura,gajiya da kasala sun mamayeshi,haka ya
sanya dole ya kashe wutan dakin ya fada gado,idanuwanshi still kan kujerar
tata,sannu sannu idanuwan suka dinga lunshewa bacci ya rinjayesu.

       Ko da ya tashi da safe abu na farko daya fara takawa shine takalminsa,tsaki


ya ja sanda ya tuna jiya bai kwashesu ba ya kaisu muhallinsu,ya saba da zarar ya
cire bai zuwa ya taddasu wajen,haka ya duqa cikin kasala ya janyesu gefe sannan ya
wuce,yana shiryawa yana sake duban duk wani muhalli da takanyi kai kawo a wurin da
safe irin wannan,musamman inda ta saba zama tayi karatun qur'ani ko taja carbi,kai
ya girgiza yana tsaki tare da tuhumar kansa me ya sameshi ne haka?,a gurguje ya
shirya ya fice zuwa office.

      Ko da ya dawo yau dinma kamar jiya,bai shigo da wuri ba,haka ya dinga


wasiwasi cikin dukka ayyukanshi,kanshi ya shafa idanuwansa a lumshe,yana tunanin
tsananin sabo ne ke dawainiya da shi,don me zata zauna cikin tunaninshi haka?,don
me zai kwana ya tashi ya wuni cikin tunaninta ita daya?,bai taba fuskantar irin
wannan yanayin ba tsawon rayuwarshi,to yau ko cikin baccinsa ma bai samu hutu
ba,sai da ta kawo masa ziyara,wanda hakan ha sabbaba masa yin wankan tsakiyar
dare,hakan kusan sai ya zame masa kamar al'ada ko wani jarrabi cikin kwanakin,idan
yau baiyi ba gobe zaiyi,duka ya tattara hakan ya dora bisa mizanin sabo da kuma
cikakkiyar lafiya da Allah ya bashi.

       Cikin kwana na biyar da tafiyar tata cikin dare bayan yayi wanka ya dawo sai
baccin yayi nashi waje,haka ya dinga juyi shi kadai,baisan me yasa garin baki daya
ya daina masa dadi ba ya fita masa a kai,miqewa yayi ya janyo wayarshi ya hau
binciken da baisan dalili ba,cikin haka hannunshi ya kai kan bigiren hotuna,tunani
yake bari ya gwada abinda yaga rannan tana yi,yana tsammanin zasu debe masa kewa
kamar yadda yazo ya tarad da ita tana kallon hotunan cikin wayarshi,hoton farko
dake bangaren camera nata ne,cikin shigar doguwar riga,da sauri ya wuce zuwa hoton
gaba nan ma ita ce,sai ya sake wucewa,nashi hoton ya gani,ya jima tsaye kan hotonsa
sai ya samu kansa da dawo da hoton baya,kamar wanda ake umarta ya sanya hannunshi
yayi zooming,komai ya fito tar cikin hoton,tana tsaye gaban mudubi tana
murmushi,fararen idanuwanta zuwa dan qaramin bakinta mai dauke tattausan labba yake
kalla,bai manta laushin da yaji a wajen,bai manta hasken wadan nan idanuwan ba,da
sauri ya fita daga hoton ya ajjiye wayar,ba shakka sha'awa ce kawai ke fusgarsa,ita
ke damunsa,amma me yasa baijin haka wajen su'ad tun asali?,shima bai sani ba,yaye
bargon yayi ya koma toilet ya daura alwala ya dawo ya shimfida abun sallah ya tada
nafila.

*******     ******     *******

        Washegari a makare ya isa office duk da sunyi da hamza huzaifa da lamin


zasu hadu,dubansa lamin yake sanda almustapha ke yiwa jakarsa mazauni shima yana
neman zama,yayi kyau cikin suit mint green wanda suka haska farar fatarshi data
jiqu da hutu,agogon hannunsa lamin ya kalla
"Maan ban sanka da karya alqawari ba,saidai yau gashi ka saba,but idanunka suna
nuna ma kamar baka samu isashshen bacci ba"
"Shi kuwa ya samu isashshen bacci,uban wa zai hanashi bacci yana shi daya a daki,d
same thing fa yanzu muke" inji huzaifa yana duba wani file kamar bashi yayi maganar
ba
"Gaskiya ka fada my guy" inji hamza wanda tun dazu yakeso ya takeshi
dama,idanuwanshi yacu gaba da zuba musu bayan ya sarqe yatsunshi cikin juna,duka
sai da suka gama iskancinsu sannan lamin yace
"Ga allocation din da gwamnati ta bamu ka duba" ya fada yana tura masa file
gabanshi,banza ya masa,yaja wayar landline ya bada umarnin yanka masa ticket da zai
tashi daga dubai zuwa nijeria wanda zai sauka a aminu kano international airphort
kano,ji yake tamkar wani abu na janshi zuwa nijeria,baibtaba tsammatar tafiya cikin
tsukin wadan nan kwanakin ba,ya kife wayar ya musu transfer kudinsu sannan ya ja
file din yana dubawa ba tare da yace musu uffan,kana dubansa kasan halinne ya
motsa,kusan duk sun sani,shikam hamza yaci alwashin sai ya sanyashi magana
"But maan me zaka je yi kano" sai da ya daga kai ya dubeshi
"Ka mance zan aurar da qanne?"
"Amma ai ina cewa jiya muka gama maganar next week kaman friday haka zamu wuce baki
dayanmu har da su huzzy"
"I change my mind" ya fada kai tsaye
"Ko kuma she changed your mind ba" sake dagowa yayi yana dubanshi
"Me kake nufi?"
"As i said" ido ya zuba masa yana duban hamzan kamar mai nazarin wani abu,sai
murmushi ya qwace masa,girgiza kai yayi ya maida kansa kan file yana ci gaba da
kada kai,su huzaifa na dariya qasa qasa
"Iam telling you,he became crazy wallahi cikin watan nin nan,shi kadai sai ka
ganshi yana murmushi,kun tuna yadda murmushi ke masa wuya a baya?,kana wasa da mata
maan,mata ba abun wasa bane,duk yadda kake ganin u r powerfull nasu power din yafi
naka,so ka bisu a hankali man tun ba'a saka ka fara kneeling ba kana begging"
"Saurara malam,naga ka fara wuce gona da iri,ni...ni zanyi kneeling ina
begging,begging for what?"yayi saurin tarar numfashin hamzan
"For love ko?" Inji huzaifa yana rufe bakinsa da wata takarda saboda shegiyar
dariyar dake sakadarshi
"God forbid wlh,an gaya muku kowa irinku ne?,mtsweew,kunga idan wannan ta kawoku na
tashi na barmuku office din,idan kun gama kwa kirani,i have alort to do" dole duka
suka zama seriouse suka hau tattaunawa kan abinda ya tarasun,kowanne yana so ne
yaga yadda maan zai fara buga nashi love din da wadda yakeso,duk cikinsu ba wanda
bai kwana da sanin cewa shi din mutum ne dake bala'in qaunar soyayya cikin
rayuwarshisau tari idan suna hira ko siyan gift wa 'yammatansu tabe baki yake yace
basu iya komai ba duk yadda suka kai ga qure adaka,wani irin mutum ne mayen
love,shi yasa suka jimanta masa a sanda baiyi dace da dai dai ra'ayinsa ba,a nutse
suka soma tattaunawa kowa na maida hankalinsa kan lamarin,bude sabbin reshe da suke
so suyi a qasashe biyar kowanne branch zai baiwa daya daga cikinsu ya riqe
ragama,bawai don kowannansu bai mallaki abun kansa ba a'ah,tsabar qauna yarda da
aminci dake tsakaninsu ne,da kuma koyi da yin abota mai kyau da doctor almustapha
ke da buri da kwadayin yi irin na mahaifinsa professor mukhtar.

Ga almustapha da su'ad zuwa nijeria,muje zuwa readers..............


*Ummu muhammadiyya.*

*mrs muhammad ce*👑


*Ummu muhammadiyya.*
📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

8⃣5⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

*wannan page din kuma naku ne*

*sparkling son sorians by batool mamman*

*Allah ya bar zumunci*

_____________________________________

         A qalla ya kusa minti talatin zaune cikin motar a qofar gidansu,ya dubi
agogo karo na kusan biyar yaja dan qaramin tsaki,baisan me ya jawoshi qofar gidan
ba,to idan ya shiga yace me?,me ya kawoshi?,la'asar ne bare yace malam yazo
gani,bai da tabbacin yana cikin gida a wannan lokacin,tun suna hanya ya dinga kai
kawo cikin wayarsa bangaren adana lambobi baiga komai ba da zai iya amfani da
shi,ya motsa labbansa da niyyar bawa drivan umarnin yaja motar su wuce sai yaga
fitowar malam din,sanye da shadda milk babbar riga,fuska akwai ruwa da alama alwala
ya kammala masallaci ya nufa zaiyi sallar la'asar,cikin hanzari ya balle murfin
motar ya fito,dakatawa malam yayi ya zubawa wajen ido sanda yake qarasowa
"A'ah,mustapha ne?,saukar yaushe?yanzu dama tasan da zuwanka amma ta fita unguwa?"
A ladabce ya fara shirin rusunawa malam ya dakatar da shi da hanzari
"A'ah,miqe kada ka bata jikinka" duk da haka sai da ya dan rage tsawonshi suka
gaisa
"Bari na baka ruwa ka daura alwala idan mun dawo sai mu shiga ciki ko?" Malam ya
fada yana niyyar juyawa ciki,jin haka ya sanya drivansa saurin komawa mota don
dauko masa ruwan riba,da hannu ya dakatar da shi,suna tsaye malam ya iso da butar
ya miqa masa,ya koma saman dandamalin qofar gidan ya fara daura alwalar,a hankali
yara suna fara giftawa suna kallonshi,kafin ya kammala sai ga yara sun soma taruwa
suna kallonshi,a tsakaninsu suke qus qus din balarabe ne wlh,murmushi malam ya saki
don ya jisu,karbar butar malam yayi ya aiki daya daga cikin yaran ya maida gida
sannan suka wuce masallacin tare.
     Tare suka jero da malam din suna hira jefi jefi har suka qaraso gidan,da kansa
malam din ya bude masa sitting room yace ya shiga ya zauna,bai musa ba ya shiga ya
zauna din yana qarewa falon kallo,ciki malam ya koma ya sake kiran sumayya ya
shaida mata duk abinda take ta baro ta taho tayi baqi,cikin mamakin wanne irin baqi
tayi haka tace masa tana dab da shigowa unguwar ta iso tuntuni.

       Cikin sanda ta shigi soron,idanuwanta kan takalmin sau ciki dake qofar
sitting room din,cikin gidan ta wuce kai tsaye,mama ta taras a falo tana wanke wani
rubutu,tun da tazo taga tana yinsa kullum da yamma batasan dai ko na meye ba,baki
sake maman ta kalleta
"Me kika shigo kuma yi?,baqon ai yana sitting room"gabanta ke faduwa hakanan da
wani irin tsoro
" waye mama?"
"Idan kin shuga kya gani,tsaya ki karbi wannan ki shanye tunda kin riga da kin
shigo" inji maman tana juye wani rubutun daga wata jarka wanda ke gauraye da zuma
ta miqa mata,bata musa ba ta karba ra kwankwade,sannan ya zare niqab dinta daga
saman zabgegen hijabin dake jikinta,don tunda tazo ta koma wannan shigar,sakamakon
yadda aketa tanka canzawar da tayi,bugu da qari da yawan kallon da take fuskanta
wajen maza idan ta fita,jakarta ta sabule ta ajjiye saman kujera ta dubi mama
"Kayana an kawo gugar?"
"Akwatin ma a hade yake,ba jibi ko gata zaki wuce ba?"
"Eh amma mama nikam banson tafiya wlh,da sai ranar daurin aure kawai" harararta
maman tayi
"Ban koya miki sabawa umarnin miji ba,randa yace ki tafi koda yau ne tafiya zakiyi"
murmushi ta saki kawai ta juya ta fice,tunda tazo maman bata da aiki sai ja mata
kunnen tabi miji.

       Tun kafin ta kai ga shiga dakin take ji qamshin wani turare kamar ta
sanshi,hannu ta sanya ta yaye labulen bakinta dauke da sallama,idanu ya zuba mata
yana dubanta,baki daya ko ina na jikinta a lullube yake tun daga saman qafarta har
zuwa kanta da hijabi,wani sanyi yaji ya ratsashi,karon farko yaji shigar tayi
masa,ba abinda ke nunawa a jikinta,idanu suka hada ta saki labulen tana takawa a
hanakali kamar mai taka qaya,wani shegen kwarjini yayi mata,ya cika mata idanu baki
daya,bai fasa kallonta ba har ta qaraso kan daya daga cikin kujerun dake zagaye da
falon ta yiwa kanta matsugunni,gababshi kewaye da ruwa da lemuka saidai babu wanda
ya taba
"Sannu da zuwa" ta fada tana dubanshi qasa qasa
"Ina kika je?" Ya tambayeta maimakon amsa
"Gidan aunty na,aunty salma"
"Wa kika tambaya?" Wannan karon dagowa tayi ta zuba masa idanu cikin mamaki,taga
dai dole idan tazo ya sani zata gidan 'yan uwa dai,janye nashibidanun yayi wannan
karon,kallon da take masa yana sake kasheshi da narkar da duk wani sashe mai
muhimmanci dake jikinsa
"Tashi ki dauko kayanki mu wuce?" Ranta ya baci,take idanunta suka hada qwalla
"Amma sai jibi ai zan wuce abujan ko?,yau fa kwana na shida fa anan din?"
"Haka nake da buqata idan kuma ban isa ba to" idanunta ta kawar qwallar na zirarowa
a idanunta,ta miqe tamkar zata rushe da kuka ta fice.

      Kuka ta sanyawa maman da qyar ta ciyo kanta ra gaya mata abinda ya faru,idanu
maman ta zuba mata
"Shikenan don yace zaku wuce zaki zo kina rusan wannan kukan?,da can kinsan zaki zo
din ne ka din ya barki?,so kike ku taru duk ku zama taron tsintsiya babu shara,ai
da nasan abinda kike wa kukan ma da tuni naci mutuncinki,tashi ki dauko kayanki"
maman ta fada tana miqewa zuwa uwar dakinta,waya ta dauko ta kira malam ta shaida
masa,yace Allah ya tsare baya kusa ya fita daga unguwar amma ta tabbata sun
tafi,idan ta zauna me zata musu.

         A tsaye ta sameta a falo tana goge hawaye riqe da jakar matafiya mai
taya,hannun maman dauke da wani babban kwali
"Ga tsaraba nan ki kaiwa surukar taki"
"To mama,abdallah fa?"
"Zasu zo da malam daurin aure ran asabar din in sha Allah idan babanshi ya
barshi,shi bai ta taki ma,ko maganarki ake bai damuwa,Allah ya riga ya sanya masa
son jama'a,Allah ya tsare hanya sai munyi waya,kibi mijinki shine aljannarki"
"Na gode mama" ta fada tana karbar wani rubutu cikin jarka a hannun mama sai
qamshin kanunfari da zuma yake ta saka jakarta duk da batasan na meye ba.

        Maimakon taga sunyi hanyar airphort sai kawai taga sunyi gidan baba dake
kano,bata tanka masa ba har suka isa gidan,shima waya yake tayi da ma'aikatan
asibitinsa har suka je din,fes suka tadda dakin nashi kamar da mutum a ciki,hakan
baya rasa nasaba da ma'aikatan dake gidan kulli yaumin koda masu gidan basa
nan,gefan gado ta zauna har yanzu idanuwanta na fidda hawaye,kayan jikinsa ya soma
cirewa saboda yana da buqatar wanka,baiko dubi sashen da take ba,hakanan kukanta ke
taba zuciyarsa fiye da ko yaushe,meye abun kukan?,toilet ya shige ya rufo qofar.

       Har ya fito a nan ya taddata,ya gama shiryawa tana nade a wajen,silifas ya


zira ya bude qofar dakin ya fice,miqewa tayi a hankali ta fidda hijabin jikinta ta
shige toilet,wanka tayi ta hado da alwala ta dawo ta fidda kayan shafawarta,sallar
ta soma yi,sannan ta shirya tsaf cikin sababbin kayan data siya a wani gurin saida
kayayyaki,gown gown ne fitted masu roba wanda suke saukowa har qauri,matsatstsen
dogon hannu gareta,rigar tabi lafiyar jikinta sosai ta fitar mata da qira,gashinta
ta shafawa mai ta taje sannan ta daureshi da qaramin ribbom,hakan ya bawa jelar
damar fitowa sosai da nuna irin yawan da gashin yake da shi,gefan kujera ta samu
tayi zamanta abunta,ko dankwali bata nema ta daura ba,sai ta jawo wayarta tana
danne danne tana duba watsapp dinta,wanda tunda aka bude mata bata bi ta kanshi ba
sai yanzu,har yanzu ranta a dan bace yake,saboda tana ganin yana mata mulkin kama
karya ne kawai,a duk sanda yaso tafiya da ita saidai ta ganshi kwatsam,kuma yace
lallai ta taho su tafi haka ake?.

Qofar aka turo,almustapha ne hannunshi dauke da takeaway,amsa sallamar tayi ba


tare data daga kanta ba,hakan ya bashi damar qare mata kallo son ranshi,karon farko
da ya ganta cikin irin shigar turawa
"Hasbunallahu wa ni'imal wakil" ya fadi cikin ranshi saboda wani abu da yaji na
yawo cikin jikinshi
"Komai ma yi mata kyau yake ne?" Ya sake tambayar kanshi har zuwa sanda ya qarasa
qasan carfet ya zauna yana fidda abinda ya siyo,harar kayan tayi a fakaice tana
rayawa cikin ranta itakam ta gaji da wannan ciye ciyen,wato za'a koma 'yar gidan
jiya,da iliminta na iya girki gaskiya ba zata zauna ta qare a takeaway ba,ta lura
baki daya aqidun turawa sun ratsashi.

Abincinsa ya fara ci hankali kwance yana qarewa shigar tata kallo a


fakaice,ta zama tamkar wata 'yar baby ko yarinya 'yar sha hudu
"Zo nan" ya fada yana wani cin mur,daga kanta tayi ta kalleshi,babu faraga saman
fuskarsa hakan ya sanya ta miqe tsam ta soma takawa zuwa inda yake,kasa dauke
idanunshi yayi daga kanta,komai yana juyawa da kuma motsawa tamkar wadda ake bawa
umarni,zakayi tsammanin da gangan take aikata hakan,saidai ko kadan haka nata salon
tafiyar yake,haushin da take ji ya sanya bata ma yi tunanin saka hijabin ba,salon
tafiyar tata ya sake kashe almustapha,abu na farko da yake marmafi da muradin wajen
macen da zaya auda tun da can bayan,sanin wannan dalili ya sanya su'ad koyon irin
tafiyar da yake so din,saidai duk yadda ka kai ga aro abu ka yafa ba kamar yadda
yake a halittar ka ba,nuni yayi mata da kusa da shi,cikin shan mur ta zauna har ma
fiye da inda ya nuna matan,qamshin turarukanta suka soma kai saqo qwaqwalwarsa,nuni
yayi mata da plate din da yake cin abinci,kamar zata saki kuka haka ta sanya
hannu,saidai baki daya ta kasa sakewa bare taci,ga idanunshi da suka mata nauyi
wanda ya azasu kacokam a kanta,so yake lallai sai ya gano wani abu na daban dake
tattare da ita,wanda yake haddasa masa jin wani irin mai nauyi cikin zuciyarsa da
qirjinsa,ya rasa meye wannan mai qarfi dake yawan fusgarsa zuwa gareta.

Shi ya soma tsame hannunshi,ya shiga toilet yayi brush,kai tsaye saman gado
ya nufa ya zauna,ya kawo laptop dinsa ya soma aiki,jifa jifa yana dubanta tana
zaune gaban abincin wanda har yanzu kusan wasa kawai takeyi da shi,kasala da wani
irin feelings da yake ji ya hanashi ci gaba da aikin,sai ya kashe cumputer baki
dayanta ya ajjuyeta saman bedside,hannayenshu ya hade guri daya cikin zuciyarshi
yana wani dan tunani,ya dan bita da kallo sanda ta miqe tana tattara kwanukan,ta
gyara wajen tsaf,sannan ta shiga bandaki don sauya kayan baccinta ganin har ya
sauya hasken dakin,idanunshi bisa kanta sanda ta fito din,abinda yake ji ya dinga
bunqasa,ya hanashi sukuni,tilas ya miqe yana fidda numfashi ya miqa hannunshi ya
kunna fitilar gefan gado,waiwayowa tayi suka hada idanuwa
"Dauko min ruwa" ya fadi yana lumshe idanunshi numfashinsa na fita da sauri,ganin
sauyawar yanayi tattare da shi ya sanya tayi tsammanin bai jin dadi,sai ta miqe a
hankali,ta isa ga freezer ta ciro ruwa ta hada da kofi,gadon ta haye baki daya ta
tsiyaya ruwan ta miqa masa,hannunshi ya sanya ya karba ya kafa kai ya shanye,miqa
mata ya sakeyi ya mata nuni da idanu kan ta dado masa,sake tsiyayawar tayi ta miqa
masa,amsa yayi sai yayi jifa da kofin tare da fincikota cikin jikinsa wanda tuni ya
soma rawa numfashinsa na fita da sauri,lullubeta yayi cikin qirjinsa yana lalubar
bakinta,tsoro ne ya kamata wanda hakan ya bayyana har cikin idanunta,ganin hakanne
ya sa ya sauya salo,cikin kunnuwanta ya shiga gaya mata wasu kalamai wanda suka
mata nauyi a qwaqwalwa da kunnenta,sannu a hankali suka zare duk wani tsoro da ya
mamayeta,suka cire duk wani qarfi da yayi saura a gabbanta,zata iya cewa bata san
ya akayi ba,saidai ta sake tsintar kanta cikin duniyar mustaphan,duniya mai cike da
al'amura masu nauyi da tsayawa a zuciya ruhi da gangar jiki,wannan karon yaci
galaba wajen sanyata sake masa,ta bar mata ragamarsa ya jata inda yaga dama,ba
laifu wannan karon ma taji a jikinta,cinyoyinta suka dinga mata ciwo.

Sai da komai ya kammala sannan ta farga,nauyi da kunya suka sanyata


kuka,itakam me yasa sam bata da wayo ne bata ganema wayonshi sai ya gama
budirinsa,yana jin kukanta a sanda yake hutawa yana sauke numfasji tare da shaqarsa
d'ai d'ai,yana jin wani wasai a qirjinsa da gangar jikinsa tamkar waccan karon,wata
iska ta musamman yake ji yana shaqa a qofofin hancinsa,yatsunsa ya tura cikin
sumarta yana yamutsa gashin ta anutse,santsi da sulbinsa na aika saqo har cikin
qwaqwalwarsa,hakanan yana sake burgeshi,salon yadda yake matan ya sanya kukanta
raguwa,sannu a hankali wani irin bacci data jima bata ji irinsa ya ziyarceta.

A nutse ya zareta daga jikinsa ya kwantar da ita saman filo,hannunshi ya


sanya ya yaye gashinta da ya rufe fuskarta,fuskartata ta bayyana na mai dauke da
lemar hawaye
"Lazy girl" ya fada murmushi na kubce masa,a hankali ya sauka daga gadon yana maida
tufafinshi,ya taka ya qarasa gaban mudubin dake dakin,hannunshi ya dora kan
fuskarshi yana shafata a hankali,murmushi ya kuma subuce masa sanda ya tuna kalaman
da suka dunga subucewa daga bakinsa suna fitowa cikin awannin da suka shude,shi
kadai ya soma magana da kanshi
"Wai meke damunka almustapha?,kaine kuwa?,yaushe ka koyi maqalema mace?"
"There is something special tattare da ita" ya fada a fili,girarsa ya dage yana
tambayar kansa tare da son tabbatarwa
"Really?" Ya kuma tambayar kansa,murmushi ya kuma saki yana dan dukan kanshi
"U r crazy man,gaskiya hamza ya fadi kenan" kafadanshi ya daga ya juya zuwa toilet
don tsaftace kanshi.

Wannan karon ma haka ta dinga qunbiya qunbiya,ita kanta batasan ya akayi ta


sake masa haka ba,kunyar kanta ta dinga ji,shikam yana zaune abinshi yana
karyawa,yayin data kasa sakewa riqe da cup din tea tana juyashi da cokali,ta lura
tun dazun yakeso ya takaleta da magana saidai taqi bashi fuska
"Hey" ya fada murya can qasa,fararen idanunta dake burgeshi ta daga ta dubeshi
"Come here" ya bata umarni yana dubanta da wani kallo qasa qasa,bata son musu
tsakaninsu,sai ta dire cup din ta miqe zuwa inda yake,inda ya nuna matan gabansa ta
dawo ta zauna,batasan me yasa yake yawaita son kiran sunanta ba,ci gaba yayi da
dubanta kamar dalilin da ya sanya ya kirata kenan,a qalla minti goma sannan ya ture
plates din dake gabansu
"Let me tell you something,baki iya making love yadda nakeso ba,sai kuka,sai
kunya,wadanne irin lusaran maza kika taba aura?" Maganar ta mata zafi sai ta daga
kai tana dubanshi,tuni qwalla ta cika mata ido,wannan cin fuska ne,yana nufin har
da mukhtar cikin lusaran?
"Can i teach you how i want you to be?" Kai ta girgiza,sai ta saki kuka,dariyarsa
yake boyewa,hawayen dama kawai yakesin gani cikin idanunta,a jiya ya kura da wani
kyau da idanuwanta sukayi sadda qwalla ta cikasu,kamata yayi suka miqe tsaye baki
dayansu,bai saketa ba har sai da suka isa gaban mudubi,yana tsaye a bayanta
"Look at your self,i think crying is ur hobby ko?"duban fuskar tata yayi kamar
yadda yace,shabe shabe da hawaye kamar ta abdallah,sai ta dubi tashi fuskar,wata
kunya ta kamata tayi qas da kanta,mannata yayi a jikinta ya dora kansa saman
kafadarsa,hucin numfashinsa ya shiga kunnenta,tsigar jikinta ta tashi
"na baro wata qasa na iskeki,wannan tarbar na cancanta?,you must learn yadda zaki
dinga tarbata..."
"Ai na iya" ta fada da sauri cikin subutar baki saboda yadda ya sake mannewa da
jikinta,murmushi ya subuce masa ganin yadda ta amsa da gaggawa tun bai gama fadin
abinda zai fada din ba,kallonshi take tana duban yadda yake murmushin,wani kyau
taga yayi mata
"Daina kallona" ya fada yana dan hade rai kaman bashi ba,itama sai ta sake hade
rai,juyo da ita yayi suna fuskantar juna hannayenshi aka qugunta,a hankali tamkar
mai rada ya soma zayyano mata dukkan yadda yakeso ta dinga masa idan suna tare,idan
ba gab da su kake ba ba lallai kaji me yake gaya mata,wayyo Allah kamar qasa ta
tsage ta shige haka ta ji,idanunshi a kanta yake maganarshi kanshi tsaye,ko kunyan
duban idanunta baiji,wanne irin mutum ke shi da bai da kunya,zille zille ta soma yi
saboda yadda maganar ta soma fin qarfin kwanyarta,muryarshi ratsata take,salon
maganarshi daban ne,murya ce mai matuqar tsada da daraja a tarihin rayuwarta,sai
yayi shiru ya tsaya cak yana dubanta tana mutsu mutsu
"Haddacewa nake so kiyi,shi yasa nake gaya miki a yanayin da ba zaki manta ba"
shiru tayi ta rasa abin cewa,karata yayi da jikinsa cikin qirjinsa
"Tsaya anan idan kin gaji da tsaiwa ne naga qafafunki na rawa kici gaba da haddace
abinda nake gaya miki" sake sauya salon muryarshi yayi yana ci gaba da gaya
mata,wannan karon hatta da bugun zuciyarta sai da ya sauya,ta rintse idanuwanta
tsigar jikinta na tashi,ya kwashe a qalla minti talatin kafin ya dan janyeta
"Ina so na gani practically,zamu fara gwada wannan,shirya min ruwan wanka,zanje na
dawo qarfe hudu zamu wuce abuja ki zama ready" dama neman gun kubuta take,da
hanzari ta juya har qafafunta yana sarqewa har sai da yace
"Kula" bata bi ta kanshi ba ta shige toilet din,gefan bathtube ta zauna tana sauke
numfashi kamar tayi gudun famfalaqi saboda yadda bugun zuciyarta ya qara
gudu,maganganunshi ke mata yawo ko ina cikin sassan jikinta,muryarsa mai mai dauke
da wani amo na ratsata tamkar yanzun yake maganar,curewa tayi waje daya murmushi na
subucewa a tattausan lebanta.

*kuyi manage sabgogi sun sako kai,sai ranar lahadi idan Allah ya yarda*

*gareku 'yan uwana al'ummar qasata,ka sani cewa quri'arka itace 'yancinka,kana da
damar zaben duka mutumin daka ga dama,quri'arka zata iya zama sanadin jin dadi da
walwalar al'ummar qasarka,hakanan zata iya zama silar shigarsu qunci,saidai kar ka
manta da wannan,RANAR QIYAMA ZAKA TSAYA GABAN MAHALICCINKA KA BADA HUJJARKA NA
DALILIN ZABAR MUTUMIN DAKA ZABA DIN,kada ka manta tsayawa gaban wanda ya halicceka
babban lamari ne,mu tsaya mu zabi shugaba na gari,wanda zaton alkhairin da al'umma
suke masa ya rinjayi na sharrin,MU ZABI CANCANTA BA JAM'IYYA BA,hakanne kadai zai
sanya mu saka qwarya a gurbinta,kada mu yarda wasu su shiga rigar jam'iyya su
cucemu,mu duba cancanta da dacewa,mu yiwa kamu alqalanci,kada mu jefa kanmu a
fitina da musibar da bamusan ranar qarewarta ba,Allah kasa mu dace ka yi mana
jagoranci kada ka barmu da iyawarmu*

*muyi zabe lafiya cikin aminci da kiyayewar mahaliccinmu*

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

8⃣6⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

*Allah madaukakin sarki yana cewa*

*haqiqa muminai 'yan uwan juna ne kuyi sulhu tsakanin 'yan uwanku*
_____________________________________

           Qarfe uku saura na rana suna zaune bayan motar driva na jansu,tattausan
tafin hannunshi na cikin nata,yana zaune gab da ita sabanin daa da kowa ke zama
tashi shiyyar,kunya ta sanya ta maida kanta bangareb window tana duban hanya cikin
baqin glass din da motar take da shi,yatsunsa ya sanya ya juyo da fuskarta
gareshi,ya dage gira daya
"Ina son miki qari kan abinda na fadi miki dazu,zayyano min naji kin haddace?" Wata
iriyar kunya ta kamata,ta yaya zata iya maimaita kalaman dazu masu nauyi da
girma,kanta ta qwace daga hannunshi ta sake maida kanta ga window murmushi na son
kubce mata,ganin haka ya sanyashi janyota jikinsa ya sanya hannu ya matseta
"Maganinki zanyi,naga alama baki fara daukan lacture ko daya ba,yadda nake daban
haka nakeson matata ta zama ta daban,you must be ready,qarin karatu guda daya,dole
ki koyi zama a jikina,bazan lamunci zama a mabanbantan wurare ba ba,idan baki son
haka ki daina zama waje daya da ni" ya fada yana shan mur,baki ta murguda wanda
yayi nasaran hangota,cikin zuciyarta tana mita,wuta ce ta dauke mata sanda taji
hannayenshi cikin rigarta,ta daga kai ta dubeshi tana narke fuska,idanunshi
lumsassu ya zaro mata waje yana mata nuni data daina kallonshi,tilas ta sauke
qwayar idanunta,tana ji tana gani haka ta haqura ya dinga yadda yaga dama da
ita,sai da yaji tsaiwar motar sannan ya zare hannunshi da jikinshi,hannun nasa ya
sanya ya gyara mata rigarta da yafen mayafinta,wanda atamfa ce a jikinta ta dora
mayafinta saman ka,kanta na a qasa cike da jin nauyi har ya kammala,bata dago ba
sai da taji yace
"Oya,lets go".

        Tayi zaton ganinta a airphort sai ta gansu cikin wani makeken guri wanda
yaso yi mata zubi da gida,mutane ke kai kawo,kama daga qananun yara saffa saffa da
kuma manya,yana fitowa wasu tarin ma'aikata suka qaraso wajem,cike da girmamawa
suka tarbeshi,a mutunce yake gaisawa da su,sannan ya saka hannunshi cikin na
sumayyan sanda suke masa rakiya zuwa cikin wani babban gini dake gabansu,ta daga
kanta a hankali a naj taci karo da wani rubutu cikin manyan haruffa daga saman
gidan wanda aka rubuta MUHAMMAD ALMUSTAPHA ORPHANS HOUSE,cikin ranta take rayawa
gidan marayu dama gareshi.

       Babban office aka bude wanda shine mallakinsa,office din nada girma
qwarai,akwai kyau tsari da wadatar tsafta ko da yaushe,sun sani haka yake,ya saba
kawo musu ziyarar ba zata,sai a gama waya da shi yau anjima ku ganshi cikin
gidan,duka yana haka ne saboda ya tabbatar kowa ya riqe amanar aikin da aka
bashi,saman doguwar kujerar cusion suka zauna shi da ita kafin su shiga gaisawa da
wadanda ya dorawa nauyi da alhakin kula da gidan,cikin nutsuwa da sanin aiki kowa
ke masa bayani kan nashi bangaren da yake riqewa,kusan mintina talatin kafin ya
buqaci kewaya fadin gidan.

       Hannunshi tsam cikin nata tafin hannunsu a hade,kunya duka ta kamata,baijin


kunyar jama'ar da suke tare?,eanda ta lura wasu sai satar kallonsu suke,a hankali
suja fara kewayawa bangaren makarantar yaran inda suke karatu,makaranta ce mai
zaman kanta,nursery primary zuwa secondry duka cikin gidan suke,bangaren wajem
wasannin yara daga cikinsu,gurin koyon sana'ar manya,da dan madaidaicin asiniti don
duba lafiyarsu,duk inda suka zo wucewa suka ci karo da wasu idan manya ne sukan
qaraso fuskarsu dauke da madaukakiyar fara'a,abinda zai baka mamaki yadda suke
bashi hannu kai tsaye suyi musabaha cikin yanayi na sabo da jan mutum a jiki,idan
mata ne sukan duqa cikin girmamawa su gaidashi su wuce suna murna,yara qananu maza
da mata da gudu suke qarasowa wajensa,yakan daga su ya sumbacesu,ko ya shafa kansu
idan sunyi girman da zaya dagasu,idan yaga wani cikin yanayin da bai masa zai
tambayi ba'asi ko dalilin barinsa haka?,bare ma da wuya kaga wani cikinsu cikin
mummunan kama,kowa neat yake cikin tsafta da tufafi mai kyau,tun tana satar
kallonshi ta gefan idanu har ta koma ta gaban idanuwa,karon farko da taji ya
burgeta a rayuwa,wanne irin mutum ne shi mai tausayi haka,sauqin kai jin qai da son
yara?,yadda yake mu'amalantarsu abun yayi masifar burgeta,ko banza tana da
maraya,tasan ciwon rashin uba,bare wadaj nan da ba'a rasa yaran da ake kira shegu a
cikinsu,wanda basu da kowaba duniya,an yardasu tun suna da qananun
shekafunsu,basuji ba basu gani ba,ba'a barsu da tabin da aka haifar musu ba na
rashin fitowa ta hanyar data dace ba,sai da aka sake cika rayuwarsu da tabo da
quncin rashin sakin waye uwa uba kuna dangi a garesu,ba shakka yayi wani abu mai
girma arayuwarsa wanda koda shi daya yayi a duniya ya cimma nasara,ma'aiki S A W
yana cewa 'nida mai kula da maraya kamar haka muke a aljanna(sai ya kwantanta da
yatsansa dan manuni dana tsakiya)' me yafi wannan alkhairi na zama maqoci a aljanna
wajen fiyayyen halitta?,ba sai kayi da yawa ba,ko guda daya ka kula da shi kana da
wannan garabasar bare kuma kayi serving rayuwar daruruwa,koda baka jin rahama da
tausayi cikin zuciyarka kana jinta kamar a qesashe ka dimanci shafa kan maraya
kamar yadda ma'aiki ya umarci wani sahabi,Allah ka bamu iko ka bawa masu ikon da
qargin cikinmu ikon taimakawa marayan.

         Sannu a hankali suka ci gaba da takowa,dubanta yayi kana ua dauke kai yana
jawota zuwa jikinsa sosai,kunya kamar qasa ta tsage ta shige,kasa daurewa tayi
"Ammm,akwai mutane fa da suke tare da mu"
"Shshshs,na fiki sani ai ko?,ko wani abu na daban na aikata bayan haka,it seems kin
soma gajiya da tafiyar" ya qarasa fada yana tarota sosai,shiru tayi don ta fuskanci
ci gaba da bayanin bashi da wani amfani,har zuwa sanda suka qarasa dakin kwanan
yaran,don baya shiga sashen 'yammatan,yana baiwa masu kula da su mata ne su dama
tambayi matsalarsu,a nan auka ci karo da wata yarinya wadda ta nufoshi da
gudu,durqusawa yayi ya dauketa yana sakin murmushi,yana tausayin yaran,yana jinsu a
jikinsa,ba shakka rayuwarsu akwai ban tausayi,ka tashi bakasan hatta wadanda sukayi
silar kawoka duniya ba,me yafi wannan ciwo?,yana dauke da ita suka ci gaba da
takawa wanda ya sanya sakin sumayya daga jikinsa,sam taqi yarda ya sauketa,yarinyar
akwai surutu da wayo,tambaya take masa kan me yasa ya dade bai dawo ba?,ko da ya
amsa mata sai kuma ta waiwayo ga sumayya tana tambayar wacece wannan,waiwayowa yayi
ya kalli sumayya
"Sai ki bata amsa" ya fada yana tsareta da ido,murmushi ta saki wanda ya bayyana
fararen haqoranta tana duban yarinyar,maqe kafada tayi
"A'ah uncle kai zaka fada min" gira ya dage murmushi na subuce masa yana duban
yarinyar wadda shi ya sanya mata suna randa aka tsintota ya sanya mata amatullah
"Matata ce abokiyar rayuwata,qawata kuma qanwata" ya qarashe fada idanunsa na kan
sumayyan,wani abu ne ya tsirga mata daga kai har tafin qafa,janye idanunta tayi
tana maimaita kalamanshi
"Mata ta masoyiya?,yaushe na zama masoyiyarsa?" Waiwayawa yayi ya miqawa daya daga
cikin masu kula da yaran amatullah sanda suka isa bakin office dinsa yana fadin su
jirashi yanzu zai fito madam ta gaji zata huta.

       Shike gaba tana bayanshi,suna qarasa shiga ya waiwayo da hanzari cikin


shammata ya hadeta da qofan office din da faffadan qirjinsa,yayin da ya sanya
hannunsa ta bayanta yana murzawa qofar muqulli,qugunta ya kama ya riqe da hannu
daya,yayin da ya dafe qofar da daya hannun,hucin numfashinsa na sauka saman
fuskarta,ya cika mata idanu ya mata wani mugun kwarjini
"Uhumm.....baki yarda bane da nace kedin matata ce kuma masoyiyata?" Ya tambayeta
kanshu tsaye,jin tayi shiru yasa ya dora
"If kina doubting kiyi magana" ya sake fada yana dage mata girarshi,qarar wayarshi
ya ceceta daga kallon da yake mata,ya dan ka baya yana amsa kiran wanda daga driva
ne yake tuna mishi kada su makara har jirgi ya tashi
"Ok" kawai ya fada ya ja da baya,saman teburin ya nufa ya dudduba wasu takardu
sannan ya nufi qofa wanda tana tsaye nan tana qoqarin didaita numfashinta,hannunta
ya sanya cikin nata kaman yadda suka shigo suka fice bayan ya bar key din jikin
qofar yasan akwai mai kullewa,a nan ya samu ma'aikatan,ya yabawa kowa yadda zasuji
qwarin gwiwar ci gaba da kula da ayyukansu,sannan ya umarci dalhatu wanda shine
shugaba baki daya daya turo mishi bayanan dukkan wata matsala damuwa ko buqatar da
suke da shi ta emil dinsa,idan da hali a dauki masa vidiom duk wani mai matsala ko
wata buqata koda a rubuce idan zasu iya a masa sending,zai samu lokaci ya duba a
nutse in sha Allah,ya bude 'yar jakar dake hannunshi ya musu rabon kudi bawai don
ya gaza albashinsu bane,wannan sabonshi ne haka yake duk sanda yazo,wanda wannan na
daya daga cikin abinda yasa suke son yazo din da kansa,ya sake jadadda musu
muhimmanci amana sannan suka fara tako masa don yi masa rakiya.

       Gab da zai shiga motar tashi ya hangosu su uku,matasan yammata ne wanda zasu
doshi shekara sha shida shida riqe da wata a tsakiyarsu tana dingisawa,sai da suka
matso sosai ya kula da jini dake diga a qafarta,cikin tashin hankali ya kirasu suka
yo wajensa,benci ya sanya aka dauko suka dorata akai,duk sun rude suna tambayar
meta taka suka ce kwalba ce,hankalinshi tashe ya tsugunna da kanshi sanda suke
yunqurin aje masa kujera ya dakatar da su,cikin rudewa yake yunqurin kama qafar ya
duba inda ta shiga din caraf yaji an riqe qafan,sumayya ce,kusa da shi ta tsugunna
ba tare data dubeshi ba,yayin da shi kuma ya biya da kallo yana janye nashi
hannun,hakanan kawai taji wani abu ya soketa sanda ya tsugunna gabanta yana qoqarin
kama qafar,batasan ta kai wajen ba,daga qafar tayi ta hasko mishi wajen tana duban
'yar budurwar
"Kina budurwa me ya kaiki yawo ba takalmi har ki taka kwalba haka?" Ta tambayeta
"Takalmin nake duba inda na ajjiyeshi ban kula ba she kwalbar na gaba na sai na
taka" kai ya daga ya basu umarnin shiga clinic ya gaya musu abinda zasu dauko
masa,cikin sakanni suka dawo,ya dauki wani daj qarfe da zai zaqulo kwalbar ya
tunkari qafar,da sauri ta sanya hannu zata karba,sai ya sakar mata yana dubanta
cikin mamaki,shi ya dinga nuna mata yadda zatayi har ta gama tayi mata
dressing,tana cire safar hannun nata bayan ta gama qasa qasa yake dubanta,yana
mamakin yadda tayi aikin perfectly,tayi kicin kicin da fuska,baisan me yasa ta
hanashi yin aikin ba.

Suna zaune cikin mota murmushi ya subuce masa sanda wani tunani ya fado
masa,kai ya kada yana cije lebansa na qasa,ya miqa hannunshi ya damqo nata hannun
dake ajjiye saman cinyarta,waiwayowa tayi tana dubanshi,ido daya ya kashe
mata,murya can qasa wanda sai ka mugun kasa kunne zaka iya jiyo me yake cewa
"Kada ki yarda ki soma kishina tun yanzu" fuska a hade ya fada,cikin mamaki take
dubanshi,sai ta samu kanta da tabe baki
"Na meye zanyi kishinka?"
"Saboda na lura kin fada tarkon sona,ko kina jayayya"mamaki ya sake kamata,yaushe
hakan ta faru da zai fadi haka,cikin dakiya tace
" qwarai kuwa"da qarfi ya janyota ta sake matsowa kusa da shi,idanuwansu cikin na
juna yana dubanta kamar zai cinyeta danya,daga idanuwanta zuwa jajayen labbanta da
suka sha jambaki,ji yake kamar ya cinyesu
"Me yasa kika hanani ta qafarta?"
"Wa kenan?" Ta ambata cikin dakiya,duk da yadda takeson janye idanunta saboda yadda
kallon ke aika saqo har cikin qwaqwalwarta,murmushin gefan baki ya saki,he love her
style har cikin zuciyarshi hakan ke burgeshi
"Kin qware wajen pretending,uumm?" Ya sake fada yana jifanta da wani salon kallo,so
take ta janye idanunta amma ta kasa,har sai da ya samu nasarar jefa kasala da
mutuwar jiki tattare da ita
"Idan haka ne,kada ki sake hanani aikina ko ma akan waye" ya fadi yana sakinta
"Dama ba hanaka nayi ba,taimakonka kawai nayi" ta amsa tana gyara zamanta
"Really?,dis is d begining of love,taimako and tausayi,alright?"ya fadi yana daga
kafadunsa cikin i dont care manner,shiru tayi maganarsa na mata kaikawo,bata son ya
sake kasheta da wannan mayun idanun nashi hakan ya sanya batayi musu shi ba.

Karo na biyu ta sake shigowa garin abuja a matsayinta na matar almustapha


suruka ga baba prof,sai ta tsinci kanta cikin tsantsar kunya da nauyin ahalin
gidan,sanda suka isa alamu na nuna gidan ya soma karbar baki kamar yadda hakan ya
zama al'adar gidan duk yayin da wani sha'ani ya tashi,kai tsaye bangaren ummee ta
nufacu zuwa,saidai ya sanya hannunshi ya riqe nata hannun ya sauya akalarta zuwa
nasu bangaren
"me kika yimin sa zaki nufi wani gun,idan na kammala duka abinda zanyi kina iya
zuwa but not now" shiru ta masa tana jin yadda idanuwa sukayi yawa akansu,akwai
'yammata zaune harabar gidan suna sheqar iskar almuru wanda ke busowa kasancewar an
kusa sallar magariba,hakanan garin yana dan hade da hadari mai bada iska,sai
yanayin ya dinga haifar da wani yanayi cikin zuciyarta,sai ta samu kanta da lafewa
a jikinsa har suka shige bangarensu,sai da suka bacewa idanuwansu sannan suka dauke
kansh daga wajen,daya daga cikin 'yammatan ta doka hannunta saman tebur
"Kan bala'i,wai ya akayi haka ne ta faru?,wacce iriyar rashin sa'a garemu da aka
gaza samun ko daya daga cikinmu ta shiga rayuwar man din can?"
"Rashin sa'a babba ma kuwa,sai nake ganin fuskar yarinyar ma kamar na santa
fa"dariya dayar ta saki
"haba sakina,bakiga yanayinta ba,ba lallai bafa ma a qasar nan ta tashi ba
itama,kinsan man din nan yake da bala'in aji da daukar kai,dukanmu munsan
ra'ayinshi da aqidarsa irin macen da yake buri,da alama kuma ya samu,don wallahi
wannan sai taci uban su'ad a komai da komai"da sauri wadda da alama duka abun yafi
tsumata tace
"Yes,gaskiyanki shuhuda,u know what?,ina ganin ma fa soyayyar da yake mata akwai
banbanci,i never ever seeing him rungume da su'ad,but ku dubu wannan fa,tana
jikinsa,dan gararin idanunshi a wanke,na tabbata ya ganmu but ko a jikinsa,kai i
love this man wallahi naso ace ni na samu wannan sa'ar,dole eesha ta shiga wani
hali" ta fada abun na tsumata,ci gaba sukayi da tattaunawa kowa na fadin albarkacin
bakinsa,'yammata ne dabkowacce ke jin ta burunqasa,kowacce tana burin zamantowa
suruka cikin gidan,wadda dukkansu sun kwana da sanin cewa a gurinsu babbar sa'a ce
ka zama wani ahali na jini cikin gidan,ko yaya sha'ani yake na gidan basa wasa da
shi,mutane ne masu son budawa da kuma babbar harka,idan kuwa suka iso gidan suna
samun dukkanin yadda suke so,duk da kowaccensu mahaifinta ba baya bane shima,saidai
hausawa sunce baba ma da babansa,kafi wani wani ya fika,haka Allah ya qaddari
rayuwarmu,yadda da hakan kadai shi zai sama maka rayuwa mai cike da wadatar
zucci,da kuma cikakkiyar godiya ga Allah bisa dukkan wani bigire da ya azaka,Allah
kasa mu dace,ka bamu wadatar zuci wadda itace babbar wadata itace babban arziqin
duniya.

Sannu a hankali suke takowa zuwa bangaren ummi,jifa jifa suna wuce mutane
da suka yo sammakon zuwa bikin tun farkon satin,sanye take da abaya baqa mai zubin
dinkin buba,ta yane kanta da mayafin rigar,yayin da yake sanye da qananun kaya
shirt da trouser baki daya shima baqaqe,zo kaga wani kyau da sukayi,musamman da
yake riqe da hannunta saboda yadda ya lura akwai yawaitar 'yan sanya idanu,takanji
wani nauyi duk sanda ta tuna yadda ya ritsata awa daya da suka shude a toilet daure
da towel tana shirin yin wanka,yana jaddada mata wajibcin yin wankansu tare fuska
daure,saidai baki daya yanayin da ya ganta ya sakar masa da jiki,ya zuba masa
kasala da wani irin feeling a jikinsa,yayin data yayibi wani towel din ta rufe
kanta hakan ya tunzurashi ya dinga takowa inda take har ya qureta a bango
"Yau zaki san kinyi kuskure,me kike boyemin" ya ambata yana dauke towel din dake
kanta,gashinta ya bazu zuwa kafadarta,abinda ke sake burgeshi da tafiya da shi
kenan,baya ta sake ja taha qoqarin boyewa cikin jacuzzi,cikin sa'a ya samu nasarar
danqo ta,idanunta suka fito ganin yana niyyar sanyata cikin bathtube,tsoron dama
yake son gani cikin idanunta,wani abu daban take koma masa mai kyau,bai bari ba
kuwa sai daya sanyata sannan ya soma rage kayan jikinsa
"Saiki jira na gama nawa wakan sannan kiyi naki tunda baki son muyi tare sannan
kuma cikin toilet dina kike ba naki ba"
"Amma ka bari na fita idan ka gama na dawo"
"Is too late" ya fada ko a jikinsa yana tubewa abinsa,idanuwanta ta runtse sanda
yake qoqarin cire bixer din da shi kadai ya rage,sai qyarma take,bata taba ganin
jiki mai lullube da siffar qarfi haka muraran a gabanta ba,gargasar jikinsa kawai
abar kallo ce,karon farko data soma ganinsa a hakan,ko a jikinsa ya kammala
wankansa tas sannan ya nade jikinsa da towel ya fice.

Dawowa tayi daga duniyar data tafi sanda taji yana matsa hannunta,tuni sun
iso qofar falon ummeen ita yake jira ta cire takalmanta,a nutse ta zaresu sannan
suka sanya kai ciki,shi yayi sallama yayin da suka jiyo muryar ummee tana
amsawa,kunya da nauyi suka cika sumayyan,kamar ta koma bayanshi ta boye haka ta
dinga ji,tana qoqarin zame hannunta dake cikin nashi amma yaqi bata dama,saima rada
daya soma yi mata
"I want to show them i care with amanar da suka bani,nasan haka ne so ya kamata
suma su gani,sai suyi alqalancin waye ya kasa kula da tashi amanar ko?" Sunne kai
tayi ganin idanun ummee na kansu,fuskarta dauke da murmushi da kuma mamaki,don ta
taji yara na fadin zuwan nashi bata yarda ba,don an riga da an saba,yawanci sai ana
ya gobe daurin aure yake zuwa,wani lokaci ma sai ran daurin auren,awa daya kafin a
daura ko minti talatin,musamman idan na yaran 'yan uwa ne,suma sai na kusa saboda
tsabar busy,amma yau sai gashi kwanaki shida saura a daura auren,wannan wane irin
gagarumin canji ne haka ke tunkarar rayuwar yaron nata,bata gushe ba tana musu
barka da isowa fuskarta tamkar gonar auduga,yayin da eesha dake gefe bata daga kai
ba tana danne dannen waya har sai da taji muryarshi,karaf idanunta suka fada
kansu,zumbur ta miqe tsaye tana rarraba idanu,kada dai ace ta fara samun matsalar
idanuwa,wannan yarinyar ya aura?,ko daga bacci ta tashi duk sauyawar da taji da
samun cikakkem hutu dake kwance a jikinta ba zata manta ta ba,haka kawai yarinyar
ta tsaye mata a rai
"Mutanen UAE" haka ummin ke fada wanda wannan kawai ya isheta amsa,sai ta hau
girgiza kai ta shige dakin da ta sauka da gudu,sai sannan hankalin ummen ya kai
kai,takun gudunta yaja hankalin almustapha da ya kai sumayya har gaban
ummee,kunyarta ta sake burgeshi karo na biyu musamman sanda ta zame daga samn
kujera zuwa qasa gaban ummeen,abinda bai taba gani kenan ba wajen su'ad,yana zama
kujerar dake daura da ummin yace
"Waccar fa?,sunzi zasu fara haukar nasu kenan ko?"
"Kai kuma kazo zaka fara kenan ba"
"A'a ummi ni ban da case da kowa,just su kiyaye rules din da na sawa zuwansu gidan
nan"
"Allah fa ya kawo mu,amiran umman khalipha ya fama da wannan" ta fada tana duban
sumayya,alamun qarfi taba ga mai qiba,daga yanayin fuskar almustapha kawai ya isa
ya sanar mata akwai gagarumin sauyi daya fara nasar rayuwarsa,yanayinsa baki daya
akwai sauyi koda shi din bai san ko ya lura da hakan ba,kunya ta sake kamata tayi
qas da kai tana gaidata,ta amsa cike da kulawa da farinciki,shima tashi gaisuwar ya
dora ta amsa cikin jin dadi tana tambayarsu ya suka baro dubai
"Sai kuma gaku tun yau?" Ta tambaya cikin mamaki,satar kallonta yayi wanda ummin ta
kula da haka
"Eh ummi,akwai wani aiki da nakeson yi,shi ya taso ni dole,tunda naga yayi daidai
da date din daurin auren" ta fahimci salon magana ce kawai ta qwatar kai,tunda da
aiki ne da tuni ya shaidawa baba,amma ko baban baisan da zuwanshi ba.

         

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

8⃣7⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

*ya hayyu ya qayyumu bi rahmatika astagis,aslih li sha'any kullahu,wala takilni ila


nafsy darfata aynin*
___________________________________

Qarfe takwas na safe ta farka bayan baccin data koma bayan ta kammala sallar
asuba,babu kowa a dakin sai ita daya,alamu sun nuna ma ya fita,gefe daya ta tarar
da kayan break fast,komai da komai irin wanda zata iya ci,toilet ta shiga tayi
wanka ta dawo ta gyara dakin sannan ta sanya kayan taja kayan ta karya,kwanciya ta
sake yi bayan ta gama,ba dadewa wani baccin yayi awon gaba da ita,bata farka ba sai
data ji ana knocking qofar,ta miqe ta isa ga qofar,ga mamakinta a bude take
muqullin ma na jiki yau bai rufe ba kenan.

Matashiya ce sanye da kayan ma'aikatan hotel din,cikin murmushi ta dubi


sumayya ta gaidata da harshen larabci cikin kokwanto,don bata da tabbacin zata
ji,murmushi ta saki tana mamakin jin larabci mai kyau a bakin matar,tasan yawanci
larabcinsu ba irin wanda ake mana amakarantu bane ta maida mata,sai ta sake fadada
murmushinta ganin cewa tana jin yaren,ta miqa mata wani abu a nade da wata leda mai
qyalli tana shaida mata abincin ranarta ne,sannan ta nuna mata tarin lemuka da ruwa
tace idan ba damuwa zata sanya mata a fridge,matsa mata tayi tana fadin
"La ba'as,tafaddal" ta koma ciki ta biyota,tana tsaye ta gama shirya komai sannan
ta maida qofar ta rufe bayan tayi mata godiya,sai data fara sallar azahar sannan ta
bude,gasashshiyar kaza ce da soyayyar taliya sai hadin coleslow,ba wani da gawa
taci ba ta rufe kasancewar bata jin yunwa.

Kusan haka ta wuni ba cas ba as,har kwanciyar ma ta isheta,ita ba sanin kan


hotel din tayi ba ballantana ta fita,sai daga bisani ne ma ta koma bakin window din
dakin tayi zamanta kasancewar tana ganin mutanen dake kai komo ta nan.

Kusan haka zaman nasu ya kasance har kusan kwanaki goma,da safe zata tadda
ya fita amma ga breakfast dinta,da rana wannan matar zata kawo mata lunch,da
yammaci ta dawo ta tambayeta koda wani abun,sai kuma na dare zata sake kawo mata
shima,sau tari kafin ya dawi tayi bacci,sai haduwa tayi wuya a tsakaninsu idan ba
da asubahi ba,sai data ta farka taga an fidda abincin da bata cinye ba a ajjiye
mata wani,abinda ta fuskanta shine shi din mutum ne wanda bai san dadin jikinsa
ba,mutum ne da ya baiwa sana'a da business muhimmanci mai tsoka cikin
rayuwarsa,bashi da wani lokaci sai na kasuwancinsa,bugu da qari kuma ta lura da
yadda matsalan kamfanin ta sanyashi a gaba,sam ba haka rayuwarsa ya kamata ta
kasance ba,ya qare qarfinsa wajen kasuwanci ba kawai,tana ganin hakan bai dace
ba,ita kanta ta soma qosawa da zaman garin,don baki daya bata ga wani amfani da
zamanta ke da shi ba,tunda bata ganin wanda take zaunen saboda shi,saidai kullum
taci ta sha ta kwanta,hakanne ya sanya yau ta qudurce ba zata yi bacci ba har sai
ya dawo,tanas son tayi waya da 'yan gida,mama,malam abdallanta,zainab da halima
baki daya,ga anty dije,layinta tunda suka shigo qasar ya daina amfani,kuma batasan
inda zata samu wani layin ba bare fa nemesu.

Tana idar da sallar magariba ta shiga tayi wanka,zama tayi bakin mudubi bayan
ta fito ta mutstsike jikinta da turaren humra bayan ta shafa mai,ta goge fuskarta
da powder sannan ta wadata lebbanta da man lebe mai taushi da qyalli,kwalli ta
zizarawa fararen idanuwanta wanda hakan ya sake fito da kyawunsu sannan ta gyara
jagirarta,kai tsaye ta wuce gun kayanta ta fito da atamfarta,holland ce dark brown
ne jikinta,yayin da aka yi maya ado na mint green da yarfi yarfin fari,riga ce da
zani simple,saidai rigar tayi maya cas a jikinta,daurin ture kaga tsiya tayi saidai
baiyo gaba sosai ba,wanda yake fitar da kyan fuskarta da tulin gashinta dake
daure,takalmi ta sanya plate fari qal,sabone shima kamar yadda kayan jikinta suke
sabbi,wani masifar kyau tayi,kallo daya zaka yi mata ya tabbatar maka cikakkiyar
BAHAUSHIYA CE,a qalla tasan zata iya kashe awa biyu kafin ya shigo,hakan ya sanya
ta yanke shawarar fita waje ko hakan zai ribaci idanunta har ya dawo.

Karo na farko data fara fitowa tunda suka shiga dakin,doguwar corridor ce a
qawatacciya mai kama da falo wadda ke dauke da dakuna ajere reras cikin tsafta
qamshi da tsari,kamar zaka zuba abinci a qasa kaci,a hankali ta dinga takawa,har ta
fice daga corridor din bata ga kowa ba,ta karya kwana ta fita wata varender wadda
aka tanadeta saboda hutawa,an tsarata da kujeru da 'yan shukoki cikin qananun
tukwane masu kyau,daga nan kaya iya ganin harabar hotel din sarai da dukkan abinda
ke kai da kawowa,ta nan zaka iya sauka zuwa qasa ko kuma ka wuce zuwa ciki,hakan
yayi maga,sai ta jita sakayau,ta tsaye dafe da makarin varender wanda yake na
silver ne tana kallon komai daidai fuskarta a washe tana more iskar gun da kalle
kallen da takeyi.

A qalla sai data share awa biyu sannan taji ta soma qosawa,hakan ya sanya
ta juya a hankali ta koma ciki,har yanzu bata jin bacci,saboda haka ta koma bakin
window din dakin ta sake tsayawa hannunta harde a qirjinta bayan ta cire mayafin
dake lullube a kanta ta ajjiye.

A gajiye ya turo qofar dakin,sam baiyi tsammanin samunta ido biyu ba kamar
ko yaushe,amma duk da haka bai fasa sallama,jin an amsa masa ya sanyashi daga
idanunshi cikin mamaki yana dubanta,itama nata idanun cikin nashi suke,sai ta saki
hannayen nata ta ta ko a hankali tana janye idanunta daga nashi
"Sannu da zuwa" ta furta cikin sanyin murya lokacin da take yunqurin karbar jakar
hannunsa,sai ya sakar mata cike da mamaki karo na farko da wata ta soma yi masa
hakan ba masinjansa ba,juyawa tayi cikin nutsuwa ta nufi inda taga yafi ajiye jakar
don yi mata mazauni,sai ya tsinci kansa da binta da kallo da idanunshi,ta zama
cikakkiyar bahaushiya zam,karo na farko daya taba tsayawa ya dubi wata matashiyar
bahaushiya cikin shiga ta atamfa,ashe atamfa sutura ce har haka dake fidda ainhin
mutuncin BAHAUSHIYA HAUSA DA HAUSAWA?,ganin tana niyyar juyowa ya sanyashi saurin
janye idanuwanshi ua soma ragewa kanshi rigar samanshi yana ratayeta a mazauninta
"An dawo lafiya?" Ta kuma ambata cikin yin qas da murya wanda hakan ya sanyashi jin
wani yam a jikinsa,bata tsaya sauraren amsar sa ba,don tuni ta wuce toilet,ruwan
wanka ta hada masa mai dumi bayan ta wadatashi da irin turarukanshi na wanka da
yake amfani da su,ta jawo lallausan towel mai yalwa ta rataye masa sannan ta fito.

Yana zaune ne bakin gado yana cire agogon hannunshi bayan ya rage riguna
biyu dake jikinsa,saura wandon coat din da t.shirt mai dogon hannu dake can
ciki,jira yake ta kammala nata uzirin ta fito ya shiga yayi wanka,yana ganin
fitowarta ya moqe yana balle botiran rigarsa tare da shigewa.

Kan kujera ta koma fa zauna tana janyo littafin da anty dije ta bata wanda
sam ta manta da shi sai yanzu,shafin farko ta soma budeww,rubutu ne kamar haka
"A sanda kake son ganin rashin isar namiji duk kuwa isarshi,d'ana masa tarkon mace"
"Matuqar kin amsa sunanki na mace zaki iya sauya mijinki a duk sanda kika so ko
kika ga dama,domin kuwa su din tamkar qananun yara suke" murmushi ya subuce
mata,kunya ta kamata kamar antyn na gabanta,sai ta janye littafin wani tunani ya
fado mata
"Da gaske haka yake?,indai kuwa hakanne zata yi gwaji koda kuwa a gobe ne,sai ta
miqe ta lalubo takarda da biro inda ta fuskanci yana ajiyar abubuwan rubutu,ta koma
saman kujerar ta soma tsara rubutu,tana yi tana murmushi saboda tunanin ta yadda
zata isar da takardar da kuma saqon.
Dai dai fitowarshi kenan idanunsa ya fada kanta,dan zuba ido yayi yana
dubanta,fararen haqoranta a waje,me take rubutawa da ya sanyata nishadi?,bayan ban
bata wani abu da ya cancanci tayi farinciki haka ba?,wannan ne karon farko da yaga
murmushinta muraran haka,sai ya janye idanunshi yana qarasowa cikin falon,baisan me
yasa duk sanda ta hada masa ruwan wanka yakeji dadinsa fiye da wanda zai hada
kanshi ba,dumin yana masa daidai,qamshin yana burgeshi,gajiya na saurin sauka daga
jikinsa,tayi nisa a rubutunta bata ji fitowarshi ba sai qarar bude sif,da sauri ta
maida kanta ganinshi sanye da rigar wanka.

Har ya kammala shiryawa bata gama ba har sai daya zauna cin abinci sannan ta
gama,ta ninke takardar tana murmushi ta daga pillow dinta dake saman kujera ta saka
a qasa,yana cin abincin amma a zahirance hankalinsa duka na kanta,baisan me yasa ya
damu da abinda takeyi din ba,bayan shi mutum ne da bai damuwa da lamuran da ba
nashi ba,sai ta nade qafafunta saman kujeran ra rungume pillow a qirjinta tana
satar kallonshi,sau uku suna hada idanu kowa yana basarwa,a na hudun suka kama
juna,sai ya gyara zamanshi,cikin yanga kamar wata mace ya soma magana a hankali
"Ina fatan ba damuwa bace ta hanaki bacci kamar yadda kika saba ba?" Kai kawai ta
kada masa idanuwanta na duban bezar da aka yiwa filon ado bayan ta dauke idaon nata
daga kan abincin da yake ci,tana mamakin ta yadda mutun zai dinga cin wadan nan
abunuwan da dare kadai wai sune abincin darensa,banda hutu da kudi da yasa jikinsa
da fatarsa murjewa da babu abinda zai hana ya shiga sahun ramammu,saidai babu qashi
a jikinsa wanda zai nuna maka ramarsa,amma idan ya samu kulawar data fi haka ba
shakka jikinsa sai yafi haka cika,ajjiye spoon din hannunsa yayi
"To me ya hanaki bacci as usual?"motsa bakinta tayi itama a yangance tamkar bata
son yin maganar ta maida masa
"nothing"yanayin yadda labbanta da suka sha lips balm suka motsa ya sanyashi tsaida
idanuwanshi kansu,sai kuma ya janye yana ci gaba da cin abincin a nutse
"sai haquri,haka nake haka aikina yake"ya sake fada
"ba matsala"ta amsa a taqaice itama,duk da yayi mamakin yadda ta amsa din amma bai
nuna ba,zai iya tuna duk sanda su'ad ta kawo masa ziyara ta sameshi cikin aiki haka
har ta koma tana mita da qorafi,shi a kan kansa yasan yana hora kanshi da aiki
over,saidai yana ganin hakanne ya dace da shi,baiso ya baiwa kansa wata kafa da
zaiji wani feeling a jikinsa da zai hanashi sakewa,dubai qasa ce ta cin gashin
kai,zaka iya duk harkokin da kaga dama,mata sai kalar wanda ka zaba babu qabilar da
babu,mai ko wanne irin kyau kuma,musamman idan kana da abun hannunka har inda kake
sana'arka za'a kawo maka tallarsu,kai ko ba'a kawo maka ba su da kansu idan suka
samu wargi zasu kawo kansu,musamman idan kayi musu koda ba zaka biya ha zasu iya
kasancewa tare da kai,bazai iya tuna adadin mutanen da ya daina hulda da su ta
sanadiyyar haka ba,idan kuma yana ganin qimarka ya yanka maka babban warning,(da
wannan nakeson jan hankalin matan da mazansu ke tafiye tafiye,ku tsaya tsayin daka
ku kula da mazanku,na tabbatar babu kalad matan da basa gani,wadanda sun fimu
komai,matuqar akwai fahimtar juna tsakaninki da mai gida kuka zauna yana bakin
labarin qasashen da yake zuwa zaki ji irin wadannan labaran,wanda da dama marasa
tsoron Allah sun fada harkar neman mata saboda suna ganin suna wata duniyar babu
mai ganinsu,ko kuma ke kinyin sakacin da har yaga wata mara kintsin ta
burgeshi,wanda tsoron Allah da irin kyautatawar da kike masa shi kadai zai
tsallakar da shi,Allah ka tsare ka kiyaye mana musulminmu a duk inda suke).

Kana dubanshi zai yi wuya ka dauka ba bacci yake ba,sakamakon lamo da yayi
saman gadon cikin tattausan bargo yana sauraren wani recording na tattaunawar sirri
da hamza yayi da qananun ma'aikata yayi recording bada saninsu ba ya turo masa don
gano bakin zaren matsalar dake shirin kunno kai a companyn,a tunaninta yayi bacci
saboda haka ta miqe ta ajjiye littafin hannunta ta dauki kayan baccinta ta shiga
toilet ta sauya
"La haula wala quwwata illa billah...." Ya fada qasa qasa yana jan numfashinsa tare
da kulle idanuwansa,ba wani tsiraici bane da rigar baccin saidai yadda ta lafe a
fatarta ya fitar da sigarta ya kuma haskata,daga sanda ta fito bai sake fahimtar
audion din da yake saurare ba,sai yaci gaba da binta da idanu har ta kai ga yafa
mayafin ta kwanta abunta bayan ta gama addu'o'inta,saidai a banza,tamkar bata yafa
ba haka yake gani,ya tabbatar bazai sake samun nutsuwa ba matuqar tana a
haka,zumbur ya miqe zaune saman gadon,ya miqa hannunshi ya kunna qwan dakin bayan
ya rufe jikinsa da bargo,hasken da ya mamaye dakin shi ya farkar da ita
"Nemi hijabin sallarki ki saka,wannan kayan sam basu dace da ke ba" ya fada cikin
dakiya yana kau da kai sannan ya gayar filonsa ya maida kansa ya ya kwanta bayan ya
kashe wutar dakin,ba musu ta ja hijabin ta zura tana mamakin me maganarshi ke
nufi?,ita dai tasan ba aibu a kayanta,asali ma suna da kaurin da yawonta a dakin
zata iya,baya ga haka ga mayafi data lullube jikinta da shi,ture tunanin tayi gefe
absa dole saboda bacci da yaci qarfinta.

******** ****** *********

Yau kan idanunta aka kawo break din,tana zaune saman kujera lokaci lokaci
tana satar kallonshi bayan ta tabbatar ta sanyabtakardarva muhallin da zai fara
karo da ita a duk sanda ya buqaci aiki da jakar,hannunta riqe da cuo din tea data
hada bata kai ga sha ba,ya fiya ado kamar mace,haka take gulmarsa cikin ranta,tsaf
ya kammala shirinsa ya dauki wayoyinshi da jakarsa,da sauri ta isa gabanshi,sai
kuna ta rage saurin bayan ta isa dab da shi,cup din ta miqa masa tana
kallonshi,shima ita yake kallo,ummee,ummee ce ta fado masa a rai,ita kadai duk
duniya har yau ke masa haka,tunawa yayi da wace ita wajen ummee da baba,sai yasa
hannun damanshi ya karba sannan ya koma gefan madubi yadan jingina kadan daukar yin
hani da shan abu a tsaye daga ma'aiki S A W,a nutse yake kurba yana dubanta kadan
kadan inda take zaune tana wasa da yatsun hannunta,baifi rabi ya sha ba ya tako a
hankali inda take,wanda bata ji takunshi ba sai qamshinsa gab da ita,ya dire cup
din a teburin dake kusa da ita,murya qasa qasa ya furta
"Thanks" ya juya yana niyyar fita
"Ina zan samu layi ina son yin magana da 'yan gida" tsayawa yayi cak,kafin ya daj
dawo da baya kadan,ya fidda wayoyinsa dake aljihunsa ya zari daya ya sake dawowa
kusa da ita ya ajjiye
"Aro" ya fadi a taqaice kafin ya fice.

Bin wayar tayi da kallo,fara ce qal kamar hannu baya tabata,wayar kanta sai
tayi mata kwarjini,saka hannu tayi ta dauka,qamshinsa daya ratsa dukkan wani abu da
yake mu'amulanta shi ya kama wayar ita kanta,bata taba ganin waya mai kyau data
burgeta haka ba,tasa hannu ta shafa screen din ya bude,kasancewar babu password a
kai.

Murmushi tayi ta ajjiye wayar gefe,sai data yi wanka ta karya sannan ta zauna
sosai saman kujera ta soma kiran duk wanda zata kira din daya bayan daya ciki kuwa
har da ummee wadda ba qaramin murna tayi da jinta ba,ta sake jaddada qorafinta na
kullum ta kira almustapha kan ya bata sai yace yana company shin bai hutawa ne
shi?.

Tafe yake yana duba wani file da daya daga cikin manyan ma'aikatansu
wanda shine mataimakin hamza a sashen da suke kula da irin auduga da zararrukan da
suke siya daga wasu kamfanoni,takardun jimillar audugar da suka shigo da su ne yake
dubawa,dab da zai shiga elevator sukayi kacibus da hamzan,sai ya miqawa wancan da
ake kira ramadan yace anjima ya kawo mishi ya qarasa dubawa,don su kammala lissafin
dukkan kudin da suka fita ta wannan fannin.
"Ya dai yau naga kamar kadan so makara baka shigo da wuri ba"
"Jiki da jini ke kawai"
"Gaskiya ne,me kake tunani kan audion daka saurara jiya?"
"Mu qarasa na yi maka bayani", a haka suka qarasa office din.

Kan kujerarsa ya nufa kai tsaye ya zauna yana dora jakarsa saman
teburin,yayin da hamza ya fara bude fridge ya dauko ruwa yana sha,qoqarin bude
jakar ya fara yi amma mazugin ya cije,ya daga jakar don ganin mai ya hanashi wucewa
sai yaga takarda lanqwashe a jiki,cikin mamaki ua ciro takardar ya soma
warwareta,rubutu ne a tsare tamkar da injin buga rubutu aka tsara shi,sannu a
hankali ya soma bin rubutun yana karantawa,yana karantawa kanshi na shiga
duhu,shawarwarine a tsare game da yadda zai warware matsalar kamfanin cikin
sauqi,daya bayan daya kowacce kalma dake qunshe cikin takardar mai muhimmanci
ce,kanshi bai fita daga duhu ba sai da yazo layin qarshe
"ina fatan alkhairi tare da fatan warwarewar matsalar cikin sauri,saboda ka dawo
nutsuwarka,iyalinka na da buqatar zamanka waje daya da kuma samun cikakkiyar
nutsuwarka,kulawar ubangiji ta tabbata tattare da kai" sosai kalaman suka dinga
ratsashi,sai ya samu kanshi da maimaita kalaman,karon farko a rayuwarshi da ya taba
samun wadan nan kalamai masu kyau da tsari daga wajen wata mace dake qarqashin
ikonshi,a hankali murmushi ya subuce masa sanda ya kammala karanta sadarar karo na
biyar
"Lafiyanka qalau kuwa zaka zauna kana dariya kai kadai,mutumin da murmushin naka ma
wataran sai anyi kamar za'a biya kafin a ganshi?"
"Hauka nake" ya bashi amsa kai tsaye cikin gatsali yana gintse fuskarsa tare da
miqewa tsaye,takardar ya dunqule zaiyi jifa da ita yana jan tsaki sai kuma ya
fasa,ya daga takaddun dake gabanahi ya saka ta a tsakiyarsu,hakanan sai yaji wani
sashe na zuciyarsa na bashi qwarin gwiwar gwada amfani da shawarwarin dake qunshe
cikin wasiqar,jawo wayar land line yayi dake gabanshi ya fara latsawa,cikin
qanqanin lokaci ya bada umarnin tara dukkan ma'aikatan dake cikin kamfanin a babban
dakin taro dake kamfanin,freezer ya isa ya ciro ruwan shima yana kurba a
hankali,binsa hamza yake kallo kafin yace
"Wai meke faruwa haka musty?"
"Zaka gani" bakinsa yaja yayi shiri,yasan tunda ya fara magana haka a taqaice ba
mai sanya shi fadadawa,tilas yayi shiru har sanda aka isar masa da saqon gama
haduwar ma'aikatan baki daya sannan ya dubi hamza
"Taso muje,meeting ne na qarshe".

Cike dakin taron yake da baki daya ma'aikatan kamfanin,kowanne zaune kan
mazauninshi cikin tsari,shigowarsa ya sanya kafataninsu miqewa cike da girmamawa,ba
wanda ya zauna sai da ya zauna kan tashi kujerar ta musamman wandda ke a
center,hamza ya zauna kan wadda ke daura da tashi sannan suka zauna,kowa ya shiga
taitayinsa don sun san kan matsalar da har yau ake tattaunawa,musamman da
kowannensu yasan halayyar ogan nasu,sosai ya kashingida tare da lafewa cikin
kujerarsa yana duban kowa daya bayan daya,wanda hakan ya sake ladabtar da su,a
hankali ya soma jefa bayani daya bayan daya yana karantar yanayin kowa cikin
tataccen turancinsa,cikin qanqanin lokaci dakin ya soma rudewa,wata uwar tsawa ya
daka tare da dukan table din dake gabanshi,shiru dakin taron ya sake yi,kowa ya
sake shiga taitayinsa,dorawa yayi da bayanin wanda cikin qanqanin lokaci gaskiya ta
fara fitowa,tsawon sa'a biyu sai gashi komai ya bayyana,ya bawa kowa hukuncin daya
dace da shi,wadanda suka cancanci ya dakatar ya dakatar da su saboda ya zama jan
kunne a guresu,tare da kafa sabbin dokoki masu tsauri sannan ya sallami kowa.

A hankali yake jin nutsuwa da kwanciyar hankali sanda yake takawa don komawa
zuwa office dinshi,bai taba tsammanin shawarwarin dake rubuce zasu warware damuwar
cikin sauqi haka ba
"Wai maan,ya akayi komai yazo da sauqi haka"
"Daga Allah ne......inaso mu zauna mu tattauna kan yadda ya kamata mu fara noman
audugar da muke amfani da ita da kanmu.....but amma yanzu zan wuce,zamu hadu gobe
in sha Allah" binshu yaje da kallo,yau almustapha ne zai bar office tun la'asar?.

Shirt ce a jikinta irinta mata wadda ta fidda shape din jikinta mai gajeran
hannu,sai wrapped skirt mai roba wanda ya zauna mata daidai jikinta,kanta ba
dankwali tunda ta idar da sallah ta cire hijabin sallar tata ta ajjiye gefe,kwance
take rigingine saman kujera riqe da wayar tana duba hotunan ciki,zaman kadaicin ne
ya isheta,hakan ya sanya bayan ta kammala sallar la'asar ta sake daukar wayar tana
duba hotunan don debe mata kewa,don tunda ta gama kiran da zatayi ta ajjiye wayar
bata kuma tabata ba sai yanzu.

Kusan duka hotunan shi ke ciki,wanda da alama ba'a cikin wayar aka
yiba,turasu akai kawai,babu hoton da baiyi kyau ba ciki,da yawa daga ciki da alamu
baisan am daukeshi ba,baki daya sanye yake da suit,bata taba ganinshi da shigar
manyan kaya ba tunda take,tamkar bature haka yake wajen sanya sutura,ta shagala
sosai wajen kallon hotunan,daya bayan daya,sannu a hankali ta soma sakin
murmushi,ko cikin hotunan halayyarsa tana fitowa,kusan duka adake yake cikin
hotunan wani kuma zaka sameshi cikin aiki yake ko yana bada umarni.

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

8⃣7⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

*SANARWA DA BABBAR MURYA*

*BA NUFIN MU CIN ZARAFIN WANI KO BATAWA WANI BA,SABODA GUDUN RUBUTA MUNANAN AYYUKA
CIKIN LITTAFIN AYYUKANMU,WANDA SAI MUN TSAYA GABAN UBANGIJI MUNYI BAYANI RANAR GOBE
QIYAMA,AMMA TURA TA KAI BANGO,AN FARA SHIGA SHINGENMU ANA MANA BARNA,BAYAN MUN KAME
KANMU DAGA DUKKAN WANI ABU DA ZAI ZAMA SHIGA HURUMUN WANI BATANCI KO CIN ZARAFI A
GAREMU*

*GAREKU MASU SATAR FASAHA ZANCE KO BARAYIN ZAUNE*

*Ina mai shaidawa duk wani mahaluki da yasan cewa yaci da gumi na,ya dauki wani
littafi nawa da na zauna na bata lokacina na rubutashi da hannu na don al'ummar
ma'aiki su amfana,MALLAKINA ya kaishi wane waje ya saida yana zuba kudin a
aljihunsa cewa NI SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA BAN YAFE BA,BAN YAFE BA,BAN YAFE
BA,KUMA INA ROQON ALLAH YAYI MIN SAKAYYA KAYANA DA AKA DAUKA ANA SAIDAWA*

*GAREKA KO GAREKI BARAUNIYA A OKADA,DUK WANDA YA SANSHI KO YA SANTA YA ISAR


MASA/TA*

*ABADAN DAYA SATA KOTA SATA,AKA KAISHI OKADA ANA SAIDAWA AKAN KUDI NAIRA DARI
BIYU,NACE ALLAH YA ISA BAN YAFE BA,INA ROQON ALLAH KUMA YA FITAR MIN HAQQI NA
MATUQAR BANI NA ZALUNCESU BA SU SUKA ZALUNCENI,TUNDA BAN TABA DAUKAR HAQQIN WANI
MALLAKIN WANI NA MAIDA SHI MALLAKINA BA,ALLAH YA BIMIN HAQQINA,INA FATAR ZAKU SADAR
DA WANNAN SAQO ZUWA GARESU*

*SANNAN WANNAN LITTAFI DA NAKE RUBUTAWA DAMA SAURAN LITTATTAFAINA,MALLAKINA NE,NA


YISHI NE KYAUTA BA NA SAIDAWA BA,A DUK SANDA NAKE DA BUQATAR SAIDAWA ZAN SIYAR
DIN,AMMA BAN BAIWA KOWA IZINI YA SIYAR MIN BA,WANDA KUMA YAYI HAKAN NA BARSHI DA
FITOWAR RANA DA FADUWARTA,NA BARSHI DA MAI SAMA,MUGA ALFANUN DA ZAI SAMU CIKIN
KUDIN DA KA SAMU TA HANYAR SAIDA ABUN SATA*

*WALLAHI WALLAHI ALLAH MU GUJI CIN HAQQIN WANI,BILLAHILLAZAI LA ILAHA ILLA HUWA DUK
WANDA KA GANSHI RAN QIYAMA YA QETARE TO BABU HAQQIN WANI A KANSHI,WANNAN ALQAWARI
NE NA UBANGIJI,SAI YA FITARWA DA DUK WANI BAWA HAQQINSA KAN DAN UWANSA,KODA DABBA
CE TA ZALUNCI 'YAR UWARTA DABBA*

*ALLAH KASA MU DACE*


_____________________________________

        ta fahimci salon magana ce kawai ta qwatar kai,tunda da aiki ne da tuni ya


shaidawa baba,amma ko baban baisan da zuwanshi ba,koma meye tana maraba kuma tana
fatan alkhairi da samun wannan kyakkyawan canjin,sai ta saki murmushi
"Masha Allah" ta fada tana maida dubanta ga sumayya
"Me zaku ci,ko zaki shiga kitchen ki sama muku ko snacks ne,yau duka ma'aikatan na
can baya suna aikace aikace suma"
"Am ok ummee" almustapha ya fadi,farinciki ya mamayetq,ta tabbata tunda ya fadi
hakan hakanne,sai ta waiwaya ta dubi sumayya
"To kefa amira?"
"Nima ummee na......"
"Qarya take,ba abinda naga taci tunda muka taho" almustapha ya katseta yana tsareta
da ido,murmushi ya subucewa ummee,salon da bata taba gani wajen almustaphan ba yau
sai gashi da shi
"Maza shiga ki samu wani abu kici,halan shi kin sama masa wani abun yaci ke baki ci
komai ha ko?" Cikin kunya tana murmushi ta miqe kanta a qasa tayi kitchen din,yayin
da ya bita da kallo yana yabawa salon kunyarta,yanayin yadda take ganin girma da
darajar mahaifansa,tunanin yadda cikin qan qanin lokaci kan ya gama shiryawa ta
hada misi wani hadadden patatoe salad ya fado masa,ya jima baici hadin salad da ya
masa dadi irin wannan na,murmushi ua dan qwace masa,yanayim takun ta na burgeshi,ya
dauke kai sanda ta kai ga shigewa kitchen din,sai suka hada ido da ummee,shi yai
qasa da kai kunya na lullubeshi,ita kuma ta dauke kai tana sakin murmushin tsantsar
farinciki,waskewa yayi da cewa
"Ummee ya adam bai qaraso bane?"
"Ka fadi haka mana tunda wannan karon ka rigashi zuwa,ina zaton sai wajen laraba
zai qaraso,amma dai ni'ima ya hadato da yaran sunyo gaba,dazun da safe suka
sauka,shi da fahariyya sai ran laraban"kai ya gyada cikin gamsuwa
"Kunje kun gaida maamaan ne?"
"A'ah"
"To bari ta fito sai kuje ku gaisa,da alama itama batasan da zuwan naka ba,babanku
kam baya gari,ya tafi jigawa ta'aziyyar wani abokinsu da ya rasu,amma gobe ma zaya
dawo" ta fadi tana daga wayarta dake ringing wanda amira ce ke kiranta,bayan sun
gaisa take shaida mata zuwansu sumayyan,ihu ta saki har almustapha dake zaune yana
jiyota,hararar wayar yake kaman amiran ma wajen,magiya ta dinga kan ummee ta bata
sumayyan ta kira wayanta a kashe,dai dai sanda sumayyan ke fitowa daga kitchen
din,ummi ta miqa mata wayar,a ladabce ta amsa ta koma gefe tana fidda
murmushi,addu'a kawai take kada amiran ta baro zance ta bata kunya,ai kuwa zuba ta
hau yi
"Amma namecy kinci amanar qauna da baki gayan har kin iso abuja ba,halan soyayya ta
fara zaqi har kin soma mancewa da kowa sai wannan miskilin mijin naki,ina fatan
kina bada wuta wajen sukurkuta masa shi muga ta tsiya,tab ai wallahi jibi nima zan
taho Allah,ina fata kin samo mana tsaraban baby,wallahi har so nake naga
babynku,kyau tako ina,wazai dauko uwa ko uba?,wa yaga ya man ya baby" gaba daya
kunya ta cika sumayyan,yadda almustapha kadai ya kafeta da ido tasan yanajin komai
amiran ke fada,ta sanshi sarai da kaifin ji,yunqurin datse kiran take sai ya miqa
mata hannu,a hankali ta tako ta miqa masa wayar,ya kara akunnensa sanda amiran ke
cewa
"Wayyo soyayyya zamu sha kallo......"
"Gidanku mara kunya fitsararra,idan naga qafarki gidan nan jibi sai na karyata na
zubar,idan kin musa kuma bismillah" ya datse kiran,daga bangaren amira sai ta kwabe
fuska zata sanya kuka,saifullah dake zqune gefanta ya dunga tiqa dariya har da
qwarewa da lemon da yake sh,haushi ya sanyata daukan filo ta dinga maka mishi shi
kuwa yana fadin
"Maganin aku kuturu mai shegen zance kenan,tun dazun nake kwabarki kiyi a hankali
may be suna tare amma kika qi ji,tunda kuwa ya man ya fadi haka ke da zuwa gida sai
ana gobe daurin aure"kuka kuwa ta sanya taba buga qafa
"wallahi wallahi ban yarda ba,don kawai kaji ya almustapha ya fada ko?"sai ta saki
filon ta wuce bedroom alamaun taji haushi ya miqe da sauri ya bita domin yayi
lallashi.

        Boye dariya ummin ta shiga yi tana basarwa,don itama taji wani abun,sauka
yayi daga bangaren kira ya shiga wajen adana lambobi,da dai dai ya dinga bi har ya
iso wajen lambar da ya tabbata tata ce saboda ga hotonta nan saman lambar,ya dauki
wayar shi ya kwashe lambobin ya adana a tashi wayar,ganin yadda kunya ta rufe
sumayyan yasa tace
"kuje ku gaida maamaa,daga nan ku wuce sashenku sai da safe ma hadu"
"To" ya fada yana sauke qafarshi wanda ya dora daya kan daya ya miqe ya isa gefan
ummin ya ajjiye mata wayarta
"Sai da safe ummee" suka hada baki wajen fada sai da ya waiwayo ya dubeta,dauke
kanta tayi ummen ta amsa
"Sai da safe,Allah ya bamu alkhairi".

       Kusan bangaren anty maamaa wannan karon yafi jama'a,hakan baya rasa nasaba
da kasancewar ita keda bikin wannan karon,auren yara biyu tak duka maza da Allah ya
bata,baki ta kama itama
"almustapha?,tun yanzu?"murmushi kawai ya saki yana fatan kada ta sake cewa wani
abu saboda 'yammatan dake falon,bai ko zauna ba hannunshi zube a aljihun wandonshi
ya soma gaidata,ta amsa cikin farinciki itama,don ta tabbata lallai hasashen baban
ya soma zama gaskiya,tunda ga mustpha ya waiwayi gida ana daurin auren qannenshi
saura kwana shida,sumayya kam tuni tana wajen humaida,wadda sukayi farinciki ganin
juna,ya waiwaya bayan sun gaisa,ganinta wajensu ya sanya ya basar ya juya ya
fice,cikin sakewa suka gaisa da anty maman tana dan tsokanar sumayyan kafin ta miqe
ta fice ta basu wuri,ta sake sosai cikinsu humaidan aka dinga hira,abinka da mata
gwanayen gulma,kusan kowa kallon sumayyan yake,kowa da irin gulmar dake cinsa
arai,yayin da dama daga cikinsu ke jin dama sune sumayyar,a qalla sai gashi sun
kwashe wajen awa daya suna shan hirarsu,don humaida har kiran amira tayi ta saka
handsfree aka dan taba da ita,hakan ya sake tsokalota taji kamar tayi tsuntsuwa ta
taho.
       Tun da ya shigo yaje duba agogo yana kasa kunne amma yaji shiru,har ya
kammala shirin kwanciya cikin wasu hadaddun pyjamas masu shegen kyau da suka haska
shi,yana son ya daure ya basar amma sai zuciyarsa ta gaza,a hankali ya sauko ya
soma takawa ya sauka qasan benen,ya bude dakunan baccinta bai ga alamun ta shigo
ba,ya koma sama ya bude dakin baccinta dake sama nan ma babu alamun an
shiga,dakinshi ya koma ya zauna gefan gado yana son samin meke sanyashi damuwa haka
da lamuranta?,laluba lambarta fake cikin wayrsa wadda yayi servinn dazu yayi sannan
ya shiga bangaren aikawa da saqonni ya tura mata gajeran tex
"Come back", suna tsaka da hiransu saqon ya shigo,sai abun ya daure mata kai
kasancewar bata da lambarsa,daga bisani ta ajjiye wayar tana zaton batan kai saqon
yayi ba wayarta zai shigo ba,mintina goma suka shude shiru,ya sake lalubo lambar ya
kira,bugu kusan uku sannan ta daga ta kara kunnenta,yana iya jiyo hayaniyar su ta
cikin wayar,haka kawai tasha jinin jikinta duk da batasaj number din ba
"Assalamu alaikum" ta furta a nutse,har cikin zuciyarsa sallamar ta ratsashi,cikin
zuciyarshi ya amsa a fili kuma yace
"Bance ki dawo gida ba?" Ta fahimci muryar sarai amma sai tace
"Waye ke magana?"
"Ok,baki gane ba kenan?"
"Eh" ta fada tana sani
"Well" ya ambata shima yana katse wayar,sai ta ajjiye wayar yana qoqarin saukowa
daga saman gadon.

       Anty maamaa ce ta sauko daga sama tana duban sumayya


"Lalala amiran umman khalipha?,me kike har yanzu baki wuce gida ba?,ya zaki baroshi
shi kadai waya gaya miki ana wannan sakacin,tashi ki wuce tun bai biyo sawunki ba
wallahi" ta fadi don tasan halin mustaphan sarai,murmushi ta saki yayim da su
humaida suka sanya dariya,humaida tace
"Allah sarki mu da yake warin takalmi muke mu kwana muna hira ma ko anty"
"Yo wa ya damu da ku?", ta fada tana juyawa sama tare da yiwa sumayya sallama,dif
dariyansu ta katse baki daya,kowa ya kama kanshi,hakan ya sanyata dagowa,sai ta
ganshi tsaye cikin kayan bacci,takowa ya dinga yi a nutse har inda take sandare a
atsaye,yasa hannu ya zare wayarta dake hannunta ya dauke cak,baki daya 'yammatan
sukayi mutuwar zaune na wucin gadi har ita sumayyan,ko a jikinsa ya juya dauke da
ita ya fice daga falon.

       Kallon kallo aka soma yi tsakaninsu,humaida ce ta soma tuntsirewa da


dariya,abun ya matuqar burgeta,kamar a fina finan india
" to wallahi tunda guy din nan ya soma haka mu rufawa kanmu a siri mu dinga kora
masa matarsa da wuri,idan ba haka ba wataran sai munga abinda idanuwanmu ba zasu
iya dauka ba"
"Wai shi dan air ba" inji wata daga cikinsu,wadda a zahirin gaskiya hassada take ji
cikin zuciyarta,don itama taso ace ta zama daya daga cikin matanshi
"Ba wani dan air wallahi,har ga Allah abinda ya sanya nakesom auran irin mazan
nan,nuna so babu limit ko a gaban waye wallahi,wani miskilin namijin bai iya nuna
miki qauna ba,idanunshi basa gani balle suji kunyar kowa" dariya suka sanya suka ci
gaba da tattaunawa kowa na fadar albarkacin bakinshi.

         Bai direta ba sai da ya saita mata hanyar matattakala,ya harde hannunshi


yana mata nuni da idanu kan ta hau,babu musu ta haura saman kunyar abinda ya mata
cikin jama'a na kama ta har cikin dakinshi,qofa ya maida ya kulle ya waiwayo cikin
shammata ya turata saman gadon,baki daya ya danneta,ya dora mata nauyinshi,fuskarsa
kawai ya dago yana dubanta,idanunshi cikin nata suna musayar numfashi,sosai ta gane
kuranta,numfashinta ya soma mata nauyi
"Qirjina ka daga ni"
"Eh ai so nake na nuna miki banbancin,don na lura kin soma rainani saboda kinga
makwancina.....me kike gayawa amira take rawan qafan zuwa ta sameki?,sannan me kike
gayawa wadan can shashashan suke babbaka dariya kaman hauka sabon kamu?" Narai
narai tayi da idanuwa,yatsansa ya dora saman lebansa yana fadin
"Shshshshsh,banson wani kuka,idan kuwa kika sake kikayi yau tilldown zanyi sai an
miki ruwan zafi"cikin taushin murya a shagwabe da son qwatar kanta tace
"Allah babu komai ka yarda dani"sosai ta masa kyau,shagabarta ta taba zuciyarsa
qwarai,murmushi na son qwace masa amma ya dake,bai son ta gwada abinda su'ad taso
dauka dabi'ar yi,wato kwarzantashi da yabonshi da fadan qwarewarshi a kan
shimfidarsu gurin qawayenta,randa kunnensa ya ji masa Allah ya sanya ranar ta
soma,mutum biyu ta gayawa,ranar taga tashin hankalin da bata taba gani ba,don cewa
yayi tunda ta gaya musu to ta sa a ranta sai ya auresu babu fashi,har ciwo sai da
yaso kamata,babu shiri ta fatattakesu sukayi baran baran bata sake ganinsu ba,da
qyar ta sha kanshi
"ta yaya zan yarda da ke?"
"Saboda da gaske nake,ba aninda zan gaya musu,nasan fa haramunne mace ta dinga
fadin sirrin mijinta,Allah ya la'anci mai aikata hakan"murmushin da baiso dole ya
kubce masa,sai ya samu kansa da sanya hannunshi kan hancinta yana jan hancin
"au Allah,ashe ni din mijinki ne" kunya ta kamata,ta rasa inda zata tsomala
ranta,sai kawai ya rintse idanuwanta
"Kada fa ki tsammaci na haqura,dole ki bani wani abu da zai sanyani na haquran,idan
ba haka ba,Allah yau sai jikinki ya gaya miki" ya fada yana shan qamshi,da sauri ta
bude idanunta,kamar zata saka kuka
"To ni mai zan baka?,banda abinda zan baka"
"Akwai" ya fada yana jifanta da wani kallo wanda shi kansa baisan yana mata shi
ba,sosai take amsar saqon da yake aikata mata,sai ta kasa janyewa daga kallonshi
tamkar masu kallon quda,nuni yayi mata da bakinshi yana cewa
"Kiss me,shine kadai zai sanya na haqura" da sauri ta dago kanta da niyyar yi masa
din don ya barta,nauyinsa da kunyarsa take ji amma shi baya gani ne wai,tana dora
bakin nata ya hade su waje guda ya shiga sarrafa shi yadda yake so,bashi ya barta
ba sai da ya tsotsi lips dinta son ranshi,da gudu ta fada toilet,tana iya jiyoshi
cikin rarraunan murya mai taushi yana cewa
"Be carefull,ke da su yanzu akwai banbanci"mamakinsa take,wai almustapha ne
haka?,dama haka yake?,tayi maganar a zuciyarta tana tsaye gaban mudubi tana duban
kanta murmushi ya qwace mata,wanka ta sake yi saboda kwanciya sannan ta daura
alwala ta fito.

       Gaban drawer ta ganshi tsaye ya zuge jakarshi,jikinta ta shafe da turaruka


bayan ta shafa mai wanda ya qarawa fatarta laushi,ta taka a hankali ta isa inda
abun sallah yake ta shinfida zata yi shafa'i da wutiri,har ta idar yana tsaye kaman
mai nazari,qaramin tsaki ya saki ya koma gefan gadon ya zauna ta daga kai tana son
dubanshi,wai meke sauyashi haka ne?,dazu da zata shiga toilet murmushi ne kwance
saman fuskarshi amma yanzu ba haka bane,can qasa taji yace
"Gobe adam zaizo zamu wuce jigawa wajen baba,i think sai wajen alhamis zamu dawo
tare da shi"
"Allah ya nuna mana" ta fada tana miqewa ta fahimci kayan sawarshi yake son hadawa
ya kasa,hakan ya sanya ta qarasa bakin cupboard din ta soka zaqulo kayan daya bayan
daya,sai ya bita da kallo,yana son yaga damuwar tafiyar da zaiyi ya barta ko
qanqani ke saman fuskarta,mutum ne shi mai son a kula da shi,rashin hango hakan da
baiyi ba sai ya sake dagula masa lissafi,sam baison zuwa jigawar nan,saidai umarnin
baban babu abinda zai hanashi binsa matuqar hakan bai sabawa mahalicci ba.

         Wani tsakin ya sake ja,yanajin duka lissafinshi ya dagule,bai taba jin


wata tafiya ta dameshi ba sai wannan 'yar qanqanuwar tafiya da bata kai matsayin
komai ba a irin tafuye tafuyen da ya saba yi,ya bar gida tsawon wata da watanni
ba'a ganshi ba shima baiga kowa nashi ba
"Bar kayan,zan samu wasu a can,zo nan" ya fada yana dubanta,ta waiwayo sannan ta
tako a hankali zuwa inda yake,da idanu ya nuna mata hijabin jikinta,gabanta ya
fadi,bata tsammaci zai ce ta fidda shi ba shi ya sanya ta gwada wata riga da amira
ta bata,ta mance da ita baki daya sai yau cikin kaya ta ganota,idanunshi a kanta
yana tabbatar mata da cika umarninsa,haka ta sanya hannu tana ji tana gani ta cire
din
"Sunbahanallah" ya fada da wani irin amo,hannunshi ya bude mata yana jingine da
gadon,sai taci gaba da takowa har inda yake ta shige jikinsa ya rufe hannayensa
yana shinshinar qamshinta,ta jima ajikinsa yana abinda ranshi keso,zuwa sannan ya
soma sakin layi,a kunnenta ya rada mata
"Naso na barki to have some rest,but i will miss you gobe,zan iya kasancewa
dake?,kin amince?" Kanta ta daga masa cikin kasala
"Thank you,thank you soo much" ya fada cikin murya mai cike da shauqi,yanayin yadda
ya tafi da ita ya tilasta mata bashi cikakken hadin kai wanda hakan ya yi masa dari
bisa dari.

      Tana jikinsa amma tunaninta yake,wannan daren ya sake zamar masa na


musamman,wani abu ya tsaye masa game da ita,ji yake kamar ya nemi alfarma wajen
baba ya barshi a nan,ko kuma ya dauketa su tafi tare,saidai babu damar hakan,ya
tabbata tunda baban ya nemi ganinsu wani muhimmin abu zasu yi a can.

        Yana tsaye yana shiryawa itama tana tsaye kusa da shi tana miqa masa duk
abinda zaiyi amfani da shi,yau din ma dai surukuta suke taqi kallonshi,duk da yadda
taso ta morewa kallon nashi,sakamakon shigar shadda da yau yayi,duk da cewa ba
dinkin tazarce bace amma tayi masifar yi masa kyau,kwalliyar taso ta tafi da ita
don dai kawai ta maze,ga kuma kunyar da jiya ya bata,har ya kammala shiryawa tsaf
ta miqa masa kofin hadden coffe wanda ta daidaita masa zafinshi,kofin na riqe a
hannunshi,tururinsa da qamshinsa na shiga masa hamci,yayin da dukkan idanunsa da
tunaninsa suke kacokam a kanta,ya lura sarai shigar tayi mata,amma bai furta mata
ko nuna mata ba
"Wai dama haka aure yake?,haka ake ji?" Yake qiyasatawa a ransa,a hakan yasan bata
gama sakewa da shi ba,baisan wanne matsayi ta bashi cikin zuciyarta ba baya ga
matsayin miji,sarari yake nema wanda zai zauna ya dasa mata zazzafar soyayyarsa
cikin zuciyarta,don har yau baisan a wanne rank ta bashi ba,sai data gaji da shirun
ta waiwayo ta dubeshi
"Yana sake hucewa,yaya kuma na jiranka"
"Eh jira dama nake ki gama yajin aikin kallona din sai na sha" ya fada yana kai
kofin bakinsa,kai ta kautar tana murmushi a boye,a haka sai ka rantse bai iya
magana ba sam,amma idan ya yankota a nutse sai ta tsaya maka.

        Ta baya taji ya ruqota,ya mannata da jikinsa kansa saitin kunnenta


"Me zan samu?" Ya fadi yana duban wani kwantaccen gashi dake wuyanta mai
santsi,shiru tayi tana tunanin me yake nufi,ganin bata ce komai ba sai ya dora
"Zan wuce,kada ki fiya fita wajen gidan nan,coz nasan akwai baqi da yawa da za'a
iya yi a kwanakin nan,ok?"kai ta gyada tana jin wani iri babu dadi,sakinta yayi
sanda wayarshi ta soma ruri ya duba yaga yaya adam ne,wanda ya gama shirinsa shi
kadai yake jira,ya tsammaci ma shi zai rigashi gama shiryawa kamar yadda aka
saba,sai gashi wannan karon almustaphan yana son ya makarar da su,juyawa yayi a
hankali zaya fice,sai ta biyo bayanshi cikin sanyin jiki tace
"adawo lafiya,Allah ya tsare hanya,a gaishemin da baba"saqon yayi masa dadi,sai
yayi kamar zai juyo sai kuma ya fasa,ya amsa da
"ok" yana ficewa,bayanshi tabi da kallo,bata taba ganin mutumin da kayan hausawa
suka masa kyau har haka irinsa ba.

       Haka kawai take jin ba dadi,wani yanayi na shigarta,qarfafa jikinta tayi ta


gyare ko ina tsaf,sannan tayi wanka tare da yin madaidaiciyar kwalliya ta yafa
wadataccen mayafi ta fice wajen su ummee,sai data shiga ta gaida,gidan babu laifi
ya sake cika,ga jikoki nam sun soma halartar gidan,yaran huda anty farida da
'ya'yan adam yaran kishiyar ni'ima data taho da su,a wajen maamaa ta hadu da
ni'iman,fuska sake suka gaisa,hira ta dan gudana tsakaninsj,haka nan ni'ima ta
kwantawa sumayya kamar yadda sumayyan ta kwantawa ni'ima,daga bisani tace bari taje
wajen ummee,a can ta tuqe wajen ummeen,cikin siyasa ummen ke janta da hira tana son
taji ya zaman nasu yake,sosai tayi qoqarin nuna mata komai lafiya yake,hakan ya
sake faranta ran ummeen matuqa,sai ga amira da azahar a gidan,ranar sunga
tabara,tunda taji labarin yaa man din sun tafi jigawa tace sai ra taho,ya saif ya
iya da tabara,haka ya barta amma da sharafin wuni kawai zata dinga ta dawo,wunin
baki daya ya zowa sumayya cikin sakewa,hankalinta kwance,babu gilmawar eesha
sam,bata san ina tayi ba,bata san meke faruwa ba don haka babu abinda yazo ranta
gamenda eeshan,bata koma sashenta ba sai bayan isha'i,kasa zama tayi,baki daya
sashen nata yayi mata babu dadi,hakan ya sanya ta koma neman 'yan kwana,da fari
kowa qi yayi,sabida sashen ba wajen zuwan kowa bane,daga mai sashen har uwar
gidansa ba masu jan jama'a bane,humaida da humaira suka ce sai sunje,hakan ya sanya
nadiya da yusra binsu suma,a dakin gadonta na qasa ta saukesu,hakan ya debe mata
kewa matuqa,don suna tsaka da hira bacci ya kwashesu.

         Washegari ummee ta danqa mata kayan fitar biki kamar yadda ta yiwa ni'ima
fahariyya da su'ad,haka ummeen take,duk wani sha'ani idan ya taso sai ta yiwa
jikokinta da 'ya'yanta kayan fitar biki,macace mai hannun kyauta,hakan ya sanya
mutane da dama kejin dadin zama da ita,kowa takan masa dinkin ne daidai da
ra'ayinsa ko abinda taga zaya dace da shi,godiya sosai ta yiwa ummeen har taso tafi
wadda ni'imah ke mata,bangarenta ta koma ta dora girki,karo na farko,girki tayi
musu mai shegen dadi wanda ya janyo wasu ma bangaren nata,ta diba wani da kanta ta
kaiwa ummeen,ba qaramin burgeta abincin ya yiwa ummee ba,ba shakka almustapha ya
dace,ya samu macen da suka jima suna masa addu'ar ya samu,godiya ta dinga mata har
hakan ya bata kunya,har gidan wanda ke musu dinki yazo ya karbi dukkan dinkunansu
wanda zai gama musu ne a kwana biyu kacal,abinka da kudi qare magana,shi dama haka
dinkinshi yake,manya mutane yakewa dinki saidai fa babu saba alqawari,kaman qaramin
kamfani ne,yana da ma'aikata,kowa da abinda yake hadawa,wani hannu,wani gaban
riga,wani bayan riga,wani kalmasa haka dai da sauransu

Laila,khalipha,hafiz da minal duka sun shigo,ta rasa yaya zatayi da laila,ta


addabeta,duk bayan mintina sai ta tanka ta
"Wai,wallahi ansha da mami da batazo taga yadda 'yarta ta koma ba,don Allah
khalipha zaka ce anty summynmi ce wannan" da yake shima uban magana me sai ya biye
mata sukayi tayi,dariya ta shata ta gode Allah,batasan sanda lailan zata daina
shegen surutu ba haka,antyn dijen ce taqi shigowa,ta dinga kiran layinta tana
qorafi amma saidai tayi dariya tace zata shigo,gashi ita babu damar fita tunda bata
sanar masa zata fita ba,haka kuma kunya take ba zata iya kiranshi ba,

Ranar laraba mai qunshin dakewa su ummee tazo har gida,daki ne babba aka
ware a can bayan gidan anan take zama idan tazo musu qunshin,ummeen da kanta tasa
aka kira mata sumayya tace ta shirya za'a yi mata qunshi,qarfe hudu na yamma aka
gama mata baki daya ja da baqi,kowa yasan yadda lalle ke yiwa farin mutum kyau
walau ja ko baqi,kamar ka cire hannun saboda yadda ya zanu ya zauna sosai kamar
dorashi aka yi,ita kanta ummen sai da tace masha Allah,ta dubi sumayyan tana cewa
"Kije kinyi baquwa,umman khalipha sai yau taga damar zuwa" farinciki ya cikata,
bata iya tsayawa ta qarasa cire lallen na hannunta sai ta miqe ta nufi sashen
nata,da gudu ya qarasa ta rungume anty dijem,sarkin kuka har ta soma tara qwallar
"Au ashe har yanzu baki girma ba sumayya?,inaga tare zaka daina kukan quruciya ke
da abdallah da alama" sai ta saki antyn tana dariya,daki suka shige da anty
dijen,farinciki fal zuciyarta,kallo daya zaka yiwa sumayyan kasan cewa kwanciyar
hankali ya fara samuwa,kasa gayawa antyn komai tayi,sai take jin kunyarta,to ita
din ma bata damu sai taji ba,ta dai sake jan hankalinta kawai,sun jima tare kafin
antyn fa fidda wasu kayayyakin gyaran jiki ta bata
"Hajiya lami ta kawo min su,suna da tsada amma akwai kyau,wannan wata hadaddiyar
dilka ce,kwana biyu kadai zakiyi amfani da ita zaki ga yadda zaki sauya,da kanki
zaki nemesu nan gaba" sai wata gumbar aya ta kankana data dabino da madara,sabo
dadinta da gardi tuni sumayyan ta kusan cin rabi a haka suna zaune suna hira,riqe
antyn tayi sai da akayi sallar magariba sannan ta tafi,kasancewar bangaren nata
babu kowa duka suna gidan amare sunje musu kamu.

Sai data yi sallar sannan ta janyo kayan dilkar ta soma hadawa tana fadin
bari ta gwada,ta gama rsaf ta shafe jikinta bayan awa daya ta murje ya shiga
wanka,ba shakka mai kyau ce haka ta dinga fadi a ranta yadda fatarta ta sake wani
santsi bayan na da,su humaida basu shigo ba sai wajen tara da rabi,har ta shirya
zata kwanta ma,yau bata jin qwarin jikinta sosai,tun safe tunaninsa ya dinga kawo
mata caffa,tunda ya tafi bata ji muryarsa
"Akuyar daure ta samu sake yau mun wataya wallahi wannan miskilin mijin naki bai
nan" humaida ta fada tana dariya tare da tsokanar sumayya,murmushi kawai ta saki
cikin kara da yakana tace
"Ai kunfi kusa" baki humaira ta rufe
"Rufamu ki saya mu,wacce kusar?,ai shi bashi da kusa,matanshi kadai za'a cewa sunfi
kusa,shekara nawa amma har yau kamar bai san mu su waye dinsa ba,ku dai ku dauki
mijinku kuje ku qarata"
"A'ah fa,kada kuma a wuce gona da iri" inji sumayya cikin zolaya,dariya suka sanya
baki daya,kusan wannan hirar ce ta sake dauke mata hankali.

Cikin dare baccin nata ya katse,ita kadai ta dinga juyi saman gadon,tana
kallon yadda su humaida ke baccinsu hankali kwance,wayarta ta janyo tana
dubawa,babu wani abu sabo tattare da ita,sai ta samu kanta da lissafin awannin da
suka rage gare ya waye musu zuwa ranar alhamis.

Washegari tana wajen ummee amma baki daya hankalinta bai wajen,tana yi tana
duba agogo,tun la'asar ta koma sashenta,awanni suka dinga shudewa amma babu labarin
dawowarsu,a haka dare ya cimmata,cikin daren ta kasa bacci,ta miqe a hankali daga
dakinta ta haura sama zuwa nashi dakin,ta tura qofar ta kunna fitilar wayarta ta
haska makunni ta kunna qawayayen dakin,a hankali ta qarasa bakin gadon ta zauna,da
kdanu take bin ko ina na dakin da kallo,wanda dazun ta gyarashi fes,komai a
killace,wani irin yanayi take ji mai kama da kewa,sai ta qudundune cikin bargo tana
sakin ajiyar zuciya,qamshinsa take shaqa har cikin qwaqwalwarta,juyi ta shiga yi
daga farkon gadon zuwa qarshensa,haka kawai taji zuciyarta ta karye kuka take so
tayi,hawaye ne masu dumi suka fara zirya saman fuskarta,cikin haka taji wayarta na
fidda sauti mai dadi,da fari ta tsorata,amma daga bisani ta tattara hankalinta ta
janyo wayar,babu suna akan lambar,amma sai taji zuciyarta ta tafi kan ta
daga,karata tayi a kunnenta ba tare da tace komai ba
"Baki bacci ba ko?,dama jikina ya bani hakan"tsumammiyar muryarsa ta ratsa dodon
kunnenta,bai damu data amsa ba ya dora da tambayoyinsa
" me ya hanaki bacci qarfe daya saura na dare?"zuciyarta ta kuma karyewa da jin
muryarshi,hawayenta ya qaru,sam batasan kukan nata ya fara fidda sauti ba sai da
taji amon muryarsa ya dan qaru sabanin dazu da take kama da ta maijin bacci yana
fadin
"Subhanallah?,me ya sameki?," rasa me zata ce masa tayi,sai 'yar qaramar sheshsheqa
da take fitarwa,to me zata ce masa?,tace masa ta kasa bacci?,ko tace masa gidan ba
dadi?,duka saboda me?,sabida shi ko saboda wani dalili na daban,idanunsa na lumshe
daga can bangaren yana sauraren sheshsheqarta,cikin sanyin murya yace
"Is ok,ya isa,ya isa.....tunda ba zaki gaya min ba ni bari na gaya miki,saboda ke
na kasa bacci,saboda baki a kusa da ni,tunaninki da kewarki tunda nazo banji dadin
garin nan ba,ta yaya kika yiwa zuciyata ta'addanci har haka ba tare da na farga
ba?"shuru tayi kukan ya dauke duf tana saurarensa,ya qware wajen watso kalaman dake
taba zuciya,wai da gaske ma ita yake gayawa haka?,kodai yaudararta yake son yi?
"kema haka ne a zuciyarki uhmmm?" Ya ambata cikin salon rada wanda ya sake
hautsinata,baki ta turo kaman yana gabanta
"Umm ummm.nifa ba haka bane"
"To meye?" Ya fada dariya na qwace masa wadda baisan ta fito ba,jin shiru bata ce
komai ba sai ya dora
"tunda ba haka bane sai na bari sai wani satin na dawo,dama aiki ne ya tsare mu yau
din bamu dawo ba na gama komai kenan a hankali na taho daga baya ko?koda zuwa satin
sama ne"shiru tayi qirjinta na bugawa
"shikenan.....sai da safe tunda ba wani abu sabo"
"Nifa bance ba....." Tayi hanzarin fada tana tsoron kada ya kashe wayar,abun ya
bashi dariya ya kuma burgeshi tare da tabashi,hakan dama yakeson ya ji ko ya
gani,reaction dinta kawai ya wadatar da shi
"To me kika ce?"
"Ba komai" ta fada a shagwabe
"Uhm,to shikenan,muna hanya tomorrow in sha Allah" sai ya datse wayar daga
haka,wani sanyi taji yana ratsata wanda batasan dalili ba,murmushi ya kubce
mata,sai ta soma goge ragowar hawayen fuskarta tana jin kunyar kanta kuma daga
baya,ya ta bari har ya ganota?,oho itama bata sani ba ta baiwa kanta amsa,sosai ta
kwanta saman gadon tana 'yan tunane tunane,zuciyarta fes,quncin da take ji ya
ragu,da haka bacci yayi awon gaba da ita nan cikin dakinshi saman gadonsa.

*ko wanne namiji ya banbanta da wani,wani abunda ke burgeshi shike bawa wani
haushi,so ya kamata mata mu kula mu lura musa nutsuwa,mu banbance meke burgesu duk
qanqatarshi,da kuma meke basu haushi duk girmansa,ba lallai abinda waccan tayi ya
burge mijinta ba ke in kinyi ya burge naki,qasaitacciyar mace na zuba ido tasa
nutsuwa ta karanci yanayin mijinta ,Allah yasa mu dace.*

*ina masoyan SU'AD,to fa ku shirya ku hada qarfinku waje guda,a next page jarumar
taku zata iso gidan baba prof,to ko ya zata kaya Allah masani,sai kawo mata gudun
mawa,lol*😜😜😂🤪😂

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

8⃣8⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

*wa qadimna ila ma amilu min amalin faja'alnahu haba'an mansura*

*YAN UWA MU YAWAITA KARANTA WANNAN AYA,ALLAH YAYI MANA MAGANIN MACUTA AZZALUMAN
SHUGABANNI,WADANDA SUKA TASAMMA KASSARAMU SU KUMA KASSARA QASARMU,ALLAH YA FIMU
SANIN NUFIN KOWA DA ABINDA KE QULLACE A ZUCIYAR BAYINSA,ALLAH KAYI MANA MAGANINSU
KO SU WAYE,KODA CIKIN GIDAJANMU SUKE,MATUQAR ZASU ZAMA BALA'I GA AL'UMMAR MUSULMI
BAMU DA QARFI BAMU DA MADOGARA SAI KAI YA ALLAH,KAJI QANMU KO DON QANANUN YARA DAKE
RAYUWA A TSAKANINMU*
______________________________________

        Sallar asuba ce ta farkar da iya,sai data kammala sallar sannan ta sauko


qasa ta dawo wajensu humaida,tsokanarta suka dinga yi kan ina ta gudu?,bayan sunsan
oga baya nan,murmushi kawai tayi tana tuna abinda ya faru daren jiyan,mamakin kanta
ta dinga yi,batasan me ya sameta haka ba.

        Bata damu tayi wanka tunda wuri ba,zani ta daura saman kayan baccinta ta
zura hijabi suka fice tare da su humaida ta gaida mutanen gidan,hada hada tayi yawa
a gidan kasancewar gobe daurin aure,babu abinda zasuyi cikin gidan kasancewar komai
na gidan da za'a gabatar akwai ma'aikata wadanda zasuyi,qarfe goma ta koma bangaren
nata,ta kintsa ko ina,saiga sallamar mai kitso da anty dije ta gaya mata zata turo
mata ita,babu bata lokaci ta fara mata,'yar maiduguri ce,ba qaramin iya kitso Allah
ya hore mata ba,ga sauri a wajenta,cikin awa biyu ta gaka yarfa mata shi wanda ya
zauna a kanta kamar an saqa shi,baki daya jelar ta kwanta gadon bayanta,rabon da
tayi kitso irin haka har ta manta,sannan kai tsaye ta wuce kitchen dinta,samun
kanta tayi da tunanin me zata tana dar masa wanda zaya burgeshi,murmushi ta saki
sanda ta gama wassafa mai zata dafa sannan ta hau aiki.

       A wanni biyu kacal ta kammala,abinci iri biyu tayi,daya na baba ne daya na


almustapha,tuwon alkama ta yiwa baban miyar karkashi wanda ya tuqo sosai yana
santsi,dakinta ta koma ta sheqa wanka sannan ta fito tayi sallar azahar,tana shirin
fara shiryawa ta jiyo shigowarsu amira,saukowa tayi jin amiran ma qwala mata kira
"Wallahi tunda na shigi nake jin qanshi iri daban daban,me kika girka ne haka?"
"Zaki ci?"
"Na waye?"
"Yayanki mana" ta fada tana juya ido,baki amiran ta rufe
"Wallahi duk maitata na haqura,wannan sanwa tafi qarfina" dariya sumayyan ta saka
ta haura sama tana fadin ina zuwa,komawa tayi ta shirya cikin kwalliyar atamfa
peach ce da adon yellow,fitted riga da skert wanda aka yi masa wata iriyar
wrapper,ta zauna ta tsara daurin dankwali tamkar head din amare ya zauna dam a
kanta,cas cas kayan suka mata kamar a jikinta aka dinka,ta bi jikinta da turate ta
feshe shi sannan ta sauko,babu wanda bai tanka adon nata ba,har suka sanyata
dariya.

Har misalin hudu da rabi na rana hira sosai suke wadda ta dauki dadi
matuqa,ta sake a cikinsu ana kwasar cafta,turo qofar falon da akayi shi ya maida
hankalinsu wajen,almustapha ne,sanye da straight leg da longsleeve shirt,qafanshi
snickers ne baqi,idanunshi saye da glass mai haske wanda kana hango qwayan
idanunshi,hannunshi soke a aljihunsa kafadarsa rataye da jaka,tuni shiru ya ratsa
falon kowa ya kama bakinsa,wadanda suka cire mayafi suka fara lalubarsa suna
yafawa,tunda ya shigo idanunshi na bisa kanta,cikin izza yake takowa har zuwa
tsakiyan falon,baki daya suka hau gaidashi,amsawa daya kacal yayi musu baki daya ya
haye saman,tsam ta miqe tana fadin
"Ina zuwa"
"A'ah madam saidai mun ganki" inji humaida tana qyaqyata dariya,harararta sumayya
tayi saboda shirin bata kunya da takeyi ta juya ta haye saman.
Bakin qofar ta tsaya gabanta na duka,wani farinciki taji na mamayarta,cikin
zumudi da son basarwa ta tura qofar dakin ta shiga,yana tsaye ya baiwa qofa baya,ko
takalminsa bai cire ba bare a kai ga zama,waiwayowa yayi baki dayansa ya motsa
bakinsa yana amsa sallamarta,idanunsa duka suna kanta,wani abu yaji na
ratsashi,kyawun da yaga tayi masa ba mai misaltuwa bane tun daga qafafunta da yasha
lalle ja da baqi ya qawata qafar ya bita da kallo ya dire a kafadarta wanda jelar
kitsonta ta sauka,takowa yayi a hankali kamar mai sanda ya tsaya gan da ita,wanda
tsaiwar baida maraba da runguma,tana niyyar bude baki ya rigata
"Kinsan zan dawo kika tara min wadancan?,sauka ki sallame su idan baso kike ayi
abun kunya a gabansu,ke zaki ji ba dadi don na fuskanci kunyarki tayi yawa ni ko a
jikina" daga kai tayi ta dubeshi,sai ya kashe mata ido daya,da sauri ta dauke kan
ta ta juya da hanzarinta,a iya zamansu kadai ta soma fuskantar sa,ta soma gane
sauyawar yanayiyyika tattare da shi,fargabarta daya me zata gaya musu?,zata ce su
fita su bata waje?,riqota taji yayi,ta sake juyowa suka hada idanu
"Kada ki jima,kizo ki shiryani kayan jikina sun dameni" ya fada a wami
shagwabe,wata bahaguwar kunya ta mamayeta,saita qara wuta zata fice kamar zata
hantsila,haka ta dinga sauka har ta kai qasan.

Wayam taga falon babu kowa,wani dadi ya kamata don batasan me zata ce da su
ba,abinda bata sani ba shine tana hawa saman amira ta dubesu
"To 'yammata nifa warewa zanyi wlh tunda mai gu yazo,gwara mu bashi waje tun bai
koremu ba da kanshi"
"Ai naga take takenshi zai aikata kadan daga aikinsa" inji shukra
"Nikam dama wai haka yake ya man?" Inji humaira,dariya amira ta saka
"Ai yafi haka ma,sarari ne bai samu ba sai yanzu,yana auren waccen iccen ina zamu
sani" dariya suka sheqe da ita sanda suke ficewa daga sashen don baki dayansu
haushin su'ad suke ji,girman kanta da dagawarta sun girmeta,data tashi baya dauki
dai dai ita ba,ganin babu kowa ya sanyata juyawa ta koma.

Har yau still bai yi komai ba,saidai wannan karon yana zaune ne bakin
gado,qarasowa tayi tana taku cikin wani salo har ta iso gabanshi,ta duqa baki daya
da zummar cire masa takalmin qafanshi tana gaidashi wanda hakan ya baiwa qirjinta
damar fitowa,dif yaji tunaninsa ya dauke,yaci gaba da morewa kallonta har ta gama
fidda masa takalmin da safa,ta miqe da niyyat hada masa ruwan wanka,sai ya fisgota
ta dawo saman cinyarsa ta zauna,ya soma shinshinar wuyanta yana cewa
"Qarya kike wallahi,kin damen da kuka sannan na dawo ki gaza duban qwayar idanuna
naga yadda kikayi missing dina,ko lacture din tamu baya zo nan ba" ya qarasa fada
yana zira hannunshi cikin rigarta,muhallin da tun dazu data tsugunna ya tsone masa
ido
"Uuummm" ya fada yana shinshinar jikinta,qamshinta na tafiya da tunaninsa,tsam ya
hadeta da jikinsa yana magana can qasa
"Uhhmmm,tell me yaya kikayi missing dina?"
"Nima ban sani ba,bansan ha zance ba" ta furta a tausashe idanunta na lumshewa
"Kin kasa cin abinci saboda ni?ko kin dinga jinki wani iri duk saboda
ni.....oya....tell me.....gaya min gaskiya kada kiyi qarya"
"Yes,duka na kasa....na kasa"
"Why,meye dalili?" Ya sake tambayarta idanunshi a lumshe cike da shauqi
"I dont know....ban sani ba"
"So ne?"
"Nooooooo" ta fada tana jan kalmar cikim jin kunya tare da tura kanta a wuyanshi
"Nace kada kimin qarya fa,tashi ki gayan" ya fadi yana qoqarin hade fuskarsu waje
daya,goshinsu ya hade kamar yadda tsinin hancinsu ya hade,suka fara musayar
numfashi,muryarta a sanyaye tace
"Kace kaima baka iya komai,kaima so ne?"
"Yeah,feeling ne dake yawo cikin zuciyata da ban taba jin mamakamancinsa ba,so that
na yarda so ne,sone unexpected....."nannauyar ajiyar zuciya ta sauke,abu guda suke
ji a cikin zukatansu lokaci guda,indai ko haka ne ita din ma son ne?,amma ta yaya
zuciya daya ke iya son mutum biyu,taso mukhtar yanzu kuma almustapha?saidai idan
tayi rantsuwa ko kaffara ba zata yi ba,abinda take ji a yanzu bata taba jinsa kan
wata halitta ba,ba mamaki dalili kenan da ya sanya ta gaza gane meke damunta
"Why you keep silence?" Kai ta girgiza duk da fuskarsu na hade waje daya tana kuma
sauke numfashi
"Babu komai"
"Akwai....na sani bazanji irin wannan abun ni kadai ba at the first time in my
life,idan baki sani ba lissafo min me da me kike ji,ko yaya...konyaya inason naji
wani abu mai dadi,lafazi mai dadi kamar yadda sauran maza keji" a hankali ta soma
lissafa masa kamar mai koyon magana
"Tsoro....kunya.....nauyi....tausayi...kewa son ganinka....damuwa....faduwar
gaba......" Sai tayi shiru tana jan numfashi wanda ke cakude da nashi mumfashin da
qamshin lallausan turarensa,yana mata kwarjinin da bazata iya kammala fada masa
ba,murmushi ke fita daga fuskanshi,dukka wadan nan sun tabbatar masa akwai wani abu
mai girma dake son wanzuwa cikin zuciyarta dangane da shi,don kada ya matsanta mata
da yawa sai janye fuskarshi daga tata
"Is ok,hakan ma ya gamsar da ni,hadamin ruwan wanka kafin a kawo min abincin da
nayi order" sai ta kwabe baki tana dubanshi
"Abinci na jiranka,no need sai ka yi order" ta fada taba niyyat shigewa toilet
din,murmushi ya sake kube masa,binta yayi da kallo har ta shige,ba shakka akwai
banbanci,akwai banbanci wanda kullum sai yaga wani sabon abu,tunda suke da su'ad
bata taba jera abinci yana jiransa ba,duk da orser yake amma ganda take kafin ya
fito ta fidda komai daga park dinshi ta ajjiye masa inda ya dace.

Yana shiga wanka tayi hanzarin ficewa ta dauki abincin baba ta kaiwa anty
maamaa kan ta bashi sannan ta juyo ta dawo,saidai tayi nawaa,saboda tana tura dakin
ta ganshi har ya fiti,qugunshi daure da towel yana shirin soma shafa mai,sai ta
dauke idonta
"Ina kika je?"
"Naje gaida baba ne"
"Amma dai kin gani gidan a cike yake har da maza ko?" Sai ya danja tsaki
"Banjin gidan nan zaya zaunu,ki shirya zamu basu waje" idanu ta fidda tana son
tambayarsa inda zasu,saidai taja bakinta tayi shiru,ta qarasa inda yake zaune gefan
gadon ta lakato man ta soma shafa masa,daya daga cikin lacture din da yayi mata,duk
inda ta motsa binta kawai yake da kallo,baki daya ta kashe masa jiki,sai ya miqa
hannu ya karbi man yana cewa
"Barshi kawai,kasala kike saka min,jeki shirya,bana so magariba tayi mana a
nan",bata jima da yin wanka ba amma ta fuskanci mai muradin haka ne,shi ya sanya ta
juya ta koma bayi,ta cika turaren wanka a ruwan ta sake wani wankan,sanda ta fito
bai saman,tuni ya sauka qasan,bai iya jira ba yayi sarving kansa ya fara cika
tumbinsa,dadin abincin ya dinha zagayawa wata duniyar da shi.

Cikin minti qalilan ta shirya cikin riga da skert na lace,ta yafa mayafi
hill shoes ne a qafarta,yana zaune saman kujera qarar takalminta ya sanyashi daga
ido,ba qarya tayi kyau,kome ta sanya kyau yake mata,saidai wani kishinta ya
rufeshi,gani yake idan ta fita haka kowa ma kalleta zaiyi,bazai iya barinta ta fita
hakan na,da idanu yayi mata nuni shigarta bata masa ba,tq kalli jikinta sai ta juya
ta koma samam,ta fidda kayan jikin nata tana tunani,bangaren atamfofinta ta nufa,ta
ciro wata super,kalarta tayi kyau qwarai,itama riga da skert ne masu fidda shape
qwarai,sai ta fitar da lafaya wadda ta dace qwarai da atamfar ta nannade jikinta
tamkar 'yar maiduguri,takalmi da jakarta mahadin juna ce,takalmin na da tudu
maimakon na dazu mai tsini,sak ta fito a bahaushiyar kanuri tun kafin ta gama nada
lafayar,wajen nannadota ta baya hannunta ya gaza kaiwa,tana yunqurin janyo inda ya
nade din ta hangoshi cikin mudubin,qarasowa yayi ya sanya hannunsa ya juyo da ita
suna fuskantar juna,da kanshi ya qarasa nada matan sannan yaja baya rungume da
hannunshi yana kallonta,yana matuqar son tayi shigar arewa,shugar na burgeshi wani
lokaci har tafi ya abaya kyau,kwalliya na burgeshi,wani bangare ne na abinda yake
so a wajen matarsa,kasa daurewa yayi,ya hada yatsanshi manuni da babban dan
yatsansa a hankali ya furta
"Kinyi kyau" murmushi ta sakar masa tana saqala jakarta suka jero suka fito lokaci
lokaci yana satar kallonta.

Ko ina mutane ke kai kawo kowa na sabgarshi,saidai duk inda suka gifta sai
sun wafci ganin wasu,su burge wasu,masu hassada kuma su tanka,kacibus sukayi da
fahariyya wadda tabi sumayya da kallo,tuni almustapha yayi gaba abinshi,dama idan
baiso ba ba shiga shirginta yake ba,har gwara ni'imah yana ganin yanayin hakayyarta
da hankalinta ya banbanta dana wannan sukan gaisa a mutunce cikin ganin mutuncin
juna,fahariyya kam sai yaga dama,don bai daukar raini ko wargi,yanayin nasu ya
burgeta saidai haka kawai kishin sumayyan ya soketa,fuskar sumayyan da fara'a ta
qarasa wajenta tana fadin
"Ina yini maman hibba?" A yatsine kamar wadda ka yiwa dole ta amsa da
"Lafiya ya kike?"
"Lafiya qalau wallahi,tunda kika iso bamu samu mun hadu ba sai su hibban na gani"
"Oh Allah?,k'nnn,ina ciki ina hutawa"
"To yayi,ki gaida yaran" ta fadi tana juyawa sabida ganin yanayin fahariyyan,yayin
da ta bisu da kallo,ba shakka ba haka aka so ba qanin miji yafi miji kyau,a da tana
kishi da su'ad wadda mijinta ne kawai yafi nata mijin komai da komai,a yanzu kuma
saiga wadda mijin nata yafi nata,hakanan ita dinma ta fita,shi ya bude mata sai da
ya tabbatar ta shiga ya rufe sannan ya zagaya ya shiga wajenshi,hakan ya tsayawa
fahariyya a wuya,su'ad suna dan dasawa wani lokaci rashin jituwarsu yafi yawa,amma
sai gashi yau taba taya su'ad din kishi,ya akayibtayi sake haka ta faru?,lallai
bari ta iso,ta fada aranta tana yin gaba ta bar wajen,yana yunqurin tada motar tace
"Su ummee fa,basu san bama nan ba" sai da ya tada motar sannan ya amsa
"Ba ruwansu da mu,we r free".

Baki daya gidan ya tafi da ita,kaf rayuwarta bata taba katarin shiga gini
irin wannan ba,gida ne wanda idan baku manta ba yake mallakin almustaphan,wanda
babu wanda yasan da zaman gidan banda shi din,a hankali suka dinga ratsawa,basu
tuqe ko ina ba sai lafiyayyen bedroom dinshi,wanda kusan dukkan abinda ke jere a
ciki ba daga nijeria ya fito ba,bedroom ne wanda kallo daya zaka yi masa kasan cewa
mamallakinsa yasan abinda ake kira da TSARI,dole tsarin dakin ya burgeka,komai na
ciki fari ne qal,tun daga qwayaye,bed lamp fenti,kayan gadon,labulaye,bedsheet,sofa
guda biyu,table na galss,tiles da rug dake ajjuiye can gefe guda,hatta da qofar
bayi zuwa ga ac ta girke dake tsaye kusurwa daban ta dakin,tattausan qamshi da
sanyi mai dadi ke gauraye a dakin,ya matuqar burgeta,tana tsaye idanunta na kan
tafkeken frame mai ruwan gold da aka rubuce ayatul kursiyyu da wani daura da shi da
aka rubuta addu'o'in bacci kala kala ya qaraso gareta ba tare data sani ba,a
hankali ta maido kanta gareshi,babu wani space a tsakaninsu baki daya ya
hadeshi,batasan me yasa yake son ritsata haka ba,baisan nauyin da yake haifarwa
zuciyarta ba,jakar hannunta ya sabule ya ajjiue gefe guda,yasa hannunshi duka biyun
ya riqe kafadarta,cikin sanyi yace
"welcome to my world" murmushi na fita saman fuskarsa
"I wish zan samu wani gagarumin abun da bazan taba mantawa da shi ba" murmushin
itama ta saki,hannunta ya kama yana duban lallenta
"Ya miki kyau,but daga yau jan kawai nakeso,yafi lafiya ya kuma fi yimiki kyau,at d
first time da naga wannan abun hannun wata kusa da ni sosai kamar haka,yana muku
kyau"
"In sha Allah" ta fadi,sai ya saki hannun ya zamw dankwalin kanta,hannunshi ya dora
saman kitson yana shafawa
"Wow,masha Allah" ya fada har cikin zuciyarsa saboda yadda kitson ya burgeshi,ya
jima baiga kitso haka ba kan mace,har ya manta cewa mata na kitson,inda ya qarasa
girmanshi dai ba kitso suke ba,haka matarshi a nata ganin kitson wai qauyanci
ne,tafi ganewa taje a sanya mata gashin da zatayi parking tamkar nata,a haka ya
zarce da warware mata lafayar dake jikinta tana tsaye idanuwanta alumshe,sannan ya
janyeta zuwa ni'imtaccen gadonshi wai tazo ta nuna masa yadda akayi kitson,daga nan
labari yasha banban.

******* ****** ********

Yana zaune abinsa hankali kwance kan kujerun dake falon kamar wanda sam bai
da niyyar zuwa daurin auren ma,zirga zirga take tsakanin kitchen da dining area
cikin wani hadadden lace da aka yiwa dinkin buba,duk inda ta gifta idonshi na
kanga,shigar tayi masa,shi baiqi suyita zama a hakan ba,sam baya son su je
gidan,don ya tabbatar zuwa yanzu hayaniyar dake cikin gidan sai Allah,baki daya
hankalinta ya soma yin gida,awa daya da rabi ya rage lokacin daurin auren yayi,amma
taga shi kamar ma ko a jikinsa,sai data kammala ta tako gabanshi ta russuna
"Breakfast din ya zama ready,nd saura awa daya da rabi fa lokaci yayi" kanshi ya
mirgina yana sake kashingida
"Koda babu ni ai ba za'a fasa daura auren ba,ban amshi waliccin kowa ba" kai ta
rausayar ta miqe,sai ya janyota cikin jikinsa ya soma shinshinarta,yasa hannu ya
ture dankwalinta yana shafa jelar kitson
"Kinyi kyau,wannan kitson ya yimin" sai ya soma yamutsata,wayarshi ita ta katse
masa qudurinsa,ummee ke kira sai ya gyara zamanshi,ta tambayi lafiya ne saboda ta
aika sashen anata bugu ba'a bude ba,yace komai lafiya,bata tsaya jin komai ba tace
to alhamdulillahi ta katse kiran dama lafiyar take son ji,a akasalance ba don yaso
ba ya karya sannan ya koma dakin don ya shirya.

Tayi ready,hatta da mayafinta na yafe a jikinta,tukunshi taji,a hankali ta


daga kanta
"Fatabarakallahu ahsanul khaliqin" ta ambata har bakinta na motsawa,sanye yake da
shadda fara qal dinkin tazarce sai walainiya take,hular kansa baqace kamar yadda
takalminsa na kamfanin batozzi halfcover yake baqi,agogon fata dake daure a
tsintsiyar hannunshi ma haka,karon farko data soma ganinsa cikin shigar manyan kaya
haka,kasa daina satar kallonshi tayi har ya qaraso gabanta
"Mu wuce ko?" Ya tambayeta,ba musu ta miqe din,tana niyyar gaba ya riqota
"Wallahi baki isa ba,u have to say something,na lura shigar na burgeki,nayi saboda
ke kice zaki wani fuske" yadfa yayi kicin kicin yaso bata dariya
"Masha Allah tayi kyau"
"Ita tayi kyau ko ni nayi"
"Kaine"
"Allah ya ceceki yau da babu inda zaki fita har sai jibi zamu bar gidan nan" ya
fafa yana yin gaba ta biyo bayanshi tana sakin murmushi,tabbas ba qarya yayi
kyau,sai ta tuna yadda su'ad ke kishinsa duk sanda ake sha'ani cikin gidan bata so
taga ya gifta don kada a kalleshi?,haka zasu ratsa gidan kenan?.

Qarfe tara da rabi taxi dake zirga zirgar kai jama'a daga airphort zuwa
gidajensu ta sauke su'ad din qofar gidan baba prof,ta kira layin almustapha tana
son shaida masa azo a dauketa don abun kunya ne tana matar fitaccen mutum kamar
doctor elmustaphan ta shiga motar haya har ta gode Allah bai daga ba,dole daga
qarshe dai ta dauki drop din motar ta kawota gida,wanda ta mance when last data
shiga motar haya a rayuwarta cikin nijeria ko da a america ne sai ta kama take
shiga din,tun daga harabar gidan take ganin al'umma saidai babu wanda ya isheta
kallo,a haka ta dinga ratsawa dauke da jakar ratayenta qatuwa,ko baba mai gadi da
ya matso yana mata sannu da zuwa da niyyar kuma amsar jakar hannunta ya kai mata
bangaren nata bawai don mutuncinta ba,saboda daraja da girman baba da almustapha
ne,wani matsiyacin kallo ta watsa mata tana tsartar da yawu
"Kada ka soma matsowa inda nake,bastard" ta fadi tana wucewa ciki,kusan duka
wadandanta taras 'yan zafin kaine saboda haka ba wanda ya kulata har ta shige
bangarenta,hakan ya mata ciwo,dama ga zargi fal cikin ranta sai take ganin da gayya
aka mata hakan.
Sauyin yanayin qamshi da ya samu falon ya tabbatar mata da zarginta na ba
shakka almustapha na abuja,kuma tare da yarinyar,tunda ta kira layikansa na nan
qasar duka sun shiga,wanda abaya idan bai naija layinsa baya shiga saidai ta gwada
na wata qasar,kai tsaye ta nufi samanshi,ta tura dakin ta shiga,neat dakin
yake,saidai shima akwai cakuduwar wani qamshin bayan qamshinsa data sanshi da
shi,wanda bata raba dayan biyu qamshin yarinyar ne,kishi ya lullubeta,wai ya akayi
haka ne?,me yasa ta tafi har ta basu sararin cakufuwa danjuna haka cikin kwanciyar
hankali,me yasa bata zauna ba ta daga musu hankali,kowa ya qeaci almustaphan idan
zai iya,wanda tana da tabbas ita ke da nasara,sabida tana da gogewa da wayewar da
zata iya aiwatar da haka,yanzun ma ai bata makara ba(a cewarta)sai ta ja qofar
dakin ta rufe ta nufi nata dakin,komai yayi qura,bata jin zata iya amfani da
dakin,dole ta samu ma'aikatan gidan su gyara mata,sabida haka ta koma dakin
almustapha ta sake wanka ta shirya cikin wando wanda daga same yake a dame,daga
qasa kuma wajen qafafun ya bude sosai,riga ta sanya spaghetti hand wadda ta dameta
dai dai jikinta,gashinta ta taje ta daureshi,sannan ta janyo takalmanta masu tsini
hade da igiy kamar zata tsokale idanun duniya ta daura,'yar hula ta samu ta sanya
akanta wai din idon jama'a sannan ta feshe jikinta da turare ta sauko qasan tana
fatan shigowar almustapha bada dadewa ba don daidaita tsakaninsu.

Gab da zata fice sukayi kacibus da fahariyya tana shigowa,baya suka ja


suna wa juna kallon kallo,tsaf fahariyya ta qarewa kayan jikin su'ad kallo,tasan ko
na wanne kamfani ne,bazau wuce armani ko D&C ba,don bata siyan kaya a kamfani mai
arha,lallai almustapha ya tsaya mata fahariyyan ke rayawa a ranta,waskewa tayi
"Ai naga shigowarki nace bari na leqo mu gaisa,ban tsammaci zuwanki ma bikin ba"
"Bashi ne ya kawoni ba"
"Da alama kam,tunda na lura kaman ma bakisan mai gidan bai sashen ba" idanu tabi
fahariyyan da shi
"Tun yaushe?" Ta tambayeta
"Jiya da dare sun fita shi da amaryarsa" wani qunci ya ziyarceta,ina ya dauketa
suka tafi?,wato ma basu kwana gidan ba?,bai taba mata haka ba duk yadda bata qaunar
zaman gidan
"Da kyau almustapha,ni almustapha zaiwa haka?"
"Ai kadan ma kika gani,matuqar baki sanya himma kin fiddata daga gidan ba,ni ga
tawa nan ta zamarmin ciwon ido,bata haihuwa amma ta fini power da fada wajen mai
gidan,sai kiyi kamar kinayi" ta fada tana juyawa ta fice,burin ta ya cika,dama so
take ta tura mata takaici,ta kuma samu nasarar haka.

Da qyar su'ad ta iya jan qafarta ta fice saboda neman masu mata gyara,kishi
da baqinciki ya cika mata zuciya,yaushe har tayi wannan saken da har wata ke
watayawa da almustaphanta yadda taga dama?.

Duk da cinkoson masu wucewa gidajen amaren daurin auren hakan bai sanyashi
tsaida motar waje ba,dai da ya dangana da oarking space wanda tuni ya yiwa drivansa
waya yazo ya sameshi a nan ya kaishi inda za'a daura auren,kashe motar yayi ya
jingina da kujerar yana dubanta qasa qasa,sai daya gaji don kanshi sannan ya bude
bakinsa
"Kijr but,banson ki cika yawo cikin gidan,nan da awa daya nasan gidan zaya sake
cika da mutane,ki zauna gu daya" kai ta kada tana mamakinshi,wannan tsananin da
takatsantsan duka na meye?,hannunta ta dora zata bude qofar motar ya hangin gungun
angwayen tafe cikin shigar babbar riga,hayaniyarsu nata tashi,bisa dukkan alamu
yanzu zasu wuce wajen daurin auren ne
"Wait....." Ya gada yana miqewa daga jinginar da yayi,haka kawai ranshi ya baci
daya hango alqasim a cikinsu,ita dinma ta ganshu ta gane kuma me yasa ya
tsaidata,sai da suka wuce sannan yace
"Muje" ya furta yana cire belt dake daure a jikinsa,ya bude murfin motar itama ta
bude ya zagayo suka daidaita kafada kana suka jera.

A hankali ta daga kai ta dubeshi sanda ta hangi sa'ad na takowa,cak su'adan


ta tsaya sannan ta canza direction zuwa inda suke,kanta ta daga ta dubi
almustapha,sarai shima ya ganta,amma sai ta lura da cewa ko a jikinshi,ba wani
yanayi nashi da ya sauya,hasalima hannunta da ya kama bai saki ba,suka ci gaba da
takawa su'ad itama na takowa zuwa nahiyar da suke idanunta qur bisa kansu duka su
biyun.

*mrs muhammad ce*👑

✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

8⃣9⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

*la haula wala quwwata illa billahil aliyyul azim*

*la'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin*


_____________________________________

     
  Ci gaba tayi da tunkararsu ba tare data dauke idonta daga garesu
ba,tamkar zuciyarta zata fito waje saboda tsananin kishi,kamar ta kurma ihu ko zata
ji sauqin abinda ke sukar zuciyarta,bata taba jin bala'i irin wannan ba
arayuwarta,ashe a baya duka qaryar kishi take kan almustapha?,almustaphan nata ne
riqe da hannun wata haka?,sun kuma jero suna tafiya kan bigire guda?,ko a jikinsa
wai an mintsini kakkausa,shi sam baiyi zaton ganinta ba ma a wannan lokaci,sai da
suka qaraso dab da juna sannan ya zame hannunshi daga na sumayyan ya dubeta
"Idan kika shiga bana so ki fito,bana son yawo ki zauna waje guda,nasan duka nan
za'a dawo akwai walima da zasuyi" sai ta samu kanta da narke masa cikin wani irin
salo
"Ina so naje wajen umman khalipha fa,tunda nazo ban shiga ba" girarsa ya dage salon
ya matuqar qayatar da shi
"Ko zakin ba yanzu ba,idan na dawo zan sanar miki" kai ta gyada tana jifanshi da
wani irin qayataccen murmushi daya sake narkar da shi
"Ok,to a dawo lafiya,Allah ya tsare hanya" idanu ya lumshe addh'a ta masa
dadi,qarakin murmushi ya subuce masa
"Amin,thanks" kai ta gyada tana juyawa cikin takunta na nutsuwa,baki daya idanuwa
su'ad ta bita da shi,ji take kamar ta fincikota ta yarfa mata mari,ba'a tabacin
fuskarta irin haka ba,a gabanta wata ke soyewa da mijinta?,ita dun da dukkan
'yammatan danginsa sunsan halinta sarai ko cikakken kallo bata so taga ka fiya masa
yanzun zata ci miki mutunci?,saiga wata a gaban idanunta tana narkewa mijinta,ga
sumayya kuwa sanda ta juya sai ta dinga jin wani abu na mintsininta cikin
zuciya,sai taji kamar ta koma,me yasa ta barsu su biyun?,zuciyarta ta
cunkushe,kallon data lura su'ad na mata bai dameta ba,qarfin gwiwar da bata taba
jinsa kan kishiya ba wannan karon shi take ji,ba abinda zai sanyata taci gaba da
barwa wasu matan mazanta,ta tabbata ko ba'a gaya mata ba babu zancan zaman arziqi
tsakaninta da su'ad,ta santa tun ba yau ba,ta santa tun kafin miji ya hadasu,bata
da kirki bata da mutunci,bata ganin girman kowa,a haka taci gaba da takawa
zuciyarta dake cike da kishi na bata shawarar ta waiwaya amma ta daure zuciyarta ta
hana kanta aiwatar da hakan.

      Yatsan tsakiyarsa da babban yatsanta ya hada ya murza a fuskar su'ad din


wadda tabi sumayya da kallo,kishi ke sukarta,sam bata gane ma sumayyan ba,saboda ba
duka wanda yayi mata qaramin sani irin wanda su'ad din tayi mata bane zai iya
tantanceta ba tashi guda,idanunta da suka kada ta dauke ta maida kan
almustapha,shigar jikinsa kadai ta bata mamaki,bata taba ganinsa da manyan kaya ba
tunda suke sai yau din,wani qyama da takaici ya kamata,ya auri 'yar nijeria arewa
ta fara zuba masa duhun kai kenan,to wallahi bazata lamunta ba,wata babbar riga
harda hula sai kace wani limami,bakinta na rawa cike da tsantsar kishi tace
"Almustapha?,ashe da gaske baka sona?" Shanyayyun idanunshin nan kawai ya zuba mata
yana dubanta
"Almustapha ka dubi yadda kake nuna qauna da kulawa ga wata bayan ni,dama zaka iya
aikata hakan?" Ci gaba yayi kawai da dubanta,karon farko da ya soma ganin aibun
irin shigar da takeyi,cikin qasarsa gidansu kuma gidan iyayensa surukai a garesu,ba
shakka ta nan shine babban mai laifi,amma sam bai gane illar hakan bane sai
yanzu,tunu hawaye ya soma wanke mata fuska,sai ya saki hannayenshi ya sake matsowa
inda take ya kama hannayenta,ya sani qwarai kishi abu ne mai zafi cikin zuciya,abu
daya ne wanda zai janyo mata ta rasa dukkan wata dama daga gareshi shine taci gaba
da hauka da tashin hankali
"Enought.....daga gani na sai kuka,ya isa" wani ratsawa wadan nan taqaitattun
kalaman sukayi har cikin zuciyarta,sai kawai ta fada jikinsa rungumeshi tana sake
sakin kukan,hakan bai dace ba saboda suna tsakar filin gidan,kowa ma na iya ganinsu
a haka,dagata yayi daga jikinsa yana fadin
"Zan wuce ne wajen daurin aure kada na makara,ki koma ciki,but ki sauya kayan
jikinki kafin na dawo zuwa atamfa lace ko shadda,coz akwai maza da zasu shigo da
yawa bayan dawowar tamu bana son kowa ya sake zuwa ya ganki da wannan shigar,ya
kamata ta zama tsakamin ke da ni ne kawai cikin gida,understand?"mamaki ya kusa
kasheta,bai taba furta mata makamanciyar wannan maganar ba sai yau,me yake son
maida ta ne,irin kidahumar matarsa?,taga sarai shigar jikinta,ta nannade kanta da
wani material kamar gawa ba wajen shan iska,itakam ba zata iya ba
"sai na dawo ko?" Bata saba yi masa a dawo lafiya ba ko wata addu'a tun da can ma
da ake zaman dadi bare yanzu,saboda haka har ya juya ya koma wajen motarsa driver
ya bude masa ya shiga suka fice tana tsaye wajen,ashariya ta lailayo ta qunduma
cikin harshen nasara,tana jin nemawa kanta 'yanci ya zama dole,ba zata taba lamunta
ta zauna cikin irin wannan rayuwar ba,da wannan tunanin ta tattaka cikin sassarfa
ta wuce nasu bangaren.

        Wajen anty maamaa ta soma shiga ta gaidata,suja gaisa da dukka 'yan uwanta
a mutunce ta musu Allah ya sanya alkhairi,cikin farinciki tare da yabawa suke
amsawa,lokaci daya ta burgesu ta shiga ransh,don babu wanda su'ad ta taba duba da
irin wannan sigar tsawon saninsu da ita,ta dan kashe wasu mintina masu dama kamin
ta wuce wajen ummee.

         Dukka 'yammatan yau na falonta,amira uwar daba na cikinsu anata


sabga,tsokanarta suka shiga yi har ta rasa na karewa,amiran tace
"Ku dubarmin wannan mata,daga dawowar miji saiki tattara ki bishi,wai ku don Allah
baku gajiya da zaman hotel?" Duka kan cinyarta sumayyan ta kai mata
"Baki da kunya fa,nu yayarki ce ko kin manta?"
"Tuba nake,Allah ya ja da ran babbar yaya" dariya duka suka saka,barkwancinsu abin
sha'awa ne da burgewa,ta gaisa da kowa cikin fara'a da mutuntawa,eesha dake zaune
tun shigiwar sumayyan gaba daya sauran fara'ar da tayi rara a fuskarta ta bace
bat,kusan a wannan bigiren tafi kishin sumayya fiye da su'ad,saboda su'ad din kusan
bata da wani amfani ko tasiri mai yawa cikin zuciya da rayuwar almustapha,babban
abin tashinbhankali kuwa data gano wasu sabbin sauyi da halaye da duka almustaphan
ua qaro matuqar yana tare da sumayya,itama eeshan bata dameta,ita a yadda taje ji
yanzu ko kishiya bazata bari ta dameta ba,balle wata wadda batasan me ya hadata da
uta ba,abinda ta sani dai kawai eeshan nada izza izgilanci da jin kai,tun daga
sanda tazo gidansu a kano tun bikin amira,ita kuwa a rayuwarta zata iya mu'a mala
da kowa tayi haquri da shi banda mutum mai wadan nan halayen,don bata ga abinda
zara nuna mata ba,mutunci da rufin asiri dai dai bakin gwargwado Allah ya basu,to
kuma name zata zubda mutunctakarta ta dan adam kota yarda a zubda mata?,amiran ita
ta miqe don raka sumayyan sama wajen ummee,suna haurawa saman ta dubeta
"Kinsan wajen ummee mijinki ya gaji halinshi,miskilancin tsiya rashin son
hayaniya,daga wajen anty mamaa fa ta dawo wai kanta ke ciwo tana daki kwance"
harara ta watsawa amira
"Eh kam su ai sun huta,ba irinku ba akun kuturu" baki amira ta riqe
"Iyeee,wai yau ya man kike tarewa?"
"To ya ranki?" Ta fada tana juya idanu,suka sanya dariya baki daya,ran amira ya
mata fes,burinsu ya cika,dangantakar da suke fatan ta qullu tsakanin sumayya da
almustapha bisa dukkan alamu Allah ga qulla ta cikin ruwan sanyi.

       Knocking suka yi mata ta basu umarnin shigowa,amira ke gabasai sumayya,tana


zaune a dakin ita da qannenta biyu da yayarta,idanunta kan sumayya fuskarta qunshe
da fara'a,yayin da kunya ta yiwa sumayya katutu,don ta tabbata tasan ba gidan suka
kwana ita da almustapha ba,a ladabce ta qarasa ta duqa tana gaidasu suka amsa a
sake,nabila qanwar ummee wadda itama babba ce don tana da yara samari ke tsokanar
sumayya
"Har yau baku kai mana ziyara kano ba,duk da dama wannan sarkin hade gabas da
yamman sai sallah sallah yake zuwa mana,saidai ki jisu suna waya da mai martaba,da
alama ma baisan jikinsa ya motsa ba bai gaya masa da tuni kin ganshi ya tashi
hankalin kowa" dariya suka sanya ummee tace
"So nake kafin ya koma i yayi qoqari ya kaisu baki daya ita da su'ad din,don ita
dinma dudud zuwanta nawa?"
"A'ah kibar ta wannan,itakam tunda baquwa ce sai ya kaitan,idan tana da sha'awa da
kanta zata ko tasa ya kaita" inji hajiya saudat yayar ummee,hira suke kadan kadan
kafin su fice don komawa bangaren anty mamaa,tsabar hadin kai da fahimtar juna ya
sanya duk sanda wani abu ya taso cikin gidan walau na hajiya mamaa ne kona hajiya
kilishi wato ummee 'yan uwan kowaccensj basa qasa a gwiwa wajen zuwa,run daga kan
matasa yammata zuwa manya,akwai hadin kai da fahintar juna mai yawa
tsakaminsu,kowanne family sunsan kowanne,haka 'yamnatan kowanne vangare na mu'amala
dana kowa,kasanceqar duk sha'ani za'a hadu,sai duka suka zama kamar family daya.

       "Ina almustaphan ya shiga ne?" Akunyace ta amsa mata


"Ya wuce wajen daurin aure ne"
"To masha Allah" inji ummeen dadi yaja ratsata,
"Allah ya saka da alkhairi fa amiran umman khalipha,naji dadin yadda na fara ganin
sauyi wajen almustapha,bama ni ba hatta da babansu,Allah ya qara miki juriya da
qwarin gwiwa,naji labarin abokiyar zaman taki tazo,ina son inja hankalinki da don
Allah kada ki biye mata da duk wautar da zata zo da shi,ki dauke kanki kiyi haquri
da ita,idan kika fuskabci akwai abindabtake miki na cutarwa da ba zaki iya dauka
ba,ki samu mijinku cikin salama ki sanar masa ya warware muku matsalar,kada ki soma
yarda ki biye mata ku dinga abinda ba dai dai ba,kada ki yarda saboda ita ku dinga
bata ran mijinku kinji"
"insha Allah ummee"
"Allah yayi miki albarja,ya akbarkaceku da zuriya dayyiba" addu'ar tayi mata
nauyi,amira ce ta cafe
"Amin ummee,kai Allah dai ya nuna mana ranar,ummi da ido daya zaki bacci ina jin"
ta fada cikin tsokana tana qyaqyata dariya,murmushi ya subucewa ummee
"Kinci gidanku,kin maidani kakarki ko?" Ta fada tana harararta,murmushi itama
sumayya tayi,gwara da zancan ya tsaya nan kada ta hanata sukuni gaban ummeen.

       Bata jima ba ta wuce bangarenta,sanda ta shiga babu kowa falon,sai ta shige


dakinta ta ware lafayar dake jikinta,kitchen ta wuce kai tsaye ta soma tunanin me
zata dafa mishi?,don tuni ta sani wajen ummee baicin abincin taro idan ana
yi,yankewa tayi tayi masa jallop din couse,sai ta tanada masa wani abun shan,shine
zata gama cikin sauri kafin su shigo,cikin qanqanin lokaci ta hada komai ta dora.

Cikin mintina ta kammala jallop din wadda ta wadata ta kayan lambu da kuma
hanta wadatacciya a ciki,kammala komai tayi waje guda ta soma hada lemo,shima bai
dauketa lokaci mai tsaho ba ta gama ta kammale komai waje daya ta soma gyara wajen.

Cikin takun isa da izza ta shigo kitchen din,ta sauya kaya kamar yadda ya
umarceta,a yanzun tana sanye da fitted gown na wanu lace mai azabar kyau da
tsada,saidai bata daura dankwalin ba,sam sumayyan bata ji shigowarta ba,sai takun
takalmanta masu tsini wanda ke haduwa da tiles din wajen suna bada wani sauti,a
hankali ta waiwayo ta dubeta,sai ta dauke kai taci gaba da aikinta ganin ta shigo
mata ne ba tare da sallama ba,bata tsaya ko ina ba sai data ci birki a gaban
sumayyan wadda ke wanke sink data kammala amfani da shi,wani kallon sama da qasa ta
yiwa sumayyan cike da tsantsar raini wanda sumayyan bata ma san tana yi ba bare ya
dameta,aikin gabanta kawai take ci gaba da yi,itakam bata hango komai tattare da
ita ba banda kyau da take da shi,sai tsantsar duhun kai,idan banda haka meye
hadinta da daura zani?,meye na shiga kitchen tamkar matan daa?
"Ke" ta ambata cikin gatsali,sam bata nuna ta san da ita take ba,hakan ya quleta
"You african women dake nake" nan ma tayi banza da ita taci gaba da dauraye wajen
tana gogewa da qaramin towel dake hannunta,hannu ta dora kan kafadar sumayyan ta
juyo da ita suna fuskantar juna,murmushi sumayyan ta saki sannan ta dora hannunta
saman na su'ad din ta saukeshi daga kafadarta tana fadin
"Sallama ya kamata ki soma kafin shigarki waje a matsayinki na diyar musulmi" ta
juya taci gaba da aikinta,wani abu ya tsaya mata,itama za'a koyawa abinda ya dace
"Banga dama ba kuma bazanyi na,domin bani da shamaki cikin shiga duka inda naso a
cikin gidan nan,gida dai na mijina ne so mallakata ne,ba wanda ya isa hanani shiga
duk inda naso a sanda naso" waiwayowa tayi ta sake saki mata murmushi,mata na baki
mamaki a yawancin lokuta,wato su duka son kansu ya musu yawa ne?,babu zaman lafiya
idan su suka sameka cikin gidanka kamar yadda babu zaman lafiya idan kai ka tadda
su,saidai zuwa yanzu ta tsike ya kamata itama ta shiga a dama da ita
"Oh sorry fa,may be labarin shafa fatihar dake tsakanin sumayya da almustapha bai
isa kunnenki ba,idan kuwa har ya isa kunnenki to ya kamata kisam cewa nima matarsa
ce kamar yadda kike matarsa,so kinga kenan matsayinmu daga,babu wanda nima zaimin
shamakin shiga inda nakeso,saidai ni nawa addinin ya gayamin duk inda zan shiga na
nemi izinin mai mallakin wajen kafim shigar tawa,wannan kadai shi zai sanyani neman
izini bawai don nima ba matar doctor mustapha bace" kalamanta sunyi matuqar qona
mata rai,ita take kallon idanuwanta take gaya mata cewa itama matar almustapha
ce,sai ta gyara tsaiwa fuskarta na sauya launi saboda kishi
"Anzo point din,dama abinda nazo na baki shawara kenan a kai,ina mai baki shawarar
sawunki a likkafa ki fita rayuwar mustapha,ki tattara ya naki ya naki ki koma gidan
ubanki tun baki gamu da tuggun kishiya ba" abun ma sai yaso baiwa sumayya dariya,ta
matse towel din data gama wankewa bayan ta gama goge gogenta ta dubu su'ad
"Ina zaton ke din farin shiga ce kan tuggun kishiya ko?,to mu ba yau muka fara gani
ba,zagi kuwa ban tashi naga ana yi ba,don nasan makomar wanda ya zagi iyayen
wani,shawara kuwa da kike ambata ai ciwo ce,baya ga haka ma kina iya riqe abarki
wataqila nan gaba zata miki amfani" daga haka ta juya kan qafafunta ta soma takawa
da niyyar barin kitchen din,zage zage su'ad din ta soma yi,tana son yayuaba baqa
kamar yadda aka gaya mata saidai babu cikakkar hausa,hakan ya sanya ta dinga hadin
gambiza da turanci
"Idan baki wasa ba nice ajalinki" shine kalmar qarshe data shiga kunnen sumayya
yayin da take niyyar fita,hakan ya sanya ta waiwayo tana sake jifanta da murmushi
"Idan numfashina a hannunki yake yau kada na kwana a duniya" ta juya ta fice
abinta,sam ko a jikinta,tasan sarai zata fuskanci sama da haka ma daga
wajenta,saidai ba yau farau ba balle zuciyarta ta quntaya,meye ba'a yi mata ba?,har
farautar rayuwar tata anyi.

Toilet ta fada ta sake wanka,sannan ta shirya cikin atamfa plain zani da


fitted riga,ta fuskancu shigar na yawan qawatar da almustapha,yakan yawaita binta
da kallo duk sanda ta yita,tana tsaka da shafa mai bayan ta sanya kayan ta jiyo
sallama,hakan ne ya sanyata fitowa daga dakinta ta ratsa ta corridor dinta ta fito
falon,abida ce matar hamza,cikin farinciki ta tarbeta ta jata sukayi dakinta
"Wai wannan wawuyar ta dawo ne na sameta tana zirga zirga tsakanin falo da dakinta
ta kasa zama" abidan ta fada sanda take shirin zama saman doguwar kujerar dake
dakin,sumayyan na saman dressing chair tana kwalliya,baki sumayyan ta tabe kana ta
saki murmushi
"Gata kuwa kin ganta"
"To Allah ya kyauta,sai ki sake zage damtse ki rungumi mijinki" dariya ma ta baiwa
sumayyan har sai data dara,daga nan suka shiga hirarsu,tana gaya mata ai ta dan
jima ma wajensu ummee,hamzan ne ya sauketa ya wuce wajen daurin aure su da lamin,ta
nan zasu dawo idan an kammala daura auren.

Bata fi minti talatin ba ta jiyo sallamarshi cikin muryarshi mai cike da


izza da kwarjini,kamar wadda aka yiwa allura ta miqe,dariya abida ta saki sumayyan
ta kalleta cikin dan jin nauyi don ta tabbatar qila yadda taga tayi saurin miqewan
take wa dariya
"Mene ne" kai ta kada
"A'ah babu komai jeki abinki ina nan ina jira" ta fada tana miqewa saman
kujerar,feshe jikinta ta sake yi da turare sannan ta fice.

A hankali ta tura qofan dakin baccinsa dake sama cikin nutsuwa,idanunshi


cikin nata bayan muryar su'ad da ta soma dukan dodon kunnenta,shike fuskantar qofa
su'ad ta juya baya,magana take cikin bacin rai harda qwallarta a idanu,yayin da ya
zuba hannunshi cikin aljihun wandon shaddarsa yana dubanta,tuni ya cire babbar
rigar sai 'yar sama da dogon wando,baya ta koma a hankali da niyyar komawa tunda ta
fuskanci wata magana suke wadda wala'alla abune da su'ad din bazata so taji ba,a
hankali ya motsa baki har yau bai daina kallonta ba,ta masa kyau matuqa,komai nata
mai nutsuwa ne da shiga cikin zuciya cikin wani irin sanyi
"Zo nan" ya kirata yana ci gaba da kafeta da idanu,maganan da yayi ya sanya su'ad
yin shiru daga rattabo maganar da take yi,ta waiwaya a hankali idanunta kan
sumayyan,bawinciki ya sake ninka mata fiye da na dazu,har wani canjin kwalliya
take,ita har a nuna mata ado,gabanshi ta qaraso,kafin tace wani abu ya bata umarni
"Rage kayan jikina ki hadakin ruwa,ina sin yin wanka" idanu ta dan fiddo,ta yaya
hakan zai kasance ga su'ad wajen na tsaye,yadda ya kafeta da idanu tasan zata jama
kanta wani abunne hakan ya sanya ta nufeshi ta soma balle masa botiran gaban
rigarshi cikin taushi da sanyi,idanunsa ya dauke daga kan sumayyan ya mayar kan
su'ad
"Uhmmmm,ci gaba ina jinki,na taho da jama'a na jira na" kai ta kada tana yunqurin
danne hawayenta don kada sumayya ta ganta bare ta rainata,ta sani sarai tunda har
ranshi ya baci sai ya horata,koda zata ciyo kansa to sai ya hukuntata,wanda bai iya
hukunci ta dadin rai ba,idan ya maka sai kaji babu dadi
"Ka barshi kawai,idan ka dawo mayi maganar"
"Ke kika tada maganan yanzu kk?,bayan na gaya miki cewa ki barta sai na nutsu,ki
qarasa kawai idan ba gaka ba daga wannan muhallin banson na sake jin komai daga
gareki,idan na dawo zan ganku ne kawai baki daya ina fata kin fahimta" ita kanta
tasan indai har zaman lafiya take so da mustaphan to ta bar maganan,ta yarda ya
gabatar da su wa juna,idan yaso ta ruwan sanyi zata dafa yarinyar,zata ga
barikanvi,zata ganar da ita rainin america ba irin na nijeria bane,zata nuna mata
akwai banbanci,za kuma ta nuna mata almustapha nata ne iya daya da ita kadai ya
dace.

Busy busy,need ur prayers,we shall meet tomorrow in sha Allah.

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

9⃣0⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

*YA UBANGIJI KADA KA JARRABEMU DA AZZALUMAN SHUGABANNI SABIDA ZUNUBANMU KAJI


QANMU,YA ALLAH DUK MAI NEMAMMU KO NUFINMU DA SHARRI ALLAH KA MAIDA MASA DUK ABINDA
YA YI TANADI A KAN KANSA YA KOMA MASA*
____________________________________

       Kai kawai ta kada ta juya ta fice daga dakin,bata so tayi wani abu da zai
sanya almustapha yayi misbehaving dinta gaban sumayyar,don ta riga data sani ta
bata masa rai qwarai,ta kaishi bango,hakanan fushinsa bai da kyau ko kadan,idanunsa
ya dauke daga kanta bayan ta fice ya dubi sumayyan sanda ta gama,daga boxer sai
singlet,da idanu ya nuna mata singlet din,a kunyace ta cire mishi,ya sake nuna mata
boxer din,sai ta kauda kai tana turo baki,itakam ba zata iya ba,shi ko nauyin su'ad
baiji ba zai wani ce ra cire masa kaya,zata juya kenan ya janyota jikinta,ya
matseta cikin jikinshi yana goga fatar jikinsa jikin tata,tsigar jikinta ta zuba
saboda yawan gargasar dake jikinsa
"Ina zaki baki gama ba?"
"Na gama mana,na bar baquwa ne a qasa"
"Idan ina nan kisa a ranki babu wani a gidan nan sai ni da ke,abidan ce baquwa?,ki
tambayeta haka takewa hamza?" Shuru tayi murmushu na qwace mata,sakinta yayi ya
nufi bandaki yana cewa
"Kayan nan akwai zafi,but akwai dadi da kyau kayan al'ada" kanta ta maida inda ya
yasar da babbar rigar,kana kallonta kasan bata jima jikinsa ba,hakan yake ko a can
din ma cireta yayi ya riqe a hannunshi,gefan gadon ta koma ta zauna,wayarshi ta
soma ruri,musaddiq ke kira,ganin haka ya sanya ta daga ta shaida musu wanka yake
"Au shine ya zube mu a wannan da yake shine agwagwa sarkin wanka?,tell him muna
jiranshi" murmushi kawai tayi ta datse kiran,abotarsu na burgeta,kawai sun dauki
kansu daya ne baku daya su shidan,qaraso yayi ya miqa mata hannu sai ta dora wayan
saman tafin hannunsa,ya fara shafawa yana tambayarta waye ta sanar masa,sai ya dan
tsuke fuska
"Why you permit him yaji muryanki?"
"Afuwan" ta fada a sanyaye,sai ya dan saki fuska yana ajjiye wayar tare da takowa
inda take zaune,gab da ita ya zauna har suna gugan juna
"Ina da kishi,matsanancin kishim da bansan ina da shi ba sai da muka kasance
tare,please ki kiyaye"
"In sha Allah", mai ta dauko ta soma shafa masa bayan ta gama tsane masa jiki,duk
inda ta zagaya ko ta gifta qamshinta na bibiye da ita tare da cika masa hanci,cikin
wani cotton yadi fari qal mai adon ash ya shirya,ba qaramin kyau kayan suka masa
ba,sai ta dinga satar kallonshi ba tare data sani ba,shigar na qawatar da ita,jikin
bango ya rutsata tsaye,tana shirin yin qasa da kanta ya riqe fuskan
"gulma.....kema kin iya,me yasa ba zaki bude baki ki magana ba?" Murmushi ta
saki,sai ta saka idanunta sosai cikin nashi ta juyasu tamkar mai yin faari,hakan ya
rudashi,ya sanya tattausan lebbansa ya sumbaci idanun nata,qarar wayarshi ta katse
masa abinda yake shirin yi,ummee ke kira,ta sanar masa baba na son ganin sumayya a
falonshi,ya sauke wayar yana dubanta
"Baba ne ke kiranki,but bana so ki fita,a cike wajen yake,muje na rakaki"
"To" ta amsa ta juya da niyyar ficewa,har ta sanya qafarta waje yace
"Hey" juyowa tayi tana dubanshi,da hannu yake kwatanta mata
"Ina hijabinkin nan babba wanda ya sauko qasa?"kai ta gyada
" yauwa,shi zaki sanya"
"To" ta amsa tana ficewa,wayarshi ya ciro ya kira su lamin ya shaida musu yana zuwa
zaije wajen baba ne ya dawo,a dakin ta tadda abida har ta soma gyangyadi
abinta,tace tana zuwa
"Babu komai,gama uzurinki,ni wannan kwanciyar ta fimin komai dadi" murmushi tayi ta
fice tana tausayin abidan,tayi nauyi qwarai,duka duka watanni kadan suka rage mata
ta haihu,ba lallai ma tabi hamza a gida taje tunanin zama har sai ta haihu din.

       Tana gaba yana biye da ita kamar wani body guard,hakan ma yayi masa,tunda ko
banza yana morewa kallonta,kasa control din kanta tayi sa'ar da taga malam da
abdallah,da gudu yaron ya nufota ta duqa ta tarbeshi ya fada jikinta ta rungumeshi
"Ammi......ashe nan kika dawo kin bar gidan umman khalipha.....laaaaaa,daddy?" Ya
katse maganar tasa ya dora da wannan sanda suka hada idanu da almustapha wanda ke
tsaye hannayenshi harde a qirji,sosai abun ya masa,sai ya tuna sanda ya ganta da
hijab cikin ranakun bikin amira,ta bude hannunta kamar haka yaran suka
shige,kwadayin samun yaranshi ya taso masa ya kuma sake nunkuwa fiye da da,don a
wannan lokacin haka kawai yaji yafison yara fiye da baya,yana jin dama ace abdallan
nasa ne,yaron ya shiga zuciyarshi,amma tana nufin itace mamarshi?,Allah ne ya
kiyaye bai kai mata bugu ba randa ta bugeshi kenan,sam bai sani ba,barin jikin
sumayya yayi ya nufo almustapha,cak ya dagashi sama murmushi na subucewa daga
fuskanshi,sama ya dinga juyashi abdallahn na dariya,yana son ayi masa hakan dalilin
da yasa ya kasa manta almustapha kenan,dauke kanta tayi wani farinciki na ratsata
ta isa gabansu baba ta duqa,cikin qauna ladabi da girmamawa take gaidasu,cikin
kukawa baki daya suke amsawa kafin baba ya dora
"Haduwa tayi wuya mamana,tunda kuka dawo ban ganku ba" kai ta sadda qasa tan
murmushi
"Ummee tace kaje jigawa ai sanda muka iso"
"Gaskiya ne kam,ina fatan komai lafiya?,ko da yake alamu sun nuna hakan,saidai muci
gaba da binku da addu'a" murmushi taci gaba da yi ba tare data tanka ba,dai dai
sanda almustapha ya qaraso ya durqusa gabansun kamar yadda sumayya tayi ya soma
gaidasu suna amsawa,ta dan saci kallonshi sanda yake tambayar mama da yaya
abubakar,baba ne yace a basu waje da sauri malam yace
"Haba muhtari,waye baqo cikinku,me zan gaya mata me zata gayan,ka daina min haka"
dariya baba ya saki ya koma ya zauna,hira suka taba sama sama duk da sumayya ta
kasa sakewa,daga bisani ta dauke abdallah ta basu waje,malam din ba sai ta kawo
masa komai ba,idan ta aikata hakan ma kamar tayi rashin kunya kenan,don ita kanta
ba zata iya qayyade yawan abincin dake gabanshi ba.

        Suna tafe abdallah na kafadarta duk nauyinsa,tana tambayarsa yana rattabo


mata labarai kala kala
"Ummu abdallah" taji an ambata daga bayanta,almustapha ne,cikin kunya ta sauke
abdallah,ya qaraso ya karbi hannunshi
"Don me zaki fito ki barni ni kadai,wuce sashenki" ya fada yana gyarawa abdallah
hannun rigarshi,ba musu ta wuce ta barsu a nan.

        Wajen ummee ya wuce,kasancewar duka yau bai shiga ya gaidata ba,tana cikin
baqi ta miqe ta bishi saman,ta samu daya daga cikin kujerun ya zauna,abinda ya
burgesu yadda abdallan ya duqa har qasa ya gaida ummen,ji take da ana qwacen d'aa
da ta qwace abdallah ta baiwa almustapha,saidai babu komai duka tushiya daya
ce,tana fatan wadda ta samar da wannan ta samawa nata dan itama,cikin kulawa da
juna suka gaisa sannan yace
"Su'ad fa ta shigo kun gaisa?"
"A'ah,amma wataqila ka ganta,ai ba tafiya zata yi ba yau din,ko zuwa gobe ma duka
daya ne zamu gaisa" take ranshi ya baci har fuskarshi ta nuna hakan,dama ya zargi
haka saboda baiji baba ya masa maganarta ba,duk yadda akayi shima baisan da zuwanta
ba,ko zai lamunci komai amma banda bangaren iyayenshi,sun fiye masa kowa da komai a
rayuwarshi,yana da azamar miqewa ta dakatar da shi
"Bance kaje kuyi bacin rai ba har hakan ya kai kunnen babanka gida cike da jama'a"
ajiyar zuciya ya sauje,tafi kowa saurin karantarsa abinda yayi niyya kenan yaje ya
sameta,ya dan jima wajen ummeen suna tattauna lamuranda suka jima basuyi hira akai
ba kafin ya fita daga bangaren.

        Wajensu hamza ya koma,ya taddasu har sun gama ciye ciyensu,wanda duka
sumayyan ce ta sa aka kai musu,ba qaramin faranta masa hakan yayi ba,a da aikin
ummee ne,ga hidimar baqinta ga na abokanshi,wannan karon kam kafin ummeen ma ta
farga har tasa an gama musu komai,musaddqi ke cewa
"Munci mun qoshi,saura a turo mana amarya mu gaisa" wani shegen kallo ya watsa
masa,suka tuntsire da dariya baki daua,hamza kam murmushi kawai ya saki yana qarewa
almustapha kallo,kusan yafi kowa cikinsu farinciki da samu sauyawar rayuwar abokin
nasu,ko makaho ne kai kana kallonshi kasan cewa akwai sauye sauye masu girma
tattare da shi.

         Sai yamma sannan malam yayi shirin komawa kasancewar a jirgi yazo a nan
kuma zai koma,ba yadda baba baiyi da shi ya bari sai gobe ba amma yawi,yace zasu zo
zuwa na musamman,lokacin sumayya na raka abida da nafisa wadanda suma zasu koma
"Amma malam da zaku bar mana shi ya kwana biyu wajenmu?" Murmushi malam ya saki
yace
"Gaku nan gashi" ai kuwa yana jin abinda aka fada ya noqe kafada yana narke
fuska,dariya malam ya saki shida baba
"Shifa kamar wanda aka haifa tare da gidansu,baison matsawa nan da can,ki baya ga
haka ma abdur rahman na tabbata sai ya biyo sahu idan ba'a koma da shi ba,don yana
dari dari ya bafa shi gani yake kaman bazai dawo ba" sumayyan tana ji tana gani
cike da kewa abdallah ya tafi,taso qwarai ya zauna wajeta yayi wasu kwanaki,tana
tsaye tana duban motar data daukesu zata kaisu airphort harda baba,sai da suka fice
sannan ta saki ajiyar zuciya,ta baya taji an rungumota,ta dan firgita kadan,sam ta
mance hana tsaye gefanta,tun daga sanda yarom ya tafi yaga sauyin yanayin
fuskarta,habarshi a saman kafadarta ya rada mata
"Ba ke ba,nima ina buqatan yara,zakiyi himma ki bamu namu da wuri my wife?"tilas
murmushi ya kubce mata,kunya ta kuma kamata,ta soma yunqurin raba jikinsu saboda
idanun mutane,duk da wajen ba gun wucewar jama'a bane sosai,amma tana iya hango
eesha na tahowa da alama hanya ce ta biyo da ita ta wajen,shima sarai ya ganta,ya
kuma gane abinda yasa sumayya keson qwacewa,sai ya ma sake hade fuska ya kuma
janyota cikin jikin nasa sosai
"baki amsa min ba my life"
"Am ready" da sauri ya juyo da ita suna fuskantar juna
"Really?"kai ta gyada a kunyace,sai ya soma juyi da ita wajen,cikin kunnenta ya
rada mata
"ki zama cikin shiri yau"sai ta sinne kanta,ya soma manna mata kisses wanda hakan
yaso tsaida bugun zuciyar eesha,qara sauri tayi ta bar wajen zuciyarta na
bugawa,tsaki ya ja sanda ta gama wucewan
"stupid....ki kula da yarinyar can,banson wata hulda tsakaninku" inda ta wuce din
sumayya tabi da kallo sai ta maida kallonta wajensa,gira ya daga mata kafin ya raba
jikinsu,cikinsa ya soma shafawa da hannunshi yana yamutse fuska
"Yunwa" ya furta a hankali,sanoda tun safe rabinshi da abinci,idanu ta zari
waje,shaf ta manta
"Am really sorry don Allah,Allah na yi maka abinci tun dazun na zaci kaci na bikin
ne" ta fada cikin kwabe fuska,yana son salon maganar nan tata,sai ya sake mata
murmushi ba tare da ya shirya ba
"Ban haqura ba" ya fada yan akwaikwayon salon maganar tata,dariya ya bata har sai
da farareb haqoranta suka fito,idanu ya zuba nata yana kallon yanayin dariyar tata
cikin ban sha'awa da burgewa,sai data gama tsaf sannan yace
"Zan turo a dauka min abincin" ya furta yana takawa kan qafafunshi ya matso dab da
ita
"Wuce ciki tukunna" juyawa tayi sai da yaga ta wuce ciki sannan shima ya wuce

       Qarfe biyar da rabi na yammaci aka soma shirin zuwa dauko amare,dai dai
lokacin ya shigo cikin gidan,kwance ya sameta saman gadonshi,idanunta baki daya sun
tasa sunyi jajur da su,kanshi ya dauke daga bangarenta,su'ad ta cancanci dukkan
wani hukunci daga wajenshi,abubuwan bacin ran data yi masa ba zasu qirgu ba,bai
mata yadda baba ya bata lokaci yana musu nasiha ba,da kuma yadda shima yayanka mata
warning amma hakan duka bai hanata tsallakewa tayi tafiyarta ba,bugu da qari kuma
saboda ta raina mishi iyaye ta dawo cikin gidansu amma babu wanda ya isa ta
nemeshi?.ta lura idan batayi da gaske ba wankin hula zai kaiya dare,don wasu
takaddu ya diba ya juya yana da nufin sake ficewa,da gudun tsiya ta cimmasa,ta
rungumoshi ta baya tana sakin kuka,cikin turanci tace
"Kayi haquri ka yafemin,nasan na bata maka na maka abubuwa marasa dadi,amma duka
kai ka janyo da aka hada baki da kai aka dauko mana wata cikin rayuwarmu" dan
janyeta yayi daga jikinsa ya waiwayo yana dubanta cikin bacin rai
"Har yau baki hankali ba,duk sanda kika fahimci kinyi kuskure mayi maganar da
zamuyi" ya sake juyawa da nufin ficewa,maqalqaleshi tayi bakj daya wanda hakan ya
tilasta masa tsayawa,cikin kisaa ta dinga fidda kuka tana bashi haquri,bata da wata
mafita data zarve hakan,tasan bazai taba iya shallakewa kukanta ba,kasancewarsa mai
yawan tausayi da rashin son kuka,a hankali ya janyeta zuwa gadon suka zube baki
daya,hannunshi ya sanya ya goge mata hawayen,har yanzu tana maqalqale a jikinsa,sai
da gama goge matan kafin ya dora
"Tun ba yau ba na baki damarki tafi a qirga kan ki gyara,idan baki gyara ba duk
abinda ya biyo baya kada kiyi kuka da ni,duk da hakan kika sanya qafa kika shure
maganata,mutum nawa kika tadda a nan gidan?,su me ya cisu da suka zauna tare?,me ya
gutsiresu gayamin?" Ya fadabyana zuba mata idanu,wani abu ya takoreta,haushin su
ummee ya sake kamata,ta tabbatar yana mata kwatance ne da su,tilas ta bude baki a
cunkushe tace
"Ba komai"
"So ki iya bakinki ki kyautata kalamanki,kada ki manta wandanda suka sanya baki kan
auren su su waye a wajena,iyaye na ne wadanda ba wani abu da matsayinsa yayi dai
dai da su ko mene ne shi a duniya" shiru tayi haushi na cikata,tsanar mutanen na
sake cikata,itakam wlh bata ga abinda zai sanya ta fasa yi musu abinda tayi niyya
ba,amma sai ta kawai ta gyada kai a sanyaye
"Amma almustapha baka daina sona ba har yanzu?,sannan kayi missing dina" murmushi
ya subuce masa na gefan baki,kai ya gyada
"Duk yadda kika fada haka ne" qanqameshi tayi tana jin quncin dake ranta na raguwa
"I love u,i love u so much my dear",nan ta narke ta dinga dauka masa alqawuran
sauya duk wani abu da baiso,daga qarshe ta masa alqawarin ta bar karatun zata zauna
da shi,zata yi dukkan abinda yake so,daya daga cikin abinda ya sake sauko da shi
kenan

      Ta jima tana kwatanta yadda zata kirashi ta sanar masa tafiyan nasu,bata son
sake shiga dakin balle ta gansu irin na dazu,ba mafita dole ta soma kiran lambar da
take kyautata zaton tashi ce,wayar na kusa da shi sai ya miqa hannu ya
dauka,capital S ya sanyawa sunan tun wancan lokacin,sai ya daga ya kara kunnenshi
ba tare da yace komai ba,sallama tayi ya amsa mata kafin shiru ya biyo baya
" amm,dama.....dama ni da amira ne zamu je gidan amaren ana tafiya"shiru ya danyi
kafin ya amsa
"Kice ta wuce ta tafi,ke kuma kizo ina nemanki" ya kashe wayar daga haka,cikin
mintuna sumayya ta turo qofan hade da sallama,tayi kyau cikin wani yadin material
mint blue mai haske wanda aka yiwa adon baqi,dinkin doguwar riga ne wadda ke da
shape na umbrella,ba qaramin kyau shigar tayi mata,ta baro mayafinta a daki bata
yafa ba,hakan ya bayyana asirin jelar kitsonta da kuma baqaqen fashion data saka
wadanda suka qara haska farar fatarta,duk yadda yaso ya kaucewa kallonta ya kasa
har su'ad ta lura da hakan,a nutse ta qaraso tana dauke idanunta daga kansu,wani
abu data tabbatar zuwa yanzu kishi ne ya riqe mata wuya,saboda su'ad na jikinsa
kamar zata shige cikinsa,kanta na kafadarshi,abinda ya hanata zama kenan tana daga
tsayen tace
"Gani"
"Na ganki,u look so beautiful,da da wannan shigan zaki tafi wani gidan amare?,ba
inda zaki" duk da hakan bai mata dadi ba amma kishin dake cinta yafi mata zafi kan
furucinsa,sai kawai ta juya tana cewa
"Ba damuwa" mamaki ya kama su'ad,taso ace ta masa musu sun fara sa'insa ya bata
mata rai kamar yadda nata ran yake a bace,amma sai taga akasin hakan,kishi ya sake
maqureta sanda taji su'ad na ambatar wash na gaji yake cewa ta kwanta ra huta,bai
son ta qara kuka.

        Daki ta shiga ta fada kan gado idanunta na mata zafi kamar yadda zuciyarta
ke mata,bata tabajin makamancin wannan kishin ba akan duka mazajen data aura har da
mukhtar kuwa,sunan Allah ta dinga ambata kadan kadan har ta soma ji zuciyarta na
mata sanyi,miqewa tayi ta isa gaban mudubi tana duban kanta,sai ta soma zargin
kanta da zafafa kishi?,meye ne a ciki?,su'ad matarsa ce,meye ke bai miki ba kema?ta
tambayi kanta,sai ta saki murmushi tana baiwa kanta qwarin gwiwa,ganin lokacin
sallar magariba yayi sai ta shiga bayi ta daura akwala,ta dawo ta sake sabunta
kwalliyarta ta zura haijabi ta tada sallah,bata bar kan abun sallar ba sai wajen
takwas na dare bayan tayi sallar isha'i tare da karatun qur'ani saboda ta sake
samun nutsuwar zuciya,ta kuwa sameta,don sakayau take jinta,bata san ya tsarin
gidan nasu zai kasance ba,hakan ya sanya batayi gigin dora komai a matsayin abincin
dare ba,sai data gama sallar ne ma ta shiga kitchen,cikin qanqanin lokaci ta shirya
haddaden salad,ta fere abarba ta markada ta tayi lemon abarba wanda yaji flavour
mai dadin qamshi.

       Tana fitowa a kitchen suka kusa karo,yana sanye da shirt da trouser dukkansu
baqaqe,sun matuqar yi masa kyau,kallo daya zaka yi masa kasan cewa ya sake wanka
ne,kishi na nemon taso mata ta danneshi,ya tsareta da idanu,sai kuma ya sake
matsowa dab da ita,ta dan matsa baya ya sake biyota,sai da suka dangana da jikin
bango,sunkuyo da kanshu yayi daidai kunnenta ya rada mata wata magana data sanyata
saurin kallonshi,sai kuma ta sake yin sauri ta kauda kanta,murmushi ya saki ya kamo
fuskarta saitinsa
"Me kike kitchen da daren nan" cikin cool voice tace
"Abincin darenka,amma ban sani ba ko ka qoshi" ba qarakin burgeshi tayi ba,wanu
banbarakwai yake jin kansa,abinci direct ba tare da yayi oder kashe kudi ya jira an
kawo masa ba
"Thanks" ya furta a sanyaye,idanunta ta watsa masa kafin tace
"Dutyn kowacce mace ne" sai ya dage giranshi yana murmushi
"Oh haka ne?" Da idanu ta amsa masa,sai ya lumshe idanunshi kafin ya bude,wannan
idanu nashi na tafiya da shi,sau tari sukan so karya dukkan wata mzantaka tashi
lokaci guda,su kuma tafi da nutsuwarshi.

       Yana tsaye yana duban nata suka ji takun sawun takalma,su'ad ce cikin
qananun kaya riga da wando wadanda suka dameta sosai,zamewa sumayya ta danyi ta
goce,sai ya bita da kallo yana fadin
"Sorry madam,zan ganku ne ke da ita"
"Yes sir" ta fadi cikin wani irin salo da ya sanyashi murmushin dole.

     Tuni hakimar ta hakimce saman kujera qafa daya kan daya,kusa da su'ad din ya
zauna sannan ya kama hannun sumayya dake qoqarin zama waje daban ya janyota wanda
hakan har yayi sikar fadawarta jikinshi,da sauri ta tashi tana daure fuska ta zauna
kusa da shi kamar yadda ya buqata,hannun kowacce ya sanya cikin nashi,wanda hakan
yayi tasiri a jikinsu da zuciyarsu baki daya
"Dukkaninku kowacce cikinku tasan cewa ita matata ce,sadaki na biya na kawo kowacce
cikin gida na qarqashin kulawata da sunan matata ko?,.....to ba dogon zance zanyi
ba,ku zaina lpy bana son fitina ko tashin hankali ko hayaniya duk kun sani,ba wanda
zan saurarawa matuqar ya nemi tada fitina ko hargitsa zaman lafiya,saboda haka ku
kiyaye" cikin dabara sumayya ta janye nata hannun kana qasa qasa tace
"In sha Allah" don ita bata ga meye abun tashin hankali ba imdai da su'ad ne,tashin
hankalin da ba yau ta soma fuskantarshi ba,abu daya ta snai wannan karon babu mau
fiddata daga gidan,koda QADDARARTA kuwa zata yaqeta da addu'a wadda take fatan ta
sauya mata ita da iko da kuma izinin ubangiji
"Ina da magana" su'ad ta fada qunci na cika mata zuciyarta,din gani take ajinta ya
fado raga raga matuqar ma qawayenta suka samu labarin ita aka yiwa kishiya
"Ya za'ayi da rabon kwana?,sannan girki kowa mai aikinshi ta masa,kuma ban lamunce
mutum ya ganka ba cikin ranata" kafada ya dage gami da girarshi
"Wannan tsakaninku ne,kawai abinda na sani shine,da rana ina da ikon yin mu'amala
da kowa,sannan zanyi magana da duk wanda naso,da darene zaki kwana da ni,zancan
kwana kuma bibbiyu kaman naga ana yi,idan ma ba haka akeyi ba abarshi hakan" sai ya
dubi sumayya
"Can i have my dinner?" Bata ce komai ba ta miqe tsam ta wuce kitchen,su'ad ta
rakata da harara kafin ta maida idonta ga almustapha
"Kada kace min aninci gida zaka ci,kuma abincim waccan?"fuska ya bata yana dubanta
" bana son kowaccenku ta dinga min zanca 'yar uwarta,mind your own business" ya
dauke kanahi daga gareta,rabe baki tayi har tau halin yana nan sannan ta narke
fuska tana dubanshi
"Me zan ci as dinner ne dear,yunwa nake ji" yana sauya tashar dake kan t.vn zuwa
wata yace
"Akwai komai a kitchen ko?,ki samawa kanki wani abu mana" idanu ta zaro kamar wadda
aka sheqawa mari
"Habba dear,so kake nayi baqi,kamar wata baqauya,kawai zanyi order nan da few
minute nasan za'a kawo min" ta furta tana latsa wayarta tana neman lambar gidan
abincin da suka saba order idan suka zo garin.

      A nutse ta fito da komai,ta iso gabanshi ta soma shiryawa,kishi ya cika


su'ad,ta rasa me zata yi ta bata ranta,ta lura kamar ma bata gabanta,bazai yiwu
wata 'yar nujeria 'yar arewa wadda bata san kanta ba ta dinga bata ranta a  banza
ba ba tare data rama ba
"Dear..." Ta fada a shagwabe,waiwayowa yayi ya dubeta ba tare da ya amsa ba
"Amma yau kwana na ne ko?"
"Like how?"
"Eh,haka za'ayi,ban qoshi ba dear...." Ta fada tana sakin murmushi
"But its better a fara rabawan daga gobe ko?,tunda bansan da zuwankin ba bare mu
tsara haka" fuska ta bata wanda sumayyan ta lura da haka,sai ta saki murmushi tana
duban almustapha,ido daya ta kashe masa cikin tausasa murya tace
"Baqonka fa annabinka,babu komai na bar matan,nima na huta ko?,jibi sai mu hadu"
haka kawai yaji ranshi ya baci kamar yadda ran sj'ad din ya baci,duk da taji dadin
bar matan data yi amma sai ta tsuke fuska ta hau daddanna waya,harara ya jefeta da
ita ya janyo plate din salad din wanda ada yake zumudin ci amma manarta ta sanya
kaso hamsin cikin dari na shauqin salad din nashi ya tafi,ganin tana niyyar miqewa
ya sanyashi cewa su'ad
"Daukomin cumputer na a daki" a kasalance ta miqe,daya daga cikin abinda ta tsana
ya aiketa tana zaune tana hutawa,qafa ya sanyawa sumayya dake niyyan barin wajen,ai
kuwa ta fado samansa baki daya,ruqon tsauri yayi mata wanda ya sanyata jin zafi,ta
saki qaramar qara
"Wa ya baki iznin yin kyauta da kwananki ba tare da yardata ba?sabida kin tsaneni"
idanu ta qwalalo sannan a shagwabe tace
"Gani nayi ta fini buqatar ka"
"Ok,ke kin gaji dani kenan?"
"A..a'ah...ba haka bane bafa"
"Kin gudu ne baki tsira ba,zaki biya bashin da sai kin gwammace bakimin kyauta da
kwanana ba,oya miqe kiyi feeding dina" ya fada yana sakinta,boyayyen murmushi ta
saki,itakam bai dameta ba hakan,saboda tana son ta shiryawa wannan zamanne
sosai,sai ta sanya su'ad ta banvance tsakanin aya da tsakuwa,zata gane matan areea
ba kanwar lasa bane kamar yadda take hasashe.

     Gabansa ta tanqwashe qafa cikin wani irin salo da ita kanta bata san tana yi
ba ta soma zuba masa cikin plate,baki daya ya raja'a a kallonta har baisan da
isowar su'ad ba wadda ganinsu haka take jin kamar ta sanya bakin bindiga ta harbe
sumayya,baisan me yasa take daukan hankalinshi haka ba,komai tayi daban yake
ganinshi da na saura,hannu ya sanya ya amshi cumputer din ya budeta,kan ta gaka
zuba kasa salad zuwa lemo ya soma danne dannenshu,tura plate din tayi gabanshi
"Bismillah"bai dubeta ba yace
"u seen what am doing,so feed me" ya fadi yana bude bakinshi"
"Amma rana ta ce nike da right da zanyi feeding dinka ba ita ba" tayi hanzari katse
sumayya,sai kawai sumayyan ta tura spoon din bakinshi ba tare data dubeta ba,tamkar
ma wani qwarin gwiwa taji ta qara mata,sai da ya hadiye na bkinshi sannan yace
"Ki bari idan kin girka naki sai kiyi feeding dina,ba adalci ta hada ke kuma ki
bani,gwara ra qarasa ladan" kusan da biyu ya fadi hakan,tun ba yau ba yasha fama da
ita kan ko ruwan coffe ta hada mishi amma bata taba gwadawa ba,kanta ta dauke don
ita din ma tasan bazata taba yarda ta shiga kitchen da sunan yi masa abinci ba,sam
ba zata iya ba,ai ranan tana jin qila sai ta kwanta asibiti an qara mata ruwa,ina
zata iya shaqan qaurin abinci warin gas da zafinshi.

*YA UBANGIJIN ANNABI MUHAMMADU KA ZABA MANA SHUWAGABANNI NA GARI,YA ALLAH KANA
GANINSU,KA SANSU,KASAN FILI DA BOYENSU,ZAHIRI DA BADININSU,ALLAH IDAN AKWAI
MUMMUNAN NUFI DA QUDURI BOYE CIKIN ZUCIYARSU KAN BAYINKA,ALLAH KA KARYASU KARYUWAR
DA BAZASU TABA DORUWA BA HAR ABADA KO WANE SHI YA ALLAH,ALLAH KAI KACE MU ROQEKA
ZAKA AMSA MANA,ALLAH KAYI MANA WANNAN GATAN,KADA LAIFUKANMU SU SANYA KA SALLADA
MANA SHUGABA AZZULUMI MARA IMANI,ALLAH KAYI MANA GATA ALFARMAR SHUGABA MASOYINKA
DAN GATANKA ANNABI MUHAMMAD S A W*

*BANDA NI CIKIN RIKICIN ZABE,MU JEFA QURI'ARMU CIKIN NUTSUWA DA BIN DOKA,ALLAH YASA
MU DACE,SAI ALLAH YA KAIMU RAN LAHADI KUMA IDAN MUN SAMU DAMA*

SUBHANAKALLAHUMMA WABI HAMDIKA,ASH HADU AN LA'ILAHA ILLA ANTA,ASTAGFIRUKA WA'ATUBU


ILAIKA
*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

9⃣1⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

*Allah S W T yana cewa*

*HAQIQA DAN ADAM MAI YAWAN ZALUNCI NE MAI KUMA BIJIREWA*


______________________________________

Sai da ta kammala bashi sannan ta tattare dukkan kwanukan dake wajen tayi
kitchen da su,ta tsaya ta daurayesu ta maidasu muhallinsu,daga kitchen din ta
lallaba ta shige dakinta,fin bata son komawa cikinsu,bata ga ma amfanin komawar ba
baki daya,sai data shiga toilet ta sake wanka,ta sauya kayan bacci sanda ta nufi
gadonta.

Shiru tayi saman gadon ita daya,juyi ta dinga yi daga wannan bangare zuwa
wanacan,baki daya dakin yayi mata girma da fadi,ta manta yaushe rabon ta xa kwana
ciki daya ita daya kamar haka?,qwan wutar lantarkin dakin da aka kunna shi ya
sanyata yin firgigit ta daga kai,almustapha ne tsaye bakin qofa harde da
hannahenshi,sanye yake da kayan bacci ruwan hoda kalar da su'ad tafi so kenan,sun
masa kyau sun haska kalar fatarshi,idanunshi a kanta ya dinga takowa a hankali har
ya qaraso inda take,shigowanshin bai sanyata tashi zaune ba,tana daga kwancen take
kallonshi irin kallon qasan idanun nan,wani abu ke sukan zuciyarta.

Kai tsaye gadon ya hauro bai bata lokaci ba ya danneta ya aza mata
nauyinshi,murya qasa qasa yace
"Baki damu da ni ba ballantana ki tsaya muyi sallama ba ko?" Qoqarin tureshi take
ta miqe saidai ta kasa,cikin nishi tace
"Ba haka bane,bacci nake ji shi yasa" dagowa yayi yana duban fuskarta yayin da taqi
yarda ita din ta kalleshi
"Uhummm,yaushe kika fara qarya?,ko dama can maqarayaciyar ce,idan bacci kike ji me
ya hanaki yi yanzun?"
"Akwai abinda na tsaya yi ne" dagata yayi yana 'yar qaramar dariya
"Gaskiya ne,coffee nazo ki hadamin in sha kafin na kwanta" ya ambata yaba gyara
wuyan rigar baccibsa wadda ke da V shape,dagowa tayi ta dubeshi
"Amman ita yafi cancanta ta dafa makan,tunda gunta kake" ta fada tana qoqarin
hadiye kishin dake taso mata,eh tabbas ya sani ita zata dafa din,amma shi kansa
yasan wasa ne ma,ta yaya su'ad din zata iya wani dafa mishi coffe koda ta iya bayan
yasha wanka ta harde saman gado tana jiranshi?,hasalima ita ta bashi daman ya kira
masu aikin gidan su dafa mishi
"Bazan samu ba kenan?" Kai ta kada tana yunqurin sauka daga kan gadon,binta yayi da
kallo,kayan duk da na bacci ne amma sun amsheta sosai,ta sake kyau a
idanunshi,saukowan shima yayi ya biyo bayanta,ta dora hannun saman hijabinta da
niyyar sanyawa ta fice ya riqe hannun nata,dagowa tayi suka hada idanu
"Muje na rakaki kitchen din,a haka nake son ganinki" ba musu ta saki ya sanyata a
gaba suka fice.

Cikin kitchen din yana tsaye jingine da freezer hannunsa harde a


qirjinsa,duka motsinta da kaikawonta idanunshi na kanta,komanta a nutse a tsaftace
abun burgewa,ta gama komai ta zuba cikin dogon cup wanda yake da riqe zafi ta miqa
masa,hannu biyu ya sanya ya amsa yana murmushi,tun kafin yasha din kwadayi ya
kamashi,qamshin ya cika masa ciki,baisan yau wanne kalar coffe tayi
masa,ganyayyakin da yaga tana hadawa dabanne
"Thank you" ya furta a tausashe,har cikin zuciyarta lafazin ya sauka,sai ta samu
kanta da maida masa martanin murmushinsa
"Albarka nake son ka sanyamin" ta fada a kunyace,murmushinsa ya fadada
"Qwarai albarka tafi lafazina na thank you,Allah yayi miki albarka" ya maimaita har
sau uku tana amsawa da amin,gaba ya sake sanyata suka fice,sai dayaga ta shige
corridor dinta sannan ya juya ya haura sama da tea din hannunshin,don a bedroom
dinta na qasa tayi kwanciyarta bata ma yi sha'awar hawa na saman ba.

***** ****** ***** ****

Misalin sha daya da rabi ne na safiyar washegari,yana tsaye kanta sanye da


wani lallausan yadi ruwan qwaiduwar qwai,hannunsa zube cikin aljihun wandonshi yana
dubanta sanda take shiryawa,baki daya ji take jikinta kamar ba'a jikinta yake
ba,kwana sukayi jiya suna abu daya ba cikakken barci,gashi yau tunda asussuba ya
tasheta wai tayi wanka tayi sallah,hakanan ta tashi ba don taso ba,ta tsani yadda
yake tilasta mata tashin asubar nan,agogon hannunshi ya duba,tunda gari ya waye ba
wanda ya fita a dakin shi da ita
"Ki sauri zamu je mu gaida su ummee ne kada baba ya fita" tamkar ya soka mata wuqa
a qahon zuciyarta haka taji,me zata je tayi musu,magulmatan mutanen?
"Gaskiya bazan samu zuwa yanzu ba kaje kawai na shiga daga baya" take yanayin
fuskarshi ya sauya,me take nufi?,a hakanne take cewa ta sauya zata dinga duk abinda
yake so?,ashe ma wasu halayen ta dado?,tunda ada ko sau daya a rana takan shiga ta
gaidasu sai gashi yanzun tana neman sake bijirewa
"Kada ki yadda su'ad,kada ki yarda tun ba'a je ko ina ba tafiyar nan ta sake
watsewa,kada ki yarda raina ya baci kan hakan?,sai na maimaita miki abinda na fada
miki jiya kenan ko?,to iyayena sunfi min kowanne mutum muhimmanci da daraja cikin
duniya koda kuwa wane shi,ba'a haifi macen da zata rainamin iyaye ba wallahi ko ita
din wace" ranta ya sake baci,biyayya tamkar wanda suka shanye?,tana son zaman
lafiyarta hakan ya sanya ta miqe ta soma lalubar kayan da zata sanya,riga da wando
ta dauko cikin kayanta ta soma qoqarin sanyawa,wani kallo ya watsa mata
"Ki nemi wasu kayan ki sauya,kin daina wannan shigar matuqar ba ni da ke bane
kawai" kasa daurewa tayi tayi kicin kicin da rai
"Wai duka meye haka ne almustapha?,me ya shiga kanka ne ya canzaka haka?"
"Tunani da gayara.....dole ki sauya kamar yadda kike ganin kamar na sauya,sabida
wannan shine dai dai"
"Amma meye hadin sauyina da tufafin da zan sanya" soma takawa yayi zaya fice daga
dakin,ya fuskanci idan ya tsaya biye mata sai ta sanyashi ciwon kai
"Ki sauya kaya na mutunci ki sameni qasa,fine..." Ya fadi yana bude qofa ya fice
daga dakin,kayan data debo din ta watsar gefe daya cikin huci,hakanan tana ji tana
gani ta shiga dakinta ra dauki atamfa riga da skert ta sanya,sai yalolon mayafi
data yane kanta da shi ba tare data damu da daura dankwakin ba,duk da dai sun
matseta amma sunfi wadancan.

Tana cikinsu anty farida huda da amira dake falon ummee suna hirarsu tamkar
sun shekara da sabawa da sumayyan,karyawa suke a qasan tiles din falon husna na
saman cinyarta tana bata tea kadan kadan da cokali yayin da suke karyawa suka
sauran banda ita,tun takwas ta kasa komawa bacci bayan ta farka daga dan baccin da
ya kwasheta bayan sallar asuba,hakan ya sanya ta miqe ta shiga kitchen,cikin awanni
biyu tayi kunun gyada da alala lafiyayye,ta diba nata ta ajjiye sannan ta samu wasu
warmers masu kyau ta zubawa ummee da baba,wanka tayi ta shirya cikin shadda maroon
mai adon milk doguwar riga ta yane kanta da madaidaicin milk din mayafi ta
fita,taci sa'a kuwa ta tadda ummee zata wajen baban ta bata nashi bayan ta bata
nata itama,tayi zamanta cikinsu farida suna hirarsu gwanin sha'awa wanda a baya
basu samu wannan damar ba.

Sallamarshi ta sanya dukansu waiwayowa suna amsawa har da sumayyan,saidai


ita ta dauke kanta ne taci gaba da baiwa husna tea din da takeyi,har ya qaraso
idanunshi na kanta,ta iya shigar hausawa ainun,duk yayin da tayi shiga takan tuna
masa da ummensa zamanin quruciyarta,bazai manta salon adonta ba,husna tayi kyau a
hannunta tamkar diyarta,kujera daya suka zauna da su'ad din wadda tunda ta shigo
sumayya ta tsone mata idanu,a ladabce suka gaisheshi baki daya ya amsa yana
tambayar farida ina yaran tunda yaga yaran huda a hanya,tace jiya abbansu yazo ya
daukesu,sunyi kaduna gidan kakanninsu za'a soma bikin qanwarshi next week,ba yabo
ba fallasa suka gasheta kasancewarta matar yaya a wajensu duk da sun girme mata,ta
amsa hanci a sama,don babu wanda bata jin haushinsa,tana ganin duka bakinsu daya da
shawararsu aka kwaso mata abokiyar zama,sumayya ta dan waiwaya kadan ta
gaidashi,sai ya amsa mata kamar sauran,cikin basarwa da dakiya,wanda hakan ya dan
sosa ranta,zuciyarta tasi karyewa,ta tuno rayuwarta gidan mukhtar tsakanin fa'iza
da zainab,rayuwar gidan lukman da karima,kada fa ace dare daya tak zai soma sauya
mata,ya rusa dukkan wata alaqa data soma ginuwa tsakaninsu,zuciyarta ta daure ta
gaida su'ad wadda bata kulata ba tunda suka shigo gun,amma itama ganin ta girmemeta
yasa ta gaidata din,banza tayi da ita tamkar ba da ita take ba,falon ya dauki
shiru,itakam ko a gefan takalminta,don ta saba ganin hakan wajen kishiya,tunda ta
sauke nata nauyin falillahil hamdi,har sai da almustapha ya maida wayarshi aljihu
ya dubeta ta gefe daya
"Ba dake ake ba?"
"Lafiya lau" ta fada a dake,zuciya ta zowa amira wuya,haushi ya tuqeta,don me ma
sumayyan zata gaidata,me yasa batayi watsin tsiya da ita ba itama,shine zata zo
tana ma mutane dagawa da daga kai?.

Shigowar ummee falon ya sanya su miqewa,ummee ce ta tsaida sumayyan saura


suka shige ciki,a ladabce cikin qauna da kulawa ya gaidata,ta amsa fuskarta fadade
da fara'a,su'ad itama ra gaidata kadaran kadaham,duk da tana jin ba don almustapha
dake wajen ba wallahi ba zata gaidata haka ba
"Ya kika baro su khaulat din" sai data raya,munafuka kamar gaske cikin zuciyarta
sannan ta amsa da
"Lafiya lau"
"To masha Allahu"
"Inaga sai kayi hanzarin zuwa ka tadda baban naka,don ina tunanin zai fita,na
barshi yana karyawa"
"To ummee"
"Me za'a kawo maka me zaka ci?"ta tambayeshi tana dubanshi,kunya ta kama sumayya ta
sadda kanta qasa,tana ganin kamar ummee zata ga ita din ma ta gaza tunda gashi yana
shirin komawa 'yar gidan jiya cin abinci wajenta,saidai ita ummeen tuni ta fahimci
cewa yau ba kwananta bane,indai kuwa hakanne kamar yadda take zato ba shakka bazaya
samu abin kari ba saidai yaci a waje
"me kuka dafa?"
"Akwai tea,akwai chips,sai farfesun kayan ciki da amira tayi,sai kuma amiran umman
khalipha data kawo alala da kunun gyada" satar kallonta yayi sanda ita kuma taje
duban wani waje,duk da sarai taji alamun yana kallonta din,yaushe rabon shi da yaga
kunun gyada ko alala ya mance tsahon lokacin,yaushe har ta tashi ta gama dukkan
wadan nan ayyukan har ta shirya ta fito
"A kawomin abinda ya samu" duban su'd dake hakimce ummee tayi
"Su'ada shiga kitchen zaki ga kayan jere,ki deba masa abinda zai iya cinyewa" dauke
kan da ummeen tayi ya sanya bata lura da sauyawar fuskar tata ba,gani take da gayya
ummeen tayi mata haka,ita waccar baqauyar me ya hana ta aiketa sai ita,wanzuwar
almustapha a wajen shi ya takawa abinda ta taka burki,miqewa tayi cikin bacin rai
ta nufi kitchen din.

A qalla sai data bata wasu mintuna masu dama kafin ta fito dauke da farantai
kamar wadda ta dauko duniya,ba zata iya tuna ranan data shiga kitchen tayi wani
aiki kamar haka ba,tana isowa ta saki tray din har da suka tsorata saboda yadda ta
soma yarfe hannu tana kiran Allah,hanzarin kama hannun yayi yana dubawa,tsammani
yake ko qonewa tayi,saidai ba haka bane,daukan kwanukan da tayi takewa haka,tsam
ummee ta miqe saboda takaici
"Idan ka gama ina saman" ta fada tana niyyar haurawa,sai sumayyan itama ta miqe ta
rufa ma ummeen baya,binta yayi da kallo kamar ya dakatar da ita,domin ko gaisuwar
da sukayi bata yi masa ba,ji yake kamar ya shekara ne bai ganta ba,amma sai ya dake
ya maida kallonsa ga su'ad,hararar wasa ya jefa mata
"Raguwa,sai kace wadda ta qone,oya....yi serving dina" tamkar wadda tayi aikin
shekara haka ta dinga zuba abincin,wani bakin kwanukan duka ya baci.

Da kansa ya haura saman don kiran sumayyan suje su gaida baban,umme ta gaya
mishi tana daya dakin tare da su farida,sanda ya shiga anty farida na toilet,huda
ta shiga kitchen damawa yaronta madara,sai amira dake zaune kusa da sumayyan wadda
ke rabawa husna gashinta tana daure mata shi suna hirarsu qasa qasa da amira da
alama gulma suke,turo qofanshi ya dakatar da su,idanunsa har yau a kanta,da idanu
ya yima amira alamun ta fita,tsam ta miqe
"Koma ki dauketa" ya nuna mata husna da ido,komawa tayi ya dauketa daga cinyar
sumayya ta fice,bata motsa daga inda take ba sai ta wayance ta karkade jikinta duk
da ba wami qura ko gashinda ya zuba,ta soma hada qananun ribbom din dake zube qasa
tana maidawa cikin ledarshi,gabanta ya qaraso ya tsugunna,ya riqe hannunta tsam
dake tattare ribbom din,sai ra dagi ta dubeshi da fararen idanunta
"Shariya?.....ni zaki dinga sharewa haka?,hmmm lallai yarinya bakisan waye
almustapha ba" zuciyarta ta karye,wani irin qaunarshi lokaci guda taji tana kutsawa
cikin zuciyarta,kallon da yake mata kadai na dabanne,zuciyarta ta raurawa wanda
batasan dalili ba,ta shagwabe masa ba tare data shirya ba
"Ni kuma?.....me kuma nayi?"sai tsugunan ya gagareshi ya zauna sosai a gabanta
"ki tashi da safe baki neme ni ba ki fice binki?,kiyi breakfast abunki duka babu
ni?,kin daina damuwa da ni ko?"
"Ni vance haka ba sai kai zaka fadi?" Ta furta a zuciyarta,ta bude baki zatayi
magana qofar bandakin ta bude,anty farida ce ta fito,ganinsu a hakan ya sanyata
qara mai ta fice a dakin
"Ya man abun ya motsa kenan,yanzun ne ake baje kolin da da ba'a baje ba" take
gulmarshi cikin ranta a haka ta qarasa dakin umme tana tuntsirewa da dariya
"Me haka lafiyarki?'ummee ta tambayi farida
"ba komai ummee,eata soyayya na gano ana bajeta yanzun nan" shiru ummeen tayi tana
ci gaba da sabgarta,don ta gane inda zancan ya nufa.
"So kake naje na buga muku qofa?,ko so kake na yi ma abinci ba ranar kwana na
ba?"
"Ko?" Ya fada yana dage mata gira tare da kallon lips dinta da suka burgeshi,shiru
tayi ba amsa,tana qoqarin sadda kanta ya riqe fuskarta,sai da ya tsotsi lebunan son
ranshi sannan ya kamata ya miqar tsaye
"Muje mu gaida baba",yana tsakiyarsu haka suka jera,kowacce da abinda take ji cikin
ranta.

Ranar kusan wuninta tayi wajensu huda,sai da yammaci laila tazo da su


khalipha harda hafiz,nan ta dinga kwasarshi
" kai kam hafiz rashin son jama'arka ya baci wlh,yanzun sai yau zaka zo
gurina"dariya yayi
"Kiyi haquri anty sumayyanmu" basu bar gidan ba sai wajen gab da magariba,bayan
laila ta bawa sumayyan saqon da anty dijen ta kawo mata.

Washegari gidan anty dijen ta yiwa tsinke,da qyar ya barta,sai da hamza ya


kirashi zasu fita sannan ya mata tattaki har qofar gidan ta shige,sosai taji dadin
wunin wajen antyn,ta rabauta da sirrika masu yawa,da kanta ta baiwa antyn kudi a
sake kawo mata dilkar nan saboda yadda ta karbi fatar jikinta,saidai a sanyaye ta
dawo gida saboda albishir da antyn tayi mata na cewa uncle farouq ya sanyi gida
zasu tashi daga nan,hakan ya daga hankalinta,amma abun alkhairi ne ci gaba ne ya
samesu dole ta tayasu murna.

Sanda ta dawo gidan gimbiya su'ad na zaune a falon qafa daya kan daya,an
tsuke ana danna waya,yayin da ma'aikatan ta da aka dawo mata da su suke kitchen
suna girka abincin dare,ko sallamarta bata amsa ba,itama bai dameta ba tunda ba
zamanta take ba,ta wuce dakinta kai tsaye abinta,sai data gama duk abinda take
sannan tayi wanka,sallar magariba ta soma yi,ta shirya cikin riga da skert na
atamfa,tana son atamfa har cikin zuciyarta,lite make up tayi ta murza daurin
dankwai sannan ta fesa turare,ta dubi kanta a mudubi yadda fatarta ta sake
kyau,juyawa tayi ta fice a dakin don shiga kitchen ta samarwa kanta abinda zata ci
kafin akira isha'i,tunda kowa zai dinga girkinsa ne shi da mai gidan ranar
girkinsa.

Har yanzu tana falon zaune,saidai wannan karon ta sauya kayan jikinta,riga da
wandon ne amma fari da yellow,fukarta radam da makeup,tsaki ta jiyota ta ja sannan
ta furta
"Villager,always atamfa atamfa,thats d problem of arewa women" maganarbummee na
kada ta soma yarda suyi cecekuce ta fado mata,don haka ko ta waiwayo ta dubeta
batayi ba bare ta nuna taji abinda take fada,bata da lokacin cecekuce sam tana
tunanin ta wuce wannan babin,a da can zamanin da take da qananun shekaru ma bata
yiba ballantana yanzu?,daqiqi shike maimaita aji amma ba mai qwaqwalwa ba,kai tsayi
ta nufi kitchen,gab da zata shiga qofar tata kitchen din ma'aikatan suka fito sanye
da unifoarm da warmers da suke shiryawa wajen dining,a ladabce suka gaisheta,ta
amsa musu fuska sake tayi gaba,tana jiyo ashariyan da su'ad ke dura musu saboda
gaidatan da sukayi
"Uban wa ya dauko ku wa kuke wa aiki?,zaku koma inda kuka fito wlh duk randa naga
wata na mata wani abu,talaka talaka ciwon kai ne wallahi" kai ta gyada tana mata
fatan shiriya,ita sam mai aiki ma bata burgeta bata cikin tsarinta,idan bata tashi
ta yi hidamawa gidanta ba daga wayewar gari zuwa faduwar rana to meye
amfaninta?,taci ta kwanta tayi bayan gida?,idan ya cika akwashe?,abinci mai sauqi
ta dora cikin tukunya mafi qanqanta a cikin tukwanenta,cikin kitchen din ta zauna
hannunta harde a qirji tana tunani kadan kadan har ta kusa kammala ta juye ta fito.
Tana fitowa a kitchen din yana shigowa falon,da ita ya soma tozali tunda
tana tafiya ne zuwa dakinta,boyayyen murmushi ta saka tana son basarwa,saboda duba
daya tayi masa ta karanci tsantsar gajiya tattare da shi,batasan ina hamza ya jashi
ba dai yau kam,ido daya ya kashe mata alamun na ganki ne zamu gamu,ta kauda kai
tana masa sannu da zuwa,yana amsawa ta kutsa kai corridor dinta abinta ta barshi da
su'ad wadda ta taso da dan hanzari tana tsammanin wajenshi sumayyan ta
nufa,murmushi ya sake mata kamar yadda ta sakar masa,saidai baki daya rabun
hankalinshi na gun sumayyar,wayoyinsa ya miqa mata ta karba yana kama qugunta
"Kinyi kyau" ya furta yana kallonta,idanunta ya juya kanta na kumbura,a duniya tana
son taga ta fifita fiye da kowa,tana son taga tafi kowa,sama suka haura tana zuba
masa yauqi.

Turus yayi sanda ya dubi bathtube din yaga wayan babu ruwan wankan da ya
sanya ran samu ciki,yana daga bandakin ya qwala mata kira,ta ajjiye wayarta da take
dannawa ta amsa cikin qosawa ta miqe,tunda ta dawo ta tsiri chart da qawaye da
abokai tunda yanzu ba'a kusa ba kuma ranar komawa,da idanu ya mata inkiya da bahon
wankan sai ta tambayeshi me yake nufi
"Ruwan wanka" hannunta ta yarfar sannan ta taka a hankali ta soma tara masa ruwan
"Ka fara zama sangartaccen,naga da kai ke hada ruwan dear da kanka ko?,gaskiya an
bata min kai" ta fada sanda ta duqa yadda bazai iya gano fuskarta ba taba hade rai
"U can go if you can'nt do it"
"Sorry" ta fada cikin wani salo,yana tsaye har ta gama hadawar ya zare towel dinshi
ya shige,ruwan ya masa zafi amma bai tanka mata ba ya miqa hannunshi ya kunna
famfon ruwan sanyi ya saisaita zafinsa.

Hannunshi riqe da cokali yana dubanta har ta gama zuba mishi ta zauna a
gajiye
"Kai,wai dama haka hidimar aure take?,dole mata su dinga cewa aure akwai wuya" ta
fada tana langabe kanta tana dubanshu,haushi bai barshi ya tanka mata ba,sai yaja
plate din kawai gabanshi ya sanya cokali ya fara ci,duka duka me tayi yau din?,zai
iya lissafa dukkan abinda tayi da yatsun hannunshi
"Dearrrr" ta fada a shagwabe
"Ni zanyi feeding dinka nima yau"ware hannyenshi yayi sannan ya ajjiye cokalin,ta
matso cikin zumudi ta soma bashin,ci kawai yake,sai yake jin akwai banbancin
dandano mai girma tsakanin girkinta da wannan girkin,hakan ya ma su'ad daidai yadda
take bashi abincin ya mata dadi,saidai zata so ace sumayyan na wajen,don itama ta
cusa mata haushi
"dear ka kira ta mana ko akwai abinda yayi mata a nan ta diba?" Hakan ya
burgeshi,sai yayi zaton hankali ta soma,ba musu ya janyo wayarshi ya kirata.

Wayar na hannunta tana neman number malam tunda ta kira ta mama bata shiga
ba,gaidashi take sonyi,tunda ta zubo abincin taji ta kasa ci,baki daya cikinta ya
cushe bayan yau ba wani abun kirki taci ba,a nutse ta daga kiran ta amsa,to tace
sannan ta miqe,sai data sake tsayawa gaban mirrow ta sake shafa hoda ta mutstsika
turare sannan ta fito,idanunta ya sauka kansu sanda take kai cokalin abincin
bakinsa,da hanzari ta dauke kanta zuciyarta na bugawa,sai ta dinga karanto la'ilaha
illa anta subhanaka inni kuntu minazzalilm,tana gayawa kanta matarshi ce,kema kinyi
gabanta,so meye itama don tayi,dubanta yake sanda take takowa,fuskarta sake da
murmushi har ta iso,dadi ya kama su'ad,sai ta sake tura plate din gabanshi tana ci
tana bashi
"Sannunku,wai *our man*, wannan abinci sai da ruwa ko anty na,let me help you" wani
kallo ya jefeta da shi mai cike da ma'anoni masu tarin yawa sautin muryarta dab da
kunnenshi na ratsashi,,salon maganar kadai abar burgewa ce,sumayyan ta balle murfin
gorar ruwa ta tsiyaya cikin cups guda biyu ta tura gabansu
"Thanks" inji almustapha
"No thanks,albarka" murmushi ya sake yana hadiye lomar bakinsa
"Allah yayi albarka,ga abinci wai ko zaki ci?"ya fadi cikin ginshira da ajjiye
kowanne lafazi d'ai d'ai,Sai ta soma bude warmers din,ba abinda ya bata sha'awa,ta
qarshe ce taga farfesun zallar tsoka da kayan lambu,sai ya bata sha'awa har da
hadiyar yawu,sam bata so ci ba amma sai ta tsinci kanta da zama sosai ta sanya
plate ta dibi gwargwadon wanda take tunanin zata iya cinyewa
"Wannan ya isa" ta fada tana duban su'ad wadda take jin wani abu ya tokare
wuyanta,sam wannan dabarar batayi ba,me zata yi mata ne ta huce?
"Na gode anty" ta fada tana sakar mata murmushi,don ta tabbatar ba'a banza tasa aka
kirata ba,akwai wata a qasa,koma meye ta tura mata aniyarta,juyawa tayi a nutse ta
wuce abunta zuwa dakinta,ba haka su'ad sam taso ba,taso taga zallar bacin rai
baqinciki da kishi idanunta,idan da hali ma ta tanka ayi bacin rai,kuma daga bisani
ta janye almustapha su wuce sama,hakan ya dagula ranta,fara'arta da walwalarta ya
ragu sosai har suka kammala suka bar wajen.

Tana shiga ta tadda wayarta na ruri,amira ke kira da yake tun jiya


almustaphan ya kora kowacce dakinta,ta ajjiye plate din ta daga kiran nata tana
zama gefan gado fuskarta qunshe da murmushi,suka soma gaisawa cikin barkwanci,ta
tambayeta ummee ta bata saqon wani dabino tace "eh,na meye ne?" Dariya ta sanya
"Sai kinci kawai basai na gaya miki ba"nan ta gaya mata yadda zata dinga ci kafin
su shiga wata hirar kuma,tsahon mintuna talatin kafinnsuyi sallama,ta sauke wayar
ta maidata silent saboda dare,idanunta ya sauka kan farfesun data shigi da
shi,murmushi ya subuce mata,itakam tasan akwai dalilin yi mata tayin da su'ad
tayi,bata manta lafuzan data jefeta da su ba dazu,sannan ta lura da kallon data
bita da shi,haqiqa jiya ba yau ba,ita din yanzun ba yarinya bace,zata iya banbance
salon kowanne kallo da kishiya tayi mata dai dai gwargwado,sai ta sake sakin
murmushi tana kada kai tare da neman tsari kan duk wani sharri,sake nadewa tayi
abunta ba tare data bi takan dukkan abinciccikan ba,nata da nasun ta soma danne
dannen wayarta,duk yadda taso taqi cin farfesun amma sai qamshinsa ya dinga cika
mata hanci,yawunta ya dinga tsinkewa,janyo shi tayi ta sanya spoon ta fara ci,idanu
kawai ta dinga lumshewa dadin na ratsa harshenta,bata ankara ba ta tashi da kwanon
baki daya,mamakin kanta ya cikata,itadai tasan ba wani hadi na musamman aka yi masa
da zai sanyata santi haka ba har ta iya tashi da shi,hannunta ta wanke a toilet
gami da yin brush,ta kuskure bakinta da hadin kayan qamshin baki sannan ta sauya
kayan bacci ta dawo ta nade saman gado,wani irin bacci ya dinga fusgarta bata
ankara ba tuni yayi awon gaba da ita.

*mrs muhammad ce*👑

✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)
9⃣2⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

*Assalamu alaikum warahmatullah MY DEARS FANS*

*ina son nayi amfani da wannan damar damun wajen sanar muku da cewa,lallai ne ni da
sauran marubuta 'yan uwana muna buqatar ku dinga yi mana uziri*

*nasan cewa akwai da dama da suke turon saqonni na gaisuwa da tambayoyi ta


numberta,saidai wani lokaci saqon yakan iya yin kwana biyu uku sati daya zuwa biyu
ma wani bai samu reply ba,hakan baya rasa naba da yawan saqonnin da nake fama da
shi,nakan samu saqo wallahi sama da dubu takwas cikin wayata daga na groups zuwa
private charts,banda na Wattpad,face book kuwa wannan sai na samu lokaci ma,kunga
idan kuka duba abun da yawa,ka zauna kayi typing mai tsaho,kayi editing,ka tura
cikin duka groups din da kake ciki,akwai masu comment ka zauna ka amsa musu,kunga
baki daya wannan lamarin bazai yiwu ka iya aiwatar sa shi lokaci daya ba,sau tari
wasu basa fahintar haka har wani ma kan gaya maka baqar magana saidai kawai ka
shanye kayi masa kawaici*

*masu numberta kuma ta kira da sukemin plashing don son annabi su daina min
plashing,wlh bana qaunarsa,sannan kiran dare,'yan uwa dare fa mahutar bawa,wasu
kuma kira da asuba,su fadar maka da gaba ka dauka wani mummunan abu ne ya
faru,wanda yake kira kuma bana dagawa shima yayi uziri,wayata a silent take ban
fiya barinta a ringing ba,wasu lokuta kuma ina rejecting to sometimes ina typing ne
idan layin yana cikin wayar da nake typing da ita.*

*ina fata fans kun fahimceni,duk wanda yaga yayi min magana baiga reply ba yayi
haquri,wani saqon na danne wani idan sukayi yawa,sau tari ma idan ina online ka
turo shi yana sama sama ina qoqarim amsawa,mu dinga yiwa juna uzuri,nasan duka
qauna ce kuma na gode,Allah yasa mu dace ya bamu ikon ci gaba da haquri da juna*

______________________________________

      Kusan a makare ta tashi,idanunta cike taf da bacci tayi sallah,saman abun


sallar ta sake bingirewa bacci na fusgarta,sama sama ta jiyo muryanshi,tsaye yake a
kanta cikin farar jallabiya yana kallonta,bata tantance shi sosai ba ta gaidashi
tana daga kwancen idanunta na lumshewa,cikin mamaki ya amsa yana kallonta,sai yaga
ta juya taci gaba da barcinta,ya jima tsaye yana kallonta qudundune cikin
hijabi,yana mamamin wanne irin bacci take haka?,tsawon wasu daqiqu yana tsaye kafin
ya juya ya fice.

        Qarfe tara na safiya ta sake farkawa,barcin tamkar bai isheta ba,ga mutuwar
gabbai,sai ta shige bandaki tayi wanka saboda taji qwarin jikinta,duka dai
sammakal,amma dai kasalar ta ragu,gaban madubi ta shirya cikin gown mai A shape ta
wani material mai kyau,ta yane kanta da qaramin mayafi wanda ya dace da material
din ta wuce kitchen,falon fes yake da alama masu aiki sunzo sun gyara duk da dama
ba datti yake yi ba,rasa abinda zata dafa tayi,ta jima tsaye tana tunani,sai kawai
ta dauko dankalin turawa ta fere,ta dora a wuta ta dafashi,ta sauke ta
murmusheshi,kifin gwangwani ta bude ta murmusheshi saman dankalin,ta zuba mai a
kasko tu juye dankalin da kufin,a hankali take juyawa tsawin mintuna sannan ta kada
qwai ta yanka albasa a kai da maggi ta juye kan dankalin da qwan taci gaba da
juyawa har sai da qwan shima ya soyu sannan ta juye a plate,ta tsiyayi ruwan shayin
da yaji kayan qamshi ta fito falo.

       Kacibus sukayi da anty ni'ima matar yaya adam,cikin fara'a ta sauya akalar
tafiyar tata
"A'ah,anty ni'ima,shigo mana" itama fuskarta dauke da fara'ar ta qaraso,duka sukayi
masauki saman kujerun falon,sumayyan ta janyo center table ta dora plate da cup dim
hannunta suka soma gaisawa da ni'iman sannan tayi mata tayi,abun ya burgeta duk da
bata san meye ba ko ya akeyi,ba musu ta sanya hannu suka soma ci,sumayyan ta
tambayeta ko a zuba mata ruwan zafin tace alhamdulillah,wannan ma ya isa,suna ci
suna hira tamkar sun shekara tare.

        Tas suka tashi da shi,ni'ima ta kalli sumayya


"Kai amiran umman khalipha,wannan abun yayi dadi,amma fa akwaisa kwadayi,ya ake
yinshi?" Dariya ta saki
"Kai anty ni'imah,simple abu ne fa" a tsanake ta kwatanta mata yadda tayi din
sannan ta dauke farantan tayi kitchen da su ta dawo suka ci gaba da hirarsu.

         Tare suka sauko tana biye da shi a baya,ji take tamkar ta dawo da kwanakin
baya,bata so ta tuna cewa yau zata sallamawa waccar 'yar qauyen mijinta da tafi so
fiye da komai a duniya,sam fuskarta babu walwala haka suka ci gaba da takowa,muryar
ni'ima ya jiyo,ya waiwayo ya dubesu,cikin girmama juna suka gaisa,sannan sumayya ta
gaidashi tana dan dauke kai,kishinsa itama take ji har cikin zuciyarta,saidai bata
son ta nuna,dining din da masu aiki suka shirya da kayan kari suka nufa,yayin da
ni'imah ta miqe
"Bari na wuce,ko wajensu ummee ban shiga ba" sam bata son ni'iman ta tafi,taji
dadin zuwanta,sai ta miqe tana fadin
"Bari na dauko mayafi mu shiga tare,nima ban je ba" tana nan tsaye sumayyan ta
shiga daki ta dauko mayafinta,hankalinshi na kansu duk da yadda su'ad ta tare gaba
da baya,da biyu take yin komai,a nutse ta qaraso bakin dining din a ladabce tace
"Zanje mu gaisa da su umme ni da anty ni'imah" ba tare da ya dago ba yace
"Ni din ma banje ba,ta wuce ma taho" sam bataji dadi ba,sai ta dawo a sanyaye
"Anty ni'imah tare zamu fito" murmushi ta sakar mata
"ba damuwa sai kun fito"daya daga cikin kujerun dake falon ta samu ta zauna tana
jiranshi ya kammala,tana iya jiyo duka abinda su'ad ke fadi,hirar darensu na jiya
take ta sako mishi yana basarwa,jin bacin rai na neman mamayarta ya sanyata miqewa
tsam tayi shigewarta dakinta.

        Tana gaban mudubi tana gyara zaman kayan makeup dinta ya shigo cikin
nutsuwa,har yanzu ranta a bace yake,sai taqi dagowa ta dubeshi duk da yadda take
jin tsaretan da yayi da idanunshi
"muje na kammala"ya fada a a taqaice
"Kuje na taho" itana ta maida masa da yanayin da yayi mata maganar,sarai ya
fuskanci ranta a bace yake
"Muje nace"
"Nace na taho" shiru ya ratsa na wasu muntuna
"Ummu abdallah" da hanzari ta daga kai ta dubeshi,ita yake kalla da shanyayyun
idanunshi masu dauke da wani irin magadisu mai qarfi da tasiri,yana kallon yadda
cikin kwana biyu fatarta ta skma sauyawa tana wani qyalli,ko idanunshi ke mashi
gizo?,ya tambayi kansa,shidai yaga sauyi qwarai tattare da ita,kawar da kanta
tayi,saidai sunan yayi mata dadi har cikin ranta,cikin qaramin lokaci ya soma
saukar da sanyi a ranta,shima sai ya dauke nashi kan,ya taka zuwa inda mayafinta
yake ya dauko,ya iso gabanta,sai ji tayi ya soma yafa mata yana fadin
"Idan baki shirya takawa da qafafunki ba,am ready to carry you,komai ta fanjama
fanjam" dan qanqani daga cikin aikinsa kenan,hakan ya sanya yana gamawa ta motsa
tayi gaba yabi bayanta.

        Kamar jiya haka suka rankaya su ukun baki daga,saidai ita bata dawo
bangaren nata ba sai wajen qarfe biyu,bayan ta bada saqon abubuwa da take ganin
tana da buqatar amfani da su,bayan ta kammala sallar azahar din dakinshi ta
haura,dai dai sanda su'ad ta fito cikin heavy makeup,idanunta manne da sun glasses
da cogen takalminta tana karkada muqullin mota tare da taunar chewing gum ta fice
bayan ta watsawa sumayyan wani banzan kallo,kau da kanta tayi itama tana jan
tsaki,ya ilahi batasan ma me yasa take kishin almustapha haka ba.
        A yamutse ta tadda dakin,ita ta gyara kowacce kusurwa ta dakin,ta dauko
sabon zanin gado ta sauya,ta gyara toilet,ta hada dukkan under wears dinshi ta
tsaftace da hannunta ba tare da taimakon washing machine ba ta shanya cikin toilet
din,tana saukowa aka kawo mata saqon,ta amsa ta nufi kitchen kai tsaye.

       Lafiyayyar sakwara ta shirya tare da water leaf soup,wadda taji ganyen water
leap,ogun,ganda,tsokar na da stock fish,blander ta jawo ta niqa aya da kwakwa da
dabino ta hada lemo ta sanya a fridge,nono mai kyau da aka siyo mata ta hada da
fura ta dama bayan ta wats kwakwa a ciki ta saka shima cikin fridge,sai data
tabbatar da kammaluwar komai sannan ta rufe kitchen dinta da key,don bata mance
rayuwar da sukayi da fa'iza ba,wuyat data sha kasancewar kitchen dinsj
daya,kalanzir gishiri,suger duka a girkinta,murmushi ta saki tana rayawa a
ranta,duniya labari,ko ina fa'iza ta shiga yanzu ohi,Allahu A'alamu.

     Lokaci ta bata sosai a toilet tana murje jikinta,ita kanta mamakin yadda
fatarta ke sheqi da laushi tayi,saidai tana ganin kayan gyaran jikin data yi amfani
da su ne suka amsheta,kwalliya tayi maras yawa saidai ta dace da kyakkyawar
madaidaiciyar fuskarta,ta sake kuma fito da armashin kyanta,ta jima tana saqe saqen
wanne kaya zata saka,wando ta ciro belted high top wide leg trouser ash colour ta
hadashi da long sleeve t.shirt fara qal wadda aka yiwa adon ash daga wuyan rigan
zuwa qasanta,kisonta ta raba jelar gida biyu ta kama kowanne da qaramin ribbom
ash,ba qaramin kyau tayi ba,duk wani tudu da kwari na jikinta ya fito turarukanta
na musamman tayi amfani da shu,wadanda qamshinsu ke tashi a hankali har su gama
cika hancin mutum,kwalabar turarenta babba ta dauka bayan ta kammala komai,ta zira
wani irin plate din farin takalmi mai taushi ta soma bin duk inda burner take a
gidan tana zuba turaren,a haka har ta qaraso falon.

        Tana durqushe kusa da burner din dake bakin matattakala tana zuba turare a
ciki taji an bude qofar sashen,batayi tsammanin ganin kowa ba hakan ya sanya ta
fito haka,a nutse ta juya,almustapha ne a gaba su'ad na biye da shi
"Hasbunallahu wa ni'imal wakil" ya ambata yana lunahe idain nasa sanda idanunshi
sukayi tozali da nata,karon farko da ya soma ganinta cikin suturar da ta bayyana
duk wani structure ta jikinta,su'ad dinma idanuwanta na kanta,mamaki da kishi suka
cikata,take wani bacin rai ya lullubeta,dama yarinyar tasan sanya ire iren
kayansu?,ba sai an gaya mata tahowarta din nan taga shigen kayan a shagon da take
siyayya acan,taso siyosu saboda tasan zasu burge almustapha kuma sun burheta
itama,bugu da qari kayan sabbin design ne da suka fito sati sati uku kacal da suka
wuce,amma saboda kudin hannunta yayi qasa ta haqura,kishin yanayin halittar da
Allah yayi mata ya cika mata zuciya,ba zata manta ba har mai ta saya na qara
mazaunai da qirji amma almustapha ya hanata shafawa,ya zaunar da ita yana gaya mata
irin illolin dake tattare da irin wadan nan mayukan da kuma na bleeching,duk da
bata taba bleeching ba ita,natural farinta ne,to amma ko banza yau gashi ya dauko
mai abun,ita tana zaune,kewayeshi tayi ta wuce corridor dinta da zaya kaita ga
dakinta kai tsaye,zuciyarta na tafasa,kamar ta shaqe kanta,ta wurga jakarta saman
gado tare da tuje mayafin kanta ta wurgar shima tana yamutsa gashin kanta
"No....no,it can't" ta dinga maimaitawa tana girgiza kai,sai ta sake takowa a
hankali ta dawo corridor din nata,ta tsaya tsakanin labulayen da suka rabata da
hango falon kai tsaye,ta sanya hannu ta yaye labulen ta yadda zata iya hangosu.

      Tattausan murmushi ya soma sakin mata idanunshi cike taf da mayen


qaunarta,ita dinma duban shi take fuskarta dauke da murmushi,duban cikin idanunshi
kadai sun gamsaf da ita,wani irin qauna take ji na daban na ratsata,qwafin gwiwa
game da shi take ji,ya bude dukka hannayenshi yana mata alama ta taho,sai ta noqe
kai kamar qaramin yaro yaso quya cikin wani salo na daban,ya motsa bakinsa cikin
muryarsa da har gobe take sake daukaka darajarshi cikin idanunta
"Don't kill me babe,taho please" a yangance ta soma takowa,sai ya kasa jiranta har
ta qaraso inda yake,ya soma shima takawa a hankali suka hade tsakiyan
falon,kyakkyawan masauki yayi mata a qirjinsa yana sakin wawuyar ajiyar
zuciya,baisan ta taka wannan matsayin cikin zuciyarsa ba karo na biyu sai a yau ya
sake tabbatarwa,qamshin dake tashi kawai jikinta ya isar masa samun nutsuwa da
kwanciyar hankali,sumbarta ya soma yi a ajejjere tako ina cikin nuna zallar soyayya
da shauqi.

       Cikin matsanancin tashin hankali ta saki labulen ta shiga dakinta a sukwane


ta soma ball da jakarta data yar a bakin qofa
"No almustapha,no,why u r doing this" ta ambata tana dukan bango da hannunta,kana
ta tafi saman madubinta ta soma watsar da dukkan abinda ta gani samanshi suna sauka
qasa gami da tarwatsewa saman tiles,wannan bai isheta ba sai data dauki kwalbar
turarenta ta doka jikin madubi,tunu ya tarwatse dai dai ya kuma yi silar yankarta.

        Qarar wannan fashewar kayayyaki ita ta dawo da almustapha hayyacinsa,idan


dai dai kunnuwansa ke jiye masa daga dakin su'ad ne,cikin hanzari ya raba sumayya
daga jikinsa ya juya zuwa dakin,hawaye shabe shabe ya sameta tanayi bayan tarwatsa
gashin ta dake daure da tayi,bata damu ba tana ci gaba da jifa da dauk abinda
hannunta ya kai kai ciki har da t.v plasma dake manne a bangon dakin ta kwada mata
make up kit din data wawuro,riqota yayi yana ambatar
"Meye haka su'ad,hankalinki daya kuwa" yunqurin qwacewa take
"Leave me almustapha,leave me" ganin haukar tata da gasje take ya sanyashi daka
mata tsawa wadda ta sanya sumayya dake tsaye falo hankalinta yayi matuqar tashi
"U r mad?!,baki ganin wai me kike yi ne?"
"I know almustapha,am going to kill my self ma gaba daya" tsatstsauran riqo yayi
mata sanda yaga tana laluben kwalabar dake farfashe a wajen,ya damqeta baki daya ya
hankadata saman yamutsatstsen gadonta,ranshi ya kai qololuwar baci,sai kace tabin
jinnu?,yanzun nan fa suka shiga gidan tare lafiya lau,binta gadon yayi ya mata
riqon tsauri tana gunjin kuka tare da yunqurin qwacewa.

         A qalla sun tasamma kashe mintuna goma a haka kafin ta soma sassauta
haukan da take yi,sai kuma kuka da taci gaba da yi,cikin fargaba da nutsuwa sumayya
tayi sallama bakin qofar dakin,a karon farko kenan,sanye da dogon hijabinta har
qasa,waiwayowa yayi da jajayen idanunshi ya zubeta kanta,wadda ita kuma idanunta ke
qarewa yadda dakin ya hargitse kallo,ko bai bata amsa ba ta soma hasashen abinda ke
faruwa,ba zata manta ba,ba zata manya daren data yankeshi a hannu ba sanadin kishi
"Jeki am comming,everything will be okey" kai ta jinjina ta juya ta fice,idan da
tasan ma abinda ke faruwa kenan ba zata bata lokaci ta shigo duba abinda ke faruwa
ba,ranta ya dinga baci,me mata suka mayarda kishi ne?,tabbas babu halittar da bata
da kishi,kishi halitta ce,kuma dole kayi kishin abinda kake so,hatta dabba tana da
kishi,to amma meye amfanin hankali kenan?,meye amfanin ilimi?,meye amfanin girma da
shekaru?,sai ta tsinci kanta ta mai jan tsaki data tuna zainab fa'iza karima ga
kuma su'ad.

        Miqewa yayi cikin takatsantsan don ma qafanshi da sau ciki ya laluba inda
suka ajiyan kayan akwatin taimakon gaggawa,ya qaraso inda take,har yau qwalla na
bin idanunta,tsugunnawa yayi ya soma mata dressing inda ta yanke ba tare da yace
komai ba,idonta na kanshi ta soma maganganu cikin dashewar murya,tsaf ya fahimci
abinda ya jawo mata aikata hakan,baya ga kishi har labe kenan ta soma?,abinda ya
tunzura shi kenan,yana jin kamar ya dauketa da mari zuciyarsa na tausarshi,har ya
kammala wanke mata tsaf,yayi kama hannunta ba tare da ya dubeta ba yayi mata
allurar rage radadin ciwo ya maida akwatin muhallinsa ya juya da niyyar ficewa,qam
ta riqe hannunshi ciki marairaicewa
"Kada ka tafi ka barni na roqeka almustapha,kada kaje wajen yarinyar nan,duk abinda
kake so zan maka" idanunsa da suka sauyi launi kadai da ya watsa mata ya sata
laushi kaso hamsin cikin dari
"Sake ni!" Ya fada a tsawace,sakin nasa tayi yaja baya baki bude tana kallonshi har
ya fice a dakin,a falo ya tsaya ya fiddo wayarsa ya kira ummee yace ta turo
ma'aikatan nan dakin su'ad zasuyi dan wani aiki,ya gama ya maida wayar aljihunsa ya
wuce bedroom dinshi.
       Har suka zauna cin abinci alamun bacin ran basu sakeshi ba,hakan ya matuqar
taba ranra itama,yana zaune saman dining ya hade hannayenshi waje guda yana
dubanta,qoqari yake ya saita kanshi don kada ya shiga haqqinta ko ya sanyata damuwa
kamar yadda yaga kuzarinta ya soma raguwa,baki daya warmers din ta bude wanda take
qamshi ya cika wajen,sai ta koma kujerar dake daura da shi ta zauna,idonta cikin
nashi tana sakar masa murmushi,a hankali ta sanya hannunta saman hancinsa ta ja
madaidaicin hancinsa da ya zauna das bisa fuskarshi ya qawata kyawunsa
"Me zaka iya ci ciki mu gani?,kai din cikakken bahaushe ne?ni duka ma fa nakeso ka
cinye" ta qarashe maganar taba dage masa girarta,murmushi ya subuce masa lokaci
guda,ya raba hannyenshi yana rarraba ido tsakanin kwanukan,abincin da ya jima baici
ba kenan,kusan ya manta ma da ita a jerin abinciccika,ya maida kallonshi kanta
"Kina son miji lukuti me qiba kenan" qayataccen murmushi ta saki masa
"Idan na cinye wannan abincin duka yau anan gun zan kwana,bazan iya kai kaina daki
ba" dariyar data riqe ce ta subuce mata,ganin yadda ya soma kwatanta yana shafa
sumar kanshi
"Dariya kike?,ke zakiji a jikinki,don ba lallai ki iya daukan lukuti ba idan na
qara qiba" kunyar maganar ta bata,sai ta soma gunqurin zuba masa abincin yana binta
da kallo,komai nata burgeshi yake sake yi duk kwanan duniya,dabi'u da al'adun masu
burgewa da kuma mabanbanta kullum yake sake gani wajenta,wasu ya manta da su tana
tuna masa su daya bayan daya,wasu yana sane da su saidai baisan inda zaya gansu ba
yau gasu cikin gidanshi a gabanshi,spoon ya amsa da niyyar fara ci,sau ta langabe
kai tana dubanshu,yau wani irin abu take ji yana fusgarta zuwa gareshi
"I promise to feed you when we r together"
"Thanks" ya fada murmushin na fita a fuskarshi
"No" ta fada tana girgiza kai,ya gane mai take nufi,zuwa yanzu ya fara
fahimtarta,tafi qaunar ya sanya mata albarka fiye da godiya,hakan baya rasa nasaba
da muhimmancin albarkar wajenta fiye da godiyar,shima hancinta ya ja
"U r smart,barakallu fiki"
"Wa laka" itama ta maida masa,ta debi abinci ta kai bakinshi da cokali,sai yasa
hannunshi ya amshe cokalin ya ajjiye
"Da hannunki nakeso ki bani" ba musu ta sanya hannun,ta miqa bakinsa yayi bismillah
sannan ya soma amsa,kasa cewa komai yayi sai jinjina kai da yake a fakaice,wasa
wasa sai gashi yaci leda hudu,ya dubeta suka hada idanu sai suka qyalqyale da
dariya baki dayansu
"U r the best cooker apart from my mom da na sani" yabon yayi mata dadi qwarai,sai
ta jangi jug na tana tsiyaya masa lemon da tunda ta fara zubashi ya zuba masa
idanu,ta cika glasa cup ta kai bakinsa,ya kurba,sai ya cire yana duban cup din tare
da hadiya na bkinshi
"Kunun aya?" Kai ta gyada masa,dariya ta subuce masa,yayi qas da murya
"Kinsan barnar da yake min ko?,halan kin shirya gyarota" ido ta zaro don har ga
Allah batasan komai a kai ba,matsowa ya sake yi dab da ita,cikin kunnuwanta ya gaya
mata komai,kunya ta sanyata sunne kai,sai yayi relax jikin kujera yana dubanta
murmushi na fita a fuskarshi
"Can you remember our first night?,the day i start......." Sai ya kasa qarasawa
yana dariya
"Hamza......shi ya hadani da shi,ashe gata yayimin,ya zama silar shigata wata
sabuwar duniya mai qunshe da ababan mamaki da jin dadi masu tarin yawa,sai ta dire
cup din tana dariya idanunta a qasa,riqe hannun nata yayi caraf yana fadin
"Saikin qarasa bani ai,kin dandana min zuma a baki kuma ki janye,u r at my side
ai,nasan ba matsala ko?" Haka ta dinga zuba masa yana shanyewa,ya masa dadi qwarai
da gaske,cup biyu yasha qwarara sannan ya haqura jin yadda ya qoshi,ya jima baiji
qoshi a jikinsa irin hakan ba.

        Darene data kaishi wata duniya da bata taba kaishi ba,duk wani hanya data
sani da wadda ya koya mata wadda ke tafi da mutum sai data masa,abinda ya sake
sukurkutashi kenan,ya kuma sanyashi tafiya mai nisan gaske cikin kogin sonta.

        Suna idar da sallahr asuba ta dauke wayoyinshi baki daya ta kashe,taci


alwashin maida shi mutum mai cikakken lokacin kansa,tayi alqawarin rage masa jibgin
sabgogi da hidindimu da yake wuni yi,walau yana kano abuja america ko dubai,babu
hutu cikin lokutansa baki daya,tamkar kuwa ta sani yau qarfe goma na safiyar zaiyi
taro da dukka ma'aikatan asibitinsa dake abuja,sannan sunyi da hamza zasu je yaga
gonakin da suka siya domin fara noman auduga,wanda hakan zai sake habaka
kamfaninsu,tare da rage musu kudaden da suke kashewa wajen sayen zare da auduga
wajen wasu kamfanoni na waje,hakan kuma zai kuma samar da ayyuka ga matasan
qasarmu.

       Tana gaban mudubi tana qarasa daurin dankwalinta goma na safe sanda
almustapha ke kwance saman gado yana bacci nannade cikin bargo,cikin cikakkiyar
nutsuwa da kwanciyar hankali,knocking aka fara da qarfi tamkar an samu bangon
dakin,barin abinda take yi tayi tana tunanin waye?,sai ta dauki turarukanta ta fesa
sannan ta nufi qofar ta bude a hankali,su'ad ce a wani birkice,babu wannan
kwalliyar kwata kwata tattare da ita,neman hanya take kawai zata sanya kanta cikin
dakin,lura da haka ya sanya sumayya rage fadin qofar ta hanyar karo qofar ta riqeta
a hannu,sauran wajen da yayi ragowa kuma ta tsaya tana dubanta
"Anty su'ad lafiya kuwa?"kallo ta watsa mata mai siffar harara
"bake nake nema ba matsa kiban waje" murmushi ta saki cikin kwanciyar hankali da
nutsuwa
"Kin manta kin shardanta cewa kowa dan girkinsa ba ruwan miji da 'yar uwata?,ke
kika fadi hakan,amma kasancewar nasan akwai haqqinki rataye bisa wuyanshi bazan
hanashi ganinki ba,amma banda yanzun don Allah,don bacci yake,yana buqatar
isashshen hutu,amma idan ya tashi na gaya masa"
"Ke baki isa ki hanani ganinsa ba wallahi" ta fada a zafafe,sai kawai sumayya taja
baya ta kuma maida murfin qofar ta rufe.

        Baqinciki ya hanata aikata komai,sai kawai ta juya ta sauka tana laluben


wayarta ta nemi almustaphan kawai,saidai kash ta buga rashin sa'a tunda sumayya ta
jima da kashesu,batayi tsammanin ya farka fa,saidai tana waiwayowa suka hada ido da
shi,yana zaune daram yana kallonta,hannunsa ya bude mata fuskarshi a dan tsuke cike
da miskilanci,a nutse ta iso gareshi ta fada jikinsa a tausashe ya maida hannu ya
rufe
"Hausa girl" ya rada mata a kunneta,shigar atamfa tana mata kyau tana kuma
burgeshi,dalili da ya sanya take yawanyi itama kenan
"Meyw dalilin kashemin wayoyi,sannan aka qi tashina?,kina son na soma halin da ba
nawa ba karya alqawari?" Ya fada har yanzu tana jikinsa,kai ta girgiza
"You need some rest"
"I know,kuma nima bansan fitan,ya kamata ace idan nazo qasata ina hutawa sa
iyalaina kadai basai wani sabgar ya shigo cikin wadan nan lokutan ba,sai yanzu na
gane muhimmancin hakan.....amma duk da haka zanje meeting da ma'aikata a asibiti,so
ki shirya,zaki min rakiya?"kai ta gyada masa,sosai taji dadi,ko banza zata miqe
qafa,tunda tazo banda gidan anty dije bata je ko ina ba
"Ok,shirya min ruwan wanka"
"Jiranka ma yake" ta furta itama cikin salon rada,sai ya matseta cikin jikinsa
"Kina son hanamu fitan ma kenan baki daya ko?" Da sauri ta girgiza kai tana
dariya,don tasan me tayi masa
"Dagani to" ya fada yana dubanta,ta janye jikinta a hankali sannan ya miqe ya shige
toilet din.

        Tare suke saukowa baki dayansu,cikin shigar cikakkiyar bahaushiya


take,plain zani da riga fitted,tayi daurinta das biasa kanta,lullubinta har saman
ka,yayin da ya kasance shi kuma cikin yadin kufta da aka yiwa aiki irin na gidan
sarauta,cikin kayan da ya bayar ayi masa tun daga randa ya fahimcu ire iren shigar
na burgeshi,
"Wait" ya fadi yana nufar wajen su'ad,gefan kujera ta samu ta zauna tana
tsumayinsa.

       Fitowarta daga wanka kenan daure da towel,tana ta qamshin shower gel dinta
mai matuqar tsada da take amfani da shi duk din saboda tattalin fatarta,ranta a
quntace yayi sallama,ciki ciki ta amsa shima don tasan yadda suke qarewa da shi
idan bata amsa ba,abu na farko data fara shine qorafin taje wajensa sumayyan ta
mata rashin kunya,ta kira wayoyinshi kuma a kashe,bai ko tanka mata ba ya duba
ciwukan nata
"Suna zafi har yanzu?"kai ta girgiza tana tabe baki,ya qarasa bakin mudubinta ya
ajjiye mata kudi
"baka ce komai ba na maka magana but ka share" ita batasan bacin ran mutum bane?,a
nutse hannayensa cikin aljihunsa ya dawo inda take tsaye
"Bakisan abinda kika aikata jiya ba dai dai bane?"kafada ta daga
"to sai me,kishinka nake kuma dole na nuna"idanunshi ya zuba mata wanda ya sanyata
rusunar dole ta janye nata idanun,cikin bacin rai yace
"Wannan ba kishi bane hauka ne,kin dauki aqidar da ba taki ba kin yafawa
kanki?,daga ranki ya baci saiki hau yanka kanki koki yanka wasu?,zubar jini wannan
baki daukeshi a bakin komai ba?,zan miki warning na qarshe,kinyi na farko kinyi na
biyu,kada ki yarda ki sake na uku,if not zan dauki mataki a kanki,take note" ya
fadi yana juyawa ya fice a dakin,tabbas ba qaramin illa baqin al'adu ke mana ba da
yaranmu,sai yaji baki daya zaman wata qasar bashi da fa'ida karon farko a
rayuwarshi,ya tabbatar sanda suna zuwa islamiyya a america da su'ad bata yaye kanta
ta daina zuwa ba wasu halayen nata ba zasu ta'azzara har haka ba.

Wajen ummee suka fara biya,cikin farinciki ta tarbesu suka


gaidata,farinciki fal ranta,yau almustapha ne ya kusa dosar sati biyu a abuja bai
nemi komawa inda ya fito ba,wanda ta tabbatar da da ne da tuni ya koma din,a qalla
ma yayi kwanaki uku kacal,sallama suka yi mata ta rakasu da addu'a suka fice,suka
gaida anty mama sannan suka wuce,don baba ranar baya nan,sun fita shi da su mahmoud
angwaye.

         Kana ganin asibitin kasan nashi ne,baida maraba da na kano har tsarin
ginin,tun a hanya yake karbar gaisuwar ma'aikata manya da qanana,yana riqe da
hannunta har suka shiga babban office dinsa,ya mata mazauni kan daya daga cikin
kyawawan kujeru masu siffar duniya dake office din,baki daya ma'aikatan asibitin ba
wanda baisan da zuwanshi ba,hakan ya sanya kowa ke cikin taitayinsa,landline dake
office din yayi amfani da ita,aka tabbatar masa da cewa duk wanda ya dace yana
babban dakin taron dake asibitin suna jiranshi,ya ajjiye wayar yana dubanya,itama
shi take kallo,yanayin jagorancinsa na burgeta,yasan abinda yakeyi,komai nashi kan
doka da tsari yake
"Zanyi missing dinki na kusan two hours,ko zaki rakani muje muyi meeting din mu
dawo?" Hakanan taji tana sha'awar binsa,murmushi ta saki tana gyada masa kai,hakan
ya masa dadi,ba musu ya kama hannunta bayan ya dauki laptop dinshi da yake ajjiye
record na komai suka wuce.

       Cikin girmamawa ma'aikatan suka miqe baki dayansu,bai tsaya ko ina ba sai
kan babbar kujerar da take tashi ce shi daya,janyo mata ita baya yayi,ta dubeshi
sannan a hankali cikin nutsuwa ta zauna,daga kai yayi ya baiwa kowanne damar zama
kowa ya koma mazauninsa,laptop dinsa ya bude a gabanta ya kunnata,yana tsaye kan
sumayyan har komai ya daidata,wani cikin ma'aikatan ya miqe yana daukan kujerarsa
ya kai masa,hannu ya daga masa yayi qaramin murmushi yace ya barshi ya gode,tsaiwan
ma is ok,a hankali suka soma tattauna abinda ya tarasu,tsahon wasu mintuna,ya
waiwaya da niyyat soma shigar da abubuwan da yake buqata,a fakaice yake dubanta
cikin mamaki,tuni tayi misa wajen shigar masa da muhimman batutuwan,cikin qwareea
da nutsuwa,baisan ta iya sarrafa computer haka,saboda bai taba ganin ta taba masa
tashi ko ya ganta da ita ba,kawai sai ya dora hannunshi saman nata hannun dake kan
madannan computer din ya dan matsa a hankali alamun dariya,murmushi ta saki ba tare
data dago ba taci gaba da abinda take.
*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
.
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

9⃣3⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

*ya Allah ka sanya farinciki a zukatan musulmai,ya Allah ka wadatar da talakawan


cikinsu,ya Allah ka qosar da duk wanda ke cikin halin yunwa,ya Allah ka dawo da
matafiyanmu lafiya,ya Allah wanda bashi ya masa yawa ka biya masa,ya Allah ka
tufatar da wanda ke cikin tsiraici,ya Allah duk wanda ke da mummunan hali cikin
musulmi ka gyara mana halayyarsa,ya ubangiji dukka wanda yake cikin tsananin
baqinciki ka yaye masa*

*ya Allah*

*ka fada cikin qur'aninka mai girma*

*idan bayina suka tambayeka game da ni kace musu lallai ni makusanci ne*

*ya Allah*

*kai kayi umarni da mu roqeka(zaka amsa mana),ka kallafawa kanka amsawa(addu'ar


bayinka),ya ubangiji ka amsa mana,ka biya mana dukkanin buqatunmu,ka cika mana
burikanmu ya ARHAMAR RAHIMIN*
_____________________________________

         Ya jima zaune saman table din office din yana duba yadda ta shigar da
komai a tsare,wani abun ma da shi bai taba yunqurin dubashi ko shigar da shi
ba,murmushi ne keta fita a fuskarshi,ya dauke idanunshi sanda ta fito daga bandaki
bayan ta daura alwala zata tada sallah,da kallo yake binta,yana jin cewa ya samu
wata babbar kyauta ne daga Allah,cikin watanni Allah ya sauya rayuwarshi sauyin da
bai taba zaton akwaishi ba.

        Har ta sallame sallar yana zaune yana dubanta,sai ya miqe ganin ta gama
yana daukan hularshi wadda tun dazun yake cireta yana riqeta a hannu saboda rashin
sabo
"Lets go,muje muyi lunch" ya fada yana dubanta,ta shafa addu'an ta waiwayo,cikin
shagwaba tace
"Kashe kudi ko?,muna da komai a gida muje na dafa maka wani abun" kai ya girgiza
"Gida?,ba yanzu ba,ba yanzu zamu koma ba",bata sake tankawa ba juya ta janyo
jakarta ta bude,ta fidda qaramar hoda ta gyara fuskanta,ta ciro turarenta ta matsa
a hannunta ta goge jikinta da shi,yana daga tsaye qamshin ke dukanshi,sai ya tako
ya tsaya a bayanta,ya riqe hannunta dake riqe da turaren yakai hancinsa,lumshe
idanu yayi
"I love iy,ina son wannan qamshin" murmushi ta saka,ta maida turaren jaka suka jera
suka fito.

        Tafiya ta wasu mintuna suka qaraso qofar katafaren wajen cin abincin,wajen
cin abinci ne da kusan duk wanda ke garin yasan da zamansa,domin yana dacewa da duk
yanayin da kake so,kaman almustapha da baisom cin abincin cikin jama'a,yakan kama
waje na musamman wanda yake kaman VIP,saidai yana da tsada fiye da sauran
guraren,qofar shigar wajen ma na musamman ne kamar yadda kujeru da teburan wajen
suma suke na daban.

         Daya daga cikin ma'aikatan wajen ne ya qaraso cikin rawar jiki,don ya


tabbata yau sunyi babban kami,cikin girmamawa ya rusuna ya gaidashi,ya amsa sanda
ya miqa hannu yana amsar na'urar dake hannunshi ya soma duba abubuwan da yau suke
da shi,bayan ya zaba yawa can kitchen din sending na abinda yake buqata da number
sit dinsu kamar yadda tsarin wajen yake sai ya tura na'urar gabanta,dubanshi tayi
ya mata alama da idanu ta zabi abinda take so,maida idanuwanta tayi kai ba tare
data taba ba tana qarewa list din kallo,haka kawai taji babu abinda ya bata sha'awa
a ciki,hannunta yakai kan irin abinda yayi order itama ta dannan kawai ta daga
wayan da niyyar miqawa ma'aikacin,almustaphan yahi saurin karba daga hannunshi ya
miqa masa ya karba ya juya ya bar wajen,ya motsa bakinshi da niyyat cewa wani abu
wayarshi ta soma ringing,sai ya fasa fadin abinda zaya ce din ya soma laluban
wayarsa dake aljihun wandonshi duk da bai dauke idanunshi daga kanta ba,ta rasa
wane irin kallo ke wannan duk sa'ad da suke tare,duk yadda taso ga yawaiya dubanshi
idan suna tare ita kasawa take saboda nauyi da kunya,yana soma amsa wayar kamar
hadin baki tata wayar ta dauki ringing,ta cirota a jakarta tana dubawa,halima
amarya ce,murmushi ta saka cikin nutsuwa ta daga suka soma gaisawa,daga bisani ta
miqawa abdallah dake kusa da ita,aifa nan ya dinga zuba yana bata labarai kala
kala,harda labarin ya gama nursery one zai shiga nursery two,idanunta ta lumshe
tana tasbihi ga Allah,ba shakka shekara kwana,a yanzu a qalla abdallah ya tasamma
shekara biyar kenan,tun tana daurewa har ta biye masa ta dinga sakin qaramar
dariya,abdallah badai wayo ba,hatta cikin halima sai da yace cikin mummy ta zama
qato yace baby zata siyo mana sabuwa,sai data gaji sannan tace
"Baiwa mummyn to wayar,duka ka cinye mata credit" haliman ya miqawa sukayi
sallama,ta kashe ta soma qoqarin maida wayar jaka
"Ummu abdallah" taji ya ambata a tausashe,daga kanta tayi tana dubanshi,sai yanzu
ta lura,tunda ta fara wayan idanunshi na kanta,kunya ta dan kamata ta janye
idanunta,qasa qasa yayi da murya tare da matsowa dab da ita
"Ya kamata nima a bani nawa abdallah haka.....i need him tunda an hanani wannan
ko?" Kai ta sunne tana murmushi,ya bata kunya ba kadan ba salon yadda yayi
maganar,dai dai da isowar ma'aikata biyu dauke da abincin nasu,suka ajjiye gabansu
suka jiya suka wuce,ba bata lokaci ya warware spoon dake nannade ya sanya cikin
abincin ya soma ci a nutse kuma a yangance,itama cokalin ta sanya saidai ta kasa
kai koda loma daya bakinta,gaba daya abincin taji bai mata ba kuma,duk da yadda
yayi kyau tun a ido balle a kai baki,yana ankare da ita,naman dake gefan abincin ta
jawo ta cinyeshi tas,suna hada ido ta kau da kai,take kunya ta kamata,batasab me
yasa ta yin haka ba,hannu ya daga ya kira wani ma'aikacin wajen da yazo kawowa wasu
mata da miji da suka shigo yanzu wajen nasu order din
"Kuna da meat haka,gasashshe?" Cikin rusunawa yace
"Eh amma ranka ya dade ya qare saidai ko zata jira,amma akwai farfesun kayan ciki"
"Jeka kawo" ya fada yana yagar tissue ya gige bakinsa,komawa yayi ya jingina da
kujera yana dubanta,duk sai kunya ta dabaibayeta
"Nifa bana ci" ta fada a dake
"Bake dama nace a kawowa ba" ya bata amsa yana ci gaba da nazarinta,mintina qalilan
ya dawo dauke da bowl na tangaran mau kyau ya ajjiye sannan ya juya ya tafi
"Bude wannan bowl din ki dauka kici,bance kuma kice wani abu ba" ya qarashe
maganarsa yana jan wayarshi yana dannawa cokalin ta ajjiye ta jawo bowl din ta
bude,habawa wani yawu ta hadiya kaman mayya,farfesun kayan ciki ne hanta tumbi qoda
sai zuciya,ajjiye murfin tayi ta saka cokali ta soma kaiwa baka,wani dadi ya
ratsata,kaman ta dauka ta juye a cikinta ta huta da tauna haka ta dinga ji,ci kawai
take ba kama hannun yaro,bata ankara ba sai ganim kwanon tayi babu komai saura
romo,sai a sannan ta tuna da wanda ke gabanta,ta daga kai kamar munafuka ta saci
kallonsa qasa qasa,ita kuwa yake kallo,mamakin yadda take cin abinci haka yau a
gabanshi a sake yake yi,yayin da ita kuma take zaton naman da yaga tana ci ne,sai
ta bata fuska ta janyo tissue din itama tana goge bakinta,kanshi ya dauke yana
murmushi qasan ranshi
"Wai itama lallai bata son raini" ya fada a zuciyarshi yana miqewa,ma'aikacin ne ya
sake dawowa,almustapha ya miqa masa atm card dinshi yace su cira kudinsu su kawo
masa card din mota.

        Sallaman drivan yayi ya amshi muqullin motar,da kanshi yake tuqasu,motar


shiru sai sanyin a.c dake ratsa jikkinansu,hakan yayi tasiri wajen haifar mata da
kasala,kafin kace wani abu bacci yayi awon gaba da ita,cikin mamaki ya taba
qirjinta,ya akayi bacci ya dauketa haka da wuri?yake tambayar kansa,ya dan tabata
kadan ta bude idanunta wadanda suka dan qara girma saboda baccin da ya dauketa
"In daukeki ne?" Ya fada yana daga mata gira,kafada ta noqe kamar yarinya,sannan
cikin kasala ta zuro qafafunta waje ta fito bayan ya zagaya da kanshi ya bude mata
qofar,kallon gidan ta dinga yi kamar waccan karon,gidan da suka taba zuwa
ne,murmushu ta saka qasan zuciyarta,gidan yana burgeta sosai,a haka suka dinga
takawa har suka qarasa ciki,wayoyinshu ya zube ya kutsa bedroom din ya bude ya
shiga da niyyar rage kayan jikinsa,zamewa tayi saman kujerar wani bacci mai dadi na
sake kwasarta.

        Tsayawa yayi cikin mamaki yana dubanta,daga shiganshi zuwa fitowarsa har ta
sake wani baccin?,sai ya koma shima daya daga cikin kujerun ya dauki system dinsa
ya fara aikin dake gabanshi.

         Tsahon awa guda yana tsaka da aikinsa yaga miqewarta zumbur kamar wadda
aka tsirawa allura,a gigice take neman hanyan toilet saidai ta rasa,kafin ta sake
wani yunquri aman da take dannewa ya kubce mata,cikin wani irin zafin nama ya
tareta sanda ta soma yunquri mai qarfi wanda yaso zubar da ita a wajen,yana riqe da
ita har ta kammala aman baki daya,duk wani anu data ci daga safiyar yau zuwa dazun
yafita baki daya daga cikinta
"Kai na" ta fada tana dafe da goshinta saboda yadda yake sara mata kamar zai rabe
biyu,sai da ya bata ruwa ta kuskure bakinta sannan ya riqeta har zuwa bedroom din
ya zaunar da ita gefan gado,bata iya zaunawa ba sai ta sulale ta kwanta,wayarshi ya
ciro ya sanarwa ma'aikatan su shigo su gyara wajen ya ajjiyeta cike da damuwa ya
tako inda take,gabanta ya durqusa ya riqe hannunta cikin nashi
"Me ya sameki haka?,daman baki da lafiya amma baki gayan ba?" Kai ta girgiza
"Meke miki ciwo?"
"Kaina.....da......" Sau ta kasa qarasawa duk da yadda mararta ke mutstsukarta
"Uhmmm,dame?" Ya fada yana miqewa ya dawo kusa da ita
"Marata.....Cikina" a hankali ya sakera ya miqe,kai tsaye dakin da ya ware cikin
gidan tamkar qaramin asibiti na gidan ya nufa,ya duba magungunan ciwon ciki da na
ciwon kai ya kawo mata,sai da ya tabbatar ta sha sannan ya umarceta ta kwanta,yana
zaune gefanta hannunshi saman goshinta,addu'a yake tofa mata lokaci bayan lokaci
haf wani bacci yazo ya fauceta.

         Tun yana duba agogo har ya haqura ya daina,yana ganin tilas su kwana cikin
gidan don bazai iya tashin ta ba,da qyar ta tashi tayi la'asar da magariba ta koma
ta sake kwanciya,wayarsa ya ciro ya lalubi lambobin su'ad,ringig biyu ta daga
"Ina ka tafi almustapha,wai me yasa baka ganin qimata ne?,bani da lafiya amma ka
dauki matarka ku bar gidan tun safe har dare baka damu da halin da nake ciki ba?"
Ta fada tana niyyar sakin kuka
"Yanzun ma ba yau zan dawo ba,ina tunanin sai gobe,kada ki damu din baki ga
shigowata ba ki rufe sashen kiyi kwanciyarki" bau tsaya jin me zata fada ba ya
katse,don ya tabbata bacin rai kawai kunnuwansa zasu jiye masa,kiran hamza ne ya
shigo ta daya wayar tashi ya daga yana karawa a kunnensa
"Ya zamuyi haka dakai fisabilillahi ka ajjiyemu muna jiranka?" Banza yayi dashi
kamar ba da shi yake magana ba,sai da ya mula don kansa yace
"Kada ka saka min ciwon kai malam,matar gidan tace bata buqatar naje wani guri so
kowa ma dole ya haqura da ganina"
"Wace?,wai su'ad?" Ya tambaha cikin tantama,don dai itakam yasan haka bata taba
faruwa ba,kuma bata isa hana almustapha ficewa ba duk sanda yaso
"Shafa kaji" ya amsa masa cikin gatse,tuni hamza ya hasaso wace ce,dadi ya
lullubeshi ya dinga tuntsira dariya,amma don tsiya sai yace
"Wooo mutumina,yaushe mata suka fara juya akalarka?"
"Kasan dai halina ko hamza,zan iya biyoka har gida wallahi naci maka dama ba yau
muka soma ba" bai damu ba yaci gaba da kwasarsa har sai da ya katse wayar,texs ya
dinga jero masa kan ya daga suyi maganar ya daina tsokanar,da qyar yaciyo kansa ya
daga suka shiga maganar da zasuyin,tuni su hamzan sunje sunga guraren sunyi,zasuyi
kyau da noman audug,an gama shurya komai ma kawai ma'aikata za'a samu shikenan a
shiga aiki.

        A hankali ta motsa tana bude idanunta,baki daya a yanzu wasai take ji bata
jin komai,idanunsa a kanta yayi mata sannu,shi ya taimaka mata ta miqe duk sa bata
jin komai
"Kiyi wanka sannan kici abinci,me zaki ci?"dan shiru tayi sannan a hankali kamar
mai tsoron fada tace
"nama"
"Irin na dazu?"kai ta gyada masa,miqewa yayi ya fice falo din bada oder ita kuma ta
shige bandaki,a gaba ya sanyata bayan ta fito wanka ta shirya cikin kayan
bacci,tana cin naman yana kallonta suna zaune a dandagaryar,dukkan alamu sun nuna
tana jin dadinshi sosai,sai data kammala tace
" ba gida zamu wuce ba?"kai ta kada
"Noo,a nan zamu kwana,baki jin dadi sosai har yanzu ko baki fada ba na sani" kai ta
mirgina,don bata son su kwana din hakan ya dasa wani abu a zuciyar su'ad
"Am feeling better,zamu iya tafiya"
"Am not feeling better ni kuma...." Ya fada yana jifanta da wani kallo hannunsa
nade a qirji,hannunshi ya miqa ya jawota,ya ware qafafunshi ya sanyata a tsakiya
habarshi saman kafadarta saitin kunnenta,cikin yin qasa da murya yace
"Tunda muka zo gidan nan babu abinda kika bani ko qwaqwqwaran kiss ban samu ba,sai
amai sai bacci.....you know gidan nan na love ne,shi yasa na kawoki.....me zan samu
ne?" Kunyarshi ta kamata,ta sake kafewa a qirjinsa kanta na qasa
"Wai ma na tambayeki......meke damunki?"
"Dazu ciwon kai ne,amma yanzun ba komai"
"Haka akeso......zan samu wani abun to?" Ya fada yana juyo da ita suna fuskantar
juna,idanunta ta saka a nashi,sai ya kashe mata ido yana sake tausa murya
"Pleeeeaaaase......ko kadan ne" a kunyace ta daga masa kai,ya miqe da hanzari yana
dariya tare da dagata suka wuce babbar headquater.

*****   ******   *****    ******

      
      A safiyar ranar yana tsaye yana shiryawa gaban mirrow,yayin da itama taje
tsaye gabanshi suna fuskantar juna,sanye take da da wata gown mai dogon hannu,wadda
tsahonta bai qarasa idon sahu ba,mai roba ce rigar saboda haka tayi cif a jikinta
tare da fitar da duk wani tudu na jikinta,baqa ce sai touches na fari,ta yane kanta
da wani farin dan kwali mai tsaho don bai kai mizanin mayafi ba,sabuwa ce batasan
da itaba cikin gidan da safen ya dauko ya bareta ya bata yace ta sanya tunda basu
zo da shirin kwana ba,hannunta dauke da suit dinshi mai three pieces,neck tie,vest
da safarshi,tana miqa masa da dai dai yana amsa yana sanya kowanne a muhallinsa a
jikinsa,kusan hakan ta sabar masa,ita ke kiqa masa komai shi kuma yana
shiryawa,babu magana tsakaninsu saidai salon kallon da kowanne kewa dan uwansa yana
sadar da saqo kai tsaye zuwa gareshi ba tare da ya magantu ba,wani yare suka dinga
amfani da shi a tsakaninsu dake wanzuwa tsakanin zuciya da zuciya,lokaci lokaci
zaga daya daga cikinsu ya saki murmushi,a haka har ya kammala komai tsaf,yayi kyau
cikin black nd white suit,ya kammala sanya safanshi ya dago,sai ya janyota jikinsa
cikin ba zata,ta baya ya rungumeta ya dora hannayenshi a qugunta,sam taga ma kaman
bai da niyyan maidata gida a yau din,a hankali ya ware tafin hannunshi ya soma
shafo har saman damammen cikinta,sau da yawa yana mamakin yadda wai a haka har ta
haihu amma har yau cikinta a dame yake,darensu na jiya kawai yake tunowa,irin
jarumtar data nuna,shi kansa sai da yaji cewa kada ya cutar da ita fa
"Yau zamu wuce gida ko?" Kai ya girgiza
"Ba yau ba,saikin warke" narkewa tayi tare da rage fara'ar fuskarta duk da bai iya
gajin fuskar baki daya sai gefanta
"Amman anty su'ad fa yau girkinta ne"
"I know babe,think dai sai magariba sannan aka shiga time dinta ko?,so sai na dawo
tukunna,zan fita just one hour zan dawo,ya kamata na dinga hutawa hakanan" shiru ta
danyi na wani lokaci
"kin gaji da ni kenan ko?gwara mu koma gida?"baki ta bude tare da waiwayowa tana
dubanshi,kai ta girgiza alaman a'ah,sai ya saki qaramin murmushi wanda ya sanyata
sake juya masa baya itama tana dariya qasa qasa,mamaki wani lokaci yake bata,wai
wannan almustaphan ne ya koma haka?
"Me ya saki ciwon mara ne jiya?ina fatan ba irin na wancan karon bane"ya sauya
akalar maganar
"Nima ban sani ba" ta fada a shagwabe,sai ya sanya hannunshi saman mararta ya danna
"Wash" ta fada saboda dan zafin da ta ji,cikin hanzari ya juyo da ita suna
fuskantar juna,idanunsa cikin nata a rikice yace
"Yaushe rabonki da al'ada?" Idanunta ta juya alamun tunani,idan zata iya tunawa tun
sanda ya daukota ya taho da ita daga kano ba tare data shirya ba,idanu ya zuba mata
yana ci gaba da kallonta,sai kuma ya kama tafin hannunta yana kalla kamar mai neman
wani abu,wani irin riqo yayi mata
"Please when last kika ga period dinki....tell me" sai ta tsorata ta fara zaro
idanu ganin yadda ya rude lokaci daya,cikin rawar murya tace
"Tun.....tun sanda muka taho daga kano....sanda nayi ciwon mara" riqeta yayi ya
ajjiyeta bakin gado,binsa tayi da kallo sanda ya juya ya fice,dakin nan mai kama da
qaramin clinic ya shiga,ya dauko syringe ya dawo ya sameta zaune,yana daga tsaye ya
farke,idanu ta fiddo,idan akwai abinda ta tsana a duniya allura ce,rabinta da ita
kuwa tun haihuwar abdallah,qarasowa gabanta yayi ua duqa,ya riqe hannunta ya janye
hannun rigan yana duban cikin idanunta,tayi wani kicin kicin,qwalla kwance can
qasan idanunta,ya gama fuskanta sarai tsoron allura take,sai ya basar ya daura
farar robar da zata bashi daman ganin jijiya,ta runtse ido sanda allurar ta
ratsata,ya zuqi iya jinin da yake so sannan ya warware mata robar ya zare syringe
din ya miqe
"Ina zuwa" ya fada yana nannade syringe din da tushu ya fice da sassarfa,binsa tayi
da kallo sai da ya fice sannan ta janye idanunta,da baya ta koma ta kwanta cikin
ranta tana tunanin me zaiyi da jininta kuma?,sai tsoro ya dinga shigarta,kada dai
ace wata cutar ya gano a jikinta,gabanta ya fadi,sai ta gaza kwanciyar ta zauna
daram samam gadon tana ambatar sunan Allah
"Ya ilahi,kada dai a ce har yau ban gama bitar SHAFUKAN KUNDIN QADDARA TA BA" ta
ambata a ranta hawaye na qwace mata tsoro na dabaibayeta,yanzu ina zata saka ranta
ina ta nufa idan wani abu ya hango tattare da ita?,ta ina zata soma rayuwa bayan
tuni ya riga data haqiqance wani qaqqarfan abu wanda idan har akwai abinda yafi so
qarfi to ba shakka ya kama zuciyarta dangane da shi,ya riga da ya dasa shaquwa
qauna shauqi da bege mai zurfi fadi da girma cikim qirjinta,tsoka da jininta
"Ya rabbi ka kula da ni" ta fada wata qwallar na bin wata.
*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽

✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

9⃣4⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

*Allah madaukakin sarkin yana cewa*

*CENE DA SU HARAM DA HALAL BAZAI DAIDAI BA,KODA KUWA YAWAN HARAM DIN NAN YA QAYATAR
DA KAI(KO YA BAKA MAMAKI),KUJI TSORON ALLAH YA MA'ABOTA HANKULA DON KU RABAUTA*
_______________________________________

        Tamkar wanda aka jefo haka ya shigo dakin,hantar cikin sumayya ta kada,sai
ta sake qudundunewa a zaune ta cusa kanta tsakanin cinyarta,muryarsa taji saman
kanta cikin wani irin amo
"A ina kika samo wannan cutar,ba dake nake ba" tsananin rudewa ya sanyata daga kai
ba tare data shirya ba,abun mamaki fuskarsa wani annuri take fitarwa,kafin ta kai
ga yunqurin komai ua sureta baki daya ko nauyinta baiji ya soma juyi da
ita,qanqameshi tayi sosai hawaye na zirya saman kumatunta,batasan me take ji ba
cikim zuciyarta zuwa yanzu,ciki?,ciki kums ita din?,tayi zatombdaga abdallah ta
gama,shin da yaya ma aka samu abdallah?,ciki jin abun take tamkar almara,a hankali
ya direta saman kujera ya duqa bisa gwiwoyinshi baki daya,hannunsa ya sanya cikin
nata tafin hannun yana matsawa,sai motsa bakinsa yake amma ya rasa kalmar da zai
furta,ita din ma shi take kallo,tunda suke zata iya rantsewa bata taba ganin annuri
saman fuskanshi kaman haka ba
"I dont know me zan fada,ummu abdallah......pls idan mafarki nake taimakeni ki tada
ni,i cant blieve it" sai ya kasa zama ya miqe daga durquson da yayi,ya kama
hannunta tsam ya miqar da ita,bai tsaya ko ina da ita ba sai clinic din cikin
gidan,ya hau nuna mata gwajin da yayi,itakam ba abinda ta gane tunda ba bangarenta
bane,jin tayi shiru sai ya daga ta baki daya ya aza saman gadon scanning,ya kunna
na'ura ya daidaitata sannan ya janye rigar dake jikinta ya dora na'uarar bayan ya
zuba cream saman cikinta
"Ya salam.....ya salamm....oh my god..." Abinda ya dinga maimaitawa kenan yana ci
gaba da yawo da na'urar saman mararta yana kallon allon scanning din,cikin wani
irin sanyi ya gyaara mata rigar bayan ta dagata ta zauna sosai,ga mamakinta hawaye
ne fal idanunshi,ya Allah wanne irin so yakewa haihuwa haka?,tamkar yaji abinda
take rayawa a ranta ya soma girgiza kai
"Bansan ina son haihuwa har haka ba sai a yanzu,da gaske ne nima ashe zan iya zama
uba?,zan iya ganin jinina?" Tamkar ita yakewa tambayar da ita kanta bata da
amsarta,hannunshi ya dora saman mararta
"Alhamdulillahil lazi bi ni'imatihi tatimmus salihat" ya furta hadi da fitar da
nannauyan ajiyar zuciya,har a lokacin juya lamarin take cikin mamaki
"Ki tambayi duk abinda kike so a duniya zan mallaka miki shi matuqar mallakata ne
please,ki roqeni ina son ko yaya ne na faranta miki nima..."ya fada yaba matsa
yatsun hannunta
"Baki ce komai ba ummu abdallah....ko baki murna....ko ba zaki iya ba kaman yadda
kika taba gayan a dubai?" Da hanzqri ta girgiza kai
"Bana son komai,kawai ki riqe amanata,kada ka wukaqanta ni,sannan nima bani ke
badawa ba ai Allah ne ya baka"
"Ya bani ko ya bamu?....kada dai kice min har yau babu wani matsayi da na taka
cikin zuciyarki?" Murmushi ta saki,sai ya sake matsowa tare da yin dan tsalle ya
haye shima gadon,duka hannuwanshi ya sanya ya kamo fuskarta
"Tell me wanne matsayi ke gareni?.....bana son baby na yazo duniya ya fuskanci
babanshi is nothing" so take ta qwace fuskarta saboda yadda yake azawa qirjinta
nauyi da yawa amma ya qiya,sai ya koma magana da gaske
"Am seriouse madam,am not even hear you kina fadin i love you,baki taba fada
ba,why?"
"Ba komai" ta fada a sanyaye
"Bakya sona?" Ya sake tambayarta,shuru ta masa zuciyanta na bugawa,wannan tambayar
titsiye ce kawai,ta yaya zaiyi wannan maganar
"Sumayya!" Ya kira sunanta karon farko a rayuwarsu cikin wani irin taushi wanda ya
tilastata daga kai ta dubeshi
"Bana soyayya da wasa kowa ya sanni,idan nace ina son abu zan tabbatar da hakan har
daukewar numfashina bana canzawa,sonki na tabbatar bai shiga rayuwata don ya tafi
ba,na fara sonki a lokacin da ni kaina ban sanshi ba......kin shigo rayuwata da
tarin alkhairan da banga kamarsu ba..." Shiru yayi yana maida numfashi sannan ya
dora
"Gaya min kina sona indai kina son naci gaba da rayuwa" kunya ta kamata,tana
yunqurin kau da kanta ya sake tallafe fuskar
"Nooo,a yau a wannan muhallin bana buqatar kunyarki.....ki gayan abinda nakeso
naji"
"I....love...you" ta fada ararrabe cikin muryar rada,idonshi ya lumshe kalmomin na
ratsashi tamkar ranar aka soma gaya mishi su
"Basu gamsar da ni ba.....please.....i need more"kafeshi tayi da idanu sanda nashi
idon ke lumshe,tana jin yadda wani feeling da so mai zafi ke ratsa jininta,qaunarsa
na fusgarta da wani irin qarfi
"ina sonka da dukkan zuciya ruhi da gangar jikina.....ban taba jin so irin wannan
ba a duniyata sai wannan karon,na tabbata kai na dabanne shi yasa Allah ya
jarrabeni da qaunarka.....ina sonka baki dayanka bawai wani abu da ka mallaka
ba....kai din dai zallarka kai nake......." Idanunshi da ya bude tar tsakiyar nata
shi yasa ta gaza qarasa furta abinda take son fada,zallar soyayyar da take gani a
qwayar idanunsa kadai ta isa sake narkar da masoyi
"Wani irin zazzafan so nake miki ummu abdallah....taba qirjina kiji yadda ya sauya
bugu daga jin kalamanki" ya kama hannunta yana mannawa a qirjinsa saitin
zuciyarsa,ba shakka bugunta ya sauya,da mamaki take dubanshi,da gaskene mutane masu
tsananin miskilanci da rashin lura da sabgar wasu,yawan shiru basu iya fadawa
tafkin soyayya ba?,ta tabbatar da cewa irin son da take gani cikin qwayar idonsa da
wanda yake furta mata ba irin nata bane,jikinsa ya janyota yana sakin qatuwar
ajiyar zuciya
"Na gamsu da kalamanki matata,uwar 'ya'yana da yardar Allah" kusan awa guda suka
bata cikin dakin suna jaddada kalaman soyayya tsakaninsu,wanda wani abun
almustaphan bai taba tunanin shi kanshi zai iya faruwa ba tsakaninsu,kusan ya samu
yadda yake so,irin soyayya da kulawar da yake muradi.

      Maganar fitarshi tasha ruwa,ya lalace wajen sumayyan,abun har dariya ya dinga
bata,ya kasa ya tsare,data motsa ya hau tambayarta,nama ya sanya an kawo mata shi
kala kala ya kusa kala biyar,soyayye,gasashshe,farfesu,mai romo duka ita daya,taci
kuwa ta more son ranta,gaba ya sanyata yana kallo abinsa yadda naman ke mata dadi
kamar mai shan zuma,itakam sam ko a jikinta har mamakin hakan ta dinga yi,yadda
take abinta gaba gadi.

Sai bayan sallar la'asar sannan suka shirya,tayi kyau abinta cikin
lafaya,duk inda ta gifta binta yake da kallo,wani kyau na musamman ta qara,suna
hanya kafin su qarasa ya sake tambayarta me take so?,kai ta kada alamun babu
komai,qarfe biyar da rabi suka isa gidan,tun a mota naman taji yana mata suya a
qirji tare da taso mata,hakan ya sanya bata jirashi ba tayi gaba zuwa bangarensu.

Jiri ne ya dinga dibanta,ta dinga takawa a hankali har ta kai cikin


falon,zubewa tayi kan daya daga cikin kujerun ba tare da ta iya qarasawa ciki
ba,aman dake taso mata ya soma galabaitar da ita,hakan ya sanya sam bata lura da
su'ad dake hakimce kan daya daga cikin kujerun ba,ta tsuke cikin riga da
wando,plate ne a hannunta mai dauke da yankakkiyar apple tana jefawa
bakinta,sumayyan ta yunqura da niyyar tashi ta qarasa ciki take aman ya balle
mata,cikin hanzari su'ad ta miqe taba jefa mata kallon banza cike da
qyanqyami,durqushewa tayi a nan tana ci gaba da kwarashi
"Wannan wanne irin iskancin banza ne da wofi,banda tsabagen wulaqanci ki rasa wajen
amai sai da kika zo gabana ina zaune ina hutawa?"ta fadi tana nazarin sumayyan
sosai,tunanu ya darsu a ranta,taci gaba da dubanta tana yatsine fuska,sam bata damu
da itaba bare ta fahimci me take cewa ko take yi,ta kanta take,dai dai lokacin da
almustapha ya qaraso,wani kallo ya watsawa su'ad,tunda ya shigo ya cimmata tsaye ko
kusa da wajen bata dosa ba,ya san halinta sarai sai ya dauke kanshi,cikin hanzari
ya iso gabanta ya durqushe yana riqe da ita saboda yadda take yunquri mai
wahalarwa,sai data amayar da dukkan naman data ci,sannu kawai yake jera mata,ya
miqe da kanshi ya ciro ruwa ya bata ta kuskure bakinta tana maida numfashi,kamata
yayi ya zaunar da ita saman kujera ya amshi maqullan dakinta da niyyar bude mata
tukunna kafin ta tashi ta isa ga dakin.

Duk da yadda take a galabaice amma sai data daga kai ta dubi su'ad sanda ta
sheqe da wata shaqiyyar dariya
"Su ciki manya,oh Allah ya rufamin asiri,wallahi yarinya kin tashi a aiki,sai yanzu
zaki san baki da wayau" dariya ta sake saki
"Allah ta inganta" ta fada farinciki fal ranta,hango yadda komai zaizo qarshe
tsakanin sumayyan da almustapha cikin sauqi,mutum ne shi mai bala'in tsantsami,ta
tabbatar bazai iya daurewa qazantar laulayi ba sam,itakam wanne tsautsayi ne zai
aiketa daukan ciki?,ai gwara da tayi mai dungurun gum haihuwa da damuna,ta raba
kanta da haihuwar rabuwa ta har abada,yanzun irin wadan nan wahalhalun ina zata iya
da su tana tsaka da morewa duniyarta,rangaji taci gaba da yi murmushi na fita a
fuskarta
"Hahaha.....zamu ga ya zata kaya kuma,sannunki da kayan nauyi" lumshe idanunta tayi
tana sauke numfashi a hankali,bata da lokacin sauraren shirmenta sam,don ra
fuskanci akwai wani abu da take son gaya mata wanda ta tabbatar ba zayayi amfani
gareta ba,koma ace baki day bai shafeta ba,dawowa ya sake yi cikin falon,gabanta ya
qaraso,ya sunkuyo inda take jingine da kujerar yana duban qwayar idanunta,cikin
taushi yace
"Sannu babe......" Kai ta gyada tana lumshe idanu sannan ta bude
"Zaki iya tashi?" Langabe kai tayi
"Saidai ka dagani"kusan da biyu ta fadi hakan saboda su'ad dake tsaye ta zuba musu
idanu,zuciyarta kamar ta tsinke
"Daukarki ma zanyi cancankat" ya fada yana gyara hannun suit dinshi murmushi na
fita a fuskarshi
"Meye hakan almustapha?"waiwayowa yayi yana barin gyara hanunshi da yake ya zuba
mata ido
"amman dai kasan cewa ranar girki na ce ko?,bai kamata ace kana tabata ba"hannunshi
duka biyu ya riqe qugunshi
"Zoki taimaka mata ta tashi" ya fada a dake,ranshi a bace yake yana qoqarin dannewa
ke kawai,tunda ya tafi tsakamin jiua da yau babu wanda ta shiga ta gaisar a cikin
mutanen gidan,sannan yana jin sautin dariyarta bayan shigarsa daki,saidai bai ji me
take fadi ba,fuska ta bata
"Gaskiya bazan iya ba,ta gama aman yanzun sannan na tabata?....a'ah gaskiya" ta
fada tana kada kai,juyawa yayi ba tare da ya sake dubarta ba ya daga sumayyan cak
ya wuce da ita,binsa tayi a zabure ranta a bace,cikin tsantsar mamakin yadda ya
taba jikinta babu wannan qyamar bare qyanqyamin,me yake nufi kenan?ya shirya ci
mata fuska ne?,sai kuma ta dakata a bakin qofar dakin saboda tuna wani abu da tayi.

Gyara mata kwanciya yayi ya rage mata kayan jikinta sannan ya sumbaceta a
goshi
"Ki kwanta ki huta,banson ko qwaqwqwarar magana ki sake yi,zan kawo miki maganin
tsaida amai.....zanje nayi wanka yanzun"
"Na gode" ta furta a tausashe,murmushi ya saki yana shafa saman kanta,ji yake
tamkar ya maidata jikinsa su koma abu daya
"Shshshshsh......nine da godiya,kin manta cewa babban gift kika bani wanda ba wanda
ya taba bani kwatankwacinshi?"murmushi ta sake masa,ya sake sumbatar labbanta masu
taushi dake burgeshi sannan ya soma takawa da baya da baya ya fice,ido ta rufe
bayan fitarshin,tabbas so shike iya juya mutum ya sauya masa halayya komai girma
isa da qasaitarsa.

Saura kadan yaci karo da ita sanda yake fita don bai tsammaceta a wajen
ba,dauke idonshi yayi yayi gaba tabiyoshi a baya tana sauri don ta cimmasa,daidai
sanda daya daga cikin ma'aikatan dake shirya abincin dare a kitchen ta fiti,da
hanzari ta koma da baya zata koma kitchen din ganin tahowar almustaphan
"ki qarasa bakin qofan can ki gyara wajen ya baci da amai"
"To yallabai" ta furta kanta. aqasa cikin ladabi
"Amma girki take mana,ya za'ayi ta je ta taba qazan......"harara ya watsa mata
wadda ta hanata qarasa fadin abinda take da niyyar fada,yayi gaba ta sake bin
bayansa.

Yana tsaye yana ragw kayan jikinsa yayin da take tsaye bayanshi tana
lissafo qorafe qorafanta daya bayan daya,tie dinshi ya cire ya wurgar saman
gadon,cikin zafin nama ya fincikota sandan take tsaye bayanshi ya zaunar da ita
bakin gadon da yake tsaye,ba waramin tsorata tayi ba da ganin yanayinshi,cikin
kakkausar murya ya soma magana
"Wace irin macace ke da bakisan komai ba sai qorafi da tashin hankali?,wace iriyar
macace ke da komai na mijinki bai dameki ba,lalurarki da buqatar ki itace gaba akan
ta kowa,a haka kike so na kyautata miki?, ahaka kike so naji dadin zama da
ke,bakisan komai nawa ba,bakisan duk wani abu da ya shafeni ba,na dauka laifi nane
da fari na zaunar dake na karanta miki komai da yadda nakeson komai ya zama amma a
banza,shin wai sai yaushe zaki sauya ne?,sai yaushe?,dame na rageki da shi na dukka
haqqinki da Allah ya dora min?me kike so nayi miki?"ya qarashe maganar yana jin
zafi har cikin zuciyarshi,idanu ta zuba masa tana dubanshi,idanunsa ya lumshe yana
komawa da baya ya zauna,qoqarin cooling temper dinsa yake,baiso wani abu ya bata
zallar farincikin da yake ciki a yau.

Kuyi manage da wannan,ba lallai gobe wani ya samu banyi alqawari ba,naso yau na
barshi sai gobe na hada na turo muku mai yawa amma nasan zaku fison a baku ko kadan
ne.
*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

9⃣5⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

*LA HAULA WALA QUWWATA ILLA BILLAHIL ALIYYUL AZIM*


___________________________________

      Zuba masa ido kawai tayi tana jin wani zallar bacin rai na ratsata,hawaye na
bin kuncinta,ji take a duniya ya gama tozar tata,ya gama wulaqantata,a dacan ba
haka ai ta sanshi ba,ta ina zata fara debo irin rayuwar da yake da muradi,sam ko
daya ita ba zata iya ba
"Yanzu na sake tabbatarwa cewa baka qaunata almustapha,kanka tsaye kake gayan wadan
nan maganganun?" Ta furta tana nuna qirjinta da yatsa,a nutse ya daga idanunshi ya
zuba mata su,wato wanda yayi nisa baijin kira,barin hali sai mutuwa?,duk yadda ya
kai ga dorata a hanya kenan qaryarshi ta sha qarya,bazata taba fahimta ba,ya
fuskanci duk abinda yake gaya mata ashe bata bakinsa yake,kwanaki biyun da yayi
dakinta ya bata lokuta sosai yana nusasheshe da ita abubuwa da dama,ta kuma kwantar
da kai ta nuna tana dauka,ashe duka busa yake mata cikin kunnuwanta ba magana ba.

        Tsam kawai ya miqe ya ci gaba da rage kayan jikinshin,ya daura towel ya


shiga toilet,yana tsaye riqe da qugunshi yana tarawa kanshi ruwan wanka ta turo
qofat,hankalinshi kaf bai wajen,ya kasu gida biyu,wani na wajen sumayya yana
tunanin tayi bacci kuwa?,yayin da daya ke kai kawo kan halaye da dabi'un su'ad
"Kana nufin kai maisheni banza da baka da lokacinta kenan?,amma ita waccar ai kana
da nata lokacin ko?,har kana iya kamata bayan qazantar data futar,wanda iyakar
sanina da kai kana da qyanqyamin da bansan lokacin daka zama haka ba" shiru yayi
mata baice mata kanzil ba,iya tsahin rayuwarshi mutum ne da baya son
hayaniya,tubewa yayi ya shige bathtube abinshi ya barta tsaye,sai ta fashe da kukan
baqinciki ta juya ta fice zuwa uwar dakin.

          A nutse yayi wankanshi,ranshi na sake fari da haske a duk sanda ya tuna


cewa nan da wasu watanni shima zai zama baba,nan da wasu watanni zai dinga gajin
gilmawar yaro ko yarinua cikin gidanshi,yaron da za'a kirashi da
d'anshi,mallakinshi,jininshi,murmushin farinciki ne ya subuce masa sannan ya miqe
ya fito.

        Kwance rub da ciki ya tadda ta tana rusgar kuka,ya bude ma'ajiyar kayanshi
ya fitar da shirt da trouser ya sanya,ya shirya tsaf abinshi ya fice ya sauka
qasa,dining ya wuce yayi serving kanshi yaci abinci ya qoshi sannan ya wuce zuwa
sashen ummee.

         A kwance ya taddata tana kallon news a al-akhbar,sallamarshi ta sanyata


miqewa ta zauna tana amsawa,suna ranta shi da sunayyan tun jiya da bataji motsim
daya daga cikinsu ba,ya qaraso wajenta fuskarshi dauke da murmushi ya zauna gefanta
suka soma gaisawa
"Ya sumayyan take?"ummin ta tambayeshi ba tare data tambayi su'ad ba,rabonta data
shigo ta gaidasu tun shekaran jiya da suka shigo tare da shi,amma ita hakan ba
damuwarta bace tunda dama ba zamansu take ba zaman mijinta take,indai kuma suna
zaune lafiya lau to da sauqi
"Lafiya.....na barota tana bacci"
"To masha Allah" hira suka shiga yi irin ta da da uwa,cikin daqiqu kadan ta
fuskanci yaron nata na cikin farinciki da annashuwa qwarai,sai ta danganta hakan da
cewa tsantsar farinciki kulawa da walwalar da yake samu ne daga wajen abokiyar
zamanshi,ya jima gurin ummeen sosai sunyi hirar da suka jima basuyi irinta ba,bai
bar wajen har bayan sallar magariba,sai da aka kirashi a waya ya qarasa baqin get
wajen masu gadi da kanshi ya amshi saqon da ya bayar ayi masa order.

          Sanda ta farka taji dadin jikinta sosai,hakan ya sanya ta shiga toileta


ta hada ruwan wanka mai dumi ta wanke jikinta,ta dawo gaban madubi daure da towel
ta janyo kujera ta zauna kai,don kasala take ji ba zata tsaiyawa ba,haka kawai take
jin wani farinciki da annashuwa tana ratsata,ta dinga kallon kanta a madubi tana
sakin murmushi,lokaci lokaci tana shafa cikin nata wanda yake a dame da
hannunta,itakam ciki na zuwa mata a bazata,tun yanzun Allah ya dasa mata so da
qaunar abinda take so tamkar yadda taso abdallah tun kafin ta haifeshi,gababta ya
yanke ya fadi sanda ta tuna irin gwagwarmayar da tasha hannun zainab,tsantsar
makirci zalla da kuma wuyar da tasha kafin abdallah ua kai labari,ambaton sunan
Allah ta dinga yi tana nemawa kanta da abinda ke cikinta tsari tun daga
lokacin,bata fatan makamancin abinda ya faru da ita wancan karon ya sake maimaituwa
da ita, akasalance ta dinga shafa man gabanta na faduwa ta wani bangaren.

        A nutse ya turo qofan dakin wanda sam bata ji ba saboda yadda hankalinta
yayi gaba,takowa yake amma idanunshi na kanta yaja qarewa halittar Allah
kallo,saboda banda qirjinta zuwa mazaunanta ba inda yake a rufe,dogon wuyanta da
santala santalan cinyoyinta a bayyane suke,fatarta data sake kyau sai sheqi take
yi,wani qaunarta da shauqinta na fusgarshi,a haka ya qarasa ya sanya hannayenta ya
rufe idanunta,taushi da sanyin hannunshi kadai sun isa gaya mata waye?,ballantana
da zuwa yanzun koda bata ganshi ba matuqar yana muhallin da take sai jikinta ya
bata,matuqar tasiri yayi cikin rayuwarta,ya mallaki duk wani tunaninta,shiga da
fitar numfashinta na tattare da nashi,bata son ta fiya zaqewa ne da yawa
kawai,tunda ta sani cewa ba ita daya bace ta mallakeshi.

       Sautin murmushin dat fitar kadai ya sanar da shi ta gane waye,shima yana
murmushin ya cire tafukan hannunshi daga fuskarta yayi kissing wuyanta a
tausashe,sannan ya zagaya gabanta ya dane saman mudubin yayi zamanshi hannayenshi
harde a qirjinsa bayan ya ajjiye ledan takeaway din daya shigo mata da shi na
abinci yana ci gaba da qare mata kallo,baki daya ta takura,kunya ta lullubeta
"Me yasa baki taba zama nayita kallon ki a haka ba bayan kinsan hakan ashe ba
qaramin qayatarwa gareshi ba?" Murmushi ta saki cikin kunya,bai tsaya jin amsarta
ba ya dora
"Tunanin me kike haka ummu abdallah?,kinsan hakan yana da illa ga lafiyarki?"kai ta
gyada sannan ta maida masa amsa
"Babu komai abu abdallah" sosai sunan ya masa dadi har qoqon ranshi,sai da ya
lumshe idanunshi sannan ya bude bisa kanta
"Kada ki cemin bakiyi bacci ba"
"Nayi,na farka ne naje nayi wanka da sallah" ta fada tana murmushi
"Ummee na gaisheshi" idanu ta dan zaro
"Shine kayi tafiyanka baka tsayani munje na gaisheta ba ita da baba,kwana nawa ban
gansu ba" ta qarashe maganar a shagwabe,binta kawai yake da kallo,ko iya nan ta
samu wata madaukakiyar daraja da baiga macen data sameshi ba,ta maida iyayenshi
tamkar naga,tana sonsu so na bilhaqqi,ya samu kabarin tun kafin suyi aure take
sonsu da ganin girmansu,abinda har yau su'ad ra kasa fahimta daga gareshi,mutum ne
shi wanda da iyayensa kadai zaki iya cinsa da yaqi,saboda daraja da matsayi ya basu
bana wasa ba,yace bazai taba yin wasa da aljannarsa ba,duk duniya idan suka take
masa ita babu mai bashi,ki ubangijinsa bai isa ya tunkara ba bayan babu kyakkyawar
alaqa tsakaninshi da su,saboda yardar Allah tana tattare da yardar iyaye,hakan
fushinsa yana tare da nasu fushin,sirrin nasararsa da daukakarsa ba'a komai take ba
face ga albarkar iyaye,koda bata mallaki komai wanda za'a sota ba yana da yaqinin
ya samawa yaranshi uwa ta gari,ya tabbata yaransji zasu tsira da sanin girman na
gaba
"Yanzun ma banje wajen baba ba,shirya idan na idar da isha'i zan shigo muje" ya
fada yana duba agogonshi tare da sauka daga saman madubin
"Ina fata amma baka gayawa ummee komai ba ko?" Ta fada saboda tana jin
nauyinta,bata son ummeen ta fuskanci akwai wani abu,murmushi yayi,ya gano sarai mai
take nufi
"Don me zanqi gaya mata?" Tuni idanunta sukayi qwalqwal da hawaye,sai ya dawo da
baya,ha dagata suna fuskantar juna,nauyi ya cikata,yadda yake sake qare mata kallo
a kaikaice
"Banason naga wani abu mai kama da hawaye a fuskarki......kinsan me?" Kai ta
girgiza tana dubanshi
"Nima kunya nakeji,bansan me zance musu ba,espicially baba,na masa ba dai dai ba
sanda ya bani aurenki ya damqa min amanarki....yanzu idan nace kina da ciki kinsan
me zaice?" Kai ta sake girgizawa,sai ya jawota ya rungumeta tsam,jikinsu na gogar
na juna,ya dora bakinshi a kunnenta
"Zai iya rayawa a zuciyanshi....dan banza,yace baya so ashe har yayi aiki irin
haka?" Dariya ta qwace mata cike da kunya,sai ta tura kanta a qirjinsa tana dariya
qasa qasa,shi dinma dariyar yake ya dan janyeta yana dubanta
"Ki shirya muje,idan kin shirya jin wannan kunyar sai a sanar mai,amma nikam ban
shirya ba gaskiya,ga abinci nan kici kafin na dawi,ba nama kawai zalla ba za kiyita
ci" ya fada yana juyawa,dan rage dariyar tayi tana bin bayanshi da kallo
"Me kayi masa naba dai dai dinba sanda yace ya aura maka ni?....." A ba zata
tambyar tazo masa,sai ya tsaya cak ba tare da yaci gaba da tafiyar ba,jin yayi dif
ya sanyata tace
"Kace masa baka sona ko?" Ta baiwa kanta amsa tana ci gaba da duban bayanshi,a
nutse ya waiwayo sannan ya sake takowa zuwa gabanta,hannunshi daya ya dora kan
kafadarta ya riqe yana dubanta
"Sumayya......daga kanki ki dubeni" ya bata amsa cikin kakkaurar murya,a hankali ta
daga kan ta dubeshi
"Ci gaba da kallon qwayar idanuna,ina son ki bawa kanki amsa ne,kada na fadi ki
dauka wasa nakeyi" a hankali ta saka idanunta cikim nashi,tsahon mintuna aqalla
hudu,kamar masu kallon quda,saiga tsaiwa na neman gagararta,tuni ta janye daga
kallon nashi,ba zata iya jurewa ba,ya tareta suka fada gefan gado
"Uhmmmm,zaki iya explaining?"kai ta girgiza tana niyyar tureshi,murmushi ma subuce
mata,sai yanzu ta karanci wayau yayi mata,yau ta sake yarda da maganar anty dije da
tace vatasan sanda sumayya zata girma ba
"Ko ni kike so nayi miki?" Da sauri ta dora hannunta saman bakinshi yana girgiza
kaj,sai yayi murmushi yana sauke hannunta daga kan bakinsa
"Okey......daga yau duk ranar da kika sake min tambaya makamanciyar wannan zan
hukuntaki fiye da haka,mace nada dataja wajena.......macen ma matar aurena
na......matar aurena wanda ta soma kawon cikakken farinciki cikin
rayuwata......kinsan wani abu?.....uwar d'ana.....dole ta zama ta daban,dole na
bata wani matsayi na musamman,koda kuwa kuturwa ce gurguwa ce makauniya ce....balle
ke...ke din da kika zama wata ta musamman a dukka tarihin rayuwata,kika kafamin
tarihin da ban taba cin karo da shi cikin rayuwata ba" tabbas ta gamsu,ta gamsu
koda bai fada ba,miqewa yayi
"Ki shirya zan kiraki muje mu gaidashi"kai kawai ta iya gyadawa,har ya fice
kowannensu na murmushi.

         Saman kujerar falon sama ya tadda ta wannan karon zaune,sai ua dauke kai
kamar bai ganta ba yayi niyyar wucewa ciki,ganin haka ya sanyata cikin hanzari ta
isa gareshi ta rungumeshi ta bayansa,cikin salon kwantar da murya ta soma fadin
"am sorry my dear,am sorry,ba nufina na bata ranka ba,u know i love you thats
why,but am sorry"baisan ya zaiyi ta zama yadda yake so ba,har ga Allah bai nufin
tozarci ko wulaqanci gareta,saboda bazai manta hadisin da annabi ke wasiyya ga maza
su kyautatawa mata da alkhairi ba,but hakan baya nufin idan ta kauce kayi qoqafin
nusashsheta taqi kabi dukka hanyoyin da zaka ladabtar da ita wadanda suka dace ba
tare daka cutar da ita ba,hannunshi ya sanya ya zagayo da ita gabansa ya sanyata a
jikinshi
"shikenan,ya wuce,amma kiyi qoqarin sauyawa,kiyi koyi....." Sai kuma ya katse bai
qarasa din na,saboda bai kamata yayi mata misali da itan ba zata ga kaman cin fuska
ne
"Ki gyara ki zaka yadda nake so,koda ba duka ba kiyi qoqarin kamantawa"
"Thank you,thank you verry much" ta fada cikin farinciki,don ba zata iya missing
wannan daren ba,ta tabbatar ya juya mata baya ba komai bane wajenshi,ko a jikinsa
tun sanda suke su biyu bare yanzu da yake da wata,alwala ya daura ya fice
masallaci,sanda ya dawo zai sake fita ta tareshi kan ina zaya je yace zashi gaida
baba
"Sau nawa kika je gaidasu bayan bana nan?" Ya tambayeta yana tsareta da ido,sai ta
rausayar da kaibtana son basarwa,ranshi ya quntata,amma gyara yake son kawowa,dole
yabi abuna hankali cikin hikima
"U know what?" Da sauri ta juya tana dubanshi gami da girgiza kai
"Duk yadda zaki soni....ko hadiyeni zaki kina fiddo ni,zan qaryata son da kike min
matuqar baki bawa iyayena darajar data fi wadda kika bani ba" ya gaya mata da yaren
da zata fi ganewa,sosai zancan ya shigeta,cikin zuciyarta ya soma mitan wanne irin
sone wannan da zaya takurata da taso iyayenshi,itakam bata ga ana irin haka ba a
al'ummar data taso,kuna iya kai iyayenku gidan gajiyayyu ma idan suka soma zama
nauyi kanku,ko ka kai qararsu ga hukuma matuqar suna takura ka,kana iya komai gaban
idanunsu ma ba kwaba ba hantara,suna yin nasu zasuyi,amma shi ko hugging dinta bai
taba ba a gabansu,randa ma tayi gigin yin hakan sai da ya sabar mata,daga haka bata
sake gwadawa ba,to kuma haka kawai ba zamansu take ba zai tilastata hulda da
su,wannan qaddara da yawa take,ba yadda ta iya ta shiga daki ta sauya kayan jikinta
zuwa gown,sakakkiya ce ba'a matse take ba,har ya soma sauka tabi bayansa,yaji dadi
sosai har y fuskanshi ya nuna hakan,wanda itama hakan ya sanyata jin dadi cikin
ranta.

       A bakin qofa ya tsaya yayi mata knocking,koda taji tasan cewa shine,sai ta
zura dogon hijabinta kan riga da skert dake jikinta ta fito,sun sanyashi tsakiya
saidai ba wadda ke cewa da 'yar uwarta kanzil,suna tsaka da tafiya hibba ta hangosu
ita da hibban yaran fahariyya da adam yayan almustapha,gudu ta debo ta iso inda
suke kai tsaye ta ruqunqune sumayya iya qarfinta tana kiran anty
"Sake antyn taku hakanan kada ta fadi hibbah,bata jin dadi" cewaf almustapha,tana
dariya ta gaidashi hibban ma haka,suka gaida su'ad sannan suka gaida sumayya
"Anty...tun ran nan rananan din cannnn.....da kika je zaki bamu labari baki bamu ba
har yanzu" murmushi ta saki tana shafa kanta,tana mamakin kaifin qwaqwalwa irin ma
yarinyar da har yau ta kasa mancewa sa maganar
"Zan baku in sha Allah"
"Yaushe anty"
"Ba yanzu ba sai ta warke" almustapha ya fada
"Abbanku na gida?" Ya kuma tamyarsu,hibban ne ya amsa,yace suje suce yana sin
ganinshi amma ya shiga wajen baba tukunna
"Yana wajen baba prof din ai muma daga can muka fito"
"Is ok,ku shiga gida to ba kyau yawo da dare" da gudu suka juya suja wuce shi,su
kuma suka ci gaba da takawa
"Anya son yaranki baifi nawa ba" murmushi ta saki
"Yara ai rahama ne,ko wajen ubangiji sau tari albarkacinsu muke ci,ba don su ba da
wataqila ko ruwan sama mun daina samu" ta fada tana murmushi tare da dan
dubanshi,kusan da biyu ta fadi haka,raddi ne kan maganar da su'ad ta gaya mata dazu
na ta gama aiki tunda ta dauki ciki
"Gaskiya ne" ya furta a fili,cikin zuciyarsa yana sake jinjinawa baiwa da fasahar
zancanta,tsaki takeso tayi amma dole ta bame bakinta,don bata son abinda zai bata
daren nasu.

         Da sallama suka shiga wajen baba,yana tare da adam yayan almustapha suna
hirarsu,kusan ranar sumayya zata ce ta soma ganinshi,akwai 'yar kama
tsakaninsu,kana ganinshi zaka san jininsa ne,saidai almustaphan ya fishi kyau da
quruciya,ran baban yayi qal ganinsu dukkansu su ukun a tare,murmushi yaqi yankewa
daga fuskarshi ya tarbesu suka zauna suna gaidashi
"Sa'adatu(da yake wani lokaci hakan yake kiranta,abinda ta tsana kenan,ita aginta
bata suna ne)yanzu muka gama waya da babanki"
"Allah sarki" kawai ta fadu,har ga Allah haushin tsohon take ji,gani take shine
ummul Aba'isin komai ma da ya faru da ita,kanwa uwar gami,sai ya waiwaya ga sumayya
wadda ta gama gaida yaya adam a mutunce
"Maman tun daga randa naci tuwo kuma sai kiyi batan dabo,inata nemanki na bada
tukuici" qas tayi da kai tana wasa da yatsun hannunta kawai,ya tambayi lafiyarsu
baki dayansu suka amsa mai,ganim almustapha sun soma hira da adam yasa almustapha
yace suje wajen ummeen shi zaizo,su'ad ita ta fara yin gaba,sumayya na
bayanta,ganin tayi wucewarta bata ko saurari bangaren anty maamaa ba ya sanyata ita
shiga ta gaidata,taji dadi kuwa sosai,bangaren itama sai ita daya,dama can yaran
mazan ba zama suka fiya yi ba,bare yanzu da kowa ya kama nashi gidan,don su a waje
suke zaune,saidai kowanne yace idan yana sha'awa zasu zo suyi kwana biyu cikin
gidan tunda suna fa wajensu,sosai taji dadi suka dan taba hira atsaitsaye ta wuce
zuwa sashen ummee,tana gab da shiga su'ad ta fito tana hura hanci,ganin tana
yunqurin bangazarta ya sanyata ja gefe,wani kallo su'ad din ta watsa mata sannan
cikin harshen turanci tace
"Banza" murmushi ta jefeta da shi,cikin salon nuna qwarewa itama ta karya nata
harshen da salon data koya a uk
"Banzayen ai suna da yawa ba daya bace,suna da yawa,bansan wacce daga ciki kike
nufi ba"cewar sumayya sannan ta juya hankali kwance tayi shigewarta.

        Cikin kulawa suka gaisa ta samu gefan ummin ta zauna,bakin kowanme yayi
nauyi,sumayya ya kunyar ummin ita kuma yau ummin surukuta ce ta motsa,saidai duk
motsin sumayya tana lura da ita,sai take ganin ta soma sauyawa baki dayanta,jefi
jefi suka dinga hira da ita har almustaphan ta shigo ya taddasu,baiyi zaton zai
sameta har tsawon lokacin a nan ba,a sannan ummi ta shiga kitchen tana hanyar
fitowa ta jiyoshi yace
"Baki gaji da zama ba?,akwai magungunan da zaki sha fa?"
"Me ya sameta?" Ta fada tana fitowa akitchen din tana fatan jin abinda zuciyarta
keta faman raya mata,kanshi ya shafa yana jin nauyin ummin
"Ciwom ciki ne,kuma tana shan magani yanzu haka yana samun sauqi" ta san zurfin
cikinshi qwarai,sai ta zauna tana cewa
"Allah ya sawwaqe,lallai kam ki kula da shan magani"ta miqawa sumayya wani dan bowl
na plastic mai garai garai wanda akayi wrapping dinshi,maganar tata sai ya jita
kamar a baibai,gaba yayi cikin jin nauyi yana cewa ta taso su tafi,ummi ta bita da
kallo sanda ta miqe tayi mata sallama,sai taji tamkar ra tsaidata taji ainihin meke
damunta,saidai kuma koma meye tasan indai da gasken ne abinda take zato to nan da
wani dan lokaci qanqani zata fasu,suna ficewa ta samu kanta da yin
sujuddushshukur,duk da bata tabbatar da cewa hakan bane,wani farinciki data jima
bata ji irinsa ba yana ratsata,tamkar bata taba riqe jika ba.

*******     ******    *********

      Bai taba riskar kansa cikin farinciki ba irin na wadan nan kwanakin,bai taba
tunanin haka samun d'a yake dadi ba sai wannan karon,ashe daa baki daya hasashene
kawai yake yi,sumayya kam na fama da laulayi sosai,saidai Allah ya bata wata juriya
da qwarin gwiwa,tana matuqar qoqari wajen boye ma almustapha,saboda kullum kwanan
duniya tunaninshi na kanta ita da abinda ke jikinta,bai da sukuni yana gida koko
baya gida,dawainiya yake da ita bilhaqqi,idan da yana da iko numfashi ma shi zaya
yi mata,bata taba cin karo da soyayya kwatankwacin wannan ba,bata taba zaton ita
din sumayya abar soce har haka ba,bangaren su'ad kuwa gani take Allah ya sita da
bata taba gwada daukan ciki ba,musamman duk randa amai ciwon kai ko zazzabi ya make
sumayyan,da yake sautari yanzun tana yawaita zaman falo,haka kawai sai taji bata
sin zaman dakinta,a falo kawai take jin dadi,idan zata kwana tana amai ba abinda ya
shalli su'ad,saidai ta watsa mata baqar magana
"waya kaiki da zaki cikawa mutane kunne da kakari?"ba yau ta soma gani ba balle ya
dameta,saidai idan taga dama ta rama wani lokaci kuwa tayi banza da ita,abu daya ke
damun su'ad shine yadda wani lokacin take vcin karo da zallar kulawa da sumayya ke
samu daga wajen almustapha,tarairaya da damuwa,kalar wanda taci burin yayi mata
koma fiye da haka,abu daya kawai ta sani shine indai sai ta dauki wannan kayan
wahalar to kuwa ba zata samu wannan abun na,jira kawai take sumayya tayi nauyi kota
haife,ta tabbatar a sannan duk wata gayya zata watse.

       Ko daya sumayya bata bari laulayinta ya hanata yin duk abinda ya dace
ba,saidai abinda ba'a rasa ba wanda dole ka gaza saboda sauyawar yanayi,a hakan ma
takan faki idanun almustapha ne ko,idan baya nan,idan kuwa ya dawo kaman yayi
kuka,takan sanya dariya tace
"amman dai kai likita ne,ku kuke bawa matan mutane shawara su dinga motsa jiki
sanda suke da juna biyu ko?"cafkota yake ya hukuntata son ranshi,ba hukunci na duka
ko zagi ba hukunci ne zallar qauna.

       Ummi taso daurewa amma ganin dukkansu ba wanda ke da niyyar sanar mata komai
bayan raga dukka wasu canje canje da suka wajaba ga mai ciki,randa ta gaji ta tsare
sumayyan tazo gaidata da safe,kunya ta kamata,ta sumkuyar da kai,kamar zata nutse
haka take ji,murmushin farinciki ummu ta saki tana furta alhamdulillah a fili kafin
tace
"shine kika biye masa amiran umman khalipha zaku boye mana?,kyaci gidanku"itakam
kunya take ji,don ko anty dije ta kasa gaya mata,da yake kwana biyu basanan sunyi
tafiya ita da yara da mai gidan baki daya bikin 'yar qanin babanshi dake
bauchi,kuma sun dan jima a can shi yasa ko rashin lpyr bata sani ba,zaunar da ita
ummi tayi ta dinga zayyano mata dukkan wasu dabaru na kula da kai da ciki,ta kuwa
qaru sosai,ummi tamkar ta jawo dare yayi haka takeji don wannan kyakkyawan labari
ya isa ga kunnen baba prof.

        Yana zaune baban yana shan fura,jifa jifa yakan daga kai ya dubi ummi dake
zaune gabanshi,ba don ya qoshi ba ya ajjiye mazubin yana dubanta
"Fadi kawai abinda ke bakinki....ummin su adam yau tunda na shigo naga bakinki nata
motsi,tunda naga hakan nasan akwai magana sarauniyar miskilanci yau zan sha labari"
murmushi ta saki,har yau baba bai daina tsokanarta ba,bai daina tuno mata gamonsu
ba akaron farko wanda shi ya zama silar wanzuwar alaqar mai albarka dake tsakaninsu
a yanzu
"Babban albishir ne wannan,bai kamata na baka shi haka ta sauqi ba me zan samu"
murmushi yayi ya maida bayansa jikin kujera
"A'a a'ah,bazan fada ba sai naji girman albishir din tukunna"
"Kasan girmansa kuwa?"
"Har yakai na ganin sule na?"
"Yana da alaqa ai da sulen naka" jin ta ambaci sulensa ya sanya shi gyara zamanshi
"Wanne irin albishir ne haka zuwairiyya gaya min"
"Mun samu qaruwa fa agidan nan?" Dubanta yayi
"Ke ko maamaa?" Dariya ta saki yana toshe bakinta
"Kai.....haba prof..rufamana asiri don Allah,muna haihuwa surukai nayi....mamanka
ke da juna biyu?"
"Maman tawa biyu ce ai wacce?"
"Mai dakin almustapha" daukewa wutar baba tayi kafin yace
"Allahu akhbar!,Allahu akhbar!!,kilishi.....da gaske kike ko da wasa,kada fa ki
sani nayi abun kunya" dariya sosai ta dinga yi masa ganin yadda ya diriri ce
"Ta bakinsu nima naji,dama na jima ina zaton haka"kabbara hamdala da hailala baban
ya dinga saki,tammat burikansa sun cika a rayuwa,Allah yayi masa baiwa ba shakka,a
take ya daura alwala yayi sallah raka'a biyu ta godiya wa ubangiji,kallonshi kawai
ummi take,gani take kamar yama fita jin dadi qwarai nesa ba kusa ba.

Daga daya bangaren sumayya ke fitowa daga bandaki bayan tayi wanka saboda
kwanciya,wankan da bata samu yi ba sai a lokacin,ta hada har da kanta ta
wanke,saboda sam ta tsani zuwa salloon,tunda almustapha ya taba gyara mata a gida
taji tafi son nashi,yana zaune saman gado yana aiki kan system,fitowarta ya ja
hankalinshi,ya daga kai yana dubanta,tayi kyau cikin rigar bacci,tana gaban mudubi
tana daukan mayuka da hand drayer dinta ta zo dab da gadon ta jona ta sannan ta
miqe,ta daga kai suka hada ido da shi,kusan ta saba da irin wannan kallon daga
wajen almustapha,abun mamakin kuma idan suka fita sai ki wuceshi baima san dake
ba,hakanan bai fiya gane mata ba,amma batasan ya akai ya koyi irin wannan kallon
haka a kanta ita daya ba,iska ta hura masa a fuska suka saki murmushi tare
"baka sanni bane?"
"Kullum sabuwa kike koma min,daga zuciyata har idanuna,i dont know why?,ko kin iya
sihiri ne?" Murmushi ta saki tana juya ido
"Yessss....tunda har na iya sihirce zuciyarka" kai yake gyadawa yana qaramar dariya
"Na yarda kam,tunda gashi kin hana mu koma wajen aiki....amma in sha Allah next
week zamu wuce dubai baki daya,kinga...sai munfi sakewa ko?,saboda ina buqatar
kulawa sama da haka gaskiya" fara'ar fuskarta ce ta ragu,baki daya taji baga qaunar
sake komawa garin,duk da taji yana maganan gidanshi zasu wuce,amma tana ganin gwara
kawai ita ya barta nan ya wuce da su'ad ita taji da kanta,system din ya ture ya
amshi drayer din daga hannunta ya zaunar da ita a gabanshi ya soma busar mata da
kan
"Nikam ko?,ina ganin kawai da zaka wuce da su'ad ni ka barni nafi son nan" wani abu
ya taba zuciyanshi,tana zaton zasu iya raba gari shi da ita?,kwana biyun ma da yake
ba tare da ita ba shi daya yasan me yake ji
"Ba haka na tsara ba" ya fada a taqaice,don bai son ta sake cewa komai
"Amma ko don yanayin jikina wai ko?"
"Na fiki sanin hakan ai"
"ina son cikina ya sake......."
"Shut up sumayya,kada ki gayan abinda kike ganin ya dace mana...."ya fada a
kausashe.

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*
*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

9⃣6⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

*wata rana annabi S A W yazo wucewa ta wasu* *qaburbura guda biyu,sai yace da
sahabbansa*
*"haqiqa(mutanen dake cikin kabarin) ana musu azaba,ba kuma wani* *babban abu bane
yasa ake musu azaba* *saidai(ma'abocin kabari daya)ya kasance baya suturtuwa daga
fitsari,amma dayan* *SHI KUMA YA KASANCE YANA YADA ANNAMIMANCI"*

*sadaqa rasulul karim*

*qalubale ga munafukai,qalubale ga masu daukan zantukan wancan bangare su kaiwa


wancan,su dauki naka su kai wa wani bangare,qalubale ga masu haddasa husuma,masu
qiren qarya don su haddasa husuma da rigima tsakanin mutane,qalubale a garesu baki
daya,GA MAKOMARKU NAN,RUWANKU KU GYARA RUWANKU KUCI GABA*

*FITINA AKWANCE TAKE ALLAH YA LA'ANCI MAI TADA TA*

*FADA CE TA MA'AIKI*

*ABINDA KUKA SHIRYA BAI YIWU BA,SAIKU SAKE SABON SHIRI,NI DA MAMUHGHEE DUKA BA
JAHILAI BANE,MAIMAKON SHARRI DA KUKA SO QULLAWA SAI ALLAH YA JUYA ABIN YA ZAME MANA
ALKHAIRI,GODIYA TA TABBATA GA ALLAH*

*ubangiji na cewa*

*YAKU WADANDA KUKA BADA GASKIYA DA ALLAH,IDAN FASIQI YAZO MUKU DA LABARI,TO KUYI
BINCIKE KADA KU AFKAWA WASU MUTANE CIKIN JAHILCI/RASHIN SANI,SAI KU WAYI GARI KUNA
MASU NADAMA AKAN ABINDA KUKA AIKATA*

*HAQIQA DUK WANDA YAYI AIKI DA UMARNIN UBANGIJI BA ZAIYI DANA SANI BA,MUN GODEWA
ALLAH DAYA SA MUKA KASANCE CIKIN MASU IMANI*

*ALLAH KA SHIGA TSAKANINMU DA SU,KA FI KOWA SANIN BAMA NUFIN KOWA DA


SHARRI,TSARKAKE ZUCIYARKA SAI ALLAH YA KUBUTAR DA KAI*

*muna muku fata Allah ya shiryeku,don wannan mummunan ciwo ne kuke dauke da
shi,ciwon dake iya dawwamar da bawa cikin azabar kabari*

*ALHAMDULILLAH*
_______________________________________

           Shiru ne ya ratsa dakin,bata sake cewa komai ba,kamar yadda shima bai
sake cewa komai ba har ya gama mata gyaran ya hade mata shi waje guda,tana kwance
lamo tunani kala kala cikin zuciyarta,har ga Allah bata marmarin binsa,ba don komai
ba saboda ta horu cikin abdallah,tana tsoron sake faruwar wani abun,su da zasu tafi
can wata qasa wata uwa duniya,wazai tallafeta idan wani abu ya sameta wanda bata
fatanshi?,shi da ba zama yake ba,ko yaushe aiki aiki?.

         Washegari ya sake birkice mata,sanda suka je gaida su baba da ummee,ya


sanar musu komawarsu ranar lahadi kwanaki uku masu zuwa,ita dinma ummen so take ya
barta nan cikin ya sake qwari tukunna,baya ga haka tana tunanin haukar su'adah kada
ta yiwa sumayya saukarsa,tun sanda ta yanki almustaphan take jinjina batun,dannan
daga bisani itama tazo raiwa kanta illa,to wayr ba zata iya yiwa ba kuma?,hakan ya
sanya kamar tasan zaizo da zancan tafiya ta gayawa baba shawararta,yayi na'am da
hakan,don shi kansa tsarin yayi masa,ya wuce da su'ad din ya bar sumayyan bayan
wata biyu yazo ua dauketa.

       Sanda ummee ke rattabo masa bayanin kanshi na wasa,kusan tare suka daga
kansu gaban sumayya na faduwa,kada fa yayi zaton qararshi ta kawo kan ba zata bishi
ba?,da hanzari ya daga kanshi yana duban ummee,a hankali ya motsa bakinshi
"Amma ummee nan da can din duka daya ne ai,zata samu dukkan kulawar data dace"
"Ba daya bane almustapha,ka barta nan ta sake koyon yadda zata kula da kanta,a can
fa kada ka manta bata da kowa..."
"Amma ummee tana da ni" ya amsa ummin bako kunyar nan fuskarshi,hankalinshi a tashe
yake,kawai yadda zai tafi ya barta yake kwatantawa,ji yake sam ba mai yiwuwa bane
"Munsan da kai din ai,awa nawa kake zama a can din....kaga...magana ta wuce tashi
ka tafi,kada ayi visa da ita" a hankali ya miqe bai ko dubi sashen da take ba,duba
daya zaka yiwa fuskanshi kasan yana cin fushi,ya juya a nutse ya ficea
binshi,binshi tayi da idanuwa kamar zata sanya kuka,bacin ran data gani kawai saman
fuskarshi ya daga hankalinta
"Amirah" taji ummi na kiran sunanta,da sauri ta maida hankalita wajen tana amsawa
"Kada ki damu kinji,rabu da shi,ciwon 'ya mace na 'ya maca ne,kina wannan halin na
yau lafiya gobe babu ta yaya zaki tafi inda baki da mataimaki sai Allah,qyaleshi ko
yayi fushi zaya sauko,ni nasan bazai iya fushi dake ba" maganan ummin ta qarshe ta
bawa sumayya kunya,sai tayi qas da kanta tana amsawa da to,duk da haka zuciyarta
bata nutsu ba.

       Sallamar amira kamar wadda aka jefo ita ta katse maganan da ummi ke gaya
mata,da gudunta ta kwaso bata zube gaban kowa ba sai sumayya,ruqunqumeta tayi tana
cewa
"Wayyo matar yaya na,kin biyamu wallahi,Allah jiya kasa bacci nayi,labarin yazo mun
katsam,anty farida ce ta gayamin,sai naga gari kaman da gangan yaqi wayewa don kada
nazo na ganki" kunya ta kama sumayya,zungurinta take kan tayi shiru amma ina amira
ma ba fuskantarta take ba,ganin yadda kunya ta kama sumayya ya sanya ummi miqewa
tsam ta basu waje,ummi na fita ta dalawa amiran duka a cinya,wajen take sosawa tana
dariya
"Ba komai,wallahi koda zafi ni banji zafin ba,bakya laifi ai ko kin kashe dan
su'ad" dariya suka bushe da ita baki dayansu sannan sumayya tace
"Kefa iskancin naki ma naga sabon lasisi kukaje ke da saifu aka yi masa,antyn take
ma kin daina anty saidai su'ad gatsal,ke kin isa ki kashe mata daa ba sai tayi
gunduwarki ba" dariya ta sake saki harda tafa hannu
"Wa ya gaya miki son 'ya'yan take,ai ni tuni na san da wannan.....ke mubar zancan
waccar.....amiran umman khalipha da gaske anty farida take?"
"Shafa kiji" ta bata amsa tana hararta,dariya ta saki
"Ai wlh duk wanda ya kalleki yasan da magana.....amma fa kin rame da alama kina
shan jiki....Allah ya raba lafiya,kai Allah ya nuna mana wannan rana,zamu karya
qugu da kwankwaso"
"Ki komawa saifu a gurguwa ko?"
"Ba komai sai ayi maleji......can na gano mai dakin naki"
"Amira baki da mutunci,waye mai dakina"
"Waye banda yaya maan,waishi kuwa har yau bai daina wannan shegen dacin ran nashi
ba,na gaidashi ko amsani baiyi ba ya figi mota ya fice kaman wanda aka yiwa dan
banzan duka?" Shiru sumayya ta danyi,wato a fusace yake kuma cikin fushi ya fita
kenan
"Ranshi ne a bace amira"
"Haka kullum yake"
"Malama ki kiyayi zagarmin miji a gabana......" Ta fada tana hararta,dariya ta saki
sosai harda kwantawa qasa
"Ikon Allah....yau da bani da aure da nasha haushi,gayamin me akayi masa"
"Anqi din" ta fada tana tureta
"Habba....nice fa ta hannun daman" ta fada tana lallashinta,sai data ga dama don
kanta sannan tace
"Dubai yakeso mu koma ni shi da su'ad,daren jiya nace mishi su tafi ni sai cikina
ya dada qwari zan taho,ya nuna bai amince ba,yau ummi tace masa ya barni a
nan,kaman yadda jiya nace masa.....amira zaiyi tunanin na kawo qararsa ne"
"Dai dai kenan....kina zaton a barki cikinki bai qwari ba kibi waccan mai qirar
amurkawan ta murqushe mana baby?,sai jikinki yayi qwari yadda baki buqatar
mataimaki....ya almustapha kuma qyaleshi,tunda ummee ta fada haka dole zai haqura"
shiru tayi tana nazari,kusan maganarsu na kan hanya,ba yau tasan mugun halin
kishiya ba,ita sam bata ma yadda da yadda su'ad ke nuna cikin ko a jikinta ba bai
dameta ba.

        Fitowar ummi ta sanya amira miqewa ta daneta tana cewa


"Ummina,i missed you"
"Nikam bansan me yasa saif ke biyewa shirmenki ba,duka duka yaushe kuka zo gidan
nan wai?" Rai ta bata tana janyewa
"Wai ummi nufinki tun yanzu kin fara gajiya da ni,kinsan bazan iya zama ba banzo
naga matar yaya ba,qaruwa fa muka samu" ta fadi tana maida kallonta gun sumayya
data kauda kai tana mata dariya
"Gaskiya ne,kun kyauta ai" ta fadi tana zama amiran ta zauna tsakaninsu suna
gaisawa.

        Kusan nan ta wuni saboda ba ranar kwananta bane bare ta koma gida
aiki,zuwan amiran ya debe mata kewa sosai,sunsha hira kaman ba gobe,abinda bata
sani ba shine,dawowan almustapha gida uku yana dubata ya tadda bata nan,abinda ya
sake qona masa rai kenan,gani yake ita ta kai maganan wajensu ummi,abinda bai duba
ba shine daga daren har wayewar gari suna tare baiga ta fita ba,ta ina zata iya kai
qararshi.

         Sai bayan magarib ta baro bangaren,a sannan yana saman dining zaune da
niyyar cin abincin dare,ya tasa abincin ne kawai a gabanshi,abu goma da ashiri ,ko
kusa baya son abincin kuku,sannan ga damuwar sumayya a gefe guda,da sallama ta
shiga falon,yana daga can saman dining,binta yayi da kallo cikin bacin rai ba tare
da ya amsa sallaman ba,tun kayan safiya ne a jikinta abinda bai taba gani ba,hali
take so ta sauya?mema taci wunin yau bayan yasan banda nama saiko shinkafa 'yar
kadan take iya sawa cikinta,magungunan ta na yau ya duba baki daya ba wanda
tasha,tana dab da shiga balcony da zai sadata da dakunan baccinta ta jiyo
dakakkiyan muryarshi a atsawace yana kiran sunanta,hanjin cikinta ya kada ta runtse
idanunta kafin ta waiwayo
"Daga ina kike?"daga kai tayi ta dubeshi don maganar ta mata banbarakwai,yana zaune
ya hade hannayensa cikin na juna yana dubanta
"wajen.....waj....ummi"ta fada cikin dan daburcewa,sai ya miqe tsaye yana zuba
hannayenshi a aljihun wandonshi ya dan tako kadan zuwa bakin step din dining din
"Ba sai kinyi haka ba zaki nuna baki qaunar kasancewa tare da ni,duka ba wannan ce
damuwata ba...me kika baiwa babyna yau?,....tsaftar jikinki wanda tun kayan safe ne
jikinki"
"Ai naci abincin da amira......"
"Amira?.....amira ita ta tsaidaki kenan ko?,ita tazo?" Ya fada cikin sigar tambaya
da jin zafi,shiru tayi bata amsa ba,hakan ya sanyashi cikin hanzari ya fara saukowa
daga kan step din zuwa qasa yana fadin
"Na baki mintina goma ki tabbatar kin sake wanka...ki canza kayanki....ki dauki
abincinki kici kisha magani..." Ya qarashe maganar cikin huci yana kewayeta ya
fice.

         Dariya su'ad ta saki wadda ta riski zancanshi na qarshe


"Sai haihuwa manya.....kinga kadan daga illolinta ko?,har kin fara qazanta
kenan.....baki sani ba,bama zama da qazami,hakan yana nufin kin fara saitawa kanki
hanya"ta fadi tana saukowa daga sama tsuke cikin riga da dogon trouser qoqarin
daidaita kanta tayi kafin ta qiriqiro murmushi
" wani ko zai shekara baici ba wa ya damu da shi?,ke dai kiyi ta kanki,wadda ba'a
damu da wuninta cikin gida ko waje ba,koda watar qasar ce kuwa ta shekara can,duka
daya wajen wanda ya ajjeta"ta juya ta shige ta bar su'ad abin na mata zafi a rai,da
ita take,tana yaba mata magana ne kan zamanta america almustapha na dubai,ranta ya
baci qwarai,ta tsaya nan saman matakalar bene tana ciza yatsa.

        Duk data rama hakan bai hana zuciyarta suya ba,komai zai mata ya kasance su
biyu,bata son ace har gaban su'ad yana yi,haka dabi'arta take ko a gidajenta na
baya,sai ta fashe da kuka maimakon ta shiga bandaki yin wanka sai ta fada saman
gado tana ci gaba da rusa kuka.

       Bangaren ummi ya wuce direct zai saukewa amira,taimakon da Allah yayi mata
ko layin motarsu bata gama ficewa ba ya shigo neman nata
"Sun tafi yanzun nan,lafiya?" Ummi ta tambaya tana karantarshi,fushi ne taf cike a
zuciyarshi da fuskarshi,batasan me ya taboshi haka ba,tunda ita bata dauki maganan
hanasu tafiyan ta kai haka ba
"Ba komai...." Ya fada yana juyawa wannan karon a sanyaye ya fice,sai ta bishi da
kallo kawai ta girgiza kai tana ci gaba da yin abinda take.

        Yana shiga su'ad ta taroshi,har saman dining ya zauna tana karairaya fari
da karkade karkade,babban abin takaicin sai da yace
"Bani abinci" yana lumshe ido saboda yunwa da fushi,yau duka saboda bacin rai baici
komai ba,zuba masa tayi ta tura gabanshi tana debo masa labaran da sam basu
shafeshi ba tana masa,idan yayi loma daya sai ya jima baiyi ta biyu ba,ga surutunta
da ya soma hawa masa ka,sam labarin da take bashin sake caja mishi kai yake,labarin
abokanta karatunta maza da mata,duka bata lura da hakan ba bare ta sarara,rabin
hankalinsa baki daya ya karkata bangaren sumayya,yana so yaji daga gareta,haka
kawai ya kasa nutsuwa,baya so kuma ya shiga haqqin su'ad ya bar ta wajen hakan bai
dace ba.

        Wayarta dake daki ta soma kira tana sanar mata da sunan wanda ya
kirata,qawarta ce zulee,wadda idan suka soma waya tana bata labarin bayan dawowarta
nijeria har sai a qalla sun kashe kusan awa,da hanzari ta miqe tace mishi tana
zuwa,kai kawai ya kada yana ci gaba da tura abincin,qoqari yake ya ture tunaninta
daga zuciyarshi amma ya kasa,daga qarahe dai ya tabbatar bazai iya din ba,ture
plate din gabanshi yayi wanda ya sanya abincin zubewa ya miqe,kai tsaye ya durfafi
dakin.

        A kwance ya cimmata kamar dazun tana fidda hawaye,taji motsin shigowarsa


amma bata motsa ba,qare mata kallo yayi sannan ya sauya akalarsa zuwa bandaki,ruwan
wanka ya hada mata sannan ya dawo dakin gadon ya tsaye a kanta cikin dakiya
"Tashi ki wuce kije kiyi wanka,wannan ya zama last da zan kanki kina kuka,idan ba
haka ba ranki zaiyi mummunan baci" a kasalance ta miqe tana rangaji tare da qwalla
ta shige bandakin,locker dinta ya jawo ya fidda magungunanta ya ajjiye,ya shiga
kitchen dinta ya fiddo plate ya juye gasashshen naman daya siyo mata da shinkafa
'yar kadan a gefe guda.

       Tana yafe da qaton towel ta fito,a sanyaye ta qaraso bakin gadon ta


zauna,tura mata dan table din daya saka abincin da magani yayi a kai ya juya a
hankali ya fice,yayin data bishi da kallo qwalla na taruwa a idanunta.

       Cikin dare ya kasa bacci,ji yake kamar yaje ya roqeta ta bishi amma wani
sashe na zuciyarshi na hanashi,a hankali ya sauka daga saman gadon,ya zura slippers
dinsa ya fice bayan ya dauki wayarshi,qofar ya tura a hankali,dakin lullube yake da
duhu,ya ci gaba da takawa har ciki bayan ya kunna fitilar wayarshi,har lokacin
itama bacci bai dauketa ba,wani iri take ji cikin jiki da zuciyarta,tana jin
shigowarshi tayi hanzari rufr idanunta tare da qara yin luf tamkar mai yin
bacci,ragowar hawayen dake maqale a fuskarta ya tona asirin baccin qarya take,ya
dauki wajen minti biyar yana duban kyakkyaar fuskarshi,fuskar dake sanyaya mishi
rai,fuskar da duk duniya ayanzun bayan ta umminsa yana jin yafi qaunarta,don me
zata guje mishi a sanda yake tsaka da tsananin buqatarta ita da abinda yake
cikinta,kada dai ace har yau bata sonshi?,har yau bai cimma nasarar zama wani sashe
na rayuwarta ba?,sai ya juya a hankali zuwa inda ya ajjiye mata abincin,yasa
hannunshi ya bude,ba abinda ta taba aciki,ya duba magungunan ta balla ta sha
duka,hankalinshi yaji ya tashi ranshi ya dugunzuma,sai ya kunna wutar dakin baki
daya
"Wakeup" ya fada a taqaice,shiru tayi ita adole bacci take
"Ki tashi nace miki!", ya fada a dan tsawace,cikin hanzari ta miqe,daukan abincin
yayi ya isa gabanta ya zauna suna fuskantar juna,cokali ya sanya mata ya mata alama
da ido kan ta dauka taci,hannunta har rawa yake saboda yunwa,hakan ya sanya ya
amshe cokalin ya soma bata a tausashe duk da fukarshi a dinke take,a hankali ta
soma karba,tana ci tana satan kallonshi,saidai ko kadan yaqi ya kalleta,
"Abu abdallah"ta kirashi tana kallonshi,yana son sunan qwarai amma wannan karon sai
yaqi dubanta,hakan ya karya mata zuciya ta kuma sakin kuka harda 'yar
shashsheqa,sai ya ajjiye cokalin yana hade yatsunshi waje daya tare da zuba mata
ido,kukanta na ratsa zuciyarshi tamkar ana yankar tsokar zuciyarshi,tsahon minti
biyar sannan ya motsa bakinsa
"yanzu fisabilillahi ni me nayi miki?me ke damunki?" Ya fada murya can qasa a
tausashe,wanda hakan ke nuna raunin dake cikin zuciyarshi
"Kain....ne" ta fada cikin sheshsheqa,ci gaba yayi da dubanta kafin yace
"Saboda Allah a dakeni a hanani kuka?,saboda ni ban da bakin kukan?,kinsan zafin da
nakeji a qirjina?,ina tunanin har yau baki gama yarda da wacece ke cikin rayuwata
ba shi yasa kike son aikata min haka,amma babu komai....Allah ne ya jarabceni kuma
ina fatan ya yayemin,tunda baida amfani sanya mutum cikin zuciya,da can da ban
sanya ba kinga rayuwata lafiya lau..." Bata ji dadin furucinsa ba,sai ta sake sakin
kuka
"Kayi haquri don Allah"
"Zan haqura ne kadai idan kika shaidawa ummi zaki bini,ke kadai zaki fada mata ta
yarda" kai ta girgiza,ba zata iya watsawa ummin qasa a ido ba,tace mata
meye?,kafadanshi ya daga sannan ya miqa mata ruwa,tare da tsareta da ido,tilas ta
sha ya kauda kayan ya ja mata bargo zuwa saman cinyanta ya gyara mata filo,bai sake
sauraran komai ba ya kashe qwan ya ja mata qofar ya fice.

Washegari yaje kaima baba qara,saidai duka bakinsu daya da ummi,hakan ya sake
jagula lissafinshi,haka ya fice jikinsa ba qwari,baki daya sai yaqi zaman gidan,ya
wuni waje,yayin data wuni begen ganinshi,amma bata ga gilmawarsa ba,wuni tayi bata
leqa ko ina ba tana daki akwance abinta.

Randa ta amshi girki ya rage saura kwana biyu su tafi abida ta haihu,su'ad
anata rawar kai tare da shirin tafiya,jifa jifa idan sun hadu a falo tana yadawa
sumayya habaicin zasu tafi banda ita,ita tana tsammamin uban tafiyar ne yace ba
zata je ba,sabida tana laulayi,ko kallonta batayi bare tasan tana yi,ita ayanzun
fushin almustaphan yafi komai daga mata hankali,kaf ta laluba walwalarta ta rasa,ji
take kamar taje ta cewa ummin zata bishi,saidai hakan ba mai yiwuwa bane,kawai
kunya mai tsanani tattare da hakan.
Ana ya gobe zasu tafi suka je yima abida barka,ta samu santalelen danta
namiji tubarkallah da shi,babyn ya burge su su duka,sai taji kwadayin son ta haihu
ya sake kamata,ta shafi cikinta ta cikin mayafi tana ddu'a cikin ranta,tana son
taga ta tara yara da yawa,wanda ta fuskanci ra'ayin almustaphan ma kenan,su'ad kam
dama bai mata tayin zuwa ba,don ko yayi mata dama bata zuwa,don ba shirin arziqi
tsakaninta da abida,ta raina ajawalin abida yayin da ita kuma abidan bata daukan
raini sam,bata roqa komai daga gareka ba don haka kada ka raina mutincinta,kowa ya
tsaya matsayinshi,ya dauki sumayyan bayan sun biya wani katafaren shago sun mata
siyayyan kayan barka masu yawa kyau tsada da kuma quality,har ita abidan sai da ya
saya mata kayan fitan suna masu kyau bawai don hamza ya gaza ko bai da shi ba,kawai
ya wuce komai a wajensa,ya dora musu kudin dinki dubu dari a saman kayan,tun jiya
take dubanshi,duk abinda yake kawai gashinan ne babu karsashi sam tattare da
shi,tana jin hamza na kwasarsa kan me ya sanyashi laushi amma yayi masa shiru bai
ce masa uffan ba,shi ya tuqasu hakan ya sanya su biyu kenan suka fita,a parking
space ya tsaida motar ya kasheta,sai ta kasa fita tana dubanshi kawai,bai dubeta ba
ya dage gilasan motar,ya kwantar da kujerar ya miqar da bayanshi a kai,hakan ya
nuna bai da niyyar fita kenan,ta jima tana dubanshi kafin tace
"Kayi haquri don Allah" ya jima shiru kafin ya bude idanunsa da suka kada
"Da kikayi me?"
"Na rashin tafiyarmu tare" ta fada tana murza yatsunta
"Ba abun damuwa bane ai tunda bake kadai bace" maganar ta soketa,ranta ya
baci,kishi ya soma cinta
"Haka ne" ta fada tana dora hannunta kan mabudin motar ta bude ta fice,ta gefan ido
ya bita da kallo,ya rasa yadda zaiyi controlling kanshi,bai taba damuwa da wani abu
haka ba,sonta ba qaramin mamaya ya yiwa zuciyarsa ba,yana son ya daure kan rashin
tafiyar tasu tare ko don abinda ke jikinta amma ya kasa,tun yanzun kewarta ke
damunshi,nan yaci gaba da kwanciya,baison ya shiga ya taddata cikin rashin walwala
ko kuka,hakan na tabashi,bashi ya shiga ciki ba sai sha daya na dare.

A falon qasa ya tadda su'ad sanye da kayan bacci,tsaye bakin t.v tana shan
ruwa cikin gora,dubanshi tayi tana sakin murmushi,wani dadi ke ratsata a kwanakin
nan,ta fuskanci kamar akwai wata a qasa tsakanin sumayyan da almustapha,bugu da
qari kuma ga tafiyar da zasuyi daga ita sai shi
"Welcome" ta fada tana murmushi
"Yauwa....baki bacci ba?" Fari tayi da idanu tana cewa
"Wlh ban kammala shirina bane"dubanta yayi cikin mamaki,don bai taba ganinta cikin
zumudi haka ba irin wannan lokacin,don ko tafiya ta kamasu tare wano lokaci idan
tana wata sabgar saidai su raba flight ita ta biyoshi
"Ya kamata kam ki gama da wuri,don tafiyar safe ce"
"Ba damuwa ai" ta sake fadi tana faari
"Sai da safe" ya fada yana ci gaba da takawa,binsa tayi da kallo kafin tace
"Ok goodnight" ba haka taso ba,so tayi ta bata masa lokaci a nan,har sumayya ta
gaji da jira taga bai shigo da wuri ba,koma tazo ta samesu tare.

Sanda ya shiga tana gaban mudubi sanye itama da kayan bacci tana gyara
gashinta,kaya ne da bata taba sanyasu ba cikin kayanta,sun bala'in karbar
fatarta,abinka da mai yaron ciki,ga wani kyau na musamman data ajiye,kanshi ya
dauke ranshi na suya idan ya tuno gobe warhaka basa tare?,har ta kammala shirinta
ta kwanta bai gama nashi ba,bacci ya soma rinjayar idanunta,cikin baccin taji ya
janyota cikin jikinsa ya rungumeta tsam,shiru tayi ba tare data yi qwaqwqwaran
motsi ba,saqonni ya fara aika mata kafin daga bisani su shiga babbar headquater.

Sosai ya moreta tamkar wani mai biyan bashi,sam bata isarshi ko yaji ya
gaji da ita,kamar ana sabunta masa ita ne,tana kwance jikinsa baki daya gabbanta
sun mutu,amai ya dinga taso mata,ga yunwa da take ji,bata ankara ba ta soma
sheqashi,ya miqe da hanzari ya riqeta gam,sai data amayar da duk abinda taci,tana
jikinshi bai damu da yadda ta bata shi ba,sai daya gyara mata jikinta sannan ya
gyara gadon ya sauya zanin gado ta koma can,yace ta zauna ta huta kafin ta sake
kwanciya
"Abinci" ta furta a hankali,da kanshi ya shiga kitchen karon farko ya dumama mata a
na'ura sannan ya kawo mata,yana zaune opposite dinta yana kallon yadda take cin
abincin hannunshi rungume a qirji,zallar tausayinta ke ratsashi,bai taba zaton haka
mata ke dawainiya da shan wahala da ciki ba sai yanzu,a haka har wasu ke iya yadda
ayi musu cikin shege?,su haifan yaro su iya yarwa?,ko su bayar?,ko su kashe shi da
kansu?,sai ya tuna gidajen marayunshi da irin yawan yaran da ya qunsa,
"A irin wannan halin kikeso na tafi na barki ke daya?" Ya samu kanshi da furtawa a
sanyaye ba tare da yasan furucin ya fita ba,dubanshi tayi itama cikin sanyi tace
don kewarshi ta fara bugunta tun jiya
"Haka ummi suka tsara,nasan saboda qaruwarmu sukayi hakan,kuma na tabbata ummi zata
kula da ni fiye da yadda zaka yimin,dukkanmu ta fimu sanim zafin haihuwa" ko yaushe
kalaman girmama iyaye daga bakinta sune gaba dan komai,idanunsa ya lumshe yana jin
kamar yace ya fasa tafiyar,ji yake kamar zasu rabu ne ba zasu kuma ganin juna ba,da
sauri ya kori wannan mummunan tunanin daga ranshi tare da yin ta'awizi.

*saura naji an zage mustapha tsaf,lol😂😂kada kuyi qorafi,duk dadin zamanku wataran
dole a samu sabawa juna*

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

9⃣7⃣
*Bismillahir rahmanir rahim*

*Allah madaukakin sarki yana cewa*

*haqiqa Allah ma'abocin falala ne abisa mutane,saidai,yawancin mutane basa gode


masa*
______________________________________
        Wani dare suka gabatar wanda kusan rabinshi basu samu bacci ba,sai da suka
idar da sallar asuba wanda shi yayi limanci sannan wani bacci mai nauyi ya
dauketa,dubanta ya dinga yi saman abun sallahn,tausayinta yake ji,daren jiya kawai
amma sai yaga ta fada baki daya,kanshi ya dauke a hankali yana ci gaba da karanta
azkar dinshi.

         Bugun qofan aka soma yi a kai a kai,wanda hakan yayi sanadin farkawar
sumayya,a hankali ya miqe yana mamakin waye wannan,bude qofan yayi,su'ad ce tsaye
cikin kayan bacci tana jifarshi da murmushi
"Lafiya?" Ya tambayeta cikin mamaki,fuskarta dauke da murmushi tace
"Cewa nayi ko zaka zo muje ka shirya" waiwayawa yayi ya dubi agogon dake manne
bangon dakin,baki daya qarfe bakwai da minti hamsin da hudu na safe,sai ya maida
kanshi wajenta
"Halan baki ji qarfe nawa nace miki zamu tafi ba ko?,sha biyun rana shine har zan
fito ma shirya yanzun?" Kasaqe tayi,tayi nufin janyeshi ne,yadda sumayyan ba zata
sake ganinshi ba,wataqila ma sai bayan sun dawo
"Shikenan" ta fada gwiwa a sage tana juyawa,ya maida qofar ya rufe sannan ya tako
zuwa cikin dakin,tana zaune tana murza yatsunta a inda ta tashin,da alama ba isarta
baccin yayi ba bugun shi ya tasheta
"Ina kwana" ta gaidashi kanta a qasa
"Lafiya lau,ya jiki" ya tambayeta yana komawa inda ya tashi ya sake zama
"Alhamdulillah" ta maida masa tana miqewa,toilet ta nufa ya bita da kallo har ta
shige.

*Bayan awa hudu*

Kwance take lamo cikin dakin dake bangaren ummi wanda ta ware mata,tun bayan
awanni hudu da tafiyarsu babu abinda ta iya tsinanawa sai juyi da take daga farkon
gadon zuwa qarshenshi,ba wani loko ko saqo dake jikinta wanda kewarsa sonshi da
qaunarshi basu bi sun illata mata ba,hango sallamarsu take da kuma sallamarsu
tsakanin shi da ita,hawaye ya gangaro mata ta sanya hannu ta sharce,har ya tafi
tana iya hango damuwa qarara kan fuskarshi,furucinsa na qarshe sanda ya sanyata
cikin jikinshi suna sauraron bugun zuciyar junansu
"Ki taimakeni ki bini.....ki cewa ummi zaki" a sanyaye ta girgiza kai duk da tana
kwance qirjinshi
"Bazan iya ba.......kunya nakeji....kayi haquri" bai sake cewa uffan ba face zareta
da yayi daga jikinshi,ya fiddo kudi da kuma daya daga cikin ATM dinshi ya ajjiye
gefanta,ya tsugunna gabanta a hankali ya yaye rigar jikinta zuwa saman cikinta,ya
dora tattausan lebbansa ya sumbaceta sannan ya miqe,duka wannan abun da yakr yaqi
yarda ya dubeta kamar yadda take nacin duban qwayar idanunshi,a hankali cikin
takinshi ya juya har ya fice daga dakin idanunta na kanshi.

Ba irin sallamar da takeso suyi ba kenam,saboda haka tunda ya fita take


faman kiran layinshi saidai ba'a daga ba,bata daina kira ba har sai da aka tabbatar
mata wayar a kashe take,abinda ya sake karyar mata da zuciya kenan har yanzu yake
fidda hawaye,zuciya da gangar jikinta baki daya a quntace suke,wunin ranar baki
daya a quntace tayi shi,duk da yadda ummi ke nan da nan da ita,duk abunda take
buqata dama wanda bata buqata ta tanadar mata shi.

Bata sake tabbatar da cewa lallai almustapha ya zama wani sashe na


rayuwarta ba sai da dare yayi,baki daya bacci ya gudu a idanunta,fafur yaqi
zuwa,dole ta shiga bandaki ta daura alwala ta yi sallolinta yadda zata iya,duk
juyin da zata yi sai ta dibga hangoshi gefanta sanda yake bata kulawa,cikin jikinta
take jin tamkar ta rasa wanu babban sashi daga jikinta.

Washegari kallo daya ummi tayi mata ta fuskanci batayi bacci ba,wannan
dalili ya sanya ta sanyata gaba sai data tabbatar ta samu isashshen bacci,ta sani
fushin mijinta ke damunta,saidai baki dayansu kuwa suyi haquri,don ba zata taba
bari wani abu mara dadi ya faru ga sumayya ba,idan da ace su'ad din mai aiki da
tunaninta ne babu abinda zai sanyata rabasu,zata barau suyi tafiyarsu tare,amma a
irin wannan qadamin da ake ba zata lamunci tafiyarsu wata uwa duniya ba a sanda
sumayyan ke da buqatar taimako,a yammacin ranar iyalan adam suma suka shirya komawa
lagos wajen mijinsu,sumayya na zaune falon ummi tana kallon wani comedy,babu abinda
ya dauke mata na daga kewarshi da take,saidai ya dan dauke hankalinta,anty ni'imah
ce ta shigo cikin shirinta,sanye take da doguwar riga ta atamfa da yalwataccen
mayafi,bayanta hibba ce da hibban,sai nasrin da take riqe da hannunta,yaran baki
dayansu sanye suke da qananun kaya,sam gori da rashin mutuncin fahariyya bai hana
anty ni'imah riqon 'ya'yan tamkar ita ta haifesu ba,bugu da qari ya adam din
tsayayye ne a tsaye yake hakan shi ya sauqaqa tsiya da wariyar launin fata da
fahariyya taso koyawa yaran,fuskokinsu ita da sumayya dauke da murmushi suke
gaisawa,su hibba suka gaidata suka shige kitchen kiran ummi,murmushi ni'imah ta
sakeyi tana duban sumayya
"Sannu anty amarya(yadda yaran sukan kirata wani lokaci kenan),ashe qaruwa muka
samu" a kunyace sumayya tayi murmushi ba tare data amsa ba
"Allah ya inganta ya raba lafiya ya kawo na 'yan baya" nan ma bata masa ba saboda
kunya,dubanta tayi
"Ina miki addu'a kice amin wallahi,haihuwa ai babbar ni'imah ce" ta fada wani abu
na taba ranta,yanayin fuskarsa ya dan sauya,dubanta sumayyan tayi tana karantar
yanayinta,wani yanayu data taba tsintar kanta can baya shekaru biyar zuwa shida a
baya ya soma dawo mata,tasan me take ji,ba shakka ba kowanne mutum ke iya fuskantar
yanayin da mata irin su ni'imahn ke ciki ba sai wanda ya taba tsintar kanshi
ciki,al'amari ne mai taba zuciya da tsayawa a ran dukkan wata diya mace sata tsinci
kanta cikin irin wannan jarabawar,sai ta tsinci kanta da kamo hannun ta,ta daga kai
suka hada idanu,tuni qwalla ta cika idanun ni'imah,qaqalo murmushi tayi sumayya ta
maida mata
"Kada ki damu anty ni'imah,lokaci wataran sai kinga gamkar ba'ayi ba,kinsan na taba
tsintar kaina cikin yanayin da yafi naki muni?" Cikin mamaki take duban sumayya,kai
ta jinjina mata alamar tabbatarwa
"Kan na samu abdallah na sha wuya anty,ba wanda ya taba tsammatar abdallah zaizo
duniya....amma yanzu fa.....kinga kamar ba'a yi ba ko?,to kema kusan hakane in sha
Allah"
"Allah ya amsa amiran yaya musty...don yanzu bata umman khalipha bace" ta fada tana
qoqarin maida qwallarta tare da jin sanyi cikin zuciyarta da addu'ar da sumayyan
tayi mata,daidai sanda ummi ta fito tana cewa
"Wai tafiyar ce ne?"
"Eh wlh ummi" anty ni'imah ta fada cikin girmamawa tana murmushi,qarasowa ummin
tayi ta zauna sukayi sallama,sannan ta miqe suja fice sumayya na dagawa su hibban
hannu.

Da dare sai ga babbar 'yar anty farida sajida,ummu tasa aka daukota duk don
sumayya taji dadin zaman gidan,tunda gidan ya dade babu kowa,sajida akwai hankali
nutsuwa da wayo,hakan ya sanya sumayya ta fara jin dadin zama da ita sosai,akwai
surutu,a qalla zatayi shekara goma sha biyu,ta nan gidan take tafiyarta
makaranta,idan ta dawo sumayya tayi mata qarin karatun addini,tunda a sannan an
musu hutun islamiyya.

*Bayan sati daya*


Sha biyu saura na sare tana saman gadonta,sajida na gefanta kwance,tuni ta
jima da yin bacci,kamar kullum tunaninsa ke faman yi mata kaikawo cikin
zuciyarta,idan har cikin sati gudan tace ta samu walwala ta minti biyu tayi
qarya,duk da tsantsar kulawa da take samu daga bangaren mutane ukun nan,ummi anty
maamaa da shi kanshi baba prof,tun daga randa ya kira ummi ta sanya dukkan
kulawarta kan wayarta ko zata ga kiranshi amma babu shi ba alama,ko saqon tafi da
gidanka bata ci nasarar ganin gilmawarsa ba daga gareshi balle kira,kusan sau uku
tana jinsa suna waya da ummi amma bai taba nemanta ba,wayar tata ta janyo ta bude
tana duban lambobin wayarshi data dauka daga wayar ummi,amma gefe daya na zuciyarta
ya hanata kiranshi,akan me ma zata nemeshi bayan shine a haqqu daya nemeta,ya sani
ai tana son binsa amma dole subi umarnin na gaba da su,haka taci gaba da juya wayar
a hannunta wanda ba jimawa wani zazzafan a mai ya taso mata,tuni ta miqe cikin
hanzari,saidai bata kai ga kaiwa toilet ba ta durqushe a nan ta soma kelayashi ba
qaqqautawa.

A daidai wannan lokacin almustapha ne zaune bakin system yana aiki,tun


yanayi da qarfinshi tuquru har ya soma gazawa,baki daya ta tafi da dukkan wani
walwala da karsashinsa,hatta da manya da qananun ma'aikata sunsan walwalar yallabai
ta ragu,duk da dama can shi ba mai yawan fara'a bane,amma karsashinsa da son
aikinsa cikin kaso dari babu hamsin,hannunshi ya dora saman kanshi yana shafa bayan
ya jinginar da bayanshi jikin makarin kujerar,a hankali zuciyarshi ke masa
quna,wani bala'in qishirwarta na ratsashi,ji yake a lokacin da yana da ikon komawa
tsuntsu ba abinda zai hanashi yin fiffike ya isa gareta,duk wani qwarin qwiwa da
burin yin aiki da ya taho da shi babu su duka sun yi nasu guri,duk wani alwashi da
yaci na nesantarta tunda bata buqatar zama tare da shi ya ruguje,kwanaki bawaki
kacal da baiji ta jinsa yake tamkar wani dabaj cikin jinsin mutane,yanzu haka cikin
jikinshi zuciyarsa ke gaya masa idanunta biyu batayi bacci ba,idanunsa ya bude ya
janyo wayarsa kamar ko yaushe,ya bude hotonya tun wanda tayi cikin wayar sanda suna
dubai da doguwat riga,hotunan da yayi mata a dubai garden glow wanda batasan da su
ba,wadanda sukayi bala'in yin kyau,tamkar ta kirata ta amsa,hannunshi ya sanya yana
shafar fuskar tata,kewayaen labbanta wadanda idan ya tuna taushinsu tsingar jikinsa
ke zubawa,kyakwawan idanunta da kwantacciyar sumarta,tamkar wanda aka bawa aikin
zana taswirar fuskarta haka ya dinga zooming yana qare mata kallo,wata wawuyar
ajiyar zuciya ya saki tana jin zuciyarshi kamar zata fito waje,ba tare da ya shirya
ba ya samu kanshi da yin dialing number dinta,ya zubawa wayar ido yana sauraren jin
koda saukar numfashinta ne,saidai wayar harta qaraci rurinta ta tsinke ba'a daga
ba.

Sumayyan na zaune dirshan a inda tayi aman tana maida numfashi,ta hangi
wayar na haske,saidai ko data miqe ta dauko taga number dinshi ce sai ta maidata ta
ajjiye,ranta na wani irin baci,sai yau zaya nemeta,sai yau yaga daman magana da
ita?,wato kota mutu ko tayi rai ko?tunda yana da wata matar,zuciyar kishi ta soma
saqa mata wannan maganan,hawaye ne ya balle mata wani mahaukacin kishin su'ad na
ratsata,ta shiga toilet ta dauko mopper ta gyara wajem fes sannan ta dawo saman
kujera ta zauna tana maida numfashi,tana kallon wayar nata fidda haske alamun kira
ne,amma saita lumshe idanunta ma ta daina ganin wulgawar haskenta baki
daya,hangoshi kawai take shi da su'ad cikin walwala wanda hakan shi ya sanya kenan
ita ya bagarar da ita.

Baki daya hankalinsa ya dugunzuma,tunda yake ita ce mutum ta farko a duniya


daya taba kira sama da sau biyu,duka shi ba wannan bace damuwarshi,me ya hanata
daga kiranshi bayan jikinsa na bashi idanunta biyu?,tun yana zaune har sai da ya
miqe tsaye,baisan sanda ya samu kansa yana kiran layin ummi ba ha tare daya tuna
cewa dare ya fara nisa ba ko kuma tana wajen baba,cikin tsakiyar baccinta taji
qarar wayar tata,dama ba wani nisa can baccin nata yayi ba,gama sallolin nafikarta
kenan ta kwanta din ko hijabin jikinta bata cire ba,macace mai yawan tashi
dare,bata fiya kashe darenta baki daya wajen yin bacci ba,sunan almustapha data
gani ya dan sata faduwar gaba
"Lafiya dai almustapha sha biyu da minti biyar na dare?" Sai a sannan hankalinshi
ya koma jikinshi,ya dan gyara muryarshi
"Aaaa.....dama....ba komai...inata kiran sumayyah bata daga bane" ajiyar zuciya ta
saki
"Ka sani fa lokacin bacci je yanzu,kuma kasan muhimmancinsa wajen mace mai ciki,ka
bari da safe ka kirata ko ita ta kiraka don na tabbata yanzun ta dade da yin
bacci,don yau ana gama sallar isha'i taje ta kwanta" gabanshi ya soma faduwa,addu'a
yake kada Allah yasa ummi ta tursasashi kan ya bari sai goben,shi kadai yasan me
yake ji a qirjinsa game da ita,muryarta kawai yake da muradin ji,Allah yasa ta
fahimceshi
"Batayi bacci ba ummi.....don Allah ko zaki hada....." Sai kuma ya kasa
qarsawa,nayin ummin yake ji,itama a nata bangaren kasaqe tayi,tausayi irin na d'a
da uwa ya kamata,ta tabbata ba zaya samu rabin kulawar da yake samu wajen sumayya
ba,tsanin miji da mata sai Allah,kada kuma ta shiga haqqinsa da yawa
"Barin kai mata" cewar ummi
"Yauwa ummi thanks" ya fada cikin wani irin zumudi tare da sauke ajiyar zuciya
wadda har sai da ummin ta jiyo,murmushi ta saki tana saukowa daga saman gadon,tasan
halin yaronta sarai,tun yana qarami bai iya son abu ba,bai iya sanya abu a zuciya
ba,duk abinda yake so bai riqonsa da wasa,hakan ya sanya tun da can baya ta duqufa
masa addu'ar samun mace ta gari wadda zata masa yadda yake so ba tare data wahalar
da shi ba.

Qofar dakin data ji an turo shi ya sanyata bude idanunta,suka hada ido da
ummin sanda ta kunna wutar dakin
"Me kike zaune kikeyi amira?,da gasken ashe baki bacci ba"murmushi ta dan qaqalo
"gajiya nayi da kwanciyar sai na zauna na dan huta"
"Ko dai wani abu ke damunki?,ki gayan gaskiya" kai ta kada kanta a qasa
"A'ah ummi babu komai,kawai na gaji da kwanciya ne"
"To ko dakina zaki koma?" Ta fadi tana qarasowa gabanta
"Nan din ma yayi fa ummi"
"Indai akwai wani abu da bai miki dai dai da yadda kikeso kada kiyi nauyin baki ki
sanar min......mijinki ne dama ya tasoni....maimakon ya kira taki wayar" ta fada
tana dan murmushi tare da miqa mata wayar sannan ta juya zata fice
"Idan kin gama ki barta nan wajenki ko zuwa safiya na karba" ta fada tana ficewa
tare da rufe mata qofar,wayar sumayya tabi da kallo sanda ta sake ruru,sunanshi ya
fito baro baro,sai ta kauda kai kibiyar kishi na sukarta,wani kiran ne ya sake
shigowa,a hankali ta shafa wajen amsawa ta daga ta kara a kunnenta
"Sumayyah!" Ya fada a tausashe cikin salon muryarshi dake ratsa zuciyarta,muryar
nan da take mutuwar so,
"Sai yau kaga daman nemana?,ba ruwanka da hakin da nake ciki ko?,dama ba sona kake
ba baka damu da ni ba...."
"Sumayyah" ya sake kiran sunanta karo na biyu ya katse ta a tausashe,kiran sunanta
kadai ya karya mata zuciya kawai sai ta saki kukamai hade da sheshsheqa,idanunsa ya
lumshe bugun zuciyarsa na qaruwa
"Ya salam!" Ya dinga furtawa can qasa tana shiga cikin kunnenta,ita kanta batasan
me ya saka ta kukan ba,daga inda yake tsayen sai tsaiwar ta gagareshi,komawa yayi
saman kujerar shima yayi kwance rigingine,wani dafi take zubawa zuciyarshi ba tare
da ta sani ba,nadama ta kamashi,me yasa ya watsar da ita don kawai taqi binshi,shi
kansa yasan cewa kansa da kansa ya hora,yama fita jigata,sabida shi din ya rasa
komai,duk wani abu data sabar masa da shi a yanzu babu,sannu a hankali ta soma
tsagaita kukan don kanta,bayan taji zuciyarta ya soma yin sanyi
"Kiyi haquri" ya fada kamar yana mata rada
"Ki yafemin.....na kasa sabawa ne.....na kasa daurewa rashinki....kamar maraya haka
nake jina....am really sorry banyi da niyya ba" ajiyar zuciyar itama ta sauke,tana
jin yadda kewarshi ke illatata,kalamanshi kamar sake tunzura qaunarsa suke cikin
zuciyarta,saidai sarautar ta motsa,sai tayi mishi shuru kaman bada ita yake ba
"Summy....kice wani abu mana" yadda ya kira sunan nata sai taji kaman mukhtar,sake
narkewa tayi cikin kujera ta kuma qi cewa komai din
"Samayyahh...." Ya kuma kiran sunanta,ya gane cewa kawai azabtar da shi take
sonyi,kamar ya saki mata kuka haka yake ji
"Ki kulani ko don babynmu mana,i missed him alort shima fa" nan ba amsa,amma can
qasan ranta wani sanyi na ratsata,wanda yayi tasiri har saman fuskarta,ta soma
fidda wani boyayyen murmushi
"Wallahi tallahi na rantse idan baki ce min komai ba a gobe zaki ganni abuja"
dariyar da take boyeea ta qwace mata,zata fi kowa son hakan,saidai bata masa adalci
ba idan har tasa daga komawarsa cikin sati guda ya kashe kudin ticket dinshi ya
sake dawowa,me zata cewa su ummi ya kawoshi
"My happiness...." Ta amsa mishi cikin wani irin salo wanda ya saukar da gungun
farinciki wa zuciyarshi,ya sauke qatuwar ajiyar zuciya
"Ki tabbatar min da cewa kina lafiya keda baby na"a shagwabe tace
"ba wani.....bayan baka damu dani ni da babyn ba...."
"Ya ilahi....daina fada don Allah kada ki sani cikin wani hali.....ki fadi abunda
zai miki yanzu wanda zan wanke kaina,wanda zai nuna miki tsantsar damuwar da nayi
da ku"
"Just kiss me...." Ya subuce daga bakinta ba tare da tasan ta fadi hakan ba,wani
wawan kiss ya bata ta cikin wayar wanda babu inda bai aika saqo ba cikin gangar
jikinta da ruhinta sannan ya dora
"Ku raba ke da baby na"
"Baby yana godiya.....ka kwanta da safe mayi waya,sabida su'ad" ta hada kalaman da
qyar,idanunshi ya daga ya dubi qofar bedroom din da take ciki,tunda suka zo ungulu
ta koma gidanta na tsamiya,wani abun ma don yana taka mata birki ne
"Ban yarda ba" ya maidawa sumayya amsa
"Da gaske my happiness.....kaga idan ni kama haka ko bazanji dadi ba" shiru yayi
yana murmushi kamar tana gabanshi,sunan data kirashi da shi ya tsaya masa
"Da gaske ni happiness dinki ne?"
"Sosai.....ban kuma sake tabbatar da hakan ba sai yanzu,na rasa farinciki da
walwala na tsahon sati guda sabida batan dabo daka yiwa rayuwata,sai gashi cikin
mintina qalilan da jin muryarka komai ya dawo min,farinciki na yadawo,sai tsananin
kewarka da nake ji kamar zata rabani da ruhina..." Ta bashi amsa kai tsaye tare da
katse kiran saboda tana ji tayi amfani da kalamai masu nauyi,mutuwar zaune kawai
yayi daga wancan bangaren,kalan soyayyar da yake da buqata,kalan soyayyar da yake
nema ido rufe yau gashi Allah ya bashi,baki daya ta gama kasheshi,dan qaramin ihu
ya saki shi kadai kaman wanda ya soma zaucewa,gaskiya wannan karon baya jin zai iya
bin umarnin su baba,ko sato matarshi sai yayi,bazai iya jurewa zama ba tare da ita
ba,haka ya dinga jera kiranta amma tawi dagawa,daga bisani ta tura masa saqo tana
shaida masa bacci zatayi sai da safe,wanda ita kanta bata gaji da jin muryarshi
ba,tayi hakanne kawai don kada ta shiga hurumin su'ad.

Bacci tayi wanda ta jima bata yi irinsa ba,cikin nutsuwa da kwanciyar


hankali da walwala,wanda har kusan makara tayi sallar asuba,ita kanta ummi
washegari taga canji sosai,komai nata cikin walwala da kuzari take,kaman yadda kowa
yaga sauyi tattare da almustapha har cikin kamfani,ciki har da su'ad,wadda ita bata
lura da bai cikin walwala ba,koda ra kura ma watsar da shi tayi ta tsammaci
miskilancin nashi ne ya motsa,koma shi dinne ita ba damuwarta bane tunda dole ya
zauna da ita,hakanan kuma kudi taba samunsu fiye da yadda ma takesl,abu daya ke
damunta yadda ya tikastata saka digayen kaya,haka duk inda zata sai ta
tambayeshi,ko zuwa cinema ma ya hanata baki daya,yadda taci burin sakewa da
qawayenta bata isa ba,saidai suzo gida su sameta,shima dole su kama gabansu gab da
lokacin dawowarshi.
******* ****** *******

Baki daya ya zame mata wani chewing gum din waya,indai ka ganta da waya tofa
almustapha ne,har sajida ta soma ganewa,da taga ta soma waya zata basu sarari,duk
wani motsinta ha san da shi,wani sa'ilin har kukan shagwaba yake mata kan ta gudo
zaya shirya mata komai,saidai kawai taci dariyarta tace bata iyawa,da wanne idanun
zata kalli ummi da baba?,.

Cikin sati uku kacal ta soma sauyawa,jikinta yayi bul kamar ka taba jini ya
fito,laulayi ya fara sauqi sai dan abinda ba'a rasa ba,yanzun kuma sai shegen
kwadayi data koya,ci wannan ci wancan,duk da bata rabu da na hannun daman nata ba
wato nama,ita kanta mamakin sauqin wannan cikin take.

Kwananta shirin anty dije ta dawo,ta gaya mishi zata wajenta,bai hanata ba
yace ta gaidata ta kuma kula masa da kanta,sajida ta dauka suja tafi bayan ta yiwa
ummi sallama,ummi ta bada wasu tararuka masu kyau ta kaiwa anty dijen.

Da minal mutuniyarta taci karo suna wasa da khalioha,dukansu suja durfafota


da gudu,ta daga minal tana mata waqarta ta tsokana tana ta dariya abinta tana cewa
"Anty sumayya na girma fa yanzu"
"Ai naga alama,irin wannan kumatu haka?" Sumayya ta fadi sanda anty dije ke fitowa
zuwa falon
"Kai kai kai,sauketa....sauketa nace" anty dije tace da sumayya,murmushu tayi tana
sauke minal din,kaddai antyn har ta gano ta,numfashi anty dije ta sauke
"Ki rufan asiri sumayya don Allah kizo gida na lafiya ki koma lafiya" wannan karon
dariya ta baiwa sumayya sai data qyace
"Kai anty....kai anty.....wai meye don ma dauki minal,naga ko da can ina daukanta"
daquwa antyn ta watsa mata
"Da kika ce amma banda yanzu,na haramra,idan baso kike almustapha ya saka mu a
black list ba ko ya dauremu baki daya" yatsina fuska sumayyan tayi
"Habawa,shi ya fara" ta bi bayan antyn zuwa dakin hara bayan abida ta gaidata nan
ta barsu da minal da khalipha.

Laila da hafiz ne a dakin suna gyaran kaya,rungume sumayya laika tayi niyya
anty dije ta harareta tana mata gargadi,ita dai bata gabe ko meye ba ta gaida
sumayyan daga bisani ta hau zuba mata surutu,hafiz dama ya gama abinda yake cikin
dakin,shi dama ba gwanin surutu ba,suja gaisa da sumayyan suka dan taba hira ya
fice,laila kuwa sai da anty dije ta koreta ta hadata da qarasa girki a kitchen
sannan ta fice,fuskar anty fes,farinciki kaman ta hadiye sumayya,kallo daya zaka
mata maga sauyi baro bari tattare da sumayyan,ta zama wata matar hutu
"Waini zaki boyewa ciki sumayya?,to amira ta gaya min tun muna can" dariya ta saka
tana kama baki.
"Oh su amira an iya gulmaaaaa"
"Abin farinciki ai ba'a biyeshi,ko abbansu khalipha bakiha dadin da yaji ba,yace ko
shi yasa rannan da suka hadu da man fuskar nan kaman gonar auduga,abinda bai taba
gani ba" dariya suka sanya baki dayansu,ranar hira suka yi sosai da anty dijen,basu
koma gida ba sai bayan sallar magariba.

A falon ummi tayi sallama tana riqe da hannun abida suna hirar masu tsaron
gidan da suka ga an sauya,ummin ce zaune tana kallon labaran duniya,ta amsa musu
dai dai lokacin da eesha ke fitowa daga daya daga cikin dakunan dake falon,sanye da
gown mara hannu,kanta ba dankwali sai waya riqe hannunta tana dannawa,bisa dukkan
alamu bayan fitarsu gidan anty dije ne ta iso gidan,idanu suka hada eeshan ta
jefeta da wani kallo,yayin da sumayya ta dauke kanta ta waraso ciki ta yiwa ummi
murmushi,ta zauna kan kujera kaman yadda eesha ta samu kujera daya ita ta zauna
"Wato gida dadi ko?,sai yanzu?" Murmushi tayi tana cewa
"Bansan lokaci yayi haka bama ummi,umman khalipha na gaidaki"
"Ina amsawa....kin tafi kin bar wayarki gida wancan sarkin kiran ya kira ya kusa
sau hamsin" cewar ummi,sai tayi murmushi tana miqewa,don itama wuni daya kawai amma
tayi kewarshi,sajida ce ta gaida eesha ta amsa tana tambayarta mamanta
"Au eesha bakiga sumayya bane?sumayya ga eesha zata mana hutu kan ta wuce
school"sai data daga kai ta dubeta sanda take shirin wucewa,wani kishinta na
sukarta fiye da yadda take kishin su'ad,kyau da hutun daya ratsata ya tsaya mata
awuya,komai nata yaji yadda akeso,itama sumayyan juyowa tayi,ta dan saki fuska
saboda maganan da ummin tayi
"na ganta...mun wuni lpy?" Ta fada adake
"Lafiya ya mutan gidan..." Tafada tana yin gaba,qasa qasa ta amsa mata bata sake
juyowa ba tayi wucewarta,ta rasa me ya tsarewa eesha a rayuwa,taqamaimai batasan me
tayi mata ba,ta san dai kawai rashin jituwarsu tun fara ganin eeshan data yi,sanda
amira ta biyota kani satin bikinta,abinda kawai ta sanyawa ranta eeshan nada raina
talaka,wanda idan har haka ne ita kuwa ba zata bari ta taka ta ba,tunda itama ta
mutuntata ta karramata.

Bata sake saukowa ba tana can suna soyewarsu da almustapha kaman su hadiye
juna,wanka kawai tayi ta kirashi ya katse ya biyota,ya jima kwance dama ya kasa
tsinana komai,muryar tata kawai yake sonji,sun jima suna hirar sannan yace da ita
"Af....naso na manta....kaman dazun naji ummi na cewa aisha tazo ko?" Dan jim
sumayya tayi sannan ta amsa
"Eh haka ne"
"Well....,ban so ki shiga shirginta,ki tuna ko yaushe akwai banbanci tsakanin ki da
ita" kai ta kada tana mamakin me yasa sam ba jituwa tsakaninsu,ya washi
ganinya,bata manta randa ya sake nanuqeta ba a bayan gida bayan ya hango tahowar
eeshan,ba shakka ruwa baya tsami banza imma dai ta taba masa wani laifi irin wanda
baya so ayi masa ko kuma wani abu makamancin haka
"An gama yallabai"
"Ba yallabai ba....wancan sunan nake so" dariya ta qyalqyale da ita
"To my.....happinesssssss...." Ta fada a rarrabe tare da jan S din wanda sautinta
ya ratsa dodon kunnenshi
"Ohhhh....babe....ki shiga hankali fa...so kike ki tsokaneni ko?" Dariya ta kuma
saki
"Ni na isa...kaga ma Allah ya bamu alkhairi sai da safe"
"Kina kashen waya gobe zan sa a satoki a kawo min ke,bar wayar a haka ki gama
shirin baccinki kizo na saki bacci" idanu ta zaro,tasan me zaiyi mata
"Kudin wayanka fa na tafiya"
"And so what?" Ya tambayeta a tausashe
"Ok...am sorry,amma fa zan iya minti arba'in kamin na gama shirina"
"Ba damu bane" ya furta yana kwance rub da ciki saman sofa
"Okeyyyy,sai na dawo"
"Take care..." Yace mata kaman ya hanata tafiyan.

*to ga eesha tazo?ko me zai faru?,ku biyoni muje*

Assalamu alaikum fans,ya haquri da ni,sabgogi ne ba yadda bawa ya iya,kana naka


Allah na nashi,wani lokaci suyita zuwa maka ajajjere kuma dole ka aiwatar da
su,haka zamuyita haquri har mu kammala labarin,ina gaisuwa gareku baki daya,Allah
yasa mu dace.
*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

9⃣8⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

*Allah S W T yana cewa annabin rahama sanda ya shiga damuwa kan rashin musuluntar
kafirai*

*haqiqa kai(annabi muhammad S A W)baka shiryar da wanda kake so,saidai Allah yana
shiryar da wanda yaga dama*

Saboda haka 'yan uwa kayi qoqarin nusasheshe da bawan dake kan bata,shiriya ka
barwa Allah tashi ce.
______________________________________

         Washe gari qarfe tara na safiya ta farka da wata iriyar yunwa,kasancewar


jiya suna tsaka da waya da almustapha bacci ya dauketa ba tare data ci abinci
ba,sajida na gefe tana ta baccinta ta shiga toilet ta wanke bakinta sannan ta dawo
ta daura zani kan rigar baccinta ta zura hijabi ta fice.

      Kitchen ta shiga tana yin sallama,mai aikin ummi uwani na tsaye gaba gas tana
fere dankalin turawa ita juyo cikin sakin fuska ta amsa,hakanan take son
sumayyan,ta yaba hankalinta sosai,sam basu taba jin dadin zama da abokiyar zamanta
ba shi yasa suke mamakin halayyarta,hasalima umarni ne kawai tsakaninsu,ka saba
kuma taci mutuncinka ko gaban waye,kaman bayi take daukansu,gefe daya eesha ce
sanye da kayan bacci tana jingine da freezer,hannunta daya riqe da cup,daya hannun
kuma waya ce tana amsawa,uwani duka ta girme musu don ta kusa sa'ar ummi,mai
aikinta ce da suka jima tare,amanarta da hankali yasa tasu tazo daya da ummi,tunda
sumayya ta dawo wajen ummin ita kewa sumayya komi duk abinda take da buqata,fuskar
sumayya qunshe da murmushi ta qarasa kusa da uwanin sanda take yunqurin gaida
sumayyan tayi maza cikin girmamawa ta soma gaidata,ta amsa tana fadin
"Halan wani abun kike da buqata uwar dakinmu?" Murmushi sumayyan tayi
"Ai naga ma kaman aiki kike ko?"
"Ba matsala fadi abinda kike so sai ayi miki ai......"
"Ba aikin wanda zakiyi har sai kin gama min nawa" eesha ta fada tana sauke waya
daga kunnenta idanunta a akansu
"Ai duka zan iya hajiya aisha....nata aiki yafi mu....."
"Bakiji me nace bane?,ko sai na sake maimaita wa?" Ta kuma fadi a
gadarance,murmushi sumayya ta yiwa uwani
"Kada ki damu baba uwani...ci gaba da aikinki" ta fada tana matsawa gaba,ta samu
tukunya ta dauraye ta zuba ruwa da duka kayan qamshin da take buqata ta dora saman
daya gas din,sannan ta bude freezer ta fitar da nama ta zuba masa ruwa don ya narke
ta janyo kujera ta dawo gefan baban ta zauna suna hira jefi jefi,wannan dabi'a ta
sumayyan na daya daga cikin abubuwan da ya sanya baki daya ma'aikatan ke
qaunarta,bata dauki rayuwa da zafi ba,komai nata a sauqaqe yake,idanuwan eesha na
kanta,baqinciki ya cikata,so tayi taja zancan da tsaho ta yayyaba mata magana ta
qona mata rai,saidai anyi katari sumayyan bata bi ta kanta ba,wani wawan tsaki ta
ja sannan tace da baba
"Saura bayan fitata ki kama aikin wasu,zan shiga wanka kafin ma fito a shirya min
saman dining"
"To" kawai baban tace da ita,sai ta juya ta fice tana wani taku tana jin kanta dai
dai da kowa,da kallon takaici sumayya ta bita sai data fita ta dauke kai,batasan me
ta dauki rayuwa ba,yanzu kaman baba data yi sa'a da uwarka idan ba dole ba ma
yaushe zaka sanyasu wani aiki
"Kiyi haquri baba don Allah" sumayyan ta fada cikin rashin jim dadi,dariya baban
tayi
"Banda abinki uwar daki ai babu komai,tana cin albarkacin hajiya ne da
alhaji,dukkansu su da yaransu an shaida mutanen arziqi ne,don wannan tayi ai ba
komai na lokaci ne zata koma inda ta fito" kai ta jinjina kawai suka ci gaba da
hirarsu,kusan tare suka gama,wanda hakan yayi dai dai da shigowar sauran
ma'aikatan,suka gaisa baki daya sannan ta fice ta basu waje,bayan an kai kayan
karin dining saboda harda ummi tayi,gasashshen nama ne da kayan lambu,sai breadin
inibi da ruwan shayi,na eesha kuwa chips ne da qwai sai nata ruwan shayin.

          Ta tadda sajida ta farka harta gama gyara dakin tayi wanka abinta,sam
yarinyar anty farida bata yi mata rainon yaran masu kudi ba,ta iya qananun aikace
aikace dai dai da ita,ta iya shata tsaf da gyaran gado,ta gaida sumayyan sannan ta
shige toilet tayi nata wankan,ta shirya sannan suka sauko,sun tadda ummi itama ma
saukowa a dining suka hade baki daya harda eesha,a ladabce sumayya ta gaida ummi ta
amsa fuska sake tana tambayarta ya jiki tace alhmdlh
"Amma dai ai zuwa yanzu amai ya tsaya ko?" Kai eesha ta dago tana duban
sumayyan,tunda tazi take zargin hakan dangane da sumayyan saidai bata da tabbas sai
yanzu,kanta a qasa cikin jin nauyi ta amsa mata da eh
"Alhmdlh haka ake so Allah ya qara afuwa"
"Amin" tace da ita,kafin ta sake cewa wani abu yaron gidan da ummi ta aika ya soma
danna qararrawa daga bakin qofar falon,sumayya zata miqr ummin ta dakatar da ita,ta
miqe da kanta ta tafi amsowa,jawo kwanukan data yi abincin tayi ta soma budewa tana
zubawa cikin plates uku,nata ummi da sajida,yayin da eesha ke gefe daya tana jefa
chips bakinta,gaba daya abincin yayi mata,hakan ya sanya sumayya na gama zubawa ta
kai hannu ta bude ta janyi wani plates din
"Ci zakiyi ne?" Sumayya ta tambaya,don tana so ya kai mata ne har wajem sha biyu
zuwa daya kafin nan an gama girkin rana,din bata fiya son wahalar da masu aikin ba
tayi ta sasu dafa mata abinci kamar kanta aka soma ciki,banza tayi da ita kaman ba
da ita take magana ba,sai ma fara yunqurin diba da tayi,hakan ya qona ran
sumayya,hakan ya sanya ta sake maimaitawa
"Magana nake dake" sai a sannan ta daga kai ta dubeta
"Tunda ba abincinki bane saiki sauraramin ko?"
"Gaskiya kika fada,amma kiba nawa bane ni na dafa saboda haka sai wanda naga dama
sannan zaici" ta fada tana janye flask din ta maida murfin ta rufe shi ruf,sajida
ta miqawa tace ta kai mata daki,ta amsa kuwa tana murna ta haye saka da shi,din
jiya itama eeshan sai data zalunceta don kawai ta takata bata sani ba,hakan ya bata
ran eeshan matuqa,tana ganin kamar ita zata sumayyan zata yiwa haka?,idan ma da
tasan cewa ita tayi da ba zata nuna kwadayinta a kai ba,amma tunda har hakan ta
faru dole ta taka mata birki ko don gaba
"Kece matsiyaciya,ba sabanba,duk inda dan talaka yake sai ya nuna hali?" Idanunta
ta watsa mata,a fuska zaka rantse bata damu da maganar data watsa mata ba,a nutse
tace da ita
"Ko 'yar qaruna?" Isowad ummi wajen yasa sumayya ta ja abincinta ta soma ci,cikin
murmushi ummi ta dubi nata plate din ba tare data lura da sauyin yanayin fuskar
sumayya ba
"Wannnnan dai ba girkin uwani bane....sumayya ya aka haihu a ragaya?" Ta fahimci
sarai me take nufi,tuni ta hanata yin komai,itakam bata iyawa ta wuni sur ba tare
data tsinana komai ba,murmushi tayi kanta a qasa
"Ummi na gaji da kwanciya ne,sai naje ja tayata muka yi"
"Ki dai dinga kula,don wannan mijin naki wallahi yazo yaga ba dai dai ba sai ya
daga hankalin kowa" ta warashe tana dariya,ta ja plate dim gabanta ta soma ci cikin
zuciyarta taba yaba qwarewar girkin sumayya,gefe daya na zuciyarta kuma yana
tausayawa almustapha,tasan ko ba'a fada ba yayi kewar abinci mai kyau dadi da
tsafta.

        Eesha na gefe ta cika tayi bam,gani take maganar ummin na qarshe ma kamar
da ita take,wato ciki ne da ita shine take wannan iskancin?,jan kujerarta tayi baya
sannan ta miqe,binta da kallo ummi tayi sannan tace
"A'ah,ya haka"
"Na qoshi ne ummi,zan koma bacci" ta fada tan zare jikinya daga wajen
"Aikin kenan fa,sam baku gajiya da bacci,kudai rago ko don saboda aure"
"Uhmmm....." Kawai ta fada tana nufar daki.

        Ko data shiga kasa zaune tayi bare tsaye,ta kai ta kawo ta rasa
sakat,zuciyarta kaman ta fashe,batasan kishin sh'ad da takeyi salama bane akan na
sumayya sai yanzu,wayarta ta cilla saman gado sannan tabi lafiyar gadon tana
tunanin ina mafita?,tilas ta samawa kanta qofar shiga gidab mustapha koda tsiya
koda tsiyatsiya.

       Itakam bayan sun gama wucewarta tayi wajen anty maamaa,dawowarta kenan daga
sashen mai gidan wanda yanzun ya fita
"Uwar biyun mu" anty maama ke tsokanarta,dariya ta saka,tana jin kunyar antyn ita
kanta
"Baki gajiya kullum sai kinzo gaidani?,da kinyi zamanki ma" ta fada suna gaisawa da
sajida data rakota,hira sukayi sosai abinsu,anty maama babu ruwanta,tana da sauqin
kai da dadin zama tun asali,abinda yasa zamansu yayi qarko kenan da ummi.

      Suna tsaka da hira mahmoud ya shigo,ya sake wata qiba da haske,ta jima rabon
data ganshi,fuskarshi qunshe da murmushi yake fadin
"Antynmu matar yayanmu"
"Ka fadi haka mana tunda kayi wuyar gani kai da mus'ab,amaren ma rowarsu ake mana
har yau ba'a kawo mana su ba" ta fada cikin sigar tsokana,anty maama na gefe tana
dariya
"Habba anty,sashen naku ne kaman wani tsaro naga yaa man ya qara masa,tunda ya
fahimci alqasim abokina ne shikenan naga ya soma nima ciccije min,kinsan halin
mutumin sai a hankali,dama yaya lafiyar kura" ya fada bayan ya zauna daura da anty
maama yana dariya
"Kaci gidanku,yayanka ne,sannan banda tsaurin ido a gaban mace ka dinga sille mata
miji ha'an?" Dariya suka sa baki dayansu sannan suka fara gaisawa ya dora da cewa
"Amare gobe zasu zo dukansu,sun so zuwa dubaki ance bakiji dadi ba,to sai naji ya
man ya koma dubai na tsammaci tare kuka koma"
"Kace gobe muna da manyan baqi,to Allah ya nuna mana"
"Ke tsohuwa,yaiushe sirutunki ya ragu ne?" Ya tsokani sakida dake zaune gefe,dariya
ta saki
"Yana nan bai ragu ba"
"Au to,na fasa tayaki murnar da nayi niyya" dariya sunayya tayi,akwai wasa
tsakaninsu,shikam mahmoud ba ruwanshi,wani lokaci akwai ban dariya sumayya ta fada
tana dariya,hira sukayi abinsu sosai kafin daga bisani ta musu sallama ta koma
wajen ummi.

       Data koma eesha ce kawai a falon,itama bata zauna ba daki ta koma ta nade
kan gado,saboda lokacin yin wayarsu da almustapha ya kusa.

********   *****   *********

        Washegari akayi rasuea maqotan gidan baba prof,hakan ya sanya duka ummi da
anty maama basa nan suna gidan rasuwar,gidan daga ma'aikata sai ita sai
eesha,sajida ma ta bisu,ga baqi da zasu zo matan mus'ab da mahmoud,hakan ya sanya
bayan sun gana wayarsu da mama,zainab,halima,abdallah da yaya yahansu,kowa sai data
kirashi suka sha waya sosai,credit mai yawa ta qarar,sannan ta tashi ta shiga wanka
kasancewar bata yi wanka da wuri ba tana fitowa a wankan ta shirya cikin wani yadi
mai azabar kyau cikin lefanta,ta dubi kanta a madubi,ta zama wata classy
sumayya,ita kanta tasan ta sake kyau da sauyawa sosai,hannunta ta dora saman
cikinta data fara jin alamun dagawarsa,murmushi ta saki har cikin ranta tana jin
farinciki,tana qissima yaya almustapha zaiyi duk randa yazo yaga cikin nan ya
fito?,turare ta fesa ta yane kanta da siririn mayafi medium size ta fito daga
dakin.

       A falo ta samu eesha saman kujera qafa daya kan daya anata sana'ar danna
waya,daga kai tayi ta dubi sumayya,duk da batayi makeup ba amma ba qaramin kyau
tayi ba,ta dan zubawa material din jikinta ido,tana da irinshi,daga dubai mamarta
ta kawo mata shi,yana daga daga cikin kayan ta da take ji da su,wani kishi ya cika
kata ido,dinkin doguwar riga ne wanda ya fitar da sigarta,ta zuba saitin cikinta
ido,baiyi fitowar da kowa zai iya ganewa ba,amma matuqar ka qware wajen gulma sa
ido da iya munafunci kallo daya zaka yi masa ka gane tana dauke da yaron ciki,wani
abu ya tsaya mata a wuya,cikin da bai isa zama mutum ba ya tsone mata ido,saboda ta
fuskanci kowa maraba yake da shi,faranta ran kowa yake banda ita,land line dake
falon ta dauka tayi kira sashen ma'aikata,tayi sa'a kuwa baba uwanin ce ta dauka ta
buqaci ganinta
"Gani nan uwar daki" ta ambata,bata tsaya falon ba tayi shigewarta kitchen taba
jiranta,qwararan mintuna biyar saiga baban
"Baba....yaufa zamuyi baqi me za'a tana darmusu ne?,amarensu mahmoud?"
"Eh gaskiya ya kamata,me kike buqatar ayi musu?,ai saiki fada ki samu waje ki
zauna" dariya tayi
"Baba,wai haka zanta kwanciya kamar ruwa?,kema kin sani motsa jikin ai yana da
muhimmanci ko?,yanzu bari kiga" nan ta tsara ma baban abinda za'ayi,baba na tsaye
ita tana daga zaune suka soma aikinsu,suna yi baba na bata labaruka suna hirarsu
abinsu,kafin su kammala kusan shigowar eesha hudu,tazo ta bude freezer ta fice,ko
waiwayowa sumayya bata yiba bare ta nuna taga shigowarta,ita dai abun na daure mata
kai,ta rasa meke tsakaninsu?,bayan da suka kammala sumayya ta dora tuwan semo wanda
duja baifu malmala shida ba,tayi miyar kuka wadda taji nama da tantaqwashi,ita take
sha'awa,tana dab da barin kitchen din amira ta fado,daga gidan mutuwar take,saboda
suna da alaqa da familyn saifullahi
"Uwar biyu" ta soma fadi sannan ta bude freezer ta dauki ruwan sanyi ta sha sosai
saboda ranar da ake yi,sumayyan na tsaye tana dubanta
"Ya na ganki haka afujajan" kai ta kada
"Ke dai bari kawai,wallahi bacci kazo nayi kafin yamma na wuce gida,drivan ma na
sallameshi na karbi key din na koma da kaina" dariya ta danyi
"Wannan bacci wannan bacci amira anya qalau kike,jiya fa ina jiyo ummi na miki fada
kin dora girki kinje ki kwanta kin barshi ya soma qonewa,vanda Allah ya sanya mai
aikinki bata tafi gida ba gobara zaki hada"
"Shaye shaye na fara" ta fada cikin sigar tsokana
"Ko kuma da kin riga kin sha din ba" itama ta maida mata cikin tsokanar suka soma
takawa don ficewa daga kitchen din suna dariya
"Allah amiran yaya musty(da yake taa sauya mata suna)bansan meke damuna ba,yanzun
fa ko saif bana iya jira ya dawo kan ya dawo na jima duniyar bacci"
"Tabdi....kije kiga likita kam,Allah yasa kema kin biyo sahu?"
"Allah ko?,kaddau bakin saif ya kamani?" Ta fada tana fiddo ido
"Ke dalla,meye ne kika wani waremin idanunkin nan irin na yayanki kamar ni nayi
abun" ta fada sanda sukaqaraso cikin falon eesha na zaune,dariya amira ta saki har
da d'an ihunta
"Kice kawai yayana rikitaki yake da idanunshin nan,kinsan Allah sunfi nawa kyau,ni
kaina lokacin ina qarama cewa nake muyi musanye,Allah yasa ki haifo mana mai kama
da shi"murmushi kawai tayi tana tuna yanayin kallonshi,yadda ya iya hukunci da
ido,yana rikita ta ba qarya ba a duk sanda ya ritsata da kallonshi,murmushi ya
subuce mata a sarari ba tare data sani ba
"yar is,kinzo ko ki nemi hanyar gidan ko?,wallahi kada kiyi aure ki tsammaci zan
dinga jelan zuwa gidanki" sumayya ta tsinci amira na gayawa eesha,dariya eeshan
tayi
"Ke kuwa zuwa ya kama,idan akayi 'yar gida ai kinga ko bako qaunar Allah dole
kizo,ko banza na zama yayarki"ta fada da biyu,tabbas maganan ta samu shiga zuciyar
sumayya,ta kuma fahimci sarai inda zancan eesha ya dosa,saidai batasan ka wa take
maganan ba,mahmoud da mus'ab har yau basu cika wata biyu da aure ba,ya adam bai
garin ma baki daya matanshi biyu ga yara kusan hudu,ya girme mata ma
sosai,almustapha fa?,wani sashe na zuciyarta ya gaya mata,sai ta soma juya zancan a
hankali cikin ranta
"Ah lallai fa,ga mai yawan rai kenan.....kinga bacci zanje nayi na wasu
awannai,bari naje na dawo sai mu qarasa zancan....wai nikam me ya samu number
salama bata shiga?" Ta tambayi eeshan tana yin gaba
"Salama?,bakisan muhsin ya sauya mata layi ba,bikinta bai wuce one month ba yace
bai sonta da tsohon layinta,but dazun ma tace na tura mata num dinki ba mamaki kiji
ta kiraki"
"Kice akwai shagali....saura ku sai ku bada himma" ta fada tana dariya
"Me kike ci na baka na zuba" eeshan ta fada tana yatsina fuska
"Eesha shegiyar gari....wai ina bash ne?"
"Standby zaki ce,jeki dawo kizo na gaya miki"
"Alright"Amiran ta kuma fada tana bin bayan sumayya da tunitayi gaba.

       Suna shiga amira ta kama kafadar sumayya dake qoqarin daure gashinta don
shiga wanka
"ke wai baki karanci komai tattare da eesha ba?,ba kya ganin irin kallo da take
binki da shi" murmushi sumayya tayi duk da itama abun ya tsaye mata a rai,har yau
kuma bai daina bata mamaki ba
"Kinsan wai yaya man take so?"amira ta fada tana kecewa da dariya ta fada saman
gado,maganar ta daki sumayya,sai yanzu ta gano abinda ya sanya eesha bata
qaunarta,amma sai ta dake
"to Allah ya tabbatar da alkhairi" harara amira ta watsa mata sannan tace
"Haka zaki fada?,ke yanzu fatar kishiya kikewa kanki banda waccar da take gabanki?"
Cikin dakiya tace
"To meye?,bakiji abinda kema kika fada ba,nima wata nazo na taras"
"Amma wallahi baki son ya almustapha amira,da eesha da su'af meye
banbancinsu?,qasar haihuwa ce kawai ta raba su,ai ko mata sun qare bazan masa fatan
auren eesha ba wkh duk da tana 'yar uwata,amma duk dan uwa na gari zaya so yaga
nashi na auren magartacciyar mace kaman ke"
"Lallai kam,idan rabonshi ce ai ba wanda ya isa ya hana ko?" Ta fada a fili tamkar
ba komai,cikin zuciyarta kuwa kaman zata fashe
"Allah ya tsari gatari da saran shuka,kinsan ma duk cikin yaran family ba wanda sam
basa hada inuwa da yaya almustapha irin eesha?,itafa ta sanya ya saka dokar hana
samarinsu zuwa gidan nan matuqar suka zo hutu da sallah,tun randa ya ganta da wani
cikin mota suna har harkoki"
"To Allah ya kyauta,kedai kwanta kawai kiyi baccinki"ta fadi tana daukar towel
saboda ta sake watsa ruwa
"naqi din,kuma kamar a kunnen ya almustapha kin masa mugun fatan auren eesha"dariya
ta baiwa sumayyan saboda yadda tayi kicin kicin kaman ance mata saif zai qara
aure,toilet ta shige don ta tabbata ta biyewa amira sai su bata lokaci a wajen.

         Tana fitowa wayarta ta soma ringing,tana dubawa sunan almustapha ne a


sama,murmushi ya subuce mata,halan yau 'yan rigimar ne a kusa,dududu awa uku fa da
gama wayarsu,sai ta zauna bakin madubu ta daga kiran ta kara kunnenta tare da yin
sallama
"kewarki nake" ya soma fada,murmushi ta sake masa mai dan fidda sauti har cikin
kunnenshi
"Awa uku da rabuwarmu fa?"
"Jinta nake makan shekara uku,ummu abdallah kaman ma baki tausayi na,ashe haka so
yake wahal da zuciyar mutum?,kinsan yanzhn haka wani asibiti ke buqatar taimakona
za'a yiwa matan wani aiki amma na gagara zuwa,ko naje din ma nasan ba abinda zan
iya aiwatarwa....please my summy kiji tausayina mana" ya qarasge zanacan a
shagwabe,dariya ta saki salon magananshin ya tsumata
"Wallahi abu abdalla ka zama wami shagwababbe,anty su'ad ta lalata ka"
"Zaki gane hakan idan na kamaki a hannu,kinsan Allah....ranan ko babynmu bazan
tausayawa ba bare ke,zaki zo hannu" ya fada yana katse kiran,murmushi ta dinga
fiddawa,bata ajjiye wayar ba sai data tura masa sms da tasan zata haukatoshi sannan
tayi switchoff din wayar yadda koya kira bazai sameta ba,ido ta lumshe tana sakin
murmushi,ba qarta ita kanta tasan ba qaramin rashin mijinta tayi ba
"Laila majnoon,idan kun gama baqin sunzo" amira dake kwamce ta fada,ita kanta abun
ma burgeta,wato haka yaya almustapha yake baje soyayyarshi,amma idan ka ganshi a
waje sai kace wani zaki,musamman idan ya soma muzuran nan nashi ko bada umarni,baka
ce ya taba dariya ba,amma yanzu ya wani narke kaman dan yaye,sam ita sumayya ma ta
manta da ita sai da tayi magana
"To 'yar sa ido" dariya suka sanya baki daya,amira ta miqe daga saman gadon ta
zauna sosai
"Seriouse amiran yaya musty....wai meye sirrin don Allah,salon soyayyarkun nan a
bani nasha don Allah"
"Min indillah" ta bata amsa tana ciro kayan da zata saka
"Da gaske?"
"Biya sai na gaya miki"
"Ko nawa ne ko zan nada indai za'a gayan" dariya ta baiwa sumayya sosai,ita kanta
wani lokaci ta zauna ta kanyi mamakin kansu,ita da kanta batasan akwai duniyar data
qunshi zallar farinciki har haka ba sai yanzu,duba da irin bigire na nau'in rayuwa
daban daban data afka,taso mukhtar a sanda bata mallaki hankalinta ba,a sanda bata
banbance so qauna da shaquwa,wasu mata sun shiga rayuwarsu sun kawo naqasu wa
farinciki da shaquwar dake tsakaninsu,sannan bayan duka wannan tazo ta rashi a
sanda bata da kowa sai shi kadai ta mallaka,bata saba da kowanne namiji ba sai
shi,tazo ta auri lukman bisa tsautsayi da qaddarar data hauta na dole sai ta shiga
rayuwar wasu,daga qarshe ta samu almustapha,wanda ta sameshi ne a lokacin da
hankali ya gama gameta,ta gama sanin zaqi da madaci,so qauna da shaquwa da
kuma,tasan dama da hagunta.

         Aina da asma'u sune matan mus'ab da mahamoud,dukkaninsu basu fi sa'annin


sumayya ba,koda zata girme musu bazata basu shekara ba,bare kana ganinsu zaka musu
kudin goron sa'anni ne,dukkaninsu wayayyu ne masu matuqar kirki,karatunsi da
wayewarsu bai hanasu kasancewa 'yammata nutsatstsu masu cikakkiyar tarbiyya
ba,kowacce ta samu tarbiyya daga gidansu,kamar asm'u wadda makaranta daya sukayi
karatu da mahmoud wata private university dake nan garin abuja,saidai tana matakin
farko ne mahmoud yana matakin qarshe,kamun kanta da nutsuwarra shi ya fara jan
hankalinsa,abinda bai fiya gani ba wajen 'yammatan dake manyan makarantu na
jami'o'i,bare irin nasu makarantun na yaran masu da shi,kowacce ta dauki tabara da
rashin tarbiyya rashin cikakken kamun kai a amtsayin wayewa,wannan ya zama ruwan
dare cikin makarantunmu na walau na gwamanti ko kuma na kudi.

      Dukkaninsu suna da kyau  abinsu,faran faran da mutane,nan suka hadu suna hira
abinsu,irin hiran farkon haduwa ba sakin jiki can da yawa,eesha na gefe tana hura
hanci,ta dora qafa daya kan daya,ta san asm'u,duk da wuce asm'un da aji daya,hakan
ya sanya ko ayanzun ka take jin ta fita,gidan 'yan uwansu take,bugu da qari ita
dangin miji ce,su dinma da yake kowacce ta iya takunta daga gaisuwa basu damu da me
take ba,a haka ummi tazo ta taddasu,hakan ya mata dadi qwarai,ta kuma yaba da
tanadin da sumayya tasa aka musu,hatta da anty maamaa sai data ji dadi,duk da
alkunya data yi tace baqin ummi ne dama,sunje dai sun gaisa da ita sannan suka dawo
suka ci gaba da sabgoginsu.

         Basu tafi ba sai yamma liqis bayan sunyi musayar lambobin waya,cikin motar
mus'ab duka zasu koma,sun tafi suna yabawa da sumayya,cikin qanqanin lokaci suka
saba da hirarta suka a baki suka isa gida.

        Tunda suka tafin eesha ta dawo falon qasa ta zauna bayan data tabbatar ta
gama shirya duk wani abu data tanada,rana saka ran cewa wani dalili ya sauko da ita
daga dakinta zuwa kitchen din,hakan ya sanya ta kasa ta tsare ta zauna a falon,tana
danne danne waya tare da kallon wani film a MBC action amma rabin hankalinta ja
matattakala zuwa qofar kitchen din,duk wani ma'aiki da zai buqaci shiga kitchen din
ta sallameshi tun yamma,ummi dama ita ke da girki taga fitarta zuwa sassan baba
prof.

         Sajida ce ta sauko da sauri sauri,sannan da hazarinta irin mai tattare da


quruciya ta nufi kitchen din,cikin hanzari ta dakawa sajidan wata iriyar tsawa data
sanyata tsayawa cak
"Uban me zaki shiga ciki kiyi kanki na rawa?" Kaman zata saki kuka tace
"Anty amira ce tace na dauko ovaltine zata hadamin wani abu" sosai abin yayi mata
dadi,da alama haqanta zai cimma ruwa,sai ta sake kaurara murya tana zare mata ido
"To koma kije kice mata nace ba zaki shiga ba,idan ta matsu ta sauko da kanta ta
diba" tsayawa sajida tayi tana dubanta,don a ganinta ita kanta eeshan ta yiwa
sumayya rashin kunya,bugu da qari ma gidan ba wanda akewa get na amfani da wani abu
tunda basu gaji rowa ba,kowa na gaban kanshi je ciki kuwa harda ita eeshan
"Ba zaki wuce ba kika tsareni da ido ko sai na qaraso nan na babballaki na zubar"
ganin hargagin da take mata ya sanya ta dole komawa saman da sauri.

        Sumayyan na zaune riqe da qaramin qur'ani tana karanta falaq da nasi da


ikhlas tana qarashe addu'anta sajida ta dawo,maganan da eeshan ta gaya mata ta
daure mata kai,bata ce komai ba ta gama addu'ar ta shafa,sannan ta miqe da hijabin
jikinta tace da sajida
"Zauna,bari na debo miki"
"To" sajidan ta fada sumayya ta fice,dadi ne ya dinga ratsa eesha sanda taga
sumayya ta shige kitchen din,tuni ta ajjiye wayar gefe ta miqe tsaye tana shirin ko
ta kwana murmushi na fita a fuskarta.

        Sam sumayya bata lura ba har sai data dauko gwangwanin ovaltine din ta
dauki hanyar fitowa,ji tayi ta tafi baki daya sululu zata kifa ta baki
"Hasbunallahu wa ni'imal wakil" ta furta,cikin wani irn hanzari ta saki gwangwanin
ta dafe freezer dake daf da ita,duk da haka sai da qafarta ta amsa ta rintse ido
tana sake kiran sunan Allah,da gudu taga shigowar eesha wanda hakan har yaso ya
sake firgitata ta soma dudduba jikin sumayya tana cewa
"Innalillahi wa inna iliahi raji'un,me ya sameki?,kinji wani abu ne?,me ya samu
jikinki?" Shigowar ummi cikin rudani wadda shigowarta falon kenan taga eesha ta
runtumo kitchen din da gudu ta biyo bayanta,sumayya ta soma yu qurin tashi ummi ta
nufeta,eesha ta dakatar da ita tana qarasawa wajen sunayya tana taka wajen cikin
taka tsantsan ta kama sumayya tana dudduba qasan data fadj
"Ai babu ma abinda ya sameki" eeshan ta fada haushi na cikata,so tayi tazo ta ganta
male male cikin jini,ta fadi kan cikinta tayi barin dan tayin dake cikinta,wani
irin kallo sumayya ke bin eesha da shi wanda ita eeshan bata kula ba,baqincikin
rashin cimma nasarar da bata yiba kadai ya cika mata qoqon zuciya,ta dora dukkan
alamomin tambaya kan eeshan,zainab ce ta fara fado mata a cikin abdallah,take
jikinta yayi sanyi,gabanta ya yanke ya fadi taci gaba da nazartar eeshan a
fakaice,duk wasu abubuwa da take son gani ta samesu,tuni ta janye baya ta bar
sumayya hannun ummi ummi na duban wajen
"Me ya kawo miyan kuka nan wajen har ya janyo miki faduwa,subhanallah" ummi ta fada
tana janye sumayya daga wajen
"Ita tayi ta mai shegen warin daddawa" ta fada tana yatsine fuska,kai sumayya ta
gyada
"Ni nayi,sai gata kuma ta taho har nan" ta ambata tana duban eesha,dauke kanta tayi
ta juya ta fice daga kitchen din tana kumbura
"Bakijin dai komai a jinki ko?"
"Eh ummi,ba komai" ta bata amsa tana miqewa
"Bi a hankali,idan kina jin wani anu ki fada,don Allah nidai daga yau na yafe
shigowa kitchen din nan" ummin ta fada cikin damuwa
"To ummi" ta fada tana nufar qofar kitchen din,zuciyarta cike fal da mamaki,me ta
yiwa eesha,don tana son almustapha sai ta nemi rayuwar dan cikinta,d'an kuma wanda
take iqirarin tana so,lallai dole ta sanya ido da takatsantsan da eeshan,don ba
zata taba lamunta yaran da tun kafin ta haifesu su dinga shan wuya ba haka kawai ba
tare da laifinsu ba,biyo bayanta ummin tayi,sai data sake tabbatarwa komai lafiya
sannan hankalinta ya kwanta,saukowa qasa tayi,ta tara ma'aikatan dake kula da
kitchen baki daya ta tsawatar musu,sannan taja kunnensu da kada ta kuma gani sun
bar sumayyan ta shiga kitchen sannan ta sallamesu kowa ya koma muhallinsa bayan sun
gyara gurin.

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

9⃣9⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

*Allah S W T yana cewa*

*duk wanda ya aikata daidai da qwayar zarra na alkhairi(komai qanqantarsa) zai


gani(cikin littafin ayyukansa,zai ganshi a rubuce kuma za'a masa hisabi da hukunci
a kansa),hakanan duk wanda ya aikata dai dai da qwayar zarra na sharri zai ganshi.
__________________________________________

          Tun daga lokacin sumayyan ta zubawa eesha ido cikin nutsuwa,tana kula da
takatsantsan da duj wanu taku nata,a bangaren eesha kuwa ko daya bata sauya
qudurinta ba,ko da yaushe tunaninta daya na yadda zata illatar da sumayyan ne.

   ******    ******    *******

      Qarfe goma da rabi ranan ta sauko bayan farkawarta daga bacci wanda kusan
almustapha ne ya tasheta,sai data gama biye masa sannan ta shiga tayi wanka ta
shirya ta sauko don ta karya,bata da damuwa tasan cewa komai na shirye,tun daga
randa wancan abun ya faru bash sake barinta shiga kitchen ba.

        Tare suka sauko da sajida,ummi na sashen anty maamaa,sajida ta wuce dining


don ta karya,ita kuma kiran halima da ya shigo wayarta ya sanya ta wuce saman
kujerun falon ta zauna tana amsawa,qarar sajida data jiyo shi ya sanyata sakin
wayar ta miqe,bata jin nauyin jikinta haka ta nufi sajida da tayi zaman 'yan bori
saman step na dining area,wajen ta isa tana dagata gami da tambayarta
"Faduwa nayi anty" ta bata amsa tana shirin sakin kuka saboda qafarta ta bugu
sosai,idanunta sumayya ta kai wajen sai taga ruwa ne ya zube wajen
"Ya akayi kika zubda ruwa haka sajida?"
"Bani bace nima haka naga wajen,kuma ban kula ba har sai da na fadi" wani tunani ne
ya darsu ran sumayya,ta sanya hannun ta cikin ruwa sai taji yana santsi da qanshin
klien,to waye ya zubda ruwa haka?,tasan cewa babu yadda za'ayi ma'aikatan su zubda
ruwan su tafi ba tare da sun gyara ba,ummi bata nan sajida ba ita ta zubar ba
"Eesha" zuciyar sumayya ta raya mata,kai ta girgiza,batason ta zargeta bayan bata
gani da idanunta ba,riqe sajidan tayi don dawo da ita saman kujera,tana juyowa suka
hada idanu da eeeshan,sai ta juya ta shige dakinta,mamaki ya kama sumayyan,wai me
eeshan ke nufi,take ranta ya baci,ta zaunar da sajida saman kujerar ta kama qafarta
tana mammatsawa,gefe guda ke mata ciwo,sai ta isa bakin dispenser ta tari ruwan
zafi ta dawo kusa da sajidan ta gasa mata qafar sosai,cikin ikon Allah wajen ya
saki,ta shafa mata man zafi a wajen sannan taje da kanta ta goge wajen sannan ta
hada mata abin break din taci ta kwanta.

       Tana saman kujera zaune kanta a qasa,ranta a tsananin bace yake,don me zata
dinga neman cutar da ita?,tana tunanin dai dai gaggawar unguwar zoma ta bari a
haihu ko?,ta bari su hada miji tukunna,meye na hanzarin son cutar da ita tun
yanzun,saqar data dinga yi kenan cikin zuciyarta,qara qofar dakin eesha tayi,itace
ta bude ta fito,tana tafe dai dai ta hura hanci,idanunta da suka kada saboda bacin
rai ta zuba mata
"Aisha..." Ta kira sunanta cikin kakkausar murya wadda ta sanyawa eeshan tsayawa ta
kuma juyo tana dubanta
"Jan kunne nakeso nayi miki na qarshe....duk abinda zakiyi kiyi qoqari ya tsaya iya
ni,kada ki bari sarkarcinki da haukanki ya sake taba wani cikin gidan nan,yanzun da
kin karya musu yarinya kuma kice me?,haka rannan kika watso ruwan zafi saura kadan
a fuskar sajida,kina gidan kakanninta kina cin arziqinsu kina neman salwantar musu
da jikoki?"maganar sumayyan ta qarshe ta sosa mata rai,ita zata yima gori bayan ita
ya cancanci ta yiwa gori
"idan kuma banji jan kunnen naki ba me zaki iya diyar malamai masu ci da buzu da
tawada?"murmushi ta sake mata sannan ta bata amsa cikin nutsuwa
"alhamdulillah da na kasance diyar malamai magada annabawa,zancan rashin jin
gargadina kuwa....koni zan iya miki hukunci.....amma da yake ni din mai uwace a
gindin murhu,kunnen mutum daya maganar zata je kiga yadda dunuyarki zata gigita" ta
fahimci sarai tana son hadata da almustapha ne ko shi ko baba,to har gwara ma baban
akan shi din,kuma ta sani sarai qarshen lamarin bazai mata da dadi ba
"Duk abinda zakiyi baki isa ki hanani shiga gidan almustapha ba wallahi,baare ma ya
sameshi bare kuma na gida" murmushi ta kuma yi
"Kan me zan hanaki dama?,nima fa wata ta taras,sannan kuma ba kanku na soma zama da
abokan zama ba,abu guda kawai nakeso daga gareki.....koda zaki auri almustapha to
ki kiyayi taba lafiyar jama'ar da basu ji basu gani ba.....ki taqaita
haukanki....ki adana shashashanki har zuwa sanda zaki shiga gidan nashi"tana
yunqurin maidawa ummi tayi sallama,hakan ya sanyata dole yin shiru,bata ji ke suke
fada ba taga dai sajida kwance
"a'ah lafiya kuwa?" Ta tambayi sajidan tana dubanta
"Ruwa ne ya zube sai na fadi" ta bata amsa,gefe ummin ta samu ta zawa
"garin yaya ruwa ya zube a wajen?" Ta tambaya cikin mamaki,wannan karon sumayya ce
ta karbi zancan
"Wallahi ummi,sashen dai ba kowa,ni da ita kuma tare muka sauko sai ihunta kawai
naji" waiwayawa ummin tayi tana duban eesha
"Aysha ya akayi ruwa ya zube wajen?"
"Nima ummi ban sani ba"
"Bake na bari wajen ba kina karyawa?" Sai ta langabar da kai
"Tea ne ummi,ina so ma goge kuma na mance naje na kwanta"
"Amma ya kamata ki dinga kulawa tunda kinsan yadda wajen nan ke da santsi,ko su
lami kika saka zash goge,yanzu da amira ce ta taka wajen Allah ne kadai yasan me
zai faru,ki kula sabida gaba"
"To" ta fada tana zumbura baki ta koma daki,ranta cike fal da baqincimi,ita wacce
iriyar mara sa'a ce,kuma wai ummin har take goyon bayan wata bare a kanta,lallai
kam ba zata qyake wannan abu ba zatayi mai gaba daya ne kawai komai ta fanjama
fanjam,ruwa ummi ta buqata ta gasawa sajida wajen,sajidan tace ai anty ta gasa
mata,hakan yayiwa ummin dadi,daya daga cikin abinda yasa har kullum take sumayyan
ke sake shiga ranta kenan sanin ya kamata,ba qaramin jin dadin zama take da ita
ba,ba shakka da zaiyiwu riqe sumayyan zatayi wajenta har ta haihu,amma tasan hakan
ba maiyiwu wa bane,ita kanta tasan alkunya almustapha kawai yake mata,wanda dukkan
alamu sun nuna ya fara gajiyawa,don ya soma yi mata qananun qorafi,ko haka kawai ba
gaira ba dalili sai ya dinga tashinta cikin dare yana sata kaiwa sumayya waya.

***** ******** ******

Kimanin takwas ne na dare yau ta kwanta da wuri,so take tayi bacci sosai,jin
kanta take kamar wadda ta shekara batayi bacci ba saboda yau tayi tashin wuri,don
haka yau tun magariba ta kashe wayarta don ta huta sosai,har ta kwanta qishirwa ta
tasheta,ta miqe ta zura hijabinta ta sauko qasa,cikin sandata bude fridge ta dauki
ruwa saboda duk saman babu ruwa mai sanyi,ummi ta hana ta sha shi yasa ake ajjiye
mata mara sanyi,ita kuma qaunarshi take,idan bata sha ba har wani abu take ji ya
tokare mata qirji.

Tana tsaka da bude robar taga fitowar eesha ta haura sama,da alama wajen
ummi zata,kamar tace mata ummin na sashen baba sai kuma ta fasa tunda ba shirginta
take shiga ba,ta kammala shan ruwan ta ta maida robar ta rufe ta kama matattakalar
benen ta soma haurawa saman,tana tsakiya eeshan ta fara saukowa,bata dubeta taci
gaba da hawa abinta,tana step din qarshe eeshan ta iso inda take,wata wawuyar
bangaza da bata zata ba bare tsammata eeshan tayi mata,wanda hakan ya sanya
sumayyan yin taga taga baki daya tayi baya,ta gama saddaqarwa ta gama yawo,saboda
step.ne ya kusa ashirin wanda ba shakka idan har ta samu nasarar komawa da baya sai
ta gangara ta kan kowanne,cikim azama tare da kiran sunan Allah taji kamar an
turata gaba,singalin qafarta ya daki qasa ya bafa wata qara,ta sanya hannayenta ta
dafe qasa sanda take faduwa,wanda banda hakan da saman cikinta zata fada,suma
hannayen qarar suka bayar ta zube ta gefen hannunta na dama daidai sanda taji
muryar ummi cikin qaraji tana fadin
"Hasbunallahu wani'imal wakil,innalillahi wa inna ilaihi raji'un aisha!!" Ta
qarashe fadi tana haurowa saman cikin wata iriyar sassarfa da gaggawa,idanu eesha
ta soma fiddawa gabanta na wata matsananciyar faduwa,tasan tata ta qare,ya akayi
har ummi ta iso wajen bata lura ba?.

Tuni ummi ta isa inda sumayya ke yashe,azaba da radadin da hannunta da


qafarta daga buge kadai sun isheta,ambaton sunan Allah akwai take tana jin yadda
qashin qafarta ke zugi da tsuko,a rude ummin ke tambayarta da qyar ta bata amsar
qafafunta,ta matsa qafar sai ta sanya qara sabida azaba,cikin matsanancin bacin rai
ummi ta waiwaya ta dubi eesha
"Ashe baki da hankali eesha?"
"Wallahi ummi....." Ta soma fada cikin rawar jikibda rawar murya,tsawa ta daka mata
wadda ta sanya hantar cikinta kadawa tana gaya mata ta bace da wajen,sai da taga
saukarta sannan ta maida hankalinta ga sumayya taba mata sannu,tausayinta na
kamata,taimaka mata tayi sai data jinginata da kujera sannan ta dauki waya ta kira
baba da anty maamaa.

Kusan lokaci daya suka shigo,salati anty maamaa ta dinga yi,shi kanshi baban
shiru yayi ranshi na sosuwa,ba bata lokaci ya kira driver yasa ya fito da mota suka
sanya sumayyan ciki
"Inaga ba asibiti ya kamata aje ba,wajen masu gyara za'aje a duba mata qafan da
hannun,tunda Allah yasa bata fadi kan cikin ba" inji ummi,hakan ya sanya baba ya
kira mutumin dake musu irin wannan aikin,basu da nisa sosai shi yasa bai bata wani
lokaci ba ya iso.

Sai daya duddubata sannan ya tabbatar musu qafarta gocewar qashi ce,hannun
kuma targade ne,zaiyi mata gyara,dui wanda ke wajen sai daya tausaya mata,tasha
wuya sosai wajen gyaran,haka ta dinga hada gumi taba kiran sunan Allah kaman zata
suma,murqususu take ga ciki a gaba daya fara tasawa,kafin a gama ta hada gumi
sharkaf,ya gama ya baiwa ummi maganin da za'a ringa shafa mata da kuma yadda za'a
kula da wajen,yace duk bayan kwana bibbiyu zaizo ya dinga dubawa,godiya baba yayi
mishi sannan ya sallameshi.

Kusan kasa runtsawa sukayi baki daya,sai daga bisani baba ya fara
tafiya,anty maamaa kam bata iya tafiya ba ita kanta sai wajen biyu na dare,ummi
kuwa kwanan zaune tayi tare da sumayyan,sajida ma da qyar tayi bacci,duk tausayin
sumayyan ya cikata,eesha kuwa tunda ta shige ba'a sake jin motsinta ba,ita so tayi
cikin ya zube idan yaso ayi mata hukunci baki daya,ran ummin ya kai maqura wajen
baci,tausayin sumayya kawai ya isheta,ta riga ta gama yanke hukunci a gobe aysha
zata bar gidan,kome mamanta zata fada saidai ta fada,don ba zata yarda tana jibtana
gani a bata amana ba kuma ta kasa riqewa,me zata cewa almustapha idan wani abu ya
samu cikinsa?

A dakin ummin ta kwana,nan ummi ta kawo mata ruwa da roba ta daura alwala
saboda yadda qafar tayi mata tsami,a hankali ta waiwayo tana gaida ummin bayan ta
idar da sallar,amsawa tayi tana tambayarta jiki ta amsa mata alhmdlh,sannu ta sake
mata tare da bata baki kan abinda eeshan tayi,ita kunya ce ma ta kamata,sai kace
ummin ce ta aikata?.

Qarfe biyun rana ummi ta isa dakin eeshan ta taddata kwance,zumbur ta miqe
tana gaidata,a tsautsaye ta amsa tana ajjiye mata kudi
"Ki tashi maza ki shirya ki wuce gida,koda wasa kada kice zaki sake dawowa gidan
nan a yanzu,tunda ba yau ashe kika soma qoqarin aikata mata hakan ba,idan banda
tsabaar rashin mutunci eesha bata ci darajata ba a wajenki?,ko duka bata ci darajar
wannan ba ai taci darajar dan tayin dake cikinta ko?,to ki tashi ki shirya ki wuce
gida" kuja eesha ta saki,abinda take bege wato so yake yayi mata nisa,garin neman
gira zata rasa idanu
"Yanzu ummi sabida ita zaki raba zumuncin dake tsakaninmu?" Cikin mamaki ummin ta
waiwayo tana dubanta
"Van raba ba,amma a yanzu dai na raba har sanda zata bar gidan nan,na riga na gama
magana da mamanki" ta juya tana ficewa,abun takaicin ma sam bata ga nadama tattare
da ita ba,don ko qafar benen bata taka da niyyar zuwa dubata kan abinda tayi mata
ba.

Wunin ranar yini tayi tana tofa fatiha a wajen,haka ya kawo mata sauqi
sosai kan radadin dake damunta.

****** ***** *******

Ranar da abin ya faru baki daya bai samu zama sosai ba,ayyuka sunyi musu
yawa can company,sau uku yana kira yaji a kashe.

A gajiye ya dawo,a falo ya sami su'ad din,tana kwance dai dai saman
kujera,sanye da gajeran wando da qaramar vest iya ciki,ko ina baja baja da kwalayen
data gama ciye ciye,yayin da bacci mai nauyi yayi awon gaba da ita,tsallaketa yayi
ya nufi bedroom dinshi kai tsaye ya rage kayan jikinsa,duk abinda yake tunanunta na
mqale a ranshi,yau daya tak da baiji muryarta ba jinsa yake kaman maraya,yayi
tsammanin zai iya share mata kaman yadda ta shareshi amma sai yake ji abun ba mai
yiwuwa bane a wajenshi,towel ya dauka ya wuce bathroom yayi wanka.

Ko mai bai iya shafawa ba bare ya ya sanya kaya ya janyo wayarshi ya soma
lalubar wayarta,a kashe aka sake ce masa take,sai yaji hankalinsa bai kwanta,lambar
ummi ya soma laluba cikin sa'a ta shiga,fitowar ummin daga dakin kenan taga
shigowar kiran
"Ummi an yini lpy?"
"Lpy lau almustapha ya aiki?"
"Alhamdulillah" sai kuma yayi shiru,halin nashi ya motsa,itakam da zaiyu shirun da
yafi mata,tasan wal'alla sumayyan yake nema,ita kuma batasan zancan yaje
kunnenshi,tafiso matarshi ta warke saidai yazo ya tadda labari kaman ma ba'a yi ba
"Ummi.....sumayya" ya fada kaman mai tsoron fadin
"Uhmmmm,wani abu ne?"
"Tun jiya bamuyi magana ba,ko zan samu jinta?" Kaman ta hanashi saidai ba yadda
zata hanashi magana da matarshi
"Kashe zan kai mata"
"Ummi batta a haka zan jira" dariya ma yaso bata har sai data ce
"Almustapha?,kaman wanda network din zai gudu?" Kunya ta kamashi amma sai ya dake
yayi shiru yana sauraron tafiyar ummin.

Tana zaune ta gama shirin baccinta tana karanta wani qaramin littafin
labarai na larbci,qafarta na saman matashi mai laushi,hannunta daya na ajjiye saman
cinyarta,wayar ummi ta miqa mata tana cewa
"Almustapha" littafin ta ajjiye ta karba gabanta na faduwa ta kara kunnenta sanda
ummin ke juyawa ta fice,shiru yayi kawai yana saurarenta tamkar baya kan layin yana
hadiye wani abu,fitar numfashinta kawai ya soma samar masa da nutsuwa,sallama tayi
masa sai da ya bada tazarar wasu sakannni sannan ya amsa
"Why sumayya why?,wato idan ban nemeki ba ba zaki neme ni ba?"
"Ba haka bane.....wayarce bansan inda ta fada ba"
"Kaman yaya?" Ya tambayeta,da sauri ta gyara zancanta
"Amm...ina nufin ta dauna daukan chargy ne" tsaki ya ja sannan yace
"Kamanni ace wayar matata ta har takai matsayin da don kanta zata daina daukan
chargy?,ki cire layukanki ki bar amfani da ita,gobe da safe za'a kawo miki
wasu,daya ni kadai zan dinga kiranki da ita always ta zama akunne kusa da ke,dayan
kuma ki kira duk wanda kika ga dama"
"Na gode Allah ya saka da alkhairi ya qara arziqi"
"Amin.....nifa gaskiya na fara gajiya,haquri na ya kusa qarewa fa....a qa'ida ai
cikinki ya shiga wata uku...am a doctor nasan yadda zan kula da mata ta" gabanta ya
fadi,yau bisa dukkan alamu rigima yake ji tunda taji muryanshi ta fuskanci
haka,tayi qas da murya
"Habba mana.....duka saura sati nawa lokacin da suka ce ya cika,ka qara haquri mana
please kaji?" Shiru kawai yayi yana sauraren muryarta yana nazari
"Me ya sameki?" Taji ya furta kai tsaye,sai ta hau fiddo da idanu tana kalle
kalle,ta daga wayar ta duba voice call ne ba vedio call ba bare tace yana ganinta
"Ni?...ba bau komai me ka gani"
"Akwai wani sauyi tattare da muryarki,kuma jikina ya bani haka"murmushi tayi duk
don ta dauke hankalinsa
"wrong doctor,baka canka dai dai ba,am fine,ina shirin yin bacci ma ummi ta shigo"
"Ban yarda ba,but....tunda kince haka ne is ok,ki kunna wayarki kafin a kawo wata"
"An gama yallabai" murmushi yayi,yanajin kaman tana lallabashi ne kawai ya sauka
daga kan layin,sai kawai ua datse kiran yana jin wayar kawai bata yi masa
ba,jikinsa bai bashi ba,sam ma ba irin wannan hirar yakeso suyi ba,hankalinsa baki
daya yayo nijeria.

Ajiyar zuciya ta saki da taga ya datae layin,da alama halin ne yau ya


motsa,dole ta tashi sajida ta sanyata ta dauko wayar ta jona a chargy sannan ta
kunnata kafin ta kwanta.

****** ****** *******

Washegari misalin sha daya na safiyar ranan yana tsaye gaban mudubi yana
shiryawa,kominshi a nutse a tsare,ya gama komai tsaf yana taje sumarshi ya janyi
wayoyinshi dake gefe,tun jiya da ita ya kwana cikin ranshi,yana jin mawuyacine idan
baiyi rashin ta ido ba yaje kawai ya daukota,yana jin kaman sun shekara goma ne
basu ga juna ba,number baba ya soma don ya gaidashi kaman kowacce safiya,idanunshi
suka sauka kan takardar dake gefanshi,ya saka hannu ya dauko ya bude ta,ranshi ya
baci sosai ba wai don kudin da ya kashe kawai kan takardar ba,sai na yanda su'ad
tayi burus da maganarshi.

Yana tsaka da duban takardar ta fito daga wanka tana tsane jikinta da towel
"Yanzu wai har ka shirya zaka fita,nifa gaskiya na gaki da wuni a gida ni kadai
kaman mayya,bayan nasan wuraren shan iska birjik amma ka hanani zuwa ko guri daya"
"Mene wannan?" Ya tambayeta yana nuna mata takardar,daga kai tayi ta kalleta sai
kuma ta basar tana hade rai
"Nifa gaskiya banda interest shi yasa na ajjiyeta" ranshi ya kuma baci,ya gyara
tsaiwarshi yana kafeta da idanunshi masu sanya mutum yin laushi
"Kinsan nawa na biya miki?,kudin mutum nawa na biya ake kadai don kije ki koya ke
kadai din?"
"Sai na biyaka kudinka kamin total,amma bazan iya zuwa ba gsky,ai ba ajina bane ba
aganni wani ina koyon girki,haka kawai Allah ya maka arziqin da zamu iya daukan
kowanne irin cook kawai sai na bata wa kaina lokacin koyon dafe dafe?" Ta amsa
mishi ba tare data dubeshi ba ta soma shafa mai,kai ya gyada yana qoqarin hadiye
bacin ranshi,ya maida takardar saman madubin ya ajjiye,shi kadai yasan hukuncin da
zaya yanke mata,sai ya janyo jakarshi ya riqe a hannunshi,daya hannun kuma yana
riqe da wayoyinshi ya soma takawa zai fice
"Ka mance yau zani siyayya?" Ta furta cikin harshen nasara,banza yayi da ita yaci
gaba da takawa har ya fice.

A falo ya tadda mai musu girki ta kammala shirya abinci,cikin girmamawa ta


rusuna da harshen larabci ta gaidashi ya amsa yana tsaidara,jakarsa ya bude ya
fidda rafar kudi irin na qasar dubai masu azabar kauri da yawa ya miqa mata,shaida
mata yayi ya sallameta a aiki ga wannan taje na nemi sana'a tayi,cikin rawar jiki
ta sanya hannu biyu ta amsa,ita kanta tasan kudin ba qananun kudi bane,zasu isheta
yin duk sana'ar da takeso,tabbas ba qaramin taimakonta yayi ba,ta duqa tayi masa
godiya mai yawa sannan ta fice.

Yana kurbar tea yake lalubar lambarta,muryarta kawai yake so ya soma ji a


wannan safiyar kafin ya fice,daidai lokacin da a wancan bangaren sumayya take
takawa a hankali har ta fice daga dakin saboda mai gyaran ya gaya mata ta dinga
takawa ko yaya ne.

Sajida na tsaka da mopping tsakar dakin ta jiyo ringing din wayar


sumayyan,ajjiye mop stick din tayi ta nufi inda wayar take,sai taga sunan man,tasan
halinshi sarai,idan ya kira mamarsu kiran ya zama miscal yayita fada kenan,hakan ya
sanya ta daga ta sanar masa yanzu zata kaima sumayyan kada ta zama
misscall,gaidashi ta soma yi sannan tace
"Antyn ta fita tattaka qafarta,amman bari na kai mata" jikinshi ya sake bashi irin
yanayin jiya,sai ya ajjiye cup din hannunshi yana tattara hankalinshi gareta
"Tattaka qafarta?,me ya samu qafan?" Ya tambayeta yana addu'an kada dai ace cikin
ne ya soma sanya mata kunburin qafa har yanzu
"Faduwa tayi" gabanshi yayi wani mummunan faduwa,a rude yace
"Subhanallah?,garin yaya?"
"Anty aysha ce ta turota daga upstair" bai san sanda ya miqe tsaye zumbur ba,cikin
matsanancin tashin hankali da qaraji yace
"Upstairs?,mahaukaciya ce ita?,me ya sami qwaqwalwarta?"tsoro ya kama sajida kaman
ita tayi laifin,cikin rawar murya
"ban sani ba uncle"ganin yarinyar ta tsorace ya sanyashi qoqarin sanyaya ranshi
saidai bakan ya gagara,sai ua rage sautin muryarshi yana tambayarta yadda akai abun
ya faru,bata boye masa komai ba ta kwashe duka ta gaya masa,harda nata wanda ta
zuba ruwan klien ta fadi,ranshi ya kai qololuwar baci
" kada ki gayawa kowa munyi waya kin gayan me ya faru,ok?"
"Yes uncle" ta fada tana addu'a cikin ranta Allah yasa unclr man yaci uban anty
aysha,dama taji haushi sosai abinda ta yiwa anty amira,har kuka tayi,kullum kuma
sai ta tausaya mata idan taga tana dingisa qafarta.

Ya jima jingine jikin kujera yana huci shi daya kamar wani mayunwacin zaki,ya
rasa wanne hukunci ne ya dace da yarinyar,ba shakka mutum biyu ne rak a duniya
zasuyi masa haka ya qyalesu daga ummi sai baba,ya kamata ya nuna mata wa ta tabo,ya
kamata ta gane kuskurenta,baiga dalilin ma da zai sanya ya qyale ta ba,data aikata
mishi wannan abun data aikata din gwara tayi masa gagarumar sata,gefe guda haushin
sumayyan ya kamashi,don me zata boye mishi?,me yasa ba zata gaya mishi ba,yanzun da
wani mummunan abu ne ya sameta haka zata yi shiru,batasan muhimmancin lafiyarta a
gareshi ba?,kai bama lafiyarta ba,batasan muhimmancin kanta baki daya tattare da
tashi rayuwar ba,bazai iya jira har sai ya koma gida sannan ya dauki mataki
ba,hakan ya sanya ya soma lalubar lambar CP,bugu uku kacal ya daga,bayan gaisuwa
sama sama da kuma ya bayan saduwa ya soma shaida masa abinda yake da buqata,eesha
yake so su kamo mishi ita su sanya masa ita bayan kanta,kuma ko waye yazo nemanta
kada su sake su bada ita,kai baya so ma su bari asan a station din da suka
ajjiyeta,duk da baban eeshan wani ne amma sahun gwiwa ya take na raqumi,hakan ya
sanya ba musu suka amsa mishi bayan ya musu bayanin laifin data aikata,ya tambayi
mahmoud adress na school dinsu ya aika musu,a yau yaje da buqatar ta kwana bayan
cell,wayar ya kashe yana furzar da iska,tabbas sai ta gane shayi ruwa ne.

Yana tsaka da duba number ma'aikacin kamfanin jirgin fly emirate dake yankar
masa ticket su'ad ta sauko,cikin taku dai dai kai tsaye ta haye dining,ta soma jawo
kayan break din tana duba abinda ma'aikaciyar ta dafa ba tare data lura da sauyawar
yanayin almustapha ba,tsaki taja don ita duka abincin bai mata ba,choice din
almustapha ne,kenan bata mata nata ba,baki ta bude ta shiga qwala mata kira,saidai
har tayi ya gama shiru maqatau ba dalilinta,sai ta miqe da niyyar shiga kitchen
nemanta tana zazzaga masifa,banza yayi da ita har taje ta gama bulayinta ta
dawi,zuwa sannan ya gama waya da su,saidai dole yayi haquri yabi jirgin gobe da
safe shine zai sauka dubai to abuja direct,hakan bai masa ba amma tilas ya karba
haka,miqewa yayi ba tare da ya damu da qarasa karyawar ba,sai daya sauka daga step
din sannan yace mata
"Na riga dana sallameta,tunda ba tare na auroku ba"
"Wata zaka sauya mana?" Ta tambayeshi ba tare data fuskanci me yake nufi ba
"Ki shirya fara girki da kanki karon farko tunda kika zama matar aure" ya bata amsa
yana ficewa,zumbur ta miqe ta sauko da hanzari tabiyo bayanshi tana cewa
"Haba man,ya zamuyi haka da kai?,kaima kasan abinda bazai taba yiwuwa bane"
"Saiki maidashi mai yiwuwar" ya bude motar da kanshi duk da qoqarinbda drivern keyi
wajen bude masa motar ya shige abinshi tare da bawa drivern umarnin ya shiga su
tafi,binsa tayi da kallo baki daya tunaninta ya koma ga kitchen,gata can gaban
tukwane tana fama da gas,kai ta girgiza wlh abinda bata taba yi ba ba zara fara ba
yanzu,cikin fushi ta koma ciki kai tsaye ta shiga daki ta dauko wayarta,lambar
hajiya khaulat ta soma nema wanda cikin sakanni ta daga,sai ta fashe mata da
kuka,daga daya bangaren ta soma fadin
"Yaya?,lafiya?,waye ya taban ke?"
"Mommy man ne,wai kinji ya kori kuka na wai na fara girki da kaina daga yau,don
kawai ya siya min foam na catering school nace bana iyawa,kuma na gaya masa ya
gayan nawa ya kashe na buyashi,yanzu don Allah mommy nayi kama da wadda zata shiga
kitchen zafi da tururi na qonata?" Wani shegen tsaki haj khaulat ta ja
"Shegen yaro tsagera,sai shegen zafin kai da taurin zuciya,to bai isa ba wlh,bamu
aura masa ke don ki dafa masa abinci yaci ba,idan ma iya daukan nauyin mai girkin
ne bai iyawa ko kuma girkin ne bata iya ba,nan kusa da mu akwai qwararrun masu
girki professional zan aiko muku da daya,a aljihuna zan dinga biyanta,cikakkiyar
baturiya ce ba abinda bata iya dafawa ba" murmushi su'ad ta saki tare da ihu
"Shi yasa nake sonki mamana wallahi"
"Uhmmm" tace
"Ni wlh wannan yaro ba don abinda ya mallaka ba da tunu na rabaku,qabli da ba'adi
iri daban daban,yau wannan tsurfar gobe wancan?,duk ya maidaki wata mara 'yanci"
"Kai mummy kada ki kwafsa mana haba da Allah,ke matsalarki kuma kenan auren mutu ka
raba mukayi,kawai ki turotan ni zan biya kudin visa da ticket cikin satin nan keso
tazo"
"To shikenan babu damuwa"da haka sukayi sallama su'ad na aje wayar k babu damuwa a
ranta ko kadan,saima ta hura saman dining din ta soma karyawa tana tunanin inda
zata musu order abincim dare kafin ya dawo.

To fans alhamdulillahi rabbil Aalamin,yau zamu tsaya anam sai kuma bayan zabe idan
Allah ya kaimu,amma wannan karon zamu iya kaiwa lahadi bamu dawo ba,idan kuma ya
samu lahadin to amma banyi alqawari ba kada na kasa cika muku.
Ina kira ga dukkan wani dan qasa da ya tsaya ya fidda son zuciya ya zabi shugaba na
qwarai,wanda ko gaban Allah ya riqi kyawawan hujjojin da zai bawa ubangijinsa kan
zaben mutumin da yayi,dukkanmu muna da hankali muna ga da tunani munsan abinda ya
dace.

Ya Allah muna roqonka da kyawawan sunayenka da siffofinka wadanda muka sani da


wadanda bamu sani ba,ka zaba mana shuwagabanni na gari,wadanda suke qaunarka suke
qaunar fiyayyen halitta suke tausayin bayinka har cikin zukatansu,suje tsoronka da
tsoron gamuwarsu da kai,wadanda suka tsaya bada wata manufa ba sai ta taimakon
Al'umma,ya Allah duk wanda ya tsaya da wata manufa Allah ka karya mana shi koshi
waye,Allah ka nuna isarka ka tallafi raunanan bayinka.

Ya Allah duk wanda zai kasance alkhairi a rayuwarmu data addininmu Allah ka damqa
masa ragamarmu ko muna so ko bama so,Allah ka zama jinmu ganinmu dama
furucinmu,Allah kayi maja jagoranci alfarmar shugaba annabi muhammad S A W

'Yan uwa da garuruwansu ake fama da rikici Allah ka tsayar da wannan tashin
hankali,ka zaba musu shugaban da zai zama farincikin zukatansu,sanyin idaniyarsu
alfarmar shugaba S A W.

Mu guji saida quri'armu domin kuwa QURI'ARKA ITA CE 'YANCINKA,duk dan adam din da
bai da manufa akwai babban gyara cikin rayuwarshi.

Daga qarshe ina son jan hankalinmu da cewa AKWAI RAYUWA FA BAYAN ZABE kada muci
mutuncin juna aibata juna ko bata ran juna sabida wanda mukeso yaci wanda baya so
shi ya fadi,basu suka hadamu ba bai kamata su raba mu ba,alkhairi muke nema da
kyakkyawan shugabanci,Allah kayi mana zabi mafi alkhairi ka kyautata qarshenmu.

WANNAN KIRA NE BAGA AL'UMMAR GARI NA KAWAI BA,KIRA NE GA DUKKAN WANI DAN QASATA
NIGERIA,ALLAH YA TALLAFI QASARMU.

Subhanakallahumma wabi hamdika,ashhadu an la'ilaha illa anta,astagfiruka wa atubu


ilaika.

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)
1⃣0⃣0⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

*subhanallahi wa bi hamdih,subhanallahil azim*


______________________________________

        Har yaje ya dawo abun na damunsa cikin rai,ko cikin company ranan kowa
yasan lallai an tabo oga,duk wanda ya kuskure sai ya sha fada idan ma baice ya bawa
mutum hutun satittika ba,har ya dawo din bai sake kiran sumayya ba ko wani cikin
gidan.

       Bayan sallar isha'i bayan yayi wanka,sanye yake da vest da boxer yana zaune
saman dining,fitowa tayi daga kitchen dauke da ledoji niqi niqi a hannunta ta zauna
saman dining ta soma fiddo da dinner din data musu order,idanu ya zuba mata yana
kallonta,yasan za'a rina,lallai raina shi su'ad tayi,bata ji me ya gaya mata kafin
ya fita ba kenan
"Wannan fa?" Ya fada yana nuna abincin da idanunshi
"Abinci ne na mana order"
"Shi nace miki zanci?,da na order nake so kinsan dai na fiki iyata ko?,wanda kika
dafa cikin gidan nan nakeso" kai ya lanqwasar tana dubanshi
"Amma dai kai zaka bawa wani labarin ban taba dafa wani abu ba ko?"kafada ya daga
in idont care manner
"Wannan ke ta shafa,tunda na baki dama ki koya,so wataqil dama can kin iya ko shi
yasa kika wulaqanta foam din kanshi da na saka kudade masu yawa na siya miki"
"Iyawa ne gsky bazan yi ba,tunda nasan kana da arziqin da zaka iya dauka min kuku
ko nawa nake da buqata"
"Ba kuku bane matsalata,abincin mata ta nake so naci,ke ba zakiyi min abinda nake
so ba saidai ke nabi ra'ayinki.....to ba zaiyiwu ba,ni ba sakaran namiji bane,dole
ki sauya,dole ki koma kan tsarin da nakeso tunda na fahimci ke bakisan lallashi ba"
a fusace yake maganar,yana kaiwa nan ya miqe a zafafe ya shige dakinshi,binsa tayi
da kallo har ya wuce,ta dauke idonta tana tabe bakinta,kome zayayi ba zata lamunci
yin wami girki ba kamar 'yar aiki,jawo tata ledar tayi ta bude ta soma cin
abincinta hankalinta kwance,

       A daren da kanshi ya soma hada kayanshi cikin wata qaramar jaka mai kyau ta
matafiya,ba wani kaya zai diba can ba saboda ko ina yana da kayan amfaninsa komai
da komai,su'ad na nade saman gado tana kallon wani horror film,jakar da ya fita da
ita ya janyo ya bude ya ciro ticket ya ajjiye gefan su'ad
"Ki shirya gobe da azahar zamu wuce nigeria" da hanzari ta dago ta dubeshi,sam bata
taba zaton haka ba,itafa bataqi su dauna zuwa ba ma baki daya tunda ta daukoshi wa
ta ajjiye can da zata damu sai taje
"Me zamu je yi a can din?,naga duka bamu yi cikakken wata biyu kai daya da rabi ma
da dawowa ba....nikam gaskiya da ka sani na america ka siya min,tunda ina da sauran
visa ta bata qare ba naje na qarasheta"
"Sai kin dawo" ya bata amsa cikin halin ko in kula,farinciki ne ya kamata
"To zaka siya min din?" Waiwayowa yayi yana dubanta
"Kudin da na miki transfer accnt dinki jiya....duka ina kika kaisu?" Fuska ta
bata,ya iya saninta tunda suke da shi babu lissafi tsakaninsu,bai taba mata irin
haka ba,ko yau ta nemi kudi gobe ta nema zai maya transfer ba tare da ya damu da me
zata yi da su ba
"Na kashesu" shuru ya mata bai sake bi ta kanta ba yaci gaba da abinda yake,yayin
da ya barta cikin qila wa qalan zai biya ne koko a'ah?.

         Qarfe sha biyu na rana ta fito daga luctures,takowa take cikin yauqi da
isa inda zata jira drivan ya dawo daukarta,har yau bata da walwala,ranta a bace
yake,ta qullaci sumayya qwarai,ba ita kadai ba hatta da ummin ta sanya bigiren da
zata sanyata,gani take ma duka ummin ce ta hana ruwa gudu,banda haka tana da
tabbacin matuqar ta yiwa almustapha izinin aureta ko musawa bazaiyi ba tilas ya
amince,sanda tazo mata da kukanta haquri ta bata,tana nuna mata almustaphan bai
jima da yin aure ba bazaiyiwu ace ya sake wani nan kusa ba,kawai taci gaba da
addu'a idan rabonshi ce ita dole zasuyi aure,sai yanzu take shinshinar cewa sonta
ne kawai bata yi ta fake da haka.

        Tun daga nesa ta hango tahowar motar 'yan sandan amma sai ta dauke kai
saboda tasan bata da wata alaqa da su,ga mamakinta gabanta suka tsaya,a wulaqance
ta daga kai tana dubansu zata soma zazzage musu ruwan masifan sunzo gabanta sun
tsaya sun tada mata qura,fitowar daya daga cikin 'yan sandan ya tsaya qiqam gabanta
shi ya katse mata masifar data so yi
"Malam lafiya?" Hannunshi ya saka a aljihun gaban rugarshi ya fito da ID card dinsa
ya nuna mata yana cewa
"Suna na inspector uba labaran,ina fata kece Aisha jamil?" Kai take gyadawa
"Eh yes nice,ya akayi kazo gabana kamin wani qiqam?"
"Akwai qorafi a kanka wajen yunqurin aikata laifi,sabida haka muna gayyatarki zuwa
ofishinsu ki riqe bayananki duka kya yisu a can" miqewa tayi cikin masifa
"Me kake nufi malam,wannan wanne irin iskanci ne,rashin mutuncin naku na 'yan sanda
haf ya kai haka,kawai kazo ka sameni kace wai ana tuhumata,waye yake tuhumar
tawa?,wai tsaya ma malam kasan wace ni kuwa?"
"Eh mun sani,wanda kuma ke tuhumar taki ya fiki shi yasa muka zo tafiya da ke" wata
gajeriyar baqar mace dake sanye da unifoarm ta fada tana qarasowa gefan
eeshan,kallo daya zaka mata kasan fuskarta babu rahama
"Lallai kunyi kuskure,baru na kira mahaifina qila watan rasa aikinkune ya kama" ta
fada tana yunqurin fiddo da wayarta daga jaka,damqe jakar matar tayi ta karbeta
daga hannunta tana fito da ankwa daga aljihunta tana duban eeshan
"Ko ki wuce salin alin mu tafi,ko kuma ta qarfin tsiya mu saka miki wannan sannan
mu tafi da ke" wanu gagarumin baqinciki ya rufe eesha,ta tabbatar matuqar tayi
gardamar matar haka zata aikata mata din,bugu da qari kuma ga mutane sun soma cika
a wajen,yawancinsu sun santa,sun san dagawa da daga kai irin nata da taka duk uban
wanda taga dama,bata ragawa kowa,kada ma dai a ce babanka ba wani bane
"Kawai ki wuce ku tafi sister eesha kada su qaqaba miki wannan qarfen ki kafa
tarihi" cewar titi kenan hatsabibiyar yarinyar da suke takun saqa da eesha kaman
suna ganin hanjin juna,saboda kowa na taqama da kudin ubanshi,sauran 'yan
jam'iyyarta suka sheqe da dariya,ba yadda zata yi,da wani tozarcin ya sameta a nan
gwara ta bisu koma mene sa qareta a can,haka ta taka matar ta bude mata motar ta
shige suka rufe suka ja suka bar wajen.

       Cikin motar ta kallesu tace


"Ni bansan me nayi ba,amma ko mene ku bude jakata akwai kudi nasan su kuke nema
zasu isheku ku raba" wani kallo matar ta watsa mata,tuntuni ta fuskanci yarinyar
tana da dagawa da izgilanci
"Ko nawa ne jakarki wanda ya turo mu idan su muke buqata zai iya linka mana su"
haushi ya tuqeta,cikin tsiwa da masifa tace
"Ni dinma zan iya,akwai atm cikin jakar,ku dauka ku ciri ko nawa kuke so a
ciki,nasan dai kudin ciki duka sun muku yawa"
"Munce miki bama so ki rufe mana baki,laifi kikayi kuma dole mu kamaki"
"Mtsweew,ai matsiyaci ko a tandun mai ka sanyashi ka tsamoshi qamas zai fito,kada
Allah yasa kuso,labari ya kai kunnen babana zakuyi biyu babu ne,ba kudin ga kuma
asarar aikinku da zakuyi"dariya matar tayi,tabbas ba dan yace kada su taba
lafiyarta ba da sai ta bawa wannan fuskar da rake taqama da ita lafiyayyun marin da
har ta mutu ba zata taba mantawa da su ba
"ina jin baban naki ne ma idan baiyi wasa ba zai rasa hanyar cin abincinsa,dom
wannan mutumin lallai an taboshi,ban taba ji yasa an kama wani saboda kan kanshi
ba,kuma wallahi kika sake mana magana ko rashin kunya sai na magutsa bakinki a nan
na sauya miki kamannin fuskarki" ba shakka eesha naji da fuskarta,ganin yadda matar
ta soma huci tana fito da jajayen qananun idanunta ya sanya eeshan yin laqwas,ranta
da zuciyarta na tafasa,so take kawai tasan waye yayi mata wannan tozarcin da tunda
tazo duniya ba'a taba yi mata irinsa ba,lallai bata da maqiyi kamarshi ko waye.

         Suna isa station din suka karbi duka kayanta,sannan aka bude wani daki
wanda ba kowa suka saka ta ciki suka maida qofa suka rufe,kukan baqinciki ne ya
qwace mata ta soma maganganu tana zage zage,ba wanda ya kulata sai data gaji don
kanta tayi shiru,dakin ta fara bi da kallo kusurwa kusurwa,banda duhu da wari ba
abinda ke tashi ciki,ga kukan sauro tun yanzu da ranar Allah,ina ga dare
yayi,tsaiwa tayi taqi zama sabida qyanqyamin wajen da takeyi,sai daga bisani da
taga ba sarki sai Allah qafafunta na neman sandarewa tilas ta tsugunna tana
hawaye,addu'a kawai take Allah ya kawo babanta,ba shakka dukka 'yan sandan sai ta
sanya an koresu daga bakin aiki.

         Qarfe biyu da rabi na rana ya sauka a filin sauka da tashi na jiragen sama
dake abuja,a masallacin dake cikin filin ya sallaci azahar,zuwa sannan drivanshi na
nan abujan ya iso da daya daga cikin motocinsa na hawa ba bata lokaci suka dauki
hanyar gida.

          Suna zaune ita da ummi da sajida ne kawai,ummi da sajida na saman


kujera,yayin da sumayya ke zaune qasan carfet sajida na ware mata kalabar da amira
tayi mata guda takwas sanda tazo dubata,wadanda jelarsu ta sauka a bayanta,hira
suke kadan kadan suna tuna haujar amira sanda taji abinda eesha tayi,cewa tayi
wallah har gida zata Allah ne kadai take tunanin zai rabasu da eesha,zagi kuwa
ranan babu wanda eesha bata shashi ba,sanda ummi taji ta hanata zuwa amira harda
qwallar takaici,ita sam bata damu da ko yaron cikin dake jikinta ba,so take kawai
taje su casheta,ta rasa ita da amira wa yafi wani quruciya ne.

        Shirt ce ajikinta mai shirt sleeve irin ta mata fara qal wadda aka yiwa
adon pink,sai A line skert shima pink ne kaman adon pink dake jikin rigar,mayafin
da ta dan yane kafadunta da shi fari saboda nauyin ummi da take ji duk da ita ba
ruwanta ita tace ta dinga saka su tana shan iska,kalbar an tsafe biyar bata taje ba
saura uku.

       A nutse ya sanya hannunshi ya turo qofar falon tare da sallama kan labbansa
duk da bai bude muryarshi sosai ba,fararen idanunta ta daga suka sauka cikin nashi
sanda yake takowa cikin falon ummi na masa duban mamakin zuwan ba zata,sosai ta
dauki hankalinshi tayi wani fresh ta qara kyau kaman zane,amma sai miskilancin ya
motsa,haushin abinda tayi masa ya taso masa,sai ya janye idanunshi daga kanta ya
maida kan ummi fyskarshi kadaran kadaham
"Lafiya dai ko almustapha wannan zuwan ba zata?"
"Lafiya qalau..." Ya fadi sanda yake zaman saman daya daga cikin kujerun falon
idanunshi kan qafar sumayya dake miqe saman filo,wani abu ya tokareshi,wato abun
har ya kai a nade mata qafa haka?,cikin ladabi yake gaida ummin tana amsawa,ta lura
da yanda qafar sumayyan ke jan hankalinsa sai tace
"Kaga tsautsayin da ya faru ko?"
"Na gani" ya fadi kawai yana duban qafar,yanayin yadda ya amsa din kaman yasan
komai sai ya bata mamaki,ita dai tasan bata gaya masa ba haka ma sumayya,sai tayi
shiru ba tare data idasa bayanin ba,miqewa ummin tayi don son basu waje tana cewa
"Me za'a kawo maka?"
"Ruwa....ruwa ma ya isa"
"To....taso sajida ki kawo masa" badon babu ma'aikatan da zasu kawo masa din ba don
ta basu waje nw ta fada tana yin gaba.

       Har suka bace a falon idanunshi na zube qur a kanta,baki daya wani nauyinshi
take ji ya koma mata wani baqo,tunda suka soma jituwa basu taba nesa da juna haka
ba,ribbom ta janyo tana qoqarin tattara gashinta waje guda
"Barka da zuwa,an iso lafiya?"ta ambata tana kunyar kallonshi,bai amsa ba kaman
yadda bai bai dauke ido daga kallonta ba,a nutse ya miqe tsam daga inda yake ya
tako a hankali zuwa gabanta,durqusawa yayi saman qafafunshi,ya sanya hannunshi ya
daga qafar tata dake miqe saman filo ya soma warware nadin da aka yiwa qafar,idanu
ta zaro sannan cikin sauri tace
"yau zaya zo ya cire da kanshi tunda....."wani kallo ya watsa mata da idanunshi da
ke cike taf da bacin rai,da sauri ta janye idanunshi shi kuma ya maida kai yaci
gaba da warwarewar,bai dakata ba sai da ya gama tas sannan ya yar da tsumman gefe
cikin tsantsami,duk da cewa ba wani abu yayi ba fes yake,miqewa yayi tsaye ya miqa
mata hannunshi alaman ta taso,fargabar tashin take da kuma fargabar taka
qafar,gashi lokaci guda ya sauya mata,babu annuri ko kadan kan fuskarshi,ba yadda
ta iya haka ta zira hannunta cikin nashi ya dagata ta miqe tana rintse ido.

    Baki daya tayi luu zuwa cikin jikinshi saboda ragowar radadin da qafarta take
mata,qirjinsa ta fada tana riqe da shi,kusan lokaci guda suka saki ajiyar
zuciya,duk yadda yaso boye tasa sai data bayyana sabanin tata da tayita a
boye,abinda ke cunkushe cikin zuciyarshi yaji ya soma sauqi,nauyin da qirjinsa yayi
ya soma raguwa,wani wawan shauqi kewa da qauna ke ratsashi,take wani abu ya soma
kai kawo cikin jikkunansu.

         Sajida ce ta fito dauke da cups da gorar ruwa,zata koma da baya almustapha


ya dakatar da ita
"jeki dauko mata hijabi cikin kayanta"
"To" ta amsa tana dire cup din sannan ta juya ta haye sama da gudu,dan janyewa tayi
daga jikinsa tana dubanshi,so take ta tambayeshi ina zasu bayan mai gyaran zaizo
duba qafarta amma ta kasa,yayi mata kwarjini da yawa,daure fuskarshi ya hanata
katabus,har sajida ta sauko ta miqa mata hijabin ta sanya ya dubi sajidan
"Ina ummi?"
"Wanka ta shiga"
"Idan ta fito kice mata mun tafi"
"To,a dawo lafiya" cewar sajida tana juyawa ciki,da idanu ya mata alaman su
tafi,saidai ta kasa yin gaba,ji tayi kawai yayi sama da ita ko a jikinshi ya soma
takawa da ita ya fice daga falonsatar kallon idanunshi take,wadanda tayi kewarsu
matuqa da gaske,bata sake yarda da abinda take ji tattare da shi ba sai yanzu da
suke tare da juna,hada ido sukayi sai ya dauke kai yana ci gaba da takawa zuwa
ma'ajiyar motoci,kunya ta cikata,ganin jifa jifa ma'aikatan gidan na giftawa,saidai
duk wanda ya sako kai ya gansu sai ya koma baya ya lafe yana jiran wucewarsu,ko a
jikinsa shi kam,sabida tun asali duk abinda zaiyi yanayinsa ne kai tsaye matuqar ya
dace da ra'ayinsa ya kuma yi masa dai dai,bai direta ko ina ba sai cikin mota sit
din baya,shima ya shiga ya baiwa driva umarnin yaja suje.

          Shiru ne ya biyo baya cikin motar,kanta na qasa baki daya tana takure,bai
ce mata uffan ba shima,duk da yadda yake jin cikin zuciyarshi game da ita kaman ya
jawota ya hadiyeta,farinciki ya sake mamaye zuciyarshi musamman sanda yaga matashin
cikinta ya soma kutso kai waje,saidai dole ya nuna mata fushinsa ko don gaba,kada
ta sake maimaita irin wannan kuskuren,shine mutum na farko da yafi cancanta ace
yasan dukkanin wani abu da ya sameta na dadi ko akasin haka,yana son su zama verry
close,aminan juna,qawaye,dangantakarsu ta zama daga gangar jiki har zuciya,qofar
wannan gidan nashi wanda ta yiwa laqabi da lovehouse suka kutsa,a katafaren wajen
parking din ababaen hawa ya tsaida motar,almustapha ya bude motar sannan ya sanya
hannu ya dauketa baki daya ya taka anutse zuwa ciki,bai sake ajiyeta ba sai daya
dangana da madaidaicin clinic dake gidan bisa gadon kwantas da marasa lafiya,duk
wani abu na amfani da zaya buqata ya janyo kusa da gadon bayan ya girke kujera
gaban gadon ya zauna ya soma aikin da yake da buqatar yi.

        Da ido take bin duk wani motsinsa,sam yaqi kallonta ma ballantana taga
fara'a kan fuskarshi,yaqu furta komai gareta,lokaci sukan hada ido sai ya hade
girar sama data qasa kawai ya sake dauke kai,sosai ta shiga damuwa,idanunta sukq
dinga tara qwalla,to me tayi masa haka?,itakam har yau bata san abinda tayi masa
ba,sai da ya gama scan ya duba komai,ciki harfa edd dinta,ya tabbatar da cewa komai
lafiya sannan ya koma kan qafar,a nan ne ma ta dinga jin dan ciwo sama sama sanda
yake tabawa,ya gama ya ciro wani mai mai zkama da vaseline ya shafa mawa dai dai
wajen sannan ya dagata ta zauna.

      

           Gab da sallan magariba ya fito falon inda take zaune,shirye tsaf cikin
wani tattausan yadi na maza fari mai adon ash,dinki ya bala'in yi masa
kyau,takalmin qafarshi sau ciki ya dace da shigar da yayi,babu hula kanshi sai
agogon fata da yake daurawa a hannunshi,inda ya ajjiye mata abinci ya kalla,babu
wani abu data ci a ciki,sai ya dauke kanshi baice da ita komai ba har sai da ya
gama daura agogon sannan ya qarasa gabanta,wrapping din da aka yiwa plate din ya
yage,ya sanya cokali a ciki ya miqa mata tana tsareta da ido,jiki a sanyaye ta
karba zuciyarta na karyewa,wai ke ta masa haka ne?,ko fushin tafiyar ne har
yau,amma ita ai tasan sun sasanta wannan matsalar,hasalima ko shekaran jiya sun
raba dare sosai suna waya yana tsumata da kalamanshi,amma tsakanin jiya da yau baki
daya ya sauya?,haka ta dinga cusa abincin ya tsiyaya mata ruwa ya miqa mata,sai da
yaga ta shanye sannan ya juya yana ficewa tare da fadin
"Ki samu waje ki kwanta" ya fice daga gidan,can qasan zuciyanshi tausayinta ne
kwance,ya sani cewa inda su'ad ce eeshan ta yiwa haka da tuni labari ya sha
banban,wanne irin haquri gareta haka?,har kuma ta kasa sanar masa abinda ta
masa,tabbas itama sai taji a jikinta kaman yadda ta gwada mata rashin tausayi.

          Da kanshi ya isa station din ta hanyar drivansa,sun gama magana da cp tun


a hanya bai kusa amma tana nan a station din,cikin girmamawa DPO ya fito ya
taryeshi,farinciki ya cikashi yau ga mutum kaman doctor muhammad almustapha cikin
station dinsu,office dinsa ua saukeshi suka zauna daga shi sai shi suka gaisa
sannan ya suka soma tattaunawa kan eeshan
"Ranka ya dade me zai hana kawai a kaiku kotu?" Murmushi almustapha yayi yana
girgiza kai
"A'ah,iya nan ma ya isa,banson maganar taje kunnen kowa ma bare kotu,ba wulaqantar
da ita nake so nayi ba,so nake kawai ta gane girman laifin data aikata.....zan iya
ganinta?"
"Me zai hana.....kai....bala!" Ya qwalawa dan sandan dake kan kanta kira,cikin
girmamawa ya shigo ya sara masa sannan ya qame
"Jeka fito da yarinyar nan wadda ta zagi asabe jiya ta kakkwada mata mari"
"Yes sir" ya fada yana juyawa cikin hanzari,dubanshi almustapha yayi
"Amma officer na gaya muku kada wanda ya daketa ko?" Cikin girmamawa yace
"Sorry yallabai,wallahi yarinyar ce sam bata da kunya,ga bakinta baya mutuwa,an
kawo mata shinkafa da mai da yaji ta kwafar tana durawa asabe zagi,to dama tun jiya
da suka je daukota take zaginsu,asabe kuma ba haquri shine data fusata ta zabga
mata mari"
"Kada ta qara to"
"In sha Allahu yallabai" ya fadi dai dai sanda aka shigi da eesha,wadda tsahon
kwana daya da wuni baki daya ta soma sauyawa,tun daga fuskarta da yatsun asabe suka
fito rada rada,ga sauro ya yagi rabonshi a fatar da ake so da tattali da kashe mata
kudi wajen siyan mayuka masu tsada,dauda ta soma zama ajikinta,ita kanta jinta take
baki daya ta soma muzanta tun daga yau,matar da a rana sai tayi wanka sau uku biyu
a rana,sai gashi rabonta da wanka tun na jiya da safe da tayi kafin ta fito
makaranta,tana ganin almustapha wani dadi ya saukar mata,tuni ta fara qissima yadda
zata ci uban baki daya 'yan sandan
"Ya man" ta fada cikin farinciki,saidai yanayin fuskarshi ya sage mata gwiwa,bata
wani kawo cewa shi ya qulla mata wannan abun ba,tafi bada cewa miskilancin nashi ne
ya motsa,amma koma meye tunda zai ceceta ayi shi daga baya,kujera dan sanda ya tura
mata saitin almustapha,kallon banza ta watsa masa tana tunanin ya soma ladab tunda
yaga babban mutumin da yazo belinta,zai nuna shi na Allah ne sabida ta sassauta
masa idan ta tashi hukuntasu
"Zaka ci ubanka wallahi duk sai kun rasa aikinku" ta fada cikin tsiwa da
gadara,idonta kaman zai fado saboda harara,wani abu mai tauru ya hadiye dan
sandan,ba shakka ba din sanin waye a gabanshi ba da sai ya gabza mata mari kaman
yadda sabe tayi mata dazu,ya lura babu digon kunya ko mutunci tattare da yarinyar
sam,ba wanda ya furta mata sai DPO da ya daka mata tsawa cikin kakkausar murya yana
bata umarni ta zauna,sai data ja tsaki sannan ta zauna DPO ya fice tare da daya dan
sandan suka barsu su biyu.

        Idanunshi ya tsareta da su yana kallonta,yayin da ta soma sheshsheqar kuka


sannan ta fara magana
"Kaga abinda suka yimin ko ya almustapha,cin mutunci har cikin makaranta tsakiyar
dalibai" bashi labarin yadda komai ya faru ta soma yi,yana kallonta baice uffan ba
har sai data gama,cikin izza ya motsa bakinsa
"Ni na sanyasu ba wani bane" cikin mamaki da tsoro take dubanshi,ya tsareta fes da
ido yana mata kallon banza ranshi a bace,zamanshi ya daidaita sosai ya zauna saman
kujeran yana ci gaba da kallonta
"Kin soma zama 'yar ta'adda,wadda keson kashe uwa da abinda ke cikinta ko?" Idanuwa
ta zaro gabanta na faduwa,ta shiga uku indai yaji wannan zancan,qirji ta dafe tana
nuna kanta
"Ni din?,yaushe?a ina?"kai yake gyadawa yana jin baki daya ya raina masa wayau
ma,shi kam babu abinda yafi tsana sama da qarya,shi yasa sam bai iya ta ba,ko zai
maka me yafiso ka gaya masa gaskiya,qila gaskiyarka ta cece ka a wajensa
"Ni kike tambaya?,da kyau" sai ya miqe tsaye
"Duk randa kika tuna lokaci da wajen da kika aikata abun kya fito" kuka ta
saka,kunya nauyi da baqinciki duka suka cikata,
"Wallahi sharri akemin" wani kallo ya mata sannan ya juya ba tare da ya sake bi ta
kanta ba ya fice,a kan kanta ya samesu,suka sake tattaunawa da DPO ya sake jaddada
masa baiso kowa yasan inda take tsare,sannan koda an sani bai lamunce a bada
belinta ba,ya fiddo kudi ya danqa masa kudin abincinta ya kuma yi musu ihsani
sannan ya tafi.

        A hankali ya ke takawa har ya isa cikin dakin baccin nashi,sam baiyi


tsammani ba ya sameta zaune saman abun sallah,tana sanye da kayan bacci riga da
wando sai hijabi dake jikinta,kana duban idonta kasa kuka ta sha ba kuma kadan
ba,da qyar ta daga kumburarrun idanunta ta dubeshi sannan tayi qasa da su tana masa
sannu da zuwa,yarrrrrr yaji tsigar jikinsa ta zuba,ranshi ya baci,duka eesha ce ta
jawo faruwar hakan?,kayan jikinsa ya cire ya daura towel,sannan ya isa gaban ac ya
kunnata saboda zafin da yake ji,hannunshi yaji ta riqe sanda yake yunqurin wuceta
"Don Allah kayi haquri.....idan wani abu nayi maka ka yafemin...ko ka gayan na nemi
yafiya wajenka" ta fada cikin rawar murya,tamkar wani abu aka zuba masa haka yaji
cikin jikinsa,sai ya dawo a hankali gabanta ya zauna sosai,idanunsa dake bayyana
tsantsat bacin ranshi yake dubanta da su
"Sai ta kasheki sannan za'a gaya min sumayyah!" Ya fada abun ma taba ranshi,sunanta
fes cikin bakinshi cikin wani salo
"Wanne irin ganganci kika si yimin da rayuwar mutum biyu masu matuqar muhimmanci a
waje na?" Ya qarashe maganar cikin salon tambaya,shiru tayi kawai kanta a
qasa,hawayen da take maqalewa suka balle mata,sai ya sake matsowa dab da ita suna
jin dumin numafashin juna
"Sumayya!.....da wani abu ya sameki fa?,ya kike tunani?,kina tsammanin zan ci gaba
da rayuwa kaman yadda kowanne dan adam keyi?....kinsan kuwa muhimmancinki a
wajena?,me yasa bazan zama mutum na farko da zamu raba lafiyarki da akasinta
ba?,mutum na farko da zamu raba jin dadinki da akasinsa ba,kinsan me nake so matata
ta daukeni?,amininta abokinta mafi kusanci da ita,bana so matata ta raba matsalarta
da kowa,bana so ta raba damuwarta da kowa,so nake na zama jigonta majinginarta,don
me zaki boyen abu mai hatsari irn haka?saidai wata ta gaya min?,ba don Allah ya
kiyaye ba kinsan me zaya faru a gaba?" Tuni kuka ya qwace mata,cikin muryar kukan
tace
"Har yau bakasan wace sumayya ba,sumayya ta saba ganin hakan cikin rayuwarta,taga
sama da haka ma,shi yasa bata dauki hakan baqon lamarin da zai girgizata sosai
ba,abinda ta saba gani yau da gobe ne,fa'iza,karima,uwa uba zainab" ta furta tana
son danne kukanta,sai jikinsa yayi sanyi,ya kasa jure kukanta,sai ya janyota cikin
jikinsa ya matseta tsam,suka soma raba radadin dake cikin zuciyarta,cikin wani irin
salo yake rarrashinta,wanda hakan ya bashi nasarar tsaida kukan nata cikin
taqaitaccen lokaci
"Su waye su zainab?me suka yi miki haka?" Ya tambayeta tana kwance a
jikinsa,nannauyar ajiyar zuciya ta sauke,sannu a hankali ta soma warware masa ita
din wace ba tare data boye masa komai ba.

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

1⃣0⃣0⃣1⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

*Allah S W T yana cewa cikin qur'aninsa mai girma*

*IDAN ZAKUYI UQUBA KUYI UQUBA DA GWARGWADON MISALIN ABINDA AKA YI MUKU UQUBA DA
SHI(ma'ana idan zaku rama wani abu da aka yi muku ku rama gwargwadon abinda mutum
yayi muku babu qaari)IDAN KUKAYI HAQURI SHINE MAFI ALKHAIRI GA MASU HAQURI*

Sadaqallahul azim
__________________________________

         Da fari labarin dariya ya dinga bashi,quruciyarta ta dinga burgeshi tana


masa dadi,ya dinga leqa fuskarta yana tsokanarta,a hankali sai yanayin ya sauya ya
koma na kishi,zallahn kishin mukhtar,yayi shuru yana saurarenta,daga bisani kuma
sai mamaki ya bijiro masa,tausayi shi ya zama abu na qarshe,kafin ta gama bada
labarin saiga hawaye shabe shabe kan fuskarta,yayin da zuciyar almustapha ta dinga
motsawa,ji yake kaman ya dawo da hannun agogo baya,kamar ya dawo da baya ya ciro
fa'iza zainab har ma da karima ya hukuntasu,lallai dole ta dauki eesha ba a bakin
komai ba,tausayin abdallah da qaunarshi suka kamashi,ashe maraya ne,marayan da tun
kafin ya iso duniya ya fara fuskantar qalubale na rayuwa,lallai dole yayi maganin
eesha,bazai yarda ta sake fuskantar irin wannan rayuwar ba.

       Dubanta kawai yake bayan ya gama rarrasarta,mamakin irin rayuwar da take


kawai yake,saidai zuciyarsa cike take fal kishin dukka mazajenta,ina ma ace shi ya
fara samunta tun a wancan shekarun,da lallai ba shakka bazai bari tayi irin wannan
rayuwar ba,saidai kuma qaddara data rigayi fata,ko a hannunshin ne tunda yazo cikin
KUNDIN QADDARARTA dole hakan ya faru da ita.

        Kwanansa biyu cikin gidan baya fita ko nan da can,wata sabuwar rayuwa mai
cike da soyayya da qauna suke shimfidawa cikin gidan,wata kulawa sumayyan kr bashi
wadda ada can bai taba hakaito ta iya bawa miji kulawa kwatankwacin haka ba,duk sai
ya narke ya koma wani shagwababben qarfi da yaji,jinsa yake tamkar qarakin
yaro,irin soyayyar da yake hasashen samu ga matar aurensa ita yaje gani zallarta ba
algus,shima baiyi qasa a gwiwa wajen bata kulawa ba,ji yake kaman ya lasheta ita da
abinda ke cikinta,sau tari yakan sata ta saka qananun kaya kawai don yaga zaman
cikinsa a jikinta,wata qimarta ke dada hauhawa cikin zuciyarshi,ta zama wata ta
musamman cikin rayuwarshi,labarinta ya tsaye masa a wuya,yana jinjina mata yadda ta
fuskanci duk wani qalubale na rayuwarta,yaci alwashin sai ya shafe duk wani tabo da
yayi saura qasan ranta da qarfin qwanji da na zuciyarsa.

        Randa suka cika kwana uku a gidan,bayan sallar magariba ne,yana zaune a
falo sanye da gajeran wando da vest duka farare qal,qafafunshi harde yana kallon
wrestling,fuskarshi qunshe da murmushi duk da ba abin dariya ake ba a allon
t.v,yayi shiru yana sauraren fitowar sumayya daga kitchen,wanda yasan me ya qulla
maya shi yasa yake dariya,kukan shagwabarta ya jiyo tana fitowa a kitchen din,sanye
take da vest itama da wando iya gwiwa baki dayansu blue da pink,kayan sun fito da
cikinta muraran ya zauna das a jikinta,gashinta na daure a ribnom qwaya daya ya
sauja bayanta sai qyalli yake,wanda aikin almustaphan ne shi ya gyara maya shi dazu
da yamma,waiwayowa yayi yana kallonta hadi da qunshe dariya ya dage gira ya ware
mata hannayeshi alamun ta taho
"Babe....me ya faru?" Harararshi take tun kafin ta iso
"Nama na.....ina nama na?" Sake qoqarin boye dariyarshi yake ya soma zagaya
idanunshi sannan yace
"I think akwai bera ko mage fa gidan nan,dazun naji motso a kitchen may be su shuka
janye" sai ta sake sakin kuka ta fado jikinsa a hankali,da sauri ya tarbeta yana
sakin dariya,ya cusa hannunshi bayanshi ya ciro kwanan ya dire mata
"Hala baki kallon mudubi....gaba daya kina cin nama yana komawa kumatunki yana
zama" ya qarashe yana dariya,dariya itama ya bata,sai ta harde hannayenta tana
kallonshi
"Okey.....yanzu ya kake so ayi,na daina ci kenan?" Hannunsa ya daga sama
"Ni bance ba,ci abinki tunda baby na so...." Magananshi ta katse sanda wayarshi ta
dauki ruri,ummi ke kira,sai ga miqa hannu ya dauki wayar yayin da ya maqaleta a
kunne,ya soma bude plate din yana motsawa sumayya naman don ya huce yadda zai mata
dadin ci.

       Gaisawa sukayi don yau duka basu je sun gaida su ba


"Almustapha ka kira gwagwgwanka hasiya ka mata jaje fa,yau kwanaki hudu ba'a ga
aisha ba ba'asan kuma inda take ba,anyi nema har an gaji"
"Wace aisha ummi?"ya tambaya tamkar bai santa ba din
"Aisha 'yar gidan asiyan uncle balarabe?"
"Ohhh....Allah ya bayyana"ya fada yana miqawa sumayya naman cikin bakinta
"Nace ya kamata kasaka hannu ko Allah zai saka a ganta,barinta gidan nan da kwana
uku abin ya faru,tunda Allah yasa kana da idon sani ka saka hannu ko Allah zaisa a
ganta"
"Ummi....ku barta kawai,alhakine fa.....kisa taso yi cikin gidan Allah ya tsare,may
be alhakin ne yake wahal da ita" ya fada kaman da gaske baisan komai ciki ba
"Almustapha......qaniyarka,qanwarka ce fa,tunda har Allah ya tsare din mai ya taso
da wannan maganar?,c'mn ka sanya hannu a nemota hankali asiya a tashe yake"
"Zanyi qoqari ummi in sha Allah"
"To Allah yasa a dace,ina 'yata" murmushi yayi ya dubi sumayya dake kallonshi
"Gata nan....nama take ci"murmushi ummi ta saki cikin jin dadi
"qyaleta kar ka tseta,ka gaidamin ita,jikin nata kuma fa?,daka dauketa ka hana mai
magani qarasa aikinsa" murmushi ya saki
"Zan kawo miki ita gobe,zaki mamaki ummi,ya za'a yi ina likita a kira mai maganin
gargajiya ya taba min mata?"baki ummin ta riqe tana murmushi,wannan qauna ba qarama
bace ta tabbata almustaphan kewa sumayya
"sannu masu mata,mu ai da yakeazanmu basa sanmu da idan irin haka ta samemu suke
kiran masu maganin gargajiyar su dubamu" sai kuma kunya ta kamashi,ya saki dariya
yana katse wayar da sauri.

      "Uh,me kike kallona?" Ya fadiwa sumayya yana lakace mata hanci,kai ta girgiza
"Don Allah baby ka barta ta koma gida haka" ta fada a shagwabe,fuska ya dinke
"Wa fa?"
"Aisha mana,kaga hankali yanzu ya tashi,ya kamata ta koma gida"shuru yaui kaman
bazai tanka ba,yaci gaba da miqa mata naman,sai da yaga taqi karba sannan yace
"sati guda na diba mata kuma sai ta yishi,kiyi addu'a a sanda ta cika satin ta
yarda ta aikata abinda ta aikata din,matuqar ta sake maimaita min abinda tayi tace
sharri ne aka mata wallahi sai ta sake wani satin har sai ta yarda ta amince ta
kuma nemi yafiya,zuciyata ba zata lamunci cutarwa tattare da ke ba,ki fitar da
kanki daga maganar nan banson kice komai bare ki nunawa ummi na aikata hakan....kin
gane?" Shiru tayi kawai ta gyada kai,don ta fuskanci ya dauki lamarin da zafi
qwarai.

   *******   *****   ********

        Da yammaci suka shirya kaman yadda ya alqawarta kaita wajen ummi,tayi kyau
cikin atamfa vlisco,ta cika sosai fatarta ta sake fresh,ta zama wata 'yar duma
duma,duk inda ta gifata sai ta bat ragowar qamshinta,duk yadda yasi dauke idanunshi
daga kanta hakan ya gagara,daga bisani janyo abarsa yayi ta sauka jikinsa tana
dariya
"Baby.....so nake na gama fa mu tafi,na qagu naje naga ummi"
"Anya fitar nan kuwa yau zata yiwu?" Idanu ta zaro tana dubanshi
"Saboda me?" Murmushi ya saki,ba qaramin kyau ta sake masa ba data zaro idon,ya
saka hannunshi ya ja hancinta
"Kinmin kyau,ya kamata muje mukai wa babynmu ziyara ko ba haka ba madam?" Ya
qarashe yana kashe mata ido,ta fuskanci sarai me yake nufi indai yace zai kaiwa
baby ziyara ne da shi yake fakewa,ta rasa ya akai ya sake ninka jarabarsa kan
tada,sai ta soma tureshi tana bubbuga qafarta
"Ba wani ziyara.....yau wajen ummi kawai zamu" dariya ya soma yana cusa hancinsa
lungu da saqo na jikinta yana shaqar daddadan qamshinta tare da yamutsata,tsuwwar
da wayarsa ta fara shi ya sanya shi sakinta yana dubawa,ya ajjiye wayar yana
dubanta da idanunshi da suka rage girma tare da sauya kala
"Hamza ya iso shi da matarshi,yace zasu wajenmu ne can gida nace masa bama
nan,dazun na tura masa adress sun iso" gyara daurinta da tuni ya wareshi ta soma
tana cewa
"Ok,to muje mana" kai ya girgiza yana kallonta
"A hakan zan fita?,bayan kin yamutsani,so kike hamza ya shekara yana addabata da
tsokana kenan,jirani minti biyar na watsa ruwa" ya fada yana miqewa harda dan
tsallenshi ta bishi da kallo har ya shige bandakin,murmuahi ta saki tana gyafa
kai,wani irin mutum mai bala'in dadi zama tayi katari da shi cikin rayuwarta,sau
tari idan yayi wani abun sai taga kaman ba almustapha ba,mayen soyayya ne na
qarshe,yasan darajar auratayya da qimar matarshi.

        Yana maqale da hannunta suka iso harabar  gidan inda hamza ke


tsumayinshi,gurim abida sumayya ta isa fuskarta qunshe da murmushi tana yunqurin
amsar baby,yayin da almustapha ya qarasa wajen hamza
"Maan.....yaushe ka soma shiga cikin wannan duniyar taka?" Ya fada cikin sigar
tsokana murya qasa qasa
"Lokacin shigarta ne yayi" ya fada yana fidda qaramin murmushi,dariya hamza ya saki
irin ta mugunta yana dan dukan saman hannun almustapha
"Musty.....kace kawai kaima kayi dumu dumu cikin soyayya kaman yadda mukayi"
"Na sabawa Allah?....ka fita a idona fa hamza" bai fasa dariyarshi ba,yana jin dadi
yaga ya kwashi almustapha
"Ina mutane na suzo suga yadda ake bugata"
"Dallah malami idan zaka shigo muje,idan ba zaka shiga ba ka sauka lafiya" ya fada
yana yin gaba,wanda su abida tuni sun shige,binsa yayi yana ci gaba da
dibarsa,shikam murmushi yake a boye,babu wanda ke kwasarsa son rai koda cikin
abokanshi irin hamza,ya zaiyi da shi?,abotarsu haduwar jini ce daga Allah ne.

       "Kai matar maan...gaskiya gidan nan naku ya tafi da ni,anya ba nan zamu zo
ku bamu daki ba?" Abida ke tsokanar sumayya sanda take jere mata abun motsa
baki,dariya sumayya ta saki
"Kunfi qarfin daki,saidai a baku sashe" dariya itama abidan tayi
"Na tabbata waccar batasan da gidan nan ba....inda ta san da shi wallahi nan zata
dawo da zama,ki godewa Allah sumayya,kin shiga rayuwar maan fiye da zatonki,kallo
daya mutum zai masa yasan yana cikin zazzafar soyayyarki,baki ga yadda yake ta
kaffa kaffa dake ba da ido kawai bare aikinshi,ba shakka soyayyarku ta
dabance,saiki yi qoqari kici gaba da riqe kambunki wajensa" murmushi ta kuma saki
bayan ta zauna gefan abida ta sake amsar baby suhail
"Gaskiya ne,ni kaina wani lokaci ina mamaki,ni a tunani na banda komai da za'a min
irin wannan soyayyar" murmushi abida tayi tana zuba lemo a cup
"Ke kike ganin haka malamarsu,duk wanda ya san kanshi kallo daya zai miki yasan kin
cancanci haka,wanda ba lallai ke kisan da hakan ba" hirarsu suke irin ta mata wadda
ba'a rabasu da ita idan sun hadu har tsahon wani lokaci kafin mustapha ya turo
qofar
"Jeki kiji da mijinkin can kafin na fito,kija masa kunne ya rage shiga hurumin da
ba nashi ba" murmushi kawai abida tayi ta  miqe ta fice tare da bar musu suhail
dake hannun sumayya,qarasawa yayi inda take zaune,ya hadasu baki daya ya rungume
yana lumshe ido
"Ya Allah ka nuna min nima,kina kyau da yaro babe" murmushi ta saki,ya janye
jikinshi baya kadan ya karbi suhail ha kwantar
"Tashi ki gyara,tare zamu fita baki daya zasu gaida ummi suma" kusan shi ya
shiryata cikin lafaya saman atamfar dake jikinta,sannan yace
"Muje ko?" Ya fada yana saba yaron a kafadarshi
"To ka bani shi" cikin shagwaba,ido ya zaro sannan ya kada kai
"A'ah.....muje,dazun ma bakisan kaman a zuciyata ba sanda kika daukeshi" tare suka
taka yana mata magana wanda ta sata ta dinga sakin murmushi.

       A motar hamzan suka isa gida,baki daya suka rankaya sashen ummi,sun taddata
cikin falonta sanye da hijabi,qaramin qur'ani ne a hannunta,yayin da gefe daya t.v
ke kunne saudi qur'an ke aiki cikin volume can qasa,daga qasa kuma sajida ce zaune
take gyara sarqar duwatsu da baba uwani ta bata,ajjiye qur'anin tayi cikin
farinciki take amsa musu,yayin da sajida ta miqe itama cikin farinciki ta nufi
sumayya
"Anty...nayi missing dinki,Allah yasa kin dawo kenan" almustapha ne ya dan harareta
"Dama 'yar gidanku ce?" Ya tambayi sajidan,sai ta girgoza kai tana dariya tare da
rufe bakinta
"To oya samu waje ki zauna tun baki bigeta ba" ya qarashe maganarshi ko
ajikinsa,bai damu da hamza dake ta masa signa na ummi na dubanshi ba
"Zoki zauna tun bai bigeki shi din ba" ta fada cikin yanayin abun dariya,dariya
suka saka baki daya yayin da kunya ta kama sumayya tayi qas da kai,shi dinma yaji
kunyar sai ya hau shafa kanshi yana basarwa.

     Tarba ummi ta musu sosai,ta sake abinta cikinsu sunata hirarsu,basu suka fita
ba sai da aka kira magariba,suka wuce masallaci suka barsu nan ita da abida,bayan
sun dawo suka dunguma baki daya suka nufi sashen baba,sanda ya gansu shima
farinciki ya cikashi,sannu kawai yakewa sumayya,shi kadai yasan farincikin da yake
ciki,nan ma hirarsu suka dinga yi da baban
"Almustapha....wai bakaji me ya samu 'yar uwarka aisha ba?" Baba ya tambayeshi
"Naji ummi ta gayan"
"Ta gaya maka ka sanya hannu wajen nemanta ko Allah zaisa a dace?" Kai ya kada
"Ta gayan,zan qoqarta" kallo daya hamza ya masa yasan cewa akwai qulalliya,yana iya
gane yanayin almustaphan ta farat daya,suka hada ido da hamza sai mustaphan yasha
mur,da ido hamzan ya tambayeshi ya akai,sai ya share kawai,a nan suka ci abincin
dare tare da baban,su kuma suka koma wajen ummi anty maamaa bata nan tayi tafiya
bare suje wajenta,ganin har sun gama basu fito ba yasa sumayya jan abida suka shiga
wajen anty dije,nan gidan ya rude,duk yaran na nan,duka minti ashirin suka mata
sumayya tace zata dawo idan sun dawo gida suka fito,ran anty dije fes,ba shakka
tafi kowa murna da wannan aure.

      Suna fitowa daga bangaren baban hamza ya dubeshi


"Maan....nasan halinka baka da kirki idan baka ga dama ba,me yarinyar mutane tayi
maka ka batar musu da ita?"
"Dakeni ubana sai in gaya maka" kai ya girgiza
"Seriouse almustapha...ka kama musu yarinya kuma kana wani cewa Allah ya bayyanata
don iya shege?" Kanshi ya shafa,har yay yana jin haushin abun,haushin yarinyar yaje
ji ainun,yanajin dama yana wajen tayi yunqurin turo sumayyan ba shakka ita zai
wurgo
"Abinda tamin mutum biyu ne a duniya zasuyi shi na qyalesu,babe taso hankadowa daga
bene bata ko lura da abinda ke jikinta ba" kai hamza ke kadawa,eh lallai almustapha
zaiyi fiye da haka ma akan wannan
"Bata kyauta ba sam.....amma kayi haquri ka fito da ita ko don iyayenta" kai shima
ya kada
"Na riga da na rantse sai tayi sati,saboda haka kada ma ka bata yawun bakinka,sai
jibi zata fito" ya sani kaifi daya ne shi,tunda ya fada din bazai canza ba,tilas ya
haqura ya qyaleshi.

  ******    *******  ********

     Da yammacin ranar ya isa policestation din,kaman waccan karon a office din DPO
suka zauna,ta rame zuwa lokacin tayi baqi kaman ba ita ba,ba abinda jikinta yake
sai buga tsami,baki daya taji ta muzanta gaban almustaphan,kallon da yake mata
kadai ya sata jin nadama,ga kunyar yanayin da take ciki,bata san cewa haka zai faru
ba da ko kallon banza bata yi mata ba
"Ya akai 'yammata?,kin tuna kece kika yi aikin ko har yau sharrin ne dai aka miki?"
Kai ta kada hawaye na zubo mata,don bata fata ace ta sake komawa dakin nan koda na
sakan daya ne
"Nice wallahi...." Fuska ya sake dinkewa
"To me tayi miki?"
"Wallahi sharrin zuciya ne da sharrin shaidan"
"Qarya kike.....saboda kina sona shine zaki kashemin mata?,na miki kama da sa'an
aurenki?" Sai tayi shiru magana ta mata nauyi
"Nace na miki kama da wanda zai kwasheki?" Ya sake tambayarta a tsawace har yana
buga teburin wajen,tsoro ya kamata da sauri ta hau girgiza kai
"A'ah....kayi haquri"
"Kinsan me?" Kai ta kuma girgizawa
"Yadda qasa ta haramta wajen jemage ya takata saidai qarar kwana,to haka aurenki ya
haramta awajena....sumayya da kike gani...tabata dai dai yake da tashin hankalin
rayuwarki"
"Kayi haquri don Allah ya almustapha" yatsanshi ya dora saman lebansa sannan yace
"Ai baki horu ba,zaki koma ne baban naki da kike taqama da shi har kike zagin na
sama dake kike tutiyar zaki hanasu cin abincinsu ki ciresu daga bakin aikinsu ya
nemoki yayi kuma belinki" ya fada yana miqewa alamun tafiya zaiyi,tuni ta saki kuka
ta sauko qasa tana roqarshi tana bashi haquri,sai da ya gama shan qamshinsa sannan
ya waiwayo,ya nuna mata kujerarta yace ta koma kai,tuni ta miqe ta koma
"Zaki tafu gida yau bisa wasu sharadai,sharadi na farko....sumayya....kada ki yarda
ko kallon banza ya hadaku bare kiyi yunqurin taba jikinta,saboda indai ina raye ta
gama shan wuyar mata irinku.....sharadi na biyu wallahi kiki dora da halinki na
wulaqanta jama'a zaki dawo cell,ba kuma wannan cell din ba,inda sai kinyi sati
bakiga hasken rana ba,and last...ruwanki ne kice ni na kamaki na kulle...ruwanki ne
kiyi shiru duk daya" yana kaiwa nan ya miqe,cikin zumudi tace
"Na gode...baxan sake ba in sha Allahu"
"Damuwarki" ya fada yana ciro kudi a aljihunsa ya jefa mata ya fice,a can ya basu
umarnin su bata jakarta da sauran kayanta,ya riga ya bata kudin mota,ya sallamesu
suna masa godiya ya wuce.

        Kwanansu goma yace ta shirya wannan karon ba inda zashi sai da ita,da
kanshi ya murje idanunshi ya tunkari baabaa kai tsaye da maganar,murmushi kawai
baban yake yana kallon yadda mustapha ya zama mara kunya yanzu,duk da hakan ya masa
dadi,alamune dake nuna zama na dadi tsakaninsu,sai yayi niyyar tsokanarsa,saboda
haka ya hade fuska
"Sannu mara ta ido,umminnaka kenan kana nufin batayi dai dai ko bata iya riqo ba
ko?,to ka tafi akwai sauran wasu watannin nan gaba ta biyoka tunda ba riqe ta
zamuyi ba ai" anty maamaa dake boye dariya tace
"Haba prof,ka barshi mana ya dauki matarsa,ina cewa nan ganin gida naje kwana uku
amma ka matsanta sai na dawo"
"Ba ruwanki bilkisu" baban ya dakatar da ita,cikin damuwa ya daga kai ya dubi
baban,ji yake kaman ya rusa ihu,murya a shaqe yace
"Idan na tafi ba lallai na dawi nan kusa ba"
"Kada ma ka dawo sai ta haihu" wayyo kadan ya rage ya rusa ihu,sai kawai ya ware
baki daya ya fito masa amutum
"Don Allah baba kayi haquri idan laifi nayi ka bani matata,wallahi zan......"
"Allah ya tsare hanya sai kun dawo" ya fada dariyar daya qunshe tana fitowa,kunya
ta kama almustapha,lallai yaro yarone komai shekarunshi kuwa wajen babba,sai ya
fara shafa kai ya miqe zumbur yana musu sallama,suka amsa suna rakashi da dariya.

        Shima da yaje sai daya wana sumayyan yadda akayi masa,yace nan zata ci gaba
da zama shi zai koma,ta amsa amma baki daya kamar wadda aka zarewa laka,sai da suka
gama shirin kwanciya sannan ya cafkota yana mata dariya
"Iyeeee,ashe yarinyar ta sab ciwon miji ko?" Dariya ta kubce mata tana kai masa
dukan wasa tare da fadin sai ta rama.

  ******    ******    ********

       Sama sama cikin barcinta ta dinga jiyo tamkar muryarsu shi da su'ad,tunda
suka iso qasar ta lura akwai abinda ke faruwa tsakaninsu,saidai ta dauke kanta
tunda bai shafeta ba kuma basu sanyata ciki ba.

        Randa su'ad ta iso da baturiyar kukunta ranar daga sumayyan har su'ad ding
sunga tashin hankali da ainihin almustaphan,su'ad na daga kai suka iso gidan tare
da ita,ta kuma bata umarnin shiga kitchen ta dafa musu ita da almustapha nau'in
abinci kala kala tunda girkinta ne,da yake sun riga su'ad din isowa da kwana
biyu,hakan ya sanya sumayyan bata bi ta kanta ba ta miqa mata kwananta.

       Tunda aka jere abincin ya dinga binsu da kallo daya bayan daya,kallo daya ya
musu yaji baki daya basuyi mishi ba,zuciyarshi ma sam ta kasa aminta cewa order
tayi musu
"Wadan nan abincin fa daga ina?" Ya tambayeta yaba dubanta,murmushi tayi tana zaton
ta burgeshi ne
"Kuku na taho mana da ita ta musamman,kuma mommy ce zata dinga biyanta" wani abu ne
ya tsaya masa a wuya,baturiyar mai dafa abinci cikin gidanshi wadda baisan da
zamanta ba?,babban abinda ya fara baqanta masa rai wai mommy ce zata biyata
albashi,me suke nufi kenan?,ya gaza shi din,wani abu mai daci ya tsaya masa
awuya,mutum ne shi da baisan raini,irin mazan nan ne da basa buqatar tsinke ki
taimaka masa da shi cikin gidansa,Allah ya hore masa yafi qarfin duka
buqatunshi,bai marmarin ko daga waje ayi ma iyalansa kyautar abin amfanin
gida,yafiso komai suyi amfani da abinda ya fito daga aljihunsa,kallo yaci gaba da
binta da shi wanda take jikinta yayi sanyi,ta rasa wanne irin kallo ne
"Ce miki akayi na gaza daukar nauyin kuku?,ke zaki bada labarin cewa babu irin
kukun da bazan iya ajjiyewa cikin gidana ba ko daga ina yake daga fadin duniya,sai
dai me?,banda ra'ayi,ke din ke nakeso ki shiga kitchen da kanki a matsayinki na
matar aure ki dafa min" sai a sannan ta gane har yanzu yana kan bakansa,tun a can
mummyn ta riga ta zigota kan kada ga yarda ya tauyeta tunda ba shi zai biyata
ba,hakan ya sanya ta fara fadin maganganu,ransa ya baci ainun,ya sanya mata ido
kawai,da yaga bata da niyyar saurarawa ya daka mata tsawa,wadda ta kada hantar
sumayya dake cikin nata falon tana kallon film tare da shan fruit,tsoro ya kamata
ra ture plate din gefe tana kiran sunayen Allah
"Na baki nan da minti goma ki tattarata ta bar gidan nan"
"Ba inda zata almustapha wallahi" ta bashi amsa daidai sanda kodaddiyar baturiyar
ta fito,sanye da mini skert  wanda idan tayi kyakkyawan tsuguno ba abinda zai
hanaka ganin mazaunanta da t shirt mai gajeran hannu,wani baqinciki ya sake
shaqeshi ya dakawa baturiyar tsawa cikin yaren da zatafu fahinta yake sanar mata ta
wuce ta tattara duk abinda tazo da shi ta fice masa daga gida,tuni ta soma rarraba
ido don bata taba zatar haka ba,idan ta fita din ma ina zata?,sai su'ad din ta
rushe da kuka iya qarfinta ko hakan zaisa almustapha ya sauya qudurinsa,ihun kukan
su'ad din shi ya daga hankalin sumayya,ta tsammaci ba lafiya,sabida haka ta yafa
mayafi saman doguwar rigar dake jikinta ta fito zuwa babban falo,dai dai sanda
mujadala ta harqe tsakaninsu,tuni yace ta hada kayanta itama ta bita,wanda hakan ya
sage nata gwiwa,maimakon hana mai girki tafiya sai ta koma qoqarin yadda ita din
zata zauna,kallo daya zaka yi masa kaga zallar bacin rai shimfide a fuskarsa,ita
kanta sumayyan sai da tsoro ya kamata ganin yadda ya birkice,da addu'a a bakinta ta
nufi inda yake zaune saman dining yana fuskantarsu,gefanshi ta tsaya cikin kwantar
da murya
"Haba yallabai,haba.....bai kamata ba,ba fa cikin qasarmu muke ba,yanzu ta yaya don
kawai ta maka laifi zaka ce tabi baquwar fuska subar gidanka?,kasan kuma yanzun
qarfe nawa,a karamcinka ko mai aikin bai kamata kace ta fita ba,koba komai macace
mai rauni,balle kuma matarka ta sunna....kayi haquri don Allah ka sawa zuciyarka
ruwan sanyi,yanzu kaga baki daya fushinka ya hautsina gidan ummm,ina kake so musaka
ranmu?" Shiru yayi yana sauke numfashi sannan ta juya ga su'ad
"Anty....tunda baiso kiyi qoqari gobe ki saya mata ticket ta koma a zauna lafiya
don Allah" harara ta wurgawa sumayyan amma bata ce komai ba,saboda ko banza taji
dadin ganin almustaphan yayi shiru,miqewa yayi ya dauki muqullin motarshu dake
ajjiye kan freezer ya fice,dukkansu suka bishi da kallo,sai da ya gama fita kowacce
ta dauke idonta,suka hada ido sumayya da su'ad,sumayyan tace
"Don Allah anty kiyi qoqari ki karanceshi ku daina musayar yawu haka da shi,gaban
baquwa fa ba don Allah yasa bata jin yaren ba,haramunne mace ta dinga daga murya
sama data mijinta,miji sama yake da kai dole ka saukar da kanka qasa ka bishi,tana
janyowa kanta tsinuwar mala'ikun Allah" ta fada a tausashe
"Ke da Allah sauraramin,a naku tsarin ba,ba wanda yafi wani tsakanin mata da miji
kowa mai 'yancin yin yadda yaga dama ne,wai wa ya saka da ke ma?" Kada kai tayi
babu alamun jin haushu a fuskarta
"Allah ya baki haquri idan kinji haushi"ta juya a nutse ta shige falonta ta zauna
taci gaba da binda take,saidai lokaci lokaci hankalinta na kan agogo,har ta soma
gajiya da zaman ta buqaci kwanciya bata ji motsin shigowar almustaphan ba,har dare
ya soma shiga sha daya da kusan rabi,duk da su a can daren ba komai bane
wajensu,hakan ya daga hankalinta,ta dauki wayarta ta dinga qoqarin nemansa saidai
sam bata samunshi,sai data gwada a qalla wajen sau biyar ana shida ta dace ya
shiga,a jiyar zuciya ta sauke
"haba yallabai,ka tashi hankalinmu fa" shima ajiuar zuciya ya sauke,muryarta ta
soma rage masa bacin ranshi
"Me ya faru?"
"Ka fita cikin iyalanka cikin fushi,sannan kuma har war haka ace baka dawo ba ai
dole hankalinmu ya tashi ko?"
"Lafiya nake,kawai yau bazan kwama gidan bane,sai gobe idan Allah ya kaimu,ki
kwanta kiyi bacci sosai,good night" ya katse wayar yana jin dadin yadda ra kula da
shi har ta nemeshi,ya tabbatar idan su'ad ce kota nemeshi qorafi ne abu na farko da
zata fara ba tare da kwantar da murya ba,ranan haka ya kwana sai da safe sannan ya
dawo cikin gidan,to sai gashi yanzu tana tsaka da bacci ta soma jiyo muryansu,wanda
hakan ya sanyata farkawa ba shiri,uwa uba da kuma yunwa data fara tambayarta,har ta
shiga toilet rayi brush ta fito tana jiyosu,ga yunwa tana sadakarta,bata so ta fita
ta taddasu haka,amma dole ta sanya hijabinta ta fice sanoda yadda cikinta ya soma
motsawa saboda yunwa.

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

1⃣0⃣2⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

*ya zul jabarutu wal malakutu wal kibriya'i wal'azmati*


_____________________________________

       Tunda ta fito ta fuskanci maganar dai kusan kan shiga kitchen ne,ita kanta
ta gaji da wannan jeka ka dawo magana daya tak mai sauqi amma ta rasa dalilin su'ad
na qin yarda da maganar tashi,har zata rabe ta wuce sai kuma ta fasa sakamakon tuna
fadar Allah da tayi
"Haqiqa muminai 'yan uwa ne kuyi sulhu tsakanin 'yan uwanku", a nutse ta qarasa
wajen da suke tsaye,ta sanya hannunta ta riqe hannun almustapha ta gefe ta yadda
su'ad din na zata gani ba ta soma matsawa a hankali idanunta cikin nashi,cikin 'yan
kwanakin nan su'ad tasa ta ga halinshi da bata taba gani ba,ta fuskanci yana da
fushi saidai yakan jima ba'a ga fushinsa ba,barshi dai da miskilanci wannan
tambarinshi ne,sai data fuskanci hankalinshi ya soma dawowa gareta yayin da su'ad
rayi carko atsaye tana jiran kota kwana
"maan" karon farko ta kirashi da sunan da mutane ke yawan kiranshi,saidai yaji
sunan ya zama wani sabi na musamman daga bakinta,a tausashe hadi da karyar da wuya
tace
"Bai kamata ba....." Dakatar da ita yayi da hanzari ra hanyar daga mata hannu
sannan ya waiwaya ya dubi su'ad
"Option ne na baki,na kuna rantse yau ko zaki kwanta asibiti sai kin dafa tea din
nan,naga wanda zaya sake min order din abinci cikin gida na" yana fadin haka ya
zame hannunshi daga nata ya wuce zuwa sashensa,da kallo suka bishi,yayin da gaban
su'ad ke faduwa,ta tabbatar da cewa yau din matuqar bata yi abinda yace ba babu
abinda bazqi iya faruwa ba,saidai ta yaya zata ta ina zata soma tunkarar
kitchen?,sai kawai ta wuce fuuu kaman guguwa ta shige kitchen dinta,sam abun baiwa
sumayya dadi ba,hakan ya sanya batayi qasa a gwiwa ba ta bishi zuwa dakinsa.

      Yana tsaye gaban window,hannayenshi zube cikin aljihun wandonshi,qoqari yake


yayi controlling kansa tare da hana zuciyarsa aikata abinda take raya masa,so yake
yaga ta ina ya gazawa su'ad,ci?,sha?,sutura?,kudin kashewa?,walwala ko adalci,duka
babu,babu ko daya daga ciki,hasalima ta wani bangaren tafi sumayyan samun wasu
abubuwa,tunda suka fara tarayya da sumayya bazai iya tuna rana qwaya daya tak da ta
tambayeshi wani abu ba,saidai shi don gashin kansa ya bata,ko idan su'ad din ta
tambaya yayi adalci itama ya bata duk da bata tambaya ba,abinda ya lura ma shine
tara su take,ba abinda take da su,shi kansa yasan babu wani anu qwaya daya da na
kusa da shi bama iyalinshi ba da zasuyi kukan basu da shi ko yafi qarfinsu,shi a
ganinsa babban abun kunya ne ma ace kai din wani je,ko Allah ya maka rufin
asiri,ana maka kallon mai rufim asiri,a ganka cikin kama kai kyau amma iyalinka a
wahale ko cikin mummunar kama,wannan shine babban abin kunyar da magidanci zai
aikata wanda zai jawo masa tur da ala wadai a bakunan al'umma.

       "Abu abdallah" ta furta a nutse,tunda yaji sunan yasan itace,amma hakan bai
sanyashi ya waiwayo ba,sai ya nutsu yana jin yadda take takowa zuwa inda yake
tsaye,bata dakata ba sai data sha gabanshi,ta tsaya tana dubanshi idanunta cikin
nashi kaman yadda nashi yake,duk da cewa a cikin hijabi take,duk da cewa daga bacci
ta tashi batai wanka ba,duk da cewa ba ko digon kwalli cikin idanunta amma bata
fasa yin kyau ba cikin idanunshi,kyanta cikarta da kamalarta sun fito muraran,ta
jima tana kallonshi wanda sannu a hankali dumin da zuciyarsa tayi ya soma sauka,da
wannan damar tayi amfani ta soma cewa
"Ina ganin bata haka ya kamata ka bullowa anty ba....bazaiyiwu dare daya kace sai
ta maka girki ba bayan can bata saba ba,a mata haquri a bata dama ta koya
tukunna...."
"Wacce damar?,wacce dama za'a bata ne sumayya?" Ya furta cikin sanyi,saidai daga
yanayin yadda yake maganar kawai kasan ranshi akwai sauran damuwa a ciki
"Akwai damar data wuce na sai mata rana guda cikin ranakun makaranta catering
school?,ta koya ita kadai?,cikin gida ko a can duk wanda take so?......daga yau
bana son ki sake sanya baki cikin wannan matsalar...ki barmu" ya fada cikin salon
dakatarwa,yawu ta hadiye kafin ta sake lanqwasa murya
"Kayi haquri idan hakan ya bata maka,banyi ba da niyyar shishshige...rayuwarka
rayuwata ce,haka nan rayuwarka rayuwar su'ad ce,hakan na nuni da cewa dukkaninmu
abu guda ne...kwanciyar hankali nutsuwa da zaman lafiyar dayanmu yana da amfani a
garemu baki daya,bazanso ace kullum kai da ita ba kwanciyar hankali ba....hakan zai
iya shafata zai iya shafar iyalin da muke son samarwa nan gaba,tunda dai muna tare
da ku"idanu ya zuba mata yana karantar tsantsar gaskiyar dake cikin zuciyarta da
takeson fadi,hankali nutsuwa da karamci ne zallah cikin kalamanta,don me yasa ta
samu dama irin wannan maimakon tayi qoqarin tarwatsa zamansu da su'ad ta mallakeshi
ita daya saima take qoqarin gyarawa?,kyakkyawar zuciya ce itace amsa,wadda ba
kowanne bawa Allah yake wa baiwarta ba,sai 'yan baiwa daga cikin bayin
nasa,maimakon ya bata amsa kawai sai ji tayi ya janyota cikin jikinsa ya juyata da
hanzari ya rungumeta ta baya yana shinshinarta,duk da cewa batayi wanka ba amma
hakan bai hana wannan qamshin nata mai sanyi fita daga jikinta ba,dumin fatarta ya
dinga ratsawa cikin tashi,hannunshi ya dora saman cikinta yana yawo da shi,wani
farinciki na maye gurbin bacin ranshi,duk sanda ya farka da shi yaje farkawa cikin
ranshi,kullum yana lissafe da ranar da zaya iso cikin duniya
"Wannan ne abu mafi muhimmanci da ya kamata ace kinyi zaki tsaya kina wani tsarani"
dariya ce ta kubce mata ta soma qoqarin boyeta
"Au tsara ka ma nake yaya?"
"Waye yayan naki,yau kuma yaya na zama?" Girarta ta dage sanda yake leqo fuskarta
"Eh....ko nayi laifi?"
"A'ah....bakiyi ba" ya fada yana cikata tare da durqusawa gabanta,tasan me zayayi
tunda ya fara kware mata hijabi,ba dama su tsaya inuwa daya sai ya fara lalubar
cikinta,baya ta ja tana ware ido tare da kada masa yatsa alamar a'ah,sosai idanun
nata suka fito sun sake wani fari tas da su,hakan yaso shagaltar da shi
"Sulhu nazo nema ba gaidaka muka zo yi ba" sai ya miqe daga durquson da yayi yana
ci gaba da kallonta tare da nuna kanshi da yatsa
"Ni kuka yiwa haka?,zamu hadu,awa ashirin cif suka rage" dariya ta saki ganin yadda
yake kwatantawa da hannunshi,ta juya taba niyyar ficewa,duk da yadda tayi kewar
lafiyayyar fatarsa amma hakan bazaisa ta bashi dama suyi wani anu sq zai sosa ran
su'a din ba,abinda ko ita aka yiwa ba zata taba jin dadi ba
"Amma kaman zazzabi naji jikinki ko?" Waiwayowa tayi tana dubanshi
"Ina jin hakan idan na tashi da safe,amma da nayi wanka shikenan bana sake ji"
"Ko nazo na dubaki?" Ta gane sarai wayo yake son yi mata sai ta saki qaramar dariya
sannan ta juya ta fice tana cewa
"Mun yafe".

       Kacaniya sosai ke tashi a kitchen din kamar wadda zata dafa abincin baqi
dari,ta rasa inda zata tsomala kanta,gefanta sumayyan ta nufa da niyyar dafa ko
couse couse ne sharp sharp tunda tana da miyar hanta a fridge,har ta dauko tukunya
taji su'ad ta fasa ihu,da sauri ta waiwayo kana ta nufeta,tukunya ta soma dorawa
bayan ta kunna gas din,sai da tukunyar ta dauki zafi sannan ta taro ruwa ta soma
zubawa,tururin da taga ya taso ya nufo hannunta shi ya sata sakin qara ta yarda cup
din ruwan nan ua tarwatse a wajen har ya kashe wutar gas din gas ya soma fita,da
hanzari sumayya ta qarasa tana ambatar subhanallah ta kashe gas din,sannan ta dubi
su'ad data janye gefe
"Amma dai bakiji ciwo ba?" Harara ta watsa mata,dukkan komai itace ummul aba'isin
data tsiri yi masa girki da ya sashi cewa itama sai tayi,da can ai basu san dora
tukunya gidan ba idan ba kuku ne yake nan ba,ganin bata amsa mata ba ya sanyata
nufar wajen ta sauke tukunyar daga saman gas din ta zubda ruwan ta zuba sabo sannan
ta sake kunnawa ta dora,inda suke ajiyan kayan tea ta nufa ta hada ganyayyaki masu
dandanon da tasan almustapha naso ta dinga gwadawa tana zubawa ta gama ta sanya
ganyan shayin ahmad tea ciki sannan ta maida murfi ta rufe,su'ad na gefe haka kawai
taji kishi ya rufeta yadda taga sumayyan nayi,itakam bata lura ba tace da ita ne
kawai
"Idan ya dahu zakiji yana qamshi sai ki juye a flask" tsaki ta bita da shi
"Nima na iya ai basai an nunan iyawa ba" bata bi ta kanta ba tayi ne dama kawai
saboda mijinsu,tunda ta sani tunda ya kafe tofa sai tayi kuma sai ya dandana ko
baici ba,idan bai masa ba dandanon baci zaiyi ba haka zaya fita da yunwar cikinsa.

       Tana tsaka da bare plaitain ta soma jiyo qamshin dahuwar shayin,cikin flask
din tea na alfarma dake kitchen din su'ad ta zabi daya ta fiddoshi ta bude ta
ajjiye cikin sink,tukunyar ta tsurawa ido,yadda take tururi kawai ya sanya ta
tsorata,ta yaya ake juyewa kawai take tunani,haka tayi qundunbala ta janyo towel
hand socks dake maqale a hanger da suke ajiye towels na kitchen ta zura a
hannunta,murfin ta fara budewa tayi wancakali da shi nan ma tayi gefe tana haki,ta
dauki a qalla minti biyar ta rasa ya zata sauke,murmushin mamaki ya qwacewa
sumayya,ashe da gaske akwai irinsu su'ad a duniya?,wannan mece a cikin mata,sai
kawai ta miqe ta isa bakin tukunyar ta ciri safa daya ta sauke tea din tana juyeshi
a flsk din,tana tsaka da juyewa ta matso kuda da ita
"Waike wa ya sakaki,ce miki akayi bazab iya ba?" Sai data gama juyewa ta daga kai
ta kalleta
"Na san zaki iya ai,kawai taimako ne kuma ba laifi hakan ko a musulunci" shiru tayi
tana daure fuska tare dq zare idanu har ta gama ta kulle flask din bayan ta
daurayeshi ta wuce gurin nata sabgar.

      Kusan dai har ta gama bata san me su'ad ke ciki ba,tana gamawa ta juye
plaitain dinta ta dumama liver souce dinta ta fice ta bata kitchen din.

       Tun daga lokacin matuqar tana kitchen din zata mata iya gyaran da ya
dace,bata damu da duk abinda zata fada ba,tana yine kawai saboda almustaphan,tun
tana masifa har ta dawo saidai harara,sau tari dariya take baiwa sumayyan,saboda ta
lura da cewa tsabar girman kai ne kawai ke dawainiya da su'ad din,wani lokaci
qunshe dariyarta take kawai idan tana girki,abin sai wanda ya gani,taka hau yanar
gizo ne ta dubo yadda ake yi,wani abun bai ciyuwa hatta gurin wanda ya takura din
sai ta dinga yi,idan har ya ciyu to ranan sumayya na kusa ta sanya hannu,cikin
qanqanin lokaci su'ad din ta fara gane shayi ruwa ne,tayi roqon tayi magiyar ya
samo mata mai aiki yayi funfurus da ita,har kukan takaici da wuya duka sai da
tayi ,ya share tamakar baisan tana yi ba,don wannan ce kadai hanyar da zai hora ta
kan iskancin da take ji saman kanta,har sumayya a wani dare take roqarshi ua samo
matan wadda zata kama mata,saboda tana ganin yadda ake gwagwagwa wajen dafa shayi
ma kawai,har yau ta kasa dauke yadda ake,ita dinma shiru ya nata kaman baiji me
tace ba,ganin hakan ya sanya taja bakinta ta tsuke,tasan tunda yayi hakan baison
zancen ne,sai da ya tabbatar ta dahu sannan ya samo wadda zata dinga taimaka
mata,da sharadin tare zasu dinga yi tana ganin yadda akeyi.

      Abu na gaba daya soma jan hankalinta shine yadda ta fuskanci maan din na nuna
tsantsar kulawa da riritawa ga cikin dake jikin sumayyan,da fari ta dauki abun duka
wasa,sannu sannu ta soma fahimtar soyayyar da bata taba gani yana yiwa wani abu ba
ita yake gwadawa abinda ke cikin dako duniya bai iso ba,bata tabbatar da haka ba
sai a wani yammaci wanda ranar sumayya zata karbi girki.

       Tun da yamma tana zaune babban falonsu,bata faye zama cikinsa ba sai jifa
jifa amma yau ta kasa ta tsare,sam sumayyan bata damu da zamanta ba,sabgoginta take
hankali kwance,zuwa qarfe biyar ta gama shirya masa dining tsaf da kalar abincin da
yace yana so,bayan itama ta hada wanda ranta ke so,shinkafa ta dafa ta zuba wake a
kai ta bare kifin gwangwani a kai,sannan ta soya manja ta yanka salad tumatir
albasa da cocumber,tana da yajinta tun daga gida wanda kusan shi ya tada mata
kwadayin cin fara da man ma,salad dinne kawai bata gyara ba don haka ta barshi ta
shiga wanka,ta shirya tsaf cikin wani wando ya lafe a jikinta kamar a jikin nata
aka dinka shi,da kadan ya zarta gwiwa,wandon baqi ne hakan ya sanya ta saka shirt
fara,ta gyara gashinta ta daureshi da baqin ribbom ya sauka har saman
kafadunta,fashion tayi amfani da su baqaqe masu adon farin stone ajiki,lite make up
ce a fuskarta wadda tasan tafi burge almustaphan,feshe jikinta tayi da turare
sannan ta laluba cikin kayanta ta zaro abaya,har ta zura sai kuma ta cire,sam yau
sai taji bata sha'awar saka ta,bata bari su'ad ra ganta cikin irin wannan
shigar,yawanci tafi zama haka sanda suke falonshi ko nata falon su biyu,wasu
slippers masu kyau baqaqe da suka bayyana kyan farar qafarta ta zura sannan ta tako
a hankali ta fito.

      Qarar bude qofar falon nata da rufewa ita ta soma jan hankalin su'ad
din,idanu ta zuba mata baki daya,sannu a hankali wani kishi ya soma sokarta na
ganin yadda sumayyan tayi kyau kamar 'yar tsana,kai kace drowing ne na girly,cikin
da take tsammani zai batata sai gashi ya zame wani ado a jikinta,ya shiga wata na
biyar ya zauna daras a jikinta abin sha'awa,ko daya bai tafi  da hips da boobs da
take da su ba saima qara fito da su da yayi,karon farko data soma ganinta cikin
yanayin shigar,a hankali ta janye idanunta daga kanta kishi na nuqurqusarta,da ciki
ma kenan ina ga tana ita kadai?,ta yiwa kanta wannan tambayar,da qyar ta iya hadiye
yawu ta maida idanunta kan t.v taci gaba da kallo ba don tana fahimta ba,itakam
dukkan abin nan da take batasan tana yi ba,kanta tsaye ta shige kitchen tana daga
tsaye ta soma gyaran salad dinta.

        Tunda ya shigo baki daya tayi gaba da dukkanin imaninsa,ruwa ya shigo sha
amma baki daya ya nemi qishirwar ya rasa,sai kawai ya harde hannunshi a qirji ya
jingina da qofa yana kallonta,baiso ma tasan ya shigo bare ya ta daina
kaikawonta,ilahirin jikinta yake bi da kallo,wani sanyi da farinciki na saukar
masa,godiya yakewa Allah cikin zuciyarsa,ba shakka duk yadda yaso ga son dai daita
matsayinta cikin zuciyarshi da sauran mata yasan yayiwa kanshi qarya,abune ba mai
yiwuwa ba,koda ciwon makanta da ciwon bacewar tunani zai kamashi yana da tabbacin
zai iya gane randa yake ranar girkinta,tun daga harabar gidan da yake iya ajje
motarsa kama da duk wani lungu da saqo na gidan sauyawa yake,ba'a magana qamshi
tsafta da sauransu,sai yake jin kamar harda iskar gidan ma sauyata ake,babu mamaki
ko don tsananin soyayyarta da kullum kwanan duniya ake linka masa ne?.

        Sai data gama yankawa ta isa gaban famfo ta tara shi cikin ruwa,da hanzari
taji an jawota,ko da daga bacci ta tashi tasan waye,mannata yayi da jikinsa ya
zagaye hannayensa saman cikinta,sannan ya dora kanshi kan kafadarta
"Barka da dawowa....barka da dawowa sanyin idaniya hasken cikin gidansa....tun dazu
naji yanayin gidan ya sauya ashe yariman maza ne ya iso" baisan sanda ta juyi da
ita suna fuskantar juna ba,idanunta cikin nashi tana masa wani irin kallo,shi dinma
kallon yake jifarta da shi,ya gaza cewa komai,ko yaushe furucinta na musamman ne a
gurinsa,duk abinda zata furta ya isa kunnenshi mai dadi ne,mai laushi ne,mai taushi
ne mau faranta zuciya tare da zare mata gajiya da baqinciki,kasa cewa komai yayi
sai kallon kallo tsakaninsu tare da jifan juna da murmushi,bakinsu kawai ya hade
waje daya yana aijata mata da wasu kisses masu zafin gaske,ganin yana neman wuce
gona da iri a muhallin da bai dace ba ya sanyata tureshi suna maida numfashi,ya
matsa din amma bai bar jikinta ba,dubanta yake da rikitattun idanunshi da suka
sauya lokaci daya,cike da shauqi yake dubantan nata
"A kitchen muke fa" ta fada a shagwabe,hancinta ya kama ya dan jaa
"To waye ya jawo?,irin wannan shigar ko gaban wa na ganki hakan na iya faruwa" ya
fada da qyar cikin muryarshi dara fara jirkicewa
"Bamu gaisa da baby ba" murmushi ta saki
"Wannan baby......wanne irin qauna ne haka my maan" kada kai kawai yayi yana
murmushi,qugunta ya riqo baki daya da hannayenshi
"Qauna?,indai wannan ce qauna to kam bakiga komai ba,babu abinda kika gani
babe....banajin zan iya bayyana qaunar da nake mishi ko mata,daga cikin dalilan da
ya sanya kenan ban damu da duba me zaki haifa min ba,ko me kika haifamin ina so ina
maraba da shi,gudan jin muhammad almustapha ne da summyn malam" murmushi ta saki
sosai saboda sunan da ya kirata da shi har fararen haqoranta na bayyana,dubanta
yake shima yana murmushi wani farinciki na shigarshi,da kanta ta yaye masa t.shirt
din dake jikinta zuwa saman cikinta,ya durqusa a hankali hannunshi saman cikin.

     wani wawan tsaki mai shiga kunnuwa suka ji anja,su'ad ce wadda tun shigowarshi
cikin kitchen din ta kasa samun nutsuwa,baki dayan hankalinta ya karkata kitchen
ne,ta kasa zama har sai data biyo bayansu,kusan duk rabin maganar tasu cikin kunne
da idanunta suja yisu,wanda sam basu san da shigowar tata ba banda yanzun,ko kusa
ko alama bata taba sanin cewa haka almustaphan ke qaunar haihuwa ba,tayi tsammanin
cewa ra'ayinsu daya a qidarsu daya,saboda ganin ko alama bai taba mata magana kan
rashin samun juna biyunta ba,abinda bata sani ba shine yana sawa rashi lokaci
ne,idan yayi zata haifa masa,bugu da qari yana tausayim macen da bata haihu
ba,hakan ya sanya yake ganin girma da qimar ni'imah har gobe
"Amma dai wannan abun bai dace ba ko?" Ta fada zuciyarta kamar zata fadi
qasa,waiwayowa yayi yana dubanta
"Shigowa kai tsaye ba tare da yin sallama bane bai dace ba ko ko meye?" Kasa cewa
komai tayi don tasan ita ta kawo kanta,ta sani cewa duk ranan girkinta hatta da
zurga zurga sumayyan bata fiya ba,data gama uzurorinta ta masa sallama shikenan sai
da safe,mazewa ta sake yi kishi na cinta
"Kitchen wajen kowa ne,na shigo daukar abu sai na fasa saboda ku?"
"Yaushe kika fara labe?,kina tsammamin banga shigowarki ba?,kina tsaye tsohon minti
goma?" Mamaki ya cikata,bata yi zaton ya ganta ba,da shigowa daukan abu tayi niyyar
fakewa tayi boren qarya,da idanu ya tsatstsareta yana hukuntata da kallonshi,wanda
ta san fassarar hakan sarai,duk sai ta daburce,numfasawa yayi ya dauke kanshi daga
gareta fuskanshi daure ya maida ga sumayya data soma wanke salad dinta
"Muje ki shiryan ruwa nayi wanka"amsa masa tayi da to,ta rufe salad dinta ta ajjiye
gefe sannan ta ratsa ta fice,sai data fice daga kitchen din sannan ya maida
kallonsa ga su'ad dake tsaye tana cije baki cikin takaici,a hankali ya tako zuwa
gabanta,daf da ita ya tsaya tazarar dake tsakaninsu bata da yawa
"Me yasa ko yaushe baki daukan gyara?,baki gyaran kuskurenki cikin sauqi?,Kada kiyi
abinda zai siya miki raini,ki guji yin abinda bai dace ba,abinda duk kikasan ba'a
yi miki ki nisanci yiwa wani,umarni na baki ba shawara ba" baya ya danja sannan ya
juya shima ya fice,yafi kowa sanin halinta,tafi gane tsauri,daukar sauqi take
tamkar wata isa ce tata tasa ake mata hakan.

       Dukkanin maganganunsa ba damunta sukayi ba a yanzu,abu daya tak ke mata yawo


cikin kwanya da qwaqwalwa,so qauna kulawa da tsantsar soyayya da ta gani zalla a
qwayar idanunshi yana nunawa ga ciki dama wadda ke dauke da cikin,me yake shirin
faruwa ne?,shine tambayar da take wa kanta,a hankali qwaqwalwarta ta soma mata
tariyar wasu shekaru can baya da suka shude,shekarun da a cikinsu ta fidda
mahaifarta,a sanda anty kubra ke zabga mata fada,a lokacin da take gaya mata tayi
kuskure,take gaya mata zata iya dana sani a gaba,take shaida mata matakin kama
almustapha a hannu da kyau shine ta ajjiye masa iri,ta hada jini da irin gidan
baban,shine zata samu dukkan abinda take so,zata zama tasu ta har abada,jinta take
kawai a sannan,gani take labarin qanzon kurege ne kawai,tunda bata ga wani damuwa
ko alamu tattare da da almustaphan ba,saidai a yanzu jikinta ya soma sanyi,wutar
kishi ta soma nuna mata akwai wani abu dake shirin faruwa,tattalin da take gani
wajenshi a kanta ya zarce soyayyar da yake mata ita daya face harda ta abinda ke
cikinta,indai ko haka ne itace mafi cancanta data samu wannan launin soyayya da
qauna mai ratsa gangar jiki da zuciya,saidai zata sanya ido taga shin abinda take
hasashen haka ne?.

*gobe ina da uziri,idan kuka jini shiru saidai kuyi haquri,duk da zanso ace na
muku,so nake mu kammala littafin nan kusa in sha Allah,na gode*

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

1⃣0⃣3⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

*Allah S W T yana cewa*

*kuyi guzuri,amma mafi alkhairin guziri shine TSORON ALLAH*


___________________________________
        Cikin nutsuwa da kwanciyar hankali take renin cikinta,wanda bata taba sanin
hakan kwanciyar hankali ke da dadi ba yayin rainon ciki sai yanzu,bata da wata
matsala yanzu gaba daya a kafatanin rayuwarta,kullum kwanan duniya farinciki ke
sake riskar rayuwarta,tako wanne bangare rayuwa na mata kyau fiye da yadda take
so,gefe guda ga mai gidanta mai share kukanta yana tare da ita ako da yaushe,ba
abinda ta nema cikin rayuwarta ta rasa,ko da yaushe suna waya da dukkan 'yan
gida,halima tuni cikinta ya tsufa dab take da haihuwa,abdallah har yau na wajensu
ya dawo wajenta baki daya,ya zama tamkar danta,kai idan ba gaya maka akayi ba
bazaka taba cewa basu suka haifeshi ba su da abdur rahman,zainab ma ta samu wani
cikin bayan barin da tayi,amira ana can ana fama da laulayi wanda ya sanyata tayi
laqwas,ashe da wasa farin garki,nafisa qawarta matar auwal itama ana can ana
fama,ko yaushe suna waya tare da yiwa juna fatan sauka lafiya.

       Sulaiman wato malam mahaifin sumayya tuni lamura sunyi nisa,ci gaba ake ci
gaba da samu cikin gidajen gonakinsa,ya dauki ma'aikata sosai da zasu kula masa da
gidajen gonar nashi dake gwambe kano da abuja,shike kula da na kano,na gwambe sun
sake diban samarin dake cikin ainihin karkararsu,na abuja kuwa ya bar komai wajen
baban tunda yafishin sanin ya yanayun garin yake,tuni malam din ya soma zama wani
na musamman shima,gida ya gina musu yalwatacce wanda aka qawati shi da kayan alatu
da more rayuwa,sashe biyu ne madaidaita hakan ya sanya yaya abubakar dauko meenat
matarshi suka dawo daya sashen da yaransu guda uku,hakan ya yiwa mama dadi
qwarai,don dama gidan ya zama sai ita kadai,gashi ya mata girman da bazata iya zama
ita kadai din ha,amma dawowarsu amina da jikokin maman hakan sai yayi mata dai
dai,zumuncin baba da malam din kuwa sai abinda yayi gaba,don basu cikakken wata
basu ga juna ba,ko malam din yazo ko kuma baba yaje,da haka wani lokaci suke zuwa
da matansu,wanda hakan ya haifar da sabo sosai tsakanin anty maamaa mama da kuma
ummi.

       Ta gefan hajiya su'ad kuwa baki daya ta gama karance takun almustapha tsaf
ta gane komai,son haihuwr yake kaman ya jawo randa yaron zai fito duniya,cikin
qanqanin lokaci jikinta yayi sanyi ya mutu baki daya,a hankali ta soma tunanin me
yasa bata fahimvi yana son yara ba?,me yasa bata gane ba?,tun daga sanda yace zaya
bude gidan marayu da yanda yake nacin zuwa yaci ace ta karanci cewa shi din mutum
me mai son yara da son mu'amala da su,kullum kwanan duniya ta kwanta tunaninta
shine yadda zata gyara kurenta,ta yaya zata ganta da ciki?,ta yaya zata haihu?,har
yau abinda ke sakadar zuciyarta kenan,batasan da wa zata yi shawara ba,anty kubra
ce,saidai ta tabbatar cewa fada zata sha kafin daga bisani tace ita din ba
ruwanta,da mamarta kawai zata shawarta,saidai maman sunyi tafiya da babanta basa
samun zama,lokaci kawai take jira na dawowarta ta zauna susan yadda zasu gyara
lamarin.

  ******  *******    ********

       A hankali take tako lallausan carfet dake dakin zuwa inda yake zaune shirye
cikin jallabiya ta maza dark brown,ya dora hirami akanshi wanda ya dace da
jallabiyar,hannunshi daure da baqin agogo,system ce gabanshi yana rage wasu ayyuka
yayin da yake tsumayin fitowarta,zasu je siyayyan kayan baby ne,duk da cewa yana
daga gida zai iya fadin duk abinda yake so a hado masa daga dukkan kamfanin da
yakeso cikin fadin duniya,saidai yana so su fita su shiga kanti da kanta don
sumayyan ta tattaka da qafafunta tayi zagaye saboda lafiyarta.

       Sanye take da abaya peach mai adon duwatsu masu qyalli,peach mai turuwa da
mai haske,tayi rolling da wani wadataccen mayafi  dark peach,plate shoes ne a
qafarta shima kalar rigar,sosai cikinta ya fito kai kace yau ko gobe ne
haihuwar,wanda alokacin baki daya bai wuce wata bakwai da sati biyu ba,a jikinsa
yaji fitowarta ya daga kai a hankali yana kallonta,baisan sanda murmushi ya subu ce
masa ba,aduk sanda kake da buqatar ganin fara'a qarara kan fuskarshi to yayi tozali
da sumayya tana takowa zuwa gareshi dauke da cikinsa,duk duniya shine abu na farko
dake faranta masa rai a duk yanayi ko matakin da ya tsinci kanshi,sau tari yakan
ayyana me zata haifa cikin ranshi,jikinsa na bashi cewa twince ne musamman idan
yana mata awo,saidai bai taba sha'awar duba meye acikinta ba,yace koma meye yana
marhaban da zuwanshi,miqeww yayi tsaye ha cimmata a inda take kafin ta qaraso,ya
bude tafin hannunshi ya sanya nata yana murmushi
"Wai wannan cikin naki anya babe?"
"Mene?" Ta tambayeshi tana daga gira,tattausan murmushi ya sake mata yana kada kai
"Shikenan.....muga qafar taki,ina fata ba kumburi ko?" Silifa din ta zame tana
tayashi duba qafar tare da cewa
"Eh yanzu kam babu,tun jiya bai sake yi ba" gabanta ya durqusa yana mammatsa qafar
kafin ya miqe yana cewa
"Masha Allah,Allah ya raba lafiya" dariya ta qwace mata ta dubeshi yanayin yadda ya
furta maganar kaman mace
"Amin abu abdallah"
"Ummu abdallah...da zarar kin haihu fa za'a sauyan suna,saboda na zama daddyn yara
da yawa,zan koma ABUL AULAD ke kuma UMMUL AULAD" idanu ta lumshe tana jifanshi da
wani kallo,sosai sunan yayi mata,tana mamaki idan taju yana larabci,duk da hakan
bai rasa nasana da zamanshi cikinsu,kai take gyadawa cike da gamsuwa
"Hakan yayi,amma har yara nawa zamu haifa da suka zama AULAD?" idanunshi yadan zaro
yana kallonta
"Ko dozen haka ai sunyi ko?" Dariya ta tuntsire da ita shina yana tayata
"Eh lallai kayi dariya mana,bakusan yadda ake ji ba,a haifa muku kawai" qugunta ya
kama suka fara takawa yana bata amsa
"Da gaske wallahi Allah nake miki,ina son naga wannan ya dane min wuya,wannan ya
zauna acinya,wancan ya kaman kunne,wannan yana jamim hanci,wannan yamin fitsari
wancan yamin bayan gida" dariya sosai ta kamata yadda ya taqarqare yana zuba
bayani,har sai sata dafe cikinta tare da dakatawa da tafiya tana dubanshi
"Kace nanny zaka koma kenan cikin gidan?" Giranshi ya dage mata
"Laifi ne?,bakisan ma'aiki yana taya matanshi ayyukan gida ba?,sunnah ne fa"
murmushi taci gaba da yi,sai yayi bala'in burgeta ba kadan ba,haqiqa kyawawan
halayensa basa rasa nasaba da iliminsa
"Haka ne,Allah yasa mu dace"
"Amin beauty" ya fada yana jan hancinta wanda ya bude ya sake girma,sai ta kwabe
fuska tana dubanshi shi kuma yama boye dariyarsa
"Kawai kace mummuna mana ha'an?" Dariyar ta qwace masa baki daya,yasa hannu yana
toshe bakinsa,sai ta soma kukan qarya tana buga qafa daya don babu damar yin rigima
sosai,riqe hannayenta yayi sosai yana bata haquri kafin yace
"Ba wani yanayi da zaizo wanda zai sanya na kasa ganin kyanki,ko yaushe ke mai kyau
ce a wajena,ko da kuwa duka duniya basa gani,bare ma ha wannan ba,matuqar dabi'unki
na tattare da ke ko kece sarauniyar munana na duniya haka nakeson abata,kinsan me?"
Sai ta kada kai tana sauraronshi
"Dabi'a furuci lafazi da mu'amala sune abu na farko dake tallata dan adam,sune
abubuwa dake jefa soyayyar mutum cikin zukatan kowanne bil'adam,koda mutane basu
shirya sonka ba,sai kyawawan dabi'unka su rinjayesu su soka,haka kika mamayeni
babe,sonki ya cika qirjina" murmushi tayi ta sadda kai,shima fuskarsa dauke da
murmushin ya saka hannunshi ya daga kanta
"Ita kunya daure take da imani,idan aka dauke daya dole daya ya tashi haka annabi S
A W yace,kenan,duk wajen da kaga babu kunya to tabbas babu imani a wajen,haka wajen
da babu imani to kunya tayi qaura,duka kin hada my summy,don haka kin cancanci duk
wanu nau'in so da kulawa" yatsunshu uku ta riqe tana dubanshi
"Ummm ummmm,daina fasamin kai"
"Kin taba ji ko ganin na miki qarya" kai ta kada alamar a'a,don bai taba yi matan
ba,koda gaskiyar da zai fada zata qona mata rai bai fasa fada din
"Na gode,ubangiji yaci gaba da shiga cikin lamarinmu" sai da yayi kissing goshinta
sannan ya amsa da amin
"Muje ki kira su'ad mu wuce ko?"
"To....." Sautin bai gama fita ba suka ji anja tsaki,suka waiwaya suna dubanta
sanda take daga labule tana ficewa,ranshi ya baci sosai,me ya kawota har cikin
falon sumayyan?,bayan can ba shigowa take ba?,bama wannan ba,tunda suke tsaye tana
wajen tana kallonsu,da wani abu suke kuma na daban fa?,ba sallama ba neman
izini?,sumayya bata ce komai ba haka shima,sai yayi gaba ta tako a hankali ta biyo
bayanshi,
"Shiga kice mata ta fito" ya fadi yana gyara agigon hannunsa
"To" ta fada tana takawa da irin tafiyar masu ciki,ya bita da kallo da idanunshi
har ta shiga.

      A falom ta sameta tana tsaye,idanunta sun kada sunyi ja,tabbas kalaman da ta


jiyo suna fita daga bakin almustaphan su suka sata shiga taji me yake gaya
mata,kalamai ne masu nauyi dake fita daga ainihin qwaryar zuciya,tana zaton
mawuyacine fa idan batayi kuskuren da zai hanata sukuni a rayuwarta ba
"Amm....anty yace ki fito zamu tafi"
"Kije kice masa ba zani ba,fitar min daga daki tun ban zagi uban ubanki ba"ta fada
cikin tsawa da hargagi idanu ta daga ta dubeta kawai ta jiya a nutse ta fice,tabbas
ba don tana tsoron abinda zai biyo baya ba da babu abinda zai hanata shaqo wuyan
sumayyan tayita jibgarta kamar Allah ya aikota har sai taga ita da dan cikin nata
sun daina motsi,amma ta tabbatar yin hakan dai dai yake da rasa komai cikin
rayuwarta,ciki kuwa harda igiyar aurenta da almustaphan.

       A tsayen ta sake taddashi ya tsurawa qofar falon ido,ta iso inda yake ta
bude bakinta zata roqeshi yaje yaji damuwar su'ad din sai ya daga mata hannu
"wuce mu tafi"kawai yace da ita yana dubanta,ba musu tayi gaba,duk sanda yake cikin
fushi yakan koma mata almustaphan nan data sani a farkon rayuwarta,rufa mata baya
yayi suka fice.

       Cikin katafaren shagon da sukayi fice wajen samar da kayan jarirai suke
zagayawa,tana daukan duk abinda taga yayi mata shima yana tayata,fuskarshi a sakw
kaman ba dazun ranshi ya baci ba,kayane masu kyau da tsada wanda jinsin mace ko
namiji zai iya sanyawa(unisex).

         Daga gefansu kadan idanunta suka dinga mata gizo,kaman nuwaira take
hangowa ita da wata mata suna zaban kayan yara maza,sai ta ajjiye rigar dake
hannunta ta taka a hankali ta qarasa wajen
"Nuwaira" ta fada a hankali,da sauri ta juyo suka hada ido,take fuskarta ta washe
da wani madaukakin murmushi,ba don tsinin cikin data gani jikin sumayya ba ba
shakka rungumeta zatayi
"Anty sumayya?.....mama kinga anty sumayya,anty sumayyarmu,wayyo yau su basma zasu
ji labari naga anty sumayya,yau ya hajiya zata ji saboda dadi" nuwaira keta jero
wannan magana ba tsayawa,matar dake gefanta tana murmushi kawai,wanda duba daya
zaka mata kaga tsantsar kaman dake tsakaninsu da nuwaira,kyakkyawar macace blcak
beauty,wadda kallo daya zaka mata kasan nutsuwa ta ratsata,tana daukw da tsohon
ciki wanda ke nuna alamar haihuwa yau ko gobe
"Oh nuwaira,nutsu mana ku gaisa ko tukunna" murmushi itama sumayyan take bakinta
yaqi rufuwa suka soma gaisawa da matar sannan ta gabatar mata da kanta
"Ni sunana rumaisa,nice mamar nuwaira,ke kuwa nasan kece sumayya,matar da lukman ya
taba aura haka ne?" Kai sumayya ta kada taba murmushi cikin mamaki
"Hakane,amma yaya akayi kika ganeni?" Murmushi itama tayi
"Dole na ganeki ai,mai gida mamarshi da duka yara kullum sai sunyi maganarki...ashe
da rabon zamu hadu"
"wallahi kam" sumayya ta fada tana duban nuwaira
"Nuwaira,kinga yadda kika zama budurwa sosai,lallai aure nan kusa kenan" dariya ta
saki cikin jin kunya tace
"Anty maman ce fa ta dawo gidan abba na" kai take gyadawa ko bata fada ba ta
tsammaci haka
"Naga alama nuwaira masha Allah,Allah ya bada zama lafiya" hango almustapha tayi
yana lalubenta da idanunshi don bai san tayi nan ba
"Ni zan wuce nuwaira ina kukayi masauki?"rumaisa ce tace
"nazo ganin likita ne amma nan da kwana hudu zamu koma,amman ki bani adresa dinki
in sha Allah zamu zo har gida,nima naji dadin ganinki don naji dukkan wani qoqari
da kikayi kan rayuwar diyata da kuma gidan baki daya,kin cancanci muzo mu gode
miki" murmushi kawai tayi sukayi musayar lambar waya,ga rubuta adress din jikin
qaramar takarda ta bata sannan sukayi sallama suka rabu.

         Cikin mota shiru sumayyan tayi,tana tunanin yadda rayuwa take sauyawa bawa
a duk sanda Allah yaso,haqiqa rayuwa abar tsoro ce ga dukkan mai tunani,wannan
kadai ya isa bawa ishara yasan cewa babu wani abu dake dawwama nan duniya banda
ikon Allah,walau dadi ko wuya,komai na wuceea ne tamkar a mafarki,gefw daya tunanin
su'ad ya fado mata
"Babyyyyy...." Almustapha ya kira sunanta wanda hakan shi ya sanyata dago kanta ta
dubeshi,sai ta dora hannunta saman nashi hannun dake kan giyar motar
"Tunanin me kike yi?" Kai ta kada
"My...meke damun su'ad?" Kai ya kada yana duban titi
"Nima ban sani ba"
"Amma ya kamata ka binciki damuwarta kaji ko?", kusan shekaran jiya abinda yayi
kenan,ya tsirata da tambaya,bata da amsa daga bisani ma kuka ta sanya mata tana
gaya masa so taje ta gansu daga shi sai ita,duj da akwai wannan cikin zuciyarta
amma babban abinda yafi damunta shine ta yaya zata dauki ciki itama kaman
sumayyan?,ta samu soyayya tattali da kulawa irin tata?,duk da babu abinda ya rageta
da shi
"bansan me take so na mata ba cikin duniya,ban rageta da komai ba,ba abinda ban
bata ba babu kuma abinda bana mata,ko yaushe qoqarin tanqwara zuciyata nake don ma
saba da halayyarta amma ko da yashe sabon hali take qirqiromin,bana son na aikata
mata wani abu da ba dai dai ha ko don mutuncin mahaifinta,ina girmamashi,ina ganin
qimarshi....amma ko yaushe kamar ina tunzura ta haka na......" Shiru yayi ba tare
daya qarasa ba,ko da can shi bai tattauna matsalar wata cikinsu da wata,ya sani
cewa inda hakan me yiwuwa ne sumayya abokiyar shawararshi ce,halayenta sunyi dari
bisa darin da ya tabbatar zata iya bashi shawara da mafita kan koma mene ne,shiru
itama tayi,ta tabbatat da cewa ya kai maqura shi yasa har yau yake furta wadan nan
kalaman,hannunshi take matsawa a tausashe har sai da taji ya saki ajiyar zuciya
sannan a hankali ta furta
"Am sorry....Allah ya shiga lamuranmu"
"Amin" ya furta yana jin dadin lafazinta.

       Maganar noman audugar da ya sanya ake masa a qasar kano jigawa da zaria ta
taso,hakan ya sanya ya shirya zuwa nigeria cikin satin,cikin ikon Allah sai kuma ga
haihuwar halima,wadda ta sauka lafiya ta samu namiji,daman can yana da niyyar
tafiyar da su don haka ra'ayinshi yake,saboda haka yace su shirya,zasu sauka kano
da sumayya,zai barta nan su wuve jigawa da zaria da su'ad tunda ita sumayyan
tafiyar zata iya yi mata wahala,hakan itama yayi mata,ko banza tasan zatayi hidimar
sunanta hankali kwance,kishin dake damun su'ad cikin zuciyarta tace sam ita ba zata
je ba,me zata je yi wani zaria da jigawa?,ta rasa wajen zuwa sai nan?,ranshi ya
baci,shima kuma ya motsa qwanjinsa ya nuna mata mazantaka yace sai taje,hakanan ba
yadda ta iya ta haqura zata bishin,itakam sumayya ko a jikinta,shiri ta soma yi
sosai tana siyan tsaraba,duk da ya hanata fitan tana daga gida take siyayyar ake
kawo mata.

       Ana gobe su nuwaira zasu tafi suka kawo mata ziyara,tana daki kwance aka
shaida mata tana da baqi,ta miqe cikin farinciki ta tar besu har zuwa falonta,duk
da nauyin data yi bata zauna ba sai data tana dar musu komai,zata dora abinci
rumaisa tace a'a sam,itama tana fama da kanta ne,suma kuma a qoshe suke snack din
kawai ya isa,bata rabo da kayan snacks zuwa su dambun nama saboda almustapha,wani
lokaci su kadai yake ci a matsayin abinci,hakan ya sanya take yinsu ta saka su a
freezer sanda zaici sai ta dauko idan na soyawa ne ta soya masa,idan na gasawa ne
ta gasa masa.

      Hira suke wadda kusan rabinsu da nuwaira suke yinta,jifa jifa rumaisa ke saka
musu baki
"Ina maman naku karima ne?" Murmushi nuwaira tayi
"Daddy ya saketa ta koma garinsu,yanzu kullum bakiga yadda take masa naci ya
maidata ba wai ta tuba hajiya tace sam bata dawowa wa,yanzu ma wai ta kusa aure a
can" kai sumayya ke jinjinawa,abinda ya faru shine,baki daya rayuwan yaran da mai
gidan komawa tayi wajen hajiya,sai kariman ta koma tamkar wata saniyar ware a
cikinsu,suna sashen hajiya suna walwalarsu tana vangarenta ita kadai kamar
mayya,duk wani qoqari na dawo da yaran rayuwarta da mai gidan amma abu yaci tura,a
hankali karima ta soma fita daga kansa,a lokacinne ita kuma ta soma gane
kurenta,tayi laqwas ta soma biyayyar qarfi sa yaji saboda ta fuskanci ba wata
mafita gareta,saidai ina tunu ta gama fita akan lukman din baki daya,bare hajiya
wadda tayi shiru ne kawai saboda darajar yaran da kariman ke da su,uwa uba kuma
tayi alqawarin ba zata sake saka dan nata ya saki wata cikin matanshi ba har
abada,don taga ishara,Allah ya kawo qarshen zaman nasu,hajiya ta wayi gari lukman
ya saki karima har saki biyu,qememe yace bazai maidata ba,don ya kamata da kanshi
tana zuba wani abu cikin abincin hajiyan,wanda magani ne qarshe aka bata matuqar
baiyi aiki ya dawo mata da rayuwar gidanta yadda take ba daa to malamin nata ya
gaya mata tayi haquri kawai,sai gashi bata zuba a sa'a ba ya zama silar tsinkewar
igiyar aurenta.

       Bayan mutuwar auren da wasu watanni hajiya ta soma sha'awar dawowar rumaisa
mahaifiyar nuwaira gidan,wadda ita daya ce ta haihu da lukman,macen kuma data fi
duka saurab matan da ya taba aura tsantsar haquri da biyayya,faduwa tazo daidai da
zama,don shi dinma rumaisan ke kai kawo cikin ranshi,tunda ya tabbatar da ceea ya
rasa sumayya,wadda kabatin aurenta a abuja ya gigitashi fiye da zato,ya soma
binciken wanda ta aura,sanda yaci karo da labarin cewa doctor muhammad almustapha
mukhtar gombe ne tilas ya aro haquri ya yafawa kanshi,saboda ya kwana da sanin
babban goro ne sai magogin qarfe,hakanan bakin rijiya ba wajen wasan makaho
bane,bayan sun rabu da karima sun hadu da rumaisan kusan sau uku a gurare daban
daban,saidai ko dubanshi bata yiba bare ya samu fuskar tunkararta,soyayyar da
sukayi bata zaci zai rabu da ita haka da wuri ba ba laifin tsaye ba na zaune,ya
karbi umarni kawai daga mahaifiyarsa,da qyar aka shawo kanya harda hajiyan wajen
lallashi sannan ta yarda aka maida aurensu,wanda dawowarta ya sake dawo da walwalar
gidan kaman zamanin da sumayya kenan,duk da hakan basu manta da ita ba kullum
kwanan duniya su da hajiya sai sunyi zancanta,wanda har rumaisa ta saba da ji,takan
zauba ta tayasu wani lokaci,ko daya rumaisa bata bari abinda karima ta yiwa diyarta
yayi tasiri a ranta ba har ta rama kan yaranta guda hudu data bari,ta hadasu ta
rungume kamar ita ta haifesu,sannan taci gana da dorawa kan tarbiyyar da sumayya ta
azasu wanda hakan yayi mata dadi sosai.

       Wannan shi ake kira da QADDARA saiga rumaisa ta zama ita din dai itace matar
lukman,dawowarra ba dadewa harkokin lukman suka bude sosai,wanda hakan bai rasa
nasaba da yadda ya maida kai wajen kyautatawa hajiyarshi ita kuma taci gaba da
binsa da addu'a,cikin qanqanin lokaci ya sake habaka,ya sauya gida da abubuwa masi
dama cikin rayuwarshi data yaranshi,basu dade da komawa sabom gida ba rumaisa ta
samu juna biyu,wanda yanzu haka siyayyar haihuwa tazo yi sanda yayarta dake
kasuwanci zata zo dubai lukman ya masu visa ita da nuwaira suka taho,wanda yace
girma yake bi,zuwa na gaba kuma mai biwa nuwaira da ita za'a babbar yarinyar
kariman.

        Basu wuce awa biyu ba suka yi sallama zasu wuce,suka rabu kowannensu na
tsokanar dan uwansa kan sai sunzo suna,ta musu alaqawarin indai tazo kano matuqar
mai gidan ya barta zata shigo ta gaida hajiya,amma su isar mata da gaisuwar tata
wajen hajiyan kafin ta iso da su basma baki dayansu,a haka suka rabu.

       Kwana hudu tsakani suma suka tashi zuwa kano,saukar yamma sukayi saboda haka
kai tsaye suka wuce gidan baba wanda nan suke sauka dama,ba haka sumayya taso ba,so
tayi ya barta ya sauka gida amma ya hade gabas da yamma ya qiya,saboda yau ne zata
amshi kwananta,farincikinsa shine sama da nata saboda haka itama ta danne tata
buqatar ta haqura.

Yana bakin gado yana shafa mai ta fito itama daga wanka,daure da towel amma
ya dage mata saboda tsinin cikinta,kallonta yake cikin shauqi yana lumshe
idanu,saboda yadda ta masa wani kyau,fatarta kana kallanta kasan ta samu hutu,ruwan
wanka yayi dai dai kan fatarta,miqews tsaye yayi ya isa bayanta inda take tsaye
gaban madubi tana tsane jikinta,ya kama qugunta ya manna a jikinsa,sai ta lafe tana
dubanshi ta jikin mudubi fuskarta wasai
"Wannan cikin naki kaman ya wuce watanninsa fa.....na qagu ya fito zuwa yanzu ya
soma hanani aiwatar da wasu abubuwa yadda ya kamata,baki daya kin zama wata
lazy,perfomance dinki ya ragu babe" kanta ta langabar saman kafadarshi a shagwabe
"Duk rawar gaban hantsin da kake sha abinka noor?" Habarta ya kama ya riqe
"Yanzun idan nace ina son mu shiga babbar headquater nayi rawar gaban hantsin za'a
barni?" A gajiye take tabbas,amma ta sani so yake ya qureta don ya samu abun
tsokana,hakan ya sanya ta dan janye jikinta ta waiwayo tana dubanshi
"An gaya ma raguwa ce ni?" Gira ya dage dariya na cinsa ya daga kafadarsa
"Wa yasani?"
"Bari in nuna maka" ta fada tana nufar saman gado,sosai dariya ke cinsa,shikenan ya
gama mata wayo,baisan yaushe sumayyar zatayi wayo ba,duk da yana maraba da irin
wannan rashin wayon nata,gunta ya isa yana qunshe dariyarsa,yayin da ya lullubeta
cikin qirjinsa,yana aika mata da zafafan saqonminsa cikin zafi zafi masu dumama
duniyar ma'aurata wadda ke qunshe da tsantsar soyayya qauna da kuma shauqi.

Ranar baki daya ba inda ya fita,da qyar ta lallabashi ya rakata kitchen ta


musu abinci mai sauqi suka dawo daki.

Washegari suka shirya shi da ita tsaf don su'ad na nade bata ga wajen fita
ba,wani qauye a 'yar gaya dake kano nan ya dauketa suka tafi shi da ita da
driver,sai wata motar guda daya a bayansu akwai PA dinshi da kuma wanda ya barwa
aikin da zasu je gani a hannunshi,gonaki ne masu fadi da tsaho wanda iya ganinka
auduga ce,sosai taji dadin zuwa wajen don ko ba komai zata tattaka,uwa uba kuma
ranar garin babu rana,sai da ya gama zagayenshi sannan ta fito suka fara takawa
tare,wajen da matan dake musu aikin cire audugar zaije yaga yadda suke,hannunta
cikin nashi yana dan tsokanarta yana mata dariya,murmushi take tanajin dadi qasan
ranta,tana godewa Allah kullum kwanan duniya da irin mijin da ya bata,bakin wata
bishiya suka nufa,Allah sarki matan karkara,rayuwarsu abar dubawa ce,cincirondon
mata ne,wasu na aikin wasu na qasan bishiyar suna baiwa yaransu nono,yayin da wasu
ke gefe suna hutawa,sosai ta tsurawa daya daga cikin matan dake bawa danta nono
tana hira data kusa da ita,yanayi take mata da fa'iza sosai,duk da wannan ta soma
komawa tamkar tsohuwa,saidai ga mai dogon nazari da tsinkaye yana mata kyakkyawan
duba zai san wahala ce ta maidata hakan da tsantsar rashin kulawa ci sha sutura da
muhalli mai kyau.

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖
*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

1⃣0⃣4⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

*la ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin*


_____________________________________

       Har ta qarasa wajen basu lura ba,sai data tsaya dab da su sannan hankalinsu
gaba daya ya dawo kanta,idanu kowa ya zuba mata yana mata kallon qurilla
"Fa'iza?" Sumayyan ta fadi tana dubanta,jin tayi shiru bata amsa ba ya sanyata sake
cewa
"Ko ba fa'iza bace?"
"Nice,nice mana" ta fada tana yanqare haqora tare da cire yaronta daga bakin
nonon,farinciki fal ranta yau cikinsu su wajen goma 'yar gayu ta mata magana ita
kadai har tana nuna ta santa,har ga Allah sam bata gane sumayya ba
"Fa'iza kece haka?" Sumayya ta fada cikin mamaki da al'ajabi
"Eh wallahi...amma na kasa heda fuskar taki"
"Sumayya ce fa....sumayya kishiyarki wadda kuka taba auren mukhtar tare" miqewa
fa'izan tayi dafe da qirji tana cewa
"Keeee.....sumayya?,da gaske?" Ta fada tana matsowa kusa da ita ta soma shafa kayan
jikinta tana qare mata kallo,sai kuma ta fashe da kuka tana cewa
"Kina nan dama sumayya?,naji labari ashe mukhtar ya rasu?" Cikin raunin zuciya ta
gyada
"Mukhtar ya rasu fa'izw,shekara kusan shida kenan"
"Wayyo Allah,dama mukhtar na raye na roqeshi gafarar cusguna muku da nayi" gefe
fa'izan ta janye sumayya,kan wasu duwatsu guda biyu dake wajen suka zauna,nan take
sanar mata labarinta,bayan fitowarta gidan mukhtar kamar wadda aka yiwa baki ba
wanda ya taba zuwa taya aurenta,ko dama can bata da farinjinin samari ko
kadan,hakanne ma ya sanya aka hada ta da mukhtar din,sai daga bisani baban yaron
dake cinyarta ya fito neman aurenta,wanda yanzu yaransu uku,wannan ne qarami,bayan
auren ba komai ta tsinta ciki ba sai wahala,matanshi hudu kowacce ita ke dauke da
dawainiyar kanta data yaranta,zai zube musu hatsi ne kawai a rumbu saura kuma ya
rage nasu,sosai taji ta tausayawa fa'izan,wato rayuwa kowa da irin jarrabarsa,hakan
duk abinda ka shuka dole wataran saika girba,ko ka jawa yaranka gadon wahala su su
girbe abinda kaine ka shuka shi,gashi dai taqi uarda ta zauna gidan mukhtar dake
cikin birni,yana da matarshi daya da rufin asirinsa qwarai,babu abinda bai dauke
musu ba na dawainiyar gida,sai gashi ta fada gidan mai mata uku,banda hatsi bai
kula da komai naku ba,ga haihuwa tanayi
"Ya taki rayuwar sumayya?,da alama komai ya miki kyau" ta fada tana qare mata
kallp,tun daga takalmin qafarta zuwa lafiyayyen material dake jikinta,dankunne
agogo sarqa da jaka,murmushi kawai ta saki sannan tace
"Kowanne bawa da kalar tashi qaddarar,kuma ba shakka duk inda kayi sai ta
bika,saidai Allah yakan yiwa bawa sakayya gwargwadon abinda ya shuka,idan alkhairi
ne bayan Allah ya gama jarrabaka sai ya maka sakamako mai kyau,haka idan sharri ne
ma" a taqaice ta bata labarin komai,ta dinga jinjina kai tana sake nutsuwa tare da
dana sani kan abinda ta aikata a baya,nan ta nemi gafarar sumayya,bata da riqo sam
ballantana ma ita bata ga abin da za'a riqe fa'iza da shi ba,don baki dayarta abar
tausayi ce,yafe mata tai sannan ta bita da alkhairi,ta tambayeta nawa take buqata
na jari,wanda zata bar wannan aikin taje ta riqe iyalanta
"Dubu uku ma ni ta isarmin" ta fafa cikin zumudi,baki dayanta kalar tausayi
ce,jakarta ta bude,ta zaro dubu goma 'yan dari biyar biyar sababbi ta miqawa
fa'izan,ai batasan sadda ta dire danta dake kan cinya ba hannu na rawa
"Don Allah kada kice min da wasa kike" ta fada bayan ta gama qirga kudin,murmushi
sumayya tayi tausayinta na kamata
"Ba wasa nake miki ba fa'iza,ki riqe kija jari,don Allah ki baiwa yaranki tarbiyya
da kuma ilimi,shine kadai gatan da zaki musu"
"Da izinin Allah sumayya na gode na gode na gode" sai ta fashe da kuka tana sake
jaddada godiyarta.

       Daya daga cikin matan ne ta iso wajen tana sanar da fa'iza ta taso za'a biya
su kudin aikinsu na yau,sannan mai gonar zai basu wani abu,daa tace ba sai taje
ba,sumayya tace haqqinta ne taje ta karba ta hada,baki dayansu suna tattare waje
daya,tare suka isa wajen,almustapha na tsaye jikin motarshi,tun dazu yake raba ido
yaga ta ina zata bullo,gefan matan itama ta tsaya cikin tausayi take dubansu,tana
godeww Allah matuqa kan ni'imar da yayi mata,ba tare da wayo ko qarfinta ba,da
idanu ya dinga binta,tausayin da ya gani zallah cikin idanunta ya sake burgeshi,ko
da yaushe dabi'arta tasha banban data saura daya saba gani masu shekaru irin
nata,take yayi wani quduri cikin ranshi,ba shakka zata dace da a bude mata wata
qungiya ta tallafawa mata marasa galihu da koyon sana'o'i,da alheri almustaphan
yabi kowaccensu,dukkansu ko sai da suka dara saboda kudin da ya basu,shi kanshi
tausayi suke bashi,ina mazansu da haqqin ciyarwa da shayarwa ke kansu suka barsu
suna wahala da fadin tashin ci da kansu,sai da suka gama kaf sannan sukayi sallama
fa'iza na sake jadda da mata godiya,ta karbi lambar sumayyan tace ko cikin gari
zata dinga shiga tana kiranta suna gaisawa lokaci zuwa lokaci.

         Yana nade saman gado yana duba saqonnin hotuna da lamin ke turo masa na
gonakin da suke nema yadda noman yayi kyau,lokaci lokaci yakan daga kai ya kalleta
sanda take shirin bacci gaban madubi,ya lura tunda suka dawo jikinta a sanyaye
yake,haka yake,tana tuna wato rayuwa garanbawul ce,haka sharri tamkar jifa ne,duk
sanda ka yishi komai daren dadewa sai ya dawo ya sauka tsakar kanka,a hankali ta
hauro gadon,sai ya bar abinda yake ya zuba mata idanu kafin daga bisani ya bude
mata hannayensa,dama abinda take jira kenan,ba bata lokaci ta isa jikinsa ta lafe
tana shaqar tattausan qamshin da yake fitarwa,bugu da qari tafin hannunta na kan
singalalin hannunsa dake cike da gargasa tana shafawa,hakan ya sakashi lumshe ido
saboda yadda tsigar jikinsa ke zubawa
"Babe....mai ya sakaki mutuwar jiki haka?,ko baby ne?" Kai ta girgiza sannan ta
soma kwatanta masa fa'izan da ya gansu tare,yace ya ganeta,nan ta bashi labarin
yanayin da take ciki,shiru yayi yana jinjina mata,ba shakka ba kowacce mace bace
haka,ya tabbata da wata ce dariya zatayi tayi shewa kafin ta shelantawa duniya,zata
ce Allah ne yasaka mata abinda fa'izan tayi mata,sau gashi ita neman hanyar da zata
fiddata daga cikin qunci take
"Kin taimaka mata ai ko?,ba sai an sake wani abun ba"shiru tayi kaman ba zata yi
magana ba sannan tace
"A'ah....ranka ya dade da zaiyiwu a qara mata jari,a baiwa mai gidan wani
qwaqwqwaran sana'a da zau kula da iyalinshi baki daya"
"Babe.....ta cutar min da rayuwarki fa?" Kai ta kada
"Na sani...amma na yafe mata,tunda gasji daga qarshe ni naci riba,Allah ya yimin
kyakkyawan sakamako da gwarzon miji kuma masoyi irinka,daya tamkar da million" ta
qarashe maganar cikin wani salo mai kwantar da rai,dariya ya dinga saki sannan ya
ruqunqumeta cikin jikinsa yana jinta har cikin bargonshi
"Duk abinda kika ce shi za'a yi" ya rada mata akunne cikin salo na rada kaman wanda
zai shide.
  ********   *****   ********

       Washegari shi da su'ad suka wuce jigawa,yayin da ita kuma ta tattara ya nata
ta nata sai gida.

       A falo ta tadda mama ita da anty meena suna hiransu tamkar uwa da da,cikin
farinciki suka tarbeta,mama kam kallon sumayyan take taba sambarka tare da godiya
wa Allah,yaran meena biyu suna makaranta sai qaramin yasir sulaiman mai sunan malam
ne,wanda baifi wata uku ba,gida kam yayi kyau masha Allah ya burge sumayya
qwarai,ta dinga shiga tana fita tana godewa Allah,har da tsokanar mama cewa bata ga
dakinsu ba,dariya anty meena tayi
"Kukam ai an gama yayinku tunda an yaye ku" suka sa dariya baki daya,a nan ta yiwa
mama barka,da anty meenan ma baki daya.

      Kusan itama anty meena nan ta zauna da su,ranan bata je gidansu masu jego ba
duk da kusan kullum sai taje,sai da zata dora abinci ta fita ta barsu,kafin sannan
yaran sun dawo daga makaranta,abin mamaki duka sun santa,don yaya abbakar na nuna
musu ita akai akai yana gaya musu sunanta,abinka da yaro da riqe abu,saidai basu
sake da ita sosai ba kaman yadda suke sakewa da su halima.

       Tare malam suka shigo da yaya abubakar,kowannensu murna fal cikinsa da ganin
sumayyan,sun sha hira sosai har ya abbakar ya gaji ya wuce bagarensa ya bar
sumayyan da malam,labari yake ta bata kan irin ci gaban da rayuwa ta samu,yana sake
jaddada mata irin soyayyar dake tsakanin baba prof da shi,da kuma yadda ko da
yaushe zumuncinsu ke sake gaba yaba habaka,sosai take sake ganin qimar baban cikin
ranta,ba shakka shi aboki ne kuma masoyi ne daya tamkar da dubu.

       Washegari suka dunguma gidan halima,baki daya harda yaran yaya abbakar
nabila da yusuf da anty meena mamansu,almustapha ya bar mata mota da driver,wanda
zai dinga kaita duk inda taje da buqatar zuwa,sanda suka je gidan 'yan barka nata
shiga da fita,'yan uwan abdur rahamn,wasu ta sansu musamman na bangaren babanshi
tunda sun hadu da mukhtar ta nan wajen,wasu kuma bata sansu ba,duk wanda ya santa a
sanda take gidan mukhtar a yanzu da ya ganta sai ya kalleta ya sake juyawa ya
dubeta,munagukan da a da suka cusguna mata baki daya jikinsu a sanyaye yake,baki
daya sun kasa zama kusa da ita,kunya da kuma ganin yadda sumayyan ta sauya ta zama
wata babbar mace duk ta cikasu,itakam bata dauki komai ba,tamkar basuyi mata komai
ba haka ta sake musu fuska,abu daya ta sani shine an rige an wuce wajen,yanzu kam
rayuwa ta baiwa kowanne certificate din abinda ya aikata,a gidan ta tadda zainab
wadda shigowarta kenan,itama tana ta fama cikinta ya shiga wata na tara,sumayya ce
nata keda wata bakwai da satittika,dukkansu suna zagaye da 'yar uwarsu,fuskarsu
qunshe da farinciki,yaron yana saman cinyar sumayyan tana kallon tsantsar kama
tsakanin yaron da babanshi abdurrahman,wato duk bawan da bai yarda da QADDARAR
ubangiji ba lallai zai ci wuya cikin lamuranshi,matar mutun kabarinsa,yau ga yaron
abdur rahman da halima saman cinyarta,sannan gata dauke da cikin almustapha,mutumin
da ko a mafarki bata taba saninsa ba,sanda qaddara ta gindaya kuma ta sanshi din
bata taba koda hasashen zama irin na auratayya zai hadasu ba,hira suke sosai gwanin
sha'awa,wadda ke nuna zallar hadin kai da fahintar juna dake tsakaninsu,abdallah
baya nan yana tahfiz sai azahar zai dawo.

        Sanda taga abdallah masha Allah,wani baragen girma gareshi,ya fara zama
wani babba,ga wani hankali da nutsuwa tattare da shi,kana gani kasan ya samu
isashshiyar tarbiyya,girma yake abdallan sosai,sanda ya ganta fuskarshi washe da
fara'a ya iso gefan cinyarta bayan ya gaida duk wanda ya taras cikin falon yana
fadin
"Ammi....ashe kinzo baki gaya min ba?"murmushu ta saki ranta fes,tana sake ganin
girma da qimar abdur rahman har da ma haliman
"to ai gashi yanzu ka ganni ko?"
"Ammi kinga munyi sabon baby ko?,wai abba yace da ni yake kama?" Ya fada yana wasa
da 'yan hannun jaririn dake cikin safar hannu,murmushi sumayya ta saki
"Sosai ma,kama kai" murmushi ya saki cikin jin dadi,nan ya soma bata labarin
makaranta,kai kawai take kadawa tana murmushi,ganin abun take kaman mafarki,kaman
ba ita ta haifi abdallah,qaunar yaron nata da tausayinshi suka dinga ratsata,ta
kasa daurewa har sai data dora hannunta saman kanshi sanda ya kawo mata ruwa mai
sanyi ya ajjiye mata yace tasha ta shafa a hankali ta furta
"Allah ya yi maka albarka kai da sabon qaninka mai kama da kai"
"Amin ammi na", basu suka bar gidan ba sai dare,don sai data jiraci dawowar abdur
rahman tayi masa barka,yaji dadin zuwan nata sosai,yayi zaune abinsa a cikisu,sun
dan taba hira,wanda yawanci kam abdallah ne,yanayin baiwar da Allah yayi masq,akwai
basira da hazaqar karatu qwarai da gaske,wanda hakan ya sanya ake masa tsallaken
aji,a hasashensu bazai wuce shekara goma ba zai shiga j.s,kayan barka ta yiwa babyn
masu yawa kyau da tsada,akwati guda,sannan ta yiwa halima atamfofi biyu lave
biyu,mayafi takalmi da jaka,ta mata godiya itama,saidai bataso godiyan ba,don bata
ga abinda zata samu nak duniya 'yan uwanta basu mora ba,sai wajen takwas suka koma
gida bayan sun sauke zainab har qofar gidanta suka taho da abdallah,tace bata yafe
zuwan ha itama sai anzo mata har gida,tayi murmushi ta amsa mata,ranta fes ta koma
gida,baki daya 'yan uwan nata suna cikin rayuwarsu cikin wadata da walwala,ba wata
maiatsala a cikinsu,ci sha sutura da muhalli mai kyau kowacce bakin gwargwado ta
mallaka.

       Washegari ya abbakar ya sake tareta suka sake lissafi kan dukiyar


abdallah,abin ba'a cewa komai sai albarka Allah ke sawa dukiyar,ta nunku fiye da
zatonsu,bayan sun gama ta fidda tsaraba cikin kwalaye wanda batasan da ita
ba,almustapha ya tanada kawai taga ana sauke mata su,haka yake,mutum ne da idan
zaiyi alkhairi bai fiya son a sani ba,zaiyi abunsa ne a boye,shi yasa ko zaman
tsarabar bata san da shi ba,na mama daban na malam daban,har da yaya abbakar,saura
yace ta baiwa wanda taga ya dace cikin 'yan uwa,sai yammaci ta sake shiryawa suka
fice ita,abdallah,yusuf da nabila sai gidan anty yahanasu,ba qaramin murna tayi da
ganinsu ba,duk da abdallah dama bai sati biyu abdur rahman bai kai mata shi ba,sun
zauna hira nan taji duk abinda ke gudana,auren jamila da fatima Allah yayi za'a yi
din,saidai kayan gado nason kawo tsaiko,don ma abdur rahman ya dauke nauyi duk
abinda za'a ci ko a sha a bikin har a gama,kowa cikin dangi ya nade hannu,dama can
danginsu ba masu riqe zumunci bane,hakan ya sanya ko sanda iyayensu suka mutu ita
taci gaba da riqon mukhtar,sosai taji ba dadi,ta dauki nauyin kayan gadonsu jamilan
da fatima,kunya da nauyinta suka ishesu,godiya suka dinga mata,itakam bata kula
ba,iyalan mukhtar sunfi qarfin komai a wajenta,ko banza abdallah ya hada haduwar da
babu rabuwa cikinta,data koma gida sukayi shawara da ya abbakar da malam,ta barwa
yaya yahansu gidansu wanda suka zauna a qarshe ita da mukhtar kyauta,tunda yanzu
dukiyar abdallah ba komai bane don su barwa yayan gidan,kuka kam haka ta dinga
yinshi,har sai data saka sumayya qwalla,tace mata babu komai haka rayuwa dama
take,nan yayan ta fara shiryen shiryen komawa,tunda fes yake akan shiha lokaci
lokaci ayi gyara yaya abbakar bai barshi haka ha don kafa ya lalace,gidan da suke
ciki kuma zasu saka 'yan haya,sumayya tace ta dinga amsar kudin tana buqatunta na
yau da kullum da su.

      Suna suka sha hankali kwance,tayi kyau sumayyan sosai,duk wanda ya santa idan
ya kalleta sai ya sake dubanta,kana kallon nata zaka san cewa nutsuwa da kwanciyar
hankali sun samu muhalli cikin rayuwarta,a nan ta barsu drivanta ya dauketa ya
maidata gida wajen mama,tafison ta ganta kusa da ita.

********    ******   ********

      Da safe suna zaune falon mama ita da abdallah,yusra da yusufa da maman suna
karyawa,yaran na gabanta baki daya kowa na karyawa tana fama da su,gyarawa wancan
kofi gyarawa wancan zama,kayan bacci je jikinta ko wanka bata yi ba,yunwar data ke
ji ta sanyata zama karyawa,ya abbakar dake shirin fita shi ya shigo yana fadin
"Mama...ga surukinki zai shigo ki gaisa...da alama sauri yake halan ka wucewa
zasuyi" sam bata gane wa ya abbakar din yake nufi ba,kafin ta farga har mama ta
masa izini,sai muryarshi taji a bakin falon yana niyyar shigowa.

       Almustapha ne sanye cikin shadda dinkin tazarce,riga da wando,kanshi babu


hula sai sumarshi dake kwance tana zuba qyalli,yayi kyau maqura har taji gabanta na
faduwa sanda suka hada ido,ko yaya suka danyi kesa da juna na kwanaki sai taji ya
sake zame mata sabo,ta soma tattare kofunan yayin da ya shigo ya tsugunna gaban
maman yana gaidata,cikin jin kunya irin na surukuta suka gaisa,yana yi yana satar
kallonta,ta kasa daga kai ta dubeshi kaman ta nutse,su yusra suka gaidashi yayin da
abdallah ya isa gabanshi ya durqusa yana murmushi ya gaidashi,hannu ya miqa masa
sukayi musabaha shina fuskanshi dauke da murmushi,yana son yaron sosai cikin
zuciyarshi,saidai tarihin sumayyan da yaji yasan bazasu bashi shi ba,saidai yana
kan bakanshi ko nan gaba sai ya dauke yaron,yadda yaron ua sake nutsuwa da girma
sai yaji dama danshi ne,dama jininshi ne,saidai ko a yanzun yana jinsa cikin
jikinsa tunda akwai jinin sumayya tattare da shi
"Tashi kije mana sumayya" mama ta bata umarni sanda almustaphan ya gama gaisheta ua
fita zuwa dakin saukar baqi,a kunyace ta amsa,ta koma daki ta zura hijabi ya sake
feffesa turare,dui da cewa qamshi ya kama jikinta,ko daga bacci ta tashi baka rasa
jin qamshi a jikinta,don sai ta shafe loko da saqo na jikinta da turare ko ba
kwananta bane kuwa,ko da basu tare.

       Yana tare da abdallah hannunshi cikin nashi,da alama tambayoyi yake masa kan
karatunshi,yana bashi amsa,kuma yana bashi amsa yadda ya kamata don akwai alamun
gamsuwa tattare da shi,shigowarta ya sanya abdallan zame hannunshi ya fita ya basu
waje,tsaye tayi suna duban juna,ya miqe ya isa gareta ya hadata da jikinsa
"Meye haka?,salon horo ne ko kuwa?,ni zakiyiwa qwalele?,kinsam bazan juri kallonki
haka ba ko?" Murmushi ta saka tana ajiye boyayyar ajiyar zuciya,dududud satinsu
guda basu ha juna ba amma tana jin kaman sun yi wasu watanni masu dama
"Tsoro nake ji ne?" Ta furta a hankali
"Tsoron me?"
"Ina tsoron ko kazo tafiya da nine ba tare da na shirya ba,in sake tafiya in bar
mama" murmushi mai sauti ya subuce masa,sannan ya soma rada mata
"Hakan naso matata,saboda mi kadai nasan yadda nayi kewarki,saidai idan hakan bai
miki ba...zan iya zama na jiraki har tsahon sanda zaki gama abinda kike yi,ba
abinda bazan miki ba,kinsan saboda me?" Kai ta girgiza alamar a'ah,sai ya juyo da
ita suna fuskantar juna idanunshi cikin nata
"Ke din macace ta musamman,mai fifita farincikin mijinta akan nata,mai fifita
buqatarta akan tasa,ina sane da cewa,sau tari kikan dauki zabina ki bar naki,kikan
gabatar da komai nawa gaban naki,kin maida kanki tamkar baiwa a gareni" sai ya
saketa ya durqusa gabanta kan gwiwarsa
"Don me nima bazan zama bawa a wajenki ba?,wannan shine qarshen adalcin da zan
miki,Allah ya halicci zuciya da son mai kyautata mata da qi da kuma gudun duk
abinda zai munana mata" bata ankara ba qwallar zallar farinciki ta subuce mata
cakude da murmushi,jin kanta take tana shawagi a sama,cikin wata duniya wadda take
mata kwatankwanci da duniyar SARAUTAR MATA,sai ya miqe da hanzari ya rungumeta ta
baya saboda cikinta ya masa shamaki ta gaba,sun jima a haka sannan ya janye yana
dauke mata hawayen da yatsansa
"Ko a yanzun ma ka buqaci mu tafi ni mai biyayya ce a gareka" kai yake girgizawa
cikin farinciki
"A'ah....kije ki gama shirinki a nutse" kai itama ta girgiza
"Um...um,bazan barka kana jira ba haka noor,kaje ka dawo"
"Na yadda,amma zaki rakani asibiti?,zanje na duba bayin Allah"
"Sam'an wa d'a atan noor" murmushi ya saki kalman ta masa dadi,kissing dinta yayi
sosai,sannan yace mata zaya dawo da yammar su je.

        A nutse ta fara shirinta,tana yi lokaci lokaci murmushi na qwace


mata,lallai kam gaskiyar masu magana da suke cewa namiji tamkar yaro yake,sannan
idan kika maida kanki baiwa shima zai zamto bawa a wajenki musamman idan yasan suka
haqqoqinki da Allah ya dora masa.
       Da la'asar sakaliya ya iso kuwa,ya dauketa suka tafi,a nan yake tambayarta
abdallah,tace babanshi yazo ua dauke abinsa,tana dariya tace shikam ko yauahe gani
yake kaman zan daukeshi ne
"Akwai kam lokaci,lokacin da zamu daukeshin kuma babu yadda zaiyi" murmushi tayi
don bata data cewa,kaman kowanne lokaci sunji dadin zuwanshi,suka dinga gaidasu
cikin girmamawa,kan ya wuce office sai da ya bincika,komai yana tafiya kan tsari da
kulawa tamkar yana nan,daga bisani suka wuce office din yana maqale da ita.

      Murmushi yaga taba saki sanda suka shiga office din,ya tambayeta mai ya
fari?,sai ta kada kai tace mishi ba komai,kamota yayi ya matseta,ta saki qara a
shagwabe,ya sake tambayarta,cikin muryarta mai sanyi tace
"Kawai ina tuna last zuwanmu office din nan,abinda ya faru" shima ya tuna sai ya
saki murmushi ya lumshe idanunsa ya bude sannan ya kashe mata ido
"Na tuna babe....amma kada ki soma cewa zaki tsokaneni....kinsan me?,wani kwarjini
kikamin wanda ban taba jin wata diya mace duk fadin duniya tun tasowata tamin ba a
sannan na kasa miki scan,sannan ga wani shock da naji sanda naga skin dinki....kai
babe,you are unique wlh" dariya ta saki ta dora kanta kan qirjinsa,daga gefe
idanunta suka sauka kan hotunan mukhtar dake saman table dinsa,ta qurawa hotunan
idanu,a hankali ya maida kansa inda yaga ta maida hankalinta,sai ya jata zuwa
wajen,ya sanya hannu ya daga hoton yana kalla kafin ya dubeta
"Mukhtar?" Ya fada cikin sigar tambaya,idanu kawai ta zubawa almustaphan
"Am sorry" ya fada sannan ya hadesu waje guda ya yagasu qananu ya ajjiye saman
teburin sannan ya waiwayo ya dubeta
"Ina da kishi a kanki babe.....am sorry if i hurt you" ya fadi yana duban idanunta
da son karantar yanayinta,saidai taqi bashi dama,hannunta ya kama yana ci gaba da
kallonta bayan ya matso da ita dab da shi har suna musayar numfashi
"Na yarje miki ki masa addu'a,ki sashi a addu'o'inki,amma banda nan" ya dora
hannunshi saitin zuciyarta
"Nan din mallakata ce ni daya har ABADAN"knocking din da aka yi shi ya qwaceta,don
ya soma dora mata wani nauyi,tamkar yana jiran amsar da zata bashi,daya daga cikin
nurses din ne ta shigo dauke da file na mutanen da zai gani,cikin harshen turanci
ya tambayeta na mutum nawa ne?,tace masa talatin,yace mata ta rage guda goman
qarshe ta maida musu ashirin zai iya gani
"Sir....suna son ganinka da gaske ne goman da kace a cire din...."da hannu ya
dakatar da ita kana ya mata nuni da idanu kan ta rage kaman yadda yace
mata,qarasawa tayi ta irga ta debe din,sumayya ta matso kusa da shi murya can qasa
"sorry sir,ayi haquri a gansu" hararar wasa ya jefa mata
"Ke zaki tayani?,da wuya fa?"
"Na maka alqawarin ba zaka gaji ba,ina gefanka fa?"
"Really?" Ya fada yana dage mata girarsa guda daya,idanunta ta juya kafin tace
"Yes sir" tana sakin murmushi,kiranta yayi ta dawo da su din sannan ya sa mata
kujera daura da shi ta zauna,da dai dai da dai dai patient ke shigowa yana
dubasu,wani abun wanda yasan zata iya ya sanyata ta tayashi,wanda ba zata iya ba
kuma yayi abinshi tana kallo,suna tsaka da haka wata budurwa ta shigo,kana kallonta
kasan tana ji da kanta,cikin yauqi ta zauna kan kujerar da marasa lafiyan ke zama
suyi bayani,sai fama take tana wani basarwa,sam bai daga kai ba bare yasan wanda ya
shigo,hankalinshi na kan sumayya dake cike takardar wadda ta fita take shigar da
wasu abubuwa da yace ta shigar,akwai fikira tattare da ita da basira mai dimbin
yawa,komai tayi sai kaga hikima a ciki,tamkar likita haka ta tsara komai yana
kallonta murmushi irin na gefen baki na fita kadan kadan,hakan ya sake sanyawa ya
tafi da patient din data shigo
"Me kika karanta ne?" Ya tambayi sumayya fa kanta ke duqe tana rubuta kwanan
wata,dubanshi tazo yi sai suka hada idanu da ita tana dubansu,hakan ya sanya
maimakon ta bashi amsa sai ta masa alama da idanu na ana jiranshi,sai a sannan ya
dauke kai ya dubi patient din,murmushi ta sakar masa,ya dauke kai yana bude file
din nata
"Me sunanki?" Ya tambaya saboda yaga kaman ba suna kan file din da alama sabo ne
"Meela" ta bashi amsa tana yauqi
"Meye ne meela?" Ya tambaya a akausashe don ya soma jin haushin yadda take wani
gwalangwaso
"Eh da shi ake kira ne amma real name din ja...."
"go straight to the point,akwai masu jira,meke damunki?" Ya tambaya yana rubuce
rubucensa,sumayya na gefe dariya na son qwace mata,ya koma sak doctor almustaphan
dan gidan baba prof data sani a baya,nuqu nuqu ta soma yi saboda ganin sumayya a
wajen,tsaf ya karanceta,sai kawai ya rufe file din nata ya tura mata gabanta
"Zaki iya tafiya" ya fada yana kafeta da mayun idanunshi
"Ai..ai sirri ne" ta fada cikin in ina,juyawa yayi ya dubi sumayya da dariya ke
ci,amma sai ka zata batasan meke faruwa ba
"I said the door is opened ko?" Ganin cewa da gaske yake ya sanya ta samawa kanta
nutsuwa ta soma masa bayani,magunguna ya rubuta mata yace taje ta karba ya
sallameta ta miqe ta fice.

Dariya sosai sumayya ta saki kafin nxt patient ta shigo


"Me?" Ya tambayeta yana kallonta,da kanshi kuma ya saki fuskar yana dariya,ya gane
me takema dariyan,sai ya cafko yatsunta ya soma lanqwasa mata,ga dariya ga zafin
lanqwasa matan da yake,da qyar ta qwaci kanta
"Ku kam mata wlh i dont know.....kai...kai" ya fadi ba tare da ya gama fadan me
zaice din ba
"Duka ke kika jawomin,da tuni na gama mun tafi ina gida ina hutawa,ko baby bamu
gaisa da shi ba" ya fada yana shafa cikinta,turo qofan da akayi ya sanyashi janye
hannun nashi,a nutse yaci gaba da dubasun har ya gama sannan suka tattara suka nufi
gida.

Cikin falon nashi dake dauke da dakin bacci biyu suka sameta kwance tana
kallo,sanye da riga shimi doguwa zuwa gwiwa,gajeran hannu ne da ita hannun
vest,ciki ciki ta amsa sallamar tasu sannan ta daga ido ta bisu da kallo.

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

1⃣0⃣5⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

*Allah S W T yana bayyana kansa cikin qur'ani mai girma da*


*FA'AALIL LIMA YURID(mai aikata abinda yakeso*

*ya Allah muna gareka kayi mana jagoranci*


_____________________________________

*Wannan shafi sadaukarwa ne ga*

*HAUWA'U AG tare da diyanta AHMAD*

        Ba wanda ta amsa sallamarsa a cikinsu,hakan ya sanya sumayya tayi wucewarta


ba tare data sake cewa komai ba.

        Satinsu biyu dai dai a kano suka koma dubai,bayan sun ziyarci gidan
maimmartaba sarkin rano,mahaifin ummi,tsoho mai ran qarfe,karon farko kenan da
sumayya ta kai ziyara,tsantsar soyayyar da tsohon kewa almustaphan ta shafi
sumayya,kowa haba haba yake da su yana neman wajen ajjiuesu,taga kara taga
karamci,ba qaramin dadi zuwan yayi mata ba,duk da bata samu zuwa gidajen sauran
'yan uwa ba,amma tayi alqawarin duk sanda tazo kano toba shakka zata sake zuwa
musu,kyautar girma tsohon yayi musu shida matanshi,duk da mahaifiyar ummi ta
rasu,amma matan baban nata sun daukeata tamkar diyarsu,suna farinciki da juna suka
rabu,tun a sannan ummi taso riqe sumayya har sai ta haihu amma almustapha ya
shafawa idonshi kwalli yace ba yanzu ba zai kawota idan lokacin yayi,yayin da cikin
zuciyarshi ma sam ba haka bane,don baida niyyar kawota din,yana ganin meye
amfaninsa a matsayinsa na likita kenan.

      A hankali kwanaki suka ci gaba da wucewa,ba abinda ta daga qafa ko ta sauya


game da kyautatawar da takewa almustaphan,dukkan wani abu data sani cewa yana so
takan sanyashi gaba da komai nata,lamarin su'ad kam sam baya damunta,duk wani
iskancinta da tambotsanta basa gabanta,sai taga dama ma zata ganta bare wani sabga
ya hadasu,abu daya take qoqari a kai shine tausar almustapha a duk sanda ta
kunnoshi,sam bazata so ace su'ad din tabar gidan na,kullum fatanta shine Allah ya
shiryata ta gane illar abinda take yi,ta tabbatar da cewa duk duniya bata da wata
mafita matsawar almustapha ya sawwaqewa su'ad tofa za'a ce itace sila,bayan duk
wanda zaiyi alqalancin baisan meke wakana game da zamantakewar auren su'ad din
cikin gidan ba,saidai hasashe dai kawai.

       A haka cikinta ya shiga watanni tara har ya soma yunqirin shiga na


goma,kallo daya zaka mata ba zaka so sake dubanta ba sabida tausayi,sosai cikin
yayi wani girma har wani lokaci sai ta tallafeshi idan tana tafiya saboda girmansa
da yadda ya sauko qasa,ta sauya kamanni sosai kamar ba sumayyan ba,munin da tayi a
da nafila ne,har bata son kallon kanta a mudubi,sau tari idan taga almustapha na
kallonta sai ta kau da kai tana tunanin munin da tayi yake kallp,saidai shi sam ba
haka bane cikin zuciyarshi,tsananin tausayinta ke damunshi,ba don kada yayi riga
malam masallaci ba da tuni ya yankata ya cire mata cikin ta huta,yakan tallafo
fuskarta ya saki murmushi
"Ki daina boyen fuskarki,a hakan kinmin kyan da ban taba ganin kin yimin irinsa
ba,kinsan me?" Sai ta kada kai cikin murmushi
"Da zaki sake zama haka nan da wata takwas ma bayan kin haife wannan cikin ina
so,da nafi kowa murna"
"Kayimin addu'a Allah ya rabani da wannan ma lafiya"
"Yadda zuqar numfashina ya zamemin dole haka wannan addu'ar ta zamemin dole" ya
fada yana karata da jikinsa tare da shafa bayanta a hankali yana ci gaba da yi mata
addu'a cikin ranshi.
       Semina ce ta kamashi ta sati guda wadda za'a yi a china ta 'yan kasuwa,sam
yace ba zashi ba,ita ta tausashi da qyar tace ba'a jiran haihuwa sai sanda Allah ya
kawota,ko kadan baison tafiya don ko fita ya rage,tausayi take bashi matuqa,hatta
tashi sai tayi da gaske take iya yinsa ko shi ya dagata,ita ta tayashi hada
kayanshi tana yi tana tsokanarshi wai ya zama rago,jawota yayi jikinsa yana dan
mintsinarta yadda ba zata ji zafi ba yana murmushi
"Laifin wa?uhmmm babe,bake kika maidani haka ba?" Dariya ta saki,ta jawo hannunsa
ta dora saman cikinta
"Laifin wannan ne ba nawa ba"sake matseta yayi a jikinsa yana sakin murmushi,tasan
duka hanyar da zata sashi nishadi.

       Sai da ya hadata da babban asibitin dake qasar wanda anan yake musu aiki
lokaci lokaci,ya basu lambarta lambar gidan da adress,sannan itama ya bata number
dinsu,sannan ya karba mata nurse guda daya wanda suka tanada saboda jinyar marasa
lafiya wadda zata dinga zuwa tana kwana da ita,sam bai fadawa ummi ba don ya
tabbatar cewa zatayi ya turota nigeria,shikuwa baison ko daya abinda zai rabashi da
ita dai dai da minti daya

       Tattaki ta masa har zuwa cikin falonta,kasancewar ranar girkinta ne,ya


jawota kusa da shi ya riqe dukkanin hannayenta cikin nashi yana duban qwayar
idanunta
"Kimin alqawari zaki kulamin da kanki har na dawo,ba tunani ba damuwa,kinyi
alqawari?" Murmushi ta sakar masa mai kwantar da zuciya ta gyada kai
"Nayi maka noor,Allah ya tsaremin kai ya dawo min da kai lafiya"
"Amiiin baby na" ya furta yana lumshe idanunsa sannan ya matso da ita gab da shi
yayi kissing goshinta zuwa wuyanta.

       Tare da su'ad suka rakoshi har bakin mota,sai da driver ya ja suka fice
sannan kowacce ta juya zuwa ciki,wani kallon banza take jifar sumayyan da shi gami
da jan dogon tsaki,bata kulata ba don idan da sabo ta saba,tayi wucewarta ciki
abinta.

   *******    ****   ********

     Bayan kwanaki biyar da tafiyarshi ne inda suke saka ran dawowarshi jibi,tun
safe take jin ciwon mara kadan kadan,saidai bata gayawa ko nurse dinta ba saboda
tunda cikinta ya shiga wata na goma take fama da irin hakan kadan kadan lokaci zuwa
lokaci,yanzun ma fitsari ne ya tasheta,sai data dauki a qalla minti biyar ta iya
yunqurawa ta miqe,mararta ta amsa sai data ce wash sannan ta iya miqewa a daddafe
ta qarasa bandakin mararta na ciwo sosai,koda taje fitsarin kadan tayi sai ciwon da
ya dadu,dawowa tayi cikin dakin ta soma kai kawo a tsakar dakin,a jikinta take ji
tabbas naquda take,bata da maraba da abinda take ji lokacin haihuwar abdallah.

      Tsahon awa daya tana gumurzu babu sassauci,hakan ya sanya ta fito falo a
daddafe,ta dauki waya ta kira lambar nurse din,cikin sakanni kadan ta iso ta dubata
ta tabbatar haihuwa ce,saidai akwai saura,asibitin ta sanarwa,babu jimawa saiga
mota sun aiko da ita suka daukesu suka wuce,su'ad taji motsinsu,ta dauka wasu ne ta
leqo da taga sune ta koma tayi kwanciyarta abinta.

      Daki ne na musamman suka bata,dauke da na'urori kala daban daban bayan ta


sauya riga zuwa ta asibiti,tun tana daure ciwon har abun ya soma wuce
tunaninta,naquda take haiqan saidai haihuwa tawi zuwa,tun biyu na dare har gari ya
waye haihuwa bata zo ba,daga gefan almustaphan ya kira wayarta yafi a qirga saidai
ba amsa,saboda sun baro wayar a gida,ya kira su'ad tace bata sani ba,bata gama
bashi cikakkiyar amsa ba ma ta kashe wayarta,yayita kira switchoff,take hankalinsa
ya tashi,sai sannan yayi dana sanin me yasa ko baba uwani baisa an kawo ba?,kai
tsaye ya kira asibitin nan suka shaida masa tana nan tun daren jiya,ranshi ya baci
hankalinsa ya tashi,fada ya hauyi kan me yasa basu shaida masa ba?,sannan ya za'ayi
su barta tun jiya har yanzu wayewar gari tana naquda har ta kusa cinye awanni da
aqa'idar likitoci ba'a so ta gama su bata haihu ba,haquri suka shiga bashi,bai
sauraresu ba ya katse layin ya soma tattara ya nasa ya nasa ba tare da ya kammala
abinda ya kaishi ba,hankalinsa gaba daya yayo dubai,jinsa yake kaman yayi tsuntsuwa
ya ganshi a can.

        Qarfe hudu na yamma ya iso dubai,kai tsaye ya yiwa drivan umarni ya wuce da
shi asibitin,kai tsaye ya wuce dakin da take,kwance take saman gadon,kallo daya
zaka mata kasan cewa ta jigata qwarai,duk sanyin dake dakin bai hanata gumi
ba,muryarshi kawai taji ta daga kanta taba dubanshi,tuni ya ajjiye jakar dake
hannunsa ya qarasa inda take,nurses din dake dakin suka fice daya bayan daya,tafin
hannunta ya laluba ya sanya nashi hannun ciki,hannunsa saman kanta yana shafawa a
hankali,baki daya zuciyarsa ta karye
"Baby......sannu baby" ya fada idanunsa cikin nata,ga mamakinsa murmushi ta sakar
masa a wahalce
"Ka dawo?"
"Eh...." Maganar tasa ta katse sanda ta furta
"Hasbunallahu wa ni'imal wakil!" Cikin madaukakin sauti ta soma murqususu cikin
matsanancin ciwon da ya taso gadan gadan,tamkar dama jiran zuwan almustaphan
yake,yanayin yadda yaga tanayi ya sanyashi sake dubata da kanshi,nan ya tabbatar
haihuwar ce,nurses din da suka fita ya kirawo don su taimaka masa,din bashi da
qwarin gwiwar da zai iya karbar haihuwar shi kadai,yana riqe da ita yana gaya mata
addu'o'i tana maimaitawa cikin wahala,a qalla mintuna goma kafin jaririyar ta samu
isowa duniya,kukanta ya karade ilahirin dakin baki daya har zuwa waje,basu gama
tantance komai ba ta sake wani yunqurin,wani sabon kukan ya sake karade dakin suka
hadu suka cika ilahirin dakin zuwa harabar dakunan da kukansu,nurses din ne suka
dauke yaran yayin da baki daya hankalinsa ya raja'a a kanta,gumin da ya mata
sharkaf ya soma goge mata yana jero mata sannu babu qaqqautawa,dubanshi take yadda
ya rude baki daya,kukan yaran na yawo cikin kwanyarta,tasbihi take wa ubangijin
talikai,yau gata a karo na biyu ta sake samun diyoyi,diyoyin da suka fito daga
tsatsonta,kasa dauke idanunata tayi daga shiyyar da yaran suke sankda nurses suka
gama rabasu,kukansu suke sosai suna wutsil wutsil da qafafu da hannyensu,sakayau a
yanzu take jinta kamar sun fita da duk wani ciwo dake damunta.

       Cikin mintuna qalilan nurses din suka soma gyara yaran,shi kuma ya gyara ta
da kanshi a wani daki daban,komai ya kammala,aka maidata zuwa wani dakin ita da
yaran baki daya.

        Zaune take saman gadon sosai tana jingine da bango,murmushi ne sosai kan
fuskarta wanda har sai da ya sanya haqoranta bayyana,idanunta taf da qwalla sanda
almustapha yake nufota dauke da daya daga cikin jariran wadda ke nannade cikin wasu
irin kayan sanyi masu azabar kyau set da abun daukansu,gabanta ya qaraso shima
idanunsa cike da qwalla yana dubanta tare da duban babyn,miqa mata ita yayi sai ta
dauke idanunta qwallar data cika mata idanu tana gangaro mata saidai har yau
murmushin dake kan fuskarta bai bace ba,da hanzari ua sake matsarta ya kama
hannunta yana matsawa cikin rauni da rawar muryar da bata taba ji daga gareshi ba
yace
"Kada kice zaki ji kunya babe....karbi diyarki ki gani in dauko miki
dayar....duniyarmu ce baby duniyarmu....daga ni sai ke sai su karbi ki gani", ya
qarashe maganar yana dora mata yarinyar saman cinyarta,tuni ta sanya hannu ta
karbeta,cikin sakanni qalilan qaunar data ke musu taji ta soma ninkuwa cikin
zuciyarta,sak jinin gidan baba prof,kana dubanta ko makaho ya shafa yasan jikar
mutanen gwambe ce,photocopy na almustapha,sake komawa yayi ya dauko dayar ya dawo
saman gadon ya zauna sosai kusa da ita yana bude mata fuskarta
" kalli usaina baby.....ba wadda ta miki kara?"ya fafa yana sakin dariya wadda ke
qunshe da zallar farinciki,jinsa yake yau kaf duniya babu dan adam din da ya kaishi
farinciki,ba wanda kuma ya kaishi sa'ar zuwa duniya,itakam murmushi kawai take
bakinta ya gaza furta komai,Allah kenan,buwayi gagara misali,cikin rayuwarta kaf
bata taba kawowa kanta haihuwa bama bare kuma aje ga haihuwar 'yan biyu,dai gashi a
yau,Allah yayi mata kyautar da bata taba hasashenta ba,haqiqa Allah mai tsananin
karamci ne,sosai almustaphan ya dinga sumbatu wanda tasan na tsantsar farinciki ne
tana dubanshi tana dariya,ita din ma jinta take saman wata duniya ta farinciki tana
yawo,ta kasa dauke idanunta daga yaram,ba don yaranta bane,amma zata iya cewa bata
taba ganin jarirai masu ban sha'awa irinsu ba,sam ya mance da ya wanu kira gida ya
fada sai data tuna mishi,a sannan ne ya dauko wayarshi,ummi ce mutum ta farko da ya
soma kira,danda yake gaya mata tsaye ta miqe tana kabbara,bata qarasa jin zancan ba
ta rankaya falon baba,saidai kash kafin ta isa tuni anty maamaa ta rigata kai
labarin,wanda ta jishi je sanda take shigowa wajen ummi,a take baban ya mata
kyautar kudi masu tsoka,ta dinga ma ummi dariya tana cewa saidai a tara a
gaba,itama dariyan ta dinga tace rabonki ne,duk yadda baban yaso sakaya
farincikinsa abun yaci tura,haka shima ya dauki waya ya dinga kiran abokai da 'yan
uwa yana sanar musu,cikin lokaci qanqani labarin haihuwar ya karade kowanne
sakaye,tsakanin baba da malam sai aka rasa wanda za'a yiwa murna,amira kuwa da anty
dije kukan farinciki suka sanya,ta dinga kiran almustaphan tana roqonshi zata taho
yace sam,sai ta saka kuka,tana so ace cikin dangi itace mutum ta farko data fara
daukan yaran,abu daya ne ya saka mata haquri hoton yaran da ya dauka ya tura mata
ta email adress dinta,don shi baya watsapp.

      Da kanshi ua sallami matarshi bayan ya tabbatar da cewa komai lafiya suka


kama hanya zuwa gida,yana bayan motar shi da ita,baki daya yaran na hannunshi ya
hana mata ko daya,ji yake idan ya rufe idanu zaiga kamar mafarki kamar almara,ashe
duk arziqinka duk dukiyarka,duk farincikin da kake taqama kana ciki bai gama
kammaluwa ba matuqar baka samu diyoyin da zaka alaqanta da jininka ba,ashe zallar
farincikin da zata fadeshi sai randa ka ganka dauke da zuriya taka ta kanka.

        Daidai sanda suka nufi gidan su'ad na tsaye tsakar dakinta tana amsawa
wayar da suke da mahaifiyarta
"Nifa gaskiya su'ad na soma sarewa,kinga tsantsar farinciki da doki da professor
yake ciki sanda ya kira mahaifinki kamar ranar aka soma haifa masa jikoki,anya kuwa
su'ad ba muyi kuskure ba?,ina da yaqinin Allah kadai yasan dukiyar da zasu samu su
kuma mallaka tun suna qananunsu,wanda dukkan abinda suka samu zai koma fa hannun
mahaifiyarsu ne" qatuwar ajiyar zuciya ta saki
"Bama wannan ba momy,wallahi na tabbatar na shiha uku,duk wani soyayya da tattali
da adalci da almustapha ke qoqarin gwadamin ina da yaqinin sai ta ragu,tun cikin
bai fito duniya ba kinga abinda yake?,ina ga ya fito sannan kuma twince mommy?,shi
yasa nake tunani anya ba zamu sake plan ba?,na nemi dalilin haihuwa nima ko don na
sake janyo hankalinshi zuwa gareni baki daya?"
"Dqlla can rufewa mutane baki,ke ta soyayyarsa ma kadai kike,soyayyar vanza,ana
miki maganar kudi abokan tafiya qare magana,so nake fa ki zama cikin jerin
attajiran da duniya ke lissafinsu kaman yadda a yanzu mijin naki yake,ke kadai ce
fa 'yata ke daya na mallaka,saboda haka ina so naga kinyi shaharar da ko d'a
namijin da yayi shekara arba'in yana gwagwarmaya baiyita ba"
"To yanzu ya za'a yi momy?"
"Cikin satin nan kisan yadda zakiyi kizo nan mu warwareta"
"An gama" ta fada tana katse wayar saboda motsi da taji kaman ana shigowa,a hankali
ta tako ta fito zuwa falon,almustapha ne riqe da baby daya,wata mace mawociyarsu
'yar asalin qasar saudiyya dauke da dayan,fuskarta a washe tana tana yaba kyawu da
girman yaran cikin harshen larabci,duk da bata fahimtar me take fada amma daga
yanayin matar tasan tana yabawa ne da yadda yaran suke,idanu ta zuba musu tana
karantar fuskar almustapha wanda bata san da dawowarshi ba saibyanzu,tunda sukayi
magana ya tambayeta sumayya tace bata sani ba bai kuma kira ba hakanan bata bi ta
kanshi ha itama,iya tsahon zamanta da shi bata taba ganinshi cikin wannan hali na
matsanancin farinciki ba, saidai ba wanda ya kula da ita a cikinsu saboda tana daga
bayan labule ne har suka shige.

      Yana fitowa daga dakin ya lura da ita,fuskarshi sake yake dubanta,bacin rai
da take dannewa ya taso yafi qarfinta,sai kawai kuka ya qwace mata,sai ta juya da
gudu gudu ta koma ciki,tausayinta ne ya sauko masa lokaci guda,yana tunanin rashin
samun tata haihuwar shi ya motsa mata,wanda hakan zai iya faruwa ga kowacce
mace,kowanne lokaci kuma yanayin kan iya motsuwa cikin zuciyarki har ki kasa
controlling din kanki,sai ya rufa mata baya,samunta yayi kuwa zaune saman kujera
tana buge buge da hannunta,dama ace dama ace ce fal cikin zuciyarta,zata so a ce
itace ta samu wannan yaran ba sumayya ba,wai shin me ya hanata tsayawa ko guda daya
ta samu ne?,ba shakka tana ji a jikinta lokaci yayi da zata tashi ta dawowa da
kanta dama ta samun haihuwa a gareta,a tausashe ya zauna gefanta yana riqeta,baison
idan wani abu ya sameta ta dinga irin wannan acting din dake nuna zallar rashin
yarda da qaddara,cikin taushi ya soma ce mata
"Am sorry dear....ba kuka zakiyi ba,addu'a zakiyi Allah ya kawo mana,komai a duniya
yana da lokaci sannan komai yai farko yana da qarshe banda ikon Allah,matuqar kina
da rabo ta babu makawa sai kin haifa kema"
"Ko bani da rabo wallahi sai na yishi,sai na haihu nima" tsauri maganar tayi
masa,haqiqa ba qaramin illa da tasiri dabi'un yahudawa marasa tauhidi suka yiwa
su'ad din ha,saidai yana da burin sosai wajen ganin ta daidaitu,duk da hakan ma
alhamdulillah,ya rabata da shigar banza ya sata tsaida sallah,koda kuwa zata yita
ne bayan wucewar lokacinta
"Subhanallah,kiyi istigfari,babu bawan da yafi qarfin QADDARA,saidai addu'a na
maida MUMMUNAR QADDARA ta koma zuwa KYAKKYAWA,ki roqi Allah sai ya kawo komai a
sauqaqe,ba wayonki ko dabararki ba,ita kanta ada can an taba kiranta juya,an fidda
mata rai zata haihu,amma a yanzu gashi ke ya faru?" Cikin hikima yake gaya kata
kalaman kwantar da hankali,saidai jinsu take kaman busat sarewq,abu daya ne ya dan
kwantar mata da hankali,kasancewa da yayi tare da ita duk da ba ranarta bace,da
kuma yadda yake lallashinta,saidai ba shakka cikin satin nan zata san yadda zata
wuce america don bazata juri rasa cika burin data qudurtawa ranta ba.

      Maqota biyu da suke da su wadanda ba yarenta ba saidai 'yan uwantaka ta


muslunci da tsananin kirki da suke da shi,wanda batasan suna da shi ba sai yanzun
da haihuwar 'yan biyu dake da farinjini suka sa tasan hakan,suna kula da ita
sosai,akai akai suke leqota da kalar abinci da kulawa da sukewa maijego,akwai mai
tayata zama guda daya daya samu wanda ta kasance mutuwar qasar ghana ce,zaman
sana'a yasa take zaune a qasar,sai ta kasancewa sumayya tamkar yar uwa,sosai matar
ke kula da ita,tana da qoqari da zafin nama qwarai,babu abinda sumayyan ta nema ta
rasa,hatta da shi mai gayya mai aikin idan ya fita sha daya,biyat na yammaci ya
dawo gida,koda yashe burinsa ya ganshi tare da su,a haka ma idanun su'ad yasa ya
dan rage wasu abubuwa tare da danne daukinsa,don har ga Allah tausayinta yake
ji,yasan cewa rashin haihuwa babbar damuwa ce dakan iya zamewa wasu matan ciwo
cikin zukatansu,abinda bai sani ba shine ta soma girbar abinda ta shuka ne ba tare
da shi karan kanshi ya sani ba,wani tsananin son hauhuwa ne ya mata mugun kamu
cikin kwanakin da basu haza hudu ba,sosai walwala da kuzarinta ya ragu,kishin yaran
da uwarsu baki daya ya gallabeta,ko sau daya tak bata taba kusantar dakin sumayya
ba bare tace zata ga yaran,wani abu ke tokare mata wuya duk sanda taji sautin
kukansu,ji take kaman ta kaudasu ko ta samu hutu.

       Daga daya bangaren kuma tuni ummi ta gama duk wani shirinta na zuwan yaran
da mamarsu,kwana biyu taji shiru hakan ne yasa ta tuntubeshi,sai yace 'yar matsala
ce aka samu wajen siyan ticket,tuni ta baroshi,wanne matsala ce za'a samu wajen
siyan ticket kawai?,shi kansa yasan qaryar bata hadu ba saboda ba sabonshi bace,ko
kadan ne kawai baya son su tafi su barshi,baya jin zaman garin zai yiwu gareshi
idan suka tafi din,shi a son ranshi duk maison zuwa cikin gidan nasu zai siya masa
ticket,wanda bai da visa zai masa suzo suga yaran,sam bazaiyiwu ba ummi ta gaya
masa,su a wajensu tamkar haihuwar fari ne,saboda haka dole ya kawo 'yar mutane a
kula da ita sosai,sannan itama tana da yan uwa tana son zama cikinsu ai,shikam
baiga wacce kulawa akeson bata ba bayan wanda take samu nan daga wajensa,yana
kallonta take saka towel cikin tafasasheshen ruwa ta gasa kanta sosai,ta fito taci
abinciccika masu gina jiki,ga magungunan da yasa zasuyi mata matuqar amfani a jiki
da take sha,hakan ya sanya hatta da ruwan nono ta samu wadatacce,kana kallonsu zaka
san kulawa kam sun sameta,daga ita har yaran kai kace sunfi kwanaki hudu da
haihuwar,warshe dai haquri ya baiwa ummi yace suna tahowa.
       Sai ana ya gobe zasu cika kwanaki bakwai sannan ya siya musu ticket har da
shi da su'ad zasu tafi,dakin su'ad ya fara zuwa,ya taddata zaune tana latse latsen
waya,sam sumayya bata gaya mishi bata taba zuwa taga yaran ba,shima kuma bai taba
kawo ba zata shiga din ba,gefanta ya samu ya zauna yana fuskantar fuskarshi a sake
sosai,kai ta daga ta dubeshi,as usal bata iya sannu da zuwa ba ko gaisuwa
"Baki gajiya da danna waya?" Ya tambaya yana daukar remote ya rage saitin kidan
dake tashi a tv
"Idan ban danna ba me kake so nayi?" Ta tambayeshi cikin yanayin bacin rai,idanu ya
zuba mata yana karantar yanayinta,sai kuma ya hadiye ya dauke kanshi daga fuskarta
yaba bata amsa
"Karatun qur'ani,istigfari da sauransu"
"K'nnnnn" ta ce a taqaice,tun daga ranar zuciyarta da shaidan suke gaya mata ta
gama burge almustapha fa,yanzu ba sonta yake ba ba kuma qaunarta yake ba,yaranshi
da uwarsu su kadai yake so da qauna,bayan babu wani abu da yayi mata wanda ke nuna
haman,illa ma lallashinta da yake saboda yana tunanin rashin samun nata yaran na
kanta ke damunta
"Gobe zamu shiga nigeria,su ummi sun matsa sai mun dawo a yi suna a can kowa yaga
yara"qafafunta ta miqe ranta na baci
"wannan ku ta shafa sai kun dawo" idanunsa ya qanqance yana dubanta,wati mai hali
bai fasa halinsa,duk yadda yake tattali da rarrashinta wato shi din banza ne baisan
ciwon kanshi ba?
"Kamar yaya fa?" Ta tambayeta yana son qarin bayani
"Ai suma su ummin tsabar gulma ce,babu gidan uban da zani,wato nake inje aji dadin
nuna ni gani ban haihu ba wata tazo bayan bayana ta haihu ko?,to bazanje ba,dama an
dade ana ruwa qasa na tsotsewa,muna fukin auren ma duk ha sune sila ba sabida kai
an tsaneka ba'a sonka" cikin tsananin bacin rai ya daka mata tsawa,nunata yake da
yatsa cikin bacin rai
"Hey idiot.....Kar ki soma kuskuren fadin maganar banza kan mahaifana,ki kintsa
bakinki kada furucinka ya jawo miki nadama......iyayena sun fiye komai da komai da
na mallaka nake da shi,su din wasu abubuwane masu daraja da babu kamarsu,kudi ko
qarfin iko basu isa su baka su ba.....ban gaya miki zamu nijeria ba wai don ina
neman shawararki ba,umarni nake baki kaman yadda wadanda suka isa da ni suka bani
umarni nabi,kema dole kibi umarni na don na isa da ke" ya miqe yana niyyar ficewa
ranshi a bace
"To wallahi ba inda zani daga nan nima gidanmu zan wuce ai ina da gidan uba...."
Waiwayowa yayi yana mata wani kallo daya sanyata rusuna ba tare data shirya ba
"Really?,....ok,indai haka ne idan kinje kada ki sake ki dawomin gida kinji
ko?,ruwanki kije nigeria ruwanki kije ameria amma ki zauna acan,kada qafarki ta
dawo gidan muhammad almustapha" yana kaiwa nan ya wuce yana mai buga qofar cikin
fushi,kanta ta dafe,tabbas bata da wata mafita,zai iya aikata dukkan abinda yace
din,saidai ta gama rayawa ranta abinda zatayi,zuwa gida babu fashi.

          Da sallama bakinsa ya shiga dakin sanda take gaban sif tana fidda kayansu
tana shiryawa cikin akwati,yaran na kwance cikin gadonsu suna bacci hankalinsu
kwance,cukin tsafta da qamshi,a qunshe suke cikin kayan baby masu taushi
pink,yanayin muryarshi kawai taji ta saki abinda take ta waiwayo tana dubanshi,duk
sanda taji muryarshi haka tasan ranshi a bace yake koda yayi yu qurin boye mata,bai
dubeta ba har ya isa gaban gadon yaran ya bude dan net din dake matsayin qofa ya
zura kanshi,kissing kowannesu yayi yana lumshe idanunshi,qamshinsu da kyan da suka
yi suna ratsashi,kaso hamsin cikin dari na bacin ranshi take ya kwaranye,sai da ya
gama duddubasu sannan ya sake rufesu,ya waiwayo suka hada idanu da sumayya,kusan
tare suka sakarwa juna murmushi,qare mata kallo yake yana takowa inda take
tsaye,rigar jikinta ta kamata ta fidda surarta qarara,ga na shanunta fa suka cika
sun zauna das jikinta har wani qyalli suke,hankalinshu bai kwanta ba sai da
yasanyata cikin jikinsa ya dora hannayenshi saman qirjinta yana yawo da shi yana
lumshe ido
"Me kike a tsaye...ke da na gaya miki bacci nakeso kiyi?" A tausashe tace
"Na gaji noor,kuma gobe zamu wuce kaga dole na hada mana kayan da zamuyi amfani da
su ko?" Kai ya kada
"noo,kada mi wahalar da kanki,babu wani abu da zaku dauka a nan,akwai komai can an
tanada" mamaki ya kasheta,kada dai ya gaya mata ya sake wata siyayyar ne bayan
wadda yayi a nan,bakinta ta bude da niyyar magana,saidai ba bata dama ba ya hade
bakin nasu waje daya ya soma aika mata da saqo.

      Da qyar ta qwaci kanta gajin yana yunqurin wuce makadi da rawa tana maida
numfashi,da baya ta soma ja ya dinga binta idanunsa kafe a nata yana dariya
"Me na tsorata haka babe?"Kai ta langabe
"jego fa nake noor...ni wallahi na yafewa anty su'ad kai ka manta yadda mukayi da
kai jiya?"
"Don kin yafe kata kuma sai ki haramtamin romancing dinki?,baki isa ba
wallahi,wannan tamkar rai da numfashi ne kinga babu mai rabawa ko?"
"Haba noor ka tausaya min mana" ta fada kaman zatayi kuka sanda ya cimmata,kamata
yayi sosai yana duban qwayar idanunta
"Toni cewa nayi zanyi wani abu?,kawai dai a barni na dinga hutawa,kuma Allah idan
kika yarda kika wani zauna zaman me ake cewa zaki gani shayi ruwa ne,ko an miki
tayi kice kawai ni zaki biyo,sati daya kawai zamuyi mu dawo,if not kuwa wallahi
takanas zan baro dubai na taho nigeria suburbudarki in koma abina" sosai kalmar ta
bata dariya har tana toshe bakinta,yayin da shima ya saki qaramar dariyar yana rage
zafi,motsin farkawar usaina ya sanyashi sakinta
"Kina da zabi kan sunayen yaran nan?" Kai ta kada tana kallonshi
"Bani da zani,duk abinda ka yanke dai dai ne" murmushi ya saki,ko yaushe tana maida
shi yana jin kansa tamkar wani sarki,komai yayi da rayuwarta bata da zabi dai dai
ne,hakan ke qara mata qima a idanunshi
"Amatullah da amatur rahman" idanunta ta juya tana murmushi,sunayen sun mata,sunaye
ne masu kyau da ma'ana,bai bi iyayi ko dadin suna a baki ba
"Allah ya musu albakarka,ya sanya ma'anar sunayen ta bisu"
"Amin ya rahman ya rahim"shi yaje ya daukota ya kawo mata ita,har yau bai taba
ganin tana shayar da su ba quru quru,hakan ya sanya yau ya titsiyeta,ganin ta tsaya
nuqu nuqu ya sanyashi zura hannunshi da kanshi ya dauko mata ya sa mata a baki
sannan ya sake daidaita mata riqonta yadda isaka ba zata shiga bakin yarinyar ba
sanda take shan nono,dubansu yake cikin shauqi qauna soyayya da burgewa,har sai da
tayi kaman zata tsole masa ido tace
"Kada ka cinye mu mana ha'an?" Qawataccen murmushi ya saki,ya jawota jikina yana
cewa
"Da zai yiwu hadiyekun zanyi na huta wallahi baki daya,saboda bansan ya zan fassara
miki yadda nake jinku cikin zuciyata ba" lumshe idanu tayi,kalamansa na
ratsata,tana godewa Allah tare da qarawa kanta qwarin gwiwar yadda zata ci gaba da
yi masa biyayya don ta mallaki zuciyarsa fiye da yadda ta mallaka a yanzu,saboda
sau da yawa kyautatawa itace ke mai da d'a ya zama bawa,to itakam kyautatawar da
take masa ta sanyashi ya zama tamkar bawa a gareta.

   ******     ******    *******

       Cikin cikakkiyar kama da kamala take sanye cikin atamfa riga da zani da
wadataccen mayafi,haka almustapha ke sanye da wani yadi irin na sarakai da aka yiwa
aikin gidan sarauta,takalmi zuwa hular kanshi duka irin na gidan sarauta ne,sunyi
kyau sosai,zallar farinciki qauna da girmamawa juna ta bayyana a tsakaninsu,su'ad
ma na sanye da doguwar riga ta gown,saidai a sake take bata kama wani sashe na
jikinta ba,almustapha ke dauke da hassana ita kuma na dauke da usaina,karon farko
data fara daukar yaran,wanda ganin idanun almustapha yasa ta daukesu,tana son tayi
wani abu da zai barta zuwa gida,saidai tana ji kaman tayi jifa da yarinyar,kamar
wadda ke dauke da garwashin wuta haka take jinta,tun daga harabar gidan ya isa ya
sanar maka akwai baqi a gidan,hakan kuwa yake,anty farida da yaranta,huda da
yaranta,oga amira,anty ni'imah wadda ta taho da hibba da hibban sun bar biyu a gida
legos tare da mamarsu sai ana ya gobe suna zasu iso.

      Ashe baki daya suna daga gefe suna jiran qarasowarsu ciki,take kowa yayi
tsaye bakin motar fuskarshi qunshe da murmushi,ba don shakkar ya man din ma da suke
ba da babu shakka tuni sun ruge bakin motar suna rigengeniyar daukarsu,amma duk da
tsare gidanshi hakan bai hana amira saurin amshe usaina dake hannun su'ad ba,tunu
ta sakar mata dama neman mai dauka take,a rayuwarta kusan zata iya irga sau nawa ta
dauki jariri,ko da can ita ba mai son yara bace,balle ma ina ta gansu,anty maamaa
ita ta karbi hassana,take waje ya kacame da murna,hayaniyarau ta soma tashi,suna
mata sannu tare da nuna tsantsar farinciki da kyautar da Allah ya yiwa ahalin nasu
na 'yan biyu,wanda wannan ne karon farkonda suka samesu,hakan ya sanya shi janye
sumayya zuwa sashen ummi wadda alkunya ta sanyata bata fito ba tun basu saka shi
ciwon kai ba.

      Nauyi da kunya suka hanata hada ido da ummi,itakam wannan karon ummin yakice
ku yar tayi,don sai data rungume sumayya cikin jikinta tana mata sannu sannan ta
zaunar da ita saman kujera bayan tasa an kashe ac da fankar dake falon,a nan kowa
ya shigo hira sabuwa murna da hada hada ta tashi,gefanta ya zagaya ya rada mata
"Kada ki bari su wahalarmin da daughters,kema ban yarda kiyi hayaniya can ba" a
kunyace ta gyada kai,suka hada ido da wasu daga cikin wadanda ke wajen,sai ya tsare
gida ya fice abinsa zuwa bangarensu wanda can su'ad ta nufa dama.

       A ranar nafeesa dake garin tazo qaraso gidan,suna tare har anty dije,sai ga
abida ma wadda dama su tun jiya ita da hamza suka yo gaba,tana son duba mamarta da
aka kwantara asibiti duk da ta warware ma,bata samu kanta ba sai da suka tafi,sanda
ta sake wanka ta kuma ci abincin,yaran ma tuni anty maamaa ta wankesu ta shiryasu
tsaf zasu wajen baba su gaisa,ta dan kama kumatunsu taba cewa
"Saura kuje ku qwace mana miki kuma,kubar ganinku haka farare nunar rana" dariya
amira dake zaune wajen tayi
"Haba maamaa kema kinsan saidai kuyi haquri keda ummi,gwamnatinku ta rushe rumumus"
ta fada itama cikin raha wanda ya sanyasu darawa.

       Ita amira da anty maamaa suka fito suka nufi sashen baban,hanya suka ci karo
da almustaphan tare da su'ad,wanda da alama can zasun,hakan ya sanya maamaa miqawa
su'ad ummulkhair tace
"Sai ku qarasa kawai ko na shigo daga baya daman zai kawo mishi kununshi" kamar ba
zata karba ba har suka so fahimtar haka,saidai tasa hannu ta karba sheqeqe,kau da
kanta sumayya tayi kaman bata gani ba,yayin da amira bakinta ya fara rawa tana son
yin magana sumayya ta danneta,ashe hakan ya taba ran almustapha
"Kula mana" ya fada a kausashe,dolenta ta gyara riqon suka ci gaba da takawa,saidai
amira bata yadda ba tana biye da su'ad a baya har suka isa.

      Bayyana irin farincikin da baban ya shiga ma bata baki ne,har qaramar qwalla
sai da dauke yana tasbihi ga Allah,basu jima da shigowa ba anty maama ta daeo,saiga
mahmoud wanda shima bakinsa ya kasa rufuwa,ko kunyar baban da anty maamaa baiji ba
yake cewa ya Allah shima ya bashi kaman hakan,addu'a yayi musu baban sosai mai
tsaho wadda har tasa su'ad ta soma qosawa,ta dinga sakin tsaki a boye,guda daya ya
shiga kunnen almustapha ya waiwayo yana dubanta,sai ta dake ta saki murmushin yaqe
cikin duniyanci sannan ta sake maida kai wajen baban,sai da ya gama ya miqa musu
yaran,ya yiwa sumayyan addu'a itama sosai,tun tana amsawa har kuka ya qwace
mata,alkhairai yake roqa mata na duniya dana lahira,amsawa take tana kuka addu'ar
na sauka cikin zicuyarta tana fatan Allah ya amsa,sai da ya gama da ita sannan ya
sanya almustaphan da su'ad a ciki,suka shafa ya jawo wani file wanda da alama
musamman ya ajjiyeshi saboda wannan zaman,takaddu ya fito da su ya ajjiye gaban
sumayya
"Ba abinda bazan iya yiwa yaran almustapha ba,kaman yadda babu irin biyayyar da
baiyi min ba,hatta da mahaifina ya soshi tun yana tsumman goyonshi,ba don mahaifin
yaran baida shi ba ko ya gaza,a'a,nayi ne saboda murnar zuwansu duniya kaman yadda
nake bawa kowanne jika na,saidai su din tasu kyautar ta musamman ce kaman yadda su
da iyayensu suke na musamman a wajena" a nutse yake musu bayanin abubuwan da ya
mallakawa yaran,wanda duk wanda ke wajen yasan cewa eh lallai ba qaramin matsayi da
alkhairi yaran suka zo da shi ba,kyautar ta girgiza su'ad har ta ringa jin kaman
kunnenta ba dai dai yake jimata ba,hakan yasa ta saki duk aninda take ta tattara
hankalinta tana sauraren sha tara ta arziqin da baban kewa yaran,daga bisani ya
rufe da baiwa sumayyan kyautar kujerar umra da kuma sabuwar mota fil wadda take
qirar wannan shekarar,koda cikin masu kudi ba kowa ya samu zarafin yin orderta
ba,kyautar data sanya su'ad sakin kukan da taso dannewa,motar da take qulafucin
samu?,motar da take tattalin kudinta dinta siyeta saiga haihuwa ta siyawas
sumayyana bagas,miqewa tayi tana rushin kuka ta fice yayin da kowa ya bita da
ido,kusan kowa yasan abinda ya taba ranta amma dattako irin na dattijon sai yace
almustapha ya tashi yaje ya rarrasheta
"bata da lafiya ne zata je tasha magani ne"
"To Allah ya sawwaqe" bai iya amsawa baban da amin ba tsabar takaici,tabbas baiyi
qarya ba,hassada mugun ciwo ne,hassada tana cinue kyawawan ayyukan mutum kamar
yadda wuta kecinye yayi,ka tashi ran qiyama baka da komai cikin kyawawan ayyukanka
duka hassada ta cinye.

        Cikin kwanaki hudu da zuwamsu duk wani dan uwa dake kusa yazo yaga 'yan
biyu,yaran sunzo da wani irin alkhairi da farinjini,kowa cikin farinciki yake kaman
a sannan familyn suka samu jika na farko,kullum gidan baya rabo da jama'a tako
ina,ko yauahe qofar gidan a bude take,suna kuwa tun kafin ranan yinsa kullum yinsa
ake,saboda ci da sha da ake yi a gidan kullum kwanan duniya,duk wanda zaizo da
kyautar da zai ajjiyewa yaran,saboda kowa ya fuskancu yaran 'yan gaban goshi ne ta
kowanne bangare,ita kanta ummi da kyautar data musu haka anty mama,bare manyan
iyaye anty farida hida da anty ni'imah,hakan ya sake daga hankalin su'ad matuqa,har
takai bata da katabus sai tagumi qunci da bacin rai,bata da magana sai da tuni ita
ke amsar wannan abubuwan,da tuni itace a wannan bigiren.daga sunan akayi aka
maidashi dai dai da randa yaran zasu cika sati biyu a duniya,suna saura kwana hudu
saiga malam da mama,tayi matuqar mamaki da farinciki,kwana biyu sukayi,mama ta
siyawa yaran barimar gwal da zobe,sai awarwaron azurfa wanda ya musu yawa saidai
nan gaba sa saka,randa suka tafi washe gari saiga halima zainab data haihu wata uku
kenan ta samu namiji,sai anty meena,har da abdallah,yaya abbakar ne kawai bai samu
zuwa bawayyo ranar kasa cin abincin kirki sumayya tayi saboda murna,abin kam ba'a
cewa komai,haka ta zauna cikinsu tana jin dadi sosai,dan uwa akwai dadi,duk wanda
ya rasa dan uwa yayi kuka kam

        Ranar suna ta kasance baabbar rana ga duka ahalin,hidima akai qwarai da


gaske kaman ta bikin aure,ranar har kukan farinciki sumayya tayi,babu shakka duk
bawan da yayi haquri da qaddara mara kyau gaba Allah zai musanya masa,kuma Allah
baya dauke maka wani jin dadi koya jarrabeka khaka kawai sai don ya musanya maka da
abinda shi yafi alkhairi a gareka wanda kai bakasan da hakan ba,alkhairi kam
sumayya ta sameshi wanda bata taba tsammanin samunshi ba,washegarin suna aminan
qwarai musaddiq lamin hamza usman da huzaifa suka hada qawatacciyar walima,wanda
iyakan abokansu ne da makusantan mai jego,ranan almustapha yaga tsiya,hamza ya
kwasheshi son ranshi,cewa yake
"Iyeeeen ba,ashe dai ba jarumin qarya bane,duk tsare gidan nan ba'a banza ba,twince
ne ke tafe,amma fa rashin son raini da hayaniya ya zama na banza,ashe tsula
tsiyarka kake a daki kaman ba....." Duka ya kai masa wanda da qyar hamza ya
kauce,su lamin suka dinga kwasar dariya,can anjima sai ya matso gefan kunnenshi
"Yallabai....a bamu sirrin mana,ga wadan nan manyan gaurayen an sanya ranar aurensu
shekara daya masu zuwa(lamin musaddiq da huzaifa)"
"Zaka gane kuranke ne wallahi hamza kafi kowa sanina ban da kyau" sai da ya masa
haka sannan ya shafa masa lafiya,anci am sha an rashi cikin raha da walwala,bayan
kowa ya yiwa aminin masa kara da kyauta ta bajinta,don almustaphan ba baya ba,ya
riqe aboka qwarai da gaske,bashi da qyashi ko hassada,komai ya taso naci gaba
burinsa ya sanyasu a ciki su samu kowa ya samu ci gaba,kusan duka gaban idanun
su'ad aka gabatar da komai,hakan ya sanya tun dare ta tashi hankalinta zata
gida,kuka ba irin nau'in wanda batai masa ba,amma yayi biris da ita,don bata dauko
hanyar da zai barta ba,lafazinta kawai ya isa ya sanya a hana mata duk wani abinda
take so,qarahe ma falo ya dawo yayi kwanciyarsa,yana jin kewar sumaya,don a qa'ida
kwananta ne,amma jego ya raba tsakaninsu,dako banza zaya samu kulawa da
tattali,tsaki ya dinga ja yana juyi,wai dama haka jegon yake?,yanajin wannan jegon
bazai iya da shi ba,idan suka hanashi tafiya da ita nan da next week ba shakka zai
saceta ne su gudu,su basusan halin da yake ciki ba sai suce dai tayi wani jego.

Washegari tun qarfe tara baba ya kirayi wayarshi yace yazo yana son
ganinsa,sanda ya isa shi daya ne
"Ka siyawa su'adatu ticket taje taga gida" shine unarnin da baban ya bashi,ba musu
ko jayayya tsakaninsu har abada,hakan ya sanya bai tambaueshi bai kuma yi masa
bayani ya amsa da to ciki girmamawa,ya kuma siya din,saidai da ya siya baban ya
kaiwa ba ita ba,daga hakan baban ya gano lallai ba son ranshi bane,saidai tunda ya
riga da ya siya haka ya danqa mata,har ta tafi bata ga qeyarsa ba,hakan ba
damuwarta bane,tasan cewa lokaci qalilan ya rage ta samu dukkan kulawar data
keso,zata shuka tsiyarta za kuma ta zuba iskancinta yadda taga dama,haka take
rayawa a ranta.

Jakarta kawai ta ajjiye suka fito ita da mommyn nata,ta riga data siya musu
tikitin jirgin qasa har ya zuwa unguwar da sibitin yake da zama,tafiya ce ta kusan
awanni daya,wanda cikin awa daya da rabi suka isa ga ofishin ainihin likitan da
suke nema,doctor james,haifaffan qasar america,mutum da ya tashi da tsantsar aqidar
yahudawa ta aihini,sannan ya ginu kan qiyayyar musulunci da musulmai,ko kadan baya
qaunar musulmi a zuciyarsa,qwararren likitane na gyni wanda ya qware ya kuma
shahara wajen saida sperm yin dashe d'a dana qwayayen haihuwa,shahararsa ta sanya
mummu kashe kudade masu yawa domin su ganshi don samun biyan buqatarsu,da idanu
yake kallonsu bayan ya gama jin abinda ya kawosu,uasan tabbas ba mai yiwuwa
bane,haihuwa ga macen da babu mahaifa tattare da ita kwata kwata,saidai kuma tunda
aka masa transfer na sunayensi cikin system dinshi ya tabbatar da musulmai ne,baya
jin kuwa zai barsu su fita a office dinsa salin alin ba tare da ya zaluncesu
ba,wanda wannan shine babban burinsa,agender dake gabanshi tsakaninsa da wani
shahararren mai kudi dake garin nasu ya fado masa,hakan ya sanyashi sakin
murmushi,ba shakka zuwansu yayi daidai,haka faduwa tazo dai dai da zama,murmushinsa
ya jefa musu zaton cewa nasara ce qarara ya hango,sai ya karkace ya zuba musu
bayanin cewa zata haihu kamar kowacce mace,zasuyi mata aikin da bazata farka ba sai
da juna biyu,nan da kwanaki uku ta taho asibitin zasu soma aikin nasu,kudi kadan ya
yanka musu ahakan ma ya karba ne kawai don kada ya darsa zargi cikin zuciyarsu
saboda yasan cewa kudaden da zaya samu zasu mai dashi cikin jerin sahun masu kudin
garin,zuciyarsu fes suka bar asibitin,tun a sannan su'ad din ta fara hasashen irin
abubuwan da zata shuka bayan bayyanar ciki a jikinta,bata jin zata dagawa wani
cikinsu qafa,kowa sai ta takashi dai dai da abinda yayi mata.

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*
*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

1⃣0⃣6⃣

*KADA KI WUCE BAKI KARANTA BA*

*SHIMFIDA MAI MUHIMMANCI*

*bismillahir rahmanir rahim*

*Allah S W T yana fada cikin qur'aninsa mai girma*

*ku koma izuwa ubangijinku ku tsarkake aiki dominsa,tun kafin azaba tazo
muku,sannan ba za'a taimakeku ba(da hana saukar azabar idan baku tuba ba*

*kubi kyakkyawan abinda aka saukar izuwa gareku daga ubangiji tun gabanin azaba
bata zo muku bagatatan bakuyi hasashen zuwanta ba*

*tun kafin rai bata ce ba "ya asarata/tabewa ta bisa sakacim da nayi a janibin
Allah,haqiqa na kasance cikin masu wasa*

*ko tace "da Allah ya shiryeni da na kasance daga cikin masu tsoron Allah*

*ko tace lokacin da taga azaba  " da ace ina da damar komawa izuwa duniya izuwa
duniya dana kasance daga cikikin mash kyakkyawan aiki*
______________________________________

*WANNAN SHAFIN SADAUKARWA NE GA MEELA ADEEL DA SAURAN DUKA MASOYAN SU'AD*

      

    Kallo daya zaka yi masa ka tabbatar da cewa ba cikin nutsuwa walwala da


kwanciyar hankali yake ba,tunda ya diro qasar bayan kira da ya samu na gaggawa daga
hajiya khaulat kwana ashirin da tafiyar su'ad din bai sake samun isashen bacci ba
cikin nutsuwa,me ya sameta haka har ta fice hayyacinta bata gane kowa?,me ya kawota
asibiti cikin wani gari wanda ba nasu ba bayan gidansu suka yi da shi zata je?,me
ya sameta haka meye dalili?,babban abinda ya daga masa hankali shine doctor
james,wanda a cewar hajiya khaulat shike duba su'ad,tare sukayi karatu da
shi,dalibi me cikin jami'ar da yayi karatu,ajinsu daya course dinsu daya,hasalima
yana daya daga cikin mutaben da basa shiri sam,saboda aqidarsa ta qin jinin
musulunci da musulmai,uwa uwa yana matuqar adawa da qoqarin da almustapha ke da
shi,yana daga cikin gungun dalibai 'yan adawarshi,kusan ma shine shugaba,jamea
baida kirki ko kadan,bai da tausayi kuma bashi da imani,dalilin wai laifi da suka
aikata shi ya sanya aka koreshi yana shekarar warshe a makarantar,saidai sunji
labarin ya sauya qasa ya qarashe karatunshi har ma ya bude asibiti,tunda yaje basu
hadu da james ba,duk sanda zaije asibitin suna sabani ne,randa suka hadu ya jima
yana kallon almustapha,irin kallon da ya sake sanya shakku cikin zuciyar
almustapha,bugu da qari daya buqaci bayani kan meye damuwar su'ad bayanin da yayi
masa sam bai gamsheshi ba hakan ya sanya ya quduri shiga aikin da kanshi a
matsayinsa na likita.

       A ranar yayi waya da wani farar fata abokinsa,wanda yake da asibiti shima
hafin gwiwa da gwamnati,almustaphan ya sanya aka hada masa daki guda da dukkan
abinda yake buqata,wanda a yau ya shirya yin bincike a kanta.
      Kaman ko yaushe tana kwance iskar oxcygen na taimakawa numfashinta,yayin da
hajiya khaulat ke gefe cikin fita hayyaci,tunda take bata taba fuskantar tashin
hankali tsahon rayuwarta ba irin wannan karon,idanuna sun yi luhu luhu,tayi kuka
har ta gaji,batasan wanne irin aiki ne haka doctor james ya yiwa diyar tata qwaya
daya tilo ba wanda ya sanyata shiga wannan matsanancin halin,sanda taga almustapha
ya shigo dakin jikinta har rawa yake,kwarjini yake mata sosai irin wanda ada can
baya baiyi mata ba,a mutunce ya gaidata yana maida kallonshi ga su'ad tare da
tambayarta jikin nata,ba amsa sai kuka data sanya,ranshi a jagule yake qwarai,ya
qagu ya duba abinda ke faruwa,shigowar ma'aikatan jinyar ya katse duk abinda haj
khaulat din keson gaya masa,sai data ga suna daukar su'ad daga gadon da take zuwa
wanda suka shigo da shi mai taya da alama zasu fita da ita ne sannan ra magantu
cikin rawar baki
"Mustapha...ina..ina zaku da ita"
"Zanje nayi nawa binciken ne,saboda bayanin da james yayimin bai gamsheni
ba,nasanshi ya sanni tun ba yau ba" ya fada yana ciro wayoyinshi ya ajjiye gefe
guda,ita dinma tana shanshano wani abu,din bata yarda da cewa aikin da suka buqata
din kadai yayi mata ba
"Amma yau professor da alhaji zasu iso,inaga a bari su iso din ko?"
"Ina so kafin suzo din in san amsar da zan basu kan me ya sameta,tunda ku da kuke
tare sanda abun ya sameta baku san meye sababi ba" ya fadi haka sanda yake takawa
ya fice yana bin bayan masu turatan.

      Sanda ya haska fitilar nan mai tsananin haske abu na farko da idanunahi suka
fara masa karo da shi hudar dake qasan cibiyarta da kuma wadda ke gefan hannun
hagunta,saidai daya ta warke daya kuma danya ce,gabanshi yayi mummunan
faduwa,addu'a yake Allah kada ya tabbatar da abinda yake tsammani,a hankali cikim
qwarewa da hikima ya jona duk wata cumputer da yake da buqata wadda zata taimakawa
bincikensa cikin sauqi ya soma aikinsa cikin lura da taka tsantsan.

       Cikin awa guda qwaqwalwarsa ta soma yamutsewa,ba abinda yake ambata sai
innalillahi wa inna ilaihi raji'un,gumi ya hada sharkaf,sai ya saki duk abinda yake
ya koma saman kujera ya zauna,nanya manyan lamura biyu kowanne yana sukuwa cikin
qwaqwalwarsa,kowanne buqata yake ya soma sarrafashi,su'ad babu mahaifa tattare da
ita?,babu qodarta ta hannu hagu an illata mata ta dama?,duka aikin waye
wannan?,aikin waye?,ta shiga nanatawa kanshi tambayar,cikin wasu qalilan sakanni
idanunshi suka kada suka koma jazur,ya dinga fidda huci kaman kumurcin maciji,wani
bala'in tausayin su'ad din ya mamayeshi,me ta yiwa wani har ya mata haka?,waye ya
aikata mata haka?"
"Zai wuce doctor james" wami bangare na zuciyarshi ya bashi amsa,a fusace ya miqe
cikin tsananin fushi
"To amma me ya hadasu da shi?,me ya kawosu wajenshi?" Cak ya tsaya sanda wani sashe
na zuciyarshi ya jefo masa wannan tambayar,a hankali ya koma ya zauna yana kiran
sunayen Allah dafe da kanshi.

      Ya jima kafin ya samu ya yiwa kansa control,tabbas sai ya saka nutsuwa indai
yana son komai ya dai daita,a hankali kaman wanda aka yiwa dukan tsiya ya miqe ya
hada mata qarin ruwa ya zuba magungunan da yasan zasu taimaka mata sannan ya sanya
ma'aikatan suka maidata dakinta,kai tsaye ya fice daga asibitin shida drivansa.

        Bai koma gida ba sai daya samu dukkan bayanan da yake so cikin kwana daya
tal,abinda yaji kan doctor james yayi matuqar girgizashi,saidai ya hada dukkan wasu
hujjoji da bayanai waje daya,banu nutsuwa ko ta qwayar zarra tattare da shi haka
yayi wanka ya sauya kaya,yana ganin tarin misscal na sumayya da saqonni saidai ya
kasa karantawa ko yabi kiran haka ya sake ficewa.

       "Kiyi haquri ki kwantar da hankalinki kada ki jawo mana ya gane abinda ake
ciki,in sha Allahu Allah zai baki lafiya" kai ta girgiza
"Ki qyaleni mummy,ki barni,kinsan me likitan ya aikata a gareni?,almustapha akwai
nakeson gani,na tabbbatar da cewa rayuwata tazo qarshe kuma wuta zanje bayan na
mutu" ta fada kuka na qwace mata,dai dai sanda almustapha ya turo qofar,ajiyar
zuciya ya saki sanda ya ganta idanunta biyu,har ma sun cire mata oxcygyn din dake
hancinta,idanunta a kanshi har ya shigo,ya qarasa gaban gadon mummyn ta janye baya
gabanta na dukan uku uku,hannunshi su'ad din ta kama ta riqe qam tare da sakin kuka
"Shshshs....ya isa,ki daina kuka a irin wannan yanayin" ya fada yana shafa kanta
cikin tausasawa
"Qyaleni almustapha nayi kuka,kasan me na aikata maka?,kasan me nayi maka?"kai yake
kadawa bacin ranshi na sake tasowa yana qoqarin dannewa
"bance ki gaya min ba,ni kuka kawai nace ki bari" zata sake magana kenan aka turo
qofar dakin aka shigo,baba professor ne sai alhj abdus samad mahaifinta da kuma
ummee,daga baya sumayya ke biye da su da 'yan biyu wanda sam bai tunanin zuwanta
ba,duba daya ta masa taga rama sosai tattare da shi,yayin data dubi su'ad kuma sai
hankali ta ya tashi matuqa,cikin mutuwar jiki ta qaraso ciki,haj khaulat ce ta miqe
tana musu sannu da zuwa suka amsa suna samun wajen zama,banda alhj abdus samad da
ya qarasa gadon da su'ad ke kwance,sannu yayi mata saidai shiru tayi taqi amsa
masa,sunyi tunanin ko zafin ciwo ne,baba prof ne ya sake mata sannu ba tare da
tunanin zata amsa ba,ga mamakinsu sai ta waiwayo,ta daga hannunta ta yafici
baban,cikin mamaki ya miqe,ya isa gefan alhj abdus samad ya tsaya
"Baaba,idan mutum ya haihu haka rayuwa take ka qyale yaronaka yayita abinda ransa
yake so?,kaman ba haka bane,saboda naga yadda wasu masu yaran suke hana yaransu
abinda ransu yake so,amma kaman zalunci ne hakan nake tunani a da,sai yanzu da
lokaci ya quremin nake shanshano akwai dalili" kowa yayi mamakin maganar tata,amma
sai baba ya gyara zama
"Ba d'a ba ko babba daya girma yana buqatar wanda zai dinga masa burki yana
saitashi kan hanya,ya hanashi ba dai dai ba ya sashi dai dai" kai take gyadawa
cikin gamsuwa
"Kaman yadda ka so ka nunamin a baya nace maka bana so kada ka sakemin haka?" Idanu
suka hada da alhj abdus samad,bashi da zabi illa yace mata eh
"To wannan meye?"
"Gata ne kakewa rayuwar yaro" dubanta ta maida kan alhj abdus samad
"Wannan ne mahaifina amma baimin haka ba,bai taba tsayawa ya damu da halin da
rayuwata ke ciki ba,bai taba zama ya tsawatar min ba,bai tana tsayawa ba bare yaga
nayi dai dai ko na kuskure ba,ko yaushe kasuwancinsa ne gaba da komai,kanje gida na
qaraci zamana ba tare daya sani ba...."
"Su'ad,wai me kike fada haka?" Haj khaukat ta tasi tana fada,saboda kada ta kwance
musu zani a akasuwa,sosai idanuta suka firfito tana duban hajiyan
"Kada kice komai,inaga qwara shima a kanki,tunda tare yake barinmu ni da ke,duk
abinda nace ina so komai girmanshi baki taba cemin a'ah ba,kince talaka ba mutum
bane,talaka abun qyama ne na yarda hakanne,naga dabi'u masu yawa a wajenki na doru
akai,wanda hakan ya sanya nake ganin namu dabi'un ne kawai daidai,dau tari zanga
wasu dabi'um da suka burgeni,amma da zarar nayi niyyar aiwatarwa sai tarbiyyarki ta
rinjayi tunani na na watsar,duk abinda nayi dai dai ne,sam baki taka rawarki ta uwa
ba,ne zance dake momy?,cikin rashin sani kika dorani kan wannan hanyar ko kinsan ba
dai dai bace kika nakasta rayuwata kika dorani?" Shiru ya ratsa dakin,kusan kowa
jikinsa yayi sanyi qalau,sumayya tuni ta soma qwalla cikin mayafinta,wani abu take
ji yana ratsata,tausayi ne,ita din shaida ce kan su'ad wata iriyar hargitsatsiyar
rayuwa take
"Baba...." Ta kira sunanshi tana kallonshi,sai ya amsa yana sake nuna kulawarshi a
gareta
"Ina jin ciwo cikin jikina,ina ji sama sama sanda doctor james ke cinikin
qodata,ina jinsa,amma bansan me zan karanta ba wanda zai qwaceni daga sharrinsa,tun
yana dariya yana gayamin bansan cewa babu amana tsakanin bayahude da musulmi
ba?,bansan cewa basa sonmu nasa qaunarmu ba?,bansan cewa ba zasu taba taimakawa
musulmi a banza ba ba tare da wata boyayyiyar manufarsu qasan ransu ba,yace har
abada....baba.....magana ta qarshe ta kunne na yaji yace min,wani abokin karatunsa
musulmi yaji yana gayawa 'yan uwansa cikin littafinmu Allahn mu yace "yahudu da
nasara ba zasu taba yarda da kai ba har sai kabi addininsu"(wannan haka yake aya ce
da tazo cikin alqur'ani mai girma,babu yadda babu amana tsakanin musulmi da
bayahude matuqar ba addininsu kabi ba,saidai su nuna maka a baka kawai amma sam
zuciyarsu ba haka take ba,kuma har yau muna kan wannan qadamin saidai mun kasa
fahinta,bama kuna ganewa din har sai sun amana illa sannan zamu zo muna kaico,Allah
kasa mu dace),wannan ne lafazin qarshe da yayi min" sai ta saki kuka cikin wahala
yayin da sautin kukan sumayya ya fito,qirjinta ya dinga wani bugawa,tsoro ya
kamata,lamarin har yayi girman haka?,rabata da qodarta?,sannan ta juya tana duban
almustapha da ya kasa motsawa,ya dunqule hannayenshi cikin aljihunsa ya
zubasu,idanunsa sun kada jajur
"Zo don Allah....zo" tace da shi,da qyar ya iya takawa zuwa inda take,hannunshi ta
kama
"Da fari dukanmu munyi kuskuren zamantakewa ni da kai,saidai nawa kuskuren yafi
naka,tunda har ka rigani gane kuskuren,ka kuma yi qoqarin maidoni hanya amma na
bijire,tun kafin nan,naqi mu'amala da matan abokanka,naqi mu'amala da yarena
addinina 'yan asalin qasar iyayena bare na gane kuskurena ta silar zamana da su na
gyara,gani nake tunda arziqinsu bai kai na mijina ba basu isa ba,ba komai bane
su,ban ganin su da gashi,kamin rarrashi a boye wanda daga ni saikai sai Allah muka
sani naqi,kazo kamin na fili amma naqi,ban manta lafazin da ka yimin tafiyata ta
qarshe wanda daga ita sai sabon aurenka KADA KI ZARGENI NAN GABA....kaci gaba da
yimin qoqari naci gaba da sanya qafa ina shurewa,bayan babu abinda ka daukemin na
game da haqqina harda wanda bai zama dole a kanka ba,baka fasa adalci tsakaninmu
ba,hakanan duk wanda zaiyi ba daidai ba tsakaninmu zaka tsawatar masa,zata daumi
nata laifin ta bada haquri ina kallo,amma nikam....sam sam...gani nake nafi qarfin
juyawar namiji,nafi qarfin a zaunar da ni ana min fada,na dauka cewa namiji da mace
duka dai dai suke......"
"Silence please su'ad" ya fada yana qoqarin tsaidata,dukka wannan ba shine gabanshi
ba,plan dinsa ta yadda zai samo doctor james,murmushi ta saki
"Ka barni na fada na roqi yafiya mana,nasanka farin sani,nasan tunaninka a yanzu
kawai na yadda zaka dauki fansa kan james don tunda mommy ta gayan kamin gwaje
gwaje ina da tabbacin kaga abubuwan da na rasa a halitta ta,na rasa qodojina na
kuma rasa mahaifata"
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" dukkan wanda ke dakin ya furta cikin tsakanin
kaduwa,banda momy wadda ta zube a qasa ba tare data shirya ba,duk da cewa furuci
daya ne yake sabo a wajenta
"Eh....doctor james shi ya saida min qoda ga wani mutumi,amma mahaifa ni da kaina
na kai kaina aka cire min ita" rintse idanunsa almustapha yayi
"Hasbunallahu wani'imal wakil" ya dinga furtawa can qasan ranshi,bakinshi ne kadai
ke motsawa
"Nayi tunanin cewa haihuwa bata da wata rana matuqar kana da kudi,na dauka abu mai
kyau nayi tunda mommy ta juya tata mahaifar,almustapha,idan kaso ka yafemin idan
kuma ba zaka iya ba duk daya nasan idan na mutu wuta zan tafi,amma dai ina roqonka
ka yafemin" ta fada tana zubda qwalla,rasa me zaice yayi?,a wacce duniya yake
ciki?,hannunta ne kawai riqe cikin nashi,hango sumayya tayi dake sharar qwalla
"Zo...zo kema" sautin kukanta ne ya dadu,firgici da tsoro na cikata,wacce iriyar
duniya ce wannan muke ciki?,da qyar ta iya tashi a daddafe ta isa gaban gadon itama
saitin kanta
"Duk naga abubuwan da kike a zamanki da almustapha,wanda a sannan wani abu ya kange
zuciyata na kasa ganin kyawun hakan bare nayi koyi,wanda ina da tabbacin ko nice
shi a wannan bigiren dole na soki,a baya laifinsa nake gani,amma a yanzu na
tabbatar da cewa baida laifi ko kadan,banfa san kwanansa da tashinsa ba,bansan
cinsa da shansa ba,bansan me yakeso da wanda ke qona ranshi ba,duka ba ruwana,kawai
ya jiqani da kudi ya bani freedom shikenan,girki kadai nasan na taba yi masa wanda
zai iya dan shiga sahun nuna kyautatawa bayan shi din tunda muke da shi ban taba
nema na rasa ba wajensa,koda zan jera wata ina tambaya,don me ya samu mai masa
dukka irin wannan kulawa hakan zai kasa sonta?,ki yafemi kema duk da ba lallai
yafiyar taki ta amfane ni ba" kuka ta saka sosai,tana jin su'ad kamar 'yar uwarta,a
iya zamanta da ita banda furuci ko kallo bata taba wani abu na cutarwa a gareta
koma bayan wannan ba,akan me zata riqeta?,meye zainab karima da a'iza basuyi mata
ba?,tamkar zata shide ta furta
"Ki daina fadin haka,ki daina yanke qauna daga rahamar Allah,kowanne bawa da kalar
qaddarashi,bakisan rayuwar da nayi ba abaya wanda ban taba tunanin a yanzu zanyi
rayuwa irin wannan ba,ki godewa Allah daya sanya kika gane kuskuren naki,duk wanda
kuma ya yafe maka ta karbu har a wajen Allah,nikam bakiyimin komai ba,ba abinda
kika yimin,na yafemiki ina roqon Allah ya baki lafiya,ki yafemin nima idan na taba
bata miki koda da mugun kallo ne" murmushi ta saka
"Kina da zuciya mai kyau wanda na tabbatar da kece na ganki cikin ciwo irin haka ba
lallai na tausaya miki har nayi miki kuka haka ba,baki taba yimin komai ba saboda
ko yaushe kina takatsantsan da hakan,koda kin yimin ma ya wuce har bada.....ki riqe
almustapha da kyau wallahi kun dace....ya hada duk wani hali mai kyau amma rashin
samun tarbiyya ta gari daga iyaye na gari ya janyo min na kasa riqeshi har na mori
rayuwa mai inganci....ki kawo min 'yan biyu na sake ganinsu,na tabbatar da ace na
zauna nayi rayuwa mai kyau da tuni ni haifesu....ummi" ta kira ummi dake gefe,itana
qarasowa tayi
"Duk cikin yaranki kinfison almustapha,amma kika yi haquri kika zuba min ido ina
yiwa rayuwarshi yadda naga dama,kinso nunan hanya kaman yadda baba yayi amma na
taka miki birki,a ranan na miki rashin kunya gatse gatse wanda ina da yaqinim baki
gayawa kowa ba sai yanzu dani na fada,kiyi haquri ki yafemin ummi,ki nema min
gafara wajen duk wanda na taba batawa" itama ummin share qwalla take,tana ajjiye
mata ummulkhir da ummu kulsun gefanta tana dubansu su'ad din
"Ba wanda baya kuskure cikin rayuwarshi su'ad,ma'aiki yana cewa tabbas ba don kuna
ainata zunubi ba da tuni Allah ya tafiyar daku ya halicci wadansu,kuskure siffa ce
ta dan adam saidai mafi alkhairinsu sune masu tuba,na yafe miki har abada,Allah ya
tashi kafadarki don ya ara miki daman a nan gaba"
"Na gode ummi" ta fada tana shafa kansu ummulkhair a hankali ta furta
"I love you my kids"ta fada tana jin qaunar kyawawan yaran har cikin zuciyarta.

       Alhj abdus samad dake dafe da kanshi wanda tuni hawaye suka wanke fuskarshi
sharkaf ya matso ya kama hannunta bayan ummi ta debe yaran ya soma neman
gafararta,ya tabbatarwa da kanshi cewa ba shakka yayi babban kuskure na sakaci da
sanya ido a rayuwar da iyalinahi keyi a matsayinsa na uba,wanda yake mai kiwo ne
za'a tambayeshi a kan abinda aka bashi kiwo
"na yafe maka daddy...amma ko nan gaba Allah ya azurtaka da wasu yaran ka kula da
su,na tabbatara addininmu yana da tsari wajen bawa yaro tarbiyya kabi wannan
tsarin,ina da yaqinim shi kadai ne ingantaccen tsari" hawayenshi ya dinga sharewa
yana jera mata addu'a suna amsawa,wanda yana gamawa ya miqe ya fice,wata nadama na
shigarsa,shi kansa sai a yanzu ya farga,meye amfanin dukiyar da yake yunqurin
tarawa wadda ta hanashi tsayawa ya duba gidanshi da rayuwar da suke kai?,qememe
su'ad din taqi yarda ta kalli mummyn ko tayi magana da ita,so take kawai ta ganta
bata dakin,kaman wasa abun amma sai gashi ta birkice da gaske,tilas mummyn ta fita
hannunta saman ka tana kuka.

      Ranar baki daya sumayya ta dinga kula da su'ad din,sosai su'ad din taji
dadj,don addu'o'i ta dinga tofa mata wajen da tace yana mata ciwo,duk inda ta mata
addu'ar kuwa sai taji ya lafa sai kuma idan ya sake tasowa,qarfe shida na yamma
almustapha yace su wauce masauki ya kaisu,qi sumayyan tayi tace a barta a nan,ummi
tace bazai yiwu ba ga yara,duka duka kwansu talatin ko arba'in bata cika ba,duk da
nauyin ummin da take ji amma hakan bai hanata sake roqarta ba,baba ne ya sanya baki
su barta din,tunda dakin baida maraba da gida ba wata matsala bace,fuskar su'ad
kawai zaka kalla kasan taji dadin hakan,sai ta saki murmushi,ranan kusan kwanan
zaune sukai da su'ad din,tuni 'yan biyu sukayi barci,itakam tana zaune,tayi sallah
ta zauna ta huta,duk motsin su'ad din tana ankare da shi,itama su'ad din idanunta
na kan sumayya,sai yanayin nata ya dinga burgeta,sam batasan da wannan rayuwar ta
yawan yin sallah ba,banda ma almustapha ya tsaya kanta a tsaye sallar ma ta farilla
ojoro take mata,sai daga bisani ya sanyata ta gyara da qyar
"Zanso nima inyi sallahr nan haka,akwai lada ko?" Murmushi sumayya ta saki,tana jin
tausayinta har cikin zuciyarta,kana kallonta kasan gagarumin ciwo ke cin jikinta,a
haka ma akwai kulawa kenan
"Akwai lada mai tarin yawa,sallah tana kusantar da bawa zuwa ga ubangijinsa" kai ta
kada
"To ya za'ayi ina son nayi nima,king tun isha'i ban sake ba"miqewa tayi ta iso
gareta saboda ganin tana yunqurin gyara hannunta,a tausashe ta gyara mata tana cewa
"ba lallai sai sallah ba kadai zata kawo miki lada,ko jinya ma idan kanayi ai
kankarar zunubi ce,idan kina so kina iyayin istigfari salatin annabi da sauransu
kina daga kwance"
"Ok,kaman yaya?" Koya mata tayi,ta kama ta dinga yi,a hankali ta dinga jin sanyi da
sauqi cikin jikinta da zuciyarta,ta dinga satar kallon sumayya sanda take shayar da
ummulkhair tana sha'awar rayuwarta,ashe rayuwa mai dadi nutstsiyar rayuwa itace
rayuwar da addinin musulunci ya tanada ya kuma koya mana?,lallai iyayenta sun yiwa
rayuwarta babban gibi.

       Sanda almustapha ya kawosu da safe sannan ummi tace ya dauketa ya kaita gida
ta huta anjima sai ta dawo,ba musu ta amsa,kowa yaji dadin yadda yaga salama
tattare da su'ad din,suna tafe cikin mota shiru,yana dauke da amatullah wadda ke
barci yana wasa ya hannunta,yayi kewar yaran sosai,sai yaga kaman an qara musu
girma da wani wayo,sosai kamanninsu ke fitowa da shi,zuciyarshi a cunkushe take
matuqa,babban abinda ke gabanshi yanzu yadda zai cimma doctor james,duk da alhj
abdus samad yace ya qyaleshi kaman yadda su'ad din tace ita ta jawa kanta,duk
abinda mutum yayi kanshi,saidai sam zuciyarshi bata nutsu da haka ba,har suka isa
dakin daya kama musu a hotel din wamda babban falo ne da dakuna uku a ciki baice
komai ba,ya kwantar mata da yaran sannan ya miqe suka hada idanu,duk itama sai take
jinta ba dadi
"Ki wanka ga abinci can,ina zuwa" ya fada yana juyawa,binsa tayi da kallo kawai
tana kada kai,baki dayansu sun zama abun tausayi cikin qaramin lokaci har ita din.

       Cikin kwana goma sha hudu sumayya ke kwana da su'ad din,zama suke cikin
asibitin tamkar ya da qanwa,a nan ta koyawa su'ad din wasu abubuwan da take ganin
ya kamata ace ta sani,sukan zauna suyi hira sosai da ita cikim sakewa kaman sun
jima da soma mu'amala,jikin su'ad din da sauqi sosai,har takan iya zama sumayyan ta
jinginata,ita ke gyara mata jikinta,ta bata abinci,ta daura mata alwala idan
lokacin sallah yayi,tana yawan sanya sumayya ta jera mata amatullah da amatur
rahman tayi ta magana da su kaman wasu manya
"Ki musu tarbiyya irin taki don Allah" hakan su'ad ke yawaita fada,murmushi sumayya
keyi tace
"Tare zamuyi musu har ke,kema mamarsu ce"
"Zanso hakan" abinda takan fadi kenan wanda sumayyan ta kasa gane me hakan yake
nufi.

Hatta almustapha yaga sauyi qwarai wajenta,da ya shigo takan gaidashi ko


tayi masa sannu da zuwa,abinda bai taba gani ba,hakan ya masa dadi qwarai ua
faranta masa,yakan zauna cikinsu ya bada wasu mintuna suyi hira su duka,duk da bai
zama waje daya,ba wanda yasan inda yake zuwa daga shi sai Allahnshi,idan dare yayi
yazo ya musu sallama shikenan sai gobe da safe.

       Wani dare bayan kowa ya tafi ya barsu,yan biyu na saman gado cikin neat suna
bacci su'ad ta kalli sumayya
"Wai baki kewar maan,naga ko sau daya baki taba binshi ba" murmushi ta saki
"Kin manta jinyarki nake,ladan kuma da ake samu wajen yin jinyar mara lafiya ba
kadan bane" kai take gayadawa cikin gamsuwa,duk wani furuci da sumayyan zatayi
akwai qaruwa a cikinsa
"Wai nikam rannan kaman naji kina min magana kan rayuwarki,bani labari mana?"
Dariya ta saki tana kallonta
"Kina son ji ne?" Kai ta kada
"Eh idan babu takura,don na tabbatar zan samu wani darasi a ciki"
"To qara kunne biyu" dariya ta saka
"Na qara" a nutse sumayya ta warwarewa su'ad labarinta,gyada kai kawai take,jikinta
yayi matuqar yin sanyi qwarai,wato akwai mutane shigenta ko irinta da yawa a duniya
"Gaskiya rayuwarki baki daya darasi ce,ke din ta daban ce" ta fada tana jinjinawa
yadda sumayyan ta fuskanci rayuwa haka,gyaran murya sumayya tayi wanda ya janyo
hankalin su'ad daga duniyar tunanin data tafi
"Nikam in roqi wata alfarma mana wajenki"murmushi tahi,ki roqa ko mene idan baifi
qarfina ba
" so nake ki yafewa mommy,kada ki manta uwa uwa ce komai lalacewarta,na tabbatar
soyayyar da take miki ce ta kaita ga kasa tasawatarwa da tsayawa kai da fata wajen
ganin ta hanaki aikata abinda kike so matuqar ba dai dai bane,ta kuma doraki kan
dai dai din,ba zaka taba iya biyansu abinda suka yi maka ba har abada"murmushi ta
saki ta kamo hannun sumayya
"Mummy,ina son mummy sumayya,saidai yadda ta tarwatsa rayuwata ta kasa gyarata tana
qona min rai a duk sanda na tuna hakan,na jima da yafe mata sumayya,na mata haka ne
ko don gaba,duk da cewa ko a yau na tafi na barta ba zata sake samun wasu yaran
ba,amma wannan ya isheta izinar da zata bawa 'yan baya labari"kai ta kada
"naji,amma gobe ki furta mata cewa kin yafe mata,ki daina gudun ganinta don Allah"
murmushi ta saka sumayya na sake shiga zuciyarta
"Naji in sha Allah zanyi,nasan tunda kika dage kan maganar kika gyaramin babu kyau
abinda nake,zanso ace zan haihu da na sakawa 'yata sunanki" ta fada wani abu na
taba zuciyarta,hawaye ya sauko saman fuskarta,goge mata sumayyan tayi tana cewa
"Ki daina kuka,ki godewa Allah da lafiyar da kike samu"
"Na gode" ta ce da sumayya
"Ba abun gode min,haqqina ne dama na kula dake din koba komai miji daya fa muke"
murmushi suka sakarwa juna,ranar sunyi hira sosai da su'ad din har take gaya mata
"Naga amira na sonki,da fari haka nima ta soni,halina yasa ta gujeni,ki tayani bata
haquri don na mata ba dai dai ba da yawa wanda yasa ta daina hulda da ni"
"Amira bata da riqo,kuma ke matar yayanta ce,na tabbatar komai ya wuce a
wajenta,don kullum sai ta kirani ta tambayeni jikinki,abinda ya hanata tace na baki
duk sanda ta kira kina bacci,ni kuma banson tada ke" murmushi ta saki don maganar
ta mata dadi,sai da suka raba dare sosai sannan sumayya ta daura alwala ta tada
sallah,ta baiwa su'ad carbi ita kuma taci gaba da azkar,sanda ta idar ta waiwaya
sai taga carbin ya fadi hannun su'ad din,idanunta alumshe alamun bacci yayi awon
gaba da ita.

*Bayan awanni uku*

Zaune take kawai a gabanta ta zuba mata ido tamkar mutum mutumi,sam kukan da
yaran ke tsalawa bai shiga kunnuwanta bare tayi yunqurin daukarsu,dubanta kawai
take lokavi bayan lokaci tana kiran sunanta,saidai babu wani alami dake nuna motsa
bare ta amsa,tun kan ya qaraso dakin yake jiyo kukan yaran,hakan ya sanya ya qara
sauri cikin hanzari ya isa qofar dakin ya bude ya tura,a kansu su biyun idanunsa
suka sauka,sai ya sauya akalar tafiyar tasa daga wajen 'yan biyun zuwa inda su
sumayyan ke zaune,kallo daya ya yiwa su'ad dake kwance gabanshi yayi mummunar
faduwa,tamkar wanda aka bigewa gwiwoyinshi ya qarasa bakin gadon ya duba hannyenta
zuwa saitin zuciyarta inda take aiki,abinda yaji ya tabbatar masa da cewa babu rai
jikin su'ad din,duk da haka zuciyarshi ta kasa gasgata masa,take ya hautsina kayan
aikin dake dakin,ya dinga gwaje gwaje,wanda yana tsaka da aikin abokinsa mai
asibitin ya shigo dakin da niyyar duba mara lafiyan,kallo daya ya mata ya tabbatar
ta mutu,hakan ya sanyashi janye almustaphan cikin harshensa na turanci yace
"Kayi haquri,ta rigamu gidan gaskiya man,Allah ya jiqanta" tuni sumayya ta qarasa
rushewa da kukan dake cinta,suka hadu ita amatullah da amatur rahman suka gauraye
dakin,baya almustapha yayi ya jingina da bangi yana furta innalillahi wa inna
ilaihi raji'un.

*bayan awa daya*

Dukkansu suna zaune a babban falon dake asibitin wanda na likitan ne ya basu
su zauna,kowanne ka dubi fuskarsa cikin baqinciki take,hatta da mazan dauriya kawai
suke,saidai almustapha bai iya daurewar ba,karon farko da suka soma ganin hawaye
kan fuskarshi,abinda basu taba gani ba tsahon rayuwarshi da su,ummi ma hawaye take
sharewa lokaci zuwa lokaci,yayin da sumayya ke kuka tuburan,idanunta da fuskarta
gaba daya sun kumbura,yayin da fuskar ta hadu tayi jazur,ummi dake gefanta ita ke
lallabata ta bawa yaran nono,tana shayar da su cikin hijabin tana kuka,ba shakka
mutuwa kota wanda baka sami bane tana da ratsa jiki da sanya wani sabon imani a
zuciyar dan adam,ballantana wadda ta sani sun zauna tare tsahon shekara nesa da
juna,gab da zata tafin kuma sukayi zama irin na yaya da qanwa,yaushe zata manta
haka?,haka mutuwa take,takan dauke mutum a sanda bai shirya ba hakanan masoyansa
basuyi sallama da shi ba,sai mutuwar mukhtar ta fado mata,kukanta ya sake
daduwa,wanda hakan ya sake karya zuciyar duka sauran,ba shakka sunga irin zaman da
sukayi a tsakaninsu cikin sati uku kacal kafin ta mutu,haka suka dinga bata baki
kafin su fara tattauna abinda ya zaunar da su din bayan an kai gawar su'ad
mutuware.

Alhj abdus samad ne ya fara magana


"Zamu wuce nigeria da gawarta,bama gawarta ba har maman tata ma"
"Amma alhj kaji fa sunce ita khaulat ta samu stroke,haka zamu tafi da ita" cikin
tsantsar baqinciki yana goge qwallarsa yace
"Daga rana irin ta yau professor na bar zaman qasar nan har abada,zamu koma qasarmu
ta gado da zama,babu abinda na tsinta a zaman qasar nan banda baqinciki da
tarwatsewar iyalina tunda har na kasa control dinsu,kowa yana vin gashin
kanshi,Allah ya jiqanki su'adah ya gafarta miki" ya qarasa fada yana shafe sabbin
hawayen da suka zubo masa da tafin hannunshi
"Hakan yayi,a mata suttura cikin dakin mijinta" inji ummi,da wannan shawarar suka
soma neman izinin tafiya da gawar su'ad,cikin kwana biyu rak suka samu kasancewar
abun na masu da shi ne.

Cikin dakinta dake abuja aka mata wanka aka shiryata,almustapha na tsugunne
gaban gawarta yana mata addu'a,sosai yayi mata addu'a tare da jaddada yafiyarshi a
gareta,sannan ya bawa sumayya guri,alhj abdus samad da duk wani makusancinta,inda
aka turo mommy a keke,kuka ta saka ta soma magana,saidai maganar bata fita ba'a jin
abinda take fada,sakamakon bakinta daya karkace tun faduwar data yi sanda tayi ido
hudu da gawar sy'ad tana ihu tana ita daya ta mallaka ya zata yi mata haka,daga nan
ta sume,bayan ta farfado kuma ta gamu da wannan cutar,sosai sumayya ta qunshe kanta
a tsakanin qafafunta tana sakin kuka sanda aka dauki gawarta aka fice da ita zuwa
gidanta na gaskiya,tabbas duk wanda yayi damara don duniya ya kwanceta,Allah ya
bamu sa'ar tafiya,kasa mu riskeka sanda kake farinciki da mu ya Allah.

A nan gidan dake abuja suka zauna karbar makoki,kaf 'yan uwan sumayyan ba
wanda baizo mata ba,haka yan uwa da abokan ariziqi suka dinga zirya,har eesha ba'a
barta a baya ba,tazo jikinta cikin matuqat sanyi,tana tuna yadda suke takun saqa da
su'ad din,tana tuna yadda su'ad ta dauki rayuwarta kusan dai dai da yadda itama
take jin kanta,hakan ya qara mata mutuwar jiki,sai data dangana da sumayya tayi
mata gaisuwa,sannan ta roqi gafararta kan abinda ta nata a baya,murmushi kawai
tayi,mutuwa kadai ta ishi mai hankali aya,me ya mata zafi da zata tsaya saka wani
mutum a ranta,itakam mantawa ma take da faruwar abin sai idan wani abu ya taso da
zai tuna mata da hakan,tace ya wuce har abada,'yan biyu sun jima hannunta,sosai
yaran suka shiga ranta,bul bul da su cikin tsafta gwanin sha'awa,duk da mamarsu na
cikin alhini amma fes suke,don ummi ke sawa baba uwani ke kula da su akai akai,ba'a
maidasu wajen sumayyan sai sun buqaci nono.

Kwanaki bakwai akayi kaman yadda al'ada tace kowa ya watse,aka fidda duk wani
abu na su'ad din aka miqawa iyayenta,don almustapha cewa yayi ya yafe,bazai iya
amsar komai nata ba,ranan mummy khaukat tayi kukan da bata taba makamancinsa
ba,tayi nadamat da bata taba tsammanin akwai kamarta ba,ta dinga kallon sumayya
tana son gode mata amma babu baki,iya jinyar su'ad kawai zuwa mutuwar nan ta
karanci irin kyakkyawar zuciyar da take da ita,da hannu ta dinga mata godiya haka
aka turata kan keken guragu suka fice a gidan.

Washegari kwana takwas kenan almustapha ya taddata tana gyara dakinta,ita


daya ce su amatullah suna wajen ummi,duban junansu suke kowa na kallon irin
sauyawar da dan'uwanshi yayi,shaida mata yayi zai koma america,amma baya so ta
gayawa kowa can ya tafi,din su dubai yace zai koma,fatan alkhairi ta masa don ta
fahimci me zai komar da shi din,itama tana goyon bayanshi,bai kamata mutane irin
doctor james ace sun kubuta ba haka nan akwai.

Qasa ce da bangarorinta suke da wariyar launin fata da qyama ga


musulmai,amma hakan ko kadan bai karya masa gwiwa ba,bai wani tuna cewa shi din
baqo bane,ya dan sha wuya amma bai haqura ba sai da ya tabbatar an kamo doctor
james an yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya,sannan an qwace duk wani license
nashi tare da rushe asibitin da ya gina,wanda hakan ya dauki almustaphan tsahon
watanni biyar,bai waiwayi gida ba sai bayan wadan nan watanni,satin guda da
kammaluwar lamarin,da wani yammaci wanda a wannan lokacin sumayyan na kwance,bata
taba jinta cikin matsi da takura irin na wannan lokacin ba,rashin ganin almustapha
har tsahon watanni biyar bata zaci ma zata iya jureshi ba,a kusan kullum sai taci
karo da saqonshi ta email dinta na ban haquri da alqawarin dawowarshi nan kusa,bata
da amsa face Allah ya bada sa'a,ta tsawaita haqurinta qwarai da gaske,saidai har
zuwa yau shiru kake ji,duk sanda ummi ko professor sukayi qorafi,takan nuna ita ta
bashi dama babu komai yana gab da dawowa.

Qarar wayarta ita ta dawo da ita daga tunanin da take,ta miqa hannu ta daga
ta kara a kunnenta ba tare data damu da duba mai kiran ba
"Assalamu alaikum warahmatullah" muryar nan mai daraja da qima a wajenta,muryar nan
da take bawa girma,muryar nan da babu tamkarta ita ta ratsa dodon kunnenta,tamkar
an cire duk wata laka dake jikinta haka taji wata muvuwar kasala,zuciyarta ta
karye,take qwalla ta cika idanunta
"Wa'a laikumussalam warahmatullah" ta amsa masa bayan ta sauke ajiyar
zuciya,idanunsa ya lumshe daga can bangaren yana duban kansa a madubi,ya sauya
kaman bashi ba,ya rame saidai ya fara cikowa cikin sati guda,zaya so ace sai daya
murmure sosai kafin ya koma mata saidai dauki da son ganin ahalinsa bazai barshi
ba,sautin yaji kaman na sheshsheqar kukanta
"Ya salam" ya furta yana zama gefan gado
"Ummu abdallah ki yimin rai don Allah ki daina kukan nan" ya fada a tausashe,a
hankali ya dinga tsarata cikin kalamai masu taushi da di,har sai daya sauke mata
duk wani abu dake cikin zuciyarta sannan ya jefeta da albishir mai dadi
"Rana ita yau,ki jirayi mijinki masoyinki,ki masa kyakkyawan tanadi da tarba ta
musamman,ki gayawa daughters(amatullah da amatur rahman)duk wanda nazo na tadda ya
fara gwada tafiya shine best friend dina" murmushi mai dauke da sauti ya qwace
mata,ba qaramin dadi albishir din yayi mata ba,uwa uba takan yi dariya duk sanda
yake magana da yaran kaman sa'anninshi,saboda tsabagen wayo hat sun soma shaida
muryarshi da fuskarshi ta hanyar hoto da kuma waya da sukeyi
"In sha Allah" ta furta cikin tsantsar farinciki,a qalla sai da suka kashe awa daya
cikakkiya yana sake wa soyayyarshi service kafin suyi sallama,ya jiqata ya tsumata
da kalamanshi qwarai da gaske,wanda ta dinga sakin murmushi ita daya kaman
tababbiya,kasa zama sashen tayi,ta zura hijabinta ta miqe zuwa sashen ummi,inda su
amatallah suke can tun sassafe.

Sanda ta sanarwa da ummi zancan dawowar cewa tayi cikin zolaya


"To sai a fara shiri da kyau ko?" Kunya ta kamata ta sadda kai tana gyarawa
amatallah kalbarta data soma zamewa.
In sha Allah last page na zuwa muku nan da anjima,ku zama ready........

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*


(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

1⃣0⃣7⃣

*bamu kasance masu azaba ba har sai da muka aiko da dan aike(manzo)*

*haqiqa mun aiko ka manzo(annabi muhammad)kan al'ummah,Allah ya isa shaida*

*wanda ya yiwa manzan Allah biyayya haqiqa yabi Allah*

*haqiqa mun shiryar da shi hanyoyi biyu(dan adam)kodai ya zamanto  mai godiya ko ya
zamto mai kafircewa*

*haqiqa mun halicci mutum  daga digon maniyyi dake cakude da ruwan mace da namiji
muna jarrabashi da takhlifi(nauye nauye na shari'a Allah na nufin jarrabarsa a
sanda ya dace)saboda haka muka sanyashi mai ji mai gani*

*haqiqa wannan gargadi ce ga talikai to wanda yaga dama sai ya riqi hanya izuwa
ubangijinsa*

_____________________________________

Sosai ta shiga gyara cikin satin bata zauna ba,ummu kam ta daure mata
qarqashi ta kwashe mata su amatallah,duk wani abu daya kamata ta aiwatar da shi,har
kwaskwarimar bangarenta sai data yi,kafin ranar dawowarshi komai ya zama neat.

Ranar da zai dawo din mahmoud ne zaya je dauko shi,kafin isowarshi ta shirya
tsaf cikin shigar cikakkiyar bahaushiya atamfa,ga mata cas a jiki dinkin ya zauna
mata,yaran duka ta shiryasu cikin kaya iri daya komai da komai,sun fito sak a
twince dinsu,sunyi wani kyau da girma,sanda taji isowar tasu sai ta kasa zaune ta
kasa tsaye,kai tsaye wajen baba ya wuce,ya taddashi tare da matan nashi,ba wanda
baiyi farinciki da ganinshi ba,sai a sannan ya yiwa baban bayanin me ya zaunar da
shi,shiru baban yayi yana jinjinawa namijin qoqarin da yayi cikin qasar daba tashi
ba,aqalla ya kusa mintuna talatin kafin ya wuce sashensu.

Awa uku da shigowarshi amma ta kasa zama,sai qirqirarwa kanta aiki data
yi,zirga zirga take tsakanin kitchen da falo,duk wani motsinta yana kan idanushi,ya
ganeta sarai,tana nufin sai ya sake sabon yaqin neman soyayyarta?,kunyarta keson
musu shamaki,yana zaune ne da boxer da singlet fara qal bayan yayi wanka,ba abinda
ke fita jikinsa sai qamshi mai taushi na turaren safirul hubb da wasu nau'in
turarukan,tuni amatallah da amatur rahman sukayi bacci kan qafarshi dake miqe,sai
ya yunqura ya miqe da su saman kafadarsa sanda ta sake zuwa ta kwashe duk abinda
yayi amfani da shi zuwa kitchenbda alama wanke wanke zata yi,sai da yaje ya kwantar
da su din sannan ya nufi kitchen din.

Tana tsaye gaban sink kuwa tana wanke wanken,taji shigowarshi amma sai ta
kasa waiwayowa,a hankali ya qarasa bayanta,ya sanya hannayenshi ya kamo qugunta ya
manna da nashi,sannan ya hade bayanta da qirjinsa ya dora habarshi saman
kafadarta,nannauyar ajiyar zuciya ta saki saboda wani saqo na musamman da jikinsa
ya aikata mata
"Wani abu kake so" ta furta qasa qasa
"Ke nake so maman 'yan biyu?,wai baki da labarin nayi kewarki ne?" Sai ta ajjye
kwanukan alamar tabar wanke wanken,abinda ahi bai sani ba kunyar shi take ji sosai
ta rasa dalili
"Um um ci gaba da wanke wankenki,zamuyi hirar a haka....bani labarin bayan rabuwa
baby....nikam nayi rayuwa ne kawai,gani nan tamkar mutum mutumin,ina rayuwa ne
tsahon wata biyar ba tare da nasan nau'in dandanonta ba,amma alhamdulillah,tunda
alwashin da naci na cikashi" ajiyar zuciya ta saki tana dauraye wani kwano
"Bansan ya zan misalta maka ba noor,rayuwa babu kai ashe tamkar gangar jikin da
babu ruhi ce,kullum sai nayi kukan rashinka,raba dare nake ina kokawa da
tunaninka,sai inji kaman ka tafi kenan,kaman ba zaka dawo ba kaman yadda anty su'ad
ta tafi...." Sai ta saki kwanukan ta juyo tana kallonshi,sannan ta lafe a qirjinsa
kaman mai tsoron wani abu
"Don Allah noor.....kada ka sake tafiya ka barmu haka,ni da yara duka muna
buqatarka" dagota yayi suna duban juna kafin ya sakar mata qayataccen murmushi mai
kwantar da rai
"Ba zata sake faruwa ba my summyyy,ni dinma ina tsananin buqatarku cikin
rayuwata....,bari in nuna miki kadan wani dan yanki daga cikin yadda nayi kewarku"
bai saurari komai ba ha dagata baki daya tana dariya da roqon ya sauketa zata taka
amma ya qiya,yace baiso tayi komai wannan karon shi zai sarrafata yadda yaga
dama,zai kuma dauke duk wani aiki daya zama nata ya hada da nashi duka yayi.

Tun da suka haura saman sai kukan amatur rahman ne ya sauko da shi,bako kunya
ya daukesu duka ya kaima ummi,baga ce komai ba ta karbesu ya sanya qafa ya fito
abinsa ya koma sashen nasu,ranan kuwa can suka kwana,bai karbosu ba itama ummin
bata aiko musu da su ba,da yake yaran sun riga da sun saba,ba kuma su fiye shan
nono ba,hakan duka bai masa ba,ji yake gidan yayi kadan ya dauki soyayyarsu,da safe
ko karuawa basuyi ba ya sata ta shirya suka fice zuwa gidanshin nan,wanda anan
kadai yake gani zasu baje kolinsu,ya kuwa baje kolin sin ranshi,ya yiwa soyayyarsa
cikin zuciyarta service ta sake dawowa sabuwa fil,ya kuma sake dasa mata yadda zata
soshin,irin soyayyar mai zafi mai tsayawa a rai,wanda bata barin zuciya ta huta
bare gangar jiki,yayi qara'i iya son ranshi ita kuna ta durqusa ta tallafi dukkan
nau'in abinda yazo mata da shi,na hadda ta haddace,na karba ta karbeshi yadda ya
kamata.

Kwana daya da wunu taji bai zancan su koma gida,dukan kararta da alkunyarta
taci tura,yaranta na cikin ranta abinka da uwa,tana zaune tana miqa masa kayanshi
da dai dai yana shiryawa tace
"Allah yasa su amatu zaka dauko min"kai ya girgiza
"Wa?a'ah,ai kisaka rai kin yayesu kawai,tunda ummi ta gayamin babu abinda basu
ci....ke infact ma zaki soma rainon ciki ne" gira ta dan ya mutsa a shagwabe
"Wake da cikin,ni?,ni ban gaya maka ba" bai kulata ba har sai da ya gama fesa
turarenshi sannan ya fincikota jikinsa ba tare data tsammaci hakan ba,haka ne ya
sanyata fadawa jikin nashi gaba daya
"Ke kike da ciki,tsakamin kwanakin dawowata ni na tabbatar da cewa nayi ajiya,kuma
ni na gaya miki,kema kuma zaki ga alama nan da four to five weeks....am telling
you" dariya tayi kawai tana maida abun wasa,dariyar shima yayi sannan yace
"Zamu ga wanda dariyarsa zata kasance ta nasara"
"Allah ya nuna mana" ta fada cikin basar da zancan,wasa wasa sai ga 'yan biyu shiru
har sati guda,suma kuma suna gidan basu komai ba,randa suka cika sati biyu saiga
ummi da yaran,cikin girmamawa da kunya ta tarbeta,ummun tace ga 'yan yaye ta dawo
da su sunzo kuma ganin gida da Allah ya sanya alkhairi,mamaki ya cikata,wato
almustapha yace musu sun dawo nan ne sannan ta yaye yaran,kusan awar ummin biyu
sannan ta musu sallama ta tafi ta sanar musu anty maamaa da baba suna nan zuwa.

Abun kaman wasa saiga zancan almustapha ya tabbata,da kanta tayi gwaji da
PT strip,kuka ta saki cike da tsoro da fargaba,tayi firgai firgai da ita tana jiran
dawowar almustapha,ina zata iya da twince wata bakwai ga wani sabon cikin,sanda ya
dawo takw gaya masa dariya ya dinga kwasa abinshi hankalinsa kwance
"Sanda nake gaya miki kin dauka da wasa nake?" Takaici ya cikata,wato shi ko a
jikinsa ma,sai abinci da ya jawo yanaci yana baiwa su amatullah sunata darunau
abinsu,sai ta fashe da kuka ta miqe ta shige daki,cikin mamaki ya bita da kallo din
bai zaci haka ba,sai yaji wani abu na susar ranshi,mamaki bai cikashi ba har ya
gama bawa yaran abincin,kafin ya kammala abinda zaiyi sun bingire da bacci,hakan ya
sanya ya kwashesu suka shiga dakin,tana takure waje daya tana jan hanci da alama
taci kukanta sosai,sanyasu yayi cikin gadonsu dake gefe daya,ya tofesu da addu'o'i
sannan ya nufeta,ya jima yana kalllnta kafin yayi qas da murya
"Me ya saki kuka sumayya?!" Tun kafin ta bashi amsa wasu sabbin qwallar suka biyo
kuncinta
"Yanzu don Allah ya dace ace na sake samun wani cikin?" Kai ya kada
"Eh ya dace mana,tunda har Allah ya baki yasan cewa ya dace ne" sai ta barke da
kuka tana fadin ni wallahi bana so,tun yana lallashinta sai ya fahimci da gaske
take,ya tunzura sosai,maganganun data dinga yi suka qona ranshi matuqa,kanshi ya
dinga lallasa bai tsitstsinka mata mari ba,sai kawai ya miqe ya dauki kayanshi ya
fice a dakin,ranar farko da suka taba raba makwanci kenan tun randa ta zama ita
kadai.

Wasa wasa sai qaramin abu ya soma zama babba,dan abu qalilan saita sanya
kuka,ta daina kulashi sam,iyakarta da shi gaisuwa sai ko girko,shima sai ya daina
ci kota dafa din,yadda ta dafa haka zata zo ta dauke,hakan na bala'in qona mata
rai,sam bata jin dadin zaman gidan,amma gani taje itace da gaskiya ita ya kamata a
bawa haquri ai,bini bini kuka,ko su amatu ke fada ko rigima yanzu zata sanya
kuka,wani lokaci yazo ya kwashe abinsa ta qaracu hamcininta ita kadaj,wani lokaci
su kwana ma wajensa,tana can ta kasa bacci saboda rashinsh amma ba zata nuna ko ta
sauko ba,abinda ya bata masa fiye sa zato,a hankali ta soma rama,ga laulayi tana
fama da shi,cikin haka Allah ya kawo halima abujan sunzo wani seminar ita da abdur
rahman ta leqo ta wunan musu,baki kawai halima ga sake tana duban sumayya,yo aiko
ita ba zata tafka wannan shirmen ba,shi yasa data shigo tana yabon gida sai uhmm
kawai take cewa,abin ma haushi ua bata ta kasa ce mata komai ba harta tafi,dadin
abun ma su 'yan biyu babu abinda sukayi,sai girma da suka dada da qiba kaman ana
jansu,ashe mama ra zayyanewa komai,ranan raga tashinnhankalin da bata taba gani
ba,jin muryar maman ta sauya ya daga hankalinya,ta mata fada kaman ta cinyeta,ta
kuma tabbatar mata matuqar bata sauya ba to kaman a kunnen malam,ta kuma sani
gamonau bazai mata kyau ba,a rannan ta zauna ta yuwa kanta bita daya bayan
daya,istigfari ta dinga yi sanda ta dawo hayyacinta,ta tuna girman zunubin data
dauka a wannan tsakanin abinda ta yiwa almustaphan,a ranan ta duk abinda ta danja
baya da yi duka ta miqe tayi,tayiwa 'yan biyu kwalliyarsu duk da dama bata fasa
ba,amma ta yau din ta musamman ce,ta barau falo cikin kekunansu ta shiga nata
wankan,tunda ya shigo ya fahimci sauyi a falon,bai ce komai ba ya kwashe yaransa
daketa bangala masa dariya da daga masa hannu kowa na son ya soma daukarta,dariya
ta saki ya kwashesu baki daya ta haura sama da su,sannan ya kwashi kekunansun ya
kai dakinsa,koda ta fito taga bata gansu ba tasan ya shigo kenan,duk sai taji ba
dadi,tabbas bata kyauta ba,ada bai shiga ko fita sai da saninta,amma yanzu duka ta
bata wadan nan lamuran,sai data gama shiryawa tsaf cikin wasu sabbanin qananun kaya
data taba siya a dubai,bata taba amfani da su ba sai ranar,tayi masifar kyau kai
kace sumayyar nan ce 'yar sha takwas,kaman bata haifi yara har uku ba,ta koma saman
dining ta kwashe abincin ta jera kan wani kwando mai kyau ta haura saman da su.

Sanda ta tura qofar dakin yana zaune saman gado da su abinsa,ko ina birjik da
kayan wasansu kala kala,daya na saman qirjinsa daya na saman cinyarsa yana dan kada
qafar a hankali,yana dan bubbuga bayan amatur rahman dake saman qirjinsa,da alama
bacci suke ji kuma daf yake daukarsu,don ya saba musu idan zasuyi bacci hakan yake
musu,da zarar kuwa ya musun baccin zai daukesu ba wuya,abin sai ya burgeta duk da
cewa ba karon farko taka hakan ba
"Yanzu mahaifi uba irin wannan shi zaki hanawa samun yara?" Zuciyarta ta
tuhumeta,sai ta sake jin rashin kyautawar tata sosai
"Sannu da zuwa" ta fada a sanyaue,daga kai yayi ya dubeta sai kuma ya kauda idanun
nashi,ta masa kyau ba kadan ba,ji yake kaman yaje ya rungumota,saidai miskilancin
ya motsa,ga bacin ranta dake sakadar zuciyarsa
"Yauws" ya amsa can qasa wanda da qyar ta jiyo amsar,sai data kammala shirya komai
baice mata qala ba,ta matso kusa da shi ta sunkuya tana fadin
"Sannu da zuwa.....barin dauke maka su kazo kaci abinci"
"Dakata,barmin su ai kaya na ne ko?" Ya dakatar da ita ba alamun zafi tattare da
shi,amma sigar da yayi maganar kawai kasan akwai fushi cikin maganar tasa
"Wai naga ga abinci..."
"Bazam ci ba,a qoshe nake...." Sai kuka ya qwace mata,idanunsa ya lumshe yana
saurarenta,baiso baison yaji kuka ko kadan,sai yaja qaramin tsaki wanda ya sake
karya zuciyar sumayyan,miqewa yayi ya janyo gadajen 'yan biyu ya sakasu a ciki,ya
tofa musu addu'a,sannan ya dawo saman gadon ya tattare dukkan kayan wasan nasu da
kofunansu da ya hafa musu abinci da feeders ya kammale su waje daya,ya sake dawowa
ya miqe bayansa jikin fuskar gadon tare da miqe qafafunaa,har yanzun kukan take
bata tsagaita ba,yana jin kamar ana jan ranshi ne,qarasowa tayi gabanshi kanta a
qasa ta durqusa
"Kayi haquri don Allah ka yafemin,nasan cewa ni mai laifi ce a gareka"
"Laifi?,na mefa?,bayan kina jin kinyi daidai sai kuma daidanki ta koma laifi"
hawayenta suka sake qaruwa ta sake qas da kai
"Na sani,na cancanci duk wani hukunci,amma kayi haquri ka yafemin don girman Allah"
har cikin zuciyarsa kalaman suka kai ziyara,sai sun sake taso masa da bacin
ranshi,maganganun data dinga gaya masa a sannan
"Ke zan bawa haquri ai,tunda ba'a miki dai dai ba ko?" Kai ta kada
"Ba haka bane"
"To yaya ne?,sumayya ki gayamin,me na rage ki da shi da kike tantamar haihuwa da
ni?,mene da ake buqata wanda bakya samu?,meye aibuna?dame na gaza miki?,ci sha
sutura ko muhalli?,ki gayan daya daga ciki?,me kike so nayi ina kike so na saka
raina,meye laifina?,akan me zanqi na haihu?,meye Allah baiyimin ba,ina da arziqin
da ko 'ya'ya million za'a haifa min zan iya daukar nauyinsu,zan iya kula da su,to
me yayi saura?,me ya rage min?,so kike ki tunzari ni?,ki tunzurani nayi abinda
banyi niyya ba?,kinsan mata nawa ke kawomin kansu na auresu?,duba nan" ya fada yana
bude wayoyinshi a zafafe kamar yadda yake maganar cikin zafi ya shiga fannin
saqonni ya bude kana ya tura mata dukkan wayoyin gabanta
"Su'af bata yi arba'in ba baban yarinyar da na yiwa aiki ambassadorn nijer yake min
tallan 'yarshi,duba qasa bayan shi ga saura nan,mutane iri daban daban,ba wadda
idan nace ina so za'a hanani,so kike na dauko wata cikinsu dolen dole na kawo
rayuwarmu?" Kuka ta fashe da shi qwarai fiye dana dazu,tausayinsa da tausayin kanta
ya kamata,tabbas gashinan har da hotunan wasunsu
"Kayi haquri don Allah man kayi haquri,wallahi na daina,ina son cikina ina son
abuna,kuskure ne" sai tausayinta ya kamashi ganin yadda yake take kuka haiqan,hade
hannayensa yayi waje guda yana dubanta
"Yanzu ya kike so ayi,a cire miki cikin?" Wata harara da batasan da ita ba ta watsa
masa
"Wallahi banaso ina son abuna ba wanda zai cire min" a zahiri da ranshi ba'a bace
yake ba tabbas dariya ce zata zo mishi,amma da yake yana cikin bacin rai sai harar
tata ta saukar masa da sanyi cikin zuciyarsa,ya lumshe idanu sannan ya ware mata
hannayenshi,tamkar jira take sai kuwa ta taso da hanzari ta fada ya rufeta ruf ta
sake narkewa da wani salon kukam
"Relax baby...relax" ya fada yana shafan sumar kanta dake fake waje guda,a hankali
kukan ya ragu ta soma sauke ajiyar zuciya
"Kace musu kana so?" Ra furta a hankali
"Suwa?" Ya tambayeta yana dan tunani
"Au" ya fadi bayan ya tuna,sai ya sanya dariya har sautinta na fitowa,wato wani
kishi da da can bata da shi a yanzu zata koya
"Bance musu ba,amma indai kika sake cewa bakison baby na dake jikinki to ki
tabbatar zan auro saliha tayi ta haifo min yara iya yadda nakeso..." Bai qarasa ba
ta cika masa kunne da kukan shagwaba
"Sorry sorry....bazan sake fadi ba indai kema baki sake ba" ya fada yana dariya
tare da sake gayyatota zuwa cikin jikinsa tayi lamo tana dariya ciki ciki,kusan
tare suka sauke ajiyar zuciya kowa najin wani nauyi na sauka daga qirjinsa,saboda
ba qaramin kewar juna sukayi ba,ba wanda bai jigata ba cikinsu dauriya kawai
sukayi,a ranan an biya bashin soyayya qwarai,dama ance fushin masoya hutu ne.

Rayuwa mai cike da tsafta da ingantacciyar soyayya ke gudana cikin


gidan,gida ne da suka ginashi cikin so qauna da aminci,kowanne farincikin dan
uwansa shine nasa,dukkansu kowa ya qoqarin ganin ya kyautatawa dan uwanshi,sai da
cikinta yayi wata biyu cif sannan suka daga dubai da kyawawan 'yan biyunsu,sun tafi
sun bar mutane da kewarsu,a can dinma gida ya saiya musu mai dauke da falo daya
kitchen mai girma da corridor biyu,daya dakunan baccinsu shi da sumayyan,daya kuma
na yaran da spare din wani guda,a nan dinma ingantacciyar rayuwa suka shimfida,duk
abinda yakeso shi take masa,kaman yadda duk abinda takeso shi yake mata matuqar bai
saba dokar shari'a ba.

***** ***** ****** *****


******* ****** *******

       Qatuwar harabar gidan dattijon tsohon professor muhammad mukhtar wanda aka
sake sauyawa ginin gidan fasali qawace yake da nau'o'in ado kama daga yadiddika
balan balan da launin qwayaye iri iri,kujerun zama da tebura ma alfarma,carfet
carfet da ka qawata wajen,iya ganinka yara ne ke sha'aninsu wadanda ba zasu gaza
shekara biyar zuwa qasa ba,sai kuma manya jifa jifa wadanda 'yan uwa ne na
jimi,daga qofar iya wajen da aka tanada saboda sha'anin makeken hotone na
amataullah da amatur rahman,yan biyu kyautar Allah,'ya'ya ga doctor muhammad
mukhtar,hamshaqin attajirin nan wanda ya mallaki kamfanoni na sarrafa abaya da
mayafai a qasashen duniya daban daban,babban mai noma auduga afadin nijeria,mutum
da ya mallaki manya manyan gidan marayu da gajiyayyu wanda babu irinsa a fadin
africa dake taimkao ga wadan nan mutane,mijin macen data zama haske wa al'ummar
nigeria bama yankinta arewa kawai ba,matar data mallami centers na koyawa mata
sana'o'i,centers na horar da yara 'yammata matasa,macen data shahara wajem gina
makarantu da masallatai,matar data yi fice wajen samar da maqabartu,tallafawa
tsofaffi da masu rangwamen gata wato hajiya sumayya sulaiman abdu,sannan jikoki
wajen dattijo mai cike da dattako da karamci,tsohon ambassador muhammad mukhtar
gwambe,yau rana ce ta musamman wanda ilajirin jikoki da 'ya'ya wanda suka fito daga
barin familyn mukhtar na uwa da uba,da kuma na abokai,da duk wanda ya hada alaqa da
sumayya dukkansu suna gidan,rana ce ta murnar zagayowar ranar haihuwar amatullah da
amatur rahman,wanda suke cika shekara uku da haihuwa,duk yara matan dake wajen suna
sanye cikin dogayen riguna fara qal da aka yiwa don baqi wanda kyauta doctor
almustapha ya bada a rabawa suk wanda ya halacci wajen,mazan ma jallabiya ce ta
maza fara qal da baqin hirami a kansu,wajen yayi kyau matuqa da irin adon da aka
masa na fari da baqi,shewa yaran suka sanya sanda aka iso da qaton cake din 'yan
biyun cikin kwali aka sanyashi a muhallinsa aka budeshi jiran fitowarasu kawai ake.

        Daga daya bangaren yaran suka fito,sanye da gown golden mai adon baqi,ta
cikin tsahonta ya kai gwiwa mai gajeran hannu,sai ta saman mai dogon hannu,kallo
daya zaka muau idan bakasan au wayw iyayensu ba kace daga jinsin karabawa aka dauko
su,sun kwashi kyau ta kowanne bangare,sunyi kyau matuqa da gaske,takalmin qafarau
kawai abun kallo ne,kana dubansu kasan sunji gata iya gata,daga bayansu kuma hajiya
sumayyace dauke sa wani yaro wanda saika rantse usainin sumayya ne saboda
kama,sanye yake cikin wando na yara three quater da baqin takalmi hightop na
yara,sai farar shirt a jikinsa mai gajeran hannu,kan yaron na kwance saman
kafadarta,kar kaso kaga sumayyan a lokacin tayi kyau na qin qarawa,sanye take da
wani lafiyayyen lace wanda kyawunsa da tsarywarsa kadai ya isa ya gaya maka shi din
mai tsada ne,peach ne mai dan turuwa,wanda aka yiwa ado d'ai d'ai da mint
green,komai nata ya dace da shigarta,ita dinma kana dubanta kasan cewa Allah yayi
halittar mace a wajen,wadda kyau da nutsuwa suka hadu suka nuna hutu da tsantsar
nin dadin da take ciki,murmushi kawai take sakewa sanda taga yawan yaran da wajen
ya tara,ciki kuwa harda yaran yaya abbakar,yaran halima da kuma yaran zainab,yaran
farida huda da uwar gayya amira wadda ke cikinsu tana ta qoqarin saita wajen,sai
yaran mahmoud da mus'ab mace da namiji,ga kuma yaran lamin da usman,musaddiq da
huzaifa ne basa qasar banda nasu yaran saidai ayi hotuna a tura musu,baki daya
wajen ya rude da hargowar yara badon komai ba sai hango boss dinsu amatur
rahman,yarinyace mai tsokana rawar kai da surutu,itace usaina saidai tafi 'yar
uwarta iya komai,saika rantse itace babba,kusan duk yaran dake wajen dan team dinta
ne,dai dai ne suke sabga da amatullah,itakam zamu iya cewa tayo gado ne,gadon
miskilanci rashin son magana da shiru shiru,hakan ya sanya amatur rahman ta rainata
qwarai,don ma maibi musu ,a hakan ma sumayya tayi tsaiwar daka a kansu,wani lokaci
MUKHTAR wanda shike bi musu wanda yaci sunayen mutane biyu shike shigarwa amatullah
din,suna kiranshi da qarami yayin da almustapha ke kiransa da aboki,amatullah da
amatur rahman kuma daughters,idan daya zai kira zaya ce daughter,qaramin dake
hannun sumayya kuma shine MUHAMMAD mai sunan baban professor suna kiranshi amir.

      Cikin lokaci qanqani aka soma gabatar da bikin birthday din,wanda yayi
masifar qayatarwa,yara sun wala sunyi farinciki qwarai da gaske,a qalla sai
magariba sannan suka soma haramar tashi,masu tafiya aka fara zuwa daukansu,masu
kwana cikin gidan kuma kowa ya shiga ciki.

       Bayan amira wadda kwana zatayi ra saka duka yaran mata sunyi wanka sai ta
fice zata wajen ummi ta bawa qaramin yaronta nono,wanda yaranta biyu,babbar itace
farha sai qaramin hadim,sumayya ta bari da su tana tsakiyarsu tana fama da su kan
kowanne ya nutsu,mai cin abinci yaci mai kwanciya ya kwanta,wahalar da ita suke
sosai don amatur rahman ta hada gang sunata tayi,miqewa tsaye tayi kawai tana
kallonsu
"Wannan yarinya halan fitinar amira ta dauko ne?" Ta raya haka cikin
zuciyarta,qaramar dariya taji an saki a bayanta,hakan ya sanyata waiwayowa a
hankali,almustapha ne tsaye ya jingina da qofa,hannayenshi harde a qirjinsa yana
murmushi da alama ita yakewa dariya,sauke hannyen nashi yayi ya fitota da hannu,don
tabbas idan ya sake ya shigo cikin dakin yaran ba zasu barshi ya fita da wuri ba,ta
gane sarai me yake nufi,sau ta dubi jikinta,don tunda aka tashi daga wajen batayi
wanka ba,abinda take ta sauri tayi kenan kada yazo ya sameta a hakan,sai gashi bata
cimma nasara ba,kafadarshi ya dage hadi da girarahi ya watsa hannayenshi yana
murmushi alamun babu ruwanshi,ta nuna kanta da yatsa alamar niko?,ya kada mata kai
yana nufin eh din,sai kawai ta juya ta dubi su amatallah tace
"Amatu.....ga abul_aulad" take kowa hankalinsa yayo kan qofar,kafin kace meye sun
moqe aun dunguma kanshi,wayyo sumayyan ta gama masa tsiya,yau yasan ciwon kai babu
fashi,idan ba'ayi da gaske ba ma duk yadda ya ciwa yau din buri bazai iya aikata
komai ba,tana masa dariyan mugunta ta zame ta barshi da su,hakan ya bata damar yin
wanka ta shirya tsaf,sannan a gurguje ta shirya masa abinda zaici sannan ta dawo
wajensu.

       Daga bayansu ta tsaya tana kallonsu tana sakin murmushi a jejjere,babu


shakka haihuwa rahama ce,yara ni'imah ce,koda shashancinsu kawai wani lokaci abun
debewa zukata kewa ne,almustaphan da baison hayaniya ko kwaramniya ko qanqani yau
sai gashi tsakiyar yara,ya bude musu kwalin chaculets wasu na cin
gugguru(popcorn),wasu na fama da ice cream,baki daya sun bata mishi jiki,amma ba
yadda ya iya haka yake biye musu,sai data gaji da kallonsu don kanta taga sun fara
cakar da shi ya soma riqe kai sannan ta qarasa wajen tana masa dariya,ya daga kai
suka hada ido,maimakon harar nuna ta masa laifi fa yayi niyya sai gashi ya buge da
zuba mata idanu yana kallonta kaman zai cinyeta,sai data kada hannunta saitin
fuskarshi,ta zauna gefan madina 'yar gidan abida ta biyu ta janyi guggurun ta soma
ci,gardin madara dana zumar dake ciki na ratsata harda lumshe ido
"Madam,u r pregnant fa?kinsan yaushe nayi shi?,randa zamu baro dubai,unforgotable
night din nan da kika bani"ya rada mata saitin kunnenta sanda yadda ba wanda zaiji
sai su Cak ta tsaya da taunar ta waiwayo tana dubanshi,tasan tunda ya fada din
mawuyacine idan ba hakan bane,saboda ba yau ya fara ba kamar wani mai gani har
hanji,duk sanda yaui cikinsa shike gaya mata kuma daga qarshe ya tabbata
hakanne,haka sukayi cikin qarami da cikin amir,tana son nuna alhinin dake cikin
zuciyarta amma tasan sharadin yin hakan bata manta ba,yace duk sanda ta sake nuna
bata son cikinsa ta tabbatar da cewa ta bashi license na qara aure ne,har yau diyar
ambassador na nijer na nan,duk da an kusa bikinta idan yace yana so babu abinda zai
hanasu bashi
"amma likita don Allah?"
"Na auro saliha?" Kada kai tayi da sauri
"Amir fa,shekararsa daya da rabi yanzu fa"
"Sanda kika haifi aboki shekarar su amatu daya da wata hudu,me ya sameki?" Kai ta
kada
"Ba komai"
"Kada fa ki yiwa Allah butulci,kin manta sunan da ake kiranki a baya"
"Asragfurullah" ta ambata da sauri,har yau bata mance rigimar cikin qarami ba,anty
ni'imah cewa tayi tana so a bata ita,tun a sannan jikinta ya sake sanyi,sai yanzu
zata sake gwadawa abinka da dam adam kayan Allah
"Taimakeni ki sallami yarankin nan don Allah nima aji da ni" ya fada yana langabe
kai gwanin tausayi kaman gaske,bushewa tayi da dariya don ya bata dariya,cikin wayo
da dabara ta dinga kaisu daki suna kwanciya har da amir kuwa duk da dafarsa,amatur
rahman kawai ta rage,ta kafe kai da fata sai an fara bude gifts da suka samu a
daren,tun tana daurewa har ta bata haushi ta kai mata duka,tako sameta cinya da
daku sosai,kuka ta saki ta soma sosa wajen yayin da sumayyan ta rufeta da hargowa
kaman zata sake kai mata wani dukan,kallonta kawai almustaphan yayi sai ya dauke
kai,ya janyo amatur rahman din ya yaye rigar jikinta,abinka da farar fata wajen
kuwa yayi jazur sosai,shafa mata wajen ya aoma yi yana hura mata cikin salon
nusarwa yace
"Ba'a yiwa mama musu da taurin kai,haba amatu...ke da kike babba....baku ganu su
ikram da su affan duka kin girme musu kuma sun tagi sun kwanta,baki son mama ta
huta ne itama?" Kai ta gyada alamar tana so a sanyaye
"tun jiya mama bata zauna ba uhm,ki bata haquri kuce ba zaki daina ba" a sanyaye ta
dubi sumayya da tayi kicin kicin da rai,ranta na wanu irin baci,wanda abinda tayi
mata baikai bacin ran da take ji ba,don idan da sabo da tasa ba da halin amatur
rahman
"Ammi....kiyi haquri" da yake suna kiranta da sunan da abdallah ke kiranta
ne,saboda duk hutu anan yake zuwa yayi,akwai sabo da shaquwa sosai tsakaninsu
tamkar uwa daya uba daya,su kansun a yanzun sun dauka babansu shi ya haifeshi,an ce
musu shine babbansu yana kano ne yana karatu sai ya gama zai dawo,qin amsa mata
tayi sai data maimaita sannan tace
"Naji....tashi kije ki kwanta" miqewa tayi har ta soma takawa tace
"Ammi....amma yaya abdallah da yace zai kiramu bai kira ba fa"
"Ban gaya miki jarabawa yake ba baya waya sai ya gama?!" Ta fada mata a tsawace,sai
ta juya sum sum ra fice zuwa dakin,yayin da almustapha ya zuba mata ido,sai da
yarinyar ta fice sannan ta ja tsaki suka hada ido da shi,dauke kai yayi ya miqe ya
wuce nashi bedroom din,sannan ta miqe ta bishi a baya.

       Sanda ta shiga har ya shiga wankanshi,qwafa tayi ganin ya hada ruwan wankan
da kanshi kenan,abinda ya kasance aikinta ne ita keyi,hakan ya sanya ta zauna tana
hade rau ta janyo wayarta ta soma neman mamanta,ba jimawa ta daga,sunyi hira sosai
ta tambayeta 'yan jikokin nata tace duka sunyi bacci,suna gamawa ta katse ta kira
halima suka gaisa ta hadata da abdallah wanda keta karatun common intrance za'a
shiga secondry,suka gama hirarsu ta masa addu'a sannan ta kira zainab itama suka
gaisa,tace gata kwance shiru gidan ba dadi duk sabida ba hayaniyar yara,gashi sabon
gida suka koma sabuwar unguwa,dariya tayi tace idan zaki kwanta ma kiyi baccinku
gwara kiyi,donsu yanzu haka ma sun jima da yin bacci,dariya tayi suka dan taba hira
sannan ta katse ta kira nafisa,itama yaran nafisan na wajenta su biyu,sunyi hira
abinsu sosai irinta qawaye kafin suyi sallama,daga qarshe ta kira yaya yahansu
wadda a yanzun ta bata jari take business ba saida atamfofi,ba qaramin ciniki take
ba,sosai rayuwarta data yaranta dake gidan aure ta inganta sai son barka,dai dai
sanda ta ajjiye wayar ya fito yana tsabe jikinsa da towel,suka sakw hada ido ta
kauda kai,dariya yake qoqarin boyewa amma ya kasa,ya sani cewa ta koyi fushi cikin
kwanakin tun kafin tasan cewa tana da cikin,wanda yasan baya rasa nasaba da cikin
da take da shi,kowanne ciki akwai irin yanayin da yake zuwa ma mace da shi,yadda ta
hade rai ya sanya dariyar fitowa a dole,sai ta juyo ta dubeshi take ta saka kuka
kaman qaramar yarinya,dariya yake sosai ya ajjiye towel din ya tako zuwa inda take
"U r craying like a baby,ko qarami bazayayi irin wannan kukan ba,wai mema aka
miki,you beat my daughter bance dake komai ba,shi ya bata miki rai ko kuwa?"
"Wallahi hancina kakewa dariya" ta fada taba shafa hancin wanda sai yanzu taji
alamun ya bude kaman cikin 'yan biyu,wata dariyar ce ta sake hardeshi,yayin data
qara volume na kukanta,ganin tana kukan bilhaqqi ya sanya ya fara damunsa,sai ya
sassauta dariyan ya tako gabanta,kan gwiwoyinshi ya durqusa,yasa duka hannyenshi ya
kama kunnuwansa yana cewa
"Is ok...am sorry...am really sorry babe,idan baki huce ba kimin duk hukuncin da
kike so" sai ta fara sassauta kukan tana kallonshi,tsahon minti biyar kafin tace
"Labari zaka ta bani har na awa daya" dariya ta sake kamashi wannan karon ya
maidata,yasani sarai mugunta ta shirya masa,ra ina zai iya surutu na awa daya ai da
sai yasha magani,sai ya narke mata kalan tausayi ya sanya tafin hannunshi duka biyu
a kumatunsa alaman tagumi
"Wayyo ummina....kina ina ana punishing dina"salon yadda yayi maganan dole ya baka
dariya,sai data daara sannan ta maze
"ba ruwan ummi a nan,ita ta aikeka kayi tsokana?....so tunda karanta labarai ya
maka tsauri sai kayi kamun kunne ko tsallen kwado wanne yafi maka?" Hannayenshi ya
hade waje daya yana jujjuya kai
"Almustapha yau kaga ta kanka wallahi,ka tabo uwar biyun nan" idanu ta zaro
"Wa ya gaya maka 'yan biyu zan haifa?"
"In sha Allahu,kisa ido ki gani,zuwana umara na qarshe kafin ki samu cikin su na
roqa,kuma nasan in sha Allah Allah ya amsa" harararshi tayi,sai ya saki dariya ya
miqe yana dagata
"Kinga....naga labarin babba ne,muje kiyi wanka kizo kiji" shi ya rakata ya kuna
tsayata ta gama wankan suka dawo dakin tare.

     Tana jikinsa yana daddanna cumputer yana,bangaron hotunan dake cikin cumputer
din hannunshi ya kai,hotunansu amatallah ne amatur rahman aboki da amir,hutuna ne
kala kala,wasu cikin gidansu,wasu a makaranta,wasu bakin ruwa wasu sanda suke fita
shan coffe,wasu kuma a wasu park park da ya saba kaisu duk qarshen sati idan bai
samu dama ba kuma bayan sati biyu ko sumayya ta debesu su fice,da yake dubai gari
ne da suke da yawan wajen shaqatawa sai wanda ka zaba,yana son yaranshi qwarai,yana
son moment din,sanda zai kaisu wajen wasan yara,ya zauna daga gefe guda yana lura
da duk motsin kowannensu,yana musu hoto ko vedios,yana kalla yana murmushi,bashi
kadai ke ganin kyawun yaran nashi ba,kowa cikin dangi yana fadan haka,sun fita
daban,haka tarbiyyarau abar kwatance ce da misali,duk da zamansu a baquwar qasa
hakan baisa sunyi sakaci da tarbiyyarsu ba,hankalin su na tashi qwarai ko yaya suka
ga wani canjin dabi'a a wajensu har sai sun tabbatar sun gusar da haka,sai da ya
gama kallon tana tayashi suna tattaunawa ko halayen kowanne cikin yaran nasu sannan
ya fita ya soma nuna mata wasu sabbin estate da ya gina cikin abuja,sai da ya
kammala tsaf sannan yace
"Daya naki ne,akwai kudi da na saka miki cikin accnt ki duba" idanu ta zaro zatayi
magana,sai ya dora hannunshi kan lebansa
"Kada kice komai,a duk sanda kika haihu nayi yunqurin yi miki kyauta sai kice
a'ah,wannan karon kam kada ki hanani kuma kada kice komai" qwalla ce ta cika a
idanunta,sai ya soma share mata yana murmushi tare da cewa
"Kin cancanta,kinfi qarfin komai a wajena" godiya tayi masa sosai da addu'a mai
bala'in shiga zuciya da ratsa jiki,bayan ya gama amsawa ya sake cewa
"Akwai abinda nakeso a yuwa su'ad da mukhtar,abban abdallah"
"Sadaqatul jariya?" Ta tambaya da sauri,murmushi yayi yana dubanta
"Eh....dama nasan abun yana ranki,na sanya wani yaro sharu ya binciko min qananun
hukumomi dake kano gwambe katsina da jigawa wadanda ke buqatar ruwan sha,masallatai
da makarantu,zamu gina Allah ya sanya ladan a mizaninsu,muma zanyi mana,saboda
halin rayuwa,duk da gidajen marayu dana gina,da qungiyoyin da tallafi da nake
badawa hakan bai gamsheni ba,zamu qara sabida mu tadda kyakyawan guzuri a
lahaira,ke ni ummi baba malam har da anty maamaa" kuka ya qwace mata,ta rasa da
bakin da zata masa godiya,wanne irin taushin zuciya gareshi haka
"Allah yayi maka kyakkyawan qarshe,ya rabaka da iyayenka lafiya" addu'arta ta
qarshe da shi kenan,idanu ya lumshe yana amsawa don ba qaramin dadi addu'ar tayi
masa ba
"Na gama shirya komai,in sha Allah za'a bamu abdallah da zarar ya gama junior
secondry a dubai zaiyi senior da jami'a baki daya har sanda zaice karatu ya
isheshi" murmushi ta saki tana goge hawayen farinciki
"Danka ne noor,duk yadda kayi dai dai ne"
"Ina son abdallah baby...Allah ne baiyi zai fito daga tsatsona ba,ina jinsa kaman
dana na ciki na" murmushi kawai take,ko yanzu babu abinda abdallah ya rasa banda
mahaifi wanda ya haifeshi,amma a rayuwarshi saidai ya yiwa wani ma,kafin tace komai
wayarta dake gefe ta dauki ruri,sunan zainab kano ke yawo,ta miqa hannu zata dauka
ya rigata daukar ya kashe wayar tana kallo
"Time dina ne,na tsani abinda zai dinga shiga tsakanina da ke,banson abinda zai
dinga hanani kallonki" murmushi kawai tayi,tasan da biyu yake fadin haka,ta rasa me
yasa duk mutanen da suka munana mata yafi riqar zainab akan kowa,bai hanata tayi
mata duk abinda tayi niyya na alkhairi ba amma baison tarayyarsu ko kadan,zainab ce
ke kiranta wadda sun hadu da ita ne randa ta qaddamar da bude qungiyar ta ta
taimakon nakasassu da masu buqata ta musamman dake cikin gidan yari wanda zainab na
cikinsu,ranar tayi kuka tayi kuka wanda hakan ya sake bata ran almustapha kaman
yadda zainab din itama tayi kuka kaman ta cire idanunta,zainab ce babu qafafu
biyu,tana rayuwar tantal bataiti,bata da cikakken wajen zama,mamarta baqincikinta
ya kasheta,babansu ya koma qauyensj bayan ya aurar da qannanta,danta nafi'u kuwa an
saceshi an nemeshi sama da qasa an rasa,daga bisani bincike ya tabbatar masu yankan
kan data so saida abdallah ne da basu sameshi ba suka ce ba zasu haqura ba tunda ta
saka musu rai suka daukeshi suka salwantar
"Ba za'a sake ba yallabai in sha Allah" ta furta tana murmushi,sai ya saki
murmushin shima,ya janyota jikinsa sosai yana shaqar qamshinta wanda ko tafiya yayi
yana daya daga cikin abinda ke tsaya masa game da ita acikin ranshi.

       "Ranar lahadi zamu wuce kano da duka yaran nan a maidasu gida,sabida
birthday kin dauko musu yara haka kawai...tab..wallahi nikam bani iya barin yarana
su motsa nan da can" duban idanunshi take tana dariya,Allah ya zuba masa qaunar
yaranahi,inda Allah yayi taimako hakan bai sanya sun sangarce ba yana tsawata musu
da nasiha idan sukayi ba dai dai ba,cikin salon tsokana tace
"Wai da zan barsu nan gidan wajen ummi ma idan zamu koma ko na kai wasu kano
wajensu zainab"
"Allah ya baki sa'a" kawai ya fada yana kashe system din ba tare daya dubeta
ba,hakan ya bata dariya sosai
"Ni na isa?,tuba nake yallabai,Allah ya taimakeka,da kai da kaya ai duka mallakar
wuya ne,ko ni kaina banda iko da kaina sai abinda ka zaratar" wani juyi yayi cikin
zafin nama ya juyeta qasa ya danneta yana duban qwayar idanunta,itama shi take
kallo kowannensu na fidda murmushi,suka soma musayar numfashin juna
"Sai yaushe zaki daina kambamani ne haka,farinciki da umarni na ne ko yaushe gaba
da komai naki koda baki so"cikin siga ta rada da muryarta mai tsananin laushi tace
tana girgiza kai
"Babu wannan ranar,banganta ba noor....mijine kai na musamman daya tamkar da
miliyan.....inaso naci gaba da kasancewa Mace ta gari a gareka,na shiga qabarina
kana mai yarda da ni"
"Kin dade da amsa wannan sunan baby.....a mace ta garin ma keta musamman ce...,da
mutum na bawa dan uwanahi mutum aljanna tun a duniya da tuni na baki sunayyah!,na
godewa Allah da ya sanya kika zamo cikin KUNDIN QADDARATA"fari tayi da idamunta
cikin tsantsar farinciki da jin dadin lambar yabo da cikakkiyar yardar data samu
daga mijinta tace
" nice da wannan godiyar MY MAAN,NA GODEWA ALLAH DA YA CIKA KUNDIN QADDARATA DA
ZALLAR FARINCIKI DA SAMUN MIJI NA GARI KAMAR KAI,YA SAUYA KUKA NA YA KOMA
DARIYATA,FARGABATA DA RASHIN TABBAS YA ZUWA YAQINI DA CIKAKKEN TABBACI"dariyar
zallar farinciki ya saki yana sake qanqameta
"indai haka ne saidai muci gaba da damqawa junanmu zallar qauna soyayya da yarda,mu
kuma yi addu'ar haduwarmu a aljanna ki zame min jagorar mata na ta gidan aljanna"
kai ta jinjina tana sake shigewa jikinsa tana jin wani aminci gewaye da da dukkan
rayuwarta
"INDAI HAKA NE INA MANA FATAN HADUWA GIDAN ALJANNA"
"allahumma amin ummu aulady"ya furta cikin zafin nama yana hade bakinshi da nata ya
shiga aika mata saqonni,nikam nace Allah ya bar qauna na fice na bar musu dakin,a
bankali na fice daga gidan ina musu bankwana dasu,tare da musu kyakkyawan fata har
zuwa qarshen rayuwarsu,da ci gaba samun dawwamammen farinciki.

*SABO TUREKEN WAWA,KOMAI YAYI FARKO YANA DA QARSHE BANDA IKON ALLAH*

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah madaukakin sarki wanda ya banbamta
tsakanin bata da shiriya,ya bambanta tsakanin haske da duhu,tsira da amincin Allah
su tabbata ga shugaban talikai annabi muhammad S A W.

Ina godiya ga daukacin ilahirin fans dina,na kusa dana nesa,wadanda na sani da
wanda ban sani ba,ina miqa matuqar godiyata,grouos din da nake ciki da wadanda bana
ciki,jinjinata a gareku HUGUMA CONVERSATION ROOM DA HUGUMA NOVELA ROOM,haqiqa
qaunar da kuke nunamin ba kadan bace,ina fatan Allah ya faranta muku fiye da
tunaninku,sauran groups bazan manta da ku ba

ZAMA NA AMANA GROUP


HAUSA NOVELS NA UMAR DALHA
HAUSA NOVEL
ZAUREN BIEBIE ISAH DA NOVELS SHELF
INSPIRING STORIES
MAMAN HANEEF NOVELS
MAMAM AYSHA NOVELS
KUNDIN HASKE
HASKE FANS GROUP
DA KUMA QUNGIYATA TA

HASKE WRITERS ASSO

BAZAN WUCE BA BAN GAIDAKU BA

MAMAN KHADIJA
HAJJA
RANO
KDEEY
DA KUMA ME SUNAN SURUKATA

AYSHA DAN SABO


ALLAH YACI GABA DA HADA KAN MU

INA SAKE GODE MUKU


SIS SAHURA
SIS RUQAYYA
SIS TASH
MARIYA SB

JAZAKUMULLAH BI KHAIR

MASU SON A QARA TSHON KUNDIN QADDARATA

ina mai baku haquri,komai yayi farko dole yayi qarshe,hakanan duk abinda duk
dadinsa wataran zai fita daga kai ne watan watarana,muyi haquri tunda saqon ya
isa,muyi fatan samun lafiya da tsahon rai watarana sai mu sake haduwa a gaba.

ZANSO BAYAN TAYA MURNAR KAMMALAWA NAJI WANI DAN TSOKACI DAGA BAKUNANKU GAME DA
LITTAFIN HAKAN ZAI BADA MA'ANA.

ina sake miqa godiyata ga Allah da ya aran rai da lafiya,ya kuma bani ikon kammala
wannan littafi nawa,a daren laraba 20/3/2019,ina roqon ubangiji ya yafemin dukkan
kura kuraina dake ciki,dai dai din ciki Allah ya datar da mu ya sanya min a mizani.

Ina miqa qoqon barata da kuyimin addu'a ko sau daya ne,ku roqamin Allah ya cikamin
burina alfarmar sayyadina rasulillah S A W.

Na gode.

Ga maiso ya duba status dina don ganin 'yan biyu😄😄

Subhanakallahumma wabi hamdika,ashhadu an la'ilaha illa anta,astagfiruka wa atubu


ilaika.

#mrs muhammad ce.


#ummu muhammadiyya.

An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na


www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na
yake yake dana soyayya

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu
kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama
sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana
magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490

A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci,
duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna
neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman
munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai
fi kyau ku riga dauko PDF da DOC

Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai
wayarku

This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng


You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to
download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography
including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490
its free we do not charge for our services

Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted
biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not
blame us

Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we
are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day,
any time you can visits our site and download it

Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF
or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
__

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽

You might also like