You are on page 1of 6

DARASI DAGA RAYUWAR MAGABATA 1

DARASI DAGA RAYUWAR MAGABATA 2

FITA TA (1) DARASI DAGA RAYUWAR FUDAILU


BIN IYAD

DAGA RAYUWAR FASHI DA MAKAMI ZUWA GA RAYUWAR


MALUNTA
Waye fudailu bin iyaad?: Sunan sa Fudailu bin iyaad bin
mas’oud Alyarbou’I, an haife shi a wani gari da ake kira
samarqanda a cikin shekara ta dari da bakwai (107) bayan hijirar
annabi Muhammad (saw), kuma ya taso a wani gari da ake kira
Abyurod. Wato dai a takaice fudailu bin iyaad ya rayu ne a dai-dai
lokacin da tabi’ai1 suka rayu, kuma daya daga cikin manyan
tabi’ai (RH)

Class:[Name of Class]

Name:[Student Name]
Fudailu bin iyaad ya kasance sana’ar sa a wannan gari na Abyurod

1Tabi’ai sune wadanda suka biyo bayan sahabban annabi Muhammad (saw),
Thesis Advisor:[Type the thesis advisor's
basu ga annabi ba, amma dai sun ga sahabban sa.

name]
DARASI DAGA RAYUWAR MAGABATA 3

shine fashi (wato tare hanyar fatake da ‘yan kasuwa) ya kwace


musu dukiyoyin su.

Wata rana da daddare ya nufi gidan wata mata da nufin yayi


mata fashi, haura katangar gidan na ta ke da wuya sai ya jiyo
sautin wani mai karatu yana karanta fadin Allah madaukakin sarki
[[shin lokaci bai yi bane ga wanda suka yi imani zukatansu su
‘kaskanta saboda ambaton Allah ba?]]2 da jin wannan ayar sai
fudailu a take a wajen ya koma da baya yana mai cewa “tabbas
lokaci yayi ya ubangiji, tabbas lokaci yayi ya ubangiji”. Bayan ya
koma da baya sai hanya ta riske shi a wani wuri daban ( ba inda
yake tare mutane yana kwace musu dukiya ba) sai ya jiyo wani
ayari na fatake suna cewa “kada mubi wannan hanyar yanzu
domin fudailu yana nan zai kwace mana dukiyar mu, mu bari idan
asuba tayi, gari ya waye sai muyi tafiyar mu cikin aminci”.

Da jin abinda wannan ayari suke tattaunawa akan yadda zasu


kubuta da dukiyar su daga haduwa da fudailu bin iyaad, sai fudailu
yace “kaico na! Kullum ina nan kan hanya ina raaya dare ina
sabon Allah ta hanyar kwacewa mutane dukiyar su, nan kuma ga
2 Surah ta 57/16
DARASI DAGA RAYUWAR MAGABATA 4

wasu daga ckin musulmai sun kasa tafiya izuwa ga kasuwancin su


saboda tsoro na? Nan fa sai fudailu bin iyaad yace: “ya Allah! Na
tuba ka yafe mini, ya Allah! Na tuba ka yafe mini, ya Allah na
sanya tuba na ya zamanto mai makotaka da dakin ka mai alfarma
(ka’aba)”3 daga wannan ranar fudailu bin iyaad (RH) ya daina
fashi ya koma neman ilimi da bibiyar malamai. Gari na wayewa,
rana na wucewa har sai da fudailu bin iyaad (RH) ya zamanto
babban malami a cikin tabi’ai, da duniyar ilimi baki daya. Haka
nan an rawaito cewa sai da manya-manyan tabi’ai da
tabi’uttabi’una suka zauna gaban sa suka kwashi irin abinda Allah
madaukakin sarki ya bashi na ilimi.

3Abin nufi shine: zai koma makkah da zama yana bautawa Allah a
masallacin harami.
DARASI DAGA RAYUWAR MAGABATA 5

Fudailu bin iyaad (RH) sai da ya zauna a gaban manya-manyan


malamai na duniya da ake ji da su wancan lokacin yayi karatu
wanda har izuwa wannan lokaci da muke ciki babu kamar su a
duniyar ilimi, daga ciki akwai:

 Imam sufyan Athauriyy.


 Al’amash.

Haka nan daga cikin daliban sa akwai babban malamin mazhabar


nan ta shafi’iyyah da ake kira da:

 Imam Ash-shafi’iyy.

YABON MANYAN MALAMAI GA FUDAILU BIN


IYAAD:

Malamai da yawa sun yabi fudailu bin iyaad (RH) ta fuskoki da


yawa, daga cikin malaman da suka yabe shi akwai:

 Ibn Mubarak yana cewa: “babu wani mutum a doron kasa da


ya kai fudailu bin iyaad falala (da daraja) a waje na”.

Fudailu bin iyaad ya rasu a shekara ta dari da tamanin da bakwai


(187) bayan Hijirar annabi Muhammad (saw)

DARUSSAN DAKE CIKI:

 Kada ka aibata wani don kaga yana aikata sabon Allah, domin
baka san yadda karshen rayuwar sa zai kasance ba, kai ma
baka san yadda karshen rayuwar ka zai kasance ba. Idan kaga
mutum yana sabon Allah ka nema masa shiriya wajen Allah.
DARASI DAGA RAYUWAR MAGABATA 6

 Kullum ka kasance mai yawan tuba izuwa ga Allah, domin


Allah mai karbar tuban bawan sa ne.

 Tabbas lokaci bai kure maka ba wajen neman ilimi, har yanzu
kana da sauran lokaci.

 Kada kace: “tunda na jima ina sabon Allah, lallai Allah ba zai
karbi tuba na ba” idan ka fadi haka tabbas ka munanawa Allah
zato, domin shi Allah a koda yaushe mai karbar tuban bawan
sa ne. Allah ka bamu ikon yin aiki da abinda muka karanta,
Amin!

Moukhtar Isa Yahya (Abu Muhammad)


Domin shiga Zauren: 08107975219

You might also like