You are on page 1of 733

WATA KISHIYAR

(Alkhairi CE KO SHARRI)

Na Maryamah_MrsAM

TALLAH TALLAH TALLAH

"ASMA'U Baban Ali ya kirayeni da ainihin suna na wanda ko a lokacin Auransa da AMIRA da muke kan
ganiyar zuba rashin Mutunchi ba haka yake kirana ba "MA'UNA" shine sunana a bakinsa kuma a gaban
kowa duk kuwa da baqin miskilanci irin nasa, a gaban wanda yake matuqar kunya ne yake kirana da
"HUSNA".

"ASMA'U ASMA'U ASMA'U sau nawa nawa na kira sunanki".. tun be kai ga qarasa ba nace "Sau uku
ENGINEER BASHIR AHMAD" dan nidin fa ba baya bace a fagen iya fitsara kawai dai shekaru suka sa na
farayin sanyi amma a wannan gabar dole na fito masa a ainihin MA'U ta wadda ya sani shekaru goma
sha shida da suka gabata bawai ASMA'U uwar Aliyu, Jafar, Farida, Abdallah, Ahmad da Muhammmad ba.

Qara gyara tsayuwata nayi ina kallonsa ganin yanda yake bina da kallon dana tabbatar na zallar mamaki
ne jin sunansa a bakina Gatsal bako Sakayawa, lallai ya manta dawa yake magana, a zatonsa nayi tibis be
san haryau da saurana ba sedai baa tabo ni ba. Kansa ya girgiza yana qoqarin kokawa da hukuncin da
zuciyarsa take ayyana masa, wani sashe na ingizashi akan yayi inda dayan ke kwabarsa da nuna masa
zafa ta iya kwabewa amma idan ya ja da baya ai ma zata raina shi kuma yabi abinda take so kenan.

Kai ba wannan ba raini biyu ma tunda itama ma AMIRAN zata qara tabbatarwa duniya be isa da ASMA'U
ba tunda gashi ya bata umarni taqi tabi. Se ya gyara tsayuwarsa tareda qara tsuke fuskarsa da dama can
bata da fara'a sam, wani kallo yake jifanta dashi da yasan yana ladabtar da koma waye amma banda
wannan kangararriyar Matar. Cikin kaushin murya yace
"For the last time ASMA'U ina baki umarnin kiyi resigning daga aikin ki ki tattara yara ku koma Gombe
d....."

"Na gaya maka bazan bar aiki na na koma Gombe ba saboda zaka kawo Matarka Lagos" nayi saurin katse
shi.

"Se ki zaba ko auranki ko kuma aikinki" ya fada cikin sautin dake nuna zallar bacin ransa.

Qara jinjina qarfin hali da rainin wayonsa nayi a raina, yau na shirya ganin qarshen rainin hankalin Bashir
dan haka nace

"Idan har saboda matar ka kake so nabar aikina to na zabe shi BASHIR"

"Haka kika ce"

"Eh"

"Kije na SAKE KI SAKI DAYA idan yaso se ki zauna da aikin naki".

Wani irin dum naji kunnena ya dauka, wallahi wannan kalmar itace mafi muni ji a rayuwata gaba daya,
wannan rana tafi kowacce duhu a tarihin rayuwata.

"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un Bashir dagaske kake" na fada cikin yanayin da ni kaina bazan iya
fasaltawa ba

"Oh baki yarda ba? To kije na qara miki DAYA badan babu kyau ba ma sena cike miki ukun ki kinga se kiji
dadin yin aikin ki dakyau" ya fada daidai sanda yake shirin ficewa daga dakin.

Wani jari ne ya kwashe ni ya yar akan gadon dake bayana, Allah ne ya rufa min asiri, a yanda nake na
tabbata in a qasa na fadi babu abinda ze hana barin jikina shanyewa.

"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, Allahumma ajirnifimusinati wa'allifni khairan minha" cikin ikon Allah
kalaman da bakina ya shiga maimaitawa kenan. Duk yanda naso kwakwalwa ta tayi tunani na kasa
tamkar kan saka super glue an liqeta haka naji nanda nan kaina yai dum kafin kace meye numfashina ya
fara sama sama ba shiri na fara laluben inda Inhaler ta take wadda sabuwa ce na shigo daukowa dan ta
cikin jakata ta qare.

Seda na zuqa sosai sannan numfashina ya fara dawowa daidai amma fa kwakwalwar na nan a toshe. Kai
ido na fa ya soye bama alamar Hawaye zasu fito, to kukan maganin me ma zeyi mun?

Ni Ni Asma'u yau Bashir ya saka? Wallahi ko a mafarki naga Bashir ya sake ni nasan shedan ne amma
gashi kamar a zahiri hakan ta faru. Ina cikin wannan yanayin naji an turo qofar dakin, nasan yarana
dukka suna makarnata kuma lokacin tashinsu beyi ba.

Nima rabon ganin wannan baqar rana ya saka ni daukar Excuse din rashin lafiya wai dan na huta na
zauna da Habibina mu sasanta sabanin da muketa samu a dan tsakanin nan ashe ashe....

"Zaman me kikeyi? Ki tashi kisan inda dare ya miki dan gobe nake so azo a sakawa AMIRAH sabon kaya
Zuwa Weekend zata dawo dan haka na baki grace of today ki hada ya naki ya naki kinga yanzu komawa
Gombe dole" kalaman Bashir kenan da suka fi dafin maciji a wurina haka ya juya yabarni ni bame rai ba
ni ba sumammiya ba.

Dakyar na miqe na rarumi hijabi na, dole na nemi inda zan tsugunna kafin qarewar yau nida yayana. To
tunda BASHIR ya iya sakina Allah na tuba watsi dani akan titi kuma ai shi yafi komai sauqi. Kofar gidan na
fito ina tunanin ina zan nufa? Flat din da yake jikin namu ido na ya fada, idan ban manta ba Abokin aikin
Bashir ne a ciki wanda tsautsayi ya fada masa a ka koreshi daga aiki dole ya saki gidan tunda dama Office
ne suke basu dan haka yanzu babu kowa a ciki.

Gidan dake kallon namu na nufa nan kuma Ogan Bashir ne a ciki da nake kira da Baba saboda sunan
Mahaifina ne dashi dukda be haifeni ba amma kadan ya rage, nasan yana gida kaman yanda Bashir yake
nan yau suna hutune company su dan haka na shiga danna door bell ba saurarawa. Banyi zaton nayi
sallama ba lokacin da Anty Matar sa ta biyu ta budemun qofa haka na nausa kai dan fa bazan iya cewa
wallahi ga abinda nakeyi ba ni kaina cikin Sa'a kuwa Baba na zaune a palour yana Kallon News na isa
gabansa na durqusa.

"Hajia Ma'un Bashir" haka suke tsokanata kai kowa na Estate din ma haka yake kirana kadan suka sanni
da Maman Aliyu wasu Maman twins.
"Meya faru" ya fada dan se sannan ya lura da yanayin fuskata. Banyi kuka ba amma kallo daya zakamun
ka hango zallar tashin hankalin da nake ciki se kawai na tsinci kaina da cewa "Baba Flat din Maman Boda
zakamun hanya a bani haya na shiga yau dan Allah".

"Bangane ba? Me ya samu gidan naku? Ina Bashir din?" Duk ya jero mun wadan nan tambayoyi da daya
kadai nake jin zan iya amsawa dan haka na bude baki dakyar nace masa

"Baba BASHIR ya SA KE NI SAKI BIYU kuma yace na tattara kayana a yau nabar masa gida kafin ya dawo"
na qarasa ina Rushewa da kukan da se yanzu na samu damar yinsa. Kuka nake tamkar raina ze fita inda
Baba da Anty keta faman zabga salati suna qarwa.

"Asma'u ya sake ki fa kika ce? Me kikayi masa har haka??"

Wace ce ASMA'U?

Wanene BASHIR?

Me ASMA'U tayiwa BASHIR da har ta cancanci wannan hukunci haka???

Amsar ku tana cikin Sabon littafi na Me suna WATA KISHIYAR (ALKAHIRI CE KO SHARRI)

Wannan salon na daban ne na kuma tabbatar muku bazan baku kunya ba kuma ina fatan kar ku bani
kunya.

I to tell 10

10 to tell Ozers

WATA KISHIYAR
(Alkhairi CE KO SHARRI)

Na Maryamah_Mrs AM

Page 1

Lagos Nigeria

Cikin sauri nake har hada takaddun ina qara duba agogon hannuna dukda nasan dakyar idan bazan
makara, qarfe Tara jirginmu ze tashi zuwa Kano dan halartar wani conference meeting da aka turani
daga office din mu. Gaba daya befi saura 45 mins Taran tayi ba inda na dan samu kwanciyar hankali babu
nisan tazara tsakanin unguwar tamu zuwa Airport din. Buda qofar dakina da akayi da dan qarfi ya sani
cewa " not now please" azatona daya daga cikin yara nane sedai shirun da naji yasani waiwayawa,
megidan ne da kansa wato ENGINEER BASHIR AHMAD da nake Kira da Baban Ali Yara kuma suna ce
masa Abbi, Aliyu sunan babban Dana wanda Sunan Amininsa ne ya saka masa da ya rasu sati biyu kafin
na haifi Aliyun.

Fuskar sa a hade duk da kasancewarsa dama ba mutum bane me fara'a amma dai ai yanayimun nidai.
Kallona yake kamar yanda nima nake kallonsa fuskata dauke da gajeran murmushi nace "Baban Ali ka
ganni har yanzu ko? Wallahi Amna ce tayi mun shirme tun jiya da dare nace ta zubamun papers din nan
a jaka ashe batayi ba (Amna Qanwata ce kuma Autar mu danake ruqo bayan rasuwar Mahaifin mu da
Mahaifiyarmu ta sake aure).

"Uhm" kawai yace mun yana nufar gaban mirror na, ban damuba na qarasa zuge jakata tareda ratayata
na dauki wayata dake gefe kafin na nufi qofa da niyyar fita

"Idan kin dawo zuwa end of the month ku fara shirya zaku koma Gombe" muryarsa ta doki kunnena,
"To meya faru kuma? Bari dai in na dawo se muyi maganar a nutse" na sa kai na fice daga dakin. Already
Emmanuel Driver office dinmu na waje yana jirana dan haka da sauri na fita ina amsa a dawo lafiyan da
yara suka biyo ni suna yimun.

Bayan na nutsu a bayan motar zuciyata ta tafi tunanin me zamujeyi a Gombe kodai wani abune ya faru a
bangaren sa? To bangarensa mana dan nidai ko da safiyar nan nayi waya da yan uwana kuma ba abinda
akacemun ya faru to ko Matar tasa ta haihu ne? Aa in haihuwa tayi ai kaitsaye zece Amira ta haihu bawai
kawai zakuje Gombe ba. Haka dai naita tunane tunane har zuwa Sanda Jirgin mu ya tashi.

A matuqar gajiye na shigo gida kusan qarfe 9 na dare, se yanzu nai dana sanin qin bari na kwana a Kanon
dan jirgin 6 na biyo na dawo saboda ban gayawa yarana zan kwana ba nasan bazasuji dadi ba
musamman da yake Gobe Saturday ne munsaba zama a gida. Bayan nayi sallar Magriba da Isha naci
abincin da Aliyu ya kawo min, ina zaune tsakiyarsu kowa da hirar da yakeyi mun wani irin farin ciki yana
cikamun zuciya. Tabbas yaya rahma ne, a duk sanda na kalli yara na ina jin tamkar bani da sauran wani
damuwa a rayuwa se fatan Allah ya rayamun su.

Amna qanwata dake matsayin babbar Yata a yanzu nada shekaru 15 tana SS2 se Aliyu shekaru 13 ya
shiga SS1 saboda Jumping da makarantarsu suka masa dan Yaro Masha Allah yana da qoqari tamkar
Mahaifinsa. Jafar ke bi masa se Farida, Abdallah, se yan biyu na masu shekaru 5 Ahamd da Muhammad
su Shidan nan sune rayuwata ban kuma hadasu da komai ba.

Har qarfe 11 muna zaune duk da irin gajiyar da nayi dan har wani ciwo kaina yakeyi, sauqin dana samu
tun a kano na aika da report din komai Office dan haka Weekend din nan bacci zan shaqa. Sallamar
Baban Ali ce ta katse ni na dago ina kallonsa da mamaki dan Duk hirar da muke a zatona yana Dakinsa
dan shi dama be fiya zama ayi irin dogon hirar nan dashi ba, gaba daya muka masa sannu da zuwa ya
Amsa yana nufar dakinsa. Se a sannan na tuna ko kirana beyi ba yaji ya na sauka, Se na miqe nima ganin
kamar baya cikin yana yi me dadi dan in lafiya seya dan tsaya damu ko ze shige dakin ga kuma fita da
yayi da daren nan, tashina yasa suma duk suka miqe mukayi exchanging Hugs kafin Mazan suka nufi
dakinsu matan ma haka.

A tsaye na same shi yana cire rigarsa na qara sa taya shi ina cewa "Ashe baka nan, na tambayi yara
sukace kamar Zoom meeting kukeyi kana daki"

"Uhm" ya kuma amsa mun. Nan da nan naji raina ya baci dan gaskiya ina da saurin Hasala amma fa ina
da sauqin kai rainin hankali ne bana so, to rainin hankali mana ace wani inje kano in dawo a ranar ai ya
tambayeni ya hanya koda yake dama duk satin nan tunda ya dawo Weekend naga yana wani fuzga ban
kula shi ba nasan qiris yake jira ya sauke abinda ita yar Gwal din baze iya mata ba. A raina naja tsaki
tareda cewa "Dan rainin hankali wato ga bolarka can Yarinya ta bato maka rai kazo ka juyemun to bazan
tanka ba". Ganin ya shiga Toilet yasa na fita, dakinan yaran na shiga can na tarar da Ahmad da Moh suna
kwasar Dambe abun haushi wai Jafar na musu waqa Su Casu bame rabasu, haka suke kamar Kaji kullum
fada kamar ko yaushe kuma akan Gado ne saboda Bunk ne dasu Aliyu da Jafar se nasu Muhammad,
Ahmad da Abdallah Babban gado suke kwana su ukun to wai se ace A gadon Yah Jafar za'a kwanta shine
a sama dan haka yau in wannan ya kwana gobe wannan amma rigima irin ta Ahmad se yace sedai dan
uwan ya bashi kwanansa. fada na musu kafin kwantar dasu dukka a gadonsu muka karanta Azkar din
bacci naja musu qofa tareda kashe fitila.

Amna da Farida tuni sunyi bacci suma Adduar na qarayi musu ma ja musu qofar na shiga dakina, jikina
na qara gyarawa tareda daukar wayata na ja qofar na fita. Har Baban Ali ya kwanta ganin rigima yake
nema yasakani kashe fitilar da ya bari a kunne nima na nemi wuri nesa dashi na aje muqamiqina wata
gajiya na sake saukar mun.

"Kufa fara Shiryawa Next week zaku koma Gombe" ya sake fada, sena gyara kwanciyata ina cewa "Allah
ya kaimu dan wallahi na gaji bacci nake so inyi kuma na biye masa surutu zamuyi tayi dan dai yasan
abinda yake fada bame yiwuwa bane tunda na fara aiki ai bama zuwa Gombe se lokacin hutu shima ba
kowanne ba se yayi corresponding hutun Yara da nawa ko kuma da wani babban dalili amma rana tsaka
ana tsakiyar Term yace wani tafiya ko yar Gwal din ce ta haihu wlh bazan bar aikina na tafi ba duk sanda
nai hutu naje mata Barka. Ina wannan mitar bacci yai awon gaba dani da ban farka ba se Qarfe 7 harda
Rabi na safe.

Yau Baban Ali halin fulani ya motsa kenan ko ya tashe ni sallah dan gajiya ce ta danne ni banajin ko juyi
nayi a baccin nan. A gurguje na dauro Alwala nai sallah bayanna idar da azkar dakyar na miqe dan bawai
baccin ya sake ni bane na fito palour, Amna da Farida na zaune Se Ahmad dake bacci a kan Three sitter.
A tare suka gaida ni na amsa ina tambayan ina Su Jafar Amna ce tace sun fita Jogging da Abbi

"Kunyi karatun Asuba ne" na tambayesu suka amsamin da eh

Mamaki ya qara kamani amma na dake na shiga kitchen Tea nake so nasha kafin na koma bacci. Kafin na
fito sun koma dakin su har Ahmad sun dauke shi daga wurin dan haka na zauna kan Dining ina shan Tea
ina tunanin meya ke damun Eng ne haka. Haka na qarasa na koma baccina wanda koda na sake farkawa
12 harta gota na rana.
A dakin nai wanka na shirya kafin na fito ina jin gajiyar ta sake ni. Palour kamar Gidan biki saboda
hayaniya Farida da Jafar na musu akan wani film da suka kalla. Da gudu Ahmad da Moh suka nufoni har
suna neman kadani na riqe hannayensu muka qarasa cikin palour.

"Ina Abbi" na tambayesu dan koda na farka ban ganshi a dakin ba kuma dai nasan Saturday Sunday yana
gida seda babban Dalili yake fita kafin su bani amsa ya shigo da sallama ciki ciki, kallo daya yamun ya
dauke kai tareda nufar kan Dining ya aje abunda ya shigo dashi, jin an fara kiran sallah yace su tashi suyi
Alwala suka wuce masallaci da Mazan mu kuma muka tayar da tamu a Gida.

Abun mamaki bayan sun dawo kuma se gashi ya zauna a palour tareda yaransa suna hira dan nidai
kitchen na shiga na fara qoqarin dora mana abincin rana dan na dare a waje zamu je muci in yaga dama
kenan. Da wuri na gama dan Garnished spaghetti na mana se na dumama Grill Fish din daya shigo dashi
ko a ina ya samo da safen oho. Farida da Amna na kira suka jera komai akan Dining kafin muka zauna
gaba daya banda Abbi dake amsa waya sena dakata har ya gama sannan na masa maganar Abincin.

"Kifin kawai zaki kawomun da juice" ya fada. Ban kawo komai ba dan nasan spaghetti bata wani dame
shi ba amma dai yana ci musamman irin wadda nayin, na hada abinda ya buqata na kai masa sannan na
koma muka ci gaba da cin abincinmu. Koda muka gama wurinsa Twins suka koma da Abdallah Jafar da
Aliyu suka kwashe kwanuka zuwa kitchen tareda wanke wa Amna da Farida kuma daki suka shiga Farida
zata yiwa Amna tsifa. Nima palour na koma muka hadu muna yar hira sedai abinda na fahimta Baban Ali
yaransa kadai yake amsawa dana saka baki se naji yayi shiru tsam na miqe Ahmad ya tashi shima ze bini
dan haka yake indai muna gida da na dauke qafa ze aje tasa nace masa "koma ka zauna aiki zanyi" ban
ma shiga dakinsa ba na shige nawa.

Kwanciya nayi kan gadona ina replying whatsapp messages daga nan muka shiga hira da yayata Alawiyya
da muke Uba daya, tamu tazo daya nan na shiga bata labarin abinda Baban Ali ya tsiro dashi kuma.
Dariya tayi tana cewa "kedai da Engineer Miskili kafi mahaukaci ban haushi" nan muka ci gaba da firar
mu ban san lokaci ya tafi ba seda naji ana kiran La'asar.

A dakin nayi sallata ina idarwa na shiga wanka, daidai na fito naji Knocking nasan yaran ne basa
shigomun daki sena basu izini koda kuwa Ahmad da Muhammmad da suke qanana. Bayan na amsa
Abdallah ya shigo, sak kamanninsa da yanayin Miskilancinsa irin na Bashir ne sedai duk cikin yarana ya
fisu haquri wannan kuma halin takwaransa wato mahaifina ya gado. Cikin sanyinsa Yace "Mami Wai Abbi
yace kiyi masa text na abinda zamu taho miki dashi".
Se naji wani dus kamar yaya na masa text? Ba tare zamu tafi ba? Har na bude baki da niyyar tambayarsa
se kuma na fasa nace masa " Kacewa Abbi ya leqo ina son magana dashi". Da toh ya amsamin kafin ya
fita ya barni da mamakin wannan sabon rainin hankalin.

Abbi

Lokacin da yaron ya gaya masa saqon har sun shiga mota ya ma kunnata, ganin idon su ya sahe cewa
yana zuwa ya fito yana qara daure fuskar sa. Tana shafa wa santala santalan cinyoyinta mai ya sameta,
yaso ya shagala da binta da kallo dan a duniya ASMA'U takai duk inda mace ake so takai, Asma'u mace
ce guda harda Rabi wallahi ta ko ina ta hadu bakuma ze taba manta halaccinta a rayuwarsa ba shikansa
ya kasa gane dalilin da yasa yake mata wasu abubuwan. Waiwayowan da tayi tana qoqarin sakin towel
din jikinta dan sam bata ji motsinsa ba yau saurin juya fuskarsa dan a wannan bangaren baya taba iya
tsallake tarkonta. Jikinta tamkar Magnet yake ga idonsa, a kullum gani yake kamar qara mata kyau da
sura akeyi Ma'u bata tsufa.

"Au Abbi ka shigo ashe, Ban gane me Babana yake fada ba yau kuma danwaken zagaye zakumin kenan"
na fada ina cigaba da zura rigata dan nayi sauri na shirya nasan Bashir baya son jira sam a zatona ma
dalilin daya sa zasu fita su barni kenan.

"Nop banyi niyyar fita dake bane, kiyimun text din abinda zaki ci mu taho miki dashi in kuma beyi miki ba
shikenan" kawai yasa kai ya fita.

Se na raka bayan sa da kallo kawai kamar wata doluwa, " tofa Baban Ali kodai gamo yai da Aljanu ne" na
tambayi kaina ina qara cika da tsabar mamaki.

Share

Share
WATA KISHIYAR

(ALKAHIRI CE KO SHARRI)

Na Maryamah_Mrs AM

Page 2

WATA KISHIYA(ALKAHIRI CE KO SHARRI)

Ni kadai tsuru kamar mayya a gida har qarfe 10pm ga gyangyadi inayi amma na kasa shiga daki na
kwanta saboda tsoro gashi har sannan basu dawo ba. Tsayuwar motarsa da naji ta sani miqewa daidai
lokacin da Ahmad ya kwaso da gudu yana kwallamun kira "Mami Mami"

"Na'am Ahmad meya faru" na fada ina tare shi, labarin inda sukaje ya fara bani, gurin wasan da ya kaisu,
Favorite restaurant dina sukaje suka ci abinci daga nan suka tsaya Cinema sukayi kallo abinda ya saka su
yin dare kenan.

Saboda gajiya kowa dakinsu suka nufa, dakaina nayiwa Twins wanka na shirya su kafin 11pm gida yayi
tsit duk sunyi bacci sannan na shiga dakina raina yana suya,

Tsabar bacin rai ko takan take away din da sukamun ban bi ba nima wankan na shiga ina sake danne
zuciyata na shirya na nufi dakin Baban Ali.

A kan gado na sameshi yayi daidai yana amsa waya fuskarsa dauke da wani shegen murmushin da bazan
iya tuna rabonda yayi mun shi ba ko ba'a fada ba nasan da Amira yake waya dan Baban Ali bashida
kwashe kwashen yammata, Ada ni kadai ce a rayuwarsa kafin ya kwaso min Alaqaqai.

Wayar dana tarar yana yi ita ta qara bata mun rai saboda wannan ai wulaqanci ne ko? Nasan matar sa ce
amma ya kamata nima ya mutuntani idan zeyi wayarsa se ya nemi kebantaccen wuri bawai cikin dakina
akan Gado na ba, wannan sabuwar ta'asar da ya samu ta fara kaini bango dan haka ban san sanda na
saki wani wawan tsaki ba ina janye ido na daga kansa bayan mun hada ido.

"Ke dawa kike tsaki?" Ya tambayeni still wayar na kunnensa.

"Ni da waye a dakin" na fada raina na qara quna.

"Anty ce ko" na jiyo muryar Amira na tambayar sa daidai sanda na duqa kusa dashi dan na dauke Safar
daya ajiye akan gadon sena daga sauti yanda nasan zata jiyo nace "Nice din yar iya ko kina da magana
ne"

"A ko yaushe ina gaya miki ki ringa jan girmanki ko? Amma shikenan" ya fada yana miqewa daga kan
gadon ya nufi qofa. Wani baqin ciki ya tokare mun wuya, kawai na haye gadon na kwanta tareda fashe
wa da kuka.

Duk yanda nake daurewa se Bashir ya qure ni tunda ya auri yarinyar nan ban sakeyin sati ba tare da nayi
kukan baqin ciki ba shikenan ni a haka zan qare? Bansan sandaya dawo dakin ba na dai farka cikin dare
naji mutum ya kwaqumeni aiko na ingizashi da qarfi har seda ya farka na tashi daga gadon na shige
toilet. Fitsari nayi na dauro Alwala, hijabina na zura na fara jero Salloli tare da dogayen Addua.

Kamar kullum a duk sanda muka samu sabani na fara sallar dare nan haka ze zabga tagumi yana kallona
in ya gaji shima ya to Alwalar ya tada Sallah (bawai dan banayi ba Aa nafi tsawaita Idan mun yi fada dan
karna kwanta kusa dashi dan duk bala'i bama raba gado ) nasan me yake tunani qila qarar sa nake kaiwa
gurin Allah ko wallahi ko daya duk abinda Bashir yake mun ban taba yi masa Allah ya isa ba sedai ma in
roqi Allah daya yafe masa ya kuma bashi ikon Yin Adalci a tsakanin mu ya ci gaba da bashi yanda zeyi ya
kula damu. Ko ba komai nasan Bashir yana sona nima kuma ina sonsa to ban rabu dashi a lokacin Matsi
ba se yanzu da dadi ya samu se in tafi in barwa yar taka haye?? ina ba wannan magana.

Ban sallame ba har seda aka kira sallar Asuba, ina kallonsa ya fita masallaci kafin nima na tashi nayi
Raka'atanul fajir sannan na bada Farillah. Rashin samun bacci cikin dare yasa ina idarwa ko Azkar ban
samu yi ba na koma bacci, sanda na farka goma harta gota dan haka anan dakin nayi wanka na shirya
kafin na fito palour.
Ko ina qalqal sun gyara dan ko kadan banyi wasa wurin koyawa yarana aikin gida ba komai nidasu
mukeyi bani da me aiki tunda har kuma yanzu dana ke fita aiki da safe kafin mu fita mukeyin komai
tunda kuma ba wuni muke a gidanba baya yin datti. Babu kowa a palor se Baban Ali yana aiki a system
dinsa ya dago yai mun kallo daya tareda mai da kai ya cigaba se na qarasa kusa dashi ciki ciki nace masa
ina kwana dan har yanzu haushin sa nake ji, se ya amsa ba tareda ya kalleni ba.

A dakin Boys najiyo hayaniya da alama PS sukeyi tunda suna da Tv a dakin nan suke yin Game dukda
lokaci da yawa yana dauketa saboda karsu shagala da wasa a qi karatu amma Weekend dama aikin
kenan wani sa'in hardashi zasu hada anan palour suyi.

Kitchen na nufa dan naga sun kwashe kayan kan dining, a roba na tarar da dankali ciki ruwa an yanka su,
nasan Amnace ta ajiyemun tunda tasan nafison dankali da an kwashe daga wuta nan da nan na maida
man da sukayi suya na zuba kafin na debo kwai guda uku na fasa tareda zuba abubuwan da nake da
buqata a ciki, ina kwashe dankalin na maida wani pan din na soya kwai, scramble nayi dan ban fiya son
me fefe ba na juye akan plate din chips na zuba Ketchup a gefe na fito. Ta gabansa na wuya ina juya jiki
tareda baza masa qanshin turarukan dana fesa aikuwa naji yanda yaja numfashi da ajiyar zuciya ina
kuma jin idanunsa akaina har na zauna a dining amma kafin na juyo ya dauke idonsa, girgiza kai nayi ina
sake cika da mamakin Bashir a raina haka naja kayan tea na hada ina ci ina dan kallon drama da akeyi a
Tv.

Har na gama ci babu wanda ya leqo a yaran Gogan ma anata latsa laptop kamar besan Anyi digona a
palour ba sena taso na dawo cikin palour na nemi 1 sitter dake facing nashi na karkace ina latsa wayata
nima. Whatsapp na shiga group dinmu na Secondary na bude aikuwa na tarar da chats bila adadin, ban
samu damar bi ba saboda wasu ne suke qara shigowa se kawai na fara bi daga nan. Ban karanta message
din mutum hudu ba na fuskanci dalilin ubannin messages din dana gani ashe Labor zaayiwa kishiya
(Labor prefect dinmu da muna school kuma abin dadin qanwar daya daga cikin yan ajin namu qawarta ta
hannun dama zaa auro mata, tasan mijin zeyi aure amma bata san yarinyar ba se yau da taje karban
lefen Qanwar Qawarta taga dangin Mijinta ne yan kawo lefen )

Wata muguwar dariya na sheqe da ita har ina kwarewa da ta saka Baban Ali dagowa ya zubamun ido,
yasan Ma'u sarai tabbas mugunta ta gano shine dalilin wannan Dariyar. Be gama tunanin kuwa ba na
fara voice note still ina dariyata nace "Alhamdulillahi layi ya fara ja ashe? To Allah ya qarawa mazajenmu
budi suyi ta auran mana qannemu" na tura ina sake sheqewa da wata dariyar ganin yanda Safiya Sani
Labor keta kumfar baki da daukan Alwashi kala da kala ita ma yayar Amarya Zulaiha Balarabe tana aiko
da nata.
Masifar da Safiya takeyi seta tunamun da lokacin da za'ayimun tawa kishiyar mun hadu gurin gate
together dabanyi niyyar zuwa ba saboda a lokacin bana cikin nutsuwata. A kallo daya zaa gane damuwar
da nake ciki duk na hargitse, na tuna yanda ta sakani a loko tana mun wa'azi.

"Wallahi Asma'u kin bani mamaki kin kuma bata wayonki kamar wadda bata san Allah ba, duk ina
karatun islamiyyar da kikayi? Kin karanta Alqur'ani tsaf kin haddace da fassara amma kina nema ki kasa
aiki dashi. Karin auran nan kinsan umarnine na Ubangiji in har Namiji nada hali da biyu akace ya fara
sedai ko in baze iya adalci ba ko kina so kice Bashir ba Adali bane?? Sannan ma ke ai kiji dadi koba komai
kinsan wadda za'a auro miki ciki da bai baki da fargabar azo a tarwatsa miki gida tunda Ai Amirah kusan
tarbiyyarki ce ma. Haka matar nan ta dage tanamun wa'azi har na sauketa kan layin gidanta mukayi
sallama na wuce a raina ina Addu'ar insha Allahu itama se an mata taji in da dadi (Ni fa alokacin duk
wanda ya bani haquri se na masa Addu'a Allah yasa shima a masa kuma Alhamdulillah gashi tana
karbuwa kuwa ).

Wani mulmulen ashar ta dannomun bayan taji voice dina nan kuwa na samu nayi na ci gaba da kunnata
kafin kace me fada yabar kan Yayar Amarya ya dawo kaina harta na jcewa qila dani aka hada baki nace
oho dai aikin gama ya gama biki saura 2 weeks , wannan nishadi ya mantar dani wanzuwar Baban Ali a
gurin har wurin 12 sannan yara suka fito muka ci gaba da sabgogin mu. Gaba daya dai haka muka cinye
weekend din ba dadi tsakanin mu Monday muka koma aiki. Office dinsa yafi kusa da makarantar yara
dan haka kullum shi yake fita dasu ni kuma tunda ina rigashi tashi sena biya na debo su amma yau bayan
mun fito gaba daya har Ahmad ya kama handle ze bude gaban mota ya dakatar dashu da cewa "kuje
Maminku ce zata kaiku"

Sororo nayi ina kallonsa araina nace meye haka toh sukuwa yara suka dauki Murna dan dama mitarsu
kullum yawanci Friends dinsu Momys dinsu ke kawo su school dalilin ma daya sa na dawo ina dakkosu ke
nan dan da duk shiyake hadawa. Tafiya ta qaru haka nayita sauri gudun makara na samu na ajiyesu
amma dukda haka ni seda nayi latti dan school din tana gaba da office dina innaje sena dawo baya while
shi kuma yana gaba da school din dole seya wuceta zeje nasa office din.

Wuni nayi ina mamaki wato duk sati da sabon salon da ze bullo dashi? Allah dai ya kyauta.

A daddafe muka cinye satin kullum kuwa sena makara dan kafin na kaisu na juyo traffic ya fara haduwa,
abun takaicin wani sa'in zamu hadu a hanya har Horn ze mun in na tsaya ajiyesu ya wuce ni abin na qona
mun rai ni kuma nayi alqawarin bazan masa magana ko na tambayi dalilin dayasa yake hakan ba nasan
dai duk sare sarin neman fitina ne in tanka su samu nayi dani a dangi to an dena (Dangin fulani dangin
magana ).

Muna haka Weekend ya zagayo wannan karon ma yaransa ya diba suka fita yawonsu, abunda ya
ragemun haushi ranar Saturday wuni nayi rama baccin gajiyar sati daban samu nayi ba danayi sannan
Sunday fita mukayi nima da Matan layin mu dama muna haka once in a month zamu hada picnic muje
beach a dan warware takaicin Namiji mu shaqi iskar duniya to wannan Lahadin ma can muka wuni dan a
gida na fita na barsu ma muka dawo kusan lokaci daya.

Yanda Bashir ya tsume haka nima na tsume na fita a sabgarsa sam tunda haka yake da buqata ina jinsa
ze raba dare yana waya da Amaryarsa har inji yana ce mata tayi haquri ta kusa dawowa kusada shi ai,
wani lokacin naji haushi wani sa'in nayi mamaki kai Namiji dai a barshi kawai.

A da idan aka cemun Bashir ze sake kallon wata mace da sunan soyayya zance qarya ne amma daga
sanda ya koyamun hankali ko ji nayi mace na shan Alwashi akan Namiji zan dakatar da ita dan tabbas
Akan Bashir na sake yarda da akace Namiji Badan goyo bane (Inji Asma'u fa 😁).

Ranar Laraba na tashi da ciwon kai da ya saukar mun da zazzabi, ina nade akan gado har Bashir ya fita
masallaci, a zaune na iyayin sallah ina idarwa na koma kan gado na nade har ya dawo ya fara shirye
shiryen fita office. Dukda ya ganni akwance which is unusual hakan be saka ya tambaye ni dalili ba
abinda yai matuqar qona mun rai ace har mun kai matsayin haka kamar wasu maqiya to wai duk me yayi
zafi ne?

Seda ya gama shirinsa tsaf sannan ya kalleni

"Yau bazaki je aiki ba kenan? Se ki tashi ki miqasu karsu makara" yasa kai ya fice daga dakin. Wasu
hawayen baqin ciki ne suka fara tsere a fuskata, idan Bashir ya gaji da zama dani gara ya fito ya fada mun
yafi wannan Kisan mummuqen da yakeyimun ai, shigowar Jafar ta sakani share hawayena, ya matso
kusa da ni yana cewa

"Mami mun shirya fa ko Abbi ne ze kaimu yau?" Cikin muryata da kuka ya fara dishewa nace mace

"Kuje maza ku bishi Jafar bani da lafiya"

Nan da nan fuskar yaron ta chanza zuwa tausayi yace "sorry Mami kinsha magani toh?
Bari na hado miki breakfast to Abbi baze kaiki Asibiti ba?"

Dole na qirqiro murmushin dole nace "it is not that serious Jafar Kaina ne yake ciwo nasan stress ne
dana qara hutawa ze dena, maza kuje ku tafi and don't tell your brothers ku wuce Makaranta kawai
Allah yai muku Albarka ya bada Ilimi me amfani" na qarasa ina dafa kansa se ya amsa da "Amin Mami
Allah ya baki lafiya, Bye love you" ya mun peck a goshi ya fita da sauri dan su kansu kwana biyu ba wani
gane kan Abbin suke ba.

Yana fita na miqe dakyar na tsaya bakin window ina hangensu,

Shiya gaya musu Abbi ne ze kaisu dan haka suka fita da sauri dan har ya gama Shan Tea ya fita yama
kunna mota. Da ido ya bisu ganin sun jere masa a gaba, cike da baqin miskilancinsa yace " yadai kunzo
kun mun layi a gaba?"

"Abbi Mami ce tace kai zaka kaimu bata da lafiya" cewar Jafar.

Seda gabansa ya fadi jin bata da lafiya dan ciwon Asma'u ba abune me sauqi ba, irin mutanen nan ce da
suke dadewa basuyi ciwo ba amma in ya kwanatar dasu kamar bazasuyi ba. Harya niyyata daya koma
yaji me yake damunta se wata zuciyar tace masa qila dan taja attention dinsa ne ya sakata kwanciya tace
musu bata da lafiya dan Asma'u can pretend yasanta sarai dan haka ya qara gintse fuska tareda bude
qofar sa ya shiga yana cewa "kuje ku ce mata tazo ta kaiku you are getting late"

"Abbi kana jifa yace bata da lafiya base ka kaimu ba tunda hanyar zaka bi" Farida ta fada dan ita yar gaba
gaba ce daman, be amsata ba yai wa motarsa key ya qara gaba se suka rakashi da idanu gaba daya
kamar yanda nima Mamakin sa ya nemi kashe ni a tsaye BASHIR dai shine haka? BASHIR dana sani me
jarabar son yaya da tattalinsu kamar kwai, to kodai shiga tsakanin mu akayi da BASHIR ne?????

WATA KISHIYAR

(Alkhairi CE KO SHARRI)
Na Maryamah_Mrs AM

Page 3

A salube suka shigo gidan gaba daya suka zauna A palour banda Abdallah daya zarto dakin da nake, yana
ganina ya wullar da school bag dinsa ya taho da gudu jikina se ya sa kuka, nasan kukan me yake Abdallah
akwai son karatu indai ba ciwon gaske ba baya Missing school.

Bubbuga bayansa nake da sigar rarrashi ina qoqarin hana nawa hawayen fitowa.

“Mami kinga Abbi ya tafi ya barmu kuma Yah Jafar ya gaya masa bakida lafiya amma ya tafi” ya fada in
between tears, se na jashi zuwa gefen gadon dan jin kaina yana dada sarawa ga zazzabin na sake
ruruwa.

“Ka dena kuka, sauri yakeyi yana da meeting ne shiyasa”

“Mami bafa yanzu bane se 10 naji yana waya da Uncle Samuel ai”

“Abdallah bana hana ka ba, idan babba ya fada maka magana ka dena jayayya”

“Amma Mami...”

“Shiii ya isa kirawo mun Amna se na kira muku Uber ya kaiku” na katse shi dan bana son aja maganar,
fita yayi ba jimawa Amna ta shigo itama fuskarta da damuwa.

“Ki dauko wayata kiyi muku order Uber bazan iya driving ba bana jin dadi” na fada mata ina kaiwa
Kwance jin jiri na dibana.

“Mami ko mun tafi ma kafin muje mun makara bazaa bude mana get ba sedai kiyi waya ki fada bazamu
zo ba”.

Agogo na kalla tabbas kafin a samu uber su tafi lokaci ya qure dan haka na miqa mata hannu ta bani
wayar, Number da suka tanada dan wani uzuri nayi dialing dakyar ina ringing kadan suka amsa, cikin
muryata dake nuna halin da nake ciki nayiwa receptionist din bayanin Bazasau samu zuwa ba bani da
lafiya Abbinsu kuma yayi tafiya, fatan samun sauqi tayimun tareda cewa idan gobe ma babu me kawo
ayi musu Registration na school bus tunda tana zuwa har nan estate din namu, shaf na manta da zancen
ma school bus se yanzu dan haka ba bata lokaci nace tayi kawai.

Har na gama Amna na tsaye bayan na aje wayar tace “Mami in kawo miki ko tea kisha se kisha
Paracetamol kafin Abbi ya dawo kuje Asibiti?”

Kai na daga mata ta fita ba dadewa se gata da try ta doro tea se toast bread da kuma paracetamol da
ruwan roba. Da daddaya suka shigo suka mun sannu har sannan Amna na tsaye seda na shanye ta
ballomun maganin nasha nakwanta sannan ta fita.

Koda na farka bayan Azahar na danji dadin jikina dan zazzabin ya sauka sefa ciwon kan da sauran jiri da
nake ji, wanka na lallaba nayi na dauro Alwala a raina ina qara mamakin Baban Ali da haryanzu ko waya
beyo yaji sun tafi ko basu tafi ba. Agunda nai sallah na zauna naji anyi knocking, izinin shigowa na bada
Aliyu ya shigo da Sallama hannunsa dauke da Babban try da suka dora abinci.

“Mami kin tashi tun dazu muke leqowa kina bacci”

“Na tashi Yaya (haka nake kiransa saboda qannensa su saba) ina su Ahmad naji shiru?” Na tambaye shi

“Bacci suka kwanta bayan mun dawo daga masallaci, Maman Ruth ta shigo muka ce mata kina
bacci(Maman Ruth maqociyarmu ce)”

“Lallai an samu yanda ake so bacci yanzu, me kuka dafa ne” na fada ina jawo try din gabana.

“Irish porridge Yah Amna ta miki mu kuma Rice and Beans muka ci da fish”.

Kwanon na bude faten se tururi yake da qamshi kai kace Wata babbar chef ce tayi girkin. A plate na zuba
wanda zanci muna dan hira da Aliyu har na gama ya kwashe kayan ya fita se nima na fito palour dukda
dauriya kawai nakeyi amma kaina yana ciwo sosai, ban idasa zama akan kujera ba wani irin jiri ya kwashe
ni daga nan ban sake gane komai ba nidai na farka kawai Na ganni kwance a gadon dana tabbata na
Asibiti.

BASHIR
Tunda ya bar gidan hankalinsa ya kasa kwanciya, har ya kai get din estate din ya juyo da niyar daukansu
se kuma Shedaniyar zuciyar da take ingizashi ta sake yi masa fanfo. Har ya kai office yana tunanin sun
taho ko basu taho ba lokaci lokaci yana duba Mirrow koda ze hango su a bayansa amma shiru harya
wuce makarantar tasu. Yana shiga Office be zauna ba ya kira layin makarantar ya tambaya ko sunzo nan
matar ta sanar dashi Madam ta kira ta bada excuse ai haka ya aje wayar jiki a sanyaye jin dagaske dai
ashe bata da lafiyar ba lambo tayi ba kaman yanda yayi tunani, duk haka ya shiga aiki sukuku babu kuzari
har sanda ya shiga Meeting kafin su shigama yana Kallon kiran Amira amma yaqi dagawa dan se yaji
yana jin haushin ta ita ce ummul Aba’isin ta komai da yake faruwa ai.

Tun yana sallar Azahar da be samu yi ba se qarfe uku bayan sun fito daga dogon meeting din da suka
share awoyi sunayi wayar sa take ta qara dan ya manta be sakata a silent ba, yana sallamewa wani kiran
ya sake shigo wa ya zarota a fusace dan ya ayyana Amira ce kadai zata iya masa irin wannan kiran
mahaukatan sedai ya cika da mamaki ganin Number Asma’u da yayi saving da MA’UNA akan screen. Be
kai ga dagawa ba ta yanke kafin ya yi wani abu aka sake kira se yai saurin dannawa dan tabbas yasan ba
lafiya ba.

Muryar Aliyu ce cikin kuka yake ce masa “Abbi kazo Mami ta yanke jiki ta fadi tun dazu bata motsi” ai se
yaji tamkar a saka guduma an bugi kwakwalwarsa Asma’u ta fadi meya sameta? Innalillahi.

Ikon Allah ne ya kawo shi gidan kawai yana shiga ya tarar dasu a zagaye da ita suna kuka kamar wadanda
aka cewa ta mutu se ya matsa da sauri ya dagota yana jijjigata “Asma’u Asma’u ya shiga kiran sunanta.
Danshin da yaji a hannunsa daya tallafo qasan ta ya saka shi duba wurin Jini ya gani wanda duk basu lura
ba se yanzu ai kuwa yaran suka sake rudewa da Kuka kamar me shikansa dauriya yayi ya dagata tareda
cewa Amna da Aliyu su fito suje Asibitin sauran Yaran kuma yace su Shiga gidan Maman Ruth kafin su
dawo dan Anty(Amaryar Ogan sa ta take flat din dake kallon nasu) ta tafi Zamfara garinsu bikin
qanwarta.

Bashi da Nutsuwar da ze ja mota dan haka yau Amna da kullum yaga Asma’u ta bata driving se yayi bala’i
to gashi yau ta masa rana, ita kanta jikinta rawa yake cikin ikon Allah dai suka qarasa asibitin dan basu da
nisa sosai.

Emergency a ka karbe ta, bayan kusan Hour daya Dr Bolaji ya fito daga dakin da suka shiga da Asma’un.
Alama yayi wa Bashir daya biyo shi office

Se ya kalli Amna da Aliyu da fuskokinsu suka kode saboda kukan da suka sha,
“Ku jirani a nan ina zuwa” ya fada tareda bin bayan Dr Bolaji.

Bayan ya nutsu a office din Dr Bolaji ya kalle shi tareda turo masa takardar daya gama rubutu.

“Strees da damuwa suka hadar mata har ya jawo jininta ya hau sosai shine kuma yai sanadiyyar fitar
cikin jikinta, ga wannan kaje ka kai Pharmacy zasu baka bill na kayan da akayi amfani dasu se ka karbo
wadannan magungunan kuma, Allah ya taqaita abun amma ku kiyaye faduwa irin wannan ko a gaba ze
iya jawo mata Paralyze bama dai fatan hakan” Dr Bolaji ya fada cikin harsheb turanci yana maida kai ga
takaddun dake gabansa, kamar kazar data sha ruwan zafi haka Bashir ya miqe ya nufi Pharmacy din dan
karbo magunguna.

Sanda ya dawo ya tarar da Nurse ta fito daga dakin da Bedsheet a hannunta daya baci da jini da kuma
kayan jikin Asma’u da suka kawota dasu. Tambayan ta yanda zaayi da maganin yayi tace ya shiga dasu ya
ajiye zata dawo yanzu seya tura qofar dakin a hankali ya shiga.

A ciki ya tarar da Aliyu da Amna kowannensu na share hawaye nan da nan yaji shima hawaye da be zata
ba sun sakko masa, shikenan ya rasa Babyn da be masan dashi ba. Allah ya dorawa Bashir jarabar son
Yara a rayuwarsa, ya kance shi beqi ya haifi yara Ashirin bama in ya fadi haka Asma’u se tayi dariya tace

“Haba se kace Akuya in dai ba kuma mata hudu zakayi ba”. A lokacin ya kan ce mata ke zaki zama Akuyar
kuwa kiyi ta zubo su dan kinsan nidai babu gurbin wata mace bayan ke a cikin rayuwata. ko bayan data
haifi Yan biyu Asma’un taso tayi planing acewarta yaran sun isa haka amma ya fitittike yace idan tayi
koda be sani ba be yafe ba dan shi yana son yaga ya tara zuri’a masu yawa kuma Alhamdulillah yanzu
Allah ya hore masa yana da yanda zeyi ya kula dasu, yasan bazatayi ba shi yasa dadewar da tayi bayan
Yan biyu be dame shi ba yasan daga Allah ne bayan haka dama ance in shekaru suka fara ja haihuwar na
ja baya ita ma kuma Asma’un na kusan shekaru 33 ne yanzu.

A hankali ya ajiye ledar kan drawer dan Nurse tace karsuyi motsi me girma daze farkar da ita ya qarasa
gefen gadon yana kallonta tayi wani fresh tana bacci kaman bame ciwo ba se ya rankwafa kanta tareda
kissing goshinta, under his breath yace “get well soon my Ma’u, I’m sorry for hurting you”.
Zaman kurame sukayi shida yaran kowa na tunanin abinda ya dame shi basu Ankara ba se jin kiran sallar
Magriba sukayi se a sannan ya tuna ai ko La’asar beyi ba. Shida Aliyu suka tafi masallaci har suka dawo
kuma bata farka ba dan haka cikin damuwa ya koma gurin likita yana gaya masa.

“Babu damuwa mun mata Alluran bacci ne dan ta samu ta huta sosai jinin ya sauka zata farka amma se
zuwa cikin dare, kaje kawai kayi settling bills babu buqatan me jinya Nurses din mu zasu kula da ita”.

Jiki a sabule ya koma dakin, Gurin da Su Aliyu suke ya kalla yace su tashi su tafi gida

“Abbi ni zan kwana a nan” cewar Amna

“Aa baa barin me jinya mu tafi da safe kafin ku tafi school se mu biyo ku dubata”. Dakyar suka tafi har shi
kansa ji yake kaman ya sake zama sedai tuna sun bar sauran yaran yasa dole suka tafi bayan ya biya
kudin duk abinda ya kamata ace ya biya din.

ASMA’U

Basufi awa uku da tafiya ba na bude ido lokacin qarfe tara na dare harta dan gota, jinina yana da qarfi
sosai ba kasafai Allurar bacci take daukata na dade ba. Sakayau na tashi kaman an zare mun qaya dukda
bansan ainihin abinda ya same ni ba amma babu ciwon kan babu jiri se kawai kasala da nake ji da kuma
bakina da sam ba dadi. Ina qoqarin miqewa Nurse ta shigo tana ganina ido biyu ta fada da fara’a tana
cewa “Sannu patient har kin farka lallai kina da qarfin jini muda muke tunanin se kin kai gobe ma”

“Murmushin na mayar mata cikin muryar marasa lafiya nace “gashi har na tashi kam amma naji dadin
jikin ma sosai ai”

“Karki tashi Bari na sake duba Bp na gani” ta fada ganin ina qoqarin miqewa daga gadon, zama na koma
nayi ita kuma ta dauko Abun auna BP, seda ta gama ta kalleni still tana murmushin tace “kinga kuwa yayi
normal bari na hada miki ruwa to ki wanke jikinki dukda naga bakiyi staining bama se kici abinci”

Kallon rashin fahimta na bita dashi fahimtar haka ya sakata Dafani tace “I’m sorry kin samu miscarriage
saboda faduwan da kikayi”

“Miscarriage kuma? Cikine dani daman?”


“Eh almost 3 months ma baki sani ba?” Ta jefin tata tambayan, se lokacin na gane a fili nayi magana.
Sena qaqalo murmushin dole to ban ma san me zance ba dadi zanji ko rashin dadi ma oho nan ta barni
ta shiga toilet din, mintina kadan ta fito bayan ta tara mun ruwan. Ita ta rakani har toilet din kafin ta
baroni na fara wankan.

Sosai naji dadin ruwan bayan na gama nayi brush da sabon tooth brush din data ajiye mun na saka pant
da pad da duk a nan na gansu sannan na daura sabon towel babba na rufo kaina da qarami na fito ina
jina wata sakayau a raina ina yaba tsarin Asibitin komai nasu tsaf kamar A Turai.

Turus na tsaya kofar toilet din ganin Mutum a zaune bakin gadon dana tashi wanda da alama an kuma
chanza bedsheet din kai, haka kawai na tsinci kaina da daure fuska abinda yai ma yara da safe yana
dawomun se kawai na juya da niyyar komawa cikin toilet din yai zuruf ya miqe tare da biyo ni kafin na
samu damar rufe qofar ya turo ta ya shigo ciki bani da zabi kawai na durqushe a qasa na fashe masa da
kukan da ban san nima na menene ba

WATA KISHIYAR

(Alkhairi CE KO SHARRI)

Na Maryamah_Mrs AM

(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)

Page 4

Zama yayi shima a qasan tareda janyoni jikinsa ya rungume yana bubbuga bayana a hankali, cikin
qaramar murya yake cewa “I’m sorry Ma’una I’m sorry” ni kuwa kaman yana cemun ki qara volume ne.
Kuka nake dagaske kukan takaicin daya dade yana shaqamun, qara tuno wasu abubuwan nake ina
qarawa kukan nawa Armashi nasan Bashir baze hanani ba zebarni nayi iya yina ne a cewarsa kuka rahma
ne idan yayi yawa ne yake zama matsala.
A duk sanda irin haka ta faru ko yayi mun wani abu da har takaini da zubda hawaye dama shi ba Namiji
bane me bada haquri duk kuwa girman laifin da yayi zedai saurare ki da kunne duk irin mita da qorafin
da zakiyi se kinci babbar Sa’a ne zece miki “Uhmm” in ta kai maqura daya san shi yake da laifi shine ze
rungume ni a jikinsa nayi kukan iya yina yana bubbuga baya na har nayi shiru dan kaina to yau an Auna
arziqi har na samu arziqin sorry, Miskili kenan aka ce kafi mahaukaci ban haushi.

Se ya tunamun da lokacin rasuwar mahaifin mu kamar haka ya riqeni nai kuka a jikinsa har seda naji
wani kaso na radadin zuciyata ya ragu sannan ya rabu dani ya koma gurin karbar gaisuwa.

Nurse ce ta dawo dakin, sheshshekar kukana da ta jiyo daga toilet ya sakata bude kofar da sauri a
zatonta ko wani abun ne ya same ni amma se ta tarar damu

“Haba Alhaji ya zaka barta tana kuka bayan kasan condition dinta please patient taso ki zo ki saka kaya a
jikinki kar sanyi ya kamaki”. Fincikewa nayi daga jikinsa na fito ina ci gaba da sheqa kukana, kamar
qaramar yarinya haka ina saka kayan baccin data ajiyemun ina kuka har na gama na dauki Mug din tea
data hadamun na hausha ina kurba ina kuka kai abun ma abun dariya. Tsayawa tayi kawai tana kallon
ikon Allah dan Bashir dai ba sabon abu bane a gurinsa indai Rigimar Ma’u ce, ganin dai dagaske nake ya
saka Nurse fita ta kirawo Dr Bolaji.

Tare suka shigo, kallona yayi ya nufi inda Bashir ya tsaya wanda kallo daya zaka masa ka hango tashin
hankali da damuwar da fuskar sa ta kasa boyewa, ban san me yace masa ba naga sun fita waje se Nurse
din ta juyo wurinata miqa mun magunguna data ballo tana cewa “kiyi shiru kishanye tunda ya tafi se ki
kwanta na mayar miki da drip din”

Shirun nayi ina jan majina da ajiyar zuciya hancina kuwa yayi jajir kamar me mura na hadiye kwayoyin
tare da gyara kwanciyata raina Fes, a zuciyata nace “Wallahi kadan ka gani yanda zanyi kwanan Asibiti
dalilinka kaima bazaka runtsa da dadi ba, ko minti goma ban qara ba bacci ya sure ni ga gajiyar kuka ga
allurar baccin data qara a ruwan ko na samu na huta.

Daga ita har Dr Bolaji daya dawo kallona kawai suke Dr yai murmushi ya nufi qofa yana cewa “This
Madam na correct trouble maker”

Nurse ta saka dariya kawai tabi bayansa dan dakko abubuwan da zata buqata ita zata kwana dani.

BASHIR
Tuqi kawai yake gaba daya baa nutse ba kansa in banda sarawa babu abinda yakeyi, a duniya babu
abinda yake rudashi da hargitsashi irin Asma’u. Matar nan Tasan duk wani lungu da saqo da zata shiga ta
tado masa da hankali (kuji fa) in banda fitina irin tata shi yanzu ai ta lafiyarta yake yi amma yaga alama
ita neman tada zaune tsayene kawai a gabanta yanzu. Yana tafiya yana jin yadda wayarsa take ta faman
vibrating Daidai ya faka motar kira ya sake shigo masa, a mugun fusace ya daga dan yasan Amira ce.

Tun dazun ya gaya mata yana da uzuri idan ya gama ze kirata amma shine take zabga masa kira kamar ta
na binsa bashi a qalla ta masa missed calls sunfi 100. Yana daga wayar ta fara magana cikin Son
kwaikwayon salon da Asma’u take magana dashi tace

“Yayana ina ta kiranka tun dazun baka answer ba kafasan duk yau banji muryar ka ba ga baby ma yana ta
misss.....” tsabar takaici be bari ta qarasa ba ya daka mata tsawar da seda cikinta ya juya sannan ya
cigaba

“Ke wacce irin wawuya daqiqiyar yarinya ce, kin kirani nace in na gama abinda nake zan kira ki amma shi
ne kika ci gaba da kira kamar kina bina bashi ko? Shiyasa Ma’u ta fiki dan ita bata da shishshigi da
wannan mugun takurar, Stupid ki sake kiran wayata wallahi in bani na kiraki ba zakiga hukuncin da zan
dauka akanki” qit ya kashe wayar.

Wani huci yake fitarwa kaman kumurci, gaba daya yaji bala’in haushinta yake ji dan itace ummul
aba’insin ta komai dayake faruwa. Dukda bata shigo rayuwarsa ba da bata juya masa daddadar rayuwar
da suka gino me cike da so, qauna da sadaukarwa ba shida Ma’un sa.

Yafi minti 30 a cikin motar yama rasa tunanin me zeyi se sannan yaran suka fado masa a rai ba shiri ya
fito daga motar ya shiga gidan. Gaba daya suna zaune a palour sunyi zuru zuru alamun sun sha kuka sun
qoshi har yan biyu basuyi bacci ba, suna ganinsa suka nufe shi gaba daya tareda sake fashe masa da
sabon kuka daya sa gaba daya yaji dama shima yayi kukan ko zeji sauqin abinda yake ji a ransa.

Dakyar ya samu sukayi shiru, Amna ya tambaya sunci abinci tace Aa, dare ya rigada yayi dan 12 harta
gota dan haka yace ta hada musu cornflake kawai su sha. A qaton bowl ta hado shi suka hadu kowa da
spoon suna sha yana kallonsu dan bayajin ko ruwa ze iya bita maqoshinsa. “Kai anya ze iya rayuwa babu
Asma’u kuwa?” Ya tambayi kansa

“Idan ta mutu fa” wata zuciyar ta qara tambayarsa


“Kai ina insha Allahu ma sena rigata mutuwa” ya fada a fili ba tareda yasan a fili yake maganar ba da
Alama Ma’u na dab da zarar dashi

Bayan sun gama yace suje su kwanta amma qememe Suka qi yana tashi suka bishi Amna Farida da Aliyu
ne kawai suka zauna a palour, ba yadda ya iya haka ya jera su akan gadon ya shiga toilet ya dauro alwala
ya fara sallah dan yasan bama ze iya bacci ba yau, haka yai ta jera salloli in ya gaji ya huta har bacci
barawo yai nasarar sace shi.

HAJIA AMIRAH

Sororo tabi wayar da kallo hawaye na kwace mata ta kalli Mamanta Adda Fatu da har tafi Amirah kidima
dan a hands free ta saka wayar, ita dama bata so ta sake kiransa ba tunda yace ze kirata amma Adda
Fatu ta sata a gaba dan a yau take so ya aikowa da Amirah kudaden da sukayi qaryar zatayi siyayya
saboda tafiyarta Lagos amma wani uzurin daban take so tayi dasu.

“Adda kin gani ko bamu samu biyan buqata ba yanzu mun ballo matsala Allah kadai yasan yanzu
hukuncin da zeyi mun” ta fada tana share hawaye.

“Ke dalla can ba abinda zeyi miki qarshe ma kiga ya kira ki yanzu ya baki haquri ta yuwu wani ya bata
masa rai kika taka sahun barawo” bata qarasa rufe baki ba sukaji alamar shigowar message wayarta,
baki washe Adda tace “kingani ko duba muga ko kudin ya sako”

Ita dai Amirah jikinta be bata ba dan tasan waye Bashir a tsorace ta bude message din ashe MTN ne suke
gaya mata zata iya aron kati dan nata ya kusa qarewa. Wata muguwar dariya Ummi qanwar ta ta sheqe
da ita tana tashi zaune daga kwanciyar da tayi tace

“Wai ke kin yarda Yaya Bashir ne ze kiraki ya baki haquri to sannu uwarsa, ai wallahi ki shirya ma Allah
kadai yasan abunda ze biyo baya dan kinsan sarai fadansa kamar na kurma yake baya mutuwa”

“To se kijie ki saka shi ya dauki matakin ai dan uwarki shegiya me baqar fuska” Amirah ta fada tana
hayayyaqo mata
“Gata nan a zaune ai uwar tawa baqar fuska kuma na gode keme farar ai gaki nan kin zama Bora a gurin
miji, Allah dai ya rabamu da auran cin Amana” Ummin ta mayar mata dan itama ba baya bace gurin
fitsara. Nanda nan fada ya kaure a tsakaninsu seda Adda Fatu ta zuzzunduma musu Ashar sannan suka yi
shiru kowa tana harar yar uwarta.

“Shegu kuda baku gudun abun magana a daren nan kunsan an kasa kunne a jiyo zancen mu a yada shine
zaku min tijara kishiyoyi naji ni kubarni nayi tunanin mafita ma kun hanani” ta fada tana hararar su duka.
Yunqurawa Amira tayi dan cikinta yayi girma sosai ta shiga daki har tana takewa Ummi qafa da gangan

“Salon na taba ki wani abu ya same ki ko to bazan kula kiba aniyarki ta biki” Ummi ta fada.

“Tashi ki shige kafin na rade ki yar kwal uba” Adda Fatu ta fada tana neman madoki, setayi saurin barin
wurin dan tasan tsaf zata sha dukan kuwa.

Tunani ta shiga yi ta yanda zata samu kudi kafin wayewar gari, bashi ne tun na lokacin Auran Amirah har
yau bata gama biyaba kusan shekara biyu dan a zatonta zasu samu a hannun Bashir din ganin yanda
Ma’u take wadaqa sedai tunda akayi auran ita dai bata ga kyautar dunkulalliyar dubu dari yayiwa Amiran
ba, ze dai aje mata komai na buqata amma baze bata kudi ba.

Ganin ba mafita kuma ta tabbatar kaman yanda matar tace da safe zata biyo kadin kudinta ko kudi ko
kayan kudi tofa rashin mutunchi zata mata dole ta nemi mafita qarshe ta yanke shaqarar zuwa gidan su
Bashir din gurin Nafi ai ita Uwarsa ce idan ta kira shi baze qi dagawa ba, da wannan shawara ta kwanta
akan asubanci zatayi kafin matar tazo insha Allahu ta dawo.

LAGOS

Malam Bashir kuwa dakyar ya iya farkawa da Asuba kansa kaman an dora masa Dala tsabar ciwon da
yake masa, basu iya fita masallaci ba a gida sukayi sallah suka hau shirin makaranta dan zasu fara biyawa
Asibiti su duba Mami.

Tea suka dafa suka soya kwai suka karya, basu daukar mata komai ba se kaya kala daya wanda zata saka
idan An sallameta tunda Asibitin nada uniform na marasa lafiya baa buqatar kaya haka abinci ma a can
ake basu..
A hankali ya tura qofar hadi da sallama, a nutse ta dago ta kalleshi tareda amsa sallmar, fuskarta dauke
da wani kyakykyawan murmushi. Magana take yi da yaranta kowa na gaya mata yanda yayi missing nata.

Qara shigowa yayi idanunsa akanta yana qarewa kyakykyawar fuskarta me cike da kalama kallo ganin
yanda Omo blue din Uniform din Asibitin ya amshi fatar ta matuqa kamar wasu kayan kwalliya. Aliyu ne
ya bashi kujerar da yake zaune akai still idanunsa akan ta yaja ya zauna dukda daqi sake dagowa
ballantana ma su hada idanu da ita.

Shigowar Nurse da taje kawo mata breakfast yasa ta daga kanta Yaran suka shiga gaida Nurse din tana
amsa musu da kulawa, Dan gyaran murya yayi tareda kallon yaran yace “kuje mota ku jirani kar mu
makara idan mun taso se mu sake biyowa aga Mami ko? Basu musa ba da daddaya suka fice bayan sun
mata Addu’ar samun sauqi itama Nurse aje kayan tayi ta gaishe shi kafin tayi waje abunta.

Cikin sanyi jiki ya miqe zuwa gefenta da tun kafin ya qaraso ta dauke fuskarta zuwa dayan side din, be
haqura ba ya bita, can qasan maqoshinya furta “How are you feeling now? Ina ne yake miki ciwo?”

“Oh really ka damu ne daman da lafiyata toh Alhamdulillah Yanda kaso be samu ba jinina ya sauka ya
dawo dadai”. Be kula maganar taba ya sake matsarta yana cewa “Why? Me yasa baki gayamun that you
are pregnant ba??”

Ita se a yanzu ma ta gane dalilin wannan fake concern din wato saboda cikin da ya zube, murmushi tayi
me kama da yaqe tana tashi zaune sosai tace

“Baban Ai kenan, to ina ruwanka da ina da ciki ko bani da shi naga yanzu ai baka damu dani da yaya nane
bako? Ko da yake dama ai bazaka damu ba tunda qaddarace tasaka kuka hada Zuri’a dani

Yanzu ai gashi za’a haifar maka jininka yayan dangi na meye zaka damu akan wanda Allah ya taqaita
samuwarsa bare yazo shima a barshi a titi a bula masa qura ko yaje makaranta ko kar yaje duk ba
matsalar ka bace.

Wallahi Baban Ali kayi nasarar doramun Hawan jini amma ina tabbatar maka bazan bari ka nakastamun
rayuwa ba idan kuwa haka ta faru sedai muyi mutuwar Kasko”.
Kaman wanda aka dasa haka ya bude ido da baki yana Kallon ta, kai wannan Mata wai ita bata yafiya ne
a ko yaushe burinta ta ringa hukuntaka da kuskuren da ka aikata? To in ba haka ba meye na dawo da
wadannan maganganun marasa dadi? Yana shirin maida mata da martani wayarsa ta dauki qara, hadiye
bisashshan yawu yayi kafij ya zaro wayar yana tattara kalaman da ze bata amsa dasuba zuciyarsa.

Sunan “DADA da ya gani ya saka shi saurin daga wayar ya kai kunnensa. Cikin harshen fulatanci ya shiga
gaisheta ta Amsa tana tambayarsa Asma’u da yara.

“Bashir Meya sami wayarka Amirah tace tun jiya tana kira baka dagawa” ta fada bayan sun gama
gaisuwar.

“Qarata ta kai kenan, ai kuwa seta gane bata da wayo” ya ayyana a ransa a fili kuwa se yace

“Dada Ma’una ce bata da lafiya tayi Bari muna Asibiti tun jiyan”

“Subhanallahi a garin yaya” ta tambaya muryarta na nuna Alhini se ya sake narkewa abin tausayi yace

“Nima ban sani ba ina office aka kirani wai ta yanke jiki ta fadi ina zuwa muka hato Asibiti” ya yanko
maganar da shi besan gaskiya ya fada ba ko qarya. Asma’u dai kallonsa kawai takeyi tana qara mamakin
Bashir a ranta, miqo mata wayar yayi seta tsaya kamar bazata karba ba kome ta tuna kuma ta karba.

Sama sama ta gaida Dadan tareda amsa ya jikin da take mata dan itakam ai sun shata ta warke abinda
mutanen nan suka mata ta yaya zata manta dashi?

Kallonta Bashir yake a ransa baya jin dadin yanda alaqar Dada da Ma’u ta lalace be kuma san ta yanda ze
gyarata ba, yasan sun mata laifi amma Ma’u ma akwai ruqo da kafiya ai.

Miqo masa wayar tayi ya karba sukayi sallama da Dadan sannan ya kashe. Hannu yaki ze riqe nata tayi
saurin janyewa se ya girgiza kai kawai yace “Ki kwanta ki huta bari naje mun makara ma idan mun taso
zan ga Dr ance be shigo ba yanzu naji yaushe zeyi discharging naki”

Bata amsa ba shima be saka rai ba dan haka yaja qafafunsa ya fice yana sake kallon Wayarsa dan ganin
da gaskw sun makara din.
Asma’u kuwa da harara ta raka shi kafin ta zumburi baki tana qunquni tace “wato in dawo kaci gaba da
Gallazamin ko toh ba inda zani se na tatike Aljihun ka qat na huta wallahi”

Ita kadai tayi ta sababi har bacci ya dauketa sannan tayi shiru.

Bashir kuwa sauri sauri ya kai yaran har an rufe get dakyar suka karbe su suna ta masa qorafin in suka
sake makara bazasu karbe su ba shida ya ajiye su ya wuce nasa aikin da baya zaton ze amfani komai yau.
Gaba daya shima ji yake kamar bashi da lafiya ga wani mugun bacci dayake jin idon sa yayi fici fici har
wani yaji suke masa,haka ya lallaba ya qara sa office din.

GOMBE

Bayan da Dada ta ajiye wayar se ta maida hankalinta kan yayartata Adda fatu datayi kamar bata gane me
Dada da Bashir din suka tattauna ba.

“Ashe Ma’u ce bata da lafiya tayi bari suna Asibiti” Dadan ta fada.

“Allah sarki Allah ya bada na aike” Adda Fatu ta amsata a ranta kuwa murna tayi gara ma da cikin ya
zube ita duk wadannan yayan data zuba bazata haqura ta barwa Amirah itama ta samu rabonta ba ita
dai fatan ta Allah yasa ba ita Amiran ta gado ba dan ta fara ganin sare sarin hakan, seta gyara zamanta
tana cewa

“Kinga daman maganar shirye shiryen tafiyarta lagos din nan ce lokaci nata tafiya yace ze turo mata kudi
tayi siyya anan kafin ta tafi yanda kinga in lokacin haihuwa yayi ta howa kawai zatayi komai na jiranta a
nan to kuma naga yana nema ya shiriran tar da maganar ga yarinya kuma ko baccin kirki wallahi bata iya
yi to Allah ya hada ta da jarababben ciki gara dai yazo ya tattarata su tafi dan nikam na fara gajia
gaskiya”.

Kallonta kawai Dada tayi ita kam Adda Na bata mamaki da kunya wallahi in ba haka ba ina ita ina irin
wannan magana ai tsakaninsu ne can ko amma ita babu ruwanta tana manta cewa Matsayin Suruka take
a gurin Amira ba kowacce magana ya kamata ta ringa yi da ita b, dakyar ta bude baki tace

“To Adda nake ga siyayya ai bawata matsala tunda in kayane ai can Lagos sun fimu in taje din se su siya
acan su turo kuma ni da zaki ji ta tawa ma da tayi haquri ta yi zamanta a nan tunda yana zuwa sati biyu
dan gaskiya abinda ake shirin yi ba Adalci bane. Yarinyar nan Asma’u mun mata abubuwa da yawa ni
wallahi har kunyarta nake ji to yanzu kuma akace wannan gaskiya ya zama da daukar Alhaki kuma.
WATA KISHIYAR

(Alkhairi CE KO SHARRI)

Na Maryamah_Mrs AM (Marubuciyar Rubutacciyar Qaddarah)

Page 5

“Ban gane ba Nafi me kike nufi da ta haqura da binsa ko baki gane halin da yarinyar nan take ciki bane,
yarinya na buqatar mijinta a kusa idan kuma ba halaka ake so ta fada ba se naji, nifa dama na gane take
takenki kina so ki fifita bare akan yar uwarki ko Nafi. Kuma da kike zancen za’a shiga haqqin Asma’u ita
Amirar daba uwace ta haifeta ba ai ba’a shiga nata haqqin bako” Adda Fatu ta fada cike da jin haushin
Dada, se Dadar ta gyara zama tareda cewa

“Ni ba haka nake nufi ba amma gani nayi ai tun farko tare suke a can, yanzu ko cewa akayi suringa yi
idan wannan ta je ta kwana biyu se wannan taje kinga bame yiwuwa bane tunda Asma’u tana aiki a garin
bakuma ze yuwu muce tabar aikin ta ba tunda idan Amira ce a matsayinta muma bazamu bari a mata ba
ko?

Ni dai a nawa ganin Adda ayi haqurin shi yafi a zauna lafiya tunda har komai ya daidaita tsakaninsu bana
son wata rigima ta sake tasowa kindai san sharadin da Malam ya kafa mun dan Allah bana so ya sake
ganin laifina akan lamarin gidan Bashir”.

Se Adda Fatu ta miqe nan da nan ta fara sababi da fadan maganganu ta inda take shiga bata nan take
fita ba, ga baqin cikin rashin samun biyan buqata a gurin Bashir gashi da Alamu wannan Karon Nafi na
nema ta bata matsala amma ina bazata sabu ba wallahi dole tasan abinyi. Miqewa tayi still tana masifar
ta nifi qofa,

“Wato Nafi kina ganin yanzu kinkai matsayin da zaki qalubalance ni ko? Kin manta duk halaccin da nayi
miki a rayuwa saboda qasa ta dade da cinye Naman Baffa da Inna dole ki watsar da maganar su tunda
kina ganin yanzu kema Kin kawo qarfi. Na gode zan kuma tafi amma daga yau kisa a ranki baki da sauran
wata yar uwa data rage miki a duniya tunda kin zabi Matar danki akaina da Yata shikenan Nafi na yafewa
Duniya ke” ta qarasa tana rushewa Kukan munafunci wanda dashi take cin galaba akan Nafin.

Ta kuwa samu yanda take so dan nan da nan hankalin Dada ya tashi ta shiga son nuna mata ita fa ba
abinda take nufi ba kenan,

“Idan har da gaske kike kuma kina so na haqura nida kawai kiyi yanda zakiyi Bashir ya dauki Amira ta
koma kusa dashi, kuma baze yuwu yace Ze kwashe su su dukka ya kai can ba se dai ki saka shi ya dawo
da daya ya dauki daya idan kikayi haka shine kadai Ze sa na haqura in ba haka ba wallahi ki saka a ranki
baki da wata Yar uwa Fatu a raye”

Ita dai Dada son su rabu lafiya ya saka ta amince mata, dole ta hado yan kudaden hannunta dubu 30 ta
bata tace gashi nan ta kaiwa Amirar ta riqe kafin Bashir din yazo se a san yanda zaayi haka ta rakata har
get Addan na sake jadda da mata fa akan tana nan tana jiran saka mako da haka suka rabu.

Numfashi ta sauke bayan ta dawo cikin palour ta tazauna, gaba daya ta tasa ina zata kama akan wannan
al’amarin. Har ga Allah bata so ta sake yin wani kuskuren akan na baya amma ya zatayi da Adda Fatu yar
uwarta tilo a kaf fadin duniyar nan bata da kamarta. Addan tayi mata komai a rayuwa ya kamata ace ita
ma ta saka mata da abinda ta mata. A zatonta Auran Bashir da Amira ya isa ga tukuicin kyautatawar
amma se yanzu take dana sanin ma aikata hakan domin kamar ta bude wata qofa ce da Addan ta mayar
da ita tamkar birin wasanta.

Ko da yaushe cikin daga mata hankali take tunda akayi wannan auran da ita dai bata ga amfaninsa ba in
banda bacin rayuka da ya janyo da yawa, shigowar Nazir Autan ta ya sakata dagowa ta kalle shi

“Yanzu na hadu da fitinanniyar yayar ki a hanya seda tayi mun fashin 10k wallahi, gaskiya Dada ki ringa
yiwa Adda fada abubuwan da takeyi basa dacewa. A yanzun fa ga kudi a hannunta amma ta tsaya suna
fada da Dan Napep dan yace a 200 ze kaita gida”
“Hmm Allah ya rufa asiri kawai Naziru amma ni lamarin Adda ya fara bani tsoro, yanzu ma fa kaji abinda
ya kawo ta” tiryan tiryan ta labarta masa yanda sukayi.

“Wallahi Dada ki kiyayi matar nan, ni dai ina ga Asiri take yi miki ma kike wasu abubuwan idan ba haka
ba dan ta riqe ki ai ba baiwarta bace ke da kuma zata ringa juya ki yanda taso. Tun farko abinda muka
guda a hadin wannan auran kenan amma kika rufe ido kika ce se anyi zumunchin ku ya qara qarfi ko ai
gashi tun ba’aje ko ina ba kinzo kina dana sani. Shima Yayan banga qaddarar daya gani a jikin wannan
mara mutunchin yarinyar ba daya yarda ya aure ta”

“To Naziru yaya zanyi Adda yar uwata ce da bani da kamar ta ka sani kuma farincikin Yayanta shine nata
idan banyi mata ba a rayuwa ta wa zan yiwa?”

“Ai kuwa gashi nan, kafin da ki sake yanke wani hukuncin se ki tuna cewa Auranki kema yanzu lilo yake yi
a garin faranta mata kuma baza muso ace Uwar mu ta shiga zawarci a wadan nan shekarun ba” ya fada
ya miqewa dan ya fita dan dagaske Bala’in haushin Adda yake ji har ma da Dadan da yake ganin tana
biye mata ne.

“Allah ma baze sa ba Naziru zan lallabata insha Allahu babu abinda ze faru ma” Dada ta fada itama tana
miqewa dan neman abinda zata ci, ko karyawa batayi ba Adda ta doko mata sammako.

ADDA FATU

Bayan barinta gidan Dada gaba ta qara dan kuwa bazata koma gida yanzu ba dan tuni Amira ta gaya
mata matar tazo karbar kudinta gata nan a tsakar gida tana ta zuba Rashin mutunchi akan Adda ta fito ta
bata kudin ta sunce mata bata nan amma taqi yarda, gara ta qara gaba ko Allah ze sa ta dace ta samo
wani abun koda taimakon da zesa Bashir ya turo musu kudin ne. Gidan Aminiyarta Haj Balaraba ta wuce,
ta sami Balaraban a qofar gida an kira mata me Napep zata fita unguwa.

“Fatu daga ina da safiyar nan haka” ta fada tana qoqarin rufe gida.

“Ke zan tambaya Balaraba keda nasan se ki kai 12 ma baki tashi ba”
“Hmmm ta ina Kishiya na neman sabautani ina naga ta bacci, kinga yanzu ya akayi dan ni a tafe nake
neman taimako zan tafi” Balaraba ta fada tana jefa muqulli a cikin jaka.

“Ai kawai muje dan nima matsalar ce ta kawo ni ma tattauna a hanya” nan suka fada Napep Balaraba ta
fada masa inda ze kaisu. Suna tafiya Adda Fatu na jerowa Hajia Balaraba matsalinta.

“Ni na rasa wane irin shegen yaro ne Bashir wallahi naje gun malaman naje gun Yan Bori amma an kasa
cin galaba akansa, ke har fa nafi ganin aikin kissa idan tayi masa akan na asirin nan wallahi dama Da Nafi
nake samun yanda nake so a gurinsa to itama naga alamar tana so tayimun Bore. Ga shegiyar me kayan
can da kika hadani da ita bashi kamar na masifa na kasa biyanta”.

“Tab ai seda na gaya miki daman ita fa Indo in kaci bashin ta wallahi toshe maka hanyoyin samu yake
kika ce bakomai shiyasa kika ni kudi hannu muke sabga da ita gata bata san sabo ba akan dubu daya seta
keta miki rigar mutunchi”

“Ai na gani kuwa yanzu haka fa tana can gidan tana ta tijara nidai na ce su Ummi su kulle qofa kar su bari
ta shiga bare ta daukar kun wani abun, kudinta Dubu dari biyu yai saura da Mun samu kan Bashir zan
tattara na biyata mun rabu kenan”.

“To ai shi wannan yaron fa se kin dage masa gaskiya amma bari muje nan gurin, Maman lurwanu ta
kwatantamun tace aikinsa sha yanzu ne dan shi yai mata aiki akan Isah ya saki Kishiyoyinta dukka biyun
rana daya yanzu bakiga yanda take shanawa a cikin gidan nan ba ita kadai” cewar Balaraba

“Kice Allah, ashe gara da nayo nan Allah yasa qarshen wahalata kenan (ko kuma farkon wahalar ki ba) in
samu ina kafa Amira da kyau sannan in waiwayo kan nawa qananan kwarin ko da yake ni da zaman su da
babu duk daya ai kin sani” haka suka ci gaba da tattauna wa har suka isa unguwar da aka mata
kwatancen sedai ta kasa ganewa, sunyi tambaya kowa yace be san mutumin da suke nema ba kuma ta
kira Number Maman Lurwanu a kashe.

Kamar Adda zatayi kuka ta kalleta tace “yanzu Balaraba ya zamuyi dan Allah wallahi na gama saka ran
waraka ta zo” kafin ta bata amsa Me Napep da tunda ya dakko su bece komai ba, tsaf ya gama nade
hirar su ta hanyar voice note daya kunna tareda fahimtar matsalar ko waccen su se ya kashe mashin din
yace musu bari ya kama ruwa kafin su gama yanke shawara.
Can Nesa dasu yaje ya zaro wayarsa ya shiga kiran abokinsa aransa yana ayyana Banza ta fadi daga can
bangaren aka daga wayar ana cewa “ungulu baka jewar banza da alama ta samu”

Dariya yayi kafin yace “yi maza ka shirya area, ka duba whatsapp na tura maka saqo nan da minti Ashirin
zan qaraso idan ta saitu”

Dayan ya bushe da dariya yace”an gama kwaro kamar kasan wallahi dama ina ta lissafin ta inda zam
samu kudin yiwa Latifa Anko gashi ta matsamin kwana biyu babu kasuwa, Allah dai yasa ta waru, se kun
qara so toh” sukayi sallama.

Gurinsu ya dawo harda karbar pure water a wani shago ya fasa ya zubda rabi ya taho yana wanke
hannunsa,

“To hajia ina muka nufa yanzu” ya tambaye su bayan ya kunna Mashin.

“Maidamu inda ka dakko mu kawai” Balaraba da abun duniya ya ishe ta ta fada, se ya cilla suka dau
hanya yana jin yanda suke ta jimami. Daidai wani gidan mai ya tsaya ya sha, seda ya dan bata lokaci
sannan suka ci gaba ya gama shirya abinda ze gaya musu se yayi gyaran murya.

“Am nace Hajia kuyi haquri fa dukda ban gane kan damuwar taku ba amma idan kuna so akwai wani guri
da wancan satin nakai wasu passengers, can na jirasu suka gama gaskiya daga yanda naji sun fito nasan
sun samu biyan buqatar data kai su, kun gama saqon daya daga cikin su daga Kano tazo ashe suka karbi
Number dazu naje na karbo zan saka mata ta tasha akai mata” ya fada yana bude dan gurin da suke zuba
kudi ya zaro baqar leda, basu san mene ne a ciki ba gadai shi harda suna da Number waya an rubuta ta
wanda zaa turawa saqon. To wanda kwakwalwar sa ta toshe ai se a hankali ba tareda tunanin komai ba
suka ce ya kai su, a ransa ya ayyana “Madallah” ya cilla kan mashin suka dau hanya dan yasan zuwa
yanzu an kimtsa komai dukda haka seda ya sake yi masa text ya tabbatar masa komai is ready su taho.

Tafiyar yan mintina takai su layin gidan har qofar gidan me dauke da shago se kuma soro na shiga cikin
gidan. Wasu yan samari biyu ya gani daga gefe kan dakali yai musu sallama tareda tambayar su ko
Malam yana nan
“Ai kuwa ya fita amma nasan ba dadewa zeyi ba qilan ma yana hanya.. au ka ganshi ma muna maganar”
daya daga ciki ya bashi amsa. Se ya nufi gurin Wizy abokinsa daya sha uwar babbar riga harda wani
rawanin iskanci shi a dole ga malami ya miqa masa hannu suka kashe amma se ka zata musa baha
sukayi. Cikin daga murya Yanda su Adda zasu jiyo su Wizy yace “Mal Kamar kaine ka karbi saqon hajia
Larai dazu ko lafiya dai ko mantuwa kayi”

“Eh wallahi Malam nine ba mantuwa nayi ba wasu iyayen daki na na rako ne”

“Ah to to bismillah ku shigo ka barsu anan kuma kai Iliya me yasa baku bude musu shago sun shiga ba ko
ka kaisu cikin gida gurin Maimuna kan nazo” ya fada yana hararar samarin da suke zaune. Seda Iliya yayi
dagaske gurin riqe dariyar sa kafin yace “Malam ai ta fita gidan suna itama kuma ka tafi da muqullin
shagon ai”

“Anyi haka ya fada yana bude musu kofar suka shiga gaba daya, bayan sun zauna Me Napep yace bari
yaje daga waje idan sun gama shima se yazo a bashi taimakon kasuwa.

Malam ya jawo faranti me dauke da yashi ga kuma carbi me dubu ya hau ja yana muimui da baki nan
kuma yana faman zane zane sannan ya dago ya kalle su “toh hajia dawa Zamu fara?” Ya tambaye su.

Hajia Balaraba ce ta fara matsawa tace “Malam ni matsalar kaina ce a fara dani dama..” se ya dakatar da
ita, “ki bari mu duba abunda bamu fahimtaba se kiyi mana bayani da kuma matakin da kike so a dauka.

Tiryan tiryan ya ringa jera mata zance kamar me gani a film kai har abinda basu fada Me Napep yaji ba
seda Wizy ya canka ya fada se kuwa tace kai Malam aikuwa hakane wallahi, yana ta tiqar dariya a qasan
ransa to ai labarin duk daya ne dukma wadda tazo indai akan kishiya ne banbancin basu da yawa. Seda
ya gama ratta ba mata zance Adda da me gefe ta gama yin Ammana sun zo inda zaa magance musu
matsalar su harta gama Ayyano Yanda zasu juya Bashir kaman Tanda a waina.

Tsaf Hajia Balaraba ta gama gaya masa yanda take so ayi nan kuwa ya yanka mata 50k babu neman ragi
ba komai ta cake masa su to taji sauqi akan ubannin kudin data ke kashewa babu biyan buqata. Allonsa
ya jawo da tawada ya hau rubuta abunda in zaka kashe shi be san menene ba ya gama ya miqa mata da
kwano da ruwa yace ta wanke idan taje gida ta guntsi rabi ta fesa a kofar dakin kishiyar ko inda tasan
zata taka rabin kuma ta kuskure baki ta zuba a miya kowa na gidan yaci to daga nan babu me jin
maganar wani se tata.
Wasu qullin Jan Maganin da kore ya sake dakkowa ya bata su kuma yace ta ringa jiqawa kwana 7 tana
sha sannan ya qara mata da wani kuma a jarkoki guda biyu yace ta juye a bokiti ta qara musu ruwa ta
ringa sha shima mijin ta san yanda zaayi yasha koda tea ne ta dafa masa dashi sauran aiki kuma karta
damu zeyi daga nan shidai idan buqata ta biya kar a manta dashi (kuji dan banza Koren Magani na
sabara da Jan magani yake ba wa duk wadda tazo se na cikin jarka kuma maganin Basir ne ko banza ai ya
temake so ko ).

Adda ce ta matso aka buga mata nata duban se ya kalleta “Wace Mace ce haka gata nan dai Fara
kyakykyawa kamar ma bata da lafiya tana gadon Asibiti”

Ai caraf ta amshe “Asma’u ce ita ce kishiyar yar tawa” gyara zama yayi yana ayyano yanda ze tatsi matan
nan yace

“Kamar a kudu take fa wannan kai” se yai shiru kafin ya ci gaba

“Tab di hajia akwai babban aiki a gabanki fa dan koma wacece wannan tasha kan shi wannan mutumin
sosai dan kuwa Arnan kan dutse ne suke mata aiki an hada shi da gungun Aljanu suna gadinsa gaskiya
wannan aiki yafi qarfina”

“Ai Adda kamar zata rushe da kuka tace “haba Malam ba abinda ya fi karfinka ai (haba Adda Allah ne
kadai keda maganin komai) ka duba ka taimakamun nidai a tarkato mana hankalinsa ai ko baya auran
yata ni me tsayawa na nema masa taimako ce tunda dana ne ai dan yar uwata”.

Zama ya gyara yace “abinda kamar wuya gaskiya kin san aiki da kafiran Aljanu akwai wahala amma in
zaki saki kudi ayi musu yanka kinsan su jini suke so to wala Allah a dace”

“Malam indai zaa samu biyan buqata ba matsaka yanzu kamar me zaa yanka?”

“Gaskiya hajia a qalla za’a yanka musu raguna 20” seta dafe qirji tace Malam ina zan samu kudin nan
yanzu fa nake maka bayanin na biyan bashi ma nake nema ni a fara rufemun bakin matar nan ma
tukunna ta manta da zancen kudin”.

“Wannan duk ba matsala bane kuma zaki iya ringa bayarwa a hankali ai in kin so ma kiringa yankan da
kanki amma akwai kalar dabbobin da ake so da kuma abinda ake fada in za’ayi yankan in kina da wanda
ze miki duk sena gaya miki ai”
“Aa malam zaa mata komai anan” Hajia Balaraba ta fada

“To ba matsala”

“Kamar nawa kenan Malam” ta tambaya

“To akwai qauyen dana ke siyo dabbobi ana samun qosashshen rago dai daga dubu Arba’in kinga a qalla
guda koma dubu Dari hudu kenan amma zaki iya ringayi a sannu in so samu ne dai cikin wata biyu a
kammala aikin”.

Nan dai Adda ta zazzage masa dubu tamanin kudin data harhada zata rage biyan bashi tace in an kwana
biyu zata kawo abinda ya samu, ita be bata komai ba se wani abu kamar goro yace idan matar tazo ta
saka a bakinta ta ringa taunaqmwa tana mata magana kamar remote haka zata controlling nata aikin
Bashir kuma Wannan Ze duqufa yai tayi itama Amira jin tana da ciki ya nemo wani garin Maganin zaqi
dana sanyi da aka aike shi ya kaiwa Yayar sa da take da ciki ya bata yace ta kai mata tayi tasha zuwa
sanda Bashir zezo daya kwanta da ita anci rabin aiki.

Kamar wanda yai musu kyauta suka ringa zabga godiya ya basu Number wayar sa suka fito Me Napep
har ya gaji bacci ya dauke shi fitowarsu ta farkar dashi,

“Gaskiya kun dade hajia yau balance kawai zaku bani na maida Machine din nan na huta dan har na
gama gajia” ya kunna suna shirin tafiya har sun ja Iliya ya tsaidasu akan Malam yace ya manta da
taimakon kasuwar ne, se suka koma ya barsu a cikin mashin ya shiga.

Be zauna ba 40% 60% suke raba duk abinda suka samu Wizy se dauki 50% ragowar 10 ya bawa su iliya
da sauran masu yi musu cover a harkar, cas ya cake masa kudin sa tareda bashi wata qatuwar takadda
da aka nade kamar laya yace zasuyi waya ya fito, ransa fes suka kama hanya bayan ya saqala Takaddar a
gaban mashin wai ta kiran customers ikon Allah kuwa duk inda suka gifta se an tsaidashi yace drop ne
har ya ajiye Hajia Balaraba ya wuce Da Adda Fatu dan tace gara taje ta kai mata ta fara sha tunda yau
Alhamis a qa’ida gobe Juma’a ze zo

To se muce Allah kauda tsautsayi da Asara


WATA KISHIYAR

(Alkhairi CE KO SHARRI)

Na Maryamah_Mrs AM

(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)

Page 6

Da Isar Adda gida bata ko zauna ba ta jiqawa Amirah maganin da aka bata tace gashi nan tayi tasha Zuwa
goben sega yanda za’ayi.

“Adda kin ganin ze zo ne ko kin manta yanda mukayi dashi jiya da daddare” Amirah ta fada cikin sanyin
jiki.

“Ke dallacan barshi ai idan be zo bama baze samu nutsuwa ba saboda sabon malamin nan da muka
samu da zafin sa in gaya miki kedai kakarmu ta kusa yanke saqa, ai da lamarin ki sun gama daidaita zan
juya kan wannan me baqin jinin itama ai taimaka a samo mata wani zaman ya isa haka” ta fada tana
Kallon Ummi. Se Ummi tai zarab ta miqe tana cewa

“Wa ni wallahi na yafe dadai irin Auran Amira kullum kina tafe ba biyan buqata gara in zauna banyi ba
duk randa kika gaji kya barni na Auri Auwalu da nake so yake so na”.

Mafice Adda ta cilla mata tana auna mata Ashar

“Shegiya da bata gaji arziqi ba da dai wallahi ki auri wannan faqirin gara kiyi ta zama ina kallonki ba
auran, duk yayan gidan nan wa kikaga ta auri ko Malamin Jami’a bare malamin makarantar primary”

“Wato Fatu bazaki dena yin munanan kalamai akan Yaran nan ba ko? Amma ki ci gaba ai kina gani Idan
Alkahiri kike shukawa kanki koma akasin haka” Alhaji Murtala da basuji shigowarsa ba ya fada, be ko
qaraso ba ya juya kawai dan yasan wani qarin bacin ran ze jawa kansa. Tun kafin ya fito da safe ta bar
gidan haka duk a kunnensa Indo Tazo tayi tijarar ta dakyar Yaran gidan Maza suka lallaba ta ta tafi dan
shi qin fitowa yayi. Ya gaji da halin masufar da Fatu take jefashi a kullum shi be san Adadin bashin daya
biya mata, idan baazo yau ba gobe se anzo to ya gaji.

Yanzu ma maganar ya shigo ya mata akan ta nemi kudin matar ta bata idan ba haka ba tace gobe idan ta
dawo da police zata zo to wallahi sedai su kulleta dan shi sisi baze sake biya mata ba ai badan ita kadai
yake nema a rayuwarsa ba.

Adda kuwa ko a jikinta ta cigaba da gayawa Amirah yanda sukayi da malami da kuma tabbacin da ya bata
da an gama ai Bashir ze dawo hannunsu.

“Amma fa Adda ni bana yarda idan akace wai Anty tana wa Yaya Bashir Asiri ke kanki Adda kin san ba
haka bane”

Hararar ta Adda tayi kafin tace “Ji banza, idan tanayi se tace miki zata fito fili a sani ne? Ko kuma ace da
batayi to daman me zatawa Asirin bayan kusan ita ce Mijin shi Matar yanzu kuwa daya bunqasa ai
bazatayi sanya wata tazo ta taya ta ci ba. Ni in zaki karbi abu kiyi kawai kiyi kafin ki fara saka wasiqasi ki
bata mana aiki dama ni ina zargin bakyayin yanda akace shiyasa komai baya tafiyar mana daidai to ke
kika sani wallahi kina ji kina gaji zata kado ki waje ki dawo mujere ana mana Dariya” da haka ta shige
dakinta dan yin Sallar Azahar da La’asar da suka sameta a tafe ga Magriba an fara kira.

Amirah ma jiki a sanyaye taja jug ta fara bankawa cikinta ruwan magani dukda qasan ranta bata jin
Bashir zezo wannan satin amma dai gara tasha saboda tsaro se sannan ta tuna bata gayawa Adda yanda
a ka qare da Indo me kaya ba, ta cicciba zuwa dakin Addan ta tarar tana sallah se itama ta wuce nasu
dakin dan yin Sallar.

WASHE GARI

Qarfe bakwai a qofar gidan tayiwa Indo ta shiga biga gate baji ba gani dan ta rantse wallahi yau ko ita ko
Fatu a garin nan ita zata rainawa hankali lallai bata san wacece Indo ba. Alhaji Murtala da fitowarsa
kenan ze tafi wata Jana’iza ya qarasa ya cire sakata ta hankado qofar saura qiris ta bige shi tayi ciki
abunta se kawai ya girgiza kai tareda juyawa ya kunna motarsa, Aminu daya daga yaran gidan ya qarasa
bude masa gate yai ficewarsa dan bama ze tsaya yaga yanda zata kaya ba.
Adda Fatu da tunda tajiyo bugun ta janyo abinda Malam Wizy ya bata ta bantara se taga kaman Namijin
Goro amma kai bashi bane qila kama ce ita dai ta afa baki ta hau tauna harda guara zama akan kujera
tana jiran shigowar Indo se kuwa gata kaman an jefota ta fado.

“Fatu bani kudina kafin na yaga miki rigar rashin mutunchi a unguwar nan” ta fada tana huci, se Adda ta
miqe tana qara bantarar magani ta tauni ta nufo Indo tana cewa

“Ke Indo fita ki tafi karki sake dawo wa gidan nan ki manta da zancen bashi a tsakanin mu har abada idan
ma da wasu kudin a jakarki yanzu cirosu ki bani”

“Fatu hauka ne ya sameki ko to bari kuwa yanzu zan sauke miki shi wallahi ina batun ki bani kudina kina
min wata maganar banza harda in qara miki wasu to bari kiga” Indo ta fada tana ja baya ganin Adda ta
nufo ta tana sake maimaita kalamanta se zare ido takeyi ai bata yi aune ba se Ji tayi Indo ta dauke ta da
wani gigitaccen mari daya sakata furzo da goron ba shiri ta kife gurin tana kururuwa dan ji tayi kunnenta,
indo bata haqura ba ta sake kai mata Mahangurba a hanci aikuwa take ya fashe ya fara bulbulo da jini
sannan ta bita ta turmushe ta hau duka, Adda ba hakin kwace wa se ihu take tana neman dauki.

Kishiyoyinta uku duk suna tsaye a bakin kofa da yayan su mata ransu qal akan wannan abu se Ummi da
Amira a gefe suna taya ta ihun ba damar kai mata dauki 😂. Se da tayi mata lilis sannan Samarin gidan
suka kawo taimako dakyar aka kwaceta Indo na jaddada mata wallahi ko kudinta ko kuwa kullum seta zo
ta nada mata na jaki dan ta bar maganar police ma da kanta zata kwaci kudinta sannan ta fice daga
gidan.

Adda fuska tayi luhu luhu se hawaye da ajiyar rai take ga hanci ya fashe a ranta Allah ya isa take jerawa
Malam Wizy akan wannan abu daya bata gashi nan ba biyan buqata se bugu data sha a banza, bari Suga
na Bashir idan taga ba nasara dole ta koma ya biyata kudinta dan bazata dauki asara biyu ba. Ita se
yanzu ma taji wani tsautsayi ya kaisu yarda da Dan Napep din nan? Anya ma ba hadin baki bane shida
Hajia Balaraba suka kaita a cinye mata kudi amma ai itama Balarabar ta bayar. Bari tayi ta kanta yanzu
zata kirata taji yanda akayi. Ummi ce ta kamata ta kaita daki ta hada mata ruwan Me zafi a toilet ta shiga
dan gasa jikinta, dakyar ta iya watsawa ta samu dai Habon ya tsaya ta dauro towel ta fito ta haye gado
kan kace meye wannan zazzabi ya rafke ta se rawar sanyi take.

(To Adda Allah ya qara lafiya ya kiyaye na gaba ).


Kafin yamma dai jiki ya qi dadi dole suka kaita asibiti tasha Allurai suka dawo da magunguna gashi har
sannan babu Bashir babu labarin sa kuma ta kira Dada ma wayarta a kashe, kukan baqin ciki ta fashe
dashi da tsoron haduwarsu da Indo gobe.

Mu koma Lagos

Qiri qiri Asma’u ta qi bari a sallameta acewarta se tayi sati, Dr beqi ba tunda sabga ce ta kudi qaruwar su
ce dan haka yace wa Bashir dole ta zauna suyi monitoring Bp nata na wani lokacin kafin a sallame ta. A
kwana biyun nan idan kaga Bashir se ya baka tausayi yanda yayi wurjanjan dashi har a office an gane
bashi da nutsuwa dole suka bashi leave na 1 week saboda ya samu ya kula da yaran kafin a sallami
Asma’u, sauqin sa daya yaran sun rage kokekoken tunda kullum yanzu da safe ze kai su da daddare ma
su koma.

Shi ya ma manta da wata Amirah sam bare zancen zuwa Gombe yau ranar Sunday kaman yanda ya saba
bayan ya kawo yaran, suna gurinta Abokinsa Abdurrahman da Matarsa suka zo dubata, su suka tafi da
yaran gidan su akan da dare idan ya gama se yaje ya dauke su su tafi gida ya dan rage zirga zirga.

Suna zaune kamar kurame bame cewa komai, ita tana chatting a wayarta shi kuma ya tasa ta a gaba
yana kallo ganin yanda ta sake wani mugun fresh tayi kyau alamar ta samu hutu ba abinda yake
damunta shi kuwa banda uwar rama da baqi da yayi to ga Damuwa ga babu abinci me kyau daya saba
kwasa dan yanzu suma yaran mata yassara kawai suke ci dama Mami ce take tsayawa ayi abinci me kyau
to bata nan dan haka baya iya ci ko sun dafa in yunwa ta dameshi ne ma zeci Indomie yasa tea in ba
haka ba Snacks da lemo ne rabin abincin nasa.

Dagowar da Asma’u tayi tana dan murmushi tareda tsare shi da ido tace “wannan week din bazakaje
Gombe bane”

Se a sannan manAmirah ta fado masa ya tuna rabonda suyi waya tun ran Laraba be kiratan ba yasan
kuma itama bazatayi gigin kiransa ba tunda ya mata warning. Numfashi yaja kafin yace “Wallahi na ma
manta shaf kuma ko waya banyi nace bazan shigo ba gashi har yau Sunday, ya kamata kam na kirata”.

Kishi ne ya dan tsikareta ta wani fannin kuma tana yabawa Bashir dan ba laifi yana kaman ta Adalci wani
Sa’ilin. A farko farko se sati biyu yake zuwarwa Amiran ze tafi Friday ya dawo Monday da safe to da aka
samu qarin kudin jirgi dole ya chanza tsarin zuwa Qarshen wata, daga bayannan kuma bata san dalili ba
wani Sa’in se ya jera sati uku hudu ma duk weekend se yaje duk kuwa da ayanzu kudin jirgin ma yafi da
ita dai bata taba tambayarsa dalili ba haka nan ko tare sukaje Gombe ko kwana na wa zasuyi bata da
Kwana a yanda suka tsarawa kansu shida Amaryar sa kuma da taimakon Adda to ita hakan be dame ta
ba tunda daman idan taje ba zama take ba a lokacin take samun ziyartar yan uwa da sauran abubuwan
da akayi bata nan.

Tana kallonsa ya zaro waya ya shiga kiran Amiran ringing biyu kuwa ta daga tana fashe masa da Kuka,
kallon Ma’u data juya baya ta kwanta yayi ya tabbatar ta jiyo kukan Amiran se ya miqe ya nufi qofa yana
ce mata “kukan kuma Na mene kinsan bana so”

Wani qululu ya tsayawa Asma’u, wato itace banza a wajensa da in zata mutu tana kuka baze ce ta bari ba
kenan ashe ita ta zata so ne yasa yake barinta ta fitar da damuwarta ashe tsabar be damu bane kai Anya
kuwa Bashir ya taba sonta a ransa??

Abubuwa da yawa da ada take daukar haka yaje se a yanzu take ganin banbance banbance ko kuma
dama Haka Mazan suke ko wacce Mace da yanda halayyarsu taje a wajen ta? In kuwa haka ne Sun Amsa
sunansu na Hawainiya.

AMIRAH

Sanda Bashir ya kirata suna zaune da Addah da har yau fuska bata daidaita ba ko jiya Indo ta dawo Allah
ya taimaketa Alhaji na Nan, shi ya kashe rigimar cikin Kudinta da yake hannunsa yake juya musu da a
qalla sun kai 2 Million yau ta kirbi dari gobe Hamsin a wayonta kudinsa take ci da yaga fa da gaske Fatu
ba hankali ne da ita ba dole ya saka akayi rubutu kowacce cikin Matan da kudinta dake hannunsa ya
kuma gaya musu duk wadda ta nemi kudi indai ba abinda ya zama dolensa ba to a cikin kudinsu suka ce
sun yarda kowa ta saka hannu to ita Adda a nata baqin wayon da ganin tasha kansa bata dena ba ta ci
gaba dacin kudinta hankali kwance ba tareda ta sani ba shi kuwa yana lissafe da komai ga kuma takaddu
saboda Adar rai. To tun jiya daya fita ya yanke shawarar cikin 500 din data rage mata ze biya mata
bashin nan dan ba ita kadai ba harda shi take zubarwa mutunci maqota kullum na jiyo an zo karbar bashi
gidansa bayan Allah ya rufa masa asiri.

Jiyan Indo na zuwa ya fito a gaban Fatu ya zaro kudi ya bata ta qirga su cif sun cika tace mata “Allah ya
taimakeki wallahi da dukan yau se yafi na jiya kuma wallahi ko da wasa karki kuskura naga qafarki kinzo
neman abu gida na dan ance ba kunya ce da ke ba se ki dawo” ita dai tayi muqus harda yiwa Alhaji
godiya yace mata
“Godiyar me zakimun a cikin kudinki na biya miki ai ba nawa ba tunda haka kika zaba se kiyi tayi wata
ran idan ba kiyi hankali ba suturar da zaki daura se ta gagare ki indai baki dena cin bashi ba.

Yana fita wayar Bashir na shigo wa Adda ta zabga Hamdala tace kin gani ko a sannu a sannu komai ze
daidaita maza ki daga ki rushe da kuka duk kibi ki hargitsa shi ki samu yazo ko ya turo mana wani abun,
haka akayi tana dagawa ta saka kukan.

Seda ta tsagaita ta gaishe shi ya amsa yana tambayarta jikinta tace da sauqi.

“I’m sorry Amirah ranar nayi miki ihu raina ne a bace Wlh ga Ma’una bata da lafiya a lokacin ke kuma kin
dame ni da kira”

“Ba komai Yayana ya wuce yanzu ya jikin Antyn? Ban sani ba ai dana kira na mata sannu dukda idan na
kirata ma bata amsawa kaga yanzu kosu Aliyu ta hanani magana dasu”

“Qorafi dai qorafi halin daya tsana da Amirah kenan a rayuwarsa” ya ayya a ransa a fili kuwa se yace

“Ta samu sauqi, se zuwa Next week zan shigo insha Allah akwai abinda kike da bugata ne?”

Se Adda ta zungureta tana rada mata tace kudi se tace

“Uhm uhm Ba komai maganar siyayya ne kawai daman se kuma ni Yayana ina so in dawo kusa da kai
gaskiya saboda....”

“Amirah I’m looking forward to that ok maganar kudi kuma idan mun gama zan saka miki wani abun
kafin End of the month saboda nayi hidimar Asibiti duk na kashe kudaden hannuna yanzu”

“To shikenan amma dai gaskiya Yaya nidai ko wani gidan ne se ka samar min da zan zauna amma irin Na
Anty nake so me kyau sannan fa yaya karka manta da zancen canjin kujerun irin natan” ta sake fada dan
harga ranta fa ita tunda ta tashi burinta kawai shine ta kamo Asma’u ta ko ina.

“Naji ki gaida su Adda” ya fada yana qoqarin kashe wayar jin tana so ta bata masa rai,
“Bama ta da lafiya bari na bata kayi mata sannu” ta fada kafin ta miqa mata kuwa qit ya kashe wayarsa
dan itama Addan haushin ta yake ji dan abu da yawa ita take dora Amiran akai, idan banda bata da
tunani kwana nawa basuyi waya ba amma da abinda ya kamata ta tare shi kenan? Bayan haka yanzu fa
yake gaya mata bashida kudi amma ita wannan baya gabanta buqatarta ce kawai a gaba. besan dalilin ta
na gasa da Ma’u ba komai ta gani a gurinta yunqurinta se itama ta samu, tana mance cewa Asma’u na
aiki tana da abin kanta abu dayawa ko beyi mata ba zatawa kanta.

Gudun karta ishe shi ya saka shi yi mata transfer 100k saura 200k kenan kudin siyayyar kayan haihuwa
dana fitar suna da tace ya bata, yace sun yi yawa ta ringa masa mita da qorafin bala’i dole ya yarda ze
batan kota qyale shi.

shi tunda Asma’u take haihuwa baya tunanin ya taba bata dunqulalliyar dubu Hamsin wai da sunan tayi
siyayya shi bata ma taba tambayarsa ba, duk abinda ya dakko ya bata idan yana dashi karba take idan
ma bashi dashi haqura take yan uwanta su mata harma ya samu Arziqin shaddar fitar suna shima.

Baze taba manta Haihuwar Abdallah ba da tace ya saka mata sunan Babanta yace mata sedai ta se masa
rago hakan kuwa akayi ta siyo raguna har biyu ta kuma cewa Yan uwanta da Nasa shi ya siya har yu har
gobe ya kalli yaron se yaji wata kunya da Nauyin sa dana Uwarsa ya kamashi, shi wallahi a duniya in yai
wani abun se yaga kamar dai shafar Aljanu yake samu su saka shi yayi abu daga baya yazo yana dana
sani (Shafar Aljanu ko iskanci ba )

Dakin ya koma Ma’u najinsa tayi shiru kamar me bacci ya gaji da tsayuwa ya qaraso ya mata peck a goshi
ya fita yanaso yaje gida ya dan yi bacci tunda yaran basa nan yau shima ya dan huta kafin gobe Monday.

Su Addah kam Kudi na shigowa suka hau Murna “Ke yar nan kinga abu kaman wasa aikin malam ya fara
kama Bashir to wannan aka gama aiki kuma ai ban san yanda zamu taka shi ba yanda muke so. Ita
waccan shegiyar dama itama ba a zaune take ba dole nata yaqi tasiri amma tunda mun rabu lafiya
shikenan, yanzu bari an jima zan kira Malam se ya nada account mu sake tura masa ko kudin biyu ne
tunda na bada na biyu ayi a gama aikin nan mu fara shan romon damokaradiyya”

“To Adda amma da mun bari dai akwana biyu a sake samun wani abun wannan mudan rage siyayyar
mana” cewar Amira.
“Ke dallacan ba gara a gama ba nasan ko million goma kika ce ya baki kawo wa zeyi”

“Kuma fa haka ne, to ki kira se a tura masa din”

“Allah dai ya kauda bacin rana” Ummi ta fada tana miqewa kafin ta karbi duka ko Ashar daga gurin Adda
ai kuwa ta shiga aika mata dasu tana ce mata yar baqin ciki haka zata qare tana gani suna abin arziqi
banda ita.

Wai ya Hajia Balaraba ta qare da maganin Malam Wizy ne??

WATA KISHIYAR

(Alkhairi CE KO SHARRI)

Na Maryamah_Mrs AM

(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)

Page 7

A bangaren Hajia Balaraba kuwa cike da farin ciki ta bude gida ta shiga ganin har sannan Kishiyarta bata
dawo daga gurin aiki ba, cikin sauri ta fito da rubutu ta huda leda tareda guntsa ta feshe kofar dakin
Amarya tana cewa “Shegiya maza ki dawo ki taka ni Alhaji yaiyo waya daga kasuwar ma yace ya sake ki
base ya jira ya dawo ba” ta qulle ragowar gudun kar ya zube ta qarasa qofar ta.

Mayafinta kadai ta ajiye ta shiga kitchen ta hau kicikicin dora girki qarin farin cikinta ita ce da girki dama
kai yau koda ba itace da girki ba ai dole tasan yanda za’ayi ta aiwatar da aikin nan tanayi tana tuna irin
cin mitunchin da Alhaji yai mata dazu da safe kafin ya fita kuma ta tabbata duk Amarya ce ta zugoshi har
yana iqirarin tabar ganin sun tara yaya da jikoki tsaf seya yanka mata tikitin zawarci.
Itadai tunda Malam na kan Tudu ya kwanta dama kamar ya tafi da duk ayyukan da Tayi akan Alhaji ne
komai ya karye shekara da shekaru tana cin duniyarta da tsinke se yanzu da tsufa ya kusa cin mata ne
zata fara karbar taskun namiji ina bazeyuwu ba ai.

Tsaf ta gama hada lafiyayyar Miyar taushenta kafin ta dakko qaramar tukunya ta sare wata wadda zata
ci, nan da nan dakko ragowar rubutun Malam Wizy ta kurbe tas ta kuskuro dattin bakinta da komai ta
watsa musu a miya ta sake kurbe ragowar ta zuba ta juyata dakyau ta rage wuta ranta fes dan gani take
kamar ma aikin gama ya gama.

Tana cikin malmala tuwan autarta me suna Ruqayya ta shigo ta dawo daga makaranta dan tana shekarar
ta ta qarshe ne a GSU da mamaki ta kalli maman tata kafin tace “Hajia kece dakanki yau a kitchen ina
Baba Zulai din”

Bata ko dago ta kalleta ba tace “Taje gida Sa’adenta batada lafiya ina ga se gobe zata dawo”

“Kai dukda haka da mamaki ace Hajia kina girki lallai yau zamu kwashi dabge bari nayi sauri nayi wanka
nayi Sallah muzo mu kwashi ganima”

“Zaki kwashi ganima dan uwarki duk zan kulle bakinku ai na ga ta inda zaki ringa kaiwa uban naki gulma
idan na taba kudinsa” ta fada bayan Ruqayyan ta fita daga kitchen din

Oho bata ma san tanayi ba dakin ta ta nufa a ranta tana ayyana tabbas akwai wata a qasa dan ita dai tafi
shekara Goma rabonda taga Hajia tayi girki da kanta Baba Zulai ce take yi musu ko kuma ita idan taba
gida. Ita zata iya cewa ma idan kaga Hajia a kitchen to an gama Abinci ne idan harda na Baban zatayi
barbade daga baya ma daya gane yai Allah ya isa yama zo kuma ya dena cin abincin kwatakwata se baya
bayan nan taga ya dawo yana ci.

Ita kuwa Hajia tana sauke tuwo ruwan Tea ta mayar ta saka lipton dinta da kayan qanshi sannan ta zuba
jiqon Wizy, bata matsa ko ina ba seda ta kammala tsaf ta hada komai ta kai kan Dining sannan tashi ga
dakinta tai wanka ta fara jero Qara’in salloli.
Seda akayi Isha Alhaji ya shigo, kai tsaye part din Amarya ya shiga dan akwai kayan daya manta da safe
da ze tafi kasuwa yana so ya dauka kar gobe ya sake mantawa. da mamaki ya kalleta dan ya zata ta tafi
aiki tunda tace masa Night Duty ne da ita. tana ganinsa ta miqe

“Yawwa Alhaji dama kai nake jira tun dazu”

“Lafiya Abida baki tafi aikin ba? Jiran me kike mun?” Ya fada yana kallonta. Seta miqa masa wayarta
kawai ba tareda tace komai ba, karba yayi yana duba screen din sega video Hajia Balaraba tana kici kicin
zuge jaka, baya jin me take cewa amma fes yaga sanda ta ciro leda ta guntsi rubutun ta feshe kofar dakin
Amarya ta tafi”

Se ya miqa mata wayar dason jin qarin bayani.

“Wallahi Alhaji yanda ka gani dinnan kasan ka fita ka barni kaina yana ciwo dan haka sena kwanta dan
ban ma samu zuwa Barkar Haula da nace maka zan fita ba, se bayan La’asar na ma idar da sallah na tashi
zan leqa na karbo Kati se naji motsin a bude qofa, in duba ta window fa shine naga Maman Suhaila na
wannan ta tsaya tana maganganu tareda bude jaka wayata na hannuna ni kuma shine na kunna video
saboda kar a maimaita irin ta wancan karan data zuba magani akace qarya nakeyi yanzu dai ga Hujja ka
gani da idonka, nidai ban fita ba koma na menene kai kadai ka tsallaka shi se kasan yanda zaayi azo a
karya dan bazan yi ta zama a daki ba kona fita a sabautani a banza”.

Wani irin tuquqin baqin cikine ya rufe Alhaji har huci yakeyi, wato duk Allah ya isar dayai wa matar nan
bata daddara ba kenan? Shin wai se Yaushe Balaraba nutsu tasan Annabi ya faku ne ita dai duniya ce
kawai a gabanta to kuwa Insha Allahu Allah baze sake bata ikon maidashi halin data jefa rayuwarsa a
baya ba shi wallahi badan kar duniya ta zageshi ace ya saki matar sa auren shekara Arba’in ba da rabuwa
zeyi da ita ya huta amma yanzu babu wand ze dubi abinda ta aikata masa shedai a dora masa laifi ace Ya
wulaqanta Uwargidansa.

Cikin fushin daya gaza boyewa ya fita, mintina kadan ya dawo tareda wani yaro ya shigo palour ya bar
yaron a kofar dakin tareda nuna masa gurin yace ga inda zeyi fitsarin nan yaro kuwa ya tsula abunsa
Alhaji ya fita ya nuna masa famfo ya taro ruwa suka sheqe a gurin nan da nan ya wuce daman tiles ne.
Ciki ya dawo yace da Abida ta biyo shi yai gaba tana baya se palour Hajia Balaraba.

Tana zaune ta hakimce akan kujera ta sheqa kwalliya ta garari ta kuwa yi kyau sosai dan Hajia Balaraba
akwai kyan jiki da gayu kai bazakace tabawa Hamsin baya ba. Tana ganin Alhaji ta miqe da fara’a da
nufin tarar sa sedai ganin Amarya a bayansa yasa ta gintse fuska a ranta tana tunanin meya faru kuma
dan ita bata ma lura da yanayin fuskar Alhajin ba.

“Balaraba me kika zuba a qofar dakin Abida?” Ya tambaye ta cikin kaushin murya. Qirjinta ne ya fara
luguden daka zuciyarta kaman zatayi tsalle ta fito saboda razana, ya akayi ya sani to ko wani ya ganta
ne? Ita dai a hasashenta babu kowa a gidan dan Tunda da zata fita seda ta saka muqulli ta kulle haka
data dawo dakanta ta bude kofar, koma menene bazata bare a gano ta dole tasan yanda zata kare kanta.

Qoqarin daidaita nutsuwarta tayi tana daure fuska tace “Bangane me kake nufi ba Alhaji wani sharrin
kuma aka sake qullomin yau ma? Ni duk yau ma ban fita daga part dina ba bare har naje qofarta na zuba
abu”.

Kallon takaici da tsana yake binta dashi, se ya miqawa Abida hannu tayi saurin miqa masa wayarta.
Video yayi playing ya miqawa Hajia Balaraba dake ta taraddadin me nene a cikin wayar Abidan, ai seda
ta kusa Sakin fitsari a gurin saboda kidima nan danna zufa ta shiga keto mata.

“Wane La’anannen ne ya dauki wannan video” ta fada bakinta yana rawa tsabar yanda ta rikice, zata
sakw magana ya miqa mata hannu ta bashi wayar yana cewa

“Kici gaba Balaraba sharri dan aikene ki sani duk nisan indai kika aika shi watarana seya dawo miki,
tunda har kin raina Allah ya isar da nayi miki akan in kika sake yimun wani abu ko wani daga cikin
iyalaina shikenan na barki da Allah kuma matakin qarshe dazan dauka shine wallahi Balaraba idan kika
sake zuwa gidan wani malami kika aikata wani abun sihiri a cikin gidan nan kai na ko kan wani nawa, na
sani ko ban sani ba to ki sani a bakin aurenki”

Cikin tsananin razani ta dago ta kalle shi dan bata taba zaton tsaurin hukuncin ze kai haka ba, ta bude
baki da niyyar neman sassauci yace “Karma kice komai dagaske nake kuma ba igiya daya ko biyu ba
dukka ukun nake nufi idan kuma kika aikata a bayan idona ba tare da na sani ba muka ci gaba da zaman
aure dake wannan kuma na barki da Allah shi ze bimin haqqin zaman zina da kika sa nayi ba tare da sani
na ba” yana kaiwa nan ya shige dakin sa da yake a part din nata, Abida ma jiki a sanyaye ta juya ta fita
aka bar Balaraba da dora hannu aka tama tasa kuka zatayi ko ihu?
Wannan shi ake kira da An bata biyar goma bata gyaru ba (Dama ai duk wanda yace tukunyar wani
bazata tafasa ba tabbas tashi ko dumi kuwa ba zatayi ba).

Lagos

Seda Ma’u ta cike satin nan daya raya cif aka sallameta, da safe bayan Bashir da yara sunzo sun tafi
tacewa Dr ya sallameta haka. Da kanta ta karbi Discharging later ta hada yan kayanta kafim ta kira Uber
ta cale gida (tsiyar garin da baka da dangi kenan).

Koda ta isa gidan bata zauna ba seda ta gyara ko ina tsaf ya dawo mata yanda take so sannan ta shiga
hidimar dora girki kuma, aikin ya jata da yawa dan har bayan La’asar sannan ta kammala komai ta jere
akan Dining kafin ta koma dakinta kuma ta fada wanka. Tsaf ta shirya cikin wani hadadden cotton lace
Army green da akayiwa dinkin Fitted gown datai bala’in yi mata kyau ta fito mata sauran quruciyarta.
Indai gayune dole a cirewa Ma’u hula wannan ko a zamanin yammatancinta babu kamarta a kaf
qawayenta tana da kyau ta kuma iya daukar wanka ga farin jini Allah ya mata abinda ya sa ta zama ta
daban kenan da sauran.

Daurin nan ta kawo shi gaban goshi bayan ta fake gashinta qasa qasa sannan ta saka cogenta ta qara
feshe jikinta da turaruka ta shiga juyi a gaban mirrow dan ta burge kanta da kanta ballanta na Kuma
Bashir ya ganta tasan duk yanda yake qyashin ya yaba kwalliyarta yau kam se idanunsa sun fado qasa
qilan a garin kallo.

Mint flavored chewing gum ta jefa a bakinta kafin ta fito palour ta samu kujerar dake facing kofar
shigowa ta dora daya kan daya tana girgizasu tana danna waya ba koyi minti biyar da zama ba ta jiyo
tsayuwar motarsu, seta qara gyara zaman ta dakyau tana sauraron shigowarsu.

Aliyu ne a gaba dauke da Laptop bag din Bashir se school bag dinsa daya goya a baya se ga sauran a
bayansa. Gaba daya suka nufe ta cike da murnar ganinta a gidan, Aliyu ne yace

“Mami this house can never be complete without you Allah Mami da baki nan ji nake kamar a kango
muke kwana amma yanzu tundaga qofa kawai naji it feels like home again ashe kece kika dawo ciki”
Dukan wasa ta kai masa tana cewa “Oh Ali yammata kam se sun bani da dadin bakin nan naka Allah dai
ya nuna mun lokacin” se ya rufe fuska wai shi kunya yana cewa “Kai Mami ki dena kunya nake ji”

Gaba daya suka saka dariya, se a sannan ta daga kanta ta kalli inda Malam Bashir yaci burki tunda ya
shigo, seta qara fadada murmushinta tana cewa

“Aa Baban Ali yane ka tsaya ka shigo ka zauna mana ko ka qara sa ciki”.

Bashir

Numfashinsa ne ya dauke na wani lokaci sanda yai arba da fuskar Ma’u, tayi masa kyau matuqa gaya da
har ya kasa iya cire idanunsa daga kanta. Maganar da tayi ce ta fargar dashi kamar dama me jiran
umarninta kuwa se ya taho, kusa da ita inda Farida ke zaune ya daga Faridan cak ya zauna a gurin tareda
dora ta a cinyarsa kafin ya maida kallonsa kan Asma’u yace “to naga ne hankalin ki yana kan yaranki
kamar ma ni baki ganni ba” ya fada yana kafeta da kallon nan nasa me saka Yammata fadawa soyayyarsa
ba tare da sun shirya ba.

Irin kallon da shi ya ringa qara rura garwashin soyayyarsa a zuciyarta har ya tada gagarumar wuta da
hauyau ba’a samu ruwa ko iskar da sukayi nasarar kashe ta ba.

Seta tsura masa nata kyawawan idon tana hango abinda zuciyarta ce kadai take da tafsirinsa, a cikin
idanun Bashir kadai take iya hango tsabtatacciyar qaunarta wadda babu Algus ko digo a ciki amma
ginshiri da baqar izzar sa suke hana bakinsa iya furtawa. Har gara gangar jikinsa takan gaza bashi hadin
kai gurin boye sirrin zuciyar tasa dan a duk sanda suka hadu gangar jikinsa na sarrafuwa ne kawai bisa
umarnin zuciyarsa bawai kwakwalwarsa da take nan kamar wadda akeyiwa hayaqin wiwi ba, yanzu yai
abin arziqi an jima ya tafka na tsiya.

Ganin irin kallon qudar da Abbi da Mami sukewa junansu ya saka Amna kama hannun twins manyan
kuma suka tashi gaba daya kowa suka shige dakinsu, miqewar Farida daga kan qafarsa ta ankarar dashi,
seya janye idanunsa cikin son basarwa shima ya miqe yana ce mata

“Zan samu abinci kuwa? Gaba daya yau coffee ne kadai a cikina”
“Ai fa ga Kuku ta dawo dole ka nemi abinci babu tambayar ya akai na taho ni kadai ban kiraka ba balle jin
ya jikina” ta ayyana a zuciyarta, a fili kuwa seta ce “kayi wanka first, ga abinci nan yana jiranku” se ta
miqe ta nufi dakin su Amna.

Se ya rakata da ido kuwa kamar zasu fado din, yanda take juya qugunta da ya fito sosai saboda yanda
rigar ta bawa komai haqqinsa ga qarar takalmin qafarta da yake ji kamar qararrawa a cikin
qwaqwalwarsa. Wasu busassun yawu ya hadiye tareda lasar lips dinsa da suka bushe kafin yace
“Hmmm” (inji me ciwon haqori ) karaf a kuwa a kunnen Asma’u daidai sanda take tura qofar dakin su
Faridan

“Idan baka chanza hali ba Bashir wata rana sedai ka farka ka ganka a kabari Maganganun da kake
dannewa sun shaqe maka wuya, ayi mutum bakin na son magana amma baqin rai ya hana shi Allah yai
mana magani dai”.

Guri ta nema ta zauna dan ba abunda zatayi a dakin dama ta tashi ne kawai dan ta bashi damar kallon
kwalliyar tata da kyau. Ahmad daya fito daga toilet alamar wanka a ka masa ta shiga shafawa mai kafin
Muhammmad ma ya fito, tsaf ta shirya su, kafin su gama an kira Sallar Magriba dan haka tace suje suyi
Alwala ita ma ta fita dan zuwa tayi a bakin qofa suka kusa cin karo da Bashir wanda da alama shima
wankan yayi ya chanza kayansa zuwa Jallabiyya Baqa da tayi bala’in masa kyau duk da kasancewarsa ba
fari qal ba, Bashir nada kyau irin na Maza me sanyi daya hadu da kwarjinin da Allah ya bashi.

“Kayi kyau Baban Ali” ta fada da zuciya daya dan ita bata iya munafunci irin nasa ba kuma rashin yabon
kwalliyarta be taba sare mata guiwa akan ta denayi ba.

Kallon ta yayi yana dan Murmushi kafin yace “Koh?”

Seta amasa masa da sarar sa tace “Uhm” tana qoqarin kauce masa a ranta tana mita. A zaman shekara
Goma sha shidda baza ta tuna ranar da a karan kan Bashir ya budi baki ya yabi kwalliyar ta ba tun tana
qorafi idan tayi se ta tambayeshi tayi kyau sannan ze yaba har ta gaji ma ta dena, yanzu da yaranta suka
girma kuwa indai tayi kwalliyarta se sunce Mami kinyi kyau shiyasa ma ta dena damuwa da yabawar
Bashir dukda abun da zafi amma ya zakayi (Mazan hausawan Mu Allah ya shirye ku dai ).
Wuce shi tayi ta shiga dakinta itama ta daura Alwala shi kuma ya hada kan yaran suka fita. Data idar da
sallah zama tayi ta qara gyara fuskarta dakyau sannan ta fito, sun zauna a Dining da gani ita suke jira dan
haka ta qarasa gurin.

Seda tayi serving kowa sannan ta zauna suka fara cin abinci kowa na santi karma Bashir yaji labari dan
kunnensa har motsi yake. Besan yawan abincin daya nada ba seda ya qara saka serving spoon ze debo
abincin a karo na uku bayan wanda ta zuba masa yaji wayam aiko suka kwashe da dariya suna kallonsa.
Seya bata fuska kamar yaro yace

“To ai yunwa nake ji for almost a week fa bamu ci abincin Mami ba, please Mami karki kuma tafiya ki
barmu, we are so sorry mun ji jiki wallahi, we missed you alot”.

“Zobon da Asma’u ta kurba ne ya sarqe ta ba shiri ta watso shi tsabar yanda mamakin kalaman Bashir
suka nemi kasheta a zaune.

“Bashir dai data sani ne yake wannan maganar?” Kai ita kam badan ciwo ba dadi ba da tace ta ringayi
duk wata ko Allah ze saito mata Bashir zuwa abinda ta dade tana fata.

WATA KISHIYAR

(Alkhairi CE KO SHARRI)

Na Maryamah_Mrs AM(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)

Page 8

To Aka ce mata da Miji se Allah dan kuwa Ma’u da Basharin ta suna qulewa a daki sukai muqus aka shiga
sharafin soyayya dan dama an dade ba’a hadu ba qarshe har makara tashi bacci sukayi. Safiyar ranar duk
su biyun da ka kallesu zaka san suna cikin walwala.
Ta cancada kwalliyarta da skirt and blouse na Atamfa komai ya fito se juyi take tana saka kwakwalwar
Bashir jijjiga. haka ta hada musu breakfast me rai da lafiya suka ci suka wuce makaranta dukda sam be so
yau ta zama ranar aiki ba ya so ace suna gida yau yaci duniyar sa da tsinke ya more amma ba komai ai
Gobe Friday zasu hadu.

Suna fita Qarasa yan abubuwan da suka rage mata tayi kafin ta shiga dakin ta ta kwanta dan huce gajiyar
da Bashir ya tara mata, “Bashir is too good” ta ayyana aranta. Wato yasan ta yanda duk ze wanke laifinsa
ta wannan fanni gwanin malami neda ta tabbatar samun irinsa se an tona.

Tana tsaka da tunanin shauqin daren jiyan ta jiyo qarar door bell da kuma ringing din wayarta. Wayar ta
fara jawowa ta duba, Anty ce matar ogan Bashir dake Flat din da yake kallon nasu, seta miqe tareda
daukan Qaramin mayafi dan dankwalin kanta ya zame.

A palour suka zube tare da Anty da ta farayiwa Asma’un tsiya tun daga qofa”

“Kai Ma’u kinga wani kyallin goshi da kike daga fitowa daga Asibiti har za’a maida wani kenan”. Daria
Asma’u tayi tana cewa

“Haba dai ai na gama nikam wadan nan ma sun isa Allah ya raya mana sisi na kwai zan ci gaba dayi”

“Inafa kika gama kedai ki shirya dan qila wasu biyun ne a tafe”

“Ba amin ba Anty” ta tare Antyn.

Gaisawa sukayi kafin Antyn tace mata

“Shekaran jiya na dawo wlh se dare ma nashigo Honey yake cemun Ai kina Asibiti ba lafiya, har zamu zo
jiya da magriba kuma yace sun hadu da Baban Aliyu a Masallaci ya ce masa kin dawo gida”
“Eh wallahi jiya da rana aka sallamoni ai gaskiya Anty kinsha gida kusan 3 weeks fa” Asma’u ta fada.

“Ki bari kedai zama nayi na huta nayi gyara sosai dan anan ba wani lokaci kake samu ka baje yanda kake
so ba mutum na saka maka ido” cewar Anty tana bawa Asma’u hannu suka kashe

“Kai Anty a ringa tausayin Baba na dai karki qarasa mana tsohon mu”

“Ke barni fa dole na kwaci kaina sarai kin san Uwargida na bata wasa da gyara dole nima na zage kar a
raina ni.

Hira suka shigayi Anty ta shiga fito da abubuwan da tayo wa Asma’u tsaraba tana cewa “Gashinan se a ci
gaba da gashi ban ce ki raga masa ko na second daya ba atoh” suka tuntsure da dariya Asma’u tana cewa
“Anty baki da dama”. Se wurin 12 sannan ta mata sallama ta tafi bayan ta rakata qofa ta dawo tana
tattare kayan zuwa dakinta a ranta tana qara jin qaunar Antyn dan yanda ta dauketa take kula da ita
kamar qanwarta da suka fito ciki daya.

Anty Suwaiba matar Engineer Abdullahi Gusau ce ogan Bashir.

Itace Matar sa ta biyu uwar gidan ta ma anan Lagos take da zama amma ba unguwarsu daya ba. Mace ce
me tsananin kirki dukda ta dan girmi Asma’u amma yanda take mu’amalantarta kaman qawaye ko
shaqiqan yaya da qanwa suke dan tunda suka fara haduwa jinin su ya hadu da Asma’un.

Ita kanta Asma’u tana ji da Antyn dan Ita tunda suka hadu rabon da tace ta siyi wani abun gyara da
kudinta, a koda yaushe Anty cikin yo musu aike kaya gangariya daga Zamfara garinsu take kuma duk
sanda Asma’u ta tambayeta nawane ta biya seta nuna bacin ranta. Ta kance da Asma’un

“Ni a qanwa na dauke ki, banida kowa a Lagos seke yanzu”.

Wasu daga cikin kayan ta fitar ta fara amfani dasu a ranta tana hasaso haduwarsu da Malam Bash dan
tasan yau kam se tafi jiya Armashi. Kafin ta gama an kira sallar Azahar dan haka tayi alwala tayi sallar
sannan ta kwanta zuwa La’asar kafin tasan abinda zata dafa musu kuma.
Couscous tayi musu da miyar hanta ganin lokaci ya qure, setayi marinating kifin da zata gasa musu su
qara dashi zuwa can anjima kafin a kwanta. Yauma batayi wasa ba gurin cin kwalliya ta daukar magana
dan har tafi ta Jiya. Wasu riga da skirt ta saka na kanti Oxblood da suka kama jikinta kamar tanayin nishi
zasu yage. Bata daura dankwali ba ta faka dogon baqin gashinta daya sha gyara se qanshi yake yi kafin
tabi kowanne lungu da saqo na jikinta ta shafe da hadaddun turarukanta da ita kadai tasan wadanda
take mixing da duk bala’in kwakwkwafin mutum baze taba cankar wane turare bane.

Abaya ta fitar Baqa tareda mayafinta ta ajiye a gefe saboda yaranta maza ne, dukda qanana ne tana
takatsantsan da irin shigar da zata fita gabansu da ita. Qugin motarsa data jiyo ya sakata saurin dora
abayar ta yafa qaramin veil dinta akanta tareda zura slippers din ta ta nufi waje dan ta taro su.

Bashir

Fitowarsa daga mota yayi kyakykyawan gani, Ma’un sa ce kamar wata yar budurwar Balarabiya, tundaga
nesa ya fara shaqar qamshin da takeyi wanda be taba jin sa a jikin wata mace ba bayan ita. Tamasa kyau
yanda tayi rolling mayafin ya zagaye kyakykyawar fuskarta tareda bayyar da gaban gashinta daya ke nan
luf a kwance ya qara qawata kwalliyar tata.

kallonta yake har besan sanda wayar hannunsa ta subuceba. Yana jin yanda yaran suke zuzuta kyan da
tayi amma nasa bakin kamar wanda aka sakawa qaton kwado a ka kulle ya kasa koda budeshi se idanu
daya zuba mata kawai.

Qarasawa gaban sa tayi ta durqusa tareda dakko masa wayar da ya yar bata miqa masa ba se jinta yayi
gaba daya ta rungumoshi, saitin kunnensa ta furta “Welcome home SH (sweet heart)”. Kamar wanda ta
tsoma a ruwan qanqara haka ya daskare a gurin yana jin kamar ya shide saboda muryarta da kuma
numfashinta daya sauka a cikin kunnensa. Hannunsa ta kama ta zura masa wayar kafin ta juya tabarshi
da shaqar qamshinta, batayi ko taku biyar ba taji an janyota ta baya yai mata wata kyakykyawar
runguma tareda sauke mata kiss a gefen wuyanta da mayafi be ida rufewa ba.

Zaro ido tayi tana riqe hannunsa, “Baban Ali a waje fa muke” ta fada ganin gogan na neman kauce hanya
se a sannan ya farga dan shifa a lokacin ita kadai yake gani se kuwa yaja hannunta qii suka shige cikin
gidan dan tuni yaran suka kama gaban su. Mantawa yayi da batun wata yunwa da gajiya daya kwaso
suka shige dakinsa kai tsaye , ai be ida birkicewa ba seda yai arba da ainihin kwalliyar Ma’unsa tuni labari
ya chanza.
Basu fito ba se qarfe goman dare, Babu kowa a palour alamar yaran harsun kwanta. Ma’u da duk tayi
laushi ta nemi kujera ta zauna Bashir kuwa Dining ya wuce dan se yanzu yake jinsa kamar ze fadi saboda
yunwa. Ya manta sam rabonsa da abinci tun na safe. A Babban plate ya juyo dukka abincin ya sakko da
shi inda take ya ajiye sannan ya koma ya dakko kwanon Fish din da Amna ta gasa.

Yana ci yana bata a baki har suka cinye se wani tarairayarta yakeyi kamar kwai, yanda yake rawar jiki da
ita se yake tuna mata da lokutan baya a sanda yana Bashir din Ma’u kafin zaman majalisa da sababbin
abokai ya sauya mata shi zuwa wani mutum na daban. Tana tuna irin gata da tarairayar daya ringa nuna
mata a shekarar farko ta aurensu. A lokacin ya kan sakata taji tamkar tafi kowacce mace dacen miji duk
kuwa da bata samu yanda take so ta bangaren kayan more rayuwa ba amma soyayya da tattalinta da ya
ringayi yafi mata komai dan dama ita ai dan soyayya ta aure shi bawai kudi ba.

Suna gama cin abincin dakin suka koma, ta gaji tibis dan haka ta haye gado ta kwanta yana matsa mata
jikinta. Wayarsa ce tayi qara, a tare suka duba sunan Amira da ta gani yana yawo yasa ta dauke kanta.
Satar kallonta yayi karaf kuwa suka hada ido, haka kawai yaji wani abu kamar nauyin Asma’u ya kamashi
cikin son basar wa ya dauke idonsa ba tareda ya amsa wayar ba.

Kiran da ya yanke wani ya sake shigowa ya sakata cewa “ka daga mana ba kiranka akeyi ba” seya dauki
wayar, be zauna anan ba ya fita falo. Da kallo ta bishi tana qoqarin hana shedan yin tasiri akanta “Itama
matarsa ce matsayinmu daya da ita” ta fadawa kanta sejin hawaye kawai tayi suna bin fuskarta.

Bata san randa zata dena jin zafin yankan bayan da suka mata ba. Da ace wata can Bashir ya aura koda
cikin dangin nasa ne damuwarta bazata kai haka ba amma fa Amirah, Amirah data dauka tamkar Amna.
Yarinyar da ta gama sanin sirrinta ciki da waje ita ya auro mata a matsayin kishiya se kawai ta rushe da
kukan takaicin da duk sanda ta tuna yanda auran Bashir ya kasance seta yi shi.

Babu wanda ze gane zafin da takeji se wadda aka kwatantawa irin abinda akai mata, se yanzu take ganin
dalilin da yake saka wasu matan aikata abubuwa da dama akan kishiya ko ma mijin kansa dan wallahi in
akayi maka wani abun in ba me qarfin imani da tawallaki ba se kaji kamar bazaka yarda ba se ka dauki
mataki. Har bacci ya dauketa Bashir be shigo ba se Asuba ta farka ta ganshi a bayanta.

Ko a fuska bata nuna masa komai tayi sallah a dakin sannan ta fita gurin yara dan jiya basu samu ko yin
magana ba. Seda ta hada musu abinci suka shirya tareda zama suka fara breakfast sannan ta koma dakin
ganin Baban Ali be fito ba.
A tsaye ta ganshi yana zuge jakar da yake tafiya da ita Gombe, dauke kanta tayi kamar bata gani ba tana
cewa”Sun shirya fa gasu can sun fara cin abinci basu jiraka ba” tayi gaba da niyyar shigewa toilet dan
bata so yai mata maganar tafiyar sa sedai tun kafin ta shiga ta jiyo shi yana cewa

“Ke zaki dauko su daga school yau zan wuce Gombe ne daga office bazan dawo ta nan ba” ba tareda ta
juyo ba tace masa “Allah ya tsare ka gaishe su” tai shigewarta abinta.

Bin kofar yayi da kallo kafin jiki a sanyaye ya dauki Laptop bag dinsa da jakar kayan ya fita, seda ya kaisu
mota sannan ya dawo shima ya hau Dining din amma se ya kasa taba komai.

Shiru yayi yana kallon yaran suna cin abincinsu har suka gama Ahmad ya kalleshi yace “Abbi ina Mami
zamu tafi”

“Kuje mu tafi wanka take yi” ya fada yana miqewa. Har sun fita ya juyo zuwa cikin gidan, Bayaso su rabu
da bacin rai kodan albarkacin farin cikin data bashi a kwana biyun nan. Harya kama Handle din dakin
shegiyar zuciyar da take masa famfo ta zugo shi “to me kayi da zaka ke bata haquri ma?” Zuciyar ta raya
masa, Seya saki qofar ya juya kawai.

Asma’u da ke zaune tana jiran tsammanin zuwan Bashir ya rarrasheta, ajiyar zuciya ta sauke jin an taba
qofa harda qara narke fuska tana ayyana abinda zatayi ta gigitashi se taji shiru, the next thing ko se jin
tashin motarsa tayi ta yaye window da sauri har sun wuce se qurar daya tayar, baki bude take kallon
motar harya qule mata, “Hmmm” ta sauke numfashi kawai ta shiga shafa mai, bataso ta tuna abun ma
bare ranta ya baci ita dai addu’arta idan Bashir nada rabon ganewa to Allah ya maido shi kan hanya.

Gombe gidan Addah

A daren ranar da Bashir ya turo musu da kudi tayi ta kiran Number da Malam Wizy ya basu bata samu
ba, bata haqura ba tayita gwada Number har washe gari amma shiru gashi ta kira wayar Hajia Balaraba
ma a kashe.

Jikinta dabe gama warwarewa bane ya hanata fita ta bari akan zuwa talata tasan ta warke seta je gidan
Hajia Balaraban ta dai ci gaba da kiran wayar tasa ko zata samu cikin Sa’a kuwa ranar Laraba da safe tana
kira ta shiga.
Ta gama ringing ba’a dauka ba seda ta sake kira aka daga. Muryar wata tsohuwa taji daga ji taji duniya
har ta gaji tana cewa “kai ku duba nan waye ya bugo, Wizy da qaninsa Iliya suna zaune a dakin Kakarsu
daidai lokacin sunzo gaishe ta, miqa wa Wizy wayar tsohuwa tayi tana sake cewa ya duba ga gani.

Sallama Adda ta sakeyi, fes Wizy ya gane muryarta se yai saurin datse kiran ya miqe yana cewa Kaka
yana zuwa.

Can wani lungu ya buya yayi recharging wayar kaka ya dannanwa Adda kira.

“Salamu alaikum malam ina wuni” ta fada cike da zumudi

“Lafiya lau dawa nake magana” ya tambaya irin be gane ta din nan ba

“Nice Malam wadda Sani ya kawo mu (sunan da Me Napep ya gaya musu kenan)

“To to hajia ya gida naji ki shiru da alama buqata ta fara biya kenan”

“Wallahi malam na danyi rashin lafiya ne kwana biyu kuma na kikkiraka ma wayar a kashe” Addah ta
fada

“Eh wallahi kwana biyu kam na kashe waya dan na shiga halwa ne inata ayyukan ku dafatan ana ganin
haske ko”

“Sosai kuwa Malam ya fara samuwa”

“To haka ake so yanzu to ya akayi?” Ya sake tambayarta.

“Dama na samu wasu kudin ne nace bari na turo a ci gaba da aikin mu sameshi gaba daya”

“Kin kyauta kuwa ai ina tabbatar miki idan aiki ya kammala hajia nasan indai kin riqe amana har ni
dinnan se kin mun kyautar kujerar hajji” Wizy ya fada yana tsallen murna jin wata banzar zata fado.

“Insha Allahu kuwa malam yanzu dai ka bada akawun a tura kudin nan ayi a ci gaba”
“Ba matsala da mun aje waya zan turo miki” sukayi sallama yana qara karanta mata qanzon kurege.

Harya fara typing account details dinsa wani tunani ya kawo kansa, idan ta tashi fa za’a Iya tracing dinsa
ta banki, se yai saurin gogewa ya danna mata kira. Tana dagawa yace

“Hajia nace kudinnan ki cire su, akwai yaro da na aika qauye ya siyo ragunan wasu aiki bari naji in be tafi
ba se ya biyo ya karba kawai ya wuce” da haka sukayi sallama.

Minti kadan ya sake kiranta yace ze turo yaro, nan ta zayyana masa Address ashe ma basu da nisa ya ma
gane gidan daya daga cikin yaran mijinta abokinsa ne. Isma’il me Napep ya dannawa waya suka tafi
tareda wani qaninsa me suna Nasiru da yai shigar me zuwa kasuwar qauye. Ko kafin su Iso Adda ta aika
Ummi an ciro mata 80k kudin rago biyu yaro na zuwa ya shiga har palour ta ta bashi kudi ya jefa a buhu
ya fice.

Gaba suka qara aka tsaya kowa aka bashi rabonsa ya zuba a Aljihu Malam Wizy ya zare sim din Kaka ya
ballashi biyu ya zubar yana cewa “mun tatseta ya isa haka” suka sheqe da dariya.

To Addah Allah ya maida Alkahiri ya kiyaye na gaba.

WATA KISHIYAR

(Alkhairi CE KO SHARRI)

Na Maryamah_Mrs AM(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)

Page 8
To Aka ce mata da Miji se Allah dan kuwa Ma’u da Basharin ta suna qulewa a daki sukai muqus aka shiga
sharafin soyayya dan dama an dade ba’a hadu ba qarshe har makara tashi bacci sukayi. Safiyar ranar duk
su biyun da ka kallesu zaka san suna cikin walwala.

Ta cancada kwalliyarta da skirt and blouse na Atamfa komai ya fito se juyi take tana saka kwakwalwar
Bashir jijjiga. haka ta hada musu breakfast me rai da lafiya suka ci suka wuce makaranta dukda sam be so
yau ta zama ranar aiki ba ya so ace suna gida yau yaci duniyar sa da tsinke ya more amma ba komai ai
Gobe Friday zasu hadu.

Suna fita Qarasa yan abubuwan da suka rage mata tayi kafin ta shiga dakin ta ta kwanta dan huce gajiyar
da Bashir ya tara mata, “Bashir is too good” ta ayyana aranta. Wato yasan ta yanda duk ze wanke laifinsa
ta wannan fanni gwanin malami neda ta tabbatar samun irinsa se an tona.

Tana tsaka da tunanin shauqin daren jiyan ta jiyo qarar door bell da kuma ringing din wayarta. Wayar ta
fara jawowa ta duba, Anty ce matar ogan Bashir dake Flat din da yake kallon nasu, seta miqe tareda
daukan Qaramin mayafi dan dankwalin kanta ya zame.

A palour suka zube tare da Anty da ta farayiwa Asma’un tsiya tun daga qofa”

“Kai Ma’u kinga wani kyallin goshi da kike daga fitowa daga Asibiti har za’a maida wani kenan”. Daria
Asma’u tayi tana cewa

“Haba dai ai na gama nikam wadan nan ma sun isa Allah ya raya mana sisi na kwai zan ci gaba dayi”

“Inafa kika gama kedai ki shirya dan qila wasu biyun ne a tafe”

“Ba amin ba Anty” ta tare Antyn.

Gaisawa sukayi kafin Antyn tace mata


“Shekaran jiya na dawo wlh se dare ma nashigo Honey yake cemun Ai kina Asibiti ba lafiya, har zamu zo
jiya da magriba kuma yace sun hadu da Baban Aliyu a Masallaci ya ce masa kin dawo gida”

“Eh wallahi jiya da rana aka sallamoni ai gaskiya Anty kinsha gida kusan 3 weeks fa” Asma’u ta fada.

“Ki bari kedai zama nayi na huta nayi gyara sosai dan anan ba wani lokaci kake samu ka baje yanda kake
so ba mutum na saka maka ido” cewar Anty tana bawa Asma’u hannu suka kashe

“Kai Anty a ringa tausayin Baba na dai karki qarasa mana tsohon mu”

“Ke barni fa dole na kwaci kaina sarai kin san Uwargida na bata wasa da gyara dole nima na zage kar a
raina ni.

Hira suka shigayi Anty ta shiga fito da abubuwan da tayo wa Asma’u tsaraba tana cewa “Gashinan se a ci
gaba da gashi ban ce ki raga masa ko na second daya ba atoh” suka tuntsure da dariya Asma’u tana cewa
“Anty baki da dama”. Se wurin 12 sannan ta mata sallama ta tafi bayan ta rakata qofa ta dawo tana
tattare kayan zuwa dakinta a ranta tana qara jin qaunar Antyn dan yanda ta dauketa take kula da ita
kamar qanwarta da suka fito ciki daya.

Anty Suwaiba matar Engineer Abdullahi Gusau ce ogan Bashir.

Itace Matar sa ta biyu uwar gidan ta ma anan Lagos take da zama amma ba unguwarsu daya ba. Mace ce
me tsananin kirki dukda ta dan girmi Asma’u amma yanda take mu’amalantarta kaman qawaye ko
shaqiqan yaya da qanwa suke dan tunda suka fara haduwa jinin su ya hadu da Asma’un.

Ita kanta Asma’u tana ji da Antyn dan Ita tunda suka hadu rabon da tace ta siyi wani abun gyara da
kudinta, a koda yaushe Anty cikin yo musu aike kaya gangariya daga Zamfara garinsu take kuma duk
sanda Asma’u ta tambayeta nawane ta biya seta nuna bacin ranta. Ta kance da Asma’un

“Ni a qanwa na dauke ki, banida kowa a Lagos seke yanzu”.


Wasu daga cikin kayan ta fitar ta fara amfani dasu a ranta tana hasaso haduwarsu da Malam Bash dan
tasan yau kam se tafi jiya Armashi. Kafin ta gama an kira sallar Azahar dan haka tayi alwala tayi sallar
sannan ta kwanta zuwa La’asar kafin tasan abinda zata dafa musu kuma.

Couscous tayi musu da miyar hanta ganin lokaci ya qure, setayi marinating kifin da zata gasa musu su
qara dashi zuwa can anjima kafin a kwanta. Yauma batayi wasa ba gurin cin kwalliya ta daukar magana
dan har tafi ta Jiya. Wasu riga da skirt ta saka na kanti Oxblood da suka kama jikinta kamar tanayin nishi
zasu yage. Bata daura dankwali ba ta faka dogon baqin gashinta daya sha gyara se qanshi yake yi kafin
tabi kowanne lungu da saqo na jikinta ta shafe da hadaddun turarukanta da ita kadai tasan wadanda
take mixing da duk bala’in kwakwkwafin mutum baze taba cankar wane turare bane.

Abaya ta fitar Baqa tareda mayafinta ta ajiye a gefe saboda yaranta maza ne, dukda qanana ne tana
takatsantsan da irin shigar da zata fita gabansu da ita. Qugin motarsa data jiyo ya sakata saurin dora
abayar ta yafa qaramin veil dinta akanta tareda zura slippers din ta ta nufi waje dan ta taro su.

Bashir

Fitowarsa daga mota yayi kyakykyawan gani, Ma’un sa ce kamar wata yar budurwar Balarabiya, tundaga
nesa ya fara shaqar qamshin da takeyi wanda be taba jin sa a jikin wata mace ba bayan ita. Tamasa kyau
yanda tayi rolling mayafin ya zagaye kyakykyawar fuskarta tareda bayyar da gaban gashinta daya ke nan
luf a kwance ya qara qawata kwalliyar tata.

kallonta yake har besan sanda wayar hannunsa ta subuceba. Yana jin yanda yaran suke zuzuta kyan da
tayi amma nasa bakin kamar wanda aka sakawa qaton kwado a ka kulle ya kasa koda budeshi se idanu
daya zuba mata kawai.

Qarasawa gaban sa tayi ta durqusa tareda dakko masa wayar da ya yar bata miqa masa ba se jinta yayi
gaba daya ta rungumoshi, saitin kunnensa ta furta “Welcome home SH (sweet heart)”. Kamar wanda ta
tsoma a ruwan qanqara haka ya daskare a gurin yana jin kamar ya shide saboda muryarta da kuma
numfashinta daya sauka a cikin kunnensa. Hannunsa ta kama ta zura masa wayar kafin ta juya tabarshi
da shaqar qamshinta, batayi ko taku biyar ba taji an janyota ta baya yai mata wata kyakykyawar
runguma tareda sauke mata kiss a gefen wuyanta da mayafi be ida rufewa ba.
Zaro ido tayi tana riqe hannunsa, “Baban Ali a waje fa muke” ta fada ganin gogan na neman kauce hanya
se a sannan ya farga dan shifa a lokacin ita kadai yake gani se kuwa yaja hannunta qii suka shige cikin
gidan dan tuni yaran suka kama gaban su. Mantawa yayi da batun wata yunwa da gajiya daya kwaso
suka shige dakinsa kai tsaye , ai be ida birkicewa ba seda yai arba da ainihin kwalliyar Ma’unsa tuni labari
ya chanza ️.

Basu fito ba se qarfe goman dare, Babu kowa a palour alamar yaran harsun kwanta. Ma’u da duk tayi
laushi ta nemi kujera ta zauna Bashir kuwa Dining ya wuce dan se yanzu yake jinsa kamar ze fadi saboda
yunwa. Ya manta sam rabonsa da abinci tun na safe. A Babban plate ya juyo dukka abincin ya sakko da
shi inda take ya ajiye sannan ya koma ya dakko kwanon Fish din da Amna ta gasa.

Yana ci yana bata a baki har suka cinye se wani tarairayarta yakeyi kamar kwai, yanda yake rawar jiki da
ita se yake tuna mata da lokutan baya a sanda yana Bashir din Ma’u kafin zaman majalisa da sababbin
abokai ya sauya mata shi zuwa wani mutum na daban. Tana tuna irin gata da tarairayar daya ringa nuna
mata a shekarar farko ta aurensu. A lokacin ya kan sakata taji tamkar tafi kowacce mace dacen miji duk
kuwa da bata samu yanda take so ta bangaren kayan more rayuwa ba amma soyayya da tattalinta da ya
ringayi yafi mata komai dan dama ita ai dan soyayya ta aure shi bawai kudi ba.

Suna gama cin abincin dakin suka koma, ta gaji tibis dan haka ta haye gado ta kwanta yana matsa mata
jikinta. Wayarsa ce tayi qara, a tare suka duba sunan Amira da ta gani yana yawo yasa ta dauke kanta.
Satar kallonta yayi karaf kuwa suka hada ido, haka kawai yaji wani abu kamar nauyin Asma’u ya kamashi
cikin son basar wa ya dauke idonsa ba tareda ya amsa wayar ba.

Kiran da ya yanke wani ya sake shigowa ya sakata cewa “ka daga mana ba kiranka akeyi ba” seya dauki
wayar, be zauna anan ba ya fita falo. Da kallo ta bishi tana qoqarin hana shedan yin tasiri akanta “Itama
matarsa ce matsayinmu daya da ita” ta fadawa kanta sejin hawaye kawai tayi suna bin fuskarta.

Bata san randa zata dena jin zafin yankan bayan da suka mata ba. Da ace wata can Bashir ya aura koda
cikin dangin nasa ne damuwarta bazata kai haka ba amma fa Amirah, Amirah data dauka tamkar Amna.
Yarinyar da ta gama sanin sirrinta ciki da waje ita ya auro mata a matsayin kishiya se kawai ta rushe da
kukan takaicin da duk sanda ta tuna yanda auran Bashir ya kasance seta yi shi.

Babu wanda ze gane zafin da takeji se wadda aka kwatantawa irin abinda akai mata, se yanzu take ganin
dalilin da yake saka wasu matan aikata abubuwa da dama akan kishiya ko ma mijin kansa dan wallahi in
akayi maka wani abun in ba me qarfin imani da tawallaki ba se kaji kamar bazaka yarda ba se ka dauki
mataki. Har bacci ya dauketa Bashir be shigo ba se Asuba ta farka ta ganshi a bayanta.

Ko a fuska bata nuna masa komai tayi sallah a dakin sannan ta fita gurin yara dan jiya basu samu ko yin
magana ba. Seda ta hada musu abinci suka shirya tareda zama suka fara breakfast sannan ta koma dakin
ganin Baban Ali be fito ba.

A tsaye ta ganshi yana zuge jakar da yake tafiya da ita Gombe, dauke kanta tayi kamar bata gani ba tana
cewa”Sun shirya fa gasu can sun fara cin abinci basu jiraka ba” tayi gaba da niyyar shigewa toilet dan
bata so yai mata maganar tafiyar sa sedai tun kafin ta shiga ta jiyo shi yana cewa

“Ke zaki dauko su daga school yau zan wuce Gombe ne daga office bazan dawo ta nan ba” ba tareda ta
juyo ba tace masa “Allah ya tsare ka gaishe su” tai shigewarta abinta.

Bin kofar yayi da kallo kafin jiki a sanyaye ya dauki Laptop bag dinsa da jakar kayan ya fita, seda ya kaisu
mota sannan ya dawo shima ya hau Dining din amma se ya kasa taba komai.

Shiru yayi yana kallon yaran suna cin abincinsu har suka gama Ahmad ya kalleshi yace “Abbi ina Mami
zamu tafi”

“Kuje mu tafi wanka take yi” ya fada yana miqewa. Har sun fita ya juyo zuwa cikin gidan, Bayaso su rabu
da bacin rai kodan albarkacin farin cikin data bashi a kwana biyun nan. Harya kama Handle din dakin
shegiyar zuciyar da take masa famfo ta zugo shi “to me kayi da zaka ke bata haquri ma?” Zuciyar ta raya
masa, Seya saki qofar ya juya kawai.

Asma’u da ke zaune tana jiran tsammanin zuwan Bashir ya rarrasheta, ajiyar zuciya ta sauke jin an taba
qofa harda qara narke fuska tana ayyana abinda zatayi ta gigitashi se taji shiru, the next thing ko se jin
tashin motarsa tayi ta yaye window da sauri har sun wuce se qurar daya tayar, baki bude take kallon
motar harya qule mata, “Hmmm” ta sauke numfashi kawai ta shiga shafa mai, bataso ta tuna abun ma
bare ranta ya baci ita dai addu’arta idan Bashir nada rabon ganewa to Allah ya maido shi kan hanya.

Gombe gidan Addah


A daren ranar da Bashir ya turo musu da kudi tayi ta kiran Number da Malam Wizy ya basu bata samu
ba, bata haqura ba tayita gwada Number har washe gari amma shiru gashi ta kira wayar Hajia Balaraba
ma a kashe.

Jikinta dabe gama warwarewa bane ya hanata fita ta bari akan zuwa talata tasan ta warke seta je gidan
Hajia Balaraban ta dai ci gaba da kiran wayar tasa ko zata samu cikin Sa’a kuwa ranar Laraba da safe tana
kira ta shiga.

Ta gama ringing ba’a dauka ba seda ta sake kira aka daga. Muryar wata tsohuwa taji daga ji taji duniya
har ta gaji tana cewa “kai ku duba nan waye ya bugo, Wizy da qaninsa Iliya suna zaune a dakin Kakarsu
daidai lokacin sunzo gaishe ta, miqa wa Wizy wayar tsohuwa tayi tana sake cewa ya duba ga gani.

Sallama Adda ta sakeyi, fes Wizy ya gane muryarta se yai saurin datse kiran ya miqe yana cewa Kaka
yana zuwa.

Can wani lungu ya buya yayi recharging wayar kaka ya dannanwa Adda kira.

“Salamu alaikum malam ina wuni” ta fada cike da zumudi

“Lafiya lau dawa nake magana” ya tambaya irin be gane ta din nan ba

“Nice Malam wadda Sani ya kawo mu (sunan da Me Napep ya gaya musu kenan)

“To to hajia ya gida naji ki shiru da alama buqata ta fara biya kenan”

“Wallahi malam na danyi rashin lafiya ne kwana biyu kuma na kikkiraka ma wayar a kashe” Addah ta
fada

“Eh wallahi kwana biyu kam na kashe waya dan na shiga halwa ne inata ayyukan ku dafatan ana ganin
haske ko”

“Sosai kuwa Malam ya fara samuwa”

“To haka ake so yanzu to ya akayi?” Ya sake tambayarta.


“Dama na samu wasu kudin ne nace bari na turo a ci gaba da aikin mu sameshi gaba daya”

“Kin kyauta kuwa ai ina tabbatar miki idan aiki ya kammala hajia nasan indai kin riqe amana har ni
dinnan se kin mun kyautar kujerar hajji” Wizy ya fada yana tsallen murna jin wata banzar zata fado.

“Insha Allahu kuwa malam yanzu dai ka bada akawun a tura kudin nan ayi a ci gaba”

“Ba matsala da mun aje waya zan turo miki” sukayi sallama yana qara karanta mata qanzon kurege.

Harya fara typing account details dinsa wani tunani ya kawo kansa, idan ta tashi fa za’a Iya tracing dinsa
ta banki, se yai saurin gogewa ya danna mata kira. Tana dagawa yace

“Hajia nace kudinnan ki cire su, akwai yaro da na aika qauye ya siyo ragunan wasu aiki bari naji in be tafi
ba se ya biyo ya karba kawai ya wuce” da haka sukayi sallama.

Minti kadan ya sake kiranta yace ze turo yaro, nan ta zayyana masa Address ashe ma basu da nisa ya ma
gane gidan daya daga cikin yaran mijinta abokinsa ne. Isma’il me Napep ya dannawa waya suka tafi
tareda wani qaninsa me suna Nasiru da yai shigar me zuwa kasuwar qauye. Ko kafin su Iso Adda ta aika
Ummi an ciro mata 80k kudin rago biyu yaro na zuwa ya shiga har palour ta ta bashi kudi ya jefa a buhu
ya fice.

Gaba suka qara aka tsaya kowa aka bashi rabonsa ya zuba a Aljihu Malam Wizy ya zare sim din Kaka ya
ballashi biyu ya zubar yana cewa “mun tatseta ya isa haka” suka sheqe da dariya.

To Addah Allah ya maida Alkahiri ya kiyaye na gaba


WATA KISHIYAR

(Alkhairi CE KO SHARRI)

Na Maryamah_Mrs AM (Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)

Page 9

Gombe

Ana kiran magriba Bashir ya shiga gidan sa na Gombe, tun qarfe hudu da rabi suka sauka tazarar tafiyar
daga Akko zuwa Gombe ta kaishi Magriba.

A qofar gidansa Me Taxi din daya dauko shata daga Airport ya sauke shi ya fito dakyar yana jan qafa ga
yunwa ga gajia tiqis saboda yau yasha aiki a office ga kuma tafiya dukda a jirgine.

Yana qoqarin bude get din a ransa yana ayya Allah yasa ma ta dawo gidan dan yana daga ciki rashin
sanin ya kamatan Amirah a duk sanda zezo hankalin ta be taba gaya mata tazo ta gyara gida tayi girki
dan tarbarsa ba se in ya tuna mata. Dama can tun tana yarinya yasan qazama ce ta gaske daga baya ne
zama da Asma’u ya sa tadan chanza tareda koyar wasu abubuwan amma dukda haka tsaftar biri gareta.
Zata yi wanka ta gyara jiki amma fa duk dattin guri haka zatayi zamanta.

Yana jefa qafa busassun ganyayen bishiyar da suka zube ne suka masa Maraba. Compound din ya hada
uwar qura dama ga shi an fara Sanyi da Hazo a garin. Takaici ya qume shi danya tabbata bata dawo ba
kenan.

Bangaren Asma’u ya nufa dan yasan yace zeje dakinsa na part din Amiran ma ransa ne ze qara baci. Seda
ya kunna wutar bangaren sannan ya bude palour ya shiga da Bismillah. Komai na nan a kintse yanda ta
barshi, cike da gajiya yake daga qafafunsa ya haye benen da ze kaishi dakinsa. Nan dinma fes dashi ya
saka hannu ya yaye ledar da take shimfidawa akan Katifa bayan ta cire bedsheets din saboda qura
sannan ya zube kayan daya shigo dasu.
Toilet ya fada ya dan daurayeshi yayi wanka tareda dauro Alwala ya fito. Harya idar da sallah beji alamar
waniya shigo gidan ba ransa ya qara baci amma seya danne kawai ya janyo wayarsa ya kira Qaninsa
Naziru ya kawo masa motarsa dayake amfani da ita anan. Bayan ya kashe se yayi dialing number Asma’u,
deep down yanajin kaman dazu da safe be kyauta mata ba.

Har wayar ta qaraci ringing dinta bata daga ba, ya sake kira nan ma shiru se ya maida akalar kiran zuwa
ga Amirah dan yaga alamar hankalinta ragaggene. Ai a qalla yaci ta kira taji yazo ko kuwa tunda tasan da
zuwan nasa yau amma still itama bata dauki wayar ba.

Ajiye wayar yayi a kan gado cikinsa na cigaba da qugin yunwa shikadai se sakin qwafa yakeyi da ayyana
hukuncin da ze dauka akan Amirah. Kusan minti 20 Naziru ya kirashi ya iso, se ya dauki wallet dinsa da
keys ya saka a Aljihu ya fita. Naziru na ganin sa ya fito daga motar da niyyar bude get ya shigar masa da
ita Bashir din ya dakatar dashi da cewa

“Muje ka kaini naci abinci yunwa nake ji”.

Suna tafe babu me cewa qala kowa da kalar tunanin da yakeyi a zuciyarsa, Naziru ne ya datse shirun da
tambayar Yayan nasa Su Aliyu yace suna lafiya. Wani restaurant ya kaishi be fita daga motar ba ya bawa
Naziru ATM yace ya yiwo musu take away ya karba ya tafi a ransa yana mamakin meya faru Amira batayi
masa girki ba, tunawa yayi da tana da ciki se yai zaton ko shi ya hanata girkin amma dai ko yaya ne
mutum ya taho gari ya gari har Lagos ai ko Indomie ta daure ta girka masa shidai ya siyo abincin ya fito.

Bashir kuwa bayan Fitar Naziru wayarsa ya zaro ya duba ko wata daga cikinsu ta biyo missed call dinsa
amma yaga wayam. Na Ma’u be dame shi sosai ba dan yafi gasgata bata kusa da wayar ya santa sarai ko
fada suke bata qin daukar wayar sa sedai ta daga tayi shiru amma ita wannan yarinyar fa?

In tana da hankali ai ita ya kamata ta kirashi ko amma gashi haryanzu ana neman 8 na dare bata kira ba.
Har qofar gida Naziru ya kaishi ya shiga da Motar kafin ya fito yai masa sallama da niyar wucewa ya
tsaidashi yace su shiga ciki.

Har saman ya kaishi yace ya gyara masa dakin dan baze iya kwanciya a ciki haka ba Bashir akwai tsafta
koya datti yake a guri baya so abinda yake qara Masa son Ma’u kenan tsabtar ta ciki da waje ya jinjija
mata ta wannan fannin sosai.
Har palour seda Naziru ya gyara tsaf ya goge ransa fal mamaki dan ya tabbatar yanzu Amirah bata gida
to ko bata san ya zo bane? Shidai ya gama tattara komai ya tsaya jiran yayan nasa daya shiga daki ya fito.
Kudi ya bashi yace ya hau mota tareda ce masa idan yaje gida ya cewa Dada seda safe ze shigo ya bishi
ya kulle qofar ya dawo.

Yana shiga palour Asma’u ta kirashi se ya qarasa kan kujera ya zauna dakyau yana amsa wayar.

Asma’u.

Lokacin da Bashir ya kirata wayar ta na hannunta tana chatting da Umaima yayarta ce da suke Uba daya
amma ita take bi a cikin gidansu. Akwai shaquwa sosai tsakaninsu dan kusan bata da Aminiya ma sama
da ita. Hira suke yi tana gaya mata tafiyar Bashir din Gombe da yanda suka rabu.

“Ma’u kenan nidai bazan gaji da ce miki ki qara haquri akan wanda kikeyi ba, zuwa yanzu inda sabo ma ai
yaci ki saba da wannan mood swings din nasa, ki watsar lamarin sa idan yayi dariya kiyi in ya daure kema
haka. Ki kuma ci gaba da addu’a idan ma wani ne yake shiga tsakaninki dashi Allah ya miki maganin sa”
cewar Umaima.

Tana cikin yi mata reply kiransa ya shigo tacewa Umaiman “kinga ma yana kira”

“Ki daga kiji me zece”

“Barshi kawai bazan daga ba se zuwa anjima sun kwanta zan kirashi” cewar Ma’u. Dariya Umaima tayi
tana cewa

“Haba ai kuma ba zaki biye mata ku taru ku zama daya ba tunda ke kinsan abinda ya kamata, ki daga
kuma karki nuna masa wani bacin rai ko wani abu dukda nasan ki ma Ma’ulle akwai sanin ya kamata ai”
tayi maganar cikin sigar tsokana. Da “toh” Asma’u ta amsa ta ta kashe Datan bawai dan zata amsa kiran
ba dan ta qudurce a ranta seta koyawa yarinyar nan hankali taji idan abinda take mata da dadi yanda
take kiransa duk sanda taga dama kamar ita kadai take dashi.

Yanzu nema ta rage ada bata tashi kiransa wataran se sha biyun dare sun kwanta bacci, farkon wannan
cikin nata ma lokacin tana laulayi akwai ranar da suna tsaka da soyayyarsu wurin 2 na dare ta kirashi wai
ta kasa bacci se Amai take shine ta kira shima ta tashe shi.
Baqin ciki kamar Asma’u ta fasa ihu har bata san sanda ta fizge wayar ta tuttura mata ashar ba kuma
saboda rashin adalci irin na Bashir qarshe ita yaji haushi akan me zata zageta bata ga cewa lalura ce ta
sakata kiransa ba ranar kwana tayi tana kukan baqin ciki ai kuwa seda tayi masa yajin kusan wata dakyar
ya shawo kanta ta sakko.

Sedata mula dan kanta ta gama komai sannan ta shiga daki ta kirashi, a yanda ta lissafa yanzu dole suna
zaune ne suna hutawa dan haka tayi niyyar jan hirar har se illa masha Allahu harda loda kati a wayarta
saboda tsaro (Sorry Ma’u wrong timing ).

Lafewa ta sakeyi a cikin gado sanda ya amsa wayar ta gaishe shi da tambayar ya hanya ya amsa mata da
lafiya lau.

Rai rai ta saki jiki suka ringa hirar da sun manta rabon da suyi irinta, shi mamakin yanda ta sake kamar ba
abinda ya faru ita mamakin yanda yake amsata sosai kamar ba Bashir ba yau ba Miskilancin nan babu
baqin rai. Yanda take masa shagwaba kamar wata sweet sixteen yana biyeta gaba daya tagama narkar
dashi a zaune, Hira tayi dadi tama manta da batun wai dan ta musgunawa kishiya yasa ta kirashi sema
kwantowa kansu ruwa da sukayi gaba daya ta rudashi da salon da take masa magana shima ya rudata da
masa salon, dakyar suka rabu a wayar lokacin 12 harta gota shima Asma’u ce ta kashe ganin yana neman
sakata a uku to ai shi ga matar sa nan itafa sedai ta kama pillow batasan Gogan har ya fita shiga tashin
hankali ba.

Haka ta kwanta tana juyi Kafin bacci ya saceta ranta fes koba komai dai Ta qunsawa Amirah.

Bashir

Yana zaune bayan sun gama wayar se zufa yake sharewa duk da sanyin Ac daya karade palour dan gaba
daya Asma’u ta warware masa notin kai. Dakyar ya miqe ya nufi fridge din daya kunna tun dazu ya dakko
ruwan sanyi ya kwankwada yana sauke ajiyar zuciya Haushin Amirah na sake ninkuwa a Zuciyarsa har ya
gama wayar nan beji shigowar kiranta ko message ba gashi yanzu dayan dare ta kusa idan banda bata da
hankali ai yaci ta kira taji ko lafiya ya taho ko be taho ba amma ina da dai ya mata alqawarin kudi ne be
cika ba da yanzu ta ishe shi da kira kamar yaci bashin ta. Kwafa yayi a ransa yana jin kaman gobe ya juya
Lagos kawai tunda zuwan nasa beda muhimmanci tunda bata damu ba.

Haka ya daddafa ya kwanta kafin ya samu bacci ya daukeshi.


Gidan Addah

Wuni Addah tayi tana bankawa Amira jiqe jiqen yan bori da magungunan mata ko tsoron halin da take
ciki kar wani abu ya sami babyn basayi, bata haquraba seda Amiran ta fara sheqa Amai tukunna aka
koma cushe cushe dana hayaqi. Bayan maganin gurin Wizy ta tura an sake karbo mata wasu duk ta
banka mata a cewarta gara a hada hannu da yawa ayi maza buqata ta biya.

Babu lissafin zuwa ta gyara gida bare aje ga batun yi masa girki sukayi zaman su na jira yazo da kansa
yace su tafi tunda a kwanakin ta sami kansa suna abin arziqi dan kiran da tayi masa jiya da daddare ma
kuka ta saka masa akan ita dai yazo tana missing nasa in ba haka ba zata hawo jirgi ta zo Lagos sedai
Anty ta basu daki.

A lokacin yasha mamakinta dan shidai Rashin kunyar Amirah na daure masa kai ko kadan bata jin
nauyinsa wanda sam ba haka Asma’u take ba. Ma’u bata masa irin wadannan maganganun gatsal ta dai
san signs da signals da take amfani dasu wanda suke bala’in burge shi da qawata zuciyarsa dan kullum
cikin qara masa sabon ilimi take amma ita wannan se zance a baki ba abinda ta sani idan an zo wajen.

Se bayan Magriba ta shirya taci uwar kwalliyarta dan tasan zuwa sannan ya sauka Gombe. Ita sam
tunanin taje ta gyara gida be zo mata da daman duk sanda zezo shi yake tuna mata to jiya da be magana
ba itama tunda tsaftar ba damunta tayi ba se bata je ba a ganinta ai befi sati uku da zuwansa na qarshe
ba gidan beyi datti ba ai. Tana zaune Adda na qara karanta mata yanda za’a yi suna jiran zuwan Bashir
shiru se ji sukayi ana rufe qofar gidan ta kalli agogo 12 saura.

Seda gabanta ya fadi sanda taga missed call dinsa tun wurin bakwai ya kirata. A yanda ta lissafa sunyi
waya sanda ze taso yace mata yanzu zasu taho kenan lokacin da ya sake kira yana Gombe ai ita yaci ta
kira taji ya sauka.

To yanzu ya zatayi ta kirashi ne ko Aa haka tayi ta wasi wasi bata ko iya tankawa Addah dake faman
sababi naqin zuwan Bashir din ba har tana da safe zata je ta samu uwarsa taji dalili dan baze ja mata
asara ba wallahi.

Ita dai Amira daki ta shige ta chanza kaya dan Addah tace karta kuskura tayi wanka ance se ya kwanta da
ita tukunna saboda abubuwan da ta sassaka, haka ta kwanta tana zullumin haduwarsu dan dai ta haqura
bazata kirashi yau ba gara ta bari da safe se taji duk yanda ake ciki tasan dai ta kwafsa tabbas dama yaya
ana lallabawa ne kuma yanzu ta sake ballo musu ruwa.

Tunanin qaryar da zata yanka masa in sun hadu ta shigayi amma duk wadda ta hado seta ga ze dago ta
qarshe ta fawwalawa Allah kawai ta kwanta duk yanda goben tayi shikenan.

Washe gari Bashir tun qarfe takwas ya nufi gidansu, tun daga waje yake jiyo tashin muryar Addah data
taso Amirah a gaba suka taho gurin Dada dan jin ina Bashir ya maqale dan ita bata magana a hankali.
Bacin ransa ne ya nunku wato har sunada kwarin guiwar kawo qarar sa kenan ko? Se kawai ya juya dan
bama ya so ya shiga yayi abunda ran kowa seya baci dan haka se kawai ya juya da niyyar fita, ya rigada
ya makara dan tuni Addah ta hango shi ai kuwa ta shiga taratsin kiran sunan sa akan ya dawo bashida
zabi ya juyo jin Dada ta saka baki fuskar nan a dinke kamar wanda yaga mutuwarsa ya nemi guri ya
zauna yana muzurai.

Kallo daya yai wa Amirah data duqar dakai kamar munafuka dan bata so suka hadu a gidan ba yanzu se
yace ita ta kawo qarar bayan wallahi Addah ce, seda tace kar suzo amma taqi gashi yanzu ta ja matana
jangwam.

WATA KISHIYAR

(ALKAHIRI CE KO SHARRI)

Na Maryamah_Mrs AM

(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)

Page 11

Wannan karan dai Amirah ta samu yanda take so dan Har ranar Monday da safe da Bashir ze tafi basu
sake samun sabani ba. Tayi iya qoqarinta wurin ganin ta tsaftace ko ina kaman yanda yake so shima ya
sake da ita sosai ya mori weekend dinsa dukda dai a wannan bangare fa ya dade da cirewa Asma’u hula
dan kuwa tayi zarra amma itama Amirah babu laifi yana samunta yanda yake so.
A bangaren girki ne dai tunda yazo be ci abincinta ba gidan Dada yake tafiya yaci na rana na dare kuma
ya siyo idan ze dawo saboda shi tun usuli dama baya cin abincin me ciki gani yake wannan Amai da tofe
tofen da sukeyi har cikin abincin yana shiga.

Ko Ma’u dakyar ya fara cin abincin ta lokacin da tana da cikin Aliyu shima seda ya ware lokaci ya tsaya
akan ta ya tabbatar da ingancin yanda takeyin sannan ya saki zuciyarsa dukda ita bata fiya yin ciki me
Amai ko tofe tofen miyau ba.

To balle wannan da kullum tana tafe da Gwangwani wani Sa’in ma tana magana bakinta cike da yawu
yana zubowa seda yai dagaske ta dena yace ta ringa samun wani abun ci tana sawa a bakin ze hana
taruwar yawun sannan fa ya samu lafiya se kuma liqe liqen chewing gum din da ta koma ci wani lokacin
har kan kujera ko kan carpet yarda shi takeyi ba abinda ya dame ta.

Bashir Tun ranar Asabar dinnan basu sake waya da Asma’u ba, ita bata kira ba shima be kirata ba tadai yi
masa text kan zasu fita ran Saturday da Sunday kaman yanda suka saba yace to tareda aika mata da kudi
dukda bata tambayeshi ba.

Ranar lahadi da yamma ya dauki Amirah sukaje gidansu, A nan ya barta suka fita da Amiru qaninsa daya
zo daga Katsina a ranar can yake aiki yana zaune da iyalansa. Bayan isha ta idar da Sallah tana zaune
Dakin Fainusa qanwar Bashir ce da take zawarci, Fainusan bata nan taje bikin qawarta Dada kuma tana
dakin Baban su Bashir taje bashi maganin sa na dare.

Bangaren shiru seda ta leqa ta tabbatar babu kowa sannan ta dannawa Addah kira dan kwatakwata bata
samu sun tattauna komai ba dan Bashir na gida kusan ko yaushe in ya fita kafin tayi ayyukan ta gudun
bala’insa kan ta gama ya dawo ita kuma Addah ba karatu ta iya ba bare suyi chatting Ummi ba shiri suke
ba bare ta karantawa Dadan. Seda ta jera mata kira biyar sannan ta daga dan so take suyi shawarar
abinda za’ayi kafin subar wurin Dada tunda itace makamin yaqin nasu.

Addahn na dagawa babu gaisuwa ba komai tace“Addah gamu a gidan Dada fa kuma da safe ze tafi
haryanzu beyi maganar tafiyar tawa ba”

“Au nida naji ki muqus ai nazata komai ya kammala dama yanzu nake so nakira ki wato tunda kura tayi
lafiya har kin manta dani”.
“To dai ba lefi Addah, yanzu dai ya za’ayi kinga da safe fa ze tafi”.

Motsin da ta jiyo ya saka ta saurin cewa Addah “nidai kishiga whatsapp dinki kiyimun voice na abinda
zance mata dan wallahi muka bar nan kinsan dai ba iya magana zan masa ba” tayi maza ta kashe wayar.

Fainusan ce ta dawo, gaisawa kawai sukayi ta shiga hidimominta batareda ta sake koda kallon Amira ba
dan basa shiri. Ta girmewa Amiran amma tunda ta Auri Bashir ya zamana dan girman da take basu ma ta
dena a cewarta yanzu matsayin Yaya take a gurinsu tunda tana auran Wan su dukda dama dai tun usuli
ba Kunya ce da ita ba.

Tana zaune tana duba waya kusan minti goma sega voice din Addah tayi maza ta kunna tareda saka
wayar a kunne

“Kinajina bude baki zakiyi ki mata magana kice befa ce miki ki shirya ba dan haka tayi masa magana dan
gaskiya fa ke kina cutuwa bazaki zauna ba” qasa rayi da murya sosai kafin tayi mata reply tace

“Addah anya kuwa Dada fa yanzu surukata ce nifa wallahi kunya nake ji”

“To dan ubanki se ki zauna ai, kina dai jin abinda Jummai yar Bori ta fada tace indai ba kusa dashi kika
koma ba babu aikin mu da zeyi tasiri to tun wuri kafin wannan din da muka dan samu yayi ya sake shi
kiyi ta kanki” Addah ta fada cikin masifa.

Shiru Amira tayi tana jimamin abun a ranta anya kuwa zata iya dosar Dadan dan duk wannan abun
Addah ce takeyi mata yaqin amma fa yanzun ne kadai damar ta. Bata da burin daya wuce ta Mallaki
Bashir ta same shi sama da yanda Anty Asma’u ta same shi.

Ita ma yaringa yawo da ita a gaban mota duk inda ze shiga ya nuna ta a matsayin matarsa ya kuma ringa
nuna yana sonta a gaban kowa.

Tana zaune tana wasiqar jaki Dada ta leqo dakin, “Amirah kina zaune shiru ki fito palour kici abinci”
Dadan ta fada
Da “toh” ta amsa kafin ta yunqura tabi bayan Dadan Fainusa ta rakata da harara tareda tabe baki dan
taji maganar Amiran batasan dai Me Addah ta fada ba ko akan me suke maganar.

A palour kuwa Bayan Amira ta zubo abinci ta zauna tana tsakura Dada kuwa Ta maida hankalin ta kan Tv
dan dama ita bame sakewa da mutane bace. Amirah ta dago yafi sau goma da niyyar yi mata magana
seta kasa daga qarshe dai tayi qundumbala kamar an fuzgo maganar tace

“Dada kiyiwa Yaya Bashir magana gashi har gobe ze koma beyi zancen tafiya ta ba kuma” ta qarasa tana
sunkuyar dakai ganin yanda Dadan take kallonta. Shiru Dada tayi kamar bazata tanka ba se kuma ta
sauke numfashi tace

“Munyi magana da Addah na gaya mata ki zauna anan tunda tun farko da ya baku zabin jeka ka dawo ke
kika qi kafin ma Asma’u ta fara aiki lokacin dan haka yanzu bana son wata fitina ta sake tasowa ki yi
haquri ki zauna a inda ya ajiye ki ko dan lafiyar jikin ki ma yanzu kama ta yayi ki hada hankalin ki guri
guda kiyi fatan Allah ya sauke ki lafiya”.

Seda Amirah ta harari Dada qasa qasa wanda sarai tana ankare da ita kafin tace “Toh ai Dada lokacin ma
shi yace nace na fi son zama anan din Anty ze bari acan kuma yanzu ma bani nake son komawa ba ai
saboda Dan sa ne nake son zama a kusa dashi”. Ido bude Dada take kallonta har ta qarasa, bata iya ce
mata komai ba illah

“Allah ya rufa asiri” ta maida kai ga kallon da takeyi dan abin yafi qarfinta kuma.

Amirah jin tayi shiru ta tabbatar da bazata sake cewa wani abu ba, se sannan ta gano wautar da tayi cikin
salon son kare kai ta fara cewa “Dada ba abinda kike tunani bane wallahi ni kawai...”

“Idan kin qoshi ki kai abincin kitchen zan koma gurin Alhaji in Bashir sun dawo ina can” Dada ta fada tana
miqe wa jin da gaske so take ta baro wata maganar in ba haka ba menene kuma nayin bayani gaskiyar
magana Addah ba tayiwa yarinyar nan goyon kirki ba ace yarinya bakinki babu control a gaban kowa ki
fadi duk abinda yayi miki, Allah ya sawwaqa toh.
Tana fita Amirah ta shiga kiran Addah a waya tana dagawa ta sakat mata kuka tana cewa “Addah kin
gani ko nace miki bazan iya ba kince sena mata magana gashi yanzu na bata komai”

“Dan ubanki me kika ce mata a garin yaya? Rashin hankalin naki kikayi ko ni wallahi na rasa wace
Asararriyar yarinya ceke da komai baki iya siyaya da kissa ba se wauta da rashin hankali kika saka a gaba
yanzu me kika ce da ita?”

Tsaf ta gaya mata yanda sukayi da Dadan, Ajiyar zuciya Addah ta sauke kafin tace “Ni na zata ma wani
babban abu ne rabu da ita na lura Nafi so take ta kware mana baya amma bata isa ba wallahi yanda ta
saba tursasashi yayi abu yanzun ma haka za’ayi. Ki kwantar da hankalin ki ki rabu dasu muna zaune se ya
dawo ya dauke ki wallahi in sun san wata basu san wata ba kedai yi qoqari ki amshi wani abu a hannunsa
a turawa Malam a qarasa aikin nan Idan muka samu yanda muke so ko ita Nafin se mun so zata ganshi”
fanfo ta cigaba dayi mata da bata dabarun yanda zata wanki Bashir din kafin sukayi Sallama.

Gajia tayi da zamanta zame takwanta akan kujera bacci ya kwasheta, Bashir kuwa se qarfe goma ya
dawo gidan, seda yaje sukayi sallama da iyayensa kafin ya shiga palour ya ganta harta fara bacci.
Tashinta yayi suka tafi basu koyi sallama da Dada ba. Da suka isa gida ma kwanciya tayi dan baccin yaci
qarfinta.

Washe gari tun Kafin a kira Assalatu ya tashi Amirah, tana qunquni tana komai seda yasa ta gyara ko ina
dukda beyi datti ba tunda kwana biyun tana kula da komai. Qarfe 6 suka sauketa a qofar gidan Addah,
be shiga ba dan haushin Addan yakeji haryanzu dama basu sake haduwa ba tun waccen ranar dukda har
kasuwa yaje ya gaida Baban Amiran kamar yanda yakeyi duk sanda ya shigo gari, duk yanda Amiran taso
ya shiga wi yayi yace ta gaisheta kawai sauri yake qarfe 7 jirginsu ze tashi sannan ya kawo 50k ya bata
sukayi sallama Naziru ya kaishi Airport ya juyo da motar.

Murna gurin Addaha kaman wanda ya basu 50M. Shi dama bame kyautar kudi bane idan ze tafi dai
komai ze ajiye mata na amfani sanda tana zama a gidanta Ummi taje ta tayata zama. Da ta koma tafiya
gida ma be fasa ba duk qarshen wata ze sa akai Buhun shinkafa carton din taliya, macaroni da Indomie
harda Mai da Maggi ga Kayan Tea sannan in ze tafi ya bata 10k kuma duk sati yana saka musu Katin
waya na 1k ita da Asma’u Idan kuma zataje Asibiti Nazir ne ya ke kaita ya dawo da ita.

“Yanzu cire Goma ki riqe a hannunki bari na kirawo Malam ya turo a karba in kuma A Akawun za’a saka
masa toh. Nidai Alkahiri ya hada mu da Me Keken nan shekara da shekaru muna yawon rabar da kudin
mu a banza babu biyan buqata kinga rana daya mun tsinci dami a akala” Addah ta fada tana qoqarin
kiran wayar Malam Wizy, kira Daya biyu ana ce mata Switch off amma bata lura bama se sake kira
takeyi, wayar ta miqawa Amirah tana cewa

“Ke jimin me matar nan take cewa be wayar taqi shiga”

“A kashe take Addah” Amirah ta fada bayan ta sake kira.

“To bari mu saurara zuwa anjima na sake kira dan bazanyi wasa ba gara ayi wuta wuta a gama aikin nan
bari ma Babanku ya fito inaga yau ze bamu ribar mu duk na hada a tura masa kawai a qarasa”.

Ita dai Amirah neman guri tayi ta kwanta dan bacci ne fal idonta.

Har kusan Magriba Addah na gwada layin wizy baya shiga, seta kalli Amirah dake cin Abinci a gefenta
tace “Bari kiga na kira Hajia Balaraba itama tunda muka dawo ba waya da alama ta samu kan gidan se
muji idan ta kama gobe mu koma kawai ko da abinda ze qara bamu ma” kai Amirah ta daga mata kawai
nan ta maida akalar kiran kan Hajia Balaraba sedai itama kamar Wizy waya a kashe harta gaji ta bari
akan Gobe idan Ummi ta dawo zata karbi Number Ruqayya a gurinta (Ummi tana gidan yayarsu da suke
uba daya ta haihu).

Gidan Hajia Balaraba

Waccen ranar yanda suka watse suka barta ta dade a zaune a gurin tama rasa tunanin me zatayi, wai
itace bata da Sa’a ne ko kuwa aikin Malam ne beyi ba? Tana zaune tana tunanin me zatayi, wannan
hukuncin da Alhaji ya dauka yayi mata tsauri da yawa ta yaya ma za’ayi ta zauna bazata fita neman
taimako ba? Dole da sake idan dama taqi se a kona hagu ai saqesaqen yanda zata wanke kanta ta farayi
a zuciyarta har zuwa sanda taji Alhaji ya sake fitowa daga dakinsa. Cikin qarfafawa kai guiwa ta miqe
tana cewa

“Alhaji kayi haquri wallahi sam ba abinda kuke tunani bane, kafin gida ne na karbo mana ba kuma iya
dakinta na saka ba wallahi kaga kwana biyu unguwar nan anan fama da sace sace shi....” kallon da yake
binta dashi ya sakata hadiye sauran maganar ta. A tare suka juya Gurin Dining da Ruqayya ke qoqarin
zuba tuwo abinta dan tana wanka bata ma san wainar da aka toya a gidan ba.
“Mayar da miyar nan Ruqayya ki miqomin harda na shayun” ya fada murya a dake dan dukda be gani ba
ya tabbatar ta saka wani abun aci ba kuma ze bar kowa yaci ba dan ba yau ta saba ba ita idan ta tashi
abun tana ma ba kansa kadai yake tsaya wa ha kowa da kowa take hadawa na gidan.

Karbar flask din yayi ya shige kitchen dasu Hajia Balaraba naji tana gani ya kwarara miyar a sink din ya bi
da ruwan Tea kafin ya dauraye ya kora ruwa. Idon sa ne ya sauka kan wani flask daban a ajiye ya janyo
ya bude, murmushin takaici yayi zargin sa ya tabbata duk sanda tayi irin haka seta ware nata daban be
bata lokaci ba ya dauka tareda sabon plate da spoon se koma Dining.

Tuwon sa ya diba ya zuba miyar ya miqawa Ruwayya ragowar yai shigewar sa daki ya bar Balaraba a
tsaye da baqin ciki goma da ashirin, abincin ne sauran taqamarta taso ta lallashe shi yaci gashi yanzu ya
zubar da miyar wadda ta ajiyewa kanta kuma ya kwashe duk wuyar da taci tayi girkin nan me kyau
amma bata da rabo sena baqin ciki bata san sanda hawaye ya fara zubo mata ba kamar yarinya.

Dakin ta ta shige tayi kukan ta me isarta ta share, ta kuma quduri niyyar ko bataje da kanta ba se tayi
aike daga yanzu ma bazata qara karbar aikin da zatayi dakanta ba gara ta samu wanda ze yi mata komai
da kansa bate ma har ta kuskure asake kamata.

Washe gari tana zaune Alhaji ya shigo dakinta, wayar ta na hannunta tana shirin kiran Addah ta gaya
mata yanda akayi su kuma yi shawara ya shigan. Hannu ya miqa mata ta bashi wayar cikin mamaki ta
miqa masa tana tunanin to me kuma ya fatu yanzu? A gaban ta ya cire layin ya balla, kafin ya kalleta yace

“Wallahi ko da wayar wani kika karba kikayi amfani da ita ki kira wani Boka Ban yafe ba” ya sa kai ya fice
ya barta da baki a bude.

Matakan tsaro na gaske ya saka mata ba waya ba fita ita ma kuma ya hana kowa zuwa gurinta har kuwa
da Yayanta da suke gidan aure. Ruqayya kanta cewa yayi ta tattara ta koma Hostel haka me aikinta yace
karta dawo ta zauna ta qara hutawa na wani lokaci duniya fa tayiwa Hajia Balaraba zafi Raba zafi inuwa
quna gashi babu abokin shawara ita da Alhaji kuwa sedai tajiyo qarar bide qofarsa ko rufewa.

Seda Addah ta jera kwana biyu tana kiran Hajia Balaraba da Wizy dukka bata samu ba, ranar Talata ta
yanke shawarar zuwa gidan nata ta gano ko lafiya.
Dakyar da sidin goshi Me gadi ya barta ta shiga shima seda tayi masa qaryar Ita Yar uwar Hajia Balaraba
ce suna ta kiran wayarta ba’a samu shine tazo taji ko lafiya, be barta ba seda ya kira Alhaji ya shaida
masa sannan yace ya qyaleta ta shiga.

Halin da taga Aminiyar tata ya girgiza ta nan ta shiga tambayar ta meya faru, Hajia Balaraban na kuka ta
shaidawa Addah komai harda sharadin da Alhaji ya gindaya mata.

Addah tayi buqwi tana sauraronta kafin tace “Ikon Allah kinga dama akace magani dace ne to ni kuma
kinga dai mun dace wallahi dan yanzu lafiya lau abubuwa suke tafiyar mana. Kema din nasan akasi aka
samu wannan shegiyar ta ganki amma da abubuwan sun kammalu na tabbatar yanzu wani zancen ake
ba wannan ba Allah dai yajiqan Malam na kan tufu shine Maganin Fitinannen Alhajin nan naki mtsw”
taja tsaki kafin ta dora da cewa

“Yanzu dai ai cewa yayi idan kika qara zuwa ko a sharadij nasa shikenan kiyi zamanki ni zan koma insha
Allahu za’a gyaro komai base kinje ko kunyi waya ba”

Cikin jin dama dama Hajia Balaraba tace “Yawwa Aminiyata shiyasa nake qaunar ki wallahi yanzu to zaki
gane gurin? Dan Allah idan kinje ki gaya masa so nake ayi mun maganin Alhaji yafi da kamuwa yanda ko
kara na ajiye ba ze tsallake ba ke ko magana in banace ya bude baki ba karya yi”.

Da haka sukayi Sallama Addah ta kama hanyar zuwa Gurin Malam Wizy.

Tiryan tiryan ta nunawa Me Adaidaita hanya har qofar gidan Malam dan Addah akwai gane hanya, da
dan mamaki ta kalli shagon na Malam Wizy da ta gani cike da kayan provision ana siyar wa. Gaba tacewa
Me Adaidaita ya qara ko basu zo gidan ba sedai har suka kai qarshen layin suka jiyo babu wani gida me
kama dashi ma.

Fitowa tayi ta tsaya dason tabbatar da nan din ne gama dakalin da suka ga yaran nan a zaune ranar,
qarasawa tayi gurin me shagon suka gaisa kafin tace

“Dan Allah tambaya nakeyi me shagon nan”


“To hajia ai gani”

“Aa ba kai ba Malam nake nufi” ta bashi amsa.

“Malam kuma Malam wa?”

Wata sabuwa inji yan caca ita ai se yanzu ta tuna da ko sunan sa bata sani ba, cikin ta ne ya bada qululu
ta daure tareda korar abinda zuciyar ta take hasaso mata tace

“Malam dai wanda yake zama a shagon nan Mijin Maimuna me wannan gidan” ta fada bayan ta tuno da
sunan matar malam din.

“Toh gaskiya hajia ban san wanda kike nema ba, hasalima nan shagona ne nafi shekaru goma ina saida
kaya a ciki gida kuma da kike magana ba gida bane kangone da Almajiran waccen makarantar suke
kwana zaki iya leqawa ki gani” me shago ya fada yana nuno mata makarantar daga nesa.

Addah bata qi ta tashi ba ta leqa gidan, kamar yanda ya fada kuwa incomplete ne ta cikin ga kayan
Almajirai nan tsubi tsubi, wata hajijiyace ta kwasheta jin zancen da wani saurayi da yazo siyya shagon
yakeyi

“Tab Malam Musa Allah dai yasa ba itama tafada komar Wizy bane dan a satin nan mata sunfi Goma da
suka zo neman Malam” yana kaiwa nan ya karbi kayansa yayi gaba yana wa Addah dariya.

Allah sarki Addan mu Allah maida Asara

WATA KISHIYAR

(ALKAHIRI CE KO SHARRI)

Na Maryamah_Mrs AM

(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)


Page 14

Seda Amirah ta kwana daya a daren rana ta biyu akayi mata aiki cikin ikon Allah aka ciro mata yar
qaramar yarta bakwaini me tsananin kama da Farida, sosai Bashir yayi murnar samun mace sanda aka
nuna masa babyn kafin aka sakata a kwalba, tun cikin daren kuwa ya ringa buga waya yana gayawa
mutane haihuwar.

Ya kira wayar Asma’u lokacin harta fara bacci dan basu dade daga dawowa daga Asibitin ba suna can ma
aka shiga da ita aikin, ganin dare ya fara ga yara yasa ta tafi gida.

“Masha Allah, Allah ya raya ita kuma ya bata lafiya, kace Farida tayi yar uwa Abokiyar shawara” ta fada
bayan data daga wayar.

“Wlh fa sema kinganta kamar su daya kamar sanda kika haifi Faridan girma kawai ta fita” Bashir ya fada
cike da doki kafin sukayi sallama. Baccin ta ta koma dan dama tunda suka dawo ta rufe gida tasan ba
dawowa zeyi ba dan jiya ma can ya kwana seda safe yazo yayi wanka ya chanza kaya bare yau da ya
samu ya ai ba batun zuwa gida kuma.

Washe gari da wuri ta tashi ta hau shirye shirye dan tana so taje gidan su yau ga zuwa Asibiti. seda tayi
girki tayi musu farfesun Kaji ta soya doya sannan ta damawa Amirah kunun gyada dukda bata san ko
zata faracin abinci yau din ba sannan ta dafa Tea suka shirya gaba daya ita da yaran suna ta murna data
gaya musu sunyi qanwa. Se gurin goma sannan ta hada komai suka tafi.

Dakin danqam da yan dubiya yan gidan su Bashir da kuma Dangin Amiran se hayaniya sukeyi dan ta
farfado tun da Asuba. Ba yanda Likita beyi dasu ba subarta ta huta amma sunqi qarshe haushi yaji yai
tafiyarsa ya barsu ya kuma gayawa Nurse kar wanda ya nemeshi in wani abu ya faru dan ya gaji da
halinsu kuma.
Aliyu da Jafar ne a gaba sunyi kama kaman kwandon da ta zubo Abincin su kuma suna binsu a baya suka
shiga dakin da Sallama. Fuskarta dauke da Fara’a suka shiga gaisawa da mutanen dakin tayi musu barka
kafin ta juya kam Amirah da tun shigowar Asma’un ta daure fuska tam taqi koda kallon sashin da take.

“Amirah sannu ya jiki?” Ta tambaye ta idan ta amsa ta to ku da kuke karatu kun amsa abin yai bala’in
bawa Aisha Babbar Yayar su Amirah da suke uba daya haushi har seda tayiwa Amiran magana tace “Kina
ji tana miki magana saboda raini da wulaqanci bazaki amsa ba”

Bata ko motsa ba kuwa sema cuna uban baki gaba da tayi dama fuska duk a kumbure tana qunquni.
Asma’u kam ko a jikinta, yo ita bata ga abin da zesa Amirah tace bazata kulata ba idan kishin nema ai ita
ya kamata tayi tunda aita aka aurewa miji, Allah ya raya ta sakeyi musu kafin ta juya da niyyar fita dan
dama yaran tunda suka gaishe su sukayi waje abinsu, dab da zata fita ta jiyo muryar Addah na tambayar
waya kawo abinci ashe tana bandaki seta juyo ta dawo cikin dakin.

Har qasa ta durqusa ta gaisheta, fuskar Addah kuwa a washe ta amsa mata tana tambayarta ina Mazajen
nata tace suna waje

“Au shine suka fita ba su bani kudin cefane ba ai kuwa su dawo dan bazan yarda ba” Addah ta fada cikin
sigar wasa. Murmushi kawai Asma’u tayi ta miqe tana musu sallama ta fice.

Wato Yanda Addah ta wanke idanunta bata taba nuna wani abu akan auran Amirah da Bashir na bala’in
daure mata kai, mutum, ka kalleshi kawai. A reception ta hadu da Bashir daya je gidansu ya dauko Dada
dan Naziru yana makaranta yau, cikin mutuntawa ta gaisheta tareda yi musu barka Dada ta wuce ciki
Bashir kuma yabi bayan Asma’un.

“Har kun qaraso kenan, yanzu nake so dama na tafi gidan nayi wanka na huta wallahi duk na gaji” ya
fada yana jingina da motar da tuni su Jafar suka shige bayan sun gaisa da Dada.

“Ya kamata kam, abincinka na nan ma na ajiye maka nayi zaton kafin mu fito zaka dawo kuma naji shiru,
mu zamu wuce Babban gida qila idan zamu dawo da dare mu sake shigowa mu duba su” Asma’u ta fada
tana qoqarin bude motar,

“Bazaki je kiga babyn ba?” Ya tambayeta


“Ai bazasu bari ba ka sani ba komai Allah ya bata lafiya idan lokacin fito da ita yayi zamu ganta ai mu da
zata dawo gidan mu da zama ma”

“Eh kuma haka ne, bari na shiga na fito to nima na wuce ku gaida mutanen gidan ban samu na shiga ba
wallahi Yanzu ma da zamu fito naga Kamar Alhaji Qarami dasu Yaya Mudassir a qofar gidan ashe yana
gari”

“Eh yazo daurin auran yarinyar Amininsa ne jiya saurin da nake tayi kenan ma mu tarar dashi ance yau ze
koma” da haka sukayi sallama ya shige ciki ita kuma taja mota suka nufi gidansu.

A can dakin kuwa bayan fitar Asma’u dayawan su sukayi wa Amirah caa akan abinda tayi bata kyauta ba,
Addah ce ta tambayi meya faru Anty Aisha ta gaya mata.

“Ai ni na rasa kalar wannan yarinyar dan barikin nan ma na mata bata iya shi ba ke se baqin kishi quru
quru meye amfanin sa”

“Wallahi fa Addah in nice ita yanda Anty Asma’u ta mayarda komai ba komai ba ake gaisawar mutunchi
ai wallahi sake wa zanyi mu ci gaba da yanda muke amma kin zauna kina quntatawa kanki ita kuwa kina
ganinta cikin walwala ji jikinta dan Allah wannan shegen Lashin nasan wlh yafi 100k ga zobuna a
hannunta ji qanshin turare dan Allah har yanzu be bar gunnan ba” inji Samirah qanwar Bashir da suke
Sa’anni da Amirah.

Hirar su suka ci gaba dayi aka shiga da take qonawa Amirah rai dan duk yabon Asma’u sukeyi ga dabgen
kaji suna ci abinsu a haka Dada ta shigo ta same su ta kuwa ji dadin Abincin da ta tarar Asma’un ta kawo
dukda ita ma ta taho musu da abinci amma tasan ba lallai ya isa ba tunda kusan duk yaran suna nan.

Asma’u kuwa hankali kwance suka isa gidansu wanda layi daya ne ya raba su da gidansu Bashir dan seka
bi ta qofar gidan su Bashir din ma zaka shiga layin da gidansu yake da yake close. Cike da murna Seidu
dan Baba Buzu daya daga cikin masu gadinsu tun na quruciya daya maye girbin Babansa yanzu ya
wangale mata katafaren get din gidan na Alfarma ta shiga.
Tabbas gidan ya amsa sunan sa na Babban gida domin kuwa layi guda ne gidan haka tun daga get da
katangar gidan zaka san cewa ba qaramin gidan me Arziqi bane. Tana gama parking a inda aka
tanadarwa motoci gasunan birjik da alama yau akwai mutane da yawa a gidan yaran suka fita da gudu
saboda hango cousins dinsu yaran Yayye da qannen Asma’u da sukayi se lokacin ta tuna yau Sunday
kusan dukka yan gidan da suke a cikin garin Gombe Mata da Maza suna zuwa gida yau da iyalan su su
wuni tun zamanin da Mahifinsu yake raye har yau kuwa basu fasa ba.

Seda ta gaisa da Samarin dake zaune a bakin get yawanci duk masu aikin gidan sannan ta shiga cikin
gidan, part din Hajia Babba ta nufa dan a irin wannan lokacin tasan acan zata samu kusan kowa ai kuwa
tana shiga katafaren palour nata fuskarta ta qara fadada da Murmushin ganin yan uwanta harma da
wanda batayi zato ba.

Kai tsaye inda Hajia Babban take ta nufa Farar Bafulatana da a qiyasi ta bawa Sittin Baya amma jin dadin
da take ciki ya boye shekarunta “Maraba Maraba da mutanen Lagos” take fada sanda Asma’u ta nufota,
seda ta zauna dab da qafafunta tana daukar wani Dan yaro daya ruqo mayafinta da bata san ko dan
waye ba sannan ta shiga gaisheta.

Cike da qaunar junan data ginu a tsakaninsu suka shiga gaisawa da sauran yan uwanta da suke a palour
se tsiya suke mata wai ta qara kyau tayi wani haskee ta zama wanke ka taba ita dai se dariya kawai take
musu. Suna cikin gaisawar Alhaji Qarami ya shigo Aliyu na take masa baya dan dama mutuminsa ne.

Gaishe shi tayi ya amsa mata cike da kulawa yana tambayarta aiki babu dai wata matsala ko tace babu
sannan yayi wa Hajia Babba Sallama bayan yayi musu gajeriyar nasiha da tunatarwa daya saba yi musu a
duk sanda suka hadu da yawa irin haka akan su riqe zumunchin da Mahaifinsu yasha wahalar gina su
akai, seda yabi duk wanda yake zaune da dubu biyar suda yayan su kaf sannan ya musu sallama Driver sa
ya ja shi suka wuce Abuja inda yake zaune da iyalansa. Ance daman babban wa makwafin uba to tabbas
sudai sunyi dace dan kuwa Alhaji qarami ya maye musu gurbin uban da suka rasa.

A gaba ta saka yaran suka zaga saran part biyu na matan gidan suka gaisa Hajia Ummah da Hajia Anjin
kafin suka wuce sabgarsu ita kuma ta koma part din Hajia Babba inda sauran yan committee suke jiranta
a tattauna.
“Ke ashe Kishiyar ki ta haihu, dazu naji Abbas yana gaya wa Hajia Babba” Ikilima yayarta ta fada, seda ta
cire yafinta ta ajiye a gefe ta zame dankwalin yayi baya sannan tace “wallahi fa ta haihu an mata CS jiya
da daddare an ciro mata baby girl”

“Ayya CS ne Allah ya bata lafiya ya raya abinda aka samu” cewar Anty Hauwa matar yayansu Sunusi suka
amsa da Amin gaba daya.

“Kinje kenan?”

“Naje mana daga can nake ma yanzu”

“Cab kuma kika kwashi jiki kikaje nifa wallahi Yah Asma’u kina bani mamaki na rantse da Allah in nice
kallon banza yarinyar nan bata ishe ni ba bare na arziqi wallahi bazan je dubata ba, bata da mutunchi
kwatakwata baki san abinda ta mana ba ranar sunan Rufaida(qanwarsu ce itama tana auran Yayan
Amirah da suke uba daya) wai saboda bata da kunya ta kalle mu muna zaune wai bamu gaisheta ba idan
Bashir ne ai dole mu gaidashi tunda mijin yar mu ne dan haka matsayi daya take dashi a gunmu ita
Kishiyar yayar muce , wallahi Anty Habi ce kadai ta hanamu nada mata dan iskan duka ranar amma da se
mun koya mata hankali” cewar Amina daga yanda take maganr zaka gane zallar takaicin Amirah da take
ji.

Dariya Asma’u tayi tace “to ai se ku gaisheta meye a ciki zuwa dubiya kuma kema zakije dan ciwo na
gaba da komai sannan ranar suna dole kuzo asha shagali daku”

“Tab Allah ya rufa asiri” Aminan ta fada tana tura baki. Dariya suka saka mata dan dama indai aka fara
wannan dramar Amina bata da dama a fili take nuna jij zafin Amiran harma dana Bashir din dan ita fa
tunda yai auran nan ta dena gaishe shi. Tace yanda beji kunyar ciwa yar uwarta fuska ba itama bazata ji
kunyar dauke kai idan ta ganshi ba taqi gaishe shi.

Asma’u ta kance wai

“Amina inda kece a matsayina ban san me zakiyi ba” ita kuma tace

“Ai wallahi yah Asma’u da ko tsirena su Alhaji Qarami zasuyi na gama auran nan dan bazan koma ba”.
Ranar wunin dadi sukayi suka sha hirar su kamar karsu rabu, se bayan isha suka fara watsewa bayan tayi
musu Alqawarin zata bi kowacce gidanta su gaisa da kyau tunda zata kwana biyu a garin.

Daga ita se Abdallah suka koma gida sauran yaran kowa ya kama gabansa dan daman idan suka zo indai
ba tareda Bashir ba basa zaman gida in yana nan ne yake matsesu baya taba bari suje ko nan da can su
kwana yanzun ma abinda yasa ta barsu yana cikin wannan digimi be zama lallai ma ya fuskanci basa
gidan ba.

Seda ta biya Asibiti ta sake dubasu, a can din dai ta kuma samun sa kuma suka barshi sukayi gida yace se
ya taho har suka kwanta dai be dawo ba seda Asuba sannan taji motsinsa dan a dakinta suka kwanta ita
da Abdallan.

Washe gari Litinin Bashir yayi sammakon komawa aiki bayan yabar komai da zaa buqata hannun Naziru,
ranar ma bata wuni gida ba, gidan Yaya Bilkisu taje da suke ciki daya kuma ita kadaice yanzu a Gombe
Babbar Yayarsu Anty Suhaima tana America da mijinta se Junaidiyya da take Abuja sauran uku mazane
biyun qannenta yan biyu Bilal da Nasir suna karatun masters a China se yayanta daya Muslim yayi aure
tuni yana zaune a Rivers da matarsa da yaransu biyu da A Lagos yake shima akayi masa transfer.

Sosai suka sha hira da Yayar tata har dare kamar karsu rabu, sun yi sallama akan Nan da kwana 7 zasu
tafi Yola tare gurin maman su dukda ita Asma’u taso nan da kwana biyu ta wuce amma Yaya Bilki tace ta
bari se anyi radin sunan yar Amirah idan yaso ko bata samu taron sunan ba babu matsala amma yanzu
in ta tafi ze iya zama abin magana ai a kan hakan suka rabu.

Haka taci gaba da zaga yan uwanta har ana i gobesunan Amirah bayan la’asar tana zaune ta jiyo
hayaniya an bude get. Ta window palour ta ta leqa da mamaki take kallon su Addah dake fitowa daga
mota da Amira tana takawa dakyar bata ga jaririyar ba tana asibitin ita har yanzu.

Bangaren Amiran suka nufa seda suka shige sannan ta koma ta zauna tana mamaki tasan dai yau za’a
sallameta dan ya gaya mata da tun Jiya daya dawo amma batayi zaton nan zata dawo ba kodan yanayin
jikinta amma ita meye nata. Seda tayi sallar isha da dogon hijabin ta a jikinta ta nufi part din Amiran da
kulolin da ta zuba tuwo da miyar kukar da ta saka Amna tayi.
Seda tayi sallama uku sannan suka jiyota ta tura qofar ta shiga duk sukayi wani tsilli tsilli alamar basu da
gaskiya da gulmarta sukeyi a lokacin ta shiga. Bayan sun gaisa ta sakeyi mata ya jiki yau dai ta amsa bata
zauna ba tayi musu sallama ta koma gurinta.

Washe gari suna da Asuba a masallacin unguwarsu aka radawa yarinya suna taci sunan Addah Fatu,
Asma’u na daki Farida take gaya mata Amma Anty Ummi tace Iman zasu ringa kiranta, setayi Murmushi
kawai ta tuna sunan Farida da tace nan ma ya saka mata Maryam sunan mamanta tunda yace ba sunan
Dada ze saka ba ce mata yayi shi bashi da ra’ayin yiwa wani takwara, ko Aliyu daya saka raayin kansa ne
badan Aliyu Abokinsa ba kamar yanda ake zato.

Ana Abdallah kuwa cewa yayi ta siyi rago haka kuwa ta siya, haka aka yanka wa Baby Iman ragunanta
biyu ba’ayi wani taro ba ranar tunda tana Asibiti har sannan sun dai qudurce a ransu fa se sunyi daga
baya, dalilin ma daya sa suka dawo da ita gidanta kenan saboda duk abunda za’ayi ayi akan idon Asma’u
dan Amirah tace shagali zatayi na kece raini.

Washe gari Suka soye naman su ko hanji basu Aikawa Asma’u da bama su san asubancin barin garin tayi
ba ita da yara zuwa yola, suka rabe abinsu tas dan Bashir ma ya tafi tun safe kuma har nasa rabon suka
cinye.

Toh maji ma gani dai

WATA KISHIYAR

(ALKAHIRI CE KO SHARR

WATA KISHIYAR

(ALKAHIRI CE KO SHARRI)

Na Maryamah_Mrs AM

(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)


Page 13

Addah, abinda ya faru waccen ranar.

Kuka riris Addah ta shigayi bayan data tabbatar da cewa Malamin nan dan damfarane, qarin tabbacin
data samu tana tsaye wata da ta yankawa kanta kazar wahala ita ma ta zo neman malam Wizy anan suka
samu daya daga cikin Almajiran ya fede musu abinda yake faruwa.

Wato dama shi ance aikinsa kenan kuma takamaimai basu san dan wacce unguwa bane. Haka yakeyi duk
sanda suka tashi zasu je inda ba’a sansu ba su kama guri idan sun gama cin kasuwarsu ta watse ba zaka
san ina sukayi ba.

Haka suka dauki hanya da me Adaidaita tana faman rusa masa kuka batayi aune ba taga yayi kwana da
ita wata hanya daban, da taso tayi masa ihu ya zare mata wuqar dake boye a qugunsa dole Addah tayi
shiru se yan idanu tana hawaye haka tana ji tana gani seda sukaje inda babu mutane ya kwace jakarta
data zubo kudin raguna biyu ga kuma wadanda Hajia Balaraba ta bata na nata aikin duk ya kwamushe
harda wayar ta sannan ya buga mata abu akai ta suma kafin ya kwasota ya kawota Asibiti ya tsere
abinsa.

Seda ta kwana 4 a Asibitin sannan aka samu kanta ta dena iface ifacen kudinta da takeyi shima se bayan
da Alhaji Murtala yayi mata horror sannan ta dauki dangana a fili a zuciya kuwa baqin ciki kamar zeyi
ajalinta. Abu goma da ashirin gashi babu damar ta raba baqin cikin da wani ayi mata Allah shi qara dan
ko Amirah bata jin zata gayawa bare tsautsayi yasa wani yaji zancen.

Amma fa wallahi an cuceta, Dubunta fa har dari da sittin dan iskan yaron nan ya lashe ga Hamsin din
Balaraba. Wai ma wace toshewar basira ce ta same su kai wannan ibtila’i da yawa yake, amma bazata
haqura ba wallahi insha Allahu seta nemo wanda ze mata aikin da Wizy ze kawo kansa da kansa ya
biyata kudin ta (baki daddara ba ashe 😂😂).

Haka dai tace a sallame ta ta warke suka koma gida taci gaba da jinyar zuciyarta.
Dama damanta ma yanda Bashir yake ta rawar jiki akan ciwon nata, kamar yanda yace ya turowa da
Naziru dubu dari yace ayi hidimar Asibiti dan ko babu auran Amirah ai Addah uwa take a gurinsa ze kula
da ita kamar yanda zeyiwa Dadansa dan ma dai Addar se a hankali dai, already kuma Alhajin ya biya
komai dan haka Nazirun ya danqawa Amirah kudin yace ko zasu buqaci wani abu inji Bashir. Wadan nan
kudi ta qudure a ranta da taji dama dama zata kaisu a shaqo mata wuyan wizy kuma (Ai me rabon shan
duka baya jin bari dama 😂).

Ganin yanda Bashir din yake ta tasu dan kullum sau biyun nan Safe da Dare se ya kira yaji ya jikinta yasa
taga dama ta samu na yadda zata tura Amirah gurinsa, (wai nikam dole ne 😂😂 Allah sa dai ba rabon
wahala ke kiran Amirah ba itama). Tunda sun gwada wacceb hanyar bata yuwu ba dan haka suka sake
wata.

Sun san yanda Bashir yake da son yara ya kuka kwallafa rai akan cikin jikinta dan haka yanzu shine target
dinsu, Addah batayi sanya ba ta karanta mata duk yanda zatayi, da Bashir din ya kira waya zata
langwabe yau tace kanta anjima cikin ta, Aa jiri ne yake damu ta shidai se yace mata taje Asibiti ta kuma
rage yawan zurga zurga saboda halin da take ciki. Ganin an kwashe sati biyu ana haka be ce ze zo ba ko
ita ta tafin yasa suka shirya sabon plan.

Ranar Juma’a data kama Sati biyu kenan rabonsa da Gombe da daddare suna cikin waya tace bari tayi
fitsari, bata kashe wayar ba ta ajiyeta akan sink ta dauki hand shower tana tsiyayar da ruwa kaman me
fitsari se kawai ta fasa ihu.

Bashir da acan bangare yana riqe da waya yana jiran ta gama ya miqe a sukwane jin ihunta har yana
tunkude cup din da Asma’u ta cika masa da Kunun Aya ya tuntsure a qasa take kuwa ya fashe.

“Lafiya meya sameki” ya tambayeta a kidime, seta fashe masa da kukan qarya tana cewa “Jini, jini ne
yake zubomun” ta ci gaba da kukan.

Sosai hankalin Bashir ya tashi, idan be manta ba wancan karan da haka ta fara zubar da jini kafin Wani
lokaci jaririn ya mutu a cikinta se inducing dinta sukayi ta haihu dan haka yake taka tsan tsan da abinda
ze sake janyo faruwar hakan.

“Subhanallahi a garin yaya toh ko kinyi wani abun ne daya fi qarfin jikinki?” Ya tambaye ta
“Nima ban sani ba kuma ni banyi komai ba, dama ba tun yau ba ya fara kawai gaya maka ne banyi ba
bana so hankalin ka ya tashi” Amirah ta fada tana sheshshekar kuka, a ranta Addu’a takeyi Allah yasa
yace zezo dan wallahi qafarsa qafarta itama se taje an ci uwar da ake ci acan tare da ita.

“Kin gane ki gyara bari na kira Naziru yazo ya kaiki Asibiti yanzu” maganar sa ta katse mata tunani, se ta
dan diririce dan bata zaci zece aje Asibitin ba amma kuma idan taqi tasan wata matsalar zata kwantowa
kanta in kuma sukaje akaga ba haka ba nan ma ba tsira zatayi ba, daurewa tayi tace masa

“Aa karbar shi dare yayi yanzu kuma bada yawa bane ai da nayi tsarki ma ya dena zuwa, sannan Anty
Ramle tana gida (Amaryar babansu Nurse ce) koda wani abu ya taso zata iya taimaka min kafin muje
Asibiti”.

Sallama sukayi ya kashe wayar Badan ya gamsu da maganarta ba dai ya qyaleta tunda yasan Anty Ramle
tasan aikinta sosai zata kula da ita amma koma menene zuwa safiya dole taje Asibiti dan baze dauki
ganganci ba, kai qila gobe ya tafi ma dakansa ya kaita gara in ma wani abune a shawo kan matsalar da
wuri.

Tsakin daya sakeyi a karo na ba adadi ya saka Ma’u daga kai ta kalleshi, tunda ya barar da kunun Ayan ta
kwashe kwalaben tareda goge Gurin kawai ba tareda ta tankashi ba dan taji duk maganar da sukeyi. A
ranta tadan tausayawa Amiran in da gaske takeyi dan dai duk mace tasan wahalar ciki da haihuwa dole
in kaga wani dashi ka tausaya masa.

Bata tambaye shi abinda ya faru ba shima kuma be gaya mata ba har sukaje kwanciya, juyi daya biyu ya
saki tsaki kai har abin ya fara bawa Asma’u haushi amma ta jure bata tanka masa ba sema danna kanta
da tayi cikin pillow ta tilastawa kanta yin bacci. Wai kuma ashe shirun data yi laifine se jinsa tayi yana
cewa

“Wai dan wulaqanci kina jina amma bazaki iya tambayata meya faru ba ko?”

“Ikon Allah” ta fada a ranta, a fili kuwa daga kai tayi ta kalleshi sau daya ta juya ta rufe idonta ba tareda
tace masa komai ba, ai bashi kadai ya iya miskilancin ba.
Bashir kuwa jin ta masa shiru ya qara tunzurashi, kwafa yayi yana sake zabga tsaki kamar ze katse
harshensa, ga damuwar halin da Amiran take ciki ga share shin da Ma’u tayi ta juya masa baya. Wayar sa
ya dauka ya shiga duba jirgin Lagos to Gombe a gobe Asabar amma babu dolensa ya haqura, Haka yai ta
juye juyensa har shima baccin ya dauke shi.

Asubar fari ya dannawa Amirah kira, tana can tana sharar baccinta har wayar ta qaraci ringing bata ji ba,
seda ya kira sau biyu ana uku ta daga cikin magagin bacci.

A tsaitsaye suk gaisa ta tabbatar masa da komai lafiya babu abinda yake damunta yanzu sannan sukayi
sallama yana jaddada mata ta shirya anjima Naziru ze zo ya kaita Asibiti ta amsa shi da toh bawai dan
zata je din ba to me yake damunta ma.

Suna gama wayar ya maida akalar kiran kan Naziru, gaya masa yayi yaje ya kaita Asibitin duk abinda ake
ciki ya sanar dashi sukayi sallama.

Asma’u tana kwance akan gado duk tana jinsa, mamaki take yanda gaba daya ya rikice, ganin yana
neman ya hanata baccinta yasa ta miqe ta bar masa dakin ta koma nata ta kwanta.

Har yamma bata san ya aka qare da jikin Amirah ba, ita bata tambayeshi ba shima be mata maganar ba
dan wani shareta ma ya shiga yi a dole wai haushin ta yake ji ita abun ma se ya bata dariya. Da yamma
ma kudi ya bawa Ahmad yace ya kai mata su fita su siyo abinda suke so shi bazashi ba ta kuwa karbe su
ta zuba a jaka suka shige kitchen da yara suka hau yin shawarma suka gasa kaza da zasuci da daren se
smoothy na Ayaba daya ji madara.

Ta bayan kitchen dinsu akwai fili da suka gyara ya zama kaman wani garden wurin suka shirya abincinsu,
kowa yayi wanka yasha kwalliya kamar masu zuwa wani guri suka haucin abincu ba tareda anyiwa Bashir
daya hakince a palour tayi ba. Tunda suka fara gasa kazar qamshin ya fito dashi ya zauna yana jiran a
gama a kawo masa amma yaga sun tattare sun tafi baya. Ganin da gaske fa zasu cinye yaja zaune yana
jiyo dariyar su cikin nishadi se ya miqe ya tafi gurin ya tsaya a kansu yana muzurai.

Gaba daya suka kwashe da dariya, sunsan dama ba ze iya dauke kai ba Bashir da Nama kamar kura in ya
gani se ya ci haka kuwa ya zauna yana zare ido aka ci dashi tas suka dauka pictures kafin kiran magriba
ya tayar dasu.
Seda suka zo kwanciya Asma’u take tambayarsa yaya jikin Amiran yace mata da sauqi tayi masa fatan
samun lafiya shikenan kuma fushin ya wuce aka shiga sabgogi.

Lafiya lau suka cinye satin, yara sun fara exam ta third term zasu samu hutu me tsaho nan da sati biyu da
wannan damar Asma’u take so tayi amfani ta dauki leave ita ma dan ta kwana biyu bata je Gombe ba,
sannan tana son zuwa yola ta duba Maman ta da jikinta yake yawan motsawa kwana biyun nan.

Ranar Wednesday daya rage saura kwana biyu kenan yaran suyi hutu, already ta rubuta takardar
hutunta har anyi approving tana so ne a ranar friday su wuce Gombe dan babu jirgin Saturday. Da
daddare bayan sun gama dinner suna zaune a palour ita da Bashir yaran na dakunan su suna Karatu
Muhammmad da Ahmad kuwa sunyi bacci dan su sun gama tasu exam din.

Kallon Bashir dake duba wasu takaddu tayi tace “Baban Ali kayi mana booking flight din kuwa mufa mun
gama hada kayan mu”

Ba tareda ya dago ba ya bata amsa da cewa

“Waini saurin me kikeyi ku tafi ku barni ni kadai”

Murmushi tayi kafin tace “ba haka bane, kaga na dade rabona da gida inaso mu dan kwana biyu na zaga
dangi ga kuma tafiyar Yola ma gara mu je da wuri ai”

“Hakane” ya fada ya ci gaba da aikin sa.

Gombe

Daga ciwon qarya Amirah ta fara na gaske, haka nan se taji kanta ya sara mata ko in tana tsaye ta fara jin
dumm kamar jiri ze kayar da ita idonta ya ringa mata dundumi bata gani da kyau amma Saboda rashin
sanin ciwon kai sam bata bawa abin muhimmanci ba ta cigaba da sabgoginta idan ta gayawa Bashir yace
taje Asibiti ma bata zuwa Sedai ta karbi kudin a hannun Naziru ta kashe.

A hankali kuma se ta fara kumburi, farko qafarta ce ta fara Se Addah tace mata alamu ne na ciki ya tsufa
babu komai ta dai ringa dan tattakawa haka, sau biyu Antu Ramle na mata magana akan kumburin tace
ta shirya suje Asibiti amma taqi qarshe ma tace ta dameta ita a rabu da ita ana haka kuwa ta ci gaba da
hawa kafin kace me tayi himm ga ciki shima ya qara girma.
Safiyar Friday dakyar dama ta tashi daga kan gado, Addah data shigo dakin take gayawa bata jin dadi
tace mata ta daure tayi wanka ta shirya to se suje Asibiti haka ta yunqura ta shiga bayin, wai dan
daurewar da jikinta yayi ya warware ta sakarwa kanta ruwa masu zafi gaba daya bayin ya turare kan
kace me numfashinta ya fara sama sama yana neman daukewa ba shiri ta yunquro ta fito cikin tsautsayi
tana fitowa ta yanke jiki ta fadi cikin tashin hankali suka kwasheta zuwa Asibitin da take Awo.

Lagos

Ranar Friday da zasu tafin yaran basu je makaranta ba dan babu abinda zasuyi takardar hutu kawai za’a
basu kuma already an turo musu ta email daman, jirgin qarfe 6pm zasu bi zuwa Gombe amma tun kafin
la’asar sun gama komai hatta jakunkunan su sun loda a mota. Se murna sukeyi kamar suyi tsuntsuwa su
gansu a Gombe haka suke ji.

Qarfe biyar sukaji tsayuwar motar Bashir dan daman yace ze dawo da wuri ya kaisu Airport sedai daga
yanayin daya shigo gidan tasan ba lafiya ba.

“Kuje Mota ina zuwa” ya fada yana shigewa dakinsa, yaran suka fita amma ita se tabi bayan sa. Sanda ta
shiga yana waya gaba daya ya birkoto wata shelf daya ke ajiye files dinsa na office da alama wani abu
yake nema.

“Ayi duk abinda ya kamata kafin nazo yanzu zamu taho insha Allah” taji ya fada kafin ya kashe wayar ya
shiga diban wasu daga cikin filea din daya zubar. Ita ya miqawa yace “Joseph na waje please ki bashi
zamu yi waya”

Karba tayi ta fita a ranta tana tunanin meyake faruwa ne toh, haka ta miqawa Joseph files din tana shirin
kowa se gashi ya fito bayan ya kulle gidan gurin wutar gidan ya nufa ya kasheta gaba daya, seta kalleshi
tana cewa “akwai kaya a freezer fa zasu lalace”

“Please muje kawai” ya fada yana bude motar ya shiga itama seta bude gaban ta shiga kawai ya tayar
suka tafi. A Airport din ya ajiye motar suka tashi zuwa Gombe gaba dayan su Asma’u nata mamakin wai
me yake faruwa ne dan dai ba dashi suka shirya tafiyar ba yanayin data ganshi kuma bata zaton ze iya
mata wani bayani, koma dai yaya ne Allah ya kaisu lafiya zasu gani Allah dai yasa Alkahiri ne.
Gombe

Daga Airport direct Asibitin da suke zuwa Naziru ya wuce da Bashir da Asma’u yaran kuma Sa’ad wanda
Nazirun yake bi ne ya kwashe su a tasa motar suka wuce gidan Dada.

“Hasbunallahu wani’imal wakeel” ta furta lokacin da tayi Arba da Amirah dake kwance tayi wani irin
kumburi kamar zata fashe, cikin tashin hankali ta kalli Bashir da shima ganinta a hakan yai bala’in tayar
masa da hankali.

A yanda akayi masa waya beyi zaton abun yakai haka ba. Yana Office da Safe Isma’il yayanta da suke Uba
daya ya kirashi wai Tana tsaye ta yanke jiki ta fadi dama dai tun Kwana biyu take yawan yi masa qorafin
ciwon kai da jiri, ya cewa Naziru ya kaita Asibiti ya kuma je amma taqi zuwa Nazirun ya gaya masa. Beyi
mata magana ba dan dama bashine karo na farko ba da zata ce bata da lafiyar in yace akai ta Asibiti taqi
zuwa sedai ta karbe kudin ta kashe kawai yanzun barinta yayi se yazo sannan ze kora mata warning se
kuma ga wannan abun ya faru.

Da aka kawota Asibitin likitan yake gaya musu jininta ne ya hau sosai da sosai ga kuma alamun
preeclampsia tare da ita (jijjiga) kuma daman tuntuni ya gaya mata duk sanda taji wani sauyi ko alama
tazo a dubata tunda cikinta ya shiga wata na 7 toh awon ma seta ga dama take zuwa gashi yanzu abinda
ba’aso ya faru se fatan Allah ya kawo sauqi kawai.

Suna tsaye jungun jungun Bashir ya tafi office din Dr, acan yake gaya masa dole sedai suyi mata aiki in
dai ana so a ceto rayuwar ta dan barin ta da cikin ze zamar mata hadari.

“Toh Dr ai kuma cikin be isa haihuwa ba” Bashir ya fada a sanyaye

“Wannan ba matsala bane Engineer idan an cire shi zamu sakashi a kwalba ne mu cigaba da kula dashi
har sanda ze isa dauka amma yin aikin yanzu shine kadai maslahar mu, bansan wace irin yarinya bace ita
da bata damu da lafiyar jikinta ba ta yaya ma akayi tana zaune har takai wannan stage din batazo Asibiti
ba tunda ba abu ne da yake faruwa lokaci daya ba”
Shidai Bashir bashi da ta cewa, takardar da likitn ya bashi yasa hannu, yace su kwantar da hankalin su
babu komai insha Allah zasu ci gaba da monitoring nata su samu jinin ya sauka kafin a shiga da ita aiki
suyi ta yi mata Addu’a kawai.

A reception daya fito can lungu ya hango Addah ansha kuka an gode Allah se yan idanu kawai take
kiftawa se sannan ya samu suka gaggaisa dasu kafin yacewa Asma’u da tuni jikinta ya mutu tabi Naziru
ya kaita gida ta hutu jinawa ze taho. Fatan samun sauqi tayiwa Amiran ta bi Nazirun suka wuce gida.

Na Maryamah_Mrs AM

(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)

Page 14

Seda Amirah ta kwana daya a daren rana ta biyu akayi mata aiki cikin ikon Allah aka ciro mata yar
qaramar yarta bakwaini me tsananin kama da Farida, sosai Bashir yayi murnar samun mace sanda aka
nuna masa babyn kafin aka sakata a kwalba, tun cikin daren kuwa ya ringa buga waya yana gayawa
mutane haihuwar.

Ya kira wayar Asma’u lokacin harta fara bacci dan basu dade daga dawowa daga Asibitin ba suna can ma
aka shiga da ita aikin, ganin dare ya fara ga yara yasa ta tafi gida.

“Masha Allah, Allah ya raya ita kuma ya bata lafiya, kace Farida tayi yar uwa Abokiyar shawara” ta fada
bayan data daga wayar.

“Wlh fa sema kinganta kamar su daya kamar sanda kika haifi Faridan girma kawai ta fita” Bashir ya fada
cike da doki kafin sukayi sallama. Baccin ta ta koma dan dama tunda suka dawo ta rufe gida tasan ba
dawowa zeyi ba dan jiya ma can ya kwana seda safe yazo yayi wanka ya chanza kaya bare yau da ya
samu ya ai ba batun zuwa gida kuma.
Washe gari da wuri ta tashi ta hau shirye shirye dan tana so taje gidan su yau ga zuwa Asibiti. seda tayi
girki tayi musu farfesun Kaji ta soya doya sannan ta damawa Amirah kunun gyada dukda bata san ko
zata faracin abinci yau din ba sannan ta dafa Tea suka shirya gaba daya ita da yaran suna ta murna data
gaya musu sunyi qanwa. Se gurin goma sannan ta hada komai suka tafi.

Dakin danqam da yan dubiya yan gidan su Bashir da kuma Dangin Amiran se hayaniya sukeyi dan ta
farfado tun da Asuba. Ba yanda Likita beyi dasu ba subarta ta huta amma sunqi qarshe haushi yaji yai
tafiyarsa ya barsu ya kuma gayawa Nurse kar wanda ya nemeshi in wani abu ya faru dan ya gaji da
halinsu kuma.

Aliyu da Jafar ne a gaba sunyi kama kaman kwandon da ta zubo Abincin su kuma suna binsu a baya suka
shiga dakin da Sallama. Fuskarta dauke da Fara’a suka shiga gaisawa da mutanen dakin tayi musu barka
kafin ta juya kam Amirah da tun shigowar Asma’un ta daure fuska tam taqi koda kallon sashin da take.

“Amirah sannu ya jiki?” Ta tambaye ta idan ta amsa ta to ku da kuke karatu kun amsa abin yai bala’in
bawa Aisha Babbar Yayar su Amirah da suke uba daya haushi har seda tayiwa Amiran magana tace “Kina
ji tana miki magana saboda raini da wulaqanci bazaki amsa ba”

Bata ko motsa ba kuwa sema cuna uban baki gaba da tayi dama fuska duk a kumbure tana qunquni.
Asma’u kam ko a jikinta, yo ita bata ga abin da zesa Amirah tace bazata kulata ba idan kishin nema ai ita
ya kamata tayi tunda aita aka aurewa miji, Allah ya raya ta sakeyi musu kafin ta juya da niyyar fita dan
dama yaran tunda suka gaishe su sukayi waje abinsu, dab da zata fita ta jiyo muryar Addah na tambayar
waya kawo abinci ashe tana bandaki seta juyo ta dawo cikin dakin.

Har qasa ta durqusa ta gaisheta, fuskar Addah kuwa a washe ta amsa mata tana tambayarta ina Mazajen
nata tace suna waje

“Au shine suka fita ba su bani kudin cefane ba ai kuwa su dawo dan bazan yarda ba” Addah ta fada cikin
sigar wasa. Murmushi kawai Asma’u tayi ta miqe tana musu sallama ta fice.

Wato Yanda Addah ta wanke idanunta bata taba nuna wani abu akan auran Amirah da Bashir na bala’in
daure mata kai, mutum, ka kalleshi kawai. A reception ta hadu da Bashir daya je gidansu ya dauko Dada
dan Naziru yana makaranta yau, cikin mutuntawa ta gaisheta tareda yi musu barka Dada ta wuce ciki
Bashir kuma yabi bayan Asma’un.
“Har kun qaraso kenan, yanzu nake so dama na tafi gidan nayi wanka na huta wallahi duk na gaji” ya
fada yana jingina da motar da tuni su Jafar suka shige bayan sun gaisa da Dada.

“Ya kamata kam, abincinka na nan ma na ajiye maka nayi zaton kafin mu fito zaka dawo kuma naji shiru,
mu zamu wuce Babban gida qila idan zamu dawo da dare mu sake shigowa mu duba su” Asma’u ta fada
tana qoqarin bude motar,

“Bazaki je kiga babyn ba?” Ya tambayeta

“Ai bazasu bari ba ka sani ba komai Allah ya bata lafiya idan lokacin fito da ita yayi zamu ganta ai mu da
zata dawo gidan mu da zama ma”

“Eh kuma haka ne, bari na shiga na fito to nima na wuce ku gaida mutanen gidan ban samu na shiga ba
wallahi Yanzu ma da zamu fito naga Kamar Alhaji Qarami dasu Yaya Mudassir a qofar gidan ashe yana
gari”

“Eh yazo daurin auran yarinyar Amininsa ne jiya saurin da nake tayi kenan ma mu tarar dashi ance yau ze
koma” da haka sukayi sallama ya shige ciki ita kuma taja mota suka nufi gidansu.

A can dakin kuwa bayan fitar Asma’u dayawan su sukayi wa Amirah caa akan abinda tayi bata kyauta ba,
Addah ce ta tambayi meya faru Anty Aisha ta gaya mata.

“Ai ni na rasa kalar wannan yarinyar dan barikin nan ma na mata bata iya shi ba ke se baqin kishi quru
quru meye amfanin sa”

“Wallahi fa Addah in nice ita yanda Anty Asma’u ta mayarda komai ba komai ba ake gaisawar mutunchi
ai wallahi sake wa zanyi mu ci gaba da yanda muke amma kin zauna kina quntatawa kanki ita kuwa kina
ganinta cikin walwala ji jikinta dan Allah wannan shegen Lashin nasan wlh yafi 100k ga zobuna a
hannunta ji qanshin turare dan Allah har yanzu be bar gunnan ba” inji Samirah qanwar Bashir da suke
Sa’anni da Amirah.
Hirar su suka ci gaba dayi aka shiga da take qonawa Amirah rai dan duk yabon Asma’u sukeyi ga dabgen
kaji suna ci abinsu a haka Dada ta shigo ta same su ta kuwa ji dadin Abincin da ta tarar Asma’un ta kawo
dukda ita ma ta taho musu da abinci amma tasan ba lallai ya isa ba tunda kusan duk yaran suna nan.

Asma’u kuwa hankali kwance suka isa gidansu wanda layi daya ne ya raba su da gidansu Bashir dan seka
bi ta qofar gidan su Bashir din ma zaka shiga layin da gidansu yake da yake close. Cike da murna Seidu
dan Baba Buzu daya daga cikin masu gadinsu tun na quruciya daya maye girbin Babansa yanzu ya
wangale mata katafaren get din gidan na Alfarma ta shiga.

Tabbas gidan ya amsa sunan sa na Babban gida domin kuwa layi guda ne gidan haka tun daga get da
katangar gidan zaka san cewa ba qaramin gidan me Arziqi bane. Tana gama parking a inda aka
tanadarwa motoci gasunan birjik da alama yau akwai mutane da yawa a gidan yaran suka fita da gudu
saboda hango cousins dinsu yaran Yayye da qannen Asma’u da sukayi se lokacin ta tuna yau Sunday
kusan dukka yan gidan da suke a cikin garin Gombe Mata da Maza suna zuwa gida yau da iyalan su su
wuni tun zamanin da Mahifinsu yake raye har yau kuwa basu fasa ba.

Seda ta gaisa da Samarin dake zaune a bakin get yawanci duk masu aikin gidan sannan ta shiga cikin
gidan, part din Hajia Babba ta nufa dan a irin wannan lokacin tasan acan zata samu kusan kowa ai kuwa
tana shiga katafaren palour nata fuskarta ta qara fadada da Murmushin ganin yan uwanta harma da
wanda batayi zato ba.

Kai tsaye inda Hajia Babban take ta nufa Farar Bafulatana da a qiyasi ta bawa Sittin Baya amma jin dadin
da take ciki ya boye shekarunta “Maraba Maraba da mutanen Lagos” take fada sanda Asma’u ta nufota,
seda ta zauna dab da qafafunta tana daukar wani Dan yaro daya ruqo mayafinta da bata san ko dan
waye ba sannan ta shiga gaisheta.

Cike da qaunar junan data ginu a tsakaninsu suka shiga gaisawa da sauran yan uwanta da suke a palour
se tsiya suke mata wai ta qara kyau tayi wani haskee ta zama wanke ka taba ita dai se dariya kawai take
musu. Suna cikin gaisawar Alhaji Qarami ya shigo Aliyu na take masa baya dan dama mutuminsa ne.

Gaishe shi tayi ya amsa mata cike da kulawa yana tambayarta aiki babu dai wata matsala ko tace babu
sannan yayi wa Hajia Babba Sallama bayan yayi musu gajeriyar nasiha da tunatarwa daya saba yi musu a
duk sanda suka hadu da yawa irin haka akan su riqe zumunchin da Mahaifinsu yasha wahalar gina su
akai, seda yabi duk wanda yake zaune da dubu biyar suda yayan su kaf sannan ya musu sallama Driver sa
ya ja shi suka wuce Abuja inda yake zaune da iyalansa. Ance daman babban wa makwafin uba to tabbas
sudai sunyi dace dan kuwa Alhaji qarami ya maye musu gurbin uban da suka rasa.

A gaba ta saka yaran suka zaga saran part biyu na matan gidan suka gaisa Hajia Ummah da Hajia Anjin
kafin suka wuce sabgarsu ita kuma ta koma part din Hajia Babba inda sauran yan committee suke jiranta
a tattauna.

“Ke ashe Kishiyar ki ta haihu, dazu naji Abbas yana gaya wa Hajia Babba” Ikilima yayarta ta fada, seda ta
cire yafinta ta ajiye a gefe ta zame dankwalin yayi baya sannan tace “wallahi fa ta haihu an mata CS jiya
da daddare an ciro mata baby girl”

“Ayya CS ne Allah ya bata lafiya ya raya abinda aka samu” cewar Anty Hauwa matar yayansu Sunusi suka
amsa da Amin gaba daya.

“Kinje kenan?”

“Naje mana daga can nake ma yanzu”

“Cab kuma kika kwashi jiki kikaje nifa wallahi Yah Asma’u kina bani mamaki na rantse da Allah in nice
kallon banza yarinyar nan bata ishe ni ba bare na arziqi wallahi bazan je dubata ba, bata da mutunchi
kwatakwata baki san abinda ta mana ba ranar sunan Rufaida(qanwarsu ce itama tana auran Yayan
Amirah da suke uba daya) wai saboda bata da kunya ta kalle mu muna zaune wai bamu gaisheta ba idan
Bashir ne ai dole mu gaidashi tunda mijin yar mu ne dan haka matsayi daya take dashi a gunmu ita
Kishiyar yayar muce , wallahi Anty Habi ce kadai ta hanamu nada mata dan iskan duka ranar amma da se
mun koya mata hankali” cewar Amina daga yanda take maganr zaka gane zallar takaicin Amirah da take
ji.

Dariya Asma’u tayi tace “to ai se ku gaisheta meye a ciki zuwa dubiya kuma kema zakije dan ciwo na
gaba da komai sannan ranar suna dole kuzo asha shagali daku”

“Tab Allah ya rufa asiri” Aminan ta fada tana tura baki. Dariya suka saka mata dan dama indai aka fara
wannan dramar Amina bata da dama a fili take nuna jij zafin Amiran harma dana Bashir din dan ita fa
tunda yai auran nan ta dena gaishe shi. Tace yanda beji kunyar ciwa yar uwarta fuska ba itama bazata ji
kunyar dauke kai idan ta ganshi ba taqi gaishe shi.

Asma’u ta kance wai

“Amina inda kece a matsayina ban san me zakiyi ba” ita kuma tace

“Ai wallahi yah Asma’u da ko tsirena su Alhaji Qarami zasuyi na gama auran nan dan bazan koma ba”.

Ranar wunin dadi sukayi suka sha hirar su kamar karsu rabu, se bayan isha suka fara watsewa bayan tayi
musu Alqawarin zata bi kowacce gidanta su gaisa da kyau tunda zata kwana biyu a garin.

Daga ita se Abdallah suka koma gida sauran yaran kowa ya kama gabansa dan daman idan suka zo indai
ba tareda Bashir ba basa zaman gida in yana nan ne yake matsesu baya taba bari suje ko nan da can su
kwana yanzun ma abinda yasa ta barsu yana cikin wannan digimi be zama lallai ma ya fuskanci basa
gidan ba.

Seda ta biya Asibiti ta sake dubasu, a can din dai ta kuma samun sa kuma suka barshi sukayi gida yace se
ya taho har suka kwanta dai be dawo ba seda Asuba sannan taji motsinsa dan a dakinta suka kwanta ita
da Abdallan.

Washe gari Litinin Bashir yayi sammakon komawa aiki bayan yabar komai da zaa buqata hannun Naziru,
ranar ma bata wuni gida ba, gidan Yaya Bilkisu taje da suke ciki daya kuma ita kadaice yanzu a Gombe
Babbar Yayarsu Anty Suhaima tana America da mijinta se Junaidiyya da take Abuja sauran uku mazane
biyun qannenta yan biyu Bilal da Nasir suna karatun masters a China se yayanta daya Muslim yayi aure
tuni yana zaune a Rivers da matarsa da yaransu biyu da A Lagos yake shima akayi masa transfer.

Sosai suka sha hira da Yayar tata har dare kamar karsu rabu, sun yi sallama akan Nan da kwana 7 zasu
tafi Yola tare gurin maman su dukda ita Asma’u taso nan da kwana biyu ta wuce amma Yaya Bilki tace ta
bari se anyi radin sunan yar Amirah idan yaso ko bata samu taron sunan ba babu matsala amma yanzu
in ta tafi ze iya zama abin magana ai a kan hakan suka rabu.

Haka taci gaba da zaga yan uwanta har ana i gobesunan Amirah bayan la’asar tana zaune ta jiyo
hayaniya an bude get. Ta window palour ta ta leqa da mamaki take kallon su Addah dake fitowa daga
mota da Amira tana takawa dakyar bata ga jaririyar ba tana asibitin ita har yanzu.
Bangaren Amiran suka nufa seda suka shige sannan ta koma ta zauna tana mamaki tasan dai yau za’a
sallameta dan ya gaya mata da tun Jiya daya dawo amma batayi zaton nan zata dawo ba kodan yanayin
jikinta amma ita meye nata. Seda tayi sallar isha da dogon hijabin ta a jikinta ta nufi part din Amiran da
kulolin da ta zuba tuwo da miyar kukar da ta saka Amna tayi.

Seda tayi sallama uku sannan suka jiyota ta tura qofar ta shiga duk sukayi wani tsilli tsilli alamar basu da
gaskiya da gulmarta sukeyi a lokacin ta shiga. Bayan sun gaisa ta sakeyi mata ya jiki yau dai ta amsa bata
zauna ba tayi musu sallama ta koma gurinta.

Washe gari suna da Asuba a masallacin unguwarsu aka radawa yarinya suna taci sunan Addah Fatu,
Asma’u na daki Farida take gaya mata Amma Anty Ummi tace Iman zasu ringa kiranta, setayi Murmushi
kawai ta tuna sunan Farida da tace nan ma ya saka mata Maryam sunan mamanta tunda yace ba sunan
Dada ze saka ba ce mata yayi shi bashi da ra’ayin yiwa wani takwara, ko Aliyu daya saka raayin kansa ne
badan Aliyu Abokinsa ba kamar yanda ake zato.

Ana Abdallah kuwa cewa yayi ta siyi rago haka kuwa ta siya, haka aka yanka wa Baby Iman ragunanta
biyu ba’ayi wani taro ba ranar tunda tana Asibiti har sannan sun dai qudurce a ransu fa se sunyi daga
baya, dalilin ma daya sa suka dawo da ita gidanta kenan saboda duk abunda za’ayi ayi akan idon Asma’u
dan Amirah tace shagali zatayi na kece raini.

Washe gari Suka soye naman su ko hanji basu Aikawa Asma’u da bama su san asubancin barin garin tayi
ba ita da yara zuwa yola, suka rabe abinsu tas dan Bashir ma ya tafi tun safe kuma har nasa rabon suka
cinye.

Toh maji ma gani dai.

WATA KISHIYAR

(ALKAHIRI CE KO SHARRI
Na Maryamah_Mrs AM

(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)

Page 14

Seda Amirah ta kwana daya a daren rana ta biyu akayi mata aiki cikin ikon Allah aka ciro mata yar
qaramar yarta bakwaini me tsananin kama da Farida, sosai Bashir yayi murnar samun mace sanda aka
nuna masa babyn kafin aka sakata a kwalba, tun cikin daren kuwa ya ringa buga waya yana gayawa
mutane haihuwar.

Ya kira wayar Asma’u lokacin harta fara bacci dan basu dade daga dawowa daga Asibitin ba suna can ma
aka shiga da ita aikin, ganin dare ya fara ga yara yasa ta tafi gida.

“Masha Allah, Allah ya raya ita kuma ya bata lafiya, kace Farida tayi yar uwa Abokiyar shawara” ta fada
bayan data daga wayar.

“Wlh fa sema kinganta kamar su daya kamar sanda kika haifi Faridan girma kawai ta fita” Bashir ya fada
cike da doki kafin sukayi sallama. Baccin ta ta koma dan dama tunda suka dawo ta rufe gida tasan ba
dawowa zeyi ba dan jiya ma can ya kwana seda safe yazo yayi wanka ya chanza kaya bare yau da ya
samu ya ai ba batun zuwa gida kuma.

Washe gari da wuri ta tashi ta hau shirye shirye dan tana so taje gidan su yau ga zuwa Asibiti. seda tayi
girki tayi musu farfesun Kaji ta soya doya sannan ta damawa Amirah kunun gyada dukda bata san ko
zata faracin abinci yau din ba sannan ta dafa Tea suka shirya gaba daya ita da yaran suna ta murna data
gaya musu sunyi qanwa. Se gurin goma sannan ta hada komai suka tafi.

Dakin danqam da yan dubiya yan gidan su Bashir da kuma Dangin Amiran se hayaniya sukeyi dan ta
farfado tun da Asuba. Ba yanda Likita beyi dasu ba subarta ta huta amma sunqi qarshe haushi yaji yai
tafiyarsa ya barsu ya kuma gayawa Nurse kar wanda ya nemeshi in wani abu ya faru dan ya gaji da
halinsu kuma.
Aliyu da Jafar ne a gaba sunyi kama kaman kwandon da ta zubo Abincin su kuma suna binsu a baya suka
shiga dakin da Sallama. Fuskarta dauke da Fara’a suka shiga gaisawa da mutanen dakin tayi musu barka
kafin ta juya kam Amirah da tun shigowar Asma’un ta daure fuska tam taqi koda kallon sashin da take.

“Amirah sannu ya jiki?” Ta tambaye ta idan ta amsa ta to ku da kuke karatu kun amsa abin yai bala’in
bawa Aisha Babbar Yayar su Amirah da suke uba daya haushi har seda tayiwa Amiran magana tace “Kina
ji tana miki magana saboda raini da wulaqanci bazaki amsa ba”

Bata ko motsa ba kuwa sema cuna uban baki gaba da tayi dama fuska duk a kumbure tana qunquni.
Asma’u kam ko a jikinta, yo ita bata ga abin da zesa Amirah tace bazata kulata ba idan kishin nema ai ita
ya kamata tayi tunda aita aka aurewa miji, Allah ya raya ta sakeyi musu kafin ta juya da niyyar fita dan
dama yaran tunda suka gaishe su sukayi waje abinsu, dab da zata fita ta jiyo muryar Addah na tambayar
waya kawo abinci ashe tana bandaki seta juyo ta dawo cikin dakin.

Har qasa ta durqusa ta gaisheta, fuskar Addah kuwa a washe ta amsa mata tana tambayarta ina Mazajen
nata tace suna waje

“Au shine suka fita ba su bani kudin cefane ba ai kuwa su dawo dan bazan yarda ba” Addah ta fada cikin
sigar wasa. Murmushi kawai Asma’u tayi ta miqe tana musu sallama ta fice.

Wato Yanda Addah ta wanke idanunta bata taba nuna wani abu akan auran Amirah da Bashir na bala’in
daure mata kai, mutum, ka kalleshi kawai. A reception ta hadu da Bashir daya je gidansu ya dauko Dada
dan Naziru yana makaranta yau, cikin mutuntawa ta gaisheta tareda yi musu barka Dada ta wuce ciki
Bashir kuma yabi bayan Asma’un.

“Har kun qaraso kenan, yanzu nake so dama na tafi gidan nayi wanka na huta wallahi duk na gaji” ya
fada yana jingina da motar da tuni su Jafar suka shige bayan sun gaisa da Dada.

“Ya kamata kam, abincinka na nan ma na ajiye maka nayi zaton kafin mu fito zaka dawo kuma naji shiru,
mu zamu wuce Babban gida qila idan zamu dawo da dare mu sake shigowa mu duba su” Asma’u ta fada
tana qoqarin bude motar,
“Bazaki je kiga babyn ba?” Ya tambayeta

“Ai bazasu bari ba ka sani ba komai Allah ya bata lafiya idan lokacin fito da ita yayi zamu ganta ai mu da
zata dawo gidan mu da zama ma”

“Eh kuma haka ne, bari na shiga na fito to nima na wuce ku gaida mutanen gidan ban samu na shiga ba
wallahi Yanzu ma da zamu fito naga Kamar Alhaji Qarami dasu Yaya Mudassir a qofar gidan ashe yana
gari”

“Eh yazo daurin auran yarinyar Amininsa ne jiya saurin da nake tayi kenan ma mu tarar dashi ance yau ze
koma” da haka sukayi sallama ya shige ciki ita kuma taja mota suka nufi gidansu.

A can dakin kuwa bayan fitar Asma’u dayawan su sukayi wa Amirah caa akan abinda tayi bata kyauta ba,
Addah ce ta tambayi meya faru Anty Aisha ta gaya mata.

“Ai ni na rasa kalar wannan yarinyar dan barikin nan ma na mata bata iya shi ba ke se baqin kishi quru
quru meye amfanin sa”

“Wallahi fa Addah in nice ita yanda Anty Asma’u ta mayarda komai ba komai ba ake gaisawar mutunchi
ai wallahi sake wa zanyi mu ci gaba da yanda muke amma kin zauna kina quntatawa kanki ita kuwa kina
ganinta cikin walwala ji jikinta dan Allah wannan shegen Lashin nasan wlh yafi 100k ga zobuna a
hannunta ji qanshin turare dan Allah har yanzu be bar gunnan ba” inji Samirah qanwar Bashir da suke
Sa’anni da Amirah.

Hirar su suka ci gaba dayi aka shiga da take qonawa Amirah rai dan duk yabon Asma’u sukeyi ga dabgen
kaji suna ci abinsu a haka Dada ta shigo ta same su ta kuwa ji dadin Abincin da ta tarar Asma’un ta kawo
dukda ita ma ta taho musu da abinci amma tasan ba lallai ya isa ba tunda kusan duk yaran suna nan.

Asma’u kuwa hankali kwance suka isa gidansu wanda layi daya ne ya raba su da gidansu Bashir dan seka
bi ta qofar gidan su Bashir din ma zaka shiga layin da gidansu yake da yake close. Cike da murna Seidu
dan Baba Buzu daya daga cikin masu gadinsu tun na quruciya daya maye girbin Babansa yanzu ya
wangale mata katafaren get din gidan na Alfarma ta shiga.
Tabbas gidan ya amsa sunan sa na Babban gida domin kuwa layi guda ne gidan haka tun daga get da
katangar gidan zaka san cewa ba qaramin gidan me Arziqi bane. Tana gama parking a inda aka
tanadarwa motoci gasunan birjik da alama yau akwai mutane da yawa a gidan yaran suka fita da gudu
saboda hango cousins dinsu yaran Yayye da qannen Asma’u da sukayi se lokacin ta tuna yau Sunday
kusan dukka yan gidan da suke a cikin garin Gombe Mata da Maza suna zuwa gida yau da iyalan su su
wuni tun zamanin da Mahifinsu yake raye har yau kuwa basu fasa ba.

Seda ta gaisa da Samarin dake zaune a bakin get yawanci duk masu aikin gidan sannan ta shiga cikin
gidan, part din Hajia Babba ta nufa dan a irin wannan lokacin tasan acan zata samu kusan kowa ai kuwa
tana shiga katafaren palour nata fuskarta ta qara fadada da Murmushin ganin yan uwanta harma da
wanda batayi zato ba.

Kai tsaye inda Hajia Babban take ta nufa Farar Bafulatana da a qiyasi ta bawa Sittin Baya amma jin dadin
da take ciki ya boye shekarunta “Maraba Maraba da mutanen Lagos” take fada sanda Asma’u ta nufota,
seda ta zauna dab da qafafunta tana daukar wani Dan yaro daya ruqo mayafinta da bata san ko dan
waye ba sannan ta shiga gaisheta.

Cike da qaunar junan data ginu a tsakaninsu suka shiga gaisawa da sauran yan uwanta da suke a palour
se tsiya suke mata wai ta qara kyau tayi wani haskee ta zama wanke ka taba ita dai se dariya kawai take
musu. Suna cikin gaisawar Alhaji Qarami ya shigo Aliyu na take masa baya dan dama mutuminsa ne.

Gaishe shi tayi ya amsa mata cike da kulawa yana tambayarta aiki babu dai wata matsala ko tace babu
sannan yayi wa Hajia Babba Sallama bayan yayi musu gajeriyar nasiha da tunatarwa daya saba yi musu a
duk sanda suka hadu da yawa irin haka akan su riqe zumunchin da Mahaifinsu yasha wahalar gina su
akai, seda yabi duk wanda yake zaune da dubu biyar suda yayan su kaf sannan ya musu sallama Driver sa
ya ja shi suka wuce Abuja inda yake zaune da iyalansa. Ance daman babban wa makwafin uba to tabbas
sudai sunyi dace dan kuwa Alhaji qarami ya maye musu gurbin uban da suka rasa.

A gaba ta saka yaran suka zaga saran part biyu na matan gidan suka gaisa Hajia Ummah da Hajia Anjin
kafin suka wuce sabgarsu ita kuma ta koma part din Hajia Babba inda sauran yan committee suke jiranta
a tattauna.
“Ke ashe Kishiyar ki ta haihu, dazu naji Abbas yana gaya wa Hajia Babba” Ikilima yayarta ta fada, seda ta
cire yafinta ta ajiye a gefe ta zame dankwalin yayi baya sannan tace “wallahi fa ta haihu an mata CS jiya
da daddare an ciro mata baby girl”

“Ayya CS ne Allah ya bata lafiya ya raya abinda aka samu” cewar Anty Hauwa matar yayansu Sunusi suka
amsa da Amin gaba daya.

“Kinje kenan?”

“Naje mana daga can nake ma yanzu”

“Cab kuma kika kwashi jiki kikaje nifa wallahi Yah Asma’u kina bani mamaki na rantse da Allah in nice
kallon banza yarinyar nan bata ishe ni ba bare na arziqi wallahi bazan je dubata ba, bata da mutunchi
kwatakwata baki san abinda ta mana ba ranar sunan Rufaida(qanwarsu ce itama tana auran Yayan
Amirah da suke uba daya) wai saboda bata da kunya ta kalle mu muna zaune wai bamu gaisheta ba idan
Bashir ne ai dole mu gaidashi tunda mijin yar mu ne dan haka matsayi daya take dashi a gunmu ita
Kishiyar yayar muce , wallahi Anty Habi ce kadai ta hanamu nada mata dan iskan duka ranar amma da se
mun koya mata hankali” cewar Amina daga yanda take maganr zaka gane zallar takaicin Amirah da take
ji.

Dariya Asma’u tayi tace “to ai se ku gaisheta meye a ciki zuwa dubiya kuma kema zakije dan ciwo na
gaba da komai sannan ranar suna dole kuzo asha shagali daku”

“Tab Allah ya rufa asiri” Aminan ta fada tana tura baki. Dariya suka saka mata dan dama indai aka fara
wannan dramar Amina bata da dama a fili take nuna jij zafin Amiran harma dana Bashir din dan ita fa
tunda yai auran nan ta dena gaishe shi. Tace yanda beji kunyar ciwa yar uwarta fuska ba itama bazata ji
kunyar dauke kai idan ta ganshi ba taqi gaishe shi.

Asma’u ta kance wai

“Amina inda kece a matsayina ban san me zakiyi ba” ita kuma tace

“Ai wallahi yah Asma’u da ko tsirena su Alhaji Qarami zasuyi na gama auran nan dan bazan koma ba”.
Ranar wunin dadi sukayi suka sha hirar su kamar karsu rabu, se bayan isha suka fara watsewa bayan tayi
musu Alqawarin zata bi kowacce gidanta su gaisa da kyau tunda zata kwana biyu a garin.

Daga ita se Abdallah suka koma gida sauran yaran kowa ya kama gabansa dan daman idan suka zo indai
ba tareda Bashir ba basa zaman gida in yana nan ne yake matsesu baya taba bari suje ko nan da can su
kwana yanzun ma abinda yasa ta barsu yana cikin wannan digimi be zama lallai ma ya fuskanci basa
gidan ba.

Seda ta biya Asibiti ta sake dubasu, a can din dai ta kuma samun sa kuma suka barshi sukayi gida yace se
ya taho har suka kwanta dai be dawo ba seda Asuba sannan taji motsinsa dan a dakinta suka kwanta ita
da Abdallan.

Washe gari Litinin Bashir yayi sammakon komawa aiki bayan yabar komai da zaa buqata hannun Naziru,
ranar ma bata wuni gida ba, gidan Yaya Bilkisu taje da suke ciki daya kuma ita kadaice yanzu a Gombe
Babbar Yayarsu Anty Suhaima tana America da mijinta se Junaidiyya da take Abuja sauran uku mazane
biyun qannenta yan biyu Bilal da Nasir suna karatun masters a China se yayanta daya Muslim yayi aure
tuni yana zaune a Rivers da matarsa da yaransu biyu da A Lagos yake shima akayi masa transfer.

Sosai suka sha hira da Yayar tata har dare kamar karsu rabu, sun yi sallama akan Nan da kwana 7 zasu
tafi Yola tare gurin maman su dukda ita Asma’u taso nan da kwana biyu ta wuce amma Yaya Bilki tace ta
bari se anyi radin sunan yar Amirah idan yaso ko bata samu taron sunan ba babu matsala amma yanzu
in ta tafi ze iya zama abin magana ai a kan hakan suka rabu.

Haka taci gaba da zaga yan uwanta har ana i gobesunan Amirah bayan la’asar tana zaune ta jiyo
hayaniya an bude get. Ta window palour ta ta leqa da mamaki take kallon su Addah dake fitowa daga
mota da Amira tana takawa dakyar bata ga jaririyar ba tana asibitin ita har yanzu.

Bangaren Amiran suka nufa seda suka shige sannan ta koma ta zauna tana mamaki tasan dai yau za’a
sallameta dan ya gaya mata da tun Jiya daya dawo amma batayi zaton nan zata dawo ba kodan yanayin
jikinta amma ita meye nata. Seda tayi sallar isha da dogon hijabin ta a jikinta ta nufi part din Amiran da
kulolin da ta zuba tuwo da miyar kukar da ta saka Amna tayi.
Seda tayi sallama uku sannan suka jiyota ta tura qofar ta shiga duk sukayi wani tsilli tsilli alamar basu da
gaskiya da gulmarta sukeyi a lokacin ta shiga. Bayan sun gaisa ta sakeyi mata ya jiki yau dai ta amsa bata
zauna ba tayi musu sallama ta koma gurinta.

Washe gari suna da Asuba a masallacin unguwarsu aka radawa yarinya suna taci sunan Addah Fatu,
Asma’u na daki Farida take gaya mata Amma Anty Ummi tace Iman zasu ringa kiranta, setayi Murmushi
kawai ta tuna sunan Farida da tace nan ma ya saka mata Maryam sunan mamanta tunda yace ba sunan
Dada ze saka ba ce mata yayi shi bashi da ra’ayin yiwa wani takwara, ko Aliyu daya saka raayin kansa ne
badan Aliyu Abokinsa ba kamar yanda ake zato.

Ana Abdallah kuwa cewa yayi ta siyi rago haka kuwa ta siya, haka aka yanka wa Baby Iman ragunanta
biyu ba’ayi wani taro ba ranar tunda tana Asibiti har sannan sun dai qudurce a ransu fa se sunyi daga
baya, dalilin ma daya sa suka dawo da ita gidanta kenan saboda duk abunda za’ayi ayi akan idon Asma’u
dan Amirah tace shagali zatayi na kece raini.

Washe gari Suka soye naman su ko hanji basu Aikawa Asma’u da bama su san asubancin barin garin tayi
ba ita da yara zuwa yola, suka rabe abinsu tas dan Bashir ma ya tafi tun safe kuma har nasa rabon suka
cinye.

Toh maji ma gani dai.

WATA KISHIYAR

(ALKAHIRI CE KO SHARRI)

Na Maryamah_Mrs AM

(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)


Page 15

YOLA

Su Asma’u sun isa yola lafiya sun kuma samu tarba me kyau daga mamansu da suke kira da Goggo da
bakinta yaqi rufuwa ganin yayan nata da kuma jikokinta a gabanta ba qaramin faranta mata yayi ba. Se
sannu da zuwa take musu tama rasa wanne zata kama ciki idan ta janyo wannan yaron se saki ta kamo
wancan su Asma’u har seda sukayi kwallar kewar Mahaifiyar tasu.

Seda suka nutsu sukayi sallolinsu sukaci abincin da Abokiyar zaman Goggon Innawuro ta kawo musu ga
fura me sanyi da gardi sannan Goggo tayi musu jagora zuwa bangaren megidan su gaishe shi.

Fari kyakykyawan bafulatanin me kamilalliyar fuska dake cike da haiba da hasken salati yana nan a yanda
Asma’u ta sanshi tunda tayi wayo sedai a kwantar a tayar tun zamanin da suke zuwa Tareda Baffan su
dubashi wanda kuma tun kafin a haife ta yake wannan ciwon kimanin shekarun sa Arba’in kenan a
kwance yana wannan jinyar da har yau Allah ne yanke masa ba sedai fatan ta zamo masa kankarar
zunubi.

Seda sukayi dagaske gurin danne kukan tausayin bawan Allahn dake musu maraba daga kwancen ya
miqa hannu ya kamo Abdallah yana cewa “Zo nan Abdullahi bawan Allah madallah da Amini na kwarai,
Rahmar ubangiji ta dawwa ma tare da takwaranka a makwancinsa”.

Akan shimfidar sa da take a gyare ya zaunar da Abdallah sannan ya janyo Arif din Yaya Bilki yana cewa
“wannan kuma me idon yan Chinese dinfa wanene” seda sukayi dariya gaba daya Innawuro tace “Toh
takwaranka ne Isma’il dan wajen Bilkisu”

“Toh toh yi haquri ta kwara gajiyar hanya ce ta rufe idon ko nasan anjima zasu bude irin nawa”.

Cikin mutuntaka suka gaisa ya tambayesu sauran Yan uwansu da kowa da kowa duk suka amsa lafiya
daga nan ya shiga saka musu Albarkar da bakinsa baya gajiya da ita a kullum suka hadu ko suka gaisa a
waya. Sun dan zauna kafin yace suje su huta haka suda suka sha hanya, a nan suka bar yaran suka koma
Dakin Goggo jikinsu dukka a sanyaye.
“Allah sarki Baffan Yola wannan jinya dai taqi ci taqi cinyewa Allah yasa kankarar zunubi ce” Asma’u ta
fada tana kwanciya akan gado Goggo da Bilkisu suka Amsa da “Amin”. Basu ja wata hira ba suka kwanta
aka barwa gobe dan sun gaji gaskiya.

Washe gari bayan sun je sun gaisa da Innawuro da Baffa suna zaune a palour Goggo suna cin Wainar
Gero da Kunu me kyau da Innawuron tayi musu dan tasan suna son sa sosai. Goggo dake zaune daga
gefe ta kalli Asma’u tace “Ma’u ya Abokiyar zaman ki kuwa kuna dai zaune lafiya koh”

Seda ta tsame hannunta kafin tace “Muna lafiya Goggo to ina muke ganin juna bare wani abu ya hada
mu ina Lagos tana Gombe”

“Haka ake so ai dama wani sa’in raba gidan yana da amfani idan har akwai wasu matsaloli amma dai ko
zuwa gaba idan ta fara tara iyali itama dole ya hade ku saboda a samu daidaiton kawuna tsakanin su dan
dai nasan baki tashi kinga ana yan ubanci a gidan ku ba kuma zaki kaishi gidan wani ba”.

“Haka ne Goggo ai tama haihu fa shekaran jiya akayi suna” Yaya Bilkisu ta fada jin Asma’u tayi shiru bata
ce komai ba.

“Kai Masha Allah me aka samu? Kuma cikin satin da aka fita fa Bashir din ya kirani Allah yasa kuwa beji
babu dadi ba banyi masa barka ba ban sani ba ai da har ita Dadan tasu da Fatu na kira na musu barka,
miqo min wayata nan Bilki ki gani karma na sha’afa da batun”.

Wayar Yaya Bilkisu ta bata ta kuwa shiga kiran Bashir sedai be Amsa ba saboda lokacin aiki ne seta maida
kiran kan Dada ita ma seda ta kusa katsewa sannan ta daga. Cikin mutuntaka suka gaisa Dada ta
tambayeta ya me jiki tace jiki gashinan se fatan Afuwa.

“Ashe kuma an samu qaruwa wallahi ban sani ba se yanzu muke zancen dasu Asma’u nake ji”

“Asma’u? Sunzo yola ne?” Dada ta tambaya dan bata sani ba Bashir din be gaya mata ba daman kuma
tasan Ma’u ba Sallama zata mata ba yanzu.
“Eh wallahi sunzo tun jiya ita da Bilki, Allah ya raya yayi Albarka, haduwa tayi wuya amma Insha Allahu
ina sa ran zuwa Bikin Hashim (Qanin su Ma’u da suke uba daya) anyi abubuwa da yawa Gombe ban
samu leqowa ba”Goggo ta fada, da haka sukayi sallama ta kashe wayar bata ajiye ba ta dannawa Addah
Fatu kira.

Itama lafiya lau suka gaisa tayi mata barka harta bawa Amirah waya suka gaisa da Goggo tayi mata
sannu sannan ta kashe wayar ta maida hankalin ta kan Asma’u da tayi kinini da fuska dan tasan seta
mata maganar qin gayawa Dada tafiyarta.

“Wato Ma’u bazaki chanza ashe, wai ni shin Nafi ce tayi miki kishiya ko Bashir da zaki bi ki qullaci baiwar
Allah ki ringa gaba da ita. Sehi wanda ya miki laifi kina zaune qalau dashi amma kina raina uwarsa”

“Ni wallahi Goggo ban rainata ba me nake mata? Duk wani girma da ya kamata in bata ai ina bata to me
ake so kuma nayi”

“Oh kina ma da bakin mayar min kenan, yanzu ina bata masan kin taho nan ba kin kwaso mata jikoki har
shida kin biyo wannan hanyar bata sani ba, ba fata ba idan wani mugun abu ya faru kuma fa sedai kawai
suji sama”.

“Toh ni yanzu Goggo ai ba haqqi na bane na gaya mata Danta ne ya kamata ya sanar da ita tunda ai ya
sani da izininsa muka taho ai”

“Haka ma zakice, to maza ki kirata yanzu a waya ki bata haquri kuma kodan gaba ki kiyaye kar irin haka
ta sake faruwa” Goggon ta fada.

“Dan Allah Goggo karki tilastani yin wani abun kuma dan kinsan bazan bijirewa umarninki ba, wane kalar
haquri ne banayi, tunda Bashir yai aure sau daya na taba daga waya na kawo miki qarar sa akan yayi
mun wani abu ai badan baya yimun din bane dan kince mun naje na shanye komai nayi haquri ne.
Bazan iya ci gaba da alaqa dasu ba abinda ya zama dole zanyi amma wallahi na yanke duk wata alaqa ta
baya da kika sani tsanina dasu ga yar uwarsu nan se tayi musu abinda suke ganin ni bazan iya ba”. Ta
qarasa maganar hawaye na sakko mata

Ta rasa me Goggo take so ta zama, a zatonta kowa irinta ne me tsananin hakuri, yakana da dauke kai
akan komai? Ko kuwa duka maza kalar Mazajen data zauna dasu ne masu Adalci da sani ya kamata?
Sannan kowane yayi dacen kishiyoyi na qwarai da dangin miji na gari. Sun fa qare tuni irinsu amma ita
Goggo bazata gane wannan baudadden zamanin da muke ciki da ko cikin yayan da mutum ya haifa yake
nuna banbanci dan daya yafi daya wadata, Namiji yake fifita buqatar wata mace akan wata saboda
alaqar jini, sannan surukai suke zabar jinsu akan sauran surukai da suke baren su.

Ita Dadan ai da bakinta tace mata Dama sun dade suna son dorar da zumunchinsu kuma ta hanyar hada
auratayya ne kadai haka ze yiwu ko to gashinan sun hada ta kuma janye ta basu guri suyi yanda suke so
se kuma ace seta cusa kanta cikinsu ina sam fa bame yuwuwa bane.

“Toh yanzu menene na hawaye kuma daga magana” Goggo da jikinta yayi sanyi ta fada ai kamar Asma’u
na jira kuwa ta fashe da kukan gaske harda sheshsheqa. Haka sukayi zukudi duk suna kallonta ranau
babu dadi musamman Goggo, seta janyo Asma’un jikinta tana cewa

“Kiyi Haquri nasani ba’a kyauta miki ba, ba’a miki daidai ba kuma badan nafi son su nake cewa kiyi
haqurin ba Aa sedai ina so ki rabauta da ladan da Allah ya tanadarwa masu yinsa. Idan kika jure kikayi
haqurin idan ma sun zalince ki ko anan ko acan se Allah ya saka miki amma kiyi shiru ki dena kuka dan
Allah”.

Dakyar ta tsagaita kukan tana ci gaba da share hawayen dai dai Innawuro ta shigo dakin.

“Ashsha Maryam me yasa kike haka duk sanda yarinyar nan tazo se kin saka ta kuka dan Allah menee
haka” Innawuro ta fada tana janye Ma’un gareta kafin taci gaba da cewa

“Nasan zancen daya ne akan mijinki da danginsa, Duk abinda suka miki na cutuwa kar kiyi shiru Asma’u
kiyi magana ki kwaci yan cinki, ki tsarkake zuciyarki kar ki nufi kowa da sharri kar kumaki bari su raina ki
da sunan wai kina da haquri ko ita da take gaya miki hakan saboda Allah be jarabceta da irin wadannan
fitintunun na zamani bane shiyasa take ganin kamar kowa irin zaman ta yake yi.

Share hawayenki dan Allah karki ragawa duk wanda yace ze taka ki ki rama kinji Ma’u”.
Dadi kalam Innawuro suka mata ai kuwa ta share hawayenta aka dauko wata hirar daban. Suna zaune
Sauda da Maimuna Yaran Innawuro sukayi sallama sunzo wa su Ma’u sannu da zuwa nan suka shiga
hirar yaushe gamo dan dama Saudah qawarta ce sosai.

Se yamma suka fita tare dasu Saudah sukaje gidan Hamma Isah Babban Dan Innawuro matarsa ta haihu
suna gidan a ka kira waya aka fada. Washe gari kuma suka fara zaga dangin Goggonsu ta ko ina sune har
Mambila daman haka sukeyi, basu fiya samun damar zuwa ko yaushe ba amma duk sanda suka zo se sun
zaga ko ina sun gaisa da dangi tareda kai musu abun arziqi hakan kuwa ba qaramin dadi yake yiwa yan
uwan Goggon dadi dan ko basu kai musu komai ba zuwa a gaisa din kadai ya wadatar.

Mu dawo Gombe 😂😂

Amirah na ci gaba da jinyar jikinta da kuma shirye shiryen shagalin sunan data rantse seta yi dukda
haryanzu basuyi maganar da ogan ba amma jira takeyi da an sallamo baby Iman, ita kanta Addah
wannan karon tace mata ta haqura gaba inda rabo se tayi kudin da ze bata se suyi wata hidimar dasu
amma Amirah ta qeqashe qasa Allan fir se tayi. A cewarta haka kawai duk qawayenta tana gani in sun
haihu yanda ake raqashewa kamar biki sannan ita ace kartayi wallahi ita ma se sunci uwar sabada kowa
yazo ayi bushasha asan itama fa me kudinnan take aure se kuma Addah tace haka ne fa toh suyi kodan
ma a maido musu da bikin gudummawar da sukayi.

Ranar Talata da daddare lokacin data tabbatar yana gida ta danna masa waya dan tana so ya bata
kudaden da zata siyi kaya ta bada dinki ga kuma shirye shiryen suna. Bashir na zaune a palour yana shan
Tea da cake gaba daya dauriya yakeyi amma zaman kadaicin ya isheshi gidan ya masa wani wawakeke
saboda babu Ma’u a ciki ji yakeyi kamar ya kirata yace ta dawo.

Abinci kansa se kame kame yake in yunwa ta ci shine dole yake zuwa Restaurant yaci gaba daya besan
me yasa wannan karon dan girke girken data saba masa ta saka a frizzer idan zatayi tafiya irin haka
batayi ba, ya saba da sedai ya bude ya dauko yayi microwaving yaci to yanzu ko miya ce kadai itama ta
qare dan Ma yayi dabarar sakawa a kunna wutar gidan bayan sun tafi wancan ranar daya tuna da
abubuwan zasu baci gidan yayi wari dan haka ya saka aka karbo spare key na gidan a Estate
Management Anty ta shiga ta qarasa kashe musu duk wani abu da ze iya kawo matsala aka bar frizzer.
Yana cikin tura Cake din Wayar Amirah ta shigo ya harari wayar sannan ya daga a dake dan ya san
labarin gizo baya wuce na qoqi, indai Amirah ta kira shi to ko tambayar kudi ko qorafi in yana son jin
yanda suke sedai shi ya kirata.

Bayan sun gaisa se duk sukayi shiru, yanayin dataji miryarsa ba walwala tasan dakyar in zata samu yanda
take so amma haka ta daure taja numfashinta tace

“Abban Iman dama naji shiru ne baka ce komai ba akan siyayyar kayan Iman da nawa kasan wancan da
ka bani unisex muka siya na amfanin farko farko”.

Seda ya mula sannan cikin dakewa dan karta kawo masa wani wargi yace “ke yanzu kayan me kuma kike
magana kina fama da kanki?”

“Kayan barka mana” ta fada itama tana dakewa.

“Ni babu kudin wasu kayan barka da zan baki abinda nake dashi na bawa su Dada zasu hada da na
gurinsu a siya wannan kayan Al’adar data ce na zata ma sun kawo muku”

“Basu kawo ba inaga se gobe” ta fada a cukule dan ba haka taso ba yanzu ma sune zasu siyo kayan aka
san irin wanda take so? Sannan itama nata duk se sun gama gane wa kenan kafin tayi kwalliyar gaskiya
bazata yarda ba sedai ya bata ko kudin Lace daya ne da zatayi kwalliyar Suna dashi dan haka ta gyara
zama tace

“Toh shikenan amma dai se ka bani na siyi wanda zanyi fitar suna dashi danne kamata kowa ya gani ba
sena saka”.

“Suna wane sunan kuma” ya tambayeta da mamaki dan dai yasan ai shekaran jiya akayi radin suna ko?

“Taron suna mana, idan an sallami Iman dole zamuyi tunda ai na farko ne kaga”.
“Karki kuskura wallahi idan bakiji tausayin kanki da jikinki ba to kiyi ke kadai amma ko da wasa karki sako
mun ya a ciki ke ko yan barka ki ka ringa bawa yata aka jagwalgwalata se ranki yayi mummunan baci
wallahi bare har ki tara mata hayani ya akai. Ke yanzu ko lafiyarta qalau ma ai kya dagamun qafa kodan
kashe kudin da nayi a Asibiti kice ba se kinyi wani taro ba bare yarinyar har yanzu kina ganin yanda
take”.

Seda ta tunzura baki kamar yana gaban ta tace “ to kowa ya haihu ana suna se ni ace baza’ayi nawa ba
nidai se nayi gaskiya”

“Allah ya baki sa’a” ya fada tareda kashe wayar, ya fuskanci so take ta qure shi seya saita mata
kwakwalwar ta sannan zata dawo kan hanya. Allah ya bata ikon yin taron sunan tabbas seta gane waye
Bashir kuwa.

Amirah

Hararar wayar tayi harda murguda baki tace “Dan rainin hankali wallahi se nayi kuma seka bada kudin,
naga matar ka duk haihuwa ai setayi suna na Alfarma sanda ma baka dashi bare ni yanzu dole ma ka
nemo su ka bani. Labarta wa Addah komai tayi tace ta rabu dashi ze bayar bari dai a sallamo yarinyar ai
taji Likitan yace Alhamis ko Juma’a zasu iya sallamar su ko, haka sukaci gabada tsare tsaren su.

Washe gari gurin goma na safe Suna zaune a palour tareda yan gidansu da suka sake zuwa dubata harda
kishiyoyin Addah dukka biyun da matan yayyenta kamar aike sega Sallamr Dada ta shigo Naziru da
Fainusa da Ihsan na biye da ita da akwatuna guda biyu ga kuka saitin baho da Qaramin gado me net.

Nan suka shiga musu maraba suka zauna aka gaisa kafin Dada ta kalli Addah tana cewa “Addah ga kayan
barka nan nace dai ya kamata a kawo tunda al’adace gashi munyi sa’a ma yan gidan nasu suna nan.

Addah baki har kunne nan aka shiga zuge jakun kuna ga kaya nan tabarakallah komai yaji Babbar kayan
jaririyane tsala tsalan riguna da sauran tarkacen kayan baby na yan gayu seta tsakiya kuma kayan
Amirah Atamfofi guda biyu Madam Getzner daya se Laces masu kyau suma biyu kayan da gani kaf
kasanba qanana bane harda mayafi kalar lace daya da jaka da takalminsa.
Amirah na nade akan kujera Lace din da aka hadowa da takalmi da jaka ya tafi da ita amma kuma batajin
zata saka tunda mutane sun gani.

“Gasunan dana gurin Bashir da gudummawar yan uwansa dukka aka hada mukayo siyayyar” cewar
Dada.

“Kaya sunyi sosai Allah ya qara arziqi yasa lafiya ta kashe, Se ki fito da na gurin ku kema su gani ko Fatu”
Inna Gaji dake faman daga kaya ta fada.

“Fatu ai se ku fito dana ku ko tunda gasu su gani” ai Addah ji tayi kaman ta kwadawa Inna Gaji mari
wannan tonon silili da take neman yi mata a gaban kishiyoyi sun kuwa zuba ido da kunnuwa suna jira suji
me za’a ce dan Al’adar gidan su haka akeyi da an kawo kayan gidan miji suma zasu fito da masu a hada
amma ita ko pant bata siya ba.

Rasa ta cewa tayi dan haka ta shiga kame kame tana yaqe Dada ta taimaka ta kwaceta da cewa “kai se
kace wani abun bare ai bamu raba daya biyu ba duk gasunan ai na dangin uwa dana miji kune dai zaku
fito da naku yanzu dangin uba” tayi maganar cikin sigar wasa akabat Addah da sauke ajiyar zuciya da
yaqen dole.

Dada bata jima ba tayi musu sallama ta fita Addah tabi bayanta.

“Kai Nafi kin ceceni wannan shegiyar Gajin dason qure mutum haihuwar data zo lokacin ta beyi ba ina
naga ta siyan wasu kaya ga wannan lalura”

“Hakane” Dada ta bata amsa.

“Yauwa dama yau nake so nazo muyi maganar taron suna da za’ayi idan an sallamo yar, kin san yanzu se
ya zama abin magana idanba’ayi ba fa”

“Wace irin magana kuma Addah bayan kowa yasan halin da uwar da yar suke ciki, dan Allah kibar
wannan magana Allah ya kaimu gaba ai ba gamawa tayi ba se ayi”. Cewar Dada
“Kiji ki Nafi da wata magana to in kin manta bari na tuna miki Binta ba bakwainin kika haifeta ba(Babbar
yarta) kuma haka muka shirya taron suna akayi”.

“Amma Addah bazaki hada zamanin Binta dana wannan yarinyar ba, Binta a sannan ba ma waye da
zuwa Asibiti ba qarewarta a gida na haifeta yanzu kuwa abu ko da anyi shi babu matsala tunda zamani
yashiga cikin abubuwa koya kika kuskure se kiga an samu akasi azo ana dana sani nidai a shawara ku
haqura nasan kuma shina Bashir din baze bari ayi ba”. Dada ta sake fada ranta fal takaicin Addah.

“Wallahi se Anyi jikar tawa ta fari kuma takwarata kice bazanyi suna ma baqin ciki ma kikemun kenan
ko”

“Wane irin baqin ciki kuma Addah nima ai jikata ce ko ban haifi Bashir ba”

“Toh in ma dai hada baki kukayi kedashi yace baza’ayi ba tun wuri ki gaya masa wallahi suna ba fashi ya
lalo kudade ya bata da zatayi hidima in ba haka ba rai ya baci” tana gama fadar haka ta juya fuuu tayi
ciki.

“Dan Allah Dada muje wallahi ko Yaya ya yarda bazasuyi sunan ba ai dai ni zece nabada kudin ko zamu
gani” Naziru ya fada yana huci, haka suka shiga motar suna tafe shida Fainusa suna debewa Addah
albarka Dada dai bata iya ce musu komai ba gaba daya ta tafi tunanin meke damun Addah a rayuwa ne.
Su yanzu inda hankali ko cewa akayi suyi ai sace Aa amma har tana rantsuwar ae sunyi, to wannan karon
zata ja itama bazata takurawa Bashir ba kuma ko sunyi galaba akan sa ya yarda seta hana, zata nuna
mata bafa tsoro yasa take mata biyayya ba.

Allah dai ya mana maganin abinda yafi qarfin mu.

WATA KISHIYAR

(ALKAHIRI CE KO SHARRI)
Na Maryamah_Mrs AM

(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)

Page 16

Ranar Juma’a Bashir ya dawo Gombe kuma ranar aka sallamo baby Iman, Bashir da kansa ya dakkota
bayan da ya dawo dan daman shi ya hana likitan sallamar su akan se yadawo saboda matsawar da
Addah tai masa akan zancen shagalin suna.

Amiran bata daddara ba washe garin randa sukayi maganar seda ta sake kira ya kuwa yi mata tatas dan
dama sunyi waya da Dada ta gaya masa yanda suka kwashe da Addahn dan haka ya qara tabbatar mata
da wallahi ko sisin sa baze bayar ayi wani suna ba idan bata gode rai da lafiyar da Allah ya basu ita da yar
ba ta godewa Azabarsa. Ai kuwa itama Addah batayi sanya ba ta karbe waya ta masa wankan tsaf ta
kuma sake tabbatar masa fa taron sun ba fashi.

Shekara da shekaru tana rabar da kudin Barka da biki, haka auran Amiran kaman na munafukai basu
barta tayi shagali ba yanzu ma a haifar mata jika suce Aa, to kuwa bazata sabu ba shidai ya mata shiru
harta qaraci kumfar bakinta ta kashe ya kuwa rangadawa Amirah text din gargadi tunda ga ranar ma be
sake kiranta ba idan ma ta kirashi baya dauka se yau Juma’a daya dawo garin suka hadu.

Yaso ma da ya tafi ya karbo yarinyar shi kadai sedai kuma ya tuna Amiran na buqatar a karanta mata
yanda zata kula da yarinyar yasa yace ta shirya su tafi se gata ita da Hajia Addah aka shige mota.

Sau goma suka hada ido da Addah se sun jefi juna da harara ita da Bashir can dai da abin ya isheta tace
“Bani kake harara ba Bashir Uwarka Nafi da Amadu su kake harara mara mutunchin kawai, kuma duk
baqin cikinka suna ne se munyi se dai kayi bindiga ka mutu”.

Kici kanki be ce mata ba har suka je Asibitin, sosai likita yaja kunnensu akan kula da Iman, Banda wanka a
tsundumata a ruwa, suna tsaye ya saka Nurse ta kwatanta musu yanda za’a ringa wanke mata jikin
shima ba kullum ba musamman yanayin garin sanyi ya kankama.
Sannan ya dora musu da bayanin in so samu ne mamanta kadai zata ringa daukarta kar a jagwalgwalata
su tabbatar kuma ko yaushe tana cikin dumi kar ake fitar da ita cikin iska ko sanyi a kula da kayan da za’a
ringa saka mata kuma.

Sallama sukayi suka tafi bayan ya basu ranar da zasu dawo ganin likita.

Bashir be yadda ma an dauke ta a hannu ba cikin Baby carrier daya siyo tundaga lagos ya sakata ya
dauka Addah ta hau salati da salallami wai ya saka ya a kwando to duk bala’in sa dai ko mayu ne su se ya
basu yar in sunje gida tunda ba da ita ze ringa yawo ba,

shida be tankata ba. Seda ya ajiyeta dakyau ya maqala belt din ko ina sannan ya shige ya tada mota har
sukaje gida kuwa Addah bata saduda ba se sababi takeyi.

A gidan ma suna zuwa da kansa ya bata feeder ta fara sha dan bottle feeding suke yi kafin ya bawa
Amirah taci gaba da bata yana tsaye, seda ya tabbatar tasha yanda ya kamata ya dagata kamar kwan da
baya so ya fashe ya sakata a kafada tayi gyatsa kafin ya kwantar da ita a dan gadonta. Seda ya dauketa
hoto a wayar sa sannan ya juya.

Kallo daya yayiwa Amirah dake doka uban Murmushi saboda ganin irin tattali da kulawar da yake
nunawa yarinyar, ta san yanzu ko Albarkacin Iman seta qara matsayi a zuciyarsa shi kuwa gogan tsaki ya
buga ya fice daga dakin dan haushinta yake ji.

Yana fita Addah da jama’arta suka duru daki ganin Baby, kamar me tattaro kaya ta zura hannu zata
cukumota Amirah kuwa tayi caraf ta riqe tana cewa “Haba Addah bakiji me likita yace bane shine zaki
kawo mata wannan cafkar ai seki ballata”.

Suka kwashi salati ita da jama’arta kafin ta fara masifa tana cewa “Eh lallai yanzu na yarda ba iya Bashir
ne tanbadaddenba harda ke, yo in banda tanbada ni uwarki zaki hana na dauketa har ni zaki gayawa kar
a karya miki ya, to da ban haihu ba yau se nayi kuka kiji da jinki seda na haifi Goma na binne takwas gaku
nan biyu a raye harke ma kinyi yar kanki zaki nunamun sanabe da iyayi”.

Inna Gaji ce ta ceci Amirah tace “Ba haka bane Fattu yanzu dai barta mu kalla daga haka dan Allah
abunda in muna da tsahon rai watarana da qafarta zata taka ta hau jikin duk wanda take so” haka aka
lallaba Addah kowa ya leqa yarinya dake baccinta masha Allah kyakykyawa da ita kowa se yace ta kwaso
kaman nin yayan Ma’u.

Addah dai bata haqura ba seda ta daukota Amirah na kumbura baki tana komai,

“Oh ni Fatu wannan abu kamar yar kyanwa, kwanta karna manta Dan mutum ne nayi jifa dashi” ta fada
tana maida yar cikin Gadonta kafin ta harari Amirah data cika baki da iska tayi qwafa ta fita daga dakin.

Bashir kuwa yana fita Part din Ma’u ya bude ya shiga, ya zuqi qamshin da a gurinta kadai ya sanshi dan
gidanta na nan dana Lagos qanshi su daya duk kuwa da bata ciki ya rigada ya kama Gurin se a sannan ya
tuna dakin masu jegon ma daya shiga kodan Air freshener beji ba bare Turaren wuta.

Wanka ya farayi ya yi sallar Isha da shafa’i da wuturi sannan ya shiga kitchen ko ze samu abinda ze ci
tunda can basu bashi ba. ya yi sa’a kuwa cikin Freezer ya samu farfesun kayan ciki dama mutuminsa ne
nan da nan ya dumma ya dauki bread ya hada tea ya fara ci. Seda ya kusa cinye wa naman suna ya fado
masa a rai, kunsan mutuminku ko kura Albarka nan da nan ya qarasa cinyewa ya dauki waya ya dannawa
Amirah kira dan baya so ya koma su hadu da Addah.

Amirah na cikin waya da Tailor data bawa dinki dan tuni ta kai musanyen lace din da aka sako mata na
barka ta karbo wani ta bada dinki da sauran kayan da zatayi amfani dasu a lokacin ma tailor yana gaya
mata ya gama ne gobe ze kawo ya karbi bakance din kudinsa, ganin kiran Bashir yasa ta cewa Tailor tana
zuwa ta amsa wayar da fatan Allah sa Zancen sunan ze mata.

“Kizo ina son ganin ki, ki taho mun da nawa kason Naman” ya fada a taqaice. Seda cikinta ya bada
qulululu dan bata taba zaton ze tambaya ba. Tas suka rabe naman nan ko gutsiren hanji beyi saura ba ita
yanzu me zata ce masa?

Ai kuwa beci ta manta ba aduk sanda Anty Asma’u ta haihu kasawa yake ya tsare se an cire masa nasa
kason, tana kuma yawan jin Asma’un na qorafin daga baya se ya biyo wanda aka aje mata ya cinye ta
rasa wane irin so Bashir yakewa Nama a rayuwarsa dukda gashi yanzu ita sun hada sun lamushe.

Haka ta zari mayafin ta ta fita tana taraddadin me zata ce masa, a qofa taci karo da Addah ta dawo daga
raka baqin ta.
“Ke kuma ina zaki fita a daren nan da danyen jego” ta fada tana kallon ta ganin ta da mayafi.

“Yaya Bashir ne yake kirana”

“Oh to se kin dawo” Addah ta fada tana rabeta zata wuce se Amirah ta ruqota tana rartaba ido.

“Ya akayi se wani qifta ido kike kamar an kama Kwarto?”

“Addah wai cewa yayi in taho masa da kason naman sa na suna” cewar Amirah.

“To se ki tafi ai” Addah ta fada tana son wucewa ciki.

“Kin manta Addah ya qare fa babu ko diddiga yanzu me zan ce masa”

“Ke dallah matsa ki ban guri se kice masa ya qare ko kice an hada an kaiwa Nafi bashi kenan ba”.

“Addah wace Dadan kuma kin manta itama fa baki basu ba wanda aka ware musu bashi kikace a bawa
su Hajia Salamatu ba da suka Zo barka kika ce ta rabawa yan group dinku?”.

Se Addah tayi kasaqe tace “haka ne kuma fa, tab di amma fa mu ma munyi gwari wallahi to yanzu ya
za’ayi?”

“Nima ban sani ba” Amirah ta fada tana marairaicewa. Ta tabbatar laifin cinye nasa kadan ne akan idan
yaji ko su Dada ba’a aikawa dashi ba.

“Kinga yanzu kije kawai in ya tambaya kice kin manta, idan ya biyo sahu ni kuma zan ce masa Muzuru
sun shigo sun cinye bamu sani ba se in nuna masa duddugar bashi kenan ba, shima ai yasan dangin ku da
yawa ya wani se miki rago biyu ai yayi kadan” (😳) tana gama fada tayi ciki abinta, nama dai sun cinye ba
kuma a isa ace su biya ba.
Amirah kuwa jiki a mace ta shiga palour, ga abinda yake a gabanta amma ta bige da kallon qurilla taga
me aka chanza a ciki i lai kuwa taga sabuwar Kantamemiyar Cinema Tv bango guda da Asma’un ta saka
kana ganin muatanen ciki kamar zasu fito, sannan ta chanza Dining dinta ba na da bane ga wasu
hadaddun Kwanuka akai shikansa Turkish Centre carpet din ba wancan bane kamar.

Kallonta Bashir yake ba laifi ta sace amma bata gama dawowa daidai ba ga cikinta nan haryanzu da
girman sa Allah dai yasa kar tayi tumbi dan a duniya ya tsani tumbi a jikin mace kuma da Allah ya
taimakeshi Ma’un sa haihuwa Biyar amma har yau bata da tumbi ko dan tana kula da jikinta ne oho?

yanda yaga Amiarn tana kalle kalle yasa ya girgiza kai kawai kafin yace “Malama ko zauna mana kin tsaya
mun akai. Zama tayi kan Kujerun da suka dade da tsole mata ido ta kuma quduri niyya itama fa se ya
mata irin su yanzu ko ga qarin Dining ma da TV duk irinsu take so itama a siya mata.

Sake gaishe shi tayi ya amsa hankalin sa akan Tv, jin shiru bata miqo masa komai ba ya sakashi kallonta
yace “Ina naman” dan fa shi har ya dakko a exotic drink coconut and pineapple dinsa da ze hada ya kora
nama seta hau kame kame tana sosa kai tace “uhm uhm daman”

Idonsa akanta yace “malama daman me kin tsaya kina wani kwana kwana in ma wani abu zaki
tambayeni bani dashi ki bani namana ki tafi daman kiran da na miki kenan”.

“Ai naman ne ya qare” ta zabi da ta fada masa gaskiya kawai komai ta fan jama fanjan.

“Ya qare?” Ya tambaye ta, se daga masa kai alamar Eh dan ta kasa kuma bude bakinta saboda kallon da
yake mata.

Daurewa yayi ya danne bacin ransa kafin yace “ toh kun kai gidan Dada kun bawa Ma’una nata ko?”

“Ai se tafi da rikicewa, kai ta juya masa alamar Aa cikin tsawar da seda ta zabura yace “Malama ki bude
baki kiyi mun magana ko”
Jiki na rawa tace “Ni wallahi ban sani ba kasan bani da lafiya su Addah ne suka raba ban san kota kai
musu ba dan ni wallahi ko yanka daya banci naman ba”.

Ya tabbatar basu bawa ko daya daga ciki ba kenan, dan haka kawai yace ta tashi taje kafin ya jawo
wayarsa ya danna kiran Dada yana saita fushinsa. Bayan ta daga suka gaisa, tambayarta yayi an kai musu
naman suna kuwa tace Aa.

“Kar kace zakayi magana Bashir nama dai Allah na tuba kullum ai muna ci, ba wani Abu kasan yan gidan
su nada yawa kowa ze so a qulla masa” Dada ta fada da son kwantar masa da hankali dan tasan Bashir
da Nama.

Seda yayi kokawa da bacin ransa kafin yace “Amma Dada raguna har biyu manya ne fa ba wai qanana ba
su soya su cinye ko yanka daya su kasa kai wa uwata idan ni da na siya banda mutunchin da zasu bani
sannan ga Ma’u da yara gaba daya suna cikin gidan a soya duk su kasa basu”.

“Kadaiyi haquri” Dadan ta sake fada kafin su kayi sallama. Ransa a bace ya shiga dakinsa ya kwanta se
kuma ya ja wayar ya kira Asma’u dan yau duk basuyi waya ba.

“Ran Alhaji Bashir Baban Ali ya dade” ta fada cike da nishadi dan hirar sa suke yi da Yaya Bilki ya kira.
Murmushin da beyi niyya bane ya kwace masa kamar wanda ake watsawa ruwan sanyi yaji zuciyar sa na
huce wa, muryarta kadai ta wanke masa bacin ran Naman suna seya gyara kwanciya yana cewa

“Ba wani nan bayan kunyi tafiyar ku ma kin manta dani inaga sena biyo ku sannan zaku dawo”

“Haba dai kwatakwata fa kwanan mu biyar yau cikin weekend muke saka ran dawowa ai” Asma’u ta
fada.

“Shikenan ma kinga da kun dawo se mu wuce kawai, na gaji da zaman gwauranta kan nan”.
Dariya tayi kafin tace “oh kana Gombe kenan”

“Eh na shigo dazu, an sallamo Fatima yanzu tana gida”.

“Masha Allah Allah ya raya mata ya bata lafiya, ashe Addah aka saka”.

Da “Amin” ya amsa ya share tambayar ta ta. To me take so yace mata in dai ba son tada zaune tsaye
kuma ba.

Yaran ya tambayeta tace sunyi bacci suka dan taba hira kafin sukayi sallama bayan sun gaisa da Yaya
Bilkisu.

“Kinji mutuminki nace ashe Addah aka saka yayi kamar beji ba” Asma’u ta fada bayan ta ajiye wayar.

“Kema da neman magana kike wallahi me kike so to yace miki?” Cewar Yaya Bilki

“Me kuwa zece daman kinga ai ta ta uwar tafi tawa a gunsa shiyasa ya saka mata sunanta”.

“To da be saka ba dama Addini ne yace dole ayi ko kuwa da ze zama laifi” cewar Goggo da shigowarta
kenan. Muqus Asma’u tayi, dan tasan idan ta tofa wata fada ne zata sha ita kam se taga kamar Goggo
tafi son Bashir a kanta ma wani lokacin, bargo taja ta rufe har kanta hankali tacewa Yaya Bilki “idan ta
fita ki gaya mun” jin Goggo ta ci gaba da magana.

Seda Goggon ta fita kuwa ta bude tana cewa “Ita Goggo bata san takaicin da ake qullawa mutum ba tayi
ta rufeshi da fada, wai fa kinji ma cewa yake idan mun koma se mu bishi mu tafi ni nama fasa tafiya
Sunday din sena tabbatar ya koma tukunna. Sati uku mukayi dashi munci biyu se na qarasa sati na
wallahi dan har Bauchi nake so Naje wa Alawa sannan naje Jos ma”.

“Ai kuwa da ba kwana zakiyi a Bauchin ba nima da naje Alawiyya har tayi mitar ta gaji ban taba zuwa ba”
inji Yaya Bilkisu

“Kai haba dai amma baki kyauta ba wallahi ina Gombe ina Bauch” cewar Asma’u
“Ba haka bane kinsan yawan ci abin zuwan haihuwa ce to kusan tare muke haihuwa kota rigani kona
rigata amma daya baya Arba’in to sedai mu hadu a gida”.

“Eh to hakane”. Hira suka ci gaba dayi kafin sukayi bacci.

A Gombe kuwa washe gari Bashir ga haushin cinye masa nama gana tambayar kudi da Amirah tazo ta
fara masa da sassafe, buyagin gaske yai mata ya faffada mata maganganu son ransa qarshe ta fita tana
kuka da dana sanin zuwan daman Qawarta Husna ce ta tsara mata yanda zataje ta same shi gashi babu
biyan buqata se baqin ciki ta kwaso tana shiga dakin ta kuma ta tarar da Addah ta cika baho da ruwan
zafi ta tube Iman tana shirin tsumbulata tai mata wanka.

Da mugun gudu Amirah ta tare ta hannun ta ya shiga cikin ruwan da sauri ta cire jin zafin ruwan ta
yayimi towel ta nade Iman tana kallon Addah data saki baki da Hanci tana kallonta itama.

“Dan ubanki saboda zan mata wanka shine kika buga wannan tsallen kamar wata yar ball kika kwace ta?
So kike a bar ya mace ba wanka kusan sati biyu da haihuwa tayi warin qashi To wallahi ba da ni ba dole a
wanke mata dattin mahaifa”.

Ita dai Amira bata kula ta ba, se jijjiga Iman da ke dan kukan da ko muryar ba’aji dakyau take dan ta
firgita, jin Addah bazatayi shiri ba yasa tace “wai Addah baki ji me likita yace bane gaskiya idan ba zaki
mata irin yanda yace ayi ba ki bar wankan kawai zan nunawa Inna Gaji ta ringa mata. Haka kawai idan
wani abun ya sameta ai nice da Asara kuma ji ruwan da kika saka kamar wanda zaki fige kaza”.

Salati Addah ta debo ta dire kafin ta shiga auno mata ashar tana cewa “kiji mun yar banza ni kike
shatawa layi akan wannan magen dan bazance mutum ba to kinyi da yar halak in na sake taba ta kice
shegiya nake” ta mike tana gyara zani tana ci gaba da banbaminta.

Inna Gaji da shigowarta kenan ta tambayi ba’asi Amiran ta mayar mata seta dubi Addah tace
“Wallahi Fatu kin fiya tada zaune tsaye in ba haka tunda ga abinda likita yace se kibi na dan lokaci ne ko
cewa akayi zata dawwama ba wankan ne se ki mata yanda suka ce.

Yanzu kizo ki zunduma musu ya a ruwa bayan naji ance tana da munoniya wani abu ya faru kinsan dai
wannan sirikin naki manta komai zeyi wallahi har ni nan da babu ruwa na qila se yayi qarar mu ai
wannan ruwan yayi yawa...kaii” maganar ta katse bayan data tsumbula hannu a ruwan, seta kalli Addah
ido waje tace

Fatu kice kisan kai kika shirya wannan ruwan ko uwarta bata wanka da me zafinsa shine zaki jefa wannan
tatsitsiyar yar a ciki? To nidai inaga watan tafiyata gida ya kama dan bazan iya zuwa polisteshan bada
sutotimen ba”.

Addah da tayi tsilli tsilli dakyar tace “nifa ji nayi jikin ba kwari shine nake so na gasata jikinta ya hade
amma tunda banyi abin kirki ba shikenan kuda kuka iya se ku mata” fuu tayi waje.

Wunin ranar haka ta yini mita duk wanda yazo seta gaya masa abinda Amirah tayi mata kuma dai kowa
ita yake bawa laifi.

Ganin dai dagaske Bashir baze bada kudin taro ba Addah ta shiga ta fita da abinda Baban Amirah da yan
uwanta suka hada da bashin Jama’a duk ta ganganda za’ayi bikin suna. Kayan abinci dama ba matsala
bane sunyi akan na Store dinta za’a diba ayi komai.

Kaji kawai zasu siya se ruwa da lemo da kayan snacks se kuma kayan rabo da Amirah ta nace se tayi dan
har ta kira me hoto yazo ya dauki Baby wanda za’a saka ajikin Jaka da Memo. Duk shirin nan basu
gayawa Dada ba tunda tace bada yawunta ba balle Bashir da ya rantse ya kuma rantsewa baza’ayi ba
shiyasa ma suka tsaida ranar Laraba bayan ya tafi litinan sannan zasuyi sunan.

Allah kaimu ranar suna lafiya

WATA KISHIYAR

(ALKAHIRI CE KO SHARRI)
Na Maryamah_Mrs AM

(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)

Page 19

Tunda Bashir ya qulla tsiya ya kuma tabbatar Naziru ya kulle gidan dan sun sake yin waya ya gaya masa
ya je dakko su Amna a gidan qawarsu a sannan ce masa yayi ya wuce ya kaisu gidan Bilkisu yayar Asma’u
kawai dan idan yace gidan Dada zata zargi wani abu kuma baya so labarin ya isar mata da wuri.

kashe wayarsa yayi dan karma wani dayake ganin mutunchi ya kirashi ya roqeshi. Beko qara minti goma
a gidan Musa ba ya tafi yana tuqi a ransa yana wassafa irin hukuncin da ze dauka akan Amirah tunda har
ta take dokarsa ta nuna bata jin maganarsa tabbas ze nuna mata shima ba kanwar lasa bane.

Daya isa gida shikadai ya ringa safa da marwa a cikin palour yana kwafa tabbas se ya hukunta yarinyar
nan hukunci me tsanani, tunanin halinda Baby Iman take ciki yake yana fatan Allah yasa yarinyar tana
lafiya wani abu be sameta ba hakan ze dan rangwanta wa Amirah hukuncin da zeyi mata amma ya
rantse tabbas wani abu ya sami yarinyar nan se kansa besan me ze mata ba. Yana so ya kira Ma’u amma
bayaso ya kunna wayar wani kiran ya shiga qarshe haka ya haqura ya zauna jiran lokacin daya diba kafin
ya sake kiran Naziru.

Gidan suna kuwa gagarumin ruguntsumi ne ya sake tashi. Ana tsaka da dambaruwar yanda za’ayi a bude
qofa, dangi da qawayen Addah sun taru suna mata tijara sun cika palour Amirah taf kaman an sakko
daga Idi daidai da iska me kyau babu ta shaqa se kaya kaya akeyi.

Amirah na durqushe se rasgar kuka take har sannan akan yarinyar da harta gaji da komawa da
numfashinta ta kwanta laqwas kamar mara rai ita duk wannan hayaniyar ba ganewa take ba, buqatarta a
samu me kai mata ya Asibiti dan ta dade da saddaqarwa yau kashi ta ya gama bushewa.

Addah data gaji da tijara da cin mutunchin da Jama’a suke mata ta zaro Key ta cillawa Hajia Mariya datafi
kowa hasala a cikin matan dan ita aka dira daka, so take kawai ta fita ta san nayi dan ko karan hauka ya
cijeta bazata doshi gidan mijinta yanzu ba se da wannan mota da bata san uban da ya sace ba dan haka
ta yanke shawarar daga nan office din Yan sanda zata ta bada report daga can kuma tayi gidansu dan
tasan waye mijinta sarai haka kawai ma yayi bala’i bare yau da aka taboshi da lasisi.

Cafkar key din tayi tana watsawa Addah kallon wulaqanci tace “da karki bayar wallahi da sena tubeki na
dauki muqullin nan yau” ta fara kutsawa da niyyar zuwa bude qofa Hajia Hassana ta katseta tana cewa

“Mariya wannan muqulli fa aikin banza ne dan ta waje wani hatsabibin yaro ya kullo mu wallahi. Kuna
tsaka da hayaniya dazun nan Uwargidanta ta raka baquwa ta bude kofar tana fita yaron nan ya danno
daga waje ya rufe jeki duba ma ki gani babu kwadon nan ta ciki”.

Kafin ma ta qarasa dayawa sun dauki sabon kukan tashin hankalin rashin sanin wane kalar bala’in ne
kuma yake tunkaro su, To bala’i mana in ba haka ba ta yaya za’a ce an kullo su ta waje ma bata ciki ba
yanzu suyi yaya su fita dan dai wannan katangar gidan basu isa su tsallakata ba.

Ummi ce da tuni itama ido sukayi mici mici saboda kuka ta sunkuci Iman tana ceda Amirah “nidai matsa
ki gani wannan hayaniyar da hucin numfashin kadai sun isa su qarasata muje ko a Napep ne mu tare mu
kaita Asibiti” ta nadeta a cikin shawl din ta kyau ta juya da niyyar fita kamar ana jiran ta kuwa dif wutar
palour ta dauke duhu ya mamaye ko ina bame ganin wani a ciki.

Gaba daya guri ya sake rikicewa da ihu dan kina tsaye sedai kiji an wafce miki jaka nan aka shiga
turereniyar fita ana faduwa duk wadda kuwa ta fadi sunanta sorry dan taketa za’ayi ana neman hanyar
tsira a garin haka aka dungure mata Tv ta fado qas tim Centre table kuwa daman tuni ya karbi rabonsa
se fatan kar wani ya taka kwalba a garin gudu.

Wata qara me kama da rugugin tsawa a ka fasa kafin sukaji faduwar abu tim a qasa, sabon gudu ne ya
falle ga duhu ba wanda yasan takamaiman ina yake dosa aka ringa gwabza karo ana faduwa kuwa kafin
kace me anyi wada wada da kayan palour Amirah,

Seda aka kwashi a qallah minti goma se ga haske ya dawo ai kan kace kwabo wayam sun fice daga palour
an dawo tsakar gida kowa tayi cirko cirko fuskokin mata jagejage da hawaye wannan Suna ko jaraba?

Addah data ja qafa da niyyar gudu itama caraf aka riqeta cikin abinda befi sakan uku ba ta saki fitsarin
tsoro ganin sunyi ido hudu da Hajia Mariya dake yashe a qasa da ko ba’a gaya mata ba tasan riqaqqun
iskokanta ne suka tashi. Tun da tace an sace motar nan abinda take taraddadi kenan dan indai ranta ya
baci se sunzo kuma Al’amarin bazeyiwa kowa kyau ba dan Aljanunta basu da mutunchi yanzu basuqi
suyiwa kowa na gidan sunan nan bulala dari dari ba.

Sake yunqurawa tayi da niyyar gudu Mariya ta miqe cikin muryar yara tace mata “Addah fatu muje
washan goyo ja’ayi yau kowa seya goya ni in ba haka ba nayi masha buyayay goma ke zaki faya kuma”

“Quuuu” cikin Addah ya bada qara, yo ai badanba gara bulalar akan tace a goyata. Ita kadai ma Hajia
Mariya ba kadan bace qaruwar mace ce ta gaske bare idan wannan yar Aljanar tata tazo me son goyo
seta Allah in kuma bakayi ba kaci na jaki. Addah naji tana gani ta tasata a gaba suka fito inda Jama’a
sukayi cirko cirko ta dane bayanta kuwa.

Zanso kuga idon Addah haka ta goya hajia Mariya tana nishi kamar zata mutu ta kaita ta dawo da ita
amma taqi sauka tace se an sake haka ta kuma sahu daya da ita sukaje suka dawo sannan ta sauka. Zaba
ta ringayi wanda ze goyata in ka tsaya gardama sedai kaji dundu kamar an buga maka guduma kuma in
ta hau marasa qarfi suka fadi nan ma ta hau tamola da mutum aifa gida ya sakw zama kamar gidan
Allura se kuka ake wannan jaraba har ina.

Aliyu dake cikin dan dakin da Change over da Solar su ta gidan yake ya kwashe da dariya har yana kaiwa
qasa. A kan idonsa komai yake gudana dama jira yake gari ya qara duhu ya kashe haske ya qara musu
tension akan wanda suke ciki gashi kuwa yayi ga kuma sabon show an samu kai amma fa abu yayi kyau
kuma yaji dadi, fitowa yayi ya wuce part dinsu, knocking biyu Jafar ya bude masa ya shiga yana Dariya.

Asma’u dake zaune akan kujerar Dining suna waya da Yaya Bilkisu ta gayavmata su Farida suna can
Naziru ya kaisu ta dago ta kalleshi, tun ma kafin tayi magana yace “Mami kinga yan suna kuwa ga wata
can tana Aljanu tace se sun goyata kowa takalminta a hannu lipstick duk ya goge”.

Duk yanda taso dakewa tayi masa fada kasawa tayi ta fashe da dariya dan tana hango harabar gidan dan
tarwai yake da hasken fitulun da aka zagaye shi dasu, saboda ma taga komai dakyau yasa ta dage
labulaye suka rage hasken fitulun palour duk drama da akeyi akan idonta ne tana ganin haske ya dauke
kuwa jikinta ya bata Aliyu ne dan ta san aikinsa ne kashe wutakuma dazu ta ganshi a zaune a qofar
power room din magana ce kawai bata masa ba ta wuce.

“Allah ya shiryeka, kar naga ka sake fita in ba haka ba ranka ze baci” ta fada tana miqewa.
“Sunan wani film waishi daga murna” ta fada tana shiga kitchen dariya fal ranta, Yogurt ta dauka da cups
biyu ta koma dakinta inda ta bar Rahma tana sallar Isha tunda yaranta sun samu mafaka ai shikenan ita
kam.

Abuubuwa sun sake rikicewa Addah ido ya raina fata, data san haka ce zata faru kuma da bata kulle
qofar ba gara tabar kowa ta tafi gidan ta idan yaso tayi Allah ya isa amma gashi yanzu an bata goma daya
bata gyaru ba. Dakyar ta samu ta zillewa yar zulai Aljanar Hajia Mariya tayi bayan gidan gashi ta Rasa
wanda ze kira mata Dada dan ita kadaice kuma madafarta a yanzu idan ma ba’a san wandaya kullo su ba
ita zata iya nemo wanda ze zo ya buge kwadon amma wannan garqamewa da akayi musu idan wuta ta
tashi fa Allah ya kiyaye subi ina su fita?

To kuma kiran Dadar ma ba hali dan an sace waya kuma tasan babu me bata aron tasa idan ma an bata
ita ba haddace Number ta tayi ba, dabara ce ta fado mata arai, bari taje gurin Ma’u ta kira mata Bashir ai
shine me gida dukma tsiyar da za’ayi sudai a bude su tukunna jama’ar data tara su tafi wannan bala’in ya
ragu dan dai kam taga suna yau ganin idonta bakuma ta fata Allah ya sake maimaita mata irin wannan
taron. Sadadawa tayi ta faki ido ta zagaya ta kofar kitchen din Ma’u.

Kamar zata balla qofa haka ta ringa doka musu bugu tanayi tana wai waye gudun kar wani ya ganita Har
Jafar ze bude Aliyu ya riqo shi yana cewa “kai baka da hankali ko to jeka bude musu baka san me yake
faruwa a gidan nan bane” se Jafar din ya fasa amma be zauna ba ya tafi ya gayawa Ma’u.

Ta yar hudar jikin qofar ta hango Addah fuska tayi qozai qozai abunka da fara daurin da aka dandasa
mata dazu yayi ta kansa ga kunnenta daya da dan kunne daya babu ta tabbatar bata ma lura da hakan
ba. Bude mata qofar tayi tana shigowa kuwa takai qasa tana rushewa da kuka kamar qaramar yarinya.

Kiyiwa Allah Asama’u ki kira Bashir azo a budewa mutanen nan qofa su fita kafin su kashe ni nidai nayi
dana sanin wannan qaddararren taron suna ashe rabon wahala ne yasa muka nace se munyi” ta sake
rushewa da kuka harda sheshsheqa.

Ba qaramin dauriya Ma’u tayi ta riqe dariyarta ba amma dukda haka da Addah a hayyacinta take seta
gane dariya take mata tace “toh Addah meya faru kuma ni da naji shiru an dena kida ma na zata kun
tashi ne.
Wayar Baban Aliyu kuwa a kashe take fa dan na kirashi tun dasu naji amma bari na same kira ko yanzu
ya kunnata” ta fada tana danna wayar ta lalubi Number sa ta danna kira, kai kodan ta sake kunno musu
shi idan be sani ba ai yasa ta kirashi sedai kamar dazu data kira ce mata akayi a kashe take.

“Wallahi Addah a kashe take” ta fada tana janye wayar a kunnenta

“Kiramun Nafi dan Allah ita ta samo mana wanda ze bude mu” Addah ta katseta seta maida akalar
kiranta kan Dada itama seda ta mata kira biyu sannan ta daga ba tareda ta yi magana ba ta miqawa da
Addah wayar ta karba tana rushewa da Dadan da kuka.

“Nafi na shiga uku na hada taron masifa da Bala’i yau ki taimake ni yar uwata ki kawomun dauki” Addah
ta fada cikin matsanancin kuka. Dada da harta kwanta dan cikin ikon babu wand aya kirata ya gaya mata
wannan Al’amari dan yayanta da sukaje suna bayanda Asma’u da Amirah suka gwanya musu rashin M
fushi sukayi suka bar gidan, ragowan dangin da suke can kuwa tunanin su kirata be zo musu ba koda
yake rabi da kwatan yan suna an kwamushe musu waya wadanda suka tsira kuwa sunyiwa tasu boyo me
kyau kafin a sane ta.

“Addah lafiya, meya faru? A ina kuma? Dada ta tambayeta cikin damuwa da jin kukan nata tasan ba
lafiya ba amma Number Asma’u data gani yasa hankali be tashi da yawa ba tasan koma mene ne da
sauqi.

Addah kukan ta taci gaba dayi, ganin da Asma’u tayi bata da niyyar ansawa Dada ya sakata karbar wayar
ta danyi mata bayanin iya abinda ta fuskanta da lamarin.

“Ashsha abu beyi kyau ba, yanzu waye ya kulle gidan? Shi Bashir din ya sani?” Dada ta tambaya se
Asma’u tace mata

“Muma bamu sani ba Ai, Baban Ali kuma ban sani ba gaskiya ko yasan maganar dan wayarsa a kashe
take tundazu dana kira”.

“Shikenan bari nayiwa Amiru magana gashi can yana cin abinci daman nan gidan naku ze taho ya dauki
Rahma in yaso se suzo da Naziru yanzu Allah ya kiyaye gaba” Dadan ta fada zuciyarta sam babu dadi,
yanzu wannan wane irin abune ai yanzu Allah kadai yasan inda maganar sunan nan zata tsaya sun jawo
musu abun fada a gari. Fitowa tayi daga dakin ta ta tarar da Amirun a tsaye yana niyyar fita dan sunyi
sallama ta shiga ciki.
“Amiru ka nemi Naziru ku tafi tare gidan Yayan naku ba lafiya ba”.

Da”Allah ya kyauta” ya amsa mata ya fita yana dannan kiran wayar Naziru dan shi duk a zatonsa be wuce
a ce rigima ce tsakanin Ma’u da Amirah ba, a hanya ya dauki Naziru daya maze kamar besan me yake
faruwa ba, gama wayarsu da Bashir kenan ya kirashi da wani layi yace masa duk me za’ayi karya kuskura
ya bude gidan nan qasa da qarfe goma na dare yanzu kuwa har tara ta gota dan haka ya qara musu awa
daya se sha biyu ze bude su kuwa.

Kamar wata boarding school ranar hutu haka suka tarar da qofar gidan cike da motoci, yawanci mazajen
wadanda Allah ya taimakesu suka tambaya kafin suka fito ne an kuma san inda suka tafi da sukaji shiru
suka biyi sahunsu se wadanda yan uwansu suka kira su dauke su.

“Kai lafiya kuwa gidan meyake faruwa haka” Amiru ya fada se Naziru ya marairaice kamar na Allah yace

“Yanda ka gansu yaya nima haka na gani, mu qarasa mugani Allah yasa dai lafiya. Bakin get suka qarasa
inda wasu suke qoqarin yanke kwado amma kamar na tsafi yaqi yankuwa wasu daga gefe kuma suna
musu magana akan su bari, ta yaya zasu budewa mutum gida bada izininsa ba duk abinda yake ya dawo
su tabbata yana kansu.

“Wai meyake faruwa haka ne” Amiru ya tambayi masu yanke kwado dan shi tunaninsa ya tafi kodai
gobara ko wani babban Al’amari ne kuma yake faruwa amma kuma hmga kwado ta waje ga kuma
kururuwar mata suna jiyowa daga ciki suna ihun a taimaka musu.

“Kagane Alhaji nima bansan me yake faruwa ba gaskiya Beb dita ce ta kirani tace nazo na dauketa a
gidan nan tazo suna daman ni na kawota dazu se kuma tace na taho da me yankan kwado idan zan zo
kaji iya abinda na sani nidai” shugaban masu kiciniya da kwado ya fada.

Se Amiru ya kalle shi cikin masifa ce“wannan wane irin rashin hankali ne, meye a cikin gidan da har zaku
zo ku budewa mutum ba tareda izininsa kona wanin sa ba idan wani abun nema ai se ku fara neman
izinin me gidan tukunna”.

“Megida ka ganmu nan dukka jiran a bude gidannan muke takamaimai babu wanda zeje maka yasan me
yake faruwa dayawan mu munji shiru ne matan mu basu dawo ba muka biyo sawu wasu kuma kiransu
sukayi a waya suzo su dauke su kaji yanda abin yake” wani mutum ya sake fada, se Amirun ya zaro
wayarsa bayan yacewa Me Yankan ya tsaya ya dannawa Bashir kira cikin Sa’a kuwa ta shiga.

Basu ko gaisa ba Bashir da yasan kiran ko na menene yace masa

“Ni na saka Naziru ya kulle gidan kuma wallahi duk wanda ya budemun gida kafin sha biyu na dare se
nayi sharia dashi” qit ya kashe wayarsa. Se Amirun ya juya yana kallon Naziru daya sha kunu

“Bani key din Idan yaso se yayi shari’ar dani” ya fada fuska babu wasa.

“Amma yaya kasan dai ni laifina ze gani ai kuma...”

“Zaka bani ko bazaka bani ba, daman kasanabinda yake faruwa muka taho amma baka gayamun ba
kayita biye masa kunawa mutane shirme. In ba haka ba matan auran zaku kulle har se sha biyun dare
saboda shirme” fada sosai Amiru ya rufe Naziru dashi, wayarsa da ta shiga qara ce ta katse shi ya daga
Ummi ce cikin kuka take gaya masa halin da ake ciki dan a zatonta yana Katsina shiyasa tun tuni bata
kirashi ba.

“Tundazu ina bakin Get din na rasa ta inda zan fita na kai yarinyar Asibiti Yaya tsoro nakeji karta mutu a
hannuna” ta fada cikin kuka. Nan da nan hankali sa ya qara tashi, Naziru da yake kusa dashi duk yaji me
take fada tun kafin ma ya masa magana ya zaro key ya bude gidan ba tareda ya saurari Mazan da sukayo
masa caaa akan daman shi ya kulle amma ya barsu suna shan sanyi a tsaye.

Yana bude qofar da Ummi yaci karo da azama ya karbi Babyn suka juya shida Amirun tabi bayansu suka
shiga mota kafin Mata suka fara tseren fitowa kamar an sako kaji daga keji wata dankwali a hannu wata
da takalmi qafa daya babu dai me cikakkiyar nutsuwa a cikinsu kowa tayi ta kanta. Suna dai kam da yawa
sunce ko su suka haihu sun yafe bare a sake gayyatarsu suje.

Cikin qasa da minti Goma sha biyar gida ya rage Me jego da Addah da Inna Gaji se wasu dangin su Addah
da basu fi biyar ba ga Hajia Mariya data sha goyo Aljanar ta tafi har sannan shame shame bata farfado
daga Iskokan data hau ba.
Inna Gaji da ta rakube a lungu ce ta fito tana cewa “Allah na tuna Allah karka kuma hukuntani da irin
wannan bala’i na tuba wallahi bazan sake zuwa taron suna ba” babu wanda ya kukata se ajiyar zuciya
suke saukewa, dakyar Hajia Hassana ta numfasa tace

“To Fatu se a san yanda zaayi da Mariya a kaita gida dan kinsan duk sanda tayi irin haka seta kwashi
kwana biyu ko uku bata farfado ta dawo daidai ba nidai wannan suna naku ya shiga tarihi wallahi kar
Allah ya sake maimaita mana...”

Jiniyar Yan Sandan data karade gidan ta sakata yin shiru, toh fa wane bala’in ne kuma ya tunkaro???

WATA KISHIYAR

(ALKAHIRI CE KO SHARRI)

Na Maryamah_Mrs AM

(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)

Page 20

A kofar gida Alhaji Kabiru Dangaske ya faka motarsa data yan sandan dake tare dashi. Kofar gidan
wayam kamar anyi ruwa an dauke kai bazakace gidan Engineer Bashir ne daka kwashi uwar Sabada dazu
ba dan tuni ko wacce ta kama gabanta dan dare ya farayi musamman gashi garin sanyi daman. Mata
biyu yan sanda doguwa da gajeriya da suka zo dasu ne suka shiga gidan dan qofar a bude take.

Mamaki ne ya kamasu tsakar gidan ga kujeru Birjik wasu ma sun karye kamar wanda akayi wasan dambe
a gurin ko ina dai kacakaca daidai da kayan DJ fa nan sukabarsu tunda suka samu hanya suka fece to ana
ta kai wayake ta wasu Kayan kida 😂😂.

“Naga part biyu ne ina zamu shiga” gajeriyar ciki tayi tambayar
“Nima haka na gani mu koma gurinsu muji ina tracker ta tsaya” dayar ta bata amsa suka juya inda
ragowar tawagarsu suke.

“Oga mun shiga amma gidan part biyu ne wanne guri matar take?” Yar doguwar ta fada.

“Inaga ku shiga tare kawai bana son bata lokaci nifa” Wani Dan baqi tsamurmurin mutum dayasa uwar
babbar rigar shadda Getzner se maiqo take daga gani shine Alhaji Kabiru Dangaske ya fada.

“Ai baze yuwu ba mu shiga gidan matan aure ba Alhaji sedai su matan da dai zamu samu ayi mana
sallama da me gidan ne idan ya bada izini se mu shiga kuma kaga layin babu kowa, ku je na daga hannun
hagu dai direction din yake nunawa”.

Komawa sukayi kai tsaye kuwa suka nufi part din Amirah dan shine a hannun hagu din suka tsaya abakin
qofa sukayi knocking.

Bugun da suka jiyo anayi ya qara hargitsa musu ciki dan daman tunda suka jiyo jiniya kowa tasha jinin
jikinta, Inna Gaji kuwa daman kuka ta saka tana tambayar wai wane tsautsayi nema ya tsayar dasu ne a
gidan bayan wannan uban bala’in da aka sha yanzu idan wani abun nefa yazo ya sake rutsa dasu ta tafi
ta kulle qofa ilai kuwa gashi ana bugu.

Hajia Hassana ce tayi qarfin halin tambayar waye jin muryar mata ta dan sauqaqa musu tsoron har taje
ta bude qofar sedai ganin mata da uniform yasakata ja da baya tana karanto wa’innahu sulaimanu dan
itafa duk tashin hankali ayi shi amma aduniya tana tsoron Allah tana tsoron hukuma.

Tsakiyar palour suka tsaya suna qarewa palour da akayi wa wada wada kallo,

“Amm muna neman Hajia Mariya ne” yar gajerar ta fada tana qara tsuke fuska ganin yanda duk suka
zuba musu ido ai kuwa a tare suka nuna musu Mariya dake kwance shame shame tana bacci”.

“Meye haka ku tashe ta mana tana kwance cikin wannan tarkacen wai meya faru haka a gidan ne?”
Doguwar ta fada kafin ma su amsata Gajetiyar ta katseta da cewa “Ba wannan ya kawo mu ba muyi aikin
mu kawai” ta qarasa inda Hajia Mariya take kwance ta shiga tashinta amma shiru bata motsa ba.
Dagowa tayi ta kalli su Addah da sukayi tsilli tsilli a gurin tace “Nauyin baccine da ita haka?”

“Ranki ya dade yanzu ta sauka daga iskokai ne wani lefin tayi ake neman ta station?” Hajia Hassana ta
tambaya. Ba tareda officer ta amsa mata ba ta juya tana cewa dayar “ina zuwa” ta fita.

A qofar gidan tayi musu bayanin abinda aka fada musu, Alhaji Dangaske ya hau kumfar baki shifa a shiga
a dakkota kawai haka takeyi duk sanda ta aikata wani abu seta hau iskokai To wallahi wannan karon ko
bulukiya t hau se dai a kulle su ita da Aljanun nata.

Inspecta da suke tarene yace taje tayi musu sallama da me gidan ta koma minti kadan ta dawo tace baya
nan.

“Wato ni za’ayiwa wasan kwaikwayo kuna tsaye kuma Naga alamar bazakuyi abinda ya dace ba ni bari
na shiga dakaina na fito da ita dan wallahi wannan karon Mariya bata isa ba, ta saba salwantar mun da
qananan abubuwa ko nata tace an sace to wannan karon bazan dauka ba ina gani ta sabautamun
miliyan Ashirin a sama ba taci bulus seta biyani ko mota ta ko kudina fita kuma ba izinina da takeyi taje
ita da Allah dan na gaji”. Ya tattare riga ya doshi Gate inspecta na tsayar dashi amma yaqi.

Yana zura qafarsa Amiru na faka mota Suka fito da sauri ganin yan sanda, da sauri Naziru ya qaraso yana
tambayarsu lafiya se Alhaji Kabiru ya dakata ya yo baya yana cewa

“Yawwa Samari gidan kune ko? To shiga ka fitomun da Mariya qawar Fatu data zo suna gidannan ka
gayamata wallahi idan bata fito ba tunda wadannan dana zo dasu basu da amfani mopol zanje na dakko
ai tasan halina”.

Amiru ne ya qaraso gurin shima Ummi daman wucewarta tayi bata ko kallesu ba tayi cikin gida. A taqaice
Naziru yayiwa Amiru bayanin abinda ya fahimta cikeda takaici Amirun yacewa Alhaji Kabiru da Inpectta
su biyo shi dan abin nasu Addah ya kaishi maqura.

Yanzu haka Iman nacan a NICU sun barota wanda dakyar likitan ya karbeta yace tunda uwarta bata san
ciwon kanta ba subarta kawai su koma gida idan ta mutu Allah yasa qarshen wahalar da zata sha kenan
dan shidai be taba haduwa da Uwa da Ya marasa tunani irin Addah da Amirah ba, dakyar suka roqeshi
suka karbeta yanzu dai sun baro an jona mata oxygen da sauran tarkacen wayoyi sedai su bita da
Addu’ar samun lafiya dan su da kansu sun cire rai da yarinyar.

Dirar mikiya sukayiwa Palour Amirah, Hajia Mariya da farfadowarta kenan tayi arangama da Alhaji
Kabiru ai take qirjinta ya bada daram dam.

“Gasunan ku duba wadda kuke nema ku tafi dare yayi ya kamata a rufe gida” Amiru ya fada yana qara
hade rai. Ba bata lokaci Matan yan sanda sukayi ram da Mariya suka tisa qeyarta akayi waje Alhaji Kabiru
na zuba tijara se muce Allah ya bada yanda za’ayi a biya Kabiru kudin motarsa

suma basu tsaya ba suka fita, a qofar Asma’u ya tsaya ya kira Rahma da harta fara bacci ta fito suka tafi
lokacin sha biyu harta gota, a gidan suka bar Naziru ya kwana saboda gudun abunda ka iya faruwa kuma,
seda ya duba ko ina kafin ya kulle gidan ya kwanta a dakin Aliyu.

Su Hajia Addah dai kamar masu kwanan keso haka suga safiya ido biyu kowa da abinda ya dameta
Asubar fari kuwa wadanda suka kwana suka dade akabar Addah da Amirah se Ummi da itama tace gida
zata tafi anjima bazata iya wannan masifa ba kafin takwas na safe kuwa se su biyu kawai ga uban barnar
da akayi a dakin sun ma rasa ta ina zasu fara.

Dakin Bashir Amirah ta nufa da niyyar tayi wanka saboda bala’in tsamin da jikinta yai mata kafin su san
abinyi sedai ta tarar da qofar a rufe se a sannan ta tuna da Anty Aisha ta bawa key jiya kuma ita bata ma
sake ganinta ba gashi babu waya bare ta kirata dole haka ta shiga dakinta ta binciko inda ta boye key din
toilet data rufe dan kar a bata cikin Sa’a sega na Dakin Bashir a gurin da alama anan ta boye mata.

Da murnarta ta dauki key din ta fita, Addah na zaune akan kujera ta rafka uban tagumi abin duniya ya
taru ya mata yawa dare daya harta zabge tsabar Tashin Hankali yanzun ma tayi zurfi a tunanin yanda
zasuyi su gyara gurin kafin azo tunanin neman kudin da za’a biya bashin da suka karbo bata maji fitowar
Amirah ba se ihun salatinta data jiyo a dakin Bashir ba shiri ta miqe ta bita.

“Na shiga uku Addah shikenan sun kashe ni wallahi Yaya Inaga yanka ni ne kuma kawai bazeyi ba”
Amirah ta fada hannu aka tuni idonta ya fara tsiyayar da hawaye lokacin data ci karo da murfin
Wardrobe din Bashir da aka fashe ga kan Mirrow dinsa wayam babu ko kwalli suma an kwashe wai iya
abunda idonta ya gani kenan Allah kadai yasan dame dame aka dauka kuma.
Ita kanta Addah seda hankali ta ya qara tashi dan duk a zatonsu tunda qofar na kulle bala’in be taba can
ba basusan ta nan Al’amuran suka fara sauka bama 😂

“Dallah can ki mana shiru aikin gama dai ya riga ya gama duk ma abinda za’ayi daga baya ne me afkuwa
ta afku ni dai yanzu ciro sarqar nan ki gani mu Adana su kafin suma bala’in ya dirar musu nidai wannan
Ya dakika haifa kamar yar Allah bani ta jefa mu a masifa (babu ruwan Iman ku dai kuka jefa kanku uku ah
to 😚😚).

Wata sabuwa inji yan caca ai seda Amirah ta shafa wuyanta taji wayam sannan ta ankare babu wannan
sarqa dama babu batun awarwaro tun tuni su ta ankare da sun zube amma a sannan bata su takeyi ba,
yanda take rarraba ido ne yasa Addah a fusace cewa “bazaki ciro bane kike tsareni da ido ko kuma
daman ta kice” ta wara idonta akan Amiran.

“Shikenan ashe ba Mariya kadai ce take da rabon zuwa Birsin ba harda ni wayyo Allah na na shiga uku na
lalace wannan wane irin bala’i ne suke bibiyata sahu sahu ni fatu?” Kuka riris Addah takeyi, sarqar da
hayota tayi dakyar Hajiya Inna Qawarta tayi mata hanyarta a gurin wata qawarta.

Seda ta bada dubu dari kudin Haya sannan ta bata takaddun gidanta dashi kadaine kadarar datayi mata
saura a yanzu akan idan wani abu ya samu sarqarta sedai a siyar ta cire kudinta ta bata chanji to a qalla
da sarqar da abin hannu sun kai na kusan miliyan biyu gashi babu ko daya se warin dan kunne daya ne a
kunnen Amiran to ita kuwa yau ta shiga ina taga haske wannan Asara kan asara babu biyan buqata?

Rasa me bawa wani haquri akayi cikinsu ita Amirah tana kukan haduwarsu da Bashir ita Addah tana na
sarqa seda suka gaji dan kansu sannan sukayi shiru kowa tayi wanka suka shiga gyaran guri kafin kuma
su san abinyi a gaba. Tsakar gida suka watso sharar Addah ta fita ta samo yara suka shiga sharar tsakar
gida aka tattare kujeru masu lafiya aka ware karyayyu gefe suma kafin masu su suzo ayi lissafi haka suka
tattaro kwanuka da kulolin abinci suka bayar yaran suka wanke komai bayan yaran sun gama ta biyasu
suka koma ciki sukayi zugun zugun.

Babu wanda yayi tunanin zuwa duba halin da Iman take ciki a cikinsu tunda dai Ummi ta gaya musu tana
Asibiti shikenan daman ko wancan kwanciyar da tayi bayan an sallamota ba kullum take zuwa ba, da aka
fara bata abincine taje zuwa tayi pumping Nonon da za’a bata daga baya ma a gida takeyi ta zuba a
Container da suke bata akai shikenan. Seda sukaji Yunwa na neman hallaka su suka nemi abinci suka ci
suka ci gaba da zaman jiran tsammani kuma.

A bangaren Bashir kuwa Tun a daren Dr Ishaq ya kira yana zuba masa ruwan masifa kamar shine Amiran,
bayan sun gama ya kira Naziru ya gaya masa yanda akayi harda qarin maggi da gishiri abinda ya qara
tunzura zuciyar Bashir din kenan ya shiga kiran wayar Amirah amma Allah ya taimaketa wandaya sace ya
kashe dan kuwa daya sameta a waya Allah kadai yasan yanda zasu kwashe a daren, Ganin be sameta
seya maida akalar kiran kan Asma’u.

Tana nade akan gadonta bayan ta gama shirin bacci har sannan Bata bar mamakin abubuwan da suka
faru ba yau a gidan nasu kiransa ya shigo. Daga yanda ya amsa sallamarta tasan ba qalau ba se tayi shiru
tana jin yanda yake magana ta inda yake shiga bata nan yake fita ba masifa yake mata akan me yasa tun
farko bata gaya masa zasuyi taron sunan ba.

Galala ta saki baki tana sauraronsa ganin fa ba shiru zeyi ba yasa ta katse shi da cewa “Dakata Malam
wai ko baka san wa kakira bane To Asma’u ce ba Amirah ba”.

Cike da masifa yace “oh maganar banza zaki gayamun kenan ce miki nayi bansan wanda na kira ba ai
koma mene laifinki ne tunda kina gaba da ita ya kamata ki nuna mata abinda yake daidai da ba daidai ba
data tace zatayi taron seki hanata tunda kinsan bana so”.

“Ashema ni ce gaba da ita, meye darin gami na da ita da zatayi abu na hanata ko an saka ni a ciki
ballantana kuma nima gani nayi anayi. Kuma da kake maganar daidai ko rashin sa qarewarta naga da sa
hannun yan uwanku tayi komai danginku kaf babu wanda bezo gurin ba su a cikinsu babu wanda yasan
daidai kenan, kuma naga ai ita da uwarta suka shirya kamai se kuma kazo kana gayamun wani qabali da
ba’adi dan Allah in baka da abin fada ni bacci zanyi kabarni inji da hayaniyar da suka jazamana a gida har
sha biyu sannan muka samu salama Allah yasa kar cikin dare kuma wata sabuwa ta taso”.

Jin da yayi ta fitittike masa yasan halin Ma’u sarai itama ba baya bace seya sassauta muryarsa yana cewa
“Kina nufin dangina ne basu san daidai ba kenan, kuma da kikaga za’ayi ai seki kirani ko a wayane tun da
safen ki gayamun ni na tsaqatar amma fa kalli duk abinda akayi se a gari naji ke baki kirani da kanki kin
gaya mun ba”.

“Nidai ai kasan ban iya sa ido da munafunci ba bare kace duk abinda wata takeyi sena kwasa na gaya
maka, bayan haka tsakanin ku can nasan koda yardar ka suke abunsu? Yanzu dai aikin gama yarigada ya
gama mudai ka tiro azo a chanza mana keys din gidan nan kar muje wani ya sata shima muna zaman mu
a ringa diro mana da daddare tunda yau gungun barayi aka hada a gidan”.

Dagaske dai yaga alama Asma’u neman sa take ta magana tunda gashi shida ya kira yayi fada amma ta
samu se gasa masa maganganu takeyi dan haka yace mata

“Shikenan, da safe ki daure ki leqa Asibiti kiga jikin Iman koda wasa karki bari ta sake taba mun yarinya..”

“Nan fa daya, zuwa dubata zanje da sassafe ma kuwa insha Allah amma batun kar uwarta ko wasu su
tabata be taso ba ka nemi wani ka saka wannan aikin amma bani ba. Ba abinda yai mun zafi da lamarinsu
ka sani” Asma’u tayi saurin katse shi. Se da yaja kwafa sannan yace mata seda safe suka ajiye wayar ta
gyara kwanciya tana cewa

“Haka kawai can ta qare muku kunfi kusa ni ai yar kallo ce irin haka kuma yanzu aka fara duk abinda
ba’ayi shi dan Allah ba ai qarshen sa kuwa dana sani ne fal, Allah sarki sun jawa yarinya bata ji ba bata
gani ba zanje na ganota da safe insha Allah badan halinsa ba” tana motar taja bargo tayi kwanciyarta
bacci ya dauketa.

Bashir kuwa yanda yaga rana haka yaga dare, ina ace gobe Friday ce ba Alhamis ba amma yanzu dole ya
jira se goben ya tafi Gombe kafim nan yasan matakin da ze dauka akan daga Addan har Amiran.

Su Addah dai wunin Alhamis ziri cikin rashin nutsuwa sukayishi, masu kujeru sunzo sun kwashe akayi
lissafi kusan dubu Ashirin na wadanda aka lalata a drawer dakin Bashir Amirah ta lalubo aka biya DJ ma
yazo ya kwashe sifikunsa yanzu ya rage me sarqa da kuma masu qananan bashi da basu biyo sahu ba.
Har dare suna zaune suna saqawa da kwancewa babu wanda ya sake zuwar musu ko Dada da tayi zaton
zatazo shiru har dare basu ganta ba gashi babu waya da alama ma su kafai suka wuni a gidan dan tun
Azahar sunji fitar Ma’u itama bata leqa ko jaje tayi musu ba.
Amirah shirun Bashir yafi daga mata hankali koda yake ta ina ze kirata ma tadai tabbatar gobe Juma’a ze
zo Gombe Addua dai tayi tana kan yi ta Allah ya rufe bakinsa akan wannan Abu to bamu sani ba kota
karbu Allah dai ya kaimu juma’ar mu gani.

Washe gari kuwa qarfe hudu yana Gombe, kai tsaye Asibiti ya nufa a can ya tarar da Asma’u data sake
komawa dan halin data ga yarinyar jiya ya tsaya mata arai matuqa. Ganin da Bashir yayi wa Baby Iman ya
sanyaya masa jiki dan ya ma cire rai da yarinyar. Wani kalan numfashin wahala takeyi idan ta jashi kamar
qirjinta ze burma, sanyi ya mugun shiga jikinta ga rashin kaita da wuri da sukayi.

A hanya Asma’u ce tayi ta qarfafa masa guiwa ganin yanda yayi shiru damuwa qarara a fuskarsa, tasan
Bashir yana son yaya amma wannan yarinyar ma dai daban take a zuciyarsa taga alama to amma ya zeyi
abinda Allah ya qaddara dole ya faru. Suna isa gida ta shige part dinta shi kuma ya nufi na Amirah da
tundaga qofa yake jiya hargagin muryoyin dabe tantance kona waye ba.

Kallo daya yayi musu Addah, Amirah se mata biyu dabesan ko su waye ba ya dauke kansa kai tsaye ya
wuce dakinsa yana jin Addah na cewa

Alhamdulillahi ga me gidan ma yazo amma be tsaya ba, to ya tsaya yayi musu me tsaf dai ze iya hada su
duk hudun ya nada musu na jaki ko ze rage wani abu daga baqin cikin da yake ji a cikin zuciyarsa.

Murmushin takaici ya saki lokacin da idonsa ya sauka kan aika aikar da akayiwa dakin, kansa ya girgiza
kawai ya juya ya fito daidai daya daga cikin matan tana cewa

“Wallahi daga nan se kotu zan wuce dan bazan tsaya ma yansanda su batamun lokaci ba, ni zaki yaudara
ki bani takaddun bogi? Seda na nemi Dillalai muka je suka ga gidan ayi masa kudi muji idan chanji zan
baki ko ciko zaki mun aka ce na bada takaddu suna dubawa sukace mun na bogi ne da an riga an siyar
aka gano ni se anyi qarata to wallahi kafin ki kaini prison ke zaki fara zuwa.

Ni daman jikina seda ya bani tun zuwanku amma Innah tace mun babu matsala to kuwa ku zaku dauki
Asara ki riqe warin dan kunnen ki siyar kya samu na daukar lawyer dan nidai kudina cis na sani gobe ma
ku sake daukowa kanku abinda yafi qarfin ku kuce se kunyi”.
Jin fitowarsa tasa Addah tun kuda Amirah tayi qasa da murya tace “ kiroqeshi yai mata magana in ba
haka ba mun shiga uku wallahi banida sauran wani abu kuma”.

Bata so ba amma ya zatayi seta tare gaban sa ta fashe masa da kukan da inda haka kawai ne kowa
tayiwa shi seya tausaya mata dan kuka ne da kana jinsa kasan meyinsa yana cikin tashin hankali ne ta
shiga cewa

“Dan girman Allah yaya kasa baki matar nan tayi haquri ta bamu lokaci za’a biyata.....”

“Dauuu” ya kwasheta da marin da kaf seda suka rufe fuska dan ji sukayi kamar su akayiwa bata dawo
daga gigitar ba ya sake sauke mata wani a daya bangaren kafin ya hankadata gefen kafin ya nunata yace

“Na rantse da Allah idan na sake shigowa na tarar dake a gidan nan sena illa taki, ya fice yana huci
tabbas kuma idan ya sake tarar da ita se ya mata dukan mutuwa yau a gidan nan.

WATA KISHIYAR

(ALKAHIRI CE KO SHARRI)

Na Maryamah_Mrs AM

(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah

Page 21

Ihu Amirah ta fasa na zafi biyu ga mari ga maganar tafiya gida, me yake nufi badai sakin ta Bashir zeyi
ba? Wannan tunani yasa bata san sanda ta bishi da gudun bala’i ba tana kiran sunan sa lokacin harya kai
kan Balcony Ma’u ze shiga.
“Na rantse da Allah kika qaraso nan Amirah sena karyaki, karayar da babu me iya gyara miki ita kuma
karki bari na fito kina cikin gidan nan idan kuma so kike ki qure ni shikenan” ba Amirah da yai wa
maganar ba hatta da Ma’u dake cikin palour seda ta tsorata, yanda yai maganar cikin tsananin masifa
idanunsa sun kada sunyi jajir harwata qwallar bala’i ce ta taru a cikin su yasa ta kasa tunkararsa harya
haye sama yana hada stair case bibbiyu.

Amirah kuwa Kamar wanda ya sakawa pause haka ta bishi da kallo kafin ta juya zoqai zoqai ta koma part
dinta tana toshe baki gudun kar ma sautin kukan ta ya fito ya dawo ya tattaka dan tayi bala’in tsorata da
hanayinsa . A qofa suka hade dasu Hajia me gwal data bi Amiran da kallo kafin ta ja uban tsaki tana
kallon Amiran tace “kadan ma kuka gani Allah yasa shima ba wata satar aka qunduma masa a daki ba,
kinga Hajia muje nidai na gama magana in sammaci ya iso ma hadu a kotu kawai” ta yi waje abunta tana
ci gaba da yada musu da magana.

“Toh Fatu Allah fidda A’i daga rogo mun tafi” Hajiya Nuratu qawar Addah datayi musu hanyar sarqa ta
fada dan ita kasa magana tayi ma tunda sukazo se ta juya tabi bayan Me gwal itama. Se Addah ta kalli
Amirah data zube a qasa tana kecewa da sabon kuka.

“Kukan me zaki zauna kiyi, shiga mu hada abinda zamu dauka muje kawai dan in kin zauna nasan ba
mutunchi ne dashi ba ze miki abinda ya fada ne toh gara mu tafi gaban uwarsa duk abinda za’ayi akan
idonta”. Dakin Amiran Addah ta shige tana sababi ta fara tattara komatsanta zuciyarta ko kamar tayi
bindiga wannan bala’i har ina?

Har Addah ta gama ta yafo gyalenta Amirah na zaune tana Kukan da bashi da Amfani.

“Au kina zaune ko to shikenan ni kinga tafiyata se kiyi tayi idan kuka ze miki magani” Addan ta fada tana
nufar qofa, se Amirah tayi saurin riqota cikin kuka tace

“Addah idan na tafi ina zani? Kinsan dai idan na biki gida qila sena gwammace hukuncin Yaya akan na
Baba to ina zanje”

“Gidan uban sa mana, ni daman nace ki bini gida ne gaban Nafi zaki je ki zauna duk ma wacce za’ayi ayi
da wanne zanji idan kin bini gidan da nawa tashin hankalin koda Masifar Ubanki”.
Daki Amiran ta wuce ta shiga hada kaya a akwati tana kuka amma taji dama daman cewa gurin Dada
zata tafi dan dai ko hauka tayi bazata je gidan su da sunan itace me laifi ba yanda Babansu yake a zuciye
da lamarinta harda Addan ma tasan qiris yake jira wallahi ya samu dama akansu yaci musu mutunchi.

Tare suka fice kowacce da jaka tana Ja Addah na gaba taba ta sababi ko tausayin Amiran da haryanzu
jikinta bawai ya warke bane bataji ba bare ta karbar mata uwar akwatin da take ja ita dai masifarta
kawai take, seda suka ci tafiya har bakin titi kafin suka samu Napep da ze kaisu gidan su Bashir.

A qofar gidan Dada me Napep ya ajiye su, Amirah da tunda suka taho bata dena kukan nan ba kasa
daukar jakarta tayi se me Napep din ne ya shigar mata da ita har tsakar gidansu Bashir din.

Alhaji Ahmadu na zaune a tsakar gidan akan Kekensa Naziru da physiotherapist da yake dubashi suna
tsaye a kansa bayan sun dorashi akan keken dan gama Exercise dinsa kenan suka shiga Addah na Masifa
Amirah na kuka gaba daya suka juya suna kallonsu, wuce su Addah tayi bata ko kalli barin da suke ba
itama Amiran ta rufa mata baya sallamar me Napep ce ta saka su Nazirun juyawa daga kallon su Addah.

Akwatin Amirah ya dire musu ya kalli Naziru yana cewa “yi musu magana su bani kudina na wuce dan
Allah”

“Nawane kudin?” Naziru ya tambaye, bayan ya fada masa ya zaro daga aljihunsa ya bashi.

Me Napep na fita shima Physiotherapist din yayi musu sallama ya tafi dan ya gama aikinsa, kama keken
Naziru yayi da niyyar maidashi dakinsa ya dakatar dashi da cewa

“Kaini daki Naziru” Alhaji Amadu ya fada dukda yaso ya zauna a tsakar gidan yasha iska amma zuwan
Fatu baze barshi ba, yanzu haka yana jiyo bambaminta daga palour Dadan amma baze kula suba dama
ya fada musu ai ayi dai su gani idan Tusa zata hura wuta kuma gashi da alama dai tun ba’aje ko ina ba da
sun fara karbar sakamakon abinda suka aikata.

A palour Dada kuwa Addah ce take sababi kamar zata hadiye harshenta,

“Daga abin arziqi se ya zama na tsiya, yar nan naga kuma jikar kuce yanzu ta girma ace cikin yan uwanta
kaf itace ba’ayiwa taron suna ba ai setace ba’a qaunarta. Ni kinga tafiyata gata nan ku qarata nima inje
naji da masifar nawa mijin dan nasan su Binta munafukai sun kaimasa rahoto tun jiya” Addan ta fada
tana kwasar jakarta data watsar tun shigowarsu, bata saurari Dada dake mata magana ba ta fice abinta
ranta tana qissima duk abun Bashir be isa yayi a gaban Dadan ba tasan zata ta ka masa burki.

Bayan Fitar Addahne Dada ta mayar da hankalinta kan Amirah dake durqushe har sannan tana kuka,

“Amirah yanzu kina ganin biyewa Addah da kike kuna aikata duk abinda kuka ga dama daidai ne ko? Ke
bazakiyi hankaliki zauna a gidan auranki lafiya ba se ki ringa biye mata kina saba umarnin mijinki to ki
sani dai shi Allah babu ruwan sa, idan ya tashi ke kadai ze kama da laifin saba umarnin miji banda Addah
tun wuri idan zakiyiwa kanki fada ki bi hanyar gaskiya kiyi dan nidai babu ruwana da duk wani shirginki
yanzu” tana gama fadan haka ta miqe ta shige dakinta ta bar Amirah na cigaba da share hawaye.

Sosai ranta ya baci da abinda ya faru a gidan Bashir din, ta rasa meyake damun yayarta ta har ji takeyi
daman itace gaba da Addah qilan da ta ringa dorata akan hanya ta dena wadannan abubuwan zubda
mutunchin da take yi amma ya zatayi sedai tayi ta binta da addua kawai.

Wayar Bashir ta kira bayan ta shiga dakin, lokacin yana tsaye kan Asma’u yana zuba mata ruwan tijara
kaman itace Addan ko Amirah. Yanda yake bambamin tasan ransa yakai qololuwar baci yasa bata
tankashi ba ta sunkuyar dakai kawai tana jinsa saboda Bashir Miskiline, ko zeyi rashin mutunchi a ruwan
sanyi yake dafa mutum. Auran Amirah nema taga yana neman ya mayar dashi mafadaci tunda yanzu
yana iya bude baki yai fada idan an masa laifin sabanin da da ko laifi ta masa sedai ya dauki gaba da ita
ko yayi ta gasa mata aya a hannu ta ruwan sanyi yanda ko qararsa ta kaiwa wani baza’a yarda ba dan
babu shaida.

Sau biyu wayar tana qara amma be kula ba se ana ukun ya zarota da niyyar kashewa dan a lokacin
bayajin ze iya magana da kowa sedai ganin suna Dada yasakashi saurin dagawa bayan ya zauna akan
kujera dan Uwa ba wasa ba, a magagin mutuwa ne kadai yakejin baze iya amsa kiranta ba amma inda
yaji ya kuma gani ko halin yaya ne seya amsa idan yaso ya bata uzuri ya kira daga baya.

Gaisheta yayi ta amsa tana karantar bacin rai a cikin muryarsa, kiran da tayi masa ta so ta tambayeshi ne
shiya tura Amirah gida amma yanayinsa yasa ta fasa dan tasan qarshe wani laifin zata jangwalo mata
yace ta kai qarar sa danhaka se tace cikin taushin murya

“Bashari idan babu abinda kakeyi kazo gida yanzu mana ina son magana da kai”
“To Dada gani nan zuwa” ya fada yana miqewa dan daman yana da niyyar zuwan a yanzun yaje ya gaya
mata abinda Addah da Amiran sukayi dukda yasan ta sani amma dai gara yaje da kansa yaji ko harda sa
hannunta a ciki.

“Ku shirya gobe da safe zamu wuce kuma a mota zamu tafi” ya fada yana kallon Asma’u da kanta yake a
sunkuye har sannan kafin ta dago harya kai qofa, kallonsa tayi tana zare ido a fili ta furta “kan bala’i
Gombe to Lagos a mota” miqewa tayi ta bi bayansa da sauri dan baza’ayi wannan gangancin da ita ba,
haka siddan Allah ya rufa musu asiri ya basu yanda zasuyi subi jirgi se yace a mota zasu tafi kamar ma
itace tayi masa laifin kenan aikuwa wallahi bazata sabu ba shidai ya tafi su zasu jira Moday din su tafi
dan daman already sun siyi tickets ta barsu a bude saboda bata san sanda zasu tafi ba.

Ya kunna motar yana qoqarin bude get ta shige ta zauna, tana jin yanda yake kallonta a jikinta amma
taqi daga kai bare su hada ido dan gara aje gaban Dadan itama ta saka baki a wannan al’amari kar goben
tayi ma suzo suna wallahi tallahi. Tafiyar kamar ta kurame harsuka isa gidan Dada, ta rigashi shiga gidan
dan sanda suka isa daidai ana kiran Magriba shi seya tsaya ya daura alwala ya shiga masallaci ita kuma ta
shige gidan.

Amirah na zaune har sannan a palour ta dena kukan dai se ajiyar zuciya take fuskarn nan ta kumbura tayi
jajir abinka da Farar fata ansha kuka. Kallon kallo sukayi da Asma’un kafin ko wacce ta dauke kanta gefe
Ma’u ta nemi kujera ta zauna tana zaro wayarta daga aljihun Diguwar rigar jikinta ta danna Number
qaninta dan karya mayar da yara gida ba kowa da yake suna nan Babban gida tunda safe ta kawo su.

Fitowar Dada da hijabi a hannunta da alama itama alwalar tayo ta kalli Amirah tace “au haryanzu kina
zaune a qasa sanyi na shigarki da danyan jiki se ance ki tashi ko? Kiyita zama jikinki ne ai bana wani ba”
ta fada tana zura hijabinta inda Abun sallarta yake ta nufa se a sannan ta ankare da Asma’un dake zaune
seta sassauta fuskarta tana cewa “Aa Asma’u Yaushe kika shigo”

“Yanzu na shigo Dada ina wuni” Ma’u ta fada tana zamowa daga kan kujerar, seta amsa mata tana cewa

“Ki shiga kiyi sallah bari nima nayi gashi can har an yi raka’a daya” ta tayar da Sallah ita kuma Ma’u ta
miqe ta shiga dakin Fainusa dukda ba sallar zatayi ba seta nemi gefen gado ta zauna tana duba wayarta.
Batafi minti uku ba Amirah ta shigo tana jan akwati, kallo daya tayi mata ta ci gaba da dannan wayarta
ita kuma ta jingine jakar tana dafe gefan kanta dayake sara mata ga wani jiri jirin yunwa dake son kayar
da ita haka ta daddafa ta shige toilet dan wanka take son tayi.

Da ruwan zafi sosai ta gasa jikinta dan yanzu base ance tayi ba tsamin jikin kadai yana sa ta shiga
hankalinta ta gargasa jikin gashi taci sa’a jikinta me kyau ne tuni dinkin ya kame in banda ma kata’in da
take jefa kanta aida ta fi haka warwarewa.

Sanda ta fito har sannan Ma’u na nan ta sake bararrajewa akan gado da alama waya takeyi, a darare ta
ja akwatinta ta ciro duguwar riga da undies ta sake komawa toilet din ta sako kayan ta dauro alwala ta
fito daidai sanda Dada ta leqo tana kiran Asma’u, bayan ta idar tana zaune ita ba lazimi ba tayi zuru akan
sallayar aka bude qofar.

Dadan ce ta sake dawowa, cikin bacin rai tace mata “wai bazaki tashi kije kici abinci ba Amirah ko kin
manta jego kikeyine idan kuma wani kike jira ya kawo miki se ki zauna”.

Yunwa takeji ta gaske dan haka ta miqe salaf salaf ta fito palour inda take jiyo muryar Asma’u da Naziru
da alama hira suke, a tsakiyar palour ta tarar dasu, Asma’u nacin tuwo da miyar kuka shi kuma yana
mata hira, wuce su tayi ta nufi kitchen tana kaiwa daidai qofar Bashir ya shigo da sallama ciki ciki ai se
kawai ta qame a gurin ta kasa gaba ta kasa baya, bata so su hadu ba, a yanda ta tsara in ta shige daki
bazata sake fitowa ba abincinma idan an gaji a ringa binta dashi har seya bar garin gashi yanzu tun ba’aje
ko ina ba sunyi kicibus.

Shi kuwa Bashir bema lura da ita ba ya nemi guri kusada Asma’u ya zauna, Dada ce ta shigo itama daga
Gurin Alhaji tan cewa Naziru yaje Alhajin na kiransa. Kallon Amirah dake tsaye kamar an dasa ta tayi tace

“Ke kuma lafiya kike tsaye kin qi gaba kinqi baya” kidan duma zuciyar Amirah ta shigayi daidai sanda ta
waiwayo idanunta suka hadu dana Bashir, wani mugun kallo ya aika mata dashi daya saka hanyar cikin
ta kadawa bashiri ta shige kitchen din ta fara matsar kwalla.

“Me yarinyar nan takeyi a gidan Dada oh danace ta tafi shine ta taho gidanmu saboda raini ko tam” ya
fada yana sakin qwafa dagani yama rasa me zeyi kawai. Seda Dadan ta zauna tana kallonsa tace
“Dalilin kiran dana maka kenan ai nima ina zaune sukazo ita da Addah sunce kace ta tafi gida”

“Eh nace ta tafi gida Dada wannan yarinyar bata da mutunchi ta raina ni ban isa na bata umarni tabi ba
se abinda ta rayawa kanta, seda na gargadeta nace baza’ayi taron sunan nan ba amma saboda ta nuna
mun ban isa ba taje tayi”

Bakiga dakina irin barnar da akayimun ba iya abinda na gani kenan ma Allah kadai yasan me aka dauka a
ciki tunda ban duba ba, shikansa gidan karkiso kiga yanda suka maidashi. Ga Iman can a Asibiti babu
tabbacin ta tashi sannan saboda ma sun raina mun hankali na dawo na tarar da wata mata ta biyo karbar
bashinta wai ni suke cewa na roqar musu ita tayi haquri. Wallahi Dada Idan yarinyar bata kama gabanta
ba ta bari hannuna ya sauka akanta sena mata dukan mutuwa wallahi....”

“Babu inda zataje kar kuma ka fasa mata dukan mutuwar” Alhaji Amadu da Naziru ya turo akekensa ya
katse wa Bashir Hanzari, se suka juya gaba daya suna kallonsa bayan da Nazirun ya kawo shi tsakiyar
Palour.

Kallon Bashir da yake ta qoqarin hadiye malolon daya tokare masa wuya Alhajin yayi ya girgiza kai kafin
ya Kalli Dada yace “Ina Amiran take kirawo ta nan” Miqewa Dadan tayi ta shiga kitchen suka fito tareda
Amirah dake risgar kuka kamar an ce mata Addah ta mutu ta nemi can gefe ta zube tana ci gaba da
kukanta.

Kallonsu Alhaji Amadu yayi daya bayan daya ya tsaida idonsa akan Asma’u da tunda ya shigo ta tsame
hannunta daga cikin tuwon ta gyara lullubinta, se ya saki wani murmushi da bazaka tantance na mene
ne ba ya kalli Bashir yace

“A lokacin da zaka auri Amirah me nace maka”

Sunkuyar da kai Bashir yayi yana cigaba da komawa da abinda yake taso masa idanunsa sun kada sunyi
jajir,
“Ba magana nake da kai ba” Alhaji Amadu ya katse shi cikin daka tsawa se Bashir din ya dago da sauri
yana kallon mahaifin nasa, kalaman sa suna dawo masa daya da daya a kwakwalwa ranar dayazo yace
masa ze qara aure ze auri Amirah diyar Addah tamkar a yanzu yake fada masa su.

“Sharadi zan kafa maka Bashir, yanda ka dakko auran nan to ka tabbata Babu Yaji har qarshen
rayuwarku. Ina raye ko bana raye idan ka rabu da yarinyar nan ban yafe maka Ba Bashir kaje ku zauna
duk wuya duk dadin da zata zo maka dashi”

“Kace babu Yaji babu saki” Bashir ya fada da kyar kamar me ciwon haqori.

“Madallah, ka tashi ka dauki iyalan ka ku tafi aje ayita haquri, daman shi wanda ya siyi rariya ai yasan
zata zubda ruwa”.

“Asma’u ya gidan ya Mutane nawa dazu sun shigo Ina bacci kafin na yunqura kuma suka fice” Alhajin ya
fada yana maida hankalinsa kan Asma’u. Seta sunkuyar da kanta tana dan murmushi tace “ lafiya lau
Baba suna Babban gida ai yanzu zaka gansu ma tunda na fada musu ina nan”.

“To masha Allah, yaushe zaku koma hutu ya qare ko?”

“Eh Baba daman litinin muka shirya dazu kuma yace wai gobe zamu tafi amma a mota gashi bamu
qarasa shirye shiryen mu ba” Asma’u ta fada tana janye fuskarta gefe dan karma su hada ido da Bashir.

“Wane irin tafiyar mota kuma ana zaune lafiya, ko a zamanin da da muke tafiye tafiyen ai munji jiki bare
ku yanzu da baku saba ba ga yara kuma, kudai jira litinin din dai kubi jirgin safe kamar yanda kuka saba,
Allah yayi muku Albarka yaci gaba da ruqo da hannunku” Baban ya fada suka amsa gaba daya da Amin.

Naziru na zaune kamar ya buga tsalle tsabar yanda da Al’amuran suka masa dadi, yanda aka tilasta
Yayan nasa maida Amirah gida ya mugun masa dadi aransa fadi yake “Allah ya qara ai kadan ma ka gani
in bakayi da gaske ba wataran se sun saka a kulleka kana zamanka da matar rufin asiri ka kwasowa kanka
kaska.
Baban ne ya katse shi yana cewa “zo Naziru ka maidani na kwanta kaji Dare ya farayi” yayi musu sallama
Naziru ya maidashi.

Kamar kurame haka sukayi jugum jugum a gurin, Amirah dai a tsorace take da hukuncin na Baba dan
data bi shi su koma gara ta zauna agidan kai gara ko can gidan su ne ace ta tafi ita kuwa Ma’u ba abinda
ya shalleta masifa ce dai tasan zeyi ya gama tunda dai an rushe zancen mota ai shikenan, shikuwa oga
Bashir har wata zufa yake kamar wanda ya hadiyi kunama.

Makwallaton wuyansa se sama yake yana qasa ya kasa furta komai se “hmmm” kawai. Miqewa yayi
dakyar ya iya ce musu su tashi su tafi ya fice ko sallama be yiwa Dada ba, Asma’u ce ta fara miqewa
tayiwa Dada seda safe tabi bayansa Amirah dai ko motsi ta kasayi.

Kallonta Dada tayi tace “ki tashi ko so kike ki qara wani laifin a gurinsa” ai kamar tana jira ta sake
fashewa Dadan da kuka tana cewa “Dan girman Allah Dada ki roqi Baba Ya barbi yau na kwana a gidan
nan idan sun koma Lagos sena tafi wallahi idan na bishi yau kashe ni ne kawai Yaya bazeyi ba Dada dan
baki san irin abubuwan da nayi masa bane” ta qarasa tana sake rushewa da kuka.

Miqewa Dada tayi tana cewa “koma mene ai ke kika ja gara ki tashi ku tafi dan nima bazaki ja mun wani
fadan a gun Alhaji ba kije kawai ba bu abinda zeyi miki” tayi shigewarta daki ta barta.

Amirah tana kuka tana komai ta hado jakar Naziru ya daukar mata suka fita yana mata dariyar mugunta,
dakyar ta bude bayan motar ta shiga dan tuni Asma’u ta kame a gaba abunta cikin ranta qal da wannan
abubuwa da suke faruwa.

Afuwan qundumemen uzuri ne ya riqeni kwana biyu amma komai ya dawo daidai zaku ci gaba da jina
insha Allah

WATA KISHIYAR

(ALKAHIRI CE KO SHARRI)
Na Maryamah_Mrs AM

(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)

Page 22

Gudu ya ringa fellawa dasu kamar masu barin gari sanda ya tsayar da motar a bakin Get kuwa har qauri
takeyi, a Get din ya watsar dasu yai gaba dan Amirah bata ko samu damar daukar Akwatinta ba Asma’u
ta saka key din hannunta ta bude musu Get suka shiga.

Yanda taga Amiran tana tafe tana layi se ta bata tausayi dan haka ta qarasa ta riqo kafadarta ai kamar
me jiran majingini kawai ta fashe mata da kuka tana cewa”Dan Allah Anty ki bashi haquri, wallahi ba
laifina bane Addah ce kema kin santa ita tace se anyi”.

Asma’u bata tanka ta ba har suka shiga dakin Amiran ta zaunar da ita akan Kujera tana qarewa palour
kallo baki bude saboda mamaki. Duk wani abu daya danganci glass an fasa harda Tv ba’a barta ba daidai
da labulaye duk duk an sauke su qarafunan sun karyo.

Ajiyar zuciya tayi kafin ta Kalli Amirah da har sannan kukan take tace “Kiyi shiru komai zai daidaita Insha
Allah, ina zuwa”.

Part dinta ta koma, Farfesun Tsokar rago ta ciro a freezer ta dumama kafin ta hada Shayi a qaton Mug ta
dora su a kan Try hade da Bread ta dauka ta koma part din Amiran. Bayan ta ajiye su ta sake komawa ta
debo mata tuwon semo da miyar danyar kubewa da tayiwa Bashir bema ci ba ta sake komawa part din
Amiran.

Tana zaune a qasa ta zamo daga kan kujerar riqe da cikinta tana murqususu, da sauri Asma’u ta ajiye try
din ta nufeta tana “lafiya Amirah meya same ki?” Ita dai se juyi take tana malele

kuwa akan Tiles saboda bala’in qullewar da cikin yayi mata.

Dakyar ta nutsu ta kamata ta koma kan kujerar, Shayin ta fara bata a baki tana karba, kurba uku tayi
Amai ya taso mata ko kafin ta miqe tayi shi a Gurin Asma’u na tsaye se sannu take mata. Bowl babba ta
dakko ta debo ruwa a babban kofi da dawo gurin Amiran, ta zuba mata ta kurkure baki da dauraye
fuskarta Ta koma yaraf ta kwanta tana sauke Numfashi.
Abincin ta ajiye mata nan ta shiga ci kuwa dan Aman ya taimaka ya bude mata ciki ita kuma ta dauke
robar ta tafi dakko mopper da packer, Duk Kyankyami irin na Asma’u haka ta daure ta kwashe aman tsaf
ta zuba ruwan omo ta goge Gurin kafin ta sake saka ruwa ta goge tas ta nemi freshener amma bata
samu ba sanda ta gama itama ma Amirah ta cinye farfesun tsaf ta shanye shayin se ajiyar numfashi
takeyi.

“Nagode Anty Allah ya biyaki” ta fada tana sunkuyar da kai, se Asma’u tayi murmushi kawai tace
“bakomai, ki samu kisha magungunan ki se ki kwanta ki huta. Ga ragowar abincin nan koda zaki buqata
anjima Allah ya qara kiyayewa” ta fada tana nufar qofa.

Tashi tayi ta rakata tana sakeyi mata godiya ta kulle qofarta gam ta ciki karma ya dawo kenan ya shigo
bata kwashe kwanukan ba ta haye kan kujera se baccin wuya ya kwashe ta.

Asma’u ma tana komawa part dinta kulle qofar tayi idan Bashir ya dawo da akwai key a hannunsa dan
sunyi waya yaran sunce a can zasu kwana ma bazasu dawo ba. Sama ta wuce ta shiga wanka, seda ta
gyara jikinta tsaf lokacin har sha daya tayi ganin Bashir be shigo ba yasa tayi kwanciyarta kawai dan
daman dai yau koya dawo tasan bazasu kwashe qalau ba.

Bashir

Yana sauke su kai tsaye tsohuwar unguwar da suka taso ya wuce gurin Bala, Abokinsa ne tun na yarinta
tare suka tashi a unguwarsu su Hudu Bashir, Marigayi Aliyu, Bala da Sadiq yayan Asma’u su hudun
Abokaine na rai da rai tun daga Primary ajinsu daya har jami’a sannan suka rabu kowa ya karanci course
dinsa daban.

A qofar gida ya tarar da Bala da yan majalisar sa kamar yanda yayi tunani, kashe motar yayi tareda jan
kujerar baya sosai ya tokare qafarsa da stiyarin motar , zafafan numfashi yake saukewa a jere a jere
zuciyarsa jinta yake tamkar ana soyata a mangyada.

Me yasa meye dalili daya kasa samun nutsuwa tunda ya auri yarinyar nan? A shekara biyu an tafi ta uku
da qara auransa be sakeyin sati daya na cikakken farinciki ba wai dama haka qarin auran yake ko kuma
shine beyi dace ba.
“Me yasa baka nemi wata ba me yasa se Amirah zaka aura Bashir? Yau da ace wata daban ka aura
wallahi ko mata uku ka auro lokaci daya bazan damu kamar wannan auran da kayi ba amma shikenan
haquri ko nayi haquri. Idan dan Allah kayi Bashir Allah ya bamu zaman lafiya ya bani ikon cinye jarabawar
da yayi mun, idan kuma kayi ne dan kaci mutuncina to Allah baze bari na tozarta ba ba kuma zaka samu
nutsuwar da kake iqirarin samu ba” kalaman Ma’u na qarshe wanda daga su bata sake tayar masa da
hankali ko wata magana ba sanda ya auri Amirah.

To wai alhakin nasa ne ko nawa shidai Allah ya sani beyi auran nan da wata manufa ba yayi ne kawai dan
yana ra’ayi bakuma dan ya tozarta Matarsa ba kamar yanda take tunani amma gashi nan shi yake karbar
sakamakon sa da Hannun hagu wai ta ina toh ya kuskure?”

Glass din window da aka kwankwasa ya dawo dashi daga tunanin daya tafi, se ya dago yana gyara
zamansa. Seda ya saita yanayinsa sannan ya bude qofar ya ziro dogayen qafafunsa yana sake kokawa da
dacin ransa kafin ya fito gaba daya.

“Kaga Na Ma’u Angon Amirah uban Aliyu ko dubu ta taru” Bala daya gaji da jiran fitowar Bashir din ya zo
ya kwankwasa masa glass ya fada cikin sigar tsokana sedai yana yin fuskar Bashir din tasa ya gintse
maganar tasa.

“Lafiya kuwa Engineer kaga idanunka” Balan ya sake fada, se Bashir yaja tsakin da ya aure shi ya bude
murfin motar ya koma ciki yana cewa Balan ya zagayo. Cikin zaquwa Bala ya shiga motar dason jin meya
faru, dan Bala irin mutanen nan ne masu son bin kwakwkwafin duk wanda suke tare se sun san komai
nasa.

Shiru sukayi na kusan minti biyar, Bala da gulma take cinsa har ya gaji ya ceda Bashir din “Engineer wai
yane kodai akan climax kake ne kaima ka fara busa eh yane”

Wani mugun kallo Bashir ya jefe shi dashi kafin dakyar ya bude baki yace “Abinda banyi da quruciyata ba
shi kake mun fatan yi yanzu insha Allahu har na mutu nida hayaqi sedai na murhu balle na kai ga shan
wata kwaya kai dai da ka riga ka illata rayuwarka shikenan amma ka ringa tunawa Yaranka Mata ne
kodan su ya kamata ka dena abinda kake yi”.
Hade rai Bala yayi dan yasan dama qarshe seya jefe shi da maganar, tun suna secondary Bala ya fara bin
wasu Sa’anninasu a unguwa har suka koya masa dabi’ar shaye shaye, babu yanda basuyi dashi ba akan
ya dena amma ina qarshe har yaso koyawa Sadiq da taimakon Allah da jajircewar Iyaye beyi nisa ba ya
bari amma shi Bala ya rigada yayi nisa dukda abun nasa harda daurin gindi daya samu gurin Babarsa dan
shi kadai ne danta Namiji.

Lokacin da aka ringa ankarar da ita akan ta ringa masa fada seta nuna an takura mata Da ba’a qaunar sa
seda yayi nisan da baze ji kira ba sannan tazo tana kuka da idanunta akan dabi’ar tasa dan seda takai
kayan maye har a cikin gida sha yake babu abinda baya ta’ammali dashi in banda Giya da Cocaine har
kuwa ta mutu da wannan baqin cikin toh yanzu dai yayi sauqi saboda girma da iyali daya tara amma fa
ko yanzu ba abin kunya bane a gurinsa ya murza wiwi yasha ko a gaban waye su kansu su Bashir dan dai
babu yanda suka iyane suka ci gaba da zumunchi dashi musamman Bashir da Yake ganin Balan na bashi
shawarwari daidai da ra’ayinsa.

Shiru suka sakeyi kafin can Bashir ya mula dan yana buqatar abokin tattaunawa, idan so samune Sadiq
ya kamata ya gayawa dan yafi Bala hankali amma tun auransa da Amirah alaqarsu taja baya dan a
lokacin gani yake Sadiq din ya goyi bayan qanwarsa dan haka ya zage ya masa rashin kyautawa shi kuma
da zuciya ya fita sabgarsa sam yanzu babu wata kwakwkwarar mu’amala tsakanin su daman ga
banbancin gari yanzu ga aiki yasha kan kowa.

Labarin duk abinda ya faru da hukuncin daya dauka da wanda Baba ya dauka shima ya bawa Balan, Bala
dayai zuku di kamar gaske yana sauraronsa ya jinjiga kai yana cewa “kai Engineer kafa debo da zafi
wallahi, nifa daman wannan Addan taku kasan yar bala’i ce tun duniya na kwance bazan manta sanda
muke zuwa gidanta ba lokacin tana kiwon kajin nan in muka kwamusu daya haka zata biyo mu har layi
tana sababi, amma ai ita Amiran tayi fa. Ka jure kawai tunda ka samu yarinya me kyau duk abinda ze zo
ai daga baya ne”.

Baki bude Bashir yake kallonsa, wai ma wannan ya gane kan matsalar sa kuwa yake masa wannan soki
burutsun koda yake shima da laifin sa wani sa’ilin ina shi ina shawara da dan wiwi? Tsaki ya buga kawai
tareda yaiwa motar key yace masa “Malam sauka seda safe”

Bala ya kwashe da dariya yana cewa “ah da wuri haka kodayake gara kaje ka lallashi yar Babynka wallahi
baka san wahala suke yanzu ba ko kodan kai Allah ya baka zuqa zuqa har biyu ka ajiye a gida baka san
yanda kan gayu yake gwaruwa yanzu kafin su samu wadannan kalolin ba”
“Bala sauka ko na tafi da kai” ya sake fada a fusace, se Bala ya balle murfin motar ya fita yana ci gaba da
yi masa dariyar qeta yace “Haba Engineer ai daman ba’a samun abu biyu ka hada kyau da zaman lafiya ai
baze yuwu ba mu dai da muka auri munanan ba gashi muna qalau ba wayake jin kanmu...” fizgar motar
Bashir yayi Allah yasashi ya matsa gefe ya koma majalisarsu yana ci gaba da dariya a ransa yana cewa “Ai
baka ga komai ba wallahi, yanda ban samu abinda nake so ba kai ka samu, a baya dai kaji dadi amma
bazaka sake samun kwanciyar hankali ba”.

Bayan Barin Bashir gurin yawo ya ci gaba dayi a mota dan baya so ya koma gida ko waccensu haushinta
yake ji, seda sha biyu ta buga sannan ya kama hanyar gida bada ban ba ma Hotel zeje ya kama amma
yanda duniyar nan take yanzu abu qalilan seya jefaka a masifa wani ya ganshi be san meya kaishi ba a
canza masa manufa, gidan ya dawo masu gadin layinsu na zazzaune suna hira mutum biyu suka taso
suka bude masa get bayan ya aje motar ya koma yayi musu dan ihi sani ya koma ciki.

A tsakiyar part biyun ya tsaya ya riqe qugu yana balla musu harara kamar masu dakin ne a gabansa,
fitilun palour Amirah a kunne suke, daga inda yake yana hango cikin palour tarwai ta window saboda
babu labule kamar ya share sedai tunawa da Maganar chanza key da Asma’u tayi masa ya saka shi dosar
gurin dan be san ko an sace din ba da gaske.

Da key din hannunsa yayi amfani ya bude qofar tana kwance akan kujera ta duqubqune ya isa kanta ya
tsaya ya, ganin yanda ta bar kwanuka ya sa ya fara kiran sunanta. Amirah kuwa Kamar a mafarki taji
muryar Bashir yana kiranta, tana bude ido kuwa ta ganshi akanta ai ba shiri ta buga wani uban tsalle tayi
gefe sedai kafin ta kai qasa yai azamar riqota dan shi kansa ya tsorata da yanda ta miqe din ba shiru suka
zube qasa, a tare suka saki qara shi ta zafin buguwar rashin tsammani data same shi ita kuma ta azabar
da taji cikinta ya dauka danji tayi kamar dinkin ze bare.

Kuka riris ta saka gana tsoron abinda ze mata gana azaba abinda ya hadu ya qara qular da Bashir qoqari
yake ta tsaya tabar mutsu mutsun amma ita se qara zillewa take tana ihun yayi haquri a zatonta
dukanta zeyi, ganin tana bata masa lokaci yasa ya daka mata wata uwar tsawa yana ce wa “wallahi ko ki
rufe mun baki kona make ki a gurin ki tsaya mu gani ko kinjiwa kanki ciwo”.

Tsit tayi se shatato kwalla take hannu ta akan cikinta dayan kuma ta rufe baki, yanda take matsa cikin ya
tabbatar masa da tana jin zafi ya saka shi cewa ta tashi ta biyo shi yayi gaba tana binsa a baya a
dudduqe, seda ya kashe fitilun ya kulle qofa kafin suka shiga motarsa, wallahi badan yana tsoron kar
wani abun ya sameta Allah ya kamashi ba da barinta zeyi jikinta ya gaya mata. Haka ya sake fita daya
saura suka nufi Asibiti shi yana jera tsaki ita tana kuka qasa qasa.

Basu bata lokaci ba dan an tabbatar musu babu komai motsawa gurin yayi amma dai ta kiyaye irin
hakan, Allurar kashe zugi suka mata kafin suka kamo hanya kamar abokanan gaba har suka zo gida yana
tsayawa ta wuce sedai tuna bata da key ya sakata rakubewa tana satar kallonsa. Har ze shige part din
Asma’u shima ya tuna da bata dakko key dinba dan haka ya qarasa ya bude mata qofar be amsa Nagode
din da take ce masa ba ya wuce abinsa.

Kitchen ya fara tsaya wa ya dauki Yoghurt me sanyi kafin ya hau saman, beyi zaton samun Ma’u a dakin
ba amma yana budewa qamshin Airfreshner dana turarukan baccinta suka masa sallama besan sanda ya
fara sauke aji yar zuciya ba dan har ga Allah qanshin sun san yaya masa rai.

Akan dan teburin da yake dakin ya ajiye yoghurt din da tarkacen keys dinsa da wayoyi kafin ya cire rigar
sa ya shiga toilet. Wanka yayo da alwala, bayan ya fito ya shafa mai sama sama ya zura jallabiyya Ya fesa
turare lokacin har biyu ta gota kafin ya kalli Gabas ya tada sallah.

Raka’a biyu yayi a sujjadarsa ta qarshe ya dade yana yiwa Allah kirari kafin ya dora da istigfari tareda
neman zabin Allah akan dukkan al’amuransa ya rufe da salatin Annabi kafin yayi tahiya ya sallame. Ya
dan jima hana lazimin La’ilaha illah anta subhanaka inni kuntu minazzalimin har seda bacci ya fara
fuzgarsa sannan ya tashi yana jin nutsuwa na saukar masa. Seda ya sha yoghurt din dan yunwa yake ji
sannan ya kwanta ya juyawa Ma’u da bata san da dawowarsa ba baya.

A kusan tare suka farka da Asuba, ya cuna baki Gabas ta cuna Yamma kafin ya miqe tayi wuf ta shige
toilet tayo fitsari tareda chanza pad ta koma ta kwanta kafin ma ya gama shirin Masallaci bacci ya sake
kwasheta.

Da safe ma haka suka tashi, ya hada fuska tam yana zaune a palour yana kallon labarai ita kuma tana ta
kaimawon hada masa breakfast, bayan ta gama ta masa magana daga “Toh” be sake ce mata komai ba
kuma be motsa ba se itama ta share kawai dan dai fushin ai ba nata bane, idan kuma zancen komawa ne
ai indai yar gaskiya za’abi batayi laifi ba. Dibar Abincinta tayi ta wuce dakinta taci, bayan ta gama ta fito
sukayi kici bus ze shiga zata fito ta rabe masa ya wuce kafin ta fito.
Abincin ta fara dubawa taga yaci da yawa ma tayi dariya a fili tace “na zata shima cikin fushi kake dashi
ai” ta shiga tattarewa ta sauka qasa da kayan. Tana cikin dauraye kwanukan taji motsinsa ya bude qofa,
ta window ta ga fitarsa tana ganin yanda yai diri diri a tsakanin parts din me kuma ya tuna ya wuce ya
kunna motarsa ya bar gidan.

Ragowan Abincin ta juye ta yafa mayafinta ta kaiwa Amirah. Tana zaune a palour tun jiyan a nan ta
kwana sallah ma duk anan tayi kuma har lokacin bata kwashe kwanukan jiya ba ga plate din data sake cik
tuwo bayan sun dawo shika a bushe.

Ba qaramar kunya ce ta kamata ba ganin Asma’u, duk se taji ta muzanta saboda yanda Asma’un ta sheqa
wanka da wata Atamfa doguwar riga se qanshi take ita kuwa tama zaune cikin kwanuka da kayan jiya a
jikinta seta hau soshe soshen tana gaida Asma’u da tayi mirsisi kamar ma bata ga komai ba.

Kayan ta dire mata tana cewa ta juye ta bata kwanukan kafin ta duqa ta kwashe na jiyan a ranta tana
cewa “Na san darajarsu bari na kwashe abuna” bata ko saurari Amiran dake cewa ta barsu yanzu zata
tashi ta wanke ba, ganin haka yasa ta tashi ta shiga kitchen ta juye ta daurayo kwanon da zallar ruwa ta
kawo mata. Karba Ma’u tayi tana cewa “se ki nemi abinda zaki ci da rana tunda naga kin warware” tayi
waje abinta.

Wannan abincin taci tayi nak sannan ta tashi ta dan tattare gurin ta shiga dakin ta tana qarewa
Hadadden Gadonta da aka rushe bedside din kallo. Ita dai yan sunan nan sun cuceta wallahi dan dai bata
hango ranar da Yaya ze sake mata wasu kayan ba yanzu ma ta samu ya haqura ya sakko daga fushin nan
ma kafin wani zance ya biyo baya.

Wunin ranar zir Bashir a waje yayi shi, itama Ma’u bata zauna ba ta fita harhado sauran kayayyakin da
take buqata da ba’a samu acan dan haka se yamma lis ta dawo bayan ta biya ta dakko yara. Koda suka
dawo ma basu zauna ba kayansu suka hade tsaf dan gobe Sunday tanason suje su wanke kai da kitso
Monday se Lagos.

Sanda Bashir ya dawo yaran sun kwanta Amnah ce kadai idonta biyu tana karatu dan da sun koma sati
biyu zasu fara SSCE, da niyya tijara idan basu dawo ba ya shigo gidan se Allah ya ceci Ma’u tana kitchen
ta jiyo Amna na gaishe shi yana tambayarta yaushe suka dawo tace dazu. Kitchen din ya leqa suna hada
ido ya wani qara shan kunu tayi masa sannu da zuwa ya daga kai ya fice ya haye sama qasan ransa yaji
dadin ganinta.
Seda suka zo kwanciya ta gama duk hidimominta taji muryarsa yana cewa “akwai abinda kuke buqata
ne?” Seta dakata daga saka hular da takeyi ta kalle shi yana zaune a bakin gadon yanda yayi maganar
yana fuskarta wani guri daban, kallo daya zaka masa kasan akwai abinda yake damunsa gaba daya yayi
laushi.

Kusa dashi ta koma ta zauna, seda ta shagwabe fuska sosai ta tara kwallar qarya a idonta kafin ta riqo
hannunsa, waiwayowa yayi seda ta tabbatar ta saka kwayar idon ta cikin tasa yanda baze iya kaucewa ba
sannan tafara magana tana cewa

“Haba Baban Ali Haba Na Ma’u wai fushin ne haryanzu ina kake so na saka kaina naga haske bana ganin
Murmushin ka? na tuba nabi Allah kayi haquri indai batun Tafiya a motane na yarda gobe muyi asubanci
mu tafi idan kana tare damu nasan babu abinda ze same mu se ikon Allah”.

Duk yanda yaso ya janye ya kasa dan riqon da tayi masa da kaifin idonta yayi tasiri a jikinsa, daman
dauriya ce kawai amma yana buqatar ta, yana buqatar me kwantar masa da hankali kuma Ma’u ita
kadaice duk damuwar daya shiga a duniya take iya magance masa ita har in yana tare da ita tana saka shi
ya manta komai sedai daga baya ya tuna shi yasa duk sanda matsala take tsakaninsa da ita yake ji kamar
ya zauce dan babu me masa magani.

Fuzgota yayi jikinsa ya mata ruqo me tsauri tana jin yanda zuciyar sa take bugawa jikinsa har wani rawa
rawa yake, cikin dasashshiyar murya yace “Badake bake fushi ba Ma’una, me yasa, meyasa ita bazata ji
magana ta ba me yasa koda yaushe take sakani ciwon kai”.

Seda Ma’u ta murguda baki ta harareshi dukda be gani ba a zuciyar ta tace “taya zan sanin maka ba kai
ka kwasowa kanka ba” a fili kuwa seta qara riqeshi cikin kwantar da murya tace “Kayi haquri” . Yanda ta
fadi haqurin yasa yaji tamkar ta watsa masa ruwan sanyi a zuciyar sa, kissing goshi ta yayi kafin yace “Na
haqura Yar Aljanna”.

Cikin tsananin farin ciki ta dago ta kalli kyakykywar fuskarsa tace “To Na kawo maka abinci, yau duk
nasan baka ci komai ba ga fuskar ka nan ta nuna”.
“Muje ki bani” ya fada yana daga ta gaba daya, seda suka sauka har qasa sannan ya ajiyeta Amnah da ta
gama hada littattafanta zata shiga daki tayi saurin saka littafin a fuska tana tafiya da baya da baya.
Rankwashi ya kai mata da wasa cikin harshen turanci wanda dashi yakewa yaran magan yace “gidan ku
me kike yi anan baki kwanta ba haryanzu”

Dariya tayi ta dan janye littafin tace “Abbi karatu Saura two Weeks mu fara WAEC fa”

“Ok maza je ki kwanta karki manta kiyi Addu’a” ya fada yana zama akan kujera, seta juya tana cewa
“Good night Abbi”

“Good night Amna” ya fada daidai sanda Asma’u ta fito da plate din daya zubo masa dambun couscous
se kunun aya a Jug.

“Good nigh Mami” Amna ta sake fada, seda Ma’u ta ajiye kayan akan centre table kafin tace “Good night
Amnan Abbi”.

Dariya Bashir yayi yana cewa “fadi ki qara kam Amnan Abbi” murmushi kawai tayi, a ranta tana jin dadi
yanda Bashir ya dauki qanwar tata tamkar yar da ya haifa a cikinsa dan gani take kamar yana mantawa
ma ba yarsa bace, tunda riqon Amna ya dawo hannunta be taba sauya wa daga yanda ya karbi yarinyar
ba ko a fuska, komai ya tashi yiwa yaran itace farko a matsayin first born dinsa. Cikin dadin rai yaci
abincinsa ta tattara suka wuce Aza rum.

WATA KISHIYAR

(ALKAHIRI CE KO SHARRI)

Na Maryamah_Mrs AM

(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)

Wattpad @MaryamahMrsAm
Page 23

Ranar litinin kamar yanda muka saba tunda muka yi sallah muka hau wanka da shiri dan jirgin bakwai za
mubi ga tazarar zuwa Airport Akko dago Gombe. Shida bata qarasa ba muna bakin Sienna da ake kwasar
mu in munzo ko zamu tafi. Yaran sun gama shiga ina tsaye daga qofar ina jiran Bashir da yake qara
dudduba cikin gidan kafin ya rufe ina murmushin hirar su Naziru da Ahmad yanda yake biye masa kamar
wasu Abokai.

Ba dade wa Bashir din ya fito yasha Suit kalar Dark Blue farar cikin nan har wani daukar ido haskenta
yake, seda yayi Addu’a ya tofa kafin yaja qofar ya rufe se ya nufi part din Amirah yana cewa Nazirun “ka
kunna motar mana ka tsaya kana surutu” ya shige nida Naziru muka rakashi da ido.

Ashe tana gidan nayi zaton tun jiya ta wuce gida yanda ta saba ana washe gari mu tafi take farayin gaba.
Cikin motar nima na shiga na zauna ina duba agogon wayata ganin shidan ta yi harda minti biyar.

Bashir kuwa a daki ya tarar da Amirah hankali kwance tana baccinta, shurin qafarta yayi ta farka a firgice
tana zare ido ganinsa yasa tayi saurin nutsuwa ta shiga gaishe shi. Be amsa ba ya cilla mata rafar 200
dubu Ashirin kenan yana cewa

“Zamu tafi Naziru ze kawo miki kayan Abinci, wallahi koda wasa kika saka qafarki a qofar gidan nan ki
tabbata kin fita kenan mtsw” ya ja tsaki ya juya dan har yanzu bala’in haushinta yake ji gashi an hanashi
hukuntata.

Harya kai qofa ta zaburo ta biyo shi da sauri dan kuma yanzu hankalin ta ya koma kan yarta, ga Nononta
da suka dameta da ciwo saboda cika, saurin ce masa tayi “Dan Allah yaya zanje naga Iman” tayi maganan
cikin rawar murya kaman kuwa yana jira ya jefa mata wani mugun kallo kafin yace

“Ya zama kuskure na qarshe da zakiyi tunaninyi ki sake dora hannunki a kan yarinyar nan, da kina sonta
kika jawo mata ciwo sannan tunda aka fita da ita daga gidan kin tambayi yanda take bare kije ki ganta?
Idan ke bakya qaunarta ni inasonta dan haka nayi miki iyaka da ita kota warke bazan dawo miki da ita ba
tunda bake kadai bace zan kaiwa wadda zata kular mun da ita” yana gamawa yasa kai ya fice ya barta
tana rusa kuka.

Abinda baze ma yiwu ba kenan taya ze raba ta da yarta ce masa akayi bata sonta? Ai tasan tana Asibiti
kuma a kwanakin in ma tace zataje ba bari ta zeyi ba shi yasa amma wallahi bazata yarda ba dole ma ya
barta ta fita kai ita bama zata iya zama a gidannan ba sedai ta tafi gidansu, ta yarda acan din bazata fita
ko ina din ba amma badai a nan ba.

Tana son magana da Addah amma babu hali, ita ba waya Addah ma haka dukda da tana da wayar samun
Addah bazeyi wahala ba ko a wayar Ummi ne. Tunda suka rabu a gidan Dada basu sake magana ba bata
san yaya Addah ta qare a nata gidan ba tilas kuwa tana buqatar magana da ita, ya dai tafin ko Nazirun in
yazo anjima ta roqeshi ya siyo mata ko Key pad ce a cikin kudin da Bashir din ya bar mata.

GIDAN ADDAH

Ranar bayan Addah ta bar gidan su Bashir Napep ta hau ya kaita gidanta. Alhaji Murtala na tsaye a qofar
gidan da wasu mutane su biyu Addah ta sallami me Napep zata shige ya dakatar da ita.

“Yawwa ga Hajia Fatun ma ta dawo” ya fada yana nuna musu ita. Se Addah taci burki ta bisu da kallo
daya da daya amma bata ga fuskar data sani ba dan haka se ta saka kai ciki kamar bataji maganar da
Alhajin yayi ba harta tura get ya dakatar da ita dacewa

“Wallahi kika shiga gidannan se ranki yayi mummunan baci Fatu” Alhajin ya fada cikin kakkausar murya.
Se Addah taja da baya jiki a sanyaye, to su waye wadannan kuma? Wane jafa’in ne ya sameta.

Takadda daya daga cikinsu ya miqo mata yana cewa “Hajia gashi sammacine daga kotu ana qararki akan
laifin damfara”.

“Damfara?” Addah ta fada da qarfi tana dafe qirji tareda zaro idanu waje

“Ni Fatu wana damfara?” Ta sake tambayarsu hankalinta in yayi dubu ya tashi.
“Akwai bayanin komai a ciki idan kunje kotu zakiji cikakken bayani kafin sannan kina iya neman lauya da
ze tsaya miki” dayan mutumin ya fada, sallama sukayiwa Alhaji kafin suka hau mashin din da suka zo
suka bar Gurin.

Addah data gama jiqewa da zufar tashin hankali ce ta kalli Alhaji Murtala da yake jifanta da wani irin
kallo data fassara dana tsana da takaici yace “Daman na fada miki Fatu tun kina dauko magana kina cin
riba wata rana se kin dakko ta wanda yafi qarfin ki.

Se kije ki san yanda zaki kare kanki ko kuma ki fara shirye shiryen tafiya gidan prison tunda halinki yaja
miki” yana gama fada ya shige cikin gida Addah ta rufa masa baya tana kuka kamar yarinya.

Bata tsaya ba har cikin uwar dakinsa inda ya shiga, Hajia Binta yar tsakiyarsu na cikin Toilet tana
wankewa taji shigowarsu da kukan Addah seta leqo tana cewa “Aa Alhaji lafiya waye yake kuka... Au
Addah kece lafiya dai waye ya mutu?”

“Kiga mutuwa akanki munafuka kuma duk sharrin da kuka kitsa masa sedai ya koma kanku” Addah ta
fada cikin hargagi, dariya Hajia Binta tayi harda tafawa tana cewa “Ikon Allah se kallo, da alama dai bana
an kwaso me zafi”

“Fita ki bamu wuri” Alhaji ya katseta, seta hade fuska tana cewa “kamar yaya Alhaji in baku guri bayan ni
nake da aiki ko Alfarma za’a nema ai ba ta haka za a zomun ba” kafin yayi Magana Addah ta tareshi da
cewa

“Alhaji muje gurina Dan girman Allah”. Shiru yayi kamar baze amsa ba se kuma ya miqe yayi waje ta bishi
a baya yana jin Hajia Binta na fadar maganganun an shiga haqqinta dan ba haka taso ba, dayace ta fita
zata fitan in yaso ta labe inda zata ji kan zancen tas gashi yanzu ta jashi dakinta.

Addah kuwa tiryan tiryan ta labartawa Alhajin duk abinda ya faru da basussukan jama’ar data ci da
yanda sarqar Hajia me Gwal ta salwanta dama yanda suka rabu yanzu ga zancen sammaci”.
Takaici ya gama qume shi, shidai Fatu qaddarar sa ce amma ba komai lokaci yayi daya kamata yayi
maganinta ko yaya me taji a jikinta amma yanzu bari a gama wannan case din tukunna.

“Wanda yaja ruwa ai shi ruwa ze doka, takaddun gidan original suna hannuna gobe se muje gidan matar
aje da Dillalai suyi masa kudi a siyar a biya kowa kudinsa, Allah ya tsare gaba idan zaki gyaru” ya tashi ya
fice ya barta tana ajiyar zuciya dan bata zaci abubuwan zasu zo da sauqi haka ba. Ita yanzu koma menen
ai a siyar a biya wannan jarababbiyar matar, ita da tunda Allah ya halicceta ko Police station bata taba
zuwa bare a ganta a gaban Alqali gara komeye a siyar a bata kudin su rabu lafiya. Da wannan ta samu
sa’idah har ta iya kwantawa tayi baccin gajiyar da batayi ba.

ASMA’U

Gaba daya sukuku mukayi tafiyar babu wani kuzari har muka sauka Ikko, a Airpot din muka rabu Drivern
Bashir ya kwashe mu shi kuma ya dauki Shatar Taxi ya wuce office daga nan. Yanda nayi tsammani gida
na nan ya hada kari, bamu ko zauna ba na rabawa ko wa aikin da zeyi, Ahmad da Muhammad da suka
fara mun rigimar wai Yunwa dukda munsha Tea kafin mu taho ga Cake da sukaci a jirgi se na turasu
gidan Anty suna fita kuwa se gasu sun dawo wai Aliyu da Jafar suje inji Anty, Breakfast ne data shirya
mana ta basu wanda ya zamar mata kamar dole duk sanda mukayi tafiya irin haka bata gajiya seta kawo
mana.

Nan da nan kafin wani lokaci mun qalqale ko ina har kayan da muka dawo dasu kowa ya jere nasa na
amfani kuma an adana su a inda ya kamata.

Bayan Azahar Muna zaune muna huce Gajiya Anty ta shigo su Ahmad na binta a baya da kulolin Abinci,
bata gaji ba wai abincin rana ta kuma kawo mana, matar dai tana da kirki kwarai nayi sa’ar maqociya.

Kan Dining suka koma Amna ta zubo nawa ta kawo mun cikin palour ina ci muna hira da Anty suna
gamawa kuwa duk suka shige daki wai bacci se Anty ta miqe tana cewa bari ta barni nima na huta.
Tsarabar Kindirmo me kyau da Dambun fura se Kuka da kayan qamshi na dakko mata daman na ware su
daban na hada mata da wani turaren wuta da Alawiyya yayata take hadawa ta bani yana da kyau sosai
mukayi sallama ta wuce gida.

Na raka ta kenan David yaron da Bashir yake aikowa wani lokacin ya kawo saqo ya tsaya a qofar gidan,
kayan amfani ya kawo su kayan miya, veggies, Nama, kifi, dankali, doya plantain duka dai kayan amfani
da za’a nema ya siyo, qofar kitchen ta baya na bude masa suka shiga da kayan shida me Uber daya kawo
shi.

Dole na fasa kwanciyar na shiga ware komai ina saka shi gurinsa kafin na gama har uku tayi dan ban
nemo yan tayi ba ganin sun gaji yasa na barsu su huta. Bayan na gama na shiga dakina, zama nayi akan
gadon ina miqa Kafin na dan kishingida ina duba waya ganin da sauran kusan 30 mins kafin ayi la’asar
yasa na kwanta wai in dan matse ban tashi farkawa ba kuwa se qarfe biyar harda rabi na yamma na miqe
ina salati ganin irin baccin da nayi, anyi la’asar tun tuni ga Bashir nasan yana dab da gida yanzu kuma
Azumi yake.

Alwala na farayi nayi sallar bayan na idar na shiga wanka. Ban wani jima ba ina fitowa na shafa mai sama
sama na goga yar hoda da kwalli se lip balm kafin na fesa turare, doguwar riga na saka ta wani plain
material Silk Dark green an masa dinkin kamar Jallabiyar qirar Turkey babu adon komai a jiki se maballai
da aka jera a jikin wuta zuwa qirji guda uku da kuma bakin hannu. Mayafin ta na yafa a kaina wanda be
kai kalar rigar duhu ba na zura flat shoe baqi na fito da wayata a hannu ina tunanin me zan dora masa
mara wahala da zan gama da wuri.

“Mamina” Ahmad ya fada yana rungumeni, se na janye shi gefe ina cewa “Ina zuwa Ahmad Abbi ya kusa
dawowa gashi ban masa abin buda baki ba” ai ban qarasa rufe bakina ba naji tsayuwar motar da nake da
tabbacin tasa ce a qofar gida. Kitchen din na fada da sauri a rainaina cewa “shikenan yau an bani”dan
Bashir baya wasa da abinci. Idan yayi azumi yafison kafin asha ruwa an gama jere masa komai a gabansa
yanda bama ze jira komai ba.

Da niyyar dafa masa tea in soya kwai na shiga in yaso kafin yaje sallah ya dawo ko couscous ne na turara
masa, nasan dakyar idan yaran nan sun ci farfesun kayan cikin da Anty ta kawo dazun ba tunda ba son
shi suke ba se in hada masa ya qarata, mita ce dai nasan sena sha ta yau dan babu ruwansa baze duba
irin aikin da muka sha a gidan ko gajia ba tunda kawai nasan yana azumi dole na tanadar masa abincin.

Amna da Farida na tarar Amna na kwashe dankali daga mai Ita kuma Faridan na yanka Fruits a bowl,
suka kalleni a tare suna murmushi “Mami kinsha bacci, naga yamma tayi nace bari mu hadawa Abbi
kayan shan ruwa” Amna ta fada tana kashe Gas din bayan ta qarasa kwashe dankalin.

“Allah dai yayi muku albarka, na manta shaf ma kuna gida ai” na fada ina qarasawa kan Island inda suka
ajiye kwanukan da aka zuzzuba abincin na bude na farkon.
Farar shinkafa ce se ganyen parsley da aka yi garnishing na maida murfin ina cewa “Aa su Chef Amna
harda wani ganye ganye aka zubawa Umfafar. Farida ta miqomun spoon tana cewa “Mami ci sauce din
kiji ni nayi ko Yah Amna”.

Na karba na bude kwanon miyar, sauce din hanta da qoda sukayi se qamshi take na kai baki dadin ya
ratsani, se na ajiye spoon din, “dagaske ita tayi Amna”

“Ita tayi Mami kawai gaya mata yanda zatayi nake se kuma na bata measurement na komai” Amnan ta
fada.

Lallai ashe mun samu sabuwar chef, Yayi dadi sosai amma karki fadawa Abbi ki bari se ya gama ci
tukunna”. Ina rufe baki Bashir ya shigo kitchen din, Farida ta ajiye wuqar hannunta ta nufeshi tana masa
oyoyo.

“Me kike a Kitchen Farida da wuqa a hannunki bana hana ba” ya fada yana kallon fuskarta, ssannu da
zuwa nayi masa ba tareda na amsa tambayar tasa ba dan dani yake ba Farida ba. Ledar hannunsa ya
miqo Amna ta karba yace “ki sake warming nasa” ya juya suka fita yaja riqe da hannun Farida.

Fruit Salad din na qara sa hadawa, muka fito da kayan dukka muka jera a Dining lokacin har an fara kiran
sallah. Dabino na koma na dakko masa da ruwa mara sanyi na ajiye akan stool din gefen kujera sannan
na zubo fruits din a dan qaramin bowl na ajiye daidai sanda ya fito daga dakinsa da alama alwala yayi.

Ina kitchen ina hada kayan da zan soya masa kwai suka fita masallaci dan shi bazaki soya kwai ki ajiye
masa ba ya fiso daga kasko se farantinsa. Kayan cikin na dumama na fito da Balangun da Amna ta saka a
Oven shima na juye masa a bowl a raina ina jinjina qaunar Bashir da nama. Seda na soya kwan bayan sun
dawo na ajiye masa komai sannan na shiga dakina na barshi da yaran suna tayashi shan ruwa.

Dana idar da sallah ma ban fito ba, miqewa nayi ina chat da yan uwa da abokan arziqi har aka yi Isha. Ji
nayi ana kwankwasa qofa. Aliyune, bayan ya shigo yace “Abbi yana kiranki”

Da “toh” na amsa na miqe ya qara powder da turare na yafa mayafi na na fita.


Suna zaune a kan kujerun Palour sun cika ko ina, “ikon Allah wai duk bataliyar nan yayan Ma’une” na
raya a raina kawai na tuntsyre da dariya se suka juyo dukka suna kallona.

“Lafiya kike dariya” Bashir ya tambayeni, seda na zauna a kusada shi kafin nace “ganin yaran nan nayi da
yawa nake mamakin wai duk nawa ne”.

“Da sauran wasu ma a gaba ai” ya fada yana kallona da wani kalar expression, kallonsa nayi nima har
sannan fuskarsa bata koma daidai ba da sauran alamun damuwa da bacin rai akanta nace “Aa ni ai na
gama, na barwa yan baya gashinan sun fara ai” harya bude baki zeyi magana wayarsa tayi qara, Dr Hadi
ne pediatrist din da yake kula da Iman. Daga wayar yayi bayan ya miqe ya shige dakinsa nima sena tashi
na qarasa kan Dining na debi abinci.

Ina ci muna yar hira da yara, ina kammalawa suka kwashe komai aka kai Kitchen muka tattare palour qal
dan kusan komai da dare mukeyinsa daman saboda fitar safiya muna gamawa nace suje su kwanta gobe
akwai school.

Dakina na koma na sake wanka na shirya tsaf na tafi dakin Bashir, yana kwance rabin jikinsa akan Gadon
qafafunsa kuma a qasa ya harde hannu a qirji yana kallon sama da alama tunani yake. Banajin yaji
shigata har seda na ajiye wayata da Zoben dana zare daga hannuna akan Bedside sukayi qara sannan ya
dago a dan zabure.

“Yadai?” Na tambayeshi se ya girgiza mun kai alamar babu komai kafin ya miqe ya shiga toilet. Ina shafa
addua ta ya fito daga toilet din daure da towel a qugunsa, kallonsa nayi sam bazakace Bashir ya fara jiyo
qamshin Hamsin ba saboda kyan jikinsa, a tsarin halitta befi ka bashi shekaru 35 zuwa 37 ba amma a
zahiri shekarunsa 45 ne.

Har ya shafa mai ya saka kayan bacci riga da wando light blue ina zaune ina kallon sa, yanda yake
abubuwa a sabule kamar mara laka harya gama ya kashe fitilar tareda hawa kan Gadon ya janyoni jikinsa
ya dora kansa akan qirjina mukayi shiru bakajin komai se qarar Ac a dakin, kusan minti goma a zatona
ma bacci yayi naji ya riqo hannuna sosai yana cewa “bana so na rasa ta”.
“Qum” naji kaman an jefeni da dutse dan a sukwane zuciyata Amirah ta kawo mun sedai kafin nayi
magana naji ya sake cewa “bana son na rasa Iman Ma’u, ina son yarinyar kwatankwacin yanda nake son
Farida, na dade inawa Farida fatan ta samu yar uwa se yanzu Allah ya bata gashi ina neman rasata”.

Wato wani sanyi naji a raina, sena gyara kwanciya ta ina cewa “ba abinda ze faru da izinin Allah zata
tashi, naga jikin ai da sauqi jiya da muka je koh?”

“Eh da sauqi sosai, yanzu ma kiran da Dr yamun su naso su sallameta ne” ya fada yana tashi zaune sosai.

“Kai masha Allah, Allah ya qara lafiya” na fada ina gyara kwanciya harda jan bargo a zatona maganar ta
qare sejin Bashir nayi yana wani soki burutsu

“Idan an sallamota ina so zan kawo ta nan” ya fada. Naji ba wai banji shi ba amma son na tabbatar da
ma’anar maganar tasa yasa na dago na kalleshi kafin nace

“Ban gane me kake nufi ba zaka kawo ta nan, Amiran nan zasu dawo ne ban sani ba?”

“Aa ba Amirah ce zata dawo ba Iman nake nufi zan kawo miki ki riqeta na bar miki ita”.

“Ikon Allah” na fada a fili kafin na tashi zaune sosai na ina kallonsa,

“Ka kawota nan fa kace Baban Ali jaririyar da ko wata bata cika a duniya ba, me ya samu ita Amiran da
bazata iya riqe yarta ba. To ai ko mutuwa tayi tunda tana da uwa a raye zata karbeta bare da ranta ace
za’a raba ta da yar data sha wahala kafin ta sameta ah gaskiya kaima baka zo da maslaha ba”.

Kallona yake har na kai qarshen maganar, nayi zaton ze balbaleni da masifa ne yace seya kawo yarinyar
amma aka sin haka sema wani marairaicewa daya sakeyi ya kamo hannuna yana cewa

“Kin fita cancanta daki tarbiyyantar mun da yaya, sam waccen yarinyar bata da tunanin da zata iya kula
da kanta ma bare wani. Kina gani bataji tausayin yarinyar ba suka jaza mata wahala bana tunanin zata
iya rainon yarinyar”.
Sakato nayi ina ji da ganin ikon Allah rainin hankali da tsakar dare, ace ta haifi amma bazata iya kula da
ita ba ni ga jakar Ÿaÿa shine za’a dakko wata bakwaini a kawo mun lallai zanga uban da ya isa kuwa.
Fizge hannuna nayi na kwanta tareda juya masa baya nace

“Ai Kowa ma be iya ba daga baya ya koya itama a hankali zata iya tunda babu wanda baya son dan sa”
naja bargo na rufe har kaina. Shiru naji har kusan minti goma beyi magana ba be kwanta ba nima ban
sake motsawa ba tun ina mita a raina har bacci yai gaba dani amma ahu daya na qudurce wallahi ko
sama da qasa zata hade bazan zamar masa yar raino ba.

Ban kuka ga uban daya isa ya saka na karbi yarinyar ba.

WATA KISHIYAR

(ALKAHIRI CE KO SHARRI)

Na Maryamah_Mrs AM

(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)

Page 24

Gombe

Bayan Naziru ya kaimu Airport kai tsaye kasuwa ya wuce ya siyi duk abinda Bashir ya gaya masa ya kaiwa
Amirah. Tana zaune a palour bayan ta gama kukan ta yai sallama ta amsa fuska a kumbure be kulata ba
ya shiga kwaso kayan da taimakon Almajiran daya kira suka shigar mata da su Kitchen.
Har ya gama bata ko sake kallonsa ba dan haushin sa takeji tasan shi yake qara zuga Bashir din ma akan
komai, seda ya kai qofa ta tuna da zancen waya seta miqe da sauri tabi bayansa tana kwalla masa kira ya
kuwa shareta kamar beji ba seda yaje gurin mota tana biye dashi.

“Meye kike bina kamar naci miki Bashi” ya fada yana harararta, inda haka kawai ne seta rama amma
tunda abu take nema seta karyar da kai tana cewa “Dan Allah Yaya Naziru waya zaka siyo mun da layi”.

Seda ya harareta kafin yace “waya? Me zakiyi da waya ina taki?”

“An sace” ta bashi amsa kai tsaye.

“Toh ai shikenan gara da aka sace, kuma ni sa’an kine ko dan aikenki da zan siyo miki waya ke baki da
qafa ko baki san inda ake siyarwa ba” Nazirun ya fada. Seta marairai ce tana cewa

“Dan Allah ka taimaka mun Yaya”. Kwafa yayi kafin yace

“Kawo kudin toh badan halin ki ba”

“Nagode” ta fada kafin ta qirgo dubu biyar da dari biyar ta bashi, ya karba ya irga ya kalleta yace

“Saboda a gidan ku ake qera wa ko waye ze siyar miki da wayar dubu biyar”

“Yaya Tecno fa me keypad ai bata wuce haka ba”

“To se kije ki siyo kin tsaya kina batamun lokaci” ya fada yana miqa mata kudin, setayi saurin dakatar
dashi tana cewa “yi haquri dan Allah nawa ce se na ciki”

“Dubu goma ce sannan ki bada dubu biyu kudin mai tunda babu siyo miki waya a lissafin da aka mun. Ba
yanda ta iya tana ji tana gani ta zare dubu goma sha biyu da dari biyar ta bashi ya tafi, idan da abun nata
da mutunchi tasan a kyauta ma siyo mata zeyi amma yanda tasan yana jin haushinta ma tayi mamakin
da yayi saurin karbar aiken.

Ciki ta koma ta tafasa ruwan zafi ta dakko kayan Tea a siyayyar da ya yo mata harda bread ta zauna ta
karya, tana zaune a gurin ya dawo ya miqa mata leda da kwalin wayar a ciki da layi harda katin dubu
daya ta karba tayi godiya harya juya ta kuma tsaida shi tana cewa

“Dan girman Allah yaya ka roqar mun Yaya Bashir ya bari naje na ga Iman kaga fa tun da aka kaita Asibiti
banje ba”.

Wani banzan kallo ya mata kafin yace “karki rainamun hankali dan kin ga na biye miki malama, dacan
baki san tana Asibitin ba se yau? To bari kiji ya gayamun sharadin daya gindaya miki kuma wallahi na
baza CIDs a layin nan ki sake ki fita dan nasan ba tunani ne dake ba tsaf za’a iya zugaki ace ki fita ai be
sani ba kinga kuwa auranki ya mutu” yana gama fada ya juya ya fice yabar Amirah da baqin ciki ya cika
mata ciki kamar tayi bindiga.

Dakinta ta shiga tana duba wani littafi da ta kwafe numbobinta a lokacin Ummi nata mata iskanci wai
rashin aikin yi me sa hauka gashi yanzu ze mata rana. A garin neman littafin ta samo tsohon layin ta da
ba sosai take amfani dashi ba, da murna ta saka tana Addu’a Allah yasa basu kulle shi ba ai kuwa tana
gwada kira ya tafi amma babu kati seta loda katindaya siyo mata ranta fes ta samu numbobin harma da
wasu masu amfani da bata dasu a wancan layin.

Ummi ta kira ta hadata da Addah, tiryantiryan Addah ta bata labarin yanda akayi anje an siyar da gida
miliyan uku da dubu dari shida, an biya me Gwal kudinta Miliyan Daya da dubu dari tawkas da Arba’in
dan seda ta kawo resit din sarqar aka je da warin dan kunne gurin masu gwal suka fadi nawa gram din sa
yake sannan aka buga lissafi a gurin aka siyar da warin ma aka bawa Addah kudin.

Ragowar masu bashi ma tas seda Alhaji ya cire wa kowa aka biya dan abinda yai saura kuma ya riqe a
hannun sa yace ze saka mata a kasuwa, ta qarasa tana cewa “Nayi baqin ciki amma dai hankali na ya
kwanta da yanzu qila ina firzin, yanzu idan an kwana biyu kuma se muga yanda za’ayi ki maida
abubuwan da aka lalata miki yanzu dai ki kwantar da kai ku shirya da Bashir dan a jikinsa zaki samu ni
kuma zan nemo mana hanyar da zamu bi ta qarqashin qasa a samu komai daidai ba matsala”.
Sallama sukayi Addah na gaya mata kartazo gida yanzu ta bari se an kwana biyu tukunna se a sannan ta
gaya mata yanda sukayi da Bashir.

“Ki rabu dashi, lambo zamu musu dagashi har uban naki zan nemo mana inda za’a tasar mana kansu dan
shi kansa Alhajin shi ya siyi gidan sena san yanda na dawo da abuna amma yanzu muyi luf tukunna, zan
turo miki Ummi seta taya ki zama. Waccen Magen yar kuma gara ki barta a Asibitin ma in aka dawo miki
da ita qarin wahala ne” .

Da haka sukayi sallama ta dan ji dama dama tunda an kashe waccen babbar wutar.

LAGOS

Kusan kwanan zaune Bashir yayi dan farkawata biyu ina ganinsa ido biyu yana faman tunanin da ban san
koh na menene ba, yo ina dalili haka kawai ze saka kansa a damuwa akan abinda yasan bame yuwuwa
bane ba ma. Ko masallaci basu fita ba a gida sukayi sallah yana idarwa kuma ya koma ya kwanta, ganin
haka yasa na fita na fara hadawa yara abin kari su kuma suna shirin makaranta.

Indomie na soya musu dan har na dakko doya Abdallah yace bazasu ci ba sauran ma suka amsa Aliyu
daya baya cin soyayyar Indomin na soya masa kwai ya hada da Bread suka karya. Har suka gama ba
Bashir ba labarin sa, se na miqe na shiga dakin dan in gaya masa sun shirya fa.

Yana zaune a gefen gadon ya dafe kansa da hannu biyu na shiga.

“Baban Ali lafiya dai baka shirya ba ga yara can suna jiranka” na fada ina zama a gefensa. Beyi magana
ba ya tashi ya shiga Toilet minti kadan ya fito yana goge hannunsa da qaramin Towel, Rigar jikinsa ya cire
ya dora Jallabiyya akan dogon wandon sannan ya dauki key da wayar sa ya fita yana cewa “kiyimun
kunun gyada da kosai” ya sa kai ya fice.

“Ko ba kunun gyada da qosai” na fada a fili ina hararar qofar daya fita, gadon na shiga gyarawa, babu
dattin komai a dakin dan haka na dauke robobin ruwan da muka sha da dare na fita dasu. Seda na jiqa
wake wanda daman bayarwa nake da yawa a gyara a surfa mun se a shanya shi ya bushe idan na tashi
amfani kawai jiqawa nake na markada. Na debi gyada da farar shinkafa suma na jiqa.
Palour na koma na gyara palour da Dining din tsaf na kunna turaren sannan na shiga wanka. Riga da Zani
na saka na Atamfa na kashe dauri jelar kitson da aka mun two step sun zubo kan bayana. Juyi nayi a
gaba mudubin nida kaina na burge kaina bare kuma Bashir ya ganni dukda ba cewa zeyi nayi kyau ba
amma nasan har ransa ze yaba ai.

Seda na markada gyada da shinkafar na saka danyar citta da kanumfari dan kadan dan kar yayi baqi
sannan sake wanke blander na zuba waken na markada shi da attaruhu da Albasa se yar tafarnuwa.
Kunun na fara damawa bayan yayi kauri na zuba ruwan lemon tsami yayi fari tas gwanin sha’awa na juye
a Flask ragowar kuma na zuba a Wani qaramin flask din da niyyar na kaiwa Anty idan na gama.

Ina ajiye Flask din kunun akan Dining Bashir ya shigo da sallama ciki ciki na amsa ina kallonsa tareda yi
masa sannu da zuwa.

“Yanzu zakaci na siya qosan?” Na tambaye shi, se ya girgiza mun kai yana cewa bari nayi wanka tukunna
ya shiga daki na bi bayansa.

Seda ya fara shafa mai bayan yayi wankan na fita na dora ma suya na yanka Albasa sannan na shiga buga
qullina sosai bayan na saka kwai guda daya saboda ya qarawa qosan laushi, gishiri na saka da daskomiya
dan kadan se Albasa dana yanka qanana na shiga suyar qosan, gaba daya kasko biyu da dan kadan nayi
dan bashi da yawa, ina kwashe na qarshen na jiyo shi yana kira na sena kashe wutar na juye a Bowl na
dakko na fita palour.

Yana zaune a Dining din ya saka Jeans blue da Farar Short sleeve a gabanta an rubuta “HANDSOME” na
kalleshi da murmushi nace “handsome indeed”. Murmushin ya mayar mun na ajiye kwanon na jawo
Babban Mug na tsiyaya masa kunun na saka Sugar yace na saka masa Madara a raina nace “sarkin son
dadi” na gama na tura masa komai gabansa harna zauna na tuna da kunun Anty sena miqe ina cewa

“Bari na kaiwa Anty kunun nan”.

A bakin qofa na miqa mata na juyo duk yanda ta keta magiyar na shiga amma naqi dan nasan in muka
zauna qilan se Bashir ya biyo baya. Bayan na koma zama nayi nima na zuba kunun ina juyawa na kalle shi
nace “Wai yau hutu ka samu ne bazaka office ba?”

Seda ya cinye qosan bakinsa kafin yace “Eh zamuje fieldwork ne Delta so an banu kwana biyu mu shirya”
“Toh Allah ya taimaka” na fada naja kununa da qosai na fara ci. Ya rigani tashi daga wurin nima ina
qarasawa na kwashe komai naje Kitchen na ajiye dan na gaji gaskiya tun asuba idan na huta anjima na
wanke su.

Kan Three sitter na kwanta ina cewa “wash na gaji wallahi anya bazan nemi me aiki ba”

Hankalin sa nakan Tv ya ce mun “idan da takura se ki nema din ai amma bame kwana ba”

“Nima ai bana son me kwanan, abinda yasa ma ban damu dame aikin ba kaga ba wuni muke a gidan ba
zaman gaba daya weekend ai” na fada ina gyara kwanciya ta yanda zan kalli TV dakyau.

“Hakane” ya fada, se ya juyo yana kallona kuma yace “me kika yanke akan maganar mu?”

Kallon rashin fahimta na masa, ya gane hakan se yace “maganar da mukayi jiya da daddare nake nufi kin
gama shawara?”

Na gano me yake nufi se nayi murmushi nace “Wai maganar Iman? To tunanin me zanyi ai tun jiya na
gaya maka amsata ko” na fada ina kafe shi da ido kamar yanda yake kallo na shima, se ya sauke
numfashi ya dan zamo gaba yana hade hannyensa guri daya yace

“look Ma’u Alfarma zakiyi mun ki karbi yarinyar nan, kinsan uwarta sarai ba wai nutsuwa ce da ita ba
bare har ta iya kulawa da wani halayenta duk se a hankali. Yarinyar nan mace ce karta tashi taga abinda
takeyi ta dauka daidai ne, bana so ta tashi daban da yan uwanta ina so ta samu kula da tarbiyya irin
daya....”

“Anzo dai dai gurin” na raya a raina ina sheqa murmushi, tashi nayi dakyau na zauna kafin nace

“Wai tsaya Baban Ali, da baka yarda da tarbiyyar ta ba ka aureta har ka hada zuri’a da ita”, se ya watsa
hannu ya koma cikin kujerar sosai kafin ya juyar da kai gefe daya yace “ba haka nake nufi ba, beside
Amirah ai tarbiyyar kice itama kawai.....”
“To ai ka gama magana, tarbiyya tace kaga zata koyar da ita harda qari ma ko, sannan idan ma wani hali
ne da ita na daban da baka so yarinyar ka ta dauka ai aikin gama ya gama tunda har ta dauki cikinta
jininsu ya gauraya ta haifeta sannan tasha Nononta duk wani halayya kuma ai ta gama diba sedai ai fatan
na kirkin su rinjayi na banza ko?”

Zancen gaskiya ka bar mata yarta, nasan ma duk wannan maganar da kake bata sani ba dan bazata yarda
ba itama. Babu uwar da tana ji tana gani za’a rabata da yarta hakanan ba wata gagarumar jinya ba ko
mutuwa kai ko mahaukata se anyi da gaske ake iya raba su da Yayan su bare ita yar tilo haihuwar farko
ko nicefa bazan baka ba.

Idan Dan rashin lafiyar ta ne Allah ya hore maka ai ka barta a Asibiti suyi ta kula da ita har zuwa sanda
suke ganin tayi kwarin da zata juri ko wanne kalar yana yi amma ba maganar ka bani ita, nawa ma idan
za’a ragi wasu aciki bayarwa zanyi”.

Shiru yai yana kallona harna dasa aya ina sake turo dankwalina gaban goshi, ajiyar zuciya yayi kafin yace
“yanzu dai bazaki karba ba kenan?”

“Allah me iko, da Hausa fa nayi maka jawabi dalla dallah amma kake sake tambaya ta kuma?”

“Eh saboda kinsan ni bana son dogon surutu, amsa daya nake buqata Eh ko Aa kawai” ya fada a dan
hasale alamar ya fara barin cool site dinsa ze koma Bashir dinsa na gaskiya, se kuwa na tura baki gaba
nace “Toh a taqaice dai bazan karba ba”.

“Shikenan, amma ina da ikon da zan kawota cikin gidan nan ko tunda gida nane” ya fada yana miqewa,
nima sena miqe tsaye jin wani qundumemen rainin wayo,

“Tabbas gidanka ne ka isa ka dakko kowa nene ka kawo shi ciki, zaka iya kawo ta tunda itama gidan
ubanta ne ai se ka hado dame kular maka da ita, ko kuma kai zaka aje aikin ka ka zauna rainon duk ba
matsala ta bace ni” na fada ina dauke kai gefe, ina jin yanda yake qare mun kallo kafin yaja tsaki tareda
sakin kwafa ya shige daki na rakashi da harara ina cewa a fili
“Wallahi ba tsaki ba kome zakayi sedai kayi, bazan karbi raino ba, rainon ma yar Amirah yarinyar da duk
zamana da ita idan dana ze tsaga guri saboda kuka bazata dauke shi ba balle aje ga tsarkin kashi ko
wanka shine ni ga jaka yanzu ta haifa za’a dakko a kawo mun in riqe mata toh ko daga turu aka kuntota
qarewar rashin nutsuwa sedai duk handa za’ayi ayi”. Tsaf nasan yaji ni dan da qarfi nayi saboda yajin, na
koma kan kujera na zauna, se kuma na miqe na dakko wayata na dokawa Dadar su kira dan fa karma inji
wata magana daga baya.

Ringing biyu ta dauki wayar, a taqaice na gaisheta ta amsa kafin na shiga koro mata jawabin yanda
mukayi da Bashir, na rufe da cewa “Iya gaskiya ta na fada ko bana aiki bazan riqe mata ya ba kowa ya
kula da nasa Allah ya taya masa, idan kuma Ya dage akan hakan to sedai na bar masa nawa nima ya
nemo wadda zata riqe masa su ni intafi”. Shiru Dada tayi har na kai qarshe sannan ta numfasa tace

“Ya kirani ya gayamun kuma na gaya masa wannan ba me yuwa bane, todai yanzu duk se hankalin ku ya
kwanta tunda Allah ma ya raba muku gardamar ya karbi abarsa, se kowa yayi haquri ya maida wuqar”
Dadan ta fada cikin sanyin murya,

“Hasbunallahu wani’imal wakeel, ta rasu jikin ne ya sake tashi?” Na tambayeta a rude dan maganar ta
dake ni dagaske, “ta rasu yanzu Likitan ya kira Naziru yake gaya masa lafiya lau dan yau sukayi niyyar
sallamarta ma har an yi mata wanka ma sun bata madara tayi bacci to daga baccin ne kuma bata farka
ba”.

“Allah yasa me ceto ce, ya musanya mana da wadda tafi ta Alkahiri” Na fada a sanyaya tareda sauke
wayar daga kunne na, ina dagowa muka hada ido da Bashir daya fito kamar wanda aka koro.

“Se ki zuba ruwa a qasa kisha, da baki karbeta ba ta mutu” ya fada yana jifana da wani irin kallo kamar ni
na kashe masa ita. Sena miqe na nufe shi ina cewa “karbarta ko akasin haka be isa ya chanza hukuncin
Allah akanta ba tunda babu dayan mu daya halicceta ko kuma ranta yake hannunsa dan haka ko tana
gidan nan tunda wa’adinta yayi dole ta mutu, in zuba ruwa a qasa nasha kuma bani zaka gayawa ba
Uwarta da tai sanadinta can zakaje ka gayawa dan ita ta nuna a fili bata damu da ita ba” na wuce shi na
shige dakina tareda banko qofa, in banda ma rainin hankali ji abinda fa yake cewa fa.

Ina ciki naji tashin motarsa alamar fita yayi a raina nace a sauka Lafiya Allah ya gani qilan zamanta ze iya
zama fitina shiyasa Allah ya karbi abarsa, Har qarfe biyar ina dakin fito ba, gaba daya zuciyata a jagule
take ga alhinin rasuwar Iman ga soki burutsun Bashir na sake kiran Dada nayi musu ta’aziyya ta cikin
wayar ina iya jiyo kururuwar Amirah da muryoyin mutane wasu na tausarta wasu kuma suna mata fada
akan kukan da takeyi.

Na tausaya mata harga Allah Kuka kam dole tayi shi wannan duka wani kan wani amma yata iya haka
Allah ya tsara abinsa masu samari da yammata ma ake dauka bare ita jaririyar da ba dadewa tayi ba.

Har na miqe da niyyar zuwana dora abinci wani tunani yazo mun, ta yuwu fa Bashir ya tafi Gombe be
gayamun ba ga yara a makaranta lokacin tashin su tuni ya wuce, Hijabi na na dauka da wayata na fita,
bari naje na ari motar Anty na dakko su dan tawa tana gurin Service ba’a dawo da ita ba, ina kulle qofar
gidan motar sa na tsayawa da yaran ya dakko su se na bude na koma ciki ina jiransu.

“Mami ina zakije” Abdallah ya fada bayan daya rungume ni, “Da zuwa zanyi na dakko ku na zata Abbi ya
tafi Gombe” na fada ina kallon Bashir daya shigo a sanyaye kaman wanda aka sheqawa ruwan sanyi.

“Abbi yace Baby Iman ta rasu wai Mami” Farida ta fada fuskarta kaman zatayi kuka, sena riqo hannunta
ina cewa “ta rasu Farida” kaman tana jira kuwa ta saka kuka tanacewa “kenan banida sister mace yanzu
har fa na fadawa friends dina yau a school step mum din mu ta haifo mun baby sis”

“Dallah malama yi mana shiru, kina kallon yarinya kamar mage dama ai kinsan mutuwa zatayi kuma ai
ma...”

“Shut up You are very stupid Aliyu” Bashir da yake shan ruwa a dispenser ya katse Aliyu cikin tsawar da
harni seda na tsorata amma ko gezau yaron nan beyi ba sema ido daya zubawa uban suna kallon kallo
kamar wasu zakaru.

“Zaka wuce daga nan ko sena zo na same ka wawan yaro har fada kake daman mutuwa zatayi kenan so
kake ta mutu koh” Bashir din ya sake fada cikin bacin rai, se na saki hannun Farida da Abdallah na miqe
da niyyar yin magana Aliyu ya rigani yana cewa
“Toh ni Abbi me nace kawai dan na fadi gaskiya wayace su jagwalgwalata sannan su sakata a sanyi ai
dole ta mutu....” be rufe bakinsa ba Bashir ya dauke shi da mari da har seda gefen bakin sa ya fashe
kafin ya fizgo shi ya hau dukansa.

Kuka yaran suka saka gaba daya ganin abinda be taba faruwa ba a gidan yau Bashir ne yake dukan Aliyu
kamar wanda ya samu jaki, tsakiyar su na shiga ina qoqarin kwatar Aliyu da ko gezau sema cewa da yake
yi

“Ai daman seda nace miki ki koreta daga gidan mu muguwa ce kika qi seda ta aure shi, gashi nan yanzu
yafi son su akan mu tunda ta haifi yarinyar nan kina kallo yanda hankalinsa ya koma kanta komai ita har
comapany da ze bude da sunan Farida ma ya chanza na gani sunanta ya saka, shi yasa kullum nayi sallah
sena yi Addu’a Allah yasa ta mutu dan akan Abbi ze iya yin komai gashinan kuma kina gani”.

Bige bakinsa nayi ina fashewa da kukan nima dan na kasa tare dukan da Bashir yake masa shi kuma
yaqiyin shiru nasan kalaman sa ne suke qara tunzurashi seda ya gaji dan kansa kafin ya kyale shi ya shige
dakinsa ya banko qofar ya barmu muna rusa kuka kamar nan ne gidan mutuwar.

Wannan wane irin bala’ine, ni na kashe yarinyar ko Yara na da ze huce akan mu? Ai kuwa wallahi da sake
zan dauki komai amma banda irin wannan dukan da kalaman da basu dace ba akan yarana.

WATA KISHIYAR

(ALKAHIRI CE KO SHARRI)

Na Maryamah Farouk

(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)

Wattpad @MaryamahMrsAm
Page 25

Ina kuka ina gasawa Aliyu fuskarsa da ta kumbura sosai saboda marin daya sha a hannun Bashir,
tausayin sa ya cikani tabbas be kyauta ba amma ai dukan yayi yawa, Yanda ya zage ya ringa dukansa
kamar wanda yake dambe da sa’ansa.

Gaba daya yaran suna tsaye sunyi cirko cirko kowa fuska da hawaye kana kallonsu kasan a tsorace suke,
bude qofar da Bashir yayi da qarfi yasa suka zabura kafin kace meye wannan sun maqalqaleni wani kan
wani Jafar yana cewa “kice masa yayi haquri Mami dan Allah karya doke mu”.

Tausayinsu da matuqar takaicin Bashir ya sake qume ni, na daga idanuwana da har sun qanqance saboda
kuka na kalleshi yana tsaye shima mu yake kallo, fuskarsa a daure tam haka idanunsa sun kada sunyi jajir
har wata jiniyace ta fito a goshinsa. Daga tsayen yace mun “Ina kika saka mun folder dana ajiye akan
Gado”.

Ayanda nake jina Banyi niyyar tanka masa ba amma saboda yaran da suke gurin bana so na bada qofar
da zamu ringa raba hali a gabansu dan hakan ze shafi tarbiyyar su, “Ina zuwa” nace masa kafin na miqe
na kama Aliyun da zuwa sannan jikinsa ya rufe da zazzabi me zafi amma saboda dakiya da taurin kai har
sannan ko digon kwalla babu a idonsa.

Dakinsu na rakashi, ina tsaye ya shiga ya watsa ruwa a jikinsa ya fito dakyar ya kwanta akan gadonsa. A
cikin first Aid box dinsu na ciro masa Paracetamol na bashi yasha, ina zaune a gefen kansa nace

“Aliyu kana babba kai kake so ka raba kan qannenka ko, irin abinda na koya muku kenan ka tsaya
mahaifinka yana fada kana fada Aliyu?”

Se a lokacin ya saka kuka yana cewa “Mami Abbi ya canza wallahi ya dena son mu, da bakwayin fada
amma yanzu kullum se sukunyi kuma duk akan Anty Amirah ne. Mami yanzu fa da muna tahowa yana
waya da Abokinsa Uncle Bala yana ce masa daman bakya son yarinyar yace ze kawo miki ita kinqi yanzu
gashi ta mutu hankalinki seya kwanta ai”.
Shiru nayi ina shafa kansa, wato a gabansu ma ya fadi haka kenan, tabbas shi ya bada qofar da yaran
zasu ga baqin sa ko bayan haka yana sane Aliyu ai photocopy dinsa ne daman, duk wani hali daya ke
taqama dashi Aliyun ya kwasa harda qari dan badan ma Irinta Allah ya bawa Aliyun a matsayin uwa ba
da ba qaramin wuyarsa za’a sha ba.

Numfashi naja kafin nace “koma menene karna sake gani, Abbinku yana sonku ka sani irin son da
yakeyiwa Iman, ba fata ba yau ko daya daga cikin mu ya rasa irin damuwar da ze shiga kenan kasan
halinsa kuma idan yana cikin damuwa Fada yakeyi da kowa. Dan haka ka kiyaye Aliyu karna sake jin wata
magana irin haka kaine babba komai kayi qannenka suna koyi da kai ko so kake Allah yayi fushi daku
kuna sabawa mahaifinku?”

Girgiza kai yayi a sanyaye, na ci gaba da cewa “yawwa Haidar dina kar a sake, gobe kuma ka same ahi ka
bashi haquri kaji ko dan yanzu dai be huce ba”

“Insha Allah Mami bazan sake ba” ya fada.

“Yauwa Allah yayi muku albarka ya kulamun da rayuwarku”

“Amin Mami, I kove you”

“I love you more” na fada tareda kissing goshinsa kafin na ja masa bargo na fita.

Seda na lallaba sauran suka cire uniform na dora farar shinkafa dan ina da miya na barwa Amna ta duba
sannan na tafi dakin nasa.

Ina tura qofar yana sako kai ze fito, ya watsamun kallon banza na mayar masa da martani na shige se ya
biyo ni yana cewa “Wato daman abinda kike gayawa yaran nan kenan kina koya musu mugun hali har
Aliyu yana fadar na fi son Amirah akan su ko?”

Banza na bawa ajiyarsa, na jawo drawer dana saka folder na dire masa akan gadon kafin na miqe na nufi
qofa.
“Ma’u” ya kira suna na kafin yaci gaba da cewa

“Wato Ma’u kin rainani, saboda wulaqanci da rashin mutunchi ina miki magana shine kika sa kai zaki tafi
bayan tara yayana da kike yi kina cusa musu tsana ta a zuciyar su ko?”

Tsabar mamaki daskarewa nayi a guri daya na kasa gaba na kasa baya, wace kalar kwaya Bashir yasha
ne? Ko kuma rasa Ÿa hauka ne ko a kansa aka fara, kai da alama dai kawai Bashir ya shirya ci mun
mutunchi ne idan ba haka ba ya gama jibgar mun Da sannan ya kalleni yace wai ina masa wulaqanci da
rashin mutunchi, waiwayawa nayi na gyara tsayuwata sosai ina kallonsa

“Wulaqanci ko rashin mutunchi ba tarbiyyata bane dan da ace na iya da bamu kai shekara goma sha
shida tare da kai ba, batun in tara yaran ka kuma in cusa musu tsanarka..” na dan dakata tareda qara
taku biyu na dawo gabansa sosai, murmushi nayi me kama da yaqe kafin na ci gaba da cewa

“Base na zugasu akan ka ba, yanda kyakykyawar mu’amalarka gare su ta sa suke sonka haka sababbin
halayen daka tsiro dasu zasu bi su goge duk wannan so da shaquwar da kake gani a tsakanin ku, sannan
kayi a hankali duk abinda yaro ya gani a gurin iyayensa tarbiyyar da ze tashi da ita kenan musamman kai
me Ÿaya maza zasu tashi su zata abin kirki kake aikatawa kaga haka zasu tafi da matan da.....”

“Ya isheki Asma’u” Bashir ya katse ni cikin hargagi tareda daga hannunsa ya nufoni da niyyar mari, sedai
ko me ya tuna ya janye tareda kaiwa Bangon dayake bayan mu naushi sannan ya juya ya dafe kansa yana
huci kamar wanda ya hadiyi kunama.

Tabbas na tsorata, na kuma saddaqar sheya shararamun mari a yanda ya nufo ni amma taurin zuciya da
dakiyar dana dorawa zuciya ta bata sa baki na ya mutu ba,

kallonsa nayi da kallon da ni kaina bazan iya fassara shi ba, na tsana ne ko na takaici da baqin cikin
abinda Bashir yakeyi mun nace
“Nima dukana zakayi kamar yanda ka kusa illata danka gashi can kwance, to ka tabbata hakan shine abu
na qarshe da kwakwalwarka zata raya maka akaina dan wallahi Bashir sekayi dana sanin dora hannunka
a jikina da sunan duka, har Mahaifina ya koma ga Allah ban taba ganin ya dagawa daya daga cikin
matansa murya ba ballantana har ya dake su se kai kake tunanin zaka daki yar sa? Toh bismillah” na fada
ina zare masa ido kamar wani dana.

Naga alamar se nayi masa haukan gaske sanann ze shiga hankalin sa, wata irin tsanar Amirah ce tayi
mun dirar mikiya dan itace sila, ita ta janyo komai da yake faruwa da be aure ta ba da haryanzu muna
cikin zaman lafiyar mu da qaunar juna amma tunda ta shigo rayuwar mu abubuwa suke rinchabe mana
bamu taba rufa sati ba tareda munyi tashin hankali da Bashir ba.

Shiru mukayi gaba daya, ni ina jiran ya sake wata magana ko yunqurin marin nawa dan wallahi sena
gwada masa nima yar buyagi ce yau amma se yai shiru, kiran Sallar Magriba ya sakashi shigewa Toilet ya
bugu qofar da qarfin gaske se na bishi da harara kafin na ja dogon tsaki na fice daga dakin.

Seda na tashi Aliyu na sake bashi awa paracetamol bayan yaci abinci yayi sallah kafin bacci ya sake dauke
shi, gaba dayan su basu da walwala haka na daure na ringa tausarsu har sukaci abinci sunayin sallar isha
kuwa kowa ya nemi makwanci sa har yan biyu da suke qanana sun shiga nutsuwarsu dan Muhammad
dayaga Bashir ya fito daga dakinsa ze shiga Kitchen ma kuka ya saka ya rirriqe Jafar.

Ina kallon yanda yai turus yana kallon yaron, duk da fuskarsa bata nuna ba amma jikinsa yayi la’asar
daga gani cike yake da nadamar abinda ya aikata amma izza irin tasa bazata barshi aga gazawarsa ba.

Palour na dawo na zauna bayan duk sun shiga daki ina jiran kota kwana, jira nake naji ko Bashir zece na
bashi abinci ko ya sake gayamun wata maganar banza a daren nannayi masa wankin babban bargo
amma shiru har sha daya ina zaune ban sake jin motsinsa ba.

Dakina na shige nayi wanka, Idona sun soye bana jin bacci dan haka nayi Alwala nayita jera salloli ina
kaiwa Allah kukana har seda gabbaina suka gaji kafin na kwanta ina ci gaba da jan carbi.

Nayi niyyar washe garin na kira Amirah da Addah nayi musu gaisuwa amma wallahi na fasa, na kuma
shirya duk wanda ya sake bude baki ya gayamun zancen banza a gidan nan bazan daga qafa ba sena gaya
masa na wofi.
Da safe ban jira shi ba na shirya yara na kaisu Makaranta a motarsa daya bar Key akan Dining be dauke
ba. Tare muka fita da Aliyu bayan na bada excuse din bashida lafiya na wuce dashi Asibiti aka sake duba
shi suka rubuta masa magani muka dawo gida.

Ina Kitchen ina dama masa wa Aliyu custard naji fitowar Bashir daga daki, sena dawo bakin qofar na leqa
tareda kasa kunne ina jin Aliyun yana gaishe shi, se ya amsa harda tambayarsa yaya jikinsa yace da sauqi.

“Abbi kayi haquri bazan sake ba” naji Aliyun yana fada, se Bashir yace

“Ya wuce Aliyu kaima kayi haquri ina cikin fushi ne na dake ka gashi har naja maka ciwo, kaci abinci muje
na kaika Asibiti a duba ka” Bashir ya fada, se Aliyun ya nuna masa ledar magungunan da muka siyo yace

“Mami ta kaini yanzu ga magani ma an bani”

“Ok Allah ya qara sauqi, ka huta sosai kaji bari naje office nakai papers din nan.

“Yawwa yaron kirki ga shi tashi kasha” na fada ina ajiye masa.

Nida Aliyu muka wuni a gidan ya warware har yana tayani aiki munata hirar mu, qarfe hudu har na kira
Uber zan tafi dakko yara se gasu sun shigo wai Driver Office dinsu Abbi ne ya dakko su.

Bashir ne dawo gidan ba se 9 na dare, muna zaune muna kallo ya shigo da sallama hannunsa dukka biyu
da ledoji, Kallon cikin ido mukayiwa juna kafin na janye nawa ina tabe baki yara suka tashi suna masa
sannu da zuwa ya amsa ya basu ledojin hannunsa manya guda biyu ya wuce da qaramar dakinsa.

Be dade da shiga ba ya kwalawa Aliyu kira ya tashi ya tafi sauran suka bude ledojin, tarkace ne kowa
Abinda yafi so ya siyo masa, indai yaudara ce ya kware daman, ya zuga rashin mutunchi sannan ya siye
ka da abinda yasan kana so. Ina jinsu suna tsallen murna banbi takansu ba.
Aliyu ne ya fito ya debi abinci a plate ya hada da ruwa da cup akan Try yaje ya kai masa ina kallonsa ban
ce masa komai ba ya sake dawowa ya debi zobon dana hada ya kai masa.

Da gudu ya fito daga dakin yana tsalle da ihun murna na waiwaya ina cewa “kai meye haka zaka zo kana
mana ihu akai”

“Kukalla ku kalla” ya fada yana daga kwalin wayoyi iphone X guda biyu, Amna ya jefawa daya kafin ya
zauna cikin zumudi ya shiga bude ta hannunsa.

“Yaya waya aka siya muku” Jafar ya fada yana komawa kusa dashi,

“Wallahi Mamai waya ce, yeee munzama yan gayu muma Faree mun samu tayim snap” Amna ta fada
tana daga wayar tata Fara ta Aliyu Baqa. Duk su biyun suka dawo kusa dani suna nuna mun, na karba ina
cewa “iye yan gatan Abbi gaskiya kun gode Allah ya sanya Alkahiri ya sa lafiya ta kashe”.

Gaba daya sun cika gurin da ihun murna, sun dade suna nacin a siya musu waya amma yaqi yace se sun
gama secondary school idan zasu kira abokansu sedai su karbi tawa ko tasa kowannensu dai yana da
Laptop itama dan dokar makarantar suce amma yanzu da yake neman shiri yake da yaran shine ya siyo
musu da kansa, Bashir kenan.

Ana tsaka da murnar ya fito da plate din abincin, Jafar ya tashi da gudu ya karbo yana cewa “Abbi mufa,
se yaushe za’a siya mana?”

“Ba yanzu ba Sheik baku isa riqe waya ba amma zan chanza muku PS 5 gobe kuma za’a kawo muku” ya
fada yana zama akan kujerar da take kallon wadda nake kai. Sabon ihu suka dauka harda yan biyu dan
suma sun koya musu Game, ba damar a samu zama a gida anyita buga PS sena gaji wani lokacin na
dauke.

Ina kallon yanda yake ta wani murmushi yana jin dadi ganin yaran na murna an shirya kenan, yana
kallona na sake hade girar sama data qasa, sen miqe ma ina cewa Farida idan sun gama tura hotunan da
sukeyi daga wayata ta miqomun na shige dakina a jikana ina jin yanda ya bini da kallo amma ban
waiwaya ba.

A dakin ma ban zauna ba, wanka na shiga nayi shirin bacci, sena dakko Backpack din da nake zuwa office
da ita na fito da kayan ciki ina dubawa dan nima ranar Monday zan koma aiki in Allah ya kaimu, gajiya da
jiran Farida nayi sena leqa dan ina so na kwanta har sannan suna zaune Bashir na nuna musu ko menene
oho a wayarsa.

“Farida bani wayata, bazaku tashi kuje ku kwanta ba ko gobe akwai school fa” na fada daga bakin qofa.
Seta taso da gudu ta bani ta sake komawa,

“Oh ina magana duk kunyi mun shiru ko” na sake fada, se Bashir ya dago yace

“Babu aiki gobe Workers day”

“Au toh, seda safen ku” na fada ina juyawa ciki.

Harna kwanta naji message ya shigo wayata, kamar bazan duba ba sedai na janyota, Bashir ne

“Ina son magana dake” ya rubuta. Guntun tsaki nayi na maida wayar na ajiye naja bargo na,

Befi minti uku ba tsakani kira ya shigo, sauri nayi na sakata a silent, ina kallo seda yai kira uku nai likimo
abuna dan bazan dauka ba, wato nice baze lallaba ba tunda ya shirya da yayansa shikenan ba ina cikin
wannan tunanin naji an turo qofa.

Luqus nayi harda wurga qafa gefe dan fitila a kashe take ni a dole bacci nakeyi, ina jinsa ya kunna hasken
ya tsaya akaina yana kallona.

“Ma’u Ma’u” ya fada yana bubbuga pillow da nake kai, senayi miqa tareda qantsarewa ina salati irin an
tashen nin nan nayi mici mici da ido ina kallonsa nace “Lafiya zaka zo kana tashina a bacci”.

Seda ya zauna gefen qafafuna ya wani kumbura baki yace “baki ga message dina ba da calls dina ba?”
“A mafarki ka turomun halan” na fada ina tura baki gaba. Se da yayi kwafa sannan yace “saboda abinda
ya faru yasa kika dauki fushi dani, naga wanda na doka din ma mun shirya se kece zaki ci gaba da gaba
dani”

“Ni kuma inyi fushi dakai ana me Baban Ali space dai na baka ka gama zaman makokin idan ka dangana
kayi tawakkali se mu ci gaba da magana” na katse shi ina gyara kwanciya, gajeran tsaki yaja kafin yace

“Oh banida tawakkali kenan”

“Ni awa ince baka da tawakkali, hausa nayi maka bawai abinda nake nufi kenan ba” na fada ina danne
dariyar dake neman kufce mun ganin yanda yai kinini da fuska yana jan iska.

“Gobe da asuba zamu tafi Delta inaga zamuyi kwana biyar ko sati saboda tafiyar nema yasa ban tafi
Gombe ba”

“Allah ya kaiku lafiya ya dawo daku lafiya” na fada a qagare dan na fara jin baccin gaske, se ya miqe yana
cewa “ta so muje can, ban hada kaya ba kuma ina so nayi bacci kinga fitar Asuba zamuyi”.

“Yi gaba gani nan” na fada ina miqewa kamar zan shiga bandaki, yana fita na rufe qofar na murza key, a
fili nace “Dan rainin wayo sedai ka tafi babu kayan kuwa” nai hayewata Gado na kwanta ina jinsa yana
kiran suna na yana kwankwasa qofar a hankali nayi biris dashi harya gaji ya tafi, duk randa ya koyi karbar
laifinsa, ya iaya bada haquri ma shirya.

Da Asuba da muka hadu kamar kububuwa ya wuceni ya shiga kitchen, ya gama diri dirinsa ya fito daman
nasan ba abinda ze iya tsinanawa mutumin da inaga ruwan zafi kadai yasan yanda ake dafawa. Amna ya
kwalawa kira ta fito daga dakinsu yace maza ta soya masa kwai.

Ina kallonsa ya shiga dakin ya fito yana doka uban tsaki ya kalli inda nake ya sake komawa seda ya shiga
sau biyu ana ukun ne yace “Dan Allah Ma’u kizo ki hadamun kaya su Musa har sun kusa qarasowa”
“Au wai baka hada kayan ba me kake jira toh” na fada ina tashi zaune akan kujera.

“Kin sani ban iya ba ke kike hadamun, please Ma’u”.

“Badan halinka ba muje” na fada ina miqewa. Kusan rabin wardrobe din ya watso su qasa, cikeda takaici
na shiga hada masa kayan a qaramar akwati na gama ina zugewa ya shigo da kofin shayi a hannunsa ya
ajiye akan mudubi yana cewa “har kin gama”

Ban amsa ba na shiga kwashe na qasan ina mayarwa, horn da muka jiyo daga waje yasa na dakata na
daukar masa Laptop bag dinsa shi kuma yaja akwatin muka fito, Jafar na tsaye a kofar dakin su ya gaishe
shi yace “Abbi a kawo fa”

“Za’a kawo Sheik ina sauran yan uwanka”

“Sun koma bacci Abbi”

“Ok idan sun tashi ka gaya musu na tafi Delta zamuyi waya idan na sauka” ya fada yana tafiya.

“Allah ya tsare Abbi” Amna da Jafar suka fada. Daga bakin qofa na tsaya ya miqawa Driver Akwatin ya
karbi jakar hannuna bayan na masa Adawo lafiya naja kofar na koma ciki. Seda na kwashe kayan da ya
zubar tsaf ina mita “Abinda ko Su Muhammmad baza suyi mun ba shi yake yi, da yake buqatar kansa ce
ai ya iya roqa a masa mtsw” naja tsaki.

A dakin na kwanta na qarasa baccina.

GOMBE

Acan Gombe kuwa ranar talatar da safe Bashir sukayi waya da Naziru ya gaya masa yaje Asibiti ya karbi
Iman daga nan ya wuce da ita gurin Dada kafin ya gama yanke abinda za’ayi.
“Ni se nake ganin yaya da kayi haquri, be kamata ace ka raba Uwa da yarta ba idan kayi haka kamar ai
bakayiwa Amirah da ita kanta Babyn Adalci ba. A yanayinta tana buqatar dumin uwa da kuma Nono ko
dan ingancin lafiyarta” Naziru ya fada bayan da ya gama jin umarnin yayan nasa.

Shiru Bashir yayi, Tabbas gaskiya Nazirun ya fada amma toh amma meye amfani mayar mata da ita ma
yanzu bayan ta riga ta yaye ta kusan sati bata sha Nonon ba se madara ai dakyar ma idan zata karba
yasan, kuma fa shi ya gama yanke hukuncin sa ta hakane kadai ze hukunta Amirah taji a jikinta yanda
gobe bazata sake gwada yin abinda tayi ba.

“Kaje kawai ayi yanda nace, na rigada munyi magana da Dadan, zuwa Next week idan na samu dama
zanzo nan Lagos zan dawo da gurin Ma’u”

“Anty kuma? Ita tace zata riqeta?” Naziru ya tambaya cikin mamaki. Se Bashir din yace

“No, bata rigada ta amsa ba amma ai gida nane ina da ikon sawa da hanawa ko”

“Hakane” Naziru ya fada sukayi sallama, a ransa yana mamakin wannan zallar rashin Adalci irin na dan
uwan nasa. Tayaya zaka taba jaririya da uwarta ka dauka ka kaiwa wata wadda ita kanta tana da buqatar
me taimaka mata. Ÿaÿa Bakwai nefa a gaban ta take kula dasu ga shi sannan kullum seta fita aiki ai
wallahi ko ita kanta yanzu kamata yayi yace ta dakata da haihuwa ta ji da abinda yake a gabanta balle
har ya dauki raino ana zaune lafiya ya kai mata.

Daman lokacin daga wanka ya fito dan haka ya zura rigarsa ya cewa Dada bari yaje Asibitin ya karbo
yarinyar “Amma fa Dada kiyi masa magana idan ba haka ba wallahi ze janyo abinda za’a zo ana samun
sabani daga qarshe kuma ace za’a ga laifin Anty Ma’u” ya fada yana tsaye daga bakin qofa.

“Ka rabu dashi Naziru, gurin uwarta za’a maida ta, shi a ina ma ya taba ganin anyi haka? Idan so yake ya
kaita cikin yan uwanta se ya bari idan Allah ya rayata ta isa sakawa a makaranta a sannan yana da hujjar
da ze iya dauketa ya maida ita can ko dan ta samu ilimi irin na sauran amma ba yanzu ba. Ni wallahi na
rasa me yake damun Bashir, mutum tamkar wanda yake da wani motsi a kansa”.
“Ba wani motsi wallahi Dada tsabar samun gurine tunda yaga duk sharar daya debo kina goya masa baya
shiyasa”.

“Yanzu dai jeka, idan ka dawo se muje tare can gidan nasa, dukda ya kamata na kirashi ma yabar
yarinyar nan ta koma gida tayi jego ko ta dawo nan dole se an taimaka mata kafin ta saba ai” Dada ta
fada, Naziru yayi mata sallama ya tafi Asibiti.

Yana zuwa ya tarar da wannan tashin hankalin, bashida karfin guiwar kiran Bashir dan haka likitan ne ya
kirashi shi kuma ya kirawo Dada ya gaya mata.

Bayan an gama cike ciken takardu ya saka hannu aka bashi gawar, be iya tafiya ba seda Ya kira Sa’ad
Yayansa da yake bi yazo suka tafi tare suna kaita gida Dada tace suje su dakko Amiran sannan ta kira
Ummi a waya tace suzo ita da Addah yanzu.

Fadar tashin hankalin da Amirah ta shiga bata baki ne dan sumanta uku ta ringa kururuwa tana ihu
kamar wadda ta hau bori, se da Goggo Ladi qanwar Alhajin su Bashir tayi mata tatas sannan aka samu ta
lafa da ihun amma fa bata dena kukan ba.

Addah kanta tasha kuka fadi take daman yan baqin ciki basu so aka haifeta ba gashi yanzu anyi
manaqisar da seda aka rabata da duniya su dai Allah ya isan su bazasu yafe ba.

Babu wanda ya ko bi ta kanta, da dare yayi zata tafi da Amirah Alhajin su Bashir ya hana yace ta barta
acan dan yasan idan sun tafi ma a maimakon ta taishe ta Allah kadai yasan abinda zata je ta kitsa mata
kuma.

A wayar Ummi Bashir sukayi magana da Amirah, yanda ta ringa ya bala’in daga masa hankali gaba daya
tausayinta ya rufe shi. Allah ya sani yana son yara kuma wannan yarinyar haka kawai yaji duk cikin Ÿaÿan
sa tafi shiga ransa kamar sanda aka haifi Farida sedai har nata ya zarce Faridan.
Badan Assignment din da yake gabansa ba da a ranar yaso yaje amma ya mata Alqawari daya gama zezo
Gombe, ya ringa rarrashinta yana gaya mata kalamai masu kwantar da hankali tareda Alqawarin kwanan
nan zasu samu wata qilan ma yan biyu, da haka ya samu tayi shiru har tayi bacci sannan ya kashe wayar.

Kunsan December watan hidima ne weddings everywhere

To all the December brides Allah bada zaman lafiya

WATA KISHIYAR

(ALKAHIRI CE KO SHARRI)

Na Maryamah Farouk

(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)

Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 26

Har Bashir ya gama kwanakin sa a Delta ba wani magana mukeyi ba, a ranar da ya tafi dai bayan sun
sauka ya kirani haka washe gari da safe kafin su fita field munyi waya bayan nan kuwa har suka kwana
hudu be sake kirana ba nima kuma ban kirashi ba.

A tunani na ko aiki ne yayi masa yawa, dan daman yawan ci idan yana field bamu cika yin waya ba shine
dai idan ya samu lokaci ze kira to wannan karon ma na dauka a hakan ne.
Ranar Lahadin da suka kwana hudu da daddare muna zaune wayar Aliyu dake kusa da ni tayi qara,

"Aliyu wato har ka rarrabawa Jama'a Number ka ni bani da ita koh, waye yake kiranka da daren nan?" Na
daga wayar ina dubawa.

"Super hero" naga an saka, na gane Number Bashir ce sena miqa masa ina cewa "uhm uhm su Bat Man
ne ko Spider man naga an sa super hero".

Gaba daya suka saka dariya, Aliyu ya daga wayar suka gaisa, ban san meya gaya masa ba nadai ji yace
"toh ga Mamin ma ko na bata ka gaya mata?"

"Tam Abbi bye" ya sake fada kafin ya kashe wayar yana kallona.

"Mami, Abbi yace Mr Kunle ze zo yanzu ya kawo saqo, akwai kudi a bedside drawer dinsa ki bashi 20k".

Kamar wata sokuwa haka nake kallon Aliyun harya gama. Abubuwan mamakin da yawa, ashe Bashir
yana da lokacin kiran waya nice baze kira ba.

Sannan yaushe muka fara haka da ze fadi abu ni baze kirani da kansa ya gaya mun ba sedai ya kira Aliyu?

Wayata dake kan centre table na janyo na danna power button dan na tabbatar ko a kashe take be
sameni ba ya kira Aliyun naga a kunne take. Ga network dina full to meye dalili?

"Hmmmm" na fada a fili kawai na ci gaba da kallon da muke, ba'a jima ba kuwa aka danna Door Bell
Jafar yaje ya bude se gashi da Babban Package da alama PS din da aka ishe ni da naci kamar nina ce zan
siya aka kawo.

"Mami yana jiran saqon wai" ya fada bayan ya zauna ya fara budewa Abdallah na taya shi.

Se na waiwaya na kalli Aliyu nace


"Kaje ka dakko masa baya gaya maka inda suke ba?"

Seda yai dan jim kafin ya miqe ya shiga dakin nasa, be jima ba ya fito da kudin a hannunsa ya miqo mun
yana cewa "Gashi na dakko".

A hasale nace masa "zaka tashin mun akai ne ko yaya, ina kai ya gayawa saqon kuma kazo kana
nunamun me zanyi dasu".

Zugui zugui ya fice ya kaiwa Kunle kudin ya dawo. Ina kallon yanda yake satar kallona ganin na dora qafa
daya kan daya ina girgizawa duk sanda suka ga ina haka to sun san zuciyata a kusa take, ina iya make su
idan suka matsamun.

Hayaniyar da Jafar da Aliyu suka fara suna qoqarin jona PS din da Tv tasa na daka mutsu tsawa ina cewa
"ku bace mun a nan, ba gobe Monday ba shine a wannan lokacin kuke shirin dasa wata Game, ku tattara
ko yanzu na fasata wallahi".

Kama kansu sukayi sum sum gaba daya suka watse, ina zaune ina sakin tsaki, son na tabbatar da zargina
sena janyo wayata na dokawa Bashir kira na kuwa taki sa'a akace call waiting.

A da, indai na kira Bashir ko da wa yake waya se ya dakata ya amsa kirana, ba qaramar waya me
muhimmanci bace zan kirashi ya kasa katseta amma yau har ta gama ringing ta yanke be daga ba.

Na sake kira nan ma be daga ba, seda na jera masa kira hudu amma bawan Allahn nan ko a jikinsa kuma
har sannan call waiting.

Agogo na kalla, tara harda rabi tayi, nasan babu wani official call da ze ce yana yi yanzu, kuma na tabbata
bada Dada yake waya ba dan sanin da na mata da Tayi Isha take kwanciya to da uwar wa yake waya da
baze amsa tawa ba?
"Amirah" zuciya ta ta raya mun, se ta yuwu kuwa din. A jiye wayar nayi ina jiran ya biyo baya amma har
goma da rabi shiru ba kiran Bashir babu labarinsa, sena miqe jiki a sanyaye na shiga dakina.

Tunani na shigayi ko na masa wani abu a wayar da mukayi qarshe, iya hasashena ban gano komai ba dan
lafiya mukayi hira kamar ma be tafi muna fushi da juna ba. Haka na ringa juyi a gado ina tunane tunane
to wane sabon shafin ne kuma ze bude mun, koma dai menene Allah ya bamu wuce wa lafiya da haka
bacci yayi awon gaba dani.

Daga mamaki mani abun na Bashir tsoro ya koma bani, dan fa washe gari be biyo kirana ba, da yake na
koma aiki nima ranar na shiga busy ban wani nutsu ba se da daddare na duba wayar na tabbatar da be
kira ba kuma qarin abun mamaki da magriba ma seda ya kira Aliyu ya bawa dukka yaran sukayi waya
harda tambayar me ze taho musu dashi.

Nidai ido na kawo na zubawa sarautar Allah, duk tsiya dai ze dawo gidan se inji me ya faru kuma.

Na zata ranar Larabar ze dawo tunda itace cikar sati da tafiyar su daman kwana biyar yace ko sati to
gashi har yau Talata dan haka na saddaqar se gobe ze dawo.

Bayan na tashi aiki na biya na dakko yara, dukda magriba ta kawo kai haka na biya wata yar kasuwa da
ake siyar da Dangin su Kaji masu rai, Bashir yana son Danderun Zabi dan haka na siyi manya guda biyu
aka yanka su aka fige kamun muka kamo hanyar gida Ba mu muka isa ba se ana shirin shiga sallar Isha
saboda holdup.

Jakata kawai na ajiye muka shiga Kitchen tareda Amna, seda na wanke Zabon tsaf yanda nake so kafin na
saka a kwando su tsane na bar Amna ta hada kayan hadi dan tana fashin sallah ni kuma na tafi nayi
magriba da Isha .

Sanda na dawo ta hada komai na marinate dan tasan yanda nake so, seda na saka wuqa na huda jikinsu
sosai yanda kayan hadin zasu shiga na shafe lungu da saqo na ko ina ya juqu sannan na nade a Foil paper
ya nadu da kyau, Already ta kunna oven yayi zafi dan haka na dora su akan Baking try da aka zuba ruwa
na kunna wuta sama da qasa na rufe.
Ban san sanda ze dawo ba da safe ne koda daddare dan haka A daren nan seda na hada masa zobo irin
wanda yake so na saka a fridge, na gyara zogale na yanka Albasar da zanyi masa Dambun shinkafa nice
harda dakan gyada kamar aljana na turara tsakin shinkar na saka komai a fridge yanda gobe kawai sedai
na hada.

Na gaji tiqis, haka na koma palour na kwanta ina yi ina duba naman dana saka ina qara ruwan dan karya
qone nice har qarfe biyu, jin bacci na neman fin qarfina na kashe kawai tunda nasan zuwa yanzu yafi
rabin dahuwa in Allah ya kaimu gobe na ci gaba.

Dakyar na iya tashi sallar asuba dan ji nayi kamar ma ina kwanciya aka tashe ni. Haka ina yin sallah na
koma kan aikin, ga shirin yan makaranta da ni kaina. Qarfe bakwai muna breakfast Bashir ya kirani.

Rai a sake na amsa wayar duk da qasan zuciyata akwai haushin qin kirana da yayi amma na daure dan
babu qarya nayi kewarsa sosai, rabon da mu kebe tun muna Gombe.

A dake ya amsa gaisuwar da nayi masa, mukayi shiru gaba daya kafin ya nisa yace

"Yau zamu dawo In sha Allah zuwa dare zan shigo gida".

"Masha Allah, Allah ya dawo daku lafiya nayi kewarka da yawa". Na fada cikin shauqin da na kasa
dakatar da kaina.

Wani miskilin murmushi yayi kafin yace "Na sani ai"

"Oh ka ma sani kenan" na fada adan shagwabe.

"Zan kiraki anjima" ya fada, ko kafin na bashi amsa ya katsewa wayar, sena ajiye na ci gaba da kurbar Tea
na rai fes.

Seda nayi yar murya sannan aka bar yaran suka shiga makaranta saboda mun makara, School Bus nace
su biyo idan an tashi kawai dan inaga idan Bashir ya dawo kawai zan masa magana su ringa bin school
bus din kamar zefi sauqi.
A office ma ban wani maida hankali ba, qarfe biyu na dauki excuse na tafi gida. Seda na gyare gidan qal
na chanza Bedsheet din dakin Bashir na saka turaren wuta.

Kayan harkar dana hada na shanye kafin na dakko wani hadin dilka da Anty ta bani na na mutstsike jikina
tsaf na turara sannan na dauraye jikina na koma Kitchen.

Na riga naci qarfin aikin tun jiya, Danderun na duba yayi luguf dan tun shigowata na ci gaba da bashi
wuta gaba daya gidan ya dume da qamshinsa ga na turaren da nayi se suka hadu suka bada wani kalar
qamshin yan gayu, nan da nan na hada Dambuna sannan na dora tuwon semo da miyar Danyar kubewa
taji naman rago dan Bashir yana sonsa.

Kafin Magriba munyi wanka nida yaran munyi kwalliya yanda kasan ranar sallah. Wata Atamfa na saka
Batik Maroon da akayiwa dinkin A line me dogon hannu babu ado a jiki se aikin stones da aka mata se
walwali takeyi na kashe daurina na baza qamshi duk inda na juya yara se sun ce "kai Mami kinyi kyau
wallahi" ni kuwa se jin dadi nakeyi.

Ina tahiyar qarshe a sallah naji waya ta tana qara kafin nayi sallama ta katse. Bayan na idar na janyota
dan nasan Bashir ne, ilai kuwa wani kiran nasa ya sake shigowa.

"Ranka ya dade Mijin Ma'u, ka iso nazo na bude maka qofa ne" na fada da yar dariya.

Dariyar shima yayi cikin jin dadin sunan dana kira shi yace

"Mun dawo amma ban qara so gida ba"

"Masha Allah, sannunku da dawowa, muna jiranka nida yara mun shirya maka babbar tarba".

"Dagaske, me kika tanadar mun?" Ya tambaye ni, seda na gyara zama kafin nace

"Duk abinda kake so" na bashi Amsa.


"Ke kadai nake So Ma'una" yayi maganar cikin wani salo da yayi mun dirar mikiya dan har seda naji
kamar numfashina ya tsaya na dan lokaci, jikina ya karbi saqon sa dagaske, se na yi qasa da murya kamar
me gudun wani yaji abinda zan fada nace

"Na tana dar maka kaina, kai kadai nake jira Farin cikin Ma'u". Na fada sannan muka kashe waya. Cike da
zumudi na tashi na mayar da dankali na na sake gyara fuskata sosai na qara turare. Palour na dawo
muka zauna motsi kadan mu kalli qofa kowa ya qagara Abbi ya dawo har dai aka kira Isha Malam Bashir
shiru.

Tafi tafi fa har qarfe tara babu Bashir gashi yara har sun fara qorafin yunwa suke ji, se na tashi a sanyaye
na dibar musu abincin bayan sun shimfida Table mat a qasa dan kar a bata gurin suka zauna suka ci.

Muna zaune goma ta buga zuwa sannan hankalina ya fara tashi anya lafiya kuwa gashi na kira wayar sa
har sau biyu bata shiga daga qarshe ma aka ce a kashe take.

Muna tsaye tsuru nida Amna da Aliyu dan ragowar sun kwanta, Aliyu ya kalle ni yace "Mami ko naje na
tambayi Baba Audu naga yana gida".

Se a sannan ma tunanin yazo mun da mu gayawa Baban, na dago kai da niyyar bashi amsa wayata dake
hannuna tayi qara alamar shigowar message. Number Bashir ce, sena bude da sauri na fara karantawa

"I'm sorry Ma'una, na wuce Gombe" Abinda ya rubuta kenan.

Wani duhu ne ya gifta idona na saki wayar a qasa nayi baya kamar zan fadi Amna da Aliyu suka riqe ni,

"Mami meya faru? Wani abu ya samu Abbin?" Aliyu ya shiga tambayata a rikice, dakyar na iya cewa

"Dauko mun Inhaler" se ya sake ni ya tafi da gudu dakina. Wayata Amna ta dauka ta bude, ina kallon ta
bayan ta karanta message din ta goge daidai sanda Aliyu ya dawo yana bani Inhaler ya karbe wayar aga
hannunta yana cewa
"Na gani me aka turo" se ya bude ya kalle ta yace "Ni banga komai ba, Mami wai menene?".

Seda naji numfashi na ya daidaita, Ina da Asthma kuma yawan ci baqin cikin Bashir ne yake motsamun
ita dan ni da na shiga damuwa ko tashin hankali zanji numfashi shina yana sama sama.

"Ku tashi kuje ku kwanta babu komai, ashe ma basu taho ba" na fada ina qoqarin miqewa. Se Aliyu ya
zuba mun ido kamar be yadda da abinda na fada ba, seda na sake maimaitawa sannan suka miqe.

Hannuna ya kama yace "Mami muje ki kwanta toh"

"Aa Aliyu sena kwashe abincin nan karsu lalace" na fada cike da qarfin hali dan na matsu subar gurin ko
zan samu damar fashewa da kukan daya tokare mun maqoshi.

Qarfin hali kawai nayi muka kwashe kayan, ina shiga dakina na jingina da qofar na fashe da wani irin
kuka na zallar baqin ciki da takaici, wannan wane irin wulaqanci ne, meyasa kwata kwata Bashir baya
darajani?

Meyasa ze yaudareni yace yana hanya sannan ya zagaye ya tafi gurin Kishiyata? Idan ya ce mun Gombe
ze wuce ai bazan hana shi ba tunda itama matarsa ce amma wannan ai zalunci ne yasa na bata lokaci na
na shirya tarar sa sannan ya zagaye ya tafi gurin wata.

Haka na kwana ina kukan baqin ciki idona sunyi luhu luhu ga wani azababben ciwon kai daya kamani,
sauqi daya dana samu Amna ba zataje makaranta ba saboda wani satin zasu fara WAEC ita ta shirya
yaran ta basu abinci sannan tayi musu order Uber suka tafi.

Ina zaune a gaban mudubi ina shafa mai bayan na samu nayi wanka dakyar ta shigo da Try ta dora Mug
din shayi da plate din dankalinda kwai. Akan Coffee table ta ajiye kafin ta zauna akan daya daga cikin
kujerun.
"Mami" ta kira suna na, sena waiwayo nayi mata kallo daya na mayar da kaina.

"Mami kiyi haquri dan Allah, wallahi ba laifin Abbi bane kin san su Anty Amirah har gidan bokaye suna
zuwa qilan Asiri sukayi masa" ta fada muryarta na rawa alamar kuka zatayi.

Sena juyo na kalleta ina murmushi nace

"Kinsan menene Amna?" Seta girgiza kai alamar Aa, numfashi naja kafin naci gaba da cewa

"Abbin ku be kyauta mun ba, inda ya fadamun ba yau ze dawo ba kinga da ban sha wahalar hada masa
abinci ba. Kina kallo fa jiya ko baccin kirki banyi ba ina gasa masa zabo amma duk wannan wahalar ta
tashi a banza kuma fa da magriba ma fa seda mukayi waya yace sun dawo yanzu ze taho gida".

Na qarasa ina share hawayen daya zubo ta gefen ido na, gaya matan da nayi se yasa naji wani sanyi sanyi
a zuciyata.

"Haka ne Mami, nidai kiyi haquri ki dena damuwa daman abinda suke so kenan"

"Na haqura Amna, kije ki kwanta ki huta toh nima idan na karya bacci zanyi" na fada ina miqewa na bude
wardrobe na dakko Doguwar rigar Yadi me laushi na saka. Tura abincin kawai na ringayi dan bakina sam
babu dadi. Bayan na gama na sha Paracetamol na kwanta.

Dakyar ya yakice tunanin abinda Bashir yayi mun na samu bacci me nauyi ya dauke ni, gana jiya da banyi
ba ga bashin na shekaran jiya.

BASHIR

Tun washe garin da ya sauka a Delta da daddare suna waya da Amirah tana ci gaba da yi masa kukan
data ara ta dorawa kanta.
Cikin kukan take cewa "Kowa ya kira ni yayi mun gaisuwa dangi na kusa da na nesa amma banda Anty, ai
ko ba komai tsakanina da ita ya kamata ace tayi mun gaisuwa ko su Aliyu ma ai duk ya kamata su kirani
ko banza qanwarsu ce" .

"Ma'u bata kira ki ba?" Ya tambayeta da mamaki,

"Bata kirani ba mana inda ta kira ai Zan gaya maka indai kuma ba murna take da mutuwar Iman ba".
Amiran ta bashi amsa. Wannan fushin cewa bata kira Amirah ta mata gaisuwa ba shi ya hana shi kiranta
har tsahon kwanakin da yayin.

Ko ranar data kirashi da Amiran suke waya, sanda kiran ya shiga harga Allah yaso ya daga dan yayi
missing dinta amma daya gayawa Amirah nan da nan ta rikice ta fara masa kuka, basu kuma gama wayar
ba se gurin sha biyu dan haka suna gamawa bacci ya kwashe shi.

Gaba daya yanzu shi tausayin Amirah yake ji. Koshi me Ÿaÿa Shida rasuwar yarinyar nan ta tabashi sosai
bare ita me guda daya sannan ga irin wahalar da tasha shiyasa yake biye mata ko zata samu sassaucin
abinda take ji.

Rabar laraban kuma da zumudin son ganin Asma'u ya taho, yasan be kyauta mata ba ya kuma bari ne se
ya dawo sannan ya goge laifinsa, sanda ya kirata dagaske yana Lagos saukar su kenan amma suna ajiye
waya Amirah ta kirashi tana kuka tamkar ranta ze fita.

Akan gashi har anyi sati da rasuwar Iman amma beje ya ganta ba.

"Ni daman nasan baka sona Yaya, baka qaunata farin cikin Anty da Ÿaÿan ta ne kawai matsalar ka baka
damu da ni na rayu ko na mutu ba. Karinga tunawa nima matarka ce kamar ita, kuma ina da haqqi akan
ka. kuma idan har ban yafe ba kasan Allah babu ruwan sa seya kama ka da haqqina". Tana gama fadar
haka ta kashe wayar ta, bugun duniya kuma taqi dagawa.

Gaba daya ji yayi hankalinsa ya tashi, shifa duk abinda za'ayi kar a saka batun Allah ya isa. Ya fito kenan
ze taho gida suka hadu da daya daga cikin Directors dinsu shima dan Gombe ne suka gaisa se yake gaya
masa Gombe ze tafi yanzu.
"Sir Daman akwai jirgi yau ko a mota zaka tafi" Bashir din ya tambaye shi, se yayi murmushi yace

"Haba Engineer mota kuma a daren nan ai kayi mun fada, a jirgine His excellency yazo wani taro, kasan
Abokina ne, toh na samu alfarma za'a rabani Private Jet mu tafi.

"Ai Sir ku manayan mutane ne da zan samu a rabani nima ai dana biku na dana" ya fada yana shafa kai,
se Director yace "dagaske kake ko wasa se na kira Protocol naji idan ze samu".

Beyi zaton za'a samu din ba kawai ya amsa, yana kiran protocol din kuwa yace su taho yanzu su akw jira.
Babu damar yayi wa Director wasa da hankali dole ya bishi suka tafi dukda shi kansa yasan be aikata
daidai ba, amma yasan Asma'u tana da Fahimta, gara ya fara gyarota da Amirah sannan ya dawo kan
Ma'un sa dan yasan ita bazata taba yi masa Allah ya isa ba kome zeyi mata.

A Flight mode ya saka wayarsa dan karma ta kirashi besan me zece mata ba, seda ya sauka a Gombe,
yana kan hanyar zuwa gidan su ya tura mata da wannan Text din.

Sanda ya isa har sun rufe gida seda ya kira Naziru ya bude masa tukkana. Da mamaki Nazirun yake
kallonsa, ya karbar masa Jakar suka shiga ciki kai tsaye ya wuce dakinsu da Jakar shi kuma Bashir ya
wuce Dakin Dada dan burinsa yanzu yaga Amirah yaga halin da take ciki.

Palour babu kowa dan har sun kashe fitulu alamar sun kwanta, kai tsaye dakin Fainusa ya nufa inda
yasba ze samu Amiran. Har ze tura qofar ya daka saboda tuna ba ita kadai bace a dakin baisan a yana yin
da ze tarar dasu ba seya dakata.

A hankali yayi knocking, seda ya buga sau uku sannan Fainusa ta taso ta bude qofar tana hamma a zaton
ta ma Dada ce, seta yi saurin saita kanta ta shiga gaishe shi, a ranta tana mamakin daga ina da tsohon
daren nan kuma.

Fita tayi daga dakin ta koma palour shi kuma ya shiga. Abin mamaki matar da Tace bata iya bacci da ta
kwanta mafarkin Iman takeyi se gata tana shaqar baccinta kashirban se a iya sace ta ma bata sani ba.
Tashinta ya shiga yi amma ko motsi se wasu surutaj banza data ringa masa qarshe ya haqura ya koma
dakin Naziru ya kwanta dan already Nazirun ya gyara masa Gadon sa shi kuma ya koma Dakin Sa'ad ya
kwanta.

Juyi ya ringa yi kawai ya kasa baccin, tunanin halin da Ma'u take ciki kawai yake. "Allah sarki Ma'una yar
Aljanna nasan ke me haquri kuma zaki fahimce ni" ya fada a fili kamar yana gabanta. Dakyar ya samu
yayi bacci ya qudurce a ransa dai In sha Allah gobe ko a mota ne seya tafi Lagos.

WATA KISHIYAR

(ALKAHIRI CE KO SHARRI)

Na Maryamah Farouk

(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)

Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 27

Amirah

Da Asuba duk tashin da Fainusa ta ringa yiwa Amirah tayi sallah ko motsi batayi ba. Ba wai dan bata jin
ta ba, A’a kawai ita ta tsani wannan tashin Asubar da sukeyi tun kafin ayi assalatu.

Tana lafe akan gado ta jiyo Fainusa tana gayawa Dada zuwan Bashir din jiya da daddare, seta miqe
zaune. “Kardai ya shigo ya ganni ina sharar bacci” ta fada tana zaro ido.

“Wayyo ya zanyi yanzu” ta sake fada a fili tana tunanin mafita. Tunda akayi rasuwar take masa qaryar
bata iya bacci da daddare shi yasa kullum suke raba dare suna waya se yayi dagaske take barinsa ta
kwanta.
Jiyan ma abinda yasa bata kirashi ba baccin taji da wuri, seta shirya a ranta da safe in sunyi waya se tace
masa ai tasan ya koma gida ne bata so ta kirashi Anty taji haushi toh yanzu gashi qilan ya ganta wai ya
ma akayi be gaya mata ze zo a jiyan ba. Yanzu ita wace qaryar zata zabga masa?

Ganin ba mafita ya sakata tashi da niyyar ta yiwo alwala idonta ya sauka akan Maganin tari akan
Mudubi. Nan take ta tuno ranar sadakar uku aka siyowa Yaron Anty Amina Babbar Yayar su Bashir da
take aure a Bauchi, se akayi rashin sa’a aka karbo na manya dan haka bata bashi ba ta ajiye a dakin.

Da sauri ta dauke shi, seda ta leqa ta jikin qofa ta hango Dada da Fainusa suna Nafila kafin ta bude kofar
Toilet a hankali ta shiga ta tuttar da fin rabin maganin a rariya kafin ta koma ta kwanta bayan ta ajiye shi
saitin kanta ta bar kwalbar a bude.

Har qarfe shida tana kwance a gurin, Fainusa data gama Azkar dinta ta shiga dakin yin wanka dan zata
fita gurin aiki tana koyarwa a makarantar secondary dake kusa dasu ta tarar da Amirah a bararraje tana
bacci babu Alamar ta tashi tayi sallah.

“Lallai yarinyar nan, daman baki tashi bama kikayi sallar nidai naga randa zakiyi hankali” ta fada bayan
da ta danawa Amirah duka a cinya ta bude ido da sauri dan dukan ya shigeta.

“Akan me zaki zo ki dakeni, Allah ya isana wallahi” ta fada tana sosa inda ta dake tan.

“Ni kike yiwa Allah ya isa mara kunyar banza kawai” Fainusa ta hayayyaqo mata, Dada da tajiyo
hayaniyar tasu ta shiga da sauri tana cewa

“Bismillahi safiyar taku tayi zaku fara ba, kamar masu ganin hanjin juna yanzu kuma me akayi?”

“Dada wai fa wannan mara kunyar tunda na tashe ta da Asuba ashe bata tashi tayi sallar ba, shine yanzu
fa dana shigo na sake tashinta ta fara zagina tana mun Allah ya isa”.
Bude baki Amirah tayi da niyyar magana ta hango Bashir ya turo qofa, se kawai ta fashe da kukan qarya
harda sheshsheqa tana cewa

“Wallahi Dada ba haka akayi ba, ni ban ji sanda ta tashi ni ba ban ma san safiya tayi ba kawai yanzu tana
shigowa ta hau dana mun duka wai na kwanta ina bacci kamar wata kafura bayan tasan ko baccin bana
iyayi, kuma ni maganin mura nasha shine bacci me nauyi ya kwashe ni” ta fara qoqarin miqewa, tana
sane ta ture kwalbar maganin dan sauran na ciki ya zube ita kuma ta koma dabas ta zauna a dole jiri take
gani.

Sake yunqurawa tayi ta miqe se ta tafi kamar zata kife Bashir yai saurin tarota yana cewa “yi a hankali
mana” nan idonsa ya saka akan kwalbar maganin, seda ya zaunar da ita kafin ya daga kwalbar yana
kallonta yace “Amirah kina hauka ne, syrup kika sha saboda kin kasa bacci?”

Kuka haiqan ta saka masa tana cewa “to ni yaya ake so nayi? Bana iya bacci ni kadai nasan damuwar da
nake ciki babu wanda ya damu da ni har kai din ai baka zo ba bate kasan halin da nake ciki”.

Seda ya yi qoqari ya hadiye bacin ransa, kafin ya sassauta murya yana cewa “shikenan, yanzu ki daure
kiyo alwala kiyi sallah, lokaci yana qara ja” ya juya ya fita jin ana kiran wayar sa.

Seta miqe tabi bango, dab da zata shiga bayin ta waiga tareda ballawa Fainusa harara ganin babu wanda
yake kallonta ta shige ciki.

Daga Dada ko har Fainu bude baki sukayi suna kallon wannan Drama, ita Dada mamakin yanda zata ce
bata bacci kuma kowa babu me kula da ita, to wanne baccin ne batayi yarinyar da duk dare seta leqo su
kuma ta ganta tana baccin ta qalau kai har na rana yi take, gaba daya fa jimamin na kwana biyu tayi ta
ware se idan taga idon mutane ne zata wani koma kalar tausayi duk fa tana ankare da ita.

Ita kuwa Fainu Murmushin takaici tayi ta nemi gefen gado ta zauna tana cewa “Allah ya kyauta” lallai
Amirah ba qaramar makira bace, kullum tana jin yanda take kalallame shi a waya tana raina masa
hankali to Yayan shima ba kirki ne dashi ba bare ka gaya masa gaskiya amma dai jiki magayi.
Sanda ta fito Fainusa kawai ta tarar a dakin, bata so ba dan har wani kwararrabe fuska tayi a zatonta
Bashir yana nan ganin Fainusan yasa ta saki tsaki ta dauki Hijabinta tana cewa “aikin banza mutum bashi
da aiki se sa ido”.

“Wai Amirah ni sa’ar kice? Ni kike gayawa wannan dan uwarki” Fainusa ta fada tana miqewa tsaye

“Karki sake zagar mun uwa nidai” Amirah ta fada tana murguda baki,

“Idan na zaga me zakiyi?” Cewar Fainusa tana qara matso Amiran,

“Nidai karki sake zagina dai tam” Amiran ta fada kafin ta juya ta tada sallah, idan badan tsoron kar ko
Bashir yana kusa ba da ramawa zatayi ai uwa bata fi uwa ba.

Kwafa Fainusa tayi, taso ta fadi wani abun da be mata ba wallahi seta tsinkawa shegiya mari idan yaso
duk abinda Yayan ze yi yayi. Ai daman saboda taga tana auranshi ne yasa ta raina uban kowa ko amma
zatayi maganin ta wallahi.

“Haka kawai dan mutum yana baqin cikin ana auran dan uwansa baze iya dauke kai yaga ana abin arziqi
ba shine ze takurawa mutane, idan anji haushi mutum ya koma gidan mijinsa mana” Amirah ta fada
daidai sanda Fainusa ta fito daga wanka.

“Idan gidan uban ki nake zaune se kice an takura miki, sannan aure da kike magana kibi a sannu
qaddarar zawarci bata wuce kan uban kowa ba” tana fadar haka ta qarasa gaban mirrow ta hau
shiryawa, amma tabbas yau se yar iskar yarinyar nan ta bar mata daki.

Ita Amirah zatayiwa gorin zawarci yarinyar da a shekaru ta girme mata da har shekara shida shine zata
tsaya tana gaya mata wadannan maganganun dan kawai taqamarta tana auran yayanta? Tabbas dole
tayi maganinta wallahi.
Ita kuwa Amirah sum sum ta fice daga dakin ganin yanda fuskar Fainusan ta chanza tasan tsaf zata iya
rufeta a daki ta nada mata mugun duka. Tayi tunanin zata taradda Bashir a Palour seta ga babu kowa,
zama ta tayi tana jiyo motsin Dada a Kitchen din amma hankalin ta be bata ya kamata ta shiga ta taya ta
aiki ba.

Bayan Bashir ya gama amsa wayar, harya danno Number Asma’u ze kira se ya dakata. Wani nauyinta
yake ji besan me ze ce mata ba idan ya kira. Seya karkata kiran zuwa Number Aliyu amma a kashe.

Dadi ma yaji da ya sameta a kashe dan qilan ya zama yana tare da Ma’un hakan kuma ze zama qari akan
laifinsa.

Dakin Alhajinsu ya shiga ya same shi a zaune kan sallaya yana lazumi. Bayan sun gaisa da mamaki Baban
yake tambayarsa yaushe yazo.

Seya shiga shafa qeya yana cewa “jiya da dare Baba, Engineer Sha’aban na biyo zasu taho tareda His
excellency bayan mun dawo daga Delta.

“Kace ko gida ma baka je ba kayi yo nan” Baban Ya fada yana kallon fuskarsa, rasa abin cewa Bashir yayi
dan haka yayi shiru kawai.

“Ka kyauta, tashi kaje” Baban ya fada ya maida hankali ya ci gaba da jan carbinsa.

Yana fitowa ya tare Naziru da ya fito daga Palour Dada da Kofin shayi a hannunsa.

“Ji mana” ya dakatar da Nazirun kafin ya fara masa magana wayar sa tayi qara. Team leader sune yake
gaya masa ranar Monday suna da presentation, dan haka yau idan sun huta gobe Friday zasu hadu a
office dan su tattara reports din hannun kowa” bayan sun yi sallama Bashir ya kalli Naziru yace

“Kayi mun booking morning flight gobe”.


“Ai Yaya babu jirgi fa, an samu yar matsala sun dakatar da jirgin Gombe zuwa lagos till further notice.
Sedai ka hau mota kaje Kano tukunna ka tafi ta can”.

Kallon sa Bashir yayi kamar me son ganin gaskiyar maganar a fuskar sa, da hannu yayi masa alama da ya
tafi, kafin ya lalubo Number Wani Agent da yake siya masa ticket ya kira.

Irin bayanin da Nazirun yayi masa dai ya maimaita se ma qari daya masa akan Yau jirgin qarfe bakwai da
rabi ne se na sha biyun rana, gobe kuma babu jirgin Safe se Shidan yamma.

Godiya ya masa ya kashe wayar kafin ya shiga lissafin yanda zeyi, qarfe 10 na safe ake buqatarsa a office
goben, dama babu zancen yau dan jirgin safe ya tafi yanzu kuwa qarfe takwas na safe ta gota, indai ba
fiffike zeyi ba baya tunanin akwai ta yanda ze isa Kano kafin sha biyu na rana. Goben da yayi tunanin
samu ance sena Magriba shida yake da Meeting qarfe goman safe to yanzu yaya zeyi??

Wai wane tsautsin ma ya saka shi tahowa yanzu gashi ya saka kansa a cakwakiya da hargitsin da yake
jiransa a can gida, Mafita daya ce kawai Ya tafi a Mota in sha Allahu dai daga nan zuwa cikin dare ai ya
isa. Da wannan shawara yayi Na’am dan haka ya juya ya shiga palour Dada.

Amirah na kwance akan kujera ya shiga seta miqe ta zauna tana gaishe shi, kujerar dake kallonta ya
zauna ya amsa dai dai sanda Dada ta fito daga Kitchen din ta try a hannunta. Fainusa ta kwalawa kira ta
fito cikin shirin fita, Try din ta bata tace ta kaiwa Alhajin su sannan ta kalli Bashir tace

“Yanzu zaka karya ne ko se an jima?”

“Eh yanzu Dada, dana gama zan kama hanya ne ma”.

Daga ita har Amirah kallonsa sukayi,

“Da wuri haka?” Dadan ta tambayeshi, se ya miqe yana cewa “Wallahi Emergency ne ya taso mun a
office, kinsan jiya muka dawo toh kuma ana buqatar wasu bayanai gobe gashi na taho dasu nan kuma
babu jirgi dole mota zan bi”.
“Tab amma kaima da ganganci kake, me yasa ka taho kasan kana da ayyuka a gabanka. Yanzu a yanda
hanya take zaka bi mota har Lagos, to kana da tabbacin ma zaka isa kafin goben nan ina se dare motocin
suke tafiya koh?” Dada ta fada tana riqe baki.

“Addu’a za’a mana Dada In sha Allah zamu je lafiya, yanzu dana shirya zanje Tashar, Idan babu masu
tafiya yanzu inaga Zan dauki Shatar mota ne kawai na tafi dan kinsan su office babu ruwan su dole na kai
musu takaddun nan gobe qarfe goma”

“Toh Allah ya rufa asiri, se kije ki hada masa abin karyawar ki kai masa tunda sauri yake” Dadan ta fada
tana kallon Amirah data daskare a gurin. Dakyar ta yunqura ta tashi, lallai ma. Daga zuwansa jiya da
daddare zece yau ze juya, wallahi qarya yake ta tabbata babu wani kiran office kawai Matarsa ce tace ya
dawo shine ze fake da wani aiki ai kuwa bazata sabu ba wallahi.

Kayanta hada ta kai masa Dakin Nazirun, sanda ta shiga yana wanka, seta nemi guri ta zauna tana jiran
ya fito dan babu yanda za’ayi ta barshi ya tafi wallahi.

Da gudun bala’i ta fada jikinsa tareda fashewa da kuka lokacin daya fito daga wankan, gaba daya yayi
baya kamar zasu fadi Allah ya taimaka ya dafe bango dan a bazata ta fado masa se ya tureta daga jikinsa
yana cewa “ke mahaukaciyar ina ce zaki fadowa mutum haka idan da na fadi naji ciwo kuma fa, mtsw”
yaja tsaki yana hararar ta.

“Yanzu dan Allah ko tausayina bazaka ji ba, daga zuwanka jiya ko zama bamuyi ba kaji damuwata ba yau
zaka ce zaka tafi saboda wadda ka baro acan tafi ni, shi kenan kaje, amma sedai ka zaba ko ni ko ita
wallahi dan na gaji da yanda kake nuna banbanci a tsakanin mu. Gara ka rabu dani kaje can ka zauna da
matar so”.

Kallonta ya ringayi har ta kai aya. Wai ya zaba ko ita ko Ma’u shi abun ma dariya ya bashi a ransa yace
“idan zabi za’a bani dole sedai na zauna da daya yarinya aike zan saitawa hanya, na rabu da Ma’u nabi
ina naga haske??

A fili kuma se ya saki murmushi ya janyo ta jikinsa yace “Allah ya huci zuciyarki haba Amaryata, yanzu
kina kallo ko gida banje ba jiya na taho garin nan ko iya wannan be isa ya nuna miki yanda na damu dake
ba.
maganar na zaba a tsakaninku kuma ai bata taso ba kinfi kowa sanin Yanda Nake Son Ma’u, ban kuma ga
abinda ze raba ni da ita ba se mutuwa sannan kema saboda ina sonki na aure ki dan haka ki dena kawo
maganar rabuwata da daya daga cikin ku.

And official call na samu dole na bar garin nan a yau, idan kuma so kike a kore ni daga aikin na rasa kudin
siya muku abinci shikenan”.

Qara lafewa tayi a jikinsa, taji haushin yanda ya wani fadi yana son ma’u amma ai ba qarya bane ita ma
ta sani, ganin yana cikin yana yi me dadi yasa ta ce bari ta gwada sa’arta.

Tana jikinsa suka qarasa kan gadon ya zaunar da ita ya dakko mai ya fara shafawa, taya shi ta shiga yi
kafin cikin muryar shagwaba tace “Yayahh”

Kallon ta yayi ba tareda ya amsa ba, ganin hankalin sa yana kanta taci gaba da cewa

“Toh naji Yaya ka tafi amma da ka gama abinda zaka yi ina jiranka ka dai san alqawarin da kayi mun ni
uku nake so ma ba biyu ba” ta fada tan rufe fuskarta da hannayenta.

Murmushi yayi yace “karki damu, just be ready for me”.

Murmushin ita ma tayi kafin ta ci gaba da cewa

“Se kuma Yaya gaba daya kayan dakina an lalata su kuma...” ganin kallon da yake mata lokaci daya
fuskar sa ta chanza ya sakata yin shiru,

“Uhm ina jinki kuma me” ya tambaye ta yana saka rigar sa, seta girgiza kai tace “ babu komai”

“Gara da ya zama babu komai din” ya fada yana zama ya jawo kayan abincin ya fara ci. Seda ya gama tsaf
ya zuge jakarsa sannan ya kalleta yace
“Karki sake kawo mun maganar kayan dakin ki ko wani abu, saboda banyi lissafin nawa damage din nace
a biya ni ba ko?

Zan tafi yanzu, zuwa gobe ki koma gida”.

Seta marairaice fuska kamar zatayi kuka tace “Dan Allah yaya gidan yayi mun girma da yawa tsoro nake
ji, ka barni na koma gidan Addah kaga in nace zanzauna anan ma kullum fada muke da Anty Fainusa”.

Seda ya kalleta na dan wani lokaci kafin yace “ok ki koma din, shikenan ni zan tafi”.

Ganin bata motsa daga gurin ba sema yan hawaye da take gogewa yasa yace mata

“Come on babu ko goodbye” ya fada yana dagata tsaye, light kiss ya mata kafin ya saketa yayi gaba ta
bishi a baya. A qofar dakin Alhajin su taci burki, harya saka qafa jij ta tsaya yasa ya waiwayo ya kalleta

“Shigo mana” ya fada yana qarasawa ciki. Se Alhajin ya dago ya kalleshi yana murmushi yace “Amirah ce
ko, ka barta kawai ban san menayi mata da bata iya zuwa mu gaisa ba”.

“Hmmm” kawai ya iya cewa sukayi Sallama da Baban yayi masa fatan sauka lafiya ya fito. Shareta yayi ya
shiga dakin Dada itama sukayi sallama kafin ya fito har Naziru ya saka masa jakar sa a mota.

Tana bayansa kamar Jela suka fita, tunda yaji bata zuwa tana gaida Baban ransa ya sake baci, gaba daya
dana sanin zuwa ma yake yi dan dai babu biyan buqata se kayan takaici daya kwasa kawai haka ya shige
motar Naziru yaja tana tsaye kamar ta kurma ihu, yanda suka faro a dadin rai taso su qarashe haka ko ba
komai ta samu kudin kashewa yanzu gashi ya tafi da sabon fushi.

Sanda suka isa ya taki sa’ar samun qaramar mota sharon saura mutum biyu dan haka ya biya kudin
mutum biyun kawai ya shiga suka dau hanya. Seda tafiya ta fara miqawa sannan ido ya raina fata.
Rabon daya je Lagos a mota kusan Shekara Goma sha biyu kenan sanda ya taba samun wani aiki har aka
kirashi interview daga qarshe aka ce wai ba’a dauke shi ba.

Wannan aikin ko lokacin daya same shi da aka kirashi documentation harda ticket din jirgi Alhaji Qarami
ya hada masa na zuwa da dawowa tundaga nan kuwa da Al’amura suka bude masa shida tafiyar mota
sedai inda jirgi baya zuwa.

Akace tafiya yankin Azaba tabbas Bashir ya kwashi Azabar tata. Wata irin tafiya yayi da a rayuwarsa ze
iya cewa be tabayin me wahalarta ba. Haka suka kwana suna tafiya sau uku kacal suka tsaya shima
sallah kawai sukeyi wasu su nemi abinda zasu ci sannan a qara wuta.

Bashir dai Azumin dole yayi in banda ruwa babu abinda ya shiga cikinsa har suka Isa Lagos da Asubar
Ranar Juma’a.

Firkai firkai dashi kamar wanda ya qwato daga hannun Yan Kidmashin ya shiga kwankwasa gidan bayan
da Shatar Taxi din daya dauko ta sauke shi.

Lokacin Asma’u na kitchen sauran yaran kuma suna zaune a palour suna qarasa saka sport wear dinsu
dan yau Juma’a. Da farko duk basu zaci gidan ake kwanwasawa ba tunda waye ze zo musu da sassafen
nan shida ma yanzu tayi.

Jin Basu bude ba yasa Bashir neman dutse ya hau buga qofar kamar an aiko shi dan a yanda yake ba
shida qarfin da ze fara binciko keys a jakarsa, daga ciki Asma’u ta fito daga Kitchen din tana kallon yaran
da sukayi cirko cirko tace

“Waye wannan yake mana bugu kamar mara hankali” seta nufi gurin qofar. Seda ta leqa ta yar bular da
ake ganin mutum, da mugun mamaki taja baya. Fuskar Bashir ce, tasan a kowanne yanayi bazata kasa
gabe shi ba amma da seta ce wannan me kama da shi ne.
Qofar ta bude da sauri tayi gefe ganin yana neman fado mata ya wuce ciki bayan ya watsar da kayan sa a
bakin qofar, seta kwalawa Aliyu kira ya tafi da sauri ta nuna masa kayan tana cewa “shigar masa dasu
dakinsa” ta juya ciki tana mamakin daga ina yake.

Bashir kuwa Yana shiga ya zube akan kujera, yunwa, gajiya da bacci sun hadar masa gaba daya. Kallonsa
yaran suka shigayi kamar sunga baqo kafin suka gaishe shi ya daga musu kai dan baze iya bude baki ba.

Yanda Asma’u tayi kamar bata san da wanzuwarsa a gurin ba yayi bala’in bashi mamaki, shirinta ta ci
gaba daya yi. Yana kallo suka qarasa cinye abin karin su yaran sukayi masa sallama suka fice gurin mota
ita kuma ta shiga daki ta dakko jakar ta.

Ina sane nayi tamkar na manta dashi a gurin, yana ganin nayi hanyar qofa yai saurin dakatar da ni da
muryarsa a har dashewa tayi saboda yunwa yace “Ma’u baki ganni ba zaki tafi kuma”.

Seta na dakata na kalle shi, da dan guntun murmushi a fuska ta nace “Na ganka Baban Ali ai nayi maka
sannu da zuwa tunda ka shigo ko baka ji ba?”

“Hmmm” ya fada kafin ya yunqura yana cewa “Nagaji wallahi a mota na taho, gashi qarfe goma ya
kamata inje office ki taimaka mun da abinda zanci bari nayi wanka”.

Se da na saki wata dariyar takaici, ina kada key din hannuna nace “wato ka rantse dai se ka biyo mota
toh ai gashi dai kaji abinda ake ji. Abinci kuma akwai komai na buqata a Kitchen se ka nemawa kanka
kaga mun makara ma se mun dawo” na juya nayi tafiyata ina jin yanda ya raka ni da kallo har na kulle
qofar.

Wato daga dan rainin hankali se Bashir, Allah ya qara. Abinci kuwa babu komai a Freezer mun cinye
kwana biyun nan kuwa ban zauna ba bare nayi ko miya ce na ajiye.

Malam Bashir kuwa dakyar ya iya miqewa ya shiga Kitchen din, ya zata ze samu ko ragowar abinda
sukaci ne ya tarar da wayam, ya bude Freezer nan ma danyun nama ya tarar babu ko guntun abinci.
Cike da takaici ya bude Fridge din shima babu komai se tarkacen ruwa da lemo se wani guntun nama ya
samu a foil paper ya dauka da sanyin sa da komai ya cinye.

Ganin fa babu mafita ga yunwa ga lokaci na sake qure masa yasa ya kunna Fanfon Kitchen din ya tari
ruwan zafi, Madara da Milo ya zuba sosai ya dagawa daya ya kwankwade ya sake hada wani yasha rabi
ya hango bread ya dauka ya hada, seda yaji cikin sa ya dan farfado sannan ya haqura yaja kafafuwansa
ya tafi daki.

Wayar s ya fara sakawa a chaji dan tun a hanya da dare ta mutu, Yau daya se be ji haushin abinda Ma’u
ta masa ba, idan da haka kawai ne tayi masa wannan wulaqancin yasan me raba su se Allah amma yau
daya tuna girman nasa laifin se yaga ai ba komai tayi masa ba.

Kamar me maye haka yana layi yayi wo wanka ya fito, badan ba kwanciya zeyi ya dan rage bacci amma
yasan tabbas ya kuskura ya kwanta a yanda yake jin baccin nan qila sedai ya farka yaga magriba tayi.

Bayan ya saka kayan sa ya tattara abinda ze buqata kafin ya kunna wayarsa yayi order Bolt, se ya fito
qofar gidan ya zauna kamar wani Almajiri, yunwa yake ji dan ba wai ya qoshi bene kawai haqura yayi
idan ya fita se yaci abincin sannnan ga bacci har ji yake kamar zazzabi ze rufe shi, haka ya hau motar suka
kama hanya.

A cafeteria office din su yaci abinci, Patrick abokin aikin sa da suka shiga tare ya ringa kallonsa da
mamaki ganin yanda yake lodar abinci kamar wanda ya shekara be ci ba, kasa daurewa yayi yace masa

“Bash lafiya kuwa ji yanda kake cin abinci?”

“Bazaka gane ba, rabo na da abinci tun shekaran jiya”.

Dakyar ya iya kaiwa qarshen meeting din, suna gamawa suka fita sallar Juma’a. Bayan sun dawo Office
din sa ya koma ya kwanta ya ringa bacci ba shi ya farka ba se qarfe bakwai shima Security da suke bi
office office ne bayan an tashi suka ga fitilar sa a kunne dan haka sukaje su duba ko lafiya tunda be saba
kaiwa dare a gurin ba.
Haka ya tattara a gida ya wuce gida, da murnar sa ya shiga dan tun daga waje ya jiyo qanshin tuwo da
miyar kuka harda man shanu abinka da me jin yunwa.

Ya bude qofar ya shiga, fuska a sake Ma’u tayi masa sannu da zuwa harda tambayar ya akayi yau ya dade
yace bacci ne ya kwashe shi.

Da zumudinsa yai sallar magriba da Isha ya sako jallabiyya ya dawo palour aka kame akan kujera yana
jira ayi masa tayij abinci ya kwashi gara amma har kusan minti goma da zaman sa yaji shiru sema harkar
gaban su kawai suke.

Gyaran murya yayi yana kallon Ma’u dake dannan waya yace “Akwai abinci ne yunwa nake ji”

Seta dakata ta dago ta kalleshi da murmushi tace “ai kuwa babu dan ban san zaka dawo ba”.

“Kamar ya baki san zan dawo ba ce miki nayi zan tafi wani gurin ko yaya, sannan nida gida na ayi abinci
ace baza’a a jiye mun ba saboda me? Haka fa dazu da safe kika ce mun akwai abinci na duba ko ruwan
zafi baku ajiye ba” ya fada a hasale, dan ya rigada ya gama saka rai da Tuwon.

“Ko ajikina na sake gyara zama nace “Aa abin bana zafi bane bafa Baban Ali, gani nayi yanzu ai Idan
zakayi tafiya baka fada seka isa inda zakaje toh gudun kar mu ringa asarar abincin yasa mukeyi dai dai
cikin mu, idan kace zaka ci se a dafa dakai”.

Abubuwa sun sha kaina, idan na samu sarari zaku jini gobe idan kuma ban samu dama ba se Monday In
Sha Allah
WATA KISHIYAR

(ALKAHIRI CE KO SHARRI)

Na Maryamah Farouk

(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)

Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 28

Washe Gari Asabar tunda nayi sallar Asuba na koma bacci ban farka ba se goma na safe. Ko yaya Bashir
ya qare jiya oho dan tunda na gaya masa babu abinci naji ya fara jan kwafa da tsaki na kwashi qafafuna
na bar musu gurin, dan karma a biyo ni a dameni seda na murzawa qofata key sannan na kwanta.

Tsaf na shirya cikin wani Material baqi doguwar riga bayan nayi wanka, tundaga dakin nake jiyo kaya
kaya alamar Game suke ko ana musu akan wani abun ina bude qofata Yan biyu na suka taso da gudu
suka riqe ni.

“Kai ni yunwa nake ji karku kadani me kuka ci ne” na fada ina kama hannayensu, se Ahmad yace
“Indomie Yah Amna tayi mana da Tea Abbi kuma gashi can yanzu aka soya masa Irish”.

Kallon inda yake nuna mun nayi muka hada ido da Bashir daya watso mun wata harara kamar idonsa ze
fado, duk yanda naso na basar seda dariya ta kufce mun dan haka na wayance ina nufar inda yake nace
“Baban Ali barka da safiya, kace kaima yanzu ka tashi? Bari nazo muci dan Allah yunwa nake ji idan bamu
qoshi ba se a qaro wani” nayi maganar ina jan kujerar da take kallonsa na zauna.
Ban damu da shirun daya mun ba na fara hada Tea na ina masa surutun da na tabbatar sake qular dashi
nakeyi, na gama naja kwanon dankalin, sena bude baki ina kallonsa nace

“Kai Duk wannan da kai kadai zaka cinye shi?”

Can qasa kaman an fuzgo maganar daga bakinsa naji yace “Banci abinci da daddare ba jiya da yunwa na
tashi”.

Kallonsa nayi, naji tausayinsa kadan dan nasan Bashir da abinci ci ne dashi kamar dan kwallo, cikin
jimamai nace “Ayya meyasa ka kwanta da yunwa da ka saka Amna ko Spaghetti ce ta dafa maka ai”.

Shiru ya sake yi mun, nima ban sake magana ba na fara cin abinci na, ya rigani gamawa, seya miqe ya
shiga dakinsa ba dadewa ya fito ya chanza kaya ya saka Caftan na Yadi kansa babu hula. Key din motarsa
ya dauka, be mun magana ba ya fice yara suna masa a dawo lafiya.

Harya tada motar se gashi ya shigo, ko me ya tuna oho se ji nayi yana cewa “zan fita amma ba jimawa
zanyi ba saura yauma karku ajiye mun lunch”.

“Wa ya isa yaqi ajiye maka, jiyan ma aka si aka samu baka ce zaka dawo ba, amma yanzu tunda munsan
kana nan ai zamu girka da kai” na fada ina dan murmushi. A raina nace “da bakayi magana ba wallahi
yau ma dakaga Akuya sedai ka siyo ko kayi wunin yunwa.

Jellop rice nayi da pepper soup din tarwada, sena yiwa Bashir pepper meat dan baya cin Tarwada shi se
gasashshiya.

Muna cikin yin lunch Amna ta kalleni tace “Mami idan mun gama muje gidan Baba?”

“Za kuje ku dame su ko kunsan dai yau Weekend Baba yana nan zaku hana shi hutawa”.
Bashir ne yace “Baya nan Ya tafi Zamfara tun jiya, idan kun gama kuje dama yau baza mu fita ba sedai ko
gobe”.

Muna gama cin abincin kuwa bayan sun tattare kwanukan suka tafi ita da Farida dasu Ahmad, Aliyu da
sauran kuwa Ball suka dauka suka tafi Filin da suke bugawa gidan ya rage daga ni se Bashir.

Qin zama nayi na shiga qaqale qaqalen ayyuka dukda na fahimci nufin Bashir, ganin da yayi bani da
niyyar saurar sa, ina tsaye ina goge show glass din farantai a Gurin Dining kawai naji anyi sama dani, duk
yanda naso nayi tawaye a dole fushi nake amma yaqi bani dama, daman abin be kai zuci ba kuma nima
nayi kewar sa nan da nan nima na bada kai bori ya hau sosai kuwa na gigita Bashir.

Ina zaune a gaban mirrow ina Busar da kaina bayan nayi wanka ya shigo dakin yana waya, ta cikin
mudubin muka kalli juna murmushi me kyau da narkar da zuciya ya sakar mun kafin ya qaraso ta bayana
yana taba Gashina yaci gaba da maganar sa be jima ba ya kammala seya ajiye wayar akan mirrow ya
karbi Dryer yana cewa “Dama baki wahalar da kanki ba dan ba’a gama ba”

“Wasa kenan” na fada ina zaro ido, saman da yai dani yasa sauran maganar suka maqale ban samu kaina
a hannun sa ba seda aka kira Magriba.

Ranar haka mukayi kwanan farin ciki duk fushin nan seda Bashir ya bi ya kore mun shi. Se wani nan nan
yake dani ranar ba’ayi wata doguwar hira ba kowa ya tafi ya kwanta. Muna kwance a dakin sa nayi pillow
da dantsen hannunsa yace

“Dan Allah Ma’u karki sake horani da yunwa kinji”

Dariya na sheqe kafin nace “wannan din ma bada gayya nayi ba, aka si kawai aka samu”.

Lafiya qalau muka cinye Weekend din mu ranar Monday Amnah suka fara WAEC, da yake practical suka
farayi sha biyu zasu fito dan haka nace mata ta taho gida kawai idan ta gama sauran idan sun tashi Zan
dakko su yanda muka saba.
Dawowar da Amnah takeyi da wuri ya sake ragemun abubuwa da yawa dan kafin mu dawo ta ci qarfin
girki wani lokacin ma zata dafa musu nasu idan nazo sedai nayi wa Bashir kawai. ne da wuri.

Har aka ci sati uku banji Bashir yayi zancen zuwa Gombe ba kuma da alama ko waya basayi da Amirah
ban dai sani ba ko a cikin gidan ne bayayi se ya fita waje yake kiranta.

Ranar wata Alhamis daya kama Sati hudu da dawowarsa da daddare muna kwance Text ya shigo
wayarsa, Number Amirah ce dan da sunanta yayi saving, na fishi kusa da ita dan haka na miqa masa yana
daga kwance se naga ya tashi zaune.

Kamar wani mara gaskiya ya kalli wayar ya kalleni muka hada ido sena basar na gyara kwanciyata daidai
sanda wayar ta shiga qara alamar kira se ya tashi daga kan Gadon ya fita waje.

Tashi nayi nima na zauna, Kusan Awa daya yana wayar sa har sannan kuma bacci yaqi daukata, bawai na
damu bane da kiran Aa harga Allah ina tsoron abinda ze iya zuwa ne kuma dan a duk sanda muke zaman
lafiya kamar tauraruwa me wutsiya yarinyar nan seta wargazashi.

yana bude qofa nayi luf kamar me bacci, ina jinsa ya tsaya akaina yana haskani da wayar dan fitilar dakin
a kashe take kafin ya zagaya ya kwanta shima.

Da Asuba yake ce mun daga Office Gombe ze wuce.

“Ai ka kwana biyu daman baka je ba, ka gaishe mana su idan zaka dawo Dan Allah zata taho mun da
saqo a gurin Maman Ayman (Bilkisu) saura kace ka manta” na fada ba tareda damuwar komai ba.

Ni na hada masa dan abinda ze tafi dashi dan baya daukar kaya muka rabu salin Alin kowa ya tafi aikinsa,
sanda jirginsu ze tashi ma seda ya kirani ya gayamun yanzu zasu tafi nayi masa fatan sauka lafiya mukayi
sallama.

Gombe
A ranar da Bashir ya tafi itama ta koma gidan Addah cikin dacin rai. Naziru ne ya kaita bisa umarnin
Dada, suna zuwa suka ci karo da Addah a qofar gida da alama fita zatayi.

“Yawwa shiga da kayan ki fito muje” Addah ta fada tana kallon Amirah, seta wuce ciki ta ajiye jakarta ta
fito, Nazirun ne ya rage musu hanya har zuwa gidan wata tsohuwar qawar Addan da tace wai mijin
matar ne ya rasu zata je mata gaisuwa.

Suna shiga basu zauna ba dan a shirye suka sameta itama tace su tafi. Amirah dai ranta fal mamaki toh
ina zasuje haka dai ta bisu su ka hau Napep ya kaisu Tasha suka hau motar Dukku.

Bayan sun isa can ma ashe ba iya tafiyar kenan ba, Babura suka hau daga tasha suka dauki hanyar wani
surququn Jeji kafin su isa kuwa jikin su ya gaya musu da iska gashi lokacin sanyi da Hazo musamman
Amira dan daman doguwar rigar Abaya ce a jikinta tayi rolling da mayafin rigar har wani kadawa taji
haqoranta nayi tsabar sanyi.

A wani dan qauye suka sauka da gaba daya bukkokin garin basufi shida ba, Masu Baburan suka tsayar
kafin Hajia Maliya tayi musu jagora zuwa bukkar data fi kowacce girma. Sanda suka shiga ciki seda
Amirah ta dawo da baya da son tabbatar da daidai take gani ko kuwa gizo idonta yake yi mata.

Wato daga waje bukkace ta kara irin ta fulani amma abin mamaki idan ka shiga tamkar ka shiga dakin
wani hanshaqin me kudi. Ciki da palour ce, palour Gaba daya a malale yake da Carfet Ja me shegen
laushi har wani lumewa qafarsu take a ciki ga kujeru royal an zagaye gurin dasu, yanda gurin yai dumi ya
tabbatar mata harda Room heater aka kunna.

Zama sukayi ita da Addah se qarewa gurin kallo suke, Hajia Maliya kuwa da alama ta saba zuwa babu
mamaki a fuskarta. Zubgurar ta Addah tayi tana cewa “Maliya ina kika kawo mu karfa muje gurin yankan
kai ne”.

Dariya Hajia Maliya tayi tace “ke fa Fatu shegen tsoro ne dake” daidai nan wani dan fari dogo siririn
Bafulatani ya bude qofar uwar dakin ya fito.
“Aa Hajia kune ashe tun dazu nake tsammanin zuwanku naji shiru saura kadan ma muyi sabani” ya fada
yana zama a qasa inda aka qara shimfida wata darduma ga tarkacen kayan aikinsa akai.

“Mune fa Malam kasan tafiyar mutane da yawa basu shiryo da wuri bane” Hajia Maliya ta fada. Gaisawa
sukayi yana tambayar ta bayan rabuwa nan suka dan taba hirar aikin da yayi mata da irin yanda taji
dadinsa su Addah dai anyi tsuru.

“Wannan itace Fatu yar uwata da nayi maka baya ni wannan kuma Yarinyar tace Amirah” Hajia Maliya ta
gabatar masa dasu Addah, seya gyara zama yana cewa toh toh bismillan a gurguje dan sauri nakeyi zan
shiga garin ne nima zanje gidan Gomna.

Matsawa Addah tayi gabansa tace “Allah gafarta yanzu dai matsalar wannan yarinyar itace a gabana dan
tawa me sauqi ce”

“Ki fadi taki kawai Hajia itama ai tana da baki zata fadi tata ko” malamin ya katseta. Se Addah ta gyara
zama tace

“Malam abubuwan da yawa gaskiya amma kadan daga ciki dai kaga Kishiyoyina uku nice ta fari. Da gaba
daya gidan a hannuna yake daga Alhajin har su matan ni nake juya su ko kara na ajiye wa mutumin nan
be isa ya tsallake ba amma yanzu Malam karka so kaga yanda yake mun wulaqanci a gaban kowa ci mun
mutunchi yakeyi yanzu duk kishiyoyi sun rainani,

gashi yayan su duk sunyi aure sun samu gidan hutu ni kuma biyu ne dani fa kacal na samu daya ta daga
to gidan me mata ta fada dayar kuma yanda kasan wadda aka watsawa jinin baqar jaka ko tsayayyen an
gagara samu se tarin matsiyata dake sintirin zuwa gurinta”.

“Ya sunan me gidan naki da kishiyoyin?” ya tambayeta se tayi sauri tace

“Alhaji Murtala, su kuma matsiyatan akwai Binta da Nasiba se Memuna”.

Shiru malam yayi yana ta jan carbinsa daya shafe da turare Addah se zura ido take yana kallon bakinsa
da yake motsi kamar tasan abinda yakeyi, minti biyu ya dago yana kallonta yace
“Se haquri dai Hajia banajin wani aikin ki ze sake tasiri akan Mijin nan naki dan yanzu ya farka shima a
tsaye yake da Addu’a da neman tsari, kishiyoyi kuma ai ke kike shiga harkar su kuma ni cikinsu banga
wata da take jifanki ko wani abu ba”.

Raurau tayi kamar yarinya tace “yanzu malam babu yanda za’ayi wallahi yanzu ko dan abinda nake samu
a hannun Alhaji ya dena, kwanan nan da rigima ta hadani da wata mata akan kudi, gida na da na saka
yan haya ya siye ya biyata kudin ni da so nake inda yanda za’ayi ma a dawo mun da gidan”.

Dariya malam yayi yace “Hajia sama da shekara Arba’in fa kina yanda kika ga dama da bawan Allahn nan
yanzu kuma Allah ya taimake shi ya kwace shi daga hannunki ki qyale shi mana.

Ki godewa Allah ma daya ci gaba da zama dake dan yana sonki idan da zaki ajiye komai ki bishi zakiji
dadin zama dashi sosai Allah na tuba kwana nawa ya rage muku gaba daya ma da kike tashin hankalinki?
Gida kuma inda rabonki idan ya mutu se ki samu wanda ya fishi. Bismillah matso ke” ya qarasa maganar
yana nuna Amirah.

Addah zata sake magana Hajia Maliya ta riqe mata hannu tana girgiza mata kai, se tayi shiru kawai ranta
gaba daya a dagule. Wannan wane irin abu ne? Yanda Maliyan ta zuzuta mata shi ta zata da tazo
buqatarta ta gama biya amma tazo se wasu maganganu marasa kai aka gaya mata.

Jiki a sanyaye Amirah ta matsa gabansa, ya dago ya kalleta yana murmushi yace Hajia ya akayi?”

“Ni malam bani da wata matsala kawai so nake ya ringa so na yanda yake son matar sa”

“Kunji Asararriya ba” Addah ta katseta kamar zata kai mata duka kafin taci gaba da cewa

“Shiyasa nace ka barni nayi maka bayani malam dan wannan sallamammiya ce bata san ciwon kanta ba”.

Seda Malam yayi dariya sannan yace “toh Hajia ina jinki”. Gyara zama Addah tayi ta shiga koro bayani
“Kanaji malam, shi mijin nata Bashir Dan yar uwata ne. Da dabara muka samu har ya fara sonta ya aure
ta. Toh munyi haka dan zumunchi sannan kuma ko ba komai dan na samu me taimakamun tunda ni kaga
bani da Da namiji toh Amma yana da Mata.

Ita Matar Asma’u sunanta ta riga tasha kansa gaba daya abinda ya mallaka akanta yake qararwa daga ita
se yayanta, shekara biyu da auran nan amma ba uwar daya tsinana mana se rashin mutunchi salo salo
daga wannan se wannan kuma ita matar tasa na can kusa dashi a Lagos ita kuma wannan ya barmun ita
anan se sanda yaga dama yake leqo ta nayi nayi ya maida ita can amma abin yaci tura”.

“Toh ita matar shekarar su nawa a tare kuma yayan su nawa” Malam ya tambayi Addah yana murmushi
dan matar dariya ma take Bashi, se Addah ta karkace tace

“Inaga ta sha bakwai suke yanzu, haihuwar ta biyar harda tagwaye da anyi magana se ace ai ita tare suka
sha talauci”. Seda Malam yayi dariyar qarfin halin Addah kafin yaja qasarsa ya baza yana cewa

“Toh yanzu Hajia in banda qin Allah irin naki ta yaya kike so ya fifita matar daya aura shekara biyu akan
wadda suka shafe shekara goma sha bakwai tare Ai koda Arziqinsa ya aure su dukka su biyun bazaki taba
hada shaquwar shekaru goma sha data kwananna ba sannan ga zuri’a har shida a tsakani”.

“Toh nidai malam ko ma menene dai ina so Amirah ta zama mowa a gidan sannan ya ringa sakar mata
hannu yana mana bushasha idan so samu ne ma ni banqi Ma’u tabar gidan ba dan indai tana nan be
zama kallai mu samu yanda muke so ba”. Addah ta fada tana hura hanci, se Malam ya dago ya kalle ta
yace

“Hajia ribar musulmi ya mutu ya shiga Aljanna ni bana kashe aure sedai na qulla qilan Hajia bata gaya
miki ba kinganni nan bana aiki in cutar da wani sedai nayi maka kai ka samu mafita sauran zunubai na
ma sun ishe ni bazanyi dakon haqqi ba”.

Seda ya gama irga carbinsa kafin ya mayar da hankalin sa kan Amirah yace
“Ita uwar gidan naki ma tana dab da fita, sannan mijinki duk kalar asirin da zakiyi masa tasirinsa qalilan
ne akan sa baze dade ba ze karye. Ko ita da kuke ganin ta mallakeshi bada Asiri bane kawai ta iya zama
dashi ne amma bawai dan tana jin dadi yanda kuke zato ba.

Shawarar da zan baki itace kije ki gyara kanki ki gyara zaman ki kawai shi me son kyalekyale ne tun farko
abinda ya ribace shi harya aure ki kenan kuma itama matar sa da abinda take galaba akan sa kenan
amma batun ya so ki sama da ita babu shi, dan ko mutuwa tayi ba na jin akwai wadda zata iya maye
masa gurbin son da yake yi mata”.

“Toh malam na gode, se kuma matsalata malam haihuwa biyu kenan nayi ta farkon bezo da raina ba ta
biyun kuma sati uku da haihuwar ta koma daman bakwaini ce” Amirah ta fada a sanyaye,

“Wannan Kuma daga Allah ne itama mahaifiyarki ai haka tayi ko, randa yaso se ya baki rayayyen” ya fada
yana miqewa.

Kamar anyiwa Addah Bushara da aljanna baki har kunne tace “Malam kace zata fita yaushe kenan amma
bazata dawo ba ko?”

Banza yayi mata ya shiga dakin daya fito minti kadan ya dawo da daurin wata saiwa da kuma garin
magani a leda ya miqawa Amirah yace “ki tafasa ki ringa sha ze gyara miki jiki wannan kumburin ya sabe
tunda bakiyi wanka ba wannan kuma kisha da madara ko Kunu Allah ya qara rufa asiri amma a shawarce
dai da kin nutsu dan kalar mijinki ko kinyi asiri idan baki san yanda zaki tafiyar dashi ba wahalar banza
zakiyi”.

Godiya tayi masa ta miqe, Addah ta kalleta tace ina zaki je kuma?”

“Shikenan ai ko Hajia na sallame ku koda wata magana” ya fada yana kallon Hajia Maliya se Addah tayi
caraftace “malam baka ce komai akan daya yar uwar tata ba batun aure babu tsayayye”.
“Shidai malamin Primary da kika qi shine mijin idan kuma kika daga za’ayi dayan biyu ko ki mutu ayi ko
kuma a haife miki shege a gida” ya fada ba tareda ya kalle ta ba, se Addah ta dage qirji tace “na shiga
uku Malam na mutu fa kace?”

“Hajia Da wani abu ne ko shikenan” ya sake fada yana kallon Hajia Maliya, seta miqe tana cewa “Aa
babu komai malam daman yau rakiya nayo ni ai al’amura se godiya kawai, Fatu bada abin sadaka mu
tafi”.

Kallonta Addah tayi da niyyar Magana Malamin ya rigata da cewa “Kuje tayi mun sadaka da kudin Allah
ya yafe mun zunubaina” daga haka sukayi masa sallama suka tafi.

Seda masu babur suka sauke su a Tashar Dukku har sun shiga mota Hajia Maliya ta kalli Addah tace
“Fatu bakiyi sadakar bafa ko se munje cikin gari?”

“Ke dallah rabani da dan rainin wayo, aikin me yayi mun da zanyi masa sadaka wani Allah ya yafe masa
ashe yasan abinda yake babu kyau kenan” Addah ta fada a fusace dan sam ita ba abinda taso ba kenan,
dukda wani sashe na ranta yayi fari da aka ce Ma’u zata fita amma ita so tayi ayi mata abinda idan ta
fitan bazata dawo ba.

“Ai aikin gama ya gama tunda har kika taka kikaje gurinsa kema kin debo naki kason zunubin kuma dole
ki bada kudin nan kinsan dai ba’acin kudin malamai a zauna lafiya” itama Hajia Maliya ta hayayyaqo
mata.

“Gashinan nidai Allah ya saka mun” Addah ta gada tana cilla mata yan dubu dubu guda biyar, se Hajia
Maliya ta cafe ta fita daga motar tana cewa “Ya saka mun dai nida na kawo ki ke da ba’a miki abun
arziqi, Yara Almajirai ta samu ta bawa kudin kafin ta koma motar mintina kadan ta cika suka dauko
hanya.

Da suka sauka a tasha ma sama sama sukayi sallama kowa ta kama gabanta, suna zuwa gida kuwa
Amirah ta tafasa saiwar nan ta fara sha dan tafi mata magungunan da Addah ta karbo kwana ki tana ji
Addan nata bala’i waya sani ko shima hadin bakine da Maliya irin nasu Wizy ita dai bata kula ba harta
gaji tayi shiru dan kanta.

Suna dan yin waya da Bashir lokaci zuwa lokaci badai kamar da ba kuma yawanci da rana ne idan yana
gurin aiki da ya shiga gida kota kira baya dagawa ta rasa abinda yasa. Randa ta yi masa qorafi ma seda
suka samu sabani har yayi mata yaji kusan kwana hudu be kirata ba toh da yake neman shir takeyi tana
so ta karbi kudi a hannunsa ta danyi wasu abubuwan shi yasa ta kira ta bashi haquri.

Kwananta uku da dawowa sukayi baquwa, Amaryace da aka kawo gidan da yake kallon nasu daman
matar gidan ta rasu tun tuni se yanzu mijin ya sake aure.

Amarya Sa’ada da kadan ta girmi Amirah amma bazawarace auranta daya tana da yaya biyu ma suka
rabu da mijinta cikin dan lokaci sabo sosai ya shiga tsakaninsu da Amiran da yake mijinta ba mazauni
bane kusan kullum in ta gama ayyukanta se ta shiga gidansu Amirah kota kira ta ita taje suyi hira a haka
har ta karanci Amiran ta gane irin zaman da sukeyi da Bashir har ma da kishiyarta.

“Amma kedai anyi mara wayo wallahi, yarinyar ki dake kin maida kanki baya ita me haihuwa biyar itace
star a gurin miji kina zaune. Inda kinsan kanki wallahi da tuni sanda ze tattarota ya dawo da ita nan ke ki
bishi bama ze sani ba” Sa’ada ta fada ranar da Amiran take mata qorafin Bashir yaqi kaita inda yake aiki.

Kwananta Arba’in da biyar da Haihuwa Sosai kuma taji dadin maganin da Malamin nan ya bata dan duk
sauran kunburin nan bata fi sati tana sha ba ta neme su ta rasa jikinta ya dawo dai dai rashin kwarin da
takeji ma duk ya ragu daman kuma aikinta tuni ya kame yayi kyau dan haka ta fara shirye shiryen tarbar
Bashir.

Tunda ya tafin nan be sake ce mata ze zo ba itama kuma ganin bata gama shirya wa ba ya saka bata ce
masa yau she zezo dinba amma yanzu da take jinta garau dole ta nemo shi dan haka ta chanza salon
hirar su yanzu, babu ruwanta ko yana offfice ta kirashi seta san yanda tayi ta rikitashi da salo kala kala da
ta koya a gurin sabuwar qawarta Sa’ada.

Wayar da sukayi ta qarshe ma wani Text Sa’ada ta rubuta mata tace ta tura masa, duk bala’in taurin
kansa se ya sauke ya taho gurinta idan kuwa taga bezo ba to ta sallama kawai Asma’u tasha gabanta har
gaban abada Bashir baya Sha’awar wata Mace idanba ita ba ilai kuwa tana tura masan ta kirashi ta sake
gigitashi da kalamai masu kashe jiki se ji tayi yace gobe zezo Gombe,

da tayi masa qorafin ba,a share gida bama cewa yayi babu komai ta shirya daya zo se suje Hotel kawai ai
kuwa kamar tayi me dan murna tun a Daren ta fara shirya kaya da abubuwan da zatayi amfani dasu ji
takeyi kamar ta janyo safiyar tayi.

Bashir ya sauka Gombe lafiya kamar yanda suka tsara da Amirah yana sauka ya kirata dan da Naziru ya
dakko shima a hanya ya sauke Nazirun ya karbi motar ya wuce gidan Addah yana zuwa ta fito suka tafi.

Babban Daki me kyau ya kama musu, su Amirah se rawar kai ake itama yau an fita yawan shanawa da
miji, dan hoton nan da akeyi mata da miji anje chilling ita sedai ta gani a gurin qawayenta saboda duk
sanda zezo gurinta a Gomben seta jangwalo tsiyar da zasuyi in ma an shirya fitar ta rushe shiyasa take
shaqar takaici idan taga hotonsu da Ma’u Fitar Asabar da Lahadin nan da sukeyi toh itama wannan karon
in sha Allahu zata dage babu abinda ze bata mata wannan lokacin hotuna kuwa sedai zuciyar wasu ta
buga dan haushi.

Sosai sukaji dadin zama a hotel din nan an murji Amraci an more, washe gari Asbar da safe yaje gidan su
Ya gaida su Dada be dade ba ya koma, sun sha yawon su kuwa Joint joint ta dinga janshi ansha hotuna
sosai ya kuma yi mata shopping sosai. A yar Keypad dinta ta tura hotunan saboda me memory ce, ta
daure ta cije batayi masa zancen waya ba ta bari ta gani zuwa ya tafi tukunna karta ballo wata tsiyar.

Seta tuna maganar malamin nan daya ce idan ta kwantar da hankali zata ji dadin Bashir Asiri ba wani
tasiri zeyi akan sa ba gashi kuwa ta gani dan cikin lumana ya amince ze chanza mata Tv da Set din Tv
stand da Centre table harya bada kudin Tv da deposite din su Centre table din duk da dai Tv ba irin ta
Asma’u bace amma itama babba aka siya mata 53’ ina laifi?

Randa ze tafi kuwa harda ita suka kaishi Airport tana narke masa kamar karsu rabu suna dawowa gida
Naziru ya ajiye ta ba’a rufa awa biyu ba se gashi da sabuwar IPhone 11 pro inji Bashir a kawo mata harda
layi me Data.

Murna kamar Amirah tayi me ta ringa kwasar Shoki tana tsalle nan da nan ta kirashi tayi masa godiya
“Indai zaki chanza ki dawo irin haka babu abinda bazanyi miki ba Meerah” Bashir ya fada. Cike da sabon
jin dadi sukayi sallama ta kashe wayar nan da nan ta hada ta ta dora layi ta shiga downloading
WhatsApp, a wayar Ummi ta saka Memoryn ta ta tura hotunan zuwa sabuwar wayar ta tana cewa “yau
akwai fafatawa kenan, dole nawatsa hotuna a Internet kowa ya gani” (An kuma ashe tuban muzuru
kikayi toh Allah sa a wanye qalau dai )

Biki mukeyi se Monday In Sha Allah zaku ji ni

WATA KISHIYAR

(ALKAHIRI CE KO SHARRI)

Na Maryamah Farouk

(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)

Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 29

Asma’u

Alhamdulillah shine abinda zance dan yanda komai yake tafiyar mun lafiya lau ba tareda wata matsala
ba. Dukda aikina na office ya dan qaru dan yanzu har tafiye tafiye zuwa sauran states na Nigeria nake yi
amma saboda goyon baya dana samu daga Bashir se abin yazo mun da sauqi musamman da tafiyar tawa
bata wuce kwana daya a mun dade ne mu kwana biyu.
Tuni Amna sun gama sun gama SSCE tana zaune a gida se jiran sakamako kuma abinda ya qara
sauqaqamun abubuwa kenan dan kona dade a waje bani da tunanin na dawo gida na tarar da wani aiki.

Baban Ali da Amaryarsa kuwa se sam barka dan naga wani shiri sukeyi yanzu bini bini yana hanya an tafi
Gombe, ina yawan kama shi yana waya da daddare dukda yanzu ya denayi a daki sedai ya fita ko kuma
naga Text dinta idan ta turo har mamaki da dariya abin ya ke bani na tabbatar wannan ba dabarar ta
bace ta samu wani da yake dorata a hanya ne.

Ni kuwa sosai hakan yayi mun dadi ko babu komai hankalin na ya kwanta yanzu ne zamuyi kishi na
hankali kowa ta iya Allonta ta wanke dan haka bana wasa babu daga qafa idan ya tafi kafin ya dawo
nayiwa kaina Gyara gangariya yanda zan kwance masa kai na shafe duk wani gigi daya taho dashi.

Sannu sannu rayuwa na shudawa kusan wata biyar kenan rabon mu da Gombe, tuni akayiwa Yara
register da School Bus zata dauke su ta dawo dasu abinda ya sake sauqaqamun zirga zirga ma kenan
tunda idan Bashir ya kaisu ni nake dawo wa dasu toh yanzu kuwa suna rigani dawowa ma tunda daman
kullum se sunyi jira bayan an tashi kafin a dauko su.

Jikin Goggon mu ne ya sake tashi da har seda aka kawo ta nan Lagos Asibiti wanda Alhaji Qarami Babban
Yayan mu ne ya dauki nauyi dukda yanda muka so ya barmu muyi amma yaqi harya nuna bacin ransa
akan mun banbanta tsakani kenan.

Satin ta hudu a Lagos shima dakyar dan kwananta uku a Asibitin aka sallameta amma zata ci gaba da
zuwa ganin likita na tsahon sati hudu dakyar da ban baki ta yarda zata zauna a gida na wai ita bazata je
godai godai ta zaunawa siriki a gida ba seda Bashir din yasa baki sannan fa ai kuwa ranar zuwanta na
qarshe washe gari ta koma Yola tareda Amnah da Faridah zasu yi kwana biyu dan su Faridan sunyi hutun
Term.

Tafiyarsu da kwana biyu Bashir ya tsiromun da wani sabon hali, a da duk dadewa baya wuce sallar
Magriba a waje shima se ta qure kenan ko da zeje wani guri seya dawo gidan dai ya shirya sannan ya tafi
amma a kwanakin nan se ya kai Tara Goma be shigo gida ba.

Ranar farko qarfe Tara ya dawo a gajiye na tare shi, seda yayi wanka na kai masa abinci yana ci nake
cewa “yau kayi dare Baban Ali ina ta kiran wayar ka kuma bata shiga ba”.
“Eh aiki ne yayi mun yawa shiyasa na tsaya na dan rage wasu abubuwan” ya fada yana ci gaba da cin
abincinsa. Har ga Allah na yarda saboda ya samu qarin girma kwananan dan haka nasan ayyukan zasu fi
nada dalilin daya saka washe gari ma daya kai goma ban damu ba da yake ma ina dan fama da ciwon kai
ka fin ya shigo nayi bacci seda Asuba Aliyu ya ke cemin jiya se 10 Abbi ya dawo.

Abinda ya fara jan hankalina da dadewar tasa yanda abin ya zamar masa jiki dan seda ya jera kwana
hudu kullum kuma a maimakon ya rage lokaci qarawa yakeyi, a ranar na hudun data kama Asabar, tun
Daya na rana yayi wanka ya fice wai zeje gurin Musa abokinsa akwai wani aiki da sukeyi tare beyi awa
biyu da fita ba nayi baquwa.

Maman Shukra maqociyar muce a Estate din da muka fara zama kafin mu dawo nan rabon da mu hadu
har na manta ma ina zaune se gata.

Bayan na gabatar mata da kayan ciye ciye na zauna ina sake yi mata sannu da zuwa. Yanda take kallona
tunda ta shigo ya tabbatar mun bakinta akwai magana dan Maman Shukra akwai gulma sedai na
tabbatar da bata qarya, duk labarin data fada maka to kodai ba gaba daya bane idan kabi diddigi seka
gano gaskiyar.

Kallonta nayi da yar dariya nace “Maman Shukra wace jarida muka samu dan tunda kika shigo naga
bakin nan naki yana motsi”.

Seda ta kora ruwa me sanyi kafin ta kalleni tace Maman Farida Engineer yana gida kuwa?”

Ina dan murmushi nace “ai kuwa kunyi sabani danba dadewa ya fita yaje gurin abokin aikinsa suna wani
aiki ne”.

“Aiki, lallai aiki kuwa” ta fada tana kama baki. Sena maida hankalina gaba daya kanta na kalleta da son
jin qarin bayani.

Qasa tayi da murya kafin ta fara cewa


“Nidai ba zan fada miki dan na hada ki husuma da mijinki ba sedan kawai ki tashi tsaye ki dauki matani
tunda wuri kina dai kallon halin da nake ciki kullum cikin fargabar kar kana zaune a zo a shafa maka
alaqaqai”.

Wato tunda ta fara magana qirjina ya shiga kidan Mandiri, ko bata fayyace mun komai ba na rigada na
gano inda maganar ta ta dosa dan Mijinta ba qaramin dan Akuya bane, saboda tantiranci har gida yake
kai mata mata seda tayi da gaske da taimakon Allah sannan ya rage ba wai ya dena dukka ba. Jin da tayi
nayi shiru ina kallonta yasa taci gaba da cewa

“Baban Shukra ne yazo mun da soki burutsun sa wai Mijin qawar tawa da kike qara zugani ina masa
rashin mutunchi ashe duk kanwar ja ce shi da shi yau sun hade a Jungle ya dakko wata Babe me zafi,
banyarda ba tunda nasan halin sa ba sanin me yakeyi bama yake wani lokacin se washe gari wallahi
Maman Farida mun fita da daddare za’a siyowa su Hisham Icecream mukayi kicibus da su a gurin,

Saboda Baban Shukra ya tabbatar mun seda muka jira su suka gama abinda zasuyi suka fita yabi bayan
su har Hotel din da take mukaje kafin muka tafi gida. Washe gari ma ya sake cemun ya ganshi kamar ma
daki ya kamawa yarinyar a gurin yake zuwa yana tafiya in taqaice miki jiya gurin 11 ma video call ya
kirani ya nuna mun su a Gurin swimming pool kin ga har hoto ya musu kiga evidence fuskarta ce daibata
fito ba”.

Idan da Maman shukrah tasan yanda maganganunta suka jefani da ta dade dayinshiru amma seta
miqomun wayarta tana cewa “kin gani karma kice qarya nake”.

Duk yanda naso na hana ido na kalla abin ya gagara, a fili na furta “Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un” ina
dafe qirjina jin kamar zuciya ta zata bullo ta fito, dagaske Bashir ne ga fuskarsa nan yana murmushi ya
rungume wadda bansan ko wacece ba ta juya baya dan haka ba’a ganin fuskarta.

Har Maman Shukra ta qaraci surutanta ta tafi ban sake gane komai ba, dakyar nayi sallar Magriba da Isha
na nemi guri a palour na zauna ina jiran naga ta inda Bashir ze bullo.

Gaba daya ido na sun soye kaina ya qulle na ma rasa ta ina zan faro tunani kalmar “Innalillahi wa’inna
ilaihi raji’un” kawai nake maimaitawa wadda ta taimakamun wajen zama cikin hayyacina.
Ina zaune a palour har qarfe sha biyu na dare ina jiransa ga wayarsa na kira yafi sau nawa amma se ace
not reachable har Musan na kira shi kuma wayarsa a kashe.

Hankali na a tashe ina ta zagaya Palour ina kuma sake gwada wayar sa cikin Sa’a ta shiga daidai sanda
naji tsayuwar motarsa a waje se na kashe na tsaya jiran shigowarsa.

Yanda yaci burki yana kallona ya tabbatar mun be so ya tarar dani ido biyun ba amma saboda iya
duniyanci irin na Namiji se ya wani chanza fuska zuwa kalar gajiya ya fara sakin wasu guntayen tsaki yana
langwabewa, zuciyata na dukan uku uku na nufe shi, a raina Addu’a nakeyi Allah yasa abinda Maman
Shukrah ta fada ba gaskiya bane sedai ina qarasawa dab da shi Qamshin Turaren Humrah da kuma
shatin Jambaki daya fito radau a gefen kumatunsa da wuyansa suka yi mun sallama,

Dum naji a kaina kamar wadda aka kwadawa guduma, Ban yarda daidai idona ya gani ba dan haka da
saurin gaske na riqo fuskarsa na kunna torch light din wayata na haska da kyau se ya janye yana cewa

“Ma’u lafiyarki kuwa, me kike nema a fuskata kuma?”

“Kai zan tambaya Bashir daga ina kake? Turaren waye a jikinka sannan ga shatin Lips din mace nan a
Fuskar ka Bashir daman zaman da kakeyi a waje abinda kake yi kenan to yau Allah ya toni asirinka?” Na
fada cikin tashin hankali ina ja da baya, se yayi saurin riqoni ganin ina neman fadawa kan Centre table ta
baya na fizge cikin faga murya nace

“karka kuskura ka tabani, daman an gaya mun ana ganinka da mace amma saboda yardar da nayi dakai
yasa ban taba kawo wa raina zakaci amanata ba, kana da Mata har biyu dame muka rage ka Bashir zaka
fita waje kana zubar mana da mutunchi? Wace yar iska ce ka ajiye a Hotel kake zuwa Gurin ta har
mutane suke ganinka ana daukar hotonku?”

A zabure ya kwalalo ido waje yana kallona yace “Hotona Ma’u? Waye ya dauke mu?”
“Oh ta tabbata kenan ka aikata, kana zaton Asirinka ze rufune? Toh Allah ya tona ka na gani kuma
mutanen duniya ma sun sani duk me maka kallon mutumij kirki ka zubarwa da kanka mutunchi a
gurinsu” na fada wasu hawaye masu zafin gaske suna zubo mun, Se ya sake matsowa yana qoqarin riqe
ni yace

“Ya isa Ma’u karki tayar da yara a bacci ki bari muje daki zan gaya miki komai ba abinda kike zargi bane
wallahi”.

Wani banzan kallo na watsa masa kafin nace “Dawa zakaje dakin? Idan kaga na dara daga nan toh ka
gayamun wace yar iska ka ajiye a hotel yara kuma ai bakayi tunanin su ba kaje kana zubar musu da qima
kana raba musu abin gori a gari”.

Duk yanda Bashir yaso dana sassauta na zauna muyi maganar qi nayi, gani nake yama raina mun hankali
tunda alama ya nuna maganar Gaskiya ce dan da nace naga hotonsa ai be musa ba abinda ya qara
dagamun hankali kenan na shiga rusa kuka ina cewa “Ka cuce ni Bashir ka cuce ni idan har mugun
halinka ya shafi yayana bazan taba yafe maka ba”.

“Wallahi Asma’u ba abinda kike tunani bane ta yaya tun da quruciyata ban nemi matan banza ba se
yanzu da girma ya fara kamani na tara iyali? Ku biyu fa nake da ku wace ni’ima ce Allah beyi muku ba da
zan fita waje na nema?”

“Ita waccen din da ka ajiye qanwar uwarka ce kenan” na fada a mugun fusace nayi kansa dan rainin
hankalin nasa kuma ya fara yawa, ganin da yayi na taho gadan gadan se ya matsa yana cewa “ba wata
bace Ma’u Amirah ce, wallahi Amirah ce tazo nasan bazaki yarda ki sauketa a gidan nan ba shiyasa na
kaita Hotel”.

Wani burki naci tareda qamewa a inda nake ina rarraba ido tsakanin idonsa da bakinsa, so nake na
tabbatar da abinda kunnena yaji ko kuwa ba daidai bane, se ya matsoni yana sake cewa “Amirah ce tazo
wallahi tun last week Sunday, nima ban sanda zuwanta ba seda ta sauka tace mun gata a Lagos, ban san
yanda zaki dauki maganar ba shi yasa na kasa fada miki wallahi amma gobe ma zata tafi”.
“Bashir dakai da ita kuje Allah yayi muku yanda kuke mini” na fada cikin wani irin sanyi kafin na juya na
shige dakina kfain ma ya biyoni na sakawa qofar key. Kan gadon na fada na fashe da kukan da ko
mutuwar Mahaifina banyi irinsa ba.

Kuka ne na zallar baqin ciki da takaici wannan wane irin abu ne? Anya Bashir yana da hankali da tunani
kuwa, yana lissafi kafin ya aikata wani abun?

Idan ya gayamun Amirah zata zo me zanyi, kai ko be fadamun ba ina zaune ta shigo gidan na ya zanyi da
ita ai gidan sa ne kuma ko bata auran Bashir ita me iya zuwa gidansa ta zauna ce amma shine ze dauketa
ya kaita Hotel ya ringa satar hanya yana zuwa mutane suna ganinsa yanzu Allah kadai yasan mutum
nawa suke masa kallon Fasiqi ya ajiye farka a Hotel.

Inajinsa yana buga qofar yana magiya na bude amma nayi banza dashi na tashi nayiwo alwala nayi na
tada sallah ina yi ina kuka ban idar ba seda aka fara kiraye kirayen Asuba, ina idar da Sallar Asuba kuwa
wani wahalallen bacci ya kwashe ni da ban farka ba se sha biyun rana shima qiqi qiqin da ake da qofa ne
yasa na bude ido na.

Ina dafe da kaina dayayimun nauyi na nufi qofar jin surutan mutane kamar ma ballata ake so ayi se na
murza key din naja baya ganin yanda Bashir ya fado kamar an cillo shi, a bazata ya rungumoni ban yi
wata wata ba kuwa na hankadashi da dukkan qarfina yai baya Allah ya taimake shi bango ya tare shi, ina
kallon securities din daya gayya toh suka juya suka tafi.

Be daddara ba ya sake nufo ni yana cewa “Ma’u lafiya kike tun jiya kin kulle qofa babu irin bugun da
banyi ba gaba daya kin tayar mana da hankali ga yara can se kuka sukeyi”.

Tsaki nayi na juya na cire Hijabina na shige bandaki na bar shi a tsaye a gurin, sanda na fito baya nan,
riga kawai na zura dan banida nutsuwar da zan saka komai a jikina, bakina har wani daci yake mun
saboda bacin.

Lokacin da na fito Suna zaune shida Matarsa da ban san sanda tazo ba sunyi tsuru kamar masu jiran
Sadaka. Kallo daya nayi musu na wuce Kitchen inajinsa ya taso ya biyo baya na seda muka shiga ciki
sannan na waiwaya na kalle shi nace “kasan Allah ko ka fita ko kuma ka kalli nan (na nuna masa
bangaren da wuqaqe suke) gasu nan kala kala in ka qureni se nayi maka aika aika na huta da takaici” ai
kafin na qarasa fit ya fice daga Kitchen din duk yanayin bacin ran da nake ciki seda nayi dariya sosai dan
dagaske ya tsorata.

“Allah ya tsare ni da irin wannan zuciyar” na fada a fili kafin na zuba ruwa a kettle na kunna kafin ya
tafasa na hada kayan shayi a babban kofin dan bazan bari baqin cikin Miji da kishiya su naka sani ba.

Shayina me kauri na hado na zubo dambun nama a bowl na dakko ledar biredi, kamar bansan da tsurom
mutane ba haka na nemi kujera na hakince sannan na kunna Tv ina shan shayina ina kallo.

“Ma’u ga Amirah kin ganta wallahi ita ce ba wata daban ba na yarda nayi kuskure tun farko da ban sanar
miki da zuwanta ba amma kiyi haquri”.

Yanda yai maganar kamar wanda yayi wa babarsa wani qundumemen laifi yazo bata haquri harda wani
zamowa qasa saboda tsabar iya sharri ga muryar sa har rawa take yasa na kalle shi, seda na cinye biredin
dana tura a bakina na kora shayi sannan cikin dan murmushi nace

“Oh wannan be ishe ka ba kenan seka qulla mun sharri a sake tafiya dani a baki ace na mallake ka har
durqusamun kake ba?

Ni tunda nake dakai ma ka taba bani haquri ne amma da yake yau kana so ka qaramun baqin jini shine
kake duqawa ai shikenan, ni na gama magana ta tun jiya duk abinda mutum yayi mun na barshi da Allah”
daga nan na ci gaba da cin abincina ina jinsa ya qaraci naci da magiyar sa amma tafi ka mutu bance masa
ba.

Amirah da ta shaqa tayi tam daman ga takaicin dakko ta dayayi tun da sassafe ya ringa surfa mata ruwan
masifa ga abinda ta janyo masa nan ana yawo dashi a gari an ce ya ajiye karuwa ya taso ta a gaba wai
tazo su bawa Ma’u haquri tun bakwan safe take zaune se yanzun dana fito ga wannan Dramar da yakeyi
kuma har wata kwallar takaici ce ta taru a idonta. Cikin muryar bacin rai tace

“Ni Yaya ka dakko ni tun safe ko wanka banyi ba bare naci abinci gashi yanzu Azahar tayi gaskiya ni
yunwa nake ji”.
“Waya hana ki kici abincin ai gaki ka Kitchen nan duk bake kika jawowa mutane ba” ya hayayyaqo mata,
seta miqe zata tafi Kitchen din nayi sauri tare ta da cewa “Ji mana, karki shigar mun Kitchen malama ku
koma can inda ya aje ki ki nemi abinci ba’a nan ba” ban qarasa cinye biredi na ba na daure ledar kawai
na kwankwade shayin na tashi. Seda na kullo qofar Kitchen din da mukulli na zare kafin na shige dakin su
Aliyu na bar Bashir da Amirah baki sake suna bina da kallo.

Aliyu da Jafar na zaune da alama duk suna jin abinda yake faruwa se nayi murmushi na zauna ina cewa
“me kuka bawa yan biyuna har yanzu basu tashi ba?”

“Game sukayi tayi Mami basu kwanta da wuri ba jiya dakyar suka tashi dazu suka ci abinci ma” Jafar ya
fada. Whatsapp na bude a wayata ina shiga message din Maman Shukra ya fado nayi murmushi na bude

“Maman Farida ina fatan dai bada tashin hankali kika tunkare shi ba ko, kinsan fa irin wannan abun se a
hankali da Addu’a kuma in ba haka ba a maimakon a samu sauqi se ka qara tunzura mutum” ta rubuta,
se na mayar mata da cewa

“Ai baki sani ba, ashe Amaryar sa ce tazo sh ya sauke ta acan kin gansu tun dazu ya dakko ta tana nan”.

“Tab amma se abar Engineer, to ke me kakace yanzu?”

“Me zance kuwa, gasu can na barsu a palour ni ina daki ma bacci zanyi se anjim mayi magana” na fada
dan na datse hirar.

Alawiyya yayata na duba naga bata online, fita nayi daga dakin na koma nawa dan ina so na l kirata,
sanda na fito palour Bashir kadai na tarar har na wuce na yi kwana na shiga dakinsa. Addu’a nake Allah
yasa tana ciki yau na gwada musu danyan kai daga shi har ita se Allah ya temaketa babu kowa har Toilet
na duba bata ciki na kullo qofar na fito se ya tare ni yana cewa

“Ta tafi gidan Ghali daga can gobe seta wuce Gombe” (Ghali dan wan Baban su Bashir ne).

Wunin ranar zir haka yayi shi a palour daya ji motsina ze taso yana so yayi mun magana amma naqi bashi
fuska sam da daddare ina jinsa suna waya yana ta masifa nidai qala bance masa, daya biyo ni dakina ma
abinda tun tsahon zaman mu a gidan nan be taba kwana a ciki ba yana kwanciya na juya mukayi kai da
qafa yana fita sallar Asuba kuma na saka Key.

Haka muka cinye satin, har zuciyata na huce kodan irin ban haqurin da ya ringa yi mun amma ban nuna
masa ba, yanzu dai ina dafa abinci dashi kuma in yayi mun magana ina amsawa sakin fuska ne dai babu
na kuma dena shiga sabgarsa sannan na koma dakina da kwana kullum kuwa se ya bini.

Bansan ya suka qare da Amirah ba nasan dai ta tafi, dukda abinda ya aikata ai ba laifi bane ko babu
komai ai matarsa ce daman ai yana da ikon kaita ko ina amma yanda ya biyo da abun ne babu tsari a ciki.
Dan haka fushin kwana biyu na qara kafin na ware muka koma daidai kamar bamu samu wani saba ni ba.

Amirah

Da baqin ciki da takaicin Ma’u da Bashir ta koma Gombe, har kuka tayi sanda take labartawa Addah
abinda ya faru.

“Se kinga yanda ya rikice Addah harda durqusawa yana bata haquri a gaba na ita kuma se yankwana shi
takeyi saboda ta nunamun ta isa dashi. Saboda wulaqnaci fa gidan Ghali ya turani na qarasa kwana
sannan da zan taho ma Taxi yasa ta kaini Airport se a waya mukayi sallama”.

“Tab lallai Asma’u ta gawurta yanzu Bashir din ne ya duqa mata, lallai dole mu sake tashi tsaye. Ni ina
ganin komai yayi lafiya yanda kwana biyun nan aketa abin arziqi ashe da sauran rina a kaba” Addah ta
fada tana kama baki.

“Ai wallahi bata ci bulus ba, yanda ta rusa mun tsarina nima sena rama” Amirah ta fada, daga nan suka
shiga qulle qullen yanda zasuyi su rama abinda Ma’u tayi mata.

Lagos

Ranar Juma’a data kama litinin a koma makaranta Amna da Farida suka dawo, ban gayawa Bashir ba na
saka Naziru ya siya musu Tickets dan daga Yola Gombe aka kaisu se ganinsu kawai yayi ai kuwa ya ringa
masifa akan me zan doro masa yara a jirgi su kadai me yasa ba’a gaya masa yau zasu dawo ba yaje ya
taho dasu ko shi Nazirun ya rako su nidai nayi banza dashi tunda sun dawo ai magana ta qare.
Monday qalau muka rabu kowa ya tafi aikinsa ranar na dan jima a office saboda shirin Tafiya Abuja da
mukeyi wani conferees se bayan Magriba na shigo gida. Seda mukaje kwanciya sannan nake gayawa
Bashir dan saura sati daya tafiyar.

“Lallai Big woman anya nima bazan zo a dan sama mun guri ba naga fa kuna kwasa da yawa a office din
nan naku” ya fada da dan murmushi yana danne danne a wayarsa, sena gyara zama ina cewa

“Kaidai bari wallahi yanzu ma fa package din tafiyar nan naji Accountant yana cewa kusan 700 huns za’a
bamu each kudin TP da accommodation ni daman gidan Alhaji Qarami zan sauka kaga sena soke kudina,
Goggo nake so ma na biyawa Umarar Azumin su tafi tareda Maman Ayman”.

“Hakan yayi kyau, nima idan na samu yanda nake so se mu tafi da ke ita kuma Amirah se taje Hajji”.

“Allah ya yarda toh” na fada sannan muka ci gaba da hira har bacci ya dauke mu.

Weekend din daya kama satin da za’a shiga zanyi tafiyar ranar Asabar da daddare na sake gaya masa
zancen tafiyar base ranar Monday ya ganni da jaka ba.

Yana zaune na kawo masa coffees da yace yana so nake masa zancen ina cewa “Allah ma ya taimake ni
Amna na gida yanzu da bansan yanda zanyi tafiya harta sati guda ba”.

Shiru ya mun yaci gaba da shan coffee dinsa nima se na mayar da hankali na kan Tv seda ya mula dan
kansa se cewa yayi “wai dole ne se kinyi tafiyar nan?”

Ban waiwayo ba na bashi amsa “Kaji Baban Ali da wata magana, tun fa last week na gaya maka, me ze
kaini toh idan ba dole ba”.
Tsakin daya ja ne ya saka ni waiwayawa na kalle shi, fuskar nan a mugun hade seda gaba na ya fadi dan
rabon da nagan shi a irin haka an kwana biyu.

“Lafiya” na fada ina gyara zama na fuskan ce shi da kyau, se ya miqe kawai ya shige dakinsa nima na rufa
masa baya.

“Kibar tafiyar nan kawai dan bazan iya zama har sati guda ni kadai ba” ya fada yana cire rigar jikinsa da
alama wanka ze shiga. Sena marairaice cikin lumana ina cewa

“Haba Engineer satin fa kamar yaune qilan ma baza mu kai haka ba, kayi haquri ka daure In Sha Allah
gaba idan haka ta taso zan nemi a chanza wani dani amma yanzu lokaci ya qure kaga jibi ne fa tafiyar”

A maimakon ya sakko se nagama kamat fetur na qarawa wutar dan hargagi ya shiga yi mun yana cewa
“nidai na gaya miki kawai, ke ni aikin nan ma gaba daya bana sonsa daman idan mace taga tana samun
kudi gani takeyi kanku daya tunda babu abinda zata nema a gurinka, kai ta yaya ma za’ayi mutum yana
da mata amma ta tafi wani guri tayi har sati daya meye marabar sa da gwauro” bam ya shige Bandaki ya
bugo qofar sena rakashi da ido kawai ina karanta Hasbunallahu wani’imal wakeel a zuciyata.

Abin ya motsa kenan, haka naja jiki a sabule na fice na koma dakina. Rasa wanda zan kira na gayawa
wannan abu nayi ina zaune sega kiran Babbar yayar mu a dakin mu Anty Suhaima da take America ta
kirani.

Bayan mun gaisa mukayi shiru dan babu sabo sosai tsakanin mu saboda ita da wuri tayi aure ta auri dan
Abokin Baffan mu yan Kano ne a lokacin Baban sa shine Ambassador na Nigeria a America dan haka
tunda tayi aure can aka kaita kusan shekara Ashirin da biyar yanzu.

Jin shirun naw yayi yawa ya sakata cewa “Ma’u lafiya kuwa kamar akwai abinda yake damun ki” haka
kawai naji kuka ya taho mun ba kuwa ta hanani ba ta barni na yi abuna seda nayi shiru dan kaina kafin
na gaya mata yanda mukayi da Bashir.

“Daman baya son aikin naki tun farko ne ko yaya” ta tambaye ni,
“Wallahi Anty be taba nuna baya so ba, tun ma ba yanzu ba kinsani kafin wannan nayi wau qananun
ayyukan kuma be taba hanawa ba a koda yaushe yana bani goyon baya, yanzun mafa ya yarda yau ne
kawai dana sake gaya masa zancen tafiyar shine kuma ya bullo da wannan maganar”.

“Shikenan, ki rabu dashi ki ci gaba da Addu’a zuwa goben ku sake maganar idan be yarda ba ki haqura
karki tafi ba tareda izinin sa ba idan yaso ki gayawa Alhaji qarami se aji me yake nufi da aikin naki daman
ai zaman aure dole akwai qalubale Ma’u Allah dai ya sa mu dace kawai” nasiha taci gaba da yi mun kafin
mu ka gaisa da yaranta dukka su hudu sannan mukayi sallama bayan na tura musu da Number Aliyu da
Amna da suka ce.

Ban koma dakin Bashir ba a zato na kuma ze biyo sahu amma har dare ya tsala naji shiru.

Da safe na sake tun kararsa da maganar se kuwa cewa yayi “In dai izinina kike nema toh ban yarda ba”
ya sa kai ya fice daga gidan.

Yana fita na dannawa Dadan su kira dan kuwa bazata sabu ba, tas na gaya mata yanda mukayi tace na
kwantar da hankali na zata masa magana, ilai kuwa da daddare ina zaune se gashi fuskarsa nan kamar
Hadari yace

“Wato qarata kika kai Gurin Dada ko? Shikenan kije amma ki tabbata sena dauki hukunci akan hakan”.

“Tunda dai ka barni ai zance ya qare” na fada bayan daya fice daga dakin, washe gari na cale zuwa Abuja
bayan na barwa yara komai da zasu buqata karma ya huce haushi na akansu.

Amirah

Sosai ta kunnowa Bashir wuta tunda ta fuskanci shi mutum ne me son a girmama shi ba kuma yason
raini se tayi amfani da wannan damar gurin nuna masa ai Asma’u ta raina shi kuma abinda take nuna wa
mutane kenan cewa tafi qarfinsa.

Da Samirah qanwar sa suka shirya komai dukda ita Samiran bata san amfani da ita Amirah tayi ba. Tana
zaune ta kirata take bata labarin abinda ya faru ai Bashir ya durqusaw Ma’u, Smairah kuma irin masu
dan banzan surutun nan ne idan taji abu kamar dukka dangi kowa yaji ne dan haka kafin kace me
wannan Labari ya karade kowa kamar wutar Daji cikin haka maganar ta koma kunnen Bashir.

Amma saboda rashin Adalci irin nasa a maimakon ya ji haushin Amirah data fada tunda a gabanta akayi
se laifin ya koma kan Ma’u a cewarsa da batayi masa boren da tayi ba ai da be durqusa matan ba har
Amiran ta samu abin yayatawa ba wannan fushin ya qudure a ransa.

Kwana biyu tsakani har ya huce tayi masa zancen biyawa Goggonsu Umarah se akayi dace washe gari
Bala ya kirashi, suna cikin waya yake ce masa

“Mutumina ashe Ma’u ta siyi gida nan kusa damu, jiya mun zagaya ta gurin naga gidan hadadde nake
tambayar na waye akace na matar ka ne kamar ma guda biyu ne fa ko Su Aliyu ta siyawa ne”.

“Anya kuwa Ma’u ta siyi gida ba tare da na sani ba me zatayi dashi, ina ga dai ba nata bane sedai wata
daga cikin yan gidan su ko” Bashir ya fada.

“Lallai Bashir baka san mata ba, ka manta lokacin baya kenan yanda yan uwanta suka tinga zugata akan
karta doraka akan dukiyarta. Yanda take karbar kudin Hayar gidajenta ga Albashi me tsoka ai dole ta
ringa siyan kadarori tana boyewa baka sani ba,

nifa wallahi nama ga baikenka kana zaune na tabbatar yanzu ta ninkaka sau uku a arziqi wallahi in
bakayi wasa ba kwanan nan zaka zama mijin Hajia se yanda tayi dakai tunda tafi qarfin komai babu
abinda zata nema a gurinka.

Da zaka ji ta tawa ma kasa ta ajiye aikin nan wallahi dan tana dab da finka Albashi bashi ne taqamarka
ba”.

Wadannan maganganun na Bala dana Amirah su suka yi tasiri a ransa dan yana ganin abinda Balan ya
fada gaskiya ne.
Tunani ya shigayi Rabon da ya dauki kudi ya bata ma shi harya manta daidai da kudin sati na man mota
da yake bata yafi wata shida be bayar ba kuma bata tambaye shi ba.

Daman cefane baya yankewa a gidan kusan zece buhun huna kadai yasan yana siya amma sauran
abubuwa tunda daman ita yake bawa kudin tayi mantawa yake kuma bata tambayarsa haka zega komai
a ajiye. Yanzu a satin daya wuce ta ce masa Bilal ya turo mata wasu motoci idan yana so ita ma zata
chanza tata ko School Fees din makaranta na wannan term din ita ta biya se daga baya ya mayar mata
da kudinta gashi kuma a kullum cikin yin suturu na alfarma take daga ita har Yaranta har shi tana siya
masa takalma da Agogo ga turaruka.

Wadannan abubuwan daya hasaso a shirmensa su yake ganin zasu sa tafi qarfinsa har ya kasa juyata
gashi kuma sauran mutane ma sun fahimci cewa Asma’u tafi qarfinsa a ganinsa babbar gazawa ce kamar
shi ace matar sa tafi qarfinsa dan haka dole ya dauki mata ki akai.

Kunsan December ansha Bukun kuna

Allah ya bawa Amaren mu zaman lafiya ya kawo na yan baya.

WATA KISHIYAR

(ALKAHIRI CE KO SHARRI)

Na Maryamah Farouk

(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)

Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 30
ASMA’U

Cikin kwanaki biyar muka gama abinda ya kaimu, ada naso na yi weekend na huta ne har nadan zaga
dangi amma saboda yanayin rabuwar mu da Bashir yasa na fasa daga gidan Alhaji qarami ko gidan
Yayata Junaidiyya da mijinta yayi Accident, naso naje na dubashi amma gudun kar sauran suce banje
musu ba yasa kawai na haqura.

A ranar Juma’ar da muka gama na bi jirgin dare zuwa Lagos.

Kadaran kadahan Bashir ya karbe ni, ban damu ba na shiga sabgogina ina dai ta qoqarin ganin komai ya
daidaita a tsakanin mu amma yaqi bada hadin kai sam.

Ranar Talata da daddare bayan mun gama cin abinci Bashir da Aliyu suka fita siyo Biredi sauran yaran
kuma duk suka koma cikin palour ni kuma na zauna a Gurin Dining din ina danna waya, kiran Muslim
Yaya nane ya shigo wayata, mun dan jima muna magana kafin mukayi sallama yana kashewa Khadija
qanwata ta kirani.

Abdallah ne ya taso ya kawo mun littafinsa na quantitative reasoning ya kakare a wani guri daman ina
jinsu da yayyan yanata su koya masa kowa yaqi dan haka na saka wayar a speaker muna hirar ina nuna
masa.

Hirar wata faccalarta takeyi mun, babansu yana da kudi kamar su kashe shi amma irin matsolon nan ne
ba’a cin kudin sa se akayi dace data tashi aure ta auri me kwadayi dan shi dalilin auranta ma saboda
kudin baban nata ne.

Tofa tunda akayi aure yaga babu lashi se rashin mutunchin yau daban na gobe daban qarshe ya yiwo
mata kishiya ma shine yanzu ba’a dade ba baban nasu ya rasu anyi musu rabon Gado ta samu kudi sosai
se kuma ya dawo kamar yaron ta se yanda take so yakeyi har Kishiyar ma yanzu ya mayar mata da ita
kamar me aiki kome take so shi za’ayi a gidan nan.
“Wallahi Anty se kin ganshi jiya da mukaje sabon gidan da tayi yana tsaye yanda kika san dan aiki daga
tayi motsi ze zaburo yace Hajia me kike so Hajia me za’ayi, ni ban taba ganin meson zuciya irin Rabi’u ba
wallahi” Khadija ta fada.

Dariya nayi ina cewa “kudi ake gaya miki huce takaici kenan, ai idan mace ta gawurta zakiga har mijin ma
wani shakkar ta yakeyi balle kuma kishiya. Shiyasa kika ga mun dage muna neman su maganin
wulaqanci” na fada dai dai sanda Bashir da Aliyu suka shigo, wani kallo dana kasa fassara ma’anarsa ya
yimun kafin yasa kai ya shige dakin sa.

Hirar mu muka ci gaba sannan mukayi sallama lokacin na gamawa Abdallah Homework din se na tashi
daga gurin nima na shiga dakin Bashir.

Qarar ruwa da naji yasa na gane yana Toilet, sena zauna a gefen gado ina jiransa ya fito.

Kudi nake so na ara a gurinsa ina so na qarasa mana siyayyar kayan sallah dan haka nakeyi kafin lokacin
yazo na siyi komai idan ya bani kudin se nayi wasu hidimar dasu yanzu kudaden hannuna duk na tattara
na bada kudin Umarar Goggo daman Kudin Hayar da zan karba na saka rai dasu to su kuma tun kafin
suzo ma na bada Aron su.

Seda na barshi ya gama shiryawa ya zauna sannan nace “Baban Ali Aron kudi nake so dan Allah”.

Shiru yamun ban damu ba na cigaba da cewa

“Kasan na gaya maka zancen tafiyar Goggo to na bada kudin, wadanda kuma nake saka rai na hayar
gidajen nan wallahi Yaya Abubakar ya rance wai ya cikawa su Bilal sun tada ginin gidajen su bayan
Babbar Sallah nan muke saka ran bikinsu”.

A maimakon ya amsa ze bani ko baze bayar ba se ji nayi yace “Lallai Ma’u karanki ya isa tsaiko.

Wato ban isa ki tambayeni kudi ba sedai kice na ara miki ko? To bari kiji ni ba sakaran namiji bane da har
kike tunanin dan kina riqe wasu yan kudade zaki fi qarfina, inaji har fada kikeyi kudi maganin wulaqanci
idan mace ta gawurta miji zeyi shakkarta to bari kiji ko kin fi Dangwote kudi ina nan a matsayin mijin ki
kuma baki isa na biki ba.
Daman tunda kika fara aikin nan naga halayenki da yawa sun chanza, saboda zan fita nema kema ki fita
kina ganin kanmu daya ba? to ya zama dole zan dauki mataki, ki fara shirin ajiye aikin nan”.

Kamar sokuwa haka na ringa binsa da kallo har ya gama magana. Dan Allah meye laifina anan? Daga
neman rancen kudi shine ze tado wadannan maganganun haka.

Sena sake matsawa kusa dashi ina cewa

“Yanzu saboda Allah Baban Ali rashin tambayar ka kudi da nakeyi ashe nan ma laifi nake ada da nake
tambayar ka kuma cewa kayi ai na ishe ka da bani bani kai bakaga amfanin Kasuwancin da nake yi ba
wai dan Allah me yasa ba’a maka gwaninta ne??

Kuma ni a yaushe kaji nace nafi qarfin ka ko ina so ka bini idan dai ba neman tada zaune tsaye ba daga ji
mutum yana waya se kace dakai ake baka san hawa ba baka san sauka ba.

Maganar aiki ko kuma wani kudin daban da nake samu kasan idan da tarawa nakeyi da yanzu na kai inda
nakai wallahi amma ko na samu jikinka suke komawa tunda kafin na amfani kaina da biyar na amfana wa
yaranka da dari. Yaushe rabon da ka dauki sisinka ka bani da sunan wata hidima tawa kota yaran nan?

Siyowar da kakeyi da kanka ma tunda kaga idan ya qare inayi ka sakar mun se sanda ta raya maka
sannan zaka siyo ko ka bada kudi a siyayyar.

Idan ba sallah ba na manta rabonda yau Baban Ali ka kawo dankunne kace gashi wannan naki ne kuma
kullum kana ganina da sabon abu amma baka taba tambayata a ina na samu ba duk ba sauqin ka bane,
idan da bani da abinyi ai duk nauyin a kanka suke”.

“Oh gori zakiyi mun kenan daman ni nace ki ringayi ko ke kika dorawa kanki?

To ki dena, daga yau karki sake saka silenki a hidimar gidana kota yayana ki gani idan bazan iya ba” Ya
fada a fusace.
Haka kawai naji zuciyata ta karye wani kuka yana neman taho mun, wai me zanyi na burge Bashir a
rayuwa ne? Duk abinda nayi aje a dawo wata rana se ya zama abin fitina, seda na dauke hawayen daya
zubo mun akan fuskata kafin nace

“Ko baka fada ba nima bazan sakeyi ba idan yaso seka gani in abin kirki nake maka ko akasin haka” daga
haka naja bakina nayi shiru ina goge hawayen da suke zuba daga ido na dan na kasa hana su fitowa.

Meyasa maza ba’a iya musu a rayuwa ne? Idan kika zauna baki nemi na kanki ba a goranta miki idan kin
tashi kin nema shima baki tsira ba to ya ake so kayi?

Wayar sa ce ta katse mana shirun da mukayi se ya daga yace “zan kiraki” kafin ya kashe.

Ina lura da yanda yake satar kallona yana zuba tsaki se na dena goge hawayen na barsu kawai suna shata
se ya miqe gaba daya ya bar mun dakin yana fita kuwa na fashe da kuka me sauti harda sheshsheqa.

Bashir

Gaba daya jikinsa yai sanyi da ganin hawayen nata, shi da kansa yasan be kyauta sam Asma’u bata
cancanci wani abu a gurinsa ba bayan kulawa da tattali amma dole tasa kashi yin koma menene dan a
nasa ganin an fara dakko sare sarin da zata fi qarfin nasa saboda sam ada ai ba haka take ba.

Idan ya gaya mata magana tana ji amma yanzu abinda tasa a gaban ta kawai shi takeyi. Bata yij shawara
dashi sedai kawai ta gaya masa zatayi abu kaza in aka ci gaba da haka ai wataran ma se tayi sannan ze
sani dan haka ya quduri niyyar kawai ta aje aikin nan tunda shi yake sake bude mata ido tana hulda da
manyab mutabe tana ganin rayuwa kala kala.

Kwana biyu a tsakanin gaba daya na dauke masa wuta na fita a sabgarsa na kuma qudurce a raina yar
biyar dita Bashir baze sake ci ba. Dakansa ya sakko ya ringa neman shiri dayaga yanda na watsar dashi
seda na gara shi kuwa sannan na haqura amma fa ba wai na chanza ra’ayi ba jira kawai nake wata yayi
na fara tatike Aljihun Bashir.
Sati biyu tsakani wata ya qare kuma a satin nasan zeje Gombe, ina sane na zauna na rubuta uban list kai
harda abinda muke dasu seda na rubuta na hada total dina kusan dubu dari da Ashirin, ana gobe ze tafi
ina jinsa yana mitar an qara kudin jirgi seda ya gama na miqa masa takardar ina cewa

“Ga wannan karna manta ka tafi, na manta Gas din mu ya qare shima qaramar cylinder da tayi saura ita
aka saka jiya sannan lemon yan makaranta da Biscuits suma babu na manta ban rubuta”.

Takardar ya karba ya duba se ya dago ya kalleni yace “Wannan kudin duk na menene haka kusan dubu
dari da Ashirin?”

“Shi yasa fa na rubuta maka komai dalla dalla da kudinsa karma kace qari nayi maka ko wani abu” na
fada ba tareda na kalle shi ba, seda yaja wata qwafa kafin naji yace

“Yanzu kudin zan baki kenan?”

“Ka siyo da kanka ma duk daya ne ai” nayi saurin katse shi. Beyi magana ba mintina kadan naji wayata
tayi qara alamar shigowar message na jawo na duba Alert ne na dubu dari da Hamsin daga Bashir nayi
murmushi nace

“Sun shigo harda qari ma muka samu toh mungode Allah ya qara budi”.

Washe gari ya tafi Gombe.

Weekend din a daddafe nayi shi dan gaba daya bana jin dadi, zazzabin dare ne yake damuna safiya nayi
kuma naji garau na bari akan Monday idan be dena ba zanje Asibiti.

GOMBE

Wato wata Irin ladabi da biyyaya Amirah ta ara ta yafawa kanta wanda duk hudubar Sa’ada ce. Jikinta na
bari Daman yanzu da yace zezo zataje ta qalqale gida a gyara ko ina dukda dai da taimakon Ummi harda
Sa’adan ma suke zuwa wani lokacin sannan idan yazo tana iya qoqari tayi tsafta harya tafi a bangaren
girki ne dai har yanzu da saura yana ci yana qorafi dan baya masa kamar na Ma’u.
Wannan zuwan da yayi sosai yaji dadinsa ga tarairaya yana samu da kula kamar wani jariri babu aikin
office babu hayaniyar yara.

Butulci irin na dan Adam a yanzu se yake ganin Yafi samun yanda yake so a gurin Amirah musamman da
yanzu ta dena masa qorafin da tambaye tambayen kudin da takeyi gashi a karan kanta ta canza sosai
komai tana yi yanda yake so.

Suna zauna ana gobe ze tafi tana bare masa Ayaba yana ci ya kalleta yace “kina son zuwa Lagos?”

Sam Amirah bata kawo da ita yake ba dan a bazata maganar tazo mata har seda ya sake maimaitawa
kafin tace “Meze hana mana Yaya ai kowacce mace zata so ta zauna kusada mijinta daman, wani gidan
zaka samar min kenan”ta fada tana danne zumudin ta, lallai ta yarda kissa tafi Asiri tunda gashi yanzu
hankali kwance tana samun abubuwan da suka wahala suka kashe kudinsu a banza akansu.

“Aa ina ganin zaku ringa karba karba ne dan baze yuwu na ajiye ku gaba daya acan ba”.

“Toh Anty fa ya zatayi da aikinta” ta fada tana gyara zama a ranta tana Addu’ar Allah yasa matsala suka
samu daman ta lura tunda yazo bata ga sunyi waya ba.

Seda Bashir yasha ruwa kafin yace “Ina ganin zata ajiye aikin ne kawai idan yaso ta cigaba da
kasuwancinta kema ya kamata ki samu wani abinyi zaman haka ya isa”.

Tamkar Amirah ta taka rawa haka taji amma ta dake, cikin kisisina tace “Toh yaran kuma fa su acan za’a
barsu ko suma nan zasu dawo?”

“No su zasu zauna can saboda School”

“Amma Yaya indai makaranta ce anan ma fa akwai ko wacce iri kake so, ni ba wannan ba ma abinda yafi
damuna Tarbiyyar su kasan fa yaran da suka tashi a Kudun nan duk zaka gansu se a hankali ko a gida ana
musu tarbiyya tunda kullum suna fita su cakudu da yara kala kala se kaga anayi tana warwarewa. Ni da
zakaji shawarata ka dawo dasu nan ga makarantu nan na kudi masu kyau a saka su”.

Shiru Bashir yayi yana tunani, baza’a hadama karantun boko nacan da na nan ba amma maganar
tarbiyya tabbas tayi gaskiya abinda yasa ya hana Amna yin Jamb wannan shekarar kenan yace ta bari se
next year saboda kafin nan ta dan qara girma da wayo yana tsoron turata Jami’a cikin Yayan Arnan nan.

Su kansu su Aliyun yasan badan Ma’un ma Jajirtacciya bace irin yaran da suke cakude dasu a makaranta
da sun debi dabi’un da ba nasu ba.

“Haka ne kuma, shikenan zanyi magana da Ma’un se muga yanda za’ayi”.

Litinin ya koma Lagos da wannan qudurin a ransa. A daren ranar suna cin abinci bayan ya gama ya kalli
Asma’u da tunda suka zauna ta kasa cin komai yace “Inason magana dake idan kun gama” ya wuce dakin
sa.

ASMA’U

Yana tashi nima nabi bayansa gaba daya jikina baya mun dadi dan haka ina shiga na kwanta akan gado
ina jiransa ya fito daga yin Brush.

“Daga Next month Amirah zata fara zuwa nan”.

“Wata sabuwa” na fada a raina, sena miqe zaune ina kallonsa nace “toh ni mene ne nawa a ciki idan
Amirah zata zo ko a nan gidan zata sauka ne?”

“Ina nufin ke zaki tafi Gombe idan zata zo, then se ku tsara yanda kuke ganin lokacin da kowacce zata
ringayi a nan din”. Ya fada yana zama a gefena.
Yanzu kam na gane inda ya nufa, wato tsohuwar magana ce ta taso kenan yaje ta sake masa fanfo akan
tanaso ta dawo nan. Zaune na tashi na jingina bayana da Allon gadon nace “Toh Baban Ali ya zanyi da
aiki na kuma? Sannan Yara suma ya za’ayi dasu?”

“Maganar aiki na gaya miki zaki ajiye daman yara kuma dasu zaku tafi duk wadda take Gombe se su
zauna a gurinta”.

“Kan uban nan lallai ma” na fada ina kallonsa kafin naci gaba da cewa

“Yanzu saboda matarka tana so ta dawo nan shine zakace na ajiye aiki na amma kasan sam wannan ba
adalci bane ko?”

“Ke zaki koyamun yanda zanyi adalci kenan, toh ki dauka duk yanda yayi miki amma na gama magana
dole ki ajiye aikin ki Ma’u ki koma Gombe tunda haka na tsara” ya fada yana kallona.

Seda na qare masa kallo dan na tabbatar da gaskiyar abinda yake fada kafin na sassauta muryata ganin
dagaske neman rigima yake nace

“Haba Baban Ali, ka manta wuyar dana sha kafin na samu aiki nan, mutum nawa ne suke nema Allah ya
zabe ni akan su ya bani amma yanzu lokaci daya kace na ajiye. Da ace muna da Branch a Gombe da babu
musu zan nemi transfer in koma can amma yanzu kawai dan kana so ka kawo wata ni kuma seka tauyeni
kace na bar aiki na ai bakayi mun daidai ba.

Ni bani da matsala zaka iya dawo da ita ko a cikin gidan nan ne ka bata daki amma dan Allah kabar
maganar aikina ina son sa ban kuma shirya barinsa a yanzu ba”.

“Shikenan tunda kina son aiki ki, seki zaba ko shi aikin ko kuma umarnina” yana fadar haka yaja bargo ya
rufe har kansa nima sena fice nabar masa dakin.

Sam abin ma dariya ya bani lallai akwai match me zafi a gidan nan to Allah ya bawa me rabo sa’a.
Washe gari tsaf na shirya zan fita aiki, ina tsaye ina barwa Amna sallahun abinda zata girka ya fito muka
kalli juna se cewa yayi

“Kiyi mun tuwo da miyar Kubewa da rana za’a zo a karba”

“Naman rago zaki sakawa Miyar Akwai soyayye ma a Freezer seki diba” na fada ina zuge jaka ta dan duk
a zatona da Amna yake seda naji yace

“Dake nake ba ita ba, daga yau ma karta sake yimun girki kuma kullum za’a ringa kaimun lunch office”
yana gama fada yasa kai ya fita na bishi da saurin. Sanda na fito yana tsaye a jikin motarsa.

“Ban fahimci abinda kake nufi da nayi maka lunch ba ka manta zanje aiki ne” na fada ina kallonsa, idan
ya amsa ni to motar sa ma tayi magana, ya kunna mota ya bata wuta, harya taka ya leqo ta window yace

“Banyarda ki dara qofar gidan nan ba” ya qarawa motarsa wuta ya barni a tsaye.

Kamar mara laka haka naja qafafuna na koma cikin gidan, akan kujera na zube ina sauke numfashi,
dagaske dai Bashir yake ya na so ya rabani da aikina kenan. Badan ina tsoron Allah da fita zanyi sedai duk
abinda ze faru ya faru amma yau zan haqura idan yaso ya dawo naji me yake nufi dani tukunna.

Anty Suhaima na kira ina kuka na shaida mata komai tunda daman da ita muka fara maganar ai, haquri
ta bani tace yanzu zata kira Alhaji qarami ta gaya masa duk yanda mukayi zanji ba’a rufa awa guda ba
kuwa sega kiran Alhaji Qaramin.

Shima din nasiha yayi mun akan na kwantar da hankali na shedan ne kar mu bashi qofar da ze farraqamu
ya tabbatar mun kuma ze kira Bashir din yayi masa magana.

Ban san yaya sukayi ba dan daya dawo be kulani ba fuskar nan dai kamar ta shanu haka muka kwana
kamar abokan gaba. Washe gari dan na gwada Sa’a ta na shirya kuma akayi dace tafi kuma mutu be ce
dani ba hakan yayi mun dadi alamu sun nuna sunyi magana da Alhaji Qarami kenan kuma ya barni naci
gaba da zuwa aiki.
Haka muka cinye sati biyu cir ana wannan yanayin duk iyakar qoqari inayi gurin kyautata masa dayi masa
duk abinda nasan yana so amma kallon banza ban ishi Bashir ba bare na arziqi haka idan zan kwana ina
masa magana baze daga kai ya kalleni ba ko wani abin yake so sedai ya kira daya daga cikin yaran yayi
masa.

Abinda na lura dashi shine harda zugar mutane a cikin abun nasa kuma daman na san Bashir halinsa ne
daukar shawarar wasu indai ka gaya masa abinda yayi daidai da ra’ayinsa tofa shikenan.

Haka dai nake lallabawa ina taka tsantsan da duk abinda ze qara mun laifi a gurinsa ga zazzabin da yake
damuna kullum qaruwa yake ga kuma sabuwar damuwar Bashir gaba daya na susuce har wata rama
nayi,

A bakin Aliyu naji cewar Monday zuwa Laraba su Bashir bazasu yi aiki ba an basu hutu, nan da nan nima
na rubuta letter akan bani da lafiya naci sa’a akayi mun approving da wuri dan daman duk wanda ya
ganni yaga mara lafiya.

Nan da nan na shiga shirye shiryen yanda zamu gyarota da Bashir dan wannan zaman doya da manjan da
mukeyi bayamun dadi kuma a zahiri na fishi cutuwa sedai nima qudurce a raina indai yana tunanin
abinda yakeyi ne zesa na sakko na bi ra’ayin sa na ajiye aiki na na koma Gombe ya dakko wata Mata ya
kawo nan to kuwa bazan chanza ba.

Idan da ace wani uzuri can na daban yasa ya yanke hakan zan iya karba amma wallahi indai akan Amirah
ne a wannan gabar na shirya karbar komai

WATA KISHIYAR

(ALKAHIRI CE KO SHARRI)

Na Maryamah Farouk
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)

Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 31

BASHIR

Ransa fes ya bar gidan ranar dan ya tabbatar da Ma’u bazata fita batareda izininsa ba. Zuciyarsa ta kasu
biyu, wata tana gaya masa abinda yayi daidai ne inda wata take nuna masa kuskuren abinda yake shirin
aikatawa kuma kamar rashin Adalci ne.

Shikansa ya tabbatar da aikin Ma’u rufin asirinsa ne kamar yanda ta fada kudin jikinsa yake komawa
shida yayansa.

Haka yayita juya abun a ransa har ya isa office, Lokacin da suka fita break kiran Alhaji Qarami ya shiga
wayarsa, yayi matuqar mamaki amma daya tuna abinda ake ciki seya goge mamakin.

A mutunce suka gaisa sannan Alhajin ya fara cewa

“Engineer yanzu Suhaima take gaya mun wata magana wai ko ka hana Ma’u zuwa aiki ne ko menene
dai, nasan halinsu qilan wani laifin tayi maka koh?”

Kame kame Bashir ya shiga yi yama rasa abinda zece masa, se Alhajin yayi murmushi irin na manya. Yana
sane yayi masa haka tunda Suhaimah ta fada masa komai harda dalilin daya saka yace tabar aikin amma
yana so ne yaji gaskiyar komai a bakinsa hakan da yayi ya tabbatar masa da son kaine kawai irin nasu na
maza ya saka shi aikata hakan.
Seda yayi gyaran murya kafin yaci ga da cewa “Koma mene dai yanzu ina roqa mata arziqin a barta taci
gaba da aikinta, kuma koda gaba wani abu ya sake tasowa nine uban Asma’u ni ya kamata ka gayawa
zan dauki mataki akai” daga haka dukayi sallama ya kashe wayar.

Sam hakan be yiwa Bashir dadi ba, akan me zata kai qarar sa gurin sa saboda tasan Alhaji Qarami yafi
qarfin yayi jayayya dashi ko ya nemi alfarma a gurin sa yaqiyi, yanzu gashi saboda qanwar sa ya sauke kai
yana roqonsa bayan ko shi aikin nasa da yake taqama dashi bazar Alhaji Qaramin ce.

Yana hanyar komawa gida suna waya da Amirah Yake gaya mata abinda ya faru

“Amma wallahi Yaya sun ma raina maka wayo, kaida gidanka amma ace dan ka yanke hukunci wani yazo
ya warware shi kawai dan suna da kudi se su ringa zuba iko a duk inda suka ga dama, gaskiya seka tashi
tsaye koda yake aikin gama ya gama ai tunda har ka bada qofar da zasu ringa yanke maka hukunci a gida
kaga gaba baka isa ka sa ko ka hana ba se a kai qarar ka inda akasan bazaka musa ba” Amiran ta fada
kafin taci gaba da yi masa fanfo

Da yake abinda yake so ne nan kuwa ya hau kai yayi daram akayi sa’a akayi Sa’a daya tuntubi Bala da
maganar shima, da yake duk kanwar ja ce duk irin Abinda Amiran ta fada ya dora nasa akai, wannan
dalili da hujjojin da suka kafa masa na cewa daga inda wasu suka fara shiga cikin hukuncinsa tsakaninsa
da Ma’u toh raini yazo dan tasan duk sanda ya fada mata abinda be mata ba tana da inda zata kai a
tilasta shi ya chanza, wannan yasa shi ya kasa ganin kyautatawa da duk qoqarin da Ma’u ta ringa yi na
son ganin ta wanke kanta.

Se yake ganin duk ihu ne bayan hari, ta rigada tayi abinda tayi dan tayi ta nuna wa duniya be isa ba shi
kuwa yayi Alqawarin bazata ga gazawarsa ba dan haka su zuba su gani da kanta zata haqura tace ta bar
aikin nan dan babu gudu babu ja da baya.

ASMA’U

Ranar Litinin da wuri na tafi Asibiti dan daren jiya kasa bacci nayi ga zazzabi ga wani ciwon mara dakyar
naga safiya. Ina zuwa bayan likita tayi mun tambayoyi kai tsaye ta turani lab inda suka dauki jini na da
fitsari suka ce na jira a waje. Minti 30 tsakani Nurse ta kirani dan har an kaiwa Dr result.
Ba qaramin mamaki nayi ba jin wai ciki ne dani dan ko kadan ban kawo hakan ba har likitan tana tsokana
ta wai haihuwa Biyar amma na kasa gane alamun ciki. Seda tayi mun scanning, cikin sati 9, magunguna
ta rubutamun da zasu taimaka mun da zazzabi da kasalar da nake fama dasu na karba a pharmacy kafin
na wuce gida raina qal kamar an mun bushara da Aljanna.

Ada na ce na gama amma yanzu damun cikin nan naji dadinsa sosai dan nasan shine ze zama silar
daidata tsakanina da Bashir.

Sanda na koma gidan ya fita daman Amnah yareda sauran yara suka fita taje makarantar ana neman su
dan suna shirye shiryen yi musu graduation party.

Ban zauna ba saboda murna duk se naji na warke ma, dakin Bashir na shiga na gyaro shi tsaf na wanke
Toilet na saka qamshi, kafin na nemi guri me kyau na ajiye takardar test din Asibitin inda nasan
hankalinsa ze kai.

Dakina na koma nima na sake wanka na sheqa kwalliya sosai dana san dole na burge Bashir, Dumamen
tuwon da mukayi jiya naci da baqin tea kafin na sakeyin brush na dawo palour na zauna zaman jiransa.

Se gurin sha biyun rana ya shigo, na miqe fuskata dauke da murmushi na nufe shi amma kafin na qarasa
ya dakatar dani ta hanyar daga mun hannu se na tsaya din kuwa ina kallonsa ya wuce ni ya zauna akan
kujera.

Jiki a sanyaye nima na koma na zauna, idonsa akaina yace “Weekend din nan zaki Tafi Ita kuma Amirah
tazo”.

“Wai dan Allah Baban Ali me yasa kake da son tada zaune tsaye? Ina mun gama da wannan maganar ko.
Nagaya maka ni bani da matsala da zaman Amirah amma banga dalilin da zesa ni a takurani ace na koma
wani waje ba saboda ita, tazo mana kowa ba zaman ta zatayi ba namene se an shiga haqqina wai” na
fada ina yatsina fuska dan harga Allah na gaji da maimaita abu guda.

Kullum daga ya zauna zancen kenan Amirah zata zo toh ko Addah ce tazo mana ina ruwan wani.
“Oh hakane, wato kina ganin kin isa kenan a zaton ki dan kin kai qarata ze sa na chanza ra’ayina ne? Ni
ba irin namijin da ze zauna yan uwan matarsa suna tsara masa yanda zeyi bane kin kuma fi kowa sanin
idan nayi niyyar yin abu babu uban da ya isa ya saka ni ko ya hanani”. Bashir ya fada yana kallon cikin ido
na, sena miqe tsaye nima ina kallon sa nace

“Duk abinda zakayi ya tsaya kaina ni kadai karka ce zaka zagar mun Yaya dan ni nasan mutunchinsa
kuma ko banza wallahi Alhaji Qarami yafi qarfin raini a gurin ka dan yayi maka abinda duk duniya babu
wanda yayi maka shi, ko gani kayi za’a zage shi kamata yayi ace se inda qarfin ka ya qare”

“Ni kike gayawa haka Ma’u ni kike gorantawa cewa Yayanki yayi mun abinda babu wanda yayi mun shi
ko?”

Shiru nayi masa dan idan na bude baki nasan bazan fadi abu me dadi ba dan gaskiya Bashir ya qure ni na
tabbatar so yake sena zazzage masa galan din rashin mutunchi daga nan se ya juya duk wani laifi zuwa
kaina tunda daman neman sanadi yakeyi, ina jinsa yana ci gaba da fadar maganganu son ransa ban tanka
shi ba qarshe ma nayi wucewa ta dakina na ina shiga ya biyo baya na yana cewa

“Wato ga mahaukaci ina miki magana kin tafi kin barni a tsaye ko lallai Ma’u kina so kiga asalin kala ta
kenan”.

A fusace na juya nace “wace kalar taka ce tayi saura da ban gani ba Bashir, ai duk wata fuska ta ka ka
rigada ka gama bayyana mun ita na gani na kuma san da wanda nake zaune dan tsahon shekarun da
mukayi a baya Kura ce da fatar Akuya nake zaune da kai. Daman mutane sunyi gaskiya da suka ce baka
tantance halin namiji se randa ya qara aure.

Wallahi ka bani mamaki Bashir ban taba tsammanin ka a cikin layin maza masuyiwa matansu butulci ba a
lokacin da suka samu wasu.

Dame na rage ka, ta ina na gaza? Dame ita wacce kake fifitawar ta fini?
kullum hanqorona na burge ka nayi maka abinda zaka ji dadi amma a koda yaushe sakamakona baya
zama me kyau anya ka taba sona kuwa?

Karkasa na yarda da cewa ka aure ni ne kawai dan biyan buqatar kanka yanzu da kake ganin ka samu
yanda kake so kake neman ka mayar dani bolar da zaka juye sharar ka duk a sanda ka debo ta idan ba
haka ba meye laifi na? Ko kuma ni ban cika mace ba nata matancin yafi nawa da yasa kake take nawa
haqqoqin dan biyan tata buqatar.

Wallahi Bashir idan baka yi a hankali ba zaka tashi cikin jerin mazan da zasu je lahira da shanyayyen jiki
saboda ka gaza Adalci a tsakanin matanka, idan ma kana tunanin idan kayi mun abu zan yafe ko ban
kaiwa Allah qarar ka ba Bashir yana kallo kuma se yayi mana hisabi nida ku” nayi maganar cikin muryar
da take nuna qololuwar bacin raina dan gaskiya nakai bango na kuma shirya tarar ko menene tunda naga
alamar Bashir ya fara daukar kawaicina a matsayin sakarci shiyasa yake kawo mun duk shirmen da yaga
dama.

“Ni kikewa fatan na tashi da shanyayyen jiki Ma’u saboda nabaki umarni a matsayina na mijinki kinqi
bi?” ya fada muryarsa na rawa idonsa ya kada yayi jajir har wasu jijiyoyine suka fito a cikinsu, banji ko
dar ba a raina ba na gyara tsayuwata ina kallonsa ido cikin ido. Se ya girgiza kai yayi kwafa kafin yace

"ASMA'U, ASMA'U, ASMA'U sau nawa nawa na kira sunanki?

Dukda yanda Asma’un daya kirani ya dake ni dan na manta rabon da Bashir ya kira ainihin sunana amma
se na dake, hannu biyu na saka na riqe quguna nace

"Sau uku ENGINEER BASHIR AHMAD" dan ni ma fa ba baya bace a fagen iya fitsara, kawai dai shekaru da
yanayin rayuwa suka sa nayi sanyi amma a wannan gabar dole na fito masa a ainihin MA'UN BAFFAH ta
wadda ya sani shekaru goma sha shida da suka gabata bawai ASMA'U matar Bashir uwar Aliyu, Jafar,
Farida, Abdallah, Ahmad da Muhammmad ba.

Qara gyara tsayuwata nayi ina kallonsa ganin yanda yake bina da kallon dana tabbatar na zallar mamaki
ne jin yanda ni na kira nasa sunan gaba daya ma Gatsal bako Sakayawa,
Sena saki wani guntun murmushin takaici, lallai Bashir ya manta dawa yake magana, a zatonsa nayi tibis
ne ko? be san har yau da saurana ba sedai ba’a tabo ni ba.

Kansa ya girgiza yana qoqarin kokawa da hukuncin da zuciyarsa take ayyana masa, wani sashe na
ingizashi akan yayi inda dayan ke kwabarsa da nuna masa zafa ta iya kwabewa amma idan ya ja da baya
ai ma zata raina shi kuma yabi abinda take so kenan.

Kai ba wannan ba raini biyu ma tunda itama ma AMIRAN zata qara tabbatar wa duniya be isa da ASMA'U
ba tunda gashi ya bata umarni taqi tabi. Se ya gyara tsayuwarsa tareda qara tsuke fuskarsa da dama can
bata da fara'a sam, wani kallo yake jifanta dashi da yasan yana ladabtar da koma waye amma banda
wannan kangararriyar Matar. Cikin kaushin murya yace

"For the last time ASMA'U ina baki umarnin kiyi resigning daga aikin ki ki tattara yara ku koma Gombe
d....."

"Na gaya maka wallahi Bashir bazan bar aiki na na koma Gombe ba saboda zaka kawo Matarka Lagos"
nayi saurin katse shi.

"Shikenan, Se ki zaba ko auranki ko kuma aikinki" ya fada cikin sautin dake nuna qololuwar bacin rai
yana harde hannu biyu a qirji yana bina da kallo, daga inda nake ina iya jin yanda yake sauke numfashi
kamar wanda ya hadiyi kunama.

Qara jinjina qarfin hali da rainin wayon Bashir nayi a raina, wato ni nice rumfa sha shirgi ko ga Uwar
garke wai na tattara yara mu koma Gombe, to kuwa yau na shirya ganin qarshen rainin hankali da duk
abinda Bashir yake taqama dashi dan haka nace

"Idan har saboda MATAR KA kake so nabar aikina to na zabe shi BASHIR".

"Haka kika ce"


"Eh Haka na fada”.

Seda ya hadiye wasu qulalai da suka tokare masa maqogaro, kaso tamanin na zuciyarsa yana kwabarsa
amma kashi Ashirin ya rinjayi harshen sa

"Kije na SAKE KI SAKI DAYA idan yaso se ki zauna da aikin naki".

Wani irin dummm naji kunnena ya dauka, wallahi wannan kalmar itace mafi munin ji a rayuwata gaba
daya, wannan rana tafi kowacce duhu a tarihin rayuwata.

"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un Bashir kasan me ka fada kuwa? dagaske kake" na fada cikin yanayin da ni
kaina bazan iya fasaltawa ba

"Oh baki yarda ba? To kije na qara miki DAYA, badan babu kyau ba Asma’u da sena cike miki ukun ki
kinga se kiji dadin yin aikin ki dakyau ba tareda nayi miki rashin Adalci ba" ya fada daidai sanda yake
ficewa daga dakin.

Wani jari ne ya kwashe ni ya yar akan dake, Allah ne ya rufa min asiri na fada kan gadon da yake baya na.
A yanda nake na tabbata in a qasa na fadi babu abinda ze hana barin jikina shanyewa.

"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, Allahumma ajirnifimusinati wa'allifni khairan minha" cikin ikon Allah
kalaman da bakina ya shiga maimaitawa kenan jikina yana wani irin rawa tamkar wadda aka jona mun
shocking.

Duk yanda naso kwakwalwa ta tayi tunani na kasa dan ji nayi tamkar an saka super glue an liqeta, se zufa
ce take ketomun ta ko ina kaina yai dum kafin kace meye numfashina ya fara sama sama ba shiri na fara
laluben inda Inhaler ta take wadda sabuwa ce daman dazu dana fita na siyo, dakyar na samota bayan
dana zazzage jakar dana fita da ita a qasa saboda yanda nake a rikice jikina yana rawa.
Seda na zuqa sosai sannan numfashina ya fara dawowa daidai amma fa kwakwalwar na nan a toshe. Kai
ido na fa ya soye bama alamar Hawaye zasu fito, to kukan maganin me ma zeyi mun?

Ni? ni Asma'u yau Bashir ya saka? Wallahi ko a mafarki naga Bashir ya sake ni nasan shedan ne amma
gashi kamar a zahiri hakan ta faru.

Ina cikin wannan yanayin aka sake turo qofar dakin, nasan yarana dukka suna makaranta kuma lokacin
tashinsu beyi ba.

Nima dai rabon ganin wannan baqar rana ya saka ni daukar Excuse din rashin lafiya wai dan na huta na
zauna da Habibina mu sasanta sabanin da muketa samu a dan tsakanin nan ashe ashe....

"Zaman me kikeyi? Ki tashi kisan inda dare ya miki dan gobe nake so azo a sakawa AMIRAH sabon kaya
Zuwa Weekend ita dana isa da ita zata dawo dan haka na baki grace of today ki hada ya naki ya naki
kinga yanzu komawa Gombe dole"

kalaman Bashir kenan da suka fi dafin maciji a wurina haka ya juyawa yabarni ni bame rai ba ni ba
sumammiya ba.

Dakyar na iya miqewa na rarumi hijabi na, dole na nemi inda zan tsugunna kafin qarewar yau nida
yarana. To tunda BASHIR ya iya sakina Allah na tuba watsi dani akan titi kuma ai shi yafi komai sauqi a
waje sa.

Kofar gidan na fito ina tunanin ina zan nufa? Flat din da yake jikin namu ido na ya fada, idan ban manta
ba Abokin aikin Bashir ne a ciki wanda tsautsayi ya fada masa a ka koreshi daga aiki dole ya saki gidan
tunda dama Office ne suke basu dan haka yanzu babu kowa a ciki.

Gidan Baba na shiga dan nasan yana gida kaman yanda Bashir yake nan tunda Office dinsu daya, haka na
ringa danna door bell ba saurarawa.
Banyi zaton nayi sallama ba lokacin da Anty ta budemun qofa na nausa kai ciki kawai dan fa bazan iya
cewa wallahi ga abinda nakeyi ba ni kaina cikin Sa'a kuwa na tarar da Baban na zaune a palour yana
Kallon News, se kawai na isa gabansa na durqusa.

"Hajia Ma'un Bashir" ya fada yana murmushi. haka suke tsokanata kai kowa na Estate din ma haka yake
kirana kadan suka sanni da Maman Aliyu wasu kuma suce Maman twins.

"Meya faru" Baban ya sake fada dan se sannan ya lura da yanayin fuskata. Banyi kuka ba amma kallo
daya zakamun ka hango zallar tashin hankalin da nake ciki, se kawai na tsinci kaina da cewa

"Baba Flat din Maman Boda zakamun hanya a bani haya na shiga yau dan Allah".

"Bangane ba? Me ya samu gidan naku? Ina Bashir din?" Duk ya jero mun wadan nan tambayoyi da daya
kadai nake jin zan iya amsawa dan haka na bude baki dakyar nace masa

"Baba BASHIR ya SA KE NI SAKI BIYU kuma yace na tattara kaya na a yau nabar masa gida kafin ya dawo"
na qarasa ina Rushewa da kukan da se yanzu na samu damar yinsa. Kuka nake tamkar raina ze fita inda
Baba da Anty keta faman zabga salati suna qarwa.

"Asma'u ya sake ki fa kika ce? Me kikayi masa har haka?” Baba Ya fada bayan daya tashi tsaye ya goya
hannunsa a baya, sena dago cikin matsanan cin kukan da nake dan har kamar zan shide nace

“Wallahi Baba banyi masa komai ba, kawai saboda yace na ajiye aiki na saboda Amirah nace bazanyi ba
shikenan yace se naje na zauna da aikin nawa”.

“Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un, meya ke damun Bashir da ze yanke wannan danyan hukuncin ba tare da
shawara ba? Wacece ma Amiran?” Baban ya fada yana kallon Anty da tayi mutuwar tsaye jin
musabbabin sakin, cikin tsananin bacin rai tace
“Amma Wallahi Bashir ya isa Asararre yanzu akan wannan tanbadaddiyar yarinyar me zubin Aljanu ya
sake ki lallai Namiji se a barshi”.

“Wai wace yarinya ce ina tambayarki” Cewar Baba, se Anty ta kalle shi tace

“Wacece kuwa idan banda wannan yar iskar maci Amanar yarinyar da yayi mata kishiya da ita, shine cin
Amanar be ishe su ba yanzu seda suka raba ta da auranta. In sha Allahu se Allah ya saka miki kima dena
kuka Alfarmar Annabi se yayi nadamar da bazata amfane shi ba a rayuwa tunda dai shi wawa ne”.

“Ya isa haka Halima wannan wace irin magana ce, ka mata kuje ciki bari naje na ga Bashir din ni” Baba ya
katse ta, se ya dauki Glass dinsa na qara qarfin gani da wayar sa ya fita Anty ta zauna akan kujera tana
sake tsinewa Bashir da Amirah nidai in banda aikin kuka babu abinda nakeyi.

Sanda Baba ya fita rashin ganin motar Badhir ya tabbatar masa yafita dan haka ya kirashi a waya itama
seda ta kusa katsewa sannan ya daga.

“Bashir kana ina ne nazo gida baka nan” Baba ya fada bayan da Badhir ya daga wayar.

“Na dan fita ne” Bashir ya fada murya a cunkushe kamar wanda aka yiwa duren dusa.

“Idan ka dawo kazo ina son ganinka” Baban ya sake fada kafin ya kashe wayar ya koma cikin gida. A inda
ya bar mu nan ya tarar damu ina ci gaba da rusa kuka Anty na faman debewa Bashir Albarka.

“Yanzu Halima a maimakon ki tausheta shine zaki zauna kina fadar maganganu kina sake daga mata
hankali ko kin kyauta, ki samo mata ruwa tasha, Asma’u kiyi shiru haka, na kira Bashir din yanzu ze zo”.
Baba ya fada bayan daya zauna akan kujera.

Sassauta kukan nayi na shiga jan rai ina ajiyar numfashi kamar zan shide, dakyar na dan zuqi ruwan da
Anty ta bani dan jinsu nayi sun min daci a baki, na hade kai da guiwa ina ci gaba da hawayen da na kasa
tsaida su, wai ni yau aka saka? Ni Bashir ya saka saboda Amirah.
Kusan mintina 30 aka buga gidan, Anty Baban ya kalla kafin ma yayi magana tace “wallahi yallabai bazan
bude masa ba, ni gara ka fita can ka same shi a waje dan idan ya shigo zan iya duddura masa Ashar ma”.
Se Baban ya girgiza kai kafin ya miqe yaje ya bude qofar da kansa.

Tare suka shigo da Bashir da kallo daya zaka masa kasan ba’a cikakken hayyacinaa yake ba. Idanunsa
sunyi jajir sun koma ciki ga jijiyoyin kansa sun fito rudu rudu. Guri ya samu ya zauna ba tareda ya kalli ko
gefen da nake ba, nima sau daya na kalle shi na mayar dakai ina ci gaba da share hawaye na dukkan mu
munyi shiru se Baba ya katse shirun da cewa

“Bashir me ya hada ka da Asma’u har ta kai ga yanke irin wannan hukunci mara dadi, koda yake abinda
ya faru ya faru dawo dashi bashida amfani dan haka koma menene haquri shine maganinsa dakai da ita
duk kuyi haquri ka maida ita dakinta tunda da sauran zama bama se wani ya san Abinda ya faru ba”

Luguden duka qirjina ya shigayi na dago na kalli Bashir ina jiran naji amsar da ze bawa Baban, ina ma ace
yace daman wasa yake yimun ba dagaske bane ba. “Daman ana saki da wasa ne” zuciyata ta raya mun,
sena sun kuyar da kaina qasa ina jin wani abu me tauri ya taso ya tokaremun maqogaro daidai sanda
Bashir yake cewa

“Ayi haquri kawai Baba amma ko zan maida ita ba yanzu ba, taje kawai lokacin data san muhimmanci na
idan da rabo se mu koma”.

“Kai dai za’a gayawa haka Bashir kaine zaka san Muhimmancin Asma’u a lokacin da ta rigada tayi maka
nisa, se kayi kuka da idon ka kayi nadamar da bazata amfane ka ba wallahi tunda baka godewa Ni’imar
ubangiji ba ka shirya godewa Azabar sa” Anty ta fada cikin Masifa kamar zata rufe Bashir da duka kafin ta
juyo kaina inda nake durqushe ina kuka tace

“Ke kuma kukan me zakiyi kanki aka fara sakin mace ko yaya idan wani yaqi ka da yini wani da shekara
ma ze soka har zaki damu dan wani Bashir da dama can ba ajin auranki bane ya sake ki, in sha Allahu
akan idonsa zakiyi auran da se ya gigita shi tashi muje” ta fincikeni muka shige dakin ta.

Bansan me suka tattauna da Baba ba ya shigo ransa a matuqar bace yana cewa “Lallai yaron nan bashida
mutunchi Halima, yanzu ka saki mace da yaya shida har kana iqirarin ta bar maka gida a yau zaka kawo
wata se yanzu na fuskanci kan abun daman akan ze dawo da kishiyarta nan ya saketa kenan, babu komai
duk wanda ya cuci wani a cikinsu Allah ya saka mas.

kuje ki tayata ta hada kayanta zanje Management office yanzu naji yanda za’ayi su bada gidan”.

WATA KISHIYAR

(ALKAHIRI CE KO SHARRI)

Na Maryamah Farouk

(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)

Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 32

Tareda Anty muka koma, Bashir na zaune a palour muka wuce dakina. Wayata dana gani ta tunamun da
gida, wazan kira na gayawa wannan mummunan labarin??

“Alhaji Qarami” zuciyata ta raya mun, nan da nan na danna masa kira cikin sa’a ringing biyu ya daga yana
cewa “wato a kwanakin nan dai Ma’u tana yi dani irin wannan kira akai akai haka”.

Kuka na fashe masa dashi sosai ya shiga tambayata ya akayi, dakyar na iya tsagaitawa na gaya masa
cewa Bashir ya sake ni. Seda yayi salati ya sanar da ubangiji kafin yayi shiru na wani lokaci yace

“Ma’u kowa da kalar qaddarar sa a rayuwa kiyi haquri ki dauka jarabawa ce daga ubangiji idan kika jure
se ki samu saka mako me kyau. Yanzu kina ina?” Alhaji Qarami ya fada cikin jimami, seda Naja
sheshsheqa kafin nace
“Yace ya bani iya yau na kwashe kayana na bar masa gidan sa Yaya yanzu ina gidan kayan nake hadawa”.

“Shike nan, ki hada iya abinda ya samu, bari na kira Abubakar dan yace mun yau ze shigo nan din idan
yaso ko hotel ne se ku zauna kafin gobe a duba miki gida zuwa muga yanda hali ze yi, ki dena kuka
sannan karki kira kowa a gida ki gaya masa kinji ko”.

“Toh Yaya Nagode Allah ya saka da Alkahiri “ na fada kafin mukayi Sallama naci gaba da taya Anty hada
kayan dan tuni ta sauke kayan wardrobe dina tsaf tana ta durasu a akwatuna. Seda muka kwashe komai
dan seda muka Hada da manyan Jakunkunan Bakko da muke zubo abubuwa daga Gombe daman in na
cire kayan ciki sena ninkesu na ajiye da rabon zasu min rana ashe. Har kayana na dakin Bashir seda ta
kwaso komai bayan da tayi masa watsa watsa da nasa a qasa.

Da muka gama da nawa kayan dakin yaran muka koma, lokacin Bashir ya bar gidan suma muka shiga
hada musu kaya kowa a akwati kafin wani lokaci mun gama Anty ta fita ta samo samari suka ringa dauka
suna kaiwa gidanta.

Mun fito da akwatin qarshe kenan Yaya Abubakar ya tsaya da motarsa a qofar gidan, rabon da yazo
tunda Bashir ya auri Amirah suka samu sabani sedai mu hadu dashi a gida idan naje Gombe ko muyi
waya.

Kai tsaye na fada jikinsa na fashe da kukan dana samu dakyar ya tsaya mun dazu yana bubbuga baya na
yace “kiyi shiru Ma’ulle abinda yake so kenan yaga gazawarki bayan shi yayi asara bake ba”.

Tare dashi muka shiga gidan Antyn muka tarar da Baba ya dawo, cikin mutun taka suka gaisa Baba ya
shiga bashi haquri akan abinda ya faru kamar shi yayi laifin sannan ya gaya mana ya samu approval an
bani gidan kuma harda 50% discount akan kudin hayar ma suka bayar kuma ya biya yanzu ze kira
kamfani masu wankin gida suzo su gyara yanzu se muje mu ga gurin ga Key nan an bashi.

A tare muka fita gaba daya, gidan lafiyar sa qalau dan daman ba’a dade da renovating nasa ba qura
kawai yayi se yana saboda babu mutane a ciki, muna tsaye ma sega kamfanin daya kira sunzo da kayan
aiki cikin qasa da awa daya suka wanke gidan tas har bangwaye seda suka wanke ko ina ya dauki kyalli.
Bansani ba Ashe tunda muka shiga Yaya Abubakar ya kira Alhaji Qarami ya gaya masa maganar gidan, se
ganin motar kayan furnitures nayi sunzo da saitin gado da kujera harda labulaye da carpet kamar wasu
kayan Amarya nan da nan suka shiga daurawa.

Muna fito wajen gidan motar makaranta ta sauke su Aliyu, da mamaki suka tsaya suna kallon gidan
Farida tace “Mami gida zamu chanza naga ana saka sabon kaya a nan”

Gaba daya kasa kallonsu nayi dan ji nayi wata sabuwar karaya tana zuwar mun, yaya zasu ji idan suka
gane mun rabu da mahaifinsu? Fitowar da Yaya Abubakar yayi daga cikin gidan ta ceceni daga
tambayoyinsu suka nufeshi da murna nan take na sulale na shige gidan Anty ban san Aliyu yana baya na
ba seda naji ya ruqo hannuna yana cewa

“Mami meya faru, kukan me kikeyi?”

Aliyu ya wuce shekarun da zance zanyi masa wayo, kai tsaye ina hawaye nace masa “Aliyu mun rabu da
Abbinku, kuje ku duba idan akwai sauran abinda ban dauko muku ba a dakin ku wan can gidan zamu
koma”.

Gaba daya se yaron ya kasa magana ya tsaya yana kallona, a sanyaye ya saki hannuna ya juya ya fita
daidai sanda Itama Aman ta shigo ina jinsa yace mata suje waje na raka su da ido har suka fice daga
gidan.

Rayuwa kenan, dan Adam yana tafe besan abinda ze same shi a mintunan da suke gabansa ba, dazu da
safe na tashi da yaqinin gyaruwar Al’amura a tsakanina da Bashir, ga labarin abin farin cikin daya same
mu bansan mummunar qaddara na tafe tana shirin shafe duk wani farin ciki da nake shiryawa ba.

Shafa cikina nayi, Allah sarki shi kuma tasa qaddarar kenan baze tashi a tsakanin iyayensa ba.

Da taimakon yaran kafin sallar Magriba mun shirya gidan nan tsaf yayin da muka yiwa gidan Bashir qat
dan kaida fata Anty ta kafe sena dauke duk abinda yake nawa ne a cikin gidan nan haka kuwa akayi yara
suka ringa jidar kaya qananan se murna suke wai mun chanza gida.
kayan Kitchen dina tsaf Gas da qaramar Freezer da muke zuba nama kadai aka bari dan sune nasa
babbar me qofa Biyu Yaya Muslim ne ya bani ita da suka tashi daga gidan su na Lagos ya koma Rivers,
haka kayan amfani ko ko cokaci Anty bata bari ba harda su spices seda ta tattare.

Haka palour Kujeru da Da Tv se Dining kadai ya tsira dasu sefa gadon dakinsa dan na dakina ma da
kudina na siya, wanda ya saka mun shi na cire na sakawa Farida da Amna a dakinsu dan haka masu
daurin Gado na gama hada sabon Anty tasa suka hau kwanto nawa tace ko baze hadu a yau ha su
kwance a ajiye gobe su dawo su hada.

Har bayan Isha muna jigilar kaya daga tsohon gida zuwa sabo, mungama tattaro komai wanda ze saku a
lokacin muka saka ragowar muka barwa gobe idan Allah ya kaimu se a qarasa.

Na fito raka Yaya Abubakar ze tafi masaukinsa daidai lokacin Bashir ya dawo, tundaga waje ya fahimci
aika aikar da akayiwa gidan dan ga winduna nan hanhai babu labule ana hango ciki, a sukwane ya shiga
gidan, kai tsaye dakin yaran ya leqa ya kuwa yi sa’a se katakwayen gadajen su ya tarar dan mun kwashe
katifun saboda bacci a zuwan gobe suma se a dakko su.

Cikin tsananin Bala’i kamar zeyi aman wuta ya tunkaro inda muke

“Ke kadai nace ki tafi bance ki daukar mun yaro ko daya ba” ya fada yana kallona.

Seda na watsa masa wani banzan kallo kafin nace

“Wannan ne kuma kayi kadan Wallahi Bashir, saki dai na saku kuma kamar yanda kace na barmaka gida
kafin gobe gashi nan ka gani Allah be hanani inda zan zauna ba amma maganar yara baka isa in bar maka
yarana a hannunka ba”.

Sosai rigima ta barke tsakanin mu shi yana rantsuwar sena bashi yaransa ni ma ina ta bazan bayar ba,
Yaya Abubakar ne ya katse mu da cewa “Ya ishe ku haka, wane irin shirme ne zaku zo kuna neman
tarawa kanku mutane a titi ga yara duk suna kallon ku akan abinda be wuce ku zauna ku sasanta ba.

Ki shiga Gida Ma’u zamuyi magana”


Sena juya ina cewa “ka gaya masa bazan bayar ba idan ya takura kuma seadi kotu ta raba mu” nayi shige
wata gida.

A waje kuwa Asma’u na wuce kafin ma Abubakar ya fara magana Bashir din ya katse shi da cewa “Ka
gani cikin lallama ka gaya mata ta bani yarana dan wallahi bazan bar mata su ba ballantana ta koya musu
dabi’ar raini da kafiya irin tata”.

Seda Abubakar ya qare masa kallo kafin yaja qwafa, ba qaramin danne zuciyarsa yayi ba yace “Naji, zata
baka amma kayi haquri kabarsu yau. Nayi maka Alqawari gobe za’a baka yayan ka”.

Shiru Bashir yayi kamar me tunani se yace “Shikenan, Amma wallahi goben idan ba’a bani ba se anyi
tashin hankali”

“Babu da wanda zakayi tashin hankali Bashir dan babu wanda yake da lokacin ka, kuma kayi a hankali
idan ba haka ba seka rufta kanka a inda duk ihun ka bazaka iya fitowa ba” yana gama fada masa haka ya
shige motarsa ya bar Bashir da cizon yatsa.

BASHIR

Ko kusa beyi nadamar abinda ya aikata ba dan a ganinsa yayi irin abin nan na ya tauna tsakuwa dan Aya
taji tsoro. A tunaninsa dole Asma’u zata bishi ta roqe shi ya maida ita dakinta, shi kuma ya qudurce se ya
gama wanata son ransa tukunna ta gane muhimmancin sa sannan se ya mayar da ita. A lokacin yasan ta
biyu ta yanda ko kara ya ajiye mata bazata tsallake ba.

Be damu da kwashe kayan ma da tayi ba, sema guri daya samu a palour ya dora kafa daya kan daya, a
cikin kudin da yayi niyyar biya musu umara shida itan ya yi order sabon gadon da za’a saka a dakin da ta
cire nata da kuma labulaye kai kujerun ma chanza su ze kawai idan yaso kayan Kitchen in Amirah tazo se
ta siyo da kanta tunda shi be san abinda ake buqata ba.

Koda ya shiga dakinsa ma yaga kaya a watse be wani damu ba yasan duk cikin haushin sakin ne yasa tayi
haka, se kawai ya tattare ya watsa su kan gado yayi shigewarsa Toilet yayi wanka kafin yayi shirin bacci
ya zauna akan kujera da wayarsa a hannu.
Cikin sa da yayi qara ne ya tuna masa da yau fa be ci komai ba, se ya miqe ya fito palour kai tsaye ya
wuce gurin Dining sedai kafin ma ya qarasa ya hango shi wayam daga teburi se kujeru, yar Show gilas din
kwanukan da ta qawata gurin ma an dauke bare yasa ran samun wani guntun abinci.

Dolensa ya sake fita ya siyo abincin a waje a ransa yana cewa “Dole yarinyar nan ta dawo a satin nan dan
bazan iya sintirin zuwa siyen abinci ba, yana gama ci ya ahige daki yayi kwanciyarsa abinsa.

ASMA’U

Qarfe 11 na dare ina zaune akan abin sallah tun bayan da nayi sallar Isha ban tashi ba, gaba daya hankali
na yayi nisa da inda nake na yi nutso a cikin kogin tunanin abubuwan da suka faru dani tun daga
haduwata da Bashir har zuwa yau daya yanke alaqar da take tsakanin mu.

Tiryen tiryen komai ya ringa dawo mun lokutan da suka kasan ce masu dadi a cikin rayuwar mu da
wadanda suke aka sin haka, haduwar mu ta farko da Bashir wadda har muka qulla soyayya a tsakanin
mu nake tunawa.

ASMA’U ABDULLAHI TUKUR shine cikakken sunana. Baffan mu Alhaji Abdullahi haifaffen Kumo ne ta
Jahar Gombe.

Yana da matan aure guda hudu Hajia Babba da Hajia Umma rana daya aka saka musu lalle se Hajia Anjim
kafin ya auro Goggon mu Maryam daga qarshe.

Ita Goggon mu yar Asalin Numan ce kuma Babanta shine limamin garin a lokacin. A yanda aka gaya
mana asali ba Baffan mu Goggon zata aura ba, Baffa Sama’ila Amininsa ne saurayinta wanda har an saka
musu rana cikin tsautsayi a ranar da za’a daura auran ya gamu da mummunan hatsari akan hanyar su ta
zuwa Numan daga Yola wanda yayi sanadiyyar tabuwar lakar bayansa dalilin da yake kwance kenan har
yau yana jinya.

A lokacin su Baffan mu sun riga su isa garin, bayan da aka samu wannan mummunan labari hankalin
kowa ya tashi har aka watse daga taron daurin aure seda Baffa Sama’ila ya bar wasiyyar akan Baffan mu
ya auri Maryam dan beyi zaton ze tashi ba, haka kuwa akayi se kawai gani sauran matansa sukayi yazo
da Maryam da suka je bikin Amininsa a matsayin kishiyarsu babu kuma wata jayayya ko tashin hankali
suka karbeta tamkar yar uwa.

Zaman gidan mu zama ne me tsafta tsakanin matan guda hudu wanda suke kishi gurin kyautatawa
mijinsu da qoqarin ganin ko wacce ta zama ta gaban go shi bata hanyar cutar da yar uwarta ko tashin
hankali ba.

Allah ya azurta Alhaji Abdullahi ta kowanne bangare domin ya masa arziqin Dukiya, mata da kuma Yaya
saboda seda ya haifi Yara 42 inda biyu suka mutu tun kafin a haife ni yanzu haka mu 40 cif muna raye
Maza 24 mata 16.

Mu 8 ne a dakin mu, maza uku mata biyar.

Zan iya cewa kusan nice mafi soyuwar ya a gurin mahaifina kodan ina da sunan mahaifiyar sane amma
dai kowa ya shaida nidin yar gata ce ta gaske, Baffan mu yayi matuqar qoqari gurin bamu tarbiyya
tareda hada kanmu dan bamu san wani abu wai shi yan ubanci a gidan mu ba mun tashi tamkar tsintsiya
baka taba banbance yan wannan daki dan kowa inda yake so yake warkajamin sa.

Dukda kasancewar Baffa beyi boko ba amma yayansa ya bamu damar yin ilimi iya yanda kaso kuma mata
da mazan mu, baya tsawwalawa, dukda anayiwa mata auran wuri a lokacin sam shi babu ruwansa idan
yayyen mu mata sun gama secondary school yana basu zabin aure ko makaranta wanda kika dauka shi
zakiyi dan tun duniya na kwance Baffa yake fitar da yayansa mata qasashen waje suyi karatu, idan ma
kuma kina karatun kika fitar da miji dukka ze miki auranki.

Nice ya ta Ashirin da bakwai a gidan mu, Ma’u kwalisa shine laqabin da akeyi mun a makaranta saboda
yanda Allah yayi ni dason gayu abin ya hade mun da irin qirar halittar da nake da ita dan haka nake bawa
gayu haqqinsa yanda ya kamata.

Tun muna SS1 na qudurce a raina nifa dana gama secondary aure zanyi duk kuwa da yanda nake da
qoqari sosai a makaranta nidai kawai aure nake so abinda ze baku dariya shine ko saurayin bani dashi
dan bana kulasu, ni a lokacin ma duk wanda yace yana sona tofa ya zama abokin gaba ta har tsokanata
yan gidan mu sukeyi indai kana so muyi rigima dakai to ka nuna wani kace saurayi nane.
Ranar da muka fara haduwa da Bashir wata rana ce mun taso daga islamiyya da yamma, muna hanya
wani da Ake kira Ibbah saurayine dan layin mu daya nace shi ala dole sona yake yi mun taho a hanya
kawai ya tare mu.

Ibbah girman Ingila ne acan aka haife su dan basufi shekara biyar da dawowa Nigeria ba dan haka gaba
daya dabi’unsa na turawa ne abinda yasa nake qara tsanarsa kenan muna tafe muna hirar mu se ganin
sa kawai mukayi a gaban mu ya kalleni yana murmushi yace “Hey pretty yau na kamaki bazaki gudu ba,
tsaki nayi masa na murguda baki kafin na kauce ina cewa

“Aikin banza mutum kamar maye yayi ta bin mutane, se kayi tayi ai dan wahala” nayi gaba abina se ji
nayi caraf ya riqomun hannu banyi wata wata ba kuwa na kwashe shi da mari kafin na hau zazzaga masa
tsiwa ina zaginsa.

Tahowar da Yaya Abubakar din gidan mu da Abokanan sa uku yasa na dakata ina hararar Ibbah dayayi
mutuwar tsaye yana kallona, Yayan ne ya tambayi meya faru Alawiyya tayi caraf tace masa “Ma’uce ta
Mari Ibbah saurayinta” tun kafin ta gama na juya kanta da masifa ina cewa

“Ta ina ya zama saurayina wallahi karki sake hadani dashi niba saurayina bane” kawai na saka kuka
kawai se suka samun dariya dan yanda nayi abun seka rantse wani mugun abu aka jinginani dashi.

Daya daga cikin Abokan Yaya Abubakar wanda ban sanshi ba, cikin taushin murya yace mun “waya gaya
miki mekyau tana yin kuka rabu dasu ba saurayin ki bane ki share hawayenki”.

Haka kawai naji ya burgeni, na saka hannuna na goge fuskata tsaf kuwa fuu nayi gaba na barsu suna ci
gaba da yi mun dariyar ina jin Yaya Abubakar na bawa Ibban haquri kafin ya taso su Alawiyya a gaba suka
biyo bayana.

“Ma’u danja Ma’u rigima daga ance mutum saurayinki kawai ki kama kuka ke wai baki san kin girma ba”
Bala daya daga cikin Abokan nasu ya shiga taokana tun kafin ma na bude baki Yaya Aliyu da duk yafi
sauran abokan su kirki ya tareshi da cewa
“Zaka fara ko Bala, Ma’u kyaleshi yi shigewar ki gida” seda n harari Bala na murguda masa baki kafin na
shige dan sam bana son Balan nan saboda yana shan Taba nasha ganinsa yanayi ni ban ma san me yasa
su Yaya suke kula shi ba.

Da Daddare muna zaune a palour Baffa muna hira yanda muka saba nake bashi labarin abun da ya faru

“Wani sabon abokin Yaya Abubakar ne yace na dena kuka amma su da duk se dariya ma sukeyi mun” na
fada cikin shagwabar da idan ina gaban Baffana jina nakeyi kamar wata yar jaririya zuba tabara nake son
raina idan akayi sa’a Goggo na kusa ta make ni.

“Banda dai tsiwa irin ta Mamana ya zaki mari mutum kawai dan yace yana sonki, ki kiyaye kar a sake
kuma gobe kuje har gida dasu Alawiyya ki bawa Ibrahim din haquri kinji ko” Baffan ya fada. Sena
marairai ce nace “toh Baffa bazan kuma ba.

Washe Gari Alhamis kuwa bayan mun taso boko da yamma babu Islamiyya mukaje har gidan su Ibbah na
bashi haquri, da yake yana da sauqin kai yace shi harya manta ma Maman sa se nan nan take dani wai
yarinya me kyau da hausarta wata iri ta hado mana kayan dadi muka tafi muna gulmarta wai su a dole
turawa.

Muna zuwa qofar gidan mu muka ci karo dasu Yaya Abubakar yau ma su na zaune, gaishe mukayi ina ta
satar kallon na jiyan nan daya maida hankali yana danna waya so nake naga ko zeyi mun magana amma
har muka shige gida be ko dago ya kalle mu ba.

Baki na tunzura nayi wucewata dakinmu, inajin su Alawa suna cewa nazo mu raba kayan da Maman au
Ibbah ta bamu nace bana ci nayi kwanciyata ina jin haushin da ban san koma mene ne ba.

Da daddare Yaya Abu yace na dafa musu Indomie, ina gamawa na juye a flask na bawa Khadija ta kai
musu ina zaune a palour Hajia Umma se gata wai naje inji Yayan yana kirana.

Suna zaune a tsakar gida daga gefen inda akayi kujeru na sumunti da tebura, su hudun dai kamar kullum
ga kular Indomin a tsakiya an cinye tas Yaya Aliyu ya kalleni yana cewa “wai Bashir ne yace ne yadda ke
kikayi girkin nan ba shine muka kiraki ki gaya masa da kanki”
“Wai daman Yaya Bashir kaine” na fada da mamaki ina kallon wanda aka kira da Bashir din. Se yanzu
kuma nagane fuskarsa Bashir din gidan Baba me Mota ne, rabon dana ganshi har na manta tunda su ka
fara zuwa Jami’a shi aka ce A Zaria ban sake ganinsa ba kusan shekara shida yanzu.

“Daman Fainusa tace Yayansu ya zama dan gayu ashe dagaske take “na fada ina zama a gefen Yaya
Abubakar, se Bashir ya dago ya kalle ni yana murmushi yace “dagaske? Har nakai ki gayu?”

Rufe fuska nayi da mayafina irin naji kunyar nan, sosai na ringayi masa tambayoyi meyasa na dena
ganinsa yace makaranta ce tasa saboda nisa baya zuwa gida se qarshen shekara, duk sanda yake zuwa
mu kuma bama nan munyi tafiya. Haka na shantake seda Goggo ta aiko kirana sannan na tafi.

Tundaga wannan ranar kullum da daddare idan na dafa musu indomi zanje na zauna ina taya su hira
kuma duk saboda Bashir dan haka kawai nake jin ina son yin magana dashi, haka ko a cikin gida banida
labari se na Bashir yayi Bashir yace kaza ana haka muka fara shirin qualifying exam daga ita zamu shiga
SS3.

Bashir ne yake tayani karatu yana ganar dani inda ya shige mun duhu, wannan kusancin da muka qara
samu ya saka Shaquwa sosai ta shiga tsakaninmu dan idan na wuni ban ganshi ha har ji nakeyi kamar
bani da lafiya gashi lokacin sun fara Service dan ma anan Gombe yakeyin nasa.

Banfarga cewa nayi nisa a soyayyar Bashir ba saboda ban ma san menene so ba, abu daya dana yarda Ya
zama wani bangare na jikina haka ina bala’in jin haushin na ganshi yana magana da wata mace ranar
haka zan wuni ina qunci.

Yaya Bilkisu ce ta fara haska mun cewa son Bashir nakeyi, nayi futu futu nace qaryane ni ba wani so
kawai dai Allah ne ya hada jinin mu amma a qasan raina ina jin dama hakan ta kasance yace yana sona
dana ji dadina kuwa.

Mun shiga SS3 kamar anyiwa Samari bushara da zuwa gurina sukayi mun caaa saboda yanda kyau da
surata suka sake bayyana sosai, ban kuma canza hali ba ina nan ina tatawa duk wanda yace yana sona
rashin mutunchi a qasan raina kuma ina cike da damuwa da takaicin me yasa shi Yaya Bashir baze ce
yana sona ba se wannan banzan Balan ne ranar ya wani ce wai yana so na se kace nayi masa kalar
budurwar yan shaye shaye.

Muna second term aka fara Registration na Jamb, duk su Alawiyya sunyi ni kuwa ranar da za’a kaisu siyi
qin zuwa nayi nace banida lafiya, washe gari da yamma Su Yaya sun shigo gida ake hirar, Ina ji Bashir na
tambayar kowa course din daya cike nayi banza dasu sanda yazo kaina har seda Junaidiyya ta tabo ni
sena tura baki nace

“Ni ba zanyi ba”.

Kafe ni yayi da idanunsa masu sakani a wani irin yanayi da bansan na menene ba yace

“Me yasa bazakiyi ba?”

“Haka kawai” na fada ba tareda na kalleshi ba, se ya miqe yace na biyo shi muka fita can tsakar gida inda
muke zama muna hira.

Idonsa akaina na sunkuyar da kai ina wasa da yatsun hannuna yace mun “me yasa bazakiyi Jamb ba”

“Ni babu komai kawai bana so nayi” na fada ba tareda na kalle shi ba.

“Toh aure kike so kenan?”

Sena dago da sauri na kalleshi, ganin ni yake kallo se na sauke idona ina tura baki nace

“Ni ban ce haka ba”.

“Toh idan ba aure kike so ba me yasa bazaki ci gaba da karatu ba bayan ma ko saurayin baki dashi wa
zaki aura ma”.

Harara qasan ido nayi masa kafin nace “Allah ze kawo ne Idan lokacin yayi”

“Idan kuma yanzu ya kawo fa” ya fada cikin qasa da murya, se na daga kai na kalleshi.

“Allah kasa yace yana sona” na fada a raina tamkar kuwa Bashir yaji ni se ji nayi yace
“Idan kuma ni ne mijin naki fa Ma’una zaki aure ni?”

Abunku da ba kwaila tsabar murna se kawai na tashi nabar gurin da gudu ina dariya ina jinsa shima yana
mun dariya abinda ba kasafai ya fiya yi ba.

Kan gado na na hau na ringa tsalle ina ihun murna, Yaya Fati Dake kwance akan Nata gadon ban sani ba
ta tashi ta rufeni da fadan wane irin shirme ne zanzo ina wa mutane tsalle a gado kamar wata yarinya.
Sena fada kanta ina cewa

“Tsallen murna ne Yah Fati ki barni nayi”.

“Murnar me kikeyi” ta tambayeni bayan data daga ni daga jikinta.

“Bazaki gane ba Yah Fati kawai kedai se lokaci yayi” tashi nayi na shige Toilet nayo alwala, inajinta tana
cewa Allah ya shirye ni nidai na tayar na ringa jero sallolin godiya ga Allah daya sa Bashir yace yana sona.

Washe gari dakansa ya tasani a gaba mukaje nayi register Jamb, Law na ciki muka gama komai muka
koma gida.

A hankali soyayyar mu ta bayyan kusan kowa yasan abinda yake tsakanina da Bashir. Da yawa gani
sukeyi kawai shirme nane haka shima a bangaren Bashir lokacin daya gayawa Aliyu halin da muke ciki se
yace masa

“Anya Bashir kana ganin abin nan me yuwuwane?”

“Me yasa kace haka Aliyu” Bashir din ya tambaye shi, se ya ci gaba da cewa

“Kawai gani nayi kamar akwai tazara me yawa tsakanin mu dasu, ka ture abotar mu da Abubakar
wannan ba wani abu bane amma ka fahimceni da wuya kaga mace ta fito daga gidan Attajiri ta auri na
qasa da ita sedai shi namiji me kudi ya auri diyar talaka, sannan idan ka dubi irin mazajen da yaran gidan
su suke auri babu qaramin mutum a ciki ita kanta Ma’u a kalar da Allah yayi mata Bashir ko a gidan
talauci ta fito ba matar qaramin mutum me fafutukar neman abinda ze rufawa kansa asiri irin mu bace
ba”.

Shiru Bashir yayi dan tabbas Aliyun yayi gaskiya. Shidin ba dan kowa bane Babansa me rufin asiri ne
kawai Ma’aikacin gwamnati me da yake dab dayin ritaya kuma ba wani babbaba kusan yanzu shi ake
saka ran ya zama jigo a cikin gidan su tunda shine Namiji Babba yayar sa daya da qanne biyar,

a yanzu ne ma ya gama makaranta yake bautar qasa kafin ya fara fafutukar neman aikin yi kuma.

Amma tabbas yana son Asma’u kuma itama ya yarda tana sonsa ba kuma ya fatan ace ya rasa ta.

“Haka ne Aliyu, ka taya ni da Addu’a Allah ya zaba mana abinda yafi Alkahiri toh”

“In sha Allahu, Allah ya sadamu da akhairan mu” Aliyun ya fada.

Wannan maganar da sukayi da Aliyu seta sa ya dan fara ja baya da Ma’u musamman yanda a yanzu
kullum yaje gidan ze tarar da zaratan samari yayan masu qunbar susa a manyan motoci sunzo gurin
Ma’un duk da bata fitowa amma hakan se yake ganin kamar wata rana zata iya chanza ra’ayi ta zabi
wani daya fishi dan haka se yayi baya da zuwa gidan.

Da yake itama suna shirin fara SSCE se bata damu ba dukda indai sun hadu se tayi masa qorafin me yasa
yanzu baya zuwa gidan sosai se yace mata aiki ne ya masa yawa dan yanzu ya samu temporary aiki a
wani company yana zuwa.

Cikin dan lokaci su Ma’u suka gama Jarabawar su, kamar kuma yanda Alhaji ya saba a shekarar ya kaisu
gaba daya suka sauke Farali tafiyar da sukayi kusan rabi da kwatan tsarabar da tayiwo ta Bashir ce harda
yan gidansu. Randa suka dawo bata jira yazo ba ta hada akwati guda ta kai masa har gida tayi sa’a ta
same su gaba daya yan gidan suna nan harda Alhajinsu dan haka bata zauna ba suna gaisawa ta tafi.
Bayan tafiyarta Su Fainusa suka bude akwatin suna zaro kayan ciki, sosai mamaki ya kama su ganin uban
tsarabar se Dada ta kasa haquri tana kallonsa tace “Bashir ni meke tsakanin ka da yarinyar nan haka irin
wannan uwar tsaraba data kawo mana?”

Fainusa ce tayi caraf tace “Dada soyayya sukeyi, ina jin a Islamiyya ma Ma’un Bashir ake ce mata”. Se
Bashir ya harareta yace “ke waya tambaye ki? Tashi a nan kona mammake ki”.

“Ikon Allah, Anya bata fi qarfinka ba Bashir kaida zaka dauko daidai”

“Daman mace tana fin qarfin namiji ne Nafi?” Alhaji Amadu ya katseta, seta girgiza kai tace

“Gani nayi Alhaji idan ka kallemu ka duba gidan data fito kar ace son zuciya ne yasa ya nemi auranta”.

“To ai Annabi ma yace ana auran mace dan Asali da kuma dukiyarta kinga in hakan yayi ma ba laifi bane
ballantana nasan ma ba hakan bane, idan matarsa cea se kiga Allah ya qulla abun, kiyi masa fatan
Alkahiri kawai” cewar Alhaji Amadu.

“Hakane Allah ya tabbatar da Alkahiri toh ai Asma’u yarinyar kirki ce”. Daga haka suka ci gana da
hirarrakin su.

WATA KISHIYAR

(ALKAHIRI CE KO SHARRI)

Na Maryamah Farouk

(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)


Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 33

ASMA’U

Mun rubuta jarabawar Jamb cikin Nasara kuma ko wannen mu ya samu isashshen makin da ze samar
masa gurbin karatu a fannin daya zaba yanzu se jiran sakamakon SSCE mukeyi.

A dan tsakanin Baffa ya taramu, daman munsan maganar bazata wuce ta aure ba dan haka tun kafin
ranar kowa ta fitar da zabin ranta dan dukkan mu wannan karon yan Aure ne maci gaba da karatun a
can.

Da Daddare muna zaune a palour Baffa ni, Alawiyya, Yaya Fati, Yaya Bilkisu se Junaidiyya mune yan
candyn Bana, cikin sakin fuskar da Baffa yake da ita a cikin iyalansa muka dan taba hira kafin ya gabatar
mana da maqasudin kiran namu.

“Na kiraku ne dan naji ra’ayinku dukda dukkan ku nasan kunyi jarabawar shiga Jami’a me kuka zaba aure
ko kuma Bokon za’a ci gaba?”

Seda muka kalli juna muka qara sunkuyar da kawuna kafin muka hada baki gurin cewa “dukka gaba daya
muka zaba Baffa”.

Alhaji Qarami da yake gurin ne ya shiga tsokanar mu da cewa “wato gaku cinye du ko zaku ce wani
dukka kuka zaba to baze yuwu ba sedai ku dauki daya” se Baffa ya katse shi yace
“Aa bana so karka takuramun yara, shiyasa bana saka iyayenku mata a cikin magana ta dan karma wata
ta tilasta su fadar abinda ba ra’ayinsu ba shine kai yanzu zaka zo kana tsokanarsu ko, gasunan se su gaya
maka su waye surukan naka idan yaso se ka ci gaba da bincike muga abinda hali zeyi”.

Da daddaya kowa ta fadi sunan rabin ranta, nice ta qarshe harda gyara zamana na bude baki zanyi
magana Alhaji Qarami ya tare ni da cewa

“Ai ke nasani Amaryar ta Excellency ko?” (Yusuf kusan abokin Alhaji Qarami ne dukda a shekaru Alhaji
Qaramin ya girme masa sosai, yaro ne a cikin manya da Allah yayi masa nasibi sosai a rayuwa, Asalinsa
dan Bauchi ne kuma guri daya suke aiki da Alhaji qarami a Abuja tunda yaga Ma’u yace a duniya nan shi
yaga mata haka kuwa take garashi kamar kwallo amma be sare ba kullum yana kan binta.

Yanzu haka ya shiga siyasa ne ya tsaya takarar Dan Majalissar Taraiya dan yace se ya kai har shugaban
qasa in Allah ya yarda shiyasa suke kiransa da Excellency).

Lokaci daya na hade fuskata kamar ban taba murmushi ba ina kallonsa nace “Ni Bashi bane Alhaji
Qarami ai na gaya masa ni ina da wanda nake so”.

“Haba Ma’u yanzu kice bakyason Yusuf duk yanda yake bala’in sonki kullum cikin hidimar ki yake yana
hanyar zuwa gidan nan” Alhajin ya fada, sena tunzura baki gaba kaina a qasa nace

“To ni nace yayi mun ne ai tun ranar da ya fara zuwa na gaya masa nacin sa ne yasa kashi ci gaba da
zuwan ai”.

Ze sake magana Baffa ya tare shi da cewa “ya isa Muhammadu barta ta fadi zabinta babu dole a
al’amarin aure”.

Karkacewa nayi ina murmushi nace “Ni Baffa Yaya Bashir nake so”.

Se Baffa ya kalli Alhaji Qaramin da son qarin bayani, cikin takaicin qin zabar Abokinsa da banyi ba yace
“Wai wannan yaron Bashir Abokin Abubakar dan gidan Alhaji Ahmad na qasan layin nan take nufi”.
“Toh toh na gane dan waje Amadu me Mota kenan toh ai babu laifi se aje a cigaba da addu’a Allah ya
tabbatar mana da Alkahiri gaba daya”(Inkiyar Baban su Bashir ce saboda ya tabayin Direban Babbar
mota yana saurayi tun sannan ake kiransa haka)”.

Godiya mukayi wa Baffa kafin muka fice kowa ranta qal.

“Amma Ma’u baki kyauta ba tayaya Babban Yaya ze miki magana ki musa masa” Bilkisu ta fada bayan da
muka yi gaba nida ita, sena kalleta nace “kiji ki Yah Bilki da wata magana, so kike nayi shiru haka kawai a
cuceni yanda yake so na auri abokin nan nasa tsaf ze iya zuga Baffa, yanzu kuwa dana fada a gabansa
kinga ai nayi maganin abun”.

“Dukda haka da kin sani bari kikayi ki same shi ke dashi ki gaya masa, kuma ni wallahi nafi miki sha’awar
Yusuf din ma gashi Kyakykyawa dan gaye ga Kudi”.

“Ai se kije ke ki aure shi nidai bana so” na fada ina harararta, Alawiyya data qaraso gurin mu

Tayi caraf tace “ga ma Uncle Fahad banza duk samarinta na arziqi ta rasa wa zata zaba se wannan me
girman kan tsiyar da ita kadai yake yiwa murmushi a gidan nan”.

Hayayyaqo mata nayi ina cewa “Eh shidin na zaba ba’a son Fahad din saboda dan uwanku ne baza’a
aureshin ba sedai haushi ya kashe ku, Nida Yaya Bashir kuwa nan gani nan Bari yan baqin ciki sedai su
mutu”

“Allah ya baki haquri ni ba da wata manufa na fada ba ta Bashir” Alawiyya ta fada dan ita baiwar Allah ba
ruwanta bata iya wa fitinata. Banza na musu nayi shigewata daki ban qara kula kowa ba inajinsu suna ta
maimaita zancen kowa aka gayawa se yayi mita na rasa me yasa basa son Bashir.

Idan ma lissafin su bekai sauran manemana Arziqi ba ni wannan baya gaba na dan Arziqi da rashinsa duk
nufine na Allah, zaka iya auran mutum yana dashi ya tsiyace ko kuma ka aure shi bashi da komai daga
baya ya samu wadatar nidai kwanciyar hankali nake nema kuma a gurin wanda kake so yake son ka
kadai zaka same shi.
Dan haka inason Bashir ko a bukkar kara ze ajiye ni na yarda zan rayu dashi har qarshen rayuwa indai
akwai so da qauna ba matsala.

Cikin dan lokaci maganar auran mu ta taso kuma a daidai lokacin makarantu suka fara sakin Admission,
Alawiyyah da daman ATBU ta saka saboda daman saurayinta dan Sarkin Bauchi ne lokacin har ina
tsokanarta nace Allah yasa se ta samu Admission acan kuma yaqi auranta toh Allah ya taimaketa ta samu
ga batun aure ma har an kawo kayan nagani inaso na alfarma abinka da gidan sarauta.

Ni, da Yah Fati da Yah Bilkisu harda Junaidiyya duk GSU muka cike su ukun dukka sunansu ya fito a first
Batch kowa ta samu course din da take so amma ni har aka saki second batch babu sunana bayan kuma
gaba daya ma makina ya fi nasu a Jamb din.

Har aka fara Registration Admission dina be fito ba qarshe har makarantar seda akaje amma wai babu
sunana sukace wai sedai a sakani a yan Alfarma a bani wani course din daban nace bana so abarni kawai
inda rabo badi sena sake Jamb haka kuwa akayi se Alhaji Qarami yace bazan zauna ba ko Diploma ce
naje nayi kafin wata shekarar nan da nan kuwa aka samomun diploma a Computer Science na fara.

An kawo goron Yah, Fati da Yah Bilki suma anan cikin Gombe ne suka samu nasu mazajen duk yayan
Babban gida nida Junaidiyya ne ba’a rigada an kawo ba ita dai anzo tambaya Dan Abuja ta samo yaron
wani Minister abinda ya dakatar da kawo kudin ma wai Babansa ne yayi tafiya se qarshen watan da
muke ciki zasu zo.

Ganin duk anyi maganar su amma nida Bashir shiru yasa hankali na ya fara tashi. Sau biyu ina sake masa
magana bayan da aka bashi damar ya turo amma se yace na qara masa lokaci akwai abinda yake jira
gashi kuma a kwanakin gaba daya ma ya janye da zuwa gidan mu musamman da Yaya Abubakar baya
nan, daman shi a Kano yayi service se Allah ya taimake shi gurin suka riqeshi.

Seda muka ci sati kusan biyu Bashir yana mun wala wala har takai Baffa ya sakeyi mun akan yaji shiru
saboda yana so a hada gaba daya a aikawa da gidajen mazan sa rana shiyasa yake so yasan shirin Bashir
din.

Ranar dana gaji da zilliyar tasa takanas na kama hanya muka tafi gidansu tareda Alawiyya wadda da
dakyar ta yarda zata rakani, muna tafiya tana zagina wai in banda asara ga Maza da suka amsa sunansu
suna bina amma na nace se wani Bashir gashinan yana wulaqantani kuma tsabar rashin zuciya na dauki
jiki zan je gidansu. Nidai ban kulata ba har muka shiga gidan.

Kai tsaye Dakin Dada muka shiga, da yake daman na saba zuwa gaishetan se hakan be zama wani abun
mamaki na daban ba. Mun sameta tareda Yayarta wadda naji suna cewa Addah da yaranta guda biyu
babbar bazata wuce shekara shida zuwa bakwai ba se qaramar itama zatayi hudu haka.

Matar nada matuqar kirki ga faran faran da Jama’a nan da nan ta shiga hidima damu musamman da taji
ance budurwar Bashir ce bakinta har kunne take tambayar wacce daga ciki aka nuna mata ni.

“Wai wai zuqi masha Allah, ashe yanda Bashir yake sunkuyar dakai har ya iya zabo mace haka kai Allah
ya nuna mana lokaci musha biki, sannunku sannunku” haka tayi tayi dauke wannan ajiye wannan nidai
kaina yana qasa ina ta Addu’ar Allah yasa ya shigo amma har mukayi kusan minti talatin shiru bayan
kuma sanda muka shigo na ga qofar dakinsa a bude alamar yana gidan.

Naziru qaramin qaninsu ne ya shigo, ya qaraso inda nake da dan gudunsa ya zauna yana gaishe ni da
yake muna shiri dashi sosai, seya miqe da gudun sa yace “bari naje na gayawa Yaya ga Anty Ma’u tazo”
be dade ba se gashi sun dawo tareda Bashir din muna hada ido na tabo Alawiyya nace mu tafi daman
jiran da nake kenan nasan dole ai ze bimu.

Mukayi musu sallama bayan mun ajiyewa Dada ledar dana zubo turarukan fesawa dana wuta da
sababbin kudi yan hamsin hamsin na dubu biyu Addah ta dauke ledar tana zuba mana godiya kamar ita
aka bawa mudai muka tafi.

Seda muka danyi nisa da gidan sannan Bashir ya biyo mu, sama sama suka gaisa da Alawiyya tayi gaba ta
barmu, se ya kalleni yana cewa “Jiya munyi waya amma baki gayamun zaki zo ba”

“Me yasa zan gaya maka tunda baka son mu hadu yanzu, daman zuwa nayi in gaya maka dan karka ji a
gari, tunda dai ka gagara turowa zan bawa wadanda suka shirya dama. Na kuma gode da batamun lokaci
da kayi da duk alqawarirrikan qaryar da kayi mun akan zamu rayu tare” ina gama fadar haka nayi gaba
na barshi a tsaye ina jinsa yana kwala mun kira nayi banza dashi.
A zatona ze biyo mu amma har muka je gida babu ko sahunsa, abinda ya qara qona mun rai ya tabbatar
mun dagaske kenan daman Bashir yaudarata kawai yayi ba aurena zeyi ba yasa na gama fadawa a
soyayyarsa sannan yanzu ze gudu ya barni. Ranar haka na kwana ina kuka, gashi ko a waya be kirani ba,
babu wanda yabi ta kaina a gidan,

Hajia Anjij cema da safe da ta ga yanda idona ya kumbura ta jani tanayi mun nasiha da nayi haquri, lokaci
da yawa abinda muke so be zama lallai shine Alkahiri a gare mu ba dan haka na fawwalawa Allah, idan
Bashir mijina ne se munyi aure idan kuma Allah be yi ba duk nacin mu sedai mu haqura.

BASHIR

Tun lokacin da Asma’u ta gaya masa zancen an ce ya turo gida se maganar ta rabe masa biyu, bangare
daya na farin cikin ya kusa mallakar Ma’unsa se kuma daya bangaren tashin hankalin da me ze aureta?

Har yanzu bashida komai be kuma bawa wani ajiya ba, dan aikin da yakeyi dubu goma ce ake biyansa a
wata wadda dawainiyat karan kansa ma ba isar sa takeyi ba ga qannensa suma da qananun buqatunsu
tunda Babansu yayi ritaya, kudin garatutinsa suya har hada yake dan juyawa ana samun abinda za’ayi
cefane a gidan yanzu gaba daya duk burinsu akansa suke na ya samu aiki toh ta ina kuma ze fara
daddago maganar aure.

Kullum da wannan zulumin yake kwana yake tashi ya kuma rasa dawa zeyi shawara baze iya tunkarar
Abubakar ba, Aliyu kuwa tun tuni daman ya gaya masa ya rabu da Asma’u dan tafi qarfinsa toh se a
yanzu ya ga gaskiyar abinda yake fada din amma kuma baya jin ze iya rabuwa da ita saboda sonta ya riga
yayi masa irin shigar da fitar rai ce kadai zata iya raba shi da shi wannan dalilin ya sa yake zille mata dan
ganinta ma kullum qara rura wutar sonta yake a zuciyarsa sannan ya rasa ta yanda ze fahimtar da ita
halin da ake ciki.

Maganar data gaya masa dazun ba qaramin tayar masa da hankali tayi ba, gaskiya bazata sabu ba. Dole
ya nemi mafita dan yana ji yana gani baze iya zuba ido wani ya raba shi da Ma’u ba ya rusa duk wani tsari
da mafarkin sa akanta.

Jiki a sabule ya koma cikin gidan, palour Dada ya shiga ya tarar dasu ta zazzage turarukan tana ta
santinsu gaba daya ta kwashe se kwalli daya ta barwa Dadan wai ai kullum ana kawo mata na yau
rabonta ne kudin ma seda ta raba biyu ta dauka, ganin yanda Bashir ya shigo kamar kazar da tasha ruwa
yasa suka dakata suna kallonsa.

“Lafiya Bashir ka shigo kamar wanda aka zarewa qashi” Addan ta fada tana kallonsa, se ya ja guntuntsaki
yana kallon Dada yace “Dada maganar da mukayi dake akan sunce mu tura ne, kinsan tare ake so a hada
dana sauran toh shine yanzu tayi fushi har tana cewa kawai zata bawa wasu dama tunda ban shirya ba”.

“Me zanji haka magana babu dadin ji, kai yanzu Allah ya kashe ya baka shine ka tsaya salubanci da sunce
ka tura din amma ba’a je ba to uwar me kake jira?” Addah ta fada tana gyara zama.

Shiru Bashir ya mata, dan shi kwata kwata baya so tana shiga sabgarsa ma, Dada ce tace

“Toh Addah kin manta har yanzu be samu aiki bane, aure ai baze yuwu ba babu abinyi dame ze riqe
matar?”

“Sannu Nafi, kai Allah Nagode maka da Halin Nafi. Wane irin aiki kuma kuke magana mutumin da Allah
ya kawo masa hanyar arziqi, yanzu in banda rashin tunanin irin naki har kwa tsaya kuna zancen wani aiki
ga babban aiki ya samu.

Ka samu yarinya irin wannan daga babban gida tana sonka kuma iyayenta sun yarda zasu baka qarewar
aiki harda gida da mota se an hada maka nasan kai dai kawai ka tura ayi magana asan dagaske kake seka
gaya musu baka da aikin yin Aradu zasu samo maka tunda yarsu tana sonka.

Kai ashe Nafi kina dab da ja mana Asara kai Jama’a Allah kayi magani”.

Kallon ta kawai suke har ta gama hayagagarta, se Bashir ya miqe ya fice a ransa ya na qudurce kawai ze
gayawa Alhajin su aje, idan yaso su abar maganar nasu bikin zuwa sanda Allah ze sa ya samu madafa
tunda ya rarraba CV dinsa a gurare yanzu jiran tsammani kawai yake yi. Kasa zama yayi a gidan ya fice,
yana so ya kira Ma’u kuma yana tsoron abinda zata sake gaya masa Allah Allah kawai Yake Alhaji ya
dawo ayi wacce za’ayi kawai.
Addah kuwa ci gaba tayi da surutan ta har tana cewa Dadan idan ma maganar kudi ce se a nemo Bashi
ayi komai da an gama biki abinda ya samu a tattara a biya.

“Kiji ki Addah wane irin bashi ana zaune qalau dan Allah, babu komai idan Allah ya nufa matarsa ce to se
kiga Allah ya kawo hanyar da za’ayi komai cikin rufin asiri. Haka suka rabu dai Addah na sake jaddada aje
ayi maganar nan kar su bari damar nan ta wuce su.

Bashir kuwa Alhajin su na dawowa da yamma ya shaida masa, ba tareda wani ja inja ba kuwa ya amince
shima abinda yace Allahn daya taso da maganar ze hore yanda za’ayi komai cikin rufin asiri, tun a daren
ranar ya tashi qaninsa ya aikashi gurin Baffan su Asma’u akan a basu dama zasu kawo goron gaisuwa, a
take kuwa yace duk sanda suka shirya suzo, washe gari kuwa suka hadu da Qannensa guda biyu da
Amininsa daya sukaje aka kai gaisuwa.

Tarba me kyau suka samu daga gurin Baffan da yayyen Ma’u biyu manya, nan da nan aka qulla magana
sedai sun nemi alfarmar a qara musu lokaci akan wata shida da Baffa yace ya yanke ranar auren.

“Kasan haryanzu Alhaji be samu wani aiki na gaske ba, yar buga buga ce kawai akeyi ana dai saka ran
samun aikin nan kusa, abinda yasa muka zo din ma saboda kaga kar aga kamar wasa ne abun” Aminin
Baban su Bashir Malam Salisu ya fada.

Se Baffa yayi murmushi yace “Babu komai Malam Salisu in sha Allahu babu abinda ze gagara, kuje kuyi
shirinku iya abinda ya zama dole sadakine se ya nemi muhallin da ze ajiyeta duk abinda ya kakare masa
yazo ya sameni babu komai” suka yi sallama suna ta godiya, haka suka koma gida suna ta yabon dattako
da karamci irin na Baffa, dan lokacin da sukaje gidan daya daga qannen Baban su Bashir din har yana
cewa anya za’a barsu su shiga kuwa shi Bashir me ya kaishi dakko abinda yafi qarfinsa.

ASMA’U

Ina kwance ina ta baqin raina tun jiya har yanzu ban ware ba, gaba daya na rasa ya ma zanyi dan bazan
iya hasaso rayuwa da wani namiji da ba Bashir ba. Addu’ata kawai Allah ya mantar da Baffa karya kuma
tado mun da maganar har zuwa sanda zamu samu mafita.
Ina cikin wannan tunanin Baba Jummai shugabar masu aikin gidan mu ta shigo dakin ta sakar mun guda
a tsakiyar kai, da saurin gaske na toshe kunne ina zare ido ita kuwa se sake rangada abarta take ragowar
na taya ta.

“Uwar dakina ta zama amarya mun shaida mun tauna goro da alawa Allah ya nuna mana randa zamu
sha taushen daurin aure” ta fada kafin ta sake kwasar wata gudar.

Wani mugun bugawa qirjina yayi, waye ya kawo goro na? Na shiga uku kardai fa Baffa ya amsa wa wani
daga cikin manemana magana.

Dafe qirji nayi na qara fito ta idanu waje nace “Baba Jummai gorona aka kawo dawa?”

“Wato Uwar dakina kina nan da halin ki na tsokana, baki ma san waya kawo goron ba kenan, to wannan
Me gidan da baya dariya ne Engineer kike ce masa kowa” Baba Jummai ta fada.

Se naji kamar an kwararamun ruwan qanqara a tsakiyar kaina, wata wawuyar ajiyar zuciya nayi kafin na
koma na kwanta ina yiwa Allah tasbihi. Gaskiya Bashir ya shammaceni.

Waya ta ce ta dauki qara, a jikina na ji cewa Bashir ne, seda na tura baki kamar yana gabana kafin na
daga wayar.

“Amaryata” ya fada cikin qaramin sauti, shiru na masa ina ta faman juya baki kamar yana gaba na ina
jinsa yayi murmushi yace “Fushi ake yi dani ko Ma’una ayi mun afuwa. Gani a qofar gida nazo bada
haquri”.

“Ni bazan fito ba” na fada cikin muryar shagwaba, se ya marairaice shima yace

“Haba mana Amaryata so kike yi na kasa bacci dan Allah ki fito na ganki mana kafin nan da wata shida na
dauke ki gaba daya ki zama tawa”.
Rufe fuska ta nayi ina murmushi nace “Dagake bazan fito ba, nima ai jiya banyi baccin ba kaga mun yi 1-1
kenan ka tafi se bayan sati uku zaka sake ganina”.

“Kice kawai sena zare sannan, ki taimaka mun nidai ki fito na ganki ko minti daya ne ki koma na yarda”.

Seda naja masa rai kafin na zura dogon hijabina har qasa na fita, a palour na tarar da Goggo da su Nasir
suna kallo naja hannun Mimi yar dakin Hajia Umma ce muka fita.

Bashir na tsaye daga bakin Get gurin masu gadi, har wurin naje nace masa”A nan ka tsaya maimakon ka
zauna, muqarasa toh”.

“Aa Gimbiya daman zuwa nayi naga kyakykyawar fuskar ki sannan na kawo miki wannan(ya miqo mun
wata farar leda da kwali dan kwali qarami a ciki) ina so na kwanta da wuri gobe zanje wata Interview kiyi
mun Addu’a Allah yasa a dace”.

Karba nayi ina cewa “In sha Allah za’a dace, Alah ya bada nasara”.

“Amin” ya amsa mukayi sallama ya tafi ina juyowa mukayi kicibus da Fahad sun taho shida Anwar yayan
Alawiyya da take bi.

Fahad qanin Hajia Anjin ne shine auta a gidansu, Fari kyakykyawan saurayi me qirar larabawa ga iya
soyayya dan da ace da Fahad na fara haduwa kafin Bashir inaga da yayi nasara akaina saboda iya tsara
zancensa.

Hararar sa nayi ta gefe ganin irin kallon da yake mun yana murmushi kafin nace “Uncle Fahad ina wuni”

“Karma ki wani ce mun Uncle, yau dai naganshi daman akan wannan Kika qi ni Asma’u gaskiya kin fado
da yawa, har naji sauqin radadin da nake ji tunda nafi wanda ya kasanin sau dari wallahi kuma har yanzu
ban cire rai akanki indai ba gani nayi an daura miki aure ba bazan cire ran zaki zama mallakina ba” Fahad
ya fada yana kafeni da idanunsa masu kama dana mage, sena fizgi hannun Mimi nayi gaba ina cewa
“Se kayi ta saka ran ai kar Allah yasa ka cire, wai ace ba’a san mutum amma su kamar mayu sun nace
kuma ahakan dai shi yayi mun baku ba”

“Indai akanki ne ki kirani sarkin Mayu ma qarewa kenan Asma’u dan sena cinye ki hankalina ze kwanta”.

“Daga murya nayi yanda ze jini nace “sedai ka ci kanka dan kurwa ta daci ne da ita” na murguda masa
baki harda fari da ido kafin na shige inajinsu da Yah Anwar suna mun dariya.

Haka kawai duk wanda yaga Bashir seya kushe mun abuna, su kyau da kudi yake a gabansu ni ba matsala
ta bace ba.

Sannu sannu watanni naya shidewa harya rage saura wata daya bikin mu kuma a daidai lokacin muka
gama jarabawar semistar farko a ND1 zamu shiga hutu.

Sosia hankalina ya kwanta tunda zancen auren mu da Bashir ya kankama nayi fresh abina na qara kyau
da haske musamman ga gyaran jiki da tuni Hajia Umma ta fara tsuma nan da nan jikina ya sake mudewa
ko ina ya cika bazaka taba iya mun kallo daya ka dauke ido ba se ka qara.

Bashir kansa wani lokacin idan ya kalleni yakan ce “anya Ma’u banyi zari ba kuwa ki kalli kanki ki kalleni
ai se ace dan aiken ki ne ni” in ya fadi haka se nayi dariya nace

“Kai dai ka godewa Allah kadai dan shi yake yiwa bawa kyauta irin wadda beyi zato ba.

Ana biki saura sati uku aka kawo Lefen Junaidiyya daga Birnin Tarayya Akwati na dukan Akwai saiti hudu
masu shida shida. Kaya kam sedai ace masha Allah dan komai yaji harda danqareriyar sarqar gwal dinta
yar dubai ga kudin da suka doro akai dubu dari haka dangi a ka dauka ana ta murna yarinya tayi Goshi
sati daya zagayo aka kawo na Yah Fati da Yah Bilki rana daya suma bangaren kowanne sunyi Bajinta
akwatinan su Dozen Dozen da dubu hamsin hamsin akai.
Na Alawaiyya ne qarshe ana saura Sati daya suma suka dunguma masu algaita nayi maroqa nayi aka
kawo sha tara ta arziqi kai komai dai se sambarka mutane anata yabawa kowa fadi yake saura Na Ma’u
kowa naso yaga Lefeen ama’u yasan ba qaramin Miji na fallo ba nidai a raina nace kwaji dashi idan ma
gulma ce ta qare muku dan ni banji komai ba da ganin Lefen su na taya su murna kuma ban damu ba dan
tuni Baffa ya gaya mun yacewa Bashir ba se yayi lefe ba ya nemi gidan da ze sakani kawai, dan haka ma
ya bayar da kudi masu yawan gaske yace aje Kano a hado mun duk abinda Amarya zata buqata sannan
duk wata hidima zanyi ta biki Alhaji Qarami yace na gaya masa ze bani kudin to me ze dame ni kuwa.

Har satin biki Bashir nata fafutukar neman gida, duk yan gidaje masu kyau idan ya tambaya se yaji kudin
ya shallake Aljihunsa gashi kuma a qalla dai yana so ya samarwa Ma’u muhalli me kyau kodan halaccin
da akayi masa a zamanin nan adauki Mace kamarta daga irin gidansu a bashi babu lefe ai wallahi an
gama masa komai.

Dakyar ya samu wani gida anan unguwar su babu nisa sosai, gidan dukda tsoho ne amma fasalinsa nada
kyau 2 bedroom flat ne se babban palour harda Gurin Dining ga Kitchen da dan qaramin store sannan
daga waje akwai wani dan palour haka qarami ga bandakin baqi a tsakar gidan se dan fili da ze ci mota
daya.

Da yake ginin tsohone sunyi dakunan manya a wadace duk girman gado zasu iya dauka kuma da akwai
bandaki a kowanne daki matsalar da babu tiles sumuntine a dakunan palour kadai suka sakawa tiles din.

Tareda Aliyu suka sha buga bugar neman gidan, bayan sun samu bayan ya biya Aliyun yace masa ya
kamata ya gayawa Ma’u tunda tun wancan satin take masa maganar gidan dan tuni anje anga na sauran
har ma jiya an tafi kafin Abuja da Bauchi na su na cikin Gomben ne yayi saura, da za’a siyo kaya ma da
farko Anty Saratu Babbar Yayarsu Mace itace akan yin order kayan daman tafi kowa jin takaicin auran
Bashir da za’ayi cewa tayi baza’a siya musu iri daya da Asma’u ba dan tasan Bashir bashida gidan da za’a
zuba su, seda Hajia Babba tayi mata kaca kaca tace kuam karta kuskura ko cokali abanbanta in yaso idan
an rasa inda za’a zuba a bawa Ma’un kayanta ko siyarwa ne tayi tasan dai an mata yanda akayiwa yan
uwanta.

Ita dai Goggo nata Ido, ko Suhaima data kira tayi qorafi cewa tayi babu ruwanta matar mutum kabarinsa
kuma ita bata ga aibun Bashir ba da za’a ce baza’a aure shi ba.
Washe gari sukaje da ita da Bashir din da Aliyu se Alawiyya yar uwa ta rai da rai. Ita kam gidan ma ya
mata a haka, bandaki ne matsalar dan duk ya dafe nan take a cikin kudaden data karba ta ware ta bawa
Bashir din dakyar ya karba tace a canza kayan bandaki har tiles din qasa dana bangon a cire, ya hada da
abinda yake hannunsa ayi sauran gyare gyare da fenti idan yaso dakunan se a saka carpet kawai a ciki,

Haka kuwa akayi a cikin kwana biyu se ga gida ya dawo sabo dan gyara aka masa gangariya kai bakace
tsohon gidan nan bane, ana i gobe kamu kuwa aka je aka jera mata kayan ta sega gida ya fito shar yaji
kaya yan order. Gadajenta biyu Yan Turkey masu kyau da tsada ga kujeru na alfarma da kayan kallo kai
duk wani abu da ake siyawa yar gata an sakawa Asma’u haka kayan Kitchen sosai Goggo ta gwangwaje
su da kuloli tunda duk Baffa ne yake siyan Electronics iyaye mata su saka abinda babu ai kuwa tayi
qoqari kai baka ce auran Yaya uku take ba.

Tsaf aka shirya gida har yan jere na cewa wai daman qaramin guri yafi kyan kwalliya se suka ga kamar
jerenta na neman yafi na masu manyan gidajen kyau.

WATA KISHIYAR

(ALKAHIRI CE KO SHARRI)

Na Maryamah Farouk

(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)

Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 34

Ranar Juma'a aka daura aure na da Bashir, Juma'ar data shiga cikin jerin rana kun tarihin rayuwata na
farin ciki da bazan taba mantawa da su ba. A qa'ida ranar da aka daura aure a gidan mu ake kai Amare
amma mu ba'ayi haka ba saboda Dinner da manyan Yayyenmu suka shirya zasuyi a daren ranar sauran
Yayyen mu mata se tsiya sukeyi wai an fi son mu su kuwa kamar ana jira da an daura ake kwashe su.

Da yake tun ana sati daya da biki muka san da shirin Dinner, nasan dole sauran Angwaye zasu
gwangwaje suyi shiga ta alfarma tunda suna dashi dukda Bashir ma nasan ze yi iya qoqarinsa amma baze
iya kamo su ba saboda tattalin arziqinsu ba daya bane su duk masu dashi ne.

Haka na samu Baffan mu na tasa shi da naci seda ya bani shadda yadi goma cikin irin wadanda yake
dinkawa ni kaina bansan kudinta ba kawai dai nasan suna da kyau kuma ko cikin Mutane ina dadewa
banga wanda ya saka irinta ba sefa manyan irinsa.

A gurin Yah Mustapha na samu hula harda takalmi daya siya dan daurin aure saboda duk gidan mu ya
fisu gayu, dakyar ya bani wai order su yayiwo takanas seda mukayi ma zan biya kudin rabi nidai dana
samu suka zo hannuna nace a gudunmawar sa, yana ji yana gani na masa fin qarfinsu se na bawa Yah
Abubakar shaddar nace ya kaiwa Bashir dinki tunda abokinsa ne yasan Size dinsa na roqeshi dan Allah
karya gaya masa ina so na bashi mamaki ne.

"Ma'u kenan, yanda kike son Bashir kike tattalin sa Allah yasa kar wata rana yayi miki halin mu na maza"
abinda Yah Abubakar ya gaya mun kenan a lokacin da se naji jikina yayi sanyi.

Gaba daya daman na lura dashi kamar hadi na da Bashir beyi masa ba na rasa dalili dan har tambayarsa
na tabayi yace mun babu komai, da yake daman shi ba mutum ne me yawan magana ba se na bar
maganar kawai nasan idan da Bashir nada wani mugun abu baze barni na aure shi ba.

Tsaf na hade kayan nan bayan an dawo daga daurin aure angwaye sun shigo aka dauki hotuna, masha
Allah gaba dayan mu munyi kyau kuma ko wacce ta dace da zabin ta se fatan Alkahiri dangi da abokan
arziqi suke yi mana. Suna shirin ta fiya nayiwa Sadiya qawata rada dan daman ita na bawa ajiyar Kayan
tayi maza taje ta dakko su, seda suka fita tabi bayan Bashir din ta bashi.

Muna zaune a bangaren da qawayen mu anan ta hira irin wadda ko wanne qawayen Amarya sukeyi idan
ana biki, hayani ya na tashi wayata dake hannuna tayi qara, Bashir ne daman zaman jiran kiransa nakeyi
sena miqe da sauri na shige bandaki na kullo qofar ko naji maganar sa dakyau.
"Ma'una kayan menene wadannan, ina kika samo shadda me bala'in tsada haka?" ya tambayeni bayan
dana gaishe shi.

"Kamanta an jima akwai Dinner da za'ayi, kalar kayan da zan saka ne zamuyi Anko".

"Ina sane har ma nayi dinki nima, mantawa nayi sam ban ma gaya miki kalar nawa kayan ba ai" ya fada
daga daya bangaren, sena marairaice nace

"Se ka ajiye su gobe ka saka idan za'ayi budar kai nidai yau wannan nake so na gani a jikinka".

"Shikenan an gama Amaryata, na tabbatar yau ke kadai ce zaki fini yin kyau a gurin nan"

"Haka nake so Angona yafi na kowa, se anjiman idan kunzo, kar dai ku bata lokaci qarfe takwas zuwa
Goma Baffa yace za'a tashi" daga haka mukayi sallama na kashe wayar.

A filin tsakar gidan mu aka shirya za'ayi dinner, tun la'asar masu decorashan din da aka dakko suka
katange iya inda suke buqata suka fara aikin su, kafin magriba sun gyara guri tsaf se ka rantse wani
babban dakin taro ne.

Seda mukayi sallar magriba sannan aka fara shirya amare, munyi kyau har mun gaji cikin dinkin riga da
skirt na wani hadadden material da akayi mana kowa da kalar nata da ze dace da shigar Angonta,
munsha daurin goggoron mu me kyau dan fa fashion designer guda aka dakko ta shirya mu dukda a
sannan ba'a fara kwalliya me fente fenten nan ba amma ta tsatso mana kyau da iya abinda ake amfani
dasu a sannan.

Har mun saka kayan sarqoqin mu Hajia Umma tace mu cire, saitin sarqa, awarwaro da zubuna ta kawo
mana na gwal qirar dubai wanda sallama ce Baffa yake bawa Iyayen mu mata kudi su siya mana idan za'a
kaiki dakin ki saka shi ta bawa kowacce nata ta saka nan da nan kwalliyar mu ta qara qawatuwa se
walwali mukeyi ta ko ina.
Seda mukayi sallar Isha'i sannan muka fita babban palour inda kafatanin yan gidan mu mu a lokacin mu
talatin da tara ne muka hallara ga Baffa da Matansa Hudu aka shiga daukar hotunan family.

Lokaci daya hawaye suka balle mun kamar sauran na jira kuwa muka dauki kuka wiwi wanda nasan na
zallar murna ne Baffa kansa seda ya kauda kai gefe ya goge kwalla ganin irin wannan arziqi da ubangiji
yayi masa.

A ko da yaushe kalmar godiya ga Allah bata taba barin bakinsa, ya bashi lafiya, ya bashi arziqin mata,
dukiya da Tarin Yaya ya kuma shirya masa su, sannan be jarabce shi da wani babban Alkaba'i daya dame
shi a rayuwa ba banda qananun abubuwan da kowanne mumuni ba'a gaza jarabtar su dashi to shi kuwa
me zeyi idan be godewa Allah ba da kuma Addu'ar neman cikawa da Imani dan abinda ya rage masa
kenan a yanzu.

Bayan mun gama hoto da yan gida Angwaye ma suka shigo, kowa yayi kyau amma wallahi Bashir dina ya
fisu dan se ya zama tamkar wani wata a cikin taurari kamar yanda na zama Zara cikin yan uwa na, haka
muka sha hotuna musamman da iyaye da manyan yayye suka fita aka bamu guri nan muka baje kojin mu
aka dauki hotuna kala kala kafin muka dunguma zuwa gurin dinner.

Taro ne akayi shi a tsare harda Baffa duk fulatancinsa seda Yayyen mu suka tilasta shi ya dan zauna a
teburin da aka shirya masa da Aminan sa da be ma san an gayyato su ba, ganin su ya sa ya saki jiki haka
iyayen mu mata Goggo ce dai seda aka kai ruwa rana dan seda muka yi mata hawaye nida Yah Bilki
sannan ta fito se wani jan mayafi take tana rufe fuska yanda kasan ita kadai ce bafulatana a gurin.

Cikin Awa biyun nan akayi komai aka tashi, anci an sha abinci na alfarma qarshen dai yan gayun Yan
Abujan ma sun yaba gashi komai a tsare babu kida balle ayi rawa irin slow music din nan aka saka kawai
aka ci abinci aka dauki hotunan tarihi seda aka fara watse wa nema qannen mu suka dage se an saka
musu kida ai kuwa waqa biyu aka saka Baffa na hango yanda aka hade mata da Maza ana rawa yace a
kashe kowa ya tafi haka muka kwana ana ta hirar taron nan dan babu qarya munji dadin sa.

Washe gari da wuri aka miqa mu. Munsha kukan rabuwa, Junaidiyya aka fara tafiya da ita dan jirgi sukabi
qarfe goman safe suna tafiya yan Bauchi ma suka dauki Amaryar su, kafin qarfe biyu an tafi kai Yah Bilki
da Yah Fati ni kadai nayi saura tunda kusa da gida ne.
Seda aka dawo daga kai su aka baro wadanda zasu tsaya musu budar kai kamar yabda kowa yasan
Al'adar mu ta Gombawa, anayin sallar La'asar nima aka kwashe ni se gidan su BShir inda za'ayi budar kai
na.

Seda aka damqani a hannunsu, ga kayan garar da kashi biyu akayiwa ko waccen mu, ta gidan su miji
daban tamu daman tun da akai jere kowa an kai mata gidan ta sannan ga turame da kwanuka harda
Saitin Gado da akeyiwa Uwar miji seda akayiwa kowacce babban Gado dan Dubai haka aka kai musu.

Bayan sun biya kudin budar kai da Turmin zani da tabarma nan qanne da abokan wasan Bashir suka fara
zuwa kowa ta ajiye kudinta se ta fadi sunan da ta sakamun, wannan yar farar yarinyar da muka gani
randa muka zo gurin Bashir ta taho da gudunta da naira goma a hannunta.

A inda taga ana ajiye kudin ta ajiye kafin ta kama mayafina cike da rashin ji har tana neman ture mun
daurin dankwali ta bude fuskata tana cewa "Na saka mata ANTY" mata suka dauki guda kowa ya yaba da
ganin kyakykyawar Amaryar Bashir, hannunta na kama na zaunar da ita nace "Yaya sunanki?"

"AMIRAH" ta fada tana yar dariyar yarinta, nan da nan naji ta shiga raina saboda ina da son yara daman
gata yar fara kyakykyawa da ita.

Anyi Budar kai lafiya seda aka kira sallah aka tashi, yan uwana sun mun kara dan ba qaramin kudi suka
zuba mun ba haka dangin Bashir ma ba laifi sun mun liqi sosai bayan an gama qawayena suka tattare
mana kudin mu muka koma dakin Bashir inda nan aka gyara aka sauke mu.

Anan muka kwana se washe gari muka tafi gidan mu daga ni se Bashir dan daman ba'a raka amarya mu
iya kacin su gidan su miji se ku qarasa keda shi kawai.

Soyayya me tsafta suka shimfida a cikin gidan auran mu, ban qara tabbatar da Bashir yana qaunata ba se
a yanzu dan a aikace yake nuna mun duk abinda bakinsa baya iya furtawa.
Cikin sati daya da mukayi wata irin shaquwa me qarfi ta sake shiga tsakanin mu dan kullum muna manne
da juna babu inda yake zuwa se masallaci da yayi sallah kuma ze dawo gida kuma har zuwa sannan babu
wanda yazo mana kullum gidan mu a kulle muna ciki muna kashe juna da soyayya.

Matsalata daya da Bashir dan irin taya aikin nan da naji ana cewa Angwaye na taya Amaren su shi
bayayi, yana zaune zanyi komai na sedai na kawo masa idan muka ci abinci yana zaune zan tattare
kwanuka naje na wanke qarqari ya zo Kitchen din ya tsaya ina aiki muna dan hira idan yan maganar na
kansa kenan dan Bashir be fiya magana ba, miskiline seta raya masa sannan ni kuma gani da dan banzan
surutu dole da qarfi da yaji tasa yake biye mun wani lokacin kuma na qaraci maganata idan na ishe shi ya
jani ya kashe bakin maganar da Zazzafan Kiss shikenan.

Seda muka kwana goma sannan muka fita, da yamma Aliyu yazo da yar motarsa one door daya siya dan
shima ya samu aiki tuni kuma da yake bashida wani nauyi akansa shiyasa har ya iya siyan mota.

Muna tafe yana tsokanata wai me nake bawa Bashir a dan lokaci haka yayi kumatu ya yi haske shima ze
zo a ringa samma sa miyar Amarya ko ze dan farfado nidai murmushi kawai nakeyi irin najin kunyar nan
har muka je gidan su Bashir.

Cikin farin ciki Dada ta karbe mu harda Anty Amina Babbar yayarsu da bata koma Bauchi ba tunda tazo
biki. Haka sukayi ta jana dan saki jiki nidai ina ta sunkuyar da kai, da Dada taga haka se ta tashi ta barmu
ai kuwa na dan sake dasu dan basu da duhun kai nan da nan muka saba mukayita hira. Dab da Magriba
Alhajin su ya dawo, seda sukayi sallah kafin Anty Amina ta rakani muka gaisa se saka mun Albarka
yakeyi.

A gidan mukaci abincin dare sannan Aliyu ya dawo muka tafi bayan na ajiye musu tsarabar da na kawo
na manta ta a motar Aliyun ina jin Dada na Tambayar Bashir mun shiga gidan su Addah kuwa yace Aa,
tace yayi qoqari ya kaini mugaisa.

Da muka fita a zatona zamu shiga gidan mu dan tun tuni a qagare nake, saura qiris ma na dauki Fainusa
dazu muje amma dai na danne .

Ganin da nayi Mun dau hanya har mun wuce gidan yasa na tabo Bashir nace
"Baza muje mu gaida su Baffa bane naga mun wuce gidan?"

Be tareda ya waiwayo ya kalleni ba yace "Ai ni munje dasu Aliyu ranar nan mun gaishe su, ke kuma ba
yanzu ba. Se kinyi wata sannan zamuje" ya maida kai suka ci gaba da maganar su da Aliyu. Tsabar takaici
bansan sanda kuka yazo mun ba. Muzo har unguwar ina kallon kofar gidan na mu yace wani bazan shiga
ba se nayi wata amma ai shi munje nasu gidan idan Adalci ne me yasa be bari duk maje lokaci daya ba.

Sakin kuka na nayi ya fito fili, Yah Aliyu ya shiga bani haquri yana cewa Bashir "muje mana ko a
tsaitsayene ta gansu" amma mutumin nan mirsisi yaqi magana har muka isa gida Aliyu ya ajiye mu na
shige na barsu a waje yana wa Bashir din mitar be kyauta ba.

Ranar haka na share shi, bayan mun kwanta ina jinsa yana wani shafani nai masa banza qarshe yaja tsaki
ya juya ya kwanta nima na gyara kwanciyata a raina nace "kaima kaji yanda naji idan da dadi ai".

Haka na tashi washe gari babu walwala, nayi duk abinda na saba na koma daki na kwanta, ina kallonsa se
zarya yakeyi yana kallona amma dan baqin hali ya gagara bude baki yayi mun magana haka muka wani
har dare dadai yaga abin nawa bana qare bane se jinsa nayi a cunkushe yana cewa

"Dan bamu shiga gida jiya bane wai kike ta wannan Fushin to shikenan wani satin se kije" nayi masa
banza kuwa tunda shi baze iya bani haquri ya rarrashe ni ba ai shikenan. Dakyar ya samu na sakko shima
seda ya yarda randa na cika sati biyu ze kai ni nan da kwana uku kenan sannan na haqura, washe garin
ranar da yamma yace na shirya zamu je gidan Addah ashe ma unguwar mu daya suna ta bayan layin mu
ne.

Sam Addah ta kasa zaune ta kasa tsaye sanda mukaje, haka ta ringa kawo mun Abubuwa se sannu da
zuwa take mun kamar wadda tazo daga China ina kallon Bashir se hada fuska yake da gani abin be masa
ba yaran Abokanan zamanta da yaransu suka ringa shigowa muna gaisawa da yake akwai yammata da
yawa Sa'annina a cikinsu dama wadanda suka girme ni nan da nan muka saba.

A nan Bashir ya tafi ya barni yace ze dawo da magriba, Amirah na naniqe dani qaramar Ummi ce me dan
qyuya bata sakewa da mutane Addah kuwa ta ringa bani labarai kala kala anan nake jin ashe su kadai ita
da Dada iyayensu suka haifa anyiwa Addah aure ba dadewa suka rasu dan haka Nafi(Dada ta koma
gurinta har tayi mata aure).
Na zata tana da wasu yayan bayan su Amirah a cikin hirar da muke naji su kadai ne yayanta tace dai ta
haihu duk basu tsaya ba dan Babban Danta ma ya girmi Amina yayar Bashir.

Da zamu tafi haka ta hada mun kayan yaji su citta da kanumfari da daddawa dasu kuka harda Barkono se
kuma tace bari abarshi a daka se a kawo mun daga baya, Amirah harda kukanta da zan tafi wai seta bimu
seda Bashir yayi mata jan ido sannan ta koma muka rabu da alqawarin zasu zo daman sun barmu mu
dan huta ne tukunna.

Kwana biyu naje gidan mu, wannan tun safe na tafi ai kuwa nasha Fada gurin Goggo kamar tayi me wai
tunda nake wa na taba gani tazo gida sati biyu da aure sena tattara na tafi bazan zauna ba aikuwa na
ringa kuka dakyar Baffa ya bata baki ta haqura na kuwa bar mata dakin ta na koma gurin Hajia Babba har
dare seda zan tafi naje mukayi sallama tana sake buga mun warning din karta sake ganin qafata idan ba
wani abu ake a gidan ba, a hanya Bashir yayi ta tsokana ta wai gashinan, da yace bazan zo ba ai harda
daukar fushi dashi yanzu gashi naje din an koroni.

Haka rayuwa taci gaba da mirginawa. Su Addah da kishiyoyinta uku masu kirki suma duk sunzo haka
yaran gidan suna zuwar mun musamman da yanzu Bashir ya koma aiki in ya fita se gidan duk kadaici ya
isheni in suka zo musha hirar mu kafin ya dawo sun tafi.

Tunda Amirah taga hanya kullum seta zo, abinda na lura shekara shida amma ba'a sakata a makaranta
ba kuma duk sauran sa'anninta na gidansu suna zuwa. Dana tambayi Addah dalili tana dariya take
cemun

"An kaita fa in gaya miki se tayi ta kuka wai bata son makaranta, ni kuma nace ina dalili tunda bata so
yanzu a barta, in ta qara wayo dakanta ma zata ce a sakata".

Mamaki ya kashe ni, wai shekara shida se wani lokaci zatayi wayo ta zauna a makaranta? Abinda na lura
dashi daman sam Addah ta sangarta yarinyar nan yanda kasan goyon gwarawa babu kwaba gata da
shegiyar rashin kunya ga barna duk abinda ta gani seta lalata abinda yake hadani da ita kenan ma na fara
gajiya da zuwan naya dan kullum tazo seta bata mun wani abun.
Akwai randa tazo inada wata yar Aku ta roba me magana, ina son Akun nan tun banfi shekara goma
Hajjin su Anty Suhaima ta siyomun ita. A lokacin tace a kantin ita kadai ce tayi saura har Goggo tace
baza'a siya ba dan rigima kawai zata zo ta hada a gida idan sauran suka gani amma Baffa yace se an
siyowa Mamansa suka kuma yita nema ba'a samu wasu ba.

Tun sannan nake ta boyonta ko wasa bana fitowa da ita ayi kai in kana so kayi wasa da ita sedai mu shiga
daki kuma ka biya ni kudi shekararta Tara yanzu na qudure har Yayana se sunyi wasa da ita.

Da yake babu wuta lokacin ni kuma ina Kitchen ina girki sena dakko mata na saka mata batir wai ta samu
abin wasa.

Ina Kitchen ina jinta tana magana Akun na maimaitawa, se ji nayi tana qundumawa Akun zagi ita kuwa
Aku ta maimaita.

"Yada wasan zagi Amirah ki dena babu kyau" na fada daga cikin Kitchen, se tace "Anty ita ce komai na
fada se ita ma ta fadi irinsa" tana gamawa Akuma Ta maimaita.

"Bazaki dena kwaikwayata ba ko" Amiran ta fada caraf Aku ta sake fada itama, se abin ma ya bani dariya,
ina shirin in leqo na gaya mata rikodin Akun takeyi duk abinda mutum ya fada itama seta maimaita se ji
nayi Amiran nacewa

"Shegiya mahaukaciya wallahi kika sake kwaikwayona sena cire miki kai" ba kuwa ta rufe baki ba Aku ta
dauka sena leqo ina cewa

"Ke Amirah bana hana ki zagi ba in banda shirmenki batiri ne da ita tana rikodin...." maganata ta maqale
daidai sanda tayi wurgi da Akun nan da qarfin gaske ta daki bango take ta tarwatse komai ya kama
gabansa.

Tsabar takaici kasa ko motsi nayi, yanzu Akun da har nagama tawa yarinyar ko kwarzane be sameta ba
shine yanzu zata rada mun ita da qasa? A fusace na qarasa inda take na miqar da ita tsaye ina zare mata
ido nace
"Amirah bakida hankali me yasa zaki fasa?"

Se kuwa ta wani murguda baki cike da fitsara tace "Na fasa din, ai seda na gaya mata ta dena
kwaikwayona harda fa zagina take yi yanzu dana fasa se naga yanda zatayi".

Saboda haushi ban san sanda na kai mata ranqwashi ba, kamar zanyi haqaye nace "kin san shekarun
Akun nan kuwa ta ma girmeki amma saboda shegen rashin jinki shine zaki fasa mun ai kuwa sena zane ki
yau a gidan gobe ma ki sake yimun barna".

Fincikewa tayi ta nufi gurin Akun, injinta da shima ya cire ta hau tattakewa tana cewa "kika ranqwashe
ni toh na fasa na fasa din ayi koma menene".

Lallai rashin kunyar yarinyar nan ta isa dole na koya mata tarbiyya tunda bata da ita ai kuwa na jata
Kitchen na zari tsintiya na shiga tsula mata a jiki daman rigar ta me kamar Bea ce bata da hannu ai kuwa
dukan ya shigeta tana tsalle tana ihu ina tsula mata ina cewa

"Gobe ki sake yiwa wani rashin kunya tunda ke fitsararriya ce". Seda na mata lilis kafin na saketa, ta
kwasa da gudu tana kuka ko ta kan Takalminta da Hijab bata bi ba ta bar gidan ni kuwa ko a jikina na
tattare fasashshiyar Akuna idona ya ciko da kwallar takaici ganin babu ta yanda za'ayi ta hadu, a kan
Centre table na ajiye jin abincina na kamawa a Kitchen.

Ina kwashe abincin Bashir ya dawo, yasan yanda nake son Akun nan da mamaki ya kalli pisis din da suke
ajiye ya kwalo mun kira na fito ina masa sannu da zuwa.

"Meya samu Akun taki? waya fasa ta haka?" ya tambayeni yana kallona, se ji nayi hawaye ya silalomin na
bude baki da niyyar magana hargagin Addah ya katse ni.

A sukwane ta fado dakin tareda Amirah a bayanta da har sannan bata dena kuka ba tayi tumu tumu da
ita qasa har cikin gashinta da naci wuya jiya na gyara mata shi tsaf da niyyar yau zamuyi kitso da gani
birgima tayi a qasa.

Ke Asma'u me Amirah tayi miki zaki kama ta kiyi mata wannan dukan kamar kin samu jaka" Ta fada tana
hura hanci.
"Ni ba abinda nayi mata Addah kawai dan na fasa waccen shegiyar Akun shine ta kama ta dokeni da
zabori" Amirah ta fada cikin kuka kafin Addah tayi wani abu se ji mukayi

"Fuu" Bashir daya fi kusa da Amiran ya dauketa da mari ta kuwa kwala ihu dan marin ya shigeta da
gaske.

"Zaki wuce daga nan ko sena tattakaki fitsararriyar banza da wofi, wato ke kika fasa har kina sake fada
kuma an hukuntaki shine zakije ki kai qara toh zuwa kukayi a rama miki ko me" ya hayayyaqo mata
kamar ze sake rufe ta da duka tayi bayan Addah tana hadiyar zuciya dan tuni kukan nata ya tsaya.

"Idan ita ba'a rama bata ba ai kai seka zo ka dakeni dan ubanka se insan ka isa ka tarewa matar ka fada"
Addah ta fada kafin ta juyo kaina tace

"Ke kuma wannan ya zama na qarshe da zaki sake dukar mun Yarinyar idan ma ba cin zali ba akan ta fasa
abin wasa kawai ki hau dukan ta to wallahi karki sake" ta juya fuu suka fice ni kuwa na rakata da ido.

"Maganin ki kenan ai da kike jawo yarinyar kece baki san halin ta ba amma Yanzu gashi ta fara nuna miki,
mtsw" ya ja tsaki ya shige dakinsa ya barni a tsaye.

Daga wannan abu naja baya gaba daya da Addah dan ba'a fi kwana uku ba se gata da Amiran ta kawo su
harda Ummi wai zataje unguwa akayi sa'a Bashir yana nan yace mata muma fita zamuyi ta ringa mita
kuwa nidai suna fita na sakawa qofa muqulli to ina dalili yaro yayi maka ba daidai ba in ka hukuntashi a
zo har gida a gabansa a ci maka mutunchi to ni banga ana haka a gidan mu ba.

Bata haqura ba dan ba'a rufa sati ba ta kuma zuwa wai tazo duba mu kamar ma ba'ayi komai ba, ranar
nayi Farfesun kaji akan da daddare se na soya mana doya muci dashi. Bayan na kawo mata ruwa da lemo
na koma Kitchen din, har ga Allah banyi niyyar zuba mata ba dan kadan nayi. Ina da dambun nama harda
kilishi su nayi niyyar na kawo musu se ji nayi tana cewa

"Asma'u zubo mana farfesun mana idan da biredi ki hado mun".


Se nayi tsam a Kitchen, a raina nace "ikon Allah" na dai samu dan bowl na saka mata cinya daya da rabin
qirji dan fa be kai gudar kaza bama wanda nayi nasan Bashir kadai se ya tashi dashi ma.

Ina ajiye mata ta kalli kwanon, se cewa tayi "meye wannan kika zubo haka, a gidan dan nawa a kawo
mun wani abu kamar na roqa, matsa nan ki gani" ta miqe se gani nayi ta shige Kitchen abinta, ina tsaye
ta dawo da kular naman dukka da biredin dana manta ban dakko mata ba ta zauna ta hau ci ta nayi mun
hira.

Abinda yafi qarfin ka aka ce seka mayar dashi wasa, haka na zauna ina kallon ikon Allah ta cinye tas har
tana cewa wai tayar mata da kwadayi kawai yayi. Da zata tafi babu kunya tace idan muna da danyan
nama na bata, na shiga Kitchen zan debo mata se gata ta biyo bayana, ta debi kwai, taga kayan miya
suma ta diba nidai na saka mata kaza daya a leda daga yanda ta karba nagane kamar ta raina ne nayi
saurin tare ta da cewa

"Daga gidan gonar Baffan mu aka kawo mun, kinsan idan ya fitar da kaji yana rarraba mana da kwai" se
tayi wata yar dariya tace

"Au uhm kunji dadin ku kuwa" mukayi sallama ta tafi. Ina sane na mata haka dan karma tayi zaton dan
nata da take iqirari ne yake siyowa bare har tayi iko dasu, daga gidan mu aka akawomun dan har yau
kayan miya kadai Bashir yake siyowa sedai idan munyi sha'awar jan nama ya siyo danye ko gasashshe
saboda tunda muna da komai na cefane kamar ma bama taba kayan garar nan, sannan kaji basa yanke
mun da kwai.

Idan na aika a siyomun a gidan gona Baba Idi Manager kyauta yake bani ko a bani ninkin na kudin dana
bayar.

Da naci da komai Amirah ta dawo zuwa tun Bashir yana fada shima har ya haqura sauqin ta daya mun
koma makaranta dan haka bana zama Asabar da lahadi ne kawai take zuwa shima daga baya na
takurawa Bashir akan yaje ya samu babanta yayi masa magana akaita makaranta haka akayi kuwa aka
sakata har Islamiyya ma shikenan muka samu sauqin abun.
Watan mu shida da aure ranar da safe ina zaune Yah Bilki ta kirani take cemun wai Goggo ta haihu, a
kwance nake amma seda na miqe zaune nace "kinsan me kike fada kuwa haihuwa fa kika ce wace irin
haihuwa ana zaune lafiya yaushe ma ta samu ciki?"

"Wallahi dagaske, ni kaina bakiji yanda nayi mamaki ba amma kuka fa nayi zargin haka dan zuwan da
nayi na qarshe nidai naga cikin amma se nayi zaton ido nane wallahi yanzu Su Bilal suka zo suke gaya
mun munyi Auta"

"Ikon Allah amma yanzu dan Allah wace irin haihuwa ce haka yaya nayi suma suyi gaskiya daga wannan
an gama" na fada se Yah Bilki tasa dariya tace

"Se ki gayawa Baffan ki ai bani ba, nidai gobe zanje naga Baby kefa?"

"Nima in na taso makaranta inaga in biya goben yanzu dai ai bazata kori mutane ba ko daman abinda
bata so a gani kenan yasa take kora ta in naje" na fada ina dariya, se tayi dariya itama tace

"Yo ai sanin hali, yanzu da kin sani har na America tuni da labari ya tarar dasu, shikenan se mun hadu
goben" mukayi sallama.

Bashir na dawowa na gaya masa ina ta mita dan me Goggo zata haihu shida cikanki be qara ce mun ba
tunda yace Allah ya raya.

Washe gari kuwa daga makaranta gida na wuce, abin Allah ina ganin yarinyar naji ta shiga raina, haka na
tasa Goggo a gaba kamar wata kakata da zolaya data gaji ma daki ta shige ta barmu Baffa kuwa se nan
nan yake da Yar Babyn me kyau da akayiwa Huduba da Aminatu muka yi mata laqabi da Amna.

Ranar a gidan muka wuni da yawa munje ga matan yayyen mu maza da muka tashi tafiya kowa ta kama
hanyarta a motarta muka fito tareda Yaya Fati ina cewa "Bari na biki ki sauke ni a gida toh tunda kece
yar hanyar mu" daidai mun qaraso inda Yayan mu na biyu a gidan Alhaji Yasir yake tsaye yana waya.

Muka gaishe shi har mun gota ya tsayar dani sena dawo.
Seda ya gama wayar ya kalleni yace "ke dawa zaki tafi"

"Yah Fati ce zata sauke ni a gida" na fada ina dan wasa da hannuna dan yafi Alhaji Qarami zafi daukar sa
muke kamar shine babban Yayan,

"Ta tafi, kije Bello ya kaiki gida, ga wannan" ya fada yana miqo mun kudi da ban san ko nawa bane, sena
karba nayi masa godiya na juya inda Yah Fati take jirana nace mata

"Ki tafi Kawai, Baban Sharifa yace naje Bello direbansa ya kaini, kinga har kudi nasa mu ma se jibin zaku
zo dai ko?"

"wallahi kina sharafin ki yarinyar nan komai aka tashi ace ke wani tausayin ki ake ji a gidan nan bayan
babu abinda kika rasa ta wani fannin ma kin fimu jin dadi dan dai ana ganin mu a qaton gida ne kawai,
shikenan bari naje dare yana qarayi" muka yi sallama muka rabu.

Kwana biyu dayin haka da daddare muna zaune aka buga get, Bashir ne ya fita ya bude se gashi ya dawo
wai gurina aka zo sena zura hijabi nabi bayansa.

Ina zuwa na ga Bello ne direban Alhaji Yasir daya dawo dani ranar nan da wata dalleliyar mota Toyota
qirar shekarar baqa dukda dareni amma kana ganin yanda take qyalli.

Gaisawa mukayi nace da Bashir "Bello ne direban Alhaji Yasir fa" se yace "oh ai ban san shi ba.

Key da takaddu Bellon ya miqo mun yana cewa "Gashi Alhaji yace a kawo miki, tun jiya ma naso kawowa
wallahi takaddun ne basu kammala ba se dazu, mota fa tayi kyau Hajia Allah ya sanya Alkahiri ya tsare ki
da sharrin qarfe".
Tsabar murna bansan sanda na dane Bashir ina dariya ba nace "wayyo dadi munyi mota muma munyi
mota"

shima dariyar yake ya riqeni ganin muna neman faduwa Bello ya juya ze tafi irin yaji kunyar nan na
tsayar dashi na shiga gida da gudu cikin kudin da Alhaji Yasir din ya bani ranar nan na qirgo dubu biyar na
bashi ya ringa kuwa zuba mun godiya ya tafi.

A daren na kira Alhaji Yasir nayi masa godiya "Ba komai, ki tabbatar idan kina buqatar wani abu ki ringa
gaya mana" ya fada kawai ya kashe wayar.

Na kira Baffa na gaya masa shima yace "Inye yar gatan Yayanta kice se munzo dani" nayi dariya. Haka na
ringa kiran yan gidan mu ina fada musu abin arziqi kowa ya taya ni murna, badan dare yayi ba ma ba
abinda ze hana ni ta fiya gida yanzu na nuna musu, haka nayi bacci da ido daya, bini bini na daga labule
na leqa motar nan Bashir se dariya yake mun.

WATA KISHIYAR

(ALKAHIRI CE KO SHARRI)

Na Maryamah Farouk

(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)

Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 35

ASMA’U
Muna cikin wata takwas da aure me kamfanin da Bashir yake aiki ya rasu dan haka akayi rabon gado
yayansa suka saka kamfanin a kasuwa abinda ya tilasta wa ma’aikata barin aikinsu.

Wannan dalili yasaka Bashir dawowa zaman gida a koda yaushe saboda har sannan babu wani aiki daya
samu ya dai rarraba CV amma babu inda aka kirashi. Da farko abin yazo mana da sauqi saboda
Alhamdulillah kusan komai na buqata muna dashi a gida dan abinda ba’a rasa ba muke siya irin su kayan
miya ko ganye da dai sauran masarrafi dan haka idan na fita makaranta se nayi amfani da kudaden da
suke hannuna na siyo mana komai yanda zamu dan kwana biyu tunda kudi basa yanke mun.

Duk sati Baffa yake bani kudin makaranta dan shi yake dauke da nauyin karatuna ga kuma na man mota
da ake hadamun dashi yanzu.

Ta inda matsala ta dan bullo mana rashin lafiyar da Baban su Bashir ya fara, bayan kaishi Asibiti suka
tabbatar da cewa yana da Suga da hawan jini ne suka taso masa lokaci daya seda yaci kudi sosai kafin
lafiyarsa ta samu sannan aka dorashi akan magani abinda ya turgude dan jarin kasuwancin da yake yi
kenan dan da kudin akayi duk hidimar Asibitin sa.

Ganin da nayi rayuwa ta fara yi musu matsi, kuma Baban da yake fita ya nema musu na cefane gashi a
gida babu wadatacciyar lafiya. Bashir baya aiki a yanzu Amiru yana shekarar qarshe a Jami’a, Afiya tana
Level 1 se Fainusa da Sadiya da suke secondary daga Sa’ad,Samirah har Naziru lokacin a primary suke.

Akwai ranar da mukaje duba Baban da da yamma, abinda ya daga mun hankali muna zuwa na tarar da
Dada tana yi musu kwadon garin kwaki harda Baban da yake fama da Siga a sannan shi aka zuba masa
yaci. Abun ya bala’in daga mun hankali.

Bayan mun koma gida washe gari banyi shawara da Bashir ba na dauki Buhun shinkafa biyu, taliya,
macaroni, semovita komai biyu ga pastar mai hatta Maggi seda na diba na hada sannan na tsaya a hanya
na siyi kayan Shayi da kayan miya na tafi gidan.

Yara na samu a qofar gidan suka shigar da kayan, motar Aliyu dana gani ya tabbatar mun da Bashir yana
gidan dan daman tun safe yau ya fita dan haka ban shiga ba kawai na wuce gidan mu. A can na tarar da
Junaidiyya wai ta zo gida haihuwa ga Yah Bilki ma tazo da tsohon cikinta haka Yah Fati Alawiyya ce dai
nata be isa haihuwa ba ni se a sannan ma tunani na ya tafi ga rashin samun cikin da banyi ba.
Dukda ina son yara amma hakan besa na taba damun kaina da sena samu ciki dole dole ba kuma shima
Bashir ko sau daya be taba mun maganar ko nuna wani abu akan hakan ba gaba daya mun barwa Allah
shi ke bayarwa idan lokaci yayi nasan zamu samu namu muna.

A gidan na wuni har dare dan ina son naga Baffa, se bayan Isha ya shigo gida ashe Yola yaje daurin auren
Yar Baffa Sama’ila.

“Mamana ya akayi ne har yanzu baki tafi gida ba” ya fada bayan dana gaishe shi, sena marairaice fuska
nace

“Baffa Kasan Alhajin su Bashir bashida lafiya ko”

“Na sani wallahi ai na dubashi ma sanda yana Asibiti sannan bayan sun dawo ma na sake leqa gidan,
ciwo ne babu dadi yanzu kuma abinda ake ta fama dashi kenan wannan Siga Allah ya tsare mu dai”.

“Amin Baffa, daman wata Alfarma nake nema idan babu damuwa” na fada ina gyara zamana. Se ya
kalleni yace

“Gidan ku Ma’u ni zaki kalla kice kina neman Alfarma a gurina, idan banyi muku abu ba wa kuke dashi a
fadin duniyar nan daya fini?

Kar na sake jin haka, ki tambayeni kai tsaye abinda kike so ko menene shi a duniyar nan zanyi miki dan
duk abinda na mallaka domin na inganta rayuwar ku ne” Baffa ya fada cikin dakewa alamar babu wasa a
maganar sa. Sena saki murmushi. So da qaunar Baffan nawa tana qara ratsani nace

“Wallahi Baffa gani nayi gaba daya rashin lafiyar nan ta saka sun shiga wani hali, kaga yanzu baya iya fita
kasuwa ga Bashir kuma aikin da yakeyi ma an siyar da kamfanin shine nace ban sani ba ko akwai abinda
zaka iya yi akai”.
“Ash sha yanzu shi Bashir din baya aiki kenan, kinga ko jiya seda mukayi maganar da Muhammadu
(Alhaji Qarami) yace mun yana iyakar qoqarinsa akan maganar aikin, kinsan qasar tamu ne yanzu da
lamarin aiki ko kana da hanya fa idan wanda yafi ka yazo se kiga an samu tangarda.

Sannan yace daman su masu kwalin Irin nasa me martaba ta daya (first class) suna wahalar samun aiki a
ma’aikatun mu na cikin qasa saboda yawanci manyan gurin suna ganin kamar in suka dauke su zasu fisu
sedai a ma’aikatu mallakin qasashen waje su daman sunfi buqatar irinsu din ze ci gaba da bada takaddun
in Allah yaso za’a dace.

Shiyasa ni nafi ganewa kasuwanci amma ku yaran yanzu gaba daya kun ta’allaqa akan aikin gwamnatin
nan da gaba daya abinda kuke samu a wata se kiga Dan kasuwa ya same shi a sati daya wani ma cikin
yini, yanzu dai ki turomun shi, idab yana da sha’awa yazo kasuwa idan Allah yasa yana da nasibi a ciki se
ki gani.

Maganar Alhaji Amadu kuma zan duba abinda za’ayi, kama daga kan rashin lafiyar tasa har zuwa
matsalar iyalin se muga abinda Allah zeyi”.

Sosai na ringa zubawa Baffa Godiya da Addu’oin fatan Alkahiri, har na tashi zan tafi ya tsaidani da cewa

“Yawwa na tuna kuwa Jiya Manager Bankin da nake ajiya munyi magana naji yace zasu dauki Ma’aikata,
shi bangaren nasa ze iya aiki a banki ne?”

Cikin farin ciki na koma ina cewa “Eh Baffa, shi aikin banki indai ka iya kwanfuta da kana da lissafi a
takardun ka zasu dauke ka, kuma duk yana dasu”

“Toh bari na kirashi yanzu naji idan da hali se ya fara wannan din kafin sanda Allah ze kawo wani”.

Ina tsaye ya kira Manager ya kuma amsa tareda cewa ze turowa Baffan Email yanzu a tura da CV din,
sannan ranar Litinan yaje Bankin ya same shi da hardcopy na takaddun.

Haka na koma gida raina qal na tarar da Bashir ya rigani komawa yana zaune yana shan Shayi.
“Se yanzu” ya faaa yana kallona, seda na ajiye jaka da mayafina na zauna kusa dashi tareda rungumo shi
nace

“Canki”

“Kinsan ban iya cankar abu ba ko” ya fada yana kallon fuskata, sena dakko wata ta na bude inda na
rubuta Email din na miqa masa ina cewa “Gashi yanzu kaje Cafe ka tura da Soft copy na CV dinka sannan
ranar Monday zaka kai hard copy din”.

Kallona yayi da rashin fahimta, nan da nan na gaya masa yanda mukayi da Baffa na rufe da cewa “Idan
kuma kafi son kasuwar yace kaje ka same shi, ni da zaka hada dukka ma kana aikin kana taba kasuwancin
se ya fi yanda su Yaya sukeyi.

A zatona zanga farin ciki a fuskar Bashir irin wanda nake ciki amma se naga akasin haka, cikin daure
fuska ya kalleni yace

“Yanzu Ma’u har kin fara gajiya ne yasa kika tafi nemar mun taimako a gidan ku, daman dazun ina gida
an kai kaya yaran suka ce kece kika kawo yanzu kuma kinzo da wannan”.

Tsabar mamaki ma kasa rufe baki nayi na tsaya ina kallon Bashir, a zatona abun kirki nayi ashe shi a nasa
girman kan gani yake baya yaci kenan na nema masa taimako a gidan, se kawai na miqe na kwashi
gyalena da jaka na ajiye masa Key din motar ina cewa

“Ban shigo da ita ba tana waje naga ka datse get din da kwado” nayi shigewata daki. Yanzu fisabilillahi da
ace na samar masa aiki da kuma na zama ni nake dauke da dawainiyar mu wanne yafi? A zatona tunda
ya fadi hakan baze yi ba se gashi washe gari yana ce mun ya tura ranar litinin din kuma yaje ya kai
Takaddun cikin ikon Allah ba’a rufa sati ba sega shi sun tura masa da takarda sun daukeshi aikin wani
satin ma ze fara zuwa.

Haka muka cigaba da tafiya zuwa yanzu duniya tayi mana daidai, Baffa ya dauke nauyin makarantar
Sa’ad, Samirah da Naziru ya saka su cikin foundation din sa da yake biyawa Marayu da wadanda
iyayensu basu da qarfi makaranta, shikansa Alhajin ya saka Ahmad Yayan mu da yake likita ne yana aiki
da Asibitin Malam Aminu Kano su acan ana samun tallafi daga qungiyoyi dan haka ana daukar nauyin
magungunan masu lalurori ansamar wa Alhajin kyauta yanzu ake bashi magani ga ganin likita duk sanda
ya tashi har kanon yake zuwa tunda sunfi mu kwararrun likitoci se gashi a dan lokaci ya dawo hayyacin
sa ramar da yayi duk ta cike ya koma fita kasuwarsa yanzu sannan ga Kayan Abinci da ake rabawa
maqota yanzu suma duk wata se an kai musu Albarkacin surukuta nasu rabon ma daban yake.

Dan haka yanzu dan abinda Bashir zeyi musu be wuce na neman Albarka da duk da yakewa iyayensa ba
idan yana da hali ni kaina yanzu se sambarka dan babu abinda Bashir ya rageni dashi ya karbi ragamar
gidan sa komai yana yi yanzu har kudin makaranta yake bani daman tuni na bashi mota ta saboda zuwa
aiki wanda dakyar ya karba acewarsa Wanda ya siyamun bazeji dadi ba, be karba bama seda na kira
Alhaji Yasir din a gabansa na gaya masa Bashir ya samu aiki dan haka na bashi motata saboda sauqin
zirga zirga tunda ni ina dab da kammala karatun Jarabawa zamu fara,

“Babu komai ai taki ce kina da damar yin duk yanda kika so, daman saboda bana so naga kina hawa
motar haya ne ko ki ringa neman lift yasa tunda mijinki ne kinga ze kaiki ko ina kuma ya dakko ki, Allah
yaci gaba da baku zaman lafiya mu shine fatan mu kawai” Alhaji Yasir din ya fada.

“Wallahi Ma’u rayuwar gidan mu tana burgeni, yayunku nada mutunchi sun kuma riqe girmansu ba
tareda nuna banbanci ba ko yau Baffan ku ya mutu bashida damuwa yasan kanzuri’arsa a hade take ba
kamar yanda yake faruwa a yawancin gidajen masu kudi ba da zaki ga kowa yan dakinsu ya sani kuma
burinsu ace sune a gaba sun fi sauran” Bashir ya fada bayan da muka gama wayar, se nayi murmushi
nace

“Idan Namiji ya zama tsayayye a gidan sa tabbas kan zuri’arsa zata hadu, amma daga inda ka nuna
banbanci tsakanin matanka shikenan kayiwa zaman lafiya gibi a gidan ka dan yayan ko wacce zasu tashi
wasu na ganin an fi son uwarsu sune yan gata sauran kuma zaau qullace ka na ganin kana wulaqanta
uwarsu ka banbantata da dayar kaga baza’a taba samun zaman lafiya ba.

Kaima idan ka tashi qara aure kayi koyi da halin Baffan mu wallahi zakaji dadin rayuwarka”

“Ni ai dan ke kadai aka halicceni Ma’u babu sauran gurbin da wata zata sake samu a cikin zuciyata” ya
fada yana janyo ni jikinsa.
Haka rayuwa taci gaba da shudawa. Nagama Diploma ta har sakamakon mu ya fito Bashir ya siya mun DE
form dukda ban so ba yace gara naci gaba na gama lokaci daya na huta kawai.

Zaman gida da nake yanzu yasa Amirah ta dawo da zuwa, ba laifi yanzu ta dan saitu tunda ta qara girma
ga makaranta da take zuwa kuma nima ba kamar da ba da bana saurara mata yanda zan tarbiyyan tar da
Dan dana haka haka nake kula da ita dukda wani sa’in in ta koma taja gayawa Addah haka zata qaraci
mitar ta nidai bazan kukata ba.

Indai har zata ci gaba da turomun ita to kuwa dole na saita ta yanda nake so. Yanzu kusan kullum a nan
take wuni dan Addah bata zama, tun safe in zata fice qantalinta zata kawo mun Uniform din Islamiyyar
Amiran da farko har Ummi ta fara Bari Bashir ya hana kai tsaye yace mata karta sake barinta dan
matarsa ba me raino bace ai kuwa munga ruwan masifa dan har Dada seda ta karbi rabonta haka dai aka
dena se Amiran ake barmun.

Wani lokacin ma har kwana takeyi idan Addah tayi dare bata dawo ba ko Bashir yace ta tafi ta zauna a
gun Sauran Matan gidan se nace Yabarta kawai dan har ga Allah ina son yarinyar daman rashin jin ta ne
ya ke hadamu nima kuma zuwa yanzu na fara sha’awar ajiye nawa Dan dan duk su Alawiyya sun haihu
shekarar mu daya da kusan wata takwas yanzu da aure amma ni shiru.

Akwai ranar da na taba yiwa Bashir maganar nace masa ko zamuje Asibiti yace muna Aa

“Komai lokacine kuma bamuyi dadewar a har zamu ce zamu Asibiti ba, mu qara haquri Allah yasa jinkirin
ya zama Alkahiri” ya fada dole na haqura.

Da zaman haka da nakeyi akwai wata makaranta a qasan layin mu nacewa Bashir zan nemi koyarwa acan
be hana ni ba kuwa dan da kansa ma yaje ya tambayarmun suka ce naje ai kuwa aka sauke ni zan ringa
koyarda yan JS1-3 Computer Science, qarfe 8 nake shiga 12 na gama classes dina in tafi gida kuma sosai
nake jin dadin aikina haka yaran suna ganewa dan Allah yayi mun baiwa ta iya magana, sannan yanda
nake da Sakin fuska yasa muka saba sosai da dalibaina.
Cikin hukuncin Allah se gashi na samu ciki wanda sam ban san dashi ba seda ya kai kusan wata uku a
jikina sannan naje Asibiti saboda rashin ganin Al’adata na tsahon lokaci se gashi gwajin farko an tabbatar
mun ina da ciki bayan an yi scanning aka gayamun watanninsa.

Tun ina Asibitin na kira Bashir na gaya masa, sosai kuwa ya nuna murnar sa yace na tafi gida na huta
kafin ya dawo haka muka kwana ranar cikin farin ciki kamar mu ciro dan haka muka ringa kallon hoton
scanning din da ba ganinsa ake yi sosai bama.

Kamar kuwa cikin nan na jiran a san dashi se Laulayi ya taso ni gab, kuma wani abu safiya nayi idan
Bashir ya fita haka zan wuni da zazzabi da ciwon kai amma duk inda La’asar tayi kafin ya shigo gida na
ware dan haka ko nayi masa qorafin baya yarda musamman idan ya dawo banyi girki ba ya ringa mita
kenan in ce bani da lafiya kuma yace shi be gani ba.

A daidai lokacin kuma Admission dina ya fito, wannan karon na samu daman Business Administration na
nema sun bani Level two haka na fara jigilar zuwa makaranta ga ciki ga karatu dan ma farkon semester
ne, randa naji ba kanta kwanciyata nakeyi a gida naqi zuwa, haka muka ci rabin zangon, an tafi hutun
Midsemeater aka tsunduma yajin aikin da ba qaramin dadi abun ya mun ba na ringa Addua Allah yasa
kar a koma sena haihu.

Haka mukayi ta lallabawa, ina rainon cikina, Addah kullum tana tafe da kayan kwalamar da tasan zan so
amma fa idan tazo ita ma haka zata koma da niqi niqin tsaraba dan duk abinda idonta ya kai se ta dauka
ni kuma bana hanawa sedai Bashir yayi ta fada idan ya gani ko ya tambayi abu nace babu dan yasan ita
kadai ce take zuwa ta dauka.

A lokacin su Fainusa sunyi candy dan haka suna zuwar mun sosai wata ran ma ni zan kirasu idan naga
kwana biyu basu zoba haka zasu wuni suyi warkaja min su son rai, kayan sawata da duk suka mun kadan
saboda ciki haka zan tattara in basu, kayan kwalliya turare duk zuwa da abinda zan basu har seda ta kai
ta kawo ko bikin qawaye zasuje gurina za’ayi aron su takalmi, jaka sarqa wani lokacin in suka karba nace
su barshi.

Lokaci daya maganar auran qannen Bashir Mata su ukun ta taso. dafarko auran Afiya aka saka, wane
tudu wane gangare se ji nayi a bakin Addah wai ai gaba dayansu za’a hada”.
“Ni nacewa Nafi a hada yaran nan dukka kawai lokaci daya a huta to me za’a jira tunda duk da tsayayyun
maneman su gasu da garin jiki ai bata jerasu a gaba su zamar mata kamar wasu kishiyoyi ba.

Tana wani ya za’ayi hidima zatayi yawa bayan ga Bashir Allah ya rufa masa asiri aikin Banki fa yakeyi har
a tsaya ana wani zancen kudi” Addahn take gaya mun.

Niko banda “Allah ya sanya Alkahiri” ban ce mata komai ba dan mamaki take bani yanda take ji da aikin
Bankin nan na Bashir seka rantse wani babban Manaja ne a CBN idan ba haka ba ta yaya za’a tattago
auran yaya mata har uku kuma a dan qurarren lokaci kwata kwata wata hudu fa suka saka rana. Ai ko
bashi da nasa hidindumun a bashi isashshen lokaci ya shirya balle ga hidimar haihuwa a gabansa dan
kusan lokaci daya bikin ze kama da haihuwata.

Haka Bashir ya ringa mita kullum ya zauna saurin me akeyi da za’ace su uku za’a hada ina laifin Afiya da
Sadiya dan duka duka Fainusa bata cike sha shida ba kawai girman jikine yasa aka mata tsallake a
makaranta suka gama tareda Sadiyan.

Haka naci gaba da rainon ciki na a can kuma suna ta shirin biki, Alhajin su yayi iya qoqarin sa ya bada
kudin gadajen Amaren kowa daya harda katifa dan shi kansa ba’a san ransa aka saka auran duka ba
amma bala’in nacin Addah da har ta zuge Dadan itama ta hau ta zauna dole yasa musu ido sannan ya
kira Bashir ya gaya masa karya kuskura ya takura kansa su saka shi yin hidimar data fi qarfinsa akai
kowacce da abinda Allah ya hore tunda sun nace se anyi.

Dan haka gaba daya dan Albashin nasa da duk wani saving dinsa ya basu akayi musu kujeru
gudummawar da aka samu daga sauran yan uwa da abokan arziqi suka harhada aka yi abunda ya samu.

Ido kawai na zubawa Bashir ganin har cikina ya kusa fita daga wata na takwas amma ko pant din jariri be
siyo ba ko ya bani kudi yace na siya se hidimar auran qannensa yake yi. Raina ya sosu da abin har na
kasa haqura wata rana nayi masa magana se ce mun yayi

“Ma’u kenan saurin me kike yi ki bari a haihu mana ko bakiga hidimar data ke a gaba na bane duk
qoqarin da nayi kina kallo kullum da sabon abunda zasu ce akai ni gaba daya ma na gaji Allah Allah nake
ayi bikin nan kowa ya huta”.
Sosai naji zafin maganar sa a lokacin, cikin bacin rai nace masa “Amma shima wannan abu me
muhimmanci ne kuma kasan dai kaine meyi sannan ba yau kasan ina da ciki zan haihu ba tun ma kafin
maganar bikin ta taso cikin ne a gaba yanzu kake cewa a bari a haihu tukunna cikin da ko a yanzu za a iya
haife shi amma ko rigar da za’a saka masa bamu tana da ba ai shikenan” na tashi na bar masa gurin.

Nakuma qudurce a raina bazan sake masa magana ba dan daman tuni na sissiyi wasu wasu kaya unisex
dana gani suka mun kyau se kawai na hada akwatina ta zuwa Asibiti na jingine in yaso naga iya gudun
ruwan Bashir.

Wannan Abun yasa gudummawar danayi niyyar bayarwa ma na maida abata tunda a take takensa nasan
ba abin arziqi zeyi mun idan na haihu ba nayi amfani da kudin na toshe wata kafar, Addah tayi shaguben
harta gaji akan biki nata matsowa wai matar babban Yaya bance komai ba, ai ni ma ina da wayona ni na
iya bauta musu amma abinda yake doke ayi mun saboda tasu buqatar tafi tawa ana nema a tauye ni
sannan na kwashi gudummawa na bayar lallai ma se kawai nayi dariya nace mata

“Ai babban yayan ya wakilce ni yayi komai sedai mu jira Allah ya kaimu musha biki”.

Ana saura sati daya bikin Matan gidan nu suka aika wa Dadan da saitin Kuloli manya guda uku, a ranar ta
kirani a wata tana ta godiya wai an kawo kula masu kyau da tsada daman suna ta yanda za’ayi a qara
musu duk wanda suka siya ba wasu na arziqi bane yanzu gashi an samu sun gode sosai.

Haka kawai kuma se naji nauyin qin bayar da komai din da nayi, dan haka washe gari naje Awo da yake
da mota na fita dan Asabar ce Bashir yana gida sena Biya na siyi wasu kulolij masu kyau guda uku da
zannuwan gado manya masu abun rufa suka uku na wuce gidan Dadan na kai mata.

Taringa zubamun godiya amma qiriqiri Addah dana tarar ta nuna sunyi kadan, har tana cewa “Yanzu a
matsayin ki guda a nuna wadannan kayan ace ke kika kawo ai se a raina ki ni dana ga wadanda akace an
kawo daga gidan ku inji su hudun duka se naji wani iri nida na dauka mota za’a sauke mana” da wasa da
dariya tayi maganar amma duk me hankali ai yasan me take nufi. Dan haka nima cikin wasan na mayar
mata da martani nace
“Yo Addah kin manta ance taqamar mace gidan mijinta kudin uba ai ado ne kawai, kuma a iya qarfin
mijina nayi wannan ai kuwa na kai a yabamun su kuwa da suka bayar fa kara suka mun bawai dole ya
zamar musu fa se sunyi ba”

Washe garin ranar muka tashi da Alhinin Rasuwar Aliyu Abokin su Bashir, mutuwar ta dake ni kwarai dan
A jiya bayan na dawo a gidan na tarar dasu shi da Bashir harda Bala suna hira, yana ta tsokana ta wai
bana jin nauyin jikina nake iya tuqi nace masa ai Laifin abokinsa ne da be kai ni ba, na wuce ciki na barsu
yana ta faman yi mun Addu’ar sauka lafiya ashe rabuwar kenan da safe se kiran Bashir akayi wai ya rasu
da Asuba anji shi shiru be fita Masallaci ba Qaninsa ya duba shi aka tarar babu rai.

Mutuwar Matashi akwai firgitarwa musamman ta mutun irin Aliyu me mutunchi da mutunta Jama’a ya
samu shaida ta kwarai sosai, haka muka tafi Jana’iza Allah sarki Mamansa se Kuka takeyi su biyu ne
Yayanta daga shi se qaninsa haka budurwar da ze aura da suka zo Abin tausayi gaba daya se jikina ya
sake yin sanyi da lamarin duniya.

Tunda akayi rasuwar Bashir ya zama wani iri, ranar kwana uku, ranar kwana uku da daddare muna zaune
shiru yake cewa

“Allah sarki Aliyu, ranar kafin ki shigo yake cewa mun Wallahi Bashir kayi dacen mata Allah yasa mu a
danshin ka dan Allah ka riqe yarinyar nan da kyau dan Alkahiri ce a rayuwarka kuma matar rufin Asiri ce.

Kaga dai a yana yin da kukayi aure gashi a hankali abubuwa suna ta warwarewa bata nuna gazawarta ba
ni kuwa kana kallo yarinyar nan Momy ba yar kowa ba amma ta dauki buri ta dorawa kanta wai fa dana
kaita taga gida na rainawa tayi wai ban dora bene ba, ta shiga kawo mun wasu tsare tsaren banzanta, Ni
fa in ba’ayi wasa ba auran ma fasawa zanyi.

Idan da rabo nayi a Aljanna, ashe bamu sani ba tafiyar ma tazo gangara” se ga hawaye ya zubo ta gefen
idonsa.

Jikina ya qara macewa dakyar na iya cewa “ Allah ya sa muyi kyakykyawan qarshe, waya sani ko nika
mutuwar zanyi”

“Karki sake fadan haka In sha Allahu lafiya lau zaki haihu” ya fada yana kama hannuna.
Wannan rasuwar ta rage kaifin shagalin bikin su Fainusa dan duk wani makusancin Bashir yasan Su su
hudun nan tare suka tashi, Ranar Asabar data kama kwana shida da rasuwar Aliyi aka daura auran a
ranar kuma kowa aka kaita gidanta. Daman Banje kai Amare ba dan gidan mu ma na tafi da hayaniyar
yan biki ta fara yawa se dare Bashir yaje muka tafi gida.

Kamar ciwo na jira kuwa yana yin parking nayi wani ciwon baya da mara lokaci daya sunyi mun sallama,
se Bashir ya shiga ya dakko mun Akwatina muka kama hanyar Asibiti. Tsabar takaici ina cikin azabar
ciwon da nakehi kamar haihuwar ta taho gab ne wai Bashir tambayata yakeyi yanzu ya za’ayi idan
haihuwa ce bamu siyi kayan Baby ba bansan sanda na qunduma masa zagi shiga kayan babyn ba nace ya
mun shiru ko ya sauka a motar,

Haka muka qarasa aka shiga filin daga, zo kuga idon Ma’u a labor room ashe aka ce wasa Farin girki
wannan ciwo sallama ne, haka dai akayi ta gumurzu har Asuba, cikin ikon Allah Ana kwada kiran Assalatu
na santalo qaton Baby na me kama da Bashir sak kamar an tsaga kara hasken Fata ta kawai ya dakko.

Murna a gurin Bashir kamar ya taka rawa, kafin Gari ya gama haske Asibiti ya fara cika da dangi na harda
nasa, Hajia Babba da Hajia Umma ne suka zo, a kunne na radawa Hajia Umman akan tace gida zasu wuce
dani dan tun farko farko danayiwa Bashir maganar wankan gida yace ba wannan maganar ban sake ba.

zuwa rana kuwa da likita ya tabbatar babu wata matsala aka bamu sallama Hajia Umma tace gida aka yi
dani, ze musa Addah ta tace muje babu komai daman sunyi niyyar kawo nin, saboda haushi ko sallama
Bashir beyi mana ba ya kama hanya ya tafi.

Oho nidai muma mukayi tafiyar mu gida, daman na dade da hada kayan tafiya wankan muna zuwa aka
tura su Khadija gidan suka dakko mun ina ta Addu’ar Allah yasa kar a tambayi ina kayan wanka da sauran
abubuwan da ake siya ilai kuwa kafin ma mu qaraso Hajia Anjin saka su Baba Jummai sun shirya mun
dakin da zan zauna duk wani abun buqata na zaman jego an tana da.

Seda muka kwana muka wuni sannan Bashir yazo shi ala dole fushi yake yi, ko a jikina jegona kawai
nakeyi ingantacce haka yarona Aliyu da tun a Asibiti yayi masa Huduba shima yana samun kula sosai.

Kwanan mu biyar aka kawo kayan barka daga gidan su Bashir tareda ragon suna. Yan rigunan su ba laifi
da turamen Atamfa uku nawa, haka aka taresu cikin karamci suka tafi yan barkar da suka tarar yan uwan
mu nata yan qananan maganganu dan kowa yayi zaton yanda yanzu ya samu budi babu laifi zeyi abinda
yafi haka ni kuwa ko a jikina dan dama ba jiran abinda zasu kawo nake ba, ko sanda na masa magana
kawai dan haqqinsa ne ya kamata yayi.

Ranar suna munsha shagalin mu, na ringa shiga ina fita ta Alfarma. Amirah da tun kwana biyar da suka
zo tana gurina da yake anyi hutun makaranta daman nayi mata dinku na duk inda na shiga tana nan yan
gidan mu suyita tsokanarta ana yar Anty tayi dariya.

Zaryar da Bashir ya ringayi ta saka aka tattara ni satin mu uku muka koma se na tafi tareda Baba Jummai
da zata qarasa mun Arba’in.

WATA KISHIYAR

(ALKAHIRI CE KO SHARRI)

Na Maryamah Farouk

(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)

Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 36

Shekarar Aliyu daya na samu cikin Jafar, nasha kuka sosai saboda ba qaramar wuyar raino nake ci da
karatu ba sannan yanzu kuma ga wani sabon cikin har rigima se da mukayi da Bashir ya kuma tabbatar
mun se ya bata mun rai in har wani abu ya samu cikin nan bisa gangancina.
Haka na hada ciki da raino ga karatu da lokacin ina Level 3 ga hidimar gida idan na fita makaranta duk
yammar da zanyi haka zan dawo nayi girki da abubuwan dana fita banyi ba kuma Bashir babu ruwansa
ko yaya na kuskure ya ringa mita kenan.

Ganin Aliyun yana cin abinci sosai yasa na tambayi Bashir ko zan ringa barinsa a gurin Addah idan zanje
makaranta, da farko qi yayi seda na tasa shi da kuka sannan ya yarda washe gari kuwa da zan fita na
hada masa duk abinda nasan ze buqata na kaishi gidan.

Faran faran ta karbe shi musamman daman na hada dan ihisani na kaimata, na tafi makaranta ta hankali
kwance tunda nasan za’a kulamun dashi.

Ranar qarfe biyu na taso, tun daga Get din gidan nake jiyo kukan Aliyu gabana ya yanke ya fadi na qara
sauri ina shiga na tarar dasu a tsatstsaye akan Aliyu da yayi faca faca da ruwan kwata yana ta tsanyara
kuka abin tausayi.

Da sauri na qarasa na daga shi, a bakin Mama Binta Kishiyar Addah nake ji wai Amirah ce ta dauke shi
suka fita waje wasa shine wai ta ajiye shi ya tsallaka kwata ya fada ciki, ita Addah bama ta gidan tuni ta
fice, haka na dauke shi muka tafi gida raina duk a bace.

Idan ba wulaqanci ba taya za’a barta ta fita dashi har ya fada kwata. Seda ina masa wanka naga inda ya
kuje a jikinsa, haka na lallabashi yayi shiru bayan na bashi abinci da paracetamol na ruwa dan jikinsa yayi
duki kafin na goya shi na shiga aiki ina tunano irin tijarar da Bashir zeyi mun idan ya samu labari.

Ilai kuwa yana dawowa ya fara dudduba yaron kamar yasan me ya faru se ji nayi yana kwala mun kira,
haka muka kwana yana masifa ya kuma ce karna sake kai masa yaro ko ina nima din daman ba sake kai
shi zanyi ba.

Haka na ci gaba da karatu da raino cikina wanda yana wata takwas Bashir ya sake rasa aikinsa
sakamakon korar ma’aikata da Banki sukayi haka suddan kuma ta rutsa har dashi.
Sosai muka shiga tashin hankali musamman yanda korar tazo musu ba tareda tsammani ba gashi a
lokacin shekara ta qare lokacin biyan kudin Hayar mu yayi ga shirin haihuwa ta shi kansa Bashir din a
sannan ya koma Mesters kuma kowa yasan yanda Masters yake da cin kudi.

Haka nayi ta qoqarin kwantar masa da hankali da nuna masa In Allah ya yarda komai ze zo da sauqi mu ci
gaba da Addu’a kawai Allah ze kawo mafita.

Hidimar yanzu data farkon Auran mu ba daya ba, a wancan lokacin muna da ajiyayyun kayan abinci
wanda sune jigo sannan sauran buqatun mu ba wasu masu yawa bane yanzu kuwa shi yake siyan kayan
abinci ga qaruwar Yaro da shima akwai nasa buqatun na yau da kullum da dole suna buqatar kudi
chanjin rayuwar da muka samu se nan da nan ta nuna a jikina musamman saboda yanayin da nake ciki
ga tsohon ciki ga karatu da yazo mana gangara.

Haka muka ci gaba da malejin rayuwa kullum cikin saka ran samun budi daga qofofin ubangiji, da dan
abinda nake samu daga kasuwancin da nakeyi nake riqe damu dan sam Bashir beyi wani tanadi ba ba
kuma zan dorawa yan uwana nauyin da Allah ya sauke musu ba dan iya zumunchi sunyi mun ya kamata
ace yanzu kuma shima ya jajirce ya riqe gidan sa.

A sanda yana aikin Babu yanda banyi da Bashir ba akan ya ringa cire wani abu a Albashin sa duk wata
yana saving amma yaqi. Shi irin mutanen nan ne da a rayuwarsa idan ya samu kudi kawai a biya buqatar
da take a lokacin baya ajiyewa saboda buqatar kota kwana.

Nayi nacin har na gaji akan bayan aikin yaje ya samu Baffa suyi maganar kasuwar ya ringa gwada wata
sana’ar ko babu komai ya zama mutum yana da wata madafar bayan albashi saboda gudun bacin rana
akwai sanda har magana ya gaya mun wai ko fata nake masa ya rasa aiki ya ringa fushi yana jin haushi na
daga nan nace bazan sake masa magana akan yin wata sana’a ba.

Abinda na lura dashi wannan a halin mazan Bauchi da Gombe yake sunbada amanna da aikin Gomnati,
kadan daga ciki ne suka yarda da kasuwa, Nidai dana tashi gidan mu naga ba’a zaman banza zan ci gaba
da saida saidena dan bazan dogara da se abinda miji ya dakko ya bani ba.
A wannan yanayin na haifi Jafar, wannan karon a gida na na zauna daman kuma ban saka rai da samun
komai a gurin Bashir ba kodan halin da muke ciki ma da yaya ya biya kudin haya haka dai akayi suna na
kuma samu Alkahiri sosai daga yan uwana.

Bayan haihuwar Jafar abubuwan da suka faru ba masu dadi bane dan sosai muka shiga matsin rayuwa,
tun muna iya siyan kayan abincin wata a ajiye har seda takai mun koma awo a kullum na abinda za’a
dafa kuma duk nice qarfin riqon gidan a abinda nake samu zan bashi yayi a haka har seda muka cinye
jarin nawa duk ma abinda zan samu a haka yake qarewa tunda komai da shi mukeyi babu wani abu da
yake shigowa Bashir daidai da ci gaban karatunsa da tallafi na yake yi seda takai har mota ta na siyar na
bashi kudin akan ya kama wata sana’ar sedai wane tudu wani gangare kudin suka narke, Bala ya bawa
akan ze saro masa kaya daga Lagos wai yan Fashi suka tare su suka karbe sukayi masa dukan tsiya dan
seda yayi kusan wata a kwance yana jinya.

Haka muka ci gaba kullum ina hanyar zuwa gida karbar kudi seda ta kai ni da kaina na fara jin kunyar
hakan na dena zuwa, aiki kuwa kullum ina tafe, ina Teaching ga wasu training centers dana ke koyarwa
suma duk dan dai mu rufawa kan mu asiri seda ya zama wata rana idan mun samu abinda zamu ci da
rana sedai ni dashi mu haqura da na dare yara suci nakan kwana ina kuka wani lokacin idan na tuna
yanzu fa akwai wadanda tunda suka somi rayuwa cikin irin wannan qunci da matsin suka tashi ko?

Idan kaga yanda na koma sena baka tausayi yanda kasan nice Mijin ba Bashir ba dan shi yana zaune a
gida zan fita aiki na dawo kuma na dafa abinda ya samu muci wannan abun yana bala’in baqanta ran yan
uwana kuma yana daga dalilin daya sa duk suka zuba mun ido suga gudun ruwana ni kuwa ko a jikina,
Ina son Bashir bana jin duk abinda zanyi masa na fadi kuma ko banyi dan shi ba zanyi dan yayana dan
haka ban taba jin haushin kaina akan abinda nake yi ba.

Abin takaici daya lokacin qannen sa da sukayi aure Allah ya taimake su gaba daya sun samu gidan hutu
dan haka yanzu gidan su basu da wata matsala ko wacce na iya qoqarin ta se kuma ya zamana sun ware
Bashir domin ko gidana yanzu babu wadda take zuwa tunda bani da abinda zan basu.

Ita kanta Dadan yanzu wani gani gani takeyi mun idan munje gidan babu wannan sakin Fuskar irin nada
wanda duk cikin zugar Addah ne, a cewarta baqin ciki da kyashi ne ya hana nasa a bawa Bashir kudi a
gidan mu na gwammace mu zauna cikin talauchi ni da shi din saboda wai ina baqin cikin yana wahaltawa
yan uwansa sama dani, a raina nace ashe sun san da yana da shi din ma su ya ringa wahaltawa bani ba
dan kafin ya mun abu daya ya musu goma sannan wane baqin ciki zanyi da har zan zabi zama cikin
Daidai da Addah se in manta rabonda na sakata a ido ko su Aliyu na kai gidan ba’a minti Ashirin se a
dawo mun dasu tace fita zatayi, Amirah kanta yanzu ta rage zuwa idan nace mata me yasa se tace Addah
ce take hana ta rayuwa kenan se kana dashi mutane suke yi da kai a duniya.

Ana cikin haka wata rana Bashir ya shigo gida cikin tsananin murna yake nuna mun saqon gayyatar da
wani wani kamfani suka aiko masa daga Lagos, a cikin ayyukan da Alhaji Qarami ya ke ta fafutukar nema
masa se yanzu Allah yasa daya suka gayyace shi, a yanda yake gaya mun mutum biyu za’a dauka kuma su
biyar aka gayyata Jarabawar gwajin nan da kwana uku ze tafi.

Tun daga ranar na fara Azumi ina Yiwa Bashir Addu’ar nema sa’a. Gogan kuwa se shiri yake ya binciko
tsofaffin littattafan sa yana ta karatu. Ana gobe ze tafi da daddare har wurin daya yaha zaune yana fama
da takaddu na kalleshi nace

“Baban Ali da ka ajiye karatun nan haka ka huta Addu’a ya kamata muyi tayi dan a irij wannan abun fa
sa’a ake nema ba wai karatu ba”.

“Ma’u kenan, a irin karatun da nayi na tabbatar da duk tambayar da sukayi mun sena amsata sannan
duk wata kwarewar aiki da zasu nema ina da ita, kedai kawai ki fara shiri dan har na hango mu a Lagos”
ya fada yana ci gaba da bude littafinsa, se na ja numfashi na gyara kwanciyata nace

“Toh Allah ya tabbatar da Alkahiri”.

Washe gari ya hau mota se Lagos, kwanan sa biyu ya juyo bayan sunyi Jarabawar ya dawo da tabbacin
kamar ma ya samu aikin dan har yana ce mun “ko mutum daya zasu dauka nasan nine, bakiga yanda su
kansu masu Jarabawar suka ringa jinjina qoqari na ba”

Ni kuwa nace masa

“Kadai ce In sha Allahu, kuma muci gaba da Addu’a idan rabo ne za’a samu”.
Sati daya sakamakon ya fito amma babu sunan Bashir wasu mutum biyu daban ne dan daya ma babu shi
a wadanda sukayi Jarabawar tare, ina jin abokin da yayi yana gaya masa wai dan wani Minister ne aka
aiko da sunan sa dole aka cire mutum daya aka saka shi.

Haka Bashir ya ringa qunci da bacin rai akan rashin samuwar aikin, duk yanda naso na nuna masa komai
na rayuwa rabo ne idan Allah be tsaga da naka ba duk wuya haka zaka haqura bazaka samu ba amma
yaqi fahimta qarshe ma abin ya zamar mana rigima har yana gaya mun magana akan niyyar samar masa
aiki ne kawai ba’a yi ba aka wahalar dashi idan ba haka ba duk hanyar da muke da ita ace an rasa ta inda
za’a samar masa aiki me yasa su yan gidan mu mata da maza da sun gama makaranta suke samun aiki ga
Abubakar tuni ya samu chanjin aiki daga inda yake a Kano zuwa NNPC.

Ganin fa yana neman ya raina mun hankali yasa nima na horance masa, nayi masa tatas na gaya masa ai
ba haqqi na bane na samar masa aiki dan haka idan ze tashi ya nema tun wuri ya nema kuma na cire
hannuna daga duk abinda ya shafi sabgarsa, idan har ya aureni ne saboda ya samu kudi toh ya sawwaqe
mun kawai.

Wannan abun ya bala’in dagawa Bashir hankali se gashi har yana bina yana bani haquri akan sharrin
shaidan ne shi ba abinda yake nufi kenan ba, haka muka ci gaba da jalan ta rayuwa yau fari gobe baqi a
haka na kammala karatuna na fara hidimar qasa.

Ranar wata Talata da bazan manta da ita ba, muna zaune da yamma nida Jafar dan a lokacin Aliyu ya
fara zuwa Islamiyyar da take cikin layin mu. Shekarun sa uku a sannan tuni bakinsa ya bude sosai dan
haka nake hadashi da Amirah suna tafiya kuma sosai yake karatun dan in aka dawo ya ringa tilawa Bacci
kadai yake saka shi yayi shiru.

Lokacin zafine kuma babu wuta dan haka na shimfida mana tabarma a tsakar gidan muka zauna Jafar
nata wasa da Yar motarsa me Batiri ni kuma ina duba takaddun Test da nayiwa dalibai na a makaranta
Aka bugo Get, Hijab na na saka na leqa, Alhaji Buba ne me gidan da muke haya shida wani mutum da
wani saurayi me kama dashi daga gani dan sa ne.

Seda gabana ya fadi da ganinsu dan nasan zancen baze wuce na kudin haya ba amma ai da sauran kusan
wata biyu nan gaba haka muka gaisa nace musu Bashir din baya nan.
“Eh ba wurinsa muka zo ba munzo ne mu duba gidan daman mun riga mun gama magana dashi” Alhaji
Buban ya fada. Sena kalleshi da mamaki dan ban gane su duba gida ba,

“Wani abu aka ce ya samu gidan Alhaji” na fada ina kallonsa, se ya girgiza kai yace “Shi Bashir din Beyi
miki bayani ba? Hidima ce ta taso mun yaro na zeyi aure dan haka ina buqatar gidan nan ze zauna a ciki,
dalilin zuwan mu kenan yanzu ma dan ya duba ya gani ko akwai wani abu da za’a chanza kafin lokacin
bikin” Alhajin ya fada ba tareda damuwar komai ba.

“Amma kuma Alhaji muna da sauran lokaci kafin kudin hayar mu ya qare ko ba wannan ba ma ya kamata
ka bamu notice da wuri domin mu nemi inda zamu koma ko?”

“Ta yuwu kece baki da masani domin shi mun dade dayin magana dashi daga lokacin kuma zuwa yanzu
ya kamata ace ya nemi wani gurin daban, maganar ragowar kudi kuma ba matsala bane zan mayar muku
da abinda yayi saura a kudin hayar ku dan haka se ku fara shiri zuwa nan da sati daya nake da buqatar
gurin”.

Seda na hadiye abinda ya tokare mun maqoshi kafin nace “Shikenan, zamu tashi in Allah ya yarda amma
yanzu babu yanda za’ayi ki shigar mun daki se ku jira idan mun kwashe kayan mu daga baya ku duba” ina
fadar haka na mayar da qofar na rufe.

Bansan hawaye nake ba seda naji Jafar yana goge mun fuska se kawai na saki kuka ganin haka yasa
shima yaron ya fashe da kukan.

Kuka ne na zallar baqin ciki da takaicin nake yi, yanzu saboda Allah ace an bamu notice mu tashi daga
gida Bashir ba ze gaya mun ba kenan da se ranar da aka bashi ta cika zece na fita ko kuma se masu gidan
sun watsar mana da kayan mu tukunna.

Kwata kwata ni banga Lefin Ahaji Buba ba tunda gidansa ne yana da damar da ze buqace shi a duk sanda
yaso sannan ya gayawa Bashir din tuni nice beyi niyyar gaya mun ba to yanzu ina zamu dosa wane tanadi
yayi mana?
Da dare yana dawowa na tare shi da maganar

“Na sani kuma ina ta qoqarin ganin an samu wani gurin har yanzu dai babu, samun gidajen yayi wahala
sannan kuma sun qara kudi” Abinda ya gaya mun kenan yaja bakinsa yayi shiru.

Nayi masifar nayi bala’in amma ko kallo ban ishi Bashir ba qarshe na fashe da kuka haka na kwana ina
tunanin mafita a raina, idan nace zan jira naga abinda zeyi bana tunanin samun mafita daga gareshi dan
ko an samu gidan nasan bashi da kudin da ze biya dan chanjin da za’a bashi ba isa zeyi ba qarshe dai ni
din ni zanyi fafutukar yanda za’ayi.

Kafin safiya na yanke zuwa gurin Baffa na, shi kadai nake dashi da ze share mun hawaye masan kuma
baze kasa sama mun mafita ba dan ko kusa ban hasaso rabuwa da Bashir ba akan wannan dalilin, gari na
waye wa kuwa na shirya yara muka tafi gidan mu saboda haushi ko Bashir ma ban gayawa inda zani ba
shima be tambayeni ba.

Kuka na fashewa Baffa daya zuba mun ido yana kallon yanda na lalace na fita hayyacine kamar wata
matar qauye. Seda na gama lissafa masa matsalolina yana ji, murmushi yayi kafin yace

“Ko wanne aure da kalar qalubalensa Ma’u ayi ta haquri zan duba naga yanda za’ayi kafin lokacin da
suka dibar mukun, tashi ko shiga cikin gida ku karya kin debo yara ga Sheik Jafar nan da gani bacci be
ishe shi ba”.

Haka na wuni a gida ranar ina jin kamar kar na tafi duk yanda Na ringa shan zagi a gurin yan uwana kowa
na fadar ni na jawa kaina.

“Ba kalar mutanen arziqin da basu zo kanki ba Ma’u amma kika nace se wannan Bashir din da ba
mutunchi ne dashi ba. Ki ajiye maganar bashi da shi a gefe dan mu ba itace matsalar mu ba Aa girman
kansa da yake hana shi fita ya nema shi ya jefa ku a duk halin da kuke ciki shi se aikin office zeyi ko ke ce
yar wahala yana zaune ki fita ki nemo masa.

Se kije kiyi tayi, ina dai jiye miki ranar da dadi ze zo ya dakko miki yar tayin cin arziqi ta hanaki zaman
lafiya idan ma be yar dake a sannan ba tunda kin gama masa aiki” Anty Zubaida Yayar mu ta biyu a Mata
dana tarar a gidan ta gayamun.
Haka suka ringa gayamun maganganu kala kala wanda ko dar banji a raina akan Bashir ba, abinda na
yarda na kuma amincewa zuciyata Bashir yana so na ba kuma ze taba juya mun baya ba dan haka zan
taimakeshi da iya qarfina in har ni ina dashi.

Da zan tafi Goggo ta sake yi mun nasiha akan nayi haquri na zauna lafiya da mijina kar na yarda da
abinda yan uwana suke gayamun. Allah sarki ita kadai ce take qaunar Bashir a gidan mu se ko Baffa da
bazance ga bangaren da yake ba. Haka na koma gida ba tareda na cewa Bashir komai ba.

Kwana biyu a tsakani Baffa yace naje gida, a gaban Yayyena dukda suke gari da Iyayen mu ya mallaka
mun takardun gida wanda aka siya da sunana sannan ya bani kudi naira miliyan biyu a sannan yace naja
jari.

“Ku zama shaida nayiwa Asma’u kyautar wannan gidan sannan ga kudi nan taje suja jari ita da mijinta su
riqe kansu”.

Haka na tattaro na dawo gida cikin dimbin farin ciki bayan Yah Abubakar ya karbe kudin daga hannuna
yace naje nayi tunanin abinda zanyi dasu. Godiya sosai na ringa zuba wa na kuma qudurce a raina in sha
Allahu bazan sake komawa gida da niyyar neman wani taimako ba.

Zanyi tunanin abinda zanyi da kudin ba kuma zan gayawa Bashir batun su ba gida dai gashi nan muje mu
zauna a ciki.

Da na nuna masa takardun gidan ma kada ran kada han fuskarsa, washe gari mukaje muka ga gidan.

Sabon gida ne me kyau ginin zamani a cikin GRA Flat me dauke da Qaton palour da Dining se dakuna
bibbiyu a cikin corridor hagu da dama ko wanne da bandakinsa a ciki ga qaton kitchen da store tsakar
gidan kansa a qalla zeci mota uku zuwa hudu sannan ga dakin me gadi.

Ni kadai na ringa tsalle ina murnata Allah sarki Baffana Allah ya biyashi da Aljanna, tun a ranar muka fara
kwashe kaya, a kwana na uku muka tare bayan da yan uwana da Abokanan Arziqi suka rakani kowa se
yaba guri yakeyi yanda yayi kyau dan har kujeru da labulaye na sake.
Satin mu daya a unguwar na fahimci matsalar masu kantina da take damun gurin duk abinda kake nema
seka fita can babban titi ko kaje kasuwa.

Ni da nake neman abinyi se na yanke shawarar bude provision store kawai dana gayawa Yah Abubakar
shima yayi na’am da maganar nan da nan yasa aka fashe dakin me gadi aka sake ciyo filin cikin gidan aka
yi babban shago a gurin.

Lokacin da nakeyiwa Bashir zancen muna zaune se yake cemun “ai kuwa hakan yayi dan kinga ko ni ma
se na ringa zama a gurin kafin na samu wani abinyin”.

A lokacin ba qaramin dadi naji ba, dan daman tunanina kenan amma ina tsoron na gaya masa ya fassara
maganar da wata manufa ko yace na rainashi shi yasa na yanke kawai zan sa a nemo min yaro da ze
ringa zama tunda ga qofa anyi ta cikin gida na ringa leqawa naga yanda abubuwan suke tafiya.

Cikin dan lokaci aka hada shago sosai aka shaqe shi da kayan masarufi harda su ruwa da Lemo duk muka
zuba cikin ikon Allah kuma ya samu karbuwa dan sosai ake ciniki kafin cikar wata biyu seda ya zamana
har buhun huna muke siyarwa na kayan abinci da muka ga ana yawan tambaya.

Bashir ne yake zama se wani yaro Shafi’u dayazo yace ze ringa taya shi. A dan qasan mu yake maraya ne
ake ruqonsa a gidan qanin Babansa sedai beyi sa’ar mariqiya ba ai kuwa na riqe shi sosai gashi da
amana.

Shekarar mu daya a gidan na sake haihuwa yar mace da se naga kamar Bashir yafi yin murna akan ta
sama da sauran haihuwar da nayi har na ringa tsokanar sa wai saboda an samu Dada ne yasa yake
murna amma yace Aa shi ba sunanta ze saka ba.

A raina har na dauka ko ni zeyiwa kara ya saka Goggona se ji nayi ya mata huduba wai da Aisha Farida.

“Ni na zata Dada ko Goggo zaka saka ai” na fada bayan daya gaya mun sunan, se ya kalleni yace
“Bani da ra’ayin yiwa wani takwara, ko Aliyu da kuke zaton sunan marigayi Aliyu ne kawai ra’ayin
kainane”.

Haka naci gaba da rainon Faridata dan tuni an saka Aliyu da Jafar Makarantar Boko da Islamiyya.

Nisan da mukayi dasu Addah be sa Amirah ta dena zuwa ba dan yawanci duk Juma’a se sunzo
musamman tunda na haifi Farida wani lokacin ta kwana daya ko biyu wani sa’in ma ni zan kira Addah
nace ta turo mun ita tayi mana kwana biyu dan yanzu ta fara zama yammata ta rage fitsara da rashin
kunya abu daya yake hadani da ita qazanta da rashin son aiki dan in tazo se nayi da gaske take kama
mun ayyuka ga bata guri haka zasu ci abinci su bata ko ina idan bani nace a kwashe ba sedai su zauna a
cikin dattin.

Daman batayi mun raino qarqari ta in zanyi wani abun na ajiye mata Faridar ta kula da ita amma fa ko
zata kwana tana kuka Amirah bazata goya mun ita ba bare naci arziqin tayi mun wankin yara ko yi musu
wanka ba tayi to kanta ma se nayi dagaske take wankan bare tayiwa wani.

Watannin Farida Shida Allah ya karbi rayuwar Baffan mu sanadiyyar ciwon ciki da yayi na kwana daya har
seda aka kaishi Asibiti inda acan ya rasu. Fadar irin tashin hankalin da muka shiga ma bata lokaci ne,
munyi kukan rashin Baffa babban bango ya fadi se dai mu bishi da fatan Alkahiransa da halinsa na gari su
bishi. Rasuwar Baffa da kwana Arba’in aka yi mana rabon gado kamar yanda ya bar wasiyya bayan an
gama tattara komai kowa aka bashi kason sa.

Wannan karon ma ba’a bani komai nawa a hannuna ba dan ana gama rabon Yah Muslim ya danqawa
Alhaji qarami nawa dana Amna. Bansan dalilin da yasa sukeyi mun haka ba, amma koma menene banyi
magana tunda nasan baza su cutar dani ba.

Seda Alhaji qarami ya gama tsara duk yanda yake ganin yayi sannan ya sameni har gida wata rana yake
gaya mun, mota biyu ya kawo mun cikin rabona yace gashi nan se na dauki daya na bawa Mijina daya.
Na samu gonaki manya har biyu yace za’a ci gaba da noma su kamar yanda akeyi dabbobi na suma ze
zuba mun su a gidan gonarsa.

Akwai fili manya guda biyu dana samu se ya bani shawarar tunda mun samu wani gida me flat takwas a
Abuja aka raba mana ni biyu, Junaidiyya biyu se nasa guda hudu idan na yarda ayiwa kowanne kudi muyi
musanye ya karbi filayen ya bani gida itama idan tana so ayi haka mu ringa karbar kudin hayar duk
shekara dan a cikin gari suke nan take na amince na kuma bar masa duk sauran abubuwa a hannunsa
yaci gaba da kular mana dasu kafin ya tafi ya turamun zunzurutun miliyoyin kudade na a account da seda
jikina yayi sanyi da ganinsu.

Rayuwa kenan, shi wanda ya tara su yanzu tasa ta qare muma da muka samu wata rana haka zamu tafi
mu barsu, shawara muka yanke akan gidan mu kar a tabashi, abar shi a yanda yake tunda kowa sun san
kason su kowa mahaifiyarsu tana ciki sannan muka samu Qaton fili muka siya akayi Babbar Makarantar
Islamiyya da masallaci Muka kuma bude foundation ta tallafawa Marayu da mabuqata me sunan
ABDULLAHI TUKUR KUMO FOUNDATION ladan Allah ya kaiwa Baffan mu.

Duniya sabuwa tuni al’amura suka daidai tar mana. Na bawa Bashir mota daya sannan na hada masa da
kudade masu nauyi, Alkahiri babu wanda na manta dashi dan hatta su Fainusa da suka yanke alaqa dani
yanzu sun dawo kuma ban qisu ba na karbe su da hannu biyu ba wai dan bani da wayo ko ban san me
nake yi ba, Aa shi wanda kafi a rayuwa har abada ka fishi arziqi kuma kashi ne kowa yazo ya dangwala.

Har sannan Bashir na zama a shago amma ba na qofar gidan mu ba dan a cikin kudi na na bude babban
super market acan kan titi shine manager muka dauki ma’aikata tsohon kuma na barshi a hannun Shafi’u
da sabon yaron daya samo yake tayashi saboda na mayar dashi makaranta se da yamma yake zama a
Gurin.

Bayan fitar Su Goggo takaba kawai ta taso da wata maganar wai zata koma Yola ta daura aure da Baffa
Sama’ila. Qiri qiri muka nuna qin Amincewar mu gaba daya seda Alhaji Qarami ya tsawatar mana sosai
akan me yasa mu zamu haramta abinda Allah ya halasta, babu wanda ya isa ya hana mahaifiyarsa qara
aure a cikin mu gaba daya ko da kuwa cewa sukayi zasu kawo mazan cikin gidan mu tunda dai suka da
kason su.

Haka muna ji muna gani aka daura musu aure da Baffa Sama’ilan ta shirya komawa Yola nan na tada
sabuwar rigimar sedai ta bar Amna bazata tafi da ita ba a wannan karon dai na samu goyon baya se
kuma rigima ta koma tsakanin manyan cikin mu mu Ashirin da bakwai a sannan maza da mata masu
aure kowa yace shi ze riqeta daga qarshe dai nayi nasara riqon Amna ya dawo hannuna wanda Bashir da
kansa ya goya mun baya aka bani ita.
Riqon Amna da na karba wane tudu wane gangare se ganin Amirah nayi da faggon kaya Addah ta kawo
ta wai Addahn zasuyi tafiya zata je Niger, daga tafiyar sati biyu taji dadi da su Addan suka dawo se cewa
tayi bazata tafi ba, Bashir zeyi fada nace ya barta ta zauna zan riqe dan har ga Allah ina son yarinyar
kuma ina so naga tarbiyyarta ta inganta dan duk in tazo mun sena ga abinda beyi mun ba a cikin
halayyarta wannan shine mafarin dawowar Amirah hannuna.

Sosai Allah ya sanya Albarka a cikin kasuwancin mu, kudin da na bawa Bashir a cikin super market din
shima ya saka ake juyawa, wata dabara da nayi masa muka zauna akayi rubutu kudinsa da yake ciki nace
masa ya cigaba da juya su duk ribar daya samu ya barta a ciki karya cire sannan za’a ringa biyansa a
matsayinsa na manager kamar sauran ma’aikata, da Allah ya sakawa abin Albarka se gashi muna neman
yin kankan kan dashi a mallakin shares na super market din.

Salin Alin muke zaune rana daya Bala da rabon dana ji duriyar sa har na manta yazo mana ziyara. Faran
faran muka gaisa na basu guri shida Bashir na koma ciki, bansan me suka tattauna ba bayan tafiyarsa na
fara ganin chanjin fuska a gurin Bashir.

Kwanaki biyu a tsakani ya dena fita super market, a rana ta uku ne nayi masa magana se ce mun yayi

“Akwai sauran Ma’aikata nasan zasu kula da komai”

“Amma baban Ali kasan dai yanda mutane suke yanzu idan babu idon ka zasu iyayin yanda suka ga
dama, ka manta rungon lissafin da suka ringa yi mana kwanaki ko” daga wannan maganar da banga abin
zafi a cikinta ba se Bashir ya hau fada yana cewa

“Ni na gaji naga alama kin mayar dani wani yaronki kina zaune ina miki neman kudi ko? wato kina so na
saka ido a Shago dan kar a cuceki amma kika kasa aminta ki damqamin gadonki a hannuna na kula miki
dashi. Daga yau na dena zuwa, kinemo wanda ze ci gaba da kular miki da gurin” haka yai ta fadar
maganganun sa ni dai na tsaya kawai ina Jin ikon Allah.

Kusan sati baya fitar dan haka na nemi Nasir qani na ya maye gurbinsa a gurin sannan ga Naziru qaninsa
da daman yana zuwa na kwashe shi shida duk tsiyatakun da yake ji dasu na watsar dan ni yanzu
hidimomin gabana sun ishe ni.
Beci gaba da zuwan ba amma dai ya dawo yana neman shiri dani, nima ban nuna masa komai ba muka ci
gaba da sabgogi cikin hukuncin Allah se gashi ya sake samun aiki a Ma’aikatar haraji ta qasa reshen
Gombe.

Aikin da Bashir ya sake samu ya tabbatar mun da cewa idan har yana dashi babu abinda baze yi ba,
rayuwar mu se sambarka idan ka cire sabanin irin na yau da kullum da a kowanne gidan aure anan
samun irinsa bani da wata matsala da Bashir.

Albashin sa nada tsoka dan haka a wannan karon na bashi shawara daya siyi gidan da muke ciki ya zama
nasa, kai tsaye ya amince yace ze ringa biyana duk wata na yarda, da na gayawa Yah Abubakar a take ya
karbe takaddun yace kuma A ringa tura kudin ta account dinsa har zuwa sanda ze biya sannan a chanza
suna ya koma nasa abun nan kuwa ya qona ran Bashir ya ringa mita yana masifa nidai bance masa komai
ba cikin qanwanin lokaci kuwa ya biya kudin tsaf aka chanza takaddu aka bashi ni kuma Yayan ya siyar
mun da shagunansa guda biyu a wata babar plaza dan ina so na fara siyar da kayan yara Anty Suhaima
zata ringa turomun su daga UK.

Bayan Farida na haifi na sakw haihuwar Da Namiji, kai da fata a wannan karon na kafe se Bashir ya
sakamun sunan Baffana, dan gaske kuwa ya murzawa idon sa toka yace sedai na siyi ragon suna, dukda
naji zafin abun amma haka na siyi manya manyan raguna guda biyu harda Bijimin Sa na qauri aka
yankawa Abdallah na.

TUSHEN MATSALATA

Shigar Amirah Ajin Babbar Sakandire yazo mata da wani sabon tashen fitsara da rashin mutunchi.
Amirah Kyakykyawar Yarinya ce Fara tas me gabaren girma a shekaru sha hudu qugunta ya bude qirjinta
ya cika tazama budurwa sosai da bazaka yarda ba idan aka fada maka shekarunta.

Abinda ya fara hadani da ita shegen rawar kai da kule kulen samarinta dan har ta kai an fara zuwa
sallama da ita. Zuwan saurayin na farko da kaina na fita na kora masa jawabin karya sake zuwa, hakan da
akayi kuwa saboda rashin kunya har gurin Addah takai qarata wai ka korar mata saurayi. A sannan da
Addahn tayi magana na ce mata
“Tunda kika bani ita ta zama yata dan haka zan lura da ita ne a matsayin uwarta idan kuma ba haka ba
sedai ta dawo nan se tayi duk yanda take so amma muddin tana gabana Ba yanzu Amirah zata fara kula
samari ba, se ta gama makaranta idan bata da burin ci gaba a sannan na yarda zamuyi mata aure”.

Jin da tayi nace ta koma ya sa ta haqura har da yiwa Amiran fadan da be kai zuci ba muka koma gida
ashe bata deba ba, idan suka tafi Islamiyya seta tura sauran yara ta tafi warkajamin ta se lokacin tashi
yayi su dawo wata rana Allah ya dawo da Bashir da wuri gida ya kamata a can farkon layi a motar saurayi
suna zance har yana bata Ice cream a baki, ina Kitchen suka shigo tun daga get yana tamola da ita ashe
an dade ana kai masa gulmar a unguwa yau Allah yasa ya gani har da daddare tana satar hanya ta fita
hira ban sani ba.

A wannan karon ma dagewa yayi yace seta koma gida taje can kome zatayi a gaban Addahn amma zata
lalace a nan ba ace a gidan sa ne, seda nayi ta bashi baki sannan itama naja mata kunne dakyau kafin ta
shiga hankalinta.

Gashinan na yau dana gobe

WATA KISHIYAR

(ALKAHIRI CE KO SHARRI)

Na Maryamah Farouk

(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)

Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 37
Takun kumi Bashir ya sakawa Amirah na daga gida se makaranta hakan ya taqaita duk wata firirita data
fara dan yanzu ba inda take zuwa ba kuma wanda yake zuwa gurinta ban dai sani ba ko idan ta tafi
gidansu tana yin hirar a can. wata rana nayi baquwa, maqociyata ce Maman Ahmad ta shigo muna zaune
su Amirah suka shigo daga makaranta.

Uniform dinsu irin me guntun skirt din nan me da riga me dogon hannu se doguwar safa da dan qaramin
hijabi dan haka sosai kayan suka bayyana qirar jikinta musamman ga wata tafiya data samu a kwanakin
nan takeyi tana gantsaro qirji.

“Maman Aliyu wai qanwar kice wannan ma” Ta tambaye ni bayan da suka wuce ciki, se na kalleta ina
murmushi nace

“Eh, qanwata ce me kika gani?”

“Qanwarki ciki daya ko kuma ta dangi?” Ta sake tambayata ba tareda ta bani amsa ba,

“”Gaskiya ba qanwata bace,qanwar Baban Ali ce diyar yayar mahaifiyarsa”

“Lallai Maman Aliyu se a barki, yanzu duk yayan danginsu qanana ki rasa wa zaki dakko se wannan
qatuwar budurwar zaki ajiye a gida wai cousin din mijinki kina kallon Yarinya wanda be sani ba in ya
kalleku ma se yace kishiyoyine wallahi nidai bazan iya ba, kema kuma tun dare ne miki ba kisan abinyi
tam” Maman Ahmad din ta fada.

Se nayi murmushi nace “Girman jiki ne fa kawai Maman Ahmad ko sha shida bata cika ba ina ga idan ma
Bashir kike tunani nasan babu abinda zeyi da ita ko aure zeyi baze nemi qaramar yarinya ba balle
wannan da sam ba tsarar sa bace”

“Ai wallahi ta wuce kice mata yarinya dan duk abinda mace take taqama dashi gashi nan a jikinta dadin
da dawa ga quruciya meze dami namiji da qananun shekarunta bayan kina kallo yanzu yayin yan sha
shidan sukeyi, shiyasa randa kika aiko su da Amna ko palour ban bari sun shiga ba dan Abban Huzaifa
yana nan shi daman ido a farar fata, tun wuri kisan nayi wallahi kafin kiji kidan Janaral a sama”.
A lokacin jin Maman Ahmad kawai nayi bawai na dauki abinda take fada da muhimmanci bane dan na
yarda a zuciyata Bashir baze taba kallon Amirah a matsayin mace ba balle har yayi sha’awar auranta.

Yarinyar da banda kyara da tsangwama babu komai tsakaninsa da ita har haushi nakeji idan yayi mata
wani abun, barar magi na bawa Amirah idan har na kuskura Bashir ya sani to ranar baze ci abincin ba
saboda yanda yayi mata tambarin qazanta balle har takai ace ze aureta na tabbatar wannan ko a mafarki
ba abu ne me yuwuwa ba.

Shigarta SS3 yasa ta qaro wani sabon tsagwaron rashin kunya da fitsara. Ganin ta takeyi kai daya dani
dan yanzu idan na gaya mata magana ma se ta ga dama zata aikata, fita kuwa ko Bashir ze kasheta idan
ta dawo setaje daman tuni ta sallama Islamiyya ta dena zuwa qarin daurin gindin data samu a gurin
Addah harma da Dada kanta dan sunce data kammala makaranta aure zasuyi mata dan haka dole a
barta ta fara tsayuwa da samari ta samu wanda zasu daidai ta a ciki.

Nima banqi ta tasu ba tunda har aure za’ayi mata ya kamata a barta ta farayin zancen dan haka koda
Bashir yace sedai tabar masa gida ko kuma in zatayi zancen ta ta tafi gidan su se nace masa baza’ayi haka
ba.

Dakyar na lallashe shi ya yarda sedai ya kafa mata sharadan kar ta kuskura ta mayar masa da gida centre
tara samari duk randa ya ga sama da mutum biyu suna zuwa gurinta se ya mugun saba mata daga nan ta
fitar da wanda take so a ciki ta sallami daya amma da yake me kunnen qashi ce kullum da wanda zata
gayyato yazo gidan.

A cikin samarinta akwai wani Yaro Sadam, irin fitinannun yaran masu kudin nan ne. Tana bala’in sonsa
musamman yanda yake mata barin kudi duk sanda zezo haka ze ciko ledoji niqi niqi da kayayyaki ya
kawo mata sannan haka zebi su Aliyu da kudi idan sukaje suka gaida shi wani sa’in harni yake shiga ya
gaisar,

yana da kirki amma idonsa a bude yake na kuma tabbatar ita kanta Amiran ba dagaske yake son ta ba
duk yanda kuma naso na nisar da ita qarshe dukda ba kai tsaye ta fada ba se jin ta nayi tana cewa duk
baqin cikin mutane seta auri Sadam da kowa ze ringa wani ce mata ba auranta zeyi ba, daga ranar na
cire bakina a sabgar samarinta, Allah Allah nake ma ta qarasa makarantar ayi mata auran kowa ya huta.
Bazan taba manta wata rana da mukaje gidan Dada ba, akwai wani Lace me kyau da tsada da nayi mana
nida Amiran da Amna harda Farida da sallah shi muka saka ranar mukaje.

Muna zaune kamar an matsi bakin Addah se cewa tayi “Baku ganku ba wallahi Abin sha’awa kamar wasu
Uwar gida da Amarya”.

Ban kawo komai ba a raina nayi murmushi muka yi hirar mu muka gama, har mun tashi zamu tafi Addah
take cemun

“Ni kuwa wata shawara nake nema Asma’u, kinga nida Nafi mu kenan shaqiqai da iyayen mu suka haifa,
gara ita ma Allah ya bata yaya da yawa ni kuwa kin gansu nan biyu kamar kunnuwa.

Shine nayi wani tunani ina so ko bayan ranmu zumunchin Yarana da nata ya dore kinga ta hanyar
Auratayya ne kadai hakan ze tabbata. Toh yanzu ina so na gabatatar mata da maganar cikin yaranta
maza daya ya nemi Amirah ko ya kika gani?”

“Kai Amma kuwa kinyi tunani me kyau Addah idan abin ya yiwu kuma zakuji dadi wallahi Allah ya
tabbatar da Alkahiri yasa zamu ga lokaci” na fada sak da zuciya daya dan dagaske naga kyan tunanin ta,
Auran zumunchi yana da dadi idan yayi kyau.

A lokacin tunanina gaba daya kan Amiru ya tafi dan shine me shirin aure a sannan amma kuma sam basa
shan inuwa daya da Amirah saboda rawar kanta.

“Idan Allah ya qulla abun haka zasu shirya su zauna tare” na raya a raina.

A haka muka ci gaba da lallabawa har Amirah ta fara rubuta Jarabawar fita daga sakandire lokacin ina da
tsohon cikin yan biyuna.

Daman iya WAEC tayi, dan haka suna gamawa ta tattara kayan ta ta koma gidan Addah haka kawai ba
tareda wani abu ba, nima ban takurata ba, nadai tambayeta ko wani abu aka yi mata tace Aa daga nan
na barta ta tafi.
Ranar da na haifi yan biyu ranar Bashir ya samu aiki a wani Babban Oil company a Lagos. A tsakanin
watanni uku Alhaji Qarami ya tura masa da Advert dinsu yace ya cike, yana rashin mutunchi da fadar
maganganun sa dai ya cike din cikin ikon Allah kuma da yake se a sannan rabon sa ya tsaga se gashi suka
gayyace shi Interview shine yanzu kwasam muna Asibitin sun aika masa da Email cewa sun dauke shi
aiki.

Fadar irin farin ciki da murnar da muka shiga ma bata baki ce, Allah kenan me kyauta da qari a kuma
sanda yaso. Lokaci daya ya bashi kyautar yara har biyu sannan ya qara masa da tukuicin Aiki me gwabi
irin wanda ya dade yana fatan samu se gashi ya same shi a sanda be taba zato ba.

“Albarkar yan biyu kenan, yanzu Legas din zaka koma kenan? Daman ina so naje legas nima naga yanda
take yanzu tunda dana zeje kaga na samu gidan zuwa” Addah ta fada cikin murna kamar ta taka rawa
musamman jin yanda su Amiru suke ta zuzuta irin aikin da Bashir din ya samu da kuma Albashin da ze
ringa kwasa a wata.

A ranar aka sallamo ni na koma gida, da Daddare Bashir ya shigo dakina, fuskarsa dauke da murmushin
da na dade banga irinsa ba. Seda ya dakko yan biyu daga cikin gadonsu kafin ya dawo kusa dani ya zauna
yana kallona yace

“Wane suna kike so a saka musu”

Se da na kama baki ina yar dariya nace

“Tofa, yaushe aka fara haka? To bana dai bani da kudin siyan raguna har hudu dan haka ka saka musu
duk abinda kaga yayi maka”.

“Kina so ki ringa dawo da abinda ya rigada ya wuce, dagaske nakeyi, ki zabar musu sunan da kike so kin
cancanci fiye da haka ai” ya fada yana kallona.

“Toh Daya dai a saka masa sunan Baba dayan kuma na bar maka zabi”
Da daddaya yayi musu huduba, seda ya gama ya miqo mun Hassan yace “Ga Ahmad” sannan ya bani
Hussain shima yace “Muhammad Tukur”.

Sosai naji dadin karar da Bashir yayi mun ta saka sunan Alhaji Qarami dan kuwa ya cancanci sama da
haka a gurin mu.

Wannan haihuwar dai nayita da qafar dama dan sosai Bashir yayi bajinta ya gwangwaje ni da zadaddun
sururu na fitar suna haka yaran ma akwatunan su tsaf aka ciko da kaya, ga kuma kayan takwara da Alhaji
Qarami ya jido mana abin dai se sam barka haka shagalin sunan da mukayi kansa bazakace haihuwa ta
biyar bace tamkar sunan Aliyu da akayi shi lokacin ina cikin gata na a gidan wannan kuwa ya samu qarin
tagomashin cigaban zamani.

Tuni Bashir ya kama aiki a Lagos bayan da ya dauki leave a tsohon gurin aikin sa a matsayin ze tafi qaro
karatu saboda baka barin aiki kai tsaye har sekaga kamun ludayin wanda ka samu tukunna. Shi kadai ya
tafi Lagos duk qarshen wata yake zuwa Gombe.

A cikin shekara daya da fara aikin Bashir rayuwa ta qara sauya mana sauyi irin na Alkahiri, ba qananun
kudi yake karba a Albashin sa ba sannan ga Kasuwancin mu da Allah ya sakawa abin Albarka tuni mun
sake bude branches guda biyu bayan na farkon a wasu unguwannin ga kuma harkar siyar da baqin mai
daya kafa bayan daya fara sabon aikinsa ya zamana yana supplying daga kamfanin zuwa gombe ya
rabawa yan sari abin dai se godiyar Allah kawai.

A shekarar ya biyawa Dada da Alhajin su Aikin Hajji suka tafi tare da shi kansa bayan sun dawo ya sake
biyawa Addah da Anty Amina Babbar yayarsu harda Amiru sukaje Unarar Mauludi.

Bayan dawowar su Addah da sati daya sega Amirah ta dawo mun harda jakar kayanta bayan kusan
shekara guda da barinta gidan, yanda sanda zata tafi ban hanata ba haka yanzu ma data dawo ban
tambayeta dalili ba ban kuma chanza mata ba muka ci gaba da zaman mu kamar baya.

Abun daya fara hadamu bayan ta dawo wasu halayen data tsiro dasu, Duk lokacin da Bashir zezo gari
yanda zanyi shiri nayi kitso dasu lalle haka Amirah ma zatayi tamkar matar gidan taci kwalliya itama
ranar da ze dawo ta kame a palour.
Sannan a da idan har Bashir yana gida indai bashi ya zaunar dasu ba da daddare daga mun gama cin
abinci zasu shige dakinsu tunda ko wanne daki na saka musu Tv idan ma kallo ne zasuyi acan wannan
karon kuwa tun dawowar ta idan muna zaune itama zata nemi guri ta zauna ne babu ruwanta.

A ranar farko data fara zaman dakansa ya mata magana ta tashi hakan be hana washe gari ta sake zama
ba har tana tsoka baki a cikin hirar da mukeyi nan ma yayi mata kaca kaca kafin aka samu sa’ida har ya
tafi basu sake haduwa guri daya ba.

Wani rainin hankali data samu ma se ina waya da Bashir din zata zauna ta tasa ni a gaba tana kallo, idan
nayi mata magana se tace mun wai

“Wallahi Anty soyayyar ku da Yaya tana bala’in burgeni shi yasa nake zama nayi kwas, Kai Allah nima ya
bani miji irin yaya mu kwashi romon soyayya”.

Wani lokacin kuka tace “Dan Allah Anty ki ringa koyamun yanda zan mallake zuciyar mijin da zan aura
nima na zama kamar ke a gurinsa ya ringa riritani irin yanda Yaya yake miki” idan ta fadi haka se nayi
dariya nace

“Nidin har wani riritani Baban Ali yakeyi kenan, miji kuma ai banga kin dakko hanyar samun sa bama dan
ni rabon da naga kinyi waya da wani a gidan nan ko anzo gurinki har na manta man Amirah anya lafiya?”

“Lafiya lau Anty, kedai ki taya ni da Addu’a kowa se yayi mammakin mijin da zan aura”.

Hutun da Bashir ya sake dawowa ta bullo da sabon salo, wannan karon se dare ya tsala irin 10-12 nan
kawai zata sako qananun kaya wando skin tight ko Pencil skirt daze fito mata da surarta ta kai babu
dankwali ta saki dogon gashin ta ta bazo turare ta fito tana miqe miqen iskanci irin ala dole daga bacci ta
tashi har kuma ta kalle mu tace wani

“Au har yanzu Anty bakuyi bacci ba? Ruwa na tashi zan sha mun manta bamu shiga dashi dakin ba”
sannan ta tafi tana rangwada ta bata lokaci a Kitchen kafin ta koma daki.
Na daya na biyu ranar a daren na same ta naci mata mutunchi musamman abinda ya qara tunzurani
ganin yanda Bashir ya ringa binta da kallo har yana cemun wai me yasa na dena saka irin kayan nan, ban
kuwa yi qasa a guiwa ba na bi bayanta nayi mata tatas tareda kashedin kar na qara ganinta a gaban
Bashir ba tareda hijabi ba.

Washe gari da safe yace su shirya ya kaisu gidan Dada gaba daya harda Yan Biyu zasu tafi, muna tsaye a
palour suna jiran Amirah se gata ta fito da wata fitted gown ta Atamfa ta kamata tsam kamar zata yage
idan tayi numfashi me kyau se dan mayafi data rataya a kafada.

Ina kallon yanda Bashir yakalleta kafin ta qaraso inda muke nace ta juya ta canzo kaya ina jiran naji ya
dora nasa fadan se cewa yayi ta wuce su tafi baya son bata lokaci ya tasa su gaba yana baya suka barni
tsaye kamar bishiyar da aka dasa.

Haka na kusan wuni ina saka da warwara ni kadai akan sababbin halayen na Amirah da na kasa fassara
ma’anarsu, shin da wata manufa takeyinsu ko kuwa haka kawai? Idan ma yin kanta ne kawai shi kuma
Bashir fa da baya ganin laifin abinda take aikatawar fa?

Gaskiya bazan zuba ido ba saboda zuciya bata da qashi, kodan gudun afmuwar barna dole na taka mata
birki tunda Bashir ba muharramin ta bane shedan yana iya qawata masa ita ya kuma tunzura zuciyarsa
ga aikata abinda be kamata dukda na yarda da Bashir ba kuma na masa tunanin wani abu makamancin
haka amma fa zuciya bata da qashi.

Allah sarki ni a sannan sam zancen ace wata aba me kama da soyayya tsakanin Bashir da Amirah be taba
zuwar mun ba kawai ina daukar abin da takeyi a matsayin tashen fitsarar dake kanta daga irin kalamanta
a yanzu kuka nake ganin kamar aure take so dukda ina mamakin dalilin da kwata kwata yanzu samarinta
babu me zuwa ko waya ta dena yi dasu se na mayar da hankali na cikin yayyena marasa aure na fara
qoqarin samo mata wanda zasu daidaita dashi.

Abinda ya raba mana gari da Amirah kwata kwata na sallama ta ta barmun gida gaba daya a wani zuwa
da Bashir yayi mana, a lokacin dama na fara gajiya da hakayenta saboda kullum sabon salon da zata
bullo mun dashi. Gaba daya ta gama raina ni dana rasa menene musabbabin rainin dan har takai Amirah
ta shiga dakina ta bude cikin kayana ta dauki abinda take so ba tareda ta tambayeni ba sedai kawai na ga
abu a jikinta duk fada da masifar da zanyi mata kuwa baze hana gobe ta sakw yi ba dukda haka naci gaba
da haquri nake zaune da ita saboda a yanzu idan nayiwa Bashir qorafi baya cewa komai sabanin da da
qiris yake jira tayi abu ya samu nayi.

Abinda ya faru da yasa na tilasta mata barin gidan kuwa shine zuwan da Bashir yayi qarshen wata.
Fasalin ginin gidan mu corridor ne guda biyu hagu da dama ko wanne da dakuna biyu daya na kallon
daya a ciki dan haka na dauki daya nawa dana Bashir dayan kuma ya zama dakin su Amirah, Amna da
Farida daya kuma na yara maza.

Bayan da Bashir ya gama weekend dinsa ranar litinin ya koma Lagos a ranar saboda tsabar gajiyar dana
kwasa a hannunsa Se Amirah ce ta hadawa yara abin tafiya makaranta suka bi Amiru da ze kai Bashir
Airport ya sauke su a makarantar.

Da misalin sha biyu na rana na fito daga dakin Bashir bayan na gama ramuwar bacci gidan shiru se
Amirah kadai a zaune a palour tana sana’arta ta kallon Indian series yan biyu suna gidan Dada an kaisu
yaye kusan sati biyu kenan ba’a dawo dasu ba. Dagowa tayi da murmushi tana kallona tace

“Sannu Anty se yanzu kika tashi”

“Yawwa Amirah sannu da gida, me kuka rage yunwa nakeji wallahi” na fada ina zama a gefenta.

“Na dai feraye miki dankali bari na soya” ta fada tana miqewa, mintina kadan ta soyo dankalin harda
kwai ta kawo mun nasa ta hado mun shayi na zauna na fara ci”.

“Ai dole kisha Baccin Gajiya Anty irin wannan gurza da kika sha a hannun Yaya jiya kai, gaskiya Anty dole
ki shirya ni idan zanyi aure yanda nima zan rikita shi ya ringa sambatu irin na Yaya...”

Kwarewar da nayi da shayin dana kurba tsabar kidimar jin magangan ta suka sa tayi shiru ta miqo mun
ruwa tana yi mun sannu. Kallonta kawai na ringayi zuciyata tana luguden duka a raina ina ta maimaita
“Hasbunallahu wani’imal wakeel”.

“Dagaske Amirah taji mu’amalar mu da Bashir? Tun yaushe hakan ya fara sannan ita kadaice ko har
sauran yaran ma duk suna ji?” Tambayoyin da nayiwa kaina kenan dana rasa me bani amsar su, tabbas
wannan dalilin shine silar rainin da naga Amirah tayi mun shi a yanzu har ma da Bashir din kansa ashe a
banza take kallon mu amma ta ina ko ta yaya taji? Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un.

Ganin da tayi na dena tarin ba tareda damuwa ko tunanin komai ba taci gaba da magana tana cewa

“Wallahi Anty kum....”

“Rufe mun baki Amirah” na fada cikin tsananin bacin ran da fuskata da muryata suka nuna kafin na ci
gaba da cewa

“Ashe baki da hankali ban sani ba? Saboda tsabar rashin mutunchi da rashin kunya har ki iya tsayawa
kina maimaita wadannan maganganun a gaba na sa’arki na zama, wallahi se na yi mugun saba miki” na
qarasa ina huci bayan dana ture kayan abincin gaba na dan gaba daya komai ya fice daga raina ita kuma
sum sum ta tashi daga gurin ta shige dakinsu.

Wannan abun kunya har ina, tabbas Bashir irin mazan da basa iya rufe bakinsu ne a lokacin da yake
mu’amalar aure amma ban dauka ihun nasa har yana karade gida da Amirah zata iya jiyo wa ba
musamman idan ka duba tazarar da ke tsakanin dakin sa da inda nasu dakin yake dama dai a dakina ne
ana jiyo duk motsin da akeyi a dakin Bashir.

Haka na wuni cikin rashin sukunin zuciya dan Amirah tuni ta fice ta tafi gidan Addah ina nan sukuku har
yara suka taso daga makaranta su kansu seda suka gane bana jin dadi.

Da magriba muna Kitchen da Amna ina girki tana dan tayani da wasu abubuwan, tun tuni nake saqawa a
zuciyata na tuntubeta da dabara naji ko suma suna jin wani abun ina ta fargabar amsar da zan samu
tunda dai daki daya suke kwana, me nauyin bacci ma taji bare amma da sam bata da nauyin bacci amma
kuma ya zama dole na tambayeta kodan nasan matakin da zan dauka saboda tarbiyyar su, ina ta hiqilo
akai kar naje tufka nakeyi ta baya tana warwarewa.

Gundumbala nayi nace “Amnah, ni kuwa jiya kinji wani motsi ko maganganu a gidan nan da daddare?”
Seta dago daga yankan Albasar da takeyi tace “motsi kuma Mami gaskiya ban ji komai ba in banda
karatun da kika kunna a Mp gurin qarfe uku ma dana tashi zanyi fitsari shine naji ya mutu na fito na duba
ashe chaji ne ya qare na jona kuma dai banji komai ba wallahi”.

Ajiyar zuciya na sauke me qarfi kafin na sake cewa “Ni kuwa se na ringa jin kamar ana hayaniya da
daddare bama iya jiya ba, duk sanda Abin ku yake gari ina ji ta windon dakinsa kuma dana tambayi
Amirah ma se tace mun itama tana ji”.

“Toh Mami qila daga qidan su Faisal ne (maqotan mu ta gefen da dakin Bashir yake) kin san suna da
yawa kuma Raliya tace suna kaiwa har qarfe uku wataran basuyi bacci ba suna kallo musamman
weekend, Anty Amirah kuma daman ai a dakin ki take kwana itama kinga zata ringa ji”.

“A dakina take kwana kuma?” Na tambayi Amna da mamaki, seta daga kai Alamar da gaske tace

“Eh mana Mami bake kika ce ta ringa kwana a can ba duk sanda Abbi yake gari wai kince idan ana barin
daki babu kowa Aljanu suna kwana a ciki shiyasa duk sanda zaki kwana a dakin Abbi to ita kuma a dakin
ki take kwana se da Asuba take dawowa nan”.

“Lallai watan cin kutumar uban Amirah ya kama” na raya a zuciyata. Ban taba sanin yar is kar yarinya
bace mara mutunchi se yau, daman dakina take zuwa ta kwanta tayi mana labe kenan saboda taji abinda
muke tabbas kuwa a yau ba se gobe ba seta bar gidan nan wallahi.

Muna cin abinci ta shigo gidan sadaf sadaf kamar munafuka se tayi turus da ganina a zaune dan nasan
hasashenta ina daki saboda idan na idar da sallar Isha se nayi shafa’i da wutri na danyi lazumi na kafin
nake futuwa palour yau din kuma da magribar nan Period yazo mun.

Kallonta nayi daga sama har qasa a fili na ce “kan uban nan” ina miqewa tsaye sosai na qare mata kallo,
Kayana ne a jikinta, Wata Atamface falle biyu na siya saboda kyan da tayi mun akayi mun fitted straight
gown dikin yaqi shigata saboda ya matse, tunda ta gani take nacin na bar mata ni kuma naqi saboda ina
son Atamfar kuma na nema tsaf an rasa samun wata se plain yadi tailor ya siya yace ze gyara mun dinkin
shine taje ta dauka ban sani ba dan da zata fita ma Hijabi ta saka har qasa ban ga kayan jikin ta ba.
Irin kallon da nake jifan ta dashi ya sakata qarasowa tana cewa “Dan girman Allah Mami kiyi haquri
wallahi dan Allah...” tas na kwasheta da Mari kafin na nuna mata qofar dakin su cikin kaushin murya
nace

“Minti goma na baki ki shiga ki cire mun kaya ki kuma tattara yanaki ki wuce gida yanzun nan dan bazan
sake zama dake ba tunda baki da tarbiyya”.

Kuka ta saka mun tana tambayata wai me tayi dan Allah nayi haquri na sake jaddada mata wallahi seta
bar gidan nan a yau, tunda har take yi mana labe wata rana kuma ai leqa mu zatayi idan ba’ayi sa’a ba
haka ta tattara a daren ta wuce gida tana fita muka kulle gida na kuma kashe wayata dan na tabbatar
idan Addah bata biyo sahu ba toh kuwa zata kira waya.

Washe gari kuwa qarfe bakwai da rabi A gidan tayiwa Addah, mun fito zan kai yara makaranta naji ana
dukan Get, Musbahu yaron shagona yaje ya bude se gata kamar an wullota ta hau tijara da diban
Albarka akan me zan korar mata ya ita da gidan dan uwanta.

“Gata nan ai a gaban ki ki tambayeta me tayi mun” na fada ina kunna mota, ina ji tana ta zuba rashin
darajar ta nayi banza dasu na zuba yara a mota, dai dai zan fita naji tana cewa

“Wallahi baki isa ba Asma’u, baki isa kice me kadai zaki mallake Bashir da dukiyarsa ba se Amirah ta
dawo cikin gidan nan kuma a lokacin baki isa ke koreta ba” nidai nayi zooming na fice na barta a tsaye
tana kumfar baki.

Dariya ma ta bani wai na mallake Bashir da dukiyarsa nayi me dasu, su kudi suka dama da har suke ganin
ya tara wata tsiya dab dai ni har yanzu ina masa Kallon Bashir din dana sani me tun bashi da komai, idan
ma ba haka ba babu wanda ya tayani shan wahalar sa a cikin su idan ma nace zan mallake shi ni kadai ai
banyi laifi ba ko.

WATA KISHIYAR

(ALKAHIRI CE KO SHARRI)
Na Maryamah Farouk

(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)

Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 38

Se bayan dana kai yaran na dawo sannan na kunna wayata, kiran Dada ne ya fara shigowa na daga na
gaishe ta daga yanda ta amsa nasan labari ya isarmata kenan.

"Akan me zaki kori Amirah daga gidan Bashir Ma'u" ta fada bayan da muka gaisa.

Lallai wato gidan Bashir tana gaya mun ba gidana bane kenan, murmushi nayi, babu kunya tiryan tiryan
na karanta mata abinda ya faru da duk abinda Amiran ta fada mun dama sauran abubuwan da takeyi a
cikin gidantsaf seda na tsara mata.

Seda tayi jum da na tabbatar na kunya ne kafin tace "To ai koma menene be kamata ki koreta ba haka da
se kija mata kunne ko ki kawo mana qararta mu se mu tsawatar mata, yanzu dai se kuyi haquri ta dawo
kuci gaba da zama Allah ya kiyaye gaba".

"Wallahi Dada bazan sake zama da Amirah a gidan nan ba, ta koma gidansu idan auranta ya tashi bazan
fasa yi mata duk abinda idan a hannuna take zanyi ba amma fa ba dai gidan nan ba" na fada kai tsaye
dan ganin ana nema ayi mun fin qarfi, ita bataga illar abinda tayi ba kenan har ake cewa nayi haquri ta
dawo to kuwa baze sabu ba.
Muna gama waya na kira Bashir na kora masa jawabi dan tun a jiya da daren nake ta neman wayar sa
ban samu ba se text message na bar masa. Yanzun kuwa yana amsawa na kora masa abinda yasa nace ta
tafin, zuwan Addah harma da wayar da mukayi da Dada.

"Wallahi bazan sake zama da yarinyar nan ba kama gaya musu"

"Daman ai ke kika gayyato ta gidan tun farko ai ni meye nawa a ciki?" Bashir ya fada.

Bansan dai ya suka qarke ba a batun Amirah kwanaki kadan tsakani ya tayar da maganar komawar mu
Lagos dan ya samu gida babba da ze wadace mu. Nayi zaton za'a samu matsala dasu Dada saboda kes
din Amiraj da mukayi amma se naji shiru haka muka fara shirye shiryen dan a lokacin ana Third term ne
har yara sun fara shirin jarabawa, daga sun gama zamu tafi se a saka su sabuwar makaranta su koma
sabon session.

Lokacin da zamu tafi gida gida nabi duk nayiwa kowa Sallama har gidan Addah naje muka rabu faran
faran tana cewa se sunzo dan tana son zuwa Lagos in muka nutsu zata zo tayi mana sati har bakin ruwa
se an kaita nace Allah ppl ya nuna mana lokacin ta hada mana tsarabar kayan qamshi da su daddawa
harda man Shanu ga dambun nama da tayiwa Jafar dan shine mutumin ta.

Haka muka tattara muka koma Ikko, gidan da Bashir ya samu babban gida ne me kyau yana cikin rukunin
gidajen manyan ma'aikatan su.

Flat ne me dauke da manyan dakuna guda biyu se madaidaita suma biyu ko wanne kuma da Bandaki a
cikin sa, ga qaton palour da Gurin Dining, Kitchen, store sannan ta bayan gidan da akwai babban fili da
akayiwa shuke shuke daga gefe akayi garden.

Gida dai masha Allah kuma Bashir ya saka komai na buqata a ciki. Se da nayi dagaske kafin na iya daure
kewar gida na saba da garin, dan ma nayi sa'ar maqociya wadda take matar Ogan Bashir ce Anty Halima
mutuniyar kirki, ita ta qara wayar mun kai da zaman Lagos na gane kan kasuwa ya zaman ina sarar kaya
na turo dasu ko ina kake so a fadin Nigeria.
Kamar wasa naga tallan daukar ma'aikata na wani kamfani da suke hadahadar ma'adanan qasa anan
Lagos, a lokacin na cewa Bashir zan cike ya kuma bani goyon baya na nemi aiki cikin ikon Allah se kuwa
na samu suka daukeni matsayin meyi musu tallace tallace.

Na kama aiki ba dadewa wata rana kwasam muka samu baquncin Addah, Dada harda Amirah. Sosai
mukaji dadin zuwan su dan baka gane dadin gida se randa kayi nesa da yan uwanka kwanan su hudu
Addah da Dada suka juya aka bar Amirah da alokacin wai an saka ranar auranta da wani yaro Bashir
shima sunansa dan Abokin babban su Bayan sallahr Azumi da sati daya.

Dalilin kawota kuwa saboda acewarsu na koya mata yan abubuwan da ya kamata ta iya, nayi dariya
kuwa nace duk abinda bata koya ba a zaman kusan shekara goma da mukayi tare banajin zata iyashi a
watanni biyu kacal, haka dai suka tafi suka barmu na kuwa dage tsakani na da Allah ina dora yarinyar
nan akan hanya ta hanyar nusar da ita komai.

Tunda tazo sau daya Saurayin nata Bashir yazo da yake anan Lagos shima yake zama, nidai itin yanda
naga yana ta dari dari da ita bayan ya tafi na kasa shiru seda nayi mata magana nace

"Wai ni Amirah hada ku akayi da Bashir ne?"

"Aa Me kika gani Anty?"

"Gani nayi yanda yaqi sakewa dazu da yazo musamman tunda Baban Ali ya dawo jikinsa fa har wani
rawa ya ringayi".

Dariya tayi tace "haka fa yake Anty ni wallahi har tunanin yanda ma zamu zauna dashi nakeyi, nida nake
son na samu miji mu sha soyayya irin taku da Yaya shi yasa fa na samo me irin sunan sa ma. Nidai ki
taimaka mun Anty ki koya mun duk irin abubuwan da kikeyi nima na zama star".

Hade rai nayi, na fuskanci Amirah dai se gyaran Allah sauqin ta dai za'a mata auran taje ta qarata in huta,
haka muka ci gaba da zama ina koya mata duk wasu abubuwa daya kamata macen data san kanta ta iya
su.
Bilhaqqi nake bata sirrika da kuma gyara tamkar yanda zanwa qanwata ciki daya kafin cikar wata daya
kuwa ta fara hawa saiti dayake ita ta saka kanta hatta girki yanzu tana qoqari sosai dama abun nata
harda qyuiya da qyashi suke hanata tayi a lokacin baya yanzu da yake a rajin kanta ne wani lokacin kafin
na taso daga aiki ma ta gama abinci, gyaran gidane dai se a slow, zata ci kwalliya amma gurin da zata
zauna be dameta ba.

Tsakanin ta da Bashir dai bana ce komai ba dan daga gaisuwa wata magana bata qara hadasu idan yana
zaune ma bata fitowa tana daki tana chatting din daya zamar musu dabi'a yanzu daga ita har Bashir dan
shima yanzu muna zaune bini bini yana danne dannen waya wani lokacin kuma se naga ya zauna yayi
shiru kawai kamar akwai abin da yake damun sa dan inbanyi qarya ba se nace har rama yayi amma se na
ta'allaqa hakan qila da yanayin aiki, a haka muka shiga watan Azumi wanda ya rage saura sati biyar bikin
Amirah kenan.

Ranar da aka kai Azumi na uku bayan ansha ruwa Addah ta kirani take gayamun sunje ganin gidan
Amirah.

"Gidan yar taki yayi kyau Ma'u sena kin gani daki uku mijin ya bata da palour se ku yunquro dan kinsan
gidan kishiya ne dole ki gwangwaje yar taki".

"Gidan kishiya kuma Addah dama Bashir din ya taba aure ne" na fada da mamakin maganar tata, se ta
shiga in da in da tana cewa

"Au Faccala nake so nace miki, gidan su daya da matar wansa wannan kishin ai har yafi na kishiyoyi zafi,
zan saka a turo miki da kudaden da Babanta ya bayar a siyi gado dana gurina da za'ayi mata kayan
Kitchen tunda ai kece uwarta".

"Hakane kuwa to Allah ya sanya Alkahiri ya nuna mana lokaci babu damuwa, a turo din kinsan daman
kaya anan sunfi kyau da Sauqi se mu siya a kawo kawai" daga haka mukayi sallama Allah a raina naji
dadin karamcin da akayi mun aka dorani akan har kar bikin.

Haka na tasa Bashir da nacin se ya siya mata gado daya se a hada da na gurin Babanta biyu kenan daki
dayan in mijin yaso se ya gyara abinsa amma Bashir ya dage akan shi bazeyi ba bashida kudi saboda a
sannan gini yakeyi, ya rushe gidan mu na Gombe ya siyi filin kusada mu an qara ana mana sabon gini
kuma daga yanayin plan din nasan dole zeci kudi.
Dana takurashi daga qashe yace dubu dari yayi niyar bada gudummawa nace sunyi kadan gadon nan fa
dole shi ze siya mata haka dai ya haqura daga qarshe ya yarda yace na ranta masa kudin muka siya mata
gado me kyau dan dubai a sannan ma dubu dari hudu muka siye shi irin nawa dana siya na chanza na
dakina na mayar da na ciki dakin su Amna.

Hidimar da nayi ta kayan auran Amirah ko bikin Farida nake yi se haka dan wallahi bazan iya lissafa nawa
na kashe mata ba a kayan Kitchen Anty Halima har fada ta ringa yi mun tace dangin miji nakeyiwa
wannan hidimar a maimakon nayi musu gwaninta qarshe baki zan janyowa kaina suce da kudin dan
uwansu nake wadaqa amma na toshe kunnena nayi mata.

Haka na tattara kaya rankatakaf aka kwasa a mota aka kai Gombe sannan muka ci gaba da gyaran
Amarya kuma da shirin biki dan har dinkunan ta duk nan aka kawo na bawa sabon tailor da nayi ya yi
mata dinkuna na daukar magana biki kawai muke jira.

Randa aka kai azumi na Ashirin da biyu Bashir yazo mun da Albishir din ya biya mana Umarah nida Yara
Gaba daya kuma wai a gobe zamu tashi abin ne da kamar baze yuwu ba shiyasa be gayamun ba se yau
da safe sannan komai ya kammala.

Nayi murna kuma banyi ba. Murnar da nayi ta tafiya Umarar ce da kuma yarana dukka gaba daya abinda
na dade ina mafarkin yi inda naji rashin dadi kuma ba tare da Bashir zamu tafi ba dukda sati biyu zamuyi
dakyar idan tarar da bikin Amirah qila ranar da aka gama zamu dawo amma.

Haka muka tashi hada kaya a daren dan ma tashin namu bana safe bane, ta waya na kira gida mukayi
musu sallama washe gari tun safe Amirah ta fara tafiya Gombe, harda kukanta wai bana nan za'ayi biki
gaskiya zataje ta cewa su Addah a qara sati se na dawo haka na rarrasheta ta tafi, mun samu delay
najirgi dan haka se qarfe 7 na Magriba muma muka tashi zuwa qasa me tsarki muka bar Bashir shi kadai
yana ta daga mana hannu.

Mun sauka qasar madina lafiya, sosai na kama ibadah ta dan ko kusa ban bari hidimar yara ta hanani
ribatar goman qarshe da muka shiga ba. Kwanan mu biyar muka tafi Makka muka dauki Haramin umarar
mu, bayan mun sauke nan ma a kullum ina Masallaci ina ibaduna, kwanan mu biyu aka sallace banyi
sanya ba na duqufa sosai ina ta kaiwa Allah kokena. Adduata duk akan Iyayena, Yarana da Mijina tareda
sauran Al'umar musulmi baki daya.

Ranar Juma'a data kama Lahadi zamu dawo Nigeria da yamma mun fita kasuwa da yara wayata dake
cikin jaka ta ringa qara, seda muka shiga shagon nacewa Amna zu zagaya su dauki abubuwan da suke so
kafin na dakko wayar na duba,

Rahma ce Amaryar Amiru da mamaki nake kallon tarin missed calls dinta gida shida se na fara qoqarin
kiran ta dan tabbas nasan ba lafiya ba irin wannan kiran nayi sa'a kuwa ringing biyu ta amsa wayar.

"Maman Aliyu wane labari naji dan Allah kice mun ba gaskiya bane" ta fada ba tareda ta bari ko gaisawa
munyi ba. Se naji gaba na ya fadi, daman dauriya nakeyi, a kwanakin kullum cikin faduwar gaba nake da
quncin zuciya na rasa me yake damuna shiyasa ko da yaushe ina cikin Harami ina sallah ko karatun
qur'ani su kadai suke sanyayamun zuciya na kuma fawwalawa Allah ya iya mun koma menene yake tun
karo ni dan a duk sanda naji irin wannan yanayin to tabbas wani mummunan abu ne yake shirin samuna.

"Maman Aliyu bakya jina ne kin yi shiru k baki samu labarin abinda yake faruwa bane" Rahma ta sake
fada abinda ya fito dani daga duniyar tunanin dana luluqa.

"Wani abun ne ya faru Rahma ban sani ba wallahi Allah dai yasa lafiya" na fada a sanyaye, se tayi shiru
kafin cikin wani yanayi tace

"Tunda baki sani ba bazakiji a bakina ba Maman Aliyu amma ki kira Yaya Bashir yanzu base anjimaba kiji
komai" kafin nace wani abu ta yanke wayar.

Seda na kira Bashir sau uku amma be daga ba, ganin magriba ta kusa sena haqura muka qarasa siyayyar
mu muka koma masauki akan zuwa bayan Isha se na sake kiransa idan na dawo daga masallaci amma
sam na kasa samun nutsuwar zuciya.

Kira na ringa doka masa abinda ya bani mamaki ko ince ya fara bani tsoro ganin na kira yafi sau Ashirin
wayar tana qara amma ba'a daga ba sena mayar da akalar kiran nawa kan Amiru dan na sake kiran
Rahman itama bata amsa ba.
Kira biyu ana ukun Amiru ya daga. Cikin sanyinsa muka gaisa se mukayi shiru gaba daya ni ina jira naji
yace wani abu ne ya samu Bashir shima yana jiran jin dalilin kiran, ni na katse shirun da cewa

"Baba Amiru Bashir kunyi waya da Bashir kuwa yau"

"Eh mun yi waya bamu dade da rabuwa bama na barshi a gida yanzu na fita"

"Oh yana Gombe ashe, nayita kiran wayarsa ne amma ban samu ba shine nace bari na kiraka naji ko
kunyi magana yau shikenan se an jima" na kashe wayar. Daga yanayin sa sam banji cewa wani abu ya
faru ba to me yasa Rahma zata kira ta daga mun hankali??

Qoqari nayi na yakice tunanin daga zuciyata muka shirya muka tafi masallaci, ina cikin yin shafa'i da
wutri wayata da sam na manta ban saka ta a Silet ba ta dauki qara lokaci daya gaba ya yanke ya fadi da
har seda na dafe qirji na shiga nanata Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un a zuciyata.

Ina sallamewa na jawo wayar na duba, Alawiyya ce ta kirani, sena miqe kawai ina shirin bin bayanta wani
kiran ya shigo sena yi saurin daga wa na saka wayar a kunnena.

"Ma'u bansan daga ke har mijinki yan kutumar uba bane se yau, anya ba asirce ki yayi ba kike zaune
dashi ya kulle miki baki? yanzu ace za'ayi miki kishiya duk duniya ki kasa gayawa kowa sema ki tsallake
kibar qasar wai kin tafi Umara sedai kawai muji a gari, shikenan ai Bashir ko gaki gashi nan tun ba'aje ko
ina ba kin fara karbar saka makon ki a hannunsa".

A duk maganganun Alawiyya babu abinda na tsinta banda kalmar kishiya data fada, seda na da dage
piller masallaci jin jiri yana neman kadani.

"Lallai wato ga mahaukaciya tana magana kin yi mun shiru ko Ma'u, shikenan amma ki tabbata kin nemi
wata yar uwar da zaki raba baqin cikin Bashir da ita dan wallahi bazaki dora mun hawan jini da takaicin
mijinki ba, mtsw" taja tsaki.
Seda nayi da gaske na iya bude baki nace

"Alawa ni duk ban gane abinda kike nifi bane waya gaya miki Bashir yayi aure?"

"Kina nufin baki sani ba to maza shiga whatsapp yanzu na tura miki hotuna kigani se ki tabbatar wa idon
ki" tafada kafin ta kashe wayar.

Wata wawuyar Ajiyar zuciya na sauke lokacin da naga hotunan da Alawiyya ta tura mun. Hotunan Bashir
ne da Amirah tareda sauran yan uwan su wanda na tabbatar na daurin auran Amiran ne amma ai na zata
se gobe Asabar aka saka a katin data tura mun kuwa.

Da daddaya na ringa binsu da kallo Bashir yaci uwar Babbar riga fara gasu Addah nan baki ya gonar
Auduga an washe shi ina shirin bude na qarshe da naga kamar kati ne kiranta ya sake shigowa.

"Yanzu kin yarda ko kuwa dai kina tantama" ta fada".

"Haba Alawa haka kawai kin saka hawan jinin dare daya ya nemi kamani a marrar nan kike mun zancen
kishiya. Amirah cefa kin manta da bikinta akeyi hotunan daurin auren nefa duk kika bi kika kidima kanki".

"Allah ya yafe miki Asma'u ya nuna miki hanyar daidai, shikenan tunda ni na kidima kaina ba lefi idan
kika dawo hayyacin ki se muyi magana dan naga alamar kwakwalwarki ta juye Ma'u kina buqatar saiti
amma ki nutsu ki sake kallon hotunan dakyau ga wasu can ma na qara tura miki" Alawiyya ta fada
sannan ta yanke waya.

Hotunan na sake bi da sababbin Videos din data turo mun na Amirah data sha kwalliya tayi kyau suna ta
shaqiyanci, akan katin dazu na sake tsayawa na bude shi na fara karanta abinda aka rubuta.

"DAURIN AURAN ENGINEER BASHIR AHMAD DA AMIRAH MURTALA" Abinda na gani an rubuta kenan,
daga Bashir din har Amirah ko daga bacci na farka naga sunansu na san sune ballantana wannan ga gurin
daura auran nan masallacin dake layin gidan Addah ne hakan ya sake tabbatar mun da gaske dai Nawa
Bashir din ake nufi bawai wani na daban ba.

Wayar hannuna ce ta dauki qara, ban san ya akayi na daga kiran ba nidai naji muryar Anty Halima tana
cewa

"Asma'u dagaske ne ko wasa yanzu a duniya Bashir ya rasa irin cin Amanar da ze yi miki se ya tura ki
wata qasa sannan ya daura da yarinyar da kika riqe?"

Iya abinda naji kenan lokaci daya tsikar jina suka zuba kaina yayi mun dum kamar wadda aka kwadawa
guduma daga nan ban sake sanin inda nake ba se farkawa nayi na ganni a gadon Asibiti.

Waya ta da nagani a gefena na jawo na sake budo hutunan dazu dan in tabbatar gaskiya ne ko qarya. Ina
kunna Data kuwa kamar ana jira messages rututu suka fara shigo mun alamar dai magana ta baza gari ga
status din yan gidan su Se a sannan ma naga status din Jama'a ashe an yi posting hotunan sosai hankali
na nae bekai kai ba.

Tun yaushe aka shirya hakan? Daman Bahsir da Amirah suna soyayya ina zaune dasu ban taba ganin
wata alama ba?

Wai ma me nayi wa Bashir a rayuwa dana cancanci irin wannan sakayyar bayan tarin dumbin
sadaukarwa da Alkhairan da ni da yan uwana muka yi masa.

Wane irin mugun hali ne dani da har ya kasa gayamun zeyi aure sedai naji a duniya bayan daya rigada ya
daura me nayi masa dan Allah?

Sannan Ace duk matan duniya manya da yara farare da baqar fata Bashir ya rasa wadda ze aura se
Amirah yarinyar dana gama bautawa tun tana qanqanuwarta har girma yanzu ace da ita zanyi zaman
kishi yarinyar data san sirrina, na bude mata duk wasu sirrika da nake taqama dasu saboda yanda na
dauketa tamkar qanwata na gyarata saboda ta samu daraja a gurin mijin da zata aura yanzu ashe duk
mijina nayiwa wannan tanadin? Ni za'a yaqa dasu?
"Yah ubangiji kaika halicceni, kai ka tsara mun rayuwata tun kafin wanzuwa ta a doron duniya Allah
kasan zan iya shi yasa ka dora mun na roqeka nayi tawassali da sunayen ka tsarkaka nayi tawassali da
Annabin ka Muhammad SAW Allah in har sunyi dan su cutar dani na roqeka karka basu ikon ganin
gazawa ta, ka sanya min juriya da dakiyar tun karar duk wani qalubale da zan fuskanta a rayuwa.
Ubangiji ka sauqaqa mun dau wani ka bani zuciyar da zan iya dauka" na fada a fili ina fashewa da wani
irin kukan baqin ciki.

Wallahi ko kadan banji haushin auran da Bashir yayi ba, da ace wata ce daban zan shanye na danne
bazan taba nuna masa komai ba har in ga iya gudun ruwan sa amma Amirah fa Amiran Addah me yasa
se Ita? Da ace Ummi qanwarta ya aura nasan bazan ji baqin ciki irin wanda nake ji yanzu akan auran
Amirah da yayi ba.

"Amirah zata dawo gidan nan kuma a sannan baki isa ki koreta ba" kalaman Addah suka dawo mun a
kwakwalwa ranar da na kori Amirah daga gidana a Gombe. Ashe abinda suka shirya yi mun kenan daga
ita har Dadan suka dakko kishiyata suka kawo mun da nufin na gyarata su kuwa wasu irin mutane masu
saka Alkahiri da sharri ta ina na kuskure musu a rayuwa da suka zabi hukunta ni ta irin wannan hanyar?

Kuka na ringayi wanda tun likitocin da suka dubani suna bani haquri har suka haqura sukayi shiru, bana
buqatar sauran bata lokaci a qasar tunda daman ba dan Allah ya turani ba dan ya aiwatar da nufin sa ne
to yaci galaba amma nima dole na koma Nigeria muyi wacce zamuyi da Bashir dan bazan taba hada miji
da Amirah ba.

Yana da damar ya auro mun mata uku mu zauna amma ba Amirah yarinyar da nakewa Kallon Yata ita ce
ze hadani kishi da ita baze sabu ba.

Sanda na koma Hotel din da muke na tarar da yara zuru zuru dan da aka kaini Asibiti can suka koma
saboda a qa'idar su ba'a barin dan jinya.

"Ku hada kayan ku yau zamu tafi" na fada ina hargitso duk abinda hannuna ya kai kansa ina sakawa a
jaka. Seda na gama sannan na tuna da ai Passport dinmu ma baya hannunmu yana gurin Agent din da
Bashir ya hadamu dashi, wayata na dauka na shiga kiran nayi sa'a tana shiga ya daga.
"Malam Isah kayi mana booking jirgi idan da akwai Yau ka, ka fada mun kudin ko nawane zan biya wani
abu ya taso mun bazan iya jira har se gobe ba" na fada ba tareda na amsa gaisuwar daya fara mun ba.

"Amma Hajia me ya faru haka, bayan haka kuma ai Ticket din ku bana komawa Nigeria bane Dubai zaku
wuce daga nan na zata ai Engineer ya gaya miki ma"

"Isah dakai da Dubai din da Engineer kunci abu ta kazan ubanku" na lailayo wata Ashar me maiqo da ni
kaina bansan na iya ta ba na kora masa kafin na ci gaba da cewa

"Ka kawo mun passport din mu nan da Awa daya idan ba haka ba wallahi se nayi qarar ka nace safarar
mu kayi, kasan ina da duk wasu bayanai naka da zan bayar ka kuskure lokacin baka zoba ka gani".

"Kiyi haquri hajia ku shirya yanzu zan turo mota da zata kaiku Jiddah ni ina can yanzu haka akwai jirgin
da ze tashi yau da daddare bari na bincika idan da akwai guri se a siya" Isah ya fada jin abin yafi qarfinsa.

A dakin muka bar kusan rabin kayan mu dan bana buqatar abinda ze bata mun lokaci bate har aje ana
maganar wani awon kaya ko wani abu muka hau mota se Jiddah gaba daya ma gani nayi motar bata
sauri, ina ma ace zan iya rufe ido na ganni a Nigeria, ina buqatar naje naga da wadanne idanu Bashir da
danginsa zasu kalleni.

Mun samu jirgi amma se munyi jiran Awa goma sha biyu kafin tashinsa, haka Isah ya nema mana hotel
gaba daya ya rasa meya faru haka gashi kiran duniya Bashir yaqi dagawa daga qarshe ma ya kashe wayar
gaba daya Asma'u kuwa bega fuskar da ze mata tambayar abinda yake faruwa ba ma dan haka yaja Aliyu
yana tambayarsa ko mutuwa akayi

"Nima ban sani ba, kawai daga Masallaci aka kaita Asibiti kuma data dawo mun kasa tambayarta abinda
ya faru idan mukaje gida koma menene se mu gani" Aliyun ya bashi amsa.

Haka muka hawo jirgi se Nigeria ya sauke mu a Kano,Asuba ranar lahadi muka sauka tun a AirPort na
samu shatar mota ta kwashe mu kafin Goman safe mun sauka a Gombe muka ci burki a qofar gidan su
Bashir cikin Sa'a nayi kyakykyawan gamo da Ango Bashir da tun daren Alhamis rabon da ya sake daga
wayata.

WATA KISHIYAR

(ALKAHIRI CE KO SHARRI)

Na Maryamah Farouk

(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)

Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 39

A qofar gidan motar mu ta tsaya, idona akan Bashir da suke tsaye tareda wasu mutum biyu da ban gabe
su waye ba.

“Ku jirani karku fito” na fadawa yaran, seda na yi kokawa da duk wani rauni da karayar zuciyar daya taso
mun kafin na bude motar na fito ina gyara mayafin kaina gaba daya mutanen gurin suka bini da kallo
banda Bashir da tunda muka hada ido ya maida kansa qasa kaman wanda aka kama yayi qarya.

Kai tsaye cikin gidan na shiga, nayi sallama ina jiyo hayaniyar su daga cikin dakin Dada amma ba’a Amsa
ba dan haka na nufi can din, har na kai bakin qofar naji an kira sunana, sena waiwaya.

Alhajin su Bashir ne yana tsaye daga qofar dakinsa ya yafito ni da hannu sena juya na koma gurinsa.

Ina durqushe a gabansa kusan minti biyu kafin yaja numfashi yace dani

“Asma’u kiyi haquri nasan an cutar dake amma zan roqeki Arziqi kar kice musu komai yanzu, ki barsu
akwai ranar da su da kansu zasu maidawa junan su martanin abinda sukayi miki.
Na sani Qarin aure ba haramun bane amma ta yanda aka shirya naki sam be kamata ba. Ya zama zamba
cikin aminci. Ki sani Ita Amana daya ce kuma wanda yacita baya taba zama lafiya, idan har Bashir da
uwarsa sun qulla wannan aure dan su ci mutunchin ki Asma’u in Allah ya yarda muna raye ko mun mutu
se sunga sakayyar cin Amanar da sukayi miki.

Ina qara roqonki da kiyi haquri, ki qara akan wanda kike yi in sha Allahu bazaki tabe ba, duk me neman
gazawarki akan idonsa zakiyita ci gaba da yardar Allah”.

Kuka nakeyi dagaske a raina ina hasaso irin tarin qaunar da na nunawa Bashir da Ahalinsa, a tsahon
zamana dashi kusan shekara goma sha uku yanzu bazan iya cewa taka maimai ga wani abun laifi daya
taba hadani da wata daga cikin su ba, a kullum cikin kyautata musu nake iya qarfina kuma duk albarkacin
so da qaunar da nakeyi wa Bashir din ce ta shafi su amma ace a gurinsu basu da abokin hamayya seni.

Sosai nasha kuka na ba tareda Baba ya hanani ba in banda “kiyi haquri Asma’u” babu abinda yake cewa.

“Naji zan haqura Baba bazan tanka musu ba amma kayi haquri bana jin zan iya ci gaba da zama da
Bashir. Bazan iya ci gaba da zama cikin Ahalin da basa qaunata ba Baba. Sannan Baba Amirah fa, yarinyar
dana raina da hannuna ita zan hada miji da ita wallahi bazan iya ba.

“Zan bi umarnin ka a yanzu zan koma ba tareda na cewa kowa cikin su komai ba amma Baba karka
roqeni ci gaba da zama da Bashir saboda ina girmamaka bazan iya tsallake unarninka ba amma tabbas
zan cutu. Zuciyata zata iya bugawa a dalilin haka muddin zan zauna inuwa daya da Amirah a matsayin
kishiyata” na fada cikin sheshsheqa me qarfi.

Se Baba yayi murmushi wanda da ganinsa na takaici ne kafij yace

“Asma’u ke Yarinyar kirki ce sannan abar Alfaharin duk Miji me hankali da yayi katarin samun irin ki
sannan ko wanne uba zeyi alfaharin zamtowarki Suruka a gare shi.
Bazan so na rasa nagartacciyar suruka irin ki a cikin zuria’ata ba domin ke din mayafi ce da kika lullube
Bashir duk kuma ranar da wannan mayafin ya yaye ba baki nayiwa Bashir ba tabbas se rayuwar sa ta
shiga cikin gararin rayuwa.

Idan har ki ka ce bazaki ci gaba da zama da Bashir ba ni me tsaya miki ne in tayaki kwatar yancin kanki
amma yanzu kije ki samu nutsuwar zuciya, karki yanke hukunci cikin fushi idan kika nutsu duk abinda
kika yankewa zuciyarki ki dawo ni ki gaya mun in Allah ya yarda zan baki goyon baya dari bisa dari ki
share hawayenki yanzu”.

“Baba bana tunanin ina da buqatar yin wani dogon nazari ka taimakeni kawai kasa Bashir ya sawwaqe
mun dan ina da yaqinin ko ba yanzu ba watarana se sunyi nasarar fiddani daga dakina” na fada cikin
kuka, se ya tare ni da cewa

“Haba Asma’u ke da na sanki jaruma ya zaki karaya tun yanzu ki bada qofar da za’a ci galaba akanki?
Maganar su fitar dake daga dakinki kuka babu wanda ya isa yayi Abinda Allah beyi ba, kije gida ki huta ki
bawa zuciyarki haquri idan kuma kinga bazaki iya karbar Al’amarin ba ki dawo zan tsaya miki”.

“Shikenan Nagode Baba Allah ya qara girma”

“Nima na gode Asma’u Allah yayi miki albarka keda zuri’arki gaba daya”. Haka mukayi sallama da Baba
seda yasakani na share hawayena tas yace naje na dauraye fuskata a bayin da yake cikin palour sa kafin
na fito.

Ina fitowa naci karo da Dada da yayanta sun fito daga dakinta, Yanda kasan anyi ruwan sama an dauke
haka sukayi shiru gaba daya suka zubo mun idanu kamar wanda sukaga wata sabuwar Halitta nayi musu
kudin goro gaba dayabna watsar na nufi qofar fita.

Sanda Na fita ban tarar da Bashir a waje ba se Naziru suna tsaye a jikin motar da muka zo tareda yara.
Kallo daya nayi masa na kama murfin motar na bude se ya riqe yana cewa

“Wallahi Anty babu sa hannuna basu gayamun ba se ana gobe za’a daura, da nace zan gaya miki Dada
tace duk wanda ya kuskura ya sanar dake wallahi se tayi masa baki shiyasa ko Yaya Amiru da kika kira
jiya ya kasa gaya miki komai” ban bi takansa ba na cewa me motar muje na nuna masa hanya ya qara sa
damu gidan mu gidan Baffana. A waje na barsu ana sauke kayan mu bayan na sallame shi na wuce ciki.

A yanzu babu abinda nake buqata sama da na kebe ni kadai a inda zan sha kukana kar wani ya rarraahe
ni. Dakin Hajia Babba nayi masauki na haye can qarshen gadonta na saka kaina a cinya na ringa rirgar
kukan da wadda akayi wa irin abinda akayi mun ce kawai zata fahimce ni, tambayar kaina nakeyi me
nayiwa Bashir a rayuwa daya qullaceni yaga ta haka kadai ya kamata ya rama.

Ina jin matan gidan mu suka ringa shigowa suna bani baki amma na toshe kunnena, nasha kukana seda
naji Numfashi shina yana barazanar daukewa kafin na bawa kaina haquri na koma sauke ajiyar zuciya
kawai ga wani masufaffen ciwon kai daya dirar mun maqogarona kuwa kamar ze tsage saboda bushewa
dan in ban manta ba rabonda ko ruwa ya wuce ta cikinsa tun kafin na samu wannan baqin labarin.

Har dare ina cikin dakin sallah kadai na tashi nayi na koma na kwanta ba tareda na ko kalli kayan abincin
da Hajiyar ta kawo mun ba. Haka ta zauna akaina tana ta faman yi mun nasiha dana gaji da jinta sena sa
mata kuka dole ta tashi ta bani guri, qarin abinda yake damuna ganin har zuwa sannan banji komai daga
Bashir ba, be zo ba be kuma kirani a waya ba haka na kwana kafin safiya jikina ya rijice dole se da aka
danganani da Asibiti.

Gwajij farko likita ya tabbar mun da jini na ne ya hau sosai abinda ya saukar mun da mugun ciwon kai
kenan ga kuma zazzabi me zafi, shawara ya bani da koma menen yake damuna nayi haquri na kuma
fawwalawa Allah domin lafiyata tana gaba da komai, duk wani al’amari na rayuwa baze tafiyar mun
daidai ba idan babu lafiya daga nan yayi mun Allurai da zasu taimaka mun zafin jikin ya ragu da ciwon
kan ya bani magunguna muka tafi gida.

Seda akayi mun wuqa wuqa sannan naci abinci nasha maganin ban dade ba bacci ya dauke ni seda na
shafe awanni ina yi kafin na tashi.

A yammacin ranar Alhaji Qarami yazo, bashi kadai ba kusan yayyena dukka seda suka zo gida aka taru
masu tsinewa Bashir nayi masu bani baki sunayi. A bakin su nakeji wai ashe jiya da daddare ma yazo
gidan ma, nidai ina kwance ina jinyar zuciyata.
Seda muka kwana biyu da dawowa a daren ranar da daddare ina kwance a daki da carbi a hannuna ina ja
Jafar ya shigo yace wai naje inji Dadyn Abuja. Da dogon Hijabi na har qasa nayi sallama a Palour Hajia
Babba kaina a qasa seda na kai tsakiya sannan ido na ya sauka akan Bashir da Bala se Abdulkarim Dan
Qanin Baban su ne, ba tareda na qara ko taku daya ba na juya da niyyar fita Alhaji Qarami ya dakatar
dani dole na koma na samu can gefe kusada qofa na zauna ina jin zuciyata kamar an watsa fetur an cinna
mata wuta.

“Asma’u mijinki ne yazo bada haquri shine nace a kiraki tunda ke akayiwa laifi ke ya cancanci abawa
haquri ko” Alhajin ya fada yana kallona, kafin ya miqe yana sake cewa”ki matsa ciki kin zauna a bakin
qofa ga dare idan kun gama ki same ni gurin Hajia Umma ina son ganinki”.

naji shi sarai amma ban dago ba ban kuma matsa daga inda nake ba ya tsallakeni ya fice daga palour, be
san jira kawai nakeyi ma na samu wata dama na fice na bar musu gurin dan bazan iya musa masa ba tun
farko dalilin da ya sa na zauna ma kenan.

“Gamu munzo guiwoyin mu a qasa Asma’u munsan ba’a kyauta miki ba ni kaina wallahi bansan abinda
ya faru ba kenan se daga baya amma ki dubi girman Allah kiyi haquri, kuskure dai an rigada anyi shi sedai
muyi fatan Allah ya kiyaye na gama amma yanzu kiyi haquri ku karbi qaddara a yanda tazo muku”
Abdulkari ya fada, se na daga kai na kallesu ina shirin buda baki nayi magana Bala ya rigani da cewa

“Allah ya huci ran uwar gida sarautar mata, kinsan fa kinsha kan mutumin bala’in tsoronki yakeyi shiyasa
ya kasa gaya miki zancen auran nan. Kuma ma ni gani nayi ai ba wani abu a ciki tunda qanwarki ce
daman da aje a dakko miki Bare wadda baki san halin ta ba Uwargida ai gara ta gida ko, easy kawai ki
shanye a koma a ci gaba da gashi”

“Sedai a koma a ci gaba da gasa ubanka Bala” na fada a fusace ina miqewa tsaye kafin na nuna Bashir da
yai tsamo tsamo kamar kazar data sha dukan ruwa ya zate ido yana aikawa Bala da mugun kallon
katobarar dayayi nace

“Kai kuma tun da sauran burbudin mutunta juna a tsakanin mu ka rubuta takaddata ka aiko mun da ita
dan wallahi Bashir kayi kadan ka wulaqanta ni kayi mun kishiya ta rashin mutunchi, idan kuma kaqi
tabbas kotu ce zata raba auran mu da kai” ina fadar haka na juya amma kafin na kai waje Bashir da
bansan tasowarsa ya riqe ni kamar dansanda da Barawo yana cewa
“Bazan iya ba Ma’u, na sani nayi kuskure amma wallahi rashin sanin ta inda zan fara gaya miki maganar
yasa na aikata haka. Basan a ya zaki kalleni ba Ma’u idan nace miki zan qara aure. Ni kaina na rasa ta
yanda Al’amura suka juya har na fara son Amirah na yarda kiyi mun duk irin hukuncin da kikaga ya dace
komai tsananinsa zan dauka amma bazan taba iya rabuwa da ke ba Ma’u”

Wani tuquqi ne ya taso mun, yanzu har Bashir ya iya kallon tsabar idona yace dani wai yana son Amirah
lallai na yarda In da ranka zaka sha kallo. Hannayensa daya riqeni na banbare daga jikina ina cewa

“Tunda kana sonta seka je ka zauna da ita amma ni dai wallahi na gama zaman aure dakai ko kaine autan
maza Bashir kaje ka zauna da matar so tunda na gamayi maka rana”

“Kiyi haquri dan girman Allah Ma’u ki yafe mun ki bani dama na wanke kaina nayi miki Alqawarin babu
abinda ze chanza a tsakanina dake saboda wannan auran, Ina sonki ina qaunar ki ki dauka wannan abun
yana cikin qaddadarar mu daga ni har ke” ya fada yana qoqarin sake kama hannuna nayi baya ina cewa

“Qaddarar ka dai kai kadai kuma ka matsa karka sake rabar jikina idan ba haka ba Bashir sena kwada
maka mari wallahi”. Sosai na birkice nayi masa tijara yanda ne taba tsammani ba a rayuwar sa, na hada
da Balan da Abdulkarimun nayi musu zagi na tsamar nama kafin na jadda da masa akan ya kawo mun
takaddata dan wallahi na gama zama da Bashir na yarda su Addahn suci galaba a kaina. Dana hada miji
da Amirah gara na fita na bar mata gidan ta zauna dashi ita kadai.

Bangaren Hajia Umma na wuce gurin Alhaji Qarami, banko bashi dama yayi magana ba na fashe masa da
kuka ina rantsuwar bazan komawa Bashir ba ya saka shi ya kawo mun takaddata na tsane shi na tsani
zama dashi. Haka yayita bani haquri ya kuma tabbatar mun da cewa tilas Bashir ya sake ni tunda har na
nemi hakan amma yanzu na kwantar da hankalina kodan jinina da akace ya hau a samu ya sauka kar
kuma na sake janyo wa kaina wata matsalar.

Haka na kwashe sati biyu cif a gida muna kan wannan danbaruwar, kullum Bashir se ya zo kamar maye
haka ze durqusa yana bani haquri nima kuma ban fasa ci masa mutunchi da jaddada masa cewa ya bani
takaddata ba tunda ba’a aure dole nace na gama.

Gashi makarantar yara kullum se kiran waya sukeyi an koma tuni lafiya basu dawo ba nace musu mun
bar gari ne za’a zo a fada officially a cire su haka gurin aikina ma da suka tuntubeni tunda hutun sati uku
na dauka gashi na haura kawai se nanemi takaddar hutu ba tareda biyan Albashi ba, dan bazan bar aiki
na ba saboda a yanzu ne nafi buqatar sa Idan Bashir ya sake ina da buqatar neman hanyoyin da zan ruqe
kaina da Yayana dasu.

Bazan manta ranar da Dada da Addah suka wanko qafarsu wai sunzo biko na ba, na yaba da tsantsar
rashin kunya irinta mutanen nan. A ranar nayi musu abunda Bahaushw yake cewa idan Malam beji
kunyar hawa Jaki ba to shima Jakin baze ji kunyar kada shi ba.

Na fito musu a yar zamani na wanke su tas da soso da sabulu na kuma sake jaddada musu da idan sunji
haushi su saka Dan su ya sake ni su gani tsakanij ni dashi waya rasa na raka su da Allah ya isar abinda
sukayi mun kuma in sha Allahu nan kusa zasu ga sakayyar yaudarata da sukayi haka suka kwashi kafafu a
sanyaye dan ba Dada ba Addah kanta da bata raina abin kunya tayi mamakin yanda na sakawa idona
toka nayi musu tas.

Daukata sukeyi a duk yanda suka takani zan biyune shiyasa ma yanzun suka zo saboda horon da Bashir
yaje yayi musu akan kodai suje su bani haquri na koma dakina ko kuma ya saki Amirah tunda ita ce duk
musabbabin tashin hankalin da akeyi.

Wai mutane saboda qin Allah se kaga sun kirani da sunan wai ban kyauta ba abinda nayi wa iyayen
Bashir tunda auren daya qara ai ba haramci bane da zance ni bazan zauna da kishiya ba.

Har da wadda take cemun ilimina be amfana mun komai ba ina Karatun islamiyyar da nayi ina Bokon
nawa zan zauna ina ja ina jayayya da abinda Allah ya halasta, ban dagawa ko wace yar iska qafa ba na
kuma roqi Allah duk wadda tace nayi Haquri Allah yasa ayi mata abinda yafi nawa muni idan yaso se taji
in ma rashin tawakkalin me ya sakani yin haka ko yaya.

A cikin wannan yana yi wata rana muka samu baquncin Goggo da tunda aka fara wannan abun sau daya
mukayi magana da ita shima ni na kirata kuma tace mun nayi haquri daga haka bata qara komai ba.

Ina kwance a daki aka kirani a lokacin idan ka ganni se na baka tausayi, na rame na fige fuskata babu
komai daga ido se dogon hanci ina shiga palour idona ya sauka akan Bashir daje zaune a qasa, ban lura
da sauran mutanen da suke ciki ba na hau kansa da masifa ina cewa
“Wallahi ko maye ne kai Bashir haka zaka ganni ka kyale tunda nace banayi banga wanda ya isa ya
tilastani ci gaba da zama da kai ba, ka tashi ka tafi tun kafin nasa azo a fitar dakai mara zuciya kawai”

“Idan baki saka an fita dashi ba baki isa fitsararriya mara mutunchi ba Asma’u” muryar Goggo da ban san
da zuwan ta ba ta katse ni kafin ta ci gaba da cewa

“Ashe duk rashin mutunchi da diban Albarkar da akace kinayi dagaske ne kuma a gaban ku Hajiya kuna
kallo aka rasa wanda ze tsawatar mata. Saboda bakida mutunchi Mijin naki kike sakawa a gaba kina fada
masa irin wadannan maganganun ku to bari kiji shi Allah babu ruwansa ze hukuntaki ne akan laifin ki na
sabawa miji da ci masa mutunci babu ruwan Allah da cewar Bashir ya auro miki wadda bakya so anyi
miki ba daidai ba dan haka tun wuri ki dawo cikin hankalinki kafin ki kanki wuta da qafafunki.

Sannan saboda kin zama yar kanki se abinda kika tsarawa ranki zakiyi shine kike iqirarin zaki kashe
auranki saboda kanki farau kishiya ko kuma kece ta qarshe da za’ayiwa ko?

Ki idan kina da hankali ma ya kamata ki tashi jiniyoyij wuya akan za’a miki kishiya, gidan mu mata nawa
Ubanki ya aura gamu nan mu Hudu ya mutu ya bari kin taba gabin wata tayi tashin hankali da yar uwarta
a cikin gidan nan?”

“Amma Goggon su bazaki hada mu dasu ba, ko bayan haka hanyar da Bashir yabi tayin qarin auransa ce
bata dace ba kuma ko wacce mace akayiwa irin haka dole ranta ya baci ai” Hajia Anjin ta tare Goggo jin
yanda take ta surfa fada, se Goggon ta kalleta tace

“Saboda ya auri yar uwarsa ne take tashin hankali dan ba’a gaya mata ba, ai ba kansa aka fara ba tunda
ubanta ma a sanda ya auro ni ai baku sani ba tafiya yayi bikin abokinsa ya dawo muku da ni a matsayin
kishiya me yasa a sannan ku baku yi tashin hankali kunce bazaku yarda ba?”

“Aa Maryam Allah ya jiqan Alhaji bazaki taba hadashi da wannan yaron ba domin Alhaji Adali ne gamu
nan dukka bari kiji kafin A daura auran ku da Alhaji seda ya kira mu a wayar landilayin da daddaya ko
waccen mu seda ya gaya mana abinda ya faru ya kuma sanar mana da cewa ze aureki bisa wasiyyar
Sama’ila dan haka da yardar mu da Amincewar mu Alhaji ya auro ki, sannan tunda tace bazata koma ba
ai Asma’u ta wuce yarinta bare ace za’a zabar mata abinda zatayi”

Hajia Babba ta fada sauran suka amsa da “kwarai haka aka yi.

“To shikenan tunda kun daure mata gindin tayi duk rashin mutunchin da take so kun bata goyon baya ni
baza’a hada kai dani ba, Ke Asma’u idan na isa dake ki tattara ya naki ya naki yanzu ki bi mijinki, kuma
diban Albarkar da kikayiwa uwarsa da yayarta kije ki basu haquri, dan cikin matan yayyen ki kaf babu
wadda ta taba duban idon mu ta gaya mana maganar banza balle mu yayanmu suje suyiwa na wasu”.

Tunda suka fara mahawarar na durqushe a gurin ina Kuka, wato qarata Bashir ya kai gurin Goggo ita
kuma ta goya masa baya. Da sauri na daga kai na kalleta hankali tashe jin irin umarnin data bani, se nayi
saurin matsawa kusada ita ina cewa

“Amma Goggo...”

“Karki ce mun komai sedai kuman idan kin shirya nuna mun ban isa dake din ba shikenan” ta yi saurin
katse ni, se na mayar da kaina qasa na ci gaba da kuka me ciwo, ya zalunce ni kuma ha hadani da
mahaifiyata Bashir wane irin mugun mutum ne a rayuwa.

Haka naja qaqafuna na koma daki na shiga tattara kayana ina kuka yarana da suka biyoni suna tayani. Ina
cikin hada kayan Hajia Babba ta shigo dakin,

“Ki bar shirin yanzu Asma’u tace ku bari zuwa jibi se ki koma. Kiyi haquri ita rayuwar Ya mace daman
haka da qalubale wata rana komai ze zama tarihi in sha Allahu” haka tayi ta bani baki har seda naji
zuciyata tayi sanyi na kwanta a kan Gado ina saka da cin alwashin irin gashin qumar da zanyiwa Bashir
idan har na koma gidan sa. Shi da sake jin dadin zama dani har abada.

Washe gari Goggo ta koma bayan ta sake yi mun kakkausan gargadi akan idan na sake ta sake jin wani
abu se tayi mummunan saba mun, na koma gidana na zauna kuma duk abinda zan gani naje nayi haquri
karna kuskura na dauki dabi’ar kai qara ko na ce zan sake yin yaji.
“Asma’u badan bana sonki yasa nayi miki haka ba, nasan ba’a kyauta miki ba amma hakan baze zama
silar da zaki bar uban yayanki ba idan kin rabu da Bashir saboda kishiya qarshe dai wata zaki je ki tarar a
duk inda zaki fada to menene amfanin haka” Goggo ta fada cikin lallama bayan da ta gama yimun fadan
kuma, sena share hawayena tunda yanzu ta sakko se muyi magana ta fahimta nace

“Wallahi Goggo ni ba qarin auran sa ko rashin gayamun da beyi bane ya dame ni amma me yasa ze auri
Amirah?”

“Saboda yana sonta kuma ita Allah ya zaba masa kin san dai duk yanda mutum yaso da son kasancewar
abu idan Allah be hukunta hakan ba baze faru ba ko, haka duk yanda ka kai ga qin abu idan Allah ya
qaddara faruwar sa babu abinda ya isa ya tsayar da hakan to kar kiyi jayayya da hukuncin Allah Asma’u,
ki dauka daman tun kafin wanzuwar duniya yanda Ubangiji ya qaddara ke matar Bashir ce haka itama
aka rubuto matar sa ce dan haka dole se ya aure ku.

Maganar munafunci ko yaudarar ki da sukayi wannan ki barwa Allah komai kina zaune se kiga ya saka
miki a ruwan sanyi kinji ko kiyi haquri kar kuma wannan dalilin yasa kice zaki quntata zamanki da mijinki,
a yanzu ne ya kamata kija shi a jiki dakyau ki bashi dukkan kulawa da soyayyar data kamata saboda ba ke
kadai bace, duk abinda ya rasa a gurinki ze same shi a wani gurin daga nan kuma se hankalin sa ya fi
karkata can saboda zuciya ai tana son me kyautata mata ke kuma daga qarshe se kiga kamar dan ya
samu wata ne ya watsar dake bayan ke kika bada damar hakan.

Dan haka bani da damuwa akan ki Ma’uta nasan zaki riqe kanbun nan naki na Uwargida sarautar mata
dakyau ina so ki nuna musu cewa ke din fa badai mutum ba se Allah, Allah yayi miki Albarka ya ci gaba
da kareki a duk inda kike”.

Kalaman Goggo sunyi tasiri sosai a zuciyata dan gaskiya ta fada da ace wata daban aka auro mun
davkuwa tabbas na nuna mata cewa kishi da MA’U ba wasa bane se ta shirya amma a duk sanda na tuna
wa Bashir ya aura se naji bazan iya amfani da ko daya daga cikin abinda ta fada din ba.

Haka ta koma Yola washe garin ranar nima yan uwana suka raka ni gidan mu na Gombe bayan da suka
hadu suka sake yi mun nasiha da rarrashi, banje na bawa su Dada haquri ba itama kuma Goggon bata
tsananta ba tunda na yarda zan koma din ta rabu dani.
Gini yayi kyau sosai kuma an saka komai na amfani sabo daga yanayin kyau da tsaruwar kayan na
tabbatar da aikin Yan gidan mu ne sunyi zumunchi sosai suka hada mun gida kamar na wata sabuwar
Amarya ko tsohon lokaci nada ba’a saka a gidan ba.

Yanda kowa ya ringa yabawa ni kuwa baqin sa nake gani dan da gidan da mamallakinsa a yanzu basa
gabana ko kadan biyayyar iyaye ce ta dawo dani cikinsa.

Bayan kowa ya watse Bashir ya shigo yanda kasan wasu Baqin da basu taba haduwa ba haka muka zama,
shi yana kaffa kaffa dani karya yi abinda ze zama laifi ni kuma na baiwa Banza ajiyarsa ina ta sabgogina se
shi da yaransa yake ta magana yana tambayarsu abubuwan da suke buqata wanda sarai nasan dani yake
naji dadi da suka ce masa babu.

Su kansu yaran daga kan Amna zuwa Farida ba wani sakewa sukayi dashi ba Abdallah da yan biyu ne
babu abinda ya sha musu kai suke ta murna sunyi kewar Abbi. Aliyu daman yafi kowa daukar zafi, kuka
ya ringayi da gaske lokacin da yaji maganar auran ya kuma dauki fushi da uban ko yau din da muka dawo
ina kallon yanda yake cika yana batsewa.

Da daddare gurin qarfe tara muna zaune a palourn qasa muna hira muka ga an bude qofa, da yake irin
wadda bata buduwa ta wajen nan ce nasan Bashir ne shine yake da key dan haka ban ko kalli qofar ba na
sake hada rai na zubawa TV ido.

Da sallama a bakinsa ya shigo, takun qarar takalmin da naji bayan muryarsa ya saka na waiwaya da
mamakin naga shi da waye haka karaf idona ya sauka cikin na Amirah data sha Kwalliya da wani Material
Cotton baqi me Pink din flowers dinkin riga da skirt sun kamata dam se wani dan yalolon gyale data yafo
a kafada.

Cikin abinda be wuce second biyar ba na qare mata kallo na mayar da kaina zuwa ga TV ina nanata
“La’ilaha illah anta subhanaka inni kuntu minzzalimin” a zuciyata saboda jin wani abu yana tasomun
kamar zanyi aman zuciyata har wata zufa naji tana tsatstsafo mun.

Ta gefen ido nake kallon sanda suka zauna akan kujera, ina jin qamshin turaren data saka ya baza gurin
irin turaren da nake amfani dasu ne na Maryam collection ta zauna a kusa da Bashir sosai kamar zata
shige jikinsa shi kuma se turata yake yi abin ma se ya bani dariya na dan yi murmushi a raina nace “yaro
yaro ne” amma ban ko juya na kalle su ba.

Ina jin yaran suka hada baki suka gaishe shi ya amsa a zatona zasu gaida Amirah se naji dif sun ma mayar
da hankali akan film din da muke kallo Bashir da qarfin hali naji yana cewa wai

“Baku ga Antyn ku ba baku gaisheta ba”

“Wacece tana ina ai mu kai kadai muka gani Abbi se Amirah” Aliyu ya fada yana kafe uban da kallo
wanda mamaki ne nasan ya hana Bashir din magana. Yanda kasan bana gurin haka nayi musu dayake
film din yazo qarshe ana gamawa yaran suka miqe dan daman abinda ya zaunar da mu kenan nima se na
shiga qoqarin miqewa Bashir ya dakatar da ni da cewa

“Ma’u ina kuma zaki je gurinki fa muka zo” sena koma na zauna na waiwaya ina kallon sa da murmushi
akan fuskata wanda a badini kuka nakeyi cikin zuciyata amma nayi Alqawarin wannan yarinyar bata isa
taga gazawata ba, se a yanzu nima na dawo hayyacina tabbas idan na bar mata gidan ta ci galaba akaina
dan haka zan zauna kuma ba zaman dadi ba kowa se yaji a jikinsa.

“Amirah baki gaida Antyn ki ba “ ya fada bayan dana zauna, Amirah da ta hada fuska bakin nan kamar ze
tabo POP tace “Nima ai yayanta basu gaishe ni ba, kana ji fa wannan marakunyar Aliyun cewa yayi ma be
ganni ba kuma baka ce komai ba”.

Dukda qasa qasa tayi maganar amma tsaf naji ta a raina nace “zanci uwarki ne yarinya mu dai ke zuwa”.

Kamar me jira kuwa l Bashir ya hau masifa yana fada mata maganganu, abin haushi abin dariya dramar
tasu ganin abin bana qare bane na miqe nace masa

“Ka rufe mana qofar idan kun fita” ban ko saurara ba na haye sama na barsu a gurin. Har na kwanta
Bashir ya shigo dakin, da saurin gaske ya nufoni kafin ya qaraso na dire daga gadon ban yi wata wata ba
na izge Fitilar gefeb gadona daga soket na daga ta na nuna masa ina cewa
“Wallahi ka kuskura hannunka ya tabani sena yi maka rotse da wannan, badai ka hadani da Goggo ta
tilastani dawowa gidan ka ba, ka tabbatar da ka kaiwa tashin hankali katin gayyata da hannunka”.

Yanda nayin ya tabbatar masa dagaske idan ya matsa zan iya kwada masan, daga nesa ya ringa yi mun
magiya da nayi haquri na saurare shi amma nayi masa banza haka ya qaraci nacinsa ya fita ya bar mun
dakin.

Haka muka ci gaba da rayuwa a gidan tsakanina da Bashir daga kallo se harara shi kuma kullum yana nan
a lalace gurin roqona da bani haquri amma nayi kunnen uwar shegu dashi dukda qasan raina na fara
hucewa bafa wai dan na manta da abinda yayi mun ba Aa sedai kawai na yarda cewa komai muqaddari
ne a rayuwa daman tun a lauhul mahfuz an rubuta faruwar wannan al’amari a rayuwar mu.

Kusan sati biyu ranar ya same ni da batun komawa Lagos saboda hutun daya dauka ya qare, a lokacin
bani da zabi kodan aikina da makarantar yara da suke zaune a gida ya kamata na koma sannan hakan ze
dada nisan tani da Amirah dukda ko a yanzun ma tun ranar farkon suka shigo bamu sake haduwa ba.
Haka muka fara shirye shiryen tafiya, ana i gobe zamu tafi ban san meya shigar da Ahmad bangaren ta
ba se kukan sa muka jiyo a waje Amna ta tafi da gudu ta dakko shi ina duba fuskar yaro naga shatin yatsu
da alamar marinsa akayi.

Cikin tsananin bacin rai na tambayeshi waya mare shi, yana kuka da maganar sa da bata gama fita ba
yace “Anty Amirah ce, da safe Abbi ya nuna masa gurin yace tana ciki shine yaje suyi wasa (Sun saba
tana wasa dasu) saboda na zubar da Tea ban sani ba ta mare ni”.

Zan dauki komai amma banda taba mun yara musamman ma ya zamana da cin zali amma tayi kadan
dana taka gurinta nayi mata kashe di dan haka zan jira wanda ya ajiyeta yazo shine daidai yina. Da
yamma Bashir ya dawo, yana shigowa Ahmad din ya tafi gurinsa da gudu ya fashe da sabon kuka yana
gaya masa abinda ya faru.

“Ka ja mata kunne karta kuskura ta sake taba mun yara idan ba haka ba zan dauki mataki” na fada ba
tareda na kalle shi ba. Se ya juya da Ahmad din a hannunsa suka fita ban san me yace mata ba dab da
magriba dan har nayi alwala naji ana buga qofa.
Farida nacewa taje ta bude, tana budewa kuwa ta turo qofar da qarfi dan qiris ya tage ta buge Faridan,
seda ta qaraso tsakiyar Palour ta wani tsaya ta kama qugu tace “Saboda munafunci shine za’a hadani da
Mijina dan na daki yaro, ai barna yayi mun kuma ko yanzu wani ya sake zuwa yayi mun wani abu se na
daka yaro sedai duk abinda za’ayi ayi, mtsw aikin banza kawai...” ban bari ta kai qarshen rashin kunyar
tata ba na kai mata wani bahagon mari cikin sa’a na sameta dakyau na doke bakin fitsarar take kuwa
leben ta ya fashe kafin ta gama gane abinda ya faru na sake kai mata wani ta dama ta fasa qara ta dafe
kunci dama da hagu tana ihu daidai lokacin Bashir ya shigo.

Ban damu da shigowarsa ba ko ihun da takeyi na nunata nace “wannan gargadi nayi miki duk ranar da
kika sake tako qafar ki gurin nan ki qaddara ma gaisuwa ce ta kawoki ba wai kinzo yimun fitsara da
rashin kunya ba wallahi se nayi miki dukan da zaki kasa tashi, wawiya mata hankali kawai” na juya na
haye sama Bashit yabi bayana muka barta a gurin tana zunduma ihu.

“Ma’u meya faru” ya fada bayan daya tarar dani”

“Kaja mata kunne tafi kowa sanin ni ha sa’arta bace idan tana ji da rashin kunya da fitsararta ni daidai
nake da ita zan koya mata hankalin da bata dashi” na juya na tayar da sallah ta na barshi a tsaye.

Washe garin ranar muka koma Lagos, Sanda muka je na tarar Bashir ya sake gyara mana palour an
chanza komai na ciki, sannan ga sabuwar mota me kyau model din shekarar a ajiye a inda nake saka
mota ta, lambar jikin tsohuwar tawa dana gani a jiki ya tabbatar mun da tawa ce.

Haka ya ringa yi mun abubuwa har makaranta ya chanzawa yara ya mayar da su wata da tun farko naso
a saka su yace tayi tsada abubuwa dai kala kala wanda duk na neman shiri ne, daga qarshe dai bayan
dogon jan rai da ban haquri dana sha kala kala daga gurin Bashir na haqura na sakko muka dawo zaman
mu lafiya badan na manta abinda yayi mun ba sedan ban isa na jada hukuncin Allah ba.

Iya horon da zan yi masa nayi ya kuma sauke kai ya bani haquri da tarin alqawarurruka kala kala
Albarkacin son da nake masa da dattijantakar mahaifinsa ga kuma Alfarmar Mahaifiyata daya shiga na
cire komai daga zuciyata ta na nemi muqulli na kulle wancan baqin littafin na rayuwar mu muka bude
sabon babin rayuwa me cike da qauna da Aminci, haka rayuwa taci gaba da gara mana yau fari gobe baqi
har kawo wannan lokacin da me afkuwa ta afku, Bashir ya yanke igiyoyin auran mu a lokacin dana gama
ammana da bashi rayuwata.
CiGaBaN LaBaRi

Afuwan Uzuri ya riqeni kuyi manaji da wannan

WATA KISHIYAR

(ALKAHIRI CE KO SHARRI)

Na Maryamah Farouk

(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)

Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 40

CiGaBaN LaBaRi

Sosai kaina ya dauki ciwo har ina jin kamar jiri ne yake dibana daga zaunen se kawai na sulale akan abin
sallar na kwanta tareda duqunqune jikina cikin hijabi, Hawaye ne ya silalo daga idona nasa gefen hijabin
na share tareda jan majina.

Ina sha Allahu na gama kuka akan Bashir, tun a baya ya kamata na fuskanci cewar ba nice a gabansa ba
ya aureni ne saboda wata buqata ta qashin kansa amma na ringa yaudarar kaina da cewa Bashir yana
sona.

“Bashir na sonki Ma’u akwai dai wani Al’amari daya tilasta faruwar hakan amma Bashir baze sake ki yana
cikin hayyacinsa ba” bangaren zuciyata wanda ya bawa Bashir Amanna dari bisa dari ya raya mun, se naji
kamar sauran bangaren na zuciyar tawa sun karbi wannan batu, girgiza kaina nayi a fili nace
“Ina baze yuwu ba, ban kai wannan lalacewar ba, Bashir ko kaine Autan maza in Allah ya yarda na gama
aure da kai, ko son ka ze kashe ni sedai na mutu da na sake zama dakai” se kuma na Fashe da kukan dan
kasa dakatar da kaina.

“Mami kiyi haquri ki dena kuka” Amna da bansan lokacin data farka ba ta fada tana dafani, sena tashi
zaune na janyota jikina na rungumeta na sake fashewa da wani kukan na gaske dan daman ina da
buqatar wanda ze rungumeni nayi kukan. Seda nayi me isata kafin na rarrashi kaina zuwa sannan itama
kukan takeyi.

Na tashi dakyar ta kamani na shiga bandaki nayi fitsari tareda sake aabuwar Alwala kafin na fito ta
shimfida mun bargo akan inda na tashi dan nace bazan hau gado ba.

Ni kadai na ringa juyi a qasan dan ko kusa bacci beyi alamar daukata a daren ba ga wani ciwon mara
dayake taso mun idan ya murda se ya lafa nasan baze rasa nasaba da halinda nake ciki ba shima dan
cikina yana tayani baqin ciki.

Da safe qarfe shida Anty ta kirani akan Aliyu da Jafar suje su karbo musu abin karyawa, qarfe bakwai da
yan mintina sun gama shirin su tsaf na tafiya makaranta na dakko muqullin mota na bawa Aliyu kenan
dan Antyn ce zata kaisu muka ji ana dannan Door bell,

“Kuje maza inaga ga Antyn can karku makara” na fada da kyar dan dauriya kawai nakeyi ni kadan nasan
abinda nake ji a jikina dama zuciyata gaba daya. Suna fita Amna data tafi rakasu ta dawo da sauri tace
mun

“Mami Abbine” dukda yana yin danake ciki haka na miqe a fusace nabi bayanta in ga dalilin daya kawo
shi, kafin na fita har yaran sun gama shiga mota banda Aliyu daya kafe daga qofar gida na tarar uban
yana cewa “bazaka zo ka shiga mu tafi ba kana bata mana lokaci”

“Ni ku tafi kawai bazan je tareda kai ba” Aliyun ya fada kai tsaye ba tareda ya kalle shi ba, Bashir ze sake
magana nayi saurin katse shi da cewa “sauke mun yara malam waya nemi taimakonka bare kace zaka kai
min su makaranta, ke Farida ku fito ga Anty nan zata kaiku” daidai sannan Anty ta qaraso gurin.
Ko kallon inda nake Bashir beyi ba sema fada daya balbale Aliyu dashi akan yazo su tafi amma yaron nan
ko gezau yana tsaye, a fusace ya nufo shi da niyyar ya jashi nayi saurin shiga tsakiyar su, zanyi magana
Anty tace mun

“Ya isa Asma’u ku dena haka a gaban yara, kai Aliyu wuce ku tafi ke kuma muje ciki”.

Kallona Aliyu yayi, cikeda takaicin abinda Antyn tayi mun na daga masa kai alamar yaje Bashir yayi kwafa
ya shiga motar shima yaja suka tafi kafin Anty ta kama hannuna muka shiga gidan.

“Haba Anty me yasa zakiyi mun haka akan wanne dalili zan bashi yarana ya kaimun su makaranta”

“Asma’u kenan, ke Bashir ya saka amma na fiki jin takaicin abinda ya faru. Yara kuma karki manta fa
yayansa ne babu yanda za’ayi ki rabashi dasu baya ga haka yanzu nema zaki sakar masa nauyin su dan
wallahi daidai da gishirin da zaki zuba musu a abinci daga yau se Bashir ya siya. Duk wani abu da Uba
zeyiwa Yayansa dole ki bar masa yayi musu yanzu taimakon da kikayi masa a da saboda kina matarsa ne
yanzu kuwa bazaki ci gaba da kular masa da Yara ba tunda ya sake ki.

Yanzu ki tashi kije kiyi wanka bari na koma na dakko miki naki abincin toh kici se muje Asibiti bakiga
yanda kika zabge a dare daya ba dan Allah ki saki zuciyarki Asma’u abinda ya faru ya rigada ya faru sedai
mu kiyaye faruwar na gaba kuma”.

Haka ta fita ta barni, na miqe nima duk zuciyata babu dadi na shiga wankan, sanda na cire pant din jikina
naga kamar jini jini a jiki daman tun dazu naji kamar zubar abu daga jikina amma ban mayar da hankali
ba, haka nayi wankan na fito a sanyaye.

Doguwar riga na saka na zumbula hijabi kamar me takaba, ko turare ban iya sawa jikina ba na dawo
palour na zauna shiru ina jin marata na mintsinina na hada kai da guiwa kai baka ce nice Ma’un nan yar
kwalliya da kyale kyale ba.

Tare suka dawo gidan da Baba, be zauna ba daga tsaye yayi mun sannu ya sake yi mun gajeriyar nasiha
ya wuce gurin aiki bayan ta raka shi ta dawo ina nan na rafka uban tagumi.
Se da Anty ta takuramun kafin na iya shan shayi ina kurbarsa kamar madaci haka nake jin sa a bakina,
duk sona da dankali gashi yana tururi har wata hanta ta gasa mun se qamshi suke yi amma yau banji sun
burge ni ba bare naci se faman bani baki takeyi nidai jin ta kawai nake amma hankali na yayi nisa da inda
muke.

Sallamar Yaya Abubakar ce ta dawo dani hayyacina. Cikin mutuntaka suka gaisa da Anty Halima yana ta
yi mata godiyar yanda take kulawa dani tace babu komai ai ani qanwarta ce.

“Ma’u yaya babu dai wata matsala ko” ya fada bayan dana gaishe shi, sena ajiye kofin hannuna nace

“Babu komai Yaya amma fa shi ya tafi da yaran makaranta, nifa Yaya ka gaya masa babu ruwansa da
yarana kawai ya fita a sabgar su”.

“To in banda abinki Asma’u an taba raba yara da ubansu ne Bashir fa kin rigada kun hadu dashi babu ta
yanda za’ayi ki raba. Maganar kuma ya dena shiga sabgarsu ai bata taso ba dan yanzu nema ze shiga
lamarinsu sosai, and ki sani in har kika nuna masa qulafucinki akan yaran nan da wannan damar zeyi
amfani ya ci gaba da quntata miki idan kuma ba kin shirya komawa masa kici gaba da karbar wulaqanci
ba shine seki dage kuyita rigima akan yaran dan haka tun wuri ki cire maganar yara a ranki, ko dauka
dake ko babu ke zasu rayu kuma babu abinda ze same su se wanda Allah ya qaddara

“Abunda nake gaya mata kenan nima ta cire wani zacen yara a ranta tunda ma gaki gasu ko ya karbe su
fa kamar kuna gida daya ne dan be isa yace ze kullesu ya hanasu zuwa gurinki ba haka kema idan a
hannunki suke bazaki hanasu zuwa gurinsa ba.

Ni nan da kika ganni ai kin sani tawa uwar tun ina shekara uku ta fita daga gidan mu ta barni ina
watangaririya a tsakar gida tsakanin matan uba babu takamaiman mariqiya sannan Babanmu ma bame
jan yara a jiki bane bare na samu gatansa uwa ta kuma tayi mun nisa a lokacin Maradi ta tafi tayi aure
seda na girma na mallaki hankalina sannan na je inda take amma ba gani ba ban mutu ba babu kuma
abinda ya same ni, dan haka ki share komai Ma’u ki bi yaranki da Addu’a ko a hannunki ko a hannun
ubansu Allah ya kula miki dasu”.
Haka suka hadu sukayi ta yi nidai jin su nakeyi amma bana zaton akwai abinda za’a fadamun da zesa na
barwa Bashir yarana, saki dai na saku amma fa dole abarmin riqon yarana koda kuwa ze sakar mun
nauyin su gaba daya zan dauka zanci gaba da kulawa dasu.

Wayata dana bari a daki Amna ta kawo mun ana kira, Yaya Bilki ce na daga wayar na saka a kunnena.

“Asma’u abinda ya faru kenan? Yanzu Anty Suhaima ta kirani take gayamun amma wallahi Bashir ya cika
butulu wanda besan halacci ba” ta fada cikin sanyinta, se nayi murmushi kawai nace “hmm” dan ban san
abinda zan ce mata ba.

“Amma Goggo bata sani ba, Alhaji Qarami yace kar a gaya mata ze kirata da kansa saboda kin san
yanayin jikinta yanzu be kamata a gaya mata abin tashin hankali ba” ta sake fada, daga nan mukayi
sallama tana sake jaddada mun da nayi haquri.

“Ki tashi yanzu ki samu ki kwanta dan da ganin fuskarki bakiyi bacci ba, nima zanje yanzu yau zan qarasa
aikin da nazoyi zuwa dare zan dawo In sha Allah” Yaya Abubakar ya fada yana miqewa yayi mana sallama
ya tafi.

Mintina kadan Anty tace itama bari taje gida ta dan kintsa guri kafin masu daura gadon su dawo a gyara
dayan dakin, sena miqe ina cewa “Bari na kwanta a nan toh, Amanah zoki kwashe kayan nan ki saka su a
Kitchen” na nufi kujera da niyyar kwanciya Antyn tayi saurin dakatar dani tana cewa

“Tsaya Asma’u karki zauna kinyi staining”.

Da sauri na juyo da hijabin jikina na duba, se kuwa ga Jini nan sosai a jiki da yake ruwan qasa ne me
haske gabana ya yanke ya fadi dan ba period bane sedai idan cikin jikinane yake zuba, yanda taga rikice
ne ya sakata cewa

“Lafiya Koda matsala ne?”


“Akwai matsala Anty muje Asibiti dan Allah kafin cikin ya samu matsala”.

“Ciki kuma daman ciki ne dake” Anty ta fada cikin mamaki, ban Amsa taba na wuce daki na canza riga da
hijabin jikina muka fita.

Clinic din da yake cikin estate din mu mukaje dan gani nakeyi kafin mu kai Asibitinda nake zuwa ai cikin
ma ya gama zirarewa. Muna zuwa suka dauki jinina kafin Likita yace na kwanta yayi mun scanning,
“incomplete abortion” yace, ina ji ina gani suka sakamun wata kwaya, ban wani ji ciwo sosai ba saboda
cikin qaramine sosai cikin dan lokaci abinda yayi saura ya fita akayi mun allurai suka bani magunguna
muka wuce gida.

Banji dadi ba dan dagaske na kwallafa rai akan cikin nan, Amma na fawwalawa Allah dan shi kadai yasan
dalilin yankewar igiyar aurena da Bashir a jiya sannan ya taqaitamun iddarsa a kwana daya kacal, Allah
yasa hakan ya zama Alkahiri a rayuwar mu gaba daya.

Haka na wuni ranar jikin quncin zuciya musamman da abin ya zamar mun duka biyu, Qarfe hudu motar
makaranta ta kawo yara kafin sannan har An dakko gadajen su Aliyu Anty ta gyara musu dakin, kayan su
da ba’a gama jerawa ba jiya suna qarasa komai ita da Amna nidai ina kwance a daki ina ta faman tunane
tunanen makomata tunda dai yanzu na tabbatar da aure tsakanina da bashir ya qare ko a gobe ina iya
daura sabon aure.

BASHIR

Bacci ya kwasa sosai tamkar babu wani abu daya faru, qarfe biyar na asuba ya farka, ganin babu Ma’u a
gefe yasa ya zauna yana jiran ta fito daga bandaki shima ya shiga yayi Alwala dan an kusan shiga sallah,
seda ya shafe kusan minti goma a zaune jin shirun yayi yawa yasa ya miqe ya kwankwasa qofar yana
cewa

“Wai me kike tayi ne har yanzu baki fito ba so kike sena makara ko..” yai shiru ganin qofar ta bude amma
babu kowa a ciki, tsaki yayi ya shiga ya dauro Alwala ya fito, se daya kunna fitila yaga yanayin da dakin
yake ciki sannan kwakwalwarsa ta tariyo masa abinda ya faru jiya.
Idan yace beji komai ba yayi qarya, haka ya zura jallabiyya ya kama hanyar masallaci shi kadai duk se yaji
wani iri dan ya saba tareda Aliyu Jafar da Abdallah suke zuwa.

Haka ya dawo gida ya zauna a palour ya dafe kansa, yana so ya ga rashin kyautawar abinda yayi amma
zuciyar data ingizashi tayi qoqari ta kare komai ta yanda laifin Ma’u yake ci gaba da gani har yanzu.

“Wai ma me tayi mun ne?” Ya tambayi kansa, bashi da me bashi amsa ga guilty consciousness (na manta
fassarar da hausa ) yana neman kama shi se kawai ya miqe ya shiga wanka dan baya so ya bawa
zuciyarsa wata dama da zata sa ya zargi kansa da laifi(Yawwa na tuna 😂), haka yayi wanka ya shirya yana
ta tsaki, ga kayan duk a watse haka ya tsinto wadanda ze saka ya shirya ya sake fitowa palour, babu
abinci haka ze riqe yunwarsa idan yaje office yaci gashi daren jiyan ma ba wani abin kirki yaci ba.

Bayan ya dauki yaran suna tafe a zuciyarsa yana ayyana da sun dawo dole su koma gidansu, kwana daya
kenan ta fara saka musu wani abu a zuciyar su a kansa inga ya barcmata su qilan wata rana suce ma ba
shine ubansu ba, haka ya sauke su a makaranta ya wuce office, seda ya fara tsayawa Cafeteria ya siyi
abinciya zauna ze fara ci kenan Amirah ta kirashi dan yanzu kira sau ukun nan rana safe dare setayi masa
sun gaisa.

“Ina cin abinci idan na gama zan kiraki” ya fada bayan da suka gaisa.

“Kai amma yau ka makara har yanzu baka fita ba takwas ta wuce fa ko hutun naku be qare ba?”ta fada
da mamkin jin wai abinci ma yake ci yanzu,

“No ina office, acan nake karyawa yau” ya fada kafin ya kashe wayar, yasan yanzu ci gaba zatayi dayi
masa tambayoyi. Ilai kuwa yana hanyar shiga office dinsa bayan ya gama cin abincin ta sake kira, kamar
ma baze daga ba amma daya tuna yana so ya gaya mata ta shirya idan so samu zuwa jibi zata taho seya
daga wayar bayan daya zauna akan kujerar sa.

“Ya akayi Yau Anty ta barka kaje cin abinci a office kuma ko bata nan?” Ta fada da son jin gulma. Ba
amsa mata ba yace
“Ki fara shiri zuwa jibi zaki taho nan”.

A bazata abin yazo mata dukda tasan da zancen komawar amma bata zata da wuri haka ba kuma ya
akayi ma Ma’u ta yarda da tsarin ko kuma gida ze raba musu dan haka cikin murna tace masa

“Har an samu gidan ne Yaya ko Anty ta yarda zata dawo nan ita?”

Shiru Bashir yayi, abin ya masa nauyi a zuciya yana kuma buqatar wanda ze fadawa yaji sanyi dan haka
besan sanda bakinsa ya subuce yace mata

“Bama tare yanzu mun rabu da Ma’u”.

Duk yanda Amirah take cikin farin cikin maganar tafiyarta lokaci daya komai ya tsaya mata, “Yaya kun
rabu ka saki Anty kake nufi Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un a garin yaya” ta fada tsakaninta dan Allah dan
ko kusa ko alama ba abu bane data taba hasaso faruwarsa.

Dukda take kishi da Ma’u bata taba yi mata fatan a saketa ita ta zauna ba, tasan irin so da qaunar dake
tsakanin Bashir da Asma’u tun tana yar yarinya bata taba hasaso wani abu da ze kawo rabuwarsu ba
idan ba mutuwa ba.

Gaba daya ma seta rasa me zata ce masa, haka sukayi sallama jikinta a sanyaye ta ajiye wayar tana ta
jimanta abin a ranta.

“Ke kuma lafiyar kika rafka taguma kamar wadda ubanta ya mutu” Addah data shiga dakin ta ajiye kayan
shanya ta fada tana kallon Amirah, se Amiran ta janye tagumin da tayi tace

“Uhm Addah wani abun tashin hankali Yaya yake gayamun yanzu wai ya Saki Anty”.
“Amma ban taba sanin ke dai Asararriya bace sallamammiya se yau Amirah, saboda an saki kishiyar ki
shine kika rafka tagumi kamar wadda akacewa Murtala ya mutu, to dan uwarki idan ba’a saketa ba ke
taya zaki samu fawa a gurin miji kullum kina rabe kamar wata mara galihu wannan ai abin kiyi rawa kiyi
shewa ne ta tafi ta barmiki gida kiyi yanda kika ga dama bari ma ki gani” ta taqarqare ta rangada guda
tace

“Allah na gode maka mun yada kwallon mangwaro mun huta da quda, ai wallahi daman duk wanda yaci
tuwo dani miya yasha, seki fara shiri yaushe zaki tafi can din yanzu?”

“Wai jibi yace Addah” ta fada a sanyaye dan fa ita bata ga abin farin ciki da sakin Ma’u ba.

“Toh bari kiga in bazama karbo taimako, idan da wasu kudi a hannunki ki kawo na hada naje can qasa
gidan su Mero wasu yan haya sun shiga tace mun matar tana bori kuma ta iya aiki bari kiga naje na
karbo miki maganin kafi dana mallaka, ai yanzu za’a fara wasan ita kanta Nafi seta gane shayi ruwane
wallahi” ta yayimi hijabi tayi waje tana ci gaba da handala an saki Ma’u.

Amirah na zauna tana ci gaba da jimaminta Sa’adaha ta shiga gidan, itama dai kamar Addah harda
gudarta tace

“Yo ke Allah ne ya kashe ya baki se ki tashi a tsaye da kissa da kisisina ki riqeshi gam wallahi, ki kuma san
duk yanda zakiyi kar a bar miki yara dan dasu zakiyi zaman kishin in bata nan ki zugashi ya bata yaranta
can su qarata ke kuwa ki samu guri ki zuba isar ki yanda kike so bakiganni ba shida yaransa se dai in sun
hadu a gidan Hajiyarsa su ganshi, da kisisina na hana ya dakko su ban kuma fito fili na nuna bazan riqesu
bane ba idan mun hadu se inyi ta jansu ina yaushe zasu zo mana a gefe shi kuma nayi duk yanda zanyi ko
ance su kwana baze barsu ba to kema haka zaki zama dole ki koyi wayo da dabara shine zakici ribar zama
dashi.

Haka ta ringa yi mata famfo da hudubar tsiya Amirah kuwa ta hau kai tayi zaman dirshen nan da nan ta
ware Sa’adah ta kwaso mata tarkacen magungunan mata sannan suka fita kasuwa ta sissiyo wasu
abubuwan dan ya tura mata da kudi bayan sun gama waya.
Addah kuwa daga gidan yar Borin gidansu Dada ta wuce. A tsakar gida ta saka kujera yar tsuguno Bayan
data karbe Lemo me sanyi data gani a hannun Naziru ta kwankwade tas ta yarda robar kafin ta kalli Dada
tace ke

“Ke Nafi na taba ki da arziqi”

“Meya faru Addah, tunda kika shigo daman fuskarki ta nuna akwai labari me dadi”.

“Ki bari kedai, bana dai Allah ya taimake mu, mun yarda kwallon magwaro mun huta da quda” ta fada
tana washe baki,

“Toh fa ban gane ba wane wane gwallon mangwaron aka yar?” Dada ta fada tana gyara zama.

“Bashir mana Allah ya rabashi da alaqaqai an sakar mana kurwar Da m ya saki Asma’u”.

Kamar saukar Aradu haka su Dada sukaji maganar, seda ta kalli dakin Alhajin su Bashir tana fatan ace
bacci yakeyi dan da ta san zancen da Addah tazo dashi kenan bazata bari suyi shi anan ba, cikin qasa da
murya tace

“Addah wannan wace irin magana ce babu dadin ji haka shi Bashir din ne ya gaya miki ko wa?”

Addah kuwa qara gyara zamanta tayi ta ware murya tace “Ke dagaske fa dazun nan ya kira Amirah yace
ta shirya jibi zata tafi dan ya saki Asma’u kinga baya zauna gida babu mace ba kai Naziru be gaya maka
ka siya mata tikiti bane” ta qarasa tana kallon Naziru da yayi mutuwar tsaye.

“Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un, Hasbunallahu wani’imal wakeel Amma Bashir Amma Bashir kai Jama’a
wannan abu da me yayi kama” Dada ta kwashi salallami tana juya hannu hankalinta idan yayi dubu ya
tashi, se Addah ta saki baki tana kallonta tace
“Ke ban gane ba, murnar ce tasa kika rasa abin fada ko kuwa tunda dai naga wannan ai abinda muka
dade muna buri ne ko yanzu Allah ya tabbatar mana, kin gani ma yanzu naje na karbo abubuwa. Wannan
Mantau ne yanda tunaninsa ze shafe baze ma tuna da wata Ma’u ba, wannan kuma kafine da Mallaka na
ita Amiran dan kin san ba haqura fa Asma’un nan zata yi ba yanzu se kiji zata dawo tunda bamu san saki
nawa ya mata ba Allah ma dai yasa uku ne muga ta tsiya”.

Dada dai ba bakij magana, ga tashin hankalin saki da akace an yi ga wannan barbada da Addah takeyi ta
tabbatar duk a kunnen Alhaji Amadu, ita kuwa Addah ta gama su badadinta ta saka Fainusa da duk
jikinta itama yayi sanyi zubo mata abinci.

Ta tabbatar Alhakin abinda su Dadan suke yiwa Asma’u ne Allah ya ke rama mata akanta gashi nan tana
zaune kusan shekara biyar a gida bayan da kishiya taci ubanta sannan aka sakota, dakyar yanzu ta samu
wani suka daidaita gashi yanzu wannan ta kuma bullowa qila akanta zasu sake ganin wata sakayyar ita
dai tsakaninta da wannan Addah se Allah ya isa kawai.

Ayi maneji kafin zuwa dare in sha Allah

WATA KISHIYAR

(ALKAHIRI CE KO SHARRI)

Na Maryamah Farouk

(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)

Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 41
Addah tana cin abincinta tana sake gayawa Dada da tayi zugudi yanda za'ayi. Da tasan halin da Dadan
take ciki a sannan ma da tayi shiru tuntuni. Seda ta kwashe abincinta tas tayi gyasa kafinta dauraye
hannunta tana cewa

"Kinga kirashi muji zancen sakin nan da kunnen mu karma qarya shegiyar yarinyar can takeyi kinsan fa
daman ta iya ta, qilan dan fada sukayi kar mu gama murna muji sabon labari".

"Nidai Addah da kin tashi kinje gida kawai daga baya mayi magana" Dada ta fada tana waiwayen dakin
Alhajin su Bashir daidai lokacin kuwa ya turo kekensa ya fito daga dakin.

Fuskarsa ba yabo ba fallasa suka gaisa da Addah, ba tareda ya ko kalli inda Dada take ba ya kira Naziru
daya kafe a guri daya kaman gunki yace ya kaishi waje.

A qofar gidan kuwa bayan Naziru ya ajiye a gurin da yake zama suyi hira da mutanen sa se ya kalli
Nazirun yana murmushi yace

"Kaji abinda uwarku da yar uwarta suka aikata ko? Ni sam ba wannan Nafisan na aura ba ban kuma san
lokacin data zama me son kanta da son zuciya irin haka ba. Amma shikenan, suma ai sun haifa".

"Kayi haquri Baba" Naziru ya fada,

"Kai zan bawa haquri ai Naziru ku da Allah ya jarraba da uwa mara tunani, kuyita Addu'a Allah ya tsare
ku da fadawa hali irin wanda dan uwanku yake ciki dukda shi da kansa ya jefa kansa ba wani ya aike shi
ba, idan kuwa harta tabbata Bashir ya rabu da yarinyar nan, hmmm Allah dai ya rufa asiri" Baba ya fada
yana zaro kudi a aljihunsa ya miqawa Naziru yace

"Karbomin katin Mtn na kirashi naji, wayata babu kudi".

"Bari na tura maka ta Banki Baba" Naziru ya fada sannan yayi masa transfer katin ya danna wayar Bashir.

BASHIR
Se da gabansa ya fadi da yaga kiran Alhajin su dan muddin ba abu me matuqar muhimmanci ba Alhajin
baya kiransa sedai shi Bashir din ya kirashi.

Yasan kiran baze rasa nasaba da maganar sa da Ma'u ba labari yaje musu kuma wannan yarinyar ce zata
fada dan se daga baya ma ya shiga dana sanin me yasa ya gaya mata? Dukda ko ba yanzu ba ai dole
zasuji amma qila se kafin sannan ya gama daidaita komai.

Be daga ba seda wayar ta katse yabi bayan kiran a ransa yana shirya abinda ze fada masa.

"Barka da Rana Baba" Bashir ya fada bayan da Alhajin ya daga wayar, se ya mayar masa da cewa

"Barka dai Muhammadu ya aikin ya iyali?"

"Duk suna lafiya Baba, muna cikin aiki ne ma yanzu idan ba damuwa zuwa anjima idan muka fita sallah
sena kira" Bashir ya fada yana goge zufar da tafin hannunsa yayi a jikin rigarsa, Allah yasa ba wannan
maganar Baban ya bugo suyi ba dan besan me zece masa ba

"Ai maganar tawa gajeriya ce tambaya daya ce zan maka seka ci gaba da aikinka, shin dagaske ne ka saki
Asma'u?" Maganar Baban tayi masa dirar mikiya nan da nan ya fara in ina kamar wani sabon kurma duk
yabi ya rude, dakatar dashi Baban yayi da cewa

"Nutsu mana Malam Bashari tambaya ce fa me amsa da Eh ko Aa amma duk ka rikice kamar wanda
Alqali ya titsiye, kaga aiki kakeyi ka amsamin na kashe wayata shikenan".

Yanda yayi maganar a dake ya tabbatar wa da Bashir ba a cikin lokacin wasa yake ba, dan haka dole ya
kama kansa kamar qaramin yaro yace

"Eh Amma..."
"Riqe bayaninka ai ka amsamin, yanzu dai ina so naji ka tuna rabar daka zo mun da zancen zaka auri yar
gurin Fattu abinda na gaya maka?"

Shiru Bashir yayi ya rasa ma wani abu ne ya dabaibayeshi,

"Dakai nake magana kayi shiru fa Bashir" Baban ya daka masa tsawar data sakashi magana babu shiri
yace

"Na tuna Baba"

"Me nace maka?"

"Ka tambayeni dole akayi mun nace maka Aa ra'ayin kaina ne, sannan ka sake tambayata me Asma'u tayi
mun nace maka babu komai"

"Daga nan kuma fa?"

"Ka gayamun cewa Asma'u matar rufin Asirice kuma mayafi ce data lullube ni, idan kishiya zan yi mata
naje na nemo yar gidan mutunchi wadda tasan qimar kanta na hadasu amma na kafe nace ni Amirah
nake so".

"Ba shakka kafiya tayi amfani. Tun ba'aje ko ina ba ta rabaka da uwar gidanka uwar yayanka shida ko, to
ka dai bi a sannu Bashir idan bakayi sa'a ba duniya da kanta zata koya maka karatun da ka kasa ganewa,
seka zubda hawaye a lokacin da babu amfanin da zasuyi maka, ita matar fari komai mugun halin ta tana
cin wannan darajar ta kasancewarta tushiya bare kai da Allah ya datar dakai da samu mace ta gari yar
gidan mutunchi shine kaga ta wannan hanyar zaka gode masa ba madallah, gaka ga Fattu nan da yarta
sun isheka bada misali a gaba" yana gama fadar haka ya kashe wayarsa.

Sosai yake jin baqin ciki da takaicin abinda Bashir ya aikata, me yasa tun a lokacin da Asma'u ta nuna
bazata zauna dashi ba be goya mata baya ta barshi tun a sannan ba? Daya san haka zata faru a gaba da
koda qarfin tuwa se Bashir ya bata takardarta a lokacin da ita da kanta ta buqata amma ba'a tara sani da
ikon Allah, shi yanzu da wane ido ze kalli yarinyar da Ahalinta.
Wayarsa ya shiga lalubawa ya shiga neman Number Alhaji Qarami dan a yanzu shine matsayin uban
Asma'u, cikin Sa'a ya samita kuwa ya dannan masa kira.

Cikin mutun taka suka gaisa kafin suka shiga jimamin abinda ya faru kafin yace ya turo masa da Number
Goggo ze kirata da kansa tunda Alhajin yace bata sani ba.

Suna gama wayar kuwa ya tura masa dan shikansa yana ta taraddadin ta yanda ze sanar mata da
wannan labari a irin yanda ta daukaki Bashir kamar dan data haifa.

Cikin sa'a Alhaji Amadu yana kiran Goggo ta daga wayar, bata da lambar ya sani dan haka yayi mata
bayanin shine nan suka sake gaisawa tana tambayarsa jiki da su Dada ya amsa da duka lafiya kafin suka
yi shiru.

"Hajia abu ne mara dadi ya faru amma ina so dukka muyarda da komai muka gani a rayuwa muqaddari
ne daga ubangiji ya na yin abinda yaso a kuma sanda yaso" Alhaji Amadu ya fada bayan daya katse masu
shirun.

Goggo cikin rashin fahimtar inda zancen sa ya dosa dukda tasan dai baze wuce akan Asma'u ba dan haka
tace masa

"Amma Alhaji meya faru ne ban gane maganar da kake yi ba".

"Kiyi haquri Hajia kuma ki fahimceni, magana ce akan Asma'u da Bashir, kinsan da aure da mutuwa da
haihuwa lokaci ne dasu kuma idan Allah ya saukar dasu babu wani abu da ya isa ya canza faruwar hakan
to a wannan gabar ma Allah ya saukar da ikonsa ya kawo qashen wa'adin zama tsakanin Asma'u da
Bashir".

Salati Goggo ta kwaso ta dire, cike da jimami tace "Yanzu yarinyar nan seda ta kashe auran hankalin ta ya
kwanta wai me Asma'u take nema ne a rayuwa? Yarinya ace zuciyarta babu salama shekaru kusan uku
da yin abun nan na zata ta haqura komai ya wuce ashe ita akwai abinda take qulla kai Jama'a wadannan
yara namu Allah dai kayi musu Albarka".
"Sam wallahi Hajia ba laifin Asma'u bane, bama tun yanzu ba tun tuni duk abinda ya faru ita akayiwa laifi
kuma aka danneta aka sakata yin biyayyar dole saboda ita an isa da ita.

Shi Bashir din ne dai daman gaban kansa yake yi a komai to yanzu ma ya sake nuna mana ya isa da kansa
ya isa yanke hukunci babu shawarar kowa yayi saki ba tareda sanin mu ba be kuma gaya mun ba se
matar sa ya gayawa yanzu na tsinci zancen a bakin yar uwar tasa na kirashi kuma a waya ya tabbatar
mun da haka akayi,

Dan girman Allah kiyi haquri, munyi magana da Alhaji Tukur yace mun baki sani ba saboda sun rasa ta
yanda zasu gaya miki wannan al'amari shiyasa nace ni bari na kiraki da kaina na sanar dake Bashir be
kyauta mana ba be kuma kyuatawa kansa ba.

Idan Bashir yana da hankali ko dan irin qaunar da kika nuna masa kika fifita farincikin sa akan na yar da
kika haifa wallahi ko zaginsa Asma'u takeyi yaci ace taci wannan darajar ya daga mata qafa ballantana na
tabbatar da ko kallon banza bazatayi masa ba".

"Karka yi saurin yanke hukunci cewa laifinsa ne Alhaji ita kanta Ma'u yarinya ce me naci da kafiya, wanda
yake zaune da ita ne kadai yake gane halin ta tsakanin mace da mijinta kuma se Allah, Allah kadai yasan
irin quntatawa da baqin halin da take masa" Goggo ta katse shi a sanyaye dan abin ya dake ta kwarai,
Me Ma'u tayi wa Bashir har haka da yayi zafi ya sake ta.

"Allah yasa hakan shi yafi Alkahiri" Goggo ta fada bayan dogon ban haquri da Alhajin ya sake yi mata,
haka suka ajiye waya jikinta gaba daya ya mutu,

"Allah sarki Ma'u ita kuma tata Jarabawar kenan akan abinda take so".

Alhaji Amadu kuwa bayan ya gama wayar sa yasa wani saurayi Abokin Naziru da ya zo wucewa ya turashi
zuwa cikin gida, har sannan suna zaune a tsakar gidan Addah na zuba masifa da besan ko akan me takeyi
ba, haka ya gungura kekensa ya shige daki ko a fuska be nuna musu yasan me akayi ba ya kuma qudurce
baze taba yiwa Nafi maganar ba koda kuwa ita ta kawo kanta da kanta, ze ci gaba da Addu'a Allah ya
raya shi ya kai lokacin da zasu girbi abinda suka shuka, a rabar ne ze silleta tas ya yada mata da
maganganun da suka dade suna ci masa zuciya.

BASHIR

Suna ajiye waya da gaba daya ji yayi rasa me yake yi masa dadi a rayuwa. Har a yanzu shi bega abinda
yayi ba ya kuma san babu me fahimtarsa adan an tashi kowa bayan Ma'u zebi baza'a duba martabarsa ta
matsayin mijinta da ita take takewa ba.

Babu abinda yafi daga masa hankali da a kullum Alhaji yake maimaita masa watarana se yayi kuka da
idonsa akan Amirah wannan ai baki yake yi masa kawai kuma ita Amiran nan fa ba irin wadda ya sani a
baya bace yanzu ta chanza ta gyara duk wasu halayenta marasa kyau da ake gani a baya ita kuma Ma'un
da akewa kallon ta kirki yanzu ita ce take masa abinda baya so.

koma dai menene aikin gama ya gama saki dai ya rigada ya furta dukda yanzu dai yaga yayi zari da yayi
mata saki har biyu dan daya ya kamata yayi na gargadi amma dai ba matsala,

ze cigaba da lissafi se ya rage wata daya ta gama Iddah sannan ze ce ya mayar da ita, Dukda yasan
tabbas zeji jiki na rashin Ma'u a kusa dashi abinda be taba koda mafarkin faruwarsa a rayuwar su ba
amma ita ta janyo musu haka, daga ita har shi dole su shiga gararin rayuwa kafin komai ya daidaita dan
ta wannan hanyar ce kadai ze horata ta yanda gaba ko ance ta sake musa masa magana bazatayi ba bare
har ya bata unarni taqi bi.

Haka ya ringa saqa da warwara har lokacin tashinsa aiki yayi, yasan yanzu yara sun koma gida, ze barsu
daga nan zuwa Jibi Amirah tazo dan ko ya dakko su yanzu baze iya musu hidimar da suke da buqata ba
dole se mace dan haka dai ze ci gaba da ja har zuwa sannan dan idan yayi shiru kar ta dauka ze bar mata
yaran ne.

ASMA'U

Ganin har magriba tayi Bashir bezo da wani tashin hankali ba yasa hankalin tavya dan kwanta tayi
tunanin ko ya haqura ya sakar mata ragamar yaran ne tunda taji sunce ya dawo harma su Ahmad sunje
gidan ya basu Chocolate.
Bayan Isha tana zaune wayarta tayi qara, shareta tayi dan ta gaji da amsa waya. kamar wutar daji labarin
mutuwar auranta ya karade Gombe se kiranta akeyi ana mata jaje ta rasa ta bakin wa maganar ta fita
amma bata raba daya biyu Bashir ya gayawa matarsa, ko yan uwansa su kuma suka kwaza a duniya
daman mutane kuma masu jiran qiris nan da nan labari ya zagaya.

Har wayar ta qaraci qararta bata ko duba ba can sega Amna ta fito daga daki da wayarta a hannu ta miqa
mata tana cewa

"Goggo ce tace ta kiraki baki dauka ba".

Karbar wayar tayi ta saka a kunnenta kawai dan ta tabbatar labari ya rigada ya isar mata yanzu.

Cikin sanyin daya aureta yanzu ta gaida Goggon kafin tayi shiru tana jira taji ta inda zata rufeta da fada
amma ga mamakinta se ji tayi tace

"Ma'u kiyi haquri, shi aure raine dashi Idan lokacin mutuwarsa yayi koda dalili ko babu se an rabu,
sannan kowa da kika gani da irin qaddarar sa a rayuwa, mutuwar aure bata da dadi amma kar hakan ya
sa ki dauka gazawarki ce ta janyo ko kuma wani ne silar hakan Aa babu wanda ya isa ya qulla aure ko ya
kashe shi se Allah dan haka ki dauka cewar wa'adin da Allah ya dibarwa zamanki da Bashir ne ya qare
kawai.

Kar kuka ki ce zaki saka kanki a damuwa ko wani abu kinji kiyi Addu'a Allah yasa hakan shi yafi Alkahiri,
saki nawa ne?"

Cikin karyewar murya nace mata "Wallahi Goggo ma Banyi masa komai ba, kawai saboda yace se ba bar
aikina saboda Amirah Shikenan abinda ya faru"

"Na sani Suhaima ta gaya mun komai kiyi haquri yanzu dai saki nawa ne?" Ta sake tambayata, seda naja
Majina dan ta tuno mun da kukan da na bari nace mata

"Saki biyu ne kuma nayi bari dazu da safe".

"Subhanallahi Bari kuma a garin yaya daman kina da ciki ne" Goggo ta tambaye ni muryarta cike da
Alhini, seda na tsagaita kukan nace mata
"Nima ban sani ba se shekaran jiya naje Asibiti na dawo ban ma kai ga sanar masa ba ya sake ni".

"Yanzu be san da maganar cikin bama bare barin kenan, ai kuwa ya kamata tun wuri a gaya masa tunda
kinga kenan kin gama Iddah kar yaje yayi ta lissafin Bogi tunda da sauran igiya a tsakanin ku" Goggon ta
fada, da mugun mamakin maganar ta nace

"Yanzu Goggo har kina zaton cigaban zama tsakanina da Bashir, ai Goggo ko shine autan Maza na haqura
dashi. Sakina fa yayi sakin wulaqanci akan kishiya wallahi sedai ya zauna da ita wadda yake so har
qarshen rayuwarsa ko ze mutu dan nagama auransa, dan Allah a wannan karon kar kice zaki tilastani
komawa gidan Bashir in dai ba so kike zuciyata ta buga na mutu kowa ya rasa ba" na fada ina qara
fashewa da Kuka.

Qarshen abinda Goggo zata sakeyi mun a yanzu ta maida ni gidan Bashir, ba dan na dena son Bashir ba
wannan nasan wani abu ne da har na mutu yana raina amma na tsani zama dashi ba kuma na fatan Allah
ya kawo dalilin da ze maidani gidan sa.

Duk da yana yin da take ciki seda tayi yar dariya kafin tace

"Ni ban ce ki koma gidan Bashir ba amma idan zama be qare a tsakanin ku ba haka zaku gama duk
abinda zakuyi kuma ku koma ku ci gaba da zama dan haka duk abinda zakiyi karki tsananta ko dan
Albarkar zuri'ar da take tsakanina ku.

Sannan maganar yara idan har ya matsa ki bashi yayansa kar kice zaki tsaya ja in ja dashi tunda yana da
me riqe masa shikenan, ke kuma zamanki a nan baze yuwu ba zuwa safiya zan kira Alhaji Qaramin kodai
ki nemi transfer ki koma can Abujan gabansa ko ki aje aikin ki dawo gidan ku ki zauna amma bazaki
zauna ke kadai anan ba".

A gaba daya tsarikan na Goggo babu wanda naji yayi mun, bana jin zan iya bawa Bashir yarana maganar
Transfer kuma ko barin aiki ta manta aikin akansa aka sake ni sannan na barshi ai kuwa na tashi a tutar
babu, amma yanzu bazan musa mata ba zan barta tayi magana da Alhaji Qaramin na tabbatar shi baze
bari a rabani da yayana ba ko aikina.
Haka mukayi sallama tana sakeyi mun nasiha na kuwa ji dadin magana da ita sosai muka rabu tana
jaddada mun dana sanar da Bashir maganar ciki da kuma Barin da nayi dan gudun abinda kaje ka dawo,
haka na kwana da niyyar gobe idan yazo kai yara makaranta zan gaya masa tunda da alama bega
takardar dana ajiye masa ba.

BASHIR

Yauma dai a hanya ya siyo abincin sa haka ya dawo gidan na nan a yanda ya barshi sema qarin datti da
yayi saboda qurar qasan gado da suka watso masa palour dazu. Haka ya shiga dakinsa yayi wanka gaba
daya gurin ya hargitse masa ya rasa ta yanda ze fara mayar da kayansa cikin wardrobe tunda ya saba da
an kawo masa guga Ma'u ce take jera komai a inda ya dace.

Haka ya zura jallabiyya ya dawo palour ya kade kujera ya zauna ya bude abincin, loma uku yayi ya ture
gaba daya abincin ya fice masa daga rai dan bakinsa ya saba dame dadi, dukda wannan din ma me dadin
ne amma dandanok girkin Ma'unsa ya banbanta dana kowa shikadai ne abincin da ko iya qamshinsa
yana rage masa yunwa dan shi fa abinci indai ba nata ba ko yaci baya jin ya qoshi sedai kawai cikinsa ya
cika maganin yunwa amma ba wai dan ya gamsu da cewa abinci yaci ba.

Yana zaune yana dannan waya su Ahmad suka shiga gidan da gudunsu, Ganin sune ya debe masa kewa
har aka kira sallah suka tafi masallaci tare, yana kallon Aliyu ko inda yaje yaron be kalla ba yayi murmushi
kawai da suka dawo zaau tafi ya dakko Chocolate ya basu harda ta sauran kafin ya raka su har qofar
gidan suka shiga, yana jiyo qamshin abinci da alama girki sukeyi.

Badan kar mutunchinsa ya zube ba babu abinda ze hana ya shiga yaci amma ya qudurce a ransa dole ya
koyawa Ma'u hankali ta yanda da kanta zata bishi ta bashi haquri, a qalla se tayi kusan kwana dari da
wani abu kafin cikar Iddarta dan watan ta me kwana talatin da shida ne kafin sannan kuwa ta biyu liqis ta
yanda ko kara ya ajiye bazata sake tsallakawa ba. Haka yaja jiki ya wucw yana hadiyar yawu, qarshe se se
shayi yasha da wani guntun cake da Allah yasa basu dauke ba ya hada da dambun nama shima a irin
wanda take masa ne ya ajiye a office ya tuna yana mota ya dakko shi.

Seda yaje kwanciya idonsa ya kai kan farar takardar da tun jiya ya ganta amma be duba ba, daga
kwancan ya janyota ya bude yana mamakin ko tasa ce ma ya manta sedai tambarin Asibiti da sunan
Ma'u daya gani yasa ya qara hasken fitila dan ya gani da kyau.
"Kai Allah na gode maka, Wallahi Allah yana sona" ya fada a fili cikin farin ciki, wannan wata dama ya
samu ya tabbatar se Asma'u ta kawo kanta da kanta musamman da yawancin cikinta suna qara mata
buqata yana zaune zata zo har inda yake ta bashi haquri kai wannan abu ya masa dadi.

Hotonsu dashi da ita da yake akan bedside drawer ya dakko yana shafa fuskar ta, ranar Anniversary
dinsu na shekara Goma suka duke shi daga shi har ita suna dariya ya manta dariyar me sukeyi a lokacin.

Sumbatar fuskarta yayi kafin yace

"Kiyi haquri Ma'una, nasan sena fiki azabtuwa da rashin ki a kusa dani amma ke kika jawo mana, taurin
kanki da kafiya ya saka komai ya faru amma yanzu ga dalilin da ze dawo mun dake cikin ruwan sanyi na
samu, Ina son ki Ma'una".

WATA KISHIYAR

(ALKAHIRI CE KO SHARRI)

Na Maryamah Farouk

(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)

Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 42
Ranar Juma’a Amirah ta tafi Lagos, da yake saukar Yamma tayi seda Bashir ya tashi daga gurin aiki
sannan ya biya ya dakkota suka wuto gida.

Ina zaune dakina Jafar ya shigo da gudu yana cemun

“Mami Abbi ya dawo”.

“To sannun sa Jafar” na fada ina duba wani document da aka turomun daga gurin aikin mu.

“Ai Mami ba shi kadai bane ma tare suke da Anty Amirah” Jafar ya sake fada, se naji kamar an saka mun
stop, na dago na kalli yaron kamar me son tabbatar da abinda ya fada se kuwa ya daga mun kai yana
sake cewa

“Ita ce tazo gasu Ahmad can ma sun tafi gurinta kuma naga da Akwatunan kayanta qila ta dawo gidan
kenan ko Mami?”

“Kaje ka kirawo su magriba tayi” na fada kafin na mayar da kaina kan abinda nake yi amma sam ban
gane komai ba. Idan nace zancen zuwan Amirah be dake ni ba nayi qarya ta tabbata kenan dagaske
saboda ita Bashir ya sake ni tunda ga ta nan ya kawo ta nan din.

“Allah kaine Allah, kayi mana sakayya akan duk wanda ya cutar damu” na fada a fili bayan na ajiye Tab
din hannuna dan sam na dena gane abinda nakeyi. Tagumi na rafka, se kuma na janye nace da kaina
“Tagumin fa be ganni ba, tun wuri gara na tattara shirgin Baban Ali a gefe na fuskanci abinda ze tun karo
ni a gaba” ina fadar haka na miqe na shiga Bayi nayi wanka.

Ina cikin shafa mai Muhammad ya shigo da leda a hannunsa da ban san ko menene a ciki ba.

“Mami wai gashi inji Anty Amirah ta kawo miki tsaraba” ya fada yana ajiye ledar a kusa dani, har ya juya
ze fita na janyo shi, se da na zare masa ido kafin nace
“Dauki ka fitar can bola kayar, idan na kuma ganin ka shiga gidan nan idan sena cire maka kunne, wuce
kaje ka kirawo Ahmad daman kune masu shegen yawo ai bini bini kun tafi can”.

Haka na cigaba da shiryawa ina mita, seda na sake tara su gaba daya naja musu kunne akan babu su
babu zuwa gidan Amirah, idan ma uban suke son gani se su jira ai yana fitowa su ganshi a waje su wuto
gida amma ban yarda wani ya sake ya je gurinta ba.

Washe gari da yake Asabar ne bamu tashi da wuri ba se gurin goman safe dan haka kafin muci abinci
muyi wanka an fara kiran sallar Azahar.

Aliyu ne ya sa su a gaba suka wuce masallaci da suka tashi dawowa shi kadai ya shigo ba tareda sauran
ba.

“Aa Yaya ya naganka kai kadai ina qannen naka” na tambaye shi ina gyara Hijabin jikina dan zan leqa
gidan Anty, bata jin dadi kwana biyu itama.

“Mun taho a hanya sukaga Abbi shine ya jasu gidansa” Aliyun ya fada yana zama akan kujera, se nayi
qwafa nace “wato basuji abinda na gaya musu jiya ba ko nasan Jafar ne ze jasu za kuwa su dawo su same
ni, Faridah taso ki rakani ke kuma Amna idan kin gama cin abincin in zaki zo toh” na fada ina nufar qofa.

Kallo daya nayiwa gidan Bashir shima bisa kuskure na shige gidan Anty, ban zauna ba ganin Baba yana
gida dan a zatona yana gidan uwargidansa ne yau dan haka a tsatstsaye nayi mata sannu yana ta in
zauna mana nace Aa anjima na dawo muka fito, ina sako qafata waje nayi kyakyawan gani da Bashir
tareda matarsa saboda tsabar sabon salon munafunci ta dauki Ahmad se rinjayarya yake kamar zasu fadi
suka shiga mota, inajin Ahmad din yana cewa

“Mami, Abbi ga Mami nan ba tareda ita zamu je ba” ko iskar su ban waiwaya na kalla ba na shige gida.
Ban kai ga cire Hijabi na ba naji an turo qofar an shigo ga kuma qarar takalmi qwas qwas alamar dai
macace se na waiwaya naga waye ido na ya sauka akan Amirah.
Fuskarta dauke da Fara’a ta qaraso cikin palour nidai ina tsaye har ta samu kujera ta zaune tana waige
waige. A lokacin Allah kadai yasan abinda nake ji a cikin zuciyata amma na rigada nayiwa kaina fada,
badai ni na sake yin wani tashin hankali akan Bashir ba tunda dai yanzu babu abinda muka hada dashi
dan haka nima sena fasa cire Hijabin na zaune a kujerar da take kallonta fuskata a hade ba tareda nayi
magana ba.

“Ina wuni Anty” ta fada tana wata dariya kamar kwarkwar, seda sake tsuke fuksa kafin na amsa da
“Lafiya” a taqaice.

“Tun jiya naso na shigo wallahi na gaishe ki kuma se gajiyar hanya ta hanani ga gidan nazo na tarar dashi
duk ba a kintse ba shine fa nayi yan gyare gyare har yau da safe, yanzu ma fita zamuyi wai twins ne suke
son Ice cream zamu je a siyo Ina Farida da Amna ban gansu ba su” Amirah ta sake fada tana bin lungu da
saqon palour da kallo duk ina ankare da ita, zanyi magana Farida ta fito daga dakinsu, kallo daya kuwa
tayi mata ta zumburi baki ta juya ciki ma ta fasa fitowar ita kuwa Amirah se wani murmushi takeyi na ala
dole ita ta iya bariki.

Jin bata sake cewa komai ba yasa nace mata

“Zaki iya tafiya tunda mun gaisa ko, amma mu nan bamu saba da shige shigen maqota ba. Kowacce
mace a gidanta take zama dan haka karki sake shigowa mana mun gode” nayi maganar raina a sake kai
ba kace mun hada wani abu nida ita ba.

Na sani gulma da munafunci ne ya shigo da ita dan ta nuna mun tazo, sannan taga yaya na zama tunda
Autan Maza ya sake ni ko? To gani dai garas a cikin hayyacina, sema fari da kyau danayi saboda ni idan
na rame ido na da hanci qara fitowa sukeyi ga kuma hutun dana samu kusan kwana nawa ina zaune a
cikin Ac sannan da wani hadin ridi da Madara da Anty takeyi mun duk yamushewar da nayi a kwanaki
biyun nan na warware fatata ta nuna jin dadi.

“Uhm toh shikenan bari naje nasan Yaya yana ta jira, se mun dawo” ta fada tana miqewa, har ta kusa fita
ta waiwayo tace

“Anty gurin nan yayi kyau har yafi can gidan ma wallahi”.

“Allah ko, se ki gayawa Bashir ya zuba miki irin kayan idan kuma nan din kike so se mu baki” na fada ba
tareda na daga kai na kalleta ba, itama bata ja maganar ba ta fice tareda ja mana qofa.
Naga qoqarin ya kwarai da tsantsar rashin kunya da har ta iya dakko qafa ta shigo mun gida ko kuwa
tana nufin tace mun bata san bana tareda Bashir bane, koma dai yaya yau daya dai na danne zuciyata
duk irin abinda ta ringa ayyano mun da nayi mata na daure amma tabbas duk randa ta sake gigin
shigowa ban san abinda zanyi mata ba, su kuma dan uban su zasu dawo su tarar dani se sun gaya mun
me suka rasa a gurina da suka tafi yawon roqo gurin Bashir.

AMIRAH

Ganin da tayiwa Asma’u lokacin data fito daga gidan Anty sam be gamsheta ba. Bata zata cewa a dan
tsakanin abinda be ko kai sati daya ba Ma’un zata iya dangana da abinda ya sameta har ta ganta tana
yawo akan qafafun ta kamar babu abinda ya faru.

Mantuwa Bashir yace yayi ya koma cikin gida, yana shiga itama tayi saurin fita daga motar tabi bayan
Ma’u.

Ba qaramin girgiza tayi da ganin tsaruwar sabon gidan Ma’un ba tunda dai tasan babu silan Bashir a ciki
wato ita wata sabuwar duniya ma ta bude ta qawata gida kamar ba wadda aka saka ba tana walwalarta,
ta kuma yi zaton ganinta ze batawa Ma’u rai har tayi fada ko wani abu daga nan ta samu damar da zata
sake qunsa mata takaici dan sosai su Addah da Sa’adah sukayi mata hudubobin tsiya tunda suka ji Ma’u
tana kusa da gidan.

Sun karanta mata yanda duk zatayi ta uzzura mata ta yanda ita da kanta zata bar kusada Bashir idan taga
bazata iya daukar abubuwan da Amiran take yi mata ba amma se gashi ko a kwalar rigarta bata ga
alamar ganin ta ya daga mata hankali ba, kai ita se take ganin kamar ma qarya ne babu wani sakin ta da
yayi dan daga ita har shi din bata tsammaci ganinsu a hayyacin su ba har gara Bashir ya rame amma
Ma’u fa kyau ma taga ta qara abunta.

Haka ta ringa cizon yatsa a mota ga Bala’in da yakeyi mata akan wane dalili ta shiga gidan, ta qudurce a
ranta tabbas seta gallabi Ma’u ta bar unguwar nan dan bazata juri haduwarsu da Bashir kullum ba
sannan ga wadannan mayun yaran da tun zuwan ta jiya suke zurubtu a gidan, gara suyi can nesa dan in
ba haka ba ze zamana an kashe miji ne ba’a sare kansa ba.
Fitar da tayi niyyar warwasawa yau itama gata a gaban motar Bashir a Lagos sun fita shan Ice cream
qarshe haka suka dawo kowa yana hada rai yaran ne kadai suke ta jin dadinsu shi kuma ya biye musu har
wadanda ba’aje dasu ba seda akayiwo wa tsaraba.

Da suka dawo gidan ma kayan sa yace ta shiga ta gyara masa sukuma suka baje a palour da yaransa suna
ciye ciye da buga game baqin ciki kamar ta fashe daga zuwa rana daya za’a fara haka lallai dole a sake
sabon lale.

Wayar ta ta dauka ta shiga kiran Sa’adah tunda itace malamar tata, bugu biyu ta daga tana tsokanarta da
cewa

“Uwargida Amaryar Engineer, ashe kin kunna waya ai bari nayi ku gurji Amarci kwana biyu tunda an
dade ba’a hadu ba daga baya se musha labari”

“Wayake ta zancen wani Amarci yanzu Anty Sa’adah” Amirah ta fada tana jan tsaki, daga dayan
bangaren Sa’adah tace

“Bangane me kike nufi ba, kardai ki cemun period din dawowa yayi bana ce miki kisha pills ba ze dauke
ko baki sha ba”.

“Duk fa ba wannan bane yanzu, ni kin ganni tunda nazo jiya ma nake aiki kamar jaka. Gida kaca kaca ga
gyaran dakina tsabar wulaqanci masu saka gadon a ciki suka bar kwalaye da sauran tarkace, haka ya
tasani a daren sena gyara, dan ma na taho da Miya kin gani sefa da na dafa mana taliya mukaci, ga
shegun Yayansa sunzo sun tasa mutane a gaba saboda haushi ma nayi bacci na barsu ban san lokacin da
suka tafi ba.

To kin ganni yanzu ma dai na taqaita miki tun safe aikin nake, harfa fita mukayi wai ze siyowa Yaran Abu
gasu can mun dawo suna palour ni kuma ya saka ni ninkin kaya” ta qarasa maganar cikin tsantsar takaici,
badan hudubar da aka mata akan ta kwantar da kai ba da wallahi tun a yau gayyayar zata watse dan ita
fa ba aikatau tazo yi ba, zuwa tayi ta mori miji taji dadi a toh.
Dariya Sa’adah ta ringa sheqa mata abinda ya sake qular da Amirah kenan tace

“Wannan ai wulaqanci ne, na gaya miki matsalata kuma kin mayar dani abin dariya shikenan, bari na
kashe wayata, barima kiga na gaya masa nifa bazan yi ba dan na gaji wallahi sekace jaka”.

Seda Sa’adah ta tsagaita da dariyar kafin tace “toh ai Amirah dole nayi dariya, nifa bari kiji wallahi na
dade banga sakaryar mace irin ki ba amma fa kiyi haquri.

Ce miki akayi a banza kake mallake mijin daman ai se kin zama jakar, a gabansa ki zama kamar baiwa se
yanda yayi dake ko takaki yayi kar kice komai shine zaku zauna shiru bame jin kanku ki zama ta gaban
goshi yanda ko wani ne ya kawo aibun ki ze tare miki kuma ki more shi yanda kike so tunda yana juya ki
shima, ko bakiga ni har wanki nakeyiwa Yallabai ba, idan kuwa ina gabansa biyayya ko ubana Albarka”

“Tab wallahi bazata sabuba kuwa dan ni bazan iya ba. Haka kawai sena zauna kenan na zuba ido se
yanda akayi dani ai kuwa bazan iya ba ni indai wannan shine dabarar gara ma nabi ta Addahn kenan a
nemi inda za’a kaishi a mallake mun shi ta qarfi amma indai se na zamar masa jaka babu ni a wannan
tsarin” Amirah ta fada.

“Ai kuwa indai kina so ki samu yanda kike so a gurin namiji yanzu dayan biyu ne, kodai ki zama kurma
makauniya ki sakar masa ragama duk abinda yayi daidai ne bazaki musa masa ba ko kuma ace ke kike
wahalta masa da aljihunki to shine zaku zauna lafiya ba tareda an ji kanku ba.

Dan muddin kika ce in ya bada umarni zaki kawo taki shawarar to kuwa kun ringa samun sabani kenan. A
cikin Maza yanzu kadan ne suka fita zakka da zaki ga sun bawa matansu haqqin da ya kamace su,

Idan kuma yawon Malaman kikaga yafi miki seki daura aniya, ki dai sani wata rana zanin da zaki daura
ma se ya gagare ki tunda kullum kina kan hanyar kaiwa wasu daga zaune kudin ki kuma shi Asiri ko kinyi
se kin hada da kissa wallahi randa kuma ya karye se kin fi kare wulaqanta”.
Shiru Amirah tayi dan gaskiya Sa’adah ta fada, yanzu dai gashi tun yaushe suke yawon rabar da kudin
daga can inuwar su tsugunna a waccen amma babu biyan buqata, gashi yanzu cikin lumana komai yana
tafiya yanda take so to amma kuma ita ai bata zaci haka zaman ze kasance ba.

Cikin sanyin murya tace “Toh yanzu Anty Sa’adah ya zanyi dan gaskiya akwai matsala”

“Yawwa yanzu kika dawo kan hanya” Sa’adah ta fada kafin ta ci gaba da cewa

“Kina ji ko, batun gyaran gida wannan daman ai aiki ne dukda ban san Kishiyar ki ba amma a yanda kuka
bani labarinta mace ce data san kanta dan haka yanzu dole ki dage idan baki zarta ta ba toh kuyi kan kan
kan.

Tsafta dole ki dage gyaran gida ko ina yayi qal ki saka turare Allah na tuba ma wane aiki ne a gyaran
gidan keda ba wani wawakeken Mansion ne dake ba dan Duplex ne fa, sharar palour, Kitchen da
mopping dinsu dai wannan dole kullum kiyi.

Haka dakinsa, da kun tashi bacci ki gyara gado, yana shiryawa ya fita ki share ki wanko bandaki kija qofar
shikenan fa se kuma gobe. Naki dakin zaki iya ki ringa tsallaken kwanaki tunda ke kadai ce babu me
shigar kiki, kwanuka idan kina girki daga kin bata ki wanke idan anci abinci ma ana gamawa ki wanke,
dan girki dai cin mutum biyu da safe ne fa se na dare ba shikenan ba duk meye abin wahala a ciki dan
Allah.

Sannan ki ringa wanka dan Allah sau biyu dai a rana meye a ciki kayan kwalliyar nan gasu nan kina dasu
kar kije ki ringa zama yanda kike a nan kamar wata me takaba da zani da T shirt dan dole ki dauke masa
hankali daga kan kowacce mace ta yanda ze manta da tsohuwar matar sa ya shafeta daga lissafinsa
tunda yana da ke sabon jini”.

“Toh ai Anty Sa’adah katangar mu daya fa da gidan data koma ga yaran tun jiya na gaya miki suke
zuruftu a gidan nan ko tunawa dani ma bayayi” Amirah ta sake fada, se Sa’adah ta danyi murmushi tace
“Dadina dake komai se an koya miki, yo Allah na tuba ko a cikin gidan ku take idan kinsan yanda zaki riqe
shi tsaf ai wallahi bata ishe shi kallo ba, yara kuma da dabara zaki janye su, daman karki basu qofar da
zasu ringa shigo miki idan baya nan.

In kuma yana gidan sukazo kar kiji kunya ko a gabansu ne kije jikinsa ko kiyita yin abinda zaki ja hankalin
sa dakansa ze ce su tashi su tafi, yana dawowa gida ki saka abinki a daki yanda baze ma samu kansa ba
bare ya gayyato miki su a hankali se kiga shi dasu se in ya fita sun hadu ne ma ze ringa tunawa da zaman
su, ke dai kiyi komai yanda ya kamata zaki sha mamaki wallahi”.

Haka ta ringa yi mata huduna data tsiya data kirki sukayi sallama. Da yake dai quiya a jininta take kayan
dai gasu nan haka ta shirya masa dan ma ya sake kaiwa an goge dan haka zuba su kawai tayi. Tana cikin
jera masa Suits ya shigo dakin,

“Har kin gama kenan” ya fada yana kallon ta hannun ta wadda kuma ita ce ta qarshe da zata rataye.
Seda tayi fari da ido ta lankwashe murya kafin tace

“Na gama fa, duk na gaji wallahi hannuna ya qage kayanka yawa Yaya kamar na mace”.

“Koh?” Ya fada yana wuceta ya bude bangaren da ake zuba masa manyan kaya, Amirah kuwa kumbura
baki tayi, a ranta tace

“Ba sannu ba komai ze ce mun wani Ayya, Aa Ayyo mutum dai besan gwaninta ba.” Baya ida tunanin ba
taji shi cikin fada fada yana cewa

“Meye wannan kikayi? Haka ake jera kaya daman ji yanda kika loda su se kace wani motar kasuwa,
malama sauke su tas ki gyara komai da kika gani irinsa daban zaki jera.

Shaddoji daban kuma kalolin su zaki duba kiyi su a jere sannan dayaj side din ki saka yadi ka, nan gurin
Neck tie ake ajiyewa kin wani cusa mun hula baga inda suke can ba

Mtsw komai ke baki iya ba se kinyi wa mutane shirme, kina tsaye ki fara sauke su yanzu ki gyara” ya
qarasa da daka mata tsawa.
Amirah da tayi mutuwar tsaye, yanzu duk wannan uban aikin data sha ze ce basuyi ba seta sake aikuwa
bazata iya ba, haka kawai me ya hana shi yayi da kansa tunda ba haka akeyi ba, tsawar daya daka mata
ya saka ta fara sauko da kayan ba shiri, haka tana ji tana gani da hawayenta da komai seda ta mayar
dasu tsaf yana tsaye akanta sannan ya saka ta share dakin ta goge qal ta kuma wanke toilet kafin ya rabu
da ita. Tana gamawa kuwa ta wuce tsohon dakin Ma’u inda ya saka mata sabon Gado ta ringa rusa kuka.

Indai kuwa haka zaman Lagos din yake kuwa wallahi bazata iya ba sedai ya maida ita can Gombe ya
zauna shi kadai, ta zata da ta ke kukan ma ze bata haquri amma se gani tayi yaja Laptop ya kunna ma ya
shiga aikinsa haka data gama ba godi bare na gode ta wuce tana kuka be tankata ba qarshe ma se jin
tashin motar sa tayi alamar fita ma yayi.

ASMA’U

Se bayan La’asar yaran suka shigo da ledoji niqi niqi na kayan da suka siyo. Kallo daya nayi musu gaba
daya suka shiga nutsuwarsu, karadin da suka fara na bawa su Faridah labari kowa ya kama kansa.

“Wallahi Jafar na sake ganin qafarka ka jasu kunje gidan can sena saba maka, idan banda shegen
kwadayi me zakuci da bamu dashi a nan, ina shekaran jiya da kuka Raka Yaya Airport seda ya fara kaiku
kuka siyi kayan kwalamar duk ba gasu can kun cika mun Fridge da tarkace ba ko kuwa wani sabo kuke so
da ni baza ku gayamun ba wa ma kuka tambaya da kuka dibi qafa kuka tafi har wani guri” Na fada ina
tsare su da ido, duk sukayi shiru Yan Biyu har sun fara yar kwalla ganin ina musu fada kuma na daure
fuska, Jafar ne ya marairaice yace

“Mami kiyi haquri dan Allah bazamu sake ba, na zata ai tunda Abbi ne bazakiyi fada ba kuma shi yace
muje bamu muka roqe shi ba ko Abdallah?” Se Abdallan ya yi saurin daga kai yana cewa

“Seda ma mukace mu baza muje ba Anty Amirah tace se munje Allah kuwa ki ma tambayi Abbin kiji”

“Naji, karku sake” na fada har sannan fuskata a hade. Ni ba fitarsu da Bashir ce ta bata mun rai ba akan
me Amirah zata fitar mun da yara shine haushi na.
Waiwaya wa nayi na gansu har sannan a tsaye nace “me kukeyi kuka kun tsaya mun aka, kuje ku ajiye
mana idan kuma ci zakuyi to se ku zauna”.

“Toh Mami ai baki ce kin haqura ba tukunna” Jafar ya sake fada, se nace masa

“Na haqura mana Jafar, ku wuce ciki”

“To Mami ai baki saki fuskar ki ba, kuma gashi har wannan Shawarman da kike so na siyo miki, naje na
dumama miki a microwave?” Ya sake fada yana marairaice fuska, nasan nacin Jafar yanzu idan ban saki
fuskar ba se ya kai dare anan yana mun magiya dan haka nayi murmushi nace

“Je kayi toh” da sauri suka wuce Kitchen da kayan, haka badan raina yaso ba naci Shawarmar da aka siya
da kudin Bashir, tare muka qarasa wunin mu dan sallar Magriba da Isha ma a gida sukayi saboda ruwan
sama daya sakko.

Washe gari ma muna gida har yamma se bayan da akayi sallar La’asar suka fita qofar gida suka raba ball.
Ina zaune akan kujera ina jin Dramar Amna da Farida akan kwalliya ala dole ita Farida wai tafi Amna
sanin Fashion tana zabarwa Amnan kayan da zata saka na prom din su ita kuma tace basuyi mata ba.

Wayar Faridah ta miqo mun tana cewa “Kalli fa Mami dan Allah ai wannan ne zeyi mata kyau ko, itafa
Yah Amna bata san me ake yayi ba”

“Aike kin sani naga alama” na fada ina karbar wayar daga hannunta, shigowar da Abdallah yayi da gudu
ce ta sakani dagowa daga kallon wayar nace

“Kai kuma menene haka, bana hana ku wannan guje gujen ba se kaje ka fadi ko”. A gaba na ya tsaya
yana haki yace

“Mami Abbine, gashi can a qofar gida wai se mun dakko kayan mu mukoma can gidan, ga Baba can ya
tsayar dashi suna magana”.
Ina shirin bashi amsa Anty tayi sallama ta shigo daga tsaye take cemun

“Asma’u Bashir ne, gashi can yana rantse rantsen se yara sun koma hannunsa, dan Allah karki tsaya
tashin hankali dashi, idan dai ya kafe ki barshi nan da can din ai duk guri daya ne”.

Miqewa nayi nima har ina fatali da wayar Amna ban lura ba nace “Bazan bashi yarana ba Anty, Be auri
matar da zan barwa tarbiyyar yarana ba kuma ko mutuwa nayi badai dangin Bashir su riqe mun yara ba
wallahi”.

Daga waje nake jiyo maganarsa yana gayawa yaran su shiga su dakko kayansu, zan fita Anty ta ruqoni
tana cewa

“Karki fita, kijira idan ya shigo da kansa se kuyi magana kuma ni banga abin tashin hankali ba akan yara
dai bayan kuna guri daya a zaune”.

Yaran ne suka shigo Aliyu akan Gaba suka wuce can ciki suka tsatstsaya sega Bashir a bayan su yana
jaddada musu dasu hada kayan su su wuce gida.

“Harke zaki hana mun yara shiga gidan ubansu ko, toh dake da itan duk zan nuna muku baku isa ba, zan
dauke yarana ita kuma dole ta riqe su tunda gidaj ubansu ne bana uban wani ba” ya fada yana kallona,
daman jira nake yi dan haka nima a fusace nace

“Seka gorantawa wanda ubansa bashi da gida, Ÿaya kuma tunda ba wani ya haifar mun su ba banga
wanda ze dauke su ba, ita kanta matar taka bata wadatu da tarbiyya balle na a bata kula da wasu”.

“Kar ki zageni Ma’u, Ÿaya kuma nawane halak malak ke din yar karere ce dan haka dole su koma gidan
ubansu yanzu kuma ba da bata lokaci ba”.
Zan sake magana Baba ya dakatar dani da cewa

“Wai me kukeyi haka yanzu daga ke harshi kenan baza’ace ku bar abu ku bari ba kunzo gaban yara kuna
irin wannan abun me kuke koya musu kenan?

Kai Bashir ka wuce muje, ke kuma Asma’u ku hada musu kayan ku tura masa Ÿayansa tunda yana da
mata daman ai haqqin ruqonsu a hannunsa yake”.

Kuka na fashe dashi ina cewa “Akan me ya sake ni sannan yace ze raba ni da yarana wannan ai rashin
Adalci ne”.

Wayata na dauka na shiga kiran Alhaji Qarami, kira biyu na masa be dauka ba dan haka na juya akalar
kiran zuwa Goggo. Tunda yanzu tana goyon bayana gara na gaya mata ko zan samu wanda ze tsaya mun
dan gaskiya bazan bawa Bashir yara ba sedai ayi duk yanda za’ayi.

Tana daga wayar na fasa mata kuka ina gaya mata yanda akayi, seda ta gama jina tsaf kafin tace

“Toh Ma’u Menene a ciki tunda yana da yanda ze riqe yaransa se ki bashi, kin fiya son damun kanki
wallahi ke kanki ai sauqi kika samu seki nutsu idan an kwana biyu ki nemi wani mijin kiyi aure dan kinsan
zaman ki haka baze yuwu ba tunda yayyenki sun daure miki gindin ki zauna a can to ki bashi yaransa ki
raka su da Addu’a, a ko ina suke Allah ya tayaki tarbiyyantar dasu”.

Kashe wayar nayi dan na manta ma Goggo duk abinda ya tashi ai bayansa take bi, ina shawarar kiran
Alhajin su Bashir din kiran Alhaji Qarami ya shigo.

“Asma’u ki tattara su daga kan Aliyu har zuwa Tukur ki bashi yaransa, bana son wata doguwar magana ki
rabu dashi. Yara ko bangwan duniya ya kaisu dole wata rana se sun nemeki da kansu dan haka dan Allah
karki tayar da hankalin ki ki tayar da na wasu, mun gaji da Bashir Bashir kullum babu fashi.

Bafa akanki aka fara sakin Mace ace ta bada yara ba dan haka please Ma’u ki bashi ki kuma sararawa
kanki haka haba” Alhaji Qarami ya fada tun kafin nayi masa qorafin, daga jin yanda m yake magana na
tabbatar da ransa a bace yake maganar ta ishe shi, daman shine dogarona da ze tsaya mun To gashi
shima yabi bayan su dole bani da zabi na bawa Bashir yarana.

Ina Kuka sunayi Baba ya tasa su a gaba har qofar gidan Bashir ya barmu muna hada musu kayansu, tas
muka tattara komai wani abun ma a hannu aka dauke shi Anty dacAmna suka kai musu.

Dakina na shiga na ringa riskar kuka wannan rashin Adalcin da akayi mun.

AMIRAH A DAREN JIYA

Na Maryamah Farouk

(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)

Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 43

AMIRAH A DAREN JIYA

Se dare Bashir ya koma gida har sannan tana nade tana jiran yazo ya rarrasheta. Bayan sallar Isha ya
shiga lokacin ta gaji ta fito palour tana zaune tana kallo ga yunwa tana ji amma ta kasa tashi ta girka
abinda zata ci, jira takeyi ya dawo se suje su siyo abinci.

A sake ya shigo gidan tayi masa sannu da zuwa ya amsa kafin ya ajiye ruwan dispenser daya siyo ya
dawo palour ya zauna yana cewa

“Kawo mun Abinci yunwa nake ji”.


Seta tsaya tana raba ido, wane abinci kuma yanzu ita da take jira ya dawo su siyo shine ze zo yana wani
tambayarta dan haka ta gyara zama a shagwabe tace

“Nima fa Yaya yunwa nakeji, kai nake ta jira tun dazu ka dawo se muje muci abincin”.

“Saboda babu kayan girki a gidan nan ko kuma baki da hannun da zaki dafa ko yaya?” Ya fada cikin
muryar bacin rai, zata qara magana ya daka mata tsawa yana cewa

“Ki wuce ki samar mun abinda zanci Yanzu bana son bata lokaci, sannan daga yau ma idan zakiyi girkin
dare ki ringayi tareda yara anan zasu ringa cin abinci”.

Harta miqe ta koma ta zauna tana cewa

“Wane Yara zan ringa girki dasu ba a gidan su suke ba sannan kuma ni zan ringa musu abinci gaskiya
bazan iya ba”.

“Ba wai shawarar ki na nema akan zakiyi ko bazakiyi ba umarnine tunda gidan ubansu ne dole ki dafa
abinci ki ajiye musu ko bazasu ci ba, kuma kitashi ki samar mun abinda zanci yanzu karki bata mun rai”.

Miqewa tayi ta tafi Kitchen din tana mita “haka kawai wallahi babu dan da zan yiwa girki yaran ma suna
gurin uwar su ace ni zan basu abinci wannan ma bame yuwu ba bane ai”

Haka ta dora ruwa ta saka kwai guda biyu sannan ta dora wata tukunyar ta hau dafa musu Indomie, a
maimakon ta jajjaga attaruhu ta zuba se kawai ta saka dakakken Yaji ko Albasa bata saka haka ta zuba
masa a plate da kwai kwalli daya a gefe ta saka fork ta kai masa.

Akan centre table ta ajiye, ta koma ta dakko masa ruwa da lemo sannan ta dakko nata abincin harta fara
ci sannan Bashir ya fito daga dakinsa ya chanza kaya da alama wanka yayi.
Seda ya zauna akan kujera kafin ya kalleta yace “Ina abincin nawa?”

“Gashinan tun dazu na gama baka fito ba Allah yasa ma bata huce ba”.

Wani kallon banza yayiwa farantin da abinda yake ciki kafin ya saka hannu ya dauka ya tona Indomin da
cokalin ciki yana kallonta yace

“Ni zanci wannan abun? Meye wannan kikayi? Idan ma Indomin zaki dafa haka akeyi duk kayan hadin da
suke a cikin Kitchen kika gagara sakawa shine zaki kawo mun abu kamar na yan birsin ga wani kwai guda
daya akai”.

“Wallahi Yaya ka fiya qorafi kaci mana kaji ai tayi dadi ba gashi ni har na kusa gama cinye tawa ba kuma
wane hadi za’ayiwa Indomie bayan wannan harfa yaji na zuba a ciki dan tayi dandano....”

A mugun zuciya ya wulla mata farantin Indomin Allah ya taimaketa be qarasa kanta ba ya fadi a qasa ya
tarwatse abinka da tangaran, a tsorace ta kalle shi, ya miqe yayi yo kanta se kuma meya tuna ya kaiwa
Iska naushi kafin ya zari key din motarsa yana cewa

“Allah yasa na dawo na tarar da gurin nan a haka” ya juya ya fita.

Badan tana tsoron abinda kaje ka dawo ba babu abinda ze sakata gyara gurin haka ta dakko tsintiya da
mopper ta kwashe fasashshen tangaran da Indomin ta kai shara kafin ta saka ruwa ta goge gurin.

“Haka kawai mutum se baqar zuciya kamar kuturu ina laifina dan Allah dama na dafa, ni da yasan baze ci
ba se ya bani na qara dan ban qoshi ba yanzu ya wa mutane Asara aikin banza kawai” haka dai ta gyara
gurin tsaf ta wuce dakinta ta fada wanka, tana fitowa ta shiga shiri shafa wancan goga wancan ta gama
ta saka wata hadaddiyar Night gown ta gyara gashinta tsaf ta wuce dakin Bashir dan har ga Allah a matse
take.

Tana kwance tayi daidai tana chatting ya shigo dakin fuskar nan kamar hadiri, to jiki da jini gashi daman
kwana ya dade rabonsa da abin dole ya ajiye fushi suka raya sunnah kafin sukayi baccinsu cikin salama
dukda seda a ka kusa sake wani fadan da yace taje tayi wanka tace seda safe, dataga yana neman bata
mata farin cikin data samu dole tayi wankan suka koma sukayi bacci.

Washe gari ma lafiya qalau suka tashi, ta cije ta daure tayi duk abinda ya kamata akayi sa’a kuwa harta
hada masa abin karyawa suka zauna beyi qorafi ba. Seda ya gama suna zaune a palour yake cewa

“Yaran nan kinji shiru har yanzu babu wanda ya shigo ko basu tashi bane”.

“Eh qilan kasan jiya an sha ruwa gari yayi sanyi may be shi yasa basu fito da wuri ba” ta fada a fili a ranta
kuwa zagi take auna musu tana Addu’ar Allah yasa kar su zo.

“Bari naje na karbo katin wuta shaf na manta jiya dana fita ban siya ba naji kuma mitar tana qara” ya
fada yana miqewa, seda ya sako jallabiyya ya dauki muqullin motarsa kafin ya fita, yana fita itama ta
miqe akan kujera ta kwanta ranta fes a qarshe dai ta samu irin rayuwar da take so ita da Yayanta a gidan
su su kadai suna zuba soyayya.

BASHIR

Yana fita qofar gida ya ga yaran suna Ball, gaba daya suka gaishe shi banda Aliyu da tunda suka hada ido
ya juya baya yana hada fuska se kawai Bashir din ya girgiza kai tareda yin qwafa ya kama hannun
Abdallah yana cewa

“Kun tashi daman me yasa baku shgo gida ba toh?”

“Abbi Mami ta hana tace idan muka sake zuwa gidan seta cire mana kunne ko Yah Abdallah” Ahmad yayi
zuruf ya fada dan daman duk cikinsu shine me dan banzan surutu ai kuwa Aliyu ya kai masa duka yana
cewa

“Waya tambayeka me shegen surutun tsiya kawai”.

“Idan ka sake dukan sa Aliyu sena saba maka, ita Ma’un ce tace kar ku sake shiga gidan yayi kyau zan
nuna mata kuwa na fita iko a kanku” Bashir ya fada kafin fuu ya juya ya koma cikin gidansa.
Amirah da har bacci ya fara daukanta bude qofar sa ya farkar da ita se ta miqe tana goge ido tace

“Wai har ka dawo? daga dan kwanciya ashe bacci ne yayi gaba dani ban sani ba”.

“Wai me Ma’u ta dauki kanta ne har ni zata ce Yarana karsu sake shigowa gidan nan saboda taga na saka
mata ido na barta dasu ko? To shikenan ai kuwa a yau zasu bar wajenta idan yaso se naga wanda zata
sakw hanawa zuwa wani gurin, ki fitar da kwalayen da kika zuba a can dakin yanzu zan fita za’a kawo
sababbin gadaje a saka musu tunda ta kwashe wadancan, Amna da Farida kuma se su zauna a dakin ki
kafin zuwa na samu wasu kudin suma a gyara musu dakin su” ya fada a mugun fusace ya wuce dakinsa
dakko Atm dan ya manta ma dazun daze fita be dauka ba.

Har yakai bakin qofar Amirah data miqe tsaye tace “cabdi wadanne yaran ne zasu dawo gidan nan ni
nace maka zan riqe maka yaya ne ko yaya? Harda ma wasu in basu dakina su zauna wallahi baze yuwu
ba babu dan wanda zan riqe ehe”.

“Idan sunzo seki kore su kinji ko tunda baki da hankali ni zan koya miki har in fadi magana ki tsaya a
gabana kina cewa ba za’ayi ba to ki jira na fito na tarar da ke anan gurin wawiya kawai” ya shige dakin
ransa idan yayi dubu ya baci.

Me matan nan suka dauke shi ma? Ita waccen ta hana masa Yara zuwa gidan sa ita kuma wannan tana
cewa baza su zauna a gidan ba, to ze gani idan gidan ubanta ne seta hana su ita kuma Ma’u ze kwace
yaransa yaga in akwai abinda zata iya yi akai.

Sanda Ya fito Amirah ta shige dakinta dan haka yaja qwafa ya fita, yaso ya tarar da ita wallahi da se
jikinta ya gaya mata tunda yaga alamar ita se an taba lafiyarta sannan take nutsuwa idan banda ma
rashin kunya shi a matsayinsa Amirah zata kalla ya fadi abu tace bazatayi ba? Illar auran qaramar
yarinyar kenan yarinyar da aka haifa akan idonsa ya raineta a gidansa da auran wuri ma yayi yasan tsaf
se haifi kamarta amma yanzu tunda taga makwancinsa shiyasa take iya tsayawa a gabansa tana masa
fitsara zeyi maganinta kuwa.

Amirah kuwa Dakin ta ta shiga, a fusace ta danna kiran Addah tana daga wayar kuwa ta saka mata kuka
tana gaya mata yanda akayi.
“Kayyasan nan to ke me kika ce masa yanzu” Addah ta bada daga daya bangaren,

“Me zance masa kuwa Addah na gaya masa wallahi babu dan da zan riqe shine wai idan gidan uban wani
ne se na hanasu zama ya gani”.

“Kina jina ko, lalabashi kuje a hakan zuwa musan abinyi dan ba mutunchi ne dashi ba kar muje ya sako
mun ke kamar yanda ya saki uwarsu. Suzo din kisan mummuqe zaki musu a gabansa ki nuna kina son su
a bayan idonsa kici ubansu yanda da kansu zasu gudu kinga qarshe se kefin ya koma kan uwarsu yace ita
ce ta kitsa musu mugun abu” haka Addah tayi ta lallaba ta dakyar ta sauka ta yarda zata bashi haquri
idan ya dawo ta kuma karbi yaran idan yaso a hankali ta gasa musu aya a hannu yanda zasu gudu da
qafarsu su bar mata gidan.

Kafin ya dawo kuwa an kawo gado, haka ta danne baqin cikinta ta tsaya suka saka kayan harda
wallpaper aka chanza musu masu suka gama suka tafi ta dawo palour ta zauna tana jiran taga
shigowarsa da yaran tana nan zaune kuwa se gasu daya bayan daya suna shigowa kowa fuska jiqe da
hawaye.

Muryar Bashir da tajiyo daga waje alamar shima yana dab da shigowa ya saka ta tashi ta taro Yan biyu
tana cewa

“Meyasa kuke kuka da nan da gidan Mami ai duk daya ne kuje fa kuga yanda aka gyara muku dakin ku
yayi kyau sosai”.

“Karki sakw tabasu kuma babu ruwanki damu a gidan nan kiyi harkar ki muyi tamu in ba haka ba kuma
zaki sani” Aliyu ya fada yana fizge su daga hannunta kafin ya wuce dasu dakinsu yana sake balla mata
harara Amirah kuwa da kallo ta bisu kawai baki bude, badan Bashir na waje babu abinda ze hana taci
uwar yaron nan yau amma ai suna hade, Bashir din zeyi nisane wallahi seta koya masa hankali.

Kowa tayi ta zauna sega Bashir kaman wanda aka wullo, kallo daya yayi mata, yaso ace ta ci gaba da tata
fitsarar ya ida saita mata nata hankalin tunda ya gama da Ma’u amma sabanin haka se yaga ta miqe tana
murmushi tace
“Yara sun shigo suna kuka, ina ta lallashin su ma suka wuceni suka shige daki. Kaje ka lallabasu dan Allah
badadi yaro ya ringa kuka”.

Wuce ta yayi ya shiga dakin nasu, suna nan har sannan sun hada kai suna kuka musamman Faridah da
take ita kadai yau Babu Yah Amnah, Aliyu dai yana tsaye yana huci dan a fusace ya waiwaya da aka bude
qofar ya zata Amirah ce ganin Bashir se ya mayar da kai gefe yana ci gaba da lissafi a ransa.

Bashir kuwa tsayawa yayi, seda ya irgasu kamar wasu yayan kaji kafin ya sake fita fuu kamar iska ya tafi
gidan Ma’u, yayi Sa’a qofar a bude take dan tunda suka fita tana zaune tana kuka Ita da Amnah Anty
kuma tana zazzaga mata masifa dan ta gaji da lallashin se ganinsa kawai sukayi ya fado yana cewa

“Ina Amnah? Nace ki tattara mun yarana shine zaki rage wasu akan wane dalili ke wuce mu tafi” ya
qarasa yana kama hannun Amnah da tunda ya shigo ta miqe, tundazun taso ta bisu amma kukan da taga
Mamin nayi ya sakata tsayawa daman jira takeyi idan tayi shiru se ta tafi daga baya.

ASMA’U

Toshe kunnena nayi naqi jin lallashin da Anty takeyi mun dan kuwa ba abinda zata fada mun tunda taqi
hanawa Bashir ya kwashe mun yara, kuka nakeyi haiqan, daman ba wai na gama mantawa da abinda ya
faru bane Aa kawai dai na bawa kaina haquri ne na dangana shine yanzu za’a sakeyi mun fami.

Bashir ya rabani da aure na, ya kuma rabani da yarana sannan kuma ace nayi haquri wai na dena kuka ai
wannan zance ma be taso ba babu wanda ze fahimci halin da nake ciki se wanda masoyi ya tabayi masa
yankan qauna a rayuwa.

Shigowar da Bashir yayi ban ko daga kai na kalle shi ba seda naji yaja maganar Amna tazo su tafi kafin na
dago fuskata data jiqe da hawaye tayi jajir na kalle shi nace

“Ina tunanin abinda ka fara sha Bashir yana gaya maka qarya. Yaranka kace na baka kuma na baka, idan
ka manta ne kuma bari na tuna maka Amnah ba yarka bace qanwata ce babu kuma abinda ka hada da
ita dan zama na takeyi a gidan ka yanzu kuwa bata abinda ta manta a gidan ballantana ta koma su dai da
yake gidan Ubansu gasu can an baka itama zata zauna a gidan da aka biya da kudin ubanta”.

Wani kallo ya watso mun da na kasa fassara kona menene idanunsa sunyi fici fice har wata kwallar
masifa ce ta taru a acikinsu, nuna ni yayi da hannu yace “bani da lokacin ki yanzu dan ba gurinki nazo ba,
idan kuma kin isa seki hanani tafiya da ita mu gani” ya fizgi Hannun Amna zasu fita na jawo ta baya da
qarfi har seda ta fizge daga hannunsa kafin na daka mata tsawa nace

“Wuce ciki, kai kuma ka fita idan ba haka ba wallahi se nayi maka abinda harka mutu bazaka taba
mantawa dani ba. Maganar lokaci kuma har abada karka tabayin lokaci na Bashir saboda a sanda kake
tunanin kayi lokacin nawa kafin nan ni kuma nayi maka nisa tamkar tazarar sama da qasa sedai kallo.

Daga yau ka dauka cewa bamu taba hada komai da kai a rayuwa ba Bashir, aure ne dai ya qare a
tsakanin mu yara kuma da suka hada To gasu nan kaje ka kwada su ka cinye duk tsiya dai baka isa ka
canza musu wata uwar ba Asma’un nan dai tana nan a matsayin uwarsu”

Na dakata na share hawayen fuskata kafin na cigaba da cewa

“Daga yau idan Anyi duniya dan manzon Allah na gama qunsar takaicinka Bashir kuma ka qaddara cewa
naka shafin baqin ciki da zubda hawayen yana dab da budewa a rayuwa” Ina gama fadar haka na wuce
daki na barshi a tsaye yana bina da kallo, jiki a sanyaye kamar wanda aka zarewa laka ya juya ya fice
daga gidan.

“Allah yasa da gaske kikeyi, dukda da ciwo amma idan kika daure kika mayar da komai ba komai ba Ma’u
zakiga ribar hakan a gaba. Bance ki dena son Bashir ba amma Ki share daga zuciyarki, ki gayawa kanki
koda Bashir ko babu shi zaki ci gaba da rayuwa ki kuma tsohuwar Asma’un ki wani koke koke duk ba naki
bane abinda be faru ba shi ake tara wanda ya faru kuwa sedai a kiyaye maimaita irinsa.

Kina kallonsa yanda yake abubuwan sa tamkar babu abinda ya faru, gidan da kika fita ya dakko wata ya
saka dan ya nuna miki dake din da babu ke babu abinda ze chanza masa kuma walwalarsa yakeyi amma
ke yana takalarki da duk abinda yasan ze quntata miki kuma ki biye masa ina dalili?
Ai wallahi yanzu shi ya kamata ki nunawa yayi babban Rashin da baze taba maida irinsa ba, ki tattara
hankalinki guri daya ki koma aikin ki, ki ci duniyarki da tsinke dama ce yanzu ubangiji ya baki ta ki samu
duk abinda kika rasa a baya.

Kin auri Bashir saboda kina mugun son sa yanzu kingani ga damar ki ta se irin mijin da kike so zaki samu
kin kuma san kura kuren da kika tafka a zaben baya yanzu zaki kiyaye su shine kuma zaki zauna kina
baqin ciki da abinda Allah ne ya so ki ya qwato miki yan cin ki.

Koda ace gaba zaki koma gidan Bashir Ma’u ina so kafin lokacin yasan kima da darajar ki ta yanda koda
Allah ya sake qaddara zama a tsakaninku zeyi miki ruqo na gaske da bare sake bari ki kufce masa ba,
amma kin zauna abu kadan ya jangwaleki kiyita masifa yana jin dadi haka mana Ma’u ki farka daga
wannan magagin da kikeyi” haka Anty ta cigaba da gaya mun maganganu har seda ni kaina na ji haushin
kaina kafin ta barni ta koma gida.

BASHIR

Sosai yanayi da kalaman Ma’u suka dake shi, babu abinda yafi tayar masa da hankali irin hawayen daya
gani suna zuba daga idonta, me yasa shi a koda yaushe yake zama silar kukanta ne? Wai takamaimai
meye dalilin daya saka ya kasa bawa Ma’u irin kulawar data kamaceta tukuicin sadaukarwar ta a gare
shi?.

A duk sanda ya kalli cikin idonta yana hango tarin so da qaunar sa a ciki irin wanda yake saka mutum
aikata komai domin farin cikin wanda yake yiwa wannan soyayyar amma a yau sam bega hakan ba illah
tarin tsanar sa da dana sanin kasancewa dashi daya hango a cikin idanunta da suke zubar da hawayen
nadama.

Harga Allah yana son Ma’u, yana kuma tsoron kar wannan abun daya aikata ya saka ta tsane shi domin a
duk sanda So ya koma qiyayya yana zamowa me zafin gaske, idan kuwa har ace tarin so da qaunar da
Ma’u take yi masa suka rikide zuwa Qiyayya tabbas ya shiga gararin rayuwa dan kuwa babu wani ruwa a
duniyar nan da ze ishe shi wanke kansa yayi hasken da zata kuma kallonsa harta maida masa da wannan
so da qaunar daya rasa.

Abu daya ne idan ya tuna yake sakashi jin dama dama wato cikin jikinta, a qallah yana da watanni bakwai
kwarara da ze taka duk irin rawar da yake so daga qarshe ko taqi ko taso ya mayar da ita dakinta a
sannan kuma ko sama da qasa zata hade babu wanda ya isa ya saka shi ya qarashe sauran igiyar datayi
musu saura a tsakanin su koda kuwa Ma’u zata ringa yankar naman jikinsa ne saboda qi sedai ya mutu
sannan ta samu yanci amma badai ya sake sakinta ba wallahi.

Da wannan tunanin ya koma cikin gida, duk yanda yaso ya rarrashi yaran sunqi sauraren sa haka ya
haqura ya qyale su, a cikinsu ma yafi tausayawa Faridah da take mace ita kadai, da Amnah tana nan
bashida ko wacce damuwa yasan zata kula dasu tamkar Ma’u tana nan amma yanzu besan yanda zeyi da
Faridah yasan bazata sakw da Amirah ba.

“Kodai na mayar da ita gurin Ma’u?” Ya raya a ransa,

“Kai amma ai in nayi hakan kuma na kwafsa na gama buyagin banza tun ba’aje ko ina ba kenan taga
gazawata, haka zata haqura har ta sake da Amirah da sauqi ma tunda ba nisa Ma’u tayi ba kullum zasu
ringa ganin ta a hankali ma zasu warware su saba da zaman kafin komai ya daidaita mu ci gaba da
rayuwar mu cikin farin ciki” Alhaji Malam Bashir ya sakw ayyana hakan a ransa.

Da rana Amirah tayi iya yinta ta musu jalof din shinkafa taji busashshen kifi da nama, ganin Bashir na
zaune data gama harda zuwa ta kirawo su suzo suci kai tsaye kuwa Aliyu yace bazasu ci ba.

“Yaya kaje kayiwa yaran nan magana su fito suci abinci mana ni naje sunce sun qoshi” ta fada tana zama
a kusa dashi, seya miqe ya shiga dakin, suna nan jugul sun dena kukan dai amma kowa yayi tagumi.

“Oya muje muci abinci se mu fita yawo ko ina kuke so muje?” Ya fada yana tsugunnawa a gaban gadon
da yan biyu suke zaune, su daman basu tsawwala ba dan ba wani fahimtar budurin da akeyi sukayi sosai
ba kawai duk abinda Aliyu ya fada ne sauran se su mara masa baya shiyasa suka suke zaune a dakin
amma tun dazu Ahmad yake zungurin tagwan nasa yana masa radar su fita shi ya gaji sa zama, daman
yunwa suke ji dan haka suka miqe da saurin su ya kama hannu su suka nufi qofa.

“Baban Mami fa? Bazaka bi mu ba?” Ya sake fada yana kallon Abdallah daya rabe guri guda, se yaron ya
maqe kafada yace

“Aa ni gurin Mami zanje”.


“Toh muje kaci abinci seka tafi Mamin ko?”

“Abbi nima haka” Farida ta fada kamar zatayi kuka. Se ya waiwaya yana mata murmushi yace

“Muje toh kuci abinci me son zuwa gurin Mami ya tafi wanda zamu je yawo mu fita toh” nan da nan suka
hau murna suka bi bayansa banda Aliyu da Jafar da suke tsaye nan fuska kamar Hadari, shima be kula
suba, ai su ba yara bane kamar sauran idan yunwar cikin su ta ishe su zasu fito su nemi abinci.

Haka suka ci abincinsu da yaran ya biye musu sunata labari, zuciyar Amirah kamar ta fashe tsabar baqin
ciki, taso ace sunqi cin abincin in yaso ta huta da sake yi masa wani girkin da daddare seta ajiye abinta
amma yanzu shine zasu wani fito suci gashi se wani biye musu yake suna surutu duk sun bata gurin ai
kuwa bari su gana sedai su gyara ko kuma shi din yayi dan ta gaji wallahi.

Bashir kuwa suna gamawa yace suje gurin Mamin kafin ya shirya se su tafi, haka suka kwasa da gudu
zuwa gidan be ko bi takan Amirah dake mitar an bata guri ba ya shige dakinsa ya shirya tana kallonsa ya
ci kwalliya yace mata sun fita da yara kar tayi girkin dare zasu taho da abinci.

ASMA’U

Muna zaune shiru su Faridah suka shigo da gudu suna rige rigen fadawa jikina. Da murnata na tare su
wata zuciyar tana cemun

“Badai ya haqura ya dawo mun dasu ba kai amma da kamar wuya”.

“Mami unguwa zamu je da Abbi yanzu Yah Amnah ki chanza mana kaya” Ahmad ya fada.

“Iye yan gatan Abbi to ai kayan naku suna can gidan kuma na jikin ku ma babu abinda sukayi zaku iya
zuwa dasu” na fada ina duba rigunan jikinsu na cire musu rigar sanyin da na saka musu dazu saboda
garin da dan sanyi sanyi yanzu kuma yanayin ya daidaita.

“Mami nima na bisu” Amna ta fada tana kallona, sena daga mata kai kawai alamar “Eh” da saurinta
kuwa ta shiga daki ta hau shiri Faridah ma ta bita dan ita kayan ta ba dukka aka kwashe ba daman. Suna
gama shiryawa muka jiyo horn dinsa daga waje sukayi mun sallama gaba daya suka fice.
Ajiyar zuciya na sauke me qarfi bayan fitarsu dan kaso saba’in cikin fargabar rabani da yarana da Bashir
yayi ya kau dan a zatona ze rabani dasu ne kwata kwata ya hanamun ganin su amma indai har haka za’a
cigaba komai ze zo da sauqi kenan.

Yan gyare gyarena na tashi na shigayi bayan na gama na hau kwaba musu cake na tafiya makaranta
tunda basa zuwa da abinci acan suke basu harna rana shiyasa se nayi musu dan abin tabawa su tafi dashi
bayan sun karya a gida shima Bashir na zuba masa to yanzu kuwa sedai Can Matar sa tayi masa indan
zata iya su dai zan ci gaba da yi musu yanda na saba in zasu tafi na basu.

Ina cikin kwabin cake din Aliyu da Jafar suka shigo, ina kallonsu nace

“Aa ku ban da ku aka tafi yawon kenan?”

“Ban da mu, Mami akwai Abinci?” Jafar ya fada yana nufa yana bude tukunya, Aliyu kuwa kan deep
frizzer ya hau ya zauna yana kumbura fuska,

“Ali mazan fama ya akayi ne ko kaima yunwarce ga abinci nan ku diba ku ci to”.

“Wallahi Mami watarana sena sumar da matar can idan ta sake shiga harkata” ya fada yana sake hura
baki. Se na ajiye Mixer hannuna na juya dakyau ina kallonsa nace

“Wace mata zaka sumar kuma Aliyu?”

“Amirah mana” ya bani amsa kai tsaye.

“Kana jina ko Aliyu, karku kuskura kuce zaku saka abinda ya faru tsakanina da mahaifinku a rai har hakan
ya shafi alaqarku dashi.

Rabuwar mu qaddarah ce daga ya rigada ya tsara iya lokacin da zamu zauna kunga babu abinda ze
chanza hakan, sannan tsakanin ku da matarsa babu rashin kunya dan ba ita ta raba mu ba Allah ne ya
kashe auran mu.
Koda wasa karna ji dayan ku yayi mata wani abunda ba daidai ba dan idan ma kunyi a maimakon ku ce
kun rama abinda akayi mun qaramun laifi zakuyi aringa cewa ni na saka ku dan haka babu ku babu
sabgarta. Duk abinda kuke nema a gidan baku samu ba kuzo nan shikenan”.

“Amma ki gaya mata wallahi Mami duk randa ta qara zagar mun uwa ko tace zata dakeni kafin ta fara ni
zan doketa tam” Aliyun ya sake fada kafin ya sauka daga kan freezer ya fice daga Kitchen din gaba daya.
A yanda yayi maganar hatta da muryarsa se najita kamar ta Bashir idan yana cikin fushi se kawai na bishi
da kallo kafin nace

“Allah ya shirya ka ya rage maka wannan zafin zuciyar” se na juya kan Jafar dake kwasar abinci nace

“Meya hadasu da matar Babanku yake cewa ze daketa?”

GIDAN BASHIR BAYAN FITAR SA

Bayana Bashir ya fita seda Amirah ta tabbatar taji tashin motarsa alamar sun tafi ta sake leqawa taga
basa nan kafin ta kulle qofar ta ciki ta yanda dole se an buga zata zo ta bude.

Dakin su Aliyu ta wuce kaitsaye, A zaune ta tatar dashi da Jafar suna magana sama sama tana shiga ta
kama qugu daga bakin qofa cikin isa da taqama tace

“Ku tashi ku fito, kai Jafar kaje ka share abincin da qannenku suka zubar kai kuma Aliyu ga kwanukan can
a Kitchen seka shiga ka wanke”.

A tsakanin su babu wanda ya tanka mata dan ko inuwarta basu kalla ba suka ci gaba da maganar su,
wata Asharvta lailayo ta aika musu da ita kafin cikin Masifa tace

“Wato ga yar iska ina muku magana kunyi mun banza ba kuna zato zan zauna kamar jaka na dafa muku
abinci ne a bata guri na gyara duk kuna zaune babu me tayani? Naga da uwar ku tana nan shara wanke
wanke duk ku kukeyi mata dan haka yanzu ma lazim kuyi idan kuna so kuci abinci a gidan nan”.
“Seki bari wadanda suka bata suzo su gyara miki ai kuma aike ba uwar mu bace da zamuyi miki aiki,
abinci kuma daman bamu ce ki dafa mana ba dan ko kin dafa bazamu ci ba. Kuma daga yau karki sake
shigowa dakin nan idan ba haka ba se kin raina kanki Allah” Aliyu ya fada yana tsatstsareta da ido kamar
wani Sa’anta aikuwa tayi kansa fuuu da niyyar kwasa masa mari ya goce hannunta ya bugi katakon gado.

Sosai taji zafi dan da qarfin ta ta kai mari ta riqe hannun tana girgizawa da cije baki Jafar ya kwashe mata
da dariya kuwa nan da nan ta shiga zaginsu tana cewa

“Shegu yan iska marasa mutunchi wallahi se naci ubanku yau a gidan nan naga me kwatar ku” bata
daddara ba ta sake yin kansu, seda taje daf da Jafar zata kai masa Duka ya matsa da sauri kusada Aliyu
daya harde hannu a qirji yana ayyana abinda zeyi mata idan ta kuskura ta tabashi, a yanda yake jin
haushin ta badan wani abu ba da wallahi rufeta zasuyi su mata shegen duka dan daga shi har Jafar din
masu manyan gabbai ne girmansu ya zarta shekarunsu.

Yana cikin wannan tunanin ta kuma kawowa Jafar dake mata dariya duka tana aunawa Uwarsu ashar ai
kuwa ya saka mata qafa ta baya ta tafi kamar zata fadi kafin tayi gaba ji kake Qum ta buga goshi a bango
da qarfin gaske kafin kace me gurin ya tashi.

Ihu ta kwalla tana shafa gurin dan ta bugu ba qarya ji tayi kamar ma har idonta buguwar, tana kuka tana
zaginsu suka tsallaketa suka fice daga gidan ma gaba daya.

WATA KISHIYAR ALKAHIRI CE KO SHARRI)

Na Maryamah Farouk

(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)

Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 44
Har Magriba Amirah na sharbar kuka kamar qaramar yarinya ga takaicin qulun da goshi ta yayi gashi har
yanzu Bashir basu dawo ba ta kira shi kuma bema tsaya ya saurareta ba yace mata se ya dawo ya kashe
wayarsa.

Seda akayi sallah suka shigo gidan da ledoji niqi niqi na kayan maqulashen da suka siyo.

“Kai Anty kalla wani bump a goshinki” Abdallah ya fada yana kwashewa da dariya qannensa na taya shi
tayashi.

“Bari muga, faduwa kikayi a toilet? yah Aliyu ma ya taba yin haka kun tuna?” Farida ta qara tana qoqarin
kai hannunta kan goshin Amirah a mugun fusace kuwa ta doketa har seda ta fadi qasa dai dai lokacin da
Bashir ya shigo gidan.

“Baki da hankali me tayi miki da zaki bugeta haka idan taji ciwo fa” Bashir ya fada yana dago Farida daga
qasan, se kuwa ta kwararrabe fuska tana matsa hannunta tace

“Abbi hannuna akansa na fadi” se hawaye sharr kai kace wadda ta karye ko wani abu.

A rude Bashir ya shiga duba hannun, ya jefawa Amirah mugun kallo yace

“Wallahi idan wani abu ya samu hannunta se kin gane kurenki saboda baki san zafin ta ba shine zaki
tureta ta fadi uban me tayi miki”.

Itadai Amirah gaba daya ma seta kasa magana, daga shigowarsa baze tambayi ba’asi ba se ya hauta da
Fada harda yi mata gorin haihuwa, tana shirin buda baki ya tare ta da cewa

“Dallah tashi ki dubo mun man zafi na saka mata, kuma wallahi koda wasa karki sake yin abinda ze taba
mun lafiyar yara dan bana hada komai dasu kin sani”
Baiwar Allah haka ta tashi zugui zugui ta dakko masa se hadiyar zuciyata takeyi tana rarrashin kanta dan
kartayi kuka a gaban yaran su mata dariya, haka ya shafawa Faridah man zafin ita kuwa saboda sharri se
sake langwabewa takeyi ya gama ya dorata akan kujera se sannu yake yi mata, yana juya bayansa tayiwa
Amirah dake tsaye tana kallon ikon Allah gwalo kafin ta koma ta noqe a cikin kujera sauran yaran suka
wuce dakin su suna yi mata dariya.

Bashir kuwa dakinsa ya shige, da walwalarsa ya shigo gida amma daga dawowa har ta bata masa rai.
Yana cikin cire riga ta shigo dakin, se a sannan ya kalli fuskarta yaga kumburin goshinta, ba tareda wata
damuwa ba ya kalleta yace

“Meye wannan a fuskarki kuma bugewa kika yi?”

Kamar tana jira se hawaye shaaaa harda sheshsheqa tace masa

“Ba su Aliyu bane suka tadeni na fadi shine na buge goshi ita kuma Faridah suna shigowa tazo zata taba
naji zafi na tureta shine ka dauka da gangan nayi”.

“Su Aliyu suka tadeki kika fadi kamar yaya? Meya hadaki dasu da har zasu tadeki?” Ya fada yana
tsatstsareta da ido, kanta a qasa tana tunanin qaryar da zata shirga musu yanda idan suka dawo ze rama
mata, can ta dago tace

“Kawai fa dan na sake shiga nace su fito suci abinci shikenan suka hau zagina shida Jafar, ban kulasu ba
na juyo zan fito kawai Aliyu ya sakamun qafa na fadi kuma suka fice sunayi mun dariya. Yanzu dan Allah
kamar ni ko babu aure tsakanina dakai ai akwai yan uwantaka ya kamata su girmamani amma ba haka
ba se ma kaji irin zagin da sukayi mun ta uwa ta uba” ta qarasa tana goge majina da hannun rigarta.

Bashir kuwa sakare yayi yana ji da ganin ikon Allah, wai suka tade ta ta fadi to ai koda Aliyu da Jafa nada
girman jiki ya tabbatar Amirah bazata tsaya su kada ita ba tunda itama ba kadan bace idan ma sun kayar
da itan dole akwai abinda ya hado su dan haka kawai bazasu kamata da komawa ba.

“Kina ji ko? indai kina so ki zauna lafiya da yaran nan to ki kama girmanki a cikin gidan nan. Babu ruwanki
da shiga shirgin Aliyu ko Jafar. Su ai ba kamar twins bane da se kin ajiye su kin zuba musu abinci ko su ci
abinci ko karsu ci ba damuwarki bane abunda yake naki ki dafa musu ki ajiye idan sunji yunwa da kansu
zasu fito su nema.

Bana so na sake jin wani abu makamancin haka ya faru wai kin shiga dakinsu har ta kai ku gayin rigima
wani yaji ciwo, ki kiyaye”.

“Oh abinda ma zaka fada kenan, laifina ka gani yanzu bana su bama kenan? Toh wallahi bazan yarda ba,
daman na bari ne ban dauki mataki ba ina jiran seka zo amma tunda bayansu kabi wallahi se jikin yara ya
gaya musu a gidan nan dan babu shegen dan da ze taka ni in saka ido ina kallonsa” Amirah ta fada tana
miqewa tsaye zata wuce, a fusace Bashir ya tsayar da ita yana cewa

“Na rantse da Allah kika sake kiran yarana da shegu sena chanzawa bakin ki halitta tunda ke baki da
hankali ba kuma kisan abinda zaki fada ba, sannan karki fasa dukan su ni kuma babu yaron da zan
tsawatarwa a gidan nan idan ya miki rashin kunya tunda abinda kika zaba kenan” fuu ya wuce daki ya
barta a tsaye tana qunquni.

Tana tsaye a gurin su Aliyun suka shigo, ta waiwaya ta kalle su, badan ba wallahi seta tsinka musu
maruka koma ta rufe su da duka dan gani takeyi zata iya, amma tsoron abinda Bashir ze iyayi ya sakata
watsa musu harara kamar idonta ze fado suma kuwa basu bata lokaci ba suka maida mata har Aliyun
yana cewa

“Da magana ne?”

Seta ja tsaki kawai ta wuce dakinta, tabbas da sake dole ta dauki matakin gaggawa tun kafin abubuwa su
rin cabe mata yanda bata tsammata ba daga uban har yaran seta dauki mataki akan su ta yanda babu
wanda ya isa ya sake nuna mata yatsa a cikin su.

Haka ta kwana saboda tsabar takaici ko dakin Bashir bata je ba, sanda Faridah ta shiga zata kwanta ma
da masifa ta hauta yarinyar na kuka ta tafi dakin uban lokacin yana zaune yana aiki a laptop dinsa. Gobe
Monday, gashi yana da ayyuka a gabansa da yake so ya qarasa dalilij da ya saka be fita ya kulata ba
kenan se kawai ya cewa Faridan ta hau Gadonsa ta kwanta ya ci gaba da aikinsa yana ayyana hukuncin
da ze dauka akan Amirah.
Washe gari da Asubar fari ya buga mata qofa sanda zasu wuce masallaci akan ta fito ta samar musu abin
karyawa da wuri.

Har suka dawo kuwa yar gaske bata leqo ba dan daman daya tasheta yana fita ta koma baccinta dan tace
ba shegen da zata yiwa girki da Asubar nan su tafasa ruwan shayi akwai komai har Buredi su sha ita bata
saba wannan wahalar ba.

Sanda suka suka shigo a zatonsa ta tashi tayi sallar harta shiga Kitchen dan haka dakinsa kawai ya wuce
ya tashi Faridah yace taje dakin Amirahn tayi wanka ta shirya shima ya shiga wanka.

Da dari dari Faridah ta shiga dakin se ta tarar da Amirah ta shanya baki tana bacci abinta dan haka sadaf
sadaf ta shige bandakin ta rufe a hankali dan karta tasheta, har kuwa ta gama wankanta ta shirya ko
motsi Amirah batayi ba, saboda neman tsokana ta kwashi turaren Amirah ta feffesa da sauri ta kwashe
kayan data cire ta fella gidan Ma’u da gudu dan ita daman Uniform kadai ta dauka a kayanta komai yana
dakinsu na gidan a can ta barsu.

Sanda ta je ta tarar da Amna na hada Breakfast Ma’u na wanka dan sun makara tashi da safen, tana
ajiye kayanta ta wuce Kitchen takwashi dankalin da Amna take soyawa tana cewa

“Yah Amnah ki qara wani nasan yanzu yunwa zata koro su Yah Aliyu zasu zo har Abbi, bafa ta tashi daga
bacci ba haryanzu Anty Amirah bare ta bamu breakfast” se ta miqe da sauri kuma ta shiga hada tea tana
cewa “bari na zuba a Water bottle na sha a mota dan nasan yanzu Abbi ze fara a fito a fito bata rufe
bakinta ba sega sallamar su Aliyun yan biyu suka tuga Kitchen da gudu jin qanshin abinci babu bata
lokaci kuwa suka dirar wa Dankalin dan ma kamar Amna tasan za’ayi haka ta soya da yawa daman niyyar
ta ta zuba musu su qara ko a mota kafin suje makaranta.

Tas suka cinye kowa ya dauki container cake dinsa da inibi da yar cakulatin da ake saka musu Suna haka
ma’u ta shigo Kitchen din ta shirya tsaf cikin wata doguwar rigar Jallabiyya baqa da bata da Adon komai
ta saka hula a kanta kafin tayi rolling mayafin rigar hannunta riqe da qaramar handa bag Fara se qamshi
me sanyi takeyi.

ASMA’U
Da mamaki na kalli yaran ina cewa “ku kuma daga ina haka da sassafe se dambe kukeyi da abinci kamar
wadanda sukayi kwanan yunwa”.

“Mami ai tashin yunwar mukayi shiyasa ba’a bamu abin karyawa ba” Jafar ya fada yana dariya,

“Allah ya rufa asiri, se kuyi saurin kunsan yana jiranku” na fada ina rufe baki kuwa sega horn din Bashir
kamar wanda ze tashi gari.

Tareda su muka fito tunda sun cinye abincin na haqura idab naje office na nemi wani abun, kallon
second daya nayi wa Bashir daya bude mota ya fito a fusace inaga da binsu cikin zeyi, har zan wuce se na
sake waiwaya wa nace

“Baban Ali ina kwana” be amsa ni ba nima kima daman ban saka raiba, na kunna mota ta na ajiye jakar
na sake komawa ciki dan na manta da wayata. Sanda na fito sun yafi nima naja na wuce nawa uzurin a
raina ina ta mamakin ya akayi Amirah bata basu abin kari ba?

“Qila tana ta baccin nan nata na asara” na ayyana a zuciyata kafin na tabe baki na ci gaba da tuqina.

BASHIR

Qarfe bakwai saura ya fito daga dakinsa tsaf cikin shirin tafiya aiki, gaba daya wani daban ya ringa jinsa,
kayan kansu ji yai kamar ba daidai ya saka ba seda ya ringa kallon kansa a mudubi ya tabbatar dai daidai
yake kafin ya fita palour.

Ya rigada ya saba daga litinin zuw Juma’a Ma’u ta ware masa Suit din da ze saka hatta da takalmi da
agogo komai seta ajiye masa sannan idan ze shirya tana tsaye tana taya shi ya gama ta fesa masa turare
sannan su fito suci abinci cikin nishadi kafin kowa ya tafi aikinsa.

A shirye ya tarar da yaran, Aliyu ne yayiwa yan biyu wanka ya shirya su tsaf kowa ya fito goye da jakar
makarantar sa suka zauna a palour shiru dagani shi suke jiran fitowar sa. Yan biyu ne suka gaishe shi ya
amsa dan sun rigada sun gaisa da ragowar tunda Asuba, seya kalli kan Dining yaga wayam dan haka ya
nufi Kitchen a zatonsa tana ciki amma yana zuwa nan ma babu kowa babu ma alamar an girka wani abu
a cikin sa.

Dakin Amirah ya tafi yana shiga tana miqewa zaune da alama tashinta kenan ta gantsare tana miqa, cikin
muryar wanda ya tashi daga bacci tace

“Kai qarfe nawa ne naga harka shirya yaya ko daman da Asuba kake fita?”

Be amsa tambayarta ba, ya ce mata “kinyi sallah?”

Shiru ta masa alamar bata yin ba kenan abinda ya qara bata masa rai a mugun fusace yace mata

“Da zan fita sallah ban tasheki ba sannan na gaya miki kiyi mana abin kari da wuri shine saboda rainin
wayo kika ci gaba da baccinki ko?”

Seda ta zauna sosai kafin ta kalle shi tana tura baki tace “ni banji sanda ma ka tasheni ba, kuma abin kari
baga kayan shayi nan ba harda buredi kawai ruwa za’a saka a kettle fa kawai shine sena tashi nayi muku”
ta qarasa tana juyar da fuska gefe, Bashir kuwa kallonta kawai ya ringa yi, badan ba seya kwada mata
mari wallahi amma dukan Mace ba dabi’arsa bace, dan haka ya juya kawai yana cewa

“Wallahi Kinji na rantse idan na dawo na tarar da wani abu ba yanda ya kamata ba a gidan nan se kin
gane kurenki tunda naga alamar ke ba’a gaya miki magana kiji da kunnenki to masan maganin ki” bamm
ya buga mata qofa ya fice.

Amirah kuwa ko a jikinta ta miqe tana cewa “oho dai, girki ne bazanyi ba haka kawai ni ban haifa ba a
ringa sakani tashin Asuba. Dama kai kadai ne na daure nayi amma wallahi bazan girkawa wasu qattin
yara har shida abinci da Asuba ba suci su zageni ko to sedai suje uwarsu ta basu badai ni ko in ka gaji ka
ringa dafa musu” tayi shigewarta bandaki, ba ita ta gama rashin hankalinta tayi sallar Asuba ba se kusan
takwas na safe.
Bashir kuwa yana fitowa yaga basa palour, yasan bazasu wuce gidan Ma’u ba a ransa yaji wani sanyi ko
banza zaman ta a kusa dasu Alkahiri ne.

Yaransa basu taba tafiya makaranta basu karya ba ko shi kansa se dai idan baqin halinsa ya motsa yaqi ci
amma babu ranar banza da bazata dafa masa abinci ba amma yanzu daga zuwan wannan yarinyar ta
fara yi musu horon yunwa dole ya taka mata burki.

Yana sane ya ringa fafara musu horn ga haushin yasan yanzu suna can suna cin dadi shi kuwa sedai yaje
yaci a Cafeteria kawai yayi manaji gashi har an fara saka masa ido kwanakin nan da yake ci acan har suna
tambayarsa ko dai Madam tayi tafiya ne yace musu Eh yanzu hakan dai zeje yau ma amma daga gobe
dole ta shiga hankalinta, idan batayi wasa ba harna rana seta girka ta aika masa dashi kuwa.

Ganin da yayi wa Ma’u y sake hasalashi, tayi qara fari tayi kyau abinta a yanda ta fitan nan babu me
mata kallo matar aure ma bare har a hasaso mata yaya shida dole itama yaja mata kunne gaskiya tunda
dai haryanzu ai da auransa akanta. Haka ya wuni ranar a gurin aiki cikin quncin dashi kamsa be san na
menene ba, sanda ya tashi ya tsaya ya siyi fruits da kaza kafin ya wuce gida.

ASMA’U

Hankali kwance na ringa tuqina harna isa ma’aikatar mu, muka gaisa da abokanan aikina cikin mutun
taka suna yimun sannun rashin lafiyar danayi qaryarta har na zauna ranar aka bani tukuicin saki nidai se
yaqe nake ina amsa musu dan a yanzu bana son wani abu da ze ringa tunamun da wancan Al’amari.

Se da muka fita break din rana Olivia wata abokiyar aikina ta same ni ina cin abincin da se a sannan na
samu na siya.

Cikin harshen turanci take cewa

“Asma’u Juliet tana gaya mun wata magana ranar amma ban yarda ba wai dagaske ne kun rabu da me
gidanki baku tare yanzu?”
Sak nayi ina kalllon Olivia, daman Olivia irin mutanen nan ce maso shegen gulmar bala’i duk wani abu na
ma’aikatar nan kaji shi a bakinta ka rasa ta inda ma take samun labarai akan mutane kuma idan taji
daman ka qaddara kamar anyi yekuwa ne dan kowaanne ma’aikaci se labarin nan ya isar masa.

Dagaske yanzu dai mutane sun dena kiwon akuya sun koma mutum tabbas, Juliet din da take magana
qawarta ce ni kuma a estate dinmu take budurwar wani abokin aikin su Bashir ce a gidan sa take da
zama bama fa layin mu daya ba suna can qasan mune amma ace har labari ya kai musu ashe dai ba a
arewa kadai mata suka iya gulma da sa ido ba harda suma a nan kudu.

Bude baki nayi da niyyar bata amsa Maman Islaha qawata ta gurin aiki ta qaraso wurin, cikin fada fada
tace da Olivia din

“Wannan wane irin rainin wayo ne zaki ajiyeta kina mata wannan tambayar ina ruwanki da auranta da
kike tambaya akai ita wadda ta baki labarin meya hana ki tsayawa kiji inganjinsa a gurinta? Dallah
malama bar gurin nan tunda baki da aiki se soka baki a rayuwar mutane da shegiyar gulma kawai” sosai
ta balbaleta da fada dan Maman Islaha irin yarabawan nan ne da basa daga qafa.

Olivia kuwa simi simi ta bar gurin tana waiwayena, mayar da kai nayi ina juya abincin dan gaba daya ya
fita a raina Maman Islaha ta dafa ni tana cewa

“Ki manta da ita kici abincinki ni wallahi mamaki kika bani ma da baki dauke ta da mari ba ace kina zaune
tazo tana miki irin wannan maganar se kace ubanta ne ya kashe miki auran, idan kuma mijinki take so
tun wuri se ki san me ake ciki...” seta dakata ganin ina hawayen da ni kaina bansan sanda suka fara zuba
ba.

“Maman Faridah lafiya meya faru?” Ta fada a rude tana ruqoni, sena saki kukan gaba daya ina cewa

“Yanzu dan aurena ya mutu shikenan har na zama abin gulma ana yayatani a duniya kenan?”
“Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un auranki ya mutu Maman Faridah dagaske? yaushe? Kardai yarinyar nan
son mijinki takeyi din da gaske kiyi mun magana” ta jero mun tambayar daga ganinta kasan hankalin ta
ya tashi da jin maganata.

Seda na tsagaita kukan dan har hankalin masu cin abinci ya fara dawowa kanmu kafin nayi mata bayanin
komai cikin sanyi tun kafin na kai qarshe ta qundumo wata ashar me maiqo da yarbaci ta aunawa Bashir
ta qara lailayo wata ta watsa mun kafin cikin fushi tace mun

“Amma kin bani mamaki Maman Faridah yo se me shi ya tafka asara fa ba ke ba dan wallahi harya mutu
baze taba maida kamar ki ba shine har zaki tsaya kina kuka wani ana yayata ki a duniya an dade ba’a
fada ba tunda ba kanki faru ba sakin aure har a sakeki akan kishiya kintaya kina wani zubda hawaye
mtsw,

Kansa ya cuta in sha Allahu se kin samu me sonki wanda yasan darajar ki kuma akan idonsa zega yanda
za’a ringa tarairayarki sedai ya hadiyi zuciya ya mutu, Allah ya kaimu ki gana iddah ni kaina ina da
Candidates se wanda kika zaba kika darje”.

Haka Maman Islaha taci gaba da gaya mun maganganu da suka sake bani kwarin guiwar yakice Bashir
daga rayuwata, har tana ce mun se na chanza shiga tunda yanzu bani da aure na dena zumbula
wadannan Dogayen rigunan da suke boye dirina se nayi dariya nace mata

“Maman Islaha ko da aure ko babu dole in rufe jikina in kare mutunchin kaina, bafa yarinya ce ni ba
sannan ga yara ina dasu nan da kika ganni ma babu lissafin sake aure a gabana zan ci gaba kawai da
neman kudina na kula da yarana shikenan”.

A ranar bamu tashi da wuri ba saboda mitin din gaggawa da mukayi, abin takaici ina zuwa na kunna
motata taqi tashi bayan nasan lafiya qalau take ba’a ko yi sati uku ba da a ka kaita a dubata a sannan
dinma ba abinda ya sameta shine yanzu zata mun halin qarfen nasara.

Ina tsaye ina ta faman zabga tsaki, David daya daga cikin yaran da suke kula da gurin pakin ya qaraso
yana tambayata lafiya nagaya masa abinda ya faru shine ya bude gaban motar yana duddubawa duk ya
gama yan dabarunsa amma taqi tashi, haka na kwashe kayana daga ciki na kulleta, ga Magriba tayi gashi
duk yan arear mu sun wuce haka dai na kira uber dukda bana son hawa da daddare.
Ina tsaye a daga can gaban get ina jiran me uber wata dalleliyar mota Marsandi qirar shekarar da muke
ciki baqa wuluk se qyalli ta wuceni, da ido na bita a raina ina yaba motar aga quginta kadai zaka san ba
qaramar mota bace a raina nace

“Allah kayi mana arziqi muci me kyau mu saka me kyau mu hau mota me kyau” ina cikin haka se ganin
motar nayi tana dawowa da baya. Matsawa nayi daga inda nake ina waiwaya wa bayana dan naga
tazarar gurij da cikin ma’aikatar mu idan ta kama da abin gudu in fece kar inje masu satar mutane ne se
gani nayi motar ta sake biyo ni ai kuwa na daga qafa na fara sauri, sunana danaji na ciki ya ambata ya
saka na juya da sauri na kalle shi.

“Asma’u” ya sake ambata yana kallona, nima kallonsa nakeyi ina so na tuna ko na sanshi amma banga
alamar hakan ba.

Baqi ne amma ba irin wukuk din nan ba fatarsa a goge take alamar hutu da jin dadi sun ratsata a kallo
daya zaka tabbatar da kyakykyawa ne irin kyau na maza me cike da kamala. A zaunen da yake na
tabbatar da dogone irinsu Bashir sannan yana da cikar halitta bashida qiba amma jikinsa a murde yake
alamar yana daga qarfe daga damtsen hannunsa da yake a bude ma zaka tabbatar da hakan.

Gaba daya a abinda be wuce second talatin ba na qare masa kallon, nayi guntun tsaki dan ban gano wata
alama da take nuna na taba sanin ko me kama dashi ba a rayuwa qila irin samarin nan ne ya canki suna
akayi sa’a ya fada daidai se kawai na juya na fara tafiya a raina ina mitar abinda ya tsayar da me Uber
kusan minti talatin shiru bayan a map naga yana dab da inda nake. Maganar da saurayin ya sakeyi ce ta
sakani juyawa a sukwane ina kallonsa

“Ma’u danja wutar baya Ma’un lelen Baffanta” ya fada yana sakin wani murmushi daya saka gabana
yankewa ya fadi.

“Yusuf” na fadi sunan a rarrabe ina qare masa kallo dan ya fito daga cikin motar ya jingina shima yana
kallona. Murmushinsa me kyau ya sake yi mun kafin yace
“Har kin tuna ni kenan da yake kinji kirarin naki ko, daman na fada miki ko kin manta fuskata a rayuwa
na barmiki abinda bazaki taba mantawa ba gashi kuwa ina fada har kin gano ni, me kikeyi a gurin nan ga
duhu ya yi haka?”

Jinsa kawai nakeyi ina kuma qare masa kallo dason tabbatar da dagaske Yusuf din ne dai ko kuwa wani
ne daya san tsokanar da yakeyi mun ada, se kuma dana nutsu na gane shidin ne amma canjin daya samu
a rayuwa tabbas ya zarta ace ka gane shi a kallo daya yanda kasan wanda aka saka a inji akayi masa qare
qaren abubuwa, Babban abinda yafi bani mamaki ma yarintar da ke tattare dashi.

A sanda nasan Yusuf ma a qallah ya haura shekara talatin kenan yanzu yana hararo hamsin ne amma
nake ganinsa kamar yanzu ne yake talatin din da yan kai.

“Ki dena kallona haka karna komawa matata a rabi ina tambayarki me kikeyi a nan baki amsa ba” ya sake
fada cikin sigar tsokana ya baro jikij motar zuwa inda nake tsaye, se naji kunya na sunkuyar da kai ya
gane kallon qurillar da nake masa.

Ma’aikatar mu na nuna masa ina cewa “Daga gurin aiki nake motata ta lalace tana ciki shine na fito ina
jiran Uber da nayi order”.

“Anan kike aiki Masha Allah Ma’u shiyasa mana seda nayi dagaske na iya gano ki, idan ba damuwa muje
sena ajiye ki shiga motar haya da daren nan babu dadi.

Ban musa masa ba, muka qarasa ya bude mun gaban motar wani sanyi da qamshi suka bugoni har seda
na lumshe ido ina shiga naji na wani lume a cikin kujera kai jama’a kudi dai yayi a rayuwa.

“Wace unguwa mukayi” ya fada yana kallona, se na gaya masa ya kunna motar muka fara tafiya shiru,
Yusuf ne ya katse mana shiruj yana cewa

“Yaushe kuka dawo lagos da zama nasan dai a Gombe kikayi aure koh?”
“Eh Gombe nake bamufi shekara shida da dawowa nan din ba ai bayan daya samu chanjin aiki” na fada
ba tareda na kalle shi ba.

“Ban sani ba ai, ina yawan shigow Lagos dan bana sati biyu banzo ba ga qanwata a gari ai da na tinga
shigowa muna gaisawa. Ina Mijinki Bashir ne sunan sa ko wanda ya kasamu karma muje fa yaji haushina
na dakko masa mata babu izini yanzu yaranki nawa?” Ya sake fada hankalin sa na kan titi, seda na
waiwaya na kalle shi kafin nace

“Yana nan, yanzu yaranmu shida harda twins kaifa?”

“Kai lallai rabone ya kore mu yara shida ai ba wasa ba kice dana matsa da yanzu ana irgamun shekaru
goma sha a qasa” ya fada yana yar dariya nima nayi dariyar ina cewa

“Ba wani nan kawai dai komai ka gani da yanda Allah ya shirya faruwarsa ne kawai”.

“Hakane amma dai ai Ya shammaceni da yawa ya rabani da Ma’u lokacin da na tabbatar nafishi sonki” da
sauri kuma ya buga sitiyari tareda rufe bakinsa yace

“Astagfirullah, Afuwan Ma’u wallahi na manta nake dawo da maganar baya”.

Murmushi kawai nayi se nace “wai ma ya akayi ka gane ni?”

“Ma’u kenan, wallahi ko fuskarki ban gani ba seda na dawo da baya kawai zuciyata ce naji ta buga irin
bugun da ke kadai kike sakata tayi shiyasa na tsaya dan na tabbatar ko ba kece bace tabbas akwai abinda
yake da alaqa dake a gurin shiyasa na tsaya se kawai naci karo dake, kinsan dai ke baki chanza kama ba
kyau da qiba kawai kika qara amma kina nan a Ma’un nan dai me yawo babu dankwali”.

“Yusuf ka bari”

“Na bari Ma’u, Allah na tuba ka yafe mun kasan bada niyya nakeyi ba kawai dai kai ka jarabceni da son
baiwar nan taka har na rasa yanda zanyi a rayuwata”. Yanda yayi maganr har fuskar ta nuna gaskiyar
abinda ya fada ya sakani sunkuyar dakai na qasa, gaba daya se naji kamar ya daure ni da igiyoyi, haka
muka qarasa tafiyar kamar kurane shine ma yake tambayata kwatance har muka qarasa bakin Eatate
din.

“Ko na sauke ki anan ki qarasa?” Ya fada yana kallona se nayi murmushi kawai ya shige da motar bayan
da ya sauke glass suka kallemu ganina ya saka masu gadi bamu hanya tunda sunsan motar bata gurin
bace.

Har qofar Flat dina Yusuf ya paka motarsa, na riqe jakata a hannuna ina cewa “Nagode sosai Yusuf, ko
zamu shiga ku gaisa da yaran?”

“Tab so kike Mijinki ya harbeni kenan, ki bari dai tunda naga guri ai kuma se kun gaji dani zanzo naga
yarana sedai idan kuma mijinki ne ya hana, ina fata dai babu matsala kawo kin da nayi ko?”

“Ba matsala, Nagode sosai ka gaida madam da yara, baka ma gayamun su nawa bane”.

“Zasu ji, guda daya ce Ma’u tana nan ta isheni da fitina yanda kika san ke kika haifeta” yayi maganar
yana miqomun wayar sa dake dauke da hoton wata kyakykyawar yarinya fara tas kamar yar turawa
amma kamanninta sak da Yusuf din bazata wuce sa’ar Abdallah na ba.

“Kai masha Allah, ya sunanta” na fada ina sake kallon sauran hotunan nata.

“Baki ji ba nace miki Ma’u takwarar ki ce”

“Wasa kakeyi amma ko? Ina hajia baka saka sunanta ba zaka ce sunana ka saka” na fada ina kallonsa.

“Wallahi Ma’u ke nayiwa takwara, bama ita kadai ba na qudurce a raina ko yaya mata goma zan haifa
sunanki zanyi ta maimaita musu”

Yanda yayi maganar cikin wani yanayi ya sakani kama hannun motar zan bude ina cewa
“Nagode kwarai toh ka gaida takwara, idan tare kukazo seka kawo su mu gaisa” na danna mabudin naji
qofar a rufe, daga bangarensa ya danna wani abu qofar ta bude, mukayi sallama na wuce ina jin yanda
kayan jikina suka kama qamshin da motar takeyi.

“Tab tsautsayi ace ina gidan Bashir na shigo lift din nan da yau tsirena kawai zeyi ya huta” na fada a fili
ina kaiwa qofar gidana se ji nayi naci karo da mutun, ina daga kai muka hada ido da Bashir da idonsa ya
kada yayi jajir ga wasu jiniyoyi da suka tashi a goshinsa alamar yakai qololuwar bacin rai.

“Wane Dan iska ne ya sauke ki a mota Ma’u” ya fada yana kallona.

WATA KISHIYAR

(ALKAHIRI CE KO SHARRI)

Na Maryamah Farouk

(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)

Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 45

"Magana nakeyi miki Ma'u nace wane dan iska ne ya saukeki a mota a cikin wannan tsohon daren?"
Bashir ya sake fada cikin hargagi.

Ban tankashi ba haka ban matsa daga inda nake tsaye ba sema waiwayawa nayi na kalli wasu samari su
uku da suka zo wucewa suka tsaya kallon mu gashi kuma ko wanne da waya a hannunsa.

"Ka matsamun na wuce gasu can suna kallonka idan kuma so kakeyi suyi maka video seka bada himma"
na fada kafin na raba shi zan wuce cikin gidan se kuwa ya biyo ni kamar wani kububuwa ya sake shan
gabana yana cewa
"Kinsan Allah idan baki gayamun waye wancan ba ba video ba ko gidan Tv zasu dakko su kawo gurin nan
sedai duk wacce za'ayi ayi amma bazaki shiga gidaj nan ba".

Wata dariyar rainin hankali nayi kafin naja da baya ina kallonsa nace

"To wai kai a na me kake so kasan waya kawo ni, kana da matsala da hakan ne? gida kuma kalli dakyau a
qofar gidana kake ba wai gidanka naje zan shiga ba da zakace zaka tare ni dan haka ka matsamun na
wuce malam banyi sallar magriba ba ga Isha ta tarar dani"

ina gama fadar haka na sake yin gaba da niyyar shiga gidan ba zato se ji nayi Bashir ya fincikoni ya watsa
ni baya, takalmin qafata ya gurde na tafi zan fadi Allah ya taimakeni na durqushe ai kuwa ina dagowa
banyi wata wata ba na sauke masa wani bahagon mari da ni kaina seda na aikata sannan na gane
menayi.

Wallahi a lokacin mantawa nayi da Bashir ne a gabana, gani nayi tamkar wani random guy ne haka nan
yayi mun wannan wulaqancin ni kuma zuciyata izani naga ta haka kadai zan rama abinda yayi mun se
bayan danayi marin sanan na dawo hankalina amma se na aro dakiya na dorawa kaina na gyara
tsayuwata sosai ina kallonsa nace

"Koda wasa karka sake yunqurin dora hannunka a jikina dan tuntuni ka haramtawa kanka hakan, sannan
daga yau babu ruwanka da duk abinda ya shafeni, aurene tsakanina dakai kuma ya qare dan haka ina da
yancin yin duk abinda naso ko shiga motar wanda naso ba tareda kai ko wani ya tuhumeni ba ka kiyaye"
na dauki jakata da wayata da suka fadi na wuce shi zuciyata kuwa kamar ana kidan mandiri, seda naga
na tura qofar na shiga be janyoni ya watsa mun marin daya fi wanda na masa ba sannan na sauke ajiyar
zuciya ina share gumin dana hada a goshi.

BASHIR

Wata qara yaji "quuu" kamar gidan radio sun tashi daga aiki haka ya ringaji a kunnensa. Ba zafin marin
ne ya sakashi suman tsaye ba Aa tsabar mamaki da tsoro ne wai shi, shindin dai ENGINEER BASHR
AHAMAD yau Asma'u ta mara da yatsunta guda biyar kuma da gaske ido biyu ba magarki ba abun ya
faru?
Harta gama surunta ta wuce kallonta kawai yakeyi, ji yakeyi dama ace wani ya tashe shi ya zaman
mafarki yakeyi dan wannan abun beyi kama da wanda ze faru a gaske ba ace yau shi Ma'u ta daga hannu
ta mara akan yana tuhumar waya kawota gida a mota sannan har take iya gaya masa aure ne ya hadasu
kuma ya qare dan haka babu shi babu sabgarta, seda ta shige gida ta rufo qofa sannan ya motsa.

Ya waiwaya inda samarin dazu suke yaga basa nan, waya sani ma ko sun nadi abinda ya faru kafin suka
wuce oho. Gaba daya kansa nema ya qulle ya rasa me ya kamata yayi, binta zeyi ya rama marin da tayi
masa ko kuwa ci gaba zeyi da bin ba'asin wanda ya kawota? Kokuwa ya wuce gida ne ya qarasa cin uban
waccen yarinyar da tayi masa jalof din taliya da kifi me qaya a matsayin abincin daren sa wai mema zeyi
a ciki yanzu??

Harya juya kalaman ta suka sake dawo masa "karka sake yunqurin dora hannunka a jikina dan hakan ya
haramta a gareka"

Se kawai ya fasa tafiya ya bi bayanta zuwa cikin gidan, dole ya dakatar da Ma'u daga wannan dogon
mafarkin data shiga ya nuna mata cewa haryanzu igiyar auranta tana hannunsa.

A da yayi niyyar seta zaunu ta nemi sulhu dan kanta amma yaga alamar hakan gangancine, yau wani ya
kawota gida harta daga hannu ta mareshi gobe kuma besan abinda zata sake aikatawa ba dan haka yabi
bayanta dan ya katse mata duk wasu fukafukan rashin kunya data daura a jikinta.

ASMA'U

Turo qofar da akayi ce ta sakani waiwaya da saurin ina ja da baya dan nasan Bashir ne, seda na matsa
ciki dakyau dan na cire takalmana daman na riqe qugu da hannu biyu kafin cikin tsiwa nace

"Wai meye kuma meka manta a gidan nan da zaka ringa shigomun duk sanda kaga dama gaskiya baze
yuwuba, yara ne na baka abinka baka da sauran hujjar da zata ringa kawo ka cikin gidana dan haka yau
ta zama rana ta qarshe da zaka sake sako wadannan qafafun naka anan" na qarasa maganar ina girgiza
jiki kamar wata me fada da Sa'arta.

Da hannu ya nuna ni kafin ya nuna kansa yace


"Ni kika mara ko Ma'u? Ni kika mara saboda a matsayina na mijinki ina tuhumar ki wanda ya dakko ki a
mota da aure na a kanki ya kawo ki gida shine kika daga hannu kika mare ni"

"Malam ka dai gyara kalaman ka tsohon mijina dai ko ka mantane saki biyu masu kyau ka hada ni dasu
kaga kuwa yanzu ni matar me rabo ce, shima da ka gani Bazawarina ne yana cikin sababbin yan takara
wanda Allah ya bawa sa'a shi ze dauka..."

"Ya isheki Ma'u" ya dakamun tsaqar data sakani yin shirun dole ina sake matsawa cikin palour dakyau
saboda gudun kota kwana. A fili nake ganin harzuqar da yayi da tsananin bacin ransa wanda ko dazu
dana mareshi banga hakan ba.

"Qarya kike yi ke tawa ce kuma dan ni kadai aka halicce ki, Wallahi kika sake danganta kanki da wani
Namiji Ma'u se na miki abinda baki zata ba" Bashir ya fada cikin daga murya da har seda Faridah da
Amna suka fito daga cikin dakinsu amma kallo daya ya musu suka maida qofar garam suka kulle.

"Saboda na sake ki ne yasa kika samu lasisin da zaki ringa yawo a gari maza suna daukar ki a mota ko kin
manta da cewa har yanzu kina cikin iddar aurena, to kici gaba da yin duk abinda kikaga ya dace dani
dame mu zuba mu gani wanda zeci riba, amma ki tabbatr duk dan iskan da na sake ganinki dashi se
munyi shari'a".

"Kayi shari'a dasu awanne dalili Bashir saboda sunyi maka me" na fada ina binsa da kallon sama da qasa,
ba abinda ya bani dariya irin daya ce wai ina cikin iddar auransa.

"Saboda sun tsaya da mata ta alhalinbata gama iddah taba" ya bani amsa yana kallona. Seda nayi dariya
kafin na dauki jakata ana ajiye na bude na zaro takardar Asibiti ta shedar barin da nayi, daman yau nayu
niyyar tura masa da ita dan jiya Goggo ta sake kira ta jaddadamun na sanar masa gudun rigima.

Takardar na miqa masa ina cewa" Bashir nida kai fa Allah ya raba tsakani, gashinan ka gani da idonka tun
wuri ka goge wannan tunanin na wata iddah daga zuciyarka dan tuni Allah ya yaye mun.

BASHIR
A mugun kidime ya daga kai ya kalli Asma'u bayan daya karanta abinda a ka rubuta a jikin takardar,
kalmar Abortion' (Abortion itace medical term na bari ba Miscarriage ba 😨 kar yan uwansu Addah suce
Ma'u ta zubar da ciki 😂😂) din da kawai ya gani ya saka wata zufa ta shiga tsatstsafo masa gaba daya ma
se yaji iskar gurin tayi masa kadan se ya shiga fifita da takardar hannunsa yana cewa

"Ma'u ki gaya mun gaskiya tsakaninki da Allah bari kikayi dagaske ko wasa kikeyi".

"Lallai Bashir, kaga alamar wasa anan gurin ne ko kuwa, baqin cikin ka ya saka shima cikin yaga baze iya
zama ba ya kama gabansa ka kalli date din dakyau ka gani in yaso seka hada sadakar uku data bakwai
duk kayiwa Yar dan inaga ma macece" na fada irin ko a jikin nan nawa amma can qasan zuciyata ina jin
zafin rasa aurena da cikina da nayi.

"Wallahi Ma'u na mayar dake, na maida auran mu fada miki ne kawai banyi ba" Bashir ya fada cikin
yanayin da yake bayyanar da tashin hankali da yake ciki, ni kaina a kidime na kalle shi, duk yanda nake
son Bashir nake qaunar zama dashi se naji hankalina ya mugun tashi da jin kalamansa na wai ya mayar
dani, a rude nace masa

"Yaushe ka mayar dani Bashir yaushe ka yi hakan kuma wanene shedar ka"

"Tun ranar da na karbi su Aliyu a daren na qudurce a raina na mayar dake amma ban gayawa kowa ba"
ya sake fada ya na matso inda nake, senaja baya da sauri ina sauke wasu tagwayen ajiyar zuciya nace

"Idan ma ka mayar dani ban komu ba Bashir tunda baka gayamun ba kuma baka gayawa kowa ya zamar
maka shaida ba sannan ni a washe garin ranar daka sake ni Bashir a ranar nayi bari ka duba daye din da
yake jikin takardar nan idan ma baka yadda ba kaje clinic din da kanka zasu tabbatar maka.

Dan haka tsakanina dakai yanzu be wuce zumunchi irin na wadansu da wani abu ya taba hadasu ba
shima albarkacin zuri'ar da take tsakanina dakai, bayan wannan ka qaddara Bashir baka da wata alaqa
dani a rayuwa ba ka kuma da hutumij da zakayi mun katsalandan a rayuwa.
Mun rabu rabuwa ta har abada ka gogeni daga cikin lissafin rayuwarka dukda nasan ka dade dayij hakan"
shiru nayi da maganar da nakeyi jin kuka yana neman kufce mun, bana buqatar na karaya a gaban Bashir
balantana har yayi tunanin akwai sauran burbushin soyayyarvsa a zuciyata.

"Asma'u karki ce haka, ta yaya kike zaton alaqar mu zata yanke kema kinsan wannan bame yuwu ba
bane, muje a kinyi barin na yarda kin fita iddah amma ai da sauran igiyar auran mu ko yanzu zamu iya
zuwa Limamin masallacin can ya mayar mana da aure nasan ko Engineer Abdullahi ze yi miki walicci ni
kuwa na isa na karbarwa kaina aure, dan Allah mubar maganar nan Ma'u bazan iya ba, bazan juri ganinki
tare da wani mutum ba zuciyata zata fashe" Bashir ya fada yana sake damqe takardar dana bashi.

Tsaki nayi dan naga abin nasa ma tsagwaron rainin hankali ne dan haka na kalleshi nace

"Bashir fita zamu rufe gida"

"Naji zan fita amma ki gayamun kin yarda za'a mayar mana da aure ko gobe ne tunda yanzu dare yayi, na
sani Ma'u kina sona bazaki taba iya rayuwa babu ni ba dan haka mu manta da komai mu koma wa auran
mu kinji Ma'u".

"Bashir kenan, wato kasan ina sonka bazan taba rayuwa babu kai ba ko ashe tunanin ka kenan shiyasa ka
ringa garani kamar kwallo baka san qima taba bare daraja, ka auro muj qanwar bayana da nagama shan
wahala akanta sannan ka fifita ta sama dani daga qarshe a dalilinta ka hada ni da saki ka rabani da
yayana ko duk saboda kana tunanin ina sonka bazan iya rayuwa babu kai ba tunda tare aka daure
ruhinmu aka jefi cikij duniya ko?

To bari kaji, ka qaddara kaine numfashina kasan dai idan babu shi babu rayuwa ko? To dana koma zama
dakai Bashir na zabi na mutu akan ka, idan sonka shine Ajalina to ka je ka fara irga kwanakin da suka
ragemun dan wallahi Bashir na gama auranka na gama zama dakai ko kaine autan maza sedai na mutu
ban sake aure ba, mugu me saka soyayya da qiyayya wanda be dauki dan Adam a bakin komai ba" na
qarasa maganar kuka yana kwace mun sena shige dakina na bar Bashir da yake jinsa kamar an sare masa
qafafu tsabar yanda jikinsa yayi sanyi.

Kuka na ringayi kamar zan shide, Allah ya sani ina son Bashir na kuma san har duniya ta nade da bazan
dena sonsa ba amma in Allah ya yarda ko zan mutu na haqura dashi.
Bani Bashir yake so ba, alfarma yayi mun ya zauna dani tsahon shekarun nan saboda ina son sa badan shi
a qashin kansa yana sona ba.

Meyasa ban taba gane hakan ba se a yanzu, me yasa tuntuni nake daukar kalaman yaudarar sa a
matsayin so ashe duk na ya cimma wata manufa ne yanzu daya gama samun yanda yake so a rayuwa
gashi nan ya fito mun sak a halayyarsa ta gaskiya.

Hannayena na daga sama ina kukan nace

"Allah kaine shaidata naso Bashir saboda kai badan wani abu ba kamar yanda kayi mana umarni da mu
so mutum dan Allah sannan na kyautata masa da dukkan iyakar iyawata a zaman aurena dashi, Allah
kagani halin dana shiga Ubangiji na roqeka kayi mun sakayya da mafificin Alkhairinsa, idan kuma bani da
rabon samun farin cikin Namiji a rayuwata Allah ka sanya mun dangana har zuwa ranar dazan koma gare
ka" na shafa Addu'ata kafin na shige goge hawayen fuskata amma sun kasa tsayawa, haka na shiga
bandaki, ina wanka ina kukan harna gama na dauro alwala nayi sallar magriba da Isha.

Ina kam abin sallar ina ci gaba da kaiwa Allah kukana anan bacci yayi awon gaba dani ban ma sani ba.

BASHIR

Ikon Allah ne kawai ya kaishi gida yana shiga ya zube akan kujera yana sakin numfashi a jere a jere
tamkar wanda yayi gudun kilomita goma. Gidan shiru da alama duk sun kwanta yaran haka Amiraj beji
motsinta ba daman tunda ya dawo dazu ta bashi shirmen abincin data dafa yayi mata tijara ta shige daki
baya tunanin ta sake fitowa hakan ma dadi yayi masa dan tabbas idan sukayi ido hudu da ita a yanzu dai
a yanda yake jinsa din nan to komai yana iya faruwa.

A daddafe ya tashi ya shige dakinsa yana jin yanda kansa yake juya masa kamar an kunna fanka ga wani
abu me maiqo da yake taso masa kamar zeyi amai haka ya zauna a qasa gefeb gadonsa ya hada kai da
guiwa ya rasa ina ze kama abin duniya ya hadu yayi masa yawa

"Dana koma gidanka na zabi na mutu, idan sonka shine ajalina Bashir kaje ka fara irga kwanakin
mutuwata dan na gama auren ka" kalam Ma'u suka ringa masa tilawa a kwakwalwa.
"Allah karka jarabce ni da wannan, Allah ka sani bazan iya dauka ba, nayi kuskure Allah dan darajar
Annabinka Muhammad SAW kayi mun sassauci karkasa wannan ya zamo mun qaddadar da bazan iya
dauka ba Allah karka rabani da Asma'u" sambatun da ya ringayi kenan shikadai kamar zararre, wayarsa
ya zaro faga aljihu ya fara laluban numbobi, waze kira ya gayawa damuwarsa? Waye ze bashi sharar
yabda ze gyara wannan kuskuren tun kafin dare yayi masa.

"Bala" hannunsa ya tsaya akai, ba bata lokaci kuwa ya dannan masa kira cikin Sa'a bugu biyu Balan ya
daga yana cewa

"Engineer Mijin Asma'u, na Amirah ko dubu ta taru"

"Bala akwai matsala, ina cikin masifa ina cikin tashin hankali ka taimaka mun ka gaya mun yaya zanyi na
fita wallahi zan iya rasa raina Bala akan wannan tashin hankalin" Bashir din ya katse Bala kamar ze fashe
da kuka ko da yake tuni ma ya fara na zuciya kawai dai hawayen ne suka qi fitowa a fili".

"Subhanallahi Bashir meya faru badai korar ka akayi daga gurin aiki ba?"Bala ya fada

"Wallahi gara na rasa aikina Bala, gara na bayar da komai dana mallaka a rayuwa ta da abinda nake
shirin rasawa"

"To menene meyake faruwa kayi mun bayani yanda zan fuskanta se musan ya zamu kamo bakin zare
wane abune haka daya fi dukiya muhimmanci a gurinka Bashir?" Bala ya sake tambayarsa a tsorace dan
gaba daya kalaman Bashir din firgita shi sukayi.

"Asma'u, itace Bala, Ma'u tafi mun komai zan kuma iya bada duk abinda na mallaka akan fansar ta, Zan
iya bada raina akan Ma'u ka sani Bala" Bashir ya fada dakyar dan qirjinsa ya fara yi masa nauyi, wani irin
zafi zuciyarsa take masa kamar wadda ake watsawa ruwan zafi, Tsakin da Bala yayi ne ya katse masa
tunani kafin Balan ya ci gaba da cewa

"To me Ma'un tayi maka yau kuma yanzu? Kai wai kullum baka da aiki sena kawo qarar Ma'u ne haba ni
wallahi na gaji da jin Ma'u tayi Ma'u tace idan ka gaji ka saketa kawai kowa ma ya huta mana".
"Bala na saki Ma'u shine Bala'in da nake ciki a yanzu ta gama iddah kafin na mayar da ita kuma tace
bazat sake komawa gida na ba ta gama aure na" Bashir ya fada kamar ze fashe da kuka.

"Kace ka saki Ma'u harta gama Iddah Bashir" Bala ya tambaye shi da son tabbatar da daidai yaji ko kuwa
kunnensa ne yajiyo masa abinda ya dade yana fatan faruwarsa.

"Dagaske nake Bala na saki Ma'u saki biyu kuma tayi bari a washe garin ranar dana saketa kaga kenan
iddarta ta ciki ka gayamun ya zanyi na shawo kanta ta haqura mu koma auran mu wallahi ina son matata
idan na rasata zan iya mutuwa ka sani Bala" Bashir ya sake fada a matuqar raunane.

Bala kuwa seda yayi matuqar qoqari gurin danne farin cikinsa kafin ya aro damuwar qarya ya saka a
muryarsa yace

"Ashsha Mutumina ya akayi haka a garin yaya? Amma dai koma yayane aikin gama ya gama yanzu sedai
nemi mafita kuma ayi fatan Allah ya kiyaye na gaba.

Kana ji ko ni nasan Ma'u duk fushin da zatayi ba wani me yawa bane kasan irin son da takeyi maka, dan
lokaci kawai zaka bata dakanta idan ta sakko zata nemeka ku daidaita kaima kasan duk abinda zata fada
buyagine kawai amma Ma'u bazata iya rayuwa babu kaiba kowa ya shaida hakan"haka Bala ya cigaba da
dorashi a keken bera har seda ya yarda kafij sukayi sallama.

Suna kashewa kuwa Bala ya daka tsalle yana cewa

"Allah na gode maka, badai kai wawa bane ka raina ni'imar da Allah yayi maka zaka gabe kurenka wallahi
muje zuwa yanzu aka fara wasan Ma'u kuwa nasan bazan same ta ba amma tunda kaima ka rasa ko haka
aka tashi wasa nayi nasara kuma in sha Allahu bazat taba dawo maka ba".

Allah sarki Bashir shi kuwa Sosai kalaman Balan suka kwantar masa da hankali dukda wani bangare na
zuciyarsa yana so yaqi karban hakan dan a yanayin da Ma'u ta nuna tabbas yaga chanje chanje da yawa a
gareta yana kuma jin gaskiya ta fada a maganganunta amma yasan so ba qarya ba, ba kuma ya zaton
Ma'u zata taba tsanar sa a rayuwa ta bakin Balan zafin abinda ya mata ne ya sakata fadar duk wasu
maganganu amma idan ya bata lokaci ta huce yasan zasu daidaita.
Da wannan ya lallashi kansa ya koma kan gado ya qudundune yana so ya manta maganganunta amma ya
kasa ga wani irin tsoro da tashin hankali dayake shigarsa a duk sanda ya tuna kalaman ta na dazu har
wani zazzabi yaji yana neman kama shi.

Anya ze iya bin shawarar Bala na ya bata lokaci harta huce dan kanta? Ya lura idan mafa fushin tayi ba
kadan bane dazu fa har mari yasha, kai ina baze tsaya ya zuba ido yana kallo kwado ya masa qafa ba, a
wannan gabar dole ya ajiye girman kai ya kwato Ma'u tun kafin yan iskan mazan Lagos su hure mata
kunne.

Haka yaringa hada lissafi yana warwarewa, a ranar dai yanda Bashir yaga rana haka yaga dare sabanin
Ma'u da ta shaqi bacci me cike da mafarkai masu dadi.

Washe gari haka ya farka kamar bugagge, ga damuwa ga rashin bacci lokaci daya gaba daya suka nuna a
jikinsa seka zata yayi sati yana jinya idan ka ganshi. Amirah ma dai yau ta kama kanta, danfa jiya da
daddare jijara yayi mata ta gaske akan taliyar da har daddawa ta saka mata gashi taji kifi amma loma
daya Bashir yayi ya ture ya ringa surfa mata cin mutunchi wai bata iya komai ba haka yaran ko dandane
basu ci ba suka gudu gidan uwarsu acan suka kwaso abinci tana kallo suka ci suka bata guri kuma haka ta
share gudun sake yin wani laifin a gurinsa.

Da safiyar ma harda hawaye seda tayi da tana hada musu abin kari, doya da kwai ta soya sannan ta dafa
zallar ruwa ta jefa Lipton ko arziqin kanimfari da citta be samu ba alhalin gasunan tunda ya siyo bata ko
kwashe su daga kan inda ta ajiye ba bare ta zuba komai a ma'adanar sa.

Haka ta gama hada abincin nan kafin dukan su su fito, tana tsaye yaran suka fara fitowa tacewa yan biyu
suzo suci, harta fara hada musu shayi Aliyu yana fitowa ya kada kansu suka tafi gidan Maminsu suka bar
Amirah tsaye tana binsu da kallo tama rasa abin cewa.

Fitowar da Bashir yayi ta sakata waiwaya wa ta kalleshi, a kallo daya ta hango damuwa qarara a fuskarsa
amma ina ba wanann ne a gabanta ba, yana zama a Dining din ta dira masa qorafin sunqi cin abinci Aliyu
ya jasu sun fita ita dai ya kirasu dan bazata hana kanta bacci tasha wahalar banza ba sannan suqi ci in
kuwa ba haka ba zata ajiye musu daga yau har gobe se sun cinye sannan zata sake yin wani girkin.
Bashir daya gaji da jinta, ga damuwar da take kansa ga ta surutun data tsaya masa akai tanayi ya ture
plate din data saka masa doyar ya tashi dan daman sam cin yunwa kawai zeyibawai dab ta masa irin
yanda Ma'u takeyi ba, jiya beci abincin dare ba, ya fita ya nema ya ga babu motar Ma'u a waje abinda ya
kaishi gidan kenan yana tsaye se gata ta dawo yayi wannan mummunan ganin haka ya kwana da
yunwarsa gashi yanzu kuma tasa abincin ya fita daga ransa saboda qorafi.

"Yanzu Yaya ina maka magana shine kaima zaka ture ka tashi ni me aka mayar dani a gidan nan ne a
tilastani nayi girki sannan aqi ci wallahi bazata sabu ba ba kuma zan iya ba" Amirah ta fada tana shan
gabansa.

"Amirah ki rabu dani, ki kuma kama kanki a cikin gidan nan idan ba haka ba zaki ja nayi miki abinda zaki
zo kina dana sani tunda duk ke kika jefani a masifar danake ciki, matsa mun daga hanya na wuce" ya
fada a hankali amma sautin maganar ya sakata shiga hankalin ta.

Da gani akwai abinda yake damunsa idan kuma ta matsa tasan tabbas zeyi abinda ya furta din dan haka
ta matsa masa tana qunquni qasa qasa shidai ya fice ya barta a tsaye.

Yana saka qafarsa a waje idonsa suka sakeyin mummunan gani a karo na biyu, Asma'u ysaye da wani
basamuden Beyerabe suna dariya ga jakarta a hannunsa ya riqe mata yana mata alamar da tayi gaba ta
shiga motarsa kamar wani saurayi yazo daukar budurwarsa zasu fita ita kuma se washe baki takeyi ta
shiga motar yana tsaye mutumin da besan ko waye ba yaja suka wuce Bashir daya dafe motar sa jin jiri
yana neman watsar dashi a gurin.

"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, Ma'una ce nake gani a gaban motar wasu mazan daban bayan ni Allah
me na tuba ka yafe mun kuskuren da nayi ban butulcewa Ni'imar ka ba wallahi sharrin zuciya da shedan
ne suka ingizani" ya fada yana jin ina ma ya samu hawaye ya zubo masa ko ya samu sauqin radadin da
zuciyarsa takeyi masa daga jiya zuwa yau, yana tsaye har besan sanda yara suka fito daga gidanta suka
shiga mota ba seda Jafar yace masa

"Abbi mu tafi mana karmu makara" sannan ya shiga ya tafa motar, tuqi kawai yake amma ikon Allah ke
tafe dasu a haka ya samu ya sauke su ya wuce aikinsa da bashi da tabbacin ze iya tsinana komai yau idan
yaje
To Bashir tsautsayi da Asara Allah ya kiyaye

WATA KISHIYAR

(ALKAHIRI CE KO SHARRI)

Na Maryamah Farouk

(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)

Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 46

ASMA’U

Bacci nasha sosai abuna se Asuba na farka zuciyata wasai kamar wadda aka daukewa wani nauyi daga
kanta. Yanzu babu wani sauran abu a tsakanina da Bashir, aure dai ya qare shima kuma yasan da hakan
sedai muyi Addu’ar Allah yasa hakan shi yafi mana Alkahiri gaba daya.

Muna cikin karyawa da yara da tun sassafe suka zo Abokin aikina Prince Yemi ya korani, shaf na manta
da yau zamuje gurin wasu mutane ne da muke nema su saka saka hannun jari a kamfanin mu seda ya
kirani yake tambayar na shirya tunda wucewa zamuyi base mun biya ta office ba.

Mota ta jiya can na barota dan haka nace masa dan Allah ya biyo ya dauke ni kawai tunda muna ta Area
daya ba a wani dade ba kuwa se gashi yazo.
Haka kawai ranar naji ina son yin kwalliya, kodan yanzu na tabbatar da bani da wata igiya akaina ne oho.

Straight gown na saka ta Atamfa blue datayi bala’in bin jikina amma bata kamani ba nayi dauri na a
gaban goshi na yafa shantili yellow daya dace da Atamfar na kawo baqin takalmi hill da yar jaka itama
baqa na saka, nayi kyau kwarai kamar wata yar late twenties idan ka ganni bazaka ce na ajiye tarin yaran
da suke gabana ba.

Tare muka fito da yaran dukka sanda Yemi yazo dan nasan duk inda Bashir yake yanzu ya yi shirin fita
shima. Dukda qasan zuciyata se naji kamar be dace yau ma ya sake ganina tareda wani ba amma babu
yanda zanyi haka na fito, Yemi yana da faran faran da kuma tsokana, yana ganina nan da nan ya shiga
tsokanata wai nayi kama da sarauniya, ya karbi jakar hannuna harda bude mun qofar mota na shiga Yara
natayi mana dariyar ganin yanda abinda Yemin yakeyi, to su ina ruwansu basu dauki hakan da wani abu
ba ko dan wai ace ina da aure be kamata yayi mun haka ba.

Ina kallon yanda Bashir ya bimu da kallo da yanda ya zaburo mota yabi bayan mu sedai Alah yasa
tundaga gate din Estate muka rabu kowa ya kama hanyar sa. Muna tafe muna tattauna abinda zamujeyi
lokacin, seda muka sake biyawa ta gidan Olivia muka dauketa tana ganina se wani washe baki takeyi ni
kuwa daga gaisuwa ban sake kulata ba muka ci gaba da tattaunawar mu da Yemi.

Mun isa Guest house din mutumin da zamu je yiwa tallan, tun daga Bakin qofa zaka san me gurin ya ci ya
tada kai. Harabar gidan kanta cike take da motoci na alfarma kana ganinsu kasan ba hawan su akeyi ba
kawai dai an siya an ajiye saboda an rasa abinda za’ayi da kudin haka aka shigar damu wani palour me
kama da reception muka zauna muna rarraba Ido dan gaba dayan mu wasu qauyawa muka zama da
ganin Aljannar duniya.

Olivia kuwa da Patrick da muka tarar a can Selfie suka shiga dauka abinsu nida Yemi ne wai mukan dan
kame kan mu muna kallon gurin seda muka kwashe awa biyu cif muna jira kafin aka yi mana iso gurin
mutumin.

Wato wata hadaddiyar daula muka sake tararwa, palour ne qaton gaske na alfarma da fadarsa ma bata
bakine kaini fitulun da aka saka ma kadai sun ishe ni kallo wallahi haka muka nemi kujeru muka zazzauna
su kansu irin na yan gayun nan ne harda wani guri da ake dannan wa su koma gado ga abin tausa kai
masu kudi dai sunji dadi abinsu.
Anan ma seda muka sake jiran kusan minti Ashirin har seda muka fara qosawa sannan mamallakin gidan
ya fito, Farine sosai dan tsurut dashi dagani ya hada jini da fulani seka rantse dan aiki ne, badan hotonsa
da yake a palour ba da bazan yarda gurinsa muka zo ba.

Cikin girmamawa muka gaishe ni ina ta mamakin wai yanzu duk wannan uwar daular ta wannan dan firit
din mutumin ce, yana nan lange lange kamar baya cin abinci se kudi kamar zasu kashe ni.

Nice me bayani, haka na dage na ringa watsa masa bayanai akan muhimmancin saka hannun jarin da
zeyi da kuma ribar da ze samu akan hakan, na gama bayani na tsaf yana ji se gyada kai yake kamar
qadangare yana kallona, seda na qare tas na zauna Yemi ya dora da nasa se mutumin nan jin mu kawai
yakeyi bece komai ba.

Gaba daya se jikin mu yayi sanyi, sosai kamfani yake da buqatarsa mun kuma saka rai da samun nasa
amma da alama bayanan namu basu shige shi ba tunda gashi ya mana shiru, haka muka fara tattare
takaddun mu kowa fuskarsa ta chanza yanayi, wayarsa ya dauka yayi kira ko minti biyar ba’ayi ba sega
wnai mutum ya shigo daganinsa kaga Lawyer.

“Kuje dasu ayi ku kammala deal din a zuba ko nawa suka buqata babu matsala” mutumin ya fada har
sannan idonsa akaina, ai kamar zamu taka rawar murna haka muka shiga zuba masa godiya yanda kasan
wadanda yayiwa wata gagarumar kyauta ko da yake kyautar ya mana dan Allah kadai yasan kudin da
zamu zamu akan qulla yarjejeniyar nan.

Muna shirin tafiya ya tsayar damu, PA dinsa ya kira se gashi shima da jaka ya ajiye a gabansa, da ido ya
nunawa PA ya budeta se gani mukayi yana zaro rafofin daloli ya miqawa ko wannenmu daya sannan ya
sake dauko complement card aka bani se kawai na karba ina juyashi a hannuna dan basan me zanyi
dashi haka dai mukayi sallama muka tafi tareda Lawyer muka wuce kamfani.

Ranar cikin farin ciki na dawo gida jakata cike da daloli, a hanya na tsaya wani shopping mall na siyawa
yara kaya kowa set biyu designers masu kyau nima se gani ina lissafi da dollar irin na yan gayu, seda na
gama diban kayan idona ya sauka akan wasu singlet da boxers na maza, har na kai hannu na dakata
zuciyata na tambayata

“Wa zaki daukarwa?”


“Allah sarki Baban Ali, da yanzu harda kai za’aci kudin nan” na fada a fili ina wucewa bangaren turaruka
na dibi wanda nake amfani dasu sannan na quce gurin takalma na daukarwa Amnah wani me shegen
kyau da zata hada da gown din prom din su da za’ayi wannan Juma’ar me zuwa.

Sosai na kashe kudi, niqi niqi na wuce gida da kaya ina zuwa na tarar da yaran duka suna nan muka shiga
dasu ciki, plates din Abinci dana gani ya sakani cikin sigar wasa nace

“Wai ku baku iya zama a gidan mu sedai kuzo nan ku cinye mana abinci kullum toh gaskiya ya isheku
haka kun mayar da Yah Amnah kuku meye amfanin Antyn ku da bazata girka muku ba”.

“Tab ai wallahi Mami bata da amfani kuwa, ni tausayin Abbi ma nakeyi kar ulcer ta kamashi dan rabon
danaga yaci abinci a gidan nan tun kina nan fa” Jafar ya fada yana zaro kayan cikin ledar, ban tankashi
ba, na bisu da kallo yanda suka rude suna murna kowa yana daga kayan sa se kawai na shige dakina na
barsu.

A gefen gado na zauna ina tunanin meyasa Amirah bata girki? Su yara basu da matsala tunda gashi suna
ci a nan amma Bashir fa me yake ci shi da sam bashida jumurin yunwa

“Ina ruwanki idan ma ruwa yake sha” zuciyata ta rayamun, sena miqe ina qoqarin cire rigata wayata
dake cikin jaka ta hau qara.

Cirota nayi na duba, Number ce wata irin special Number kamar me ita ne ya zabi abarsa dakansa na
dubata dakyau batayi mun kama da wadda na sani ba dan haka na mayar da wayar na ajiye dan ban fita
daukar wayar da ban sani ba.

Message ne ya shigo bayan data katse an rubuta “ki daga wayar, wanda kukayi yarjejeniyar kasuwanci
ne” se nayi saurin nemo Number zan kira dan a zatona Barrister dazu ne a raina ina Allah yasa ba wata
matsala bace ta faru kuma dan har an karbi account Number mu a kamfani za’a saka mana kudin aikin
mu na kuma gama lissafin kudin sabuwar motata zan cika dasu yanzu idan aka fasa ai mun ga bonu.

Kiran daya sake shigowa ne yasa na dakata, na daga tareda yin sallama.

Seda akaja aji kafin wanda ya kira yayi magana cikin harshen hausa yace
“Meyasa baki kira ba tun bayan da muka baki kati dazu”.

Wayar na cire daga kunnena na sake dubawa, number ce idan kuma banyi qarya ba kamar wannan dan
tsamurmurin mutumin da mukaje gurinsa dazu sena mayar da wayar kunnena, cikin dari dari nace

“Bangane wa yake magana ba”.

“Oh babu laifi, sunana Ambassador Mutallab Ali” ya fada

Seda na zauna akan gadona na qara riqe wayar dakyau kafin nace

“Ranka ya dade barka da dare, ina fatan dai ba wata matsala aka samu da takaddun da muka bayar ba?”

“Aa, idan da harkar data shafi aikice ko kudi wasu ne daban suke gudanar mun da ita, wannan kuwa
abune daya shafe ni ya shafi rayuwata dan haka ni da kaina zanyi shi. Ba tareda bata lokaci ba tun zuwan
da kukayi dazu na ganki kuma kinyi mun a matsayin matar aure, idan kin aminci ina so na cike mata ta
hudu dake amma dukka matana ba tare suke ba, kowaccen su qasar da take zama ta banbanta data yar
uwarta dan haka kema zaki zbai inda kike so ki zauna ne ni bani da damuwa da hakan”.

“Ikon Allah se kallo” na fada a zuciyata, a fili kuma sena samu kaina da cewa

“Ranka ya dade kayi haquri amma ni matar aurece”.

“Asma’u kenan, baki da aure domin suffarki ta nuna kamala. Babu yanda za’ayi ki fito da irin shigarki ta
yau alhalin kina da aure dukda hakan ba wani abu bane ga amma na tabbatar da ko shi mijinki baze taba
bari ki saka kayan da zasu bayyanar da kyanki haka ki tafi qulla alaqar kasuwanci da wasu maza ba ko da
yake bansan irin mijin da kike aure ba”.

Mamaki ne ya kamani kwarai, ya akayi ya san sunana sannan har ana iya gane macen da bata da aure
daman tunda dai ni banyi kala da budurwa ba bare yace sannan daga kira ka fara zayyana mun wani
zancen aure harda wasu matansa uku ni Asma’u ce zan fita daga gidan me daya na fada wa uku Allah ya
mun tsari.

Kai duk ba wannan ba Allah na tuba ina ni ina wannan mutum haka firit kamar ruwan aski? Ai wallahi ko
qaruna ne shi qarewar kudi yanzu dai in rabu da Namiji Kamar Bashir naje na auri wannan busashshen
da na kasa tantance tsufane ya figeshi haka ko kuwa abinci ne baya ci kai qilama sickler ne kaga kuwa
Bashir se yayi mun dariya dakyau.

“Kinyi shiru Asma’u baki ce komai ba” ya katse mun shirun. Dabara ce ta fado mun ta yanda zamu rabu
lafiya tunda dai shi wannan ya wuce mutumin da zance zan wulaqanta ko na kora dan haka nace masa

“Tabbas ranka ya dade mun rabu da mijina amma gaba daya be wuce sati biyu da faruwar hakan bama
kaga ban gama iddah ba yanzu baze yuwu na saurari wani namiji ba”.

“Hakane, toh babu damuwa zan jira dan na yaba kuma rabona ce ke, ki turamun da account Number
dinki yanzu za’a saka miki saqo”

“Babu komai na gode Rabka ya dade na dazu daka bamu ma ya isa”

“Ni nayi niyya idan kuma baki turo ba zanyi waya har kamfanin naku yanzu su turamun daga can” ya
sake fada, gaba daya maganar tasa ta gundureni, dan haka da sauri nace

“Toh shikenan zan tura maka yanzu, Nagode Allah ya qara arziqi” qit na kashe wayar ban ajiyeta ba seda
na dannan masa block, na dakko katin daya bani nabi duk numbobin jiki nayi saving dan karma ya kira da
wata Number na daga ban san shi bane.

“Haka kawai toni ko auran zanyi ai ba irin ka zan aura ba” na ringa mita ni kadai na shige bayi.

Ina sallar Isha su Abdallah m shigo da gudu yacemun wai nayi baquwa, seda na sallame kafin na fita
wajen da hijabin jikina ina mamakin wacece wannan zata zo mana da dare haka.
Turus nayi ganin Amirah dake tsaye farar fuskar nan tayi jajir kamar ma mari tasha. Cikeda fitsara ta
waiwayo tana cewa

“Wallahi kijawa Yaranki kunne dan ni ba jakar su bace da zan ringa dafa abinci su tsallake au qi ci kuka
ubansu yazo yana mun fada kuma wallahi duk abinda aka mun akan su zan rama ehe”.

“Yanzu qara kika kawo ko jan kunne kika zo kiyi mun? Wai ma bana gaya miki karki sake shigowa gidan
nan ba? Ina ruwana da shirgin ku mena hada dake da zaki shigomun gida kina fadamun magana.

Naga alama kin kwana biyu jikin ki be fada miki ba toh kiyi a hankali idan ba haka ba kuwa sena ladabtar
dake tunda naga ke baki da hankali ba kuma ki da tunani, abinci kuwa a gidan ubansu suke ko suci ko kar
suci dole ki dafa ki ajeye musu idan kuma kinqi kinsan sauran base na gaya miki ba, wuce ki fita tun ban
lakada miki na jaki ba anan” na qarasa ina nuna mata qofa, nazata zata sake magana se naga ta juya tana
qunquni ta fita a fili na fuskar ta

“Mara kunyar banza, ai da kin tsaya na koya miki hankali. Ku kuka (na juya kan yaran) daga yau ku ringa
tsayawa a gidan ku kuna cin abinci idan baqu qoshi ba se kuzo nan ku qara kunji ko”.

“Wallahi Mami bata iya abinci ba, jiya fa data saka wani kifi a spaghetti har yanzu ina jin qayarsa a
wuyana qarshe fa a bola ta juye abincin kowa yaqi ci” Jafar ya fada kafin nayi magana Faridah tayi caraf
tace

“Waifa doyar da bamu ci da safe ba ta dumamawa Abbi shine ya ringa mata masifa, yanzu ma yana daki
a kwance Kamar Bashida lafiya ina ga kuma yunwa yake ji, Mami ki bamu abinci mu kai masa dan Allah”.

Tsayawa nayi ina kallonta, dagaske Bashir bashida lafiya to me ya same shi? Na san dai yunwa tana iya
kwantar dashi dan sam bashida jimirinta toh amma ni ina ruwana meye nawa a ciki shida ya dakko yar
gwal ai seta dafa ta bashi.

Da zasu tafi Faridah da shegen naci seda ta dibar wa Bashir Friedrice da pepper chicken din da Amna tayi
ga hadin kosulo abin dai ba’a magana na qara musu da zobo roba biyu sadaka nace ta kai masa.
BASHIR

Gaba daya haka ya wuni a office ya rasa me yaje masa dadi, ga damuwar rabuwarsa da Ma’u da se yanzu
abin ya fara dukansa daya tabbatar da ta kufce masa se yayi da mugun gaske kafin ta sake dawowa
hannunsa.

Ya rasa wa ze gayawa damuwarsa, a wannan karon be karbi shawar Bala ba gani yake kamar bazata
fiddashi ba, amma wani lokacin idan ya tuna irin son da Ma’u takeyi masa se yaga kamar duk buyagin
iska kawai takeyi na dan lokaci zata sakko su koma zaman su.

Wai ma shi me yayi mata ne? A iya saninsa laifi ta masa ta qi bin unarninsa kuskure daya da yayi shine
daukar matakin saki a cikin fushi kuma har biyu, daya sani hutu ya bata na lokaci ya fita sabgrta har se ita
da kanta ta dawo ta nemi shiri ta kuma yarda da sharadin daya bata kafin su daidaita amma yanzu ya
lalata komai, ya bi rudin shedan ya rabu da Ma’unsa.

Ita wadda Shedab din yayi masa kururuwa akanta gashi nan ya dakko ta idan bada gasha shi babu abinda
take yi ko iya horon yunwar da take masa aka barsu na shekara daya yasan dakyar idan bazatayi ajalinsa
ba wai shi wannan wane irin bala’ine yake tun karar rayuwarsa.

Wayarsa ya dauka ya shiga neman Number Amiru qaninsa da tun ranar da zancen sakin Ma’u yaje
Gombe ya kirashi dan yaji menene gaskiyar zancen ya kuma tabbatar masa da anyi daga ranar basu sake
magana ba.

Ya kirashi sau ba Adadi amma Amirun baya dagawa daga baya ma blocking dinsa yayi, haka Naziru ma
baya amsa wayarsa to yan uwansa ma kenan kuma shi bashi da sauran wani shaqiqij Abokin da ze
tattauna wannan matsalar in banda Balan se Abubakar da ko giyar wake yasha be isa ya tun kare shi a
yanzu ba.

Abdulkarimu ne ya fado masa a rai, ba bata lokaci ya danna masa kira kuwa akayi sa’a ta shiga seda ta
kusan tsinkewa kafin ya daga wayar
“Alhaji Bashir yaushe rabon da ka nemeni tunda giwa tayi lafiya ka samu kan Madam shikenan ka watsar
dani” Abdulkarim ya fada bayan da suka gaisa. Seda Bashir yaja numfashi kafin yace

“Abdulkarim ina cikin Bala’i na rasa yanda zanyi wallahi ka taimaka mun”

“Allah yayi mana maganin abinda ya damemu, lafiya dai Bashir meya sameka haka kake dangana kanka
da Bala’i?”

“Abdulkarim hau ce ta hauni, nabi dokin zuciya na saki Ma’u gashi yanzu harta gama iddah ban mayar da
ita ba na rasa inda zan kama ji nakeyi kamar zan haukace, yanzu har ta fara kula wasu Mazan sau biyu
ina ganin ta a motar Maza Abdul” ya qarasa maganar kamar ze fashe da kuka saboda yanda yakejin zafi a
duk sanda ya tuna ganin da yayiwa Ma’u na jiya dana yau din.

Salallami Abdulkarim ya ringayi yana cewa

“Ka saki Ma’u Bashir wace irin hau ce kai kuwa take binka haka ka rasa matar da zaka saka a rayuwa se
Asma’u, Asma’u fa Bashir toh wallahi babu ruwana, abu daya zan iya maka inyi maka Addu’ar Allah ya
taqaita maka wahala na kuam roqeshi karya maido maka da Asma’u rayuwarka dan baka san darajarta
ba”

“Idan Allahn naka ne seka roqeshi karya dawo mun da ita din, na kiraka ka bani mafita shine zaka zageni
kayi mun fatan tsiya ko? Daman nasan ba qaunar zama na da ita kake yiba, to dakai da duk sauran masu
jin dadin abinda ya faru kuna kallo Ma’u zata dawo mun sedai baqij ciki ya kashe ku ku mutu”.

“Allah ya yafe maka Bashir” Abdulkarim ya fada kafin ya kashe wayarsa.

Bashir kuwa hada kansa yayi da teburin gabansa yana sauke numfashi, babu abinda yake cizon zuciyarsa
irin idan ya tuna ganin da yayiwa Ma’u da wasu, Matarsa Ma’u da wasu qartin maza da sunan zawarci.
“Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un, Allah ka kawo mun dauki, Allah karka barni da iyawata” ya fada a fili
yana sake wawurar wayarsa, dole ya ajiye duk wani abu a gefe ya kira Baba, ko ze zageshi kai idan ma ta
kama yaje ya tsugunna a samowa Baban bulala ya zane shi duk ya yarda indai ze saka baki Asma’u ta
haqura ta dawo masa dan yasan a yanzu dai su biyu ne zasu iya shawo masa kanta babu musu ta yarda
daga Baban se Goggonta, shi kuwa dai rashin kunyar tasa bata kai ya tunkari Goggo a yanzu ba dan yaci
ace kafin ya saki Ma’u ya tuno da karamcin matar amma duk ya hada ya take to wai shi me tayi masa ne
ma??

Sallamar da Baba yake ta faman kodawa ce ta dawo dashi hankalin sa ashe wayar ta shiga tuntuni yana
can zurfin tunani be sani ba.

“Barka da rana Baba, ya qarfin jikin?”

“Barka dai Bashari, jiki Ahamdulillah idon ka kenan se yau zaka kirani ko da yake kaida kake da Amarya ai
dole ayi maka uzuri” Baban ya fada babu wata damuwa a muryar sa.

“Ayi haquri Baba” Bashir ya fada yana gyara zama, yanda yaji Baban a sake ya qara masa kwarij guiwar
fadar abinda yake ransa.

“Ba komai ai nima ban ce kayi laifi ba, ya iyalan naka gaba daya da yaran kuna lafiya dai ko?”

“Lafiya lau Baba sedai Ma’u ce dai..” se kuma yayi shiru ya kasa ci gaba da magana, Alhajin da yaji yayi
shiru yace

“Me Ma’un tayi kuma? Lafiya dai ko wata matsalar ce ta sake tashi?”

“Daman Baba naje ne jiya da niyyar mu sasanta na mayar da ita dakibta, shine take gaya mun wai tayi
bari bayan mun rabu dan haka iddarta ta cika tuntuni babu kome tsakanin mu”

“Kai masha Allah barka barka abu yayi dadi gaskiya, ai kuwa na kirata da mun gama wayar nan tunda
nima laifinka ya shafe ni kwana biyu ta dena kirana” Baba ya fada cikin murna kamar be ji abinda Bashir
din ya fada ba.
“Baba kamar baka gane me nake cewa ba” Bashir ya fada a rarrabe, se baban yayi murmushi yace

“Nagane Bashir, kace Ma’u tayi bari ko iddarta ta cika. Murna nake tayata da Allah ya dubi kyakykyawar
zuciyarta ya rabata Mijin da besan darajarta ba butulu irinka, wannan kadai ya isheka ishara ka gane
cewa Allah yana arawa mutum dama ne a rayuwa idan yayi wasa ta subuce masa shikenan sedai ya
mutu yana nadama da dana sani, yanzu daka kirani me kame so nayi maka?”

Kwata kwata kalaman Baba basu dami Bashir ba dan ya tsammaci fiye da haka ma, shidai fatansa Baban
yayi iya fadan da zeyi ya haqura tunda dai ai bazece yafi son farin cikin Ma’u akan nasa ba.

Seda ya sake marairaicewa sosai kafin yace

“Na karbi kuskurena Baba duk abinda ka fada gaskiya ne kuma na yarda, zan chanza hali wallahi zan
dena duk abinda kasan inayi na rashin kyautawa kasa baki Ma’u tayi haquri ta koma dakin ta”.

“Toh fa da wuri haka Malam Bashir kuma ni wannan lissafin ai bani zaka yiwa ba ita wacce kayiwa laifi
can zaka samu ka bawa haquri ka gaya mata ka chanza ko kuwa kayi shawara dani sanda kayi sakin”

“Ko naje Baba bazata saurareni ba tace ta gama aurena dan girman Allah Baba kaji tausayina ka saka
baki nasan kai kadai ne zaka saka baki ta haqura ” Bashir ya fada kamar ze fashe da kuka

“Amma Allah yayiwa Asma’u Albarka, in gaya maka gaskiya Bashir indai da shawara ta ne bazan taba
barin Asma’u ta koma gidanka ba zan kuma ci gaba dayi mata Addu’ar Allah saka mata ladan haqurin da
tayi dakai ya bata mijin da ze yasan mutunchinta, Idan Wannan ya sa ka kirani to se anjima kar kuma ka
sake kiran wayata indai akan wannan shirmen ne” kafin Bashir ya sake cewa wani abu Baba ya kashe
wayarsa.

Ji yayi zazzabi na neman rufeshi, ya hade kansa da guiwa yana jan Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un a
zuciyarsa abinda yake dauka ze zo masa da sauqi gashi se komai yana sake rincabewa, ya zeyi? Waze
kama? Ta ina ze fara? Duk be sani ba.
Haka ya qarasa wunin ba tareda ya saka ko ruwa a cikinsa ba ya kamo hanyar gida dan bashida wata
nutsuwa, se a sannan ma ya ji daya sani Azumi yayi da wannan wunin yunwar yana shiga ya tarar da
Amirah tana masifa Ahmad ya zubar da Lemo akan carpet tanayi masa magana ya gudu waje,

Tun kafin tayi masa magana ya tareta da cewa

“Bana jij dadi, ki barni dan Allah karki qara mun damuwa akan wacce nake ciki, ki hada abinci na ki kawo
mun daki” ya shige ciki ya barta.

Yana wanka ta shiga da Try ta zubo doyar dazu da safe a plate se Sauce din Hanta da Albasa da ta dan
qarayi saboda doyar tayi Armashi ga Lemo me sanyi na Exotic da ruwa duk ta ajiye masa.

Yana fitowa ana kiran sallah dan haka ya zura jallabiyya ya tafi masallaci seda ya dawo ya tsaya a Kitchen
ya fara hada shayi kafin ya wuce dakin dan gaba daya hanjinsa sun qulle, yana bude farantin ya fara
kwala mata kira, Amirah na can ta sake wanka tana kwalliya ta jiyo kiran nasa, seta zura hijab ta fito tana
mitar

“Haka kawai daga dawowarka shikenan kuma mutum baze huta ba zaka fara kiransa kamar wani saboj
makaho” da wannan mitar ta tura qofar ta shiga babu ko sallama.

“Meye wannan kika kawo mun” ya fada yana nuna doyar, seda ta harare shi ta qasan ido kafin tace

“Doya ce, naga da safe baku ci ba kuma kar ayi almubazzarancinta shiyasa na ajiye na dumamata yanzu,
gashinan har sauce fa nayi maka dan kaji dadin ci”.

“Tunda kike kin taba ganin an maimaita mun abinci a gidan nan, bama wannan ba ke kike siyan abincin
da bazaki dafamun abinda nake so ba ko kuwa” ya fada a nutse dan bama shi da qarfin yin masifar a
sannan.

“Ni fa na gaji da wannan abun, duk abinda nayi ban iya ba a gidan nan, ance bana girki idan kuma nayi a
qi ci akan me wallahi daga yau idan na dafa in za’a kwana goma ba’a cinye ba shi zanyita maimaita wa ba
ruwana ai ni ba yar aiki aka dakko ba balle ace...” bata san tasowarsa ba se saukar tagwayen mari dataji
akan fuskarta, kafin ya angizata waje, ya sake komawa ya kwashi try din abincin ya watsa mata sannan
ya kullo qofarsa.

Dafe qirjinsa da yayi masa nauyi yayi ya fada kan gado da baya, beyi aune ba sejin wasu hawaye masu
dumi yayi suna gangarawa zuwa cikin kennensa a maimakon ya hana kansa se kawai ya bude baki kamar
qaramin yaro ya shiga rera kuka irin na wanda duniya tayiwa daurin Goro.

Ayi haquri dab Allah

WATA KISHIYAR

(ALKAHIRI CE KO SHARRI)

Na Maryamah Farouk

(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)

Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 47

Kuka me sunan kuka Bashir yayi tamkar wanda aka cewa Dada ta mutu, seda yaji wani kaso na
damuwarsa ya kafin ya shiga bandaki ya wanko fuskarsa ya dawo ya zauna tareda rafka uban tagumi ga
Yunwa se sakadar ciki aa takeyi dan takaici shayin da ya hado ma be sha ba harya huce.
Yana zaune a gurin seda yaji hajijiya na neman kadashi kafin ya miqe da kyar dan dole ya gita ya nemi
abinda zeci kafin yunwa ta kashe shi, yana bude qofar ya ga Faridah a tsaye, da Alama kwankwasawa
zatayi.

"Abbi kaga Anty Amirah ko, dan kawai na tambayeta kai shine ta zage ni" Faridah ta fada tana hararar
Amirah dake zaune can kan kujera tana kada qafa. Komawa ciki yayi Faridah ta bishi ta kwandon Abinci
ta ajiye tana cewa

"Abbi ga Abinci, a gurin Mami na karbo maka kaga harda zobo ta ce a kawo maka sadaka".

"Sadaka, Almajiri na zama kenan lallai Ma'u" ya raya a ransa kafin ya hadiye wani tsinkakken yawu sanda
qamshin shinkafar ya dake shi, ga Kaza mutuniyarsa.

Faridah na shirin Zuba masa a plate ya karbe kular gaba daya ya saka cokali ya shiga cin abincin kamar
wanda ya shekara yana Azumi seta miqe ta koma kan kujerar dake dakin ta zauna tana kallonsa.

Cikin dan lokaci Bashir ya tashi abincin nan tas Ya shanye Zobo Faridah dai se kallonsa takeyi, seda yayi
gyatsa tareda hamdala kafin ya kalli Faridan ya miqa mata hannu alamar taje. A jikinsa ya dorata ya
sumbaci goshinta kafin yace

"Nagode Faridah ta kamar kin san Abbinki Yana kewar Abincin Mami".

"Abbi yah Amna ce tayi ai, kuma Abbi tunda Anty Amirah bata girki kaima ka ringa zuwa gidan Mami
kana ci mana kaga mu a can muke cin abincin mu me dadi" Faridah ta fada tana marairaice masa,
murmushi yayi yace

"Ai ba laifina bane Mami ce bazata bari ba, amma ki gaya mata da kanki ki roqeta ta dawo nan gidan ko
ni na ringa zuwa can se mu ringa cin abinci tare duka yanda muka saba ko?"
"Toh Abbi amma bakaine ka koreta daga nan gidan ba ai nasan bazata sake dawowa ba sedai kai ka ringa
zuwa can, gobe da safe zan gaya mata tunda yanzu dare yayi"

"Shikenan, dauke kwanukan kije ki kwanta Allah ya yi miki Albarka"

"Amin Abbi" ta fada tana hada kayan a kwando ta fice taja masa qofar.

Wani irin sanyi da nutsuwa Bashir yaji a zuciyarsa, to kodai maganar Bala gaskiya ce da yace ya bata guri
idan aka kwana biyu zata huce su daidaita tunda gashi kuwa yaga alama.

Idan har Asma'u zata aiko masa da abinci to kuwa in yayi haquri yana zaune zata neme shi su shirya,
daman ya sani duk abinda zata fada iya fatar baki ne be kai zuciyarta ba. Ya sani Ma'u tana sonsa kowa
kuma ya shaida hakan shima yana sonta amma ya rasa me yasa mutane suke da tantama akan son da
yakeyiwa Ma'unsa.

Tashi yayi yaje yayi brush ya dawo kan gadon ya kwanta gaba daya jikinsa ya mutu tunda ciki ya dauka
bacci kawai yake da buqata, wayarsa ya jawo ya rubutawa Ma'u text

"Nagode Ma'una, uwargida na har a Aljanna" yana turawa ya saka wayar a silent ya ajiye zuciyarsa qal ya
kwanta tareda jan bargo dan gani yake kamar ma har sun shirya da Ma'u ai, hannunsa ya miqa ze kashe
makunnin filtila ya jiyo kamar Muryar Faridah tana kuka, se ya miqe ya fita palour yana zuwa kuwa ya
tarar da Amirah ta cukumeta kamar me danbe da sa'arta tana cewa

"Ni za'a nunawa Bariki, a zubo abinci daga wani guri a baki ki kawowa mijina ko to wallahi duk abinda
aka zuba bazeyi tasiri ba, zama na daram a gidan nan babu yanda aka iya dani ke kuma sena miki dukan
tsiya ta yanda gobe bazaki sake karbo abu ki kawo masa ba" Ta kaiwa Faridan Mari ya tareta a fusace ya
tunkudeta gefe yana cewa

"Wai ke wace irin shedaniya ce da baki taba so a zauna lafiya, saboda dazu na barki shine yanzu zaki
kama mun yarinya kina duka akan me?"
"Akan me ma kake tambayata? Da kasan kana son abincin uwar tata me yasa ka koreta daga gidan ai da
seka barta ta zauna tayi ta girka maka kana ci dan haka yanzu wallahi baka isa a ringa shigo maka da
abinci daga wani guri kaci ba, kodai kaci wanda na dafa ko kuma ka zauna da yunwa idan ka fita can waje
ka siya kaci ehe" Amirah ta fada tana girgiza jiki a gabansa,

Tsabar mamaki Bashir ya gagagara cewa komai, yanzu shi take tsayawa a gabansa tana gaya masa be isa
yayi abu ba a cikin gidansa ba bata jin tsoron bare shakkar gaya masa duk abinda taga dama lallai
Amirah.

Jan hannun Faridah yayi zuwa dakinsa kafin su qarasa kuwa Amirah ta tare qofa tana cewa "Ai wallahi
bazata sake kwana a dakin nan ba idan banda rainin hankali ni ina matar gida ka koreni daga dakinka
sannan ka bar yarka ta kwana a ciki baze yuwu ba".

"Amirah ki matsa mun daga hanya bana cikin yanayin da zan biye miki yanzu" ya fada yana kokawa da
bacin ransa, Amirah kuwa ko a jikinta sema qara babbake hanya da tayi tana murguda baki tasan dai
qarqari yace ze mareta ko to kuwa ta dena tsayawa ya daketa kamar wata jakarsa.

Ganin da yayi ta kafe a qofar bata da alamar matsawa ga shi sauran yaran duk sun fito suna kallo yasa ya
sassauta murya yace da Faridah

"Wuce dakin Antyn ku ki kwanta, ke kuma shiga ciki muyi magana"

"Nifa na gaji tun wuri ka nemar mata Gurin ka nemar mata gurin kwana, haka kawai banida sirri nida
dakina" Amirah ta fada cikin qunquni tana hararar Farida data tafi dakinta, wucewa Bashir yayi ciki tabi
bayansa tun kafin ta zauna ya juyo a mugun fusace yana cewa

"Wannan ya zama karo na qarshe da zaki sake gaya mun magana a gaban yayana, sannan ke kike
zamana ko ni nake zamanki dan Saboda baki da tarbiyya zaki kalleni kice ban isa nayi abu ba, so kike ki
qure ni ko Amirah? Bazaki ji dadin abinda zan miki ba wallahi ki bar ganin ina daga miki qafa, ranar dana
waiwayo kanki bazaki ji da dadi ba"

"To nima a dena yimun abinda bana so indai ana son zaman lafiya" ta fada ba tareda ta kalle shi ba, da
mamaki ya ke kallonta, kallon wai daman haka take ko kuwa yanzu ne tazama hakan.
A da dai duk rashin kunyarta bata tsayawa a gabansa ymta gaya masa magana sedai taqi bin umarninsa
amma yanzu a gabansa qiri qiri yana fada tana fada bata ko shakkarsa yaushe suka fara haka.

Gani yayi idan ya biye mata qarshe ze iya lakada mata dukan da zata kasa tashi se kawai ya haye gado ya
barta a tsaye tana ci gaba da qananun mita, har kansa yaja bargo, yana jinta ta kashe fitilar ta hau kan
gadon tana matsawa jikinsa ya tureta yana cewa

"Kika sake tabani sena kwada miki mari wallahi, saboda bakida kunya ki gama zagina sannan kizo
kusadani dallah matsa can kafin na make ki"

"Allah dai yana kallo idan kuma aka take mun haqqina ba yafewa zanyi ba ehe" ta fada tana murguda
baki kafin ta sauka daga gadon ta koma kan kujera.

Zaune Bashir ya tashi shima ya zuba mata ido kawai yana kallonta amma taqi bari su hada ido, shi tayi
wa Allah ya isa? Shi Amirah ta ke zagi harda Allah ya isa

Wani irin tuquqi zuciyarsa ta shiga yi masa idonsa ya kada yayi jajir kamar wuta, cikin kakkausar muryar
da seda ta bata tsoro yace mata

"Fita daga dakinan, idan kika bari nazo inda kike sena illataki Amirah, kuma wallahi ko tashin Faridah
kikaje kikayi daga bacci yanzu se nayi miki dukan da na lahira seya fiki jin dadi wawuya mara hankali
kawai".

Da sauri ta fice, a palour tayi kwanciyarta ko banza dukkan su zasuyi kwanan baqin ciki, yanda ya bata
mata itama tayi masa fiye da haka ai su zuba su gani ita da shi za'a ga wanda ze gaji tunda tagane duk
abin nasa ma hargagin qarya ne.

Bashir kuwa kasa kwanciya yayi sya shiga safa da marwa a dakin, Allah sarki Ma'u a zaman sa da ita baze
taba cewa ga ranar data zageshi ko ta gaya masa maganar da zata sosa masa rai haka kawai ba.
Iya qarshen ladabi da biyayya tayi masa amma ya raina abinda takeyi yake ganin kamar bata girmana shi
irin yanda ya kamata qarsheya saketa a dalilin wata, watan da gata nan tun ba'aje ko ina ba ta fara
tsayawa a gabansa taba qare masa tanadi tabbas kuwa dole ya dauki mataki akan hakan, ya hukunta
wadda batayi masa laifin komai ba balle ita data siya da kudinta dan haka ta shirya karbar sakamako
daidai da abinda ta aikata masa.

Washe gari ta kama Juma'a tun asuba ya gayawa Amirah ta hada musu abin karyawa, yanayin yanda yayi
magana ya saka bata musa masa ba ta dai bishi da harara daya fita tana idar da sallah ta hau firar
dankalin kafin bakwai ta soya tas harda qwai ta dafa ruwan shayi.

Yana zaune a palour dan da wuri ya shirya ya fito tagama jera komai, yaga alamar saken daya bata ya
saka raini shiga tsakaninsu a yanzu ne ze tabbatar mata da be chanza ba yana nan a Bashir dinsa data
sani.

A daure yace mata taje ta kirawo yaran suzo su karya, suma kuma basu musa ba harda Aliyu duk suka
zauna a Dining din kowa ya hada shayi, Aliyu ya turawa yan biyu farantin daya zuba musu dankali Ahmad
na taunawa ya watsoshi waje yana cewa

"Kai kai muba haka Mami take yi mana ba".

Ahmad ya fada yana bata fuska, ai kuwa Amirah ta zaburo masa tana cewa

"Aa ba Mami ba uwar Mami ce ba haka takeyi muku ba shege me qaton kai"

"Se dai taki uwar Addah, kuma wallahi kika sake zagar mana uwa se mun hadu mun miki duka a gidan
nan" Aliyu yayi wo kan ta kamar ze daketa a lokacin, seda ta ja baya gurin kujerar Bashir daya hada
hannu biyu yana kallonsu kafin tace

"Ni zaka daka ashe zaka iya dukan uwarka Asma'u kuwa in dai zaka dake ni"
A mugun zuciye Aliyu yayi kanta kafin Bashir ya miqe har ya kai mata gula da qafa ta sunkuya ya sauke
mata qafar a daidai kunne ai kuwa ta fasa qara ta zube a gurin be tsaya ba ya sake yin kanta amma kafin
ya kai mata wani dukan Bashir ya tareshi tareda zabga masa mari.

"A gabana Aliyu zaka daki matata?"

"Ai a gaban naka ta zagi uwata kuma baka hanata, wallahi tunda ka saki uwarmu akanta itama bazata
taba zama lafiya a gidan nan ba, ku tashi mu tafi" Aliyu ya fada babu ko dar a fuskar sa, ya kada
qannensa waje suka fice suka bar Bashir da Amirah a gurin.

Amirah dake durqushe a qasa ta riqe gefen fuska tana kuka ta kalli Bashir tace

"Kana kallo sun tafi bayan ya kurmantar dani, wallahi bazan yarda ba se an bi mun haqqina"

"Dallah ki rufewa mutane baki, duk ba ke kika jawa kanki ba? Sau nawa zan gaya miki ki dena shiga
sabgar sa a kan me zaki zagi uwarsu sa'arki ce? Sannan ai ba qarya Ahmad din yayi ba kin soyawa
mutane abu salam babu ko digon gishiri tayaya ze cuwu, se ki tashi kije ki samu ruwan dumi ki gasa gurin
idan da man zaitun ki tsiyayaqa kunnen gobe ma ki sake zagin musu uwa su sun san darajar ta" yana
gama fada shima ya dauki jakarsa ya fice.

Yauma dai haka ya fita beci abinci ba shidai bashi da maraba da gauro yanzu gauron ma mara galihu.

A bakin motar ya hango su Asma'u tayi parking daidai gurin suna magana kafin ya qarasa taja motar ta ta
wuce dan haka ya bude musu motar suka shiga, haka ya kaisu makaranta ya ajiye su sannan ya tafi ya
siyo musu breakfast a wani gidan abinci kusa da gurin ya sake kai musu kafin ya wuce office dinsu
zuciyarsa kamar zatayi bindiga saboda takaici.

AMIRAH

Suna fita ta tashi dakyar ta dakko wayar ta ta dannawa Addah kira, a speaker ta saka dan da gaske fa
kunnenta yaji duka tana dagawa ta saka mata kuka tana cewa

"Wallahi Addah na gaji bazan iya ba, haka kawai na zama kamar jaka shi ya dakeni sannan yanzu takai
yayansa su dake ni nidai na gaji tahowa kawai zanyi"
"Ki taho ina? Ni Fattu kashe ni kuke so kuyi ne ko me, nan ga wannan shegiyar ta dibgo mun abun kunya
ke kuma kina shirin kaso auranki ki dawo to bazaku kasheni ba koma menene yanzu ki dakata mun na
kashe wanann wutar kafin ta fasu idan yaso se na dawo kanki" Addah ta fad cikin tashin hankalin da
muryarta ta kasa boyewa.

Cikin rashin fahimtar maganar Addahn Amirah tace

"Addah meya faru? Wane irin abun kunya kuma aka dakko miki badai bashi kika sake ciwo aka zo ana
miki cin mutunchi ba?"

"Yo ba gara in ci bashi ba ko birsin ne a kaini da abinda wannan yar iskar yarinyar tajawo mun, ciki fa
cikina haihuwa Ummi tayo har wata uku yanzu ina zaune ban sani ba.

To wallahi na gaya mata zubar dashi zamu tafi yanzu ayi dan bazata ja mun abinda za'a ringa zundena a
garin Idan na wuce ba shi kuma shegen matsiyacin da yayi mata daga baya inyi qararaa tunda ai na raba
shi da yata yaqi barinta seda ya dibga mata ciki tukunna" Addah ta fada cikin masifa se haki takeyi,

Amirah na jiyo kukan Ummi daga gefe tana cewa "ni wallahi baza'a cire ba, haka kawai ance mutuwa
akeyi. Ki kyaleni ai Jawad din ya yarda idan na haihu zamuyi aure"

"Sedai ki auri ubanki, na gaya miki indai ina raye bazaki auri wannan matsiyacin ba wallahi" Addah ta
zabura tayi kanta, can ta wullar da wayar ma da alama ta manta da cewa waya takeyi.

Zugudi Amirah tayi da waya a hannu cikin tashin hankali, ciki dai cikin shege Ummi ta yi to yaushe hakan
ta faru? Zama tayi akan gado ta rafka tagumi radadin da takeji a kunnen ma ya tafi saboda jin sabon
tashin hankali yanzu me Alhajin su zece idan yaji wannan maganar ta tabbatar da sedai Allah ya tsare
amma da wuya auran Addah be mutu ba a dalilin wannan abun amma.

Ummi ta cuce su koda yake ba Ummi ba Addah zatace ta cuci Ummi tunda babu yanda batayi akan ta
barta ta auri wanda take so ba amma ta kafe cewar bazata aureshi ba saboda bashida komai, shegun da
take yawan ambatarsu dashi gashi yanzu ya tabbata ai seta shirya goya shegen jika.
Wanann maganar ce ta kashe wutar abinda ya faru da safe, haka ta wuni jiki a sabule batayi musu girki
ba daman yaran suna dawowa gidan Ma'u suka wuce shima Bashir daya dawo yaganta a yanda ya fita ya
barta kwafa kawai yayi ya sake wanka ya fice be kuma dawo gidan ba se bayan data kwanta.

ASMA'U

Da safe ganin harna shirya yara basu shigo yasa nayi tunanin sun koma cin abinci a gidan su kenan, toh
itama Amna ta huta, a tsatstsaye na karya dan ina sauri mukayi sallama da Amnah ina fitowa na gansu
cirko cirko a qofar gidansu fuskar Aliyu dana kalla ta tabbatar mun wani abu ya faru.

A gabansu na tsaya da mota na sauke glass, dukkan su suka gaishe ni na tambaye su lafiya Jafar na shirin
magana Aliyu ya galla masa harara yace mun babu komai. Sena tabe baki nace "toh yayi, ina Abbin naku
kuke tsaye anan kun kusa makara fa" ina rufe baki na hango an bude qofar, nasan Bashir ne dan haka
nayi musu sallama kawai na wuce haka nan bana son haduwa dashi kuma.

Gurin qarfe goma ina zaune a office wayata tayi qara, ta true caller naga sunan me kiran YUSUF IBRAHIM
WUNTI ina gani na gane Yusuf ne dan haka na daga wayar na kara a kunnena tareda yin sallama.

"Barka da rana Hajia" Yusuf ya fada daga daya bangaren sena amsa da cewa

"Barka dai Excellency"

"Ashe baki manta sunan ba" ya fada yana dariya sena mayar masa da amsa da cewa

"Haba dai ya za'ayi na manta, waya sani ma ko sunan ya tabbata yanzu dan Majalissar Jaha ne kai ko na
taraiyya?"

"Haba Hajjaju ai tuni muka tsallake nan, sanata nake meci a yanzu kuma Gomna me jiran gado in Allah
ya yarda" Yusuf ya fada, sena bude ido da mamaki kamar yana kallona nace

"Dagaske amma babu labari ko a gurin Alaqiyya ban taba jiba ita da take yar garinku, toh Allah ya
tabbatar da Alkahiri kace na kusa zama qanwar Gomna".
"Toh ai baki taba neman koda labari na kinga bazaki sani ba, duk kuma sanda zanje gida se muyi sabani
ace kinso kin tafi shiyasa amma yanzu da Allah yayi zamu sake haduwa kinga a arha na ganki a hanya, ya
gida ya yarana na shigo Lagos ya kamata nazo na gansu ki sanarwa da Oga kar nazo yayi mun rotse"

Yanda ya fadi rotsen seda nayi dariya nace "ba abinda zeyi maka ai yasan kai Yayana ne ko, ba damuwa
toh yaushe zaka shigo?"

"Injiwa ta ya za'ayi ya yarda da wannan nima bazan fara shigar masa gida ba a waje zan tsaya ki turo
mun yarana na gansu kar naje mun sha haduwa ma ban san su bane ko da yake bayanda za'ayi naga
jininki na kasa ganewa, ina jin ko a taron Arfa naga wanda ya shafeki sena gane shi wallahi

Zan zo gobe da yamma, idan babu damuwa zan sa a kawo takwarar ki anjima kafin nazo kin san an
kawota gurin Hajia to ban samu na shiga Bauchi ba ita kuma ta saka rigima se an kawota gurina, inaga na
saka a kawota nan din dan idan aka kaita Abuja ma bani da lokaci acan saboda aiki"

"Ok ba damuwa a kawota, ba tare zasu zo da mamanta ba?" Na tambayeshi, a maimakon ya amsa mun
se yace

"Shikenan se goben In Allah ya kaimu kiyi saving Number ta nasan yanzu ma qila sa'a naci kika daga
tunda baki da ita"

"Ai naga sunan a true caller na gane kaine, Allah ya kaimu goben a gaida Madam" daga haka mukayi
sallama.

Dana tashi a hanya naga wani boutique da suke siyarda rigunan yara masu kyau, na tuna gobe ne fa
Graduation partyn su Amna jibi kuma suyi prom kuma Faridah bata da kayan da zata saka goben dan
haka na tsaya a gurin na siya mata riga me kyau, har na gama na tuno da za'a kawo mun wata yarinyar
dukda bani da tabbacin ze bar mana ita ne ta kwana a nan nace bari na siya mata.

A hoto dana ganta dai nasan bazata wuce tsahon Abdallah ba amma dan na tabbatar sena kira wayar
Yusuf amma line busy
Text yayi mun cewar yana busy akwai wani abune?

Sena mayar masa da cewa menene tsahon Takwara da size din takalminta ba'a dauki lokaci ba ya
turomun kuwa na siya mata kalar ta Faridan da takalmi harda su Ribbon dan naga tana da gashi kafin na
wuce gida.

Ina zuwa na tarar dasu sunyi kaca kaca da gidan na kuwa hausu da Fada akan su gyara na wuce dakina
ina shiga Jafar ya biyo ni a baya tas ya kwashe abinda ya faru dazu ya gaya mun.

Sosai raina ya baci akan abin, wane irin rashin hankali ne ze saka Aliyu ya daki Matar Babansa da ko bata
aure shi ba matsayin uwa take a gurinsa cikin bacin rai nace ya kiramin shi na hadasu su biyun tunda
sune manya nayi musu tatas nace kuma idan ya koma ya bata haquri sannan na kira sauran na tara su
gaba daya na sake ja musu kunne akan duk wanda na sake jin ya mata ko kallon Banza ne se ransa yayi
bala'in baci, haka na wuce daki na barsu Aliyu ya cika kamar ze fashe har na tafi na koma na sake masa
warning akan karya kuskura ya taba Jafar dan nasan qarshe se ya huce haushin gayamun da yayi akansa.

Ina Wanka najiyo wayata na qara, da yaje na kammala sena dauro towel na fito kafin na daga ta katse
sega wani kiran ya sake shigowa.

Yusuf ne, ina dagawa muka gaisa yace

"Gata can a waje sunzo amma taqi fitowa daga mota, dan Allah ko zakije ki lallaba ta idan kuma taqi su
wuto da ita kawai nan bansan ya zanyi da ita bane meeting mukeyi nasan zan iya kai qarfe biyu ma kafin
na gama".

"Zama ta yarda in sha Allah bari naje na gani" na fada kafin na kashe wayar. Dogon Hijab har qasa na
zura na saka takalmi na fito har sannan yaran suna zaune suna kallo, Abdallah na ganin na fita ya biyoni,
a qofar gida naga motoci guda biyu masu numfashi da wasu qarti su biyu a gaban daya daga cikin motar.

Number Yusuf na sake dialing tana shiga ya katse se naga wayar daya daga cikin qattin tayi qara ya daga
da sauri kafin ya juyo inda muke se gashi da dan gudunsa ya taho gurin.
Cikin girmamawa kamar ze durqusamun ya gaisheni cikin harshen turanci kafin ya nunamun motar da
take a rufe yace tana ciki.

Gaban motar na qarasa na kwankwasa super tint windown motar, kusan minti daya aka sauke shi wani
ni'imtaccen qamshin yan gayu ya daki hancina har seda na lumshe ido kafin na bude fuskata dauke da
murmushi na kalli cikin motar mukayi arba da wata farar mata irin fara fat din nan dan duk farina se na
ganni na zama wata kala a gabanta siririya me dogon gashi da ta barshi a bude, a yanayinta ma zan iya
kiranta da bauturiya ko kuma dai ruwa biyu amma ba hausa ko Fulani bace wannan.

Qara fadada fara'ata nayi, dan naga yanayin yarinyar Yusuf a fuskar ta dan haka na tsammaci itace
matarsa, cikin harshen turanci na miqa mata gaisuwa dan bana tunanin wanann zataji hausa, ta
amsamun a wani yatsine har seda abin ya sosamun rai nan da nan kuwa nima na datse fara'ar dan ban
son wulaqanci a rayuwata.

Cikin yauqi da iyayi tace mun "kece Asma'u?"

Sena daga mata kai kawai ina kallonta ta waiwaya daya bangaren da bana hango wanda yake zaune tace

"Sweetheart kije ga Namesake dinki nan zaki zauna a gurinta, ki zama yarinyar kirki kinji"

Cikin muryar yara da kanaji kasan yaron ma sangartacce ne Yarinyar ta fara mana tana cewa

"Ni bazan je ba gurin Dady na zanje"

"Dadynki bashi da lokacin ki na gaya miki kece kike ganin yana sonki amma baya sonki sam, idan ba haka
ba ya za'ayi ki taho tundaga United State amma ya kasa zuwa ya tare ki sema yace a kaiki gurin wata
stranger ki zauna hmm" Matar ta fadawa yarinyar seka rantse da wata babba Sa'arta takeyi ni kuwa ina
daga gefe ina kallon ikon Allah.

Wannan wace irin uwa ce me qoqarin turawa yarta wata aqida da zata sa ta tsani mahaifinta?

Ganin dramar bazat qare ba ya saka na zagaya daya barin da take, badan kar Yusuf yaga rashin kirki na
bama qyale ta zanyi su tafi amma bansan dalilin sa na cewa a kawota ba tunda ga uwarta amma yanzun
ma sau daya zan lallabata idan bata yarda ba su sauka lafiya.
Qofar na bude da murmushi na na miqa mata hannu seta dakata daga bubbuga qafar da takeyi ta zuba
mun ido

"Muje ko kinga dare yayi Momy tana so ta tafi gobe da safe se na kaiki gurin Dady da kaina" na fada cikin
lallashi, seta kalleni ta kalli uwarta data wani tabe baki ta dauke kai gefe, kai na gyada mata alamar
tabbatar wa se kuwa gashi ta zuri qafafunta sena dagata na fito da ita daga motar ashe ma afili batafi
girman Yan biyu ba.

Qato daya ne ya bude boot ya ciro mata akwatinta ta yangayu me shegen kyau ga wata qatuwar Teddy
da tayi girmanta ma ya wuce da kayan bakin qofa ya ajiye, a taqaice nayiwa matar sallama na juya seta
dakatar dani, ta bude jakarta ta zaro wata farar takarda ta miqo mun, da rashin fahimta na kalleta se
tace

"List na abubuwan da Sweetheart take ci ne"

"Ikon Allah" na fada a fili na sa hannu na karbi takardar na shige gida ina jujjuyata a hannuna, muna
shiga muka tarar suna kallon wani cartoon na Bluey ne sunan sa kome ta kuwa dage ta kwala sunan a
kunnenan babu shiri na ajiye ta ta wuce da gudu cikin palour, ganin sun cikia ko ina kan kujerun bata
tsaya ba ta dane Cinyar Aliyu da yake kujerar data fi saiti da Tv tayi zamanta.

Se kawai muka tsaya muna kallonta, ita kuwa ba abinda ya shafeta dariyarta takeyi da alamar tana son
abinda take kallon.

"Mami wacece wanna" Aliyu ya fada yana sauke ta daga jikinsa amma taqi saukar, se nayi murmushi
nace "sabuwar qanwa kuka samu tazo mana weekend, gobe Babanta zezo zaku ganshi" na wuce ciki na
barsu.

Akan Mirror na ajiye takardar ina mamakin wannan wace irin mata Yusuf shi kuwa ya aura ko a ina ya
samota se Allah.

Seda na gama shiryawa tsaf na kalli agogo nasan lokacin sun fara shirin tafiya dan haka na fito, ina sako
qafata ido na ya sauka akan Yar Amana tana zaune tayi daidai tana cin wainar fulawa da Manja da alama
yanzu sukayita farar rigar jikinta tayi kaca kaca ta canza kala.
"Na bani ni Asma'u me kuka bata haka" na fada ina qarasawa gurin da sauri, seta dago tana yar dariyar
yarinta cikin turancinta da kana ji kasan rainon America ce tace

"Mami da dadi amma akwai yaji"

"Waya ce ku bata Amna me yasa baku tambayebi ba kafin ku bata" na fada ina janye farantin se kawai
naga yarinya ta fara birgima kamar me hawa bori, Amna na dariya tace

"Wallahi Mami ban san ma sanda suka shirya ba Jafar ne yayi musu gashi can ma yana soya sauran a
Kitchen"

"Kun kyauta, idan cikin yar mutane ya baci se kusan yanda zakuyi da ita ai" na fada ina akiye mata
kwanon na koma na dauko wayata na shiga kiran Babanta.

To a takardar fa wasu lissafin abincinsu can na turawa yan gayu aka rubuta sunzo sun hadata da fulawa
da manja, saurin fa da nayi kenan na fita ko oat ne na saka su hada mata tasha dan banida tarkacen dana
ga an rubuta a takardar.

Nayi Sa'a kira daya ta shiga ya daga yana cewa

"Badai yar rigimar taqi zama ba"

"Wa ai gata can muan shigowa ma ta shiga sabgarta, Mamanta ce ta bani list na abincin da take ci, todai
in gaya maka ina daki kafin na fito su Jafar suka dura mata wainar fulawa da yaji na dauke na hanata ci ta
farayi mun bori shiyasa na kiraka kar muje cikinta ya birkice ga dare yayi" na fada masa.

Dariya sosai yayi yana cewa "Ma'u kenan sarkin ci ai indai taga abinci setaci ko wanne iri ne, ki manta da
wata takadda na rasa me yake damun Intee Allah yasa dai batayi miki halin nata na wulaqanci ba"

"Aa ba komai gaisawa kawai mukayi ta tafi, to shikenan ba matsala kenan mu bata duk abinda muke ci"
na sake tambayarsa
"Ki bata komai, dambu fura tuwan dawa ba abinda Hajia bata dura mata a Bauchi tun bata kai haka ba
me kuma ya sameta tsabar matsala irin ta uwarta ce kawai" ya sake fada, se nace masa

"Allah ya rufa Asiri, goben da wuri zaka shigo dan zamu fita, zamuje Graduation din su Amna qarfe
goma"

"Kai masha Allah har Amna ta gama secondary school dagaske dai tsufa ya fara kama mu, ba damuwa a
wacce makaranta ne idan na samu dama sena shigo nima"

Sunan makarantar na gaya masa mukayi sallama, ina jiyo ihun Ma'u takwara na fita naga meya faru na
tarar wai su Faridah ne zasu tafi ta kama qafar Jafar ta riqe da gani dai dashi aka qulla abota se tsalle
take tana ihun bazasu tafi ko kuma seta bisu, kamo ta nayi ina rarrashi amma ina qara zillewa take yi,
qarshe dakyar na samu ta haqura shima seda nace Faridah ta zauna ta kwana suka zille sauran suka tafi
na saka Amna tayi mata wanka suka kwanta a raina ina Addu'ar Allah sa kar Bashir yace zeyi tashin
hankali a daren nan cikin Sa'a kuwa har muka kwanta shiru.

Washegari

WATA KISHIYAR

(ALKAHIRI CE KO SHARRI)

Na Maryamah Farouk

(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)

Wattpad @MaryamahMrsAm
Page 48

WASHE GARI

Washe garin ranar da wuri muka shirya saboda su basayin African time irin namu na yan Arewa. Sosai
nayi kwalliya da Doguwar rigar Lace baqi me Golden din zare na yafa mayafina a kafada na saka coge
nida kaina na yaba kwalliyata dan na fito cas dani.

Da muka fito zamu tafi Anty se tsokanata take wai taga alamar fa Zawarcin nan me lasisi nake zuba to
dai nayi a hankali kar na sa maza suringa karo a hanya a garin kallo na.

Bashir ne ya tafi da yara mazan a motar sa harda Amirah suka tafi, daman bamu hadu ba a bakin Amnah
naji cewar da Amiran aka tafi nayi murmushi kawai a raina ni kadai nasan tsiyar da zan qulla mata tunda
nidai ban gayyaceta ba ai, A motata muka tafi tareda Anty da yammatan harda sabuwar yata da tasha
kwalliya dan tun dare na gyara musu gashin su ita da Farida sunyi kyau sosai cikin rigar jiya kamar wasu
Yaya da qanwa haka muka rankaya muka tafi.

Sanda muka isa lokacin an fara shiga dakin taron, sallama Amnah ta mana ta wuce gurin Yan ajinsu ni
kuma na tsaya dakko Get pass dan suna motata tun ranar da aka kai mana ban cire su ba nasan su Bashir
ma basu shiga tunda dole su jira pass din, murmushi nayi sanda na fito dasu na qirga.

Guda goma ne cif, daman guda hudu suke bawa ko wanne dalibi idan kana son qari seka siya dan haka
na qara guda shida ya zama teburi daya muka kama kenan, nida yarana banda Amnah mu bakwai se
Anty ta takwas ga Bashir tara ragowar daya kuma daman na siyane kawai dan teburin me Goma ne to
yanzu ga sabuwar yar da nayi shi kenan mun cike shi.
Haka kawai naji dariya ta kama ni sanda na hango Amirah yanda taci uwar kwalliya kai ka rantse wata
dinner auren qawarta zata tafi se wani karairaya take a gefen Bashir hannunta cikin nasa, wani ikon Allah
se banji komai a raina ba illah ma dariya data bani kawai dan a yanda take abun kana gani kasan irin da
gayyar nan take dan ta bata mun bata san ko a kwalar rigata ba.

Mijin nata ma da da na dauka na dora akai yanzu na sauke nima na huta.

Seda na qara gyara fuskata tsaf kafin na kulle motar na fito ina gyara zaman gyalena a kafada daya, cikin
takun yauqi da yanga na qarasa inda su Bashir suke ina jin yanda idon mutane yayi mun caa a raina na
shiga karanta 'A'uthubikalimatillahi tammat min kulli shaydanin wa hammatin wa min kulli aynin
lammati' saboda mugun ido haka na qarasa inda suke kallo daya nayiwa Bashir daya watso mun
idanunsa da suka fara rinewa da bacin rai nan take na dauke kaina ina murmushin qeta.

A saitinsa na tsaya fuskata dauke da murmushi na gaishe shi, be amsa ba se matsowa da yayi bayan ya
saki hannun Amirah da tunda ta ganni ta shaqa tayi fam se wani harare harare takeyi kuma dai baze
wuce tsabar hassada da baqin cikin gani na bane ya saka. A daidai kunnena ya tsaya idonsa akan fuskata
yace

"Meye kike yi haka Ma'u baki kalli kanki a mudubi ba da zaki fito a haka cikin wannan kwalliyar? Jifa
yanda maza suke kallonki dan Allah ki koma nasan bazaki rasa Hijab ko Abaya a mota ba ki saka".

Wata siririyar dariya nayi kafin nayi qasa nima da murya yanda shi kadai ze ji abinda na fada nace masa

"Ai daman saboda mazan su kalleni nayi, ko ka manta a kasuwa nake yanzu ne?"

Ina fadar haka na janye daga kusa dashi ina ji ya na kira sunana amma nayi kamar ma banji ba, katinan
hannuna na fara bawa yaran da akwai table Number dan haka sukayi gaba, na miqawa Anty nata na
miqawa Bashir daya sannan na juya ina cewa Anty

"Muje toh, Baban Ali seka shigo koh" nayi gaba abuna dan ban nuna nasan da wanzuwar wata halitta ma
a kusa dashi ba, hannuna ya riqo da sauri na waiwaya na watsa masa wani mugun kallo da ni kaina
bansan na iya shi ba, se yayi saurin sakina yana cewa
"Yi haquri amma dan Allah kije ki.."

"Karka sake mun haka, da mutunchi na kazo kana kamani a gaban mutane bana so, sannan baka da
hurumin da zaka gaya mun abinda zanyi yanzu ko wanda zan bari ka gane" na fada ina qara daure fuska.

Ina kallo ya hadiye wani abu qut kafin ya marairaice fuska ya sake cewa

"Nace kiyi haquri ai, naga kati daya kika bani ina na Amirah?"

Juyawa nayi na kalli Amiran da ya ce se numfarfashi takeyi kamar wadda zata haihu na maida idona
kansa nace masa

"Na iya wadanda aka gayyata kenan, bama buqatar qarin gayyar sodi" ina gama fada na bi bayan Anty da
ta dade dayin gaba daman.

Bansan yanda suka qare ba, munfi kusan minti sha biyar da shiga kafin na hango su sun shigo Amirah na
bayansa fuskar nan kamar ka tsira mata Tsinke ta fashe tsabar yanda ta kumbura, acan kejerun yan
regular naga ya sama mata sit ta zauna, ya dan duqa da alama magana yake gaya mata kafin a fusace
naga ya taho inda muke zaune.

Na zata masifa ze zo yayi na qara tamke fuska ta tsaf se naga yana zuwa yaja kujerar da tayi saura ya
zauna ya gaida Anty ta amsa masa sama sama nidai na mayar da hankali kan cultural dance da akeyi ina
jin yanda idon Bashir yake kaina amma naqi kallon barin da yake.

Wayata dake ajiye akan teburin ce ta dauki qara, yanda kasan shi aka kira ya bi wayar da kallo na kai
hannu na dauka, Yusuf ne da nayiwa saving da Abban Takwara, saboda qarar kida banajinsa dan haka na
tashi nayi tacan baya gurin inda kujerun su Amirah yake, ta kusa da ita na wuce ina giftawa naji ta saki
tsaki ban kulata ba na wuce na amsa wayata.

Gaya mun yayi yana waje nace ya jirani gani nan zuwa, na sake zuwa na wuceta dan banida lokacin da
zan tsaya ina kula wannan yarinyar. Seda na koma sit dina, jakata na bude na ciro ragowar kati daya dan
Ma'u Jafar ne ya dagata da yake ta sangarta ta lankwashe a jikinsa yanda kasan wata yar Yaye dan haka
basu karbi katin taba muna shiga ya bani na saka a jaka.

Ina kallon yanda Bashir ya bini da kallo ganin na ciro wani katin daga jaka, se na juya na cewa Anty ina
zuwa na wuce ta saitin Bashir ya shaqi qamshij da nakeyi kuwa kafin ya ajiye numfashi na wuce shi ina
juya mazaunan da Allah ya hore mun shi kuwa Ya bini da kallo da baki a sake har na qulewa ganinsa.

A qofar gurin naci karo da Yusuf, wani dace shaddar jikinsa yanda kasan tare muka siya da kayan jikina
sunyi bala'in dacewa.

Cikin mutuntaka muka gaisa da wani dana gansu tare babban mutum ne sosai wai shima Sanata ne
akwai yaransa biyu a yan Graduation din, ba'a ma karbi katinan mu ba muka shiga tareda Yusuf din kai
tsaye teburin da muke zaune na wuce gaba yana bina a baya.

BASHIR

Tunda yaga Asma'u a gurin gaba daya ta sake kwance masa notin kai. Kwalliyar ta tayi bala'in tafiya da
imaninsa ga wani kishinta daya taso masa Ganin yanda maza suke binta da kallo.

Tana bashi katin nan da ta juya haka ya rakata da ido gani yake kamar qara mata quruciya akayi dirin
jikinta ya sake fitowa, yana can aikin kallonta tsakin da Amirah tayi ne ya dawo dashi hayyacinsa se ya
kalleta sanda take cewa

"Yanzu kana kallo ta tafi bayan kaji abinda tace wato nice ma gayyar sodi ko kuma kayi shiru baka ce
komai ba"

"To so kikeyi na kamata da kokawa nace seta baki ko kuma nawa zan baki? Daman ai ba gayyatarki ki
akayi ba gayyar sodin kika zo.

Kinga ki kama kanki wallahi karki sake kice zakiyi mun shirme a gurin nan zan bata miki rai" Bashir ya
fada cikin bacin rai, wallahi da a Gombe nema tafiyarsa zeyi ya barta idan yaso ta koma gida dan dai
kawai nan bata san hanya bane.
Amirah data shaqa iya wuya, dakyar ta danne bacin ranta tace

"To yanzu a waje zaka barni ka shiga ciki kenan" ta fada kamar zatayi kuka

"Seki koma mota ki zauna dan dai ni ban san a inda zan samo miki kati ba kuma nan ba irin taron da kika
saba zuwa bane ko ba'a gayyace kuba ku shiga su komai a tsare sukeyinsa" Bashir ya fada yana hararar
ta, se kawai ta saka masa kuka tana cewa

"Da kasan wulaqanci zaka mun idan nazo tun a gida se kace bazaka dani ba amma yanzu kace na tafi
mota bayan ga katuna can a hannunta harda wasu daban ta gayyato se nice baza'a bani ba"

Tsaki Bashir yayi ganin tana neman tara masa Jama'a dan har an fara kallon su yace mata yana zuwa ya
tafi Gurin securities din bakin gate.

Seda yaci wuya dakyar ya samo mata regular card shi kansa dubu goma aka siyar masa, daya bata a
maimakon ta gode seta hau sabon qorafi wai ba irin nasu bane dan ko a kala katin ya banbanta.

Banza ya mata suka shiga ya rakata kujerarta se raba ido take ganin Jama'a kala kala yanzu da wannan
shagalin za'a mata buqulun zuwa tab, Allah ya kaimu Na Aliyu wannan ai dan mijinta ne itama dole tana
teburin gaba tunda yanzu ance mata gayyar sodi.

Hakata zauna wani mugun kishi ga kyashi da hassadar Ma'u na dukanta. Duk abinda ta gani a jikinta ji
takeyi dama itace, simple lace me Azabar kyau ga zobuna da awarwaron gwal suma qira mara hayaniya
sun qara fito da kwalliyar ta sosai qarin baqin cikinta yanda Bashir ya kasa dena kallon Ma'un ba daban
ba da se tace su tafi kawai amma ina setaga kwal uwar daka sannan idan sun koma gida se ayi uwar da
za'ayi.

BASHIR

Kwarewa yayi da ruwan da yake sha a daidai sanda Ma'u da Yusuf suka ratso dakin taron kamar wasu
shaqiqan masoya fuskokinsu dauke da murmushi. Ba Bashir kadai ba, da yawa mutane seda suka bisu da
kallo haka suka qarasa har teburin Yusuf ya daga Ma'u qarama data fasa ihun murnar ganinsa ya zauna a
gurin suna fuskantar juna da Bashir.

Fuska a sake ya miqawa Bashir da yayi suman zaune hannu dukda can qasan zuciyarsa bazeyi qarya ba
daurewa kawai yayi amma sosai yake Adawa da Bashir din daya rabashi da macen da yake so sama da
kowace mace a rayuwarsa.

Ya wargaza masa mafarkin shimfida rayuwar aure me ciki da aminci da qauna qarshe ya barshi da
gantalewa da zama macen da bata dauki aure a bakin komai ba.

Malam Bashir kuwa bin hannun Yusuf yayi dake daure da wani shegen Agogon diamond a tsintiyar
hannunsa, kai Cufflinks dinsa kadai abin kallo ne wani irin tuquqin baqij ciki da kishi suka taso suka shaqe
masa wuya kawai ya mayar da kai gefe ba tareda ya karbi musabahar ba, ko a jikin Yusuf ya maida
hannun gurin su Aliyu duk suka gaisa yana tambayar su sunayensu dan ko shine Bashir din akan Mace
kamar Ma'u zeyi abinda yafi haka shi yama ga qoqarin sa daya zauna teburi daya dashi ai

Gaisuwa me kyau sukayi da Anty Halima nan da nan suka shiga hira kamar sun san juna dan shima akwai
faran faran da mutane halinsu yazo daya dukda da ita da gayya ta qara sakewa suke hirar saboda ta
turawa Bashir takaici se gashi kuwa Hira ta barke tsakanin Yusuf da sauran Yaran Ma'u qarama na qara
maimaita masa sunayen su se dariya suke mata dan bata iya fada ba ya kalli Asma'u yace

"Gaskiya kin iya bida yara kiga yanda yarinyar nan ta sake lokaci daya anya bazan bar miki ita ba kuwa"

"Ai na yara kadai ba har manyan in gaya maka ta iya tafi dasu ta kowacce hanya me sauqi ko me daci, ka
bar mana ita kawai mun samu qarin ya" Anty ta fada tana dariya ta gefe kuma tana hararar Bashir da ya
kumbura dan har kamar yafi Amirah kumbura yanzu.

Shigowar yan Graduation ce ta dakatar dasu daga hirar, nan da nan aka shiga gabatar da abinda aka je yi,
an raba musu kyututtuka sosai Amna ta samu lambobin Yabo dan ita ta lashe Best Student ta shekarar
aka kira Iyayenta, Ma'u na miqewa Bashir shima ya tashi daga kan stage ta hango Amna na tsalle tana
nuna mata bayanta tana waiwayawa se ganin Alhaji Qarami tayi tareda Matarsa ta biyu da daya daga
cikin Yaransa Abdullahi da suke cewa Baffa.
A tsakiyar Mu nida da Bashir Amnan ta tsaya akayi mana hoto se wani washe baki yake shi ala dole ga
Baban Amnah, ganin Alhaji Qarami da Yah Muslim da shima bamu san da zuwan sa ba sun qaraso gurin
se Bashir ya dan matsa yana shafa kai amma Alhajin ya sake mayar dashi gefen Amnan su kuma suka
tsaya daga gefe da gefen mu aka sake daukar hoton.

Haka sauran yaran dukka suka shiga akayi ta hotuna harda su da Anty. Hoto daya muka dauka tare da
Yusuf ya mana sallama ya fita saboda kiransa da akayi.

Amirah tana daga can qarshen tana hangomu baqin ciki kamar tayi bunga dan securities ne ma suka tare
hanya kar su yan regular su shiga gurin VIP.

Har kwalla seda tayi saboda baqin ciki, tana gani muka gama hotunanmu cikin farin ciki muka sauka
kowa ya koma mazaunin sa kafin taro ya koma na ciye ciye da maqulashe.

Abubuwa ne gasu nan birjik se wanda kake so a ka ringa ajiyewa, ita kanta Amirah ba qaramar gara aka
ajiye mata ba amma saboda qalata idonta nakan teburin su Bashir har seda ta kasa daurewa ta zaro
wayar tavta rubuta masa text tace

"Yaya naga abincinku ba irin namu bane, ka rage mun zanci nima"

"Ai se kici idan ke mayya ce ko kuma daga yunwa kika fito" Bashir da ransa yayi bala'in baci ya mayar
mata da Amsa. Tsabar haushi gaba daya ma ta saka abincin ya fita daga ransa ya ringa zabga tsaki su dai
yan gurin ba wanda ya kulashi abincinsu suke loda kawai.

Qarfe sha biyu taro ya tashi, bayan abincin da aka ci a ciki harda wani Take away aka sake binsu dashi, Su
Ma'u na tsaye aka kai mata nasu ta bude boot aka zuba Anty ta kama baki tana cewa

"Duk wannan abincin da muka ci a ciki qara raba wani suke yi lallai se a gaishe su"
"Yo ba dole ba wannan uban kudade da suka caji iyaye banda contribution da suka samu daga sauran
mutane ai dole kiga sunyi bushasha" shiru nayi lokacin dana hango Amirah na cacar baki da daya daga
cikin rabon Abincin da alama hanata yayi se na nunawa Anty gurin yanda kasan da Bashir nake shima ya
bita da kallo.

A tsawace ya kira sunanta, se gata ta taho gurin tana qunquni, "haka kawai a komai se an nuna banbanci
bayan duk abu daya muka zo kuma"

Mudai gabada ya ma dauke kawunan mu gefe mukayi dariya na cina a zuciya, Allah ya sauwaqawa wasu
dai da shegen kwadayi suke.

Qarasowar Alhaji Qarami, Yah Muslim tasa na qara fadada murmushi na,

"Gashi bamu zo da mota ba, taxi muka hawo daga Airport yanzu kuma ina so na leqa gurin Olabode nayi
masa ta'aziyyar Matarsa kafin dare mu wuce nasan kema baki je ba ko Asma'u" Yaya Muslim ya fada
yana kallona, sena kama baki nace

"Wallahi Yaya na manta, bama wannan ba gidan ne bazan iya kai kaina nikadai ba shiyasa Amma yanzu
seka kwatanta mun zan samu lokaci naje kar yace seda kazo mukaje tare".

Motata ya karba shida Alhaji Qarami suka shiga suka tafi dan shima akwai inda zeje, Bashir ma tuni ya
kwashi yaransa da Amaryarsa da take ta faman zumbure zumburen hanata karbar take away da yayi ya
rage saura Ni da Anty se Anty Hadiza Amaryar Yaya da zamu wuce gidana tare da ita kafin su dawo dasu
Amnah.

Guri muka samu muka zauna muna ci gaba da hira dan Amnah har sannan tana can suna hotuna da
qawayenta. Yusuf ne ya taho gurin yana cewa

"Aa baku tafi ba Ma'u? Ina sauran Yaran dasu Alhaji Tukur?"
"Sun wuce gida, Alhaji Qarami kuma sun fita da Yah Muslim, muma Amnah muke jira mu tafi, ka ganta
nan ma zuwa" na fada ina miqewa tsaye. Wayata na zaro ina cewa

"Bari na kira mana Uber muma mu wuce toh"

"Aa bari na sauke ku mana, nima naje mun gaisa da Family colleague dina na dazun nan da kika gani"
Yusuf ya fada, se muka bishi gaba daya zuwa gurin wata Arniyar mota High Lander.

Duk suka shige baya harda su Amnah akan dole ni na shiga gaba muka kama hanyar gida muna tafe
Yusuf dasu Anty suna ta hira amma na kasa aka musu baki saboda duk se nake jina a takure ko dan
yanda duk sanda zan daga ido se naga yana kallona har tsoro na fara ji kar muje ya zubar damu a haka
dai muka qarasa gida lafiya.

Tundaga Nesa na hango Bashir a zaune akan motar sa ya zubawa hanyar shigowa layin namu ido kamar
me jiran wani abu, kamar da gayya ma naga Yusuf ya taka motar tayi wata qara da take nuna lafiyar
injinta kafin ya fizgeta ya cake a qofar gidana, muna tsayawa wayata ta sulale qasa dan haka na duqa ina
nemanta kafin na ganota har su Anty sun fice daga motarya rage daga ni se shi a ciki.

Murfin motar na kama da niyyar budewa ina cewa "mungode, zaka dawo anjima tareda su Yaya ne ko se
kazo daukar takwara?"

Shiru yayi mun, sema gyara zamansa da yayi ya juyo gaba daya yana jifana da wani irin sanyayyan kallo
daya saka naji tsikar jikina sun fara tashi bashiri na sauke kaina qasa ina ci gaba da kiciniya da qofa amma
taqi buduwa.

"Kinyi kyau sosai Asmy, amma kamata yayi ace kwalliyar nan ido na ne kawai ze ganta kuma ni kafai zan
shaqi wannan ni'imtaccen wamshin naki. Bazan gaji da kallonki da yiwa ubagijij daya halicceki tasbihi ba
Asmy dan yayi miki suffar da a kallo kadan take iya sanyaya zuciyar wanda yayi tozali dake, ina ma zan
iya ci gaba da kallon ki har qarshen rayuwata nasan bazan taba gajiya ba".

Jikina ne ya dauki rawa saboda yanda kalaman Yusuf suka shigeni, qara damqe wayata da jakar hannuna
nayi yanda kasan wata mara gaskiya nace "Ka bude mun qofar na fita kaga..kaga"
"Mijinki yana kallon mu ko?" Ya fada yana gyara zamansa kafin yayi wata siririyar dariya yaci gaba da
cewa

"Idan na samu dama anjiman zan dawo idan kuma banzo ba may be Monday nazo na dauki Ma'u m.
Zadai muyi waya kawai" yana gama fada ya sun kuyo ta barin da nake ba shiri na dauke numfashi ya
kuwa kwashe da wata dariya ya dannan wani abu a jikin qofar yana cewa

"Ke kika kulle kanki bude mini zanyi amma ji yanda gaba daya kika dauke wuta kamar mara jini" nidai
ban kulashi ba na kwashi qafata nayi waje, ina direwa kuwa da sauri nayi baya na jingina da motar ganin
Bashir a gabana da yana numfarfashi kamar me cutar Asthma.

Yana shirin bude baki na gewaye shi na wuce ina hada hanya dan fa har sannan jikina rawa yakeyi, daga
bakin qofa na tsaya ina daidaita nutsuwa ta, sena waiwaya na kalli inda na bar Bashir a tsaye na hango
Yusuf ya sauke glass din wundo da alama magana sukeyi.

na seda naja iska na fesar kafin na tura qofar na shiga dan a bude suka barta.

BASHIR

Har suka isa gida Amirah na zuba masa mita da qorafin an mata wulaqanci amma tafi ki mutu be ce mata
ba gaba daya hankali da tunaninsa suna kan Ma'u daya baro acan.

Yana tsayar da motar a qofar gida ya waiwaya yace mata

"Ki dauki nawa a Boot gashi can kici shikenan dai ko?"

"Ai ba shikenan ba, bayan ma duk lefinka ne. Da ka nuna inada daraja da qima a matsayina na matarka ai
komai nima zuwa za'ayi ana girmamani ayi mun amma fa ji irin wulaqancin da kayi mun ka kama ka kaini
can qarshen bango kamar wata mara galihu ko hoto baka ce nazo ayi dani ba seka..."
"Kinga fita, ki wuce gida sauri nakeyi ni akwai inda zanje" ya fada a hankali can qasan zuciyarsa yana
qoqarin danne fushi da bacin ran da suke taso masa. Yaga alamar ita bata gajiya da tashin hankali shi
kuma a yanayin da yake ciki yanzu nutsuwa yake da buqata bawai qarin wata damuwa ba.

Fitar tayi tana masa qunquni, shidai yaja motar yayi gaba. Niyya yayi ya koma ya dauko su Ma'u tunda
yaga ta bayar da motarta amma se yayi tunanin tazarar gurin kafin ya isa qila sun samu abun hawa sun
taho gida.

Yusuf ne ya fado masa arai kar dai ya zama shi ze dawo dasu, nan da nan kuwa yaji kansa na neman yayi
ciwo se kuma ya tuna da ai tun suna cikin Hall din Yusuf ya tafi be tsaya an tashi dashi ba wannan
tunanin ya dan kwantar masa da hankali dan haka ya yanke shawarar ya nemi guri ya tsaya daga farkon
Layin ta yanda zega duk motar da zata shigo ciki dan idan ya koma qofar gidan sa waccen jarababbiyar
yarinyar seta dagula masa lissafi har Ma'un ma ta wuce be sani ba.

Yana zaune a gurin kusan Awa guda motar Yusuf ta danno kai, plate number motar da aka saka WUNTI 2
yabi da kallo ya tabbatar bata cikin Estate dinsu bace sedai idan wasu ne sukayi baqi, seda suka matso
kusa dashi ya hango Ma'u zaune a gaban motar yanda suka saje ita da Yusuf din seka rantse da Allah
wasu Mata da Miji ne sabon aure sukayi anko zasu je unguwa ga wani kallo me nuna so da yaga Yusuf
din yana yiwa Ma'u ita kuma ta sunkuyar dakai tana murmushi.

Wani Yum yum yaji akansa lokaci daya kamar an tsikara masa abu a qirjinsa har seda ya dafe saitin
zuciyarsa yana sakin numfashi ajere a jere, ya tabbatar idan ya miqe a sannan to kuwa seya fadi idan
beyi wasa ba ya hadu da paralyze abinda ya dakatar dashi kenan ya zauna yana kokawa da nutsuwarsa,
gashi ya kasa dena kallon motar har ta tsaya mutanen ciki suka fito dukka banda Ma'u abinda ya qara
masa hauhawar jini kenan haka ya dafa motar ya sauko yana jin jiri na kwasar sa amma ya daure.

Seda ya kwashi kusan minti biyar a tsaya kafin ya iya daga qafarsa ya fara tafiya yana rangaji, duk takun
da yake kusanta shi da motar ji yakeyi kamar anan suka masa wuqa a maqoshi idan ya tuna Ma'u ce a
ciki tareda wani qato da besan me yake gaya mata ba.

Ji ya ringayi kamar ya debi duwatsu tundaga nesan ya yita rotsawa gilasan motar har se sun rugurguje
amma baze yuwu ba dan yasan irin su ba qaramin duka zasuji ba ace sun balle haka ya qarasa Gurin
zuciyarsa kamar zata fashe ya kai hannu ze kwankwasa Ma'u ta bude qofar gabansa ya yanke ya fadi
ganin irin yanayin data fito, yanayine irin wanda take shiga lokacin da take cikin maye da shauqin
soyayya.

Bude baki yayi ze mata magana ta rabe shi ta wuce gaba daya se hankalin sa ya kasu biyu, ita ze bi ko
kuma tsayawa zeyi ya fara cin uban wannan me bibiyar masa matar tukunna?

Maganar da Yusuf yayi ce tasa ya wai waya ya kalle shi

"Yallabai barka da rana ashe gaba kayi dazu bamu samu mun gaisa ba ya aiki ya su Madam?? Yusuf ya
fada yana miqo masa hannu fuskar dauke da wani shegen murmushi.

Kallon hannun da yake bashi yayi ya sake kallon fuskarsa, 'qut' ya hadiye yawu kafin ya bude baki dakyar
yana nuna Yusuf yace

"Ka fita daga sabgar matata, idan ba haka ba sena koya maka hankali ta yanda ko kallon matar wani
bazaka sakeyi ba bare har magana ta hada ka da ita".

Ko a jikin Yusuf se ya janye hannunsa da Bashir yaqi karba yana murmushi yace

"Yallabai ni kuma meya hadani da matarka nida ban ma san tare kuke ba seda zaku tafi na hango ku zaku
shiga mota, ai ni ko kalar fuskar ta bansani ba bare wata mu'amula ta hadani da ita".

Wani banzan kallo Bashir ya watsa masa kafin a harzuqe yace

"Karka raina mun hankali, ni kake cewa baka san matata ba, to bari kaji wallahi ko a hanya na sake ganin
ka kalli Ma'u se nayi qararka na bata maka career badai taqamarka siyasa ba?

To sena gayawa duniya cewa kai Manemin matan aure ne idan yaso se naga ta yanda zaka tsira da
mutunchinka".

Dariya sosai Yusuf yayi harda dukan sutiyari kafin ya kalli Bashir daya shaqa iya wuce ya nuna shi yace

"Oh wai akan Asmy kake magana daman ai cemin zakayi tsohuwar matarka se nafi ganewa.
Toh tunda anyi haka yanzu bari nayi amfani da wannan damar nayi maka jajen wautar daka tafka ka rabu
da Mace kamar Asmy bayan ka manta akwai irin mu a waje da duk sallah biyar ta duniya da zamuyi a
rana se mun roqi Allah ya bamu mace kamarta.

Nagode maka kwarai daka sako min ita a daidai lokacin da nake tsananin buqatar ta, na kuma yi maka
alqawarin zan riqe Asma'u na bata kulawa da soyayyar daka gaza bata, kai amma ka tafka Asara yallabai
se in ce maka Allah ya mayar da Alkahiri ko da yake naga ka samo wata me fada akan Abinci a gurin taro
ko?

Irin matan nan in gaya maka ba'a zuwa gurin kunya dasu dan se sun zubar maka da mutunchi a ringa
kallonka kamar baka yi musu komai Alhalin tsabar rashin godiyar Allah ne kawai. Kayi haquri fa amma
dai dole in gaya maka kayi wauta Allah dai ya mayar da Alkahiri" yana gama fada ya dage gilashin
motarsa yayi gaba yana cigaba da yiwa Bashir dariya.

Bashir kuwa tsabar yanda ya tafi wata duniya na wucin gadi besan sanda Yusuf ya bar gurin ba se qugin
motarsa yaji. Ya juya ya kalli motar ya waiwaya ya kalli Gidan Ma'u wai ma takamaimai laifin wa ze gani
anan.

Yanzu har Ma'u ta bawa wani dama ya maye gurbinsa a rayuwarta Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.

YUSUF

Wato rai fes sunan wata Atamfa haka ya ringa tuqinsa yana murmushi shi kadai idan ya tuna yana yin
fuskar Bashir sanda yake gaya masa magana.

Tun ranar daya hadu da Ma'u da daddare yana sauketa ya kira Alhaji Tukur ya gaya masa yau ya hadu da
Ma'u babu bata lokaci kuma ya sanar masa da zancen mutuwar

Wanda yayi bala'in yi masa dadi ya kuma jin jinawa wauta da hauka irin na Bashir amma daya tuna cewa
Allah shi yake qulla aure ya kuma rabashi a sanda yaso se ya gode masa ya kuma tabbatar da Allah ne
yake son sa shiyasa be sake hadasu shi da ita ba se a yanzu da take babu igiyar kowa akanta.
Yana sane yake nuna mata kamar besan komai ba dan yafi so ita da kanta ta gaya masa bata da aure a
sannan ne ze dakko tsohon littafin soyayyarta ya karkade shi ya fara biya mata shafi shafi dan yayi
alqawarin a wannan karon babu gudu babu ja da baya se inda qarfin sa ya qare amma se ya mallaki
Asma'u kuma in sha Allahu rabonsa ce.

WATA KISHIYAR

(ALKAHIRI CE KO SHARRI)

Na Maryamah Farouk

(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)

Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 49

ASMA'U

Kai tsaye dakina na wuce sanda na shiga gidan ban ko tsaya jin Anty data tareni da tsokana ba na wuce.
Seda na cire kayan jikina da naji kamar harda su gurin tare mun numfashi kafin na watsa ruwa na saka
doguwar riga mara nauyi na fito har sannan tunanin Yusuf da kalamansa suna mun yawo a qwaqwalwa.

Anya kuwa Yusuf be san aurena ya mutu ba amma idan ya sani me yasa ze tsaya beyi mun maganar ba?
Da wannan tunanin na dawo palour na tarar da Anty Hadiza ita kadai tace mun Anty taje gida ta dawo.
Hira muka shigayi da Anty Hadiza, itama ba baya bace wurin zance nan da nan ta shiga kwashewa Bashir
Albarka.

"Ni wallahi naga qarfin halinsa irin yanda ya iya tsayawa a gaban mu bayan duk rashin mutunchin daya
tatawa mutane, kinsan da Alhaji ya kirashi akan maganar ya bar miki yara me yace masa? Cewa fa yayi
shi baze bar Yaransa a hannun Mace ba yana buqatar ya basu tarbiyya kiji dan abu ta kazan uba ko ina
tarbiyyar take a gurinsu da yake iqirarin baiwa wasu oho.

Allah ne yaso ki ya rabaki da Shi tun yanzu dan wannan mutumin tantirin mara mutunchi ne wallahi qila
da se kin kai shekarun da baki da yanda zakiyi ko yaka ki zeyi dole ki haqura ki zauna sannan zece ze
sakeki.

Ni wallahi ma sena raina ajinsa dana ga ita matar so din, me mace kamar ki, da se ya bari idan ya auro
wadda ta fiki sannan se yayi duk kadifirin rashin mutunchinsa amma yanzu ai baya yaci wallahi ba kuma
ze taba maida kamar ki ba In Allah ya yarda"

Nidai "hmmmm" kawai nake ce mata dan har a sannan tunanina yana kan Yusuf ne, so nake na
tambayeta ko sunyiwa Yusuf zancen amma sena dake, kai dole ma yasan da maganar nan qilan wani
dalilin ya sakashi qin yi mun zancen dan haka zan saurara na gani zuwa wani lokaci.

Se qarfe bakwai na Magriba Anty Hadiza suka tafi bayan Alhaji qarami sun dawo gidan ya sakeyi mun
nasiha tareda jan kunnen na kula da kaina na kuma kare mutunchi na a duk abinda zanyi.

Yusuf be zo ba be kuma kirani a waya ba, nima sena rabu dashi nasan dai baze wuce qila zuwa gobe yazo
daukar Ma'u ba tunda litinin akwai makaranta dukda bansan a ina take karatun ba.

A bakin Farida da taje gidan su dakko abu naji Bashir bashida lafiya, ko me ya same shi oho nidai haka na
kwanta ba tareda na sake bi takan maganar ba a dalilin haka ma ranar har yan biyu a nan gidan suka
kwana.
BASHIR

Yana kallon motar Yusuf har ta bace masa kafin ya dafe kansa daya sara da hannu daya ya daga
qafafunsa da sukayi sanyi ya wuce gida, a tsaye ya tarar da Amirah ta riqe qugu tana zazzagawq Su Aliyu
da suka hada PS anan palour suna game su kuwa babu wanda ya ko daga kai ya kalleta abinda yake
gabansu kawai sukeyi tana jin shigowar Bashir din ta juya cike da masifa tace masa

"Gara daka zo kai tunda Ubansu ne zasuji maganar ka. Idan banda iskanci da wulaqanci gardawa dasu
zasu zo su zauna mun a palour harda wani qarin dorin dosano da suka samo sannan ina musu magana
sun mayar dani kamar wata mahaukaciya sunqi kulani ai idan uwarsu ce bazasuyi mata haka ba".

"Amirah ki na gaya miki ki dena zagar musu uwa koh? Amma idan baki bari ba in sun rama karki kuskura
kice zaki kawo mun qara, ki barsu suyi sabgarsu.

A sati sau nawa suke zama a gidan da har ze zama abin magana dan yau daya sun zauna a palour zaki zo
kinawa mutane tashin hankali, dan Allah ki kyakeni na huta" Bashir ya fada kafin ya rabeta ya wuce,
dakinsa ya shiga ya bude first aid box dinsa yana neman paracetamol dan sosai kansa yake masa ciwo
amma be samu ba.

Palour ya sake komawa ya kwalawa Aliyu kira, Aliyun ya ajiye pad din game din ya tashi yaje ya same shi
a zaune bakin gado ya dage kai da hannaye biyu.

"Aliyu idan kuna da paracetamol a dakin ku kawo mun idan kuma babu ga kudi nan ka dauka mota kaje
pharmacy din tsallake ka siyo mun maganin ciwon kai" Bashir ya fada dakyar dan idan yayi magana ji
yake kamar ana sara masa abu akansa.

Abin Da da uba duk yanda Aliyu yake jin zafinsa ganin yana yin da yake ciki seda ya sanyaya masa jiki,
cikeda tausayi ya dauki muqullin motar Bashir din dan basu da paracetamol din suma, be dauki kudin
daya nuna masa ba ya juya ya fita.

Baffan Abuja yacewa yazo ya rakashi nan da nan suka tafi, hana da kudi cikin wanda Bashir din yake basu
ko Ma'u wani lokacin a ciki ya hado masa magungunan ya tsaya a wani gurin siyar da Abinci ya siyo masa
sakwara da miyar Egusi da wani gashin nama da akeyi a kusa da gurin dan ya lura be ci wani abun kirki
dazu ba kuma Antyn su batayi girki ba suka hado komai kafin suka dawo gida.

Sosai Bashir yaji dadin Abincin, yana ci yana sakawa Aliyu da yayi tsaye a gurin Albarka. Seda yayi nak
yasha maganin ya kwanta kafin Aliyu ya barshi ya fita, yana bude qofa suka ci karo da Amirah zata shiga
se yayi saurin tareta da cewa

"Bashi da lafiya ki barshi ya huta"

"Idan naqi fa ubana se ayi yaya?"

"Nidai na gaya miki ki barshi ya huta idan ba haka ba ai baki manta gamon mu sau biyu ba idan aka sake
na uku se kin gane kurenki, sena cire miki haqori in yaso naga da bakin da zaki ringa yiwa mutane
hayaniya a gida, tunda kika zo kin mayar mana da gida kamar kasuwa mu bamu saba ba" Aliyun ya fada
yana sake daure fuska sosai.

Seta ganshi kamar Bashir dan kwabo da kwabo haka yake da Bashir har kuwa halin be baro ba sedai
abinda ba'a rasa ba da kuma banbancin kwaba daga gurin uwa da suka samu, kwafa tayi dan tana tsoron
Allah tana tsoron yaron nan bashida mutunci, na farko ya fasa mata goshi na biyu kunne tasan idan ta
matsa dagasken yana iya sauke mata haqora kuma yaci bulus tunda ubansa babu matakin da ze dauka

Seta juya dakinta tana ci gaba da zage zage shima ya wuce gurin game dinsu ba tareda ya kulata ba.

Maganin nan da Bashir yasha ya sakashi bacci sosai dan se ana daf da magriba ya farka ko La'asar beyi
ba. Seda ya watsa ruwa saboda yanda jikinsa ya yi masa ba dadi amma yaji sauqin ciwon kan dukda yana
farkawa hoton Ma'u da Yusuf ne ya fara gilma masa a ido yayi saurin rufewa jin yanda zuciyarsa ta buga
da qarfi, a dakinsa yayi sallolinsa be ko fita palour ba yana jiyo hayaniyar Amirah da be san ko da wa
takeyi ba se ma ya sakawa qofarsa muqulli.

Naman dazu yaci da lemo dukda yayi sanyi amma bayaso ya fita ma balle ya hadu da Amirah ta qara
masa ciwon kai, yana yin isha ya sake kora magungunan saboda yanda yaji tunanin dazu na neman tado
masa da Sabon ciwon daya fi na dazu, dole ya dauki mataki baze zuba ido ba yana ji yana gani wasu
wawaye su ringa kula masa mata har suna gaya masa magana.
Dole ya nemi Ma'u su daidaita dan yasan itama bazata taba bawa wanin sa dama ba koshi wannan
shishshige mata yakeyi bawai dan tana so ba (A naka tunanin kenan malam Bashari 😂).

WASHE GARI

WAI YA LABARIN MUTANEN GOMBE KUWA???

GIDAN DADA

Tun ranar da labarin sakin Ma'u ya sameta tabi duk ta tsangwami kanta, ko kadan abun beyi mata dadi
ba kuma da ace Bashir yayi shawara da ita bazata taba bashi goyon bayan aikata hakan ba to a wanne
dalili ma ze saki Ma'u??

Babban tashin hankalin ta irin yanda Alhaji Amadu yayi mirsisi kamar besan abinda ya faru ba bayan
lokacin da Naziru yaje yana mata buyagi akan abinda Yayan nasu ya aikata ya tabbatar mata da Alhajin
ya kira Bashir din sunyi magana amma ita bece mata komai ba har yanzu da aka kusa dosar wata da
maganar.

Tasan Alhaji ta kuma san shirun sa ba Alkahiri bane bata san ta inda ze kamota ba, tsoronta Allah kar
wannan abin itama ya zama sanadiyyar igiyar auranta kamar yanda ya taba ambata mata a baya da in
har bata zare hannu daga sabgar gidan Bashir ba tabbas ze iya yanke igiyoyin da suke kanta idan yaso se
taji dadin yin abinda take so tunda ne isa da ita ba to yanzu ma irin yanda ya dauke mata wuta baya
shiga sabgarta sam dan ko abu yake so sedai ya kira Fainusa tayi masa abin yana mugun damunta har ta
fara tunanin ko da gaske itama an sake ta ne kawai gaya mata ne beyi ba kuma tana tsoron ta tunkare
shi da maganar tajiyo hakan ne dan bata san ina zata dosa ba, aure shekara Hamsin ba kadan a saketa ta
kama ina toh??

Da hantsin ranar Tana zaune a dakinta ta rafka uban tagumi abinda duniya ya taru yayi mata yawa, tun
shekaran jiya da Addah ta sanar mata da Sabon bala'in da Ummi ta janyo musu ta sake rasa sukuni. Dan
shege a zuri'ar su wannan wane kalar tashin hankali Ummi take neman jefa rayuwarsu a ciki? Idan aure
take so me yasa tun farko bata fada ba in ma bata da me sonta ne ai ko a tsakanin Naziru da Sa'ad ita me
iya tursasa daya ya aureta ne a taru dai a rufawa juna Asiri amma yanzu wannan abu data jawo musu ina
zasu saka kansu a garin nan??
Shigowar Fainusa da kukan data fasa ne ya dawo da ita daga tunanin data tafi, a gigice ta ke tambayarta
meya faru? fainusan na kuka take cewa

"Dada Umar ne, na gaya miki nafi sati ina kiran wayar sa kota shiga baya dauka shine yanzu ya daga yake
cemin wai nayi haquri ya fasa aurena. Ya rasa ta yanda ze gaya mun ne shiyasa idan na kirashi baya
dauka na kuma tambaye shi dalili yace mun ba komai, ni yanzu yaya zanyi Dada? Shekara Shida kenan fa
ina zaman jira yanzu dakyar Allah ya kawo mun mijin kuma shima ya gudu yanzu ya ake so nayi da
rayuwata?"

Kuka sosai takeyi, Dada tayi tsam ta kasa cewa komai. Tunda auranta ya mutu da uban da ta shekara
shida kenan an tafi ta bakwai kamar wadda aka watsa wa jinin baqar jaka babu wanda ya sake zuwa yace
yana sonta, da kyar da Addu'a Allah ya fitowa Fainusa da Umar din nan har ya turo manyansa anyi
magana sukace sati biyu zasu dawo da komai da komai a tsaida ranar daurin aure yanzu kusan wata daya
kenan babu su ba labarinsu shine ze bullo da wannan maganar kuma kai su dai suna ganin hawa hawan
tashin hankali.

"Kiyi haquri, ni tsoro nakeji nayiwa Alhaji magana yanzu kinga tunda Yayanku ya saki Matarsa Ahaji be ce
mun komai ba ina tsoron na jangwalo shi dan kinsan gani yakeyi kamar da saka hannuna a faruwar abun
nan.

Ki bari a qara kwana biyu idan yaso ko Amiru ne se na saka ya kira Umar din shi yaji menene matsalar se
a magance ta" Dada ta fada da son kwantar mata da hankali, se Fainusa ta fizge daga riqon datayi mata
tana cewa

"Nidai kije kiyi masa magana dan idan na rasa Umar mutuwa kawai zanyi duk duniya bayan da Iro ya
sako ni babu wanda ya qara ko kallona da sunan so se shi sannan yanzu yace ya fasa wallahi gara kawai
na mutu na huta da wannan baqin cikin da nake gani. Duk sakayyar abinda kukeyiwa wasu akaina take
qarewa, nayi aure naje Miji da kishiya sun wahalar dani sannan yanzu bayan na gama cin benci na samu
wani dakyar shima ya gudu to gara na bar gidan nan na koma wani gurin ko Allah ze dubeni ya cireni
daga bala'in da kuka jefa rayuwata a ciki".

Sosai hankalin Dada ya tashi, tasan Fainusa ba hankali ta cika ba itama tsaf tana iya yin abintzata illata
kan nata kamar yanda ta fada kota gudu daga gidan dan haka jiki a sanyaye ta miqe zuciyarta na bugawa
kamar zata fi to ta nufi dakin Alhaji Amadu.
Yana zaune yana sauraren radio ta shiga ya daga kai ya kalleta sau daya ya mayar da kansa a ransa yayi
murmushi yace

"Da wurwuri haka"

"Alhaji barka da hutawa" Dada ta fada tana qasa da kanta kamar wadda taje wani baqon guri, seya rage
radio yana kallonta yace

"Barka dai Nafi, halan batan hanya kikayi yau kika shigo dakina ko?"

"Batan hanya kuma Alhaji, zuwa nayi naji ko laifi nayi naga kwana biyu gaba daya ka shareni a cikin gidan
nan kamar baka san da zamana ba ko wani abun kake so sedai ka saka su Naziru suyi maka ban sani ba
ko wani laifi na aikata maka a cikin kuskure"

"Nidin kuma Nafi? Aa baki mun komai ba gani nayi dai ai daman ba se na kiraki ko na saka ki aiki kikeyi
mun ba to bansan ko gajiya kikayi ba kika janye shiyasa nake saka yayana gudun karna takura miki da
hidimomina tunda har kin qosa da kanki" Alhaji Amadu ya fada yana murmushi qasan ransa kuwa
mamakin Dada kawai yakeyi, ya sani buqatarta ce ta kawota danya jiyo wasu daga maganganunsu ita da
Fainusan daya leqa da niyyar kiran Fainusan shiyasaya dawo ya kunna radio a zuwan besan wainar da
suke toyawa bama.

"Kayi haquri Alhaji wallahi ba haka bane, gani nayo kamar kayi fushi dani akan abinda yaron nan ya
aikata ne shiyasa ni kuma bansan ta yanda zan wanke kaina a gurinka ba nasan laifina kake gani" Dada ta
fada tana qara sunkuyar dakai.

"Duk wanda yayi na gari ai kansa Nafi, bari nadan kwanta na huta tunda naga Azahar da saura, idan
Sa'adu ya shigo kice masa da yamma ze kaini Gidan Malam Isah na sake dubo jikinsa tunda Naziru yace
wuni zeyi a makaranta yau" ya fada yana tura keken sa zuwa bakin gado, Dada ta miqe da niyyar taimaka
masa ya dakatar da ita.
Dakansa ya hau gadon ya gyara kwanciyarsa dab daman matsalar baya ce ta saka yake qagara miqewa
amma tunda Yan biyun gidan su Ma'u suka kawo masa wani ganyaye na gargajiya daga Chana wancan
dawowar da sukayi ake dafa masa shayi dashi duk wani ciwon daya shafi qashi yaji sauqin sa cikin ikon
Allah, bama shi kadai ba duk tsofaffin da suka bawa a unguwar tasu kowa se dai sambarka dan yanzu
yana kama abu ya miqe akan qafafunsa tafiya cedai wannan ya fawwalawa Allah shi ya bashi qafafun
kuma yanzu ya karbe abunsa ransa ma wata rana karbar abinsa zeyi balle wata qafa da da ita da babu
duk yana iya gabatar da uzurirrikan rayuwarsa.

Kwanciya yayi ya juya baya jin har sannan Dada na dakin se ya juyo yana cewa

"Nafi akwai wani abun ne kuma naga kin zauna kinyi shiru?"

Seda ta hadiyi yawu kafin ta iya cewa

"Alhaji daman akan maganar yaron nan me neman auran Fainusa ne,dazu ya kirata yace wai ya fasa
shine nake so naji ko zaka tuntubi waliyyan nasa muji menene matsalar idan da yanda za'a gyarata"

"To ikon Allah ya fasa kuma yace? To Allah yasa hakan shi yafi Alkahiri" ya fada ba tareda wata damuwa
a fuskarsa ba.

"Alhaji tana can fa tana ta kuka har tana cewa mutuwa zatayi ko ta gudu ta bar gari dan Allah ka kirasu
muji ko da akwai abinda za'a iyayi" Dada ta sake fada kamar zatayi kukan itama.

Seya yunqura ya tashi zaune yana cewa

"Me auran shekara Goma sha bakwai ma an saketa babu wanda ya biyo ba'asi ko yace a mayar da ita se
ita da ko tsayayyar magana ba'ayi ba?

Idan ta mutu ai shikenan kinga ta huta guduwa daga gida kuma in shi ymta zaba to ta jira zuwa Juma'a
zan bada sanarwa a masallaci cewar na yanke alaqa da ita ko an ganta a wani guri kar wanda ya
alaqantata dani ba yata bace dan karma taje ta kwaso mun damuwa irin wadda kuka jefa Alhaji Murtala
a ciki" ya qarasa maganar yana danna wayar sa.
Da sauri Dada ta daga kai ta kalleshi, ya akayi yasan da maganar cikin Ummi bayan Addah ta tabbatar
mata babu wanda ya sani shiyasa suke neman hanyar da Asirinsu ze rufu kafin abu ya fashe kowa ya sani
in har kuwa Alhaji yasan zancen to babu shakka labari ya rigada ya gana gari sune suke shirmen su da
tunanin babu wanda ya sani kenan.

Muryar mutumin daya kira a waya ce ta katse mata tunani, tana ji suka gaisa kafin Alhajin ya ke ce masa

"Yanzu Me dakina take samuna da maganar cewa Unaru ya janye maganar aure ko? Shine nace bari na
kiraka na tabbatar daga bakinka tukunna"

"Wallahi Alhaji nima da safiyar yau dinnan ya same ni yake gaya mun na kuma yi masa fada na gaya
masa be isa ya mayar damu qananan mutane ba, yanzu haka ka ganni shiri nake zanje na samu uwarsa
na gaya mata halin da ake ciki shiyasa ma ban kiraka ba na bari se mun gama yanke sa rana tukunna
sedai kawai ka gammu" mutumin ya fada daga daya bagaren

"Aa Alhaji baza'ayi haka ba, babu wanda fa yayi masa dole akanta shi ya gani yace yana so dan haka
yanzu ma bamu san dalilinsa na cew aya janye ba. Ka barshi kawai Allah yasa hakan ne yafi Alkahiri
amma batun a tilasta yaro ma be taso ba shine ma'auri ba kuma auran fari ba bare ace za'a bashi
shawara rajin kansa yasaka shi tunanin qarawa tunda kuma ya janye a qyale shi kawai" Alhaji Amadu ya
fada kai bazakace yar sa ake cewa an fasa aure ba.

Haka sukayi sallama wancan yana ta faman bada haquri da alqawarin idan komai ya daidaita zasu zo,
yana kashe wayar ya kalli Dada data saki baki tana kallonsa yace

"To kinji dai abinda ya fada. Idan aure take so anjima zan bada sanarwa a masallaci duk wanda yake
sonta yazo zan bashi sadaka har sadakin ma ni zan biya masa idan kuma taqi ai kinji abinda na fada a
farko seta zabi abinda ya mata a ciki.

Ni yanzu kin cinye mun ma lokacin baccina bari na tashi nayi ta hailala da istigfari maganin masifa kafin a
kira sallar" ya qarasa yana janyo carbinsa.
Haka Dada ta kwashi qaqafunta ta fice, a bakin qofa taci karo da Fainusa da ashe tana labe tana jin
komai bata kulata ba ta wuce dakinta can qurya ta shiga kiran Addah a waya.

GIDAN ADDAH

Addah na tsaye akan Ummi dake kwarara amai a bandaki tana zazzage mata ruwan masifa da bala'i kiran
wayar Dada ya shiga. Bata daga ba ta ci gaba da sababinta, magani ne ta karbowa Ummin na zubar da
ciki tana shi shine ta amayoshi tas kuma wannan shine karo na uku data kashe kudi aka karbo mata
magani amma ciki na nan daram ko girgiza beyi ba.

Kiran wayarta da ake tayi babu qaqqautawa ya saka ta fito cikin bala'i ta daga tana cewa

"Wai Nafi wannan wace kalar lukutar masifa ce da zaki ringa kirana kamar naci miki bashi ki barni naji da
abu daya mana haba"

"Addah dole na kiraki ai, kika cemun babu wanda yasan da zancen cikin Ummi amma ya akayi har Alhaji
ya samu labari anya kuwa magana bata fasu ba Addah?"

"To idan ma magana ta fasu Nafi se akayi wace kutumar uba eye nace se akayi me? Da zaki ce mun
Amadu yasan zancen waya sani ko a munafuncinki kika gaya masa tunda kema ai ba sanin zuciyarki nayi
ba waya sani ko kina cikin masu farin ciki da abinda ya same ni in ba haka ba shi mijin naki yana
kanannade a kujera ta ina ze jiyo wani labari?

Ni karki sake kirana indai ba mafita kika samo mun ba, kuma abin kunya ai ba kanta farau ba kumaba ita
zata rufe ba wasu da yawa Allah kadai yasan shegu nawa suka haifa aikin banza kawai" ta kashe wayarta
kafin ma Dadan ta sake magana.

Kan Ummi data fito daga bandakin da kyar ta koma tana cewa

"Dan uwar ubanki ba kwanciya zakiyi ba tashi zakiyi mu tafi gidan Balaraba yanzu ai Qanwarta sarai ta
taba yin ciki sukaje aka cire muje ta raka ni gurin dan dole se abin nan ya fita ko bangon duniya zancen
yaje qarewarta se an cire idan yaso senaga shedar da za'a bayar idanan tashi gulmar".
Kuka Ummi ta saka tana cewa ki qyale ni Addah in dai ba so kike na mutu ba dan Allah ki rabu dani.
Qaddarata ce tazo a haka kuma kece sila dan haka ki barni na haife abinda yake cikina ban sani ba ko
shine silar kaffarata a gurin ubangiji"

"Wallahi sedai ki mutu dan ubanki dama amfanin me zakiyi mun idan kin rayu bayan abin kunyar da kika
janyo mana, ki tashi tun wuri mu tafi kafin nazo na haye kanki na murqusheki daga ke har shegen dan
cikin naki ku mutu kowa ya huta".

Haka Ummi tana ji tana gani Addah ta tasata a gaba tana kuka suka tafi. Matan gidan da sukayi cirko
cirko suna kallonsu dan duk abinda ta ke fada sunji saboda ba a hankali take magana ba.

Daman sun san da qishin qishin din maganar yanzu gashi sun tabbatar suna fita kuwa Binta da tafi kowa
tsugudidi ta shige daki ta dauki wayarta ta kira Alhaji Murtala.

Yana zaune a kasuwa a daidai lokacin wani Amininsa Alhaji Yero ya same shi da maganar cikin Ummi
daya ji a bakin Matansa.

Hankalin Alhaji Murtala yayi qololuwar tashi da jij maganar wata irin tsanar Addah yaji tana saukar masa
shidai tunda ya auri Fatu bazece ga wani abun Alkahiri daya same shi ta dalilin ta ba a kullum cikin jefa
shi a masifu kala kala take.

Kiran wayar Binta na shiga ya daga, ba maganar gaisuwa ta shiga rattaba masa cewa

"Alhaji ka kira Addah duk inda take ta dauki Ummi tana kuka da komai sun tafi tackaita a zubar da ciki
kar yarinyar nan ta mutu mu shiga uku ka kirata ka dakatar da ita".

Wata zufa yaji tana sakko masa, kiran wayar Addah ya shigayi tana ringing amma bata dagawa seda ya
kirata sau goma a na sha daya ta kashe wayar. Babbar rigarsa ya cire saboda yanda yaji tana neman
shaqeshi ya ringa safa da marwa a cikin shagonsa yana ayya na irin wulaqancin da zeyiwa Fattu a
wannan karon, tabbas yakai bango kuma dole ya dauki matakin da ze shigar da ita hankalinta.
Wayar Amirah ya shiga kira ringing biyu ta daga tana gaishe shi, be amsa mata ba cikin kakkausar murya
yace mata

"Ki kira uwarku ki gaya mata wallahi idan wani abu ya samu Ummi a sanadiyyar zubar da cikin data tafi
kaita se na daureta dauri har qarshen rayuwarta sannan ki gaya mata daga inda ta tafi karta dawo mun
gidana na saketa saki biyu" yana gama fada matan ya kashe wayar sa.

Sosai zuciyarsa take tafarfasa, Addu'arsa Allah yasa kar wani abu ya samu Ummin dan wallahi bega
wanda ze hana shi shari'a da Fattu ba.

Hajia Addah kuwa Napep suka haye se gidan Hajia Balaraba suna tafe a hanya tana surfawa Ummi zagi
har suka isa.

Ta tarar da Hajia Balaraba tana wanka dan haka suka zauna a palour suna jiranta ba adauki lokaci ba
kuwa se gata ta fito daga dakinta a kallo daya Addah ta hango irin yanda tayi sanyi laqwas kamar ba
Balaraban data sani ba mace me izza da taqama.

"Aa Fattu kece yau a gidan namu yaushe rabo" Balaraba ta fada tana zama akan kujera, se Addah ta tabe
baki kafin tace

"Zaki fadi haka mana tunda kin samu yanda kike so kij watsar dani bayan da kika kaini gidan dan damfara
ya cinye mun kudi ai dole kice yaushe rabo, ni ba wannan ta kawo ni ba ma.

Likitan da ya cirewa Sarai qanwar ki ciki zaki hadani dashi wannan tsinanniyar yarinyar taje ta kwaso
mun abun kunya dama yana qare da maqiya ballantana yanzu ta janyo mun abun magana a ringa nunani
a gari"

"Kai kai Fattu ki bari dan Allah, irin wadannan mugayen kalaman da muke jifan yaran mu dasu su suke
tasiri akan su suke lalatasu.

Ummi a garin yaya me ya kaiki irin wannan abu ke da nake yiwa kallon nutsatstsiya ko yar uwarki da take
da rawar kai ta gama yammatancinta lafiya Me ya sa Ummi" Hajia Balaraba ta fada cikin Jimami.
Ummi ta qarawa kukan ta volume tana cewa "Wallai Hajia sharrin shaidan ne kuma da laifi Addah, seda
na gaya mata ga wanda nake so tace ko zan mutu bazan aure shi ba"

Duka Addah ta kai mata tana cewa "Na fada din yanzu ma na maimaita ko zaki mutu bazaki aure shi ba
shegiya da bata san ciwon kanta ba.

Ke kuma ni ba mayar da zance ne ya kawo ni ba ki bani lambar waya ko Adireshi na tafi dan a yau nake
so ayita ta qare kafin maganar taje kunnen ubanta".

"Cikin wata nawa ne?" Balaraba ta fada tana janye tagumin da tayi, se Addah tayi caraf ta ce

"Ko wata tara ne se an cire shi babu ruwanki kawai nidai ki hadani da me aiki badai maganar kudi bace
zan bayar ba matsala"

"Dan Allah Hajia karki barta ta kaini cikin fa wata hudu ne wallahi mutuwa zanyi Nasan gara ta barni ko a
gurin haihuwarsa na mutu nasan nayi shahada Allah yasa haka ya zamar mun kaffara" Ummi ta fada tana
sake rushewa da kuka, se Addah tayi kanta da duka Hajia Balaraba ta shiga tsakani tana bata haquri

"Fattu Yarinyar nan tafiki gaskiya, ko sarai da kikaga a lokacin munje an cire wata biyu ba'a ko busa masa
raiba magani kawai ya bata tasha cikin ya fita amma wannan wata hudu fa, kisan rai zakiyi qarshe idan
ba'a dace ba itama a rasata gaskiya kiyi haquri ki dauki qaddarar data zo miki a haka tunda ke kika
jawowa kanki. Yarinya ta kawo mijin aure kinqi ai dole ki karbi duk sakamakoj daya biyo baya kuwa".

"Tashi mu tafi dan Uwarki ai ba ita kadai tasan likitan zubar da ciki ba ke ni da kaina nan ma sena zubar
da shege idan na naushe ki yanzu" Addah ta fada tana finciko Ummin, se Balaraba tayi saurin tareta da
cewa

"Ba a nan ba wallahi ku fita can idan ma kin kasheta a daure ki ke kadai baza'a ce a gidana a kayi ba"
haka ta taso qeyar Addah har Get Addah na zazzaga rashin mutunchi tuni yan unguwa suka fara taruwa
ana kallonta haka dai ta angiza qeyar Ummi har tati tana kuka kafin suka samu Napep kai tsaye tace a
kaita wani Sha ka tafin Private Asibiti data taba zuwa duba wata qawarta a can qasan gurin GSU, a yanda
taga kalar likitan ta tabbatar ze iyayin komai in dai ze samu kudi.

Ita se yanzu ma ta tuno dashi da meze kaita gurin wata balaraba harta bata lokacin ta a banza.

AMIRAH

WATA KISHIYAR

(ALKAHIRI CE KO SHARRI)

Na Maryamah Farouk

(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)

Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 50

AMIRAH
Wuntsulawa tayi daga kan gadonta zuwa qasa tayi zaman yan bori. Number wayar Addah ta shiga nema
cikin tashin hankali ta ringa kira amma a kashe seta mayar da akalar kiran zuwa Ummi itama dai amsa
daya aka bata wato a kashen.

Bata san sanda kuka ya kwace mata ba, ita ba sakin da Babansu yayiwa Addan ne ya dameta ba illah
zancen zubar da ciki dataji. Bazata taba manta qawarta wata Harira Sani ba lokacin suna Sakandire tayi
ciki a gurin zubarwa ta mutu tun daga sannan take bala’in tsoron abinda ze hado ace za’a zubar da ciki.
Yanzu idan Ummi ta mutu yaya zatayi bayan duk duniya bata da wata shaqiqiyar yar uwa sama da ita.

Ganin ta kasa samun wayoyinau yasa ta yanke shawarar kiran Sa’adah maqociyarsu, tasan bazata rasa
sanin wani abu da yake faruwa ba nan da nan ta danna lambar tayi sa’a tana shiga kuka ta daga.

“Anty Sa’adah ki taimaka mana ki kaiwa Addah waya nayi ta kiran layin ta dana Ummi baya shiga”
Amirah ta fada bayan da tayi qoqari sosai gurin danne kukan ta.

Sa’adah dake kwance akan gadon ta tayi daidai dan tashinta daga bacci kenan ma ita ta yatsina fuska
tareda hararar wayar kafin tace

“Ayyah ai kuwa anyi rashin sa’a kin ganni ina gidan mu a can na kwana jiya.

Idan ba sauri kike ba anjima kadan zan tafi idan yaso sena kiraki kuyi maganar”

“Shikenan toh idan ban same ta ba na sake kiranki” Amirah ta fada tana kashe wayar.

Daga can bangaren kuwa Sa’adah tsaki taja kafin a fili tace “gayyar tsiya kawai, ni blocking number ki ma
zanyi bazaki sake samuna ba tunda ku baku san mutunchi ba haka kawai da na saki baki sedai inji ana in
matsa za’a shigo da Amarya ko toh Allah ya toni asirin ku gashi nan kuma yayi mun sakayya ya hada ku
da dan shege” ta sake tabe baki tana gyara kwanciya.

(Abinda ya faru mijinta ne ya ringa soyayya da Ummi a boye ba tareda ta sani ba se daga baya shine ta
janye alaqa dasu gaba daya)
Amirah kuwa rasa wa zata kira tayi, fuskarta shabe shabe da hawaye, daga ita se yar bingikar rigar baccin
ta net data kwana da ita wanda hatta da pant din jikinta ana gani ta fito daga dakinta da tun jiya data
shige bata sake fitowa ba kai tsaye ta wuce su Aliyu dake zaune a palour suna karyawa ta nufi kan Dining
inda Bashir yake.

Wata muguwar tsawa ya daka mata daidai sanda ta isa kansa ta tsaya. Kallonta yakeyi da idanunsa da
suka chanza kala nan take saboda bacin rai dakyar ya bude baki yace mata

“Ke wace irin dabba mara tunani ce zaki fito a haka ki wuce ta gaban Yara samari? Saboda baki da
tarbiyya ko baki kuma san mutunchin kanki ba bace mun daga nan kafin na kifar dake”.

Duk yanda ta tsorata da irin tsawa da hargagin da yake mata bata ko motsa taku daya daga inda take ba,
cikin kuka tace masa

“To nima ai dole ce ta fito dani, Baba ya kirani yace ya saki Addah kuma ta tafi ta kai Ummi a cire mata
ciki tsoro nake ji karta mutu ban san ina zan saka kaina”

“Zaki matsamun daga nan ko se nayi ball dake mahaukaciyar banza kawai, ta mutu mana ina ruwan wani
ko ni na aike? Wallahi kika bari na miqe sena karya miki qafa idan yaso naga da yanda zaki sake fitowa
nan gurin” ya fada yana qoqarin miqewa amma ciwon kan daya samu dakyar ya barshi ya sake dawo
masa yanzu sanadiyyar bacin ran da zuciyar sa ta shiga.

Waiwayawa yayi inda su Aliyu suke zaune yaga babu kowa seya sauke ajiyar zuciya a hankali ya kalli
Amirah data juya dakinta tana rusa ihu hannaye biyu akai. Ture abincin gabansa yayi wanda shima Aliyu
ne ya hada musu dan ita gwanar se yanzu ma yaga idonta tun jiya da yamma.

Gaba daya kansa ya masa zafi, ya fahimce wannan yarinyar kwata kwata batasan me takeyi ba. Idan ma
yace ze cigaba da zama a gidan qara masa ciwo zatayi se kawai ya dauki muqullin motarsa ya fice daga
gidan.
Yana fitowa yayi mugun gani, Asma’u ce tsaye da wannan mutumin daya tsana sama da kowa a duniya
yanzu suna magana se dariya sukeyi kamar wasu masoya.

A fusace ya nufi inda suke sedai kuma meya tuna yaci burki ya koma da baya zuciyarsa na masa zafi
kamar wanda ake watsawa tafasashshen ruwa.

Motar sa ya bude ya shiga ya kifa kansa akan sitiyarin yana sauke numfashi a jere a jere, ya tabbatar idan
har yaci gaba da ganin Ma’u da wani namiji zuciyarsa tana iya bugawa ya mutu lokacin sa beyi ba.

A zatonsa tunda har ya bata haquri yace su komawa auransu zata saurareshi ko dan darajar so da kuma
yaran da suke tsakanin su amma se yake gani kamar ma ta goge shine ma daga babin rayuwarta.

Al’amuranta kawai take yi kamar babu wani abu me suna so daya taba shiga tsakaninsa da ita, to wai
yanzu wa ze kaiwa kukansa ya samr masa mafita ne??

Bala ne ya fado masa arai, se ya janyo wayarsa ya kira lambar Balan a ransa yana lissafa tsahon lokaci
rabonda suyi waya tun ranar daya gaya masa ya saki Ma’u.

Seda ya kirashi sau biyu amma ta qaraci qararta ba’a daga ba be haqura ba ya sake kira dan dai yau
Sunday yasan Balan yana gida ko baya da haka yana da buqatar wanda ze tattauna dashi ko zeji sanyi a
ransa.

Sake kira yayi yana ringin daya aka kashe, ya kalli wayar dan ya sake tabbatar da rejecting kiran akayi
seya sake dannanwa tana shiga kuwa aka sake kashewa abin yayi bala’in bashi mamaki dan tunda yake
da Bala be taba qin daga masa waya ba kai ko lokacin aiki ne balle har ya kira ya katse se yau amma dai
ya kyautata masa zato qila yana wani uzuri ne a lokacin.

Motar ya kunna kawai ya hau titi yayi ta tafiya idan ya gaji da tuqin ya samu guri ya tsaya gaba daya
zuciyarsa ta hargitse da tunanin Ma’u, ya kasa hasasowa kansa rayuwa babu ita.
Sati biyun nan kadai yaji jiki dauriya yakeyi dan karya nuna gazawarsa amma yaga alamar a wannan
karon Ma’u ta daura aniyar kaishi qasa so takeyi se taga raunin sa.

ASMA’U

Da safe Yusuf ya kirani akan ze zo anjima ya dauki Ma’u, dakaina na tashi na hada mata kayanta da yan
abubuwan da ba’a rasa ba a nake dasu duk na hada mata kafin na koma daki na kwanta amma sena kasa
komawa bacci.

Tunanin makomata na shigayi a yanzu. Har yanzu na kasa yarda da cewa dagaske Bashir ya cire ni daga
rayuwarsa ba kuma ya buqatar sake zaman aure dani tunda tun waccen ranar be sake tarata akan
makomar auran mu ba kai ni bamu sake haduwa ba ma se jiya a gurin taron su Amnah.

Wasu hawaye ne suka zubomun na saka hannu na share, tabbas dole na yarda da gaskiya komai dacinta
cewar Bashir baya sona, alfarma yayi mun ya aureni ya zauna dani saboda tarin soyayyar dana nuna
masa.

Haka nan se kuma banji haushin sa ba, so ba qarya bane dan ni zan bada shaidar hakan kuma ba’a
tilastawa zuciya taso abu na yarda duk hasasheb da nakeyi akansa a baya kawai dan ni ina cikin mayen
sonsa ne shiyasa ban taba ganin laifinsa ba amma yanzu na gane Bashir baya sona idan ma ya soni to be
kai ko kwatan irin son da nayi masa ba, qaddara da rabon haihuwa ta tsawaita zaman mu yanzu kuma da
Allah ya kawo qarshen gashi ya raba mu.

Dole na haqura da Bashir na koyawa zuciyata yanda zata rayu ba tareda shi ba duk da nasan ba abu bane
me sauqi dan da soyayyarsa na raini zuciyata idan har nace zan cire shi gaba daya daga raina na tabbatar
daidai yake da zare duk wata walwala da jin dadi da sukayi saura a rayuwata ko da yake meya tage mun
nema?

Tunda Bashir ya sake ni nayi ban kwana da farin ciki, duk wata walwala da nake nunawa a iyakan fuskata
take amma qasan zuciyata Allah kadai yasan irin wutar da take ruruwa a ciki amma dole na na koyi
rayuwa ba tare da shi ba.
Dole na daraja kaina na haqura dashi tunda har ya fito ya nuna mun alfarma yayi mun daya zauna dani
tsahon lokaci yanzu daya samu zabin ransa ya gwammace rabuwa da ni uwar yayansa saboda farin
cikinta.

A yanzu babu lissafin aure a gabana dan na rufe, bana tunanin akwai sauran gurin da zan iya saka
soyayyar wani kuma bayan Bashir a cikin zuciyata.

Zan riqe kaina na tsaya da kafata na nemi na kaina na zamarwa mata irina da muka dauki soyayya da zafi
madubi na kuma haska musu cewar rabuwa da Mijin da kike so ba shine qarshen rayuwa ba, sannan duk
son da kake yi wa mutum idan har ya nuna baya buqatarka a rayuwarsa ka barshi koda kuwa hakan yana
nufin rasa komai naka in dai zaka tsira da mutunchinka.

Ina cikin wannan tunanin bansan lokaci yaja ba seda naji wayata tana qara ina dubawa naga Yusuf ne
ashe har qarfe goma da rabi na safe tayi.

Bandaki na shiga na wanko fuskata kafin na dora dogon Hijabi har qasa akan riga da wandon baccin da
suke jiki na, ina shirin Fita Farida ta shigo tana cemun ga Dadyn Little yazo muka fito tare har qofar gida
inda yake tsaye jikin wata shegiyar mota ya saka qananan kaya a raina na ringa mamakin yanda sam
Yusuf baya tsufa, duk sanda na ganshi gani nakeyi kamar qara zama yaro yakeyi.

“A kwana a hantse se kyakykyawa, Allah yasa dai ban tashe ki daga bacci ba” ya fada fuskarsa dauke da
murmushi yana kama hannun Farida, nima murmushin na mayar masa ina cewa

“Aa, ai tun sanda mukayi magana dazu ban ma koma ba ina zaune, ban ma zata da wuri zaka zo ba ai”.

“Ta matsa na mayar mata da yarta inaga gobe zasu wuce” ya fada yana bina da wani kallo da gaba daya
ya saka ni diriri cewa. Sakin hannun Farida yayi yace mata taje ta hadawa Ma’u kaya tana wucewa ya
matso inda nake tsaye yana cewa

“Kinga yanda kike wani kyalli kuwa daman ashe kin fi kyau babu kwalliya ban taba sani ba”
Saurin ja da baya nayi nace “Yusuff..” be bari nayi magana ba yayi saurin tareni da cewa

“Yi haquri, ni kaina idan ina tare dake kasa riqe bakina nakeyi amma dagaske kin yi kyau Ma’u, ina so
naga Mace da Hijab ga wannan qamshin naki ya ilahi Allah kadai yasan yanayin da yake jefani”

Juyawa nayi, seda na kai bakij qofa nace masa

“Bari ta fito, na gode kwarai Allah ya qara zumunchi”

Se kawai ya tuntsure da dariya harda sunkuyawa yana kallona yace

“Matsoraciya, naga ma rowar gidan naki kike yi mun ko bayan nasan miskilin mijinki baya ciki. Wai ma ya
akayi kika bari ya ajiye ku maqotaka da kishiyarki? Kinga idan nine ko qasa bazan hada muku ba bare
unguwa daya saboda bazan yaba bari wani abu ya sosa miki rai ba indai ina da ikon hanawa”.

Cikin gida nayi shigewata ina jin yanda zuciyata take bugawa da qarfi kamar wadda tayi tsere, na rasa
dalilin da yasa indai Yusuf yayi mun magana nake shiga irin wannan yanayin, yanzu da ace ina da aure
muka hadu dashi haka zamu ringa dibar wannan dakon zunubin??

Seda nasha ruwa me sanyi dukda banci komai ba kafin na wuce dakin Amnah na tarar suna drama da
Ma’u ta riqe akwatinta qam baza’a fita dashi ba.

Duk yanda naso na lallabata na nuna mata Dadynta ne yazo amma fafur tace itafa bazata tafi ba taga
gurin zama, haka ta ringa birgima tana buge buge a qasa mamaki yasa kawai na tsaya ina kallonta ni ba
abin na mammaketa ba ubanta na waje dan da ace yan biyu ke yi mun tabarar da tuni naci ubansu dan
ni ba’a haka dani wannan yarinyar kuwa naga alamar an gama sangartata se a hankali kawai.

Dole na fita na gaya masa, badan naso ba ya shigo gidan, yayi lallashin duniya taqi ji qarshe a wuya ya
dauketa tana kwala ihu kamar wadda aka sace ya sakata a mota yaja suka tafi muna daga mata hannu,
haka muka wuni yara sukuku abu kadan ace Little kaza ni kaina nayi kewarta dan tana da shiga rai barta
da yar banzar barna kamar beran turawa.
GOMBE

ADDAH

Tiryan tiryan me Napep ya kaita har qofar Asibitin data kwatanta masa saboda saurin da take ko musu
batayi ba ta dakko kudin daya ambata mata ta bashi ta shiga jan Ummi da dauk ta galabaita suka shiga
ciki.

Kai tsaye gurij Nurse din dake bada kati taje ta ce mata likita suka zo gani aka yanka mata kati dari biyar
ta zaro ta bayar, babu mutane da yawa a gurin, mace biyu suka tarar su na uku ganin yanda Ummi take
kuka ma Nurse din ta dauka ko ciwo ne dan haka ta roqar musu alfarma Gurin wadan da suka tarar ta
ciki na fitowa suka shiga.

Likitan na zaune kai idan ka ganshi me hankali dai baze yarda ya dubashi ba saboda yanda yake a
hargitse sam be mayi kala da likitoci ba, ba bata lokaci Addah ta zayya na masa abinda yake tafe dasu da
kuma buqatarta.

Shiru likita yayi yana kallonta, Addah da taga yayi shiru ta har ziqo tana cewa

“Ko bazaka iya bane ka fada ka zuba mana ido kamar maye yaga nama, ni karka bata mun lokaci idan
baka yi mu qara gaba ai likitocin kuna da yawa”.

Seda yaja numfashi kafin yace “cikin wata nawane Hajiya?”

“Wai wata hudu tace, kana ji ko karka damu da wani watannin sa ka markade mun dan banza ko nawa
ne zan biyaka”

“Yawwa daman maganar ta kudi ce Hajiya tunda kinga cikin ya girma dole cireshi zeyi wahala dan haka
se kun biya kudi da yawa amma tunda kince babu matsala to za’ayi aiki zaki biya dubu dari biyu da
hamsin ne kudin aiki se kuma dubu hamsin na magunguna da jini da zamu siya saboda tsaro gaba daya
kinga dari uku kenan” Likita ya fada yana wani murmushi da gani banza ta fadi
Dafe qirji Addah tayi ta zaro idanu waje tace “Likita dari uku fa kace cire cikin? Ina laifin in baka dubu
hamsin shima saboda naji kace da wahala amma da ni dubu talatin ce kaga na ruqo ta” ta qarasa tana
bude yar jakar ta ta zaro kudi, seda likita ya ha tareta kafin yace

“Bata mun lokaci daman kawai zakiyi Hajiya ba aiki kuka zo ayi muku ba. Kinsan hatsarin da yake cikin
abinda kika zo yi kuwa idan fa aka samu matsala aka kamani daurin shekaru zansha a banza ki gudu
abinki kinga ku tashi tunda naga wasa nema ya kawo ku na samu na duba sauran da suka zo da gaske”

Ganin da Addah tayi ga samu ga rashi yasa ta marairaice tana cewa

“Dan nan ba wasa bake ba kudin ne daka fada sunyi yawa amma yanzu shikenan, kayi mana ragi naji
abinda zan bayar In sha Allahu baze gagara ba”

“Ki bada dubu dari biyu shine qarshen magana idan beyi miki ba ga hanya nan” ya fada yana hade rai,
Addah tayi shiru, a jakarta gaba daya dubu hamsin ne ribar kasuwarsu da Alhaji ya bata jiya, tama tabasu
basufi Arba’in ba yanzu ina zata kwakwulo dubu dari da sittin ta hada dan bazata taba bari wannan
damar ta wuce ta ba.

Ajiyar zuciya tayi ta kalli likita tace

“Shikenan na yarda, yanzu ga dubu Arba’in zan baka idan yaso ta zauna zanje gida na karbo ragowar
sena kawo maka”

“Aa ai ba anan za’ayi aikin ba Hajiya, inada guri daban da nakeyi kuma se da daddare zaku zo zan baki
lambar waya da Adireshin gurin se ku same ni acan” Likita ya fada nan da nan Ummi ta qara wa kukan da
takeyi qasa qasa qara, mayar da hankalin sa kanta yayi yana cewa

“Ki rarrasheta Hajiya ta dena kukan nan dan idan jininta ya hau za’a iya samun matsala a gurin aikin.
Yanzu zan rubuta muku magani ku siya a waje daya zata shanye shi yanzu dayan kuma idan kunje gida
kamar saura awa hudu ku taho yin aikin ta saka kwaya daya a qasan harshen ta zasu nuna muku ko
wanne da yanda zaku yi dashi din”.
Godiya sosai Addah ta ringa zuba masa kamar wanda ya bata kyauta, ta kawo dubu talatin da biyar ta
bashi biyar din zata siyi maganin sannan suyi kudin mota.

Tana fita kuwa a dan gurin siyar da maganin Asibitin nasa suka tsaya ta siya a take ta saka Ummi seda
tasha na shan suka kama hanyar gida tana ta lissafin inda zata samo kudi.

Amirah ce ta fado mata a rai, daman shegiyar yarinyar tunda ta tafi bata tuna da ita ba balle ko biyar
bata aiko mata da ita nan da nan ta kunna wayarta ta shiga kiran Amiran.

AMIRAH

Tana zaune a daki tana kuka, san baqaqen maganganun da Bashir ya gaya mata basu dameta ba ita
yanzu ta yanda zata samu Addah ta hanata abinda tayi niyya take, tana tsakanda aikin kukan kiran ya
shiga.

Da sauri ta faga wayar tana cewa

“Addah kina ina ne tun safe nake neman wayar ku bana samu ke da Ummi?”

“To uwata, an baki ajiyata ne da kike tambayar ina naje ko yaya ina ruwanki? Ni yanzu kirani nayi ki tura
mun kudi zan samu POS na tsaya yanzu na basu lambarki ki sako kudin na cire”

“Addah me zakiyi da kudi? Ina Ummi? Kun koma gida ne Baba ya kirani dazu yana cewa...”

“Wai dan uwar ubanki Amirah zakiyi abinda nace ne ko tambayoyi zaki tsaya yimun kamar alqaliya?

Baba ya kira yace miki ubanki ina ruwanada wani Baba babo mata ni wutar gaba na ta isheni yanzu, na
samu wanda ze cirewa yar uwarki abin kunyar data kwaso mana kudin nake hadawa yanzu anjima zamu
koma ayi aiki” Addah ta katse Amirah.

Se Amirah ta zaro ido kamar tana gabanta tace


“Addah mutuwa akeyi wallahi kin manta Harira lokacin tayita zubar da jini har seda ta mutu dan Allah
Addah karki sa na rasa Ummi kinga ita kadai ce yar uwata.

Ki qyaleta ta haihu wallahi ko ni zan dauki abinda zata haifa na riqe nasan Yaya baze hana ba”

“Idan kika sake cewa wani abu se kinci ubanki Amirah, bazaku kasheni ba yanzun nan zan turo miki da
akawun na fasa zuwa POS din ma zan shiga gidan Talatu kawai mu zauna a can zuwa lokacin da zamu
koma idan yaso se na turo miki da ko na Dan ta ne ki saka kudin nasan in muka koma gida wannan Uban
naku ba lallai ya sake barina na fita ba” tana gama fadar haka ta kashe wayarta tana aunawa Amirah
Ashar shidai me Napep se leqenta yake ta mudubi Allah Allah yake ya sauke su ya samu wanda ze bawa
labari.

Amirah kuwa tana jin Addah ta kashe waya ta shiga neman layin Babansu, yana dagawa kai tsaye ta gaya
masa Addah na gidan Anty Talatu ta kashe wayar tana Addu’ar Allah yasa Babansu yaje kafin su Addah
su koma inda tace.

Addah kuwa a gidan Anty Talatu suka yada zango, yar uwarta ce yayan mata suke yar bala’i ce ta gaske
itama dan har tafi Addah rigima.

A tsakar gida suka tarar da ita tana wa wata jikarta masifa, ko sallamar Addah bata amsa ba seda taji
yarinyar na gaida Addan sannan ta waiwaya inda suke tana huci.

“Aa Fattu kune a tafe? Ku shigo mana ita kuma wannan me aka mata ta dora hannu aka tana kuka? Nifa
bana son fitina shiyasa kikaga bana qaunar baqar yar nan taki saboda mugun halinta gara Amirah tafi
mun ita sau dubu”

Cikin dakinta suka shiga tana gaba suna binta a baya. Seda ta kawo musu ruwa me sanyi da Fura, ta futa
ta bawa jikar tata kudi tace taje qaro taliya leda daya dan gama miyar ta kenan sun maida ruwan taliyar
yarinyar ta juye tayi wanka dalilin masifar tata kenan.
“Daga ina haka Fattu da uwar ranar nan fatse fatse keda bakya gajiya da yawo” Talatu ta fada bayan data
zauna.

Se Addah ta janye tagumin data buga tace “ki bari kawai Talatu wannan yarinyar ce ta kwaso mun tashin
hankali” nan ta zayya na mata abinda yake faruwa.

Anty Takatu ta hau salallami tana tafa hannu tace “yanzu Ummin? Ke da nakeyiwa kallon ta kirki kai
yaran yanzu se abarku abinda se dai muji daga nesa shine kika kawo mana a cikin zuri’ar mu Allah ya
wadaranki dai Ummi”

Nan suka hadu suna ta nanata zancen, seda ta dafa musu taliyar suka ci kafin Anty Talatu ta kalli Addah
tace

“Ni Fattu maganar zubar da cikin nan ki barta kina gani dai ance mutuwa akeyi wallahi, yanzu abinda duk
ya kamata ayi shine tunda tasan uban ciki a nemo shi a taru a rufawa juna asiri ko yaya ne ayi musu aure
shikenan”

Hayayyaqo mata Addah tayi tana cewa

“Ban gane abar ciki ba in barta ta haihu kenan a ringa nunani a gari ace nayi jika shege to bazata sabu ba
wallahi, kuma zancen aure da kije badai da wannan matsiyacin ba sedai idan mutuwa nayi”

“Ai kuwa idan baki mutu na zakiyi ta goya shegu tunda ke zuciyarki irin ta kafiran farko ce. Yanzu tashi
zakiyi mu zagaya nan baya gidan me sittin tara a kwantar da cikin daga nan a nemo yaro idan sukayi aure
wata kadan se a tayar dashi dukma uban da za’a fada dai daga baya ne tunda sun rigada sun yi aure”.

Shiru Addah tayi qasan zuciyarta ta yarda da shawarar Anty Talatu, miqewa sukayi Anty Talatu tace
Ummi ta shiga ciki ta hau gado ta huta kafin su dawo suna zuwa qofar gida sukaci karo da yan sanda a
tsatstsaye.
“Lallai Asabe, ba nace ta bani sati daya zan biyata kudin ta ba shine zata hadani da hukuma ai kuwa
wallahi tayi ta kudinta muje duk uwar da za’ayi ayi amma bazan biyata ba kuwa” Anty Talatu ta fada dan
a zatonta wata mata da rigimar Adashi ta hada su tace zata dakko mata yan sanda ce ta turo su.

Fitowar a Alhaji Murtala daga mota ce ta dakar dasu Addah ta shiga zare ido tana komawa bayan Anty
Talatu.

“Gata nan yallabai” ya fada yana nuna musu Addah nan da nan yan sanda mata biyu sukayi kanta se ta
sake riqe Talatu tana cewa

“Me kuma nayi Alhaji? Wane munafunchin aka qullamun da zaka dakko mun yan sanda saboda ka
tozarta ni”

“Ai kin rigada kij gama tozarta kanki Fattu, ina Yata take? Se na tabbatar da lafiyar ta idan wani abu ya
sameta daga nan kotu zamu wuce dan se nayi shari’a dake Fattu” ya fada cikin tsananin dacin rai.

Anty Talatu ce ta tare yan sandan da suke neman jan Addah tana cewa

“Ummi tana ciki Alhaji lafiyarta qalau, bari na kirawo maka ita ka ganta wannan kuma ai abu ne na cikin
gida be kamata ace ka saka hukuma a ciki ba”

Daga bakin soron gidan ta tinga kwalawa Ummin kira, Ummi da har bacci yadan fara fizgarta ta fito jin
muryar Talatun tana fita tayi arba da Baban su seta fada jikinsa ta fashe da kuka tana cewa

“Dan Allah Baba kar ka bari ta kaini a cire mun mutuwa ake yi ni kuma bana son na mutu”.

Riqeta yayi sosai a jikinsa zuciyarsa na tafa sa, tausayinta ya cika shi ya tabbatar duk abinda ya sameta
qaddara ce da kuma halin Fattu ya janyo.
Cikin bacin rai ya kallo yan sandan yace “ku rabu da ita tunda naga Yata kuje kawai zan zo station din
anjima na gode”

Sukayi masa sallama suna harar Addah sukaja mota dan sun so sun samu damar moreta.

A motar sa ya saka Ummi ya zagaya ze shiga Addah ta biyo shi ba ko dar tana cewa

“Bari nazo mu tafi Alhaji, Talatu se munyi waya ko zan kiraki idan naje gida”.

“Idan kinje wane gidan? Da alama baki ji saqona ba kenan” Alhaji Murtala ya fada yana dakatawa daga
shiga motar da zeyi, Addah ko qoqarin bude mota take tana cewa

“Saqon me kuma wa ka bawa ya bani? Ni ba’a ce mun komai ba”.

“To bari na gaya miki yanzu da kaina, na yanke igiyoyin aurena biyu da suke kanki, ma’ana na sake ki
Fattu saki biyu”

“Alhaji ka sake ni fa kace kuma har saki biyu? Uku fa kenan ko ka manta akwai daya daman?” Addah ta
fada cikin ihu tana ja da baya hannunta aka, seda ya shiga motar ya danna lock kafin yace mata

“Ina sane Fattu na gaji da halinki na dade ina Addu’ar Allah ya yakice mun ke se yanzu ya karbi Addu’ata,
zan ma aiko miki dashi a rubu ce saboda shaida” yana gama fada yaja motar sa Addah kuwa kamar
sabon kamu ta bishi da gudu tana ihun ta shiga uku ta lalace.
WATA KISHIYAR

(ALKAHIRI CE KO SHARRI)

Na Maryamah Farouk

(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)

Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 51

Seda motar Alhaji Murtala ta bacewa Addah kafin ta tsaya tana haki ta dora hannaye biyu akai tana rusa
ihun ta shiga uku ta lalace

“Ni Murtala ze saka? Shekara Hamsin da aure ace zanyi zawarci gidan ubanwa yake so naje yanzu wallahi
be isa ba, ban saku ba dole na koma” Addah ta ringa sambatu tana rusa kuka.

Anty Talatu ce ta ruqota suka shige gida tana cewa

“Se kace kanki aka fara saki ji yanda kika bishi da gudu kamar wata karya. To Fattu ai ya miki da kyau ma
daya tsaya a iya sakin dan ni na dade ina hasaso miki haka a irin tashin hankalin da kika dade kina
kwasowa bawan Allahn nan. Ni da ban kaini Jaye jaye bama aka sake ni bare ke? Kawai muje ki share
guri ga daki nan na kusa da nawa ki shiga ki zauna Allah ya kiyaye na gaba”.

Kuka sosai Addah ta ringa sharba se kace qaramar yarinya. Anty Talatu tun tana bata haquri har abin ya
bata haushi ta tashi qarshe ma ta fice gaba daya ta bar mata gidan ta tafi karbo zubin Adashen mutane
dan ita uwar Adashe ce.
Se bayan Magriba ta dawo gidan, lokacin Addah tayi kukan ta dangana, dukda ba haqura tayi ba ta bari
ne zuwa gobe da safe zata koma gidan ta idan Alhaji yaqi kuma zata bi Aminansa da yan uwa a saka baki
dan bazata iya barin gidan nan ba.

Toh ta kama ina dan zaman ta da Talatu tasan ma ba me yuwuwa bane kawai dai zata zauna na dan
lokaci kafin komai ya daidaita.

Tana kan sallaya bayan ta idar da sallar Isha Talatu ta shigo tana ta masifa akan matan sunqi bada zubi. A
qofar daki ta zaune kan taburma, Addah ta leqo kamar wata me takaba murya duk ta dashe saboda kuka
tace

“Talatu se yanzu? Tun dazu nake zuba ido na jiki shiru ga duhu seda wannan yarinyar ta dawo ta kunna
mun fitila”

“Ba dole ki ganni yanzu ba Fattu, Mata saboda bala’i sun qi bada zubin Adashi ai basu isa ba, gobe dirar
Asuba zan wa kowacce kafin mijintavya fita sedai ayi wacce za’ayi”.

Guri Addah ta samu kusa da ita ta zauna ta rafka uban tagumi, ga damuwar saki ga Yunwa tana
sakadarta dan ita sam bata da jumurin Yunwa.

Shinkafa Talatu ta sake dora musu suka ci da miyar dazu kafin suka kwanta tana ta jan Addah da hira dan
ta saki jikinta amma ina tayi shiru idan ka ganta bazaka ce wannan Addahr bace yar rigima.

Washe gari Asubanci tayi ta tafi gidansu Amirah, a qofar gida suka ci karo da Alhaji Murtala yana tsaye
kamar daman jiran zuwanta yake yi kanta a qasa ta shiga gaishe shi ya dakatar da ita da cewa

“Lafiya Malama? Me kika zo yi mun a gida?”


Gaba daya yau se taga yayi mata wani kwarjini tsoronsa ma taji tanayi, murya a rarrabe tace masa

“Dama, am dama Alhaji kayan sawa ta nazo dauka”.

“Ki jira a nan, bari a kawo miki” ya fada yana shigewa ciki, ta yunqura zata bishi kafin ta shiga ya mayar
da qofa tana ji ya kullo ta ciki se ta saki baki kawai tana kallonsa.

Tana nan tsaye kusan minti goma se gashi da Akwatu na biyu babba da qarami ya tura mata gabanta
yana cewa

“Sauran idan kika samu gurin zama se ki sanar mun na saka a kwashe miki kayan dakinki dukka dukda dai
da kudina kikayi su amma zan baki” ya sake shigewa gida ya bar Addah da ta qame saboda tsabar
mamakinsa.

Murtala dai Murtalan da ko kara ta ajiye be isa ya tsakkake mata ba shine yayi mata wannan korat karen
yau??

Almajirai tasaka suka daukar mata akwatunan nata, har tayi gaba ta tsayar dasu daidai gidan Sa’adah ta
shiga buga mata qofa.

Sa’adah na tsaye da mijinta ta rakoshi ze fita sukaji ana buga get, shi yaje ya bude, yana ganin Addah ya
tsugunna har qasa ya shiga gaisheta ta amsa tana tambayarsa Sa’adah na ciki ne a daidai lokacin da
itama ta qaraso gurin, tana ganin Addah ta wani hade fuska, murya a daure ta ce mata

“Gani ya akayi?”

“Wace irin magana ce haka Sa’adah Addan kike cewa gaki ya akayi haka qatsal?” Mijinta ya fada yana
kallon ta.

Seda ta harare su daga shi har Addan sannan tace


“To ba nemana take yi ba nace kuma gani ko da wani abu bayan wannan?”

Ze sake magana Addah tayi saurin dakatar dashi da cewa

“Aa babu komai, daman kudi nazo ki aramun zanyi tafiya idan yaso zan saka Amirah seta tura miki ta
banki”

“Bani da su” Sa’adah ta fa mata kai tsaye tana juya wa da niyyar barin gurin seta dakata ganin Mijinta ya
dage rigarsa yana lalubo kudi daga Aljihun wando.

“Kan bala’i, ba yanzu na tambayeka kudin kacemun baka dasu ba shine zaka dauka ka bawa wannan
matar yanzu? To duk munafunci da kitimurmurar da kuke qullawa kai dasu na sani kuma wadda kake
rawar qafar akanta cikin shege tayi se naga ta tsiya” Sa’adah ta fada tana kama qugu.

Be saurareta ba ya qirga dubu Ashirin cif ya bawa Addah ta kuwa karba ta hau godiya kamar zata
durqusa masa, be saurari zage zageb da Sa’adah takeyi ba yaja motarsa ya bar gidan.

Addah kuwa me Napep ta tare bata tsaya ko ina ba se Asibitin da sukaje jiya dan tana so ta karbo dubu
Talatin da biyar dinta data bada kafin Alqalami.

Tsayar da me Napep din tayi, da yake Nurse din ta gane ta tana shiga kai tsaye tace ta ciki na fitowa ta
shiga ofoshin likitan haka kuwa akayi tana shiga likita ya dago da murmushi a fuskar sa yana mata sannu
da zuwa.

Gaisawa sukayi, ta gyara zamanta tace

“Likita se kaji mu shiru jiya ko? Chanza shawara mukayi abinda ya kawo ni yanzu ma kenan na karbi dubu
talatin din dana baka ka riqe biyar din kan ma ladan ajiya”.

Tunda Addah ta fara magana litita ya gintse murmushin da yakeyi, se da ta kai aya kafin ya kalleta yace
“Wane kudi kike magana Hajia? Yaushe kika zo nan kuma kudin ma kika bani” ya fada fuskar sa hade
kamar da gaske. Se Addah tayi yar dariya tace

“Lallai likita aiki ya sha maka kai, baka gane ni ba nice fa nazo da yarinyata jiya za’a cire mata ciki kace na
bada dubu dari biyu na bada talatin da biyar akan zan taho da cikon idan zamu can inda kace mu same
ka din”.

“Inaga dai kinyi makuwa Hajiya, sannan maganar zubar da ciki fa naji kinayi ni ba aiki na bane dan haka
ki tashi maza ki nemi wanda kika bawa kudinki tunda wuri ma kafin lokaci ya qure miki”

Ganin fa dagaske yana neman raina mata hankali yasa Addah ta fara daga murya tana bala’i, Nurse din
da take bada kayi ce ta shigo da sauri tana tambayar ba’asi likita ya rufeta da fadan akan me zasu ringa
barin masu tabin kwakwalwa suna shigo masa, haka ta iza qeyar Addah suka fito tana ji tana gani aka
korata waje ta ringa Allah ya isan kudinta har suka je gidan Dada inda tace me Napep ya kaita.

Dada na zaune a tsakar gida abin duniya ya taru ya mata karo, Gaba daya bata jin dadin zaman gidan
saboda yanda Alhaji ya dauke mata wuta. Naziru da Sa’adu daman tuni sun dena wunin gidan bacci
kadai yake dawo dasu ga Fainusan da suke dan harkoki tare itama ciwo ya lafketa tun jiya da akayi
maganar fasa auranta take kuka seda zazzabi yayi mata ligib sannan ta haqura.

Zaman da tayi a tsakar gidan ma wayar Bashir da ta manta rabon da suyi magana take ta kira amma baya
dagawa. Sababin da Addah ta shigo tana yi ne ya sakata janye tagumin tana kallon qofar shigowa.

A kurar kusada Dadan ta zauna tana tsinewa me Napep din daya dakkota akan wai ya tsuga mata kudi ita
bataga zaman jiran da yayi mata a Asibiti ba.

Kallonta kawai Dada takeyi da akwatunanta data ga dai mitar bazata qare ba taja Numfashi tace mata

“Ina zaki haka da Akwati niqi niqi Addah?”

Kamar wadda aka tunawa se kuwa Addah ta fashe da kuka tana cewa
“Dole ki ganni da Akwatu Nafi, Murtala ya sake ni sannan ya koroni. Dakansa ya shiga ya hadomun
kayana Nafi saboda tsabar wulaqanci” se kuka.

Salati Dada ta ringayi tana tafa hannu tace

“Yanzu shi Babansu Amirah me yayi zafi haka? Akayi haqurin kusan shekaru hamsin ma se na dan taqin
da yayi saura kai amma wannan abu beyi dadi ba, Allah yasa hakan shi yafi Alkahiri”

“Wane Alkahiri ne acikin saki Nafi? Nidai yanzu idan Amadu yana ciki ki masa magana ya roqar mun
arziqi Alhaji yayi haquri ya mayar dani dan gaskiya ba zan saku ba, tsofai tsofai dani naje ina nace ansake
ni? Da can banyi zawarci da jajayen sawu ba se yanzu da girma ya cimmani bani da sauran mamora
wallahi baze yuwu ba”.

Nan suka shiga Daki Dada ta hau hada mata abin kari kafin Alhaji Amadun ya dawo. Se gurin sha biyu ya
shigo daga dubiyar da be samu sunje jiya da Sa’ad dinba, tun daga tsakar gida yake jiyo maganar Addah
ya girgiza kai a ransa yace

“Tazo kenan, koda wace fitinar take tafe yau kuma se Allah” ya shige dakinsa ba tareda ya keqa su ba. Ba
jimawa Dada ta shiga, bayanin dalilin zuwan Addah tayi masa, cike da jimamin abun yace ta kirawo
Addan tana zuwa ta zube a gabansa ta shiga rusa sabon kuka, abin nata kamar tashin iska, tun dazu take
warkajamin ta ta manta da an sake ta se yanzu da taga Alhajin ta tuna.

A wayarsa ya kira Alhaji Murtala suka gaisa a mutunce kafin yace masa

“Idan babu damuwa Alhaji akwai maganar da nake so mu tattauna ne ko zuwa dare zan iya zuwa gida na
same ka”.

“Indai maganar Fattu ce Alhaji muyita yanzu dan babu buqatar zuwan ka ka sameni” Alhaji Murtaa ya
fada.

Se Alhaji Amadu yace “toh idan kace hakan, zan roqar mata arziqi kayi haquri ka mayar da ita dakinta,
mata haquri akeyi dasu Alhaji sannan aka iya share shekarun da suka wuce ana haquri se da aka zo
gangara tukunna dan darajar Allah kayi haquri taci arziqin zuri’ar da take tsakani”.
“Wato Alhaji bana buqatar na gaya masa wacece Fattu dan sharrin ta har cikin gidan ka ya iso, tunda na
aureta kamar qaddara ban taba kwanan farin ciki a rayuwata ba a kullum daga wannan bala’i se wannan
zata kwaso mun, yanzu kana gani kaf dangi da zuri’ar mu babu wanda irin wannan qaddara ta taba
fadawa se ni a sanadin Fattu kuma to ni kuwa naci gaba da zama da Fattu saboda me indai ba kuma so
nakeyi wata rana ta janyo mun Ajalina har gida ba” Alhaji Murtala ya fada, daga muryarsa zaka karanci
irin dacin abinda da yake ji a zuciyarsa.

Alhaji Amadu yaja fasali cikin jimami shima yace

“Na sani Alhaji ni kaina shaida ne amma abinda ya faru kaida kanka yanzu ka kirashi da qaddara, kaga
kuwa kota sanadin Fattu ko bata sanadin ta ba abinda Allah ya hukunta faruwarsa seya faru da haka ina
dai sake roqar mata arziqi, kayi haquri ka maidata dakinta Allah yasa hakanya zamar muku kaffara”.

“Daga yanda ka dage kana roqona na tabbatar bata gaya maka saki nawa nayi mata ba ko? To saki biyu
ne. Kasan dama akwai daya tun shekarar dana auro Binta shekaru Ashirin da biyar kenan yanzu na
cikashe mata biyu ya zama uku kenan babu kome, taje Allah ya hadata da daidai ita a gaba ni kam Allah
ya yaye mun” Cewar Alhaji Murtala.

Se Alhaji Amadu ya juya ya kalli su Dada da suka zauna kamar masu daukar karatu har sun fara jin dadi
ko Allah ze sa a dace yace

“Kayi haquri Alhaji, wallahi ban sani ba badan haka ba me ze kaini neman sulhu? Shikenan Allah yasa
hakan shi yafi Alkahiri” ya amsa masa da Amin tun be kashe wayar ba ya fara sauke musu kwandon bala’i
ita da Dadangaba daya a kan me zasu mayar dashi mutumin banza bayan sun san saki uku ne.

Hawaye Dada ta fara yi tana rantse rantsen itama bata sani ba ya hadasu yayi musu tatas suka fito daga
dakin ko wacce fuska da Hawaye.

A wayar Dada ta sake kiran Alhaji Murtala ya daga cikin masifa yake ce mata
“Ina ganin mutunchinki Nafi karki sake kirana indai akan abinda ya shafi Fattu ne wallahi idan ba haka ba
zaku sha mamakina “

“Nice Baban Amirah dan girman Allah kayi haquri, ni ko bazaka mayar dani ba to ka barni naje nayi
zaman Yayana” Addah ta fada cikin kuka.

“Wadanne Yayan zakiyi zaman su? Amirah dake gidan mijinta ko kuma Ummi dana Tura Katsina itama
data haihu zan daura mata aure dashi uban cikin nata, tsakanina dake Fattu Allah ya isa bazan taba yafe
miki ba kin cuce ni ki bata mun zuri’a amma kije dan kanki” yana gama fadar haka ya kashe wayarsa,
tana sake kira aka saka mata line busy alamar ya toshe layin ma gaba daya.

Kwananta biyu a gidan Dada sukayi uwar watse ta kama gabanta, Alhaji Amadu kuwa daman ido ya saka
musu koda Dadan ta roqeshi akan Addah zata zauna a gidan be hana ba dan ko ba komai Fattu jininta ce
babu yanda za’ayi ya raba su amma ya saka musu ido yasan halin su ze raba gashi kuwa tun ba’aje ko ina
ba gayyar ta watse.

Gidan Anty talatun dai ta sake komawa, nan din ma bata rufa sati ba sukayi fada qarshe dai har kasuwa
tabi Baban su Amirah tana kuka akan ya rufa mata Asiri ya barta tayi zaman Yayanta baqin ciki da takaici
kamar ya kashe shi saboda irin wulaqanci da tayi masa har cikin kasuwa fa.

Wani daga cikin abokansa ne ya saka baki akan ya taimaka ya bata gurin zama, dakyar da taimakon Allah
ya bata daki daya da bandaki a wani gidan Hayarsa ya kuma ce ze ci gaba da bata ribarta duk wata tunda
kudinta ne, taje ta kwashe kayan dakinta tas ta siyar katifa kadai ta bati da yan kayan amfani ta koma
gidan.

Haka dai da dadi babu aka kafa zaman zaman take tana ciyar da kanta, ba ta dai haqura ba, tana nan
tana tanadi zata nemi duk yanda za’ayi a shawo mata kan Alhaji Murtala ta koma dakinta dan bazata iya
wannan zaman ba dan ci uku ba wasa ba.

BAYAN WATA UKU

LAGOS NIGERIA
A cikin watanni ukun nan abubuwa da yawa sun faru na dadi da na rashin sa. A bangaren Ma’u dai Abin
dadi ne ya sameta na qarin matsayi data samu a gurin aiki domin yanzu itace babbar manaja gaba daya a
sashim su na siye da siyarwa ga kyautar danaareriyar mota da akayi mata da kuma kudin haya da
kamfani ya dauke mata banda sauran Alawus kala kala da take samu.

Zuwa yanzu ta rigada ta saduda da komai rayuwarta takeyi ta jin dadi idan ka ganta bazaka iya mata
kallo daya ka dauke ido ba saboda yanda hutu da jin dadi suka ratsa ta ta sake zama wata hadaddiyar
Mace me aji bazaka taba mata kallon wadda ta haihu har biyar ba tafi kama da irin manyan Yammatan
Abujan nan da suka kwana biyu basuyi aure ba.

A yanzu bata da wata damuwa a gabanta idan ba aikinta ba. Tana da isashshan lokacin kanta ta je duk
inda take so a sanda taso dan wani lokacin Ranar Juma’a zatayi musu booking jirgi ita da Amnah su tafi
Abuja ko Gombe suyi weekend su dawo, tun yaranta na damuwa har zuwa yanzu sun rigada sun saba da
rayuwar gida biyu.

Idan tana nan zasuje mata idan bata nan kuwa basa damuwa zasu zauna a gidan su ne kawai tareda
Abbinsu daya dawo kamar wata matar kulle daga gida se Office, dan yanzu se anyi dagaske ne zakaga
Bashir a qofar gida ma bare ya tafi wani guri.

ASMA’U

Yau ta kama Lahadi na tashi da shirye shiryen tarbar Yusuf daya ce mun ze zo, zuwa yanzu na saddaqar
da Yusuf yasan aurena ya mutu dukda be fada mun ba amma yana yin yanda yake kirana a waya dukda
ba ko yaushe ba se muyi sati biyu uku kafin ya kirani, amma a duk snada ya kira se ya gaya mun wasu
kalamai da zasu saka na rasa nutsuwata na tsahon lokacin da zamu dauka kafin mu sake yin waya.

Tun safe na tashi nake ta shirya abinci, nasan Yusuf a wancan lokacin shima irin Bashir ne suna da son
abinci dan haka na tsaya na shirya masa kafiyayyun abinci dukda bansan meya fi so ba amma nasan dole
zasu burge shi.

Ina jera abincin akan Dining Bashir ya fado mun a rai, se nayi murmushi kawai a fili na furta

“Rayuwa kenan, sekaga abu ya faru ya wuce kamar ba’ayi ba”.


mamaki nakeyi yanda gaba daya Bashir ya fita daga zuciya kamar wanda aka wanke da ruwa dan idan ba
ganinsa nayi ba ko kuma yara sun ambaci sunan sa wallahi mantawa nakeyi da shi a lissafin rayuwata
gaba daya.

Ba kuma dan na dena sonsa ba, Aa wannan abune da Allah ya halicci zuciyata dashi kuma na yarda Son
Bashir shine Jarabtata amma nayi qoqari na saka kwado na qulle babin sa a zuciyata na kuma dage da
kaiwa Allah kukana akan in har Rabuwata dashi Alkahiri ya kawo mun dangana gata kuwa na gani dan
yanzu babu wani abu nasa da yayi saura da nake ji a tattare dani.

Saurin kawar da tunanin nayi daga raina daidai lokacin da yaran suka shigo daga sabuwar Islamiyyar da
aka sake bude a cikin Estate din Asabar da Lahadi da safe sauran ranakun sati bayan sallar Magriba zuwa
Isha.

daman anayi daga baya suka dakatar da ita shine yanzu aka sake ginin sabuwa harda bangaren matan
aure dan nima ina shirye shiryen shiga.

Ina ganin sun bar baje a palour na qara sa ina cewa

“Aa ku tashi karku bata mun guri, kodai ku shiga can qaramin palour ko ku fita da kujeru waje dan baqi
zanyi bana so gurin ya baci”.

Daya daga cikin daku nan dana mayar musu qaramin palour suka shige Jafar Acici ya shiga Kitchen ya
hau bude bude yana cewa

“Mami tun daga farkon Layi fa nake jin qamshin abincinki yawuna duk ya tsinke kuma nasan da kanki
kikayi yau ba Yah Amnah bace”.

“To su Acici ai seka shanye yawun naka tunda ya tsinke dan bazan sammaka abincina ba” na fada ina
janye Babar kukar dana zuba musu nasu abincin a ciki, magiya ya shiga yi mun da farantinsa a hannu ina
dariya wayata tayi qara se na ajiye masa kular ganin Yusuf ne yake kirana na fice daga Kitchen din.

“Badai har ka iso ba” na fada bayan dana amsa wayar,

“Na iso mana gani a qofar gida” ya fada cikin zolaya se nayi dariya nace
“Toh shigo mana, ka tsaya kuma daga waje?”

“Lallai yau dan gata nake har cikin gida aka gayyace ni? To me aka shirya mana ina fatan dai Wannan
mutumin baze fasa mun kai ba”

“Kana ina yanzu?” Na tambaye shi ba tareda na amsa masa maganar sa ba dan na rasa dalilin da yasa
yake son sako zancen Bashir idan muna magana.

“Yanzu zan fito daga Airport kuma kai tsaye gurinki zan wuto dan ba qaramin kewar Wannan
kyakykyawar fuskar taki nayi ba”

“Allah ya kawo ka lafiya” na fada kafin na kashe wayar. Wanka nayi saurin Fadawa, a gurguje na shirya.

Riga da skirt na saka na Atamfa da ya zauna a jikina sosai nayi daurin daya dace da fuskata kafin na bi
jikina da sanyayyan turare, ina cikin daura Agogo kiransa ya sake shigowa ban daga ba saboda naji dirar
mota alamar ya iso kenan se kawai na dauki gyalen daya dace da kayana na yafa har saman kaina na fito.

Seda nazo tsakiyar palour nayi turus ni kadai, yanzu fa Bazawari na ne yazo kenan zan fita na taro shi ko
ikon Allah rayuwa kenan kana taka Allah yana tsara maka yanda yaso.

Fitowa Aliyu yayi daga palour da suke na waiwaya na kalle shi,

“Mami fita zakiyi?” Ya fada yana kallona.

Gaba daya Aliyu ya rikide ya koma Bashir, tsahonsa, tafiyarsa kamanni sa haske kawia ya dara Bashir dan
dukda gaba dayansu ba farare bane tas amma suna da haske Farida ce kadai Fara a cikin su kuma ita
kadai ce take kama dani amma hatta da muryar su gaba daya iri daya ce haline akullum nake Addu’ar
Allah ya banbanta musu.

“Mami” ya sake kirana se nayi firgigit na kalle shi nace “Eh baqo nayi yana waje”
“Baqo kuma Mami? Wane irin Baqo?” Ya tambayeni yana tsatstsare ni da ido.

Sena hada rai ina kallon sa nima nace

“Kaje ka shigo dashi, Uncle Yusuf ne” se na juya na shige dakina ina jin yanda ya bini da kallo.

Ban dade da shiga ba naji an buga qofa, Aliyun ne ya leqo fuskarsa ba yabo ba falla sa yace

“Ya shigo gashi a palour” ya juya abinsa.

Seda na dan ja lokaci kafin na fito, suna zaune gaba daya yaran Banda Aliyu, yanda suke hira ana dariya
seka zata sun shaqu ne ko sun dade da sanin sa.

Tunda na fito Yusuf ya zuba mun ido yana kallona har na qarasa kujerar da take kallon wadda ya kai
Ahmad ya tashi na zauna kaina a qasa ba tareda na bari mun hada ido ba.

“Mami wai bezo da Little ba” Jafar ya fada kamar zeyi kuka, Dariya Yusuf ya saka masa yana cewa

“Tana can har a bacci kiran Yah Jafar takeyi, sun koma makaranta amma da da ita zan taho daman dan
itama tana so tazo gurinka, amma na maka alqawarin da kunyi hutu indai Abban ku ya yarda zan tafi da
kai gurin ta idan zan koma”

Murna Jafar ya shigayi yaja qannensa suka nar gurin. Ni mamaki ma ya bani, se kace wanda be taba
zuwa Bauchi ba ko kuma duk murnar ganin Little din ne oho.

“Gimbiya Asma’u” Yusuf ya katse mun tunanina, ban san sanda na saki wani lallausan murmushi ba
kamar Gimbiyar kuwa ina qara sunkuyar da kai.

“Kinsan irin haka kike fitowa idan nazo zance shekarun baya, banbancin kawai waccen Ma’u kwaila ce
kuma tazo tana tunzura mun baki tana hararata wannan kuma babbar macece tanayi mun murmushin
da ze qarasa kassara zuciyata” Yusuf ya fada cikin wani irin sauti, se nayi saurin rufe fuskata da tafukan
hannayena inajin yanda zuciyata take bugawa kamar zata fito.

“Ya zaki rufe dan Allah ki bude mun naci gaba da kallon kyakykyawar fuskarki kin san kuwa yanda nayi
kewarta” Yusuf ya sake fada ya ilahi ji nayi kamar kawai nayi tsuntsuwa na bace a gurin saboda yanda
kalamansa suke rugurguza mun jiki da zuciya.

Dariya yayi yana kallona yace

“Wai daman ke raguwa ce ban sani ba? To kuwa ki shirya, magana ta kadai tana firgitaki ranar da kika
zama mallakina kuma se yaya karfa ki bani kunya Ma’u”.

Wannan karon ban san sanda na miqe ba se gani na nayi na kusa kaiwa daki Yusuf kuwa yace me zeyi
idan ba dariya ba ya samu guri ya ringa kyalkyalata son ransa nidai na shige daki na zauna bakin gado ina
sauke numfashi kamar wadda tayi tsere.

Wasu Butterflies nake ji kamar suna mun yawo a kwakwalwa, Allah ya sani ina son soyayya, ina son a
tarairayeni a nuna mun duniya babu yani koda kuwa qarya mutum yakeyi amma abinda na rasa kenan a
rayuwar aurena da Bashir.

Bansan Miji yana gayawa matarsa kalaman soyayya ba, bansan me ake kira da tarairaya ba ko kalmar I
love you se na shekara ban jita a bakin Bashir ba, ba qaramin gigicewa bace ta ke sakashi yayi magana
idan muna mu’amala a sannan ne kadai bakinsa yake bin qarfin zuciyarsa ya furta abinda beyi niyya ba
qila shi yasa yanzu yan wadan nan kalaman na Yusuf suke neman au rikita mun yar kwakwlawata.

Qarar da wayat tayi ne ya mayar dani hayyacina,

“Ki dawo nayi alqawari bazan sake cewa komai ba gaisawa kawai zamuyi na tafi dan a gajiye nake sosai
wallahi” Yusuf ya fada bayan dana amsa wayar.

Kamar me zuwa gaban suruki haka na tafi idona a qasa na sake samun can gefen kujera na rabe ina jinsa
yana mun dariya qasa qasa amma naqi dagowa balle na bashi damar da zamu hada ido.
“Bari na tafi Asmy, na gaji sosai wata irin tafiya daga Washington amma se kace wanda ya taho daga
China”

Se na daga kai na kalle shi nace

“Wai ba daga Bauchi kake ba daman? Na zata ai kace kaje ganin su takwara ne”

“Suna America ai, ke dai kiyi ta tayani da Addu’a nima a wannan karon Allah ya datar da ni na samu
mace ta gari, na gaji da wannan gantalallen auran wanda dashi kusan gara babu ni ina wata duniya
matata tana can wani guri itama” ya fada fuskarsa na nuna rashin jin dadin abinda yake fada din.

“Ikon Allah kaji wata gantalewa kuma” na fada ba tareda nasan a fili nayi maganar ba seda naji yace

“Kinsan sunan da Hajiya ta sakawa auran kenan wai auran Gantali” ya qarasa yana dariya. Murmushi
nima nayi nace

“Allah to ya rufa Asiri” ya miqe yana cewa

“Amin”.

“Har zaka tafi ko ruwa baka sha ba sannan ga abinci kuma na yi maka fa” na fada nima ina miqewa
tsayen, se ya waiwayo muka hada ido yace

“Dagaske? Kai amma na gode yau nima zanci girkin Asmy daman tunda na shigo nake jin qamshi shiru
kawai nayi kar kice na fiya kwadayi, amma sedai na tafi dashi dan so nakeyi naje na yi wanka na chanza
kayan nan”.

A manyan Aluminum take away na juye masa hadin potato salad wani kuma Pepper chicken, na hada
masa da Flask din da na zuba hadaddiyar party Jallop rice dan dai nasan babu wanda baya cin shinkafa
indai dan Arewa ne dayan kuma Stit fry Egg noodles da taji shrimp.
Harda Lemo da Ruwan duk na tarkada yara suka ringa fit dasu se gani nayi suna shigowa da wasu irin
qananan Akwatuna masu Kyau irin na yan gayu kowa da guda daya Jafar ne ya shigo janye da guda biyu
shi kuma.

“Mami tsaraba UncleYusuf ya kawo mana, ga wannan na Yaya Aliyu ne” ya fada yana miqo mun guda
daya.

“Bana so kudai da kuke kwadayayyu se kuyita karba ai” Aliyu da bansan yana gidan ba ya fito daga dakin
su Amnah yana maganar, hararar sa nayi ya kalleni ya dauke kai, kamar ze zauna se kawai ma ya kada
kansa ya fice daga gidan gaba daya ni kuwa na bishi da ido kafin na mayar da hankali na kan sauran da
suke faman bude bude akwatunan su.

Kaya ne kowa kala biyu da takalmi harda Agogo da turare, bana buqatar a gaya mun masu tsada ne dab
Designers ne nagaske da kana kallonsu kasan sunci kudi.

Wayata na dauka na wuce daki ina kiran lambar Yusuf din

“Wannan kayan fa hidimar tayi yawa ai kuma ace ko wanne se da aka siya masa gaskiya sunyi yawa” na
fada bayan daya daga wayar.

“Akwai wani abu naki a ciki ne?” Ya tambayeni, sena girgiza kai kamar yana gabana nace

“Aa” na bashi amsa

“To qorafin me kikeyi? Yarana na siyowa bake ba, idan ma kishi kike saboda ban yi miki tsaraba ba toh
sedai kiyi haquri bandake” ya bani amsa yana murmushi.

Murmushi nima nayi nace

“Mungode, Allah ya qara budi”


“Karki sake gode mun dan kinfi qarfin duk wani abu a gurina. Zan iyayin komai saboda Farin cikin ki
Asmy, zamuyi magana idan na qarasa masauki in naci abinci sannan se nayi tunanin idan kin cancanci
tukuici”

Da haka mukayi sallama ni kadai na ringa murmushi ina kallon wayar hannuna bayan da na kashe, wato
soyaya tayi a rayuwa malam.

ENGINEER BASHIR

WATA KISHIYAR

(ALKAHIRI CE KO SHARRI)

Na Maryamah Farouk

(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)

Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 52
ENGINEER BASHIR

Watanni ukun da suka shude Bashir yayi su ne cikin wata rayuwa me cike da qunci da rashin sukunin
zuciya. Ya sake zama shiru shiru duk da daman shi ba me yawan magana bane amma a yanzu kana
kallonsa zaka san shirun sa yana da nasa ba da tarin damuwa da yake ciki.

Abun ne ya hadar masa goma da Ashirin, kewar Ma'unsa tana neman zauta shi ga rashin kula da rashin
abinci me kyau da baya samu a gidansa kullum se tashin hankali da hayaniya idan ya fita har baya so
lokacin tashi aiki ya dawo gida.

Gaba daya a yanzu idan ka ganshi se ya baka tausayi yanda gaba daya ya fige ya fita hayyacinsa,
hidimomi sun sako shi a gaba, wata daya da rabuwarsa da Asma'u gaba daya ya kasa gane kan cefanen
gidansa.

Be taba sanin cewa Neman da Asma'u takeyi rufin asirinsa bane se ranar daya dawo daga aiki ya tarar da
Amirah ta dafa masa farar shinkafa ta soya manja da yaji ta ajiye masa a ranar Azumi yayi, kuma kafin ya
fita da safe ya gaya mata azumin yakeyi be shigo gida ba seda yayi sallar magriba dan haka yana shiga
kan Dining ya wuce kai tsaye dan ya ci abinci.

Yana budewa yayi arba da abinda ta ajiye masa gaba daya se ya gagara bude baki ma yayi mata magana,
mai da yaji a gidansa abinda rabon dako a ido ya ganta tun zamanin da yana Jami'a shine yau aka dafa
masa a matsayin abin shan ruwa.

Yar gasken kuwa daya tambayeta dalili kai tsaye ta gaya masa cewar kayan miya sun qare kuma ita bata
da kati a wayarta bare ta kirashi ta sanar masa shiyasa taga daya dawo bata girka komai ba tunda tana
da yaji gara ko fara da mai dince tayi masa.

Yanzu shine ajiye buhun huna, shine cefane, dai da Maggi se ya siyo ya ajiye mata sannan in dai bashi ya
duba ya sake siyowa ba babu ruwanta abinda yake da akwai shi zata sarrafa tayi abincin da kusan kullum
Asarar sa akeyi dan yaran basa ci shi kuma bashida nutsuwa da kwnaciyar hankalin da zeci da yawa, da
ya zauna cin abinci in sha Allahu seta qirqiro abinda zata bata masa rai ya tashi daga gurin.
Ya rasa wace irin macece Amirah da bata taba tashi kawo qorafi da mita se a lokacin da za'aci abinci ko
lokacin kwanciya wadannan abubuwa suka taru suka sake dagula masa lissafi.

Be qara shiga uku ba seda Amirah ta fara laulayi. A iya saninsa bayan haihuwar da tayi an saka mata
Implant a Asibiti saboda ta huta jikinta ya dawo daidai amma se gashi ba'a rufa shekara ba ta samu wani
cikin.

Lokacin da yayi mata magana akan ya haka ta faru kai tsaye tace masa cirewa tayi sanda zata taho
saboda itama tana so ta tara Yaya a dena mata gadara dasu, be ja ba ya barta tunda ai jikinta ne ta sani
idan dadi taji idan ma wuya ce duk tafi kowa sani shidai tunda ta fara Amaye Amaye da wasu abubuwa
ya tattarata ta koma dakinta dan wata muguwar qazanta ta farayi abin dai ba'a cewa komai.

A bangaren matsalar Ma'u kuwa yankewa kansa shawara yayi akan ze saka mata ido ne yaga iya gudun
ruwanta, ze jira daga nan har shekara har zuwa sanda zata huce ta saurare shi a sannan baze sha
wahalar shawo kanta ba su komawa auransu amma babu qarya yayi kewar Asma'u koma yace yana kan
kewarta, fuskarta, muryarta, qamshin ta da gayunta daddadan girkinta ga murmushinta me saka shi
manta kowa da komai kai wallahi dole ya maido da Asma'u rayuwarsa dan kuwa tabbas rasata babbar
Asarace a gareshi.

Yanzu haka tun daya rabi da ita baya iya bacci saboda tunanin ta, idan kuwa har bacci yayi nasarar sace
shi me nauyi to cike yake da mafarkin Asma'un.

Abu dayane yake dan kwnatar masa da hankali yanzu da be sake ganin wannan mutumin yazo gurinta
ba, tun waccen ranar ma babu wani Namiji da ya sake gani tare da ita idan ba Yemi ba wanda ya bincika
ya tabbatar abokin aikinta ne kawai babu wata alaqa a tsakaninau bayan ta aiki.

Sedai kuma guiwar sa tana yin sanyi irin yanda yaga gaba daya ta ci gaba da rayuwarta babu wata alama
da take nuna tana da damuwa ko tunawa da shi dan yanzu ko sun hadu a hanya gaisawa sukeyi kamar
wasu maqota, yanda zata gaisa da sauran mutanen da suke cikin layinsu shima irin wannan gaisuwar
take yi masa babu wani abu da yake nuna sun taba hada wata alaqa ta soyayya bare har aje ga batun
aure amma kuma baze sare ba, zeyi ta binta a hankali har zuwa sanda ita da kanta zata sakko ta neme
shi.
A ranar Lahadin yana kwance a dakinsa kamar yanda yanzu ya mayar da hakan dabi'arsa zaman daki
kamar wata sabuwar Amarya. Amirah ce ta shiga dakin fuskar nan qozai qozai da ita kana ganinta kaga
me yaron ciki duk ta firgice ta saka doguwar rigar bacci cotton ta daura zani akai kanta ko dankwali babu
ga gashinta me laushi duk ya tashi.

Kan gadon ta nufa ta zauna daidai kansa se yayi saurin miqewa zaune ya matsa can gefe yana hade
fuska, Amirah da abin ya mugun bata mata rai, bakinta cike da yawun da yake yawan taruwan mata tace

"Wai wane irin wulaqanci ne haka se kace wata kashi daga nazo kusada kai zaka tashi sannan ka dena cin
abincina gaba daya mun zama kaman wasu yan haya a gidan nan kowa sabgar gabansa yake yi"

"Malama ki wuce kije kiyi wanka kuma karki sake zuwa kina mun magana da yawu a bakinki. Sannan na
miki magana akan ki ringa suturta jikinki kin qi ko? Shikenan" Bashir ya fada yana miqewa ya shige
bandaki ya barta tana banbamin fadab bazatayi wankan ba ai jikinta ne ba nasa ba.

Sanda ya fito bata dakin, shiryawa ya shigayi, yasan tunda ta fara wannan neman rigimar to idan ya
zauna gidan dole se ta saka shi yayi hayagaga shi kuwa yanzu ciwon kan da yake fama dashi kullum ma
ya ishe shi ba se ya qara wani ba.

Yana tsaye yana warming mota kamar ance ya kalli qofar gidan Ma'u yaga wasu lafiyayyun motoci guda
biyu a ajiye ga Bouncers hudu majiya qarfi se fareti suke a qofar gidan.

A farko tunaninsa Alkasim ne yazo, yayan au Ma'u ne babban dan sandan farin kaya ne yasha shine me
yawo da wadan nan mutanen ko a Gombe idan yana gida haka Zasuyita zagaye unguwar.

Harya shiga motarsa ze tafi ta mudubi ya hango ana fito da kwanukan abinci, cike da mamaki ya dakata
ai kuwa idonsa sukayi mummunan gani da mutumin daya fi tsana a Yanzu ya fito daga gidan yana zuba
murmushi kamar wanda akayiwa Albishir da Aljanna.
Be gama cika da mamaki ba seda yaga Ana ta fitowa da yara akwatuna suna dauka, yana nan tsaye suka
wuce shi kamar da gayya ma har wani quuu suka taka motar suka fice da gidu Bashir ya bisu da ido
zuciyarsa na tafasa saboda bacin rai.

Kashe motarsa yayi ya nufi gidan, a bakin qofa suka hadu da Aliyu daya fito fuskar nan kinini kamar
wanda aka daka sukayi wa juna kallon kallo kamar wasu zakaru kafin Aliyun ya rabe shi ze wuce se yayi
saurin ruqoshi yana cewa

"Waye ya fita daga gidan nan yanzu?"

"Saurayin Mami ne, Uncle Yusuf" Aliyun ya bashi amsa kai tsaye kafin ya janye hannunsa ya yayi gaba.

Seda Bashir ya dage bango kafin ya iya tsayawa da qafarsa. "Saurayin Ma'u?" Ya maimaita maganar a fili
yana bin bayan Aliyu da ya tafi ya barshi da kallo.

Dagaske Ma'u ta bawa wani damar shiga rayuwarta bayan shi? Wannan irin kata'i ne yake taso masa
daga qirji yana shaqe masa wuya kalamar saurayi da Aliyu ya gaya masa tayi masa zafin da gara ace wuta
ya fi masa sauqi akan jin wannan mummunar maganar.

Fasa shiga gidan yayi ya juya dan tsoro yakeji, idan ya shiga ya samu tabbacin maganar da Aliyu ya gaya
masa daga bakin Ma'u ya tabbatar zuciyarsa kawai bugawa zatayi a take ya mutu dan baze iya dauka.

Yana dafe da qirjinsa dakyar ya iya kwasar qafarsa ya koma jikin motarsa yana sauke numfashi kamar
wanda yayi gudun 10KM. Gaba daya jinsa yake shi ba a sama ba ba a qasa ba, qafafunsa kansu rawa
sukeyi beyi aune ba se ganinsa yayi dirshen ya zauna akan kwaltar da take qofar gidan kawai se ya mayar
da kansa ya hade da guiwa yana jan numfashi.

"Lafiya Engineer kake zaune a qasa meya faru?"yaji muryar da be tantance ko ta waye akan sa ba, dakyar
ya dago yana nuna masa kansa da qirjinsa daga nan be sake sanin abinda ya faru ba se farkawa yayi ya
ganshi kwance a gadon Asibiti.
Dafe kansa da yayi masa nauyi yayi ya tashi zaune yana qarewa dakin kallo, "me ya same shi? Waya
kawo shi Asibiti?" Qoqarin cire qarin ruwan da aka saka masa ya shigayi, Shigowar da likita yayi tareda
wata Nurse a bayansa ya dakatar shi.

"Kai kai Engineer ya zaka cire bayan be qare ba" likita ya fada fuskarsa dauke da murmushi ya shiga
gyara masa ruwan. Dakansa ya saka masa abin duba Blood pressure ya gama karantawa yana fadawa
Nurse din ta rubuta ya sake saka abin gwada zafin jiki nan ma ta rubuta kafin ya kalleshi yana ci gaba da
murmushin yace

"Mun gode Allah jininka ya sauka zafin jikin ma babu yanzu akwai inda yake maka ciwo ne?"

Kansa ya nuna masa, da alama dai likitan akwai Fara'a dan murmushinsa ya qara fadadawa yana cewa

"Ze dena amma sekayi qoqari kaima ka cire duk wata damuwa daga ranka, a shekarunka dai baka
buqatar na tsaya ina gaya maka abinda ya kamata kayi ko karkayi, abu daya dai shine lafiya tana gaba da
komai.

Bansan menene damuwarka ba amma koma yayane ka daure ka rageta dan jininka ya hau sosai, sannan
akwai Yunwa a tattare dakai abinda yake qara maka qarfin ciwon kan kenan da kuma rashin bacci, indai
zaka kiayaye yawan tunani ka kuma ringa cin abinci me kyau in sha Allah komai ze daidaita".

Kallonsa kawai Bashir yakeyi harya gama bayaninsa yana murmushin dai yacewa Nurse ta hada masa
shayi yasha se ta bashi magani. Ruwan ya cire masa saboda ya samu ya shiga bandaki ko yana da uzuri,
jiki ba kwari Bashir ya wuce Bandakin, tunanin da aka hanashi ya shigayi lokacin da Asma'u ta hadu da
Hawan jini sanadiyyar auran Amirah da yayi ashe shima nasa rabon yana tafe sanadin rabuwa da ita.

Brush yayi ya dauro Alwala dan besan awa nawa yayi a kwance ba. Nurse din ya tambaya waya kawo shi
kuma tun yaushe tace bata san wanene ba amma tun jiya da rana ne yanzu kuma qarfe goma na safe
harya gota.

Buda ido yayi sosai yana kallonta, kwana yayi a sume kenan?
Sallah ya tayar harya fara a tsaye yaji baze iya ba seya koma ya zauna. Seda ya biya duka bashin sallolin
da suke kansa kafin Nurse ta miqa masa shayin data saisaita ta shiga bude wasu kuloli daya gani a ajiye
ta shiga zuba masa soyayyan dankali da kwai se farfesun kayan ciki da shaqa daya yayi wa qamshin su ya
gane daga ina suka fito.

"Waya kawo abincin nan?" Ya tambayi Nurse din. Seda ta ajiye masa kafin tace

"Yaranka ne suka kawo, jiya da dare ma sun kawo abinci baka farka ba aka bayar dashi wannan da zasu
tafi makaranta suka kawo".

"Su kadai suka zo ban da mamansu?" Ya sake tambayar ta.

Tana tattara kayan aikinta tace

"Bansani ba gaskiya su kadai dai suka shigo nan Maza biyu da mata biyu" tana gama fada ta yi gaba se ya
dakatar da ita akan ta dauke ragowar abincin ta fita dasu tana masa godiya.

Kamar wasa se gashi ya tashi da abincin tas har yana jin dama bece ta fita da sauran ba, bayan shayin
data hada masa seda ya sake hada kofi daya ya qara nan da nan yaji ya farfado se ya shiga neman
wayarsa yayi sa'a kuwa ya ganta an ajiye masa akan durowa so yake ya kira office dinsu ya bada uzuri
yana dannawa hotonsu tareda Ma'u da yake kan screen din yayi masa sallama nan take zuciyarsa ta
buga dum

"Saurayin Mami ne" maganar ta shiga yi masa yawo a kwakwalwa.

Jifa yayi da wayar ta daki bango ta tarwatse, ya dafe kansa da hannu biyu yana jijjigawa saboda yanda ya
taso masa da ciwo lokaci daya cikin sauri aka turo qofar dakin, likitan ne tareda Nurse din dazu dan
dukka dakunan Asibitin da akwai CCTV a ciki suna lura da halin da halin da mara lafiya yake ciki.

Allura Likitan yayi masa nan da nan bacci ya dauke shi, ya kalli Nurse din da damuwa yace

"Har na fara tunanin bashi sallama saboda yanda Komai nasa yayi normal kinga kuma lokaci daya komai
ya birkice, ina tunanin akwai wani abu da yake tunawa da yake tayar masa da hankali kunyi magana
dashi ne dazu?"
"Bamuyi magana ba, kawai ya tambayeni waya kawo shi Asibiti nace ban sani ba, se ya tambayi abinci fa
na gaya masa yaransa ne suka kawo amma banda mamansu shi kenan".

"Kuma kinsan abin da mamaki, wanda ya kawo shi makwafcinsa ne, sannan yaransa sunzo amma babu
matarsa amma dazu da safe Maceceta kawo su sedai baya shigo ba, a mota ta jirasu suka wuce.

Ki zauna ki kula dashi, zanje zagaye duk abinda yake da akwai ki sanar dani" daga haka ya fita yabar
Nurse tana gadin Bashir.

ASMA'U

Ina kwance a dakina gama wayarmu kenan da Yusuf daya kira yana tayi mun santin abinci ina masa
dariya se ga Aliyu ya shigo gaba dayansa a birkice dan ko Knocking beyi ba ya fado dakin.

"Meye haka Aliyu, wane irin iskanci ne zaka shigo mun daki babu sallama" na fada ina tashi zaune.

"Mami, Abbi ne bashi da lafiya" ya fada kamar zeyi kuka. Sena yatsina fuska nace

"Allah ya bashi lafiya, ko kuwa ni likita ce da zaka zo ka gaya mun? Idan jikin yayi zafi da yawa ku tafi
Asibiti mana ai zaka iya tuqashi ko ya kira Samuel ya kaishi".

"Mami Faduwa fa yayi a qofar gidan, Dadyn su Sa'id ne ya tafi kaishi Asibiti shida Mr Uche" Aliyun ya
sake fada se na waiwaya na kalleshi,

"Faduwa kuma? A garin yaya?"

"Nima ban sani ba, a qofar gidan nan na barshi na shiga can gidan se kawai Malam Sani ya leqo ya gaya
mun wai ya fadi yanzu an tafi kaishi Asibiti".
"Allah ya bashi lafiya" na fada a sanyaye.

"Mami zanje na ganshi"

"To seka dawo, kayi masa sannu" na fada ba tareda na kalle shi ba.

"Mami ke bazaki je ba?" Aliyun ya sake fada yana kallon qasa, harara na banka masa nace

"Fitar mun a daki, sannan idan zaka je ka nemi motar haya dan idan ka dauki mota ka tafi VIO suka kama
ka karka ce ka sanni".

Ina jinsa yana qunquni ya fita, ban iya yin baccin da nayi niyya ba na shiga tunanin to me ya janyowa
Bashir faduwa tuntube yayi kome tunda bema shigo mana nan ba dai dan da zanji yara sun fada kuma
yaushe rabon Bashir da gidan nan ma tun zuwan sa na qarshe wanda har na mareshi.

Da zasu dora abincin dare Amnah tace mun zasu dafa harda Abbi su kai masa nace musu toh, ganin dare
yayi kuma babu me kai su yasa muka tafi tare, a waje na tsaya suka shiga da abincin basu jima ba suka
dawo wai bacci yakeyi, muka kamo hanyar gida duk jikinsu a sanyaye se naji nima na damu dukda
banganshi ba amma yanayin da fuskarsu ta nuna ya tabbatar mun bashi da lafiya dagaske kai ni tunda
nake da Bashir ma zan iya irga sau nawa ciwo ya kaishi Asibiti.

Muna shiga gida Yusuf ya kirani, ban daga ba seda na gama sallamar yaran muka rage aikin gobe da safe
tunda Monday ce duk zamu fita kuma dukkan su a gidan suka ce zasu kwana. Seda nayi wanka na shirya
kafin na dauki wayar.

Agogo na kalla naga har sha daya saura dare yayi, sena mayar da ita na ajiye kawai idan Allah ya kaimu
da safe na kirashi kawai ina ajiyeta kuwa ta fara qara alamar kira, sena dauka Yusuf din ne nayi
murmushi na daga na saka a kunnena.

"Ina fatan ban katse miki abinda kike yi ha dan nasan dai yanzu bakiyi bacci ba" Yusuf ya fada.
"Aa yanzu naga missed call dinka ma se kuma naga dare yayi nace da safe na kira se kuma ga kirankabya
shigo" na fada ina kashe fitila me haske na koma kan gadon na zauna.

"To ai ke zaki iya bacci bakiyi magana dani ba, ni kuwa kinga ko bazan iya ba, shiyasa na baki isashshen
lokaci kafin na sake kira".

"Uhm" na fada ina kaiwa kwance amma maganar sa ta dakar dani na tashi zaune dakyau ina zare ido

"Na kasa daure wa Asmy, jan rai da jan ajin naki yayi yawa. Tun tuni nake jira ki gaya mun da bakinki
auranki ya mutu amma kinqi, nayi haquri a lissafina yanzu kin gama iddah na kasa jurewa dan naga
alamar baki da tausayi idan na biye miki haka zakiyi ta gara zuciyata.

Yanzu dai nasan na riga kowa saka Number wallahi dan haka karka kice zaki kawo mun uzuri, nidai gani
na sake dawowa a karo na biyu da qoqon barar soyayyarki Asmy, ina roqon ki amince dani ki bani dama
na shiga rayuwarki mu rayu a qarqashin inuwa daya a matsayin ma'aurata".

Miyau kawai nake hadiyewa qut qut ina zate ido ni kadai a daki har ya gama maganar sa ban iya cewa
komai ba. Seda muka kwashi kusan minti goma ba magana kafin ya yanke shirun da cewa

"Kinyi shiru Asmy kice wani abu dan Allah, bance ki soni dole ba dan kin dade da gaya mun bakya sona
ba kuma zaki taba sona ba na yarda, ni ina sonki kuma na tabbata qarfin son da nake miki ya isa ya riqe
auran mu base kin taimaka da komai ta bangarenki ba.

Nidai kawai ki bani dama na shiga rayuwar ki, idan Allah ya yarda bazakiyi dana sani ba.

Zan baki abinda ya dace dake, zan shayar dake madarar soyayyar da ko a mafarki baki tafa hasaso irinta
ba nidai kawai ki amsa mun ki bani dama" ya qarasa da qaramin sauti kamar me shirin yin kuka.

Se gani harda jan bargo na rufe qafata da sukayi sanyi, inda yasan yanda kalamansa suka qulle mun baki
da jijiyoyi gaba daya da yayi shiru amma ina sema qara wuta da yayi yana zayyano mun kalaman da suke
kassaramun jiki.
Irin Kalaman da a kullum nake mafarkin jinsu daga Bakin Bashir se gashi har na qaraci zamana dashi be
taba ko kwatanta gaya mun irinsu ba.

Yusuf be kyaleni ba seda yayi mun lilis da kalaman da suke bayyanar da tarin qaunar sa gareni dan
wannan ya wuce a kirashi da so. Haka mukayi sallama ba tareda na iya bashi amsar komai ba dan zama
nayi kamar wata farin shiga a lamarin.

Wai kuka zuciya da jaye jaye seta ringa rayamun dama ace Bashir ne yake gayamun maganganun nan da
lashakka sena narke a gurin nan sedai a sakani a ruwan qanqara na hade.

Haka nayi baccina cikin nishadi cike da mafarkai masu dadi wai gani nida wani da ban gane fuskarsa ba
muna tsinkar furan soyayaa wani lambu me cike da Ni'ima harda yan dagwai dagwai din yara mata guda
biyu masu kyau da gani ma yan biyu ne.

Washe gari haka na tashi cikin nishadi muka hada abin kari harda Bashir aka zubawa muka biya suka
sake shiga su kadai suka ajiye kafin muka wuce na kaisu makaranta. A hanya suke gaya mun har sannan
bacci yakeyi se abin ya fara bani tsoro na qudure idan mun dawo da daddare se mu sake zuw amu duba
shi tunda abin na gaske ne ko babu komai Uban yayana ne ba kuma shida wasu dangi a garin bayan mu,
to wai ina matar sa ma take? Na tambayi kaina daidai sanda nake ajiye mota ta a inda aka tanada danyin
fakin.

Sanda na shiga office na tarar da wasu clients guda uku masu son zuba hannun Jari, nan da nan na shiga
hidima dasu nan da nan kuwa muka qulla yarjejeniyar.

Da kaina na hada musu coffee muka sha kafin kafij suka saka hannu a takardu muka basu wanda zasu
tafi dasu na ajiye namu, na rakosu bakij office na juya ciki kenana daya daga cikinsu wanda kana ganinsa
kasan Bahaushe ne ya dawo da baya da murmushi

Nima murmushin nayi nace "yaya dai?"

"Mantuwa nayi" ya bani Amsa yana zaro wayarsa daga Aljihu ya miqa mun
"Na manta ban karbi numbar Hajiya ba saboda ko akwai wani abu se na kiraki".

"Ai da akwai Number a jikin Letter headed dinmu, idan kana da wani enquiry seka kira" na fada ina zama
akan kujerata, se ya ja kujera shima yana cewa

"Ki dai bani da kanki bata kamfani ba lambar wayarki nake so tunda dake muka qulla kasuwanci".

Irin masu tsinannen nacin nan ne, daya tasani gaba seda na bashi lamba sannan ya sarara mun, sema
daya gwada kira yaga ta shiga wayata dake ajiye tayi qara sannan ya haqura ya tafi yace mun sunansa
Hayatuddin.

Mamaki na ringayi me yasa yanzu Maza suke tunkarata suce na basu lambar waya wai tayaya suke gane
banida aure yanzu tunda nidai babu abinda na chanza daga yanayin shigata ko mu'amala amma yanzu
ranaku daddaya ne zan fita ba tareda wani ya tare ni ba, baga masu aure ba saboda tsaurin ido harda
samari dan akwai ranar da na shiga Shoprite seda nayiwa wani dan banza tatas a gurin wai yazo ze biya
mun kudin kayan dana siya.

Kafin na koma gida har Amnah ta shirya abincin da zasu kaiwa Bashir sanda na isa har sunyi wanka suna
zaman jirana. Ina shiga suka fara sintirin zuwa tambayar yaushe zamu tafi yaushe zamu tafi dana ga zasu
dame ni nace inaka sake tambayata an fasa zuwa shine na samu sa'idah, seda mukayi sallar Isha, ina
cikin yafa mayafin Abayar dana saka kalar Maroon data karbi fatata kamar ka sace ni ka gudu Kiraj Yusuf
ya shigo wayata.

Haka kawai naji murmushi ya kwace mun, wayar mu ta jiya da daddare na tuna dan duk yau bamuyi
magana ba ya dai yi mun wani mugun text da safe dan seda muka fita break din rana ma na gani ina
karantawa kuwa na goge dan ji nayi yana neman ya tsaga mun zuciya biyu bayan na rigada na saka zaran
kirtani na dinketa tsaf ta yanda babu abinda ze sake hudata ya shiga.

"Ran gimbiya ya dade" ya fada cikin sakakkiyar muryar sa.

"Tareda naka" na bashi amsa ina fesa turare.


"Ki saka kadan dan Allah, bana so wasu su ringa jiye mub qamshin ki baki san irin yanda nake kishinki ba
ko?" Ya fada daga cikin wayar,

Seda na janye na duba naga ko video call ne amma naga normal kirane, mamaki ya kamani ya akayi
yasan me nakeyi se ji nayi yace

"Mamaki kikeyi ya akayi na sani ko, ruhina da naki a hade suke, duk abinda kike yi ina ji a jikina"

"Hakane" na bashi Amsa se ya fashe da dariya yace

"Gani a qofar gida nazo zance"

"Se dai ka daki gurbi dan bana nan"

"Kina ciki, shiryawa kikeyi zakuje duba Babansu Farida a Asibiti ya fadi jiya bashida lafiya" Yusuf ya fada.

Ko be fada mun ba nasan Ya gamu da Jafar dan shine me shegen surutu kamar ya qone akai.

"Ku fito se mu je tare na duba shi" ya sake fada kafin ya kashe wayar.

Tareda Driver sa yazo, dan hakaMota biyu mukayi tashi da tawa muka tafi.

Su Aliyu ne a motar da Driver yake ja, nida yammatan a motar Yusuf muna tafe se jansu yake da hira ni
kuwa duk nabi na takura kaina sedai ya kalleni yayi murmushi har muka qarasa bayan da ya tsaya a wani
guri ya siyi fruits harda kaza da ruwa da Lemo kafin muka wuce.

Tundaga qofar dakin kana iya jiyo karadin Amirah, Yaran ne suka farayin gaba nida Yusuf muka shiga a
qarshe mun jera kamar wasu Mata da Miji yana rada mun yanda muka dace wai se kallon mu akeyi da
murmushi a kan fuskata nayi sallama muka shiga dakin idona akan Bashir daya zabga uban tagumi kamar
wanda aka cewa Dada ta mutu.
BASHIR

WATA KISHIYAR

(ALKAHIRI CE KO SHARRI)

Na Maryamah Farouk

(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)


Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 53

BASHIR

Se gurin Azahar ya tashi daga baccin dolen da Likita ya saka shi. Jikinsa a matuqar mace yayi wanka ya
saka uniform din marasa lafiya da aka bashi kafin yayi sallah ya sake komawa kan gadon ya kwanta.

Abinci Nurse din dazu ta kawo masa, loma daya yayi ya ajiye dan yanda yaji shi salam babu dandano
haka yayi ta zare ido ga yunwa yana ji se Fruits ya iya sha da Yoghurt kawai har kusan qarfe uku tun yana
tsammanin zuwan wani harya fitar da rai se a sannan ma ya tuna da yau Litinin ashe, be je aiki ba kuma
be kira ya bada uzuri ba.

Wayarsa ya dauka ya shiga kiran Engineer Musa abokinsa, bayan sun gaisa musan yaje masa ya jiki yace
masa idan sun tashi aiki zasu zo su dubashi dan Oga Abdallah ya sanar cewa yana Asibiti.

Mamaki ya ringayi da har gashi ya kwana ya hantse ana neman awa 24 da barin sa gida amma babu
Amirah babu alamarta.

Yanzu ace da lissafi kuwa a Gurin nan mijinki ya fita ya kwana be dawo ba ai ko a waya ta neme shi taji
lafiyarsa tunda be saba hakan ba amma ze saka ido ya gani daga nan zuwa anjima ya koma gidan se yaji
abinda zata ce masa.

Yana cikin yin sallar la'asar se gata kamar an jefota dakin yana sallamewa kuwa ta dira masa mitar ya
za'ayi bashida lafiya har a dauko shi a kawo ahi Asibiti sannan ne za'a gaya mata daga baya saboda bata
da muhimmanci a gurinsa.

"Saboda ba'a gaya miki bane ya hanaki zuwa tun jiya kiga halin da nake ciki?" Ya fada yana tsareta da
ido, seda ta zumbura baki gaba kafin tace
"To ai gani nayi ba'a buqata ta shiyasa nayi zamana nasan dai duk tsiya in ma mutuwa kayi dole a sanar
mun tunda ni ce dai matarka ba wata ba" ta qarasa tana juya ido, se kawai ya girgiza kai ya koma kan
gadon ya kwanta tareda rufe ido kamar me bacci.

Yana jin ta tana tambayarsa jikinsa yayi banza da ita, tayi maganar harta gaji amma kamar meyi da dutse
ko motsi daga qarshe dan kanta ta miqe tana cewa

"Qila bacci yayi, bari naje waje na wasa qafata kafin ya tash" ta fice abinta.

Tana fita ya bude ido ya raka ta da harara tareda dogon tsaki, haka ya zauna rabi da rabi ido biyu da
bacci saboda Allurar har sannan bata gama sakinsa ba dagoya kawai yake ya saka wa qofa idon yana
dakon zuwan yaran idanze fadi gaskiya ma harda jiran Abinci yake dan na safen da yaci ya taso masa da
tsohon kwadayin girkin Asma'u.

Har akayi sallar Isha Amirah na zaune tana zuba masa surutun da sam ba fahimtar ta yakeyi ba, ya hade
girar sama da qasa qarin haushinsa da likita yace baze sallame shi yau ba se ya sake kwana kuma shi
bega amfanin zaman nasa ba dan bazasu iya yi masa maganin abinda yake damunsa a yanzu ba.

Suna haka yaji an turo qofar yaran suka shiga, a jikinsa yaji Asma'u tana kusa dashi be gama tunanin ba
kuwa ya daga kai kenan yayi kyakykyawan gani daya saka zuciyarsa ta tsallake bugu.

Har suka shigo cikin dakin idanunsa akansu, yanda take zabga murmushi shi kuma yana mata rada seka
rantse da Allah su kadai ne a cikin dakin dan babu alamar wai suyi tunanin wasu na kallonsu.

"Qut" ya hadiye wani abu me tauri, lokaci daya idanun yan maza yayi jajir kaman wanda yasha duka,
Fuska a washe Yusuf ya miqa masa hannu yana cewa

"Barka da dare Engineer, ya jiki kuma? Allah yasa kaffara ne"


Kallon Yusuf din yayi ya kalli fuskarsa, gaba daya ma se ya kasa bude baki dan ji yayi kamar an saka masa
tsumma a a bakin, Yusuf da ya ga bashida niyyar bashi hannu ya janye yana murmushi ya waiwaya kan
Amirah da itama tayi kinini da fuska yace

"Madam yame jiki? Allah ya qara sauqi toh".

"Amin" ta amsa can qasa dan gani tayi ya mata kwarjini kafin ta wurga ido gefen da Ma'u take tsaye
kaman anyi mata dole tace

"Anty Ina wuni?"

"Lafiya lau, ya me jiki?" Asma'u ta amsata ba tareda ta kalle ta ba.

"Baban Ali ya qarfin jiki? Allah ya qara afuwa" Ma'u ta fada tana kallon Bashir daya zubawa Yusuf ido
ganin yanda shi Yusuf din ya kafe Ma'u da wani mayan kallo kamar ze cinyeta.

Ji yakeyi kamar ya tashi ya shaqe Yusuf din kowa ma ya huta, yanzu da wannan kwalliyar ya dakko ta
suka taho yana shaqar qamshin turaren? Abinda yake mallakinsa yanzu suke rabawa tareda Yusuf din.

"Asmy muje ko? Dare yana yi kuma kinga ko zama bamuyi ba muka taho" Yusuf ya fada cikin kwantar da
murya kamar me magana da yaro, murmushi Ma'u tayi masa ta fara tafiya tana cewa

"Allah ya qara sauqi, Aliyu ku debo kwanukan safe ku taho dasu" tayi gaba abinta ba tareda ta sake
kallonsa ba se yaran suka miqe suna yi masa seda safe suka fice gaba daya banda Aliyu.

"Zoka kwashe wannan abin daya shigo dasu" ya fada yana nuna masa ledar Fruit da kajin da Yusuf ya
siyo ko yaya akayi ya gane shi ya siya se Allah.

Juyawa Aliyun yayi ya kalli Uban kafin ya bankawa Amirah harara ya juya ya fice abunaa ba tareda ya
dauke ledojin ba.
"Kana kallonsa yana hararata ko? Wallahi sena ci uhan yaron nan zamu koma gida ne. Daman jiya ni
kadai suka bari na kwana a gidan ka kirasu ma ka gaya musu..."

"Tashi ki fita" ya fada a tsawace har seda ta zabura ta miqe, har tayi gaba ta koma ta dauki ledar kazar
tana cewa

"Idan bazaka ci ba ni na dauka dan daman banyi girki ba dazan fito" tayi gaba abinta tana ci gaba da
qunquni.

Samuel da tuntuni yake jiranta a reception ya miqe rai bace ya fita tana binsa a baya, a kusan tare suka
isa gida dasu Ma'u, saboda bala'in sa ido a qofar gidan ta tsaya.

Tana hangen Ma'u da Yusuf suna magana kafin sukayi sallama ya shiga motarsa Driver yaja suka wuce.

A kan kujera ta jefar da dankwali da jakarta ta zauna, gaskiya bazata sabu ba, ta yaya za'ayi ace daga
rabuwar Ma'u da Bashir har ta samu madadinsa kuma dan gayu me kudi da take ganin kamar yafi Bashir
din komai da komai wai me yasa a duk sanda take ganin ta taddo Ma'un seta sake tsere mata ne?

Dole ta tashi tsaye, bazata zuba ido tana kallo Asma'u tayi gaba ba, tunda har ta rabu da Bashir tana
fatan ta qare rayuwarta a haka tana kallonta a matsayin da da ita take kai(Fata na gari lamiri Amirah )

ASMA'U

A qofar gida muka tsaya bayan da yara duk suka shige ciki, Kallona kawai Yusuf yake yana murmushi har
seda na gaji nace

"Ni zan tafi dare yayi kuma gobe ina da aiki"

"Toh agogo, ni ban gaji da kallonki ba ai" ya fada yana gyara tsayuwa.
"Ai kuwa an kusa rufe gate kaga kwanan mota ya kamaka yau a cikin Estate" na fada ina juyawa kamar
zan tafi yayi saurin shan gaba na yana cewa

"Haba hajjaju ki barni mana na kalleki, gobe fa zan tafi se nayi sati daya ban sake ganin fuskar nan taki
ba".

Kamar yarinya haka na tura baki ina hararar sa qasa qasa, se ya faramun dariya yana cewa

"Kinga Asmy ta tana dawowa yanda na santa a hankali, shikenan ki shiga ki kwanta kiyi bacci amma fa
kiyi mafarki na".

Murmushi nayi masa na kauce ina cewa "seda safe mun gode da zuwar mana dubiya kuma"

"Dole na dubashi dan kinsan yanzu banida masoyi sama dashi, tunda ya iya sako mun ke ai ni ya gama
mun komai a rayuwa. Ina ga gobe ma zan koma na sake dubashi kafin na tafi"

"Allah ya yafe maka" na fada ina bude qofa se yayi saurin dakatar dani ya koma gurin motar sa, wata yar
qaramar leda ya miqo mun na karba ina mamakin meye wannan a ciki dan qanqantar ta tayi yawa".

Godiya nayi masa na wuce, ina jin yanda yake bina da kallo har na shiga gida na kullo qofar kafin ya shiga
motarsa suka tafi.

Ban tsaya ba na wuce dakina dan yaran da alama sun kwanta ma, ian shiga na zare rigar jikina ya rage
Doguwar riga ta roba me siririn hannu da na saka a ciki na fada kam gado na zazzage ledar da Yusuf ya
bani.

Yan qananan akwatuna ne suka fado guda biyu, na dauki na Farko na bude, wani hadadden zobe ne a
ciki tsabar handa ya burgeni ban san sanda na ciro shi na zura a hannuna ba yanda ya zauna seka rantse
an gwada ni kafin aka qera shi, juya hannun na ringayi ni kadai ina murmushi.
Kamar ya sani ina son zobe musamman wannan ya tafi dani, dutseb da yake ka sa ma se na ga kamar
Diamond wallahi amma ya za'ayi Yusuf ya siya mun Diamond ring.

Dayan akwatin na bude shi kuma yan kunnene qanana sosai maqale dan kamar zallar dutseb nema
akayisu dashi, ban bata lokaci ba na cire na kunnena na saka su.

Qanana ne sosai amma idan kaga yanda suka yi kyau a kunnena seka dauka wani babban dankunne na
saka. A daren nan na ringa daukar hoton kunnena da zoben, na rasa wa zan nunawa ina shiga whatsapp
naga Alawiyya a online ban bata lokaci na kuwa na tura mata da hotunan se gashi ta kirani ina dagawa ta
fasamun ihu a kunne tana cewa

"Ma'u Allah ya bamu ya taki, kin shiga zawarci da qafar dama. Ashe ina da rabon ganin Diamond ido da
ido a duniya ai kuwa zanzo kallo a cikin satin nan".

Dariya sosai na ringayi, indai tsokana ce ka samu Alawiyya ka gama, ban gama dariyar ba ta sake cewa

"Gobe idan zaki aiki ki saka hannun nan a gaba yanda kowa zega menene a jiki su san fa Yar uwata ta
faso gari wallahi"

"Aa cire hannun zanyi nakai Museum kawai kinga afi zuwa kallo dakyau" na fada mata.

"Ke tsaya ma wai waya baki ni inata murna ban tambayeki ba, ko da yake qila nasan Yarabawan Lagos
din nan ne ko kin san daman ance sun iya kashewa Mata kudi kamar hauka, nidai dan Allah ina daga gefe
ki ringa tunawa da yar uwarki kinji"

"Allah ya yafe miki Alawiyya, ni seda safe wai ina Baban Dija kiketa wannan ihun a daren nan?"

"Ni ki gaya mun dan Allah wa kika samo mana" ta fada tana marairaicewa, kamar an fizgo maganar daga
bakina se ji nayi nace mata
"Yusuf Wunti ne"

Ta buga ihu har seda nayi saurin cire wayar daga kunnena ina jiyo yarinyar da take goyo Afifa ta fasa
kuka da alama itama ta tsorata.

"Wallahi a satin nan se nazo Lagos wannan maganar bata waya bace kai Allah na gode maka Allah na
gode maka, kwanta kiyi bacci yar uwa qila gobe ki ganni kawai dan bazan iya jira ba" Ta fada cikin
tsananin murna kamar wadda akayiwa kyauta kafin ma nayi magana ta kashe wayarta, murmushi nayi a
fili nace

"Allah ya shirya ki Alawa"

Har na ajiye wayar se kuna na janyota na shiga rubutawa Yusuf saqo

"Nagode kwarai amma da baka wahalar da kanka ba"

"Zan iya kira?" ya dawo mun da amsa, kamar nace Aa se kuma zuciyata ta ce mun baze ji dadi ba dan
haka na mayar masa da amsa

"Eh" se gashi kuwa ya kira din.

"Bana so na kira ki fara mun qorafin bacci zakiyi amma da bamuyi magana ba nasan ni yau sedai nayi
kwanan zaune kawai" ya fada a hankali.

"To ai yanzu seka kwanta tunda munyi magana"

"Yanzu kuwa ranki ya dade, karki manta kiyi mafarkina zan kiraki da safe ki bani labari".

Haka mukayi sallama na kwanta rigingine ina tunani, yanda Yusuf yake yi mun tamkar wasu saurayi da
budurwar da suke kan ganiyar soyayya ganai nakeyi kamar ma ya manta da na taba aure harda tarin
Yaya.
Ian daga kwance ina ta faman saqa da warwara, idan naji kamar zuciyata zata karbi tayin Yusuf se kuma
dayar ta bijiro mun da Bashir, ganin kaina na neman yayi ciwo yasa na tattara su duka na watsa gefe na
gayyato baccin dole ina ta kallon zoben hannuna da yake qyalli a cikin duhuj dakin.

Zumbur na tashi na zauna na kunna fitilar wayata na haska cikinzoben sosai, tunawa nayi a jikin akwatin
naga wani Rubutu kamar Letter A da Y anyi musu wani irin design daya ta shiga cikin daya kuma kamar
na hango hakan a cikin dutsen ma ina haskawa kuwa sega wasu qanann rubutu da seka nutsu sosai zaga
gansu cikin dutsen

'Yusuf loves Asma'u' aka rubata, kamar yarinya haka na qanqame hannun nan nayi bacci dashi.

BASHIR

Wani irin zafi da ciwo zuciyarsa ta ringayi masa, a da tuna kalmar saurayi da Aliyu ya gaya masa kadai
take tayar masa da hankali a yanzu daya Gansu a tare bashi da buqatar qarin bayani fuskokinsu kadai
sun isa shaidar alaqar da take a tsakaninsu, yanzu daman Asma'u zata iya son wani namiji a rayuwarta
bayan shi??

Yanzu harta manta da rayuwar da suka gina tsahon shekaru a yan kwanaki ta iya mantawa dashi ta karbi
tayin wani Namiji bayan shi abinda ko a mafarki be taba tunanin faruwarsa sannan har ta iya zuwa
gabansa dan ta nuna masa cewar a yanzu fa baya gabanta ta tigada ta gama da shafin rayuwarsa gaba
daya.

Dafe qirjinsa yayi saboda azabar ciwon da yake masa, tun yana zaune har seda ya kwnata saboda yanda
wani ciwo ya masa rubdugu lokaci daya ya shiga numfarfashi kamar me shirin mutuwa, hankali tashe
Likita da Nurses suka rufu akansa domin ceto rayuwarsa.

Seda sukayi dagaske kafin bacci ya dauke shi dan fizge ruwan da aka daura masa ya ringayi seda Likitan
ya sake gayyato wani suka hadu suka danne shi Akayi masa allurar baccin a jiki kafin ya kwanta lakwas
yana kiran

"Asma'u karki rabu dani, wallahi ina sonki Ma'u karki zabi wani a kaina"
Cikin dare ya farka cikin ikon Allah jikin ya masa sauqi nauyin da qirjinsa yayi masa dazu ya sauka, kulolin
daya gani suka tuna masa da yunwar da yake ji nan da nan ya janyo kwanukan ya bude.

Tuwon shinkafane da Miyar danyar kubewa dataji naman rago da manshanu.

Ba maganar wanke baki ya zuba ya fara ci loma biyu yayi kamar qaramin yaro ya fashe da wnai irin kuka
irin wanda yake bayyanar da quncin da zuciya take ciki ya kifa kansa a qasa ya ringayi.

Likita ne ya shiga dakin dan yayi hasashen yanzu ya farka dan yaga jininsa nada qarfi Allurar bata dadewa
take sakinsa yana shiga ya tarar dashi yana kuka ya isa gurinsa da sauri ya dagoshi yana cewa

"Subhanallahi meya faru badai jikin bane? Wane guri yana maka ciwo ne?"

Saitin zuciyar sa ya nuna masa, likita ya kamashi ya koma kan gadon kafin ya shiga hada na'urar dake
jikin gadon ze sakawa Bashir din sw ya dakata jin Bashir din yana cewa

"Ina sonta Dr, bana so na rasata na rasa yanda zanyi ni na bata komai yanzu kuma bansan ya zan gyara
ba".

Zama Likita yayi a kusa da shi ya zare farin gilashin idonsa yana kallon Bashir yace

"Daman Mace ce damuwarka, Wacece ita?"

"Asma'u, mata ta ta farko kuma uwar yayana. Likita banaan ya akayi shedan yayi mun kururuwa ba nabi
rudinsa na rabu da ita wallahi ina son matata amma duk duniya kowa ya kasa fahimtata".

Shiru Likita yayi yana kallon Bashir na wani lokaci kafin ya dakko kwanon da ya saka abinci ya miqa masa
yana cewa

"Kaci se muyi magana, ina zuwa" ya tashi ya fita ya barshi.


Tura abincin kawai yakeyi, wani bangare kuma yana jin kamar ya sauke nauyi daya furtawa wani cewar
yana Son Asma'u. Amma me yasa likita ya tafi ko dai shina be yarda yana son nata ba kamar yanda kowa
yaqi yarda dashi?

Haka ya ringa tura abincin har ya gama yasha ruwa sega Likitan ya sake shigowa hannunsa riqe da wata
farar roba da gani ta magani ce.

Robar ya bude ya debo kwayoyi qanana guda biyu ya miqawa Bashir yana cewa

"Kasha, ze taimaka maka ka samu sauqin ciwon qirjin".

"Likita kaima baka yarda ina sonta ba ko? Kaima kana ganin bada gaske nakeyi ba" Bashir ya fada ganin
Likita na qoqarin sake fita bece masa komai ba, se ya waiwayo yana murmushi yace

"Bani zaka gayawa ba Malam Bashir, shawara daya zan baka In dai kana so kaci gaba da rayuwa me dadi
ka sauke duk wani girman kai ka nemi abinda kake so. Ita mace ba'ayi mata gadara ka hanzarta kafin
lokaci ya qure maka, gobe da safe zamu sallame ka in Allah ya kaimu tunda na fuskanci ciwon so ne yake
damunka mu kuma bamu da maganinsa sedai mu baka shawarar yanda zaka sauqaqawa kanka indai ba
kana so ka saka kanka a hatsarin kamuwa da ciwon zuciya ba".

Haka ya kwana yana juya maganganun Likita a ransa, qarfe goma na safe aka bashi sallama, kamar mara
galihu haka ya tattara Samuel yazo ya dauke shi ya kaishi gida sanda ya isa yar gasken da alama ko tashi
daga bacci ma batayi ba se ya wuce dakin sa shima ya kwanta akan gado yana ci gaba da saqe saqe.

Kiran Bala ne ya shigo wayarsa, kamar ya share sedai ya daga dan haushinsa yakeji tun ranar daya katse
masa kira be biyo baya ba se yau.

"Allah ya taimaki Engineer Allahh sa ban katse maka aiki ba" Bala ya fada yana yar dariya.
Shiru ya masa be damu ba yaci gaba da cewa

"Gani a Lagos na shigo yanzu, idan anjima ka tashi aiki se na shigo nan ta gurin ku"

"Banje aiki ba ina gida yau" ya fada a cunkushe

"Oh dan Allah? Ta bari yanzu naje na kama daki idan na ajiye kayana se na shigo gidan, a sanarwa
Madam dam ko Karyawa banyi ba na taho" Bala ya fada daga daya bangaren, se Bashir ya ajiye wayar
yana cewa

"Seka iso toh".

Wa ze gayawa tayiwa wani girki ko ya manta da wacce take a gidan sa ne yanzu yake wannan maganar.
Wanka ya shiga yayi, yaji dadin zuwan Balan dan yana da buqatar wanda zasu tattauna akan lamarin
Ma'u, baya so ya sake yanke hukunci ba tareda shawara ba.

Se daya Bala ya iso gidan yaciyo uwar kwalloya kamar me zuwa daurin aure. A palour suka zauna Amirah
ta kawo masa ruwa da lemo daga nan ta shige daki basu sake jin duriyarta ba.

"Mutumin wai Ina Ma'u ne banji labarinta a Gombe ba ko kun daidaita ban sani ba?" Bala ya tambaya
yana shan Lemo.

Bashir yaja tsaki yace

"Tana gidanda yake kusa da namu, kasan wai har Ma'u ta manta dani ta fara sabuwar rayuwa tareda
wani mutum daban bani ba" ya qarasa cikin jin zafin abinda ya ke fadar.

"Dagaske kai amma naji dadi" Bala ya fada cike da murna se kuma daga baya ya gano shirmen da yayi
saboda yanda yaga Bashir ya zuba masa ido yana kallonsa se yayi saurin wayancewa yana cewa

"Ina nufin naji dadi da kace tana kusa daku kaga yanda zaku fi samun daidaito da wuri kenan"
"Bazata saurare ni ba Bala, idan ta ganni nunawa take kamar bamu taba hada komai a rayuwa ba Ka bani
shawara ya zanyi na dawo da Ma'u rayuwata Bala kai kafi kowa sanin ina son Matata"

"Na sani Bashir amma yanzu yayi wuri da ka nuna karayarka, kafi kowa sanin irin son da Ma'u takeyi
maka na tabbata bazata taba iya rayuwa da wani namiji idan ba kai ba. Ko kaganta da wani is sedai tayi
dan ka gani rabka ya baci amma na tabbatar badan wai tana son sa ko akwai wani abu a tsakanin su ba.

Ka qara haquri mutumina karka manta fa laifi tayi maka ka hukuntata idan ka karaya yanzu ka bata qofar
da a gaba zata taka ka yanda take so".

"Laifin me tayi mun Bala? Nifa nayi mata laifi na tirsasata yin abinda yake son raina saboda taqiyi na
yanke hukunci ba tareda tunanin abinda hakan ze jawo mana ba.

Da bakina na saketa nace ta barmun gidana kana zaton zata manta wannan ta sake dawowa gareni?
Bafa abinda tayi mun son zuciyata ne kawai ya kaini da dana sani" Bashir ya fada a matuqar karye.

Bala da yake faman antaya masa harara yayi saurin tareshi yana cewa

"A wata hudun shine har ka karaya haka kake nema ka zubarwa da kanka mutunchi haba Bashir, kai kana
zaton Asma'u zata iya zaman aure da wani ba kai ba wallahi ko bayan shekara dari nasan kai zata zaba.

Kai duk duniya fa babu wanda besab irin son da take yi maka ba dan haka ka kwantar da hankalin ka
mutumina, in banda kai ma yanzu ga yammata nan a gari birjik basu auruba se bazawara me yaya shida
kake zaton daga rabuwarta dakai zata samu miji?

Ka saki jiki mutumina ka ci gaba da harkokin ka muna nan wallahi zata zo har cikin gidan nan ta nemi ka
mayar da ita".

Kallonsa Bashir yake har ya gama magana. Ko kusa bega alamar abinda Bala ya fada a wannan karon me
yuwu ba bane amma idan ya tuno tarin qaunar da takeyi masa a baya fa se yaga kamar hakan zata yuwu.
Amma ze gwada koda na wata dayane ya gani amma fa daga haka baze iya qara haquri ba, in har bata
sakko ba to shi ze ajiye girman kanya nemi sulhu da ita kamar yanda likita ya bashi shawara.

A gidan Bala ya wuni har dare, abinci kuwa se siyowa sukayi dukda har sannan ba wai ya ji garau bane.

Haka ya qarasa cinye satin kafin ya koma aiki yayi iya qoqari gurin rage damuwarsa amma abin ya
faskara akullum cikin tsoro da fargaba yake kwana da tunanin rasa Asma'u. Sam ya kasa samun kwarin
guiwar da Bala yake ta nanata masa yana ganin lokaci yayi da zeje ya zube guiwoyinsa a gabanta ya
roqesta koda kuwa zata sake koda masa marine indai hakan ze sakko da ita daga fushin da take dashi ya
amince ta tsinko darbejiya ma ta dake shi son ranta.

Ayi manaji da wannan please na shiga hidimomi ne

WATA KISHIYAR

(ALKAHIRI CE KO SHARRI)

Na Maryamah Farouk

(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)


Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 54

Washe garin ranar tun goman safe Bala ya sake zuwa, yau ma wuni sukayi dai suna ta tattaunawa duk
dai akan Asma'un ne har kuma yamma Bala beyi shirin tafi ba seda Bashir da kansa ya tambayeshi wai ba
yace aiki ne ya kawo shi ba yaushe ze fara.

Cikin kame kame Balan yake ce masa

"Eh daman aikin na kwana daya ne mun gama kawai dai ina so na huta ne. Ni na gaji da zaman gida ma
mu fita waje mu sha iska kuma ita wannan matar daman haka take bata dafa abinci ne?"

Shiru Bashir yayi masa harya qaraci surutunda yayi shiru, be haqura ba bayan wani lokaci ya sake ce
masa su fita waje dole ya takurawa Bashir din seda suka fita wajen suka saka kujeru suka zauna.

Basu jima a gurin ba motar makaranta ta sauke yara, gaba daya suka gaishe su, Bala ya kamo hannun
Abdallah yana cewa

"Abdallahn Mami an dawo kenan. Ya naganku a school Bus ina Mamin taku?"

"Daman a school bus muke dawowa" Abdallah ya fada yana shigewa cikin gida yabi bayan yan uwansa.

"Wai mutumin ta dena dakko yara daga makarantar kenan?" Bala ya fada yana yar dariyar nan irin ta
wanda yaso munafunci akayi sa'a ko kallonsa Bashir beyi ba hankalinsa yana kan wayarsa da yake
dannawa.

Kusan minti talatin wata hadaddiyar mota Toyota latest model Baqa ta kunno kai cikin layin, daga Bashir
har Balan da ido suka bita harta tsaya a daidai qofar gidan Ma'u, seda aka kwashi yan mintina kafin qofar
ta bude ta zuro fararen qafafunta da suka sha Jan lalle sukayi shar dasu ga wasu hadaddun takalma na
yan gayu masu tsinin dunduniya data saka.
Lokaci daya ta fito gaba dayanta, tana sanye da straight gown ta Ash din Leshi tayi daurin nan nata na
tsokano sharia kunnenta saqale da AirPod tana murmushi da alama waya takeyi ba tareda ta kalli ko ina
ba ta qarasa bakin qofa ta kwankwaso Amnah tazo ta bude tareda karbar jakar hannunta suka maida
qofa suka rufe.

A tare Bashir da Bala suka sauke wata Ajiyar zuciya. Shi Bashir tashi ta ganin Asma'u ce ita kadai ta fito
daga motar saboda yanzu har fargaba yake yaga sabuwar mota me kyau a layin tunda Asma'u ta fara
kule kulen nan idan yaga mota ta shigo zuciyarsa ta ringa lugude kenan harse yaga wanda yake cikinta
sannan hankalinsa yake kwnaciya.

Bala kuwa tsabar yanda Haduwar Ma'u ta tafi dashi ne se bude baki yake amma ya kasa cewa komai
harta shige gidan se ya sauke ajiyar zuciya ya waiwaya yana kallon Bashir yace

"Kaga wata Arniyar mota Alaji ga kuma hadaddiyar mata ta fito daga ciki kai ina ma ace na samu irinta ai
wallahi komai ma zan iya bayarwa indai zan mallaki wannan".

"Asma'u ce fa" Bashir ya fada yana jifansa da wani kallo, Bala kuwa ko a jikinsa sema tabe baki da yayi
yace

"Ita dinfa, Allahna tuba ni ko Asma'u na samu ai da mugun gudu zan karbeta dan ni nasan darajar irinta.
Ai wallahi ban taba sanin kai lusari bane se randa kace mun ka saki Ma'u, yo Allah na tuba ko yankar
naman jikina zata ringayi ai zan jure kai in fita ma a kalleni ace ga irin matar da nake aure ma ai martaba
ce".

Sakin baki kawai Bashir yayi yana kallon Bala daya dage yana rattabo magana, Lusari daya kira shi ma be
dame shi ba kamar jingina kansa da Ma'u da yayi. A mugun fusace ya shaqo wuyansa jin yana ci gaba da
maganarsa yace

"Idan ka sake hada kanka da Matata sena yanke maka harshe..."


"Malam tsohuwar matarka dai ko ka manta ka sake ta ne, kuma wallahi dan dai bazata saurareni bane
amma duk da haka ma bari kaji sena gwada sa'a ta waya sani ko rabo na ne ya rantse Allah ya matse ka
ka saketa" Bala ya fada yana banbare hannun Bashir daga wuyansa.

Tsabar mamaki Bashir daskarewa yayi a gurin be dawo hayyacinsa ba seda Bala ya kusa barin layin ko
kafin ya yunqura ma ya bace masa.

Naushi ya kaiwa Iska cikin azababben kishi da fushin da suka turnuqeshi.

Kenan angiza me kantu Bala ya ringa yi masa yana nuna masa aibun ta yana qara kambama masa
laifuffukanta har seda ya rabu da Ma'u shine yanzu ze zo yana cewa idan ya sameta shi baze rabu da ita
ba. Wai ma ina hankalinsa yake da duk be taba lura da hakan ba se yanzu?

"Kaico na dana zama me daukar zugar was akan iyalina, kaicona ni Bashir da na fifita lalataccen Aboki
akan masu gaya mun gaskiya" ya fada yana dafe kansa.

Cikin gidansa ya koma suka hadu da yan biyu zasu fita da gudu ya kauce musu yana binsu da kallo cike da
tausayin kansa.

Haka kawai ya raba musu kai ya saka suna rayuwa tsakanin gidaje guda biyu. Shidai ya yarda da qaddara
ce ta gifta data tilasta rabuwarsa da Ma'u kuma Allah kadai yasan hikimar sa tayin haka. Baze sare ba
yanzu nema ze daura dambar gyaran kuskurensa ya kuma maido da Asma'u cikin rayuwarsa kota halin
qaqa.

Dakinsa ya shiga ya tarar da Amirah tayi daidai akan gado tana sauke numfashi, fuskarta ya kalla kafin ya
kalli qasan Tiles yaga amai ne a Gurin. A mugun fusace yace mata

"Ki tabbata kafin na shiga na fito kin gyara gurin nan yanda kika tarar dashi idan ba haka ba na lahira se
ya fiki jin dadi yau a gidan nan" yana gama fada yayi gaba ze shige bandaki ya jiyota cikin kuka tana cewa

"Nifa bani da lafiya, zuwa ma nayi na gaya maka shine amai ya kamani gaskiya bazan iya tashi bama bare
na gyara guri".
"Ko mutuwa kike kina tashi se kin gyara gurin nan, duk gidan nan nan gurin ne yayi miki kama da kizo ki
zuba qazantarki? Amma karki kwashe ki jira na fito na tarar dashi a nan" ya shige Bandakin ya barta a
gurin.

Yanayinsa da ta gani tasan tabbas ba tausaya mata zeyi ba idan ya fito din, haka ta tashi ta dakko
tsintsiya da abin kwashe shara ta debe kafin ta debo ruwa da mopper ta gyara gurin se haki takeyi tana
gamawa ta wuce dakinta ta ta fada kan gado kawai ta fashe da kuka.

Wannan masifa har ina? Ace kana da ciki amma banda hantara da kyara ba abinda yake shiga tsakaninka
da uban cikin se baqin rai to ko ana so ko ba'a so seta haife cikin nan sedai baqin ciki ya kashe mutum.

Bashir kuwa yana shiga ruwa ya sakarwa kansa ba tareda ya cire kayan jikinsa ba. Kalaman Ba ne suke
masa yawo a kwakwalwa suna barazanar fasa masa ita.

Shi Bala zece yana son matarsa? A yanda ya dauki Bala ya zata ko mutuwa yayi se inda qarfinsa ya qare
gurin kare masa martabar gonarsa amma se gashi da ransa rabuwa kawai sukayi yana iqirarin idan zata
so shi ze aure ta gaskiya dole ya koyawa Bala hankali ta yanda ba matarsa ba ko wata can a gari aka saka
baze sake sha'awar cewa ze aureta ba.

Tsabar yanda kansa ya dauki zafi haka ya fito jikinsa na digar da ruwa ya manta da kaya a jikinsa seda ya
kai tsakiyar dakin kafin ya ja tsaki ya koma ciki, wanka ya sakeyi ya fito.

A gurguje ya shirya, gidan Musa yake so yaje yanzu yana buqatar wanda ze fadawa abinda yake ransa ko
zeji dadi.

Sanda ya fito bebi takan Amirah ba, a bakij qofa ya hadu da Jafar ya taho da paper bag a hannunsa suna
zuwa kusa yaji qanshin Snack be bata lokaci ba ya miqawa Jafar din hannu ya kuwa bashi ya tsaya kawai
yana kallonsa.

Meatpie ne guda uku manya a ciki, se ya zaro daya ya miqawa Jafar din Murya a cunkushe yace masa
"Dakko mun Exotic ne sanyi" Jafar ya kwasa da sauri ya wuce Kitchen kafin ya dawo har Bashir ya kunna
mota yana bashi kuwa ya qara gaba.

Yana tafe yana cin Meat pie yana kora lemonsa can qasan zuciyarsa kuwa yama rasa wanne tunani ze
kama yayi a haka ya qarasa gidan Musa ya tarar be taso daga aiki ba se ya kirashi a waya yace masa yana
hanya ya kusa qarasowa dan haka ya jira shi.

Seda sukayi sallar Magriba sannan suka shiga gidan. Musa na tattare kayan da suke kan kujera yace

"Se haquri Engineer kasan gidan Gwauro ko ina ma zubarda kaya muke tunda bamu da masu tattare
mana"

Bashir dai yaqe yayi har Musa ya gama ya dakko musu ruwa da Lemo da Abincin daya taho dashi ya
zauna se ya kalli Bashir da yayi shiru ya zubawa guri daya ido yace

"Yadai Bash naga kayi shiru ko dai jikin ne har yanzu?"

Numfashi Bashir ya sauke yana gyara zama yace

"Musa akwai matsala ina jin kamar kaina ze fashe wallahi damuwa tayi mun yawa".

Musa daya debi abinci ya kai baki yayi saurin hadiyewa yana kallon Bashir ya gyara zama yace

"Wace irin Matsala kuma Bashir meya faru?"

Ba bata lokaci Bashir ya shiga lissafa masa abinda ya faru tun daga kan dalilin sakin Ma'u har zuwa
yanayin da ake ciki a yanzu haka da maganar da Bala ya fada masa. Musa da tuni ya sume a zaune yana
kallon Bashir seda ya kai aya kafin yaja numfashi ya dire yace

"Gaskiya Bashir ka tafka wauta qundumemiya ma kuwa kai wa yace maka ana rabuwa da matar fari,
matar dakuka sha wahalar ku tare sannan yanzu ka saketa akan wata can da ka ganta rana tsaka Bashir
ka rabu da matar ka uwar yayanka gaskiya ka bani kunya ka kuma bani mamaki tsahon lokacin nan ace
baka tare da Asma'u amma baka gaya mun ba.

To ni yanzu me zanyi maka ma ai ka riga kwabarka tayi ruwa sedai na baka haquri kawai Allah ya kawo
maka dangana amma duk macen dakayiwa haka ka sake ta akan yar uwarta mace gaskiya da wuya tayi
haquri ta sake dawo maka dan ka rigada ka nuna mata iyakarka ka nuna mata cewar waccen ta fita
martaba da mutunchi a gurinka to zaman me zata sakeyi da kai?"

"Haba Musa kaida nazo neman mafita a gurin ka ya zaka ringa magana haka?

Dan Allah ka taimakamun ka bani magita ina son matata bana so na rasata" Bashir ya fada kamar me
shirin saka kuka.

Musa kuwa Ido ya saka masa yayi tagumi yana kallonsa har yayi ya gama sannan yace

"Kanaji ko shawarar da zan baka kawai ita ce ka tafi malam ka gwada sa'arka, wani girman kai duk ba
naka bane yanzu dan ka rigada ka kwafsa yawwa kaje ka sauke kai qasa ko roqeta in Allah ya soka ta
haqura ta dawo maka shikenan amma dai Asara kam ka tafka wallahi".

Haka suka rabu da Musa ya koma gida yana sake tunanin abinda ya gaya masa kuma ya tabbatar hakan
shine mafita dole ya nemi yardar Asma'u dan baze tsaya yayiwa kansa salalan tsiya ba.

Ya tarar da Amirah na fama da kanta tayi amai ta galabaita kamar bazata kai ba, dole ya dauketa suka
tafi Asibiti saboda yanayin jikin dole se gado aka bata. Seda ya biya duk abinda ya kamata kafin ya barta
ya tafi gida da yaje be tarar da Yaran ba Aliyu ne kadai yace sauran suna gidan Mami. Be damu ba yayi
kwanciyarsa, dan yanzu yafi samun kwanciyar hankali ma idan suna can saboda anan sun ringa tsokanar
Amirah ita kuma tayi ta sababi tanazage zage.

Washe gari ya kamata ya koma aiki haka ya tattara ya fita seda ma ya kusa isa ya tuna da Amirah dake
Asibiti be biya ya dubata ba bare ya kai mata abinda zata ci duk da dai Asibitin suna bada Abinci.
A waya yayi order abinci ya basu Adireshin Asibitin dan baze iya komawa ba, haka ya wuni sukuku a
gurin aiki se sannu ake masa dan duk a zatonsu jikin nasa ne har sannan be gama warwarewa ba haka ya
tashi kai tsaye ya wuce Asibitin dan duba halin da Amiran take ciki.

Da kuka haiqan ta tareshi tana masa qorafin baya sonta be damu da ita ba tunda ya banzatar da ita a
Asibiti be sake bi ta kanta ba. Ganin mitar bame qarewa bace ya tafi ya barta dan abinda yake kansa ma
a yanzu ya isheshi bayay buqatar qarin wani abun kuma.

Ya isa gida ya kasa tsaye ya kasa zaune. Tunanin yanda ze tunkari Ma'u yakeyi, meze ce mata? Ta yaya ze
tunkareta?

Wayarsa data dauki qara ce ta katse masa tunani, shnan Dada da ya gani ya sakashi dagawa da sauri.

Bayan sun gaisa take ce masa

"Bashir Ashe Amirah bataji dadi ba har tana Asibiti?"

"Eh wallahi Dada jiya da daddare ne zuwa yau amma gobe ma zasu sallameta ai" Ya fada yana mamakin
waya kirasu ya gaya musu bata da lafiya.

"Toh ai shikenan Allah ya bada lafiya amma ya kamata ta samu wani babba a kusa da ze ringa kula da ita
saboda yanayin jikin kaga tana da zafin laulayi dole seta samu mataimaki"

"To ai anan din ma ba abinda takeyi tun tana da lafiyar ma se shirme kawai ta iya" ya fada a hasale

"Haka za'ayita haquri dai, seka turo da kudin jirgi na wanda ze zo ya tayata zaman dai, ya bangaren su
Asma'u kuwa in ce dai abubuwa sun dai daita ko?"

"Hmmmm" kawai Bashir ya fada daga nan sukayi sallama dan besan me ze ce mata ba ma, qarin haushin
sa ma wani da tace za'a turo ya taya Amirah zama in dan ta shine a barta ta gane kurenta wallahi haka
ba yadda ya iya ya turawa da Naziru kudin dan yana tunanin Fainusa za'a turo ko banza gidan ya samu
kulawa ai.

Shiru ya sakeyi yana tunani, kiranta zeyi ko kuwa kawai zuwa zeyi suyi magana fuska da fuska?

Yanke shawarar ya fara kiranta yayi a waya nan da nan yayi Na'am da wannan shawara ya shiga loda
lambar wayar Ma'u da ya dade da haddacewa ya dannan mata kira.

Seda tayi ringin harta katse bata dauka ba, be haqura ba ya sake kira nan ma bata daga ba seda yayi
mata kira uku ana hudu ta daga cikin muryar nan tata me sanyi tayi masa sallama.

Shiru yayi, ta sake maimaita sallamar se kawai ta kashe bayan data ja qaramin tsaki. Be sare ba ya sake
doka mata kira, cikin dan fada fada ta daga wannan karon tace

"Waye wai? An kira ni kuma anqi ayi magana" jin ya sakeyin shiru ta sake kashe wayarta shi kuwa tsabar
mamakine ya daskarar dashi wannan karon, kenan ta goge lambarsa ma kai ko ta goge ai bazata ce bata
gane lambar akai ba shi Ma'u zata ce waye sannan ta kashe masa waya???

ASMA'U

Wato wata irin sabo da shaquwa da ban taba tsammani ba ya ringa shiga tsakanin na da Yusuf. Zuwa
yanzu idan muka wuni bamuyi magana ba ji na nakeyi kamar bani da lafiya.

Dukda ba wata doguwar magana mukeyi ba amma duk sanda ya kirani seya gaya mun maganar da zatayi
Rugurugu da zuciyata ta tsaya mun a zuciya har zuwa sanda zamu sake magana.

Aikina kawai nasa a gaba gefe ina kurbar madarar soyayya a ruwan sanyi wadda har yanzu ni ban yarda
wai ina son sa bane,kawai ina jin dadin magana dashi na kuma dauke shi kamar wani Aboki ne domin dai
so dayane kuma Bashir nayi wa shi.

Daren yau ina zaune nayi daidai a qasa ina duba wasu takaddu dana taho dasu daga office, gaba daya na
gaji, Allah Allah nake na gama na kwanta na huta ga yara da suka isheni da hayaniya na korasu daki dan
gaba daya yanzu kusan rayuwarsu a nan gidan sukeyinta tunda Bashir ya kwanta rashin lafiya suka dawo
kwana anan gidan Aliyu ne kadai yake komawa se fa Jafar wata rana idan yaga dama ya bishi su tafi gida.

Wayata da na saka a chaji ce ta dauki qiwar in tashi na dakko tasaka na barta tayi tayi harta katse dan
kanta idan na gama na kira dan nasan baze wuce Yusuf ba ko sabon Mayen daya maqalemun
Hayatuddeen.

Jin ana ta kira ba qaqqautawa ya sakani jan tsaki na miqe na jawota, lambar Bashir ce, na tsurawa wayar
ido ina so na gano dalilin da ze saka Bashir kirana a waya yanzu to qila yace Yayansa su tafi gida ko amma
me yasa baze kira Aliyu ba tunda yana da waya ko Amna se ni ze kira?

Ina wannan tunanin har kiran ya sake katsewa wani ya shigo sena daga na saka a kunnena tareda yin
sallama. Shiru naji anyi, na cireta na duba dan na tabbatar ko kiran katsewa yayi amma naga sakannin
suna tafiya na sake maimaita sallama naji ba'a amsa ba se kawai naja tsaki na kashe.

Ta yuwu ma bani ze kira ba ko kuma besan kiran ya taho bama gaba daya ina qoqarin ajiyewa se ji nayi
ta sake daukar qara alamar shigowar wani kiran hakan ya tabbatar mun da yana sane kenan wulaqancin
nasa ne ya motsa dan haka na gyara zama tare da dagawa nace

"Wai waye ne yake kira ana magana kuma anyi shiru? Idan baka da abin fada ni ina da aikin yi" na sake
kashe wayar.

To haka kawai ze ringa kirana yamun shiru me zan masa, ni kadai nayita mita ina ci gaba da duba
takadduna can jimawa se shigowar saqo naji nayi banza da wayar ban tashi dubawa ba seda na gama
abinda nakeyi kaf na je kwanciya dan har na manta ma seda na janyo ta zan saita Alam kafin naga saqon
akan wayar se na bude na fara karantawa kamar haka.

"Zuwa ga Ma'una. Nasan ni mai laifi ne a gareki kuma na karbi kuskurena da hannu biyu sannan a shirye
nake da karbar ko wanne irin hukunci daga gareki in har hakan ze saka ki huce daga abinda ya faru.

Kiyi haquri mu komawa kyakykyawar rayuwar da muka faro ko dan saboda so da qaunar da yake
tsakanin mu.
Bashir".

Dogon tsaki naja bayan dana gama karanta saqon nasa nan take na goge. Ashe ma nayi haquri ne mu
komawa rayuwar mu, juyawa nayi na kwanta ina rufe idona na tashi na zauna ina sake tuna dalilin daya
saka Bashir yimun sakin wulaqanci.

Akan Mace fa, me daura zani da dan kwali Macen ma yarinyar dana raina da hannuna harta zama abin
sha'awar daya gani ya aura ya hadamu zaman kishi da ita a saboda ita ya kassaramun rayuwa ya hadani
da zawarci shine yanzu saboda tsabar rashin kunya ze turo mun wannan saqon yana tunanin wannan ya
isa ya wanke tarin laifin sa a gurina kenan? Lallai ba shakka ya dauke ni sakarya.

Baccina na kwanta, washe gari da wuri muka fita tun a hanya kuwa na kaftawa yaran warning akan kan
kar wanda ya sake zuwa ya kwanar mun a gida kowa ya zauna a gidan ubansa. Idan taqamarsa su to
yanzu na rigada na saki zuciyata ko da su ko babu su a tare dani babu abinda ze chanza daga walwalata.
Na barsu a hannun ubangiji nasan ze kulamun dasu.

Sau kusan hudu ina ganin missed calls dinsa a office dinma amma naqi dagawa to me ze gayamun wai?
Ko kuwa ni din an gaya masa sakarya ce da zezo yana wani kirana a waya kuma na kulashi.

"Ko dan darajar so ai zaki iya saurar sa Ma'u" wata zuciya ta raya mun se gashi yau nida kaina na
qundumawa wannan zuciya tawa me qoqarin tsayawa Bashir zagi, ban haqura ba na janyo wayata na
goge lambarsa daga ciki sannan na dora layin akan tsarin da kiran baquwar lamba baze shiga ba sedai
naga missed call ni na kira dan idan ma nayi blocking nasa ze iya chanza lamba ya kira amma yanzu kuwa
koda ace ze sake lamba dari bazata taba shigowa ba.

Ina shirin tashi Yusuf ya kirani. Duk wunin ranar bamuyi waya ba saboda ya gaya mun tun daran jiya
daman yana da Meeting se sanda ya samu sarari ze kira shine se yanzu.

"Nayi fushi" ya fada bayan da muka gaisa.

"Me kuma ya faru? Kai da waye zakayi fushi?" Na tambaye shi dai dai sanda na shiga motata.
"Badai se yanzu kike tashi daga aiki ba?" Yusuf ya tambayeni sanda yaji na kunna motar, seda na mayar
da wayar jikin sipikar motar kafin na amsa shi da cewa

"Wallahi se yanzu, kwana biyun nan ayyuka ne suke yi mun yawa shiyasa nake dadewa a office"

"Gaskiya aikin nan yana wahalamun da mata ya kamata na dauki mataki akan sa fa, ko dai a rage
yawansa ko kuma suyi asarar haziqar ma'aikaciya wadda mayar da kamarta se an duba".

Murmushi nayi ina ci gaba da tuqina nace

"Naji kace kayi fushi, me akayi maka ne?"

"Oh tambaya ma kikeyi? Kece mana. Gaba daya yau ko kirana bakiyi kinji ya nake ba ko da yake daman ai
baki damu dani ba, ni kadai nake damuwa dake idan banji lafiyarki ba amma ke nasan ma mantawa
kikeyi dani idan ban kira ba".

Yanda yayi maganar ne ya bani dariya har seda na dara kafin bace

"Haba dai waya gaya maka ban damu dakai ba?"

"Ni na ga haka da kaina amma ki fada naji idan kin damu dani din"

"Na damu da kai mana ko ban fada maka ba kaina ai ka sani" na sake fada. Seda yaja wani murmushi
kafin yace

"Na dai jiki kawai amma ni banga haka ba. Kinga ni ina sonki amma nasan ke duk duniya ma baki da
maqiyin daya kaini yanzu".
"Haba wacce irin magana ce wannan Yusuf? Taya zaka ce bani da maqiyi kamar ka yaushe na gaya maka
haka?"

"To idan ba gaskiya bane ki fada da bakinki cewar kina sona mana sena yarda" ya sake fada yana yin
qasa da murya kamar me rada. Ba tare da tunanin komai ba nace

"Ina sonka mana Yusuf kaifa dan uwa....."

"Karki qara komai kin rigada kin gama magana ai tunda har kika furta kina sona da bakin ki yanzu zan kira
Alhaji Qarami na gaya masa. Daman yace na nemi soyayyarki shi kuma ze tsaya mun da izinin Allah a
wannan karon sena sameki Asmyta" Yusuf ya katse ni ciki tsananin murnar da muryarsa ta kasa boyewa.

Be barni nayi magana ba ya kashe wayar, mamaki da dariya suka kamani duka lokaci daya. Wai da
girmana da komai Yusuf yayi mun wayo dukda ni bada wata manufa na fadi Ina son sa ba kawai dai na
fada hakan ne jin yanda yayi magana bawai dan har cikin zuciyata abin da yake raina kenan ba.

Tuqina naci gaba dayi hankali kwance harna isa gida. A bakin qofa na tarar da Bashir a tsaye ya harde
hannaye da alama ni yake jira, na gama daidaita fakin kafin na fito fuskata a sake na shiga gaishe shi ina
qare masa kallo yanda naga gaba daya ya zabge yayi baqi kamar wnada yayi jinyar shekara daya.

"Bari na shiga sena turo maka yaran seda fa na gaya musu su ringa zama a gidan ubansu amma saboda
rashin ji irin nasu shine suka taho Yi haquri yanzu dana shiga zan tattaro maka su kuwa" na fada ina
qoqarin wuce shi na shiga gida seya dakatar dani da cewa

"Ba gurinsu nazo ba Ma'u gurinki nazo ina so muyi magana".

"Toh gurina kuma?" Na fada ina kallonsa da mamaki, be amsani ba na ci gaba da magana ina cewa

"Kaga yanzu na dawo ko sallar magriba banyi ba ga gajiya na kwaso, idan ba abin sauri bane ka bari ko
zuwa gobe Juma'a da wuri zan taso ko kuma Weekend ma kawai kaga ina gida se muyi maganar"
"Maganar sauri ce Ma'u, na kiraki a waya ma bata shiga na tura miki da saqo duk babu amsa" ya fada
yana tsatstsareni da ido. Ko a jikina, gaba na sakeyi ina cewa

"Koh? Qilan saboda idan banyi saving lambar ba kira baya shigowa ne, to tunda kace abin sauri ne bari
idan na dan huta zan aiko yara se su gaya maka" na fada ina tura qofa na barshi a tsaye.

Har qarfe tara na gama cin abinci kenan sega Abdallah wai Abbi yace yana jirana. Da mamaki na kalle shi
nace ina Abbin yake dan nifa shaf na manta da mun hadu da wani Bashir ma har munyi magana ban
qarasa cika da mamaki ba seda Abdallan yace mun wai ai yana qofar gida tun dazu ya saka kujera ya
zauna.

Haka na saka dogon hijabi ba na fita saboda dai wulaqanci babu kyau. Yana nan zaune kamar wani sabon
Almajiri na zauna a Empty kujera dana tarar ina cewa

"Kasan shaf na manta ma da munyi magana, koda yake ban zata zama kayi ba tunda nace idan na gama
zan aiko yara su kiraka ai".

Zamowa qasa naga Bashir yayi kamar wanda yaje neman gafara a gaban Dada ya kama qafata na janye
ya riqe qasan hijabina yana cewa

"Ma'u haquri nazo baki akan abinda ya faru tsakanin mu. Wallahi nayi nadama, sharrin shaidan ne ya
angizani kuma na gane kurena na yarda idan babu ke a tare dani rayuwa ta bazata taba cika ba. Dan
Allah ki yafe mun ki Yi haquri mu koma wa auran mu nayi miki alqawari baza kiyi nadamar komawa zama
dani da dan nasan kina sona nima ina sonki zamu ci gaba da zaman mu cikin aminci kamar yanda muka
faro shi".

Ido kawai na saka masa ina kallon wannan wasan kwaikwayo har ya kai qarshe kafin na miqe ina cewa
"Ka tashi dan Allah ko da yake kai naga baka tsoron kaga hotonka a Ticktock yanzu idan ba haka ba meye
na durqusa mun. Asma'u ce fa Bashir daka danqara mun har saki biyu saboda matar so ka kuma bani
rana daya tak dana tattara inawa inawa na bar maka gida har ka manta wannan shine zaka zo kana
durqusa mun wai nayi haquri na komawa auranka?

To bari kaji, shi son da kake iqirarin a koma Saboda darajar sa daga sanda ka tsinke igiyoyin auran nan
suka tattaro Son gaba daya sukayi awon gaba dashi, dama ai saboda auran ne ko tunda babu shi kaga
babu sauran wani so tsakani na dakai, ko da kaga ina gaisuwar mutunci dakai darajar zuri'ar da take
tsakanina dakai ne amma badan haka ba kai Bashir baka isheni ni Asma'u kallo ba ka sani.

Ada tabbas na So ka amma a lokacin da bansan menene So ba ba ayanzu da na hadu da limamin So ya


fayyace mun shi na gane ma'anarsa ba. Dan haka idan kana mafarkin ni zan komawa auranka to ka tashi
dan kuwa tamkar a baka tsinke a ce ka zunguro sama ne kaga kuwa wannan abu ne da baze taba yuwu
ba kayi sake Bashir nayi maka nisan da har abada bazaka tarar dani ba"

ina gama fadar haka nayi shigewata gida na barshi a tsaye zuciyata kuwa yanda take bugawa ina
tsammanin wanda yake tsaye kusa da ni ma ze iyajin bugunta.

A karanta da haquri, wani qundumemen uzuri ne ya taso mun beyond my control [11/02, 12:17 am] Sisi
love:

WATA KISHIYAR

(ALKAHIRI CE KO SHARRI)

Na Maryamah Farouk

(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)


Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 55

BASHIR

Kamar wani dolo haka ya rakata da idanu harta bacewa ganinsa kafin ya sauke ajiyar zuciya me qarfi ya
miqe daga durqushen da yayi yana jin kamar an sare masa qafafu tsabar yanda jikinsa yayi sanyi.

Tabbas Wannan ba Asma'u daya sani bace data jiqu cikin so da qaunar sa, ba Asma'un da take shiga
damuwa saboda damuwarsa ba bace wadda take hana kanta bacci a duk sanda yake cikin damuwa ko
bacin rai wannan wata Asma'u ce ta daban a gabansa.

"Idan ma kana mafarkin zan koma gidan ka to ka farka dan nayi maka nisa na har abada Bashir kayi sake"
kalamanta suka ringa dawo masa a sanda yake jefa qafafunsa inda shikansa be sani ba dan burinsa a
sannan ya ganshi a cikin gida kawai ya samu makwanci.

Shirim ya fada kan kujera ya dafe kansa da hannaye biyu yana juya shi. Wai menene SO?Yaya SO yake?
Menene tattali da kulawar da mace take da buqata wanda Asma'u ta rasa a gurinsa da har take iqirarin
ta samu wanda ya fayyace mata su?

Allah shine shaidar sa yana son Asma'u son da duk duniya be taba yiwa wata mace irinsa ba. Yana sonta
tana kuma da wani matsayi na daban a zuciyarsa ta yanda tayiwa sauran mata zarra amma kowa ya gaza
fahimtarsa mutane suna yi masa gukunci da zahirinsa ne kawai ba tareda sanin ainihin abinda yake cikin
zuciyarsa ba wai me yasa kowa ya gaza fahimtarsa?

Dole ya san abinyi ba ze zuba ido yana gani ya rasa Asma'u ba faruwar haka daidai yake da yankewar duk
wani farin ciki da walwala daga cikin rayuwarsa ya shaida hakan dan kuwa gashi a iya lokacin da suka
rabu tun sannan be sake kwanan farin ciki ba. A kullum sabuwar damuwa da tashin hankali ne suke dirar
masa.

Gidansa ya rushe, nutsuwar sa ta gushe lafiyarsa kanta ta tabu a cikin qasa da watanni shida besan yaya
ze tsinci rayuwarsa ba ace ze qareta ba tareda Asma'u a cikin ta ba.

Wai ma wane ibtila'i ne ya haushi da har ya kaishi ga sakin Ma'u?

"Qaddarah" zuciyarsa ta raya masa se ya dafe kansa da hannu biyu yana fadin

"Hasbunallahu wani'imal wakeel" a fili yana jin yanda qirjinsa yake masa quna wanda ya zame masa jiki
yanzu a duk sanda ya zauna yana tunanin makomarsa da Ma'u to se yaji wannan ciwon kamar
numfashinsa ze dauke wani lokacin.

Wayar sa ya janyo daqyar idanunsa sunyi jajir sun kawo ruwa, lambobinsa yake bi yana karantawa ya
rasa waze kira a yanzu. Duk wadanda ya kamata ya fadawa damuwarsa a yanzu ya dade da datse alaqa
me kyau a tsakaninsu saboda a da yana ganin kamar suna masa katsalandan a rayuwarsa da qoqarin
nuna masa yanda zeyi gashi yau ranar su tazo amma bashi da kwarin guiwar kiransu.

Lambar Bala ya kalla, wani tuquqin baqin ciki ya taso masa nan take ya danna mata block tareda goge ta
gaba daya. Ba tun yanzu ya kamata ya ankare da ingiza me kantu da Bashir yake masa ba amma se yanzu
da komai ya lalace sannan ya fito masa da ainihin kalar sa gaskiya.

"Allah sarki Aliyu, Amini na kwarai Rahmar Allah ta kai maka" ya fada yana dauke kwallar data ziraro
masa ta gefen ido, yana kewar Aliyu da gasken gaske Aboki ne irin wanda ya zamar masa dan uwa
wanda samun irinsa se an tona.

Aliyu ne kadai yake iyawa da halinsa, koda ace ya nuna masa gaskiya yaqi binta baya haqura ze yi ta naci
da nusar dashi har se dan karan kansa ya fahimci hakan ya kuma ya aikata abin hirar su ta qarshe ta sake
fado masa snada yake jaddada masa daya kula da Asma'u domin matar rufin asiri ce Allah sarki ashe shi
ya hango masa abinda shi be gani ba gashi yanzu a daidai sanda Asirinsa ke neman ya bankade Aliyu
baya nan ballan tana ya tayashi maido da mayafin ya lullube rayuwarsa.
Abubakar ne ya fado masa a rai, shi kuwa be yi wannan riqar da ze iya tunkarar Abubakar a yanzu ba
bayan duk abubuwan dasuka faru tundaga auransa da Amirah zuwa yanzu daya sakar masa qanwa ya
tabbatar ma baze saurare shi ba idan kuwa ya saurare shi to tabbas maganganu ze yayyaba masa da se
yayi dana sanin kiransa.

Haka ya ringa saqa da warwara, shi da kansa ya tsinewa hali irin nasa yafi sau dubu ganin cikin lambobin
sama da dari biyar da suke cikin wayarsa ya rasa shaqiqi daya da ze kira ya gaya masa damuwarsa ya
bashi shawara akai.

Duk wadanda zasu bashi shawarar arziqi yayi fada dasu a lokuta mabanbanta lokuta amfabin zama da
mutane lafiya kenan a rayuwa yanzu gashi yana cikin damuwa amma ko cikin yan uwansa da suke ciki
daya ya rasa wanda ze tunkara dan ba saurarar sa zasuyi ba.

Wayar sa ce tayi qara, da sauri ya daga ganin Naziru ne me kiran a ransa yana Addu'ar Allah yasa ya
sakko ne ya neme shi suyi magana dan yana da yaqinin ko iya Naziru idan ya shiga maganar ze iya shawo
masa kan Ma'u saboda dab dakinta ne akwai kyakykyawar alaqa sosai a tsakaninsu.

A cunkushe kamar an wa Naziru dole ya gaida Bashir, ya amsa masa kafin yayi shiru yana jiran yaji
abinyze fada

"Jirgin qarfe bakwai da rabi zata biyo idan sun sauka zata kirawoka" Naziru ya fada a taqaice.

Be damu da sanin wacece me zuwan ba yace masa

"Zan tura maka da Lambar samuel yanzu idan sun sauka kawai ta neme shi ze kawota gida, yawwa
Naziru dan Allah...." qarar da wayar tayi alamar an kashe ce ta katse masa magana Wato Naziru ya gama
jin abinda yake da buqata ya kashe masa waya.

Tagumi ya buga a gurin, ga damuwa, ga Yunwa ga ga kai abubuwan ma sun masa yawa. Tunawa yayi da
ko sallar Isha beyi ba yasa ya miqe dakyar ya wuce dakinsa.
Gaba daya ko ina a hargitse yake komai yana nan zaune da kafafunsa daidai da takalman sa duk inda ya
cire ya ajiye anan suke basu matsa ba yo daman waye ze gyara masa?

Badan ya tsawatar bama da har dakin nasa zata ringa sauke kwandon hauka da rashin hankalinta a ciki
ai.

Haka ya dauro Alwala ya fara jera salloli yana ta kaiwa Allah kukansa har seda gabbansa suka gaji kafin
ya zauna yana jin yanda cikinsa yake karta.

Dole ya tafi Kitchen ya hada shayi ya sha da burodi dan babu komai idan basu din ba sannan ya sake
dawowa ya zauna a palour se sannan ma ya tuna da beji motsin yaran ba se ya miqe ya leqa dakinsu
Aliyu.

Gaba dayansu suna ciki sun kwanta bacci, dakin Amirah ya koma bega Farida A ciki ba seya sake komawa
kai tsaye ya kunna filita ya qarasa kusada kan Aliyu ya tsaya yana kiran sunansa.

"Ina Faridah?"

"Tana gidan Mami" Aliyun ya fada a cuskule kamar ma daman ba bacci yake yi ba se ya juya yana ce
masa

"Kayi muku Addua seda safe" ya kashe fitilar yaja musu qofa.

Ranar dai kwanan zaune yayi idan yayi sallah ya gaji se ya zauan ya hau jan charbi har aka kira Sallar
Asuba suka fita masallaci suna dawowa ya kwanta saboda wani bacci daya ji yana neman fin qarfin sa.

Can kamar a mafarki ya ringa jiyo karadi da hauragiya kamar ta Addah, qofar dakinsa dayaji ana duka
tasa yayi juyi yana jan tsaki saboda katse masa daddadan mafarkin da yakeyi ya bude ido dakyar yana
tambayar waye
"Nice nan Bashir gamu mun iso" ta fada daga waje. Dakyar ya iya tashi ya bude qofar a ransa yana
mamakin wanene ya turo masa wannan matar? Kaf dangi a rasa wa za'a turo musu se Addah ai ba
taimaka musu zatayi ba sedai ta qara masa yawan damuwar dayake ciki.

"Fisabilillah saboda wulaqanci irin naka Bashir seka turamun wani qedari da ko zo na kashe ka be sani ba
duk ka gama kadamun hanta kasan da yanda na iya gano inda ma yake a cikin iyafot din ina zuwa kuma
naganshi wani basamusen Arne. Nidai badan sunyi turanci da Naziru ba kuma Nazirun ya gaya mun na
bishi babu komai Alqur'an da sedai nayi ta yawo a iyafot din idan suka gaji da ganina na nuna musu
hotonka ai nasan dai baza'a rasa wanda yasan inda kake ba" Addah ta shiga jera masa bayani tana riqe
da wata qatuwar Akwati kamar wadda tayo hijira.

"Ya akayi suka barki kika taho da wannan jakar" ya fada yana kallon Akwatin tata.

Seta gyara tsayuwa tace

"Kaidai bari ai Allah ya tsinewa mutanen nan seda sukawa jakata tsirara kamar wadanda na sako uwarsu
a ciki, dakyar fa seda Yaron nan Naziru ya biya wani kudi wai nayi lodi da yawa kafin suka barni na wuto
da ita dukda haka seda suka kwashe mun wasu abubuwan wallahi nidai nayi Allah ya isa".

Juyawa yayi ze koma ciki dan kansa harya fara masa ciwo da wannan surun nata se kuwa ta tareshi tana
cewa

"Ina kuma zaka? Ita Amirar tana ina ko bata ji shogowata bane? Sannan ina zan ajiye kayan nan ga
Yunwa ni ina jin ai se a bani abin kari".

"Ina zuwa" ya fada yana shigewa ciki tareda murzawa qofar key. Wayar Dada ya shiga kira yana shafa
goshinta ko tsayawa gaisuwa beyi ba yace mata

"Dada me yasa zaki turo mana Addah kin manta matsala ce matar nan nida nake neman sauqi ya zaki
qara mun damuwa?"
"Toh Bashir idan ba ita ba wa kake so tazo karka manta fa ita ta haifi Amirah kuma ko ba haka ba yar
uwata ce kaga tana iya zuwa gidan ka ta zauna ai. Nidai Koma mene ne dai se kayi haquri ka dauke kai
kwana nawane da Amirah ta warware ai zata dawo ne ta barku ko" Dadan ta fada.

Sallama sukayi dan bashida abinda ze kuma fada toh mema zece bayan aikin gama ya gama ai tun kamin
ta taho ya kamata a gaya masa da se ya dauki mataki yanzu kuwa ya zeyi ma da ita.

Wanka ya shiga yana jiyo yanda take ta mita tana buga masa qofa harya shirya tsaf kafin ya bude qofar
ya fito.

"Wannan wane kalar wulaqanci ne haka, ka barni a gantale ko masauki baka bani ba idan Nafi ce tazo
haka zaka barta a tsaye ka shige daki ka rufo qofa koda yake mantawa nayi ai ba mutunchi ne dakai ba
daman to ina ita Amirah tunda uwarta ce ni ai bazata wulaqantani ba".

"Nifa bance a turo ki bama kawai ki jira yanzu za'a zo a mayar dake Airpoki wuce gida" Bashir ya fada
cikin hade rai.

"Ai wallahi ko ubanka Amadu be isa ba dan naga guri nan zama me nawuda ta samu katifa duk baqin
cikinka se naci arziqin da kuka tare a nan bakwa tunawa da mu se abinda kuka ga dama kuka yafa mana
ina ita daya shegiyar nace maka tunda ita na haifa ai bazata koreni ba" Ta fada tana riqe qugu kamar
wata qaramar yarinya.

"Tana Asibiti se gobe za'a sallamota" ya fada a cuskule yana qoqarin wuceta.

"Yau naga abinda ya ishe ni, to ka kaini Asibitin mana kana jan qafafu kamar na zalbe zaka wuceni
zamane daram ba inda zani sedai baqar zuciyarka ta kashe ka shege me baqin halin tsiya@ ta fada tana
gyara mayafinta. Ba tareda ya kalleta ba kuwa yace mata

"Ba'a zaman jinya ki jira da Yamma wanda ya kawo ki ze zo seya kaiki ki dubata ku dawo" yana gama
fada yayi ficewarsa dan gara yayita yawo a gari yana qona mai daya zauna a gidan nan wannan
birkitacciyar tsohuwar ta chaza masa kai.
Rasa abinyi Addah tayi, ta shiga Kitchen ta duba gadai kayan abinci amma bata san ya zata yi amfani da
kayan wutar ba dan Gas cooker dinsu ma soft touch ne. Palourta dawo ta tsaya tayi sa'a sega Aliyu ya
fito daga daki da Kofin shayi da farantin daya soya dankali da kwai ga ragowar nan be cinye ba seta
nufeshi tana washe baki tace

"Yawwa Dan Albarka taimaka nima ko shayi da kwan ne ka bani wallahi Yunwa nake ji ban karya ba na
fito, bani wannan na fara dashi kafin ka hadomun wani" ta fada tana qoqarin riqe farantin hannunsa.

Kallon daga ina ya mata kafin yayi kwana ya fasa shiga Kitchen din da yayi niyya, akan idon Addah ba
tareda ya kalata ba ya fita qofar gida ya zazzage abincin a inda suke zubawa karnukan da suke gadi abinci
ya sake dawowa ya wuceta ba tareda ya kulata ba.

Haka ta ringa masifa kamar zata ari baki amma dan gaske yayi banza da ita qarshema Tv ya kunna ya
hada Game dinsa ya fara bugawa daidai Nan Jafar ya shigo, shine me farat farat nan da nan ya gaishe ta.
Shi ya rakata har qofar gidan Ma'u be shiga ba dan yasan qila tayi masa fada se ya koma gidansu yana
shiga kuwa Aliyu yayi kansa da fada kamar ze dakeshi shi dai yayi shiru be amsa masa ba.

ASMA'U

Cikin filo na cusa kaina dana dafe da hannaye bibbiyu, na kasa yarda Bashir ne ya durqusa a gabana yana
bani haquri sannan waini Asma'u na iya gaya masa maganganu haka ba tareda wani dar ba.

"Kar fa ace na dena son Bashir da gaske" na fada a fili ina tashi zaune. Tagumi na rafka hannu biyu gaba
daya na rasa me ma yake damuna. Ina jin wayata dake gefen gado tana ta qara amma naqi dubawa dan
nasan dayan uku ne ko dai Bashir ko Yusuf ko kuma dayan Mayen Hayatuddeen.

Gaba daya daren haka na qarar dashi ina juyi da tunane tunanen da ni kaina bansan me nake tunawa ba.
Saboda rashin samun wadatacce bacci da ciwon kai na tashi idona yayi ja kamar wadda tayi kuka.
Da yake Asabar cema abin yazo mun da sauqi nayi wanka na saka riga mara nauyi kafin na fito palour na
tarar da Amnah da Farida suna cin abinci.

Bayan mun gaisa Amnah ta tafi kawo mun abin kari se Farida ta dawo kusada ni tana cewa

"Mami kin san me?"

"Meya faru sarkin labari?"

"Mami, Addah ce fa tazo yau, gasu can se fada suke da Abbi yace seta tafi shi bece a turota ba ita kuma
tace ba inda zataje. Nidai Mami na dawo nan gidan da kwana dan Kinsan halin Addah fada ne da ita har
da dadddare nasan hana mu bacci zata ringayi".

"Ikon Allah" na fada ina karbar Kofin shayin da Amnah ta hadamun, hankali kwance na shiga cin abincina
har na gama ba tareda na bawa Farida amsa ba can qasan raina ina mamakin dalilin zuwan Addah.

Ina shirin tashi daga gurin naji an doko sallama bana buqatar qarin bayani nasan wacece lokaci daya na
hade fuskata tsaf yanda kasan ban taba dariya ba a duniya ina kallon qofa daidai sanda ta shigo cikin
palour fuskar ta dauke da wannan dariyar tata dana kira data qeta tana cewa

"Ga baqin Asuba ko da yake rana ta daga ai. Se kuka ganmu babu sanarwa ko?"

Ban amsa ba sema harde hannu da nayi a qirji ina qare mata kallo har ta zauna akan kujera. Idan ba ido
na ba se naga ta zabge babu wannan qibar kuma tayi baqiqqirin kana ganinta kasan tajin qari matuqa.

"Asma'u ina kwana?" Maganar ta ta katse ni, daga tsayen na amsa mata da

"Lafiya" na qara daure fuska. Ina kallon yanda ta bini da ido alamar mamaki qarara akan fuskarta kafin
kuma ta waske tana cewa
"Uhm daga dayan gidan naku nake, kinsan qanwar taki bata da lafiya an kwantar da ita a Asibiti ciki ne
da ita shine fa nazo zaman jinya ashe u Asibitin naku ba'a kai musu me jinya.

Jirgin Asubanci muka biyo ko karyawa banyi ba, ga Bashir da baqin hali wallahi ko ruwa be bani ba in
gaya miki ya ma fice ya barni a gida ni kwal kamar mayya ni ba iya amfani da kicin din ku na zamani nayi
ba shi kuma wancan me kama da uban nasa ko kallon arziqi be mun ba shima daya.

Shine fa na fito waje sena ci karo da dan kirki Jafaru yace na shigo nan na samu na sakawa abakin salati".

Tsam nayi ta gama rattabo jawabin ta kafin na juya dakina ina cewa

"Ayya gashi kinyi rashin sa'a fita zamuyi muma. Koma ba haka ba baki sanar mana da zuwanki ba dan
haka ba'a dafa dake ba".

Sena waiwaya na kalli yaran da sukayi tsuru suna kallon mu nace

"Ku tashi ku shirya fita zamuyi"

"Mami ina?" Abdallah ya tambayeni, sena harare shi nace

"Inda ka aikeni ubana".

Ina shiga dakin na kwalawa Amnah kira ta biyo ni da sauri.

"Ko ruwan fanfo ku ka bata senaci uban mutum wallahi ku wuce ki shirya Yan biyu ku jirani a waje" na
fada cikin sigar umarni.

Harna fara qoqarin chanza kaya wata zuciyar tace mun to akan me zan fita ma ta koma inda tazo meye
hadina da ita toh? Se kawai na kwanta akan gado na sake kwalawa Amnah kira nace mata
"Kije ki ce mata ta fita zaku rufe gida ne" jim naga tayi alamar bazata iya ba, na ja tsaki ina miqewa nace
"matsa mun daga nan"

Na bi bayanta muka fito har sannan Addah na zaune ta rafka tagumi kamar wadda akawa mutuwa.

Fuska a daure ba tareda na kalleta ba nace

"Ki koma can gidan ina so mu rufe qofa saboda baqi masu shigo maka ba tareda iso ba".

Allah sarki se kuwa ta miqe tsam da natacviyar qatuwar pos dinta dana rasa uwar datake durawa a ciki
tana kallona tace

"Toh bari naje, amma dan Allah ko gayan biredi idan kuna dashi ki bani sena hada shayi koda ruwan
sanyi ne nasha tunda naga madara a can din".

"Kije za'a kawo miki" tayi mana sallama kuwa ta fice.

Kwai na saka Amnah ta soya mata guda shida nace su hada mata da biredi sinqi daya me yanka yanka ta
bawa Jafar idan yaje ya jona mata ruwa a kettle seta sha shayin na sake komawa dakina ina shiga wayata
dake kan mudubi ta fara qara.

Yusuf ne, na daga da sallama ya amsa yana cewa

"Amaryata barka da safiya" Yusuf ya fada daga daya bangaren

"Wacece Amaryar ka?" Na tambayeshi ina gyara zama se ya bani amsa da cewa

"Wata ce, yau zan shigo Lagos nayi kewar ki da yawa da naso na bari se sati na sama amma naga bazan
iya ba ke din kawai nake so na gani dai"

"Wancan satin fa kazo" na fada se yayi saurin katse ni da cewa


"Idan kika ce na zauna sena haqura ya zanyi girmanki ne amma wallahi dagaske nayi kewarki ni kadai
nasan yanda nake azabtuwa da rashin ganinki din nan. Ki taimaka mun ki zama mallakina dan Allah ko
hankalina ya tattaru a guri daya na dena raba shi".

"Uhm" na fada kawai dan ban san me zance masa ba.

Sosai ya kwantar da murya yana cewa

"Asma'u bana so na sake yin saken da zaki kufce mun, ki amince dani na miki Alqawarin bazakiyi dana
sanin bani amanar kanki ba. Na yarda ko bakya sona wallahi zan zauna dake qaunar da nake miki kadai
ta isa ta riqe auran mu nidai kawai ki amince mun dan yardar ki kadai nake nema.

Tunda na rasa ki ban sare ba, a kullum cikin Addu'a nake idan harda Alkahiri a tsakanin mu Allah ya
tabbatar dashi gashi yanzu bayan tsahon shekaru da har na sare na cire raina akan ki Allah ya karbi
Addu'ata ya dawo min dake cikin rayuwata dan Allah Karki sake jefa zuciyata a cikin quncin da ta rayu
dashi tsahon shekaru".

"Yusuf wai ka manta da da yanzu ba daya ba, waccen fa Asma'un daka so budurwace me qarancin
shekaru yanzu kuwa kana magana ne da Asma'u da ta zama uwa haihuwa biyar fa Yusuf yaya shida a
hakan kake sona?"

"Wallahi ke nake so Asma'u kedin nake so ba wata suffa taki ba. Ba aure daya ba ko haihuwa biyar ba
idan mazan duniya dukka kika aura kika haifa musu Yaya zan zauna dake saboda ke nake so ba wani abu
naki ba.

Yayanki kuma yayana ne Asma'u ko ban aureki ba ni zan iya riqe miki su idan har buqatar hakan ta taso
ballantana ace ina auranki ai basu da wani uba kuma sama da ni. Dan girman Allah ki tausaya mun naci
darajar tarin qaunar da nake miki ki bani dama na shiga rayuwarki in Allah ya yarda bazakiyi dana sani
ba".
Gaba daya yabi ya daureni da jijiyoyin jikina, magiya yake mun akan na amsa zan aure shi ni kuwa na
rasa me zan ce masa a lokacin.

Idan na Amsa Yusuf anya banyi gaggawa ba? Meye tabbacin da nake dashi akan zan samu banbancin
rayuwa a gidansa sama da irin wadda nayi tareda Bashir?

Idan na auri wani daban yaya makomar Yayana zata kasance tunda nasan ko dama da qasa zasu hade
Bashir baze taba bari dan sa yayi agolanci a wani guri ba sannan na tabbatar shika mijin da zan aura baze
yarda da zama na a kusada Bashir ba idan na bar nan to yaya makoma da tarbiyyar yarana zata zama?

Kamar ya shiga zuciyata se ji nayi yace

"Nasan me kike tunanin Idan kika aureni zan dauke ki daga kusada Yaranki da aikin ki tabbas zanso
hakan saboda zan buqace ki a kusa dani amma in har kinfi son zama anan din zan iya haqura na lamunce
miki in har hakan ze faranta miki rainya baki nutsuwar zuciya".

Sosai ya bude mun wuta, na rasa dalilin daya sakashi ma taso mun da wannan maganar a yanzu, duk
yanda naso na zille yaqi bani dama gashi ita kanta zuciyata a yau taqi bani hadin kai gurin furta kalaman
da zasu saka Yusuf din ya haqura da qudurinsa akaina daga qarshe a dole muka rabu akan ya bani sati
daya nayi tunani na yanke shawara akan makomar tarayyar mu.

Acewarsa mu ba yara bane da zamu zauna muna jan lokaci idan har na yarda na aminta dashi a matsayin
abokin rayuwata a shirye yake daya zamemin bangon jingina.

Wannan maganar ta mantar dani batun Bashir na shiga Sabon lissafi da komonton hukuncin da zan
yanke akan Maganar Yusuf.

Harga Allah idan har son zuciyata ne zan zabi na koma dakina na zauna da Bashir amma ina tuna cin
zarafi da wulaqancin da yayi mun ya sake ni akan yar uwata mace se naji sam koda na koma gidan sa
bani da sauran wata qima ko mutunchi a idanunsa. Idan har ze iya tsinka igiyoyi biyu na auran shekara
goma sha bakwai akan macen daya aura shekara uku bayana to tabbas qarasa dayar bazata yi masa
wahala ba.
Amma zan miqa komai ga Allah zan nemi zabinsa duk kuma abinda yafi kwanta mun a rai zan karbe shi a
matsayin zabin da Allah yayi mun wannan na qudurce a raina babu kuma bata lokaci na tashi da kaina na
shiga Kitchen, ina da tukunya babba da nake girkin Sadaka a ciki nan da nan na dora Jalof din shinkafa
me kyau ban dauki lokaci ba na gama na zuba a robobin take away masu murfi.

A qatuwar roba muka jera su, dakaina na dauka a mota muka fita can kan wata hanya inda daman muke
kai abincin na ringa rabawa mutane Musulmao harda wadanda ba musulman ba duk wanda na bawa
zance kayi mun Addu'a Allah yayi mun zabin Alkahiri a cikin rayuwata nayi hakan kuma da kyakykyawan
yaqinin amsuwar Addu'ata.

BASHIR

A wani gidan abinci ya karya, rashintakamaiman gurin zuwa ya saka yayi zamansa a gurin kawai yana
kallon masu shigowa suna fita.

Kusan awa daya yana zaune shidai baze ma iya cewa ga abinda yakeyi ba can dai ya miqe ya fita yana
qoqarin bude motarsa yaji anyi masa sallama daga bayansa.

Waiwayawa yayi, Macece budurwa a qallah zatayi shekara Ashirin da biyar zuwa sama ba fara bace
amma fatarta bata da duhu kuma ba wata shahararriyar kyakykyawa bace sedai yawan Fara'arta ya
taimaka gurin fito mata da kyau me sanyi.

Sallama ta sake maimaita masa fuskar ta dauke da murmushi seya dakata daga bude motar yana qare
daure tasa fuskar ya amsa ciki ciki yana kallonta.

"Sunana Zulaiha, kayi haquri fa na tsayar dakai, tun dazu naga shigowarka. Alamun ka sun nuna kana
tareda damuwa qarara. Idan kana da maganin damuwarka kayiwa kanka idan kuma baka da shi to koma
menene yake damunka ka fawwalawa Allah yin tagumi da zama shiru bazeyi maka magani ba" ta fada
cikin murmushi tana kaiwa qarshe kuwa ta juya ta barshi a tsaye kamar ta dasa shi.
Jiki a sabule ya shiga motar, harya kunna ta kuma seya kashe cikin dakiya da jarumta ya danna kiran
lambar Abubakar dan har seda ya kulle ido kafin ya kira ringin daya biyu uku aka daga Abubakar yayi
sallama daga bangarensa.

Cikin faduwar gaba Bashir ya amsa sukayi shiru gaba dayansu kafin can Abubakar yace

"Wayake magana ban gane lambar ba"

"AB goge lambata kayi? Bashir ne fa" Bashir ya bashi amsa a sanyaye dan jij ko lambarsa ma bashi da ita.

"Ayya Yi haquri kasan mutanen da yawa wanne Bashir kenan? Kayi mun bayani yanda zan gane".

Seda yaja fasali a ransa ya maimaita La'ilaha illah anta subhanaka inni kuntu minazzalimin kafin yace

"Nasan ko baka da lambata ai muryata bazata bace maka ba, Bashir ne dai naka kuma Mijin qanwar ka
Ma'u".

"Eh to nawa Bashir din dai ko banga lambarsa ba na haddaceta akai (sunada qani Bashir) sannan cikin
qannena babu wadda take auran Miji me suna Bashir gaskiya.

Ok kace Ma'u ko? To Ma'un dana sani a gidan mu ma bazawara ce bata da miji sedai ko idan tsohon
mijinta kake nufi sunansa Bashir" Abubakar ya fada cikin irin lafazin nan na ko a jikina.

Shi kuwa Bashir har wata zufa ce ta shiga keto masa. Toh ta ina ma ze fara masa magana jin irin wannan
amso shi da yake bashi yana nuna masa cewar babu sauran wani abu tsakanin su kenan yama manta
dashi a babin rayuwarsa.

Daurewa yayi muryarsa har tana rawa rawa yace

"Am Abubakar na sani abubuwa da yawa sun faru a baya da sedai nace kayi haquri laifi na ne kuma na
karbi kuskurena in sha Allahu zan gyara dalilin ma daya saka na kiraka yanzu kenan na baka haquri akan
komai aya faru sannan na nemi shawarar ka akan yanda ya kamata na gyara sauran kura kuraina".
"Toh a taqaice dai ni abinda zan iya ce maka shine kasan hausawa sun ce yanda aka dama haka za'a sha,
to nima sedai na maimaita maka hakan nace maka ka koma gefe kawai ka nade hannu ka karbi duk wani
sakamako a yanda yazo maka Malam Bashir, batun laifi kuma ni bakayi mun komai ba.

Idan zan tuna ka gaya mun babu ruwana da sabgar gidanka ko dan kana auran qanwata bashi ya bani
damar gaya maka abinda zakayi da wanda zaka bari ba, tundaga sannan na sake tsoka bakina a cikin
sabgar gidan ka?

To na menene yabzu zaka sako ni kuma?

Ita abotar ka yanke ta tuntuni, auratayyar ma ka sakar mun qanwa to me yayi saura a tsakanin mu yanzu
babu dan haka dan Allah karka sake kirana akan wani shirme naka can idan ba haka ba kaga yau na amsa
ka a mutunce ko, ka tabbata idan ka sake a ranar zaka gane kuskuren ka zan sauke maka fushin shekara
da shekaru dana shanye ban nuna maka ba" yana gama fadar haka ya kashe wayar sa.

Ajiyar zuciya Bashir ya sauke dan ya tsammaci fiye da hakan ai to tunda ma aka tsaya anan ai ya gode
Allah har ya samu kwarin guiwar sake tun karar sa kuwa idan aka kwana biyu.

Hanyar Asibiti ya dauka ko ba komai Ya kamata ya je ya duba yanda ta kwana gashi har rana ta kwale
yanzu. Yana isa tun daga farkon ward din yake jiyo tashin muryar Addah cikin masifa ga wata muryar da
be tantance ta waye baita kuma ana yarbanci da alama itama masifar takeyi, kansa ya sara masa yaji
kamar ma yayi kwana ya fasa shiga.

Ya akayi tazo da wuri bayan ya gayawa Samuel se yamma zeje ya daukota sannan ita dawa take fada a
Asibiti kuma? Badan kar taje ta jajibo masa wata fitinar ba da juyawa zeyi ya barsu su qarata amma dole
ya qarasa cikin dakin daidai sanda matar da suke fadan ta jefowa Addah irin qaramin flask din shayi na
silver akayi rashin sa'a ta goce ya fadi tim akan qafar Bashir daya shiga dakin tsautsayi ashe be rufu da
kyau ba kuwa ruwan zafin ya kele masa a qafa ga zafin buguwar da yayi ga azabar ruwan zafi besan
sanda ya fasa qara yana sakin wayarsa da muqullin da suke hannunsa ba suka fadi qasa.

[12/02, 11:23 pm] Sisi love:


WATA KISHIYAR

(ALKAHIRI CE KO SHARRI)

Na Maryamah Farouk

(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)

Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 56

“Innalillahi Addah ta qona shi” Amirah dake zaune akan gado ta dora hannaye biyu akai tana fada.

“Kan bala’i kika qona shi To wallahi kin taro ruwan dafa kanki daman ni kika so ki la’anta kenanAllah ya
kareni tsiyarki ta fada akan Dana ai kuwa bazamu yarda ba daganan har kotun qoli” Addah ta sake
hayayyaqowa matar dake tsaye tana numfarfashi.

Irin shinqimemiyar nance ta gaske, itama cikin masifa da yarbanci ta hayayyaqowa Addahn, wato da gani
fadan a duhu akeyinsa dan babu me gane yaran wani a cikin su gefe kuma ga Nurses biyu da suna ta
faman bada baki amma ko wacce ta kafe taqi haqura.

Cikin radadin Azaba Bashir ya juya ya fita daga dakin dan har seda ya cire takalmin qafar da ruwan ya
zuba. Kai tsaye dakin likitan da yake duba Amirah ya nufa yana dingisa qafa suka ci karo dashi a hanya

“Yawwa Engineer wannan wace irin mata ce ka kawo mana gaba daya tazo ta tayar wa da mutane
hankali kamar ta manta Asibiti tazo? Muji ka fita da ita kuma karta sake dawo mana. Kai itama matar
taka bari kawai a rubuta muku sallama idan yaso ta ringa zuwa daga gida ana dubata kawai” Likita ya
tare Bashir tun kafin shi yayi masa magana.

“Ka taimaka ka fara dubamun qafata farko ruwan zafi suka watsa mun” Bashir ya fada yana zama a kan
kujerar dake gaban Office din likita, se likitan yayi saurin durqusawa ya kama qafar yana haskawa, Dakin
wanke ciwo suka tafi Allah ya so shi qunar iya sama ce dan haka magani kawai aka saka mishi ya rubuta
masa wanda ze siya yasha sannan ya gaya masa ya dan dakata da saka takalmi saboda karya takura fatar
ta kwaye.

Saboda baqin ciki ko dakin be sake komawa ba yayi tafiyarsa gida a ransa yana ayyana irin abinda zeyi
musu daga Addan har Amiran idan suka dawo masa gida.

Hajia Addah kuwa abinda ya faru Bayan ta dawo daga gidan Ma’u ranta a jagule da irin tarbar da Ma’un
tayi mata. Sam bata taba tsammatar haka daga gareta ba saboda yanda tasan Ma’u da haba haba da
lamarinsu ada idan suka je gidanta kamar zata goyasu saboda kirki amma yau ita tayiwa wannan korar
kai tsaye ba tareda wata shakka ko shayi ba koda yake ada Suruka take a wajenta a yanzu kuwa babu
sauran alaqa sedai ta kara kawai ai.

Babu abinda ya qara tayar mata da hankali irin nutsuwa da kyan da taga Ma’un ta qara ga uwar daula
data zuba a gidan ta dan yafi na Bashir din sau biyar wallahi jifa wasu kujeru tana zama akai taji ta ta
lume qa qamshi ta ko ina duk se taji ta raina gidan Bashir yanzu data dawo ba kamar zuwanta dazu ba da
ta ga gidan kamar wadda taje wata Villa yanzu kuwa se taga duk ya zamar mata wani qauye dama ga
rashin gyara gaba daya dai abin ya zama se a hankali.

Tana zaune ta zabga tagumi Aliyu nata buga Game dinsa dan be nuna alamar ma yaji shigowar mutum
ba sega sallamar Jafar da kwandon Abinci. Bata jira ya qaraso ba ta taro shi dan dagaske yunwa takeji,
badan bazata gane ta inda suka shigo unguwar bama da fita zatayi tunda da yan kudinta a jaka ta nemi
abinci to Lagos kuma abinci ai se kalar wanda ta zaba zataci.

Haka ta zauna tana ci tana zubawa Ma’u Albarka seda ta cinye kwan nan tas da sinqin biredi ga qaton
kofin data zuba shayi tayi gyatsa kafin ta dakko wayarta tana kallon Jafar tace
“Kai Allah dai yawa uwarku Albarka yasa kuma kuji qanta, ungo nan ka duba zakaga wata lamba da aka
kira qarshe ta wani qedari ce da ubanku yace ze zo ya kaini Asibiti na duba Antyn ku kirashi maza kace na
shirya idan kuma zaka rakani to se mu tafi tare”.

Lambar Samuel Jafar ya nemo ya kira ya gaya masa saqon Addah, yana qunquni ya amsa gashi nan zuwa
dan dazu daya dakkota har suka Zo tana zabga masa masifa dukda bajin abinda take fada yake ba amma
yasan zaginsa takeyi.

“Kai nima dai Jafaru zaka fara koyamun turancin nan tunda naga garin gaba daya kowa shi yakeyi karna
fita wata rana na manta hanyar gida na rasa waze dawo dani” Ta fada tana dariya bayan daya miqa mata
wayar yace Samuel din yana zuwa.

“Allah yasa na ki fitan ki bata daman yan yankan kai na garin nan sunfi son irin ki masifaffun tsofaffi ai”
Aliyu dake gaban Tv ya fada ba tareda ya juyo ya kalle ta ba, nan kuwa ta hau sababi tana fadar sedai a
sace uban sa badai ita ba shege me baqin hali. Dake dangado ne kuwa ya manna mata hauka tayi tayi ba
ita ta haqura ba seda Jafar ya gaya mata ga Samuel ya dawo sannan ta fita, tayi tayi su tafi tare yaqi dan
yana Tsoron Maminsa haka ta kama hanya tana ci gaba da mitar ta.

Har bakin dakin da Amirah take Samuel ya rakata ta tura qofar tareda doka uwar sallama kamar me
magana da yan sama dai dai nan abokiyar zaman Amiran da aka kawo jiya da daddare tana fama da
matsanan cin ciwon kai dakyar aka samu tayi bacci a sannan Mahaifiyarta dake jinyarta na zaune suna
hira jefi jefi da Amirah cikin harshen turanci sega sallamar Addah.

Cikin sauri tayiwa Addah data shigo tana sake jaddada sallama da qarin ko bacci sukeyi ne alamar tayi
shiru da hannu tana nuna mata yarinyar da har ta fara mutsu mutsu alamar tana son farkawa.

“Ji wata masifa Allah ya tsaga mun baki a ringa mun alama wai nayi shiru in ke bakya amsa sallama ai ita
Amiran yar musulmai ce balle kice duk kune aikin banza kai” Addah ta fada cikin daga murya tana kaiwa
zaune kan kujrar dake gaban gadon Amirah kafin taci gaba da cewa

“Haka kika qanjale Amirah sannu ko da yake iya jarabar Bashir kadai ta isa ta ramar dake kai wannan
Bashir dai ko azababbe daga zuwana fa harya...”
“Dan Allah Addah kiyi shiru dakyar aka samu tayi bacci wallahi kanta ne yake ciwo sosai” Amirah ta katse
ta kamar zatayi kuka ganin yarinyar ta fara riqe kanta da alamar ta farka daga baccin kenan. Cikin masifa
Addah ta waiwaya ta kalleta tace

“To ni ina ruwana? Ni na dora mata ciwon da za’a hanani magana ko yaya ina da akwai dakin masu kudi
da mutum ze zauna shi kadai me yasa basu kama can ba se kuma ni a takurani ke dallah karki qaramun
bacin rai akan wanda nake ciki”

Kuka yarinyar ta fara dan ba ita da take ciwon kai ba ko me lafiya dole kansa ya buga irin yanda Addah
take taqarqarewa yana daga murya kamar me magana da yan sama. Masifa ta shigayi ita dai matar tana
ta qoqarin kama yarta dake fizge fizge ganin abin ya fara yawa yasa ta fita da gudu se gata ta dawo da
Nurses guda biyu suka rufu akan yarinyar qarshe se fita da ita dga dakin sukayi saboda yanda Addah ta
qiyin shiru gashi anyi anyi ta fita daga dakin taqi se zabga salallami take wai wannan wane kalar sharri ne
daga zuwanta se kace wata mayya yarinya zata fara fizge fizge to Allah ya isanta.

Tana cikin sababin matar data bi bayan yarta ta tabbatar da lafiyarta ta dawo dakin ba tareda Addah ta
ankare ba tayi kanta tana zazzaga mata masifa cikin yarbanci bakinta ne mutu ba itama ta shiga zaginta
da Hausa Amirah dai ka tsakiya tana basu haquri amma babu meji data ga suna neman bawa hammata
iska seta koma kan gado ta zabga tagumi kawai tana kallonsu da abin yayi tsamari shine matar ta jefawa
Addah flask dai dai sanda Bashir ya shigo tsautsayin ya fada akan sa.

Shiru sukayi gaba daya suna kallon Bashir din daya juya ya fice daga dakin, matar ta dora hannu tana yan
tsalle tsalle irin nasu tana kiran Jesus Addah ko harara ta maka mata tace

“Ai wallahi se mun daure ki, badai kin qona mun Da ba wato da kasheni kikayi niyya ko? To ki shirya
yanzu za’a turo miki sammaci wallahi” A fusace ta juya kan Amirah da duk ta rikice tace

“Ke kuma kukan uwar me kikeyi dallah taso muje mu ga halin da qafar take ciki idan ta sale Aradu sena
qonata itama haka kawai zata nakasa mun dan Yar uwa bazan kyaleta ba.
Suna fitowa daga dakin Nurse ta taresu ta miqawa Amiran Farar takadda ta sallama dole suka koma suka
hau tattare kaya.

Haka suka fito harabar Asibiti neman duniya babu motar da Aka kawo Addah balle kuma ta Bashir da
daman basu saka ran ganinsa ba. A wayar Addah Amirah ta shiga kiransa dan ta gaya masa an sallame su
ya turo Samuel ya kaisu gida, kiran Farko harta qaraci ringin be daga ba ana biyu kuwa aka ce mata
wayar ma a kashe take.

Lambar Samuel din da Addah ta nuna mata ta kira ya daga suka gaisa kafin ma tace sake magana ya gaya
mata Oga ya aikeshi Abeokuta ze kai wani saqo kamar zata rusa kuka haka ta kashe wayar suka samu
qasan wata bishiya suka zauna gashiba wani gama jin qwarin jikinta tayi ba dan cikin nata bana me zafin
laulayi ne ga Addah da taqi yin shiru se masifa take wai an musu wulaqanci yanzu ta ina zasu koma gida.

Dabarar sake kiran Samuel tayi akan ya gaya mata kwatancen unguwar tasu idan yaso ko Taxi ne se su
hau ta kaisu, hakan akayi sukayi shahada suka hau Taxi dan Addah tana shiga ta tuna da fatan da Aliyu
yayi mata dazu nan da nan ta jawo jarbi ta hau ja baki ya mutu basu suka saki ransu ba seda suka gansu
a qofar Estate din kafin kowacce ta saki ajiyar zuciya.

Har qofar gida ya ajiye su, suka sauke kaya Addah ta zuge jaka ta ciro dari biyar ta bawo me Taxi ta qyafe
tana jiran ya miqo mata chanji. Kallonta yayi ya kalli kudin kafin ya juya kan Amirah ya fara tambayarta
kudinsa tunda ita ce mejin Turanci.

Tambayarsa tayi nawa yace mata dubu goma zasu bayar tunda Drop suka dauka ta waiwaya ta kalli
Addah tace

“Addah dubu goma ne kudin motar, ki bashi dan Allah idan mun shiga ciki se mu warware na gaji ni jiri
nake ji” ta juya zata shige cikin gida Addah ta fizgota tana cewa

“Dan fashi ne ya dakko mu ko yaya? Wannan tafiyar Asibitin da bata fi nayita a qafa ba inda nasan hanya
ita ce zakice a bashi dubu goma saboda ubanki ne ya bani ajiyar kudin?
To banda su, dari uku nayi niyyar bayarwa shima saboda an shigo damu ciki ne amma da a bakin get ya
ajiye mu dari dari zan bayar seki nemi dubu taran ki cika masa” ta mayar da dari biyar din cikin jaka ta
harhado yan hamsin da dari na dari uku ta watsa masa tayi gaba abinta.

Kamar Amirah zatayi kuka ta shiga roqon ta data bayar zata biyata dan ita sisi bata magani a hannunta
ko a cikin gidan gashi babu motar Bashir ballantana tace yana gida zata shiga karbo ita kuwa Addah fafur
taqi qara ko sile sema masifa da take zazzagawa me Taxi daya juya P cap baya yana jira yaga zasu bashi
kudinsa ne ko se ya dauki mataki.

Ganin suna neman bata masa lokaci gashi wadda yaga kamar kudin a hannunta suke na neman shigewa
gida yasa ya fizge jakar Addah, babu bata lokaci ya zazzage komai a qasa sega kudi kuwa suka zubo ya
irigi dubu gomansa cif ya shige mota ko kula ihun barawa da Addah take zundumaqa beyi ba ya qara
wuta abinsa to masu wucewa ma babu wanda ya kulasu dakyar Amirah ta turata suka shige gida se dafe
kanta take daya dauki ciwo saboda bala’in Addah.

A cikin gidan ma Sabon tashin hankali ta dasa mata akan kudinta ganin babu sarki se Allah yasa ta shige
daki ta kullo kanta, wayarta ta shiga dubawa dan ta kira Bashir ko ze zo ya kashe wannan wutar ta ganta
amma babu chaji seta jona ta shiga wanka saboda jikinta sam babu dadi.

Lokacin data fito wayar tadan caju, lambarsa ta shiga kira yanzu a kunne take amma kiran na shiga za’a
katse shi ta kira yafi sau biyar qarshe dan kanta ta haqura ga yunwa tana ji amma tsoron karonsu da
Addah idan ta fita palour yasa ta gwammace ta sha ruwa da wani Biscuit da yake a dakin ta kwanta ledar
magungunanta kansu suna palour haka ta haqura bata sha ba.

BASHIR

Daga Asibiti kai tsaye gidan Musa ya wuce dan yanzu can kadai yake iya zuwa ya rage zafi tunda Musan
shi kadai ne bashi da mata.

Cikin jimamin abinda ya sami qafarsa ya tare shi, ya ringa masa sannu kuwa qasan ransa kuwa dariya ce
fal musamman dayaji wai da surukarsa ake fada tsautsayi ya fada kansa suka qonashi shi kuwa Bashir
wace irin sirika yake da ita me fada da mutane a Asibiti?
A gidan ya wuni zir, duk dai hirar da sukayi akan yanda ze gyarota da Ma’u ne dan ya gayawa Musan
yanda sukayi da Abubakar, shi ya qara bashi kwarin guiwa akan ya ci gaba da binsa yana bashi haquri
wata rana ze dace sannan kar ya daga qafa a Gurin Ma’u duk irin wulaqanci da cin kashin da zata masa
ya daure daman ance ai ramuwar gayya tafi ta gayya zafi amma idan yayi haqurin buqata ta biya
shikenan shi yaci riba.

Shi ya sake bashi shawara ya ringa tura mata text na ban haquri akai akai. Gyara zama Musa yayi yaci
gaba da ce masa

“Kaifa matsalar ka Bashir na fuskanci gaba dayanka se a hankali yar soyayyar nan naga alamar baka iyata
ba se tsare gida da hade fuska kawai. Sufa mata da ka gani suna son tattali da kulawa ko baka da sisi
indai mace na samun nutsuwa da Farin ciki a gurinka zata Yi haquri ta zauna dakai amma ko kafi qaruna
kudi indai ta rasa wannan ba ko wacce bace dukiya take a gabanta zata iya rabuwa dakai ta tafi inda aka
san darajarta ne ko kuma tana tare da kai ta ringa kula wasu cana waje da suke bata kulawa suna
yabonta.

Da yawa maza mu muke bada qofar da matan mu suke aikata wasu abubuwa da basu kamata ba a bayan
idon mu. Yanzu misali kaine kullum cikin hade rai a gidanka, kaida matarka idan taga haqoranka to
magana kakeyi babu dariya babu lafazi me dadi balle ace tayi kwalliya ka yaba ko ka zauna kayi wasa da
raha da ita tsakanin ku se bada umarni kamar wata yar aiki da ubangidanta dan Allah ta yaya kake
tunanin idan ta hadu da wanda ze bata duk irin wadannan kulawar data rasa a gurinka ba bazata kulashi
ba?

Ba kowacce mace ce take da qarfin zuciyar daure wasu abubuwan ba, wata koda ba ta sigar fasiqanci ba,
wata da sunan aboki zakaga ta hadu da wani namiji da zasu zama kamar wasu Qawaye ko Aminai duk
wani sirri nata daya kamata ta yi shi tare dakai shi ze maye mata gurbi ya zama abokin shawararta se
kaga matar aure wai tana da wani Besty duk waya ja Mijinta kuma ka tabbatar duk dakon zunubin da
zatayo tare za’a kasafta muku dan kai ka yanka mata tikitin da har zata kula wani banza can da auranka.

Ka duba yanzu ko a gurin aikin mu yanda mata suka lalace matan aure kaga suna qazamar rayuwa suna
mu’amala da wasu mazan a waje da bana auransu ba a kaso goma idan ka tarasu bakwai wallahi
mazansu nada sa hannu cikin fadawarsu wannan halakar saboda basu da ma lokacin su ballantana su san
damuwarsu har su maganta musu ita da yawan maza muna dauka kudi shine maganin ko wacce matsala
idan ka wadata mace shikenan ka gama mata komai wanda sam abin ba haka yake ba dole ka kula da
matarka ta kowanne bangare ka tabbatar da cewa ka toshe mata duk wata buqata idan kayi haka kuma
kaga wata matsala ta faru seka qaddara cewa jarabawa ce kuma daga ubangiji amma ba wai dan kai ka
bayar da qofar faruwar hakan ba.

Dan haka nidai shawarata Bashir ka canja takunka, ba Asma’u ba ko wacce mace zaka zauna da ita dole
ne kasan qima da martabarta. Ka sani cewar ba Alfarma kayi musu daka auresu ba ballantana ka dauka
dole suyi haqurin zama dakai da halinka Aa zamane na ibadah da Allah ya hadaku kowa yana da haqqi
akan dan uwansa”

“Haka ne kuma zanyi qoqari na gyara kuskurena Musa dan ina buqatar Ma’u a rayuwa ta wallahi” Bashir
ya fada bayan daya sauke tagumin da yayi.

“Au saboda ka dawo da Asma’u zaka chanja hili kenan? Bashir bari fa na gaya maka gaskiya Halinka cikin
goma bakwai basu da kyau ta fannin zaman takewa. Kai bafa matanka ba kadai mu kanmu haquri muke
dakai wani lokacin saboda shi hali zanen dutseaka ce ba’a chanza wa mutum shi amma a wannan karon
in har kana so lamuranka su daidaita dole fa seka daidaita sahu a to.

Kai in banda ma halinka Bashir a zamanin nan ka samu mace kamar Asma’u bafa ajinka bace wallahi in
ma gaya maka gaskiya Allah ne kawai ya kashe ya baka ka samu tana sonka take hidimta maka da jikinta
da Aljihunta, matar nan fa ko daure fuska kayi se hankalinta ya tashi. Ka tashi ka tafka mata kishiya ta
wulaqanci koni Namiji naji zafin abinda kayi ballantana ita sannan ka qara mata da tukwuicin saki kai ni
idan ta haqura da wuri ta dawo maka gaskiya bata mun daidai ba”.

Daure fuska Bashir yayi tamau yana kallonsa yace

“Karka kuskura kace mun kaima kana son matata dan shine mafi girman kuskuren da zaka aikata, mu
kadai ne a gidan nan yanzu zan murqusheka ka mutu Ba wanda yasan meya faru”.

Dariya Musa yayi harda fadowa daga kan kujera kafin yace

“Maida wuqar Malam ashe daba ka fara ban sani ba. Ai ni idan zan so Ma’u bazaka sani ba, qila se kaji
nayi aure kawai kazo gidana ka ganta a matsayin matata amma ni sam ba haka nake ba, babu kuma haka
a tsakanin mu kawai dai ina nuna maka irin girman asarar daka tafka ne a rayuwarka kuma idan baka
hanzarta ba kana ji kana kallo sedai ka mutu kana cizon yatsa da daka sani ka mayar da yayanka marayun
dole ka rabasu da uwar su haka kawai”.

Ganin da yayi daga shawara kuma abin na Musa na neman ya koma wulaqanci yasa yayi masa sallama ya
kamo hanyar gida, a hanya ya tsaya wani guri da suke siyan Shawarma da wani Gas meat da Ma’u take
bala’in so ya siya da yawa ya hado da Madarar ruwa da kwali itama kalar wadda take sha kafin ya kamo
hanyar gida.

A qofar gidanta ya ci burki, a waya ya kira Amnah yace tazo ba tareda ya fito ba ya ce ta bude bayan
motar ta kwashe ledojin ciki.

Ya dade a mota kafin ya fito qafa daya da takalmi daya babu ya dauki tasa ledar Naman da Madarar ya
shige gida, Hajia Addah na zaune a palour ta tasa Amirah data gama zaman dakin ta fito a gaba har
sannan dai zancen dubu goma yaqi ci yaqi qarewa.

Kallo daya ya musu sanda Amirah ta masa sannu da zuwa ya wuce daki tabi bayansa, tun dazu take jira
ya dawo ita dai ya taimaketa ya biya Addah kudinta kota samu ta shaqi iska a gidan yana shiga dakin kan
ya rufo tayi wuf itama ta fada ya kuwa balla mata harara ta sunkuyar da kai se ya wuce ya ajiye ledar
hannunsa ya shiga bandaki.

Tana zaune se hadiyar yawu take saboda qamshin naman da duk ya cika dakin ya fito, kamar munafuka
tayi qasa dakai tana gaishe shi ya amsa a taqaice yana cire rigar jikinsa ganin taqi fita yace mata

“Lafiya?”

“Am daman Yaya an sallamo mune na kiraka da wayar Addah lokacin baka dauka ba na kira Samuel
shima yace mun...”

“Na sani na aike shi ba gashi kun dawo ba se akayi yaya to?” Ya katseta murya a cunkushe, qasan ransa
har yana tunanin wane hankali ne yazo mata da har tayi tunanin zuwa ta duba shi kodai Addah ce ta
sakata dan yasan a kalar nata tunanin dai bazatayi ba, maganar tace ta katse shi da take cewa
“Daman Taxi muka hawo ta dawo damu, shine seda muka zo yace wai kudin motar dubu Ashirin tunda
drop muka dauka to Addah ce ta biya tun safen take ta mun masifa akan na biyata kudinta kuma ni ko
sisi bani dashi nayi ta kiranka ma dazun kana rejecting gata can wallahi ko abincin kirki ta hanani naci da
masifarta”

Wani mugun kallo me nuna zallar bacin rai yake aika mata, wato kudi take da buqata tun dazun dalilin
kiran da ta ringa masa kenan, qonewar da uwarta taja masa ma bata dameta balle taji ya qafarsa kawai
kudi ze bata a mugun fusace ya nuna mata qofa ba tareda yayi magana ba.

Amirah dake ta Addu’a a ranta Allah yasa ya bata goman ta ajiye dan tunda tazo sile biyar bata hadasu
ba kai ko katin waya bashi ne kusan dubu biyar taci na Mtn saboda ya dena saka mata, da tana Gombe
kuwa duk satin Allah yar dubu dayar nan dai seya saka mata wani lokacin ma biyu ga yar cuwa cuwar da
takeyi ta karbi kudi a hannun Naziru na cefane anan kuwa shi yake siyo komai kuma se abinda ta gani
kawai dan waca wacar nan data san anayi a gidan bata san me yasa yanzu kusan komai a qididdige yake
ba ba yanda ta saba ganin sanda Anty tana nan komai na danqare a Freezer ba sedai su bude su diba.

Ita da yake ya raina mata hankali se abinda yaga dama yake siya ya ajiye kuma idan ya qare abinda yake
ci ze siyo da wuri, daman nama ne yafi damuwa dashi, tana son kifi amma tunda tayi masa wani farfesun
kifi ita kanta dai ranar data ci haka qarnin yayi ta taso mata be sake siyowa ba tayi nacin harta gaji to
tunda ta samu ciki ma ya dena cin abincinta, daman yaran ba ci suke ba sedai su dafa abinda suke so ko
su shigo dashi daga can gidan sedai tayi ta qara qararta ita kadai ga cikin me dan banzan kwadayi haka
zata yita hadiyar yawu idan ta jiyo qamshin abincin makwafta.

Tsawat daya daka mata ce ta dawo da ita daga tunanin data tafi dan ashe yana ta mata magana ma bata
ji ba, da sauri ta tattari qafarta tayi waje tana fita suka kusa karo da Addah dake labe a bakin qofa cikin
matuqar takaici Amirah ta kalleta kafin ta wuce dakinta wata kwalla na sakko mata.

Bashir kuwa sallah kawai ya tayar dan idan ya tsaya takaicin Amirah yana iya shaqe shi kawai aga ya fadi,
so kuma yake yayi isha ya zauna ya tsarawa Ma’u Saqo ya tura mata dan ya qudurce indai soyayya ce
matsalar to kuwa ko Sharukan se dai yazo ya kwashi kos a gurinsa a wanna karon.

ASMA’U
Bayan dana dawo daga rabon abinci sallah kawai nayi na kwanta dan na gaji sosai bani na farka ba se
dab da magriba. Kiran Yaya Abubakar na gani guda biyu na shiga bandaki na wanko fuskata da bakina
kafin na dawo na zauna na danna kiran lambar sa.

Bayan mun gaisa yake cemun

“Dazu Bashir ya kirani a waya wai yana bani haquri, ban san rashin kunyarsa harta kai haka ba se yau
tukunna nadai ja masa kunne akan karya kuskura ya sake kirana in ba haka ba yasan sauran”

“Lallai Baban Ali shi har yana da qarfin guiwar kiran ka kenan, haka fa jiya yazo qofar gidan nan wai yana
bani haquri harda durqusawarsa” na cikin mamakin tsaurin idon Bashir.

“Asma’u” ya kira sunana da sautin da yake nuna muhimmancin abinda ze gaya mun sena gyara zama
dakyau na amsa ina sauraronsa yaci gaba da cewa

“Kafin ki auri Bashir kin taba tambayata abinda yasa bana farin ciki da auran ku ko to yau zan baki amsa.
Bashir Abokina ne kin sani tun na yarinta dan haka nasan halinsa ciki da bai, halayyata da tashi sunyi
kamanceveniya ta wani bangaren saboda dani dashi murdaddun mutane ne da ake shan wahalar gane
gaban mu.

A bangaren auratayya muna da buqatar samun tsayayyar mace me taurin zuciya da ra’ayin riqau ta
yanda dole sedai ko mu zubda makaman mu mu bita ko kuma ya zamana anyi 50 50 ma’ana kowa ya
riqe bangare daya bawai wadda zamu taka yanda muka ga dama ba kuma ta biyu.

Baki dace da Bashir ba saboda ke mace ce me sanyin hali da saurin yarda tareda sadaukarwa inda ace
Aliyu marigayi ne ya nemi auranki dukda yaso hakan amma Bashir yayi masa shigar sauri, a lokacin da na
zamo kan gaba a komai saboda nasan bazaki taba nadamar zabarsa ba saboda halayyat ku kusan daya
ce, dake dashi zaku ringa rige rigen kyautatawa junan ku amma Allah be hukunta faruwar Al’amarin a
haka ba ya qaddara cewar Bashir din dai shine Mijinki harda rabon zuri’a a tsakanin ku.

Banaqin Bashir saboda shima mutumin kirki ne kuskurensa kuma ajizanci ne irin na ko wanne dan Adam
kuma na tabbatar da nima da ace irin ki nake aure da ko ba dukka ba se an samu kwatankwacin halayyar
Bashir a cikin gidana saboda nasan duk abinda na dakko zata yarda kuma ya zauna.
Bance Bashir baya son ki ba amma ki sani son da kike masa ko nace kina bayyana soyayyarki sama da
tasa shi kansa wannan babban dalili ne da Namiji ze riqe ya kuka juyaki duk ta yanda yaso saboda yasan
kina sonsa zakuma ki zauna dashi a duk yanda yake.

Abinda nake so na gaya miki Ma’u, Bazan hanaki ba idan har zuciyarki ta aminta da ki koma gidan Bashir
amma ki riqe abu guda daya shine ke din dai kece ba wata sabuwa ta daban ba haka Bashir yana nan a
Bashir din da kika sani babu abinda ze chanza daga halayyarsa ta ainihi duk wani chanji da ze zo miki
dashi na dan lokacine dole wata rana se an koma gidan jiya.

Karki duba kowa ko wani abu ki duba makomar rayuwar ki, Kin cancanci samun rayuwa me cike da Farin
ciki Ma’u kiyiwa kanki gata, idan har farin cikin ki yana tareda Bashir ki koma gidansa ku zauna zamu ci
gaba da binki da fatan Alkhairi kamar yanda muke miki a koda Yaushe idan kuma kina da zabin daya fishi
Allah ya tabbatar miki da Alkahiri yasa kiyi farin ciki dashi na har abada”.

Shiru nayi kamar wadda aka zarewa laka har Yaya Abubakar ya gama mun magana dakyar na iya cewa

“Nagode Yaya, nima a yanzu banida wani zabi se abinda Allah ya zaba mun, in sha Allahu yau zan fara
istikara ina kuma fatan Allah ya saka mun duk abinda yafi Alkahiri a zuciyata Nagode kwarai Yaya Allah
ya saka da Alkahiri”

“Babu komai Allah ya jishshemu Alkhairi, Ina Yaran ina fatan dai babu wata matsala ko?”

“Babu komai Yaya, ai yanzu ma kusan anan suke dan bacci ne kawai yake mayar dasu can gidan shima
wani lokacin anan suke kwana kuma baya magana dan Farida daman ta dawo nan gaba daya”

“Toh haka ake so, kin gani ko tashin hankalin daman bashi da amfani yanzu gashi a ruwan sanyi ai kusan
sun dawo hannunki, Allah ya wuce mana gaba”

“Amin yah rabb Nagode yaya a gaida su Anty Nasiba” daga haka mukayi sallama ina ta juya
maganganunsa a raina, matsaya daya dai na zauna akai itace ta neman zabin Allah tunda shine dahir
Bayan sallar Isha ina zaune ina lazumi sega Amnah da leda niqi niqi tun kafin ta ajiye qamshin abinda
yake ciki ya doki hancina nan take kuma na gano na ina ne.

Kallonta nayi da alamun tambaya ta ajiye su kusada ni tana cewa

“Abbi ne ya kirani a waya yace na kawo miki”

“Zaki tattara ki wuce mun dasu daga nan ko yaya, me yasa daya kiraki baki zo kin gaya mun kafin ki fita
ba” na fada ina rufeta da fada. Setayi rau rau kamar zatayi kuka tace

“Mami Abbi ne fa ba wani ba, kuma ai...”

“Amnah ni kike gayawa Abbi ne ba wani ba Abbin ubanki ne ko yaya? Ki shiga hankalinki Amnah kuma ki
kwashe kayan nan ki fita dasu kafin na bata miki rai”.

Kayan ta diba seda ta kai bakin qofa kafin ta waiwayo ta kalleni tace

“To mu zamu ci Mami idan ke ba zaki ci ba”

“Amnah se naci ubanki idan na taso wallahi ki tattara ki mayar masa idan ba haka ba zamu gamu”

Da sauri ta fice ta barni ina mita ni kadai, qamshin naman kuma seya tado mun da tsohon kwadayi dan
ina bala’in son Gashin gurin. Seda nayi Shafa’i da wutri na nayi Addu’oi kafin na fito palour ina jin badan
dare yayi ba da tabbas sena fita na siyo naman nan dan dai bazanci na hannun Bashir ba.

Turus nayi daga bakin qofa ina kallonsu yanda sukayi face face da naman sunaci wasu nacin shawarma.

“Yanzu Amnah me na gaya miki?” Na fada ina kallonta, se tayi saurin ajiye Naman hannunta tana zare
ido tace
“Wallahi Mami shiya ce mu cinye kuma ma seda Addah da Anty Amirah suka diba da gaba daya ma suka
qwace seda Abbi yayi ta masifa kafin suka bamu kuma Addah ta sake biyo mu ta dibar musu”

“Shikenan ai kun kyauta, idan kin gama ki dafa mun Indomie ki kawo mun” na fada ina komawa ciki.

Wayata na dauka, Ina so na kira Yusuf wata zuciyar kuma tana hanani. Saqo ne ya shigo wayata, Bashir
ne na bude na fara karantawa bansan sanda na bushe da dariya ba saboda ganin irin abubuwan da ya
rubuto wato kalaman soyayyane kala da kala a ciki gaba daya se naga abin wani banbarakwai.

Ina gama karantawa na goge shi ina tuno da wani saqo da Yusuf ya turo mun dazu da yamma se kawai
na danna kiran lambar sa.

“Allah yasa muga Annabi” ya fada yana daga wayar, senayi murmushi me sauti nace

“Amin”.

“Amma Asmy batan lamba kikayi ko?”

“Me ka gani?”

“Babu komai, kawai dai nasan kina sane bazaki kirani a waya ba sedai tuntuben lamba kikayi”

“To shikenan bari na kashe tunda haka kace” na fada kamar zan kashe din se yayi saurin tare ni da cewa

“Aa bafa haka nake nufi ba, Allah ya taimaki Amaryar Yusufa barka da dare toh ya kike?”

“Barka dai Excellency ya aiki ya Jama’a?”

“Aiki Alhamdulillah kinsan kuwa yau wunin Site nayi na dawo duk na gaji wallahi Asmy, ya gida ya yara ya
kuma kewata?”

“Ni na rasa irin son kudinka dai Yusuf, idan ba haka ba dan Allah ina kai ina Wani supervision na aiki?
Dan Allah ka barwa sauran Jama’a suma su samu mana”
Dariya yayi yace

“Asmy kenan, nifa ko Inyamuri baze nunamun neman kudi ba, dazu naje wani qauye zamu siyo gyada
muna zuwa suka lullube motata nace kai ku matsamun ni ba wannan ya kawo ni ba neman Halal na fito
yau”.

Dariya sosai nayi, daga nan muka shiga hira har Amnah ta kawo mun Indomin, Allah Alah nake mu gama
magana ba tareda ya taso mun da zancen dazu ba, seda zamuyi sallama kuwa yace

“Saura kwana shida, ina Addu’a Allah yasa naji Alkhairi”

“Amin Allah ya sa muga Alkahiri” nima na fada daga nan mukayi sallama.

Ban kwanta bacci ba se gurin uku da rabi na dare, sosai nayi sallolina da Addu’oi na rufe da sallar Istikara
tareda kyakykyawan yaqinin samun haske a cikin al’amarina na kuma bude zuciyata ko Bashir, ko Yusuf
ko ma wani ne daban Allah ya zaba mun zan karbe shi nayi fatan ya zame min siradin zuwa Aljannah.

WATA KISHIYAR

(ALKAHIRI CE KO SHARRI)

Na Maryamah Farouk

(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)


Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 57

BASHIR

Iya bakin qoqarinsa yakeyi gurin aiwatar da abinda Musa ya gaya masa, duk yanda yasan ze shawo kan
Ma’u yi yake amma kamar wadda yake qarawa wuta fetur daman baya samun ta a waya duk ubannin
saqonnin da yake tura mata kuwa bata taba maido masa da ko guda daya ba.

Ya rasata ina ze sameta suyi maganata fahimta, baya son zuwa gidan ta tunda tace masa bata so amma
dole ya zama me gadin qarfi da yaji, da wuri yanzu yake baro office yazo kanlayi ya kasa ya tsare amma
ko sun hadu ma wani shashasha take mayar dashi dan daga gaisuwa bata ma bashi damar magana zata
wuce abinta.

Abun na bala’in ci masa tuwo a qwarya, ga azumi yana gaba towa baya so suyi azumi a wannan yanayin.
Gidansa daman tuni yafi qarfin sa in har yana son nutsuwa to fa sedaiya fita waje dan karadi da surutun
Addah kadai ya ishe shi. Shi bata barshi ba ita Amiran da take fama da kanta itama bata tsira ba ga jaye
jayen magana da take dakko masa haka kawai seta wanke qafa ta shiga gidan maqota kuma in dai taje
seta takalo wani abun haka za’ayi ta tararsa ana kawo qararta sedai yai ta aikin bada haquri.

Kusan sati ana wannan yanayi ranar yana zaune da daddare a dakinsa haka kawai zuciyarsa ta ayyana
masa kiran Goggon su Ma’u.

“Nasan tana sona da Ma’u kuma ita kadai ce zata fahimceni a yanzu in Allah ya taimaka seta shawo mun
kanta a sanyi komai ya daidaita” ya fada a fili yana janyo waya cike da kwarin guiwa ya shiga kiran
Goggo.

Seda ta dan jima tana ringin kafin ta daga da sallamarta suka gaisa yanda suka saba yana tambayarta
jikin Baffa tace da sauqi kafin itama ta tambayeshi su Amirah da yara yace duk suna lafiya se sukayi shiru
gaba daya.
“Lafiya dai ko Bashir naji kayi shiru” Goggon ta katse masa shiru, seda ya hadiyi wani yawu kafin ya gyara
zaman sa ya sunkuyar da kai kamar yana gabanta yace

“Daman Goggo kira nayi in bada haquri, wallahi nauyi da kunyarki ta saka tun lokacin da abin ya faru na
kasa kiranki se yanzu dai na daure nace bari na kira”.

“In banda abinka Bashir meye abin bada haquri kuma kamar wanda ya aikata wani laifi, shi zaman aure
ai raine dashi idan lokacin mutuwar sa yayi kuma ba yanda aka iya ko da dalili ko babu haka ana so ba’a
so za’a rabu, karka ji komai wallahi Allah yasa hakan shi yafi Alkahiri a gare mu baki daya” Goggo ta fada
a sake babu damuwar komai tattare da ita.

Cike da qarfin guiwa Bashir ya shafa kai yace

“Hakane wallahi duk abinda ma ya faru Goggo laifi na ne kuma dai sharrin shaidan ne amma yanzu na
gane kuskurena kuma in Allah ya yarda haka bazata sake faruwa ba”

“Ai ita rayuwa daman haquri akeyi amma babu komai ai koma dai laifin waye a cikin ku Ai abubya wuce
Allah yayi wa kowa zabin Alkahiri a gaba”

“Ai Goggo Alkahiri dai yana nan tare damu dan in sha Allah zamu koma kuma babu abinda ze sake
faruwa a gaba se Alkahiri, badan ma wancan tsautsayin daya faru ba ai da yanzu ma ta dawo dakinta qila
tana shirin haihuwa koma ta haihu amma yanzun ma muna saka rai in Allah ya yarda kafin Azumi komai
ze daidaita.” Bashir ya sake fada da qarfin guiwa.

“Toh haka da sauri har kun daidaita kenan?” Goggo ta tambaya cikin mamaki, se ya shafa kai kamar yana
gabanta yace

“Aa dai tukunna, kinsan mutuniyar ne akwai rikici itama wani lokacin to har yanzu dai inata ban baki ne
amma taqi ta bani dama amma nasan dai in aka ci gaba zata haqura shi yasa ma na kira yanzu ko za’a
dan taimaka a saka baki tunda tana jin maganar ku qila tafi saurin sakkowa”.
Seda Goggo taja ajiyar zuciya tana jinjina qarfin halin Bashir kafin ta iya ce masa

“Eh to ai duk da na gari da yake so yaga daidai dole yaji maganar iyayensa. Zancen mu saka baki kuma ai
bata taso ba Bashir dan a yanzu Addini da kansa ya bata damar zabar abinda take so dan ta wuce
Budurwa bare ace za’a fada mata yanda zatayi.

Idan taga tana da sha’awar zama dakai mu masu yi muku Addu’ane idan kuma tace Aa shikenan se muce
Allah zabawa kowa rabon Alkahiri”

Yanda kasanta saka guduma ta kwade masa guiwoyi haka yaji duk ya rikice har wata zufa ce ta tashin
hankalo ta shiga zubo masa. Cikintawar murya yace

“Goggo a haqura kuma dan Allah a dai duba ko dan darajar yaran nan Goggo be kamata mu rabu ba”

“Yo Bashir mantawa kayi dasu sanda ka saketa ne? Kuma ina duk cikinsu babu me shan Nono. Daidai da
Biyu sun isa su riqe kansu su zauna ba tareda uwarsu ba shekara Bakwai ai da yawa idan ma kuma kana
ganin bazaka iya riqe su bane seka kawo mana daman kai ka damu da abaka yayanka amma mu muna so
zamu riqe su Allah ya raya har zuwa sanda zasu mallaki hankulan kansu.

Sannan daman ina so na kiraka akan zancen Farida, kaga ita mace ce to na nemi alfarma ka barwa
uwarta ta riqeta samarin kuma su zauna dakai shikenan. A gaida matar gidan Da yaran se anjima” tana
gama fadar haka ta kashe wayar bata ma bashi damar sake wata magana ba.

Kamar wanda akawa mutuwa haka ya zabga tagumi tunda Goggo bata goyon bayansa toh ina ze kama??

ASMA’U

Sosaina dage da kai kukana da neman zabi zuwa ga sarkin sarakai. A wannan taqin tsakanin Yusuf din da
Bashir har na rasa wanda yafi uzzurawa rayuwata dan yanzu Bashir ya dage saqon ban haquri da
kalaman soyayya karo da karo seya turo mun Ashirin a rana haka kiran waya sedai nayi ta ganin missed
calls dinsa tunda nayi blocking layin se kawai nayi murmushi na share.
Sauqin dana samu da Yusuf tafiyar gaggawa data same shi zuwa qasar Turkiyya zeyi wata daya dan se
cikin azumi sannan ze dawo.

Yanzun kam Wasai nake jin zuciyata duk wannan qunci da takura da nake ji da wata makauniyar soyayya
yanzu ya yaye, ina matsayin da zan iya karbar ko wanne irin al’amari hannu biyu bani da wata matsala
tartibiya, rayuwata kawai nake a kullum kuma ina nanata Addu’ar neman zabin Allah a dukkan lamurana
ba tare da na gajiya ba.

Shirye shiryen shigowar watan ramadan muka fara, ana saura kwanaki uku a dauki azumi ranar da wuri
na taso daga aiki saboda ina so muje muyi siyayyar abubuwan da bamu dasu.

Seda mukayi sallar magriba kafin muka fita, na saka simple doguwar riga da hula se na yafa siririn mayafi
a kaina muna tafe muna hira da Jafar dana dauka yamun rakiya. Ina ajiye mota ya juyo yana cemun

“Lah Mami ga motar Abbi, shima yazo siyayya daman dazu da safe naji yana cewa Anty Amirah tayi list
tace wai sedai su taho tare..”

“Jafar na hanaka wannan shegen surutun amma baka ji tambayarka nayi ko yaya” na katse shi ina
qoqarin fita daga motar. Biyo bayana yayi muka shiga supermarket din, kai tsaye Gurin buhun huna
muka fara biyawa dan akwai Kunu da qosan sadaka da ake mana duk azumi sanda muna tareda Bashir,
wannan karon ma bazan fasa ba. Dan har a Gombe ina so ayi dan sosai na samu rarar kudin hayata bana,
an fitar da lissafin zakka da komai amma dukda haka na samu kudi har mamaki nake to wai da duk ina
suke shigewa da bana gane lissafin ne.

Wake da Gero se pastar mai muka siya na bar musu tunda motata bazata dauka ba sa kawo mana gida
se muka wuce cikin kantin muyi abinda ya kaimu, ina tafe ina amsa wayar da Goggo ta kirani. Saka
Albarka ne da addu’ar fatan nasara da dacewa a duniya da lahira taketa zubamun dan se yau aka gaya
mata batun Umarar dana biya mata.

“Idan naje zan dage da yi miki Addua Ma’u, Alah yasa da an sallace ki fitar da miji kiyi aure dan zama
haka ba qimar mace bace sam” ta fada. Sena marairaice ina cewa
“Kai Goggo gaba daya wata nawa ba auran biyar fa shine har zaki fara maganar na sake wani, nidai ba
yanzu ba danni makaranta ma zan koma na qaro karatu”.

“Sanda Mahaifinku ya mutu Allah ya jiqansa watan mu biyu da fita takaba na daura aure da Modibbo
dukda shekaruna ba kuma nayi aure dan wata buqata ko jin dadi bane Aa nayi ne dan samun lada da cika
wasiyyar mahaifinku seke yanzu da quruciyarki zakice bazakiyi aure ba.

Me kika dauki kanki ne Asma’u? Gaba daya fa shekarunki Talatin da shida ne a duniya dan kinyi aure da
wuri kin tara Yaya ne yasa kike daukar kanki kamar wata uwar mata kome? A yanzu fa da akwai
yammata Sa’anninki dama wanda suka girme miki da ko auran fari basuyi ba ballantana kice kin kai
shekarun da maza bazasu so ki ba.

Ina da duk labarin wadanda suke sonki ai, ba’a rufa sati ba har nan Yayanku ya rako wannan yaron Yusuf
ya gaishe ni sannan a nan ma Himu dan gurin Addah Sadiya (Yayar Goggo ce) yayiwa Yayanki Muslim
magana shi ya dakatar dashi shi yasa ma bakiga yazo ko ya kiraki ba.

To ki tsayar da hankalinki wallahi daganan zuwa a sallace ko ki fitar da miji ko ki tattara ki koma can
gidan ku ki zauna dan bazan lamunci zamanki a bariki ke kadai ba aure babu wani Muharrami, ke ko
kunya ma bakyaji yanzu a fara sallama da Amina ke gaki uwarta babu aure wa ze dauke ku da
muhimmanci ma”.

Baki na tura jin daga maganar arziqi ta koma fada kuma. Jifa kuma inda ta juya wace Amnan za’ayi
sallama da ita yanzu fisabilillahi? Ni dana san ma wannan maganar zata tayar da tunda ta kira na bata
uzurin ina waje idan naje gida na kirata.

Fadan ta taci gaba dayi dan itama fa Goggo akwai Mita in ta kama zance daya, daga qarshe ta rufe da
zancen kwashe kayana na gidan Bashir na Gombe

“Ko da Bashir din kuka daidaita ne naga babu wanda yayi maganar kwashe kaya ko kuma kin bar masa
ne ban sani ba? Daman cikin satin daya wuce ya kirani yana wasu soki burutsun banzansa nidai ban bashi
fuska ba” ta fada.
Se a sannan ma tuna ma da inada wasu kaya a gidan Bashir na Gombe , cikin qaguwar karta kuka
daddago wata maganar nace

“Za’a kwashe Goggo, kinga ai bamu zo gari ba muqullin kuma yana nan tare dani shiyasa, amma da
munzo hutun sallah in Allah ya yarda za’a kwashe”

“To yadai fi dan karma naji wani zancen kome ko wani Abu indai ba kuma haka Allah ya qaddaro ba gara
ayi addu’a Allah ya hada kowa da rabonsa na Alkahiri”.

Wani iri naji, wato duk yanda take son Bashir yau da kanta take cewa babu zancen kome gidan sa lallai
Bashir ya bata rawar sa da tsalle.

Sallama mukayi, jafar ya dauki qatuwar Trolly muka fara zuba kayan da muka zo siya. Can gurin da ake
ajiye su nama muka ci karo da Bashir da Aliyu daga uban har dan kowa ya kalli gefe ya tura baki sama
kome suke jira oho ga dai trollyn da suka fara zuba kaya nan a gabansu.

Kallo daya nayi musu na mayar da hankali na kan Freezer na fara ciro abinda nake da buqata ina sakawa
a cikin Trolly, gaba daya hankali na ya tafi a abinda nakeyi se jin magana nayi daidai kunnena har seda na
tsorata na dago da sauri muka hada ido da Bashir dake tsaye dab dani.

“Meye haka zaka tsoratani” na fada ina harararaa qasa qasa, se ya marairaice kamar wani yaro yace

“Ma’u me yasa bakya amsa kirana? Idan na turo miki saqo ma bakya bani amsa me nayi miki dan Allah?”

Kallonsa nayi tareda jan gajeran tsaki se kawai na juya ina cewa Jafar

“Muje, in suka bar gurin se mu dawo”

“Kiyi hauwa dan Allah ki tsaya, kinga muma shopping muka zo gaba daya na manta abubuwan da kike
siyo wa na taho da Aliyu yace shima be sani ba” Bashir ya fada yana shan gaba na.
Se na tsaya ina kallonsa a raina nace

“Tunda ba kai kake siyowa ba ai daman bazaka sani ba”

“Dan Allah Ma’u” ya katse mun tunani kamar ze durqusa mun tsabar yanda yake kwantar da murya. Ni
mamaki ma yake bani wai Bashir dai me kamar Boss shine yake karya murya haka yana roqona ashe
daman ya iya ikon Allah.

Ba tareda na kalle shi ba nace

“Me dame zaku siya”

“Duk abinda ya kamata na girki saboda Azumi banda kayan abinci da mai” yayi saurin bani amsa.

Tare muka ringa zagayawa, ina da list dina a kai dan haka komai na dauka se Aliyu ya daukar musu ina
kallonsa se bata rai yake haka tunda ya gaishe ni be sake magana ba kamar wanda akayiwa dolen zuwa.

Siyayya mukayi da yawan gaske dan daman ni abinda ya kawoni kenan cefanen mu yayi qasa sosai, da
mukaje gurin biyan kudi na zaro ATM dina zan bayar yayi saurin tarewa ya miqa nasa ban ja ba na maida
abuna Aljihu ai daman tare zamu ci da Yayansa.

Seda aka loda mana kayan mu tsaf a mota na kalleshi fuska a sake nace

“Baban Ali se da safe toh a gaida Iyali mun gode” na kama murfin motata zan shiga ya riqe yana cewa

“Dan Allah ki unblocking dina, kuma koda wani layin na kira bata shiga ki taimaka ina so muyi magana ne
tunda kin ce bakya so nazo gida”

“To shikenan zanyi” na fada bawai dan zanyi da gasken ba Aa dan kawai ya qyale ni na tafi. A tare muka
jera ina gaba yana bayan mu har gida.
Ina shiga na tarar da an kawo mana kayan dinkinmu na sallah. Seda muka gama jera siyayyar da mukayi
kafin na fito da kayayyakin nawa ne dana Amnah da Farida ina dubawa nace

“Yaushe aka kawo kayan?”

“Kuna fita yazo, yace nasu Aliyu se wani satin za’a kawo wai Be gama wadanda aka kai daga baya ba”.

Wani shegen Lace na daga ina dubawa da mamaki dan dai nasan babu shi a kayan dana bayar dinkin
sena kalli Amnah nace

“Wannan kamar ba namu ba inaga Hassan ya rikice ya sako mana kayan wasu, miqo mun wayata na
kirashi naji”

Wayar ta bani na shiga kiran Hassan Tailor, seda muka gaisa yake cemun nayi haquri fa be hado dana
mazan ba ya bari ne a gama dukka saboda na baya da Alhaji ya kai sune ba’a qarasa ba.

“Wane kaya aka sake kawowa kuma Hassan? Sanan naga qari akan namu ma inaga na wasu ne ka hado
dasu fa”

“Aa Hajia dukka Alhaji ne ya kawo su wancan satin ai” ya bani amsa.

Sallama mukayi ina ta mamakin wai Bashir ne ya kai, ashe yasan shagon Telan kai abubuwan mamakin
nasa dai suna da yawa.

An kama Azumi Ramadana, yanda nake fita aiki na dawo a nutse har na kama wasu ayyukan gida yana
bani mamaki. Sena tuna Azumin da suka wuce tun bayan dana fara aiki haka nake fita hayyacina kafin
sallah kuwa sena zabga uwar rama saboda aikin gida dana office ga Bashir da tsurfa kala kala haka zan
dawo nayita dora tukwane ina saukewa wannan karon kuwa Allah ya hutar dani, ga Amnah a gida ga
Baba Harira.
Ita take zuwa duk azumi take tayamu da aikin kunu da qosan sadaka yar uwar mijin Anty ce anan Lagos
suke ta hadani da ita. Wannan karon ma tun ana saura sati daya na kirata randa za’a dauki azumi kuwa
se gata tazo, daman haka take zuwa se zamu tafi Gombe sallah kafin ta tafi shiyasa nake samun hutu dan
kafin na tashi aiki na koma gida ma sun gama hada mana komai na shan ruwa.

Ranar Talata an kai azumi na goma sha daya, an shiga goma ta wuya in ji hausawa aikuwa dai ranar naji
wuyar gashi akayi sa’a ranar naci uban aiki a office se kusan qarfe biyar da rabi na kama hanyar gida
qarshe ina shiga ana kwada kiran sallar magriba.

Na samu har an fitar da abincin sadaka can masallacin da ake kaiwa ga kayan shan ruwa nan da suka
hada sun shimfida babbar ledar cin abinci a qasa dukka yaran suna gidan harda Aliyu yau dan shima wani
baqin rai yake ji dashi idan yazo sau dayan nan muka gaisa bana sake ganinsa yana can gidan su yana
neman fitinar kakarsu.

Muna shan ruwa Yusuf ya kirani, bamu jima muna magana ba mukayi sallama yana jaddada mun cewar
duk buda bakin da zeyi seya kai sunana gurin Allah ina dariya. Mun je sallar Asham muna dawowa na
hadu da Bashir daya coge a qofar gidan mu da gani gudowa yayi daga masallaci dan ana idarwa muka
taho kafin maza su fara fitowa.

“Ma’u dan Allah ki saurara zamuyi magana” ya fada yana matsowa inda nake.

“Baban Ali an sha ruwa lafiya?” Na fada fuska a sake ina harde hannu a qirji, seya shafa kansa yana cewa

“Ba lafiya ba, a taqaice ma ni ban sha ruwa ba. Amirah bata da lafiya sosai jikinta ya sake tashi, Addah
kuma kinsan bata iya irin abincin da nake ci ba, ni duk ba wannan bama Ma’u dan girman Allah, dan
darajar watan nan da muke ciki kiyi haquri mu komawa auran mu.

Wallahi nayi madamar duk abinda na aikata kiyi haquri kuskurene kuma bazan sake ba. Gaba daya
rayuwata da sukurkuce babu abinda nake ganewa Ma’u.
Tunda kika tafi rabon da nayi bacci me dadi, a kullum cikin Yunwa nake wuni daidai da dakina sedai idan
na gaji da kaina na gyara gaba daya gidan ma ya hargitse babu gyara babu qamshin ki Ma’u.

Gaba daya Azumin nan da akayi dore nakeyi kuma idan an sha ruwa ma dakyar nake samun abinda zan
iyaci wani lokacin ma se yara sun tafi da abinci daga wurinki nake samun wanda zan karya Azumi na
Ma’u, amma ki dubi Allah ki duba yaran mu kiga irin rayuwar da suke tsakanin gidaje biyu bayan muna
da damar da zamu zauna taredasu a inuwa daya, na gaji da watangaliliya Ma’u ina buqatarki a kusa dani
ki dawo ki tallafi rayuwata”.

Baki na bude kawai ina kallonsa, shifa Bashir bama shi da kunya wallahi wai na tallafi rayuwarsa.

“Wai ni Baban Ali me kake nema dani dan Allah? Saki na fa kayi akan matarka saboda naqi nabar aiki na
koma gida ita ta dawo kusa da kai kace naje na zauna da aikin ko ba haka mukayi ba?

Me yasa baka duba yayan ba a lokacin da ka bani kwana daya rak akan in bar maka gida zaka zubawa
Amaryarka sababbin kaya?

Meyasa baka duba makomar su ba lokacin daka zo har cikin gidana kaci mun mutunchi nida Yan uwana
ka kwace yayanka duk a sannan baka san zasu ringa yawo tsakanin gidaje ba se yanzu da ka sheqa kaga
babu riba sannan zaka zo kace mun wai kayi nadama inyi haquri na koma gidanka?

Bari kaji nasan me kake nufi, ba wai kana bani haquri bane saboda ka yarda kayi kuskure Aa kanayi me
saboda ka gaza samun yanda kake so a gidanka. Dama kai ai babbar matsalarka a rayuwa cikinka ne koda
iya wannan aka barka dole ka shiga garari wato ga Asma’u girkau ko in dawo in ci gaba da dafa maka
kana ci tunda matarka bata yi.

Ba rashin gyara ba Allah yasa bola gidan ka ya zama wannan ku ta shafa bani ba kuma daga yau zan ja wa
masu kawo maka abincin kunne wallahi ko yunwa zata kashe ka sedai ka mutu amma badai ni in dawo
gidan ka in dafa maka abinci ba.
Kai bari kaji Bashir daga rana irin tayau kar na sake ganin qafarka a qofar gidan nan idan ba haka ba na
rantse da Allah sena maka rashin mutunchin da ko a hanya muka hadu bazaka mun kallo biyu ba.

“Ma’u fata kike mun na mutu? Ke da kanki yau kike kira mun mutuwa?” ya fada cikin mamaki har yana
kama baki, na galla masa harara dan da gaske na harzuqa da wannan rainin hankali na Bashir nace

“To ka mutu mana ina ruwan wani ni ina da Asara ne? Meye hadina da kai Ina Yaya ne to Allah baze
hana ni yanda zan riqe su ba in ka mutu matar ka da yan uwan ka ne sukayi Asara bani ba.

Ka fita a harkata aure ne dakai na gama bazan koma ba ka fita a rayuwata malam idan kuma dan kana
ganina a kusada gidanka yasa ka samu damar uzzurawa rayuwata toh se in tashi dan kasan gurin zama a
Lagos ba wahala ze mun ba” ina gama fadar haka na wuce ciki na barshi a tsaye kamar an dasa shi.

Ina shiga na hau kan yaran da fada.

“Wallahi duk wanda ya sake diban abinci ya kai gidansu sena ci ubansa kuma sedai ya koma can ya ringa
ci” na fada ina nuna su gaba daya.

“Toh Mami na sahur fa muke tafiya dashi” Jafar ya fada, daman nasan shi yake diba ai kuwa na
hayayyaqo masa ina cewa

“Tunda ubanka ne ya siyo ya ajiye mun dole ka ringa guzuri kana kai masa ai, to bari kuji na shan ruwan
ya isa can kuci na sahur a gidan ku idan ba haka ba wannan din ma wallahi zaku jawo in hana kai gaba
daya ma se ku tattara ku koma gidan ku kar wanda ya sake zuwa ya takura mun anan”

“Yanzu Mami saboda kawai an kaiwa Babanmu abinci shine kike fada naga wasu can ma zuwa suke ki
dafa musu su tafi dashi shine mu Babanmu zaki hana mu bashi” Aliyu ya fada yana ture kwanan gabansa.

Sena juya kansa a fusace nace


“Na hana idan kuma ka isa ka diba ka kai masa kaga yanda zanyi maganin duk wata fitsara da kakeji a ita,
saboda kaga na qyaleka kwana biyu kana iskancin dakaga dama ko shi yasa to mu zuba ni dakai ai ka
sanni ba kuma chanzawa nayi ba”

Miqewa yayi fuskar nan kamar ze fashe tsabar fushi ya nufi qofa

“In na sake ganin qafarka ma a gidan nan ma sena bata maka rai uban yan baqin zuciya kawai, baza’a
bawa uban naka abincin ba idan kunyi zuciya ku auro masa wadda zata zo ta ringa dafa masa” na fada
ina wucewa dakina.

Duk sukayi tsuru suna bina da kallo ganin yanda na horance musu. Ina ciki aka qwanqwasa na bada izini
aka shiga.

Baba Harira ce ta samu kan kujerar dake dakin ta zauna tana cewa

“Kiyi haquri Uwardakina shi yaro ba’a masa haka. Be kamata ki ringa musu haka akan ubansu ba se su
qullace ki bayan su bazasu gane abinda yake tsakanin ku ba.

Kinga ban tsawaita da son jin dalilin mutuwar auranku ba duk da nayi jimami kwarai amma shi aure ana
zaune lafiya ma in Allah ya kawo se kinga an rabu amma dan Allah koma menene ki dena nunawa a
gaban su. Zancen abinci kuma uwata ai sadaka ce idan an bashi ba’a fadi ba”.

“Baba Harira ki qyale wannan mutumin kawai ai bashi kadai bane da matarsa a gidan da surukarsa me
yasa baza su dafa su bashi acan ba shine dan bashi da kunya har ze tareni yana gaya mun se an kai daga
nan yake ci to wallahi kar ki sake bari su fita da abinci, in dole se sunyi sahur din su fito da Asubar suzo
suci anan”.

Ganin da tayi dagaske raina a bace yake yasa ta tashi ta tafi tana qara nanatamun da nayi haquri. Tsaki
na ringa saki ni kadai, nama rasa takamaiman bacin ran nawa na menene? Cewar da yayi na koma
gidansa ne ko kuwa wani abu daban?
Anci sati biyu cikin Azumi yara suka fara jarabawar term, randa aka kai azumi na Ashirin da shida suka
gama daman tun ana saura kwana biyu su qare na turawa da Bashir saqon cewar zamu tafi Gombe da
yaran dan qila shi ba zuwa zasuyi ba idan ma zasuje ina so ni na tafi tareda yaran saboda akwai bikin
qanne na maza biyu da za’ayi sati daya da sallah.

Ina tura saqon ya maido mun da amsar ya yarda daman ta ina ze hana shida yake neman hanyar shiri
dani yanzu kam shishshigigi da cusa kai ba irin wanda baya yi mun. Ana ibi zamu tafi sega Hotunan tikiti
ya turamun ta whatsapp, na budesu na duba na zuwa ne kawai yana tambayar yaushe zamu dawo ban
amsa ba na kashe Datar na sauka a raina nace

“Kudina sun huta tunda ba roqar ka mukayi ba”. Kiran Yusuf ne ya shigo mun na daga muka gaisa yana
mun qorafin qarin kwanakin da suka samu dan tun satindaya wuce ya kamata su dawo amma yanzu se
ranar sallah.

“Yaushe ne tafiyar taku zan saka ayi muku booking jirgi yanzu” ya fada

“Ai an hutashsheka ma, kaga babansu ya rigada ya siya yanzu naga ya turo mun dasu” na bashi amsa.

“Bazaku hau ba, qarfe daya gobe za azo a kai ku Airport” ya fada ta sigar bada umarni kana ji kasan kishi
ne cunkushe a qasan ransa.

“Ranka ya dade ya rigada ya siya, a daga mana qafa daman iya na zuwa ne idan zamu dawo se mu hau
naka”.

Shiru ya mun be amsa ba seda na sake magana kafin ciki ciki yace mun

“Shikenan, Amma Asmy bana son wata alaqa tsakanin ki dashi dan Allah, nasan ze ringa fakewa da
Yaransa idan na abinda ya zama dole ba babu ke babu shiga sabgarsa kinji?”
“Naji baza’a kuma ba, to ka saki ran mana se wani magana kake kamar Boss” na fada cikin sigar tsokana
a qasan raina kuwa nace

“Ji mutum se kace ka aure ni irin wannan doka haka”.

“Baki san yanda nake kishin ki ba ko? Ki bari se randa Allah ya mallaka mun ke, ranar zaki san yanda ake
tattala abinda ake qauna daga lokacin duk wani namiji da zeyi magana dake to ina tsakani” ya fada

Dariya nayi ina cewa “Allah ko to sannu sarkin kishi”

“Asmy se ana sonka ake kishin ka ai ko baki san haka ba? Ke daida bakya sona daman bazakiyi kishi na ba
in kuma kin sona to ki fada yanzu naji

“Shikenan dai, yanzu zan kwanta saboda mu tashi da wuri dan bamu gama hada kayan mu ba” na fada
ba tareda na bashi amsar tambayarsa ba.

“Yawwa gara dana tuna, idan kun isa Gombe za’a kawo kayan sallar su Abdallah. A Kano na bada dinkin
da suka gama kuma kaitsaye Abuja suka tura se kawai nace a kaiwa Alhaji Tukur qilan ma ya riga ku isa
yanzu”

“Kayan sallah kuma kaida kake da hidimomi da yawa ina kai ina qarawa kanka wasu?”

“Bana jin dadin abinda kike mun duk sanda nayiwa yaran nan abu. Qiri qiri kike nuna bakya sona Asmy
da ina da zuciya nima da tuni na haqura dake amma na kasa, tunda dai bake nayiwa ba se ki barsu su
karba in kuma bazasu saka ba to ki zubar kawai” ya fada a dan fusace.

“Ni fa sam ba haka nake nufi ba gani nayi kwata kwata yaushe ka kawo musu waccan tsarabar duk basu
saka bama suna nan daman sallah muka barwa amma kayi haquri bazan sake ba, sun gode Allah ya qara
budi” na fada cikin sigar lallashi.
“Da nayi niyar yi miki tsarabar Dogayen riguna tunda naga kina son su, yanzu nake so na fita na siya
muku keda Intee amma kin jawowa kanki na fasa nata kadai zan siya”

“Haba mana na fa ce kayi haquri, kasan fa daman ina ta so na baka sautu kuma ina tsoron kar kace na
mai dakai dan aike shi yasa nayi shiru amma a siyo mun mana ayi mun afuwa” na fada cikin shagwabar
da ban san nima inayi ba.

“Dagaske hukuncin bata mun ran da kikayi kenan, badai wannan karon ba ko zan siyo miki sedai wani
lokaci” ya bani amsa

“Shikenan toh Allah ya kaimu wani lokacin”

“Fushi kikayi?” Ya tambaye ni, se na yi murmushi nace

“Aa ba fushi nayi ba”.

“Karki damu zanyo miki tsaraba saura itama idan na kawo kice bakyaso, ki turamun da size na takalmin
ki”.

Hira kadan muka sakeyi kafin mukayi sallama na kwanta dan ina so na tashi da wuri.

Wai dan Allah ni kadai nake fama da matsalar network if yes to to ya kamata a san yanda za’ayi dani

WATA KISHIYAR

(ALKAHIRI CE KO SHARRI)
Na Maryamah Farouk

(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)

Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 58

BASHIR

Beyi niyyar zuwa sallah Gombe ba amma saboda karya shiga haqqin Amirah yasa ya tuntubeta ko zasuje.
Suna zaune ita da Addah a palour ya fito daga dakinsa da ya mayar dimun da iman yana ciki indai yana
gidan.

Ledar kayan sallar ta daya karbo dazu ya dauka ya fito palour,

Suna zaune Tayi daddaya a qasa taba cin Gyada dafaffiya ga cikinta nan daya fara girma a waje saboda
Half vest ce a jikinta kawai ta daura zani kanta babu dankwali wai zafi take ji dukda akwai wuta sun
kunna Ac suna hira da Addah da tayi shar abinta duk rama da baqin da tazo dasu babu to aci me kyau a
kwana a Ac meya dameta.

Zama yayi ya gaida Addah ta amsa tana hararar sa dan haushin sa take ji, bama ya zama bare suyi
magana da ita tun ranar nan da tayi masa zancen kayan sallah be kulata ba gashi har yanzu ana jibi sallah
koda uwarsa yake so taje idi oho.

"Ya jikin naki? Me yasa kika zauna haka a cikin sanyi gashi kanki ko rufeshi bakiyi ga dare ba bakya son
kula da lafiyar kwata kwata" ya fada bayan daya amsa gaisuwar da Amirah tayi masa.
"Kai in ka gaya mata qila taji ai mata da ciki ki zauna duk kiyita budewa Aljanu da ifiritai jiki suna kallo ai
se kiyi tayi se wani abu ya same ki kuma azo ana yaya za'ayi" Addah ta fada tana gyara zama.

"Babu abinda ze sameta In sha Allah kawai dai ta ringa kula kuma meye ma amfanin zamanki idan bazaki
ringa nuna mata abinda ya kamata tayi ba"

"Bazan nuna ba ubana nace bazan nuna ba, kaifa daman ba mutunchi ne dakai ba to ni banzo dan in kula
da ko wacce qatuwa ba zuwa nayi nima a kula dani na hutawa rayuwata a toh" ta hayayyaqo masa.

Be kulata ba ya turawa Amirah ledar daya fito da ita Addah tayi zaraf ta dauke ta zazzage kayan ciki a
qasa.

Kayane kala hudu, Atamfa biyu se Lace daya da Brocade material shima daya duk an yi musu dinkuna
masu kyau. Seda ta ware ko wanne dukda a goge suke tas ta hargitsa kafin ta watsar qasa tana cewa

"Ina nawa naga duk wasu riguna fici fici babu wadda zatamun a ciki"

"To daman an ce miki da naki a ciki ne kayan Matata ne kema ki siya da kudinki mana ai kina dasu ko ni
aka ce na miki kayan sallah?" Ya fada kansa tsaye.

Amirah kanta da take murna tana daddaga kayan dan babu wanda beyi kyai ba kana kallo kuma kasan
masu tsada ne seta tsaya tana kallonsa jin abinda ya fada tace

"Yaya Addah ce fa kake gaya mata haka"

Harara ya maka mata yana cewa

"Gobe Solomon zezo ya kaiki ki siya takalmi da mayafi zan tura miki kudin sannan na manta ban
tambayeki ba ko zakije sallah Gombe ne dan ni bazan je ba"
"Uwarka Nafi ita kake wulaqantawa Bashir bani ba shege wanda be gaji Arziqi ba. Ni zaka kalla kayiwa
gori to wallahi bazanyi da kai ba da uwarka zanyi dan ita ce daidai dani se inji idan ma ita ta baka damar
ka ringa wulaqanta ni. Idan ma banda lalacewa Bashir in haifar maka matar ka aura amma baka da
wadda ka raina a duniya sama dani ko? Nagode.

Ke kuma kina zaune yana qarewa uwarki tana di ai Shikenan gaki gashi nan kuci kanku" Addah ta fada
tana miqewa, har tayi gaba kuma ta dawo tana cewa

"Babu Gomben da zamuje uwar me muka manto acan da zamu koma dakkowa?"

Shidai be kulata ba ya kalli Amirah yana jiran tata amsar itama a sanyaye tace

"Anan zamuyi sallah"

"Shikenan, goben da wuri zezo daganan se ku biya kuyi cefanen abincin sallah"

Ya dauki wayarsa yayi danne danne kafin ya miqe ya shige daki yana cewa "gashi nan idan kunje ze kaiki
inda ake siyar da Ready made ki dauki 50k ki siya mata kala biyu ai zasu isa".

Wayarta da take gefen ta ce tayi qara alamar shigowar saqo ta janyo ta duba, dubu dari da Hamsin ya
tura mata tayi ihun murna daidai sanda Addah ta fito daga dakin da take da waya a kunne tana cewa

"To qarya zan miki Nafi? Zagina yayi ta uwa ta uba ko ince zagin mu nida ke tunda iyayen mu daya har
yana cewa idan na isa na danne shi ma kwata mana" se tayi shitu ta zauna a kujera kafin tace gaba da
cewa

"Oho dai Idan ma ke kike karanta masa cewar ya wulaqanta ni to dani dake dukka ya wulaqanta aikin
banza mana, daman nasan ai ba son zuwana nan kike ba kina baqin ciki nazo naci arziqi ke kina can to
wallahi naga guri idan ma zaki barshi ya sake hannu ya ringa yin wadaqar da yakeyi da a gidan sa gara ki
bati dan ba dawowa zanyi ba nida Gombe seda ziyara muzo a jirgi mu dawo abin mu".
"Haba Addah, a yaushe ya zageki dan Allah yanzu kin hadashi da Dada so kike ta kira tayi masa fada
bayan ga kudi fa ya turamun yace na siya miki kayan"

"To qarya nayi kenan dan ubanki nawa ya turo?" Addah ta zaburo mata, seda ta kalli qofar dakin kafin
tayi qasa da murya tace

"Dubu hamsin ce yace na dauki talatin kudin mayafi da takalmi naki Ashirin".

"Hamsin din banza da wofi uwar me za'a siya da dubu hamsin a zamanin nan, su desina takalmi da
mayafin da mata suke sawa duk a ciki zaki siya" Addah ta fada cikin daga murya.

Alamar tayi shiru karya jiyo Amirah take mata amma ina qara daga muryarta take yi abinta se Amirah ta
narke fuska kamar zatayi kuka tace

"To ke Addah Ina ruwan ki ni hakan daya bani ma na gode dan ba abinda zan suya duk ina da mayafai
kalar da zata shiga da kayan gobense muje a siyo miki naki in be isa bama sena cika miki a nawa" ta fada
qasa qasa danbata so Bashir ya jiyo su ballantana asirin cuwa cuwar da take shirin yi ya to nu.

Bashir kuwa yana shiga bandaki ya shiga yayi uzurin sa da shirin kwanciya bacci yana fitowa ya tarar da
Missed calls din Dada biyu dan haka ya dauki wayar yabi bayan kiran.

"Bashir me yasa akullum baka da aiki sena son tayar mun da hankali ne ace kullum ta Allah seka takali
Addah se kace wata sa'arka bayan kasan qarshe duk akaina abin ze qare" Dada ta fada bayan daya
gaishe ta. Dafa kansa yayi ya zauna akan gado yace

"To yanzu kuma me tace na mata? Maganar kayan sallah cefa mukayi kuma ni tsokanarta nayi da nace
bazan mata ba amma gashi can ai na bada kudin a siya mata"

"Saboda tsarar wasanka ce dole ka ringa tsokanarta ai, kuma zanin sallah ai ba yau ka fara mata ba balle
kace mantawa kayi karkuma ka manta yanzu fa matsayi biyu take dashi a gurinka ko baka mata a komai
ba ka mata na surukuta ai sannan saboda wulaqanci se ana jini sallah zaka bada kudin a siya waye ze
dinka mata toh?"

"Nifa Dada ba dan tana sirikata nake mata dinki ba kawai ra'ayi nayi dan in haka ne Goggon Ma'u ko
qualle ban taba siya na kai mata ba kuma baki taba cemun nayi mata dan tana sirikata ba, nidai na bada
kudin duk ma yanda zasuyi suyi ni ba damuwata bace tun farko ma waya gayyato ta tazo duk gashi nan
ita ba taimakon mutane take da komai ba se qara hura musu matsaloli"

"Allah ya rufa asiri toh, nidai dan Allah ka dena biye mata kuna sa'insa kodan darajar yarta in ma baka
dubi ni yayata bace, naji ku shiru da alama dai bana bazaku zo ba kenan?"

"Eh se zuwa bayan sallah in sha Allah ni zanzo, yaran dai zasu taho tareda Mamansu nasan zasu zo muku
nan da sallah" ya bata amsa,

"Uhm, ni wai ya kuke ciki ne haryanzu Bashir ba'a samu daidaito bane? Ni wallahi gaba daya ma nauyi
yasa na kasa tunkarar kowa nayi maganar nan dashi. Jiya mun hadu da Hajiya Anjin a gidan wata
mutuwa haka ta ringa sakar mun habaici mutane na tayata nidai qarshe kasa zama nayi na taho wallahi
gaba daya gari kowa laifin mu ake gani wai mun aura maka yar uwarmu mun saka ka saki uwar Yayanka
haka kawai bayan ni baka yi shawara dani sanda ka aikata abinka ba.

Dan Allah Bashir ka maida yarinyar nan dakinta dandai kasan bazaka taba maida kamarta ba, idan ma
wani surkullen aka muku na saka anata yi maka sauka da addu'oi Allah ya karya shi ya daidaita tsakanin
ku" Dadata fada cikin jimami.

"Toh Amin ina ta qoqarin haka amma Ma'un yanzu ba irin wadda kika sani ada bace, gaba daya ta canza
kamar wadda aka zuga akaina. Na ina ta addu'a Allah ya shawo mun kanta"

"Toh Allah ya amince, ai ka gani bana ka ja mana, zanin sallar da ake mana bamu samu ba Allah dai ya
rufa asiri"
Tsabar takaici sallama kawai ya mata ya kashe wayar, ba Addah ce kadai me matsala ba ita kanta Dadan
se a hankali kawai na Addah ne ya fito fili idan ba haka ba ana maganaryanda za'ayi a daidaita ita
damuwarta ma ta zanin sallah da bata samu bane Toh Allah ya rufa asiri.

Shi duk meyasa da be gane Baba kadai yake son sa da Alkahiri ba shi kadai yake hango masa illar da
rashin Ma'u a tareda shi zata haifar masa duk sauran abin da suke samu ta dalilin ta kawai shine a
gabansu ai shikenan yanzu da ta barsu kowa seya ji a jikinsa ai daga shi har su kowa ze gane amfaninta
da rashin amfanin ta.

Washe gari tun goma yayi wanka ya shirya dukda jirgin qarfe daya zasu bi, sha daya da rabi ya fito daga
dakinsa, gidan shiru dan Amirah sun tafi kasuwaga ko ina kaca kaca yanda yake tun jiya ko arziqin shara
be samu ba daidai da bawon gyadar da taci jiya yana gurin basu kwashe ba.

Tsaki yaja ya leqa dakin yaran sun tattare komai hatta Bedsheets dinsu da pillow case sun cire se tsurar
katifu akan gadajen na su ya janyo qofar ya fito, bashi a tabbacin ta fita da muqulli dan haka daya kulle
gidan ya nemi wani dan guri ya ajiye muqullin ya zaro wayarsa ya shiga kiran wayar Amiraj dan ya gaya
mata daidai sanda wata shegiyar Sienna ta shigo layin kai tsaya ta wuce qofar gidan Ma'u ta faka.

Irin masu baqin kayan nan da yake gani da wannan mutumin ne daya ya fito yaje ya kwankwasa qofar
gidan, yana tsayen dai se gani yayi suna fito da akwatunan su ana sakawa a mota, a fusace ya qarasa
qofar gidan.

Yana zuwa Suna fitowa dan an gama zuba kaya, yaran suka gaishe shi gaba daya be amsa ba ya matsa
kusa da qofa inda yake jiyo sallamar Ma'u da Baba Harira alamar suna fitowa seya matsa yana sake hade
fuska tareda ayyano abinda ze gaya mata idan ta fito din.

ASMA'U

Da wuri muka gama shiryawa dan kafin goma mun hade komai munyi wanka se dan abinda baza'a rasa
ba. Tun sassafe daman mukayi magana da Yusuf ya gaya mun zuwa sha daya ze turo wanda ze kai mu
Airport dan haka shadaya da mintina ina jin an buga qofa nasan ya iso, a shirye muke dan haka nace su
fara fita da kayan na qarasa sallamar Baba Harira sannan na kira mata Taxi da zata kaita gida dan Anty
bata nan itama bana a Zamfara tayi Azumi.
Muna fitowa na kalli yaran da sukayi cirko cirko a tsaye bayan gashi nan an bude musu qofar motar nace

"Me kuke jira kuka tsaya kamar wasu sojojine ku shiga mota in ba so kuke mu makara ba" fada ina kallon
su se a sannan na lura da Bashir daya hade girar sama data qasa yana gadin qofa, da yar fara'a na kalle
shinace

"Aa Baban Ali ina kwana? Ai da baka wahalar da kanka ka fito ba nasan dai kunyi sallama ai kafin su fito
ko??"

"Motar waye wannan zaku shiga" ya fada cikin dakiya kamar me magana da wata yar sa, ko a jikina,
jakata na miqawa Amnah ina Cewa

"Mun tafi se Allah ya dawo damu" na kama qofa zan shige ina sake cewa

"Kwa taho mudai munyi gaba" dan har sannan Aliyu da Abdallah suna qasa su basu shiga motar ba.

"Magana fa nake miki Ma'u zaki shige mota ki barni, kai dallah ku fito waje"

"Aa to meye matsalarka da sanin motar waye kuma? Ku kuma malamai idan bazaku jeba ku cire kayan
ku tsabar iskanci ana muku magana kun tsaya kuna kallon mutane"

"Yayana bazasu shiga motar ko wanne dan iska ba ku sakko" ya fada a harzuqe yana janyo Farida datafi
kusa dashi.

"Bana son abinda kake mun ka ringa takalata a gaban yara muna abinda be kamata ba, ka rabu dasu mu
tafi koda yake shikenan" na juya ina kallonsu nace

"Ku sauka, malam bude boot za'a cire kaya" na fada cikin hade rai. Baba Harira da har me Taci dinta ya
iso ta saka kayanta ta dawo da sauri tana cewa
"Aa mene haka kuma, Alhaji Bashir ba girman ka bane. Kayi haquri kaga motar ka qarama ce idanma
kace zaka kaisu bazata kwashe ku ba a takure zaku tafi wannan kuma tana da yalwa sosai ai. Be kamata
ku ringa irin wannan abun a gaban yara ba dan Allah ga mutane duk ana kallon ku"

"Shikenan kinci darajar ta wallahi kuje amma wannan ya zama na qarshe da zaki sake daukar mun yara a
motar wani banza" yaja kwafa ya juya. Ko kallon iskar daya kwashe shi ban sakeyi ba wayata ma na ciro
ina danne danne na.

Ina jin Baba Harira na magana itama naqi kulata suna gama shiga Driver yaja mukayi gaba abin mu, ta
gefen ido na hango yanda yake zabga wa motar harara se nayi tsaki a fili nace

"Iska na wahalar da me kayan kara".

Mun sauka Gombe lafiya lau, daga gidan mu aka zo daukar mu. A cikin dakunan mu na yammatanci da
yanzu babu kowa guda dayane Yaya Suwaiba da Mijinta ya mutu ta dawo gida take ciki nan aka
gyaramun daya nima na shiga na zauna.

Wani iri na ringaji a zuciyata, ada kai tsaye gidan mijina nake sauka idan munzo se munkwana mun huta
kafin nake zuwa gida mu gaisa amma yanzu wai har daki na samu na zawarci Allah kenan.

Saboda rashin ganin wata a daren ranar dole washe gari aka tashi da cikon Azumi na talatin kenan. Har
gida aka samo mana me lalle da kitso tazo akayi mana ga yan sannu da zuwa qannena da yayyena suna
ta zuwa abin dariya wai duk wadda tazo barka take mun na barin gidan Bashir kamar wadda aka sako
daga kurkuku a maimakon su tayani jimami Yah Fati ce kadai ta nuna Alhini da rashin jin dadinta.

Nidai nasan banyi rayuwar qunci a gidan Bashir da har za'a ringa murna haka da rabuwar mu ba.

A daren aka kawo kayan su Jafar na gurin Yusuf, shadda ce yar ubansu kala biyu daya doguwa daya me
babbar riga ko wanne da hula da takalmi qafa daya harda Agogo se dogayen riguna Abaya masu kyau na
Amnah da Farida.
A daren na kira wayarsa amma a kashe, se na tura masa da saqo kawai nasan in yagani ko zuwa safiya ze
kirani.

Washe gari aka sallace, munje sallar Idi mun dawo gurin qarfe sha biyu na saka Aliyu ya hada kan
qannensa suka tafi gidan su Bashir suka gaishe su, se bayan Azahar suka dawo tareda Naziru da Yaran
Amiru dukkansu da yake suka sunzo sallah harda Dan gidan Fainusa da alama shima bana an kawo mata
shi kenan.

Har cikin gida Naziru ya shigo muka gaisa ina tayi masa tsiyar ko a waya ya dena nemana yanzu laifin me
mukayi masa.

"Wallahi Anty bansan me zan ce Idan na kiraki ba, Yaya Bashir ya bata komai gaba daya ya saka kunyarki
mukeji ko yanzu abinda Yaya Amiru ya gama fada kenan yake Lagos kwanaki amma ya kasa zuwa ku
gaisa dan besan da wanne ido ze kalle ki ba"

"Haba Naziru, dan Bashir ya hada mu se kum ace dalilinsa zamu rabu, ni ban qullaci kowa a cikin ku ba
wallahi in ma banda abinka shi daya aikata muka ci gaba da gaisawa muna zaune guri daya se ku da
bakusan sanda akayi bane zaku ringa ji masa nauyi ai ba'a haka sedai idan kuma daman neman hanya
kuke kaga ae ku yanke alaqa dani bawai dan abinda ya faru tsakanina da Bashir ba"

"Haba dai Anty alaqa kuma ai yanzu ma muka qullata kin taba ganin da ya sake uwa ai baze yuwuba, ni
yanzu tsoron da nake ma kar ace za'a hanani Yayana ya jawo mun dan dai nasan baki manta alqawarin
mu ba" ya fada yana sosa kai.

Dariya nayi sosai ina cewa

"Oh ni Baba Naziru wai kai dagaske kakeyi me zakayi da wannan kwailar ga manyan yammata nan a gari?
Nida har ina maka kamun wata ma ashe kai kana nan dagaske kake ashe"

Kallon Amnah data tura baki gaba yayi yace

"Haba Anty wane irin wasa wallahi dagaske nake ni sedai idan kuma baza'abani ba in cire rai amma duk
wani lissafina ai kena kinsani Anty tsokana ta kawai kikeyi"
"Babu wanda ze hanaka Naziru indai yarinya ta amince mu kam yan shan biki ne ko Amnah" Zainab data
shigo ta tsokaneta ai kuwa ta kwasa da sauri ta bar gurin tana boye fuska.

"Yawwa Anty Zainab inaga qafarki zan kama ki tayani campain tunda naga Anty wasa ta dauki abun, nida
ina can na saki baki wai ina da uwa a bakin murhu ashe ita sagegeduwa zatayi mun gara da Allah yasa na
sani da wuri" Dariya mukayi gaba daya muka ci gaba da hira shidai jaddadamun yake fa wallahi Yana son
Amnah kuma tun tana yarinya damanya gayamun bashida mata se ita nace toh Allahya tabbatar mana
da Alkahiri.

Seda aka kira La'asar yayi mana sallama bayan ya rabawa yaran barka da sallah dubu daddaya ina ta
masa maganar yayi yawa yayi gana yana cewa

"Bamu samu zama bafa Anty akwai labarai inaga da daddare zan dawo tuna dai an yafe mana laifi"

"Allah ya shiryaka Baba Naziru, ka gaida su Baba zuwa gobe zan shigo nima mu gaisa" munayi sallama ya
wuce.

Seda aka kwana uku da sallah kafin ranar da yamma na shirya zuwa gaida Alhajin su Bashir. Ko babu
komai darajar qaunar da yake nunamun ya cancanci naje, da La’asar na kwashi Khadija da Alawiyya
muka tafi dan ranar gidan mu a cike yake maqil da Jama’a ranar ake zuwa wunin sallah wasu ma sunzo
kenan tunda saura kwana uku a fara bikin su Bilal.

Da qafa muka tafi muna zuwa kan kwana daidai gidan su Ibbah na kalli gidan ina cewa

“Oh Allah sarki rayuwa ko ina Ibbah yake oho dan nafi shekara goma sha rabona dana ganshi”

“Wato yanzu har tuno da tsofaffin samarinki kikeyi saboda kin samu yanci, yana nan kamar ma acikin
gidan yake zama da yayi aure kin san Mamansu ta rasu da dadewa da ya koma Ingila daga baya ya sake
dawowa nan” Alawiyya ta bani amsa.
Seda na harareta ina gyara zaman Gyalen kaina daya zame nace “ke se ana zancen arziqi se ki sako na
tsiya meye kuma wasu tsofaffin samari mtsw” haka muka qarasa gidan su Bashir tun daga waje muke
jiyo hayaniyar Jama’ar gidan da alama suma yau suka zo ga yaransu nan nata wasa a Gareji muna shiga
suka hau gaishe mu.

A tare muka rangada sallama kafin muka cire takalman mu muka shiga Palour Dada inda suke zaune
gaba daya suna hirar tun daga kan Anty Amina har zuwa Sadiya autarsu a mata suna ganin mu sukayi
shiru kamar ruwa ya cinye su.

Afiya ce tayi qarfin halin farayi mana maraba se Samirah da Sadiya da suke kan Three sitter suka miqe
suna ce mana ga guri mu zauna muka samu kujera kuwa muka harde aka shiga gaisawa ina lura da yanda
suke qaremun kallo kamar masu neman wani abu a jikina sena sake gyara zamana ta yanda zasuga
dinkin doguwar rigar Lashin dana saka ga qafata tasha qunshi haka hannaye na zobuna harda na aro duk
na hada na saka.

“Yanzu fa muke cewa zamu shigo gidan ai mu gaisa se gaku kunzo” Anty Amina ta fada tana dariyar
yaqe, ban tanka ta ba nayi murmushi ina duba wayata da saqo ya shigo, Yusuf ne yana gayamun sun
sauka a Abuja yanzu nayi masa sannu da zuwa da bangajiya.

“Su Asma’u ne lale maraba sannunku da zuwa” Muryar Dada ta katseni se na dago na kalleta yanda take
bude mana haqora haka kawai na saki murmushi wanda na zallar takaici ne. Daga inda nake na dan
zamo kadan na gaisheta, yanda kasan zata goyani haka ta ringa amsawa ta juya ta koma Kitchen ta
kwalawa Fainusa kira se gata ta fito da qaron Try an shaqe shi da kayan lemo ga Kwanon Dambun nama
dana Alkaki duka aka hado mana.

“Baba yana ciki ne naga bamu ganshi a qofar gida ba” na fada ina kallon Sadiyah, se Dada daketa faman
musha ruwa tayi saurin Amsawa da cewa

“Yana nan, yau din beji dadi bane shiyasa ya zauna a ciki kinsan iskar maraice yanzu seta tado masa da
zazzabi. Kusha ruwa bari nayi masa magana” ta juya ta fita.

Juyawa nayi na kalli Alawa da Khadija da suketa muzurai karma Khadija taji labari nace
“Kusha ruwa mana Khadija”

“Alhamdulillahi seda muka qoshi kafin muka fito daga gida” Alawiyyan ta fada tana miqewa, se Khadija
ta tashi itama tana cewa

“Muje Anty ku gaisa tunda gurinsa muka zo lokaci yana tafiya”

“Au gurinsa kukazo to ai shikenan, ina namu yayan suke se a turo mana su suzo gurin iyayansu” Samirah
da tun asali daman suna yar tsama tsakaninta da Khadija saboda sun taba hada saurayi qarshe kuma ba
wadda ta aure shi a cikinsu ta fada, se kuwa ta waiwaya ta galla mata harara kafin tayi magana nayi
saurin moqewa ina cewa

“Muje, Anty Amina se anjiman ku Allah bamu Alkahiri”

“Toh Ma’u ku gaida gida se mun shigo daman wallahi bari mukayi mu hadu tare gaba dayan mu se muzo
miki jaje kiyi haquri” Anty Amina ta fada tana taka mana.

Alawiyya da har takai qofa ta juyo tace

“Ku mata jaje kuma meya sameki Ma’u da za’azo miki jaje? Indai zancen rabuwarta da Bashir ce kuyi
zamanku wallahi ba se kunzo ba abu wata da watanni ai tuni muka gama karbar yan taya murnar base
kunzo bama mu yafe muku wallahi”

Gaba daya suka raka mu da ido ina jiyo Fainusa tana cewa

“Kema Anty meye haka dan Allah kina kallon yanda suka shigo suna kallon mutane kamar wasu kashi ai
gashi nan kinja sun gayawa mutane magana mtsw”

“Dallah gafara can an jawo din seki dakeni ai nasan kinji haushi” Amina ta fada tana harararta.
“Gaskiya dai Yaya Bashir ya luza ji yanda mata tayi luwai abinta zawarci ya karbeta ba irin wasu ba”
Suwaiba data fi kowa iskanci ta fada nan da nan suka fara rigima da Fainusa dan dai ita kadai ce
Bazawara a gurin kuma kowa yasan da ita take tunda daman sun ba mudai muka shige Palour Alhajin Su
Bashir inda Dada harda qara shimfida mana qatuwar Dadduma akan Carpet din dayake gurin.

Cikin girmamawa muka gaishe shi gaba daya.

“Ki gafarce ni Asma’u wallahi nauyi da kunya ta saka na kasa kiran ki, Bashir be kyautawa kansa ba amma
babu komai Allah yasa hakan shiya fiye muku Alkahiri” Baban ya fada daga kwance da alama jikin ya
takura masa da gaske.

“Babu komai Baba, nima ai nayi laifi da ban kiraka na gaishe ka ba kayi haquri”

“Aa karki kuma ai ke kika cancanci ban haquri,ki ci gaba da haqurin dai in sha Allahu zaki dauke shi a
gaba. Ina Alhaji Abdu? Dazu da safe yazo ai ya kawo mun magani kin gansu can wai shi likita ne saboda
jiya na gaya masa ina ciwon kai da daddare da zasu tafi” ya fada yana nuna mun paracetamol din da
yake gefensa.

“Au wai daman kai ze kawo wa? Yazo yana ta tambayata wai maganin ciwon kai na zatama shi ze sha na
bashi a she nan yayiwo”

“Nan yazo ai ya jima ma, amma fa nayi nayi yaci abinci yaqi wai Mami ta hana su kwadayi banda abin
Abdullahi nan ai gidan su ubansa ne ko yana inda yafi nan ne ko da yake qila ba’a fayyace masa ba” Dada
ta fada da yar dariyarta, sena daga kai na kalleta kawai nayi murmushi

“Yaushe zaku wuce saboda aiki? Koda yake akwai bikin Su Bilalu na manta se an qare zaku koma kenan”
Baba ya sake fada ba tareda yabi takan zancen Dadan ba.

“Eh se an gama biki Baba, daman sati biyu zamuyi gaba daya”

“Toh Allah ya taimaka yasa ayi a sa’a. Kema Allah ubangiji ya fito miki da Miji na gari kiyi auranki kinji”
“Amin Baba, Ai Allah ma ya kawo mata sedai ayi Addu’ar fatan Alkahiri kuma” Alawiyya tayi caraf ta
amsa.

“Kai madallah amma naji dadi ubangiji ya tabbatar da Alkahiri yasa zamu gani kai nayi murna sosai, Nafi
kinji abin Allah ko Baba ya fada har yana miqewa zaune.Dada da tun fara maganar Alawiyya tayi kasaqe
tana kallon ta tace

“Uhm” tareda yaqen dole,har muka gama hirar da zamuyi Baba nata sa mana Albarka muka miqe. Jakata
na zuge na ciro bandir din yan dari biyu sababbi dana tanada na ajiye a gabansa ina cewa

“Gashi Baba babu yawa a siyi Goro, an jima na turo su su duba jikin naka”

“Kai kai Haba Asma’u dauke kudinki kinji ai gaisuwar da kika zo mukayi ma tafi komai Nagode Allah yayi
miki albarka” ya fada yana turomun kudin se na nufi qofa ina cewa

“Dada se anjiman ku toh”. Seda Alawiyya da Khadija ko wacce ta qara aje masa dubu biyar biyar kafin
muka kama hanyar gida. Har Get Dada da duk jikinta yayi sanyi ta rakamu kafin ta juya, har mun fita
Samurah ta kwaso da gudu tana tambayata wai

“Anty zan samu chanjin sabon kudi?”

“Sabon kudi ai yana banki Samirah, ki nemi Sa’ad mana sune ma’aikatan banki” na bata amsa muka qara
gaba.

Oh ikon Allah, ada fa idan zanje gidan irin haka sena shaqe uwayen kuloli da Abinci kala kala, Dubu
Goma nan sena aje mata ta goron sallah banda wadda zan rabawa kaf jikokin gidan idan sunzo sannan
su kansu qannen nasa wasu su fake da chanjin sabon kudi wasu kuma kai tsaye ma zasu ne na basu
barka da sallah idan kuma zamu tafi nawa Yayan ko yar biyar babu me basu idan ba Amiru ba shi daman
har gida yake zuwa ranar idi tareda Sa’ad da Naziru suci tuwon sallah ya raba musu kudi amma matan
babu me karar ko dan kunne ta kawowa Farida seni jaka na hidimta musu nayiwa Yayansu kai kar Allah
ya kawo abinda baze wuce bama.

A daren ranar Alhaji Qarami yaki rani bangarensa yana tuntubata wai ya muke ciki da Yusuf?
“Mutumin nan na qaunar ko Ma’u, dukda baka shaidar Dan Adam amma ina kyautata masa zato akanki
wallahi ga danginsa suna sonki”

“Uhm toh Yaya nidai ina ta Addu’a Allah ya zabamun mafi Alkahiri dai, kuma fa shi Yusuf din nan ma ni
ban gama gane masa ba. Wai ita matarsa wane irin aure nema suke tana wata duniya yana wata nifa sau
daya naji yace yaje can inda take” na fada ina gyara zama.

“Wayaga Ballan sori, ke har lissafin wannan kikeyi ma ai in kinji ana da ita da babu duk daya to wannan
mata ta Yusuf kenan. Ita fa tsabar Gayunta ne ta girmi zaman Najeria, daman yar uban gidansa ce
Ambassador Musa Manzo ya aureta uwarta Baturiya ce.

Shikansa Baban nata irin wannan gantalallen auran sukeyi da uwar tana can America shi da sauran
Matansa suna Nigeria se sanda yai ra’ayi yaje ko ita tazo to itama Inteesar din da akwai yayarta itama
me aure ce duk haka dai suke wannan gantali da Yusuf din.

Dan haka ma ki saka ranki a inuwa kamar ma ke kadaice bakida wata kishiya dan yanda kika San ba Mata
ba wallahi. Su yawon shaqatawa da zaga duniya da kwalliya suka saka a gaba. yo tikita ta yanka masa fa
yaje ya nemi duk wadda yake so akan dai tazo Nigeria tayi zaman aure wai kuma a haka sonsa take
kamar me badan ma Allah yasaka nutsatstse neba aida yayi tambari yanzu a neman matan banza tunda
auren fa kusan shekara biyar kenan ana wannan gantalin kawai ki amsa mana musha biki se mu daura
Addu’a qanwar mu ta zama Firs Lady ai mukam ras damu” Anty Ladi da muke cewa Momi uwargidan
Alhaji qarami ta koromun wannan jawabin.

Tagumi na rafka ina jinta, ikon Allah kunji wata sabuwa kuma su haka suke kenan daga uwar har yayan?

“Toh kinji ai se kuma me kike buqatar sani ki tambayeta” Yaya ya fada yana yar dariya.

“Kai ni fa Yallabai randa mukaje ganin ginin nan nasa kwana nayi da takaicin da yanzu mu zamuje muyita
iyayi muna zuba kaya gidan qanwar mu, na ringa raya da ina da Yar data isa aure ko qanwa to fa duk ma
yanda za’ayi se an hada auran su da dai a dakko bare taci arziqin dan nasan aure ze qara.
Harfa na fara tunanin na qyasawa Suwaiba se kuma nace kar kayiwa kishiya hanyar arziqi se abu ya samu
a manta dakai kwatsam se gashi wannan abu ya wakana kai nifa harda sujudushshukur nayi kana fita
randa ka gaya mun maganar nan, yo ko zuwa nayi na dauki hoto a gidan ai an biyani wallahi”

Sosai muka ringa dariya nida Yaya musamman wai kar ta gayawa Anty Suwaiba kishiyarya ae arziqi ya
samu su manta da ita.

“Ku zauna kuna dariya shi ai yasan me muka gani wallahi keni ko bakyason sa dan Allah ki aure shi kowa
ya san gaba kika ci ba baya ba”

“Aa dai gara tana son nasa dai, ni na zata ma sun gama komai ai yanda yake addabata da waya duk
lissafina kawai mu hada danasu Bilal a daura daga baya se suyi tariya ko” Alhaji Qarami ya fada

“Ai da ka gama mun komai wallahi yallabi kawai ayi haka, kai infa aka biye ta Ma’u ba wanda zata so
wannan mijin nata me fuskar shanu ya rigada ya rubuce sunanta a Allon qarfe se ta Allah kawai gara in
ma dole za’a mata ayi a wuce Gurin”

Dariya sosia Momy ta ringa bani daman ita haka take akwai abin dariya, tana da matuqar kirki ta kuma
kama girmanta a matsayinta na matar babban wan mu babu raini haka babu wulaqanci kowa natane
sefa wanda yazo mata da abin da be mata ba bazata dauka ba.

A gaba da sakani da hudubobi dan Alhaji tashi yayi ya barmu bayan daya jaddadamun na san matsaya
dan Goggo fa dagaske tace tana dawowa dole na fitar da miji nayi aure kona tattaro na dawo Gombe na
bar aikinsa yayi sanadin gurgudewar aurena.

Ranar raba dare nayi ina saqa da warwara, daga qarshe na tashi na raya daren addu’ata dai a kullum
zabin Alkahiri daga Allah (To Hajia Ma’u kwankwasa qofa za’ayi ace fito ga zabin da Allah ya miki ko
yaya? Ke zaki saki ranki ki bude zuciyar ki sannan ne zaki fahimci abinda Allah ya zabar mikin).

BASHIR
Haka ya sallace cikin quncin zuciya da takaici da dana sanin me yasa ma be tafi Gombe ba shima. Sallah
guda haka ya zauna a gida yana zare ido dama dama ran idi yaci abinci dan Fried rice Amirah ta daure
tayi musu ranar harda Salad ga Zobo me sanyi da dabgen kaji.

Haka yaci ta a babu yanda ya iya to yaushe rabon ma daya samu kamarta din? Babu tuwon sallar nan
dasu Sinasir da waina kai gaba daya Eatate din qiyau miyau kodan qamshin abincin sallar nan da zakaji
gari ya dauka babu toh duk musulman sun wuce garuruwanau sallah shima tsautsayi ya zaunar dashi dan
be tabayi ba se wannan karon.

Yana daki yana aikin kallon status din Jama’a na sallah kowa da Yayansa sunje Ido seya tuna yanda Ma’u
take tasa shi su kashe hotuna ran sallah da duk wnada ya kalla seya yaba wannan karon ko Babbar rigar
ma ajuye ya sakata seda yaje masallaci aka gaya masa ya gyara dan sanda ya shirya ya tafi Matar gidan
bata ma fito daga daki ba bare ta taya shi shiri, daya dawo dai ya tarar ta cancada kwalliya da kayan daya
mata ta kuwa yi kyau sosai masha Allah haka gidan an gyara abinda ya sauqaqa bacin rabsa kenan
sannan ko ba komai ya dan samun abin kaiwa bakin salati.

A status din Amnah yaga hotunan su na Idi, shaddar gurin Yusuf me babar riga yaran suka saka sunyi
kyau kamar ka sace su ka gudu haka ya ringa zooming yana murmushi da jin kansa na fasuwa wai fa
yayansa ne da Ma’u, yo ko dan su ai dole ma ta haqura ta dawo su zauna.

Hoton da sukayi ita da yaran ta cakare kamar wasu qannenta sun sakata a tsakiya ya tsaya yana kallo
nan da nan ya kwafa ya dora a status dinsa kuwa. Haka ya wuni kallon hotuna Daya gaji da zaman gida
ya fita zaga gari, su Addah dai ana palour ana warkajami da Kajin da sukayi Dabgensu.

Ranar kwana uku da salllah da yamma sakakiya Dada ta kirashi tana gaya masa abin tashin hankali
zancen wai Asma’u ta samu miji sun daidaita lokaci kadan ya rage ta daura aure.

Yana zaune a gurin da yake zuwa cin abinci lokacin ta kirashin, tsabar rikicewa besan sanda ya watsar da
lemon hannunsa ba ya miqe jiki na rawa ya shiga neman layin Ma’u sam ya manta ma da cewar ta toshe
shi seda yaqi shiga sannan ya koma kiran Amnah, akayi rashin Sa’a bata gida sun tafi yawon sallah gidan
qawayenta.

Seda ya je mota aka bishi da bill dan be biya ba da ze tafi, Yarinyar nan ce ta kwanaki.
“Me yasa a koda yaushe kake cikin yanayin damuwa da tashin hankali ne Bawan Allah?” Ta fada bayan
daya bata kudin ya shiga mota.

Harara ya zabga mata yace

“Gafara daga nan kona take miki qafafu” ya figi mota yayi gaba, seta kama baki tace

“Toh daga magana? a sauka lafiya to nima maganina kenan ta juya ciki abinta.

WATA KISHIYAR

(ALKAHIRI CE KO SHARRI)

Na Maryamah Farouk

(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)

Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 59

An daura auran su Bilal munsha shagali sosai dan mun dade rabon mu da biki a gidan mu.

Washe garin ranar daurin auran ba tareda na sanar da Bashir ba muka kwashe kayana na sedai yaji a gari
mukayiwa gidan qaf tsinke bamu bari ba dan wannan dibar kayan harya fi na Lagos tunda da yan gidan
mu mukaje daidai da gadon dakinsa daya siya da kudinsa seda suka cire wai Yaya sun bani kayansa kuwa
haka suka zube masa akan Katifar dayaci arziqi aka bar masa.
Seda suka ga gida ya zama kango kafin suka haqura, na kwashi abubuwan da nake so akayi packaging
ragowar kuwa Wani shago da suke siyan kayan hannu muka kaisu, sun siya da daraja sosai dan kayan
masu qarko ne da kyau kuma basuyi komai ba tun kafin mu bar gurin aka fara wawason su suka cake
mun uwayen kudadena a akawun muka tafi zan juya su zuwa sanda Allah ze yanke mun na sake siyan
wasu. Kwana uku muka qara muka tafi dukda naso na bar su qarasa hutunsu se kuma dai muka koma
gaba daya.

Tare muka gyara gidan dukda ba wani datti yayi ba dan mun kulle ko ina sanda zamu tafi. Seda muka
gama komai nace wa Aliyu yayi wanka ya rakani mu siyo abinci saboda saukar Yamma mukayi base
munyi girki ba.

Muna tafe a hanya Yusuf da bamu samu mun hadu a Gombe ba ya kirani mukayi magana.

"Mami dan Allah ina so muyi magana" Aliyun ya fada bayan dana gama amsa wayar, sena waiwaya na
kalleshi. Tuntuni na lura da rashin walwalarsa ko biyonin da yayi nasan da dalili gaba daya ya canza
dukda daman bashi da sakin fuska sosai amma yanzu abin ya qaru ko yaushe yana cikin qunci da
damuwa.

"Ina jin ka nima daman inaso nayi magana dakai me yake damunka duk kabi ka takura rayuwarka Aliyu?"
Na fada ina kallonsa.

Ajiyar zuciya ya sauke bayan daya faka motar dan shi yake janmu saboda gurin da mukaje babu nisa
daga gida.

"Mami bana jin dadin yanda kukeyi keda Abbi, nasan yayi miki laifi amma Mami tunda ya baki haquri to
ki haqura mana ki yafe masa"

"Aliyu ni laifin me Abbin yayi mun? Kuma koma menene ba kana kallo ba ai shiyake zuwa kullum har
inda nake yana takala ta da fada dan haka shi ya kamata kaje ka yiwa magana ya dena abinda yakeyi
tunda har kayi hankalin gane badaidai bane" na fada fuska a daure dan karma ya kawo mun wani
shirme,
"Toh amma Mami.."

"Kaga ni yunwa nake ji zaka shiga ko a mota zaka zauna" na katse shi ina balle murfin qofar. Seya gyada
kai kawai ya kashe motar muka fita yanda muka jera seka zata irin qanina ne haka muka shiga gurin na
samu guri na zauna tareda gaya masa abinda zeyi mana order.

"Assalamu Alaikum ranki ya dade" naji an fada daga gefe na na dago da sauri jin kamar nasan muryar,
Ambassador Mutallab Ali ne shida wani a teburin da yake gefen namu se wannan PA din nasa yana tsaye
yana zare ido.

"Ranka ya dade barka da rana" na fada ina sunkuyar da kai da tuno yanda na dannawa lambar sa block
tun a kiran farko qila yayi ta kira harya haqura tunda bata shiga.

"Daga kiran waya malama Asma'u se kikayi blocking dina kuma laifin me nayi?" Ya fada kamar ya shiga
zuciyata. Kaina na qas ina dan murmushin yaqe ya sake cewa

"Tunda na kira naji line busy nace to gimbiyar bata son damuwa bari a barta ta huta, kwanabiyu
abubuwa sun sha kaina shiyasa ma ban sake gwadawa naji ko an bude ni ba se gashi yanzu Allah ya
hadamu dan haka a gabana zaki bude na gani".

Wato yanda ya dage yana magana ni gaba daya ma kunya ya bani ko ganin girman kansa beyi ba yake
wani lankwashe harshe gashi kuma Abokin nasa se wata dariya yake kamar wanda akewa cakulkuli ni
duk ya bani Haushi nama rasa me zance musu.

"Kinyi shiru Asma'u, koda yake fara dakko wayar kiyi unblocking dina mayi magana daga baya dan yanzu
sauri nakeyi, Alhaji Sani ka ganta nan ita ce yarinyar danake baka labari"

"Ah ai na ganta tayi sosai kuwa bazamu bari wannan ta wuce mu ba" wanda ya kira da Alhaji Sani ya fada
cikin hausarsa da bata fita sosai daga ji ba cikakken Bahaishe bane se na fara laluben wayata akan Tebur
din da nake, Ajiyar zuciya na sauke dana tuna na manta ta a mota da zamu fito na juya na kalle shi da
dan murmushi nace
"Ai kuwa na manta ta a gida ina sauri zamu fito" daidai sannan Aliyu ya qaraso da Waiter na binsa da
ledojin abinci. Tsabar wulaqanci kallo daya ya musu ya dauke kai kamar wanda yaga kashi ya zauna a
kujera yana muzurai.

"Wannan Qaninki ne?" Ambassador ya fada yana kallon Aliyun, sena qaqalo murmushi nace

"Aa, first born dina ne, Aliyu baka ga mutane bane?"

"Nagansu mana" ya fada kansa tsaye kamar be gane yaran ya gaishe su nake masa ba. Tsabar takaici na
bude baki kawai ina kallon yanda ya hade fuska yaja Ice cream din daya taho dashi a hannunsa ya hau
sha, zanyi magana Alhaji Sani ya tare ni da cewa

"Aa barshi yaro ya gida? Ina qannenka kana taya Babanku kishi ko banga laifin ka ba".

Murmushi Ambassador yayi kafin ya miqawa PA hannu se yayi saurin bashi wata briefcase dake
hannunsa, budeta yayi ya ciro rafar Dala dari dari guda biyu ya ajiye mun daya yace

"Gashi idan kun gama seki biyu kudin muna sauri ne bari mu wuce, Yaro ka saka katin waya ko" ya ajiye
ragowar dayar a gaban Aliyu.

"Haba Ranka ya dade ai da ka barshi mun rigada mun biya ai" na fada ina tura masa kudin, gaba yayi
abinsa yana cewa

"Zan sake gwada wayar naji idan kin koma gida" ya wuce suka take masa baya bayan da Alhaji Sani ma
ya sake ajiyewa Aliyun wata Dalar harda dafa kansa yace yana yar dariya yace

"Yaron kirki me taya Babansa kishi" suka fice gaba daya.

"Wallahi sekaci ubanka Aliyu ni ka kunyata a idon mutane ka nuna musu baka da tarbiyya ko?" Na fada
kamar zan kwada masa mari Saboda haushin abinda yayi din. Ice cream din ya ture kamar zeyi kuka yace

"Toh ni Mami ina ruwana da su dazan gaishe ni ai ban san tare kuke ba tunda bada su muka zo ba"
"Zaka rufe mun baki ko sena kwade ka anan, idan ba tare muke ba daman haka kukeyi idan kunga na
gaba da ku? Ko darajar shekarunsu beci ka gaishe su ba tunda ai ba kai ba ko ubanka sun girme shi" na
fada cikin masifa.

Seya miqe tsaye ya kwashe kudin gabansa yana cewa

"Nidai kiyi haquri"

"Ajiye su dan ubanka, ka wulaqanta su saboda baka da kunya ka dauki kudin da suka baka" na fada ina
fizege kudin, saboda wulaqanci se ya saka dariya ma yana cewa

"Toh Mami ai ba roqar su nayi ba, ki bani kinga se na kaiwa Abbi ya auro wadda zata ringa dafa masa
abincin da kika ce".

Tsabar mamaki kawai bude baki nayi ina kallonsa, lallai Aliyu ko da yake ba laifinsa bane wannan yafi
kama da Tunanin Bashir qila shi yake karanta masa duk abinda zeyi to kuwa duk zasu ci ubansu shida
Bashir din.

Haka muka wuce gida dani dashi babu wanda ya sake cewa komai. Tare muka ci abincingaba aya aka
gama aka tattare gurin, Seda akayi Isha ina daki Aliyu ya leqo yana cemun ze tafi seda safe

"Ba anan zaka kwana ba?" Na tambaye shi,

"Eh zanje can gidan da safe na dawo" ya fada yana sosa kai.

"Allah ya kaimu, kuja mana qofar idan kun fita" na fada ina ci gaba da lazumi na.

Washe gari da wuri na shirya fita aiki saboda babu makaranta duk yaran ma suna bacci abinsu. Naci
gayuna, Shayi kawai nasha na dauki jakata ina cikin kulle qofa Bashir ya qaraso qofar gidan shima cikin
shirin fita aiki.

"Barka da Safiya Ma'u" ya fada yana kallona.


"Ina kwana Baban Ali?" Na mayar masa da amsa ina ciro muqullin mota daga jakata.

"Ashe kun dawo, se ganin Aliyu nayi yace jiya da yamma kuka dawo"

"Uhm wallahi saboda aiki kasani, da se satin sama idan hutu ya qare zamu dawo" na bashi amsa cikin
sauri sauri ina danna mabudin motata.

"Nace in ba damuwa inaso zamuyi magana ne dan Allah ko zuwa anjima idan na dawo se nazo gida" ya
fada yana shafa kai kamar wani yaro,

"Toh magana kuma dani? Allah ya kaimu" na bashi amsa ina shigewa motata, shiya rufo mun murfin
yana mun adawo lafiya wai sabon salo kiran sallah da usur, seda na kai qofar gidansa na hangi Amirah
tsaye cikin shiri kamar a tsikara mata tsinke ta fashe tsabar kumburi da alama fita zasuyi ya tsayar da ita.

Da yamma kuwa gurin qarfe shida sega Bashir, na fito wanka kenan dan nima ban dade da dawowa ba
sannan Farida ta shiga take gayamun ga Abbi.

"Ma'u wata magana naji da hankali na ya kasa nutsuwa da ita wai aure zakiyi" ya fada bayan da muka
gaisa. Sena kalle shi yanda gaba daya yabi ya rikita kansa duk ya sukurkuce gayun nan da yakeyi da yanzu
babu da alama ko hutawa ma beyi ba yana dawowa ya taho nan dan rigar saman kayan sa kadai ya cire.

"Toh ashe labari ya iso maka a ina kaji?" Na tambaye shi da dan murmushi a fuskata seya zaburo kamar
ze sauko daga kujerar da yake yace

"Bangane ba kina so kice mun da gaske ne Ma'u aure zakiyi? Wane irin Aure? ki zauna da wani namiji
bani ba ko hada soyayyata da ta wani a zuciyarki?"

Seda na gyara zama dakyau na dora qafa daya kan daya ina girgiza su kafin nace
"Aure kala nawa ne Bashir? Shi din dai wanda ka sani na mata da miji da zasu zauna a qarqashin inuwa
daya.

Batun na zauna wani namiji kuma da Mace yar uwata kake so na aura ko yaya? Ita kuma soyayya ai
yanzu tashi ce kadai a cikin zuciyata tuni anyi waje road da taka tsohon labari kenan".

Miqe wa tsaye yayi har yana tunkude kayan Lemon da aka kawo masa suka zube a qasa ya nunani da
hannu yana cewa

"Qarya kike Asma'u bazaki taba son wani Namiji a duniya ba bayan ni idan ma zakiyi aure da gaske sedai
kiyi kawai amma badan so ko jin dadi ba ina kuma tabbatar miki da cewa duk ma inda kike tunanin zakije
sekij dawo dan zuciyarki bazata taba aminta da wani bayan ni ba wannan alqawari nayi miki"

Ko a jikina na miqe tsaye nima ina kallonsa cikin ido nace

"A lokacin dana nuna maka kaine rayuwata Bashir ka dauka shirme nake ban san kaina ba a sannan, a
yanzu kuwa ka bude mun ido ka kuma bani damar da nayi karatun sanin matsayina da abinda ya
cancanta dani.

Oh wai fata kake mun nayi aure na sake dawo maka? Toh ai tunda na iya zama da kai da halinka Bashir ni
kuwa wane kalar miji ne zan gagara yin haquri dashi zance ma kawai kake yi wannan" ina gama fada nayi
gaba zan bar gurin yayi saurin shan gabana tareda riqo hannuna, kallon dana jefa masa na kayi hauka ne
yasa shi saurin sakina yaja baya yana cewa

"Kiyi haquri naji koma menene ki gaya mun duk abinda bakya so zan dena wallahi nidai kiyi haquri ki
dawo dakinki muci gaba da zama kinji wallahi bazan iya rayuwa babu ke ba".

Ni kuwa kaga yanzu ma na daura danbar rayuwa ba tareda kai ba, kai ni ai yanzu bama zan iya maimaita
zaman da nayi a baya dakai ba Bashir kaje kawai ka zauna da matar da Allah ya zaba maka ka barni nima
na gwada wata rayuwar haba karka zama me son kanka mana"

"Ma'u dan Allah..."


"Dan girman Allah Bashir ka fita, da nasan wannan maganar ce zata kawo ka ma da tun da safen munyita
wallahi base kazo ka tasani gaba da magiya ba ko da dole ne nace bana so bazan koma ba ka qyale ni
mana idan kuma kana da qarfi seka dauke ni aka ka maida ni gidanna ka haba" na fada a hasale dan ya
ishe ni kuma.

"Shikenan seki shirya ganin gawata dan duk ranar da kika auri wani bani ba nasan daga lokacin rayuwa ta
zata zo qarshe".

"Allah ya jiqanka, karka damu su Aliyu bazasuyi maraici ba" na fada ina wuce shi. Ina ji a jikina yanda ya
bini da kallo harna shige daki.

BASHIR

Jiki a sanyaye ya kama hanyar gidansa yana tunanin wai shi mezeyi Ma'u ta dawo masa?

Ya gwada duk yanda akace masa yayi nasa dabarun amma duk a banza kullum ma sake botsarewa takeyi
a maimakon ta sakko. Yanzu mutum biyu suka rage masa da yake ganin zasu iya shawo kanta daga
Babansu se Alhaji Qarami.

Kai shi yana kunyar Alhaji Qarami wallahi abinda ya masa a rayuwa ko darajar wannan yaci ace ya
dagawa Ma'u qafa koda ita ta takaleshi yaci ya dauke kai. Baban dai ze kira tunda dai ai duk tsiya ubansa
ne bakuma ze zabi Ma'u akansa ba kuma ai shima yana son zamansa da ita dan haka ze saka baki ta
dawo masa.

Wayar Baban ya kira amma Dada ta daga take gaya masa yana bacci saboda jikinsa ya matsa kwana biyu.
Shi se sannan ya tuna da zancen kudin maganin da ze tura musu gashi account dinsa yayi qasa sosai
saboda hidimar sallah da yayi kuma wata ya raba balle ya saka rai da zuwan Albashi.

"Kai komai ma ya rikicewa mutum kudin kansu sun dena Albarka kamar wanda ake kwashe su" ya fada a
fili bayan da yayi wa Sa'ad transfer abinda ya samu na siyan maganin, dan abinda ya masa saura baya
zaton ze rufa masa watan gashi za'a koma makaranta biyan school fees kadai ya ishe shi yana ganin dole
seya karfi wani abu a kudin super market saboda biyan kudin makarantar dan da wuya ya taba kudin
idan an hada lissafi ribar sake mayar da ita ake se idan ta qure masa ne yake taba wani abun a ciki.
Yana shiga gida ya tarar da Amirah na murqususun ciwon ciki kuma, kai Jama'a haka suka kwasa se
Asibiti likita ya ringa fada akan wai wani abun tasha irin magungunan Hausa, daya matsata qarshe take
gaya masa wai magani Addah tasa aka aiko mata daga Gombe a qaryar su na zaqi ne tunda cikinta ya
shiga kusan wata Bakwai yanzun shine ta karbo mata zancen gaskiya kuwa sabon malami ta samu ta
hannun Anty Talatu ita tayo musu aiken saboda sun gaya mata sun rasa kan Bashir din zaman dai se a
hankali.

Ya kuwa ringa bala'i kuwa yana cewa Idan wani abu ya samu cikin ita ta sani babu ruwansa tunda ita
bata tausayin kanta haka suka dawo bayan da aka bata magunguna su kansu seda ya kashe kusan dubu
Hamsin a daren.

Kwana biyu a tsakani aka kirasu a waya cewar Ummi ta haihu ta samu ya Mace amma ta koma murna
Addah ta ringayi tana hamdala da akace yar ta mutu sedai murna ta koma ciki jin wai an daurawa
Ummin aure da dai shi mijin da bata so ta aura din dan daman seda sukayi yarjejeniya da iyayensa akan
tana haihuwa za'a daura aure suka yarda dan haka ana kiran Alhaji Murtala daga can Katsina inda ya
kaita gurin wani Amininsa cewar ta haihu ya tashi ya tafi gidan su saurayin ya gaya musu. Ana sallar
Azahar kuwa a masallaci aka daura musu aure se saka ranar da zata dawo ta tare.

Kusan Sati guda gaba daya Bashir ya zama gashi nan ne, abubuwa sun rikice masa duk yanda ya dauki
shawo kan Ma'u da sauqi abinya shallake haka nacin yake roqon yake amma kamar wanda yake shika
dusa dukda shima dai da tasa irin wautar.

Wani irin biko yakeyi me kamada fin qarfi saboda a duk sanda ya tashi yi mata magana nuna mata yake
kamar ya zamar mata dole bazata oya rayuwa babu shi ba dan haka ta haqura ta dawo masa wanda sam
shi be dauki hakan da wani laifi ba gani yake kamar yana tuna mata da girman soyayyar da take tsakanin
su ne wanda ita kuma wannan abun shi yake wara qona mata rai take jin dole ta barshi ko dan ta nuna
masa cewar ba tare aka dauro rayukansu aka aiko duniya ba.

Ana saura sati daya a koma makaranta kamar yanda aka saba suka tura mata da Takardar biyan kudi
saboda daman lambar wayarta ce akai in an turo mata seta turawa Bashir din ya bada kudin.
A yanda aka saba an samu qarin kudin makaranta ga kudin littattafai saboda sabuwar shekara aka shiga
za'ayi canjin aji ga kudin jarabawar WAEC da NECO da JAMB na Aliyu da ze shiga aji shida dan haka da
aka hada lissafin sega kudi sun tasarma kusan Miliyan biyu.

Ita kanta seda ta jimanta wannan al'amari ta rasa abinda yasa makarantar suke haka basa bada notice na
qarin kudi sedai kawai idan an kawo maka teller ka gani kamar wadanda suka bawa iyayen yaran ajiya
koda yake makaranta ce ta yayan masu dashi suma karanbani ya saka suka kai yayansu ai.

Ta Whatsapp ta tura masa da takaddun lokacin yana zaune a Office be dade da gama waya da Amirah ba
da take masa zancen kudin siyayyar haihuwa gashi jikin Alhajin su ya qara zafi dan shirin kaishi Kano
akeyi ma Asibitin Malam nan ma dai duk wani lissafin kudin ne dai yanzu ga wannan ubannin kudi na
makaranta kuma sun taso masa duk a ina ze qwaqulosu?

Wai to ta yaya da duk yake hidimomin sa har ya samu rara a asusun sa ba taredaya girgiza ba?
Albashinsa Miliyan daya ne duk wata saboda babu Fansho babu garatuti idan ka gama banda sauran
alawan da suke samu kala kala musamman yanzu daya samu qarin matsayi packages harda na banza
basu ake dan haka yake facakarsa baya ma lissafi bare ya ajiye na buqatar kota kwana tunda kudinna
shigo masa koda yaushe daman Super markets dinsa Gombe sune tanadin Bayan Ritaya wanda se a
yanzu yake hango tarin gatan da Ma'u tayi masa data saka shi a harkar kasuwanci nan dan yanzu ba
qaramin habaka jarinyayi ba tunda ba'a tabasu duk ribar da aka samu ciki a ke maidata.

Text ya tura mata akan ayi masa haquri kafin a koma ze bayar nan ya shiga hado ta inda zasu fito, dole
dai ya karbi kudi a gurin Sa'ad din idanyaso daga baya ya mayar dan su makaranta babu ruwansu ba jira
zasuyi ya samu ba shawarar daya yanke kenan a take kuwa ya kirashi akan yana san ya karbi miliyan uku
se Sa'ad din yake gaya masa sunyi sarin kaya, kudin da suke dasu a qasa ko Miliyan daya bazasu kai ba na
banki kuma ze dauki lokaci dan yamamta account din ya samu matsala ta yanda sedai kudi su shiga
amma bazasu fita ba dan haka dole sedai idan zeje Gomben da kansa ya gyara tunda shine signatory din.

A daren ranar yana zaune a qofar kujera ya dasa kujera yana aikin tunani, daga inda yake yana iya jiyo
hayaniyar yara daga gidan Ma'u saboda yanda Estate din yayi shiru.

Hira suke cikin raha anata qyaqyata dariya kamar yanda sukeyi a ko wanne dare lokacin da tana gidansa
wani lokacin idan yaga dama ya zauna ayi dashi wani lokacin kuma yana daga gefe yana sauraronsu yana
murmushi dan ita irin mutanen nan ce masu biyewa shirmeb yara ta haka take sanin duk abinda suke
ciki basa boye mata tunda ta mayar dasu kamar qawayenta.

Ya ilahi me yasa duk beyi tunanin komai ba ya rusa Wannan kyakykyawar rayuwar ta gidansa? Yanzu da
ace bata kusada yaran a ina zasu ringa samun wannan walwalar da farincinin saboda yanzu sam babu
wata damuwa a tattare dasu, kamar daman a haka suka tashi tsakanin gidaje biyun musamman da baya
takura musu da zancen kwana duk inda suka so yanzu zamansu suke shiyasa Aliyu ne kadai yake rayuwar
qunci da damuwa a cikinsu kodan shine babba yafi su tunani da gane abinda yake faruwa.

"Abbi tunanin me kakeyi tun dazu ina tayi maka magana baka ji ba" maganar da Aliyu yayai tareda
girgizashi ta dawo dashi hayyacinsa. Se ya sauke ajiyar zuciya yana kallonsa yace

"Tunanin da yawa Aliyu, gaba daya kaina ya qulle ga Maminku sam ta kasa fahimta ta tayi haquri akan
abinda ya faru ban san yaya zanyi ba Aliyu".

"Abbi duk abinda ya faru ai laifinka ne, haka kawai kaje ka qara aure kuma Abbi ka rasa wa zaka aura se
Anty Amirah bayan kasan Mami cefa ta riqeta, kazo ka ringa yi mata abubuwa duk akanta kawai saboda
kaga tana da haquri sannan fa Abbi saboda ita ka sake ta sannan yanzu saboda kaga baka jin dadi bata
nan kazo kana cewa ta dawo ai kasan bazata yarda ba" Aliyun ya fada bayan daya zauna.

"Na sani kuma duk na karbi laifina, auran Amirah da rabuwata da Maminku duk qaddarace Aliyu gaba
daya ba a san raina komai ya faru ba amma babu yanda muka iya da abinda Allah ya qaddar. Ni dai
yanzu ku taimaka nasan ai ku zata saurare ku ku bata haquri ta dawo gidan nan nayi Nadama bazan sake
maimaita duk abinda ya faru a baya ba.

Idan ma so take Amirah ta koma Gombe zata tafi nidai tayi haquri a mayar da auran mu kawai zanyi
mata duk abinda take so kaji kuje dukkan ku ku sameta dan Allah Aliyu nasan ai kai bazaka so kaga
rayuwata ta shiga garari ba saboda rashin Ma'u" Bashir ya fada yana kama hannun Aliyu daya tsura masa
ido.

"Zanje na sameta dukda tace karmu sakeyi mata maganar ka amma ina so kayi mun alqawari.."
"Koma menene na yarda in har zaka shawo mun kan Ma'u duk abinda kake so zan baka" Bashir yayi
saurin tare shi. Seda ya sauke ajiyar zuciya kafin yace

"Kayi alqawarin idan Mami ta yarda zata dawo zaka saki Anty Amirah saboda nasan indai kana tare da ita
Mamai bazata taba samun farin ciki a gidan mu indai kana so ta dawo to ka sake ta kawai gidan mu ya
koma yanda yake kafin ta shigo rayuwar mu".

Kasaqe Bashir yayi yana kallon Aliyu da jin abinda yake fada, ya saki Amirah fa me yasa se wannan
sharadin ze saka na shawo masa kan Ma'u?

Shida yake qoqarin gyara kuskure shine yake so ya sake aikata wani ita kuma idan ya sakeya yanzu kuma
wata jarabawar ta sake afko masa fa gaskiya Aliyu yayi haquri banda wannan ya yarda dai ze raba musu
gida yanda suke da har na can Gomben ma idan Amiran ta koma ze raba musu kowa gidanta daban.

Hannun Aliyun ya kama yana sake marairaicew kamar wani kalar tausayi yace

"Haba Aliyu so kake na sake yin wani sakin kenan bayan nayiwa kaina alqawarin ko dukana mace zatayi
bazan sake sakinta ba. Baka san yanda nake ji akan rabuwata da Maminku ba, Baba fushi yake dani ko
magana baya mun yanzu haka su Amiru duk sun dena kulani saboda abinda ya faru so kake na sake
maimaitawa itama Dada da sauran yan uwana su tsane ni?"

"Ai daman Baba dasu Uncle Amir ne kawai suke son Mami ni ina ruwana idan sunji haushi kawai in dai
kana so Mami ta dawo to kayi alqawari zaka saketa koma zaka dawo da itama daga baya ni babu ruwana
amma yanda aka saki Mamanmu saboda ita itama taji irin yanda mukaji" Aliyun ya fada kansa tsaye
babu wata damuwa a tatttare dashi.

Bashir kuwa ido ya saka masa yana mamakin a ina ya samo wannan tunanin ko kuwa Ma'u ce ta fada
masa hakan ita take so a saki Amirah sannan ta dawo. Kansa ne ya dauki dumi, yanzu idan da gaske ya
amince zata dawo din ko kuwa kar ta sake rufta shi se daga baya yayi biyu babu ko daya.

Numfashi ya sauke yana kallon Aliyu da yayi kicin kicin yace

"Na yarda amma se randa aka mayar da aurena da Mamin ku sannan zan cika maka alqawarin"
"Ka dai san hukuncin cika alqawari" Aliyu ya fada yana kallonsa.

Kai shi abun ma ya zarce mamaki wai yau shi Aliyu ya titsiye haka yake bashi umarni, ya ya iya? Haka ya
rausayar da kai yace

"Na sani kaima se kayi qoqari ka cika naka alqawarin" ya fadi haka bawai dan har zuciyarsa ze aikata
hakan ba. Buqatar sa kawai Ma'u ta dawo idan ya samu bega kuma wanda ya isa ya sake raba shi da ita
ba ballantana wani alqawarin Aliyu can.

Haka ya shiga gida da yaqinin cin nasarar yaqin ta wannan sigar daya samu, yasan tana da rauni akan
yayanta in Allah ya yarda wannan raunin nata shi ze kaishi ga nasara.

ASMA'U

Ganin da nayi har ana saura kwana uku a koma makaranta Bashir be yi magana ba yasa na sake
tuntubarsa. Ta whatsapp call din ya kirani saboda ni nake so muyi magana dan haka na daga muka gaisa
yake cemun

"Kin jini shiru ko wallahi Ma'u bani da kudi ne, abinda na saka rai dashi ban samu ba ga shi da saura kafin
mu samu salary ina ta dai fafutukar yanda zan samu daga yau zuwa Gobe in sha Allah zan saka miki"

"Toh Allah ya rufa asiri, ayi qoqari dai kasan su bazasu karbe su ba idan ba'a biya ba. Ga siyan su takalmi
ma da jaka da dan abinda ba'a rasa ba tunda sabon session ne duk suna da buqatar a canza".

Allah sarki rayuwa shi baya zaton ma ya taba bada kudin wasu jaka da takalmi dan yawanci idan suna
Gombe a shagonta suke zuwa a dakko tunda duk tana siyarwa harda su Lunch box din da suka dawo nan
kuma sedai ya gansu da abinsu, kudin Uniform da sport wear kadai yasan in suna buqata take gaya masa
baya ga wannan sedai yaga tayi musu.
"Shikenan, yanzu zan tura miki da 1M a fara rage kudin kona mutum uku ne zuwa jibin se na ciko" ya
fada qasan ransa yana so ya roqeta da yasan bazata rasa kudi ba ta ranta masa amma yana tsoron amsar
da zata bashi tunda yanzu kam Ma'un ba ta da bace

"Shikenan toh ka tura amma fa ka tabbata Jibin ka ciko dan ni inaga ma zanje a chanza lambar nan
gaskiya can su ringa tura maka duk abinda ya kamata" na fada kafin na kashe wayar.

Wani abu naji kamar tausayinsa ya dan kamani, nasan Bashir da hidimar yayansa indai an gaya masa
yanayi ballantana kuma harkar makaranta tunda har ya ce bashi da kudi toh tabbas bashi dasu din.

Ba'afi minti biyar ba sega alert din kuwa ya shigo, wayar na ajiye na janyo durowar gefen gado na sega
kudin da Ambassador ya bamu ranar nan tunda na watsa su ban qara bi ta kansu bama dan na manta shi
kansa da yace na kira shi ban kira din ba.

A jakata na zuba su da niyar gobe idan na fita zan biya banki se na cire wanda ya turamun na hada da
wadannan na biya musu kudin makarantar kawai daman ai kudin Aliyu ne sa ci tare da qannensa.

WATA KISHIYAR

(ALKAHIRI CE KO SHARRI)

Na Maryamah Farouk

(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)


Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 60

Washe gari Juma'a kuwa da wuri na dauki excuse na kama hanyar banki, seda na fara Zuwa Access bank
na cire kudin daga akawun dina na hada da wadancan kafin na wuce Zenith inda ake saka kudin
makarantar bayan da nayi printing teller da suka tura mun.

Ina shiga bankin Yusuf ya kirani.

"Ina zuwa dan Allah zan kiraka ina banki ne" na fada bayan da muka gaisa.

"Hajjaju bari nima na turo da akawun a sakamun wani abu mana" ya fada cikin wasa

"Toh shikenan, seka turo ina jira" na bashi amsa ina shirin kashewa ya tareni da cewa

"Har transaction din miliyan nawa zakiyi da se kinje banki?"

"Kudin makarantar yara ne fa zan saka kasan basa karbar transfer dole se cash deposit za'ayi"

"Ke kike zuwa biyan kudin makarantar yaran shi Baban su aikin me yakeyi da baze je da kansa ba ko
kema irin matan da suka dauke dawainiyar yara da bata zamar musu dole ba sukeyi ce" ya fadda cikin
wani yanayi kamar na bacin rai.

Murmushi nayi nace masa


"To meye a cikin biyan school fees? Ni har PTA ma ni nake zuwa musu kai komai ma na makarantar su
lamba tace akai"

"To sannu kinyi abin kirki a tafa miki" ya fada kafin yaci gaba da cewa

"Na rasa me mata kuka dauki kanku yanzu wallahi, gani kuke kamar gwaninta ce ko iyawa ke uwa ki
dauki haqqinki ki dauki na uba duk ki hada ki ringayi in ba haka ba ina ruwanki da harkar makarantar
yara?

Iya abinda ya shafe ki shirin su na tafiya makaranta kula da tsaftar su da abinci shikenan se bitar karatu
idan sun dawo gida ko taya Home work ni banyarda haqqin uwa bane tayi wa yara shi uban aikin me
yakeyi idan ya dawo da daddare da baze tara su yaga abinda suke koyo ba se kece zakiyi??

Abin nan yana bala'in bani haushi, Idan ka fita da safe motocin kai yara makaranta in ka hadu da goma
bakwai matane a ciki biyu daga ciki shine zakaga Driver aka daukar wa yaran yake kai su se daya ne zaka
samu uban da kansa bayan dai qarshe mutum yace yana sauri ze tafi aiki duk sauri dai qarfe bakwai
ma'aikaci yake fita kuma suma makarantu bakwai ake budesu me ze rage ka idan ka tsaya ka ajiye
yayanka kafin ka wuce naka gurin aiki

Wannan uar dawianiyar da iyaye maza muke kasa jurewa muyiwa yaran mu fa shine abubuwan da har
girman su bazasu manta ba kuma a irin lokacin ne fa kadai kake samu da zaka tattauna da yaran kasan
matsalolinsu amma ina kai agogo sarkij aiki ka fice ita mata ga aikin gida ta shirya yaran ta rufe gida ta
kaisu ta dawo ta dora daga inda ta tsaya in an tashi ta koma kune zuwa PTA kuna wannan kune wancan
duk wa ya aike ku ne

Kin ganni duk irin Busy da nake yayan Yaya Umar (Yayansa ne daya rasu) in har kikaga banje na dakko su
daga makaranta idan akayi hutu ba to bana qasar ne amma ko a ina nake se na koma na dakko su ko na
kaisu tunda boarding sukeyi haka Visiting har personal Visiting indai na samu dama ina zuwar musu
saboda ni ne matsayin uban su a yanzu ba kuma naso suga wani abu da akeyiwa wanda ubansa yake
raye su sun rasa suyi kukan maraici saboda Babansu babu abinda beyi mun a rayuwa ba duk matakin da
na kai da bazarsa nake rawa Dan haka tun wuri ki tashi malama ki San Abinda yake haqqinki da wanda
ba naki ba
Ki zauna a inda nake bari na turo yaro yaje ya saka kudin karki kuskura ki shiga bankin nan kuma wannan
ya zama na qarshe da zaki sake zuwa biya musu wani kudin makaranta idan baze je da kansa ba a barshi"
ya qarasa maganar ta sigar umarni.

Haka kuma na zauna a motar bayan ya kashe ya sake kirana mita ce dai yake tayi akan mata mun fiya
zaqewa, se kuma miji ya miqe qafa ya saba da kina masa daga baya kizo kina qorafin yaqi yayi bayan tun
farko baki sabar masa da yayi ba.

"Wai dan ma baka san ya na gudanar da nawa zaman auran ba kenan da ina ga bulala zaka sak kayimun
shege duka irin wannan masifa da kake daga zuwa biyan kudin makaranta" na raya a raina.

Ba'a jima ba sega kira ya shigo mun da lambar da ban sani ba, uzuri na bawa Yusuf na daga mutumin
yake cemun shine wanda ze karbi kudi ina ina na kwatanta masa ina da tsaya se gashi ya qaraso da
alama ma'aikacin bankin ne dan ga ID card dinsa nan a wuya.

Seda muka gaisa na dakko Teller na bashi ina zaro kudade daga jaka ya juya ya tafi nayi saurin dakatar
dahsi da cewa ga kudin se cemun yayi wai Teller kawai aka ce ya karba yai tafiyarsa. Ko minti goma
ba'ayi ba se gashi ya dawo da receipt na karba nayi masa godiya na zaro dala dari biyu na bashiya dakyar
ya karba mukayi sallama na kama hanyar makarantar kai tsaye naje na chanza Teller,

kafin na isa ya ringa kirana yana jaddadamun da naje a cire numberta a mayar data Bashir ya kashe
wayar sa yaqi bani damar da zan masa maganar biyan kudin ma da yayi oh Yusuf kenan shi ma kowa ya
aike shi yin abinda ba haqqqinsa ba oho.

Text na rubuta na tura masa na godiya da irin hidimar da yakeyi da yarana kafin na rufe da cewar na
tanadar masa da kyakykyawan labari ina jiran zuwan sa Lagos

"Ki saka ran gani na a ko da yaushe Allah yasa abinda na dade ina muradin jine daga bakinki Asmy" ya
dawo mun da amsa. Murmushi nayi dan dagaske ji nake ya kamata na amsawa Yusuf na bawa kaina
dama ta gwada sabuwar rayuwa tareda kyakykyawan yaqinin samun chanjin Alkahiri.
A daren ranar ina kwance a dakina saboda kaina da na danji yana mun ciwo aka kwankwasa qofa, Aliyu
da sauran yaran gaba daya yana gaba suna binsa a baya suka shigo suka jere mun a gaba na dago ina
cewa

"Wane kalar iskanci ne wannan zaku wani tsaya mun aka kamar masu Asambili idan ma wani abun kuke
so mutum daya baze wakikce ku ba wai bana hana ku yimun wannan gangamin bane?"

Shiru suka mun, na kunna fitila se a sannanna lura da yanayin fuskokinsu gaba daya babu walwala sun
sunkuyar da kawunan su qasa. Wata faduwar gaba naji nayi saurin tashi zaune ina cewa

Babu wanda ya amsa ba kuma su dago kai suka kalleni ba,

"Ku fice mun bana son wulaqanci ana magana kunyi shiru ku fita ku bani guri" na fada cikin tsawa dukda
qasan raina ina tsoron abinda ya saka su yo wannan gangamin haka, qafata na sauke qasa da niyyar
fafarar su tunda sunqi magana seji nayi kamar hadin baki sun rushe gaba dayan su da kuka yanbiyu suka
yo kaina da sauri suka runguneni.

"Meye haka ku fada mun dan Allah wani ne ya mutu?" Na fada a gigice ganin irin kukan da suke yi harda
Aliyu da bazan iya tuna rabon da naga kukansa ba.

Gaba daya na rikice jikina har rawa ya dauka a zatona wani abunne ya faru, Farida na janyo na girgizata
ina cewa

"Zanci ubanku wallahi kuyi mun magana menene waye ya mutu a nan ne ko a Gombe?"

Aliyu ne ya zube guiwoyinsa qasa a gabana ya kama qafata yana cewa

"Mami da girman Allah ki dawo gidan mu. Wallahi Mami Abbi yayi nadama ki dawo indai kina so rayuwar
mu ta inganta karki tafi ki barmu da wannan matar, bana bacci Mami tunda kika bar gidan mu kullum
cikin damuwa muke, Abbi baya hayyacinsa su kansu su Abdallah Mami saboda basu gama gane abinda
yake faruwa bane wallahi da ba'a kusa damu kike ba da yanzu bansan yaya rayuwar mu zata zama ba
saboda babu wanda yake kula damu shi kansa Abbi yanzu neman wanda ze sauta shi ya ringa kula dashi
yake kina kallo se ayi sati ni kadai nake kwana acan gidan kuma be damu da ya san Ina sauran suke ba,
ba'a bamu abinci acan gidan to Mami idan bakya nan waye ze bamu? ina zamuje waye ze nemo mu idan
be gammu ba?"

Kamar wadda aka watsawa ruwan sanyi haka naji nayi shiru ina jinsa su kuma suna ci gaba da kuka
tareda fadar maganganu dan Allah na dawo gidan su.

Ajiyar zuciya na sauke me qarfi jin ba mutuwa akayi ba, amma zancen rayuwar su da sukayi ya tabani
hasaso yanda suke garari tsakanin gidajen nayi a fili na furta "hasbunallahu wani'imal wakeel" Dagaske
da bana tare dasu yaya rayuwar su zata kasance? Ina zasu je su samu gatan da uwa take bawa danta?
Waye ze kulamun da tarbiyyar su? Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un Ni Asma'u yanzu yaya zanyi duk me
yasa banyi wannan tunaninba nake shirin yanke wa kaina shawara??

Gaba daya kukan nasu ya dagulamun lissafi nama rasa abinda zance musu, dakyar na iya saka hannu ina
bubbuga bayan yan biyu nace

"Ya isa ku dena kuka akan wannan maganar ce zaka tara mun yara saboda wulaqanci ka saka su kuka kai
bazaka iya zuwa kai kadai ka same ni ba se kun tayar mun da hankali?"

"Mami bani na gayyato su ba ki tambaye su gasu nan duk tare mukayi magana kowa yana cikin damuwa
mun kasa zuwa mu tunkareki shi yasa nace mu taho yanzu ki tausaya mana Mami mu koma irin rayuwar
da muka tashi a cikinta" Gwani na gwanyen ya sake fada.

Seda nayi dagaske kafin sukayi shiru na tattara su suka fita suna sake maimaitamun na taimake su na
tallafi rayuwarsu na koma gidan Babansu, wai harda yan biyu kai wannan abun ma yafi kama da wasan
kwaikwayo tabbas shiri ne Kuma Bashir ne ya shirya shi. Shiyasa dazu kenan gaba daya suka fita ashe
gurinsa sukaje ya yiwo musu huduba ta nan ya zagayo kenan tunda ya kasa yi da kansa.

Duk yanda naso na share maganar daga zuciyata na aiwatar da abinda nayi niyya tun farko kasawa nayi
da gaske ina tunanin makomar rayuwarsu. Yanzu muna tare bani da tabbacin idan nayi aure Yusuf ze
barni naci gana da zama a nan dukda ya ce ze bari kuma nasan ko za'ayi yaya Bashir baze bani su ba kai
ni kaina bazan kai yayana Agolanci wani guri ba bayan ubansu nada yanda ze riqe au to yanzu yaya
zanyi??
Abu guda uku ne, kodai na haqura na koma gidan Bashir nayi zaman Yayana, ko kuma na auri Yusuf na
zubar dasu ko kuma na hauqra da duk biyun na rungume su mu zaunaba tareda na sake wani auran ba
wanda na tabbatar bame yuwu bane dan baza'a barni nayi hakan ba to dole cikin zabi biyun farko kuwa
na dauki daya, wannene mafita? Komawata gidan Bashir bayan duk abinda ya faru ko kuwa sabuwar
rayuwar da nake yaqinin samun chanji a cikinta?? Mene kuma makomar Yarana??

Saboda tunani har wani mugun ciwo kaina ya dauka, dare yayi qarfe sha biyu harta gota amma haka na
danna kiran lambar Goggo ba tareda tunanin tsufanta ba karna tayar mata da hankali nima ina da
buqatar magana da uwata ne in nemi shawararta tunda tana sona tana kuma jin irin abinda nake ji
yanzu akan yarana baznaso na yanke shawarar da zata tauye rayuwarsu a gaba ba.

"Asma'u lafiya? Meya faru kike kiran waya a daren nan" ta fada bayan data daga kamar me jiran na
kirata.

"Kiyi haquri Goggo na tasheki daga bacci" na fada a sanyaye, se tace mun

"Ba bacci nake ba, kin ganni ina ta salloli ne da addu'a wane bacci zanyi yanzu Asma'u nida nake da
buqatu nake da yaya da nake nema musu shiriya kullum a gurin Allah"

Maganar ta kawai se naji ta sakani kuka dukda bansan kukan na menene ba.

"Goggo dagaske na haqura da Bashir badan na dena sonsa ba sedai kawai hakan shine maslahar zuciyata
bazan taba samun yanda nake so a gurin sa ba zan qare rayuwata cikin qunci da ciwon rai da baqin ciki
shiyasa na zabi haqura dashi amma Goggo yaya makomar yarana zata kasance idan na auri wani daban
na tafi na barsu?

Matarsa ba zata iya riqe min suba bansan yaya tarbiyyarsu zata kasan ce ba musamman a gari kamar
Lagos Goggo dama a Gombe ne akwai wadanda zasu saka ido akan su saboda su Goggo bazan iya
tsallake wa na sake wani aure ba ki bani shawara me ya kamata nayi?"
Shiru ta mun harna gama magana ina gunsheqara kuka, seda nayi iya yina nayi shiru kafin tace mun

"To yanzu kira kikayi ki gaya mun zaki koma gidan mijinki ko yaya?"

"Goggo shawarar ki nake nema ban san meya kamata nayi ba" nayi saurin bata amsa. Se da tayi wani
murmushi kafin tace

"To Ma'u ai maganar ki ba tayi kama da ta wadda take neman shawara ba. Cewa kikayi bazaki iya tafiya
kibar yayanki ba to ai seki koma gidan ubansu kawai ki riqe su daman ba abinda kike so ba kenan duk
meye na wani kuka ni kin tayar mun da hankali abinda befi ki tura mana da saqo a waya ba akan zaki
mayar da aure muzo mu taya ki murna shikenan fa.

Addu'ata kullum Allah yayi miki zabin Alkahiri, idan so nane bazan so ki koma inda ba'a san darajarki ba
tunda har Allah ya fito dake ba kuma wai ke kika nemi sakin nan ba amma tunda kin zabi ki koma Allah
yasa hakan ya zamo miki Alkahiri" ta qarasa maganar a sanyaye.

Yanda take magana kadai ya isa ya nunamun bata ji dadin abin ba, qarasa hadiye kukana nayi nace mata

"Goggo ba cewa nayi zan koma gidan Bashir ba wallahi nima na gaji, na yarda bani ce a gabansa amma
Goggo makomar Yarana nake dubawa. Dazu suka zo suka sameni suna kuka akan nayi haquri na koma
gidan su.

Goggo ba'a basu abinci komai na rayuwar su a nan sukeyinsa idan zasu kai dayan dare babu wanda ze
biyo sahub su aga suna ina yanzu da bana nan ya ya zasuyi?"

"Saboda an san suna da inda zasuje shi yasa, saboda yasan zakiyi musu shiyasa ya sake sun da kuma su
yake amfani yake karya lagon zuciyarki tunda ya fahimci sune raininki.

Waime kika ce kina tsoro ne ma tarbiyyar su karta lalace ko? To bari kiji Allah shine yake shiryawa ko a
gabanki suke idan Allah be taya miki ba baki isa su gyaru yanda kike so ba.
Idan kuma kika mutu kika barsu a hannun nasa da matar tasa yaya zakiyi se hakan ya zama silar
lalacewarsu ko yaya?

Na yarda iyaye suna taka muhimmiyar rawa a gurin gyaruwar yayansu amma karki kuskura ki saka tsoro
ko tunanin ke zakiyiwa kanki ki yarda da Allah ki bashi amanar Yayanki ki bisu da Addu'a duk bangon
duniyar da suke zata iske su.

Yaya nawa suka lalace a tsakanin uwa da uba? Nawa suka zama nagartattu ba tareda uwarsu ko ubansu
ba?

A sanda Bashir ya sake ki meyasa be kawo Tarbiyyar yayansa ba ya kwace su yace a bashi abinsa ai
saboda yasan ze iya ne ko, to in har shawarata kike nema Asma'u akan zancen auranki da Bashir ni
Maryama nace ki haqura dashi ko qaddara iyakar zaman da Allah yayi zaku zauna kenan.

A sanda kika so ki balle auran ni nayita tausarki ina nuna miki kiyi hauwa ki zauna badan bana ganin
cutarwar da take ciki ba Aa sedan bana so muyiwa Allah katsalandan. A kullum ina yi miki addu'a Allah
ya zaba miki mafi Alkahiri tsakanin zamanki da Bashir se gashi lokaci daya ba tareda tsammani ba shida
kansa ya qosa dake ya sallame ki sakin wulaqanci Asma'u ko iya wannan a zatona ya isa ya sa ki hankalta
ki cire shi daga zuciyarki.

Karki yiwa kanki abinda zaki dawo daga baya kina dana sani, idan Yaya ne ki cire idonki akansu na
tabbatar Miki daga sanda yaga babu ke ko kin dena damuwa da al'amuransu ze mayar da hankalin sa
tunda ai kin fi kowa sanin halinsa akan Yaya baze taba barin abinda ze cutar dasu ba.

Ko ba wannan ba ai Addini ya baki damar da zaki karbe su ki riqe su idan kin dage kina iya kai maganar
zuwa ga hukuma zata kwatar miki su ta baki amma ki sani zaman dan wani da uban wani abune me
matuqar wahala dashi kadai idan bakiyi sa'a ba ya isa ya dagula miki lissafi ya hanaki zaman lafiya da duk
mijin da zaki aura.

Duk yanda wani ze nuna miki son yayanki ba lallai ya dore ba Asma'u dan yau da gobe tafi qarfin wasa
musamman wadannan yayan naki kinga ko Ali kadai ya isa ya kaso miki aure dan wannan dan Halin
ubansa tsaf ya kwashe.
Ki barsu Mazane dama kyansu gidan ubansu munyi magana da Bashir din nace ya baki Farida itama bake
zaki riqe ba idan kinyi aure daga ita har Amnah tattaro su zakiyi ko ki mayarwa da Hajiyar ku Gombe koni
ki kawo mun su nan dukda Qarami daman ya dade yana zancen dauke Amnah ni na hana nace su bar
miki ki qara sa ladanki amma yanzu dole in kika sake aure ki barsu dan baki dan irin zamanda zaki tarar
ba duk da muna miki fata da yaqinin na Alkahiri in Allah ya yarda zaki dace da irin rayuwar da kike fata,
zakiyi farin ciki da zabinda kikayi".

Har Goggo ta dasa aya kuka nake dan na fahimci bazata goya mun baya akan batun komawa gidan
Bashir ba ba kuma ta fahimci abinda nake nufi game da tarbiyyar Yayana ba. Mutane suna daukar
Tarbiyyar Namiji a me sauqi ni kuwa a gurina tafi ta Yaya mata wahala saboda su kina iya matse su ku
zauna a gida Namiji fa? Duk inda kika kai da taka tsantsan se sun balle sun fita su cudanya da Yara kala
kala Allah ne kadai ze kare maka su tareda saka ido da jajircewar ka.

"Kuka baze miki magani ba, duk irin halin da kika shiga kar ki sare da yiwa yayanki da na sauran musulmi
Addu'a bari kiji wani sirri a duk sanda kikayi addu'a me kyau ga dN wani mala'iku zasu taya ki da yiwa
naki yayan irin wannan Addu'ar to meyafi wannan dadi

Asma'u Addu'a itta ce rigakafin da zaki musu ko da ke ko babu ke.Harshen uwa nada tasiri akan yayanta
haka Addu'ar ta tana bibiyar su koda bayan ranta walau ta Alkahiri ko ta sharri shiyasa yana da kyau mu
ringa kyautata kalami ga yayanmu saboda wani abun da wasa zaki furta shi ki manta wani lokaci kiga yayi
tasiri akan Yaro ki shiga tashin hankali da tunanin ya akayi yaronki yake abu kaza baki san cewar da
bakinki kika jefe shi da wannan abun ba.

Dan haka ki cire tsoron lalacewarsu dan wai bakya tare dasu ki barsu a hannun Allah bi jahi rasulillahi
babu abinda ze same su se Alkhairi amma zama da Bashir kuwa kin gama shi Ma'u ki barshi har abada
Allah ya sanya wa abinda kukayi a baya albarka. Se da safe ni zan kwanta zuwa an jima na tashi, kema da
wannan kukan da Allah kika kaiwa kukan naki yayi miki magani" Goggo ta sake fada kafin ta kashe
wayarta.

Bawai dan na sauka akan ra'ayina ba Haka na tashi na dauro Alwalar ina sallah ina kuka, Addu'a nayita ni
kaina bansan adadin abinda na roqa ba qarshe bacci ya kwasheni akan sallayar se farkawa nayi na ga gari
yayi haske tarwai.
Wunin ranar haka nayi shi babu suku ni sam, a zuciyata ni kaina ban aminta da kome na gidan Bashir ba
amma idan na dubi yaran se naji zan iya sadaukar da farin cikina in dai rayuwarsu zata inganta.

Da yake asabar ce ina gida babu inda naje, da yamma lis sega Anty ta shigo cikin farin ciki da mamaki na
tarbeta dan ban san da dawowarta ba seda muka zauna take cemun wai tun jiya da yamma ta dawo ta
tsaya gyara gyare gyare ne shiyasa bata kira ni ta gaya mun ta dawo ba.

"Amma Anty baki kyauta ba maimakon ki kirani na tayaki gyaran shine se yanzu zaki shigo" na fada

"Kiyi haquri kinsan ba wani datti gurin yayi ba tunda Yallabai yana yawan zagayowa, ni ba wannan ba
tashi mu shiga ciki kiga kayan arziqi nan dan hadi nayo miki na musamman naku na Amare gara muzo
mu fara abinda ya kamata da wuri"

Shiru nayi tareda sun kuyar da kaina qasa dan bansan taya zan fara gaya mata chanjin shawarar da nayi
ba Idan na tuna irin ihun murnar data ringayi randa na gaya mata zance wa Yusuf ya turo maganar auran
mu ta ringa saka mun albarka yanda kasan qaninta zan aura yanzu idan nace mata na fasa ai inaga
dukana kawai zata yi ta huta.

"Meya faru kuma ina magana kin sunkuyar da kai qasa?" Ta fada tana kallona

"Anty, ni ina ganin aurena da Yusuf baze yuwu ba saboda..." bata bari na fada mata dalili na ba ta kwashi
salati tana tafa hannu tace

"Ai na dade ina addu'ar Allah ya tsareni da ganin wannan rana ashe tana tafe ni Halima, ai wallahi na
sani, ke din kuma ai Ma'u kinyi asara kedai kuma na rantse da Allah daga yau karki sake nuna ma kin
sanni babu ni babu ke. Ke ni inaga tashi ma zanyi daga unguwar nan dan bazan iya kallon abin takaici ba
bani da damar gyara wa ke yanzu har akwai abinda Za'a gaya miki akan Bashir ki yarda ki koma gidansa?

Muna zaune gani gaki yallabai ya roqe shi dan darajar zuri'ar dake tsakaninku yayi haquri ya maida ke
kafin ma wani yaki abinda ya faru amma ya qeqashe qasa yace ko zaki koma ba yanzu ba se kin gane
kuskurenki ki sannan yanzu kin gane shine zaki koma masa ba to Allah ya taimaka ki koma kijr ku qarasa
igiya dayar daga nan seki share daki kiyi zaman yayanki kuma tunda ya rigada ya tsafance ki bazaki iya
rayuwa babu shi ba se kije kiyita komawa kuma na rantse ko qofar gidana kikazo sena miki rashin
mutunchi mara zuciya kawai" fuuu ta kwashi kayan data shigo dasu tayi waje, duk yanda na bita ina
tsayar da ita amma taqi saurarona se zagina take tsabar masifa yau Sokkotancin ma ta komayi tana aiko
mun da wasu qunduma qunduman ashar da ban san ma'anar su ba.

Haka na cinye Weekend gari yamun zafi dan dai Ashar ta kowacce kwana karbarta nake dan Goggo seda
ta kira yan uwana kaf ta gaya musu wai zan koma gidan Bashir ko a yaushe mukayi haka da ita oho?

Alawiyya damab cewa tayi daga randa na koma na qaddar ba uba daya ya haife mu ba se na tafi na nemi
yan uwana marasa zuciya ko kuma na maida Dada uwata kawai se su san qauanr da nakewa Bashir da
ahalin sa ta kai duk cikin su an rasa wadda ta fahimci dalili na, bayan nasan zasu iya yin fiye da haka
suma idan da akan su hakan ta faru amma ni na rasa wanda ze bani goyon baya.

Ranar Litinin aka koma makaranta saboda yanayin da nake ciki babu wani shiri da nayiwa yaran dan ko
maganar siyo jaka da takalma ma banje ba tsofin nasu suka saka nace idanna taso aiki zan biya na siyo
musu.

A tare muka fito Bashir na qofar gida yana jiransu, yanda ya amsa gaisuwar da nayi masa se naji
guiwoyina sunyi sanyi dan a wani basarwa ya amsa yana dannan wayarsa ko dagowa ya kalli inda nake
ma beyi ba balle wannan binbini da ban haqurin da yake mun duk sanda muka hadu.

Har naje office zuciyata cike da tunanin chanjin da na gani a tattare dashi, ban dade da shiga ba Yusuf ya
kirani wai ze shigo yau da daddare, kai wannan mutum shima akwai dan banzan naci na fada a fili ina jan
tsaki bayan dana ajiye wayar. Se a sannan na tuna da ashe fa ni nace masa yazo akwai labari me dadi tan
kace akwai cakwakiya kuwa dai.

"Madam Asma'u ki godewa Allah, baki rufa shekara da mutuwar auranki ba har kika samu me sonki da
aure bada lalata ba shine kike mita kina cewa yafiya naci? To wallahi kiwa kanki qiyamullaili. Ni nan na
isheki ishara shekara ta bakwai kenan da fitowata kina kallo duk wanda zezo wata manufa ce take kawo
shi badai aure ba shi kansa tsohon mijin nawa dana zata ze dawo tunda yai bikon farko farko na tsaya
jan aji ya tafi yayi auransa ya manta dani" Sahiba sakatariyata ta fada cikin jimami.
Kallonta nayi ina juya maganganunta a raina, maganar tsohon mijinta da ta zata ze dawo tafi tsayamun a
rai to kodai nima Bashir ya gaji da bani haqurin ne yayi zuciya a yanzu da ni kuma na sakko nake shirin
koma masa idankuwa hakane gaskiya ina tsaka me wuya ko ince ina shirin sakin reshe na kama ganye ai
kuwa dole na sake lissafi.

Wunin ranar tsaf harna tashi aiki ko qyallin Saqon daya saba aiko mun ban gabi ba bare naga kiransa har
na koma gida bayan dana tsaya nayiwa yara siyayyar da nace zanyi.

BASHIR

Dukda zuciyarsa tana cike da taraddadin yuwuwar shawo kan Ma'u da Aliyu yayi masa alqawari amma
haka ya dage yake bawa kansa qwarin guiwa. Saboda gudun ta zargi wani abu yasa ya dauke qafa daga
zuwa inda take ko a waya ya dena takura mata tunda tace ya rabu da ita to ze bagarar a haka har zuwa
sanda zega yanda abubuwan suka daidaita.

Sanda ya dauki yaran suka kama hanya shida kansa yaji kamar abinda yayi kuma be kyauta ba se yaji
kamar ya kirata ya bata haquri amma ya kanne shi a nasa tunanin duk salo ne da zesa karta zargi yana da
hannu a gurin tura mata yaran su roqeta. A gurin aiki kansa ya gwada tura mata saqo yafi sau biyar yana
fasawa haka ya rarrafa ya dawo yana dai ta addu'ar Allah yasa komai ya tafi daidai dukda Aliyu ya gaya
masa akwai alamun nasara a cikin shirin nasu dan yaga gaba daya Mamin tayi sanyi kuma ko waya bega
sunayi da Yusuf din ba a kwana biyun.

Da daddare bayan ya dawo daga aiki ta window dakinsa yana tsaye yaga giftawar motar daya tabbata ta
wannan Mayen ce dan shi kadai yake zuwa layin da irinsu. Kaya yake canzawa cikin sauri ya qarasa ya
fito dan baze lamunci yana qoqarin gyara wani banza yana zuwa yana warware masa ba. Yana kaiwa
Palour yaci karo da Ahmad daya shigo gidan da gudu yana kiran Muhammad.

"Kai meye haka so kake seka fadi kake gudu ko" ya fada yana tare shi.

"Moh nake nema Uncle Yusuf ne yazo yace na kirashi" Ahmad din ya fada yana qoqarin shigewa dakinsu
ya kira dan uwansa se Bashir ya fizgoshi yana zare ido yace

"Qanin ubanka ne da kake ce masa wani Uncle, dalla wuce ciki ka zauna idan na sake ganin qafarka a
waje ma sena karyata kai ko magana naga kuj sake kula mutumin nan se na bata muku rai gaba daya" ya
turashi ciki shi kuma yayi waje, gara yaje gidan a gabanta a gaban Yusuf din yaja masa kunne ya fita daga
sabgar Yaransa.

ASMA'U

Bayan sallar Magriba Yusuf ya kirani yana hanya, ruwa da Lemo kawai na sa a tanadar masa, har nace a
fita da kujera waje sega Yayyafi ya sauko, dukka yaran suna gidan banda Aliyu da tunda na dawo ya leqo
daga qofar gidan su ya mun sannu da zuwa ya koma shikenan.

Ina wutri wayata tayi qara, seda na sallame na duba, Yusuf ne, banja doguwar Addu'a ba na shafa na dan
goga hoda a fuskata da man leba na fesa turare kadan kafin na zura takalmi na fito palour da Amnah ta
gyara tsaf ta saka turare se qamshi yake babu kowa da alama sun shige daki ko sun tafi gidansu.

Da kaina na leqa na masa iso ciki,

Yana zaune akan bayan motarsa yana waya seda ya qara kafin ya sauko fuskarsa dauke da murmushin
nan nasa da baya gajiya dayi yace

"Se yanzu duk ruwa ya gama mun duka ina zaman jira".

"Banda sharri ina ruwan yake daya dake ka? Kuma wayace ma ka fito daga motar da sekayi zamanka a
ciki ai in baka so yayyafin ya taba ka. Sallah nakeyi sanda ka kira ni shiyasa ban fito ba".

"Aina hangoki shiyasa na zauna anan na kira su Ma'u yau duk ban smau munyi magana dasu ba"

"Allah sarki" na fada can qasan raina kuma wai naji haushi wai shi me mata. A sanyaye nayi gaba ya biyo
ni a baya yana tambayar ina yaran yaji shiru babu wanda yazo masa oyoyo, ban kula shi ba dan tilawar
abinda zan gaya masa kawai nake a cikin zuciyata seda muka shiga ya zauna akan kujera na wuce
dakinsu Amnah ina qwala mata kira ta fito da Hijab a jikinta alamar ita ma sallah tayi
"Gani Mami, Lah Uncle Yusuf sannu da zuwa, Jafar toga Uncle din ma yazo seka tambaye shi da kanka"
ta kwalawa Jafar kira da murnarta ganin Yusuf din.

"Ki kawo masa ruwa" na fada ina jiyawa, sega su Jafar din sun fito ashe duk suna ciki aka fara layin gaishe
shi kowa baki a washe na rasa irin sabon daya shiga tsakanin su haka, koda yake gaskiya ya iya tafida
yara yanda yake jansu a ajiki dole su sake dashi sosai.

"Yanzu sallah guda saboda rowa ko hoto daya baku turamun na gani ba. Gashi mutuniyarka album guda
ta turo a nuna maka amma kai baka tura mata ba ko" ya fada yana kallon Jafar dake ta doka uban
murmushi

"Ai ni bani da waya uncle yanzu ma nacewa Yah Amnah ta bani aron tata sena karbi Number ka a gurin
Mamy damab nayi hoton fa na ajiye mata Allah" Ya fada yana dariya

"To dakko wayar ka turamun tunda gani nazo yanzu" gaba daya suka tafi dakko wayar, ya juyo yana
kallona yace

"Kinsan Allah, jikina har rawa yake na matsu naji abinda kika ce zaki gaya mun, inada tulin ayyuka amma
na kasa haqura har wani satin dole na tsallake na taho yau ki samu ki gaya mun koma menene zuciyata
ta huta Allah yasa abinda na dade ina tsammanin jine daga gareki" Yusuf ya fada yana kafeni da kallon
nan nasa me narka mun zuciya, yawu na hadiye na sake gyara fuskata dan karna bashi damar ganin aka
sin abinda nake fada akan fuskata.

"Daman abinda nake so na gaya maka kamar yanda ka fada mu ba yara bane, maganar mu zauna muna
jan lokaci akan abu duk be kamata ba shiyasa naga ya kamata na fito na gaya maka Gaskiya ni na yanke
shawarar zan....."

"Malam tashi ka fita daga gidannan" maganar Bashir da bansan shigowarsa ba ta katse ni daga fadar
abinda nayi niyya"
"Barka da dare yallabai" Yusuf ya miqa masa hannu yana fada fuskarsa dauke da murmushi kamar bega
irin kallon da Bashir dinyake masa ba.

"Ka fita daga gidan nan nace tun kafin Ranka ya baci sannan bana gaya maka ka fita a harkar matata ba
shine kaci gaba da bibiyarta ko to ka tabbata sena aikata abinda nace maka zanyi, sena bata maka
siyarka na gayawa duniya kai mutumin banzane manemin matana aure" Bashir ya fada yana Wani huci
kamar Ya taka wuta.

"Meye haka Malam ya zaka shigo mun gida kana zagin baqona wa ma ya baka izinin shigowa kai da har
zaka kawo mun tashin hankali gida" na fada ina miqewa tsaye.

"Malama ba dake nake ba, ke ko kunya bakya ji ki ringa shigo da qarti cikin gida kina tara zawarawa
Saboda rashin kamun kai tunda ke baki san daidai ba to ni dole na kare martabar yayana dan bazaki
lalata musu tunani su dauka abinda kikeyi daidai ne ba, kai kuma tashi ka fita idan ba haka ba se kayi
dana sanin zuwan ka gidan nan yau" Bashir ya fada cikin fitar hayyaci da kishin da yake cin zuciyarsa.

"Ni kake kira mara kamun kai Bashir nice mara Tarbiyya?" Na fada ina nuna kaina saboda yanda maganar
sa ta dakeni, ban fito daga jimamin ba naji yace

"Na fada, wace mace ce zata ringa shiga da Namiji gidanta a kirata me kamun kai? To bari kiji, idan ma
kinayin haka ne danki bata mun tai kinyi a banza saboda na tabbatar miki duk wadanda suke rudar miki
da tunaninba auranki zasuyi ba. Ni din dai nine duk ma inda zakije ki dawo ina zaune sekib dawo mun
dan na tabbatar har duniya ta nade bazaki taba son wani abu bayan ni ba Ma'u idan kuma nayi qarya to
ki fda muji".

"Tab Allah Nagode maka daba ka bani damar aikata aikin dana sani ba" na fada a zuciyata kafin na koma
kan kujerar dana tashi na zauna ina qoqarin yaqi da maganganun da Bashir ya yaba mun ni Asma'u ya
kalli tsabar ido na ya kirani da mara kamun kai lallai Bashir ya isa tabbataccen mara mutunci.

Yusuf daya harde hannu yana kallonsa ne ya bude baki zeyi magana nayi saurin dakatar dashi da cewa
"Ka zauna, mema nake ce maka ne kafin ya shigo?" Na fada fuskata dauke da murmushi, zama yayi shina
yana mayar mun da murmushin yace

"Ina jinki, wannan albishir din da kika ce zaki mun fadi ina jinki".

"Oh ga mahaukaci yana magana shine dukkan ku zaku mun shiru ko? Malam tashi ka fita ke kuma Ma'u
zaki san ni kike wulaqantawa akan wani can dan iska da be san darajarki ba" Bashir ya fada a haukace
kamar ze rufe mu da duka.

"Ko dai mu bari anjima na gaya maka a waya? Kaga yanzu akwai hayaniya bazata barmu mu tattauna da
kyau ba kuma maganar tana da buqatar nutsuwa sosai" na fada ba tareda na mayar da hankali akan
shirmen Bashir ba

"Aa muje waje toh ko cikin mota dangaskiya kika ga na tafi ba tareda naji dalilin kiran nna ba toh inaga
yau bazan iya bacci ba"

Dariya nayi na miqe ina cewa

"Gaskiya dai muje nasan ko ka ji din ma duk haka take be zama lallai ka iya bacci ba yau" fizgoni da akayi
baya yasa nayi shiru ina gama daidaita tsayuwata kuwa na kwashe shida mari a mugun fusace nace

"Rashin kamun kan nawa be kai kowanne gaja ya ringa dora qazamin hannunsa a jikina ba" na waiwaya
na kalli Yusuf da yanayin fuskarsa ya chanza zuwa matuqar bacin rai nace

"Yusuf bazan iya magana yanzu ba saboda raina ya baci, kaje kawai ka gayawa Alhaji Qarami sati biyun
daya saka sunyi yawa a mayar dashi Juma'ar nan me zuwa"

"Bangane abinda kike nufi ba Asmy? Me za'a dawo dashi wannan juma'ar ko daurin auran mu kike nufi?"
Ya shiga jero mun tambayoyin a rikice, wani mugun kallo na jefawa Bashir daya dafe kunci yai mutuwar
tsaye nayi kafin nace masa
"Haka nake nufi ko yayi maka wuri da yawa.." kafin na idar da maganata ya kife a gurin yayi sujjada ya
dago cikin wata kalar madaukakiyar murna ya riqo Bashir yana cewa

"Nagode Nagode Bashir ka gaya mun dame zan biyaka a rayuwa? A da na dauka a matsayin babban
abokin Adawa ashe ban san banida masoyi sama dakai ba tunda gashi kayi silar da zan mallaki muradin
zuciyata.

Kai na rantse ka shirya samun double promotion, a ina kake aiki? Koda yake barshi zan binciko da kaina"
seya sake shi ya juyo ya kalleni

"Wife! Ina fatan wannan hukuncin ya zama mafi Alkahirin hukunci da kika taba yankewa a rayuwarki bari
naje zamuyi waya" ya kwasa da gudu kamar yaro ya fita, seda naga rufe qofar sa kafin na juyo kan Bashir
muka hada baki ni ina cewa

"Fitar mun daga gida kafin nayi maka tijarar da baka taba zato ba dan daman saboda shi na daga maka
qafa kar nayi abinda zan zubar da mutunchi na a gabansa"

Shi kuma yana cewa

"Aure zaki daura da wani namiji nan da sati daya Ma'u? Dagaske zaki iya rayuwa da wani bayan ni?
Nasan kinyi ne dan ki baqantamun rai na yarda amma ki janye dan girman Allah.

Bana nufin duk abinda na fada subutar baki nayi da kishinki da yake damuna amma kema kinsan ba
abinda nake nufi ba kenan" ya fada yana durqusawa kamar ze kamo qafafuna.

Juyawa nayi ina cewa

"Karka ja nayi abinda yayanka zasu tsaneni Bashir tunda sauran mutunchin juna a tsakanin mu ka fita,
badai ni ka kira mara kamun kai ba? Ka jira na fito daga daki yau zan nuna maka qarshen rashin kamun
kai kaji ko" na shige dakina ina tunanin me zan aikatawa Bashir da zan nuna masa bashi kadai ne saitin
kansa yake gocewa ba, nima wani lokacin nawa notinnan suna tabuwa.
Posting se baba ta gani

WATA KISHIYAR

(ALKAHIRI CE KO SHARRI)

Na Maryamah Farouk

(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)

Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 61

"Ma'u, Ma'u ki tsaya kiji wallahi ba abinda nake nufi ba kenan kema kin sani kishinki ne ya saka bansan
ma mename fada ba. Dan Allah kice mun wasa kike yi ta yaya a gabana zakice zaki auri wani? Bayan
Aliyu ya mun alqawarin ze dawo mun dake haba Ma'u dan Allah kiyi haquri ki janye maganar ki" ya fada
a rude yana biyo bayana.

A mugun fusace na waiwayo na nuna shi nace


"Wallahi Bashir ka shigo dakin nan seka raina kanka, Aliyu ko? Aliyu ubana ne daya maka alqawarin
dawo dani se ka turo shi ya dauke ni daman kai ka turo su suka zo suna mun wasan kwaikwayo to
wallahi sena ci ubansu,

ina saboda sun samu damar zuwa in da nake yasa har kake tsara musu abinda zasu zo suyi ko to daga
yau ta qare ka tattara yayanka ku barmun gida duk kuma yaran daya sake zuwa inda nake was a sena
bata masa" na qarasa ina bugo qofar har seda ta bigeshi dandab yake da shigowa dakin.

Kan gadona na fada na fashe da kukan da ni kaina ban san na menene ba. Me nayiwa Bashir dana kasa
samun soyayyar sa a rayuwa? Meye bani dashi? Ta ina na gaza daya kasa dubana ya mutuntani ko dan
darajar soyayyar da nake masa.

Wayata ce tayi qara, nasan baze wuce Yusuf ba dan haka na janyota a fusace zan kashe dan kowama
haushin sa nakeji a yanzu sedai ganin Alhaji Qarami ya saka na amsa ina kaiwa Kunnena na gaishe shi
cikin kukan da nake.

"Ma'u ina ga tare zaku dena koke koken quruciya keda Takwarana yanzu kuma me aka miki da kike kuka
a daren nan?"

"Alhaji Bashir ne, wai yazo har cikin gidan nan yace....."

"Allah ya rufa asiri, tsakanin ki da Bashir kuma Ma'u ai babu me shiga, ke kika bashi fuskar da ze zo ai
koma menene yayi miki tunda ance Ki bashi Yayansa kinqi kinga kuka yanzu kika fara. Ni ba wannan
bama, Yusuf ya gaya mun yanda kukayi, har na kira Baffa Isiya da Baffa Madu na gaya musu saboda a
fara shirye shirye acan se kuma nace dai bari na kiraki na sake tabbatar wa daga bakinki" Alhaji Qarami
ya katse ni alamar be damu da wani zancen Bashir dana dakko masa ba.

"Ni Yaya ba da gaske nake masa ba, kawai saboda Bashir ya fita a harkata yasa na fada masa haka kuma
ma ni kiran da nayi ma sa so nake na gaya masa yama dena bata lokacinsa ni ba aure zanyi ba" na fada
cikin sabon kuka jin abinda Alhaji Qarami ya rikito mun, waya aike shi ya gayawa Baffa Isiya? Mutumin
da ya tinga mana Tijara nida Yaya Suwaiba ranar daurin auran su Bilal akan mu fito da mazaje muyi aure
in ba haka ba ze dubo a Kumo ya aura mana babu ruwansa sedai mu koma qauye da zama.
"Toh fa, to yanzu ya kike so ayi Ma'u tun farko waya ce miki ana wasa da zancen aure ma? Yanzu so kike
na koma nace musu wasa ake maganar auran nan bayan har Baffa Isiyan yace iyayen Yusuf din idan a
shirye suke suje Gobe akwai auran Shatu da za'a mayar itama se a hada kawai goben a daura ba se an
jira wata Juma'a ba.

Dakyar fa na lallashe shi ya bari shine zakice wasa kike to kira shi da kanki ki gaya masa dan ni dai bazan
iya ba, kuma kinsan kin zalunci Yusuf, kin saka masa rai yana can ya rasa yaya zeyi saboda murna yanzu
kice wasa kike idan bakiyi wasa ba haqqinsa seya kamaki Ma'u" Alhaji Qarami ya fada cikin fushin da ban
san shi dashi ba.

"Ni Yaya inason auran Yusuf wallahi amma makomar yarana nake dubawa, ni bance zankoma gidan
Bashir ba dan inason zama dashi kawai Yaya saboda yarana kasan dai bazasu samu kulawa idan bana
nan ba...."

"Toh wayace karki koma kije mana Allah ya bada sa'a, amma banji dadi ba yanda kika maidani qaramin
mutum kika watsa mun qasa a ido a karo na biyu Ma'u babu komai, Bashir dai kike so ko to sanda kuka
shirya se ku maida auran Allah ya bada sa'a" yana gama fadar haka qit ya kashe wayarsa.

Qoqarin bin bayan kiran nayi amma yaqi dagawa daga qarshe ma ya kashe wayar, yanzu shima ya fita
sabgata to ina zan kai matsala ni Ma'u idan ta same ni? Meyasa duk suka kasa fuskantar abinda nake
nufi sunqi su dubi abin ta maslahar Yayana Aa se kawai Rashin kirkin Bashir suke dubawa.

Kiran Goggo ne ya shigo wayata, seda gabana ya fadi bansan me zatace ba, qarata aka kai mata ko kuma
chanjin labarinbe rigada ya isar mata ba haka dai na daure na amsa na saka wayar a kunnena nayi shiru.

"Ma'u yanzu nake jin labari me dadi, ubangiji ya sanya Alkahiri yasa yin na Allah ne. Kice ma abu ya
matso jiya kika kirani da wasu tsiyatakun ki kai Ma'u dai bazaki girma ba Allah ya qara shirya ki" Goggo ta
fada ina iya jiyo murnar dake cikin muryar ta.

Ajiyar zuciya na sauke jin bata san sabon labarin ba nace


"Uhm Amin Goggo, a dai ci gaba dayi mana Addu'a Allah ya zaba mana mafi Alkahiri"

"Oh kice dai da sauran rina a kaba wane Alkahiri kuma za'a zaba bayan wannan sedai ayi addu'ar Allah ya
tabbatar da Alkahirin ko? Ko dai kinsake canza ra'ayin ne Dan daman seda na Fadawa Bilki indai kece
sedai gyaran Allah kawai, akan wannan Bashir din ana iya zama taron daurin aurema kice kin fasa suma
dena murna suna wasu tsare tsare".

Cikin kuka nace

"Toh ni Goggo ya zanyi dan Allah? Kowa ya tsane ni se zagina suke dan kawai nace zan koma gidan uban
yayana, kuma ni wallahi saboda Yaran nan nake son komawa gidan Bashir ba wani abu ba amma kowa
se yace wani ba haka ba se kace idan sune zasu yarda su zubar da Yayan su tafi wani gurin....."

"Allah na gode maka ni Maryam, Ina dai gidan Bashir ne ko to ki koma Ma'u Allah ya tabbatar da Alkahiri
ya baku zaman lafiya ince dai shikenan? Kiyi haquri da muke miki katsalandan kinji bazamu sake ba"

"Ni Goggo ba haka nake nufi ba, wallahi indai danta halin Bashir ne na gama auransa, yanzu ko yau
bakiga irin wulaqancin da yazo har cikin gida yayi mana ba dagani har Yusuf har yana cewa wai banida
kamun kai ina kawo zawarawa cikin gida zan lalata masa tarbiyyar Yaya"

Salati Goggo ta jawo ta dire kafin ta dora da cewa

"Yanzu Ma'u Rashin zuciyar taki harya kai haka? Da bakin ki kike fadar yazo har cikin gidan ki a gaban
mutane ya zageki sannan kike neman mayar da kanki gidansa saboda Rashin sanin ciwon kai ko? Toh kije
Allah ya taimaka Allah kuma yasa wannan zazzafar soyayyar da kike wa Bashir kar ta zama Ajalinki.

Idan da ace kin san abinda kikeyi da ko hanyar da Bashir yabi bazaki sake bi ba amma nema kike ki sake
cusa kanki cikin rayuwarsa Allah ya taimaka ya bada Sa'a" cikin fushi sosai tayi maganar, na bude baki
tayi saurin katse ni da cewa

"Karkice komai ni ba hanaki nayi ba Allah kafin kice nima na tsaneki koma baqin ciki muke miki karki
koma gidan Abin qaunar ki ko Allah ya bada sa'a".
Duk yanda naso na fahimtar da ita amma Goggo ta baude, maganganu take fada mun da suka tayar mun
da hankali, ita batace kar na koma ba amma qiri qiri ta nuna Adawarta da komen nawa to ya take so
nayi?

Sanda ta saka albarka ma ya zaman ya kasance balle yanzu da take adawa da komen?

Ni yanzu duk ba wannan ba wnada ze dakatar da Baffa Isiya kadai nake nema, Alawa ce ta fado mun a
rai, Allah sarki yar uwata da ra'ayin mu yazo daya nasan zata iya jure duk zagin da ze mata ta nema mun
wannan alfarmar amma yanzu yanda take jin Yusuf din nan yanda kasan qanin Baffan mu haka ta dauke
shi.

A whatsapp na dubata dan dare yayi be kamata na kirata ba naci Sa'a kuwa tana online nan da nan na
farayi mata Voice note na tura.

Ina kallo ta kunna taji amma taqi bani amsa na ringa mata magiya ina roqonta se can naga ta kirani
whatsapp call jikina na rawa na daga ina cewa

"Dan Allah yar uwa kimun wannan taimakon, ba cewa nayi bazan aure shi ba amma kwana hudu tayi
gaggawa nima fushi ne yasaka ni fadar haka amma ki taimaka mun ki kira Alhaji Qarami ki roqamun
Arziqi a maidashi wata daya dan Allah"

"Uhm kinga kafin sannan kin San yanda kikayi kika kora shi ba ai ni Allah yasa ma goben kawai a daura
kowa ya huta dan wallahi Ma'u kyanki auran dole tunda ke baki san abinda ya kamata dake ba" ta fada

"Naji koma menene na yarda nidai ki mun wannan, nifa bawai bana son Yusuf kema kin sani da bana
sonsa ko sauraronsa bazan tingayi ba wallahi amma ni auran ne ban shirya ba Alawa ina buqatar lokaci
har yanzu Addu'a nake Allah ya zaba mun mafi Alkahiri" na fada cikin kwantar da murya dan fatana
kawai ta amince zata kira Yayan.

"Kina da matsala Ma'u duk wani gewaye gewaye da kike da wani neman Alkahiri wai jira kike Alkahirin
yazo gaban ki ya tsaya yace Ma'u gani nine zabin Alkahirin ki ko menene? Shifa Allah yana bawa mutum
dama ne kuma in yayi wasa da ita shine a ruwa in ma zaki nutsu ki fuskanci gaskiya tun wuri wallahi kiyi
bana miki fatan daga baya kizo kina da kin sani da kaza kika Ma'u amma shikenan"
"Naji Alawa, idan Auran Yusuf Alkahiri ne a gareni ma Allah yasa goben idan sunje ta bakin naki a daura
kowa ya huta Amma yanzu dai ki taimaka ki kira Yayan, shi idan ya gayawa Yusuf din idan sunje suce
wata daya shikenan".

"Allah dai ba abin wasan ki bane Ma'u in ma qarya kike yana iya gwada miki ikonsa a yanda baki zata ba,
shikenan zan kira shi da safe idan Allah ya kaimu" ta fada tana qoqarin kashe wayar nayi saurin tare ta
da cewa

"Da safe kuma Alawa? Kin fa san qila da wuri zasu tafi gara dai ki kirashi yanzu dan Allah kinji"

"Hala kinsha kwaya, Alhaji Qaramin zan kira sha biyu na dare ni dallah ki kyale ni duk saurin su dai ai se
sunyi sallar Asuba zasu fita ko su suka kawo sammako duniya to zan kira shi da Asuba in kuma kika sake
magana wallahi fasawa zanyi aikin banza kai se kace ma wani ne zeji miki dadin da muka dage sekin auri
me son ki ki koma gidan Bashir din kawai yafi sauqi ma" ta fada a hasale.

Shiru nayi mata dan nasan hali idan na tanka tana iya cewa ta fasa din tunda daman ba so take yi ba,
mukayi sallama na ajiye wayar na hau juyi a gado ina Addu'ar Allah yasa ta kirashi ya samu yayi musu
magana kafin su tafi dan idan har sukaje gurin Baffa to in naga ban auri Yusuf ran Juma'a ba se wani ikon
Allah.

Washe gari saboda damuwar dana kwana da ita ban iya zuwa aiki ba saboda ciwon kan daya saukar
mun, ina kwance har Yara suka tafi makaranta daman Faridah da yan biyu ne kadai suka kwana ragowar
tun shigowar Bashir jiya ban sake jin duriyar su ba.

Ina kwancan Amnah ta kwankwasa qofa na bata izini ta shigo. Bayan ta gaishe ni ta zauna daga qasa ina
kallon idon ta na gane tayi kuka dan fuskarta gaba daya ta tasa. A sanyaye ta bude baki tace

"Mami naga baki fito ba yau bazakije aiki bane?"

"Bazanje ba Amnah bana jin dadi"


"Sannu Mami, na kawo miki breakfast toh?" Ta sake tambayata. Seda na tashi zaune tareda jingina da
bangon gadon kafin nace

"ki kawo mun Baqin shayi kawai ya isa"

Ina shan shayin wayata tayi qara, Yusuf ne. Naja wani uban tsaki na ajiye dan gani nake duk shine
maqasudin matsalata a yanzu, duk da be takurawa rayuwata ba da babu me damuna akan zancen wani
aure yanzu ai bashi kadai bane yake sona amma yafi kowa naci ko dan yana ganin shi dan gida ne kowa
yana sonsa gashi yanzu ya jawo mun ni ta ina zan fara kiran wani Baffa Isiya nace masa karya amsa
maganar su?

Seda wayar ta katse ya sake kira ta kuma yankewa ban daga ba se gashi ya turo mun da saqo cewar
yanzu ze wuce Abuja kuma Wakilansa suna kan hanyar zuwa Kumo gurin Baffa Isiya se wani tarin
godiyarsa da damar dana bashi da alqawarin bazanyi dana sanin amincewa dashi ba.

Ina gama karanta saqon na shiga kiran layinsa dan in gaya masa ya dakatar dasu karsu je amma nayi
rashin sa'a a kashe, safa da marwa na ringayi a dakin kamar zanyi kuka, dana sani na daga kiran nasa qila
abinda ze gaya mun kenan a sannan na dakatar dashi amma yanzu qila kafin ya sauka na samu muyi
magana ai sun rigada sunje an gama duk abinda za'ayi gashi bani da tabbacin Alawiyya ta kira Alhaji
Qarami dan wayarta ma a kashe take.

Tunanin wa zan kira a yanzu na ringayi a raina, Alhaji Yasir? Kai bazan kirashi ba dan indai yana bayan su
Alhaji Qarami to fadan da zan sha a gurin sa ma sena gwammace na haqura na auri Yusuf ko bana sonsa
kuwa. Yaya Kabiru ne ya fado mun a rai, duk mazan gidan mu yafisu sauqin kai dan shi Ustazi ne da be
dauki Duniya da nisa ba, nasan ko yana kan ra'ayinsu nasan idan yaji nawa bangaren ze saurare ni, qila
ma ya taya ni shawo kansu.

Da wannan shawara na danna kiran lambar Yaya Kabiru. Cikin muryarsa ta ustazai masu aje gemu yace

"Assalam Alaikum Malama Asma'u barka da safiya" ya fada bayan daya daga wayar.

"Yaya ina kwana? Ya gida ya aiki?

"Lafiya lau ya kike ya yaran? Se kuma mukaji abin arziqi. Ainihin jiya da daddare Babban Yaya ya sanar
mana cewa mu tafi Kumo yau da safe ainihin za'azo neman auranki kai nayi murna kwarai wato har
alawa na fita na rabawa yaran makarantar dare nace suyi Addu'a Allah ya tabbatar da Alkahiri ai Malama
Asma'u in Allah ya yarda kam kinyi miji a wannan karon"

Gaba daya kaina zafi ya qarayi da wannan bayani da yake faman yi mun ina qoqarin tare shi amma ina
seda ya kai qarshe.

"Daman Yaya maganar ce tasa na kiraka yanzu, kuna gida ne ko kun tafi Kumon?" Na fada ina taraddadin
amsar da ze bani, cikin rashin sa'a kuwa se ji nayi yace

"Ai tun qarfe takwas muna nan, kinsan Halin Baffa Isiya baya son wasa musamman akan abu me
muhimmanci irin wannan abu, Masha Allah ai kingansu ma sun qarso yanda za'ayi yanzu ki bari idan
mun gama ainihin sena kiraki naji menene" yana gama fada ya katse wayarsa.

Kamar zan rusa kuka haka na zabga tagumi na zauna qirjina kuwa se dukan uku uku yake. Na tabbatar
idan har Baffa Isiya ya karbi maganar nan tofa rusata se dai ikon Allah ko idan shi Yusuf din ne da kansa
yace ya fasa wanda bana taba tunanin haka wai ma tun farko waya aikeni aikata hakan?

Duk wannan Bashir din ne ya jawo, gashi tunda yazo ya gama shirmensa jiya ko a waya be kirani ba balle
ya bani haqurin abinda yayi kai nima fa wata wawuya ce wallahi da har nake tunanin Bashir ya chanza
daga halinsa nada.

Message na turawa Yusuf akan idan ya kunna wayarsa ya kirani dan Allah da gaggawa ina so muyi
magana ina turawa kuwa wayar ta mutu babu chaji dan jiya damuwa bata barni na jonata da daddare ba
se yanzu da ta mutu na jona na sake kwanciya dan gaba daya jikina da zuciyata babu dadi.

Haka na wuni da taraddadin abinda zeje ya dawo, ban kuma bi takan wayata ba, daman kiran Yusuf
kadai nake tsammani me muhimmanci tunda naga kuma har gurin La'asar be kira ba nasan qila suna
Chamber ne tunda yau ranar aiki ce zuwa dare dai duk tsiya nasan ze ga saqona kuma ze kira, dole nasan
yanda zanyi na dakatar da maganar nan, ko bazan koma gidan Bashir ba to sedai na haqura da Aure dan
ban hango cewar zan iya tafiya nabar Yayana a hannun Bashir da Amirah ba.
BASHIR A DAREN JIYA

Cikin wani irin yanayi ya fita daga gidan Ma'u ikon Allah ne kawai ya qarasa dashi dakinsa ya fada kan
gado dafe da kansa da yake barazanar fashewa, yana jiyo muryar Addah da take tambayarsa lafiya
amma be kulata ba ya wuce.

"Ya Allah, ta yaya Ma'u zata auri wani bayan ni? Ta yaya haka zata faru?" Abinda yake maimaitawa
kenan yana riqe da kansa da yake juya masa, wayar dake cikin Aljihu ce ta dauki qara, a fusace ya cirota.

Amirah ce, se a sannan ya tuna dazu da Yamma Samuel ya kaita Awo kuma haryanzu bata dawo ba toh
kiran me take masa? Qarshe baze wuce qorafi ba ko kuma tana buqatar kudi kawai seya kashe kiran ya
hefa wayar kan gado ya kwanta tareda riqe kansa yana maimaita Innalillahi a ransa.

Bugun qofar sa da ake kamar za'a ballata ne yasaka shi tashi a hasale, idan kuwa daya daga cikin yaran
nan ne babu abinda ze hana jikin yaro gaya masa basu san halin da yake ciki ba zasu zo su takura masa
da bugu me zeyi musu.

Saurin Ja da baya Addah tayi ganin yanda ya bude qofar kamar ze make ko waye a wajen, kafin yayi
magana ta miqa masa wayar ta tana cewa

"Ungo, Amirah ce daga Asibiti ni bangane kan maganar ma da take yi ba gashi dai kaji da kanka".

Hararta yayi kamar baze karba ba dan baya san qarin wata damuwa akan wadda yake ciki amma se dai
ya miqa mata hannu, idan dai kuwa rainin hankalinta ne tabbas akanta yau ze sauke duk tarin bacin
ransa.

Cikin muryar Kuka Amiran take cewa daga cikin wayar

"Yaya ina ta kiranka baka dauka ba qarshe ma ka kashe wayar"

"Malama bana son sakarci da rashin hankali ko ni yaron ki ne da dole idan kika kirani sena amsa? Idan
baki da abin fada dallah ki kashe waya kinsa anzo ana bugawa mutum qofa kamar wanda ake bi bashi"
yayi maganar a hasale yana hararar Addah data saki baki tana kallonsa dan a fuskarsa kadai ta karanci
akwai matsala.

"Yaya kazo Asibiti akwai matsala, likita yace wai cire cikin nan za'ayi ni ban gane abinda suke nufi ba dan
Allah kazo" Amirah ta sake fada cikin kuka.

Tsaki yaja me qarfi yace

"Toh su cire mana ni ina ruwana, badai bazaki kiyayi shaye shayen magunguna barkatai ba ai baki gaji da
cin wahala ba, Allah ya bada sa'a" ko a jikinsa ya kashe wayar ya cillawa Addah abarya ya juya daki.

Duk abinda ya sameta ai su suka ja, yana ankare dasu kullum basu da aiki se jiqe jiqen magunguna tayita
dirka harda wanka da hayaqi yi take shiyasa ya dena cin komai a gidan dan besan me suka zuba ba
maganace kawai beyi musu ba tunda ai koma menene jikinta ne ze gaya mata bana wani ba.

Yana shiga dakin wayarsa ta sakeyin qara, a fusace ya dakko ze kasheta gaba daya se yaga Likitan da
Amirah take gani ne dan haka ya daga.

A taqaice suka gaisa likitan yace masa yazo Asibiti saboda akwai matsala babba, bashida zabi tunda
yanzu daga bakin likitane haka ya dauki muqullin mota ya fito dakyar yake daga qafarsa saboda ciwon da
kansa yakeyi ga jiri yana gani.

Sanda ya isa Asibitin sosai ciwon kansa ya qaru saboda abinda ya tarar, Jaririn da yake cikin Amirah ya
mutu a yanda sukayi hasashe ma kusan kwanaki uku kenan yanzu dan tsahon lokacin datace ta dena jin
motsi kenan samma saboda tsabar shirme da rashin sanin ciwon kai irin nata ta zauna wai se ranar
awonta ta zagayo sannan zataje Asibiti tayi qorafi.

Tagumi kawai yayi yana kallon Likitan da yake zabga masa masifa kamar ze dake shi.

"Wane irin shirme ne haka Engineer kamar wadanda baku da ilimi? Mace da ciki wata bakwai ace kiyi
kwana uku bakiji motsinsa ba kuma ki share guri kiyi zamanki a gida ba tate da tunin komai ba?
Tun farko me yasa ma da ta fara zuwa Awo tayi mana qarya?

Ta gaya mana Haihuwarta daya shine wanda akayi mata Cs babyn ta mutu daga baya se yanzu ne zata zo
tana wannan shine karo na uku banda Bari daya da tayi wace irin yarinya kake zaune da ita da bata dauki
lafiyarta da muhimmanci ba.

Tun farko da mun sani zamuyi bincike mu gano matsalar yanzu kuwa lokaci ya qure dan Babyn ma ya
rigada ya mutu a cikin ta yanzu za'ayi inducing nata ne muna fata ta iya haihuwa da kanta tunda babu
wata matsala amma ko dan gaba dole ku kiyaye.

Da akwai abinda muke kira da Rhesus factor, wani protein ne ake samun sa wajen kwayar jini (red blood
cells) wadanda suke dashi nasu yana zama Positive + yayinda wadanda basu dashi yake Negative -.

Idan ya kasance mace me Rh + tana dauke da cikin Jariri da yake Rh + to babu matsala zata haife shi
lafiya.

Amma a duk sanda ya zamana cewa an samu banbancin wannan Rh factortsakanin uwa da jaririn da
yake cikinta ma'ana uwa ta zamana cewa bata da wannan protein Rh - jaririn cikin ta ya zama Rh + a nan
ana samun matsala saboda idan kwayoyin halittar su suka cudanya suna daukar na jaririn kamar
abokanan gaba dan haka zasu saki makaman da zasu yaqeshi wannan yana janyo rasa jaririn da ake
dauke dashi idan jininsu ya hadu.

Dan haka a duk sanda mace da take bata da wannan protein a cikin jininta (Rh negative mother) ta samu
ciki idan aka tabbatar da hakan da akwai allura da ake yi masu ta Immune globulin domin kare faruwar
hakan toh abinda yake faruwa da matarka kenan wanda da tun farko mun san labarin matsalarta da
munyi qoqari gurin ganin hana faruwar hakan a gaba amma yanzu lokaci ya qure sedai ayi Addu'a Allah
ya kawo masu Albarka a gaba".

(Kuna iya neman qarin bayani akan Rh factor saboda dau da yawa mata na da wannan matsalar da take
janyo musu mace macen jarirai a ciki ko yayin haihuwa wanda ba kowanne Asibiti bane suke da kula da
kwarewar da zasu binciki hakan, Allah yasa mu dace ya bamu yaya masu Abarka).

Wannan ake kira goma da Ashirin, Haka Bashir ya samu guri ya zabga tagumi bayan da duk ya gama cike
ciken takaddu tareda biyan kudin da ake da buqata.
Amirah kuwa na can a labour room an saka mata ruwan naquda ana ta gumurzu, se gurin qarfe uku na
dare Allah ya yanke mata dan har sun fara tunanin shigar da ita Tiyata se kuma ta haihu jaririnta kamar
sauran me kama da Bashir jikinsa yayi tibis saboda zafin ciki, sosai ta ringa kuka su kansu Nurses din sun
tausay mata irin wuyar dataci gashi dama Babu ya rigada ya rasu, ana nunawa Bashir yaron kansa da
yake masa bala'in ciwo ya sara yana miqewa jiri ya kwashe shi daga nan be sake sanin inda kansa yake
ba.

ASMA'U

Har aka kura sallar magriba banji kira ko wani saqo ya shigo wayata ba, ina idar da sallah na qarasa jikin
soket din dana saka chajinda mamamkin meya faru yau gaba daya ace babu wanda ya kirani? Ai ko daga
Office nasan baza'a rasa masu kirana ba dukda na tura da saqon cewar bani da lafiya.

Tsaki naja tare da zama ganin ashe duk wannan abun wai ban ma kunna soket din ba, kunnawa nayi nan
da nan wayar ta dauka, na tashi na cire hijabin jikina daidai nan aka qwanqwasa qofa na bada izinin
shigowa kafin na koma gefen gadon na zauna.

Aliyu ne kansa a qasa ya shigo da sallama na amsa masa ciki ciki ina kallonsa nan da nan raina ya fara
baci dana tuno irin kukan da suka Zo suka ringa yi mun shekaran jiya hankalina ya tashi ashe duk shiri ne
sukayi da ubansu.

"Mami dan Allah kiyi haquri wallahi badan Abbi yace mu roqeki mukayi ba dagaske Mami muna so ki
dawo gidanmu saboda"

"Rufe mun baki Aliyu, ni zaka rainawa hankali ka hada baki da ubanku kuzo ni ku daga mun hankali ko?
Daman abinda kuka shirya kenan kuzo ku yaudareni na koma gidan ku yaci gaba da wulaqantani yana cin
mutuncina ko?" Na fada cikin bacin rai. Seya rarrafo ya kama qafata fuskar sa dauke da hawaye yace

"Wallahi Mami ba haka bane, dagaske Abbi yayi nadama kuma shiya roqeni akan mu taimaka masa ki
koma gidan mu bansan me yasa yayi abinda yayi jiya ba Mami. Ni kaina raina ya baci banji dadin abinda
ya faru ba kuma yanzu na yarda Mami duk hukuncin da kika dauka akan sa kinyi daidai na fahimci Abbi
nada wani dalili nasa da yake so ki koma gidansa ba wai dan ya chanza daga halinsa nada ze dena bata
miki rai ba.
Kiyi haquri dan Allah karkiyi fushi dani bansan abinda ze kumayi kenan ba da ban yarda na shiga
maganar ku ba".

Shiru nayi naqi kulashi, ya ringa magiyar sa yana hawaye seda na mula kafin na dauke kwallar da nima
suka fara zubo mun ina kallonsa nace

"Aliyu ina son komawa gidan ku saboda ku badan ina son cigaba da zama da Abbin ku ba kuma na yanke
shawarar haka duk kuwa da abinda ya faru jiya saboda idan na barku bansan wace irin rayuwa zaku
fuskanta ba Idan bana nan dukda bana zaton samun wani chanji na daban a gidan amma na zabi na bar
duk wani farin ciki nayi rayuwa daku dukda tun farko daman bani na zabi barin ku ba shiya rabani da ku
amma laifina kuke gani"

"Mami ban taba ganin laifinki ba saboda tun banida wayon nasan irin zaman haqurin da kikeyi da Abbi
da yan uwansa. Wallahi Mami lokaci da yawa ina ganin idan nine a matsayin ki bazanyi irin haqurin da
kike yi ba kuma kullum ina Addu'a Idan na girma karna zama irin Abbi.

Amma bazamu so ace iyayen mu basa tare ba koma menene, na zata abinda ya faru zesa Abbi ya canza,
har Alqawari nace yayi mun akan idan kika yarda kika dawo ze saki Anty Amirah amma shine jiya yazo
yayi wannan abun, gashi nan Yanzu shima abin ya dame shi tun jiya daya fita daga gida ma be dawo ba
bamu san a inda ya kwana ba"

"Aliyu koda wasa karka kuskura naji maganar banza ta shiga tsakaninka da Amirah balantana har kayi
sanadin da auranta ze mutu, ina ruwanka da ita duk abinda ya faru meye nata a ciki da har zakace se an
saketa idan zan dawo?"

"Mami wallahi duk abinda a yake faruwa itace, ko sanda Abbi ya sake ki ita ta zugashi, ranar muna hanya
ya kaimu makaranta sukayi waya ita taringa fada masa maganganu shine ya dawo ya sake ki" ya fada
kamar zeyi kuma

"Karka sake fadar haka kuma babu ruwan Amirah dan bata isa ta saka shi ko ta hana shi yin abinda yayi
niyya ba dan haka karkace zaka tsaneta ko ka cusawa yan uwanka tsanarta saboda kuna tunanin ita ta
fitar dani daga gidan ku.
Rabuwar mu daga Allah ne, idan ya qaddara zan dawo gidan ku zan dawo idan kuma bani sauran rabon
zama a tsakanin mu haka zamu haqura. Abinda nake so dakai Aliyu kaine babba duk abinda kayi dakai
zasuyi koyi ina so ka zama babban kwarai ka yi abinda qannenka zasu gane na kirki suyi koyi da kai.

Bana so ka dena wannan rashin kunyar da kakeyiwa mutanen da suke zuwa gurina ba irin tarbiyyar da
nayi muku ba kenan, ka kuma kula da qannenka. Bana so naji wani abu akanka dan idan sauran sukayi
suma nasan laifinka ne kaika saka su ko kuma kana gani baka tsawatar muku ba.

Daga yau gaba daya zaku koma gidan ku da zama cin abinci da komai acan zaku ringa yi bance karku zo
nan ba amma maganar kwana ko yin wani abu na soke gara ku koma ku koyi rayuwa a gidan ku dan be
zama lallai naci gaba da zama tare da ku ba.

Kuyi haquri haka Allah ya shirya mana idan muna da rabon ci gaba da zama tare zamu dawo wata rana"
na qarasa ina daga kaina sama saboda jin wasu hawaye suna neman zubomun kamar yanda shima
Aliyun yake kuka.

"In sha Allahu Mami zanyi duk abinda kika ce, kuma na yarda Mami duk zabin da kika dauka kiyi, ko auri
Uncle Yusuf yana sonki kuma shi ba irin Abbi bane kuma daman ko baki fada ba ina so na gaya miki zamu
koma can gidan gaba daya saboda ko jiya ina jin su suna cewa sun koreki muma a hankali dukka se mun
bar gidan Anty Amirah da yaran da zata haifa kadai ne zasu zauna a gidan dan haka zamu koma amma
Banda Farida Mami kinga ita kadai ce ba tare zamu ringa kwana ba, gara ta zauna a nan babu wanda ze
ringa kula da ita".

Ajiyar zuciya nayi na kama hannunsa ya dawo kusada ni tareda rungume ni ina shafa kansa nace

"Karka sake cewa zakayi abu saboda wani kuma ni ba korata sukayi ba zaman da Allah ya rubuta
tsakanin mune lokacinsa ya qare bawai yin wani mutum bane sannan basu isa suyi muku komai ba se
abinda Allah ya tsara,

Gida kuma ai gidan ubanku ne duk inda kukaje kuka dawo baku da inda yafi shi Dan haka ku kwantar da
hankalin ku babu komai in sha Allah"
Nasiha naci gaba dayi masa cikin laluma har aka kira salar isha'i kafin ya tashi ya fita, wayata na jawo na
kunna kafin na miqe na shiga bayi na kuskure bakina tunda ina da Alwala na fito.

Har na zura hijabi zan tada sallah wayat tayi qara sena koma na dauka dan kiran Yusuf nake tsammani,
bana so a samu wani akasi gara muyi magana dashi a dakatar da duk wasu shirye shirye tunda ni bazan
iya tunkarar Baffa Isiya kai tsaye ba amma shi Idan yace a daga lokaci ai dole a daga.

Tsaki nayi ganin Alawiyya ce take kira, nasan ma idan na daga raina ne ze baci, se kawai na ajiye na tayar
da sallata, ko kafin na idar an kira wayar yafi sau Ashirin, ko kyakykyawar Addu'a ban iyayi ba na Shafa
saboda jin yanda kira yake sake shigowa qirjina na dukan uku uku na janyo wayar ina mamakin meya
faru haka? Ban sake shiga rudani ba seda naga duk kiraye kirayen na yan gidan mu ne harda Anty
Suhaima itace ta kira qarshe ma.

Ina qoqarin bin kiran na jiyo muryar Anty daga palour tana tambayar yara ina ina matar datace ko ta
qofar gidan ta nabi seta mun rashin mutunci ita ce kuma ta biyoni to me yake faru ba?

Wayar hannuna ce ta fadi gabana ya yanke ya fadi dana tuna dazu fa naji Aliyu yana cewa wai Bashir be
kwana a gida ba har yanzu be dawo ba kuma karfa Ace Bashir ne ya mutu shiyasa ake ta mun wannan
kiran.

Jikina na rawa na tsugunna na dakko wayar tsabar yanda na rikice ma kasa dannata nayi daidai nan kira
ya sake shigowa lokaci daya Anty ta turo qofar dakin ta shigo. A tsorace na kalleta na kalli wayar
hannuna, Alawiyya ce dai take sake kira na sake kallon Anty a maimakon naga tashin hankalin da nayi
zato a fuskarta sema wani murmushi da annuri na gani ta nufoni da sauri ta rungumeni daidai sanda
itama Alawiyya dana daga wayarta ta rangada mun wata uwar guda da ta sakani saurin janye wayar
daga kunnena saboda yanda abin yazo mun babu shiri.

Kamar hadin baki sukace

"Alqawarin Allah ya cika, yau Asma'u ta zama matar Yusuf mutu ka raba in sha Allahu".

Yanda kasan wadda aka zarewa laka haka nayi baya na zauna dabas akan gado ina kallon Anty dake
kyakyata dariyarta ga muryar Alawiyya ma daga cikin wayar tana ci gabada zayyo nata zancan nidai jinsu
kawai nake amma kamar a mafarki, Aure fa naji suna cewa kuma nida Yusuf anya sunsan me suke fada
kuwa? Kodai labarin zuwa tambayar auran sukaji basu fahimta daidai ba.

"Amarya fa ta tafi hutun rabin lokaci inaga mu zamuci tukuicin nan dan da alama bata san da labarin ba"
naji Anty tana fada bayan data saka wayata a kunnenta, gani nayi ta cire ta saka a speaker naji Alawa
tana cewa

"Kin tuna me kika ce mun jiya, idan auranki da Yusuf Alkahiri ne Allah yasa idan sunje yau a daura a take
to kin gani idan ma gatsali kika yiwa Allah kinga ya gwada miki ikonsa babu abinda ya gagare shi dan
haka ko kisha ruwan sanyi kiyi murna ko ki nemi fiya fiya duk tsiya in kin mutu ma haka za'a ce Ma'u
Amaryar Yusuf ta mutu se naga qarshen qiyayya kuma" ta kwashe da dariyar mugunta.

"Kinga yar uwa barta kinji aini wannan abu yamun dadi Allah dai ya sakawa da duk wanda ya daura
wannan aure da gidan Aljanna ya raba shi da sharrin mahassada da yan sa'ido dan ya gama mun komai a
rayuwa abu daya ya rage mun yanzu na tafi gidan Bashir na isar masa da labarin Farin ciki" Anty ta fada
ina jin yanda suka kwashe da wata muguwar dariya su biyun kafin ta kashe wayar ta ajiye tana cewa

"Ma'u Amarya Ma'u Amarya ai yau tukuicin Yallabai daban yake na wannan labari aradu sena kaishi
duniyar dadi na dawo dashi ke yau ko sunan sa baze iya tunawa ba, bari naje kar a rigani fadawa Bashir
labarin nan dan ina fitowa naga shigowar motar sa qila yanzu ya taso daga aiki" ta fice abinta tana dariya
ko lura da yanda nayi suman zaune ma batayi ba ta qara gaba abinta.

ITA QADDARAR AURE, MUTUWA DA HAIHUWA ABU NE DA YA KE KASANCEWA A LOKACIN DA ALLAH YA


NUFA KO ANA SO KO BA'A SO.

ALQAWARIN ALLAH YA CIKA A LOKACIN DA KOWA BEYI ZATO BA MA'U TA ZAMA MATAR YUSUF

TABBAS HAQURI YANA TADDA RABO DUK DAREN DADEWA

HAKA ZALIKA SAU TARI ABINDA MUKE SO YAKAN ZAMO BA ALKAHIRI BANE A RAYUWAR MU KO A IYA
NAN NA AJIYE ALQALAMINA NA TABBATAR DA SAQO YA ISA INDA AKE SO AMMA MUJE ZUWA SAURA
QIRIS
WATA KISHIYAR

(ALKAHIRI CE KO SHARRI)

Na Maryamah Farouk

(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)

Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 62

YUSUF

Baze iya misalta irin murna da farincikin daya tsinci kansa a ciki ba jin abinda Ma'u ta fada. A sukawane
ya fice daga gidan yana shiga motarsa Driver yaja suka tafi,

Tun kafin su fita daga Get din Estate dinsu Ma'u ya rangadawa Alhaji Qarami waya baya so ya bata lokaci
ballantana ta dawo ta chanja magana dan yasan koda Ace abinda tayi niyyar gaya masa kenan to Juma'ar
data yanke harda tagomashin bacin ran Bashir ya saka.
Sanda ya gayawa Ahaji Qarami maganar se ya zamana tsakaninsa da Yusuf din har an rasa ma wanene
yafi wani murna nan take yace masa ba matsala ya gayawa mutanensa idan sun shirya gobe suje yanzu
ze kira Baffan su ya sanar masa.

lafewa yayi a cikin kujerar motar yana sakin murmushi ransa fes jinsa kawai yake kamar wanda akayiwa
Bushara da Aljanna tabbas ya yarda mahaqurci mawadaci kuma Allah shine meyi a sanda yaso ba'a saka
shi ba kuma a hana shi.

Hajiyar ya dannawa kira dan da ita ya kamata ya fara raba wannan abin Farin cikin ringin biyu ta daga
ckin kamilalliyar muryarta ta dattijai ta yi masa sallama.

"Hajiya barka da dare, Albishirinki Hajiya" Ya fada a jere

"Barka dai Babangida wane abin farin ciki ne haka ya faru da har muryarka ta gaza boyewa ko
taqaddamar tikitin takarar taku ce ta qare kayi nasara?" Ta fada a sake daga jinta irin mutanen nan ne
masu sakewa sosai da yaransu

Wani murmushi ya saki kamar yanagabanta kafin yace

"Wannan ai ba komai bane akan wannan albishir din Hajiya ki canka da kanki wane abu ne kike zaton ze
sakani farin ciki haka?"

Shiru tayi se can tace "Asma'u, nasan dai a yanzu idan ba zancen takara ba toh sedai ita din nasan dai
wadannan sune manyan burikan ka a rayuwa"

"Kin canka Hajiya yau Ma'u ta amsa da kanta ta bani damar na tura magabata na a daura mana aure
wannan Juma'ar me zuwa dan haka Hajiya ki gayawa su Baba Sale idan ze yuwu gobe idan Allah ya
kaimu suje, zan tura miki da Lambar Babban Yayansu se ki bashi suyi magana suji ina ne zasuje neman
auran".

"Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah, Babangida kaga abinda nake gayamaka ko? Ita rayuwa kabi
ta a sannu. Duk yanda kaso da faruwar abu idan Allah be kawo shi ba haka zaka haqura. Yanzu kaga ribar
haquri ko? Allah ya tabbatar da Alkahiri yasa yin na Allah ne, nayi murna nayi murna Babangida Allah
yasa za'ayi damu bari na kira Kawun naka yanzu kuwa na sanar masa na tabbatar shima zeyi farin ciki da
wannan Al'amari dan ko shekaran jiya dayazo seda yayi mun ciwon baki akan zancen auranka yace wasu
da yawa ma basu yarda kana da aure ba ko wannan ze iya kawo maka tangarda a cikin tafiyar siyasarka"
Hajiya ta fada cikin tsananin murna.

"Toh ai yanzu ciwon baki ya qare Hajiya in sha Allahu ki dai kirashi yanzun dan Allah kuyi magana a samu
goben aje"

"Toh sarkin zumudi gobe ai yayi wuri ina lefinzuwa jibi haka?" Ta fada cikin tsokana, da sauri ya tare ta
da cewa

"Haba Hajiya wane irin jibi kuma? Juma'a fa tace a daura aure kuma yau litinin nidai gara suje goben ayi
komai. Mansur yana nan duk abinda ake da buqata a karba a hannunsa kafin na shigo"

"Toh Allah ya tabbatar mana da Alkahiri, bari na tura ayi mun magana da kawun naku nasan yanzu yana
waje tunda ba'a dade da idar da sallah ba beci ace ya tafi gida ba" da haka sukayi sallama shi murna ita
murna.

Ranar qaryar bacci duk iya satar sa hakayaga Yusuf ya qyale dan kwana yayi yana sallahda tasbihi na
nuna godiyarsa ga Allah bisa cika masa wannan babban buri na rayuwarsa, gani yake ko Yanzu ya mutu
ya samu farin cikin da ya dade yana kwadayi. Ma'u ta amsa soyayarsa ta yarda dashi a matsayin Mijin da
zata aura.

Qarfe Sha biyu na washe garin ranar ta kafa tarihin da ko a hasase be taba hasko faruwarsa a rayuwarsa
ba. Suna zaune gaban shugaban qasa a lokacin, tattaunawa ce me matuqar muhimmanci sukeyi saboda
yana cikin kwamitin tsaro na qasa gaba daya hankalin sa rabi ne akan tattaunawar da sukeyi inda ya kasa
rabin a jiran tsammanin sakamakoj neman auran da aka tafi masa.

Kunnensa maqale da Bluetooth yana sauraran duk abinda yake faruwa acan Kumo gidan Baffa Isiya
saboda seda ya jaddadawa Qaninsa da aka tafi dashi akan suna zuwa ya kirashi a waya yana so yaji duk
abinda akayi karma suje suce a qara lokaci akan abinda ya gaya musu.
Sanda yaji an fara karanto Siga tsakanin Baba Sale Wakilinsa da Baffa Isiya wakilin Ma'u miqewa tsaye
yayi cikin tsananin mamaki haka mutanen da suke zaune tare dashi gaba daya suka saka ido suna
kallonsa dan dama tuni sun lura da hankalin sa baya kan abinda sukeyi.

Besan lokacin daya sulale yayi sujjada a inda yake ba ta godiya ga Allah lokacin dayaji wani da be shaida
muryarsa ba yana jaddada dauruwar aure tsakanin Yusuf Sulaiman Wunti da Asma'u Abdullahi Tukur se
gani akayi hawaye suna tsere akan fuskar sa, abin dariya abin takaici fuskarsa shabe shabe yana haqaye
kuma yana dariya yake gaya musu abinda ya faru, nan da nan suka hau taya shi murna dan duk wanda
yasan Yusuf yasan Asma'u, kai ko mace me sunanta ya hadu da ita se taci wannan darajar ya karramata.

Dole ya datse mitin ya fice suna ta tsokanarsa, ya ringa neman Layin Asma'u ya gagara samunta se ya
mayar da Akalar kiran kan Alhaji Qarami suka hadu suna ta jimamai dan tuni Malam Kabiru ya kira ya
zayyana masa dan shine ma Ummul aba'isin da suka sake fanfa Baffa Isiya akan a daura kawai to me za'a
jira.

"Wato Yaya nasan halin Asma'u sarai shaqiyyar yarinya ce, wato ainihin dazu da safe ta kirani. Daga
muryarta na fahimci ta kira tayi mun shaqiyancin nata ne se na yi kamar ban gane ba, tana ta wani hanya
hanya ainihin danaga zata batamun lokaci kawai nace mata muna Kumo ai gashi ma har baqin sun iso
ainihin idan sun tafi zan kirata alhalin a lukacin ma ina shan Shayi ne da Kubza ko shiryawa banyi ba"
Bayanin da Yaya Kabiru yayi wa Alhaji Qarami kenan.

Duk yanda Yusuf yaso ya daure kasawa yayi dole ya yanki tikitin komawa Lagos na qarfe shidan yamma.
baze iya ba yana buqatar ganin Ma'u a yau, ya rungumeta a jikinsa ya kirata da matarsa halalinsa aure ya
bashi ita yanzu yana da dukkan wata cikakkiyar dama da iko a kanta wai dadi kashe shi shi Yusuf yau ya
zama Angon Asmy.

Yana hanyar zuwa Airport Intee ta fado masa a rai, dafe kansa yayi, tun a daren jiya yaso ya shaida mata
maganar auran da zeyi se gashi abubuwan sunzo a yanda babu wanda yayi zaton faruwarsu.

Lambarta ta America ya daddanna ya kira amma akace masa a kashe take, seda ya hadiye wani abu daya
taso masa na bacin rai akan wannan dabi'ar ta Intee da sam bata dauke shi da qima ko mutunchi na Miji
ba. Ya tabbatar da tafiya tayi wata qasar ba tareda ta nemi izininsa ba ko da yake abinda aka sabane ai,
idan har ta gaya masa zataje wani guri to kudi ne bata dashi tana da buqatar ya bata.
Lambar mahaifiyarta ya nemo har ze danna ya tuna da a cikin watan nan da aka shiga akwai bikin
qanwarta da suke uba daya da za'ayi a nan Nigeria zata iya yuwuwa sun taho bikin ma shine bashi da
qimar da zata sanar masa seya canza akalar kiran zuwa lambarta ta Nigeria cikin Sa'a kuwa ta shiga.

Seda ta qaraci ringin ta katse ya sake kira dana dab da yankewa ta daga cikin muryar bacci tace

"Hello Sweet"

"Intee zaki taho Nigeria amma baki sanar dani ba me yasa kike..."

"Ai kaga halinka sweet qorafi qorafi baka da aikinyi kai se anyi maka laifi toh idan na gaya maka zanzo
me zaka mun? Bana son takura ne nasan ina gaya maka zakazo ka fara damun mutum da jarabarka
shiyasa ma ban neme kaba" Intee tayi saurin katse shi.

Shiru kawai yayi yana jinta, to meye ma baqo a cikin halinta ne wai shekara bakwai ai sun zama jiki sedai
ya mata fatan shiriya idan tana da rabo, tunowa da abinda yasa ya kirata ya saka shi sakin wani
murmushi a idonsa yana hango Asmynsa yana ayyana irin Albarkatun da ze diba a jikinta dan ko ba'a
fada ba daga kallo kasan Asmy irin matan da Allah ya wadata su da komai ne ma'ana kyau na zahiri dana
badini wanda ya same su sedai yai ta sujjada yana godewa Allah.

"Se mutum yayi magana ka fara fushi kuma, to jiya fa nazo ban taho da Asmy bane shi yasa ban kiraka ba
kuma kaga hidimar biki zamu fara saura sati daya ina da buqatar na samu hutu saboda kwalliyata tayi
kyau" Intee ta fada cikin shagwaba.

"Ba fushi nayi ba ai bakya laifi Yammata ya kamata kam ki huta kiyi kyau sosai kinji, dama ina so na gaya
miki ne kin tuna maganar da mukayi kwanaki ko?"

"Wacce magana kasan nifa ban fita riqe abubuwa marasa muhimmanci da basu shafe ni ba"

"Hakane, toh maganar aure na da nayi miki" ya fada bayan daya ja numfashi yana jinjina halin matarsa a
ransa
"Oh wai wannan maganar to ai tun lokacin ni na gaya maka bani da matsala da wannan kawai dai ka
tabbata idan ka tashi auran ka samu classy mace wadda idan aka nunata aka ce mijin mu daya da ita
bazan ji kunya ba kuma zata kulamu dakai dakayu sosai shine kawai ni damuwata"

"Intee kina sona kuwa?" Ya fada cikin tsananin mamakinta saboda be yarda ba duk sanda take gaya
masa gashi yanzu ta sake maimaita wa anya yarinyar nan tasan abinda take yi ma kuwa

"Ina sonka mana Sweet me yasa kake tambaya?" Ta fada ba tareda damuwar komai ba.

"Babu komai, kin tuna Asma'u? Takwarar Asmy wadda kika kaita gurinta a Lagos?"

"Uhm bazan iya tunata ba saboda bata da ajin da zan tsaya na kalleta har na gane kamanninta" ta fada a
yatsine. Murmushi yayi me sauti kafin yace

"Koh? Toh ita zan aura ko nace miki ita na aura dan yau akaje tambayar mun auranta se kawai aka daura
auran gaba daya"

"Haka iyayenta suka gaji da ita lalai me yasa Nigerians kwata kwata basu da lissafi ne se kace ana neman
kai da ita da kyanta da komai daga zuwa tambayar auranta kamar wata tsohuwa za'a bada ita babu jan
aji gaskiya an cuceta wallahi" Intee ta fada ranta a sake babu alamar wai Mijinta ne yace mata ya qara
aure balle abin ya dadata da qasa.

Dariya Ya fashe da ita jin wai babu jan aji babu komai aka bada ita cikin sigar tsokana yace mata

"Toh ai abin daga ni ne, idan kin manta na tuna miki kema fa kina ganina kika rikice kika cewa Dady idan
bani ba se kin fada rijiya haka babu jan ajin babu komai aka bani ke toh itama yanzu kin gani aka bani
ita"
"Koma dai mene ne zan koma bacci na, da kasan wannan maganar cema da text kayi mun kawai, Allah
ya sanya Alkahiri ka gayawa Amarya ta kulamun dakai sosai, Ina sonka se anjima" tana hama fadar haka
ta kashe wayar.

Murmushi ya ringa saki wato ta kowanne bangaren Intee babu abinda ya shafeta ita kanta kawai ta sani,
tayi wanka tayi kwalliya yau tana wannN qasa gobe tana waccen shikenan abinda ta saka a gaba babu
zancen wasu haqqoqin aure ballantana har ta zauna tana kishinsa to Allah ya kyauta.

Harya shiga jirgi yana ci gaba da gwada Layin Ma'u yanzu ko yana shiga dagawa ne batayi, jikinsa yaji
yayi sanyi duk karsashin da ya taho dashi yayi qasa besan wace tarba ze samu a gurinta ba. Da
amincewarta aka daura auran nan ko kuwa itama shammatarta akayi irin yanda abun yazo masa?

To koma dai yaya ne aure ya dauru ba saki ba yaji duk abinda zatayi sedai tayi amma ko duniya zata taru
bega ubanda ze iya kashe auran nan ba.

Yana sauka a Lagos kai tsaye gidanta ya wuce dan daman Driver sa na Aiport yana jiransa. Tundaga qofar
gidan yana iya jiyo hayaniya daga ciki sedai baya gane abinda ake cewa, kwankwasawa ya shigayi amma
shiru ba'a bude ba se ya koma mota da sauri ya dakko wayarsa daya bari ya shiga kiran layinta cikin sa'a
Yanzu ta daga.

BASHIR

Farkawa yayi ya ganshi akan gadon Asibiti ga ledar qarin ruwa da aka saka masa harta qare Jini ya fara
tafiya, da sauri ya zareta dan shi kadai ne a dakin babu kowa, ya jura qafafunsa qasa da niyyar tashi yana
yunqurawa Kansa ya sara yayi saurin komawa kan gadon yana dafe kan da hannu biyu.

"Sannu ka tashi kenan?" Wata siririyar nurse data shiga dakin ta fada cikin harshen turanci tana
qarasawa kusa dashi, hannun sa ta kama ta duba taga ya cire ruwan seta mayar da hannunta kansa inda
ya dafe tana cewa

"Kan yana ciwo ne? Ka kwanta tukunna na dubaka be kamata ka tashi zaune ba daman se jikinka ya qara
daidaita".
Seda taje ta yaye labulen window haske ya ratso dakin abinda ya tabbatar masa da cewar safiya tayi
kenan kafin ta dawo ta hau auna Bp dinsa dasu pulse duk tana yi tana rubutawa bayan ta gama ta kalle
shi tace

"Har yanzu jininka be sauka ba Mr, ka kwanta bari baje na kira likita ina zuwa" ta juya zata fita. Dakyar ya
bude bakinsa da yake jin kamar muryarsa ma ta tafi gaba daya yace mata

"Ina so nayi sallah"

"Kayi haquri yanzu likita zezo" taja qofa tayi waje abinta.

Kwanciya yayi kansa yana bala'in sara masa zuciyarsa kanta wani bugu take fat fat kamar zata fasa
qirjinsa ta fito kai shi gaba daya ma dubiyar juya masa take, me yasa tunda ya rasa Ma'u ya rasa
kwanciyar hankali a rayuwar sa ne shi.

Yana nan kwance har Nurse suka dawo tare da likita, Dattijone ya manyanta nan da nan ya rufe Bashir
da fada dan sanda suka shigo ma gaba daya yayi zurfi a tunani Likitan nata yi masa magana sam be ji ba
seda ya taba shi kafin yayi firgigit ya farka.

"Da girmanka da komai kake abu kamar wani qaramin yaro, ta yaya kake tunanin zaka samu lafiya bayan
ana qoqarin ganin jininka ya sauka kuma kana qara saka kanka a tunani? Koma me yake damunka yanzu
ai ajiye shi zakayi ka ji da lafiyar ka amma kana neman ka kashe kanka a banza da tunane tunane haha
mutane ku ringa yiwa kanku fada mana".

Shidai Bashir yayi shiru har ya gama dube duben sa yacewa Nurse din ta kama shi ta kaishi qofar
bandakin da yace ze shiga. A cukule yace musu ze iya, haka ya daure da bin bango ya shiga dan duk
takun da yayi ji yake kamar ana kwada masa guduma a kai.

Seda yayi sallar Asubar da ta kufce masa dan lokacin kusan tara na safe kenan, yana zaune yana lazumi
rabi kuma tunanin Ma'u yake da yanda zebi ya gyara kwabarsa. Amirah ce ta fado masa a rai da jaririnta
yayi saurin shafa Addu'a ya miqe dakyar dan se yanzu ya tuna da batun suturar jaririn ma.
Da karfin hali da komai ya gama cike duk takaddu aka bashi gawar Babyn a Ambulance suka tafi gida dan
ya rigada ya kira Limamin masallacin da suke sallah na cikin Estate dinsu.

Yanzu da a gida yake cikin yan uwansa da komai anyi shi a tsanake amma yanzu bashi me yi masa dole ya
daure duk wani ciwo ya tafi yayi.

Se bayan da aka gama Jana'izar Babyn daya sakawa Muhammad Bashir kafin ya shiga gida dukda Asibiti
ya kamata ya koma dan shi kadai yasan abinda yakeji a jikinsa bayan ciwon kai yanzu harda zazzabi ne
yake neman kama shi.

Addah na zaune zuru a palour ya tura qofar ya shiga, da bala'in sauri ta tare shi tana cewa

"Yanzu Bashir daga fita tun jiya se yanzu zaka dawo ina Amirar? Tun jiya nake kiran wayoyinku a kashe
gaba daya hankali na ya tashi har su Nafi na kira na gaya musu da tace Naziru ma ze taho a jiyan amma
Babanku ya hana wai ai da babu Lafiya za'a sani

Na ganka kai kadai ina ita Amiran? Qila ma gantalinku kuka tafi kuka barni a gida kwal kamar mayya
bayan kasan baqin halin yayanka ba kulani suke ba".

Kujera ya samu ya zauna dan baze iya tsayuwa ba kafin yace mata

"Tana Asibiti"

"Na shiga uku meya sameta? Badai wata matsalar bace kuma?" addah ta fada tana dafe qirji, se yai jim
kafin yace mata

"Ki shirya, bari na watsa ruwa muje" ya daddafa ya qarasa dakinsa.

Da sauri Addah ta shige dakin da take ta dauko wayarta da mayafi ta dawo falo ta rafka tagumi jikinta
har tsuma yakeyi. Tana nan zaune ta jiyo horn daga waje, har zata leqa sega Bashir ya fito daga dakinsa
ita se sannan ma ta fahimci layi yake idan yana tafiya haka tabi bayansa suka fita bayan da yace ta kulle
gidan suka hau motar sa da ya saka Samuel ya dauko suka koma Asibitin.
Sun tarar da Amirah na zaune suna yar hira da matar da take dayaj gadon da yake dakin da take. Tana
ganin su ta takwarkwashe fuska ta saka kuka Addah tayi kanta da saurin gaske taba tambayar lafiya
musamman da bataga cikin Amiran ba se wara ido take gefe da gefe tana neman jinjiri.

Bashir kuwa yana ganin ta fara kukan ya juya ya fice, bashi da buqatar qarin damuwa a yanzu. Dakin da
aka kwantar dashi dazu ya koma, yana shiga suka ci karo da Likitan nan ya kuwa rufeshi da fada kamar ze
kai masa bugu akan ina ya tafi? Wama ya bashi izinin tashi daga gadon da har ze kama hanya ya tafi wani
guri.

Shidai haka ya koma ya kwanta, seda ya karya da Abincin Asibitin da sam babu dandano ko kadan kafin
aka masa Allurai harda me saka bacci nan da nan kuwa yayi awon gaba dashi.

Qarfe Biyar na yamma aka basu sallama daga shi har Amiran dan babu abinda yake damunta sedai ta
koma gida kuma ta cigaba da jego Allah ya bada rayayye a gaba.

Musa abokinsa daya biya duba shi bayan sun tashi daga aiki ne ya roqa daya kaishi gida saboda gujewa
surutuan Addah da suka hau motar sa Samuel ya kaisu gida

tun data samu labarin mutuwar Jaririn fa take kuka da hawaye yanda kasan itace ma Amiran, Gombe
kuwa babu lokon da labari be isa ba acewarta dukda an saki Ma'u baqin Asirin da tayiwa Amirah na karta
haihu a gidan be karye ba ai kuwa duk inda zata shiga se taje ta nemo makarinsa sedai baqin ciki ya
kashe ta amma Amirah seta haifi Yaya a gidan Bashir.

Suna shiga gidan ya wuce dakinsa, wayarsa da ya saka a Silent ya ciro daga Aljihunsa jin tanaVibrating. Ya
gane Lambar da ta kira dukda babu suna, Bala ne, da mamaki ya ringa kallon wayar rabon da suyi
magana tun waccen ranar kusan wata nawa yanzu, lokaci daya wani bacin rai ya taso masa na tunawa da
furucin Balan akan Ma'u se kawai ya ajiye wayar ya shiga cire rigar sa yana ayyana dalilin da ze sa Bala ya
kirashi a yanzu bayan abinda ya faru har yana tunanin ze sake hada wata hulda dashi ne?

Alwala ya shiga ya dauro dan an kira sallar Magriba, seda ya saka jallabiyya a jikinsa kafin ya dauki wayar
har ze zura a Aljihu yaga saqo akai daga lambar Balan, tsaki yaja ya fita daga dakin yana qoqarin goge
saqon dan idan ma haquri yake bashi yayi ta banza dan shi dashi dai har Abada, har ya iya kallon fuskarsa
yace idan da matar daya rabu da ita zata yarda daya aureta a matsayinsa na Amininsa ai wallahi in ba
muqullin Aljanna bane a hannun Bala baya sake kula shi ba shima sedai idan shi kadai yake rabawa
sannan.

Iqamar da yaji an tayar ta saka shi jefa wayar a Aljihu ba tareda ya goge saqon ba ya qara saurin
tafiyarsa, a masallacin suka hadu dasu Aliyu, kallo daya yayi masa ya sunkuyar da kai shima be tsawwalla
ba yana kallo suka fice daga masallacin dukda yana son magana da Aliyun, dole su chanza wani plan din
tunda wannan ya rushe dan baze fa zuba ido yana ji yana gani ya rasa Ma'u ba.

Seda yayi sallar Isha kafin ya kamo hanyar gida, kiran sa akayi daga gidan abincinda yayo musu order ya
daga ya qara yi musu kwantance yana kashewa saqon Bala daya bude dazu be kai ga gogewa ba ya
dawo kan wayar.

"Ina tayaka baqin cikin yin wuf da tsohuwar matarka da akayi, gaskiya Bashir ka cika mara sa'a tunda har
ka rasa mace Irin Asma'u"

Abinda aka rubuta a saqon kenan.

Wani tsaki yaja kamar ze tsinka harshensa ya goge saqon, ransa a bala'in ya shiga magana kamar wani
sabon kamu yana cewa

"Wallahi Bala gamo na da kai baze yi kyau ba, saboda bala'i bazaka fita daga sabga ta ba ko shikenan
Allah ya hadamu zaka maimaita abinda ka rubuta yanzu, nida Ma'u kuwa mutu ka raba sedai baqin ciki
ya kashe duk me yinsa"

Ko gani dakyau baya yi ya haye kan step din qofar gidan sam be lura da Anty dake tsaye kamar wadda
aka bawa aiki ba seda ta kira sunansa.

A dan firgice ya juya ya kalleta, fuskar ta a washe tana Murmushi me kama da dariya babu wannan
hararar da take masa duk sanda suka hadu kamar zata rufe shi da duka tace

"Ai daga ciki nake ai aka ce baka nan ka tafi masallaci shiyasa nace bari na jira a nan karka dawo banga
wucewarka ba".
Tsayuwarsa ya gyara ba tareda yayi magana ba yana jiran jin dame tazo kuma dan wannan murmushin
nata toh Allah yasa dai ya zama Alkahiri

"Se mukaji Abin Arziqi a bazata, koda yake be zama lallai ya iso maka ba tunda muma duk yanzu saqon
ya same mu kaga abin Allah daga zuwa tambayar auran Ma'u se kawai iyaye sukace a daura ayi duk wasu
shiri daga baya, To me za'a jira abu ba auran budurwa ba Allah na tuba an daura aure dai akan sadaki me
daraja bana tunanin ko auranta na fari ma tayi tsadar haka, kai gaskiya Ma'u tayi Goshi".

Yanda take maganar seka rantse da Allah wata qawarsu take bawa labari ko irin shaqiqin Ma'u da ze yi
matuqar farin ciki da jin labarin, ta gama tsaf ta juya tana cewa

"Bari naje nima nayi sallar, kaini farin ciki yau ban ma san inda zan nufa ba wallahi Allah kenan wani ya
qika da wuni wani da shekaru ze soka, gashi ta fito daga inda ba'a san darajarta ba ta shiga inda suke
mararin samunta sema kaga yanda akace yan uwansa nata murna wallahi".

"Hasbunallahu wani'imal wakeel, La'ilaha'iah anta subhanaka inni kuntu minazzalimin" Bashir ya fada
yana kaiwa qasa saboda yanda yaji qafafunsa sun gaza daukar sa gaba daya, kamar me ciwon Asthma
haka numfashinsa ya shiga sarqe wa, qoqari yake ya bude baki ya dakatar da ita amma ya kasa harta
bude gidan ta ta shige tana ci gaba da dariyarta.

"Ina tayaka baqin cikin Wuf da akayi da tsohuwar matar ka" saqon Bala ya dawo masa a qwaqwalwa.
Dagaske Ma'u ta daura aure da wani ko kuwa da Bala da Anty wasa suke so suyi masa da hankali amma
ai babu wanda yasan wani a cikin su ballantana su shirya yi masa yawo da tunani ai.

Hannunsa daya masa nauyi ya daga yana so ya zaro wayarsa amma ya kasa. To wama ze kira ya tabbatar
da gaskiya ko qaryar maganar a yanzu?

Amma ai yafi kusa da Ma'un, a gurinta ya kamata ya samu tabbaci na koma menene.

Cikin azama ya yunqura ya miqe kamar bashi ne ya fadi qasa yanzu ya gaza tashi ba se gashi a kan
qafafunsa cikin sassarfa ya isa qofar gidan Ma'u ya shiga bugawa kamar wanda yazo karbar Bashi.
Abdallah ne yazo ya bude masa, kafin yayi magana ya shige ciki ya fara kwada kiran Ma'u yana wulga ido
cikin gidan yaga ta inda zata bullo.

ASMA'U

Suman wucin gadi nayi a zaune har Anty ta fice ta barni bana tsammanin ko numfashi ina shaqa a
lokacin. Qarar wayata ce tasa na gane a raye nake amma sam bani da qarfin da zan dauketa dan kwayar
idona kadai na iya juyawa na kalli wayar na sake maida ita na zurawa qofa ina jiran naga wani yazo ya
tasheni daga baccin da nakeyi.

"Mami ga Abbi nan yazo, kizo ki ganshi kamar wani abun ne ya faru gaba daya a hargitse yake" Farida
data shigo da gudu ta fada amma na gaza buda baki nayi mata magana se ido kawai dana zuba mata ido
kamar wadda ta hadu da cutar mantau.

"Mami, Mami ki taso kinyi shiru ko kema baki da lafiya" ta fada bayan data maso kusa dani ta hau
girgizani, ajiyar zuciya me qarfi na sauke nace

"Bacci nake kika tashe ni ko Farida?"

"Bacci a zaune kuma, idonki ma a bude yake fa Mami" ta fada da mamaki tana kallona. Zan sake magana
kiran da Bashir yake kwalamun ya shiga kunnena kamar ma a qofar dakin yake seta miqe da sauri tana
cewa

"Dan Allah ki taso ki gani Mami gaba daya ba'a hayyacin sa yake ba bamu san meyake damun sa ba
daman jiya be kwana a gida ba se yanzu ya dawo" ta juya da sauri ta fice ina qoqarin tsayar da ita.

Yanda yake kwala kiran kamar wanda yake gayyar yaqin duniya na uku yasa na tattara dan qarfin daya
rage mun a jikina na miqe, ina kaiwa qofar na jiyo shi cikin qaraji yana cewa

"Zaku gaya mun ko kuwa, dagaske ne Ma'u ta daura aure da wani daban bani ba? Da gaskene wani
banza ze rabi gonar da take mallakina?"
Saurin bude qofar nayi na fita jin yanda ya qarasa maganar cikin tsawa dan ni kaina seda na razana, a
dari naja da baya na riqe qofa ganin yanda ya juyo ya kalleni da idanunsa da suka rine kamar zeyi aman
wuta gaba daya kamannin fuskarsa sun chanza zuwa wani daban da ban taba ganin sa a irin yanayin ba.

"Yawwa Ma'u ki gaya mun waccen matar qarya takeyi ba gaskiya ta fada ba, ki fada mub da bakinki babu
wani Namiji daya isa ya mallake ki a duniya bayan ni" ya fada yana nufo ni, da saurin gaske na koma
dakin na turo qofa dan Na tabbatar idan har ya riqe ni to qila ni kuma a haka nawa ajalin zezo, gaga
labarin daya sakani gajeran suma se Bashir ya qarasa aikin ya murqushe ni na mutu.

Yanda yake buga qofar dakin yana kiran na bude idan ya balla ta ya shigo bazan ji dadin abinda zeyi mun
ba. Na fito na gaya masa qaryane kawai shi abinda yake so yaji kenan to ni me zance masa bayan ni
kaina ban gama tantance sahihancin labarin baki nima a cikin rudanin nake kamar sa ai an gara shi ba
abinda ya shafe shi bane ni kuwa fa, taya ma za'a ce wai an daura mun aure daga zuwa tambaya sekace
wata yar tsana.

Wayata da aka kira na janyo da sauri ban ko tsaya duba waye ba dan neman wanda ze kawo mana dauki
daga buyagin Bashir kawai nake

"Hello Asmy inata buga qofa ba'a bude ba ko baku nan ne?" Aka fada da muryar da rudun da nake ciki
be barni na gane waye ba.

"Ka shigo a bude take dan Allah kayi sauri Bashir ze illata mu dani da yara" na fada ina tsalle kamar wata
yarinya tunda dau naji ance ana waje ai magana ta qare dauki yazo kawai.

YUSUF

Duka daya yayiwa qofar da qafa ta bude idan ma a kulle take oho shidai ya bude ya fada gidan cikin
azama jin abinda ta fada. Ido hudu sukayi da Bashir dake aikin biga qofar dakinta yayi biji biji kamar wani
sabon hauka ya waiwayo a fusace jin an shigo gidan karaf suka hada ido da Yusuf suka shiga muzurai
kamar wasu sababin zakaru.
"Me ya kawo ka gidan nan? Bana gaya maka ka fita daga harkarta ba karna sake ganika a kudada mata ta
shine ka dawo to kuwa yau senayi maganinka, idan ma dakai ake hada baki saboda a baqantamun rai
duk senayi maganin ku zan nuna muku Ma'u tawace ni kadai" Bashir ya fada a zabure yana nufar inda
Yusuf yake a tsaye ya harde hannaye a qirji seda yakai dab dashi ya tsaya yana huci kamar ze kai masa
duka.

Murmushi Yusuf yayi yana kallonsa yace

"Yaka tsaya? Ka qaraso mana kayi maganin nawa ko ko ba haka kace ba?"

Muzurai kawai Bashir yake yana sake kallon Majiya qarfin da suke tsaye a bakin qofar daga bayan Yusuf
jikinau kamar wadanda aka gina da Bulo ko karan hauka ya cije shi baze yarda fada ya hadashi da daya
daga cikin su bama balle harsu biyu yanda suka zubo masa ido jira kawai suke a basu umarni su far masa
yasan.

"Ya ka tsaya ne Malam Bashir kai nake jira fa" Yusuf ya sake fada, ganin Bashir na kallon bayansa yasa ya
waiwaya shima seya saki murmushi me kama da dariya yayi musu alamar daua fita, suka rusuna masa a
tare suka juya waje se ya maida kallonsa kan Bashir cikin qasa da murya yanda yaraj da suka zura musu
ido bazasujiyo abinda yake fada ba yace

"Ashe ma duk kurarin banza kakeyi yan wadannan qananun kwarin sun tsorata ka duk fiffiqar da kakeyi
ta tashi a banza. Bari kaji abu daya ze hana na wulaqanta ka saboda wadannan yaran, bana so mutunchi
na ya zube a gaban su dan bazasu taba girmamani ba idan har na wulaqanta ka a gabansu amma hakan
bashi yake nufin idan muka hadu a inda babu ido zan saka karnukana su yagalgala ka ba.

Karka dauki shirun da nake maka a baya a matsayin tsoro ko bazan iya mayar maka da martani bane Aa
saboda a lokacin daga ni har kai laluben allura muke a duhu ba'a san hannun da ze dauka ba, amma
yanzu da na tabbatar da Allura tazo hannuna ta zama halalina mallakina yanzu zan baka amsa daidai da
duk abubuwan daka fada a baya.

Kace ina shiga gidan matan aure zaka bata mun suna ka gayawa duniya ni manemin matan aure ne ko?
To bari kaji daga yanzu idan na sake jin labarin anga koda sahun tayar motar ka ne a qofar gidan nan
sena batar dakai"
Yanda ya fadi batarwar seda Bashir ya bude ido dakayu ya kalle shi, gani yayi ya juye masa kai bazakace
wannan mutumin me yawan murmushi da fara'a bane.

"Kwarai ni ba suna zan bata maka ba dan baka da sunan da zan bata ba kuma kashe ka zanyi ba amma
zan batar dakai, babu wanda ze sake ganinka gaba daya za'a shafe labarinka Bashir.

Babu kai babu MATATA, duk abinda ya shafi Yayanka nine wakili tsakanin ku idan bazaka iya tunkarata
kai tsaye ba ka nemi wani cikin yan uwanta ka ringa magan dashi amma banyarda ba koda wasa magana
ta sake hadaka da MATATA, ina da kishin abinda nake so na kuma san qima da darajar sa idan kana
musu ka gwadani Bashir indai shirya mayar da yayanka marayun qarfi da yaji matarka tayi takabar dole
Bashir ka sake Shigowa gidan nan ko ka tare MATATA a hanya"

A nutse yayi maganar amma tamkar saukar aradu haka Bashir ya ringa jinsu a tsakiyar kansa. Kalmar
MATATA da yake fada tafi komai juya masa kwakwalwa dagaske kenan Ma'u tayi aure kuma wannan
mutumin ta aura?

Qarar bude qofar dakin Ma'u da sukaji ta saka su waiwayawa gaba dayan su a tare kowa da abinda yake
ayyanawa a zuciyarsa.

ASMA'U

Sadaf sadaf na bude qofar dakina na fito yanda kasan barawo ya shigo sata tunda na dena jiyo hargagin
Bashir na tabbatar da mun samu an kawo mana dauki kenan.

Gaba daya suka waiwayo suna kallona cikin wata irin Azama Yusuf ta iso gabana ba zato se jina nayi gaba
daya a jikinsa ya rufe ni ruf seka rantse Farida ya rungume ko Amnah saboda yanda na zama wata yar
firit a jikinsa.

Wani irin shokin naji ya taho mun tun daga tsakiyar kaina ya dire kan qafafuna, ban farfado ba naji sautin
muryarsa tareda dumin numfashinsa da yake fitar da qamshin Na'ana'a daidai kunnena yana cewa
"Karki bari linzamin kishina ya kwace Asmy, meyasa zaki fito gaban wani namiji a haka ya kallo abinda
yake mallakina".

Innalillahi, yanda kasan wadda wuta taja haka naji jikina ya dauki rawa nan da nan na shiga qoqarin
janyewa daga jikinsa amma yaqi bani damar hakan sema qara qarfin ruqon da yayi mun yayi ta hanyar
dora hannayensa biyu ya sake damqe quguna ya dora habarsa akan gashin kaina da se a sannan na lura
ashe daga ni se wata doguwar rigar shifom me hannun Bes na fito kaina ko arziqin dankwali be samu ba.

"Yusuf ka bari meye haka dan Allah? Yara fa suna kallonka" na fada a rikice jikina yana rawa jin yanda
yake qara danqe quguna yana qoqarin daidaita fuskarmu.

"Wadanne yaran? Tun kafin ki fito suka shige daki, ai kinyi qoqari sosai Asmy gurin basu tarbiyyar barin
guri idan manya suna magana" ya qarasa tareda hade bakinmu guri daya ba tareda ya bani damar cewa
komai ba, sumbatata yakeyi seka rantse da Allah babu wani abu daya iya a duniya sama da wannan ni
kuwa ina tsaye kamar Bishiya yar shekara Dari bidirinsa kawai yake cikin wani irin sauqi yanda kasan
dagani se shi muka rage a cikin duniya".

Qarar fashewar abu ta saka shi sakina dakyar yana mayar da numfashi muka daga kai a tare muka kalli
inda Bashir yake tsaye, yawun dake barazanar sarqeni na hadiye ina raba ido kamar an jijjiga bera a jarka
se na bude baki taread dora hannu akai ganin yanda hannun Bashir yake digar da jini gefe guda kuma
mudubin Console dina ne a rugurguje da alama shi ya nausa da hannunsa.

"Kash ya zaka huce akan mudubi beji ba be gani ba, wai daman kana tsaye baka yarda da abinda na fada
maka ba kenan? Ka tabbata wannan shine karo na qarshe da zaka sake ganin abinda yake haramiyarka
ka kuma fita idan ba haka ba inada tsageru daidai da kai biyu kawai ka gani anan idan kuma kana musu
ka jira minti biyar tayi yawa sena saka sun zagaye gidan ka.

Wani irin kallon da na gagara fassarawa Bashir ya bimu dashi dagani har Yusuf din kafin ya tsayar da
idonsa akaina se kuma ya juya cikin rangaji ya fice daga gidan har sannan hannunsa yana zubar da Jini.

Ya bata mun farin cikina, gaba daya ya rusamun tsarin dana zo dashi na tarbar Amaryata" Yusuf ya fada
yana kallona har sannan hannayensa na saqale da quguna wani irin abu nake yana shiga jikina duk yanda
naso na bude baki nayi masa magana kona fizge jikina na kasa yanda kasan wadda ya saka waya ya
daddaure haka nake jina.

BASHIR

WATA KISHIYAR

(ALKAHIRI CE KO SHARRI)

Na Maryamah Farouk

(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)

Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 63

BASHIR

Ikon Allah ne ya shigar dashi gidan sa, yana shiga falon ya zube a qasa kamar qaramin yaro hawaye suka
fara masa sintiri a fuska, be damu da ciwon hannunsa da har sannan jini na diqa ba ya ringa buga kansa
yana cewa

“Na rasata Na rasata, na rasa farin cikina”.


Addah data fito daga Kitchen hannunta dauke da Flask data damawa Amirah kunu tayi saurin ajiye shi ta
nufi Bashir cikin tashin hankali tace

“Waka rasa Bashir? Nafi ce ta mutu ko Amadu?” Addah ta fada tana tafa hannaye. Amirah da fitowarta
kenan daga wanka ta jiyo maganar su itama se gata, da sauri ta qarasa kusa dashi ta tsugunna,

“Yaya Jini hannunka, dame kaji ciwo?” Ta fada tana qoqarin kama hannun. Seya riqo kafadunta yana
cewa

“Na rasa Ma’una dagaske Ma’u ta auri wani ta zama matar wani daban bani ba rayuwata tazo qarshe” ya
qarasa yana sakin wani kuka me tafe da sheshsheqa.

A tare Amirah da Addah suka saki wani dogon tsaki Addah na dire nata ta dora da cewa

“Amma Bashir ka isa asararrare, yanzu dan ubanka saboda mace kazo zaka saka zuciya ta ta buga na zata
yar uwata ce ta mutu ashe kai tsabar lalacewa akan matar daka saka kake Kuka? To kaida Allah faduwar
gaban da ka sakani ban yafe ba kuma nayi matuqar farin ciki da wannan al’amari Mun yada kwallon
magwaro mun huta da quda.

Yo in banda ma lalacewa da kana sonta ka saketa ko kuwa wani sabon salon dinar Albarka ne da zaka zo
kana mana dirama a nan? Wai da uwar mema ka yanke hannunka ko dambe kaje kukayi da Sabon Mijin
ya yanke ka haka? Se ka tashi kasan nayi kafin jinin ka kuma ya tsiyaye ka shiga uku Aikin banza kawai” ta
juya ta dauki Flask din kununta tayi dakin Amirah tana ce mata

“Dallah taso ki saka kaya duk ya wani gigita mutane da danyan jego kin fito kai a bude ke ai wannan abin
ki hada walima ne ma wallahi yanzu ai se hankalin sa ya dawo kanki tunda mayyar tayi aure”.

A sanyaye Amirah ta miqe itama tabi bayan Addah tana waigensa. har ga Allah tayi bala’in jin dadin
labarin ko banza yanzu dole duk wani tunanin dawo da Ma’u da yake ya janye gida ya tabbata nata ita
kadai taci karanta babu babbaka.
Har suka rufo qofa Bashir na kallonsu kalaman Addah kuwa ji yai kamar ya shaqota ya huce duk haushin
sa a kanta. Hannu yasa ya share hawayen fuskarsa kafin ya yunqura be sani ba ya dafa hannun daya
yanke da sauri ya daga saboda zagin dayaji har tsakiyar kansa ya riqe hannun yana dubawa.

Sosai Mudubin ya yanke shi dan gashi nan naman gurin ya fito,

“Abbi ka tashi muje clinic a duba maka hannun kaga fa jini yana ci gaba da zuba” Aliyu daya shiga
gidanya fada yana kallon Bashir.

“Me yasa bakagaya munba Aliyu? Me yasa baka sanar dani da wuri ba na dakatar da ita yanzu ya kake so
nayi? Shikenan na rasa Ma’u, Mamin ku fa ta auri wani bazata sake dawowa gidannan ba”.

Kasa hada ido dashi Aliyu yayi, kamar shim hawayen yake kansa a qasa yace

“Abbi nima ban sani ba. Ita kanta Mamin nasan bata sani ba seda Anty taje ta gaya mata daka tsaya
kunyi magana zata fada maka”

“Qaryane ta sani ita ta shirya komai saboda ta qarasa kassaramun zuciyata, daman ai jiya a gaban ka ta
fada masa yaje ya tura a daura musu aure Ranar Juma’a shine daga baya ta sake canzawa meyasa?
Meyasa Ma’u zatayi mun haka? Nace na gane kuskurena kuma a shirye nake dana chanza me yasa ita
bata yafiya?” Ya qarasa maganar a tsawace.

Duk yanda Aliyu yayi dashi akan ya tashi suje Clinic din Estate din qi yayi qarshe se gidan wani Babatunde
Aliyun yaje ya kirashi, Nurse ne matarsa ce suke aiki tareda Bashir shi ya taho da Kayan aiki yazo har
gidan ya gyara masa ciwon da har dinki seda akayi a wajen.

Aliyun ne ya dumama masa abincin da aka kawo tun dazu wanda yayi order yaci yasha magungunan sa
ya kwanta, yana zaune a dakin gaba daya sunyi shiru kowa da irin tunanin da yake a ransa lokaci lokaci
Bashir yana sakin nishi saboda azabar fili data zuciya da yake ji.

Hoton Ma’u da Yusuf ya tsaya masa daram a zuciya yanda ya riqeta yake mata abinda shi kadai yake da
wannan damar ada yanzu gashi da ransa be mutu ba ta auri wani, harta sakar masa kanta yana yanda
yaga dama da ita.
“Aliyu kaje ka kwanta dare yayi” ya fada yana tashi zaune bayan daya dafe qirjinsa da yake suya, Aliyu da
har ya fara gyangyadi yayi fitgigit yace

“Abbi bakayi bacci ba? Na zata a magungunan akwai me saka bacci ai ya kamata ka huta saboda yanayin
jikinka”.

Murmushi me ciwo Bashir yayi yana kallonsa yace

“Daga randa na rabu da Ma’u bansake samun nutsatstseb bacci ba Aliyu a lokacin da nake da yaqinin
zata dawo cikin rayuwata ma kenan taya kake tunanin yanzu dana tabbatar da na rasata zan sake
runtsawa ai nida kwanciyar hankali munyi bankwana Aliyu, na rasa Ma’u na rasa farin cikina. Ta tafi da
dukkan wata walwala da jin dadi na”.

“Abbi haquri zakayi mu dauka haka Allah ya qaddaro a tsakanin ku dan na tabbatar da Mami tana sonka
amma babu wanda ze iya ja da ikon Allah. Gara kai kana da wata matar da kake so daman mu kuwa fa ita
kadai ce Mamin mu yanzu shikenan bamu da maraba da Marayu haka zamuyi rayuwa ba tareda
Mahaifiyarmu tana tare da mu” Aliyun ya fada qasan ransa yanajin wani irin zafi da tsanar Amirah.

Ya rigada ya saka ma ransa ita ce silar faruwar komai a gidan su. Ita ta wargaza musu farin ciki ta raba
iyayensu kuma yayi alqawarin badai itama taji dadi a cikin gidan su ba. Yanda zasu qare rayuwa cikin
quncin rashin uwa tabbas itama haka zatayita cikin uqubar da zasu ringa gana mata a ruwan sanyi setayi
dana sanin shiga hurumin da banata ba.

“Laifi nane Aliyu ni na biyewa rudin shedan da zafin zuciya na aikata duk abinda ya faru, a zamana da
Ma’u bata taba cutar dani tana sane ba. Tayi haquri dani da duk wasu halayya ta amma a qarshe ni na
kasa yi mata uzuri akan bijirewa son raina gashi yanzu ni zan qare rayuwata a cikin dana sanin rabuwa da
ita, kaico na dana zama me son kai a rayuwa, kaico na dana zama me rama Alkahiri da sharri.

Ina fatan abinda ya sameni ya zama izina a kanka da sauran qannenka, kada ku kuskura ku dauki
soyayyar Mace a matsayin rauni ko gazawa kar kuma hakan ya zama abinda zaku riqe wurin juya
rayuwarta yanda kuka ga dama. Tabbas duk wanda be godewa ni’imar ubangiji ba toh ze godewa Azabar
sa” ya fada kamar ze fashe da kuka. Se Aliyun ya kama hannunsa yana cewa
“Abbi haka Allah yaso kuma in sha Allahu ze zama Alkahiri. Kayi bacci bari naje na duba su Jafar naga ko
sun shigo se na kulle qofa na dawo” ya saki hannun Uban ya miqe

“Kaima ka kwanta ka huta Aliyu gobe kuna da makaranta fa”

“Na sani a nan zan kwana saboda ko zaka buqaci wani abun cikin dare” Aliyun ya bashi amsa kafin ya
qarasa fita daga dakin.

Lumahw idonsa yayi yanajin wani qarin yayyafin qaunar Yaron yana shiga zuciyarsa. Ko iya wannan abin
da Ma’u tayi masa na kula da tarbiyyar yayansa ta cusawa musu halaye da dabi’u na kwarai ta cancanci
duk wata girmamawar duniya daga gare shi, ko kaffara baze ba idan shine a matsayin Aliyu wadannan
abubuwan suka ringa faruwa akan idonsa baya tunanin wani abu bayan gaisuwa ze sake shiga
tsakaninaa da Mahaifinsa shima saboda sauke haqqine kawai.

Daren ranar be iya runtsawa ba, Nadama yake yi mara amfani dan se a yanzu yake gano tarin qatuwar
wautar daya ringa tafkawa a rayuwarsa. Ya yarda da gaske ya kasance mutum meson kansa, a koda
yaushe buqatarsa ce a gaba be taba duba wani ba idan har ze samu abinda yake so babu ruwansa ko
wani yaji dadi ko karya ji muddin buqatarsa ta biya shikenan.

Se a yanzuyake tuno tarin sadaukarwa da tarin soyayyar da Ma’u ta shimfida masa, Mace ce da ta yarda
tayi Kuka idan harshi zeyi dariya, ta yarda ta rasa shi ya samu bashi kadai ba duk wani wanda ya shafe shi
a duniya Ma’u tana rawar jiki gurin kyautata musu.

Ze iya rantsewa cewar hidimar da take da iyayensa da yan uwansa shi da suka haifa baya yi musu
kwatanta. Saboda duk abinda zeyi kafin a buqata ita tayi musu da kudin ta da jikinta hidimta musu
takeyi.

A lokacin baya idan Ahajin su yana ce masa ya riqe Ma’u da kyau matar rufin asiri ce da samun irinta a
zamanin nan yana da wahala gani yake kawai dai saboda makauniyar soyayyar da Baban yake mata ce
tasa baya ganin laifinta shi kuwa gani yake kawai tana amfani da abin duniya da take dashi ne ta siye
kowa ta yanda babu me ganin laifinta kowa sonta yake yi.
Idan ya zauna ya nutsu tsaf a zaman su ze iya rubuta sau nawa ta taba kawo masa wata buqata tata na
wani abin buqata a matsayinsa na mijinta komai yi take tayi masa tayiwa Yayanta ba kuma ta taba qorafi
ko nuna gazawa ba duk a lokutab baya gani yake rainin arziqi ne ya saka take masa haka tana ganin ta
fishi wadata dan haka bata taba bashi ma damar da ze tabuka wani abu ba a matsayinsa na Namiji,
kodaga baya daya samu Chanjin rayuwa bata sauya zani ba.

Taci gaba dayi se iya abinda ya ga kamatuwar ya dakko ya bata ne ze bata ba kuma ta taba qorafi akai
kota raina ba ganin cewar yanzu yana da halin yi a maimakon ya gode mata ya jinjina mata se ya sake
qullatarta da ganin tabbas ta rigada ta raina shi, duk tarin Arziqin daze samu tana ci gaba da kallonsa a
wannan faqirin data aura ta ringa hidima dashi.

Ya kasa ganin haka a matsayin soyayar da take masa ce tasa take tausayinsa ba kuma ta qyashin hidimta
masa ta kowacce siga. Bayan duk wannan sadaukarwar daya tashi ya saka mata da Kishiya irin wacce shi
da kansa daga baya seda ya ringa jin kunyar abinda ya aikata mata wanda duk yana cikin irin ingiza me
kantun da Bala ya ringa masa a rayuwa.

Shiya fara tunkara da batun abinda ya faraji dangane da Amirah ya kuma nemi shawarar sa akan abinda
zeyi dan ya hango tarin rashin da cewa a cikin abinda zuciyarsa take niyyar yi amma Bala ya nuna masa
cewar ai ba haramun bane. Kuma daya aurowa Ma’u wadda bata san halinta ba ai gara Amirah da take
rainonta tasan bazata cutar da ita ba.

Be zurfafa tunani ba dukda wani bangare na zuciyarsa babu yanda beyi ba na hanashi amma ya dage,
sanda ya sanarwa da Dada maganar yana ta taraddadin ya zata karbi Al’amarin ganin irin so da qaunar
da take tsakanin ta da Ma’un, a lokacin kullum bata da magana seta ya riqe yarinyar nan da kyau
yarinyar kirki kullum yaje gidan nan da sabon abun da zata nuna masa tace Ma’u ta kawo Albarka kuwa
baya zaton ko su data haifa tana saka musu ita lodi lodi irin yanda take mata amma daya kai mata
zancen Amirah se gashi tashi daya ta amince.

Hartana gaya masa sun dade suna son qulla wannan zumunchin dan da Amiru taso su hada su amma
halinsu da banbanci zaman bazeyi dadi ba. Shi kuwa daman shine uban riqonta duk wani hali nata tun
yarinta daga shi har Ma’un sun sani dan haka babu komai Allah ya tabbatar musu da Alkahiri.

Yasan ya tafka kuskure na boyewa Ma’u zancen auransa da Amirah da yayi amma ta ina ze fara? Bashi da
wannan kwaringuiwar da ze tunkareta yace mata zeyi aure kuma Amirah ze aura.
Ya rubuta Text message yafi sau dari amma ya kasa tura mata, daga baya a takadda ya ringa rubutawa
yana ajiye mata amma baya qara ko taku biyu daga gurin yake canza shawara ya dauke dan besan a
yanda zata karbi Al’amarin ba.

Sanda au Dada suka kawo Amirah gidan shi kansa yaga rashin dacewar hakan se kuma daya nuna musu
kuskuren aikata hakan amma suka qeqashe qasa suka ce ya fita a sabgar babu ruwansa dalilin daya saka
shi yanke shawarar biya mata umarah kenan ita da yara suka tafi danharga Allah seda abin yazo dab
sannan ya qara ganin kuskurensa.

Babu kuma yanda beyi ba akan afasa amma Su Addah suka ce ata fau babu wannan zance, karshe ma
daya matsa seda Dada tayi masa barazanar tsine masa idan ya kuskura ma zancen yaje kunnen
mahaifinsa na cewar ya fasa haka ta kuma yiwa su Naziru barazanar da karsu gayawa Ma’u dan daman a
wani kalar munafunci suka qulla zancen auran ta yanda hatta da mutanen gari an bagarar dasu kowa se
a bazata abin yazo masa bayan da aka daura se gashi tun ba’aje da nisa ba yake karbar sakamakon sa da
hannun haqu.

Kyale kyalen daya rude shi ya aurota ashe duk buge ne, matar da yake zaune da ita shekaru Goma sha ta
fita ta kowacce siga, shi baze iya cewa ma yau ga wata tsiya daya tsinta acikin auransa da Amirah ba
banda tashin hankula da damuwa da take jefashi aciki kala kala qarshe tayi masa me dungurungun,
sukayi amfani da halinsa na daukar zuga da zuciyarsa me cike da izza suka raba shi da matarsa da ta so
shi tsakani da Allah tun bashi da abinda ze saka a so shin.

Gashi yanzu yanaji yana gani tayi masa nisan da har Abada se dai Idan wata da wata gagarumar qaddarar
a gaba ko rabo me tsananida ze sake dawo masa da Ma’u cikin rayuwarsa amma ya tabbata ko
haukacewa Yusuf yayi baze sako masa Ma’u ba.

Kai shi shaidane tun a wancan zamanin cikin samarin da sukayi takarar neman auran Ma’u dasu babu
wanda yake tsananinsonta saboda Allah kamar Yusuf, a gabansa ta kore shi wanda yake da yaqinin shine
haduwar su ta qarshe a wancan lokaci ya kuma tafi bayan yace mata

“Idan har rabuwata dake zesa kiyi Farin ciki Asmy wallahi bazaki sake ganin fuskata ba. Da ina da dama
ko me irin sunana dana hana kunnuwanki jinsa saboda kar hakan ya ringa tuno miki dani a rayuwarki
ranki ya baci, amma ki sani ina qaunarki saboda Allah kuma bazan cire tsammanin samun ki a rayuwata
ba se randa na farka na ganni a cikin kabari tukunna zan haqura dake”

Shiyasa tun daga lokacin kai ko me suna Yusuf yaji an ambata seya tuno shi yana matuqar baqin ciki da
kishi da irin qaunar Ma’u dayake gani a cikin idanun sa wanda a haduwar su ta farko bayan shekaru
goma sha bakwai ya sake ganin wannan tarin So da Qaunar tata a idon Yusuf, a yau daya sake haduwa
dashi kuwa ya tabbatar da ze iya aikata duk abinda ya fada akanta dan ba qarya yake ba yana Son
Asma’u, irin son da tayi masa yanzu gashi Allah ya bata wanda yake mata kwatankwacinsa itama.

Seda ya share hawayenda suka ziraro masa kafinya saka hannu ya janyo wayarsa tare da hotonsa da
Ma’u da yake kan durowar gefen gadonsa. Hoton ya fara zarewa daga jinin Katakon da yake ya zura
mata ido yanda tayi kyau tana wannan murmushin nata da yake nuna irin kyan zuciyar da take dashi se
yayi saurin yin a’uziyya tunowa da yanzu fa matar wani ce ba tasa ba.

Durowar ya jawo ya saka hoton tareda katakon, zuwa gobe da safe duk ze fito dasu ya bawa Aliyu dan
idan ya barsu tare dashi tabbas baze samu kwarin guiwar chanjinda yake so ya kawo a rayuwarsa ba. Ze
cigaba da dakon sabon zunubi ne na kallo da kuma tunanin matar da bata sa ba a yanzu.

Hotonta da yake kan wayarsa ya sauke ya mayar dana yaran da suka dauka wannan qaramar sallar data
wuce gaba dayansu wani tausayin su yana ratsa shi musamman Yan biyun sa yanzu duk shine silar
komai, ya janyo musu zasuyi rayuwa ba tare da uwar su ba Alhalin tanada ranta ba mutuwa tayi ba.

Doleya jajirce ya inganta rayuwarsu baze bari suyi kukan rashin uwaba dan a yanzu shi kadai ne gatan da
zeyi musu, ya koyi darasi daga abinda ya same shi na rayuwar auran sa da Ma’u in sha Allahu kuma ze
dauki dangana ze kuma jajirce ya gyara rayuwarsa.

Duk abinda ya zama silar jefa shi a halin da yake ciki yanzu ze kiyaye shi hakan ya zamar masa izina ba
kuma ze sake bari ya maimaita kansa ba amma anya ze samu chanjin rayuwa da Mace irin Amirah??

“Kaima kana da taka gudummawar daka bayar gurin lalacewarta ta zama duk abinda ta zama a yanzun”
zuciyarsa ta raya masa kuma ya yarda da hakan sannan ya dauki turbar gyara ze yi iya qoqarinsa na ganin
ta dawo hanya su lallaba rayuwar su a haka tunda basu da yanda zasuyi da Junansu.
Washe gari kafin Aliyu su tafi makaranta seda ya tabbatar daya ajiyewa Bashir kayan karyawa da
magungunan sa akusa dan se da yayi sallar Asuba sannan bacci ya dauke shi dalilin sabon zazzabin daya
rufe shi.

Se gurin sha biyun rana ya fito daga dakinsa bayan yayi wanka ya shirya kuma Ahamdulillah ya samu
sauqin takurar da zuciyarsa take masa dan yanzu kam ya tabbatar daya rasa Ma’u, duk da baya son ko
tuna abun saboda wani daci dayake taso masa kansa yayi zafi har duhu yake gani yana gilma masa duk
sanda ya tuna a gabansa jiya wani ya rungumeta kuma yayi kissing nata.

Cikin sanyin Jiki ya fita falo ya zauna, gidan shiru babu Addah babu Amirah yanda kasan ma basu san a
halin daya shigo jiya gidan ba cikin su babu wadda ta sake leqowa bare taga yana da rai ne koya mutu.

Yana zaune akan kujera bayan ya kunna Tv ya kai tashar Sunna Tv akaci sa’a Malaminda yake wa’azi a
lokacin yana magana ne akan Aureda haqqoqin da suka rataya a kan Miji da Mata.

Nutsuwa yayi sosai yana saurara yana qaruwa da abinda ake fada a ciki. Kusan minti sha biyar da zaman
sa sega Amirah ta bude qofar dakinta ta fito.

Turus tayi da ganinsa, cikin wayancewa ta qarasa tana dan sosa kai idonta akan hannunsa da aka nade
da Bandeji ta shiga gaishe shi ya amsa mata ba tareda ya kalli inda take ba.

“Uhm daman yanzu nake cewa zan shiga na dubaka, wallahi jiya ina gama shiryawa bacci ne ya kwashe
ni shi yasa ban shigo ba” ta fada tana sunkuyar da kai.

“Babu komai ai, ya naki jikin?” Ya tambayeta yana dan kallonta. Cikin mamakinsa dan tayi zaton ze
balbaleta da fadane yanda ya saba tafe

“Lafiya lau ai babu abinda yake damuna yanzu”

“Masha Allah, Allah ya qara lafiya. Ina Addah bata tashi bane?” Ya sake tambayarta
Kafin ta bashi amsa Addah ta fito daga daki tana mita

“Ni wallahi na gaji da wannan rayuwa haba gida kamar gidan Haya dan jaraba abinda zaka ci ma seka
tashi ka dorawa kanka, naga ni dai zuwan da muka tabayi ba haka aka mana ba Alqur’an Asma’u kafin
mu tashi daga bacci yarinyar nana ta hada mana abin karyawa kala kala haka kan ya gama narkewa na
Rana ya sauka ga kayan dadi tuli, kai Allah dai ya jiqanta badan ta mutu ba yanzu gashi dan daka haifa ne
yake maka baqin ciki kar kaci me kyau shikenan ai nima kwadayina ya zaunar dani”.

Daga Bashir har Amirah babu wanda ya kulata, ta samu guri kusa dashi ta zauna tana cewa

“Au Bashir ya jikin naka? To Allah qara kiyayewa halan Sabon Mijin nata garjejen qato ne kaje ya hada
maka jini da majina? Kaima maganin ka kenan ai da naci mace tayi auranta seka qyaleta ai, ni da zaka ji
ta tawa ma da ka hada mata yayanta ka bata kasan riqon dan yanzu se uwarsa musamman wadannan
marasa mutunchin gara dai can suje su qarata da uwarsu”.

Seda yayi qoqarin gaske ya hadiye bacin ransa kafin cikin dakakkiyar Murya yace mata

“Daga yau gaba daya yaran zasu dawo nan gidan dan haka dole a canza tsarin komai da akeyi kamar girki
da sauran abubuwa. Sannan zuwa qarshen satin nan seki shirya komawa Gombe tunda komai ya
daidaita”.

“Bangane na koma Gombe ba? Munyi dakai daman idan nazo zan koma ne?” Ta fada tana zate masa ido.
Se ya dago ya kalleta dakyau yace

“Ban gane ba, da kinzo gaba daya kenan bazaki koma ba ne?”

“Yo ga amsa nan ka bawa kanka in koma Gombe nayi me? Uwar wa n ajiye a can ko kuwa so kake naje
ayita nunani tsofai tsofai dani ana zawarci nake to ba inda zani, kuma koma ba haka ba daga haihuwar
tata kwana biyu zaka ce mun na tafi uban waye ze gyaramun yar? salon ta lalace ka sako mun ita na
shiga uku to ba inda zani zama daram me naquda ta samu kayifa”.

Shiru ya mata ya ci gaba da istigfarin da yake a zuciyarsa yana kallon Program din da ake a Tv, ta ringa
Tijararta wai dan yar uwarka ne yake maka haka, ita dai bata san me tayi wa Nafi data saka yayanta suka
raina ta ba idan ba haka ba ko arziqin surukuta ai ya isa ya ringa daga mata qafa idan Nafi ce ze koreta
daga gidan sane.
Shidai kamar meyi da dutse har tayi ta gaji tafi ki mutu be ce mata ba dan kanta tayi shiru, se kuma ya
dawo zancen tana so ya saka akaita kasuwa akwai abubuwan da zata siyo na amfanin Jegon Amirah.
Ganin bazata barshi yayi jinyar zuciyarsa ba yasa ya tashi ya bar mata falon ya koma Daki, babu bata
lokaci yayi musu Booking din jirgi su uku shi, Addah da Amirah ranar Juma’a zasu tafi Gombe idan yaso
taje cab tayi jegon idan ta gama ta dawo.

ASMA’U

“Yusuf ka bari dan Allah” na fuzgo kalamandakyar ganin dagaske so yake se munyi abin kunya a gaban
yara. Saki na yayi ya zauna akan kujera yana qaremun kallo yanda jikina yake rawa kamar wata wadda
aka kama tana mugun abu seya saki murmushi me sauti ya miqo mun hannunsa na dama alamar na taho
na maqale kafada kamar wata qaramar yarinya ina sakar masa harar da se yanzu na samu ido na ya tuna
yanda akeyi ta.

“Ni kike harara ko ki bari na taso sena cinye idonki idan yaso naga da abinda zaki sake hararta ya fada”
yana yunqurowa kamar ze tashi ai kuwa na kwas nayi dakina da gudu na rufo qofa seda na jingina kafin
takaicin kaina ya kamani, meye haka nakeyi? Ni da ya kamata na fututtuke na nuna masa bacin raina
akan me ze saka a daura mun aure ba tarefayarda ta ba shine duk zanbi na wani rude daga ya dantaba ni
sekace wata kwaila aikin banza kai.

“Asmy ki bude ina muyi magana” na jiyo yana fada bayan daya kwankwasa qofar a hankali.

“Bazan bude ba ka kuma fitar mun daga gida kaima malam” na fada a tsiwace.

A zatona ze fara roqar na bude qofar ko wani abu se ji nayi yace

“Shikenan toh se anjima” ya fada ba tareda wata damuwa ba kafin nayi wani yunquri najiyo qarar bude
qofa da rufewa, se nayi saurin matsawa jikin window na daga labule ai kuwa na hango shi ya shige mota
Driver yaja sun qara gaba.

Wani qululun baqin ciki yazo ya tsaya mun a wuya, farawa da Bismillah saboda an bashi aurena a
wulaqance shine ze fara wulaqanta ki ya nuna mun cewar su Maza duk halin su daya na wani ne kawai
ya fito fili. Idan kina kasuwa kamar zasuyi miki sujjada tsabar tarairaya daga inda kika zo hannu ke da
bola banbancin ku kadan ne, se kawai na nemi gefen gado na zauna na fashe da kuka.

Ba laifinsa bane laifin yan uwana ne su suka ja mun da suka nuna masa neman kai suke dani. Wayata ce
ta dauki qara na janyota da sauri ganin Yusuf ne yake kira

“Bada amincewata aka dauramun aure da kai ba kuma ni dana ce ka tura ma wasa nake maka saboda
kawai na bawa Bashir haushi ne amma shine kaje ka saka aka daura mana aure ko to ni bana so babu
kuma wanda zeyi mun dole dan haka ina jiran ka ka dawo ka sawwaqe mun” na fada cikin kuka bayan
dana daga wayar.

Shiru yayi na kusan minti biyu dan na zata ma ya kashe wayar kafin naji ya fara magana cikin sauti irin
can qasan nan yace

“Nima ban san haka zata faru ba dana dakatar dasu saboda bazan aure ki ba tareda ke da kanki kin yarda
ba, sannan ko a yanzu bazan matsa miki ba Asmy, daga nan har zuwa shekara daya kina da dama idan
har kika ga bazaki iya zama dani ba zan haqura na sallameki saboda ni ba maye bane da zan auri mace
dole bata sona bayan ga masu sona nan birjik a gari suna neman na aure su.

Sannan kuma ina tabbatar miki tunda kika koreni bazaki sake ganina a gidan ki ba idan har ba ke kika
gayyatoni da kanki ba. Daga qarshe abinda na kira na gaya miki shine yanzu da da ba daya bane kina
amsa sunan MATAR YUSUF ne, ban yarda da fita barkatai ba tareda dalili ba, ki tabbatar duk Namijin
dana samu labari kin tsaya kuna maganar da bata aiki dashi ba ko wanene kome kuka hada dashi indai
ba jini ba sena dauki mataki akai.

Duk abinda kike da buqata ki turamun da saqo ban yarda ko man mota ki siya da kudin ki ba, idan na
samu jirgi zan juya Abuja yanzu idan ban samu ba kuma se gobe da safe” yana gama fada qit ya kashe
wayarsa.

Sororo nabi wayar da kallo, Yusuf dai dayake bina yana lallaba ni kamar kwai yau shine yake mun
magana cikin isa da bada umarni haka? Ni Asma’u yake cewa baze sake zuwa inda nake ba sena neme
shi to na neme shi yayi mun me? Ta yaya ma yake zaton ni zan kai har tsahon shekara da auransa akaina
wannan ma zance kawai yake yi ze kuwa san dani yake dan da kansa ba se kowa ya aiko shi ba ze aiko
mun da sallamata.

Tunawa da banyi sallar Isha ba yasa na tashi na shiga na dauro Alwala, har na saka hijabi Bashir da jinin
dana gani yana zuba a hannunsa ya fado mun se nayi saurin bude qofar dakin na fito daidai sanda
Amnah take goge gurin Aliyu kuma ya tattare fasassun Gilasan ya zuba a abun shara.

“Kayi a hankali kar ka jiwa kanka ciwo” na fada ina kallonsa wani tausayinsa yana ratsani dan har ga
Allah duk ciki nafi tausaya masa, kamar shi kadai ne ya damu da halin da ake ciki daga kan Jafar zuwa
qasa hidimar su kawai suke karma shi Jafar din yaji labari sam na rasa ina wannna qulafucin uban da
yake dashi a da? Gaba daya yanzu sabgarsa yake kamar ma ya manta da cewar Bashir ne ya haife su.

Daki na koma na tayar da sallata, seda na idar da shafa’i da wutri na dade sosai ina Addu’a kafin na shafa
na tashi ina jina wata iri wai fa a karo na biyu wasu igiyoyin auran sun sake hawa kaina na wani mutum
daban ba Bashir ba.

Ina kwance lamo akan gado na tunanina ya kasu gida da yawa, sabuwar rayuwar da nake shirin fuskanta,
yaya matsayin aurena da Yusuf yake in karbe shi ne ko kuwa nayi abinda zuciyata take ayyana mun na
tilasta masa har seya bani takadda ta amma wai a wanne dalili ma zanyi haka?

Zuwa yanzu idan nace bana son Yusuf har cikin raina nayi qarya dan daman tun Asali ba son sa ne banayi
ba, soyayyar da nake yiwa Bashir ce ta shafe ta kowa da har na gaza gane menene so in dai ba akan
abinda ya shafe shi ba.

Addu’a dai nayita nasa anyi mun duk akan neman zabin Allah yanzu wannan Al’amari ya kasan ce a haka
idan naja dashi ai ya zama butulci ne ga Allah na kuma ja da lamarinsa kenan tabbas baza tayi mun kyau
ba idan Allah ya barni da zabi na ina ma da tabbacin idan na kashe auran da ko kwana daya beyi da
dauruwa ba zan sake samun wanda ze so ni tsakani da Allah ne harya aure ni?

Wai meye ma laifin Yusuf ne? Koda yake tarihine yake maimaita kansa irin haukan son da nayiwa Bashir
ne ya ringa yankwana ni na nace ma liqe shine yanzu Yusuf yake gwada mun na samu dama nima zan
shuka tawa tsiyar amma fa banga alamar shi ze jure irin wulaqancin dani na shanye a tawa soyayyar ba,
koma dai yaya ne har yanzu ina a kan Batu ma neman zabin Allah, idan aure na da Yusuf Alkahiri ne Allah
ya zaunar damu ya dawwamar da farinciki a tsakanin mu har qarshen rayuwa.

Washe gari dole na shirya fita aiki saboda ina da presentation da zanyi yau na wani project, tareda yara
muka fita saboda Aliyu ya gaya mun Abbinsu yana kwance bashi da lafiya, na tausaya masa amma abin
mamaki banji irin wannan rudu da tashin hankalin da nake shigaa duk sanda wani abu ya samu Bashir
ba. Kai gaba daya yau ma ni a karon kaina naji chanji.

Wata kamala naji ta lullubeni, a gurin saka kaya ma yau seda na chanza shigata. Doguwar rigar Atamfa
na saka sakakkiya na yafa yalwataccen mayafi daidai da turarena wasu nayi amfani dasu daban irin
wanda se mun samu kusanci sosai da mutum sannan zeji qamshin su sabanin kwanakin baya da nake
fesa kwalliya ta daukar magana idan zan fita aiki.

Seda na sauke su a makaranta wani tunani ya fado mun, koba komai Yusuf matsayin miji yake a gurina
yanzu, Allah babu ruwansa da ina sonsa ko bana sonsa matsayi da hukuncin sa daya ne akaina. Wayata
na janyo na tura masa da saqon cewar na fita aiki sannan na biya na sauke yara a makaranta.

“Se bayan da kika fita sannan zaki sanar mun babu komai na yafe miki, kiyi aiki kadan karki wahalar mun
da kanki. Yanzu nima zan wuce jiya ban samu jirgi ba, Love you” ya dawo mun da amsa.

Murmushi nayi dan a yanda muka rabu jiya na zata ko ze amsa ni zanga fushi a cikin maganar sa, fatan
sauka lafiya na masa na tura se kawai na kashe wayar gaba daya dan bana so wani ya kirani akan
maganar auran nan, tun jiya da mukayi magana da Alawa ban sake daga wayar kowa ba dukda se kirana
suke nasan wulaqanci ne zasu mun ba wani abu ba dan Khadija harda tura mun saqo wai naqi Allah yaso
da baqin ciki se ya mutu ku jifa dan Allah.

Sanda na shiga office dina seda mamaki ya kusan kashe ni ganin yanda akayi wa gurin kwalliya da ballons
kamar wanda za’ayi wani qaramin party. Akan teburina naga kati me azabar kyau an rubuta

‘Happy married Life Mrs Asma’u Yusuf Wunti’ da mamaki na kalli sakatariyata data shigo tana dariya
kafin nayi magana ta rigani da cewa
“MD dakansa ya saka akayi tun jiya da baki shigo ba, shi ya kawo mana labarin kinyi aure mutane se
mamaki suke yi wai dama baki da aure mudai bamu cewa kowa komai ba. Gaskiya na taya ki murna
Madam kowa kika aura yana sonki dagaske wallahi Allah ya baku zaman lafiya”.

Kasa ce mata komai nayi dan bakina ya mutu da mamaki haka na karbi System dina data gama gyaramun
aikin da zan gabatar muka fita. Duk inda muka wuce taya ni murna ake har abin ya ringa bani kunya
yanzu da girma na haka kawai aka zo aka shelanta nayi wani aure koma wane me shegen surutun ne
oho.

Dab da zan tashi MD ya aiko kirana, da taraddadin dalilin kiran na tafi, bakinsa har kunne yake tayani
murna sannan yake tambayata na rubuta takardar daukar hutu dukda naci sati biyu a cikin hutuna na
wannan shekarar wai sun bani hutun wata biyu duk sanda na shirya sena fara.

Nidai haka na fito na baro shi a raina ina cewa hutum me zan dauka se kace wani auren fari dan Allah ji
yanda suke ta wani digimi.

Bayan sallar magriba ina zaune sega kiran Yusuf, kamar bazan daga ba se kuma na dauka a taqaice muka
gaisa ya tambayeni yara da aiki nace lafiya se ji nayi yana mun sallama wai se da safe kawai nabi waya
sororo da kallo na ma rasa abin cewa.

Mutumin nan fa dagaske yake, ai kuwa mu zuba mu gani waye ze gaji da wasan.

Washe gari Alhamis da daddare ina zaune a falo badan ina gane abinda suke kallo ba se don kawai na
ragewa kaina rayuwar quncin data aure ni tunda dai me afkuwa ta afku.

Aliyu ne ya shigo gidan da sallama dan tunda suka taso makaranta yana gida gurin Babansa da a bakinsu
naji sunce jikinsa yayi sauqi sosai ba kamar kwana biyun ba, zama yayi kusa dani ya gaishe ni se yake
gaya mun wai Abbin su yace ya tambayeni zasu zauna a gidan na sati daya ze tafi Gombe, wani iri naji,
dagaske har Bashir ya sare da wurwuri haka koda yake me nake so to yayi? Ci gaba da kulani zeyi ya take
dokar Allah ga wannan Yusuf din shima da ba gama sanin zuciyar sa mukayi ba ban sanme ze iya aikata
wa ba dan haka nace masa ya gaya masa babu matsala Allah ya kaisu lafiya.

Bluetooth ya ciro daga aljihunsa ya saka a kunne yayi yan danne dannensa a waya can se ji nayi yace
“Mami, Abbi yace in roqa masa ke ki yafe masa, Uncle Yusuf yayi muku iyaka badan haka ba da kansa ze
zo ya baki haquri ya nemi yafiyarki” Aliyu ya qarasa a hankali, ba tareda na kalle shi ba nace

“Ka gayawa Abbin ku na yafe masa ni daman be yi mun komai ba duk abinda ya faru qaddara ce da
bamu isa mu kauce mata ba”.

“Mami yace na gaya miki wallahi yana sonki, kuka be taba yi miki wani abu saboda ya wulaqanta ki ko
kuma dan baya sonki ba, rashin sanin yanda ze bayyana abinda yake zuciyarsa ne yasa ya ringayin duk
abubuwan da suka faru” Aliyun ya sake fada kansa a qasa ba tareda ya kalleni ba.

sena kama hannunsa ina murmushin qarfin hali nace

“Nagode, kace ina masa fatan Alkahiri ina kuma yi masa Addu’ar Allah ya bashi wadda ta fini”.

“Amin, seda safe bari naje na hada masa kayan da ze tafi dasu toh saboda hannunsa” ya fada yana
miqewa. Kamar nace masa ina matarsa da bazata hada masa kayan ba amma se naga ina ruwana ma.
Alhamdulillah, ko babu komai yanzu rabin hankali na ya kwanta, Bashir ya dawo cikin nutsuwarsa, Aliyu
ya dangana ya dauki girman da yake akan sa nasan in Allah ya yarda ko bana tare dasu Yarana bazasu
shiga damuwar da nake hasashe ba.

BAYAN WATA UKU

WATA KISHIYAR

(ALKAHIRI CE KO SHARRI)
Na Maryamah Farouk

(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)

Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 64

BAYAN WATA UKU

“Wallahi nagaji, ka gayamun kawai SH idan so kake na mutu kawai ka huta amma wannan jan ran ya isa”
na fada dakyar saboda yanda nake jina kamar wadda take yawo a gajimare.

“Ki mutu fa kika ce ni kuma in zauna dawa?” Ya fada da saurin sa,

“Ka zauna da baqin halin ka irin na yan Bauchi mana ai naga alamar abinda kake jira kenan safiya tayi ace
maka Asma’u ta mutu”

Wata muguwar dariya ya sheqe da ita dukda nasan shi kansa qarfin hali kawai yake dakiyar zuciya ce
kawai irin ta yan maza amma nasan ya fini a zabtuwa da kewa yace

“Da wuri haka haba Asmy karki bawa mata kunya mana, wata uku fa kacal kike cewa kin gaji dame kika
gaji toh?” Ya yi tambayar cikin sigar zolaya yana dage mun gira daya.

Baki na zumbura gaba kamar yarinya na kwabe fuska ina harar screen din wayar nace
“Wallahi nasan Asiri kawai kayi mun amma ta yaya yaushe ma ni na fara sonka haka da har nake jin
kamar zan zauce saboda ban ganka ba”

Wannan karon ina kallonsa tsabar dariya seda ya fado daga kan kujerar da yake zaune wayar ta kife a
qasa, iya quluwa na qulu banyi aune ba sejin hawaye kawai nayi suna diga daga idona dan wallahi kamar
wadda aka kunnawa wuta a zuciya haka nakeyin wani irin so da kewar Yusuf suna qonani. Idan za’a saka
mun bindiga bazance ga sanda hakan ya fara ba abu daya kawai dana sani A cikin watanni ukun nan
Yusuf yayi nasarar yin rugu rugu daduk wani qashi da tsoka da suke a cikin jikina.

“Haba mana Asmy kuka kuma ki bari dan Allah bana so” ya fada a rikice kamar ze fito daga cikin wayar.
Sena qarawa kukan shagwabar tawa qaimi ina cewa

“To ba kaine ba saboda kaga na damu dakai shine na zama abin tsokanar ka kake mun dariya, ai Allah
yana kallonka wallahi kuma nima duk ranar muka hadu sena rama duk irin abinda kayi mun”.

“Me zaki rama bayan duk wanda kikayi mun Asmy, wata na uku ba da zama ango amma nida qaton
gwauro bamu da maraba saboda tsabar mugunta fa korata kikayi kika ce karba sake zuwa inda kike ya
kike so nayi? Ina son ki da yawan da zan iya miki duk abinda kike so koda ace ni bazan ji dadi ba indai ke
zakiyi farin ciki burina ya cika” ya fada cikin sanyi da taushin muryar da ya yaqi duk wani burnishin taurin
kai daya rage mun”

“Nace kayi haquri lokacin ina cikin jin haushin an mun auran dole ne kamar wata wadda ba’a so daga
zuwa tambaya kawai aka daura mun aure” na fada cikin shagwaba yanda kasan wata Sweet sixteen,
koda yake idan ina tareda Yusuf, yanda yake shagwabani yana riritani jina nake kamar jaririyar da aka
haifa yanzu baje kolina nake ina barje shagwaba yanda raina yake so.

“Ni daman baki mun laifi ba, kuma haryanzu kece baki so dana zo inda kike ba tunda baki bani dama ba”

“Ni wallahi naqi jinin wannan halin ayiwa mutum abu yace ba’a masa ba amma kuma yabi ta qarqashin
qasa yayiya gallazawa mutane, indai da gaske banyi maka laifi ba ko ka haqura kusan wata yara kenan fa
ina baka haqurin nan amma kaqi kazo kullum kuma kace kai banyi maka komai ba” na fada cikin
shashsheqa kamar wadda take kukan gaske.
Seda ya dauke wuta na dan lokacin, yana yin kallon da yakeyi mun kansa ya canza kafin qasa qasa yace
mun

“Ki bari karki jawo mun kuma ki rasa yanda zakiyi dani, kuma yaushe kikayi wata goma kina bani haquri
banda qarya fa Asmy”

“Mugu aini ka iya saka ni a ukun ka barni da jiyi akan gado ai” na ayyana a zuciyata a fili kuwa nace

“Toh ai ni duk wata daya ba tareda kai ba a matsayin wata uku yake, kasan kuwa yanda nake rayuwa a
nan? Ikon Allah ne kawai yake riqe dani amma qila da tuni an dade dayinsadakar arba’in dina”

“Asmyyyyy” yaja sunan seda tsigar jikina gaba daya suka miqe kafin yaci gaba da cewa

“Asmy baki so ki ganni ba, kawai fada kike amma ba dagaske kike ba”

Haka kawai naji hawayen gaske suna neman balle mun wai wannan mutumin me yake so nayi masa da
ze tabbatar da ina son sa ina son ganinsa? Tun fa waccen ranar daya tafi be sake dawowa ba. Sedai ya
kirani a waya yayita zalintata yana kassaramun zuciya sannan yanzu yace mun wani wai fada kawai nake
bana son na ganshi bayan badan kar nayi abin kunya ba da tuni ni na bishi duk inda yake.

“Kinga, daga nan ina ga China kawai zan wuce akwai kayan da nayi order zasu taso zan je na dubasu
tunda idan na dawo Nigeria ma bani da abinda zanyi, kai Allah ka bani me sona na qara aure kawai na
huta da wannan shakulatun bangaron da ake mun ta ko ina” ya fada yana wani shan kunu kamar gaske.

A harzuqe nace “daga can ka wuce bangon duniya ma kawai karka dawo dan ma kaga ana sonka an
damu dakai shine zaka ringa yiwa mutane haka, ka tafi din kaida Allah tunda dai kasan ina da haqqi akan
ka kuma se naga dama zan yafe”.

Dage kafadu biyu yayi yace


“Toh ai gara na tafi sabgar neman kudina da in zauna ana garani kamar kwallo, kuma da kike maganar
haqqi Asmy kefa kika koreni kikace karna sake zuwar miki gida, to tunda bani na siya miki ba kinga dole
na kama mutunchi na ai ko”

“Yusuf dan girman Allah kayi haquri wallahi kuskuren harshe ne nayi a lokacin ba abinda nake nufi ba
kenan” na fada ina fashewa da kuka, seda yayi qoqari gurin danne dariyar sa kafin yace

“Na haqura, dan Allah ki dena kuka ke se ana maganr wasa kawai ki ringa kuka ki dena mana”

“Toh ni ya kake so nayi? Na baka haquri kaceka haqura amma banga Alama ba. Wallahi dagaske Yusuf
INA SONKA, I love you more than anything you could imagine in this world ya kake so nayi da zan
tabbatar maka ina sonka?”

“Na yarda Asmy base kin rantse mun ba”

“To kazo” na fada kawai dan na rasa me kuma zan sake ce masa

“Ki tsammaci zuwana a koda yaushe Asmy tunda kin gayyace ni da kanki” ya fada cikin wani irin farin
dana kasa tantance dalilinsa.

“Kullum roqona kike kawai nayi haquri baki taba buda baki da kanki kince nazo ba, daman na gaya miki,
bazaki sake gani na ba sedai in har ke da kanki kika gayyato ni” ya sake fada.

“Yanzu daman tuntuni kawai abinda kake jira na fada kenan? Duk magiyar dana ringa maka ba abinda
nake nufi ba kenan?” Na fada

“Baki fito kince Yusuf kazo ba, amma Yanzu da kika fada zaki ganni, kuma duk ranar dana zo ranar zaki
tare ki tabbata Ango nake babu maganar daga qafa sena kwashe gara yanda....”

“Kai dai baka da kunya wallahi” nayi saurin katse shi jin yana neman ya saki layi kuma.
“Ai bazaki tabbatar da bani da kunya ba se rabda kika zo hannuna Asmy, kedai ki shirya mun ki kuma
nemi Tissue dozen dozen saboda wannan kukan sangarta da shagwabar da kike yi ina tabbatar miki
ranar zakiyi me dalili”.

“Seda safe, na fada ina rufe fuska ta da Pillow”

“Kiyi bacci cikin Amince Wife, I love you”

“Love you more” na fada tare da aika masa da Kiss me qara irin me tara tsigar jikin nan kafin nayi saurin
yanke wayar.

Ina kallo ya sake kira amma naqi dagawa daga qarshe ya rubuto saqon yana cewa

“Kinci Bashi Asmy ki shirya biyan sa”

Dariya nayi bayan dana karanta nayi juyi ina sake ruqunqume pillow da yake jikina. Idan aka ce mun a
rayuwata zan sake son wani Namiji bayan Bashir tabbas zance qaryane amma se gashi cikin dan taqin
lokaci komai ya canza.

Wata irin sanyayyar soyaya ya ringa gwada mun da ban ankare ba seda na kai tsakiya ruwa yasha kaina
kafin na fahimci na kusa nitsewa a cikin kogon sonsa. Zuwa yanzu nayi amanna da Yusuf shine cikon
rayuwata, duk wani mafarki da burina na gudanarda rayuwar aure me cike da farin ciki da walwala ina
hasko ta a tareda Yusuf fatana ya kasance har gidan auran mu, wannan qaunar dana ke gani a gurin sa ta
zamo ta gaskiya har qarshen rayuwar mu dan na tabbatar idan har na samu akasin haka daga gurin
Yusuf, a irin yanda ya rigada ya gama illata zuciyata tabbas bazan sake moruwa ba.

Washe gari ta kama Asabar babu aiki, tun sassafe nake aikin mulke mulken Dilka da kurkum da Anty ta
hadamun nakeyinsa sau uku a sati, cikin abinda befi wata daya da farawata ba ni da kaina idan ina zuba
ruwa a jikina bana so na dena saboda yanda fatata take wani sulbi da sheqi kamar jikin tarwada.

Inagamawa nayi wanka na zura doguwar riga harda safa na tafi gidan Anty na dubata bata da lafiya.
Allah me yanda yaso bayan tsahon shekaru da suka kwashe suna neman haihuwa se gashi Allah ya kawo
musu dukka su su biyun a lokacin da basuyi tsammani ba daga ita har Abokiyar zamanta suka samu ciki
bayan da suka gwada wani maganin sanyi da ANTY ZEE MAMAN MUJAHID take siyarwa.

Tabbas na yaba da kyan maganin ni kaina saboda daga sanda na fara shansa Al’adar da nayi ta farko
nasha mamakin abubuwan daya wanko mun dan seda nayi zato ko har sannan akwai ragowar barin da
nayi da be gama fita ba tunda ba’ayi mun wankin ciki ba seda na kirata take gaya mun babu komai datti
ne kawai banyarda ba seda naje Asibiti suka sake tabbatar mun da mataccen jini ne ya fita babu wata
matsala.

Tabbas magani yayi ina kuma ina shawartar duk wata me matsalar sanyi ko abinda ya shafi Al’ada ta
gwada, masu matsalar haihuwa kuma ba’a barku a abaya ba, shi magani dace ne idan Allah ya amince se
a samu.(Ga masu buqata suna iya tuntubar Anty Zee Maman Mujahid akan 08162859027 Allah yasa a
dace).

Ina shiga ta fara dibana wai Amarya.

“Kinga yanda kike wani sheqi da walwali kuwa Ma’u, ki daga qafa haka dan Allah karki saka Bawan Allah
ya zauce fa idan ya ganki” dariya na sheqe da ita bayan da na zauna ina cewa

“Kai Anty kin fiya zolaya wallahi, ya jikin na ganki ma da sauqi ba kamar jiya ba”.

“Kinsan abin seda haka se kanayi kana dan qara wa abun gishiri bakiga yanda Yallabai duk yabi ya kidime
ba har tausayi yake dan bani wallahi amma gara ya gane ba’a samun Da da sauqi ai” ta fada tana
murmushi

“Kai Anty kema fa kin iya mugunta, karna manta ina wannan dakan na gama da wadancan duka” na fada
dan karna tuna abinda ya kaini.

“Kai Ma’u, kai Ma’u nidai babu ruwana wallahi karkije ki kashe musu Da ana zaune qalau tam”

“Anty gara ka kankaro mutunchi baka san ya matarsa take ba kinsan dai halin mazan nan namu” na fada
ina duba wayata da naji saqo ya shigo,
“Ki duba whatsapp dinki na tura miki saqo” na gani daga Yusuf.

“Banga laifinki ba qanwata gara ka kankarowa kanka mutunchi wadannan mazan zamanin masu ido a
tsakiyar kai. Jira nake kawai ku tsaida ranar tariya ai sannan ne zamu fara shiri na gaske, badai mace a
gaban ki ba wallahi sedai su biyo baya” hannu ta bani muka tafa ina cewa “se Anty na”.

Whatsapp na shiga ina bude chat dinsa naga wata yar banzar sticker daya turomun ni kunya ma ya bani
har seda na rufe ido na, Wani Pdf document na gani na bude, catalog ne na wani Kamfanin siyar da
kayan daki na qasar Turkey sena danna masa Audio call ya katse ya turo mun da cewar na masa chat.

“Wannan fa na menene?” Nayi tagging document din.

“Ki duba ki zaba, Four bedroom duplex ne da falo biyu, ragowan abubuwan dole se kinje kinga gurin, ki
tayani zabar Gadaje guda biyu nawa da Set din kujera, bana son Royal” ya maido mun da amsa. Sena
bude kayan na fara dubawa.

Ajiye wayar nayi a gefe dan ban gane abinda yake nufi ba, siya mun zeyi ko kuwa yana gaya mun irin
kayan da yake so a saka masa a gidan sa ne tunda naga yanzu saboda rashin kunya irin ta maza qiri qiri
suke fadar irin gadon da suke so ko siya musu.

Na dan jima muna hira da Anty kafin nayi mata sallama na tafi bayan ta bani Dakan da naje karba da
wata zuma data ce na ajiye amfaninta ba yanzu ba wai ita Scorpion. Ina fitowa daga gidan muka yi
kicibus da Bashir ya fito daga gidansa, Kallo daya yayi mun yayi qasa da kansa harga Allah seda naji wani
iri, murmushi na qirqiro harya gota ni nace masa

“Baban Ali barka da rana?”

“Barka dai Ma’u ya gida ya aiki?” Ya bani amsa kamar yana jira na gaishe shi. Se na amsa masa da lafiya
kafin naci gaba da tafiyata a jikina ina jin yanda ya bini da kallo har na shige gida na kullo qofa, Allah
kenan meyin yanda yaso a sanda yaso.

BASHIR
A cikin watanni ukun nan ya samu canji sosai a rayuwarsa dujda seda yayi da gakse gurin jinyar zuciyarsa
kafin komai ya daidaitar masa sakamakon Addu’a da irin nasiha da a kullum Ahajinsu yake kan yi masa
akan muhimmancin yarda da qaddara musamman irin tasa da shine silar komai.

Kusan duk wani abu na yaransa ya dawo hannunsa yanzu a gidan suke komai, tsakaninau da gidan Ma’u
sedai suje suyi wasan su dare yana yi Aliyu ze hado kansu su dawo.

Zaman sa da Amirah dai ba dadi babu wuya akace lahirar kare, bayan zaman wata daya da ya barta tayi a
Gombe ta dawo dole ya kafa mata sharuddan da in har tana son zaman lafiya dashi dole ta bi to anyi
dace ta dauka musamman saboda a Gomben ma da sukaje kwananta daya a gidan Dada babanta ya
samu labari yace ta tafi gidan su can tayi zaman jegon dan baze sake sakin wani abu daya shafi Yayan sa
a hannun Fattu ba.

Zaman da tayi da matan Baban nata sam ba me dadi bane dukda ita ta quntata kanta dan a gurinsu su
basu da wata matslaa sam. da fari ta farayi musu rashin kunyar da suka saba sanda Addah tana nan suka
taka mata birki se duk tabi ta tsangwami kanta bata sakewa da kowa haka duka tayi zaman ba dadi gashi
babu inda take zuwa babu kuma me zuwa gurinta, Anty Binta Amaryar Alhajinsu ce ta dauki ragamar
gyarata dayi mata wanka har na wata dayan kafin babu Arziqi ta tattara ta koma Lagos bayan dogayen
sharuddan da Bashir ya gindaya mata akan zamansu dan ko Addah da take gidan Anty Talatu ana ta
dibar tsiya bata san da komawarta ba se bayan ta tafi dan duk a shirinta tare zasu koma ai kuwa tasha
zagi ta kuma tabbatar mata tana tafe dan ma yanzu tana shirye shiryen yin auran kisan wuta ne kamar
yanda wani sabon Malami da Tatu ta kaita wajen sa ya gaya mata tayi kafin a gama aikin da zaa karkato
da hankalin Alhaji Murtala kanta ta koma dakinta.

Tasha matuqar wahala sosai da irin sabon salon zaman nasu dan yanzu duk wani abu da cikakkiyar matar
aure zatayi a gidan ta shi takeyi, girki sau ukun nan seta dora kuma ba irin na ganin dama da takeyi a da
ba, shiyake gaya mata abinda yake so ayi ko yaran daya fuskanci bata iya wasu abubuwan bama
makarantar koyon girki ya kaita, gyaran gida kuwa haka take wuni ta dauke wannan ta gyara wannan a
haka ma dan yaran sam ba masu bata guri bane.

Badan ma ta kasa sakin zuciyarta ta jasu a jiki ba da ko su sun isa su ringa taya ta aikin gidan idan suna
nan tunda duk abinda suka saba yiwa uwar su ne. Sauqin ta daya Bashir ya rage wannan fada da
hargagin da yake mata da tayi kuskure ada, dukda yanzu shiru shirun sa ya dada qaruwa ne ko da yaushe
ya zauna shi kadai zaka lura yayi zurfi a cikin tunanin amma ko laifi tayi masa cikin lumana yake fahimtar
da ita kuma babu laifi a yanzu yana kyautata mata daidai da yanda itama take kyautata masa shida Yaran
data fuskanci yanzu sune komai nasa dan yawan ci idan suka samu sabani to akan abinda ya shafi yara
ne.

ASMA’U

Sati daya tsakani Yusuf ya gaya sanar mun a ko wanne lokaci yana iya dawowa sannan kafin lokacin yana
so aje a duba gida dukda har sannan ban rigada na zabi kayan dayace shi ze siya ba, ina jira zanje Gombe
na zauna da yan uwana naji shawararsu akan na barshi ya siya din ko mu zamu siya da kanmu.

Daya matsamun akan zancen aje a ga gida Anty Ladi na kira na gaya mata suka hadu ita da Junaidiyya da
Anty Nasiban Yaya Abubakar se Zahra suka je ganin gidan. Na Bauchi kuma daga Gombe su Yah Fati suka
tafi suka hade da Hajia Alawa qirjin biki suka gano gidan.

Wayyo Allah ranar kam nasha surutu harna gode Allah na santin gidan da suka ringayi ga Videos da suka
dauko suka ringa turawa dangi.

A bakin su Anty Ladi nake jin gida daya zamu zauna tareda matarsa a Abujan dan na Bauchi kowa da
gidanta na sani amma a Abujan bangaren kowacce daban dan a cewarsu ma tazarar dake tsakani ta isa a
gina wani gidan a gurin filin wasanni ne ne da Garden harda swimming pool yayi a tsakiya se a bangaren
ko wacce mace yanada dakuna biyu da palour banda wani qaramin flat da yayi a farkon gidan inda ze
ringa sauke Jama’ar su yan siyasa se kuma Boys quarters a bayan gida.

Wannna zuwa ganin gida da akayi ya taso da guguwar zancen tariya kuma dan daman sunce duk ido
kawai suka saka mun, yanda kasan auran budurwa haka yan uwana suka hau shirye shirye, Yusuf ya kafe
akan zuba mun kaya a gidansa na Abuja kamar yanda ya rigada ya sakawa Intee haka kuwa akayi,
kamfani sukaje suka tsara yan uwana kuma suka shirya mun na Baushi dan kwandala ta bata shiga ciki
ba gudummawarsu suka hada data abokanan arziqi suka mun kaya na yar gata har kuka seda nayi da
naga Video gidan bansan da me zan saka musu da irin qaunar da suke nuna mun ba sedai Muyi Addu’ar
Allah yaci gaba da hada kanmu har mutuwa.
Dagaske dai Yusuf yaqi dawowa Nigeria har aka tsayar da ranar tariyata sati biyu masu zuwa ya kuma qi
bari muyi magana balle na tuntube shi naji makomar aiki na ko kuwa dai an zuba kaya ne kawai a Bauchi
da Abuja saboda idan zuwa ya kama mu.

Ranar Juma’ar daya rage saura sati daya tariyata kuma a ranar nake son daukar hutu tunda zamu tafi
Gombe gaba daya zuwa Lititin dan yara sunyi hutun Aliyu ne kawai zamu bari saboda ze rubuta Jamb.

Bayan dana karbi takardar hutuna da suka bani har wata uku aka sake qaramun da wata da ban san kota
mecece ba. Da wuri nayi sallama da abokanan aikina na kama hanyar gida dan ina so na tsaya na bada
wasu kaya a Tasha da za’ayi mun gaba dasu.

Se yamma na shiga gida, ina cin abinci muna waya da Yusuf, ni yanzu na haqura da tambayar sa yaushe
ze dawo ma tunda abin nasa ya zama wulaqanci, zancen hutun da aka bani daya mun dazu yasa takardar
da aka bani ta fado mun a rai. Farida nacewa ta dakko mun su a cikin jakata, ina budewa na zaro ido
ganin takarar transfer ce zuwa Headquarter mu ta Lagos harda qarin girma.

“Yusuf kai ne ko?” Na fada kamar zanyi kuka.

“Oh ni dai naga takaina me kuma nayi Asmy duk wani laifi ace nine, nine me?” Ya fada

“Transfer akayi mun zuwa Abuja nasan wallahi kaine bayan ba haka mukayi da kai ba kai kace zaka barni
na zauna a Lagos”

“Ni babu ruwana su sukace miki da saka hannuna a ciki? Qila sun duba miki ne inda mijinki yake amma ni
babu ruwana a ciki” ya fada yana yar dariya.

Duk se naji raina ya baci, yanzu kenan dagaske zan bar yarana na tafi wata rayuwa daban ba tare da su
ba? Me yasa tun farko yayi mun qarya yace ze barni na zauna tare dasu

“Kinyi shiru Asmy, dagaske nake miki bani na saka ba amma idan kina so se na je na nemi alfarma idan ze
yuwu su barki a inda kike, amma bakya ganin hakan da sukayi kamar yafi hankali na ze rabu da yawa ni
Ina Abuja Intee tana US ke kina Lagos bani da hutu kullum ku tausaya mun mana” ya fada kamar zeyi
kuka.

“Uhm, shikenan bari naci abinci mayi magana” na fada na kashe wayar.

Goggo na kira, tana dagawa na saka mata kuka ina cewa

“Goggo kin gani ya saka anyi mun Transfer zuwa Abuja bayan shi yamun alqawarin ze barni a Lagos
yanzu kuma yazo ya canza gaskiya ni bazan yarda ba ku kirashi kuyi masa magana”.

“Wallahi Wallahi Wallahi sau uku kenan Asma’u kika sake kirana akan wannan shirme da rashin hankalin
naki sena ci ubanki. Ke se an fara miki zaton kinyi hankali se ki sake kwanto wani sabon diban Albarkar
naki ko? Da dab ubanki idan yace ki zauna se ki zauna ke? Me zakiyi ashe baki cire Bashir daga ranki ba?
To Shikenan ki ci gaba dayi keda Allah kiyiwa kanki sanadin da zaki mutu a banza ki tafi wuta da auran
wani akan ki zuciyarki tana ga wani shashasha da be san darajar ki ba wawiya kawai” Goggo ta fada cikin
bacin rai

“Ni ba haka nake nufi ba ni babu ruwana da wani Bashir kawai saboda yarana nake so na zauna a nan
kum....”

“Se kinci kutumar ubaki dake da yaran Asma’u idan baki rufe mun baki ba, ai daman na fadawa Qarami
wannan lambon da kikayi mu saka ido na tabbatar indai Ke din dana sani ce sekin nuna halinki, to bari
kiji ni na kira Yusuf din na gaya masa yasa ki bar aikin gana daya ma amma yace Aa za dai ayi miki canjin
guri dukda kun rigada kunyi yarjejeniyar zaki zauna a inda kike.

Naga alamar so kike ki mayar dashi kamar dan da kika haifa se yanda kika ce za’ayi ko to ni bazan saka
ido ina kallonki kina iskancin da kika ga dama ba, ko ki tattara kibi mijinki ko ki bar aikin gaba daya kuma
na rantse da Allah babu dan da zaki dauka ki riqe, ita kanta Faridar dana ce an fasa ki hadasu da Amnah
zasu koma gurin qarami dan ubanki ki je kiyi zaman aure Idan kinga dama kiyi abinda ba haka ba zan
tabbatar miki da shirun da nake yi bawai dan ban iya bane ko kuma kunfi qarfina nima na iya maganin ko
wanne dan Banza” Goggo ta fada cikin matuqar fada da hargagin da ban taba jinta tana yi ba.

Bata barni ma na sake magana ba ta kashe wayarta, wannan abun ya sake dugunzuma mun hankali,
wayar Yusuf na sake kira yana dagawa na fara magana cikin kuka ina cewa
“Yusuf me yasa munyi Alqawari zaka saba sannan kaje ka hadani da mahaifiyata tun farko ai bani na
roqa ba kai da kanka kace zaka barni na zauna kusa da yarana se Yanzu dakaga na rigada nazo hannunka
zaka canza magana me yasa”

A dake ya fara magana yana cewa

“Kinaji Asmy bana son ki jawo abinda ze sa mu fara samun sabani tun daga yanzu. Koma me nace miki a
da yanzu Goggo ta tayar da wancan hukuncin tayi nata dan haka idan beyi miki ba kina iya zuwa ki gaya
mata ni kuma duk abinda tace dashi zanyi amfani. Ki duba na tura miki da saqo saboda hidimar biki idan
baze isa ba se ki gaya mun”

“Bana so me zanyi da kudinka kuma ni babu inda zanje in dai kana son auran mu sedai ka biyo ni Lagos
idan ba haka ba kowa ya kama gabansa” na bashi amsa

“Tunda ke kike aurena dole na biyo ki ai, kudi kuma ki zubar idan bakya so wannan ba matsala ta bace”
ya fada tareda jan tsaki ya kashe wayarsa.

Lallai ma wannan mutumin tun daga yanzu? Ashe daman duk kwantar da kan daya ringayi na qaryane se
yanzu ze fara fito mun da halinsa na ainihi kenan shikenan zamu gani.

A dole badan naso ba muka tafi Gombe ranar Lahadi, Nama na kadai ya rage su taru su cinye dan tuni
Goggo ta gama yayata musu na rasa yaushe ta koyi wannan halin ita kuma duk abinda nayi seta fada
musu bayan tasan daman qiris suke jira dani.

Har ranar Laraba babu abinda nayi daya shafi lalle ko kitso dukda da har walima muka shirya yi ranar
Alhamis tunda ran Juma’a za’a kaini can Bauchi amma da me Lallen ma tazo korar ta nayi ina ta baqin rai
gashi Gogan tun ran Juma’ar nan be sake kirana ba kuma ya dawo naji labarin a bakin Jafar.

Ina kwance a dakin Hajiya Babba Sumayya babbar Yar Alawiyya ta shigo tana cemun

“Mami wai kije kinyi baqo a waje”


“Wane baqo kuma kin sanshi?” Na tambayeta ina tashi zaune, se tace mun

“Eh Baba ne”

“Baba?” Na fada da sigar tambaya.

“Baba na gidansu Baba Naziru fa” ta bani amsa.

Ikon Allah, me Baba yazo yi gidan mu a daren nan kuma? Na tambayi kaina. Hijabi na na saka har qasa na
fito, a can falon baqi na tarar dasu, Baban, Bashir yasha uban baqin gilashi se Yusuf kowannen su ya
kama waya yana dannanwa Baba yana binsu da kallo.

Da sallama na shiga suka dago a tare suka zuba mun ido, ina kallon yanda Yusuf ya wani harare ni ban
daga ba kuwa nima na maka masa tawa se yayi murmushi ya sunkuyarda kai. Cikin girmamawa na gaida
Baba nayi shiru, se kuma kamar an mun dole na hadasu su biyun nace

“Ina wunin ku” babu wanda ya amsa mun a raina nace

“Maganina kenan ai”

“Asma’u se gashi mun hadu da Ango kuma muna zuwa muka tarar dashi shima daman kuma zuwan
nawa da niyyar ki kiramun shi a waya na roqi Alfarma se gashi kuma mun hadu” Baba ya fada cikin sakin
fuska yaci gaba da cewa

“Masha Allah, Allah ya sada ku da dukkan Alkahirin da yake tare da junanku ya tsare ku da dukkan sharri.
Ba tareda bata lokaci abinda ya kawo mu Bashir ne yace na rakoshi yana so ya sake baki haquri akan duk
abubuwan da suka faru a baya, sannan mu nemi alfarma akan takunkumin da Me gida ya saka masa
kodan Albarkacin yaya”

“Ni Baba babu abinda yayi mun ai kuma ko yayi na gaya masa ai na yafe masa tun tuni, in dan wannan
ne ma da be taso ka a daren nan ba ai” na fada kaina a qasa.

“Kina fada ne kawai Ma’u amma nasan nayi miki laifi kuma hankali na ne ya kasa kwanciya ina so naji da
kunnena kin furta kin yafe mun ko zan samu nutsuwar zuciya” Bashir ya fad yana zamowa daga kujera
kamar ze durqusa.
Seda na kalli Yusuf da fuskarsa ta gama bayyana kishin da yake cinsa kafin nace

“Na yafe maka Baban Ali Nima ka Yafe mun”

“Baki mun komai ba Ma’u” ya fada da sauri

“Shikenan Allah ya yafe mana gaba daya, sannan dan Allah ga amanar yarana nan, ka kula dasu kasan
bani da sama dasu a rayuwata” na fada kamar zanyi kuka, kafin yayi magana Yusuf yayi saurin cewa

“Baba wace Alfarma kace zaka tambaye ni”

Baba yayi murmushi yace

“Yaro saboda Bashir ya gaya mun ka yanke duk wata alaqa da take tsakaninsa da Asma’u koda gaisuwa
baka yarda da ita ba, shine nace zan roqi alfarmar Yaran lokaci zuwa lokaci zasu ringa zuwa gurin
mahaifiyarsu idan ka amince”

Seda ya shafa kansa kafin yace

“Ai wannan Baba daman dole ne, ni idan ma ze yarda ya bamu yaran se mu riqe babu komai ai Da na
kowa ne”

“Bazan iya ba, na dai yarda duk hutu zasu ringa zuwa gurinta” Bashir ya fada yana kallona.

“Wanan al’amari daya faru gaba dayan mu ya isa ya zamar mana izina mu kuma qara tsorata da lamarin
Allah, a duk sanda Allah ya azurtaka da samun abu kayi qoqari ka riqe shi dakyau saboda ba lallai idan ya
kufce maka ka sake mayar da irinsa ba. Ina miki fatan Alkahiri Asma’u tabbas nayi baqin ciki rasa
nagartacviyar suruka irinki a cikin ahalina, ina fatan kuma hakan baze sa ki yanke zumunchi dani ba
kodan Arziqin abinda Allah ya rigada ya hada” Baba ya fada

Se naji Hawaye na neman zubo mun da maganar da yayi ta idan Allah ya baka abu dukda nasan da Bashir
yake amma se naji kamar ni yakewa gugar zana akan matsayin da nake kai da Yusuf a yanzu. Dakyar na
bude baki nace
“In sha Allahu Baba ai kai ubana ne babu yanda za’ayi nace na yanke alaqa dakai, Nagode kwarai da irin
qaunar daka nuna mun na gode”.

“Allah yayi muku Albarka gaba daya, yaro kai dai ina tayaka murna Allah kuma ya baka ikon riqeta da
Amana Amin” yana gama fadar haka ya shiga qoqarin tura kekensa, se Bashir ya miqe ina kallonsa ya
dauke kwalla daga idonsa kafin ya mayar da baqin gilashin daya kwamo ya zura hannu a Aljihu ya zaro
wata Envelope ya ajiye a gaba yana cewa

“Ina miki fatan Alkahiri” ya tura Baban suka fice, miqewa nayi tsaye ban yi aune ba se ji nayi anyi sama
dani

“Ka sauke ni Yusuf”na fada a tsorace dan a bazata abin yazo mun

“Naqi na sauke ki se kin dena fushi dani” ya fada yana mun cakulkuli, duk yanda naso na daure na kasa
haka na shiga kyalkyaka dariya kamar wata sabon kamu na tabbatar su Bashir sun jiyo ni dan basuyi nisa
ba kuma darene ko ina yayi shiru.

“Wash Allah na matar nan fa nauyi ne dake” ya fada bayan daya direni akan qafafuna. Baki na tura gaba
ina harararsa ya miqo hannu kamar ze tsokane mun ido ina ja baya ya biyo ni muka fada kan kujerar
baya na ina qasa yana sama na se jinayi kawai ya kama Bakina ya shiga bani wani irin kiss me goge
hadda.

Dakyar na iya kwatar kaina na rarumi hijabina da tuni Yusuf yayi fatali dashi ban jira komai ba na ranta a
na kare dan naga alamar tabbas in na qara ko sakan daya za’a tafka abin kunya a gidan Jama’a.

Yusuf kuwa dafe kansa yayi ya bini da hargitsatstsuj idanunsa da suka canza kala har na fice daga dakij
kafin ya janyo robar ruwan da aka kawo musu ya balle daya ya kwankwade, beji dai dai ba ya sake
daukar wani ya shanye yayi cilli da robar har sannnan yana jin wani bala’in son kasancewa tareda Ita
yana taso masa.
Wayarsa ya zaro daga aljihu ya shiga kiran layinta yaji qarar wayar nan qasa kusada qafarsa se ya
dakkota, Envelope din da Bashirya bani ya gani a gurin ya hada ya dauka, seda ya samu ya daidaita
nutsuwarsa kafin ya kama hanya yana sunkuyar da kai dan karma ya hada ido da kowa Allah ya taimake
shi harya fice bega idon kunya ba bayan ya bawa daya daga cikin masu gadi wayar da envelop din yace
su kai mata.

Daren ranar da ciwon Mara na kwana saboda yanda Yusuf ya yamutsani ga kayan tsumin da nake amfani
dasu gaba daya suka rikitamun lissafi se gurin qarfe biyun dare na samu bacci ya dauke ni ina kallon yana
ta kirana bayan da aka kawo mun wayar amma naqi daga wa qarshe qarin wata damuwar ce gara koma
menene da safe ma hadu.

Washe gari tun Asuba natacciyar me Lallen da Alawiyya ta dakko tun daga Kano ta saka ni a gaba da naci
dole na zauna muka fara, ta zana mun hadadden Jan lallae na qasa da qasa dan bana son na Salatif, tana
gamawa kamar Aljana ta hau zana mun kitso, ko wahalar kitse doguwar Jelar gashina bataji ta kuma
debeshi yiri yiri ni kaina da nake gani a mudubi seda ya burgeni.

Kusan awa biyu lallen yayi ya kama sosai kafin aka cire se mita nake dan gaba daya duwawuna ya qage
da zaman shiyasa nafi gane ayi mun baqin lallae idan ma jan ne sedai da Sajam shi kuma se suce wai
saurin fita yake amma ai yafi saurin kamawa.

Seda muka gama kitson tsaf mukayi sallar Azahar ta doramun da baqar fulawa sega Ma’u ta fito kamar
wata fure, gyaran da fata ta ta samu da hutu ga Kitso da kalle suka sake fito da yarintata babu yanda
za’ayi a nuna maka zaratan Yayana ka yarda nina haife su, a qaryar me Lallen ma cewa tayi ta zata ban
taba aure ba, ta ringa rantsuwar qaryane da aka ce Jafar Dana ne wai dan ma bataga Aliyu da ya gama
zangamewa ba.

Kafin La’asar gidan mu ya dinke da Jama’ar da bansan sanda aka gayyato su ba, dagaske dai yinin biki
suka shirya harda masu kidan kwarya, haka nasha kwalliya da wani Arnen leshi cikin dinkunan da nayi
Aljanar me Lallen da komai ta iya tayi mun make up, muka sha shagali abinka da hidimar mata zallah
kowa tayi rawa ta gyagije an zubda galan galan masu kidan kwarya kuwa sun kwashi kudi dan ganin
dangin Yusuf mukayi daga sama qannensa da yayyensa mata, matan yan uwansa harda matar Gwamnan
Bauchi data Gombe suka hado kusan mota Goma suka zo.
Aka hadu aka yi harkar Arziqi da zasu tafi bansan daga inda Alawa ta ringa fito da kayayayki tana loda
musu musu a mota ba, harka dai akayi ta ta girma da Arziqi se godiya suke haka na rungume Alawiyya
dan ta fitar dani kunya ta kuma siyamun qima a idon dangin Miji, ni kuwa me zan saka wa wannan Yar
uba tawa me tsananin qaunata? Da ace ko wanne Yan uwa haka suke riqe zumunchi ba tareda saka
banbanci uwa a tsakani ba irin na gidan mu da duniya ta zauna lafiya.

WATA KISHIYAR

(ALKAHIRI CE KO SHARRI)

Na Maryamah Farouk

(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)

Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 65

Qarfe Hudun ranar Juma'a jerin gwanon motocin da suka dakko mu daga Gombe zuwa Bauchi suka tsaya
a qofar gidan Marigayi Malam Suleiman Wunti. Da Bismillah na fito daga mota ina qara gyara zaman
Lafayar da na nannade Jikina da ita.
"Yah ubangiji ka saka na shiga cikin su a sa'a, Allah ka wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a
gidan aure na. In sha Allahu yanda na saka qafata a cikin gidan aure na babu abinda zan aiwatar se
wanda ze saka Mijina farin ciki, na haqura na sallama komai a yabzu bani da kowa bani da komai a
Duniyata se Yusuf da yake mijina" na fada a zuciyata ina bin bayan Hajiya Aisha da take riqe da da
hannuna Qanwar Baffan Mace tilo a cikin su.

Ina jin yanda mata suka dauki guda ana sanar da na ciki ga Amarya ta iso a haka aka shigar dani inda
nake tunanin Dakin Hajiyar su ne. Falo danqam da Mata manya masu aji qamshi kala kala na tashi.

"Sannunku da zuwa maraba lale" wata me zaqin murya take fada har muka zauna a tsakiyar falon kan
wani lallausan Kilishi kaina nidai yana qasa ina ta maimaita Hasbunallahu a zuciyata.

Gaisuwa aka shigayi kamar yanda ake tsakanin dangin ko wacce Amarya dana Ango, aka gama bada
Amana, ina ji aka kwalawa wata Hauwa kira akan tazo takai Amarya dakin da zata huta kafin lokacin
budar kai, Budar kai fa sekace wata budurwa dan Allah. Nidai nabi su su biyu suka sakani a tsakiya har
muka shiga wani daki se qamshin turare yake.

"Nidai bari naga Fuskar Matar Yaya bazan iya jira se anje budar kai ba" Hauwan ta fada tana qoqarin
bude fuskata se dayar tayi saurin riqewa tana cewa

"Baki isa ba se kin biya"

"Ya haka ku meyasa bakwa girma ne se kun cire mata dankwali dallah ku matsa" wata data shigo dakin
ta fada taba matsowa kusa da mu sena dago kaina na kalle su ina murmushi a tare suka hada baki suka
ce

"Masha Allah wai zuqi, kai amma Yaya ya iya zabe" murmushi na sake yi musu ina kallon mutum biyun
da muka shigo tare dasu kamar su daya kana ganinsu kasan Yan biyu ne irin masu tsananin kama da Juna
ma.

"Sannunku" na fada ina kallonsu,

"Yawwa Amarya ke za'ayiwa sannu ai, karbi biyewa shirmen wadan nan yaran, kiyi sallah yanzu lokaci ya
rigada ya tafi kuma ba'aso akai magriba ba'a gama Budar kan ba" Babbar cikin su da a qallah zamu iyayin
sa'anni ta fada tana murmushi.
Ita ta nuna mun bandaki dan korar qannen nata tayi, na warware Laffayar jikina na shiga, ko ina qal na
kama ruwa na dauro alwala na fito a raina ina tunanin ina su Alawa sukayi, jakata tana hannunta kuma
zan dan buqaci Powder da lipstick.

Seda na idar da sallah ta sake dawowa dakin hannunta dauke da dan kit na kwalliya se Madarar kwali me
sanyi ta miqo mun tana cewa

"Kisha nasan be zama lallai hidima tabarki kinci abinci ba, ni sunana Nusaiba, ni nake bin Yaya Yusuf"

"Nagode Anty Nusaiba" na fada bayan dana karba dan tunda ita take bin Yusuf ta girme ni kenan jikin ne
irin namu da baya nuna tsufa.

"Aa fa karki jawo a janye mun tallafi yaji kina kirana Anty, barni dai ni nace miki Antyn, Idan kin gama ko
zaki gyara fuskarki ga kayan kwalliya nan" ta fada tana dariya.

Nima dariyar nayi nace "Tam Shikenan, dan Allah akwai wata da zakiga kusan kamar mu daya ko zaki
kiramun ita?"

"Ai duk wanda kuka zo kamarku daya kawai dai kin fisu kyau ne"

"Kai banda zolaya fa, toh kice Alawiyya tazo" na fada ina dariya

"Toh shikenan bari naje" ta fita bata dade ba sega Alawiyya da Zahra Aminiyata suka shigo.

"Kai amma kinyi sa'ar dangin Miji Ma'u, suna da kirki kinga yanda ake ta nan nan damu kamar wasu
gwal? Allah dai yasa su dore a haka zakiji dadin su" Zahra ta fada tana zama akan gadon da nake.

"Gaskiya dai basu da matsala dukda haka dai saura ki sake musu yanda kikayi da wadancan matsiyatan
banzan baya baya, babu shishshigi babu wulaqanci" Alawiyya ta fada
Su suka tayani na qara gyara fuskata Zahra ta daura mun dankwali dan gwanace. Ina cikin qara turaruka
masu sanyin qamshin a jikina mukaji ana kwankwasa qofa, a zatona Nusaiba ce dan haka muka ce a
shigo se ganin Yusuf mukayi yaci wata shadda yar ubansu anyi masa irin rawanin nan na malamai harda
wani kwagiri ya riqe yana dogarawa.

Rige rigen neman mayafi aka shiga yi tsakanin Alawa da Zahra abin harya bani dariya ma. "Kuyi haquri
ban san kuna ciki ba" ya fada yana dauke kai, yanda kasan wani surukin su jiki na rawa suka fice suka
barmu Alawa harda waiwayo wa tana qiftamun ido na maka mata harara dan na gane me take nufi.

"Amaryar Yusuf" ya fada yana qarasowa inda nake tsaye ya kamo ni jikinsa se nayi saurin cewa

"Jirana ake dan Allah karka bata mun kwalliya"

"Jiran mu ake dai, kuma kwalliyar daman wa kikayi wa ita idan ma na bata ai tawa ce" ya fada yana
shinshina fuskata. Kai wannan jaraba da yawa take, buga qofar da akayi tareda turowa ta taimakamun
na zille daga hannunsa wata Mata fara yar gajeriya me jiki ta shigo tana cewa

"Yanzu Excellency ka iya tsallake matan da suke falo ka shigo nan gaskiya ban sanka da rashin kunya ba,
to kaje Hajiya tana kiran ka, Amarya taso muje kinji wannan Angon naki rawar kansa tafi qarfinsa".

"Allah ya taimaki Woman Leader" ya fada yana dariya, dukda haka seda yayi mun peack akan lips dina ko
kunyar Woman leader data juyar da fuska tana murmushi beji ba yayi waje.

Ita ta sake dawo dani falon dazu da duk mutanen ciki sun fita se yan biyun da alama jiran mu suke, haka
suka saka ni a tsakiya muka fita can wani qaton fili da yake daga gefen gidan an gyara gurin da kwalliya
irin ta Kamu ga rumfuna an saka da kujeru da tebura ta ko ina yanda kasan za'ayi wani hamshaqin biki
ne.

Seda suka kaini har kan wata kujera da aka tanada saboda Ni, kaina na qasa seda na zauna naji mutum
ya jani a firgice na dago ashe Yusuf ne shi harya nemi guri ya zauna shi Budar kan tare za'ayi mana
kenan.
Seda aka bude taro da Addu'a, manyan mata suka ringa zuwa suna mana ruwan Naira da daloli Alawiyya
da Zahra na durawa a jaka yanda kasan basu san darajar kudi ba da wannan ta gama juye nata wata
hajjajun zata sake zuwa ta watsa nata seda aka kwashi kusan awa daya ana wasan kudi kafin MC ta kira
Qannen Ango akan suzo su bude fuskar Amarya.

"A dakata Yammata, Uwargida sarautar mata tace ita zata bude fuskar qanwarta" naji MC ta sake fada
danjar yan biyun nan sun taso suka koma. Ta qasan lafaya ta nake kallon qafafunta da take hardewa
tana irin tafiyar Models wato cat walk, straight gown ce a jikinta data kamata ta wani arnan leshi yanda
kasan zatayi nishi rigar ta bude dan ma bata da qiba se irin mayafin Chantilly dinnan ta dora a kafada
daya ta ruqo jaka a daya hannun tana taunar cingan.

"Oh waifa yanzu gidan wata nazo da ina nawa gidan a matsayin uwargida yanzu wannan figaggiyar za'a
kira da uwargida na Allah kenan.

Tana isowa ta bude jakarta ta fara yi mana ruwan yan dala dari dari seda ta zazzage mana rafa biyu dala
dubu biyu kenan MC kuwa se kirari take mata yanda kasan tayi tsalle ta kwashi kudin ita ko se wani
yatsina take yanda kasan an mata dole.

Da hannu daya taja Lafayar dana rufe fuskata na dago na kalleta ido cikin ido a raina ina karanta
'A'uzubikalimatillahi tammat minkulli shaudanin wa hammatin wa min kullu aynin lammati' ta kalle ni na
kalleta kafin ta wani tabe baki tace

"Kinyi kyau" da irin sautin da tayi magana nima na mayar mata nace

"Nagode" se jin Yusuf mukayi ya saki wata siririyar dariya muka kalleshi a tare ashe Video yake mana.

A tsakiyar mu ta zauna aka mana hoto se waniliqe masa take shi kuma yana faman rirriqeta na ja tsaki
qasa qasa yo mani ina ruwana, qarewar ta ya haduye ta mana su suka sani.

Haka aka ci gaba da gudanar da shagali nidai murmushi dole nakeyi dan idan na tuna yanda Intee ta
ringa wani kwanta masa ana hoto se naji raina ya bacihar seda Yusuf ya gane ya matsa hannuna da yake
cikin nasa yace
"Asmy kishi, ita bata ji haushin kin aure mata miji ba se kece kike kishi da ita" ya fada qasa qasa daidai
kunnena.

Harara na maka masa nace

"Saboda bata iya riqe mijin bane shiyasa har aka iya qwace mata shi din zata wani zo tana kwanta maka
a jiki se ta nunawa wanda be taba kwanciya a jikin ka ba"

"Wallai kuwa qarewarta ma yau a kan jikin zaki kwana ko?" Ya fada yana mun wannan shegiyar dariyar
tasa se nayi sauri sunkuyar da kai dan se yanzu na gane baranbaramar da nayi ya ringa tsunkulina kuwa
yana gaya mun maganganun da suka girmi kaina nidai haka na kanne dan kar muzo muna raba hali a
gaban Jama'a.

Seda mukayi sallar Isha a gidan su Yusuf kafin muka shiga motoci muka wuce gidana duk a zatona ma
anan cikin gidan nasu ne. Gida kam se dai ace Masha Allah dan fadar haduwar sa ma bata baki ne wai a
haka fadi suke sema kinga na Abuja ai nan a qauye kike Aljannar duniya na Abuja.

Seda akai dagasken gaske kafin Yusuf ya haqura yabar yan uwana su kwana a gidan dan har seda wata
Antyn sa Anty Mami ta kirashi a waya tayi masa tatas lokacin muna tsaye ya tsareni wai se naje nace su
tafi su koma can gidan Hajiya su kwana ko subi Alawiyya ai wasu da yawa sun tafi gidan ta me yasa
sauran zasu ce se sun kwana.

Haka ya kwashi fushinsa ya tafi harda ce mun kuma gurin Inter ze tafi ya kwana nace a tashi lafiya, to
idan ba fitina ba kawai se nacewa mutane su tafi wani guri bayan kuma duk wanda suka zauna din
yawanci yan uwan mu na Kumo dana Yola ne yan gidan mu wasu suna can gidan su Yusuf wasu sunbi
Alawiyya, su cewa sukayi ma badan dare ba da tuni sun jiya abin su su kuwa wadannan yanzu ince su tafi
ai an samu na yawo dani a dangi ko.

Washe gari kuwa kafin sha biyu kowa ya watse ya rage daga ni se halina a cikin gidan. gurin qarfe biyu
qannen Yusuf mata da maza suka zo suka kawo mun abinci zuwan nasu kuwa yamun dadi nan suka
zauna har gurin dab da magriba muna tare kafin suka tafi bayanda yammatan suka tayani muka gyara
gidan tsaf na basu kwanukan suka wuce dasu bayan na bisu da kudi nace su sha mai cikin cinikin da
mukayi jiya a gurin budar kai. Har sannan gogan fa ko a waya be kirani ba dana kirama kin dauka yayi shi
ala dole yayi fushi. Seda akayi sallar Magriba

A gurguje na sake wanka, Ina cikin yin sallah naji an bude Get, a jikina naji cewar Yusuf ne. Har na idar na
sake gyara jikina na daura dankwalin Atamfar dana saka dinkin straight gown tunda naga kayan da
matarsa take sawa kenan kuma yana so to nida nake da abinda zan nuna ai se na fita qure gayun ma.

Ina shirin fitowa daga dakin jin har sannan be shigo ya turo qofa muka kusa yin karo, hannu biyu ya bude
mun ban tsaya bata lokaci ba kuwa na fada jikinsa ya rungumeni yana sauke tagwayen ajiyar zuciya
kamar wanda ya kwana yana kuka, a kunnena yake rada mun

"Baki san yanda nake jin ki bane Asmy shiyasa kike jamun aji yanda kikaga dama amma ki tabbata yau
duk wani hukunci dana dade ina tarasu akan ki yau se na yi miki"

"To ni kuma yau me nayi maka bayan fa kashe munwaya kayi tun jiya baka neme ni ba" na fada a
shagwabe bayandaya sake ni yana kallon fuskata

"Kinyi kyau, juya na gani dan Allah na kine ko ciko kikayi?" Ya fada yana ja da baya yana bina da wani
kallo yanda kasan soko, hararar wasa na masa na shiga juyi a hankali ina cewa

"Shafa kaji" ai kuwa kafin na gama ya kawomun wata cafka na durqushe ina dariya ya bini cak ya dagani
be ajiye ni ko ina ba se kan Gado.

Kiran sallar Isha da akayi ne ya kwace ni daga hannunsa, tare muka dauro Alwala ya wuce Masallacin da
yake kusada gidan ni kuma nayi sallata a gida. Kafin ya dawo na fito na duba kayan daya shigo dasu, na
saka komai a inda ya dace Kazar kuma na sake dumamata a Microwave na hado duk abinda zamu
buqata na kawo falo ina zama ya shigo bakinsa dauke da sallama.

Kan kujerar dana ke zaune ya zauna bayan ya dagani ya mayar dani kan cinyarsa, yanda Yusuf yake
maidani yarinya qarama yana mun dadi,
"Yunwa nake ji" ya fada yana shafa fuskata, sena riqe tasa fuskar ina cewa

"Yi haquri yanzu zan kore maka ita kaji"

"Ba yunwar abinci kadai nake ji ba Asmy, harda taki" ya sake fada yana kashe mun ido daya. Sun kuyar
da kaina nayi qasa ina murmushi nace

"Duka gaba daya zan kore maka su, kai dai ka fara cin abincin yanzu sauran magana ba anan zamuyi ta
ba" ina gama fada na dire qasa kafin ma yace zemun wani abi.

Tare muka ci Kazar muka sha madara cikin farin ciki, ban cuci kaina ba dan nima Yunwar nake ji, abincin
dazu ba wani nutsuwa nayi naci ba saboda duk cikina a cunkushe yake seda na samu dazu na zagaya
sannan cikin ya daidaita dan haka na ci Naman sosai na daddaki madara dan nasan yau kam seta Allah.

A nutse Yusuf ya ja mu mukayi sallah raka'a biyu kamar yanda Annabi yayi mana unarni dayi, bayan da
muka idar ya dafa kaina yayi mana Addu'a bayan ya gama ya zauna sosai yana kallona yace

"A ina kika tsaya a karatun Addini?" Dago kaina nayi na kalleshi jin tambayar tazo mun a bazata, yo ko
aurena na fari daga sallar nan bamu qara komai ba aka wuce karatu na gaba.

"Kinyi shiru kina kallona" ya sake fada yana dab murmushi, cikin sanyin murya nace

"Nayi saukar Alqur'ani me girma kuma inada haddar Izu talatin na qasa, nayi karatun Fiqhu nayi na hadisi
na sauke littattafi da yawa kuma har yanzu ina kan neman Ilimi ban dena ba".

"Al-Qur'ani ya miqo mun na karba nayi bismillah na fara karanto fajin da ya bude mun, ina karanta Aya
uku ya karba ya sake bude wani tsagin ya bani na karanta masa se ya karba ya ajiye yayi Bismillah cikin
sautin karatunsa me dadi ya janyo mun wani tsagi daga qasa na dora daga inda ya tsaya.

Sosai ya ringa yi mun tambayoyin a cikin Fiqhu harda ma tauhidi ina bashi amsa a raina ina mamakin
yanda yake kamo hadisai yana tambayata qarin bayani akansu kai Addu'a kawai nake a raina karya
qureni dan naga yana neman kai gejin dan Ilimin da nake dashi.
Tabbas ko a wannan gabar na sake godewa Allah, fata nane auran Namiji me cikakken ilimin Addini
domin qalubale ya kan zowa mace da sauqi a gidan aure idan har Abokin zaman ta yasan haqqoqin
ubangiji a cikin zaman auran se dai nayi fatan ya zaman ya zamana yana aiki da abinda ya sani.

Addu'a mukayi muka shafa kafin ya wuce dakinsa yace idan na gama na same shi a can. Seda na sake
sabon wanka bayan dana tuttuli wata zuma da Anty ta sake aiko mun da ita wai ita Emergency, ai kuwa
taci sunanta dan ina wanka ina jin kamar fitsari nake yi haka na qarasa shiryawa nabi lungu da saqon
jikina da hadin turaren da nake amfani dasu a irin wannan lokacin.

"Allah sarki Bashir" zuciyata ta ayyanamun se nayi saurin yin a'uziyya na dakko zumbulelen hijabi na
dora akan Rigar baccin dana saka. Seda na kashe fitila da dukka soket din dakin na saka wayata a silent
kafin na ajiyeta naja qofar na fita ina jin yanda zuciyata take bubbugawa na tunkarar sabuwar rayuwa,
Allah yasa mu shiga a sa'a.

Yanda Yayi daidai akan gado ya jingina da Allon gadon ya wani watsa hannu ya bala'in bani dariya, kamar
wani mara jini haka ya ringa bina da kallo ina ta nuqu nuqun da nima ban san na menene ba, yanzu fa
shikenan bayan Bashir wani yana shirin sanin sirrina? Ina tsaye na bashi baya ban ankara ba se ji nayi ya
sureni kamar wanda ya dauki kara be ajiyeni a ko ina be se a tsakiyar gadon.

"Ka bari Alwalar kwanciya bacci zanyi sena cire Hijabin na kwanta" na fada atsorace ganin yanda gaba
daya idanunsa suka birkice kamar wani wanda yasha kwaya, be saurare ni sema janyoni da yayi nida
Hijabin ya shiga yamutsanu yana cewa

"An yafe miki yau ki bari yanzu zanyi miki alwalar" mutsu mutsu naci gaba dayi dan yanda ya cukuikuyeni
da hijabin kamar ma numfashina ze dauke fahimtar hakan da yayi ya sakashi kama wuyan Hijabin cikin
abinda befi sakan biyu ba ya ketashi se gani nayi ya sauka daga jikina gaba daya, ya sake kama rigar
baccin dana saka, tafiyayyace tun daga America Anty Suhaima tayo mun aiken su amma Yusuf ya tsagata
gida biyu yana cewa

"Bata da guri anan dakin, ke kadai nake son gani a shimfidata, nayi miki izinin ki saka Hijabi kawai shima
saboda kar Aljanu su gabe mun surar ki" ya saki wani nishi a kunnenan kafin ya kama bakina ya shiga
aikamun da wani kalar kiss me gigita kwakwalwa.
"Zan goge miki duk wani tunanin da yake kanki Asmy, daga yau bazaki sake tuna wani namiji ba bayan ni.
Zan baki haddar da bazaki taba mantawa ba zaki tabbata kullum cikin bitar karatun" ya ringa sakin
maganganun kamar acikin Maye ni kaina bawai ina wani fuskantar sa da kyau bane dan tuni jikina ya
fara amsar saqon daya aika masa ta kowanne Angle.

Wani irin Romance yake aika mun dasu masu zafi da tikita tunani, cikin dan lokaci gaba daya muka rikice,
jikina har rawa yake kamar wata farin shiga a harkar koda yake a irin makarantar Yusuf dai kam ni Farin
shiga ce. Seda ya kwashe kusan mintina talatin yana Juyani son ransa kafin ya mirginoni daga qasa na
dawo samansa ya sakar mun kiss akan maqogarona kafin ya kira sunanan da wani kalar sauti

"Asmyyyyyy" ya tallafe fuskata da hannu biyu yana kallon cikin ido na, gaza jure kallon nayi na rufe ido
rufa sejin bakinsa nayi akan idon ya sakar mun wani kiss me qara da ya saka na bude idon babu shiri na
kalle shi.

"Ki gaya mun yanzu kina sona? ina so ki gaya yanzu da kanki cewar kina sona Asmy, Ina so mu zama abu
daya da yardarki, kin Amince kin yarda kin bani kanki?"

Dukda fargabar da nake ciki haka na daure se kawai na hade bakin mu guri daya da kaina na shiga mayar
masa da irin martanin karatundana koya a gurinsa harma da qarin nawa Ilimin da ban samu dar bayyana
shi a baya ba.

Wani qaramin ihu yayi ya sake juyani daga nan labari yasha banban, ban tashi gano wautata ba seda naji
yana karanto Addu'ar saduwa da iyali kafin nayi wani Yunquri tuni ya sama wa kansa hanya me kyau ya
shiga jikina, dani dashi muka saki ihu a tare, ni nawa na yanda abin yazomun a bazata ne shi kuwa na
qololuwar gejin dadin da yaji ne na jinsa a wata sabuwar Duniya, babu bata lokaci ya shiga aikin lada
kamar wanda akace za'a biya.

Ni Ma'u naga ikon Allah na kuma yarda da fadar da ake cewa Maza suna suka tara dagaske cikin jarumai
ma akwai Jarmai. Tabbas Bashir Namiji ne na gaske dukda shi kadai na sani a rayuwata amma nasan
samun irin sa se an tona se gashi tun ba'aje ko ina ba na gano tarin banbancin dayake tsakaninsa da
Yusuf.
Tun ina daurewa ganin abin fa ya fara zarce na islama se na fara neman hanyar ceto dan gaba daya Yusuf
ya birkice mun kamar wani mayunwacin zaki wanda ya shekara goma beci nama ba, maganganu kuwa in
nace zan tsaya jin me yake fada ma batawa kaina lokaci zanyi dan na tabbata har Ahmad da Muhammad
seda ya kama sunan su yayi musu godiya, seda ya kwashe kusan awa daya yana aiki akaina kafin Allah ya
kwace ni a hannunsa ya samu nutsuwa bayan da yayi mun wata muguwar runguma kamar ze rabani
biyu.

Kwanciya yayi a gefena muka ringa mayar da numfashi kamar wasu yan tsere kusan minti goma se jin
mutum nayi yana neman komawa jikina ba shiri kuwa na bude baki na saka masa kuka dan wallahi ko
daren farko na Albarka, banbancinau kawai wannan babu budurci amma gurzar dana shi ko rabin ta
Bashir be mun ba.

"Kuka Asmy daga yi sau daya karki bani kunya mana, gara ki shirya dan Mijinki jarumi ne" ya fada yana
qoqarin hade bakin mu guri daya amma naqi bashi dama cikin kukan nake cewa

"Naji amma yau ka barni haka wallahi ban shirya ba ni ban san haka kake ba".

Miqewa yayi ya shige Toilet, har na fara sauke ajiyar zuciya ina tunanin ya barni ne se gashi ya fito jikinsa
da ruwa alamar alwala yayi kafin na sake wani yunquri ya maidamu ruwa haka ina ji ina gani Yusuf ya
kusan cinye daren nan tas yana bidirinsa yanda kasan ance masa kafin safiya zan gudu ne.

Ban samu kaina a hannunsa ba seda mukayi Sallar Asuba wanda tsabar yanda qafafuna suka yi sanyi a
zaune nayita ina yi ina sharar hawaye. Wai se a sannan yake wani rawar jiki yana lallabani, ya hado mun
shayi me kauri ya bani tareda pain killers da daman ya tanadi abunsa tunda yasan kalar muguntar daya
shirya, ya dauke ni ya mayar dani kan gadon daya chanza shimfida kamar yar jaririya haka ya ringa juyani
yana bubbuga bayana tareda huramun kunne har bacci yayi nasarar yin gaba dani.

Qarar bugun qofar da akeyi ce ta farkar dani, ina buda ido na na ganshi akwance gefena hannuna cikin
nasa ya riqe dakyau yana bacci abinsa. Wani irin kyau da kwarjini naga ya qarayi mun, buga qofar da aka
sakeyi da qarfi ta saka ya farka yana zare ido ya kalle ni na daga masa gira alamar nima haka naji se ya
miqe ya nufi qofar yana tambayar waye

"Nice sweet ka bude" mukaji an fada daga wajen, mamaki ya kamani, wacece wannan kuma zata shigo
mun har cikin gida tana kiran mijina da wani sweet?
Qofar ya bude kafin yayi wani Yunquri ta danno kai ciki tana wannan yatsinar tata tana bin dakin da kallo
tace

"Qarfe kusan sha biyu baka tashi ba bayan kasan yau zan tafi kuma" ta fada tana rungume shi.

Kan bala'i lallai ma wannan matar ta cika yar rainin hankali ta qarshen lamba, yunqurawa nayi na tashi
zaune kafin nayi magana Yusuf ya rigani ya ce mata

"Haba Intee meya kawo ki gidan nan? Wama ya bude miki qofa kika shigo? Kuma da ba se ki kirani a
waya ba kawai se dai ki shigo mana daki kai tsaye"

Key ta zaro daga jakarta ta ta miqa masa tana cewa

"Gashi, jiya ka manta su, ka duba wayarja mana ka duba wayarka mana kaga sau nawa na kiraka, ni kaga
kazo ka kaini Airport, kasan dai qarfe uku jirgin mu ze tashi idan na rasa jirgi daga nan zuwa Abuja ya
kake so nayi?"

"Ki tafi Driver daya kawo ki ya kaiki mana me yasa dole se ni zan kaiki ba mun rigada munyi sallama tun
jiya ba" ya fada cikin alamun bacin rai, seta ta waiwayo ta kalleni ni kuwa na saka musu ido kawai ina
kallon ikon Allah ita kuma haka zamuyi da ita?

"Ki ce masa ya kaini" ta fada tana tabe baki kamar wata qaramar yarinya, se na juya na kalle shi kafin ma
nayi magana yace mun

"No, babu ruwanki Asmy ki kwanta ina zuwa" yaja hannunta qii sukayi waje. Kwanciya nayi a raina ina
sake jinjina wannan Al'amari, yanzu ita sangartar tata har ta kai haka kenan, wannan idan guri
dayavzamu zauna ai wahalarta kadai ta ishi mutum dan da alama bata san daidai ba.

Bansan yanda suka qare ba dai se gashi ya dawo, babu alamar wani bacin rai ya dagani sama yana juyi
dani kafin ya ajiye ni muka shiga Toilet, shi ya saka mun Toothpaste akan brush bayan danayi fitsari ya
kunna mun fanfo na shiga wanke bakina. Tare muka gama muka fito ya sake daukata muka sauka qasa
be ajiye ni ba se akan kujerar Dining inda naga an jera abinci.

"Wa yayi girki" na tambaye shi bayan dana karbi shayin daya hadamun.

"Daga gidan Hajiya aka kawo tace tana gaishe ki" ya bani amsa.

"Ina amsawa amma ya kamata a dena kawo wa haka zan ringa dafa mana"

"Kin tabbata?" Ya tambayeni na daga masa kai.

Yinin ranar naga gata me sunan gata a gurin Yusuf dukda naji a jikina nima amma na fuskanci dole indai
ina son zaman lafiya dashi sena koyi juriya to wai ma duk tsahon lokacin nan ya yake da wannan matar
tasa ne?

Sati daya mukayi muna cin Amarci da tsinke, koda yaushe muna tare sallah kadai take fitar da Yusuf waje
dai dai da wayoyinsa ya kashe su komai tare mukeyi, ayyukan gida, wanka bacci koda yaushe ina zaune a
jikinta ko muna wasanni kamar wasu qananan yara dan har wasan guje guje muke yi idan mun rasa
abinyi sosai shaquwa ta shiga tsakanin mu da soyayyar da ban taba zata zan sake yiwa wani kalarta ba.

Satin mu biyu da aure muka tafi honeymoon, seda muka shafe wata biyu muna zagaya duniya kafin
muka yada zango a America yayi wa matarsa sati daya dan ni a hotel nace ya ajiyeni dukda ma bacci
kadai yake mayar dashi gidan kusan kullum da ya dakko Ma'u qarama ze taho da ita gurina se dare zasu
koma gida har muka cika kwana bakwai kafin muka dawo Nigeria. Cikin kwana uku muka huta aa duk
wani shiri da zamuyi, Naje Gombe nayi kwana daya mukayi sallama dasu muka tattara muka wuce Abuja
inda muka kafa sabuwar rayuwar mu me cike da Aminci da yarda da juna.

Watanni uku da suka biyo baya bayan Fitowar sakamakon jarabawar su Aliyu Yusuf ya sama musu
Scholarship na gwamnatin tarayya shida Amnah suka tafi America inda ze karanci Fasahar Zane zane
(Architecture) Amnah kuma Pharmacy, ba'a samu wata tangarda daga Bashir ba dan a gurin Anty
Suhaima zasu zauna shiyasa ni kaina lokacin da Yusuf din ya kawo mun maganar fitarsu waje ban damu
ba.
Babu dadewa Bashir ya samu izinin tafiya qaro qaratu daga gurin aikin su zuwa qasar Faransa, wannan
dalilin ya dawo da riqon Faridah da Jafar hannuna wanda da Goggo ta kafe akan itama sedai a barta a
gidan ubanta. Suka tafi tareda Abdallah da yan biyu saboda A lokacin Jafar yana Aji biyar ne a sakandire
yace baze bisu ba ze zauna ya qarasa karatunsa a nan dukda rabin zaman nasu gidan Alhaji Qarami ne
duk tsarin Goggo ne wai bazasu je agolanci ba.

BAYAN SHEKARA GOMa

ALHAMDULILLAH shine abinda a kullum bana gajiya da maimaitawa tabbas na yarda ba komai da kake so
a rayuwa yake zamar maka Alkahiri ba kamar dai Soyayya ta da Bashir, haka abinda kaqi a qarshe idan ka
bashi dama yakan zamo wannan Alkahiri da kake ta wahalar neman sa baka samu ba.

Rayuwar aurena da Bashir, shigowar Amirah rayuwar har zuwa rabuwar mu da kumaaurena da Yusuf su
kadai sun isa su zame mun izina a rayuwa. A cikin shakaru shida da auren mu da Yusuf ko nace His
Excellency Governor YUSUF WUNTI mun samu qaruwar Yaya uku, na farko nayi yan biyu mace da Namiji
da suka ci sunan Umar da Ruqayya se Autana Sulaiman da muke kira da Junior.

A tsahon shekarun nan a kullum tsakanina da Yusuf se godiya da sam barka dan ya isa Miji kuma uba da
duk mace zata bugi qirji ta nuna shi a matsayin mijinta. Bance babu qalubale a zaman auran mu ba
amma fahimtar da muke da ita ta taka muhimmiyar rawa gurin kawo daidaito a tsakanin mu dan koda
wasa Yusuf be taba kwana da fushina a zuciyar sa ba haka nima.

Tuni nabar aiki ba tareda wani ya bani shawara ba, dan abin shirita ya zamar mun dole na rubuta
resigning na tsayar da hankali na akan gidana na qara bunqasa kasuwanci na dan yanzu kasuwa kam se
Hamdala, tuni na sake bude qaton shago a cikin Abuja na zuba kayan yara, da aka kwana biyu na sake
bude Salon qaton gaske na zuba ma'aikata duk wani gayar da kwalliya na mata munayi a Gurin kuma
Alhamdulillahi komai ya samu karbuwa dan Yusuf da kansa yake sake tallata ni duk abinda nake siyarwa
da yaji wani yana nema ko ana zancen za'a siyo a wata qasa zece matarsa tana siyarwa, har tsokanar sa
abokanan sa suke idan ana son abu ace

"Wunti Madam na siyar da kaza?"

Duk sanda dayan mu ya batawa dan uwansa, ya koya mun dabi'ar fitowa na fadi abinda yake zuciyata.
Idan nayi masa laifi ze zaunar dani ya gaya mun, idan na yin fada ne ze yi mun ya nuna mun kuskure na
daga nan gurin maganar ta wuce har Abada zamu koma daidai kamar babu abinda ya taba faruwa a
tsakanin mu.

Haka tsakanina da Yan uwansa se sambarka, har bayan rasuwar Hajiyar su shekaru biyu da suka gabata
sanadiyyar Hadarin mota daya rutsa da ita sun ci gaba da daukata a matsin Yar uwa da suka bani. Suna
girmamani a matsayina na matar Yayansu nima kuma naja su a jiki ina tafiyar da kowa a yanda ya
kamata.

Hajiya Intee kuwa lokaci da yawa ma ni mantawa nake ina da kishiya dan a rayuwa idan kuna jin ace
mutum Zero tension to Intee kenan, ita dai barta da kallon wulaqanci wanda na lura da cewar dabi'arta
ce idan aka zo batun Miji ita auro ni da akayi ma qara mata wani Yanci yayi dan ta sakar mun ragamar
komai ban fi shakara ba ta tattaro Ma'u qarama aka dawo da ita Nigeria, shi kansa Mijin se ya shekara
beje mata ba se randa ta bushi iska ta kirashi ko ita tazo sannan fa badan ma Allah yasaka Adali bane
dana tabbata zuwa yanzu idanbe rabu da ita ba toh tabbas ita da babu zasu zama basu da banbanci a
gurinsa.

Bazan gaji da buga misali da Rayuwar Yayana ba wadda a koda yaushe na daga hannu na bana sauke shi
ba tareda na roqa musu kariya da shiriya a gurin Allah ba wanda Alhamdulillahi dan ubangiji ya dafamun,
ya shirya mun su da shiriyar sa da kuma jajircewa irin ta mahaifinsu dan dole na Jinjinawa Bashir ta
yanda abubuwan da suka faru suka zamar masa darasi babba da yayi sanadiyyar daidaituwar rayuwar sa.

Amnah tayi aure ta Auri Naziru qanin Bashir tun taba shekara ta uku a karatun ta yanzu haka suna Can
American inda shima ya samu aiki harda qaruwar dansu guda daya Ahmad.

Aliyu ya gama karatunsa ya dawo dukda seda ya hada harda Masters yanzu yana ayyukan kwangila
wanda Yusuf yake sakar masa sosai yake nemo masa kwangila daga ko ina dan yanzu sun dinke baka jin
kansu, wani lokacin ma zezo Bauchi bazan sani ba sedai kawai Na ganshi yace Dady ne ya kirashi zeyi
wani aiki.

Jafar nedai na hannun damana kuma sirikina dan fa hadin nan dagaske zamuyi shi da takwarata data
zama budurwa itama yanzu saboda tana da girman jiki, shekaru sha shida idan ka ganta zaka dauka tayi
Ashirin dan haka ma Babanta yace da Faridah ta qarasa karatunta ze hadasu yayi musu aure idan yaso
ita Ma'u ta cigaba a gidanta.

Yan biyu na dai da Babana sun zama yayan Amarya sedai lokaci lokaci idan sun samu hutu suzo mana,
Bashir ya qara aure tun banfi shekara uku da yin aure ba auri Sa'idah Bayerabiya ce yar wani babban
Malami a garin Lagos macen kirki data rungumi yayana ta riqe da amana tamkar ita ta haife su.

Fadar irin tashin da sukayi da Amirah ma bata lokaci ne dan har seda tayi sanadiyyar mutuwar auranta
tayi zaman shekara daya a gida dan daman akayi sa'a ta dawo Nigeria lokacin haihuwar Yarinyar da
Bashir yayi mun takwara da ita wadda daga kanta har yanzu bata qara ba, dan haka koda aka fara dauki
ba dadi akan zancen auran nasa a yanda na samu labari har cikin gidan su taje ta ambaci sunan uwarsa
da ubansa tace idan ya haifu a cikinsu ya sake ta babu bata lokaci kuwa Dada ta kirashi a waya tace ya
saketa Alhaji yace a ta fau baza'ayi haka ba.

Qarshe gidansa na Gombe ta cinnawa wuta ya qone qurmus ko tsinke ba'a fitar ba babu Arziqi ya aiko
mata da saki biyu ya kuma saka aka kwace yarinyar bayan daura auransa da Amaryar sa ta wuce da ita
Faransa suka ci gaba da rayuwarsu.

Seda taji jiki zawarci shekara shida kafin ya mayar da ita ya barta anan Nigeria cikin gidan su ya gyara
mata bangaren Alhajinsu bayan ya rasu take zaune ana gara rayuwa babu dadi babu wahala dan taji jiki
shiyasa ta yarda da duk yanda yace dan ko banza bazata taba hada zaman da irin zawarcinda tayi a gidan
su ba bata da maraba da boyi boyi, kudin da zata siyi omon wanki ma gagarar ta ya ringa yi gashi ita ba
wata sana'a ta iya ba babu kuma wanda yazo koda wasan yace yana sonta saboda yanda labarin abinda
ta aikata ya karade ko ina harya gama zawarcin.

Addah kanta da take tsaya mata tayi duk abinda taga dama ta kanta take yi dan ta gamu da wanda ya
fita iskanci, malamin daya ce tayi auran kisan wuta zeyi mata aikin da Ahaji Murtala ze mayar da ita dashi
sukayi auran akan sati biyu zatayi ya saketa se gashi yanzu ana lissafin shekara kusan Tara kenan harma
ta haqura rayuwa ta bida ita tana can wani surquqin qauye ya kafeta ga kishiyoyi uku shegun qauye sun
tasata a gaba rayuwar ta kam yanzu ta zama abin tausayi mutum dai kawai ya tsoraci Allah a rayuwa.

Ummi qanwar Amirah tana zaune lafiya a gidan mijinta cikin rufin asirin Allah sun rungumi junansu sun
zauna tamkar babu wani abu daya taba faruwa a baya. Hatta da mutanen gari tamkar an shafe musu
tarihin abin a zuciyar su babu wanda yake tunawa harta haifi yayanta guda uku yanzu.
Ban manta da Maqociya Aminiyar kwarai Anty Halima ba, itama tuni sun bar Lagos bayan da Baba yayi
ritaya sun koma Zamfara da yayanta hufu yanzu dan a jere a jere tayi su tunda Allah ya bude mata
hanya, hakan be saka mun yanke zumunchi ba kullum muna cikin waya ko chatting tana sake bani sirrika
tana aiko mun da makaman yaqi nima kuma Alkahiri na be taba yanke mata ba, duk wani abu daya tashi
na romon damakaradiyya sena sakata a ciki, ga connection da nayi mata da matan abokanan siyasar
Yusuf suna siyan kayan Arziqi a gurinta duk wadda ta siya kuwa seta koma sanna ta qara kawo mata
wasu shi yasa takance dani

"Ma'u haduwa ta dake ta zame min Alkahiri", na kance d ita

"Anty duk abotar da aka qullata domin Allah daman tana zama Alkahiri me girma fatana zumunchin mu
ya dore har gidan Aljanna".

MURFI

Ina cikin Sujjada naji an bude qofar dakina an shigo, nasan Yusuf ne, Dan duk daren duniya ko qarfe
nawa ze kai suna Meeting idan sun gama a gida ze kwana, akansa na qaryata cewar da ake yan siyasa
basu da lokacin iyalansu dan nidai nawa Mijin yasha banban da sauran.

Kafin yara su fara makaranta ko wata qasar ze tafi qafata qafarsa, har kuma Yanzu indai tafiya bata wuce
sati ba sedai na barsu a gida mu tafi balle kuma ace yana gida Nigeria ya kwana a wani guri da ba cikin
gida ba gaskiya da wuya.

Seda na sallame na Shafa addu'a kafin na kalle shi ina murmushi nace

"Sannu Excellency se yanzu"

"Kinganni fa Asmy, mutanen nan sun huramun wuta da yawa, ni kuma ina kan bakana bazan yarda da
duk wani sharadi mara tushe ba sedai idan zasu kwace tikitin takarar su su karba amma bazanyi abinda
zanje gaban Allah na kasa kare kainaba, wai har party chairman ne yake munbarazana, nace masa duk
aikin banza ne babu abinda zasu iya wanda Allah beyi ba".

Kusada shi na koma na kama hannunsa nace


"Babu komai ka tsaya akan gaskiyarka, ba abinda ze same ka da izinin Allah kuma seka cika burinka
tunda dai kaine akan gaskiya su kuma qarya kuma a koda Yaushe Gaskiya ita take Nasara akan qarya".

"Shiyasa nake qara sonki Asmy ta saboda a duk sanda na rasa qarfin guiwa kina dawo mun dashi, Allah
ya gafartawa Hajiya, maraicina kadan ne tunda ina da mace ta gari da bata mantawa dani a cikin Addu'ar
ta"

"Amin yah rabbi, ni yaushe za'a bude mun ofishin First Lady ne na qaddamar da campaign dan dai kasan
wannan karon baza'a barni a baya ba, First Lady lamba daya ba wasa ba kai wayaga Ma'u a Villa" na fada
cikin wasa ian wani buda kafada irin yanda zan ringa tafiya a Villa.

"Ga babban office dinki nan, ai kici gaba da Sallah kina taya mu da Addu'oi dan ina ganin hasken su
amma darajarki ai tafi qarfin ki fita yawan campaign dan zan iya zagewa mu daku da duk wanda yace ze
daga miki yatsa, yanzu dai kawo mun Baqin Lipton kizo kiji wani abu, ni naga wani qyallin go shi ma kike
kodai mun samu qaruwane?" Ya fad yana shafa goshi na, sena miqe ina dariya nace

"Rufa ni ka sayani, meya rage ban haifa ba ni kuwa da zan haifo shi Yanzu?"

"Bashir, ba kiyiwa Bashir takwara ba" ya fada har yanadaga murya dan na kusa fita daga dakin. Se nayi
turusna wai wayo, wani abu naji ya motsamun a zuciya kai Allah karya kawo abinda baze wuce ba sena
kalle shi ina murmushi nace

"Ai ka rigada kayi jana'izar Bashir a zuciyata dan haka bani da sauran qwan da zan haifa na saka masa
sunansa, idan kuma jinjiri kake so to sedai mu haifi Yusuf Junior a Villah idan Allah ya kaimu".

TAMMAT BI HAMDILLAH

SAQON GAISUWA GA DAUKACIN MASOYAN LITTAFIN WATA KISHIYAR A DUK INDA KUKE A FADIN
DUNIYA ALKAHIRIN ALLAH YA KAI MUKU 🙏🙏🙏

NA GODE DA JUMURIN BIBIYA DAGA FARKO HAR ZUWA QARSHEN LITTAFIN NAN ALLAH YA HADAMU A
LADAN ABINDA MUKA KARANTA NA QARUWA YA YAFE MANA KURAKUREN DA MUKA AIKATA A CIKI
MASU KIRANA A WAYA DA MASU TUROMUN SAQO NAGODE, MASU NEMANA A DUK SANDA SUKA JINI
SHIRU KWANA BIYU DAN TABBATAR DA LAFIYATA INA GODIYA SUNAYEN KU BAZASU RUBUTU BA
AMMA DUK WADDA TA GANI TASAN DA ITA NAKE KUMA NA GODE KWARAI ALLAHYA SAKA DA
MAFIFICIN ALKAHIRI

NAGODE ONE LOVE

SE MUN SAKE HADUWA A LITTAFINA ME ZUWA 🙏🙏🙏

You might also like