You are on page 1of 56

*LOKACI NE*

(Gajeran Labari)

Daga Alƙalamin

Maryam Abdul'aziz

(Mai_Ƙosai)

Godiya: Ga Allah subhanahu wata'ala da ya ba ni dama da ikon fara rubuta wannan ɗan gajeran Labarin.
Tsira da aminci su tabbata ga shugaban rahma Annabi Muhammad (S.W.A) da sahabbansa da ahlayensa
da duka mabiyansa.

Gargaɗi: Ban yarda wani ko wata su sauya min Labarina ba, yin hakan ya saɓa da doka, kuma lallai
tabbas ba makawa za a ɗau tsattsauran hukunci ga duk wanda ya yi hakan domin Labarin da rubutun
duka haƙƙin Marubuciyar ne, dan haka a kiyaye.

Ɗaya

Sannu a hankali take bin kowanne sassan ɗakin da kallo, lokaci guda ƙwaƙwalwarta ta soma dawo mata
da muhawararta da mahaifiyartana san auren dolen da take shirin yi mata, kuma wai ba da kowa ba sai
da mutumin da ya so keta mata haddinta, mashayi ɗan caca. ko da yake ba wannan ce tsagwarar
damuwarta ba illah kawai ta ga ta yi aure ta huta da gorin da ake mata, amma ya ta iya da samarin
kakarta lokaci ne kuma ba shakka zai keto ta kanta.

Ta sauke hucin iskar da ta futar daga bakinta. Gaba ɗaya ƙwaƙwalwarta a cunkushe take ,ji take yi
kantana mugun sara mata ta yiyuwu ma madaki ne ake dukanta ta shi wanda za a iya ta'allaƙashi da rodi
ko guduma. Tsakiyar kanta ce ke tsananin san tarwatsewa saboda tsabar sarawar da kan nata ya ke yi.

Rinannun jajayen idanuwanta da suka kaɗa suka yi jazur da su wanda sun jima da sauya launi ta ɗaga
tana mai kallon agogon da ke maƙale jikin bangon ɗakin. tana ji zuciyartana kuma bugawa da sauri da
sauri kamar tarago, yadda ko wanne sakanni ke kaɗawa tare da tafiyar tsinken jikin agogon.

Matashiyar budurwa ce mai kimanin shekaru ashirin da biyu wankan tarwaɗa ,tana da yalwar ga shi
wanda zaka gane hakan ta yadda gashin ya zubo mata har gadan baya ,sai matasan idanuwanta da ba za
ka saka su a matsayin manya ba ko ƙanana, sai laɓɓanta biyu masukalar ruwan hoda, ba ta da wani
kakkauran jiki sai dai tana da yalwar tsayi.

A hankali ta ranƙwafa ta miƙe tsaye jikintana wani irin kakkarwa, daidai da jirin da ya kwasheta ta tafi
taga-taga za ta faɗi, cikin sauri ta koma ta zauna da ƙyar ta iya ya fito kalmar "Hasbunallahu wani'imal
wakil" ta yafa a bakinta. Cikin hukuncin Allah wasu zafafan ruwan hawaye masu ɗumi suka shiga
kwaranyo mata a kan kyawawan kumatunta.

Karo na biyu da ta kuma yinƙurawa ta miƙe cikin dauriya da san nuna jarumta , hannunta ta saka a kan
kanta ta dafe kan da ke tsananin sara mata hawaye na daɗa kwarara daga cikin kogin idanuwanta.

Dukkan abin da Ubangijj buwayi gagara misali ya hukunta lallai ba shakka ko ana muzuru ana shaho sai
lamarin ya kasance. Mutane da dama kan nazarci wasu abubuwan daban ta fuskoki mabambanta. Duk
da kallon hadarin ka jin da wasu ke yiwa abun cikin rashin sanin ingantacciyar mafaka, har ila yau
abubuwa ke kuma cunkushewa a cikin ƙwaƙwalensu in da take musu tufka da warwara cikin wasu daƙiƙu
kuma sai su zartar da abin da zai saka zuƙatansu tararradi.

***

Jingine ya ke jikin wata dallaleliyar kyakkyawar mota wanda a ƙiyasi ba za a iya ƙiyasto adadin kuɗin da a
ka saka a ka siyota ba. Ya fi mintuna masu ɗan tsawo a wajen jefi-jefi ya kan duba agogon dake ɗaure a
saman tsintsiyar hannunsa tare da jan tsaki. "Mitsss!" Karo na uku ke nan da ya kuma jan wani tsakin
wanda in ka na daga nesa ma za ka iya jiyo shi muddin tazarar ba ta wuce taku ashirin ba.

"Abbas har yanzu ba ka wuce ba.?"

A ka jefo masa tambayar da ta saka shi kallon in da sautin maganar ta fito. Kauda kansa ya yi gefe tare da
taɓe baki kafin ya ce,

" Ban tafi ba, ina nan dai tsaye kamar bishiyar da aka dasa."

"Ni kam sai na ke ganin kamar zai fi maka ka kyau ka san na yi." A ka kuma furtawa.

"Ba na tunanin sanyawa icen da ya tanƙware mayen ƙarfe zai saka ya dawo yadda ya ke."

Abbas ya yi furucin ya na mai sake taɓe bakinsa.

"Shi ke nan tunda haka ka zaɓa, amma kamar zai fi maka kyau ka bazawa bujan bujejen burmemen
wandonka iska ka arci na kare wala Allah ka sami sa'ada."

Matashin saurayin ya ƙarasa faɗa da sakin wani guntun gajeran murmurshi. A shekaru da tsayi za su iya
yin kai ɗaya da Abbas ɗin duk da cewa Abbas ya fi shi nuna jikin girma da hutu.

Abbas bai tanka masa ba, domin ji yake zuciyarsa na matuƙar tafarfasa a halin yanzu, kuma muddin in
har ya buɗe baki ya yi magana to zai iya gasa masa maganar da zai kwana ya yini ya na jinta cikin ƙahon
zuciyarsa kuma ƙwaƙwalwarsa ba za ta taɓa mantawa da maganar ba za ta kasance kullum abar
tunaninsa.

Shi ma ganin haka ya sa ya kama gaban shi ba tare da ya sake furtawa Abbas ɗin komai ba.

Duk abin da ya ke faruwa kan idanuwan wata kyakkyawar matashiyar yarinya mai kimanin shekara goma
sha tara zuwa ashirin. Laɓe take jikin wata katanga tana hangensu duk da ba ta ji me suke tattaunawa ba
amma ya nayin fuskar Abbas ya nuna mata lallai ba magana mai daɗi ci ta wanzu tsakaninsu ba.

Ya tsina baki ta yi tana mai furta, "Wahalalle, ai sai ka daskare a wajen." ta juya daga inda take tana mai
komawa cikin gidan.

"Har kin dawo? Ya tafi ne?" A ka watso mata mabambanta tambayoyin, wanda ba kowa ba ce fa ce
mahaifiyarta Mama.

Turo baki ta yi tana mai ɗan ƙunƙuni ta ce, "A'a ni ko ƙarasawa ma ban yi ba wajensa. Mama kawai ni fa
ba na jin zan iya jin zantukan kalamansa a cikin amsa kuwwar kunnuwana."

"Iye! Lallai kin girma kin zama riƙaƙƙiyar kuɓewa, kin ta fasa kin zama talge shiyasa." Mama ta yi furucin.

"Ni Mama wai mene ne laifina a ciki ? Ba fa a yin so dole." Ta ce.

"Ba a yi. Amma dai ki yi a hankali wallahi ina jiye miki gaba." Mama ta ce.

Ba ta kuma sauraran lafuzan Mama ba ta wuce ɗaki a bin ta tana mai ƙara turo baki gaba, balle ma ta
san cewa wani ɓoyayyen saƙo Mama ke san isar mata. Mama kam ƙwafa ta yi ta cigaba da sabgoginta.

Sabon salo ,sabon kafce.

Mai_ƙosai

*LOKACI NE*

Mai_Ƙosai

FCWA

Biyu.
Wasu ruwan hawaye ne suka kuma kwaranyowa a kan fuskarta, maganar Mama da rayuwarta ta baya
suka so dawo mata sababbi dal! Ta lallaɓa a hankali ta isa bakin ƙofar ɗakin da ta ke ciki, kallon ko ina ta
ke yi kantana kuma sarawa.

"Har kin farka?"

A ka jefo mata tambaya, gyaɗa kai kawai ta yi dan ba za ta iya furta wani furucin ba a halin da ta ke ciki a
yanzu.

"Sannu, muje na nuna miki bayi ki yi alawa ki zo ki yi sallah, dan lokacin sallah har ya gota sosai."

Matar ta kuma yin furucin a karo na biyu. Duk da cewa ta zarar ta su ba ta da wani yawa a ƙirar jiki sai
dai kawai matar ta nuna mata diri.

Har banɗakin ta raka ta tare da kunna mata fanfo ta nuna mata komai sannan ta barta a ciki.

Ta ɗau tsawon mintuna goma a ciki kafin ta fito tana mai ya tsina fuska game da yarfar da hannu.

A hankali matar ta kama hannunta ta isa da ita izuwa kan sallayar da ta shimfiɗa mata.

"Dan Allah ki yi sallar, tunani ba zai amfanar dake komai ba."

Ba ta tanka mata ba ta tada iƙama kamar yadda itama ba ta sa ran jin amsa daga gare ta ba.

Ficewa ta yi daga ɗakin ta barta dan ta samu damar gabatar da ibadarta yadda ya ka mata.

Kifa kanta ta yi kan guiwoyinta biyu bayan ta idar da sallar tana mai kuma jin zuciyarta babu daɗi ga wani
ɗaci wanda ya zarce na farasitamol da ya gauraye duk ilahirin bakinta.

Ta fi mintina uku a haka kafin ta zame jikinta a hankali kamar mara laka ta kwanta kan dardumar sai ka
ce mage, wani sanyi na ratsa dukka ilahirin sassan jikinta fiye da sanyin ƙanƙara. Kalaman Mamanta suka
kuma dawo mata sababbi dal cikin kwanyar kanta.

"Ki dai yi a hankali, ina ji ye miki gaba." Ta saka hannunta ta goge ruwan hawayen da suka kuma zubo
mata a karo na ba adadi.

Sallama matar ta yi bayan ta ƙarasa shigowa ɗakin, hannunta ɗauke da ƙaramin faranti ɗauke da abinci.
Ta isa gabanta gami da furta,

"Ta shi ki sakawa cikin ki wani abun."

Tana jinta amma sam ba za ta iya furta mata ko da ƙala ba, gaba ɗaya ji ta ke yi bakinta ya matanauyi
sam maganar ba za ta iya fita ba.

"Ki ta shi ki sakawa cikin ki abinci." Ta kuma sake furta hakan a karo na biyu.

Kuma har a lokacin ba ta jin za ta iya yi mata magana.


"Dan Allah ki ajjiye duk wani tunani ki dawo cikin nutsuwarki, ki kuma daure ki ci abincin nan. Yau
kwanan ki biyu ba ki ci komai ba sai ruwa da ki ke sha shi ma ba zai wuce sau biyu zuwa uku ba." Ta
tsagaita da maganar tana mai kallon cikin idanta.

Runtse idanuwanta ta yi sosai ,a ranta tana mai jin damuwar da take ciki ba za ta taɓa bari ta iya cin
komai ba.

"Ba na jin zan iya sakawa cikina komai a yanzu." Ta yi maganar kamar wacca a ka yiwa dole.

"Na haɗa ki da girman Allah ki ta shi badan ni ba ki ci abincin nan." Matar ta ce.

Ba dan ranta ya so ba ta miƙe zaune a hankali, sai dan dai kawai matsawar da matar da ta mata kuma
ciki harda haɗata da girman zatin Allah da ta yi.

Loma ɗaya ta saka mata a baki ta ji ba za ta iya haɗiyewa ba , tari ne ya soma sarƙafeta ta soma yin ƙurin
amai. ganin haka ya saka matar miƙewa ta fice daga ɗakin. Mintina uku ta dawo ɗauke da kofi na shayi
mai kauri a hankali ta shiga ba ta a baki da kaɗan-kaɗan.Cikin ikon Allah ta sha fiye da rabi.Ta sauke
nauyayyiyar ajiyar zuciya mai ƙarfi. Kunnuwanta suka sake shiga yi mata amsa kuwwar kalmar da take
sake sakata cikin matuƙar baƙin ciki, kalmar da take jin ƙyanƙyamin kanta a duk sanda aka yarfa mata ita.

"Mai baƙin jinin da ta rasa masoyi."

Tana jin zafin kalmar sosai a ranta, to baƙin jinin me kuma? Bayan ta san tunda take ba ta taɓa rasa
masoya ba. I! mana ba ta taɓa rasawa ba tunda dai Mamantana santa ,kuma haka zalika ta taɓa tsayawa
da wani a matsayin masoyinta. Amma mene ne dalilin da zai saka mutane jifanta da kalmar gami da liƙa
mata wannan mummunar kalmar, kuma ba su tsaya a nan ba harda aro kalmar Shegantaka su jefa mata
ita.

Me ya sa mutane ba sa gane cewa; komai na duniyar nan da duk abin da ya ke faruwa cikinta muƙaddari
ne daga Lillahi wahadahu sarkin sarakuna? Me ya sa ba za su gane cewa ko wanne maƙasudin abu da
lokacinsa? Haka zalika ko wanne ɗan adam da irin tasa ƙaddarar.

"Tunanin ne dai.?" Ta jiyo tashin sautin muryar matar na tambayarta.

Kallo ta bita da shi, dan ba ta jin za ta iya ba ta amsa. Ta zame jikinta a hankali ta kwanta kan daddumar .

Ganin hakan bai sa ta hanata ba, ta san kome za ta ce mata ba za ta kuma tankawa ba hasalima ba za ta
samu kowacce irin amsa daga gareta ba balle kuma ta motsa gaɓoɓinta. kawai sai itama ta miƙe ta hau
tattara kwanukan ta fice daga ɗakin ta barta dan ta kuma samun hutu.

Wani ɗaki ta shiga daban da wanda ta fito daga cikinsa. Kallon ɗakin take yi tana mai sake nazartarsa
kamar yau ta soma ganinsa. Zama ta yi gefen gadon dake ɗakin tare da saka hannunta ɗaya saman kan
kuncinta.
Daidai da shigowar wani kyakkyawan saurayi dogo, fari,mai yalwar suma, mai matsakaicin hanci da baki,
da kyawawan idanuwansa masu shaf irin na ƙwai, mai shekara talatin da biyu. Ganinta zaune ta yi ta
gumi da duka hannayenta ga kuma alamun bata ma san ya shigo ba ya saka shi furta,

"Aunty na meke faruwa ne?" Bai ba ta damar magana ba duk da cewa sai a lokacin ta dawo daga kogin
tunanin da ta faɗa ya ɗora da faɗin,

" Kin san yawan ta gumi na haifar da hauhawar jini."

Ƴar ƙaramar dariya ta yi ,tana mai kallonsa.

" Da ɗina da kai tsantsan tsagwaran sharri, a ina aka faɗi hakan.?" Ta jefo masa ayar tambaya.

Shi ma murmusawar ya yi ka na ya ce,

" Ko dai ba a faɗa ba ni na faɗa, kuma dai tagumi babu kyau. Dan Allah ki daina ni ba na so na ganki kin yi
wani jugum kamar marainiya."

Yaƙe ta yi wanda ya fi kuka ciwo.

"Ba na samun wata damar da zan iya tunano abubuwan da suka riga suka shuɗe min sai a irin wannan
yanayin shiyasa ba zan iya dai nawa ba."

"Duk da haka dai Aunty ki ajjiye shi dan Allah, abin da ya jima da wuce ba zai taɓa dawo wa ba."

Ya ƙarasa faɗa yana mai zame mata hannun da har yanzu ba ta sauke su daga kan kuncin na ta ba. Ba ta
ce masa komai ba sai ma miƙewa da ta yi tsaye.

"Ta farka kuwa.?" ya jefa mata tambaya.

"Ta ta shi ,harma ta samu ta ɗan sha shayi. Amma yanzu dai ta koma."

Ta ba shi amsar a gajerce.

"Shayi kuma Aunty? Mai ya sa ba ki ba ta abinci ba ?" Ya kuma jefo mata wata tambayar.

"To ni ma ba na ce ba, dan kuwa tabbas banso hakan ta kasance ba, amma ba ni da ikon da zan tursasa
mata a kan hakan." Ta ce.

Gyaɗa kansa ya yi kamar ƙadangare. " Bari na ɗan leƙa na ga ni."

"A'a Musbahu, ka barta ta sake samun barcin." Ta katse hanzarinsa da sauri.

Bai mu sa mata ba, kawai sai ya saka kai ya fice daga ɗakin. Bin shi ta yi da kallo, ƙwaƙwalwartana tuna
mata da wasu abubuwa, a kullum ta kalli fuskarsa sai ta ji zuciyartana bugawa da sauri da sauri ,tana
kuma tuno mata da abubuwa ma su ɗumbin yawa.
Mai_ƙosai

*LOKACI NE*

Mai_Ƙosai

FCWA

Uku.

"Ya Ilahi"

Ta furta a hankali. Ficewa ta yi daga ɗakin ta kuma leƙawa ɗakin da take kwancan. Har a yanzu tana
kwance tana barci cike da tausaya mata ta koma ɗakinta itama ta kwanta tare da lumshe idanuwanta,
suka soma hasko mata abin da in ta tsinci kanta a irin yanayin ta ke ganowa.

Haɗaɗɗen Saurayi ne mai shekaru talatin da bakwai, fari dogo, mai siririn hanci, sai dara-daran idanuwa,
da laɓɓa madaidaita. Tsaye ya ke sai faman zuba yalwataccen murmushi ya ke yi.

Daidai lokacin da wata yarinya ta iso gare shi duk da cewa tana da shekaru wanda za sukai Ashirin da
takwas. Fuskarta ɗauke da kyakkyawan murmushi, cikin shagwaɓa ta ce,

"Yayana sannu da zuwa."

"Yawwa shaleleta, da har ina cewa bari na wuce tunda ba za a kula ni ba, kin san nifa har yanzu tsoron
matana ke yi." Ya ƙarasa cikin sigar tsokana.

" A duk lokacin da ka ke irin wannan zancan sai na ji zuciyatana dakan gunba, idaniyata ta cika taf da
ruwan hawaye, ka ji kuwa yadda ƙirjina ya ke bugawa dalilin fitar kalmomin." Ta ƙarasa kamar za ta yi
kuka.

"Tuba na ke shalelena, ni na isa na saka gimbiyata ta rarradi, lallai yau kam sai na amshi tsattsauran
hukunci." Ya faɗa ya na mai durƙusawa ƙasa.

Rufe idanuwanta ta yi da tafukan hannayenta biyu. " Ni ba ka yi min komai ba hasalima ni ce na yi maka,
dan Allah ka ta shi dan kuwa ni ce na fi cancanta da a hukunta."

Cikin shauƙin so ya ce, "Ke kam kin cika wayo, shiyasa kullum na ke ƙara jin sanki cikin zuciyata."
Ta ɗan yi far da idanuwanta, "Ni kam kullum ƙara narkewa ka ke yi cikin rai na." Ta ce cikin dariya.

Dariya sosai ya yi har sai da ya gaji dan kansa ya tsagaita, ita kam tamkar ta sami majigi ta kafeshi da
dara-daran manyan idanuwanta."

"An ya wannan son da ki ke masa ba zai ja maki wata illar ba Khausar.?"

Lokaci guda idanuwanta suka kuma hasko mata muƙabularta da ƙawarta da suke maƙotan tazara,
kunnuwanta suka shiga tariyo mata sautukan zantawar ta su. Ita ce kaɗai wacca ta ke iya raɓarta ba tare
da firgici da tsoro ba, itama kuma ta ke mu'amala da ita ba tare da ta yi mata ƙyanƙyami ba ko kallon
wani abu daban. Saɓanin yadda sauran mutanen da suke kewaye da da su suke mata tsantsan-
tsagawarar ƙyara.

"Ba na jin son da na kewa Abbas zai haifar min da da wata illa cikin zuciyata, shi ne mutumin da ya so ni
a lokacin da kowa ya ke guduna ciki kuwa har da iyaye na da suka haifeni. Koma dai hakan ta faru ni a
wajena shahadace ,kuma har abada ba zan taɓa rage wani kaso na daga cikin son shi da na ke yi ba."

Ta ba ta amsa daidai gwargwado.

"Ni kam ina jiye miki gaba ne, ka da ki sakarwa wani ragamar zuciyarki daga baya ya juya miki baya
kwatan-kwacin abin da ya faru, daga ƙarshe ya zame miki baƙin ƙadangaren bakin tulu ya barki da
tsantsar wahala, duk da cewa ina masa kyakkyawan zato."

"Dan Allah in ba za ki faɗi alheri ba to ki yi shiru." Ta faɗa ranta a matuƙar ɓace.

Ta dawo daga duniyar mafarkinta, tare da sauke ajjiyar zuciya da saka hannayenta saman ƙirjinta tana
mai jin yadda ya ke harbawa fat-fat da sauri.

"Har a bada kai na daban ne masoyina."

Ta furta hakan cikin sanyayyiyar murya tana mai share hawayen da suka daɗe da yi mata shimfiɗa a kan
fuskarta.

***

Dattijuwar mata ce ta fito daga ɗaki fuskarta babu walwala balle annuri a tattare da ita. Kai ka ce an
mata albishir da saƙon mutuwa.Taɓarmar da ke hannunta ta shimfiɗa a tsakar gidan, ta kuma maida
kanta cikin ɗakin. Mintina ƙalilan ta kuma fitowa ɗauke da maficin kaba a hannunta da kwanan sha mai
ɗauke da zallan nono ,duk da iskar da ke yalwace a tsakar gidan amma hakan bai hanata samarwa da
kanta iska daga jikin maficin ba.

Ba ta jima da zama ba wata mata ta shigo tare da kwaɗa sallama. Amsawa ta yi daga zaunen da take
bata ko motsa ba, itama waje ta samu ta zauna ba tare da ta nemi izinin matar da ke zaune ba.

"Wai har yanzu shiru, sai ka ce an aiki shirwa ko?"


Kamar ba za ta tanka mata ba, can kuma ta ce.

"Duk yadda a ka yi ta yi nisan kiwo ne, domin kuwa na jima da sanin lallai jiran gawon shanu na ke yi."

"A'a Asabe ka da ki ce haka, ai ba a cire rai ga rahmar ubangiji, Allah yana tare damu, kuma in sha Allahu
komai zai wuce kamar yadda walƙiya ta ke giftawa." Ta faɗa cikin san kwantar mata da hankali.

"Kayya dai da kamar wuya, wai ɓarawo a hannun mata." Asabe ta ce.

"To Allah ya kyauta dai, ni bari in wuce, daman na zo ne na ji ko kin sami wani labari ne a kanta.?" Ta
ida zancan tana mai miƙewa tsaye.

"Sai anjima Asabe, Allah ya kyauta lamarin." ta sake furtawa.

"A sauka lafiya, na gode." Asabe ta yi furucin. Har lokacin ba ta motsa daga in da take a zaunen ba.

****

Kakarin aman da ta jiyo daga ɗakin ne ya dawo da ita daga nahiyar tunanin da ta jima da lulawa.Cikin
sauri ta iske ɗakin ta isa gareta tare da faɗin,

"Lafiya? Me ya faru.?"

Ba ta iya bata amsa ba illa ma ci gaba da aman da take yi. A daidai lokacin ne Musbahu ya yiwa gidan
dirar mikiya, ganin abin da ya ke wakana ya sa shi saurin faɗin,

"Aunty mai zai hana mu je asibiti, na ga jikin nata kamar ba sauƙi."

Ba tare da ta kalleshi ba ta ce,

"Ina ga abin da za ayi ke nan, dan ni ma naga alamun haka, ma za jeka fito da mota mu wuce."

Juyawa ya yi ba tare da ya ba ta amsa ba ya wuce aikata abin da ta umarce shi.

Ka mata ta yi da nufin su wuce.

"A'a Aunty ki barni a hakana domin kuwa a yanzu ba abin da na fi ƙauna irin na ga na bar duniyar dan
Allah."

Ta furta hakan cikin galabaita tare da ƙoƙarin komawa ta zauna.

"Ba ki da ikon yankewa kan ki wani hukunci cikin ƙaddarar da Allah ya iya kanta miki, ina so ki sa ni duk
wani ɗan Adam da irin ta sa gwagwarmayar, ban san me ya faru da ke ba amma sai na ke jin matsalarki
mai sauƙi ce a kan ta wasu. Ki yi haƙuri muje asibitin koma mene ne daga baya kya yi shi in dai har zai
samawa zuciyarki da ruhinki salama." Aunty ta ce.
tana ji tana gani Aunty ta tasa ta a gaba suka wuce ,daman hausawa sun ce "Wai faɗan da ya fi ƙarfinka
sai ka mai da shi wasa."

Mai_Ƙosai

*LOKACI NE*

Mai_ƙosai

FCWA

Huɗu.

San da suka isa asibitin ba su wani sha wahala ba, kasancewar akwai likitan da suka saba gani wanda shi
ya zame musu tamkar likitansu.

Wasu ƴan tambayoyi ya mata kafin ya dangana ga yi mata wasu ƴan gwaje-gwaje, da ciki suka haɗa
harda na hawan jini, jin cewar tana fama da jiri da matsanancin ciwon kai.

Gwajin farko ya tabbatar da hawan jinin sai kuma ciwon gyanbom ciki da kuma zazzaɓin maleriya. Sai da
ya yi ƴan rubuce-rubucensa na wasu ƴan sakanni kafin ya kallesu ya ce,

"A bisa bincike na da na yi ya nuna min tana da hawan jini wanda shi ne musabbabin da ya sa take jin
jirin akai-akai. Sai kuma zazzaɓin maleriya da kuma ulcer(ciwon gyanbom ciki). Amma alhamdulillah zan
ɗorata kan magunguna sai dai zan ɗan riƙetana tsawon kwana biyu koma fiye da haka zuwa dai ganin
yanayin jikin nata."

Aunty ta sauke ajjiyar zuciya kafin daga bisa ni ta ce,

"To likita mun gode sosai ba damuwa a yi duk abin da ya kamata dan Allah."

Kamar yadda ya ce musu zai riƙeta hakan ce ta faru, kwanciya ya ba ta tare da saka mata robar ƙarin
ruwa.

Kallonta kawai Aunty ta ke yi tana mai kuma nazartar ta, ba ta san meke damunta ba, ba ta san wace ce
ita ba, ba ta san daga ina take ba , abu ɗaya kawai ta sa ni tsinto ta da suka yi lokacin da suke gab da
kaɗeta a kan tsakiyar titi, ganin kamar ba ta cikin nutsuwarta ya sa su ɗaukarta zuwa gida wanda shi ya
kawo su wannan ranar. Ta fice daga asibitin tana mai kuma jinjina tausayinta cikin ranta.
Washe gari da safe bayan ta ƙarasa asibitin, har ma ta tarar da ita ta ɗan sami wani ɗan sassauci daga
jiya zuwa yau.

Bayan ta samu da ƙyar da ci abinci cikin san sake kwantar mata da hankali ta soma furta mata lafuza ma
su daɗi.

"Ban san mece ce damuwarki ba, ban san ke wace ce ba amma ina so ki sakawa zuciyarki nutsuwa da
salama ki manta da komai ki mayar da komai na ki ga Allah subhanahu wata'ala, wanda shi ne
majiɓancin dukkan wasu al'amura, kuma sarki ɗaya jal! Sarki buwayi gagara misali na tabbata ki ka yi
haka to lallai ba zai barki haka ba zai da fa miki."

Ta share hawayen da suka gangaro a kan kumatunta tana mai kallon Aunty da Musbahu da ya shigo a
lokacin ka na ta ce,

"Tabbas kun min halaccin da ba zan taɓa mantawa da ku ba ko da bayan raina ku na maƙale a cikin
zuciyata. Bakina ba shi da abin da zai gode muku sai dai na ce Allah ya biya ku da gidan aljanna. In sha
Allahu kuma a yau ba gobe ba zan baku labari na za ku san ko ni wace ce, kuma za ku ji irin rawar da
ƙaddarata ta taka cikin rayuwata. Ba ta ba su damar magana ba ta ci gaba da furta,

"Suna na Hajara Hashim Jama'are. Duk da cewa na sami sunan mahaifina a bakin mahaifiyata. Ni ɗin
haifaffiyar ƴar garin Kano ce. Ni da mahaifiyata muna zaune a unguwar Ja'in. Ni kaɗai ce 'ya wajen
mahaifana duk da cewa ban rayu da mahaifina ba sai mahaifiyatana ta so cikin so, ƙauna da kulawarta. A
yadda na ji Mamana na faɗa tun ina yarinya ba ni da wani farin jini dan kuwa yara ba su fiya zuwa gareni
ko da da sunan yin wasa ba, kuma na kasance miskila ta bugawa a jarida abar kwatance, da fari ta yi
tunanin ko dan miskilanci na ne amma daga baya sai ta fahimce sam ba haka ba ne ba.

Bari na ɗan yi muku gwa-gwa-gwa cikin tafiyar kamar yadda mai koyan tafiya ke yi.

Mama na yawan ba ni labarin su ɗin ba mazauna nan ba ne ko na ce ta kance ita ba ƴar nan ba ce
hasalima zuwo ce, ita kaɗai ta zo garin Kano sai tsohon ciki, wanda bada jimawa ba bayan zuwanta ta
haifeshi in da ya kasance ta sami ɗiya mace ranar suna ko yankan da ake yiwa yara na rago ba ta yiwa
'yar ba tunda babu hali ta raɗa mata suna HAJARA wato ni ke nan. Ta kan ce min iya gata da nuna
kulawa tana ƙoƙarin ba ni ,haka zalika ma tana ƙoƙari wajen ganin ta inganta tarbiyata ta sama min
karatu, inda ta kai ni makarantar Allo da ke nan kusa da in da muke.Duk da cewa Unguwar babu irin
waɗannan makarantun sosai amma mu Ja'in ɗin in da muke zaune kamar 'yan gargajiya haka mu ke, I! to
haka ne mana tunda duk ba mu da kuɗi sai rufin asirin Allah da wadatar zuciya.

Na fara zuwa makarantar Allon sannu-sannu , Allah buwayi mai raba ni'imominsa ga bayinsa da ya tashi
raba ta masu ƙwaƙwalwa sai ya raba da ni ni ma na sami kaso na. Duk abin da zan yi in dai fannin karatu
ne to zan ɗauke shi a kaina duk yawansa.

Lokacin da na fara wayo sosai da sosai na kai shekara biyar na fara haddace alƙur'ani wanda na yi wajen
izu biyu, idan na dawo gida Mama kan min bita kuma mu kan yi bita tare da ya ke tana da nata ilimin
daidai gwargwado. Lokacin da na shiga shekara ta takwas a duniya ta yi iya bakin ƙoƙarinta wajen saka ni
a makarantar boko, Mama tana yin aikatau cikin wani gidan masu hannu da shuni, ta kan je da ni gidan a
lokacin akwai wata yarinyar Hajiyar gidan tana so na , za mu yi wasa tare duk da cewa ta girme ni a
shekaru , hakanan ko a jikin girma ba za ka haɗamu ba domin ta fi ni nesa ba kusa.

Wannan duk ina gaya muku ne ta jinsa da na yi bakin Mama duk da dai ni ma ina ɗan tuna wani abun
cikin yarintar rayuwata. Ba ta basu damar magana ba ta ɗora da,

"Haka rayuwa ta ke ta garawa yau da daɗi gobe babu, idan ya kasance ni da Mama ba mu halacci
gidan aikin ba to Safina ƴar Hajiya za ta saka a kawota ta yinar ma na, ko a zo har gida a tafi da ni
wajenta. Sai dai bamu san meke faruwa ba a iya wasu ƴan watannin da muka ɗauka da su babu wani
sauyi amma lokaci guda sai muka soma ganin canji wajen Hajiyar, zaman mu da su sai ya koma shigen
kalar na maƙiya mu koma zaman doya da manja. Guiwoyinmu ba sukammala sakewa ba sai da muka
wayi gari Hajiyar na sanar da mu ta sami wasu ƴan aikin dan haka ta sallame mu, ina kuka Safina na kuka
mu ka rabu.

Mai_ƙosai

*LOKACI NE*

(Gajeran Labari)

Mai_Ƙosai

FCWA

Biyar.

Rayuwa sannu a hankali ta soma yi mana zafi dan babu wani aiki da mu ke yi ko sana'a da za ta saka mu
sami kuɗi. Sai da mu ka yi a ƙalla sati uku a haka sannan Mama ta fara ka sa min kayan yara na soma
zama a waje ina saidawa ana ciniki sosai kasancewar yaran da ke unguwar, amma wani abin mamaki
lokaci guda kuma sai cinikin ya ɗauke wuta ɗif.

Ganin haka sai ya sa Mama ta koma saida Ƙosai ,ni ce mai zubawa idan anzo siya, ni zan kai mata
markaɗe da sanyin safiya, sai ya zamana karatuna ya fara wulagigi. Kamar wasa shi ma sai ciniki ya soma
habbaka siya ake yi ba kama hannun yara. Wani abu da zai kuma baku mamaki shi ne ; shi ma loakci
ɗaya aka ɗauke sawon siyansa, sai ya zamana duk abin da zamu kasa za a yi rububinsa da fari amma in
ya kai tsakiya sai ya daƙile, wannan ya sa Mama ta tattara komai ta watsar na koma makaranta babu
fashi, Allah ya so ma makarantar bokon ba ta kuɗi ba ce sai dai duk zango ana bada ɗari bakwai ko ta
mece ce oho! musu, mu dai sun ce mana kuɗin makaranta ne. Allo kuwa daman duk ranar labara ne ake
bada kuɗin laraba kuma naira ashirin ce.

Muna cikin haka wanda har mun ɗan soma rasa abin sawa a baki kasancewar kuɗin hannun Mama ya
taho gangara cikin ikon Allah Mama ta sami wani gida ta soma aiki tana musu wanke-wanke, da wannan
damar muka soma dawowa dai-dai.

Ina da shekara goma sha tara na kammala sikandire da taimakon Allah, da kuɗin da Mama ke samu
gidan aikinta. Sai na koma zaman gida ni kaɗai tun da Mama za ta tafi wajen aiki sai yamma take
dawowa, sai na soma jin kaɗaici sosai.

Ba zan taɓa mantawa ba lokacin da ina makarantar boko a lokacin aji na biyar gab muke da kammalawa
na kanji wata da'ira da aka haɗata cikin ajin yawancinsu masu shekaru da ɗan dama ne, ni dai bana shiga
cikinsu hasalima sai dai na ja gefe na duƙufa kan karatuna. Kuma yawancin hirarsu duk akan samari ne,
ko wacce in ta zo da irin na ta salon hirar da kuma wanda ta yi kamu da shi.

Tun maganarsu na ba ni haushi har ta soma ba ni sha'awa sai na ke ji inama ni ma na sami wanda zai ce
yana sona ya dace da ni, dan a ganina ai sai wanda kalarsa ta yi min sannan zan saurara har na yarje
masa zama saurayina. Sai ya zamana idan har su na hirar ko da karatu na ke yi to zan bari na dawo da
kunnuwana garesu.

Akwai wata da jininmu ya zo ɗaya muna gab da fita, sai ya zamana ashe ma unguwarmu ɗaya sai dai
akwai ƴar tazara mai ɗan yawa tsakanin gidanmu da na su.

Duk da ba ƙawancen kuzo mu gani ba mu ke yi ni da ita amma jin tana tsayawa da saurayi sai na kuma
shigewa jikinta sosai na kanje gidansu a sati sau uku zuwa huɗu.

A lokacin fa ina da shekaru goma sha takwas.In dai har saurayinta zai zo to ranar tarewa na ke yi a
gidansu da ni za a yi zancen ina maƙale da ita amma ni a tunani na wai ko ni ma zai ce ya na sona na ji
daɗi. Duk da sauyin fuska da nake samu daga gareshi kuma ba na damuwa dan ko ajikina wai an mintsini
kakkausa.

Duk yadda na so ta kai ga na ji an ambatamin kalmar so abin ya faskara, tun ba na damuwa har na soma
damuwa ,ina ganin mene ne aibu na in dai kyau ne ai ina da shi dai-dai gwargwado, dan ni dai banga
dame ƙawata ta fini ba hasalima zan iya cewa na fita komai na ƙirar jiki. Amma in kuka ga yadda maza ke
rubobinta ku kwace kayan marmari ci, abin ya kan riƙa ba ni mamaki na kan ji na tsani kaina , sai naga
kamar ni kaɗaice Allah ba ya so shiyasa ban sami saurayin ba.

Muna daf da kammala makaranta dan bai fi saura wata uku ba wani saurayi ya na ce min akan ya na
sona. A cewarsa dai wai ya ganni ne lokacin da nake dawowa daga makaranta shi kuma ya na ƙoƙarin
daidaita tsayuwar motarsa.

Ni kuma a lokacin har ga Allah ba na san shi, bawai dan ba shi da kyau ba a'a haka kawai ni bai min ba,
kuma ina jin yadda majalisar matan ajinmu na koɗa samarinsu akwai wacca ta ke cewa ma saurayinta
kamar ba ɗan Nijeriya ba kamar ɗan Indiya. Ni kuma sai na ji ina son na sami wanda ya ci uwar nata
komai da komai.

Ko wanne kalar wulaƙanci yi masa na ke yi amma bawan Allah ko ajikinsa , bai taɓa fushi da ni ba duk
kuwa irin abin da na ke masa.

Kamar kowacce rana an ta somu daga makaranta, bayan na iso gidanmu na iske shi jingine jikin motarsa
sanye da shadda ruwan ƙasa har ga Allah ta masa kyau sosai amma ni a lokacin ban ga hakan ba.

Ina zuwa ko kallonsa ban yi ba na doshi ƙofar shiga gida kai tsaye da sauri ya sha gabana tare da faɗin,

"Haba Hajara ,tun ɗazu na ke nan tsaye ina jiran isowarki amma kin ganni kin nuna kamar ba ki ganni
ba."

Harararsa na yi ka na na ce, "To sai me in na ganka, kai Annabi ne da zan yi ɗokin ganinka ko me.?"

Cikin sanyin murya ya ce,

"Ni ba kowa ba ne Hajara, amma ya kamata ki tsaya ki saurari abin da na zo miki da shi ko.?"

"To ubana Hashimu, ka ji bari na ɗakko maka tabarma sai ka tasa ni gaba ka ba ni darasi."

Na ƙarasa da shigewa cikin gidan na mu.

Ban ɗau lolaci mai tsawo ba na fito hannuna ɗauke da bokitin ruwa, ban tsaya wani jinkiri ba na juye
masa shi a jikinsa tare da tofa masa yawu tare da assasamasa babban gargaɗi na wuce ciki na barshi
wajen, ya tafi bai tafi ba oho! Masa ni dai hankalina a kwance. Kuma har kawo lokacin wannan lokacin
da nake baku labarin ba wanda ya tunkare ni da maganar so ko aure, amma ni sam ba na jin san shi
wallahi .

A kwana a tashi ba wuya wajen Alla, har ta kai mun kammala karatunmu har a lokacin babu wanda ya so
ni da aure ko soyayya, kuma har a lokacin shi ma bai daina so na ba, bai dai na bibiyata ba ni ma kuma
ban taɓa jin zan so shi ba , a lokacin da nake wannan haukan ban yi tunanin cewa lokaci zai zo min da
zan yi kuka ba, zan yi da na sa nin da ba'a saka mishi rana. Ni da ban da wanda ya ke sona amma wai ni
ce ke yiwa wani wulaƙanci.Har bayan kammala karatuna ya na manne da ni sai ka ce cingum, ka da ku yi
mamaki in na ce ni sam ko sunansa ma ban sa ni ba saboda ba ya gabana.

Wata safiyar Lahadi ce muna zaune ni da Mama tana tsefemin kai na sai ka ce ƙaramar yarinya wajen ƙin
tsifa haka na ke, ko da yake ma ai wasu yaran na santa. Amma zan iya cewa na fi wata yarinyar mara san
tsifa ƙinta sosai. Wani yaro ne ya kwaɗa sallama,Mama ce ta amsa ya yinda yaron ya ɗora da faɗin,

"Wai Hajara ta zo inji wani a waje."

CIkin sauri da ɗoki, bakina washe kamar gonar auduga na ce, "Je ka ce ga tanan zuwa."

Yana jin haka ya fice daga gidan da saurinsa. Na kalli Mama ina murmushi kafin na ce,
"Mama ni dai ki barmin tsifar na je na dawo." Na ƙarasa cikin shagwaɓe fuska.

Ƴar dariya ta yi kaɗan tare da furta, "Kya ci gidanku ja'ira, wato ko kunyata ma babu ko.?" Ta ƙarasa cike
da tambaya.

Ban amsa mata ba na fice da hanzarina bayan na ɗaure kaina ,alla-alla kawai na ke yi na isa naga wanda
ke kira na, sam kwata-kwata tunanina bai kawo min shi a wannan lokacin ba tun da bai taɓa aikowa kira
na ba duk tsawon lokacin da mu ka kwashe.

Ina isa na iske shi tsayi jikin motarsa, turus na yi tare da jefa masa wata arniyar harara ina mai jan tsaki.

Bakinsa washe kamar an masa albishir da aljanna ya iso gareni tare da faɗin,

"Barka da isowa gimbiyata."

Yatsina baki na yi kamar naga kashi ka na na ce, " Barka, me ya dawo da kai gidanmu, wai kai dan Allah
ba ka da zuciya ne? Ka fita daga shika-shikan sabgogina, na ce maka ba na sonka-bana sonka ko ana so
dolane?" Na jefa masa tambayoyi biyu a lokaci guda.

Allah sarki ɗan bawan Allah kai ka rantse da Allah babu zuciya a ƙirjinsa. Duk wannan bayanin da na
gama shimfiɗa masa amma murmushi kawai ya ke yi ya na mai kallona fuskarsa cike da nuna alamun na
tausaya masa ya ce,

"Dan Allah Hajara ki tausaya ki taimaka min, zuciyata gab take da tarwatsewa , ki daure ki sota ko da
sau ɗaya ne dan Allah."

Ya ƙarasa tare da haɗa hannayensa waje guda alamar roƙo.

Dariyar shaƙiyanci na yi ina mai kallonsa sheƙeƙe ka na na ce,

"Tabbas kuwa zuciyarta ka za ta yi bindiga ta tarwatse kamar yadda bam ya ke fashewa. Lallai ba
makawa zan zama lamba ta ɗaya daga cikin masu da sa mata bama-bamai a cikinta. Ka kiyaye ni, ka fita
daga sabgata." Na ƙyasta yatsuna biyu ina mai shigewa gida da sauri na barshi wajen tsaye.

Ina shiga Mama ta shiga tambayata ko lafiya, dalilin ganin da ta yiwa fuskata a haɗe.

Sai da na ɗan ja guntun tsaki wanda ba lallai na nesa ya iya jiyoshi ba sannan na ce,

"Wani mara zuciya ne a ƙirji Mama, na jima da sanar masa ni ba na san shi amma ya ƙi ji yadda ki kasan
kuturu wajen na ci, kuma wallahi.........."

*LOKACI NE*

(Gajeran Labari)
Mai_Ƙosai

FCWA

Shida.

Ta katse ni da sauri wajen faɗin, "Ke ƴar nan ki kiyaye ni Alƙur'an ,wanan wani irin tsantsar butulci ne?
Tun da na ke da ke cikin gidan nan waya taɓa zuwa ya ce a yi sallama dake? Amma yanzu kin samu shi ne
ki kewa Allah butulci? Ki ke wannan fiffiƙar? Ke ba ki ji kunya ba, ganɗai-ganɗai da ke gida zaune ba aure
bai sa kin ji wani irin ya nayi ba.?"

Fuska na haɗe ina mai kuma jin tsanarsa cikin raina, duk a kansa Mama ke min wannan wannan faɗan.

"Ni dai Mama wallahi ba na san shi har nawa na ke? Shekarun na wa nawa suke da za a ce ganɗai-ganɗai
da ni? Du-du-du fa sha tara zuwa ashirin ne fa, ni banga abin damuwa ba a kan hakan mijina zai zo sabo
dal a leda ƙin kowa san wand......."

Mama ta kawo min mangara dalilin da ya sa na yi shiru ke nan. Na yi saurin shigewa ɗaki, ni tsifarma ba
za a ƙarasa ba. Ina jiyo Mama na ta faɗa ta inda take shiga ba tanan take ɓullowa ba.

Wasa-wasa cikin sati biyu kullum sai ya zo, kuma duk san da ya zo ba wata magana mai daɗi tsakanina
da shi in ka cire masifa da tijara da na ke a sassafa masa su. Amma ko kaɗan bai taɓa yin zuciya ba bai
taɓa fushi ba kuma bai taɓa fashin zuwa ƙofar gidanmu ba cikin kwanakin.

Ban san ya a ka yi ba amma na ga su na takun saƙa da wani mai shagon unguwar mu wanda sam ni ba
ma shiri da shi. Da farko ma na za ta ko abota suke yi ashe shi mai shagon ɓakin ciki ya ke yi a kan zuwan
da shi saurayin ya ke yi ƙofar gidanmu, ya yi ta ɓata ni wajensa amma shi ya toshe kunnuwansa, baƙin
fentin da ya ke san gogamin yaƙi gogowa jikina balle shi ya ganni da shi. Na sami labarin ta wajensa in da
ya ke sheda masa mu ɗin zuwo ne ba a san asalinmu ba, sannan kuma ni shegiya ce , na ji zafin
kalmomin na sa wanda har wajen mai shagon na je na zazzage masa ruwa masifu na. Kuma na sake
baɗawa ido na toka ba na ji ,ba na ga ni na ce ni sam ba zan so shi ba."

Bayan wasu kwanaki kuma kamar a ƙalla sati uku sai na ji shi ɗif ya daina zuwa ban san dalili ba shi ya
san masa, amma ni sai na ji wani daɗi mai garɗi, a lokacin sai na ke ji na sakayau kamar wacca a ka
cirewa sarsari. Lokacin da na ke cikin nishaɗi na rabu da alaƙaƙai a lokacin ne kuma Mama ke cikin na ta
damuwar, ga yawan faɗa akan abin da na aikatana rashin kyautatawa, duk da ni ba na ganin hakan a
rashin kyautata masa da na yi. Zan iya ce muku ta shafe tsawon sati guda tana faman yi min faɗa, kuma
tana cikin damuwa na yi-na yi ta sanar mini ta ƙi. Ni dai abu ɗaya na sa ni in tana faɗan zan ƙirƙiri barcin
ƙarya ko kuma na ƙirƙiro fitar ƙarya dan wallahi ba na san faɗan Mama abin da ya faru da jimawa ma sai
ta dawo da shi lokacin.
Rayuwa ta ci gaba da garawa ,shekaru, watanni, satuttuka, kwanaki, a wanni, mintuna da sakanni suka
riƙa wuce wa. Kar ku yi mamaki in na ce shekara ashirin da biyu zuwa a shirin da uku babu wani saurayi
da ya zo gareni a matsayin batun aure ko soyayya bayan wanda ya taɓa zuwarmin harma mugun hali na
ya koreshi. A lokacin kuma ni ma sai hankalina ya soma ta shi, na ji ba abin da na ke sha'awa illa na gan
ni tsaye da saurayi ko da a ce ba da aure ba, abin ya na cimin tuwo a ƙwarya.

Mama ta kuma shiga damuwa sosai duk da ban san mece ce matsalar ta ba, hankalinta ya yi matuƙar
tashi. Dan kuwa duk in da ta gilma sai dai ka ji tashin gulmartana tashi a wajen ,habaici kam da zunɗe
waɗannan ba a maganarsu. Wasu ma fuska da fuska za su tare ta da faɗin,

"Ƴarta ta yi kwantai ,ai daman auren shege sai shege." fiye da waɗannan ma jin su ta ke yi. Ta kan yi
kuka fiye da misali wanda ni kaina ban sa ni ba sai lokacin da na dawo daga gidan ƙawata da na ke zuwa
ganin saurayinta baya, to ta yi aure ta aure shi harda yaro ɗaya, ina shiga gida na iske Mama hawaye
malala kan kumatunta, hankalina ya tashi sosai na shiga yi mata magiya akan ta sanar da ni damuwarta.

"Ina jin ɗaci ,takaici da tsantsar baƙin cikin irin mugayen kalaman da ake jifan ƴata da shi, ina jin ba daɗi
a lokacin da na ke ganinki gabana zaune a gida. Amma na san jarrabawa ce Allah ya ke yi
mana ,jarrabawa ce da Ubangijjn da ya samar dake ya ke miki, amma me ya sa za a dinga sheganta min
ke ƴa ta? Me ya sa za a dinga goranta min ke ƴa ta? Mene ne laifinki cikin ƙaddararki." Ta rushe da kuka
kafin ta ci gaba da faɗin,

"Yau zan sanar miki da abin da na jima ina ɓoye miki ko hankalina ya kwanta, kada kema wata rana ki
tambayeni ina ahlinki? Ina ne aslinki? Ka da wata rana ki tsare ni da tambayar ko dai da gaske ke ɗin
shegiyarce.?"

Ta ke na ji zuciyatana min zafi, daman da haushin faɗan da mu ka yi da ƙawatana taho gida a kan
goranta min da ta yi kan aure , Wai ni na cika yawo naƙi na yi aure na tsaya ruwan ido, shi ne zan dinga
bibiyarta dan na kashe matana ta aure, wa yasa ni ma ko auren mijin natana ke san yi?.

Ba ta san yadda na ji zafin kalaman na ta ba sosai, na ɗauka tamkar ƴar'uwa na ke wajenta ashe ni
kallon mahaukaciya ta ke yi min mai bibiyar maza har gida, mai zuwa ƙwacen miji har gidansa. Na share
hawayena na mayar da kunnuwana ga Mama da na ji tana furta."Ni da mahaifinki Hashim auren soyayya
mu ka yi sosai , duk da cewa akwai alaƙar zumunci tsakaninmu amma mu ba auren zumunci mu ka yi ba
auren soyayya ne. Kar na katse ki suna na Fatima kowa na ce min Asabe ni saboda ranar Asabar aka
haifeni. Kakana da kakan babanki uwa ɗaya uba ɗaya su ke ,ƙaddarar da ta gifta mana guda ɗaya ita ce
na rashin sona da mahaifiyarsa ta ke yi min,tun kafin auren ba ta sona, hakama bayan auren ba ta taɓa
nuna min ko da da ƙwayar zarrar ƙauna ba. Ba gida ɗaya mu ke ba, gidanmu da ɗan tazara ma
tsakaninmu da ita amma kusan kullum sai ta zo in da muke ta zageni tatas, da ya ke mahaifinki ɗan
tafiye-tafiye ne duk san da baya gari to za ta zo gareni zagi ta uwa ta uba kuma kullum sabon zagi ne zai
riske ni. Ban san me na tsare mata ba, aikin wahala kam duk yadda za ta so ta saka ni sai ta ƙaƙalo shi a
matsayintana uwa gareni zan yi komai ta saka ni in dai bai kauce hanya ba. Idan mahaifinki na gari har
wata ƙirƙirar kulawa ta ke yi min, har da aiken abinci tana yimin, ni kam ba na ci gaskiya. Yau da daɗi
gobe babu haka na ke rayuwa da ita, ban taɓa jin na tsaneta ba ko da sau ɗaya ne dalilin soyayyar
mahaifinki da ke cikin raina. Kamar yadda na taɓa gaya miki mu ƴan Jama'are ne cikin garin, duk in da ki
ka je ki ka ce"Babban gida" ba wanda bai san shi ba. Na sami sauƙin takurarta dalilin samuwar ciki a
jikina, duk da tana iƙirarin cewa cikin ba na mahaifinki ba ne, abin ya ruɗar da mu sosai ko mahaifinki sai
da ya girgiza, har sai da ya mata iƙirarin cewar a kan cikin zai iya kaita koto Alƙali ya ƙwato masa haƙƙin
sheganta masa ɗa ko ƴa da ta yi. Wannan sai ya sama mana sa'ada sai ma ta ɗauke ƙafa gaba ɗaya.
Mahaifinsa kullum ya kan nusarshi ganin ya ƙauracewa gidansu gaba ɗaya, ya kan kuma ƙara nuna masa
mahimmancin mahaifiya da haƙuri. Cikin da ke jikina ya kai wata bakwai zuwa takwas a lokacin kuma sai
wata ƙaddara ta faɗo mini, mahaifinki ya mutu bayan dogowar jinyar da ya sha duk da cewa ma ya
warke kuma a lokacin ba za ki taɓa ba kawo masa mutuwa ba amma Allah sarki bowaye gagara misali sai
ya amshi kayansa. Allah sarki mutuwa mai raba ɗa da mahaifi, mai raba masoyi da masoyi na yi kuka iya
kuka dan na san na rasa masoyi kuma uban ɗan da zan haifa ko ƴa. Bayan rasuwarsa da mako biyu
mahaifiyarsa ta ta sa ni gaba zagi, ƙyara ba a maganarsu kin san a lokacin ban yi arba'in ba ban kuma
haihuwa ba balle ace na fita daga takaba wannan ya sa ina gidansa, an so a ba ni wata ƙanwar kakatana
ce a'a ba na so na hutassheta. Duk abin da ta ke ba wanda ya sa ni, ni ma kuma ban taɓa gayawa kowa
ba sai san da mahaifinsa ya zo duba ni ba ta san ya na nan ba ta shigo ko sallama babu ta soma tijarart,
lokacin ya ji ya kuma taka mata burki amma wallahi duk da hakan ba ta daina ba. ko da ya sanar da
mahaifina yana raye amma mahaifiyata ba ta raye bai ji daɗi ba amma sai ya dake ya riƙa ba ni haƙuri.
Sati biyu ina shan baƙar wuya wajenta dan kamar tarewa ma ta yi a gidana to a cikin awa ashirin da huɗu
a wanni ƙalilan ne ba ta yi, kawai sai na ji kawai na bar mata garin shi ne zai fi. Wannan ya sa na tattaro
komatsaina na taho nan ba tare da sanin ahalina ba, ba kuma tare da sanin wa na sa ni ba, da wa zan
haɗu, na zauna ba da jimawa ba na haifeki na saka miki suna ba tare da yankan rago ba, na raineki da
akwai da babu. Abu ɗaya na ke so da ke shi ne ki zama mai haƙuri a cikin kowanne irin hali, domin kuwa
sai da haƙuri rayuwar ta ke kaiwa ga ko wanne irin ci. Ta yi shiru a wannan gaɓar.

"Mama dan Allah ki daina kuka, ni ba na damuwa da rashin aure na da wuri, na san komai lokaci ne, ban
damu da sanin ko wace ce ni ba, ina ahlina su ke ba, na san ba shakka mijina ya na tare da ni kuma zai zo
har in da na ke." Na ƙarasa faɗa ina mai share hawayen saman fuskata.

"Allah ya kawo lokacin." Mama ta furta iya hakan kawai.

Bayan kwana biyar da faruwar haka.

*LOKACI NE*

(Gajeran Labari)

Mai_ƙosai
FCWA

Bakwai.

Bayan kwana biyar da faruwar haka.

Tun ba na damuwa da maganganun mutane har abin ya soma damuna. Me ya sa mutane sun manta
komai da lokacinsa? Su waɗanda suka yi auren ai ba ikonsu ba ne ba, wannan duk cikin hukuncin
Ubangijine. Ban taɓa jin tsanar kai na ba da sai da na wayi gari ina tunano irin abubuwan da na dinga
aikatawa saurayin nan da ya na ce min ba(Abbas, wanda na ji sunansa bakin mai shago.)

Na kanji tsana mafi munin tsana a kan kaina, ina ma a ce ana dawo da hannun agogo baya tabbas da sai
na dawo da shi ko dan na amince da soyayyar Abbas, ko ni ma na samu na yi aure na huta da ɗan kiran
da ake min na mai baƙin jini, shegiya.

Na kan tuna wani lokaci da ya turo kirana na fita da ƙyar bayan Mama ta matsamin. Ina fita zuwa zaure
na laɓe jikin katanga ina hangoshi shida mai shago su na maganganunsu ni dai ban san me su ke
tattaunawa ba amma na ga fuskarsa ta sauya ba walawala wannan ya tabbatar min da cewa maganar ba
mai daɗi ba ce. Ni dai na taɓe bakina cigaba da kallonsu har lokacin da naga mai shago ya bar wajen ,na
juya ina mai ce masa wahalalle(Kullum na kan tuna da wannan kalmar.). Ina shiga gida Mama ta hau
tambayatana turo baki ina bata amsar sa har ta saka ta ke sanar min da wani saƙo,amma ni a lokacin
idona ya rufe sosai. "(Ki dai yi a hankali wallahi, ina jiye miki gaba.)" shi ne kalamanta. A she saƙo ta ke
isarmin ni ban yi zato ba.

Na kan yi kwana biyu a ɗaki ni kaɗai ina rusa kuka, duk san da kunnuwana suka riƙa tariyomin kalaman
mutane sai na ji ina ma a ce banzo duniyar ba. Mama tun abin na damunta har ya zame ma jiki, ta riga da
ta saba da maganganu.

Ranar da ba zan taɓa mantawa da ita ba, wacca ita ce ranar da ku ka haɗu da ni na haɗu da ku, ranar da
na wayi gari Mama na shirin yi min aure dole da wani mashayi, mutumin da ya so lalata rayuwata ya so
keta haddina, sanin ba zan iya zama da shi ba ga Mama ta kafe sai na yankewa kaina hukuncin guduwa
daga gida.

"Ta ya ku ka haɗu da shi?" Musbahu ya jefa mata tambayar.

Ta goge hawayen da suka mata shaɓe-shaɓe saman fuskarta ka na ta ce,

"Ban san ma ya na yi ba, ban ma san ya na so na ba, ba na manta randa na je shagon mai shago siyan
taliyar yara(Indomie) a wannan ranar na haɗu da shi, in da ya kafe ni da idanuwansa na masu shaye-
shaye yadda ka san tsohon maye. Ban san ya a ka yi ba har ya sami labarina kasancewarsa ba ɗan yankin
mu ba, a she wai zance na ya karaɗe ko ina na baƙin jinin da na yi ban yi aure ba, ni ban sa ni ba.

Ina kwance a ɗaki Mama ta shigo da yalwatacciyar fara'a shimfiɗe saman fuskarta, baki washe kamar
wacca aka yiwa albishir da aljanna.
"Tashi-tashi ma za-ma za kije waje ana san ganinki." Mama ta ce.

"San ga ni na kuma?" na tambayeta bayan na sa ki baki galala ina mai bin ta da kallo.

"I! Ma za tashi, yau dai Allah ya yanke ma na saƙarmu,lokaci ya zo."

Ba ta ba ni damar yin wata ƙwaƙƙwarar magana ba ,ta ta sa ni gaba har hanyar zaure bayan ta saka min
hijabina."

A waje na iske shi sai faman layi ya ke yi da alama ya sha ta yi mankas da shi.

Daf da ni ya ya tsaya ya soma magana cikin salo irin na ƴan shaye-shaye.

"Sanki na ke yi, kuma ni aurenki zan yi, na ji labarinki na yadda ki ka rasa mijin aure ,ga ki kuma shegiya
to zan rufa miki a siri ka da ki soma bin maza."

Ji na yi zuciyatana wata iriyar zaɓalɓala, ina ji kamar na saka mabugi na yi ta bugunsa har ya mutu. Ina
mai yi masa kallo irin wanda maye ya ke yi in ya ga abincinsa. Cikin ƙunar zuciya na ce masa,

"Ai kowa ya ga hasken rana ya san daban ya ke da na fitila. Da ni da kai sai a banbance waye zai
taimakawa wani, shi bakin rijiya ai ba wajen wasan makaho ba ne, bari ka ji na ƙara tuna maka wani abu
da ka kasa tunawa ita mace ba banza bazarar iskar damina ba ce, mutum ce mai daraja da ƙima, ba juji
ba ce da har kowa zai ce zai zuba iskancinsa a kanta, dan haka tun wuri ka san in da dare ya maka." Na
ƙarasa faɗa cikin tsantsar ɓacin rai, "Wai mai a ka mai da ni ne? Kawai dan ban yi aure ba sai kowa ya
riƙa juyemin iskancinsa?" Na tambaye kaina.

Na kammala tambayar da nufar cikin gida.

Ji na yi kawai an fizgoni ta baya take na hantsila na dira izuwa faffaɗen ƙirjinsa. Ya saka hannayensa ya
ƙanƙameni sosai, lokaci guda na soma ƙoƙarin ƙwatar kaina amma abin ya ci tura, duk kuwa da cewa
cikin maye ya ke. Ganin ba sarki sai Allah ya sa na gantsara masa cizo a kan hannunsa ɗaya wanda da shi
yafi riƙeni sosai. Ko sakanni ba a ɗauka ba ya cikani yana mai shafa hannun na sa. Da sauri na yi tsallen
taku izuwa cikin gidanmu ji na yi kawai an sake fizgoni da mugun ƙarfi har sai da faɗi ƙasa, kafin na
yinƙura na miƙe sai kawai ganin mutum na yi saman ruwan cikina, na yi bakin ƙoƙarina wajen ganin na
kubuta amma na kasa, tu ni na soma anbaliyar ruwan hawaye, cikin zuciyata ina mai addu'ar Allah ya
kubutar da ni daga kaidinsa. Ban san sa'in da algaitar maƙogaro na ta buɗe ba sai kawai na ji ina ƙwalawa
Mama kira da ƙarfin gaske. Saƙon ya isa gareta ta fito dai-dai lokacin da ya ke ƙoƙarin yaga min siket ɗina
yana mai danne ni sosai. Ji na yi na sami sauƙin nauyinsa ashe Mama ce ta kwaɗa masa kwano a tsakiyar
kansa, ina samun dama na shige gida a miliyan, ban jima da shiga ba Mama ta shigo tana sauke ajjiyar
zuciya, ni kam kuka kawai na ke yi na kasa cin komai har washe gari wanda a lokacin ne Mama ta tare ni
da maganar aurena da shi. "Aure na da mutumin da ya so lalata rayuwata."

Ta ƙarashe da matsanancin kuka, sai dai sautin kukan Aunty shi ya da kusar da na Hajara har ya saka su
bin Auntyn da kallo.

"Me ya sa ki ke kuka Aunty?" Hajara ta tambayeta cikin muryar kuka.


Ba ta tsagaita ba har sai da ta shafe sakanni sannan ta kalleta ba tare da kuma ta ce mata komai ba ta
fice daga ɗakin.

Musbahu ta kalla da san neman ƙarin bayani, shi ma hawaye na gani kwance kan fuskarsa, cikin salon
son basarwa ya shiga gogewa.

"Ki kwanta ki huta." Ya ce ya na mai ficewa daga ɗakin.

Sai ta ji ɗakin na juyamata, ji ta ke dama ba ta sanar da su labarinta ba,wata ƙila ta ɓata musu rai ne.

Sai dai saɓanin hakane wajen Aunty dan ji take kamar ta ta rayuwar ake tariyo mata, ganin raunin da
zuciyarta ta yi ne ya sakata gwammacewa ta fita.

Kai tsaye cikin mota ta shiga ta kunnata da sauri ,dai-dai lokacin Musbahu ya ƙaraso wajen idanuwansa
kanta ya ce,

"Aunty dan Allah kar ki soma tuƙa motar......." Ba ta ba shi damar ƙarasawa ba ta figeta a guje ta fice
daga asibitin. Shi ma cikin sauri ya fice daga ciki ya tare babur mai ƙafa uku ya bi sawonta.

Hajara kuwa ƙurawa ƙafar ɗakin ido ta yi, ta fi mintuna a haka tana tsammanin sake ganinsu sun dawo
wanda hakan ya gagareta ko da ƙiftawa dan kada ta rasa ganin shigowarsu.

A hankali ta janye idanuwanta daga kan ƙofar.

"Shi ke nan su ma sun gujeni." Ta furta hakan da wani irin furucin da ya sake karya zuciyarta.

*LOKACI NE*

(Gajeran Labari)

Mai_Ƙosai

FCWA

Takwas.

Kamar daga sama ta ganshi gabanta tsaye, ji ta yi ƙirjintana bugawa da sauri da sauri. Cikin san nuna
dakiya da jarumta ta furta,

"A'a kai ne ba sallama? Ƙaraso ma na." ta faɗa tana mai kallonsa.

Ya mutsa fuska ya yi yana mai raba idanuwansa kamar mai neman wani abu.

"Ina matata? Ina ki ka kaimin matata?" ya tambayeta.

"Har yanzu ni ma ba ni da masaniya a kanta." ta ba shi amsa a dake.


"Ki na nufin na rasata ko ya ya?" Ya tambayeta cikin gadara.

" Ka yi haƙuri, ina nan ina addu'ar Allah ya dawo maka da ita."

"In ma ba ki fara ba, to ki yi gaggawar farawa, ba na son harkar munafurci cikin lamarina, ko dai ma ke
kika saka ta guduwa ne? " ya ce.

"A'a ɗan nan, a kan wane dalili? Ni kaina na fi ka san na ga ta dawo ko dan........."

Ya katse ta ta hanyar faɗin,

"Ba na san kwana-kwana kamar kwalekwalen da ke fama da kansa a tsakiyar ruwa. Na ba ki nan da
wasu ƴan kwanaki idan ba ta dawo ba to lallai ke ce amaryar ta wa." Ya faɗa ya na mai ficewa daga
gidan, ya yinda ya bar Mama da zare idanuwa gami da dafe ƙirji.

Ajjiyar zuciya ta sauke mai nauyin gaske, tabbas ta ɗebowa kanta ruwan dafa kanta, tuni ta fara jin
nadamar abin da ta aikata, da ta san hakan za ta kasance da ba shakka ba ta yi masa alƙawarin auren
Hajara ba, amma ita ai a lokacin ga ni take kamar kuɓutar da ƴar ta ta za ta yi, me ya sa ba ta yi wannan
tunanin ba? Ga shi a dalilin hakan ta jefa ƴarta cikin gagari, ba ta san a ina take ba? tana raye ko a ma
ce?, Ga uwa uba ita kanta itama ta jefa tata rayuwar cikin hatsari tunda ga shi tana fuskantar
ƙalubalensa, lallai ba shakka tana cikin halin ƙa-ƙa-ni-ka-yi. Ta share ƙwallar da ta zubo mata, gaba ɗaya
jikinta ya yi sanyi kamar sanyin ruwan ƙanƙara.

***

Kariyar Allah ce kawai ta kai Aunty gida. Ba ta fi mintuna biyar da isa ba shi ma Musbahu ya isa,ganin
yadda ta yi fakin ɗin motar ya kuma tabbatarwa da kansa ba makawa ta soma samun fitar ya nayi. Cikin
hanzari ya ƙarasa cikin gidan kai tsaye ɗakinta ya wuce, da mamakinsa sai ya ga wayam ba tanan. Kamar
yadda tunanin inda zai sameta ya soma ratsa ƙwaƙwalwarsa hakance ta kasance. Keɓantaccen ɗaki ne
wanda babu komai a cikinsa sai gado da lokar ajjiye kaya(sif) sai jerin hotonan da ke maƙale a jikin
bangwayen ɗakunan ɗakin wanda aka ƙawata shi da su.

"Aunty " Ya faɗa da sassarfa. Juyowa ta yi a hankali jin amon muryarsa, idanuwanta sun kaɗa sun yi ja-
za-wur kamar an watsa barkono cikinsu.

"Dan Allah Aunty ki sami nutsuwa ko da ta sakanni ce." ya furta hakan.

Ji ta yi wasu ruwan hawayen sun kuma malala kan fuskarta a hankali ta zame jiki ta zauna gefen gadon
dake ɗakin.

Shi ma kallon hoton ya ke yi ya na mai sake jin ƙaunar mai hoton a ransa, tabbas da ana dawo da
mamaci to ba shakka da shi ne mutum na farko da zai soma dawo da ɗan'uwansa mafi soyuwa a gareshi
cikin wannan duniyar domin su ci gaba da kasancewa a tare cikin farin ciki da annushuwa.
"Aunty dan Allah ki daina azabtar da kanki, ki daina takurawa zuciyarki da ƙwaƙwalwarki na roƙeƙi." ya
yi furucin cikin sanyayyiyar murya.

"Dole ne na yi kuka Musbahu, ta ya zan manta da mutumin da ya yi mini tsantsar halacci cikin rayuwata,
ya so ni fiye da kansa, ya zaɓe ni cikin matana kasassu wacca tawayar ƙaddara ta mamaye su, ya zaɓi ya
yi rayuwa da ni duk da ƙalubalen da na fuskanta, ya bar duk wasu mata masu daraja, ƙima da tarin
mutunci, ya yi rayuwa da ni tamkar bai damu da kansa ba, dole ne na yi kuka iya kuka." ta ƙarashe cikin
wani matsanancin kuka.

Yana ji inama yana da damar da zai rarrasheta ,yana ji inama yana da damar sauya ƙaddara, yana ji
inama yana da ikon dawo da hannun agogo baya, yana ji inama duka waɗannan abubuwan ba su faru
ba.

"Aunty a duk lokacin da na ga zubar hawayenki na kanji kamar na riƙa zubawa kaina garwashi ya riƙa
zaizayar naman jikina. Idan ki na haka yaya ba zai taɓa gafarta min ba, ki tuna bamu da zaɓin da ya wuce
mu mayar da komai namu ga Allah, shi ne yafi mu son shi shiyasa ma sai ya ɗauke ma na shi dai-dai
lokacin da muke da buƙatarsa. Karki manta ko wanne abu da na sa lokacin muma lokacinmu zai zo kamar
yadda sauran bayi ke tafiya, ki sakawa zuciyarki salama, ki sakawa ruhinki aminci dan Allah."

Ya faɗa ya na mai haɗa hannayensa biyu da alamar roƙo.

Ji ta yi jikinta duk ya yi sanyi da kalamansa, amma ya za ta yi itama ba da san ranta ta ke shiga cikin
ƙuncin ba. Ba ta ba shi amsa ba ta miƙe ta fice daga ɗakin.

Bin ta kawai ya yi da kallo ya na mai kuma jin wani ƙaƙƙarfan tausayinta cikin ilahirin zuciyarsa.

Hannu ya saka yana mai shafa ɗaya daga cikin hotonan.

"Allah ya dawwamar da kai cikin rahmarsa yaya na." ya faɗa ya na mai ficewa da sauri.

A madafa ya isketa tana faman hada-hadar haɗa abinci kamar ba ita ce cikin wani hali a yanzu ba.
Murmushi kawai ya yi mata ya wuce ɓangarensa da ke cikin gidan.

***

Hajara kuwa har a wannan lokacin zuciyarta ba ta sami wata nutsuwa ba, tana jin ina ma ba ta sanar da
su komai game da ita ba wataƙila su cigaba da riƙeta har tsawon rayuwarta.

tana cikin wannan halin ne likita ya shigo . Ido suka haɗa cikin son cusa masa tausayinta har ya amince
da buƙatarta ta kafe shi da manyan idanuwanta.

"Likita ina buƙatar sallama a halin yanzu." ta faɗa a raunane.

Bai tanka mata baya shiga ƙoƙarin sauya mata robar ruwan dake maƙale hannunta zuwa wata.
"Ina buƙatar sallama Likita, ko kuma ni na sallami kaina da kaina." Ta faɗa a kausashe.

*LOKACI NE*

(Gajeran Labari)

Mai_ƙosai

FCWA

Tara.

Murmushi ya yi ya na mai sake dai-daita mata robar ruwan.

"Ba ki kamaci sallama a halin da ki ke ciki a yanzu ba." ya ba ta amsa.

"Ni dai ba na son zaman dan Allah ka sallameni." ta kuma faɗa.

"Bari ƴan uwanki su zo, su su ke da alhakin wannan." ya yi furucin.

"Ka ga Likita ni dai ka sallameni, ko kuma na sallami kaina kamar yadda na faɗa maka. Ba na son ɗorawa
kowa nauyin kaina ka sallameni kawai."

Ya sauke ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya ka na ya ce,

" Na ji zan sallameki, amma ki yi haƙuri ruwan ya ƙare saboda kema za ki fi jin daɗin jikin na ki."

Har ta buɗe baki za ta yi magana ya ɗora ya tsansa a kan laɓɓansa cikin kuma sauri ya yi furucin, "Dan
Allah."

Sauke numfashi ta yi, ta koma ta kwanta a hankali. Shi ma ganin haka ya saka shi fita daga ɗakin bayan
ya mata allura.

****

Dai-dai lokacin da Aunty ke sake shiryawa cikin dogowar riga ta atamfa ta yi matuƙar yi mata kyau sosai.
Aunty baƙar mace ce amma baƴin mai kyau, tana da dara-daran manyan idanuwa, tana da dogon hanci,
sai ɗan tsukakken bakinta ƙarami, tana da faɗin fuka sai sajen a ya kwanta gefen fuskarta luf-luf da shi.
Wayarta ce ta soma ruri alamar kira ne ya shigo. Hannu ta saka ta danna maɓallin ɗagawa tare da
karawa a kunnenta.
"Me ya sa ,to ga ni nan." Ta yi furucin da gaggawa tana mai sauke wayar daga kunnenta.

Sauri-sauri ta kammala shiryawar ta fice daga ɗakin. Madafa ta wuce ta ɗau ƙaramin kwandon da ta jera
kayan abincin da ta gama kammala shi.

"Musbahu fito mu tafi." Ta faɗa tana mai yin gaba. Jin maganar Auntyn ta sa ya saka shi saurin fitowa
daga sashen na sa. Tun kan ta ƙarasa wajen motar ta danna mabuɗinta da ke hannunta motar ta hau ƴar
tsiwa. tana zuwa ta buɗe ƙofar ɓangaren zaman direba ta ajjiye jakarta, ta koma baya ta buɗe ta saka
kwandon da ke hannunta,ka na ta dawo ta soma ƙoƙarin shiga.

"A'a Aunty dan Allah ki fito daga nan." Musbahu ya katseta ta hanyar kama murfin motar ya riƙe gam a
hannunsa.

Murmushi kawai ta yi, ta koma ɗaya ɓangaren mai zaman banza, shi ma shiga ya yi ya kunna motar yana
mai tura bakinta zuwa waje.

Mai gadi ya wangale musu makeken babban ƙyauren gidan, ya yi waje tare da ɗaukar hanyar asibiti.

Kaf cikinsu babu wanda ya ce wa ɗan uwansa uffan, Aunty kam tunani ne ya shiga kwanyar ƙwaƙwalwar
kanta tare da yi mata saƙa kala-kala kamar ƙulu da kwarashi, burinta bai wuce kawai ta isa izuwa
asibitinba.

Ba su ɗau wasu mintuna masu tsayi ba suka isa cikin farfajiyar asibitin. Dai-daita tsayuwar motar ya yi
suka shiga fitowa bayan ya kashe motar.

Lokacin da suka isa barci ta ke yi sosai, kuma hakan ya samo asaline dalilin allurar barcin da Likitan ya
danƙara mata.

Kallonta su ke yi cikin tausayawa, duk tabi ta rame sosai duk da dama ta jima a wannan siga ta ramar.

Aunty ce ta kalli Musbahu game da faɗin,

"Mu je ga Likita."

Har ya buɗe baki zai yi magana sai kawai ya ja bakin na sa ya tsuke, ya bita kamar yadda ta buƙata.

Yana zaune kan kujera, yana duba wasu takardu na marasa lafiya suka shigo bakinsu ɗauke da sallama.

Ya ajjiye takardun bayan ya amsa musu.

"Likita hankalina ya kasa kwanciya bayan kiran da na samu daga gareka, me ya ke faruwa?" Ta je fa masa
tambayar.

Sai da ya ɗan ja kujerar da ya ke kai baya kaɗan sannan ya ce,

"Na je zan sauya mata robar ruwa ta riƙa roƙona a kan na taimaka na sallameta, da na nuna hakan ba
zai yiwu ba sai ta tabbatar min da lallai ita da kanta za ta sallami kanta. Ganin hakan sai ya saka na
kirawo ki bayan na mata allurar barci ba tare da saninta, amma dai a ko wanne lokaci za ta iya farfaɗowa
dan ba mai yawa na mata ba."

Ya ida zancen yana mai kafe Aunty da idanuwansa jiran mai za ta ce.

Gaba ɗayansu sauke ajjiyar zuciya suka yi. Mushbahu ne ya yi ƙarfin halin magana gami da faɗin,

"Muna godiya Likata, kuma in sha Allahu ba za mu bari haƙanta ta cimma ruwa ba, mun yi alƙawarin
zama da ita, kulawa da ita a kowannen hali, kuma muna so kaima ka kula mana da ita fiye da yadda ka ke
mana."

"Kamar yadda ku ke a wajena haka ita ma ta ke, duk da na riga na fahimci iya abin da zan fahimta game
da alaƙarku, kuma na ji daɗin yadda ku ka nuna mata ƙauna, amma tabbas tana buƙatar hutu, sannan ya
na da kyau ta rage tunani."

"Hakane Likita tabbas alaƙarmu da ita ba ta wani jima da ƙulluwa ba, amma muna jinta kamar wacca mu
ka fito tsatso ɗaya kamar ƴar uwar junanmu." Gaba ɗaya Musbahu ya kwashe labarinta ya labartawa
Likita.

Likita ya tausaya mata sosai,ya kuma yi alƙawarin in sha Allahu zai taimaka mata da iya ƙarfinsa.

"In sha Allahu komai zai warware Likita." Aunty ta yi furucin.

Likita ya kuma jinjina musu da irin kyakkyawan taimakon da suka yi mata, ya sake yi musu alƙawarin ba
ta ingantacciyar kulawa fiye da yadda ake killace ƙwai gudun fashewarsa.

Sun ɗan tattauna sosai game da ya nayin jikin nata, wanda ya kwashesu wajen kimamin rabin awa su na
taɓa kiɗa taɓa karatu. Sai daga baya suka ɗunguma zuwa ɗakin na ta dan ganin ko ta farka. Su na tura
ƙofar suka ga wayam babu alamunta, Aunty kam ta fi kowa shiga cikin tashin hankali.

*LOKACI NE*

(Gajeran Labari)

Mai_ƙosai

FCWA

Goma ɗaya.

Da sauri Likitan ya ƙarasa jikin gadan nata ya shiga duba ya nayin yadda aka cire robar ruwan.

"Ba ta yi nisa ba, in mu ka yi sa'a za mu iya cimmata." Likitan ya faɗa.


Cikin sauri suka fice daga ɗakin, kai tsaye harabar asibitin suka nufa, har Musbahu na ƙoƙarin ficewa
daga cikin asibitin zuwa waje ya hangota jikin babbar ƙofar fita tana rakuɓe-rakuɓe da alama hanyar fita
ta ke nema ta fice yadda ba wanda zai ganta. "Me ya sa za ki aikata haka?" Ta ji saukar aradun muryarsa
na jefo mata tambayar da ya yi a bazata lokaci guda maganaɗisun kunnunwanta suka naɗo mata sautin.
Bai ba ta damar magana ba ya ɗaura da faɗin,

"Kin san cikin tsantsar adadin tashin hankalin da ki ka jefamu? Me ya sa ? A kan me?"

Ya juya ya na mai ƙwalawa su Aunty kira, da sauri suka ƙaraso wajen. Hannunta kawai Aunty ta kama ta
shiga janta zuwa ciki. Har sai da ta direta kan gado cikin ɓacin rai ta soma faɗin,

"Kin san adadin tashin hankalin da ki ka jefamu ciki? ? Ina za ki je? Mece ce ribarki a fitar idan kin yi?"

Cikin sautin kuka Hajara ta ce,

"Dan Allah na roƙeƙi ki yi haƙuri, amma ni na fison na tafi yadda bazan taɓa ɗora muku nauyi na ba, ba
na so Mamana ta same ni dan muddin ina garin nan to lallai ba shakka za ta samo ni, ni kuma ba naso na
aure mashaye." ta ƙarasa cike da sakin wani marayan kuka.

"To sai me idan an nemo ki? Ba dai auren mashayi ne bakya so ba? To ni nan zan tsaya miki har sai inda
ƙarfina ya ƙare, amma tafiyarki ba za ta sakawa zuƙatanmu salama ba, tafiyarki mugun laifine wanda ba
zai taɓa goguwa a wajenmu ba, ki na ganin kin fi kowa shiga cikin matsalar rayuwa? Saboda ba ki saurari
rayuwar wasu ba ne. Rayuwata akwai kamanceceniya da taki sai dai akwai banbanci mai tarin yawa
acikinta, ki godewa Allah baki ɗanɗani zafi mafi zafi acikin rayuwarki ba, kin san irin wahalhalun da na
sha? Kin san irin gwagwarmayar da na sha a tawa rayuwar? Kin san irin faɗi-ta-shin da na dinga yi? Ban
da ra'ayin sanar da kowa tawa rayuwar amma saboda ke yau zan fayyace miki wani sirri da na jima ina
ɓoyeshi cikin zuciyata, ƙaddarata da taki akwai kamanceceniya amma ke taki akwai wasarereniya a
cikinta, ki buɗe kunnenki da kyau ki saurari abin da zan sanar miki a yanzu." Ta ɗan numfasa tare da
goge hawayen da suka soma ziraro mata kafin ta ɗora da faɗin,

"Suna na KHAUSAR AUWAL MAHMUD, mace mai kimanin shekaru talatin da ɗaya a yanzu.Mahifiyata
Jamila Usman muna ce mata Umma. Na ta so gaban iyayena duka biyun cikin so da ƙololuwar kulawa
garesu. Mu biyune kacal wajen iyayenmu daga ni sai ƙanwata SALIMA mai kimanin shekara ashirin da
ɗaya a yanzu wanda na bata tazarar shekaru goma cif kafin ta zo duniyar.

Zaune muke cikin garin Kano,unguwar Sharaɗa.Cikin unguwa mai yalwar jama'a sosai.

Na yi firamari na a makarantar kuɗi duk da dai kuɗin ba wai na kuzo a gani ba ne, bamu da wata tazara
mai nisa tsakanin gidanmu da makarantar a ƙafa nake tafiya na ke dawowa. A cikintana yi sikandire na
tun daga aji uku zuwa aji shida. Lokacin da na kammala karatun sikandire na ƙanwatana kan ganganiyar
karatunta, lokacin ne kowa hankalinsa ya dawo kaina dangi uwa da na uba kowa ya saka min na
mujiyarsa wato ido, kacokam suka maida hankalinsukaina akan ganin na yi aure ni kam har ga Allah na fi
son na ci gaba da karatuna. Sa'ilin da na jewa da iyayena maganar sai suka nuna sam ba suso aure shi ne
ya fi dacewa da ni a lokacin.
Ina son karatu sosai amma jin furucinsu sai kawai na haƙura na fawwalawa Allah komai, sai na ci gaba da
zuwa makarantar Islamiyya tun da har lokacin ba mu yi sauka ba, a lokacin ba zan haura shekara goma
sha takwas da ƴan watanni ba.

Na mayar da hankali sosai wajen karatun Islamiyyata dan har hadda na soma yi tunda na sami isasshen
lokaci. Ba inda na ke fita daga makaranta sai gida sai dai idan aikena Umma ta yi shi ma sai ta
kama ,amma bayan wannan ni ba za ka taɓa tsinta ta a wani wajen ba.

Lokacin da muna aji shida a sikandire sautari mu kan yi zancen samari kowa za ka ji ya na magana akan
abu biyu ne; karatu da aure ,ni dai har ga Allah na fi son karatu dan ba abin da ke raina illa na ga na yi
karatu mai zurfi, shiyasa ni ko samari ba sa gabana, duk da cewa ma ni ba wanda ya taɓa tarar gabana da
maganar so ko ƙauna.

Kuma hakan bai taɓa damuna ba balle na ji wani abu a raina, ko na ji wai cewa ni bani da farin jinin
samari sam hakan bai ɗa-ɗarani da ƙasa.

Har a ka ci shekara da wata biyar da kammala karatuna ba wanda na taɓa cin karo da shi da sunan ya na
so na, maganganu suka soma yawa daga ɓangarori biyu na dangi na wato na uwa da na uba, duk da
Baba ya kan ce min shi ma ya ga ji da gani na gida ya kamatana fito da miji na yi aure maganganunsu na
cewar ya zuba min ido ya ƙi aurar da ni sai suka ƙara tunzura Baba akan lallai na fidda miji na yi aure ko
ya fidda min, kusan sati ya na min faɗa a kan wai ina korar samari shiyasa har yau ba wanda ya zo neman
aurena. Karfa kuce shekaruna sun wani ja a lokacin tunda ban fi sha tara zuwa ashirin ba. Ni dai haƙuri
na ke ba su sai kalma ɗaya da kullum taƙi barin baki na wato (Lokaci ne) ai daman komai lokaci ne haka
zalika ni ma auren nawa lokaci ne kuma zai zo, kamar yadda idan lokacin mutuwarka ya yi za ka tafi ba
tare da ƙarin ko da sakan ɗaya ba.

Ganin ba sarki sai Allah ya saka Babanmu yankomin takardar zana jarrabawar JAMB, bayan ta fito na
samu adadin makin da mai neman karantar ɓangaren shari'a ya ke samu daman ina son harkar shari'a na
ji daɗi sosai na sami gurbin karatu a makarantar kwalejin F.C.E da ke garin Kano. Na mayar da hankali na
sosai kan karatun. Wata ƙudurar Allah kuma duk wani abin da zai haɗa ni da namiji to ɓangaren karatu
ne ko mutunci shi ma iya makaranta ne amma ba wanda ya taɓa tarata da sunan soyayya ko alaƙa mai
zurfi. Ni kuma daman ban wani sa a ka ba, hakan sai na ji na fison kaɗaicinma ko babu komai na samu na
yi karatuna sosai yadda Baba ba zai ce a ajjiye karatun ayi auren ba. Bari na gajarce muku rayuwata ta
makarantar saboda ba wani abu ne ya faru cikin rayuwarba in banda ƙalubale kan karatun wanda kusan
kowa ya kan sami kansa cikinsa sai dai na wani ya fi wani, wani daga ɓangaren malamai ne wani kuma
wajen karatun ne inma ta fahimtarsa ko aka sin haka , ko kuma ta ɓangaren kuɗi.Duk da iyayena su na
ganin kamar zan fi samun masu neman aurena a can, sai dai har na kammala babu wanda ya tunkareni
da hakan ko da cikin makaranta ko waje.

*LOKACI NE*

(Gajeran Labari)

Mai_ƙosai
FCWA

Goma biyu.

Bayan 'yan watanni da kammalawata wata rana ina zaune mahaifiyata ta tasa ni a gaba kan zamuje wani
gurin wani malami dan nemamin taimako, wataƙila ko Allah zai saka mijin aurena ya zo, dan ta lura
kamar ko ina da matsala ne ko kuma dai an saka min hannu, dalilin ganin hakan da take yi bai wuce
nasaba da ganin ƙanwata ta sami mijin aure ba wanda auren ya rage ƴan watanni ƙalilan.

Banso jin furucinta ba koba komai ai komai nufine na Allah, kuma a kullum ba na cire rai daga saukar
rahmarsa izuwa gareni, wataƙila lokaci na ne bai yi ba shiyasa mijin nawa bai zo ba amma sukam sun
gaza fahimtar hakan. Ina ji ina gani Umma ta tasa ni gaba zuwa wajen malamin ni kuma ba zan taɓa
ƙetare umarninta ba. ko da mu ka je na saki jiki sosai saboda na ga baimin kala da wanda ya kaucewa
hanya ba dalilina kuwa na faɗin haka shi ne; yadda ya ke ta kwantar mana da hankali akan komai lokaci
ne kuma zai zo, sannan ya ɗorani kan wasu addu'o'i ya kuma bani tofi na dawo gida ina yi, ya tabbatar
mana da ko da ace da shaiɗanu ma in sha Allahi komai zaizo da sauƙi tunda mun miƙa lamuranmu ga
Allah buwayi gagara misali. Wata guda da farawa muka kuma komawa wajensa nan ya kuma bani
turaruka ya ce na dinga hayaƙi da su, ya kuma ƙaramin da wasu addu'o'in. Babu fashi kullum sai na
aikata duk yadda ya ce dan kuwa Ummace za ta tasa ni gaba sai na yi sai abin ni ma ya zame min jiki ko
da ta sakani ko ba ta sakani ba to zan yi. Na shafe wajen wata uku ina amfani da su kuma har lokacin
babu wani wanda ya zo ko da ƙofar gidanmu ne da sunan soyayya da ni balle ga aure. Ni kuma a lokacin
sai na riƙa jin gabana na faɗuwa na fara jin na fara yadda da maganganun mutane na cewar lallai aljanin
dare ne ya aurene, hankalina bai sake ta shi ba sai sa'ad da na tsinci kaina a gida ni kaɗai bayan auren
ƙanwata da a ka yi gidan sai ya zamana daga ni sai Umma, Baba kuwa daman ya na wajen aiki sai dare ya
ke dawowa, na shiga cikin kaɗaici sosai. Idan na je gidan ƙanwata kuwa na dawo da tunanin ni ma naga
na wayi gari na yi aure na ke kwana cikin zuciyata, wannan dalilin ya saka sai na ƙauracewa gidan nata
gaba ɗaya in dai ba Umma ce ta aiki ni ba ,shi ma dan ba yadda zan yi ne amma da da hali ba zan je ba.

Wani abun takaici, al'ajabi da mamaki da ya faru gareni wanda ba zan taɓa mantawa da shi ba, lokacin
na yi kuka iya kuka, ban taɓa zatan hakan za ta kasance da ni ba kun san mene ne?

Ta katse musu zaren labarin ta hanyar jefa musu tambaya,ba kuma ta basu damar amsawa ba ta ɗora
da faɗin, wanda su ma ba su damu ba daman gyaɗa kai kawai suka yi.

"Na shafe shekara uku da kammala karatuna har na soma koyarwa a Islamiyyarmu wacca ita ma mun
jima da saukewa. Kwatsam wata rana bayan na dawo daga makaranta ina dab da shiga gida bayan na
karyo kwanar shiga layinmu na tsinkayo muryar wani matashin saurayi na faɗin,

"Ga tanan ta dawo."

Wani daga gefensa ya jefo masa tambayar , "Wace ce?" Na kuma tsinakayo muryarsa na kuma furta,

"Ta rasa mijin aure ma na." ya ba shi amsar tare da sakin wata dariya.
"Ta rasa mijin aure kuma?" Ɗayan ya sake jefa masa tambaya.

Ya bushe da wata mahaukaciyar dariya tare da furta

"Caab! au wai kai da ba ka sa ni ba,gaskiya an barka a tasha ai wannan ina gaya maka kaf cikin layin ita
ce kwantan-kwantai in ban yi ƙarya ba za ta kai shekara ashirin da da tara gaban iyayenta, kuma ka
gantanan bata da niyyar aure, kai zance maka ma ba wanda ya nuna ta yi masa balle ya ce zai aureta.
Shiyasa na ce maka ta rasa mijin aure."

Ɗayan ya ja numfashi kafin ya ce, "To kai ba saika aureta ba." ya jefa masa maganar a ba zata.

"Tuuf! " ya tofar da yawon bakinsa kafin ya furta,

"Allah ya kiyaye na aure wacca ta yi kwantai wallahi, ai ni bari ka ji yarinya shakaf zan aura sabuwa
dalleliya wacca ba ta tsufa ba kamar irin ƴar shekara sha bakwai zuwa sha takwas, kai inma sha shida ce
zan aura kai mai zai ha na ka aureta." Ya mayar da masa da tambayar kansa.

"Ah! haba kaima ka san faɗa kawai ka ke yi, me zan yi da ma shekaru ashirin da........" Ban tsaya jin
ƙarashen zancen na su ba daman tsautsayi ne ya sa na tsaya ashe zanji mugun zance a kaina, na faɗa
gida ina matse hawayen cikin idanuwa na, zuciyatana dakan lugude, mene ne laifina a ciki dan na kai
waɗannan shekarun ban yi aure ba? Mene ne laifina a ciki dan na kai iyanzu ban sami mijin aure ba?
Shin ni na kar zoman ko kuma rataya a ka bani? Na ga dai komai na rayuwa ɗan lokaci ne, kuma komai
nufi ne na Ubangijin Sammai da Ƙassai. Ƙaddararta ce ai kamar yadda kowa ke da tasa ƙaddarar mai
kyau ko mara kyau,to me yasa za su dinga jifana da waɗannan kamalan? Wane laifi na aikata musu da za
su dinga mun zunɗe? Wane laifi na aikata musu da zai saka su tsaneni su riƙa nunan ƙyara? Na rushe da
matsanancin kuka wanda har sai da ya ankarar da Umma hankalinta ya dawo kaina, ta soma tambayata
lafiya? Me ya faru?.

Ina kuka na shiga faɗin, "Umma me ye laifina a kan hakan? Me yasa za su riƙa jifana da mummunar
kalma mara daɗi kawai dan ban yi aure ba? Wane laifi na aikata haka?."

A zato na Umma za ta mara min baya, amma sai naga ta kalleni sheƙeƙe kafin daga bisani ta ce,

"To ai sai ki yi zuciya ki yi auren kinga sai ki samawa kanki sa'adar hakan." Ta fice daga ɗakin tana jan
tsaki.

Ni kam kukana ya kuma tsananta lokacin da na ji furucinta. Me ya sa za ta ce haka alhalin ba ni na yi


kaina ba?. Ranar a haka na ƙarasa yini na cikin kuka kaina in banda sarawa na ciwo ba abin da ya ke min.
Cikin dare na ta shi na soma gabatar da sallah ina mai kai kukana izuwa wajen Ubangijin da baya barci
balle gyangyaɗi. Kusan kwana na yi ina ibada ban san sanda barci ɓarawo ya kwasheni ba.

Kwana biyu ina cikin kaɗaici da jimamin abin da ya wakana gareni cikin raunanniyar zuciyata, sai na ke jin
kamar na daina fita gaba ɗaya gudun sake tsinkayo makamantan kalmomin, sai na daina zuwa
Islamiyyar. Amma da naga koba komai ai tana ɗebemin kewa sai na koma.
Cikin kwanaki uku da komawata sai na sami ƙawa duk da a girme na girmemata dan ba ta fi sa'ar
ƙanwata ba, unguwarmu ɗaya sai dai muna da tazarar layi na gida. Zuwan da banyi ba kwana biyu shi ne
aka miƙa mata ajina da na ke koyarwa da na dawo kuma a ka ce mu ci gaba da zama a tare. Na yi murna
sosai, duk da ban wani cusa kaina wajenta ba amma ita haɗuwarmu da ita ta farko ta soma san shigewa
jikina har Aunty ta ke cemin, ni ma ganin hakan sai kawai na bada kai jiki ya hau bori.

Cikin ƴan kwanaki ƙalilan muka zama abu ɗaya, duk da ni a cikin waɗannan kwanakin ina fama da
matsananciyar damuwa, wacca har ya saka ta gane halin da na ke ciki dalilin kasa ɓoye damuwar tawa.
Tuni ta soma tambayata gami da haɗin da ta ganni, tana roƙota haɗi da haɗani da girman Allah da na
sanar da ita damuwata.

*LOKACI NE*

(Gajeran Labari)

Mai_ƙosai

FCWA

Goma uku.

Muna zaune a aji, tana biyawa ɗalibai darasi. Ni kuma gefe guda na lula duniyar tunani wanda har ban
san sa'ilin da ta ƙaraso kusa da ni ba har ta zauna, jin hannayenta kan lafaɗata ya sakani dawowa
hayyacina har na sauƙe tagumin da na yi ina mai kallonta.

Da murmushi kan fuskarta ta soma faɗin,

"Na jima da sanin cewa kina cikin damuwa Aunty domin kuwa labarin zuciya a tambayi fuska. Amma ina
ta bibiyarki amma kin ƙi sanar da ni, nasan ba ni da damar da zan iya yaye miki damuwarki, amma na
gamaki da girman zatin Allah ki sanar da ni ko na sami salamar ruhina, ban sa ni ba ko da akwai abin da
zan iya taimaka miki da shi."

Sai na ji zuciyata ta karaya ta yi rauni idanuwana suka kawo ruwa, ban san lokacin da na shiga fayya ce
mata abin da ke damuna ba.

Sai kawai naga tana hawaye, ina kuka itama sai ta rushe da kukan, ni ina kukan baƙin cikin halin da na
tsinci kaina ita kuma tana kukan tausayawa rayuwata, mun ɗau tsawon lokaci mai yawa kafin na ji ta
furta.

"Ki yi haƙuri Auntyna, komai lokaci ne idan ya zo babu mai sauya shi, in sha Allahu lokacinki ya kusa
zuwa."

Ban tofa mata ba sai kawai gyaɗa kaina da na yi. Har aka tashi tana mai bani baki, ko da muka isa
unguwarmu sai da ta rakani har gida kamar wata makauniya haka ta yi min jagora sannan itama ta wuce
na su gidan.
Tun daga lokacin kuma kusan kullum sai ta zo gidanmu,ta kan kai kusan Azahar take tafiya shi ma dan
zuwa makarantane wani sa'in ma da shirinta take tahowa sai mu wuce daga gidanmu.

Sosai take ƙoƙarin ganin san ta farantamin ta kuma saka ni cikjn farin ciki da walwala. Shaƙuwa mai tarin
ƙarfi ta shiga tsakanimu sosai, sai kuma jama'a suka soma ƙoƙarin ganin sun rabamu wai itama za ta rasa
mijin aure in tana tare da ni, amma kuma Allah bai nufa ba. Lokaci guda suna na ya rikiɗe daga Khausar
zuwa Ta rasa mijin auren, ko da kwatancan gidanmu ka ke nema daka tambayi haka za a nuna maka.

Na ci gaba da rayuwa cikin wannan halin na ƙunci dan ma dai Rabi'a na ɗebe min kewa.

Amma in dai magana ce tsakanina da Umma to ba ta wuce ta tsuniyar gizo, koyaushe maganartana fidda
miji na yi aure, ita ta gaji da ganina gabanta goɗai-goɗai da ni. Baba kuwa dai a yanzu ba ya ce min komai
domin kuwa dare ne ke dawo da shi wani sa'inma sai tara na dare zai shigo ko goma, ni kam kafin ya
dawo ma na yi barci ko da bai zo ba zan ƙirƙiri kayana. Cikin dare na tashi na yi sallolina na roƙi Allah a
kan ya kawomin ɗauki.

Sakanni, awanni, kwanaki, satittuka, watanni na shuɗewa cikin abin da ba a tunani sai ga shi an shafe
wata uku da raɗamin sunan da ba yankan rago. Abin har yabi jikina na saba da amsa sunan tun ina
damuwa har na daina damuwa. Umma ta ɗakko mai Ruƙya ya min karatu wai ko dai dai aljanine ya aure
ni mai taurin kai. Duk kuwa da cewa na sha magunguna amma shiru ka ke ji kamar anci shirwa. To shi ma
hakance ta faru ba irin karatun da ba amin ba amma ko gezau ban yi ba, sai kawai ta tattara komai ta
watsar amma kusan ko dayaushe sai ta jefo min maganar aure na fidda miji na yi aure.

Kwatsam a na haka wani malamin da muke koyarwa a Islamiyya wanda bai jima da zuwa ba dan baifi
wata ɗaya da sati ba ya nuna ya na sona kuma so na aure. Na so ƙin amincewa da shi amma da na tuna
wataƙila Allah majiɓancin lamuranne ya turo min shi a bisa amsa addu'ata da ya yi sai na amince masa
gudun kada na zama butulu ga Ubangijin talikai.

Ya zo har gidanmu ya nemi izinin Baba kuma ya yarje masa. Wajen iyayena kuwa farin ciki cikin
zuƙatansukamar su zuba ruwa a ƙasa su sha.

Soyayya mai ƙarfi ta ƙullu tsakaninmu Kullum zai kirani a waya sau babu adadi tun ba na biye masa har
na fara sabawa da kiran nasa. Rabi'a kam ba ƙaramin farin ciki ta yi ba mara misaltuwa ganin na sami
mijin aure. Takan ce min,

"Aunty ni na sani ko wanne abu da lokacinsa. Kamar yadda Mutuwa, Rayuwa da Haihuwa su ke da
lokacinsu, nasan koman daran daɗewa lokacin zai zo kuma ga shi Allah ya kawo shi. Daman an ce mai
haƙuri ya kan dafa dutse harma ya sha romansa."

Ni kam murmushi ne kawai nawa, na kan yi mata addu'ar Allah ya kawo mata miji da wuri kada ta zauna
irin zamana a gaban iyayenta.

Ƙanwata ta min murna sosai da sosai, duk da fushi take da ni a kan na yi wata biyar ba na zuwa gidanta,
da ƙyar muka sasanta da ita. Ni kam bana son zuwa ne saboda gudun sake faɗuwar gabana ,kuma koba
komai ni fa yayarta ce ai bai kyautu na dinga yawaita kai mata ziyara ba.
Wata shida bai rufa ba da haɗuwarmu ya kawo kuɗin aurena, Baba ya yi bincike iya bincike bai ci karo da
wata mummunar shaida a kansa, sai hankalinmu ya kwanta fiye da zato. Shekara guda a ka saka
aurenmu da shi ,ranar yini na yi ina tasbihi ina tsarkake Ubangijin talikai.

Wata rana muna zaune a aji muna hira da Rabi'a,duk da kwanakin ba su wani ja da yawa ba bayan saka
ranar da aka yi. Na jiyo wani mugun fitsari ya ciyo ni har marata sai da ta murɗa. Na kalleta ina ɗan cize
laɓɓa tare da ya tsina baki.

"Ya ya dai? Me ya faru Aunty? Ta watsomin tambayoyin.

Na kuma ya tsina baki sai ka ce al'adata ka na na ce,

"Ke dai bari ɗan zawo ne ya sako saƙonsa."

Ta yi ƴar dariya dan ta fahimce zance na sannan ta ce,

"To ai sai ki je ki kai saƙon. Amma kya bari yaran su dawo ko?"

Na gyaɗa mata kaina.

Da yake yaran in su na waje bama shiga bayin har sai an dawo da su daga sallar la'asar ɗin da ake fita
dan mu samu mu sake,duk da cewa banɗakin malamai daban da na ɗalibai. A she a wannan ranar a
wannan makaranta wani gagarumin bujimin tsautsayi ke kirana ban sani ba, wata ƙaddara za ta kuma
gifawa rayuwata shiyasa fitsari ya yi halinsa har na kasa riƙeshi balle in na koma gida na amayar da shi.

*LOKACI NE*

(Gajeran labari)

Mai_ƙosai)
FCWA

Gima huɗu

Na barta cikin ajin bayan dawowar yaran ,ita kuma ta kula da su,ka na na wuce zuwa idda nufi na.

"A she daman wanda ka ke so ka yarda da shi zai iya cin amanarka.?" Ta je fa musu tambayar cikin kuka.

"Fiye da zato Aunty wallahi." Hajara ta bata amsa.

Ba ta sake wani furucinba ta ɗora da faɗin,

"A she lokacin da na zagaya bayi a kan idanuwan malam ne wanda muke soyayya da shi har aka saka
mana rana. Na buɗe ƙofar bayin bayan na kammala abin da ya kawo ni da nufin fitowa na koma ajin sai
kawai mu ka yi ido huɗu da shi tsaye ya harɗa hannayensa biyu saman ƙirjinsa. Ba tare da na yi magana
ya sakar min murmushi mai wuyar fassaruwa. Ina ƙoƙarin raɓashi na wuce ya saka hannunsa ɗaya ya
taroni, na haɗe fuska da nufin magana sai kawai ji na yi na shaƙi wani abu ,ban fi mintuna ba na sulale
jikinsa idanuwa na a buɗe ina kallonsa amma ba zan iya cewa komai ba, dan komai nawa ya daina motsi
ya saki. Ina ji ina gani ta ketamin haddina ,ba ni da ƙarfin da zan iya hanashi, ƙarshe sai buɗe idanuwa na
yi na ganni kwance gadan asibiti.

Na yinƙura zan tashi na ji wani zafi ya ratsa ilahirin ƙasana fiye da tunanin mai tunani,fiye da yadda
dalma ke mannewa jikin mutum.

"Sannu Aunty kin farka?" Na jiyo muryar Rabi'a na jefomin tambayar.

Da ido nake bin ta da kallo,sai a lokacin kuma naji kaina na juyawa dai-dai lokacin ƙwaƙwalwata ta shiga
tariyomin abin da ya faru da ni idanuwana suka soma haskomin komai tamkar lokacin abin ke faruwa.
Hawaye masu zafi suka soma malalowa kan kumatuna, na fashe da wani matsanancin kuka ina mai kifa
kaina jikin filon dake kan gadan da nake kwance.
Ganin haka ya saka Rabi'a matsowa gareni da sauri tana mai riƙe hannuna ɗaya tare da shafa bayana
cikin nutsuwa.

Mun ɗau tsawon mintoci a haka kafin ta miƙar da ni zaune sai kawai na rungumeta ina sake fashewa da
wani kukan.

"Aunty dan Allah kada ki zama ɗaya daga cikin bayin Ubangiji marasa yadda da ƙaddararsu,ka da ki saka
imaninki yin rauni. Ki zama baiwa mai godiya ga Allah sai ya sake inganta miki wasu tarin ni'imomin na
sa." Ta tsagaita tana mai kallona bayan ta ɗago da fuskata.

Itama hawayen ne cikin idanuwanta wasu ma sun zubo. Na ce,

"Shi kenan ya cuceni ya lalata min rayuwata,ashe daman ba sona yake yi ba, ashe daman yaudarace
kawai da cin amanar ruhi." (Littafin Hassana Ɗan Larabawa. Na rushe da wani firgitaccen kuka.

Ba ta iya cewa komai ba sai kawai ta sake rungumoni muka kuma fashewa da kuka. Muna haka wata mai
kula da majinyata ta shigo ɗakin, ganin halin da muke ciki ya sakata dafa mu tare da tausarmu.

Ta zare robar ruwan dake maƙale a hannuna wanda ni lokacinma na lura da ita har wajen ya fara
kunbura. Sosai naga take binmu da kallon tausayawa har ta fice daga ɗajin bayan ta bani magunguna na
sha.

Mu kam kamar masu zaman makoki haka muka cigaba da zama a ɗaki sai dai kawai tashin sautin kuka da
za ka ji.

Har dare banga kowa ba sai da duhu ya fara yi sannan naga Umma ta shigo,fuskarta babu fara'a ko
kaɗan. Ganin haka ya saka ni komawa na kwanta tare da lumshe idanuwa na. Ban san ko ƙarfe nawa ba
amma ta ɗan jima da zuwa na ji Rabi'a na mata sallamar sai da safe bayan ta shafa kaina a zatanta barci
na ke yi. Na jima da tunanuka kala-kala cikin zuciyata har ban san sanda ɓarawo barci ya kwasheni ba.

Da safe na ɗan sami sauƙin raɗaɗin da nake ji. ko da na gaida Umman bata wani amsa da yalwacin
annuri ba, sai ma maganar da ta hau yi wacca ta daki zuciyata matuƙa.
"Kin kyauta. Kin yi aiki na ƙwarai da har kika kasa riƙe maitarki ki kaje kika haɗiye muciyar da za ta miki
maganinta,watanawa ya rage miki da har kika kasa iya riƙeta shekaru nawa kika ɗauka baki yi wannan
aikinba sai yanzu da auren ya zo kin kyauta." Ta faɗa a zafafe.

Ji na yi kaina na sarawa, take na fara ganin tara-tara na gaza yadda zan iya furta kowanne irin furuci,
muryar Rabi'ace ta dawo da ni daga halin da na shiga ashe Umma har ta fice daga ɗakin bayan tafiya
wucin gadin da idanuwana ,ƙwaƙwalwata suka yi.

Wai Ummace ke faɗin haka ? Me yasa za ta min mummunar fahimta? Me ke faruwa ne? Na shiga
tambayar kaina har sai da Rabi'a ta shiga shafamin bayana tana faɗamin kalamai maau ratsa zuciyar mai
sauraro.

A taƙaice dai sai da na shafe kwana huɗu a asibiti sannan aka sallameni. Cikin kwanakin Rabi'a ta kula da
ni sosai da sosai, iyayenta sun zo min sau ba adadi, Baba ya zo sau ɗaya, sai ƙanwata da take zuwa a
kowacce rana, Umma kuwa dare ne ke kawota safiya na yi za ta tafi ba ko sallama.

Sati na biyu da fitowa harma na soma warwarewa sosai,har lokacin mutane na shigowa yimin sannu da
jaje duk da mafiya yawancinsu gulma ce ke kawosu. Marasa ɗa a ido kuwa gabana gaban Umma za su
riƙa habaici da baƙaƙen maganganu marasa daɗin sauraro. Har da masu magana kwatan-kwacin irinta
Umma.

Abubuwa suka taru suka min yawa ,in kaga fara'ata ko murmushina to da Rabi'a ne,ƙanwata ta takanzo a
sati sau uku ta dubani.

Rayuwa ta soma yimin zafi ,abubuwa suka haɗu suka min yawa. Baba da Umma suka juyamin
baya ,mutane kuma suka sakani a tsakiya da maganganu kala-kala. Ba dama na fita sai an jefeni da
munanan kalamai marasa daɗi,duk da iya bakin ƙoƙarin da Rabi'a da ƙanwata ke yi na san ganin na sami
farin ciki amma hakan ya gagara.

Ji na yi kawai na gaza da irin hukuncin da mutane da iyayena suka yanke min,kowa ya gaza fahimtata.
Duk yadda naso su Umma su fahimceni abin ya faskara. Ƙarshema bayan na sanar da su abin da ya faru
sai suka ce, "Sharri zanwa ɗan bawan Allah." Munafikin kuwa sa'ad da Baba ya kirawoshi harda hawayen
ƙarya, bai ko ji tsoran Allah ba ya shiga rattabawa Baba abin da ba hakaba. Wai daman ya sha kamani da
ƙazaman hirarkin batsa ta yanar gizo ,ya sha gogemin finafinan batsa cikin wayata.
Baba ya mun faɗa sosai har takai da dukana a kan haka, kuma ya tabbatarmin da cewa ya fasa aurena.

Dole ya ce haka tunda ya ci moriyar ganga ya yada ƙwallon ai. Wannan abun ya sa na yanke hukuncin bar
musu gidan da unguwarma gaba ɗaya ko na sami nutsuwa, zanje inda ba wanda ya sanni balle a kira ni
da mazinaciya.

Cikin dare wajen ɗaya sawu ya ɗauke na salallaɓa na fice daga gidan ban ɗau komai ba sai wayata da
nufin na riƙa haskawa, na shiga tafiya sannu a hankali har ban san sanda tsautsayi ya kwasheniba wani
mai mota ya yi awon gaba da ni. A she fita ta rabon na haɗu da wanda zai tsaida ruwan hawayena zuba
ne.Mutumin da ya sadaukar da farin cikinsa a kaina ,mutumin da ya inganta rayuwata daga baƙin ciki
zuwa farin ciki.

A sibiti ya nufa da ni kai tsaye ,ya na zuwa aka tarɓemu da gaggawa. Wayata da ita ya yi anfani wajen
kiran Rabi'a wacca da safe ta iso sai ganinta kawai na yi gefena tana bina da kallo bayan na farka.
Wannan duk shi yake sanar da ni.

Likita ya shigo ya sake duba lafiyata wanda ya bamu tabbacin zai sallamemu a ranar.

An sallamemu kamar yadda likitan ya ce, ya kuma bani magunguna masu ɗan yawa wanda zan yi anfani
da su. San da muka fito na kafe a kan lallai bazan bisu ba, su ƙyaleni zan shiga uwa duniya. Da ƙyar da
siɗin goshi suka shawo kaina muka wuce gidansu Rabi'a kai tsaye dan na rantse bazan koma gidanmu ba.
Tun a hanya su ke lallashina amma kukana ya gaza yankewa.

Allah sarki iyayenta masukaramci da sanin ya kamata suka amsheni hannu biyu cikin so da ƙauna bayan
sun biyoni da nasiha mai ratsa zuciya.

Kwana na biyu kullum sai Abbas ya zo dubani, wannda na sami sunansa a bakin mahaifin Rabi'a.

Baban Rabi'a da Mamanta suka ɗauke ni zuwa gidanmu, amma Baba da Umma suka baɗawa
idanuwansu toka a kan ba zasu amsheni ba, sun manta kowanne bawa da irin tasa ƙaddarar.

*LOKACI NE*

(Gajeran Labari)
Mai_ƙosai

FCWA

Goma biyar

Duk yadda suka so fahimtar da su illar abin da su ke san aikatawa amma suka toshe kunnunwansu, sun
gaza fahimtarsu har lokacin Abbas shima ya zo a ka shiga damawa da shi amma ina sun yi nisa ƙarshema
Baba ficewa ya yi daga gidan Umma kuwa ta yi kunnen uwar shege da mu.

Cikin kukan baƙin cikin abin da iyayena biyu suka min kamar ba ƴarsu ba na ce,

"Zan tafi ,zan yi tafiya mai nisa ta har abada ba za ku sake ganina ba. Zan shiga duniya zata zame min
uwa da ubana." Ina gama gaɗin haka na fice da sauri daga gidan, ganin haka ya saka iyayen Rabi'a biyo ni
tare da Abbas. Ni kam tafiya na ke yi babu ko waige har ban san lokacin da na ji tafukan hannayen Rabi'a
kan fuskata ba, wai ashe bina su ke su na roƙona a kan na dakata da manufata amma na yi burus na
toshe kunnuwana ba na jinsu, lokacin ne kuma Abbas ya je ya sanar da ita abin da ke faruwa shi ne ta iso
gareni tare da wankamin mari kan fuskata. Na dawo cikin nutsuwata lokaci guda kuma Mahaifin Rabi'a
ya soma min faɗa da nasiha mai tsuma zuciya har ban san lokacin da na durƙushe a wajenba ina kuka
mai cin rai. Da ƙyar na miƙe muka dawo gidansu Rabi'a suka min alƙawarin zama da ni har lokacin d
iyayena za su sakko su amsheni hannu biyu.

Ni ban sani ba ashe Rabi'a ta sanar da Abbas duk abin da yake faruwa dani. Ya tausayawa rayuwata
sosai, ya shiga hidima da ni ba ji-ba-gani. Kullum ya kanzo sau uku ko biyu, in bai zo ba zai kira Rabi'a a
waya ya tambayi lafiyata, ƙarshema sai ya soma kiran lambar wayata ya na jin ko lafiyata ƙalau,tun ba na
sakin jiki da shi har na saki dan sautari Rabi'a kan ce min,

"Aunty ba na jin Yaya Abbas zai cuceki ko da da ƙwayar zarra ,dan Allah ki saki jikinki da shi." Wannan ya
sa nima sai na ji hankalina ya kwanta da shi.

Shaƙuwarmu da shi ta dabance wacca ta cusa mana so da ƙaunar juna sa'ilin da ba mu yi zato ba, na
kanji wani iri in banji daga gareshi ba ,shi kam sam baya samin nutsuwa ma sai ya ji daga gareni ko ya zo
ya ganni. Ba a ɗau wani shahararren lokaci ba ya zo ya sami Baban Rabi'a ya sanar da shi abin da ke
ransa na san aurena .
Kowa ya yi murna sosai, nima na ji daɗi fiye da zato. Iyayen Abbas sun amsheni hannu biyu ba tare da
ƙyama ba, cikin sati biyu da faruwar haka aka kawo kuɗi da tsaida rana wata biyu cif masu zuwa in Allah
ya kaimu.

Ɗauniyar da yakemin, da yadda ya ke kulawa da ni sai na ji soyayaarsa fiye da tunanin mai tunani, ina
masa san da har saida Rabi'a ta kwaɓeni a kan haka, ni kam gani nake rayuwata ma zan iya bashi a
wannan lokacin dan ina tsantsar ƙaunarshi da san shi.

Baban Rabi'a ya je har gidanmu kan maganar kuɗin aurena ,magana ɗaya kawai suka masa shi ne; "Allah
ya nuna lokaci." San da ya ke sanar da ni na ji wani abu ya tokare maƙoshina kenan hakan ba zai saka su
farin ciki ba ,saboda kawai an lalatamin rayuwa sai su tsaneni a kan me? Mene ne laifina a ciki tunda ba
ni na kai kainaba?.

A taƙaice dai wata biyun da aka saka ta riskemu, a ka soma shirin biki nan da sati guda. Ni dai na ce ba
abin da zan yi illa kawai walima itama dan Abbas ya takuramin ne shida Rabi'a wai ba za ayi biki lami ba.
Ku jifa.

Satin da ya zagayo ya kasance satin sunan ƙanwata da ta haihu ƴan biyu duka maza ku ji kyautar Allah.
Rabar ɗaurin auren ranar sunan ban kuma fasa zuwarmata ba tun da ita ba halin zuwa, ina san ƙanwata
sosai fiye da zato. Mun yi kukan rabuwa da juna da ita, tana jin kamar ta biyoni taga inda zan zauna
amma ba hali, nima kuma da man na yi alƙawarin ba zan bari ta taɓa sani ba dan na yanke alaƙata da
duka ahlina.

Wani abin da ya ɗan sa na ji raɗaɗin zuciyata ta ragu shi ne kaiwa azzalumi katin ɗaurin aurena wanda
ni da Rabi'a muka lalubo adireshinsa mu ka je.

Bayan na ba shi na shiga gaya masa kalaman da suka zo bakina.

"Ina fata za ka cigaba da rayuwa cikin azabtacciyar ƙonar rai, in sha Allahu abin da kamin sai anmaka fiye
da tunani ,in kere na yawo zabo na yawo wata rana zasu haɗu ,kuma rama cuta ga macuci ibadane na
san Allah sai ya sakamin haƙƙina ba zai taɓa barinka ba wallahi." Ina gama faɗa masa na fice daga ɗakin
na sa ,da yake gidansa ne shi kaɗai na iyayensa na nesa da shi kaɗan.

Bikina da wata biyu ,bayan tarewata gidan Abbas masoyina na sake riskar wani babban tashin hankalin
abin da ya girgiza ƙwaƙwalwatana kasa samun sukuni. Ranar da na wayi gari gani ga gawar masoyina
abin ƙaunata Abbas. Hatsari suka yi, mai tuƙa motar da Musbahu suka ji rauni sosai, amma da yake Allah
mai ikone ko ƙwarzane babu jikin Abbas lokacinsa ya yi daga ranar ba zai sake rayuwaba shi kaɗaine ya
mutu cikinsu. Na kan tuna kalamansa gareni.

"Ke ɗin ta dabance Khausar,ina miki san da ban taɓa yiwa wata ƴa mace ba, duk da kasancewar na sha
gwagwarmaya kan so, na so wata kafin ke amma ban san ba santanake ba sai da na sameki, ta azabtar
da zuciyata Khausar ke kuma kin kyautata rayata da ruwan sanyi. Samunki gareni sai naji inama tun farko
ban santa ba,dama tun farko dake na fara haɗuwa,dama tun farko ban ji santa cikin zuciyata ba. Ina
tsananin ƙaunarki Khausar ki soni ko da da ƙwayar zarrane ni kuma znn riritaki ,zan saka ki farin ciki fiye
da nawa, ki soni ki ƙaunace ni ko da bayan raina ne."

A she daman tafiya zai yi ya barni. Ba zan taɓa samun miji masoyi irin Abbas ba wanne ne dalilin da yasa
na kasa ƙauracewa gidansa, nake zaune ciki duk kuwa da cewa ya zomin a raban tumulin takabata. Ina
zaune da ɗan uwansa Musbahu wanda Alhaji Jibril mahaifinsu ya sa ya dawo gidan da zama acewarsa ba
zan zauna ni kaɗai ba, tunda naƙi amincewa na dawo kusa da su. Cikinsa nake rayuwa har kawo i yanzu,
idan na tuna da mijina abin alfaharina sai na ji inama nima na mutu na bishi ko na sami salama, na kanji
badan kashe kai kisan kaine ba da na kashe kaina sai dai na san idan na yi hakan to ni ɗin ƴar wutace sai
kawai na rungumi sunayen Allah maɗaukakin sarki.

"Aunty har yanzu baki koma ga su Ummaba, me yasa ba za ki neme su ba?" Hajara ta watsa mata
tambayar.

"A a Hajara tun barowata daga unguwar zuwa gidan Abbas na cire rayuwata daga can na ɗakko komai
nawa na taho da shi nan, na kan tambayi Rabi'a a waya ya su ke ,ta cemin kowa lafiya. Har kawo lokacin
da ta yi aure wanda banje bikinba saboda kar na shiga unguwar, Abbas ya matsamin sosai a kan naje
ganin inta kuka duk sanda ya yi maganar sai kawai ya zuba min ido bai kuma cemin komai a kan rayuwar
ba.Duk abin da zai haɗani da ƙanwata ahalina to bana yarda na raɓeshi. Musbahu shine ɗan uwana
iyayensa su ne iyayena a halin yanzu. Ta ƙarashe cikin wani irin kuka.

Suma kukan su ke yi, Musbahu, Hajara kuwa hawaye shaɓe-shaɓe kan fuskokinsu.

"Wannan shi ne mafi munin kuskure da mafiya yawan ɗaukacin mutane ke yi a rayuwarsu ,sun manta
Allah ke yin komai ga kowa,in ya soma sai ya tashi duniyar lokaci guda kuma babu mai cemasa dan me?
Abin da suka gaza fahimta shi ne komai nada lokacinsa. Iyaye kan aikata kura-kurai na rashin yadda su ke
gaza fahimtar ƙaddarar ƴaƴansu, sukan manta amanace garesu kuma ƴaƴa kiwo ne wajensu, sukan
manta da cewa duk yadda mutum yake tara yake bai cika goma ba, sukan manata da kyakkyawar
ƙaddara da mummuna wacca kowanne bawa ke da su. Lallai ya kamata su tausayawa ƴaƴansu fiye da
kansu,ya kamata su ƙaunacesu fiye da kansu, ya kamata su ja su ajiki fiye da yadda akuya ke lashe ɗanta
idan ta haifeshi." Likita ya katse musu sautin kukansu ta hanyar furucin, tun soma labarinta ya ke tsaye
wajen ya na jinsu.
Aunty ta share hawayen saman fuskarta tana mai kallon Hajara ka na ta ce,

"Tun farkon bamu labarinki zuwa tsakiyarsa na gano wasu kura-kurai na ki da kika tafka. Na farko kin
sami masoyin ƙwarai amma sai kika wulaƙantashi kika biyewa san zuciya da abin da ba za ta samu ba. Na
biyu Allah ya kawo miki mijin auren lokacin da kike buƙata amma sai kika maida kyautar da Allah ya
miki,kika wofantar da ita, baki yi anfani da lokacin da Ubangiji ya ara miki ba har ya ƙure miki, kin manta
da cewa idan hannun agogo ya wuce baya taɓa dawowa baya ya tafi kenan har abada."

Cikin kuka Hajara ta soma faɗin,...

*LOKACI NE*

(Gajeran labari)

Mai_ƙosai

FCWA

Goma shida

Cikin kuka Hajara ta soma faɗin,

"Tabbas na aikata babban kuskure,na yi wasa da damata ,lokacina ya tafi ba shakka ba zai taɓa dawowa
ba Aunty , na yi da nasani matuƙa jin labarinki ya sakani jin cewa ni ɗin cikakkiyar mai laifi ce."

"Ƙalubalen dake cikin rayuwarki da tawa akwai banbanci masu yawa." Ta kuma faɗa cikin kuka.

A hankali Aunty ta janyota zuwa jikinta tare da rungumeta tana shafa bayanta a hankali. Lokaci guda
kuma suka fashe da wani irin kuka ,duk yadda Likita ya so tsaida su hakan ya gagara har sai da dan kansu
suka tsagaita.

Musbahu kuwa wani babban fami a ka masa cikin zuciyarsa na ɗan uwansa abin ƙaunarsa. Su biyu ne
kaɗai wajen iyayensu Abbas na masa so fiye da yadda yake san kansa, duk abin da yake so shi zai masa
muddin bai kaucewa shari'aba. Hannu ya saka ya na mai share hawayen saman fuskarsa tare da ficewa
daga ɗakin. Shi ma Likita ficewa ya yi, a ka bar su Aunty su biyu, su na kuma jinjinawa tasu irin rayuwar.

"Tabbas Aunty malam mugune, kuma in sha Allahu sai yaga wulaƙancin rayuwa." Hajara ta ce.

Hannu Aunty ta saka ta toshe mata baki gami da girgiza kai ka na ta ce,

"A a Hajara ,kibar zancen ba na san tuna baya ko kaɗan,wanda ya yi da kyau zaiga da kyau ai." Daga
haka suka ja bakinsu suka garƙame shi.

Kwanansu biyu a asibitin bayan faruwar wannan lamari a ka sallamesu suka koma gida.Jikin Hajara ya yi
sauƙi sosai ta warware. Bayan sun koma gida Musbahu ya sanar da mahaifiyansa abin da ke faruwa na
daga labarin Hajara da Aunty Khausar, sosai suka tausaya musu. Mahaifinsa kuwa ca ya yi su shirya za
sukai ziyara wajen mahaifiyar Hajara.

Kwana ɗaya da fitowarsu suka shirya zuwa gidansu Hajara.

Mama na zaune gaban murhu tana iza wuta ta ji sallama da muryar ɗiyarta. Cikin sauri ta miƙe tsaye
tana mai ƙurawa ƙofar shigowa tsakar gidan kallo, idanuwanta suka ɗakko mata hotan ƴarta tsaye ta saki
baki galala tana mai bin ta da kallo.

Hajara ta ƙarasa da sauri tana mai shigewa jikin Mama ka na ta ce,

"Mamata."

Sai a sannan Mama ta zube hannayenta biyu saman bayan Hajara tana mai na nuƙata jikinta kamar ance
za a ƙwace mata ita, gaba ɗaya ta kasa magana da ƙyar ta iya furta,

"Hajara ke ce? Ina kika je kika barni ni kaɗai? Daman kina raye?" Ta shiga jeromata tambayoyi.

"Ina raye Mamana, ki gafarceni dan Allah ,na dawo gareki har gaban a bada." Hajara ta ce cikin sigar
kuka.
Sannu-sannu suka sami waje suka zauna bayan ta shimfiɗa musu tabarma, bayan sun gaisane a ka shiga
tattaunawa kan batun da ya kawo su da kuma sake bawa Mama haƙuri kan abin da Hajaran ta aikata.

Mama ta yi murna sosai jin hannun da ƴarta ta faɗa, hannu na gari. tana kuka ta soma basu labarin
bayan tafiyar Hajara, da irin cin kashin da mashaye ke mata ta soma da faɗin,

"Na zalinci kaina da yawa, ina tunanin idan na aurar da ƴata ga koma wane ne zan sami salamar abin da
mutane ke faɗi,sam na gaza anfani da ilimina wanda Allah ya bani sai ga shi na ɗakkowa kaina ruwan
dafa kaina. Ya shaidamin muddin baki dawo ba to ni ce amaryar tasa a madadin ki ."

Gaba ɗaya sun tsorata wanda ya saka su Aunty roƙan Mama a kan ta biyosu su koma can da zama yadda
bama zai dawo ba balle ya aikata abin da ya keso. Da ƙyar ta amince bisa saka bakin mahaifin Musbahu.

Nan suka tattara ƴan komatsansu wanda ba zasu ɗauka ba Mama ta shiga maƙota tana musu sallama
tana bawa masu so. Duk da rashin san da suke musu amma sabo turken wawa sai da suka ji ba daɗin
rabuwa. Har godan da Mama take aiki suka je ,matar ta ji badaɗin rabuwa, ta kuma taya Mama murna
sosai.

Satin Mama guda da komawa Sharaɗa cikin gidan Aunty wanda ta basu ɗan matsakaicin gidane zaman
mutum ɗaya wanda duk ya zo cikin raban gadon Abbas da a ka yi. Nan suka shirya zuwa Jama'are wajen
dangin Mama dan itama ta yi nadanar barowarta daga can,tana jin ya kamata ta koma ga ahlinta.

A na i gobe tafiyarne Hajara taga abin da ya tsuma zuciyarta. Aunty na ɗakin Abbas wanda in tana san
keɓewa take shiga dan rage kewarsa Hajara ta shiga tana ta sallama Aunty ta yi nisa da tunani ba ta ji ba.
Fizge hoton da ke hannunta da Hajara ta yi ne ya dawo da ita daga duniyar da ta tafi. Ido huɗu suka yi da
Hajara dake tsaye ta sandare saboda ganin fuskar wanda ke jikin hotan.

"Ab-b-bas" bakinta ya soma furtawa cikin tawar murya.

"Kin san shi ne?" Aunty ta jefa mata tambayar.

"Shi ne, shi ne wallahi Aunty shi ne mutumin da nake baki labarinsa wanda ya ƙaunace ne har na kasa
ganewa, wallahi shi ne tabbas Abbas ne dan na gane kamanninsa ba."

Ta faɗa cikin muryar kuka.

"Allah sarki daman ke ce wacca ya ke bani labari ,wacca kika wahalar da shi." Sai kuka ya kuma kufce
mata.
"Abbas ka yafemin ,na zalunce ka na zalunci kaina,na maka abin da bai kamata ba,tabbas na canci
kowanne irin hukunci." Ta durƙushe a wajen tare da wani irin kuka. A hankali Aunty ta zame hotan daga
hannunta cikin murmusuwa ta ce,

"Ya jima da yafe miki Hajara,Addu'arki kawai yake buƙata a yanzu."

Kamar wacca ƙwai ya fashewa a ciki haka ta miƙe da nufar ƙofa za ta fice daga ɗakin.

"Ina za ki?" Aunty ta tambaya ba ta, ba ta damar magana ba ta ɗora da,

"Dawo ki zauna mu yi hira." Ba musu ta dawo ta zauna kusa da ita.

"Amma na kasa gane yadda baki iya gane Musbahu ba ta yadda su ke kama,ko da ya ke ba san shi kike
yi ba wannan kaɗai ya sa dalilin da zai saka ki kasa gane ɗan uwansa. Amma makwafin idanuwanki ya
gaza bawa ƙwaƙwakwarki damar da za ki iya haddace kamannin Abbas sai ga shi Allah ya haɗaki da ɗan
uwansa da matarsa suka ƙaunace ki fiye da zato. Kada ki kuma bari dama ta riƙa kufce miki."

Ita dai shiru ta yi ,ba ta iya cewa komai ba. Gaba ɗaya jikinta ya yi sanyi.

Washe gari, tun Asuba su ke shirin tafiya Jama'are gaba ɗayansu; Alhaji Jibril, Amma mahaifiyar
Musbahu, Aunty ,Musbahu da Hajara.

Wajen bakwai suka ɗau hanya, Allah ya sauke su lafiya ,kuma Mama ba ta sha wahalar gane gidanba
tunda fitaccen gida ne sosai taga sauye-sauye cikin garin.

Tarɓa a ka musu ta mutunci da karamci,bayan ƴan gaishe-gaishe suka gabatar da kansu ga ƙanin
mahaifin Mama . Murna wajensa ba a magana jin ɗiyarsa na raye harta dawo ga kuma jika ya samu. Nan
ya sa a masa shela a ka tara masa ahlin. Duk wanda ya ganta sai dai kaga ya na washe baki ya na murna.
Mama ta sami labarin rasuwar mahaifinta ta yi kuka sosai jin yadda da ita a ransa ya mutu.

Mahaifiyar baban Hajara ta shiga ruru akan a kaita wajen Mama ta ganta. Ganin ta matsanta ya sa a ka
zo aka sanar da Mama halin da take ciki. Har gidan su Mama suka je yadda ta ganta sai da ta mata
ƙwalla, tana kwance sai dai a juyata ga baki amma ba halin motsa jiki, sakamakon zamewar sa ta yi a
banɗaki wajen fitowa sai ta kamu da matsalar shanyewar jiki.Duk ta rame ta yi wata iriya da ita kamar ba
ita ba. Ganin Mama ya sakata fashewa da kuka tana mai neman gafararta, ko da Mama ta ce mata ga
jikartanan sosai ta kuma birkicewa kuka ta ke aosai tana neman afuwar Mama.

"Bakomai ,ki daina neman afuwata ki uwa kike a gareni." Mama ta ce.

Su Hajara kam duk kuka tausayawa su je mata. Alhaji Jibril ya ce zai ɗauki ɗawainiyar nema mata magani
in sha Allahu. Sun ji daɗi sosai sun yi farin ciki.
Satinsu guda a Jama'are suka juyo zuwa Kano harda Mama Rabi kakar Hajara da za a nemawa
magani,duk da Mama taso zamanta a can amma Alhaji Jibril ya bata haƙuri koba komai ai ta zauna da
kakar Hajaran.

Bayan dawowarsu da sati biyu aka fita da Mama Rabi zuwa wani kyakkyawan asibiti dan nema mata
magani.

*LOKACI NE*

(Gajeran Labari)

Mai_ƙosai

FCWA

Goma bakwai

Cikin satin suka shirya zuwa ga ahlin Aunty wanda da ƙyar ta amince da hajan tana kuka kamar wacca
aka ce za ta bar duniyar. Wannan karan tafuyar harda Likita Mubarak.

Ranar Laraba suka yiwa unguwarsu Aunty tsinke, gaba ɗaya unguwar ta sauya ta canza mata sai ka ce
wacca ta yi shekaru masu mugun yawa.

Gidan kam sai da ta haɗa da tambaya da sunan da aka raɗa mata(Ta rasa mijin aure)sannan ta iya samo
shi.

Hajara na kallonta ta wutsiyar ido yadda take bin ko'ina na gidan da kallo,komai gani take ya sauya mata
kamar ba gidansu ba.

Sallama Hajara ta shiga kwaɗawa ,dan ta lura Aunty ta gaza furta hakan.
Umma dake ɗaki ta fito tana mai amsawa, "Wane ne ke.....?" Ta shiga tambaya. Sai kuma maganar ta
gaba ta katse mata sakamakon ido biyun da ta yi da ƴarta tsaye tana bin gidan da kallo. Ji ta yi
ƙafafuwantana rawa.

"Ƴa ta ke ce? Ko dai mafarkin da na saba yi ne?"

Duk da faragabar da take ciki sai ta ɗanji wani sanyi ya ratsata zuciyarta ashe su na santa.

Hajara ce ta kamo hannayenta tana matsasu a hankali ka na ta ce,

"Tabbas mafarkinki ya zamo gaskiya, ƴar ki ce wannan ta dawo gareku har a bada. Mu na neman izinin
shigowa da iyayenmu."

Ba ta jira amsar Umma ba ta fita ta musu izinin shigowa. Umma kuwa ɗaki ta koma jiki a saluɓe ta shiga
shinfiɗa musu tabarmar zama.

"Shigo d su ƴar nan." Umama ta ce wa Hajara.

Cike suka shiga amma banda Aunty dake ƙamw a wajen kamar wacca aka dasa.

Hajara ce ta kamo hannunta gami da faɗin,

"Aunty ki is aga mahaifiyarki." Da ƙyar ta soma ɗaga sawayenta ta riƴa jefa su cikin ɗakin tare da
samun waje ta zauna. Umma ta bita da kallo cikin so da ƙauna.

Nan aka shiga gaggaisawa tsakanin Umma da mutanen,shiru ya gyatta tsakaninsukafin Alhaji Jibril ya
ɗora da faɗin,

"Da farko dai muna bada haƙurin zuwan bazata da muka yi,sannan muna godiya d yadda aka
tarɓemu.Amma in badamuwa muna san ganin shi maigidan."

Umma ta ɗan nisa kafin ta ce,


"Ayya badamuwa bari na kirashi a waya.Bai ma jima da fita ba."Ta ƙarasa tana mai ɗaukar wayarta ta
soma kiran layin wayarsa. Cikin sa'a bugu biyu ya ɗaga nan ta somar sanar masa da abin da saƙon ta take
san isarmasa. Ya kuma bata tabbacin in sha Allahu ga shi nan isowa.

Bai wani ɗau dogon lokaci ba ya iso, nan suka shiga musabaha da kowa.

Alhaji Jibril ya soma da,

"A karo na biyu muna sake bada haƙurin ziyarar ba za tan da muka kawo. Ni suna na Alhaji Jibril mahaifi
ga mijin Khausar ƴarku, sannan mahaifi ga Musbahu ɗana biyu, waɗanan kuwa(ya shiga yi musu bayanin
su Mama.) zamu ari bakin Khausar mu ci mata albasa,muna masu bada haƙuri a bisa katoɓarar da ta
aikata ta fice daga gida ba tare da izininku ba, wanda hakan ya faru ta dalilin juya mata baya da kuka yi
saboda kawai wata ƙaddadara ta gifta mata.Ku ne kuka soma kimtsa mata guduwa cikin ranta saboda
rana inuwa zafi da kuka sakata ciki. Wani abu da iyaye ya kamata su sani shi ne; Matsayinmu na iyaye bai
kamata mu riƙa juyawa ƴaƴanmu baya ba lokacin da suka tsinci kansu cikin wata matsala, kamata ya yi
mu rungumesu hannu biyu mu mara musu baya cikin tafiyar, bai kamata mu ƙyaresu ba ko tsangwama
saboda wani kuskure na su wala'alla sunja da kansu ko aka sin haka.Ya na da kyau kowaɗanne iyaye su
tuna cewa kowanne bawa da irin tasa ƙaddadarar,sannan ƴaƴa ababen kiwone garesu wanda Ubangiji
zai tambayesu ranar gobe alƙiyama. Komai na rayuwa ɗan lokaci ne, wani har ya mutu ma bai yi
aurenba, wannan duk cikjn tsari da hukuncin ubangiji ne.Wani kuma zai shafe lokuta masu tsawo har an
cire rai ga zato sai kuma a sami kyakkyawan sakamako. In mu ka yi duba da faɗin Ubangiji maɗaukakin
sarki da ya ke cewa,

"Innamaa amruhu idha araada shai'aan ayyaƙuula lahu kun fayakuun. Ma'ana Umarninsa idan ya yi
nufin wani abu, sai ya ce masa kawai"kasance" sai ya kasance(kamar yadda yake nufi.) Suratul Yaa-
sin(sura ta talatin da shida 36,aya ta tamanin da biyu 82. Haka kuma cikin surat-ul-Mu'min(sura ta
arba'in 40 ,Aya ta sittim da takwas 68 ya na kuma cewa, "Huwal ladhi yuhyi wa yumiitu fa'idhaa ƙadaa
amran fa innmaa yaƙuulu lahu kun fayakuun. Ma'ana Shine wanda ya ke rayarwa kuma ya ke kashewa.
To ,idan ya hukunta wani al'amari,to ya na cewa kawai gare shi, "kasance" ,sai ya kasance(kamar yadda
ya ke buƙata.) "

In muka yi duba da waɗannan ayoyin sun wadatar da mu cewa lallai Allah shike komai a duk lokacin da
ya so yin abun kawai zai ce masa "Kasance" kuma abun sai ya kasance, kunga kenan bamu muke da ikon
sakawa ƴaƴanmu su yi aure ba idan muka yi haƙuri lokacinsu na nan zaizo kamar yadda kowanne abu ke
zuwa ya wuce. Mutane da dama kan yiwa kallon abubuwa da dama kallon saɓanin hankali, sau da yawa
dan ɗanki ya aure ƴar da bata haihuwa sai kawai a ɗora musukaran tsana wacca itama haihuwa ai lokaci
ce kamar yadda mutuwa take da lokaci kuma in tazo ba za ta taɓa ɗaga ƙafa ga kowa ba.Aure, Haihuwa
komai lokaci ne wani kan zo lokacin da ake sansa wani kuma zai jinkirta har ta kai ancire tsammani a
kansa sai kuma lokacinsa ya zo. Ya kamata mu daina ƙyara, hantara ga waɗanda abun bai kasance kansu
ba, kaima da ka samu damar ba kai ka bawa kanka ba ikon Allah ne."

"Ƴarku ta yi aure baku tsaya mata ba, in da ace wanda ta aura ɗan yankan kaine da a yanzu ba za ku
sameta sai dai in har ya na tsantsan santa. Abun da ya faru da ita tsakaninta da malam baku yi
kyakkyawan bincike ba kuka yanke mata ɗanyen hukunci, kun san ba halinta bane ba lokaci guda ba za
ta sauya tarbiyar da kuka mata ba ya kamata ku riƙa kyautata kyakkyawnn zato ga ƴaƴanku. Musulunci
bai yarje yanke hukunci cikin abin da ba tabbas a kansa babu bincike. Mu na masu sake baku haƙuri da
nema mata afuwa."

Baba ya goge ƙwallar da ta zubo masa da tun fara maganar Alhaji suka zubo masa. Saida ya ɗan matse
idanuwansa kafin ya ce,

"Tabbas mun zalunci kanmu ,mun aikata babban kuskure,mun wofantar da karatunmu mun manta
cewa Allah ke yin komai. ko da yake tun kan aje ko'ina ga shi nan mun suma ganin sakayyarki,duba da
kullum muka waye gari muke kwaɗaituwa da san ganinki gabanmu amma bama samun wannan damar.
Mutumin da ya aurar dake baya raye Allah ya mas rasuwa. Matarsa kuwa ta ce ba za ta taɓa gaya mana
adireshinki ba in har da gaske ɓuna sanki to mu laluboki da kanmu. Ƴarta da take ƙawa gareki ta yi aure
har yau bama ce ga inda take ba. Mun yi tunanin kaita ƙara to amma muce ƙararta kanme? Bamu da
hujjar haka. Bamu ta shi tsinkewa ba sai wnnda ya lalata miki rayuwa ya gurfana gabanmu cikin neman
gafara, ya na kuka sosai kamar ƙaramin yaro ya shiga labartamana yadda har ya haiƙemiki, har muka
gaza fahimtarki mu da sauran mutane muka yanke miki mummunan hukunci. A halin yanzu kam na ji dai
ance baida lafiya ya na kwance. Ki gafarta mana ƴarmu, lallai mun zama muna iyaye masu tauye haƙƙin
ƴarsu ki yafe mana dan Allah."

Umma kam kuka take sosao da ƙyar ta iya furta,

"Lallai mun zama daga cikin masu butulcewa hukuncin Allah,mu ka kasa yadda da ƙaddara mai kyau ko
mara kyau,bamu taɓa tunin lokaci zai zo da zamu ji kunya ba,mun ji kunya sosai ƴata lokacin da muka
gano cewa baki da laifin komai ko ƙanƙani cikin hasashenmu. Dan Allah ki gafartamana." Ta ƙarasa tana
hale hannayenta biyu waje ɗaya.

Hajara da Khausar kuja kawai su ke yi, fuskarsu taf da ruwan hawaye kwance bisa kumatunsu, wani na
sauka wani na biyo baya. Khausar kuwa ji take ƙaunar ɓahaifan nata biyu ta sale nunkuwa cikin
zuciyarta.

"Na yafe muku ya ku iyayena,bani da kamarku cikin duniyarnan,ba zan iya fushi da ku ba,ba zan iya
jurar ganin ruwan hawayenku ba ku gafartamin bisa kuskuren da na aikata mu......." Ta ƙarasa tare da
fashewa da kuka mai taɓa zuciya.
*LOKACI NE*

(Gajeran Labari)

Mai_ƙosai

FCWA

Goma takwas

"Na yafe muku ya ku iyayena,bani da kamarku cikin duniyar nan,ba zan iya fushi da ku ba,ba zan iya
jurar ganin ruwan hawayenku ba ku gafartamin bisa kuskuren da na aikata mu......." Kalamanta suka
uanke sai ka ce an datse wayar wuta daidai ɗokacin da ake amfani da wutar, tare da fashewa da kuka
mai taɓa zuciya.

Cikin hanzari Umma ta janyota zuwa jikinta tana mai rungumeta.

" Mun yafe miki ɗiyarmu."

"Alhamdulillah godiya ga ubangiji da ya kawo ƙarshen wannan al'amari, abu na gaba kuma batune a kan
auren Likita da ya ke san yi ga KHAUSAR." Alhaji Musbahu ya ce.

Khausar, Hajara ,Musbahu sai da suka zabura kamar waɗanda a ka tasa daga barci, a ba zata suka ji
maganar Alhaji. In ka cire sauran jama'ar ban da Umma da Baba da alama kenan sun san da zancen.

"Bari na warware muku zare da abawarsa."

"Bayan dawowarmu daga Jama'are mun yi Magana da likita ya shaida min cewa ya na san
aurenki ,amma sai na dakatar da shi ta hanyar faɗin ya bari muje ga iyayenki wanda shi ne shi ma ya ce
zai bimu. Na sanar da iyayenki ukun dan ya kamata su san da maganar kuma sun yi farin ciki sosai. Yanzu
kuma zamu ji ta bakin iyayenki biyu da kuma ke. Ina fata za ki amince da buƙatarsa dan na san ba za ki
wulaƙanta ba. In kuma na yi ba daidai ba to kugafar ce ni."
Cikin farin ciki Baba ya soma faɗin,

"Babu abin da ka yi wanda ba daidai ba, kai matsayin uba kake gareta. Ban san da wane baki zan gode
maka ba,na tabbata ba za ka taɓa bari ta aure wanda zai cutar da ita ba."

Ya juya ga Khausar ka na ya ce,

"Ni ba zan miki dole ba, amma ina baki shawara da ki amshe shi, ina so ki je ki yi shawara da zuciyarki
da ƙwaƙwalwarki."

Ita dai sauransukawai take yi,amma ba za ta iya rayuwa da wani bayan Abbas ɗinta ba, mutumin da ya
sota tana jin ba wanda zai iya zama da ita yadda ya mata. Da wannan tunanin nata da take yi taji taron
ya tashi bayan sun shafa addu'a.

Sai bayan la'asar su alhaji suka bar gidan bayan sun bar Hajara da Khausar. Musbahu ji yake ina ma shi
ma a ce ya zauna.

Duk yadda likita ya so ya gana da Khausar abin ya faskara,haka ya haƙura ya ce ya dawo gobe.

A daren ranar Khausar ta ziyarci gidansu ƙawarta Rabi'a ita da Hajara,ta yi kukan rashin Baban Rabi'a
wanda ya zama uba na biyu gareta, mahaifiyarta kuwa ta yi farin cikin ganinta sosai. In da ta tambayi
Rabi'a ta sanar mata tana Abuja wata biyu baya ta zo ta koma. Ta yi mamaki sosai yadda har Rabi'a ta zo
bata nemeta ba, ba kuma ta kirata ko da a wayane ba ,basu bar gidanba har sai da ta ƙarɓi lambarta da
kwatancan inda take a Abujan.

Washe gari suka zuba sammako zuwa gidan ƴar'uwarta. Sosai su ke kuka na rashin ganin junansu .Sun yi
kewar juna ba kaɗan ba. Ganin abun ba na ƙare bane ya saka Hajara shiga tsakaninsu tana mai
tsokanarsu,sai ga shi dukkansu sun shiga darawa kamar ba su ne ke yin kukan ba. Ba su baro gidan ba
sai bayan sallar isha ,shi ma ji su ke kamar kar su rabu.

Bayan sun dawo ne Umma ke shaida musu Likita da Musbahu sun zo ,harma sun nemi ta basu
kwatancen inda su ke ta sanar da su ba jimawa za su yi. Amma sun ce za su dawo.
Khausar ji ta yi gabantana faɗuwa raass, ƙwalla ta cika mata kurmin idanuwanta, ba ta iya bawa Umman
amsa ba ta shige ɗaki. Ganin haka ya saka Hajara mara mata baya.

A gefen gado ta iske ta zaune, hannu ta saka tana mai dafa kafaɗarta tare da furta.

"Na fahimci cewar har yanzu kina cikin damuwa, sannan uwa uba kina tunanin yadda za ki iya auren
Likita saboda soyayyar Abbas cikin zuciyarki,amma ina so ki sa ni komai da yake faruwa daga Lillahi
wahdahu ne. Ina so ki karɓi duk wani tsari da hukuncin da ya yi miki,ki ɗauka wata ni'imace Allah ya aiko
miki da ita shiyasa Likita ya ce yana sonki, dan Allah kada ki bari damar ta wuce."

Ta share ruwan hawayen da ke kwance saman fuskarta tana mai fuskantarta ka na ta ce,

"Ƙwarai ina tunanin yadda zanyi rayuwa tare da wani in ba Abbas ba, amma na amshi duk irin hukuncin
da Allah ya wanzar a kaina, na amince zan aure shi."

Wani daɗi ya mamaye zuciyar Hajara, ta saki dariya tana rungumota jikinta.

"Yawwa Auntyna ko kefa." Hajara ta ce.

Khausar ta yi murmushi ka na ta ce,

"Ina so kimin wata alfarma ƙanwata." Ta ƙarasa tana kamo hannayen Hajara duka biyun cikin nata.

"Ina jinki Auntyna, in sha Allahu in dai ba tafi ƙarfina ba zan miki kowacce iri ce."

"So nake ki aure Musbahu."

Ta jefa mata maganar a ba za ta.

Cikin sauri ta kalli Khausar tana mai girgiza kanta.

"A'a Aunty dan Allah.........."

"Dan Allah Hajara kimin wannan alfarmar, Musbahu na tsananin sonki sosai fiye da tunaninki, ki yadda
da ni." Ta katseta ta hanyar jefa mata maganar.
Shiru ta yi kafin ta ce,

"Shi kenan Aunty ,Allah ya shige mana gaba, amma ya aka yi kika san ya na sona?"

Sai da ta murmusa ka na ta ce,

"Tun kwanciyarki asibiti alamomin sonki suka soma bayyana gareshi na fahimci hakan ganin yadda ya
damu dake fiye da yadda na damu dake, na kuma gasgata zancen lokacin da na tuna ɗan zamanki a
gidanmu yadda ya riƙa jeleƙe a kanki,da na tutsiyeshi sai ya gasgatamin tantamata amman ya roƙeni da
kada na sanar miki har sai sanda ya farauto zuciyarki, ni kuma sanin halinki kada a kuma zagaye na biyu
ya sa na fasa sirrin na roƙeki da kaina sai a ka yi sa'a kika amshe shi hannu bibbiyu."

Hajara ta yi dariya mai yawa tare da rufe fuskarta tana furta, "Kai Aunty".

Wajen tara da kwatana dare Likita ya iso gidansu Khausar shi kaɗai ,bayan ya yi sallama zauren gidan
Baba na nan shi ya masa iso zuwa ɗakin dake soron gidan.

Khausar ta shigo bakinta ɗauke da sallama, suka shiga gaisawa.

*LOKACI NE*

(Gajeran Labari)

Mai_ƙosai

FCWA

Goma tara(Ƙarshe)

Mintuna huɗu ba wanda ya ce uffan ,ganin shiru ba ƙarau ba ne ya saka likita furta,

"Da farko ina mai baki haƙuri a bisa kutsen da na miki cikin rayuwarki, ban sa ni ba ko zan sami
matsuguni daga cikin sashen zuciyarki ko da ban shiga can ciki ba? Sannan ina fata ki zama uwar 'ya'yana
abar alfaharita. Idan kin amince zan yi zallar farin cikin da babu algus, idan ba ki amince ba zan yi haƙurin
hakan nasan Allah ke shirya kowanne lamari,amma zan yi baƙin ciki mai yawa bisa rashin samun mace
tagari da na yi. Na riga da na sanar da iyayena komai, na kuma buƙaci da su bani damar jin ta bakinki ,ko
yanzu kika amince gobe za sukawo kuɗin aure gidanku dan saka rana bana san tsaye-tsaye." Ya dire
zancen ya na kallon yadda ta yi ƙasa da kanta tana faman wasa da ƴan yatsunta goma.

Ta ɗan jima kamar ba za ta ce wani abun ba cikin sanyayyiyar murya ta ce,

"Allah ya tabbatar mana da alherinsa."

Sosai ya ji daɗin maganarta ,hakan ya nuna masa kenan ta amince kuma ya gane hakanne ta addu'arta.
Ji yake kamar ya haɗiyata dan murna.

Sosai yake janta da hira amma ta kasa sakewa da shi, cikin farin ciki ya mata sallama ya bar gidan na su.

Musabahu kuwa lokacin da ya sami saƙon Auntyn nasa na jin Hajara ta aminta da shi ya ji kamar ya zuba
ruwa a ƙasa ya dinga lasa, alla-alla yake gari ya waye ya iso gareta ko dan ganin kyakkyawar fuskarta.

Bayan kwana uku da faruwar waɗannan al'amuran a ka saka ranar Khausar da Likita, sai Hajara da
Musbahu wata biyu cif, zu ku ga murna wajen ahlin.

Mama ta so a bata Hajara ta yi bikinta a Jama'are kasancewar bikin saura wata guda za ta koma can ita
da Kakar Hajara dan ta sami sauƙi sosi fiye da zato.

Amma Alhaji Jibril ya hanata hakan, ya kuma tabbatar mata su ma ba zasu koma ba har sai bayan biki
shi zai ɗau nauyin komai,mutanen Jama'are ma za a kai mota duk wanda zai zo za a ɗakkoshi zuwa bikin.
Ba yadda ta iya haka ta sawa ranta salama.

Bayan kwanaki goma Khausar da Hajara suka shirya tafiya Abuja wajen sahibarta,cikin tafiyar har da
Musbahu dan ya na ce sai ya bisu.
Cikin hukuncin Allah ba su sha wahala ba suka samo gidan, kasancewar Musbahu ya san garin ABuja
sosai.

Sanda suka yi ido huɗu sai kuka, kukan da suka kasa gane na mene ne. Sosai Khausar kewa Rabi'a faɗa
kan nesanta kanta da ta yi da ita. Ba ta san me za ta ce mata ba, dan ita kanta bata da hujjar da za ta
kare kanta, sai kawai ta shiga bata haƙuri. San da ta ji auren Auntyn na ta murna kamar me wajenta ba
za ta iya faɗuwa ba.

Kwanansu biyu suka baro Abuja, ba su taho ba sai da Rabi'a ta mata alƙawarin kasancewa da ita har
abada kuma zuwa biki dole in dai ba rashin lafiya ko mutuwa ba.

Shirye-shiryen biki ake sosai. Rabi'a ta zo saura sati guda biki, kullum a tafe su ke babu zama.

A na i gobe ɗaurin aure suka ziyarci unguwar maciyi amana malam kamar yadda suka yi wancan karan,
katin ɗaurin auren suka kai mi shi, sai dai ganin halin da ya ke ciki sun tausaya masa. Ya na fama da
larurar ƙafa dalilin wani hatsari da ya yi a kan mashin, wanda har ya yi sanadin rasa mazantakarsa.

"Ina fata za ka halarci taron ɗaurin auren da yafi kowanne ? Dan kada a zo a baka labari ka san ance gani
ya kori ji,gwara ka ganewa idanka Khausar ba ta yara ba ce ƙananan ƙwari irinka." Rabi'a ta ce.

Cikin kuka ya soma furta

"Tabbas na san na zalunce ki sosai ,sai dai na ga ishara masu tarin yawa babi-bayan babi, na rasa
ƙafatana rasa mazantakata yadda zan yi rayuwar aure da wata babu, ba wacca za ta zauna dani dalilin
wannan, na yi magani yafi a ƙirga amma a banza dan ba wani cigaba tabbas wannan ishara ce gareni da
masu hali irin nawa. Tun anan duniya naga sakayyarki Khausar ki gafartamin ko na sami rahmar
Ubangiji." Ya ƙarasa cikin gunjin kuka.

"Na yafe maka ,Allah ya yafemana baki ɗaya." Khausar ta ce cikin raunin murya. Da sauri ta fice daga
ɗakin ganin haka ya saka su Rabi'a mara mata baya.
Satin ɗaurin aure ya shigo cikin hukuncin Allah. Ranar Juma'a aka ɗaura auren Khausar da Likita , Hajara
da Musbahu. Ɗaurin auren da ya tara dubban jama'a.

Bayan magrib a ka tara su tare da musu addu'a da kuma nasiha mai ratsa zuciya.Daga nan a ka danganta
kowacce da gidanta.

Mama kam bayan biki da kwana biyu ta matsanta sai ta koma Jama'are a cewarta mai za ta zauna yi
bayan an kammala bikin. Su na ji su na gani suka barta ita da ayarinta suka ɗunguma zuwa can.

Rabi'a ma ta koma bayan biki da sati guda. Zumunci su ke dukkansu su huɗun ba kama hannun
yara,kowa ya kasance cikin farin ciki da kwanciyar hankali. In da farin cikin ya kuma ƙaruwa dalilin auren
mahaifiyar Rabi'a da Baban Khausar ya yi. Mama kuwa Alhaji Jibril ya so aurenta ta kafe ita aure ta gama
sai a lahira ita da tsohon mijinta in sha Allahu.

Farin ciki, walwala, annushuwa da kwanciyar hankali suka mamaye zuƙatan su tare da wanzuwa
tsakanin ahlin tamkar ba su ba.

Alhamdulillah.

Sai mun sake haɗuwa a sabon wani littafin nawa.

Real Mai_ƙosai ce

You might also like